Part din nasu yai shiru bakajin motsin kowa duk lokacin kowa yafita zuwa nashi tsabgan gaban shi don ci gaban rayuwan su.
Hukuncin Allah Part 1 Complete Hausa Novel · about 236 min read
Wani irin yunwa ne ya farkan dashi daga nauyayen barcin da ya yi mai tsawo bai san inda yake ba.
A hankali ya bude idon shi inda ya kurawa silin din dakin nashi ido, can yakai kallon shi ga agogon dakin a hankali yaga har tara da rabi na,safe.
Da kyat ya iya mikewa zaune ya samu har yakai tsaye don yunwan da yake ji yai mai yawa sosai a lokacin.
Wanka yashiga yana wankan ne abinda yafaru jiya da dare ya dan fara dawo mashi a,rai.
Kai aiko na,shige su tunda wanan bakuwar yarinyar ta san da wanan zancen don yanzu nasan ta fadawa Maji halin da,ta ganni a ciki daren jiya.
Aiko idan har ta fadi sai yai mata dukan da sai an kwantar da ita asibiti sai da ya shirya tsab yafito tare da kulle dakin shi ya nufi cikin gida don ya gaida Maji ya kuma karya saidai gaban shi na faduwa badon yana son cin abinci ba da bai shiga gidan ba a lokacin.
Da sallama a bakin shi ya shiga part din nasu duk da ya hadu da mama a kofa amma bai mata magana ba ya shige abinshi tabishi da harara tana fadin mara kunyan yaro kawai tabbatacce.
Maji dake zaune saman salaya tana lazumi ta karba mai sallaman shi tana cewa sai yanzu katashine babana kowa a gidan manya da yara sun kama gaban su ko.
Yace cikin dan shafan kan shi wallahi Maji barci ne ya kara daukeni bayan mun dawo daga sallah.
Ai jiya da,dare muna ta jiran kazo kaci abinci baka shigo ba har ana batun rufe gida sai Fatima ce ke fada muna cewa.
Gaban shi yai wani faduwa ras ras kafin yaji ma yarinyar tafada wa maji din.
Maji tace take ce muna ta gan ka,,, lokacin Bintu tafito daga cikin daki tana cewa Mama a canza zanin gado ne.
Wani uwar harara ya,watsa mata saida ta kasa fadin maganan da zata kara fadi.
Maji tace ashe jiya doya kaci ka kwata gata itace ke ce muna tagan ka kana,sayen doya da kwai da dare dana aike ta.
Wani wawan numfashi ya sauke tare da dan sake fuskan shi yace eh wallahi maji shi nake son ci shiyasa na saya ai.
Fatima dauko wa yayan ku abinci shi ya karya yafita shima don ban son zaman gidan nan kamar mace.
Bintu ta juya inda yake tana cewa ina kwana yaya can kasan harshen shi ya amsa mata da lafiya kalau,
Ta juya zuwa cikin kitchen ta dauko mai abin karin shi takawo mai gaban shi ta duka don ta aje mai ya faki idon Maji yana cewa kin kuru baki fadiba dana karyaki yau wallahi.
Da sauri Bintu ta mike tabar falon don kada ya kara ce mata wani abin kuma don ko yanzu ta tsorace dashi don mashayi ba abinda bai iyayi shi.
Sunaci suna hira da mahaifiyar nashi tana dan mashi hira maikama da nasiha sai cin abincin shi yake hankali a kwance abin shi.
Daidai Bintu na shigowa taji yana cewa ni dai Maji don girman Allah ki yardan min natafi wanan wasa kiyi hakkuri ki gwadani ki gani idan ban canza ba kada ki kara bari na tafi don Allah maji.
Daka ta sadauki na riga na fada maka cewa bazan yarda da zancen tafiyan ka ba,wani kasa can da babu kowa na gida a tare da kai, nan ma da kake a gaban mu yaya muka kwashe da kai?
Bintu batasan yadda akayi ba tace mama yace don girman Allah ki barshi yaje insha Allahu zakiga canji a gare shi da yardan Allah ke dai adduan ki yake nema da yardan ki.
Da har zai bude baki yace ke wayasa bakin ki zan balballaki yanzun nan, amma sai yaji maji tace .
Fatima bar shi kawai ni nasan halin abina ke yarinya ce baki gane may nake nufi da zance na yanzu amma ba zancen tafiya a guri .
Tafiyan ma fa wai na wasan kwallo haba sai kace uwar banza da batasan ciwon kan ta ba.
Maji komai zamuyi saida adduan ku don haka kamara yayi kisawa zancen albarka ki mara mashi baya yakai ga kudirin shi.
Don ba,a san mai gobe zai iya yi ba shiru maji tayi tace kai Bintu badai iya magana ba dai kam.
Shiko Umar shiru yayi yana mamakin wanan yarinyar yadda ta iya magana haka kamar wata tsohuwa can.
Fatima naji zancen ki sainai shawara ya dan dakance ni kawai nagama nazari nagani ,
Daga haka ya mike tare da cewa cikin murya ba dadi zan fita sai nadawo Allah ya tsare tace sai kadawo.
Haka fita jiki ba karfi yabar dakin sai dai yaji dadin yadda wanan yarinya ta saka baki har Maji ta dan yi taushi sosai yagani ai.
Tun lokacin da sukai wanan magana hankalin maji bai kwanta ba sai sakawa take ta walwalewa a ran ta daga karshe dai ta watsar da zancen ma kawai.
A na cikin haka gwagon Bintu ta dawo daga kawai ta zo gidan bayan ta huta don ganin Bintun ta.
Nan suka tare ta da murna sai bin Bintu take da kallon yadda gaba daya ta canza mata a fuskan ta ta kara haske da kiba, taiwani irin kyau da ita.
Nan ta shiga yi wa Maji godiya da karamcin da tai mata akan rike mata yarta yar dan uwan ta da take hannun ta.
Maji tace haba hajiyan masa ai Fatima mutun ce yarinya ce mai dadin zama da sanin ya kamata sosai.
Naji matukar dadin zama da ita a gidan nan don ta taimaka min da abubuwa da dama a gidan nan
Hakane ma yasa nace ko kin dawo bazan barta takoma gurin ki ba sai dai mu zauna nan da ita tunda danan da can guri ki ai duk dayane kuma a shiya daya muke dake.
In dai har hakan bawai zan takura maki bane gwago tai godiya da karamcin Maji tana cewa nagode Hajiya dama ba zama nadawo nayi ba don jinya nake a can na yayata da bata da lafiya.
Shine naga na barta a nan da suna sati biyu gashi har nai sati hudu a can baku da labarina, kada hankali ku ya tasbi na rashin jina da bakuyi ba na tsawon lokaci.
Ai babu komai nasan tunda najiki shiru lafiya ne ai tunda kin san inda aka barta ai.
Nan suka dan taba hira gwago tana bata labarin rashin lafiyar yar uwarta da take jinya a kauyen su.
Da zata wuce ne ta bukaci da Bintu ta rakata ta dan gyara gida don kuran da yayi na rashin mutum a cikin shi na wani dan lokaci.
Aiki sosai Bintu tayi a gidan harda girki saida tai masu don suci tanayi tana tambayan gwagon ta labarin mutanen gida.
Sai da suka natsune Bintu takw fada mata irin rayuwan kawai cin data samu a gurin Maji da kuma irin matsalar da take ciki akan dan ta da baijin magana da bukatar shi a gurin mahaifiyar shi na son tafiya wani gari buga kwallo da yake son zuwa yi.
Gwago tace kai amma ko hajiya da ta barshi don bata san ko shine mafitan ta ba arayuwa tunda har yai mata alkawarin canzawa idan ya dawo.
Gwago tana fada irin ta manya tana fadin ai gara ta barshi ya tafi don batasan abinda Allah ya shirya ba a kan yaron.
Suna ta zancen ita da gwagon ta har dai dare yayi don haka ranan a na gidan su Bintu ta kwana da,gwagon ta suna kewan junan su.
Sai washegari da yamma ta shigo gidan cikin jin kunyan Maji da yaran ta, sai faman yi matasheri sukeyi taga gwago ta gudu masu.
Maji tace yanzu Fatima haka zamuyi dake ni da nake fadin anan zaki zauna shine kina gani gwagon ki kika gudu gurin ta ko?
Ko dama bakijin dadin zama damune dai kika boye muna hakan ?
Da sauri Bintu takai kasa tana cewa ,a,a mama ba hakana bane kawai dai na tsaya ne na kara shirya mata kayan ta.
Jeki ga abinci can a kitchen ki diba kici inji Maji tana mata magana cikin kallon fuskan yarinyar.
Mama na koshi gwago tai muna gwaben ganye mun ci dazun mun koshi sosai ban jin yunwa yanzu. Sai dai anjima in Allah ya kaimu.
Daga nan ta samu guri ta zauna tana kallon maryan dake dakilar wayan ta tana dariya ita kadai.
Sun kai wani lokaci falon yana tsit kowa yana tsabgan gaban shi sai Bintu dake ta tunane kala kala cikin ranta yadda zata zauna a gidan nan dake cike da tarin matsaloli.
Fada sukaji tsakanin mama Asiya da uwargida ya kaure sai cacan baki suke a kan yaran su.
Maji bata fita ba tana zaune a falon ta har sukaci suka sude ko magana batayi ba, sai ma Amira da tace su daici kan su munafukan banza kawai kanku ake ji.
Sai lokacin Maji tai magana dacewa Amira ban son rashin kunya fa iyayyen naki kike zagi da munafukai kuma.
Kada na kara jin wanan kalamin a bakin ki ko kin manta cewa ke ma watarana uwace a wani gidan.
Shiru Amira tayi don tasan in ta kara furta,wani abu yanzu Maji zatai cikin ta da masifa sosai.
Har masu fadan suka kare cacan bakin su da tonon asiri ba,wanda yai magana a dakin daga dakin mummy Amarya ma ba tafito ba haka ma yaran ta.
Don ita dama,yar i don't care attitude ce a,gidan harkan kowa bata shiga sai in abu yakai mata karo.
Sai da yamma sosai gwago ta shigo gidan gurin Maji inda ta aika mata da abincin dare tace kada ta girka komai ta dinga bari akai mata daga nan gidan su.
Shine gwago tashigo yin godiya gurin Maji din da,wanan irin halarcin da take gwada masu haka.
Maji tace haba dai mai masa ai yiwa kaine ina laifi duk cikin shiyan nan baki aminta,da kibar yar ki a gurin kowa ba sai gurina, kika yaba da ni ai wanan ma wani mutuncine babba.
Murmushi gwago tayi tana cewa Allah dai yabar daukaka da girma Allah kuma ya kara shirya muna yaran mu.
Ameen inji Maji tare da sauke ajiyan zuciya a fili tace bari mai masa ba boyo a tsakanin nidake yanzu.
Jin haka yasa Bintu tai saurin mikewa,zuwa ciki tabar su gurin ganin ta,shige yasa maji hararan su Amira dake zaund suma din mikewa sukayi suka shige suna zunburo baki gaba.
Maji ta kara kwantar da muryan ta kasa, tana cewa hajiyan masa ina cikin matsala da,wanan yaron na,waje na.
Yayan su Amira ke nan inji gwago maji tace shifa,wallahi sai tace cikin kariyan murya mai masa yaron nan yana son kashe ni wallahi.
Maganar safe daban ta rana,daban ya zama wa kowa kaya a gidan nan balle ko banza kin san irin zaman da muke a gidan nan.
Yanzu msi masa nifa har na fara,zargin ko yana shaye shaye ne don abinda yake abin ma bana kai sake bane.
Subbahanallahi i ji gwago Allah ya tsare ya kare hajiya amma kada ki mashi mumunan zargi haka don Allah.
Koma maye dai dole ke uwa hakkuri zakiyi kikara jan danki a jikin ki kina nusar dashi hanyan alheri har ya gane.
Mai masa ni yanzu har abin yana son yafi karfina wallahi don kinga sam yaki zancen shago kamar kowa shi kuma ba,wani sana,a yaje zuwa yi ba yadda kowa keyi.
Ina gani a gidan nan ko wani da yana kawo wa uwar n shi abin arziki daga shago amma ban dani sai ma shi Alhanin ne wani lokaci yakan ji tausayina ya dan taimaka min ko shi da kwankwami da komai yake min.
Tunda kinga ba karfine gareni ba don ni banyi karatu mai zurfi kamar sauran matan gidan ba.
Amma mai mas wanan yaron duk da haka bai zama min da ba wallahi takare da sake kuka wi, wi,wi a lokaci guda.
Ba kuka zakiyi ba hajiya kamata yayi ki kara jajirce kina mashi addua da fatan alheri, kin fasan bakin uwa taki ga "yayan ta.
Mai masa wallahi inayi sai dai kawai na kara akan wanda nakeyi don banda lokacin kai na ko yaushe sai na yarana tun bai zama haka ba ma, balle yanzu da al,amarin shi yai kamari sosai cikin gida.
Yanzu ke hajiya baki fahinci ko akwai wani buri wanda yafison yayi abin ba akan kasuwan ci din.
Saida Maji ta share hawayen da ke fuskanta take cewa, mai masa waifa shi ba komai bane gurin shi sai sha shanci wai kwallo.
Kwallo yake da ra,ayin yi maigidan mu yayi fada har yagaji yanzu ya saka mashi ido yabarshi da kwallon.
To hajiya wa ya,sani ko anan alherin shi yake ga wasan kwallon.
Wasan kwallo kuma mai masa za,a samu wa i alheri a cikin sa ?
To ba haka naji ana fadi ba wai suna samu ga harkan sosai kinga sai muyi mashi addua mugani ko anan arzikin nashi yake.
Hmmm mai masa ni wanan ai abin kunyane a gareni ace wai cikin gidan nan da na yafita zakka wai bai kasuwanci sai kwallon kafa kawai.
May zai samu a cikin wasan kwallon kafa kuma banda shashanci irin na sadauki kawai.
A,a hajiya ban son ki na fadi haka fa kin daiga ki godewa Allah idan har zaiyi wasan ya jawo mai alheri da kintsuwa ai gara a arshi ya,tafi yayi abinshi kinga,zaki rage taahin hankali don kin san inda yake.
Ni kuma nai maki alkawari insha Allahu zan taimaka maki akwai gurin malamin dazan tafi maki can kauyen mu sai yai muna istihara akan matsalarshi don muga may ke damun shi ne wai.
Don kingafa gidan ku babban gidane gaki da kishiyoyi marasa imani da tsoron Allah.
Don haka abu na farko shine mu fara,sani may ye nasabar wanan matsalar tashi ne wai ?
Shin daga Allah ne ko kuwa,saka mashi hannu akayi din a danbala makishi yakoma haka.
Hmmm mai masa ba,wanda ya saka mashi hannu shashancine kawai irin na yaran yanzu .
Ya hadu da miyagun abokai sun sauya mashi tarbiyan dana bashi tun farko don rashin tausayi irin na dan yau.
Kin taba zuwa akai maki istihara akanzancen ne ko kuwa dai haka kike gani ke ?
Gaskiya ban taba zuwa ba mai masa ina dai hasashen hakan ne kawai a raina.
Hajiya yanzu duniya tai nisa wallahi kibar mutum inda kika barshi kai kana kwana,wasu na maka hansari ne,
Balle yanzu ba,a zama kan yara ko nawane gareka dole katashi masu tsaye gurin nema masu tsari da kuma addua.
Gaskiya ni mai masa ban taba yin komai akan yaran nan ba gaskiya nidai nasan ina masu addua sosai wallahi.
Hajiya wanan zamani ai ya,wuce ko gurin mutane don zamani ya lalata mutane da son kai, don A LOKACIN MUKE,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,
A gurin da suke zaune suna magana suke jin hayaniya daga cikin gida, shiru sukayi suna saurarawa.
Labulen dakin tane ya,daga ko sallama babu ya fado masu dakin duk jikin shi yai futu, futu da kasa ga wandon shi kamar yai fitsari a ciki.
Kara shigowa yayi daga cikin dakin ya fadi kasan ties din falon jagwab dashi sai kuma ya fara nasari
n barci.
Innalillahi Baba na may ke faruwa ne haka, may ya samay ka, may akai maka, wa yai maka wanan abin haka.
Sai ta,sake wani irin kuka cikin wani murya mai ban tausayi da tsuma zuciyan mai sauraren ta.
Innallilahi wa,inna alaihim rajium Baba kada dai ace da gaske shaye shaye kake yi haka.
Cikin kuka take magana da tashin hankali, mai masa kin ga yaron nan yau yadda ya koma ikon Allah.
Allah kataimake ni ya Allah wanan yaron yau may zangani haka da idona.
Nashiga uku na lalace a rayuwata Sadauki may ka koma haka yaushe ne kafara wannan bakar rayuwan haka.
Takara daga murya tana cewa Baba na badai shaye shaye kakeyi ba cikin gigicewa take maganan.
MAJI bafa,,, abinda ya,samay ni just ,,,, relax ,, relax Maji,,, kawai,kawai dai ,,,, dan joy neeee,,,,,
Sai ya mayar da kan shi kasa yaci gaba,da barcin shi, nashiga uku mai masa yau dan nan ya, jawo min magana babba a cikin kishiyoyi da al,umma.
Baba da nasan wanan rayuwan zakayi a duniya da na barar da cikin ka na huta da ganin wanan bakar ranan da nagani yau a,rayuwa na.
Haba haji ki daina fadin hak don Allah yanzun dai musan abin yi kafin abin yai mashi illa haka.
Mai masa ai gara ace ya mutu da na zauna ina ganin shi a gabana haka.
Umm,umm hajiya don girman Allah ki daina fadan haka wa dan ki Ai babu abinda ya gagari Allah ko?
Kuka mai tsuma rai Maji takara sakawa cikin tashin hankali tana fadin da daya ke nan tilo namiji da Allah ya bani mai masa yau ga abinda ya zama min a duniya.
Ba u komai Allah ya shirya muna shi dashi da ma sauran diyan musulmai masu wanan halin.
Daga waje kofa tsakar gida kuma kishiyoyin maji a tsatsaye suna fadin ikon Allah yaukan mun ga abin mamaki a cikin gidan mu wanan bakar masifan ya,fado muna.
Hmmm lalau akwai magana da,sake don dole a,dauki mataki ga hakan kafin a lalata muna yaran mu.
Dayar kuma sai cewa tayi kai gurin bakar jaraba har an kwaso muna jikokin yan maye a gida yau ga abinda bakar jaraba ya jawo a gidan nan.
Ace wai cikin gidan nan yadda muke da mutunci a cikin shiya an samu dan maye irin haka.
Allah kai muna tsari da wanan bakar masifan ka kare muna yaran mu dama karshen so ke nan ga yaron da ba,a kwabo ai.
Haba dai ai wanan ba daga nan ba inji amaryan su kowa dai yabi nashi da addua amma ai ita Maji ba itace ta turashi zama haka ba kudai kowa ya iya kan sa don wanan masifan ta shafi kowan mi a gidan nan, ba ita kadai ba.
Ke don Allah ni ban son munafumcin banza ina ko ke bai bari ba indai sadauki ne a gidan nan.
Haka sukai ta cacan bakin su daga kofan dakin Maji da suke daga ciki suna jin cacan bakin su.
Mai masa kinji abinda nake fada maki ta fadi cikin kuka da tashin hankali.
Ai basu kamar Allah ba don ba wanda ya wuce jerabawan ubangi daga cikin su.
Ke dai kibi dan ki da adduan neman ashiryuwan daga Allah dan yanzu ke ce da matsala basu ba.
Kara jajircewa ki koma haikan gurin ubangiji tare da nemar taimako, kina bashi koda baya so ki bashi ya shanye a gaban ki ba bayan ki ba.
Insha Allahu nima zanyi kokari naga na taimaka da dan abinda zan iya gurin al,amarin.
Don kinga shi aikin shedan shiga rai ke gare shi sai mutum yai kamar zai bari sai kuma shedan ya rude ka ka koma.
Don haka yanzu ki yawaita jan shi a jiki ki kada ki biyewa maganan mutane kina nuna mai kyama ko hattara ,a,a ki jawo danki zuwa jikin ki don ki san damuwar shi.
Shigowan Bintu dauke da dan wani kwanon glass na tangaran da cibi a cikin sa yasa sukai shiru baki dayan su.
Su Amira duk suna tsa tsaye cirko cirko sai faman kuka sukeyi da tashin hankali.
Gurin da yake kwankwance sharkaf dashi ta nufa inda ta durkusa tare da dora kan shi a cinyar ta suko duk ido suka saka mata.
Amira na ganin haka ta fahinci may Bintu ke shirin yi masa don haka itama ta karaso tare da karban kwanon daga hannun Bintu.
Haka maryam itama ta guso inda suke da taimakon su ta samu ta bude mai baki da kyat suka dura mai manja da girshirin da ta hada har kusan cibi uku,
Sai ya fara wani irin tari ya bude idon shi da kyat tare da dan kara yunkurawa sai kuma bintu ta mayar da bakin shi da karfi ta rufe gam sai ko yai wani zabura tace ku danne min shi dan Allah.
Maji dake gefe tana kallon su ta kara sakewa da wani sabon kuka sosai cikin tashin hankali.
Yan mintina kadan saiko wani irin amai ya taso mai nan ya fara sharara amai kamar zai amaye kayan cikin shi a lokacin.
Amai sosai Umar yayi a lokacin sai kuma ya koma barci dan gefen su kadan.
Bintu ce ta kwashe amai don su sauran sai faman kuka suke tayi cikin tashin hankali.
Dawowa tayi falon ta zauna a cikin damuwa da tashin hankali,
Maji ce ta taso inda yake takai mai wani irin mari da duka mai gigita mutum abinda yasa shi bude idanuwan shi ke nan yana kallon ta.
Yace cikin muryan maye Maji may nayi kike duka na haka?
Uwar ka kayi dan banzan yaro mara mutunci kawai wallahi sadauki sai Allah ya,,,,
Haba mama kiyi hakkuri dan Allah kada ki furta mai mugun kalami yafi kuma nan lalace maki don Allah dai kiyi hakkuri mama takarasa cikin kuka da tashin hankali.
Mai masa tace haba hajiya watau baki dai ji abinda nake fada maki ba ke nan ko?
Wallahi idan ma yafi nan ba tsira zakiyi daga zagin duniya ba don haka ki dawo da hankalin ki guri daya kiyi nazarin magana ta.
Hannun ta ta cusa cikin aljihun shi don jin karar ledan da takeji daga cikin aljihun nashi.
Fito da ledan tayi daga aljihun nashi sai wasu kwayoyi suka zubo daga ciki da yawa haka.
Salati suka saka ita da mai masa a lokaci guda take cewa kinga abinda ya sha yafitar mai da hankali ko.
Koma ki zauna saman kujera kada ki fadi kinji hajiya akwai Allah shine zai muna maganin abin.
Ba,a san ko wacece daga cikin matan ta bugawa maigidan waya ba, sai kawai gashi yazo a sukwane gidan cikin tashin hankali shi da sauran yayyen sadauki.
Dakin maji da akace masu ya na ciki suka shiga anan suka samay shi kwance sharkaf kasa yana barci.
Nan suka samay shi da duka mai shuri na shuri mai mari yana mari saida ya farka daga barcin da yakeyi.
Suna ganin ya tashi suka jashi zuwa waje kiiii sukaci gaba da dukan shi cikin tashin hankali.
Ganin zasu halaka shine hajiyan masa ta isa gurin ta fada saman jikin shi tana tare dukan tana fadin haba Alhaji ai duka baya yi sai dai addua tunda abin yai muni ko?
Cikin takaici da bacin rai Alhajin yace mai masa bari kawai mu kashe dan banza may zanyi dashi cikin zuria ta mara mutunci kawai.
A dai yi hakkuri dan Allah abi al,amatin sannu tunda ya riga da ya aikata sai a san hanyan bi da shi kawai yafi.
Amma duka ai kara hinjira shi kawai zakuyi ba wai gyara abin ba .
Duk mutanen gidan suna tsaye tsakar gida cirko cirko sai amaryan su ce itama ta tako gurin ta kama mashi hannu zuwa part din ta duk da Alhajin yana ce mata wallahi ki barshi ya fito min gida ba dana bane wanan dan banzan yaron kawai.
Bataji ba,sai kulle kofan part din ta da tayi dashi a ciki ta,zaunar dashi nan ta shiga lalashin shi da bashi magana tana mashi nasiha.
A kan ya daina wanan muguwar akidar da ya sawa kan shi ko dan martaban iyayyen shi,
Tace ka tausayawa mahaifiyar ka Sadauki yau ka san irin halin da uwarka zata kwana aciki ai babu abi mafi muni ace yau cikin dubu nakane lalattace.
Dukar da kai UMAR yayi kasa tare da,wa i irin nadama ya,ziyarce shi a lokaci guda yake cewa mummy kuyi hakkuri insha Allahu zan daina bazan kara ba.
Tace da ka kyautawa kanka,wallahi da ka cece mahaifiyar ka daga tashin hankali da masifa.
Kuma kaje in komai ya lafa kabata hakkuri kai mata alkawarin baka sake shaye shaye har ma da mahaifinka.
Shiru sukayi ya,sadar da kan shi a kasa can takara cewa, yanzun kai ko don irin zaman da ake a,wanan gidan kowa ya tunkaho dan shi wani abu ne bai saka kai zuciya ka zama wa uwarka dan kwarai abin musali ga sauran dangi.
Maza tashi jeka kai wanka ka,tsabtace jikin ka don naji kamar sun fita daga gidan.
A lokacin su Maji suna daki hajiyan masa na kara bata hakkuri da magana mai kwantar mata da hankali, har ta dan sauko tana daukan nasihan mai masa.
Mai masa take cewa yanzu dai yana gurin kishiyar ki ta,saka shi a dakin ta ta rufe dashi nasan nasiha take mashi a can.
Wa mummy Amarya ko wa ina ganin itace dai mai daki can kusa dake karshe.
Itace maji ta fada a hankali don in ba itaba nasan indon su yayane sai dai a kashe shi ai.
Sadauki yafito daga part mummy yana tafiya cikin dan gyasawa a hankali don dukan da yasha ya taba mai kafa har da baya duk jikin shi ya farfashe sosai don dukan da yasha gurin mahaaifin shi da yayyen shi.
Wa yanda ke tsakar gida a zaune suka bishi da ido da bakar magana8 suna fadin andaiyi hasaran haihuwa wallahi.
Yadago kai ya,watsa masu harara sai dai bai tanka masu ba ya shige yafice daga gidan kawai.
Ranan Maji tayi kuka kamar ranta zaifita da,kyat mai masa ta samu tai shiru, tare da bata magana.
Gwago mai masa ta sa Maji taje taiwa Amaryan su godiya kan halarcin da ta nuna mata kan dan ta.
Maji ta shiga part din tana saye da hijjab mairuwan toka har kasa a jikin ta sai dai duk idon ta ya kumbura don kukan da ta yini yi ranan.
Da sallama a bakinta tashiga dakin inda ta dan tsaya daga kofa tana sallama daga waje.
Akai mata da iso da amsa sallaman da tayi hakan yasa ta daga labulen ta shiga daga cikin dakin.
Bayan ba,tasan dakin ta tsaru kamar na yan boko dama don komai akwai cikin dakin nata.
Amma da take ita ba ruwanta da bin dakin kishiyoyin ta,sai bata iya kaiyade abin dake cikin part din gaba daya.
A,a hajiya maijjida kece tafe yanzun fa nake son nagama da wanan dan rigiman naje gurin ki sai kuma gaki cewa karamin yaron ta da ta yaye amma ya dan tasa yagirma.
Ta kai kallonta ga yaron tace Amir kaine wai dan rigima aiko ba ruwan shi dai nagani.
Cafdi baki san komai ba ke na wanan ai fitinanne na karshe wallahi.
Yanzu fa nake zancen zuwa gurinki na kara baki hakkuri akan abinda yafaru dazun don abin ba dadi gaskiya saidai hakkuri da addua kawai Allah ya shirya muna su baki daya.
Maji tace nazo ne nai maki godiya kan irin halarcin da kikai nuna dazun din.
Nagode Allah ya saka da,alheri Allah ya kara bamu hakkurin zama da junan mu yasa wa zuria albarka.
Habba hajiya maijidda ai shi da na kowa ne danki fa da nane kamar yadda nawa suke naki.
Ke fa mutum ce mai kokari da sanin ya kamata duk irin halarcin dakike min kan nawa yaran aina sani.
Don ko dawowa sukayi ban dawo ba,daga school gurin ki ne kawai suke samun fuska a gidan nan har nadawo na,samu sunci abinci hankalin su a kwance.
Don may yau zanga naki cikin wani hali na kasa nuna bakin cikina akan hakan abin baiyi dadi ba gaskiya amma ayi hakkuri don Allah.
Hawaye ne suka zubo wa Maji daga idon ta take cewa hajiya, kubura ban san yaya zanyi da,wanan yaron ba a,rayuwa ta duk yadda ake ba yaro tarbiya nasan ina ba sadauki shi a,rayuwa amma a karshe duk ya,watsar dasu ya zabi wanan harkan na,shashan ci.
Hmm abin fa yanzu sai addua don ya fara zama ruwan dare ga matasa sai dai wanda Allah ya kare kawai shine ya tsira.
Na san zafin wanan tun a gida don ina da kani mai irin wanan rayuwan amma cikin ikon Allah yanzu ya daina ya koma normal mutum din shi kamar kowa.
Wani abinda baki sani bama shine abin fa ba mazane kawai ba harda ma mata wallahi mata ma ba,wai yara ba manyan mata hamshakai wallahi.
Ke dai kawai Allah ya gyara muna amma a lokacin muke da in kana da da namiji ko mace baka huta ba kowa da tashi irin matsalar.
Ki dai yi hakkuri kada ki sa zancen a ranki harki jawa kan ki matsala babba yazo yai maki illa a,rayuwanki.
Maji tai mata godiya inda hajiya Kubura ke cewa don Allah a dake da addua da rokon Allah kuma ki toshe kunnnen ki ga duk wani magana ko gorin da wani zai maki don ba wanda ya wuce hakan ai.
Maji takara cewa nagode Hjy Kubura nagode kwarai Allah ya saka da alheri tabar dakin tana masu sai da safe.
Ta kawo daidai tagan hjy Asiya taji tana cewa yaran ta wallahi kuyi hankalin da mashayin nan na gidan nan kunga ya fara haukacewa don haka duk wanda ya shiga tsabgan shi kun dai san ba,a shari,a da mahaukaci sai dai ace kuyi hakkuri an cuce ku.
Shigewa tayi part din ta tana jin kamar ta hade ranta yadda zancen yake mata kuna a rai.
Ikon Allah yau Sadauki dan cikina ake kirawa hauka da raina ikon Allah Allah ka taimakeni ka,shirya min wanan yaron ya Allah na rokeka.
Hajiyan masa bata zaina ba da dare ma sai gata ta dawo gidan ta kara ba Maji hakkuri inda suka kara tattaunawa akan al,amarin tai mata alkawarin shiga da fita don suga ya daina wanan harkan.
A nan tabar Bintun ta don dama ba yazo don ta,bane sai dai duk shiyan nasu ranan haka suka kwana cikin bacin rai babu maidadin rai daga cikin su.
Washe gari ma haka suka tashi sukuku duk ran su ba dadi saida safe ne Alhaji yakira su gaba dayan su ya tarasu a falon shi.
Inda ya kira sadauki da sauran yan uwan shi suka zauna don tattauna matsalar da,ya fada ciki.
Bayan gurin ya natsune maigidan yafara magana kamar haka.
Dama nataru kune nan don kowa yasan akan dalilin dana kiraku nan, batare da dogon magana ba ina son kowan ku yasani Umar gashi nan a gaba na daga yau na yafe shi daga cikin diya na.
Don ba zan zauna da dan da zai jawo min abin kunya ba a gidana, na,wuce ana nunani ga mahaifin mashayin nan can.
Kuma ka sani daga yau kada ka kara shigo min gida don kada ka bata min sauran yarana kimtsatu.
Uwargidan su tace gaskiya wanan matakin yayi daidai wallahi don gaskiya nima tun jiya nake wanan tunanen don barin shi cikin mu gamu da yawa a gida yana iya sa wani yaron yai koyi da halin shi na banza.
Mama Asiya itama ta tare zancen dacewa nima wallahi hakan yai min daidai don gaskiya barin shi a cikin mu babban hatsari ne don kada wata rana ya zo ya shawo ya kama mu da bugu.
Wani irin zafi da dacin zuciya Maji take ji shiko sadauki kan shi yana duke don kunyan mahaifiyar shima yake ji ba nasu ba don yasan shine ya jawo mata wanan sukan da ake mata mai kama da an daba mata wuka a zuciyar ta.
Assha Alhaji wanan maganan da kayi wallahi ba girman ka bane.
Ka taba ganin inda hannun mutum ya rube ya yanke ya yar dashi, don Allah ya jarabi wanan yaron da wanan lalurar shine zaka yanke wanan danyen hukuncin haka akan shi.
Wallahi baka kyauta masu ba ko kadan in kai masu haka daga shi har uwar shi.
Idan bamu jashi a jiki muka nuna mashi illan abinda yakeyi ba kyau ba, watau ya tafi ke nan yafi nan lalacewa ko?
Gidan kowa yanzu akwai matsala in hat gida babban gida ne amma kowa hakkuri yake yana boye abin shi yana jan kayan shi a jiki.
Amma ya daina shigo maka gida dakace ita uwar shi a ina zata gan shi har tasan halin da yake ciki ta tsawata ma abinta.
Da dai ka haife shi kuma jerabawa ya fado kan shi sai ayi hakkuri anema mashi shiryuwa ga Allah shine daidai.
Kai ji hajiya kubura wallahi ni ban son al,amari da munafunci uwar ahi in tana son ganin dan ta taje gidan mashaya ta,samay shi mana inda yazabi zama.
Umm,umm hajiya Asiya wallahi daji bai gama cin wuta ba ba aiwa kututure barka, kema fa uwace kamar hajiya maijidda don haka kii iya bakin ki.
Tuff tuf wallahi bakin ki ya sari danyen kashi wallahi nikan ba,a cikin kayana ba wallahi, watau baki kike min akan diyana ko ?
Ni ba baki nai maki ba gani nayi ko ita uuwar shi bataso dan ta da hakan ba, jerabawa ne dai daga Allah ya fada kan shi.
Kaidon Allah ni ya,ishe ni ban kira ku nan ba don kuzo kuna min cacan baki kiran ku nayi don ku ji shawarana.
To gaskiya Alhaji shawaran ka bai yi ba gara ka canza wani, wani irin huci Alhaji yayi yafitar da iska daga bakin shi.
Yace naji amma idan ya ganin ni wallahi ya kama kan shi inba haka ba zamu sa kafan wando daya dashi a gidan nan kaji na fada maka yaron banza yaron wofi kawai.
Tashi ka bani guri mara mutunci kawai mun sakafan wondo daya dakai a gidan nan wallahi ko.
Allah dai ya,shirya muna shi kawai za,ace amma wanan fadan ai bayi ba,wallahi tana fadin haka tamike tabar dakin cikin bacin rai, sauran suka bita da kallon ke asuwa munafuka mun san sallon kishin ki ai.
Ita ma Maji mikewa tayi tabar dakin tabarsu nan tafada dakin ta tana kukan bakin ciki da takaici.
Yau dan ta yaja mata wullakanci ga kowa agidan saboda shi anzaunar da ita ana fada mata magana son ran mutum.
Shiko Alhaji ya mutuwan son hajiya kubura badon yaso ba ya yarda da,shawaran ta don kawai kada su sami sabanine a gidan.
****** ********* ******
Tun da akai wanan case din sadauki bai kara,shigowa gidan ba yau kusan sati daya ke nan haka ranan abin da da mahaifi maji tatura maryam ta duba mata shi idan yana nan takira matashi don tana son suyi magana dashi.
Itama hajiya kubura ko yaushe tana tambaya idan yadawo ko ya shigo sai maji tace mata bai shigo ba ai.
Maryam ta samay shi a kwance dakin shi ya yi kwanciyar rigingine yana kallon saman dakin ta tsaya daga kofa tagaida,shi tafada mai sakon mahaifiyar su.
Yace taje tace gashi nan zuwa, ta dawo ta fadawa maji abinda yace mata bayan kamar minti goma sha ya,shigo gidan sai dai bai shigo ba kamar yadda ya saba ya dan tsaya daga waje kadan ya tura wani dan kannin shi ya kira mai maji dakin ta.
Yaron yashigo yana cewa yaya sadauki ne yace na kiraki yana daga waje wai.
Amira tace bazai shigo ba ke nan bari naje na shigo dashi, maji tace ai kunya marin da ne .
Amira na zuwa tace yaya Maji tace nace kashigo daga ciki mana ka tsaya nan .
Yace look Amira ki fada mata bazan shigo ba gani nan dai tazo ina jiran ta, tausayin dan uwan ta ya kamata ta juya rai a bace takoma ta fadawa uwar nasu abinda yace mata.
Maza jeki kice mashi nace bani son diban albarka shi da yai laifi ba,ai fushi dashi ba dai shine zai wa mutane zuciyan banza.
Amira na fada mai sako sai gasu a tare sun shigo gidan da ita.
Yana saye da farin shadda a jikin andanyiwa shaddan kwalliyan dan bakin kyalle a gaban rigar da fari.
Ya shigo da,sallama ya koma kaman wani kamili dashi ya ramay yai dan dogon wuya sai dan bakin da yayi.
Maji ina wuni kamar bazata amsa mashi ba tai shiru ya samu guri ya zauna a saman kujeran dakin.
Tausayin mahaifiyar shi ne ya kama shi don ita ma ta,ramay ta,fada sosai da ka kalleta kasan tana cikin rashin kwanciyar hankali sosai.
Yaya ina wuni muryan Bintu da ke mikewa zata shiga daga ciki ne ya katse mai tunanen shi a lokacin.
Lafiya kawai ya amsa mata,dashi sai kuma dan abinda ya,faru ranan yafado mai a rai din ya dan iya tuna lokacin da ta bude mai baki kan shi yana samancinyan ta ta tura mai manja a ciki.
Wani irin kunyane ya kama shi da nauyin yarinyar don yasan ta taimaka mai har sau biyu a rayuwan shi.
Maji tace kai ba,ai fushi dakai ba shine kai zakiyi da mutane ko, da kai fushi kaki shigowa may kake nufi da yin haka.
Maji ba,wai hakana bane kinji abinda baba ya fada ai shiya sa ni kuma naga gara kawai nabar shigo mashi gida kada na ja maki matsala.
Matsala kuma na yaushe sadauki akwai maysalar da kuma yafi wanan din da ka jawo min ne a cikin gidan nan.
Maji don Allah kiyi hakkuei wallahi kaddarace amma ban taba shan kwaya ba sai ranan koshi bacin raine na rashin barina nabi abokai na gurin kwallon da akayi yakaini ga hakan.
Insha Allahu bazan sake hakan ba da yardan Allah don Allah dai kiyi hakkuri maji ya fadi cikin kwantar da muryan shi.
Yanzu Baba na kana ga inin irin hanyan da ka daukar wa kanka shine daidai gareka gare mu ma.
Kaiwa kanka fada,wallahi ka dibs ka gani saboda kai aka zaunar da ni kowa na fada min irin abinda yaga dama a lokacin.
Inda ka gyara halinka duk gidan nan wa ya isa yai muna haka babu shi wallahi don ni ba ruwana da harkan kowan su.
Amma sanadiyar abinda ka aikata ji irin yadda kowa ya takamu son rashin ana fada muna abinda aka ga dama.
Maji kiyi hakkuri don Allah insha Allahu ba,zan sake ba da yardan Allah hakan ba,zai sake faruwa ba.
Nan dai taita mashi nasiha tana cewa yanzu ashe badama su Amira su yi laifi na kawo maka karan su a matsayin ka na babba a cikin su.
Ni hajiya kubura wallahi tai min komai don ta nuna min ita uwace a gareka kuma tasan ciwon kan ta ba kamar sauran iyayyen naka ba.
Don haka wallahi kaiwa kanka fada kaceci kanka kace ceni ni uwarka da yan uwanka kafitar damu daga zagi mutanen duniya.
Sun kai wani lokaci tace ya tasgi ya tafi take ce mai kuma daga yau ya tabbatar da ya dinga zuwa gida yana cin abinci bata son yana ci a waje inda batasan ko ina bane.
Yai mata godiya ya mike yabar gurin tare da kara bata hakkuri yabada baya take cewa jika don Allah kamar wani mutumin kirki can ashe mutimin kawai.
Murmushi yayi yace kiyi hakkuri maji don Allah bazan sake ba insha Allahu.
Yana fita ta sauke ajiyan zuciya tare da cewa a filo Allah ka,shiyar mun da wanan yaron dama sauran yara masu halin shi na,wanan lokacin,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
Baby yaya zamuyi ne ina son ki rakani zuwa lagos don ina da seminar da zamuyi a can, kuma dake nakeson zuwa.
