← Book details Hukuncin Allah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 4

Part din Maji ne farkon shiga gidan don sauran suna daga ciki suna ganin sun shiga ciki kusa da part din maigidan.

Hukuncin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 464 min read

A hankali na mike zaune na juya inda maryam ke ta barci ta yarda wayanta sai massage ke ta shigowa mata.
Window dakin na dan leka naga, mai shigowa a lokacin yaya sadauki na hango yana kokarin rufe motar shi.
Tafiya take a cikin rangaji irin nasu na yan maye ka
mar zai fadi ya dan dade a tsaye kafin ya bude kofan dakin shi ya shige.
Na koma bakin gado na zauna zuciyana naji ba dadi ko kadan tausayin Maji ne ya rufe min zuciya na.
Ina nan zaune naji motsinta hakan yasani sanin cewa batai barci ba idon ta biyu ke nan tana dakon dawowan dan ta tilo daya da masifa ta haushi na shaye shaye.
Haka na kwana ina matukar jin tausayin ta a raina har garin Allah ya waye muna.
Ranan bamu shiga school duk muna gida gaba dayan mu bayan na gama muna,abin karyawa don yanzu Maji ta raba muna aiki kowa da ranan girkin ta.
Na fito saye da wani buje da riga dinkin yan Niger, da hjy kubura ta sayo muna da suka je da Baba ta sayowa duk yan matan gidan hardani na samu shiga.
Ina zama nake cewa mama ina key din dakin yaya mu gyara mai, da sauri maryam take cewa nikan ba zan iya ba nagaji gaskiya yau hutu nake son yi.
Ina ganin ai yana ciki don banga ya shigo ba Amira tace naga fitan shi da safe da kayan wasa a jikin shi.
Mikewa, nayi tsam na dauki kayan gyaran wuri na fice daga part din mu nasa key din hannuna dakin ya bude.
Bin dakin nake da kallo duk da dan sauyi da dakin ya samu an saka mai kayan zamani a cikin sa.
Kafin na fara gyara na fara aiwatar da nufina da yakaini dakin, daga nan daga can ina bude wani kwali dana gani saida naja baya da sauri don tsoron da naji.
Kwayoyi ne ciki irin masu tsada da,akai muna lecture a kasan makil a cikin kwalaye.
Gaba daya na kwashe su da,sauri nakai toilet din dakin na watsa ciki nai flushing din su suka wuce,
Haka nauwa sauran syrup din da nagani kai duk wani magani sai da na turashi a toilet din ya wuce.
San nan na,gyara mashi dakin tsab nafito da sauri kafin ya,dawo ina fitowa nazo na zauna ina jiran yadda zamu kwashe dashi.
Bayan wani lokaci muna zaune sai hira muke kwasa tsakanin mu ya fado dakin idanuwan shi sun kade sunyi ja dasu.
Yan uwan shi ke mashi sannu da zuwa amma ni ko kallo bai isheni ba don nama raina da,al,amarin shi gaba daya.
Magana suke mashi amma,bai iya,basu cikaken amsa sai cewa yayi Maji wa ya gyara min daki na.
Wani kallo ta,watsa mai kamar na tsana tace wakasan yake da,kokarin haka,ba Fatima ba.
Inda nake zaune da,waya ina game ya,kalla kamar zaiyi magana sai ya kuta kawai mikewa yayi har yakai kofa yace tare da kallon inda nake zaune.
Ke kawon min abin karyawa na daki zan watsa ruwa ne yanzu.
Maji tace bana son suna shiga dakin ku idan kuna gida bari mana ta mika mai maji Amira ta fadi hakan a lokacin har na mike ko tsaye don na,shiga kitchen.
Ance abu ga manya ashe uwar ta dan fahinci da,akwai wani abu don haka ta kyale mu.
Saida na dauki kayan zuwa dakin ta saka hijjab din ta tabiyo bayana batare da sanin kowa ba.
Ina shiga ban san yana tsaye daga kofa ba sai ji nayi an kai min shaka da karfi yana fadin Uban wa ya baki izinin shigowa dakina ki kwashe min kaya.
Ina kikai min pills dina yar iskan yarinya kawai mara mutunci.
Idanuwa na,sun futo sunyi ja don matsan da nasha jinake kamar zan shude.
Yakara cewa uban wa ya,aikoki ki kwashe min kayana?
Muryan maji mukaji daga bayan mu tana cewa, ubanka ya turo ta ta,kwashe mara mutunci kawai sake min yarinya kaji.
Ya sake ni da sauri sai da naji wani iska mai sanyi ya ratsani lokaci guda, ta juya tana kallona take cewa ina abinda kika kwashe mai din?
A hankali nace mata na,yi flushing din su a toilet sun wuce, tace kwayan ke nan ko nai shiru ban bata amsa ba.
Ta nuna min hanya tace zoki wuce kinji rabuda dan iska mara mutunci kawai, da,sauri na,fita zuwa part din mu a hirgice dani.
Azuciya ta ina cewa anya zan iya kuwa wanan irin shaka haka kamar zan shude lokaci guda.
Na zauna jiki ba karfi sai mazurai nake da idona can sai ga maji tashigo na zaci zatai min magana amma sai naji tayi shiru batace min uffan ba.
Ina nan zaune sai gashi ya shigo dakin cikin shigan shi na mutunci zaka dauka wani mutumin kirkine can idan ka gan shi a lokacin.
Magana yake wa Maji babu wanda yaji may yace mata sai dai mukaji tace Allah ya tsare kawai.
Ba irin yadda ta saba mai addua ba idan yace zai tafi wani gurin.
A,a yayana tafiya kuma zakayi yau bayan jiya kadawo?.
Yace ba dadewa zanyi ba kaduna zan tafi akwai wasan da zamuyi ancan yau da yamman nan gobe zan dawo.
Har kofa suka,rakashi cikin jin dadi a ran su suna tayi mashi adawo lafiya yana daga masu hannun shi.
Maji batai min magana ba sai da rana na idar da sallah ta kwala min kira nazo da sauri ina fadin gani mama.
Samu wuri ki zauna tace min ida na na kai zaune a kasan ties din dakin nata.
Fatima fada min komai kada ki boye min don naga ke kina da hankali kinfi sauran tunane.
Nafara magana,saiga Amira tashigo hakan bai hanani fasa maganan da zan fada mata ba.
Nace tun fitan shi cikin dare jiya ana ruwa nagan shi ta,window dakin mu har ya dawo a cikin maye banyi barci ba.
Naga kuma yashigo da leda yana tangadi haka yasani sanin cewa da kayan mayen ne ya dawo a hannun shi.
Shiyasa da,safe nace zan gyara dakin nashiga ba fara neman su sai gasu na gani nan na nuna mata hoton su dana dauka a,wayana dakuma yadda nai flushing din su.
Allah yai maki albarka Fatima, da yanzu duk wanan abin shaye su zaiyi a cikin shi tayaya wanan bazai wa mutum illa ba wai.
Nan take fadawa Amira tun da yazo rai a bace yana tambayan wa ya gyara mai daki nasan akwai magana shiya da yace takai mai abinci don ban taba jin yace haka ba nasan akwai wata a,kasa.
Bin su nayi na,samu ya shaketa wai sai tafito mashi da kayan shi sai gani.
Amira tajuyo inda nake race kai Bintu akwaiki da karfin hali wallahi ai danice sai kawai na,suma.
Nace niko muddi ina gidan nan anty naga yayi abin shan sa na dauki alkawari sai nai mai magana.
Baki, gani zai kashe muna uwa da bakin cikin shine anty?
Murmushi Maji tayi sai ta kara jin Bintu ta,shiga mata a,rai sosai fiye dama baya yanzun saboda ita tai wanan kasadan haka.
Amma a fili cewa Maji tayi kiyi a hankali Bintu kin san karfin ku ba daya,ba dashi badon Allah ya kawoni ba da Allah kadai yasan irin dukan da zai maki kan kayan mayen shi.
****** ********* ******
Tuki yake amma zuciyar shi sai faman tukuki takw mai yana kitayatta idan ya samu sa,an Bintu irin dukan da zai mata watarana.
Haka ya isa ya kira maji tana kallon kiran shi amma taki daukan wayan nan ya gane har yanzu fushi take dashi ke nan.
Da yamma ma bayan sun gama,ball yakira sai Bintu dake falon ta dauki wayan tasan shine amma sai cewa tayi mai wayan bata kusa ta kashe wayan kit.
Haushi da takaicin yarinyar suka rufe shi a lokaci guda yace a fili, I will deal with dis girl.
Bari na dawo zata sha mamakina don naga akwai raini a kanta.
Ance kowani mahaluki danasa irin baiwan sai dai wanda ya,rena nasa kawai amma kowa da irin wanda,Allah yai mai.
Hakane ga,sadauki don yanzu yana cikin matasan da kasa ke alfahari dasu a fagen kwallon kafa.
Don idan yana a cikin kwallo Allah na bashi sa,an jefa kwallo ga raga, yaci duk tsananin wasa idan ya kama sai yakai gola.
Suna gama wasa washe gari ya kamo hanyan sokoto bai iso garin ba sai zuwa yamma sosai ya iso gida.
A lokacin muna,gyaran falon Maji duk da,ba aikina,bane amma ina tsaye ina,taya anty maryam mofing din kasa.
Sallaman shi yasa gaba daya suka juyo kan shi suna,mashi sannu da zuwa.
Amma banda ni da na zage ina,aikina hankali a,kwance.
Sadauki ya samu kujera ya zauna akan daya daga cikin kujerun falon nan suke ta tambayan shi ya hanya ya wasan su na can.
Naso na share shi don ina cike da takaicin makuran da yai min jiya kafin ya tafi tafiyan dayayi.
Sai nai tunanen bari dai nagaida shi kodon mahaifiyar su dake zaune din bata,rage ni da komai ba na rayuwa.
Don yan magana,sunce ko lahira wani tana cin albarkacin wani, na dan waiga gurin da yake zaune ya wani lumshe idanuwan shi nace.
Sannu da dawowa ?
Tankar a mafarki ya tsinkayi zakkakan muryan na ina,gaidashi.
Da sauri ya,wani bude idanuwan shi, yana kallo na na zaci ba zai karba sai naji yace yauwa.
Ban kara bin ta kan shi ba naci gaba da,abinda nakeyi a lokacin, ganin da nayi bai bar cikin falon ba yasa na aje mopan ina cewa anty maryam ki karasa sauran zan shiga ciki.
Dakin mu na nufa duk da magariba ne amma sai na,fada kan gado in tunanen ashe kuwa zan iya taimakawa Maji kuwa.
Shigowan Anty maryam din daki yasa ni dakatar da,shawaran da nakeyi a lokacin.
Tace lalai ma Bintu watau gudowa kikayi kikaki karasa,min aikin ko?
To tashi yaya yace ince ki hado mai abin sha yasha kafin ya tafi sallah.
Nace anty ke mai zai hana ki hada mashi nifa ban iya masifan shi wallahi.
Mutum ko yaushe a murtuke kamar mugu sai faman bakin rai da hararan mutane.
To naki yake so ai yana ganina,baice na,hado mashi ba,sai ke, yake son ya,wahalal.
Ta fadi hakan cikin yanayin zolaya tare da yin dariyar keta a fili tana ta darawa.
Nace wallahi anty badon mama ta haife shi ba,sai nace yayi gadon mugun ta,sosai.
Maryam ta juya tana fadin lalala haka,kikace mashi bari naje na,fadawa Maji kince yayi gadon mugun ta a,gurin ta don haka,baki hado mashi.
Da sauri na mike na,sha gaban ta ina cewa don Allah anty yi hakkuri kada ki hadani da mama barin fito na kawo mashi.
Dariya tasa min tace koke fa aikw ce da shegen rashin ji kike taba mai kayan shi.
Na,jera ruwa a jug da,cup cikin dan tiren su na,roba nafito mashi dashi falon .
Yana zaune a,falon har wanan lokacin ya,dauki kafan shi daya,ya,dora,a,dayan yana,kallon news din da ake a,tashan NTA.
Na kai turen gaban shi na aje da zuman na bar gurin.
Yace waye zai zuba ruwan da kika girke kamar wata,bakauya haka dake sai shegen sa ido.
A ya,tsine nace ai dama yar kauye ce ni.
Yace ke baki da kunya fa don naga kina,son raina ni a gidan nan don kin samu guri.
Nace a hankali badai a,guri ka,na,samu gurin ba ai, da hanzari na,mike na,shige ciki kafin ya,furta,wani abu.
Nan na barshi baki bude yana mamakin da,alajabina sai ya kuta,
Yana kutawa daidai Maji tana,fitowa da,alwalan ta,do ita,saidai ta jira kiran sallah kullun haka dabian ta yake.
Ta bishi da harara tana cewa kada ka,soma taba min yarinya wallahi za,ajimu dakai a gidan nan.
Da,dare muna,zaune abinci kowa ke ci sai gashi ya shigo falon wanan karon ya canza kayan jikin shi zuwa wasu kanan kaya masu matukar kyau na maza.
Ya zauna ba,wanda tai azancin mikewa ta bashi abinci nima da nake taimakon shi ina,bashi sai na,share shi kawai don yanzu ban ganin kimar shi kaman da can baya.
Waya na dake gefe yai kara don haka nakai hannuna da sauri na dauka don ganin kowaye mai kira,na.
Kabir ne, yake kirana da,sauri na dauka don kada kiran ya tsunke a lokacin.
Da murmushi a,fuskana nake cewa Assalamu alaikum sahibi rayuwa,
Ya,amsa da cewa haba Fatima kishin ruwan rashin jinki da,ganin ki yana,son illantani amma,ke ko a jikin ki baki damu daki kirani ba.
Na dan langabe kaina kamar yana,kusa dani nace, cikin yanayin tausayawa.
Nace wayyo Muhammad Kabir dina,wallahi ba,haka,na,bane kasan yanayin karatun dana,fara ne ba hutu yanzu, amma nima na damu da na gan ka ai.
Ya ce hummm saika ce dagaske Fatima keda har yanzu baki iya,sakewa dani idan ina kusa dake.
Ni dai yanzu ina,rokon ki rage wanan masifan kunyar taki haka,na adan bani gurbi nima.
A hankali na,dan saki wata,yar dariya mara sauti nace yadda kake jin rashi na a kusa dakai hakana nima yanzu nake jin naka ai.
Yace aiko danafi kowa sa,a a duniya zukekiyar yarinya kamar ki tana jin kewan tsoho kamana haka.
Maganan shi ta,sani yar dariyar da ban tashi yi ba tare da langabe kaina a hankali saman kujeran da nake kusa dashi.
Wani irin tsaki mukaji ya,sake tare da,mikewa tsaye yana fadin maji ni zan dan shiga gari sai da,safe.
Tace abincin fa,bazakaci bane yace No abarshi kawai tea zan sha idan nadawo.
Ya fita maji na fadi zaka gurin mugun halin naka ko don nasan dai can ka nufa.
Baice uffan ba sai yar guntuwar murmushin da yayi iya yake.
Yana fita daga falon maryam tace Bintu yanzu gaba,daya kin canza daga Bintu kin koma wata mara kunya,can dake.
Wayan ma,a,gaban mutane kike ba,kunya,ba tsoron kowa, Amira tace barta sai watarana yaya ya,fasa wayan nan din karamar aikin shine hakan tambayi maryam kisha labari.
Nace aiko da,ya,biya ni koda yake inma ya,fasa,aishi ya,saya,min dama shikw nan yayi amai ya lashe ke nan.
Nan suka,sani gaba suna min sheri wai suna son gani Kabir din nan daya sace min zuciya haka,ya,mayar dani wata,mara kunya haka.
Nace anty Amira,bafa yaro bane matan shi biyu da yara,biyar.
Kafin nakara,furta wani abu sukace a lokaci guda mata,biyu da yara,Bintu ?
Shine har kike wani rawan kai haka akan mai mata da,yara baki tsoron kishiya ne ke?
Nan na,basu labarin irin takakan da matarshi takawo min hargidan mu a,kauyen mu.
Cabdijam wallahi kin fara,gani ke nan may ke cikin auren mai mata yanzu banda,tarin rashin kwanciyan hankali.
Nace cikin yar murya,to anty wanda ya samu badashi za,ayi ba idan hakane yafi min zama,alheri arayuwana Allah ya,tabbatar min.
Amira,tace wallahi kina,da karfin hali ashe haka Bintu nikan danice da tun zuwan matarshi gidan mu mun rabu dashi wallahi din alama,ya nuna ko a gida,akwai matsala,ke nan.
Kafin nai magana,sai mukaji maji tana cewa, ke kada ku zugata Alkah ya,hana,auren mai mata,ne halan.
Idan ku bakuyi ita da,tasan ciwon kanta ai bataki abinda Allah ya, kawo mata,ba.
Maji aini wallahi yadda,naga,kunayi a,gidan nan bani ba,auren mai mata,kuma.
Tsuki uwar tayi tace tunda,kece Alkah basai ki zabawa kanki abinda kike so ba mugani.
Nan dai mukai tahira,akan Kabir da iyalin shi dakuma inda yake aikin shi.
Washe gari tunda safe muka,tashi da,raba tsaraban mutanen kaduna ashe dankalin Iris ya,sayo mai yawa inaga,buhu guda ne da,manjan miya,wa kowan su saida safe mukaita kasawa,aka kaiwa kowa nata,kason suka,karba,suna,godiya cikin basarwa.
Maji tana da,wanan halin komai kankantan abu sai ta,rabashi tabawa kowa agidan sai dai in abin ya tsaya,wamu, yaran tane kawai.
Bai shigo gida,ba,sai misalin sha,dayan rana,lokacin mun fita,zuwa gidan wata kawar Amira da,matar yayanta ta haihu.
Maji kawai ya,samu a part din tana,zaune tana, gyara,tasbahan ta,daya,tsinke ya,shigo.
Su gaisa take tambayan shi sai a lokacin ke nan yatashi ko yace Maji kin san na kwaso gajiya shiyasa da,muka dawo sallah na,kara kwantawa.
Yace ina yaranan suka,tafi ne ina,son a danyi min aiki ne kadan wani magani wani mutum ya bani na,hausa nake son su dafa min.
Sun fita,zuwa gidan kawar Amirah yanzun nan amma,aiba jimawa zasuyi ba a can din.
Shiru yayi sai zuwa can kuma yace amma maji wanan yarinyar sai naga kamar fitsarta, ya,fara yawa fa?
Maji tace wake nan kuma ? duk da tagane wa yake nufi din.
Yace wanan bakuwar yarinyar taki mana,
Wa wai Fatima kakw nufi kowa dai?
Ita din ke nan don ban san sunan taba ni.
Fitsaran may tai maka,ko don ta,ceci rayuwanka da,halakan shan kwayoyin data,kwashe a,dakin ka shine fitsaran da,kake gani tana dashi.
Kai haba Maji ni ba nufina,ke nan ba,wallahi amma ki duba,yadda,take waya,da,namiji a gaban mutane babu kunya a,idon ta.
Au to idan batai waya da mai sonta,ba,dakai zatayi ke nan ko?
Koko anan zan tabbata,dasu basu aure su a,rayuwan su.
Kai ni Maji ba haka,nake nufi ba,fa kawai dai ina gudun kada ta bata,sauran yaran nan ne kawai da irin fitsaran ta.
Ita Fatima ce zata bata yaran ko kai dakw abin kunya a gaban su suna,kallo kuma,babu yadda zanyi dakai.
Akwai fitsaran daya,fi yau da,girmanka,ana ganin ka a cikin maye babba da,yaro ana min dariya.
Dukar da,kan shi yayi kasa yana,dayasanin maganan dayayi a,lokacin daya sani kawai ya dauke matakin daya kudurta a,rayuwan shi final.
Nan tace gaba da,fada mai maganganu masu tsuma zuciya na irin zabar mata da mutuncin ta,da,yakeyi ga idon mutanen duniya.
Kanshi na,duke sai tafasa,zuciyar shi takeyi yarasa irin son da Maji takewa wanan baren yarinyar haka wai.
Wani irin zafin rai yakeji a lokacin tankar aradu ce ta,sauka,mashi a kirjin shi duk sanyin AC dake ratsa falon hakan bai hanashi zufa ba .
Muna,shigowa gidan da murnan mu yanayin da,muka,gan su a ciki sai da ya,tayar muna da hankalin mu.
Suna gaida shi ya,dago idon shi da,suka kada,sukai mashi ja kamar garwashin wuta ya amsa masu.
May yafaru kuma,yaya Amira take tambayan shi tare da,duban fuskan uwar su dake zaune tana abinda takeyi.
Yace babu komai Amirah kaina,ke ciwo bari naje nasha,magani dakina.
Yana,fita Amira ta juya, gurin maji tana tambayanta da,cewa anyi wani abin ne kuma,Maji ?
Shi dai ya,sani inji maji gaskiyane baiso k8n san da,anyi mai fada,sai ya,koma kamar wani namijin zaki dashi.
Shiko yana fita gidan sashen shi ya nufa yafada kan katifan shi yai lamo dashi kamar wanda,yake barci,sai dai ba barcin yake ba .
Damuwa ce ke damun shi na baisan abinda zaiyi ya,farautawa uwar shi rai yaji dadin ta,ba.
A hankali wasu siraran hawaye ke zubo mashi yasan Maji tana,da,gaskiya don yau ba mai son cikin dubu ace nashi ne ya lalace.
Ya juya,yana,cewa,wayyo ni wanan rayuwan may nayi rayuwana,ya,koma,haka,alokaci guda.
Ba dadi ga,uwana,ba,dadi ga yan uwana,haka ma wasu al,umman garin danake tare dasu ada can baya.
Shi dai yasan yayi iyawayin shi akan ya,daina wanan harkan amma,sai yayi kamar ya,bari sai kuma,ya,tsunci kan shi dakara komawa gasha kuma.
Ya Allah ka kawo min agaji cikin wanan halin rayuwan da nake ciki.
Ai hakkuri da,wanan bayawa yau nagode da,bani lokacin ku da kukeyi kullun Allah yasa,mu gama,da duniya lafiya yan uwa
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,
Yanzu al,amarin Aliyu yakai har gidaje masu sayen ruwan pure water shi suke aiken shi.
Ko kuma,su aike shi dakunan su na,gwauraye yakai masu abu ko ya dauko masu idan ya dawo su dan yi mashi dan ihi sani na kudi ko wani dan abin kwadai.
Uwaye lokaci muke yanzu da,ba,yarinya mace ce kawai zaka,nisanta tata irin wa yan nan abubuwan ba har da,namiji idan kina dashi dole idon ki yana a,kan shi tun dai in ya fara shiga adolarcent year din shi na,balaga.
To yanzun ma yakai ko yaro baikai wanan shekarun ba,yawon yara,yai yawa don sun san komai na,rayuwa,da birni da kauye.
Maria ba abinda ya damay ta binciken al,amarin dan ta sai alfahari take Allah ya hore mata da mai hazaka ga kan talla gare shi yana da sa,an samun ciniki sosai.
Bata kula da cewa wani lokaci idan yadawo baya damuwa da cin abincin gida sai dai yace mata ai ya koshi.
Daga cikin masu aiken shi a kwai wani matashi anace dashi sisko don irin wankan da yakeyi na matasan zamani.
Amma shi ba ruwan shi da yan mata sai dai yawan son wasa da yara musan man maza.
Haka yasa sisko ya ke son Aliyu sosai a rayuwan shi don yana yawan ba yaron kudi ya sayo mai abu idan ya dawo da canji ko nawa ne sai yace ya barshi kawai.
Haka yasa har Allah Allah Aliyu yake da,sisko yafito majalisar su hira idan bai gan shi ba ya kafa tanbayan yau sisko bai fito bane wai.
Shiko idan ya fito ya,shiga wasa da yaron ke nan yana dan matsan shi cikin jikin shi.
Har sai yagaji tace yaje ta sayo masu wani abu daga cikin kayan zaki ya dauki rabi ya,ba yaron rabi tace ya,dauka duka.
Su kuma mutanen dake zama,gurin basu damu da saka masu ido ba,su dai kawai suna ganin tasu ce tazo daya,kawai kamar yadda,jin mutane kan hadu.
Rana Sisko bai fito ba har kwana,biyu don haka Aliyu ya matsa,har saida,akai mashi kwatancen gidan su Sisko din.
Yana zuwa,ya,samay shi a dakin da,yake haya,daga wajen wani gidan haya kasancewar shi gwaro yake daga,dakin kofan gida.
Kwance yake dakin rubb da ciki yana kallon wani film a tv dakin shi,
Yaron ya dan tsaya daga,waje yai sallama ya gane muryan shi yake cewa,a,a Aliyu mai pure water shigo mana.
Waya gwada ma gidana yaron yace tambaya nayi aka nuna min ance baka da lafiya shine nazo dubaka.
Yace wa yaron ya zauna su nan zaune yana dan mashi wasa ne yake cewa ya ya karbi kudi ya sayo masu cock su sha da maltina.
Yaron ya,sayo suna,sha,suna hira yake tambayan shi ruwan nawa ya,dauko yace mai ta,dari uku ce yaciro dari uku ya,bashi yana cewa, idan baka,son talla tunda kaga,dakina,sai ka,dinga,zuwa muna,kallo sai na,saye ma,ruwan ko.
Cikin jin dadi Aliyu ya,karbi kudin yafita yana godiya tun daga wanan ranan take zuwa gurin Sisko don yasan lokacin da yake gida.
****** ********* ******
Raiha yanzu bata shayin kowa don ta riga ta bushe fitilar ta ko, a wani yammaci sun shirya da Nura zasu wani bukin wata kawar Nura din a wani unguwa.
Acika an yi yawa gurin taron ida shahararun yan mata ke gwada kwalliyan su.
An fara program din ne Raiha da Nura suka,ratso ta gaban mutane suka,shigo inda ake reception din.
Idon mutane caaa a kan su don kwalliyan su gaskiya,ba laifi ko a gidan wa zasu iya zuwa a hakan.
A hankali suke duban gurin da babu mutane da yawa a saman kujerun zaman dake gurin .
Can suka hango wata yarinya zaune ita kadai dan nesa da,bango take zaune.
Don haka can suka nufa suma,suka zauna sun so su basar da juna amma,sai take ce masu sannun ku fa.
Su ma,suka amsa da,yauwa ya,garin dai ta ansa da lafiya kina tare da,wani ne ?
Nura dake gyara zaman ta take tambayan yarinyar da,suka,sama a gurin ita kadai.
No ni kadai ne ina jiran wani ne dama kuma,ba,a barshi ya shigo ba wai baida pass.
Kallon junan,su sukayi sai kuma,suka,danyi murmushi kawai au shi wanan bukin har da wani pass ake nunawa cikin sa.
Yarinyar tace wai haka sukace maza ba kowa za,a bari ya shigo ba,wai sai wanda yake da pass din.
Ok ke kuma,sai kika kyaleshi kawai a,waje ya zauna yana dakonki kawai.
Sister maye naki a cikin, ne wai mu dai ba mun samu wajen zama ba kawai.
Abinda yaba yarinyar mamaki shine yadda haddadun gayu ke zuwa kawo wa su Raiha gaisuwa har saman table din da suke.
Wasu sukanyi zaton tare da yarinyar suke sai su dan so kutsa kan su gare ta sai Raiha ta dakatar dasu tana cewa kai wanan bakuwar hannu ce fa,bata san kaiba tukun.
Bayan su mata san masu ji da kan su sun tafi Nura ta juya gurin yarinyar tana cewa waike ya sunan ki ne.
Ta dago daga dannan wayan da takeyi tana cewa, wani tace ke mana.
Yarinyar tace hmm sunana Nafisa Abubakar ok anan garin kike da zamane ta amsa da cewa cikin dan dago kanta,
Eh nan ne gari mu muna zama a sama,road ne nida iyayyena.
Nan dai Nura take dan jan ta da fira da,zasu tafine sukai musayan waya.
Nafisa ta riga su fita don haka sai abin hawa yai mata,wuya a lokaci don matasa na cikin hole din sosai ana ta shan shagali a ciki.
Sunzo wuce wa ne Raiha dake driving ta hango Nafisa tsaye sanan titi sai faman kallon inda zata samu abin hawa takeyi.
Nurace tace don Allah tsaya mu ragewa wanan yarinyar hanya don yarinyar taimin wallahi.
Ban gane tai maki ba,damay tai maki ne wai a,a kema kin sani don idan ta,waye ai zata faso itama.
Nan dai Raiha tai ribas suka tsaya,suka taya mata shiga su sauketa a gida bata musa ba kodon a ganta da,wa yan nan haddadun gayun abin bajintane ai.
Tashiga suna tafe Nura tana marming din wankan dake tashi a motar tare da dan dakilar wayan ta da yazama rabin rayuwan mutanen yanzu.
Can ta dago ta juya kadan inda Nafisa take zaune komai na yan matan yana burge ta wallahi don sun matukar wayewa.
May ma,sunan ki kace tace a hankali Nafisa nake , tace ok ban nombanki watara ai za,ai zumunci ko Nafisa taji dadi dama tana so tana gudun ta zubar da kan tane garesu.
Nan sukai musayan nomba a tsakanin su inda takirata da nombanta itama tace a hankali wazan sa don ban san sunan ku ba .
Nura tace a baki bukaci hakan bane mukan ai mun tambayi naki don kin bamu gurin zama.
Nuratace zaki iya kira na da Nuriya ko Nura ita kuma wanan driver din zaki iya ce mara Raihanatu.
Wallahi sister zamuyi tsiya dake idan kina bata min suna ba Raihanatu ba yar iskan banza sunana Raiha kiji baby.
A daidai kofan gidan su da tai masu kwatance suka tsaya da motan su a daidai lokacin da Bintu ke fitowa daga cikin gidan ita da maryam.
Wani kallon banza suka,watsa masu suka,wuce su nan Nura ke tambaya wanan yaran yan gidan nan ne naga sun wani hade rai da,suka gan mu mana.
Kyale su yan kishiyane bakin ciki suke kawai dashi kuma zasu mutu yan hassada kawai.
Sukai sallama ta shiga gida suka,wuce sai sautin kida ke tashi daga motan su.
Bayan motan sadauki dake fitowa yagani tare da,bin Nafisa da harara ta make gefe ya fice abinshi.
Tana,shiga ciki take cewa,uwarta ni ban san may naiwa wanan dan mayen ba,sai ya wani kama hararana.
Da,sauri uwar ke cewa wa sadauki wallahi ahir din shi dake bari ma,na,samu uwar shi tun yanzu.
Ta mike sai dakin maji sunyi daidai da ita a tsakar gida take cewa Hawau kiwa danki fada wallahi ya,fita idon Nafisa don ban haifar mashi ita ba.
Shidake da abin fadi tab ga tsuliyane har zaicd zai sakawa wani ido akan may?
Da yake iskancin shi a gidan nan waya hanashi yin abinda yaga dama da zai wani sa,wa yarinya ido.
Baima da kunya da bai kalli inda Nafisa take ba,sau nawa yake zubar da abin kunya babu mai kwasa a gidan nan.
Kai bama gidan nan ba,duk gari kowa yasan irin tabargazan dayake mai abin kunya kala kala har basu faduwa ma.
Tana juya sadauki yana tsaye sai su maryam da Bintu daga gefe Amira tana tsaye daga kofan su cikin mamaki don ba dama ta tanka saboda mahaifiyar su ta hane su da hakan.
Maji tace tau yaya in ma sadauki nada abin fadin da har bai faduwa ina dai uban su daya da Nafisa ni ban san yadda zan raba tsajanin su ba.
Umma tace in baki sani ba,aini na sani don ba kare bin damo yabar ganin dan wanan abinda yake torokon yana samu ko zai rudeni na kasa daukan wa diyata incin ta.
Wallahi duk randa yai gigin taba min yarinyar ranan ba kwaya, yaje sha ba ko dan babule yake sha zai gane kuren shi.
Abin kunya ma hada alaka da irin ku ko barnan suna har yana wani kirarin wai yar uwan shi ce ita.
Wai may akayi ne Maji ?
Sadauki dake karasowa yake tambayan mahaifiyar tashi cikin bacin rai.
Hannu kawai Maji ta daga mashi tace babu ruwanka bari ta fada min abindake ranta dama,ba yau ba take dashi.
Kada ki min rashin kunya kan wanan tabararen dan naki mara mutunci wanda ya zama abin nune ga mutane.
Ina fatan Allah ya,shirye shi dashi da,duk wani mai irin halin shi ma.
Daga,baya ke nan bayan an kasa,ba,yaro tarbiya,tun farko sai yanzune za,a roki Allah kuma.
Ta,wuce a fusace tana fadin wallahi shege ka,fasa a gidan nan ni daku marasa mutunci kawai masu abinfadi lodi lodi kawai.
Daki suka,shige gaba dayan su suna fadin wai may kuma yafaru yanzu yanzu ne wai ?
Maimakon uwar tai magana,sai kawai ta,fashe da kuka mai tsuma zuciyan duk wanda ke kusa a lokacin.
Sadauki yace wai maji don Allah may yajawo wanan cin mutuncin ne haka wai?
Kai ma ,
Wazai ja min in bakai ba mai abin fadi lodilodin da akace aiba karya aka fadi ba ba a fadin ne ko yaushe.
May yakai ka ga yarta wata yar tata kuma ya tambaya da sauri don bai san kan wanda ake zance ba.
Maji tace Nafisa mana,
May naiwa Nafisa kuma ya tambaya a cikin mamaki?
Ai duk abinda kai mata ka,sani tunda baka rabuwa da yarta bayan kasan gorin da zai biyo min baya.
Wallahi azeemun ban cewa Nafisa kala ba kuma Allah ne shedun hakan wallahi.
Koma dai maye kaka sani kaita hi kana jamin gorin da banda baki akan shi.
Mamaki takaici, bakin ciki suka rufe mai zuciya sai muryan Bintu sukaji tana cewa aiko kowa nada abin fadi don itama ai ta haifi yar iska.
Ranan ai ganin Nafisa nayi kwance saman jikin namiji a mota shiba iskanci bane.
Ke Fatima kada kiwa yar uwar ki sheri don ta bata min rai don sheri kare ne mai shi yake bi, don haka ki bari.
Haka Allah yaso zamana acikin su don haka sai kowa yayi hakkuri.
Da,wanan bai fitar da kanshi daban acikin halin yan uwa ba da duk ban ga hakan ba.
Ta mike zuwa ciki ranta a bace mata don zafin maganan da aka,fada mata bata da,bakin mayarwa.
****** ********* ******
Wanan magana wasa wasa saida yakai maji kwace don tun lokacin da akayi shi Maji bata,kara lafiya,ba a jikin ta haka ta koma,sukuku don zancen Umma yana,gasa mata zuciyar ta sosai.
Bayan kamar sati da maganan zazzabin Maji ya tsananta ranan kwana mukayi ba muyi barci ba ,
Gashi sadauki baya gari yai tafiya Baba ma bai nan ya tafi kasar Niger state zancen noman shi.
Nace wa su Amira gaskiya ya kamata da,safe muje asibiti don bazamu zauna da ciwo ba haka a gida.
Amma sai Amirah take ce min wai mu dai bari Baba ya,dawo tukun muji mai zaice.
Da,asuba nazo tayar da ita tai sallah naga irin yadda take numfashi yana fita dai,dai.
Nace a raina kai wallahi nikan asibiti zamu da safe don in mun biye mata zata halaka a daki kwance sai paracetamol muke dirka mata.
Muna idar da,sallah Na samu Amira a kwance, nake ce mata zan fita na nemo mota idan gari yadan haska muje asibiti da mama.
Da wani mota zaku kin dai san babu mota yanzu a gida dashi akewa baba aikin gonan shi.
Nace ai akwai na haya ko?.
Ta zaci zance kawai nakeyi nafita ina mamakin hali irin na su Amira halin ko inkula da sukeyi uwar mutum ba lafiya amma su kamar ko a jikin su.
Gari na dan haske na,saka hijjab dina nafita daga gidan sai bakin titi nai sa,a na samu mai adaidaita sahu irin masuyin sakko gurin neman kudi.
Muka,shirya dashi nace ya kaimu asibitin koyarwa ta gawon nama, watau teaching hospital.
Na leka dakin su Amira suna,barcin su hankali a kwance na koma gurin Maji na samu sai nishi take guda, guda.
Cikin matsanancin tsoro da,firgici nace mama tashi muje asibiti aduba,ki.
Batai min mussuba kamar yadda na,zata, don haka na,dauki hijjab na,saka mata tare da son mu fita .
Cikin karfin hali take ce min, dauko jakata akwai kudi a ciki mu tafi dashi kada muje mu wulakan ta.
Har muka fita daga gidan kamar babu mutane kowa na,dakin shi rufe na,sayawa su Amirah kofa muka fita daga gidan.
Ban taba zuwa asibitin ba amma haka na daure muka shiga don ba wani nisa ne sosai a tsakanin mu ba.
Munyi sa,a don sanmakon mu yai muna rana muna zuwa aka kaita emergency don sunga yadda muka shigo da ita.
Bayan yan aune aunen da,sukai matane likitan yake cewa ke yarta ce na amsa mashi da eh,
Yace to ina manyan ku suke aka bari ke karama dake kika kawo mara lafiya haka acikin wanan yanayin asibiti ?
Nace, Baban mu baya gari shi da yayan mu sunyi tafiya yace alright yanzun dai zamu bata gado tare da bata taimakon gagawa tukun kafin mu auna ta muga may ke damun ta haka?
Sai da na,tabbatar da cewa an bamu gado anyi komai har an saka mata ruwa na dauki waya na kira Amirah wace cikin gigin barci take min magana.
Nace Anty gamu fa asibiti da mama an saka mata ruwa ma ko.
But tamike da mamaki azaton ta wasa ne don shirmay ta amma tana dubawa dakin Maji sai taga wayau har falo taje babu mu.
Bayan kiranta kamar kada na kira yaya sai dai nace bari na kirashi dai yasan halin da uwarshi take ciki.
Babana ta rubuta wajen sunan shi na danna kiran layin baifi ringing uku ba ya dauka yana cewa,
Maji yanzu nake son kiranki naji ya jikin don jiya Amirah ta fada min kina jin jiki sosai.
Nace ba mama bace nice Bintu gamunan asibiti da mama an bata gado.
Yace cikin wani irin murya what, anba Maji gado a,wani asibitine kuke?
Nace na,gawon nama watau Usman dan fodio teaching hospital.
Yace ke ba Amirah wayan please nace Amirah tana gida bata iso ba tukun
To wa ya kawo ta,assibitin ita Amirah tana mayye nace ta tsaya hada break ne.
Tsuki yaja tare da kashe wayan ashe bayan ya kashe Amirah yakira yace yaya jikin na maji wai may ke faruwa ne.
Tace wallahi yaya ban masan sun tafi Asibiti ba Bintu ce ta kirani take fada min yanzu wai suna asibiti.
Yace you are very stupid Amira yanzun saboda shegen barci tsiya har aka fita da Maji gida baki sani ba ke kina may ye har wanan yar kauyen yarinyar ta kaita asibiti.
Tas yai mata tare da umartan ta duk abinda take tai maza ta samay mu asibiti kafin ya bata mata rai.
Ina zaune na tasa maji da ta samu barci a gaba sai ga Amirah da maryam a gagauce.
Sun wani fuske sun dauki zafi dani ban damuba don nasan ni don Allah nayi masu.
Don danabita nasu sai dai ta halaka a gida saboda sanyin jikin su da narkewa.
Muna nan zaune sai ga likita yazo da takarda magani a rubuce yace suna bukatan wa yan nan.
Karba Amirah tayi tare da ficewa dakin dagani sai maryam ke kan mama din.
Ajima kadan sai gata tadawo da takardan tana fadin ke Bintu nifa ban san inda ake sayar da maganin su ba.
Nace a tambaya mana take cewa wai wa zata tambaya amsa nayi tare da daukan kudi ga post nafita.
Da tambaya,na gane gurin sai gani da maganin cike da leda nashigo dakin nan na mikawa nurse din dana samu tana gyara ruwan dake tafiya a jikin maji din nayi.
Shiko sadauki yana gama waya da Amirah mahaifin s
hi ya kira yake sheda mashi abinda ya faru da uwar su.
A gagauce Baba ke tambayan shi yanzu maijidda tana ina wai?
Yace tana asibiti an bata gado ita da wanan bakuwar yarinyar Fatima dake dakin ta.
Su su Amira fa suna inane da sauran mutanwn gidan da har za,a bar Fatima karamar yarinya takai ta asibiti da kanta duk an rasa wanda zai dubaran daukan ta zuwa asibiti sai Fatima karamar yarinya haka da ita.
Sadauki yace yanzu nakira su Amira ga,waya mazasu tafi asibitin suga halin da ake ciki don dai tace wai an daura mata ruwa a,jiki ko.
Allah ya sauwaka insha Allahu gobe zan dawo nazo naga abinda ke faruwa hakanan.
Suna kashe wayan sadauki ya dab furzo iska daga bakin shi kadan tare da dan gyara tsayin shi.
Agogon shi ya fara dubawa ya san idan yace zai taso daga anambara zuwa sokoto ba karamin tafiya bane don haka ya yanke shawaran samun jirgi zuwa abuja daga abuja koda da motane sai ya karaso.
Karfe, Biyun rana yana garin Abuja bai bata lokaci ba ya samu shatan mota sai sokoto,.
Suna zaune sai nice ke ta faman zirga zirga wai su yan gaye a hankali maji ta bude idanuwan ta da ta kusa yini tana barci.
A lokacin bani daki sai Amira ce zaune mun fita da maryam zuwa wani guri tace na,rakata.
Bayan ta bude ido tafara bin dakin da,kallo can tace, Fatima, Fatima, sai Amira ta mike tazo inda take kwance.
Maji kin tashi ne tace wa uwar ta, sai uwar ta ce mata eh ina Fatima ne ?, bata nan tabata amsa.
Sai ta mayar da idanuwan ta takara rufe su a hankali, kuma again.
Muna,shigowa take fada muna mama,ta,falka tana tambayan ki Bintu da sauri na isa gurin ina,fadin wani abin take so ne Anty tace batace komai ba sai ta koma barcin ta.
Ana maggariba ya iso garin a lokacin hajiya kubura ce kawai tazo duba mama sauran basu zo ba har lokacin.
Ban san da zuwan shi ba don natafi dauko kayan da za,a bukata a gida.
Ina dawowa daga gida na sauka mashi sai naji ana cewa ke pretty, Fatima,
Jin fatima yasani dan dakatawa na waiga inga mai kirana haka nan don ban sheda sunan mai shi ba.
Ya karaso gurina da murmushin shi yana wasa da key din motan shi a hannun shi.
Yace ai tun gida na,biyo bayan ki dama na dade ina son in samu time nai maki magana.
Kin gane ne wallahi kinyi min irin tsarin macen da nake son ke nan ba wani bata lokaci ki yarda dani kawai muji dadin juna dake zan maki komai wallahi koma may kike so idan kinyarda dani zan dinga saya maki anything, anything just kawai ki bani hadin kai mu more junan mu muji dadi idan gida akwai idon mutane zan sama muna wani scret place da zamu dinga hadu ehy kin gane ko.
Wani irin bakin ciki da taikacin shi suka rufe ni ban kai karshen tunane na ba,sai ji nayi yana fadi dibki don Allah wanan idan na samayki nagama neman mata wallahi.
Yana kokarin kai hannun shi ya taba min wuya ban son lokacin da nayar da pillow dake hannu na ba nakai mashi mari fayauuu,
Daga inda saudaki yake tsaye tun saukana a mashin da tareni dayayi duk akan idon shine da marin da na kaiwa yayan nashi.
Take ya dafe wurin yana cewa ke ashe baki da kunya ashe ke yar iskan yarinya ce ban sani ba.
Har ya fara takowa daga inda yake zuwa gurin da muke don yana ganin kamar Imirana zai iya dukana.
Sai yaga na daga hannu ina fadin dan iska kawai mara mutunci masu gadon iskanci kaje ai kana da kauna Nafisa ka huta da ita ni ba karuwa bace .
Imirana yace wallahi sai kin gane baki da wayau don sai kin bargidan mu wallahi shegiya yar ci rani kawai.
Ke Fatima dauki kayan ki, kishige ciki kinji da sauri najuya don jin muryan wanda ban zata ba a lokacin duk kan mu kallon shi muke yi.
Imirana yace jimun wanan yar iskan yar kauyen fa waini zata raina wa hankali haka ji mun ita.
Hannu ya daga wa dan uwan shi yace please Imirana is OK naga komai tun saukanta mashi ina tsaye gaban ku ai.
Daga haka ya kama bina a,baya ina gaba yana biye dani har zuwa cikin female ward da aka kwantar da maji aciki.
Amirah na ganin na dawo take cewa yauwa Bintu dauki kayan can da akaci abinci ki wanke su.
Sai ganin yayan su tayi a bayana da sauri tace lah yayana ka iso ashe yace eh na tsaya yin sallah ne da na iso.
Ban zauna ba na kwashi kayan na,wanko su kamar yadda tace ina dawowa kuma duk suna tsaye suna magana Amira tace Bintu zoki sayo ruwa mu aje kada dare yayi ba ruwa a gurin.
Kai haba haba Amirah why komai Bintu, Bintu dai Bintu ku kuna may ye wai please.
Nace ina kudin yake na sayo yace ke maryam jeki ku sayo a tare da ita kuna zaune sai faman bada intruction kuke kamar wasu tsufi.
Maji da ta farka tace ai basauyi ba sai dai su bada odar yi don su sarakaine.
Sai yanzun yagane abinda yasa yarinyar ta,shiga ran maji sosai yarinyar bata da kiuyuya kuma bata fushi.
Yace ina son a sake mata daki yanzu zan tafi nai magana gurin nurse yatafi tai mashi bayanin yadda za,ayi.
Muna dawiwa muka samu har ya karbo takardan canza daki ko nan muka kwasa sai sabon dakin da aka canza mu.
****** ********* ******
Dakin kudi muka koma mu kadai ne a dakin yana da tsari sosai harda dan fridge da kayan kallo a cikin sa.
Maji har lokacin magani bai sake ta ba na kafe ta da idanu sai barci take gashi duk ta wani ramay sosai da ita.
Ban san lokacin da tausayin ta ya kamani ba sai jin hawaye nayi sun zubo a idanuwana sai sauka suke a kumatuna.
Ban san ya shigo ba yana tsaye yana kallo na may kikewa kuka haka duk suka juto gareni kuka kuma Bintu sai maryam itama ta fara kuka.
Tace Tun safe Bintu ke kukan nan idan ta kalli maji nai mata magana taki bari.
Likitane yashigo dakin saye da corth din shi baka duk muka gaishe shi yake cewa tare dan taba jikin ta har idanun ta.
Zata dan samu sauki idan ta farka amma yaya akayi kuna gari kuka bari har ciwo yaci ta haka a gida.
Gaskiya data kara awa a lokacin bata samu taimako ba da zamu iya rasata wallahi.
Ya juyo inda nake yana fadin idan ta farka sai ki hada mata tea mai zafi tasha sai ki bata wanan maganin da aka sayo amma don Allah kada kiyi mata wasa da maganin don ba abin wasa bane.
Yana fita dakin na mike tare da daukan cup na fita na dauraye shi na,dawo na,saka acikin wani leda baki.
Yace Amira waya zo daga gida cikin su Umma eh to Bintu tace ina barci wai mommy ta shigo bayan ita ba,wanda yazo kuma.
Muna zaune dakin kowa yai shiru a cikin mu duk kowa da abinda yakeyi sai ga hjy Kubura itace a gaba yaranta na bin ta a bayanta.
Suna dauke da kwandon da kuloli a cikin sa da flask din ruwan zafi sai ledojin da yaran suka riko na kayan fruit.
Tana ganin sadauki take cewa ,a,a sadauki ashe har ka iso yace cikin dagawa daga saman kujeran da yake zaune kusa da maji don ya bata guri na iso mummy.
Da sauri na mike na karbi kwandon dake hannun ta, nakao saman durowan dakin na asibiti na aje.
Tace ai natafi wancan dakin na farko sukace min kuna nan ancan guri.
Yace eh mummy gurin can bai min ba mutane sunyi tawa baza,a bar mara lafiya yayi barci ba da dadi.
Hakane gaskiya amma nan din kaga is ok zata samu hutawa sosai anan din.
Likitan ya shigo ko may yace kafin wata tai magana nace zazzabine wai typhod yai mata yawa suka ce ta ce wai da sauki ai nazaci suce ciwon zuciyan tane ke batin tashi.
Nace yama ce bata da ciwon zuciya wancan daya fadi haka bai san aikin shiba.
To Allah ya sauwaka muka amsa mata da Ameen mummy tace zamu koma don dare yayi sosai gani da yara bandawo da wuri ba shiyasa ban yi girki cikin lokaci ba.
Anwar yana lake jikin yayan shi tun shigowan su dakin yagan shi ya lake mashi sai hira suke dashi.
Tamike tare da muna sallama tabar dakin muka dan rakata zuwa kofa tace ku koma abinku zanga wata kawana dake duty acan ward din.
Tana wuce muka dawo ni da maryam nace yaya a zuba ma abincin kaci ne?
Yace No barshi banjin cin abinci yanzu Amira tace yayana bari a zuba maka kaci ko kadan ne don Allah.
Hakana jawo plate na,soma zuba mai abincin wanda dafa duka ne da kayan lanbu a cikin shi sai kifi da tai amfani dashi.
Sai dan ferfesun kifi danye da tayi daban ta zuba shi a wani dan kula karami.
Shina zuba mai don nasan bai shiri da dafa duka shi sai dai da miya ko tuwo.
Na koma gefe na zauna maryam tace zuba muna abincin muci mana kin kima zauna.
Nace sai dai na zuba maki ni ba yanzu zanci ba Amira tace kinbsan bafillatace sai kafa ya dauke taci.
Hmm aini Bintu tabani mamaki jifa yadda tai saurin boye ciwon maji wa mummy harda cewa ance wanda yace tana dashi bai san aikin shi ba.
Nace eh mana yanzu da anfadi gaskiya sun samu na fadi kena a unguwa cewa bakinciki ne zai kasheta ai likita yace kaza yace kaza.
Maryam tace wallahi kamar kina zaune kuwa don tana komawa zakiga muna fukancan sun tambayeta may ke damun ta kamar da gaske da an fada masu shike nan an samu na fafi ana canza magana.
Sadauki wanda yake zaune yana shan ferfesun shi hankali kwance bai ce muna kala ba.
Suna cin abincin duk kamshi ya bude dakin sai hira suke kasa kasa kan mummy a gidan su .
Yana gama wa yadago kai muka hada ido na daure fuska na yace kwashe kayan nan anan .
Sai da ya sha ruwa yace ke may yasa bazakici abincin ba ke nace sai anjima zanci yaya nadan sha lemo dazun.
Ya dan kalleni kamar mai nazari can yace su waye zasu kwana anan don dare ya soma sai nakai sauran gida.
Maryam tace sai dai abar anty Amira tunda itace babba ko da sauri tace a,a wallahi ban iya tsayawa ni kadai don tsoro nake ji.
Baki da hankali ne idan baki zauna ba wazai zauna dama ke dakike babba wallahi yayana ban iya zama ni kadai anan gaskiya.
Nace dama ka barsu yaya dama ni anan zan kwana ai tare da mama su tafi gida su huta su.
Yace don may za,a barki ke kadai dole dayan su ta tsaya tare dake a nan ya wuce da maryam mukuma muka zauna dakin nan zamu kwana da mama.
Azaton mu ya tafi ke nan can sai gashi ya dawo dauke da ledoji ya sayo muna su kayan shayi da kwalayen drinks sai naman kaza mai zafi ya kawo muna.
Yamika muna yana cewa kuci naman kubar wa maji idan ta farka kila ta danci
Amira ta jawo ledan gamu tana fadin oya muci Bintu nace fara ci ke, nan tafara yagan naman tana kaiwa bakin ta.
Zaune yake a saitina yana amfani da wayan shi data dauke mai hankali.
Yace wai may yasa ke bazakici komai bane wai, na dan tsuke fuskana san nan na ce haka kawai .
Yace amma badon kin ci wani abuba ko kin koshi ba ko?
Nace ban karya ba yaya ban dai iyacin komai ne saboda hankalina daya tashi.
Yaya na fada maka bar Bintu haka take ita bata damu da cin abinci ba fa ita.
Ya dubi Amira yace kina nufin zata iya kwana a haka bata ci komai ba?
Haka take ko agida sai maji tai mata fada take cin abu ita.
Yace tura mata naman da kwalin drink din tasha ban musa musuba na dauki yaka gudanakai abakina da kyat nake iya taunawa na dauki drinks din nakai abikina sai naji sanyin shi yai min yawa sosai.
Haka dai na danci naman nasha drinks din kamar wace za,a kama a lokacin
Wayana yai ruri da sauri na nufi side drower dana aje wayan akai.
Ina kokarin duba maikirana a wanan lokacin don dai nasan ba Kabir bane don a lokacin yana cikin iyalinshi.
Sadauki ya kafe ni da ido don jin waya kirani a wanan lokacin kuma ko zanyi fitsaran dana saba na waya agaban mutane dayace inayi.
Na daga tare da sallama sai naji muryan gwagona tana tambayana jikin maji nace gamunan ma asibiti da ita an bata gado.
Nan take ce min insha Allahu gobe tun da safe zata shigo gari don yanzu tafi gane ma ta dinga kai kaya gari gari.
Ina kashe wayan maji tana,farkawa duk mukayi kanta gaba dayan mu muna mata sannu da jikin ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA,BA
KA DA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,,,
Kudi yabashi har dubu daya,yace yaje yasaya duk abinda yake so dashi yaron bai san girman kudin ba yadai san ko nawane don yaka,yaje ya fara sayen abinda ke ran shi.
Kayan zaki sai kayan sanyi su ya,kwasa ya sha har yafara kyautawa,abokan shi.
Ya dawo dauke da roban shi dakin sisko nan suka zauna ya sa masu wasan turawa suna kallo daga,shi sai shi a daki.
Can sai ya sauya tasha inda ake wani wasan shedana zallah.
Yaron sai ya,fara kawar da kan shi gefe sisko ya ja mai kafa yana fadi ji dan nema kaida wata rana zaka zama boss da wanan harkan kake kawar da fuska ai gara ka fara koyo tun yanzu.
Nan dai har yaron Aliyu yadan fara tsayawa yana kallo ta gefen idon shi ajima kadan yake cewa zai tafi gida sisko yace kai tun yanzu yace lokacin zuwan shi makaranta yayi ne.
Jawo shi yayi kamar wandaya,samu budurwa yana dan wani wasani dashi sai da yaji dai,dai ya sake shi da zai tafi sai da ya,kara mai dan kudi saboda jan ra,ayi gobe.
Ruwan sai makaranta,wasu, almajirai yakai yace inji wani mutum yace na bayar sadaka anan.
Shi kuma ya kama hanyan gida yana murna da farinciki ya isa gida ya mika wa uwar shi kudin ta,saura ya samu guri ya boye.
Kamshi turare taji a jikin shi tace kai kai kai ina,kasamu wanan turaren haka mai kamshi.
Nan ya shafto karya yana fadi wani yaro ya ysunci kwallaban turare shine muka dan sawa jikin mu.
Tace yaci abinci yace sai ya dawo ba yanzu don haka tace yai niya yafita koshi da kyat tasamu ya fita don ya kwata jikin shi yana mai ciwo ga kuna kayan sanyin da ya cika cikin shi dashi fam.
Amma ita da yake son kudi ya rufe mata idon ta sam bata hango illa ga rashin cin abincin da yaron baiyi a kwanakin nan ba.
Yaro idan ya,fara talla ko yarinya komai zama kamilin yaro kwana kadan da,fara tallan yaro idon shi zai bushe.
Idan sau daya kakewa yaro tsawa ya bar abu yanzu sai kayi uku masu karfi kfin ya bat abinda ka hanne shi.
Yaro idan ya fara talla baijin naiyi ko kunya fada wa babba magana yadda yaso sai dai kai babba kaji kunya.
Yanzu duk irin haka ke faruwa,da,Aliyu amma uwar bata da fahinta ita bukatar ta kawai ya kawo mata kudi a rayuwan ta.
Mahaifin yaron ya ga matukar canji akan dan shi sai dai ya danganta halin yaron sai ya dangata shi da girma yasa shi canzawa a baki daya.
Tun wanan ranan kullun sai Aliyu ya,tafi gurin sisko saboda dan kudin da yake samu gare shi.
Gashi uwar ba ido take sakawa akan yaron ba ita gurinta kawai shine, taga ya kawo mata kudin da yawa.
****** ********* ******
Tun wanan ranan da suka hadu suka zama abokai tsakanin su da Nafisa.
Ance abokin barawo barawo ne don Nafisa bata san ya akayi tafara shan abubuwan dasu Raiha ke shaba saidai kawai ta tsunci kanta a cikin shaye shaye dumu dumu da ita.
Ga uwar ta,Umma a kullun zancen ta sai zagin sadauki da yiwa uwarshi dariya bata san na dakin ta yafi illa,ba ma.
Sai dai tana kokarin ganin kowa a gidan su kada ya,san zancen har a,kyamce ta ita da uwarta kamar yadda akewa Maji da diyan ta gaba daya da abin bai shafa bama.
Yanzun takai har fitan da,su Raiha keyi zuwa wani gari tare da Nafisa suke yin shi, don sai ta,shirya karya cewa za su wani gurin yan uwan su ko gidan kawarta sai kawai su fita garin suyi kwanakin da zasuyi ba ta gidan.
Gashi ir8n na fitsara ba komai bane a gurin ta don wayewan ta tana ganin yakai haka ita.
Al,amarin ciwon maji yasa Alhaji baro aikin shi ya dawo gida don ganin yadda jikin naya yake saboda hankslin shi yaki kwantawa da jin da yayi an bata gado.
Yana isowa ya wuce asibiti direct Don ganin jikin nata, ya samu Tana zaune ina tsaye agaban ta ina we, mata lemun tana Dan sha a hankali.
Baba yashigo dakin da,sallaman shi Nan muka shiga gaishe shi dadawo daga tafiyan da yayi.
Idanuwan shi kyar akan ruwan da ke kafe daga gefen mama ya Kara juyo kallon shi a gareta Yana mata sannu da jiki.
Ganin shi yasa mu kokarin Fara barin dakin don mu kauce masu daga dakin.
Yake cewa ku tsaya abinku Fatima ance kece Kika kawo ta asibitin har aka baku gado to Yaya likitan yace yanzu .
Nace cikin dukar dakai likitan yaiwa Yaya sadauki bayani dazun da safe Kuna ya Kara rubuto wasu maganin da za,a saye.
Yace zasu kwantar da it's na sati biyu anan don ta samu Hutu sosai a jikin ta tare da treatment din ta.
Ok hakan na dakyau ai said dai ku dinga barinta tana samun barci sosai zaifi Kara mata lafiya .
Bai dade dashigowa ba sai ga sadauki ya shigo dakin ya sayo maganin da likitan ya rubuta mai yana fadin da kyait muka samu maganin babu shi nan cikin asibiti.
Yaiwa mahaifin shi sannu da dawowa tare da tambayan shi Yaya aiki a can inda ya fito.
Muna waje zaune saiga Yaya Imiran yazo don sunyi waya da baba yace sure hadu a Nan asibiti dashi.
Zan iya cewa tunda mukazo asibiti bai shigo gurin Maji ba don ya Dubai lafiyan ta Amma salmanu Dan wurin mama Asiya zuwan shi biyu Kuma harda fruit yakawo Muna.
Ya na isowa ya gan mu, zaune mu uku nan Suka fara gai da shi cikin ladabi, Banda ni dake zaune ina mashi wani kallon raini kawai.
Tambaya yayi ko baba Yana ciki suka bashi da amsa da eh Yana Nan cikin dakin.
Yana kokarin shigewa naja wani tsuki da karfi Yana ji sai dai bai juyo ba ya shige ciki kawai abinshi.
Muryan anty maryam ce naji tana cewa ke may ya hana kiki gaida yayan mu Bintu?
Nace bai isa na gaida shi bane kila don da nagaida shi inda mutumin kirki ne.
Fitowan shi yasa su yin shiru suna mashi sai anjima, bintu tace haka dai za,a kare .
Wai ke Bintu harda yaya Imiran da ba,ruwan shi da kowa, amma sai k8n tsula mashi halinki na tsiya?
Maryam tace a,a anty Amira tunda kikaga haka akwai dai koni ranan mun dawo school bakiji, abinda yake fadawa Bintu bane,
Nace aini Anty Amira idan mutum bai shiga gonata ba ni bani shiga nashi don haka kibarni kawai dashi dan iska kawai.
Haba Bintu haka,kawai ki dinga zagan muna dan uwa a gaban mu haka gaskiya zamu saka wando kafa guda dake a gidan nan.
Nace maida yukanki kube anty Amira ai ni ba haka nake ba da ace da yai min ban dauki mataki ba,ai da ko yanzu bata kare muna,ba,wallahi.
Ke dai yanzu kin zama disturb wallah kamar ba Bintu Maji ba wallahi nace lokaci ne idan baka baki sai a shaka a,banza.
Wai don Allah may ya,hadaki da yaya Imirana kodai laifin maganan ranan ne har yanzu kike kule dashi.
Nace a,a ai anan cikin asibitin muka yi case din mu dashi ban ma,san yaya sadauki na gurin ba,sai da naji ya daka mai tsawa yace mai ya sake min hannu na.
Tace ashe kin kuru, ne harda yaya,sadauki a gurin lalaima Bintu kinyi nisa sosai wallahi.
Nace marin shi fa kawai nayi saudaya shine wani abu wallahi har yanzu a kule nake dashi a raina .
Da sauri sukace mari da,gaske mari Bintu nace don ma banda karfi aida abinda zan mai sai yafi mari wallahi.
Yadda yake dan iska haka yake ganin kowa dan iskane shine harda daukan kazamin hannun shi wai zai shafa min jiki niko nakai mai mari sosai Allah yaban sa,a na samay shi da kyau.
Da sauri Amira tace don Allah da gaske marin shi kikayi nace wallahi Allah kuwa nan na,basu labarin abinda ya faru a tsakanin mu dashi har takai na mare shi.
Maryam tace dan iskan mutum kawai mara mutunci yau da wani ne da uwar shi ta samu abin kasawa a,ture tana baradawa a gari.
"Dan kowa ,dan banza ne, nata ne diyan kwarai a duniya, nace wallahi ni ko gobe yai min maganan iskanci sai na,dauki mataki ko a gaban waye.
Maryam tace ya ganki haka ya zaci irin yan matan shi da ya saba yaudara ne.
Nace shi dai jarabar shi ce ta motsa kawai har idon shi ya rufe, irin yan iskan ga ai su kowa bi suke basu da zabi mace da mai aure da mara aure in sun, samu, duk so sukeyi.
Nace Allah ya kyauta Allah dai ya,shirye mu, don wanan shima ba karamin masifa bane wallahi.
Don ai zina ya mafi komai muni a rayuwan mutum da ban kyama, ga al,umma.
Nifa ban yarda da maza don a mayaudara nake daukan su baki daya inji Amira nace ai ba duka maza bane basu da hali don ko matan ma,akwai marasa hali a cikin su sosai don sai kiga diya,mace yanzun tana abinda wani da namijin ma ba,zaiyi ba.
Har Baba yafito shi da su sadauki suka rakashi nan muka mike a inda muke zaune muna mashi a huta lafiya.
Sadauki dake tsaye ya bude motan ya dago kai ya kalli gurin da mu ke tsaye, yai muna inkiya da dakin da,maji ke ciki .
Nan take, na juya da sauri na nufi dakin suko sauran basu gane may yake nufi ba don haka suka tsaya jiran baba dake waya ya gama.
Ina shiga daki nasamu, maji ta farka daga barcin da ya dauke ta, na karasa gurin, da take ina mata ya jikin
Tace min ina yayan ku Fatima ya tafine ko yana cikin asibitin nace to na dai barsu waje da Baba zai tafi gida .
Kamar kira sai gashi ya turo kofan ganina tsaye a,bayan mama ina gyara mata filo yasa shi karasowa gurin da sauri yana cewa Maji kin falka,ashe ya jikin yanzu da sauki dai yanzu ko?
Likita ya shigo ganin ta a,zaune yake tambayan ta mama ya jikin naki da sauki ko
Ya dan dubata ya dago yana cewa abata abinci taci zuwa shidda na yamma za,azo ai mata allura.
Sadauki yace wani iri abinci ya kamata a,bata yanzu wanda zaifi mata, amfani.
Likita ya dago kai yana fadin tea mai kauri da fruit sai kuma anta da koda mai kyau ta dinga ci.
Sai kuma likitan yai shiru tare da kurama sadauki ido yace you look like U,F footballer yace cikin dakewa yes iam d one,
Nan suka fara shocking din hannun su suna gaisawa mutun yana faman dada wasan yaya,sadauki.
Likita baifi yan mintina da fita ba sai ga,wasu group din likitoci sun shigo lokacin yana gyarawa mahaifiyar shi kwanciya suke fadin lalai kuwa shine shine.
Nan suka cika dakin da surutu wa yannan group su shigo su fita wasu su shigo har abin ya fara isa ta don sun hana mama samun hutu.
Saida dare Baba ya,dawo tare da su Umma da mama Asiya ya,taso su gaba bayan ya gama masu fitina rashin zuwa duba yar uwar su dake kwance asibiti.
Inda yace na,tabbatar wallahi da dayan kune a,asibiti da maijidda sai inda karfin ta ya kare.
Nan dai yai masu tas yasa fito su zo tare su duba lafiyan ta .
Sun kai wani lokaci sai, suka mike zuwa gida, dama duk a matse suke kamar dole suka zo gaida ita.
Suna fita Mama tana kwance na mike na gyara ko ina tas a dakin tare da,kawar da,wasu kaya dake waje.
Sai ga,Sadauki ya,shigo dakin ya,aje ledan da ya,shigo dasu gurin flask ya nufa ya tsiyaya ruwan zafi tare da hada tea mai kauri sosai.
Yazo gabana ina zaune yake cewa gashi na,dube shi nace tasha tea ai kafin ta kwanta.
Fuskan shi a daure yake cewa ke zaki sha ba Maji ba, ya kara miko min yace karbi mana kisha idan kin gama ga nama a leda kici tunda wa yan nan sun tafi gida don lalaci.
Zanyi magana yace min shishsh bana son magana shaye shi kawai
Ban san ya akayi na fara kurban shayin ba saida naji na dan kai cup a bakina karo na farko.
Yace yaushe, likitan yace za,a kara mata allura ne wanda ya saura ai mata.
Nace ni ban ma tsaya tambayan shi ba,don ya ishi mutane da labarin kwallo kawai ya fita.
Ke kuma shine baki so zancen kwallo ko don kina jin haushi da hassada ko?
A kwallo ne mutum zaiyi bakin ciki ko kan may aiki wahala.
Kallona yake galala,har na, mike tsaye tare da dauko baredin na zauna a makure nasha ya dan kai kurbi hudu batare da bread ba.
Na aje tare da son na,rufe sauran sai yake cewa to ki jawo kazan kici don cikin ki ya kara,walwalewa da kyau.
Nace wanan ma,Alhamdullahi don nakoshi tace shiyasa bakya kiba har yanzu kamar a kallaki saboda baki son cin abinci.
Ya mike yaje bakin gadon mama ya dan tsaya can yake cewa ina ga shidda na safe zasuyi mata allura don gaka idan basu zo ba sai ki bisu.
Nace mashi tau ya kai kofa yake cewa idan ta farka kice mata na tafi sai da safe in Allah ya kaimu.
Yana fita naja kofan na rufe nan na, dako ledan naman na fara ci tare da karasa shan cup din tea dina.
Sai da nai nak na ture dama duk iya,shegena,a gaban mutane ne ban ita cin abinci saboda kawaicin da nakeyi kawai.
Zuwa dare maji ta,farka nan na mike ina mata sannu tare da tambayanta ko tana son cin wani abu.
Tace a,a tana tambayana su Amira nace yau a gida zasu kwana don likita yace mu dan rage yawa don ki samu hutu.
Tace hmmm kai Fatima boye su kuma,zakiyi bayan nasan halin abina sun dai tafi gida don su samu barci yau ko?
Banyi magana ba sai hira take min mai kama da nasiha tana ta bani labaran tun kafin nazo gidan su irin yadda su ke kwasa da kishiyoyin ta.
Nace mama Allah ya kyauta amma mutane kamar ba,a mutuwa sai a manta da ranan haduwa da Allah.
Sai kusan asuba,muka,samu barci sosai Allah ya taimaka na,farka da akazo yiwa mama Alluran karshe.
Ban koma barci ba na dauro alwala nahau sallaya na fara sallah har akai sallah asuba ina gurin a zaune abina.
Zaune nake inajan tasbi amma kuma zuciyata tana tunane akan hiran mu da maji daren jiya da irin wahalan da tasha a gidan miji amma tazauna tai hakkuri don yaranta.
Gashi kuma yau an wayi gari saboda dan tilon danta guda ciwo nason shigan ta.
Har na,soma gyangyadi a gurin sai jin muryan mutum nayi a akaina yana fadin ki kwanta mana ki dan huta hakana.
Yaya sadauki ne yana saye da kayan exercise na maza dogon wando da rigan shi mai dogon hannu dark blue.
Yanufi gadon mama yana duban ta sai ya juyo inda nake ina kallon su yake cewa, tasha maganin an kuma yi mata alluran kuwa?
Nace eh sunzo sunyi mata sun bata magani shiyasa mata ke barci haka don maganin barci yake sa mutum sosai.
Ya ce ba tare da ya juya ba ina ga daga wanan allura ya kare sai dai magani kawai.
Jin nai shiru yasa shi juyawa gyangyadi nake nai barci a gurin hakan ya nuna mai ina son hutu nima.
Kujera yaja zuwa gaban gadon mama yana mai kura mata ido cikin jin tausayin ta ta ramay tai baki duk ta canza kaman ta.
Yana nan zaune har wata nurse tashigo dakin take tayar da,maji zasu bata maganin safe. Shine dalilin farkawan mu ni da mama din
Sai da nurse din tagama ta tafine maji take tambayan dan nata sai yanzu yazo ne.
Yai murmushi yace maji na,tsaye nazo maki da,budurwana ta gaida ke sai na samu bata shirya ba .
Murmushi naji uwar tayi tana cewa kai kama isa kaida akaiwa mata tun kana karami kasan dai Alhaji ba zai canza maganan shi ba.
Sai yace wai wa kike nufi Maji Rahaman Baba Sani ko wa wai?
Tace itace mana ba itace matar taka ba da iyayyenku suka yima ko kw canza watace.
Yace maji ni may zanyi da Rahama yanzu ga mata yan gayu ko ina suna kawo min hari sai wace na zaba.
Dariya uwar tayi tace adaiyi sanni kada ruwan ido yai ma mutum yawa amma dai kasan zancen Rahama ba,tashi yayi ba har yanzu.
Wai maji da gaske kuke zancen Rahama har yanzu a da dawasa ne bayan ko wani shekara sai na hada toshin sallah ankai mata.
Kwanaki ma naji Alhaji na zancen yakamata wai kuyi aure ku uku tundai kai da kudi yake shigowa yanzu ko yaushe.
Yace ni gaskiya da za a bani zabi gaskiya Rahama batai min ba tayi min local da yawa gaskiya.
Murmushi uwar tayi tace kai har kana da zabi bayan ka bata tsallen ka ko?
Kuma Rahama yar uwarka ce ta jini zata zauna dakai tayi hakkuri ba,ajiku ba akan baren da kake son daukowa kan ka.
Nace ko kuma waye Rahama cikin yan uwasu oho koma wacece idan lokaci yayi ai mu ganta.
Banji ya kara magana ba sai ma motsin da yaji nayi yasa shi tuna cewa ina dakin lokacin nan ya dakai kallon shi gareni, nikan na kawar da kaina gefe ina cewa kaidai ka,sani.
Na kara hada kaina na da bango ina mai lumshe idanuwana ni adole ga mai jin barci.
A ranshi yace muna fuka kawai kamar bata jin may ake fadi wai tana gyangyadi.
Idona a rufe amma tunanen wacece Rahama ya hanani sukuni wanda ban san dalilin yin hakan ba gareni.
Tun ina barcin karya har na gaskiyan yazo ya kamani ban farka ba sai kusan karfe daya da wani abuna rana.
Duk ko da hayaniyar masu shigo gaida mama a lokacin nikan sai faman barcina nakeyi hankali kwance.
Dana farka sai naga Baba ne zaune a dakin yana ba mama abinci da hannun shi.
Naso na sulale na fita amma sai hakan baiyi ba don suna jin motsina baba ya juyo yana cewa a,a Fatima kin tashi sannu kinji.
Jeki wanke fuska kizo ki karya kinji sannu da kokari jiya mamanki tace ta hanaki barci ko?
Nai murmushi nace Baba ina kwana ya gajiyan tafiya yace Fatima aikece dagajiya ke mai jinya.
Bandakin dake dakin na shiga na,wanke fuskana tare da dauro alwala don lokacin sallah ya kusa.
Ina fitowa Baba yace oya maza zoki debi abinci ki zauna kici don mamaki tace baki son cin abinci.
Inbanda abinki Fatima ana jinya ba acin abinci ai sai ciwo ya kamaki ke ma.
Na dai daure na dan dibi kadan a plate Baba yace wanan abin fa kamar za,aba yaro dan goye kin dai ga ko ita mai jinyan taci abinci yau sosai.
Alaman sauki ya samu ke nan don haka kara kici kema kada ciwo yakama,min yar amana na.
Sallama akayi dakin gwagona ce tashigo tare da sadauki daya dauko ta daga gida don bata san guri ba.
Nan suka fara gaisuwa da Alhaji tana tambayan shi ya maijikin da kuma yadda ta kara ji.
Baba yace, ai hjy masa yar ki zamanta a gurin mu yai amfani nan ya shiga yaba kokarin da nake masu a gidan.
Gwago tace ai Bintu yatinyace maihankali saidai kuma gata abin tausayi don rashin jin dadin rayuwan da ta tashi ciki.
Sadauki yashigo dakin rugumay da wasu kayan bukatun da yasayo amma gwago sai faman ba su Alhaji labarin rayuwana da irin wahalan danasha a gurin uwar riko na har yakai Baba na da kan shi yace azo dani birni wurinta ko zan samu sassauci a rayuwana.
Mamakin gwagona dake ta zuba yake ta zage sai faman yabon wanan yar nata mara kunya take haka a gaban mutane.
Nan dai yake tambayan maji ya jikin nata shine ya katse gwagona yake cewa ko likitan ya shigo da rana dubani idan baizo ba sai ya shiga gurin su.
Mama tace ai shigowan shi biyu yau yana tambayan ka nace ka tafi gida.
Ya mike yana fadin bari na duba ko yana office din shi inda ya mike zuwa wurin likitan.
Ya samu likita a office din shi bayan sun gaisa yake fada mashi yadda maji ta samu sauki fiye da yadda suke tsanmani yace kuma gaskiya wanan yarinyar tana kokari sosai wallahi.
Yace a ran shi kai may yasa wanan manyar yarinyar kowa dai yabonta yake ne haka yar kauye kawai.
Ya daiji dadin yadda likita tabashi bayanin kan mahaifiyar shi. Don ko ba komai yanzu hankalin shi ya dan kwanta ai.
Ya koma dakin har yanzu Baba yana ciki suna hira da gwagona sai Maji dakan dan jefa masu baki jefi jefi.
Bai so haka,ba don hutu akace Maji ta samu ba yawan surutu ba gashi gwago tana sata magana kuma.
Ga mamakin shi sai yaga Maji ma ta kara sakewa sosai akan baya don yinin da sukayi da gwago suna da surutu batai yawan kwanciyar da takeyi ba ranan.
Da,ya,dawo da yamma gwago take cewa ita anan zata zauna da Maji sai dai ni na koma gida.
Yasan idan na koma,akwai matsala don gwago jikinta ya yi nauyi bazata iya abinda nakeyi ba kamar ni.
Yace ai ba matsala kubarta a,nan don koda ana son yin wani abu sai tai maku.
Haka muka zauna tun ranan da gwagona dake kawar wa maji da damuwanta.
Sarai Maji ta samu lafiya sosai yanzu har ita da kanta take bukatan sallama amma sadauki ya hada,baki da likita a barta har zuwa lokacin da sukace sunan son su sallamay ta.
Bayan na,wanke yan kayan da muke amfani dasu a,sibitin ne sai na fito waje na zauna don nasha iska don zama ciki ya isheni.
A nan inda nake zaune ya samay ni yake tambayana barci sukeyi ne dana fito nace mashi eh shiyasa nafito don kada na tayar da su.
Nai mamaki danaga yasa hankici daga gefena ya zauna wayan shi tai ruri ya dauka.
Magana sukeyi da wani akan zasu fita kasan waje wasa amma yace bazai samu zuwa ba don yana jinyar mahaifiyar shi asibiti.
Mutumin yake ce mashi da ya daure su fita don akwai kudi da yawa a wanan wasan da zasufita yi yace gaskiya sai mamana taji sauki zan iya fita wani wasa sai yakashe wayan nashi baijira mai mutumin zai fadi ba.
Yana kashe wayan ya furzu da iska daga bakin shi tare da dukar da kanshi saman cinyar kafar shi kamar wanda damuwa ta dama.
Tausayi ya bani a lokacin saidai shi ba abin tausayi ba ne don duk wanan halin da mama take ciki shine sanadin hakan ai.
Ban san ya akayi ba sai ji nayi ina cewa yaya sadauki don Allah kayi hakkuri da abinda zan fada maka bawai nakai na fadi bane amma dole tasa zan fada ma koda bazakai amfani dashi ba.
Kan shi ya dago yana kallona cikin mamaki tare da kura min ido, nikuma banji tsoron shi ba naci gaba da cewa.
Ba tare da fargaba,ba nace why baka tausayin kan ka dana mahaifiyar ka?
Nace yaya wanan ciwon ban fadawa kowa ba,kaine silar haka ga mama sanadin irin rayuwan da kakeyi yasa mama cikin waban halin.
Idan dare yayi mama bata barci ko yaushe tana kai kukanta ga Allah akan al,amarinka.
Amma kuma,,,
Sainai shiru na kasa,karasa abinda zan fadi yace amma kuma may fa.
Nace a hankali yaya sai naga kamar baka sani ba kai don kullun ba batun dainawa kakeyi ba sai kara nausa,kanka kake a cikin wanan harkan ta,shaye shaye kishiyoyinta suna fada maganan banza wanda ke saka,zurciyar ta,kara,fadawa cikin halaka.
Shiru nayi kamar yadda shima,yai shiru nace yau abin bakin cikine ace duk yawan gidan nan kaine kawai nata kuma kaine mai jawo masu magana.
Kowa fa yan
a da nashi illar amma sun boye nasu saikai dake yi afili ake ganin naka.
Don Allah yaya idan ma,sha zakayi ka tafi can nesa da ita inda ba wanda ya sani kayi abinka.
