← Book details Doctor Shazim Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 3

part din malam suka nufa

Doctor Shazim Part 1 Complete Hausa Novel · about 495 min read

zaune suka same shi a parlorn shi yana duba wani littafin addini
sallama su kayi hadi da shiga cikin suka nemi wuri suka zauna

Amsa masu sallamar yayi yayin da yake cire medical glass din dake fuskar
gaishe dashi shazim yayi  yana tambayar  shi ya jiki
"Alhmdllh ya aiki"
''Alhmdllh malam''
"to Allah ya taima ka"
" ameen malam"
fira suka shiga yi sai da aka kira sallar isha sannan suka tashi
masallachi suka nufa harda malam  ana gamawa suka dawo ciki,za su nufi part ɗin ummy malam yace  noraiz ya tafi, shi kuma yana son magana da shi, wuce wa noraiz yayi,  su kuma shi da malam suka  shiga part ɗin malam, part ɗin ummy noraiz ya nufa, ammy da ummy ya samu a parlor fatima da yarinye kuma na kitchen
Zama yayi kan sofa kusa da ummy yana mata shagwaɓa akan yunwa yake ji
"ga abinci can su fatima na girkawa"
"gaskiya ni bazan iya jiran su gama ba" ammy tace "to sai dai karka jira ɗin" ummy tace "a'a baza ayi haka ba, bari naje kitchen ɗin baza a rasa abun da zai ci ba kafin su gama "ta faɗa haɗi da tashi ta nufi kitchen ɗin , ammy tace "da kin ƙyale shi ummy, sai kace ba namiji ba "
"A'a ke dai, wasa da ciki ai bai da amfani sai ulcer ta kama mutum"
"wallahi kuwa ummy" jifan shi ammy tayi da pillow.

A chan parlorn malam,
"shazim bana son mu cire hannun mu akan lamarin su zo su yanke maka hukuncin da baka so ba, gara tun wuri ka nema ma kanka masalaha"
"in sha Allah malam,zanyi ƙoƙari,ka basu haƙuri"
"haka kake cewa kullum, har hakan yasa suna tunanin ni ke goya maka baya, kuma miyasa idan sun kira ka ba su samun ka, mansoor ma ya kirani yace yanata ne manka amma baya samu "
"bakomi, ina jin network ne "
"to kayi ƙoƙari ka kira su"da to ya amsa,tashi yayi yace zaije wurin ummy su gaisa, da to kawai malam ya amsa, part ɗin ummy ya nufa, a parlor ya same ta noraiz na kusa da ita yana cin abinci, wuri ya samu ya zauna yana gaishe ta
amsa mashi  tayi cikin kulawa hadi da tambayar shi ya aiki
"aiki Alhmdllh ummy, ya malam  da jiki "
ummy tace " jiki da sauki Alhmdllh  "
"to masha Allah, Allah ya ƙara sauki "
" Ameen" fatima ce ta nufo idan suke, gaishe da shazim tayi tana cema ummy sun gama, ga abinci can kan dinning, da to ummy ta amsa, wurin dinning fatima ta koma tana cewa"ummy na malam fa, part É—in sa za'a kai masa"
"A'a, zai shi go "bata rufe baki ba sai ga malam ɗin ya shigo, tashi suka yi dukan su suka nufi dining ɗin, bayan da suka gama,shazim ya sake duba jikin malam  ya sake rubuta mashi magunguna
Sannan suka yi masu sallama,suka kama hanyar gida Ammy da shazim mota daya suka koma yayin da fatima da Noraiz suka shiga tasu suma
Suna shiga gida Innah Asabe ta fito tana masu sannu da zuwa da tambayar jikin Malam, nan Ammy ke fada mata jiki da sauki Alhmdllh,  sannan kowa yakama hanyar bedroom dinsa, ita ma Innah Asabe nata dakin ta nufa...
Episode  11_ 12

Har yanzu kwance take kan gado kamar yanda abie ya barta sallah ce kawai take tashi tayi,  Aaimah na zaune kusa da ita tana duba book dinsu na school saboda exam da suke facing, nocking suka ji anayi Aaimah ce tace "waye" daga chan wajen taji ance "za kizo ki buɗe  ko sai kingama tambayar waye sannan"  ba shiri ta sauko daga gadon hartana niyyar faduwa saboda jin muryar wanda ke nocking din bakowa bane face ya Abdallah,  buɗe  kofar tayi tsaye yake jikinsa sanye da  gajeran wando iya gwiwa sai riga mara nauyi mai gajeran hannu
Matsawa Aaimah tayi gefe shi kuma  ya wuce ciki dai dai bakin bed din ya tsaya yana cema Aairah ta tashi, tashi tayi zaune, shima zama yayi bakin gadon yana fadin "minene ke damun ki"
"kaina ke ciwo sai zazzabi, amma naji sauki dan yanzu bana jin zazzabi"
"ok" ya fada yana kallon ta domin yasan karya take allurace kawai bata so
kuma dole sai yayi mata ita ,  hannun shi ya daura saman wuyanta zafi yaji zau "ki ka ce ya sauka zazzabin bayan gashi nan jikin ki da zafi"
"to yaya dan Allah ka bani  magani kawai, wlh bana son kayi man allura dan Allah"
"a haka zaki zama Nurse É—in ki na gudun allura,wa zai zauna ki yi mashi ita kenan bayan ke ma ba so ki ke ba?"
"dan Allah dai yaya" tafa tana hada hannuwanta
wuri É—aya alamar yayi hakuri.
"shikenan to" ya fada hadi da ficewa daga dakin
dawowa Aaimah tayi kusa da ita tana cewa "ai kuwa  nasan allurar zai maki , tun da jikin ki har yanzu da zafi" mi Aairah za tayi inba kuka ba , kuka rurus kamar wata ƙaramar ya rinya Aaimah kuma sai ƙara bata tsoro take
tashi tayi daga gadon ta fice daga dakin bedroom din Mom ta nufa, Mom fitowar ta kenan daga bathroom Aairah ta shigo kamar wacce a ka koro,  bed din mom ta nufa ta haye hadi da jan blanket ta rufe  jikinta tana cigaba da kuka
kusa da ita mom ta ƙaraso tana fadin " ke kuma lafiya kamar an koro ki, mikike ma kuka ne"
"Mom ya abdallah  ne zaiman allura"
"Yau ni naga takaina ni kubrah, shine kika shigo kamar an koroki"
Mom bata rufe baki ba sai ga ya abdallah yashi go hannunsa rike da leda,ya je  dakin su bai sameta ba
tada Aairah mom tayi magani ya fara bata da kuwa zai mata allura sun sha buduri har Mom , sai da  yayi mata jan ido tukun a ka samu ta tsaya a ka yi allurar, dama haka yake fama dasu ita da Aaimah In dai a kace ba su da lafiya to fa sai sun kusa tara masu mutane a gidan saboda allur kawai,  amma kullum Iƙirarin su shi ne su zama nurses.
kuka Aairah tasha Ba na wasa ba, sai dai ta kwana dakin Mom Aaimah ma nan ta dawo ta kwanta saboda bata iya kwana dakin su ita kadai...

WASHE GARI...

Alhmdllh ta tashi da jikin da sauki sosai bedroom dinsu ta koma tayi wanka tasa kaya mara sa nauyi
ko da Aaimah ta shigo tana tambayar ta ya jikin
"da sauki sosai"
"to Allah ya Ƙara sauki, hajiyar allura "
harara  ta bugama Aaimah, ita kuwa mi Aaimah zatayi inba dariya ba tana fadin "wallahi sister duk mijin da ya aure ki zai sha fama musamman idan shi likita ne, dan wallahi na san tara mishi mutane zaki riƙa yi muddin baki da lafiya yace xai yi maki allura"
"kice duk mijin daya aure mu dai, sai kace kema allurar ki ke so zaki wani tasa ni gaba kina man dariyar banza"
"ai wlh kinsan gara ni dake wllh"
"wlh karya ne bawani nan"
"to uwayen musu da safiya zaku fara ma mutane musun tsiya da ku ka saba, ba kamar ke Aairah daga samun sauki har zaki fara É—an banzan surutun da ku ka saba"
Mom ta fada wacce shigowar ta kenan tasame su suna ta gaddamar da su ka saba  "ke kinyi wankan ko ko dai sai kungama musun tukkuna"
"A'a yanzu zanyi" Aaimah ta fada tana nufar toilet ta shiga, kusa da Aairah Mom ta matso tana fadin "ya jikin, duk nama ga kinji sauki tunda gashi harki na musu"
murmushi tayi hadi da daura kanta saman kafadar Mom tana cewa"da sauki Mom, Aaimah ce da raini wayau waini take ma sharrin bana son allura sai kace ita ma so take" murmushi kawai mom tayi tana fadin Allah ya shirye ku,ameen MomAairah ta fada

✨VICTORIA✨

sanye take da uniform din ta, fita tayi daga office din su direct elevator ta nufa  numbobi ta danna  kofar elevator ce ta bude wasu nurses ne ciki shiga tayi ita ma
elevator na tsayawa kowa ya fice alamar sun kawo in da za su , fita tayi itama direct office din Dr Shazim  ta nufa sai da ta zo bakin kofar office din tukun ta tsaya, waige waige tashiga yi alamar rashin gaskiya
sai da ta tabbatar ba mai ganin ta tukun ta sanya key din dake hannun ta ta bude office din da sauri  ta shige ciki saboda jin alamar kamar mutum na tunkaro office din

tsi office din yake alamar ba kowa a cikin sa , sai  ac dake aiki
wurin freezer dake office din ta nufa.
budewa tayi,  cike yake da drinks kala kala, gani nayi ta dauko kwalin daya daga cikin drinks din ta a jiye saman wani dan ƙara min table dake kusa da fridge
Sannan ta sake dauko wani, a ta kaice dai  sai da ta ɗauko kusan kowace color dake ciki sannan ta maida ta rufe. 
Hannu tasa cikin aljihun wandon kayan ta, ta fito da wani gari cikin wata yar ƙaramar roba fari tas dashi , buɗe  marfin kowane kwali  na drinks din tayi sannan ta dibi wannan garin ta zuba ta girgiza,  daya Bayan daya sai da ta tabbatar ta girgiza ko wane ya girgizu sannan ta mai da  ta rufe
maida su tayi ciki ta jera su kamar yanda ta same su, rufe fridge  tayi sannan ta kama hanya ta fice ta nufi elevator ta sake danna numbobi kamar ɗazu sai ga kofar ta bude
sai da gaban ta ya faɗi sakamakwan ganin hidaya da maryam da tayi ciki tasan dole suyi zargin wani abu saboda  a wannan floor din daga office din dr shazim sai na dr kabir sauran wuraren ɗakunan marasa lafiya ne da wurin da patient ke zama dan ganin likita in sun zo, kuma gashi lokacin da  patient ke zama bai yi ba,  an dai buɗe  offices ne domin sharewa da moping.dan doctors ɗin ba bu wanda yazo
kallon kallo suka shiga yima juna ita da hidaya dan ita maryam harara kawai ta bita da ita
martanin harar ta maida ma maryam hadi da jan tsaki ta shige cikin elevator, fita su ka yi dama nan su ka nufo
"Aikin baza harara a duhu, yar wahala kawai" maryam ta fada hadi da jan hannun hidaya su ka wuce , itama tsakin tayi hadi dacewa "oho dai dr ne dai saina rabata dashi,  kuma kema zan dawo kan ki ne inna gama da ita"
Haka dai taita banbaminta a banza har ta kai inda zata sauka

A chan kuma hidaya ce ke ce ma maryam "nifa  kinsan  gani nake Victoria kamar bata da gaskiya?"
"mikika gani? "Maryam ta tambaya
"bakiga tana ganin mu ba duk tawani sha jinin jikinta,  bayan haka ma mita zo yi floor ɗin  su Dr, yanzu ba lokacin fara aiki ba, ni sai nake ganin kamar wani abun tayi"
"hmm haka ne fa kuma, ke ita ta sani chan taje taji da rashin gaskiyarta,ai Allah na sama yana kallon duk wani abu da za tayi, koma mi tayi dan kanta hidaya ita da Allahn daya halicceta"

"Wlh kuwa ita da mahaliccinta" hidaya ta fada abun da ya kawo  su suka shiga yi, suka ture zan chan Victoria gefe

Tana shiga  office din su destiny ta samu  da wasu  daga cikin nurses din da suke  zama office din
wurin destiny ta kara sa tana fadin "sister shigowar ki kena? "
"Eh yanzu nazo, nama yi tuna nin ba kizo ba, sai da naga jakan ki a locker tukun, amma daga ina haka.? "
"Mu fita daga waje na fada maki,nan kinga mutane,  kuma kin san su da bakar gulma yanzu za kiji magana wani wuri."
"haka ne kuma" destiny ta fada tana jan hannun Victoria su ka fice daga office din
sai da suka shiga wani dan corridor ku sa da office din su sannan Victoria tace"daga office din dr nake"
"kai da gaske ki ke"
"da gaske nake mana, kaji destiny na taɓa maki wasa ne, daga can nake"
"Amma ina fatan ba wanda ya ganki  ko, kuma kinyi yanda gurutu yace mu yi"
"Sosai ma kuwa, ai kamar yanda yace nayi haka nayi"
"Yawwa yanzu sai dai mu tsaya jiran sakamako kawai"
"hakane kam, kinga mu koma office kar wani ma ya fito"
"kuma fa haka"
Office din suka koma dumin shirin fita,ba su samu kowa a office din ba duk sun fita , suma basu wani jima ba suka fice..

✨Hidaya✨

Zaune su ke ita da maryam da sauran nurses din asibiti,fira su ke yi kafin doctors su shigo kowa ya kama  gaban sa zuwa in da yake nasa aikin.
suna a nan zaune dr shazim ya shigo shi da dr  kabir da Noraiz, yana gaba Noraiz da kabir na bayan shi
gaishe da su nurses din su ka shiga yi,Noraiz da Dr kabir ne kawai suka amsa masu Shazim kuwa hannu kawai ya iya daga masu
Suna zuwa bakin office din shi briefcase dinsa dake hannun Noraiz ya amsa
saboda  shi Noraiz office din Dr kabir zai wuce
Office din ya shiga,  ko ina fes an gyara sai kamshin  fresheners
tarkacen sa ya ajiye saman table hadi da zama kan chair dinsa,laptop ɗinsa ya jawo ya fara aiki a ciki, nocking  aka yi "Come in" ya ba da izin, hidaya ce ta shigo bakin ta dauke da sallama,hannunta riƙe da  files,amsa mata sallamar yayi "good morning Dr, dama nace zan iya fara turo patient"
kai kawai  ya daga mata alamar eh "ok" ta fada  hadi da ficewa ta koma wurin patient
wurin 12:00 ya gama  ganin patient din da zai gani time din har Noraiz ya dawo office din ,
"Yaya wai baka da wani abun ci ne a office dinnan?"
Noraiz ya fada yayin da yake bude fridge dake office din "to a cici ni bana ajiye komai daya danganci abinci a eko , zaka iya bari Sai munje abnoor tukunnan" kwalin lemu ya ɗauka sannan ya
rufe fridge ɗin , yana fadin "bari nas ha wannan kafin mu tafi" wurin zaman shi ya koma ya zauna hadi da bude marfin lemun, Dr kabir ne ya shigo da sallama a bakin sa  hannun sa ɗauke da  basket din abinci yana cewa "wallahi Momma har yanzu kallon yaro take man, wai abinci tasa aka biyo ni da shi saboda kawai banyi breakfast  na fito ba"
"dama ai kai yaro ne" shazim yafa yana murmushi "haba dai kai ka san wanene yaro wallahi"
"ai duk auta yaro ne"da yake kabir shine auta a wurin momman shi
"lallaima Shazim, wallahi ka rainani" katse su Noraiz ya yi yana cewa
"wallahi Momma ni ta taimaka kamar  tasan yunwa nake ji" kallon shi Shazim yayi yana girgiza kai da fadin
"Allah ya shirye ka Noraiz, duka ƙarfe  12 amma sai wani complain din yunwa kake, sai kace wani karamin yaro"
"Yaya kasan fa ina fama da ulcer" ya fada yana shafa cikin sa
"ulcer ko ragannci?"
Shi dai dr kabir binsu kawai yake da idanu yana murmushi
"to yanzu dai ku kale wannan musun, kai Noraiz zo ka zuba abinci kaci" Dr kabir ya fada
dawowa Noraiz yayi kan sofar da Dr kabir yake , plate ya dauka da serving spoon ya buɗe  food flask farar shinkafa ce,  zubawa yayi sannan ya bude dayar flask din wacce pepper soup ce a ciki,sai da ya buɗe  kowane  flask dake cikin basket din tukun ya koma gefe yana ci, Dr kabir ya zuba ma Shazim yana cema noraiz "wato ɗan tsako sami ka ki dangi ko"
dariya kawai Noraiz yayi
"Ok bakin maganar ya mutu kenan" Dr kabir ya fada yana murmushi, shima dai Shazim murmushi yayi yana cewa "baka san waye noraiz ba a kan abinci"  daga nan su kayi shiru kowa na aikin bama cikin sa
sai da suka gama Dr kabir ya nufi fridge ya dauko masu lemu da ruwa
Shi noraiz ruwa kawai ya amsa saboda ya dauko lemu tun dazu sai da suka gama tsab sannan suka tashi shazim duka tarkacen sa ya haɗa saboda da sun dawo sallah abnoor  zasu wuce shida Noraiz..

✨Aairah ✨

Alhmdllh jiki yayi sauki sosai dan yanzu haka zaune take parlor suna fira ita da Mom da Aaimah wacce taki zuwa school saboda Aairah bata je ba.
abie ne ya shigo daga masallachi sallar zuhur wurin su ya nufa zama yayi kan sofar da Aairah take yana faɗin    "ah lallai jiki yayi sauki Masha Allah" ya faɗa yana shafa kanta
Mom  tace"Jiya kana part ɗinka  da ka ga budirin yin allura"
abie yace "Allah dai ya shirya yaran nan da dan bazan tsoron allura, a haka zaku zama nurses din da ku ke so kuna tsoron allura?"
Aaimah  tace"duk da haka abie mu na iyawa Allah"
abie yace "to Allah dai yasa"
Aairah tace "ameen abie"
sun jima suna fira har wurin ƙarfe 3:00 sannan suka tashi

✨ Shazim ✨

Yau da wuri suka  bar abnoor  saɓanin kullum da sai yayi sallar magrib da isha sannan ya ke komawa gida, duk da  yanzun ma ba gida suka nufa ba gidan malam suka nufa domin su kara duba jikin sa. 
Zaune su ka same shi a parlorn shi yana duba littafi, sallama su ka yi hadi da shiga cikin,cikin parlorn,  amsa masu sallamar yayi yana tambayar  su ya aiki,  da alhmdllh suka amsa mashi
Shazim ya ce"ya ƙarfin jiki"
"Masha Allah jiki alhmdllh , yanzu ko ina ina iya  zuwa Alhmdllh"
"Masha Allah Malam, Allah ya ƙara sauki da nisan kwana mai amfani"
"Ameen ya Rabbi"
"Malam ko dai lokaci ne yayi, muyi shirin cin gumba" noraiz ya fada yana dariya
dakkuwa malam yayi mashi "lallai nuraddeen  ni kake ma fatan Mutuwa koh, to sai dai mahaifiyar ka ta mutum amma bani ba, ja'irin banza"
dariya Noraiz ya kwashe da ita yana fadin "yanzu nan malam baka san mutuwa"
Shazim dai na gefe yana jin su in ban da murmushi ba abun da yake
"mutuwa na kan kowa nuraddeen , yaushe musilmin ƙwarai zai guji mutuwa, kawai dai ana tsoron mi za'a riska in an je can"
"haka ne kam Malam, Allah dai yasa mu  mutu muna ma su Imani"
da Ameen suka Amsa su duka, nan malam ya shiga yi masu nasiha a kan ruƙo da gaskiya da kuma aiki da ita da tsare mutuncin kai, sannan ya ƙara yima shazim fada a kan  ya fitar da mata  yayi Aure shekarun sa ƙaruwa suke ba raguwa ba,  kuma mahaifiyar su bata da wani buri daya wuce taga ta aurar dasu baki daya shine kwanchiyar hankalin ta, saboda dangin mahaifin su gani suke kamar ita da malam su ka hana shi  yin aure, "Shazim ko baka so naga jikokin jajirtaccen jika na ne" duƙar da kanshi yayi ƙasa yana cewa "ba haka bane Malam,In sha Allah zanyi ƙoƙari nayi nan kusa"
"to Allah ya yarda, ya kuma za ba maka mace ta gari kai da É—an uwanka, itama fatima Allah ya bata miji nagari"
da ameen suka amsa su duka har da ummy wacce shigowar ta kenan parlorn taji suna adu'a shine itama ta amsa da ameen.
gaishe da ita su kayi , cikin kulawa ta amsa tana tambayar su ammy,  shazim  maganar kasuwancin shi da yake son noraiz ya cigaba da kula da su yayi ma malam da noraiz ɗin kan shi, "eh wannan shawara ce mai kyau,dama ya kamata ka rage ma kanka wasu abubuwan,"
"hakane,dama jiran dawowar sa nake na tattara komi na miƙa masa"
"yayi hakan Allah ya taimaka,amma ko da noraiz ɗin ya amsa ka bar hameed su cigaba da kula tare, duk da noraiz abun da ya karanta kenan, zai ƙara samun wasu dabaru wurin hameed"
"eh daman shawarar da na yanke kenan"
"to Allah ya tai maka"da ameen suka amsa
sun jima  sosai gidan malam dan sai wajen Karfe 10 na dare  sannan suka tafi gida bayan malam ya sha maganin sa,da yake yana sa shi bacci .
Suna shiga gida parlorn Ammy suka nufa anan su ka sameta ita da  Fatima zaune, sallama su ka yi , amsa masu Ammy tayi tana cewa "nayi tunanin baba ya rike ku sai kwana, ashe zaku dawo"
"Wlh kuwa zamu dawo, ya gida"
"gida alhmdllh gashi nan"
fira suka ɗan taba Ammy nace masu ga dinner din su can kan dinning  suka ce sun koshi dan sun ci dinner gidan malam
basu  jima ba kowa ya nufi dakin sa saboda dare da yaja sosai.....

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wataran dadi wataran akasin haka su Aairah sun fara zana jara bawar gama secondary school  har sun  kammala, haka zalika fatima ma ta gama  Noraiz  watan shi 2 da sati 3 da dawowa kenan.  

Zaune  ammy take bakin bed, wayar tace da ke kan bedside ta fara ringing ɗaukra wayar tayi tana kallon mai kiran, ya ya Ahmad shi ne sunan mai kiran nata, dafe kan ta tayi tana faɗin "ya salam,Allah ya sa bawani abun bane" picking tayi haɗi da kara wayar a kunne tana sallama, amsa mata sallamar na ciki wayar yayi, gaisawa suka yi, tana tambayar yasu hajiya asiya da su kairiyya, da lafiya lau ya amsa mata sannan yace
"wai A'isha mi ku ke nufi ne ke da shazim, tun yaushe nake faÉ—in idan na kira shi bana samun shi"
"kayi haƙuri yaya, tun ranar da ka kira na faɗa mashi ya kira ka, na yi tuna nin ya kira"
"yaushe zai kira,yasan zan mashi maganar da ya tsana, wacce yake ganin bamu kai matsayin da za muyi mashi ita ba"
"ba haka bane yaya, dan Allah kayi haƙuri, zanyi mashi magana ya kira ka yau"
"to, daman na kira ne dan in faÉ—a maki ina son ganinshi shi da Æ´an uwan shi a cikin satin nan"
"to yaya, zan faÉ—a mashi"
"to shikenan, sai anjima"
"to Allah ya kaimu"da ameen ya amsa haÉ—i da yin rejectin, a jiye wayar ammy tayi tana faÉ—in
"na rasa gane halin shazim, idan har bai jaman abun magana a wurin su hankali shi baya kwanciya, amma na san maganin shi" ta faɗa haɗi da miƙewa ta nufi part ɗin shi, yana parlor zaune,  tambayar shi tayi ina wayar shi, "gata nan ammy, lafiya"
"kira ya ya ahmad yanzun nan "
"amma ammy mi yasa"
"zaka kira shi ko kuwa sai ka gama tambaya ta dalili"
"A'a" kawai yace haÉ—i da É—aukar wayarshi yayi dialing number uncle Ahmad, tana fara ringing, aka É—auka, sallama yayi haÉ—i da cewa "ina wuni uncle" da lafiya uncle ahmad ya amsa, sannan ya É—aura da cewa "shazim laifin mi muka yi maka da idan mun kira ka baka É—auka, kuma kai ba zaka iya kiran mu ba?"
"bakomi uncle"
"to shikenan, ina son ganin ka abuja kai da ƙannan ka a cikin satin nan"shiru yayi baice komi ba, uncle ahmad ne yace "baka ji mi nace ba ne"
"A'a naji, amma uncle aiki na ya zanyi da shi"
"Ina sauraron zuwan ku kana ji na ko"
"eh naji" rejecting uncle Ahmad yayi batare da ya saurari mi shazim É—in zai sake cewa ba,
"sai ku shirya kai da su"
"haba ammy, ni bazan je ba"
"to wallahi bari kaji ba zaka dinga ja man zagi wurin su ba kaji na faÉ—a maka, gara ma tun wuri ka shirya ku tafi"
"to, amma sai next week "
"Allah ya nu na mana"ammy ta ce haÉ—i da ficewa ta bar part É—in...
  13
   
✨Noraiz-Fatima✨

zaune suke  parlorn Ammy, fatima na duba wani novel  yanzu ba school  sai Islamiyya, shi kuma yana aiki a laptop ɗin  sa, aje novel din tayi tana cewa
"ya noor  ka kuwa tuntubar man big bro maganar school  ɗin dan Allah?" ture laptop ɗin  yayi yana cewa "kima bar wannan maganar,dan wallahi yace kusa da Ammy za ki yi karatu,ki tambayi  Ammy ma a gabanta yace haka, har sa baki tayi amma yace a'a"
"hai wai shi ya Shazim miyasa yake haka dan Allah,to yaya ita Ammy mi zai hana tace sai nayi "
"kawai kiyi haƙuri  kiyi karatun ki anan a kwai makarantu masu kyau kamar na can zaki samu duk abun da ki ke so, kuma na san zai sama maki mai kyau da tsada"
"ya noor ya zanyi dole na hakura, Allah ka ɗai yasan dalilin sa na hana ni"
"nasan bazai wuce saboda innah ba"
"anya dai, Allah yasa haka alkairi ne"
"ameen "Noraiz ya faɗa 
(Suna da saurin fahimtar dan uwansu saboda sun ɗauke  shi tamkar mahaifin su da suka rasa tun basu san kan su ba,   sabanin wasu yan uwan idan akace mahaifin su baya da rai,za ka samu rashin jituwa da ƴan uwansu musamman suna son wani abu,da ɗan uwan yanuna masu illar dake ciki abun maimakon su fahimce shi, sai kasamu suna kullatar shi a rai wasu harsu kai da faɗin  dan yaga mahaifin su baya da rai shiyyasa yake masu abun da duk yaga dama,za su dunga ɗaukar shi a matsayin mai tauye masu haƙƙi 
abu buwa iri iri dai, Allah kasa mana ƙaunar ƴan uwan mu da fahimtar su, ka bamu ikwan rufa ma junan mu asiri ameen 🙏 )

Ammy ce ta fito daga bedroom dinta tana cewa "yaya da kanwa mi ake shiryawa ne,nake jin ƙusƙus tun a ɗaki?"
"sirri Ammy,ki zauna ayi dake"
Noraiz ya fada  yana nuna mata  kan sofa,  zama tayi  tana faɗin " ina sauraro kuwa, wane sirrin ne ake shiryawa"
fatima tace "ammy maganar makaranta ce"
"mi ya faru?"
"bakomi, ya noor ya sanar dani yan da ku ka yi da ya shazim"
"hakane sai dai kiyi haƙuri "
"dama ya zanyi ammy dole na haƙura, amma ban san mi yasa ya shazim bai son zama na abuja ba "
"nima kaina ban san dalili ba nasan dai bai wuce innah"
sun jima suna tattaunawa kan maganar, sai ga shazim ɗin ya shigo da alama daga abnoor  yake saboda yau friday dama bai cika jima wa ba saboda zuwa masallaci,  wurin su ya nufo ya na faɗin "Ammy ina wuni,mi a ke shiryawa ne na ganku zazzune a parlor?"
"lafiya lau ya aiki, sirri ne kaima zo ka zauna" murmushi yayi yana neman wuri kusa da Ammy ya zauna, gaishe da shi su fatima su kayi noraiz nacewa "ashe dama na bi ka, naga ka dawo da wuri"
"ai  kafi son zaman gida ne  sai kace wata mace, zan ga yan da zaka ƙare idan kafara Aiki"
"ai koh lallai " Ammy ta fada hadi tana mangare ma shazim  kai, sosa wurin yayi yana fadin "Ammy haka ne fa, in ba mace ba miya haɗa  namiji  da zaman gida dan Allah?" dariya fatima da Noraiz suka yi ganin yan da shazim ke bata fuska , maka masu harara yayi, shiru suka yi suna ƙumshe dariya, basu wani jimaba suna fira suka tashi domin shirin zuwa masallaci ammy kuma da fatima suka tafi daki domin yin sallah suma....

