part din ya baro , da kyair , ga idanunsa sun yi mugun yi mishi nauyi da kyair ma ya ke iya bude su
Gidan Maza Part 1 Complete Hausa Novel · about 50 min read
a haka har ya sauko kassa ya nufi dining room dan ya sha juice , ko bai samu coffee ba
ya na isowa dining room ya ga Danish da Sana zaune su na breakfast d'insu cikin annashuwa
karasowa ya yi ya janyo chair ya zauna ba tare da ya ce komai ba
haka su ma ba wanda ya ce mishi ufan , yi su ka yi kamar ba su gan shi ba ma su ka ci gaba da cin breakfast d'insu
su na zaune a haka Captain ya shigo ya na sallama , ya zo kai Danish school
da sauri Danish ya sauko da ga saman chair d'insa ya nufi Captain da gudu
bude mishi hannayansa Captain ya yi , ya karaso ya dauke shi , ya daga sama ya na juyo da shi , ya na fadin " My baby , na yi kewar ka sosai , shi ya sa ka gudo ka bar ni ko ? "
cikin shagwaba Danish ya ce mishi " Sorry My uncle "
" no ba wani Sorry , sai ka yi min kiss zan hakura "
da sauri Danish ya kai lips d'insa saman kumatun Captain ya manna mishi kiss saman kumatu har biyu
wata yar karamar dariya ya yi kafin ya kalli dining room din
ya na ganin Fahd ya san ba lafiya ba , karasowa ya yi ya na fadin " Big bro , are you okay ? "
gyada mishi kai Fahd ya yi a hankali alamun Eh
" Okay , a kawo maka coffee ko lemun ? " ya fada cikin zolaya
hararrar shi Fahd ya yi ba tare da ya ce komai ba
dariya kassa kassa Captain ya yi kafin ya kalli Sana ya ce " Sister , dauko min bag d'insa please "
dama ta ajiye gefenta , kawai ta dauke ta ta nufe shi ta mika mishi
hannu ya kai ya karba ya na fadin " Thanks , please Sister hadawa Big bro Coffee , ina ga ba ya jin jikinsa "
gyada mishi kai ta yi ta na sakin murmushi , da ga haka ya juya ya fice da Danish
sai da su ka fita sannan ta juya ta koma kitchen
da shigarta da fitowarta duk guda , dama ta riga ta hada mishi coffeen , ta karaso ta ajiye mishi gabansa
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya dauki mug din ya na fadin " Thanks "
" you're welcome " ta fada ta na barin wajen
da kallo ya rakata har ta shiga kitchen , sannan ya fara shan coffeen cikin nitsuwa , ya na sauke ajiyar zuciya a jere
sai da ya kammala shan coffeen sannan ya ajiye mug din , ya tashi ya koma part d'insa , kawai ya konta
_ GIDAN MA
_ MAHNOOR
_
a hankali ta fito da ga cikin bedroom d'inta , ta na sanye da wata gown blue da hijab zuwa kirji white
ta na tafiya kamar an zare mata lakar jiki , gidan ko babu kowa duk sun fice , har Captain , ta yi kokarin fita gidan amma ina , ko harabar gidan ba a bari sun fita ba
ta na fitowa Ma ta sauko stair ta na rike da bag d'inta alamun fita za ta yi
da murmushi a face d'inta Mahnoor ta ce mata " Good morning Ma "
" Good morning Mahnoor , ya kin yi breakfast " Ma ta cike da kula
gyada mata kai Mahnoor ta yi a hankali alamun Eh ta yi breakfast
" Okay , za ki raka ni shopping ? na san dai akwai abubuwan da ki ke bukata na yau da kullum , da ga nan ma mu sayo kayan lefenki , ko ya ki gani ? "
cike da Zumudi ta ce " Eh zan je " , ta fada dan ita a ganinta dama ce , za ta samu ta gudu da ga nan
murmushi kawai Ma ta yi dan ita ba ta san abun da ke faruwa ba cikin gidan , ta ce mata " shikenan , shiga ki shirya mu tafi "
" a shirye na ke " ta fada calmly
" okay let's go " ta fada ta na yin gaba
cikin nitsuwa Mahnoor ta bi bayanta su ka fito harabar gidan
sai dai ko da su ka nufi parking space daya da ga cikin sojojin Captain ya yi sauri ya nufi Ma , ya sara mata ya na fadin " Sorry Madam , Captain ya ce kar mu bar yarinyar nan ta fita "
Kallon Mahnoor Ma ta yi , sannan ta juyo ta kalli sojan ta ce " ka kire shi ka ce mishi mun fita ni da ita "
gyada mata kai ya yi kafin ya juya ya bar wajen
" hmmm , Allah yaron nan sai na koya mishi hankali , Mahnoor , shiga mu tafi " ta fada ta na bude bayan motarta ta shiga
ba musu ta zagayo daya gefen ta shiga , Driver ya tada motar su ka fice gidan
Ita dai Mahnoor rokonta guda su isa Mall din lafiya , ta samu ta tsere kafin Captain ya san abun da ke faruwa
ba su yi ten minutes ba su ka isa Mall din , sai da Driver ya kashe motar a parking space , sannan ya sauko ya budewa Ma
Mahnoor kuma ta sauko da kanta , ta na bin wajen da kallo ta ga ko a ina su ke ta tantance hanyoyin guduwa
a haka su ka shiga Mall din , Ma ta dauki basket biyu , ta nawa Mahnoor guda ta ce mata duk abun da ya yi mata ta dauka , kar ta damu mijinta zai biya
murmushi kawai Mahnoor ta yi mata su ka shiga mall din , su ka fara zagaye corridor din
sannan ta tsayar da Ma ta na fadin " Ma , ban ga abun da ya burge ni a nan , zan je dayan bangaran in ya so mu hadu a reception , ba zan jima ba "
gyada mata kai Ma ta yi ta na fadin " Ki kula da kanki to "
gyada mata kai Mahnoor ta yi ta na sakin wani dan karamin murmushi sannan ta juya su ka yi hannun riga
sai da ta dan yi nisa sannan ta juyo ta ga Ma har ta yi nisa , kuma hankalinta na kan abun da ta ke yi
wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta baro wajen da sauri , basket din ma nan ta ajiye shi a kassa ta bar wajen da gudu za ta bar Mall din
sai da ta iso wajen kofar shigowa , kamar da ga sama ta ji ta bugi mutum
da sauri ta ja baya ta na fadin " Sorry " ta fada ta na shirin rabawa ta gefensa ta wuce
hannu ya kai riko kugunta ya janyo ta jikinsa da karfi
sai a lokacin ta dago kai ta ga ko wanene
Dum ta ji zuciyarta ta buga da mugun karfi har sai da ta ga dishi dishi lokaci guda , har wata rawa jikinta ya fara lokaci guda
murya cike da nitsuwa ya ce mata " Na fada miki , ba za ki iya tsere min ba " ya fada gently murya kassa kassa
wasu yawu ta hadiye ba tare da ta ce komai ba , ta na kallon cikin idanunsa , irin kallon nan mai kashe jikin wanda a ke yi wa shi
Yi hakuri , dama Captain ya riga ya fada tun haduwar farko )
sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya saki kugunta a hankali , ta raba jikinsa da nata
ya riko hannunta ya na fadin " Let's go My Dear Mrs Fayd , za mu yi shopping din a tare " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda da wani dan karamin murmushi a face d'insa
nan take ta nemi nitsuwarta ta rasa , ba karamin tafiya da ita ya yi ba