Amma da zaka bari gaba daya shine alheri gareka dama kowa naka don nan gaba ba haka zaka zauna ba.
Kaima iyali zaka tara yau idan yaranka suka taso suka ganka cikin wanan halin ashe baka ganin tarihi zai iya maimaita kan shi gaba.
Za ai masu gori za aiwa matarka gori za aiwa yan uwan ka gorin hakan.
Shi wanan abin an san jarabta ne daga Allah amma kuma sai bawa yayi kokarin nisanta kan shi daga gareshi don gudun zama mujiya a cikin al,umma .
Baiwa arziki yaya duk Allah yai maka kamarya da kanka abin alfahari yadda ko wace uwa zataji dadin yin alfahari da zurian ta.
Nace amma,,,,,
Yace ke dakata haka ya isheni na kuma gode da kika kalli idona kika fada min gaskiyan abinda babu wani mahalukin da ya taba tarona ya fada min irin haka.
Nasan kinyi kokari yadda kika kalli idona yau kika fada min damuwarku akaina wanda yan uwana dangina abokaina ba wanda zai iya fada min shi.
Koke nasan saida kika shirya fada min don naga saida babu kowa a tare damu kikai min wanan magana ko haka na gode insha Allahu nima ina kokarin ganin na daina don bayanin da likita yai min a officer din shi nasan zancen da Umma taiwa majine last week ya hefata cikin wanan halin.
Da sauri nace ashe kaima ka sani yaya mikewa yayi yanackakabe wandon shi yace tundani ba mutum bane yaya zan sani.
Ya sakai ya wuce ya barni zaune a gurin take naji kamar ancire min wani dutse a zuciyana nace a raina koba komai dai na samu ya saurareni dole ne kuma daga cikin zance na yai amfani da wani yai mashi tasiri aran shi.
Ina gurin a zaune yafito hakan yasani sanin har lokacin barci sukeyi basu tashi ba.
Yana isowa inda nake yake cewa ni zan tafi idan sun farka ki fada masu cewa nazo sai na dawo anjima.
Yatafi abin shi nabi bayan shi da kallo ga mutum har mutum amma kuma babu shedun alheri tare dashi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKK8N WASU PLEASE,,,,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,,,,,,,
An sallamo mu daga asibiti bayan gwaje gwajen da akayi kan mama an tabbatar da ta samu lafiya yanzu sosai,
Sai dai likita ya kara jaddada muna cewa a guje bata mata rayuwanta, wanan kalamin na likita a gaban kowa akayi shi.
Duk yaran mama suna kusa haka yaya sadauki yakoso su zuwa gida motat tashi bata daukan mu duka don haka ni da maryam muka hawo Nepep zuwa gida da sauran kayan mu.
A kofan gida muna sauka na hango yaya Imirana da wata yarinya yar makwabtar mu ya rike mata hannu yana wasa da ita.
Kawar da kaina nayi tankatmr ban ganshi ba amma da yake baida zuciya muna kawowa kusa sai cewa yayi adon gari kun dawo.
Yaya mune kuma adon gari yau inji maryam yai dariya yace inbada abinki maryam ai yan mata adon gari ne ko?
Wanan yarinyar da Maji zata ban ita aida na more wallahi ta juya tana wa Bintu yace ita fa.
Ai babban adon garice wanan tun dai in ta samu guri zakiga ta baje ne kwana biyi lokacin caji ya fara daukan ta.
Nace ba adon gari ba adon dawa mara mutunci kawai, maryam tace ke Bintu yayan nawa kike zagi a gabana yanzu zamuyi fada kuwa.
Ban tsaya basu amsa ba na kwashi kaya zuwa cikin gida, ban san yana tsaye ba jikin motanshi sai da nazo shigewa na gan shi a tsaye ya sha bakin glass a idon shi.
Ni dai na,shige yabini da harara kawai, tun kan nashigo nake jin hayaniyan yan gidan ga kida na tashi dakin Umma.
Haka yasani sanin Nafisa tana gida a lokacin don idan tana na zakaji sauti yana tashi a dakin su.
Na samu su mama da gwagona zaune a falo nan na zube kayan suna min kun iso nace eh.
Nazauna ina cewa wai Allah mun gode ma, jiki dan tafiyan nan kikewa wai inji Amirah.
Kafin nai magana cikin muryan mara lafiya mama tace tunda baki san kwana rayen da takeyi akaina ba ai zaki fada mata hakan.
Amirah tace cikin make murya maji tare fa muke kwana da Bintu don dai na daina kwana biyu kawai.
Kudai kuka sani ace uwar mutum na asibiti amma ku har kunji dadin kwana a gida.
Ashe badon Allah ya kawomin wanan yarinyar ba sai dai na karata can ni kadai.
Gwagona tace a,a haba hjy ai bazasuyi haka don dai sunga ita din tana masu kara ne kada su raina mata shiyasa.
Mai masa bari yaran nan ban san irin su ba kodan sunga su kadaine min suke min wanan halin ban sani ba.
Amirah ta tashi tashige daki tai fushi da maganan mama, nice ma na tashi nabi bayan ta har zan shiga gwagona ke cewa dawo mana ki kwashe kayan zuwa ciki kada a barsu nan watse.
Maji tace ai kinga abinda nake fadi din waya fara dawowa cikin su ba ita ba amma batai azancin ta kwashe ba.
Suna ganin abinda sauran yaran gidan keyi sun zaci alheri ne basu san cewa suma gidan wani zasuba.
Idan kaje gidan mutane kace kai baka iya motsa jikinka kai komai sai dai ai maka aiko akwai aiki babba.
Da sannu za,a koya masu tunda basu saba da hakan ba tun farko amma ai zasuyi insha Allahu .
Allah dai ya kyauta mai masa yaran nan halin su sai su wallahi basu san ciwon kan su ba.
Koma irin yadda ake min a gidan su baya damun su dawasu ne ai basai an fada masu abinda zasuyi ba wanda ya dace.
Kiyi hakkuri hajiya kowa da ir8n halin shi amma bari zasuyi idan ana lurar dasu.
Na samu Amira a daki tana, waya nashigo dakin , tabini da kallo tace yanzu duk kokarin da nake wai maji bata gani.
Nace Anty uwa uwace duk abinda suka,fada muna gyara ne a garemu mu godewa Allah da ya barmu dasu a raye.
Wanda baida uwa fa a duniya bai kuma damai kwabamashi fa.
For god sake may ye banyi a gidan nan ne wai amma kulun maji tace banyi daidai ba.
Fadan iyayye fa takine gare mu anty tun da tace haka yanzu da ta dawo gida sai ki matsa ki kula da ita yadda zata ji dadin ki.
Kallo na tayi kamar zatai magana sai kuma tai shiru kawai nikan na koma dakin mu na,shiga wanka don duk warin asibiti nake jin ina yi a jikina.
Bayan nafito ne na tara duk kayan da mukai amfani dashi asibiti na wanke su tas sannan nadawo falo na zauna sai naga Amirah tafito.
Taje gurin mama tace a kawo maki abinci ki dan ci ko da kadan ne maji don rana yayi lokacin shan maganin ki ya kusa.
Uwar taji dadin haka sosai don ta kasa boye farincikin ta tace tau akawo min Amirah.
Ta hado ta kawo mata har gaban ta tare da ruwa da maganin gaba daya.
Maji tace mata na gode Allah yai maku albarka da haka kuke min wa zaiji mu daku.
Gwagona tace tau gashi dai uwata ta gyara yanzu ai shiya fadan yake da dadi ga yaro don ya gyara kuskuren shi.
Tajuya inda nake tana cewa ke kuma Bintu wallahi ki bar yi wa maji komai daga yau kibarni ni zan mata.
Maryam tace wallahi saidai a raba amma ban yarda nima ai ina son albarkan .
Nan dai aka wasance zance ana dariya tajuyo tana daga min gira alaman godiya nima hannu na daga mata alaman komai ya wuce.
****** ********* ******
Kabir yazo duban jikin maji da ya shigo kauyen su kamar yadda ya saba duk karshen wata da yake zuwa.
Kabir ya iso gidan namu amma bai shiga ciki ba, ya tsaya daga kofan gida inda ya zauna cikin motar shi.
Yana saye da kananan kaya amma dinkin shadda ce akai mashi karamin dinki dashi.
Sai kamshin turare yakeyi ajikin shi yai matukar kyau dashi sai annuri yake .
Waya ya buga min cewa gashi ya iso a kofan gidan da nai mashi kwatance.
Na fito acikin hijjab dina duk da nasha kwaliya daga ciki amma na rufe jikina da hijjab.
Waya yake amma hankalin shi yana a kaina yana kallon yadda nake takona ina dan waige don ban sheda motar shi ba da yazo da ita.
Saida yai min horn nagane cewa shine acan gefe daya zaune cikin motar shi.
Ina isowa inda yake ya kashe wayan shi yana min wani kallo can kasan idon shi.
Na dan duka kadan ina cewa barka da isowa ya hanya ya mutanen gida suke?
Yace duk suna lafiya suna gaida ke amma uwargida tace tana fushi dake wai baki taba kiranta kun gaisa ba.
Nayi murmushi gami da cewa karufa min asiri don Allah, yaya ina ni ina kiran ta tace banda kunya.
Yace aiko gara ki daina jin komai don Haulatu tace bata dauke ki kishiya ba a matsayin yar uwa da kuka fito shiya daya ta dauke ki.
Nai murmushi kawai tare da cewa Allah sarki aiko na gode Allah ya bamu hakkurin zama da junan mu.
Ya amsa cikin jin dadi da fadin amin my love, har kin sa naji wani sanyi a,raina da na ga wanan gidan da kike har na fara fargaban kada wani ya kwace min ke anan.
Nace haba yayana ai kyau alkawari cikawa da bazanyi ba tun farko baxaka ga ma fuskana ba ai har mukai haka dakai.
Yace nako gode da,wanan karamawan da akai mun yanzun hankalina ya kwanta sosai da jin kala man ki.
Nan muka dan dauki lokacin muna hira dashi sai dariya yake bani na yadda zamu zauna a gidan shi.
Tun daga nesa na hango motar shi tafe da karfi yazo ya park dan nesa kadan damu.
Tun karyo kwanan shi ya hango su mamaki yake irin yadda ya hangota tana dariya abinda bai taba ganin tanayi ba a rayuwan ta.
Kallon wanda suke tare yake inda yaga maishi ai ba yaro bane ya ma girmi duk yan gidan su balle shi.
Amma shine wanan yarinyar ta tsaya haka har take wasan baki a gaban shi koma may wanan zai iya fadawa budurwa har taji dadi haka.
Ko dai dama da wanan tsohon take waya tana wani kashe murya a gaban mutane ba kunya saboda wanan tsamuraren mutumin.
Wani ir8n haushi da takaicin yarinyar ne da baitaba jin irin shi ba ya kama shi.
Ya fito daga motan shi lokacin Kabir ke tambayana waye shi nace mashi yayanane na nan gidan.
Don haka yafuto suka gaisa sama sama dashi kamar mai sauri ya shige abinshi tare da gaura marfin motar shi.
Kabir ya juyo inda nake yace tau ikon Allah nace rabu dashi haka yake hutsune dama shi baida mutunci.
Dakin shi yanufa yana jin wani gumin bacin rai yana fetso mashi ya bude dakin shi ya shige hakana.
Mun dan kara dauka lokaci yai min sallama tare da mika sakon shi gurin mamana da bata da lafiya.
Nan yake ce min shi abinda yakawo ma yaji kunya don wanan gidan abin yai kadan wallahi.
Cikin mamaki nace haba aiba komai wake raina alheri sai mara godiyan Allah kawai.
Nan nasamo yara suka shiga dashi nace sukai dakin maman UF don sunfi gane ma hakan.
Mukai sallama yatafi sai banji dadin hakan ba don ban so mu rabi dashi ba don jin dadin dan kasancewar mu na dan lokaci a tare.
Har na shigo gida yana tsaye a kofan shi kamar may waya take yaji zuciyar shi na azazzalar shi tankat ya shake a lokacin.
Can kuma yai tsuki yace ina ma ruwana da yar iska komay zatayi taje tayi mana may ye hadina da itama dahar na damu kaina.
Sai zuwa dan wani lokaci ya shigo gidan inda ya samu kayan da Kabir ya kawo muna a falon mama.
Ya shigo wani iri dashi idon shi akan kayan duk da kayan ba laifi amma sai yaga ai duk komatsen banza ne kawai.
Ya samu guri ya zauna yana fadin wanan kayan kuma fa haka?
Amirah tace surukin kane yazo yaya mai neman Bintu shi yazo yakawo wa Maji na dubiya da Allah sawaka.
Ance mai mu bamu iya saye ne sai ya kwaso muna wani tarkace haka ba kyau gani.
Ko an fada mai mu makwadaita,,,,,
Kai don Allah ya isa kai wani irin suruki ne kuma maimakon kasa albarka sai kuma ka fara fadin maganan banza kawai don Allah kwashe min su zuwa ciki kinji maryam.
Maryam ta mike tana fadin ai yaya an fara kawo maku tarkace ke nan tun da maji ta tara zuka zukan yan mata haka har uku a dakin ta.
Amirah tace wanan kan nima nawa yana tafe sai aka sa dariya kawai gaba daya maji tace Allah kawo shi lafiya mugani ni dai naga ta ya ta saura naku din.
Wallahi Maji kina bata yaran nan haka fa na hango wanan yarinyar a,waje da wani tsoho tana wani washe baki kamar taga wani saurayin kwarai gaban ta.
Daga inda nake ciki ciki nace kai kaga tsoho nikan bai min tsufa ba wallahi ai aure ba inda baikai mace.
Maji tace wallahi ke dai ya ta ai in an kwana biyu zan fadawa babaku don yasani kada yaga kina tsayi dashi kofan gida yazana,min matsala.
Cikin hasala yace may kikace banji ba fadi mana naji ya fifito da idon shi waje.
Maji tace kai ban fason hauka ko kuma kayo shaye shayen nakane zaka sauke muna hauka anan.
Mikewa yayi tare da kutawa yace wallahi maji duk ke kesa yarinyar nan tana rena mutane bata jin tsoron kowa a gidan nan.
Na,sa ubana sai kai min fada ko in ba a zo neman su ba kai za,abarwa su kaita kallon su ko yaya.
Ya fita yana fada ba maijin abinda yake fadi muka kwashe da dariya kawai Amira na cewa ni wallahi yaya mamaki yake bani Allah.
Kamar Bintu za,ace wai bata isa aje saurayi ba yanzu sai yaushe ko ni Allah yaba maiso yanzu ai fiya da haka zanyi mai.
To Allah dai ya kawo wa kowa na alheri ke kuma Fatima sai aita hakuri kuma a kama kai don mazan yanzu sai a hankali.
****** ********* ******
Muna zaune da yamma ranan mukaji sallama wasu mata sai da suka fara shiga gur8n su Umma an dauki lokaci sai gasu sun shigo gurin maji sun zo gaida ita.
Nan dai suka fara gaisawa suna mata yaya jiki sai mai dan shekaru a cikin su ke cewa wallahi lokacin da kika kwanta asibiti Alhaji baya gari sai jiya ya dawo.
Shine yau mukace zamu zo nan gida mu gaidake yaya kika kara ji ya kuma katfin jikin naki ?
Maji tace Alhamdullahi na samu sauki ke nan sai matar tace ai halin dan yau inkace zaka sashi a ranka sai ka mutu ga banza su basu damu ba.
Tau anyi wani abin ne kuma hjy Saude?
Maji ta tambaye ta tace ba ance zancen yaron nan kika sa a ranki har yakai ki ga son kamuwa da ciwon zuciya ba?
Inna lillahi haka kuma kukaji to Allah ya sauwaka ni dai na san zazzabi nayi mai karfi .
Sai suka kama kallon junan su cikin mamaki sai ga hjy Kubura ta shigo dakin tana cewa a,a hjy saude yanzu nafito wanka yara kece min kun shigo ai.
Kunzo gaida hjy ne gata nan tasha allurai ta farfado kin san maleria yanzu baijin magani kadan sai da ya kaita kwance wallahi kin san bana ana sauro da yawa ita kuma sai tace bata shiga net bata son kuma hayakin coil.
Matar tace muko yanzu ake ce muna,wai ciwon zuciya ne ya kamata kan zance Faruk .
Kai ina kuma kuka samu wanan labarin haka mutum kan abin tsoro ne wallahi zazzabi tayi nima har gurin likitan nake yake min bayani.
Allah dai ya sauwa inji dayar matar da batai magana ba tun shigowan su tace ai yanzu da abu ya samay ka magana ya samu ke nan dada .
Aishine inji hjy kubura ta fara tafiya sai tace a,a sarakuwa na ashe kuna gida anyi hutu ke nan ko?
Matar tace ai suna gida anyi hutu har sun kusa komawa ma.
Ince dai kinga dan nawa ko yafitane hjy maijjida tana kallon maji don son bayani maji dai murmushi tai mata kawai bace komai ba.
Duk hiran su a kunne mu yake muna can zaune daga bayan su sai lokacin na fahinci budurwan sadauki ne tazo gaidashi.
Ni dai bari nasa akirashi ku gaisa tunda kun shigo don nasan kila yana gida naga motar shi dan shigo gida dazun.
Uwar yaran tace wai wa Faruk, kai hjy kubura kina dai zance wallahi.
Basu jima ba suka mike suna cewa zasu tafi nabi yarinyar da kallo gajera ce sosai baka bata da haske amma tana da kyauta gaskiya.
A rai na nace shine har yake kiran wata yar kauye gatashi wata irin cus da ita sai gajirta.
Har kofa maji taraka su duk da suna cewa ta barshi yarinyar ta juyo tana cewa su maryam bye bye da dan daga hannu.
Suna fita maryam tace kinga mai dogon rigan nan pink ita ce zata auri yaya sadauki tun suna yara aka hadasu diyar kanin baban mune suma ana cikin gari suke da zama suna tudun wada ne su uguwar su baban mune can.
Maji ta dawo daga rakiyan su take cewa kai matan gidan nan basu barin halin su.
Yanzu don sheri su hjy Saude zasu fadawa wai saboda sadauki ne na kwanta ciwo wai ciwon zuciya don hana ruwa gudu kawai.
Amirah tace ba kowa zai fade shi ba sai mama Asiya don itace yar bakin ciki nidai inajin su imani duk ya kashe .
Wai haka kishi yake ne kaitawa dan uwanka zagon kasa da hassada a fili haka haba jama,a wanan wani irin sheri ne kuma.
Ka zauna gaban surukan mutun harda sarakuwa kuna sukan mutun haka haba dai duniya.
Nan kuma muka fara zancen hjy kubura mama tace ni ko ba komai ai hjy kubura tana min ta wani guri.
Amirah tace namay maji jifa wai har gurin likita taje tambayan shi da gulma.
Daga inda nake nace kaman nasan haka tunda mukaje na roki likita ya boye muna wanan magana.
Ke din Bintu nace wallahi anty tace kinji ba aiko da yanzu an yada shi kashi kashi ko.
Hayaniya mukaji daga cikin gida bul su maryam suka fita don saurare wai ashe hjy kubura ce tafito tsakar gida tana fadin munafuki dai baiji dadi ba,wallahi.
Yanzu don bata zama shine ake wani fadawa mutane arasa ma inda za,ai gulma wai sai gurin sarakan mutum ace wai surikin su ya haddasawa uwarshi ciwon zuciya.
Sai ga umma dunkul dunkul tafito tana cewa in ma gulmace mu muka fada masu haka.
Karya ne muka fadi ba shine yajawo mata wanan matsalan ba don bakin shaye shayen shi daya sawa kan shi da rana tsaka.
To an fadi din ko akwai abinda zakiyi ke ma nan daban ne baki fadi ne maye baki fadi gurin aikin ku akan shi.
Ko k8n zaci bamuji ne sai anzi gida don makirci ki nuna ke tasuce, don kilibibi kawai an fadi din may zakuyi.
Haba nan sukai tawa kan su tonon asiri har saida Amirah ta kira mahaifin su yazo ya samay su.
Ran shi a bace ya samay su da fada yana cewa kun daiji kunya wallahi yau may yarinyar nan hawau ta tare maku a gidan ita da yaranta.
Kullun cikin bakin cikin ta kuke da hassada baku gajiyane wai ku, wallahi duk abinda ke gudana a gidan nan nadani ido kawai na samaku don ta Allah bata mutum ba.
Ni sadauki dana ne ko wani hali yashiga ban gydun shi don ba,a canzawa tuwo suna.
Kuma ku sani babu wace ta wuce kaddara a cikin ku don haka kowa tashiga hankalita.
Inba lalacewa ba yaushe za,aji wanan mugun labarin a bakin ku koda kuwa hakan ya zama gaskiya ne ma.
Yanzu inma hakane har zaku iya tonawa yar uwarku asiri a hakan may zaku gane gurin tonawa cikin ku asiri.
Umma tace ni banga wani abi gaddama ba agurin nan duk garin nan waye bai san abinda yakeyi ba da har za,a tsaya ana tayar da jijiyoyin wuya hakane wai.
Yace oho haka kikace tace dama hakan ne don kai baka son gaskiya shine zakazo kana son danne gaskiya.
Kafin mu mu fada masu ma ai suma sun sani ba abakin mu suka fara ji ba tunda in yai bakin shaye shayen a can kan titi yake tanbelen shi.
Duk wanan rigiman da akeyi akan idon sadaukine wanda ya dawo gida a lokacin don yai shirin fita gurin wasa.
Alhaji yace sai kuci gaba da fadi shege ya fasa indai hakane sai kafara fita kayi shela a waje kafin kazo gurin mu.
Nan kowa ya watse yabar gurin suna ci gaba da yada bakaken maganganun su a dakunan su.
Bai fasa shigowa gidan ba sai dai bakin ciki ya hana shi yin magana duk ran shi a bace yake yai murtuk da fuskan shi.
Ya samu guri ya zauna tare da dafe kan shi gwanin ban tausayi, Amira ce matace mai takawo mai abincine yace No kibarshi kawai Amirah.
Ya mike yafita daga dakin don baiga fuska ba gurin mahaifiyar su.
Batai magana ba sai ajiyan zuciyar datakeyi kawai, ganin zata sa damuwa nake cewa.
Inda daji bai gama cin wuta ba aiba ai wa kututure barka don kowa na da "ya"ya ai, balle mutum yaji dadin zagin nawani.
Amira tace ai shine ai Allah ba azzalumin kowa bane yana sama yana kallon kowa.
Nace ai shine mudai kullun fatan mu Allah yada ya daina kuma ma ai ya daina zancen su daine kawai.
Sai lokacin maji tai magana tace anya Fatima kada fa kiyi shedan zur waya fada maki ya daina?
Nace mama da,bai daina,ba ai baki ganin shi haka normal kullun nifa munyi magana dashi asibiti.
Da sauri suka kallo ni maryam tace ke Bintu kikai magana da yaya sadauki din nace wallahi ko Allah.
Tace cabdijam lalai Bintu kin kai wallahi kikace mashi may nace wanan kuma ai siri ne anty maryam.
Amma wallahi ku yarda dani insha Allahu yaya ya daina shan wanan abin saidai ban sani ba ko ya daina kwatakwata, ne
Amma gaskiya da,wuya kuma dai kan adai gidan nan ko garin nan akaracewa wai yasha wani abin maye.
Da sauri maji tace Allah dai yasa Fatima Allah yasa hakan ne wallahi ta fadin cikin ban tausayi,
Nace insha Allahu mama don na yarda da maganan shi zai daina ne din ko kuma ma ya daina kawai za,ace ma.
Maji tace Fatima ke alheri ce sosai a gare kuma ke wata haske da Allah ya jefo min cikin diyana.
Tunda kikace haka wallahi Allah na yarda da zancen ki don na karanci halinki ko
Shima dai din da gaske wallahi naga canji sosai a gare shi don banga alaman wanan shadin ba duk kwanakin nan.
Maryam kan sai mamakina takeyi tana matsa min wai sai na fada mata yadda mukayi nace ki bari inyadawo ki tambaye shi anty amma ni ba,ajin mutuwan sarki a bakina wallahi.
Wanan dalili fadan nasu yasa ya yanke shawara a ranshi zai nisanta kan shi da gida, don gudun bacin ran mahaifiyar shi kada ciwon ta yazo yatashi mata a sanadin bacin ran shi.
Sai da dare ne daya,shigo yake fadawa Maji cewa zaiyi tafiya zuwa kasashen waje kuma yana ganin zasu dan dade a can din.
Maji tai shiru kamar bazatai magana ba sai zuwa can tace sadauki ba wai ban son tafiyan ka nisa bane a,a.
Halin rayuwa irin naka nake tsoro anan ma da kake yaya aka,kwashe dakai balle kayi nisa da mu inda ba makwabi.
Yace Allah nan ai Maji insha Allahu abinda kike zato bazai faruba don wasan mu ba,a yarda mutum yai wanan dabiar ma.
Tace to shike nan sai ka samu mahaifinka ka fada mashi don yasan abinda ake ciki kada sai kashirya yaji zancen daga sama.
Ya samu mahaifin shi ya fada mashi zasufita zuwa waje kuma zasu dan jima acan suna wasa da sauran kashe nan yaja mai kunne tare da fatan alheri a gare shi.
Bayan kwana biyu ya shirya duk muna falo ya shigo sallaman su inda kowa ke mai Allah ya tsare da fatan alheri suna ta bashi sakon abinda zai sayo masu a can.
Nidai ina gefe bance komai ba bayan Allah ya tsare da nai mashi ban kara tankawa ba saida zai tafine muka fita rakiyan shi wanan karon hardani da ban fita rakiyan shi saida na fita.
Motar shi a gida ya barta yace wa Amira idan zamu school adinga zuwa dashi don dama sun iya mota su.
****** ********* ******
Yau Aliyu yana dauko talla direct dakin sisko ya nufa ya samay shi yafito daga wanka yana daure da towel a jikin shi.
Sai yaron yadan tsaya daga waje don ganin shi haka da yayi ba,sutura a jikin shi.
Yace shigo mana boy may zai sa ka tsaya daga waje sai yadan aje roban tallan shi daga waje kadan yace shigo dashi mana kada wani yagani kuma asan kana nan.
Sisko baiji kunyan cire tawul din dake jikin shi ba wai yana shafa mai haka yasa Aliyu yadan kawar da idanun shi gefe.
Dago kan da yaron zaiyi yagani ko yagama sai ganin Sisko a gaban shi gap dashi yayi tsirara haihuwan uwar shi.
Ya na mika mashi mai wai ya shafa mashi daidai cinyar shi yaron yakarba ya fara shafa mai sai wani lumshe ido dan iskan keyi a lokacin ,
Nan wasa yafara canza launi ya shiga yiwa Aliyi wasu abubuwa da yaron ya kasa hana shi yi mashi yana cewa ba kaga yadda muka kalla ba a TV ranan dakai.
Shine nake son karafa koyo kaga inka girma ka iya abinka ko nan yaron baiyi aune har yakai ga tube shi ya danne shi sai da ya biya bukatan shi ya sarara mashi sai faman ihu yaron yakeyi don yafi karfin shi sosai.
Yaron duk da sisko ya sauka a kanshi bai fasa kukan neman taimakon da yakeyi ba.
Yuka ya jawo ya nunawa yaron tare da,bashi tsoron yace idan ka fadawa wani abinda nai maka sai na yanka ka wallahi ka mutu gaba daya wawan banza mai shegen tsoron tsiya kawai.
Dakyat ya samu har yaron yai shiru yabar kuka nan yadaga gadon shi ya dauko dubu biyu yaba yaron yace yaje yasai duk abinda yake son ya saya ci .
Amma kada ya fadawa kowa abinda yai mashi inba haka ba har baban shi sai ya kashe.
Ganin yaron bai iya tafiya yasashi tare mai mashi akaishi gida yana,tajawa yaron kunne.
Yaron ya isa gida da kyat yake tafiya ya samu har maman shi ta gama abinci tana ganin shi take cewa a,a yau har ka dawo haka .
Tace aje roban ga abincinka can ka dauka kafin babanku ya dawo kadan kara fita.
Sai ya shiga daki yafito yakuma koma da sauri ya kasa tsaye ya kasa zaune.
Amma sakaren duk bata kula ba sai cewa take wai may kake nemane haka ka zauna mana kaci abinci kafita.
Sai yaje gurin frizer su ya dan dafa don ya zauna aiko sai ya saka ihu, da sauri ta aje kwanon da taje debo ruwa ta nufo shi tana fadin wai may nene haka tunda ka dawo nake cewa ka zauna amma kana min wani abu can dabo dabo dakai.
Maza zauna kaci abinci kayi kafita sai hawaye shar shar yace mama, mama wallahi ban iya zama.
Ikon Allah may yasamay ka da,baka iya zama kuma yaron yai shiru yana dan buga kafan shi tace maza zauna dan bura uba kawai ni zaka kawo wa diban albarka.
Yaje zama sai kuma ya mike da karfi yana tsala ihu yace wallahi mama ban iya zama da sauri ta kamo shi lokacin yaron ya tsananta kukan shi sosai.
Wandon shi tacire tagani ko kurjine ya samay shi aiko tafara cin karo da ajiyan maza ta hankada shi da sauri bata san lokacin da tace na shiga uku ni mariya wa yai maka wanan ta,asan haka.
Ina sai ihu yaron yake wallahi mama na bari take ta saka kuka abuna farko dayazo mata a rai shine uwarta ta kwsheshi tare da rufe gida suka nufi waje nan ta tare mai mashi sai gidan su.
Uwarta naganin yanayin su tasan babu lafiya may yafaru may ya samay shine wai?
Tana kuka tana mayarwa uwarta abinda ya faru da yaron tambayan duniya sunyi mashi amma basu gane komai ba sai kuka yake yaki fadi.
Uwarta ce kinga mariya wanan magana yafi karfina bari mu nemi mahaifin yaron nan tun abu bai lalace muna ba.
Mariya tasa hannu akai tace ta shiga uku umma baifa san yana talla ba dama.
Tace yau kan ai ba boyo don dole yasani don wanan magana,banamu bane mata.
Nan takira samari kannen maria suka dauki yaron zuwa asibiti guda kuma yatafi kasuwa kiran mahaifin shi.
A sukwane ya iso asibitin yana tambaya ana fada mashi cewa wani ne yai lalata dashi ta baya kuma asibiti sunce basu taba yaron sai an kira yan sanda.
Karasawa yayi gurin yaron yace Aliyu wa yai maka wanan abi haka a ina ka hadu dashi,
Bai basu amsa ba sai kukan da yakeyi dole suka nufi gurin yan sanda dashi nan aka tasa shi gaba da tambayin hikima irin na yansanda.
Yaron yace yace ina fadi sai ya yankani kuma ya kashe babana da kyat dai aka samu yafara magana cewa.
Ummh dama wani ne mai sayen ruwana kullun shine shine yace nazo dakin shi kullun na dinga kai ruwa yana saye shine yau yau danaje sai sai ya kamani ya danne yai min haka?
Salati uban yasa yace Aliyu dama kana tallane ban sani?
Cikintausayi da langabe kai yai maganan tare da kurawa yaron ido.
Ya juya inda yan uwan maria suke tace shike nan maria taci amanata ta cuci yaronta ta tona min asiri a garin nan.
Sai yakai zaune darsha ya sake wani irin kuka mai tsuma zuciya inspector yace yanzu ba wanan ba ku tashi muje asibiti a duba yaron nan a gani tukun don a san halin da yake ciki don da gani yana jin jiki.
Nan suka dunguma sai asibiti da yaron saida yan sada suka sa hannu likita ya fara duba yaron.
Nan yake sheda masu sai anyi mashi aiki an rage mashi abinda ya shiga cikin shi kuma aikin akwai tsada don sai sukanshe kudi dubu dari da hamsin cikin ragowa.
Uban yaro yafara rusa kuka yana ya shiga uku ina zai shiga ya samo wanan kudin haka masu yawa.
Dole aka fara neman inda za,a samu kudi don a taimakawa yaron dake cikin wahala.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,
A LOKACIN MU KE,,,,
Sun shirya tafiya zuwa lagos gurin Michael don haka Nafisa itama ta nace akan cewa dole sai tabisu.
Tare sukai tafiyan inda ya turo masu da kudin suka shiga jirgi sai lagos a gida kuma tace zata gidan wata kaunan mamanta ne ta,kwana biyu.
Ranan da takwana uku da tafiya Umma ta kira waya tana tambayanta cewa yaushe zata dawo ne don tace ga jiya zata dawo bata dawo ba kada Alhaji yasan bata gida fa.
Tace sai gobe nan uwar tai mata fada kan dole ta dawo ranan don gujin bacin ran su gaba daya.
Amma har dare Nafisa bata dawo ba haka yasa Umma ta tayar da wani wanta guda yabi bayanta gidan yar uwarta ya dauko ta.
Yaje gidan yar uwar maman nasu tace ai Nafisa batazo ba ma gidan ta kwata kwata.
Nan hankalin Umma ya tashi sosai gashi kuma ko sun kira wayan Nafisa basu samu a lokacin.
Tun tana boye damuwarta har uwar kwakwaf mama Asiya ta fara ganewa yan dakin na cikin wani tashin hankali amma da ta tambaya sanin hali sai Umma take cewa, bakomai bane dama.
Kwanan ta biyar suka dawo sokoto haja haja cikin kudi, nan uwar tasata daki da tambaya ido ya riga ya bude tace buki suka tafi na wata classmate din su gusau ta san ko tambaya Umma bazata bari ba shiyasa tai karya.
Imirana ranan kamar ya make ta yai mata fada sosai sai dai basu sani shiga yake yana fita inda ya shiga.
Don Nafisa tayi nisa ko batajin kira yanzu don kar take kallon su tasan abinda basu sani bako.
Nan uwar taga yadda take facali da kudi take tambayanta sai cewa tayi wani Alhaji ne dan canji ta hadu dashi a gusau shine yabata kyautan dollars kuma yace ma zai zo gida yaga iyayyenta.
Umma ta fara jin dadi har ta fara sake magana ita yanzu arzikin bana yaci uban na da don yarta tayo babban kamu sosai .
Wasu ko sai dai su zauna idan dan su ya tafi yayo fashi ya kawo masu kowa a gidan yasan Nafisa ta samu dan canji don sai facaka suke da kudi abinsu.
Uwar bata san cewa yarta ta wuce sanin ta ba yanzu da ita da iyamurai take hurda su ko suna son yaran hausawa don sunce sunfi iya making, love.
Idan kuma ta fita su da su Raiha sufita susha kayan mayen su suyi tatil dasu ta dawo taita barci.
Ranan Amira zata shigo taga su Raiha sun dawo da ita yanayin data gan su a ciki sai bai mata dadi ba tashigo maji na ciki take fada muna nace Anty kiyi shiru kada wani yajiki ace kina hassada da samunta tace wallahi hakane amma may zanwa hassada a wanan gurin haka.
Yanzu har takai sun fara neman junan su idan sun sha ko kafin su sha sai sunyi masha ansu a tsakanin su sannan su koma,suyi tatil dasu.
Idan abinta yai nisa ita Nafisa har kwalba take dagawa don zuwa lagos din da,sukayi saurayinta Johnson mashayi ne sosai a can takoya shan giya.
Gashi sai dare ya tsala zata dawo ba,wanda ya sani sai mahaifiyarta ce zasu bude mata gida ta shigo.
Amma har lokacin Umma hankalinta baikai ga cewa yarta ta samo sabon rayuwa ba ita gani take gajiyace dai take dawowa dashi.
Don Umma na da,wani hali indan ta,dawo aiki ta zube guri guda bata motsa jikin ta, dan damadama,idan ita ke da duty a gidan ranan zata danyi kiza kiza.
Hjy kubura ta fara jin zance Nafisa a gurin wata kawar aikinta, amma sai bayata yarda da zancen ba ta dauki maganan ba gaskiya ba tunda kawar tace har gari suke bari zuwa wani guri yawon banza kuma ita tana ganin Nafisa a gida.
Kuma abokanta su Raiha sun riga sun gagari iyayyen su babu maijin kwabo su, suji yanzu.
Ganin bata san labarin ba yasa kawarta cewa kai kila dai ba gaskiya bane kama daine suka gani suka ce itace.
Sai dai Umma ance laifi tudu ne, take naka ka hango na wani,
Zance ta shine sadauki yana can kasan waje ya zama tattacen dan iska, yana hurda da,turawa yana sayar da kwaya da fashi.
Inda Allah zai kashe mata bakinta ranan sai ga danta ya shigo da sauri yana cewa su Maji dasu mama Asiya ku kuna,tv tashan sport yau su sadauki zasuyi wasa.
Nan kuwa suka shiga kunnawa suka kai tashan wasan kwallo har falon Baban su, sai da ya kunna suna zaune aka fara fitar da yan wasa sai gashi saye da kayan wasan shi sun fito, yana saye da rigan shi an rubuta mai Umar sokoto, Nomba 9,,,
Haba take yaran gidan gaba daya suka dauki ihu suna,wallahi ga yaya sadauki ga yaya sadauki.
Nan aka fara wasa ranan duk gari ya dauki ihu sosai don ganin dangida kuma haifafen dan gari yaje fitar masu da sunan su.
Ba atashi wasan ba,saida yai masu ci biyu dada fa ihu ba kama hannun yaro wani haushi yakama Umma tace kai ku kashe min wanan shegen abin sai kace wani abin kwarai wai kwallo kafa kukewa wanan ihun haka.
Tasa aka kasshe mata TV ta baba daga dakin shi ya aiko mata su kunna Tv su ga Umar nan ana hira dashi a TV.
Rananta baiso ba amma dolen ta, ta kunnawa daidai Sadauki yana fadi cikin turanci da ba,wanda yasan cewa ya iya ta haka slays English irin na turawa yana fadin.
Yana mika gaisuwan shi da godiyan shi ga mutanen kasar shi Nigeria dakuma iyayyen shi da,sukai mai tsaye yakai ga wanan matsayin.
Haba gida ya kara daukan ihu da murna sai bugo waya mutane keyi suna cewa ku, kunna TV su gan dansu ana hira dashi a NTA sports.
Dakin Maji kan ranan ba a cewa komai don farin ciki da murna maji saida tai kwallan hamdala ga Allah.
Yayi kyau yai fari sosai hasken shi ya fito da kyau kana ganin shi kasan dadi da ni,ima ya sauka mashi.
Kwana da kwanaki bakajin komai sai zance UF kawai ke tashi a gari nan sauran yaran gidan su, suka,shiga barazana da daukan kai a gari.
Baba ya kecewa su mama bayan ya tarasu yace
yana son yaran nan suyi aure hakana don haka ai zancen zuwa gidan yan matan su ai magana.
Hjy kubura tace har da dana ke nan Baba yace aishi ma yakamata yai aure shida ke fita waje ya dade kinga sai ya dauki abinshi su tafi can su karata can.
Yace zaiga kanin shi Sani suyi magana kan Rahama don asan abinyi nan dai duk aka aje magana za,a aika gidajen matan su.
Sai dai may Baba yana zuwa gurin dan uwan shi kan zancen auren sadauki da yar shi da kowa ya dade dasani sai cewa kanin nashi yayi gaskiya shi sai sunyi shawara da matar,shi da yarsu tukun.
Baba yace ikon Allah sani akan auren yaran da,suke duk abu daya shine zakace sai kayi shawara da mace tukun kabani amsa.
Yace eh don akwai dan mahawara tun kwanaki akan zancen saboda haka abari ya kara tuntubar uwar yarinyar yaji.
Haka Baba ya bar gidan jiki ba karfi don yana da ,wuya ba,a samu matsala ba ke nan amma dai sai yabar zancen a ranshi.
Ita ko hajiya saude da mijinta yazo kan zance sai cewa tayi ita gaskiya bada ita bata daukan yar ta, taba mashayi yarinyar da kurciyar ta taje can takama hadiyan bakincikin da namiji ga banza.
Yaje can ya samu wata irin shi yar shaye shaye su daidaita tsakani su, amma bata ganin maciji da rana ta tura hannunta ramin shi da dare.
Yar ta tazo ta haifi yara lalattatu a rasa yadda za,ayi dasu yace amma dai kin san wanan magana zai iya kawo matsala tsakanina da dan uwana .
Tace zumuncin shi yadade bai baci ba ai akwai diyan dangi da yawa yaje mana ya nemay su can ba yarta ce kawai yar dangi ba ai.
Sai yaja bakin shi yai shiru don bai iya tunkaran dan uwan shi da wanan zancen gaskiya.
Shi mai daurawa sadauki aurene yau kuma ace shi da kanshi ya hana yarshi sai yaya ke nan
Maji ko da,sukai waya da saudaki tasa shi gaba kan lalai sai ya hado lefe daga can bai so ba amma don bin umurni ta ya hado kayan shi tundaga kasar Spain da sukaje wasan.
Sai murna take cewa dan ta ya kusa zama kamilin mutum tunda zai aje iyali,
Duk da dai ba son hada zuria takeyi da yar hjy Saudae ba don kansu guda da umma kuma yaran basu da kunys ko kadan.
Bayan kaman Sati uku ya shigo gari nan matasa su kai dandazo gurin zuwa taron shi da,dawowa zakace wani gwauna ne zai zo.
Mukan muna school bamusan wainan da ake toya ba a gidan don bamu san zai dawo ba a ranan.
Sai after six lis muka dawo duk a gajiye muke a lokacin, nice gaba maryam tana baya ta tsaya ba mai Napep kudin shi.
Tun a kofan shiga falon mu na fahinci akwai namiji a ciki don takalman maza danagani daga waje.
Ban kawo shi bane tunda nasan baya kasan a lokacin da yar sallamana na shigo falon.
Ina saye da,buje da rigan les da,akai min feeted dinkin ya karbi jikina pink color da,farin zare akai mai yan flowers kanani ajikin shi har bakin lace din banyi kitso ba don ciwo da kaina keyi sai dai na,wanke na daure da ribon kawai.
Na shigo ina fadin wai mamana yau kan duk nagaji, wallah,,,,
Ganin sa kawai nayi zaune ya kara haske yai kyau dashi yana saye cikin wasu kayan maza ko ba,a fadi ba kan san sukai kudin su ga wani irin uban kamshi daya hade muna falo tun daga waje zai tare ka.
Haka kawai ganin shi yasa na makale magana ta sai gabana da naji ya fadi yaushe rabon dana dan matsala a gidan mu kusan wata shidda da yan kai ke nan,
Tun tafiyan shi don ko suna vedio call dasu Amirah bani zuwa kusa ni balle nagan shi.
A hankali nakai zaune saman masangalin kujeran dake daga kofan falon ina fadin sannu da dawowa yaya.
Cikin dan basarwa ya amsa min yace kuna lafiya,
A taikace na bashi amsa da kalau na mike zan shiga sai ga Maryam tana ganin shi tasaka wani irin uban ihu tai kanshi.
Yace ke ke kinfa girma yanzu kinga yadda kuka koma,wasu big ladies da ku kuwa,?
Ta wani shake murya tace kai yaya yanzune ma fa zan cika twity cif fa.
Itako Bintu she is just 18 da yan kai yanzu kaga mu yarane har yanzu don dai ka dade baka ganmu bane kawai.
Yace baki ganin tana ganin ta girma yanzu harda bani amsa any how.
Ni kaina na san amsar dana bashi bata dace ba amma yadda ya hade fuska shi ya dace dashi ai,
Maryam tace kasan aure zatayi shiyasa ta fara daga kai.
Yace aure kuma tare da kallon maji yace badai da wanan tsohon ba dana taba gani.
Kai yaya Kabir ne tsoho wallahi dai ba tsoho bane don dai tana da mata ne kawai
Yace da karfi cikin tabaya da what?
Mata bako guda ba fa ke nan maryam tace ai Bintu babbace itace ta uku a gidan.
Yace fir god sake Maji may zaku aurar wanan wajen don Allah kuma wai mai mata har biyu ita ta ukun su,
Nace tau bisimillahi matsala ya sauka na,shige abina ciki kan shi kawai ya girgiza yace ok lalai ma yarinya ta girma kan.
Har nashiga nai sallah kada lokaci ya karasa shigewa suna falo sai zuba suke shi dai bakajin bakin shi.
Nafito dauke da abinci a dan plate na koma can nesa dasu na zauna na fara ci a hankali.
Kamar kullun fuskan shi a daure yake ba dariya amma kuma wanan yaudararen dariyan tashi da baikai cikiba yana nan shi amsa da yake ba kannen shi kawai.
Inacin abinci na jin sunana da maryam ta kira yadani dago kai shima idanu ya,watso wanda tun ina yarinya nasan da wanan kallon wanda nake dauka kallon tsana.
Tace wai Bintu don Allah ba har part mukace zamuyi mashi ba amma maji ta hana mu.
Nace kunfi kusa anty maryam ba magana na bane wanan na mike zuwa cikin kitchen din dake attache da falon mu na aje plate na shige don lokacin magariba yayi shima naji muryan shi yana ce masu zai fita yai sallah ya dawo.
Bayan na idar na samu mama a falo nace mama dama antanadarwa yaya da abinci ne tace waya fadawa zai dawo yau.
Barshi kawai kinji tunda yazo nai mashi magana yace min wai yaci a government house can yafara sauka wai.
Nace ,a,a ashe abin nayi ne ke nan abu har gidan gwauna kuma tace bari kedai mutane sun dauki kwallo yanzu kamar wani bauta can.
Amira tace ku may kuka gani mudake gida mu mukasha kallo yau kinga yadda aka rako yayan mu kuwa a gidan nan.
Motoci mashin mashin kala kala mungan su yau wai duk yaya aka rako gidan nan.
Nan dai mukasha hira har muka lakace dare yayi bamu sani ba shikuma ba dawo gidan ba har lokacin.
Halinshine idan ya,dawo bai zuwa da,tsara ba sai bayan kwana biyu su iso garin.
Wanan karon ma hakanw ta faru don sai bayan kwana uku da,dawowan shi kayan shi suka iso.
A gaskiya mun sha,tsaraba sosai don bai nuna,min yan ubanci ba a nawa ganin Amma mama sai naji mama na mashi fada wai bata son haka don may kayan su Amirah yafi nawa kyau.
Amira tace Maji haba duk abinda yaya,yaiwa Bintu sai kice ya,nuna mata banbanci mana.
Maji tace ban son hakanane nafu idan zai saya maku abu ya saya maku iri daya koda kala zai banbanta.
Shi dai shiru yayi kawai baice komai ba yasan al,amarin maji da,wanan yarinyar sai Allah kawai.
Wai ma ko yaya akayi har maji tagane hakan da sauri amma ita,wawiyar sai wasan baki take tana godiya.
Gaba daya gidan an sheda sadauki ya dawo don har kudi sai da yabawa mutanen gidan.
Sai cikin dare ya shigo yace wa Amira ta kira mu tazo mu kwaso kaya a motan shi.
Tirka sa don set din akwatina ne har uku mukai ta,kwaso bamu iya daukan manyan dole shi ya kwaso sai da,muka huta muka shiga duba kayan.
Ni har tsoro kayan suka,bani abu sai kace diba akaitayi ba kudi akasa aka saya ba don yawan su.
Mun gama Amira ta nisa tace wai yaya munga kaya har bamu iya dubawa don yawan su.
Murmushi na kullun yayi yace sunyi maku ke nan dai ko da,sauri mukace sosai ma yace yana mikewa maji idan akwai abinda babu aciki sai a,saya anan.
Ban san lokacin da nace kai haba sai kace riya wanan kaya haka aiko gidan sarki za,a kai sai haka.
Maryam tace, ke Bintu akwai abin dariya wallahi baki taba ganin lefe bane haka nace nikan sai yau gaskiya Allah dai yasawa aure albarka sukace amin gaba daya dakin
Muka kwasa sai cikin dakin muka mayar dasu can kuryan maji muka,kawo zannuwa muka rufe ba,wanda yasan anyi a gidan balle afara yadawa.
Shafa,i da,wuturi nayi nice farkon zuwa na kwanta zuciyata sai tunanen wanan irin kayan da yaya hado na laife nace a fili Allah ya kara shirya wa maji dan ta.
Na sauke wani ir8n ajiyan zuciya tare da cewa Allah gamu gare ka mai kudi yaji dadin shi gaskiya.
Wankan da nayi kafin nai sallah yasani jindadin kwanciya sai barci sai dai kuma zuwa dare ban san may ya,farkar dani ba.
Amma sai naji dirin mota an dawo da daren nan nace a,raina Allah dai yasa ba yaya bane a cikin daren nan.
Sai kawai na tsunci kaina da tashi na leka shi din ne yana rataye da corth din shi kawai sai na zarge shi.
Da sauri nai istigifar don zato zubi ne koda ya zama gaskiya da sauri na koma makwanci na.
Sai dai barci ya buwaye ni don haka na mike na fara gabatar da nafila har tsawon wani lokaci na koma na kwanta.
Sai barci da,safe ban shiga school ko maryam yau bazata dadeba can da,wuri zata dawo.
Sai na,dan kara,kwantawa sai zuwa goma nafito don na kama,ma Anty Amira aiki don zata fita yau.
Ina fitowa mukayi kicibis dashi kallo daya nai mashi na gane yasha daren jiya.
Ban kula shi ba don wani irin tsanan shi naji a,raina ya kare zuben min a idona ko lokacin mama tana ciki tana shiryawa haka ma Amira tana kitchen tana aiki.
Ke dauko min abin karyawana yace cikin wata murya na dan kalleshi nai saurin kara dauke idona.
Ya zauna yana wani lumshe idanuwan shi nasan abin bai sake shi ba har lokacin.
A hankali na,tako inda yake dauke da,kayan karyawan shi na duka saitin shi kamar zan aje kayan .
Cikin wata yar karamar murya nace mashi ka,saita kanka kafin mama ta,fahinci halinda kake ciki hankalinka ya tashi.
Don nasan kasha daren jiya kadai jin tsoron haduwan ka da Allah ka tausayawa mahaifiyar ka.
Na mike da,sauri na,barshi daidai ya mike yana gyara saita kan shi daidai don yai mamakin yadda duk yakamay amma wanan manyar yarinyar wai ta fahinci yasha jiya da dare.
Da kyat don mamaki ya iya saita kan shi sai ga uwar tafito kuwa tace a,a babana kana nane zaune ashe yace eh Maji yanzu nazo ahine ma wanan yar taki takawo min abin kari.
Fatima to nima kawo min na karya yau da Baba na tun dashi kun bashi.
Na amsa daga ciki nace mata gani tafe mama ita dai abinda akayi na kawo mata plantain ne da Irish da,kwai sai tea.
Na koma na dauko masu ruwan sanyi nabawa kowa nasa na juya nabar falon inajin su suna hira yana ce mata har yanzu yana da gajiya don bai samu hutu ba.
Nasan ya fadi hakane ya kawar da zargin wani abu a ranta nan take fada mashi cewa taji baban su yace zai kira baban su Sani yaji yadda za,ayi kan zancen auren shi.
Ban ji amsan daya bayar ba amma naji tace ai ina ga ba wani dadewa za,ayiba ayi bukin.
Bai dade ba yafito yabar gidan kada ya sake layi uwarshi ta gane shi tunda ga manyar yarinyar nan ma ta gane balle maji.
Da dare muna zaune Baba ya aiko kiran maji tafita zuwa amsa kiran shi andan jima kadan sai ganin ta mukayi tashigo rai a bace.
Idanuwan ta sunyi luhu, luhu sun kada sunyi jawur dasu duk muka bita da idanuwan mu muna kallon ta.
Amirace tace Maji may akayi kuma yaya sadauki ya dawo magana ya tashi ko.
Ta dago fuskanta ba yabo ba fallasa tace bashi bane Amirah na sauke ajiyan zuciya daga inda nake.
Tambayan ta suka matsayi nace anty kubar mama harta huce tukun koma may ye kuji daga baya.
Dalilin dayasa mukai shiru ke nan gaba daya a falon ba wani mai kwakwaran motsi sai tv dake ta aiki shi kadai.
Sai wayan mama yai kara ta dauka da alaman lalashin ta ake ga,wayan kuma kamar muryan Baba ne.
Mama na aje wayan sai kawai tasaka,wani irin kuka mai ban tausayi tana cewa ita dai gidan zata bari gaba daya ma kowa ya huta.
Da sauri na mike na isa gareta na ce mama don Allah don Annabi koma maynene kiyi hakkuri kibarwa Allah.
Ban kai ga fadin wani abu ba,sai ga yaya sadauki ya fado dakin ganin yanayi uwar yasa shi saurin karasawa gare ta yana tambaya cikin tashin hankali.
Su Amira sai faman kuka sukeyi suma hankali duk a tashe nima kukan ne yazo min lokaci guda.
Kara tambayan ta yayi tare da bata hakkuri kafin ta dan sarara kukan nata sai kuma dakin yai tsit.
Tace babana ban taba zaton Alhaji sani da kan shi zai iya muna wanan cin mutuncin ba a matsayin shi na mahaifi gare ka.
Amma sai gashi tau ya,wanke ido yana fadawa Alhaji maganan banza a kanka.
Yace bazai ba mashayi yar shi ba kaje ka samo maahayiya yar uwar ka ka,aura shi yar bata auren mashayi.
Cikin wani murya naji yaya yai magana yace maji shine abin tashin hankali ni haka ma,yafi min nono fari wallahi.
Dama don naga kina sone yasa kawai na yarda amma ni ban ga abin bata rai ba kowa ya rike nashi.
Ba aba ban ta ba ganin Alhaji na kuka da hawayen shi ba sai yau din nan akan yadda Sani ya rufe ido ya fada mai magana akanka.
Kuma yace daga nan gidan aka kai maganan gidan shi don haka ba zai yarda ka lalata mashi ya ba.
Furza iska yayi ya mike tsaye yace don Allah maji ki kwantar da hankaliki Allah yabani wata,wace tafita ba,shike nan ba.
Amira tace wallahi ko shike nan maji kinga ma,shi bai damu ba.
Maji tace Amira baku ganewa ne shima ke nan jini kuya hana yar shi wa zai bashi yar shi a garin nan.
Maryam tace gari da yawa ai maye baicin kan sa maji in sun hana yarsu sai may Allah zai bashi wace tafita da yarda Allah kuwa.
Ga mata gari da yawa birjit in wani yakika da kwana wani da yini zai nemaka.
Shiru mukayi kowa da abinda yake tunane a ranshi har yagaji da zama yafita nasan shima abin yaci mashi rai sosai.
Da safe sai gani mukayi su umma su biyu wai zasu uguwa mudai san can gidan zasu sukara bata zancen.
Haka ko akayi don gaba daya sun kara jagula al,amarin baki daya kare baici.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,,,
Tun bayan fitan yaya Sadauki a falon dakin shi ya nufa kai tsaye ya fada a kan katifan shi ya kwanta yai lamo tankar wanda yake barci, sai dai ba barcin yake ba.
Damuwa ce tayi masa yawa a ran shi a hankali wasu yan siraran hawaye suka rika silalowa daga idanuwan shi.
Ya dade a haka ya mirgina gefe daya yana fadi a fili, wayyo rayuwata may yasa nake yawan tsintar kaina a cikin mawuyacin halin komai na tashin hankali akaina yake faruwa ni kadai a gidan nan.
Allah ya jarabci rayuwana da masifa saka uwata a tashin hankali ko da yaushe .
A yadda ya lura maji ta dauki son duniya ta kwallafa mashi shi kuma gashi ya kasa bata farin cikin rayuwa.
Ya kai zaune daga kwancen da yake yana cewa ya Allah kada kasa na zamo sanadin jefa uwata a masifan rayunwata.
Gashi tunda ya tafi waje bai mai da hankali ga sha ba amma yana dawowa gida sai ji yake zuciyar shi tana azzalzalar shi sai da yaje yasha ya samu natsuwa a zuciyar shi.
Ba don wanan yar kauyen yarinyar mai saka ido ba da ta taimake shi da bai san yadda zai yi ba idan maji tafito ranan ta fahinci a buge yake.
Can kuma ya tuna zancen baffan shi wai ba zai ba mashayi yar shi ba shi dama Rahama bata gaban shi abudai ne in Allah ya nufe ka dashi ba yadda zakayi.
Tuna siffan Rahama yayi bai san lokacin da ya sake wani tsuki ba akan wanan abin har za,ai masu wulakanci shi da uwar shi a cikin gidan su.
Yana da,budurwa da ta lake mai yar adamawace amma saboda zancen Rahama da maji ta nace shiyasa ya,fita zancen ta kuma yarinyar irin masu son abin duniya din nan ne ko yaushe cikin bani bani take shiyasa bai son al,amarinta.
Sai dai abinda ya daure mashi kai shine kishiyoyin mahaifiyan shi da bai san may tare masu ba haka a rayuwa.
A,sanin shi dai komai yana masu wanda ya dace in ma ba yanzun da yaga tsana tayi yawa a tsakanin su dashi ba yake nisanta kan shi da al,amarin su.
Kiran wayan shi akayi bai tsaya duban ko waye mai kiran nashi ba ya daga wayan tare da karata a kunnen sa yace hello.
Muryan Fatiman adamawa ce tace sweety na baka kirana sai dai ni na kiraka ko?
Dan guntun murmushi ya sake iya bakin shi, yace Fatima ya akayi ne, ?
Tace my life nayi missing dinka sosai, tunda ka tafi gida baka kirani ba banji daga gare ka,ba.
May yasa kake min hakane, baka damu dani ba sai nice ke yawan nuna damuwata a kan ka,
Yai yar guntun murmushi yace Fatima bakiyi min komai ba wallahi nima rashin ki yana damuna abubuwane sukai min yawa a nan gida shiya sa baki jini ba.
Tace karike min kanka kada kaci amanata don min ni taka ce, ka sani.
Yayi murmushi tare da,cewa ban maki alkawarin ni naki bane don haka ban dauka ba.
Dariya tayi daga bangaren ta tace kanace ina wasa ne ko gaskiya nake fada maka.
Yace ni ban yi alkawari ba don ki sani aure ma zanyi very soon don har an kammala komai ko.
Cikin wata irin murya mai karfi tace what are you joking?
Yace bana wanan da ke ai gaskiya na fada maki tun farko ina da mata a gida da zan aura.
Kalaman Sadauki sin tayarwa Fatima adamawa da hankali don haka sun gama waya bayan ta kashe ta kasa zaune ta kasa tsaye shawara daya ta yanke wa ranta shi kuma zatayi.
Washe gari haka na muka tashi ba dadi a gidan kowa zuciyar shi a cushe take mai.
Daga cikin matan gidan su mama ba wace ta damu da damuwan mu sai sha,anin su sukeyi da raha da yaran su.
Hjy kubura ce kawai ta shigo dakin namu zuwa rana don Saturday ne bata fita ko ina.
Ta samu na hada wa mama abin kari ina duke ina zuba mata sugar tai sallama falon.
Muka karba mata take cewa, daidai lokacin maji nace nabar mata sugar hakana.
A,a hjy maijidda ke ma bakin son sugar ashe da yawa ni gashi na rasa yadda zanyi na daina shan wanan sugar don ba lafiya yake ba mutane a jiki ba yanzu.
Murmushi Maji tayi mata tace ni sugar dama bai damay ni ba wanan yar tawa ce ma take yawan son samin sugar ko yaushe.
Ta zauna saman kujera a kusa da maji nan muka shiga gaishe ta mummy ina kwana tace lafiya yau ana gida ba,a fita ba ne.
Maji tace sun samu hutu ne shiyasa kika gan su a gida tace ayya har hutu yazo ashe?
Nan ta juya gurin Maji tace ashe kuma haka Alhaji sani yai muna akan zancen yaran nan ?
Maji tai dan murmushi tace kila shine yafi zama alheri a rayuwan su damu ma gaba daya.
Amma gaskiya Alhaji sani bai kyauta ba yaci kafa bai yada ganye ba yadda Alhaji ya rike shi har yakai haka kuma yanzu kan yar matsalan rayuwa zai kawo wanan dalili haka.
Ai yana da gaskiyan shi don ba mai son ya dauki dan shi ya bayar inda babu tarbiya.
Haba sadauki ne baida tarbiya hjy maijidda sai dai ace kawai wanan lalurar dake kan shi.
Kuma wanan aiba wai wani abin da za,a ki mutum bane kan shi shidai kawai yana da wata manufa ga hakan ne kawai ya sha zugi daga cikin gidan nan.
Tau koma dai maye sai ya,rike dan shi shima Allah ya bashi wata wace tafita ba shi ke nan ba.
Hjy kubura tai matukar mamaki a ranta yadda maji tai saurin basar da zancen a lokaci guda.
Don ita a zaton ta abin zai jawo mata matukar tashin hankali amma sai gashi tashi daya sunga ta basar da zancen ita ma.
Shiru sukayi a lokaci guda falon babu wanda,yai magana a cikin su sai hjy Kubura ta mike, tana cewa dama cewa nayi bari nazo na jajanta maki kan al,amarin.
Maji tace nagode Allah ya saka da alheri, ai zaki kai ga sarakuwa ba da dadewa ba insha Allahu.
Lokacin Bintu ta shigo dauke da ruwan da maganin maji a hannun ta .
Sai ta ce yar gidan maijidda ni dai da ma da Bintu kika hadasu da zaifi don kin san halinta tasan nashi.
Gaba daya muka kalli hjy kubura wace ni ban ma fahinci maganan ta ba,sai da naji mama tace ai da hakan zai faru sai nafi kowa farin ciki .
Da sauri hjy kubura tace mai zai hana hjy maijidda abu tuwona maina.
Fatima tana da mijin ta da zata aura ai bada dadewa ba ma zasu kawo kayan auren ta.
Allah sarki ashe har wani ya riga mu niko tun jiya nake anyana hakan a raina, wallahi ni dai da haka zai yiyo da yafi komai sauki wallahi.
Gaskiya ba zai yuyo ba a haka ma ya suka kare kullun yana samin yarinyar gaba da hattara sai na jajirce mashi akanta.
Wanan ai ba matsala bace don bari zasuyi dasunyi aure amma wanan cin fuskan da Alhaji sani yaiwa mutane ban son a wuce lokacin auren nan Sadauki bai samu wata ya aura ba.
Komai na Allah ne inji maji tace an auri mahaukaci ma balle dan shaye shaye,
Hjy kubura tace ai shine lokaci ne dai bai yi ba amma sadauki yanzun ai abin so ne ga ko wace mace.
Zasu dawo suna da sun sani ai a baya don sun wa yarsu ai ba wani sukaiwa ba amma may ye abin kushe ga sadauki inba wanan harkan ba.
Tana fita dakin su maryam suka ce munafuncin banza kawai kamar da gaske.
Maji ta katse su tace ko na munafuncine tayi min don shine dama zaman kishin.
Tafi sauran dake ta nuna farin cikin su akan al,amarin amma ita dai ko tana da manufa ta dai nuna halarci ai.
Sai maryam ta,kwashe da,dariya tace kaji mummy da,wani zance wai Yaya Sadauki ya auri Bintu.
Kirmitsi ke nan inji Amirah, tace cikin kwashewa da,dariya, sai kuma tace wallahi fa da sun dace, don itace kawai ta karanci rayuwan shi.
Nace don Allah Anty bari zancen nan kina son ya kashe ni ke nan mama tazo ta kwashi gawata.
Maji tace da shima na kashe shi ranan yadda ya kashe min "ya.
Aka kwashe da dariya a falon nan sukai ta hira suna dariya wanda hiran tasu nake jin yana kona min zuciya daurewa kawai nayi ina dariyan yake.
Kada nai magana mama tace nima na kyamaci dan ta duk halarcin da zatai min amma saura kiris nace wa zai auri wanan kazami.
Don ni yanzu balain haushin da takaicin shi nake ji don wallahi duk yafita raina kwata kwata.
Sannu sannu aka fara rage zancen don sunga wa yanda su keyi a kan su basuma damu da zancen ba don ko a jikin su ma.
Min fita zuwa kasuwa don sayo yan abubuwan da ake bukata a gurin mu na girkin mu ni da Anty Amirah muka fita,mun bar maryam tana girki a gida.
Komai mun sayo harda ma abinda muka manta bamu saka a list ba duk mun sayo da sauran canjin hannun mu.
A gajiye muka dawo gida da kayan mu niki niki, nan muka zube a falo bamu dade da zama ba sai ga yaya yashigo wanda shigowan shi gidan ke nan tun safe da ya fita.
Tv yana kunne ya zauna suna kallo da maji suna gaisawa tambayan inda ya shiga take tunda safe haka.
Ya dan yamutsa fuskan shi yace wallahi ina cikin gari ina dan zagawa ne kawai.
Maganan da ake a tv shi ya daukewa kowa hankali a falon don photos wani yaro aka nuno bai wuce shekara sha, goma ba zuwa sha daya.
Wai wani yai mashi fyde ana neman gudun mawan gurin mutane don a,tallafawa iyayyen shi ai mashi aiki.
Salati falon ya dauka lokaci guda ga mahaifin yaron annuna yana kuka yana bayani acikin tv.
Hankalin kowan mu ya tashi nan maji tace oh wanan duniyar ina zaki damu haka yanzu wani daukan alhakine wanan karamin yaro haka ace wai kato yai mashi aika aika haka ba dadin gani.
Maji bari na,dawo abinda ya fadi ke nan ya,mike yabar falon da sauri.
Ashe yana fita asibiti ya nufa gurin da aka sanar akai taimakon kan yaron nan sadauki ya ba da kudin aikin dubu dari biyu dana sayen magani amma yace kada a fadawa mutane shine.
Amma duk da haka abin yanzu bai boyuwa don saboda al,amarin media da yai yawa.
Da dare muna zaune falo sai hira ake yana tare da uwarshi suna maganan da ta shafe su amma mu hankali mu baya a kan su.
Maganan da ake a TV ya mayar da hankalin kowan mu akan tv din labari ne akan yaron da aka nuna dazu da yamma.
Nan suke sanarwa cewa an samu wani matashi mai kishin kasa da addinin shi yazo yabiya kudin aikin yaron tare da daukan nauyin duk wani magani da za aiwa yaron har yaji sauki.
Wanan kuma ba kowa bane sai matashin dake tashe muke alfahari dashi acikin garin nan watau UF.
Shahararen dan wasan kwallon nan dake bugawa kasa kwallo yanzu ayaune kuma muka samu labarin yatafi wasu unguwanni na,tallakawa inda yaiwa mata da yara marayu kyautan kudi da kayan abinci da sutura.
Waya ya dauka ya kira wani nomba zai fara magana yaga wani irin kallo da uwarshi ke mashi na mamaki.
Yace yanzu danace kada a nuna wanan abin sai da kuka nuna amma sai mai labaran ke fadin duk da yace mu boye shi kada mu fadi wanan alheri nashi ga al,umma.
Munga ya dace ace mun fadawa duniya don matasa masu hannu da,shuni irin shi suyi kishi da halin shi suma.
For god sake banji dadin wanan nuna program din nan ba da kasa ayi cikin fushi ya kashe wayan nashi.
Sadauki muryan maji ce take cewa dashi wanan alheri keyi a gari haka bamu da labari.
Dukar da kanshi yayi kasa yana cewa maji Annabin rahama yace idan zakai alheri ko hannun hagun ka kada ya sani,
Amma kinga mutanen nan sai da suka baiyana ni a fili haka.
A dakin Umma kuma tana ganin abinda ake fadi ana yabon sadauki tace cikin wani tsawa don Allah ku kashe min wanan shegen karyan haka kafin na,bata maku rai.
Dole yaran suka kashe TV suka kunna kaset suna kallo ba don ran su yaso ba don sun fi son suga labarai akan dan uwan su saboda yanzu akan shi har wani jiji dakai suke a gari.
Baba kuma yana zaune a falon shi yaga wanan labarin sai cewa yayi Allah nagode maka da wanan baiwa da kaimin ta tsatsona.
Gidan hjy saude kuma tana kallo taja tsuki tana cewa aikin banza adai karata can, sai ga yarta tashigo dakin tana cewa yanzu ake min waya wai anga yaya sadauki yana raba alheri a tv.
Ke rufe min baki ki rabani da zancen wanan mashayi mai kyau dan maciji.
Nafada maki ki fita zancen wanan mara mutuncin, yaron da baida tarbiya ko kadan.
Rahama tace mama amma ni gaskiya na fada maki na ina son shi ko a hakan.
Bazaki so shi ba nace yaron da akace idan yasha har fitsari yake a wanda da amai kacakaca shine zaki wani ce nabarki ki aure shi bata karasa maganan taba Rahama tasa kai tabar dakin cikin turo baki gaba.
Washe gari mukayi bakuwa a gidan mu kowa bai santa ba sai dai tashigo gidan tana tako daidai da ita tana tambayan mahaifiyar U F.
Mama Asiya tai mata nuni da dakin maji cikin binta da kallon ke kuma daga ina.
Tana cewa o mun shiga uku U F kuma a gidan mu kamar gidan wasu arnaku can mukan wanan yaro yazama muna jaiba agidan nan wallahi.
Daga kofa ta tsaya tana sallamu alaikum daga ciki muka amsa mata.
Tashigo yar gaye ce ta karshe ga kyau ga ilimi yana nunackan shi a fili.
Sai data zauna take cewa maji tare da dan zaudowa saman kujeran ina wuni mama.
Lafiya kalau inji maji tace kunzo lafiya ta amsa da fara,anta lafiya kalau mama.
Sai sukai shiru maji ce tai karfin halin fadin ban fahince ki ba don ban sheda ki ba yar uwa.
Mama baki sanni ba,
well na dai zo ne nan don daki Umar U F ni yar adamawa ce ina son na auri yaron ki ne shikuma ban samu kan shi ba shiya sa nace bari na zo na nuna kaina a gare ku.
Don Allah ko daddy din shi yana gida shima mu gaisa dashi, don yasan ni na san shi.
Ikon Allah inji maji tace mahaifin nashi yanzu baya nan ya tafita yana kasuwa.
Tace ok ba matsala ai ina garin zamuga juna da dare idan ya dawo gida.
Sai ta wani harde kafan ta daya saman daya tana taunan cingan a bakin ta kas kas kas.
Mukan ido muka zuba mata wanan fitsara haka wai zamani ina zaki damu hakane?
Kai A LOKACIN DAI MU KE KAN,,,
Juyowa tayi inda muke a zaune tana cewa, sannun ku fa yan mata ya kuke cikin wani daga muna hannu?
Ni dai na mike zuwa ciki na hado mata kayan drinks na kawo mata ta karba tana cewa yauwa na gode fine girl.
Waya ta dauka ta kira layin shi mun dai ji tana ce mashi yazo gida gata nan dakin mama.
Nasan tambayan ta yayi wata mama, sai cewa tayi mummcy mana ta sokoto.
Dama na kusa karasa abinci na mike nafita, zuwa kitchen na duba girki na na samu ya dahu nan na tsaya na hado ma,bakuwar mu abinci mai kyau dashi .
Daga kitchen ina jin muryanta tana,waya sai kiran abokan ta take tana fada masu tazo sokoto yanzun haka tana dakin mumm din U F a zaune.
Sai gashi da saurin shi ya iso gidan tun a kofan gida ya sheda da gaske takeyi tazo garin don ganin motan ta da driver ta dayayi.
Tun da sadauki ya diso falon yaji wani irin bacin rai ya kama shi a ran shi yake fadin wai may mata suka mayar da kan sune yanzu?
Ya shigo da sallama a lokacin na fito daga kitchen dauke da abincin da zanbawa bakuwar mu.
Tana ganin shi ta saki wani shu,umin murmushi tare da cewa my man you think iam joking ko ?.
Ta wani shagwabe murya tana cewa I really miss you alot and i can't keep it,
Dole na biyo ka don nazo na ganka nakuma ga su mama da little sisters din mu.
Sadauki ya dan shafa sumar kan shi da hannun shi na hagu ya dan kalli inda Maji take zaune cikin kallon ikon Allah.
Don yasan yau sunga fitsara a gurin Fatima ba kadan ba don ita bata da kunya ko kadan.
Tace ya naga ka,wani bata rai ko you are not happy with me here ne?
Yace cikin yanayin su na yan duniya No ba haka na bane ban dai yi expecting din ki a nan bane.
Tace ai na fada maka zan baka surprise dama to gani yau a,sokoto kuma dakin mummcy.
Yace saukan yaushe ? tace wallahi dazun nan na iso dama nasan bazan sha wahala ba gurin gane gidan ku don sha haranka.
A kaduna na kwana shiya ka gan mu a wanan lokacin, amma fa gaskiya akwai nisa.
Yace to ya hanya?
Tai wani har da idanuwanta tare da langabe kan ta tace hanya lafiya kalai tunda na gan ka.
Sadauki ya juya inda maji take zaune ta hade rai ba yabo ba fallasa a fuskan ta a lokacin.
Ni dai na,aje abinci ina cewa, ga abinci nan tace yauwa sannu little sister wai ya sunanki ne tunda nazo kike wahala dani.
Sai da na dago daga duken da nake nace Bintu tace wawwwo, sunan mu daya dake ashe.
Amma ki daina cewa kanki Bintu kamar wata yar kauye akiraki da,Fatiman ki kawai ai nice, name ne sunan mu.
Sadauki dai yakai zaune daga dayan kujeran nan bakuwar ta mayar da hankalin ta a kan shi suna dan hira jefi jefi.
Wanka na,shiga na fito na saka wani dogon riga light gren mai kamar bubu daga sama kasa an mashi sharp yafito da sura na na,daura dan kwalin shi a kaina.
Sam na ma manta cewa da bakuwa a falon nan nafito ina cewa Anty Amirah wai yaushe ne zamu tafi gaida baban su Amata.
Wai wanan pretty din itace last born din mune gaskiya tana da kyau sosai wallahi.
Kamar bazai bata amsa ba sai can yace No diyar sister din maman mu ne ita ga dai sisters dina Amirah ga maryam itace yanzu a,matsayin last born din mu.
Yanzu ita wanan din ba blood sister dinka bace yace a dan hasale na fada maki yadda muke da ita ai ko.
Take ta hade fuskan ta, tace there's problem here yace akan may fa tace No barshi ina dai magana ne kawai.
Maji bata falon tashiga ciki don bata iya,karasa hadiyan takaicin da yazo mata har dakin ta yau.
Wanan abin haka ba kimtsi ke kiran kanta da,suna wai sarakuwarta ta ina ?
Kai duniya kowa da,tashi matsalar dai kenan yanzu ita haka duk rabin jiki kusan tsirara shine wai tazo nuna kanta a gurin sarakai a haka.
Kai wanan tanbadewar da fitsara da may yai kamane haka wai tundaga wata uwar duniya yarinya ki taso kice wai kinzo gurin na miji.
Ban kai ga zama ba naji muryan maji tana kirana daga ciki da sauri nake na nufi gurin ta.
Zaune take saman gadon ta hannunta yana rike da caunter na zikkiri take ce min har yanzu wanan fitsararar bakuwar taku tana nan ke nan bata tafi ba ko?
Nace ai zaci anan zata kwana ne don naga daga nesa ta fito.
Tsaki taja tare da kawar da kanta a gefe tace yaro zai jamin wani sabon abin fade a gida yaya zanyi na fada mashi yai gagawan fita da ita gidan nan kafin mutanen gidan nan su ankara da ita.
Nace mama bani wayan ki ta mike min gurin sunan shi nai mashi massage kamar haka.
Ka gagauta fita da ita kafin mahaifinka ya dawo yasamay ta nan.
Na tura mai ina turawa nafito daidai ya fara karantawa wani kallon ke ko yabini dashi.
Nace sannu da zama ko wani kallo ta watso min kamar tasan nice na turo mai da sako yanzu tace yauwa.
Amirah tace, yau zaki koma dai ko?
Murmushi tayi tare da,gyara zama tace a,a har kun gaji da nine ke nan ko Amirah tace a,a ha mutum ai bai gajiya da bakon shi.
Yana gama karata massage din ya dagi kan shi sai kai mukai tozali dashi ina kallon matar .
Harara ya,kara watsa min niko nai mashi dariyar mugunta a fakaice.
Muryan shi mukaji yana fadin Fatima muje na kaiki inda zaki sauka kafin dare yayi cikin diriricewa.
May kake nufi da hakan ba a nan zan sauka bane gurin mummcy ?
Yace baki da hankali ne a cikin gidan namu zaki sauka don baki da kunya to mu nan ba haka al,adan mu yake ba
Yace so ki tashi na kaiki kafin dare yayi ban son daddy na ya dawo ya samay ki a gidan nan haka.
Don mu ba haka al,adan mu yake ba ya mike don dale itama bashiri tamike tare da daukan hand bag din ta tana cewa ina mummcy muyi sallama yace ta shiga alwala ke nan.
Yana gaba tana bayan shi suka fice daga gidan aiko basu dade da fita ba sai ga Baba ya dawo daga kasuwa a lokacin.
Sai da suka bar uguwar ya sauke ajiyan zuciya tare da cewa look Fatima bai nai maki wullakanci bane da hakan amma idan har mahaifina yadawo ya samay ki a gidan akwai matsala babba wallahi.
Kakanki kin sani wanan tsarin da kikazo dashi ba tsarin mune na hausa fulani ba.
Tai wani wal da idanuwan ta tace nima nasan da hakan
amma ban dauki wanan a wani abu can da zai iya kawo maka matsala kamar ka babban yoro haka.
Yace wai ma ba wanan ba may yakawo ki garin nan ne wai Fatima ?
Fatima tai wani marairaicewa tare da kallon shi cikin wani yanayi tace,
Matsala aka samu danaji kace an maka mata agida ana batun auren ka shiyasa na kasa zama naga gara nazo ayita a kare a gaban iyayyen ka.
Sadauki ya katseta da cewa dakikazo gaban iyayyena kice masu may ?
Yace look Fatima da farko na so na karbi bukatanki gare ni amma yanzu hakan da kikai min duk kin jagula komai don haka idont think zan iyaci gaba da zama dake kuma again.
Ran Fatuma ya,sosu da jin maganan da sadauki yai mata sai dai dole yasa ta daure don tana son guy din.
Da sauri ta juyo gare shi tana cewa cikin hada hannayen ta biyu guri guda tare da marairaicewa tace don Allah U F kada kayi fushi dani.
Yin fushin ka akaina zai iya jefani cikin mawuyacin hali a rayuwana sosai wallahi don na mutu da son ka sosai wallahi.
Yayi wani guntun tsuki tare da kawar da kan shi gareta yana cewa don may zaki biyo ni har garin mu don baki da hankali.
Tace kayi hakkuri wallahi duk na,rude ne da ka fada min zakayi aure na,rasa may zanyi akai shiyasa nabiyo ka har nan.
Sadauki ya kara jan tsuki ya kalleta a wullakance yace na fada maki cewa anyi min mata a gida kuma bazan canza maganan iyayyena ba insha Allahu akaina.
Yace kuma ki sani na kyaleki ne yanzu don garin mu kikazo don haka yasa na kyale ki idan badon haka ba da na dauki mataki a kanki sosai.
Don bazan yarda ki hadani fada da iyayyena akan ki jamin wullakanci a gidan mu.