✨KATSINA✨

Abie ne da Abdallah  ke saukowa daga up stairs zasu tafi masallaci, da Mom suka ci karo a parlor ta fito daga kitchen hannun ta ɗauke  da food flask "Masha Allah irin wannan kyau haka barrister, gaskiya  kar ka sa matan mutane suyi ta kalle man miji" dariya abie yayi abdallah  kuwa duƙar  da kai yayi yana murmushi a zuciyar shi yana fadin "Mom duk da an tsufa amma ana kishi, Allah ya bani mace irin Mom" nace ameen dr
"da har ina cewa zan ƙara maki a bokiyar zama, amma ki ke faɗin  haka"
"tab wallahi  kaima kasan wasa kake, ai auren mu in kaji ana auren zobe, ba saki ba yaji ba kishiya"
dariya abie ya sake kwashewa da ita yana faɗin  "za kuwa kisan ba wasa nake ba, dan daga nan zance zan wuce" in ban da dariya ba abun da Abdallah  ke ma iyayen nasa, yana kallon su cikin birgewa
"ka dai faÉ—a,nawa jine kawai"
"ai kuwa zaki san bawasa nake ba, kaga abdallah  wuce mu tafi kar mu makara" ficewa su kayi suna jin Mom na masu a dawo lafiya
bedroom ɗin  su Aairah ta wuce, bude ƙofar  tayi ta shiga
shiri ta same su suna yi  "yawwa kun shirya kenan"
"eh"suka bata amsa
"yawwa kuyi sauri ku ƙarasa , ga abinci can kitchen mungama ku jera kan dinning sannan su mudi ma ku tabbatar kun kai masu nasu, nizan shiga nayi wanka ne kunji"
Aairah tace
"In sha Allah za muyi yan da ki ka ce, amma Mom wai ya maganar walimar mu ne, munga ba'a fara shirin komai ba,kuma fa jibi ne"
Mom tace" tana nan mana ba jibi bane, jira nake anjima yayan ku ya kaimu shopping ko kuma abie din ku,saimu siyo duk abun da ya dace"
Aaimah tace"to shikenan Mom Allah ya kaimu an jimar" ameen Mom tace hadi da ficewa daga dakin tana sake tuna masu aikin da ta sa su, suna gama shirin suka fita domin yin abun da Mom tasa su, suna kammalawa nan main parlor suka tsaya suna kallo
su abie ne da ya abdallah  su ka shigo,sannu da dawowa su kayi masu hadi da gaisawa, amsa masu su kayi abie ya samu kan sofa kusa dasu ya zauna  ya yin da shi kuma ya Abdallah ya haye up stairs, fira suka shiga yi da abie akan walimar da za'a yi masu , sun jima suna fira har Mom ta sauko tana cewa "shiyyasa naga barrister bai shigo ba, ashe kuna nan kun tasa shi gaba da abun da kuka saba watan surutu ba"
Aairah tace"kai Mom bafa surutu muke masa ba, maganar walimar mu fa mu ke yi" dinning Mom ta nufa tana faɗin 
"to yayi,sai ku taso ga abinci na jiran ku" ta sowa suka yi har da abie suka nufo dinning din, abie nace ma
"Aaimah je ki kira yayan ku, kinji"
"to abie" ta fada hadi da nufar up stairs ta nufi part din Abdallah,samun shi tayi yana waya jira tayi sai da ya gama sannan tace "yaya ka zo mu ci abinci" da to kawai ya amsa mata, ya yin da ita kuma ta fice  tabar ɗakin,komawa  dinning din tayi, wurin zaman ta na ɗazu ta koma ta zauna plate taja wanda Mom  tayi serving ɗin  kowa, shiru kowa yayi anata bama ciki hakkin sa, sai da suka kusa kammalawa sannan abdallah  ya sauko ya nufo dinning ɗin,  Mom  tace "lafiya baka fito ba tun time din da aka kira ka?"
"Ina wani ɗan aiki ne shiyyasa" ya fada hadi da neman wurin zama ya zauna plate ɗin  abinci Mom ta miko masa, Nagode ya faɗa  hadi da daukar spoon ya fara cin abincin, suna gama wa su Aaimah suka gyara wurin yayin da  su Mom suka koma kan sofa, suma suna gamawa wurin su Mom ɗin  suka dawo,  firar walimar da za'ayi masu su ka shiga yi,  basu  tashi ba sai da lokacin sallar asr yayi sannan su abie suka wuce masallaci, suma daki suka shiga domin gabatar da tasu..

mom  ce ta fito daga bedroom ɗinta  jikinta sanye da atamfa ɗinkin  riga da zani da mayafi sai jaka a hannun ta,  ɗakin  su Aaimah ta nufa  samun su tayi duk sun sha abaya black color  sunyi rolling da gyelenta sai side bag da ko waccen su ta rataya sai glass irin na gayu ɗinnan,  shirin fita suke daga ɗakin  sai ga Mom ta shigo "yawwa kun shirya  kenan to ku fito mu wuce abie dinku da yayan ku na waje mu ka dai su ke jira" Aaimah tace
"Mom ba ki ce munyi kyau ba" yan yatsu kawai Mom ta haɗa  al'amar komai yayi,  ficewa su ka yi zuwa compound din gidan in da anan suka samu abie da ya abdallah,   shiga su kayi cikin motar ya abdallah  ke driving yayin da abie ke kusa da shi, su kuma suna baya su da Mom,a dawo lafiya su mudi su ka yi masu yayin da abdallah  ya fice da motar suka hau kan titi, wani ƙaton  shopping mall ya nufa dasu, parking su kayi a parking lot dake wurin wanda aka tanada domin masu siyayya, sai da ya gama daidai ta parking din motar,  fitowa  suka yi,  cikin  mall din suka nufa,  barka da zuwa waiters  su kayi masu,inda ake ajiye cart suka nufa,guda biyu suka ɗauka,  Aaimah na tura daya tana biye da abie da ya abdallah ,  yayin da Aairah ke tura daya tana biye da Mom,siyayya suka yi sosai,sun jima  a shopping mall sai da suka tabbatar sun tanadi abun da suka san zasu buƙata  sannan suka nufi wurin biyan kudi, Abdallah ya biya duk abun da suka siya  ma'aikatan wurin suka ɗaukar  masu kayan zuwa booth, 
wurin da ake sai da snacks suka wuce pizza  da shawarma sai ice cream ya Abdallah ya sai masu  daga nan suka wuce  gidan dadi, suna isa bakin gate din gidan ya abdallah  yayi horn, mai gadin ne ya leƙo,  ganin motar  abdallah  yasa shi  komawa ciki da sauri hadi da bude masu gate, ciki ya shiga da motar parking lot dake compound din gidan ya nufa  hadi da yin parking,  sannan suka fito,booth abdallah ya buɗe, snacks ɗin da suka siya ya ɗauko haɗi da miƙama   su Aairah,cikin gidan suka nufa,  parlor ne dan dai dai matsakaici yasha royal sofas masu kyan gaske , wata yar tsohuwa ce (dadi kenan)  zaune ita da wata mata aƙalla  zatayi kima nin shekara 38 zuwa 40 ( Aunty Rabi kenan, ƙanwar abie ce,  zaune take  da dadi tun lokacin da Allah yayi ma mijinta rasuwa,  kuma gashi Allah bai bata haihuwa ba shiyyasa ta dawo kusa da mahaifiyar ta tana kula da ita)  sallama su kayi, aunty rabi   ce ta amsa masu sallamar  hadi da cewa "wannan  shi ake kira  tafi da gidan ka, wannan ziyarar bazata haka yaya"
dariya abie yayi hadi da cewa "ke dai bari kawai rabi, munje siyayya ne saboda walimar su Aairah, shine muka biyu ta nan" nan suka shiga gaisawa, wurin  dadi  suka matsa itama suna gaishe da ita amsa masu tayi cikin kulawa hadi da taya su Aairah murnar kammala makaranta da hadda nan suka shiga fira "Muhammad  yaushe ne walimar su yan biyu" dadi  ta tambaya,  amsa abie ya bata  da "jibi ne In sha Allah"
"to Allah ya kaimu" da  ameen suka amsa , miƙama aunty rabi snakcs ɗin dake hannun su suka yi, amsa tayi tana ma abie godiya,   Aairah  tace "amma dai dadi  zaki zo koh"
"In sha Allahu kuwa, ai audu zai zo ya ɗauke  ni da kansa, koh audu" ta fada tana shafa kan Abdallah  dake kusa da ita, ɓata rai yayi yana cewa, "wai dan Allah dadi bazaki daina ce man audunnan ba,  nifa sunana Abdallah , ba audu ba" dariya su ka kwashe da ita su duka ban da Abdallah  dake zabga ma su Aairah harara saboda dariyar da suke  mashi "ai inba kishiya kayi man ba, bazan daina cemaka haka ba, shima abun da zaisa na daina kawai dan karta raina min ango ne,  amma da bazan bari ba"
"to shikenan ashe baki ba cin kaza kuwa,  tunda haka ki kace" dariya suka sake kwashewa da ita, dama duk Abdallah da dadi suka haɗu wuri daya tofa zaka sha dariya , mai aikin dadi ce ta fito daga kitchen wurin su ta nufo tana gaishe da su abie,mom   tace "uwani ashe kina nan, ya kwana biyu"
"Alhmdllh" wace aka kira da uwani tace,  su Aairah ma gaishe da ita suka yi, amsa masu tayi da lafiya lau"an kammala girkin " uwani ta faɗa , aunty Rabi  tace "to shikenan, Aairah ku ɗauki wannan snack's  kuje da shi kitchen sai  ku taya  ta jera abincin  kan dinning" da to suka amsa mata,  tashi suka yi  suka bi bayan ta  , Aaimah  tace "wai Aunty uwani  ina Nuratu ne naga kwana biyu idan muka zo bama ganinta"( diyar Aunty uwani nin ce nuratu) Aunty uwani tace "Nuratu na kauye, an  kusa bikinta ina fatan za ku zo"cike da mamaki su Aairah suka ce "aure fa ki ka ce Aunty Uwani, yanzu nan nuratu harta isa aure"Aunty uwani tace
"eh mana,  duk sa'annin ta dake chan duk anyi masu aure har ma wanda basu kai taba ana masu aure, dan dai kawai ku kuna birni ne shiyyasa ku ke ganin kamar bata isa ba" Aairah tace " to Allah ya nuna mana lokacin, In sha Allah kuwa zamu je" haka suka ciga da fira Aunty Uwani na basu labarin ƙauye su kuma suna mamaki har suka kammala jera abincin kan dinning,sallar magrib da aka kira ne yasa su abie nufar masallaci shi da abdallah   Mom ɗakin  Aunty Rabi ta nufa domin gabatar da sallah , su Aairah kuwa ɗakin  Dadi suka nufa domin yin  tasu sallar, sun riga su mom dawowa parlor su da Dadi,suna ta zuba mata surutu su abie su ka shigo hara da uncle mustafa ( kannin abie wanda ke bi masa,  su biyar ne ɗiyan  dadi  abie shine na farko sai uncle mustafa daga nan sai aunty Rabi sai  uncle Ahmad sai Aunty Asma'u itace yar autar su, da Uncle mustafa ne ka ɗai  ke  katsina, kafin Abie ya dawo nan  shi kuma uncle Ahmad har yanzu  yana abuja sai Aunty Asma'u dake aure kano, Aunty Rabi kafin Allah yayi ma mijinta rasuwa  barno take Aure time din   .)  bakin su dauke da sallama suka shigo,amsa masu sallamar su kayi yayin da su Aaimah ke cewa  "uncle ina wuni"
amsa masu yayi cikin kulawa yana cewa "ya school naji yaya yace kun kammala, to Allah ya tai maka yasa a samu sakamako mai kyau" da ameen suka amsa mashi,dadi tace "yawwa mustafa naji daÉ—in zuwan ka, kamar kasan ina son ganinka kai da Mahammad "
abie yace "to fa mama Allah yasa lafiya "
"lafiya lau,maganar dai da na saba ce,  mu shiga daga ciki" da to suka amsa haɗi da miƙewa suka bi bayan dadi, bedroom ɗin ta suka shiga, wuri suka samu bakin gado suka zauna, kallon su dadi tayi sannan tace"a kullum bazan gaji da maku maganar ɗan  ƴar uwata ba, ba shi da wata a duniyar nan da zai  kalla a matsayin uwa a gare shi bayan ni , ban san wane hali yake  ciki ba, ƴar uwata zata ce ban riƙe alƙawari ba " uncle mustafa yace
"kiyi haƙuri mama,in sha Allah zamu nemo shi a duk idan yake a faɗin duniyar nan"
"mustafa kullum haka kuke cewa, amma har yau baku nemo man shi  ba, kullum sai nayi mafarkin shi yana cikin damuwa, yana buƙatar taimako na" abie yace "ki ƙara haƙuri mama, in sha Allah za'a gan shi, zanje har garin ku, nasan baza'a rasa wanda yasan inda ya koma  da zama ba"
"to shikenan Muhammad, zan zuba ido har lokacin da Allah zai bayyanar da shi" da ameen suka amsa, dadi tace "ku tashi ku koma parlor kuci abinci" to mama suka faɗa haɗi da miƙewa suka nufi parlor, a dinning suka samu su mom, wuri suka samu suma suka zauna,aunty rabi tayi sarving ɗin su , sai wurin karfe 9 da kusan minti 50 sannan suka bar gidan harda uncle mustafa su ka nufi gida,  suna isa gida, baaba larai ta fito tayi masu sannu da zuwa,  kowa ɗakin  sa ya nufa, snacks ɗin da suka zo dashi baaba larai ta kai kitchen ckin fridge bayan ta ɗauki wanda zataci, ɗakinta ta nufa ta kwanta ita ma.
Episode 14_15

WASHE GARI

Tunda suka yi sallar asuba basu koma bacci ba saboda ɗokin zuwa wurin ƙunshi da gyaran kai da za suje, ko da gari yayi haske wanka kawai suka yi suka shirya  sannan suka nufi ɗakin Mom, koda suka shiga basu sameta ba kitchen  suka wuce anan suka same ta ita da baaba larai su na shirya breakfast gaishe da su su kayi, Mom tace"wai ba dai har kunshirya ba"
"munshirya ,tafiya ma za muyi" suka bata amsa
Mom tace"to sai ku bari  kuyi breakfast tukunnan"
Aairah tace "ba fa direct saloon din zamu wuce ba, sai fa munje gidan Aunty Safiya tare da Najma zamu tafi"
"duk da haka dai kujira kuyi breakfast sannan" mom ta faɗa,  da to suka amsa mata,  dole su ka tsaya sai da suka yi breakfast ɗin sannan mudi ya kaisu gidan  ya dawo, basu wani jima ba  saboda ko da su ka je Najma harta shirya su kawai take jira, basu wani bata time ba mus'af  ya kaisu shagon saloon ɗin  da zasu je, wurin ya haɗu babu wani nau in gyaran jiki da basa yi, kama daga wankin kai har izuwa kunshi da gyaran ƙafa......

Wannan Kenan

✨Ammy_Fatima _Noraiz ✨

Zaune suke kan dinning suna breakfast, shazim  ya shigo jikin sa sanye da jogging suit white color,sai p_cap black color ,  wurin su Ammy ya nufo yana faɗin "ina kwana Ammy"
da lafiya lau  Ammy ta amsa mashi "Ammy ai da kun bari na dawo sai muyi breakfast ɗin tare"
"kai da shigowar ka ba yanzu ba, waye zai tsaya jiranka"
"amma Ammy ba gashi nashigo da wuri ba"
"yau koh" Ammy ta faÉ—a
Noraiz ne ya ce  "yaya da ƙarfe nawa zaka je abnoor  yau"
"yau bazan jeba"
"amma yaya saboda mi"
"haka nan, zamu je wani wuri ne shiyyasa, idan kun kammala breakfast  ɗin,  Ammy ku shirya" Fatima  tace "wannan wane bazata ne  haka yay "
Ammy ma cewa tayi "ina zaka kaimu" murmushi yayi haÉ—i da cewa "surprise ne, ku dai kawai ku shirya"
daɗi  suka ji saboda  sun san wani abun mamakin ne yake son yi masu bazata dashi, saboda shi idan ya so fa akwai wasa da dariya,  in kuwa baiso ba tofa zaka same shi kadaran kada ham, duk da daman akwai kyakyawar alaƙa tsakanin sa da ahlinsa, wani lokacin in yana tare da su zaka same shi kamar bashi ba,cigaba su kayi da breakfast, shi kuma part ɗinsa ya nufa domin watsa ruwa sannan ya dawo yayi breakfast , san da ya kammala nasa breakfast din dukan su sun shirya shima komawa yayi part dinsa ya shirya cikin wani haɗaɗen yadi wanda yasha ɗinkin  zama ni wurin su ya dawo,  Ammy  ce tace  "kai Masha Allah  ba ƙaramin  kyua kayi ba"
"nagode sosai ammy" gaba yayi yana faɗin "to ku taso mu tafi" tashi su kayi su ka bi bayan shi zuwa  compound din gdn, anan suka samu motar da zasu fita da ita ilya ya gama gyara ta ya fito da ita compound  , nufar motar suka yi, shi ya shiga ma zaunin driver ya yin da Noraiz ke kusa da shi Ammy da fatima kuwa baya suka shiga,  reverse yayi ya nufi gate,  a dawo lafiya su ilya suka shiga yi masu, driving yake , su  Ammy sun zuba ido ne suga shin ina kuma zai kai su, wani katafaren shopping mall na ji da faɗa  ya nufa dasu,sabon mall ne daga gani ba'a jima da fara aiki a cikin sa ba,  parking yayi a parking lot ɗin wuri sannan yace "Ammy ku fito, mushiga ciki " to kawai Ammy tace sannan suka fito,sai da suka fito su duka sannan yace "kowa ya kalli sama" kamar yan da yace haka suka  ɗaga kansu suna kallon saman shopping mall, in da aka rubuta (WHITE HOUSE SHOPPING MALL) da man yan baƙi ammy sauke kanta tayi tana kallon shazim cike da  alamar tambaya, ganin kallon da ammy keyi masa yasa shi yin murmushi yana faɗin "surprise "  cike da mamaki ammy tace "wai ni kam ina zaka kai son kuɗi ne shazim"matsowa yayi kusa da ita haɗi da dafa kafaɗar ta yace"ammy ina da ku idan ban nemi kuɗi ba mizan yi"
"haba shazim business nawa kake "
"Ammy koma nawa nake, wannan ba wani abu bane, ki sa mashi albarka kawai"
"to Allah yasa albarka ya ba da sa'a "da ameen suka amsa su duka, shazim yace "Mu shiga ciki"  ciki suka shiga ya na gaba suna binshi a baya,wani matashin saurayi ne da a ƙalla zai yi kimanin shekaru 27 a duniya ya nufo su, gaishe da ammy yayi da shazim,gaishe da shi  noraiz da fatima su kayi, da fara'a a fuskar shi ya amsa masu, shazim yace "ya aikin hameed?"
"Alhmdllh, komai na tafiya dai dai"
"masha Allah,muje ina son nu na ma su ammy ko wane part"
"ok to shikenan "ciki su ka wuce, wura re ya shiga nuna masu shi da hameed , sai da ya kaisu ko ina a cikin mall ɗin sannan suka ya da zango a office ɗin shi, hameed kuma ya koma wurin ma'aikata ,office ɗin ya haɗu sosai kamar ba office ba, ammy na kan sofa   su fatima na ƙasa kan carpet, shi kuma yana zaune kan swivel chair,ammy ta ce"shazim wuri yayi kyau Allah ya taimaka "
"ameen Ammy"  
ammy tace "yanzu wa zai kula da nan? "
"a kwai wani ƙanin hameed shi  zai kula da nan, hameed kuma noraiz sai su  cigaba da kula da wan can business ɗin amma za su riƙa kawo mashi ziyar dan su tabbatar da komai na tafiya" 
"to shikenan, hakan yayi kyau"
sun jima a office ɗin sai da rana tayi sanyi suka fito,yace su shiga ciki  kowa ya zabi abun da yake so,
da sauri fatima ta  jawo masu cart, suka shiga jidar abun da ransu ke so musamman Fatima da Noraiz, Ammy kuwa shazim ke tura mata nata cart din tana daukar abun da take so, sai da kowa ya dauki abun da yake so,  ma'aikanta wurin suka kwashe kayan suka zuba  masu a booth, sallama suka yi ma su,har parking lot hameed ya raka su,( bayan aikin asibiti shazim yana business sosai tun kafin ya fara aiki da buɗe abnoor yake business, yana sai da motoci wanda hameed ke kula da shi  yana da boutique  da gidan gona sai white house da ya buɗe yanzu, amma ba shi ke kula da su ba akwai masu kula mashida su ) mai makon ya kaisu gida wata hanyar ya kuma sake ɗauka , in da ake sai da  laptop's  ya nufa dasu yana parking suka fito shi da noraiz , su ka shiga ciki, noraiz ya zaɓar ma fatima laptop mai kyan gaske,kuɗi ya biya  suka fito zuwa mota, daga nan wuren bu ɗe ido yai ta kaisu, Ammy ba ƙaramin  dadi tajiba saboda rabon ta da ta shiga gari da sunan miƙe ƙafa har ta manta, sai da yamma likis sannan suka koma gida, godiya suka shiga yi mashi, shi kuma yana cewa dan Allah su bari mana,wannan ai wajibi ne a gare sa daya yi masu fiye ma da haka
Ammy tace "duk da haka shazim, bakaji mi hausawa suka ce ba?, yaba kyauta tukwici, tunda bamu da tukwicin da zamu baka shine muke godiya"
"to shikenan" kawai ya iya cewa , ilya ne da mai bama flowers ruwa suka shigo da kayan da suka zo dasu, su kuma kowa daki ya nufa domin watsa ruwa ,Fatima na shiga ɗaki wayanta dake ringing cikin bag ta ciro,ya dr ne ke kira, katsewa kiran yayi zata kira sai kuma wani kiran ya sake shigowa,picking tayi haɗi da sallama amsa mata sallamar yayi yana cewa"yar ƙanwata ya kike ya gida ya su Ammy? "
"lafiya lau Yaya"
"masha Allah,  ina gaishe da su sosai"
"zasuji Insha Allah "
"miye labari "
"ai ni yaya fushi nake da kai, "
"to fah, kaina bisa wuya ni kuwa mi na ai kata"
"wai ace nayi graduation, Amma yaya ko irin text dinnan na congratulations ban samu daga gareka ba kai da ya mansoor "
"Allah sarki fatima, kiyi hakuri kin ji, so naima ace nazo har Lagos din, amma kuma wasu yan abu bu wa ne suka sha kaina, amma kiyi haƙuri  kinji"
"shikenan yaya bakomi, dama yanzu baka wani ji dani,"
"kai , ya za ki ce haka "
"haka ne mana, yau she rabonka da zuwa Lagos, tun kuna mutunci da ya shazim sosai "
murmushi yayi mai sauti yana cewa"waya ce maki bama mutunci sosai yanzu"
"to baga shi nan ba yanzu baka son zuwa Lagos "
Fatima kenan, ya fada a zuciyar shi  , a zahiri kuwa cewa yayi"fatima yana yin aiki ne kawai ba wani abu ba, amma In sha Allah ina nan zuwa Lagos very soon "
"to Allah ya kaimu ya nuna mana lokacin" da ameen ya amsa fira suka shiga yi daga bisani suka yi sallama, ya mansoor ta kira shima tayi mashi ciwan baki rashin kiranta da baiyi ba, haƙuri ya shiga bata, sun jima suna waya,  
a chan parlor kuwa Ammy ce ta fito daga ɗakin  ta, Innah asabe ta samu a kitchen tana jera kayan da suka siyo, gaishe da Ammy tayi, amsa mata Ammy tayi cikin kulawa,  Inna asabe tace "mi za'a dafa yau da daddare "
"A'a ba sai an dafa komai ba munyi takeaway da muka fita"
"to shikenan "kawai Inna Asabe tace, gyara kitchen din kawai suka yi.....

✨Victoria✨

"destiny wai  kina ganin abun da  gurutu ya bamu yana aiki kuwa, kusan fa wata daya kenan bawani chanji"
Destiny tace"karki damu na yarda da Gurutu, mukara lokaci kawai, idan ma muka ji shiru mu sake Komawa kawai"
"gaskiya  abun da za'ayi kenan gara kawai mu koma"
destiny tace "to shikenan amma mu ƙara lokaci mugani"
 
✨Hidaya✨

Zaune take bakin gado wayar ta dake gefan ta ce ta fara ringing picking tayi hadi da  manna   wayar a kunne tana fadin "hello maryam ya ki ke ya gida"on the other hand maryam tace"lafiya lau hidaya"
hidaya tace  "Masha Allah"
"mi ki ke yine haka naji kamar muryar ki tayi ƙasa? " maryam ta tambaya, amsa hidaya ta bata da "lafiya lau, kawai dai ina kwance ne"
Maryam tace"ok to yayi, ya labari  doctor kinsan kwana biyu ban shigo hospital ba, ina dai fatan kin fada masa abun dake ranki"
sauke ajiyar zuciya hidaya tayi, sannan tace"ina fa maryam,wallahi da na gansa rasa duk wani kwarin gwiwata nake, sai kawai naji na kasa faɗa masa"
Maryam tace"gaskiya hidaya kina da aiki, yanzu faÉ—a masan ne yake baki wahala"
"hmm maryam kenan dan dai kawai ba ke bace a matsayi na ba ne shiyyasa"
"ba haka bane hidaya, daurewa kawai za kiyi ki faɗa masa" 
"to shikenan maryam zanyi ƙoƙari naga na fada masa nagode sosai"
"bakomi idan ma kin kasa sai mu nemi number shi, kota waya ne sai ki fada masa, fata na kawai shine ya amince dake amatsayin abokiyr rayuwa, in ga ta tsiyar su destiny da Victoria "
"to Allah yasa ya soni koda bai kai wanda nake masa ba" hidaya ta fada
"to ameen sister,  ki cigaba  da adu'a In sha Allah dr naki ne ke kaɗai"
"to Allah yasa" 
da ameen maryam ta amsa mata sun dan jima suna wayar daga bisani suka yi sallama...

✨Aairah_Aaimah✨

Ana kammala masu saloon din da kunshi  mus'af   yazo  ɗaukar  su " kai masha Allah sweetie, irin wannan kyau haka kin kuwa ga yanda kunshi nan yayi kyau?"
"nagode sosai" Aairah ta fada
Aaimah ce tace
"da yake ya mus'af Aairah kaɗai ka sani  shiyyasa kace nata yayi kyau mu ko ka kalli namu, abun yar wariyar launin fata ce"
"No Aaimah ba haka bane, na qalbie ne ya É—auke man hankali, amma kuma naku yayi kyau sosai"cewa Aaimah tayi
"shikenan ya mus'af bakomi"
"mu tafi koh"mus'af ya faÉ—a nufar motar su ka yi, Aairah ta shiga gaba,sai Aaimah da najma a baya,
gidan su Aairah ya nufa dasu,  parking yayi a compound , su Aairah suka fita , masu decoration suka samu a compound suna decorating,  main entrance din gidan suka nufa,   koda suka shiga ciki baaba larai da Mom da Aunty rabi suka samu a parlorn, suna aikin zuba souvenirs cikin jakunkuna masu dauke da sunan Aairah da Aaimah, shiga suka yi parlorn bakin su ɗauke da sallama, amsa masu sallamar su  Mom su ka yi, da gudu su Aairah suka nufi Aunty rabi, suna fadin "oyoyo Aunty, ashe kin zo"
Aunty rabi tace "na zo Mom É—inku ke faÉ—a man kuna wurin salloon, buÉ—e mugani " ta faÉ—a tana cire hular dake kan Aairah
kai masha Allah, gaskiya yayi kyau"
"na gode sosai Aunty" Aairah ta fada, Aaimah cewa tayi" to ni bari na tashi,  tun da na lura Aunty ba tani ki ke ba ta Aairah kike"
Aunty rabi tace "sorry Aaimah,  ke ma ina ta ke, mu ga naki kema" mom ce tace "to tunda abun  ƴar wariyar launin fata ce ,matso kinji ƴata naga naki harda ƙunshin" ta faɗa tana miƙama najmah hannun,   da sauri najmah ta ƙarasa wurin Mom, nan tashiga nuna mata,sallama mus'af yayi,gaba ɗaya su ka kai duban su gare shi
Mom ce tace "wai dama mus'af tare kuke?"
"eh"  yaba  Mom amsa, gai sawa su kayi har da su Aunty Rabi da baaba larai , mus'af bai wani jima ba yayi masu sallama ya wuce gida, shi ka ɗai ya tafi, a  nan Najma zata kwana.
zama su kayi nan parlor suna taya su mom aikin da suke, har suka kammala sannan suka wuce daki, wanka ko wace cikin su tayi da  sallah  magrib wacce ake kira, basu fita daga daki ba sai da suka yi har sallar isha sannan suka fice daga dakin suka nufi parlor , yanzu ma mom da Aunty Rabi suka samu a parlorn, zama suka yi sai ga abie da ya abdallah  sun shigo.

✨Lagos✨

Ammy da Fatima ne zaune a parlor bayan sun yi sallar magrib da isha suka dawo parlor  suna duba kayayya kin da suka yi shopping, fatima tace "wallahi kayan nan sunyi kyau sosai Ammy "
Ammy ta ce"ai kuwa  sunyi kyau sosai"
Fatima tace" amma Ammy yaushe yaya yace zamu tafi abuja,amma dai cikin wannan week É—in ko"
"to sai dai Idan ya dawo in tambaye shi, dan gaskiya ni bai faÉ—a min yaushe zaku tafi ba, duk da munyi magana yace next week amma ban ga yana wani shiri na alamar tafiyar ba "
"ok to shikenan Ammy" nan suka shiga duba kayan suna yaba kyan su, 
Noraiz  ya shigo  bakinsa ɗauke da sallama, amsa mashi sallamar su kayi,  Ammy na ce wa "ina ka baro Yayan naka"
Amsa Noraiz yaba ma Ammy da
"tare muke dashi, yana compound yana amsa  waya" 
Ko rufe baki noraiz bai yiba shazim ya shigo, shima wurin su Ammy ya nufo, gaishe da Ammy yayi ,  ya nemi wuri kusa da Ammy kan sofa ya zauna, Ammy ce tace "ga  abinci, kan dinning"
"to" kawi yace,dinning din suka nufa,suna kammala dinner din, fatima ta gyara wurin,su kuma kan sofa suka koma, Ammy na tambayar  shazim yaushe zasu tafi abuja
"gaskiya ina tunanin sai upper week,zanje jos wani hospital ne suke son ganina next week" 
"amma shazim naso ku tafi next week, jiya sai da Ibrahim ya kirani shi da innah nace masu kuna nan tafe next week, yan zu idan suka kira nace kun fasa gani za su yi kamar ni ke hana ku je" 
shazim yace "to ammy suyi haƙuri na dawo mana kiran emergency ne, patient sun fi su buƙatar gani na" 
"shikenan Allah ya kaimu upper week É—in" da ameen suka amsa su duka, fira suka dan taba sannan kowa ya nufi É—akin sa domin bacci......

✨katsina ✨

Kwance suke kan bed
ko waccen su sanye take da pajamas  ɗinta , Aaimah  da najma  color ɗaya white  sai Aairah dake da pink color , labari kawai suke a kan yanda walimar zata ka sance 
Aairah tace "wallahi harna ƙosa naga gobe tayi"
Aaimah tace "faÉ—i kike anaji, ni baki san yan da nake jiba, Allah dai ya nuna mana goben lpy"
da ameen suka amsa, sun jima suna tattaunawa a kan yanda walimar zata kasance , har bacci yayi awon gaba da su..

WASHE GARI  

Tun da safe suka tashi, shirye shirye kawai suke na walima, har mai makeup Mom ta ɗaukko,  wacce zata yi masu kwaliyya, zuwa  anjima, Idan lokacin walima yayi   , su Mom kuwa suma tun da suka yi sallar asuba suke cikin kitchen ita da Aunty Rabi da baaba larai, suna ida shirya abubuwan da basu gama shiryawa ba jiya.
a chan compound kuwa yasha decoration, mai kyan gaske.
wurin karfe biyu na rana gidan ya fara cika da mutane, saboda bayan la'asar za'a gabatar da walimar , har gida ya Abdallah  ya je ya dauko Dadi, sai Aunty safiyya wace mus'af ya kawo,yan uwan abie ba wanda baizo ba da ƴaƴen su , sai wasu daga cikin ƙawayen Mom , hakama ƙawayen su Aairah na islamiya da boko duk sun zo, sai abokan abie dake nan katsina ba laifi suma sun zo , gida dai ya ciki Alhmdllh.....
  
       ✨Ammy ✨

Zaune take kan sallaya tana adu'a,
wayar ta dake bedside drawer ce ta fara ringing, miƙa hannun ta tayi ta ɗauki wayar  haɗi da yin picking  bakin ta  ɗauke da sallama on the other hand cikin wayar muryar wata dattijuwar mace ce tace "wa'alaikumu salam" ammy ta ce "ina wuni innah " amsa ma ammy tayi da "lafiya" ammy tace "innah yasu alhaji ahmad  da su  hajiya turai"  da katar da ammy matar yi da faɗin "dakata aisha bawai na kira ki bane dan kiyi taman tambayoyi, na kira ne kan maganar da muka yi da ke, naga yau kusan wata kenan amma bangan su sun zo ba" ammy ta ce "dan Allah innah kiyi haƙuri, ko jiya  da daddare  munyi maganar da shazim akan zowan naso,to shine yake sanar man anyi mashi kiran gaggawa jos baza su samu zuwa ba sai sati na sama" katse ammy tayi da faɗin "dan Allah dakata man aisha, kina nufin sai abun da shazim yace kenan, ko mi kike nufi"ammy ta ce "ba haka nake nufi ba innah" on the other hand "to mi kike nu, tun yau she muke magana sai dai kice man ranar kaza za su zo amma kuma basu zo sai anyi magana ki kawo ma mutune wani uziri" shiru ammy tayi tana sauraran ta, da kaga fuskar ammy kasan cike take da damuwa "to bari kiji in gaya maki, ba ku isa ba daga ke har wannan mara kunyar, zumunci ne Allah ya riga da ya haɗa kuma dole ne ayi shi, bar ganin nayi shiru na barmaki yaran a hannun ki bawai hakan na nufin bazan iya ƙwatar su daga hannunki ba ne, saboda yara basu da wasu dangi a duniya bayan mu ɗinnan dai da kika gama rainawa ki ka sa ƴaƴanki suke ganin kamar bamu da amfani" sosai matar ta rufe ammy da masifa ammy na bata haƙuri tana gama faɗar abun da zata faɗa ko jiran mi ammy zata ce bata yiba ta kashe wayar, shiru ammy tayi ta ƙura ma wayar ido, chan kuma ta ɗaga hannun ta sama tana adu'a wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, gefen hijabin ta ta sa ta goge tana faɗin "Allah sarki yaya,Allah ya jiƙan ka ya haskaka kabarin ka " na ce ameen ammy, tashi tayi daga kan sallayar ta linke ta ta saka cikin wardrobe da hijabin da tayi sallah fita tayi daga ɗakin, fatima ta samu zaune kan sofa tana ta latsa sabuwar  laptop ɗinta wacce shazim ya saya mata, ɗago da kanta tayi tana faɗin"barka da fitowa ammy" da yawwa ammy ta amsa mata haɗi da neman wurin zama ta zauna, fuskarta da tsantsar damuwa, lura da hakan yasa fatima cewa"lafiya dai ammy,kamar kina cikin damuwa?" ce mata ammy tayi "bakomai Fatima,mi ki ka gani"
"naga duk kinyi wani iri ne ammy" amsa ammy ta bata da "gajiya ce"
"to ammy ai da kin kwanta kin É—anyi bacci kafin la'asar tayi"
to shine kawai a bunda ammy ta ce mata.....