Shiru Raiha tayi tana nazarin zancen shi a cikin ran ta don tasa abu mai wahala ya dauko mata.
Yaya zatayi da uyayyen ta a gida may zata fada masu ina zata ce masu zata tafi.
Muryan shi ne ya katse mata tunanen ta yana cewa naji kin yi shiru mana ko baki san rakani ne wai?
Hmm ba,wai hakana bane kasan in da hali koma ina ne zan iya raka ka amma ban san yaya zanyi da iyayyena ba may zance a gida.
Haba baby sai kace wata local can dan karya kawai zaki shirya masu mana kice zaki gurin wani dan uwan ki koda kauye ne kinga indan munje mun dawo sai na kai ki garin ko kwana daya kiyi sai ki dawo ko?
Nan ma,Raiha shiru tayi tana tunanen akan zancen shi don tasan abune mai wuya abarta zuwa wani guri ita kadai.
Gashi kuma tana son bin shi sosai a ranta don batajin yanzu zata iya rabuwa dashi ko na dan lokaci kadan ne.
Sai cewa tayi zan yi shawara don nasan abinda zan yi akan tafiyan.
Huci yayi don jin dadin yasamu yadda yake so daga gurin ta nan ya shiga yi mata abinda yasan tafi bukata daga gare shi har suka kai ga,watsewar su a hotel din da ya kaita.
Da zasu rabu ne yake jadfa mata cewa next week ne fa sunday tafiyan su kuma da jirgi zasuyi tafiyan, don haka yana son yasan idan zata tafi ya sai tickets din su shida ita.
Ba matsala tabashi amsa zansan yadda zanyi mu tafi din tare insha Allahu.
Wani shu,umin murmushi ya,sauke tare da,shafan dogon fuskan shi ya na cewa dat is my baby shiyasa nake kara,son ki.
Tun dawowan ta gida take ta faman sake sake a ranta sai kullawa take tana warwarewa ita kadai a ranta.
Can wani dabara ya fado mata a rai tai wani murmushi daidai uwarta ta zo shigewa take cewa, mama ina fa son zuwa kamba gurin su kaka na dubo su.
Kamba Raiha kedawa zaki tafi har kamba ? Raiha tace haba mama sai kace wata karamar yarinya ni ko makka ai ina iya zuwa ni kadai yanzu.
Kai Raiha wai may kike daukan kanki ne yanzu har nawa kike da zakice zaki iya kai kanki makka.
Yanzu dai mama da na shiga mota daga nan sokoto ba sai jega ba daga jega ga motocin zuwa garin kamba nan sai na,shiga kawai.
Eh lalai ashe ko zaki iya aiko kin kyauta bari malam ya dawo na fada mai Allah yasa ya barki dai ki tafi din .
Raiha cikin marairai cewa take cewa don Allah mama ki tayani rokon shi ya barni ba dadewa zanyi ba sati daya zanyi nadawo kawai.
To shike nan bari yadawo din muji yadda za,ayi idan zai yarda sai ki shirya ki tafi aini wallahi kin kyauta min nasha kulla tafiya na dubo su amma sai abin bai yuyuwa.
Yanzu kinga ai inkije sai ki taimaka min nasan halin da,suke ciki a can din.
Sai da,dare bayan mahaifinta ya dawo ne take sheda mashi bukatar yarsu na,son zuwan ta kauyen zu garin kamba wanda ko anje kambadi sai an shiga mota ko mashin zuwa can.
Haba nana yanzu kamar Raiha ne zamu saka a mota daga nan har kamba ita kadai a,wanan zamanin da muke ciki.
Malam insha Allahu zata iya ai yanzu tasan hanya zata iya kai kanta ita kadai bada wani ba.
Nan dai suka kama inyafito nan tafito mai nan abin mata da miji har ya yarda da zasu tafi ya bata kudi tayi sayayya da kudin mota wanda zai kaita.
Sosai Raiha taji dadi a ranta nan take ta kira Nasir take sheda mashi halin da take ciki.
Yai murna yaji dadin samun nasaran da sukayi don haka washe gari yaje yai saya masu ticket din tafiyan su.
Bayan kwana biyu suka shirya sai air port inda suka tashi zuwa garin lagos ita da shi.
A wani katafaren hotel ya sauke su ita dashi inda tun ranan ya fara nuna mata wane shi, don dama can ashe a sannu yake binta.
Bata da hutu a gurin Nasir don kusan a kanta yake kwana har gari ya,waye.
Tun tana iya jurewa halin Nasir har Raiha tafara raina kan ta da kanta don yanzu yakai bar ta baya yake ne manta.
Da farko takiya amma da tasha duka a gurin shi dole ta yarde mashi yana yadda yake so da ita.
Idan sun gama kuma ya dauko kayan maye ya dirka mata sai ta futa hankalin ta .
Sati dayan da sukayi Raiha tagan shi kamar shekara daya ne na,wahala da ukubar zugubar namiji a gare ta.
Sam babu tausaya tsakanin ta da nasir ko kadan kamar ba soyayya ce ta hada su ba don yi yake kamar ya samu boya.
Saura kwana uku ta dawo ya shiga da ita gari shida wani abokin shi suka je zaga garin da ita.
Yai mata sayayya sosai na abinda duk tagani tana so a fitan nasu taci kayan ciye ciye masu kyau sosai da tsada.
Bayan sun dawo sai taga wanan dayan abokin nashi baida niyar tafiya kamar yadda tai zaton tafiyan shi.
Ashe bata sani ba aun hada plain a tare shida Nasir zasuyi amfani da ita gashi shi ba ko musulmi bane dan uwan ta.
Nan suka samay ta da ihu da komai suka kwana a kanta suna juyata yadda suke so.
Tai kuka har tagaji tahakkura ta kyale su suka gama don kan su ka barta, abokin nashi yata yaba ma dadin ta har yana rokon Nasir da ya bar mashi ita for ever amma nasir din yaki yarda da hakan.
Yake cewa Michael ai ba,addinin su daya ba don haka ba,zai yarda ya zauna da ita ba.
Bai san bayan sunyi barci Michael ya dauki wayan Raiha ba ya saka layin shi yakira nan ya samu nomban ta.
Sun dawo arewa kwanan su daya a garin sokoto takaita garin kakan nin ta ta kwana washegari ta dawo sokoto ita dashi dake jiran ta a birnin kebbi.
Maman ta taga ta sake maimakon taje kauye tayi baki amma sai wani haske ta dan kara sai dai tayi dan rama amma fa tayi mata kyau a fuska sosai.
Yanzu ke Raiha kada dai kinje kin cinye ma yan tsofi kajin su wanan irin haske da kikayi haka anya kuwa ba barna kikayowa tsofin nan ba.
Raiha kuwa sai rankon barcin wahala takeyi don sai yanzu ta samu hutun wahalan da tasha gurin Nasir a can Iko.
Sai dai shi bai sani ba ta riga da ta yanke a ranta cewa ta gama zama dashi ke nan don yai mata wullakanci a can dama lalaba shi tayi har ta samu su dawo arewa.
****** ********** *****
Ganin yanzun ba wani ciniki take samu ba sosai yasa ta yanke shawaran samun dan almajirin da zai dinga mata talla tana bashi abinci da dan kudin sabulu kamar yadda da yawan almajirai sukeyi yanzu.
Duk almajirin da ya shigo zatai mashi tayin talla amma sai su zille suce malam ya hanasu yin talla ko kuma suce dama shara ne ko wanke wanke zasu yi amma ba talla ba.
Sai wani yaro ne tasamu yace mata zai yi Allah ya taimaketa yaron yana da kan talla sosai don da yafita kamar ya kifar ne zai dawo ya kara wani.
Haka yasa tagane fita da sana,a waje yama fi cikin gida sosai samun ciniki .
Maigidan ta yaga almajirin yai mata magana akan ta dai kula da bashi hakkin shi don kada Allah ya tambaye ta akai.
Amma,saboda dadin baki irin nata bata bari yakai karshen nasihan shi ba ta shiga bakinta akan zancen.
Maigidan dai ido ya,sa mata baice mata komai ba sai cewa yayi bani abinci nashi kada na makara zuwa daukan karatu.
Yana cin abincine yaran shi suka zagaye shi suna fada mashi makarantar su ance a,sai masu shocks da takalma.
Yakai loma,a bakin shi yana cewa aiko sun dauko min aiki yanzu hada kudin safa da takalma ai aiki a cikin wanan daman da ya fara.
Kuyi hakkuri insha Allahu zan sayo maku nan bada jimawa ba da yardan Allah.
Yana gamawa bai tsaya jiran komai ba yafita zuwa gidan babban malamin shi inda yai karatun allon shi.
A nan yake zuwa daukan karatu gurin malamin duk dare idan ya,dawo daga gurin neman kudin shi.
Yana fita ymta jawo bankin kudin ta tafara lissafawa inda taga irin ribar da ta samu gurin tallan almajirin ta.
Tayi murna kwarai don ba karamin cabawa tasamu ba ga wanan tsarin sai fadi take ai wallahi mama ta taimakeni da wanan shawaran nata.
Don gashi kwana kadan na hada,waban uban kudin haka nan ta,ware nata ta cire ma,almajiran ta nashi.
Har yaran sukai barci amma ita hankalin ta yana ga sakan zucin da takeyi itta kadai a lokaci, na ganin ta hada kudi ta sai fili da sunan nata.
Sai karfe goma mijin ta ya dawo gida ya samu yaran saman shimfidan da ya tashi ga sauro na cizon su.
Yacee haba maryama da wannan sauron kikabar yaran nan haka a cikin shi suns cizon su gani ba kudi gareni ba idan maleria ya kama su da,wani zanji.
Sayen abinci ko sayen magani da zuwa asibiti gashi yanzu zazzabi idan ya kama mutum kamar ba zai barka,ba sai ka hada da,asibiti dole ko chemest.
Nan ya shiga kwasan yaran zuwa cikin dakin kwanan su gaba dayan su saida ya kwashe su ya kaisu daga ciki.
Maria na gama abinda take ta nemi guri ta kwanta don dama a ganiye take don tun safe bata huta ba tana gudun tai barci masu sayen ruwa ko wani kayan sanyi su shigo.
A gaakiya ta godew haduwan ta da Muda almajirin ta don yaro ne ma hazaka gashi da amana.
Koda gurin lissafi tai kure zai dawo mata da canjin ta, ya bata abinta, bai sa ta gode mai ba.
Ko da daga gurin talla ya dawo bata barin ya dauki abinci komai yunwar da yake ji.
Sai yai mata shara da wanke wanke, da yan sauran aiyukan gida kafin ta sallamay shi.
Hakan ne ke batawa yaron Muda rai yana yawan yiwa yan uwan shi almajirai korafi sosai.
Wanan shine matsalar da ke damun yaron mai mata talla koda zai makara ga karatun shine sai yai mata aiki bayan kuma akan talla sukai alkawari kawai dashi.
Wata rana yana fita daga tallan ne sai gashi ya dawo jiki na makyarkyata yana jin sanyi ba lafiya.
Maimakon Maria ta ji tausayin yaron sai cewa tayi shine baka sayar ba kadowa min dashi ya tsiyaye ga banza.
Cikin rawan sanyi yaron ke fadin banda lafiya ne maman Abba sanyi nake ji sosai.
A je katafi tunda yau baka son yin tallan ke nan nagani, maman abba in kina da magani don Allah ki bani nasha.
Tace cikin tsawa banda shi kaje gurin malamin ku yabaka shida ya dauko ka mana.
Yai shiru kamar mai nazari can yace don Allah ki taimakeni da koda cikin kudina ne na biya shago nasai magani.
Babu su tafadi a cikin fada da,dan tsawa yaron yafita yana dan makyarkyatan sanyi don fever ya damay shi.
Yana zuwa makaranta ya rabke da ciwo maleria ta kama shi sosai nan malamin su ke tambayan shi ina kudin tallan shi ya bayar a,sayo mai magani yasha.
Da kyat yaron ke iya magana yake cewa na tambayi matar tace wai babu kudin.
Malamin ya hasala yafito yana tambayan wayasan gidan da Madu ke talla ya aike shi.
Suka yaran wasu sukace sun sani nan sukatafi gidan don su karbo kudin shi hannun maria.
Amma sai tace a tafi ita babu kudi a hannun ta sai dai idan ta samu zata aiko mashi dasu.
Almajiran basu fita ba suka tsaya yi mata tsageranci, akan sai ta bayar da, kudin sukai wa malamin su.
Sun dade basu samu ba dole suka bar gida taki bayarwa kuma tabi su da zagi.
Suna fadawa malamin yace kada wanda ya koma gidan subarta da Allah a bar maganan.
Shi yakai yaron asibiti akai treating din shi ya biya kudi har yaron ya samu sauki.
Bayan Muda yaji sauki yaki zuwa gidan ta nan almajirai yan uwan shi kewa makwaciyar ta hiran shi tace akawo shi ta dauke shi aiki.
Ita ta rike yaron zaman amana kamar itace ta haife shi haka yasa Maria jin wani irin kishi kamar zatayi hauka
****** ******** ******
Kamar yadda mai masa taiwa Maji alkawari haka din ne don batai sanyi a,gwiwa ba ta shirya sai wani kauye can gaba da kauyen su gurin wani malami.
Malami irin malamai na kwarai bai damu da wani kudi ba don a kauye yake kuma ita dashi yan uwane ta mahaifiyar su.
Yana ganin ta ya shiga murna da nuna jin dadin ganin ta nan yasa ai mata girki na musan man kamar yadda yan kauye suke yi idan sun ga bakon birni yazo gurin su.
Sai da dare suka samu kebewa dashi da ita suka kara gaisawa sosai, nan take, sheda mashi dalilin zuwan ta gurin shi.
Ya jijiga kan shi yana cewa matsalar ku ke nan yanzu yaran birni don kwanaki akwai wani da yazo tun daga kano har nan gurina akan wanan matsalar.
Amma yanzu ba abinda zamuyi sai dole munyi istihara don naga daga inda matsalar take, don kinga ba
dama muzo muna aiki inda muka dosa daban abinda ke damun shi daban.
Don haka ki bari sai zuwa gobe da safe sai nai maki bayani, mai masa tai mashi godiya sosai nan suka dan taba hira na yaushe rabo da junan su.
Washegari tun da,sauran duhu aka kaiwa gwago ruwa masu zafi tai wanka tana fitowa ga koko mai zafi da kosai da masa irin tasu ta kauye da badin shi.
Tace wani abu sai kauye mu a,birni ai yanzune ma,wata mace ke gyara kwanciyar ta.
Sai da ta karya tashiga ko wani lungu na gidan suka gaisa da mutanen gidan sai ta dawo dakin da akai mata masauki .
Ba a jima ba malam ya,shigo gidan ya shigo dakin da mai masa take ciki suka gaisa yai mata ban gajiyan tafiya da bakun ta.
Can yace Asmau nayi duba akan matsalar ku amma gaskiya akwai yar matsala a cikin harkan.
Don shi wannan yaron gaskiya akwai hannu ga harkan shi.
Don tun yana karami aka soke shi don haka su abubuwan bayin kan sa bane.
Yaron nagani yana da taurari masu haske sosai a rayuwan shi don hakane akayi kokari dakushe masa su don kada ya haska.
Anje anyi tambaya a kan shi amfadawa wa masu shi cewa zai zama wani abu ga rayuwan shi shine suka,sa ai mashi wanan aika aikan.
Kuma al,amarin ga yadda nagani ba wai mutum guda bane yai masa haka ,a,a suna da yawa kowa kuma da irin aikin da akai mai.
Ga miyar kifi aka bashi wanan abin shaye shayen yaci shi.
Matane da namiji guda sai dai ba zaso na fada maku su ba don gudun hadin hasu mi.
Yanzun mu matsalar mu shine mu san mafita akan zancen mu san yadda zamu nemo makaru mu kara wanan asirin na jikin shi.
Don muddin yana tare dashi ba,zai taba zama wani abin kwarai ba ga rayuwan shi.
Kin ga yadda nagani matar tana da yara uku a,raye shine dana farko a gurinta.
Su ma sauran diya matan nata biyu wallahi ba,a barsu ba don suma suna da nasu asirin sai dai suyi ta zaman gida ba aure.
Koda ma an dace sunyi auren bazasu zauna ba zasu fito don zasuji auren ba dadi.
Yan da zaai sha rubutu ne kinga sai na rubuta maki wani rubutu ki fara,zuwa masu dashi har uwar tasu tasha.
Kafin kwana biyu nan da sati biyu ki dawo lokacin na,shirya,sauran abinda da zan baku.
Gwago tace zai sha mana malam ai kasan wanan dolene asan yadda za,a bashi yasha.
Yace kin san yanzu yayin izalar nan ta sa matasa basu son shan irin abubuwan nan.
Kuma mutane ne basu gane ba ai shi a addini musulunci da kike gani kur,ani maigirma yazo muna da,warakan komai a cikin sa.
Malam zai sha yace to amma fa uwar ce zata sha tabasu da hannun ta,suma su sha hakan zai dan kawo muna saukin abin insha Allahu.
Zanbaki abu biyu zuwa uku kikai masu sufara yi insha Allahu idan sunyi badai samu ba in ma wani yakara kokarin yi masu sai dai ya koma ga maishi wallahi da izinin Allah bana mutum ba su dai kada suyi wa wani sheri a rayuwan su.
Nan ya mike yaje ya hadowa gwago mai masa abubuwan fa,zai bata yace takaiwa Maji da diyan ta Allah ya sauwaka.
Gwago bata tsaya ba ta juyo zuwa,sokoto a ranan sai dai cikin dare ta iso garin.
Don haka ta wuce zuwa gidan ta da abubuwan sai washegari take da niyar takawo wa Maji su.
******* ******** ******
Washegari ba a zuwa makaranta don haka yaran kowa yana zaune falo tare da iyalin shi.
Bintu tana daga ciki tana shiryawa don yanzu tagama gyaran guri don ita bata gajiya da aiki ko kadan,
Idan kaga yadda part din maji yanzu yake kalkalkal zakace ba mutane a cikin sa da yawa.
Wani lokaci har hajuya Kubura takanyiwa Maji ba,a tace hajjiya maijidda ki bani wanan yar taki mana.
Wallahi ni dai yarinyar taimin bata,da kiuya ko kada,akwaita da tsabta ga ta,da kwai wallahi.
Maji kanyi dariya,tace a,a kibar mi "ya ta,Allah ne yakawo min hutu ta hanyan ta .
Bintu tafito falon duk suka bita da ido har maji din, sai maji ke cewa kun gani tai aiki kuma harta gyara jikinta kuko kuna nan kuna bakin shiriritan ku da kuka saba ace gari ya,waye mace bazatai wanka ba ba kuma komai kukeyi ba. Mutane suyi ta shigowa suna,samun ku a haka.
Kai maji ko munyi kwalliya wa za muyi wa mutum ko saurayin kwarai baida.
Au sai da,saurayi ake kwalliya mace fa da kwalliya aka san ta ko yaushe don abinda kuke yi anan shi zaku je gidan mazajen ku kuna yi.
Bintu ta dan zauna daga kasa sai cewa maryam tayi kai Bintu ke kullun kamar bakuwa har yanzun baki saba ba ke.
Kila dai tsoro take ji a,a bata da tsoro wallahi, don ranan fa itace tafara zuwa gurin yaya sadauki ta kama shi.
Aini wallahi ranan Bintu ta bani mamaki sosai wallahi, don gaba daya na tsike ni a lokacin.
Maji wacce zuciyar ta ya sosu da zance amma sai take cewa ai Bintu tai kokari wallahi sosai.
Toke halan waya fada maki anabawa mutum manja da gishiri ya sha idan yana haka.
Tace nima labari naji wata yar ajin mu tanayi cewa wai duk yadda mutum yasha maye idan aga yai mashi yawa abashi manja da gishiri sai ya amaye su su rage mai aiki a jikin shi.
Ikon Allah inji maji tace Fatima shine kika gwada ke kuma gashi kuma na lura abin yai mashi amfani sosai don yasa yadan dawo cikin hayacin shi.
Amira tace wallahi aini duk mamakin Bintu ya kamani a lokacin don ni ba karamin tsorata nayi ba don na dauka ma mutuwa zaiyi ai.
Kai sadauki Allah dai ka,shirya kayan ka amma sadauki bai min da ba,wallahi.
Yaro kai kadai Allah yabani namiji amma kuma kai ke sani kuka.
Maji ki daina mashi kuka don Allah adaiyi ta addua inji Amira ta fadi cikin muryan tausayi.
Ai inayi Amira Alla dai ya,sauwaka kawai don na lura fa abin nashi yai girma sosai ko ba yanzu yafara sha ba.
Shin tsaya dai in tambaye ki Bintu wai dai ko ranan nan ma da kikace wai kin fada kwatane shine yai maki amai ga jikin ki wai.
Da sauri Bintu ta dago kai sai kuma ta dukar da kanta kasa don bata iya karya ba.
Da sauri maji ta dago kai tana kallon Bintu tace wai Fatima hakane ko kuwa?
Tace hakane Maji nan ta fada masu duk yadda abin yafaru da yadda ta samay shi a kwance har shigowan ta gidan.
Shiru sukayi dakin suna nazarin zancen Bintu kowansu yana yaba kaifin hankalinta.
Maryam tace shine da kika shigo baki fadi ba Bintu?
Haba Anty Maryam bayan nasan mama bata da lafiya shine zan fadi na kara mata ciwon kai.
Bazan fadi ba gaskiya don ban son hankalin mama ya tashi, don ba karamin tashin hankali zata shiga ba.
Baki gafa yadda yake bane nima da kyat na uya kai shi dakin shi kamar numfashina zai dauke nake ji a lokacin.
Ikon Allah wanan yarinyar akwai ki da mugun karfin hali wallahi danice ai ihu zan dinga kantarawa sai kowa yafito a gidan nan.
Da,sauri Bintu tace kai anty ai wanan rufin asiri ne ba abinda za,a bari wani yaji bane.
Kinji ke mai cewa zakiyi ihu maji ke fadawa maryam hakana tace ai Bintu yarinya ce mai hankali wallahi.
Ai kan inji Amira don akwai ta da dan banzan wayyo kun gan ta nan.
Sallaman mai masa ne ya dakatar su suka,shiga gayar da,ita suna mata ina kwana.
Maji tace a hajiyan masa ashe tafiyan naki ba mai dadewa bane har kin dawo ?
Nadawo hajiya dama tafiyan nawa ai donki nayi shi ba tafiyan kaina bane nayi.
Maji tagyara zama tana fadin ikon Allah ashe mu akaiwa tafiyan ke nan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU, PLEASE,,,,
Bayan gausuwa a tsakanin su sai kuma dan shiru yafara biyowa baya hakan yasa Maji cewa yaran ku bamu guri mana ko.
A,a su zauna ai gara suji abinda zan fada da kunnuwan su don su fahinci maganan da zan fadi da kyau.
Tsit yaran har
Maji su ka yi a falon bawanda ya koda dan motsa sai gwago ce tafara magana kamar haka.
Na tafi kauye ne gurin wani malami amma dan uwana ne can gaba da kauyen mu.
Na samay shi akan zancen wanan yaron sadauki ne amma kuma sai wani magana ta daban tafito muna.
Kin san yanzu mutane ba imani da tsoran Allah a tare dasu.
Kin san yanzun muna a lokaci, ga imani a baki amma ba shi ko kadan a zuciyan bayin Allah.
Wai kuma a haka kowa ke son shiga aljannane , ga son duniya ya rufewa mutane ido da zukatan su.
Wanan duniyan da ba bakin komai take ba ga mai imani da tsoron Allah.
Wai may kuma ya farune hajiyar masa inji Amira da take jin digon bayanin da hajiyan masa keyi yai mata yawa.
Waiko kina da hankali Amira baki da kunya fa ke ko kadan ,ina ruwan ki da zancen mu ne wai.
Hajiyan masa tace barta ai zancen ne taji shi kamar da,tsawo a zuciyan ta.
Mai masa ina,sauraren ki kinji rabu da mara kunyar nan futsarara.
A,a hajiya barta don Allah duk ba yin kan su bane ai ,abinda ke tafe dani shine.
Yaran ki gaba daya wallahi an sa masu hannu, duk yadda kike fatan samun su gaskiya a yanzu abin zaiyi matukar wuya.
Don gaba daya an lalata masu rayuwan su ta inda ma baki zata ba wallahi.
Kai ni wallahi ban son irin wannan spercition believe din na,anyiwa wani wani abu wanan ai duk shirka ne.
Hmm kawai mai masa tace tare da fadin kaiyya bazaki gane ba ke yar nan sai an makara ko?
Tiryan tiryan yadda malam ya fada wa gwago haka ta fadawa Maji bata boye masu komai ba don taga basu da niyar yarda yaran.
Tabbas kuwa hajiyan masa na tuna anyi hakan don abin nima ya tsaya min arai sosai.
Don wata rana yaya babba ta ce wai kifine ta dafa wa yaran ta zaunar da sadauki wai ga nishi da ta aje mai saida ya cinye shi tas,
Ya kusa gama cine sai ga babangida dan ta ya,shigo yana cew sadauki ya,raga mashi amma,babu kunya a gaban mu yaya take cewa wai a,shi kadai tayi kada yaba yaron,
Amma dashi sadaukin ya mikawa dan uwan sauran da ya,raga sai tai wa yaron nata jan ido akan idan yaci sai ta bata mashi rai sosai wallahi.
Daga baya ne tunane yazo min cewa may zai sa yaya ta hana babangida cin kifin bayan tace a tare ta dafa masu shi.
Wallahi ko anyi haka don ba,a fi watanni ba yaron nan yafara birkice min na rasa gane rayuwan shi gaba daya a gidan nan.
Shagon da suke fita gaba daya ma ya daina fita duk fadan Alhaji dole yasa mai ido ya bar shi don ba yadda za,a yi dashi.
To kinji ke mai cewa wai duk sharce ne na malaman tsubo kawai ko ku din ai baku tsira ba nan ta fada masu abin da su ma suke ciki a rayuwan su.
Haba gaskiya abin kan da ban mamaki inji maryam don cewa fa su Lawisa basu kai mutu. Komai ba amma kullun gidan nan sune da sabbin samari kai gaka zaune ko tsoho bai zuwa yace yana son mutum.
Amma gaskiya duk wace tai muna wanan abin inji Amira sai Allah ya saka muna wallahi ko.
Ai ko baki ce Allah zai saka maku don zai koma kan mai shi da yardan Allah.
Yanzu dai ga,wanan yace na kawo maku ku fara sha nan da,sati biyu zan koma na karbo maku sauran hadin insha Allahu.tana kokarin sance ledan dake a hannun ta.
Kuma yace da hannunki zakiba ko wani yaro yasha wanan rubutun, shikuma sadauki idan da hali yace nazo mashi da kashin shi akwai abinda zai yi dashi wanda zai sa ko warin kwaya bazai so ya sake ji ba a,rayuwan shi.
Cabdi aikuma shine babban magana wallahi don nasan ba zai yarda ba ya bani saboda shegen tauri kai ne dashi inji Maji.
Lalai nima nayi tunanen hakan tun a can amma dai yanzu yi kokari ba,shi wanan.
Ta kara fito da wani kulli yace da nonon akuya zaki hada ki bashi ya,shanye yace idan har abin yai aiki zakiga kwana biyu yana yawan barci ki kyale shi maganin ne yake aiki a kan shi.
Nan dai taba da harda wanda su Amira zasuyi wanka da hayaki dashi don makarun asirin da ke kan su harda shi gaiyar aikin.
Mai masa nagode nagode kwarai wallahi, ban ma,san kalar godiyan da zanyi maki ba ni wallahi.
Wai yanzu don Allah shi mutumin bai fadi wanda yai muna wanan irin aikin ba ne don mu sani.
Yafadi bai fadi ba yadai ce min mata biyu ne sai namiji guda kuma ba,atare suke aikin ba kowa tashi tafishe shi ne.
Yace shi bsi son tonon asiri bukatar shi dai aiki yayi kyau asamu biyan bukata don fadin zai kawo hadin hasumi.
Ikon Allah yanzun ni mai na tarewa mutane har na samu makiya daga cikin su haka..
Mai masa may nakd dashi a gidan nan daya tsone wa mutane ido dashi har za aimin haka wai ?
Nuna yaran mai masa tayi tace gasu kuwa abinda kika raina,shine ya dami wasu ai.
Wallahi Maji nafi zargin su mama da Umma don sune basu kaunan mu a gidan nan.
Kada kuyi zaton haka ya kasance basu bane din don zato zunubi ne koda ya zama gaskiya.
Kada azo ana zaton wuta a masaka,asmay shi a makera.
Hakane fa to amma gaskiya su sunfi nuna basu kaunan mu sam wallahi tun muna yara mun san da hakan.
Yanzun dai abar wanan zancen don koma waye mu barshi ga Allah shi zai saka muna.
Yanzu mai masa nawa zanba wanan bawan Allah ke nan don ni har ma na rude wallahi.
Dole ki rude ai don wanan magan ba karamar magana bace saboda yanzu a lokacin muke kana barci ana maka nasari a kai.
Nan dai suka dan taba huran lokaci tsakanin su tai masu sallama tabar su nan suna jimamay.
****** ********* ******
Da farko maganan bai so damuwan Maji ba amma da,dare yayi kasa barci tayi tana nazari akan irin zaman da take da abokan zaman ta a gidan.
Wanda dai ita taga babu ruwanta da,hassadan ko dayan su balle zurian su , bata taba tunanen wai ta aikatawa wa dan ko dayan su wani mugin abu ba koda a,baki ne.
Amma yau gashi ita an sakata gaba har yan yaran da ta haifa a gida ba,a barsu ba don hassada kawai.
Ita dake da yara uku kawsi kacal amma wai sun tsone idon masu bakwai tara da hudu.
Haba jama,a kishi haukane wai da har zaka salwantar da dan kishiyan ka kan bakar kishin da iyakar shi nan duniya sai kuma lahira inda,za,ai hisabi.
Lalai yanzu lokaci yayi da kowa zai kama taka tsantsan da dan abinda Allah yaba,shi don gujewa sherin shedanu mutane.
Gaskiya sai yanzu tasan tayi mugin sakaci akan yaran ta don ita ko goro bata taba basu ba da,sunan wai tsarin jiki.
Musan ma ma,shi sadauki wanda ya tashi tun yana yaro da shiga idon jama,a.
Don haka yake kamar dan larabawa ga kyau ga ilimi ga kunya gashi da miskilanci.
Bai shiga harkan kowa ba,agida ba har gari baki daya, bazata iya cewa ga,ainihin abokin shi na kurciya ba balle ma yanzu da ya koma hakan.
Tayi tayi ta san ko da wa yake hurda da har ya fara wanan shaye shayen amma ta rasa aini hin abokin shi.
Dan dama dama,ma,yaron malamin da,sukai karatu a gurin shi na islamiya ana ce dashi Manir shi manir hae yanzu yana zama da mahaifin shi yana koyawa yara karatu a kofan gidan su.
Don haka bata zargin Manir da wani harkan sha,shanci ko kadan sai ma jin dadin shi na aminin shi da take yi.
Don tasan ko banza zai dan dinga mashi nasiha akan sabon halin da ya dauko ma rayuwan shi.
Sai da dare ya shigo gidan har zuwa yanzu inka gan shi kamar natsatse yake sai dai gaskiya bai bari ba don bai jin zai iya barin sha gaskiya da,wuya.
Amma dai yanzu shan da yakeyi na,tsanaki ne a ganin shi yana wayo ne don kada a gane shi.
Abinda bai sani ba shine karfin adduan mahaifane ke tasiri a kan shi lokacin.
Don Alhaji yaba bada kudi ana mashi addua yanzu sosai sabanin da can da yake daukan abin da,wasa.
Ya fadawa wani amin shi a kasuwa irin halin da yaron na shi sadauki yake ciki.
Mutumin yai murmushi yace Alhaji ke nan kai kama yi arziki yaro daya ke wanan halin.
Ni wallahi har da yarana mata suka fada cikin wanan mugun rayuwan nayi nayi abin yafi karfina dole nasa wa sarautar Allah ido.
Kasan sai mutum ya,daga hammatan shi ake jin wari amma yanzu duk wanda kagani yana da matsala akan iyalin shi sai dai mutum ya rufe kawai.
Don abubuwane gasu nan ba iyaka da lokaci ya kawo muna,sai dai Allah ya kyauta kawai.
Akwai wani malamina zan kaika gurin shi onda abinda abinda zai iya maka sai ya taimaka muna dashi.
Don kasan kowa da irin abinda ya karbe shi mai yuyuwa ni banci nasaraba kai kaci.
Abubuwa da dama Alhaji keyi akan Sadauki amma ba wanda yasani a gidan har ita mahaifiyar yaron ma kanta batasan yanayi ba.
Don ita gani take ita kadai ce keda damuwa akan yaron kawai shi ai yana da,wasu.
Bata san cewa shima abin kamar yafi damun shi ba, don shi ke fita yana ganin duk gari kowa yasan da dan shi mashayi ne.
Yazama mutumin banza ke nan a idon mutanin gari ai.
Suna hanyar su dawowa ne, wani abokin shi ya tare shi hanya yana ce mai bayan sun gaisa.
Alhaji yaya akayine yaronnka ya samu abin arziki, amma kuma kukai sakaci da hakan.
Ban fahince kaba ai wani dan nawa ke nan kake nufi daga cikin su.
Yace U, F mana dan kwallon nan dake gidan ka ance an zo sayen shi yafita zuwa ghana buga kwallo amma baku yarda ba.
Kana nufin Umar Faruq ke nan ko sadauki muke kiran shi ai shifa shi.
Wallahi yaron ya iya kwallo sosai don hakane ma couch din su yai mashi hanyar fita amma wai baku yarda ba.
Sai abokin tafiyan Alhajin ke cewa kai amma kuwa Alhaji baku kyata ba da kuka hana shi zuwa ai wani hanyane na samu nan ma.
Abinda muke ganin yan kudu kawai keyin sa yau gashi ya kawo ga yaran mu.
Don Allah kubar yaron nan yaci gaba da,wasan shi kada ku lalata mashi hanyar samun shi.
Shiru Alhaji habu yayi don shi bai ma san da zancen ba a rayuwan shi don ba,wanda ya taba fada mai hakan.
Yace cikin mamaki gaskiya banda masaniya,akan wannan magan ni in ba yanzu ba din bai taba samuna da,wanan zancen ba gaskiya.
Amma zan bincika naji ko mahaifiyar shi ta san da zancen ita.
Gaskiya a bincika don kaga har team din farko sun shiga gasu sun dawo da abin arziki mai yawa wallahi.
Don Allah Alhaji kubar yaron nan ya tafi don akwai alheri so sai ga,wanan harkan don ba harkan banza bane gaskiya.
Ga yaron naka yana samun yabo sosai a gurin abokan shi dama mutanen gari don haka abarshi kawai yatafi ko zai zama alheri a nan.
Sunyi sallama da mutumin bayan sun kama hanya da abokin shine mutumin ke cewa kaga ikon Allah ko kai duk ka damu kanka gashi ashe mutane kallon mutumin kirki ma suke wa yaron.
****** ********* ******
Sadauki ya,gayar da Maji a cikin mutunci tare da tambayan ta lafiyan ta?
Maji tabashi amsa a takaice da da sauki, Alhamdullahi dama ai kaine kaso kashe ni da raina.
Murmushi kawai yayi irin nashi can saman fuska yace ayi hakkuri don Allah, insha Allahu na daina ai.
Suna nan suna dan hira shi dai yana zaune baice komai ba kuma bai ma sauraren su hankalin shi na daga maganan Maji.
Ke Amira dauko min ledan nan na,saman TV stand kikawo min ba mussu Amira ta mike ta dauko ledan take cewa kawo min ludayi a kitchen.
Bayan an kawo ludayin ta bude roban maganin ta,zuba tana mai addua a bakinta cewa Allah yasa wanan maganin yai muna aiki a jikin mu baki daya.
Babana zo nan tace tana zaune a saman salayan ta bai tsaya ba ya mike zuwa gurin uwar tashi.
Mika mashi ludayin da maganin ke a ciki tayi tana fadin duko kasha duk da bai so bai musa mata ba ya karba ya,sha ta shayar dashi da hannun ta kamar yadda aka umurce ta da tayi.
Haka taiwa Amira da maryam sai ga Bintu tafito daga cikin daki tace yaki ya ta zo ke maki karba kinji.
Bintu ta karaso kamar yadda suka sha haka itama tasha maganin daga hannun maji
Inda maji ta,shanye sauran maganin gabadayan shi da ludayin.
Sai kuma ta hada wani nasha tace a mikawa sadauki wanda ke zaune ya kurawa Tv ido kamar yana kallo.
Saida ta tabbatar yasha komai kamar yadda akace tace dauko mashi abincin shi kinji.
Ana kawowa bai tsaya ba ya karba tare da mikewa maji tana fadin ina kuma zaka tafine wai ?
ya ce dakin shi zai tafi yaci tace tau kadai ci abinci don naga kana,wani rama can.
Sai da safe ne taje gaida mijin su yake ce mata ta dagata yana da magana da ita, haka yasa Hajiya Kubura tafita daga dakin .
Yace dagata ai duk magan ta,shafe ku don ka sadauki ne zancen da zamuyi da ita.
May kuma dan nawa yayi inji hjy kubura take tambayan shi da sauri.
Baiyi komai ba wani magan ce dai aka tare ni da shi akan shi wai zancen kwallan ball din kafan da yakeyi.
Oho Allah yasa alheri ce ta samay mu akan maganan t
Tau kusan hakane dai don wai ashe sun bukace shi da yatafi ya buga masu ball a kasar ghana.
Amma sai yace wai gida an hana,shi zuwa shine nace ni dai ban sa zancen ba amma kila ita uwar shi ta san da zancen?
Eh na sani tabashi amsa amma kuma na fada mai hakan baiyoyuwa.
Kada ma ya kara min zancen shine yake ta faman fushi a kwanaki ai har yaje yai wanan aika aikan.
Kai amma hajiya maijidda baki kyauta ba gaskiya.
Ai wanan abin alfahari ga kowan mu nan ace an samu haziki daga gidan mu .
Amma may yasa ni ba a shawarce ni ba kika yanke hukunci ke kadai, maji tace Alhaji naga baka ra,ayin wanan kwallon da yakeyi ne.
Sannan kuma yana nan ma a,tare da mu yaya aka kare ballw yatafi wata uwar duniya can, inda babu mai kwaba mashi.
Haba kwabo fa daga Allah yake mu itakarmu dashi addua ne a duk inda yake, amma ai wanan wani babban abin alfaharine idan Allah yasa mashi hannu inji hajiya kubura.
Nikan gaskiya sai naga kamar hakan zai kara jefashi cikin mugun halin da yasa kan shi a cikine.
Alhaji yace yanzun dai idan ya shigo kafin na fita kice ina magana dashi don inji yaya zancen yake ne.
Majibata,dade da barin gurin maigidan na suba sai ga sadauki ya,shigo don yau sammako zaiyi ya fita saboda yana process kan fita service din shi.
Bayan sun gaisa ne maji take cewa yaya akayi Alhaji yasan zancen zuwa kwallon da kai min bayan na fada maka cewa ban ra,ayin hakan tun farko.
Cikin muryan ahi ta,rowa yace wallahi Maji ban sani ba don bamuyi maganan da kowa ba a gidan nan.
Ta ka godewa Allah da uwarka hajiya kubura don naga ta dauki abin haikan ita akan dole sai anbarka.
Na ko san tunda tai magana Alhaji yarda zaiyi ba fashi amma ya,dai ce idan ka,shigo kasamay shi yana nemanka wai.
Baba ke nema na maji tace eh ba,wanj abu bane wai yana,son jin kan maganan daga bakin ka ne.
Sadauki bai tsaya ba ya mike don zuwa kiran mahaifin shi da yake mashi,
Yana kaiwa kofa yaji muryan bakuwar yarinyar nan cikjn yar siririyar murya tana fadin Allah yasa baba ya,yarda yatafi wallahi.
Juyowa yayi ya maka mata harara yafice daga dakin yarinya karama,sai bakin iyayi ina,ruwan ta dani ne
Yarinyar nan bata,san halina,ba,sai watarana na gwada mata,zata gane kuren ta gidan nan.
Yafita yana magana,shi kadai a ran shi yana fita hajiya kubura tana kulle kofan part din ta zata fita ya ke cew mummy ina kwana.
A,a sanda sadauki sabda gagare ashe ana ganinka ni yaushe ma rabo dana saka a idona ne wai.
Yai yar murmushin shi yace ban zama,sosai ne yanzu shi yasa ba,a gani na,
Tace tau akula dai don Allah a daina rashin ji kaji Umar Allah ya tsare muna ku Allah kuma yai maka,albarka.
Yace amin yabarta taba,ci gaba da,rufe kofan dakin ta shi dai matar batai mashi komai ba amma kuma ya kasa sakin jiki da ita,
Dan dama,ma,yau har ya tsaya sundan yi dogon magana dashi ko shi don irin halarcin da ta nuna mashi ne ranan yasa yadan sake mata yau.