ta yi nisa duniyar tunaninta kawai ta ji ya ja hannunta su ka koma cikin mall din
basket ya dauka da dayan hannun ya nufi side din da a ke ajiye commodity , ya zaba mata lotion da perfume duk da ya san ba za ta rasa ba , ya daukar mata Always dan ya san Ma ba ta bata Always ba har yanzu , ya san za ta bukata
da ga nan ya ja su ka nufi bangaran kaya , nan ma ya zaba mata gown wajen biyar , da underwear kamar ya san size d'inta , Hijab , Baby doll , kayan barci , ba abun da ya bari kamar zaman har abada za ta yi bayan shi kansa ya san ba za ta wuce two weeks ba tare da shi
ita ba ta ma san wace uwar duniyar ya ke ba , kawai ya na janye da ita , ita kuma ta na biye da shi kamar rakumi da akala
sai da ya zabi duk abun da shigo mishi rai sannan ya ja ta su ka tashi reception
nan ya isko Ma zaune dan ta jima da kammala nata shopping din
ba ta yi mamakin ganin Captain ba , dama ta san sai sojojinsa sun fada mishi Mahnoor ta fita , shi kuma ya biyo bayanta
yadda ta ga ya na nuna kanta an ya ta taba ganin ya shiga irin wannan damuwar , ko lokacin da Abeeram ya konta jinya hankalinsa konce , amma yanzu ya kassa tsaye ya kassa zaune
da ya ke an riga da an yi packeged din nata kayan , na Mahnoor ne kawai ta ke jira
ko da ya iso ya mika musu basket din , su kansu sai da su ka yi mamakin ganin uban kayan da ke ciki
haka shi ma a ka yi mishi packeged din kayan Mahnoor , ya biya kudin wajen dubu dari shidda , da wani abu har da na Ma
da ga haka a ka kai kayan Ma cikin motarta , na Mahnoor cikin motarsa , tare da ita baki daya ma
a tunaninta gida zai tafi da ita kawai ta ga ya kai ta gidan Fahd
bakin kofar gidan ya tsayar da motarsa , ya sauko , ya zagayo ya bude mata ta sauko , ya riko hannunta ya janyo ta su ka shiga cikin gidan
shi ma gidan nashi cike da sojoji ya ke , duk sai da su ka sarawa Captain
amma bai amsa musu ba alamun ya na cikin bacin rai
kai tsaye cikin gidan ya nufa , sai da su ka shigo parlourn sannan ya saki hannunta
ya na daga murya ya ce " wai me ki ke tunani ? za ki iya tsere min ? Nooooo , duk wani motsinki ina sane da shi , ko zuwanki nan Nigeria da sa hannuna a ciki "
" what ? " ta fada cikin rudu
a haka har Sana ta fito da ga cikin kitchen , Fahd kuma ya sauko stair ya na sanye da Tracksuit , daga Muryar da Captain ke yi ne ya sa su ka sauko
wani dan karamin murmushi ya saki ya na fadin " Uhm , me ki ke tunani ? ki duba jami'ai nawa ke
aiki cikin MOPAC amma ke kadai a ka zaba dan yin bincike a kaina , da ya ke kwakwolwar kifi ce da ke ba ki yi tunanin komai ba , kamar yadda ki ka zo garin nan da sa hannuna haka ma ba za ki iya barin garin ba sai na yi niya , in za ki ba ni hadin kai , ki ba ni mu yi aikin nan cikin salama , in kuma ki ka ki , ki tabbatar kin shigo prison ba zan sake barinki ki fita da ga cikin gidan nan ba , ........... Oh , na manta ban fada miki ba , hukumar MOPAC sun bayar da cigiyarki cikin kassar UK matsayin criminel , kin bace kuma ba wanda ya san ina ki ke "
" what ? me ka ke fada haka ? no karya ce kawai , ka na son yi min barazana ne " ta fada kamar za ta yi kuka
bushewa da dariya ya yi har da tapi , idanunsa na cikowa da ruwa
sai da ya gama dariyarsa sannan ya ce " Sorry , sorry , Abun da na fada da farko gaskiya ne , amma cigiyarki da a ke na yi hakan ne dan na ba ki tsoro , sorry " ya kai karshen ya na wata yar karamar dariya
nan take kuka ya kubce mata , ta fada jikinsa ta na kai mishi bugu a kirji ta na fadin " Me ya sa za ka min irin wannan wassan ? ka wan yadda na ke ji da aikina ? "
cikin sigar rarrashi ya ce mata " Sorry , kawai na yi ne dan na rama abun da ki ka min yanzu " ya kai karshen ya na zagayo da hannayansa a bayanta ya rungume ta
ya kai bakinsa saitin kunnenta , cikin rada ya ce " abun da na fada yanzu ba gaskiya ba ne , amma zai zama gaskiya nan gaba in har ba ki yi abun da na ce ba "
ya na gama fadar haka ya janye hannayansa , ya na kallon ta ya ce " akwai sojoji nan waje , za su mayar da ke gida , ba tare da wani abu ya same ki ba "
ya na gama fadar haka ya juya ya fice parlourn ya bar ta nan tsaye kukan ma ta nema ta rasa
haka shi ma Fahd ya juya ya koma kan aikinsa
a hankali Sana ta tako , ta dafa shoulder d'inta
a dan razane ta dawo hayacinta ta juyo ta kalli Sana
da murmushi a face d'inta ta ce " mu je ki taya ni girki , in ya so zuwa anjima sai ki koma gida "
gyada mata kai Mahnoor ta yi a hankali dan yanzu ba ta da wani karfin sa'insa
_ REHAN
zaune ta ke cikin class d'insu ita kadai , ta na latsa wayarta ta na sakin murmushi ,
sun jima da sauka ta na jiran driver din da Barister Aabid ya ce zai turo a dauke ta ne
ta na a haka ta ji an kwace mata wayarta , a tunaninta Ashur ne dan ta bude baki za ta kira sunansa
amma sai idanunta su ka sauka kan Zee
nan take murmushin ya bace , ta mike tsaye , ta kai hannu ta kwace wayarta ta na fadin " me kuma ki ke yi a nan ? , ko yau ma kin zo yi min kashedin da ki ka saba "
da murmushi a face d'inta Zee ta ce " ko daya , na lura ba za ki hakura ki kyale Ashur ba shi ya sa na dauki mataki "
murmushi mai dan sauti Ta yi ta na fadin " au , da gaske ? to bismillah , ko cen ina ganin abotar mu ce ta kwana biyu ya sa ba na wani musayan yawu da ke , amma bari na fito fili na fada miki , kin yi kadan ki sa ni na hakura da abun da na ke so , in ma ki na takama da dukiyar mahaifinki ne kar ki manta wanene mahaifina cikin garin nan , Ashur kuma wlh kin yi kadan ki ce na bar miki shi "
ita ma Zee murmushi mai dan sauti ta yi ta na fadin " Ba zan ce ki kyale shi ba , amma ki tabbatar da ga yau ke da Ashur kun yi hannun riga , yadda ban same shi ba , haka ke ma ba za ki same shi ba , sai na raba ku , rabuwa ta har abada , ki jira ki gani "
" Oh da gaske ? to bari ki ji , ina farincikin sanar da ke cewa , 15 ga wata mai kamawa za a yi auren mu "
dariya Zee ta yi ta na dan tabe baki ta ce " Oh , da gaske ? , to Allah ya kai mu , za mu ga in zai amince ya aure ki " ta na gama fadar haka ta juya ta fice
da kallo Rehan ta rakata har sai da ta fita sannan ta saki wani dan karamin tsaki ta dauki jakarta za ta bar class din , ta na shirin fit Bill da Aryan su ka shigo class din a tare , da ga gani ba shigowar mutunci ce su ka yi ba