Ya farka mota da karfi cikin five star hotel da suka shiga da alama ran shi yakai kololuwar baci a lokacin.
Nan Fatima ta kifa kai tafara kukan tana rokon shi akan yayi hakkuri ya,aure ta zata zauna da wata su zama matan shi su biyu.
Tace na gane wanan far yarinyar dana gani itace proposer taka don naga tafaye shegen kyau.
Yanzu akan wanan karamar yarinyar kake min haka may zaka,gane a gurin yarinya karama haka ne please cikin kuka take magana.
Yace look Fatima na fada maki tun farkon haduwan mu ni ba mazina ci bane kuma ban iya,neman mata ba ina under control din iyayyena .
So kike akan ki na saba dasu ne for god sake don haka ki sauka na sama,maku masauki da safe ku kama hanya ku tafi.
And kuma na roke ki tun magana bata kaimu ga bacin rai ba kada ki kara,shiga harkata is over hakana.
Nan ya bude mota da zuman tafito su shiga ya kama mata masauki sai ma kunya da yake ji kada wasu su gan shi da mace azaci yazo yin wani masha,ane.
Cikin kuka tace no kabarshi zamu koma kaduna mu kwana gobe na koma Abuja.
Yace is better for you.
Nan tafito tashiga motan ta driver yajata tana kuka suka kama hanyan kaduna da yamma lis sosai.
Ya sauke numfashi duk da yaji tausayin ta yasan wanan shine kawai hanyan da zaibi yasamu kan shi daga shu,umancin ta akan shi.
A gida kuwa maji takai kololuwa da bacin rai sai jiran shi take ya dawo da yadawo yara yaba sokon maganin mama da kuma kaji da drinks da yasayo masu sanyi.
Yace ace yana massalaci zaiyi sallah mamatace koma may zaiyi ai zai shigo ya samay ni gidan nan.
Bai shigo ba sai da suka sallamay isha,i yashigo cikin gida kannen shi na gaida shi amma bai iya amsawa ba idon shi yana kan mahaifiyar su don jira yaji may tace mai yakeyi.
Ya zauna Amira tana fadin yayana kadawo ya bakuwar ta mu take, nan ma shiru yai mata baice mata uffan ba sai take cewa, a can ka barta ne ?.
Don Allah Amirah ki barni na huta haka na wanan tambayan ya isheni wallahi haba gaki kamar yar jarida.
Zama yayi ba,wanda yace kallah a cikin su sai zuwa can Maji ke fadi a da can baya idan ance min kana hurda da mata bazan taba yarda ba koma waye ya fada min.
Amma yanzu da yake ka fara rike kudin kanka gaskiya nai mamakin ganin wanan irin yarinyar ace wai da,su kake harka.
Allah yaceceni in ba kuma wani sabon rayuwan ne ka bulle min dashi ba aji dadin yin min sabon zagi a gidan nan.
Maryam na gaba ina bayan ta muka fito daga cikin daki mun samu mama tana mashi fada sosai kan wanan sabon halin da tagani a gare shi.
Maryam tai tsagal tana cewa ni dai kwata kwata,batai min ba mace haka yar bariki gata nan da ita sai wani iskanci take wai wayewa ke nan.
Maryam ba ga ku nan da irinta ba a gida ina yanzu Nafisa haka take shiga sai kaya ya matse ta sosai duk suran jikin ta a waje.
Amirah ke fadin haka wa maryam tace idan zagine kuma ai akwai shi a gidan ku.
Maji dai fada sosai take mashi akan mutum yayi hankali da duniya kafin ta kure mashi don duniya,ba matabbaci bace.
Baiyi magana ba sai chartting da yake da,wayar shi a zaton mu da bakuwar shi yake fira kafin ya fita zuwa gurin ta.
Amma har dare muna dakin zaune tare dashi sai hira yake da wayar shi kawai da amsa call.
Maji tace daka bar yar mutane acan may zataci sai a lokacin yai magana yace sun tafi maji.
Tace acikin daren nan suka tafi haka basu gudun dare yai masu a hanya.
Bai ce uffan ba yana zaune har dare goma da wani abu yamike yana fadin zai tafi ya kwanta sukai mai sai da safe kaina na duke ina karatu tun zaman shi ban yi magana ba a falon.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,,,
Maria duk zirga zirgan da akeyi asibiti, hankalinta a tashe yake gashi ta bude kudin bankinta asusu da take tarawa wanda sadauki ke kawo mata baikai ko dubu ashirin ba dama wanda take tarawa agida.
Kafin wani lokaci labari har ya zaga, gari ko ina yan sanda suna neman Sisko ya,gudu ya,boye gidan abokin shi can wani uguwa.
Amma haka bai sa an fasa bincike ba don a gano shi don har hukuman human right tasan da zancen a hannun ta yake yanzu.
Mahaifin Aliyu bawan Allah kamilin mutum abin tausayi sai kuka yake kawai yayi a fili yayi a zuciyar shi.
Ya rasa ina zai saka kan shi ya samu kudin da za,a ceto rayuwan yaron shi Aliyu.
Haka yasa wani matashi dake jinyan dan uwan shi a dakin yaji tausayin bawan Allah sosai.
Shine yakai sanarwa a gidan redio da kafafen yada rabarai na cikin gari don a tallafawa wanan dan karamin yaron dake shan wahala.
Shine har Allah ya taimake su labarin yakai ga idon matashin dan kwallon da suke dashi a gari watau U F umar faruk Abubakar yaji sanar wan.
A lokaci guda yaje ya biya kudin aikin tare da,bada kudin magani da wanda yaron zaici abinci har da iyayyen shi.
Mahaifin ya rasa bakin da zaiwa wanan matashin godiya sai dai yafara jero mashi addu,oi masu ma,ana acikin rayuwan dan adam kawai.
Tare da fatan samun nasara a,rayuwan shi ga,duk abinda ya tun kara na alheri.
Sisai yaji dadin adduan wannan bawan Allah sai yake gani ai, kawai kamar an zare mai wani dutse mai nauyi a jikin shi tun lokacin.
Kwana bibiyu yana zuwa ziyar su idan yana gari don yaga how far jikin yaron yake yanzu bayan an mashi aiki.
Sai da malam yaga dan shi ya samu lafiya sosai ne wani yammaci yazo gida yai wanka ya samu maria ita kadai a,gida yaran sun fita zuwa makaranta.
Ya dauki bucket ya debi ruwan wanka sai tazo zata karba ta debo mashi yace a,a ki barshi don ni yanzu ba zamana kike a gidan nan ba.
Wanan kalman ya tayarwa maria da hankali har yafito ya shirya yafita daga gidan tana a cikin tunanen kalamin shi.
Ba bata lokaci ta samu uwarta da zancen daya fada mata nan uwar tahau fada tana fadin shi wani irin mutumi ne da bai san kaddaraba koda talla ko ba talla wanan al,amarin rubutace abune ga yaron nan.
Don haka kibarshi zan fadawa wa iyayyen ki maza su samay shi aji may yake nufi.
Saidai bata san ya riga yai magana da mazan gidan nasu ba tana samun su da zance sukace babu ruwan su suje su da suka bata su gyara da kan su.
Nan yaje gurin malamin shi ida yake daukan karatu har yanzu ai mashi cigiyar yar bazawara koda kauye ne yaura kawai ya huta da halin maria.
Shi ko sisko sai bayan kaman kwana ashirin yana ganin an manta da zancen sai gashi ya fito,
Dama akwai yan sandan farin kaya da ko yaushe suna zagayen shi suka cafke shi sai police station nan aka fara jibgan shege ana gana mashi azaba sosai.
****** ********* ******
Zancen auren mazan gidan mu su yaya imirana ance sai budurwan shi ta kare jaratun NCE da takeyi za ai masu aure saura,watani su kare karatun su abinda ya,dakatar da zancen ke nan .
Amma Umma kullun akan zancen in auren yaran nan ya,tashi zanyi abu kaza zamuyu abukaza take fadi ita da mama Asiya.
Wani lokaci sukanyi hirane don maji taji taji haushi ko takaici gasu a,kullun cikin saka kunne suke don suji ko sadauki na nema wani guri suje su suke zancen.
Wata diyar kawar maji uwar taso a,hadasu kamar may amma sadauki yaki yarda da zancen yace shi aure baya gaban shi tukun na.
Amma su Umma naji sai gasu gidan suka kai suka mai karfi matar tace tasan da zance ai itace matace a hada shi da yarta shi yaki yaron.
Suka taso da kunyan su suka dawo gida da kunya da ,bakin ciki
A haka kwanaki ke shudewa,suna komawa sati zuwa watanin karatun mu sai ci gaba yake sosai ba kama hannun yaro.
Yau ni kadai nafita zuwa makaranta don maryam ta gama exam ita banjin dadin fita amma haka na daure nafita.
Sadauki da yakai wata biyu kasan turai yadawo wanan tafiyan tafiyan arzikine sosai yayi don yasamo makudan kudi a can.
Sai dana dawo na samu sunyi bako dan takura ya dawo ban samay shi a gida ba ya fita don sunce tun safe suka sauka garin.
Amma na samu tsaraba masu kyau harda waya da maryam tace ya canza muna ya sayo muna.
Sai da dare kusan tara ya,shigo gidan da sayayan abubuwan bukatu irin su sheltox sabulan wanki abubuwa masu yawa yace a,raba,abawa kowa nashi tun a bakin motan shi ya dinga ba,almajira suna kaiwa sauran part din gidan wakowa nasa.
An shigo da na Maji ke nan sai gashi ya shigo yana waya yai wani irin haske ga,wani dan saje daya bari a,fuskan shi, daganin shi komai ya zauna.
Har ya zauna bai daina,wayan da yakeyi ba sai da,ya dauki lokaci a hankan yana,wayan shi.
Jin ya gama waya yasa na fito daga dakin mu don naimai sannu dazuwa da kuma godiyan tsaraban mu daya kawo muna.
Still da,waya a hannunshi haka dai na daure nace yaya sannu da,dawowa?.
Mun ga tsaraba mun gode sai lokacin ya dago kai daga abinda yake a wayan shi.
Idanuwan shi masu kama da shi ya zana su da kan shi, yaba min sai kace wani tsohon maye.
Yana son ya bude baki ya ansa min amma kuma ya kasa maga a lokacin saboda gaba daya na canza mai nai mai wani kwarjini a fuska.
Har nabi ta gaban shi na,wuce zuwa gurin TV na dauko littafina amma bai samu damar amsa min ba.
Ina ba da baya ya lumshe idanuwan shi a hankali tare da,saurin kawar da idanuwan shi akaina.
Yace a ran shi may maji kebawa yaran nan ne haka,wai suke canzawa lokaci guda haka.
Ya manta cewa da bazarshi muke taka rawan mu yanzu gaba daya gidan don yanzu ko abinci baba ya daina saye sadauki ya dauke mashi nauyin haka ko.
A hankali ya sauke wani sanyayan ajiyan zuciya yana kuma kan aikin shi.
Ashe lissafi yake don ya fara business wanda ba kowa yasan da hakan ba a gidan.
Sai fili da yasaya ana mashi wani irin mamakeken ginan gida har an kusa kammala aikin ginan ba wanda yafadawa don zurfin ciki irin nashi.
Ya dawo da kwana biyu Kabir yazo gurina mama tasa akai mashi girki hadade wanan zuwan akan zancen auren mu da take son ayi badadewa ba yazo gida.
Sun gaisa da mama harda hjy kubura da suke daswa naciki na ciki da mama tazo sun gaisa yai masu alheri.
Bayan tafiyan sune muna zaune da Kabir saman Carpet dana shimfida muna can gefen wani dan lungun shigowa gidan .
Sai faman hira yakw min kamar kullun irin yadda ya kamu da,sona farat daya haka.
Yau sai nake jin hiran nan shi kawai banjin dadin shi sosai don yadda yake magana sai umm a,aa nake bashi amsa da eh.
Yake sheda min zai fara turo da kayan lefe a gurin maji don ai mata halarcin da take min a nuna mata itama uwace gareni yace daga baya zai turo mota akaita kauye gurin iyayyena da kayan sai a saka muna rana.
Yace ko hakan bai maki ba nace yayi kwarai da gaske don in anyi haka nafi kowa jin dadin hakan irin yadda mama take nuna min kauna abin ba,a cewa komai.
Yace Fatima ina tausayin rayuwan ki naji duk irin rayuwan da kikayi a,wajen matar babaki shine yasa na kara kwadaituwa da na aure ki Fatima.
Ban san lokacin da,wasu hawaye masu dumi suka fara silalo min ba a fuskana.
Ni dai ina godewa Allah don Allah yana sona ko yaushe yana hadani da masu kaunana sosai.
Kabir na ganin na fara kuka hankalin shi yai matukar tashi sosai yace subbahanallahi Fatima ko magana ta batai maki dadi bane yasakaki kuka haka.
Ban daina kuka ka ba,sai kara dan sauti danayi yace cikun murya karyyaya don Allah Fatima kibar kukan nan ki fada min abinda nai maki haka har yasaki kuka.
Hankici ya,dauko yasa yafara dan goge min hawayen dake silala a idanuwana yana bani hakkuri.
Har yaya sadauki ya shigo get din gidan bamu san ya shigo ba, yana ganin abinda kw faruwa da hanzari yaja da baya numfashin shi yaji yana fita da sauri da sauri idanuwan shi yaji sun rufe mashi lokaci guda bai ganin wuri sai can ya samu ya furta innalillahi wa,inna alaihin rajiun.
Yaji wata natsuwa tazo mashi yaji lokacin da kabir ke fadin Fatima ki daina,wanan kukan haka kada ki sakani kuka a gidan mutane.
Da kyat nai dan shuru cikin muryan kuka nake cewa ni kukan godiya nakewa Allah da ya hadani da abokin zama wanda yasan kimata da daraja dana iyayyena akullun Allah yana,min gata a,rayuwa na.
Haka mama ta rikeni amana duk da batasa koni wacece ba har tazo tasan kowa nawa ashe don may bazanyi kuka ba yaya kabir.
Kabir ya sauke ajiyan zuciya yana cewa wallahi duk kin daga min hankali Fatima,
Ashe kuwa zan iya rabuwa da mace kamarki a,rayuwa na,macen da,tasan dadin halarci irin haka.
Nan dai muka dan kara hira mukai sallama dashi sai mun hadu a gida garin mu akan zancen auren mu.
Yai min salama yatafi na dauki kayan da ya,kawo min niki niki zuwa cikin gida dasu sai ganin yaya sadauki nayi yana exercises a kofan shi kusa da inda muka zauna.
Ni dai na ratsa shi na shige da kayana ciki yace yar iska muna fuka kamar wanan yarinyar wai tasan soyayya irin haka kiji dashi mara kunya kawai.
Ina,shiga gida mama tace ,a,a har surukin nawa ya tafine nace eh, yace sauri yake ya isa gida kada yamma tai mashi a hanya.
Nan su maryam suka shiga bude kayan maji tace kai maryam baki da kunya,wallahi tace kai maji nima ranan da,aka,kawo min kaya ai haka tai min matace kun fi kusa ai ba a,shiga tsakanin ku sai mutum yaji kunya.
Nace Anty kowa ya dauki abinda yake so aciki amma turare abawa Baba da mama shi.
Mama tace aiko wallahi Alhaji ya yaba wacan da,yakawo maki kika,bashi .
Nace mama baba yana son turare tace sosai ma,wallahi shi ko yashe cikin saka turare yake.
Nace ai yaya sadauki ya biyo shi don ko shin yana part din nan tun daga waje mutum ke gane cewa yana gi,,,,,
Sai ganin mutum nayi a gaba na ya,watso min idanuwan shi yace munafuka kawai aikin ke kenan sakawa mutane ido kullun.
Dariya su Amira suka kwashe dashi sukace ai munki fada maki ya shigo ne tun da shi dodon ki ne ko yaushe.
Na,turo baki ina cewa ni wallahi ban son kalman muna fukan nan an tashi daga yar kauye amayar dani kuma munafuka yanzu.
Yace dama may kike ba yar kauyen ba munafukan banza kawai ka ganta sumu sumu da ita kamar ba shakiyiya ba a baya.
Kai yafa isa haka kai ke nan in kana gida yarinyar nan bata da,shakat ga rayuwan ta kawai wani irin miskilin mutum ne wai?
Yace may yakaita fadin sunana don kawai taja min fitina mara kunyan yarinya kawai shigewa nayi ranan harda kuka sai da nayi ban futo falo ba har dare ina ciki kumshe shikuma yana gida zaune.
****** ********* ******
Haka ya kwanta tunanen halinda ya gan mu da kabir yai matukar tsaya mashi a zuciyar shi inda ya,rasa may yasa abin yadamay shi haka a rai.
Wata zuciya tabashi amsa da don itama yanzu ta zama kaunan ka kada wani abu ya samay ta ya samu mahaifiyar ka ke nan.
Bai samu barci ba sai dare so sai gashi zuciyar shi tana faman azazzazalar shi kan ya dan sha wani abu ya samu relief tun da ya dawo yakw jin yadan sha wani abu kawai a ran shi.
Haka duk yana gida bai da natsuwa inba ya dan samu abin bugarwa ba ko yaya yake ya dan shawa ran shi yake samun shakat.
Yanzu kuma gashi dare yayi sosai yan san ko ina kafa ya dauke babu inda zai samu wani dan abu ya taba.
Haka ya kwana a wahalce ga tunane ga kuma son shan maye ya addabe shi a zuciyar shi sosai.
Washe gari da kyat ya samu jam,i don saura kiris ya rasa jam,i da yanzu ya zama mai jiki haka yasa a uguwar da yake gina saida yai massalaci babba a gurin don mazauna uguwan.
Zazzabi mai zafi ya rufe shi da safe yinin ranan bai fita zuwa ko ina ba saboda sana din rashin shan mayen da bai samu yi da,dare ba.
Ganin har kusan biyu bai fito ba yasa mama cewa maryam yau ko yayan ku lafiya gaba,daya bai leko gidan nan ba,fa yau.
Amirah tace aiko naga breakfast din shi a kitchen dana dawo kila kuma ya fitane tun da safe zuwa wani guri.
Mama tace ba halin shi bane hakan in yana gari ko yayane yakan shigo kafin yafita zuwa wani guri.
Maryam jeki ki dubo min dakin shi idan baya gidan ne mu sani ko kai maji zai zauna daki har wanan lokacin bai fita,ba,biyu saurafa yanzu.
Jeki ke ki du bo min shi ki gani in baya gidan ne musan bayanan yafitans ban son shegen gadamar tsiya kinji.
Maryam tana,tura kofan taji a bude yake sai dai bataji motsin akwai mutum a cikin dakin ba sai ta fara dan kwankwasa kofan da hannun ta.
Da kyar ya iya bude bakin shi yai magana yace waye ?
Tace nice yaya maryam ce,
Yace shigo kofan a bude yake ai.
Maryam ta tura kofan ta,shiga ta hango shi kwance saman katifan shi ya rufe jiki lif da katon bargon shi.
Tace yaya lafiya maji ce dama tajika shiru tace nazo na dubaka ?
Yace cikin muryan marasa lafiya,
Kice mata yau bana jin dadin jikina ne sosai amma yanzu zan kokarta na fito ai.
Da sauri maryam ta juya zuwa cikin gida tana shedawa maji halin da ta samu sadauki a cikin sa.
Maji tace subbahanallahi shi ne ko waya ya kasa dagawa ya kira yafadi baida lafiya nan maji ta mikw tare da daukan hijjab din ta ita da Amira sai dakin.
Yadda maji ta samu dan nata kwance hankalin ta yai matukar tashi sosai ta haushi da fada haba babana.
Baka da lafiya baka sanarwa mutane asani a taimaka maka sai kashige daki ka rufe kai ka dai a ciki.
Can tace wai may yake damun kane haka ?
Cikin dauriya yake ce mata murya na,rawa,
Zazzabine sai amai da nake dan yi tace subbahanallahi shi ka kwanta haka ba,wani magani ko taimako.
Barin kira Alhaji aje asibiti yace da sauri No maji barshi barshi kawai zan kira wani yakira min likita abokina yazo ya dubani yanzu.
Maji ta juya gurin amira tana fadin ke dauko min wayana a gida da sauri kinji.
Jin sunce amai da zazzabi yana jin sanyi yasa na tsaya ban tafi ba sai dana hada mai tea mai kauri sosai naje masu dashi.
Na samu sai rawan dari yake yana cikin wani hali sosai a lokacin.
Na ce wa mama ga tea mai zafi na hado mashi yasha ko sanyin zai dan rage mashi da kyata ta samu ya tashi ya wanke baki ya zauna bakin katifan daya kwance akai.
Ya sha tea din sai yacire baki maji tace ai gara kasha kafin likitan yazo ko ?
Muna tsaye daga gefe kofa cirko cirko muna kallon shi ya,shayen tea tsab kamar yadda uwarshi ta umurce shi dayi.
Sai ko a take, ga zufa ya karyo mashi a lokaci guda yana gyatsa alaman dan sauki ya samu.
Maji tace Fatima ki fimu dabara aini duk na rude wallahi komai na kasa yi ma gaba daya.
Shigowan likita da abokin shi Bashar yasa duk da halin ciwon da yake ciki ya dagi kai ya,watsa muna harara kowan mu tagane nufin shi haka muka juya sukuku damu kamar munafukai muka bar dakin sai maji ce kawai ta rage a ciki.
Likita ya duba shi ya,rubuta magani Bashar yaje ya sayo masu, bai dade ba,ya,dawo da maganin da allurai a leda akai mashi yamike wai zaiyi alwala a lokacin.
Sukace ya dan bari ya dan samu sauki sai ya,tashi yayi sallah haka ya koma ya kwanta yana numfashi guda guda.
Ni dai tun wanan zuwan da nayi gaidashi ban kara zuwa ba,suke ta faman rawan kai da abin su.
Amira ce mai jinyan shi sosai da yan uwan shi don va laifi sun nuna mashi karamci don suna zuwa gaida shi sosai gaskiya mutanen gidan.
Can cikin ran sadauki mamaki take yadda tun ranan bai kara ganina ba zuwa gaidashi ba.
Gashi har su umma suna zuwa duba shi balle ni da yasan ina da kokari sosai gurin kula da mutum.
Amma gashi duk wanan rashin lafiyan dayayi ban shiga gaidashi ba ko sau daya tun randa yafara ciwon nakai mai tea ban koma ba.
Har ya fara samun sauki sosai yana dan fitowa ya,sha iska wajen gidan su.
Tun da safe aka kirani wai babana baida lafiya kwana kusan uku ke nan bai masan inda yake ba.
Ban,san, lokacin da na kama kuka ba na tayar da hankalina sosai maji ta fadawa baba yabani dubu hamsin yace naje nagani idan abin yai nisa kwarai mukawo shi asibitin gari.
Na kama hanyan tun da,safe nai sa,a na samu mota sai kauyen mu gaskiya na samu Baba yana matukar jin jiki wai ma yaji sauki ke nan daga gona ciwon ya kamashi aka kwaso shi zuwa gida.
Na sa aka kai shi asibitin nan gari sukace gado zasu bashi mama tabawa tace aikaji irin ta idan an bamu gado wazai biya kudin magani nace ba matsala a kwantar dashi kawai.
Tun ranan na kashe kusan dubu goma sha takwasa ga magani da allurai da,za ai mashi.
Sai yamma maji ta samu waya na don tayi kira yana kashe bayan mun gaisa take tambayana yaya mai jiki nace mai jiki da sauki gamu asibiti an bamu gado ma.
Tace asha ashe jikin ko sosai ne nace wallahi mama duk baba ya ramay yakoma kamar bashi ba wallahi.
Nan dai tai mashi fatan alheri tare da,Allah yaba shi lafiya na ce amin mama tace duk abinda ake ciki na,bugo masu su sani.
****** ********* ******
Sai washegari bayan na,tafi ne sadauki ya uya,shigowa cikin gida a,falon maji ya zube bai jin karfin jikin shi ko kadan sai yawan jin amai da yakeyi.
Yakai awa biyu baiga gilmawa na ba yace maryam maryam daga inda take zaune ta amsa mashi ta mike tazo gurin shi.
Sai da ya dan jima kadan kamar wanda yake wani tunane can ya nisa yake ce mata.
Wai ina yarinyar nan take ne ?
Maryam jin tambayan nashi tayi a bazata mata sai mamaki ya kamata tace wata yarinya ke nan yaya ?
Yace wanan dake nan dakin mana gurin maji.
Tace oho Bintu daidai maji tana shigowa falon ke nan
Tace wallahi ta tafi gida jiya Baban ta aka bugo waya baida lafiya shine ta tafi yace
OK,
Maji tace wa yake tambaya ne wai ?
Maryam tace wai Bintu yake tambaya.
Tace yau kuma lafiya kake tambayan min yarinya kodai wani aikin zaka sata ne?
Yace No ban gata ba dai ne kawai tunda na tashi shiyasa maji tace jiya ta tafi gida mahaifin ta ba lafiya tace anbashi gado a can kauyen.
Yace subbahanallahi a kauye kuma za,a kwantar da mutum ga asibiti a gari.
Tace ba,sai suna da halin kawo shi garin ba Alhaji ne ma da zata tafi yabata dubu hamsi su sai magani tace dashi aka kwan tar dashi din.
So nake ka kara jin sauki sai na roki Alhaji ya bari na tafi nag jikin nashi kauyen.
Don Fatima na da kokari wallahi sosai yarinyar tana da kirki ga dadin zama ai mijinta ya dace wallahi.
Bai yi magana ba sai idanuwan shi da ya lumshe tare da dora hannayen shi saman fuskan shi yai makari dasu.
Bai dade falon ba ya tashi ya fita part din shi ya,shiga yai wanka jin karfin jikin shi yasa shi cewa bari ya fita ya dan zagayo ginan shi yagani don ya kwana biyu kwance bai fita ba.
A can kauye kuma jikin na Baba na gayanan dai ga kaman shi sai dai muce Alhamdullahi kawai.
Haka karama dani, nice komai akace nake kokarin yi ga dan kudin dake hannu na ya,soma karewa,saura dubu uku kawai a hannu na.
Gashi yau tun safe mun rasa,gane kan jikin baba yaki mashi dadi sai nishi yakeyi kawai .
Hankalina duk a,tashe yakw munyi waya da Kabir yace zai turo da sako akawo min daga kauyen su.
Gashi banga dan sakon ba har yanzu kusan karfe dayan rana ake bida a lokacin .
Nafito daga wajen asibitin na samu gurin saman wani dutse gindin bushiyan dake farfajiyan asibitin na zauna, tare da kifa kaina saman gwiwayu na nai shiru ina tunane.
Kaman daga sama nakw jin muryoyin yan gidan mu Maji tana cewa ko wani daki sukw ma ?
Da sauri na dago kaina nace lah mama sannun ku da zuwa ashe kuna hanya tafe ne yanzu.
Tace Fatima kece nan zaune yaya mai jikin maimakon na bata amsa sai kawai na fashe da kuka nace mama Baba kan sai yadda Allah yayi kawai don jikin sai munga kamar yaji sauki sai kuma ciwo ya dawo.
Sam ban san dashi suke ba sai ji nayi yace to may na kuka kuma haka ?
Zaki tari mutane da kuka ki tayar muna da hankali inane dakin da aka kwantar dashi na shiga gaba suna bina a bayan su har muka je dakin da yake kwance.
Baba na yana kwance sharkaf dashi sai nishi yake guda guda suna mashi sannu kafin ma nai magana mama tabawa tace kai Bintu akwai ki da,shiririta wallahi.
Tun dazun ga mutumi yana wahala kin tai kinyi zaman ki baki dawo ba nace mama wanda zai kawo min kudin ne baizo ba har yanzu.
Tace ba Kabir din yace ya basuwa ba shiko mi tsaidashi hakana wai ?
Muryan yaya sadauki dake kallon dakin cikin kyankyami yake cewa wai may sukace yana damun shi ne?
Sai lokacin nace mama ga mamana nabirni da nake wurin ta ta sun zo da yaranta.
Tace ayyo Allah sarki kuna sannun ku da zuwa to a,a hanya yaya sauran jama,an gurin ku,
lafiya suke inji maji, ta amsa mata akaice.
Kara tambaya yayi tare da matsawa gurin Baba ya kura mai ido a ran shi yace ashe agun shi wanan yarinyar ta,kwaso fari haka.
Ga mutun cikin wahala amma farin shi yana nan bai gushe mashi ba natural skin ke nan
Yace wa Babana may ke damun ka ne Baba?
A hankali Baba na ya nuna maran shi da hannun shi da kyat.
Yace shit kun aje mutun haka a kazamin guri haka yana ra wahala ciwo daban magani daban .
Ina likitan yake naji may sukai mai anan don musan inda za,a dora akai.
Yajuya zuwa gurin likitan muka taka mai baya ni da maryam har zuwa,dan dakin da likitan ke zama ko shi a kazance yake gurin.
Yana ganin mu zai fito yafara,washe bakin shi duk goro yasa shi yana fadin ,a,a malam Bintu yau baki mu kayi ne ?
Sun zo duba jikin Baba na ko ?
Yaya sadauki da haushin yadda dattijo kamar wanan ke wasan baki wai yaga yan mata yace don Allah likita muke nema?
Yace mallam ai ni incharge din gurin ka wani kallo yaya,ya,watsa mai yace ina,son in san may ke damuwan bawan Allah nan mahaifin yarinyar nan ya nuna ni sai malamin asibitin yace Fatima Bintu yar ma,aiki.
To gaskiya dai munan in munce ma ga ciwon daka damun shi munyi karya abu gudana dai mun bashi taimako don ya dan samu karfin jikinai kawai.
To idan babu damuwa zamu tafi dashi birni yau aje aga may ke damun shi a can yace gaskiya na hakan yana da kyau sosai walleh.
Ko ina zamu iya samun motan da zata dauke shi ya tambayi likitan yace in anyi sa,a za,a iya samun mota bakin yar kasuwa inda motoci suka tsayi.
Bai tsaya jin komai ko gidiya ba yajuya muka bi bayan ahi sai likitan ke cewa ,a,a Fatima Bintu yau tafiya za,ayi abar mu.
Daga inda yake munajin tsukin shi mudai bamuce komai ba muka bishi maryam ta shiga gaba ina baya sai inda motoci ke tsayawa a kauyen namu .
Munyi sa,a kuwa don mun samu mota daya a layi zasu tsaya dogon jinga dashi yace ko nawane zai biyasu azo a tafi kawai.
Muna zuwa ba adauki lokaci ba muka kama hanya sai sokoto da Baba dake kugin ciwo ba barci kwana da kwanaki gareshi dama mu masu jinyan shi.
Direct asibiti muka nufa dashi yashiga ya fita nan da nan likitoci suka taru kan babana suka,fara binciken matsalar shi.
Sun fara bashi taimakon gagawa tare da,wasu allurai da suke ganin ya dace dashi sai gashi ya samu barci cikin dan lokaci kadan.
Muna nan har dare yana barci sai ga yaya da,wasu samari biyu yan uguwar mu yaran shi ne don nakanga suna mashi abu yace muna mu tashi muje gida jinyan namiji sai maza.
Komai ya,sayo ya masu na bukatan su da ma wanda zasuci jiki ba karfi na mike nabisu muka tafi har da mama ta bawa mukazo gida da ita.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
IN KIN TURA MA WASU DA BASU BIYA BA DON KIN BIYA , ALLAH YA ISAR MUNA AKAN KI,,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,
Tun da safe na farka na shirya abin karyawa, da za a kai asibiti na tayar da mama tabawa,ta shirya don mu tafi tare.
Dakin mama na leka har lokacin zaune take saman salayan ta ta azzakar a gurin.
Na fara gaida ita nake cewa mama zamu tafi asibiti mu dubo Baba na kuma shirya abin karyawan su.
Kai ta,gyada min tare da daga min hannu alaman a dawo lafiya ta nuna min post in dauki kudin mota a ciki.
Mun fito lokacin duk su Amirah suna barci abinsu hankalin su a kwance sukan.
Ban san ya akayi ba ko yaga fitowan mu ne, muna tsaye daidai inda zamu samu abin hawa sai ji nayi ana horn daga,bayan mu, ban so juyawa ba amma jin horn din yai yawa yasa ni dan waigawa.
Sadauki ne zaune cikin haddadan motar shi yana saye da kayan wasa farare sai dai wadon dogo ne har kasa haka ma rigan maidogon hannu sai jan da,aka,sa,daga gefen kafada zuwa hannun rigan layi biyu.
Fuskan shi a,daure tamau dashi kaman bai taba dariya,ba ganin ya,tsaya,a gaban mu kuma baiyi magana ba na gane may yake nufi.
Bude motar nayi nace wa mama ta bawa ta fara shiga, ta sa kai tana fadin bissimillahi rahamanin rahim, ina kwana Alhaji ?
Bai amsa mata ba don baiyi tsan manin da shi take ba, sai da ta gyara zama da kyau nima na shiga bayan na zauna tare da rufe marfin kofan mota,
Wani kyatci naji yayi tare da,furzo, iska daga baki irin na jin takaicin wani din nan.
Ya wani fisgi mota da karfi yan mintina sai gamu bakin UDUTH asibitin koyar da,kwararun likitoci na wanan nahiyar.
Na bude wa mama tabawa ta fara fita daga cikin motan nazo zan fita tare da daukan basket din da muka zubo abinci a cikin shi yake cewa.
Yarinya,baki sanni ba har yanzu zaki rena min wayo bakauyar banza kawai ni driver gidan ku ne.
Naji zafi zagin da yai min amma sai na,share don dan ni ya,taimaka muna nakuma zo abin kunya ana jin harshe na sama tare dashi bai yi ba.
Amma badon taimaka wa mahaifina da yakeyi ba da yau ba abin da zai hanani rama zagin da yai min harda cewa gidan mu.
Gidan mi koda muke tallakawa ai muna da mutunci a idon duniya don bamu da abin da za,ai muna fade, a kanshi sai talauci halittan Allah kawai.
Mu, muka fara shiga dakin da babana yake kwance aciki muka samu mata san suna mashi wanka dole muka dan zauna daga waje har agama mashi wankan.
Muna nan zaune shi bai karaso inda muke ba sai zuwa can na hango shi tafe da leda a hannun shi ya nufo dakin.
Bai muna magana,ba ya zo ya,shige kamar nace kada ya shiga a gyara baba ne ashe yasan an gama,shirya shi, shine yazo kai tsaye ya shige dakin.
Can dayan matashin ya leko yana fadin ance ku shigo angama muka mike sai cikin dakin baba yana zaune Sadauki yana gaban shi yana mika mashi abinci a plate.
Mamaki nayi dana samu ya na tsaye a gaban gadon yana shayar da babana abin karyawa da kan shi.
mamaki ya rufe ni a cikin raina yadda sadauki mai daukan kai, mai izzan tsiya, mai fadin rai kamar wani mugu can akoda yaushe ba alaman rahama a fuskan shi ko kadan.
Amma kuma wai shine tsaye yake shayar da babana mutumin kauye tallaka mai jiran Allah ya kawo aci.
Tun daga kofa mama tabawa cikin muryan yan kauye ana magana a na daga murya take fadin a,a malam kan jiki yai kyau wallahi kaga ikon Allah.
Nan muka shiga gaishe su tare da,matasan nan biyu da suka kwana da Baba na a daren jiya sai lokacin na fahinci cewa wata kila hayan su akayi don suyi wanan aiki, a biyasu kudin su.
Lokaci ne, komai mairai yana gani a wanan zaman da muke a cikin sa haka.
Da kudin sai ka zama sarkin dole saboda yanayin lokaci mai kudi yafi basarake daraja a idon al,umma.
Suma kansu sarakunan suna zubar da kimar su don kwadayi ga tallaka bawan su don kawai kwadayin kudi .
Sai da,Baba na ya,shanye tea,din tas sadauki ya,barshi yana,mashi sannu nan yake cewa matasan nan zasu iya,tafiya,gida su dawo .
A tare suka,fita,dashi ya nufi gurin likita inda ya samu bayanin matsalar dake damun Baba na dole sai an mashi, theater.
Bai muna bayani ba kada hankalin mu ya,tashi don haka yaja bakin shi yai shiru sai da gwago mai masa,tazo yai mata bayani abinda za,ayi kuma a gobe za ai mashi aikin,
Da farko gwago taso ta,rude amma yana daga,mata hannu yace dakata mai masa ban son abin tashin hankali shiyasa na kiraki don na,fada maki saboda zaki fi su kwanaciyan hankali ke.
Tace tau sadauki yanzu may ake ciki yace zamu tafi tare dakw ne ki saka hannu a matsayinki na yar uwar shi.
Tare suka tafi gwago na ta,saka hannu akan aikin da za,aiwa babana gobe da dare.
Washe gari naga shiga da ficen da yaya sadauki yak
e a kan Baba na yai yawa amma sai na dauka don halinshi ne taimakon yasa yake hakan.
Washegari ranan aikin ina sauri na tafi asibiti mama take ce min dakata, Fatima.
Sai gabana ya fadi ras,ras tace bari nazo mu tafi tare kuma ban son abin tayar da hankali idan mun tafi ki natsuna sosai banda shirmay.
Nace tau, tau,mama gaba na sai faduwa,yake ina ganin kaman wani abu ya samu babana boye min kawai akeyi.
Itako mama ta bawa sai hira take cikin daga murya ba abinda ya samay ta kamar wagara.
Mun samu har anyi mai theater an fito dashi ko sadauki da,yaran nan suna zaune a gaban shi cirko cirko.
Wani kallo cikin tashin hankali muke yiwa Baba dake kwance sharkaf saman gado kamar baida rai.
Da,sauri na isa gurin shi ina cewa baba may ya samu baba ina kokarin fasa kuka a lokaci guda.
Hannu ya daga min cikin daka,min tsawa yake cewa ke shout up please kada ki muna kuka anan please.
Aiki, akai mashi baya son damuwa Fatima mama take fada min haka daga gefena da take tsaye tana,kallon yadda yake sauke numfashin shi a hankali kamar zai shude,
Ranan a haka muka wuni cirko cirko tsaye cikin tashin hankali don ance irin aiki da akai mashi is hard aiki matsala,sosai ake samu idan ba,ayi a hankali ba don a marayan maza akai mashi aikin.
Gaskiya wanan jiyan banda abinda zance wa mutanen gidan mu (gidan maji) don ba karamin kokari sukai min ba kan ciwon dake damun babana ko aikin shi tsada gare shi sosai.
Kwana uku da yin aikin ya,samu sauki sosai don yanzu har zama yake yadan dauki lokaci a zaune.
Sai dai ya,wani irin ramaywa yai baki sosai sai ya koma,wani dogo dashi.
Da,sallama na,shigo dakin da,yake ban zaci cewa yaya sadauki yana dakin ba,a,wanan lokacin don bai faye shigowa da,rana haka ba.
Jin sallama yasa su juyowa su na kallo na har da baba na dake zaune ya dago kan shi da sauri ya dan saki murmushi yace Bintu ke tashi?
Na tambayi maman ki tace min ke kwanta kin samu barci.
Nace baba na dan kwanta barci ya dauke ni kaina ke ciwo shine na dan kwanta kadan.
Yaya dake zaune kusa da babana a bak8n gado ya bashi gassashen kifi yaji hadi yana ci a hankali .
Baba na Yace tai zuwa ki nemi paracetamol ki sha keji, kada ya kaiki kwance.
Nace tau baba yace ki tai gida ai na gode wallahi Alhaji karami yai min komai duniya da lahira, wadda sunkai min suma Allah yai masu.
Mutum baka hada komai dashi ba zanan mutunci dai yai maka haka aiko ankai Allah dai ya kara daukaka da darajja.
Duk wanda ke gurin aka amsa da Ameen mamatabawa tace ai halin yarka na yya jja muna wanan alherin haka.
Shidai mikewa,yayi yafita,daga dakin har yakai kofa ya tsaya,batare da,ya juyo ba yake cewa make sure kin bashi maganin shi ida uku tayi.
Ya sa kai yafita can sai ga wani leburan asibiti ya turo kofa yace ga magani ance nakawo wa Fatima wai natane ta duba yadda aka,rubuta tasha.
Mamakin wanan sauyin rayuwa na yaya,sadauki ba ni kadai ba kowa na,mamaki ya koma wani salihi rashin yawan maganan shi ya karu mai.
Sai yana yawan aikin alheri sosai ga alumma mabukata da,rabon su ya ratsa ta,gurin shi ni dai zan iya cewa gaskiya alhamdullahi don rabon mu ya,ratsa aljihun shi tunda,mahaifina ya samu lafiya,a sanadin shi.
Don da akauye yakw sai yadda Allah yayi dashi kawai a can don ance mutum bai mutuwa,sai kwanan shi sunkare.
Sosai babana ya samu sauki gashi daga Alhaji har maji da yaranta zuwa mutanen gidan su sunzo duba ma mahaifina.
Wasu dai gulmane wasu kuma tsakani da Allah ne ya kawo su.
Kabir yazo nan asibiti ya samu baba tadan jima gurin tsaye shi bai zauna ba don girmamawa,
Yana batun wucewa,ne yaya,sadauki ya shigo dakin yana saye da, sworth farare masu kyau da tsada a jikin shi farare zakace ba dan hausawa bane kan shi yaji oil sai sheki yakeyi mai, kafan shi cikin bakaken cover shoes masu tsadan gaske ga agogon da,ya,daura mai matukar tsadan gaske.
Hannun shi yana,rike da dan key din motar shi yana juyawa a,hankali, yana shiga dakin yaga Kabir a zaune ya,sheda shi sosai ya gane shi.
Su mama tabawa aka,shi gaida Sadauki da yi mai barka da zuwa yana,wani amsawa cikin basarwa,yadda halinshi mai kama da kyankyami yake.
Kabir daga inda yake tsaye ya kurawa babana ido yana barci yajuyo gurin miskilin yana mai mika mai hannu don suyi musaba,a irin ta addinin musulunci.
Yace mai sallamu alaikum cikin mika mai hannun shi kamar mai jin kyamar hannu ya wa i basar tukun ga hannun kabir a mike can cikin sham kamshi ya dan mika mai hannu tare da,basar wa suka gaisa.
Duk da abin baiwa Kabir dadi ba ama sai ya shaye ya,dakw yana cewa sannun ku da kokari fa Allah ya,saka maku da,alherin sa.
Kamar bai jiba ya juya yana cewa ni zan tafi idan ya tashi ku kira likita yace a kirashi akwai abinda za,aimashi.
Daga haka ya fice dakin ni ina daga waje ban ma san yadda suka kwasa ba a cikin dakin.
An dan jima kadan Kabir yafito daga dakin nan na mike nazo ti mashi rakiya zuwa inda motar shi take.
Mun dan fara,tafiya,yana cewa,gaskiya jikin yai kyau don da,Alaman aikin anyi sa,a sosai gare shi.
Nace sai dai Baba ya ji jiki sosai wallahi ya dai samu gatane shine har yai saurin murmurewa haka.
Sunana naji yakira, murya a sanyaye yace Fatimatu don Allah may ke tsakanin ki da,wanan yayan naki na nan garin wanda ya shigo dazun ina ciki.
Nace wa ke nan don ban kula da,wanda ya shigo dakin ba ina can baya ni.
Yace wanan da,muka,taba gaisawa dashi acan gidan ku mana wani farin guy haka, mai dan tsawo kadan, mai karfi haka.
Nace,wai duk wanan kwatancen haka yaya sadauki ne mana dan mamana na,garin nan shi kadai ne danta namiji a duniya.
Kuma dan kwallo kila ma kana jin sunan shi don har kasan waje yake fita wasan kwallo sosai.
Nace ummumm wama suke kiran shi ne da,guy name din yan kwallo sai can na tuna nace U F sukekiranshi.
Yace au shine dama UF dan kwallon jahar nan tamu lalai ina jin sunan shi ko sosai wallahi a lailai guy din dollars sun zauna don yana kawo wuta sosai ga kasan nan anaji dashi.
Nace lalai ma ni ban damu da harkan kwallo ba balle nasan wani abu acikin sa sosai.
Sai tambayan da ya jefo min ta bazata na a kunnuwa na yana fadin to may ke tsakanin ki da shi Fatima.
Da,sauri na juyo tare da,dakatawa,da,tafiyan da nakeyi nai may tambayan hausawa tambaya cikin tambaya.
Nace washi yaya sadauki din yace sunan shi kuma ke nan ko nace eh UMAR FARUQ yake shine ma,anan UF din ai yace ok.
Nace sai ban fahinci tambayan da kai min ba nacewa may ke tsakani na dashi nace yayana ne mana, dakin mu guda dashi ai dan fa mamane na fada maka tun farko.
Yace nasani kin fada min, shima yaja ya tsaya wuri daya tare da fuskanta na da,kyau.
Fuskan shi ta nuna min damuwa acikin ta karara nace ba wani abu a tsakani da shi sai yan uwan taka kawai, amatsayin yaya yake gare ni.
Sai naga yai murmushi mai ma,ana da magana can ya nisa yace badon na fadi wani magana ai fushi dani ba dana fadi abinda nagani a zuciyar shi.
Nace kaga yana matukar jin haushi na ko wallahi haka yake mugu ne tun da nazo gidan su zama yani gaba da hattara da tsangwama.
Shi kullun yar kauye da munafuka yakw ce min don kawai yaga mama tana so na.
Fatima nace na,am sai yayai shiru can yadan harde hannayen shi gaban kirjin shi tare da kallo na ido da ido yace .
Wanan yayan naki sadauki yana son ki na hango kishin ki karara a kwayar idon shi wanda ba kowa ne zai fahinci hakan ba sai wanda ya kwantar da hankalin shi sosai zai gane hakan.
Wani kallo nai mashi na amma baka san komai ba nace, haba yaya kabir har may ya rufe maka ido yasa ka fada min wanan magana haka.
Mutumin da ko kashe ni yana iya yi don haushi da takaici na da yake ji zakace wai yana so na.
Ni may ma zanyi da wanan may bakar zuciyar kamar arnakun farko.
Wai tsaya ko don kaga ya taimakawa mahaifina ne yasa ka fadi wanan maganan?
Nasan ba,shi yai niyar hakan ba uwarshi ce ta sakashi yai taimaka muna don tasan yana taimakon mara shi a gari.
Yace to is OK tunda baki yarda ba amma watarana zakice nace nidai don Allah ki rike min amanan kanki don wallahi ina tsoro don zantafi zuciyana yana min kwankwanto ga abinda na gani.
Take naji raina ya baci nace ni wallahi yaya Kabir har ka bata min rai ko na rasa miji may zanyi da wanan mugun mara imani.
Dariya yayi yace shike nan tun da naji haka ga bakin ki da zaran an sallami baba zan turo da kaya a kawo wa mama kamar yadda nace don komai an hada kawowa kawai ya rage.
Nace ni dai yaya Kabir da dai zakayi hakkuri har na kare karatuna da zaifi sauki wallahi.
Yace wa ni ance abari ya huce shi ke kawo rabon wani don haka akarashi a gidana na san na kama abina a hannu kafin ai min sakiyar da ba ruwa.
Yabude motan shi ya shiga har ya zauna sai kuma yafito yace wallahi ina ji kamar kada na wuce nabarki da wannan mayen dana hango nai dariya nace kai zuciya mai nashe nashe wallahi.
Ni ai wanan da kakw gani yafi karfin aure na don shi ba kalana bane ka bar wanan zancen kawai don Allah.
Yace to tunda kince hakana na gamsu yanzu sosai sai mun yi waya ke nan idan na isa gida nace Allah ya tsare idan kaje a gayar min da su Antyna da yaran.
Yace zasu ji insha Allahu yatayar da mota tare da yi min horn na daga mai hannu yafice daga harabar asibitin, saida naga security sun daga mai kofa fita daga get din na juya zuwa ciki.

****** ********* ******
Kwana biyu bayan haka aka sallami babana daga asibiti sai dai sunce bayan sati biyu ya dawo a kara duba lafiyan shi da aikin jikin shi.
A zatona zasu wuce gida amma sai Baba yace ba zai bari su koma ba ya tsaya gari har sati biyun ya cika gidan gwagona aka gyara mashi nan suka zauna da mama tabawa.
Komai sadauki yana masu duk da baya gari amma bashar abokin shi yana zuwa kai da kai yana duba lafiyan su.
Hakan yaiwa Maji dadi sosai da yadawo ranan ina jin tana mashi godiya sai cewa yayi haba Maji ai taimako kamar yiwa kaine abinda ka taimaki wani dashi shine rabonka.
Ban mata da yadda yarinyar nan itama ta taimaka maki ba da kike asibiti wanan ne kawai zamuyi mata mu saka mata da abinda tai muna muma.
Allah yai maka albarka, sadauki halinka na alheri ya bika duk inda kake Allah ubangiji yasa kafi haka a rayuwan ka.
Yaji dadin wanan adduan sosai don ya kasa boye farinciki sai cewa yayi Maji ina jin dadin adduan ki akaina ko yaushe tace ba dole na ba baba na .
Kaine farin cikin rayuwan mu ni da yan uwanka dama,wasu al,umma dake ci daga gareka.
Yace mata zai fita akwai inda yake son zuwa don akwai wani da suke son hada business dashi na mai.
Tace to Allah yaba da sa,a har yakai kofa zai fita take ce mai ai na manta za,afa kawo kayan lefen Fatima nan da kwana uku insha Allahu.
Don haka nake son kudi don nai shirye shiryen taron su.
Yace maji wanan ai maganan ku ne, ni dai bana son ki zauna ba kudi a hannun ki bani jin dadin irin haka.
Idan na fita zan ciro maki kudi, sai na kawo maki idan bai isa ba sai akara maku.
Har ya juya sai yake cewa amma maji wai sauri may wanan yarinyar takeyi, hakane da take son aure.
Wani kallo ta,watso mashi, tace shi aure ga yarinyar da takai sha biyar zuwa sama har wani abu ne yanzu.
Fita yayi kawai bai tsaya ba don yasan fadan zai kawo kan shi idan har baiyi hankali ba.
Ina wanki duk ina jin hiran su nace tunda kowa irin kane da bai tsoron Allah zauna har mutuwa ta riske ka ahaka.
Kamar yadda Kabir yace ranan laraba za,a kawo kayan lefena a gurin mama hakan ne kuwa,don ranan mama da,su Amirah basu huta ba sai aikin abincin masu kawo kaya sukeyi.
Maji ta,gaiyaci abokan arzikin ta daga ko ina a cikin gari kamar yadda akeyi.
Karfe hudu na yamma gida ya cika da abokan arzikin mama masu zuwa mata karan karban kayan lefen diyar ta.
Nayi kwalliya cikin wani swiss lace kore anyi min dinkin riga da siket Amira ta daura min dan kwali gashina ya zubo daga baya.
Sai dai ban fito ba ina dakin mu zaune don kunya daga cikin kawayen mama wasu ke fadin basu gane ni ba nan mama ta,tura Maryam data kirani nazo na gaida mutanen ta.
Maryam ta shigo cikin dakin ta samayni zaune nayi shiru tace Amarsu ta ango may ye haka kuma ranan farinciki kin zauna kinyi wani tagumi dake.
Nace kai anty maryam ni wallahi ina tunanen wanan kokarin na mamana ne kawai .
Tace ke taso su hajiya Larai na son ganin ki wai sunce basu san ki ba shine maji tace na kiraki ku gaisa.
Nai wani iri nace walkahi Anty maryam kunya nakw ji tajawo min gyale na dake gefe na fari ta dora min akai amma can bayan tuntun kaina ya tsaya.
Tare muka fito fallon dasu duk a kunyace nake idona yana kasa sai da nakai kasa na tsugun na a tsakiyan falon nace masu mama ina wunin ku?
Tubarkallah masha Allahu suke fadi hajiya maijidda wanan yar taki haka kamar ita tai kan ta dayar matan tace may ma sunan ta maryam na dariya na yadda duk na tsorace tace masu Fatima Bintu.
Sukace diyar ma,aikin Allah sai lokacin na daga kai na dan kalle su sake rudewa nayi da ganin su manyan mata ne hamshakai ban taba sanin mama tana da kawaye haka ba don banga tafaye fita,ba ita.
Naje gurin matar na zauna tace Allah yasa angon naki shima haka yake kamar ki zama nayi daidai kafar matan tace kaji arziki ba yarinyar da kunyanta yaushe za,a samu yara masu kunya haka wanan nan zamani aida yanzu muna nan dasu suna rawan kai.
Matar ta dan duko tana ce min kina karatu kuwa na ce eh tace a ina ?
Nace a hankali nan state university nake two hundred level.
Masha Allahu duk a kunyace nake zaune cikin su sai hiran duniya sukeyi.
Dayar matar take ce min jeki kin ji diyata don naga kinki sakin jikin ki namike cikin natsuwa nabar falon .
Ban karasa shiga ba naji wata na cewa kai amma hjy maijidda kin ban mamaki yaushe zaki bari wanan daman ya,wuce ki haka, aida kawai kin kamawa danki wanan zukekiyar yarinyar haka ga yarinya da kunya da sanin ya kamata.
Ban fi minti goma ba da shiga masu kawo kaya,suka iso da gudan su yan uwan shi ne mata su shidda suka shigo da,akwatina set biyu masu kyau da daukan ido.
Nan nake jin an shiga guda da yabon kaya basu dade ba suka ce zasu tafi aka bisu da kayan da aka hada masu drinks, kajin da aka soya, da su snacks.
Sai kudi tukwici dubu hamsin har mota aka kai masu nan aka dawo falo akabaje aka,shiga bude kayan ana yabawa.
Naji wata na fadin inji bata da ciwon kai dai ko da sauri maryam tace har biyu kuwa.
Kai tana da kishiya fa a,a,a yarinya kinko debo da zafi kamar wanan yar yarinyar ce za,ta shiga cikin mata biyu.
To Allah ya tsare ya kare ai sai ku tashi tsaye do dai kema gaki kina fama danaki a gida.
Zuwa yamma kowa ya watse gidan aka barmu iyamu hajiya kubura ce zance naji muryanta lokacin da aka kawo kayan har aka tafi tana falon tana yaba kyaun kayan .
Sai dare muka samu kan mu sai kuma a lokacin nafito ban kai minti biyar da zama ba yaya sadauki yashigo falon.
Ina cikin kwalliya na ban cire ba idon shi suka kai ga,akwatinan yazauna yana cewa har bakin naku zun tafi ke nan.
Amira tace su wuce sunzo wallahi kagama kayan da,suka kawo muna can.
Maryann tace kai yaya,wallahi kabir yai kokari sosai wallahi yana nuna yana matukar son Bintu ji wanan uban kaya haka haddadu dasu bari na,dauko maka kagani sai ta mike zuwa gurin kayan.
Yace ke ina wasa da kene ni mace ce da zan tsaya kallon wasu tarkacen banza can.
Da sauri nadago kai ina kallon shi don jin abinda yace, ya watso min harara tare da jan tsuki yace karamar yarinya sai shegen son aure haka.
Wanan tarkace kikewa rawan kan aure jekiyi ke kika sani indai wanan tsohon ne dana ga kina rawan kai akan shi.
Nace a hankali adaibar min abina ko yafi duniya tsufa ina son shi hakana .
Baki da kunya wallahi nike fadawa hakan na juya ina magana kasa kasa nikadai inda nake zaune.
Wai sadauki ban san wanan abinba yanzu shi Kabir din ne tsoho kuma koma dai may ye haka take son abinta sai kaje can kaji dashi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
IDAN KIN TURAWA WA WANDA BAI BIYA BA BA MU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAR MUNA AKAN KI,,,,,
Maji ne zaune falon Alhaji dake cin abincin da takawo mashi, abincin yai mashi dadi sosai kullun yana son cin girkin da maji da yaranta ke hada mashi idan itace da girki.
Tv daga bangon falon da ka shigo dashi zakai arba ya na aiki yakai tashan CNN yana kallon news da akeyi.
Ahmad ne ya shigo falon da wani takarda a hannun shi, yana cewa uban ga takardun an karbo sai ka saka hannu a mayar masu gobe.
Imirana kun dawo yaya kasuwan amma kaman baiji gaisuwan da maji take mashi ba alokacin.
Saida ya gama bin takardan ya dago yana fadin, bakaji ana maka sannu ne ka kyale ta.
Ya dan juya inda maji ke zaune ya watsa mata wani kallo mai kama da harara.
Duk a idon mahaifin shi Alhaji yace yanzu kai da girman ka kana namiji kake shiga harka irin ta mata.
Imirah yace may kuma nayi baba gaisuwa ce taimin kuma na ansa a rai na ai.
Yace to lalai ashe da sauran ka kuma ka bani kunya kai da yau idan na kwanta dama, kaine zaka zama min jigo a gidana.
Ashe hasashen na ba haka bane yanzu nasan ko bani Umar zai iya hada ku ya rike min don shi banga ya banbanta wata daga cikin gidan nan ba.
Ni dama baba ai nasan baka daukan mu yanzu da wani matsayi tunda mu bamu ,,,,
Cikin tsawa Alhaji yace ashe rashin kunyan naka Imirah har yakai haka ban sani ba ?
Yau ni kake kallo ina fadu kana fadi haka kai tsaye babu jin kunya.
Imrah baiyi magana ba ya juya yafita daga dakin rai a bace sai dakin uwar shi.
Maji tace Alhaji da baka biye mashi ba ai, don ni wanan halin na riga na saba dashi ko a gidan nan .
Babu wani yaron gidan nan dake kallona da daraja a matsayin uwa sai diyan hjy Kubura kawai.
Tace don haka don Allah ka daina fadan abinda da duk kaga sunyi min a gaban ka.
Don bazasu daina ba saboda kullun huduban shedan ake masu a kaina.
To Allah ya,sawaka amma gaskiya ba zan lamunci irin haka ba a gidana.
Sai muryan Umma sukaji tana fadin anki agaishe ki din ke waye da sai angaisheki.
Shi da ya mayar dake wata tsiya sai ya zauna yai tayi amma babu mai tirsasawa diya na akan wata mace can marasa asali da ta cika muna gida da diyan tsiya diyan taulali da suka zama ma mutane alkakan kafa.
Maji dai ta fito daga dakin maigidan da kayan abincin da,ta kwaso daga gurin shi.
Muna fuka kawai tun shigowan ki gidan nan kan Alhaji ya burge saboda bakin kilibibin ki wai ke ga,saliha.
Maji tace yaya Allah ya baki hakkuri indai akan zancen nan kike magana ko ni ba da son raina yai mashi fada ba.
Rufe min baki bakar munafuka sai kinyi annamincin ki kizo kinawa mutane wani marairaicewa.
Kin iya kitihin da zaki raba miji da matan shi da yaran shi .
To wallahi hawau kiji na fada maki kinyi kadan a gidan nan muddi kikace zaki shiga tsakanin diyana da uban su.
Ke har ina diyan naki dayake kirarin zasu rike mai gida bayan ran shi?
Ba dai wanan bakin mashayin dan naki ba da duniya tasan da zaman shi yana yawo cikin gari a wukance yara na kallon shi.
Masu abin fadi har ba iyaka saura wa yan nan muna fukan masu kirarin su kamilai ne a gida a waje ko tantiran yan iska.
Kuma kin sa Alhaji yaci zarafin imiran a gaban ki, kinji dadi to ki sani indai ni na haifi Imirah har abada ba zai gaishe ki ba bashi ba duk diyana a gidan nan.
Tsiyan banza duk wani a halina ma bazai taba yin mu,amula da kuba idan kuma kin insa sai ki sa Alhaji ya sa wuka yai ta yankan su don basu gaidake ba.
Haka zai sa nasan yaji zafin, basu gaida ke ba tun da ke dashi kuka daukan min nauyin cikin su na haife su.
Banzan bazara dake mai gayyan tsiya gida masu abin fadi tab ga tsuliya kawai.
Allah ya sauwa inji maji ta nufi dakin ta da kayan dake dauke a hannun ta.
Sadauki tagani tsaye a kofan ta ya dafa, dan gishikin dakin da hannun shi daya.
Batai mashi magana ba ta shige dakin ta kawai,ran ta a bace tana mamakin irin wanan halin na uwargidan su.
Bai shiga ba juyawa yayi ya fita daga gidan ran shi a bace don wanan cin zarafi da akewa mahaifiyan su yana matukar damun shi a rayuwan shi.
Tun da safe yabar garin don bai iya tsayawa yana ganin irin wanan takaicin haka a rayuwan shi.
****** ********* ******
Zaman shi a turai yasa ya manta da bakin cikin da ya baro a gida.
Sai dai kusan kullun zai kira mahaifiyan shi su gaisa yakuma tambaye ta yaya suke da sauran kannen shi.
Yana kiran mahaifin shi shima suna gaisawa har su dan taba dan hira a tsakanin su.
Bangaren Bashar kuma komai yana tafiya masu daidai don yana da rikon Amana sosai .
Gashi kuma sadauki ya yarda da Bashar din don tun suna kana suke tare dashi, lokacin mahaifin Bashar na da rai yafi mahaifin su sadauki kudi sosai shine ke yi masu komai.
Koda sadauki ya fara shaye shaye bai hana bashar yai mu,amula dashi ba duk da hanashi da mahaifiyar shi tayi da farko.
Amma da taga alakarsu abin daga Allah ne sai takawo ido ta samasu kawai don tasan shakuwar su daga Allah ne.
Hankali shi sosai yake a kwance yana sha har yanzu sai dai ba irin na can farko ba irin shan kauyanci da kurciyan da yayi a baya.
Don yanzu ko mutum yafi aula dubara ba zai iya gane cewa ya sha wani abuba.
Haka yasa mutane ke ganin ya daina sha ne kwatakwata a rayuwan shi.
Wani yammaci ya bugowa mahaifin shi waya a yanayin da yaji muryan shi sai baji dadi ba.
Yake cewa Baba lafiya kake kuwa murmushin manya Alhaji yace lafiyata kalau sadauki sai dai dan zazzabin da ba,a rasa ba kawai.
Yace to Allah ya sawaka basuyi wani dogon hiraba yai mai sallama ya kashe wayan.
Washegari tun da safe sai yaji bari ya kira Baban yaji lafiyan shi saboda jiya, yana jin jiki.
Sai dai yana kira hjy Kubura ce ta dauki wayan suka gaisa take ce mai sadauki Alhaji ba lafiya amma gamu asibiti dashi don jiya anan muka kwana.
Hankalin shi ya tashi cikin rudewa yake tambayan ta komay ya sami mahaifin nasu.
Tace mai hawan jini ne akace kuma har ya fadi jiyan sai dai da sauki don yanzun ma ya bude idon shi amma dai har yanzu akwai jikin.
Hankalin shi yai matukar tashi yace mata don Allah ayi duk abinda ya dace dashi kafin ya iso garin.
Sukai sallama da ita hankalin shi a tashe tun a lokacin ne yafara shirin tafiya dawowa gida don ganin halin da mahaifin shi yake ciki.
Washegari Sai dare ya shigo garin don nisan inda yafito a lokacin.
Kai tsaye bai yo gida ba yace Bashar ya,wuce dashi asibiti nan ya samu yan gidan su gaba daya a gurin mahaifin shi.
Umma tana zaune a bakin gadon da Alhaji yake kwance ya shigo dakin daga cikin su wasu sunyi mashi sannu da zuwa.
Wasu ko sai harara shi kawai sukeyi yana saye cikin swoth na maza baki mai guntun hannu daga ciki yar rigace itama pink mai guntun hannu.
Sai dai bai sa aninin rigan saman ba haka yasa za,a hango tacikin sosai a fili.
Ganin Umma ta babake gaban gadon ba wanda ya isa ya matsa bakin gadon bai hana shi karasawa gaban mahaifin nashi ba.
Tare da rage tsawon shi ya duka gap da kan mahaifin nashi ya dan rike hannun shi yana fadin Sannu baba ya jikin naka yanzu.
Alhaji Abubakar ya dan juyo tare da bude idon shi da suke mai a lumshe yace,
Alhamdullahi na samu sauki sadauki ya ya hanya har ka iso ne ?
Yace eh Baba,
Likita yace kada a damay shi da surutu abarshi ya huta kawai, Umma ce ke fadawa sadauki hakan.
Yasan nufin ta bai biye mata ba yace wa mahaifin nashi Baba amma ya kamata a fita dakai zuwa wani kasan a dubaka sosai zaifi zama haka anan.
Murmushi yayi tare da rike hannun yaron yace kada ka damu Faruku ai naji sauki sosai.
Kana dai jin abinda nake fadi likita yace kada asa shi yawan magana ko ?
A hankali ya dago kai ya dan kali inda take zaune tana shimfidawa sauran iyali ikon ta.
Daga bayan ta hjy Kubura tace haba ki barsu su gana mana yanzun fa ya iso shi.
Kada ki fada min magana Kubura don ke ba kunya ne dake ba yaya zan kyale shi yana sashi magana bayan likita yaba da doka.
Hannu Alhaji ya daga masu yace don Allah ya isa hakana please,
Idan shi zakuyi min ku koma gida gaba dayan ku,
Sadauki dai yana duke ya kurawa mahaifin nashi ido dake cikin wani hali gwanin ban tausayi.
Can ya mike ya juya gurin hajiya Kubura yana fadin wani likitane mai duba shi mummy ?
Tace tau kasan likitocin yawa gare su amma dai doctor Ango shine yake shigowa akai, akai gurin shi.
Man let's go yace wa Bashar dake tsaye daga can kofan shigowa dakin.
Ajima kadan sai gashi da likitan sun shigo dakin tare nan likita ya bukaci kowa ya fita daga dakin a lokacin.
Umma kaman zatai magana sai tai shiru tamike ranta a bace suka bar dakin yaran ta suka bi bayan ta.
Har an rufe kofan sai gashi an leko akace hjy kubura ta shigo.
Wanan abin yai matukar harzuka ran Umma sosai take ganin shi sadauki da hjy kubura sun fitane ga Alhajin da za,ace ita ta fita daga dakin.
Mikewa tayi ta nufi kofan ta tura da sauri likitan dake duke kan Alhaji ya dago kan shi hjy kubura tana kokari kamashi a daura mai abin gwaji.
Likita yace haba mama munce ku dan tsaya a waje har mu gama abinda zamuyi mashi ko.
Wani haushi ya kumay ta ta buga kofan ta wucd fuuu tana cewa yaranta su zo su tafi tunda basu da amfani a gurin.
Dan ta Sagir yace haba Umma yaya zamu wuce don kawai ana mashi gwaji ance mu fito.
Sagir kai dama nasan baka da zuciya wallahi, baka san ciwon kanka ba ko kadan a gidan nan.
Sagir yace ni dai ba zan tafi ba gaskiya tace zauna wanan mashayin ya gwada maku iko anan.
Mama ma mikewa tayi tabi bayan Umma suka bar asibitin cikin fushi suna sake bakar magana kai kishi ho.
Likita yace mai nan da kwana biyu idan ya kara jin sauki zasu iya fita dashi din don dai yanzu yana jin jiki tukun na.
Sai dare sosai Sadauki ya bar asibitin don yazo gida yacewa Sagir da Mustapha zai je ya gaida maji ya dawo idan basuyi barci ba.
Ya samu har mun rufe kofa don mama bata zuwa asibitin da dare don habaici da gori ne idan taje suna nan.
Wanka yayi yajuya sai asibitin a can ya kwana gurin mahaifin shi a zaune tare da kannen shi biyu.
Cikin dare Alhaji ya falka ya gan shi zaune saman kujera a gaban shi yana barci yake cewa a ranshi Allah sarki .
Ya Allah ka kara shirya min wanan bawa naka Allah ka shirya min duk zuria ta baki daya.
Jin kaman motsin Alhaji yasa shi saurin bude idon shi ya mike yana cewa Baba yaya ne may ke damun ka ne?
Uban yai dan guntun murmushi yace Umar Faruk Allah yai maka albarka Allah ya kara shirya min kai.
Jinkin sadauki yai sanyi zuciyan shi ta fara bugawa don hankalin shi yai matukar tashi sosai a lokacin.
Nishi ya fara guda guda alaman yana jin jiki shi sosai a lokacin da sauri sadauki ya ke kiran Sagir yana cewa.
Yi sauri kira min nurse a waje sagir ya mike da sauri ya fita shiko yana tsaye sai sannu yake wa mahaifin cikin damuwa.
Nurse yashigo da sauri yana cewa bari akwai Alluran da dama za,ai mashi yanzu zai samu sauki insha Allahu.
Bayan anyi alluran da yan mintoci ne, sai ya samu barci sukan yaran basu barci ba suna tsaye a kan uban nasu har safe.
Jin kiran sallah yace su sagir su fara zuwa suyi sallah in sun dawo sai shi ya tafi.
Sagir yace yaya ku tafi kawai idan kun dawo ni sai na tafi haka sukayi suna dawowa sagir ya fita yai sallah.
Can Alhajin ya bude idon shi lokacin gari ya dan fara haske yace ba,ai sallah bane sukace mashi anyi Baba.
Yace ku taimaka min kuyi min alwala sai nayi sallah da taimakon diyan nashi su kai mai alwala yai sallah daga kwance inda yake.
Sai kuma ya koma barci suna gurin zazzaune ba wanda ya gusa daga cikin su har lokacin.
A gida kuma tun da asuba muka tashi muka hada abin breakfast don mune da girkin gidan.
Ni da anty maryam ne muka dauka zuwa asibiti don mukai wa wan yan da suka kwana dashi abin karyawa.
Muna shiga dakin da,sallama yana tsaye yaba da baya jin sallaman mu yasa shi juyowa.
Sai da gabana ya fadi danaga yadda ya sake min muka karasa muna masu ina kwana ya amsa da kyat cikin yanayin damuwa.
Yaya yaushe ka dawo yace mata jiya da dare daga inda nake tsaye ina kallon yadda Baba yake a kwance na dan dago kai nace mai,
Sannu da dawowa yaya sai lokacin ya dago kai ya dan kalle ni da sauri ya kawar da kanshi tare da cewa yauwa.
Yace ya maji suna lafiya jiya na shiga na samu kun rufe kofa ai.
Maryam tace yaya shine baka buga ba mun kai sha biyu bamuyi barci ba ni da Bintu ai.
Bai bata amsa ba yake cewa sagir su tashi su karya ga abin karyawa nan.
Sagir yace kaifa yaya naga alaman baka ci komai ba tunda kazo fa?
Yace No don't mind zan tafi gida yanzu na dawo sai karya a can idan na dawo sai ku tafi kuma kuyi wanka ku dan huta.
Bashar ya kira yace yazo ya kaishi gida yanzu, ba a dauki lokaci ba nacewa maryam mu tafi,
Tace zamu koma idan Baba ya tashi muna gaidashi don Allah.
Batare da ya juyo ba yake cewa, No ku tsaya Bashar yazo mu tafi tare ko kunzo da mota ne ?
Dariya tayi tace kai haba yaya wani mota kuma ina muka gan shi sai dai mu tare Napeo mu hau.
Dan dariya ciki ciki yai mata ba,adauki lokaci ba saiga bashar cikin jallabiya ya shigo suka gaisa yana tambayan jikin mahaifin nasu yace Not bad gaskiya.
Mukai masu sallama muka fara fita daga dakin kafin su fito mu tafi.
Muna fita maryam tace tau dada ga dodon maza ya dawo yanzu za,a fara ke nan ko ?
Nace ni gida zan tafi sai ya tafi na dawo ban iya zama mugun nan yana gari wallahi.
Ganin sun fito yasa nai shiru ba don na tashi ba yana cewa mutafin ku ko?
Nan muka bisu a baya suna gaba muna biye dasu magana suke akan jikin baba.
Baya muke Bashar na jan motar shi kuma yana gaba yana waya yadda naji wayan da abokin shi yake wayan.
Har muka kai uguwar mu waya yake cikin wani yanayi nikan mota na tsayawa na bude na fita abina ban tsaya ba.
Na shiga na samu mama tana zaune suna magana da Amira tana cewa ko sai yaushe zai shigo garin yazo yaga mahaifin nashi .
Na zauna sunacewa mun dawo nace eh tare suke tambaya yaya jikin Baba nace da sauki mun samu yana barci ne.
Tace Alhamdullahi ai barci alaman sauki ne ga mai jinya.
Maryam tashigo da ledan da ya bata a hannu n ta daganin ledojin na kasar waje ne shi ya mayar da hankalin su mama a kan ta lokacin.
Tace Maji kina da bako fa ashe yaya ya dawo tun jiya wai yazo ya samu mun rufe kofan mu.
Sai gashi ya shigo nan suka fara murna suna mashi sannu da zuwa, suka gaisa da shi.
Nan suka zauna ana magana akan rashin lafiya Baba da halin da yake ciki.
Maji tace akwai abinda ke damun shi don tun ranan da ya dawo daga kasuwa rai a bace washe gari yace ba zai iya fita ba shine har abin ya kai shi kwance haka.
Amirah tace wallahi yaya na zaci ko Baba ba zai tashi ba yadda aka kai shi asibiti rai a hannun Allah wallahi.
Sadauki yace to may Baba yake tunane haka har ya ja mashi wanan matsala kai tsaye.
Maji tace tau ana raba dan adam da damuwane ko al,amarin iyalin shi ai ya ishe shi abinne dai bai faduwa kawai.
Maryam tace ni dai nasan akwai wani abu mama don ranan mun fita da Bintu zamu tafi makaranta naga yan sanda da yan hisbah a kofan gidan nan.
Suna magana dashi kuma wallahi baba sai rantsuwa yakeyi bai zuwa ko ina shi.
Akwai dai gaskiya amma ko may ye ai muji idan yai wari.
Ka karya ne uwar take tambayan shi yace No sai nai wanka zan karya na koma asibitin na duba Baba.
Bai jima ba ya fita daga falon yabar mu nan a zaune can yafito cikin shirin shi yana fadin.
Abashi abin karyawan shi inda nake mama ta dan juyo tana fadin Fatima ba yayan ku, abin karyawa kinji.
Har na fara tafiya na juya inda yake ina cewa na hado ma da indomei ne ?
Yace see you may zanyi da indomie ni kaman wani karamin yaro can?
Kayan tea nafara kawo mashi na juya na dauko mashi kwai da irish su yaci bai sha tea din ba sai ga kira yazo likita ya shigo.
A hanya ya hadu su Umma suna jiran napep su tafi asibitin nan ya tsaya ya dauke su a tare suka tafi dashi sai wani shan kamshi Umma take a bayan mota.
Sun zasu Alhaji a zaune likita yana dubashi suka gaidashi tare suka fita da likitan yana fada mashi yadda suka kwana jiya dashi.
Maganin da aka rubuta da irin abincin da za,a bashi ya tafi ya sayo a nan ya samu da hajiya kubura da maji sun dawo suna sauka da Napep mamaki ya faea wai ina motan Baban sune ?
Zai iya cewa tun wancan karon ya fara ganin kaman arzikin mahaifin su ya fara ja baya sosai.
An bashi maganin da abinci yacu sosai ya kwanta barci don maganin da yasha.
Sadauki ganin su gaba daya yasa shi cewa dama ina son nai magana da ku don ina son nasan da,wa za,a tafi da Baba India ?
Umma tai farat tace kaman yaya dawa za,a tafi dani mana za,a ?
Hjy Kubura tace wanan ma ba magana bane wanan zance ne na jinya babu son kai a cikin shi.
Mama Asiya tace to may kike nufi ke zaki tafi ke nan ko kuwa?
Dama aikin sani,
Wallahi baki isa ba don baki kai muna can ba ni din dai da baki son a tafi dani da ni za,a tafi.
Fitayayi ya bar su dakin cikin dan hatsaniyan su da suka saba har suka falkan da
Alhaji daga barcin da yake yi.
Nan yake jin abindaya hadasu fadan yace dama kun bari don ni bazan tafi India ba dan dama dama da saudiya ne ?
Sadauki ya shigo da abokan shi suka gaida Baba nan yake cewa kace za,a kaini India ?.
Yace eh Baba,
Yace to ba zan yafi ba inda dai saudiya ne zan iya zuwa ko don na sauke farali a can nai Umurah.
Yace tau Baba idan can kake son a tafi sai a tafi din ai yace dawa za,a tafi don mu shirya passport din tafiyan.
Gaddama ya kara kaure tsakanin matan sai cacan baki sukeyi a tsakanin su.
Maji na zaune tun fara magana bace uffan ba a zance duk kuyi min shiru ban zuwa da kowan ku, da Hawau zan tafi.
Tsit sukayi don jin furucin shi, yace tun da abin naku rashin hankali ne baku damu da halin da nake ciki ba.
Dama haka zakace don ka gyara mata rai tunda dantane ya biya.
Sai dai dadin abin kowa ma dai ya hafa a gidan balle yanzu don ana ganin kaman danta ya kawo karfi, za ai muna cin fuska.
Umma na fadin haka tamike tana daukan jakkan hannun ta zata fice daga dakin.
Sadauki yace ba matsala sai aiwa kowan ku passport a tafi ai umuran can sai a dubi lafiyan ka.
Hjy Kubura tace Allah yai maka albarka sadauki wanan dawai niyan haka tace tau sai a mayar da yuka a kube, don dan albarka ya yanke hukunci.
Wani kallon banza ta watso ma hjy kubura tace yanzu ke ake ji mara kunyan yarinya kawai ni ba sa,an yinki bane,
Yaushe kuma muka zama daya tunda bori guda mukewa tsafi ni dake yanzu.
Maji dai mikewa tayi tana fadin ni zan koma Allah ya sauwa Alhaji hjy kubura tace tsaya mu tafi tare anjima nadawo.
A waje suka samu sadauki shi ya dauke su zuwa gida, a hanya yace mummy bani son wanan yawan fitinan da kukeyi da Umma ko don hallin da baba yake ciki yanzu.
Kai Sadauki wallahi yaya ta faye abin haushine ita kullun sai ta mulki mutane tamayar damu da diyan mu abin banza.
Nikuma bazan yarda tayi zaune shirim tana zuba muna iko da mulki ba kaman ita ta aje mutane.
Hajiya maijidda suka samu suke mata abinda suka ga dama a gidan gaskiya ni ban daukan hakan.
Indai sheri ne ai ta matsa yanzu tunda kazo kaga Nafisa asibitin nan da sauri maji ma tace yaya akayi.
Tace may nene ba,agiba yan hisba suna neman su sun hada party na iskanci a gari, akai ta shedana da iya shege.
An kama yan uwanta su su gudu su masu party amma ce uwa tayi wai zata Abuja ne gurin Atika kaunan ta.
To ko shine ya jawo wa Alhaji wanan abin hjy Kubura tace shine ma da dan banzan ga na wurin Asiya Ahmad dayaje ya dauko rikici.
Dole Alhaji ya sayar da kayan shi har motar shi ya biya milayan biyar da wani abu.
Sun dauka ba,a sani bane kawai don mutum baison ya fadi a ce ga bakin shi akaji.
Amma ni Nasir dina yake fada min tun dashi ya boye muna bai son a sani amma ai sune suka jawo mashi hawan jinin ba wani ba.