✨KATSINA✨

bayan sallar asr ɗakin su Aairah a ciki yake da ƙawayen su na boko da islamiya,mai makeup ta fara tsara ma Aairah makeup mai kyan gaske, wayar Aairah ce ta fara ringing,cema Aaimah tayi ta duba mata taga wake kira , Amsa ta bata da alaramma ne ( malamin su na Islamiyya ) tana picking bakinta ɗauke da sallama, bana jin mi na cikin wayar yake faɗa,"to shikenan malam" shi ne kawai abunda Aaimah tace sannan tayi rejecting tana ce ma Aairah "ya ce sun ƙaraso,su na waje"
"to Please ki fita ke da Aeesha ku shigo da su,ko ki faÉ—ama abie sai ayi ma su iso l"
"bari dai na faÉ—ama abie É—in kawai,dan na san babu hanyar wuce wa"
Aairah tace "to shikenan faÉ—a ma abie É—in kawai"
dialing number abie Aaimah tayi, picking abie yayi yana cewa "lafiya Aairah , kun gama shiryawa ne?"
"Aaimah ce abie "
"Ok kun gama ne?"
"A'a abie dama su alaramma ne su ka iso"
Abie ya ce "to bari na sa abdallah  ya shigo da su,  amma fa ku yi sauri bana son lokaci ya ƙure"
"to abie in sha Allah mun kusa"
"to shikenan" abie ya faÉ—a haÉ—i da yin rejecting call din
"sis mi abie É—in ya ce?" Aairah ta faÉ—a
"gashi can zai sa ya Abdallah  ya shigo da su"
"to kira su ki ce ga ya Abdallah  nan fitowa"
kiran su Aaimah tayi ta faɗa masu,  sannan ta  ajiye wayar, ana kammala ma Aairah ita ma aka  yi mata bayan an gama mata aka yima najma, sai friend din su Aeesha, sosai su ka yi kyau kamar ka sace su ka gudu mu samman ma  su Aairah, baƙaramin kyau su ka yi ba, shiryawa su kayi cikin wata atamfa super ɗinkin riga da skirt, sosai ɗinkin ya amshi jikin su ba ƙaramin kyau atamfar tayima fatar su ba,farar alkyabba su ka ɗaura saman atamfar, faɗin kyan da alkyabbar tayi masu ɓata lokaci ne, kamar wasu ɗiyan sarakai, mom ce ta shigo ɗakin sanye take da wani  haɗaɗɗen lace ɗinkin doguwar riga,wuyan ta da kunnan ta da hannu sun sha ado"kai masha Allah,kuce kun shirya,amma kunyi kyau sosai,kamar zan kai ku gidan miji"
dariya friend ɗin su da ke ɗakin suka yi suna faɗin"mom ai wannan ranar sai sun fi haka ba da kala" su dai su Aaimah ban da murmushi babu abun da suke mom ta sake cewa "to ku zo ku fita ku kaɗai ake jira " da to suka amsa mata, fice wa mom tayi daga ɗakin, suma tashi su ka yi su da friend ɗin su su ka fice can compound, suna gaba friend ɗin nasu na baya,maƙil su ka iske compoud ɗin da mutane, wurin da aka tana da domin su suka nufa suka zauna,ba ɓata lokaci aka shiga gabatar da walima, alaramma yayi wa'azi, sannan su Aaimah suka yi karatu, sosai walimar tayi kyau ta kuma ba da ma'ana, su Aairah ba ƙaramin burge mutane su ka yi ba, sun kuwa sumu kyaututtuka daga islamiyyar su, haka ma abie, mom, ya abdallah , dadi, granny, papi,aunty safiya,  ƙannan abie duk sun basu kyauta,  sosai su ka tara kyaututtuka daga wurare daban daban, su aunty rabi da aunty safiya su ka yi rabon souvenirs, sai wurin karfe 6:40 ana shirin kiran sallar magrib sannan aka tashi, kowa ya tafi yana yaba hazaƙa irin ta su Aairah da kuma ganin nagartar islamiyar su. 
Episode  16_17

Aaimah zaune take saman sallaya bata jima da kammala sallah isha ba Najma ta shigo hannunta ɗauke da wani madaidaicin kwali,kallonta Aaimah tayi tana faɗin"ke kuma daga ina haka da wannan ƙaton kwalin" amsa najma ta bata da"saƙwan Aairah ne inji ya mus'af " ta faɗa yayin da take ajiye kwalin kan bed,  ta sowa Aaimah tayi daga kan sallayar tana faɗin "ya mus'af dai, mu gani" buɗe kwali suka shiga yi, fitowar Aairah kenan daga bathroom jikinta ɗaure da towel,tsayawa tayi tana kallon najma da Aaimah dake kokuwar buɗe kwali, kayan da ke cikin kwalin suka shiga fitowa,qur'an ne da carpet sai counter da watch na mata haɗe da turare.
kwalin turaren su Aaimah suka buɗe suna ta fesa ma jikin su suna faɗin "ah lallai ya mus'af abun yar wariyar launin fata ce, to bari muji kalar ƙamshin turaren" ita dai Aairah ban da bin su da idanu babu abun da take, dan kwata kwata bata fahimci mi su ke nufi ba, barin bakin ƙofar bathroom ɗin tayi ta nufi dressing mirror tana faɗin "wai ku lafiyar ku ƙalau kuwa, dare ne amma sai wani fesa ture ku ke baji ba gani, wai ma ina ku ka same shi ne" najma ce tace "naki ne inji ya mus'af, tun da mu bazai bamu ba shi ne muke fesawa" tasowa Aairah tayi daga gaban dressing mirror ɗin tana faɗin "kuji tsoron Allah, shine kawai za kuyita fesawa koma ku faɗa man" Aaimah ce tace "to yanzu an faɗa maki shikenan ko" kayan Aairah ta shiga dubawa tana faɗin "kai amma nagode sosai ya mus'af, Allah ya bar ƙauna"da ameen su najma suka amsa, tashi Aairah tayi ta shirya cikin pajamas ɗin ta sannan suka shiga buɗe sauran kyaututtukan da su ka samu, sai da suka gama harma sun kwanta sannan ta ɗauki wayarta ta kira mus'af, sunjima sosai suna waya har su najma suka yi bacci, itama suna gama wayar bacci ta kwanta.

✨lagos✨

Fatima da ammy ne a kan dinning suna dinner, fatima ce kawai ke cin abincin dan ammy bata wani ci sosai ba ta tashi tana faÉ—in "ni zan shiga ciki, idan yan uwanki sun shigo kice masu na kwanta sai da safe" fatima ce tace "to ammy,amma lafiya naga kin tashi ba tare da kinci komai ba?"
"naƙoshi ne fatima, sai da safe "ammy ta faɗa, bedroom ɗin ta ta nufa, binta kawai da kallo fatima tayi, aranta tana faɗin "ko mike damun ammy ne yau"shiru tayi dan bata da mai bata amsar tambayar ta, ammy bata jima da tashi ba shazim su ka shigo shi da  noraiz bakin su ɗauke da sallama, amsa ma su sallamar fatima tayi, dinning ɗin suka nufo , warmars ɗin da ke kan dinning noraiz ya shiga buɗewa yana faɗin "mi aka dafa ne autar ammy " girgiza kai Shazim yayi yana faɗin "ina ammy ne, na ganki ke ka ɗai? "
"ta shiga É—aki "
"lafiya dai koh? "fatima ta ce "gaskiya yaya da sauƙi dai". shazim ya ce  "mi kuma ya same ta yanzu"
"wallahi yaya har yanzu mood ɗin ta sai ahankali kuma na ƙara tambayar ta mike da munta, sai cewa tayi wai lafiya lau, kuma fa yanzun ma bata ci komai ba wai ta ƙoshi" ɗan shiru Shazim yayi kamar me nazari can kuma sai ya ce "ok shikenan sai da safen ku " ya wuce part ɗin sa, noraiz yace "nifa ina tunanin wani abu ke damun ammy wanda bata son faɗa mana ba" fatima ta ce" abun da nake tunani ke nan ya noor "sun ɗan jima suna tattaunawa a kan  canzawar mahaifiyar su, sannan suma suka tashi suka nemi wurin kwanciya su....

WASHE GARI...

Ammy  na kan sofa a parlor, Shazim ya shigo da ga motsa jiki, wirin da ammy ta ke ya ƙara so, gaishe da ita yayi, amsa mashi tayi cikin kulawa, tashi yayi da nufin barin parlor tayi saurin ce mashi
"ina za ka je? "
"zanje ne na shirin tafiya yau zan tafi jos "
"ok ashe yau  zaka tafi?"
"eh ammy" ya bata amsa, ammy ce ta sake magana tana faɗin "to dawo,ina son magana da kai" to kawai yace haɗi da dawowa ya samu wuri ya zauna,magana ta fara "wai ni kam shazim mi ke da munka ne kai da ƙannan ka?"
É—ago da kansa yayi yana faÉ—in "bakomai ammy, mi ya faru? "
"ba komai,nayi maku maganar zuwa abuja amma babu wanda ya sake ce man komai akan tafiyar, Noraiz  ma da na tambayeta shi  ceman yayi ya manta" ajiyar zuciya Shazim ya sauke sannan yace "ba komai ammy, ni aiki ne yasha kaina shiyyasa" ammy tace "to yanzu bangane mi ka ke nufi ba?"
"ammy ina ganin sai dai kawai fatima da noraiz su tafi, tun da  ni jos zan tafi kuma na faɗa maki,da ace zan iya zuwa a ranar na dawo to da kawai sai na kai su ni sai na dawo" wani kallo ammy ta bishi da shi har ya gama faɗan abun da zai faɗa sannan ta ce "yanzu dai mi ka ke nufi ba zaka je ba, ban ga ne ba ko kuma dai wani abun ka ke nufi??? "
"A'a ammy da na dawo zanje in sha Allah " ammy ta ce "maganar  sai ka dawo jos   ma bata taso ba, yanda su fatima zasu je haka kaima za ka je,kai ka ɗai ne likita da baza su ne mi wani ba,in kuma maganar aikin ka ka ke nasan kafin kaje ka dawo majeed zai ji da komai na abnoor  har ka dawo, in kuma eko  ne da ka ɗauki permission nasan zasu baka, kuma duk abund a ya kamata ace kayi ai kabir na nan" kallon ammy kawai shazim yake, dan shifa har zuciyar shi baya son wannan tafiyar, shiyyasa ma ya kawo mata excuse ɗin zuwa jos  dan kawai ta cire shi a cikin masu tafiyar, amma daga ganin yanda take magana yama san ba lallai ta barshi ba, katse mashi tunanin da yake tayi tana cewa "sai wani kallona ka ke kana tunani, tafiya ce dai dole ka yita shazim" ajiyar zuciya ya saukewa a karo na biyu yana faɗin "ammy bawai bana son zuwa bane,a kullum ke ki ke faɗaman ka taimaki mai ne man tai mako da gwargwadan abun da Allah ya hure maka, ammy yau ke ki ke cewa su ne mi wani, dan Allah ki bari naje in dai abuja ne zanje idan ma ki ka ce na wuce daga jos ɗin sai na wuce amma dan Allah karki hanani yin wannan taimakon"
"babu  wani excuse fa da zaka kawo man, nariga da nagama magana, garama kawai kayi shiru dan bazan saurari excuse ɗin ka ba"
"shikenan ammy kwana nawa ki ke so muyi"
"sati biyu nake son kuyi kafin ku dawo" É—ago kai yayi da sauri yana kallon ammy jin abun da tace "haba ammy ina laifin kwana biyar"
"sati biyu za ku yi kaji na faÉ—a maka"
"dan Allah ammy kiyi haƙuri, ki maida shi kwana biyar"
"to naji sai dai kai kayi biyar É—in, ammy fatima da noraiz sai sunyi sati biyu cif sannan su dawo" ajiyar zuciya ya É—an sauke yana faÉ—in "ammy ina dai laifin ita fatima tayi sati biyun"
"bangane ba shifa noraiz mi zai sa ba zaiyi sati biyun ba?"
"Ammy kinga nace shi zai cigaba da kula da business É—ina,kinga bai kamata ace yayi sati biyu ba"
"ban amince ba to, ina masu kula da business É—in time É—in da yake makaranta"
"suna nan ammy"
"to su cigaba da kula da shi kafin ya dawo"miƙewa shazim yayi yana faɗin "to shikenan ammy, nizan shiga na shirya time yana ƙurewa" da to ammy ta bisa har zai wuce, tace "idan kaje jos ɗin kwana nawa za kayi?" murmushi yayi dama  ya san bazata taɓa hana shi taimako ba,ba tare da ya juyo ba yace  "dama kwana biyar zanyi, amma tun da kince ba sai naje ba zan tura majeed yaje kawai"
"to na fasa kaje ka dawo sai ku tafi" murmushi yayi yana cewa
"A'a ammy ki bari kawai majeed É—in yaje"
"kaci gidan ku, nace kaje zaka wani ce man majeed yaje bayan nasan kana son zuwa" murmushi yayi mai É—an sauti yana faÉ—in "to shikenan" yana juyowa ya zo kusa da ita yana faÉ—in "nagode sosai ammy na" dungure mashi kai tayi tana faÉ—in
"ni ka ke ma dariya ko, dan kasan dama bazan taɓa hanaka zuwa ba ko"
"a'a ammy ba da ke nake ba"
"to shikenan, tashi kaje ka shirya kar lokaci ya ƙure" da to ya amsa mata haɗi da miƙewa ya haye sama , fitowa fatima tayi daga bedroom ɗin ammy, wurin da ammy take kan sofa ta zauna tana faɗin "na kammala jera kayan ammy" ammy ta ce "masha Allah, Allah ya biyaki"
"Ameen ammy" fatima ta ce, innah asabe ce ta shigo parlorn gaisawa su ka yi ita da ammy sannan take cewa "hajiya an kammala karin kumallon"
"Masha Allah sannu da ƙoƙari, Allah ya saka "
"Ameen hajiya" innah asabe ta amsa sunan suna ɗan taɓa fira shazim ya sauko shi da noraiz, gaishe da ammy noraiz yayi shi shazim sun gaisa tun ɗazu,sannan suka gaishe da innah asabe, sannan suka tashi suka nufi dinning, shazim da norai basu wani jima ba suka miƙe shazim na ma su ammy ban kwana sai ya dawo,a dawo lafiya suka yi mashi, suna fita parking lot su ka nufa, mota suka shiga noraiz ke driving, suna tafe suna fira har suka kawo airport, sai da jirgin shazim ya ta shi noraiz ya bar airport ɗin ya wuce abnoor wurin majeed, acan ya wuni sai da yamma ya dawo gida.
kamar yanda shazim yace kwananshi biyar ya dawo daga jos, lokacin da ya dawo har ammy tasa fatima ta shirya kayanta.

Wannan kenan.

sanye yake da jeans da t_shirt, a hankali ya ke taka stairs, wurin ammy dake zaune kan sofa ya nufa, gaishe da ita yayi, cikin kulawa ta amsa mashi tana tambayar "yau batare za ku fita da noraiz ba ne?"
"tare zamu fita yana shiryawa ne" ko rufe baki bai yi ba sai ga noraiz É—in ya sauko cikin sauri yana faÉ—in "yaya na shirya, ina kwana ammy"
"lafiya lau" ammy ta amsa, tashi su ka yi su ka fice suna faÉ—in sai mun dawo, adawo lafiya ammy tayi masu,fi cewa su ka yi zuwa parking lot,
wata sabuwar mota dake compound ɗin gidan su ka nufa,shazim na driving yayin da noraiz ke kusa da shi,buɗe masu gate mai gadi yayi su ka fice, 
sai da suka kawo kwanar da zata kaisu eko shazim ya ɗan kalli noraiz yana faɗin "yaushe za ka fara kula da business ɗin?"
"yaya duk lokacin da kace na fara, sai na fara"
"to shikenan, idan nagama kammala tsara komai zanyi maka magana sai ka fara"
"to shikenan yaya, Allah ya kaimu" da ameen shazim ya amsa  yayin da ya ke shiga cikin eko  ɗin, parking lot ya nufa yayi parking, fitowa su ka yi su ka shiga ciki, yana gaba Noraiz  na biye da shi, har zuwa office ɗin shi, key yasa ya buɗe,ciki suka shiga,
sofa noraiz ya nufa ya zauna, shi kuwa Shazim wurin zaman shi ya nufa  ya zauna, ba ɓata lokaci ya fara aiki, nocking ɗin kofar office ɗin aka yi , izini shazim ya bada , hidaya ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, amsa mata sallamar su ka yi, gaishe da su ta yi sannan ta ɗaura da cewa "doctor patient za su iya fara shigowa?" kai kawai shazim ya ɗaga mata alamar eh yayin da ya ke mayar da kansa kan laptop ɗinsa dake gaban sa ya cigaba da aikin da yake yi 
,ok ta ce haÉ—i da ficewa daga office É—in....
  
      KATSINA

Su Aairah ne zaune parlorn mom suna kallo saboda yanzu ba school islamiya sai weekend ( saboda tunda suka gama hadda alaramma ya ware masu azuzuwan yara suna koyar wa su da abokan haddar su) mom ce ta fito daga bedroom É—in ta, ta nufo parlorn tana cewa "kufa yanzu baku da aiki sai zaman gida" Aairah ta ce "mom ai na wani lokaci ne,da mun tafi school shikenan sai mun dawo"
"haka ne kuma" acewar mom Aaimah ce ta ce "mom wai har yanzu abie bai yanke shawarar school ɗin da zamu je ba" mom ta ce "har yanzu gaskiya banji yace komai ba shi da yayan ku, amma ina tunanin bai gama yanke shawarar in da za ku tafi ba " Aairah ta ce"mom dan Allah kisa baki ya bar mu muje wani gari muyi karatun Please" sai da mom ta ɗan nisa tukun tace "gaskiya bazan yi maku wannan alƙawarin ba, saboda ba shi ka ɗai ba nima kaina nafison kuyi karatu ku nan kusa da ni, hankali na sai yafi kwanciya" Aairah kamar za tayi ku ka tace
"haba mom yaza ki ce haka, duk inda muke Allah na nan zai tsare mu da tsarewar sa " kallon su kawai mom tayi amma bata ce komai ba, tasowa su ka yi daga inda su ke suka matso kusa da ita suna dafa ƙafarta suka ce "Please mom" har suna haɗa baki, sauke ajiyar zuciya mom tayi , sannan ta ce "shikenan zanyi mashi magana duk abun da yace bana da ja"
"yawwa mom, Allah yasa ya amince" mom tace "ameen" Aairah ta ce "mom yaushe abie ya ce zai dawo"
"to ya dai ce kwana biyar zai yi" Aaimah ta ce "Allah ya kaimu, ya dawo dashi lafiya"
amsawa su kayi da ameen....

  Lagos....

Hidaya ce zaune a reception ita da maryam suna magana, maryam ce ta ce
"gaskiya ya kamata ace zuwa yanzu komai ya wuce" hidaya ta ce "baza ki gane bane maryam, abun da wahala "
"haba dai hidaya miye abun wahala a ciki" hidaya ta ɗan nisa sannan ta ce"baza ki gane ba ne maryam, wallahi dana ganshi sai na rasa duk wani ƙwarin gwiwar da nake dashi"
Maryam tace "gaskiya daurewa za ki yi, dama ace na samo number sa ne to da ko a waya ne sai ki faÉ—a masa, duk da gaskiya zai fi kyau ace face to face ki ka faÉ—a masa, ko ya ki ka gani "
"haka ne, matsalar bazan iya ba, kuma ina tsoron ya wulaƙanta ni"
Maryam tace "ki cire duk wannan tunanin na cewa wai zai wulaƙanta ki, saboda gaskiya doctor bai yi kama da wanda zai yi hakan ba"
É—an ajiyar zuciya hidaya ta sauke, sannan ta ce "shikenan, amma dan Allah ki samo man number kawai "
Maryam tace "shikenan zanyi ƙoƙarin hakan, amma mi zai hana ke ki tambayi dr kabir nasan ma zai baki"
hidaya ta ce "kai gaskiya bazan iya tambayar shi ba "
"saboda mi baza ki iya tambayar shi ba?" maryam ta faÉ—a tana kallon hidaya "kin san muddin na tambaye shi sai yaji ba'asin mi zanyi da number shi,ba wannan ba ma gaskiya bazan ma iya tambayar shi ba"
"haka ne kuma, amma ga shawara mi zai hana ki rubuta mashi sai ki ajiye mashi a office kan table É—in sa, nasan dole zai gani kuma zai karanta"
"haka ne kuma maryam kin kawo shawara, hakan kawai za'a yi "
"sai kiyi ƙoƙari wurin ganin kin tsara mashi kalamai wanda zasu tafi da imanin shi" maryam ta faɗa tana yar dariya ita ma hidaya dariyar tayi,  wata nurse ce ta nufo wurin su tana faɗin "mi ake tattaunawa ne, naga kuna ta dariya?" juyawa maryam tayi tana kallon wacce tayi magan tana faɗin "sirri ne sister Aisha" gyaɗa kai Aisha tayi  tana faɗin "ah bari na zauna nima ayi da ni" murmushi hidaya tayi, maryam ce tace mata "zauna kuwa kisha sirri" dariya su ka yi su dukan su,fira suka shiga yi akan aikin su,suna nan sai ga victoria da destiny sun fito daga office ɗin da su ke zama, wani kallon banza victoria ta bisu da shi, tsaki maryam taja haɗi da cewa "aikin banza aikin wofi, haka dai zaki ƙare yar wahala kawai" a harzuƙe victoria ta nufo wurin su tana nuna maryam da yatsa tana faɗin "ke maryam kar ki kuskura kice zaki gaya man magana,ki bari sai nayi lokacin ki tukunnan" tashi maryam tayi daga zaunan da take tana kallon victoria tun daga ƙasa har sama, sannan ta ce "idan aka faɗa maki maganar miza kiyi" girgiza kai victoria tayi tana faɗin "wallahi da sai kin gane baki da wayau, dan zan nuna maki cewa ni ba sa'ar yin ki bace " dariya maryam ta kwashe da ita tana ce ma victoria "wallahi  ni har mamaki kike bani wahalalliya kawai" a masife victoria tace "kinga wahalalliya nan bayan ki" ta faɗa tana nuna hidaya dake zaune wacce tayi kamar ma bata san da zaman victoria awurin ba, maryam tace "wallahi kin dai san ko wacece wahalalliya, waye a hopital ɗinnan baisan cewa ke yar wahala bace" a harzuƙe victoria ta matso tana shirin kaima maryam duka dan ba ƙara min haushi maganar maryam ta bata ba, riƙe ta destiny tayi tana faɗin "lafiyar ki kuwa, duka fa ki ke shirin kai mata" victoria ta shiga kiciniyar ƙwace kanta daga riƙwan da destiny tayi mata tana faɗin "rabu dani na koya mata hankali" tana huci, ita kuwa maryam cewa take "dan Allah ki ƙyaleta destiny ta dake ni" fizgewa victoria tayi daga riƙwan da destiny tayi mata sosai ta kaima maryam duka, ramawa maryam tayi ita ma,  sosai faɗa ya kaure tsakaninsu abu kamar wasa, hidaya ce ta riƙe maryam tana faɗin "dan Allah maryam kiyi haƙuri ki ƙyale ta Please"
"haba yaza kice in ƙyale ta baki ganin cin mutuncin da take man ne,duka fa ta kaiman,  ki barni kawai na nuna mata cewa bafa wai ana tsoronta bane" destiny ce tace "please maryam kiyi haƙuri" jan hannun victoria tayi suka bar wurin, saida suka shiga wani corridor sannan destiny ta saki hanun victoria tana faɗin "wai miki damun ki ne victoria, nace ki fita daga harkar su, ki fuskanci abunda ke gaban ki, kin dai san mi gurutu ya ce mana, amma kin zo kina sakarci" ajiyar zuciya victoria ta sauke tana faɗin "wallahi idan naga yarinyar ne sai kawai naji wani baƙin ciki ya turniƙe ni"
"hmmm koma mi kike ji game da ita bai kamata ki bari yayi ta siri ba tunda dai kinsan mi gurutu ya ce"
"shikenan zan kiyaye "
"da dai ya fi maki"destiny ta faÉ—a haÉ—i da barin wurin, bin bayan ta victoria tayi...

✨Shazim  ✨

Kayan shi dake kan table É—in shi ya shi ga tattarawa yana zubawa cikin briefcase É—in shi yana cema noraiz "tashi to kai,time É—in sallah yayi"
ok kawai noraiz ya ce, haɗi da miƙewa amsar briefcase ɗin yayi daga hannun  shazim, ficewa suka yi daga office ɗin suka nufi masallaci koda aka gama sallah abnoor suka wuce, suna shiga a compound  ɗin hospital ɗin suka ci karo da majeed wanda dawowar sa kenan daga sallah asr hango sabuwar mota ne yasa shi tunanin koh  shazim ne, tsayawa yayi, sai da Shazim ya gama dai daita parking sannan su ka fito shi da noraiz, ƙarasowa majeed yayi wurin su, gaisawa suka yi majeed na faɗin "noraiz kenan ɗan gidan  yayan sa, ai dama karatun doctor kayi, kaga ni kullum kuna tare  duk da ma yanzu haka ne" ɗan sosa kai noraiz yayi yana kallon shazim can kuma sai ya mai da kallon shi wurin majeed yana faɗin "wallahi kuwa ya majeed abun da naso kenan amma yaya yaƙi yarda" Shazim ne yace "to parrots zaku fara naku surutun koh, to ni kun ga tafiya ta" ya faɗa yana nufara entrance ɗin hospital, bin bayan sa suka yi suna cigaba da firar su har suka iso office ɗin Shazim, sun ɗan jima a abnoor dan sosai shazim ya duba patient anan sai da suka yi sallah magrib da isha  sannan suka nufi gida, koda suka isa gida gaishe da ammy kawai shazim yayi ya nufi part ɗin sa domin ba ƙaramin gajiya yayi ba dinner ɗin sa ma sai dai fatima ta kawo masa nan part ɗin sa, wanka yayi ya shirya cikin kayan bacci  white color, parlor ya dawo akan center table ya samu dinner ɗin sa da fatima ta kawo masa, serving ɗin kansa ya shiga yi yana kammala dinner ya wuce bedroom ɗin sa toilet ya wuce baifi five minutes ba ya fito jikinsa na danshin ruwa alama alwala yayi da brush, wurin wardrobe   ya nufa ya fito da sallaya shimfi ɗawa yayi, shafa'i da wutiri yayi, ya ɗan jima yana adu'a, sannan  ya tashi ya nufi bed ɗinsa ya hau adu'a yayi sannan ya kashe bulb ya kunna bedside lamp..
Episode 18  _19

A kwana a tashi babu wuya wurin ubangiji, har an ciye sati da wasu yan kwana ki da maganar tafiyar su shazim abuja, kullum da kalar excuses ɗin da zai ba ma ammy har  dai suka yi wannan kwana kin basu tafi ba, a gefe kuma innah ta addabi ammy kullum cikin kira take akan miyasa ba su zoba har yanzu sai dai ammy ta bata haƙuri, yau ma tun da sassafe ta kirata, tun da ammy taga kiran innah sai da gabanta ya faɗi tasan da tace mata ba yau ba zata rufe ta da cin mutunci ne, haka nan ta ɗaga wayar kamar yanda ammy tayi zargi hakan ce ta faru dan sosai innah ta cima ammy mutuncin san ranta, baiwar Allah ammy harda kukan ta, tashi tayi daga bakin gado da take zaune ta nufi part ɗin Shazim, bata same shi a parlorn ba hakan ne ya sata nufar bedroom ɗin sa tayi nocking buɗe ƙofar yayi,sanye yake scrub suit da'alama ma ya gama shirin tafiya hospital ne, ganin ammy tsaye bakin ƙofar bedroom ɗin sa yasa shi mamakin ko lafiya ta zo da kanta maimakon tasa fatima ko noraiz ya kirasa, gaishe da ita yayi, amsa mashi tayi da lafiya, daga yana yin da ta amsa mashi yasan cewa gaskiya ba lafiya, domin tun da yake da ammy bai taɓa ganin ta cikin irin wannan yana yin da ya ganta ciki ba yanzu, kafin ya sake cewa wani abu ya ji tace "wai ni kam shazim yaushe ka zama mara jin magana ne, wai har ace nizan saka abu amma kafi ƙarfin kayi abun da nake so koh" kallon yayi ammy yayi da mamaki jin abun da  tace danshi a iya sanin shi baisan mi take nufi ba dan shi harga Allah ya manta sunyi wata magana ta zuwa abuja "ammy dan Allah kiyi haƙuri wallahi ban san akan mi kike magana ba" wani irin kallon ammy ta bishi da shi tana cewa"watau saboda kagama rainani shiyyasa ka manta da maganar da mu kayi da kai koh, wai nikam Shazim wane irin yaro ne kai maganar zuwa abujar ce ka manta saboda ka raina mutane koh" sai yanzu ya ma tuna da wata maganar tafiya dan shi duk a tunaninshi ammy ta bar maganar ganin ta kwana biyu bata sake yi mashi maganar ba "dan Allah ammy ki daina cewa haka ta yaya zan raina ki,dan Allah kiyi haƙuri wallahi yana yin aiki.... " bai ƙarasa faɗar maganar da zai faɗa ba ammy ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu tana cewa "da kata man bana son jin wani excuse naka, umarni nake baka ba shawara ba kashirya gobe tun da safe ku tafi " cikin rashin jin daɗin  hukuncin da ta yanke yace "dan Allah ammy kiyi haƙuri sai jibi " tsawa ammy ta daka mashi tana faɗin "wallahi kaji na rantse gobe za ku tafi in dai na isa da kai,sannan kamar yanda su fatima za su yi sati biyu kaima sai kayi shi ,  in kuma ban isa ba zaka iya yin duk yanda ka ga dama" tana gama faɗar haka ta juya tafice daga part ɗin, komawa Shazim yayi cikin bedroom ɗin shi ya zauna bakin bed yana dafe kansa dan harga Allah baya son tafiyar nan gashi ammy tayi fushi, bashi da wani zaɓi banda ya shirya kawai gobe su tafi ko hakan zai sa ta sauko daga fushin da tayi dashi, ammy na fita daga part ɗin shi main parlorn ta nufa, noraiz da fatima ta samu kan dinning suna breakfast gaishe da ita su kayi, amsa masu tayi tana tambayar su "kun shirya kayan ku da nace ku shirya? "fatima tace "eh ammy saura kaɗan ingama shiryawa yawale nake jira ya kawo kayan guga sai na gama" ammy ta ce "ok anjima zai kawo daya kawo kishirya su yau" da to fatima ta amsa,  mai da kallon ta tayi kan noraiz tana faɗin "kai fah ka shirya naka "
"a'a ammy, wai ba anfasa tafiyar ba " kallon shi kawai ammy tayi bata ce komai ba, "wallahi ni ammy da kin haƙura da maganar tafiyar nan, dan ni wallahi bana son zuwa ko dan saboda wannan tsohuwar, tayi ta zagin mutum bayan ba wani abu mutum yayi mata ba, tana faɗin wai dama ba sonta kike ba shiyyasa muma bamu sonta, wai da papah na raye bamu isa muyi nesa da ita ba " katse shi ammy tayi ta hanyar ɗaga mashi hannu tana cewa
"ya isa haka,  kar in ƙara jin kace wani abu inba so kake yanzu nan ranka ya ɓaci ba" shiru noraiz yayi ganin kamar ran ammy ya ɓaci.

shazim ne ya sauko daga part ɗin sa ya nufo main parlorn, fuskar shi cike da damuwa,  zuwa yayi wurin  ammy ya durƙusa gaban ta yana faɗin "dan Allah ammy kiyi haƙuri " kau da kai tayi kamar ma bata son ganin shi tayi banza da shi, haƙuri ya shiga bata amma ko ta ɗaga kai ta kalle sa, tashi  yayi daga durƙuson da yana faɗin"dan Allah kiyi haƙuri, na wuce office" ko yanzu bata ɗaga kai ta kallesa ba, noraiz ne yace "yaya bazaka yi breakfast ba" ganin shazim ɗin ya nufi hanyar fita batare da ya kalli dinning ba "na ƙoshi" shine kawai abun da ya cema noraiz, ficewa yayi daga parlorn ko da ya shiga motar shi ya daɗe bai tada motar ba gaba ɗaya baya jin daɗin fushin da ammy ta ɗauka da shi, sai da ya kusan 15 minutes a motar bai tafi ba sannan yayi mata key ya bar gidan ko gaisuwar da megadi keyi mashi shi da ilya bai amsa ba ɗaga masu hannu kawai yayi ya fice..
a parlorn kuwa noraiz ne ya taso daga kan dinning ya dawo kan sofa kusa da ammy yana faɗin "ammy wai mike faruwa, naga kamar kina fushi da yaya lafiya?" amsa ammy ta bashi da "ba komai tafiya ce bai so kuma dole sai kun yi ta" noraiz ya ce "dan Allah ammy ki janye maganar tafiyar nan, ni ban san miyasa ki ke son sai munyi wannan tafiyar ba,kinsan halin innah bawani son mu take yi ba kema kin sani,su uncles ne kawai suka damu da rayuwar mu lokacin da muke buƙatar  kulawar su" ammy tace "ya isa haka,dama kai da shazim na lura halin ku ɗaya, to tafiyace sai kunyi ta gobe ma bawai jibi ba kunji na faɗa maku"
"ammy gobe fa ki ka ce"
"ƙwarai kuwa gobe nace, idan kuma ban isa ba sai inji "noraiz ya ce "kin isa ammy, Allah ya huci zuciyar  ki , in sha Allah ba zamu sake cewa komai ba game da wannan tafiyar,yanzu zamu fara shirya kayan mu goben zamu tafi in sha Allah" ammy tace "da ma dai ya fiye maku " ta faɗa haɗi da tashi ta nufi bedroom ɗin ta,  da idanu kawai suka bita, sai da su kaga shigewar ta ɗaki sannan su ka kalli juna noraiz ya ce "nifa gani nake kamar akwai abun da ke damun ammy, yan da tayi fushi akan tafiyar nan abun yayi yawa, kawai dai tana ɓoye mana ne, amma alamu suna nu na cewa tana cikin damuwa yan kwana kinnan, kuma nasan hakan da sa hannun innah" ɗan nisawa fatima tayi tana cewa "na daɗe da lura da hakan ya noor, kuma na tambayeta ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba tana ce man wai ba komi, abun da kawai ya ka mata shine mu shirya kawai gobe mu tafi, may be zata huce dan naga tayi fushi sosai"
"haka ne fatima, amma kinsan yaya baya son tafiyar nan"
fatima ta ce "amma dole yayi ta ya noor tun da ammy ta nuna ɓacin ranta, na san ko dan haka dole ya tafi " noraiz ya ce" haka ne dan bansan mi ya haɗa su ba naga tana fushi da shi kuma daga part ɗin sa ta ke "
"ina tunanin tayi mashi maganar tafiyar ne ya nuna bazai je ba "
noraiz ya ce "to ƙila, nima yanzu tashi zanyi naje na shiraya kayana, dan wallahi  nasan ta waiwaye  mu baza mu ji da daɗi ba yanda tayi fushin nan"
"dama ni ya noor tun da tayi magana nashirya kayan ganin ba'a yi tafiyar ba ne yasa na saka wasu daga cikin kayan da zani walimar school É—in mu"
"ke daman murna kike da wannan tafiyar"
murmushi fatima tayi tana faÉ—in"ina son zuwa naga sa'ada da Aunty kairiyya ne kawai"
noraiz ya ce
"za kuma ki haɗu da innah guyaba ba" dariya fatima ta kwashe da ita, tashi yayi yana faɗin "bari  nima na tashi  yanzu na kammala shirya nawa kayan tun da ba inda zani" ya faɗa hadi da tashi ya nufi part ɗin su, tashi ita ma fatima tayi ta nufi nata bedroom ɗin....