Dam ta ji zuciyarta ta buga , ta fara yin baya a hankali ta na zaro idanu
wani dan karamin murmushi Bill ya saki ya na fadin " La , tafiya za ki yi ? ba za ki jira mu ba ? "
murya na kerma ta ce " ku ban hanya na wuce "
ba musu su ka raba gefe su ka ba ta hanya ta wuce
sai dai ko da ta iso bakin kofar ta ga an medo ta , an rufe ta ta baya
wasu wahalalun yawu ta hadiye kafin ta juya ta kalle su
ba ta kai ga yin magana ba ta ga sun bushe da dariya har da kai hannu su ka tapa
sai da su ka gama dariyarsu sannan Aryan ya ce mata " Ina masoyin naki ? ya zo ya cece ki in zai iya ? "
ya na gama fadar haka su ka juya a tare shi da Bill su ka fara rufe Windows din class din
wata yar karamar kara ta saki ta juya ta fara jijiga kofar class din ta na fadin " Ku bude kofar nan don Allah , Ashuuuuu ! " ta fada da karfi ta na sakin kuka
ta na a haka ta ji an riko hannunta ta baya ,
da karfi Bill ya janyo ta baya har sai da ta fadi ta saki wayarta da jakarta , kanta ya bugu a saman tiles , nan take ya fashe ya fara zubar da jini
da sauri ta dago ta na shirin mikewa Aryan ya sa kafa ya take kafarta
wata razananiyar kara ta saki dan gaskiya ba karamin zafi ta ji ba
" Oh sorry , ban gani ba , fatan ba ki ji ciwo ba " ya fada ya na janye kafarsa
wani marayen kuka ta saki ta na fadin " don Allah ku kyale ni na tafi "
" ba mu tare ki ba , tashi ki tafi " su ka fada a tare su na komawa gefe su ka tsaya
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
(
' s
___FUNNY , DRAMATIC , REVENGE , ROMANCE & DESTINY ___
Hi everyone !
Fatan kun tashi lafiya ?
I'm here to tell you , littafin Gidan Maza is Complete Now
DUK ME BUKATA N300 NE KACAL
MY ACCOUNT NUMBER
8081129487
Khadija Sabi'u
Monie point bank
+22798999753 for evidence
FOR INFORMATION +22798999753 WHATSAPP ONLY
____ 24
wajen ya yi tsit ba ka iya jin sautin komai sai nunfashin mutum da ke fita a hankali a hankali kamar mutumin na shirin mutuwa ko ya rasa iskan nunfashi
a hankali ya ware idanunsa ya fara takawa a hankali ya nufi wajen da ya ke jiyo sautin nunfashinta
cen bayan office din Prof , sai da ya karaso wajen ya zagayo a hankali
da sauri ya rumtse idanunsa , har sai da ya sa hannu ya dafe office din dan wata muguwar bugawa ce ya ji zuciyarsa ta yi lokacin da idanunsa su ka sauka kan Rehan
ta na konce Naked cikin jini , ga kanta shi ma ya zubar da jini sosai , da kyair ta ke iya jan nunfashi har wani sama kirjinta ke yi , idanunta su ba a rufe ba su ba a bude ba , kamar ta na shirin mutuwa , da ga gani wannan kashe ta su ka so yi
a hankali Captain ya juya , ya zuge zip din jacket d'insa ya cire ya ajiye saman table , sannan ya cire T-shirt din jikinsa ya ajiye , ya dauki jacket din ya mayar , ya kai hannu ya dauki T-shirt din
lumshe idanunsa ya yi sannan ya juya dan gaskiya ba zai iya jure ganinta a haka ba , ko ba dan ta na matar da kanansa ce zai aura , kawai ba zai iya kallon halin da ta ke ciki ba ne ya san tabbas sai ya yi kuka
idanunsa a lumshe ya saka mata T-shirt d'insa , Cikin sa'a ko ta kai mata har saman cinyoyinta
sai da ya saka mata sannan ya dauke ta cak , ya mike tsaye ya nufi jakarta ya dauka ita ma sannan ya baro class din
kai tsaye makarantar ya baro
ya na fitowa ya ga sojojin Fahd sun bar wajen , motarsa ce kawai ta yi saura
kai tsaye gidan baya ya nufa da ita , ya kontar da ita sannan ya zagayo wajen driver ya shiga ya tada motar ya bar wajen
kai tsaye Asibiti ya nufa da ita , amma ba wada Talal ke aiki a ciki ba dan ba ya son sauran yan uwansa su san abun da ya faru a yanzu
ya yi wajen ten minutes a hanya kafin ya iso Asibitin , da sauri ya tsayar da motarsa a parking space , sannan ya sauko ya bude baya , ya dauki Rehan ya shiga da ita
a nan reception ya tsaya ya na ce wa nurse ya na bukatar ganin doctor yanzu
da sauri ko a ka karbe su , wasu nurse su ka kawo mishi gado ya kontar da Rehan su ka tafi da ita A&E Room , tare da doctor
shi kuma ya koma reception ya cika wasu takardu , ya biya kudin aikin da za a yi mata dan Private Hospital ne ya kawo ta
sai da ya biya komai sannan ya baro asibitin , ya shiga motarsa kai tsaye gidan Barister ya koma
bakin kofar gidan ya tsayar da motarsa bai shiga da ita ciki ba , ya sauko ya shiga cikin gidan
da sallama a bakinsa ya shigo part din Hajiyah
har yanzu dai yadda ya bar su ko motsi ba su yi ba , Ashur kuwa sai kuka ya ke kassa kassa , Barister har ya gaji da rarrashin shi , Har Hajiyah ta zo ta same shi ta na tambayar lafiya amma ya ki ba da amsa
da sauri Captain ya karaso gefensa ya zauna , ya rungume shi ya na fadin " Ashuuu , kukan me ka ke yi haka ? ba ka tsoron ka ji wa kanka ciwo ? don Allah ka daina kukan nan ka fi kowa sanin zubar hawayenku ne kadai zai iya illlata ni a duniya , please stop "
a hankali Ashur ya rage sautin kukansa ya dago a hankali da ga jikin Captain ya ce " where is My Daisy ? har yanzu ba ka samo ta ba ? "
" kontar da hankalinka na samo ta "
da sauri Ashur ya mike tsaye ya na fadin " ina ta ke to ? " ya fada ya na kallon kofar shigowa parlourn
mikewa tsaye shi ma Captain ya yi ya na fadin " kontar da hankalinka , zan kai ka in da ta ke , uncle let's go " ya fada ya na riko hannun Ashur su ka fice parlourn
ba musu Barister ya mike tsaye ya ce wa Hajiyah duk abun da ya faru za ta kira ta fada mishi
da addu'a ta raka shi har sai da ya fice part
ya bi bayan Captain su ka fice gidan
ya budewa Ashur gidan gaba ya shiga , Barister kuma ya shiga baya , shi kuma ya shiga wajen Driver ya tada motar su ka bar wajen
ya san Ashur ba zai iya tuki a wannan yanayin da ya ke ciki ba sai ya janyo wa kansa accident
cikin nitsuwa ya ke tukinsa har su ka iso asibitin , ya nufi parking space ya kashe motar su ka sauko a tare su ka nufi kofar shiga asibitin
ya na shiga a reception wata nurse ta tsayar da shi, ta ce mishi doctor na son magana da shi
tambayar ta ya yi ina office din doctor , sai da ta raka su har bakin kofar sannan ta juya ta koma bakin aikinta
sai da Captain ya sa hannu ya yi mishi knocking sannan ya shiga ya na sallama , Barister da Ashur na biye da bayansa