Daga gaban mota sadauki yace to amma may yasa Baba bai fada min ba duk wanan zancen.
Tace ina zai fadi kasan shi da zurfin ciki ai in sun kashe shi ai an huta ko ?
Har suka isa gida ba wanda yai magana a cikin su sai dai kowa da abinda zuciyan shi ke saka mai.
Waahegari bai zauna ba sai shirin tafiya yakeyi na iyayyen shi, Imirana yace aikin banza ne wanan shi yaushe yake da kudin da zai fitar da Baba waje har da matan shi.
Sai ranan tafiya, ne suka tabbatar inda suka shirya sai kasa mai tsarki, ba tare sukai tafiyan dashi ba zai samay su daga baya amma komai da za,ayi a can ya hada su da abokin wasan shi dan kwallo dan kasan sadiya da yaya sagir suka tafi.
Tafiyan su da kwana biyu duk gidan babu dadi haka dai muke zaune amma sauran yaran sai harkokin su sukeyi.
Na dawo daga sayo muna kayan miya zan shigo gida ban san da mutum tafe ba sai cin kara nayi dashi.
Ina daga kai ya wani daga min gir irin na yan iska, har na zauda shi zan shige ya rike min hannu yana fadin.
Yau shigeya kobaki so sai na kwashi gara gare ki, gidan nan sai da in munafukan uwar ki ta dawo tayi abinda zatayi.
Dama na dade ina son in more wanan lafiyen jikin naki kafin wacan gara da zaki aura ya more.
Sai naji ya jawoni gaba daya yana kokarin daukana zuwa dakin shi nasa hakora na iya karfina na cije mai kunnen shi da sauri ya sake ni ya makure yakai min mari gashi ba wanda yafito daga cikin gida balle ya taimake ni.
Na samu wuyan hannun shi na kara kaimai cizo iya karfina yaji zafi ya dinga kai min nashi a bakina.
Naji zafi na sake sai nishi yake ban san lokacin da yanka wani irin ihu ba da karfi.
Yakara cakumoni na samu sa,a na murde mai gaban shi iya karfi na ya yanka wani irin ihu daidai lokacin, sadauki dake jin kamar ana danbe a waje daga dakin shi ya leko,
Zan gudu yakara finciko ni nakara kai mai wani cizo tare da kamawa da karfin Allah.
Daidai nan naji an kai mashi nashi a bakin shi sai da ya fadi ta baya zaune dirsha.
Yace dabba kawai sauna mara hankali da,wayo kai dabban wani gari ne karasa wanda zakaiwa haka sai Fatima da take zaman kaunan ka.
Tir da halinka halin dan akuya kawai kayi girman banza wallahi, ji ka raggo kawai ji yadda ta mayar dakai jina jina amma baka ji kunya ba kace sai ka danne ta da karfi.
Ya furzo miyan daga bakin shi duk jini ne kila ma hakkoran shi sun zube ne.
Ya juya inda nake tsaye ina kuka yace dauki kayan ki ki shiga gida ke kuma.
Na duka na dauki ledan da na sayo kayan miya duk sun watse a kasa da takalmana da suke warwatse a gurin nai cikin gida da kuka na barsu nan suna fadawa juna magana.
Yana ce wallahi ba dan kwallo kake ba sai naga bayanka a garin nan yace Bisimillah shege ka fasa in baka ga nawa ba ni zanga naka ai.
Sai lokacin naga yan gidan duk sun fito waje ashe suna tsaye cirko cirko cikin tashin han kali.
Ina shiga gida na zube kasa gaban Anty Amirah ina wani irin kuka mai tsuma rai da ban tausayi.
Tana kukatake tambayana bai maki komai ba dai ko na girgiza kai cikin kuka nake fada mata ,a,a yaya sadauki ya ceceni gurin shi.
Maryam tafita ta dinga kantara mashi zagi da,ashar kamar ranta zai fita sai da sadauki yazo yace ta shiga gida hakanan.
Wayan shi ya fitar ya kira Bashar yazo ya samay shi a cikin damuwa ya yasamu abokin nashi.
Yana fito ya samay shi bakin kofan gida su dama Bashar yafita da motan shi shiyasa Imirana bai gane yana gidan ba a lokacin.
Yaya akayi man?
Ya kara cewa wai may ke faruwa ne naganka haka a ya mutse?
Yace hajiyan ka tana garine Bashar yace eh yace zan kwashi yaran nan nakaisu gurin ta har su baba su dawo.
Anyi wani abune ?
Yabashi amsa da anyi a takaice.
Ina fito da kayana falo ina fafin wallahi Anty Amirah ban kwana a gidan nan garin mu zan tafi sai gashi ya dago labule ya shigo falon .
Fuska a daure yace ke Amirah maryam ku hada kayan ku dake kuzo na kai gidan hajiyan Bashar don gobe zanyi tafiya bazan barku a gidan nan ba.
Yan gidan na kallo muka fito da kayan mu mun kashe komai na,wuta a part din namu tare da rufo kofa muka fita daga gidan.
Daga cikin diyan mama Asiya ta buga ma mutanen saudiya waya ta fada masu halin da ake ciki a gidan.
Anso boye wa maji amma sai hjy kubura ta tsinci ana maganan itace ta fada mata abindake faruwa da mu.
Hankalinta yai matukar tashi sosai ranan bata iya barci ba, don gani take kila yakai gare ni boye mata akayi kawai.
Gashi tayi kiran layin mu duk bata samay mu ba har sadauki din bata samu ba.
Ita ko Umma fada takama yi wai don anga bata gida za,a kullawa dan ta sheri haka.
May Imirana zai yi da wanan kwailar yarinyar mara fasali sai fari, duk tsiyan da aka kwaso don anga Allah ya azurta ta da yara shine ake mata hassada a gidan.
Sai ga kanin Imiranan ya bugo mata waya yana kuka yace gaskiya Umma abinda yaya yaki baida kyau fyde wa ya tashi yiwa Bintu yau saida yaya sadauki yacece ta kuma yace sai ya kashe yaya sadauki ya fadi a gaban kowa.
Nan ta hau yaron da fada tace har dashi ke nan za,a kullawa dan uwan shi sheri a gidan.
Yace wallahi Umma ba sheri bane a gaban mu akayi baki yadda akai mai jina jina ba wallahi zaban kunya.
Kashe wayan tayi don bata iya sauraren takaici gashi a gaban hjy kubura suke wayan.
Nan tahau banbami cewa dama ankawo sune don an hada baki a tozarta mata da acan bayan ta.
Hjy Kubura tace ai ba wanda yasaki zuwa ko kin manta fada dakikayi kan sai kin zo dakin zauna gida da yara ai da duk haka baifaru ba.
Amma kun kwaso jiki kunbar yaran can maynene ba zai faru ba tunda basu da tarbiya.
Nan wani sabon fitina ya fara kamar ba a kasan saudiya suke ba saboda bakin kishin su.
Muna gidan maman Bashar matar bata da matsala itama tana da yan mata guda biyu sai wata yar karamar yarinya jikan ta.
Bamu da matsalar komai a gidan don tana bamu kulawa yadda ya dace uwa tabawa diyan ta.
Gasu da addini duk da sun girma basubar zuwa isalamiya ba daukan hadda da sauran litattafai.
Zazzabi nayi na kwana biyu da wahalan da nasha Bashar da maman shi suka kaini asibiti sai da nasha allurai na mike.
Hankalin mu a kwance muke komai a gidan babu tsangwama kuma su kadaine a gidan.
Zamu zauna da uwar muyi hira da ita cikin sake jiki babu ruwan ta.
Sadauki ko ya samu jikin Baba yai sauki sosai don har yafita yai dawafi duk da da sauran jikin shi.
Sai dai yasan cewa Umma tana hake dashi don irin yadda take mashi tunda ya iso kasan.
Bai kula taba don maji taja shi a gefe tunnisowar shi take tambayan shi abinda ya faru.
Hakalin ta ya kara tashi sai dai da taji cewa ai yaranta yanzu suna can uguwar arkilla gurin mahaifiyar Bashar hankalin ta ya kwanta.
Kwana shi uku tare dasu ya tafi garin Riyahd ya barsu gurin wasu yan team din kwallo.
Nan ma ya,bugawa wasa inda ya samo riyar masu yawan gaske don yan kan har taya shi sukayi akan yadawo kasan su da wasa amma yace masu kasan shi ma suna bukatan shi.
Ya dawo suna shirin tafiya ya ba su kudi kowa tayi tsaraba wa yan uwa da yaran ta.
Umma tai matukar rudewa da irin kudin daya basu a can hankalinta ya tashi tasan in bata zake damtse ba sai wanan yaron ya zarce tunanen ta.
Maji ta samu kudi ta sayo muna kaya masu kyau da,tsada zannuwan gado masu kyau da sauran tarkacen daya dace a sayo.
Sai kuma Umna abin ya tsone masu ido wai yabawa uwar shi kudi yafi nasu ya nuna masu banbancin cewa ita ce ta haife shi ke nan.
Maji dai tana gyaran kayan ta sai murmushi tayi kawai batacewa mama Asiya uwa ka iya komai ba.
Don umma ta zugata itace ta fito fili tana maganan cikin hasala da bacin rai.
Sai dai duk iya shegen su basu yarda suyi a gaban Alhaji don yanzu zaici masu mutunci ne.
Satin su biyu da kwana hudu suka iso sokoto zakace ba jinya sukatafi ba da bauta don duk suyi kyau abinsu.
Ga zancen tafiyan su ya bi yan uwa da abokan arziki kowa ya san da cewa dan kishiyan su ne da suke kira mashayin gidan su yakai su saudiya umar da jiyan mijin su.
Saidai kan kowa na ciki na ciki jira ake a dawo gida a zazzage balain da aka kullo.
Kafin su dawo mun shigo mun gyara ko ina na part din mu muka koma gidan su Bashar muna jira su dawo gobe.
Mahaifiyar su bashar tasa ai muna gyara jiki kitso har kumshi saida ta sa akai muna, siffa mai kyau mun koma kamar wasu amare da mu.
Sai bayan sun dawo har sun huta yaya sadauki yaje ya,kwaso mu har mahaifiyan Bashar din ta rakomu gida.
Mun samu gida ya rude da murnan dawowan iyayyen su ko wani daki sai hayaniya akeyi.
Gaba dayan mu muka fada jikin mama cikin murna da farin cikin ganin ta a lokacin.
Maman su Bashar sai kallon mutake cikin sha,awa nan mana ta fara mata godiya, kan karamcin da tayi mata na rike mu a gidan ta.
Tace haba ai ba komai yaro ai duk na kowane dama absan haka tun farko da can suka zauna harku dawo.
Yaya sadauki da Bashar na zaune sai kallon mu sukeyi duk nabi na takura da zaman su a gurin.
Na mike tare da fara daukan jakkunan kayan mu da muja dawo dasu yanzu zuwa cikin daki.
Maji tace Fatima bazaki bari har ki huta ba nai dan murmushi nace mama bari na shiga dasu kawai.
Ina shiga maman Bashae tace ai Fatiman nan taki akwai kokari wallahi ko can haka nake fama da ita gurin aiki.
Mama tace ta riga ta saba bata son zama da kazanta ko kadan .
Ashe aure zatayi bada dadewa ba jiya nake jin suna mata sheri wai angon ta yazo yaga wanan kwalliyan nta sai nake tambya suke fada min an kusa bukin ta har an kawo kayan lefen ta.
Hakane hjy nice ban aika maki ba.
To Allah ya sanya alheri ai mijinta yai sa,a ya samu yatinyar kirki ta san ya kamata sosai.
Kai wanan yarinyar dai shu,umace kowa sai kaji yana yabonta ko akan may oho.
Bai zaci maganan zucin shi yafito fili ba sai jiyayi Bashar na fadin kaine kake ganin ta shu,uma amma ai Fatima mutunce wallahi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA BAMU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAR MU NA AKAN KI,,,,
Tun kawo laife na yaya sadauki ya kara tsananta min a gidan su, dan abu kadan zanyi ya dinga min fada cikin hasala da bacin rai.
Wanda shi kanshi bai san dalili yi min haka ba haka,kawai yake jin haushin yarinyar a ranshi.
Duk da maji tana mashi fadan haka amma ya kasa rangwanta kiyayyan da yake ji nawa a ranshi.
Idan yana gida ban fitowa falo sai naji ya fita daga gidan zan fito falo don nima haushin shi nake ji yanzu don a matsayin mugu macuci nake ganin shi.
Nasan kuma don saka mai idon da nakeyi ne abaya shine yasa yake jin takaicina haka.
Maji sai shirin bukina dake kara matsowa takeyi a hankali, irin su kayan kitchen da wasu uan abubuwa su take sai min.
Kabir yace idan anyi aure a sokoto zan zauna a gidan shi na garin sai idan anyi hutu zan diga zuwa gurin su Abuja.
Maji yakira ya fada mata tsarin da yayi akaina da ta tambaye shi kan al,amarin karatuna da nakeyi.
Sadauki ya shigo ya samu mama tana wayan da Kabir yana jin duk abinda suke fadi a karshe Kabir din ke cewa mama ko tsarin bai maki ba haka?
Maji tace gaskiya naji dadin hakan Allah ya albarkaci rayuwan auren ku, ya amsa cikin jin dadi da Amin mama.
Mama tace Kabir don Allah ka rike min Fatima amana don Fatima yarinyace dake bukatan kulawa yace insha Allahu mama kada kiji komai nima nasan da hakan.
Yana zaune ya fahinci da wa mama take waya ya lumshe idanuwan shi jin hiran nasu yake kamar a fili Kabir yake ya shake shi.
Sai tsuki yayi lokacin suna sallama zata kashe wayan yace tsohon banza kawai.
Kaidawa kuma kake tsuki anyi wani abin ne ko may?
Yace cikin daure fuska kawai dai nayi ne don wanan shirmay danaji anayi.
Shi waye da zai dinga yiwa mutane barazana kamar wani attajiri can.
A,a ikon Allah waikai sadauki ina ruwanka da zancen nan ne?
Ina da ka mayar da kanka abin kwarai agurin kane za,a zo neman auren yaran nan.
Yace wani maji da ban bashi ba kawai mutum ya tsufa amma yana halin yara .
Idan aure yake so bai zuwa ya samu bazawara su shirya sai yafake zai bata yar mutane.
Ya juya inda nake zaune raina yabaci don abinda yake min yafara isata, yace jita don Allah daga kawai ance mutumi a abuja yake duk kin wani rude a kan shi don kawai kije abuja.
Baki tsaya kin tsarawa rayuwan ki abinda zai fishekiba mutum da iyali haka ke karama dake may zaki gane a gurin shi inba wahala ba.
Kai dakata ya isa haka na,rasa gane dalilin dayasa kake wanan abin haka
Yadago ya kalli uwar yace may nakeyi maji iyaka dai ina fadin gaskiyane ni kawai.
Duk abinda na hango mata kun kasa hangen shi sai faman rawan kai takeyi ita zatayi aure wawiya kawai doluwa.
A,a wai sadauki kana da hankali kuwa da may wanan abin yai kama hakane wai?
Mikewa nayi fuuu, nabar falon cikin fushi na shige ciki abina don ban iya tsayawa sauraren wanan shirmay na shi.
Tun ranan idan yaya sadauki ya shigo falon duk hiran da ake haka zan mike tsam na shige daki abina.
Ranan muna tahiran mu cikin dariya har maman tamu tana saka muna baki a hiran mu don hiran wasu samari da suka zo wai suna son maryam muke yi muna dariya.
Ya shigowa suna mashi ina wuni da jan shi da hira yana batun zama namikw tsaye tsam daga inda nake zaune, ina cewa.
Zan shiga na kwanta maryam tace wazai kwanta yanzu ke da baki barci koda rana shine yanzu da yamman nan zakice wai zaki kwanta.
Ya dago lumsarsun idanuwan shi masu nuna a gajiye yake a lokacin don tun safe yafita daga gida .
Ya dora su a kaina gaba daya yaga na canza mashi na koma wata fresh sosai dani don nima ban san may mama take yawan bamu ba muna ci muna,sha na gyara jiki kawai .
Ko kiftawa bayayi don mamakin sauyawa na a lokaci guda da yaga nayi mashi a lokaci guda.
Mama taga yadda yake kallona sai abin ya bata mamaki kwarai da gaske amma sai ta dauka wani sherin yake son fadi akaina kuma.
Don haka tai shiru tana sauraren taji abinda zai fadi a lokacin tai mashi tsiya.
Maryam dai tasan yar tsama muke duk kwanakin nan ta dai dubeni saboda ta san ba,kwanciyan zanyi ba ganin yaya ne kawai yasani barin falon nashige tana ce min atashi lafiya ko?
Nashige batare da na,kara,waiga inda yake ba ballw yace ga abinda nai mashi kuma.
A bangaren sadauki kuwa, fuska ya kara,daurewa batare da ya kara bi ta kaina ba don yasan mama tana jiran shi ne.
Maryam daga inda take tai mashi kuri da ido tana dariya cikin kyata tace ban san wanan fadan na yaya da Bintu ba wallahi.
Bai tanka mata ba sai tsukin da yaja ya dan dafe kan shi yana fadin rabu da,wawiyan banza kawai gaskiya ne bata so a fada mata.
Daga gurin da maji take cikin takaici tace gaskiyan may kada tai auren ko may ?
Yace ni fadan gaskiya nake mata saurin may take da,bazata iya tsayawa ta karasa makatantar taba ne wai, duk tsoho ya, hure mata kunne bata jin kiran yanzu sai
When it's too late to her zata gane kuren ta ai.
Allah dai ya tabbatar muna da abinda yafi zama alheri a gare ta.
Ina shiga daki kamar jira kabir yakw na shiga dakin sai ga kiran wayan shi ya shigo min.
Mama ta kwalla min kira wai nazo za ai program din da nake so wasan kwaikwayo a NTA sokoto wanda nake so ina kallo ina dariya don shirin irin namu ne na mutanen kauye.
Hakan bai hanani yin wayana ba don can na manne gefe guda yadda,ba mai jin abida nake fadi.
Kallo daya zakai min ka fahinci cewa ina cikin nishadi da wayan da nakeyi ga kuma kallon film din da nakeyi a tv duk a lokaci daya.
Muryan kabir ce ta ratso dodon kunne na yana cewa Fatima nayi rashin ki kwana biyu aiki ya hana nazo na gane ki.
Nayi murmushi tare da lunshe idanuwa na na gyara zama da kyau.
Ban bashi amsa ba sai yar murmushin da nayi har yana jiyo ni a,wayan a lokacin .
Ya naji kina murmushi ko baki yarda na damu da nazo na ganki bane wai?
Na koma yin murmushi mai hade da sautin dariya wanda ya jawo hankalin kowa a kaina a lokacin.
Nace may zai hana na yarda duk da dai nasan akwai wasu a,tare da kai ba,wai wani damuwa zakayi sosai hakana ba ai.
Yace kowa daga cikin ku ina bashi hakkin shi ai nace ai nasan da hakan, yace da kyau da kika fahince ni.
Yace wai kin san wani abu kuwa nace a,a cikin dan girgiza kaina kamar yana gani na a fili.
Nace sai ka fada dai,
Yace wai ko Fatima kin san yadda nake jinki a cikin raina kuwa, ?
Wallahi da ina da iko ko kuda bazan yarda ya sauka a kanki ba.
Don ina ji a jikina ke wani abune da,Allah ya jefo min a cikin rayuwana mai muhinmanci a gareni.
Murmurshi nake irin mai kyalkyatawan nan nace kai amma kuwa nikan nayi sa,a,a,rayuwana wallahi.
Insha Allahu zanci gaba da kullan maka da kaina a duk inda nake .
Nace ni wallahi zancen kama har yasa na manta ban tabayeka lafiyan anty na ba da yara.
Yace duk suna nan lafiya yanzu tare muke da uwargida ta dan shiga shago tayi sayayyane.
A rude nace wai har na zaci ai a gaban ta kake waya dani haka wallahi.
Yace aiko a gaban ta sai nayi don ba ta damuwa tama fini matsuwa kizo gidan ai yanzu.
Na saki wata yar siririyar dariya nace kai ka taba ganin kishi har tafi ango damun akawo mata kishiya a duniya.
Yace baki san halin ta bane shiyasa amma ni nasan zanji dadin zaman ku a tare sosai wallahi.
Nace ni dai ka rufa min asiri kada dayar matarka tani tace zamu hade mata kai don muna shiya daya da ita.
Yace ai itama tasan cewa Haulatu na waya dake tai fada harta gaji tunda babu yadda zatayi.
Nace ni nasan dama idan ta sani sai anyi rikici don bata da dama,wallahi gurin kishi.
Maryam tace kai kai wanan matar dai tun ba,a shiga ba na hango ita ce matsalar ku ke da Kabir .
Dariya na kama tare da kashe ina cewa kai anty maryam watau kina jin hiran mu ashe?
Tace duk abinda kuke fadi inajin ku ai in ya damu ba sai yazo ya zauna ba yai ta kore maki kudan da baison yasauka a kanki.
Ya suke da hiran mu yakai geji yakawo iya wuya sai yaga fita dakin yafi mashi jin takaici kawai.
Ya mike yanace maji zan fita sai na dawo tace mai a dawo lafiya tare da ci gaba da kallon ta.
Yana fita Amira tace ke Bintu watarana sai yaya ya make bakin nan naki akan wanan wayan da baiso.
Mutum da mijin shi zai make ta idan yaji takaici yaje ya samo tashi matar mana shima inji maji takeba Amirah amsa.
Bai dauki lokaci ba sosai yakoma tafiyan shi don yanzu bai zama a gida shi sosai ga,wasan kwallo ga kuma business din daya fara gadan gadan na sayar da motoci da mashin mashin,
Haka yasa baida lokacin zama a gari yana fita business din shi da neman kudin shi.
Cikin dan lokaci guda sai ga sunan sadauki ya daga sosai a gari.
Abinda su mama suke gudun dai ya faru Allah ya nufi sai ya faru din don suna gani kuma suna jin yadda Allah yai ikon shi akan abinda suka so kada ya faru da dan kishiyan su.
Mama Asiya ce suna zaune suna hira take cewa, wallahi yaya wanan yoron shigen yaro ne kidiba fa,ba yan mu ba yanzu ko uban shi ya tsushe nisa ba kusa ba .
Umma tace ni wallahi ba inda na fara sanin haka zai iya faruwa damu sai wani rana da natafi dasu gurin buki.
Wata mata irin matan nan masu ido a bude take ce wa daganin na shigo da yaran gidan lokacin suna kananan su.
Matar tace wai wai wai wake da wanan hamshakin yaron haka?
Wai akwai magana nan gaba a gurin nan yaro karami haka da,wanan baiwa irin haka.
Don Allah ku daina fita dashi don gudin idon makiya don wallahi wanan da kuke gani ba karamin mutum bane gurin nan aje.
Umma tace na dauka fa da yaron nan take (Imirana) sai naga ta kama hannun Sadauki kawai tana wani zuba mashi kirari har da dukawan ta.
Tace a lokacin na dauka ko shirmay su ne na yan bori ko neman kudi sai kuma nakarajin shi a gurin maigadin ma,aikatan mu ranan shi ma ya kawo min sako gida sai ga sadauki yafito naga yana kada kai yana fadi cabdi babban mutum Allah ya raya muna kai watarana,akwai magana gidan nan.
Wallahi Asiya tun ranan nasan in bamuyi hankali ba diyan mu na zama shara a gidan nan muna ji muna gani.
Hmmm ashe bani kadai nasan da haka ba tace ni wallahi a gurin baffa malami na fara jin haka.
Ranan da,suka rakani na gayar dashi duk cikin su ba,wanda ya cewa yazo inda yake zaune saman buzun shi wai sai sadauki.
Naji yana cewa manyan gobe Allah ya taya riko Asiya ki rike yaron nan don watarana shine gatan ku ke da yaran nan.
Wallahi baki yadda wani mashe ya sokeni ba sai da na dawo gida abin ya tsaya min arai sosai wallahi.
Nasan baffa kamar mai rafanne yake da,wuya yai magana ya zama karya wallahi.
Kinga wanan makiran nasan itama tasan komai shiyasa take wani wayayya,tana nuna ita tana kaunan shi fiye da kowa.
Shekaran jiya Adamu ke ce min wai motar da yasayo yana shiga yanzu takai miliyan goma.
Ke don Allah dai ki bari tace wallahi yace haka yaji ana fadi a gari wai ba kowa kedashi ba yanzu a kasar nan.
Hmmm lalai Hawau takai makiran mace amma baki ganin wani alaman facakan kudi atare da ita kuma kin dai san yana bata dai.
,A,a ba gashi yaron nan yana fada min ba,wai shi yayowa uban odan kayan da aka,shigo masu dashi wanan wata yace kuma kayan sun samu shiga sosai.
Ai harda noman da Alhaji keyi yanzu shine mai bada kudi anayi don dai ranan naji suna,waya dashi.
Dan banzan yaro maikama da dutsen tsakar ruwa , Asiya karkare mata da cewa, wai bai san tudu ana rana ba.
Yanzu don Allah wazaice dan banza zai iya irin wanan dabara duk kwaya ta halaka shege kullun gashi a bushe kaman kayan rani.
Sai suka sa dariyan keta har suna tafawa tace aiko yanzu in sun san wata ai basu san wata ba ko?
Da yammaci, ranan laraba sadauki ya shirya yafita zuwa masana,antar shi don yaga halin da,su Bashar ke ciki da sana,an tasu.
Ranan shirin musulunci yayi wanda da,wuya kagan shi saye da tufafi irin na,al,adan hausawa.
Shadda ce gezenah mai ruwan kasa,sai maiko takeyi, sai dai dinkin gajeren hannu ce,anyi ma,rigar aiki a gaba mai kyau da daukan ido.
Sai yar hular da ya dora akan shi mai tsada kalar kayan jikin shi,takalman shi bakake sai shining sukeyi sunci polish.
Ga kanshi na tashi kamar duk kwalban ya juye a jikin shi a lokaci guda.
Gurin maji yafara shigo ya sanar da ita zai fita don har yanzu kudi bai hana shi yiwa iyayyen shi biyayya ba.
Kuma baisa yace don yayi gina yabar gidan mahaifan shi ba yanan ciki tare dasu saidai ya gyara gurin shi sosai harda na yan uwan shi.
Ina zaune antu maryam tana min kitso sai faman masifa take min ita gashina yai yawa wahala kawai nake bata.
Azaune nake ba dama na gudu daga falon gashi fuskana yana facing din inda yake tsaye yana dauko wayan shi dake ruri daga Aljihun shi.
Yace hello Bashar yaya akayine ?
Yanzu nake son fitowa tun dazu ina daki ina barci kasan wasan last week yabamu jiki sosai.
Saidai duk da waya yake idonbshi yana kan kitson da Maryam take min kur dashi gashi dole muna facing din juna dashi.
Yana kashe wayan ya mayar da shi cikin aljihun shi inda ya ciro ta da farko.
Yace maji fa?
Yanzun ta shiga ciki nasan zatafito tunda taji muryan ka ai inji maryam din.
Maryam tace yaya wanan wayan taka tayi wallahi ni dai taban sha,awa Bintu gashi kaman wanda mukaga Kabir dinki dashi ranan.
Da sauri yace ke maryam ban son iskanci wallahi ki daina hadani da wanan tsohon mai zarin tsiya.
Na muguda baki cikin tsiwa nace nikan banga tsoho ba wallahi.
Ban san ko tako nawa yayi ba,sai gashi gabana ya danko gashin kaina da karfi sai da na,sake wani irin kara,da sauri mama tafito tana fani kai kai yayane kuma wai ?
May haka dan Allah kasheta zakayine ko may ?
Wallahi maji yarinyar nan ta raina ni wallahi kan wani tsohon mijin ta can take son ta zage ni, ta zage ka tace maka may?
Maryam sai dariyan keta takw min idanuwana,sun kawo kwalla ko don har cikin raina naji dankan da,yai min.
Kadai zama babban kwabo wallahi ka ishi yarinya da sherin mijin ta tsoho ne basai ka,samo mata saurayi ba kowa ya huta.
Allah dai ya,sauwa wake son wanan bakauyan haka ko dressing ba ta iya ba balle gyara irin na mata.
Kyalkyalkyal maryam ke min dariya Amira da,tafito daga kitchen don jin karana take cewa, a,a yayana aiko wallahi yanzu ba may cewa Bintu bata iya dressing ba gaskiya.
Kallonta yayi yaja tsoki ya juta gurin maji yana fadin maji zan dan shiga gurin su bashar na,dawo yanzu.
Sai ka dawo tace mashi tare da samun guri ta zauna tana man fada na daina shiga harkan shi kada ya halakani ga banza.
Nace cikin dan kuka ina,share hawaye da bayan hannu na mama,wallahi duk anty maryam ce taja min.
Ban san may yakaita danganta,wayan shi dana Kabir ba,shine yake cewa wai za,a hada shi da tsoho kazami.
Dariya abin yaba mama tace ni dai na rasa wanan kiyayyan na sadauki da Kabir wallahi Allahbya sauwaka.
Amira tace jinin su ne bai hadu ba yace min wallahi haushin shi yake ji.
Wai babba dashi yazo zaiwa yarinya wayo itako sai shegen son maza duk ta mutu akan tsoho.
Dariya suka sa nace tunda yana jin haushin shi ba,sai ya kashe shiba in ya isa.
Har lokacin ina jin zafin dankan da yai min don har kaina naji yana sarawa wani iri.
Tafe yake cikin motan shi sai dai a hankali yake tukawa don akwai motoci da yawa saman titin a lokacin.
Wani iri yaji kamar ina cikin motan na,sake wanan razananen kara da na sake lokacin da yaja min kai.
Yace natural hair ne haka gare ta ashe nibna,dauka ko kari take ko yaushe ai.
Wawiya can zata karata dashi gurin dan tsohon ta babu ma gyara kila a karshe.
Yana faka motan daga inda ya tsaya yafito yasa remote ya kulle motar nan ya taka a hankali zuwa gurin da office din Bashar yake don yasan yana nan yaga motar shi a fake can ne sa.
Bashar na zaune yana cika wasu takardu sadauki ya shigo office din .
Bashar ya dago yana cewa kadai samu fitowa ke nan yanzu din na dauka sai ka tsaya ka cinyewa tsohuwa dan tallenta ka fito ai.
Murmushi yayi yana kaiwa zaune yace don wa ake dafa tallen dama ba don mu ba.
Gaskiya ya kamata ace kayi aure haka wallahi man, don Maji ta huta da katon gwauro haka kullun yana lashe mata talle.
Sadauki yai murmushi tare da daukan wani takardan dake gaban shi yace aiko nai aure tallen maji ba zai huta dani ba.
Kana ma min zancen aure ga babban tazurai basuyi ba balle ni.
Da sauri cikin daga kai Bashar yace wa wai Imiranah kake nufi da Ahmad?
Yace su mana kai dan Allah rabu da wanan shashan yayan namu .
Cikin dare fuska sadauki yace ban son iskanci ba yayan nawa ne kuma sha sha.
Ce wallahi shi duk gari yanzu kowa yasan shi sai aukin bin yan yara masu tallah yana latsawa a kasuwa.
Kaifa dan iskane wallahi wanan kuma ai sheri ne nasan dai yana da shegen son mata amma ban san da wanan ba kan.
Yace aiku na gida baku sani kwanaki ma naji ana kudundumin yaiwa wata yarinya mai kai shikafa layin su ciki ko yaya case din ya kare.
Bashar yau dai da sheri ka tare ni ke nan dai don nazo gurin ka dana sani na zauna gida abina ko natafi stadium.
Wallahi ba sheri bane don ina ga Baba ma yasan da wanan case din ai .
Zai iya don kwanaki a gabana wallahi Fatima ta mare shi babu ko kunya wallahi.
Naso na lalatsata ai amma sai naga tana da gaskiya din taba tayi kasan bata da kunya itako ta kwashe shi da mari kayau.
Wata Fatima ke nan kuma?
Ya dan bata fuska yace wanan dayan sister tawa dake gurin maji mana da zama.
Au kace min pretty mana gaskiya mutumina yar8nyar nan ta hadu sosai wallahi ni dai tana min.
Dariya sadauki yayi mai kama da yake yace aiko dan tsohonta zaici ubanka wallahi.
Waye dan tsoho kuma babanta yace wanda zata aura dai wani guy ne mai mata biyu wai itace ta uku .
Zokaga shegiya yadda take rawan kai nace kici uban ki indai kince rawan kaine.
Kai kai amma gaskiya an kwabsa wallahi gurin nan .
Wai ma kai kana may har ka bari haka ya kasance ga ka har kabari akaba wani kuma can.
Wani kallon rainin hankali ya watso mashi gani sai ayi may kuma ?
Yace yar gida gida mai tuwona maina kawai musha buki mukan .
Kasan fa yarinyar wallahi matar manya ce sai ta samu gurima zakaga yadda zata baje sosai wallahi.
Kai don Allah ni bashi yakawoni ba wai how far ne akan kayan can da suka shigo.
Bashar yace baka son zancen ke nan dai mubarta anan kawai ko?
Yace zancen may kuma may zanyi da wanan mai zubin yan arab da ita.
Bashar yai wani dariyan keta yace kaidai sai naba Maji shawara tafara maka hayaki da rukiya wallahi.
Ya jawo wasu takardu daga drawer shi yana mikawa Sadauki yace duba nan ka gani kafin mu koma topic din mu don gaskiya ni iam serious wallahi.
Ko tayi miji ai ana iya tayar da zance don gida bai koshiba ba a kaiwa dawa.
Karanta takardan yake bai bashi amsa ba sai can ya dago kai yace ikon Allah so quick haka sun samu shiga da,wuri.
Yace yanzu haka ma munyi magana da SMG yace min kila zasu sa mukawo masu sabon sanfarin su din suna son su rabawa sarakuna shi.
Amma ko gaskiya in haka ya kasance da muyi sa,a sosai wallahi ko.
Nan dai suka kara dan tattaunawa akan business din su inda suka fito don dama suna da alkawrin zuwa wani guri da Bashar ya damu sadauki su tafi.
A hanya sadauki ya nisa yace amma gaskiya banji dadin labarin da ka bani ba na Imirana .
Yace kai kana ga zancen ne har yanzu yace ai wallahi duk ya zubar da mutuncin shi saikace ba Alhajin ku ya haisu ba.
Shifa Ahmad cewa akayi yana sanan kayan sata sai asato mota ko mashin ya saya .
Innalillahi da karfi sadauki ya furta tare da waigo inda Bashar yake zaune a gefen shi yace wallahi man .
Wai kai kana nufin duk wanan zancen baka san dasu bane ko yaya?
Yace ina zan sani tunda ba shiga gati nake ba yawo iyakata idan ina gari ina gida ko nan gurin ka,sai ko can site din da nake gina na kawai.
Lalai na yarda baka gari gama,wanan sister din naku kwanaki saida yan hizba suka kamasu wai ance sun hada party suna abin banzan ga da mata keyi tsakanin su.
Da karfi ya taka burki yace Nafisa ko?
Yace ita wallahi naji kunyan wanan abin sosai wallahi ance ai shaye shaye takeyi sosai yanzu kowa yasani ma agari.
Subbahanallahi ya,furta yace how comes abubuwa suke zo muna haka agidan mu kaman mu kadaine a gari.
Kadai Allah ya,sauwaka kawai amma ai abin ba dadi wallahi.
Can suk shiga kasan gari gurin ginan shi irin na mutanen dana daganin gurin mutum zai gane cewa tsohon gari ne gurin.
a,kwatancen da Bashar ke mashi suka isa gidan da suke son zuwa,
Daganin gidan basai anfadawa mutum ba gidan wani masani ne na alkur,ani maigirma don ga alluna nan na almajirai daga waje birjit dasu.
Nan suka,tura ai masu iso da,maigidan sai ga,yaron ya,dawo yace ance su shigo daga cikin zauren gidan.
Wani tsohone ya tsufa sosai yana zaune saman shimfida irin ta mutanen da can baya masu fada aji.
Bayan sun gaisa da tsohon ne Bashar ke cewa malam ka gan mu sai yau muka samu zuwa ko yace tau harkokin ku na mutanen yanzu yawa gare shi.
Nan dai suka kara gaisawa Bashar yace malam kaman yadda na,fara maka bayani ne akan al,amarin wanan abokin nawa dai.
Yau gashi nazo dashi malamin yai shiru can ya dan mike zaune tare da kallon su da kyau yace.
Karbi wanan yana mai mika mashi tasbahan hannun shi dayake ja, yace ka zabi guda ko wanine ma daga ciki.
Ya dauki wanda ke kusa da farko sai, tsohon yai dan murmushi yace ai abin yazo da sauki tunda naga baka da zari.
Don da,wanine na tsaka zai dauka yana ganin yafi mai killla yawa.
Ya dinga karatu mus,mus mus dabaki can yace umm,umm Allahu akabar to Allah ya sauwaka.
Su dai suna zaune suna kallon shi can yanisa yace Alhamdullahi Bashar don al,amarin abikin ka ba acewa komai don yanzu ma kuka fara insha Allahu,
Sai dai gaskiya akwai dan matsa dana gani yanzu dai tunda bashi yakawo ku ba harkankuce ta sana,a takawo ku bati muyi abindake nan.
Nan dai yai masu wasu bayanai yakuma basu yan abubuwa tun ana gaban shi yace su sha.
Sadauki da cukin kyankyami yake ya matsu subar gurin don shi bai son irin harkokin nan gaba daya a rayuwan shi.
Bashar ne ma ya matsa mashi kan lalai sai suzo don yanzu duniya ba,a shigan ta haka kai tsaye don A LOKACI MU KE.
Sukai mai godiya tare da mikewa zasu fita bayan sun bashi, dan abincin goro don yace bai karban komai nasu don abokin kakan Bashar din ne sosai.
Sadauki dake gaba ya dafa zauren na kasa zai fita sai tsohon yace ji mana idan kaje gida kacewa mahaifiyar ka kada ta manta da zancen baya da tai alkawari kai ka gurin da aka bukaci ta kai ka a baya.
Don idan bata maida hankali ba hannun agogo kullun zai dinga koma mata bayane.
Da mamaki sadauki ya kalli tsohon sai dan tsohon yai murmushi cikin kada kan shi yace abinda nace zaka fada mata ni dai bata sanni ba ban san ta ba.
Yace cikin mamaki toshike nan malam zan fada mata insha Allahu kaman yadda kace na fada mata yace Allah bada sa,a suka ce amin suka fita daga zauren.
Duk zukatan su fam yake da tunanen zancen tsohon saida suka fara hanyane Sadauki yace kai guy man din nan fa ya bani mamaki.
A ina ya san maji kuma may yake nufi da sakon shine wai?
Bashar yace nima naji mamaki amma sanin halin malam babba yasa ban damuwa nasan wani zance ne can ya hango akan ka kuma.
Baidai son ya fadine kawai kila tunda bashi yai aikin ba.
****** ********* ******
Maji ke da duty a gidan ranan duk da dai su girkin su bawai na duka gida bane gaba daya.
Wace dai take da girki ranan itace zata girka abincin part din ta dana maigidan kawai.
Ba ruwanta da sauran part din gidan kowa shi zai girka nashi da yaran shi.
Komai da ya dace a girka sungama da wuri kamar kulun sai ta wuce sashen maigidan don ta gyara mashi daki kaman yadda sukeyi kullun kafin ya dawo gida daga kasuwa.
Amirah ta tafi kitso a wani shago cikin unguwa maryam kuma ta shiga makwabta don ganin wata kawarta da tayi rashin lafiya.
Tare zamu tafi sai banda lafiya kaina da akaja min yana matukar damuna da ciwo hakan yasa tatafi ita kadai.
Ina kwance saman doguwan kujeran dake falon na rufe fuskana da littafina da na dauko don na karanta amma na kasa karantawa saboda kaina dake damuna da ciwo.
Sadauki ya shigo falon don ya ga mahaifiyar shi akan maganan da malam yai mashi.
Nan ya hangoni a kwance,kyakyawan suran jikina danabi kujera na kwanta rigingine yafito a fili.
Farin kafa na da yake fari sol dashi ya dan baiyyana a fili sunyi fari sol gasu lub lub dasu tankar wace bani taka kasa.
Sadauki yai saurin kawar da kan shi dan ganin irin yanayin da nake a kwance cikin yar doguwar rigata mai dogon hannu da,sharp.
A hankali ya tako zuwa inda nake kwance din ya dan rage tsawon shi ta hanyan dukowa ga kirjina ya dan ban karo gaba.
A hankali yasa hannun shi ya cire min littafin dana kare fuskana dashi,
Da sauri na bude idanuwana da suke min a lumshe don ganin waye ya cire min littafi haka a fuskana don part din shiru yake a lokacin.
Daga cikin tsakiyar kaina da hancina naji kamshin turaren shi amma banzaci cewa shine a gabana ba.
Nai saurin bude idanuwana da suke a lumshe alokacin shi nagani tsaye kerere a kaina .
Haka yasa nai saurin yunkurin tashi zaune a lokacin tare da jifan shi da wani fitinanen kallo na tsana.
Yace ke ina mutanen part din suka shigane wai ?
Wani guntu tsuki naja da ban yi niyar ja ba don cike nake dashi a lokacin saboda ciwon kan daya haddasa min.
Ke ni kika ja,wa tsuki ashe baki da kunya haka ban sani ba?
Nace cikin turo baki da kokarin tashi tsaye ni halan nai maka tsikine ?
Yakai hannun shi ga dan bakina iya karfin ya murde shi da karfin tsiya, ban san lokacin da nasa kuka ba da karfi ina cewa.
Ya sadauki nimay ne maka katsane ni haka kaja min ciwon kai yanzu kuma kazo ka murde min baki.
Na karashe fadi cikin wani irin kuka nace in gidan kune baka son ganina sai in bari nima fa diyace kamar kowa.
Na juya zuwa cikin dakin da kuka na sai muka hafe da Maji dake shigowa falon, hannun ta dauke da kayan su jik dinta, da hapic na wanke bathroom.
Tsaya tayi cikin mamaki takaleshi ta kalleni cin son jin may yafaru bayan futan ta .
Sai kukana take ji a cikin dakin daga inda take tsaye, tana mai wani irin kallon tuhuma.
Tace may kai mata sadauki?
Cikin ko in kula ya nufi saman kujera ya zaune, yace shagwaba take ji kawai dai.
Kai may kaimata nace?
Tambaya kawai nayi ina kuke sai tai min rashin kunya nikuma na murde mata baki.
Kana ko da hankali sadauki?
Shin yarinyar nan tobashiyar kace ko kuwa wai?
To bari kaji wanan kukan da ka sata ko ka bata hakkuri koo na rama mata abinda kai mata.
Wa zan ba hakkuri Maji?
Tace Fatiman.
Yace cikin mikewa kai haba maji don Allah ki bari kada ta kara raina ni mana.
Kai har wani raini kake gudu bayan wanda kajawa kan ka?
Ya mike kawai yabar dakin don shima kukan da yake ji yafara shiga zuciyar shi a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,,
IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA, BA MU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAN MUNA,,,,,
Bayan dawowan su maji daga saudiya da yan kwanaki jin ba wanda ya tayar da zancen abinda akai min agidan,
Maji ta kawar da kaiwaici a idon ta inda ta samu Imirah ya dawo daga kasuwa ke nan zai shigo gida take ce mai,
Imirana ji mana sai ya dan waigo yai tsaye kerere yana kallon ta cikin rashin mutunci.
Yace ina jin ki,
Ganin babu mutunci yanzu a tare dashi yasa maji cewa ,yanzu Imirah baka ji kunyan abinda kayiwa yarinyar nan ba da bamu nan?
Amatsayinka na babba a gida anbar maka amanan yaran nan shi ne kuma kaida kanka kai kokarin keta mata haddinta?
Fuska a daure yace dama don wanan maganan kika tsayar dani ?
Saurayi nake ita kuma nudurwace zan iya shigar da kai na akanta ko hakan kuma illa ne.
Murmushin takaici maji tayi tace amma tir da halinka na dan akuya, halin maha,inta.
Idan zina abin yine jeka ka nemi yar uwar yin zinanka can kuyi tayi amma ba yar mutane da aka bani amana ba.
Murmushi yayi yace Maji kada kiga laifina yar taki ce da shegen kyau wanan aiba komai bane,
Allah ya shirye ka,Allah kuma ya tsare amma ni dai Hauwa,u ina maka kashedi akan diyan mutane a gidan na wallahi muddin ka kara yi mata wani abin tashin hankali again zan ba mutun mamaki don shiru ,shiru ba tsoro bane kuma in mutum bai jiba ya gwada ya gani.
Sai muryan Umma daga bayan su akaji tace tau isassarsa masu gida wallahi duk sherin ki baki na kakan ki ba.
A hir din ki akan diyana ina fada maki Hauwa,u ki sakan min maran diya don bani nasa danki yayi tambada ba abaya.
Haka,kawai don yar kauyen diyarki zaku saka min yaro gaba dasheri don kawai a bata mai suna.
To wallahi ta Allah ba taku ba kuma karya kukeyi nagaba yayi gaba nabaya sai labari.
Kuma kijawa karuwan diyar ki kunne da take kokarin cusa kanta gare shi tayi kwantai a kauye ankawo ta gari ana neman mashinshini a cafke.
Murmushin takaici maji tayi tace kaice yaya a matsayin ki na uwa kuma diya mace kin san zafi da munin irin abinda Imirana ya tashi aikatawa yarinyar nan amma idon ya rufe da kin gaskiya.
Babu komai ai Allah ba azzalumin kowa bane yana sama yana gani duk bayin shi.
Ta juya inda Imiran ya fara tafiya tace wallahi kaji na fada maka duk ka sake kokarin ketawa yarinyar na hadin ta sai kayi mamakina a gidan nan.
Tashige cikin part din mu duk muna jin yadda suka kwashe da Umma da dan ta maji tace kai Allah dai yasa kin kusa aure ma kowa ya huta, ki bar wanan gidan namu mai tarin fitina cikin shi.
Muryan Baba ne daga waje yake fada kamar haka amma dai ke kan anyi uwar banza wallahi.
Yanzu ashe abinda yaron nan yaiwa yarinyar nan ke nan bansani ba shine har kike fada don kunya bai ishi idon ki ba ke,
Ida da yarkice wani katon gardi haka yai niyar illantawa haka zaki fadi an mashi kazafi ne ba gaskiya bane hakan
Dama ai nasan hakace zai kasance muddin kaji ba ka tsaya kai bincike irin yadda ya dace,
Tunda da matar so dinka ake fitina to ku sani ni diyana basu da gadon iskanci masuyi dai kowa yasan su don haka sherin mutum yabishi can cikin kayan shi .
Haka Umma ta tare ta hana Alhaji ya,tsaya yai fada akan wanan zancen don idan ya matsa zagine da tonon asiri zai dawo akan sadauki da,uwar shi .
Wanda yanzu daga uwar har dan tausayi sukw bashi sosai don duk abinda zasu gujewa gudun magana agidan suna kokarin yin shi don kimar su ta riga ta zube ,
Su Umma da mama an samu gurin zagi da gori da habaici koda akan da tsinke ne.
Shiyasa yakan kawo ido yasa,wa Umma inda ita ko tana ganin kamar tafi karfin kowane a gida sai yadda tayi da kowa agidan baki daya.
Hjy kubura ce kawai bata samu ta mallake yadda ranta ke so ba amma ko ita din ba laifi don bata iya kifar mata da,gwaunati a gurin mijin su ba.
Amma wanan munafukan Hauwa,u zamani amarcin ta Alkah daine yanufi takai wanan lokacin a gidan Alhaji don gaba daya hankalin shi ya koma ga majine kamar ita kadaice mace.
A ganin su Umma ke nan a lokaci amma kuma a gurin Alhaji tausayin Maji yake jin don ya dakatar da ita ga karautun ta yadauko ta ya hada cikin matan da ke aikin gwaunati suna da abin kansu.
****** ********* ******
Yanzu abinda ya,rage bukina baifi wata bakwai ba don an dagar da zancen bukin da babana yai ciwo ne shi ya roka abari har guri ya sha iska sai ayi.
Haka kawai kwatsan ranan muna zaune sai ga sadauki ya shigo ya fito daga cikkin garine fun safe safe ya fita sai da yamman nan ya shigo gida.
Suna hira ne da maji yayin da mu muke harkan gaban mu can ya sa murya ya kira sunan Amirah ta amsa da sauri tana fadin na,am yayana.
Yace zaku iya yin aiki hajji bana kuwa don tare nike son in tafi daga club din mu na samu kyautan kujera har har biyar.
Kinga dani dake da maryan nake son mu tafi sai tsagal Maryan tace da Bintu ko?
Tsit falon yayi don sun san maryam tayi tsaga da fadi gaskiya.
Yace wanan bakauyan taje mijin ta ya kaita mana nidai ni dake da Amirah nace kina min gayyan wasu takarce can daban.
Kai ban son rashin kunya Fatima ce takarce kuma yace ba tana da miji ba taje ya kaita.
Ai dai kasan zai iya kaita tunda yana da halin shi shima maji ta fada mai hakana.
Don Allah dai yaya ka hada,harda Bintu mu tafi ita ma ta sauke don Allah tana fadin cikin dan marairaicewa kamar karamar yarinya.
Yace maryam ashe ke karamar yarinyar ce yaya zai kai ta saudiya bayan tana da miji idan yai karana fa na kai mai mata saudiya bada sanin shi ba.
Don haka ki bar wanan zance don Allah nikan da naji ta matsa zance ina duke kaina akan littafi.
Nace Anty maryam bar zancen nan nima ban faye saka kaina inda Allah baikaini ba.
Nafi kowa murna yau dajin yan uwana zasu gabas su sauke farali at early age din su.
Muryan maji ne tace ai yadda Allah ya bashi ikon , biya wa yan uwanki ko ke haka zai bashi ikon ya biya maki atafi dakw kafin kiyi aure.
Maji na fada maki wanan kujeran kayautan su na,samu nima daga wa ni kungiyan mu dake can kasan Dubai.
Jin nan babana ban son tsaya wani kace nace kawai ka bari yaran nan su tafi da yar uwar su .
Kai kanka kasan da cewa, bamu taba tsan manin irin haka ba a rayuwan mu.
Shiru yayi har maji ta gama fadan ta baice uffan ba nidai takaicin irin wanan halin da yakw min sun kai min ko ina amma indai har nai aure na bar gidan su na huta da komai ma.
Can ya dan furzo iska yace yauwa Maji na dade ina son in tambaye ki naji sai abubuwa sukai min yawa ban samu lokacin tsayawa tambaya ba.
Fadi ina jikin muma dai shiru mukayi muna saurarwn shi sai da dan garani ina kokarin yin abindake a gabana ne alokacin.
Yace Maji wai akwai wa ni tsoho da naje gurin shi kwanaki bashar ne yakaini gurin mutumin
To da zan dawo sai yake cewa idan nazo gida na fadawa mahaifiya na kada ta manta da alkawarin da tayi na cewa zata kaini da kanta gurin da aka bukaci ta kaini.
Ni din nan inji maji ta fadi cikin dan murmushi da mamaki a fuskan ta a lokaci guda.
Tace kai mutane akwai yaudara wallahi ko sai mutum yai karya ne zai samu abu daga gurin mutane ?
Shiru nayi idona akan littafi amma kuma zuciya ta tana nazarin wani zance can a baya tun farko.
Amma maji wanan mutumin wallahi tsoho ne sosai kuma ban tsan mani yaudara bane yadda yai min maganan
Don zanfita cikin murmushi yace nacewa mahaifiya na tayi niya ta tafi inda tai alkawarin zata kaini da kanta in ba haka ba gaskiya akwai matsala,babba nan gaba.
Don tana tunka ana walwale mata ne za,a mayar da hannun agogo baya sosai .
Mai makon naji maji ta tuna alkawarin da tayi a baya sai naji sun buge da zagen tsohon mutane kawai.
Suna kiran macuci ne ma yaudari don taci kudinw yake fadin haka Allah yasa dai ni ba mai zuwa gurin malamai bane da yan tsubbu neman taimakon su na dogara ga Allah.
Amirah tace ba dai maman ba kan yaje can ya yaudari wasu gaba amma ba nan ba kan.
Batare da na kalle su ba don shima mai maganan kanshi na duke ne kawai alaman surutun su yai mashi yawa.
Sai muryana kowa yaji a falon ban juyo ba ban dago kai ba nace mama kece ba karya mutumini keyi ba.
Da sauri sadauki ya dago kai yana kallona itama uwar hakane ixo ta tsura min don ban taba mata haka,ba duk zamana da ita.
Tace Fatima kikace nine nace zan kai sadauki wani guri ban kai shi ba nace eh mama ,
Kai Bintu yau kuma maji zaki kullawa sheri haka maryam ke nan ke fadin haka cikin dariya.
Na girgiza kai na nace bazan taba yiwa mama sheri ko wani nataba har abada.
Dan tabe baki yayi daga inda yake zaune yana wani game da,wayan shi na,wasan driving.
Don yakan dan taba wasan mota a America tare da,samari yan uwan shi don nishadi kawai haka har kudi suke sakawa ko kyautan wani abu ga wanda yaci.
Mama tace dada,Fatima kikace nine nai alkawari na kara cewa eh mama sai dai bazan tuna maki ba sai wani lokaci in kuma kin tuna shike nan.
Amira tace a to dama dai ba,a shiga tsakanin Bintu da maji don sun fi kusa, kila tare da ita akai zancen.
Nace ai harda ke anty don gaba dayan mu musan da zancen sai dai mantuwa kawai .
Dan dariya yayi yace wanna yarinyar Allah munafukace Maji baki dai son ana fadi ne kawai amma ji daurewa wai kowan ku yana gurin.
Dakata Babana tunda Fatima ta kuke da haka akwai magana ke nan ya mike tsaye yana fadin ni kan na fita don bsn iya sauraren shirmayn yarinyar nan gaskiya.
Yana ba da baya na,shake murya nace mama kin manta maigani yace kikai mashi sadauki inda gwago mai masa ta tafi.
A,a,a anyi haka Fatima shiku jin ina kus,kus da maji yasa shi juyowa ta ce tabbas anyi haka Amirama,tace wallahi na manta muna zaune kuwa aikai maganan.
Cikin wani fargaba Maji tace babana dawo ka,zauna don Allah da mamaki yake kallon mahaifiyar nashi don bai san may shu,umar yarinyar na tafada mata ba a lokaci guda yaga ta birkice.
Tace don girman Allah ka fada min yadda aka fada maka ka fada min a take ya kara nanata mata, sakon da tsohon ya fada mai.
Tace inko ba wani ikon Allah ba yaya akayi wani yasan wanan zancen don dai ba,a nan akayi shi ba.
Mamakin yadda maji ta rude a lokaci guda haka ya bashi mamaki matuka yace Maji injin dai lafiya ko yace cikin kallon fuskan ta ido cikin ido.
Take ya fahinci da akwai matsala ke nan yace please Maji may ke faruwa ne wai?
Ko zancen mutumin gaskiyane dai yake fada don ni ban dauki zancen da wani muhinmanci ba kada haka ya tayar maki da hankali.
Maji a sanyaye ta,ke ce mai gaskiya Babana akwai matsala saboda akwai wani mutum da haduwa kawai nayi dashi ranan ina asibiti ya shigo gaida mu yake cewa kana da matsala don Allah nayi kokari nazo dakai gurinshi ya ganka.
Nai alkawarin zan kaika amma kuma kaga na manta shaf wallahi inba yanzu da Fatima ta tuna min ba.
Ban san lokacin da na sauke ajiyan zuciya ba jin yadda Maji ta canza maganan a lokaci guda.
Don dama ina gudun ace daga gwagona zancen yafito yace zata koya wa uwarsu bin bokaye nima yana iya sakani gaba da zagi don nasan halin shi.
Yace amma Maji kin dauki zancen serious ke nan ko?.
Tace idan ba serious matter bane yaya za,ayi zancen ya fito daga gurin wanan tsohon.
Kaga ke nan maganan mutumin gaskiyane tunda ga zancen yafito a gurin ka.
Jikin maji yai sanyi sosai a lokacin don sai ta shiga tunane watau ke nan masu sherin basu daina ba ake nufi ke nan.
Tai mamaki da taji yace yanzun za,a tafi gurin mutumin ke nan tace ya kamata gaskiya .
Zan samu lokaci sai mu tafi kafin na koma ke nan don na kusa tafiya ba kuma zan dawo ba sai nazo daukan yaran nan mutafi don ta inter national zamuyi tafiyan.
Maji tace amma na fada maka da diyata za,a atafi baice komai ba har ya mike zuwa kofa sai lokacin ya ke cewa Maji sai ki shirya mu tafi dake kenan don bazan kwashi wa yan nan ba duka su zama min wahala a can.
Don nima ina son nayi inganttacen ibada banda lokacin taulali dasu gaskiya don kin san yar ki bakauya ce matar bakauye kuma.
Yana fadin haka Fita yayi daga dakin nima sai yau banji haushin shi ba don ya gama min komai a duniya.
Mutumin da adalilin shi zai shiga kasa mai tsarki ai yagama min komai wallahi ko a duniya dole nayi hakkuri dashi don iyanzu na fahinci halin shine haka gwatsale mutum a take don bai son raini.
Nikuma yar kauye ce baruwan mu da banbants babba da karami gurin fadin magana.
****** ********* ******
Maji ta tsara Baba hat ya yarda cewa zadu duba jikin Baba na ne akauye don haka muka fara shirin zuwa gurin da akai magana.
Don ta kira gwago ga waya sunyi magana akan tafiyan mu kuma gwago taiwa dan uwan nata magana yasan da zuwan mu gurin shi.
Sadauki ne dai bai san cewa da mu za ai tafiyan ba sai lokacin da za,a tafi yaga duk mun shirya tafiya yake cewa
Wa yan nan fa kuma Maji ?
Tace dasu zamu tafi don suma ina son na kaisu gurin mutumin ya gan su.
Kaman zai yi magana sai kuma yai shiru yana tsaye tsakar falon ya harde hannayen shi guri guda.
Can yace sai dai da Bashar zamu tafi ban tsan mani motar zata dauke mu ba fa.
Tace ai zamu iya matsawa mu hudu a bayan dukkan yace da yake ita wanan yar fillon ba jiki gareta ba ko?
Yadda maji tace hakane mu hudu muka matse a bayan motan muka kama hanys sai garin.
Tun shigan mu mota banyi magana ba don idan na shiga mota amai nakeyi ko yanzu shi ke damuna.
A hankali na bude ledan da na riko na shige cikin hijjab dina naita kwarara amai tun ina yi a boye har Maji ta gane da sauri tace subbahanallahi.
Fatima amai kikeyine ?
Da sauri ya juyo yana fafin oh shit,
Don Allah Bashar parke motan da sauri kada ta damay mu da wari a mota.
Fada yake yana fadin kin san baki da lafiya don gulma shine sai kin biyo mutane kuma?
Yaja tsaki aka fito da sauri na samu guri nai ta shara amai mama tana a kaina sai sannu take min.
Da ya tsaya min muka shiga mukaci gaba da tafiya, an fara tafiya cikin jan tsuki yace i hate naga ana amai wallahi.
Bashar tace kasan wasu mutane idan sun shiga mota sai su dinga amai don warin petror.
Da kyat naga,mun kawo garin kaina yana,duke sai ciwon kai dake damuna a lokacin sosai.
Gida ne irin ginan kauye na haki da itattuwan dake basu innuwa manya manya a kofan gidan.
Suka tambaya kamar yadda aka fada masu wani yaro ya shiga yai masu iso akace a shigo daga zauren.
Maji ce tafara shiga taiwa mutumin bayanin komai yace to a shigo babu komai dama irin matsalan nan sai anyi wa mashi dabara.
Dattijone fari dogo dashi baida jiki sosai sai dai yana da fatin gemu mu bamu shiga ba muna zaune a bayan mota.
Sai Bashar dake tagaba sosai bai shiga ba har sun shiga sadauki ya fito yai mashi hannu daya biyo su mana.
Sun zauna aka gaisa yake tambayan shi yaya jama,a ya aiki ya amsa tare da bin zauren da kallon irin littafan dake tare a cikin zauren da ido.
Malam ga yaron kamar yadda kai umurnin nakawo maka shi yace nagan shi hjy.
Hannu ya mikawa sadauki inda shima ya mika mai azaton shi gaisawa zasuyi sai yaji ya rike hannun nashi idanuwan shi ya lunshe yana fadin ikon Allah.
Can yace umm,umm Allah mai iko, aida sun barka da sun sha alheri fiye da tsanmanin su.
Sai ya sake hannun sadaukin yana girgiza kai yace mutane basu da imani yanzu duniya tai nisa wallahi.
Agida akwai matsala sosai hjy hakama a,waje akwaishi.
Sai dai ita matsalar ta waje ba wani matsala bane akan harkan samun shi ne.
Nan ya dago kai yacewa sadauki ka na iya gane wani bakin mutum daga cikin ku mai dan saje a fuska sai dai ma naga kaman ba musulmi bane.
Yace akwai ranan da yaba wani abu a cikin leda fari kai kadai baiba kowa ba.
Sai dai anyi sa,a kana zuwa gida ka manta bakaci ba sai bayan kwana biyu kaga ledan ka bude amma sai kaga abin ya zama baki.
Shiru yayi yana son ya tuno wanan ranan sai zuwa can yanisa yace anyi haka malam,
Amma Daniel ne abokin wasa na ne saida iyamurine shi ba musulmi bane.
Yace nagani ai .
Yace Allah ya kareka da kaci yadda wanan anin ya koma baki da haka jikin ka zai koma ayi maganin duniyan nan sai dai Allah gaskiya.
Yace amma idan baka yarda ba abinda zan baka yanzu idan ka gwada zakaga insha Allahu ba yin mu ba da yardan ubangiji bazai yarda ko hannu ya kara hadawa dakai ba.
Burin shi shine saboda kaine bai daga ba kakai mashi ko ina don yana ganin kaine ka,tare mashi wuri.
Ikon Allah inji maji tace ko ina da matsalan dai, malam yace yanzu muna A LOKACIN NE,
Ai yanzu duniya ba,ai mata hawan kawara sai dashiri ake shigan ta don mutum yana barci ana mashi nasari ne.
Bashar yace kaji abinda nake fada maka kullun amma kai baka ganewa ne shiyasa.
Shi dai nisawa kawai yayi.
Hankalin shi na gurin tunanen Daneal kawai yasan bai kaunan shi tun farkon haduwan su suka fara samun matsala amma daga baya sai ya daina tsanar shi.
Yace hjy sai zancen gidan ku gaskiya bazan boye maki ba akwai matsala sosai a gidan.
Nan ya fara basu bayani tiryan tiryan amma bai fada masu sunayen masu wanan aikin ba kamar yadda yaiwa gwago bayani a baya dama kuma,shirin da suke a yanzu.
Har kan yaranta mata da aka,asirce mata su akan suyi ta zama ko kare bai kaunan su balle mutum.
Nan kan ran sadauki yai matukar baci cikin bacin rai yake fafin wai Maji may mukaiwa wa yan nan mutane ne haka a duniya.
Kagin tai magana malamin yace hassadane kawai don sun san kokai waye shiya kawo haka kawai..
Maji tace yaran suna nan nazo dasu ai yace na sani don nagan su su uku ko?
Sai dai dayar bataki bace Allah daine yakawo maki ita cikin hikima irin na ubangi wanda duk abinda kaga ya tsara ba,a banza yake tsara shi ba.
Zaman ta gareki alheri ne sosai koda yake bama sai na fada maki ba ai kema kin sani.
Sai dai zatai aure amma dai auren yanzu gaskiya sai Allah don banga yuyuwan shi a halin yanzu.
Malam daga gurin mijin ne ko kuwa yace Allahu,a,a lamu sai gaibu sai lillahi gaskiya.
Cikin ran sadauki yace aidama nasan wanan mutumin yaudaran tane zaiyi sai yaji malamin na fadin amma akwai abinda zanba kowan su insha Allahu komai zai walwale da yardan Allah.
Sauran ma insha Allahu mazajen su zasu fito bada dadewa ba ai.
Nan dai yaba yaya sadauki abubuwan da,suka dace tare da kara jaddada mai yadda zaiyi amfani dasu.
Sai yace ace mu shigo idan mun fito sadauki ya shigo shi kadai sai uwarshi akwai maganan da zai yi dasu wanda siri ne.
Nan dai yai muna duk abindaya dace da kowan mu muka fito da yan ledojin kulin maganin daya bamu daga zauren.
Ni a lokaci duk a galabace ma nake don ni ban san wai ina da matsala ba,su dai ne na dauka masu matsala kawai.
Muna fita sukai magana ta siri sosai da mana ta fada mashi damuwan ta yai kuma alkawarin taimaka mata.
Sadauki ya shigo ya zauna mutumin ya kalle shi yace kai babban mutum ne watarana zaka tuna da magana na matsalan ka dayane shine wanan shaye shayen da kakeyi.
Duk da naga abinda sauki yanzu sosai akan ka don abin yarage maka fiye da baya can.
Yace sai kuma ka kara da hakkuri don ko yaushe biyayya na iyayye yana kai mutum ga alheri.
Yai mashi nasiha sosai akan duniya tare da kara mai wasu yan abubuwa irin nasu.
Inda yace ya tabbatar kagin ya tafi gurin neman shi yayi abinda ya bashi din.
Kudi masu yawa ya ba mutumin sai yai dariya yace ba haka nake ba ni dari biyar kawai zaku bani ko shi kada kuce naki karba ne da ban karba ba wallahi.
Sunyi mamaki sosai muka kama hanya sai sokoto koda zamu dawo naita kakarin amai saidai da yake cikina ba komai sai kumfa kawai nake zubowa.
Bashar dasu mama suna ta faman yi min sannu amma,shi ko kallo ban ishe shi ba.
Da la,asar muka iso gida tun lokacin kowa ya fara abinda aka bashi yayi daga gurin bawan Allah.
Don har bashar saida ya anso nashi shima don mutimin shi da kan shi ya bashi taimakon.
Tun dawiwan mu nikan ina dunkule saman dogon kujera harda barcin wahala saida nayi.
Anty maryam ce ta dafo min liptop da lemun tsami na dan sha shine na dan ji dama sosai.
Ya shigo falon yayi wanka ya,sauya kayan jikin shi a lokacin yasa wando da rigan na maza mai dogon hannu.
Gani a kwance na dunkule yasa ya dan tsura min ido sai yaji na bashi tausayi sosai.
Yace ke may ke damun kine yanzu kuma?
A sanyaye nace cikin bata fuska kaina ke min ciwo.
Bari in nafita sai a sayo maki magani kisha.
Nace nagode.
Wanan gidiyan da nakan yi mai idan yai min alheri yakan ji matukar dadi a,ran shi don shi mutum ne mai son yaji ana godiya gare shi.
Sosai ya mayar da hankali shi ga maganin shi da mutumin ya bashi don yai matukar yarda da zancen mutumin ba din komai ba,rashin amsan kudin su da mutumin baiyi ba.
Ya dawo ya,sayo min magani harda na amai da kuma drinks mai sanyi na kwali.
Ina kwance na na dunkule a saman kujera su na kallo ni kuma gani kwance a dunkule sai dai ba barci nakeyi ba idona biyu.
Muryan shi naji yana tambayan su ita wanan barcin takeyi har yanzun ne ko jikin ne ke damun ta?
Maryam tace tace kanta kawai ke ciwo yanzu yace ke tashi ga magani ki sha ko zai lafa maki.
A hankali na mike zaune daga kwancen da nake sai dai still ina dunkule ga hijjab ga kuna blanket dana yafa ajikina.
Na karba tare da bare maganin na kai abakina saida na dago kai naga ya tsura min ido ashe ni yake kallo daga inda yake zaune.
Da sauri na dukar da kaina kasa bban tsaya shan drinks din ba yake cewa bazaki sha juice din ba ne?
Nace a,a ban iya sha yanzu sai nakai kwance daga inda na tashi yamike zai bar falon yana cewa idan bai bari ba sai akaiki asibiti ke nan.
Ya fice daga dakin na lumshe idanuwana tare da komawa barci a lokaci guda.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
IDAN KIN TURA WANDA BAI BIYA,BA BA MU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAN MUNA AKAN KI,,,,,,,
Sadauki bai koma ba sai dai yayi duk yadda malamin nan ya umurce shi da yi a baya.
Ya kama hanya yatafi an muna E,passport na batayi tare da duk wani clearing din da ya dace aiwa masu tafiya.
Na kira kabir nai mashi albishir kamar yadda ya dace nan fada mai don ya,sani .
Sai na fahinci bai yi farin ciki ba da hakan take naji raina ya naci nace, amma ka bani mamaki yayana da zakaji alheri haka ya samay ni ka kasa tayani farin ciki.
Yace umma gaskiya Fatima ban iya munafunci ba don haka idan nace maki nayi farin ciki to na munafunce ki giskiya.
Cikin mamaki nace Yaya Kabir lafiya kake kuwa ?
Yace lafiya ta kalau Fatima ,
Wanda dai ya kaiki saudiyane ban yi naam dashi ba gaskiya.
Kana nufin wai yaya sadauki ke nan?.
Yace shi nake nufi Fatima ya,fadi a takaice kawai ba shakkan komai
Yace ina matukar kishin zaman ki da yaron nan gida guda Fatima, a duk lokacin da na tuna cewa a guri daya kuke sai naji banjin dadi wallahi.
Don ni mutum ne mai matukar kishin iyalin shi sosai ina kokarin ganin matata bata mu,amula da wasu maza koda yan uwanta ne ko nawa.
Nace amma dai kasan ni ba,watsa,tsa bace haka shima wanda kace baka kauna din ba dan iska bane hakana.
No Fatima baki fahinci magana ta bane don haka mubar zancen haka nan Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya ba shike nan ba.
Nai fushi na kashe wayan ba yadda na,saba yi mashi shagwaba ba idan zan kashe wayan.
Ni kadai maganan tai ta cina a,rai har na gaji na sake don kaina.
Nai fushi da yaya Kabir da kyat ya shawo kaina muka shirya dashi yana ta kamay kamay, wai shi ba wani abu yake nufi ba,
Hakalin shi, bai kwanta bane don kada yaya sadauki ya kwace mashi ni yahana ya aure ni ace yar gida gida za,ayi.
Jin maganan nayi cikin haushi da takaici, don may zai hada ni da yaya sadauki mutumin da yake a matsayin yayana yake a gareni.
Nan na nuna mashi ban ji dadin yadda yake min ba a matsayin yaya fa,sadauki yake gareni.
Amma shine zai ce, wai sadauki na iya kwaceni daga gareshi, ya aureni wanan maganan tai min zafi yadai bani hakkuri aka zauna lafiya.
Munsha magana gurin mutanen gidan mu da,ma,wasu yan sa ido akan zancen tafiyan mu,
****** ********* ******
Mun isa kasa mai tsarki, saukan asuba mukayi a garin kafin agama muna screening har anyi kiran sallah asuba ko.
Wasu motoci muka samu suna jiran mu su suka kwashe mu sai masaukin mu a cikin garin madina.
Bamu dauki tsawon lokaci ba muka fita zuwa masallaci don muyi sallah da ziyara kamar yadda yazo ga sunah.
Ibada muke sosai ba kama hannun yaro daga mu har uwar mu da yayan mu sai yaya,Bashar da muka zo dashi.
Aiki tukuru komai bamu da matsalan shi sai mura da ya kama mu kawai a garin don sanyin Ac da ruwan sanyi da yai muna yawa.
Yaya ke sayo muna duk wani abinda zamu bukata sai ya tambaye mu ko may zamuci daga haka har ya gane favorite abincin da kowan mu ke so.
Kwanan mu tara a na goma muka kama hanya sai garin makka nan ma mun samu anyi muna masauki inda zamu sauka .
Bamu kwana ba sai da muka je mukai dawafi a can muka kwana sai safe muka dawo masaukin mu.
Barcin gajiya mukayi bayan munyi wanka muka kwanta, mun tashi mun samu har mama ta farka tana zaune tana waya a gida.
Zaune muke a falon dagani sai ita su Amirah ana can an baje ana barci a cikin A,C.
Bashar da yaya sadaukine suka shigo dauke da abincin rana da zamuci.
Ganin da sukai min zaune a kasa gap da kafan mama nake zaune kamar wace zata koma ciki .
Fatima ke har k8n farka ke nab baki gajiya dai, mama ta karbe da cewa ai kai dai Bashar wanan yarinyar har mamaki takw bani karama da ita amma yawan ibadan ta kamar wata babban mace can wallahi.
Daga inda yake zama idon shi ya na a kaina yake cewa, addu,a takeyi wa mijinta kila ko kuma maman ta.
Ai na gode da Allah ya ban diya irin Fatima mai ibada ga sanin ya kama ta a tare da ita ko yaushe.
Kai maji kina da fasawa wanan yar kauyen yar taki kai koda yake yanzu naga,ta fara wayewa,ai don ina Allah Allah kada,tai muna,kauyancin ta, ta,bayar damu a cikin mutane muji kunya.
Nace cikin dan jin nauyi da kunya kai haba yaya wai kai kullun dai a bakauya nake a idon ka ne?
Kyaleshi Fatima ba abinda zai gwada maki yanzu na wayewa jirgine dai kin haushi don kin gama sanin komai.
Kai mama don Allah bari kada ta dauka ko jirgi shine karshen kauyanci a duniya.
Kada fa ka,zabo matar da tafi Fatima zama yar kauye muga tsiya wallahi don dai yanzu kasan Fatima ko kai sai kayi da gaske zaka gwada mata wayewa.
Aiko cikin auri yace don Allah MAN ka bari ka fa san a kasa mai tsarki muke kada yan amin su karba muna.
Nan suka dinga mashi sheri suna ta dariya yace aiko da na karkarya yar kauyen banza da duka.
Dariya nima na kama nac
e ni yanzu yaya idan ,al,amarinka ne bana jin haushi balle nayi kuka akan zancen ka.
Da can bayane da ban san halinka ba nake kuka yanzu ko kin waye ko?
Ya tambaya cikin son jin amsata daga bakina amma sai nai shiru don maji tace na kyale shi duk abinda zai fadi na dai fishi ne yasa yake jin haushi na kawai.
Bai da rowa ko kadan sai da,wanan tafiyan ya hada mu na tabbatar da hakan don duk abin da kannen shi sukace suna so shi zai masu ko nawane.
Munyi ibada munyi rokon Allah sosai ba dare ba rana muka kammala aikin mu muka fara shirin dawowa gida.
Naiwa iyayyena da yan uwana tsaraba haka naiwa Kabir shima nashi kalar tsaraban da ya dace da shi.
Munyi mamakin dawowan mu, gida muka samu an gyara ma mama part din ta gyara sosai na gaske akai mata na zamani mai kyau,.
Tafita daban daga sauran part din matan gidan an sauya mata komai nata ya koma side din ta daban yake a cikin sauran sai dai still a gida guda ake kuma farfajiya guda.
Mun shiga gida mun zama wasu abin sha,awa gurin mutanen gida sai sabon hassada ya kunno kai kuma.
Kishi kumallon mata nan zance yafara yaduwa cewa ba kudin halas bane shine muke tin kahon mun tafi saudiya wa mutane.
Wasu su, ce ai shi kan shi sadauki baya taimakon kowa,sai uwarshi da yan uwan shi ya sani kawai.
Sun manta duk irin taimakon da yake masu a cikin gida yanzu komai shine yake kawowa ayi amfani dashi a gidan don yanzu Baba yai sanyi sosai ga arzikin shi.
Ya rage saura wata biyu kacal buki na da Kabir, don haka bayan mun dawo su Baba sun shigo taron mu shida mama tabawa da wata kawar ta da tazo gulmq taga inda nake.
Nan Baba Alhaji yake bawa babana shawara kan kada ya tayar da hankalin shi akan zancen aurena.
Duk wani abinda za,ayi agurin bukin shi zai dauki nauyin yi da shi da matar shi Maji.
Baba na yace amma Alhaji auren ta na farko ke nan ya kamata ace a dan bari nima na taima a wani gurin inda ya dace dani na kauye.
Babu komai ai duk yiwa kaine don Fatima ta cancanci ai mata komai a rayuwa ai.
Sun dan yini muna sukai sallama na basu tsaraban su suka kama hanya sai gida suka koma, inda nace masu zan shigo karshen wata don nazo naga mahaifiyata .
A bangaren Kabir kuwa ji yake tankar ya lashe ni don irin so da kaunan da yake nuna min abi yai yawa sosai.
Duk da lokacin ya matso sosai amma shi gurin shi shine yadai ga an daura muna aure ace ni mallakinsa ce.
Sai kuma gashi ya dan bijiro da wani zance, wai yana son a dan kara matso da bukin don yana son zuwa wani course a lagos na wata daya.
Da zancen yazo wa Maji sai cewa tayi ace yayi hakkuri tunda an fadawa kowa sai wanan lokacin za,ayi bukin.
Da kyay dai na samu na shawo kan shi ya hakkura sai lokacin za,a daura aure daga baya sai na tare idan ya dawo.
Maryam itace ke shirya komai a kan sha anin bukin sai dariya mama da Amira suke muna.
Shiko yaya,sadauki yabi ya koma wani silent dashi koda yaushe fuskan shi a daure take bai wani walwala,
Shi kan shi din ma ba zai iya cewa ga matsalan shi kawai dai haka yake jin jikin shi ba dadi.
Haka ya daure yana yan al,amururinshi cikin rashin kuzari da walwala a tare dashi.
Kumshi da kitso da gyaran jiki duk su akai min zan fara zuwa na hadu da Kabir da,zai shigo inga mahaifiyana sai na,dawo sokoto sai gobe daurin auren mu zai dawo garin don suna,aiyuka yanzu sosai.
A gidan mahaifiya na ya iso da yamma na fito na sanay shi yana tsaye jikin motar shi nafito daga cikin gidan namu.
Murmushi a fuskan shi har na karaso gare shi yake cewa kai Fatima kinga yadda kika koma kuwa tun auren bai karaso ba kin koma haka?
May mamatake baki haka ne wai ?
Murmushi nayi kawai ,
Yace ban yarda ba don dai kawai baki son nima abani na koma hakane kamar yadda kika koma din.
Yace ya naga fusksn ki yau duk kwalliyan da kikayi amma babu walwala sosai.
Nace cikun dan yake wallahi kaina ne ke min ciwo sai faduwan gaba dake yawan damuna duk kwanakin nan.
Ya kara dan matsowa gap dani yace shine baki fada min ba ?
Kuma tun yaushe kike jin hakanne wai?
Na lumshe idanuwana nace tun kan nazo ne nake fama da hakan.
Yace da kinga likita tun acan Fatima, don asan abinda ke damun ki don kin ga nan kauye ne.
Wani irin kamshin turaren shi ne ya daki hanci na,wanda har na dan sauke ajiyan zuciyar da ya baiyyana a fili, saboda matsowan da yayi gap dani a lokacin.
Yace ko mu tafi ne ki ga likita sai mu dawo ?