   ✨SHAZIM✨

Zaune yake a office ɗin shi ya barbaza takardu kan table ɗin shi,zuba masu ido kawai yayi yana kallon da alama hankalin shi baya kansu, yayi zurfi cikin tunani ya ji ana nocking, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya bada izinin shigowa, hidaya ce ta shigo hannun ta ɗauke da files, gaishe da shi tayi hannu kawai ya ɗaga mata, ganin hakan ne yasa hidaya fahimtar yau baya san magana, dan haka kawai ta matsa kusa da table ɗin ta ajiye mashi files, ɗago da kanshi yayi yana kallonta, fahimtar mi ya ke nufi ne yasa ta cewa "dama files ɗin patient ne dake waje" sai yanzu ya buɗe baki ya ce "kwashe su ki kaima dr kabir, bazan samu damar duba kowane patient ba  yau" daga yanayin yanda yake maganar zaka san cewa baya jin daɗin
"dr baka jin daÉ—in ne" hidaya ta tambaye shi, kai kawai ya É—aga mata,É—aukar files É—in tayi ta fice, direct office É—in dr kabir ta nufa, nocking tayi aka bata izinin shiga, shiga tayi bakinta É—auke da sallama, zaune ta same shi yana aiki a laptop "good morning sir" hidaya ta faÉ—a, É—ago da kansa yayi yana amsa mata gaisuwar da tayi yana kallon files É—in dake hannun ta "lafiya dai koh hidaya, ina zaki da wannan files É—in?" amsa ta bashi da "dr Shazim ne yace na kawo maka, bazai samu damar duba patient ba yau"
"ok ajiye" ya faɗa yana maida kansa kan aikin da yake yi, hidaya tana ajiyewa ta fice daga office ɗin, saida ya gama aikin da yake yi sannan ya miƙe ya fice daga office ɗin, ya nufi office ɗin Shazim, shiga kawai yayi batare da yayi nocking ba, samun shi yayi zaune kan sofa dake office ɗin dafe da kanshi, jin alamar an buɗe ƙofa ne ya sa shi ɗago da kanshi yana kallon dr kabir da ya shigo, amsa mashi sallamar da yayi yayi, ƙarasawa dr kabir yayi haɗi da ne man wurin zama ya zauna kusa da shazim yana faɗin "hi dude, what's wrong with you, naga kasa nurse hidaya ta kai man file ɗin patient,lafiya dai ko" kallon shi Shazim yayi sannan ya ce "i'm not feeling better"
"ya salam,mike damun ka?" ɗan nisawa shazim yayi sannan ya ce "wallahi ammy ce wai dole sai na tafi abuja,  da na kawo mata excuse fushi ma tayi dani" kabir ya ce " to minene aciki da har zaka sama kanka damuwa irin haka, shawarar da zan baka anan kawai kashirya ka tafi, hakan ka ɗai zai sa ammy ta huce"
"baza ka gane ba kabir, kwata kwata bana son zuwa abujar nan"
"to ya za kayi haka nan zaka yi haƙuri ka tafi tun da ammy ta ce katafi,yaushe ne tace ka tafi"
"gobe fa" kabir ya ce "to Allah ya kaimu gobe, kai ka É—ai zaka tafi"
"a'a harda su noraiz"
"ok, Allah ya kaimu goben,  karka wani damu" shazim ya ce "ameen nagode"
"bakomai kar ka damu"
"ina ma tunanin tashi zanyi na tafi abnoor dan ban gaya ma majeed ba, sannan zan koma gida daga can"
Kabir ya ce "eh gaskiya ya kamata, da ƙarfe nawa zaku tafi ko dai sai munyi waya"
"ina tunanin da safe, dan wallahi ammy tayi fushi sosai"
"to Allah ya kaimu"
"ameen" Shazim ya faÉ—a hadi da tashi ya nufi table É—in sa ya fara haÉ—a kayan shi yana maidawa cikin briefcase, yana gama haÉ—a kayan kabir ya taso domin yi mashi rakiya, su hiday na zaune a reception su ka zo suka wuce, suna wuce maryam tace "lafiya naga dr ya tashi lokacin tashin shi bai yiba" hidaya ta ce "baya jin daÉ—i ne, dan koda na kai masa files É—in patient cewa yayi na kaima dr kabir, ina tuna nin ba zai iya zama ba shiyyasa zai tafi gida"
"Allah ya bashi lafiya" maryam ta faÉ—a da ameen hidaya ta amsa,can maryam tace"kinsan wane tuna nin nayi?" hidaya ta ce "a'a sai kin faÉ—a"
"kawo kunnan ki ki ji" matsawa hidaya tayi kusa da maryam, magana ta faÉ—a mata, sauran nurses É—in dake wurin su ka ce "dan muna kusa shine abun harada su raÉ—a ko maryam" murmushi maryam tayi sannan ta ce "komai fa na son sirri, wannan magana ce tsaka ni na da ita" wata acikin nurses É—in ce ta ce "in tayi wari maji" Æ´ar dariya maryam tayi haÉ—i da cewa "bama zata yi ba "

har parking lot dr kabir ya raka shi,  saida dr kabir yaga tafiyar Shazim tukun ya koma cikin hospital ɗin, ya zo zai shiga office ɗin shi yaji maganr hidaya tana cewa"doctor " juyowa yayi yana kallonta sannan ya ce "na'am " duƙar da kanta tayi ganin ya kafe ta da idanu "lafiya dai koh hidaya,?   kin tsayar dani kin kuma yi shiru" magana ta fara yi ba tare da ta ɗago da kanta ba "dama dr tambayar ka zanyi mike damun dr ne?" kallon ta kawai dr kabir ke yi, sannan ya ce "baya faɗa maki baya jin daɗi ba"
"eh haka ne"
"to baya jin daÉ—i ne, gida ma ya tafi yanzu"
"ok, am dan Allah ko zaka bani number shi na kira shi nayi mashi ya jiki" magana take still kanta na ƙasa,  wani kalar kallo dr kabir ya shiga binta da shi, ita kuma jin baice komai ba yasa ta ɗago da kanta, tana ɗago wa idanun ta suka sauka cikin nashi daya kafe ta dasu, kusan 5 seconds bai ce komai ba, can ya ɗan nisa sannan ya ce "dama baki da number shi" girgiza mashi kanta tayi alamar eh, "ok shikenan ina wayar ki na sa maki number" hannu ta sa cikin aljihun rigar uniform ɗin ta ta ciro wayar ta ta miƙa masa,  amsa yayi ya sa mata number, miƙa mata wayar yayi tasa hannu ta karɓa tana faɗin "nagode" kallonta kawai yayi ba tare da ya ce  mata komai ba harta juya ta bar waje bai daina kallonta ba, sai da ya ga ta ɓace ma ganin sa tukun ya murɗa handle ɗin ƙofar office ɗin shi ya shiga.....

✨ Shazim ✨

yana barin eko direct abnoor ya nufa, yana parking ya fito ya nufi main entrance ɗin hopital ɗin ba tare da ya ɗauki briefcase  ɗin sa ba, yana shiga direct office ɗin dr majeed ya nufa
nocking yayi, daga ciki aka bashi izinin shiga, kama handle ɗin ƙofar yayi ya tura ya shiga, bakin sa ɗauke da sallama, zaune dr majeed yake yana duba files dake gaban shi, amsa mashi sallamar yayi, wuri shazim ya samu ya zauna, hannu ya miƙama dr majeed suka yi musabaha
"lafiya kuwa yau naganka a wannan lokacin?"
"lafiya lau majeed, maganar tafiya abuja nan ce ta taso, ammy tayi fushi dole sai mun tafi gobe" majeed ya ce "to fah, kwana nawa zaka yi"
"kai dai bari kawai wai sai nayi sati biyu  inji ammy"
majeed ya ce "shiyyasa fa tun time ɗin da kace tace ku tafi nace maka ka tafi kawai ni zan kula da komai, amma ka ƙi,yanzu ga irinta nan ta soke kwana biyar ɗin da tace"
"baza ka gane ba ne kawai majeed, wallahi bana son zuwa ko nan da can shiyyasa "
"to ya zaka yi zumunci ne dole ayi shi"
"haka ne"
"yanzun goben da ƙarfe nawa zaku tafi? "
"da safe" shazim ya bashi amsa "ok Allah ya kaimu" da ameen ya amsa,sun ɗan jima suna magana akan magunguna da allurai da zasu yi order, sai da shazim yayi sallamar asr bayan yaba ma majeed duk abun da zai bashi, sannan suka yi sallama ya nufi gida, tsit ya iske parlor alamar ba kowa, hakan yasa shi nufar bedroom ɗin ammy nan ma ba kowa, fita yayi ya nufi up stairs part ɗin noraiz ya shiga, samun shi yayi a parlor zaune kan sofa yana kallo cikin laptop, ɗagowa noraiz yayi jin anbuɗe ƙofa , yana ganin shazim ya miƙe yana faɗin "sannu da dawowa yaya" da yawwa shazim ya amsa yana cewa "ina ammy? , naga kamar bata gida kuma banga motarta a parking lot ba, nama yi tunanin ko kai ka fita da motar"
"tun da ka fita ta fita ko breakfast bata yi ba, na tambaye ta ina zata, sai cewa tayi yanzu zata dawo, amma haryan zu bata dawo ba" jinjina kai kawai shazim yayi haÉ—i da ficewa ya nufi part É—in sa, yana shiga parlorn shi wayar shi dake cikin aljihun wandon shi ya ciro number ammy ya shiga kira, tana ringing amma ba'ayi picking ba harta katse ya sake kira sai da yayi mata 3 missed call amma bata É—auka ba, fita yayi ya koma part É—in noraiz, yana shiga yace "noraiz ina wayar ka?"
"gata nan yaya" noraiz ya bashi amsa "kira number ammy" da ok noraiz ya amsa, nan shima ya shiga kiran wayar amma ba'ayi picking ba, ƙofar parlorn su ka ji an buɗe fatima ce ta shigo da waya a hannun ta "yaya na shiga ɗakin ammy naji wayar ta na ringing, sai da na duba naga ashe kai ke kira" shazim bai ce komai ba ya fice daga part ya koma nashi, number malam yayi dialing, picking malam yayi haɗi da Sallama yana faɗin "likita bokan turai"
"ina wuni malam"
"lafiya lau, ya aiki"
"Alhmdllh "
"to masha Allah "
É—an shiru Shazim yayi, jin yayi shiru ya sa malam ce wa "lafiya dai koh shazim? "
"lafiya lau malam, dama ammy ce" sai kuma yayi shiru,  malam "yace miya samu Aishar?"
"bakomai malam, tayi man magana ne akan zuwa abuja to nace mata ina da uziri wirin aiki, to sai bata sake maganar ba tun daga ranar, yau kawai " nan ya shiga  bashi labarin yan da suka yi da ammy yau , har fushin da tayi da kuma dawowa da yayi yanzu bata gida da kuma kiranta daya ke bata ɗauka, ɗan nisawa malam yayi sannan ya ce "ta faɗa man  komi da ya faru, gaskiya banji daɗi ba, baka kyau ta ba, shi zumunci Allah ne yace ayi sa, kuma komi ya faru tsakanin ka da su ai kai ne baka kyauta ba" sosai malam yayi mashi faɗa da nasiha, akan bai kyauta ba daya bari har sai da ran ammy ya ɓaci "ayi haƙuri malam in sha Allah hakan bazata sake faruwa "
"shikenan Allah ya kyauta gaba" da ameen malam ya amsa, sannan shazim ya ce "to malam ammy tana nan ne"
"eh tana nan" ajiyar zuciya shazim ya sauke, sannan suka yi sallama da malam, bedroom ɗin shi ya wuce, jefar da wayar shi yayi kan gado, kayan jikin shi ya cire daga shi sai boxer yanufi bathroom, kusan 15 minutes ya fito ƙugun shi ɗaure da towel, shiryawa  yayi ciki ash ɗin jallabiya wuri ya samu kan sofa ya zauna, laptop ɗinshi ya jawo yashiga dan dannawa....

ammy bata dawo gidan sai da yamma liƙis, ta shigo, gaishe da ita fatima da noraiz dake parlor zaune suka yi, amsa masu tayi tana samu wuri ta zauna kan sofa, hijab ɗin ta ta cire ta miƙa ma fatima tan cewa "kai man ɗaki" da to fatima ta amsa ta tashi ta kaima mata, tana fitowa ammy ta ce "ina innah asabe?" amsa ta ba ammy da "tana ɗakin ta"
"ok "
Noraiz ya ce "ammy wai ina ki ka je ne, yaya ya dawo tun É—azu yana ta ne manki " fuska a É—aure amma ta ce
"in da ya aike ni can na tafi"
noraiz ya ce "dan Allah ammy kiyi haƙuri ki dai na wannan fushin,goben zamu tafi kamar yanda kika ce"
"karma ku tafi" ammy ta ce, magana noraiz zai yi, ta ɗaga mashi hannu tana ce "ya isa haka kar ka takura man daga dawuwa ta" jin haka yasa dole noraiz ya kama baikin sa yayi shiru, saukowa shazim ya ke daga up stairs  ya nufo parlorn, hango ammy da yayi, yana isowa parlorn ammy ta miƙe ta nufi ɗakin ta, tsayawa yayi chak ganin tana ganin shi ta tashi, binta yayi har ɗakin, yana shiga ya ganta tsaye bakin dressing mirror, ta cikin mirror ta hange shi, yi tayi kamar ma bata san da shigowar sa ba, ƙarasowa yayi har gaban dressing mirror ɗin yana faɗin "ina wuni ammy" amsa mashi tayi  da  "lafiya " daga nan ta ɗauke kanta ta koma bakin gado ta zauna, binta yayi har bakin gadon, durƙusawa yayi yana dafa gwiwar ta, haƙuri ya shiga bata, da ƙyar ta haƙura, ganin ta haƙura yasa cewa "dan Allah ki rage satin da ki kace zanyi zuwa kwana biyar "
"idan har kana son zaman lafiya da ni to kawai kayi shiru,kayi abunda na ce" da to kawai ya amsa mata, sannan ya fice daga ɗakin ya koma part ɗin shi domin yin alawala saboda lokacin sallah da yayi,yana fita ita ma ammy tashi tayi ta nufi toilet domin alawa,  yana ko mawa   part ɗin shi  alawala kawai yayi ya fito suka wuce masallaci da noraiz dake parlor yana jiran shi yana saukowa suka wuce, anagama sallah suka wuce gidan malam  basu bane suka dawo gidan ba sai wurin ƙarfe 10 sannan suka dawo, koda suka dawo ammy da fatima har sunyi bacci, suma part ɗin su suka wuce kowa ya nemi makwancin shi..
Episode 20 _21

Washe gari...

Iliya ne ke  saka trolleys ɗin su fatima a booth ɗin  mota da zai kaisu airport,
ammy da fatima da noraiz sai Shazim zaune suke kan sofa a main parlor, ammy nayi masu nasiha sai da ta gama faɗa masu duk abun da zata faɗa masu sannan suka tashi suka kama hanyar fita daga parlorn, fatima da noraiz harsun fice ammy ta tsaida shazim, tana faɗin "dan Allah shazim kar naji kar na gani dan Allah, kayi haƙuri da komi zaka gani har Allah yayi maku dawowa "
"to ammy in sha Allah" fitowa su ka yi ammy ta raka su har parking lot su ka shiga mota, tana masu Allah ya tsare hanya da ameen suka amsa mata, sannan ilya yaja motar su ka fice daga gidan ammy na ɗaga masu hannu, saida taga mai gadi ya rufe gate sannan ta juya ta koma ciki,  cike da kewarsu yanzu sai ita kaɗai cikin gidan, fatan Allah ya kaisu lafiya ya dawo dasu lafiya.
suna fita daga gidan direct gidan malam su ka wuce dan suyi mashi ban kwana, sosai malam yayi masu nasiha da  fatan isa lafiya, suna fita ilya ya kama hanyar airport,ko da ya kaisu sai da ya jira har jirgin su ya tashi sannan ya dawo gida...

✨Abuja✨

Airport, passengers ne su ka fara fitowa ta ƙofar da aka rubuta exist wacce aka tana da domin passenger, su shazim ne suka ɓullo ta wannan ƙofar yana gaba fatima da noraiz na biye da shi abaya da trollys ɗinsu a hannu, wata kyakyawar matashiya ce wacce zasu yi sa'anni da fatima, fara ce sai dai ba ta kai fatima haske ba,   da gudu ta nufo fatima tayi hugging ɗinta tana faɗin "oyoyo sister" fatima da fara'a a fuskar ta tace "ya ki ke sa'ada?" wacce aka kira da sa'ada, tayi murmushi tana faɗin "lafiya lau ya hanya" sannan ta juyo tana cewa" ya "Shazim ina wuni" amsa mata yayi da "lafiya lau" sannan ta juya tana gaishe da noraiz, da fara'a a fuskar shi yace "ai nayi tunani fatima ka ɗai ki ka gani" da murmushi a fuskarta tace "a'a ya noraiz kuma ai na gan ku" suna a nan tsaye wasu ƴan mata  kyawawa su biyu su ka iso fararene sai dai ɗaya tafi ɗaya haske, mai hasken sosai tana kama da  sa'ada sai dai ita daka ganta zaka san tana ƙarawa dana kanti,jikinsu sanye da ɓakar jallabiya sunyi rolling da gyelen jallabiyar,  wurin su su ka nufo,  mai kama da sa'ada  cike da yanga take  faɗin "hi ya shazim" haɗi da nufar Shazim da nufin tayi hugging ɗin shi, kasa ƙarasawa tayi ganin wani mumunnan kallo daya bita da shi fuskar shi a ɗaure kamar bai taɓa dariya ba, kwal kwal tayi da ido kwalla na taruwa ciki tace " haba ya shazim miyasa ka ke haka,daga na  nuna farin cikin ganinka" banza yayi mata kamar ma ba da shi take ba,gaishe da shi ɗayar tayi, cikin sakin fuska ya amsa yana faɗin "ya kika kairiyya"
"lafiya lau, ya hanya?"da Alhmdllh ya amsa mata,hugging ɗinta fatima tayi tana faɗin" nayi kewar ki aunty kairiyya"da fara'a a fuskarta tace "nima nayi kewarki" wasu maza ne suka ƙaraso wurin su su biyu sanye da uniform, suna ƙarasowa suka ce 
"barkan ku da zuwa ranka ya
daÉ—e" kallon su shazim yayi yana cewa "barkan ku dai aminu ya kwana biyu"
"Alhmdllh ranka ya daÉ—e" wanda aka kira da aminu ya ce,É—ayan ne ya ce "yallabai ya lagos?" shazim na kallon shi ya ce "Alhmdllh kamal,ya aiki?"
"lafiya lau ranka ya daɗe" sannan su ka gaishe da noraiz fuskarshi ɗauke da fara'a ya amsa, sannan fatima ta gaishe da su, amsa mata su ka yi  cikin kulawa fuskar su da fara'a,suka amshi trollys ɗin noraiz  da na shazim  dake hannun noraiz aminu na  cewa "mu tafi koh ranka ya dade" ok kawai shazim yace yana kama hanya,su aminu na gaba da trollys ɗinsu, sa'ada ce ta amshi na fatima, wannan budurwar ta gaban su tazo ta wuce fuuu kamar zata tashi sama, fatima ce tace "Aunty feenah abun ba magana" juyowa tayi ta kalli fatima sama da ƙasa fuska a haɗe tace "sannu" ta juya tayi gaba, da idanu kwai fatima ta bita, taɓe baki noraiz yayi, fuskar sa'ada da ɗan damuwa ta kama hannun fatima tana faɗin "sorry sister" ɗan yaƙe fatima tayi tana faɗin "bakomai" tsaki kairiyya ta ja a zuciyar ta tana faɗin "ko yaushe feenah zata dai wannan banzar ɗabi'ar "
parking lot ɗin airport  ɗin su ka ƙaraso time ɗin har shazim ya shiga bayan mota ya zauna, aminu na saka kayan su cikin booth, amsar trolly ɗin dake hannun sa'ada kamal yayi ya saka a booth,buɗe ma su  baya yayi, noraiz ya shiga sa'ada ta ce "kamal mu zamu tafi a motar aunty kairiyya"
"to shikenan hajiya" kama hannun fatima tayi suka nufi inda motar kairiyya  ta ke, tsaye suka same ta bakin mota,
sa'ada tace
"lafiya dai aunty kairiyya"
"babu komi, ku nake jira ne "
sa'ada tace "aunty feenah tafiya tayi?" eh kawai kairiyya tace haɗi da buɗe motar ta shiga, suma shiga suka yi fatima na gaba kusa da kairiyya sa'ada na baya,key tai ma mortar haɗi da yin  reverse tabi bayan motocin da su shazim ke ciki, suna tafiya kamal na tambayar noraiz  ya lagos da ammy, da Alhmdllh noraiz ya amsa mashi sosai su ke fira da shi har su ka kawo wata danƙareriyar anguwa ta ji da faɗa, gidajen dake anguwar ka ɗai sun isa su sa ka fahimci cewa anguwa ce ta manyan mutane, gidaje ne naji da faɗa, road road ne gasunan kala kala kowane road kalar tsarin ginin   gidajenta daban, karya kwana animu yayi ya shiga wani road bin bayan shi su kamal su ka yi shi da kairiyya , masha Allah wani haɗeɗen  estate ne su ka nufo,aƙalla gidajen dake cikin estate ɗin za su kai 20 duk da akwai wandan foundation kawai a kayi ba'a fara gina su ba,   tsarin gidajen dake cikin estate ɗin yafi na sauran gidajen dake sauran road ɗin  haɗuwa da tsari,komai na gidajen iri ɗaya ne,  tafiya su ka yi mai ɗan tsayi, sannan su ka kawo bakin main gate ɗin estate ɗin,securitys ne zaune kan bench a bakin gate ɗin estate,ɗaya daga cikin su ne ya taso ya nufo motar,sauke glass ɗin motar aminu yayi,  gaisawa yayi da security ɗin, tambayar shi securityn yayi daga ina, amsa aminu ya bashi "daga airport muke, yallabai shazim ne ya zo " leƙawa security yayi yana cema shazim "ranka ya daɗe barka da zuwa, ya hanya"da Alhmdllh shazim ya amsa masu, sauran security ɗinma tasowa su ka yi suna gaishe da shazim sannan suka nufi motar da su noraiz ke ciki suna gaishe su,cikin sakin fuska su ka amsa masu,buɗe masu gate security yayi ,ciki aminu ya danna kan hancin motar kamal na biye da shi, sai da su ka ɗanyi nisa da tafiya sannan su ka iso bakin wasu gidaje biyar dake jere duk da akwai yar tazara tsaka nin su, huɗu girman su ɗaya, ɗayan kuma yafi su girma sosai,mai girman dake tsakiyar su aminu ya nufa ,  parking aminu yayi bakin wannan ƙaton gidan wanda yafi sauran gidajen girma da haɗuwa,parking space ɗin  gidan ya nufa yayi parking, motoci ne da a ƙalla zasu kai biyar an rufe su, fitowa aminu yayi ya buɗe ma shazim ƙofa amma sai shazim yace kawai ya ɗauki kayan ya wuce, hakan yasa shi  nufar  booth ɗin motar ya fito  da trollys ɗin su ya nufi entrance ɗin shiga gidan ya tsaya,  kamal ma ya nufo nan yayi parking a parking space ɗin,fitowa noraiz yayi, su fatima kuma wani part kairiyya ta nufa da su tayi parking, fitowa sa'ada da fatima su kayi, sa'ada ta  buɗe booth ta fito ma fatima da trolly ɗin ta,ta window Fatima ta leƙa tana faɗin "aunty kairiyya sai mun shigo" da to kairiyya ta amsa, reverse tayi ta nufi wani part tayi parking, ficewa tayi ta nufi cikin part ɗin.
kallon motar feenah dake parking space sa'ada tayi, aranta tace kenan gida aunty feenah ta dawo,trolly fatima ta ja suka nufi entrance ɗin gidan ,kamal na parking noraiz ya fito ya nufi aminu dake tsaye yana jiran fitowar shazim ya kai masu trolly ɗin cikin gidan  amma bai fito ba, noraiz na isowa ya tambayi aminu lafiya, amsa aminu ya bashi da shazim ya ke jira ya fito   noraiz ya ce "ok muje kawai" da to aminu ya amsa yana gaba noraiz  na baya, buɗe ƙofar aminu yayi  su ka shiga har time ɗin shazim bai fito ba yana zaune cikin mota,haɗeɗen parlor ne mai kyan gaske dan inka shiga sai kayi tunanin ba a cikin estate ɗin kake ba, babu motsin kowa aciki sai sanyi ac dake tsara ko ina na parlorn haɗe ƙamshi fresheners,up stairs aminu ya nufa,ɗakuna ne saman sosai, wata yar hanya aminu ya bi nanma wani parlorn ne wanda yafi na ƙasa haɗuwa da tsari, wani stairs ɗin su ka ƙara nufa nanma parlor ne shima ya haɗu ga tsari mai kyau,sannan suka nufi wani ɗan corridor,bedrooms ne kusan guda huɗu anan aminu ya tsaya yana ajiye trollys ɗin yayi ma noraiz sai anjima, godiya noraiz yayi mashi sannan ya ja trolly ɗin shazim ya shiga ƙofar dake kusa da shi, ɗan ƙaramin parlor ne mai kyan gaske kusan tsarin shi ɗaya da parlorn shazim dake lagos, nan ma kamshi ne ke tashi mai daɗin gaske ga sanyin ac, bedroom ya nufa nan ma ya haɗu shima kamar na lagos ne sai dai yafi na lagos girma da wasu abubuwan, har cikin wardrobe noraiz ya saka ma shazim trollys ɗin shi,sannan ya fice daga ɗakin yanufi nashi, shima na shi ya haɗu sosai banbancin shi dana shazim bawain mai yawa bane bedroom ya nufa ya rage kayan jikin shi ya nufi toilet domin ya watsa ruwa ..