murya a sanyaye Doctor ya amsa mishi sallamarsa ya na sakin murmushi dan ya san Captain da Barister
mikewa tsaye ya yi ya ba su hannu ya na fadin " Barister Aabid da Captain Fayd a office d'ina yau , gaskiya na ji dadin hakan , dama na jima ina so na hadu da ku , ga shi kun kawo kai har gida , Bismillah ku zauna "
ba musu Captain ya zauna shi da Barister , Ashur kuma ya tsaya bayan Captain , shi da Barister kamar babu su a wajen kowane ya yi sanyi , su na so su san me ke faruwa amma ba karfin bude baki
cikin nitsuwa Captain ya ce " Nurse ta ce min ku na son magana da ni "
cikin rudu Doctor ya kalle shi ya na fadin " Kai ne ka kawo yarinyar da na duba yanzu ? "
" Eh ni ne " ya fada ya na gyada kai
" Alhamdoulilah , dama yanzu zaman da na yi kira ne zan yi headquater na ajiye kara , gwara da Allah ya sa kai ka kawo ta da kanka "
duk da ya san abun da ya faru Rehan amma sai da ya tambayi doctor da cewa " please doctor wane hali ta ke ciki ? me ya same ta ? "
ajiyar zuciya Doctor ya sauke , ya dan dauki lokaci kafin ya ce " I'm sorry , Fyade a ka yi mata , na san kuma duk wanda ya yi hakan da burin kashe ta ya yi hakan dan nunfashi ma da kyair ta ke iya yin sa , ga shi ta samu rauni a kanta , hakan ya sa ta zubar da jini sosai , ba dan an yi sa'a ka kawo ta cikin lokaci da yanzu wata maganar mu ke daban , sai dai ku yi hakuri amma dai a yanzu ta na cikin doguwar suma , in dai ba ta farka nan da 48 hours ba , to ba na tunanin za ta farka nan kusa , i'm so sorry "
wata nanauyar ajiyar zuciya Captain ya sauke, ya na shirin magana ya jiyo Muryar Ashur ya na fadin " Bro ka ce mishi karya ya ke , ba abun da ya samu Rehan "
mikewa tsaye Captain ya yi ya riko face d'insa da hannayansa biyu ya na fadin " calm down , ka kontar da hankalinka ka ji "
" No , ka na fa jin abun da ya ke fada , ina ta ke ? ina son ganin ta , ina son na gan ta " ya kai karshen kamar zai yi kuka
a hankali Captain ya juya ya kalli Doctor
" Room 5 " ya fada dan ya san kallon me Captain ke yi mishi
gyada mishi kai ya yi kafin ya riko hannun Ashur ya ja shi su ka fice
shi dai Barister ya na zaune ya dafe kai da hannu guda , bai ma san abun da zai ce ba , abun ne ya fi karfinsa
bangaran su Ashur kuma , bayan sun fito office din su ka nufi room din da a ka kontar da Rehan
a hankali su ka shigo dakin sun na sallama a tare shi da Captain
kai tsaye saman ta idanunsa su ka sauka , ta na konce sanye da wata gown blue , an yi mata dress a kai , hannunta kuma sanye da canula a na yi mata karin jini , fuskarta duk ta kunbura saboda alamun yagar da ke kai , sai ta ba ka tausayi
da sauri Ashur ya nufe ta ya riko hannunta ya na fadin " My Daisy ? Please ki tashi mu bar wajen , ni ban yarda da abun da doctor ya ce ba , please ki tashi mana " ya kai karshen ya na sakin kuka kamar wani karamin yaro
a hankali Captain ya tako gefensa ya tsaya , ya kai hannu ya dafa shoulder d'insa
tun kafin ya ce wani abu Ashur ya saki hannun Rehan ya juyo da sauri ya rungume Captain ya na kara sautin kukansa
ya ce " me ta yi musu su ka yi mata irin wannan abun ? please ka ce mata ta tashi wlh ba zan iya rayuwa babu ita ba "
cikin sigar rarrashi Captain ya ce mishi " Ashu , don Allah ka kontar da hankalinka , ba abun da zai faru da ita ........... "
bai kai karshen ba Ashur ya dago da ga jikinsa ya na fadin " me zai faru bayan abun da ya riga ya faru ? shikenan sun cuce ni ? sun yi kokarin raba ni da ita ? ko wanene ya yi mata wannan abun wlh mutuwa ce kawai za ta raba ni da shi , sai da na yi musu azabar da sun gwammace mutuwa da ita , mugaye kawai "
hannu Captain ya kai ya kara janyo sa jikinsa ya rungume , ya san halin Ashur ba karamin mugu ba ne shi ma , ko su wanene in ya kama su ba zai kashe su cikin sauki ba , gwara ya riga shi kama su ya san hukuncin da zai yanke musu
ya yi nisa duniyar tunaninsa ya ji Ashur na kokarin yin kassa ya fadi
da sauri ya taro shi , nan ya ga idanunsa a rufe alamun ya suma
a rude ya shiga bubuga kumatunsa ya na kiran sunansa amma bai motsa ba
da sauri ya dago kai ya fara bin wajen da kallo
cen ya hango wani gadon daban amma ba kowa a kai , da sauri ya sa daya hannu ya dauki Ashur ya nufi gadon da shi , ya kontar da shi sannan ya juya da sauri ya fice ya koma office din Doctor
babu ko sallama ya fado office din , lokacin da ya shigo Doctor na duba Blood Pression din Barister dan ya ga ya yi shiru kar a je jininsa ya hau
a rude Captain ke ce wa Doctor " Doctor please mu je ka duba Ashur , ban san me ya same shi ba kawai na ga ya suma , ko motsi ba ya yi "
cikin nitsuwa Doctor ya saki hannun Barister ya na fadin " Calm down , mu je na duba shi " ya fada ya na takawa ya fice , Captain na biye da bayansa
sai da su ka fita sannan Barister ya samu ya mike tsaye a hankali ya fito shi ma
kai tsaye Room din da su ke su ka nufa
ko da su ka shigo Doctor ya nufi Ashur ya fara duba shi
ya yi wajen five minutes kafin ya juyo ya kalli Captain ya ce " don't worry , jininsa ne kawai ya hau shi ya sa ya suma , zan yi masa allurar da zai sa jininsa ya sauka amma zai yi dogon barci at least 24 hours "
" okay shikenan " Captain ya fada a sanyaye
gyada mishi kai Doctor ya yi kafin ya fito dakin
sai da ya fita Captain ya juya ya kalli Barister zaune bakin gadon Rehan ya na shafa kanta a hankali
wajensa Captain ya nufa ya na fadin " Don't worry uncle , in sha Allah sai na kamo wanda ya yi mata wannan abun na hukunta shi yadda ya dace "
gyada mishi kai kawai Barister ya yi dan bai da bakin magana , bai taba tunanin wani abu makamancin wannan zai faru da yarinyarsa ba , tsoronsa guda yanzu in Ashur ya farka ya ce zai guje ta saboda abun da ya same ta , ya San ba za ta iya jurewa kashe kanta kawai za ta yi
a haka Doctor ya dawo ya same su , ya nufi Ashur ya yi mishi wata allura
a takaice dai sai wajen Sallar magriba sannan Captain da Barister su ka baro asibitin , shi ma Captain bai koma gida ba sai wajen karfe 10 , ya na cen makarantar ya na bincike ko zai samu wani abu amma ba abun da ya samu , ga shi class din babu ko camera
haka ya yi hakuri Ya koma gida , nan ma sauran yan uwana su ka rufe shi da tambaya ina Ashur ? ina Ashur ?