Na bude fararen idanuwana ce na samu sauki ai ba matsala.
Yace da gaske kinji sauki kodai baki son zuwa ne likita ya duba min ke ?
Na girgiza masa kai nace ba hakana bane kawai dai ba,wai sai naga likita bane.
Yace toh bari na bude maki mota ki zauna a ciki don kada tsayin ya damay ki ko?
Ya bude motan na shiga dayan bangaren na zauna, sai ya rufo min kofan,
Shima yya zagaya ya shiga ya zauna daga dayan bangaren .
Wani irin sanyi ne da kamshin motan ya ziyarce hanci na dana zauna a motan
Take naji wani irin kasala ya dan fara rufeni a hankali, nan muka danyi hiran mu dashi a,tsatsaye don na matsu na koma gida na kwanta.
Waya ce aka bugo mai a yadda na fahinta daga ma,aikatan su ne suke magana dashi kan ana neman shi a gurin aiki.
Bayan ya gama wayan ya kashe ya ja tsuki yake cewa kai baz,a bar mutum ya huta ba da amaryan shi.
Yanzun kuma wai aiki zamu tafi a wani kasan shine ake neman mu.
Murmushi nayi nace ai neman halak ne don haka muna son aiki ko yaushe tafi zaman jiran tsanmani.
Yani sa yace wallahi haka kawai sai nake ji kamar nace na fasa don ban son rabuwa dake ko kadan Fatima.
Nace cijin yar murya har kwana nawa ya rage ka mallake ni a gidan ka idan kayi hakkuri.
Ya shafo fuskan shi yana cewa hakane kuma fa gaskiya dai sai naga ni lokacin ma yai min tsawo sosai.
Abinda bsi taba min ba shine yau yai min don kamo hannu na yayi ya hada da nashi ya matse guri guda ba,tare da ysi min magana ba na,wani dan lokaci mai tsawo.
Cikin yar siririyar murya nace mai sakeni yaya don har yanzu fa ka san,akwai sauran lokacin hakan gare mu.
Yace cikin murya mai kasala hakane Fatima yanzun dai ina son idan kin koma saiki fadawa maryam duk wani abinda ya dace ku shirya shi da,wuri don da an daura aure abuja zamu wuce acan zaki sha amarcinki.
Kunya maganan shi ta bani da sauri na bude kofan motan kafana daya a waje nace maganan ka tana sani jin nauyi da kunya wallahi.
Yace nima haka ya dan kwaikwaye ni.
Mukai sallama dashi tinda safe ya kama hanya sai Abuja don aikin su ba hutu.
Sai da na kara kwana biyu a gurin mamana nazo gurin Baba na nai kwana daya na dawo sokoto da zama.
****** ********* ******
Mamana ta sokoto cikin gyarana take sosai abubuwa take bani na kara lafiya da gyaran jikin na.
Nai kyau nasha gyara sosai na canza gaba daya duk wanda ya ganni sai yai maganan hakan.
Amma har lokacin banjin dadi a cikin raina nasan cewa jimamayn rabuwa da su mamane yake damuna a zuciyana.
Don in suna min sheri sai naji kamar nai kuka ban son zolayan da,suke min na amarya ta angi yar shagali yar biyan bukata yar garali.
Amirah tace makullin mota ke akaba, wani sauran canji ke akaba, nikanji wani iri a raina sosai.
Ko yaushe Kabir muna waya dashi yake ce min zasu tafi kasan Benin wani taro na kasa da kasa.
Cikin dare yaya,sadauki ya dira a sokoto sai ganin shi mukayi kwatsam.
Murnan ganin shi kamar kullun yan uwan shi da mahaifiyan shi sukayi nima dai nai farin ciki da ganin shi don ban boye ba sai dana baiyyana a fili.
Ranan har ina mashi tayin abinci sai lokaci ya,dago yana kallona gaba daya sadauki yaga na sake mai .
Da sauri ya kawar da idanuwan shi daga kallona na kara tambaysn shi da cewa.
Yaya a kawo maka abinci ne kaci?
Yace au yau kuma duk murnan za,a gidan tsoho ne yasaka ake min tayin abinci haka?
Kasan fa amarya ce dole abita sannu yaya duk cikin murna ne hakan ai.
Na bata fuska na dan marairaice nace haba Anty Amirah sai ana maganan gaskiya kuma ki jefo wani zance can na fadi cikin shagwaba.
Yaushe rabo da kiba yayan mu abinci Bintu ?
Nace kai anty Amirah nifa yayanane yadda kike son shi haka nake son shi don haka kada ki bata ni gurin yayan mu ko yayana ?
See her bakiji kunya ba ni wai maji yar taki duk murnan auren ne yau take cewa nima yayan ta ne?
Yaya ni kima yar kaunar taka har zakai shakkan haka a gareni nifa yanzu banda kaman ka a duniya don ku ne uwata da ubana.
Murmushi yayi ciki ciki, yace to kawo min abincin na wuce ina yar dariyan jin dadin mun shirya da yayan mu yau.
Nakawo mai abinci na aje nace ko na karo ne yaya ?
Yace kai Maji wanan yarinyar taki fa ta rainani da yawa may kika mayar danine wai ?
Yaya nace a taikace.
Na dora da fadin wanda yafi min komai a duniya .
Yace har da dan tsohon mijin ki ke nan?
Nace ai shi mijine kai ko dan uwa rabin jiki.
Sosai yaji dadin zance na har cikin ranshi yake cewa a rayuwan shi ashe haka yarinyan nan take sauki kai ne da ita haka, ninr dai ban fahince ta ba ashe?
Waya da Kabir ya bugo min ne ya dakatar dani nabar gurin zan wuce niji yana fadin tsoho yai kira ke nan ?
Na dauki lokaci muna waya dashi sannan na fito falon na samu yana cin abinci suna fira da mahaifiyar shi.
Yana fada mata cewa maji mutumin nan fa abin tsoro ne wallahi sosai don yanzu.
Daniel bai yarda ko mu hada hanya dashi duk yadda muke da yawa a guri zakiga ya koma gefe daya.
Nace mugu ke nan dan ban Allah yafishi wallahi don ba abinda zasu iya dakai don kai daga Allah kake.
Dariya sukayi nace wallahi anty na rasa may yasa mutane suke yawan saka ma yaya wanan irin kiyayyan haka.
Maji tace hassadane kawai Fatima kin san in Allah ya haska mutum dole dama sai ya samu wanan kalubalin daga mahassada.
Mukan Allah ya kara tsare muna kai a duk inda kake yaya sai kuma addu,a don Allah akara zagewa don makamin mumunine.
Yau kan ni naga yar taki ta canza fa.
Dama haka take kaine dai baka gane ba kana ganin tana maka kokari kaiko kana ganin kamar sa idone.
Ya ce na sani maji.
Ta faye kauyancine shiyasa nake sake mata layi.
Bintu Kabir har yanzu bai dawo bane daga Benin din ?
Nace yace ysu da dare zasu sauka a lagos sai gobe zai karaso abuja zuwa jibi ya iso nan.
Ku dinga sa insha Allahu mana a zancen ku Fatima inji maji.
Nace insha Allahu mama,,
Kokefa to kuna magana kamar ba musulmai ba.
Ita fa maryam ta matsu Kabir yazo ta amshi dumus don zancen ta na kudine kawai.
Ya mike yana cewa zai shiga yai wanka yaje gun Bashar don yana son ganin shi.
Munyi hira sosai da daren kafin mu kwata bayan nai wanka nai shirin kwanciya saiga wayan kabir yana fada min suna lagos yanzun suka sauka da safe zai karasa gida.
Mundan jima muna fira sai na kwanta da farinciki a raina.
Mafarkin danayine yasa na tashi ina sallah kafin ai kiran sallah tare da rokon Allah sauki koma maye.
Da safe na dan makara nai sallah nai wanka a gaban mirro na kalli irin yadda nasha gyara na canza gaba daya kamar bani bace Bintu.
Wayan Kabir ne ya shigo yana fada min zasu wuce zuwa Abuja nai mashi Allah ya kai su lafiya nan ma sai da ya dan taba min yan maganganun soyayya sosai mukai sallama dashi.
Ga abin karyawa a gaba sai hira su Amirah keyi amma na kasaci a lokacin.
Mama tace badai auren ne ya saki tunane ba har kike kallon abinci haka a gaban ki.
Nai murmushi nace kai haba mama aure kuma bayan gaki ?
Tace gani ina gadai Kabir dinki ko ?
Amirah tace da ciwon kanki ba inji mama Sare da tace haka ranan.
Nace ni ai basu gabana Anty don duk fitanan matar shi bai taba daga min hankali ba ni.
Hajiya Kubura ta shigo da manyan ledoji guda uku nan muka shiga gaida ita.
Tace hjy maijidda ni dai ga dan nawa gudun mawar ba yawa sai ayi hakkuri dashi.
Kai hjy harda dawi niya haka takarba tana budewa ledan farko kuloline set har da flask din su sai dayan ledan turaren wutane masu kyau da kamshi sosai.
Dayan kuma kayan matane aka hada masu tsadan gaske a cikin wasu robobi masu kyau.
Godiya sosai mama tai mata su ka dan taba hira kan bukin tana cewa insha Allahu da ita za,a tafi kauyen mu gurin daurin aure.
Mama tai mata godiya tace kai haba ai shine zama tare din.
Wayasan inda zaici albarkacin yaro shima watarana Bintu ai mutum ce sosai wallahi.
Zata fita suka hade da saudauki dake shigowa a lokacin nan suka gausa dashi tafice daga falon.
Yai zaune ragwab saman kujera fuskan shi babu annuri acikin sa sai mama ke cewa may kuma yafaru nagan ka haka ?
Yace wallahi maji yanzun nake jin news wai Jirgi yai accident daga lagos zuwa Abuja da safen nan kuma akwai wani abokina da zai zo Abuja yau nasan yana cikin jirgin.
Da karfi nace Kabir,,,
Nace wayyo Allah na mama wallahi da Kabir a cikin jirgin nan dazun yai min waya gashi zai shiga jirgi zuwa Abuja.
Daga haka kuma ban san may yafaruba again ?
Ganin na tafii suuu, zan fadi yashi tsale daya yakamoni na fada a jikin shi suuu a somay.
Innalillahi don Allah ku taimaka min kubani ruwa mamatake fadin hakana a gigice cikin rudewa.
Su Amira duk sun rude suma tana cewa a bincika mana aji idan dashi a cikin jirgin ko ?
Ke debo muna ruwa a fridge don Allah kin tsaya kina surutun tsiya sadauki ke fadin haka cikin tsawa wa Amirah.
Ana yayyafa min ruwa nai ajiyanzuciya na bude idona da sauri na zabura daga jikin shi nace mama da gaske Kabir ko ?
Tace dagata a bincika inyana cikin jirgin dauko wayanta mu kira shi mugani?
Anyi kira wayan wai yana kashe.
Kara komawa nayi suuu na sumay a jikin shi yace kama nin ita ina zuwa don Allah.
Maji ta karbeni daga jikin shi tace kiramin hjy Kubura maryam.
Sai gasu tare a gigice tana fadin may ya faru maji take fada mata a takaice abinda ya faru.
Salati ta cika tace sai Allah idan bai ciki wallahi ku kunna Tv mugani don Allah.
Suna kunnawa ga jirgin annuno inda yafadi a wani daji ga yan ceto suna ta faman kawo agaji ga jirgin.
Sadauki ya shigo dakin yace bari mu kaita asibiti maji tace gaskiya kan.
Ita da hjy kubura sukazo dani asibiti nan likita yace bari a dan min allura na samu barci a gani.
Hankalin kowa a tashe yake don har Alhaji yazo asibitin da wayana sukai amfani gurin kiran matanshi dana rubutawa yaya babba.
Wayan na rigin ba,a dauka ba sai gap da zai tsinke ne wani dan yaro ya dauka yana fadin.
Maman bata nan yanzu akazo aka kwashe wai baban mu yayi hatsarin jirgi sun mutu.
Salati suka saka daga inda yake yakai kallon shi gareni ina kwance sharkaf kamar gawa sai numfashin da nakeyi kawai a lokacin.
Sadauki ne ya fara ganin sunayen wa yanda ke cikin jirgin sunan Kabir ne na ashirin da biyar daga jerin sunayen list din wa yanda abin ya faru dasu.
Kuma babu wanda ya tsira daga jirgin duk wanda ke ciki ya mutu a jirgin.
Ban falka ba sai da la,asar na dan bude idona a hankali nake bin dakin da kallo sai dai ban fahinci inda nake ba sai muryan mama naji tana fadin.
Fatima kin tashi ne sai abinda ya faru ya fara dawo min arai a hankali wasu hawaye suka fara dan silalo min a hankali daga idona.
Dafani mama tayi tana fadin Fatima kiyi hakkuri kinji duk mairai mamaci duk wanda lokacin shi yayi tafiya zaiyi.
Allah baiyi Kabir mijin ki bane, sai kiyi hakkuri kibarwa Allah .
Allah da ya halicce shi yafi mu son shi ya karbi abinshi a lokacin da yaso.
Nace a hankali cikin wani murya mai ban tausayi ,mama Kabir ya mutu ko ?
Tace Fatima sai dai hakkuri Kabir yariga mu gidan gaskiya.
A hankali na fara rera kuka mama tana dan buga min baya tana fadin kiyi hakkuri kin ji Fatima.
Shi yanzu adduan mu yafiso da wanan kukan da kikeyi.
Kubarta tayi kukan don shine zai dan sa ta samu relief.
Nai kuka sosai na wani lokaci can na mike zaune da sauri suke fadin ina zaki kuma,?
Nace sallah zanyi mama naga kamar azahar tayi mamatace sai dai la,asar yanzu kan don har munyi sallah mu.
Bayan nayi sallah na zauna gurin ina addua sai kuma na barke da wani irin kuka gwanin ban tausayi dani.
Kiyi hakkuri suke ta fada min shigowan babane yana fadin ashe ta falka Fatima sannu kinji.
Kiyi hakkuri haka Allah ya nufa dake kada ki kara wanan rudewa ki zama musulma mai imani da duk irin kaddaran da Allah ya kawo maki a rayuwan ki.
Mama taso a sallamay ni amma sai Baba da sadauki sukace abarni harda safe aga yadda jikin nawa yake sai a sallamay ni.
Washegari ganin na samu sauki sosai sai dai ban magana da kowa don wani iri nake ji kamar zan shude.
Mun dawo gida inajin ana fadin wai ance a garinsu za ai sadakan ukun shi.
Baba ya shirya tafiya inda zamu ai sadakan uku damu inji Baba.
Haka yasa sadauki ya shiya don tafiyan yaso zuwa gurin mutuwan abokin shi duk daba musulmi bane amma saboda tafiyan mu yace sai an dawo ya wuce.
Motoci uku muka kama hanya dashi har da hajiya kubura da mama Asiya umma tace wai bata jin dadin jikin ta suka barta gida.
Muna isa tun daga nesa muka hango taron mutane a kofan gidan su Kabir, din haka ya kara sani sabon kuka sosai da kyat mama ta samu nai shiru suna min fadan na natsu na daina kuka.
Muna fitowa idanuwan mutane caaa akan mu nan aka fara fadin Allah sarki ga su Bintu nan sun iso
Nan kowa ya fara fadin Allahu akbar Allah bai nufi a zarga aure a tsakanin su ba haka ya kasance.
Sai gaisuwa ake muna nan muka shiga cikin gida a dakin mahaifiyan shi muka shiga.
Mutane sukayo caaa zuwa dakin don ganina ina saye da hijjab amma duk da haka mutum zai iya gani kwaliyan amarcin da akai min a jikina.
Mahaifiyan shi kamilar dattijuwa tana zaune da tasbaha a hannun ta mu kai mata gaisuwa ni dai ban iya magana ba don kukan da yaci karfina a lokacin.
Tace Fatima haka Allah ya nufa tsakanin ki da yaron nan Allah bai nufi akwai zaman aure a tsakanin ku ba.
Nan kuka na ya fito fili mutanen dakin suna fadin kiyi hakkuri kinji Allah yabaki wani wanda yafishi.
Sai naji an rikoni tabaya ana kuka Fatima Kabir ya tafi ya barmu Fatima.
Kabir ya tafi yana mutuwan son ki a ranshi kullun yana min nasiha akan narike ki amana idan kinshigo mu zauna lafiya amma Allah bai nufa ba Fatima.
Sai muka sa kuka nida ita duk da ban dago naga fuskanta ba.
Hakkuri aje tabamu ana muna nasiha sosai mai kashe jiki.
Nan mukejin ana fafin wai shi ko gawan shi ba,a gani ba sai alkur,anin shi da tasbaha da agogon hannun shi.
Nace Kabir Allah ubangiji ya karbi bakuncin ka.
Kowa ce Amin Bintu kiyi hakkuri kinji haka Allah ya nufa daku.
Can wata tace zoku gausa da dayar matar tashi gata can dayan dakin da yan uwanta.
Ni dasu mama muka shiga dakin mun samay ta tana waya muna gaida ita bata gaisa ba.
Sai mutanen dakin ne suka gaisa damu watake cewa wanan ce dama yarinyar da zai aura din ?
Wace ta rakomu dakin tace itace Wallahi, Allah baiyi aure a tsakani ba.
Mukan ai sheri aka kwaxo muna farar kafa yaja muna hasara.
Kai amma kuwa bakiyi ba wallahi gaki dai kamar mai ilimi saidai ashe baki da tauhidi?
Hajiya kubura ce taba ta amsa da hakan.
Tace banda tauhidi aiku kuna dashi aja muna tsiya ace kada mu fadi.
Kika dai jawa kanki ke da kishi har akan mamaci inji mama Asiya ta karbe.
Kamata yayi asamay ki cikin jimamay ba cikin kishi ba haka kamar ba wace tai rashi haka ba.
Ku tashi mutafi mu gausuwa mukazo maku ba tsiya yakawo mu ba nan.
Mun fita muna jin su suna zage zage nace a raina ai in sakwatawa kuke kun hadu da mama da hjya kubura a raina.
Bamu dadeba su baba sukace mu fito nan maji ke fadawa mahaifiyar shi cewa za a aiko da kayan lefen da yai min.
Ko yanzu don anzo gaisuwane yasa ba,a zo dashi ba.
Matan sukace haba haba habadai da zafi haka.
Sai mahaifiyar shi tace wanan ai kyautane tsakanin ta dashi tun yana da rai don haka mun yafe mata ba namu bane rabontane daga gare shi.
Allah ya bata miji nagari idan antashi auren ta a fada muna kada zumunci ya yanke.
Uwargidan Kabir da zamu tafi tayi kuka sosai muka rike juna tana min addua tace zata dinga bugo min waya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
I DAN KIN TURAWA WA WANDA BAI BIYA BA MU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAR MUNA A KAN KI
Bayan mun dawo gida sokoto babu abinda mama keyi sai lalashi na tana kokarin taga na saki jikina sosai.
Amma na,kasa sakin jiki saboda shakuwa ba karamin abune ba ga dan adam.
Na kasa cire Kabir a raina gaba daya ko yaushe zaka ganni nayi zaune nai shiru ni kadai ko idan ana hira ni na zauna naita tunane ni kadai.
Yau ma zaune nake saman dogon kujeran falon sai hira suke a tsakanin su akan Ahmad dan wurin mama Asiya.
A zahiri kallon su da sauraren su nakeyi amma zuciya na tai nisa da inda suke zaune.
Sai da naji murya mama cikin fada tana magana ko shi sai da Maryam ta dan taboni na,zabura firgigit dani.
Yaya Sadauki na gani tsaye cikin kaya bakake sai kwalan rigan ke da jan kwalla daga saman shi, kamshi na tashi daga jikin shi.
Kallon mamaki yake min irin yadda na koma a lokaci daya na koma Bintu shiru shiru dani ban magana kamar ba nice ba.
A hankali ya tako zuwa inda nake zaune saman kujera na takure kaina guri daya ina makure kamar mai jintsoro.
Zama yayi daga gefen kujeran da nake zaune na dago ido in kallon shi a cikin mamaki don, bai taba zama haka a kusa dani ba.
Yace, Fatima har yanzu baki sake jikin ki ba ko kin fi son ki tayarwa maman ki da hankalinta ne,?
Na ce tare da girgiza kaina da,a,a, yace may yasa bazaki hakkura da ikon Allah ba Fatima.
A hankali na sa gefen hannun na ta baya na,share fuskana yake tabayan kinci abinci kuwa?
Kafin na bashi ansa sai muryan maryam tace maryam bata cin komai da koko sai dan ruwan liptop da take sha .
Ya mike yana cewa kina,son ke ma ki kashe kanki ke nan kibi Kabir din ko ?.
Yakareshe zancen tare da mikewa ya,bar dakin a lokacin don dama fita zaiyi.
Na dan na dan fara sake jiki saboda irin matsin da suke min gaba dayan su a part din mu.
Tun dai mama wani lokaci sai ta nuna min bacin ran ta karara a,fili nakan shiga taitayina na kama kaina.
Gaba daya nakan ji komai bai min dadi nakaji zuciyar ta a bushe komai ban so ban ra,ayi ko kadan.
Idan suna hira ko yar dariya sai naga basu damu ba ko don basu akaiwa mutuwar bace abin bai damay su ba hakanan kaman yadda yake damuna ako yaushe.
Yadda Sadauki yake kokarin nuna min kulawan shi na yan uwantaka tankar ciki daya muka fito dashi.
Shidai tausayi ma nake bashi yanzu don yasan mutuwa abune mai cin zuciya sosai kafin ya fita.
Ina mamaki ni kaina yanzu ko bai ganni ba sai yace a kirani idan nazo zaice kinci abinci ko ?
Nakan bashi amsa da eh ko a,a sai yace a dauko naci a gaban shi mama tana jin dadin yadda yake matukar nuna min kulawanshi sosai akan abinda ya samay ni.
Da zai tafi sai da ya kara yi min nasiha sosai yace kuma idan yatafi yaji ance ina wani abinda bai dace ba zai zo da kan shi ya dauki mataki.
Nace a hankali insha Allahu yaya bazanyi komai ba ai na hakkura insha Allahu.
Yace da yafi maki don kin san halina dai zan iya maki abinda nace din.
Da zai tafi hardani muka rakashi bakin motan da Bashar zaikaishi airport har ya zauna nakecewa a hankali yanzu Anty maryam shima yaya jirgin zai shiga ne ?
May waccan take fadind wai ?
Yana tambayan maryam.
Dariya take tana fada masu abinda nace nikan fuskewa nayi kawai.
Yace ko na fasa na shiga mota kada nima na mutu ko?
Bashar yace Fatima ai da motan da jirgin ko basu idan kwanan mutum.ya kare mutuwa zaiyi.
Sadauki yace kasan bakauya ce ta dauka jirgine kawai ke kashe mutane.
Har motar ta daga yace ke zo nan .
A hankali na isa inda yake zaune yace kin dai ji abinda na fada maki ko?
Nace eh yace kwana nawa wani tsohon zai bullo maki idan kinyi hakkuri don haka bana son naji kin kara somay wa maji a daki kuma.
Dariya akasa suka, wanda nima dariya abin ya bani har fararen hakorana suka dan fito yace to ke fa kullun kina cikin shawa mutane toka agida waike tsofo ya tafi ya barki.
Suna bacewa, daga layin Bashar ya sauke ajiyan zuciya yace, wallahi tausayi yarinyar ke bani Allah.
Yace akwai tausayi shiya nake kokarin gani she feel free don kada abin yai mata illa gata karamar yarinya.
Amma gaskiya ya kamata fa asan abinyi anan man don wallahi ni dai ina maka kwadayin wanan yarinyar Allah ko.
Kai Bassh kada kaja min raini please kaunata ce fa don Allah bari kada ta raina ni.
May ye abin raini anan kuma aure ne fa kasan lokacin da zaka lume ciki kana I love you baby, I miss you,
Wallahi kadai dan iska ne ga,wanan yar yarinyar bakauya zan tsaya ina wanan shirmayn haka sai kace wani soko can.
Dariya Bashar yayi yace kanace wasa nake yi to gwada kagani in baka samu kan ka ga stage din nan ba.
Jeka gwada kai da baka,san kunya ba yace nikan anan ban sani ba gaskiya sai ma ka dawo zaka gane ban sani ba ai don zaka samay ni dumu dumu wallahi.
Agurin wanan yarinyar ko a ina ai ita takace da ka ganin gurin tunima,
A wani gurin dai da nake shirin shiga very soon.
Don akawar da zancen ya jefo mai zancen kasuwancin su da haka suka isa airport din.
Sannu sannu na,fara sakewa na far normal life dina kaman yadda na,saba a baya, can.
Sai kuma na dan fahinci ashe na dan saba da yaya sadauki kwana biyu ban sani ba.
Sai yanzu da baya gari na fahinci muna kewan rashin shi agida abinda bantaba ji ba idan bai nan a rayuwana.
Saidai nasan kila dan kulawan da yake bani ne kwana biyu yadan ja muna shakuwa tsakanin mu.
****** ********* ******
Bayan kaman wata uku da rasuwan Kabir ba laifi gaskiya don zuwa yanzu na dan sake sosai na rage yawan damuwan nan da nakeyi.
Shima acan idan yai waya yakan ce abani mu gaisa kamar yadda yakan gaisa dasu Amirah.
Sai dai ni ba wani dogon magana ne mukanyi dashi ba yakan dai tambaye ni yaya karatu ya kuma gida.
Sai dai idan mun gama,waya kamar yadda nakan ji shima din haka yakanji a ranshi sai dai kosan mu yana daukan haka a zumunci ne kawai.
Yadda bai taba jin yana sona ba nima haka kowan mu dai yana son dan uwa na yan uwantaka ne kawai ba wai wani so ba can.
Yau saye nake cikin dogon riga din kin kasar Dubai da mayafin rigar ne na yafa a kaina ya dan rufe min har rabin fuskana kadan.
Na samu mama a,falo nake gaishe ta, ganin yadda nai kwalliya haka yai yasa mama tambayana yau kuma,sai ina haka Fatima?
Na ce cikin dan sakin fuska tau gani nan dai mama gidan su maman arkilla nake son zuwa nagaida ita.
Cikin mama Maji take cewa yau din ashe hjy tayi sa,a yau ranan nata ne nace Anty maryam ki daure mu tafi please ?
Tace na,fada maki ban zuwa gidan nan sai lokacin da zuwan yazo min a,rai zan tafi.
Banyi fushi ba sai murmushin da nayi ina fadin ya kamata ace ki daure mu rafi tare yafi min zuwa ni kadai.
Ranan da na tafi aini kadai na tafi kemay may kika hana kan ki rakani.
Nima yau Allah ya ban sa,an ki sosai wallahi, haka naiwa su mama sallama na tafi gidan,
Na dan dade a,saman titi kafin na,samu abin hawa sai ga wata,mota tazo wucewa tin daga nisa na gane cewa mace ce ke tuka motar a lokacin.
Naso na,sheda su amma sai na,rasa gane a ina na,san su ne ma abin ya, shige min a,rai.
Kwanan zuwa gidan mu suka nufa, suna shigewa ina samun mota na shige abina.
Maman su Bashar tayi murna kwarai da,ta gannin don bata tsanmaci zuwana ba.
Nace na shigo na gaida ita,na kuma yi mata kokarin da,tai min da,rasuwan Kabir di na.
Da hanzari tace kai Fatima kin taba ganin don iyayye sun wa dan su abu yace yazo godiya, nakai wani dan lokaci tana ta m8n nasiha a cikin hiran na mu wanda shi yafi yawa.
Nai mata sallama na kama hanyan sai gida ina,shiga na samu anyi dandali a tsakar gida.
Nace wai yau sa idawannan kuma nan aka baje ne ina gaishe su na juya,sai cikin shiyan mu bankai ga shigewa ba naji ana fadin a haye duniya tai masu dadi an mutu anbar mata kaya sai shiga da fice takeyi a cikin su.
Maji na ganina take cewa a,a shin har andawo ne wai yanzun fa kika fita Fatima.
Murmushi nayi raina a bace mama tace may kuma akayine wai naga kin futa cikin dadin rai gashi kin dawo muna a murde kuma.
Nace cikin hawaye mama kinji abinda umma take fada min wai duniya tai min zafi an mutu anbar min gadon kayan lefe sai yadda naga dama.
Tace kai Fatima ki barta mana tunda ta zama tsohuwar banza kamar ki zata tsaya kuma ta yadawa magana haka?
Ina ruwanta da ke da har wanan irin zancen zai rika shiga tsakanin ku da ita kuma?
Amira dake fitowa tana ji tace halin su ne kawai na bakin ciki da hassada irin nasu, da yarta ce ai baka jin zamcen komai akan ta.
Amma tunda zance ya kawo nan shine abin bakin ciki kuma, bamu san lokacin da yar iya tafita ba tana cewa to ai in wanan rigunan ne na jikin Bintu duk muna dashi harda Siyaman mummy a sayowa irin shi ba cikin kayan mamacin bane ta saka.
Umma ta fahinci maganan Maryam daga inda suke zaune take cewa kai shi yaro idan baida kunya bai tsoron uban kowa walleh.
Ku daiyi tayi ai anan zaku tsufa dakin uwar ku kuna taya ta kishi ko kare bai zuwa sunsuna inda kuke.
Sai kyashi da hassada in kunga yan uwa sun samu sabbin samari idon ku na sama sai kun yi kitihin da kuka rabasu dasu.
Yan banza masu abin fadi waike mara kunya kinzo mayar muna da martani ko ke da baki da kunya.
Ni ko mashayin yayan ku bai isheni ba wallahi balle ke abin banza har gobe dai ba mai abin ashha kamar ku a gidan nan, mutane kawai marasa mutinci.
Karan buga kofan shigowa gidan da,akayi da karfi shiya mayar da hankalin su gaba daya ga mai shigowa gidan.
Wasu matane su uku tallabe da,wata yar yarinya dul jikin ta jini ne tako ina kaman an yaka rago cikin tashin hankali suke fadin ina mahaifiyar,
Imirah gidan nan ?
gaba daya hankalin kowa ya koma,gare su matar sai kuka take da yarinyar tallabe a hannun ta.
Kafin wani yai maga saiga "yassanda mace ta shigo tana fadin waye uwar imiranah gidan nan?
Da sauri maryam tace kufito ga yan sanda a gidan mu wai ana neman uwar imiranah.
Hajiya kubura shigowan ta ke nan tun a kofan gida taga mutane dafifi take tambaya wani makwabcin su ke fada mata wai anzo kama Imiranah ne,
Tana shigowa takai ido akan yarinyar dake kwance jina jina hannun iyayyen ta
Tace innalillahi wa yai mata fyade kuka shigo muna da ita gida haka ne?
Yar sandan tace wani a gidan nan something Imiranah ko waye shine wai tun da safe da yarinyar tafito tallan kunu ya jata yana lalata da ita shine yai mata wanan aikin haka.
Salati muka saka gaba daya manya da yara umma ko duk karfin halinta yau sai gata tana kuka ta,shige daki.
Hjy kubura itace ta kira Alhaji tazo gida ya iske wanan tashin hankalin mai muni a gidan shi.
Ga matasan unguwa su yi dafifi a kofan gidan sunce sai an fito masu da Imirah ko su bankawa gida wuta don ya ishe su a cikin shiya da dannan masu yara.
Ranan munga tashin hankali mugan fitina a filin Allah don ga matasa na bugun gida sai an fito masu dashi wallahi.
Sai da Baba ya dawo shida kan shi yaba da umurnin a shigo a duba ko ina sako da lungun na gidan shi ko an boye shi idan za,a ganshi.
Ashe yana daga bayan dakin maji yan sandan nashiga suna fita maji ta gan shi cikin dubara ta jefa mai hijjab ya sa yaboye fuskan shi ya zo shigowa dakin mu na ganshi zanyi magana maji tai min signal da ido nai shiru, batare da wani ya gan shi ba yashige ciki,
Allah yasa wani ba wanda ya gane shi har yashige ciki, don anyi yawa sosai wani baigane wani a gidan saboda cika ga hijjib din babbane har kasa yake.
Can ta kaishi ban dakin ta ta boyeshi ta dawo waje ana taneman duniya ba a gan shi ba a gidan.
Akace tunda bai nan ya gudu sai dai a kama baban shi ko mahaifiyar shi,
Nan wani sabon fitina ya tashi a lokacin ne maji taji kaman ta fito da Imiranah duk da tasan ranan matasa na iya kashe shi yadda suke wanan ihu da ashar akan afito da Imirana din.
Baba yarinyar da akaiwa fyade yafara fadin idan na bari aka tafi da Alhaji ban kyauta mashi ba, irin yadda suke muna kokari a unguwan nan shi da dan shi Umar Faruk Sadauki.
Bani ba duk wani magidanci a uguwa nan yasan irin mutuncin da sukewa mutane don haka ni ba Alhaji ko matar shi ce tai min laifi ba dan shi Imirana ne kuma shine nai kara gurin hukuma ya bata min yarinya.
Mutanen gurin suka ce gaskiya kayi kokari kayi gaskiya a bari har aga shi macucin babu ruwan Alhaji don bai aike shi ba.
Nan Baba yake cewa ya kamata a taimaki yarinyar a tafi da ita asibiti kada tazo ta mutu saboda jinnin dake mata zuba yai yawa sosai.
Fita da yarinyar shine dalilin da yasa mutane suka,kwasa,aka fita daga gidan tare dasu Alhaji akatafi asibitin.
Masu kuka nayi masu bata fuska nayi da yaudai kan yau ne don dara taci gida zancen kiran wasu yan iska ya kare a gidan nan don ashe kowa nada dan iska har da tantirai a dakin shi.
Hjy Kubura ce take fadin haka yayin da take tafiya zuwa part din Alhaji ta nacewa yau yadda akai tonon asiri da fallasan da yakai wanan cin mutuncin da akai muna kato har cikin makewayin mu don wani katon mazinaci.
Mu kan yau wallahi ancuce mu gidan nan wanan cin fuskan da may yai kama aiko munga iyakan iska
nci a gidan nan .
Umma na ciki tana jin ta amma ta kasa magana don yau baki ya mutu murus.
Ga tashin hankali tasan yai Imirana sai Allah sai Allah Allah takeyi kada a ganshi a kashe shi.
****** ********* ******
Maji saida taga an watse ta shiga dakin ta ta bude bayi tace mai yafito yace cikin rawan murya wallahi maji idan nafito kashe ni zasuyi.
Tace nace kafito muyi maga duk sun fita don ba waje zan fitar da kai ba ai.
Yafito duk jikin shi rawa yakeyi ta zauna bakin gadon ta shikuma ya zube a kasa sharkaf ya dukar da kan shi kasa.
Tace Alhaji karami yaya akayi kai wanan aika,aikan haka wa yar karamar yarinyar nan.
Shiru yayi tace gaskiya baka kyautawa kan kaba kuma baka kyautawa iyayyen ka ba.
Mutum yana barin abin fadi kodan bayan shi da mutuncin gidan su.
Yace cikin sauke ajiyan zuciya wallahi maji sherin shedan ne kawai amma ayi hakkuri tace yanzu wanan abin ni ban san yadda za,ayi ba ma wallahi.
Tace gashi dan uwanka baya gari shikuma Ahmad nasan kona fada mai kana nan zai iya fallasaka asani.
Tace amma ka zauna anan har dare yayi mugani don kada ka fito ko fallo ne a san kana nan.
Ta mike zata fita sai kuma ta juyo tana tambayan shi da cewa kaci abinci ma kuwa?
Yace maji ban iya cin komai ma wallahi don gaba daya ban san yadda akayi nai wanan abin ba.
Maji tace bari nazo sai tafita daga dakin muna falo tace Amirah hadowa yayan ki tea mai kauri ya sha.
Da sauri suka juyo suna kallon ta da mamaki azaton su ko ta rude ne tace wa Amirah tashi mana ki hado mashi.
Tace wani yayan mu Maji ?
Tace Imiranah mana.
Yana ina maji ke ban son tambayan tsiya kuma ku kama bakin ku wallahi.
Baba basu dawo ba sai guraren sha dayan dare yazo ya shiga dayake girkin Hjy Kubura ne bai dade ba suka rufe kofa don cikin tashin hankali yake.
A lokacin da mama taji sun rufe kofa tasaka hijjab dinta tafita sai dakin Umma.
Umma na zaune a kasa sai waya take bugawa ko anga Imiranah wa yan uwanta cikin tashin hankali.
Ganin maji a dakin ta ya ta dan daure fuska a zaton ta tazo mata jajen munafuci ne na kishiya.
Sai da maji ta zauna take cewa yaya ya mukaji da hakkurin wanan tashin hankalin na yau.
Tace ai bai kare ba tunda ban san inda ya shiga ba har yanzu, don ina tsoron kada mutane su ganshi su illanta min shi wallahi.
Maji tace bazasu ganbshi ba ma ai don yanzun ma shiya kawo ni gurin ki.
Ina son mu san yaya za,ayi mu fitar dashi daga gidan nan mu san ku ma maynene abin yi yanzu?
Kina nufin yana gidan nan ko may Hauwa,u ?
Maji tace yana gurina yaya shiyasa ma nazo yanzu don ban son ko Alhaji yasan yana nan.
Wani irin ajiyan zuciya Ummata sauke tace yanzun yana inane wai ?
Yana na dakina tunda rana nakaishi ciki lokacin da taron nan yai yawa mutanr basu gane ba na bashi hijjab ya shiga ciki.
Umma da yaranta suka ce wai har sun danji sanyi wallahi .
Yanzu yaya za,ayi Sagir ?
Sagir yace wanan dai hijjab din zamu saka mai shine kawai za,a iya fita dashi daga gidan nan ko shi a cikin dubara don wallahi naga matasa a zaune kofa group group nasan ko shi suke jira ya dawo.
Nan dai aka hada plain yadda za,a fitar dashi daga gidan muna zaune sai ga Umma da maji sun shigo dakin da yaya Sagir.
Can mukaji sun fito mani tace Amirah ke da Fatima ku sako hijjab kuzo ku fita da yayan ku can gaba da layin nan Sagir zaizo ya dauke shi sai ku dawo.
Haka akayi muka futa tare da munafuki, yana bin mu solai solai har muka wuce matasan nan sai hiran sukeyi suna cewa yau suna nan ba inda zasu sai yadawo don sun san idan dare yayi ai zai dawo gidan ne.
Bamu dade tsaye ba saiga yaya Sagir da mashin yazo ya dauke shi yaciro muna hijjab din maji muka dawo mata dashi.
Garin aka bari dashi zuwa wani kauye da yan uwan su suke can.
Muna shigowa still su Umma na dakin da mama da sauri suke tambayan mu sun tafi mukace eh ya dauke shi sun tafi,
Tace cikin ajiyan zuciya wai Alhamdullahi yanzu dai sai asan abinyi don Alhaji ya hau sosai wallahi.
Duk abinda ke nan abari da safe sai a san abida ya dace ayi.
Suka fita daga dakin tsomai tsomai dasu cikin tashin hankali nan akaje aka rufe gida.
Haka yasa mutanen dake dakon shi suka fara watsewa daya bayan daya daga zaman jiran shi da,sukeyi.
Washegari haka muka,wayi gari da yansanda sun dawo kara tambaya still sai da suka kars search din gidan ko yana ciki.
Ganin bsina suka wuce suna fadin da zaran angashi a hanzarta kai shi ga hukuma kafin su dauki mataki amma dole Alhaji ya tafi ya saka hannu a furin su.
Ranan kan anga tashin hankali don Baba ya ce sai Umma ta bar maigida ta nemo danta in ba haka ba zai dauki mataki a kanta.
Umma kuka ranan yaranta kuka cikin tashin hankali duk gida ya rude da kuka.
Sun matukar ba mutane tausayi sosai ga irin yadda Baba yai mata kaca kaca a tsakar gida.
Ganin haka yasa maji takira sadauki a waya yana dauka yake cewa maji yanzu nake batun kiran ki ai.
Na kira Baba wayan shi bata shiga lafiya dai yake ko don hankalina ya tashi sosai.
Babana kabar duk abinda kakeyi kazo gida akwai matsala babba ya taso a gida jiya.
Maji may yafaru da Baba ?
Tace ba Alhaji bane yayanka Imirana ne kaddara ta hau kan shi yaiwa wata yarinya karama fyade abin ba kyau wallahi.
Salati ya saka yace yanzu Imiranah yana ina maji?
Tace yana can anboye shi nan dai ta dan bashi bayani a takaice ta dora da fadin nasan Alhaji zai dauki mataki mai zafine akan shi yadda ya hasala din nan.
Yace to gani nan zuwa maji zan taso yau insha Allahu.
Sadauki bai shigo ba sai guraren shidda na yamma ya iso garin shida Bashar suka zo gida.
Ina daga ciki mukaji muryan shi ana gaidashi shine muma muka fito don gaidashi da dawowa.
Hankalinshi a tashe yake sai fada yake akan abinda Imirah yaja masu a gari.
Bashar yace yanzu mataki guda ne mu ganshi muje dashi gurin yan sanda asan abinda za,ai mai sai kuma muga iyayyen yarinyar mu basu hakkuri haka zai kawo dan sauki abin.
Yaya abinci fa inji maryam ?
Yace maryam bari kawai mu fita mu san yadda za,ayi wanan al,amarin.
Gurin Umma ya shiga yace ina Sagir tace yafita yace Imirah din yana ina ne yanzu?
Tace yana bodinga gidan yaya hassan tun shekaran jiya da dare.
Daga haka suka fita duk ta ramay tafada kamar tai ciwon shekara daya.
Basu tsaya ba sai gatin BODIGA can gidan yayan Umma sun samay shi ya ramay ya koma wani iri dashi.
Sunyi masu bayani kamar yadda suka tsara da farkon maganan duk da haushin dan uwan da yake ji amma ya matukar bashi tausayi sosai daya gan shi.
Gidan mahaifin yarinyar da abin ya sama suka fara zuwa tare da dattijan da suka dauko daga unguwan.
Nan dai aka,shawo kan mutumin sani Allah sani manzo har ya hakkura suka basu kudi har dubu dari uku wai aiwa yarinyar magani dashi tare da biyan kudin maganin da akai mata asibiti.
Nan kuma aka dunguma sai gurin yan sanda suma a kai rana dasu don sunce dole sai sun kuleshi har hukumar dake da Alhakin wanan shatian suzo.
Haka yasa aka nemo masu alhakin irin wanan matsalan suka zo suma saida aka shafa masu nasu rabon aka kashe case din sai dai anci kudi sosai wallahi.
Daga can suka kwaso zuwa gida gurin mahaifin su yana falon shi akace ana mashi sallama.
Yana fitowa yaga su sadauki da wasu dattijan shiyan ya juta zai koma aka dinga bashi hakkuri akan ya dauki al,amatin a matsayin kaddaran rayuwan yaron ne.
Yace aiba yaune yafara haka ba kungan shinan shedanin yaro ne don har wata yarinya ya taba yiwa ciki yanzun haka dan zaman shi yakeyi.
Yaro yace ya zauna bai mayar da zina bakin komai ba.
Yace yabasu su uku nan da wata uku ko mutum bai shirya ba sai yai mashi aure da kan shi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
YA ALLAH DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA,WANDA BAI BIYA BA ALLAH KAI MIN BAKAR ISA AKAN MAISHI YA ALLAH DAMU DA WANDA DUK YA KARANTA A SANADIN TA,,,,
A yammacin da aka,sallamo sadauki baba ya tara duk ilahirin iyalin shi a falon shi yana masu magana a cikin takaici da bakin ciki.
Ku san Nafisa ce ta karshen shigowa falon tana saye cikin wani dogon riga da yai matukar matse mata jikin ta sosai.
Baba ya bita da kallo na tsana da yakaici yace cikin bacin rai ke ina hijjab dinki zaki shigowa mutane kusan tsirara haka.
Tace cikin wani bakon murya mai baiyyana wani sabon al,amari a gareta,
Baba,,, nifa ba tsi, tsira rarra nake ba don a saye nake da, da da riga a jikina.
Ido ya kura mata cikin nazarin ta yace Nafisa kanki daya kuwa yau din nan?
Warassss nake Baba may ka gani kafin yai magana Umma take cewa daga barci take fa take wanan ita shegen haka.
Yace maza jiki sako hijjab dinki na baki minti uku ki dawo nan mara mutunci kawai.
Ya juya gurin Umma yana fadin Atika ina son idan ina magana da yara na ki daina saka bakin ki daga yau.
Ki bari idan na sako sunan ki a ciki ki saka bakin ki, idan kuma kinga kamar fadi nayi kawai to kici gaba da hakan.
Yanzu saboda mugun halinki na yaro yayi laifi ki tsare ba ai mashi fada kinga abinda wanan fasikin dan naki ya jawo muna a gida.
Wai dana mane yau tunda yai laifi ko?
Au to ba danki bane dan waye a gurin nan , saunawa kina fadin ke kikai daukan cikin abinki don haka abar maki kayan ki.
Zaitai magana yace cikin daga hannu da daka tsawa ki min shiru don ban son jin kazamin kalamin ki yau a gurin nan.
Yace Imirah kai kuma abinda kai min a idon duniya banda abinda zance maka sai dai nace kaje duniya tana da fadi.
Don daga yau ina son ku sani na cire Imirah ga duk wani harkan kasuwancina.
Don ba a hada biyu a lokaci guda zina da neman arziki basu tafiya daidai.
Don haka tafi nima nema nayi Allah ya bani kaje ka nemi na kanka amma da kudi na ni Abubakar ba za,a dinga zina dashi ba.
Wanan kalamin na Alhaji ya tayarwa Umma da yaran ta hankali sosai don sun wani babban komawa baya ne ya samay su.
Yace daga yau duk wanda ya dauko min magana irin ta zubar da mutunci da kima a idon duniya wallahi ku sani na tsamay ko wanene daga cikin zuria ta.
Ni ba mazinaci bane kowa ya sani a garin nan don kaucewa zina yasa na aje iyayyen ku haka a gidan nan.
Duk wanda ya ganin a gurin mace to ka tabbatar aure ne yakaini ba yaudara ba.
Yanzu ina riba ga illanta wa mutane yarinya da kayi amma fa ka sani shi zina bashi ne karike ka aje hakan a ranka.
Haba Alhaji kada kai mashi baki mana mama Asiya ta fadi haka da sauri ta tare mashi numfashi.
Yace Asiya ki shiga hankalin ki duk kune barayin na,tsunta da baku iya kwabawa diyan ku kun bar yara sun zama ni alkakan kafa a gida na.
Sai yai shiru can yanisa yace Maijidda ke kuma kada ki ga kamar ban san komai ba da kikayi.
Nasani kuma nayi mamakin yadda kika boye, wanan mugu munafuki mazinaci akan mumunan laifin da ya aikata haka.
Dukar da kai mama tayi tare da dan nisawa Baba yace ina kwana ki akanki yaso sauke wanan iftila,in kan yar amanan da aka aje a gurin ki.
Idan da ita yaiwa hakan ashe boye shi zakiyi ke nan kici amanan iyayyen yarinyar da aka danka maki.
Gaskiya kin bani mamaki kuma kin bani kunya matuaka dana ji hakan a kan ki.
Sannan ke mai da mai hali ko ?
Kika saka danki a gaba sai da yazo ya fitar da,wanan fasikin dana so ai mashi daurin rai da rai ya karata can gidan yari inga yadda zai samu wata yar kuma ya lalata.
Cikin karfi hali maji tace Alhaji ni ba na boye shi bane don kada a hukun tashi kokuma wai ba mumunan laifi yayi ba.
Gani nayi a lokacin yadda mutane su kai dandazo suna neman shi zasu iya illanta shi.
Yace da tsawa shi da ya illanta yar wasu fa ?
Tace idan sun kashe shi ko sunyi mashi wani mugun abin a lokacin Alhaji sai abin yafi na farko muni.
Kai kuma ka hau sosai a lokacin ba shawara zaka ji ba don yadda ka hasala.
Wanan dalilin yasa nai hakan .
Amma da aka samu natsuwa ai an fahinci juna don kaddarace shima ai da yayi abin ya koma mashi ciki.
Sannan ita wanan yarinyar mutane sun sheda ta da haka take watsatsa ce ita dama.
Yace ai shi ya fita watsewa,
Maji tace na kira sadauki ne don yazo ya san yadda zaiyi akan al,amari don duk kan mu nan ai matsalar ta shafa don ba wanda bai shiga tashin hankali ba daga cikin mu.
Ke da danki ya shiga wani hali a gidan nan wa hankalin shi ya tashi ina a tsakar gida ake tsayawa ai maki gori dare da rana.
Wanan kuma ai ba komai bane don kowa ma uwace ai don dan sune suma.
Amma ni idan abinda nayi laifi ne don Allah ayi hakkuri a yafe min.
Sadauki ne yai magana yace Baba don, Allah ayi hakkuri tunda abin ya riga ya faru.
Kai dakata don Allah ai kaima zanzo gareka ne watau kai yanzu ga mai kudi ko ?
Shine zakai amfani da wanan dama gurin tallafa ma alfasha idan haka ya kasance daga daya daga cikin kannen ku yaya zakuji ne wai ?
Abinda nake son ku gane ke nan idan a cikin diyan mu akaiwa wanan keta haddi haka aka gurbata rayuwan su ashe taimakawa mai fyaden zakuyi a sake shi ?
Shiru falon yayi ba,wanda yai magana kowa na tunanen zuci daga cikin su.
Sadauki ne still ya kara yin karfin halin yin magana yace Baba don Allah ayi hakuri tun da iyayyen yarinyar sun hakkura.
Ido mahaifin shi ya watsa mashi cikin takaici yace eh maganan ta mutu ma na tunda kai mai kudi ka basu kudi ba.
Amma ni a gurina wallahi case din nan bai mutu ba dayan biyu ne ko na kai shi kotu ko kuma ya yarda cewa da zaran yarinyar nan ta kara dan tasawa zai aureta.
Da sauri kowa ya ke kallon baba cikin dago kawunan su.
Imiranah da,sauri ya dago yace haba Baba wanan yarinyar yar kauye yar talla ko boko fa batayi ba.
Au baka san haka take ba ne har ka turata daki ka kwamashe ta har ka kai ga halaka ta ?
Shiru kowa yayi ba wanda yace uffan Baba yace sannan kuma kaine zaka dinga dauka duk wani nauyi nata daga yau har zuwa lokacin da za ta tare a gidan ka.
Kuma ku sani wallahi ko bayan raina duk wanda ya tayar da wanan magana ban yafe ma maishi ba.
Daga haka ya mike zai shige ciki sadauki yace amma Baba don Allah ka barshi yaci gaba da sana,an shi da yakeyi.
Baba yace wani ai nagama magana ta yaje ya nemi tashi shima, don nima nema nayi ba gado nayi ba.
Ya shige abinshi yabar su nan a zaune kowa yai jigun jigun tsakanin su, hjy Kubura ta mike tana fadi yau dai ga irin ta nan.
Yanzu kowa na da abin fadi ke nan a gidan nan tab da tsuliya bamu kadai bane masu abin fadi ashe?
Ke tsohuwar kilakiya dama nasan a farin ciki kike don haka ya faru kuma nasan duk kece mai wanan shirin.
Iyakar ki ke nan zagin wasu naji ni dadewa nayi banyi aure har mijin ki yazo ya,aure ni gani kuma gidan zama daram ba inda zan tafi wallahi.
Ba kince lokacin da na,shigo kin bani wata uku ba dashi yau gani wata uku ya shude har da riba gasu nan min.
Sai da ki shirya don kilakiya tana nan dakin ki zaune ko kinzaci bamu san komai bane wai ?
Ni ba irin hajiya maijidda bace da kike wa yadda ranki yaso wai don takaici har da taimaka maku.
Nan da Sadauki ke dan shaye shaye a baya may nene bakuyi mata ba a gidan nan.
Yau gashi ita da dan da kike mata gori kullun sun taimake ku ai da kun gane kuren ku wallahi da ankamashi fasikin banza kawai.
Nan fada ya kici may masu hjy kubura tai masu tas ta fita maji dai tana ganin su sarke tabar falon zuwa part din ta.
****** ********* ******
Ina zaune a falo ni kadai don ban tafi gurin kiran da Baba yai wa iyalin shi ba don nasan magana ce da yashafi sirin iyalin shi.
Sadauki ne ya fara shigowa falon su maryam na bayan shi, nan ya samu kujera ya zauna tare da furzo iska daga bakin shi.
Daga inda nake zaune cikin yar siririyar muryana nace sannu yaya.
Sai da ya nisa yace yauwa sannu Fatima ke ma.
Maryam tace Fatima dauko muna salad din mu, mu sha kinji.
Namike na nufi kitchen na dauko salad fruit din dana gyara mu a a cikin wani roba mai fadi da cups din da zan zuba muna aciki.
Shina fara zubawa fruit din idon shi suna a lumshe na aje mai a gaban shi nace yaya ga naka nan na juya zan wuce.
Kamar mai rada yace ki zo ki dauki kayanki inba zaki juri bani hannu da hannu ba kuma ki tsaya nasha naji ko may nene?
Wani din nayi kamar na wuce sai kuma nai wani tunane tare da dukawa na dauko cup din na mika mai,
Bai ce min kala ba ya karbi cup din daga hannu na, zan juya na wuce yace amma kinji abinda nace maki ko?
Dan guntun tsuki naja wanda ban san zai fito fili ba yace, ai da ma na barki ki tafi din yau kiga abinda zan ma shegen kunnen nan da baijin magana.
Babu shiri na dawo daga gefen shi na dan tsaya tsaye.
Yace ya haka kuma kamar wata soja can ko bodyguide, zama nayi daga kujeran gefen shi ina cewa Anty maryam ki zuba naku kada yai sanyi har nazo.
Bai ce min kala ba ya fara kurban salad din da cibin dake cikin cup din a hankali.
Ya kai cibi uku ya dago kadan yace me sunan wanan abin kuma ne wai ?
A hankali nace fruits salad ne.
Ya dan mayar da hankali ga sha can yace waya hada shi haka ?
Nace nice nayi shi dazun da safe.
Ya nuna cup din yace ina son kullun da safe da yamma idan ina gari ki dinga hada min shi.
Zan so na sha shi kafin nasha komai da safe haka da yamma kafin na kwanta.
Kaina na gyada mashi kawai.
Yace baki ji may nace bane ?
Da sauri nace tau yaya.
Maryam tace Bintu zo dauki naki mana kafin yai sanyi ki sha.
Na yunkura zan mike sai naji tasa kafan shi ya take min kafa, wani mugun zafi naji ban san lokacin da na sake wani dan kara ba da karfi.
Da sauri na daga kai na dubeshi sai naga shi sai shan salad din shi yake hankali a kwance.
Da sauri su Amira suka dago kai amma basu ga abinda nakewa ihu ba hakanan.
Gashi shi kuma yaki daga kafanshi daya danne min nawa dashi idan na dan motsa kafana wani irin mugun zafi nake ji sosai.
Kuma yaki koda kallon inda nake balle yasa alaman cirewa.
Take idanuwana suka fara kawo hawaye, mama ce tafito daga dakinta don jin karan da nayi tana tambayan maye haka kuma kikewa mutane ihu haka Fatim?
Ban ce komai ba sai dan kukan dana kara da sauri takai kallonta ga ketan da yake min.
Tace kai amma ko anyi babban banza anan wallahi yanzu mai tai maka kake mata wanan cin amanan haka sadauki ?
Kamar badashi mama take magana ba tace bazaka cire mata wanan kauren kafan naka ba da yasha buga ball.
Sai lokavcin su Amira suka gane wani keta yake min duk tsawon wanan lokacin su dai sunga kawai ina kuka ne.
Mama ta kara cewa wai bada kai nakeyi bane sadauki ?
Jin haka yasa shi daga kafan shi a kan nawa yana yamike tsaye yana fadin, ai na fada maki sai nai maganin rashin jiki a gidan nan.
Yan tsun kafan nawa a take sukai wani irin jawur dasu bansan lokacin dana duka ina murzasu ba a hankali sai hawaye nake zubarwa shaaaa.
Can na mike cikin dan dan gyasawa nafara tafiya zuwa daki ina kuka raina a bace ina fadi a raina wanan ai cin zallun ne don kafi karfi sai ka cuce ni haka kawai.
Muryan mama maji tana fadin haba kana son wallahi in maka abin da bakai tsanmami ba kan yarinyar nan.
Yanzu mai taimaka da kai mata wanan cin amanan haka, ko kaima dai ka canza ne wai ban sani ba don ban sanka da wanan halin ba haka.
Ya ce kai maji munafukan yarinyace fa har may nai mata ne wai da zata sakawa mutane kuks haka don shagwaba kawai.
Uwarka kai mata nace,
Da sauri ya dago kai yana kallon maji don ya dade baiga ranta ya baci haka ba har tai mashi wanan kalman da fada.
Sai gashi yau akan Fatima ta zagi uwan shi, maimakon yayi fushi sai murmushi yayi yace dama haka take son ji ai munafukan banza kawai.
Fita min daga shiya mara kan gado kawai kasaka yar mutane gaba da kyashi da hassada kawai.
Maji Fatima ce zanyi kyashi kuma ?
Sai ya wani dan bushe da dariya don abin ma dariya ya bashi shi har may zai kyashe akan Fatima kuma.
Yana dariya yafita daga dakin don shi kalaman kyashin ma dariya yake bashi sosai wallahi.
Yana fita su Amira suka kwashe da dariya suna cewa kai maji wai kyashi yayane kuma zaiyi kyashin Bintu kamar wata hamshakiya can.
Ta juya gare su tana fadin in ba kyashi ba mai ya kawo haka don Allah kuma ?
Wallahi abin haushi da takaici yabani Allah kuwa haka kawai katon banza ka dannewa yarinyar mutane kafa da karfin Allah don cin amana.
Ina daga ciki naji muryan ta tana kirana da karfi na amsa da na,am nafito still dan gyasawa nakeyi har lokacin.
Tabi kafan nawa da kallo har na iso gareta tace wai may kikai mashi ne yai maki haka ?
Ina kuka ina mata bayanin yadda mukayi dashi tace bar macucin banza kawai ai zai dawo ya samay ni ne.
Something is fishing, something is fishing wooo, something is fishing somewhere,
Harara na maka mata Amira ma kallon mamaki ke kuma may ye haka dan Allah bari mana kinga ta sha,wuya tana kuka.
****** ********* ******
Wasa wasa sai ga kafa ya rure min ya dan hau ya kumbura da kyat nake iya taka shi sosai.
Take ya,saukar min da zazzabi da sanyi a lokaci guda haka ya jawo kwanciyan dole ban shirya ba.
Shiko yana fita ya shiga motan shi sai gurin da yake ginan shi yanzu har kayan gidan komai anzuba mashi a gida zakace ko an tare a cikin gidan ne.
Nan Bashar yazo ya samay shi don su fara lissafi, saboda zasu yo odan kaya kwanan nan.
Bashar na shigowa yabi ko ina da kallo a gidan ya dan nisa yace,kai gaskiya fa MAN ya kamata kai aure hakanan domin barin gida haka hatsari ne ko banza kuma a ragewa Maji consurming .
Sadauki yai dariya yace, ai sai naga kaima katon tazuru ne bani kadai ke cinye abin uwata ba.
Bashar ga zauna cikin yanayin nishadi da kuzari yana cewa Allah ba,wasa nakeyi ba ni da ka ganni nan na kusa zama family man insha Allahu.
Kai dalla jacan da zancen banzan ka kullun da bai karewa mutane saurare.
Yace ai ko zakace nace don kwanan zan baka mamaki ne sosai Allah kuwa.
Sadauki ya kwantar da kanshi a jikin kujera yace gashi ko kaji tsoho yace wai ya bamu wata uku ba.
Bashar ya mika hannun shi ga kafadan Sadauki yace na fada maka kayar da wanan daukan kan naka kawai bori ya hau idan baka iya fadawa Maji ni sai na fada mata.
Da sauri Sadauki ya dago kai ya dan kalleshi yace ka fada mata may kuma?
Cikin kashe ido Bashar yace zancen yarta mana Fatima tunda naga kai wanan shegen fadin ran naka bai bari ka fadi abinda ke cikin ranka.
Kai dai wallahi wani irin dabbane dan akuya kawai don banda kuya na rasa wace zan aura sai Fatima.
Illa ne auren Fatima din don dai kana so wallahi girman kaine kawai irin naka ke cutan ka.
Wai kasan Allah?
Bashar yace niko nasan Allah sosai wallahi ko.
Ce to ni wallahi daidai da rana daya ban taba jin digon son yarinyar nan a raina ba Allah ko.
May ma zan so ga jikin wanan maikama da takarda ne wai ?
Yanzun ma saida muka kwasa da Maji akan ta kaga na gudo nan don naga maji tahau sosai har uwana ta zaga yau akan yar kauyen nan nata.
Yace mai kawai Fatima din kuma kai ?
Nan yake bashi labarin abinda yafaru yakare da cewa kasan shagwababbane kuma muna fuka shine harda kuka da ihu don uwarta taji ta zageni.
U see aina fada maka wallahi son ta kakeyi amma kana wa mutane wani noke noke haka?
Yace ban fa son iskanci idan kuma na daina kulata ace ga batu ga zance kuma.
Wai yaya kuke son mutum yayine wai ?
Don Allah ni let's do what we here for.
Sun dauki lokaci a gidan suna lissafi yadda ya kamata tare da tsara abinda ya dace suyi a karshe.
Sai sadauki yace amma gaskiya wanan riban da muka samu ina son mu kasa shi uku bashar yace inajinka.
Yace ka kwashi kashi daya kashi daya mubawa iyayen mu dayan kuma mu samu wani abin tallafawa tallakawa dashi.
Wanan ma babban shawara ne amma nawa da kace gaskiya yayi yawa ni kadai.
Sadauki No kada muyi haka dakai please kaga kace zaka yi aure soon, to dole ne kuma kaima kafara dan wani abin dogaro da kanka hakana.
For me kaga ni banda matsala ina dai samu gwargwado gaskiya ga harkan ball din don haka bawai sai kabi ta nawa ba.
Ina fatan ka gamsu da magana ta dai ko?
Shiru Bashar yayi yarasa may zai cewa abokin nashi can yace man gaskiya ban yadda zan gode maka ba irin wanan kokarin da kake min.
Ksi don Allah just forget ni kafi min komai wallahi in har ma badon rayuwa ba ni ko abinda na mallaka ne zan iya baka duka.
Basu bar wajen basai gap da magariba suna gidan suna hiran duniya a tsakanin su.
Da zasu rabu sunyi cewa bayan sallah zaifito akwai inda zasu tafi ganin wani mutum.
Sukai sallama kowa yaja motan shi suka nufi gida maigadin gidan ya rufe kofan kuma.
****** ********* ******
Sai bayan an gama,sallah ishai ya shigo gida a gajiye yakw a lokacin maji tana falo zaune da tasbaha a hannun ta.
Sai da yake zaune yafara gaida ita da gida ta amsa mashi a dan darare ba sakin fuska.
Su maryam ma sun gaidashi tare da ci gaba da abinda sukeyi a lokacin.
Yana zaune shima waya yafara hsr tsawon wani lokaci kafin ya kashe wayan sai maryam take tambayanshi yaya abinci fa akawo ne?
Yace maryam banjin yunwa gaskiya amma ina yarinyat nan Fatima ne abinda nace ta hada min ta hada din ne ?
Eh ta hada tunda boyar kace,
Ka halaka yarinyar mutane kuma wai kazo kana tambaya tai maka aiki ne ?
Maji na halaka ta kuma dan taka kafan da nai mata wai shine matsala kuma dai ?
Wallahi yaya yazama mata zazzabi sosai tana dakima a kwance yau ta wuni don kafan ya kumbura sosai.
Kada ke nan dan wanan takin shine har da matsala haka kuma ?
Tana ina yanzu ya tambaya cikin damuwa da nuna kulawan shi akai, tana kwance mana tunda haka kake son ganin ta.
Shiru yayi na dan tsawon lokaci yana tunane shi har wani taki yai min da za,ace saboda shi an kwanta ciwo kuma.
Ai dama nace kaida ka halakata kai zaka sayo mata magani indan kadawo macuci kawai.
Murmushi yayi yace maryam kira min ita mugani yaya kafan yayi mata ne wai ni wanan cutar da maji ke kiramin.
Maryam ta mike tashiga kirana ina kwance na dunkule acikin blanket wani irin zazzabi ne ya kamani lokacin mai karfin gaske.
Ta kware bargon tana taba jikina tani yadda nake nishi yabata tsoro da sauri tafita daga dakin ta nufi falo tana fadin,.
Wallahi maji sosai ne fa jikin Bintu bakiji yadda jikin ta ya wani gashe ba sai nishi take da karfi ni har naji tsoro wallahi.
Zubur ya mike yana fadin wai tana inane ma tana dakin mu kwance tabashi amsa .
Dakin ya shiga ya samay ni a rufe yadda ta samayni da farko a hankali yadan tabani yana kiran sunana.
Ke Fatima fatima fa ?
Na amsa da kyat ,
Yace may ke damun kine wai nace a hankali zazzabi nake ji.
Da may kuma?
Da kyat nai dan mika tare da nisawa nace kafata ke min zugi sosai.
Oya taso kizo falo mugani.
Sai ya juya yafita daga dakin yadawo falo shiru shiru ban fito ba maji tace ina take ne wai?
Tana ciki nace tafito maga kafan nata ne ?
Ganin ban fito ba yasa mama mikewa da kanta tana tafiya tana bakar magana ita kadai zuwa dakin.
Yadda ta samay ni itama dai hankalin ta ya tashi da kyarta tashini in fito falon na sako kafana daga saman gado zuwa kasa sai naji wani irin zafi da nishi na karasa saukowa kan gadon.
Namike cikin karfin hali amma sai na kasa tafiya dafa bango nayi na fara bi ina daga kafa ta da kyat da kyat nakawo falon.
Bina yayi da kallo cikin tausaya min nakai saman kujeran dake kusa da kofan na dan zauna saman hannun kujera tare da dan kwantawa gurin.
Mama tace kagani ko sadauki kaga abinda kajawa yar mutane yanzu gurin mugun halin ka.
Wanan kakausar kafan naka daya saba buga ball zaka illata min ya dashi, kafan yabi da kallo yaga ya kumbura daga inda ya taka har yana walkiya.
Yace tashi muje asibiti a duba kafan nan kafin yafi haka.
Tsoron asibiti gare ni don ban son ace allura ko magani sam ban son su gaba daya.
Tashi ya kaiki asibiti kinji Fatima kada kafan ya kara hawa kuma yafi haka ko ya hanaki barci da dare.
Ke maryam dauko mata hijjab ku tafi tare da ita don Allah, mikew yayi
yana cewa ku samay ni a mota.
Yana zaune a motan shi muka fito daga cikin gida ni da maryam dana dan dafa kadan ta muna tafiya a tare.
Ido ya tsura muna har muka iso bakin motan maryam ta bude baya muka shiga yata da mota sai asibiti
Muna hanya Bashar ya kira shi yana tambayan shi yaya bai gan shi ba har yanzu ga dare yanayi?
Yace sorry wallahi ganin zamu tafi asibiti ne yanzun haka muna hanya ma.
Waye kuma baida lafiya Bashar ya tambaya ?
Yace Fatima ce kafan ta ya kumbura shine zamu tafi da ita aduba mata nan yai mashi kwatancen inda zamu tafi.
kusan a tare muka iso da Bashar gurin wani pravet asibiti ya kaimu gurin yana da matukar kyau dagani sabon guri ne don komai nasu gurin tsab yake.
Likatan yace dole sai an da jamin kafa sai ai min allura da magani don na daina jin zugin da yake min.
Wata sabuwa ai likitan yana fara taba kafan na yanka wani irin ihu da karfi duk yadda yaso yaja naki yarda don zafin da gurin ke min daidai dan karamin yatsan kafana sai walkiyan kunbura gurin keyi yana kyalli.
Bashar yace ki tsaya aja maki kafan kiji Fatima kada ya hanaki barci da dare.
Ban san yadda akayi ba sai ji nayi an rike ni ta baya nan likitan ya samu sa,an jan kafan da kyau nai wani irin juyawa wai kwace amma ina rikon da yaya yai min bai ma san inayi ba.
Duk rabin jikina yana cikin jikin shi ina gurji ina kiran wayyoni Allah na don girman Allah ku sake ni wallahi da zafi kwarai akwai ciwo sosai.
Don Allah yaya ka sakeni kada ya kasheni wayyo don giman Allah ku taimaka min kuji tausayina mana.
Kuka shabe shabe nake yi naba maryam matukar tausayi sosai, yadda nake ihun tasan zafi nake matukar ji sosai.
Suna gefe da Bashar take cewa kafan yai mata tsamine ko har zazzabi ya sakar mata.
Bashar yace idan ba,a ja ba zaifinan anjima ya hanata barci gara kawai a ja din shi yafi
Likitan ya dauko wani mai ya shafa min mai sanyi a kafan na noke kaina a jikin yaya ina kuka cikin ban tausayi.
Ya dan buga min baya yace is ok ya isa hakana please ai an gama jan kafan.
A hankali na zare jikina daga nashi ina share hawaye cikin wani irin dan kuka kasa kasa.
Haka gurin allura nace maryam ta rike ni amma ta kasa dole dai sai a jikin yaya akai min aka bani magani tare da muna bayanin yadda za, aiwa kafan.
Amma kuma cikin ikon Allah sai naji kafan yana rage ciwon da yake min da farko.
Mun fara fitowa muja barsu aciki dan anjima saiga su sun fito daga cikin asibitin
Yaya ke cewa baku shiga motan bane kuka tsaya a,waje ga sanyi na dauka ai a rufe motar take inji maryam
Bashar yacewa maryam jimana maryam sai ta dan tsaya ya samayta a gurin nikan na dan ja kafana zuwa bakin motan na tsaya magana sukayi a tsakanin su sai naga ta danyi murmushi tace taji.
Shima yaya Sadauki wani kallon mamakine naga yanawa bashar din na bangane ba fa?
Zan shiga baya yace wa maryam bari ta shiga gaba a nan na zauna ita tana baya zaune.
Mun fara tafiya maryam ke cewa wai Bintu ba dai raki ba kan anya ko kina iya haihuwa yadda nake ganin nan .
Ke wai wani irin jikine maki haka wai dan taki kadan shine kika rakwabe haka dake ?
Banyi magana ba sai dan jingina kaina da nayi ga glass din window motan kawai ina kallon titi.
Gurin wani mai gasa kaji saman hanya ya faka motar shi can dan nesa kadan yafita.
Sai gashi da ledoji har uku a hannun shi ya bude ya shiga ya zauna har ya zauna zai tayar da mota ya juyo inda nake zaune yace yaya jikin naki nace a hankali da sauki.
Sai bayan ya tayar da mota ya fara hanya sai naji kaman yace kiyi hakkuri kinji ban san haka zai zama maki ba.
Dan murmushin ciki nayi nace bakomai kaddarace haka Allah ya nufa dani.
Yace nagode.
Har muka kai gida ba wanda yai magana a cikin mu muna fita ya mikawa Maryam ledan karbi wanan kibata taci tasha fresh milk din sosai.
Muna shiga gida mun samu mama a cikin damuwa tace kun dawo na samu guri na zauna a dan takure.
Maryam tana shigowa tace wai maji yau munsha ihu wallahi, saida yaya ya danke ta tabari akaja kafan sosai.
Ya jikin naki yanzun Fatima?
Nace naji sauki mama.
Lokacin ya shigo mama tace haka kawai kajawo wa yarinya wahala haka.
Maryam tace ai ya bata hakkuri maji kuma tayi hakkuri shike nan ko?
Ke ban son shegan taka hakkuri may zai bata bayan ya cuce ta ko.
Kai maji wa yaya zai wa laifi ya bashi hakkuri inko ba Bintu ba yau.
Daga inda Amirah take tace ban taba ji ba gaskiya nima sai yau.
Shi dai baiyi magana ba guri ya samu ya zauna tare da kallon inda mama take zaune yace maji yanzun haka za saka ido ga hukuncin da Baba ta daukan wa yaya Imiranah a gidan nan.
Ni yanzu sadauki may kake so nace kasan halin mahaifin ku sarai idan ranshi ya baci sai ya ga dama don kan shi zai huce.
To amma ni naga barin shi a haka ba zaiyi ba gaskiya anyway zan ga baba din gobe a kasuwa na kara bashi hakkuri.
Amirah tace niko dai naga da kun kyaleshi wallahi, mutanen da basuki ace mune a cikin wanan irin matsalan ba.
Kamar ya akyaleshi Amirah dan uwankine fa ashe har ke zaki iya jin dadin ganin wani naki cikin damuwa ?.
Nikan naga suna hira sai na mike zan shiga na kwanta, don barci nakeji jikin still jikina da dan zazzabi har lokacin.
Kin sha maganin da aka bakine m
uryan yaua sadauki ne yake tambayana hakan.
Cak naja na tsaya na dan bata fuska nace ban sha .
Koma ki zauna kisha kafin ki kwanta yace min ba mussu na koma na zauna idan na daga .
Maryam tace ga maganin bazaki sha milki din ba kafin kisha don bakici komai ba ma.
Naman kaza da fresh milkin din takawo min kurba biyu nayi bakina ba dadi sai na aje kwalin don bazan iya sha ba zakin shi naji ya kara bata min baki.
Still magana sukeyi da mahaifiyar shi amma hankalin shi yana a gareni ganin ban ci komai ba yace maji kiwa yar ki magana ta ci tasha magani.
Fatima ko tea zakisha in baki iya shan wanan din don naga kaman yana da sanyine ko ?
Nace ,a,a mama nasha ai na dan kara kurbawa kadan na aje kwalin nan nakoma saman kujeran na zauna da kyau can kuma saina dunkule guri guda ashe barci ya dauke ni a hakan ban sani ba.
Sai da mama tai magana sukaji shiru shine suka fahinci nayi barci ne.
Maji tace gaskiya banji dadin yadda kaiwa yarinyar nan ba kadaina wanan halin karfin ku ba daya yake dasu ba.
Ko banza ita mace ce fa ysushe daga dan magana kadan zakai mata wanan horon haka ?
Shiru yayi baiyi magana ba don koshi yadda yaga ina wahala sai baiji dadin abinda yai min din ba.
Ga yanin yadda na kwanta yasa shicewa maryam ta da ita taje ta kwanta wanan kwancin sai kafan ya kara ciwo ai.
Bai wani jima ba yamike zuwa dakin shi don ya kwanta sai dai bai shiga dakin ba ya zauna daga waje gurin furanni kofan shi don ya sha iska.
Mamaki yayi dayaji har a lokacin jikin shi yana kamshin turare na na white musk danake amfani dashi ajikin shi.
Take ya tuna da yadda yaji lokacin da nake kuka a jikin shi da likita ke ja min kafa.
Tsukiyi dan ja daya tuna yadda likitan ya rike dan farin kafana wai yana shafa min magani a kafan nawa.
Haushin da yasa shi mikewa ke nan yabar gurin da yake zaune ya fada dakin shi cikin takaici.
To kai takaicin may kake ji da hakan yaba kan shi amsa a fili da oho, wanka yashiga yafito kusa da rigan da ya cire yasa kan shi.
Kamshin ne ya kara bugo hancin shi abinda ya sashi dan lumshe idon shi ke nan haka barci ya dauke shi.
****** ********* ******
Washegari kodana tashi na danji saukin kafan nawa sai dai yana da dan sauran kunburi still.
Ban fito ba sai zuwa 9,30 nafito don na karya nai wanka na saka dogon riga baka abuga farin mutum sai rigan ya haskani.
A falo yana zaune da abinci a gaban shi yana ci yana waya fitowa na ina dan dan gyasawa yashi bina da ido.
Ina kwana nai mashi Amirah tace kin tashi ashe Bintu nace eh anty tace to yay jikin naki ?
Da sauki anty na zauna yana kashe wayan yace zonan naga kafan nan ko yai sauki ?
Idan baiyi a koma a kara jamaki shi da safen nan da sauri nace a,a wallahi naji sauki yaya.
Dariya suka saka min yace no ki bari akara ja maki for second time mana zaifi sakewa.
Wallahi yai sauki sosai yaya abarshi kawai ki karya kisha maganin ki kada fever ya dawo maki.
Na amsa da to nabar gurin shi zan shiga kitchen sai ga maryam dauke da wayana dake ringing da sauri na dauka.
Bashar ne a layin yake min yajiki yace yanzu yace maryam tabadhi layina yakirani.
Na koma na zauna don ba zan iya tsawon tsayi a tsaye ba ina amsa wayan nashi.
Ya dain bani hakkuri nace wallahi ba komai nagode ai ina taka kafan yanzu nace ka gaidasu mama.
Ina kashe wayan yana watso min wani irin mugun kallon dayasani shan jinin jikina lokaci guda.
Sai na tuna ya saka min idon kancewa ina waya da maza a gaban kowa haka yasa lokacin da marigayi Kabir keda rai na daina waya a falo gaban su.
Daga inda maryam take tsaye gaban tv tace yayanane yakira ki halan nace eh shine.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,
YA ALLAH DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA WANDA BAI BIYA BA ALLAH KA SAKA MIN AKAN MAI SHI,,,,,
Zaune yake a falon fuskan shi a daure tun da ya shigo gidan yake hakanan mama ta fahince shi amna sai batai mashi magana ba.
Yana nan zaune ya dafe kan shi yai shuru tare da lumshe idon shi Amirah tafito ta gan shi zaune a gurin tace ,a,a yayana ashe ka dawo ne yace eh a takaice kawai.
Takara cewa yaya akawo abinci ko don mun san shi ke shigo dashi cikin gidan wani lokaci.
No Amira barshi kawai wanan abinda nasha dazun is ok for me, ya mayar da idanuwan shi ya lumshe su.
Can yace Amirah ta amsa da na,am yaya.
Ina wanan yarinyar take ne?
Tace wa ke nan yaya?
Yace Fatima.
Suna ciki ita da maryam ina ga kaman waya takeyi ma dana fito.
Yace kiramin ita please ?
Ta mike na fadin toh.
A tare muka fito mu uku a lokaci guda tanagaba ina bayan su .
Yadda muka samay shi yasa mu dan shan jinin jiki don babu fara,a tare dashi.
Nace a yar murya gani yaya ya dago jajjayen idanuwan shi da suka sauya zuwa ja jajir sai da gabana ya fadi.
Yace ke a ina ki san wanan guy din dana gan ku tare a waje dashi ?
Shiru nayi na dukar da kaina kasa ya dago cikin hasala yace ba ke nake tambaya ba ne ?
Nace a,anan garin yake.
Kin san ko shi waye da kike tsayawa dashi ne ?
Maryam tai tsagal tace yaya a banki yake aiki nan gari yake da zama ai kuma dan ga,,,,
Ban tambayeki ba maryam ita nake son ta fada min abinda ta sani akan shi kawai.
A hankali nace ban san komai ba akan shi yadai zo yace yana so na ne.