✨Shazim✨

wayar shi dake cikin aljihu ya fiddo, number ammy yayi dialing sai da ta kusa katsewa sannan ammy tayi picking bakin ta ɗauke da Sallama, amsa sallamar shazim yayi yana faɗin ammy ya gida, da lafiya lau ta amsa tana tambayar shi ya gajiyar hanya da kuma mutanen abuja "gajiyar tafiya akwaita ammy  Alhmdllh" murmushi ammy tayi mai ɗan sauti tana cewa "gajiya sai kace wanda yaje a mota ko a ƙafa" kwantar da kanshi yayi jikin saet ɗin motar yana shafa kanshi ya ɗan lumshe ido yana faɗin "da gaske nake ammy" ammy tace
"to yayi, ya mutanen gidan? "
"wallahi ban sani ba dan ban shiga ba"
"to saboda mi, ina fatima da mai babban suna? "
"fatima na part É—in uncle Ibrahim, noraiz kuma na part É—in mu"
"to kai kana ina? "
"ina cikin mota, yanzu muka iso ne ammy, na tsaya in kira ki ne "
"ok miyasa ku baza ku sauka part É—in Ibrahim ba kona yaya ahmad "
"bakomai ammy, shi da kanshi uncle Ibrahim É—in yasa aka gyara mana nan"
"duk da haka shazim da kuna zauna part ɗin shi, nasan shima dan ya san halinka ne, ya san ba zaka zauna part ɗin shi ba yasa aka gyara maku nan"
"ammy ba haka bane"
"to yaya ne in ba haka ba? "
"kawai ya san zamufi sakewa ne apart É—in mu shine kawai"
"shikenan shazim, amma da mun gama wayar nan  ku shiga part ɗin innah ku gaishe ta dan Allah "
"to" kawai yace dan wallahi kwata kwata bai son ganin tsohuwar
"to sai anjima, in ka shiga kace ina gaishe da su dan Allah "
"to in sha Allah za suji "daga haka yayi rejecting ɗin kiran,number malam ya lalubo bugu ɗaya malam ya ɗauka da Sallama, gaishe da shi shazim yayi, cikin kulawa malam ya amsa da tambayar shi hanya da su fatima, sun jima sosai suna waya da malam sannan suka yi Sallama, cikin aljihu wando ya maida wayar, sannan ya buɗe motar ya fice, part ɗin su ya nufa,  ko da ya shiga bedroom ɗin shi ya nufa yayi wanka ya kwanta kan bed, nocking ya ji anayi daga parlor, shiru yayi kamar yana bacci dan ya san bazai wuce noraiz ba ne, kuma ya san  ya zo ne dan su tafi parts ɗin uncles ɗin su, shiyyasa yayi shiru dan bai shirya zuwa wurin kowa ba yanzu, jin shiru yasa noraiz tunanin koh yayan nashi barci ya ke, barin bakin ƙofar yi  ya fice daga part ɗin, gidan dake kusa da wanda kamal ya aje fatima da sa'ada noraiz ya shiga da Sallama, parlo ne mai girma ya ji furnitures masu kyan gaske,tsit yake ba kowa a ciki, wani ɗan corridor ya nufa ya shiga wata yar ƙofa,nan ma wani ɗan ƙara min parlor ne,  shiga ciki yayi da sallama, kyakyawar  tsohuwa ce   zaune kan carpet jikinta sanye da atamfa ɗinkin riga da zani  sai feenah da ke kan sofa kusa da ita fuskar ta duk hawaye. jin sallamar noraiz ne ya sa feenah goge  hawayen da ke fuskar ta,zuba ma noraiz ido tsohuwar tayi har ya ƙara so  cikin parlorn  ya  neman wuri ya zauna kan sofa yana faɗin "ina wuni innah" amsa mashi tayi da "lafiya,ai nayi tunanin kaima kafi ƙarfin ka zo ka gaishe da ni kamar ɗan uwan ka mara kunya, dan nasan idan ba Ibrahim ya kira shi ba bazai taɓa shigowa nan ba saboda aisha ta riga da tasa ya gama rainani baya ganin mutunci na "
"kiyi haƙuri innah yana nan shigowa bacci ya kwanta saboda jiya bai samu yayi bacci sosai ba "
"kai dallah yi man shiru, wane haline kuma na Abdulƙadir da ban sani ba, itama fatima tafi ƙarfin ta zo ta gaishe ni koh"
"A'a innah tana tare da sa'ada na san za su shigo ne" taɓe baki innah tayi tana faɗin "Allah sa"
da ammen noraiz ya amsa  haɗi da miƙewa yana faɗin
"innah zanje part ɗin  uncle Ibrahim"
bai jira mai zata ce ba ya fice abun shi, da harara feenah ta bishi yana fita tace "kingani koh innah shima noraiz wulaƙanta ni ya ke, dan tunda suka zo ko kallon banza bai yi min ba, da ya shazim ya dizgani a airport dariya yayi sh ida fatima "
"rabu da yan banza, zanyi maganin su ne daga su har uwar tasu,kuma shi wannan mara mutuncin nasan miye maganin sa, bari dai kawunnan nashi su dawo"
"yawwa innah shiyyasa nake sonki wallahi "
"ai kar kiji komai,su dai dawo, zai san dani yake magana, sai dai kuma abun da nake so a wurin ki shine ki kama kanki  ki daina son taɓa jikin shi dan nasan halinki da ɗabi'ar banza"
"In sha Allah innah na bari bazan sake ba "
"Allah ya sa" da ameen feenah ta amsa,  suna nan  zaune suna hira sa'ada su ka shigo ita da fatima ko da fatima ta gaishe da innah cewa tayi
"sai yanzu ki ka ga damar zuwa,ai da kinyi zaman ki ba sai kin shigo ba" haƙuri kawai fatima ta bata, ko kallonta bata yiba su ka cigaba da fira ita da feenah, ganin haka ne yasa fatima cema sa'ada ta tashi suje part ɗin su aunty kairiyya,tashi sa'ada tayi su ka fice zuwa part ɗin uncle Ahmad, anan su ka samu noraiz shida mahmud,gaishe da mahmud fatima tayi, sannan suka shiga bedroom ɗin mama ( asiya mahaifiyar su mansoor )su ka gaisa tana tambayar fatima ya su ammy, sun ɗan jima suna fira da ita sannan su ka tashi su ka nufi bedroom ɗin kairiyya.

wani matashin saurayi ne ya shigo  parlorn da sallama  hannun shi riƙe da briefcase,  da sauri noraiz  ya nufe  matashin yana cewa "oyoyo ya mansoor,nayi kewar ka sosai" rungume shi mansoor yayi yana cewa "lil bro saukar yaushe?"
"tunɗazu, ina ta zuba idon ganin ka, ya aiki?" shafa kanshi mansoor yayi yana faɗin "Alhmdllh,ya su ammy da auta?" muryar fatima su ka ji wacce fitowar ta kenan daga ɗakin kairiyya  tana cewa "gani anan yaya" juyawa mansoor yayi yana cewa "autar ammy, yan graduation kice tafiyar harda ke" ɓata fuska fatima tayi tana faɗin "ai ni fushi nake da ku kai da ya dr, ko ɗan text message na happy graduation" matsowa kusa da ita mansoor yayi yana faɗin "sorry lvly sis,ba haka bane munso muzo har lagos ɗin Allah ne bai nufa ba, amma kiyi haƙuri gift ɗinki na nan na ajiye maki" washe baki fatima tayi tana faɗin "tnxs big bro"
"to shikenan autar ammy ni zan shiga ciki na watsa ruwa " mansoor ya faɗa haɗi da nufar up stairs,"to sai ka fito "fatima ta faɗa" tashi noraiz da mahmud su ka yi su ka fice,fatima anan kan sofa suka zauna suna fira ita da sa'ada.

shazim daga wannan kwanciyar  bacci yayi awan gaba da shi ba shi bane ya tashi ba sai gab da magrib, yana tashi ya nufi toilet yayi wanka haɗi da alwala,sannan ya shirya ya fito  daga bedroom ɗin ya nufi dinning, abinci yaci kafin ya fice daga  part ɗin,ya nufi masallacin dake cikin estate ɗin,ana gama sallah ya fito ya nufi part ɗin uncle Ahmad,kairiyya da su fatima  ya samu a parlor,gaishe dashi kairiyya ta sake yi tana cewa "ya gajiyar tafiya ya  shazim " amsa mata yayi da Alhmdllh sannan yace "uncle fah?" yana sama ta bashi amsa, tashi yayi ya nufi up stairs ya shiga wani ɗan ƙaramin parlor, zaune uncle Ahmad yake kan carpet, mama na kusa da shi,sallama yayi ya shiga ciki, amsa mashi sallamar su kayi, wuri ya samu kan carpet ya zauna yana gaishe da su amsa mashi su kayi cikin kulawa uncle Ahmad na tambayar su malam da ammy "suna lafiya" uncle Ahmad ya ce "masha Allah, kaje wurin Ibrahim?" shazim yace "a'a yanzu dai zan tafi" uncle Ahmad yace
"to shikenan, bari sai ka ci dinner tukunnan sai ka tafi "
"bana jin yunwa uncle yanzu naci abinci" uncle ahmad yace "to shikenan tashi kaje wurin Ibrahim É—in"
da to shazim ya amsa haɗi da miƙewa ya fice,yana fita bedroom ɗin mansoor ya nufa, zaune ya same shi yana waya, harara ya watsa ma shazim, murmushi yayi haɗi da samun wuri kusa da shi ya zauna  yana faɗin"my lover bro,wannan hararar ta mi ce ce" katse wayar mansoor yayi yana faɗin "amma wallahi ka rainani shazim ni nema lover ɗin koh"
"eh mana yaya"
"ni nama manta nayi maka magana fushi nake da kai "
"kaina bisa wuya minayi kuma lover bro" duka mansoor ya kai mashi ya kauce "Allah zanyi maganin ka idan har baka daina ce man lover bro É—innan ba"
"sorry na dai na"
"da dai ya fiye maka,kuma ka tashi ni ka bani wuri"
"afuwan ya mansoor" juya mashi baya mansoor yayi yana faÉ—in
"ka tashi nace ka bani wuri" hannu shazim ya sa ya riƙe kunnuwanshi alamar ban haƙuri yana cewa "haba ya mansoor dan Allah fa" kallon shi mansoor yayi yace
"hmm,ya hanya,ya su ammy da malam"
"suna nan lafiya "
"masha Allah"
dafa kafaɗar shazim mansoor yayi sannan ya ce "bro wai miya faru ne ake ta kiran ka amma baka ɗaga waya wani time ɗin ma a kashe, kasan ka ɓatama su abbah rai sosai " kallon mansoor shazim yayi "yaya su abbah sun ta kura dole sai nayi aure ni kuma yanzu bana da ra'ayin yi"
"ƙanina kasan mi? " girgiza mashi kai shazim yayi,alamar a'a,ɗan nisawa mansoor yayi sannan yace "miyasa baka son yin aure yanzu, duk wani rufin asiri na duniya Allah ya baka shi,to miyasa bazaka godema ni'imar da yayi maka ba" kwantar da kanshi yayi saman kafaɗar mansoor sannan yace "yaya bawai bana son auran ba ne kwata kwata,a'a nafiso su ƙara man lokaci  har nasamu wacce take sona nake sonta, amma yaya kowa yaƙi fahimta ta"
shafa kanshi mansoor yayi yana faÉ—in "karka damu bro ni na fahimce ka in sha Allah suma su abbah za su fahimce ka"
"Allah yasa yaya"
"Ameen "( a kwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin shazim da mansoor, mansoor ya girmi shazim bawai sosai ba, tare su ka taso har makaranta tare suka yi)
"tashi muje part É—in uncle Ibrahim dan nasan ba inda kaje tunda ka zo"
"nayi baccine shiyyasa"
"ok tashi muje" tashi su kayi su ka fice direct part É—in uncle Ibrahim su ka nufa, bakin su É—auke da sallama suka shiga,momy su ka samu zaune kan sofa ita da aliyu, da gudu aliyu ya taso yayi hugging É—in shazim yana faÉ—in "oyoyo yaya" É—aga shi sama shazim yayi yana faÉ—in "haidar ya kake,ya school"
"lafiya lau yaya" masha Allah shazim ya faɗa haɗi da sauke shi ƙasa yana faɗin "momy anwuni lafiya"
"lafiya lau Alhmdllh,ya hanya, yasu ammy da malam"
"lafiya lau Alhmdllh" mansoor yace "momy ina wuni" 
"lafiya lau Alhmdllh, ya aiki "
"Alhmdllh momy,uncle na ciki ne"
"eh yana part É—in shi"
"ok  bari mu shiga momy" to momy tace, tashi su ka yi suka nufi corridor dake kallon parlorn ,wani ɗan ƙaramin parlor su ka shiga, shiru parlorn yake bakowa sai ƙarar tv da ta AC, mansoor ne yace su zauna may be uncle ɗin na ciki, zama su kayi kan sofa,muryar uncle Ibrahim su ka ji daga bedroom ɗinshi cikin faɗa yana cewa "wannan ai maganar banza ce maganar wofi, amma ka bani mamaki, to bari kaji tun wuri kasan yan da za'ayi" muryar wani matashin saurayi su kaji daga bedroom ɗin yana ba shi haƙuri "dan Allah dady kayi haƙuri,wallahi mistake aka samu amma in sha za'a dawo da su,ko yanzu nayi magana da c.p dake can yace sunanan suna binciken idan su ka shige da sun samu zasu sanar da ni"
"da dai yafi, dan bazan yi asarar million dollars ba a bazan, in ma ban da shashanci irin na yaran yanzu ina ake samun matsala irin haka ai tun can ya kamata ka duba bawai sai kun zo nan ba"
"sorry dady in sha Allah za su dawo"
"Allah ya sa,ina so yanzu daka fita kasake kiran c.p É—in kaji a wane mataki su ke"
"to" fitowa saurayin yayi da wani kallon yabi su shazim dake zaune kan sofa  sannan ya kama hanyar fita daga parlorn, mansoor ne ya daka mashi tsawa yana faɗin "kayi hauka ne luqman, sa'annin wasan ka ne mu daza kallemu ka wuce kafi ƙarfin ka gaishe da mu ne"
wanda aka kira da luqman ne yace "sorry yaya ban lura da kai ba ne"
"idan baka lura dani ba, baka ga shazim ba ne, ko kafi ƙarfin ka gaishe da shi ne??"
"a'a"
"oya koma ka gaishe shi kafin ranka ya ɓaci" juyawa luqman yayi ya koma cikin parlorn, sai da yaje har gaban shazim sannan ya ce "ina wuni ya hanya" idan har bango na magana to shazim ya amsa mashi gaisuwar, dan yi yayi kamar ma bai san da wata hallita ba wai luqman a parlorn, duk abun da ke faruwa uncle Ibrahim na tsaye bakin ƙofar badroom ɗin shi yana kallon su, sake gaishe da shi luqman yayi still bai amsa ba,gyaran murya uncle Ibrahim yayi, hakan yasa gaba ɗaya suka mai da hankali su kan shi,ƙarasowa yayi cikin parlorn yana faɗin "shazim baka ji ana gaishe da kai?" maimakon shazim ya bashi amsar tambayar da yayi mashi sai ma cewa yayi "uncle an wuni lafiya" ganin ya waske ne yasa uncle Ibrahim amsa mashi gaisuwar yanama luqman alama ya tafi da ido , ficewa luqman yayi daga parlorn ( luqman ɗan uncle Ibrahim ne, shine babban ɗan shi sai feenah daga feenah sai sa'ada da aliyu, uncle Ahmad kuma mansoor ne babba sai faisal daga faisal sai mahmud sai kairiyya sai salma ) 
Episode 22_23

Kallon shazim uncle Ibrahim yayi yana cewa "shazim ya su ammyn ku da malam?"
"lafiya lau su ke"
"to masha Allah,ya gajiyar  hanaya"
"Alhmdllh"
"ka shiga wurin innah kuwa?"
"a'a, daga part É—in uncle Ahmad nake, amma daga nan can zan tafi"
"haba shazim ai tun da kuka zo can ya kamata ku fara shiga, bawai sai yanzu ba"
"haka ne uncle, na É—an gaji ne to shine sai na É—an kwanta"
"ah to gaskiya tashi ku tafi,inya so sai ku dawo" da to suka amsa haɗi da miƙewa su ka nufi ƙofa, suna fita uncle Ibrahim ya ciro wayar shi daga aljihu dake ringing, picking yayi yanufi bedroom ɗin shi.
A bakin part É—in innah su ka tsaya shazim na faÉ—in "muna shiga da masifa zata tare ni na sani" murmushi mansoor yayi yana cewa "lamarin ka kai da innah ai sai Allah "
"ai big bro innar ce ta cika matsala "
"kai kuma baka ganin zarau sai ka tsinka "
"innar ce ai sai da irin haka "
"haka dai kace,wuce mu shiga karka ƙara bata lokaci tace da ka bari sai gobe" dariya su ka kwashe da ita yayin da su ke shiga part ɗin bakin su ɗauke da Sallama,feenah su ka samu kan sofa tana charting a wayarta, tashi tayi zaune tana amsa masu sallamar da suka yi, zama su kayi kana sofa, sai kallon shazim take, shi kuwa tun da suka shigo ya ɗauke kai kamar bai ganta ba,  mansoor ne yace "ina innah take?"
"yanzu ta shiga ciki"
"ok ce mata gamu nan"
ta miƙe kenan su kaji muryar innah tana faɗin "dama kunyi tafiyar ku dan bana da lokacin ku yanzu nima" murmushi shazim yayi a zuciyar shi yana faɗin "sarki,baki taɓa shanye raɗa" kamar daga sama yaji muryar innah na faɗin
"kayi murmushi mana tunda ga mahaukaciya sabon kamu na magana"
kallonta kawai shazim yayi batare da yace komai ba, hakan dayayi ne ya harzuƙa ta daman a harzuƙe take
"kai ni daina kallona da waÉ—annan idanun ka,karka cinye ni"
da buɗar bakin shazim sai cewa yayi "dagama kin samu ina maki kallon love" riƙe haɓa innah tayi tana faɗin
"riƙe kayan ka bana buƙata"
"ke dai da kin karɓa" tsaki innah ta ja tana faɗin "sai yanzu kayi lokacin zuwa ka gaishe ni kenan,ko ko sai yanzu uwar taka tace ka zo ka gaishe da ni? "
"kusan haka,yanzunma sa'a ki ka ci har ki ka ganni "
"ba shakka mara mutunci, to koh ita uwar taka in tazo bata isa tace sai lokacin da ta gadama zata gaishe dani ba, bare kai "
"kuma fa hakane, dole ta gaishe da ke kamar yanda ke ma ki ke gaishe da magabata, so ina ganin bawani abun tashin hankali bane" mamaki ne ya kashe innah takasa cewa komi, mi shazim yake nufi,ta shi shazim yayi yana faɗin "big bro ta shi muje bacci na ke ji" kallon innah yayi yana faɗin "asuba ta gari tsohuwa mai ran ƙarfe"  sannan yayi gaba abun shi sallama mansoor yayi mata haɗi da bin bayan shazim.
da harara innah ta raka shi tana faÉ—in "bauÉ—aÉ—É—e kawai maramunci" feenah wacce fitowarta kenan daga bedroom É—in Innah tace "wai miyasa ya shazim yake maki haka ne?"
"mi yasa fa,ai ba komi bane face abun  da uwar shi ta koya mashi, ai zanyi maganin su daga shi har ita,dani suke magana"
suna fita part É—in uncle Ahmad suka wuce zuwa bedroom É—in mansoor, zama shazim yayi bakin bed mansoor na tsaye yana waya shazim ne yace "nizan tafi na kwanta naga ka kama waya"
"ok sai da safe" ficewa shazim yayi ya nufi part ɗin su, yana shiga ya nufi bedroom ɗin shi kayan jikin shi ya rage ya shiga toilet, bayan kamar minti biyar ya fito ƙugunshi ɗaure da towel, clothes set ɗin shi ya nufa, pajamas ya ciro riga da wando masu taushi ya saka sannan ya nufi wayar shi dake haske alamar kira zama yayi bakin bed haɗi da ɗaukar wayar dan yaga mai kiran shi,majeed ne picking yayi
bakin shi ɗauke da sallama  "on the other hand majeed yace " mutanen abuja, ya gajiyar hanya"
"Alhmdllh majeed, ya aiki?"
"aiki alhmdllh, ina ka ajiye wayar ka ne ina ta kiran baka yi picking ba"
"wallahi kuwa majeed time É—in da ka kira ina bacci ne dana tashi kuma naje part É—in uncles É—ina ne,yanzu na dawo, ya ake ciki"
"dama maganar kayan da mu kayi order ne sun iso"
"masha Allah, ka duba duk abun da muka yi order sun sako mana shi "
"eh na duba, sai dai akwai matsala"
"matsala, tami fah? "
"ina jin sunyi mistake ne, dan gaskiya kayan da mukayi order basu su ka kawo mana ba amma ina tunanin mistake ne su ka samu,amma ka kira kaji"
"ok to shikenan, amma abun da mamaki "
"wallahi kuwa nima nayi mamaki sosai, musamman kayan dana gani a matsayi namu"
"wane irin kaya ne?"
"abun da mamaki, amma bari na turo maka kagani da idonka" ok kawai shazim yace haɗi dayin rejecting, ba'afi one minute ba sai ga saƙo ya shigo wayar,cikin saƙon ya shiga,yana buɗe saƙon karo ya ci da kayan maye iri iri masu matuƙar tsada da haɗari ga lafiya,  ɗan zaro idanu yayi yana faɗin "ya Allah, miye kuma wannan , daga ina, na waye??" ɗan dafe kanshi yayi, sai kuma can yayi dialing number majeed tana fara ringing yayi picking
"kana ji majeed, kasan mi za'ayi "
"a'a saika faÉ—a "
"kawai ku sa su a store, ba sai an maida masu ba, ina son na san ko na waye"
"to shikenan, amma ya za'ayi da magungunan da suka kusa ƙarewa "
"karka damu zan sake ordern wasu, amma waÉ—annan ku bar maganar su kawai har sai na dawo sannan "
"ok to shikenan, sai da safe"
"ok mu tashi lafiya" yace sannan yayi rejecting ɗin kiran,tashi yayi ya shiga toilet ya ɗauro alawala,bayan 2 minute ya fito ya nufi carpet da ya shimfiɗa ya kabbara sallah, yana gamawa ya ɗauki Qur'an, ya shiga karantawa ƙarar shigowar message yaji awayar shi sharewa yayi sai ga wani message ɗin ya sake shigowa
bai koma takan wayar ba har sai da ya kammala karatun sannan ya ɗauki wayar ya nufi switch ɗin ɗakin ya kashe light nan take   bedside lamps suka kawo,hawa yayi kan bed haɗi da jan blanket ya rufe iya waist ɗin shi, sai sannan ya jawo wayar, message ya gani da baƙuwar number buɗa message ɗin yayi,yana gama karantawa ya danna power yayi switching ɗin ta, adu'a yayi ya shafa sannan ya kashe bedside lamps,ƙara jan blanket yayi zuwa chaist ɗin shi cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi...

Washe gari

bayan ya dawo daga masallaci sallar asuba komawa yayi ya kwanta, sai wurin 8:30 ya  tashi yayi breakfast bayan ya gama ya nufi part ɗin uncles ɗin  shi  domin gaishe da su,daya je part ɗin uncle Ibrahim, bayan sun gaisa yake tambayar shi yaje ya gaishe da innah kuwa, ce mashi yayi eh bayan bai je ɗin ba yace eh ne dan ya san cewa zai yi yaje, shikuma bai shirya ma tujararta ba tun da safe, yana fita daga part ɗin bedroom ɗin mansoor ya nufa, yana shiga ya sameshi yana shirin tafiya office, gaisawa su ka yi, sannan mansoor yace mi zai hana ya bishi su tafi office ɗin tare, bai yi mashi musu ba, dan shi kwata kwata baya son zaman gida kamar mace a cewar shi, shiyyasa a kullum yake ma noraiz faɗa saboda zaman gida, shiryawa yayi  su ka tafi tare,sai da yamma liƙis sannan su ka dawo, a bakin ƙaramin gate ɗin estate ɗin mansoor ya hango  feenah ta fito daga motar wani saurayi, riga da wando ne a jikinta tayi rolling da ɗan ƙaramin gyale, sai waige waige take kamar tana tsoron wani ya ganta, kwata kwata bata lura da motar su ba tana sauri ta shiga,kallonta mansoor  kawai yayi har ta shige ciki sannan yace "narasa gane mike damun yarinyar nan,amma zanyi maganin ta" shazim ne yace
"lafiya dai ko bro,kai da wa??"
"ni da feenah mana kana nufin baka ganta ba" girgiza kai yayi alamar a'a, sarai ya ganta amma sai ya fake a bai ganta ba,dan shi gani yake kwata kwata babu abun da ya shafe shi da lamarin feenah, tun da iyayenta su na sane da abunda take, kuma tushen lalacewar ta daga kakarta ne tun da ita ke goya mata baya akan duk abunda take so, so mizai hana tayi abun da taga dama tunda ta samu É—aurin gindin kakarta da kuma mahaifin ta.
ta babban gate su ka shiga, sai masifa mansoor yake, shazim na jinshi bai ce komi ba
suna shiga ciki part ɗin innah  mansoor ya nufa, yana  parking yace ma shazim ya  fito su shiga su gaishe da innah,  shazim yace "gaskiya ni nagaji zan wuce ciki, anjima na zo na gaishe ta  kawai "
"miyasa bazaka shiga ba, duk fa yau bamu gaishe da ita ba, yaka mata ace ka zo mun shiga,bafa wani jimawa zamuyi ba, dan nasan bawani zuwa da za kayi, kawai ka fito mu shiga"
"nagaji ne bro, ka bari sai anjima  "
"Please bawani jimawa za muyi ba" ok kawai shazim yace ba dan yaso ba,ya so mansoor ɗin ya bari sai anjimar,fitowa yayi  haɗi da  bin bayan shi su ka shiga ciki,innah su ka samu zaune a parlor mai aikinta na mammatsa mata kafa,sallama su kayi haɗi da ne man wurin zama,gaishe da su mai aikin tayi, amsa mata suka yi   mansoor na faɗin "barka da yamma innah,ya gida"
"lafiya lau,ya aiki"
"Alhmdllh"
"shi wannan fanɗararen yafi ƙarfin ya gaishe ni ne"
"a'a innah, kin tari numfashin shi ne "
"bana ra'ayi ne yau "acewar shazim, hararar shi innah tayi tana faÉ—in
"riƙe kayar ka,bawai ina jiran taka bane"
taɓe baki yayi,yana faɗin "dama ance abun da baka samu haɗa shi da baka so " tsaki innah taja ba tare da ta sake cewa komi ba
sallamar feenah suka ji,yanzu sanye take da doguwar riga ta material saɓanin riga da wando da suka ganta da su  ɗazu a bakin gate,amsa mata sallamar suka yi,harara mansoor ya watsa mata,gaban ta ne ya ɗan faɗi ganin hararar da ya ke jifanta da shi ne dan ita a sanin ta bata yi mashi komai ba,wuri ta samu kusa da innah sannan ta kalli shazim tana faɗin "ina wuni Ya shazim" yi yayi kamar ma bai san da shi take ba,innah ce ta ja tsaki tana faɗin "Allah dai wadar mai wulaƙanta ɗan adam" banza yayi da ita duk da yasan da shi take, sosai sharetan da yayi ya sosa mata zuciya dan har idanunta sun tara kwalla, tana matuƙar son shazim amma sai wulaƙanta ta yake yana shareta kamar bai san daga inda ta fito ba, mai da idanun ta tayi kan mansoor tana faɗin "ina wuni ya mansoor" bai amsa mata gaisuwar ba sai ma hararar ta da yayi,innah ce tace" tofa yau ina ganin ikwan Allah, daga me shareta sai mai harara, kenan kai ma ka koyi baƙin hali irin nasu o'o" tsuke fuska shazim yayi dan ya san ba da kowa take ba face shi, kallon  yanda ya tsuke fuska tayi  tana faɗin "aikin banza aikin wofi,wai duk dan kar a raina shi" yanzu ɗauke kai shazim yayi kamar bai san dawa take ba, feenah da duk ta sha  jinin jikinta, tace ma mansoor  "Yaya  mi nayi ka ke hararata ne"
"zaki sani ne" innah ce tace
"wai lafiya mansoor, mi tayi ne"
"wallahi sai na bata É—an banzan kashi a gidannan" da buÉ—ar bakin innah sai cewa tayi "ai sai ingani tun da ka koma zalunci"
"wai miyasa innah ki ke haka ne, duk ke ke É—aure mata gindi take duk abun da ta gadama"
"to na ɗaure mata gindi sai aka yi yaya" kallon feenah mansoor yayi yana faɗin "wallahi kinji na faɗa maki duk ranar da kika bari na kama ki jikin ki sai ya faɗa maki shashasha kawai" turo baki tayi tana faɗin "dan Allah kayi haƙuri yaya ni ban san minayi maka ba "
"uban waye na ganki da shi yanzu a bakin gate, kinyi shiga kamar ba musluma ba?"
gaban ta ne ya faɗin, dan bata yi tunanin wani ya ganta ba,duk dan kar a ganta ne yasa tabiyo ta ƙaramin gate, kenan tanan shima ya biyo kuma hakan na nufin shazim ma ya ganta,ya salam, ƙatse mata tunani yayi ta hanyar cewa "tambayar ki nake? "
kame kame ta fara"am.... imm dama wani class mate ɗina ne" wanka mata mari mansoor yayi, ai ba shiri tayi bayan innah tana kuka, mansoor ne ya ɗaura da cewa  "ni za kiyi ma ƙarya,saboda kin rainani, ban hanaki bin wannan ɗan iskan yaron ba,saboda ban isa in faɗa maki kiji ba shine kuka koma haɗuwa waje yana ajiye ki a baya dan kar wani ya ganki ko?"
fashewa ta sake yi  da kuka tana faɗin "dan Allah kayi haƙuri,wallahi ba shi ba ne" hannu mansoor ya kai zai jawota daga bayan innah, kakkare ta innah tayi tana faɗin "wai miye haka mansoor so ka ke kaji mata ciwo ne, to wai ma miye a ciki dan ta kula shi kai waya san adadin matan da kake kulawa" duk wannan budiri da ake shazim na zaune yana daddana wayar shi hankali kwance kamar baya ɗaki,mansoor ne yace
"wallahi ko mi feenah tayi laifin ki ne innah, tun da ke ke goya mata baya "
"eh na goya mata bayan sai aka yi yaya, da Allah ni ku tashi ku bani wuri"
"haka za kice innah? "
"Eh haka na ce, sai akayi yaya"
"to shikenan" shine kawai abun da mansoor ya ce yaja hannun shazim su ka fice, da harara innah ta raka su har su ka fice,suna fita ta rufe feenah da faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba, haƙuri take ba innah akan bazata sake ba in sha Allah
"wannan kuma ke ki ka sani, kar Allah ma yasa ki daina, dan ni ba ruwana tun da duk abu da nake faÉ—a maki bawai yana shiga kunnen ki bane, abun da ki ka ga dama shi kawai ki ke yi"
"dan Allah kiyi haƙuri innah  wallahi  bazan sake ba, yanzun ma ban san za su ganni ba ne "
"karma ki daina, kina ji kina gani zakiyi ma kanki tsiya da kanki, kuma wallahi muddin baki shiga cikin hankalin ki ba, shi wanda ki ke son kina ji kina gani zaki rasa shi,a banza"
"in sha Allah na daina"
"da dai ya fiye maki"

Shazim suna fita daga part É—in innah part É—in su ya wuce shi da mansoor
a parlorn shi su ka ya da zango, mansoor ranshi duk a ɓace saboda feenah yasha hanata mu'amula da wannan saurayin amma ta ƙi daina wa saboda yasan halin yaron ɗan isaka ne amma bata ji,ga shigar banza iri iri ta iya,ta kasa gane abun da yake nuna mata,shazim ne ya fito daga bedroom ɗin shi,kayan jikin shi ya cire daga shi sai boxer da vest, dafa kafaɗar mansoor yayi yana faɗin "lafiya, tunanin mi ka ke?" ajiyar zuciya mansoor ya sauke yana faɗin "wallahi banajin daɗin abun da feenah take, ita kuma innah sai goya mata baya take"
"haba bro miyasa zaka damu kanka, duk fa wani abu da take laifin innah ne kuma uncle na gani"
"hakane shazim, amma da ban haushi kwata kwata innah bata kyautawa, ace yarinya na aikata ba dai dai ba amma ta hana a tsawatar mata"
"gaskiya kam bata kyautawa, amma da Allah ka share da komi ka je ka watsa ruwa"
"ok to shikenan" ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi hanyar fita yana faɗin "sai na dawo"
"ok sai ka dawo" shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi bedroom ɗinshi, toilet ya shiga bayan 5 minute sai gashi ya fito sanye da bathrobe, dressing mirror ya nufa mai ya shafa ma jikin sannan ya fesa turare bakin bed ɗin shi ya dawo haɗi da ɗaukar wayar shi yayi dialing number ammy, tana fara ringing tayi picking, sallama yayi sannan ya gaishe da ita, on the other hand ta amsa mashi cikin kulawa haɗi da tambayar shi ya su innah da su uncle ahmad, amsa ya bata da suna nan lafiya lau, sannan ta tambaye shi sun faɗa mashi dalilin kiran shi da su kayi
amsa ya bata da "a'a ba su faɗaman  ba"
"to shikenan, ina auta da me babban suna? "
"auta na part É—in uncle Ibrahim wurin sa'ada, mai babban suna kuma na part É—in uncle ahmad wurin mahmud, ni ka É—ai su ka bari"
"a'a kaima laifin ka ne, ai da sai ka sauka wurin mansoor"
"a'a nafi jin daÉ—in zama ni ka É—ai ne "
"to ai kai ka sani" sun ɗanjima suna waya sannan suka yi sallama, malam ya kira su ka gaisa har da ummy, shima malam sun ɗan jima suna tattaunawa sannan shima suka yi sallama, kwanciya yayi kan bed ɗin cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi, hara sai da mansoor ya zo sannan ya tashe shi suka wuce masallaci saboda anfara kiran sallar magrib, sai da suka tsaya akayi har  isha sannan suka fito, daga masallaci part ɗin uncle Ibrahim su ka shiga, a part ɗinshi su ka same shi, bayan sun gaisa ne yake tambayar sunyi maga da uncle ahmad, amsa shazim ya bashi da a'a
"amma mi yasa muke kiran ka ba mu samun ka?? " ɗan sunnar da kai yayi dan bai taɓa tunanin uncle Ibrahim zai mashi magana akan hakan ba duk da yasan dole zasu tambaye shi, jin yayi shiru ne yasa uncle Ibrahim cewa "magana nake kayi shiru baka ce komi ba" amsa ya bashi da "bakomi kawai  yana yin  aiki ne" ɗan jin jina kai uncle Ibrahim yayi duk da ya san yana sane yasa ba'a samun shi a waya, amma a zahiri sai ya ce "to shikenan Allah ya kyauta gaba" da ameen su ka amsa,canza firar uncle Ibrahim yayi zuwa wata, sun ɗan jima  awurin shi dan anan suka yi dinner tare da shi, sai wuraren ƙarfe shaɗaya saura su ka baro part ɗin,rabuwa su ka yi da mansoor  kowa ya nufi part ɗin su, shazim ko daya shiga part ɗin su bedroom ɗinshi ya nufa, laptop ɗinshi ya ciro daga cikin bag ɗin shi ya shiga aiki, ba shi bane ya kwanta ba sai ɗaya saura sannan ya kashe laptop ɗin ya nufi toilet ya ɗauro alwala, ya dawo ya kabbara sallah, ya jima yana nafilfilu sannan ya tashi ya nufi bed ɗin shi bayan ya kashe bulbs ɗin ɗakin,kwantawa yayi haɗi da jan blanket ya rufe jikin shi, bai jima da kwanciya ba bacci yayi awan gaba dashi...
Episode 24_25

WASHE GARI

tun da safe suka fita shi da mansoor, sai da yamma liƙis su ka dawo a gajiye, shazim part ɗin su ya nufa, wanka yayi ya ɗan kwanta, duk da ya san bacci a lokacin bai da amfani, amma haka nan ya kwanta saboda ba ƙarmar gajiya ya kwaso ba, cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi, ba shine ya tashi ba sai gab da magrib, toilet ya shiga ya sake wani wankan da alwala, sannan ya shirya cikin wani farin yadi, ficewa yayi zuwa part ɗin uncle Ahmad wurin mansoor, a parlor ya ci karo da mansoor, juyawa yayi suka wuce masallaci, sai da suka yi har sallar isha tukun suka fito daga masallacin, part ɗin uncle Ibrahim suka nufa, aliyu ka ɗai suka samu a parlor yana kallon cartoon, ya na jin sallamar su ya nufi shazim da gudu, ɗaukar shi shazim yayi yana faɗin "sai kai ka ɗai, ina su momy?"
"tana part É—in dady" sauke shi shazim yayi yana faÉ—in "to yayi, tafi ka cigaba da kallon ka" to aliyu yace haÉ—i da komawa kan sofa ya zauna yan cigaba da kallon shi, mansoor yace "aliyu shazim ka É—ai ka sani ko"
"a'a, ai kai kullum muna tare " murmushi kawai mansoor yayi, haÉ—i da cewa "ok haka ne, ai shazim É—in zai tafi zai barni da kai, babu ruwana da kai daga yanzu"
"sorry ya mansoor, wasa fa nake "
"ba wani nan" shazim yace "ƙyale shi kaji, idan zan tafi da kai zan tafi ai, kana zuwa lagos koh" ɗaga mashi kai Aliyu yayi yana dariya, mansoor yace "zamu gani ai" aliyu sai tsalle yake zai bi shazim lagos.
sama su ka wuce zuwa parlorn uncle Ibrahim, zaune yake shi da momy da alama suna tattaunawa ne, sallama su ka yi haÉ—i da shiga ciki, amsa masu sallamar su kayi, wuri suka samu kan sofa suka zauna,gaishe da uncle Ibrahim da momy su kayi, amsa masu gaisuwar su kayi uncle Ibrahim na tambayar su ya aiki, da Alhmdllh suka amsa, ta shi momy tayi ta fice,fira su ke jefi jefi, luqman ne ya shigo kamar wan da aka jeho yana faÉ—in dady! dady!! ,binshi su ka yi da idanu, mansoor ne yace "lafiya ka ke luqman zaka shigo wuri ba sallama kamar wanda aka jeho"
"kullum faɗa nake masa saboda ɗabi'ar banza da ta wofi,ko kafiri bai shiga wuri ba sallama bare kai ɗan musilmi, kiran mi ka ke man haka?" duƙar da kan shi yayi ƙasa yana faɗin "bakomi" bai son yin maganar saboda su shazim daya gani,mansoor da shazim sun fahimci bai son yin maganar ne saboda ya gan su, fahimtar hakan ne yasa uncle Ibrahim cewa "fice to ka bani wuri" ba musu ya kama hanya ya fice,tsaki uncle Ibrahim yaja yana faɗin "lamarin luqman sai adu'a"
mansoor ya ce
"narasa mike damun shi uncle, tun da suka fita karatu waje É—abi'un shi su ka sauya"
"hakane, Allah ya shirya" da ameen mansoor ya amsa, shazim dai na jinsu amma baice komi ba, sai da uncle Ibrahim yace "shazim kayi shiru kamar baka a wurin"
"uncle wai ni "
"a kwai wani shazim É—in ne anan bayan kai" murmushi kawai yayi ba tare da yace komiba, uncle Ibrahim yana lure da shazim duk wani abu idan ya shafi luqman da feenah to fah ba ruwanshi,duk kuwa abunda zai same su .
mansoor ya ce
"uncle bari mu wuce sai da safe, shazim tashi mu tafi" tashi shazim yayi yana cema uncle Ibrahim "sai da safe uncle "
"Allah ya tashe mu lafiya"da ameen su ka amsa, haɗi da ficewa suka bar part ɗin, tashi uncle Ibrahim yayi ya fita daga parlorn shima,bedroom ɗin luqman ya nufa, tura ƙofar yayi ya shiga, samun shi yayi yana safa da marwa, sai kai kawo yake cikin ɗaki, a hanzarce ya juyo jin an buɗe kofa,ganin mahaifin shi ne yasa ya nufe shi da sauri yana faɗin "dady daman wannan cp dake bincike ne ya kira ni yace sun samu idan suke sai dai basu da tabbaci, amma suna nan suna bincike da sun tabbatar za su kira ni, ya kira wayarka baka yi picking ba shi ne ya kirani, shi ne nazo faɗa maka ban san wannan ɗan rainin wayau yananan ba shi da ya mansoor "
uncle Ibrahim yace "ok,wayar tana bedroom É—ina ne ban san ya kira ba, naji daÉ—in jin haka"
"dady yanzu zaka maido man da motata da ka amsa ko"
"cewa nayi sai sun bayyana sannan"
"Please dady "
"kama bar bani haƙuri, dan ba baka zanyi ba har sai na gansu ido da ido tukunnan, kaga daga yau idan na saka ka abu ba zaka sake shashanci ba"
"dan Allah dady ka bani, in sha Allah hakan ba zata sake faruwa "
uncle Ibrahim yace
"ni kaga tafiya ta,daga yau sai ka kiyaye" yana gama faÉ—a ya fice daga É—aki.