Da Umma ya hadu tafito tana sauri don ta makara kauce mata yai nufin yi don kada,su hade amma sai cewa tayi wallahi haukan yaro yakawo gareni da,uwar yaro zanyi a gidan nan.
Bai ko gaisheta ba ya,wuce abinshi gurin mahaifin nasu don amsa kiran da yake mashi.
Ya samu yana gap da fita ya,shigo falon da,sallaman shi suka gaisa yake cewa hauwa ta fada maka ke nan ina neman ka ko.
Don nasan inbashiba bazaka zo mu gaisaba ai anya Umar kana kyautawa kanka kuwa?
Baba kayi hskkuri lokacin da nake fitowa sai na samu kafita ko kuma lokacin da zan fita baka fito ba tukun.
Ba sanan ba idan maka gyara don kanka, yaya zancen dana ji na batun fita kwallon ku yake ne?
Don ban son abinda zai je ya kara saka sha shan ci kuma a bayan idon mu, anan ma muna nan kafara haka inaga babu kowan mu.
Baba insha Allahu ba,zanyi wani abinda zai bata maku rai ba ko martaban gidan mu,
Hmm daga baya ke nan amma sadauki yaushe kuma,ai kayi waka an amsa maka ko.
Don tunda harka bari kishiyoyin uwarka suka fahinci halin da kake ciki ai abu ya baci ko saidai Allah ya kyauta kawai.
Nan dai sadauki cikin dukar da kai yai ma mahaifin shi bayanin komai yadda abinyake ya kuma fahince shi.
Ga mamaki shi sai yaji Uban na cewa Allah yasa haka yafi zama maka alheri gare ka da ma muma iyayyenka.
Ya amsa a sanyaye da Amin baba insha,Allahu alheri ne ma hakan da yardan Allah.
Kadaikula don Allah ka kula,da rayuwan ka don mu shine adduan mu a gareka ko yaushe Allah yasa ayi a cikin sa,a Allah ya tsare ya kare.
Yakara amsawa da fadi a sanyaye cikin farin ciki da jin dadi nagode baba yace tare da mikewa yabar dakin cikin farin ciki.
Ya shiga dakin mahaifiyar shi da murna yana fada mata duk yadda sukayi da uban nashi.
Yace maji don Allah ke ma ki samin albarka don in baki yarda ba gaskiya babu inda zan tafi ni kan.
Sadauki Allah yai maka,albarka Allah yasa a,tafi a sa,a adawo lafiya cikin nasara.
Har kasa ya kai yana fadin Maji nagode nagode maku dake da baba nagode ma Allah baiko tsaya cin abinci ba yafita daga dakin zuwa club din su ya,sheda masu yardan mahaifan shi akan tafiyan shi.
Maji tabi bayan shi cikin tausaya mashi irin na da da mahaifi, tasan kwanaki akan bakin cikin rashin yardan su yasa shi zuwa ya sha manyan kwayoyi yazo masu gid a buge
Yau tasan cewa duk abinda yaro ke ra,ayin yi indai babu illa acikin sa tauka kyale shi yayi sai dai kai naka kabishi da,adduan da fatan alheri shine mafita.
Amma idan ka hana sai suga ba,a kaunar su bari kawsi su sha abin kawar da hankalin su ko zasu samu relief akan maganan.

Ganin yanzu bata samun kasuwar sana,anta irin farko da Mud al,majiri ke mata talla yasa hankalinta ya tashi sosai.
Saboda a yanzu ta saba da rike yan canji a hannun ta tana kadawa a bankinta na gida.
Sai gashi yanzu da kyata zata hada naira dari daya ta kada a ciki ga wuni.
Hakan yasa duk hankalin maria ya yai matukar tashi ga fridge yai ta haukan kankara shi kadai amma babu kasuwan saye kamar farko.
Gurin mahaifiyarta taje da zanjen, budar bakin uwar tace shi,Aliyu ba zai iya dan fita maki dashi ba koda a cikin uguwar ku ne yana yawata maki dashi.
Da sauri tace ,a,a,a Umma wallahi mahaifin su bai yarda sam idan yaji nasan ba karamin tashi hankali zamuyi va dashi.
Ashe ke wawiya ce maria ke zaki bari yaji ne cewa yana talla.
Mutumin dan in ya sa kafa yafita tun safe dai yamma yake dawowa, lokacin ai har kunci kasuwan ku ko kungama.
Lalai Umma haka za,ayi nagode da wanan shawaran insha Allahu gobe zan fara aza mashi talla kuwa.
Kafinta shigo gida,saida ta tsaya ta sayo ma yaron farin roban ruwa dan madaidaici irin wanda zai iya dauka.
Washegari tun safe ta tsaya shininiki bata shirya yaran zuwa makaranta ba yadda ta saba tashi da wuri ta shirya su su karya su fita tare da mahaufin su, ya aje su islamiya sai ya,wuce gurin sana,ar shi.
Da maigidan nata yai magana sai cewa tayi yau bata jindadin jikin tane shiyasa.
Shi dai ya shirya yafita abin shi amma yana mata mitar tayi ta shirya yaran su tafi islamiya kafin su makara.
Daga wanan ranan ta fara,azawa yaron talla duk da Aliyu kara mine sai da yai kuka yana fadin mama makaranta fa kada a wuce ni gurin bita fa.
Amma sai hawan shi tayi da fada cewa indan baije mata tallaba wa yake son ta azawa.
Ya dai ga duk almajirin da ta kira sai yace malam ya hana su yin talla yanzu.
Kuma gashi yasan da dan kudin take samu tayi masu dan lalurori a gidan wa yake son ta azawa talla.
Yaron haka ya dauka ranshi bai so ba ya tafi tallan ruwan yana turo baki harda kwalla a idon shi.
Da yake bai iya tallan ba shiga farko da kyat ya samu yayi dan ciniki yadawo da saura gida duk yayi zafi wasu ma duk sun yoye a roba.
Nan maria ta hau yaron da masifa da fitina har tana kirarin idan bai mayar da hankali ba yai mata, bazata sayi mashi komai ba da kudin ta.
Dole yaron ya dan kara dagewa ya mayar da hankali gurin tallan duk da ba,wani girma yayi sosai ba.
Ita uwar ganin yaron ya mayar da hankalin shi yanzu sai dadi take ji don har tana wa makwabciyar ta da ta rike almajirinta na farko habaici wai in an maka bakin ciki sai ka fashe haushi da naka tunda Allah bai hana maka,ba.
Hakana yaron tin bai saba ba yana fita da kuka har yazo ya sake jikin shi yana shiga mutane talla.
Ito ba abin da ya shille ta sai jin dadi take yi yana kawo mata kudi tana kadawa a bankin ta na gida kawai.
****** ********* ******
Raiha tun bata kula wayan Michael dake damun ta, da kiran akai akai har tazo tana daukan wayan shi.
Da farko tana ganin kamar hada kai sukayi da Nasir a kanta si da ga baya ta fahinci bada sanin Nasir din yake kiran ta ba.
Don yakan ce kada tai serving din nomban shi yadda Nasir zai fahinci cewa shine.
Don baya son Nasir yasan shine ya rusa mashi plain din shi a kanta.
Da lalashi da komai yasamu ta yarda ta tra mai da account number din da yasa ta ta,bude.
Tashin farko kudin da ya turo mata saida hankalin ta ya daga don dubu dari biyu ya turo mata ga account din ta.
Ta rasa yadda zata boye wanan kudin don haka ta fadawa mahaifiyan ta amma bata fada masu cewa ba musulmi bane shi,
Ta daice a waya suka hadu dashi yace a lagos yake aiki hankalin mahaifinta ya tashi amma da sukai waya da Michael yace ba komai yadai bata ne kyauta don ya fahinci ita diyar tallakawa ne.
Abinka ga kudi masu shiga rai sai mahaifin nata bai tsaya wani dogo n bincike ba kawai aka shiga harka dasu harda tayar da katangangidan shi daya zube badi guda.
Bai san cewa katanga mai muhinman ci agare shine ya mugun zubewa ba kan kudin.
Shiko Nasir ganin Raiha bazata samu ba yasa shi canza akalar sa zuwa gurin cigiyar wata sabuwar kamu da,zatayi daidai dashi.
Sai dai Raiha ta riga ta rusa mashi plain din shi na,wanan shekaran kamar yadda ya tsara al,amarin nashi.
Wata yammaci yafito ne daga ma,aikatar su sai ya hangi ra yarinya tsaye a,bakin titi daganin shigarta yar hannun ce don ta dan waye a fuska.
Daidai inda take tsaye yai farkin din motar shi inda ya bude yafito har inda take a tsaye.
Sun gaisa zakace ko yasan ta a bayane yake ce mata daga ina take haka ta tsaya rana yana bugun ta duk haduwan ta.
Amsan da ta bashi yass shi gane cewa tana da,wayo don sai yayi da gaske idan har tafiyan su zaiyi daidai.
Tun daga wanan ranan yafara dawai niya da yarinyar yana kashe mata masu gidan rana yadda ya kamata.
Yarinyar irin wanda idon su ya riga da ya bude da kudi da maza ne sosai ya sa shi fara ganin indan baiyi da gaske ba ba zai samu yadda yake so ba.
Tashin farko ya taya mata zuwa lagos kamar yadda yake a duk bayan wata uku don yin assignment din company su.
Ba wahala ta yarda zata bishi su tafi amma sai ya bata wasu kudin da zata sai wasu abubuwan bukatun ta da zata da su.
Kusan tare dashi suka tafi tasayo abubuwan da take so wa ranta a kasu da wani shago.
Daga baya suka shirya zuwa lagos kamar yadda ya bukaci suyi tare dashi.
Yaso yai mata irin yadda ya,saba yiwa mata don ya horar dasu amma sai ya fahinci kamar matafishi sanin bariki sosai.
Ya samu Michael yana fada mashi irin matsalar da ya samu akan sabuwar kamun da yayi yanzu.
Nan ya bashi shawara akan yabi yarinyar a sannu don mata yanzu suma sun yi wayo sosai.
Haka suka dawo bai samu yadda yake son bata training ba don in ya tura ta turai kada a samu matsala sosai da ita.
Bayan sun bar Michael ne ya bugo waya yana fadawa Raiha sabuwar yarinyar da abokin shi ya samu kuma yana son ya aiwatar da nufin shi a kan ta.
Raiha taji a ranta yarinyar ta bata tausayi don haka dole ne ta taimakawa ko wacece.
Sai bayan sun dawo ne ta samu wani abokin shaye shayen ta bashi kudi don yanzun bata da matsalar su ta ce yai mata bincike akan sabuwar yarinyar da Nasir yake target ga fitawar waje wurin safarar matan da yake a boye.
****** ********* ******
Tsaye ta hango wani guy a kofan gidan su kafar shi daya a cikin mota daya kuma ya daga waje ga waya a hannun shi.
Ganin Amira da,zata shigo gidan yasa shi saurin samun ta ya tsare ta yana fadin, barka dai.
Don Allah idan gidan nan zaki shiga ina son ki sallamo min Nafisat ne, wani kallo Amira tai mashi kamar zatai magana amma sai tace mashi kawai taji.
Tana shiga gida ta fara haduwa da Bintu wacce ta sheko ta rugumay ta cikin so da kauna zakace yar uwarta ce tajini tana cewa Anty Amira sannu da dawowa ya makarata ya hanya tare da karbar wa Amira school bag din da ke rataye a hannun ta zuwa cikin dakin su.
Mama Asiya suna waje da yaran ta sai tsaki suka ja suna fadin sai kace diyar wata,
Harda zuwa don kisisinar yarinyar nan yar kauye zuwa yi mata sanni da zuwa.
Wai ma mama may wanan yarinyar takeyi a gidan nan ne har yanzu, wallahi ban son ganin ta shegiya gata yar kauye amma ta iya ba mutun haushi da takaici gata aiki baya isan ta.
Uwarta ce ina ga kamar a nan take zaune yanzu tare da su kin san su da shegen kwashe, kwashen tsiya ai da son asani komai basu aje ba.
Dayar yar mama dake yankan akaifa tace may zas
u bata banda wahala suma ta kan su sukeyi ai.
Ni Alhaji ma yafi bani mamaki don da watace cikin mu ta ajeta da yanzu ya fara fada za,a kawo mashi bakuwa a gida cikin yaran shi ta bata mashi tarbiyan ta.
Can kuma cikin daki da Bintu ta shiga da murnan ta tana fadin Mama Anty ta dawo.
To yar gidan Anty sai kace wace ta dawo daga wani guri haka kina ta wani farin ciki dake.
Mama ai duk wanda yafita ta dawo lafiya ai masa barka da arziki inji Bintu, kai Fatima ke kan halin ki sai ke wallahi.
Amma a ran Maji dadi taji irin yadda taga Bintu tana matukar son diyan ta wanda a da can baya ba ruwan su da juna a dakin kowa kan shi daban basu damu da junan su ba.
Amma zuwan Bintu cikin su yasa koda maryam bata kusa zata bita tana fara,a tana fafin Anty maryan antyn mu ta dawo.dole ta fito
Idan kuma maryam ce ta dawo sai ta nemo Amira tana fada mata cikin jin dadi har takai suna barin abinda sukeyi suzo su tari junan su cikin nuna jin dadin su.
Yau ma hakan ne don har baya taje tana fadawa maryam dawowan Amira inda maryam tazo da murna tana wa yar uwar ta sannu da zuwa Anty don ita bata fita ba.
Nan suka zauna a falo Amira bayan ta cire kayan jikin ta tafito Bintu ta aje mata abincin da ruwa tafara ci suna hira a tsakanin su.
Tana fadin kai yau wallahi akwai rana ga zafi duk dama na matsu na dawo na cire wanan kayan nasamu ruwan sanyi nasha.
Maji tace aiko mu dake gida wanan zafin ya ishe mutun Allah dai yai muna Rahama kawai.
Yaran suka amsa da Ameen ya Allah.
Amma kila an kusa fara ruwan sama ne don zafin yau yai yawa mama Bintu ke fadi.
Sai suka sa dariya gaba dayan su maryam tana kokarin cewa ke Bintu ai haka garin nan yake da shegen zafi walla,,,,
Sai gani sukayi an daga labulen dakin kawai ashe Nafisa ce gaba daya suka juya don ganin waye haka bako sallama zai fado masu kai tsaye.
Tau yar bakin ciki ashe anzo nemana shine don bakin ciki irin naku na gado kika ki fada min, to Allah bata ku ba.
Wai dawa kike yi ne inji Amira take tambayan ta a cikin daga murya.
Ke mana yar bakin ciki mai shegen kishin tsiya kamar na uwarta ni bani na hana azo a soki ba balle ki gwada bin bakin ciki karara a fili.
Nafisa niba sa,arki bace balle don kin kwaso dan rashin mutunci irin ki yace wai ni na kiri mashi ke don rainin wayo.
Ji yar rainin hankali oho sai yanzu ai na kara gane bakin cikin ki a fili wallahi don naga aikin hassada yau,
To wallahi a haka zaku kare tanbade lalace sai bakin kitifi ku da uwar ku a daki dangin yan caca da shaye shaye.
Kafin tace wani abu ba,wanda ya san Maryam har takai inda take tako shako wuyanta ji kake tas,tas, mari biyu masu lafiya ta kwashe ta dasu.
Umma fito wallahi gasu Amira can sun tarar wa Anty Nafisa da duka inji karamar kaunarta take fadawa uwarsu.
Haba gaba daya sukayo part din Maji hankali a tashe daidai duk su kuma sunyo waje inda Nafisa take tsaye da maryam.
Maji tana fadin ke Inna Isa kyale ta haka na barta taitayi ita kadai.
Daga nesa Umma ke fadin wallahi idan kuka kara dukan ta yau sai dai duk akai mu asibiti gidan nan .
Kaji man marasa mutunci haukan ashe ba,a kan sadauki kawai ya tsaya du, dukan ku kenan ya shafa.
Ke Nafisa may yakawo ki gurin wa yan nan matsiya ta ki jawa kanki tsiyan su irin ta gado ya shafe ki ke ma.
Nan take fadawa uwarta duk abinda yafaru uwar take cewa barsu tsiyane da talauci yai masu katutu a kai shine bakin cikin su gare ki.
Hassada ko sai dai su mutu dashi a gidan nan don babu mai kama kafar mu don mun riga mun masu nisa ko.
A haka zasu kare daki tsiya tsiya kamar madallacin malam ba komai sai tarin raggaduda kawai ciki.
Saurayi kuma sai sun ga har dan gidan gwauna a gidan nan gurin ku.
Sai lokacin sadauki dake tsaye daga kofa shigowa gidan tun farkon fitina yana tsaye yana sauraren su.
Ran shi yai matukar baci irin yadda yake jin ana zagin mahaifiyar shi da yan uwan shi a kan talauci.
Su madai su Amira duk da Maji tana masu fada bai sa sun fasa mayar masu da amsan zagin da suke masu ba don harda mama Asiya ta shige tsagal cikin fitinan tana cewa ai wanan mutanen kune baku san sherin su ba dama da kowa bakin ciki sukeyi a gidan nan.
Ke Amira shige daga ciki kada na kara jin muryan kowan ku yai tsaye yana nuna masu kofan dakin su da hannun shi.
Ranshi a bace idanuwan shi sun kada saura kiris ya fashe irin yadda ya hasala.
Yaran suka bi bayan uwar su da tafara shiga ciki ranta a bace yayin da ya juya inda taron mutanen gidan suke tsaye ya watsa masu jajayen idanuwan shi akan su.
Zo mutafi kinji don wanan mahaukacin yanzu yana iya muna haukan shi akai.
Gaba daya suka watse zuwa shiyan su a can suka yada zangon su yana jin sunci gaba da fitinar su ya shiga dakin mahaifiyar tasu.
Tsawa yadaka wa su Amira akan suyi shiru hakana bai son hayaniya ya isa.
To amma yaya don kawai an raina mu shine kowa ya kwaso sharan shi a kan mu zai yaba tsiyar shi.
Nace ya isa haka ya fadi cikin tsawa hakan yasa gaba daya sukai shiru da maganan.
Nan yakai zaune saman dayan kujeran da ya saba zama idan yashigo gidan, maimakon ya zauna yadda ya saba sai kawai yayi kwance tare da dora hannun shi daya saman kan shi daya na saman kijin shi.
Ya kai wasu mintina a hakan gaba daya dakin ba wanda yai magana daga cikin su.
Bintu ce ta mike don shigewa don dai ita gaskiya zaman ta a dakin duk a tsorace take dashi.
Don gani take cewa kiris ya rage ya kamasu da dukan tsiya a dakin.
Takai gaf da kofan zata shiga taji yana cewa "Ke kawo min abinci na na fita.
Da,sauri ta juya zuwa kitchen inda ta hado mashi abinci kamar yadda ya saba hada mashi wanan karon har da spoon din da yace dashi yake ci.
Bai masu magana ba ya mike zaune kamar zai dauki abinci sai kuma ya bude a,nan falon ya fara ci a hankali.
Maji ki yace daidai zaikai spoon din shi a baki batare da ya kalleta ba kiwa yaran nan magana su daina shiga harkan mutanen gidan nan ana zagin ki a banza.
Don bazan iya hakkurin wanan mugun zagin da ake maki ba a gidan nan haka.
Talauci dai ba mune muka azawa kan mu ba Allah ne yayi mu a haka ba yin kan mu bane ai.
Amma mutanen nan da,sun tashi da,wanan zasu zage ki ke da yaran ki, don tun ina karami nake jin wanan kalman daga bakin mama da Umma a gidan nan.
Sai kuma ni da na ja maki wanan gorin na dan shaye shaye da kuma cacan da suka ce ina yi wai.
To amma ba komai Allah na gani shida ya dora min wanan lalurar shine zai yaya min shi dakan shi aduk lokaci da yaso.
Ke kuma Amira na roke ki da kuyi hakkuri da kowa a gidan nan don rayuwan mahaifiyar mu kin dai san ita ba mai son fitina bace a ranta.
Haka ke maryan wanan zuciyar taki matsayinki na mace ki rage shi don gidan wani zaki tafi.
Inda Bintu take zaune ya kalla tare da,watsa mata harara yace ke kuma da sauri Bintu ta dukar da kanta a kasa tare da mannewa jikin kujeran da Maji take zaune a kai.
Yace kada ki yarda naji ance kinjawa uwar mu bacin rai a kanki a gidan nan zaki hadu dani.
Sai lokacin Maji da takaici ya isa tai magana tace kai ku tsaya wasu,wasun ku amma kada ka hada da yar mutane da bataji batagani ba da kowa a gidan nan iyakarta imu a shiyan nan ba ruwan ta da kowa a gidan nan.
Inda na tsayar da ita anan take bata taba saka kanta ga harkan kowa ba cikin gidan nan.
Don haka tafita a ido ka kada kasa min "ya a cikin zancen ku wallahi kaji na fada maka gaskiya.
Mikewa yayi ya ce kun daiji abinda na fada maku kowa ta kiyayyeni akan hakan.
Barin dakin yayi kamar wanda aka tsakara baiko juya ba yafice abinshi har lokacin yana jin hargowan Umma daga part din su.
Zancen bai kare ba don da maigidan yadawo an samay shi da zancen yana ji yace a kira mashi su Amira da maryam tun kan hajiya Umma tafita daga gurin shi har Nafisa din.
Bayan kowar su tashigo tare da uwarta harda mama Asiya da yaranta yan mata, yana cin abincin shi hankali kwance ga hajiya kubura dake girki daga gefen shi suna zuba soyayyan su a cikin style.
Alhaji kaifa kace a kiramu kuma kabar mu a zaune kana harkan gaban ka inji mama Asiya da kishi ya kumay a lokacin na irin yadda yakeyi da mummy.
Mummy tace ke hjy Asiya ko so kike kuma yabar cin abincin ya tsaya shirmen kishin ku na kullun da baku san angirma ba har yara sun fara irin shi.
Kada ki fara ki fada min maganan banza wallahi yanzu a jimu a gidan nan don ke baki da kunya kowa so kike yabi ki kamar yadda kika mayar dashi a gurin ki.
Alhaji wanda yagama wanke hannun shi da hjy kubura ke zuba mashi ruwa yace ta mayar dawa wai ni ko wa ?
Shiru tayi don tasan idan ta tanka yanzu zai iya watse ta a gaban kowa babu ruwan shi da yara na gurin.
Gurin Amira ya juya yana cewa mamana yanzu Umman ku ke fada min wai kun taru kunwa Nafisa duka yau a gidan.
Sai kuma ya juya gurin Maji yana fadin ina bakuwar yar ki ita bata zo bane don nasan ba,a dukan Nafisa bata sa hannun ta ba.
Nafisa tai but tace wallahi danaci uban ta ko murmushi yayi tare da duban Umma yace kin dai ji tarbiyan ki ko ?
Yace wa yar mama Asiya karama hauwa kira min yarinyar dake dakin maijidda tazo da sauri yarinyar ta mike zuwa kiran Bintu.
Ta na shiga bako sallama Bintu da ke zaune hankali a tashe ta kurawa tv ido sai dai hankalin ta ba,a kallon yake ba sai ji tayi ance ke yar kauye baba na kiran ki.
Tare da watsa mata harara tana yatsune fuska tare da bin dakin da kallon wulakanci ta juya da sauri bintu ta jawo hijjab din ta dake gefe har kasa tasaka.
Tare da bin bayan yarinyar don bata masan falon baban ba duk zaman ta gidan da tayi ba ruwan ta da sanin komai.
Saida tajawo kofan dakin Maji da zata fito tasaka key tabar dakin da key din a hannun ta.
Inda taga hauwa ta shiga nan ta shiga itama tare da sallama dauke a bakin ta.
Maji da hjy kubura sai Alhajin ne suka karba mata sallaman ta da tayi tare da samun guri ta tsugun na ta sunkuyar da kanta kasa tana fadin.
Ina wuni Baba, cikin lada bi tare da sunkuyar da kanta a kasa, yace tare da nuna ta da hannu kun gani,
Sannan ya karba mata gaisuwan nata yace ku diba ke Asiya da kika samay ni kan maijjidda ta dauko bakuwar yarinya takawo min gida.
Kinga abinda tabi ta jawo ta a jikin ta tarbiya natsuwa da sanin ya kamata ga yar kauyen yar makwabtan da kika ce.
Hajiya kubura dake gefd tace kai Allah dai ya sawaka idan kuma anyi magana ace wai wani ke hassada.
Ke kubura wai may kike so ma dashi ne ki fada min don kin san daidai nake da ke wallahi.
Ai kaji maganan ke nan yanzu ku dakata da wanan bashi nakiraku yi ba anan ina son nasan may yakai har ke Amira kuka taru kuka daki Nafisa yau a gidan nan.
Anyi magana kuma uwar ku ta daure maku harda ita ta shiga zancen, ana haka kuma mahaukacin wanku shima ya shigo ya saya ya zama nashi.
Nafisa ta tare zancen dacewa baba bakin cikine fa kawai don sunga ana zuwa gurina su ba,a zuwa kiran su kamar sauran yan mata.
Alhaji yace a gidan har ake haka banda labari Nafisat ?
Allah ya kyauta kawai yace tare da girgiza kan shi cikin takaici yana kada kafan shi irin na magidantan da abu ya daurewa kai.
Yace ke tare da kallon inda Bintu take zaune yace mayye sunan ki ne ma ?
Tace a hankali Bintu Baba, yai yar murmushin manya yace Fatima bintu ke nan ko?
Eh Baba ta bashi amsa yace ki fada min abinda kika sani akan fadan da akayi a gidan nan yau.
Shiru Bintu tayi na dan lokaci kamar ba zatai magana ba sai kuma can tace.
Baba muna daki bayan anty Amira ta shigo gida nan tafara bashi labarin abinda ta sani da irin kalamin da kowa ya fadi har marin da Maryam taiwa Nafisat din.
Amma maryam wallahi kin kyauta min inji hjy Kubuta tare da kallon gurin da maryam take zaune.
Eh zaki fadi haka mana tunda ba yarki akaiwa hakan ba a gidan.
Hjy Umma ce uwargidan su mahaifiyar Nafisa ta ke fadin haka din cikin bacin rai.
Batare da Alhaji ya kalli gurin da take ba yace kubura ban son na kara jin bakin ki a zancen nan.
Daga haka yai shiru bai kara cewa komai ba kuma again, ya juya gurin Umma yace to kinji ke maimuna zagin uwarsu tayi har dakin ta kuma tana zaune babu kunya don kawai an bata mata rai akan saurayin ta da yazo kiranta ba,a fada mata ba.
Alhaji kada ka juya zancen nan fa dukan min ya akayi kuma shi nazo fada maka din ka dauki mataki a kai.
Yace wani mataki zan dauka idan kece su Amira suka shiga gidan kike sukai maki haka a gaban ki wani mataki yaran ki dake gurin zasu daukan masu ?.
Shiru Umma tayi yace ba amsa ke nan sunyi daidai dai din ke nan ko ?
Tace yanzu mai kake son nace tunda na fahinci ka daure masu gindi akan abinda sukayi sunyi daidai.
Yace kin taba gani mai kai takaka yayi nasara gurin maida magana balle harda cin mutuncin uwa a ciki.
Ai ko ke ne suka kawo wa takaka akai masu hakan iya matakin da,zan iya dauka ke nan a kan su kinji na fada maki.
Ke kuma Nafisa wani yaro ne yake zuwa gurin ki gidan nan ban sani ba har kike iya tsayawa kiwa yan uwanki cin muntunci akan shi don ya aiko kiranki ba,a fada maki ba ranki ya baci kibi yarki har daki kina zagin ta don samun guri.
Shiru Amira tayi tare da dukar da kanta cikin tsawa ya daka mata tsawa yana fadin badake nake ba nace dan gidan uban waye ke zuwa gurin ki gidan nan har kofan gida na ?
Sai ga Nafisa tana hawaye don daga ita har uwarta basu zaci abin zai juye masu haka ba a lokaci guda.
Yace tunda aure kike so ba karatu ba sai ki turo min yaron yazo ai maganan aure dashi.
Ya juya gurin hajiya Umma yace maimuna yanzun saboda Allah kin san yarinyar nan tana tara min samari a kofan gida haka shine baki fada min ba saboda Allah da girmanki ?
Idan da da dan wani dakin ne yake haka dafa a gurin ki zan fara jin wanan labarin.
Yanzun dai nafahinci ka juye maganan ya zama laifi akan mu, shike nan nida diyana bamu da shakat kan yan mayen diyanka a gidan nan.
Duk abinda sukayi shine daidai mu bamuyi daidai ba indai duk wa yan nan marasa mutincin yaran Hauwa ne ka daurewa gidin ai suje suyi tayi.
Ba sabon al,amari bane gasu nan daga dan maye sai yan iska data tara muna a gida.
Ta mike fuuu, ta fita daga dakin inda shima yabi ta da kallon takaici mama Asiya ma mikewa tayi tana fita tana fadin babu dai adalci yanzu a gidan nan.
A dakin mutun kuma ace wai shine bai da gaskiya don samun guri da daurin gindi kawai.
Ya juya inda yaran suke ya kara masu fada akan baya son ya kara jin fitina daga gare su ko ya batawa mai shi rai suka mike suka mike suka bi bayan uwayen su rai a bace su ma.
Suna ganin ba ai sharian gaskiya ba a gurin don sune da gaskiya amma mahaifin su ya danne masu gaskiyan.
Bintu ma ganin yaran sun mike yasa ta mikewa tabi bayan su amma sai taji muryan Baba yana cewa ke Fatima sai ta koma ta tsuguna don taji may zai ce mata din.
Yace ban son naji ance kin saka kanki a harkan cikin gidan nan kamar yadda ban taba samun labarin banza ba a kanki fon haka ki kiyayye kin ji .
Ta amsa da to Baba nagode ta mike tabar dakin duk tsoro ya cika mata zuciyar ta ta samu su Amira suna jiran ta takawo masu key din kofan su data rufe masu.
Hauwa kici gaba da hakkuri don ance dan kuka mai jawa uwarshi jifa yau duk yaran ki bugu daya ake masu akan danki daya daya samu matsala,
Don haka saikin toshe kunnuwan ki don babba da yaro dashi zai zage ku duk wanda ya tashi a magana gudu zai fake ya harbe ki dashi.
Sai kuma ya jijiga kan shi a cikin takaici da jin zafin sadauki a ran shi yace Allah ya kauyata.
Sai lokacin hjy kubura tai magana tace rashin dai tunane ne ga mutane ai wanan matsalar ta shafi kowa a gidan nan don ba nata bane ita kadai.
Amma hakkuri da addua bai bar komai ba Allah ya sauwaka ya kiyayye gaba kawai za,ace.
Maji ta mike tare da cewa nagode Alhaji ranta babu dadi yabita da kallon tausayi kawai.
Har takai kofa hjy kubura tace gobe dai ba aiki don Allah ki ara min yarki ta tayani gyaran daki na.
Ta juyo tana cewa wai Fatima Alla ya kai gobe ai ita yaro ba kiuya ne bata jin nauyin jikin ta ko kadan.
A daki ta samu su Amira suna dariya Bintu wai ta rufe kofa da zata, fita daga dakin.
Tace ba dole ba don ni abin wallahi yanzu tsoro yake bani ma mutane haka ba tsoron Allah.
****** ********* ******
Sadauki yana fita jin shi yake kamar yana taka kaya don bacin rai, duk wanda ya yanzu ya tashi zagi akan shi akewa uwar shi gori.
Ya madai godewa Allah da jiya bai sha komai da da yai niyar sha yasan da yau gorin da Maji zata sha akan shi Allah kadai yadan irin sa.
Gashi saida ya zuba kwayan a bakin shi sai yaji kamar ance ya furzo su waje duk ya zube su a kasa suka narke yana kallon su.
Har ya usa filin kwallo zuciyar shi sai faman sake sake take mai kan abinda zaiyi wanda zai sa Maji ta danji sanyi akan shi.
Amma ya rasa mafita akan haka, haka ya samu guri ya zauna ranan yana kallon masu kwallo kawai ya kasa tsinanawa kan shi komai a lokacin.
Sai faman kulawa da warwarewa yake shi kadai a ran shi abin duniya duk ya damay shi.

Tun bayan dawowan Raiha daga tafiya gaba daya bata son fita zuwa ko ina ko yaushe tana gida sai faman barci takeyi kamar wace tai wani aiki.
Gaba daya ta kashe wayan ta kuma ta hana kowa ganin ta tayi hakane don gujewa Nasir kawai.
Kusan sati biyu yana sintiri a kofan gidan su gashi tun dawowanta wayanta a kashe yake mata.
Ranan da ta bude wayan ta bayan kaman minti goma kiran unknown nomba ya shigo mata layin ta.
Da farko kyale kiran tayi har ya gaji ya tsunke don kan shi amma,sai gashi mai kiran bai hakkura ba ya kara kiranta again.
Cikin kasala ta dauki wayan sai taji murya cikin turanci a na cewa hey, baby,
It's me Michael, your friend from lagos, i hope you remember me now.
Cikin wata murya tace you mean, Michael Nasir friend ?
Yes it's me baby .
I called your nomber several time is switch up what happen with you baby?
Tsuki tayi tana fadin dan rainin wayo kawai har ma kana tambayana abinda ya samay ni ne wai?
Sam batai tsanmanin ya taba iya hausa ba sai taji yace don Allah kiyi hakkuri nasan bamuyi maki adalci ba shi yasa nakira layin ki na baki hakkuri don ban son abinda zai dawo a gare ni wata rana.
Maimakon tayo magana sai ta kama kuka dama gashi mahaifiyarta bata nan gida ta tafi makwabtan su .
Cikin rudewa michiel kece tayi hakkuri ta,saurare shi yana son magana da ita ne.
Da kyat ta dakatar da kukan ta yake cewa kina jina baby dama na dauki nomban ki ne batare da sanin abokina ba.
Don kawai nakiraki saboda ya bani labarin irin abinda yake maki wanda banji dadin shi ba kuma ranan ban san cewa two in one zamuyi maki ba don mun shirya dashi ne ni kadai zanyi amfani dake.
Wani abinda baki sani ba yanzun hakama yana nan yana planning din yadda zai fita dake waje, ne ya sayar dake ga turawa don ya tara kudi.
Bake ce ta farko da yai wa haka ba akwai yan mata biyu da ya kai waje daga garin ku.
Batan lokkacin da tace what da karfi ba cikin wani irin murya mai karfi.
Yace cool down my friend, kin bani tausayi ne don naga ke yarinya ce karama.
Kuma d way yadda naga kina kuka yasa kika bani tausayi, ba zan yarda ya yaudare ki ba shi yasa na kiraki na fada maki komai da fatan zaki rufeni bazaki bari yasan na fada maki komai ba.
Godiya take mai tana fadin tagode tagode yace ba komai, sai dai idan kina da account ki turo min zanturo maki da kudin ki.
Don shi ne ya hana na biya ki tun yana kuna nan yace free sex nayi dake ni kuma i can't dole ne na baki hakkin ki.
No kabarshi kawai ba komai, nagode, sai kawai ta kashe wayan.
Kifewa tayi saman dan katifan dakin ta ta,shiga gurzan kuka wi,wi tana cewa Nasir Allah ya isa tsakani na dakai wallahi.
Sai kuma tai shiru tafara tunane na, son, datakewa,Nasir ya haukatar da ita ta kasa fahintar irin son da Nasir yake mata.
Sai yanzu tafara tunanen lalai maganar Michael yana da kamshin gaskiya sosai don a wanan tafiyan ta fahinci wasu dabiun shi da bata sani ba.
Baida tausayi ko kadan son kan shi yai yawa bai damu da damurta ba ko kadan, shi kan shi kawai ya sani.
Gashi in ba dan sayayyan da yai mata ba bai bata komai ba haka ya barta tadawo gida sai dan dubu biyar dake a hannun ta.
Gashi kayan da,ta,sayo ta rasa yadda zata fitar tai amfani dashi a gani a gida, a tambaye ta ina ta samo shi.
Don har yanzun tana da sauran burbushin tsoron iyayyenta a ran ta.
Maganan Michael yai matukar tsaya mata a rai sosai don duk da bata ga Nasir ba amma matukar tsoron shi take ji a ranta.
Ko da Raiha tafara fita bata yarda ta hadu dashi ba sai guje mashi takeyi duk inda tasan zasu hadu bata yarda su hade dashi.
Wata rana tana tsaye tana jiran taxi taga wata far mota ta tsaya a gaban ta.
Bata tsaya kallon kan motar ba, sai kokarin tare mota take yi hankalin ta yana kan titi.
Ya fito daga cikin motar yana saye da shedda kalar kakin soja tai matukar yi mashi kyau sosai da haka yake yaudaran yan matan gari.
Don Allah yai mashi matukar kyau don duk shigan da yayi zai mashi kyau sosai ya karbe shi.
Baby ya karaso yana fadi kamar bata ji shi ba tayi ta kawar da kanta tana kokarin shiga motan da ta tare.
Da sauri ya karaso gaban ta yana cewa haba baby wai may ke damun ki ne don Allah na fa rasa gane kan ki.
Wani kallon tai mashi kamar bata san shi ba ta na kokarin zaunawa a motan da zata shiga.
Hannun ta ya riko da karfi yana fadin sunan for d first time sabanin baby da yake ce mata da, Ke Raiha wai may ke faruwa ne please ?
Sake min hannu tace cikin wani zafafan muryan tare da kokarin kwace hannun ta daga rikon da yai mata din.
Mamaki sosai abin yaba Nasir din don dai shi yasan lafiya suka dawo da ita daga tafiya.
Look baby Raiha ki fada min idan wani abu ya faru ne please don ban san laifin da nai maki ba ni.
Kawai ra,ayina ne hakan na nisan ta kaina dake don bakai min ba ni, maganar ta yasa shi murmushi yace to ni kin min ai.
Ko ba shike nan ba ki tsaya please muyi magana mu fahinci juna kada ki tara min mutane please.
Da,wasa ya dauki zancen amma sai yaga finfirin Raiha ta shige mota ta tafi abinta tabar shi nan tsaye.
Gurin Brosha ta tafi don dama kayan aikinta sun kare gashi kuma tana son jinta a network sosai don kwana biyun da tayi bata sha ba duk wani kala take jin kanta.
Shiko Nasir nan ta tafi tabar shi da mamaki don ya kasa fahintar abinda yai mata, saidai tunanen shi ya tsaya ne kodai yadda yai mata a lagos ne yasa tai hating din shi.
Wanan yatinyar may take nufi sai da tafiya tai nisa take son ta bata min show dina wallahi bata isa ba.
Don na riga da na fara shirin fita da ita waje gashi shegiya nasan ba karamin kudi zan samu a kanta ba don shegen dadi ke gareta.
Koni don dai son kudine kawai da ya rufe min ido aida bazan iya rabuwa da ita ba.
Gidan mahaifan shi ya nufa inda yan kannen shi suna ganin shi suka taso da murna suna mashi sannu da zuwa.
Duk cikin subabu sa,an Raiha don suna girmay mata da shekara biyar ko hudu.
Bayan ya gama gaisawa dasu ne yake tambayan
Gaban hajiyan shi dake zaune saman kushin ya zauna yana mata ina kwana.
Ta amsa cikin dakewa tana ce mashi lafiya yakara da tambayan ta ya gida da sauran al,amuran gidan, nan ma ta bashi amsa da Alhamdullahi.
Sai dan shiru, can uwar tace ashe kadawo ban sani ba yace eh inna ai yau kwanana biyu da dawowa.
Wani kallo tai mashi tace bayan Abdul yau kusan kwana biyar ke nan da yace min kun hadu dashi, zakace wai kwanan ka biyu da dawowa.
Nasir ko kana son mayar da kanka mutumin kwarai kuwa ?
Ka saki matar ka kakuma ki aure sai yawon kwasan yan mata kake a mota baka nan baka can dasu.
Wallahi kayi hattara da cutan zamani don yawa gare su ko ba wanan akwai wancan.
Dukar da kai yayi kamar wani mutumin kirki yana cewa Inna ai zanyi bandai samu wadda namu yazo daya bane har yanzu.
Don ina gudun kada akara maimaita irin na wancan karon aza kuma ba,a dace ba.
Kai din ma ai ba halin kwarai ke gare ka ba tunda baka iya zama kurum.
Ga shaye shayen da ka sawa kanka don ban tsan manin ka daina yi yanzu.
Girma dai ya kama ka in kanawa kan ka,fada kayi wallahi ni zan fitane kada kazo ka tare ni da surutun banza.
Yace Inna ina zaki sai na sauke ki dayani tunda gani na shigo.
Tace da sauri wa aganni da kai ace may ace har alfahari nake da irin halinka ina shiga mota da kai darana cikin gari.
Murmushi kawai nasir din yayi duk da,zancen mahaifiyar tashi ya soshi zuciyar shi.
Ya mike yana mata a dawo lafiya yafita inda kannen shi suke ya basu dubu goma wai su raba don yasan ko yaba inna ba karba zatayi ba don tace kudin da yake sayar da kwaya ne ita bata ci.