To ki rabu dashi daga yau kada na kara ganin kazamin motar shi a kofan gidan nan in ba haka ba sai na sa an kulle shi wallahi.
Kai wai yaya haka may yayi shi mutumin da zaka yanke masu wanan hukuncin haka ?
Maji ban yarda da shi bane don bai da record mai kyau, shine dalilina kawai.
Kallon shi mama tayi kamar zatai magana sai taji na ce nagode yaya na juya na bar falon jikina yai matukar sanyi sosai.
Ina tunanen wani irin halin banza ne ga Usman da yaya ya yanke min wanan hukunci a kan shi.
Sai kuma nace tau Allsh dai yai min zabi mafi alheri da kan shi.
Amma maganan yana ci min zuciya sosai ga Usman yana kirana amma sai naki daga wayan har ya tsinke.
Haka yai ta kirana yana min text amma ban bashi amsa ba sai daga karshe yace nagane wanan dan wullakancin yayan naki ne ya hanaki hurda ni.
Don dama tunda naga yadda yai min na fahinci shima yana kaunan ki don irin kallon da yai mi tare da kin amsa gaisuwa na.
Wanan massage din yasa na dauki waya na kira Usman din nake ce mai tir da maganan shi, don mai zai min wanan furcin ga dan uwana.
Fatima kada ki boye min nasan komai wallahi nasan shi ya hana ki kulani kada kice zaki boye min ni ba yaro bane fa.
Haushi ya kara bani nace ashe da gaske baka da mutunci usman ni ka sani kawai don matarka na lura tafi karfin ka shiyasa na daina kulla ka kawai amma kada ka kawo min wani magana can na daban.
Sai na kashe wayan na fara tunanen zancen Usman may yasa wai duk masu sona suke zargin hakane ga yaya sadauki.
Ni dai iya sani na babu wani abin soyayya daya taba hadani dashi banda hattara da tsangwama da kina da yakeyi.
****** ********* ******
Sai bayan kwana bakawai da zuwan shi muka wayi gari da abin arziki don tsaraban mota mama da Baba suka samu inda yai masu Umma kuma kyautan kudi masu yawa.
Ni dai ko tsinke bai bani ba dama tun ranan da yai min wanan magan muke zaman yar tsama dashi bani yarda mu hadu dashi.
Kaman nasan bani da tsaraba, sai Allah ya rufa min asiri ban ma fito falon ba a lokacin hayaniyan ihun su nake ji suna murna a falon.
Maryam ce ta shigo dakin inda nake tana nuna min sabon wayan ta mai matukar tsada daya canza masu da sauran tarkacen daya kawo masu.
Nace kai anty amma kun gode yaya yayi kokari sosai wallahi Allah ya saka mai da alheri.
Tace mama ta samu mota har da Baba kai ina son irin wanan tafiyan na yaya wallahi don a jike yake dawo muna idan yayi nasara ga ball din shi.
Tace a,a na fa manta sai yanzu na tuna banga yaya ya baki, naki tsaran ba ko dai abin yar sirice kuma?
Nace don Allah anty maryam daina wanan zancen kin san yaya mugu ne kada yaji zamana a gidan nan yakare da mama.
Taso muje ki ga tsaraban mu don Allah kada ta tsanmani wani abu na sauko daga gado muka fito tare da ita.
A zatona baya falon amma ina fitowa yana zaune sai dai kwana biyun da banganshi na ya sake min sosai.
Gabana ya fadi don sai zuciya ta ta fara zargin ko dai yaya koma ruwa ne wai don yanayi yau da na gani akwai magana gaskiya.
Ganin shi zaune yana waya muryan shi kaman mai jin barci ko kasala haka ya kara tabbatar min da zargina akan shi.
Na nufi inda mama take zaune, cikin murmushi nace mama ashe alheri ya samay mune haka yau ?
Eh amma ai bai gama ba don banga ya nuna min naki ba duk cikin tsaraban.
Nace kai haba mama kullun fa ana bani don yau kawai ai ba komai bane kila ya manta da nine kawai.
Murmushin manya mama tayi tace ya manta dake Fatima, haba magana dai yana da dalilin yin hakan da yayi kawai.
Ya dago still cikin irin muryan farko da yake waya ba ko darr a ran shi ya ce, wai wanan yarinyar ban mata ba ban dai sayo mata bane ai na fada mata tun a cikin waya ba zan sayo mata komai ba.
O ko gadarare ya mike tsaye tare da gyara wandon shi da ya dan takure don zama yace eh maji.
Sai ya fice ko mama sai da tai mamakin wanan irin tsauri da yai mata yau ido da ido haka don ba halin shi bane bata ansa a tsatsaye.
Yana fita dakin shi ya shiga dakin duk a hargitse haka ya kwanta rubb da ciki don tun daren jiya yai mugun hadiye kwayoyi ko zai rags damuwan shi a ran shi.
Duk abinda nake hankalina yana ga yaya sadauki don haka nace wa mama zan shiga gurin gwagona don tana gari tana fama da ciwon kafa.
Tafe nake ina tunane abinyi sai wata zuciya tace min gwada dai ki gani ko zargin ki hakane ?
Ina tura kofan ga mamakina dakin da yake a rufe ko yaushe, sai na samau shi a bude, kamar na koma don na hango shi a kwance rubb da ciki kamar yana barci.
A hankali nake bin dakin da kallo har na hango wani farin roba saman dan stoll din dake dakin yana dagwara kaya akai,
Na jima gurin ina kallon roba don zargina ya zama gaskiya ko naga evidence da idona.
Zan juya naji yace Fatima,
Jikina ya dauki rawa kamar na ruga a guje don tsoro, ya ce may ya kawo ki dakina ?
Bance kallah ba nai shiru,
Yakara cewa uban wa yakawo ki dakina nace maki?
Ya dago daga kwancen dayake yana fuskan tana idon shi duk sunyi ja jajir dasu.
Bance kala ba sai karasa shigan danayi na taka har zuwa inda roban drugs din yake na dauka nace ga abinda ya kawo ni dama kuma nagani.
Komawa yayi ta,kwanta,lamo kamar ya koma,barci nikuma ina tsaye na kasa daga kafata nai bar mashi dakin shi.
Lokaci mai dan tsawo na zaci barci ya koma duk a tsorace nake a lokacin,
Nafara tafiya sai naji yai yar dariya da sauri naja na tsaya cikin tsoro da sauraren shi.
Ga tsoro ya kamani ban san gulman da ya kawo dakin shi ba don gani kwam kuma a part din samarin gidan gaba daya.
Hawaye ne na fara zubar wa daga idona a hankali ba tare da ya dago ba yace kuka kuma again cikin magana kamar rada ya fadi hakan?
Don Allah yaya kayi hakkuri dama zargi nake tun dazun dana gan ka a haka ?
Murmushi yayi tare da mikewa zaune yace, ashe bayan gulma har kin zama C I D ban sani ba ?
Haka kawai na tsinci kaina cikin karfin halin fadin gulman da nakeyi a inda ya dace nayi nakeyin shi ba hakana kai tsaye bs ga abinda ba damuwa na ba.
Fuska a daure yace, lalaima yarinyar nan ta raina ni wallahi sosai, zaki gane baki da wayo don gobe baki karawa wani bakin shishigin tsiya irin haka.
Wani irin naji cikina ya ansa kululu nace a raina yau ko na shiga uku nakawo kaina da kaina.
Amma afili nace duk abinda zakai min nasan akan kauna mama kai min don irin halarcin da take min a rayuwana komai zan iya yi akan farin cikin mama don bata nuna min banbanci ba a cikin ku.
Shiru mukayi dagani har shi ba wanda yai magana don kukan da yaci karfina a lokacin.
Ba tare da fargaba ba naci gaba da cewa why yaya why baka tausayin mahafiyan ka why please ?
Kai kadaine da namiji da Allah ya bata a rayuwan ta kaine take tunanen samun farin ciki a gurin ta.
Yan uwanka da ma mu dake a karkashin inuwan ku gare ka muke fatan samun budi a rayuwan mu,
Amma kai yaya baka tausaya mata baka jin kan ta baka tuna irin gorin da ake mata tsawon lokaci a gidan nan a kan ka why baka tausayawa kan ka da mahaifiyan ka ne please?
Kafi son ko da yaushe ka zama abin kyama ga al,umma da kuma abin kwatance a gari yaya kawai Allah kabar wanan harka ka dage da rokon Allah da bayar da sadaka akan Allah ya rabaka da wanan halin kodon goben ka.
Ina kaiwa nan na fara tafiya zanbar dakin yace Fatima, naja na tsaya tsaye cak guri guda.
Ido ya zuba min na dan lokaci yace wanan magana ta tsaya iya ni dake a nan.
Na girgiza kaina nace har abada bazan taba tona asirin dan uwana ba ga wani kai dai kadai tsoron Allah idan wani baigani ba ko yaji ai Allah daya hanamu shan maye yana kallon ka.
Murmushi yayi tare da mikewa tsaye daga zaunen daya ke ban tsan mani har ya kawo gareni ba sai ganin shi nayi a gaba na ido da ido muke kallon juna dashi.
Banyi wata alaman ta razana ko kadan kada ya gane a razane nake lokacin dashi.
Ya nuna ni da yar yatsan shi yace ban san koke wata irin shu,umar yarinya bace da baki da tsoro haka nima ina mamakin kaina da nake tausaya maki amma tafi babu komai zamu kara haduwa wata rana.
Nace kadai tausayawa mahaifiyar ka da kan ka kafin har mukai ga kara haduwan.
Kuma bani fatan haduwan ya kasance irin wanan zargin a kan ka sai da ya zama wani abin alheri can daban.
Roban kwayan na hannu na fita daga dakin tabi bayana da kallon mamakin irin karfin halin dake gareni haka.
Sam banda tsoro ko shayin wani a idona yadda ya hango cikin kwayan idona gaskiya ce sahihiyar ta na fada mashi kuma na fita.
Ina tafe ina sharan hawaye har nakai gidan gwagona sai da na samu gidan yana rufe tafita ke nan .
Na juyo na dawo gida tareda boye roban kwayan a jikina har sai da na kai part din mu ina shiga mama tace har kin dawo ne nace bata nan tafita.
Amma kuma ya fuskanki kamar kinyi kuka na dan yi yake nace kuka kuma mama?
Banyi kuka ba mama daga haka na shiga daga ciki sai kuma mama ta fara zargin ko dai tsaraban da sadauki bai kawo min bane ya bata min rai har nai kuka?
Ina kwance daki saman gadon mu kaina sama kafana suna zufe daga kasan gadon, na dan jingina jikina da kan gado.
Ban san shigowan ta dakin ba don nai zurfi ga tunanen da nakeyi a lokacin.
Fatima naji ta ambata abinda yasani saurin dago kaina ke nan ina kallon ta da sauri ina kokari gyara zamana da kyau.
Itama dai zama tayi daga gefe na kadan tare da kura min ido kamar mai nazarin wani abu a gare ni.
Abinda yaron nan yai maki ne yasa ki kuka ko?
Da sauri na girgiza kaina nace wallahi Allah ko daya mama ko kadan ban sa haka a raina ba.
To may yasamay ki kai kuka da fitan ki yanzu, don ba haka kifita ba a gidan nan.
Dukar da kaina nayi kasa nace a hankali ba komai mama,.
Yanzu har takai lokacin da zaki iya boye min wani magana a cikin ranki.
Da sauri na kara dago kai nace wallahi mama ban boye maki ba sai nai shiru.
Bazaki fada min ba ke nan ko?
Maimakon nai magana sai na sake kuka shiru tayi tare da kura min ido har tsawon lokaci can tace nace zancen tsaraban da ya rabane yai maki cin fuska kin ce a,a.
Wallahi Allah mama bashi bane kuma ba komai, ikon Allah inji maji ba komai kike wa kuka ba to may yakawo kukan?
Mama yaya ne sai kuma nai shiru don, na tuna da zancen alkawarin da nayi bazan fadawa kowa ba.
Hakali a tashe tace yaya yai maki may hankali a tashe take tambaya may yai maki Fatima ?
Fada min mana nace may sadauki yai maki ne wai,?
Taba ki yayi ko may ?
Nace da sauri a,a mama don nagane may take nufi da tambayana tabaki yayi.
To may yai maki nai shiru nace mama ba komai bane cewa yayi wai na faye yau shiyasa maza ke ganina .
Sai naji tai ajiyan zuciya tare da dafa ni tace kyaleshi ai munyi maga in don zancen Usman ne ya fada min yaron ba mai gaskiya bane.
Nace cikin kuka tau mama ta ce ki kwantar da hankali Allah zai kawo maki wani wanda yafi Kabir insha Allahu.
Tace karbi wanan kayan daga cikin kayan lefen da ya aje ne na debo maki kema a matsayin naki tsaraban.
Da sauri cikin girgiza kai nace mama a barshi wallahi ko kadan raina bai baci da rashin kawo min ba don ai yasaba kawo min.
Au kyautana ne kuma baki bukata ko may na girgiza kaina da sauri na sa hannu na karbi kayan dogayen riguna matsu kyau da masifan tsada har guda hudu.
Nace amma mama kaman kayan su yi yawa fa tace nifa na baki Fatima nace na gode mama.
****** ********* ******
Da yamma daya daga cikin rigunan nai kwaliya dashi kaman yadda suma su maryam shi suka saka sai dai nawa yafi nasu tsada da haduwa, nisa ba kusa ba.
Sam ban san yana cikin falon ba nafito cikin dogon rigan mai maroon clour sai tsakiya a bude yake an yi mai kwalliya da wani silk dark blue da duwatsu har kasa, hannun rigan manya manya ne shara shara dashi .
Kwaliyan yai matukar karbana fa kamshi turare na na white musk da ko yaushe shi nake shafawa a jikina da tufafina.
Haka kawai ganin shi zaune yasa kirjina bugawa a lokaci guda yana zaune cikin shiga ta kamilan mutane.
Masangalin kujera kawai na dafa nace ina wuni yaya ?
Kamar kullun wanan yaudararen idon nashi ya watso min ya na kallona a fakaice, da su.
Kai Bintu wanan hadaden rigan fa kuma maryam ke tambayana don bata san dashi ba.
Nace daga mai kauna na, a takaice.
Kan shi kawai ya girgiza don jin amsan dana ba maryam din a lokaci guda, wayancewa yayi don yasan inda magana ta dosa.
Na kalli maryam nace akwai wani tambaya ne kuma anty ?
Ai ni dama nasan da,wata a kasa tunda naga ba,a baki taki a fili ba nasan zance ya canza ke nan.
Nace wanan kuma zargin ki ne anty ni uwata mai kaunata tabani shi don tasan nina dace dasu.
Da sauri suka juya gurin Maji da idanuwan su suna mamaki wanan riga mai bala,in kyau yaya akayi tabani shi gasu.
Maji bata bada fuskan tambayan ba balle su san gaskiyan maganan don haka sai kowa ya share zancen.
Ganin yanayin shi duk a tsarge ya ke lokacin saboda yana ganin sai na fadawa mama zancen kwayoyin dana kwaso daga gurin shi.
Yana zaune ya rafka uban tagumi sai sauraren zancen, kanne shi yakeyi ba tare da yai magana da kowa ba sai kace wanda aka aiko ma wani sakon tashin hankali.
Daga inda mama take a zaune muka ji muryan ta tana cewa ku tashi ku bamu guri zanyi magana da yayan ku.
Hakan yasa muka mike daya bayan daya muka koma daga cikin dakin mu.
Shiko jin abinda mama ta fadi yasa shi saurin dago kan shi da sauri yasan ta faru takare kenan yanzu sai da munafukan yarinyar nan ta tseguntawa maji zancen nan aiko sai ball da yar iska gidan nan algunguma kowa ya huta.
Tace Baba na magana nake son yi da kai akan Fatima, yace shike nan yar iska tafadi ashe.
Ba karamin kokari yayi ba gurin gyara natsuwan shi tare da dan dagowa daga kujeran yana fuskantar uwar.
Mama tace ina son ka fada min gaskiya may ya hada ka da Fatima dazun da rana tashigo gidan nan tana kuka?
Yace maji ita may ta fada maki nayi mata da ta shigo?
Kai ma kasan halin Fatima da zurfin ciki da kyat na samu ta dan fada min wai kace tana kwaso samari kala kala a gidan nan.
Yanzu har wasu samari Fatima ke dasu ina bayan wancen da Allah baiyi auren su dashi ba sai wanan da kace baka amin ta dashi ba kuma ta daina nagani.
A jiyan zuciya ya sauke yace ta rufani ke nan ashe ai nazaci bata da,wayo ne ?
Tace tunda kai mata fada kuma taji banga abinda zaisa kuma ka kara matsa mata ba akan zancen.
Murmushi yayi yace maji ni fa duk abinda nake mata a saboda ke nake matashi don tana karkashinki ne.
Idan da a, wani dakin take mai zai kaini saka mata ido da daukan mataki a kan ta amma tunda bata son fada ai shike nan.
Maji tace dakata malam yarinyar nan fa amana take a gurina ka sani amma irin yadda naga ka dauko tsangwama mata bazan lamunci hakan ba gaskiya.
Yanzu irin cin fuskan da kai mata ka bawa kowa tsaraba a gidan nan amma ita ka hana mata kayi daidai ke nan Baba ?
Amatsayinta amma a guri na ina duk abinda kaga naiwa yan uwanka ita ma ya dace kai mata tunda ni bani banbanta tsakanin su.
Waya san ta hanyan da zata taimaka muna itama watarana shi mutum fa rana garw shi ta inda ba,ai tsanmani ba.
Yace maji yin haka bada wani manufa nai mata hakan ba kawai dai dama alkawari nai mata cewa idan bata gayar da mutum bazan mata tsaraba ba.
Tace wanan matsalar kace don ni na bude akwatin kayan lefen dake aje na zaba mata wanda ta dace da ita.
Ya dago kai kamar zaiyi magana sai kuma yai shiru can yace ai shike nan ko?
Idan kuma akwai abinda ya dace akara mata daga ciki sai abata suma su Amirah abasu man shafin da turare da sauran abubuwa suyi amfani dashi.
Tunda ba wani abin kuma za,ayi da kayan ba yanzu ai, ko ?
Kamar yaya ba wani abin za,ayi da kayan ba ka manta da maganan mahaufin ku ne da yace nan da wata daya ku fitar da matan da zaku aura.
Murmushi yayi yace maji ni ina zani na nemo mata nan da wata daya hakkuri dai Baba zai yi muna har lokacin yayi.
Mama tace wanan kuma maganan ku ne da mahaifin ku idan baka fitar va ai shi ya maka mata da kan shi.
Ya zaro ido yace haba maji kamana za,ace za aiwa mata kuma ai ni yanzu na wuce wanan ko.
Wancan ma da kukayi da farko ba,aji dadin shi ba balle yanzun ace za,a sake wani kuma again idan lokacin yi yayi ai za,ayi din ne maji.
Ina ruwana ina zaune ni a dakina matsalan ku ne da mahaifin ku ni banda na cewa ai.
Duk hiran da suke da uwan hankalin shi yana akan zancsn abinda ya faru da rana tsakani na dashi.
Mama ta kwala muna kira tace ku fito tun dan uwan ku bai fita ku kara mashi godiya ya baku kayan kwaliyan dake cikin akwatinan shi gaba daya wai ku raba ku uku.
Godiya mukai mashi sai dai yana kokarin ganin idona danake boyewa a bayan Amirah.
Mikewa yayi don wayan da akai mashi yafita lokacin naji dadin sakewa sosai a falon.
****** ********* ******
Sannu sannu na dan sake jikina na koma normal na bar zancen komai a raina sadai kallon mai bisa ruwa nakewa sadauki doni na tsinke da lamarin shi yanzu.
Maryam tafito tana tambayana na bata wani handout din muna chemistry na 200 level nace ta duba a cikin jakad litattafaina yana ciki don ina kitchen ina aiki.
Zaro takardan da zatayi sai ganin roban wanan drugs din dana dauko a dakin yaya tayi.
Saman gado ta zauna tana kallon maganin tare da karanta shi a fili ta furta drugs kuma a jakkan Bintu.
Hankalin ta ya tashi sosai a kitchen ta samay ni tace Bintu zo nan ganin hankalin ta a tashe yake yasa ni bin bayan ta zuwa dakin mu.
Sai da muka kai zaune ta zaro roban daga inda ta boye fuska a daure take ce min Bintu may ne ne wanan nagani a kayan ki?
Cikin kura min ido bata ko kiftawa don son jin bayani daga gare ni cikin damuwa.
Nace ba nawa bane anty nima dauko shi nayi a wani guri na boye shi a nan da kika gan shi.
Bintu fada min gaskiya a ina kika dauko wanan roban in ba naki bane ?
Na nisa nace wallahi anty ba nawa bane nagi maki kama da mai wanan halin daidai da rana daya ne ?
Tace shi ya bani mamaki ai nake son sanin nawaye ?
Nace na dauki alkawarin boye zancen anty don Allah kiyi hakkuri amma,wallahi ba nawa bane Allah.
Sai naji tace na yaya sadauki ne ko ?
Da sauri na kalle ta nace ni ban ce ba anty.
Amma kin san zaman su haka a gurin ki hatsari ne babba kuwa a gare ki ?
Yanzu dabanice nagan su akayan ki ba kuma nasan halinki may kike ganin zai faru ?
Nace nayi kuskuren barin su a tare dani amma na aje su don sheda kawai.
Tashi kiyi flushing din su yadda kikayi a ranan tun wani bai gani ba hankalin maji ya tashi.
Yadda tace din haka nayi na zubar dasu a cikin toilet suka bi ruwa suka wuce.
Nan na barta zaune tayi shiru tana tunanen dalilin da yasa na boye mata tasan cewa na yayan sune duk yadda akayi.
Da dare da Bashar yazo ta samay shi yadda ya fahinci bata cikin hayacin ta ya sa shi matsa mata da tambaya may yake damun ta hakane wai ?
Tace matsalan yayan mune yayana ina ganin kamar bai daina shaye shaye ba har yanzu.
Da sauri yace, kai may kika gani ban tsan mani yana sha ba kuma har yanzu gaskiya.
Tace koma may nene Bintu ta san komai sai dai tana boyewa ne, nan ta bashi labarin yadda mukayi da ita da rana.
Ya nisa bayan yaji maganan ta yace tabsa tunda kikaga taki fadi akwai magana gaskiya amma yaya akayi ta samu wanan abin a gurin ta in ma nashi ne.
Tace nima shi nake ta tunane nasan tayi hakane don farin cikin maji don kada hankalin ta ya kara tashi kuma ?
Tace nima abinda na fhinta ke nan hakan take boyewa don kada aji hankalin shi ya tashi amma ba matsala gobe da safe zanzo na kaiku makaranta anan zan fito mata da zancen muji.
Yadda suka tsara haka din ne kuwa da safe sai ga Bashar mun gani a jenction din gidan mu yana jiran mu.
Muna shiga muka gaida shi yafara hanya sai dai tuki yake a hankali, sai naji yace malama Binta ya garin dai nace lafiya kalau yaya Bashar.
Ya ce ranan sai mutumina ke fada mai ta,asan da kikai mashi da kayan shi ?
Da sauri na dago kai na kalli maryam sai na dukar da kaina nai shiru bance mashi uffan ba.
Yace Binta yaya akayi kika kwaso abubuwanan a gurin shi shiru nayi babu amsa.
Yace look Binta ba boyo ki fada min komai nai maki alkawarin bazan fada mashi komai ba akai don hanyan da zamu ceto rayuwan shi nake son mu bida a cikin sauki.
Nace shi may ya fada maka don nasan na daukan mashi alkawari bazan fadawa kowa ba wanan magana.
Sai Bashar ya nisa tare da buvun sitiyarin motar shi yace ina ganin baki fahince mu bane kawai.
Nace yaya Bashar kadai gane cewa nashine ne ko to abar maganan don Allah, kyau alkawari cikawa.
To shike nan na fahince ki yanzu, amma don Allah yadda Allah ya hore maki gane irin halin rayuwan da yake shiga ina son muyi amfani da wanan daman naki guri gano abinda ke saka shi a irin wanan halaiyar.
Sai yai kaman ya bari sai kuma ya koma ciki tsunbul dashi al,amari gaskiya akwai daure kai a cikin sa sosai.
Nace nima na fahinci haka amma gaskiya ban tsan mani zan iya ci gaba da wanan aikin ba saboda yai min warning sosai akan mashi shishigi ga al,amarin shi.
Zaki ya mana inji Bashar abinda nake so dake shine kamae yadda baki tsoron fada mashi gaskiya haka zaki daure ki ci gaba da fada mai a kai tsaye.
Murmushi nayi nace anya yaya zan iya hakan kuwa yace kwarai kuwa Binta ai zaki fitar da tsoro ne ga komai ki kama aikin ki,amma fa kuma kin san aikin nason jan mutum a jiki sosai.
Nace da sauri yaya zanhi in ja yaya sadauki a jiki mutumin da kullun yake cikin hattarana da tsangwama.
Yai murmushi kafin yace wanan kuma,wani haline nashi nan dai ya fara fada min ga yadda zanyi akai nace to ba matsala zan gwada nagani amma idan naga da,wahala gaskiya bazan yi ba.
Yace zakima iya tunda kina da hakkuri kawai ki dan sake dashi shine farko.
Muna kaiwa school ya sauke mu tare da min fatan alheri nace Allah yasa muyi nasara dai.
****** ********* ******
Yana tsaye ya bada baya waya yakeyi kuma a handfree yasaka wayan nashi a lokacin.
Magana yake da wata mace sai dai magan tankar fada sukeyi yake cewa na fada maki ni mace bata a gaba na yanzu.
Don haka ki daina yaudaran kaki don baxan aure ki ba koma zanyi aure yanzu akwai qualities din abubuwan da nake so ga matar da zan aura ke kuma baki da ko daya daga cikin su so kima daina yaudaran kanki a kaina.
Ban san may yarinyar tace ba sai ji nayi tace wanan kuma matsalar kine ni da kika gannin ban taba zina ba a rayuwa ta kuma akanko ba zan fara ba.
Da sauri na juya don nashige ciki sai nai karo da dutse ina batun faduwa naji ya riko ni bai bar wayan ba kuma bai sake ni ba.
Nace a kakausan murya sake min hannuna kaji malam, wani kallo ta watso min na ki shiga taitayinki kinji ko.
Sai da ya gama wayan ya juyo gare ni yace ashe kuma banda sa ido harkin fara lebe ne kuma ?
Cikin tsiwa nace, akan may zanyi labe Allah ha rabani da annaminan ci ni fita zanyi nagan ka kuma zan koma.
Murmushi yayi yace idan ma baki taba ba ai yau gashi kinyi ko?
Amma anyway zan baki bashin na yau don kin min alkawari a baya don haka nima ya kamata nai maki uzurin na yau.
Nace aini ba don ka nayi ba don mama nayi amma ba saboda kai ba sake min hannuna na wuce.
Yai dan murmushi kadan abinda bai saba yi min ba yace ba abinda yakamata kice ke nan ba Fatima kice dai kin boyeni don baki son ace ni din mashayi ne ko ?
Amma ko banza dai ni koma maye aikin min alheri ko Fatima don haka nima zanso ace nadan yi maki ko na rana guda nane kamae yadda kikai min din.
Cikin wani shu,umin murmushi yace min tafi sai kin jini nan gaba, nima,
Na dan kalli hannuna da yai ja saboda riko da yasha a hannun shi nace mugu kawai ashe yajini yace may kikace da gudu na zura zuwa cikin gida kada ya kamani sai ganin mama nayi a gaba na tsaye.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BA KI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
YA ALLAH DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA WANDA BAI BIYA BA ALLAH KA ISAR MIN AKAN MAI SHI,,,,
Suna zaune sai hayaniya suke a tsakanin maryam da Amira suna hiran wai sun kalli wani film din biri jiya da,dare shine suke hira a tsakanin su.
Ina zaune a kan kujera na jingine jikina saman makarin kujeran nai shiru ina sauraren hiran su.
Sai dai anihi na sha jinin jikina sosai daga irin kallon tsana da yaya sadauki yake min daga gefen da yake zaune.
Na fahinci wayan da nayi ne yanzu ya jawo min wanan tsanar haka to amma ai saboda shine ,aka gaisa dani din.
Hannun shi saman goshin shi ya dan dafe kai yakai bayan shi a makarin kujera yai kwanciyar balance saman kujera ta hanyar mike kafafuwan shi.
Ganin haka nima na murde nawa fuska babu wallawala acikin sa ko kadan.
Ganin yaki ya bar falon yasani mikewa ina tafiya cikin dan dan gyasawa na nufi kofan shiga daga ciki.
Yabi bayana da kallo a hankali yana duban yadda nake taka kafana still a cikin wahala.
Yace ke zo nan kawo kafan nan nan na kara ganin yadda yayi sai a shafa magani .
Kamar na wuce don yadda yake magana cikin nuna isa, da gadara kamar dan wani sarki shi mutum ne muskilin karshe kilama shiya sa yake cin kwallo don in ya kama sai ya kai gola kamar abin tsafi sai yaci kwallo.
Shigowan Maji falon ne, shi ya katse min zancen zucin da nakayi tsaye .
Sai maryam ke fadi lah Bintu ba dai wai tsoro kike ji ba haka tun dazun yaya yace ki kai kafan ya duba ya gani, ko sai an koma asibitin ne ?
Nace cikin daurewa ni kafata normal take don banjin komai yanzu,
Yadda nai magnan tare da dan murguda baki kadan yasashi cewa cikin takaici wanan yariyar typical yar kauye ce wallahi.
Shigowan mama yasa take kallon mamaki da son tambayan ko lafiya yace cikin rashin nuna tsoro ko damuwa.
Wanan local yarinyace ance tazo a duba kafan takewa mutane maganan nosenses, wai da kafan ma baka,barta ba sadauki?
Yanzun kuma may ne mata, maji, kawai don za,a duba lafiyan kafan a shafa mata magani shine abin magana kuma.
Maji zatai magana sukaji muryan mata kaman da dan yawa suna kwada sallama a kofan dakin maryam dake tsaye tafito don taga ko waye?
Suna gaisawa daya daga cikin matar tace ance a nuna muna dakin hajiya Atika da hannu Bintu tai masu kwatance su tafi can.
Su na dauke da akwatina sa sauran kayan tarkace irin wanda ake kai kayan lefen mace kayan aure.
Maryam na fadawa Maji ta ce kayan lefe kuwa a gidan nan kaya waye ke nan kuma.
Amirah tace kila Nafisa ce ta samu miji ko Rukaiyya, shine aka kawo kayan su.
Can muka ji suna fadin bamu ba aura wa yar mu mazinaci mai abin kunya abin fadi irin haka.
Nan dai suke ta sake bakaken, magan ganu iri iri suna aibanta Imirah dashi haka yasa duk muka fahinci cewa ashe kayan lefen da akakai na auren Imiran shine gidan matan suka dawo dashi, wai sun fasa saboda labarin da suka samu na abin kunyan da yayai wa yar mutane a gari.
Daga inda nake zaune nace Allahu akbar yanzu a take Allah ke gwadawa mutun laofin shi tun a duniyan nan.
Gashi dai Umma da kafatan suka je gidan su Rahama suka aibanta yaya uwar ta tace am fasa auren yaya da yar su.
Ranan kun, manta babu irin maganan da su mama basu fadi ba, a gidan nan su ke cewa aure sai da muga anayin shi shiyan nan.
Yau ga shi Allah ya mayar masu da martani abinda suka shuka tun ba,a je ko inaba sun fara girban abin su.
Masha yin da suke fadi abin kyama gashi sai a zauna dashi ayi koma hankali a kwance sabanin dan ta katon mazinaci da ko maza yan uwan shi tsoron shi suke ji balle mata.
Muna ta hiran mu hankali kwance ban san cewa yaya Sadauki ya dawo falon ba duk abinda nake fadi a kunnuwan shi.
Ganin Amira tana kallon kofan shigowa falon yasani juyawa naga may take kallo ne wai.
Ganin shi nayi tsaye kinkam ya harde hannayen shi a saman kirjin shi,
Ya zura min ido fuskan shi babu walwala ko kadan a cikin shi ya sha mur sosai dashi.
Ina ganin shi
tsoro ya shi ya dan kamani indai har baiji abinda nace gamay da tsohuwar budurwan shi ba.
Sai kawai nai shiru tare da dukar da kaina kasa dariya maryam takeyi tace kai Bintu yanzun fa kike ta masifa kan anwa yayan ki wullakanci yau gashi Allah ya rama mashi.
Maimakon nayi magana sai ma dan kai kaina saman kujera nai shiru tare da lumshe idanuwa na kawai.
Fuska a murtuke ya karasa takowa zuwa tsakiyan falon yana cewa wani gulman takeyi wa mutane ne wai?
Nace ai bani kadai bace magulmaciya kowa ma anan gulman yakeyi akan abinda ya faru.
Yace see your mouth muna fuka ta iya maida magana kamar wata tsohuwa can da ita .
Yarinyar ta iya babban magana da gulma kamar bayerabiya.
Haushin abin da ya fadi naji nace kai nifa wallahi in mutum bai daina kirana da mugun suna ba wallahi zan ramane wata rana.
Ni natsani wanan kalman na munafuka da kake kiramin in hakane ai kaima mugune na karshe.
Cafka guda yai min akaina na yanka ihu da dan karfi ido suka sako muna gaba dayan su da mamakin yadda halaiyan yayan su ya canza yanzu da irin mugunta da yake min.
Bai sake min kai ba nikuma sai fadi nake wallahi zan fadawa mama don Allah yaya ka bari wallahi akwai zafi sosai.
Ba kince ke baki da kunya ba bari na gwada maki mugu nake naja shegen kan nan mai tsawon banza ba gyara.
Ji kan ta kamar ba mace ba kullun a yamutse ko gyara bata iya ba irin na mata, sai shegen gulman tsiya karama dake.
Wai Sadauki may yake damunka ne ban san wanan irin iskancin ba da kake wa yarinyar nan a gidan nan
Tace karya take ba mugun kake ba dubi yadda ka rike mata gashin kai kaman wani mayanki.
Ya dago kai don jin muryan mama a bayan mu ya koma ya dubi gashin da tace ya rike min bai sake ba har lokacin.
Yace wallahi maji Fatima ta raina ni gulmana nasamu tayi da su Amirah shine nake koya mata hankali.
Koyon hankalin ne a haka?
Yace maji wallahi duk kin bari ta raina ni Allah ko.
Tace rufe min baki mara kunya kawai ina maka kashe di akan wanan yarinyar amma bakaji da Baban ku zan hada ka tunda ni ka raina ni.
Jin abinda maji tafadi yasa shi sake min kai tare da kutawa yace sai na balballa ki wata rana.
Ya juya yana gyara hannun rigan shi da yai dan squeezing.
Maji ta girgiza kai tace sai nayi maganin ka wallahi akan Fatima.
Yana fita daga falon ta juyo gare ni tace Fatima ki kiyayi sadauki don ba hankali gare shi ba kada ya halaka ki a banza.
Wallahi mama ban mashi komai ba kawai ya samu muna hirane shine ni ya sauke haushi a kaina.
Tace na dai fada maki ki iya kanki dashi mugun yaro ne bai dariya sai bakin ketan tsiya kawai.
Amirah tace kai maji yayane kuma mugu yau ?
Ba mugun yake ba may yake?
Maji wallahi in kina shiga tsakanin yaya da Bintu watarana fa zakiyi kunyane barsu kawai inda kika gansu a dunkule.
Maganan da Maryam tayi yasa maji kallo na nace ni wallahi mama karya take min ba,wani abin dukule dana sani.
Shiru tayi tare da shigewa daki tabar munan falo maryam na fadi muna ganin wani sabon sallo a gidan nan.
Na ce don Allah anty bari kada ya balballani kinji dai ya fadi ni yanzun ma,in yashigo gudu zan dinga yi yafi min wallahi.
Hummm kamar da gaske nifa nasan komai wallahi.
Tare muka hada baki da Amira muna cewa kin san komai kamar yaya fa?
Tace ni wallahi tun a asibiti ranan na kara gane komai.
Jifa yadda yaya ya rugumay ki yana lalashin ki.
Nace kai anty maryam wallahi kada ki kulla min sheri don Allah rufa min asiri kada kisa yai ball dani a gidan nan.
Shidai kawai ya tsanine yasa yake min haka wallahi in gaskiyane yai maku haka mana.
Sai naga ta sa dariya tace ji min wanan fa yai muna haka mu kannen sa.
O ni ba kanwarsa bane ke nan ko ?
Koma dai may kike ai zamu sani watarana Allah dai ya nuna muna lokacin kawai zakuce na fadi ai.
****** ********* ******
Tafiyan shi yasa na sake jikina sosai don yanzu kusan wata biyu bai garin sai da suna waya da kowa a gidan.
Ko ina gurin idan an miko min bana karba sai dai nace ace ina gaidashi kawai.
Idan sun fada mai sai yace rabu da silly girl kawai inta bata iya bugawa mutum ta gaidashi ne.
Ranan da yai nasara a gurin wasan su duk kasa shen duniya sai labaran nasaran da,team din su ya samu sukeyi .
Ranan Baba da kanshi ya shigo har dakin mu gurin mama yana ta washe baki da fatin ciki yana cewa.
Maijidda kinga iko Allah ashe kowa da inda Allah yai mashi tushen arzikin shi.
Yanzu akan wanan wasan ball din Allah ya daukaka wanan yaron haka?
Yau mutanen da suka bugo min waya suna min murna da farin ciki Allah ne yasan yawan su wallahi.
Yace ba abinda zamuyi sai mu kara godewa Allah da yasa haka ne silar shiryuwan yaron nan dakuma cigaban shi.
Da yanzu yana nan yana zaman kunsa muna bakin ciki da bacin rai zube nakashe a cikin garin nan amma yanzu kinga yadda Allah yai ikon shi akan shi.
Murmushi mama tayi tace nima abin yau har mamaki nakeyi mutanen yanzu sun mayat da harkan ball kamar wani abin addini.
Baba tace Alokaci muke muddin baizai hana shi addinin shi ba ai da sauki al,amarin.
Mamatace na kulla tun fara wasan shi bai wasa da harkan addinin shi yanzu ko kadan.
Allah ke nan inji baba yace shiyasa ko yaushe adduan iyayye keda tasiri sosai akan yaro wallahi.
Ni matsalata guda shine ya aje iyali don gaba dayan su na fada masu su fito da mata suyi aure hakanan.
Yanzu shi wanan shedani gashi yarinyar tace ta fasa batayi kinga ni duk abin ya shige min duhu wallahi.
Mama tace al,amarin sai adduan mafita yana gurin Allah Allah yasan dalilin wanan jerabawan da muke cikin shi.
Da yamma yaya ta bugowa mama waya lokacin duk muna zaune a falon sun gaisa naji tana mashi murnan samun nasaran da sukayi ban san may ya fada mata ba sai dan murmushin da tayi kawai a fili.
Amirah tace abata su gaisa dashi itama sun dade da ita suna hira yace abawa maryam itama dai sun dauki lokaci dashi sai halin ta takeyi na yaya ka,sayo min abu kaza ka sayo min kaza.
Tace yaya ga Fatima ko may yace naji ta kwashe da dariya kawai tana fadin mutumiyar ce fa gata ta taso takawo min wayan.
Na dauka tare da fadin salamu alaikum sai naji yai murushi yace wa,alaikis salam.
Yaya ina wuni?
Silly girl idan ban wuni ba zaki jini, yanzu ke baki ji kunya ba ke baki iya kiran mutum kullu gaki nan kamar wata bakauya can.
Hmm kawai nace mashi yace yar kauye kawai ai zaki gane kuren ki bari na dawo zamu hadu.
Nace ni bakama iske ni don da naji zaka,dawo zan gudu na koma kauye inda nafi wayo.
Ai bako isa ba,wallahi don har kauyen zanje na dauko ki nace wa Baba gudu kikayi wa maman ki.
Murmushi nayi har fararen hakorana suka baiyyana a fili.
Nace munyi murna Allah yasa afi hakan nan gaba.
Yace nagode da,adduan ki.
Na mikawa Amirah dake kusa dani wayan maryam tace wai har an gama fadan ke nan muushi nayi na zauna kawai suna hira da Amirah yana fada mata wai may yasa aka bani waya bakauyan daba tako iya waya ba ma.
Kai, yaya wallahi kaima kasan yanzu Bintu ba bakauya bace kana dai mata sheri ne kawai.
Maryam tace abata ta manta da wani magana bata fada mashi ba.
Amirah zance kusan halin rayuwan su daya da yayanta bata faye magana ba ita kamar maryam.
Ga ta da daukan kai da son girma yar gaye ce ta karshe ga tsabta da iya,kwalliya sosai gare ta.
Maryam din ma ba laifi gaskiya amma ta fiso son jama,a kamar mahaifiyan su hailayanta yake, ita don tana da son mutane gata da saurin sabo.
Nayi sabon saurayi shima dai yana da mata daya da yara biyu yana aikin banki ne shi sunan shi Usman.
Shima Usman gaskiya ba laifi sai dai baida hali irin na Kabir, din shi mutum ne mai son daukan aji da kuma nuna shi wani ne.
Ban faye son shi ba sosai don halin shi ni gaskiya bai min ba yana da son karya sosai.
Ranan da Nafisa ta gan mu tare dashi a kofan gida yazo muna hira yadda naga ta rude mashi ya sani tsinkewa al,amatinta.
Ranan na fahinci, halinta yai nisa bata da kunya bata da ta ido don yadda ta nuna mashi ra,ayin ta afili bata boye ba.
Ina fadawa maryam abinda tai min tace kyale yar iska nan tafi auki aishi ba jahili bane yasan ko ita wacece da ganin ta.
Exam din mu na shiga 300 level yazo don haka ni yanzu ba komai a gabana sai karatu sai ko idan na fito zanyi wani aiki.
Awala nayi zanyi sallah la,asar sai na fito falo don nayi sallah don babu kowa a falon mama tana ciki tana wanka don duk yamma sai sunyi wanka sun yi kwalliya kafin dawowan Baba gida.
Amirah ko tana ciki tana chatting da wayan ta tun bayan azahar takd daki kwance don bata sallah.
Maryam tafita tace zata wankin kai don kanta yana damunta da kaikayi wai.
Bayan na idar da sallah nacire hijjab dina na jawo littafina na fara dubawa don nasan in ban dage ba akwai aiki a gareni don ba wani mugun kokari ke gare ni ba.
Saye nake da dogon rigan atamfa a jikina mai dinkin bubu anty Amira akaiwa bai mata ba tabar min shi ni dinki sai ya karbe ni kamar ni aka dinkawa shi fun farko.
Ban san shigowan shi ba don kaina yana a duke a lokacin, yana tsaye cikin fararen swoth na maza da bakar riga ta ciki mai dogon hannu.
Yana tsaye daga kofa tsayin minti biyar ganin yadda na koma yai matukar firgita zuciyar shi sosai.
Don min kuwa yaga wata biyun da yayi na matukar canza mashi a idon shi, kallona yake ko kyaftawa baiyi .
Wani zazzafan ajiyan zuciya ya sauke wanda yai daidai da jin kanshin turaren shi a hancina abin da yai sani saurin juyo a firgice kenan na kalli hanyan kofan.
A firgice na dago kai ina kallon shi, yana tsaye ya zura hanayen shi a cikin aljihun wandon shi gami da zuba min idanuwan shi.
Gaba daya na rikice da ganin shi na dan dago ina fadin a yaya sannu da zuwa.
Bari na fadawa su mama kila bata san da zaka daao yau bane, cikin lokaci daya nake fadin haka tare da mikewa tsaye.
Yace see you haka ake taron mutum duk kin bi kin wani rude dake bakauyan banza kawai.
Ban tsaya na karasa sauraron shi nidai na shig ina cewa mama, yaya ya dawo.
Ya tako zuwa ga kujera ya zauna tare da harde kafafunan shi, lokacin na kara fitowa na nufi kitchen don na kawo mashi ruwa.
Nafito da ruwan a jug lokacin su mama har sun fito ko na ce fa ruwa yaya.
Yace ba komai ne sai ruwa yar kauye?
Mama tace tau bisimillahi Allah zaka fara ke nan kuma ko kadawo takura ya dawo mata ke nan kuma.
Ya dauki cup din ruwan ya tsiyayya yace mama in ba shirmay taba ruwa kawai zata kawo min.
May kake son takawo maka runda ba wanda yasan da zuwan ka yau din balle muyi maka tanadin wani abu.
Nikan in aje ruwan na koma inda littafina yake nafara tattara su na kwasa zuwa ciki.
Ina kuma zaki ke kuma bayan ga yaya ya dawo zaki fara shegen shigewan dakin ki kenan kamar kinga kura shi yasa yake maki rainin hankali ai.
Na dan yi dariyan yake nace mama dama zan shiga ne na karasa karatuna aciki.
Zauna nace maki ba idan zaki shi dai zai fita ya bamu guri inya gama abinda yakeyi.
Ya dan kalle ni ya girgiza kai , ya bude baki cikin kyarmar murya yace, yanzun kuma da dawowa na Fatima zaki kulla min sheri kuma ?
Na dan kada idanuwa na nace, cikin yanagin yatsina nace, nikan ban maka sheri ba kaine dai kaiwa kan ka.
Yace wallahi maji yar na taki munafukace yanzu dubi da zuwana ta hana ko na samu dan kulawa daga gare ki da nai missing tsawon wata biyu da kwanaki.
Bako so hakan ba da baka dawo muna da mugun halika ba yanzun ina laifinta taga bako takawo maka ruwa kuma ka gwatsale ta haka.
Nidai hada min wanan fruits din da kike hadawa nasha don da kewan shan shi na dawo saboda can wanda muke saye babu dadi.
Murmushi maji tayi tace kai dai baka da kunya wallahi yanzun fa ka gama zaginta kuma kace tai maka aiki.
Nace bamu da fruits sun lalace wanda ya rage dariya Amirah tayi tace wallahi maji maryam dama ta fadi kibar shiga tsakanin su.
Ke kina fada kada ta hada mai itako kinga sai kokarin hadawa ma take watau tabaki kunya.
Nace hai Anty nifa don kawai naga bako ne yau yasa yabano tausayi zan hada mai amma kada ki hada ni da mamana please.
Murmushi yayi yace bari na buga Bashar yazo min dashi yanzu don Allah a hada min kafin na fito don yau a gajiye nake da safen nan fa na shigo kasan nan ban huta ba na kamo hanya don nazo na gan ku.
Ai ka kyauta inji Maji.
Ya ciro wayan shi ya kira Bashar yana sheda mashi ya kawo mashi fruits masu kyau yanzu za ai mai amfani dasu ne.
Bashar yace kai nifa yanzu ina hanyan dauko madam dina daga saloon ne kakoga bukin magaji bai hana na magaiya.
Kai dai kasani nidai na fada maka yanzun nake so kada kaje ka tsaya bakin I love you din ka can.
Dariya Bashar yayi yace kai da baka san shi ba ai sai kaita zama ta zuru kana sa yara aiki.
Watsewa zasuyi soon su barka da maji muga tsiya tunda ka zama tsohon tazuru.
Murmushi yayi, kawai ya kashe wayan, saida ya mike yake cewa wai ina wanan sodan yau ta tafi, maji tace maryam ke nan ko?
Yace ita fa ban ji motsin ta bane tunda na shigo gidan.
Ta tafi gurin gyaran kai dazun yanzu nasan ai tana hanya kila.
Yafice daga dakin a gajiye dashi uwar tabishi da kallon sha,awan yadda taga ya koma mata yazama wani babban mutum yanzu a idon ta kamar ba sadauki ta mai tabara ba.
Maryam ce ta shigo dakin da ledojin fruits da murnan ta tana ina yayan yake tana wani dube dubbe da idon ta ko ina.
Ya tafi wanka inji Amirah ta bata amsa tace yakawo muna tsaraba ne ?
Kai haba anty daga dawowan mutun baiko huta ba kina tambayan tsaraba.
To na hana ko zaki hana kuma ya bamu tsarabane yar gidan mugu.
Murmushi nayi nace ni a suwa?
Rufamin asiri na zauna da Fatima Bintu takafin kisa a canza min suna Binta munafuka.
Dariya tayi tace yanzun ko indai yayane baida wuya ajiku da dawowan shi nace yaushe kuma ai har ya fadi ko.
Murmushi mama tayi tace ni na,rasa wanan munafuncin da,sadauki ke kirawa ya ta.
Nace mama ni nasani barshi kawai inko don wanan ne ko gobe yayi shi sai nai mai munafunci.
Eyye wallahi maji wuyar yar ki yai kauri haka ashe yanzu yaya sadauki kik fada wa hakan ai kin fi kowa sanin halin shi dan kafan ki kawai ya taka amma kika ishi mutane da ihu,
Nace wallahi anty ban ma son na tuna don ba karamin wuya nasha ba a gidan nan.
Muna jin shi ya kara shigowa amma wanan karon ba dakin mu yazo ba cikin gida ya shiga gaida sauran iyayyen shi.
Duk da su diyan su basu zuwa gaida mama sai Sagir ne mai kokarin hakan cikin su don shi gaskiya daban yake a gidan sabodashi uztaszu ustazu ne haka.
Tare da Bashar suke ashe sai da suka shigo falon mu ne muka san da hakan,
Maryam da bata gan shi ba tafito da saurin ta gudu gudu tana fadin yaya sadauki ashe kana hanya bamu sani ba cikin murna da fatin cikin ta.
Ganin tare da Bashar suke yasa ta dan rage rawan kan da takeyi sai naga tawani noke cikin kunya ta dan boye bayan kujera tana fadin.
Yaya har fa wata biyu kayi da tafiya, gaskiya mu ka daina dadewa haka muna missing din ka sosai wallahi.
A hankali yace maryam nasan ai ba komai kikewa wanan tambayan ba sakon ki ne kuma ban sayo ba tunda ko murna baki min ba.
Tace wallahi yaya aiko nafi kowa murna tambayi maji kaji har party nai muna ranan ai nace ke dawa kukai party ?
Lalai ma Bintu sheri zaki kulla min don ki hanani samu wallahi na gane shiyasa yaya ke ce maki yar hana ruwa gudu.
To anty wai yau kuma lafiya naga kin wani boye bayan kujera kamar wata mara gaskiya kifito fili mana kowa ya gan ki .
Murmushi Bashar yayi nace sai cika bakin karya amma kina ganin yaya Bashar kin wani boye can bayan kujera to mun dai san komai mu dai ayi buki musha shagalin mu ko Anty Amirah?
Munafuka kawai wallahi yaya na yarda Bintu munafuka ce da gaske shegen saka idon tsiya gare ta kamar wata yar sandan ciki.
Wait, may naji wanan yarinyar na fadi ne wai kai mugu ashe ka zama dan akuya ne haka ban sani ba.
Dariya Bashar yai mashi yace akan may don ina son kaunata ko may kai wa ya hanaka fitar da naka sai wani kwanaye kwanaye kake wa kan ka abari ya huce dai shike kawo rabon wani.
Na kawo masi salad din sosai suka sha shi sai santi Bashar keyi yace kai mutumina kace min ka huta kawai.
Fuskan shi a daure yake bashi amsa a zazafe yana fadin wallahi zamu bata dakai idan kaja min matsala da raini Allah Bassh.
Wayan shi da aka kira ne ya katse masu challenges din junan su da,sukeyi.
Sai da ya ja dan tsuki yace ya akayi ne cikin daure fuska da mace yake wayan kuma tambayan shi take yau she zai dawo ne wai ?
Yace yau fa nazo gida shine kike tambayana yaushe zan dawo ko ganin mumm ban gama ba ki dai bari zan kiraki idan na fita.
Daga inda muke zaune sai naji wani dan abu kawai a raina ban dai san dalilin jin hakan ba.
Shiko yana kashe wayan yana dago kai inda nake zaune yana fadin ke zo kwashe kayan nan kada wanan mara kunyan ya cinye kwanonin gaba daya.
Fuska na yana a hade take ya fahinci ban cikin good mood a lokaci guda na koma haka to why ?
Sai muryan yaro ya ratso a kofan falon mu yana fadin wai Usman yana wa Fatima sallama a waje.
Maryam tace ga mr love lover din ki can ya iso nasan sun taso ke nan yazo ya damu mutane.
Na yunkura ina fadin babu ruwan ki anty ba dai ke yake damu ba ai, lah yanzu Bintu rashin kunyan naki har yakai haka a gaban su yaya zaki fice I love you ba kunya.
Sai ga mama tafito daga ciki tana fadin ke Fatima kin bar waya a daki sai faman ruri take ita kadai.
Na karbi wayan a hannun mama naga Usman ne nasan yakira ba,a dauka ba shine ya aiko yaron.
Hijjab din Amirah dake kusa na jawo na saka a jikina ina gyara wuyan hijjab din naji yace .
Ke bana ce ki kwashe kayan nan bane ina zaki haka kuma ?
Sai ga yaron ya dawo yace wai yace don Allah tazo yanzu yana sauri ne an kusa yin sallah.
Nace kace mai gani tafe yanzu don Allah.
Mikewa yayi kamar zasu fita shi bai fita daga kofan ba bai shigo ba ma,ana ya tare hanya ke nan ga Bashar daga waje tsaye yana jiran shi.
Na fito daga kitchen na gan shi a gurin tsaye a dan raunane nace zan wuce.
Tankar da dutse nake magana don ko motsi baiyi ba .
Ganin haka na dan jingina jikina gefe a bango ina kallon kafan shi dake cikin socks.
Waya na yai ruri na dauka nace gani tafe ai yanzu don Allah.
Bata hanya mana ta wuce ko kuma wani sallon muguntane haka kace kuma ga abinda tai maka yanzu.
A dan tsorace da jin muryan mama ya ja baya kadan nazo na wuce shi har hijjab dina yana gugan jikin shi.
Nan na fita na barsu na samu Usman zaune a motan shi ya saka kida na gaishe shi tare da tambayan shi yaya aiki?
Yai murmushi yace aiki Alhamdullahi daga can nake nace bari na biyo na gan ki kafin na isa gida don idan na shiga gida yau da wuya na fito kuma again.
Na dan dariya har hakora na suka fito nace anty na itama zata nada nata kambun ke nan ko?
Shima dariya yayi yace ai Nabila matsalace wallahi an samu wanda ya kai mata gulman ina neman ki, kuma tace min wai daga gidan nan aka fada mata.
Nace ai ko sai ka bari kada ku samu matsala da matar ka yace akan ta zan daina son abinda nake so sai dai ta san nayi.
Ban san sun fito ba sai da naji yace ikon Allah dama U F a gidan nan yake ne shine har na dan juya naga suna fitowa daga cikin gida.
Nace mai eh ai yayana ne a gurin maman shi nake zaune.
Kafin su karaso har ya fito daga motan shi naga ya nufe su yana dariya ya mika masu hannu.
Sai dai shi gogan barka kawai yace mai ya zagaya ya shiga mota hakan bai ma Usman dadi ba harni din ma dake tsaye ina kallon su.
Ban san gulman da yakaini daga ido na kalleshi ba sai ganin shi nayi ya sha mur fuskan shi tamau yai min alama da zaki fadi da ido kawai.
Ko da Usman ya dawo yake ce min ashe ko abinda ake fadi akan dan uwanki da gaske ne kuwa ?
Ance ba ruwan shimana amma ni sai naga ya wani basar dani ko don yagan ni da kaunar shine yakawo hakan.
Nace ai ba ruwan shi kila dai akwai abindaya bata mashi rai ne kawai yace Allah yasa ba don ni bane dai ?
Yana nan har gap da magariba mukai sallama ya wuce abin shi ni kuma na ahiga gida ina tunanen halin yan gidan mu har wa ya gane gidan su Usman yaje ya fada wa matar shi magana.
Suna barin gurin batare da ya kallo Bashar ba yace waye wanan guy din , Bashar ?
Wa wai wanda ke tare da Fatima yace shi mana a ina yake ne ?
Dan nan garin ne mana ni nasan shi da dadewa ina ganin kaman aikin banki yakeyi ne ai.
Sai dai guy din dan karyane tun dana san shi bai aje kan shi kusa ba akwai shi da karya sosai wallahi.
Zai iya kashe wa mace kudi sosai don ta so shi amma yana da aure don gaskiya na san na taba sanin yai aure a baya.
Tsuki yaja yace, wanan yarinyar ko ina take kwaso maza haka kamar ita kafai ce budur wa a gidan nan?
Dariya Bashar yayi yace kaida may kake nufi ne wai wanan tsaleliyar budurwa haka wa zai ganta ya barta ko don ma dai tana da kamun kai bata da rawan kai ai da yanzu kofan gidan ku ya cika da samari.
Da sauri yace wallahi da naci uban ta kuwa Allah.
Dariya sisai Bashar yake mashi yace oho dai indai mutum yace girman kaine ai gurin zurfin cikin tsiya sai asha mutum a banza.
Kafito fili kawai kabada kai bori ya hau ka tsaya kana wa mutane kwanaye kwanayen banza haka.
Wallahi Bassh kana son ja min raini Allah ni irin kane da zan bayar da kaina ga karamar yarinya haka nagane a gurin wanan yarinyar karamar yar kauye ban da tarin kauyanci.
Fatima ce yarinya U F ?
Ba yarinya bace tsohuwa ce ke nan ko ?
Sai ja tsuki tare da kawar da kan shi ga titi sai dai cikin zuciyar shi tunane yake yadda mazan yanzu basu jin kunyan hada halaka da yara kanana haka?
Wai to kai ban san yaya kake daukan kanka ba fa wanda ko 28 bai cika ba kana ta daukan kanka wani old man can.
A ganin ka ba ni kan ai nasan yanzu nakai yadda baka tsanmani don kagan ni ban girma ko ?
Dariya Bashar yai mashi yake ce mashi niko nafi kowa sanin yaya kake ai ka girmi duniya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
DUK WACE TA TURA MIN NOVEL GA WANDA BAI BIYA BA ALLAH YA SAKA MIN AKAN MAI SHI,,,,,
Fuskan ta a daure ta watso min harara tace shige ciki da wanan wasan banzan naku, simi simi nabi gefenta na shige cikin gida.
Binshi tayi da kallon mamaki shiko ko a jikin shi saima gyara hannun rigan shi yakeyi kawai.
Mama batai mashi magana ba sai kutawan da tayi ta shige ciki yace a fili i will dealing with you silly girl kawai.
Duk nabi na takura kaina sai jira nake mama tai min maganan amma shiru babu zancen haka yasa na sake gaba daya.
Rayuwa tana ci gaba yayin da takuran da sadauki ke min bai fasa ba don duk wani aikin shi nice zai saka komai wahalan aikin kuwa.
Zancen Maryam da Bashar har ya kawo gida yanzu don iyayyen shi sunzo gurin Baba.
Sadauki sai da ya dauki zafi sosai da Bashar har ya gaji ya sake don kan shi don Bashar din ya nuna mashi halin ko in kula ga yadda yake nuna mashi .
Halin zaman kishi na gidan su mama yana nan daram bai gushe ba don sai da suka samu mahaifiyan Bashar da cewa don may zata yarda ta hada zuria da wa yan nan mutane masu jinin tsiya fakirai masu gadon tsiya.
Inba yanzun ba da saudauki ya samu abakin may Hauwa,u take a gidan wace bata iya mayar da taro sisi zuciya ya mutu mata.
Amma dai yanzu ai Alhamdullahi ko don dama azziki ai gida biyu ne ko kai kayi ko danka yi ?
Mahaifiyar Bashar ce take tambayan su da hakan tace ai shi arzikin da yafi na iyayye dadi don zaka koma tankar basarake ne.
Baku jin ance bayan wuya sai dadi ba, dama cewa kukayi yarinyar bata da halin mutunci ne kila da sai na duba.
Amma Alhamdullahi, na zauna da yaran nasan halinsu don haka aure ne idan Allah yayi a tsakanin su nafi kowafarin cikin hada zuria da kamilan yara irin zurian maijidda a duniya.
Sai kuma suka fara cacan baki wai sun gane dama,kwadai ne kawai ya kai Bashar ga maryam don dan abinda yake samu ga,sadauki din.
Dama sun sani ai don haka ya raba shi da kowa nashi ya manne mashi kamar cingun.
Da,Bashar ya dawo ake fada mashi bai nuna bacin ranshi ba don yasan zasu iya hiya da hakan ma.
Amma yana barin gida direct kasuwa ya nufa gurin Baba ya fada mashi komai yace ai masu Umma iyaka dashi da uwanshi.
Ran Baba yai matukar baci sosai haka yasa shi dawowa gida a lokacin yai sa,a basu jima da dawowa daga gantalin su ba ke nan.
Ganin Baba gida ba lokacin dawowan shi ke nan ba yasa kowa mamakin ganin shi cikin wanan lokacin.
Gaba dayan su ya kirasu basuyi tsanmanin zancen bane sai da Baba ya tambaye su da cewa Atika ke da Asiya ina kuka tafi ne yau ?
Wana ta dubi waccan suka fara a tsakanin su sai umma ce yar gadara tace asibiti muka shi gaida Hanse yace abisa umurnin wa kuka tafi?
Yace bama wanan ba don na riga na barku ga Allah kan fitan da kuke yi bada izini na ba a gidan nan.
May ya kaiku gidan marigayi salisu mai engine ?
Da mamaki mama ta dago tana kallon su sai hjy kubura ce tace gidan Alhaji salisu mai engine ai gidan su Bashar din da zai auri mayam ke nan mana.
Yace eh can din?
Shiru sukayi sai Umma tace da muka je ance maka munyi wani abin ne acan.
Yace mai zaihana kuyi tunda shi ya kaiku yace da farko da Sani ya fada min kuka soke zancen auren sadauki da Rahama ban yarda ba sai yau din nan nayar da da hakan don kaidin ku ya wuce yadda nake tsamanin ku.
Na dauka duk wani "da da ya fito daga tsatsona kamar kuma dan kune a gidan nan kuma.
Ya girgiza kai yace ashe nayi kuskuren yin wanan tunanen a kanku don ku din nan ba abokan zaman alheri bane a gareni tun da har kuka, iya wanke kafan ku kuka tafi soke auren yar yaruwan ku.
Salati suka saka suna fadin yaushe akai haka su sheri a ka kulla masu kawai daga sun tafi, gaida mahaifiyan shi kawai.
Yace to yanzun dai Bashar ya samayni ya roke ni nai maku kashedi akan gidan su da uwarshi don haka duk wacce ta kara shiga harkan shi duk abinda yai mata ita tajawa kan ta tunda daini bada izzina na kuke fita ba gidan nan.
Abin bakin ciki da rashin sanin ciwon kai ace kun fi son yaran nan suyi ta zama a gida suna shashanci kamar yadda diyan ku sakeyi suna bata min suna a gari.
Abinda Nafisa keyi a garin nan waye zai aure ta a haka da ita watsatsa yau itace wancan party gobe itace gidan mashaya gata kuma gata wai a kungiyan yan madigo a gari.
Da sauri Umma tace kan yar ka yar gwal kada ka kulkawa diyata sheri don da baifi daba a duniya.
Yace sheri kan Atika aike kika kulawa kanki ke da baki kaunan dan wani da karuwa kina ganin Allah zaibar naki yadda kike so ne ke ?
Ran Umma ya baci kan bankada asirin Nafisa da ya yi a gaban kishiyoyin ta nan ta hau sababi tana borin kunya.
Yace magana daya ya rage gareku yanzu shine daga mazan har matan duk kowa ta fito da miji tai aure su bar min gida na hakana na huta da fitina haka.
Ya girgiza kai cikin takaici jin borin kunyan da Umma ke tayi wai bai kaunan ta ita da diyan ta agidan dabakin shi yake kulla masu Sheri don ya gyara zuciyar masoyan shi.
Shidai yafita bayan yai masu warning da gargadi mai karfi kan duk wace ta kara fita bada izinin shi ba har yaji sai tabar mashi gidan shi.
Maji ta dawo dakin ta cike da mamakin wanan irin bakin jinin da mutanen nan suke gwada mata haka.
Nan take fadawa yaran abinda su Umma sukajeyi gidan su Bashar daga inda nake nace ai sun kai karshen gulma indai gidan su Bashar ne Inna ce ko Bashar din ai suna daidai da su.
Waya mama ta dauka takira Inna na ta kwashe duk yadda akayi ta fada mata mama tace Allah ya kyauta nabar su ga Allah.
Buki za,ayi a family house din su Baba haka yasa yanzu su mama basu zama a gida sosai don suna zuwa can gidan gurin aikin bukin da za,ayi.
Shima yaya sadauki baya zama a gida sosai don ina ga,akwai wani aiki da yasha mashi gaban shi don sai dare yake dawowa gida.
Yauma da dare ya shigo har lokacin su mama basu dawo gidan ba suna can cikin gari.
Daganin shi a gajiye yake sai dai kuma alama ya nuna min yana cikin halin shi don ya dan sha a lokacin.
Maryam waya take da,wata kawarta Amira tana kallon wani season film a tv bayan an gaisa dashi kowa ya juya gur8n harkokin shi.
Ni dake zaune da litrafi ina karantawa na mike sai gaban shi na ce mashi a hankali control yourself mr.
Da sauri ya dago jajaye idanuwan shi ya watso su a kai na gyada kai nace ka natsu kokabar falon nan tun mama bata shigo ba.
Mamaki takaici haushi ya kama shi a lokaci guda yace cikin tsawa ke kin raina ni ko dayawa ?
Easy mr behavour self da sauri maryam ta dago ta kalle mu nace akawo maka abincib ne.
Ban sani ba ya fadi a fusace sai ya mike cikin rangaji ya bar falon ran shi a bace wanan yarinyar kodai aljannace wai ita ?
Maryam na kallona na gyada mata kai alaman ya sha yau tace oh Allah wanan masifa da may yai kama.
Mikewa tayi tabi bayan shi, sai nima na biyo su yana tsaye ya dafa bangon dakin shi bai shiga ba yaji muryam maryam tana fadin haba yaya sadauki.
Da sauri ya juyo takaraso tana fadin kada kaga laifin Bintu gaskiya take fada maka tsawa ya daga mata lokacin nakaraso gurin.
Ya bini da wani mugun harara yace sai na karya ki a gidan nan wallahi yar iska mai balain sa idon tsiya kawai.
Sai kuma yai shiru tare da kyatafa kawai ya dafa bango kan shi ya dukar a kasa.
Nace yaya kayi hakkuri bani son mama ta fahince ka a hakane wata rana kaji may likita ya fadi a kanta.
A guji bata mata rai don dazara akai mistake watara zuciyan ya buga a lokaci guda za,a iya rasata gaba daya.
Yaya kana son sanadin ka ace mahaifiyan ka ta rasa ranta kan bacin ran ka ne ko yaya ?
Maimakon yai cikin mu da masifan daya fara yadda nai tsanmani sai naga ya dukar dakan shi a kasa.
Ikon Allah sai Allah yau gani mukayi yata sadauki yana kuka kuka kuma mai ban tausayi.
Yace maryam bani sha a ko ina sai ina garin nan i don't know why nakejin irin haka kawai a garin nan ?
Idan ina garin nan in basha ba bana jin dadi rayuwana sam wallahi sai na dinga jin kaman zan kama da,wutane.
Amma kudai tayani addua kawai Allah ya kawo min agaji ga halin nan.
Bana son ace sanadina uwata ta samu matsala a rayuwan ta ko kadan bani jin dadin hakan idan na tuna.
Kuka ne ya dan fi karfin shi maimakon mu bashi hakkuri sai nima nafara kukan abinda yasa Maryann itama kuka ke nan lokaci guda.
No no ku bar kuka please zanyi kokari naga cewa na daina hakan insha Allahu.
Nace yaya idan ka fara jin haka don Allah ka dinga nafila kana kai kukan ka ga Allah don ka samu sa,idan jin hakan da kake yi.
Ya dago ya kalle ni ina makure a bango kaman zaiyi magana sai kuma yai shiru, ya dade a haka yace ku shiga gida kada wani yazo ya samay ku anan.
Har na juya nace abinci fa yaya yace No kibar shi kawai I am OK.
Kuka sosai maryam tayi bayan shigan mu gida da kyat na samu na lalashe ta har tai shiru tana tausayawa halin da dan uwan ta yake ciki.
Bintu fada min yaya kike gane yaya yasha ne wai ?
Nai murmushi na ce da farko idan kinga ya shigo da glass a idon shi to yasha sosai ke nan.
Idan kuma kin gashi ya shigo ya zauna yai shiru kaman akwai abi dake damun shi to abin yadan fara sake shine hakanan bai son yawan magana sai kasala kawai yake ji.
Sai kuma da zaran kinga yana bukatan abinci a gagauce to abinda yasha ya fita kan shi ke nan sai kiga yana jin yunwa sosai.
Zakiga yana shiru shiru sometimes to yana cikin dan maye ne zai dinga zama kaman wani salihi can dashi.
Bintu baki ganin kaman asirin da akace su Umma sunyi mashi a cikin gidan nan yake kuma kilama a dakin shine ko makamancin haka ?
Nace sanin gaibu sai lillahi anty amma hakan kuma fa magana ce sosai.
Tace in hakane yabar gidan nan ya koma gidan shi mana da zama zai fi mashi sauki nake gani.
Anty yaya zaibar gida baiyi aure ba?
Ke kinga alaman aure a gaban shine yanzu Bintu ?
Nace ai irin su mata basu gaban su anty duk matar da zai aura matsayin baibar wanan rayuwan ba sai tayi hakkuri wallahi.
Don bata gaban shi idan yasha kuma sai dai yai ta tabara yana zubar da kiman shi a idon ta da jama,an da suke tare.
Wai ke ina kika san wanan halaiyar tasu ne haka Bintu ?
Murmushin takaici nayi nace a gurin mijin mahaifiyata mashayine shima amma shi irin shan nan na yan kauye yakeyi mara fasali.
Nan nai ta bata labari na yadda mamana take hakkuri tana kuma nema mashi maganin hakan ?
Nisawa tayi tace shiyasa lokacin da su Baba Sani suka hana yarsu daga baya banji haushin su ba wallahi.
Don yau babu wanda zaiso ace nashi na cikin fitina ko tashin hankali haka ai ?
****** ********* ******
Washegari Mama ta tilsata mu kan sai mun tafi gurin buki don ayi kamun amare damu tana fada take cewa, ban san may yasa baku son yin zumunci ba wallahi.
Zumunci da kuke gani ba abin wasa bane wallahi don igiyace mai kai mutum aljanna idan Allah yaso.
Amma rashi sanin darajan shi yasa kuke sakaci da shi alhalin gaku Allah ya baku yan uwa bila,adadin a gari babu gidan wanda kuke zuwa kullun kuna kulle a gida kaman kayan wanki.
Ba don mun so ba muka fara shiri bayan sallah azuhar zuwa gurin sa lalain yan uwan su da za,ayi a family house din su
na diyan kannen baban su.
Ga ba dayan mu dogayen riguna muka saka muka daura dan kwalaiyan su akawunan mu.
Shigar tai matukar karban mu sai dai matsala motar da zata kaimu ce babu a lokacin haka yasa yaya sadauki yace mu bari ya kaimu da Amirah tai mashi magana.
Amirah ce agaba tare dashi mu muna baya a zaune sai dai ban san yaya akayi na zauna a setin mirror shi ba na gaba.
Maryam ke fadi wai yau kan sai mun sha surutu a gurin mutane yaushe rabon da naje gidan nan ni.
Amirah tace ni wallahi ba,son zuwa ne banyi ba yadda ake damun mutum yaushe zaiyi aure yake damuna.
Daga inda nake zaune nace kai mutane akwaisu da daukan wa rai shifa aure kamar rayuwa yake idan ya tashi koba shiri sai anyi shi haka ma rabuwan shi idan yazo ko bashiri sai anyi shi.
Dago kan da zanyi naci gaba da magana muka hada ido dashi ta glass din motan yadda naga idanuwan shi sai naji gaba na ya fadi daga haka naja bakina nai shiru ban kara magana ba don duk na dago kai dashi nake arba sai ma na daina daga kan nawa kawai.
Tun a kwanan gidan muka fara ganin dandazon motacin mutane da sukazo gurin kamun.
Wata mata tazo da motar ta shige gaban mu maryam tace shegiya mu akewa kurin mota mima watarana insha Allahu ki gan mu da namu.
Nace kai anty kin rage mata kaya bata masan kinayi ba ita, Allah Bintu inason naganni da mota ina ja wallahi.
Nace in Allah ya nufi ki ja sai ki gan ki dashi kuwa ai tace wai da su Umma sun mutu ranan.
Nace su kuma ai zaman su ke nan hassada wallahi basu ko tsoron haduwan su da Allah.
Allah suka sani aida basuje gidan su Bashar suke auren maryam ba inji Amirah.
Da sauri ya juya gareta yace kamar yaya wai har muka isa inda zamu sauka tana mashi bayani haka yasa bamu fito daga motan ba sai da tagama mai bayanin komai yadda akayi.
Mutanen dake tsatsaye daga waje sun matsu sugs ko suwaye a wanan haddadiyar motatar haka ga shi na cikin motan basu fito ba.
Sai da suka gama magana ya bude muna tare da tambayan mu karfe nawa zai dawo ya dauke mu Amirah tace shidda daudai yaya.
Nice na fara sako farin kafa na a waje daga gefen da nake zauna sai wata tace dama nasan wasu special ne daganin wanan uban motan haka sai gidan gwauna, muna fitowa ashe su Rahaman shi ce a tsatsaye nan shima ya hango su,
Kiran mu yayi muka dawo gare shi daya bayan daya yake muna magana kowace tana juyowa da dariya ganin ya gama magana da kannen shi yasa nima na juya zan wuce nabisu sai yace Fatima nace naam yaya yace zo nan na karasa gaban shi.
Yace don Allah kada kiyi masu kayanci agurin nan kiga dai duk ido akanku yake.
Maganan shi ce tasani dariya a lokaci guda wanda mutanen dake gurin suna zaton ko wani maganan soyayyane yake fada min hakanan.
Yana fadin haka yaja mota yana murmushi duk suka bishi da idanuwan su caaaa kowa na son ace itace ta mallaki aana haddaden guy din mai kyaun dan maci ji.
Abokan Rahama da yan uwanta ke ce mata kai amma gaskiya kinyi hasaran miji ko dai wanan yarinyance zai aura ne?
Tace a kufule kamar
yaya zai aureta anfada maku anfasa zancen namu dashi ne halan .
Nan suka shiga gaisawa da mutane yan uwa da abokan arziki ana ta masu sheri don yau bukin gidan su ne yasa su fitowa.
Buki yayi buki duk guri ya kicimay da kida don an fito da amare su hudu ne gaba dayan su a filin.
Muna tsaye gefe sai kallon amaren muke gwananin ban sha,awa nace anty Allah ya nuna muna naku muzo musha bidiri muma.
Ameen ke dai Bintu inji maryam itako Amirah cewa tayi nifa duk wanan abubuwan basu damay ni ba fa.
Nace nima nafison in zanyi aure aimin walima haddade wallahi duk yafi wana gwatsale gwatselen da mata da yara keyi.
Ji mukayi wai ana kiran dagin amaryam su Amirah su fito suyi rawa a fili basu so fita ba kuma banyi tsanmanin zasu jani tare dasu ba sai ji nayi maryam ta jawo hannu mun shiga fili tare ban iya rawa ba don ban ma,taba yi ba don haka takawa kawai nake yi a hankali.
Kaina a duke naga su maryam su falle jakkan suna min liki take guri ya hau ihu da sowa sai tambaya mutane keyi wacece ita da suke mata likin kudi haka?
Komai namu a gurin a natse muke abin mu cikin nuna sanin ciwon kai da kuma tarbiya.
Muna gefe mu kaji guri ya kaure da sowa maryam ke tambayan ko su waye wata tace wai ance wasu mashaya ne yan uwan su amaryan yan mata suka zowa kawarsu kara.
Innalillahi wacece kuma maryam taja min hannu Anty Amirah na gaba muka leka Nafisa ce da kawayen ta suke wani irin rawa gasu sunyi shega zakace akwatawan ghana ne su guri ya rude da sowa masu tir da Allah waddai suka shiga bakin su.
Daganin su a buge suke don rawan ba rawan kai sake bane har gaban samarin da suka shigo suke shigewa.
Kiran wayan da sadauki yaiwa Amirah yasa mu saurin barin gurin muka fice a filin gada ma agan su ace yar uwar su ce.
Mun shiga mota su Amira sai yankan fada sukeyi suna tir da Allah waddai da halin rayuwan Nafisa.
Maryam tace yau maganan nan sai yakai kunnen Baba ai akwai magana agidan nan yau wallahi.
Umma tagama jin kunya da nauyi ya agaban su fa su Nafisa ke wanan rawan tsiya waisu ga yan iska.
Allah dai ya shirya su damu baki daya nace daga inda nake a zaune sai lokacin yai ajiyan zuciya bai dai yi magana ba.
Maimakon mu tafi gida sai wani hanya ya dauka da mu can hanyan masarauta.
Gurin kaman company sayar da motoci ne yana tsayawa naga mutane suna nufomu suna gaiyar dashi daya bayan daya.
Amirace kawar shawaran shi da hira dama yace Amirah tace na,am yayana yace kin san gurin nan tace ,a,a yayana yace kallo signboard din can ki karan ta muna alokaci daya duk muka daga kan mu an rubuta da mayan haruffa kamar haka.
MAJI ENTERPRISISE da sauri kowan mu ke kallon shi a cikin mamaki maji suna kuma kaman na majin mu?
Natane yace cikin rashin ko in kula ya fadi hakan gurin muke zagawa muna duban motocin dake gurin latest masu kyau da tsada yakai mu wani layi yace ga layin na mata da ake yayi nan mukai ta kallon motocin cikin mamaki.
Wanan tace ai wancan yafi kyau haka sukai tayi a tsakanin su naga wani assh color nace amma wanan sai naga duk tafisu kyau kai amma dai Bintu baki san mota ba wallahi nace ina kuwa zan san su anty daga jaki sai rakumi na sani dandamama doki.
Wani irin dariya suka samin ganin yamma yayi daga inda yake tsaye yanufo yana fadin mujen ku magariba ya kusa yanzun.
Muna hanya maryam tasakani gaba da,sheri wai nace jaki da rakumai na sani dan dama dama doki.
Shima dariya yai min yace bana fada maku yar kauye bace kunki yarda dani, Amira tace ,a,a gaskiya yaya yanzun Bintu ta wuce irin bakauyan da kake nufi fa.
Yau gasgi harda rawa tayi a gaban mutane ida dane waya usa yasa Bintu rawa a bainan jama,a haka.
Yace ai bata da kunyane ki shiga rawa gaban mutane kamar wata chuss can dake, da sauri na dago kai muka hada ido a gaban motan da yake Amirah tace ai duk mune don mun fita rawa ita da take wani yauki kaman a gaban saurayin ta take.
Kila yana gurinne tunda kukaga tayi hakan kin san yar tara samari ne ita bata da kunya ai.