sai da ya yi musu karyar wai ya tafi Abuja wajen wani taro , tun da yanzu Ashur ne a matsayin sa dole ya je , amma gobe zai dawo
ba dan sun so ba su ka yarda amma sun san akwai wani abu dan Captain bai iya karya ba , in ya yi karya har wata yar in'ina ya ke dan bai san abun da zai fada ba ,
_ WASHE GARI
misalin karfe 8 na safe Captain ya baro gidan , yau Talal ya saka kai Danish school
ba shi kadai ya fito ba , sai da ya sa Mahnoor ta shirya su ka baro gidan a tare dan yanzu ma ya na gudun ta yi wani shirmen na kokarin guduwa ,
ba ta yi mishi musu ba ta bi bayansa su ka baro gidan a tare
kai tsaye Asibitin da a ka kontar da su Ashur su ka nufa
ya na janye da ita har su ka iso room din su ka shiga su na sallama
nan ta ga Ashur konce ya daura hannu saman forehead , kenan jiya karya ya yi musu ? dan ta ji lokacin da ya ce Ashur ya tafi Abuja , to me ya ke a Asibiti ?
a hankali Captain ya nufi Ashur ya zauna bakin gadonsa ya kai hannu saman face d'insa
wata nanauyar ajiyar zuciya Ashur ya sauke kafin ya ware idanunsa a hankali, kai tsaye saman Captain su ka sauka
wani dan karamin murmushi Captain ya saki kafin ya ce " ya jikin naka ? "
gyada mishi kai Ashur ya yi a hankali kafin ya juya ya kalli Rehan ya na fadin " har yanzu ba ta tashi ba ? "
a tare Captain da Mahnoor su ka juya su ka kalli Rehan
sai da ta ji zuciyarta ta karaya dan da ga gani ta san tabbas Fyade a ka yi mata an sha kawo mata irin wannan case dayawa a ce ta yi bincike a kai , to wacece yarinyar nan ? wacece ita a wajensu ? ta ke tambayar kanta
a hankali Captain ya juya ya kalli Ashur , cikin sanyin murya ya ce mishi " kar ka damu , in sha Allah za ta farka , yanzu ka tashi mu tafi gida ka yi wanka , ka yi breakfast , ka ji ? "
a hankali Ashur ya mike zaune ya sauko da kafafunsa kassa ya na kallon Rehan ya ce " babu in da zan je sai ta farka "
" Ashu , please don't be Stupid , ka na bukatar kula da kanka , kafin ka ce za ka kula da ita , so ka ke mu yi jinyar ku/ku biyu ? "
" Ba zan iya tafiya na bar ta a haka ba , I'm afraid " Ashur ya fada a sanyaye ya na kallon Captain
ya na rufe bakinsa Barister ya shigo ya na sallama
amsa mishi sallamarsa Captain ya yi kafin ya kalli Ashur ya ce " ka gani ga uncle nan ya zo , zai zauna da ita , please tashi mu tafi ka yi breakfast ka konta ka huta "
wajensa Barister ya karaso ya na fadin " Ashur , please ka koma gida ka huta , kar ka damu zan kula da Rehan har lokacin da ka dawo "
wata doguwar ajiyar zuciya Ashur ya sauke kafin ya mike tsaye ya nufi kofar fita ya fice ba tare da ya ce komai ba
a hankali shi ma Captain ya mike ya nufi Mahnoor ya riko hannunta ya ce " Let's go "
har ya juya zai fita Barister ya taro shi da cewa " Captain , wannan ita ce wadda za ka aura ? "
gyada mishi kai Captain ya yi ya na fadin " sunanta Mahnoor , babu kowa ne a gida shi ya sa na taho da ita "
" okay , ka je ka kula da Ashur , za mu kula da Rehan , yanzu momynta su na zuwa ganinta "
gyada mishi kai Captain ya yi kafin ya juya su ka fice ya na rike da hannunta , ya na kallon gabansa , ita kuma ta na kallon shi kamar ba ta san shi ba
har su ka karaso parking space , nan su ka ga Ashur Zaune cikin motarsa gidan baya , ya lumshe idanu
shiga motar su ka yi , su ka bar asibitin , su na barinta ko Motar Nasser ta shigo Asibitin ya na dauke da Amarya da Hajiyah da autarsu
bayan sun baro asibitin kai tsaye gida su ka koma , su ka sauko su ka shiga gidan a tare , Ashur bai jira su ba ya haye stair ya koma bedroom d'insa

____ 25
sai da Ashur ya Haye sannan ya tsaya ya na kallon Mahnoor ya ce mata " Please ki amso mishi breakfast d'insa wajen Chef ki kai mishi "
gyada mishi kai ta yi a hankali Alamun okay , Shi kuma ya juya ya fice parlourn ya nufi Headquater
_ AFTER TWO DAYS _
wajen kwana biyu yanzu har yanzu Rehan ko yatsa ba ta motsa ba , ga shi har yanzu sun kassa samo su ka yi mata hakan , bayan kula da ita ba abun da su ke yi
Mahnoor kuma kullum ta na biye da Captain , har headquater da ita ya ke tafiya dan ya na tsoron yanzu ma ta sake guduwa bayan ya na bukatar taimakon ta , har Ma ta yi mishi magana a kan ya kyale ta ta huta amma ya ki , ba yadda ta iya ta hakura ta kyale shi
In mu ka leko gidan Fahd kuma , abun sai dai rabbana , shiru ba me cewa wani ufan , ko Danish yanzu ya daina kula Fahd , ko ya dawo da ga school ya isko shi a parlour ba ya yi mishi magana , Sana dama ba magana ta ke yi mishi ba , ko girki yanzu Chanel ta bari su yi aikinsu , tun abun bai dame shi ba har ya fara damun sa , specially shirun Danish , sai yanzu ya fara jin abun da ya yi bai dace ba
_ MISALIN KARFE 8 NA SAFE _
_ GIDAN FAHD
a hankali ya ke sauko stair din gidan ya na sanye da Suit green color kamar idanunsa , gashin kansa ya zubo mishi a gaban goshi gwanin burgewa sai tashin qamshi ya ke , hannunsa rike da wayarsa
sai da ya gama sauko wa ya nufi kofar fita , amma ya jiyo dariyar Danish a dining room, da muryar Sana
cak ya tsaya ya juya ya kalli dining room
su na zaune su na Breakfast cike da annashuwa , su na wassa
cikin sanyin murya ya kira sunan Danish
a tare shi da Sana su ka kalli Fahd , har sai da ta yi mamakin wai da gaske Fahd ne ke kiran Danish
a hankali Fahd ya mika mishi hannu alamun ya taso su tafi
a hankali Danish ya juya ya kalli Sana , gyada mishi kai ta yi a hankali alamun ya tashi su tafi
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya sauko da ga saman chair d'insa ya nufi Fahd da sauri ya riko hannunsa ya na sakin murmushi
a hankali Fahd ya fara takawa ya na rike da hannun Danish su ka fice parlourn , Sana na zaune na kallon su ta na sakin murmushi , alamun dai aikinta ya biya
bayan sun fito harabar gidan motocinsa na jere dama ya riga da ya fada musu ya za su fita
wannan shi ne first time da sojojinsa su ka gan shi tare da Danish , ga shi ko kallo daya za ka wa Danish ka san jinin Fahd ne
cikin mota guda su ka shiga su ka bar gidan