Duk yadda yaso ya fada mata matar shi da suka rabu kazafi take mashi amma inna taki yarda da ba gaskiya bane.
Abu daya tasan yana masu shine biyan kudin wuta da na ruwan fanfon gidan nasu tun bayan da mahaifin shi ya rasu.
****** ********* ******
Ranan da matan gidan suka samu labarin tafiyan da sadauki zaiyi zuwa kasan waje sunyi ta zuba bakar magana kamar tashin hankali.
Inda suke cewa lalai maji bata san ciwon kan ta ba da har zata yarda ta barshi yafita zuwa wani guri wai ma kwallin kafa.
Itako mama Asiya cewa tayi sai dai a kare da hakan a lalace wai wasan kwallo don tambadewa kawai.
Umma sai da ta samu maigidan su da zancen tana cewa wai da gaske ne zancen da taji yara suna fadin sadauki zaifita waje wasan ball.
Yace da gaske ne mana akwai illa ne ga hakan ko yaya ?
Tace haba Alhaji yanzu kamarka da kimar ka da darajan ka,za,ace wai danka ne ke wanan abin.
Shi kwallon kafan kuma yanzu mugun abune, da na barshi nan zaune gida yana tambadewa ai gara na san ya kama wani abun.
Tace amma gaskiya Alhaji,,, ke yafa isa haka Rakiya don nasan abinda nakeyi sarai wallahi don haka na fada maki da yardana zai tafi.
Cabdi ashe akwaita gidan nan ke nan don sunan ka bai lalace ba yanzun ne ake shirin yin ta.
Ta fito fuuu, daga dakin tana zuba bakaken maganganu itakadai har zuwa dakin ta.
Ba su hakkura ba sai washegari kuma suka kara,tayar da zancen.
Lokacin haniya kubura tana kusa sai cewa tayi maye cikin wasan kuma ai wanan idan Allah yasa mashi hannu sai kiga an take akai.
A sawan kwallon ko a shaye shaye wanan dai kawai an kara turashi ne yaje ya kara yin cos kan shaye,shayen shi kawai.
Nikan wallahi idan ya dawo naga yakara haukacewa sai dai na bar ma su gidan shida uwar shi kawai don dama haka sukd so.
Allah dai ya shirya muna shi amma ai ba kai wa dan wani mugun fatan mugun abu ya samay shi.
Daya samay shi da farko ni nai mashi fata ko may kada fa mace ta daure ni da raina.
Ni yanzun ma gani nake kamar ya koma ga shaye shayen shi ne don ko yaushe yana gida kwance kamar wani malalaci sai aukin barci kawai.
Duk a kunnen maryam dake zaune a falon suke wanan hira da dane kafin maji ta hore su da rashin kunya da,tabasu amsa daidai da maganan su.
Sai da ta,dawo daki take fadawa maji abinda taji suna fadi kan tafiyan na sadauki.
Maji tace Allah ya sauwaka ai Allah yafi su ni dai ban wa dan kowa mugun nufi akan shi.
Amira tace ai ba zasu so suga ya zama abin kwarai ba tunda ba haka suke son ganin shi ba dama.
Ke kubar wanan magana duk ma abinda su ke nufi ni dai ga Allah na dogora.
Sai lokacin Bintu da bata faye shiga maganan su ba ta sa baki tace ai in ba abin mutum ba ba mai son yaga nashi ya lalace su dai suyi mashi fatan alheri kawai.
Ke kika san wanan amma ai su basu sani ba sunfi son ko yaushe su ganshi a hakanan inji Amira.
Amma maji kafin ya tafi da ki sa ai masa saukan alkur,ani maigirma Allah ya kare shi a can inji Bintu .
Ina da niyar yin hakan sai dai ban san wanda zan sa yai min ba tunda ba, baga hajiyan masa ba maji Amira tace mata da sauri.
Lalaifa haka za,ayi zan mata magana da ta san yadda zata samu na Allah da zasuyi min.
Amira tace ashe su ma wai har sun farga da wanan yawan barcin da yaya yake yi kwanakin nan
Ba sa ido bane duk abinda mutum yakeyi idon su yana a kai kamar wasu mayyu can
Mutane suce basu son suga dan uwan su a farin ciki ko kadan sai dai kullun aga kana wahalan tsiya kawai
Ai yanzun haka duniya ya koma hassada da bakin ciki yai wa mutane yawa a rayuwan su inji maryam.
Allah ai yafisu don duk abinda zasuyi Allah ya dai yana ganin su.
Uwar dai tana zaune tana jin su kala bata kare ce masu ba ga hiran nasu.
Duk zuciyar ta a jagule yake akan tafiyan da dan nata zaiyi a cijin wanan halin da ake ciki dashi.
A kullun, zancen Maji kan sadauki shine ya taimaka idan ya tafi ya kama kan shi da rayuwan shi acan.
Don Allah Baba na kada ka bamu kunya ni da mahaifin ka, sadauki yakan yi mata murmshi ne kawai yace kada ki damu maji insha Allah zan tsare kaina danan dacan kamar kuna tare da nine ai.
Mai masa ta tafi kamar yadda Maji ta bukaci da ta taimaka mata akan ai mashi addua kafin yatafi inda tabada kudi cikin asiri ko yaran ta basu san da zancen ba.
Da dare sadauki ya shigo gida inda ya samu maryam kaunan shi a tsaye gaban tsohon TV dakin su tana kwalan shi don ya tashi yai aiki don saboda tsufa ya gaji ya na tsayawa don kan shi.
Sai yake cewa ke Maryam kina ta faman kwalan Tv haka idan ya fashe fa?
Yaya idan ba dukan shi mukayi ba baya tashi sabofa ya tsufa da yawa sosai shi yasa muke dukan shi gashi za,ai program da karfe tara muna son muyi kallo.
Wani irin ba dadi yaji a,ran shi inda ya kara jin tausayin uwar shi sosai a ran shi . sai ya tuna yadda yaga dakin hajiya Kubura a ranan,
Komai akwaishi na,zamani a dakin amma su ga dakin uwar su kamar zaure ba komai a cikin shi sai yan tsofafafin kujeru da wanan tshon TV da maryam take kwalla.
Wani dogon huci yaja a fili har yasa su dago kai su kalle shi kan shi ya mayar saman makarin kujera ta baya yana shafo fuskan shi kawai.
Bintu tafito cikin wani dogon rigan atamfa wanda akaiwa dinki budade daga kasan shi.
Maji tafara sallah ishai a lokacin don haka ta waiga inda yake kwance saman kujera taso share shi amma tsoron shi take matukar ji.
Don haka takara waigawa still yana a yadda yake kamar mai barci, tace cikin daurewa yaya sadauki ina wuni.
Tankar a cikin mafarki ya tsinkayi zazzakan
muryan ta da take gaishe shi.
Batare da ya,sauke hannun shi daya kare fuskan shi dashi ba ya amsa mata da kyat da lafiya.
Tace akawo maka abincin ka ne yanzu kamar ba zai amsa mata ba sai can yace kawo min kawai.
Ta juya zuwa kitchen don ta dauko mata yai daidai da ya dago fuskan shi sai ganin bayan ta yayi tana tafiyan ta a cikin natsuwa.
Yace ke idan zaki fito ki zo min da ruwan sha daga nan, ta amsa mashi da tau kawai ta shige abinta.
Tana kitchen sai faman tunane take barkatai tana cewa, shi wanan haka Allah yayi shi da mudaden hali ne wai.
Girman kan shi da share mutane gami da nuna isa sunyi yawa don isa ma da izza wai ke yake ce mata.
Shigowan da Amira tayi kitchen din shi ya tsayar mata da tunanen zuccin da takeyi.
Amira tace abincin yaya sadauki ne zaki hada mai ta bata amsa a cikin ladabi da fadin eh nagan shi zaune nako san abinci ne ya kawo shi amma bai iya tambaya.
Amira tai dariya tace kin san shi magana ma matsalace a gurin shi kafin kiji yai magana aiki ne gare shi, dan dama idan da maji suke magana zai iya dan kai lokaci yanayi.
Tana hada abincin suke magana da Amira inda ta dauki abincin zuwa falon su inda yake zaune.
Wanan karon ta samay shi a,zaune ya dauki kafa daya ya dora ga dayan kafan shi yana kallon yadda maryam ke bugun TV nasu da karfi.
Daidai ta kusa karasowa inda yake taji yana cewa Please maryam kibar TV nan hakana idan ba zaiyi ba mana.
Bintu ta,kawo abincin a gaban shi ta dire mai zata juya yakw cewa ke mai aka dafa don banga cibi ba.
A tsorace tace mai tuwo ne shi yasa ban hado da cibi ba cikin jin tsoron shi take magana.
Da hanzari ta juya zata bar gurin yace ke dauko min cibi dan Allah ko tuwo ne ba,aci da cibine akace maki bakauyar banza kawai.
Simi simi Bintu ta juya zuwa kitchen din duk da zagin da yai mata yaci mata rai akan tai mashi abin arzikine kuma zakirata da bakauya.
Kai inji Maji da data idar da nafila take cewa kada na karajin kakirata da bakauyan nan don ba gurin ka tazo ba.
Ina laufin ta ta hado ma abinci don kai miskilancin ka bai bari ka tambayi mutane abincin ka.
Mikewa yayi tare da dauka abincin nashi yana kokarin barin falon don bazai yarda a raina shi ba akan bakuwar yarinyar Maji da bai san inda tafito ba.
A lokacin ita kuma Bintu tafito daga kitchen din dauke da cibin a hannun ta tana mika mai.
Yace ke barshi dan Allah ya fice daga falon Maji taja tsaki tace shiyasa ake ce ma mahaukaci yaji ta amma bai tsaya ba yafice kawai abin shi daga gidan zuwa part din su ranshi a bace.
Don shi bai son ai mashi fada a gaban yara kada su raina shi.
Sai bayan kwana biyu ya shigo gidan duk lokac
in yana fushi wai maji ta kunyatashi a gaban kannen shi.
Jin gidan shiru sai maryam dake zaune falo tana karatu yace mata ina Maji tace mai tana ciki ta kwanta.
Yai kamar zai fita sai kuma ya tsaya ya mayar da hankali ga maryam yace ke,
Wai wanan bakuwar yarinyar da nake gani a nan daga ina tazo tace yaya sadauki kana nufin Bintu?
Yace ina ruwana da sunan ta nace dai ita din wacece ?
Tace diyar hajiyan masa ce makwaciyar mu Maji tace ta zauna nan don hajiyan yanzun bata zama tana jiyan yarta a kauye.
Ya koma tambayan ta a nan makwabtan mu suke ke nan shine maji tace ta dawo nan kuma,?
Tace eh daga kauye tazo karatu take kuma hajiyan masan bata zama yanzu.
Wani irin tsuki yaja yace kai Maji da kwashe kwashe take wallahi shine har zata disgani a kan ta?
Maryam duk ta kagu da tambayan da yake mata kada itama nata ya samay ta.
Idanuwan shi sun yi ja sun kada sai take tsoron ko ya shawo ne a lokacin.
Yana kokarin fita daga falon Maji tana fitowa tace ina jinka mara kunya dana kwaso ta akan ka nace ta zauna ko kuwa.
Tana kallon shi ido da ido taga idanuwan shi yadda sukai mai ja sun kade kamar an watsa mai barkono a cikin su.
Tace mashi kai mai kuma ka,shawo ne naga duk idon ka ya wani sauya haka.
Sai lokacin yace kai haba Maji shike nan ni banda aiki sai sha harda rana haka.
Kuna da lokacin shane tunda kun bushe filar ku baku jin kunyar kowa a wanan yanayin,
Kamar zaiyi magana sai kuma yace ni ban sha komai ba kaina ne dai tun safe yake min ciwo.
Ya juya yana fadin yanzun ma magani na sayo bari naje nasha na kwan ta, ya juta yafita daga dakin.
Yana tafiya Maji ke fadin in ma dai ka koma shane wanan kuma ruwanka.
Amma da yafita hankalin ta bai kwanta ba sai cewa take a ranta ko ya sha din ne ko kuma barin shan da yayi ne yake haifar mashi da ciwon kan oho.
Maryam ce ta katse da cewa nima wallahi yadda naga ya shigo ya tsare ni da tambaya tsoro ya bani .
Shiko yana fita sashen su na samari ya shiga kai tsaye ya nufi dakin su don da gaskiya kan shi din ke masa ciwo don rashin shan da baiyi ba kwana biyu.
Ya fada kan katifan shi batare da yasha maganin da yace ba din, kwance yake kamar mai barci yana tunanen kodai ya dan hada ne yasha ko zai samu relief.
Yana gurin a kwance sai faman sake sake yake a cikin ran shi kodai yashane ko ya bari.
Sai wata zuciya tace mai idan kasha shike nan zancen tafiyanka ya lalace.
Don ko kowa ya yarda Mani bazata yarda yatafi ko ina ba tunda ba bari yayi ba.
Amma wata zuciya kuma tana ce mashi yasha koda kadan ne don ya dan samu sauki a ran shi.
Mikewa yayi ya jawo ledan da yake aje kayan aikin shi a ciki yana kallon su sai faman sakan zuci yakeyi shi kadai a dakin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,,,
A LOKACI MU KE,,,,,,
Bintu bata da wani matsalar komai tsakanin ta da mummy da take zaune a shiyan ta.
Don mummy dai irin wayyayun matan nan ne masu faraf faraf da mutane ba,a gane gaskiyan cikin su.
Wata, yammaci da dare, Bintu tana kwance tana barci don yayi saurin kwanciya don ta gajiya sosai gashi bataci abinci ba da yunwa ta kwanta hakana.
Cikin dare yunwa ya damay ta don haka ta bude idon ta don ta sauko saman gadon da take kwance akai.
Tana son fitowa zuwa kitchen don dauko abincin ta da bata ci ba a daidai kofan dakin mummy take jin sautin muryan ta tana waya kamar haka.
Wallahi ina fada maki yau kwanan ta uku bata gidan tana can garin su ana mugun a bu,
Yanzun haka yarinyar da take gurin ta,da nake fada maki tana dakina ta barta ba,aje da ita ba.
Wai kin san may wallahi ni kin san ba yarda nayi da su ba matan gidan nan baki daya.
Kada taje can ta yi sa,a har ta samu galaba a kaina, don nasan kowan wansu ba wai ta zauna bane.
Duk yadda za,ayi gobe ki je min gurin nan ya kasance duk abinda ma taje garin su ta kullo a lalata min shi baki daya.
Bintu bata tsaya ta karasa jin komai ba ta juya a hankali ta koma dak8n da take ciki kwance,
Jin motsin mummy tayi don haka tamike zuwa dakin da Binta take kwance a ciki tagani in itace take sauraren hiran ta,
Jin motsin mummy tafito daga dakin ta yasa Bintu lafewa tankar mai barcin da yai nisa sosai.
Mummy ta,dan duba da kyautaga barci takeyi abinta hankali kwance,tai wani irin sauke ajiyan zuciya tare da dafe goshin ta tana fadi Allah ya soni yau da kashina ya bushe wallahi.
Komawa tayi taci gaba da wayan ta wanda babu wani abin arziki da take kullawa a cikin wayan sai kishi irin na kishiyoyin lokaci.
Imani da tsoro duk sun rufe Bintu a lokaci daya na irin maganan da,taji mummy tanayi a,waya akan uwar dakin ta, Maji ke nan.
Gaba daya kara tsanar gidan taji a ran ta kwata kwata babu mai imani da,tsoron Allah kowa kan sa yasani yanzu.
Idabn da a hira wani kefada mata abubuwan da taji Mummy tana fadi akan Maji da sai inda karfinta ya kare gurin karyata maishi.
Matar da duk gidan tafi nuna tausayin ta a kan Maj da yaranta yau kuma itace take wanan sake maganan a bayan idon mutane don tsaban iya kisisina na,zamani.
Washegari haka Bintu ta,tashi ta kasa sake jikin ta,ga yunwan da ta kwana dashi harsafe tare da,bacin rai na abinda taji mummy na fadi.
Ita ma dai yanzu gaba daya jin gidan takeyi duk yafita mata a,rai baki daya ba wanda ta yarda dashi dan dama maman ta watau maji ke nan.
Don in ba kazafi zatai mata,ba,zata iya cewa tunda ta,zo zama dasu bataga wani anin assha ba daga gurin maji har yaranta sai dai matsalan shaye shayen sadauki shine kawai abin da zata ce tagani na assha a gurin su.
Bintu tafito daga daki inda ta samu mummy zaune ta gaida ita acikin ladabi da biyayya.
Sai ta mike tana cewa cikin kwantar da murya zan tafi na gyarawa mama gurin ta don ina,ganin yau zasu dawo.
Kallon mamaki Mummy take mata tace Bintu yaki nan zo zauna muyi magana ta fahinta dake.
Komawa tayi ta zauna kamar yadda aka bukace ta da yi din.
Mummy sai da ta dan ja lokaci tace ba komai yasa na ce zanyi magana dake ba,Bintu sai ganin ki yarinya mai saurin fahinta,da sanin ya kamata.
Ina,fatan maganan da zan gaya maki zaki fahince ni ba,tare da,wani manufa ba a,ranki.
Murmushi Bintu tayiwa mummy kawai a lokacin sai da Mummy ta,dan yi shiru tace gaskiya Bintu a dan zaman da nayi dake na fahinci cewa ke yarinya ce mai mutumci da sanin yakamata.
Irin yarinyar da,na,dade ina gurin samu a,raina a gidan nan na rike ta.
Sai dai kuma,gashi kin zo min a ta,wani babban yanayi mai daure kai sosai, don zaman da hajiya maijidda zai ita kawo min akasi akan bukatana.
Don haka nake neman hadin kai a gurin ki idan ta,dawo don Allah ki jajirce kice a gurina na zaki ci gaba da zaman ki.
Kin daiga ni da ita,ba daya bane,don haka ki zabarwa kanki inda zaki zauna ki samu karuwa iyayyen ki, su ma su samu ta gareki,
Don kinga ni kudi zan dinga baki duk karshen wata sabanin yadda maijidda ta aje ki sai bauta mata kikeyi bata baki komai dake da gwagon ki.
Wani irin mumunan faduwan gaba ne ya daki zuciyar ta na wani dan lokaci inda tsoro da firgici suka ziyarce ta
Kanta ta,dukar kasa inda mummy take cewa ke nake saurate fa,
Murya kasa kasa take cewa mummy ai da nan da can duk dayane ni a gareni. Don duk mutunci ne ya hadani da kowan ku.
Ok tau yanzu zabi ya rage naki sai naji shawaran da kika yanke wa kan ki.
A cikin gatse tabata zuwa zabi don ta san bazata bar kudi ba da jin dadi ta koma inda uwa tsugunne diya a kwance ba dole zata dawo nan gurin ta inda ga dadi ga sutura masu kyau, ba second hand ba. Tasan dole ne ta dawo gare ta ma don ta kashe mata zuciya ko.
Haka ta mike ta nufi part din Maji tana tafe tana nazarin maganan mummy matar da a da take matukar ganin ta da daraja da sanin ya kamata tana tausayin uwar rikon ta maji fiye da ma mijin da ya hadasu zama tare a gidan.
Haka ta shiga gurin na maji tana aiki tana tunanen irin rayuwan wanan zamanin namu da muke cikin sa yanzu.
Har girki sai da taiwa maji tare da kamsashe masu ko ina na gidan.
Sai yamma Maji ta iso gidan da yaranta suna daukin ganin Bintu wace itama haka da murna suka tari junan su cikin jin dadi tsakanin su.
Tun fitan da Bintu tayi part din mummy zuwa,taron su Maji bata kara leko part din mummy din ba har zuwa dare takwas saura sosai.
Dan, ta mai bi ma na biyu ta tura wai a kira mata Bintu zata rufe part din ta.
Sai ga yaron ya shigo duk muka juya gurin shi inda ya nufo gurin da Bintu take zaune direct yana cewa,
Mummy tace nace ki zo zamu rufe kofan part din mu dare yayi wai.
Kafin Bintu tai magana Amira ta,watso ma yaron wani fitinaneniyar harara yaron ya,noke yana cewa mummy ce tace nazo na kirata ya juya yabar dakin zuwa,part din su.
Muryan Maji sukaji tana cewa,a,a Fatima tashi kije ku kwanta ko har kin gudo ne zaki mata halin yan duniya yau yau da dawowan mu.
Tashi ki dan tafi tunda ta aiko maki da sako bai kamata ace baki je ba kinji diyata ta fadi cikin dan kwantar da,muryan ta.
Shima yaron ai iyayi tsiyane dashi mai makon ya tsaya tun can yai sallama shine ya fado wa mutane daki haka.
Ai shi yaro dan auke ne baida laifi, an aiko shi kuma ya fada ya tafi a binshi yanzu shawara ya rage namu.
Maji takara yiwa Bintu magana da ta tashi taje ai yaune kawai gobe ta dawo dakin su.
A zuciyar ta take cewa Allah sarki Maji da kin san abinda ke nan da,baki barni na tafi ba ko yau din nan ma.
Ita ko mummy tana can dakin ta saikallon kofa take a kai akai tagani ko Bintu zata zo tabar Maji akan tayin da tai mata.
Zuwa can sai ga Bintu saye da,dan hijjabin ta tashigo gurin mummy a,bisa Umurnin Maji.
Sai dai ita kuma mummy tana ganin ai tayi nasara saye zuciyar Bintu da abin duniya shi yasa ta,dawo gareta.
Bintu na fita Amira tace maji da ma kin bar Bintu don naga bada son ranta ta tafi ba wallahi.
Allah ko ai ban san bata son zuwa ba da ban tura ta dole ba amma kuma,sai naga in munyi wa Kubura haka bamu kyauta,ba tunda har ta aikomata.
ko da,ta shigo falon Mummy tabita da kallo tare da,sauke ajiyan zuciya a fili, har ta karaso tsakiyan falon nasu.
Mummy ke cewa k8n wa kanki kiyamallaini yarinya don ba mai son wahala yanzu.
Bintu da bata ce uffan ba tashige dakin da take kwana abinta tabar mommy da yaranta suna kallo zaune a falo.
Tun shigan ta bata fito ba sai washe gari ta farka kafin kowa ya,fito tai ma mummy duk aiki kamar yadda ta,saba yi a kullun tare da,dafa ma,yan makaranta abinci.
Bada,sanin kowa ba ta kwashe yan kayanta zuwa dakin maji tunda farar safiya.
Koda Mummy ta tashiga gurin ta ta samay ta zaune sai cewa tayi kinga Bintu nasan kina jin kunyar Maijidda ne ki barni da ita zan san yadda nayi da zancen ta.
Fitan mummy daga gidan Bintu ta kwashe sai part din Maji da farko taso ta boye damuwarta amma sai su Amira suka fahinci da damuwa a tare da ita.
Da suka tambaye ta sai take cewa babu komai kanta ne kawai ke mata ciwo.
Sai zuwa rana kowa na sha,anin gaban shi Kubura ta dan fakaici ifon su ta kwashe komai nata sai dan gidan gwagon ta ta bude ta shiga.
Shiga da fitan ta duk akan idon sadauki wanda yake zaune kofan dakin shi sai dai furannin gurin sun boye shi ba za,a iya ganin shi ba.
Sai bayan fitan ta ne daga gidan shikuma yamike yabi bayan sai yaga gidan su ta shiga.
Nan yakoma ya zauna a inda yake zaune cikin tunanen irin nasihan da yasha gurin kamilin kakan shi dan matashin dattijo mai dan farin gemu a fuskan shi.
Kubura ta gyara ko ina tsab tunda dakin kwanan su har tsakar gidan nasu ita kadai a gidan.
Sai da Maji taji shiru bata ga fitowan yar amanan ta ba ta ce Maryam ta diba mata ita taga may takeyi.
Da sauri Maryam ta,dawo tana fadin Maji Bintu fa bata gidan nan nake gani.
Da sauri Maji tace kodai tana bandakine ki koma ki duba min mugani.
Aikuwa har bandakin ta duba ta kuma duba gurin kayan ta babu komai nata a gidan.
Da sauri ta dawo gurin Maji tana fada mata Maji har kayan Bintu babu a gidan nan fa.
Hakali a tashe Maji ta mike zuwa dakin hajiya kubura sai dai a rufe dakin yake shima.
Ikon Allah ta dawo dakinta nan ta samu yaran ta duk a cikin damuwa Maji tacewa Amira jeki gidan mai masa ki duba min ita da sauri.
Shigowan sadauki yayi daidai da jan hijjab din Amira ganin yanayin su yasa shi kalkon su cikin mamaki yana tambayan su may ya faru ne wai.
Bintu ce bami gani ba shine zan tafi na duba gidan su.
Ke zauna naga fitan ts tana cikin gidan su don nan naga tashiga dazun da rana.
A jiyan zuciya Maji ta sauke tare da cewa akwai matsala ke nan tunda yarinyar nan tai muna haka.
Haba Maji wai may yasa kika damu da zancen wanan yarinyar ne haka bayan ita bata damu da ku haka ba.
Kai ban son rashin mutunci Fatima a dan zaman da tayi damu ni nasan irin karuwar da nasamu da zaman ta nan din.
To may akai mata da zata gudu bata fadawa mutane ba har zata kwashe tabar gida.
Nifa na ganta ban yarda da ita ba yasa na tashi na bi bayan ta amma sai naga ta shiga gidan su.
Yanzun haka ma da zan dawo naga gidan a bude da alaman tana ciki har yanzu.
Amira maza jeki ki jiyo min ko may ke faruwa da ita har ta guje muna hakan nan.
Amira da maryam suka fita zuwa gidan hajiyan masa lokacin Bintu ta idar da sallah tana zaune ita kadai ta hada kai da kujeran dakin gwagon ta inda tafi zama akoda yaushe indan tana gidan.
Da sallama suka tura kofan shiga gidan inda tun a tsakar gida suka hango ta a zaune.
Bintu na ganin su gaban ta ya fadi don in akwai abinda ta tsana shine ta koma gidan su mai tarin rikici a cikin sa.
Maryam tun bata karaso ba take fadin haba Bintu may akai maki zaki tafo gida batare da sanin kowa ba kin tayar wa Maji da hankali yau sosai wallahi.
In ba don yaya sadauki ba da ya shigo yana fadin yaga lokacin da kika dawo nan gidan.
Amira tace Bintu nasan akwai abinda ya faru ki fada muna ba boyewa zakiyi ba a ranki.
Don in har baki fadi ba ba,a san may yasamay ki ba balle asan ta inda za,a bullowa maganan.
Maimakon Bintu tayi magana sai kawai ga hawaye sun fara zubo mata shar nan ta fashe masu da kuka mai tsuma zuciya.
Duk yadda suka so tai magana Bintu taki fada masu komay ye matsalarta da har ta guje su haka a lokaci guda.
Haka suka koma gida da sanyin gwiwa suna fada wa uwar su yadda suka yi da ita a can.
Hakalin Maji yai matukar tashi si dai kuma gashi babu halin ta fita zuwa gidan don maigidan yana kasuwa a lokacin.
Gashi kuma itace zatai girkin gidan ranan nan abu ya taru ya rikice mata akai.
Itako mummy tana can hankalinta a kwance, don tasan yanzu bata da matsala don Bintu zatai mata komai kafin ta dawo gidan.
Sai yamma lis ta shigo tare da yaranta da takai suka sayo abubuwa a wani shago.
Ganin kofan ta a rufe yasa ta tunanen ko Bintu ta shiga gurin hajiya Maijidda ce sai take fadi a ranta dole nasan yadda na hana wanan yarinyar shiga gurin matar nan.
Sai dai tana shiga taga ko ina tsab an gyara amma babu alamar an dafa abinci a part din.
Don haka tafito da kanta har kofan dakin Maji tana fadin hajiya ina ya ta tashiga ban samay ta,ba a daki dana,dawo.
Tun lokacin Maji tadan fara tunanen duk yadda akayi akwai wata magana a kasa.
Maji tace hajiya ina yarda da fahinta yasa nabar wanan yarinya a gurin ki da zanyi tafiya.
Eh haka ne amma kuma ai haka ba yana nufin yarinyar bata da yancin kanta da zata zabi inda take ra,ayin zama bane ko?
Oho yanzun nagane inda matsala take ke nan ashe akwai abinda ke faruwa a gidan nan bayan tafiya na ban sani ba.
Babu komai sai alheri inji hjy kubura tace kawai dai mun shirya da yarinyar zata dinga min aiki ina biyan su, aikin san babu boyo a tsakani na dake.
Hmm tau Bintu dai bata gidan nan yanzun haka don ta kwashe kayan ta tabar gida ta koma gidan su.
Kai amma ban zaci haka,ba daga gareki hajita maijidda.
Ban taba zaton zaki yi min bakin ciki ba irin haka yanzun don kada yarinyar ta taimaka min kika kore ta a gidan nan.
Hmm ke ma kin san hakan ba halina,bane ra,ayin kantane takwashe batare da,sanin kowa ba tabar gidan nan don kanta.
Ikon Allah inji Mummy kamar zatai magana sai kuma ta juya a fusace tabar gurin zuwa part din ta ranta a bace wai Maji tai mata hassada.
Kai duniya kan yanzun ba gaskiya babu tsoron Allah a cikin ta,wai ita da za,aiwa zargin rashin gaskiya amma itace ke ganin hakan akaimata.
Maji nashiga daki Maryam tace amma kuwa Bintu munafuka ce yanzun saboda kwadayin duniya har ta uya yiwa mutane haka.
Amira tace aini tabani mamaki wallahi.yanzun ita tana ganin taiwa mutane wayo ke nan ko.
Aitazo indai Mummy ce dan abu kadan zatai mata sai duniya taji su .
Matar da bata da,yarda ko kadan inba diyan taba ita batasan kowa ba aduniya shine kwadai zaikaita gurin ta.
Maryam tace bataga daki yana kyalli ba kamar aljannan duniya dole ta gudu nan inda ba komai ai.
Kai ya isa haka dan Allah kubari muga yatinyar muji may ke na kafi ku yanke hukunci ku fara zaginta.
Da zata zauna da ita aida tun tuni tayarda da zugin da tai mata, ina jiya kince da kuka taje kwana dakin dana tura ta.
Koma may nene duk nice najawa Bintu din haka don ni nakaita da hannu na cikin rashin sani.
Maji dama aikin san mummy ba mutunci ne da ita ba don ita kanta kawai ta sani amma wanan rashin gaskiyan haka ai ya zama cin fuska.
Da yamma da maigidan yadawo maji takai masa abinci lokacin ya tafi sallah sai tadawo dakin har in ya huta ta samay shi akan ya bari ta shiga gurin Bintu taji may ke faruwa.
Amma tana zuwa gurin maigidan saita samu hajiya kubura tana mayar mai da magana akan karya da gaskiya.
Wai taimata bakin ciki akan yarinyar shine har ta koreta bayan tafita daga gidan.
Shigowan Maji ya sashi cewa madalla ga Maijiddan ai ta shigo ma dama yanzun nake nufin kiran ki.
May ke faruwa ne akan yarinyar nan ta gurinki don hjy kubura ta samay ni da wani magana sai dai ban fahinta,ba.
Murmushi maji tayi tace nima dai ban fahinci maganan ba sai takai zaune yayin da mummy tacika ta batse da Maji din.
Nan ya kara tambayan ta ta fara fada mai tun farkon barin yarinyar da tayi a gurin mummy da kuma yadda jiya akayi kafin ta tafi gurin ta ta kwanta kamar yadda mummy ta bukata.
Maji tace ni a zatona ko don a jiyadin muka dawo yasata cewa tazo ta kwanta.
Sai yau tun safe yarinyar ke daki tana kuka dana tambaye ta take cewa wai kanta ke ciwo.
Wallahi Alhaji dafa haka ban sani ba bayan nabata magani ashe ta faki idon mu ta kwashe duk kayan ta a gidan nan ta sulale ta fita ba wanda ya sani.
Saidana tura yaran ban,suka ce tana gidan su dakin gwagon ta ita kadai a gidan.
Subbahanallahi yanzun dai ina yarinyar take tana gidan su ita kadai a gidan.
Yanzun nake batun na rokeka naje naji ko may ke faruwa da ita tai muna haka amma kuma sai dazun ga hajita kubura tazo tana wani maganan da ban san dashi ba mani.
Yanzun dai ba,wanan ba ahin kun san hatsari ne abar yarinya karama kamar wanan ita kadai cikin gida babu kowa a wanan zamanin da muke ciki.
Hakan yasa fa uwarta takawota gurinki don ki rike mata ita har lokacin da zata dawo.
Don da kanta mai masa sai da taimin magana akan zaman yarinyar gidana shine ma dalilin da yasa na barta kowan ku bai sani ba.
Amma kubura kin bani mamaki wallahi yardane fa yasa maijidda ta barta a gurinki.
Yau ina wayon ki da iliminki ya tafi ina suka shiga da zaki turawa yar mutane wanan akidar na bijerewa.
Alhaji nifa ba,a kyauta zan dauketa ba kudi zan bata ita da iyayyen ta don ina bukatan taimako.
Wani irin tsuki yaja ya dauki wayan shi nomban Amira ya kira tare da babban dan,shi yace su zo yanzun falon shi.
Ba,a dade ba sai gasu yake cewa ya raka Amira tazo da Bintu yanzun nan suce inji shi.
Bintu har ta rufe gida da daki ammajin da tayi anata bugawa tare da kiran sunan ta yasa ta bude kofan tafito.
Duk ta fyde ta ramay lokaci guda da ita ta canza don fitinan daya samay ta.
A tsiwance Amira tace da yaya Imirana muke Baba ne yace muzo dake yanzun nan.
Daga haka Amira bata sake cewa komai ba ta tsaya jiran ta ta shirya su tafi.
Jin Alhaji da kanshi ke nemanta yasata dauko hijjab dinta zuwa amsa kiran inda tabiyo bayan su simi simi har falon Alhajin.
Shikan Imirana bai san komaiba ya na cewa gata nan yajuya abinshi ya fita falon shida Amirah.
Guri ta samu ta zauna a makure duk ta kode lokaci guda da ita fuskan ta duk ya wani kode mata.
Gaba dayan su kallonta sukeyi take taba Alhaji tausayi yace Fatima may ke faruwa ne.
Sai tai shiru ta dukar da kanta kasa tare da sako wasu hawaye masu dumi daga idon ta.
Ganin bazatai magana ba tasa Alhaji cewa may kike a gidan ku ke kadai baki tsoron dare wasu miyagu bata gari su shigo maki ke kadai a gida karamar yarinya dake.
Nan ma Bintu sautin kukanta takara batare da tai magana ba sai tsoron da ya kamata a cikin ran ta lokaci guda don ita batai ko tunanen hakan ba.
Yace kin fadawa maijjida abinda ya faru tsakanin ki da hajiya kubura ne.
Da sauri ta dago kai tare da cewa cikin kuka ban fadawa kowa ba Baba.
Baki kyauta ba Fatima don kinga amana kike a gurinta agurin mu ma baki daya idan wani abu ya samay ki damu uwarki zatai kuka.
Baba kuyi hakkuri amma ni na guji hafin hasumi ne akaina shiyasa na kona gida.
Baki kyauta backe nan baki rike maijida a matsayin uwaba gareki tunda har zaki iya boye mata maganan ki.
Da sauri tadago kai ta dan kalli maji tace ba hakana bane Baba ban son wani abu ya faru ne a tsakanin su don naga akwai yarda a tsakanin su.
Inda mummy take zaune ya dan kalla yace kinga karamar yarinya ma tafiki tunane wai mai ya samay kine kubura da zaki wanan danyen hukunci wa kanki haka.
Maganan nan ba abin kunya ne gare ku abokan zaman ku suji shi an yarda dake abaki amanan yarinya sai kuma ki mata wanan danyen aikin haka.
Kituna fa kema kin haihu idan wani yaiwa yaranki haka zaki ji dadi bafa rashi gatane yasa kika ganta nan ba lalurace takawo ta gurin mu.
To amma Alhaji aini naga ,,,,, dakata don Allah wallahi baki kyauta ba kuma kin bani kunya yau ace kece kikawai maijida haka a gidan nan.
Ke tashi ki koma dakin ku kuma na kashe wanan zancen a gurin nan kada naji shi wani guri don ranku zai baci.
Daga yau ke maijjida nabar maki rikon yarinyar nan a hannunki koda uwarta tadawo zanyi magana da ita kada na kara jin zancen nan ko nan gaba.
Bintu ta mike jiki ba karfi tana fadin nagode baba cikin kuka tana fita taji yana cewa ke kuma kubura wallahi duk naji kin wa yarinyar nan wani muvun kallo gidan nan sai na saba maki ta yadda baki zata ba.
Bintu tana shiga dakin da dan muryan sallama duk su Amira suka kalleta a wulakance bata gane masu ba.
Bata jima da shiga ba saiga maji tashigo tana cewa Amira hado mata tea mai zafi tasha tasha magani.
Nan taje mayar masu da yadda maganan yake sai ko suka shiga zagin hajiya kubura sai da ta tsawata masu.
Ta juta kan Bintu tanacewa Fatima ashe baki dauke ni uwa ba da gar zaki iya biye min magana irin haka tunda badawo.
Cikin kuka tace mama ban so kuyi fitina ne shiyasa naga gara kawai nabar gidan gaba daya.
Nan maji tai mata fada sosai tare da kara bata shawara akan mutanen gidan gaba dayan su.
Bintu a ranta tace nafiki sani komai yanzu ai mama nan dai su Amira ma sukai mata magana sosai akan zaman duniya.
Duk yadda suka yi da mummy ta kwashe ta fada masu komai suka shiga tsinarta da kwashe mata,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
A LOKACIN MUKE,,,,,,
Nocking din kofan take a hankali yayin da take jin sautin kida ya na tashi daga dakin, sai dai ba a da niyan bude dakin a lokacin.
Kara sautin nocking din da takeyi tayi sai ji tayi ana cewa wai waye please ke damuna haka.
Mai dakin tana bude daki sai suka fara kallon kallo a tsakanin su don ba wanda yasan wani a cikin su.
Kina neman wani please ?
Har lokacin tana tsaye ta tare kofan dakin nata ta inda mutum zai iya shiga dakin.
A,a gurin ki dai nazo.
Ni kuma ta fadi cikin dan mamaki a fuskan ta tare da dan sake fuska tana dan kada idanuwan ta cikin mamaki.
Eh duk da dai nasan baki sanni ba amma dai gurin ki din ne nazo ai.
Ok tau shigo daga ciki mana ko ?
A tare suka shiga dakin a lokaci guda suna nuna a jere da junan su.
Kujeran dake dakin ta nunawa Raiha ta zauna inda Raihan ta gane nufinta ta ta zauna kamar yadda ta bukace ta da yi.
Juyawa tayi zuwa ciki sai gata dauke da kwalin juice da cup a hannunta inda Raiha take zaune tazo ta aje drinks din tana cewa bisimillah.
Raiha ko sai bin dakin take da kallo wanda dakin yai mata kama da ta mai zaman kanta ko kuma wace tazo karatu a garin.
Idon ta ya kai akan kwalaben syrup din maye dake saman wani dan table can gefe guda.
Kisha mana bisimillah ko sai takai idon ta akan kwalaben da Raiha take kallo, tace,
Ko kema dai yar hannu ce na miko maki ki surka dasu ne?
A,a barshi kawai ni sai dare nake sha idan zan kwanta yafi min caji don ina gudun mutane su gane ina wanan harkan.
Dariya Nura tayi har fararen hakoranta suka haska daga bakin ta tana cewa.
Kai har kin bani dariya wallahi ashe da sauran ki ke har yanzu dasha da rana da dare ai ni duk daya na dauke su a gurina.
Haka dai kika ce amma akwai banbanci gaskiya baki dai ganewa ne kowa da nashi irin ra,ayin nake gani.
Kurba biyu Raiha taiwa juice din sai ta aje cup din tana kallon Nura cikin murmushi.
Nura tace ni kin barni a duhu ban fa gane kiba gaskiya har yanzu gashi kuma kince guri na kika zo.
Raiha tace eh gaskiya baki sanni ba nima haka Sunana dai Raiha amma mutane suna kirana da Raihanatu musanman ma iyayyena.
Ok ni Nura nake karatu ne yakawo ni wanan garin ina karatu a dan fodio university ne.
A ran Raiha tace shikan karatu kikazo kika buge da harka ke nan a garin da ba,a sanki ba.
Raiha tace cikin murmushi ko kin san Nasir Habbib mai aiki a sokoto cement ?
Nura tace a ranta au budurwan Nasir ke nan ta biyoni don nai mata snatching din shi a gurin ta ko?
Aiko yarinya kinzo gida wallahi don zan maki wankin babban bargo yanzun nan kuwa.
Amma sai ta kyale a fili tana cewa nasan shi kuwa kwarai da gaske anjima kadan ma zaki ga yazo nan ai idan ya taso daga gurin aiki.
Raiha tace good zan iya kiranki da Anty Nura don ko ba,a fada ba nasan kin girmay ni.