Ai duk rawan karya mukeyi da mukaga uwayen mu sun iso aikowa ya jaye gurin gabadaya aka basu fili.
Ni dai har muka iso gida ban yi magana ba shiru nayi kada ya disgani yadda ya saba yi.
Sallah muka fara gabatarwa tukun muka dawo falo muka zauna sai ga mama sun dawo daga gidan bukin.
Sai faman yi mata sannu da zuwa mukeyi maryam tace maji yau munga abin mamaki gidan saida mota da sunan ki wallahi.
Sunana kuma ?
Maryam tace wallahi maji har gurin yaya yakaimu mu gani muna ta mamaki.
Wayan Baba ne ke kiran mama a lokacin bayan ya tambaya dasun dawo tabashi amsa da eh sun dawo tana gida yanzun haka.
Nanmuka ga ta mike ta fita daga dakin zuwa can mukaji hayaniya a tsakar gida maryam tace kuyi shiru mu ji don Allah,
Kaman fada ake a tsakan gida muna ji muka kwasa zuwa waje da saurin mu Baba ne da Umma yake ta ja mata Allah ya isa akan Nafisa tana mayar mashi da amsa.
Sabon tashin hankali sai ga Amirah tashigo gidan abuge ta ita tayi tatil kawayen ta sun kawo ta kofan gida sun zube ta haka.
Ranan muga tashin hankali don Baba zubewa yayi kofan shi da sauri su mama suka tare shi suna mashi fitara.
Yaya Sagir yana gida shi ya fara jibgan Nafisa baji bagani cikin bacin rai gida sai koke koke sukeyi .
Itako sai tabara takeyi tana fadin magana irin nasu na yan maye bata fasa magana ba shi kuma bai fasa dukan ta ba.
Abinka da yan uwan taka sai ganin su Amirah nayi suna rike shi suna bashi hakuri yayi hakkuri kada ya halakata.
Yana barin dukanta utakuma Umma ta shiga jibbagan ta kamar an aiko ta tana kuka gwanin ban tausayi da ita.
Maryam.takira yaya sadauki ina jin yana kusa shi yazo ya dakatar da Umma yana bata hakkuri ya dauki Baba suka nufi asibiti dashi.
Haka muka zauna jigun jigun damu agidan babu dadi don harka ya lalace ranan baki gaba daya ya mutu wa Umma.
Can mukaji tana kuka tana fadin wallahi bata yarda yiwa Nafisa akayi talalace kaman yadda dan maishi ya lalace ita wallahi bata barwa Allah sai ta dauki fan sa.
Anyi daidai sun dawo da Baba lokacin hajiya kubura tace ji mahaukaciya kawai sai ki matsa ai kaikayi koma kan mashekiya ce akan ku zai kare yan banza.
Nan kuma suka shiga sabon cacan baki a tsakanin su da mummy sai zage zage da tonon asiri sukeyi.
Kai haba mummy ku tausayawa bawan Allah nan mana ku dubi halin da yake ciki da wani zaiji da fitanan ku ko da abinda ke damun shi.
Sadaukine yake wa mummy magana tace ai na bari sadauki amma in Alhaji ya mutu gidan nan da hjy Atika da diyan ta zamuyi kuka wallahi.
Yaran kawai gasu nan ba,a gama wani ba su jefa mutumi a wani yaya za aiyi mutum yai lafiya haka ?
Muna shiga daki bamu jima ba mama ta shigo dakin ita ma ta zauna jiki ba karfi tare da ajiyan zuciya.
Tace ni fitinan gidan nan wallahi ya fara isata abu tun ana da jajjayen sawu har girma yazi baza,a daina ba.
Tun farko shiyasa ban so zama ba wallahi babane ta tauyeni wai na zauna na saman ma sadauki abokan shawara a gida shine kukaga har nakai war haka a gidan nan.
Mani mukan ai gara da kika zauna da bamusan inda za,a haife mu ba kuma inji maryam cikin dariya.
Mama ta harare tace wawiya kawai don baki san irin wahalan dana fito cikin shi ba ko ?
Mama al,amarinki kaman na mamana,wallahi haka sukai ta,kwasa da mama ta bawa har mamana tagaji tabar mata gidan gashi ko yanzun dai sai hakali.
Maji tace haka abin yake yanzun ai a hanaka zaman lafiya gidan mijin ka in bakakai zuciya nesa ba sai ka bar gurin gaban kuma da kake hange sai dace.
Tambayam bazata mama ta jefo min daidai lokacin da na daga kaina sama ina tunanen halinda mahaifiyana take ciki a can kauye.
Wanan tunanen bayau na farashi ba walau in naji dadi ko naga wani abinda ya danganta da rayuwan ta.
Muryan mama tana ce min Fatima yayan ku ya shigo yaci abincin shi kuwa yau ?
Da sauri na dago kai ina kallon ta don tambayan ani ya bani mamaki nace ina ganin baici ba don tunda muka dawo banga ya shigo ba.
Tace dubo min shi a,waje ko yanan nai magana dashi naji may zai ba su baban ku gudun mawan buki?
Namike tare da zura takalmina ganin a cikin gida zan tsaya sai ban saka hijjab dina na ba nafita haka nan.
Na duba waje baya nan kaman nakoma na fada mata sai nace bari na leka dakin shi tunda naga wuta a bude.
Na leka sai naga kamar bai ciki hakan yasa na dan kara takawa ciki zaune yake yana shakan wani abu a wabi farin takarda haka.
Jin motsina yasa shi saurin dago kan shi da sauri mukai ido biyi da sauri na juya zanbar dakin.
Abinka ga dan kwallo tako data ya cafko ni sai jikin shi ta baya zan saka ihu ya danne min bakina da hannun shi daya.
Bakina yana matse nake ce mashi mamace tace nazo na dubaka wai tana magana da kai .
Saboda hannun shi daya ya taushe min baki bai bari yaji abinda nake fadi ba.
Birkito dani yayi daidai fuskan shi muna kallon junan mu face to face ni dashi a hankali yace may yakawo ki dakina muna fuka ?
Ya dan sauke hannun shi daga bakina nace mama ce tace nazo na,,, sai ya kara matse bakin iya karfin shi.
Mamaki da tonon asiri sai jin saukan hannin shi nayi zuwa kirjina yana fadin abinda kikazo nema ke nan bakar jarababiya kawai.
Na girgiza kai idona a rustse nace da karfi wallahi mamace ta aiko ni gurin ka.
Bai sake ni ba kuma bai fasa abinda yakeyi min ba a lokacin, wasu hawaye naji sun fara dan silalo min daga idanuwana.
Bin jikina yake a hankali da shafa yayin da nake jin saukan numshin shi a kunnuwa na cikin wani bakon yanayi.
Cizo nakai ma hannun shi nace da karfi wallahi Allah ba gulma nazo ba mama tace nazo na kiraka wai .
Daidai kirjina ya tsaya ya dakata da abinda yake min nace don Allah yaya ka sake ni in tafi wallahi mama ta aiko ni na kiraka .
A hankali yakai hanniwan shi saman kirjina yadan shafo su cikin hikima irin ta maza da sauri na dan sulale nai kasa don abinda naji a lokacin.
Kara dago ni yayi daga dan dukawan da nayi ya dago fuska na tare da hada shi da nashi ban aune ba yakai bakin shi ga nawa ya dan fara tsotso a hakali.
Nan na shiga ture shi daga jikina kaman dutse nake turawa don ko motsi baiyi ba kuma bai fasa abinda yake min ba.
Can naji ya turani da baya da karfi tare da dafa bango yace yar iska gobe ki dawo min daki kadan kika gani yau.
A hankali na dafa bango tare da dan bugewa cikin kuka nake fadin har nakai kofa wallahi ban yafe mugu mazinaci kawau aiko ta biyoni a guje ban tsata ba sai falon mu.
Yaya haka kuma da sauri mama ke tambayana tare da son jin bayani daga gurina tana kallona.
Nace cikin kuka ba yaya bane ya kai min nashi wai may yakawo ni dakin shi.
Sai gashi ashe yana bayana a lokacin sai kamshi yakeyi kamar bashi ba.
Tace kai kuma daga na aika yarinya ta kiraka sai ka kai mata nashi kai dai wallahi sadauki katon banza ne wai dadin may kake ji gurin zaluntar yarinyar nan?
Yace haka tace maki nashin ta nayi ?
Ai duk ni na ja mata hankan tana zaune zaman ta ta tashi na aike ta kiran ka na manta kai mugune gareta.
Inda nake zaune ya dan kalla sai faman zubar da miyau nake ina tofarwa tare da goge bakina da dan kwalun dana cire akaina.
Gashina daya sha gyara yana kwance hat gadon bayana yasha gyara sai walkiya yakeyi.
Murmushin ke ta ya sakar min tare da dan kashe min idon shi guda daya.
Mama tace mai dama zancen abinda zakaba iyayyen kane maza masu buki, don banji kace min komaiba har yanzu kan zancen.
Yace ni maji may zan basu kuma ?
Sadauki iyayyen naka kuma suna buki zakace may zaka basu bayan kowa yanzu yasan kana dashi.
Murmushi yayi kamar wanda yake a cikin nishadi yace OK maji sai ki fadi abin da za,a basu din ai ina ganin is OK.
Nasan aljihun kane Baba na balke na shatama ko nawa zaka iya ba iyayyen ka yace, maji ki fadi kawai ba matsala ai tace hamsim hamsin yayi ko yace kai haba haba mji adai basu koda dari biyu biyu ne ai ina ganin is ok for them,
Kai yaya har dubu dari biyu biyu baiyi yawa ba yace baiyi yawa ba Amirah bari a basu kawai.
Yana fadin haka yace maji abari har da safe sai na ciro masu na kawo maki kiba Baba ko ?
Har lokacin ina zaune sai hawaye nake zubarwa ina bakin cikin abinda sadauki yai min yau ashe dan iska ne haka ban sani ba shi da yake ikirarin cewa bai taba zina ba ashe tsohon mazinacine haka ban sani ba.
Nai zurfi a cikin tunane na nake jin muryam maryam da karfi tana fadi, da gaske yayan mu yace saka hannun shi ga aljihu yace kowa tazo ta karbi nata key din gashi sai lokacin na dan dago ina kallon su.
Keys ne ya ciro daga aljihun shi yana mika masu nakai ido ina kallon keys din .
Yace kowacen ku wanda ta zaba dazun shine nata juyawan da zasu gurina sai ganin ina kuka sukeyi.
Lah Bintu badai har yanzu kukan dan nashin da yayayai maki ki ke tayi kamar wani nashi can.
Ya dago tare da kallo yace au wai kuka takeyi bafa wani nashi sosai nai mata,ba dama nasan kukan shagwaba da jin dadi zaki tsaya yiwa mutane haka.
Ya kare maganan shi cikin lashe bakin shi kamar wani maye can nace a fili mugu azzalumu kawai na mike na shige daki cikin kuka.
Dan murmushi yayi tare da lumshe lumsarsu idanuwan shi da da tun shigowan shi falo suke mashi haka.
Ko may ya tuna sai yai murmushi tare da bude idanuwan shi caraf acikin na maji tace Baba na wai wani irin keta kaiwa yarinyan nan yau haka har kasa ta kuka.
Yace bata fada maki ba maji dan kai mata nashine fa nayi kuma ban ma samay ta sisai ba fa.
Wallahi kadai ji tsoron Allah gashi don tsaban ket kasa yar mutane kuka haka idan bata ji zafin abinda kai mata bata bacin ka haka yau.
Ai ba yau kafara mata kyeta ba amma bata taba fada haka ba ido da ido sai yau ?
Wallahi maji bata jin magana ne tafaye shegen gulman tsiya kungan ta nan.
Mi dai bata taba muna gulma ba don muke zama da ita sai dai ke da ka saka mata ido don kiyayya kake ganin haka gare ta.
Kiyayya kuma maji aiko yayana bai ma Bintu haka kawai dai ke ke ganin hakan wallahi amma ita,ai Bintu ba baya ba itama kingan ta shegen tsokanane da ita.
Anty Amirah Anty Amirah wallahi ki iya bakinki akan Bintu da yayan mu, inba haka ba watarana zakiji kunya sosai wallahi.
****** ********* ******
Kwance ya ke saman gadon dakin shi rigingine ya saka hannun shi yai crossing dashi idon shi biyu amma yanayin kwanciyan shi sai kace yana barci ne.
Saboda idanuwan shi da suke a lumshe a lokacin a hankali yake tariyo abinda ya faru a tsakanin shi da Fatima.
Hannun shi da ya sauke akan kirjin tane ya fado mashi a rai yana tunanen may ya hanashi ya cire hannun shi a jikinta a lokacin.
Murmushi yayi da yadda ya samu sa,an bakin ta ya tsose su yadda yake so son ran shi.
Wani murmushi yayi naketa yace gobe ki kara yar iskan yarinya kawai gaba abinda zan maki idan na kama ki sai yafi wanda nai maki yau.
Dariya ya kwashe yadda maji ke fadan wai ya nashi yar mutane ba gaira ba dalili don cin amana.
Yasan da yau maji tasan abinda yai wa yar nata da ya shiga uku a gurin maji da masifa sai yabar garin ba shiri.
Yakwashe da wani irin dariyan keta shi kadai yadda ya ga na koma gefe ina kuka a falo dazun da ya shiga.
Yace a fili may be this is her time to have romance with somebody ?
Ina daki barci ya gagati indona nayi brush yafi a kirga kafin na kwanta don ina ganin ya zuba min abin mayen shi ga bakina kila ga kazantan da nake ji a raina.
Har anty maryam tafara zargin may wainake ta wanke ma bakine tun daxu nace mata ina jin bakina badadi ne yau.
Tace aike ne dan abu kadan idan yaya yai maki sai ki ta faman mashi kuka shiyasa yake jin dadin yi maki kyata ai.
Kema ki zage kai ki dinga ramawa idan yai maki bawai ki zauna kina kuka ba tunda naku sallon takon ke nan a haka.
Hararan ta nayi nace don Allah anty barni kada ki kara min bakin ciki naja bargo na rufe jikina don sanyin da akafara a lokacin.
Washegari ban fito da wuri ba ina gudun in fito na hadu dashi a falon sai guraren shadayan rana nafito falon .
Ban dade da zama ba sai gashi ya shigo falon da sallaman shi nan suka shiga gaidashi ban dani da nai kaman ban gan shi ba.
Nan ya dora idon shi a kaina ko kyaftawa bai yi yace ke baki iya gaisuwa bane halan yar kauye?
Da sauri na mike tsaye zanbar falon yace kina tako daya daga gurin nan yanzu sai nai maki abinda kike so.
Cak naja na tsaya guri guda ban motsa ba daga inda nake yace look at her kamar wata takwarai can nan ko shedaniya ce ta karshe.
Na juya nace ni wallahi ba shedaniya bace sai dai in kaine shedan,,,,,,,,aiko ina ganin ya taso na ruga ciki da guda na kargamay kofan daki ina mai da haki.
Yace ashe ke karamar yar iskane ai daki bari na samay ki gurin yanzu na wujujugaki wallahi.
Daga cikin daki nace anki a tsaya din mugu kawai macuci yace ai kama ki zanyi sai kin fada min waye mugu a gidan nan.
Ban fito ba sai da na tabbatar da yafita daga gidan ina fitowa suka kwashe min da dariya Amira tace kai Bintu ga tsoro gajan magana ai shine maganin ki wallahi.
A raina nace baku san komai ba da bakuce min haka ba kuma da kun raina shi wallahi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
IDAN KIN KARANTA KO KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NE SHEDAN MUNA BINKI BASHI,,,,
ALOKACIN MU KE,,,,
Mun kama hanya sai hiran su suke shi da Bashar niko ina bayan mota zaune a takure cikin damuwa.
Bashar ne daga inda yake zaune ya dan juyo yace min Bintu gaki kinyi shiru mana.
Nai dan murmushi yake kawai nace ba komai yace ko kina son a sai wani abune?
Kai kawai na girgiza mai nace idan mun kai wani kauye zan sai dan tsaraban da zan kai wasu mama kada naje masu hannu sake.
Sai faman gudu yake shararawa da mu har sai da naji tsoron gudun da yake da mu nace komai nashi dai na muggai ne ko kashe mu yake son yi ne wai ?
Kafin wani lokaci sai gashi mun fara hangen garin sokoto daga nisa mun da kara gaba nani ya taka burkin motan da karfi sai dana nan dan firgita bani ba har Bashar dake gaban mota sai da ya kalleshi.
Muna nan zaune shiru ya bude mota yafita zuwa gefen da nake zaune ya bude marfin mota fuska a daure yace nafito ina fitowa ya mayar da marfin motan ya rufe .
Ina tsaye jikin mota ya daro hannau shi guda saman kan mota dayan kuma ya sashi daga gefen kunkuruna sai dai mota ya dafa.
Take naji cikina ya kada min fuskan shi a daure tamau yace ke dakata kiji kada kikaga nazo na dauko ki naji wanan zancen a gida ran ki zai baci sosai wallahi duk kika bari maji taji cewa nine nazo na dauko ki sai na bata maki fiye da tsanmanin ki.
Nace baka son asani may yasa kazo ka dauke da ka barni mana har lokacin da na tashi dawow,,,
Bakina ya murde dakarfi yace ke baki da kunya ko ina magana kina magana who is the master?
Jin zafi a bakina yasa na dan zille na duka sai ya komane sai saman kirjin shi na fada.
Da sauri na kara dagowa hakan yasa muka tsaya muna facing din juna face to face.
Ya dan dade yana kallona sai ya kuta ya juya ya shiga mota yana fadin kinji warning din da nai maki wallahi duk naji zancen nan sai ranki ya baci dani wallahi.
Na shiga mota idona yai ja kaman zanyi kuka ina cewa ni wallahi wanan cin zalin ya isheni don anfika karfi sai a dinga cuta maka kawai.
May kike fadi yace sai lokacin Bashar dake muna dariya yace haba ka barta hakana mana please?
Ya tayar da mota muka ci gaba da tafiya, bai tsaya ba sai wani guri da ake sayar da kayan irin na kauye na ciye ciye.
Nan suka fita sai gasu da sayayan kayan tsaraba mai yawa irin na kauye ana lodawa a buth din motan.
Muka bar gurin nidai ban san may damay suka sayo ba a lokacin muna shiga gari a play over ya samu guri ya tsaya.
Can ya tare wani mai Napep yake cewa, ya kaini gida tare da mai kwatancen inda zai kaini, yabiya shi kudin shi nan mutumin ya loda kayana a cikin motan shi.
Su mama suna zaune sai ganina kawai sukayi a bazata kawai nan suka shiga cewa la Bintu ashe kina hanya ?
Yaran da suka shigo min da kaya na diban masu rake gyada dafafa na basu suna ta jin dadi suka fita.
Naje gurin mama na rusunna na gaida ita cikin jin dadi da gani tace Fatima shike nan kinje kin samu guri kin share ai har ina batun binki ne da banga kin dawo satin nan ba.
Nai murmushi nace mama ai zan dawo tunda an koma makaranta, tace yayasu wajen mamaki suna lafiya ko nace duk lafiya kalau mama suna gaida ku.
Ta kalli tsaraban da nazo dashi tace Fatima wanga tsaraba haka mai yawa fa dariya kawai nayi a raina nace aikin mahaukaci ne.
Nan muka shiga hira dasu anty suna min sheri wai naje naga mama na kasa dawowa.
Sadauki bai shigo ba sai da yamma lokacin ina cikin daki maryam ke fada mai Bintu fa ta dawo yaya.
Yace taga daman dawowa ke nan ta samu kauye ta zauna kaman wani birni can.
Tasa min kira na fito sai ganin shi nayi a zaune nace yaya ina wuni ?
Ya amsa a kasalance da lafiya?
Kinga daman dawowa ke nan ko ?
Murmushi kawai nayi mashi na karasa gurin maryam nace gani anty tace dama yaya na kiraki ku gaisa ta fadi tana dariya.
Na juya kawai na koma ciki, ina gyara kayana ban fito ba sai bayan magariba don nasan lokacin bai nan.
Ina cin abinci kawai sai gashi ya fado falon saudaya na daga kai na kalle shi ban kara ba.
Maryam ce take ce mai yaya adebo ma tsaran Bintu na kauye yace kai maryam kayan kauye ai sai yan kauye.
Daga inda nake zaune nace, muko dashi mukafi wayau kayan kauyen don yafi bada lafiya ai.
Yace ke yanzu lafiya kike ke nan a haka kamar a karya ki?
Kafin nai magana maryam tace a,a yaya aiko yanzu Bintu ta yi kiba in kuma tafi haka ai bata kyau.
Ni wallahi duk da mace ce amma nafi son mace haka silynder da ita sharp din mutum duk dress din da yayi sai yai ma mutum kyau.
Ga Bintu kuma dagowa ce ga wanan uban farin nata kamar yar larabawa da ita.
Kai maryam don Allah ya isa haka kada kisa kan Bintu ya fashe wanan dadin haka inji Amirah?
Maryam tace wallahi anty da har haushi nake ji idan mun fita da Bintu yadda matane ke yabata amma yanzu nima nasan gaskiya suke fadi.
Watarana fa muna alwala a makaranta wata na ganin gashin Bintu ta yanka salati wai ikon Allah yanzun ke kina da wanan gashin haka kike faman boyon shi ga hijjab kullun ?
Sai lokacin yaya yai magana yace, shiyasa ta bude ai don su gani su yi magana.
Nace kai haba yaya haka kawai zan bude kaina wa nake son ya gani kuma?
Ke kika sani dai tunda an gani an yaba din ai yadda kike son agani din.
Shiru nayi wani takaici ya kumay ni a raina nace ni wallahi wanan ai zargine kawai?
Yace nakara jin kin bude wani part dinki a jikin ki sai na bata maki rai gidan nan.
Dan Allah yaya ji yadda maryam ma take wani zuzuta fatima wallahi sai kace wata sarauniyar kyau can.
Su dai suka sani shedanun yara ne wallahi kin gan su nan shiya sa duk suka fita sai maza sun biyo su don suke kiran su.
Wanan sheri da may yai kama saboda Allah haba dai yaya kana biyewa Anty Amirah tana zuga ka kawai yaya.
Ni dai wani haushi da takaici bai bari na ko iya dago kaina ba a lokacin don irin takaicin da nakeji.
Amirah tace maza kan na zuwa har ana masu yanga da kuri kafin a dauki wayan su tafadi cikin dariya.
Kai haba anty ai wanan sheri ne kawai kike kulla muna gar wasu maza muke kulawa mu don Allah,
Baiyi magana sai shirun da yayi can ya dan bude abincin da aka aje mai agaban shi ya fara ci nikan na mike na shige dakin mu.
Amirah tace kibar gudu ai don kada a ci gaba da zancen zaki shige ko?
Shima bai bi ta kaina ba yaci abincin shi ya tafi abin shi kawai.
Ban san yaya akayi Bashar ya fadawa Anty maryam su suka daukoni daga kauye ba ranan da na dawo.
Amirah na falo ta dunkule saman kujera tana chatting maryam na zaune tana gyaran farcen ta.
Maji na zaune tana gyaran wayan ta da ke hannun ta ruwa ya dan zubo mashi da take sha.
Nafito da plate a hannu na da abinci zanci na zauna na fara ci ban dade ba sai ji nayi maryam tace.
A humm wai ashe ke Bintu yaya sadauki ne yaje har kauye ya dauko ki da zaki dawo?
Da sauri na dago kaina kalle ta cikin mamaki sai banyi magana ba don ina mamakin ina taji wanan zancen ita.
Amirah tace ke kan Maryam wallahi uwar sheri ne wata Bintu ne can yaya zai je har kauye daukowa?
Maryam tace au kina nufin karya nakeyi ke nan ko,ai ga Bintu nan shi in ba shi yaje tun daga nan ya daukota ba wallahi.
Kin ma raina yaya Allah shine zai tafi har kauyen nan mai uban nisa akan Bintu.
Don in nunawa Anty Amira na kai nace to anty maryam don ya dauko ni wani abune halan ni nace yazo ?
Ni da ban ko shirya dawowa ba amma yasa ni tasowa ba shiri saboda zuwan shi.
Bintu da gaske yaya ya dauko ki wai ko may?
Nace su sukaje sukazo dani ban ko shirya ba amma ya matsa min wallahi saida mama tace na shirya su zo dani.
O lalai ma yayana shine yai pretending kamar ma bai san komai ba a ranan da ta dawo.
Bake ne ba idan ana magana akan yaya da Bintu sai ki wani kakarw ki hana a fadi ni dai ban kara magana ba ina mamakin yadda maryam taji zancen ga kunya mama duk ya kamani lokaci guda.
Nace dama,na,sani kawai tun ranan in fada mata tare dasu nadawo da yafi min yanzu gashi anji ko.
Amirah bata bar zancen ba sai da ya shigo gida har kowa ya manta ashe ita abin yana ranta.
Yashigo cikin yar fara,an shi bayan ya zube saman kujera yake, cewa maji yau naga wanan kawar taki da tun muna tsohon gida kuke tare.
Maji ta dago kai tace wata kawana kuma ke nan yace ko yar Rabin isha ake ce mata ba ?
Au kace uwar goyon ka dai ai itace tai giyon ka lokacin tana amarya a unguwar na mu da anyi maka wanka sai gidan ta.
A ina kagan ta yace can wani unguwa naje duba wani tsohon gida da akai min talla tun kwanaki ban samu zuwa ba sai yau din nan.
Naji ance wai ba sadauki maji bane nan yace wallahi ban gane taba maji ta tsufa duk ta lalace sosai dagani tana cikin wahala.
Tace Allah sarki, tun lokacin da mijin ta ya dauke ta suka koma kauye ban kara jin duriyan taba.
Yace lalai na gan ta yau kan maji tace inji ka samu abinda ka bata ?
Yace dubu goma kawai na samu na bata banda kudi ga aljihuna a lokacin amma nai mata kwatancen gidan nan ai tace zata zo.
Yauwa yayana wai ashe kai ka dauko Bintu daga kauyen su ranan da ta dawo ?
Da sauri ya daure fuskan shi kaman bashi ke fara,a ba yan dakikoki kadan da suka wuce.
Yaba ta amsa da eh mu muka dauko ta wani abin ne akayi kuma ?
Inda nake ya kalla fuska a daure nima na daure nawa tare da dukar da kaina kasa.
Amirah tace da nace karyanr wallahi da maryam ke fadi dazun ban yarda ba wallahi.
Yace naga bata da niyan dawowa school ne gashi ankoma shiyada naje nazo da ita ai.
Daga haka yai shiru maji najin su batace kallaba ko wanan lokacin ban da cewa da tayi Allah yasa yar Rabi dai tazo gidan nan wallahi na dade ina tuna ta sosai wallahi.
Mikewa yayi yana cewa zan shiga daki maji duk nagaji yau wallahi zan dan huta.
Yana fita na sauke ajiyan zuciya a hankali don nasan nawa ya samay ni kuma tunda yai min gargadi kada na fadi.
Ban taba sanin yaya yana da nombana ba sai yau ina daki ina shirin sallah naji wayana na ruri.
Ina dauka naji yace ke ashe baki da hankali gulman ki hae yakai can ban sani ba dana ce kada ki fadi sai da gulman ki yakai kika fadawa maryam abinda na hana ki.
Na marairaice nace wallahi Allah yaya bani na fada mata ba ban san inda tajiba wallahi ko.
Sai naji ya kashe wayan dip nabi wayan da kallon mamaki tare da sauke ajiyan zuciya.
Kwanana biyu da dawowa ya sa kai ya tafi zuwa kashen waje gurin wasan su don can yafi dawowa a jike idan ya tafi.
Tafiyan shi, na dawo normal kullun ina cikin yan uwana muna mu,amulan mu yadda muka saba dasu.
Bamu da matsalan komai a gidan yanzu don gaskiya Alhamdullahi, mota kowan su na dashi, haka ma sutura duk muna dasu matsu tsada, waya kowacen mu babba take riko a hannun ta duk shi ta saya muna, gurin abinci sai wanda ran mu yake so zamuci, ga uwa uba makka da muka tafi kowan mu da hakoran makka a bakinta irin na adon mata yana walkiya.
Matsala guda yanzu shine matsalan gidan su maji na fitina a tsakani kullun ga Nafisa yanzun abinta yai kamari sosai gwanin ban tausayi da ita.
Idan iskancin ta ya ishi Baba haka zaifito tsakar gida yai masu tas ita xa uwarta, sai in Umma ta gajine takan tanka itama tace.
Ba kan diyana aka fara lalacewa ba ai a gidan kan suyi ai wasu sunyi kuma nasan hannu aka samin suka lalace.
Don haka koma waye na sani kada maishi yaga kamar yaci bulus wallahi indai nice bashi akaci wallahi.
Don sheri saboda mutum yaga nashi ya lalace sai ya mayar da dan kowa lalatace a gida.
Badai na su kawai duniya zata fada ba sai an fadi na mutum tukun.
Mummy tafito daga dakin ta tace kai amma dai hjy Atika tauhidi bai sheki ba wallahi.
Ashe shi wanda kike nufi hannu aka saka mashi ke nan a lokacin yazama haka bamu sani ba ko sai yanzu da yakawo akanki ne kika san haka ne.
Kada ki manta iskancin namiji ado ne a gare shi duk yadda ya iya lalacewa bai rasa macen aure a duniya itako diya mace fa ?
Ke tsohuwar kilakiya kada ki manta mun san komai wallahi, nan kikagama tambadewan ki ba mashinshine in bashi alhajin dayazo yatara ba ya dauko muna masifa a gida.
Kin ishe mu kin ishi diyan mu wai ke adole ga yar bariki to anriga ki indai barikine a gidan nan don gidan kikazo.
A haka cure ake barikin don shifa bariki iyawa ne dama don kinga ashe nafiki iyawa ke nan tunda kika fadi.
Dariya mummy tayi tace wai a haka ashe ke bariki kikeyi ke nan ba,a sani ba ko ?
Nafisa dake daki tayi tatil da ita ta leko tana fadin Umma rabu da wanan gajar matan mai muna mazuru muna shaho.
A,,,, mu,,mun,,san komai,,,wallahi, ikon Allah ai gara kija yar mayer yar ki daki kafin wani ya shigo yaga wanga tabaran nata a fita damu waje.
Haushi da takaici ya kama umma da Nafisa ta bude bbaki zatai magana ta wani daka mata tsawa tace don Allah rufa muna baki kinji kin jawa mutum gori a gida kawai.
Haka sukan ta faman jidalin su ita da mummy da bata iy
a hakkuri idan tana habaicin ta.
Maji dai bata kan tanka mata sai dai tai shiru kawai tace tabar ma Allah kuma Allah ya tsare mata zurian ta.
Irin wanan jidalin yakan tayar wa Baba da ciwon shi wani lokaci sai ya kwanta asibiti saboda bakin ciki dake damun shi gashi duk wanda ya sanshi sai yai mashi korafi akan Nafisa abinda takeyi baida kyau a gari.
Ranan dai ya tara iyalin shi yai masu fada sosai yace da mazan da suka isa aure da matan kowa ya fiddo da miji da mata aure duk aurar dasu zaiyi gaba daya kowa ya huta a gidan dasu.
Yace kai Imirah na fada maka ka kawo mace kafin na zaba ma da kaina wallahi kaji na fada maka.
Ya juya gurin mama Asiya yace danki yace min muje gidan yarinyar da yake so aiyi zancen auren su.
Mama tace ba dai wanan yar iskan ba da ta tsohe mashi ga shekaru da komai yace shi din maye inba halin su daya ba a ina suka hadu da ita?
Tunda yace ita yake so kuma shi zai zauna da abin shi ke ina ruwan ki da zancen su ne wai?
Zan tura iyayyen shi suje nema mashi auren ta nan dagobe insha Allahu.
Mama ta tubure tana fada tana zagin Ahmad tace badai ya auri wanan karuwan yarinyar ba agidan nan.
Baba yace ai sai mu zuba mu gani tunda kece zaki zauna mashi da ita ai kina bani mamaki wallahi.
Ki fara tambayan danki yaya ya hadu da ita kafin ki fara zagin yar mutane haka nan.
Ya juya gurin mamana yace idan danki ya dawo ina son ko fada mashi sakona yafito da mata na da karshen sabon wata duk aure zasuyi muddin ina raye a duniyan nan.
Mama tace shi sadauki yana da mata kuma na yaba da tarbiyan ta kwarai yace mashs Allahu haka nake son ji dama.
Duk gurin sun so sanin wacece matar don su sani ko yar gidan maikudine ko wani kusan gwaunati can.
Don kada yazo yafi diyan su zaben yar gidan mai kudi azo ana mazu feleke a gida.
Haka dai akabar falon kowa da abinda ke cikin ranshi manya da yaran su na gidan da aka kira.
Ina daki a zaune suka shigo kowa sai gunaguni takeyi maji dai ta shige tabar mu nan zaune muna hira.
Amirah ce takira yayan ta da waya take fada mashi hukuncin da Baba ya yanke akan su.
Yai dariya yace Amirah kice mun kusa shan buki ke nan yan kanne na sun kusa zama amare.
Tace bamu ba ai harku yaya don yace wa su Maji wallahi duk fito da matan aure a aura maku dariya yai mata kawai.
Tace yaya kai kaga abin dariya ma ni wallahi duk na rude na rasa may nake ciki ma aallahi.
Yace ina samarinki ba sai ki fitar da daya ba kawai a zarga maki dashi, tace yaya ni duk fa basuyi min bane na ma rasa wa zan tsayar a cikin su ni wallahi komai ma ya jagule min yayana.
Yai dan murmushi yace kibari zandawo month end sai mu san abin yi tace ni dai da Baba zai min hakkuri ne har faba dayafi min.
Yace No Amirah ki godewa Allah fa gaki har kin gama karatunki ma may kuma kioe so yanzu inba aure ba kuma.
Tace yaya ke nan bazaka bashi hakkuri ba har zuwa gaba yace wa ni rufa min asiri please bari mu rabu lafiya da Baba don Alla dai.
Tace yaya naji maji tace wa Baba wai kai kana da mata shine mu bamu san wanan lucky girl din ba da tai wanan sa,an haka?
Yace No,No Amira maji ta dai fadawa Baba hakane kawai don ta kare ni gare shi ammani for nowa ban da kowa a kasa tukun na.
A kwai da wata wadda nake son fada masu akan ta don yar kasar ghana ce sai dai akwai matsala gaskiya.
Matsala kuma yaya ?
Yace eh don ba musulma bace Christian ce ita sunan ta Linda.
Yaya kafira kuma ?
Yace eh amma ai idan munyi aure zata musulun ta ne insha Allahu.
Tace ashe kuwa akwai case ke nan nasan maji da wuya ta yarda gaskiya don yadda bata kaunan kafirai ko kadan.
Ni dai daka jaye zancen ko zaka samu wata nan gaba ku shirya yar asali yar gari.
Yace ban ma san ni may yasa suke son mutum yai aure bane yanzu wallahi.
Amirah tace kasan maji kance ita dai muyi aure don yanzu Life is to short knowadays.
Hakane kuma fa Amirah gaskiyan maji ne rayuwan yanzu dan kalilan ne gaskiya.
Yace ni nasan zamu kwasa da parents din mu dama both don ko ita parents din ta takw ji yanzu.
Shiyasa tace zata zo Nigeria sai muyi auren mu kawai sai daga baya iyayyen ta su sani.
Amma ban yarda da wanan ba ni don ban son ni ai min haka gaskiya.
Tace yaya ai matsala shine yaran da zaku haifa zasu zama ruwa biyu ke nan fa?
Yace kai Amirah akwaiki da shirmay wallahi ni fa ban ko tunanen yin aure yanzu balle wasu iyali can .
Yaya kadai yi tunane kafin kazo da maganan nan gida don za,a samu matsala sosai wallahi.
Ki bari kawai idan nazo sai mu san yadda zamu bullo wa zancen cikin sauki haka zaifi ai.
Tace ni wallahi maji nakejiwa akan zancen nan don nasan halinta akan abinda bai mata ba.
Yace ke dai kawai kiyi shiru ban son kowa ya ji wanan zancen a bakin ki sai nazo tace shike nan .
Nan sukai sallama,dashi yace ta kwantar da hankalin ta yana nan zuwa month end insha Allahu.
Suna gama waya gulma yaci Amirah ta kasa barin zancen a ranta tace wata sabuwa wai yaya kafira zai aura fa ashe?
Muna hada baki da maryam gurin cewa kafirah fa kika ce antu ?
Tace wallahi yanzu yake fada min wallahi wai yar kasar ghana ce ita
Sunan wai ko Linda ?
Nace wayaga Leather ke nan kuma ?
Kai baima yuyuwa gaskiya kafira arniya mai fitsari a tsaye zai ce zai dauko muna.
Muji da wani irin gori da habaici gidan nan kuma ba,a gama wani ba har yau a fada wani ke nan kuma.
Ai da su Umma an samu abin dariya ke nan a gidan nan wallahi don shi za,a aza a faifai kuma ana talla lungu lungu inji maryam ke ta sababi haka.
Tace ni wallahi har girman shi ya zube min wallahi arniya fa Allah tsare mu da ita a gidan nan.
Diyan shi sai su girma suma su zama kafirai ke nan ko ?
Nace to shine daidai daahi don shima ai zuben yare ne gare shi baka taba ganin yaya kace mai dan hausawa ne kullun yana cikin kananan kaya irin nasu.
Ke Bintu inji Amirah yaya din ne mai zubin arna kuma?
Nace rufa min asiri anty kada yajini nawa ya samay ni a gidan nan kuma .
Maryann tace na rasa may yasa mafi yawan yan kwallo suke auren diyan kafirai wallahi.
A ji anty marayam fa ba,a cikin su suke ba suna ganin su kullun may zai hanasu fadawa tarkon su.
Shine ai tunda dasu suke mu,amula can suna ganin su fa ko yaushe inji Amirah.
Sai da muka watse ne zancen ya tsaya min a rai na nace cikin zuciya na ai dama muguntan mutum ke cin shi.
Yaya za,a kana dan musulmai kace arniya zaka aura a haka ma yaya aka iya dakai balai ka auro kafira mara sallah kuma.
Wanan kan sai yadda Allah yayi dashi kan don ba ranan shiryuwa gare shi ke nan kuma.
Ai su gasa junan su da mugun hali sune ma daidai da halin shi, ai tunda shi yace shi mugu ne su karata, can wallahi.
Maji suna waya take ce mai ka sayo kayan da aka taba a cikin kayan lefen ka don a cika.
Yace cikin murmushi maji ai yanzu angama yayin su kawai a rabawa yaran nan sai na hado wasu kawai amma kada a taba gold din don akwai wanda na sayo da tsada tun lokacin.
Mani tace zan dai zabi na kwarai na aje idan ka kawo sai akara ciki kawai yace duk yadda akayi maji shike nan insha Allahu idan zan dawo zanzo dasu din.
Sukai sallama tana mashi fatan alheri da saka mashi albarka tana rokon Allah ya tsare mata shi ya shirya su baki dayan su.
****** ********* ******
Kamar yadda yace karshen wata zai dawo hakan ne da yammacin asabar sai gashi a gida nan aka shiga murna ana zuwa gaidashi.
Nikan tunda muka gaisa na gudu falon na shige don ina tsoron wani disgi kuma ba wuya gareshi ysi min shi yanzu da dawowan shi.
Sai hira sukeyi maji da bata san bani falon ba tace don Allah Fatima dauko min jakata a daki na.
Maryam tace wata Fatima maji Bintu kan ai dodon ta ya dawo tashige ciki tun dazun.
Itace ta shiga ta dauko jakar ta leka ina kwance daki tana min sheri wai yaya yana kirana nace o,o, ni ya su may zan mashi kuma ne wai ?
Tace ke wasa nake maki dan Allah kwantar kada kiyi fitsari a wandon ki please ?
Ban sake ganin shi ba don bamu hadu ba dashi tun ranan da ya dawo daga tafiyan shi.
Kwanan shi biyu kawai ya juya ya koma Abuja sai da yai kwana goma sha uku ya dawo gida a jike da abin arziki.
Ko ni na lasa don ba cikin gidan ba har makwabta sun san sadauki ya dawo garin su Umma ya canza masu motar shiga don yace yana bakin cikin ya gan su a motan kasuwa suna shiga.
Ranan munyi kallon kayan lefe mun baza kauyanci bani ba har su Amira yan birni sai da sukayi kauyanci ga kayan .
Mummy tashigo ta gani sai faman mamaki takeyi da yaba kyan kayan tana cewa kai wace yar sa,an keda wanan kayan haka.
Ina son naga wanan mai kayan nasan ba karamin gida za,a kai suba haka kan.
Hjy Kubura ai shi kyawon aure albarkan shi kawai yar masu hali da yar tallaka duk dayane ga Allah Allah dai yasa andace kawai.
Hjy kubura tace gaskiya kan shine magana ai shima mai kayan da dan tallakawane yanzu baga ikon Allah ba.
Maryam tace mumuy ai sai kinhaji daganin ta gidan nan ke da sarakuwan ki kune fa yan kai kayan in Allah ya yarda.
Tace hakane fa kedai mairamu sai fa na gaji abuna namu maganin akwabe mu.
Su Umma basu shigo ganin kayan ba wai su ba,a gaiyace su suzo su gani ba don haka basu zuwa.
Mummy tace kyale yan baki ciki duk hasadane da kyashi ke cin su kawai ba wani ba,a fada masu ba ko anfada masu ma basu zuwa aini na dawo raka wa yan nan mutane ko dan basu da imani.
Inkana binta nasu sai su kona mutum ga banza da wofi da jahilcin su wallahi.
Maji batai mai magana ba sai da yakai kaman kwana goma da dawowa tace tana magana dashi.
Ya shigo suka danyi magana da Amirah mutumiyar shi ya shiga gurin maji don dama idan zasuyi wani magana da yake serious daki suke shiga shi da ita.
Ya samay ta zaune a bakin gadon ta ya zauna asaman kujeran dake cikin dakin nata.
Yace maji yaya zancen su Amirah ne tace ai akan zancen ne nakira ka nan.
Tacs baka nan babanku ya tara mu kan zancen auren ku yace yana son gaba daya kuyi aure lokaci guda nan da karshen sabon wata.
Yace ni maji dama akwai yarinyar da muka shirya da ita akan zamuyi aure sai dai matsala daya shine ita ba musulma bace gaskiya.
Da sauri maji ta dago kai tace kafira ke nan ko may sadauki?
Yace eh maji Christian ce ita, yar kasar ghanace amma idan munyi aure nasan zata musulunta ai.
Kai dakata ba cikin kayana ba wallahi.
Kada kasoma ka kara min zancen nan wallahi don zan bata maka rai sosai fiye da tsanmanin ka.
Kai baka jin kunya ban gita cikin wani gorin ka ba zaka jefani wani idan su yaya suka samu labatin nan ina kake son na jefa kaina.
Ban taba sanin rashin hankalinka yakai haka ba sai ysu din nan da har ka dubi idona ba kunya kazo min wai da zancen auren kafira da bakin ka ko kunya bakaji ba.
Idan da kana da kani ko danka yace zaiyi wanan danyen aiki yaya zakaji a ranka.
Shiru yayi bai ce uffan ba sai ya dukar da kanshi kasa ya hada hannayen shi guri guda yana dan jijiga kafan shi a hankali.
Itama mama shiru tayi don bacin ran da ya ziyarci zuciyar ta a lokaci guda bai barin tayi magana.
Sai dai shi a zuciyar shi tunane yake ta hanya Baba zai gwada yagani ko da sa,a don yasan ance Baba ne yai tsayewa Ahmad har zai auri wacce zai aura din.
Amma nashi dai akwai banvanci saboda zaman kafira bare kuma ba kabilar hausawa ba.
Muryan maji yaji tajefo mashi tambayan da sai da ya girgiza mashi zuciyan shi tana cewa.
May ke tsakanin ka da fatima ne ?
Da sauri ya dago ya kalle ta yace wata Fatima kuma maji ?
Fatima nawa ke gidan nan da kasani?
Maji badai Fatiman nan taki ba ko ?
Tace inba ita ba wata Fatiman nake nufi ?
Yace kai tsaye ni babu komai a tsakani na da ita maji?
Ance maki wani abu a tsakani na da ita halan ?
Maji tace sai an fada min ko tunda ni yarinyan ce?
Wallahi maji ni ba komai a tsakani na da ita Fatima ai a matsayin kaunata nake daukan ta in ma,wanan ne shine kawai.
Shiru sukayi ba wanda ya kara magana daga cikin su ganin maji bata da niyan kara mai magana yasa shi mikewa yana fadin shike nan maji tace tafi shike nan.
Har yakai kofa tace dakata wallahi sadauki duk ka sake har zancen arniyan nan yafito a gidan nan sai na bata maka rai yadda ka bata min a gidan nan kagin kasa a zageni acikin gidan nan dagari sai na fara yima tukun mara hankali kawai.
Yana fitowa fuskan shi ta canza kala yayin shi gaba daya ya canza a lokaci guda kaman ba yanzu ya shigo da fara,an shi ba.
Amirah tana magana dashi amma ko kallon ta baiyi ba ya fice cikin bacin rai.
Duk muka bishi da kallon mamaki muna ko may yafaru dashi oho mashi.
Sai ga mama tafito dakin tana fada ita daya tana fadin ban taba sanin rashin hankalinka yakai haka ba sai yau din nan?
Maji may kuma yayana yai maki yau kuma?
Sai da ta harari Amirah kamar da ita take fada tace bar mahankali da rashin tunane kawai wai wata arniya yake fada min zai aura don ya gwada min shi dan duniyan gaske ne.
Ashe ko dagaske yaya keyi da zancen wanan arniyan ya fada maki maji ?
Au dama kukun sani ne ke nan ko ?
Shi yanzu aka rasa wanda zai fada min a cikin tun baizo ba na tare shi mara hankali kawai.
Maji ba yana son ta bane kuma shi zai zauna da ita abarshi mana yayi abinsh,,,
Bata karasa ba aiko maji tai cikin ta da fada sai da Amirah ta kwamce da bata tanka ba gaskiya.
Maji tace ai dama zubin ku daya dashi baku san mutuncin kan ku ba balle kiji zafin danaji.
Ranan kan naga fadan mama da bacin ran ta ance mai hakkuri bai iya fushi ba sai ranan na tabbatar da hakan.
****** ********* ******
Da yamma da baba ya dawo maji taje gaishe shi tayi sa,a babu kowa agurin nan take fada mashi Alhaji dama ina son in fada maka cewa.
Yaron nan fa yar gida yake son yi don da Fatima ce zasuyi aure ban dai fada maka bane sai komai ya daidaita a tsakanin su dama.
Yanzun ko yazo angama magana itace kawai naga ta dace ya aura don yarinyar nada natsuwa da hakkuri.
Cikin farin ciki Baba yace ikon Allah haka abin yake gaskiya nai farin ciki yau dajin wanan labari don ni kaina na dade ina wanan tunanen a raina.
Sai gashi Allah ya karba min addua na a cikin sauki da dadin rai maganan tazo min .
Zanga sadauki din in mashi murnan wanan babban albishir din da kikai min.
Tafita ta barshi da dadin rai sai murna yake har ya kasa boye farin cikin shi a fili.
Washe gari Baba ya aika akira mashi sadauki anyi sa,a ya dawo daga exercises din safe da yake fita da zaran sun fito daga sallah.
Rigan jikin shi ya sauya, ya nufi falon mahaifin shi don amsa kiran shi da saurin shi don yasan ba kasafai Baba ke aikowa kiran shi ba.
Da sallama ya shiga falon ya samu Baba ya daga kofi zai kurba tea da yake sha.
Yana ganin dan nashi ya sauke kofin ya fasa kurbawa yana cewa sanda sadauki sandagagare.
Zo nan zonan ka zauna yau in gwada maka farincikina dana kwana inayi jiya.
Mamakin may baba yaji akanshi yakeyi don rabon da yaji wanan kirarin da baba kan mashi inyai abin jin dadi tun yana karamin yaron shi kafin ya fara shaye shayen su bata.
Yace matso mana Babaatsonan kusa dani naji albishir din Alheri a gurin uwar ka jiya da dare .
Tazo tana fada min kun shirya tsakanin ka da yarinyar nan Fatima zan iya cewa nafi kowa farin cikin wanan hadin naku don na dade ina maka fatan haka a raina don Fatima yarinyar arzikice a gareka duk wani namiji da yasan kan shi zai so ace ya mallaki wanan yarinyar a matsayin uwar yayan shi nan gaba.
Duk bayanin da baba keyi sadauki ji yake kaman an watsa mashi ruwan zafi tun daga saman shi har kan shi .
Yadaga kai ya fadawa Baba ba gaskiya bane wannan zancen, amma sai yaga farin cikin da mahaifin shi ke ciki yafi karfin ya musulta shi a lokacin.
Ya san da zaran yace zai fada mashi gaskiyan zancen shi bai san komai ba akai farin cikin rayuwan shi zai iya sayawa zuwa bacin rai ta zama mashi sana din tashin ciwon shi.
Wanan dalilin yasa yaja bakin shi yai shiru, yana karba irin adduan fatan Alherin da mahaufin nashi ke mashi akan zacen.
Sukai sallama ya mike gwiwan shi duk ya mutu da kyat yake iya daga kafan shi da yake takawa a kasa dakin shi ya nufa cikin wani yanayi na susucewa a lokaci daya.
Yana shiga ya fada kan katifan gadon shi yayi yayi a lokacin ya samu ko dan kuka yayi ko zai samu relief, amma abin ya faskara mai.
Wayan shi dake gefe ke ringing har yagaji ya katse don kan shi bai daga ba sai kuma ga kiran ya kara shigo mashi lokaci guda ya daga daniyar zagin mai damun shi.
Bashar ne ya daga wayan yana tsaki yace yaya akayine wai Bashar din yace yana kofan gida.
Yace shigo ina dakina yana shigo yanayin da yasamay shi a ciiki yabashi tsoro sosai.
Lafiya may ya samay ka haka kuma ?
Ya watso maahi wani harara yace ban sani ba mugu ai kana daga cikin munafukan dake son wargaza min rayuwana nasani ba yau ba.
Bashar na zama yace may kuma mukayi mi muna fukan da bamu son ganin farin cikin ka?
Maimakon ya bashi amsa sai ya juyar da kan shi kawai gefe daya bai kalleshi ba.
Wai may ke faruwa ne wai ka koma haka lokaci guda kaman wani tababe yakara tambayan shi mikewa yayi zaune daga kwanciyan da yake yana cewa.
Kana nufin baka san sherin da maji ta kulla min bane agidan nan wai ?
Innalillahi kana da hankali kuwa yau man ?
Maji ce kuma zata kulla ma sheri a rayuwanka ?
Wani kallo ya watsa mashi yace ba sheri banr may nene?
Murmushi Bashar din yayi yace don Allah may akayi ne wai ?
Yace kaaai wai maji ta fadawa Baba wai mun shirya tsakanina da wanan yarinyae mun amince zamuyi aure.
Wata yarinya ke nan kake nufi wai?
Wata yarinya kake damuna akan ta gidan nan ?
Yace kana nufin wai Bintu?
Yace ita mana.
Alhamdullahi Alhamdullahi kai wani hikima sai manya wallahi tanan maji tafito muna Allah mun gode ma.
Ya dago jajayen idon shi yana kallon Bashar dake ta kwada hamdalla haka cikin mamaki.
Yace wanan abinda maji ta kulla min da may yakama Bassh?
Maji tarasa wace zata lakaka min auren ta sai wanan solaman yarinyar da kwatakwata bata cikin tsarina.
O Lindan ce tsarin ka ke nan ko yar arniyan ka mai dan buje ko ?
Wani wawan nashi yakai ma bashar din ya kauce ma nashi ta hanyan ja baya.
Sadauki ya mike tsaye yace haba man may zanyi da wanan yarinyar ko maryam dina fa batakai shekaru ba a duniya wai itace za,ace na aura ?.
Ita Fatima ba mace kake kallon ta ba ke nan ko ?
Wallahi zakasha mamaki kace na fada ma dan hakin daka rai shike tsone maka ido watarana.
Kai may ya kawo kane ?
Yace manta yau zamu zamfara ne dakai ko kuwa?
Yace bazan tafi ba.
Dariya ya kama mashi yace kafara angwancin ke nan ko?
Zanci ubanka fa Bash wallahi idan ka kara bata min rai yanzu zan rufe daki dakai nai maka tsinanen dukan tsiya.
Bashar yace sai dai yanzu kuma ka rufe daki da Fatima amma bani ba Bashar ba ya juya yafara tafiya yace bari ma na shiga cikin nai ma maji godiyan wanan babban albishir din da kai min.
Da sauri sadauki ya jawo shi ta baya yave kada ka farashi wallahi har ta zaci ko nayi na,am ne da zancen har ina farin ciki da zancen ne.
Farin ciki kan ka kanayin shi komai dadewa zakace na fada maka ai.
Wallahi kada ka fara kaje gurin maji na fada maka, Bashar yace mai da yukan ka a kube kamanta nima maji sarakuwa tave ina kunyan ta yanzu.
Kaima kuma ya kamata ka fara kunyan ta daga yau dan ta zama sarakuwar ka kaman ni daga haka yafita dakin da sauri don yana iya shakoshi ta baya yadda yaga ya hasala.
Dan iska da ka tsaya kaga tsiya a dakin nan ya dade tsaye dafe da bango sai tsaki yake shi daya a dakin.
Sai can yaji taahin motan Bashar daga gidan ya sauke ajiyan zuciya kawai
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
ALLAH DUK WACCE TA KARANTA BATA BIYA BA KAINE SHEDA INA BINTA BASHI,,,,,
Zaune take duk abin duniya ya damay ta a ranta ga shi yanzu daga ita har dan ta sun zama abin magana a gari.
Ko a gaban ta zataji mutane suna bayar da labari yadda ma ba,ayi abin ba haka za,a zake ana labarata shi.
Kowa da,kalar abinda yake fadi a bakin shi ba dama yaron ya fita sai yara abokan wasan sbi su fara gudun shi kaman sunga dodo.
Haka zai dawo gida yana kuka yana fadin abinda yara yan uwan shi sukai mashi.
Abin duniya ya ishi mariya a ranta tai kuka har tagaji ta hakkura don kan ta babu wanda zata kai kukan ta gare shi.
Gashi zaman gidan kawai takeyi tun lokacin da aka dawo da ita daga gidan su daya tura ta manyan suka zo suka bashi hakkuri.
Ba don yaso ba ya hakkura da ita haka na amma zama takeyi ba abinda ke shiga tsakanin su.
Koma cefane ne idan ya shigo dashi sai dai ya aje mata a kofan daki ba tare da yai magana ba.
Idan kuma tana son wani abu sai dai ta tura yara su fada mashi abin da ake bukata a gidan.
Ranan dai taga yana ta gyaran wani kangon dakin shi a zaton maria shine zai koma ciki don ya bar masu dakin su sai bata kawo komai a ran ta ba.
Don dai tasan ba aure zaiyi ba mutumin da ko kudin cefane sai ya fita ya nemo masu abinda zasu ci.
Ranan wani laraba ta zaune tana wanke wanke taji wasu mata su biyar sunyi mata sallama.
Suka gaisa da ita sai suke fadin wani ne dakin da aka gyara daya daga cikin su tace, tana ganin wancan ne da ke da sabon siminti.
Basu bi takanta ba suka nufi dakin suka shiga ciki suna dan dubawa anan suka barta tsaye da mamaki.
Bata iya masu magana ba suka fita sai gasu da kaya suna shigowa dashi.
Kasa daurewa maria tayi tace wai bayin Allah daga ina haka bakuce min komai ba kun kama shigo da kaya cikin gidan mutane.
Dayar matar tace a,a shi mai gidan bai fada maki yai aure bane yau matar zata tare ma.
Ai mu amarya muka kawo yanzun haka munzo gyaran dakine ma kagin anjima mu kawo ta.
Allah ne ya taimaka maria bata fasa ihu a gaban su ba amma sai ta fada dakin ta can ta fasa abinta ita kadai tana fadin na,shiga uku yanzu da wani zanji halin da nake ciki ko da zancen kishiya kuma?
Bata fito ba sai da taji fitan matan daga gidan mayagin ta ta dauko sai gidan su ga girkin da ta dora a saman wuta nan tabarshi ta fita.
Da kuka ta samu uwar ta tana fada mata abinda ya samay ta nan uwar tashiga zagi tana fadin amma Atiku ya cika tsohon macuci wallahi.
Yanzu da yake nan yana yawo kaman almajiri ashe har yana da kudin da zaiyi aure, bamu sani .
Nan sukai ta kullawa ita da uwarta a tsakanin su har dare ya soma ta fito zuwa gida.
Koda ta koma ta samu har girki ta ya kone wuta ya mutu don kan shi nan dai ta kwashe shi haka na don bazata iya girka wani ba yadda take ji a lokacin.
Atiku na shigowa gida ta tare shi da masifa da jidali nan ya dakatar da ita yace.
Maria ki shiga hankalin ki wallahi kada na bata maki rai a gidan nan kin dai san ina da haushin ki dama to ki iya kan ki dani wallahi ko ayita a akare a gidan nan don dama kin kai min ko ina wallahi.
Nan ta shiga zage zage tana kiran shi macuci azzalumi dama ashe yana da kudi yake ce masu baida shi yanzun ina ya samu kudin aure.
Yace wanan aure kikace dole na samo shi don naji dadin rayuwa na kuma duk mata ta shigo gidan nan kikace zaki daga muna hankali wallahi sai dai ki koma gidan ku kinji na fada maki mara mutun ci da tausayi kawai.
Ke abinda kikai min a duniyan nan har kina da bakin magana don zan kara aure.
Kuma ai dole na kara aure na samu wace zata kwantar min da hankali na wadda zanji dadi da sanyin rai a gurin ta.
Ba irinki da kikai shekaru da shekaru kina gwada muna boni ni da diyana ba a gidan nan.
Don tsaban iya cutan ki harda dan ciki kika zalunta dakanki da kanki kin mayar damu abin zunde da kwantance a gari saboda tsaban kwadayin ki.
Yana fadin haka yai alwala ya fita, daga gidan ran shi a bace yana kutawa shi kadai.
Bayan sallan magariba kaman masu jiran a idar da sallah sai ga yan kawo amarya da gudan su sun shigo gidan.
A zaton maria za,a kawo mata amarya dakin ta irin na al,ada sai taga sabanin haka.
Sai ma jin da tayi lokacin yaran ta suna cin abinci a,waje matan na gardama a tsakanin su cewa.
Ko wanan ne akaiwa fyaden cikin su dayan tace karamin ne fa akace sai dayan tace a,a fa ance babban ne mai sayar da pure water uban ma bai ko san tana aza mashi tallah sai ranan da abin ya faru ya sani.
Kai amma wanan matar ta cika azzaluman mace ita tajawa dan ta wanan bakin sunan haka har ya mutu ana kwatance dashi a gari.
Wani irin zafi da radadi maria taji a ranta take ji kaman ta fito ta basu amsa amma kuma ita kadaice a gidan kada su taru su yi mata tsinanen duka don taga a tsaye suke su ma.
****** ********* ******
Haka kawai ranan na tsiro da tafiya kauye ba,shiri nacewa mama dake shirin zuwa gidan buki zan tafi garin mu yau.
Da sauri ta juyo ta fasa daurin dan kwalin da takeyi tace zaki kauye Fatima ?
Na dukar da kaina a kasa nace eh mama mamana ce bata da lafiya jiya ake fada min a waya da dare.
Tace assha amma gaskiya ban son tafiyan ki a motan kasuwa yanzu da zaki bari zuwa jibi idan angama bukin nan sai nasa a kaiki.
Nace mama yau nake son zuwa don na dawo da wuri insha Allahu ba abinda zai samay ni mama ki kwantar da hankalin ki.
Ta je gun jakkan ta na hannu ta dauko min kudi sun kai dubu goma tace gashi kiyi kudin mota dashi idan min tafi yadda kika samu jikin nata sai ki min waya nace nagode mama.
Sai da na gama shiri na tsab na fito falon lokacin su Amira ne kawai a falon ganina da jakka kamar may shirin tafiya suke tambayana.
A,a gaki kamar may shirin tafiya mana Bintu ?
Nace eh anty zani kauyen mu ne yau, gurin mamana har ma gurin babana zan leka na kara dubo shi insha Allahu.
Maryam tace yaushe zaki dawo nace sai na kwana biyu gaskiya to Allah ya kiyayye hanya.
Har kofan gida inda zan hau Napep din da zai kai ni tasha maryam ta rako ni na tafi.
Sai dai a cikin ranta bawai ta yarda da zanyi tafiya bane don ganin mahaifiyata kawai dai na gudu ne don kaucewa yayan su sadauki.
Amma sai ta sa a ranta zata saka ido taga shi wani reaction zai yi akan tafiyan nawa.
Takira Bashar din ta take fada mashi da kuma abinda itama take kullawa yace haka daidai zan tayi saka ido nima insha Allahu.
Ban isa gida ba sai da yamma don ban fito da wuri ba kuma motan bata tashi da guri ba.
Ina isa gida sai ganina mama tayi kwatsam tace a,a ke kina hanya ne ashe nan muka gaisa nafito da dan tsaraban da na kawo masu aka shiga rabawa.
Dakin da bakowa suna aje tarkace a cikin shi sai wani dayan kani na da ya dan tasa ya dan girma.
Nan na gyara na kai yar jakata a ciki tare da shimfida tabarman kaba sabo da mama ta bani na dinga kwantawa akai.
Ranan haka na kwana ina juyuyi don yaushe rabona da kwana saman tabar ma, zaman birni ya fara bata ni yanzu.
Sai tunane nakeyi ko may su maryam suke yanzu don nasan dai basu kwanta ba saboda a can dare baiyi ba sosai kila suna can suna kallon season film din da muke bi a zeecilmer .
Miskili jarababbe mugu azzalumi na furta a fili nace yanzu ai sai ka samu wata ka lalata ba dai ni Fatima Binta ba kuma.
Nace ko hutu ya kare ban dawowa sai naji ka tafi kabar kasan zan dawo macuci kawai.
Allah kadai yasan irin iskancin da yakeyi can bariki idan ya tafi babu kowa nan ma gida ya yi shaye shayen shi balle can inda babu kowa tare dashi.
Mazina ci kawai mai boye kama ashe shiyasa yake wani kallon mutane duk shakiyai ne irin shi gashi kirkiri ya rabani da Usman ba wai ban son usman bane amma saboda bakin zargin shi dole na rabu da Usman din ba don naso haka araina ba.
A haka har barci ya dauke ni ban sani ba sai washe gari kiran sallah da ya tayar dani a lokacin.
Bayan na idar da salla ban kwanta fitowa nayi na gyara gidan ko ina don yana bukatan gyara.
Ga karan gidan da akai danni duk ya tsufa har ya dan dadare daga yadda aka jera shi da farko.
Makewayin su ma haka tsufin tsumane na wani tsohon babban riga aka tare bayin dashi.
Ga kwata ya taru sai diyan sauro da kuda da gurin ya tara ya wani canza launi duk da kasa ne yashi amma rashin samun gyara yasa gurin ya canza launin shi.
Nan ma sai dana gyara nasa musa kanina ya debo tsakuwa da yashi muka zuba ya dauko wani falalen dutse muka kara dagwarawa a saman gurin don mutum ya samu gurin hawa yai wanka.
Kafin dan wani lokaci gidan ya koma tsab dashi kaman bashi kaca kaca da farko na dora ruwa muka dama kunu ina gamawa na dora sauran tuwo na gyara ma ma yaran don dashi suka saba karyawa.
Sai dana gama nai wanka na shirya tsab dani dakin da nake na gyara kafin lokacin sa girkin rana yayi.
Sai da mijin mamana naji ya fita daga gidan don bai tashi sai rana ya raba wani lokaci ma alokacin zaiyi sallah.
Na shiga gurin ta na samu tana nade kayan wankin da na samu tayi jiya da na zo.
Nace ta bari dakin na zo na gyara mata dama nan kuma na shiga gyara nafito da tulin shara daga dakin don irin gyaran da ake mai na sama sama ba,a kwakwalo komai da kyau.
Dakin sai gashi yafito tsab dashi kamar dakin mace nace mata may za,a girka ne da rana
Tai murmushi tace ai bamu girki rana sai dai da yamma idan ya dan samo muna sai mu girka jiya ma da kikazo ai sa,a ki kayi yasayo muna dawa shine nan nai muna tuwon shi har kika samu.
Haushi ne ko tausayin ta zai kamani na rasa may mama ta zaunayi gidan wanan mashayin har lokacin nan.
Yanzu gashi har sun kai ga tara yara har shidda dashi babu zancen fita gare ta kuma ke nan.
Bance mata komai ba nafita na kira musa ya sayo muna rogo da zogala a bakin yar kasuwan su.
Nai zaune na gyara shi kowa yaci ya koshi muka sha ruwa abin mu nayi hakane don mu kyale mugun mijin ta da baida katabus ga iyalin shi ko yaushe.
Dan na lura yanzun idan nazo komai bai saye in an tabaye shi sai yace a tambayi Bintu ko tana da canji a sayo.
Yana ko dawowa yake tambayan ba,a gika komai bane a gidan mamana tace ka kawo abin girki ne halan ?
Yace baga Bintu tazo ba bata sayo bane a girka din ?
Naga idan tazo takan dan yo muna dabara yanzun aci shiyasa yanzun nake farin cikin zuwan ta furin mu ai don nasan idan tazo hankali na a kwance yake da kayan bani banin ki.
Tace to bata sayo ba yau don haka sai ka canza tunanen ka kafita kasamo muna.
Yace kin tambaye tane tace maki babu a gun ta da zaki ce na fita in na fita ina zan samo tunda ba sana,a nakeyi ba ni.
Sai kawai naji yana kirana ke Bintu Bintu fa na amsa daga dakin da nake nace na,am Baba na fito.
Yace cewa nayi baki zo muna da komai bane wanan tafiyan don naji shiru har yanzu bakice muna komai ba?
Nace ban zo da shi ba a takaice.
Kallona yake don jin yadda na bashi amsa duk nima ban so bashi amsa a haka ba don ko banza mijin mahaifiya na ne shi.
Ina fafin haka na juya ban tsaya ba balle naji may zai kara fadi kuma tunda ba ta ido ne dashi ba.
Yanzun kai bakaji kunyan tambayan ta wanan magana ba haka wani sana,a takeyi ne a can kokuwa itama ba karshin wasu take bane wai ?
Yace na dai fahinci abin akwai rainin hankali watay kin hada baki da uwar ki kada ku taimaka ko to oho akan ku zai kare ai munafukai kawai.
Idan naga abin rainin wayo ne sai yarinya ta koma gidan uban ta wallahi tunda nan ba gidan su bane ?
Zance ke nan kake fadi ai matsawan ina gidan nan dole ne yarinyar nan ta zauna a gidan nan ita ma.
Yafita yana fadin oya shege ka fasa ni daku kuwa a gidan nan mama tace ai ni wallahi dana huta ta wanan wahalan.
Ni dai ina jin su nace mashayin banza kawai a raina a haka zaka kare har girma yazo maka baka bar tabara ba har yanzu.
Muryan kani na musa dake zaune ta waje naji yana fadin ni wallahi mama da ma kin gudu din mu huta da halin baba mu koma can birni gurin yaya Bintu muma mu huta kawai.
Daga daki nace kai musa baka da hankali ne ina ruwan ka da saka baki ga maganan man ya ne wai ?
Da yamma muka shirya nace su rakani unguwa duk da ban fadi inda zan tafi ba sai gidan su marigayi Kabir naje gaida mahaifiyan shi.
Matan bata gane mu ba sai da muka shiga har dakin ta muka gaisa da ita, sai dan shiru can tace ban ko gane ki ba.
Nai dan murmushi nace Fatima ce diyar Hausin dan Amo, tace Allah sarki Fatima kuwa haka akayi gaskiya ban gane ki ba wallahi.
Nan ta,rasa inda zata sani don murnan gani na tace yaushe kika zo garin namu nace mata jiya nazo Inna.
Nan muka zauna muka kara gaisuwa dasu da sauran matan gidan suna kara jajanta min mutuwan Kabir din.
Nan suke fada min iyalin shi yanzu suna sokoto zaune don karatun yaran shi daya bari.
Nace Allah sarki aiko ban sani ba dana shiga inda suke tace min dama ai a uguwar GRA yake da gida an raba gado anba kowa nashi shind ita Saude da yaran ta suka samu gidan .
Nan dai nan dan zauna har zuwa dan wani lokaci nai mata sallama muka bargida bamu ratse ko ina ba sai gida.
Mun shigo bamu dade ba sai ga yaron gidan ya biyo mu da sakon wai inji mahaifiyan su.
Ana wata ga wata sai ga wani dan kanin Kabir da suke uwa daya dashi ya aiko wai yana so na da aure yana son ya maye gurbin yayan shi da ni.
****** ********* ******
An wuni an kwana har dare duk shigowan da yakeyi a gidan baiga Bintu ba a ran shi yake tambayan wanan ko lafiya tak
e ne ban gan ta ba duk kwanakin nan ?.
Yana son ya tambaya sai daibai son raini ko tuhuman wani abu ga tambayan da zaiyi na ina nake kwana biyu baya gani na.
Da yamma ya shigo gidan baiko shiga part, din shi ya wuto cikin gida direct nan ya zube a falon mahaifiyan shi.
Wayan shi ya jawo daga aljihun shi, bayan sun gaisa dasu rasa may ke mai dadi shine ya ciro waya.
Ya fara yin game da ita sukosai hiran su suke suna kallo hankalin su a kwance abin su sabanin shi dake a cikin damuwa.
Can yace maryam
Ta amsa da na,am yayan mu .
Yace wai ina wanan yarinyar take ne kwana biyu bana ganin ta ?
Tace yaya sadauki Fatima kake nufi ?
Yace ita din mana.
Tace ta tafi kauyen su yau kwana uku ke nan taje gun mahaifan ta ne wai zata kwana biyu a can.
Wani irin faduwan gaba yaji a lokaci guda, yace a ran shi kodai saboda abinda ya faru ne a tsakanin mu ta bar gidan nan don ni.
Duk sanyin AC dana gari da akeyi bai hana ahi feso wani irin zufa ba a lokaci guda.
Take kamannin shi ya sauya a cikin, lokaci guda, idanuwan shi sun sauya kala zuwa ja a lokaci guda.
Tankar wanda aka watsa wa barkono yace a kasale yaushe tace zata dawo ne wai ?
Tace zata kwana biyu a can don haka ba rana ke nan sai dai idan mun ganta kawai.
Yace ba kun kusa komawa school ba shine zatai tafiya taje ta zauna har wani lokaci.
Maryam tace ai muna da sauran lokaci ga hutun mu yaya kila sai hutun ya kare zata dawo ai?
Maryam tace lafiya kuwa yaya kake tambayan ta cikin son kara tuhuman ta akan shi.
Yace No babu komai dama zanyi bakine shine nake son ta hada min wanan abin dama yan wasu abubuwa.
Daga haka yaja tsaki ya mike tsaye yabar falon a lokacin maryam ta dan matsa gurin Amira bakin ta tab da gulma tace a hankali.
Cikin yanayi irin ta mai rada tace wai anty may kika fahin ta ga yayan mu da yake tambayan Bintu.
Tace eh nima nai mamakin jin yana tambayan Bintu don naga shi bai damu da kowa ba ai.
Hmm baki fahinci komai ba,wallahi amma ni nasan yaya yafara kamuwa da son Bintu wallahi.
Kai haba wata Bintu can wanda ke shiga duniya yana ganin mata kala kala shine zai tsaya son wata Bintu can.
A ganin ki ba tunda ke baki san so ba har yanzu kina nan zaune a na soyewa a gida baki sani ba.
Ke dai wallahi akwai ki da shirmay tsiya maryam may zaiyi da Bintu wace kullun cikin fada suke a gidan nan .
Mugun takaicin ta fa yake ji shine ke ko yar kayan soyayya kike ganin kamar shi suke yi.
Maji da tasamu suna firan tace waye wai,?
Amirah tace wai yaya sadauki take cewa wai soyayya suke da Bintu kila a boye haba may zaiyi da Bintu ga yan mata yan gayu iri iri a gari ko ina.
Eh tun da ita Fatiman ba mutum bace ko ke kin fita kama mai kyau ba da zakice hakana.
Shi damay yafita ?
Ai da ta taimakawa rayuwan shi wallahi dayayi arziki in ya aure ta.
Ita Bintu din dai maji ?
Oh baki san shi al,amarin aure ba ke nan ashe da sauran ko ke tunda baki da fahintan komai.
Ni na dade da sanin abinda yakeyi kyaleshi kawai nayi kada najawa yar mutane matsala.
Kai haba maji don Allah kubar wanan zancen mana kada ku ja wani matsala kuma yarinya na zaman zaman ta yasa ta agaba.
Kai amma dai anty Amirah nan .
Watarana kice na fada maki ai.
Ita dai Amirah jin su takeyi kawai don tasan haka ma bazai taba yuyuwa ba ai.
Wata Bintu can yar kauye kuma ba diyan kowa ba, a gari.
Sai ma taji ranta ya ba i kawai da zancen don abin haushima ya bata ita a ran ta.
Yaya sadauki na barin falon dakin shi ya shiga ya fada kan gadon shi yayi lamo saman gado.
Tan kar wanda yake barci, sai dai ba barcin yake ba yar damuwa ce da bai san dalili ba ya dami zuciyar shi kawai.
Can ya tambayi kan shi wai may yasa har yake son damun kan shi akan yar karamar yarinya hakane.
Gashi a yadda ya lura da yarinyar bata ma gama sanin komai ba na rayuwa don akwa childish a tare da ita har yanzu a rayuwan ta.
Karancin shekaru uwa uba kauyanci bata san ko inaba daga sokoto sai kauyen su kawai.
Shi dake son mace nagani nafada na gwadawa tsara shima ya faso zai tsaya ga yar kauye kuma karama haka dako twenty bata cika ba har yanzu.
Sai yaji take wata zuciya tana gargadin shi dacewa kai baba ina kai ina wanan tunanen kuma wai ?
Washegari tunda safe yashigo yana cewa shi zai tafi Abuja yanzun nan maryam tace a,a yaya wai ya zancen bakin da kace kuma zakayi har ina shirin masu abinda kace ai masu din.
Yace No maryam ki barshi kawai sun fasa zuwa din zanyi tafiya ne nima yau din nan.
Bashar yana jiran shi a kofan gida nan suka samay shi da suka rakashi, Bashar ko a,gaban kowa bai ita boye kaunan shi ga maryan yanzu sai ya baiyana shi a fili.
Don suna fito tana dauke da yar jakan tafiyan yayan ta, da ta karba ta saba a kafadan ta.
Daga cikin mota da Bashar yake zaune suna karasowa idon shi akan maryam yake cewa Madam how far?
Ita ko tai wani shake murya tace bakomai yace ya su mama tace suna lafiya.
Har sadauki ya zauna a mota Bashar sai soyewan shi yake yi hankali a kwance.
Dallah malam ja mota mu tafi da wanan bakin shirmay naka babu kunya da kake min.
Easy man, take it easy bani nakar zomon ba fa, kaga ni fa ban hanaka ba don ni ba motsoraci bane irin ka.
Wani harara yakai wa Bashar yace wallahi zaka kaini makura Allah da wanan halin rashin kunyan da ka tsiro wa mutane daga sama.
Bashar dai yaja motan shi yanawa sahiban shi bye bye, suka bar gurin suma suka juya zuwa cikin gida.
Airport ya kai shi nan ya shiga jirgi da ya tashi da sha biyun rana suka tafi Abuja, bai so buga wanan wasan ba amma halin da yake ciki yaji kawai gara ya je ya buga ball din shi ko zai samu sauki a zuciyan shi.
Duk da kwallon da ya buga bai hana shi jin abinda yake ji a zucuyar shi ba har yanzu.
Suna waya da mutanen gida amma bai, taba jin wani yai zancen yarinyar ba ko yaji an anbaci sunan ta ko a waya.
Gashi girman kai ba zai iya barin shi ya tambayi kowa labarin ta ba don sai yana ganin kamar abinda yai mata ne yake ganin bai kyautawa yarinyar ba.
Don yana gani ai kaman zaman kaunan shi yarinyar take a gareshi amma shedan ya rude shi yai mata haka.
Yace a fili, kai kai gaskiya ban kyauta why don Allah why har haka ya kasance a tsakanin mu ne wai.
Ya dan kai wa katifan da yake kwance nashi da hannun shi na hagu da karfi sosai har sai da ya dan jin zafi a hannun shi.
A haka ya kai har sati biyu acan suna da wasan da zasu buga sati mai zuwa amma ya juyo ya dawo gida haka kawai.
****** ********* ******
Ina gurin mama na zaune na sake raina ba abinda ke damuna yanzun in ba matsalan mijin ta ba da kulun a cikin tashin hankali suke a tsakanin akan ban kawo masu komai ba.
Amma nazo ina cinye mashi abincin gidan shi a banza shi gaskiya ba zai zauna da agola ba a gidan shi.
Naso na bar garin amma sai na dake na tsaya inga iya gudun shi ko zai kore ni ne ni kuma nasan yadda zan girgiza mashi auren shi.
Sai dai ya shigo yayi haukan shi ya fita babu mai tsinka mashi a cikin mu dan dama ma ita mama sukan kwasa dashi idan abin ya ishe ta.
Gidan kowa ban zuwa kullun ina gida zaune kamar wata matar aure can dani.
Ganin shi kawai sukayi da yammacin jumma,a ya diro garin nan suka gaisa mama take tambayan shi yaya akayi kuma ya dawo ba yace suna da wasa wani sati ba sai satin sama zai dawo gida.
Yace eh maji nadawo ne nai wani abu a garin kuma da akwai wasu takardu dana manta ban tafi dasu ba da zan tafi.
Yakai wani lokaci a zaune baiga giccina ba hakan yada shi sanin cewa har lokacin ban dawo ba ke nan garin.
Ya mike ya fita kaman wani mai jin kasala a lokacin, Bashar ya kira yazo idan an fito sallah su fita.
Ranan Monday maryam tafito a cikin shirin ta zata shiga makaran ta,a waye ta samay shi ya fito daga gurin exercise .
Sun gaisa yake tambayan ta ita wana har yanzu taki dawowa ba kun koma makaranta ba tace eh munyi waya da ita tace bata san ranan da zata dawo ba kila ma,
Fuska a daure yace ina ne garin su?
Tace, a yaya baka san garin su Bintu ba kai, duk zaman ta a gidan nan?
Yace don Allah malama fara bani amsan tambayana kafin kiyi min halin ku na yan kasa tukun na tambaya cikin tambaya.
Tace can rabah take nan dai tai mashi kwatancen yadda ake zuwa garin yace inda muka tafi gaisuwan wancan mutumin da tatashi aure kenan ya rasu ko tace mashi eh can ne ya amsa mata da ok good.