_ ASHUR
a hankali su ke tafiya cikin Asibitin , ya na sanye da wani trouser orange , da shirt white color mai dogayen hannu , har ya yi wata yar rama bawan Allah saboda damuwar da ya ke ciki , duk ya yi sanyi
Captain da Mahnoor su na biye da bayansa , ita yanzu ta riga ta saba ma , bare ma da ba ta jin dadin zama gida ita kadai , gwara ta dinga fita tare da shi ta ga abun da ya ke
a hankali ya kai hannu ya turo kofar dakin ya shigo ya na sallama
ya na shigowa ya ga Nasser rike da Hannun Rehan , ta na rike da wata piece ta glass , alamun kanta ta ke son ji wa ciwo , Hajiyah da Amarya sai ce mata su ke ta ajiye amma ina ba ta jin su
da sauri Ashur ya nufe ta , ya riko hannun ya kwace glass din , ya daga hannu zai wanka mata mari amma bai sauke ba
da karfi ta datse idanunta ta na jiran saukar marin amma bai sauke ba
shi kansa ya yi hakan ne dan ya ba ta tsoro amma ba ya jin zai iya sa hannu ya daki mace a rayuwarsa , bare ma wadda ya ke so
sai da ya ga ta nitsu ya sauke hannu ya riko shoulder d'inta ya na fadin " ki na da hankali ? kashe kanki ki ke son yi ? okay shikenan "
ya kai karshen ya na janye hannunsa ya kai bayansa ya fiddo gun ya yi charging d'inta ya mika mata ya na fadin " amshi sai ki ji dadin kashe kanki haka ! "
kuka ta saki ta sulale a kassa kanta a sunkuye
a hankali shi ma ya zube saman guyiwowinsa , ya kai hannu ya tallabo face d'inta
da sauri ta buge hannunsa ta sunkuyar da kai dan ta na jin zafin ta kalle shi bayan abun da ya faru
ida zama a kassa ya yi ya sa hannu ya janyo ta jikinsa ya rungume ta ,
cikin rada ya ce mata " Yi hakuri ki daina kukan nan don Allah , ba ga ni ba ? ina nan tare da ke , ba abun da zai faru , ki yi hakuri kin ji My Daisy "
bayan kuka ba abun da ta ke yi , ji ta ke ta kashe kanta ma ba za ta ji da sauki ba
kowa ya yi zugum ya na kallon su , Hajiyah har da Hawaye a idanunta
a hankali Nasser ya koma ya zauna saman chair ya na sauke ajiyar zuciya , Amarya kuma ta tashi ta fara dauke Pieces din glass din da Rehan ta fashe , ta zuba cikin trush dan kar wani ya ji ciwo
sai da ya yi wajen five minutes rungume da ita haka kafin ya dago ta da ga jikinsa , ya daura hannayansa biyu saman face d'inta , ya dago ta , ya matso ya manna mata kiss saman forehead da kumatu
cikin sanyin murya ya ce mata " kin san halin da na shiga kwana biyun nan da na yi ba tare da ke ba ? shi ne ki ke son rabuwa da ni har abada ? kenan dama ba ki so na ? "
girgiza mishi kai ta yi a hankali , amma idanunta na lumshe
" To in da gaske ki na so na daina kukan nan , in ba ki daina hakan na nufin ba ki so na " ya fada ya na goge mata hawayenta
a hankali ta fara rage sautin kukanta har ta daina , ta na hadiyar zuciya
cikin cool voice ya kira sunanta
ba tare da ta bude idanunta ba ta ce " Na'am "
" Bude ido ki kalle ni "
girgiza mishi kai ta yi a hankali alamun ba za ta iya ba
" My Daisy , open your eyes "
slowly ta ware idanunta , har sun yi red saboda kukan da ta sha
wani cool murmushi ya sakin mata , kafin ya ce " Now Smile for me , kin san kuka ba ya yi miki kyau ko ? "
murya a disashe ta ce " me ya sa ba ka zo ba ? , ka san yadda na jira zuwanka amma ba ka zo ba ka kyale ni a cen "
" I'm so sorry My Daisy , amma ai yanzu ga ni , ki fada min su wa su ka yi miki hakan please ? "
a hankali Captain ya tako ya dafa shoulder d'insa ya ce " Ashur , ka bari har ta samu sauki mun yi mata wannan tambayar da ga baya "
gyada mishi kai Ashur ya yi kafin ya mike tsaye , ya riko hannunta ya taimaka mata ta mike tsaye
su ka dawo bakin gadonta ya zaunar da ita , sannan ya zauna gefenta , ya zagayo da dayan hannunsa a bayanta ya rungume ta a jikinsa
wani dan karamin murmushi Hajiyah ta saki kafin ta bude basket din abincin da su ka taho da shi , ta fiddo plate ta zuba abinci a kai da spoon sannan ta dawo dayan gefen Rehan ta zauna
ta debo abincin ta kai wa Rehan saitin bakinta ta na fadin " Titi , karbi ki ci "
girgiza mata kai Rehan ta yi ba tare da ta ce komai ba
hannu Ashur ya mika ya karbi spoon din , ya na ce wa Rehan " in ba ki ci ba zan tashi na tafi "
a hankali ta bude baki ta karbi abincin
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya janye hannunsa da ga bayanta ya karbi plate din hannun Hajiyah ya fara ciyar da ita da kansa
sai da ya ga ta cinye duk abun da ke cikin plate din sannan ya hakura ya kyale ta , ya ba ta ruwa ta sha , da drugs din da doctor ya ce a ba ta in ta farka
bayan ta sha ta koma jikin Ashur , ta kontar da kanta saman shoulder d'insa
a hankali Captain ya tako , ya tsuguna a gabanta ya riko hannunta , cikin sanyin murya ya ce mata " I'm so sorry Sister , kar ki damu in sha Allah ko wanene ya yi miki hakan zan kawo miki shi gabanki ki yi mishi hukuncin da ki ka so , ba sai kin fada min ba ya hakan ta faru ba , just sunayansu ni ke son ki fada min "
a hankali ta janye kanta da ga saman shoulder din Ashur , ta sunkuyar da kai , a hankali ta furta sunan Aryan da Bill
a tare Captain da Ashur su ka mike tsatsaye su na kallon juna
cikin rudu Ashur ya ce mata " My Daisy , kin tabbatar da abun ki ke fada ? Aryan da Bill ? "
dago kai ta yi idanunta cike da hawaye ta ce mishi " ka na tunanin zan yi maka karya a kan wannan abun ? "
cikin rudu Nasser ya ce " Ashur , ka san su ne ? " ya fada dan kamar yanayinsa ya nuna ya kassa yarda da abun da ta fada
a dan rude ya ce " I can't believe , na san Aryan da Bill are not a good person , but ban ba taba tunanin za su yi min irin wannan abun ba , They are my ONLY friends , " ya kai karshen kamar zai yi kuka ya na shirin takawa ya bar wajen
da sauri Captain ya riko hannunsa ya na fadin " No , dawo ka zauna tare da ita , ni zan ji da Aryan da Bill , Bro , ku shirya ku koma gida tun da ta farka , akwai Doctor din da zai dinga zuwa gida duba ta " ya fada ya na kallon Nasser
sannan ya juyo ya yi wa Ashur Rada a kunne , ni dai ban ji abun da ya ce ba