Dafatan zaki saurari maganan da nazo maki da ita da kunnen basira batare da kin fassara min zance na ba da wani abu.
Ok ke nake saurare ina jinki ai.
Da farko dai kamar yadda na fada maki sunana Raiha kuma ni haifafan wNan gari ne muna zama a uguwar arkilla ne nida iyayyena.
Sai kuma tai shiru tare da dan kallon saman silin din dakin zuwa dan wani lokaci, Nura tace ke nake saurare fa kada mu bata lokaci.
Ba zancen bata lokaci ai don magana ce mai muhinmanci da zata amfane ki nazo dashi.
Tace ok ai ina sauraren ki ko?
Raiha tace kafin Nasir ya nemay ki ni Raiha ya fara nema amma sai Allah ya tsallakar dani daga mugun nufin shi a kaina.
Kamar ya mugun nufi kuma Nura ta tambaya a cikin mamaki da son karin bayani ga Raiha din
Raiha tace niyar shi na shigewa yan mata ya sace zuciyar su da so da kauna kamar yadda yake maki a yanzun haka.
Amma fa daga baya zaki zo ki sha mamaki don ba nufin shi ke nan ba a kanki.
Nura tace a gatsale Allah ko ?
Hmmm Raiha ta dauki cup din drinks din da ta aje takara kaiwa a bakin ta tadan kurba kadan sai ta juya gurin Nura tace.
Wallahi wallahi ifan bakiyi hankali ba a karshe zaiyi safaran ki ne zuwa kasa shen turawa ya tura ki karuwanci a can ya kuma karbe passport dinki duk gudin da zaki samu sai dai dila ya turo mashi ta account din shi.
"Ke
Kada ki maisheni karamar yarinya mana kedai kinzo da tsigar nabar maki Nasir don ki yaudareni da wanan magana naji tsoro nace ban son ki sai ya koma maki ko ?
Allah sarki babu ko daya wallahi don idan da na yarda da yanzu nima nazama tarihi a gurin iyayyena da yan uwana a nemay ni a gari a rasa inda na shiga.
Amma sai Allah ya kare ni da yake banda rabon wahala nasamu wani abokin shi ya tausaya min ya fada min ainihin gaskiyan abinda ke nan.
Raiha ta mike tana cewa ni zan tafi tunda naga kamar baki yarda dani ba yanzu amma nasan watarana zaki tuna da wanan dan zaman da mukayi dake.
Ni zan tafi kuma ban tsoron ki fada mashi cewa nazo gurinki don yanzu a shirye nake da na tona mashi asiri a harkan da yakeyi .
Ta juya tare da daukan jakarta dake saman kujera tana cewa idan kin shirya saurarena sai ki nemay ni.
Har Raiha takai kofa zata murda kofan Nura tace kinga dawo ki zauna ai bamu gama magana ba tukun ko?
Baki da niyar saurare na shiyasa kina ganin kamar kishin Nasir na tare dake yasani zuwa gurin ki ko?
Ba haka na bane amma akwai wasu yan tambayoyi da zan maki ina bukatan amsa daga gareki in naji su daidai kinyi gaskiya.
Raiha ta dawo ta zauna tana kallon Nura ido da ido tace ina sauraren ki ko?
Hmm wai ma ta ina zan fara tambayan ki ne duk kin sani a caji wallahi.
Duk ta inda kika fara in na sani zan baki amsa insha Allahu.
Ok tau dan Allah kunkai kamar tsawon wani lokaci dashi Nasir din a tare dashi.
Ummm gaskiya mun kai kamar wata takwas muna tare inda a sannu ya fara koya min wasu abubuwa na rayuwa.
Kallon ta Nura tayi da kyau tace hmmm lalai ma amma ce min yayi tunda matar shi suka rabu bai kara neman wata ba bayan ni.
A,a karya yai maki don kafin ni akwai wasu da har yai galaba a kan su yanzun haka suna waje on behalf of him suna karuwanci a Spain.
Kai wai da gaske kike da zancen ki ni yar uwa wallahi ba karya a magana ta sai tsabar gaskiya kawai.
Ok ya taba zuwa dake tafiya ne ke dashi kubar garin nan zuwa wani waje?
Tace kwarai mun je lagos da sunan yatafi aiki ashe yakaini ne gurin yan commuty din su sugan ni idan zan yi sai ya dawo ya shirya tafiya na.
Mikewa tsaye Nura tayi tana fadin ik
n Allah na ko yarda da zancen ki don duk inda muka tafi sai naji ana cewa she is ok,
Very pretty you will get a high level on dis pretty,
Sai da nai mashi magana ya daina kaini ana fada min hakana don ban son jin wanan kallaman daga bakin arna.
Murmushi Raiha tayi tace a can bai nuna maki true color din shi ba ne ko ?
Kamar yaya Nura ta tambaya.
Murmushin takaici Raiha tayi tare da fara fada mata duk yadda yayi da ita a garin Iko din.
Mikewa Nura takarayi tsaye tace umm ummm na yarda da zancen ki gaskiya don nima ya jawo wani abokin shi akan na tarda mu kwana tare dasu su biyu amma bai san ina jin lokacin da suke maganan haka ba sai na bijire mashi tun kafin dare nace period yazo min.
Mikewa Raiha tayi tace nasan koke can akayi shiyasa nasa a saka min ido a kan shi nai alkawarin duk yarinyar da yai niyar batawa sai na kwatota daga halaka hannun mugu azzalumi mayaudarin banza macuci kawai.
Nan suka zauna sukai ta hira akan yadda zasu dau mataki a kan shi don kada yaci gaba da abinda yakeyi.
Tun wanan ranan suka kulla kawance da junan su inda ta rako Raiha tana mata godiya.
****** ********* ******
Tun daga kofa yake kwala wa mariya kira har zuwa cikin gidan, maria wace ke duke tana wanke wanke taji kiran a bazata yai mata yawa.
Ta mike tana fadin gani nan babban Abba lafiya dai ko kira haka daga waje babu kakautawa.
Yace cikin hasala yanzu naga malam a kasuwan mu yake ce min wai yaran nan yanzu basu zuwa makaran ta ko yaushe.
Shi Abba ma sai ya makara kullun kafin yaxo in ma har yaje din yace yai magana yan uwan shi suka ce wai talla yake zuwa.
Tace tallafa tallan may wani kallo yai mata na ban yarda dake ba fa.
Tace ba gaskiya bane in zai yi talla ai ban dora mashi ban fada maka ba balle ma nasan ba yarda zakayi ba.
Shi dai kila yara sunyi mai yawa yanzu bai gane zuwan su da rashin zuwan su shiyasa ya fadi hakan.
Yanzu ina suke ya tambaye ta tare da tsureta da idanuwan shi tace sun tafi tin da karfe hudu suna can.
Yace ai zan tafi nagani ko suna makarantan ya mika mata ledan ce fanen da yayo ya dauki buta zuwa ban daki.
Nan ta samu tafa leken zaure ko Aliyu yana tafe saiko gashi ya sayar rataye da roban shi na talla a wuyan shi.
Da sauri ta tare shi ta karbi roba da kudi tai mashi magana kuskus a kune yaron ya juya da sauri yabar gidan.
Kafin maigidan ya fito ta boye roban da kudin da sauri a dakin kayan su ta kama aikin ta.
Yafito daga ban daki yana fadin yanzu zan tafi nagani idan suna can ko kuma wasa suke tsayawa yi a hannya.
Yafita tana ce mai a dawo lafiya bai amsa mata ba don a cike yake ran shi ya baci sosai.
Don shi bai wasa da hakkin iyalin shi a kan shi don haka yake matukar saka ido akan al,amarin yaran shi dama ita kan ta matar tashi.
Tun daga nesa ya hango su a zaune gaba dayan su don haka sai bai karasa kusa ba ya juya zuwa kasuwa ko zai dan kara samun wani abin tabawa a can.
Kafin ya dawo yaran sun rigashi dawowa gida Aliyu da yuwan taci ta ishe shi abinci yafara ne
ma yaci sannan yai wanka zakace bai tafi ko ina ba .
Taja ma yaran kunne akan duk wanda yace Aliyu yana fita talla sai ta yankewa yaro kauna a gidan.
Bayan maigidan ya dawo ne yake tambayan yaran inda suke tsayawa basu zuwa makaranta da wuri yanzu.
Sai cewa sukayi suna zuwa andai canza masu ajine malam baiganin su yanzu.
Haka yasa yaja bakin shi yai shiru ya yarda da maganan su tunda ya gansu dazun a makaranta sabanin yadda malamin ya fada mai.
Haka Aliyu yaci gaba da zuwa tallan ruwan shi batare da mahaifin su ya fahinci komai ba tunda shi ba mai zaman gida bane ko yaushe.
Haka yaron ke kawo mata dan kudi itako tana bunkasa bankin ta dashi kullun tana farin ciki.
****** ********* ******
Tun ranan da akai wanan rikicin a gidan hankalin Bintu a tashe yake da mutanen gidan baki dayan su.
Ance babban gida babban magana ashe har da ita da take ganin ta kama kanta da kowa a gidan bata tsira ba ga matan gidan.
Don har da zaman ta gurin Maji ya tsone masu ido sai yanzu tagane nufin maji na bata magani tare da sauran diyan ta a baya.
Gashi yau Alhaji da kan shi yake fadin korafin da sauran matan shi sukayi a gidan kan zaman ta da Maji.
Wanda ba komai suke wa kishi ba sai basu kaunan suga ta karu da komai kankantan abu a gidan,
Wanan dalilin gitinan yasa damuwa ya dan fara yiwa Bintu yawa arai sai kafa kafa take da komai a gidan.
Tun da har mai gidan yai mata warning din shiga harkokin mutananen gidan shi da kan, shi.
Sai lokacin take mai jin zafin gwagonta hajiyan masa da tazo gidan mutane ta yar da ita kamar wata wacce bata da uba ko gata.
Da uwarta da uban da ransu a duniya amma yau ta zama,marainiyar karfi da yaji a duniya.
Ba don Maji mace ce mai halin alheri ba da bata san iya inda al,amarinta zai tsaya,ba a,rayuwa.
Amma gashi Allah ya hada ta da mace tagari wace tasan ciwon kanta tasan zafin ta a rayuwa.
Ta rike ta amana tankar itace ta haife ta ko kuma ince wata yar uwarta ta jini can daban.
Yanzu Bintu ko falon maji bata son zama da yawa ko yause tana cikin dakin su a kumshe.
Idan kuma aiki tafito yi zata yishi gudu gudu ta gaba ta kara komawa tashige daki wai ita tana taka tsatsan da kanta.
A haka zancen tafiyan sadauki zuwa kwallon farko da zai fara fita ya buga yazo masu.
Maji bata zauna ba sai faman karban taimako take akan dan nata akan shaye shaye da kuma na tsarin jikin shi.
A cikin hakane maji tace wa yaranta su shirya sukaiwa kakan in su ziyara kafin yatafi don kada sai yatafi su samu labari baza suji dadi ba.
Sadauki bai so wanan tafiyan ba amma ba yadda zaiyi ya zama dole yabi umurnin iyayen shi.
Sai faman shiri suke amma Maji bataji duriyar Bintu ba don ko falo bata fito ba don ba,a shiga makaranta ranan.
Da kanta tashiga dakin na yaran tun zuwan Bintu gidan ko yaushe zaka samu dakin tsab dashi ba wani datti a cikin shi kaman baya can da dakin yake motsutsu kowa na kyashin gyarawa .
Kwance ta samay ta ta kifa kanta a saman filon da ta ke akai.
A hankali maji takira sunan ta,da Fatima abinda ya dan sata firgita ke nan don bata san da shigowan Maji dakin ba a lokacin.
Cikin dan firgita ta amsa da na,am mama tare da saurin kokarin mikewa zaune daga kwanciyan da take.
Zama maji tayi daga gefen ta tare da dan kura mata ido tana cewa waiko lafiyan ki kalau kuwa Fatima?
May ke damuwanki ne duk kwanakin nan kin koma,shiru kina kuma nisanta kanki da kowan mu?
Dan murmushi Bintu ta kirkiro a fuskanta tana cewa ba komai mama kaina ne ke dan ciwo shine nadan kwanta.
Tun yaushe kanki ke maki ciwo baki fada min ba fatima baki sha magani ba yaya zaki ji sauki.
Shiru Bintu tayi tana fadin dama gashi zamuyi tafiya zuwa garin mu gobe tunda safe gashi kuma baki da lafiya.
Don haka dole na barki nan har mu dawo don ba,a daukan ciwo akai kauye.
Da sauri Bintu ta daga kai ta kalli Maji, sai kuma ta dukar da kanta don bata iya jure kallonta ido da ido haka.
Maji da ta fahinci may Bintu take nufi sai tace kada ki damu ba,a nan zanbarki ba gurin hajiya kubura zan barki don kwana biyu zamuyi mu dawo insha Allahu.ko kuma guda yadda dai tafiyan namu ya kasance don wanan mai tafiyan.
Bintu ta kara kallon Maji alaman ranta baizo hakan ba take cewa mama da abarni ko anan din zan iya zama ai.
A,a haba Fatima yaya zanbarki karaman yarinya dake a daki ke kadai kuma gashi ko lafiya,bai isheki ba ma.
Kada ki dmu nasan zata rike ki da kyau har mu dawo daga tafiyan, kamar Bintu tace taji sauki zata tafi amma kuma sai take cewa tau mama.
Maji tamike tana cewa don haka saiki shirya kayanki wanda zaki dauka tun yau ki koma can.
Bintu tanaji tana gani Maji da kanta ta dauki dan jakar kayan ta zuwa dakin hajiya kubura.
Nan suka dan zauna suka taba hira a tsakanin inda tai mata sallama dacewa gobe asubanci zasuyi zuwa tafiyan su.
Hakan akayi don koda gari ya waye har sun tafi ko don can ne kauyen Niger state iyayyen ta suka koma da zama don noma.
Bintu bata farka,ba don maganin da tasha mai sa barci sai zuwa takwas na safe lokacin har hajiya kubura ta shirya zuwa gurin aiki tana cikin uniform din ta.
Dakin da Bintu take ta leka tasamay ta zaune tana lazumi ta idar da sallah a lokacin.
Kin tashi Binta ya jikin naki Bintu ta amsa a sanyaye da Alhamdullahi ga breakfast din ki a falo idan kinyi wanka sai kici ni zan fita sai na,dawo.
Sai kindawo mummy ta bata amsa tare da kokarin mikewa da ga saman abin sallah da take zaune akai.
Zuwa rana kadan ta dan samu sauki nan ta mike tafara gyaran part din sai da taima ko ina tsab a part din sai bedroom din mummy ne kawai da ke a kulle bata gyara ba.
Tana gamawa tashiga tai wanka bayan tafito ne ta dan zauna sai kuma tai tunanen kada su dawo da yaran ta basu samu abinci ba.
Kitchen din ta shiga inda ta samay shi sabanin na Maji don wanan komai na zamani ne a cikin sa.
Ga kayan abinci na kala kala babu abinda babu cikin sa komai gashi kamar ba saye akeyi ba.
Ta yanke shawaran tai masu tuwo don taga kullun yaran ta na zuwo rokon tuwo a gurin maji don ita bata da time din tukawa ko yaushe busy take.
Nan ba bata lokaci ta girka tiemwon shinkafa da miyan agushi da manja tai amfani da naman da tagani a fridge din.
Gashi ranan girkintane ta kwashe a wani kula da bai saurin sanyi takara hada masu pepper surp din kayan cikin rago da drinks din hannu na kayan fruit din data gani a kitchen din.
Takara gyara gurin ya koma tsab takoma daki ta kwanta sai yamma mummy tadawo da yaran ta inda tun a,wajen part din ta soma ganin canjin yanayin shiyan nata.
Tana shiga dakin gaba daya taga duk ya canza mata sai ta tuna da lokacin da take amarya a gidan komai nata tsab yake a lokacin.
Ba irin yanzu ba da,bata da lokacin tsayawa gyara komai kamar yadda ya dace mace tana gida tayi.
Yaran suna shiga daki suka fara ihun da murnan ganin yadda komai nasu ya canza a lokaci guda.
Dan karamin sune yafara maganan abinci Bintu dake fitowa daga dakin da take ciki take cewa Anwar zo ga abinci can kazo kaci taja hannin yaron inda ta tsaya daga kofa tanawa mummy sannu da dawowa.
Mummy tace Bintu ke da baki da lafiya kika sha wanan aiki haka sannu da fama nagode.
Tana fitowa taga Anwar a hannun ta take cewa kaikuma may yafaru Bintu tace wai abinci zaici.
Uwar tace kaida andawo kace zakaci abinci har yaushe muka dawo na girka maku abinci.
Bintu tace a sanyaye mummy ai na yi girki tun dazun ma nagama bari na debo mai.
Da mamaki uwar tace kinyi girki Bintu bayan wanan uban aikin da kikasha haka.
Murmushi Bintu tayi ta juya rike da hannun yaron ta debo mashi abinci ta zauna tafara bashi.
Saiga Mummy tafito daga daki idon ta ya sauka akan plate din da yaron ke cin abinci take taga mai Bintu ta girka masu.
Wani irin dafi ne ya kumay ta tace kai amma wanan yarinyar Allah yai maki albarka.
Nan tashiga kitchen ta samu komai tsab kamar ko ina mamakine ya kama yadda karamar yarinya kamar Bintu tai irin aiki haka mai yawa ita kadai.
Gashi kuma,ba lafiya ne take dashi ba ajikin ta take taji kwadayin zama da yarinyar ya kamata don irin haka take son yaron ta dashi.
Ba,wani abinda aka taba mata ko aka lalata hatta sharan da tayi bata zubar ba ta tara a wani roba har mummy din tazo tagani idan babu abinda take so daga ciki dai a zubar dashi.
Haka mummy ta dinga jin dadin zama da Bintu kamar kada uwar rikon ta tadawo take ji.
Suko matan gidan ai nan gulma ya fara tashi akan zaman Bintu gurin Hajiya kubura na kwana biyu kafin maji ta dawo don ance babban gida ba,a raina dan magana kadan,,,,,,,

A LOKACIN MU KE,,,,
Washe gari da safe sadauki yana dakin Maji saman dogon kujera ya dan nade hannayen shi a saman kirjin shi idanuwan shi duk suna a lumshe, zakace barcin safe yau yake a falon mahaifiyar tashi.
Duk zirga, zirgan da sisters din shi keyi yana jin su sai dai idanuwan shi a,rufe suke still zakace barci yakeyi.
Maji ta,shigo dakin daga part din maigidan take, tana ganin Sadauki a falo tun da farar safiya haka sai taja tai turus tana kallon shi cikin mamaki.
Ba tare da ya sauke hannun shi dake saman fuskan shi ba, ya ke cewa Maji barka da asuba, jin haka,ya,sata sauke ajiyan zuciya takarasa gare shi cikin yanayin mamaki.
Yau kuma a,nan kazo ka,kwanta muna da,safe haka ko har yanzun kana kewar namu ne.
Murmushi kawai yayi wanda har yakai ga sauke hannun shi da ya kare fuskan shi dashi da,farko.
Maji bana son Baba ya fita bamu gaisa da,shi ba shiyasa na zo nan nake jiran ya,shirya sai na shiga gurin shi mu gaisa.
Maji ta,karaso cikin dakin tana fadin a to tin dai jiya naji ya fara tambayan ka idan ka wuce yanzu za,a jiku dashi,
Yace cikin kara kwantar da kan shi bama za,a jimu ba insha Allahu maji,
Maryam ce ta katse su da fadin Maji tun dazun nake jira kizo sauran madaran da ya,rage shine Bintu ta dauka wai tana hadawa yaya tea dashi .
Kai maryam baki da hakkuri wallahi jiyane fa kayan tean namu ya kare shine har kin fara raki haka.
Sai a lokacin ya daga idanuwan shi da,sukai ja yake cewa No ni kubar shi bazan sha tea ba,sauran tuwo nake son ci ni.
Yana kokarin tura hannun shi cikin aljihun wandon shi ya ciro kudi masu yawa yace wa marya karbi jeki sayo maku kayan tea ku karya kafin na,fita.
Tana mika hannu zata karba ne, Maji ke fadi kai haba Sadauki na fada maka ka daina wanan kashin kudin haka.
A hankali ya mike zaune da kyau yana fadin no maji ai wanan ba komai bane ki barta kawai ta sayo masu abinda zasu karya su fita.
Anjima idan na fita zan sayo masu abinda ya dace a saya din yanzun dai tafi ki samo wanda zaku karya dashi
Cikin mamaki yarinyar take cewa ai nan har dubu uku naga ka miko min yace baza su isheku bane ko yaya.
Gaba daya suka mayar da hankalin su gare shi cikin mamakin yace a kashe dubu uku a lokaci guda kan breakfast kawai.
Ke miko min kudin nan nan ki je ki sayo maku komai na dari biyu ki kawo canji wannan bai san ciwon kan shi ba.
Ta juya gare shi yayin da take karban kudin hannun maryam tana fadin.
Jiya kaje ka yi barnan kudi kunyi yadda ranku ke so yai kuma shine zaka wani ce wai su sayo kayan tea da wanan kudin haka masu yawa.
Murmushi ya dan sauke yana cewa No maji ki bata kada ki damu don wanan kawai don Allah basu su sayo abinda suke son saya.
Sauran sai su hau Napep da shi zuwa makaranta ya mike yana cewa Baba din yafito falo ne Maji tace yana falo na barshi yana karyawa ne.
Shi kadai ne zaune a falin nashi yana karyawa da,sauran tuwon da aka gyara mashi, na,daren jiya,
Bawai rashi yasa ahi cin abincin ba a,a ra,ayi dai ne kawai yafi son yaci dumamay da safe wai yafi rike mai cikin shi.
Falon na,Baban nasu yana da,dan tsarin shi xon tsari irin na,falon maza masu dan abin hannun su irin na da can baya.
Duk da zamani ya,sauya bai sa Baba canza tsarin falon nashi ba a hake yakw zama da abinshi duk da,akwai halin canzawan amma,bai canza ba.
Sadauki ya, shigo falin da,sallaman shi ya samu guri ya zauna tare da,gayar da baban nasu cikin ladabi da,biyayya.
Baba ya amsa tare da fadada murshin dake fuskan shi na jin dadin hango tarin natsuwa daga dan shi sadauki.
Baba,yace cikin yar tsokana haba dan kwallo kai kuma sai kawai ka bace wa mutane daga dawowanka jiya.
Ga shi tun jiya ina zaune ina jiran kazo nasha labarin yadda kwallon ta kaya maku a can don bamu da wani labari ko kunyi nasara ga tafiyan naku.
Cikin dan murmushi Sadauki yake cewa Baba munyi nasara da yardan Allah mun samu shiga nida abokaina da mukaje, wanda basu samu shiga ba kadan ne kuma ba musulmai bane su.
A to Alhamdullahi masha Allahu abu yai kyau gaskiya sosai haka muke son ji dama ai tafiyan nasara.
Sadauki ya dan lumshe udon shi don jin yadda mahaifin shi yake farin ciki yau da,samun nasaran shi a fili.
Shigowan su mama,Asiya da Umma da suka ga shigan sadauki gurin mahaifin shi shine suka shigo don suji kwam.
Haka yasa fuskan Baba ya canza a lokaci guda daga fara,ar da suke shi da dan shi.
Don yasan shigowan su a tare haka da biyune suka shigo don basu shiri sai gurin sheri.
Ganin shigowan su fuskan mahaifin shi ya canza ya fahinci mahaifinshi bai ji dadin hakan ba,
Don haka ba,tare da,sun tattauna komai ba kamar yaddaa sukaso yi ya mike yana fadin Baba ni zan fita adawo lafiya.
Har yakai kofa sai Umma take cewa kai baka iya gaisuwa bane ko may ne koko zuwa kwallon kara zama dan iska ya mayar da kaine wai?
Haba Maimuna a kulun kalamin ki akan yaron nan babu dadi wallahi yanzu may yai maki kuma kike kokarin yi mai wanan zagin haka.
Tau fa ai na manta dan Baba dan masu gida na ke wa fada don Allah ayi hakkuri kada a zageni nima don na,zageshi.
Hmmm Alhajin yace cikin murmshi tare da,girgiza kai yace bana son ki,da,wanan halin wallahi
yaya ke nan yanzun fa kin san dan kwallo ne ba,a wasa da al,amarin shi kuma
Umma ta lailayo wani ashar tace kwallon kaza kazan uba masu kwallo suna abin arziki ai an san inda suke ba masu zuwa tafe ba,a bayan fage.
Daga Alhaji har sadauki dake kofa yana daura igiyar takalman shi a kafan shi sai da ya,dan murmusa kadan.
Don jin abinda Umma tace mashi, Alhaji yace cikin murmushi a naku irin hasashen kuke ganin bai koyo komai ba, Amma aini Alhamdullahi don naga haske ga wanan tafiyan na sadauki a gidan nan jiyafa tare mukai sallah magariba dashi a massalaci.
Mama,Asiya ta cabe da cewa mu dai yadda akaje haka aka dawo muna don haka bamu ga wani abin yiwa mutane rawan kai ba a nan.
Mu dai in muga yaro ya kara lalacewa wallahi dole a,dauki mataki a gidan nan don ba,zamu zauna da irin mahaukata ba kullun hankalin mu a,tashe cikin gida.
Maji dake bayan su ta shigo kwashe kayan abincin da takawo wa baba tana jun komai a kunnen ta.
Har ta dauki kayan tabar dakin batace masu kalla ba sai ma dan magana akan kudi cefanen abinci ranan da zata girkawa Alhaji takeyi.
Inda sai a haka take dan samu canji ya rage ta danyi wasu lalurar ta dashi.
Anan tabar su suna wa Alhaji magana akan zuwan sadauki kwallo gari ya gari har ghana amma bai tsinano uwar kowa ba a can.
A kofa shima ya hadu da hjy kubura dake bayan Maji gurin shiga part din mai gidan nasu.
Hjy Kubura tana ganin shi sai ta fadada murmushin a,fuskan ta da dan fara,a takw cewa a,a mayan yan kwallon mu, ke nan ya gajiyan hanya yace Alhamdullahi mummy.
Ta shige tana mashi wasa shikuma ya juya zuwa dakin mahaifiyan shi wanda bai dade da shiga ba ita ma tashigo dakin dauke da kaya a hannun ta.
Koda Sadauki ya shigo falon mahaifiyan shi zama yayi tare da hade kai da gwiwa cikin damuwa.
Bintu ce ta kai hankalinta gare shi ta karaso gare shi tana fadin yaya akawo ma abincin ne yanzu.
Akwai kuma koko da kosai mai zafi an dama yanzun nan wa Baba sai a hado ma dashi.
No ki barshi kawai ya bada,amsa tace tau ko a debo maka kunun kasha kawai don tasan kamar mahaifin shi yake gurin son koko da kosai da safe.
Cikin nuna gajiya da tambayan ta yake bata amsa da fadin ke ban son komai please ki barshi nace ko.
Maji dake daga bayan su take cewa haba ina laifin ta, don taga su kafi damuwa dasu shine take maka tayi mana.
A hankali ya dago yana kallon inda Maji take yake cewa bana jin ci ne fa shiyasa kawai.
Ya sadauki kaifa kace zakaci saura yanzu shine nace Bintu ta gyara maka Amira take fadin haka.
Yaya halan anyi ma wani abu a falon Baba ke nan ko maryam ce take mai wanan tambayan.
A sanyaye yace ba ai min komai ba maryam kawai dai gajiya ce ke damuna kawai.
Yaya kun gaji da yawa kwallo ai ko na,wasa ne akwai gajiya balle irin naku na kuke na kuke sai anci.
Yayi murmushi yace ai dama shi kwallo ba hutu bane motsa jikine kawai cikin shi.
Bayan fitan yan matan daga gidan kowa ta tafi makaranta, matan gidan kuma sun futa aiki, ko haka yasa maji samun daman kebewa da dan ta don ta kara mashi nasiha akan irin rayuwan da yake dake jawo mata magana da gori.
Sosai tai mashi nasiha mai ratsa jiki akan duk wani al,amarin dake gudana a gidan takw ce mashi bata taba sa al,amarin gorin arzikin dasu yaya suke yawan yi min shi ba,agidan nan a raina.
Nabar wa Allah al,amarina don shi da ya halicce ni yasan dalilin da ya yi mu a haka.
Dara daya idan Allah yaso sai a wayi gari si gan mu yadda ba su zata ba,a,rayuwan su yace hakane maji.
Tace amma fa hakan ba,zai samu ba gare mu sadauki sai ka mayar da kan ka abin kwarai a,gurin Allah.
Don kai yanzu kamar uba kake agare mu baki dayan, mu ni da yaran nan, sai dai kuma hakan ba,zau samu gare mu ba,sai ka,zama kamili, mai addini, gujewa sherin shedan akoda yaushe.
Haka,zai sa mu cin wa manufar mu da muke fatan samu a,gare ka.
Don Allah sadauki ka,tausaya min ka,taysayawa rayuwanka,ka mayar da kanka tsarkaken mumuni dan albarka a cikin al,umma idan kai haka,ni wallahi ka gama min komai wallahi.
Yana zaune yai shiru yana sauraren hudubar da mahaifiyar tashi take mashi akan sanadiyar irin sake maganan da,ake ta,mata daga kishiyoyin ta,a,tsakar gida har da yaran su ma.
Wanan nasihan na maji da tai mashi yasa shi jin wani irin sauki a zuciyar shi kodon kalman Allah yai maka,albarkan dataita nanata mashi ne tare da neman masu shiryuwa na,alherin a rayuwan shi da,daukaka mai albarka.
Da,dare ba karamin farin ciki sadauki ya tsinci kan shi a ciki ba don duk wani abin da yake ji cikin zuciyar shi yanzu ya,kau mashi aran shi.
Hakane ma ya bashi dama,daga kwance yake kasafin irin abinda yake son yaiwa mahaifan shi don su fara,alfahari dashi a,rayuwan su.
Su dai mahaifan shi murnan su kawai suke da,farin ciki akan dan su yaje lafiya ya kuma,dawo masu lafiya yadda suke fata.
Fatan kawai dama Allah yasa wanan wasan da Allah ya,nufe shi da,zaiyi ta nisanta,shi daga,akidar shi ta,shaye shayen da ya,fara nisa a cikin sa.
Gashi kuma,da,alama Allah ya taimake su akan haka don dai ko bai bari ba ya dai rage kan don yanzu ya,dawo kamili salihi dashi ba kamar da can baya,ba da ko su sai sunyi da gaske akan shi zaiji.
Wanan rashin nuna,damuwa da,abin duniyan da,ake tsanmani daga masu irin fita wanan wasan kwallin da mahaifan shi suka,nuna mai ya kara sa,shi sanin cewa shi din dan gatane na kwarai.
Sabon halin da,ya,tsinci kanshi aciki ma shaye shaye shi ya kawar mai da gatan shi a gare su .
Adinin mu da,al,adan mu duk sun kyamaci mai wanan irin halaiyar tashi ta shaye shaye.
Wasu hawaye masu dumi ne suka dan zubu mashi daga idon shi yai saurin mayar dasu a inda suka fito.
Nan dai ya yanke hukuncin duk wasu tdare tsaren da ya dade yana planning din su a ran shi yana ganin komai ya tafi mashi yadda ya dace.
Kwanan shi biyar da,dawowa yafita daga gida tun safe bai ko shigo ya karya,ba.
Haka yasa hankalin Maji ya dan tashi don tasan yanzu yana gida ko yaushe bai fita waje.
Amma yau ga abin karyawan shi bai shigo yaci ba ga kuma na rana har ana batun kare girkin dare kuma again.
Haka yasa ta kasa daurewa tana jin shigowan Imirah gida don shi ke fara dawowa daga kasuwa ko yaushe, da kayan cefane da dan abubuwan da,suka sayo na gida.
Maji tafito inda yake tsaye yana,ba Umma sako tace a Imirana an dawo lafiya yaya kasuwan?
Ya amsa da Alhamdullahi a takaice kawai,
Maji tace don Allah Imirah ko dan uwan ka yana kasuwa ne tare da ku don bai shigo gida ba tun dazun da safe .
Yace waye dan uwa na Maji?
Duk da tambayan ya bata mata rai amma sai ta share ta,dake a ran ta tace mashi Sadauki.
Kafin yaba da amsa Umma tace, dan uwan shi don Allah gyara hausan ki mana.
Kada ki sa mashi bakin jini da zargi ga mutane, ace ko tare suke shaye shaye dashi.
Imirah yace haba Maji, may kuma zai kai Sadauki gurin ni tunda harkan mu ba daya,ba dashi.
Maji tace Allah sarki ai zatona yana tare da kune a can kasuwan, kasuwan kan ba gidan yan maye bane ai.
Ba ta dai juyo ba ta koma part din ta inda dama daga itace sai Bintu su Maryam basu dawo ba tukun.
Ba,a jima ba suka shigo dawowan su ke nan daga makarant alokacin, sai suka shiga neman abinci.
Maryam da tafita waje ta samo ruwan sanyi don sai sun saye basu da fridge a part din su.
Nan ta samu Umma nata fada dan may za,ace wai Sadauki dan uwan Imirah ne ganin maryam bai hana ta fadan da takeyi ba.
Maryam na dawowa take cewa halan anyi wani abin ne wai naji Umma na tafada wai dan shaye shaye don rainin wayo za,ace dan uwan tane.
Bintu ce tabata amsa tace kin san basu da tunane da mama take fada wai don ta tambayi yaya imiranah yaya sadauki da,bai shigo gida,ba tun da safe yau.
Ikon Allah shine kuma abin fada inji Amirah cikin nuna mamaki karara a fuskan ta.
Komai fadan su dai ai ba,a raba anta da jini ko? Don basu san cewa wata rana suma abin zai iya shafan su ba ko,
Nan Amira take ta fada ran ta a bace basu san shigowan shi ba sai ji sukayi ana cewa wai kedawa ke fada haka ne Mira,
Tace hmmm ashe ma ka dawo yaya nida su Umma mana da basu so a zauna lafiya.
Nan take fada mai abinda ya faru shiru yayi baice komai ba suma dai din hakan ne.
Maji tafito da alwala tana mashi kallin mamaki tace kai ina ka,shige yau haka ne.
Yace maji wallahi ina cikin gari kayan mune ya iso shine naje nai clearing din su a gurin da ake saukewa.
Kaya kuma wasu irin kaya ne haka yace cikin wasa yana wuce kayan yan kwallo mana maji.
Kai kan da kwallo Allah ya inganta kawai, don ya zama maka jinin jiki ko?
Fatima kawo mashi abinci kinji tun safe mutum bai karya ba yana gurin zancen kwallo kawai aranshi.
No Maji gaskiya,abar abincin nan don sha dan drinks a can kada naji yunwa saidai anjima da dare zanci.
Yaro ke fadin wai ana sallama da Umar UF a waje, inji wani mutum.
Mikewa yayi yafita saida Maji tai mamaki take cewa a ranta yau kuma Sadauki akewa sallama a gidan nan.
Allah dai yasa mutumin kirki ne ba abokan shashancin shi bane suka fara biyo shi su mayar dashi ruwa.
Amira ce ta sako zancen abinda Umma takeyi na kokarin raba su da yan uwan su don ganin su basu da komai wanda yakai ace sun hada alaka dasu.
To koma maye ai dai ai su yan uwanku ne kuma duniya ta sani to may ye abin damuwan kai a ciki uwar ta,basu amsa.
Kafin tai magana sai ga sadauki ya shigo yana zama yake cewa Amirah gobe zaku shiga school ne da safe.
Wani abin kake so ne yaya, ya na,gyara zama yake cewa bani amsa mana kafinki min halinku na yan Nigeria.
Tace idan da abinda zanyi sai na bari sai jibi ko na shiga yace dana gode sai yai shiru daga haka bai kara magana ba suke tahiran su kan wata yar uguwar su.
Dawowan Alhaji yasa Maji fita tabar su don zuwa gaidashi kamar yadda ta saba, Sai da ya mike, tsaye bayan fitar mahaifiyar su, yake cewa don Allah Amira gobe ku kwashe kayanan gaba daya kufita dashi kafin nine na safe.
Amma kada ki fadawa maji yau sai goben kawai taga kuna kwasa please angama yaya tace mashi do ita kadaice a falon lokacin su maryam da Bintu suna ciki.
Maji na,shigowa bata ga sadauki ba take cewa,a,a shi kuma wanan din ina,ya tafi ne wai,?
Bai faci abinci ba yau gaba daya Amirah tace yako fita ina ganin saida safe ke nan, nan Maji tasawa maryam da Bintu kira tace su zo sukaiwa yayan su abincin shi a dakin shi.
Tai hakane don tagani idan yana gidan ko yafita don in fita yayi to gaskiya zancen ya fara baci ke nan kuma.
Zun dauki abincin zuwa part din samarin gidan tun daga,nesa,suka gane yana cikin dakin nashi don wutan dakin da yake kunne a lokacin.
A hankali ta kwankwasa kofan don itace a gaba maryam hankalinta yana kan wayan ta.
Sadauki wanda yake zaune dakin shi yana karatun wani littafi mai ban tausayi yaji nocking din kofan shi mamakine ya kama,shi don dama har ya rufe daki ko.
Don haka ya taso ya bude don yaga wanda ke kwankwasa mai kofa a wanan lokacin haka.
Daga shi sai yar singileti da gajeren wando irin da maza ke kwanci dashi da dare idan zasu shiga kwana.
Bintu ce yagani da kayan abinci a hannun ta ya zuba mata ido baice mata komai ba.
Ganin yadda yake yasata dukar da idon ta kasa tana cewa Mama ce tace mu kawo maka abincika nan.
Dan guntun tsuki yaja yace banace na koshi ba shine sai an biyoni dashi har nan kuma.
Bai sanda maryam suke ba,saida taimagana daga bayan Bintu tace kasan maji in bakaci ba hankalinta bai kwanci ai.
Maryam na koshi wallahi yanzun na,rage yawan cin abincin nan sosai don gudun kada nai nauyi da yawa na,kasa yin wasa kuma.
Yace shiga ki aje min daga ciki, yadan jaye mata a hanya Bintu ta shiga ta aje mai a bakin katifan shi da sauri tafito bata sab yana gap da ita ba sai ji tayi tayi karo dashi.
Tsaki yaja yana fadin ke dai yar kauye ce wallahi ko baki ganine zaki tureni haka kamar baki da ido.
Yi hannkuri ta fadi cikin dan muryanta kamar zatayi kuka shi dai ya kauce mata ta,wuce ta gaban shi yai tsaki yace yar kauye kawai da ita.
Maryam dariya take take cewa kai Bintu ke dai matsoraciyace wallahi kamar wace za,a kama ko tai laifi.
Har suka shigo gida Maryam tana mata dariya take basu Maji labarin abinda ya faru.
Maji tace wallahi in yana kiramin yarinya da yar kauye sai na bata mashi rai Allah, duk wanan kokarin da yarinya ke mashi baya gani.
Washegari kamar yadda ya umurci Amirah dayi haka,tayi don ta,tayar da Bintu suka,fara aiki don ita a,zaton ta fenti zai sa ai ma,shiyan nasu.
Matan gidan kowa tana fita daga gidan daya bayan daya zuw gurin aikin su inda suke gulma a ran su cewa, kullun sharan daki kamar wani tsiyane cikin shi.
Mani dai a zaton ta gyara kawai yaran keson yiwa shiyan don karan kan su kawai.
Tara da yan mintina sukaji muryan sadauki yana cewa wasu mutane ku shigo dashi nan.
Set ne na kayan gado tare da masu hakawa aka,shigowa Maji din dasu nan masu aiki sukansuka fara aikin gyaran guri kamar yadda ya dace.
Labule sabbi, kujeri set masu dan karen tsada, fridge sabo dal dashi a kwalin shi, TV plastama babban size din sai center carpet mai laushi duk a falon.
Dakunan ta duka ukku an saka sabbin gadaje a ciki don shi ana shigo da kayan ya fita abin shi waje, bai shigo ba,balle maji da imani ya cika ta tambaye shi inda wanan abinda bata taba mafarki ba ya fito masu.
Kafin karfe biyu masu wanan aikin da yake aikin su ne har sun gama komai ko nan su Amira suka karasa sauran gyaran da yarage masu.
Sai uku ya shigo gidan da ghana most go manya manya har guda hudu niki niki dasu aka zube su a falon Maji.
Maji tace Sadauki zonan cikin damuwa da rudani take tambayan shi ina ka,samo wanan kaya haka.
Ya lura cewa ta,shiga tashin hankali yasa shi zama kasa gap da kujeran da take yace Maji ko kin manta kin gura danki tilo guda sadaukar da ranshi wa kasanshi ne.
Yace abinda kika yarda shine alherin shi ya fara zuwa maki a yau din nan duk abinda zan samu ga,wasan da nakeyi Maji nakine ke da yan uwana gasu nan.
Sai mahaifina da kuna kakannina da suka nuna min hanya madaidaiciya da ta dace dani.