Suna fita daga part É—in uncle Ibrahim, part É—in su shazim suka nufa, a parlor su ka ya da zango, wayar mansoor dake cikin aljihun wandon shi ce ta fara ringing,ciro ta yayi yana kallon screen É—in wayar baby shine sunan daya bayyana, murmushi yayi haÉ—i da picking yana faÉ—in "sorry beb, yanzu nake shirin kiran ki" muryar mace ce tace "bawani nan, da ban kiraka yanzu ba da ba zaka kirani ba"
"haba dear ya za kice haka, kin san da ace na gama abun da nake da zan kira ki"
"hmm dama haka za kace"
"haba dear,please kiyi haƙuri"
tsaki shazim yaja yana faɗin "rainin wayau" hararar shi mansoor yayi yana nuna shi da ɗan yatsa, taɓe baki yayi haɗi da cewa "rainin wayau mana, ka zauna ƙaramar yarinya ta maida ka kamar wani wawa" harara kawai mansoor ya maka mashi ba tare da ya ce komi ba ya cigaba da wayar shi.
hannu yasa ya riƙe kunnan shi yana faɗin "afuwan na kama,bazan sake ba Please" ta shi shazim yayi ya fize wayar daga kunnan mansoor yayi rejecting,da kallo mansoor ya bi shi,rasa mi ma zai ce mashi yayi, gaba ɗaya ya kashe shi da mamaki sai kace shi akace ya kama kunne, komawa yayi mazaunin shi ya zauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sai wani cin magani yake, matsowa kusa da shi mansoor yayi yana faɗin "ɗan rainin wayau bani wayata"
"wallahi bazan ba da ba"
"saboda wayar ka ce?"
"ko ba tau bace bazan ba da ba, tunda kai zubar ma kan ka aji ba komi bane a wurin ka ba"
"dallah ka bani wayata, ina ruwanka koma mi zanyi"
"wallahi kaji kunya, wai yarinya zata saka ka kama kunne, kamar wani teddyn wasan ta "
"ko Æ´ar tsana ta É—auke ni ina ruwanka tunda ba kai ta É—auka ba"
"Allah ma ya kiyaye, wane ita sai dai irinku da kuka raina kanku"
"wallahi ina tausayin ka shazim, duk randa so yayi maka mugun kamu, zaka gane baka da wayau"
"haba dai, ko zanyi so ba irin naka ba na rainin wayau"
"in dai da rai zamu gani, zaka zo nan ne ka same ni kana kuka saboda mace"
"Allah ma ya kiyaye, nafi ƙarfin mace tasa na zubar da hawaye, sai dai kai, dan da alama har kuka kake mata"
"hmmm shazim kenan, idan da rai da lafiya zamu gani ai"
"ba abun da zaka gani sai alkairi, dan Allah muma bar wannan zancen"
"za'a yi shi ne wata rana"
"naji koma yaushe za'ayi shi" kai kawai mansoor ya girgiza yana murmushi ba tare da yace komi ba, sun É—an jima suna fira daga bisani mansoor yayi mashi sallam ya fice.
tashi shima yayi ya nufi bedroom É—in sa, toilet ya shiga ya É—auro alwala
yayi shafa'i da wutiri yana gamawa ya nufi bed É—in sa bayan ya kashe bulbs É—in É—akin hada bedside lamp, wayar shi da ya ajiye kan bedside drawer ce ta fara ringing , hannu yasa ya jawo wayar yana duba mai kiran shi unknown number ce, tsaki yaja haÉ—i da rejecting,yana rejecting wani kiran ya sake shigowa "wai waye wannan zai ta kura man ne" ya faÉ—a haÉ—i da sake rejecting kiran, sai ga message ya shigo buÉ—e message É—in yayi yana karantawa, yana kammala karantawa, tsaki ya sake ja, kashe wayar yayi baki É—aya, blanket yaja ya rufe jikinshi gaba É—aya.

washe gari weekend

Momy ce da su sa'ada a kitchen suna haÉ—a breakfast feenah ta shigo jikinta sanye da pajamas masu santsi white color, sun bi shape É—in jinkata kanta sanye da black É—in hula, hugging É—in momy tayi ta baya "ina kwana momy "
"lafiya lau, kin tashi kenan? "
fatima tace
"ina kwna aunty feenah "
banza tayi da fatima har sai da momy tace baki ji ana gaishe da ke ne
"naji "
"ok amsawar ce baki iyawa "
kallon fatima feenah tayi tana faÉ—in
"lafiya" tsaki momy ta ja haɗi da mai da kanta kan abun da take, fatima ma nunawa tayi ko ajikinta abun da feenah tayi mata,abun yayi matuƙar ɓata ran sa'ada kasa daurewa tayi har sai da tace "gaskiya aunty feenah abun da ki ke baki kyautawa"
"ni ki ke gaya ma haka"
momy tace "ai gskiya ta faÉ—i" jan hannun fatima sa'ada tayi sai hura hanci take tace "zu mu fita parlor "
"a'a bari mugama aikin "
"ki zo kawai mu tafi " da hararar feenah ta raka sa'ada "zan kamaki ne yarinya, zaki san wa ki ke hura ma hanci"
kallon momy tayi tana faÉ—in
"mi ki ke dafawa ne momy?"
"to acici ban sani ba"
"momy dan Allah ki dai na ceman acici"
"bazan dai na ba" bubbuga ƙafa ta shiga yi cike da shagwaɓa, luqman shigowar shi kenan kitchen ɗi yaga feenah nama momy shagwaɓa,daga shi sai boxer black color, mangare mata kai yayi yan faɗin "sakaryar banza ji kayan dake jikin ki, ko kunya ba kyaji, ko  aliyu bazai yi  abun da ki ke ba "
"ina ruwan ka dani da zaka dake ni mugu kawai, kai bakaga kayan dake jikin ka ba sai ni azzalumi "
"ke dan ubanki ni ki ke faÉ—ama haka"
"eh an faÉ—a maka"
duka yazo kai mata da gudu ta ɓoye bayan momy, ture ta momy tayi tana faɗin "matsa ki bani wuri mara kunyar banza, kai kuma fice ka bani wuri "
"haba momy yaza kice haka, rashin kunya fa take man,kuma ji kayan dake jikinta"
"fice nace ka bani wuri kai ba ka ga kayan dake jikin naka bane, ko kunya baka ji da ƙannan ka ka ke irin wannan shigar kana yawo cikin gida" gwalo feenah tayi mashi
"wallahi zan kama ki ne "yana faɗa ya wuce kamar zai tashi sama, kallon feenah momy tayi tana faɗin "kema wuce kije ki canza waɗannan kayan tun kafin ranki ya yi mummunan ɓaci"
"haba momy, miye aibun wannan kayan dan Allah "
"ki fice nace "
"dan Allah momy kiyi haƙuri" banza momy tayi da ita, kama ma momy tayi suka kammala breakfast ɗin,mai aikin momy ce ta shigo ta kwashe flaks ta kai dinning,dawowa tayi tana faɗin "momy ina na yallabai shazim yake"
"gashinan " momy ta faɗa haɗi da miƙama mai aikin, carab feenah ta amshe flaks ɗin daga hannun momy tana faɗin "jeki kawai zan kai masa"
"A'a hajiya da kin kawo na kai masa"
"nace kije zan kai masa"da to mai aikin ta amsa haÉ—i da ficewa ta bar kitchen É—in, fita itama feenah tayi tana faÉ—in "momy bari na kai masa na dawo" bata jira mi momy za tace ba kawai ta fice.

kwance yake a bedroom ɗin sa,cikin bacci yaji ana nocking ƙofar bedroom ɗin sa, farkawa yayi ba tare da ya motsa ba ya dai buɗe idon shi, sake nocking ɗin kofar aka yi, ta shi yayi ya nufi ƙofar ya buɗe, feenah ce tsaye , kallon sama da ƙasa ya sahiga binta da shi, ganin kallon da yake mata ne ya sata duƙar da kai "ina kwana ya shazim" bai amsa mata gaisuwar ba sai cewa yayi "mi ya kawo ki part ɗi na?"
"yaya dama momyce tace na kawo maka breakfast " juyawa yayi yana faÉ—in
"ok kina iya ajiyewa kan dinning "
"haba ya shazim, dan Allah wai mi nayi maka a rayuwa ne ka ke wulaƙan ta ni, ko gaisuwa ta baka amsawa"
shigewa yayi cikin bedroom ɗin batare da ya bata amsa tambayar da tayi mashi ba, kamar ta fashe da kuka saboda tsabar baƙinci, tarasa mi tayi ma shazim ya tsane ta a duniyar nan, kwata kwata baya ƙaunar ta ya tsane ta, parlor ta koma kan dinning ta ajiye mashi haɗi da ficewa tana sharar ƙwalla, tana shiga part ɗin su ɗakinta ta nufa, kan bed ta faɗa, sai a lokacin ta fashe da kuka.

wanka yayi sannan ya fice ba tare da yaci abinci ba zuwa part ɗin uncle Ahmad,sai da ya gaishe da mama sannan ya wuce sama wurin uncle Ahmad,gaisawa su kayi ya nufi bedroom ɗin mansoor,tura ƙofar yayi bakin shi ɗauke da sallama, zaune yake yana aiki cikin laptop , ɗago da kan shi yana kallon shi "ai nayi tunanin sai na zo tukun zaka tashi? "
"ai da ka zo É—in"
"kunyi waya da A hashim kuwa?" girgiza mashi kai shazim yayi alamar a'a "ya kirani É—azu yake ce man ya kira ka bai samu ba"
"na kashe wayata ne da zanyi bacci may be ya kira ya ji a kashe"
"to ba mamki, sai ka kira shi"
ok kawai yace, wayar shi ya jawo yayi dialing number kairiyya, tana picking yace "ki kawo man breakfast part É—in mansoor" yana gama faÉ—a yayi rejecting ba tare da ya tsaya yaji mi kairiyya za tace ba, kallon shi mansoor yayi yana faÉ—in "É—azu fa da su fatima su ka shigo mama tace su zo su kaimaka breakfast su ka ce sun baro feenah zata kai maka, bata kai maka ba? "
"ta kai"
"to mi yasa ba ka ci ba?"
"saboda bana jin yunwa lokacin"
"ba ka jin yunwa ko ko dai baza kaci ba saboda ita ta kawo, wai mi yasa ka ke haka ne shazim "
"dan Allah ka rabu dani, bana ji yunwa ne lokacin, yanzu kuma ina ji, shi ne kawai"
girgiza kai kawai mansoor yayi ba tare da yace komi ba ya mai da kan shi kan aikin da yake, nocking ɗin kofar aka yi, ba da izinin shiga mansoor yayi, kairiyya ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama hannunta riƙe da tray, amsa mata sallama suka yi, ƙasa ta ajiye trayn tana jawo center table ta ajiye gaban shazim tana faɗin "ina kwana ya shazim" da lafiya lau ya amsa mata, tray ta ɗaura kan table ɗin tayi serving ɗin shi,thanks yace haɗi da ɗaukar spoon ya fara cin abincin, ficewa tayi daga ɗakin, a hankali yake cin soyayen arish kamar baya son ci,sai da yaja time kafin ya kammala, wayar shi dake gefan shi ce ta fara ringing, ɗaukar wayar yayi yana duba mai kiran, ammy ce, picking yayi haɗi da sallama yace,on the other side ammy ta amsa mashi sallamar tana faɗin "mutanen abuja "
shafa sumar kanshi yayi yana faÉ—in "ina kwana ammy"
"lafiya lau,ya uncles ɗinka da innah"
"suna nan lafiya"
"ina gaishe da su,ina Auta ta, na kira wayar ta bata ɗauka ba "
"yanzu haka ta jefata wani wuri "
"to idan ka ganta kace ta kirani" da to ya amsa yana faɗin "ammy ga mansoor za ku gaisa" ya faɗa haɗi da miƙama mansoor ɗin wayar, amsa yayi yana kara wayar a kunnen shi, gaisawa su kayi ammy na faɗin "mansoor kayi mana hijira koh "
"a'a ammy aikine ke riƙe ni"
"dama ku ai baku da wani excuse sai na aiki, yaushe rabon ka da zuwa lagos"
"in sha Allah ina nan zuwa "
"to Allah ya yarda, ka gaishe man da su baban ka"
"za su ji in sha Allah "
"to nagode" ammy ta faɗa haɗi da yin rejecting, miƙama shazim wayar yayi, amsa yayi yan dialing number malam   ringing ɗaya biyu malam yayi picking, gaishe da shi shazim yayi, cikin kulawa ya amsa mashi yana tambayar ya Abuja, sun ɗan jima suna magana daga bisani su ka yi sallama, majeed ya kira amma tana ringing ba'a ɗauka ba, mai da akalar kiran yayi kan A hashim, shima tana ringing ba ai picking ba, ajiye wayar yayi kusa da shi, fira suke shiga yi shi  da mansoor jefi jefi, har lokacin sallar zuhur yayi, ta shi su ka yi suka ɗauro alwala su ka  fice a main parlor su ka ci karo da kairiyya ta fito daga kitchen mansoor ne yace ta shiga part ɗin shi ta kwaso kayan breakfast ɗin da takai ma shazim da to ta amsa haɗi da nufar part ɗin sa, ficewa suka yi zuwa masallaci, da aka gama sallah mansoor yace su shiga part ɗin innah, da sallama suka shiga part ɗin bakowa sai mai akin innah da ta fito daga kitchen jin ana sallama, amsa masu sallamar tayi tana gaishe su haɗi da cewa, innah ta shiga sallah yanzu, ok mansoor yace wuri su ka samu kan sofa su ka zauna, shazim wayar shi da ke cikin aljihu ya ciro yana ɗan daddana ta, fitowa innah tayi hannun ta riƙe da ɗan kwalinta kanta duk furfura an mata kitson zane guda shidda da yake tana da suma ba laifi, kallon su tayi tana riƙe haɓa "ku kuma daga ina da wannan ranar" mansoor yace "ina wuni innah" lafiya lau ta amsa, kallon shazim dake ta aiki dangwala waya innah tayi tana cewa "shi kuma wanccan ya fi ƙarfin ya gaishe ni ne ko mi"ɗan taɓa shi mansoor yayi "ana magana"
É—ago da kanshi yayi yan kallon mansoor yace "ni wai" wani kallon raini wayau mansoor yayi mashi jin tambayar da yake mashi bayan yasan tun da innah ta shigo ya san da shigowar ta, innah ce tace "a'a ba kai ba mu É—an rainin hankali " murmushi shazim yayi haÉ—i dacewa "anwuni lafiya, ai ban san kin fito ba ranki ya daÉ—e" tsaki innah ta ja tana faÉ—in "da ban wuni ba zaka ganni haka ne?"
da murmushi a fuskar shi yace "ai ban sani ba"
"ai kin banza" shi ne kawai abun da innah tace, basu wani jima ba suka fice daga part É—in, da harara innah ta raka su har suka fice, parking space suka nufa, motar Shazim suka shiga, estate É—in suka bari

✨KATSINA ✨

Zaune su ke kan carpet bayan sun gabatar da sallar Asr , suna a nan zaune mom ta shigo ɗakin jikinta sanye da gown ta shadda white color anmata kwalliya da black ɗin net, hannunta riƙe da hijab da jaka da alama fita za tayi, gaishe da ita suka yi Aairah na faɗin "mom har kin shirya"
"eh na shirya, ku tashi kuje  kitchen baaba larai na can tana aiki ku kama mata "
"to mom yaushe zaki dawo "
"sai dare gaskiya, dan daga gidan granny zan shiga gidan safiya, sai dai dare"
Aairah tace "da na san zaki can da tun É—azo muka shirya mu ka bi ki "
"A'a ko da kun shirya bazan je ko ina da ku ba"
"saboda mi mom "
"koma saboda mi, ku bari wani lokacin kun tafi" hanyar fita mom ta kama tana faɗin "ku ta so kuje ku kama mata aikin" da to suka amsa suna tashi su ka bi bayanta, har compound suka rakata abie subka samu tsaye jikin mota yana jiran mom, tare zasu fita zai ajiye ta gidan granny shi kuma zai wuce gidan dadi,  a dawo lafiya su ka yi masu sannan su ka koma ciki, kitchen suka nufa wurin baaba larai, kama mata aikin suka yi suna ɗan fira, sun ɗan jima suna aiki sai gab da magrib suka kammala, cema baaba larai su kai ta tafi kawai zasu gyara kitchen ɗin da jera abinci kan dinning, da to baaba larai ta amsa haɗi da ficewa ta nufi ɗakinta, Aairah ta kaima su bala na su dinner ɗin Aaimah kuma ta jera kan dinning, sai da suka tabbatar sun kammala duk wani abu da ya dace sannan su ka nufi ɗakin su domin yin sallah, bayan sun gama sallah parlor suka dawo zama suka yi suna kallo,har akayi sallar isha, ɗaki suka koma domin gabatar da sallar, sai bayan sallar isha mom da abie suka dawo, dinner su kayi, bayan sun kammala su Aairah suka nufi ɗaki domin bacci.
Episode 26_27

Wayar Aairah ce ta fara ringing, Aaimah cewa tayi "to ni sai da safe, dan nasan indai ya mus'af ne to ke kam ba yanzu ba,  duba mai kiran tayi, mus'af ne picking tayi fuskarta ɗauke da murmushi  tace "hubby barka da dare "
"barkan ki dai my love, ya gida "
"lafiya lau "cikin sauƙin soyayya suke wayar, anan mus'af yake sanar da ita next week  zai wuce UK (can ya koma da karatun) , Aairah kamar tayi kuka dan taso ace suna ƙasa ɗaya da shi,  bata son yayi mata nisa, ta dai yi mashi fatan alkairi sun ɗan jima suna waya daga bisani su ka yi sallama.

✨SHAZIM✨

tsaye ya ke bakin window ya riƙe curtain  (labule)   yana waya da A hashim, fuskar shi  a sake su ke fira,A hashim na cewa "saboda mansoor ne kawai zan shigo gobe amma ba dan kai zanzo ba"
"to ko yanzun ma kar ka shigo tunda ina nan"
"kai dai kawai saboda mansoor "
"ai da kayi zaman ka"
sun ɗan ɗauki tsawan lokaci suna fira sannan su kayi sallama,ya juya kenan zai bar bakin window  ya hangi wasu manyan truck's guda ukku suna shigowa  cikin estate ɗin da alama  ta ƙaramin gate su ka shigo,mamaki ne ya kama shi,waɗannan  truck's daga ina kuma minene su ka ɗauko, ya jima tsaye yana kallon truck's ɗin har suka yi parking a bakin  babban store ɗin estate ɗin, mutum uku uku ne su ka fito daga cikin kowace truck, bayan truck ɗin da ke gaba su ka nufa, mutum biyu ne su ka buɗe truck ɗin su ka shiga miƙoma sauran wasu manyan kwalaye suna shiga da shi cikin store ɗin,  barin bakin window yayi       ya nufi toilet ya ɗauro alwala, sallah ya gabatar ko da ya gama sallah ya jima zaune kan carpet  bai ta shi ba, tunani ya shiga yi game da kwalayen da yaga masu truck ɗin na shiga da su cikin store,shin kwalin minene, kuma na waye,  ya jima a zaune  har sai da ya fara jin  bacci sannan ya ta shi ya kashe light ɗin ɗakin ya  nufi bed ya kwanta, bai jima da kwanciya ba bacci yayi awan gaba da shi.
washe gari kamar jiya feenah ta kawo ma shazim breakfast kamar yan da ya tsallake jiya baici ba haka ma yau baici ba ya nufi part É—in uncle Ahmad a can yayi breakfast tare da mansoor,fita su kayi shi da mansoor.

✨KATSINA✨

zaune su ke kan dinning suna breakfast, kallon abie Aaimah tayi tana faÉ—in "abie dan Allah idan zaka je gidan dadi ka tafi da mu"
"safiya ce yanzu ku bari sai da yamma sai kuje "
Aairah tace
"dan Allah abie, muna so ne muyi mata wuni "girgiza kai mom tayi tana faɗin "ku shikenan tunda aka ce ba school daga nan ƙafafuwan ku suka dai na zama wuri ɗaya "
"ba haka bane mom mun jima ba muje gidan ba ne "
"ba ma kunjima baku je ba, ina tunanin ko ranar friday kunje gidan" Aaimah tace "dan Allah dai mom" abie ne yace
"kuyi sauri ku shirya "
haɗa baki suka yi wurin cewa "yawwa abie  mungode "da sauri suka bar dinning area suka nufi bedroom ɗin su.

abie ne a parlor tsaye yana  jiran su Aairah , mom ce ke saukowa daga stairs case jikinsa sanye da jallabiya black color, wurin abie ta nufo tana faɗin "ba su fito ba ko "
"eh kinsan su da shiririta, duk taƙare tafiya zanyi idan ya so daga baya mudi ya kai su"
"afuwan abie ga mu nan" cikin sauri suke taka stairs case ɗin, sanye su ke da hijab har ƙasa onion color ,ƙarasowa su kayi, kallon mom abie yayi yace "sai mun dawo " a dawo lafiya tayi masu haɗi da juyawa ta nufi kitchen, fita su kayi abie na gaba suna bin shi a baya har compound, motar su ka shiga, Aaimah na gaba kusa da abie yayin da Aairah take baya,  fira suke cikin kwanciyar hankali har suka iso gidan dadi,horn abie yayi a bakin gate mai gadi ne ya leƙo ganin motar abie yasa shi komawa ciki da sauri,ya  buɗe mashi gate, ya shiga ciki parking lot ya nufa, sai da ya gama daidaita parking ya kashe motar Aairah ce ta fara fitowa sannan sai Aaimah, jiran abie su ka yi har ya fito su ka shiga cikin gidan tare,cikin parlor su ka shiga suna sallama tsit parlorn yake  babu kowa,wuri abie ya samu kan sofa ya zauna har zasu nufi ɗakin  Aunty Rabi sai gata ta fito tana amsa masu sallamar da su kayi, gaishe da ita su Aairah su kayi da fara'a a fuskarta ta amsa masu sannan ta nufi wurin abie "yaya ina kwana "
"lafiya lau, ya gidan "
"Alhmdllh"
"mama na ciki ne?" abie ya tambaya
"eh tana ciki "
"bari na shiga mu gaisa "da to Aunty Rabi ta amsa, ta shi abie yayi ya nufi bedroom ɗin dadi, zaune take kan sallaya ta gama sallar walha  tana adu'a, zama abie yayi gefan gadonta har sai da ta gama adu'a, waigowa tayi tana kallon abie ta ce "Muhammad kai ne tafe?"
"eh mama, ina kwana "
"lafiya lau, ya su kubra "
"suna nan lafiya, tana gaishe ki "
"ina amsawa"su Aairah ne su ka shigo da gudu su ka nufi dadi suna faɗin "dadi munyi kewar ki" basu ƙarasa ba abie ya dakatar da su da  faɗin "lafiyar ku lau kuwa,za ku wani nufe ta da gudu haka, salan ku danne mata ƙafafu bayan kun san fama take dasu,Allah yasa in ƙara ganin irin haka" ya faɗa cikin faɗa, tsayawa su ka yi suna kallon dadi kamar za su yi kuka
dadi tace "a'a da ka barsu ƙafafu ai sunyi  lafiya  ba abun da zasu man"
"kar kice  haka mama,ji fa yanda suka nufe ki da gudu, wani lokacin jinsu su ke kamar wasu ƙananun yara"
"duk da haka dai da ka barsu, ku zo nan" dadi ta faɗa tana miƙa masu hannu, matsawa suka yi kusa da ita su ka zauna "ina kwna dadi "
"lafiya lau, ya gida "
"lafiya lau"
"masha Allah" fira su ka shiga yi da dadi, abie dai na zaune yana jin su, tashi yayi yana faÉ—in "mama ni zan wuce "
"zauna ina son magana da kai" komawa abie yayi ya zauna yana faÉ—in "to Allah ya sa lafiya"
"lafiya lau" ta faɗa tana kallon su Aairah ta ce ku ɗan  bamu wuri " da to suka amsa haɗi da ta shi suka fice,  dadi tace " dama magana ne akan ɗana, tun ranar da nayi maku magana kai da mustafa ban sake jin wani ya ce komi ba dangane da maganar " ɗan nisawa abie yayi sannan ya ce
"haka ne mama, naje har garin na ku, amma ban samu wanda yace ya san inda ya koma ba, an dai ce man a kwai  wani  abokin baban sa  da suke  kasuwanci tare, amma yanzu baya garin, lokacin da  bai da lafiya babban ɗansa yazo ya tafi da shi, sun dai faɗa man ɗanna sa yana kaduna da zama"hannu dadi ta ɗaga sama tana faɗin
" ya Allah, Allah ka bayyanar da shi, hankalina ta shi yake duk lokacin da nayi mafarkin habiba,ban riƙe amana ba "  ta faɗa hawaye na  sauka a fukar ta,lallashin ta abie ya shiga yi,    hannu yasa ya  share mata hawaye yana faɗin
"ki dai na  kuka mama, in sha Allah za'a gan shi, ki daina cewa ba ki riƙe amana ba Allah yaga niyyar ki"
"Muhammad dole na ce haka, amanar yaron nan ta bar man , da ace da ubansa ya nuna bazai bar man shi ba na cigaba da kula da shi ina ziyartar shi, amma  sai  na fita batun shi, kaga kuwa ban kyauta ba "
"kiyi haƙuri komai zai wuce da izinin ubangiji, za muyi iya bakin ƙoƙarin mu ganin mun samu in da yake "
"to Allah ya yarda "
"Ameen " abie ya ce
"Muhammad wai ya jikin abokin ka, kwana biyu ba muyi waya da safwan ba da mahaifiyar shi  , ban kuma tambaye ka  ba "
"jiya munyi waya da safwan, ya sanar min an ma kusa sallamar shi , ya nemi alfarmar a bar shi can wurin su"
"ai gara yayi zaman shi can, ko dan saboda azzaluman mutanen nan "
"gaskiya a gani na gara ya dawo nan, har Allah yasa memoryn shi ya dawo"
"to Allah ya ƙara sauki , amma kana ganin idan ya dawo ƙasar nan  mutanen nan zasu barshi, baza su cigaba da bibiyar  rayuwar shi ba "
"haka ne muddin suka san yana raye baza su ƙyale shi ba,ko da nace ya dawo nan bawai zai koma can bane, a nan zai zauna tare da mu har memoryn shi ya dawo ya tuna da iyalan shi,ta hakan ne za mu iya samun  sa'a akan su, amma idan yana can ba lallai ne ya iya tuna baya ba "
"gaskiya hakan shi ya fi, dan ya ji jiki da da ƙarar kwana da tuni sun kashe shi, kuma yan da ya manta da abun da ya faru za su iya ƙara cutar da shi muddin ya koma " ɗan nisawa abie yayi yace
"haka ne, shi da yake mahaifin safwan kwanan shi sun ƙare shiyyasa suka samu galaba a kan shi har su ka  kashe shi"
"insha Allah  , Allah zai toni asirin su"
"Ameen, burina kwai ya dawo cikin hayyacin shi, ya tuna da baya "
" ameen, Allah ya bashi lafiya " da ameen abie ya amsa, sun É—an jima suna tattaunawa akan abokin abie, daga baya yayi ma dadi sallama, parlor dadi ta nufa wurin su Aairah da Aunty Rabi.