Zaka tafi garin ne yaya ta tambaye shi tare da kallon fuskan shi yace ban sani ba tambayan ki kawai nayi.
Sai batan kamar kwana biyu da tambayan maryam ranan da safe yace wa Bashar ya shirya zasu tafi wani dan kauye su dawo.
Sam Bashar bai kawo komai ba a ran shi nan yazi ya dauke shi shi yaja mota suka tafi.
Ban zuwa gidan kowa amma ranan haka kawai nace zan je na gaida kakanin mu kafin na tafi don saura kwana biyu na tafi.
Mun fita gida da kaman awa biyu suka shigo garin wani mai faci bakin titi suka tambaya gidan dan Amo shayi akai masu kwantacen gida.
Da farko da suka isa gidan yaso yai gardama ko banan ne gidan ba saboda ganin yadda gidan kaman ma yafi ko wani gida na uguwar lalacewa a shiyan.
Sallama suka ce ai masu da maigidan yaron da suka tura yace kai mai gidan kan yanzu ba,a samun shi gida yana can gurin moli.
Basu gane may yaro ke nufi yace yashiga yace wai bakine daga sokoto sun zo ganin Bintu.
Mamana tanajin haka tace, Bintu bata nan tafita amma ace su waye yace ace yaron hjy ne yazo tafiya da ita.
Jin haka yasa mama tace ace su shigo daga ciki ai su yan gidane nan ta tura yaron ya kirani gidan kakan nina, basu so shiga gidan ba amma dole suka shiga.
Shi dai bashar sai kallon ikon Allah yakeyi kawai don abin ba mamaki ba daure mai kai yayi.
Bin gidan yake da kallo da mamakin yadda dan adam ke rayuwa cikin wanan rubaben ginan haka da akoda yaushe yana iya rushewa.
Bai san cewa shigina in har akwai mahaluki a cikin shi ba Allah na karewa yadda yaso.
Tabarma mana ta shimfida masu daga dakin ta nan ma yai matukar mamaki wai dakin da ake rayuwane, acikin shi haka.
Ruwa ta debo masu acijin wani kufin silver ta sabo ta kawo masu bashar ya karbi ruwan ya dan kora a cikin shi.
Shikan bai san yaya zai iya kai wanan cup din a bakin shi ba gaskiya don tun bashar baisha ba yaji kaman yai amai.
Bayan mama ta dan fita dauko masu abin fitara ne Bashar yace wallahi kasha ruwan nan don ba haka ake neman aure ba.
Cikin tsawa yace Bashar you are very stupid wallahi.
Neman auren wa kuma can sai dai idan kaine kazo neman auren ban sani ba don kai baka raina mata naga alaman haka ?
May ye abin rainawa ga abinda mutum ke so a ran shi ?
Shiru yayi don mama ta dawo a lokacin tana mika masu abin fitaran tana fadin kuyi hakkuei akwai zafi wallahi.
Sai ga wata akuya tashigo nan ta hau saman tsadaddun takalman su ta sake mai fitsari a na shi.
A hankali yace oho shit da ido yaiwa bashar din signal ya kalli kofa abinda akuya take mashi.
Murmushin keta bashar ya sake mashi, yace don't mind my friend duk ciki ne ai.
Lokacin na shigo gidan da mamakin ko su waye aka ce sun zo nemana a lokacin daga sokoto.
Sam ban kawo cewa shine ba don sai ina zaton mamace ta turo wani ya dauke ni kila.
Ina bullo daga kofa mukai arba dashi zaune cikin fararen shaddan shi yaci starch.
Nai matukar mamakin ganin su a gidan mu dakin uwata musa ne ya hango akuyan tai fitsari akan takalmin dayan su ya shiga koran akuyan ya debo ruwa ya zubawa takalman.
A hankali na tsaya daga kofa ina masu sannu da zuwa, duk na shiga rudewa da ganin su.
Bashar yace min humm Bintu kinzo kinga mama shike nan kin manta da zancen an koma makaranta ko ?
Nai dan murmushi nace ban man taba yaya kawai dai ban tashi dawowa bane a lokacin nan.
Da sauri yaya sadauki yace sai yau she baki da hankali ne wai ana karatu zaki zo ki samu guri ki zaman ko a kauye.
Ganin zai sake layi yasa Bashar tare da fadin yanzu dai mama tace muzo mu dauke ki yau din nan don an koma school tun ranan Monday kin sani kuma.
A hankali nace yau din nan yaya yace eh haka ta bamu umurni shiyasa muka zo ai daukaki din.
Nace ni gaskiya ban shirya ba fa sai dai idan na shirya zan dawo anytime.
Kafin wanin mu yai magana sai mamana ke fadin may zaki shirya kuma ina kin yi wanki jiya kitashi kawai ku tafi tunda har kikaga hajiya ta aiko a dauke ki.
Ban so ba haka na shirya zan bisu su suka fara fita yakawo kudi masu yawa yabata yace tayi hakkuri babu kudi a jikin shine.
Sai da zantafi nace mama ki boye kudin nan kafin mijin ki ya dawo ya kwashe su kiba musa yakai maki gidan su kakale a boye maki su ku dan samu abincin abincin rana dashi.
Nakawo sauran kudin dake hannuna sunkai dubu goma nace tace ga abinda aka bata.
Mukai sallama dasu muka fara hanya ina baya sai tunane nakeyi kawai a raina.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA YA KARANTA ALLAH NAGANIN KI ZAI KARABAN MIN BASHINA GOBE GARE KI,,,,
A LOKACIN MUKE,,,,
Amaryam kan ta tare gidan angon ta Atiku maria haka ta kwana a cikin bakinciki ranan don tashin hankali.
Washegari da safe ko kafin ta gama barcin ta data saba tafito ta samu har amarya ta fito ta gyara gida ta dora ruwan zafi a wuta.
Ganin maria ta fito lokacin tana tsaye tana tara kwanon da tukanen maria, da yaran ta suka bata tun safen jiya har yau.
Bingidan maria tayi da kallon yadda ya sha gyara ko ina, ina kwana ?
Amarya Sadiya tace mata, cikin haushi ta amsa mata tace lafia kawai,
Ta wuce zuwa bayi ta kewaya tafito tafara alwala duk abinda amarya keyi tana binta da ido.
Bazata gwada wa amarya sadiya shekaru ba itma dai sadiya din zasu zo sa,a daya da maria din.
Kafin duk yaran maria su tashi har sadiya ta dama kunu, ko sai ga maigidan ya shigo wanda tun fitan shi masalaci suna can suna zikiri bai dawo gida ba sai yanzu da gari yadan haska.
Yana shigowa ya samu sadiya ta zuba kokon da ta dama ga sabbin robobin da tazo dasu gidan.
Inda taimashi sannu da dawowa ta dauka takai katon roba mai kunu kofan Maria ta girke masu ta dauki nata da mijin ta tashiga dashi dakin ta.
Sai gata tafito da sabon bucket a hannun ta ta deban mashi ruwan wanka takai mashi bayi.
Zata fito ne ta samu maria ta idar da sallah tafito waje tace mata ga kokon ku nan a kofa na aje maku sai ruwan wanka dana sa su fito su fara wanka kada su makara zuwa makaran ta .
Wani kallon banza maria ta watsa mata tace da baki gidan wake basu ruwan wanka dama kada ki kawo min sallo da iyawa don gidan kika shigo.
Kuma ki koma ki dauki munafukin kokon da kika aje don mu baza musha abin sihiri ba wayasan inda kika fito da tarkacen tsiyan ki da zaki wa mutane sihiri kice wai kin dama.
Haba yar uwa gumbane fa akayo muna shi wanda zamu amfana dashi kwana biyu a gidan nan.
Munafuka mun san irin ku wazaki cuta sai dai shi daya daukowa kan shi, bata karasa ba Atiku yafito daga dakin amaryan nashi.
Yace ke Maria wallahi ki shiga taitayin ki idan kikace zaki tirka min tsiya agidan walle na lahira nafin ki jin dadi.
Ke ga kina iskancin ki nakawo ijjiya na saka maki ba fa fin karfina na kin yi ba.
Raga maki dai nakayi don wa yanga yaran dakin ka gani ko suma yaran ba tausayin na kikayi ba da kina tasaya masu da baki kaisu mahalaka ba ke illata masu rayuwan su.
Duk wace tace tashin hankali da diban albarka zata aza min agida bani daukon shashan ci yanzo don zama da mace ba dole na ba.
Aliyu kai, Aliyu ina kake na ?
Sai ga yaron ya fito yana sharan fuskan shi yace baba gani.
Yace ku tai zuwa sallah in kun dawo ku taho ku karya kutai zuwa makaran ta kajiya.
Sai amaryam tace gama ruwan wanka ceniya ga na aza masu suyi wanka sutai zuwa makaranta.
Yace ke baki kunya ba maria, yaushe kika tashi warhaka har ki dama masu kunu su sha suyi wanka da safiya haka.
Kuna na dai ko inke baki sha diyana sha sukai inga ta tsiya yau inkin isa, in tsiya kika so ko wane irina samunai ki kai ga Atiku.
Ya juya ya wuce bandaki zuwa wanka nan yabar maria na fadi ashe akwai wadda akai agidan ga don walle in mace tace makirci ta iya gida nai ta taho wallah.
Ni dai ba tashin hankali nishigo gidan ku yi ba aure na yakkawoni kuma ni tsakani da,Allah nika zama da kowa a rayuwa na don banda mugun nuhi akan kowa.
Amma fa ki sani inkice ba wanga zama kika,bukata a gare ni ba duk wadda kika so yinai zamuyi keji na hwada maki wallah.
Ta juya ta shige dakin ta tafara gyarawa kafin mijinta da ya,shiga wanka yafito ta saka turaren wuta daki ya dauki kamshin safiya.
Maria na jin kamshi har dakin ta rayuwan ta yai matukar baci tace a fili karuwan banza kawai.
Mamakin ta bai kai karshe ba sai da taga Atiku ya fito cikin wankakun tufafin shi Sadiya ta rako shi har kofan fita daga gidan ta kai tsugunne tana fadin.
Ya Allah ka tsare muna bawan ga na ka bashi sa,a da rabo na alheri, ka bashi sa,a ga abin daya fita nemowa yaciyar da mu ta hanyar halal ya Allah ranan taga dariyan Atiku har sai da hakoran shi suka baiyyana a fili.
Duk maria tana daga kofan ta tana kallon bakon al,amarin da ya shigo masu a gida.
Atiku yafita cikin jin dadi yana fadin Ameen Sadiya nagode nagode Alkah yasa ki zama min alheri a rayuwana.
Yana fita daga gidan maria tace wai sabon kicihi can muka fito har takalman ya tsinstinke indai namiji ayi dai mu gani gidan ga.
Sadiya kamar bataji may maria take fadi ba ta,share ta dakin ta takara gyarawa tsab tafito kofinan da yara suka sh koko kafin su fita ta tattara su ta wanke da sauran kayan da tai aiki dasu.
Kagin amarya tai kwana hudun ta maria ba karamin wahala tasha ba saboda Sadiya mace ce mai tsabta da mijin su ya dawo gida kayan da ya cire na aikin shi bata bari ya kwana bata wanke su ba.
Haka dakin ta duk da ba komai a cikin shi sai ta gyarashi sau kusan hudu a wuni.
Maria sai habaici da bakar magana take yaddawa cikin gida tai ta faman fada da yaran ta tana sauke haushin uban su, a kan su.
****** ********* ******
Wanka nayi don shirin kwanciya saboda ban tsaya dogon hira ba gobe mu da lecture mai zafi da zamuyi.
Dogon riga fari mai dan hannu na dauka na saka a jikina ina kokarin daure kaina sai ga mama tashigo dakin namu.
Tace dauka niyi ai keyi barci Fatima?
Nace a a mama yanzun dai naka shirin kwanci wani abu zan maki mama ?
Na tambaya cikin dan kallon ta a cikin ladabi da nake mata a koda yaushe in muna magana da ita.
Tace, dama magana naka son muyi dake inba ki komai ke jiya.
Nace walle mama mi nikai mashin ?
Kwacinya dai naka shirin yin yanzu don gobe muna da lecture da safe insha Allahu.
Ta juya tana fadin ki saman a daki na yanzun in ke gama.
Daga haka ta juya tafita daga dakin ina gama daure kaina nabi bayan mama dakin ta.
Na samay ta zaune a saman gadon ta sai dai yanayin ta kaman tana a cikin yar damuwa a lokacin.
Ganin na shigo takw ce min zonan ki zauna Fatima tana dafa gado daga gefen ta alama take min a gurin zan zauna ke nan.
A darare na zauna dan bakin gadon kadan dan nesa da ita, sai naji ta dafa hannu na daya tana fadin Fatima magana nake son yi dake don haka ki fahince ni kuma idan magana na da takura a cikin shi kada ki damu kanki don Allah Fatima.
Nace mama hwadi dai maganan ki ai babu komai walleh na fadi cikin murmushi don nasan dai kila laifi nayi zatai min magana.
Tace Fatima ina fatan bazaki fassara min magana ta ba da wani fasara gani ke dai kinka cancanci hakan shina yasa na aiwatar da hakan akan ki.
Tace, bakomai na ba so dai nakai ki auri sadauki don dai ta kin ka san halinai kuma kina iya hakkuri akan duk wani baudaden hali nai.
Kamar a mafalki naji zancen mama take duk da sanyin da dakin ta keyi na A C sai da naji zufa na karyo min.
Tace na san cewa keta zaki iya hakkurin zama da yayan ki kuma ki rufa mai, asiri ga duk wani rayuwa nashi.
Wanga dalili dana hwada maki shina yasa na yanke hukunci a raina keta zabina dama shi din.
Tace Fatima nasan cewa a ranki zaki iya cewa missa nai maki wanga mumunan zabi a rayuwan ki .
To maganan gaskiya gani nayi duk matan da yay aure babu komai cikin wanga aure nashi in ba tonon asiri ba a garai.
Har da nima uwatai, ke har yan uwa nai sai gori ya ishe su gidan ga.
Ba yau ba na dade ina wanan hwatan ni kadai a rayuwa ta, amma na rasa yadda zan hito maki da zancen.
Amma yanzu nasan ke dan tasa shekarun ki yakai ta fahinta shinasa naga gara na hwada maki dai don ki san abinda naka kullawa a tsakanin ku.
Wagga magana kuma da naka hwadi Fatima har tai kunnen Baban ku yasan da ita.
Shima dai ya nuna farin ciki nai akan zancen, sai naji muryan ta ya canza tana cewa cikin murya mai kuka.
Fatima Allah yasani ban yi wanga hadin don dai na cuta maki ba, nayi shina dai don samun farin cikin ku baki dai.
Nasan cewa har yanzu bawai ya bar shan abinda yakasha bana ke ma ke san da haka Fatima, hwada min faina bakiyi.
Don kina gudun bacin ran da zan shiga ciki nai shina yyasa baki son na sani.
Fatima ance wanda ya rigga ka kwance yana riga ka tashi na san komai da sadauki kayi, a rayuwa nai don nita na haifi abina,.
Nasan halin rayuwa nai sarai shi dai nayi don gujewa masifan da a ciki nai tunda ya boye min shina yasa nima nabar abin aboye kaman yadda kuka boye min din.
Shin Fatima macen da ka irin wanga halin ai ta san kan ta na inda baki san kan ki ba duk wadda naka gwada maki halarci sai kin tai kin hwadai wani gurin.
Ko ni ki hwada min nasan mi yaka ciki, amma kinka iya boye zancen sai kokari kikai kiga ya bar wagga har kan ke dai.
Fatima kiwa Allah ki taimaka min akan wanga yaron don ban san mi, Allah ka nuhi ga auren ku ba.
Nasan cewa na hada ki da aiki Fatima, amma gani nayi ke ta kadai ka iya tayani wanga kwaran ba tare da anjiya ba.
Sai tai shiru kuka ne yafi karfin zunciyan ta a lokacin don haka ta kasa ci gaba da maganan ta.
A hankali na zamo daga saman gadon da nake zaune tare da durkusawa daidai kafan ta nima dai din kuka nake sosai.
Kaina ta dafa tace nasan baki son wanga hadin da naka shirin maku don shi ba son kina yakai ba.
Amma na sani Fatima an, walleh sadauki sonki yakai so daina bai sani bashi, a ruyuwa nai.
Kuma in kunyi aure duk bari shikai da yardan Allah ba zai wulakantaki ba Fatima an kuma ni ban barin hakan ya hwaru tsakanin ku.
Jin tai shiru ni kuma ina duke na kwantar da kaina saman cinyan ta sai darzan kuka nakeyi.
May zan bata amsa dashi nace ban son mashayin dan ta ko may, ?
Inace bata kyauta min ba don batai man adalci a rayuwana ba duk da nasan batai min ba din ko may zan ce mata?
In ce, mama kin cuce ni da kika hadi da danki mara mutunci mara tarbiya lalattace ko may?
Ince bata kyautawa rayuwana don da itace ta haife ni da cikin ta bazata taba min wanan zaben da tai min ba ko may?
Haka yasa naja bakina nai shiru sai kuka nake yi wanda na rasa kukan mana wani cikin tunane na nakeyi?
Shiru itama mama din tayi tana nata kukan tana sauraren nawa da nakeyi cikin tashin hankali.
Fatima nasan zaki ce ban kyauta maki ba a yanzu don bazaki gane may nake nufi da wanan hadin da nayi ba.
Amma nasan nan gaba idan ina raye insha Allahu zaki gane haka kuma zaki gode min a rayuwan ki.
Fatima gida bai koshi ba ai ba akaiwa dawa muma nan mu na bukatan kki a cikin mu, don haka mi zai sa in bari wanan baiwan taki ya tai gidan wani ina kallo bayan muma nan muna da bukatan ki a cikin mu.
Ban iya cewa uffan ba har lokacin sai naji muryan mama tana fadin tai ki kwantawan ki keji indai kega da takura ki hwada min sai a hwasa.
Da kyat na mike na fara tafiya kuka yaci karfi na don haka dashi na fita dakin mama tabi bayana da kallo tace a fili.
Fatima am sai dai kiyi hakkuri don abinda ka hissheni na nakayi ke kadai ta ka iya halin wanga baudaden yaron da Allah yya ban.
Kuka sosai nake a daki ni kadai gashi uwayen kallo suna can falo har wanan lokacin suna kallo.
Maryam kamar an tsikare ta sai gata tashigo dakin dan wakan ta, sai ganina tayi a kwance na kifa ciki ina darzan kuka ni kadai a dakin.
Mi nika gani haka shin?
Missa may ki Bintu?
Sai ma kara sautin kukan dana dan yi ban bata amsa ba, itakuma bata fasa tambayana ba tare da zaunawa gap dani tana tabani.
Bintu baki hwada min ko missa may ki shi,?
Ko sai na tai na hwada ma maji ta taho ta tambaye ki da kan ta?
Ba amsa sai ta mike zuwa kiran mama don tazo ta tambaye ni da kan ta.
Riko hannun ta nayi nace cikin kuka anty don Allah ki dawo kada kitai wurin mama don tasan ko may nakewa kukan.
Shi wai minana dan Allah missa may ki kika wanga bakin kuka, wane irin bakar dabi,ata haka shin?
Cikin wanga dare ke zauna a daki ke kadai sai kuka kikai kaman wadda aka aikowa mutuwa?
Shi ko wani na yya mutu anka bugo maki waya wai ?
Na fada jikin ta nace anty na shiga uku na lalace anty mika shirin hwaruwa dani na wai ?
Shi wai mi an kayi na wai baki hwada min don Allah na sani ?
Gashi kece kan na kira maji ta taho tagane ki shin minana hallan?
Ina kwance a jikin ta nace anty na ga boni na lalace shi mi nai wa Allah da wanga bakin rayuwa ka shirin fada min ?
Wane irin rayuwa na ka son hwada maki ?
Wai yaya sadauki mama ka son na aura Anty yaya sadauki mutumin da duk duniya baida bakiyiya irina don dai ina hwada mai gaskiya.
Wani kallo ta watso min tace Bintu auren yaya sadauki na kika wa wanga kuka haka shi ?
Dama ba soyayyana kukai dashi bana ?
Da sauri na girgiza mata kai nace ba wani zancen arziki da ya taba shiga tsakanina dashi ni dai nasan kaman annabi da kafiri muke ni da shiya.
Maji na ta hwada maki haka ko wa?
Nace ita ta ttakirani dakin ta taka hwada min bukatan ta garan.
Yanzu kibar kuka Bintu muyi magana ta fahinta da keya don wanga kuka da kikai nima kuka na kason yi.
A hankali na sasauta kukan da nakeyi don inji may zata fada min, ganin na rage tace shin Bintu ke baki son yaya na ?
Nace walleh anty ban taba so nai ba a rayuwata mi zan yi da mutumin daya tsane ni a rayuwa nai?
Tace ke yanzu zaki iya hwada ma maji baki so nai?
Ta kura min ido cikin kuka nace walleh ban iyawa anty amma da ma mama na tai min wagga magana ba gaskiya hwada ma mai shi magana nakai.
Tace to ke gani.
Ni yanzu shawaran da nika baki shina hakkuri dai zakiyi kada maji ta fahinci haka gare ki.
A yadda nasan halin nai shina kashirin balgace auren da kan shi ke ga dai ke komi bai hito ta bangare ki ba.
Ko mi kki gani ga magana ta ?
Maganan ta dutse don shine mafita a gare ni nace cikin kuka anty na gode shawaran ki na zanbi don shina kadai mahita agaran.
Tace to ke gani amma a,a kika zama cikin daki ke dai kina wanga irin darzan kuka mi da baki kirani ba tundazun muyi shawara shin.
Tace ke ga yanzu in yya jiya nasan ba karamin rigima zaiyi a gidan nan ba, tun da shi arniya mai dan buje yaka so.
Wanan magana shine ya kwantar min da hankalina nan muka raba dare muna magana akan zancen har barci ya dauke mu zuwa asuba.
****** ********* ******
Tun ranan da akai zancen naji ban kara ganin shi bani haka nake ba walwala tare dani ko kadan yanzun ma idan na dawo daga school ban zama a falo ina dakin mu.
Don ni idan da hali badon na gudu mama tace ban mata diyyauci ba da na gudu daga gidan gaba daya.
Shima haka sadauki bai shigo ba gidan tun ranan da Baba yai mashi magana.
Haka ya gaji da fushin shi ga kiran da Amirah ke damun shi dashi tana tambayan shi ko yai tafiyane bata ga ya shigo ba don ita batasan dawan garin ba.
Maryam bata fada mata ba don ta fahinci Amirah bata kaunan hadi tsakanina da yayan ta don ita a ganin ta yayan ta yafi karfi wata Bintu can yar kauye can.
Don idan maryam na magana tana min sheri kan yaya Anty Amirah bata iya boye kin da take wa hakan a zuciyar ta.
Tashiga fada ke nan da maryam tana cewa kefa baki da wayyo don Allah may ye kuma na wanan magana ba dadi ina yaya zai kai wata Bintu can kuma haka.
Ina gani maryam din tagane zuciyar yar uwar ta ne yasa ta ki fada mata komai akan halin da ake ciki.
Mun tafito zamu school muka ganshi tsaye a kofan gida shi da wani mutum da gani dai mutumin ya girmay shi sosai.
Ina ganin shi na dukar da kaina kasa ban yarda na kalli inda suke ba inajin maryam tana gaida shi ni kan ban tsaya ba na wuce abina.
Sai dai shi muna fitowa idon shi akan mu don yana facing din hanyar fitowa daga cikin gida.
Ya ramay ya dan fada kadan sai dai ba kowane zai gane hakan ba sai wanda ya sanshi sosai zai iya gane hakan.
Ina tsaye tazo da motan ta ta dauke ni muka fara hanya, sai da muka dan yi nisa take cewa Bintu nace na,am anty.
Mayasa baki gaida yaya ba ?
Shiru nayi ba amsa tace indan kina haka maji bazata ji dadi ba gaskiya na fada maki ki nuna bakomai a zuciyar ki haka zai sa tafitar da zargin komai a kan ki.
Nace anty ni wallahi ban son ganin shi ma yanzu bakiji yadda nake jiba a halin yanzu dana gan shi a zuciyata.
Kada ki damu insha Allahu komai zai zama normal amma sai inkin bi shawara na fa.
Don haka dakikeyi kin san yafi wayo zai iya hada ki da maji laifin ya koma akanki don haka ki gyara halinki tun wuri har inkina son kanki da lafiya.
Ban tanka mata ba shiru nayi tare da kwantar da kaina ga glass din motan ta kawai.
Can tace dama ina son indan mun tashi daga makaranta na fara koya maki mota.
Da sauri na dago kai ina kallon ta nace, mota anty ni ina zan samu mota kuma?
Dariya ta kyalkyale dashi tace kin san abin Allah ne yar uwa da zakice haka?
Muna wucewa ya shiga gida bayan bakon shi ya wuce daga mamane sai Amirah zaune a falo suna karyawa a lokacin.
Amirah tana ganin shi take cewa kai yayana har zan kai cigiya da sanarwa gidan redio da talabijin a kan ka.
C U yace an fada maki ni raggone da zan bace ko ni bakauye ne da zanbace maku?
Ya juya gurin mama yace ina kwana maji cikin dukar da kan shi yake gaishe ta.
Ka gama fushin ne dakakeyi halan mara hankali kawai?
Fushi kuma maji akan may zanyi fushi da abinda kike so akaina ?
O nice ma mai so bakai ba ke nan ko mara tunane kawai, dariya yayi don zagin da maji ke mai bai san dalilin shi abugi mutum kuma a hanashi kuka ke nan yace a ran shi.
Zama yayi tare da cewa bani breakfast dina Amirah ya fadi Amirah dake masu kallon mamaki bata fahinci komai ba a fadan tace.
Yayana may kuma kaiwa maji hakane wai?
Yace wallahi ban sani ba kaunata kawai dai maji na son min fada ne don taga ban shigo ba kwana biyu ni kuma aikine yai min yawa.
Amirah tashige kitchen ta hado mashi abin karyawa tafito koda tafito ta samu maji na fadin.
Kai akwai gatan da za,ai ma dayafi na daga kayi arziki ka samu yarinta gari yar arziki zata rufa maka asiri daga shi har Amirah kallon maji sukeyi don jin abinda ta fadi a lokacin tace eh ba rufa maka asiri zatayi ba may zatayi, kai may ya saura a jikin ban da ragowan maye sai ball.
Yace maji nine yarinyar nan zata rufawa asiri ko zan rufa mata dai kece kike ganina haka maji amma ai duniya ta san ba abin banza nake ba yanzu.
Wallahi maji inkina fadi haka a gaban ta dadi zataji ta raina ni don bata da kunya Allah.
To ubana sai ka rufe min baki tunda kakawo karfi yanzu ka wuce fadana yace ni bance maji cikin dariya duk yana kokari yaga ta sauko daga fushin ta.
Maji wai wata yarinya ta ki ka yiwa yayana sababi a kan tana haka?
Cikin bacin rai ta dago tace mata Fatima mana ko da me ya fita oho?
Itama Fatima in ba tauye tan danayi bata iya musa min ba mitakai dashi haka ba makari.
Maji mi yayana zaiyi da Bintu kuma yar kauye da ita ba asali ga mata yan asali da yawa a cikin gari.
Da may yahita da zakice haka, nice hwada min damay hita, ?
Shi har wani asali yakaso yabar kyau ne tun wurin wanka ai yanzu ya makara da wanan ko?
Da mamaki furcin mahaifiyan shi ya dago kai yana kallon ta sai abinci yake cusawa a cikin shi kaman dolle yake ci.
Amma gaskiya maji kaman mara galihu zakice wai da Bintu zaki hada shi Bintu may can don Allah dai Amirah ta fadi haka cikin yanayin bacin rai.
Walle Amira kihita min ga ido tun banci kaniyaki ba gidan ke ko kwatan Fatima kin kaine asali ne mi ake bukata ga asalin ba uwa da uba ba.
Hwada min wane ta rasa daga ciki?
Ko shi arzikin ga dakika gani Allah ya bashi kikawa katobara, haka.
Ita ke san inda Allah zai aje tane halan ?
Nikkara jin keyi wani magana mara dadi akan Fatima walle saina lahira yahiki jin dadi a gidan nan marasa ta ido kawai.
Amirah tahau ta cika ranta ya baci ta kalli dan uwanta hadade guy ye haka son kowa kin wanda ya rasa amma ace ga Bintu yar tallakawa zai kare.
Sai dai ba dama ta muda ko tak yadda uwarsu hau tasan yanzu nata na samun ta.
Bai jima zaune ba yamike yana fadin shi zai fita, maji bata tanka mashi ba don haushi.
Mun dawo gida a gajiye don an kusa fara kiran magariba a lokacin saboda huturu yayi.
Amirah ce a falo, zaune ina shigowa naga wani ir8n kallon banza da wulakancin da tai min.
Take nasha jinin jikina da zargin akwai wani abu bani ba
har Maryam sai da ta tsargu .
Mun shiga saida mukai sallah muka fito maryam ta fara fitowa bata dade ba nafito nima falon.
Zama nayi tare da cewa anty Amira an fara film din end of love ne?
Kamar batajini ba ta kyaleni maryam tace min yanzu za,a fara time yayi ai.
Can taja tsaki tace dama kwadai ya kawo mutum ai don kwadayin tsiya abi an asarice muna uwa da tsafi sai yadda akayi muna da ita.
Komai tsafun mutum dai wallahi sai ya bar mu kuma sai ya bar gidan nan don yawan kwadai ma har diyan mutum ba,a bari ba.
Ke dawa ye kuma Anty inji maryam, ke tambayan ta cikin kallin fuskan ta.
Ke dalla kyaleni da takaicin daka damuna yanzu don kwadai sai a asirce muna uwa tasa dan ta ya tillatawa kan shi wata gaja can mara asali.
Kai amma anty Amirah na raina maki wallahi, wanga magana kuma ina ya fito maki haka da girman ki.
Shi yaya din yace maki lakaka mashi ita akayi kan dole ko wa ya fada maki ?
Maryam kifita idona wallahi kafin na bata maki rai a gidan nan don naga ke kina ganin kin girma wawiya kawai da batasan ciwon kan ta ba.
Kasa hakkuri nayi nace Anty Amirah kamar yadda kike gani an lakakawa yaya sadauki ni haka nima aka lakaka min shi.
Don ni yaya sadauki baiko cikin irin namijin da so na aura a,rayuwa na, don kwata kwata baya burgeni.
Shi kuma asali da kike nufin bandashi uwane banda ko uba, bski fini uwa ba baki fini uba ba.
Tsafi kuma ni bamu san shi ba a gidan mu a gidan ku nazo naga a na tsafi.
Aiko tayo kaina wai zata mare ni maryam ta shiga tsakanin mu tace wallahi baki bugun ta don amsan maganan ki tabaki.
Jin hayaniya yasa mama fitowa ta samay mu tana tambayan basin may yafaru kuma mayye haka wai ?
Nan maryam ke dada mata abinda ya faru tsakanin mu da amsan da na bata.
Tace Fatima shiyasa nake son ki don baki shayin kowa gurin fadin gaskiya.
Wawiya kawai sakariya kinga har tabar ganin girma ki ta baki amsa ba yau ba nake ganin take taken ki kan Fatima gidan nan.
Uba kika fita ko uwa ki fada min nace ?
Gurin ubanki ko uwarki tazo maula kin taba jin Fatima ta roki wani abu a gidan nan duk zaman ta damu.
Ku arziki yake rudi har ya rufe maki ido kika manta da Allah, da tazo gidan nan gurina may nake dashi.
Shiru Amirah tayi karshe bata tsaya falon ba ta tashi fuuuu ta shige ciki can ta kira sadauki ta fada mai abinda ke faruwa a gidan yadda maji tai mata.
****** ********* ******
Ranan bamu zuwa school misalin sha biyu da rabi na rana maryam na baya tana wanki mama tana dakin ta tana barci.
Sai ganin mutum nayi tsaye a kaina ban san shigowan shi falon ba sai da na gan shi tsaye a kaina.
Ya nayi yana dan waige waige kamar mara gaskiya yace cikin daure fuskan shi ke jinan.
Na dago na kalle shi saudaya na dukar da kaina yace wallahi duk kika sake kika yarda har maganan maji ya zama gaskiya a kan mu sai na halakaki garin nan.
Mara mutunci kawai banza dake ina mai shawartan ki da kiyi maza maza ki sanarwa maji baki son wanan hadin kema.
Jiki dan Allah ko na rasa mace a duniya may zanyi da kucakar mace mara fasali irin ki.
Duk da zagin ya bata min rai sai nai murmushi a fili nace amma kaima kana da bakin fada mata ko don naga kaman yan maye basu da ta ido kaga kaine daidai ka fada mata idan kayo mayen ka.
Ni kasan lafiyata kalau don haka ina da kunya da daraja ba zan iya kallon idon mama na fada mata ido da ido don ban da kuya ba wai ban son dan ta gudan jinin ta.
Amma kaika nasan zaka iya tunda bata idone dakai ba inkai haka ka taimaki rayuwana da ga auren kaddara aure alkakai da zan tsinci kaina acikin shi gidan mashay,,,,,
Kau ya kwashe ni da mari daidai maryam na shigowa falon daga waje, bata tsaya ba tai ciki gurin maji.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,
IDAN KIN KARANTA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NE SHEDAN HAKA MUNA BINKI BASHI,,,,
O lala ka kai mara mutunci sadauki ka gwada min baka da tarbiya yau, dana so nace sai na bi ra,ayin Fatima akan wanan zance amma yanzu tunda haka ne abin bari kaji indai har ni ce na haife ka ko bana raye sai ka auri Fatima.
Kuma idan ka sake ta ban yafe maka ba a rayuwa na, ba sadauki ba har ni da ke tsaye sai da nakai zaune cikin kuka ina fadin.
Don Allah mama kada ki min haka wallahi bashi ba koni ban ra,ayin wanan hadi bani son shi mama na tsane shi kamar yadda na tsani mutuwa na.
Inda nake ta karaso tare da dafa ni kadan tace Fatima, bani son ki da fadin haka nasan baki so amma don ni da Allah dashi kan shi mara tunanen abinda zai je ya dawo idan ya auri wata can sabba zakiyi.
Kaina na noke a cikin kafafuna ina rusa kuka wanda baka yasa mama ta kasan lalashina a lokacin.
Sai ji nayi tana fadin kafita min a shiya tunda ban isa da kai ba baka kaunan farincikina baka damu da rayuwan ka ba balle nawa.
Zai yi magana tai mashi alama da hannu ya rabu da ita don Allah ya dan tsaya jin sai yaja kafan shi ya fita daga dakin.
Kaina ta dawo ta zauna a gefe na tare da dafani tace Fatima ina fatan kin fara fahintar manufana na son yin wanin hadin danake kokarin yi.
Don haka nake son fada maki sai kin jajirce sosai a cikin wanan al,amarin don akwai aiki sosai ja a nan gaba kafin komai ya dawo muna normal life.
Cikin kuka nace mama ni ba zan iya ba don bazan iya zama da miji mai duka ba bai da tausayi mama bai san darajan mace ba ko kadan.
Tai dan dariyan manya tace zaki iya Fatima zaki iyane na fada maki kuma ko bani raye zaki fadi da bakin ki, taimon da zaki min ke nan daya a rayuwana shine ki auri sadauki.
Don ke ce kadai yanzu nake ganin mafita a gurin ki, kece wace zata kwato min shi daga duk wani sherin rayuwa dake bibiyan shi.
Don Allah Fatima ki daure ki kanne ki fitar da duk wani shakku dake damun zuciyar ki, ki saka a ranki zaki sadaukar da rayuwan ki ne don Allah don ni kuma.
Sai naji ta fara kuka a hankali cikin kukan tana fadin Fatima ban da wani mafita da yafi wanan a yanzu haka yasa kike ganin ban tausaya maki ba.
Wanan hukuncin dana yake insha Allahu shine zai kawo karshen azzalumai masu bibiyan shi dashi wanda ba wai sun fasa ba ne har yanzu.
Don haka kada ki zargeni a zuciyar ki na nuna son kaina a gare ki yadda na haifi Amira da maryam haka nake daukan ke ma din nina haife ki da cikina.
Don duk abinda uwa ko da zaiwa mahaifiyan shi Fatima kina min a rayuwana may zai sa na bari wanan daman ya wuce wanan yaron ina kallo yaje ya dauko min wata sabuwar fitina cikin dakina.
Dan uwan mahaifin shi ma yakasa bashi yarshi kan halin da yake ciki balle wani bare can sabba ya ba shi nashi a zauna lafiya.
Hakan da nayi shine daidai a gare mu baki dayan mu sai dai a yanzu kurciya ba zai bari ki fahince ni ba.
Ba dago fuska na dake shabe shabe da hawaye nace mama na yarda insha Allahu duk abinda yaya zai min zanyi hakkuri na zauna dashi saboda Allah da kuma ke.
Ta rungumoni zuwa jikin ta tana fadin na gode Fatima na gode yadda kikai min Allah kema ya baki zuria masu albarka a rayuwan ki.
Insha Allahu bazakiyi dakin sani ba ga wanan auren da yardan ubangijin mu.
Tace tashi kije ki gyara fuskan ki kada wani ya shigo ya samay ki a haka a dauka ko wani abin ne can daban.
Yadda tace haka nayi na mike na shige dakin mu sai dai ban fito ba na zauna cikin dakin kawai.
Amirah dai ba ruwan ta dani don tamafi yayan ta daukan zafi akan zancen don kwata kwata ta daina min magana gaba daya a gidan.
Sai harara da habaici kawai ne a tsakanin mu da ita, maryam kan ce na fita zancen ta na kyale bata da wayau ne da bata biye wa son ranta ba.
Ina ji ina gani yanzu na koma wata abin boyo a cikin daki ban zama falo ko yaushe kunshe nake a cikin dakin mu ban san komai da akeyi ba a gidan.
Karatuna ne kawai ya tsayar dani garin don da na gudu na koma kauyen mu gurin iyayyena da zama amma kuma ba daman haka don karatuna zai iya tabuwa.
Ranan dai da dare na ce bari na dan fito cikin su a falo na dan zauna kadan na samu daga Amira sai maryam zaune suna hira.
Maryam na ganin na fito take cewa a,a matar yaya yau kin gaji da boya ne kin fito ki sarara ke ma kina wani shigewa daki kina kumshe kan ki a ciki kamar lalle kafa.
Nai dan dariya ina zama nake cewa anty maryam yanzun dai ke ake ji zama nake ina karatu don exam da ya kusa.
Kwadayi dai mabudin wahala ne wallahi, in mutum yace ba zai iya tsayawa inda Allah ya aje shi ba ai yana tare da wahala a ran shi.
Zaman daki kan yanzun aka farashi tinda mutum yace shi dan shishigi ne ya kai kan shi inda Allah bai kashi ba.
Ban yi magana ba sai samun guri nayi na zauna da kyau, tare da mayar da hankalina ga TV dake aiki a falon a lokacin.
Kada dai mutum ya manta matsayin shi ga Allah ya dauki kan shi ya kai inda Allah baikashi inji maryam.
Anty maryam please bar zancen nan don Allah kada mama takai ga jin may mukeyi a falon nan.
Idan ma taji ai haka kike so ke don yanzu nasan abinda ya kawo ki cikin mu kuma kuke kullawa keda munafukan gwagon ki.
Nai matukar jin zafin zancen sai na dan ritse idanuwa na tace yanzu basai ki zauna ki auri maji din ba tunda shi wanda ki ke son mannewa din ya tafi sai muga wanda zaki aura yanzu.
Ko shekara dubu zai yi a can dole dai watarana ya dawo gida aiko?
Zasu ci gaba da sokawa juna magana sai ga mama tafito daga dakin ta da waya a hannun ta tanayi.
Da wata kawarta take waya tana cewa Insha Allahu ranan laraba mai zuwa za,a je kai kayan shiyasa na bugo na fada maki don ki shirya.
Amira ta kasa kannewa da uwar ta gama waya tace kayan wa za,a kai maji ?
Kayan auren yayan ku mana.
Can kauyen ko ina?
Ki tambaye shi mana kiji daga bakin shi ko?
Amirah da ta cika ta mike zuwa daki cikin kunan rai, waya ta dauka takira dan uwanta kira daya ga na biyu ya dauka.
Yace Amirah yaya akayine?
Tace yaya yanzu nake jin maji na waya wai ranan laraba za,a kai kayan auren ka kauye.
Dariya taji yayan natayi yace as maji wish zan kyale ta tayi duk abinda zatayi don lafiyan ta da kuma gujewa fadawa fushin ubangijina akan hakkin ta da ke kaina.
Amma ai nine mai auren ko let the vegan come into my house zata rena,kanta da kanta barni da yar iskan yarinya kawai.
Amira tace amma ni gaskiya yaya ina son ka dauki mataki gada ma ayi wanan auren kwatakwata wallahi don ina jin kunua ace wai Bintu ce matar ka gaskiya.
Class din ka ka kare ga wata Bintu can yar kauye wallahi nayi hating din yarinyar nan baka ga yadda ta wani kara komadewa bane ma yanzu.
Dariya yayi yace common Amirah fita zancen kawai ki bar su maji da munafukan nan maryam da Bash duk sune masu kara zuga maji ai zata zo ta same ni ne.
Suna gama wayan da Amira sai yaji gaban shi yai wani masifan faduwar gaba don ua tuna maganan maji da sukayi kaeshe dashi kan zancen auren.
Yadda ke kullawa zai wa Fatima muddin ta shigo gidan shi ga maji tai mai sharti akai.
Domin yadda yake ji a cikin ranshi a lokacin zai iya aiwatar da komai kan wanan manyar yarinyar dake son taiwa rayuwan shi karan tsaye.
Shi yasa ma yai saurin kashe wayan da sukeyi da Amira don maganan ta na kara tunzura mai ziciyar shi ce.
Duk yadda yake son yaiwa mahaifiyar shi biyaya akan auren zabin ta da tai mashi bai tsanmanin zai iya yin adalcin aure akan wanan yar kauyen dako Abuja bai iya fita da ita balle wani uwan duniya.
****** ********* ******
Kamar yadda maji ta fada haka din ne cikin satin da ya zagayo aka kawo lefen auren mu gidan mu.
Muna school har masu zuwa kai lefen suka taru suka dauka zuwa kauyen mu gurin kai kayan.
Akwati ne har guda goma sha biyu dankare da kayan irin na zamani, tsayawa fadar abinda aka zuba acikin akwatinan, sai abin ya zama tankar kauyancine saboda babu kadai ba asaka a ciki ba.
Nan abin yazama turiruwa ga matan kauyen zuwa kallon abin arziki.
Su gwago da yake sun san yadda ake a birni su ma basu bari abarsu a baya ba don suna tallakawa, suma sunyiwa yan kawo lefen abinda ya dace suyi.
Rago gassa abin sha da sauran takarce na kauyawa irin su fura da nono dakar hannu mai kyau cikke a raba mai marfi.
Yan kai kaya suka dawo suna yaba karamcin da akai masu a kauyen mu cikin jin dadi nan su hjy kubura aka shiga rabawa masu zuwa abinda aka samo don ita mama tabarwa yuka da naman zancen.
Har da su Umma da basu tafi ba ankai masu nasu sai dariya sukeyi wai ana gaba an koma baya.
Duk matan dake cikin gari yan gayu diyan masu kudi sunki dole an koma kauye inda ba asan ciyon kai ba an dauko yar kauye.
Amirah ta bugawa dan uwanta waya ta fada mashi duk abinda akeyi a gidan nasu har zagi da dariyan dasu umma keyi saida ta fada mashi.
Sadauki ya kira waya don ya shedawa mahaufin shi shifa gaskiya ba zai iya auren Fatima ba don yana da wace yake so Linda.
Don haka yake shirin fada mai ko zai samu mahaifin nashi ya fahince shi ba da son shi maji ke shirin wanan auren ba.
Don a kullun zuciyar shi taki yarje mashi Fatima a matsayin mata a gare shi abokiyar rayuwa.
Babs ya dauki wayan tare da sallama yana cewa Umar sanda babuga sadauki.
Sai kaji irin alheri da taron da mutanen arzikin nan gidan su Fatima sukayiwa yan kai kaya ko?
Ai ni nasan ban taba dana sani akan ka sadauki bar wa yan nan wawayen iyayyen naka su Atika suna zaton auren wayayya shine zani ga aure.
Sai gashi su gidan nasu sarakan ko ruwa ba,a mutane sun sha ga wullakancin da sukai wa yan kai kayan sai kiran babu babu kaza a ciki sukeyi.
Nasan dakai da mahaifiyan ka dama mutanen arziki ne ba yau ba don komai naku a cikin nazari kukeyin shi.
Yace lafiya dai ka kirani yanzu ko?
Sadauki da ya rasa may zaice a lokacin don duk jikin shi yai sanyi sosai dajin yadda mahaifin shi yake a cikin farin ciki yace.
Dama kawai na kiraka ne mu gaisa naji lafiyan ka don bamu samu gaisawa ba jiya.
Nan dai mahaifin ya shiga sa mashi albarka tare da fatan gamawa da duniya lafiya.
Suna gama waya da mahaifin nashi ya kira mahaifiyar shi sun gaisa sai kuma shiru sai uwar ke fadin kaji dai ankai lefen ko kuma sunyiwa mutane halarci sosai a can.
Cikin murya mai nuna damuwa yace Maji ni may zance akan wanan magana tunda zabin kine.
Yanzun ma nakira Baba na fada mashi zancen nawa auren na zabina da nake so sai shima yake min magana akan wai ankai kayan lefen ko amma ni ban so akai kayan nan duka ba tunda ba wata bace can da suka san darajan kayan.
Sadauki wace irin banzan magana ce wanan kuma ko kayi shaye shayen naka ne kake son mayar da mutane kananan yara ?
Jin dadin da kayi ne yasa har kake son watsa wa mutane kasa a ido ko may.
A kan wata arniya can har idon ka ya rufe kake son yimin cin mutunci ko may ?
To wallahi kaji na fada maka, ko da wasa nakara jin zancen arniyar nan a bakin ka sai na bata maka rai fiye da yadda kake tunane.
Don haka idan an aura maka Fatima sai kai gunduwa gunduwa da ita ka zuba a buhu ka kawon gawan ta nan.
Sakaran banza mara tunane an maka gata shine kake son yiwa mutanr rashin mutuncin ka da ka saba ko ?
Haka ya kashe wayan ran shi a bace yasan dai yanzu baida wata mafita yadda mahaifan shi suka hau zancen sai anyi wanan auren dole.
Da kyat ya ja kafan shi zuwa bakin window dakin da yake zaune cikin wani katafaren hotel na kasan LasVegas.
Tun ranan kuma baida sauran wata walwala a tare dashi ga Amira ta ishe shi da kiran waya tana mashi kwarmato wai taga maji ta karbi keys din gidan shi a hannun Bashar zasu tafi da mummy su duba gidan.
Idon shi ya rufe da jin wanan bakin labarin suka soma canza launi, zuciyar shi ya dinga mashi wani radadi da zogi ya mike tsaye ya nufi fridge din falon shi nan ya bude ya dauko wani dan mitsitsin kwalba ya kafa a bakin shi.
Yana shaye abinda ke cikin kwalban ya wurgashi kasa gefen shi kwalban ya tarwatse.
Dafe kan shi yayi yana wani irin huci mai fitar da zafi daga bakin shi, yana fadin why maji why zakiyi min haka please?
May zanyi da wanan yarinyar da ko na yini daya bata iya daukan lalura balle na zama dindin din.
Kai ba shakka wannan yarinyar ta zama mashi kafen ka al,amarinta ya na matukar caza mashi kai.
Yasan idan baiyi da gaske ba zuciyar shi na iya kamuwa da wata lalura da zai ja mashi komawa baya ga harkokin shi.
Yana kwance ya saman dogon kujeran falon ya dinga karanto addu,an samu sauki a cikin mayen da yake.
Ya jawo dan filon kujeran dake gefen shi ya rungumay filon a kirjin shi tare da rintse idanuwan shi.
Yadda rayuwan shi zai kasance da zama da wanan yar kauyen yarinyar a gidan shi, wacce ko kwaliyan kirki bata iya ba kullun tana dunkule,a cikin hijjab.
A haka zazzabi mai zafi ya rufe shi, ga dubin damuwa da kadaici daya ishi zuciyar shi.
Duk da shi ba likita bane yasan gap yake da BP shi ya hau a lokacin.
Don irin yadda yake jin kan shi yana mashi sai matsanacin kasalan dake damun shi,.
Gaba daya sai ma yaji zaman garin ya ishi ra shi baki daya tankar ana hura mashi wuta.
Haka ya wuni kwance a dakin shi ko wasan motsa jiki ya kasa fita yayi sai shawara yakeyi kawai ya koma gida ai koma maye a gaban shi zaifi mai.
****** ********* ******
Sosai mama ta mayar da hankalin ta gurin gyaran mu a cikin hikima irin ta manyan mata.
Ta hayan gyaran jiki da kuma magunguna na hausa da zasu karawa mace, ni,ima a jikin ta.
Lokaci guda duk da damuwar da nake ciki da tashin hankalin wanan kaddararen auren.
Amma haka bai hana ni canzawa ba nai matukar kyau, tankar ni nai kaina a lokacin.
Cikin dare ya iso garin muna folo a zaune gaba dayan mu har mama dake ta waya da kawarta kan wasu kaya da take son a hado mata.
Da murna suka tare shi duk da dare ne amma hasken fila ya haska kowan mu.
Saudaya ya daga kai, ya kalleni inda nai mashi sannu da zuwa kaman yadda kowa yai mashi sannu din.
Cikin dan sakin fuska kadan mama tace kai kana hanyane ashe bamu sani ba?
Yadan kai zaune a kasale yake cewa wallahi tafiyan dai gatanan kaman ba shiri nayi ta nima maji.
Maryam tace Allah yasa ka dawo ke nan har a gama buki yaya don idan baka nan ba zamu ji dadi ba.
Maji ta kwantar da murya cikin tsigan lalashi tana fadin haba ya dawo ke nan mana ina kuma zai koma ai gara ayi komai dashi yana garin don jama,an arzikin shi.
Amira ta saki wani irin tsaki tana cewa kai maryam ke wallahi baki da kunya sai kace kanki ne farau din aure.
Maji tace basu bane farau saidai su yanzun ne zasuyi dole suyi dauki kuwa.
Sai kuma Amira tai fushi wai da ita maji keyi don ita bata tashi aure ba yanzu a matsayin ta na babba cikin mu.
Ta mike cikin fushi zata shige tana cewa, Allah dai yasa ni ban iya kutsawa aso ni ba balle na kawo wanda bsi sona.
Maji tace cikin takaici wawiya kawai mara hankali shekaru yakai bata sani ba sai hauka.
Sadauki da idanuwan shi suke mai a lumshe yana sauraren kowa sai dan murmusawa yayi yace,
Maji ba dake take ba ai da maryam mai shegen rawan kan tsiya take magana ai.
Zaka ci abinci ne inji mama data ga dan nata cikin alaman damuwa yake.
Yace ban jin cin komai yanzu maji dan dama dama dai ko tea na dan walwale hajina dashi kawai.
Maji tace Fatima hado ma yayan ku tea mai kauri ya sha don yafi mai zama haka nan.
Na mike don dama a takure nake zaune a gurin na shiga kitchen don hado tea din.
A fakaice ya bini da satan dan kallo duk abinda yakeyi akan idon mama amma tai tankar bata gan shi ba.
Nafito da tea din hade da jug din ruwa cikin dan karamin tire dan madaidaici nakawo mashi gaban shi.
Na samu ya rike goshinshi dake damun shi da halbawa da hannun shi daya.
Nace cikin dakewa ga tea din yaya, ya bude idanuwan shi da kyat yai min alama da na aje a gaban shi.
Sai da ya ciro magani daga aljihun shi ya bare tare da hadewa tukun ya fara dan kurban tea din a hankali don zafin shi.
Baja jin dadi ne naga kasha magani mana mama take tambayan shi da hakan ?
Da kyat yasha cokali kamar shidda ya aje cibin tare da mayar da jikin shi saman kujera ya kwanta da bayan shi a hankali.
Muryan maji yaji don a lokacin na koma cikin dakin mu, maji tace mashi.
Ka sa damuwa a zuciyar ka ko dubi yadda duk ka lalace lokaci guda, kana ganin zan cutawa rayuwan ka ne ko may sadauki?
Ya dago kai tare da bude idanuwan shi yace namay kuma maji ?
Tace akan auren da kake gani ina son tirsasa makayi ba da son ran ka ba mana.
Yace maji ni fa banda zabin daya wuce naki a rayuwana akan may zan tayar da hankalina ga abinda kike shirin yi min gata.
Mama taji dadin kalamin shi sosai a ran ta har fuskanta ya dan baiyyana murmushi kadan.
Nan ta shiga mashi nasihohi akan hakkin aure tare da saka mashi albarka kwando kwando na mata biyayyan da yayi tana mashi fatan alheri.
Sosai ya dan ji sasauci a zuciyan shi dan kasancewan da sukayi da mahaifiyar ta shi na dan lokaci, abinda ya dade baiga hakan ba a tare dashi tsakanin su.
Ni dai tun wanan lokacin ban kara bi takan komai ba don ko kallon inda yake banayi balle nasha harara.
Hakan yana matukar bata mashi ran shi sosai yakance a ran wai wanan abar ce zata zauna da mutum har ta farauta mashi ran shi yaji dadi a haka?
Mace komai bata iya ba ban da dunkulewa a cikin hijjabi kulun kaman munafuka ko muguwa.
Wama yasani ko maganan Amira gaskiy ne asrice maji sukayi don suci arzikin su.
Don shi baiga abinda maji tagani gacwanan yarinyar ba har take kokarin yi mashi baki a kanta inba hasken fata ba kawai.
Gashi baida yadda ya iya dole yasawa zuciyar shi hakkuri da wanan auren kaddaran don ya dadawa mahaifan shi rai kawai tunda suna so amma shi kan yasan an tsere mashi gurin matar gwadawa tsara kan.
Ta ko wani bangare na gidan kowa sai shirin buki yakeyi banda mummy da babu nata ko daya a cikin bukin don ita yaran ta kanana ne kwarai agidan.
Sai dai kusan tare suke harkan bukin bangare mama da ita don ta saka kanta tsunbul a ciki inda su umma ke fadin wai kwadai ne kawai ya kaita ciki don taga gurin ci.
In bashi ba ai su ma yaran su ai diyan mijinta ne may sa zatafi bada karfi a dayan shiyan kawai.
Ta bangare na ni kan ba wani abinda na shiryawa aure sai harkan bukin Anty maryam kawai nake yi kamar nima ba amarya bace,
In dan anyi min magana nakance ni ba wani bukin da zanyi sai dai dan dama dama walima indan zan samuyi.
Su mummy sun tafi sun gyara gidajen mu yadda ya dace duk da ba wasu abu za akaiba mai yawa saboda ko wani ango yasaka kayan komai a nashi gidan.
Baba yai fadan haka yace don may zasuyi mashi haka da su bari shima yai wa diyan shi nashi bajinta da ko wani abu kewa yar shi idan zatayi aure.
Kayan aiki ne aka kai muna irin na amfanin mata ko shi ba wasu masu yawa ba don sauran abubuwa irin su gas, su tv, fridge, toaster da yan kayan kitchen electronics akwaisu a kitchen din.
Yan zuwa jai kaya suka dawo suna fadawa mama abinda ya faru a gidajen mi mama tace a daikai nata da ta saya muna hakk8n mune ta sauke muna ai.
Saura kwana hudu buki ya shigo cikin gidan duk gidan a lokacin cike yake da baki yan zuwa buki yan uwan hauhuwan maji da ga garin su sunzo.
Dakin ta ya samay ta da wata yarta ta dagin su mama take ce mai bayan sun gaisa dama ina son na gan ka don gobe ko jibi nake son akai Fatima gurin iyayyen ta don su ma suyi nasu bukin a can tunda ita yar fari ga mahaufin ta.
Shiru yayi bai dago kai ba tace don haka sai naji naka shawaran akan tafiyan nata don ban san ko kana da wani shiri ba ?
Yadago idon shi da suka canza launi yace maji ni wani shiri nake dashi duk abinda kuka tsara ai daidai ne.
Ta kara cewa ina son ka basu mota da sauran kayan da zasu bukata a can akai masu don zirga zirga da amfanin su.
Baiyi magana ba nan ma shiru yayi yana tunane wa maji ke son na tura wanan bakin kauyen ya kwana can gari ba wuta ba wani abin more rayuwa can.
Ranan da za ai kamu gidan mu ya cika makil da mutane yan uwa da abokan arziki ta ko ina na bangaren dakunan gidan.
Mata mu hudu ne maza ukku, sai dai a lokacin na bata tsarin abin don duk yadda akayi dani na fito zuwa gurin kamun naki futowa nashige bandaki na kulle kaina ciki.
Mama tace a kyaleni tunda bani son fitowa agan ni ai hakan ba ibada bane ga mutane yan gulma da basu sanni ba sun cika gurin don son ganin kwam.
Sai da naji ba kowa a shiyan duk sun watse sun tafi gurin kamu nafito na zauna a bakin gadon mu nai tagumi ni kadai a dakin.
Sai ganin mama nayi tashigo dakin abinda ya dan sani firgita ke nan zan tashi tace koma ki zauna abinki na fahinci baki son ai maki kamu a garin nan sai a gaban iyayyen ki ko?
Don haka kada ki damu gobe insha Allahu za,a tafi dake can zamu washe gari muyi maki naki a gidan mahaifan ki.
Kuma kinyi gaskiya don wanan halin naki yasa nake kara kaunanki Fatima a raina don baki dauki karyan duniya ba ke a ran ki.
Muna nan zaune tare da mama a daki har mutane suka fara shigowa tana kara yi min nasiha akan duk rayuwan da zamuyi na daure nayi hakkuri watarana sai labari insha Allahu.
Ganin mutane sun fara shigowa yasa ta barni ta koma dakin ta sai lokacin ne na dan sake jikina nan na fara shirin tafiya don tace da safe zamu tafi garin mu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
IDAN KIN KARANTA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NE SHEDA HAKA MUNA BINKU BASHI,,,,
Tun da safe na na shirya komai nawa ina jiran ace nafito ne kawai, a lokacin don ko karyawa ban yi ranan.
Ina nan zaune a takure maryam ta shigo dakin tana cewa a,a matar yaya ba dai har kin shirya ba kamar mai gudun mu kuma ?
Hararan ta nayi idanuwa na sun dan ciko da hawaye a lokacin cikin murya mai kama da ta shagwaba nace haba dai anty maryam.
Nice kuma matan yaya don Allah dai ki bari mana please wallahi kina kara tayar min da hankali Allah.
Dariya ta kwashe dashi tace au to yanzu kuma may ya rage maryam ai kin zama matan yaya ko shafawa kawai ya rage insha Allahu.
Abinci mama ta aiko min ni da maryam din wai mu karya da taimakon ta na samu har na dan kurba ruwan shayi a cikina.
Ina nan ina zaman jira ina saye cikin wasu lace brown color sai duwatsun da akai mai ado dashi don nafi son dinkin riga da zani a rayuwana.
Tun lokacin da naji wa,azin mace ta rasu an rasa zani a cikin kayan ta da za,a yafa mata zuwa makabarta nake jin tsoron dinka skirt sosai, ina dinkawa amma ba ko yaushe ba.
Mama ta shigo dakin guri na muna zaune saman gado da maryam take ce min Fatima har kin shirya ne?
Maryam tace ai tuni da anbi ta nata ma ai da yanzu mai kaita ya dawo ko tundazu.
Murmushi mama tayi tace ai yau insha Allahu kuna zuwa ba fashi sai dai ban son ki kwashi kaya da yawa tunda kwana biyu kawai zakiyi a can.
Nace cikin yar muryana kala hudu kawai na dauka mama tace yayi kyau haka sai ki hada duk wani abinda kike so anjima su hajiya lami zasu kai sauran kayan ki can gidan ina son naga kafin buki ya kankama na gama da komai naku ko.
Mama koran mu ma ake kenan inji maryam tace ai muna tare balle ku da zaku zauna kusan uguwa daya da junan ku ai ba a rabu ba.
Da sauri na kalli maryam tace nima haka naji ana fadi wai nesan gidan baikai gida goma ba a tsakani.
Tace mama amma dai Bintu idan an dawo sai andawo da ita ta nan kafi a wuce ko?
Tace sosai ma kuwa tare da masu zuwa daurin aure fa zasu dawo kuma kinga su nasu can da safe ne goma na safe za,a daura naku kuma sai da rana karfe biyu na rana.
Don haka tana nan gida za, a daura naku ai insha Allahu, ko akwai wani magana kuma ?
Maryam tace a,a shike nan ai dama ina ce ko shike nan daga yau dai mun rabu ke nan.
Kun rabu mana tunda kowa zata kama dakin ta ku barni da wanan mara hankali muyi ta fama da ita.
Mama tace bari na fita kinji Fatima na aika akira min sadauki naji yaya zancen tafiyan naku kada ai rana ba,a tafi ba kuma.
Yana daki kwance yaji wayan mama ya shigo mashi ya dauka a kasale yana fadin salamu Alaikum.
Ta amsa mashi yadda ya dace tace baka shigo ka karya ba mana tin dazun ga wanan yarinyar Fatima kuma zancen tafiyan ta fa may ka shirya akai?
Yace maji bazan iya shigowa gidan nan ba yanzu don mata sunyi yawa wallahi, dariya yaba mama tace to ai duk uwayen kane a dakin zallan mu kawai.
Yace No maji gaskiya ba zan iya shigowa ba saboda yawa ba zan sake ba anan.
Tace ko abada akawo maka dakin ka ne yace shike nan maji hakan yayi.
Sai da aka shirya komai na karyawan mama tace nazo na kaiwa sadauki breakfast din shi yana dakin shi.
Wani irin faduwan gabane ya kamani amma dai haka na dake na fita da kayan a hannuna.
Ina fita na samu Abdul dan wurin mama Asiya zai fita na bashi nace don Allah ya kaiwa yaya sadauki.
Yace kai amma dai ke Bintun nan ke da mijin ki kuma kice baki iya kai mashi abin karyawa da kanki.
Na dan marairaice nace yi hakkuri yaya Abdul bashi kadai bane a dakin shiyasa nake jin kunya.
Yana min sheri ya karbi kayan ya shige mai dashi ina ganin ya shiga na juya cikin gida da sauri na.
Abdul na shiga ya samay shi a kwace ya fara gauda shi tare da aje mai kayan abincin yace kai amma dai Bintu shine tace min wai tana jin kunya bakai kadai bane a dakin bazata iya shigowa ba don Allah na taimaka na kawo ma ashe wayo tai min ke nan.
Murmushi yayan nashi yayi yace kyale yar kauye bata son shigowa ne tai maka haka .
Yace ai zamu hadu da ita ne sai na rama nima har yakai kofa zai fita yajuya yana cewa yauwa yaya UF dama ina son ka bamu kudi zanyi party da kuma ball na mu yan unguwa akan auren ka.
Yace kai Abdul party may kuma kawai da ka share da zancen wani party can ni kaga ba wani shirin da naiwa wanan auren.
Kai yaya auren da muke son aji labarin shi a gari zakace haka auren ka ne fa na farko yaya muka gaskiya zamu cashe sosai ne wallahi.
Sadauki ya mike zaune tare da jawo kulan abinci a gaban shi yace ka bari karfe biyar sai na ganka ba shi ke nan ba.
Yana cin abinci yana tunanen rainin wayyo irin nawa common abinci da zan kawo mai wai bazan iya ba sai na bayar akawo mai.
Kuma yasan da wani manufa maji tace ni na kawo mai abincin da kaina.
Yai tsuki tare da fadi a fili yar kauyen banza kawai wai a haka zan zauna da ita kuma.
Kiran wayan maji yayi tace maji yaron da kika ba abinci ya kawo min bai kawo min ruwun sha ba fa.
Tace yaro kuma ba Fatima nace ta kawo maka ba yace ni Abdul ne ya kawo min abinci yanzu.
Murmushi mama tayi tace kai Fatima wanan kunyane wai ko tsoro har yanzu ?
Kaga abinda nake fada maka gashi ka saka tsoron ka a ranta tun yanzu yaushe zata sake dakai kana mata mugun ta haka.
Tana gama waya ta nufi dakin mu ina kwance na kifa cikina a saman filo naji tana fadin Fatima yayan ku yace baki kai mai ruwan sha ba fa.
Kara faduwan gaba naji na dai ansa a fili da to mama ina mikewa zaune kamar da gaske.
Har tajuya tace ki tabbatar kece kika kai mai ruwan da kanki don in akwai maganan da zakuyi kafin ki tafi kan bukin ki sani.
Kunya ya kamani na sanin da mama tayi bani ce nakai mai abinci ba kamar yadda ta umurce ni.
Dogon hijjab dina na saka tare da daukan ruwa a jug na nufi dakin sai faduwa gabana ke yi a lokacin don nasan cewa zan samo wani sabon bacin rai ke nan kuma again.
Dan sallama na tsaya daga kofan dakin inayi cikin yar muryana yagane nice sarai sai yaki karbawa.
Na kara dan daga murya da sallaman naji yace please kada ki cika min kunne da wanan muryan naki kamar na munafukai don Allah.
Jin haka na sa kai cikin dakin yana kwace rigigin gine daga shi sai dan wando three quarter a jikin shi da yar singileti.
Na kai ruwan inda naga kayan abincin farko suke na aje tare da juyawa zan fita daga daki.
Naji yace manya kawai watau sai da kika nace sai kin aure ni ko don bakin jaraban ki da nacin tsiya.
To ki saurara sai ki shirya zama da U F don baki san koni wane ba da baki yarda da wanan bakin hadin auren ba.
Murmushi nayi nace niko nasan ko waye mijina fiye da kowa don ni san akwai aiki ja a gabana na sharan amai da fitsri irin ta mashaya.
What ya yunkuro kafin na karasa fita ya cafko hijjab dina ta baya sai naji gaban ya shake ni sosai, na sa kara da dan karfi ya karasa riko min kai tare da rufe min baki yana fadin .
Ashe ke yar karamar yar iska ce tukun may zaisa ki gudu tunda kin isa nine mai amai da fitsari ko?
Nace baka taba min bane karya nai maka idan ka manta aini ban manta da hakan ba, kaga nafi kowa sanin halinka ke nan.
Yanzu abinda yarage min na goge na kwashe idan kuma nayi arziki baka hada min da kashi ba ai na gode Allah.
Wani irin shaka da karfin shi yakai min sai da idanuwana suka fifito waje kwala kwala kaman zan somay.
Yana fadin zaki ci uban ki kuwa inkince ke yar iska ce don zaki dan dani wahalan ki a gidan.
Yace good haka ma nake so gara ki shiga shegiya na gasa maki kwakwa ga hannun ki, kagin na wullakantaki na mayar dake karamar bazawara gidan nan.
Nace shine dama sauki na in har kai min haka da sauri ka ceci rayuwana don, zaman kaddara dama kawai zanyi da kai.
Yakai wa kaina bugu da karfi sai da na gwauro da bango idona ya kawo hawaye nace dama duk matar mas
hayi wanan ne sakamakon ta ai duka da zagi da cin zarafi banyi mamakin haka ba don na shiryi taron irin wanan ddaga gare ka tun tuni.
Akan mama zan iya hakkuri da duk wani cin zarafin da zakai min matsawon hakan zai mata dadi a ran ta.
Don nasan darajan mama nasan kimar mata a rayuwana kuma ban manta da irin halarcin da tai min ba a baya.
Don haka kaga tunda wanan ne kadai hayan da take ganin zan iya saka mata da alherin da tai, min ashirye nake da na rugumi duk wani kaddaran da zan tunkara a gidan ka.
Fita min daga daki yar kauyen banza kawai mara tarbiya wace bata san komai ba sai rashin kunya.
Nace nagode na gyara hijjab dina na fito daga dakin, idona taff da hawaye, sai da na saita kaina na shiga cikin gida.
Dakin mu na koma na kwatan ina tunanen makomar wanan auren da ake shirin kullawa a tsakanin mu a haka.
Ni dake fanin da safe zamu tafi sai gamu sai sha biyu da rabi na rana muka bar sokoto zuwa kauyen mu.
Tare da rakiyan yan uwan mama da suka zo daga Niger state gurin buki sai kawaye na muyi yan layin mune kuma school din mu daya dasu tun secondary school muke tare dasu.
Mun samu gidan mu ya cika makil da yan uwa da abokan arziki, da suka zo gurin buki nai matukar mamaki yadda na samu an gyara gidan mu a lokaci guda haka.
Dakin da zamu zauna an saka katifa maya guda biyu a cikin shi, nan muka sauka bakin da muka zo dasu basu dade ba suka koma don akwai event din da za,ayi na matar Ahmad gidan su suna son zuwa.
Sai bayan mun hutane nake jin wai mamana tana gari ta zo amma tana gidan su.
Da yamma aka sakani lalai kamar yadda al,ada yake a garin mu nan aka shiga shagalin buki, sai abinci ake ta faman tukawa na farar shinkafa.
Muma munzo da kayan cima da abokaina zasuyi amfani dashi a garin don haka ba sha wani wahala ba sosai.
Sai da safe naje gaida mahaifina yake ce min Fatima Bintu kinzo kin samu alherin da mutanen arzikin nan sukai muna a gida nan ko?
Alhaji ya aiko daga can birni an gyara muna guri don baki masu zuwa daurin aure sai kuma jiya gashi da safe kafin ku iso anzo da abinci da katifo wai daga marikiyar taki ta aiko dashi.
Nace an gode Baba ya ce tau Fatima sai dai ban tsanmanin zamu kara samun lokaci irin haka dake ba.
Abinda nake son ki sani shine shi zaman aure dan hakkuri ne don yanzu so ya kare a tsakanin ku sai hakkuri.
Yi nayi bari na bari inji manya sai a zauna lafiya, kin dai san ance mijinki mutum mutane ne gashi kuma dan gidan yawa.
Don haka ki zauna da kowa da halin ki duk da nasan ki amma ki kara da hakkuri Fatima, shi hakkuri baya karewa fa musulmi.
Duk da a hasashe na ina fanin kaman wanan aure aure ne na hadin iyayye a tsakanin ku dashi halinki shiya ha har suka kwaidaitu da son zaman ki da dan su.
Don haka ki kara wani saman wanda suka sanki dashi sai kiga akarshe ke ce da riban hakkuri.
Take naji idona ya ciko da hawaye har na kasa control din su sai da suka zubo min nan dai baba yaita min nasiha akan hakkuri da zamantakewan aure da kuma sabon rayuwan da zan shiga ciki.
Mukai sallama dashi yana ta saka min albarka tare da fatan samun zuria dayyaba.
Yinin ranan haka nayi shi a kwace babu walwala tare da ni ga mutane sai masha,an da sukeyi kawai.
Da dare gwagona mai masa tazo tace nazo mu tafi gidan su mahaifiya na don ko can akwai yan uwa da suka zo buki.
Mun shiga gidan mutane sai jin dadin gani sukeyi suna ga amarya tazo gaida ku.
Nan muka shiga gaisawa da mutanen da na dade banga wasu ba sai ranan.
Sai wani lokaci na samu kebewa da mahaifiyana a wani daki dagani sai ita muka zauna a dakin.
Tace tau yarinyar ga gashi dai Allah yayi zaki aure yanzu don Allah idan kin je kiyi hakkuri da sabon rayuwan da zaki tsunta a sabon gidan ki.
Ance zo mu zauna zo mu saba ne sai dai mu mata da hakkuri aka san mu dan namu yafi na maza don mune a kasa garesu.
Kina dai ganin irin rayuwan da nake ciki ba sai na fada maki ba kin san hakkuri nake dashi don da ban hakkuri da tuni nabar gidan nan na,watsar da yaran nan.
Amma sai naga idan na fita na barsu dawa kuma zasu zauna har ya basu tarbiyan da nake son su samu saboda kinga shi wanan ba irin naki mahaifin bane.
Ina jin haka sai wani irin kuka mai karfi yazo min don tausayin mama na dani kaina.
Da kyat ta dan lalashe ni na sasauta cikin kuka nace mama ina ganin kusan rayuwa guda Allah ya jefo muna na aure.
Don kinga shima din mashayi ne ne kaman baban su musa sai dai dan banbancin su kadan ne don akwai wayewa a cikin nashi.
Mama bana son shi na tsane shi natsane shi a rayuwa na amma sai gashi magaifiyan shi ta nemi alfarma a guri na akan na rufa mata asiri na aure shi.
Mama may zanyi da mutumin da bayaji tsoron sabawa Allah bai dauki sabawa Allah a bakin komai ba.
Mama don mahaifiyan sadauki zanyi wanan auren don ba zan iya mussa mata fa bukatan taba a gare ni.
Mama ta katse ni tace amma kin bani kunya wallahi yarinyar ga ina iliminki da tarbiyan ki ya shiga da har kike ganin ba zaki iya taimakawa hajiya ba yau.
Tace da kikaga hjy ta zaboki a cikin dubu ta bukaci ki auri dan ta kina zaton don kyau kine ko arzikin ki ko wani abu can.
Tayi hakane don tana hasashe watakila tagare ki zata samu nasaran raba dan ta da waban halaiyar tashi.
Bafa don bata sonki ne tace ki auri dan ta ba suna da kudin da zasu aura mao duk macen da yake so a duniyan nan.
Amma kikaga ta nace akan sai dai ke din take so ki zauna dashi, nasan kuma tai hakane don tana ganin ke ce kila zaki iya kawo karshen wahalan nashi.
Shi fa hanyan sabon Allah shiga rai ke gare shi sosai, daga lokacin da akace wanan abin baida kyau haramun ne, sai kiji zuciyar mutum na tura shi aikata shi a ko wani lokaci.
Shiyasa akace an zagaye wuta da abin sha,awa wanda zuciya ke so, an kuma zagaye aljanna da abubuwan ki wanda zuciya bata so.
Don hakane duk wanda ya kama hanyar aljanna zai ta haduwa da abubuwan da zuciya bata so, haka kuma shi wanda ya kama hanyan wuta zai hadu da abubuwan da zuciya ke so.
Shiyasa akace daga cikin hakkurin da ake son mutum yayi shine harda biyayya ga Allah da manzon sa dama
magabatan mutum da kuma hakkurin gujewa sabon Allah.
Hana zuciya aika ta sabon da ya ginu a kanta farat daya abu ne mai wahala so sai sai mai hakkuri.
Idan kana da hakkuri zaka iya jure jawo hankalin mai yawan sabon Allah sannu a hankali ta yawan nasiha da lurar da mutum illar abinda take aikatawa.
Uwa uba kuma addu,a da nasiha ga mutum har Allah ya bada sa,a ya bari ko ya rage.
Yin fushi da mutum ko kaurace mashi baya hana mutum sabawa Allah sai dai ma ya kara kangarewa kawai.
Amma jan mutum zuwa jikin ka shike sa mutum ya rage watarana har ya tuba ya daina gaba daya.
Don haka ita hajiya taga cewa, kece kadai zaki iya taimaka mata gurin wanan yakin.
Don haka yaki babba a gaban ki yar ba don hajiya ta dora maki nauyi mai girman dauka gare ki.
Fushi zagi gori da kawar da kai ga abinda yake aikatawa yanzu ba naki bane yar baba.
Don haka wani kawar da kan ki gare shi ko ki kyamace shi ba naki bane yanzu.
Don idan kinyi haka tankar kin kara tura shi ga halaiyar da yakeyi ne na kyamata da uwarshi bata son ganin shi a ciki.
Hajiya ta wuce ki watsar mata da bukatan ta gare ki, sai dai ki kara runguma kawai da hannu bibiyu.
Zata ci gaba da magana gwagona ta leko tana cewa fito mana Bintu, dare fa ta soma kin san ba wuta garin.
Haka yasa nai sallama da mahaifiya na tana ta jero min addua irin da yadace duk uwa taiwa yar ta da zata dakin auren ta.
****** ********* ******
Waagegari tun da safe wata mota ta iso da kujeru da rumfuna suka shiga hakawa sai kuma fa mota da abinci ruwan sha na gora da leda sun iso.
Inna ta bawa ranan ta arare ta yafe itace kirjin buki arziki ya sauka mata a gida sai yadda tayi zuwa tara da rabi sai dirin motoci ke tsayawa a kofan dan gidan mu.
Haba take guri ya kaure da yan ma,abba sai kirari sukeyi fa Alhaji wani ga Alhaji wani yazo.
Zuwa can wani mai murya ke sanar da jama,a ta lasifikan shi Allah yayi lokaci yayi yau an daura auren Umar faruq da Fatima Bintu akan sadaki naira dubu hamsin.
Sai wata matar babana ta rangada wani irin guda tana fadin yau Fatima Binta kin gwada muna kin haihu a zariyan Ibrahim da maimunatu don kin jawo muna arzikin da bamu taba sanin akwaishi na garin nan.
Allah yasawa auren ku albarka yakawo muna zuri,a dayyaba masu albarka arayuwa.
Bayan dan lokaci muka ji mata na fadin ance ku gyara ga angonne nan zasu shigo gaida ku cikin gida.
Ina can boye kuryan dakin Inna tabawa naji matan tsakar gida na fadi wanan na tsakiyan dogon ai shine angon lalai Bintu kan kin yi sa,an miji wallahi da ganin shi ba karamin mutum bane.
A raina nace baku san komai ku kumbu a rufe ganin kyaun dan maciji kuke mashi haka dahi nanan cikin shi.
Ba wani bata lokaci matan da aka zo dasu suka fara cewa wai a fito da kaya zamu tafi take na saka wani sabon kuka mai tsuma zuciya.
Bashar ne ya dauko ni a motar shi sai kaunan mahaifiyata wata malaman arabiya ce ita sai gwagona dana zo birni a wurin ta, kawa yena su biyu haka muka shigo mota daya dasu.
Tun da muka fara hanya ina a dunkule sai kuka nake rusawa a hankali gwagona tana min fada wai zan jawa kaina ciwon kai a banza kamar wace za aika gidan mugun abu.
A raina nace kyace haka mana tunda kin ja min mugun rayuwa a sanadinki duk na fada cikin wanan rayuwan haka ai.
Bashar yace gwago kyale Fatima tai kuka yau don zata fada sabon rayuwa kuka ta zama dole gare ta.
Magana ce yai mata a cikin magana wanda duk cikin motan nasan sai ita kadai ce zata fahinci hakan kawai.
Gida ya cika yacika ya batse kamar may yan uwa da abokan arziki nisa da kusa birni da kauyen an hadu.
Muna na isa aka fara futowa zuwa taron mu yan uwan mama da yan uwan mahaifin su yan uwan umma da mama nasu suma ya ishe su ranan.
Ga Nafisa tayi halinta suyi party tayi tatil haka tashigo gida tana ta watsewan ta gidan Amarya yaya Ahmad kuma suma suyi nasu bushewan sai tir da Allah waddai akeyi masu ta ko ina.
Chapter 3 · 0% Book details