Don haka kwantar da hankalin ki Maji dankine ya,fara kawo karfi lokaci yayi da zamu fara shiga mutane muma ayi damu.
Maji yau ina matan gidan nan suke?
Duk sun fita gurin neman na kasu da rufin asirin diyan su, amma ke kina gida kina masu bautan da basu gani har abada.
Idan na samu bakiji dadin ba Maji ai ban haihu ba gare ki.
Wasu hawaye ne masu dumi suka zubo mata don abin kamar a mafarki take ganin shi a ranta.
Ji yayi ta dafo kan shi abinda ta dade batayi mashi ba tun yana yaro in zasu tafi makaranta take mashi haka.
Takance Sadauki Allah ya tsare min kai Allah yabada sa,a Allah ya daukaka min kai Allah ya albarkace ka da arziki ta hanyar alheri.
Yau ma da yaji ta dafa mashi kai yasan maka manci haka za,ayi sai yaji tace.
Allah nagode ma daka azurta min Sadauki ta hayan daka zaba mashi a rayuwan shi.
Ya Allah ka tsare min shi ka kare min shi daga duk wani abincutarwa da kuntatawa a,rayuwan shi Allah ka albarka ta min wanan yaron fiye da tsamanin mai tsanmani,
Ya Allah ,,,,,,, sai kawai kuka mai karfi ya subce mata ta kasa karasawa abinda tai niyar fadi daga karshe sai a cikin ranta tafadi Allah ka,azurta shi da zuria masu albarka.
Bintu ce mai karfin halin amsawa don duk kuka suke adakin gaba dayan su har ita Bintu din dake kallon ikon Allah.
Saida sukaci kukan shi ne ya,fara yin shiru cikin su yake cewa Amira dauko jakarcan na baya ki bude.
Tajawoshi dakyat zuwa gaban su inda ta bude turamay zannuwane irin na kasar ghana ciki makil dasu.
Yacd tajawo dayan kuma shima dogayen riguna ne na yan mata acikin sa su takalma da hand bags, nan suka,rude suka shiga fitarwa,
Dai dayan shadda ne ciki masu tsada suma dayan kuma kayan kantine nashi da yan kanneshi kana yasayo masu.
Nan ya,ware wa kowa naahi kason kamar yadda yasayo su tun can ghana din.
Maji tai matukar jin dadin haka a,ranta don yafara da yaddaya dace duk da nagari yayi yasamu yan uwa su sheda.
Tasan Allah ya hore mata da nagari wanda yasan zafinta da darahan ta a idon duniya ke nan.
Yace ban sayo maki kayan kitchen ba don ban san kayan da kuke so ba sai a saya a nan kawai.
Maji tace a,a dakata ko wanan ma sun isa haka wallahi.
Saidai banji ka fadi may kaiwa mahaifin ku ba har yanzu don baiyuyuwa ace ni kai min haka amma shi banji nashiba.
Yace Maji na Baba daban ne nasan ya dade yana son harkan noma don haka noma nake son yafara bana sosai akwai kudin da zan bashi wanda zai dan isheshi yafara dasu.
Allah yai maka albarka sadauki takara fadi a fil kowa yace amin cikin jin dadi da farinciki.
Gardama ya fara a tsakanin Amira da maryam gurin rabon kayan su nan ya fitarwa kowa da wanda ya sayo mata ya mika masu.
Bintu dai tana gefe tana kallon ikon Allah da jin dadin uwayen dakin ta ganin farin ciki ya sauka masu yau.
Maji tace ban fa gane ba sai duk suka joyo suna kallonta don jin may zatace dashi.
Tace naga kayan su Amirah amma banga na diyana,ba mana ko ita ba yar uwarka,bace.
Shiru sukayi gaba daya don su sai a lokacin kan su ya kawo wuta ga hakan.
Shiru yayi bai bata amsa ba kamar badashi takeyi ba ma sai da takara tambayan shi ne yake cewa ban sayo da itaba Maji.
Don may sadauki shiru yayi kawai yana dakilar wayan shi bai bata amsa ba.
Ta juta gurin su Amira tana ffadin ku miko min kayan nan a,kasa uku kowa ya kwasa.
La Mama don Allah kibar masu watarana idan ina da rabo za,a sayo dani ai.
Ba zaiyuyu ba gaskiya ku miko min nan kawai kunji tafada cikin bacin rai yace Maji bar masu sai a sayo mata a nan.
Amma maji bata saurare shi tai masu jan ido suka miko kayan inda ta raba daidai ta cirewa Bintu suna ta bata rai don may za ai masu haka.
Waya ma dole bai basuba saida dare ya shigo da guda hudu sai dai na Bintu baikai nasu kudi ba.

A LOKACIN MU KE,,,,,
Yau kwana arbain da,wasu yan kwanaki da tafiyan Sadauki don haka a wani yammaci Alhaji ya dawo kasu Maji ta tafi gaishe shi yake ce mata.
Maijidda kunyi waya da Umar yau kuwa tace bai kira mu ba don kasan kiran shi nada wahala ta nan.
Indai ba shine ya kiramu ba ni ban faye kiran shi ba gaskiya, ya dan juyo yana kallonta ciki kada kai yace haba maijidda ya wuce ki kashe dubu daya da dan kai gurin jin lafiyan shi kawai.
To Alhaji kudin fa ai yazama cacan kudi kulun gaskiya ace dubu dubu haba dai idan dai ya kira muji lafiyan shi ai.
Yace tau yace min insha Allahu gobe zai karaso gida don yau jirgin su ya,sauka Nigeria da safen nan.
Wani irin murmushin jin dadi Maji ta sauke a lokaci guda afili kuma tace Allah ya kawo muna,shi gida lafiya.
Alhaji ya amsa mata da Ameen yace da farko naji tsoron tafiyan yaron nan amma kinga da muka,bar ma Allah zabin shi gashi har sunje sun dawo lafiya.
Maji tace a hankali Alhaji nafika jin tsoro don ina gudun yaje ya kara hinjire muna a can.
Ai kawai al,amarin daga Allah ne maijidda don dai ni san ba wai r
ashin tarbiya bane ya jefa yaron nan cikin wanan yanayi.
Jerabawa ne kawai daga Allah ya zo min ta hanyan shi wanda mafi yawan mutane yanzu kowa da kalar tashi jerabawan da,ake jarabtar shi dashi.
Allah ya sauwaka Maji ta fadi a fili tareda mikewa don tabar dakin don tasan idan takai wani lokaci a ciki yana iya zama masu matsala da maigirkin ranan watau mama Asiya.
Ta koma dakin ta ta samu yaran ta kowa da waya a hannun shi suna dakala.
Sai Bintu ce da bata da waya ta ke zaune tana karatun littafin islamiyan ta da take bita.
Shigowan ta yasa su dan dogo kai suna kallon ta don sun saba idan ta je gaida Baban su tadawo suna kallon yanayin ta idan bada bacin rai ta,shigo ba don gudun ace yayan su ya aikata wani abin asha kuma.
Sai dai sunga tsatson farin ciki a fuskan ta inda kafin su tambaya take ce masu Amirah ance gobe insha Allahu yayan ku zai dawo garin nan yau sun sauka lagos gobe zai karaso gida da yardan Allah.
Gaba dayan su dadin wannan labarin sukaji don sun san tun da har yakai warhaka kuma ance sun dawo komai ya tafi normal insha Allahu .
Ba kamar yadda suke daridari ba da farko don gudin kada yaje yai shaye shayen shi a koro masu shi.
Washe gari tun da safe suka fara dan gyaran wuri da kuma yi mashi abinci na musan man dan taron shi.
Maryam ce da Bintu suka gyara mashi dakin shi tsab don komai sada suka fitar suka share suka goge mai sabon zanin gado maji tabayar suka shimfida mashi.
Wanda karfin aikin ma duk Bintu ce tayi shi ita kadai maryam sai karatun ta take a cikin wayan ta kawai.
Ganin suna aikin yasa yan sa idon fahintar kila mai dakin zai dawo ke nan.
Mama Asiya ce ta fara samun Umma da zancen cewa yau naga mutanen ki sai wani jin dadi sukeyi harda gyaran wuri.
Nafisa tace da zan shigo dazun naga suna,gyara dakin yaya sadauki ai.
Muga atsiyar da ya tsinano masu a can ai sai rawan kafa suke wai yatafi ya dawo.
Wanan dan shaye shaye may kike zaton zai ita tsinano masu a can, ai yadda yaje haka zai dawo tsula dashi dan ganye kawai.
Ranan sai kawai aka kafa dandali a tsakar gida don gulma katuwar tabarma suka shimfida wa kan su nan aka baje ana ciye ciye ana hira wai.
Maryam ce tashigo gidan tana cewa yau kan gulma yakai gulma a gidan nan bakiga har tabarma,aka baza ba manya da yaran su a tsakar gida don kawai aga may yaya zai dawo dashi.
Ni dai Allah ya kawo min shi gida lafiya yasa wanan tafiyan ta zama mai silar shiryuwan shi.
Suka amsa mata da Ameen maji.
Sun zage sai faman goge gogen falon su da babu komai sukeyi don dai ya haske kawai.
Sun gama dan har wanka sunyi lokacin suna zaune falo suna dan hira jefi jefi tsakanin su.
Suka jiyo muryan shi ya shigo gida da sallama a bakin shi, kamar muryan yaya sadauki naji a,waje Amira take fadin haka.
Hamdala Maji tayi a fili tana fadin shine ba kama ba ai taji dadi don ko ba komai ta tsinkayo canji ga yanayin shi sosai don gashi ya shigo gida har da sallama a bakin shi yau.
,Nan sukayo waje don taron shi da saurin su hae suna karo da junan su.
Kamar yadda ya tafi
daga shi sai yar jakar shi wanan karon ma haka yadawo masu sai yar karaman jakar daya goya a bayan shi.
Daga inda matan gidan suke zaune da yaran su suna shan rake suka tsura mai ido kawai.
Shine yake ce masu sannun ku da gida mama daga haka bai karasa ba ya juya zuwa part din mahaifiyar shi.
May na fada maki Asiya na fada maki tsula ya tafi tsula zai dawo muna rabu da dan matsiyaciya kawai masu gadon tsiya ta ko ina.
Dariya suka sa dasu da yaran su a lokaci guda wanda sai da ran sadauki ya dan sosu don yasan dariyar a kan shi ne.
Sai dai ya dake ya rugumi kannen shi da suka sheko suka rugumay shi suna mashi sannu da zuwa.
Banda Bintu wace take tsaye daga gefe sai dai da murna a fuskan tana cewa,
Sannu da zuwa yaya cikin yar muryan ta ko bai jita bane yadai ja kannen shi suka shige kawai abin su ciki.
Bayan su tabi suku suku da ita tana dan dariyar yake a fuskan ta.
Inda MMaji take zaune ya isa cikin farin cikin shi ya zauna kasa tare da sa kan shi saman cinyarta yana cewa Maji yaya na samay ku?
Murmushi maji tayi tace anya Baba na kwallo kaje kuwa kaga yadda duk ka canza min a lokaci guda.
Murmushi yayi yace kai haba dai maji kwallo ko naje wallahi ban ramay bane?
Sai tai dan murmushi wanda rabon haka a tsakanin su ya matan lokacin shi.
Maji ta,waiga inda Bintu take rakube tana cewa, Fatima kawo wa yayanki ruwa ko yasha Amirah tace da abinci ko gaba daya.
Nan suka shiga kitchen din tare wanda Bintu ta fara dauko abin shan da suka shirya mashi takawo mashi.
Ta duka ta aje zata juya yake cewa ke wata irin bakauya ce kinga mutum ya dawo baki iya gaishe shi ne.
Amira dake aje tire din abinci take cewa aiko ta gaida kai yaya sai dai in bakaji bane.
Maji tace kadawo ke nan ko hutawa bakayi ba zaka fara takura min yarinya ko.
Ya juya inda suka aje mai kayan abinci a gaban shi yana fadin kai kai kai Amira duk ni kadai wanan abinci haka mai yawa.
Ga,wacce tayi su nan ai da yawa tana nuna mashi Bintu dake can gefe kujera a zaune kasan ties a dakin.
Amira tace ta ba bako yake ba yau ai batai laifi ba ko don ance bakon ka annabin ka.
Sosai yaji dadin wanan karamawan da kannen shi da mahaifiyar shi sukai mashi haka wai duk shi sadauki keda wanan taron.
Shigowan hjy Kubura dakin shi ya katse hiran jin dadin ganin shi da suke yi a lokacin
Tashigo da fara,a a fuskan ta tana cewa yanzu su Anwar ke fada min wai bakon ghana ya dawo ina shigowa.
Murmushi yayi yana cewa mummy mun samay ku lafiya ko?
Lafiya kalau sadauki yaya hanya yaya can kuma I hope komai normal.dai ko ?
Inda dane Maji zatace tsakani da Allah tazo taron shi amma yanzu data rage ta, sai take kallon makirci ne ya kawo ta kawai.
Nan ta kare kitihin ta ta fita daga dakin daga inda Bintu take zaune tabi da kallon makira kawai ita da maji da suka san komai.
Maji bayan yaran sun kaure da hira tadan fito tsakar gida tun daga inda su mama suke zaune aka jefo ta da hausa.
Tsula ke nan wai tafiyan sundundun madundun yadda aka tafi haka aka dawo zaban kunya.
Dan nagada ai bai iya gado ba dama taya za,ace kagaji abu kuma ka ketare shi.
Maryam dake bayan Maji bata san tafito waje zubar da bawan lemun da suka,sha ba, sai jin muryan ta maji tayi daga bayan ta tana cewa.
Mu dai mun gode ma Allah ai yaje lafiya ya dawo lafiya yan bakin ciki da suka so kada ya dawo sai su mutu.
Da sauri Maji ta juyo kanta tana cewa ke maryam ban son rashin kunya fa da suke zancen su sun ambaci sunan wani ne.
Sadauki da suke daki suna jin amsar da maryam ta bayar sun san akwai magana a waje sai sukai shiru daga ita har sadauki din lokaci guda.
Maryam ta shigo tana turo baki gaba tana cewa yan bakin ciki kawai dama nasan sheri da ganin kwam ya,zaunar da su ai a gurin kuma sun gani.
Maji ta shigo dakin don haka maryam din tai shiru don tasan in taji tana mita,yanzu zata balballeta ne da fada.
Sai da maji ta zauna ta dube su a nutse take cewa abinda nake so daku maryam shine.
Duk wacce taji a na,sake magana a gidan nan inda ba sunan mu suka ambata ba kada wacce ta kara tankawa kowan su.
Amirah tace Maji su wasu irin mutane ne da son fitina daga dawowan mutum zasu fara sakewa mutane magana kamar suna jirace da shi.
Maji tace suna jirace mana ba hassada bane kawai rudin shedan ai komai mutum zai iya yi don jan fitina.
Fitana,suke so don sunga yadda yaje haka ya dawo masu shine abin dariyar su ai tunda dan matsiyaciya ce shi.
Murmushi kawai Sadauki yadan yi yace su suna nan da halin nasu har yanzu wai.
May zasu fasa tunda kullun mugin nufi suke sakawa akan mutane inji Amirah tana mikewa take fadi hakan.
Haka fa jiya naji Nafisa tana zagin Bintu wai yar ci rani ba bu ranan komawa gida anga wuri.
Maji tace sai dai su mutu kuwa,don ko babu ranan komawan Fatima gida a gidan nan.
Bintu tadan ji kunya ta,sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun ta.
Maji tace gani sukayi yar ci rani tafi su mutunci da sanin ya kamata shine hassadan su, don babu wanda zaice tai mashi laifi a gidan nan tunda bata shiga harkan kowa.
Ta juya inda Bintu take zaune tana cewa don haka Fatima ki saki jikin kawai ki dainawa kowa dari dari tunda ba wanda ya isa ya koreki cikin su.
Wama ya isa inji Amirah bakin ciki ne kawai da hassada don ko ranan naji yaya Imirana yana cewa, wai ina aka samu yar kwara ne haka wai.
Sai naji Umma tana mashi fada wai ina kwara din take yarinya haka da fari kamar zabaya.
Duk kan su dariya suka sa Maji tace cikin dariya kai bakin ciki ho ina Fatima tai irin farin zabaya kuma in ba,sheri ba.
A fakaice ya dan saci kallon farin Bintu da ake magana shi dai baice masu uffan ba a cikin zuciyar shi kawai yake magana shi kadai kan al,amarin kishiyoyin mahaifiyar su.
Tun suna yara yake jin suna kirawa Maji kalman tsiya har su kan su din diyan ta.
Mikewa yayi a lokaci guda yana fadin zan je dakina maji ina key dina yake ne wai ?
Yana fita daga dakin daga gurin da Bintu take zaune bata san lokacin da ta sake ajiyan zuciya ba a fili.
Duk suka juyo suna mata dariya Amira tace dodon ki ya fita ke nan ko , don naga idan yaya yana guri zakiga Bintu a,takure kamar wace za,a yanka.
Ba dole ba yana son firgita min yarinya da mugun halin shi ki saki jikin ki Fatima haka halin shi yake baudade ne shi ko yaushe.
Murmushi kawai Bintu tayi batare da tace masu uffan ba,sai mikewa tayi tafara kwashe kayan da suke a tsakar falin nasu.
****** ********* ******
Yaron yana tsaye tana loda mashi ruwa a,sabon roban da ta,sayo mashi wanda yafi na farko da yake fita dashi girma.
Don yanzu ya dan fara sabawa da,tallan ya iya,ba kamar farko da yake dawo mata dashi ba idan ya fita.
Tana gamawa ta juya inda yake tsaye tana fadin na jakka da hamsin ne na saka maka kai sauri ka,sayar kadawo kafin mafadacin ubanku ya dawo gidan.
Ya dauki ruwan da,kyat yai mata,sallama ya fita, hat ya yi nufin zuwa inda ya saba kaiwa gurin masu wasan ball sai kuma ya fasa yace bari yakai wani guri da yaga ana aikin gina.
Yana,tafe yana fadin a,saya,ruwa mai sanyi ruwa dai, mai sanyi,
Sai yaji ance daga wani gefe pure water da sauri ya juya zuwa gurin har yana,dan tuntube.
A bakin wani shago wasu matasa ne zaune su hudu suna hira sukackira shi.
Yun bai karaso ba dayan yake cewa kai amma yaron ga gaskiya yana da kyau gashi dan tallakawa yana,talla amma tsab tsab dashi wallahi.
Ai kasan wasu iyayye suna da kokarin gyara yaran su kafin su fito yafi kazo sayen abu gun yaro kazanta ya hanaka iya,saya.
Ysron na karasowa gurin su dayan yace sauke mana dama tin da,zun nake nema ruwa masu sanyi wallahi don layin mu jiya babu wuta wallahi.
Nan suka fara zukan ruwan sai da kowa yasha leda biyu biyu dan sanyin da,ruwan yayi sosai ga dama ana,dan karen zafi a garin.
Ganin da Aliyu yayi yanzu yanzu yayi cinki yasa shi dan samun guri dan nisa kadan dasu ya zauna kafin su sallamay shi su bashi kudin shi ya tafi dama ya gaji nauyin ruwan yai mashi yawa.
Da haka mutanen dake wucewa suka zo suna saye har ruwan ya,saura kadan a roban.
Sai ga,wata mai abinci tazo ta zauna daga gefen shi take ruwan ya kare ya karbi kudin shi ya juya gida da sauri ya,karo wani.
Wasa wasa,sai yagane gurin ana,samun ciniki fiye da inda yake zuwa da,farko don haka ya mayar da,wurin gurin kai tallan ruwan shi ko yaushe.
Yana mayawa kusan biyar a rana kafin ya koma gida don zuwa makaran ta da,sukeyi da yamma.
Watarana kuma in yan tsiyan sunackan maria sai tace mai idan sun tashi cin breakfast ya gudo yazo ya fita mata da ruwan ta.
Da sannu yan gurin suka fara sabawa da yaron har suka yarda dashi suka,fara dan aiken shi sayen taba abinci da sauran su.
Yakai yanzu inva ruwan shiba basu sayen ruwan kowa do shi ko yaushe ruwan shi zaka samay shi da sanyi sosai koda ba,wuta don freeze maria yana aiki sosai duk yadda aka kawo wuta zaiyi saurin daukan raba yai sanyi.
Tun maigidan yana zargin tabarbarewan karatun dan shi yana fada har yagaji ya,saka,mai ido do uwar bata bari ya,fadi tinda tasan abinda take shukawa a bayan shi.
Sosai maria take jin dadin yadda danta yake mata,talla haka tana cewa Allah ya,bashi kan ciniki sisai tayi sa,an haihuwa ita.
Tan godewa Uwarta data,bata wanan shawaran da badon haka ba da yanzu tana,nan tana,wahalan neman dan talla bata samu ba.
Kulun bankin ta,sai bunkasa yake don yana samun canji suna shiga mashi yadda ya dace.
Yanzu ji take koma mijin ta yasani baida yadda zaiyi da ita don bazata iya hanawa dan ta wanan tallan ba.
Shiko maigidan mutane da dama sun shatare shi suce sunga Aliyu yana tallan ruwa da yazo yai magana bai gand komai gareta.
Don haka yaja,bakin shi yai shiru har ranan da zai kamasu da hannun shi ranan yai alkawarin zai dauki mataki a kanta, sai ta rena kanta ga hakan.
****** ********* ******
Tunda sadauki ya fita zuwa dakin shi bai fito ba ya,samu guri ya kwanta,tare da,karewa,dakin da yasha gyara kallon mamaki.
Don yasan ba aikin su Amirah bane wanan wa yan nan malalata yaushe ma,suka,iya,gyarawa Maji guri yai kyau balle na,wani.
Da,sauri zuciyar shi da,tafara tunane tabashi amsa,da,fadin ba,aikin kowa,bane sai wanan yar kauyen ta Maji.
Bakowa zai iya wanan aikin haka,ba,sai ita wata irin yarinyace bata jin ciwon jikin ta ita aiki bai isanta ko yaushe a,tsaye take ita.
Nan dai har barci ya dauke shi inda bai farka,ba,sai da yamma lis don gajiyan da,ya,debo.
A,tare ya hada,sallah dake kan shi yayi ya,zauna gurin har lokacin da,aka,fara kiran sallah magariba,ya,wuce masallaci akai jam,i dashi.
Yaushe rabon shi da,yin haka,mutumin da komai nashi a,tsabare yake abinshi bai shiga mutane kamar mugu yake ko yaushe, sai yawan nisanta kanshi da mutane yakeyi.
Tun a masallaci suka hadu da mahaifin shi ba karamin dadi yaji ba na ganin Sadauki a jam,i tashin farko da,dawowan shi.
Sama sama suka gaisa da mahaifin nashi don akwai mutane da yawa lokacin.
Yai matukar manakin yadda mutane ke kokarin gaisawa dashi yau sabanin da can baya da mutum zai wuce ya,wuce abinshi ba mai gaida wani cikin su.
Shi girman kai mutane kuma suna kyamar dabian shi da ya tsira acikin al,umma.
Ana idar da,sallah direct cikin gida ya,shiga gurin mahaifiyar shi don bai gaji da jin dadin ganin ta,da,yayi don dan,kwana biyun da,sukayi basu tare a lokacin yasan dadin Maji sosai gare shi.
Ashe ma yawan fadan dayake ganin tana mashi wani babban gata ne gareshi.
Don zaman ta kusa dashi yafi rashin ta a kusa dashi ko yaushe.
Yana shiga falin duk suna zaune ga dan busashen falon nasu kamar kullun suna hira.
Sannu da dawowa suke mashi gaba dayan su a cikin murna kamar su lashe shi don jin shi da,suke ajiki ranan.
Cikin harshen turanci yake ce masu daidai lokacin da yake zama kai I miss you people fa.
Ina yawan tuna ku ina can ko wani lokaci wallahi,
Yace ina Maji take ?
Tana part din Baba tana hada mashi abinci yace ok yau itace da duty ke nan ?
Maryam ta bashi amsa da eh,
Zaunawa yayi dakyau yace Amirah may aka dafa ne da,daren nan ?
Amirah ta bashi amsa da tuwon semo da miyar kubewa danya.
Jeki kawo min na dan ci na fita,na,samo maku dan wani abin sha kafin dare yayi.
Maryam mai kwadai tasa ihun kai canji yaya wallahi har naji dadi har cikin raina,
Yace common see yo mai kwadan tsiya kawai tace ba haka na,bane bakaji har gori ake muna wai mu saidai abamu abamu kullun.
Wallahi wanan abin ya dade yana,bata min rai bafa rokon su muke ba kuma,da kudin mahaifin mu ake saye amma,don diyan sune a,kasuwa shine ake wa Maji gori da mu.
Bintu da,taga basu da niyar bashi abinci ta mike taje ta hado mashi takawo mashi don dama zaune take gefe tana sauraren su.
Ga abincin yana kallo ya tasa a gaban shi amma maganan da maryam tayi ya hana,shi cin abincin.
Yasan daga shi har yan kannen shi biyu ba karamin hakkuri sukayi ba agidan nasu.
Don sun taso suna ganin kalubali rayuwan iri, irin tun suna yara har yanzu da,suka mallaki hankalin su.
Shikan shi ada can baya kafin ya fara dan shaye shaye yana kokarin dan dauke masu wanan nauyi.
Amma tunda yafara shaye shaye komai ya,dagule mashi a lokaci guda.
Shi kan shi ba zai iya cewa ga dalilin da yasa ya tsiri yin shaye shaye ba,a rayuwan shi.
Haka kawai ya,wayii gari yaji yana,da ra,ayin yin haka a,ran shi.
Tunanen shi ya katse ne don jin muryan maji da yayi a gaban shi tana cewa may kuma ya faru ka,tasa tuwo a gaba kana tunane,
Ko baka iya cin abincin mune yanzu ka koyo cin dankunun mutanen kasar ghana.
Murmushi ya dan sake a gefen fuskan shi wanda sai ka kula zaka gane murmushine yayi haka.
Maji takara tanbayan shi komay yasa may shi taga yana tunane haka karo na biyu, duk yan uwan dake surutu basu kula da,damuwar da ya shiga ba.
Yace wallahi ba komai Maji gajiya ce kawai danayi yasani yin shiru haka.
Ya jawo kwanon abincin a gaban shi yafara diba a hankali a cikin plate din dake gaban shi.
Kadan yadan tsakula ya ture plate din yana fadin ya koshi da abincin.
Maji tace amma sai ina ganin kamar ba gajiya yasa kaki cin abincin ba dai, ai gajiya bai hana cin abinci tunda har naga kayi wanka ko?
Ya mike a lokaci daya bayan ya wanke hannu yana cewa bari na,dan fita na,dawo yanzu.
Da,sauri maryam tace tau yaya adawo lafiya cikin gidimi.
Maji tace dakata ina zaka bakaje ka gaisa da mahaifin ku ba daya dawo duk da yace min kun hadu a massalaci dazun.
Yace Maji da nace saida safe kafin yafita naje mu gaisa da shi da kyau nai mashi bayanin komai.
Daga inda maryam take tace shine daidai Maji bari ya fita yadawo din kawai da,safe suga juna da,Baba din.
Akwai dai abinda kuka,kulla nake gani kukuka,sani koma may ye ai ta juya zuwa cikin dakin ta.
Bayan wani dan tsawon lokaci ya,dawo da ledoji irin na super market manya har guda uku a hannin shi.
Da murna suka tare shi suna karban ledejin maji dake fitowa daga daki tana fadin Fatima don Allah kada ki gaji kinji dauko min abinci naci nima.
Zataci gaba da magana sai ganin abinda ke wakana falon nata tayi, takai idon ta ga ledojin da su Amira ke budewa.
Drinks ne snacks, su apple da nama gudan mai yawa na rago da kaza gassashe.
Take kamshi ya,gahraye falon nata a lokaci guda sai faman binsu da kallon mamaki takeyi daya bayan daya.
Bintu da ta riga tamike take cewa a hankali Mama na debo maki abincin ne?
Yace ke bar abincin nan dauko mata plate kawai ki zuba mata wanan taci tasha drinks din.
Cikin mamaki maji takai zaunr a saman dayan kujeran ta tana cewa haba Sadauki kai da ya kamata kai tanadi shine zaka biyewa wa yan nan makwadaitan ka,fara almubazaranci da kudi haka.
Murmushi kawai yayi azuciyar shi yace mamana bakiga komai ba ma tukun ai.
Amma a fili cewa yayi ai maji wanan bai hana ai tanadi don su wa naje wasan badon ku ba aci kawai bai sa ya kare ai.
To amma sadauki kana dai jin har an fara min gori yaddackaje fa haka ka dawo wa mutane tsula dakai.
Maji kada ki damu da zancen su wanan magana da sukeyi takine a gare mu yanzu.
Bintu tana kawo plate din tamikawa Amira dake ta faman bude kayan, inda Amira ta dago kai tama cewa maji may zan yago makine daga ciki?
Dakuwa Maji tamika mata tana fadin ungo naki nan ta juya inda Sadauki yake zaune tana fadin kada ka biyewa wayan nan yan kwaden don basu san ciwon kasu ba,su ba abindake ran su sai kwadayi.
Kai tanadi ga dan abinda kake samu don gaba nada yawa don kaine muke gani wani gin shikin mu gidan nan.
Maji kada kiji komai kuci kawai ai don hakane na,sayo maku din don naga kunci kun sha daga gareni nima.
Komai da ya,sayo saida Amirata sawa Maji inda shima sadauki ta zuba mai a cikin dayan plate din.
Ta juya inda Bintu take makure tana cewa bisimillah mana zo muci ko,?
Maryam data fara kaiwa abaki tace ,a,a bazataci ba kin san ita akwaita da filanci ai.
Shigowan yaron Asiya da,aka turo don yafa may suke a dakin saboda dariyan su da akeji,
Amma sai ya fake da yazo gayar da yayan sune da dawowa.
Maji tace Amira ta diban mashi inda ta yaga mai rabin kaza guda da yan sauran tarkace tabashi yafita.
Maryam tace munafuki gulma dama tazo yi ba duk gaisuwa yakawo shi ba fa.
Kai ke kan maryam wallahi ki rafe yawan zargi ina laifin shi yadawo yahi dan uwa yadawo yazo ya gaidashi.
Kila ba inji Amira maji tace ku dai kuka sani don bakujin magana.
Bintu dai na gefe tun da ta dauka saudaya,sai faman taunan shi take ta kasa hadewa duka.

Bai yarda ya,fita daga gida sai yai wanka ya gyara jikin shi kamar yadda yaji ana yabon shi da tsabta ko yaushe,
Yanzu yana ciniki fiye da farko a baya don ko bai sayar ba mutanen gurin zasu saye na karshe suce zasuyi amfani dashi da dare dashi, don da dare ana wuyan samun pure water.
Haka yasa yaron ya kara kwantar da hankalin shi da mutanen gurin da yake zaman don yanzu duk sun saba dashi ko sosai sun kuma yarda dashi yaron nada kirki yana da,wayo,
Don duk inda suka aike shi da gudu zai tafi kuma bai bata ranshi.
Ya kai yanzu taban da ake aiken shi saye ya canza sallo don dai shi bai san wani irin taba bane shidai a ganin shi ai duk taba tabane.
Amma sai dai yasan wanan yafi wanda yake sayo masu don sai anyi warning din shi akan ya boye idan an bashi kuma idan ya sayo kada ya,basu infront of mitune yai hiding din shi.
Haka ko yake ko wani irin sako zai bayar in secret zai ba mutum abin shi.
Duk hiran da matasan zasuyi a kan idon shi ne cikin kunnen shi yake shiga.
Akwai wani wanda idan ya sai ruwan shi ko nawa ne canji zaice ya bashi kawai bai karban canji gurin yaron.
Haka yasa Aliyu har Allah Allah yake yafita tallah koda lokacin fitan nashi baiyi ba.
Suma gurin da ya tun karo zaka ji suna smally ya iso ke nan yaro kana wanka,fa.
Shiko yarinta sai yaji kan shi ya,fashe yana mai jin dadi yana kokarin yin wasa da su don sun saba dashi ko.
Nan za,a fara smally sayo min sigari zo ka sayo min abinci tsalaken titi da dai sauran su.
Irin haka,watarana yazo sayen sigari sai ga wani abokin mahaifin shi yace ,a,a Aliyu wa ya aiko sayen sigari kuma?
Yace wani mutum ne a van tsalaken titi ya aiko ni aka mika mai yatafi, sai mutumin yake fadin kai amma gaskiya haka bai dace ba a aiko karamin yaro sayen irin wanan abin baidace ba da karamin yaro.
Mai shagon yace aiko kullun sai yazo ya,saye kashi da kashi ake aiko shi ni nazata ma ko mahaifin shine ke aiko shi saya.
Ina mahaifin shi ai bawan Allah ne, ina mutumin nan mai dako a bakin kasuwa mai wuce wa tunda safe yana fitowa kwanan can na malam sale.
Mai shago yace nagane shi dan shine ashe yace wallahi dan shine kai wanan mutumin ai ba ruwan shi wallahi.
Mut8m ya hadu da mijin maria yake fada mai abinda yagani da idon shi a kan yaron shi.
Bai ji dadin zancen ba, nan ya koma gida da fada anyi sa,a ya samu Aliyu a gida nan ya haushi da fada harda dukan shi sai da yayi ranan kuma yai mai fada daga ranan duk wanda ya tareshi ya aikeshi sayen taba yace Baban shi ya hanashi zuwa.
Washe gari da,aka ake shi yake fada masu cewa, an fadawa Baban shi yana zuwa sayen taba harda dukan shi akayi kan hakan.
Kai mutane dai wallahi muna fukai ne yanzu har mahaifin ka,saida ya,samu wanan dan labarin kamar wani abin sheri can.
Nan suka,bada shawaran ya canza shago kawai inda baza,a sani ba yana zuwa.
****** ********* ******
Tun dawowan su ka fara karo da kwalayen da akai amfani dasu a dakin Maji na kayan da aka haka, duk da an kwashe anzubar da saura ga kuma shirgin kayan da aka fitar a inda suka barsu dazun.
Yaran su ne suke fada masu cewa yau basu nan an sha aiki a dakin Maji don an gyara mata dakin ta kamar na amarya.
Mama Asiya bata yarda ba saida ta shiga hardakin don ganewa idon ta abinda yaran ke fada masu.
Tun daga labulen falon tafara shock don bata ma taba ganin su ba da idon ta gidan kowa ba.
Kujerin da tai tozali dazune suka saka gaban ta wani irin faduwa, don tasan bana kasar nan bane da ganin su.
Juyawa tayi don babu kowa a falon bata tsaya ba sai dakin Umma wadda itama shigowan ta gidan ke nan a lokacin.
Yaya waiko kinga abinda idona yau yaganan min may kuma kika gani zaune takai tafara lissafawa Umma abinda tagani da idon ta.
Amma sai Umma bata dauki abin da muhinmanci ba ta zaci kawai idon Asiya ya rufe ne har take dada abinda akasa don ina zasu samu kudin irin abinda take fadin tagani a dakin Maijidda.
Maji da ta idar da adduoin ta da mika godiyan ta da neman tsari a gurin Allah tafito don yi masu sannu da zuwa.
Don kullun suka dawo dama sai tai masu sannu da dawowa bata gajiya duk da gwatsaleta da watarana sukeyi.
Har ta juya sai kuma ta tsaya tana cewa yaya baku nan fa abin arziki yau ya samay ni don dan ki ya sayo min kayan daki da kudin da ya samu.
Wani dan nawa Umma ta tambaya a gwatsale cikin basar wa maji tai murmushi tace dan ki sadauki mana.
Umm,uummm, dakin dai Maijidda tunda gashi uwarshi ya sani inda danane ai da ni zaiwa.
Tace idan kin huta sai kije ki gani ki samin albarka a ciki, ta juya ta fita zuaa gaida mama Asiya .
Itama ta fada mata yau abin arziki ya samay ta daga dan ta tazo tagani don Allah.
Nani kawai tace ba wani adfuan alheri akan wanda yayi din dama ita da tasamu din.
Hjy kubura dai dama sai yamma lis take shigowa gidan kullun koda kuwa sun tashi daga gurin aiki ne bata dawowa sai ta gama gantalin ta take shigowa gidan da yaran ta a gala baice da yunwa.
Maji tana shiga daki tafara cirewa kowa tsaraban shi kamar yadda suka tsara ita da diyan ta.
Matan gidan dai sun samu turamay yan ghana masu kyau da tsada turmi biyu, biyu sai yaran su maza bandir din shadda kowan su koda kuwa yaro karamine,
Yan matan kuma dogayen riguna da turamay suma aka basu, masu kyau sosai.
Nan gida ya kaure da surutu kowa da abinda yake fadi inda babu wanda yazo godiya cikin su sai yaran ne duk wanda akabawa zai zo yayi godiya da jin dadi masu bakin hali irin na uwayen sune basu shigo ba.
Hjy kubura da aka kai mata sakon cikin mamaki tace sadauki fa ya kawo muna wanan haka don harda kwallon da danta yaba da soko saida aka sayo mashi
Bata san da zancen gyaran dakin ba saida ta shiga taga ikon Allah dare daya Allah ya kai su gaba haka.
Tace may nake gani haka hjy maijidda kice min ci gaba yazo ke nan nan ta shiga sauran dakunan tana kallo tana kada kan ta cikin mamaki don bata taba zaton haka ba.
Falo ta dawo tana fadin kai Maijidda kin ko tambayi yaron nan akan kwallo ne ya samu wanan kudin haka?
An fa kashe kudi yakai miliyan biyu a nan ma kawai fa tanayi tana kara latsa kujerun don jin kwalitin su.
Tace ina dan nawa yake sarki yan kwallo ke nan ace mutum shigan farko ya dawo da haka.
Sai bayan ta mike take cewa ja iri yako tafi da dabun da nai mashi na tafiyan kuwa.
Maji tace ai yace yaji dadin danbun sosai shi uake ci ma a can yasha ruwa kawai don bai saba da irin abincin su ba sosai ,a lai kan naga alama.ai.
Tafita tana tunanen hitan su da yan office din su dazu da safe da suke cewa ashe dan kwallon gidan ku yadawo tace cikin tabe baki yadawa yadda yatafi shiririce mana.
Wanan dan iska wani tsiya dama zai tsinanowa mutane a can ban da tambadan daya saba nasan ya tafi yana shaye shayen shi sun koro shi.
Sai dayan dake rubutu take cewa ,a,a nifa naji kanina na fadin shine ma yazo na farko don ya samo kudi sosai wallahi.
Ba gaskiya bane wallahi yadda yaje haka ya dawo tsiya tsiya dashi wallahi don ina ga baiko maganin sisi ma.
Don ya samu wani abu da naji ko gurin Alhaji ne ko inga suna facaka ko ba abinda ya tsinano.
Sai daya tace balle ma mashayi kafin fa suyi sai an bincike su agani idan kana shaye shaye basu yarda ka buga kwallo yanzu.
Balle ma bai samo komai ba suna dai ganin hakane tunda ya tafi har wani kasa yin wasa.
Sai gashi ta dawo gida ta samu zancen abokiyar aikin ta ashe gaskiya ne ke nan boyon kurwa yai masu dama.
Maji dai ta rakata da harara tana fadin muguwa aniyar ki tabiki dakin ki munafuka yar sheri, Allah ya shirye ki kawai.
Maji tace wa Amira gobe ina son a kwashe tsofin kayan nan akai wa mai masa gidan ta ita ma,ta canza.
Nan Bintu tafara murna tana godiya kafin hjy masa tazo tayi mai karfi da bakin ta.
Sai da yamma da Alhaji yadawo ya samu wanan labarin gurin mama Asiya da ta fara tsegunta mashi ciki tsigar gulma.
Yace masha Allahu kai amma ko naiwa maijidda murna haihuwa ta fara rana ke nan yau Allah ya amsa mata adduan ta .
Sai ga maji da nashi tsaraban shaddoji da su turare masu tsada ta zube mashi su a gefen kujeran da yake zaune.
Ya kalleta cikin murmushi yana fadin yanzu Asiya take fada min abin arzikin da ya samay ki ashe sadauki ya fara fitar da uwarshi.
Maji tai murmushi tace kai haba Alhaji kai kuma da kanka zakai min sheri kuma.
Suna cikin magana sai ga hjy Bintu dauke da tsaraban ta dana yaran ta tana ta faman washe baki tana fadin ga abin arzikin da mutanen ghana suka kawo muna.
Yace mata nima kinga ga nawa nan yanzu aka kawo min shi ko dubawa ban gama ba.
Mama Asiya mai girki tashigo ganin kayan hjy Kubura dana yaran ta yasa take kallo don taga sun fi yawa ga idon ta.
Nan take cewa hmm muma fa anbamu har yaran nan gaba dayan mu gidan.
Masha Allahu inji Alhajin ya fadi yana mai kai ruwa a bakin shi yace haka ake son samu idan ka samu kowa ma yasan kasamu cikin yan uwan ka.