✨Abuja✨

Zaune ya ke kan carpet  a parlor yana aiki a laptop, sanye yake da  short black color iya gwiwar sa,  sai t_shirt ita ma black color, wayar sa da kan hannun sofa ce ta fara ringing , jawo ta yayi haɗi da du ba mai kiran, murmushi yayi ganin A  hashim, picking yayi tun kafin yace wani abu A hashim yace " hey man  gani a bakin gate ɗin estate, kasan halin securityn ku da ɓakar tambaya "
"kai kuma tambayar ce baka so?"
"ni dai ka kira su bana son surutun tsiya"
"ai kuwa sai dai kai ta tsayuwa, dama ba kace wurin mansoor ka zo ba, to mi ya hana baka kira mansoor ɗin ba, shi sai ya kira su   "
"ok dan na kira ka shine zaka ɓata man lokaci, Allah ko ka kira su su barni na shigo  ko na koma in da na fito "
"yo ka kuma "kashe wayar A hashim yayi ba tare da yace komai ba, number ɗaya daga cikin security ya kira  yana faɗin "ɗan rainin hankalin yana iya komawa " picking security yayi yana faɗin "good evening sir"ba tare da ya amsa gaisuwar ba yace  "friend  ɗi na na waje ku bar shi ya shi "
"ok sir "security ya faÉ—a, rejecting kiran yayi, aikin sa ya ci gaba.

security ne ya nufi motar A hashim da ke bakin main gate , baƙar mota ce ƙirar ferrari 250 ta sha tinted, security na ƙara so wa, hannu ya sa yayi  nocking window  motar , sauke glass a kayi a hankali, arba nayi da kyakyawar fuskar ( DR ABDALLAH MUHAMMAD HASHIM , A HASHIM,  BI MA'ANA YA ABDALLAH  ) sanye yake da farin yadi, ya sha ɗinkin zamani, kallon security yayi yace"barka da aiki"
"Alhmdllh, dama yallaɓe shazim ne yace ka shigo" ok kawai ya abdallah yace, reverse yayi ya nufi cikin estate ɗin, direct part ɗin uncle Ahmad ya nufa, parking yayi a parking lot,dai daita parking yayi, wayar shi ya ciro daga aljihun gaban rigar shi number mansoor ya lalubo haɗi da dialing, bugu ɗaya mansoor ya ɗauka yana faɗin "ka iso ne , kana bakin gate"
"gani a parking space na shigo ciki"
"ok, ai da ka shigo "
"ka fito dai mu shiga tare"
"ka ji ka sai kace estate ɗin baƙon ka ne, gani nan zuwa " ok ya Abdallah yace haɗi da yin rejecting,fitowa yayi daga cikin motar ya jingina da ita yana jiran isowar mansoor,  bayan kamar seconds goma sai ga mansoor ya fito, parking ya nufo wurin shi,yana iso wa suka yi hugging ɗin juna cike da farin cikin haɗuwa da juna mansoor ya ce"barka da zuwa, ya KT"
"KT Alhmdllh yasu abbah da mama "
"lafiya lau suke, kwana da yawa"
"Alhmdllh "
"ka kira shazim kuwa?" mansoor ya tambaya,  ɗan ya tsine fuska ya abdallah yayi yana cewa "rabu da ɗan rainin wayau kawai"murmushi mansoor yayi yana cewa "ai kun fi kusa, da man can ku sababbu ne,sai in baku haɗu ba,  mu shiga daga ciki ku gaisa da mama  mun tsaya a waje muna ta surutu" ok ya abdallah yace, ciki suka nufa,main parlor suka shiga bakin su ɗauke da sallama, kairiyya ce da su fatima  a parlor, jin sallamar su ya sa su waigowa, ware idanu fatima tayi tana faɗin "ya dr a abuja" da gudun gaske  ta nufe shi za tayi hugging ɗin shi tana faɗin "ya dr a abuja, un believable" tareta mansoor yayi yana faɗin "yau ina ganin ikwan Allah, hugging ɗin sa za kiyi a gaba na "duƙar da kai fatima tayi tana faɗin "a'a yaya nayi missing ɗin shi ne sosai"bin ta da wani kallon mansoor yayi yana faɗin "to sannu" ya abdallah ne yace "rabu da shi kawai fatima " ma tsowa tayi kusa da shi batare da tayi hugging ɗin shi ba tace "ya dr, nayi mamki sosai, dama kana abuja shine ko ka faɗa man zaka zo bayan ka san ina abuja "
"sorry fatima , na ƙi faɗa maki ne dan nayi surprise ɗin ki,  ya kike"
"lafiya lau yaya, amma a nan zaka kwana ko? "
"a'a, anjima zan tafi" bubbuga ƙafa fatima ta shiga yi "haba dan Allah yaya, gaskiya nan zaka kwana" muryar kairiyya su kaji tana cewa "watao ya abdallah fatima kawai ka gani ko, har muke gaishe da kai ni da sa'ada  baka ji ba " murmushi yayi "no ba haka bane kairiyya, ya kike ya kwana da yawa"
"lafiya lau alhmdllh, ya hanya "
"Alhmdllh "
"ya abdallah nima kenan baka ganni ba ko"sa'ada ta faɗa tana turo baki "sa'adatu  sa'ar mata, ya gida"
"lafiya lau ya kt da su mom"
"suna nan lafiya "
mansoor ne ya ja hannun shi yana faɗin "mu shiga ciki ka zauna, idan ka biye masu za ku kwana ne a tsaye "bin bayan mansoor yayi har cikin parlor, zama yayi kan sofa, kusa da shi fatima ta zo ta zauna, sai sakin murmushi take kamar gonar auduga, ba ƙaramin farin ciki tayi ba da ganin abdallah
"sa'ada shiga ki kira mama" mansoor ya faɗa,da to ta amsa tana nufar bedroom ɗin mama, ta shi kairiyya tayi zuwa kitchen  "ruwa da lemu ta   kawo mashi " sake komawa kitchen ɗin tayi sai gata ta fito ɗauke  da wani bowl ci ke da yankakun fruit ta ajiye gaban shi, tnxs yace haɗi da ɗaukar ruwa ya sha,fitowa sa'ada tayi mama na bayan ta har suka iso parlor, zama mama tayi kan sofa,"abdallah yau kai ne a garin namu "
"eh mama, ina wuni, na same ku lafiya"
"lafiya lau abdallah, ya su momy ku da uncle ɗin ka  "
"lafiya lau su ke "
"masha Allah " ta shi mama tayi ta koma ɗakin ta, kairiyya ma tashi tayi ta dalilin kiran wayar ta da a kayi, ya rage parlorn daga mansoor, abdallah, fatima da kuma sa'ada, sai zuba mashi fira fatima take wani ya bata amsa wani kuma yayi murmushi, sun ɗan jima tare da su fatima har aka fara kiran sallar magrib, sannan su ka shiga ɗakin kairiyya do min gabatar da sallah su kuma suka nufi masallaci,a can ya abdallah su ka haɗu da shazim, yi yayi kamar ma bai gansu ba, murmushi kawai mansoor yayi yana girgiza kai, ya san shazim yana wannan fushin ne saboda Abdallah ,  bayan an sallame sallah, suka fito daga masallacin,tsayawa su kayi har sai da uncle ahmad da uncle Ibrahim su ka fito abdallah ya gaisa da su, suna tambayar shi su mom da abie "suna nan lafiya "
uncle Ahmad ya ce "masha Allah, ya uncle É—in ka "
"yana nan lafiya "
"ina gaishe da shi "uncle ahmad yace, tafiya su ka yi shi da uncle Ibrahim,  sai a lokacin abdallah suka gaisa da shazim,ta fiya suke shazim  na faɗin "ai nayi tunanin tun tuni ka tsufa da komawa gidan uncle"
"É—an rainin wayau ai ba dan kai na shigo ba"
"hmmm koma dai miye, sannun ka da zuwa,  ya hanya  "
"yawwa, Alhmdllh, ya kwana biyu  "
"Alhmdllh" ya faɗa a dai dai time ɗin da su ke kawowa part ɗin su shazim , ciki su ka shiga ba kowa a parlor,dama shazim ne ka ɗai ke zama part ɗin,noraiz da man tun ranar da suka zo ya koma part ɗin uncle Ahmad da zama,  direct sama su ka nufa part ɗin shazim, a parlor su ka ya da zango, abdallah na cewa "wai shazim yaushe zaka je katsina"
"zanje in sha Allah, amma saboda mom da abie zani amma ba dan kai ba "
"ya kamata dai, har yanzu fa mom bata sanka ba, gara ma abie kun taɓa haɗuwa sau ɗaya" mansoor ya ce "gaskiya baka kyauta ba, ace duk tsawan shekarun nan baka taɓa zuwa katsina ba, gaskiya nayi mamaki"
shazim ya ce "to ni dai ya isa haka kar ku cinye ni, katsina dai ce ko to zani in sha Allah " Allah ya yarda, suka faÉ—a, fira su ka shiga ta yaushe gamo, sai da aka kira sallar isha sannan su ka tashi su ka nufi masallaci, bayan sun fito daga masallaci part É—in uncle ahmad su ka nufa, suna tafiya shazim yace "amma zaka kwana nan ko"
"a'a komai dare sai na koma gidan uncle "
"pls ka kwana nan"
"sai ranar da kaje katsina sannan zan kwana nan"
shazim ya ce"kai ka sani kuma wannan, kar Allah yasa kwana " time ɗin da su ke shiga cikin main parlor,  kamar ɗazu ma fatima da sa'ada su ka samu a parlor suna kallo,sallama su kayi, amsa masu sallamar su kayi , sama mansoor ya wuce ya bar su a parlor "ya dr har na yi tunanin ka tafi" fatima ta faɗa
"ina nan ban tafi ba"
"zaka kwana nan É—in"
"a'a yanzu zan tafi "
"dan Allah ya dr ba dan ni ba " sa'ada ma tace "pls yaya,mi yasa ba zaka kwana ba "
"ba komi sa'ada " fatima tace "pls ya shazim kasa baki dan Allah ya kwana" Fatima ta faÉ—a tana kallon shazim,da buÉ—ar bakin shi sai cewa yayi
"idan ya kwana wani abun zai maki ne? "
girgiza kai fatima tayi tana faɗin "a'a kawai dai naga mun  daɗe ba mu haɗu ba " 
" to tun da babu abun da zai maki karki damu mutane" kwal kwal fatima tayi da idanu alamar kuka, kallon shazim Abdallah yayi yana ta ɓe baki yana faɗin
"kar ki damu zan dawo gobe in sha Allah "
"pls ka kwana dai dan Allah"
"shikenan fatima zan kwana saboda ke " taɓe baki shazim yayi yana faɗin "aikin banza "
abdallah ya ce "wannan kuma kai ta shafa, É—an rainin wayau " tashi fatima tayi su ka je kitchen ita da sa'ada,
"wallahi kaji kunya wai fatima zata saka kwana "
"ina ruwan ka kuma " tsaki shazim yaja yana faÉ—in "girma dai ya faÉ—i"
"ya daɗe bai faɗi ba" mansoor ne ya fito "ina ta jiran ku shigo, naji ku shiru" ta shi su kayi su ka bi bayan mansoor ba tare da sun ce komi ba, a parlorn shi suka zauna, fira suke cikin kwanciyar hankali, nocking su kaji, mansoor ne yace wanen,"fatima ce yaya, " ok shigo kawai mansoor ya faɗa, turo ƙofar su kayi ita da sa'ada kowace  hannun ta  ɗauke da tray, kan center table su ka ajiye fatima na faɗin "ya dr ga dinner" tnxs abdallah  yace, ficewa su kayi ita da sa'ada, mansoor ne yayi serving ɗin su. kan carpet su ka zauna suna cin abinci, da suka gama mansoor ya kira fatima ta zo ta kwashe dishes  ɗin, fira su ka ɗan taɓa, sai wurin 9:30 su ka yi mansoor sallama su ka nufi part ɗin su shazim, suna tafe suna fira,suna kawo bakin part ɗin su shazim, mota ce shararo da gudu  ta shigo estate ɗin ta ƙaramin gate,bin   motar su kayi da kallo har tayi parking a part ɗin uncle Ibrahim, mace ce ta fito daga motar, jikin ta sanye da hijab har ƙasa,fuskar ta da  face mask ,cire face mask ɗin tayi,  tazo ta gaban su zata wuce,taɓo shazim abdallah yayi yana faɗin...
Episode 28_29

Taɓo shazim Abdallah yayi yana faɗin
"dude wannan ba É—iyar uncle Ibrahim bace feenah?" yayi maganar yana nuna mashi ita lokacin da zata shiga part É—in su, sauri kawai take batama lura da su ba
kallonta sosai  shazim yayi, sai a lokacin ya gane ta , ce wa yayi "ita ce, wani abun ne? " girgiza ya Abdallah yayi yana faɗin "amma daga ina take a wannan lokacin, sai kace ba mace ba "
amsa shazim ya bashi da "sai ka bita ciki  ka tambayeta, tun da ka fara aikin jarida ban sani ba " murmushi ya Abdallah yayi yana cewa "kai fa matsalar ka kenan, daga tambaya sai ɓakar magana" shazim ya ce "ai kai ne da shiga abun da ba ruwan ka, ni ina zan san daga ina take "
"dole nai magana, naga ƙanwar ka ce"
"duk da ƙanwa tace, ban san daga ina take ba a wannan lokacin, kuma iyayen ta suna sane" ya faɗa haɗi da jan hannun Abdallah yana faɗin "dan Allah ma wuce mu shiga ciki, kasa mun tsaya muna maganar da bata da amfani "ciki su ka wuce,a bedroom ɗin  shazim suka yada zango , zama Abdallah yayi kan bed, shazim kuma ya shiga toilet,Abdallah  wayar shi ya ɗauka yayi dialing number uncle Ahmad bugu biyu ya ɗauka, tun kafin Abdallah yace wani abu uncle ahmad yace "Abdallah lafiya baka dawo ba har yanzu "
"a nan zan kwana ne uncle "
"ok to shikenan, sai da safe"
"Allah ya tashe mu lafiya" da ameen uncle ya amsa, rejecting É—in kiran Abdallah ya yi, fitowa shazim yayi daga toilet jikin sa sanye da bath robe , clothes set É—in shi ya nufa, pajamas ya É—auko ash color ya sa, ta shi Abdallah yayi shima yayi wanka, pajamas shazim ya É—auko mashi white color ya sa kwanaciya su kayi suna fira sama sama har bacci yayi awan gaba da su.

washe gari
tare da mansoor su ka dawo part É—in daga sallar subhi
fatima da sa'ada ne su ka kawo masu breakfast.

✨LAGOS✨

EKO

zaune su ke a reception maryam ce ta kalli hidaya tana faɗin "wai har yanzu dr jikin ne yasa bai zo hospital ba tsawan wannan kwanakin" ɗan nisawa hidaya tayi sannan tace"maryam nima ban sani ba, gashi ina kiran shi bai taɓa ɗauka ba, amma ina tunanin dan yaga baƙuwar number ne yasa bai ɗauka"
maryam tace"ba mamaki, may be shima yana cikin mutanen da basu ɗaukar baƙuwar number, Allah dai yasa lafiya, kwana biyu da bai zo ba" Ameen " hidaya tace "har nayi tunanin tambayar dr kabir sai kuma na fasa, kar yayi tunanin wani abu "
"a'a da kin tambaye shi, ba abun da zai yi tunanin, tun da yasan dr boss É—in ki ne kina da right É—in da zaki tambayi lafiyar shi "
"haka ne kuma, idan naje office ɗin shi anjima zan tambaye shi naji, wallahi duk na damu da rashin shi  kwana biyu,fata na dai ace yana lafiya"
"in sha Allah lafiya lau yake "
"Allah ya yarda " da ameen maryam ta amsa, canza firar su kayi zuwa wata, har lokacin da zasu fara aiki yayi kowa ya tashi ya nufi aikin gaban sa, hidaya tattara files É—in patient tayi ta nufi office É—in dr kabir, bakinta da sallama ta shiga, zaune yake yana du ba wasu paper's, gaishe da shi tayi tana faÉ—in "dr ga files É—in patient, za su iya fara shigowa "
eh ya bata amsa,haka ta shiga tura mashi patient har lokacin sallah yayi, da katawa yayi ya nufi masallaci domin yin sallah, sai da ya dawo daga masallaci hidaya ta same da tambayar dr shazim, cewa kabir yayi "a fuwan ban faɗa maki ba, yana abuja ne wurin uncle's ɗin shi, shiyyasa ki kaga  
kwana biyu baya zuwa, amma ba kin amshi number shi ba ai da kin kira shi "
"eh, idan nakira ne baya É—auka "
"gaskiya ba zai ɗauka ba dan ba kasafai yake ɗaukar baƙuwar number ba ba, amma nasan in sha Allah next week zai dawo "
"to Allah ya kaimu nagode "
"ba komi "dr yace, ficewa tayi daga office É—in ta koma reception wurin maryam, sanar da ita tayi yanda su kayi da dr kabir, maryam tace "dama duk yawan aikin da dr yake da shi, har yana iya barin garinnan da sunan ziyara ba aiki ba "
"to aiko gashi nan " hidaya ta faÉ—a, maryam tace "wai nikam na tambaye ki mana?"
"ina sauraron ki" hidaya ta faÉ—a
"kin kuwa tura mashi text É—in da muka yi magana da ke "
"na tura mashi ma"
"kai aikuwa ina ganin shine dalilin da yasa da ki ka kira shi bai É—auka ba"
"a'a gaskiya, saboda da number mama na kira shi, kawai dai baya ɗaga baƙuwar number ne"
"Allah dai yasa ya karanta "
" zai yi wahala ace bai duba ba  "
"haka ne "
"kar ki damu, ki cigaba da tura mashi nasan wataran zai du ba "
"to Allah ya sa " da ameen maryam ta amsa, tashi su kayi suka nufi office É—in da suke zama, suna shiga tar kacen su su ka haÉ—a domin lokacin tashin su yayi.

✨KATSINA✨

Abie ne da uncle mustafa a garden suna tattaunawa game abokin abie da za'a sallama daga asibiti zai dawo nigeria, uncle mustafa ne yace "yaushe safwan É—in yace zasu sallame shi"
"yace man next week su ke sa ran a sallame shi "
"to Allah ya kai mu next week É—in" ameen abie yace
" amma yaya kana ganin ko a nan baza su iya bibiyar shi ba "
"insha Allah baza su taɓa sanin yana raye ba, har sai lokacin da asirin su zai tonu, su duk a tunanin su ya daɗe da mutuwa "
"Allah dai ya toni asirin mutanen nan, sun cutar wannan bawan Allah kamar mi, da da ƙarar kwana da tuni sun kashe shi "
"haka ne yaya shi da yake mahaifin safwan kwanan shi sun kare  ,ai sun kashe shi"
"kisa na wulakanci ma ,amma ai Allah na nan zai toni asirin su tun a nan duniya kafin kiyama "
"haka ne kam "
Abie tace"burina bai wuce naga memoryn shi ya dawo ba,da a ce lokacin da na mai da shi China na rika bibiyar iyalin shi da ko baya nan zan iya hada hujjujin da zan maka su a court ,amma yanzu dole sai yana cikin hayyacin shi zan iya hada duk wata hujja da nake nema "
"haka ne kam dole sai ya dawo cikin hankalin shi ,Allah dai ya bashi lafiya"
"shiyyasa nace idan an sallame shi zan dawo da shi Nigeria,saboda dole sai a nan zai iya ganin abun da zai sa yatuna da baya har a samu memory shi ya dawo"
"haka ne ,amma yaya idan su ka dawo ina zasu zauna"
"shi kadai zai dawo ban da safwan da mahaifiyar shi ,saboda mahaifiyar shi ta tsorata sosai ,ko da safwan din yace zai zauna bazata bari ba  "
"ai dole ta tsorata ,baji bagani aka kashe mata miji,kisan wulakan ci"
Su Aairah ne su ka shigo garden din dauke da  bowl din fruit da ruwa da lemu ,kan table din dake wurin su ka ajiye masu ,suna gaishe da uncle mustaf ,amsa masu yayi yana fadin "anata hutu ko ,ya hutun " da Alhmdllh su ka amsa hadin da barin garden din ,kallon abie uncle mustafa yayi yace"yaushe za su yi joining university ne ,naji wasu makarantun har sun fara lectures "
abie yace "Abdallah nake jira ya dawo daga abuja ,komai na makarantar su yana hannun shi "
"gaskiya ya kamata ya hanzarta ,yaushe ya ce zai dawo "
"yace man dai next week za su dawo shida Ahmad din ,na san ya san wasu makarantun sun fara lectures"
"ya kamata gaskiya ya hanzarta "
abie yace "su matsalar ne sun nace ne akan dole sai sun tafi wani gari ba su son nan"
"da gaskiyar su yaya ,gara su fita inda idanun su zai kara budewa ,ko ba komai zasu iya mu'amula da wasu mutanen "
"haka ne ,ni bakomi yasa bana son su yi nesa dani ba ,kasan halinsu wani lokacin ba jin magana suke ba"
"haba yaya duk rashin jin su sun kai ihsan ne ,amma haka nan na turata jos karatu  duk da a gidan kanwar mahaifiyar ta take da zama ,ka bisu da adu'a kawai ba abun da zai faru da su in sha Allah, idan ma tsoron tura su kake inda ba su san kowa ba ,ai ga abuja sai su zauna gidan Ahmad ,kaga duk lokacin da su ka tashi daga lectures gida zasu dawo"
"hakan dai ne zai fi ,dan zaman hostel ne bana so ,zan kira Ahmad din inyaso kafin su zo sai su  nema masu admission"
" to shikenn yaya  hakan yayi,Allah ya taimaka "

ameen abie yace ,canza firar su kayi zuwa wata ,sun jima a garden din suna tattaunawa har sai da lokacin sallah yayi ,sannan su ka tashi su ka nufi masallaci .

✨ABUJA✨

Momy ce ta fito daga bedroom dinta ,numfashi taja a zuciyar ta tace "wannan kamshin daga ina kuma " kitchen dan tana kyautata zaton daga canne , tana tun karar kitchen kamar  ana huro mata mashi , tun a bakin kofar kitchen take fadin "wai yau mi ake girka  mana ne ,gida duk ya cika da kamshi " ta fada yayin da take Shiva cikin kitchen din ,turus ta tsaya ganin fatima da sa'ada sai kai kawo suke a kitchen aiki kawai suke bilhakki
"to fah kace yan mata na ne a kitchen,duk su ka ciki gida da kamshi, ashe yau zan ci girkin manya  " fatima tace "yawwa momy daman neman mai testing  muke "
"to a zubo man, naji Æ´aÆ´an nawa sun iya girki"
sa'ada ta shiga  buɗe ma momy  warmers, bin abinci da kallo momy tayi tana faɗin "kai masha Allah, wannan ko bakai testing ba kasan ya yai daɗi " plate da serving spoon sa'ada ta ɗauko ta zuba ma momy fried  rice da cos low spoon ta sa mata haɗi da mi ƙa mata tace " momy gashi "amsa momy tayi tana samu wuri  kan kujerar da ke kitchen ɗin ta zauna,spoon ɗaya tayi, sai kallon su tayi tana zaro ido,faɗuwa gaban su yayi kar ace abicin bai yi daɗi ba sai faɗin "momy miya faru "su ke, murmushi momy ta saki tana faɗin "kai masha Allah, wannan girki naku yayi daɗi sosai masha Allah " rungume juna su kayi suna tsalle suna faɗin "mun gode momy " feenah ce ta shigo tana ya tsine fuska da alama daga bacci take "kukuma lafiya, kuke ta ihu duk kunbi kun addabi mutane "  tsayawa su ka yi da murnar da su keyi su kai, sa'ada tace "girki fa mu kai, kuma momy tace yayi daɗi, shine muke murna " tsaki feenah taja "girki kodai jagwalgwalo,ku nan har wani girki ku ka iya " hararar ta momy tayi tana faɗin
"ki fara ci kiji kafin ki kushe masu girki " zaro ido feenah tayi tana faÉ—in "wah ni, Allah ya kiyaye " sa'ada tace
"wallahi Aunty feenah kin dai san munfi ki iya girki "  jinjina kai feenah tayi "ke ni kike faɗama haka "
"yo ai gaskiya na faɗa " duka ta kaima sa'ada da sauri ta ɓoye bayan momy "momy wai daga faɗar gaskiya zata dake ni " dukan ta sake kai mata a bayan momyn, fatima dai na tsaye tana binsu da idanu, riƙe hannun feenah momy tayi "kar ki sake ki dakar man yarinya, koma mi ta faɗa maki ke ki ja, idan bazaki yabi girkin su ba ai bai kamata ki kushe masu ba"
"amma momy baki ji mi tace man ba "
"koma mi tace, ai ba ƙarya tayi ba, kin iya girkin ne " ran feenah in yai dubu to ya ɓaci jin momy ta goyi bayan sa'ada
"momy wai miyasa kike haka duk abun da sa'ada zata man idan na ce zan dake ta sai ki hana "
"dole na hana, saboda komi tai maki laifin ki yafi yawa "
"shikenan momy tun da haka ki kace " tana gama faɗa ta wuce fuuuuu kamar zata tashi sama, sa'ada tace azuciyar ta  "nasan daga nan sai part ɗin innah"
babu wanda ya bi ta kan feenah daga momy har  fatima, aikin dake gaban su suka kama, sai da suka kammala komi suka jera abincin kan dinning,Abdallah kuma cikin basket suka jera mashi shi da shazim, dama girkin saboda shi su kayi shi bayan sun gama su ka wuce bedroom ɗin sa'ada domin yin wanka, fatima ta fara shiga wanka sa'ada kuma ta ɗauko masu kayan da zasu sa, fatima na fitowa sa'ada ta shiga , shaf shaf suka shirya su ka fice zuwa kitchen, basket ɗin da suka jera ma Abdallah suka ɗauka, direct part ɗin su shazim suka nufa,tsit part ɗin kamar ba kowa, sama su ka wuce zuwa bedroom ɗin shazim, sa'ada ce tayi nocking shiru ba'a basu izinin shigaba sake nocking ɗin tayi still shiru, fatima tace "ko dai suna part ɗin uncle Ahmad "
"ba mamaki suna can "
fatima tace "amma bari nayi nocking ɗin ɗakin ya noor may be shi yana nan" juyawa tayi zuwa bedroom ɗin noraiz tun kafin tayi nocking a ka buɗe ƙofar , noraiz ne  ya fito   shi da mahmud da alama fita zasu yi, bim su da kallo su kayi noraiz yace "ku kuma lafiya ku kayi curko curko da basket a hannu  "
fatima ce tace "daman su ya dr  muka kawo ma abinci, munyi nocking shiru"
"to ku ajiye kan dinning mana"
"a'a gaskiya ya noor, idan kuma basu dawo part É—in ba da wuri fa, zai iya yin sanyi "
"to tun da gudun yayi sanyi kuke mu sai ku bamu muci "
"a'a wallahi ya noor, ba fa naku bane, idan zaku ci yana can part ɗin momy" mahmud yace  "mu da yake bamu da galihu ko "
"ni ba haka nake nufi ba" hannun noraiz ya ja "wuce mu tafi" ficewa su kayi su fatima su ka bi bayan su zuwa part ɗin uncle Ahmad,suna shiga part ɗin mansoor su ka nufa, nocking su kayi, izinin shiga aka basu, tura ƙofar su kayi suka shiga zaune su ka samu Abdallah da mansoor shazim na kwance kan three seater idanuwan shi a rufe da a lama bacci yake, sallam su kayi, amsa masu sallamar su kayi "ina wuni ya dr " fatima tace,  gaishe da shi sa'ada tayi, amsa masu yayi cikin kulawa, sai sannan suka gaishe da mansoor ƙin amsawa yayi sai ma hararar su da yayi "ok sai yanzu kuka san da zamana ko " haɗa baki su kayi wurin faɗin
"a'a yaya "
"ba wani nan, ai na san zaman da nake da ku "
"a'a yaya "
"shikenan dai, mi aka dafa mana, naji tun da kuka shigo nake jin ƙamshi " fatima tace "abun daɗi, kuma na ya dr ne " zaro ido mansoor yayi "ai haka, abun ƴar wariyar launin fatace kenan dai " dariya fatima tayi
"wasa fa nake yaya, kaima kasan na ku ne" fatima sun shantake sai surutu su ke ganin boss na bacci,firar su kawai su ke, abun da basi sani ba idon shi biyu yana jin su banza kawai yayi da su, sai da yaji da gaske ba fita zasu yi ba sun samu wurin zama yasa shi buÉ—e ido yana faÉ—in "ke tashi ku ba mutane wuri " simi simi suka tashi su ka fice, mansoor ne yace "miye haka zaka wani kore su "
"an kore su ɗin " banza kawai mansoor yayi da shi bai sake cewa komi ba, tsaki Abdallah yaja yana faɗin "sai kace wani kafi rashin san surutu, zaka wani kore su " ta shi yayi ya nufi bedroom ɗin mansoor batare da yace masu ƙala ba, suma fita lamarin shi su kayi, mansoor ne yayi serving ɗin su basu jira fitowar shazim ba su ka kama cin abincin su, lokacin da zai fito har sun kusa kammalawa, zama yayi yana cema mansoor  "nima sai ka zuba man ko"
"in dai ni zan zuba maka sai dai kar kaci É—an rainin hankali " É—aukar plate shazim yayi yana zuba abinci ba tare da ya sake ce ma mansoor É—in komi ba.
fira mansoor da Abdallah su ke shazim kuma na cin abinci, da ya kammala fatima ya kira ta kwashe dishes É—in,

sai da yamma liƙis Abdallah ya koma gidan uncle ahmad , fatima kamar tayi kuka, sai da yace mata zai dawo tukunnan ta haƙura, tare su ka tafi da shazim da mansoor a motar Abdallah, Abdallah ke driving mansoor na kusa da shi yayin da shazim ke baya, fira suke shazim na baya yana jin su amma bai sa masu baki ba har suka iso gidan uncle ahmad.
Episode 30_31

Horn Abdallah yayi a bakin gate ɗin gidan, ta ƙaramar ƙofa mai gadin gidan ya leƙo ganin motar Abdallah yasa ya koma da sauri ya buɗe mashi gate, ciki ya shiga da motar ya nufi parking lot yayi parking.

Kai masha Allah gidan ya haɗu ba'a cewa  komi,  part biyu ne gidan,ɗaya yafi ɗaya girma,ba laifi gidan yana da girma,
fitowa su kayi suka nufi ƙaramin part ɗin,   ciki su ka shiga bakin su ɗauke da sallama, wata yar matashiyar budurwa su ka samu a parlor kwance kan sofa ta juya ma ƙofa baya, sallamar da suka yi ce ta sata tashi zaune haɗi da amsa masu  sallamar,baza ta wuce shekara 19 zuwa 20 a duniya, sanye take da  english wear's riga da skirt,  cikin parlorn su ka shiga, haɗi da samun wuri kan sofa suka zauna, gaishe da su wannan budurwar tayi tana kallon Abdallah " yaya jiya muna ta jiran ka ka dawo baka dawo ba "
"yanzu ai gashi na dawo ko "
"amma sai da yamma, wai ma ina kaje"
"to uwar masu iya surutu, ban sani ba wuce ki kira mana ummah"
"yaya nice ma mai surutun ko"
"zaki wuce ko sai ranki ya ɓaci" barin wurin tayi tana turo baki, wata ƙofa ta nufa, ba nocking kawai ta buɗe ƙofar ta shige bayan kamar minti biyu sai ga wata kyakyawar mace ta fito daga ɗakin jikin ta sanye da gown ta material, a ƙallah zata yi kimanin shekara 40 a duniya, ba fara bace amma bazaka kira ta da baƙa ba chocolate ce kamar ɗiyar ta, ƙarasowa tayi cikin parlorn tana faɗin "Abdallah daga bari naje na dawo sai kwana " murmushi Abdallah yayi ba tare da yace komi ba, gaishe da ita su shazim su kayi,fuska ɗauke da fara'a ta amsa tana faɗin "daga ziyara sai ku riƙe mana shi harda kwana"
mansoor ne yace " ai gashi nan mun dawo da shi "
"ai duk da haka" murmushi kawai su ka yi
"Ya su umman fatan suna lafiya?"
"lafiya lau su ke" fira suke da matar cikin nishaɗin amma ban da shazim, dan shi yama ƙosa su tashi, tashi tayi tana faɗin "sai fira muke ba'a kawo maku abinci da ruwa ba " mansoor ne yace "a'a ba komi yanzu zamu wuce "
"a'a gaskiya sai kunci ko da snacks ne, bari na sa Ameera ta kawo maku " tana faɗa ta koma ɗakin da ta fito ɗazu,shazim yace "ba sai ta kawo ba A hashim tafiya zamu yi " rai a ɓace
Abdallah yace "wallahi baku isa ba kuna nan har sai uncle ya dawo " ganin ranshi ya ɓaci ne yasa mansoor cewa su jira ɗin, fasa tafiyar su kayi, Ameera ce ta shigo parlorn hannunta ɗauke da tray ruwa ne da lemu, ajiye wa tayi a gaban su shazim, inda ta fito inda nake kyautata zatun kitchen ne can ta koma, sai gata ta fito hannunta ɗauke da snacks wata na biye da ita da bowl ɗin kayan marmari, a gaban su shazim ta sake ajiyewa, wacce suka fito tare ce ta gashe da su shazim, barin parlorn su kayi suka koma inda su ka fito, sai da Abdallah yayi da gaske sannan shazim yaci wani abu daga cikin abun sa aka kawo ma su, sun jima a gidan har sai da uncle Ahmad ya dawo suka gaisa, uncle ahmad yana matuƙar kama da abie sai dai abie ya fishi hasken fata,sun jima suna fira dashi, yanda ya sake masu kamar abokin su,da zasu tafi shida Abdallah su kayi nasu rakiya har parking lot.
lokacin da su ka koma estate  lokacin kusan ƙarfe goma da rabi na dare, kowa ma kwancin shi ya nufa, alawala yayi ya kabbara sallah,daya gama adu'a kwai yayi ya kwanta. 