gyada mishi kai Ashur ya yi kokarin ya fiddo wayarsa ya mika mishi
hannu Captain ya kai ya karba ya ce mishi ya koma ya zauna tare da ita
ba musu ya koma ya zauna gefenta , ya riko hannunta ya shiga rarrashin ta
Captain kuma ya juya ya ce wa Mahnoor su tafi
ba musu ta biyo bayansa su ka fito , kai tsaye parking space su ka koma cikin motar Captain su ka bar wajen
sai da su ka bar wajen sannan ta juyo ta kalle shi , cikin sanyin murya ta ce " Captain , wai me ya faru da yarinyar nan ? na ga kullum sai mun zo wajen ta , wacece ? "
" Matar da Ashur zai aura " ya ba ta amsa kai tsaye
" Amma me ya same ta haka ? har ta ke kokarin kashe kanta ? "
a hankali ya tsayar da motarsa gefen titi ya juyo ya kalle ta ya ce " in ke ce a ka raba ki da kimarki ta hanya ma fi muni ya za ki ji ? "
shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba , ta na dai kallon shi
hannu ya kai ya bude box din da ke gefenta ya fiddo wata laptop , ya daura saman cinyoyinsa ya bude ya fara dannawa
ya kai hannu guda ya fiddo wayar Ashur ya fara latsawa
ni dai ina zaune ina kallon shi ni da Mahnoor
sai da ya gama latse latsensa sannan ya mikawa Mahnoor wayar Ashur
cikin rudu ta kai hannu ta karba ta na tambayar me za ta yi da ita
tada motar ya yi ya na fadin " wani restaurant za mu je , ina son ki janyo min samarin nan biyu a parking space "
" me za ka yi " ta fada ta na kallon pic din Aryan da Bill
a hankali ya juyo ya kalle ta ya saki wani dan karamin murmushin gefen fuska ya ce " kidnapping d'insu za mu yi , kuma ke za ki taimaka min "
" what ? Kidnapping ? , no gaskiya ba zan iya ba "
wata yar karamar dariya ya yi ya na fadin " matsoraciya kawai , ba abun da za mu yi musu, kawai ki san yadda za ki yi ki janyo su parking space "
ya fada ya na tsayar da motarsa cikin parking space din wani restaurant
ya rufe laptop d'insa ya mayar cikin box din ya fiddo wasu face mask biyu , ya mika mata guda ya na fadin " Idan kin dawo da su , kafin ki shiga motar ki saka face mask din "
gyada mishi kai ta yi kafin ta bude za ta sauka
har za ta fita ya riko hannunta ya na fadin " kar ki ce za ki yi kokarin guduwa , dan ba za ki bar wajen nan ba zan samo ki "
" Kar ka damu , ko na gudu babu in da zan je " ta fada ta na kallon cikin idanunsa
a hankali ya saki hannunta , da ga nan ta fice , ta na fita ya saka face mask d'insa , ya danna wani button cikin motar , nan take wani hayaki ya fara fitowa da ga wajen , sam bai damu ba sai ma wayarsa da ya fara latsawa
bangaran Mahnoor kuma , kai tsaye cikin restaurant din ta shiga , ta na tafiya kamar ba ta san wajen ba
cen ta hango Aryan da Bill da Karim zaune saman chair , su na hira cikin konciyar hankali su na hira
wajensu ta karaso ta na sallama , a tare su ka juyo su ka kalle ta su na amsa mata sallamarta
da murmushi a face d'inta ta ce " I'm sorry na takura muku , please tambaya na ke "
" Okay "
" restaurant din Chicken Palace , please ko nan ne ? "
girgiza mata kai Bill ya yi ya na fadin " No , kin baro shi a baya "
dan dafe forehead ta yi ta na fadin " Ya Allah , wlh yaran nan sai sun kashe ni su huta , please ko za ki iya raka ni , i promise kowane zan saya mishi abun da ya ke so , pleaseeeee " ta kai karshen ta na riko hannayanta ta marairaice fuska
wani dan karamin murmushi Karim ya saki kafin ya mike tsaye ya na fadin " Guys , ku tashi mu rakata da alamun ke bakuwa ce ? "
" Eh , jiya mu ka zo ni da yan uwana ,
I Hope ban takura muku ba ? " ta fada a sanyaye
" No kar ki damu " Aryan ya fada ya na mikewa tsaye , shi da Bill su ka fara takawa su ka baro restaurant din
parking space su ka nufa ta na jan su da hira kamar ta san su , har su ka iso wajen motar Captain ta ce musu motarta ce ta ce wa Aryan da Bill su shiga Baya , akwai driver a gaba
ba musu su ka bude baya su ka shiga , har Karim zai shiga ta yi saurin riko hannunsa ta girgiza mishi kai alamun kar ya shiga
cikin rudu ya kalle ta ya juya ya kalli motar
face mask din Captain ya ba ta , ta saka , kafin ta zagayo daya gefen ta shiga
ko da ta shigo ta ga hayaki na tashi , Aryan da Bill sun sulale a kujerar baya kamar sun suma
ta na shiga ya tada motar su ka bar wajen , su ka bar Karim nan tsaye ya rasa me la faruwa
sai da su ka dan yi nisa sannan hayakin ya fara gushe wa ,
sai a lokacin ta cire face mask d'inta ta na wata yar karamar dariya duk da ba ta san abun da ke faruwa
a hankali ya juyo ya kalle ta jin ta yi dariya , kafin ya kauda kai ya ci gaba da tukinsa
tun ta na ganin gidaje har ta daina gani , ya kai itace ne kawai ta ke gani , alamun cikin daji su ka shigo

____ 26
sun yi wajen 30 minutes su na tafiya cikin dajin nan kafin ta fara hango wani gida , tsakiyar dajin , sai da abun ya ba ta mamaki
kai tsaye bakin kofar gidan ya tsaya ya danna horn , hakan na nufin da mutane a ciki
bai kai ga janye hannunsa ba wani Soldier ya bude kofar , ya danna hancin motar cikin gidan , nan bakin kofar ya tsayar da motar ya sauko
ita ma ta sauko ta na bin wajen da kallo , harabar gidan ta na cike da sojoji kuma American Soldiers , dan farare ne kal baki daya , ga gidan ya tsaru kamar gidansu na cikin gari
ta yi nisa duniyar tunaninta kawai sai ganin Captain ta yi dauke da Bill saman shoulder , wani Soldier na biye da bayansa da Aryan saman shoulder d'insa su ka shiga cikin gidan
da sauri ta taka ta bi bayansu su ka shiga cikin gidan
ta na shigowa Captain da Soldier din nan su ka nufi wani corridor sy ka shiga , ita kuma ta tsaya a nan parlourn , ta na bin wajen da kallo
a haka har su ka fito da ga cikin corridor din , Soldier din ya sa kai ya fice
Captain kuma ya karaso wajen ta ya ce " let's go "
da sauri ta tsayar da shi da cewa " No , ina mu ke a nan ? ina samarin nan biyu su ke ? "
kai tsaye ya ce mata " su na cikin bedroom "
" Me ya sa ka kawo su nan ? tsakiyar daji ? "
" Kidnapping d'insu mu ka yi " ya fada ya na zama saman doguwar sofa ya fiddo wayarsa ya fara latsawa