Yana gama cin abinci ya nufi dakin Maji don yaga abinda ake ta faman zuzutawa,
Yako gani kuma yai murna da farin ciki sosai sai faman sawa dan shi albarka yakeyi.
Bayan fitan su Amira tace ikon Allah yau Baba ne da kan shi kewa yaya sadauki wanan adduan haka.
Amma da can an zuga shi a kan shi sai faman cin mutunci da tonon asiri yakewa mutane a tsakar gida.
Maji take ce mata wanan ai haka yake duk uwa mai haihuwa sai ta samu bacin ran mahaifi akan dan ta watarana.
Don duk abinda yayi mara kyau laifin uwa ne maikyaune na uba ni dai na godewa Allah daya takaita min wanan bakin cikin da wuri.
Maryam dake kunna tv take cewa amma ai basu daina kiran shi da sunan mashayi ko?
Don ko dazun naji Umma tana fadin wai tsaraban yan shaye shaye suka samu take fadawa yaya Imirana da ya shigo.
Ba sai ta dawo dashi ba tunda bata son kayan mashayi da aka bata maganan banza kawai.
Maji dai shiru tayi batace masu uffan ba har suka gaji sukai shiru.
Da safe ne sadauki yaba mahaifin shi check din kudi yace yana so ya fara noma dashi ko za,a samu anan ma din
Bayan Alhaji ya karbi kudin yaga yawan su yake cewa sadauki duk wanan kudin haka akan kwallone kawai ka samay su.
Ya dan dukar da kan shi a kasa yace Baba a nan na samay su don ma ban yarda bane da,har wasu club sun so su sayeni amma,nace masu a,a subarni cikin club dina kawai har gaba.
Ikon Allah ashe Alhaji Sani gaskiya yake fada min cewa idan nai hakkuri Allah yasa maka hannu watarana sai na dara akan kwallon ka.
Murmushi kawai sadauki yayi ba cewa mahaifin nashi komai ba yana fita hjy kubura tana shigowa suka gaisa dashi ya fita.
Alhaji ke ce mata kingani ikon Allah kudi sadauki ya kawo min wai na fara noma dashi.
Maimakon yaji tayi murna yadda ya zata sai ji yayi tace Alhji adai binciki a gani wanan harkan amma abin yai yawa wallahi.
Ya juyo cikin mamaki yana kallonta yake cewa ban gane hausan ki ba fa kubura.
Tace ni gani nayi kamar wanan kudin sunyi yawa ace duk a saboda kwallo aka samo su haka gaskiya abincika dai aji.
Yace to kina ganin kamar da akwai wata a kasa ke nan ko ya tambaye ta don son jin may zatace.
Tace gaskiya kasan halin dan yau fa kada ya yaudare ku da,wasan kwallo ya fada wani harka na tir da Allah waddai.
Cikin mamakin jin abinda ta fadi yace assha kubura ban zaci jin wanan magana daga bakin kiba wallahi.
Sai lokacin ta tuna tayi barambarama fa don mahaifi mahaifine ai,da sauri ta gyara zancen tana cewa a,a ba wani abu nake nufi ba kasan halin dan yau ne shi yasa na ce a dai bincika kawai ba wani abu ba.
Nan dai taita kamay kamay ta tafita shi dai yana jin ta kawai baice mata komai.
Kwana biyu sai gashi zance na yawo a gari da unguwa wai ya samu kudi ba,a san inda yasamo ba sai facali yake iyayyen shi suna jin dadi.
Wasu suce wai ba kwallo aka dauke shi ba zuwa akayi dasu suka fita da kwaya kasan waje shine aka fake da kwallo kafa.
Maji dai da zancen yazo kunnen ta da farko ta so tayar da hankalin ta don sai da ta tsure sadauki a dakin ta take tambayan shi gaskiyan zancen abinda taji.
Murmushi shi na rabin fuska kawai yayi mata yace haba Maji idan wani ya fadi an yarda aike bai kamata ki yarda da wanan zancen ba don kin fi kowa sanin halina.
Ban son raini da wullakanci shiya sa na roki Allah yai min mafita na dogara da kaina.
Nan dai hankalin ta ya kwan
ta tace koma,waye yai muna wanan sherin mun barshi da Allah shikw nan.
Takara ja mashi kunne akan ya futar da ita da yan uwan shi daga kunyan duniya don mutane yanzu ake kiwo ba dabbobi ba.
Bata hakkura ba ranan da take da girki ma saida ta samu maigidan su da wanan zancen.
Yace au kema ashe zancen yazo kunnen ki amma ya kamata ace kin san halin abinda kika haifa.
Ni ban ji ko dar ba akan maganan nasan kawai hassada ne irin ta mutanen yanzu kawai.
Amma ai watarana gaskiya zatai halin ta don shi kwallo ba,sanar boye bace duniya tana sanin mutum a lokaci guda.
Ki dai yi mashi fada yai tanadi kada yaga kudi suna shigo mashi haka dayawa lokaci guda yace zai bullo da shashanci cikin rayuwan shi.
Haka yasa tattara zancen ta watsar tabar masu hassada akan danta suna zuba mashi taki.
****** ********* ******
Sadauki yana zaune a cikin falon Maji duk kannen shi sun tafi makaranta sai ita dake final exam din ta yanzu.
Wayan shi yake dakila ta hanyar yin game da ita,Bintu tafito daga cikin dakin kwanan su bata san da yana falon zaune ba a lokacin.
Tana saye da da dogon riga na atamfa a jikin ta, style din dinkin da akaiwa rigar yai matukar mata kyau a jikin ta.
Tunda ta sanyo kai falon ta gashin a zaune sai taji gaban ta ya fadi don a rayuwan ta ta tsani ta gan shi a falon zaune don yawan takuran da takeyi.
Jin motsin da yayi a zaton shi ko Maji ce tafito daga cikin dakin yasa shi daga kai ya kalleta.
Bintu ce ya gani tana kokarin komawa cikin dakin da tafito din,cikin sauri.
Yace cikin daure fuska ke zo nan kina abu kamar muna fuka dake, cak taja ta tsaya tare da juyowa inda yake zaune.
Yace ina Maji take ne ban ji motsinta ba ya tambaya cikin ci gaba da latsan wayar shi .
Tana dakin Baba tana gyarawa amma yanzun zata dawo,,,
Hannu ya daga mata yana fadin ban tambayeki ba bani abinci na naci yace cikin gadara da daure fuskan shi.
Haka ta karasa fitowa ta gaban shi ta wuce ba don taso ba inda yabi bayan ta da dan tsuki yana fadi a ranshi jita dan Allah kamar zata kare, mace haka ba kiba ko kadan.
Tafito da abincin cikin sabon kulan shi da ake saka mai abinci ta aje a gaban shi ta juya zata dauko ruwa ya kara binta da kallon haushi.
Yadan kara jan guntun tsuki wanda yai daidai da shigowan Maji falon, tace, a,a Baba na kai dawa kuma ke wanan tsuki haka kai kadai?
Yace kai tsaye ni da wanan yar kauyen mana tafito taganni shine kuma wai zata gudu anya maji yarinyar nan kuwa tana da gaskiya ya fadi tare da,dago kan shi yana kallon Maji.
Wani kallon da yaga tana mashi yasa shi shan jinin jikin shi ta,wuce zuwa ciki ta aje kayan dake hannunta.
Jima kadan tafito ta zauna tana fuskantar shi tace gaskiya banjin dadin irin yadda kakewa yarinyar nan,
Ko banza taci albarkaci na nida na ajeta a gurina bawai bata da gata bane a,a itama tana da gatan ta rayuwane kawai yasa ka ganta anan din.
Amma yarinya tana tsaye tana iya kokarinta a kan mu kai kuma,sai binta da hattara kakeyi da wani zataji na rashin iyayyenta kusa da ita ko kuwa da halinka zataji.
Ban son karatun yarinyar nan ya tsaya ne shiyasa kaga ana ajeta a gurina don itama watarana iyayyenta suyi alfahari da ita.
Ashe ba dadin ku bane yau ace a sanafin mu ta zama wani abu a duniya, ban rokeka komai don na tallafa mata ba.
Amma kasa yar mutane gaba haka da tsangwama tare da hattara ba yau ba ina lura balain tsoron ka fatima takeyi wallahi.
Wani kunci ne yaji ya rufe shi a ranshi ya mike ba tare da ya gama cin abincin da yake ci ba ya bar falon cikin fushi.
Maju da tabishi da kallo ta,tsuki tace sha sha kawai mara hankali mutane suna bakin cikin zaman ta anan kaikuma kace zaka tsiro min da naka kalar tsiyar a kanta.
Tsayin sati daya sadauki yana fushi a kan maganan gashi ya hana Bintu sakat a sashin nasu don da ya shigo ya kama hararan ta ke nan da kuma tsuki.
Allah Allah Bintu keyi ta gama exam tabi gwagonta kauyen su don dama zaman dole take a gidan.
Hankalinta yana gurin iyayyen ta da yan uwan ta don tunda tazo bataje gida ba,bata kuma ga kowa ba cikin su sai gwago dakan dan zo ta kwana biyu ta koma.
Allah ya taimaketa kafin su gama exam aka kirasu Abuja inda ya kwashi komatsen shi yanufi gurin kiran da akai masu.
Hakan ya,dan ba Bintu daman sake jikin ta har maji ta fahince ta tafi sake jikin ta idan baya nan ke nan.
Amma tana gama exam ta fito da zancen son zuwa gida don tagano yan uwanta.
Hankalin Maji yai matukar tashi a lokacin inda take tambayan ta cikin lalashi ko an mata wani abine take son zuwa gida.
Bintu tace cikin sanyi murya da,sauri a,a mama ba ai min komai ba ina dai son zuwa,nagan su ne tunda nazo banje gida ba shiyasa nake son zuwa nagano babana da yan uwana.
Maji ta sauke ajiyan zuciya tare da,tambayan idan kin tafi yaushe zaki dawo Fatima?
Don nasan ko kwana,nawa zakiyi acan saboda na tura a dauko ki in lokaci yayi.
Bintu tana,wasa da yan tsunta,da,harde su guri guda tana cewa mama sai na tafi tukun don ban san hukuncin da mahaifina zai yanke a kaina ba yanzu tunda na gama karatu na ko.
A,a Fatima idan hakane ki bari mu tafi tare sai mu kwana daya mu dawo, tare.
Da sauri Bintu ta dago kai tana fadin mama har gurin mahaifiyata nake son zuwa don mun dade bamu ga juna,ba da ita.
Eh to gaskiya hakan yana da kyau kuma ina ga,dai kila zakiyi sati biyu zuwa uku ke nan eh mama Bintu ta bata ansa da hakan wanda ta dai fadi ne don su rabu lafiya da maman nata sabuwa.
Amma yadda tajeji bata sa ran cewa zata dawo wanan gidan ba kuma da sunan zama duk da dai ba ai mata komai ba amma gidan ya fita ranta don tana gudun kada sanadin ta mama tai fada da dan ta daya shiryu yanzu.
Tsaraba sosai Maji ta hadawa Bintu na gidan mahaufinta da yan uwan ta daban wanda zata kaiwa mahaifiyarta daban.
Mota akai mata shata ita kadai Alhaji yabiya tare da bata kudi da zata rike don amfanin ta a can.
Kamar yadda akai alkawari da driver hakan yayi har kofan gida su Bintu ya kaita inda aka,ganta a bazata don ba wanda yasan da zuwan ta.
Irin kayan da,akaga a na,shigowa dashine yasa hankalin matar uban ta ya tashi, har ta kasa boyewa da zuwan Bintu din.
Nan dai kowa ya,wayance sai sannu da zuwa ake mata ana kallon yadda a lokaci daya ta canza kamanin ta gaba daya ta koma wata yar Birni da ita.
Kafin wani lokaci har zancen dawowanta ya zagaye dan kauyen nasu kowa na fadin Bintu ta dawo ta koma yar Birni da ita.
Saida dare ta samu ganawa da mahaifinta wanda ya dawo daga gona a lokacin ana gabanin magariba.
Nan suka kebe tana bashi labarin zaman ta a burni da kuma mutanen arzikin da gwagon ta,tabarta gurin su.
Takawo sakon da maji tabata na,tsaraba ta bashi yana ta murna da farin ciki.
Bintu ta sheda mai ta kare karatun ta har matar dake rikon ta tace zata ci gaba da karatun ta idan jerabawan ta ya fito.
Mahaifinta yai farin ciki da jin wanan albishir din da tai mashi sai dai kuma yasan abune mai wuya yadda ta girma haka yan uwan shi su barta taci gaba da karatu sai dai in Allah ya nufa zatayi din.
Washegari Bintu kamar yadda ta,saba zuwa daukan karatu a lokacin da take gida hakan ta shirya zuwa islamiyan su.
Sai dai ta samu yawanci yan matan da suke karatun tare sunyi aure a lokaci, dan kauye basu bari yarinya tagirma sosai suke mata aure.
Malamin nasu yai farin ciki daganin hazikan daliban shi ta dawo kuma bata watsar da karatun ta ba don taje birni.
Taso ta fara a inda ta,tsaya da karatu a gurin shi amma da,tafara biyawa sai yaji ta,wuce tsanmanin shi.
Don haka yace ta dauka a inda,take can birni haka yasa taci gaba don ta sauka bita take yanzu.
Ganin duk idon sauran dalibai yana kanta kuma suna sauraren yadda sabon sallon karatun ta yake fita.
Duk sai sha,awan ta ya kama su nan suke zuwa wai ta koya masu yadda take fitar da haruffa cikin kara harshe.
Nan fa samarin kauyen masu jin sun isa suka fara kawo kan su gareta da,sunan sun gani suna so.
Itako mama ta,bawa matar ubanta tunda ta kyala ido taga kayan maihaifiyan Bintu da maji ta bata ta sa a ranta su take so.
Bayan nata da,takawo mata da yaran ta duk sai da Maji ta ba kowan su tsaraban da zata basu in tazo.
Haka ta,bawa tasa Bintu da mahaifinta gaba da masifan kan lalai sai dai ta dauki turmin wajen ina da aka bata takai mata.
Har abin yaso yakawo sabani a tsakanin ta da mininta watau mahaifin Bintu.
Don haka Bintu ta tsiri tafiya garin da mahaifiyarta take bashiri don tabawa sai fada takeyi wai bayan tagama wahala da ita yanzun anga dadi yazo shine zatace tasan uwar ta.
Bintu dai murmushi tayi kawai tana hada kayanta tare da tunanen yadda zata zauna gida da wanan masifanna matar mahaifin ta kulun.
Ta hada duk dan abinda tasan tana so tana bukata a cikin kayan ta tafito tare da,yi masu sallama ta tafi abinta badon ta tashi zuwa ba.
Ganin ta kawai mahaifiyarta tayi a bazata don rabin ta da ita tun tana aji hudu na primary bata sake zuwa ba don maigidan ta baida dadi ko kadan.
Bai son yaga Bintu tazo wajen uwarta ya shiga fitina da mitan shi baison zuwanta tana zuwa tana hure mata kunne don ta koma gidan mahaufinta.
Ta,samu mahaifiyarta da tsohon ciki a jikin ta kuma yana bata wahala don haka tun zuwan ta bata huta ba.
Da maigidan ta ya dawo daga Kasuwan kauye ya samu Bintu tazo ya dan fara daure fuskan shi.
Saida yaga abin arzikin da tazo masu dashi don har shima ya samu shadda yadi goma.
Shine har ya dan sake fuskan shi, yazo har dakin su fuska a sake yana cewa ,a,a Bintu harda tsaraba muka samu haka mai yawa.
Har yana tambaya ko taci abinci da tazo nan dai ya karaci surutin shi ita dai Bintu kai kawai ta gyada mashi har ya fita.
Washe gari tun da safe Bintu ta tashi ta gyara ko ina na gidan nan gidan yakoma wani fes dashi.
Sai zuwa rana ta fahinci ko abinci basu dashi a gidan nan ta saka katon hijjab din ta har kasa ta fita can sai gata da kayan cefanen ta niki niki mai mashin ya kawota gida.
Bata tsaya ba ta girka masu abinci suka zauna ita da yan kannen ta suka ci suka koshi harda mahaifiyarta dake auren wahala.
Maigidan sai zuwa rana ya dawo yana yan kamay kamay shi wai tunda ya fita ko sisu bai samu ba sai dan fura da akabashi da nono yace a dama,mashi,
Matarshi ta mike da kyat ta shiga daki sai gata dauke da kwanon abinci yana mamakin ina tasamu kudi har tai masu girki.
Bayan ta aje yake tambayan ta don ya zaci taciwo mashi bashine don diyarta tazo ta girka masu abinci.
Matar tace mashi yaringa ce ta sayo ta girka muna nan ya wani washe baki yana bude kwanon yai tozali da shimkafa da miya harda nama a ciki.
Yashiga ci yana sakawa Bintu Albarka tare dakai lomar abinci a bakin shi.
Bintu da ke daki tausayin mahaifiyarta ya kamata don tasan wanan susun mijin nata bai aje komai ba sai bakin shaye shayen da yakeyi kawai.
Abu tun bata da,wayo yake haka har yanzu data girma ta zo ta samay shi a hakana.
Dalilin da yasa ke nan take matukar tausayawa Maji akan shaye shayen da dan ta yakeyi don tasa mugun abune mawuyacin abune mutum ya daina shi a rayuwan shi.
Da yamma sai gashi da dan kunshin a leda yana wargale baki yana fadin ina,diyata ne gashi ba,sayo mata dan abin mu na kauye taci don nasan can birni basu samun shi.
Bintu najin haka tafito daga dakin tana gyara daurin dan kwalinta ta nacewa gani Baba.
Ya mika mata ledan ta,karba batare da,tasan abinda ke cikin ledan ba yana fadin ki gyara kici abin marmari ne gare ku.
Ta dauko kwanon ta bude ledan zogalane da rogo dafafe da zafin shi ya sayo mata harda kulikulin da zata gyara shi ya hado mata.
Bintu ta zauna ta gyara tasamo wani kwanon silver na miya ta zuba mashi azaton ta,bazai karba ba sai gashi ya karba har ya riga su cinyewa ko.
Sai faman santi yake zubawa sosai taji dadin ganyen don ta dade bataci ganye ba haka mai yawa.
Kamar yadda tai masu girkin rana haka ta girka mazu na dare inda tai tuwon garin masara data sayo da miyar kuka yaji daddawa da kayan yaji sai kamshi ke tashi ciki.
Haka ta zauna gidan mahaufiyan ta don yafi mata dadin zama gidan mahaifinta da matar uban ta ke sakata gaba da fitina kyashi kishi da hassafa duk ta dagwara mata shi.
Satin ta biyu a kauyen bata fita ko ina kulun tana gida da yan kannen ta suna hira ko tana koya masu karatu.
Ranan dai mahaifiyarta ta matsa mata akan tafita taje gidan yan uwan ta,su gaisa.
Ba don Bintu taso ba ta shirya tare da yan kannen ta mata biyu suka fita zuwa gidajen dangin su.
Suna gap da zasu dawone suka hadu da,wani matashi daganin shi kasan bako ne a garin ko kuma dai yazo ne ba,a nan yake zama ba.
Saboda yanayin shigar shi jikin shi da suturun shi ya banbanta da na mutanen da yake tare dasu a gurin.
Tun da su Bintu suka tunkaro idon mutimin yake kanta duk da katon hijjab din dake jikinta bai hanashi kallon ta ba.
Sun kawo daidai inda suke Bintu tai masu ina wuni gaba daya suka amsa cikin washe baki, a hankali mutumin ya tambayi wanda suke tare wanan a garin nan take ne ?
Har zasu wuce sai dayan mutumin yace wa dayar kaunan Bintu a,a Dije bakuwa kukayine yarinyar ta tsaya tana cewa eh yayan mu dage Birni ne tazo.
Su dai suka wuce zuwa gidajen da Inna ta tsara masu sutafi sukai Bintu ta gaida su.
Agajiye suka dawo gida lokacin yanma tayi ko gashi batai sallah la,asar ba don haka ta shuri buta ta nufi gurin alwala don kada lokaci ya shige.
Inda ta idar da sallah tana zaune mahaifiyarta take tambayan ta kawo mata abincine tace sun koshi tasha fura a gidan kakanta.
Sai ga,yaro yana sallama yace wai ance ana sallama da bakuwar gidan nan.
Bintu dake daki a ran ta tace ai kaji matsalar wallahi shiyasa ban son fita ko ina wallahi.
Bata so fita ba amma mahaifiyarta ta takura mata akan sai tafita badon taso ba haka ta shirya tafita cikin katon hijjab din ta kamar kullun.
Wanan mutumin da tagani a cikin gari dazun shine tsaye a kofan gidan nasu ya jingina jikin shi da motar shi baka henixe,
Yana dan kada makulin motar dake hannun shi a hankali, yana ganin fitowan ta ya dan fadada murmushin shi.
Yana cewa barka da fitowa gimbiya sai kika gannin kwasan kofan gidan ku babu tsanmani kuma ko?
Murmushi tayi tana fadin ina wuni yace shaf kinga na manta bamu ko gaisa ba ko ya kuke ya garin kuma?
Ta amsa da Alhamdullahi,
Yace ko da yake nasan ke bakuwa ce a wanan garin don ban sanki ba a garin namu.
To nidai sunana Mohammed Kabir kuma ni haifafen wanan garin ne ina aiki a abuja ne ina da mata biyu da yara biyar.
Jin haka Bintu ta dago kai tadan saci kallon shi yace yes kwari kina mamaki ko nayi yaro da,tara iyali haka ko?
Gashi kuma nagani ina son karawa ta uku ke nan insha Allahu idan an yardan min.
Mahaifina shine hakimin wanan garin nine kuma dana uku a gidan mu don yan uwana da kowa nawa suna garin nan da zama nine kawai Allah yakaini wani nahiyar zama.
Ina aiki a Federal houses ne a can da fatan kin gamsu da bayani na.

A LOKACIN MU KE,,,,,,,
Zau ne take a tsakar dakin da ta gyara da sunan ta wanda babu mai shiga daga ita sai kawayen ta dakan shigo gidan jefi jefi.
Kwalaben kayan shaye shayen ta ne ta zube su a kasan tana dan mixed din su a cikin wani drinks dake gaban ta.
Mahaifiyarta ce tashigo dakin unexpected taji muryan ta a bayan ta tana fadin,
Raihanatu ina kika shiga ne haka tun safe robon ki da gidan nan ne?
Daga sama taji muryan uwar nata a dakin shigowan uwar bai hanata yin abinda takeyi ba a lokacin.
Idon mahaifiyar kar akan kwalaben maganin da take juyewa daya bayan daya.
Wanan kuma may nene kike yi haka tambayan ta ya koma akan abinda taga Raiha din tanayi a zaune daga ita sai yar farar shimi dake jikin ta.
Raiha tace cikin rashin damuwa ko tsoro magani nake hadawa na dan sha kafin na kwanta.
Amma ai wanan maganin haka masu yawa kamar ba na ciwo bane?
Raiha ta juyo tana facing din uwar ta take cewa, ba wai na ciwo bane ko wani abu kawai dai don naji garau ne a raina.
Da mamaki mahaufiyarta ke kallon ta tace kiji garau da shan wanan uban kwalaben haka.
Raiha tai murmushi tana cewa kai haba mama wanan aiba komai bane kawai dai muna shan shi ne don ya karawa mutum lafiya da karfi.
Raiha, Raiha kodai shaye shayen da yan unguwa suke fadi a kan kinayi gaskiya ne.
Hmmm Umma kada ki dauki zancen hassadan su a gaskiya mana hassada ne kawai irin na mutune da zaran sunga kaci gaba.
Tana fadin haka ta dauki cup din da ta zuba drinks din a ciki ta kwankwade Umma na cewa ke, ke, ke
Yanzu Raiha wanan uban maganin zaki durawa cikin ki kina da hankali kuwa Raiha?
Haba Umma relax ba zai min komai ba don ba yau na fara shan shi ba ai.
Innalillahi wainna alaihim rajiun, Umma take fadi yaunzu Raiha irin rayuwan da kika zabawa kanki ke nan?
Mace da ke kike shaye shaye haka ko acikin shaye shayen kuma sai naga naki yafi ma wanda nakeji karfi.
Hmmm kawai Raiha tace tare da kokarin mikewa tsaye take wani jiri ya dauke ta takoma ta zauna.
Umma ta kara saka salati tare da tafa hannun ta biyu tana fadin na shiga uku ni Lami yanzu Raiha ashe da gaske kina shaye shaye,
Sai kuka tajuya tabar dakin cikin tashin hankali ta samu mijin ta dake daki zaune yana shan shayin data hada mashi.
Ganin matar shi ta shigo tana kuka yasa shi saurin cewa, may yafaru Lami,?
Gefen shi ta samu ta zauna tana cewa malam ashe, zancen nan da muke ji gaskiya ne akan wanan yarinyar Raiha.
Zancen may ye gaskiya Lami?
Ya tambaya cikin son jin ba,asin zancen da tazo mashi dashi wanda bai fahinta ba.
Tace zancen shaye shayen da Tanimu yazo maka dashi tana yi bamu bincika ba muka haushi da fada.
Yau sai gashi Allah ya nuna min nagani da idanuwa na ta fashe da,wani irin kuka cikin tashin hankali.
Malam bai san lokacin da ya cire hular kan shi ba ya fara fifita dashi a hankali.
Yana fadin Inna lillahi wa,inna alaihim rajiun, yanzu ita Raihan abinda take yi ke nan har a gidan nan.
Ya mike cikin sauri ya nufi dakin Raiha inda ya samay ta har syrup ya fara aikin shi a kanta tana kwance daga ita sai dan shimin dake jikin ta tai dadaya da ita.
Yace ke Raiha, Raiha fa dake nake magana ko bakijina ne wai?
Raiha ta dago kai cikun mayen da ya dauki caji a jikin ta tace haba Baba please ka barni barci nake ji .
Inna lillahi yake maimaitawa don ganin abinda idon shi yagane mashi kan yarsu Raihanatu dake buge lis a cikin maye.
Haka suka kwana cikin tashin hankali a wanan daren don sun kasa runtsawa.
Malam sai fadi yake yanzu ashe kallon da mutanen shiya suke min ke nan ban sani ba suna min kallon mutumin da,ya,kasa tsare tarbiyan gidan shi.
Mutumin da baida kwabo ko tace ga iyalin shi suna,min kallon mahaifin yar maye a cikin shiya.
Lami tace nifa malam dama na dade ina,zargin wayewan yarinyar nan yai mata yawa wanan facali da take da kudi yadda,ranta ke so a ina take samun su haka.
Mijin yace bar wanan zancen Lami yanzu zancen shaye shayen nan zamuyi muji yaushe ne tafara shi har girma mata haka.
Washe gari Raiha bata tashi da wuri ba sai musalin karfe tara na safe tafito daga dakin ta don yuwan ne ya,tashe ta.
Dama shi kayan maye haka yake da zaran ya sake mutum sai ya ji cikn shi tankar babu ko hanji a cikin sa.
Sai neman abinda mutum zai zuba a cikin shi a haukace zai far ma duk abincin da ya samu yaci.
Brush tayi ta na kokarin shiga daki taji muryan mahaifinta yana kiran sunan ta alokacin.
Tai mamaki da taga har wanan lokacin baifita ba kamar yadda yasaba fita tun da farar safiya zuwa sana,an shi ta aski da yake wanzanci.
Nam Baba ta amsa mashi cikin nuna jin wani dar da kiran shi don bata san wai tayi laifi ba.
Tazo ta tsugun na gaban shi tana cewa gani Baba, wani irin kallo ya watsa mata amma ko ajikin ta.
Gani baba ta kara maimaita mashi cikin ko in kula da kallon da yake mata a lokacin.
Yanzu Raihanatu shaye shaye kikeyi a,rayuwan ki bamu sani ba ashe.
Kallon inda mahaufiyar take tayi cikin wani yanayi daya ba uwar tsoro sosai don bata san yarinyar takai haka ba ma sai yanzu ta hango a bubuwa da dama daga diyar tasu.
Baba bafa wani abu mai karfi sosai nake sha ba wanda kawai zai kara min karfi ne ta fada cikin nuna rashin jin tsoro a ranta.
Malam baisan lokacin da ya mike ba yafara kai mata duka amma Raiha ko gezau batayi ba.
Ganin haka yasa shi samun guri yazube sai wani zufa ya fara karyo mashi.
Raiha ta juya zuwa dakinta, babu ko damuwa da yanayin da taga uban ta ciki sai uwar ta ce take ta faman rusa kuka wiwi.
****** ********* ******
A Abuja an kira manyan yan kwallon da aka ga sun cancanci a kira su, daga various state din wanan kasan,
Inda sadauki ya samu daga sokoto aka sashi su uku suka wakilci jahar tasu ta sokoto state.
An kara,fahintar dasu wasu abubuwan kara wayar da kai inda anan kuma aka yaba wa su sadauki da suka halarci wasan da akayi a kasar ghana da suka tafi.
Ban wasu yan wasan suka,fara sanin su a lokacin inda akai masu bayani kan zasu dawo nan bada dadewa ba don fara wasan da zasu shiga kasashen duniya,yi.
Da zasu dawo gida anbasu kudade masu tarun yawa wanda zai amfane su a rayuwan su.
Daga haka suka,shirya dawowa gida a jike dasu ga mata sai wace mutum ya zaba amma shi sadauki duk basu a gaban shi saboda mace bata a cikin ran shi gaba daya bai ma,taba jin wai son wata mace ba,a,ranshi.
Kuma Allah ya kare shi daga cikin matasa masu sha,awa ko yaushe, shi kawai baida, wani guri sai kawai ta iyayyen shi da yan uwan shi.
Cikin dare suka sauka sokoto inda yai tashan mota ta kaishi har gida da ga shi sai, yar jakar shi kawai daya,rataya kamar kulun.
Yana isa gida cikin gida ya,shiga inda ya fara karo da Nafisa kaunar shi taci kwalliya zata fita,
Bata ce dashi kalla,ba,shima baice da itaba sai ganin da tayi bai da niyan kaucewa a hanya yasata dan jaye jikin ta ta bi bango har ya shige ciki ita kuma tafice daga gidan kawai.
Ba sabon abu bane wanan gare shi don in so goma zasu hade da Nafisa bazata taba tanka mashi ba ita.
Maji dake zaune a falon ta taji shigowan shi da sallama a bakin shi, cikin fara,a take cewa a,a kai kana hanya ne dama ashe?
Yai murmushi yake cewa, yanzun muka sauka ai bamu jima da isowa ba garin.
To yaya hanya ya kuma taro da,fatan komai ba matsala dai ko?.
Yace cikin aje jakar shi saman kujera komai Alhamdullahi Maji mun samay ku lafiya,dai ko ?
Lafiya kalau muke sai godiya ga Allah .
Jin shiru yake cewa ina,su wa yan nan suke ne naji gidan shiru mana maji ta,bashi amsa da cewa.
Amira bata dade da, shiga nan gidan su Aisha ba,wai zata karbo wasu takardu a gurin ta ita ko maryam tana ciki wai wanka zatayi.
Ya zauna da kyau saman kujeran yana fadin kai na dai kwaso gajiya,wallahi tun safe bamu zauna ba muna fitowa kuma na kamo hanya don ban iya kara kwana can kuma.
Shiru baiji ance ga abincin shi ba yake cewa wai ina ita wanan yarinyar ne tazo ta bani abunci naci yunwa nake ji Maji.
Yadan fadi cikin tsigar shagwaba da kuma langabe kan shi saman kujeran da yake zaune akai.
Maji tajuyu tana fadin wa Fatima kake nufi wai ko wa?.
Sunan ta ke nan wanan yarinyar dake nan dakin nake nufi dai.
Fatima kan ta koma gida tun gama exam din ta da tana nan kaima ai kasan da yanzu tafito gaida kai kuma ta baka abinci.
Amma wayan nan sakarkarun basu san wanan basu sai faman dakilar waya kawai suka iya su.
Ke Maryan, maryam fa baki jin yayan ku ya dawo ne fito ki bashi abinci don Allah.
Sai ga martam ta fito daga ciki da murnan ta tana fadin yaya sannu da,zuwa wallahi banji dawowan ka ba.
Nan suka gaisa da ita yana tambayan ta ya makaranta tabashi amsa da Alhamdullahi.
Ta juya zuwa kitchen don dauko mashi abincin maji tace baka bugo waya kana tafe ba,balle ai maka girkin kwarai Allah yasa dai ka iya cin jagwalgwalen nasu dai ma.
Taliya ce akai jeloup din shi da manja sai kifin da,suka,dan zuba cikin shi kadan.
Tun a ido yaga abincin bai mashi ba shi yanzu da,yasaba cin girki mai dadi a gida ko yaushe shine za,a bashi wanan busashen abincin yaci.
Yana, kai cibin farko a bakin shi yaji bai ma iya hadiye wa don salaf yake kamar ba komai a cikin shi.
Kai wa yai wanan mugun girkin haka kuma,ba test ba komai abu haka,busashe dashi?
Ai dama nasan bazaka iya ci ba,don wa yan nan komai basu iya ba ni ai tun tafiyan Fatima, wallahi duk komai ya jagule min.
Yanzu dubi falon nan kamar ba yan mata ke cikin sa ina ga,rabon shi da samun gyaran kwarai tun Fatima na garin nan,
Sai lokacin ya daga ido yabi falon da kallo yaga duk a hatgitse yake ba kamar yadda Bintu da take nan take gyara shiba.
Maji tace ina da kaman wa yan nan ba zan zauna ina masu girki da,gyaran daki su sau dai suci su mike kafa kawai.
Abu na farko da yazo mashi a,rai shine yanzu ya fara sanin advantage din zaman Bintu gurin Maji da take fadin zaman yarinyar yana da matukar amfani a,gare ta musanman yanzu daba lafiya gare taba sosai.
Ya juya gurin maryam yana fadin idan bakuyi
wa Maji abinda ya dace ba,sai wa zakuyi wa a haka zakuyi aure baku iya komai ba,a,rayuwan ku ?
Amira ta shigo tana mashi oyoyo ya,dakatar da ita,da,fada yana cewa dallah gafara mara wayo kawai yanzun ace kuna gidan nan amma zaku bar muna uwa da aiki dubi falon nan
Yanzu dubi girkin nan waye zai iya cin shi haka duba,fa ki gani abu haka,busashe dashi.
Yamike tare da tsalake abincin zai fita zuwa dakin shi maji take cewa ai gashi nan in anyi magana kace Fatima yar kauye ce to ga ranan yar kauye yau don tafi yan bitmrnin iya komai.
Shi dai yafita zuwa dakin shi ya,sakey ya,bude saida ran shi ya,baci yadda yaga dakin nashi duk dashi ya barshi hakana da datti ya tafi.
Amma ai yaga da ko yana gari yakan dawo ya samu an gyara mashi shi tsaba ya shige cikin jin dadi da,shakan kamshi.
Haka ya daure yana abu tsanda tsanda tunda yanzu yafara zuwa birane yana ganin komai net sabanin yadda yakw da,can baya.
****** ********* ******
Tun zuwan Kabir gurin Bintu sukai musayan nomba dashi tun wanan lokacin bata da,shakat dashi daya koma abuja ko yaushe a cikin waya suke.
Tun bata saba ba tana,darrr dashi har ta,fara sake jiki tana,bashi amsa idan ya,bugo yana tambayan ta,abu.
Gashi da,tambaya kamar dan jarida yake bai minti biyu bai mata tambaya kan wani abuba ko wanda ya shafi rayuwan ta ko kuma,na kauyen su.
Taji dadin zaman ta da mahaifiyar ta don dan kudin da Baba ya,bata da,wanda maji tabata sai nata da tazo dashi da kuma kabir da zai tafi yabar mata su take gubtsurawa suna amfani dashi da uwarta.
Kauye ne ba,wani abin saye inba,abinci ba ita kuma dama yarinya ce da bata damu da kashi kudi ba ga banza da wofi.
Uwarta yanzu kan tai matukar kyau, don duk komadan nan da ciki yasa ta da,yunwa yanzu duk sun bace ta murje tayi kyau da ita.
Don yanzu tana ci tana sha sau uku ga yini sabani da can da,dakyat take samun koda sau daya a wuni.
Takan kira maji ko Anty Amira da maryam suyi waya dasu don su kadaine dama take da nomban su, sai wasu class mate din ta na can sokoto din.
Maji takan tambaye ta Fatima yaushe zaki dawo ne sai dai tayi dariya tace mama ai zan dawo idan mamana ta haihu.
Maji kance to Allah ya sauke ta lafiya ta ansa da Amin mama kawai sai dai a zuciyan ta takan ce wai sai dai Allah ni da,dawowa gidan nan kan.
Amira kuma takan kira ta suyi ta mata korafi don Allah ta dawo au fitinan yaya sadauki ya ishesu duk abinda sukayi basu iya,ba,sai fada da,zagi yake masu.
Bintu takanyi dariya tace halin yaya ai sai shi ni wallahi har gobe tsoron yaya nake ji gada ya,makeni.
Ke nan harda tsoron shi yasaki gudu Bintu ai bari ya,shigo sai na fadama shi abinda kikace,
Yanzu antu maryam ko kin fadi nai mashi nisa ina zai ganni ya,ma manta akwai wata yar kauye dama ya matsu na bar gidan nabar mashi amma yasani wallahi ban bar mashi mama ba,
Au haka kikace ai gashi zaune wallahi yana jinki duk abinda kike fadi tace ai gaskiya na fadi mama ce bai so na kwace mai ni da mama kuwa sai gani sai hage mutu karaba.
Ta kashe wayan dif tana dariya don tasan babu inda zaigan ta a yanzu sai dai a,waya kuma baida nomban ta ai.
Amira na kashe wayan tana dariya ita,kadai Maji take tambayan ta ita dawa haka,tana,dariya ita,kadai?
Nan take fadawa Maji yadda,sukayi da,Bintu da,amsar da,Bintu din ta,bayar akai.
Ai gaskiya,ta,fadi yayi dawani kuma ita,dai tayi gaba kuma,bai iya,rabani da,ita din.
Anyi dace lokacin da maman Bintu ta haihu mai masa tazo zagayen gidan su don haka,maji taba da sako na,barka,da haihuwa akawo wa,Bintu tabawa mahaifiyar ta.
Gwagi bata,kawo kayan ba,sai ta biya gurin mahaifin Bintu ta,gwada mashi abin arzikin da aka aiko albarkacin Bintun shi.
Nan tabawa ta shiga sake magana wau kura da,shan bugu gardi da kwasan kudi, yanzu ne da yarinya ta girma ta juya mata baya,bayan ta gama wahala da ita ta kama uwar ta.
Ita ko uwar ba kunya don taga gurin ci shine zata wani dinga haba haba da yar da ta watsar tun tana yar ficiciyar ta sai ita tasha,wahalanta yanzun kuma,an gujeta,
Gwago ce ta,bata amsa da cewa ke tabawa kiji tsoron Allah wallahi har wani wahala kikai wa Bintu gidan nan
Ko dai Bintu ta,wahala dake da,yaran ki tana,maku bauta dare da,rana,
Ai ke baki da ko bakin magana don kiri kiri kisa yarinyar nan takasa zama gidan uban ta don bakin matsin ki na tsiya.
O lalai dangin miji dangin tsiya dama ai nasan abinda kuke fadi ke nan har kukai muna,funcin da,sai da,kuka,dauke ta don kuga yadda,zanyi.
To da,kuka,dauketa don tana,min bautan da kukace na mutune ko kuwa wai.
Tabawa ban dai baki ko tsunke a cikin kayan nan wadda akace akawai ita din zan kaiwa abinta don ban iya cin amana ba ni.
Gwago ta tattara kayan suna sa,insa da,tabawa tabar gidan dasu zuwa kauyen da,Bintu take gurin uwar ta.
Ba maman Bintu har ma Bintu din kanta saida tai mamakin wanan kyauta na bajinta da Maji ta,aiko mata dashi.
Nan aka,shiga nunawa mutane kun san bakauye ba ya boye alheri komai kankantar shi .
Anyi suna lafiya don itakan mahaifiyar bintu sai tace shigan Bintu Birni alheri ne a gare ta.
Don wanan haihuwan da alheri yazo mata sabanin wanda takeyi a baya can busai busai sai kamay kamay kawai.
Don ko Muhammad Kabir da ya mutu son Bintu yanzu sai da ya aiko da nashi alherin duk da ma Bintun bata fada mai ba ji yayi gurin abokin shi na kauyen dayasa ya saka mai ido akan al,amarin Bintu din da bata masan yasaka a saka mata ido ba.
****** ********** ******
Bayan haihuwan mama da sati biyu na shirya komawa gida garin mahaifina tunda naga mama ta yi karfi yanzu,
Ba yadda batayi dani ba akan na tsaya na kara kwanaki amma naki, tsayawa.
Mama tace to idan Kabiru yadawo bai samay ki ba fa nace mama nifa ba,wai yana gabana bane mutum da mata uku yaya zanyi dashi gani da tsoron tsiya.
Asalima ni saboda,shi zanbar garin nan idan ya tambaya kice mai na koma sokoto gaba daya.
Tace kaiyya saikace ke ba diyar hausawa ba kuma musulmai zakice kina tsoron kishiyoyi.
A,a mama ba zan iya ba naga yadda mamana na sokoto take fama da,nata don haka abin tsoro yabani.
Gara na samu yaro bakauye dan uwana,a zarga min dashi yafi min ruwan idon sunan muna Abuja.
Dariya naba mamana take cewa kai yaro dai yaro ne ai abin sa,a ne ni yanzu da nake shan wahala a,nan kishiya gare ni?
Mama,naku daban ne nace ni dai zan tafi na kwashi komatsena sai yar karamar tashar garin amma,sai na rasa mota .
Akan kada,na kara kwana a garin yasa na tare wani mai mashin mukayi ciniki dashi la,asar sakaliya, sai gani garin mu har kofan dan gidan mu.
Tun daga kofa nafara jin harshen mama ta,bawa tana fada da,wata yar yan uwanta da,ta dauko riko.
Na,shiga gidan da sallama na inda na samu kafin na,shiga mama ta kewaya ban daki a lokacin.
Dakin da nake na nufa da kaya na nasamu dakin duk kashin awaki ya bata shi kuma,wai akwai mai kwana acikin sa hakana.
Ina ciki na fara gyarawa naji muryan ta tafito daga ban dakin take zuciya ta ta tsinke, don na san nadawo wa turke na mai cabo ke nan.
Na fito waje a tsorace nake da ita nafito ina cewa sannu da gida mama mun samay ku lafiya.
A darara ta amsa min da yauwa anga dama andawo ni dai nasan ai ba gurin zuwa sai gona.
Na juya zuwa cikin dakin naci gaba da gyarawa kamar yadda,na fara da farko kafin wani lokaci dakin yai neat duk da dakin hakine da,daben kasa a,kasan shi.
Na idar da,sallah magariba naji shigowan mahaifina nan nafita zuwa yi mashi sannu da,zuwa.
A bazata yaganeni yace a,a Bintu andawo ke nan yaya,su wajen maman naki nace duk suna lafiya suna gaishe ku.
Na mike na koma dakin mu tare da kunna dan chager daki mai aiki da battery.
Daga cikin dakin namu ina jin mama tabawa tana,wa Baba na mita wai gashi na,dawo wurin ta, na kasa zama da uwar nawa.
Naji Baba yai gyaran murya yana cewa tabawa ina son ki sani nan gidan uban Bintu ne bata da gid
an dayafi mata wanan don haka tana da incin duk lokacin da taga dama ta shigo ta zauna iya adadin kwanakin da take son yi.
Jin firinan su zauyi nisa yasa na jawo wayana na kunna kira,a ta yadda ma,ba zanjiyo hayaniyar su ba.
Ban fita ba daga dakin sai washe gari tun da safe nafito na fara gyaran tsakar gidan mu dama har ta,wajen gidan.
Dama aikinane da nake gari da ban nan kuma ba mai yi kowa baida lokacin yin shi.
Na tara wanke wanke nafara saiga mama tafito tana wani yatsune fuska wai ita a lokacin ta,tashi daga barci.
Muryan ta naji daga bayana tana fadin kada kuma mahaifinki da yan uwanku su gani suce ina sakaki aikin bauta.
Bance komai ba,sai cewan danayi mama ina kwana.
Ta amsa,a,wulakance tana aikin girkin dumamay tana minti kan fadan su da Baba akaina jiya da dare sai fadi take dadin abindai nima na haifa a gidan don haka na wuce gori ga kowa balle ace min ni juya ce.
Ina kallo suka cinye dumay mayn su ita da,yaran ta ban damu ba na,shige daki sai zuwa rana dana yunwa zai kashe ni nafito zuwa bakin wani shago na,dan sayo garin kwaki yakai mudu biyu da,dan sugar na na,saka a hijjab dina na,shige dashi bata gani ba.
Ina zaune ina sha idona yana kawo hawaye sai ga,wanan yarinyar da mama ke riko ta dan zo gabana tanayi tana leken kofan mama tace don Allah ki san min nasha nima basu bani dumamay ba wai ba yawa su Lawal taba suka cinye da ita sai cewa tayi na kankare kanzo naci.
Kuma kanzon ba gishiri ba,komai wai haka zanci shi dan kadan ne bai isheni ba.
Gaba daya na tura mata kofin garin nace yi sauri ki shanye kafin ta fito tagan ki tace zan koya maki munafunci.
Tas yarinyar ta,shaye garin gaba daya tafita da,sauri take tabani tausayi.
Tun ranan duk dan abinda naci tare muke ci da ita, komai rashin yawan shi kuwa don a daki guda,muke kwana da ita.
A haka dai nai ta,zaman hakkuri a gidan mu da matar mahaifina watarana tabani abinci watarana kuma tace bayawa ancinye.
A haka kwanaki suka shude min zuwa satittika har wata ina gidan mu zaune kamar wata bare can.
Wata rana ina zaune na gama duk abinda nakeyi na gida kamar kullun sai ga wani yaro ya shigo yana cewa wai ana sallama da Bintu.
Kafin in magana mama ta karbe da fadin wanene kuma wanan da yamman nan.
Yaron da aka aiko yace yace nace mata wai kabir ne kafin mama tai wani magana na mike kawai na fada daki sai gani tayi na fito saye da hijjab dina har kasa cikin wanda Maji ta dinka min lokacin ina gurin ta.
Nace mama zan fita na gan shi daga garin su mamana yazo, ban tsaya jin may zata ce ba na,sakai na fita zuwa waje.
A jingine yake gabab motar shi kirar hilux irin ta,shiga kauye, ya,sanya wata koriyar shadda da akaiwa dinkin Jamfa harda hular ta kalar kayan.
Tun daga fitowa na yake sakar min murmushi, sai dai wanan karon ya dan kara min hasske da kiba kadan.
Barka da fitowa, kalman da ta tare ni dashi ke nan da na iso inda yake tsaye,
Tuni naji wani wani kunya ya lulubeni saboda tafiyan da nayi ban fada mai ba kuma,nan garin mu da nazo ba,services ko dayaushe.
Na dan rusun na kadan na,gaishe shi, tare da,tambayan shi yaya hanya.
Cike da,fara,a yace hanya Alhamdullahi mai gaskiya,
Murmushi nayi nace gaakiyan may kuma nayi har ake kiran min ita cikin kunya na,fadi hakan.
Sai murmushi naji yayi ya dan kalleni ya kada kan shi kawai,
Yace wallahi Fatima baki kyauta min ba haka,kawai ki kama hanya ki wuto baki fada min ba ko a waya,
Sai kawai da naji shiru natura a,diba min ko lafiya ake ce min wai ai kin dawo nan.
Gashi kuma ban samu zuwa ba,don an turani wani course a lagos sai last week na dawo gaskiya banji dadin yadda kikai min ba.
Cikin yar muryata nace to kayi hakkuri nima,tafiyan tazo min bashiri ne.
Yace gaskiya banji dadi ba don sai ma na,fara zargin kodai ban samu karbuwa bane a gurinki shi yasa.
Dan satan kallon shi nayi tukun, san nan nace a kunyace ,a,a ba hakana ne gaskiya.
Sai naji ya sauke ajiyan zuciya yace tau Alhamdullahi,
Amma kuma kin shirya zaki iya auren mai mata har biyu ki zama ta uku?
Dammm naji gabana ya fadi don an tambayeni abinda nafi kowa tsoro yanzu watau kishiya.
Na dan kwantar da murya cikin dakewa nace idan Allah yayi hakan ne ai ban isa naja da ikon shi ba.
Sai ya dan zuba min ido can yace tau kin gama magana ke nan ai tunda kince Allah.
Ban nuna wani alama najin tsoron maganan shi ba amma sai nace ai Allah shike komai dama.
Nan dai muka dan taba hira dashi yana min karin bayani a kan, shi.
Yace matar shi ta farko yar uwarshi ne garin su daya auren gida akai masu shida ita duk da dai su suka hada kan su.
Azuciyata nace kaji matsalar ba yace sai tabiyun ita soyayyace ta hadani da ita kaunar abokina ne dake sokoto lokacin ina,aiki a sokoto kafin na koma Abuja mukayi aure da ita yanzun yaranta biyu dani.
Ya,kare da,cewa sai kuma yanzu da wata farar tantabara ta,sace min zuciyana a lokaci guda duk da can baya banyi niyar karin aure ba ina ganin matana biyu sun isheni rayuwa.
Sai gashi ganin farko da nai maki naji kin kwanta min a zuciyata fiye da tsanmani na.
Dafatan zan kara samu karbuwa a gurin ki bayan mun dan taba hira yake ce min zai koma don gobe yake son ya koma,sokoto ya dauki matar shi tare suka,shigo amma ya barta sokoto taga gida.
Yace min ina zan samu yara su sauke min kaya a,bayan motan shi
Nace cikin yar murya lah, dama ka barshi zuwan da zakayi gurina shine harda dawainiya.
Yace ai nasan baku rasa ba amma ni ban saba zuwa guri babu tsaraba ba.
Yaran makwabtan mu dake wasa a kofan gidan su na kira inda suka shiga da kayan cikin gida.
Nayi sa,a mama tafita zuwa uguwa don bata zaci lokacin zai tafi ba nasan da bata fitaba a lokacin.
Kafinta dawo nida Farida yarinyar da take riko muka tsince kayan tea da su indomie muka,boye inda bata gani.
Sauran muka barsu kofan dakinta inda inta dawo zata gani.
Tana ko shigowa tai tozali da kayan sai cewa tayi cabdi jam wanan kayan alherin kuma haka fa nake gani.
Farida tabata amsa dace wa Bintu aka kawowa su, mutumin da yazo kafintai wani magana sai ga babana yadawo daga gona shima tambaya yake.
Tace yarka aka kawowa su sai ka tambaye ta ko waye nidai in kun kwaso rigiman birni babu ruwana.
Allah ya,sauwaka babana yace sai ya samin kira nafito ina mashi sannu da zuwa.
Yakece sai na dawo na samu wanan uban kayan haka na tambaya akace waikece aka,kawo wasu.
Nace eh Baba Kabir ne dan hakimin Rabah yakawo min su dazun dayazo.
A ina kika san shi Bintu, Baba ya tambaya cikin son jin inda na san Kabir, nace Baba da naje gurin mamane shine muka hadu dashi a can.
Allah ya kyata yace inda ya isa gurin kayan buhun shinkafa dan gote sai jarkan mangyda da doya mai yawa sai tumatur din leda katon guda da taliya leda biyu,
Dankari inji Baba duk wanan din muke dashi haka nace eh Baba mu yakawo wa tsaraba yace,
Baba yace Bintu idan kin san bakya son shi kada muci kayan shi yazo yai muna,tasau watarana nidai k8nga banda,shi.
Shiru nayi ban yi magana ba baba ya juta zai futa nace baba zan dauki doya da taliya naba su Ama don su suka kwaso min kayan zuwa cikin gida.
Yace hakan na da kyau ki baau yadda ya dace azato mama tabawa bazata kalli kayan ba amma dana dauki doya manya zai kaiwa su Ama sai ji nayi tace kai amma kedai baki san ciwon kanki ba,
Wana abin duka zaki basu don kawai sun kwoso maki kaya maza rage su kinji nace to mama.
Nan aka,shiga sha,ani da kayan mukan mun boye namu bata sani ba ni da farida mun samu na karyawa safe da yamma mu faki idon ta,muyi amfani da abin mu.

A LOKACI MU KE,,,,,
Zancen neman da Kabir yake min ya kewaye kauyen mu,sai ga yan uwan shi har gidan mu sunzo gaidani wai kuma suga ko wacece ni din.
Gami kuma da nuna goyon bayan su dari bisa dari akan neman da dan uwan su ke min.
Kamar yadda,dangin miji suke nuna goyon baya idan dan uwansu ya,tsiri aure, komai mutuncin da akeyi da uwargida sai an samu masu hakan daga dangin shi.
Nima hakane ya kasance dani don yan uwan kabir maza,da mata haka suke shigowa ganina,tunda ance masu nima ba a kauye nake zaune sokoto nake zama.
Basu san cewa ko a,sokoton labe nake zaune a gidan mutane kamar kuku.
A gaskiya da farko naso Muhammad Kabir kodon na samu inda na labe na,rufawa rayuwa na,asiri na huta da guzuban mama tabawa da nake ciki.
Yakan zo kusan duk karshen wata gida cikin irin zuwan da yakeyi sai yazo har garin mu da dan tsaraban shi na abin arzki yakawo muna.
Wata rana Kabir yazo wurina sai dai wanan zuwan bai dade ba kamar yadda ya saba dadewa idan yazo inda nake.
Ya ce zai koma na ya bude mota ya miko min wasu kaya dinkakku yake ce min anko yai min tare da,sauran matan shi.
Na karba nai godiya sai kuma ya kawo kudi masu yawa ya bani, amma sai nace ya,bar kudin kayan ma,sunyi min.
Amma sai ya,aje min kudin saman hijjab dina ya,shiga motan shi sai horn din shi naji na,dan daga kai ya sake min murmushi tare da jan motar shi yabar gurin.
A dakin mu saman tsohuwar katifan kadan da muke kwana akai amma na,gyara, shi mutum bai sani tsohuwace ta yagalgale saboda bed shirt da na,sa na,rufe shi lif ba,a ganin sirin ciki.
Dinkin kayane irin ta yan birni jakkuna da,takalma masu tsada sosai, sai kayan makeup set mai kyau dasu turaren suma masu kamashi sosai.
Kayan abinci yadda ya,saba kawowa haka ya ke jibge su a,kofan gidan mu yanzu tabawa shiru kake ji tsakani nada ita,sai lalashi.
Afili amma,a,kasan zuciyar ta,tankar ta soke ni takeji a rayuwan ta don kishi na take balain ji duk kiyayyan da,takewa uwana ya koma a kaina yanzu. Sai dai tana dan waye wane kawai don tasan wani lokacin nima nakan dan tsula mata tsiya yadda naso.
Don ban san ya,akayi tasan muna boye wasu kaya,ba,sai ranan ta zaci ko yanzu iri dane da,zata kwace min abina tabawa diyan ta har yan agolan da tazo aure dasu gidan mu sun fini dara a lokacin.
Sai ganin Tabawa mukayi a kofan dakin mu tayi tsaye kerere ta re da,daga labulen dakin cikin tijaran ta na yan iskan matan kauye take cewa,
Ke Bintu kwaso sauran kayan nan da kika,boye wanda aka kawo muku wai ke munafuka,shine kika boye kayan shayi wai don kada na,sha,
Ti jiya banyi barci ba ina jinku kuna sha ke da muna fukan can Farida, don haka na leka naga may kuke don haka kifito dashi nan.
A zatonta zan mike na dauko mata kamar yadda da can nake mata cikin rawan jiki.
Amma,sai taji murya na yau ina cewa,
Eh ko kingani fa,
Sai may,
Ina dai ba,sata,nayi ba,nawane ni aka,kawo wa ko ?
Don haka sai yadda,naga dama da abina Farida ce idan kince na barbata abarta mana yunwa ya kasheta.
Baki bamu abinci yadda ya dace sai dai kibawa diyan ki
Don Allah yai muna mafita shine kuma zaki nuna halin ki na hassada haka.
Eh lalai kuwa Bintu sai yau na,kara yarda kin shiga Birni tunda har ina fadi ki fadi haka,
Nace mama kece kikaja hakan don yakamata ace yanzu na ci ragowa gareki ko dan dan girman da na,kara.
Amma ke kullun sai kokari kike kiga kin mayar dani baya kin tausheni kin ha,ince ni kin fifita diyan ki a kaina.
Don banda,uwa agidan ai ina dai gidan gidan ubanane dole ko abarni na zauna ciki.
Nan tafara rafa hannayen ta cikin mamaki da lalami tana fadin eh lalai zaman bariki ya nuna kan shi yau kan.
Baba yana dawowa tafara fada mashi bata kai karshen zance ba yakwala min kira nazo, nace gani ba.
Yace Fatima yanzu na dawo gida maman ku ta tare da,zancen da ban san halinki bane.
Nan na koro mai duk kan maganan har karshen yadda mukayi da ita,da,safe.
Ya juya gurinta yana cewa Tabawa kiji tsoron haduwar ki da Allah horo da,yunwa ko dabba,ba,ai ma,shi balle mutum dan adam mai tunane.
Yanzu ba gashi a,sana din ta alheri yana sauka muna duk karshen wata sai yaron ga dan gidan hakkimi ya kawo muna abinci ba.
Nan dai har sun hau da Baba ko may ta gani sai gata ta sauko don kanta ta, dawo tana cewa haba Bintu ke diya tace kada ki yarda mutane su zuga ki ki min rashin mutunci suyi dariya.
Nace komai ya,wuce amma da safe indan Baba ya fita sai ta turo yaran ta da,kwano wai na yan mata kayan shayi ta dan kada.
Da,nafita iyawa sai na,zuba mata dan kadan a cikin roban nace akai mata hakana,baida yawa.
Shine samun saukina a gidan mahaifina da mama tabawa yanzu kadaran kadaham muke da ita.
****** ********* ******
Shine yau da Kabir yazo ya,tafi da,wuri ashe tare da,matan shi yazo sun zo yin bukin wata diyar yayan shi ne a,Rabah.
Shine yazo da iyalin shi gaba daya amaryan shi bata zama a,kauyen sai dai tazo ta,wuni takoma gidan su.
A nan aka,samu wata,tsegumama ta tsegunta mata zancen neman auren da kabir keyi yanzu.
Nan ta,tayar da,hankalinta sosai har ta tambaya,akai mata,kwatancen gidan mu sai gata,ita,da,kannen zawarori biyu.
Ni dau ina daki kwance ina kallo a,wayana,da,aka,karbo min caji sai ji murya mukayi ana,cewa,da karfi sallamu Alaikum ko nan ne Kabir Rabah ke neman aure a fitsarance suka shigo muna gidan.
Eh nan ne inji Farida da,bata san da may suka shigo muna ba,
Eh lalai ashe dole a haukace a so mai mata,biyu an matsu a,tashi gidan haki akoma alminium zalla.
A,a sannun ku da,zuwa sai wani kallon banza suke watsawa,mutane su ga yan birni a dole.
Ina, ita gajar da kabir din ya,wullakanta kanshi yazo har nan gidan wai neman aure.
Saye nake da,wani dogon riga baki cikin wanda yaya,sadauki ya,sayo muna,ghana, a jikina don dashi naiwa Kabir kwalliya da,yazo don haka ban cire ba yana a jikina.
Nai rolling din kaina,da dan kwalin kayan tsaye nayi harde da,hannuwa,daga kofan dakin mu ina kare masu kallo irin wanda,suke ma gidan mu da yan uwana .
Sai da suka juyu ne mukai arba dasu, gaba dayan su ido suka tsura min,
A cikin min kallon kurrullah tun daga kafana gar zuwa kaina o lalai kice min farar fata yabiyo mana kin sanshi maye farar mace ce ko manyace.
Nace ballw ba,farin ya,jawo shi ba,nan sai hali, don may yuyuwa yaga abinda ya,rasa,a,gida ne yazo nan.
Ke kama kanki don ko ba,a,fada,ba,nasan kece yake nema don kece ki kadan yi kama,da zubin yan birni kadan.
Ba shirmay ya,kawo mu ba ni matar Kabir ce ta biyu na,zo ne nai maki kashedi akan mijina,wallahi,
Don ko ita bakauyar dake gida, ban dauke ta wata tsiya ba balle ke dake shirin kawo kanki.
Nace hmmm mijin ki ko mijin mu yar uwa, ba,a kara aure aka,auro ki ke naga dani dake din duk ba,matan gado bane,
Balle ki manta ki kirashi da su nan wai mijin ki aikin makara da,baki tsaya kin auri wanan mai matan ba da,sai ki tsaya,ki auri wanda baida mata,a kiraki matar mai shi.
Yanzu ko tunda mijin wata zamu aura da ni dake kinga kalman mijin mu ya,shigo ke nan.
Ke wallahi, kama kanki dama ku yaran kauye haka kuke da iya magana tankar tsofafin mata.
Nace mazan mu da matan mu kuwa din shi kika gani ga bakauyen mijin ki har ya,rude ki kika,aure shi.
Sosai mukai musayan harshe da su su fadi in fadi wai tana min kashe di na rabu mata da mijin ta,inva haka ba zaki shigo ki samu balai a gidan shi.
Nace kai dama baki zo ba da,ban san balai ke gidan Kabir ba
Don da ma kabir bai a,raina saboda bai min ba amma yanzu zuwan ki sai naji ina,matukar sha,awan auren shi na zama koda ta hudu ne.
Gaskiya,zuwan ki yai min rana sosai din haka kikoma,ki fara shiri nima zan shigo da shirina sai na zo.
Ina fadin haka na juya zuwa cikin daki dama gidan ya fara cika da,mutane don jin hayaniyar da akeyi yayi yawa.
Mata ko suka,saka,su gaba da ihu da,tur da,Allah waddai da halinsu kishi wai hauka,ne da zaku zo gari wa gari ku na kishin hauka wa mutane.
Sai bayan naji tayar da motan su na sauke ajiyan zuciya saboda karfin halin da nayi don duk a,tsorace nake, kada suyi min dan banzan dukan tsiya tunda nice banda gaskiya, nike bi masu mijin su.
Lokacin da,labarin cin mutuncin da matar shi tazo har gida tai min hankalin Kabir yai matukar tashi sosai tunda safe sai gashi kofan gidan mu.
Da Baba na yafara ganawa, kafin daga baya asa a kira ni nafito ina daure da fuskana tamau,
Tun fitowa na,Kabir ya kura,min ido yana kallon yanayin da,na,fito dashi don yana son fahinta da sauki ko akwai magana.
A mutunce na durkusa na gaishe su sannan na koma gefe nace Baba gani,
Mutanen da Kabir yazo dasu suna zaune saman tabarman da aka,shimfida masu idanuwan su a,kaina karrr,
Baba yace Bintu Kabir ne ya samu labarin abinda matar shi tazo hannan gida tai maki shine yazo ya,bada hakkuri akan sabanin da aka samu da ita.
Kaina na sadda kasa nace cikin yar murya Baba gaskiya ayi hakkuri da wanan zancen don tun ba,a shiga ba an fara irin hakan
Ina ga in an shiga gidan baki daya sai ai marus ke nan lokaci daya sukace ,a,a wanan ma,ai baiyuyuwa sam.
Duk da sun fahinci kan zance na ina nufin nafasa ke nan sai suka shiga ba da baki da gyaran zance .
Shiko kabir yana zaune yai shiru kawai abin duniya ya,kai mai ko ina abinda matar shi tazo tayi ta bashi kunya.
Baba dai da yaji irin yadda suke bada hakkuri ni kuma na kafe akan sai dai a,rabu.
Sai baba yace Bintu tashi jeki ciki kawai ma,karasa,maganan dasu.
Namike nashige ina jin yadda Kabir yake sauke ajiyan zuciya daga inda nazo wucewa ta gaban shi.
Ban kara jin zancen ya tashi ba sai bayan kwana hudu sai gashi yazo har lokacin bai sake jikin shi ba dani.
Na fito saye da zani da rigar atamfa mai ruwan jan kalla, dinkin shi yai matukar karban jikina da kyau.
Son in mashi kwalelenka, ranan gyale na yafa ajikina sabanin hijjab din da ko yaushe nake rufe jikina dashi.
Na durkusa na gaida shi a cikin ladabi da biyayya tare da,tambayan shi gajiyan buki.
A,sanyayw yace Fatima kinga yadda kika,wahal dani da,kalman ki dakike fadin wai kin fasa aurena.
Don Allah Fatima koda nine nai, maki laifi, kada kice kin fasa aurena, don baki san irin wahalar da na,sha ba na ganin za,a raba ni da wanan kyakyawan halittan mai suran larabawa a hannu na.
Don Allah Fatima koma may ye kada ki kara cewa zaki rabu dani akan wata, wacce dama ita bukatan ta ke nan nayin haka.
Wallahi ranan da,muka,bar nan nayi tunane dubu a raina don sai na kasa banbance so na yasa kika ce hakan ko kina.
Nan yadan zubo min ido yanaxmai kare min kallon kurullah , akunyace na dan rufe fuskana da hannayena .
Yai ajiyan zuciya yace nagode Fatima don ko hakan ma,sheda ce ta kin sauko zaki yarda dani.
Mun jima muna hira dashi yana bani labarin irin fitin matar tashi saratu yadda sukw kwasan masifa da uwargidan shi a kan lalai ita ala,dole abar mata miji ita kadai
ko da ya zo tafiya sai yace kin hana ni shakat wallahi Fatima gashi haka nazo ban riko maki komai ba.
A hankali nace mai babu,komai, ko haka,na gode ai,
Ya ce sure ?
Nace, mashi insha Allahu.
Haka yatafi ba don ya,so ba yana ta,faman bani hakkuri ya,wuce abinshi.
Anyi wanqn rikicin da Sati biyu ina gidan mu gaban iyayyena hankali a kwance abina na fitar da komai a raina,
Ina zaune ina gyaran ganyen da mama,tabawa tasayo lanbu zamuyi miyan dare dashi.
Ina cikin gyaran ganyen ne sai naji karan diran mota ta tsaya a kofan gidan mu.
Dan dakatawa nayi da aikin nawa ina sauraren ko anyi bakine gidan daga bisani dai naci gaba da aiki na.
Gwago na ce ta shigo gidan da sallaman ta saura kiris na zubar da ganyen da nake gyarawa don murnan ganin ta danayi.
Fuskanta dauke da yalwatacen fara,a take ce min dana karaso gurin ta cikin daukin ganin ta.
Bintu baki da kirki banzaci zaki zo ki share ki zaman ki haka a kauye kin bar uwar dakin ki sai damuna take tunda na koma.
Ledan dake hannun ta na karba daidai lokacin da mama tabawa takw dawowa da makwabtan su.
Mama tabawa tace a,a yau gwagon yara ce a garin kwana biyu kin shige birni abinki.
Nan dai suka dan taba wasa tsakanin su sai kuma gwago take tambaya yayanta yana gona ke nan ko bai dawo ba har yanzu kuma tana son ganin shi.
Ba ,a jima,ba Baba na ya dawo daga daji, sun jima suna hira da babana wanda akasarin hiran akan yar uwar suce da gwago tai jinya takare.
Can tun ina jin hiran su sai na bar jin tashin muryan su, ma,ana dai za ai magana ta,siri a tsakanin su ke nan.
Zuwa can Baba na ya daga murya ya kira ni nazo, na,samu guri dan nesa dasu kadan na,tsugun na.
Baba na yace Bintu gwagon ki tazo tafiya dake ne akan umurnin mijin uwar dakin ki, na can.
Don haka,sai ki harama ki shirya ku kama hanya don kinga mota,sukutun ya bayar azo a tafi dake don ba,ayi zaki zo ki zauna haka,ba harki dade.
A take na bata rai na,tare da,dukar da kaina a kasa, baba na yace ko baki ji may nace bane Bintu.
Cikin yar karamar murya nace naji Baba yace tau yau din nan ki hada kayan ki ku tafi tunda sunyi mutunci haka nima idan na samu lokaci wuri yasha iska zan shigo naga inda kuke.
Na dago kai din nai magana gwago ta watsa min harara dole na noke kai bance uffan ba.
Namike jiki ba karfi idanuwa na,sun ciko da,hawaye amma,ba,wanda ya kula da damuwa na nafara ashirya kayana.
Kafin sallah magariba haka gwago tace sai muyi hara man tafiya kada muyi dare sosai a hanya.
Nan na,dauko yan abubuwa nabawa Farida yarinyar da zantafi na bari cikin uku ban mama tabawa,
Komai da muke boyewa,nabar mata,ban dauka,ba, sai kudin dana,bata ta boye ta tafi garin su dashi idan taga wuya,zai kashe ta a gidan.
A sanyaye na gama hada kayana raina a bace don kwata kwata ban son komawa gidan su maji don bani bukatan zama cikin wanan babban gida mai cike da tarin rikici a cikin shi.
Saboda wancan karon ma banji dadi ba don a tauye nake cikin su sai dai na kulla a raina wanan karon kan zasuga canji sosai a gare ni don su barni na,dawo kauyen mu.
Munyi sallama da kowa mun kama hanya sai dai kallo daya ya ishi mutun sanya alaman tambaya a kaina din yadda nai kicin kicin da raina.
Sai ranan naga mama tabawa ta,tausaya,mun tana fadin haba baban binta in bata son zuwa abarta mana.
Daga Baba har gwago na ba wanda yabita kanta sai kyaleta sukayi kawai.
Mun hau titi da kyau mun saki hanyar dajin mu gwago ta kalle tana cewa Bintu kin bani mamaki sai kace wace za,a kai mugun guri.
Acikin wata raunaniyar murya da take gap da,narushe da kuka nace gwago bawai mugun wuri bane.
Amma zama gidan da,baka,da,alaka da kowa,sai zaman girma,da,arziki kawai, shine nake jiyewa.
Tace da kika zauna wancan karon anyi wani abin ne sai da na nisa kadan nafara fada,mata,duk yadda aka,kwashe da,bata,garin.
Tace ni na sani ai ba yau ba Hajiya kubura munafukace ta,karshe wallahi ko.
Tsayin lokaci muna,tafiya muna hira har muka fara hango cikin garin sokoto.
Unguwan sama road muka dosa inda muka tsaya a kofan gidan Alhaji habu.
Lokacin dare yayi ko don har anyi sallah isha,i don haka cikin gidan muka shiga kai tsaye.
Na zaci gidan mu zamu shiga amma,sai naga sabanin hakan kawai mun shiga gidan masu hali.
A dan tafiyan da,nayi na,samu canji na sauyin launin gidan sosai an canza abubuwa da dama a gidan.
A kofan da aka,sake wanda ban zaci na,maji bane muka tsaya tana sallama daga kofan shiga.
Muryan maryam ce naji tana a,a mai masa,oyoyo harkin dawo ashe?
Sai tafara leken bayan gwago tagani ko ita kadaice tazohangini tayi ina,saye da lace din da Kabir ya dinka min da matan shi cotton lace ne mai laushi sosai da duwatsu caaa a jikin shi.
A razane tace maji yau kan ga yarki ta dawo gare ki gwago ta cika alkawari kowa ya huta dada.
Da sauri ta karaso gareni ta rugumay ni cikin jin dadin ganina a lokacin.
Jin abinda ta,fadi yasa Amira fitowa daga dakin ta cikin sauri tana min sannu da zuwa cikin murna da jin dadi itama.
Maji tafito a hankali daga daki ganin yanayinta yasani saurin fahintar bata da,lafiya a jikin ta.
Inda,take na nufa da,sauri na,fada jikin ta sai ta rungumayni cikin jin dadi.
Ta,dago kai ta kalli gwagona tace mai masa nagode da,wanan karamcin da kikai min dawo min da Fatima,a kusa dani.
Kai amma dai Bintu badai a kauye kike ba dai ko gaba daya kin canza kin koma wata big girl dake haka.
Nan aka faea hiran yaushe rabo bayan nadan huta anmin tayin abinci nace na koshi.
Sai Maji tace naje na gaida Baba kafin ya,shige da sauran mutanen gidan gaba daya.
Ido na,runtse gami da,cewa ya Arhamanin Rahimin, ahankali na mike nafita,duk kallo suka,bini dashi.
Ina fita maryam tace maji gaba,daya, fa diyar ki ta,sake ta canza kyaunta ya,dada,fitowa a fili, jita kamar wata wace take zaune a abuja ba kauye ba.
A falon Baba na samu hjy kubura na shiga da sallama na itace tafara cewa wa nake gani haka kamar Bintun hajiya maijidda.
Na karasa inda suke gefe kadan na tsugunna ina gaishe su Baba ya nuna j8n dadin gani sosai tare da min ba,a naje gida na lake na manta da karatu a gabana.
Na dan kai lokaci a gurin Baba yana dan min tambayoyi a kan noman mutanen kauyen mu nai masu sallama nafita daga dakin.
Dakin Umma da nake jin haya niyar su na fara shiga duk sunyi mamakin gani na a wanan lokacin da kuma yanayin da suka ganni ba,wani fita hayacin da nayi banda kara kyau.
Nan dai duk na zagaya nagaida su na,dawo dakin mu nan aka zauna a ta hira inda maji da gwago suna can gefe suna,maganan su ta mayan wanda bamu san akan may sukeyin shi ba.
Sai dai yanayin Maji ya nuna min cewa tana a cikin damuwa sosai ko ba,a fadi ba.
Ban dade dasu ba na mike ina fadin zanyi sallah dake kaina.
Nan dai bayan na idar na mika,kukana ga Allah akan ya,kareni daga duk wani rintsi ko matsalar da zan fuskanta agidan mutane.
Ban fito ba na koma na kwanta amma kuma na kasa barci sai sunayen Allah maigirma nake kira ina neman agaji a gurin shi.
Tun dawowana kula,da lafiyan maji ya koma kaina ko yaushe ina daki tare da ita.
Banga Sadauki ba kuma,ban tambaya ko ina yake ba nasan dai kila baya garin ne.
A hankali natsuwa yazo min da zamana dasu don suna nuna min kulawa sam mutum bai gane cewa ba Maji ce ra haifeni ba a gidan.
Satina biyu a,sokoto nagane yanzu yanayin gidan ya kara canzawa sosai ba ruwan wani da wani a gidan har yanzu.
Amma,akwai ci gaban rayuwa,sosai da,suka,samu don yanzu budi ya kara sanuw masu sosai.
Hankalina yafara kwanciya sai dai kullun ina kewan iyayyena da yan uwana adan zaman da mukayi da,mamatabawa da sauko da,akidar nuna min tsana,a fili datakeyi.
Kuma wani abinda ya,tsaya min a,rai shine tunanen Kabir yadda zaiji idan yazo ya,samu banan nan nabar gari bada sanin shu ba.
A haka takardan makarantana ya fito wanda ban san baba yai min process ba saida yazo a hannuna.
Ranan nai murna da farinciki garda kuna don murna,saboda ban taba zaton zan samu ci gaba da karatuna ba.
Na fara zuwa makaranta tare da Anty maryam muke tafiya don makarantar daya da ita state university muke.
Wata rana mun taso daga makaranta ga hadari ta gauraye garin da kyat muka samu Napep din da zai kawo mu gida.
Ganin iska da kura ya,taso a lokaci guda nace wa mai Napep malam don Allah ka,samu dan guri ka Parker har iskan nan ya dan rage yawa don tafiyan mu a haka hatsari ne.
Guri ya samu kamar tadda nace ya dan tsaya a gefen titi kamar ance na daga kai na hango Nafisa a cikin motan wani matashi.
Yanayin dana ganau yasa gabana faduwa da,sauri na juta gurin da Maryann take zaune sai naga hankalinta a,waya yake ita, don haka naja bakina nai shiru ban fada mata ba.
Can naji mai Napep na cewa bari mu lalaba don ga alamar ruwa nan tafe da sauri yake tuki sai gamu a unguwar mu har kofan gida yakaimu daidai ruwa yana fadowa da karfin Allah.
Take ruwa ya zubu ga iska sai kamshi yanayin garin ya canza launi alaman sabon damana yazo ke nan.
Haka muka sauka shiga gida ruwa,na kada mu yana daga muna mayafin jikin mu.
Yaya Imirana na hango can tsaye daga kofan part din shi tawani kura muna ido kamar tsohon maye.
Da,sauri muka nufi hanya shiga cikin gida duk habar kafan mu iska na dagawa yana fita a fili.
Daga inda yake naji muryan shi yana fadin kai ashe cikan nan tadawo ne tubarkallah dai kan komai tsab wallahi akwai kayan dadi a gurin nan.
Banzaci maryam taji shi ba saiji nayi tace dan iska a haka dai zaka kare gindin mata.
Mukan da,sauri muka karasa ciki muna kankamay kayan mu daya jike sharkaf da,ruwan da,akeyi.
Da karfi maryam ta rura kofan falon maji muka fada ciki a guje saukar da ajiyan zuciya nayi yain da naji ruwan bai dukan mu.
Ashe maji na,falon cikin damuwan rashin ganin mundawo kafin ruwa ya fado din sai ce muna take sannuku ku shiga ku cire wa yan nan kayan kafin sanyi yakara hawan ku.
Sam ban lura da mutum a zaune ba a lokacin sai ji da nayi Anty maryam ta,saji kara da karfi.
Da sauri na juya zan kona,waje da gudu sai naji tana fadin oyoyo yaya sadauki.
Najuya da sauri inda naga ta nufa yana zaune fuskan shi dauke da murmushi.
Yace jeki cire kayan sanyin nan kafin yai maki illa,
Cikin shagwaba tace yaya ni har na manta dasu ina murnan ganin ka ai.
Nikan ban tsaya ta kan su ba na,shige daki nafara rage kayan jikina tare da zuwa faban mirror dakinmu nayi wata futu, futu dani don jikewan danayi.
Na fada ban daki nawatsa ruwa tare da,dauro alwala nazo nai sallah.
Saida na,gama komai nafito falon ina,saye da,wata doguwar riga dark blue doguwa ce rigar har kasa hannun ta shara shara nazo na zauna falon har lokacin yana zaune suna hira da kannen shi.
Zamana yai daidai da kiran wayana da akayi na dauka ina mamakin wanda ya kirani a wanan lokacin haka.
Sai na,dan basar ban dauki wayan ba don ban san mai kiranaba alokacin.
Sai kuma ga,kiran ya kara shigowa again na dauka da,sallama ban damu da cewa wai na daga daga falon ba.
Don nasan daga inda suke babu wanda zai iya jin abinda nake fadi don tsabar kwantar da muryana da keyi.
Bayan na gaisa da may shi na nuna bangane mai magana ba.
Yace haba Fatima na zaci ko a mafarki kikaji muryana zaki sheda ai tau Kabir dinki ne wanda aka gudo akabari a kauye.
Maganan shi ce ta dab sani dariya sai duk suka juyo gareni hardashi suna min kallon mamaki.
Nan na,fara bashi hakkuri ina,fada mashi yadda tafiyan yazo min a bazata nadawo sokoto.
Amma yayi hakkuri dan banda nomba shine yasa ban fada mashi ba yakara complain kan cewa ban damu dashi badaine tasa hakan.
A hankali nace na tuba sake ba insha Allahu, abin mamaki sai naji ya kwashe da,dariya tana is alright hakan ma yafi min don yanzu zan dinga samun ki available,
Uhhm kawai nace cikin murmushi.
Ina dago ido mukai arba da yaya sadauki da ya maka min wata uban harara na kawar da kaina tare da ci gaba da waya na.
Kabir yace min yanzu yana hanya zai tafi wani gurin aiki ne amma idan ya,dawo zai kirani.
Nace tau Allah yakaika lafiya Allah ya,tsare min kai.
Ina kara dago ido muka kara arba dashi dole nace mashi cikin yar murya sannu da zuwa yaya ya hanya.
A daure ya amsa min kamar wanda akasa shi amsawa dole.
Nikan namike zuwa daki sai Maji take cewa ina kuma zaki ba,aci abinci ba nace sai anjima zanci mama.
Kai Fatima kina dai wasa da cin abinci har yanzu mutum haka bai damu da cin abinci ba.
Nikan na shige abina daki ban tsaya ta kansuba don wanan mai mugun halin dake zaune a falon.
Ban dade da shiga ba naji ruwa yakara tsinkewa kamar da bakin kwarya.
A hankali na mike don na rufe window din dakin mu dake bude don feshin ruwan dake shigowa.
Karan mota naji za,a fita daga gidan mamaki ya kamani wake da karfin halin fita daga gida a,wanan lokacin da ake tsula ruwa haka masu yawa.
Mantawa nayi ina,son nasha ruwa sai na koma falin na dauka nan nasamu Maji na magana cikin takaici.
Tana cewa yanzu fita yayi cikin wanan ruwan haka ba ko ina zai tafi ba sai gurin shegen shaye shayen su.
A duke nake gaban fridge ban san lokacin da na dago ba nace mama yaya ya koma shane kuma ?
Cikin takaici tace min Fatima bari ke dai, Allah dai ya kawo min saukin wanan al,amarin kawai.
Abu sai yayi kamar ya sauki sai kiga yaron nan ya kuma koma ma halinshi lokaci guda.
Nace anya mama wanan abin ba ci gaba ake da tufka ana,wal,wala ba kuwa?
Amirah tace nima dai hakanace daki na koma hankalina a tashe da zancen danaji mara dadi.
Sai yanzu nagane abinda ya jawa maji ciwon zuciyan da akace yana barazanan kama ta.

A LOKANCIN MU KE,,,,,
Da, tuna ne na kwanta barci bai dauke ni ba har tsawon wani lokaci ga ruwan da akeyi ba a dauke ba har cikin dare sai tsula ruwa ake kamar da bakin kwaraya.
Hasken wutan mota ce ta haska dakin da muke0 kwana a ciki nida Anty maryam don gyaran da akayi dan yi a gidan yanzu.