dan zaro idanu ta yi ta na fadin " What ? Kidnapping ? wayyo na shiga uku ni Nimrah , kuma ni na taimaka maka ? why za ka min haka ? ka sa na koma kidnappers " ta kai karshen kamar za ta yi kuka
" please shut up ! " ya fada a takaice
gabansa ta karaso ta tsaya , ta sa hannu ta kwace wayarsa ta na fadin " No ba zan yi shiru ba , kwana biyun nan da na yi na yi tunanin duk abun da na ke tunanin a kanku kawai shiri ne , amma yanzu ka tabbatar min da Eh Gaskiya ne , me su ka yi maka da za ka yi kidnapping d'insu ? shi ne za ka yi anfani da ni ? "
mikewa tsaye ya yi ya na fadin " shut up ! ke har kin san abun da ke karya ko gaskiya , da kin san irin laifin da su ka aikata da ke da kanki za ki saka gun ki kashe su , bari na takaice miki , kin gan su biyun nan ? da su da Ashur sun yi wajen 4 years yanzu a tare , tun da na san dan uwana bai taba yin friends ba sai a kansu , ya mayar da su tamkar yan uwansa ba abokai ba , ba abun da bai yi ba a kansu dan har kudin karatunsu Ashur ke biyan su , amma kin san me su ka aikata ? yarinyar da ya ke shirin aura su ka yi wa Rape , da a ce kin halin da na tarda ta a ciki da sai kin zubar mata da hawaye , kuma a haka ki ke son na kyale su ? , kuma kar ki damu ba zan ajiye su nan ba har abada , just lokacin da zan gama hujjojin laifin da su ka yi na mika su gaban kotu , ni fa ba mugu ba ne kamar yadda ki ke tunani , na tambaye ki in ba yanzu ba kin taba ganin ni ko daya da ga cikin dan uwana mun yi wani abu da zai nuna miki cewa mu terrorists ne ? "
murya a sanyaye ta ce " Weapons din da na gani cikin kayanka kuma fa ? "
murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " ba ki mamakin ganin American Soldiers cikin gidan sai Weapons ? "
shiru ta yi ba ta ce komai ba , ita sai yanzu ma hankalinta ya kawo
a hankali ya koma ya zauna ya sunkuyar da kai
cikin sanyin murya ya ce mata " ba kullum abun da a ke fada miki ya ke gaskiya ba , ina son y'an uwana fiye da rayuwata , ba na son ganin abun da zai cutar da su , haka ba zan taba saka rayuwarsu cikin hatsari ba , na so na fada miki gaskiya amma ba yanzu ba , in lokaci ya yi zan fada miki , now i just want peace please " ya kai karshen ya na jingina bayansa da sofar , ya daga kai ya lumshe idanu
tsayawa ta yi ta na kallon shi , a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta kunna wayarsa ta kalli screen din
wani cool murmushi ta saki ganin Wallpaper d'insa , kashe wayar ta yi ta ajiye saman table sannan ta zauna gefensa ta kontar da kanta a chest d'insa ta lumshe idanu
_ SANA
Zaune ta ke cikin parlourn ta na kallon Tv cikin konciyar hankali , tun fitar Fahd da Danish har yanzu ba su dawo ba , har an yi kiran isha amma shiru
ta na zaune a haka Danish ya shigo parlourn , fuskarsa duk ta baci da chocolate har rigarsa , hannayansa duk chocolate ne , sai lasar yatsu ya ke
a hankali Sana ta mike tsaye ta na fadin " Innallillahi wa'ina illaihi raji'un , Danish , ina ka gamo da wannan ubar Chocolate ? "
cikin shagwaba ya ce mata " Ni ma Daddy ne ya ban ita "
dan dafe forehead ta yi ta na fadin " wayooo ni Allah Khausaar , shikenan yanzu mu je na yi maka wanka " ta fada ta na shirin nufo shi
da sauri ya juya zai fice parlourn ya koma wajen Daddynsa
ya na shirin fita Fahd ya shigo ya na latsa wayarsa , kai tsaye Danish ya yi cikinsa ya boye a bayansa , duk ya bata mishi wando da Chocolate
kashe wayarsa Fahd ya yi ya saka cikin aljihunsa ya kalli Sana ya ce " me ya faru ? "
cikin yar shi ta ce mishi " ba kai ne ka bawa Danish Chocolate ba , dubi yanzu duk ya bata kayansa kuma na ce ya zo na yi mishi wanka amma ya gudu "
ta na gama fadar haka Danish ya ce " No , No ni ba na son wanka , ni Chocolate na ke so "
" Amma fa ciwo za ta saka ka " Sana ta fada ta na marairaice fuska
a hankali Fahd ya juya ya sa hannayansa biyu ya dauki Danish , bai damu sam da chocolate din hannunsa ba , kuma ya bata mishi kaya ba
cikin nitsuwa ya ce " Bari zan yi mishi " ya fada ya na shirin takawa ya nufi stair ya Haye da Danish
da kallo ta raka su har sai da su ka Haye ta na sakin murmushi , ko ba komai ta na jin dadin ganin yau Fahd ya dauki Danish da hannayansa har da cewa zai yi mishi wanka
kitchen ta nufa ta shiga dama ta shirya musu Diner
nan Fahd kuma bayan ya Haye bedroom d'insa ya wuce da Danish , ya tsayar da shi bakin gadonsa
sannan ya sa hannu ya fiddo wayarsa ya ajiye saman bedside drawer , ya cire watch d'insa , ya cire kayan jikinsa baki daya ya bar short
sannan shi ma Danish ya cire mishi kayan jikinsa , ya dauke shi da hannu guda , dayan kuma ya dauki kayansu ya shiga toilet , ya saka kayan cikin laundry , sannan ya tara musu ruwa cikin jacuzzi , ma su dan sanyi sannan su ka shiga a tare su ka yi wanka
bayan ya gama ya fito ya na sanye da bathrobe , ya nade Danish cikin towel kamar wani baby ya iso bakin gadonsa ya kontar da shi , ya ce " Baby , jira ni zan je na sa kaya "
gyada mishi kai Danish ya yi dan jikinsa ya yi mugun yin sanyi , bai taba yin wanka da ruwan sanyi ba , kullum Sana da ruwan gumi ta ke yi mishi wanka
jim kadan Fahd ya fito sanye da kayan barci , part din baki daya ya fito , ya nufi part din Sana dan ya san kaya Danish su na nan
ko ya shigo ya wuce dressing room , ya dauko wa Danish kayan barcinsa
ya na fitowa ko Sana ta fito da ga cikin toilet ta na na shirin daure towel a kirjinta
wata razananiyar kara ta saki , ta saki towel din baki daya ya fadi kassa
haka shi ma sai da ya saki kayan Danish da ke hannunsa , ya na kallon jikinta baki sake
da sauri ta sunkuya ta dauki towel din , ta daura , ta na kallon shi ta ce " me ka ke yi a nan ? "
shiru ya yi bai ce komai ba har ga Allah ya rasa bakin magana
wani mugun kallo ta wurga mishi kafin ta tako a hankali ta raba ta gefensa ta wuce ta shiga dressing room
sai da ta shiga sannan ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya , ya sunkuyo ya dauki kayan Danish , ya fara takawa jiki a mace ya fice part din