Haka kwana ki su kai ta tafiya har
shazim sunyi tsawan sati ɗaya da kwana biyar  da zuwa abuja,a cikin kwana kin nan kunsan kullum sai Abdallah yazo wurin su ko su suje, fatima ma da sa'ada zuwan su gidan uncle Ahmad biyu, har lokacin su uncle ahmad basu sanar da shi kiran da suke mashi ba, shi kuma bai tambayi kowa ba ya dai zuba masu ido idan  har basu sanar da shiba, yayi alƙawarin bazai tambaye su ba zai haɗa kayan ahi ne kawai ya koma logas, ya gaji da zaman abuja, aikin shi ne kawai ke damun shi, shi da yazo da niyyar kwana biyar, ya kai wannan lokacin ne saboda Ammy, amma da ba dan haka ba da tuni ya daɗe da komawa,har ammy ya kira yace shi dai zai dawo, amma sai ta hana shi tace ta zauna har sai in sun sanar da shi kiran da suke mashi, ba dan yaso ba ya haƙura.  
kullum idan  mansoor zai tafi aiki tare suke tafiya.

kwance yake kan bed ringing ɗin wayar shi ne ya tashe shi,lalubo wayar, a hashim ne ke kira ,  picking call ɗin yayi  haɗi da yin sallama sannan ya ɗaura da cewa"lafiya kira da sassafe haka? " banajin mai a hashim ke cewa, na dai ga shazim yayi murmushi da alama a hashim ya bashi amsar da ta dace da maganar da yayi,sannan ya ce "kar ka damu very soon"  sun ɗan jima suna waya sannan suka yi sallama, tashi yayi ya nufi toilet, bayan kamar minti 5 sai gashi ya fito ƙugun shi ɗaure  da farin  towel,clothes set ɗin shi ya nufa cikin ƙanƙanin lokaci ya shirya cikin wani yadi fari da baƙi mai taushi da ɗaukar hankali,  gaban dressing mirror ya nufa  kwalbar turare ya ɗauka ya feshe jikin shi,wayar shi dake kan bed ya ɗauka sannan ya fice ya nufi hanyar fita tana zuba ƙamshi, part ɗin uncle ahmad ya nufa a bakin ƙofa yaci karo da mansoor, mansoor na ganin shi yace "dama wurin ka zani, naga har kusan 11 baka fito ba kana can kwance" ɗan ya tsine fuska yayi yana faɗin
"wallahi kuwa abun da ban taɓa  yi ba  kenan, amma yau ban san ya akai ba "hannun shi mansoor ya ja yana faɗin "mushiga ciki kayi breakfast may be gajiyan jiya ne "ciki suka shiga mama da kairiyya suka samu a parlor gaishe da mama yayi kairiyya ta gaishe da shi mama na faɗin "ga breakfast ɗin ku can kan dinning " tashi suka yi suka nufi dining ɗin, kairiyya  tayi saving ɗin su tana kammalawa ta dawo kan sofa, mahmud ne yashigo shi da noraiz, wurin su shazim suka nufa suka gaishe da su, suma suka zauna domin yin breakfast ɗin.
suna kammalawa shazim da mansoor suka fice daga part suka nufi na uncle Ibrahim.
zaune take kan sofa ta juya ma ƙofa baya sallamar su ce tasa ta juyowa, fuskar ta da fara'a ta nufe tana gaishe da su, mansoor ne ya amsa amma shazim ɗaure fuska yayi kamar an aiko masa da saƙon  mutuwa
"bro ana gaishe da kai "
"naji" shine kawai abun da yace,kuka ne ya ciyo feenah ta rasa mi tayi ma shazim yake wulaƙanta ta, ace ko gaisuwar ta baya iya amsawa,  juyawa tayi da sauri ta nufi bedroom ɗin ta kukan na neman kufce mata
"gaskiya baka kyautawa, narasa miya sa ka tsani feenah kwata kwata baka son ta, in ta gaishe ka baka son amsawa wai miye duk hakan "
"ka gama"fuska da alamun ɓacin rai mansoor yace
"ok ni kake cema nagama ko yayi kyau"
riƙo hannun shi yayi yana faɗin"sorry bro kai." bai ƙarasa maganar ba saboda fisge hannun shi da mansoor yayi yana faɗin "rabu dani bana son jin komi daga gare ka" yana gama faɗa ya juya ya bi bayan feenah, ɗaga kafaɗa shazim yayi irin abun bai dame shi ba,sama ya nufa wurin uncle Ibrahim,yazo shiga kenan yaji yayi karo da mutum har sai da ya ɗan ja baya ,ɗagowa da kanshi yayi yana kallon luqman dake gaban shi tsaye  yana liliya goshin shi da alama yaji zafin karon da suka yi, kallon shazim yayi yana faɗin  "kayi hauka ne" tun kafin ya ƙarasa shazim ya ɗauke shi da wani mummunan mari har sai dai ya kusa faɗuwa, cikin azabar zafi ya ɗago yana faɗin "wannan wane irin zalunci ne azzalumi kawai mugu"sake wanka mashi mari shazim yayi har sai da ya duƙe kasa, amma duk da haka bai fasa ce mashi  azzalumi ba,shaƙo wuyan rigar shi shazim yayi haɗi da kai mashi duka a baki, wahalalliyar ƙara luqman ya saki dan ba ƙaramin zafi yaji na har bakin shi ya fashe,uncle Ibrahim ne da ya fito sai ga mansoor da feenah har da momy sun nufo sama  ta dalilin ƙarar da luqman ya saki,ganin yanda ya shaƙe mashi wuya ne yasa uncle Ibrahim cewa "shazim miye haka kashe shi za ka yi ne, wai ma miya haɗa ku ne kake mashi irin wannan dukan"
cikin kukan wahala luqman yace" ba abun da  nayi mashi ya hau duka na, da yake azzalumi ne shi" wani sabon naushin  ya sake kai ma luqman a baki, cikin sauri uncle Ibrahim ya ƙaraso kusa da su dan tun da ya fito yana tsaye ne a bakin ƙofa, hannun shazim ya fize daga riƙwan da yayi ma luqman yana faɗin "shazim baka da hankali ne illata shi kake son yi ne?" ran shazim ne ya ɓaci da maganar uncle Ibrahim,  yasan cewa luqman bai da kunya kwata kwata kuma ya raina shi ya san dole sai da dalili zai mashi wannan dukan,amma da alama laifin shi yake gani,  ce mashi yayi"eh, tun da shi bashi da hankali, bai san ina ke mashi ciwo ba"
"shazim ni kake faɗa ma haka?"     banza yayi da uncle Ibrahim sai ma kama hanyar fita yayi,  riƙo shi mansoor yayi yana  faɗin "baka ji ana maka magana za ka fice" cikin tsantsar l ɓacin rai shazim ya ce "sakar man hannu na mansoor" ƙin sakar mashi hannu mansoor yayi,  ganin bazai sakar mai hannu bane yasa shi fizge hannun shi ya fice daga part ɗin bin bayan shi mansoor yayi yana ƙwala mashi kira ,da kallo uncle Ibrahim ya bi su har suka bar part ɗin ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli luqman yana faɗin"maganin ka kenan luqman, tun yaushe nake maka faɗa akan ka daina shiga harkar shi amma baka ji, yanzu da bama kusa Allah ka ɗai yasan irin illar dazai yi maka "cikin kuka luqman yace"yanzu dady goyan bayan shi kake, duk irin wannan dukan da ya yi man"
"dole na goyi bayan shi dan na san halinka da rashin kunya, kuma haka nan bazai rufe ka da duka ba batare da kayi mashi komi ba "cikin ɓacin rai luqman yace "tun da haka ne dady, wallahi sai na rama bazai dake ni a banza ba wallahi"juyawa yayi zai bar wurin da sauri uncle Ibrahim ya jawo hannun shi yayi yana faɗin "ashe baka da hankali ban sani ba,dallah wuce ciki sakarai kawai " ya faɗa haɗi da janshi suka shiga parlorn shi aka bar momy da feenah tsaye, feenah ce tace "wai miyasa ya shazim ya tsane mu ne, ji dukan da yayi ma ya luqman dan Allah" ɗan nisawa momy tayi sannan tace "idan har da laifin shazim to na innah yafi yawa dan ita ta haddasa komi, ita tasa luqman bai ganin shazim da mutunci"
"haba momy yaza kice haka,ba ruwan innah, dama chan ba son mu yake ba"
"nace hakan,duk ba ita ta haddasa komi ba tasa kuka tsane su ku ke mashi rashin kunya,ke ma duka yaushe kika dai na raina shi,  dalla wuce ki bani wuri" wucewa feenah tayi tana turo baki ta nufi ƙofar fita zuwa part ɗin innah, a bedroom ta same ta mai aikin ta na shirya mata kaya a wardrobe, kallon mai aikin feenah tayi tana faɗin "ke tashi ki bamu wuri"ta shi talatu tayi ta fice, kallon feenah innah tayi tana faɗin "ke kuma lafiya kika korar man mai aiki? " zama tayi bakin bed ɗin tana cewa "tacika sa ido ne da gulmar tsiya"
"to aikuwa ke zaki ƙara sa man tun da har kika kore ta "ɗan ya tsine fuska feenah tayi tana faɗin "ai yanzu zan tashi sai ta zo ta ida maki"sannan ta ɗaura da cewa "innah kin san mi ya faru kuwa?"gyara zama innah tayi tana faɗin "a'a sai kin faɗa,mi ya faru"
"hmm ya shazim ne yayi ma ya luqman dukan tsiya har da fasa mashi baki"zaro ido innah tayi haɗi da rike haɓa tana faɗin "wallahi bazai yiwu ba, shikuma sai luqman ɗin ya tsaya kamar wani sakarai har ya zubar mashi da jini"
"to kema innah in ban da abunki ina ya shazim ina ya  luqman "miƙewa innah tayi tana cewa "to wallahi bai daki banza, ka gaman azzalumi yaro"ficewa tayi daga bedroom ɗin tana masifa ta nufi part ɗin uncle Ibrahim, momy da ke zaune kan sofa tun daga waje ta fara jiyo masifar innah, sai gata ta shigo, tana ganin momy tace "ina Ibrahim ɗin yake? " sama momy ta nuna mata da hannu, fuuuu innah ta wuce zuwa sama tana ta zazzaga masifa,tana shiga parlorn ta samu uncle Ibrahim shi da mansoor dake kwance kan sofa, ko sallama babu ta faɗo tana faɗin "wallahi bazata saɓuba bindiga a ruwa,ina luqman ɗin yake"miƙewa luqman yayi ya nufe ta "dan mi zaka tsaya wannan yaron mara mutuncin  yayi maka duka irin haka sai kace jaki" uncle Ibrahim ne yace
"haba innah yaza kice haka,bayan kin san halin luqman da rashin kunya dole yana da laifi"
"hakama za ka ce yaron yayi mashi irin wannan dukanl, amma kace shine mai gaskiya"
"ba wai na goyi bayan shi bane,  a'a nasan halin luqman ne da rashin kunya shine kawai , kuma kema nasan kinsan halin shi sosai" tsaki innah taja tana faɗin "shima ai ba kunyar bace da shi, kuma wallahi bai daki banza ba, idan da ya dake shi nayi shiru lokacin da yake yaro yanzu bazan yarda ba ace da girman shi ya dake shi ba in zuba ido ina kallo   idan kai bazaka ɗauki mataki ba ni zan ɗauka da kaina"
"yawwa innah shiyyasa nake ƙara sonki kin fi dady sona "
"karka damu zanyi maganin shi, fita ka bamu wuri zamuyi magana "da
to innah ya amsa sannan ya kama hanyar ficewa daga parlorn,  kallon uncle Ibrahim tayi sannan tace "kai kuma zauna "zama yayi kan sofa dake kallon wacce innah ke zaune..
  
Da yamma innah ta aiki feenah  kiran uncle ahmad, tana zuwa part ɗin ta samu su noraiz a parlor, yi tayi kamar bata san da su a parlorn ba ta nufi sama,faisal ne yace "lallai ma wannan yarin yar uncle ahmad na zaune a parlorn shi, mama na zuba mashi fura a cup ta shigo da sallama,amsa mata suka yi uncle ahmad na cewa"mamana zo ki zauna "ya faɗa haɗi da nuna mata kusa da shi, zuwa tayi kusa da shi ta zauna,"daga ina mamana? "
" daga wurin innah na ke , tace na kira mata kai "
"to, kice mata gani nan zuwa" da to feenah ta amsa haÉ—i da ficewa ta bar part É—in ta koma na innah.

lokacin da suka fita daga part ɗin uncle Ibrahim part ɗin su ya nufa ya shiga bedroom ɗin shi,da ƙafa ya tura ƙofa da ƙarfi  har yaso da tsema mansoor hannun dake bayan shin, ja da baya mansoor yayi yana kallon ƙofar kamar shazim ɗin a wurin,tura ƙofar yayi ya shiga zaune ya gan shi bakin bed, ƙarasawa cikin yayi ya zauna kusa da shi yana faɗin "shazim miyasa ka dake shi, mi yayi maka"banza shazim yayi da shi har saida ya ƙara tambayar shi, still banza yayi da shi ran mansoor ne ya ɓaci, cikin masifa yake ce ma shazim "wai bakaji ina maka maganane, ko nima shashasha ka ɗauke ni ban sani ba"
É—an nisawa shazim yayi, sannan yace"dole nayi banza da kai mana"
"ok haka kace koh "
"eh" abun yayi matuƙar ɗaure ma mansoor kai, cikin lallashi ya ce"kayi haƙuri nasan kana ganin kamar na goyi bayan luqman ne"shiru shazim yayi kamar ba da shi mansoor yake ba
"haba shazim na san kana jina"
"ina jinka mana" haƙuri mansoor ya shiga ba sai da ƙyar ya sa mu ya shawo kansa har ya dai na fushin da ya ke.

innah da feenah ne zaune a parlor, feenah ta kwanta tana daddan wayar ta, innah kuma na zaune ta ƙurama tv ido, sallama su  uncle ahmad su ka  yi haɗi da  shigowa, amsa ma su  sallamar innah tayi, wuri suka samu su ka zauna, uncle ahmad yace "innah gani feena tace kina kira na, Allah dai yasa lafiya "
"lafiya lau " innah ta faɗa haɗi da kallon feenah tace "takwara tashi ki bamu wuri " da to feenah ta amsa haɗi da miƙewa ta fita,
laɓewa tayi a  bayan ƙofar part ɗin innah, maganar da su innah ke yi take saurare  sai sakin  murmushi take, alamar buɗe ƙofa taji  za'a fito taji, hakan ya sa da gudu tabar bakin ƙofar ta ɓoye bayan part ɗin, uncle ahmad ne da uncle Ibrahim su ka fito daga part, tsayawa tayi har sai da taga shun nufi part ɗin uncle Ahmad sannan ta nufi part ɗin innah da sauri, a bedroom ta samu innah da waya kare a kunnen ta, zama tayi tsakiyyar bed ɗin innah tana faɗin "dan Allah innah kiyi sauri ki gama wayar nan Please"
daƙƙuwa innah tayi mata, dariya feenah tayi, ganin wayar innah ba mai ƙarewa ba ce yasa ta kwanciya kan bed ɗin sai sakin murmushi take kamar wacce aka yima albishir da gidan aljanna, innah ta ɗan ɗauki lokaci tana waya,lokacin da ta kammala, zama tayi ita ma kan bed ɗin "ke kuma lafiya kika zo zaki ta kura man ido " ta shi feenah tayi tana ɗan ya tsine fuska tace " dama nazo ne naji ya ku ka yi da su dady "
riƙe haɓa innah tayi tana faɗin "sannu uwata, to ban sani ba" murmushi feenah tayi tana faɗin "ai naji komi kuka ce " ɗan zaro ido innah tayi tace "dana ce ki fita  kenan laɓewa ki kayi kina sauraron mi muka ce "
"a'a ai ba duka naji abun da kuke cewa ba "
"ƙarya ki ke kinji komi"
"Allah a'a, yaushe uncle Ahmad yace su Aunty uwani zasu zo "
"ban sani ba, tashi ki bani wuri "
"dan Allah innah ki faɗa man " innah tace "naƙi in faɗa" roƙonta feenah ta shigayi akan ta faɗa mata yaushe zasu zo, amma ƙiri ƙiri innah ta ƙi faɗa mata.

✨SHAZIM✨

Kayan shi ya hau haɗawa dan yayi alƙawarin sai ya bar abuja gobe da izinin ubangiji, ya gaji da zaman jiran jin kiran da su ke mashi, shiyyasa kawai ya yanke shawarar tafiya gobe  ko da shi kaɗai ne ban da su fatima, in yaso daga baya su sun dawo, yana cikin haɗa kayan mansoor ya shigo bedroom ɗin, turus ya tsaya yana kallon shazim dake ta faman haɗa kaya, yi yayi kamar ma bai ga shigowar mansoor ba yaci gaba da abun da yake matsowa mansoor yayi kusa da haɗi da dafa kafaɗar shi yace "wai shazim kana nufin har yanzu baka haƙura ba" ba tare da ya kalli mansoor ba yace
"wa yace maka fushi nake  "
"to idan ba fushi kake ba, miye na wani haÉ—a kaya, dan nasan halinka kana iya cewa lagos zaka koma"
"faÉ—i ka ke ana jinka "
"haba shazim miye abun fushi a nan"
"wai dan Allah wa yace maka fushi nake, kawai ina son na koma ne saboda aiki na da na baro,  luqman har ya kai matsayin da zai ɓata man rai ne na koma lagos "  ɗan ajiyar zuciya mansoor ya sauke "to shikenan, amma ka bari su abbah su ce ka tafi ko"
"mansoor baza ka gane bane, aikina fa na baro tsawan sati É—aya da wani abu haba "
"haka ne shazim, amma duk da haka ya kamata ka jira kaji mi zasu ce "
"ai ba tafiya zan yi ba batare da na sanar da su ba, zan faÉ—a masu in son in tafi gobe "
"to shikenan "mansoor yace, kama mashi yayi ya haɗa duk wani kayan shi da ya zo da su, bayan sun gama masallaci su ka nufa su kayi sallar magrib har da isha daga nan  part ɗin uncle Ahmad su kaje, dinner su kayi bayan sun kammala ne shazim ya samu uncle ahmad har part ɗin shi ya sanar da shi yana so zai koma lagos gobe, ko da ya faɗa mashi cewa yayi ya bari sai nan da ranar lahadi, saboda family meeting da za su yi ranar asabar, ba dan ya so ba ya haƙura, part ɗin su ya koma kwata kwata baiji daɗin hana shi tafiya da uncle Ahmad yayi ba kuma, ammy ya kira ya sanar da ita, ce mashi tayi yayi haƙuri ya jira, ko ba komi zaiga ƴan uwanshi da ya daɗe bai gani ba dama waɗan da bai san su ba, dan bashi da yanda zai yi ne yasa ya haƙura, baya farin ciki da wannan family meeting ɗi.

✨Ammy ✨

kwance take kan gadon ummy, gama wayar su kenan da shazim ta kwanta, tunda su shazim suka tafi abuja kullum tana gidan malam, wata ranar ma a nan take kwana, yau ma anan zata kwana, ummy ce ta shigo ɗaki da sallama, amsa mata sallamar ammy tayi, bakin bed ummy ta zauna tana wash, yanzu indai tayi tafiya ko yaya take sai ƙafafun ta su kama ciwo, sannu Ammy tayi haɗi da cewa "anya ummy baza muje asibiti ba saboda ciwan ƙafafun nan"
"a'a ba sai munje asibiti ba,  yaushe ango na zai dawo?  "
"yanzu nayi waya da shi da gobe zai dawo, amma yanzu sai ranar lahadi saboda meeting da za suyi na family "
"to Allah ya kaimu, su Ahmad É—in sun sanar da shi kiran da suke mashin ne"
"a'a basu faɗa mashi ba har yanzu, ya dai ce man dawowar shi zai yi ko ba su faɗa mashi ba wai ya gaji da zama aiki ya bari, na daice yayi haƙurin su faɗa mashi "
"eh gaskiya ya ka mata  ya tsaya yaji kiran mi suke mashi "
"kin san halin shi ummy wani lokacin da baƙar zuciya "
"ai kuwa dole ya rage ta, tun da komi ma su kayi mashi shi ya jawo ma kansa "
"haka ne, ummy yaushe su mamy su kace zasu zo?" ammy ta faÉ—a
"ta ce man wani watan idan Allah ya kaimu "
"Allah ya kaimu, ina son idan za su koma na bi su na kwana biyu banje Morocco ba "
"gaskiya ya kamata kije har da yarannan "
"da su nake son zuwa musamman shazim da bai son shiga mutane "
Ummy tace "ai lamarin angon nawa ne sai adu'a " firar su suke har sai da bacci ya fara É—aukar su, sannan ummy ta tashi ta tafi É—akin malam..
Episode 32_33

Washe gari ta kasan ce friday, sun tashi da shirye shiryen tar bar baƙi, uncle Ahmad ne yace ma  Kairiyya ta samu  Feenah da su Fatima su gyara part ɗin da ke kusa da na innah.
A part ɗin innah ta same ta kwance kan gadon innah da a'lama ma a nan ta kwana, ko da Kairiyya tayi mata magana cewa tayi   "mi zai hana a sa masu aiki su yi gyaran"
Kairiyya tace "wannan kuma abbah zaki faÉ—a ma haka bani ba, tun da bani nace ayi gyaran ba " innah na zaune kan carpet tana jin su amma bata ce komi ba
"To gaskiya ni  bazan   iya ba,gara ma tun wuri kije ki samu masu aiki kuyi gyaran tare,  amma ni bazan iya ba" abun yayi matuƙar ba   Kairiyya  mamaki duk da daman tasan Feenah, ba kasa fai ake sata aiki tayi ba, in dai batayi niyya ba to fa bazata  yi ba, amma ba ta yi tunanin cewa Abbah zai iya sata abu tace bazata yi ba,
"yanzu dai mi kike nufi "
" bana jin daÉ—i, bazan iya ba "ta bata amsa kai tsaye, Kairiyya tayi tuna nin Innah zata sa baki jin abun Feenah tace amma sai taga innah tayi kamar ba bata san da zaman su a É—akin ba , kallon Innah tayi tace "Innah kina jin mi tace ko " Innah tace
"dan Allah ni karki dame ni, tun da tace bata jin daɗi, to sai ki ƙyale ta, ai sai  da lafiya ake komai " jinjina kai Kairiyya tayi haɗin da cewa "haka ne kam, gaskiya ne " tana gama faɗa ta tashi ta fice daga ɗakin, innah tace
"yau ga fitinanniyar yarin ya"da harara Feenah ta rakata tana faÉ—in "sai kace an ce mata nima yar wahala ce irin ta " ta faÉ—a haÉ—i da jan tsaki, juya kwanciyar ta tayi tana kallon Innah tace "Amma dai Innah su gwaggo uwani na zuwa yau za a yi meeting É—innan ko "
"sannu uwar yan gaggawa, saboda cin rabo ne abun kawai daga zuwa sai a kama meeting, ai a bari su huta "
"shikenan da ƙarfe nawa tace zasu baro kurfi"
"wannan ne kuma ban sani ba "

Kairiyya ko da ta fita daga part ɗin Innah part ɗin uncle Ibrahim ta nufa,  sumun Fatima da Sa'ada tayi, tace su zo su tai maka mata su gyara part ɗin da ke kusa da na Innah, ba musu su ka taso suka bi bayan ta, lokacin da suka isa part ɗin   a buɗe su ka same shi, duk a tunanin Kairiyya  Abba ne ya buɗe shi, sai da suka shiga ciki su ka samu laure mai aikin mama da saude mai aiki momy suna ka kaɓe ƙura, cewa tayi "ai da kun barshi " laure tace "A'a aikin zai yi maku yawa
Ashe  laure ce ta amshi key wurin mama ta buɗe part ɗin ta kira saude ta taya ta su graya pary ɗin, a ganinta ga su a estate ɗin mi zai sa su Kairiyya su yi akin, Kairiyya ta ce"ai da kun barshi, tun da gani ga fatima da  sa'ada  "      laure tace "A'a aikin zai yi maku yawa, ki bari kawai muyi "
Kairiyya tace "Allah kuwa da kun barshi za mu iya"
"A'a duk da haka dai " ganin sun nace ne yasa Kairiyya cewa sai dai suyi aikin tare,a haka su ka cigaba da aikin suna fira sun ɗauki tsawan lokaci kafin su gama,sai wurin sha biyu da minti arba'in da wani abu su ka kammala, part ɗin uncle Ibrahim su Fatima su ka nufa, wanka su kayi da sallah kowace ta nemi wurin kwanciya ba tare da sun nemi abinci ba  duk da suna jin yunwa.

  ✨SHAZIM✨

Kwance yake kan gado a rigingi ne kanshi yana kallon sama, idanun shi a rufe da a lama bacci ya ke, wayar shi dake kan bed side ce ta fara ringing, har kiran ya katse bai motsa ba,wani kiran ne ya sake shigowa, mutsu mutsun  buɗe idanuwan shi ya shiga yi ,buɗe su yayi yana kallon saman ceiling, ya ɗauki kusan five seconds yana kallon,  kiran na shirin katsewa ya zura hannu ya jawo ta, picking yayi ba tare da ya du ba mai kiran na shi ba, muryar majeed ce ta daki dodon kunnen shi yana sallama, sallamar ya amsa cikin kasa lelliyar murya ta masu bacci yake  faɗin"majeed kai ne "
"eh nine, kamar ma bacci kake?"
majeed ya tambaye shi amsa  ya ba shi da "kai dai bari, ya aiki"
"Alhmdllh, dama na kira ka ne saboda kayan nan da ke store, masu su fa sun fara bibiyar kayan "
"mi ya faru kace haka? "
"jiyan bayan tashi na security ya kira ni yake ce man wa su mutane sun zo bayan tafiya ta, wai sun zo da shigar jami'ain kiwan lafiya,  an turo su ne dan su yi bin cike a abnoor a kan ana ba da magani ba bisa ƙa'ida ba , sun nemi da su  buɗe masu store"
"store kuma, su yi mi kenan a ciki "
"shima tambayar su yayi mi za su yi a store shine su ka ce wai suna son su bincka magungunan da muke da su, bai dai buÉ—e ma su store É—in ba dan cewa yayi ba shi ke da makullin store ba,da ya faÉ—a masu haka sai tambayar shi su ka yi wai hospital É—in na waye, so ya dai ceman bai faÉ—a masu saboda bai yadda da su ba, in dai har da gaske turo su a kayi yasan baza su zo a wannan time É—in ba, sun dai ce zasu dawo"
"ok yaushe su ka ce zasu dawo "
"ba su faÉ—a mashi ba, sun dai ce kawai za su dawo "
"ok to shikenan, nima ranar sunday zan dawo, idan na dawo za mu san yan da zamu bullo ma al'amarin insha Allah, buri na dama su fara bibiyar kayan"
"Allah ya kaimu ranar sunday É—in"
Ameen ya amsa, sallama su kayi, mai da wayar yayi kan bed side, tunanin ya shiga"wai su waye masu wannan kayan ne?" tambayoyi yayi ta jefa ma kanshi bashi da mai bashi amsar su, ya jima a kwance shi bai koma bacci ba shi bai tashi ba, sai da aka fara kiran sallar asr, sannan ya sauka daga kan gado ya shi toilet, wanka ya sake da al'wala, shiryawa  yayi cikin wani yadi mai taushi brown color ya sa hula milk color, feshe jikin shi yayi da turare mai ƙamshi, masha kamar ka sace shi ka gudu, shoe rag ɗin sa ya nufa ta kalmi ya ɗauko brown color ya sa , wayar shi ya ɗauka da key ɗin mota ya fice zuwa parking lot, wata farar mota da bai taɓa hawa ba tun da su ka zo ya nufa, shiga yayi cikin ta yayi reverse ya nufi main gate, ya na nufar main gate wasu motoci  guda shidda su ka shigo cikin estate ɗin,ko mawa yayi yana tafiya slowly time ɗin da  ya iso bakin gate ɗin har  sun gama shi gowa, ficewa yayi ya bar estate ɗin,part ɗin innah motocin su ka nufa, parking  su ka yi, na cikin motocin ne su ka fara fitowa,wata kyakyawar mata ce ta fara  fitowa fara ce amma ba sosai ba  a ƙallah zata yi kimanin shekara 51 zuwa da biyu Aunty uwani kenan,  part ɗin innah ta nufa, ɗaya bayan su ke fitowa daga motacin, harda wata mata mai matuƙar kama da wacce ta shiga part ɗin innah sai dai tafi waccen haske nesa ba kusa ba,a ƙallah za tayi kimanin shekara 49 Aunty sadiya sunan ta ƙanwar Aunty uwani ce  , su uku suka fito daga bayan motar ita da wasu matasan  mata ɗaya da yaro a hannun ta ɗayar kuma da goyo, mai yaron  bazata gaza shekara 32  ba a duniya, sunan ta Aunty Zainab ɗiyar gwaggo Halima   ce ita ce babbar ɗiyar ta, ɗayar kuma bata wuce shekara 30,ita kuma sunan ta maryam ɗiyar gwaggo  Uwani ce,  motar da ke bayan su wasu ƴan mata ne su ka fito su hudu uku daga baya ɗaya kuma daga gaba ta fito, wacce ta fito daga gaba a ƙallah zata yi ki manin shekara 23 sunanta farida ɗiyar gwaggo Halima ce ita ma  sai  ƴan mata guda uku biyun  zasu yi sa'annin baza su wuce shekara 27  ba Asma'u da Amina kenan,dukkan su suna da aure sai dai ba wacce ta haihu Amina Anwar take aure ɗan gwaggo Halima , ɗayar kuma bata wuce shekara 25,  sai motar da ke bayan su yar matashi yar buduwar wa ce ta fito baza wuce sa'annin su kairiyya ba, sai maza su uku, motar da bayan su kuma duka maza ne manya su huɗu,du kan su part ɗin innah su ka nufa da sallama a bakin su, innah na zaune kan sofa ita matar da ta fara shigowa , tashi innah tayi tana faɗin " lale marhabun , sannun ku da zuwa" wurin zama ko wannan su ya samu, wa su kan sofa wasu kan carpet,   feenah ce ta shigo  da gudu daga ita sai vest da da wando gyelen da ta ɗaure kan ta da shi a hannu ta shigo da shi ta nufi wannan  matashiyar wacce za su yi sa'annin, hugging ɗin ta tayi "oyoyo sister yau she rabon da na ganki "
"ai baki son zumunci ne feenah "
"kaji sai kace kema zumunci kike so"
"wallahi kin san gara ni da ke "
"ba wani nan, yau she rabun ki da abuja, zaki wani ce gara ke "
babban da ke cikin su ne ya daka ma feenah tsawa yana faɗin " ke baki da hankali , baki ganin  mutane zaki wani shigo da gudu ko sallama babu, ji kayan da ke jikin ki " faɗuwa gaban ta yayi dan shaf ta manta da wane kaya ne jikin ta, ta kuma manta cewa harda ya usman za'a zo, dan bala'in shakkar sa take
"iskanci ki na nan ko,ki shiga hankalin ki da ni, kina son kafin na bar garinnan jikin ki yayi tsami, sa karya kawai " innah tace "A'a usman da kata daga shigowar ka baza ka ta kura ma yarinya ba, kai shikenan bazata nuna murnar ganin Æ´ar uwar ta ba "
wannan matar ce wacce ta shigo daga baya  gwaggo Halima tace "dama mama  har yanzu baki daina goyan bayan  feenah ba, ki duba fa yan da ta shigo ko sallama babu, ji kayan da ke jikinta  "
"dan Allah ya isa haka sadiya, daga zuwan ku za ku ta kurama yarin ya, sai É—oki take ku zo amma kun zo za ku fara tasa ta gaba da masifa "
"to shikenan , nayi shiru "
Usman yace "zaki fice kije ki canza kayannan ko sai na ɓaɓɓalaki wa wuya kawai"
jan hannun matashiyar budurwar feenah tayi su ka fice, su Fatima ne su ka shigo su  da momy  bakin su ɗauke da  sallama, amsa masu sallamar su kayi cikin parlorn su ka shiga, gaisawa momy ta shiga yi da su gwaggo uwani, su fatima gaishe da  su su kayi,gwaggo Halima ce kawai ta amsa gaisuwar da fatima tayi masu , amma gwaggo uwani yi tayi kamar ma bata san da fatima ba a parlorn sai ma tashi da tayi ta nufi ɗakin innah,da idanu kawai fatima ta bi ta idanun ta na kawo ƙwalla, gwaggo Halima ce ta lura da halin da fatima ta shiga, dafa kafaɗar tayi "Fatima ya Ammyn ku, ina su noraiz da shazim " tayi mata tambayar ne dan ta kau da mata hankali daga abun da gwaggo uwani tayi mata,
"ya noor na tare da ya mahmud, ya shazim ne dai ban san inda yake ba amma ina tunanin yana tare da ya mansoor "
"masha Allah, ya su malam"
"lafiya lau su ke " janta da fira tai tayi har sai da ta saki ranta
"Fatima mu baki ganmu ba ne " wata kyakyawar budurwa ce zaune kusa da sa'ada
"Allah sarki Aunty farida so nake mu gama gaisawa da gwaggo, ina wuni, ya hanya?"
"lafiya lau fatima, ya lagos, ina Ammy"
"Ammy na lagos "
ɗaya bayan ɗaya fatima ta bisu tana gaishe da su, wasu su amsa wasu yi banza da ita,har da masu sarka mata habaici,  da ta gaji da ganin abun da suke mata tashi tayi ta bar part ɗin ta nufi na su, hawayen da take ɓoyewa ne su ka shiga gangaro mata, tarasa miyasa gwaggo uwani bata ƙaunar su ita da ƴaƴen ta, ta ci kuka kamar mi ita ka ɗai a part ɗin har bacci ya ɗauke ta kan sofa.
A can part ɗin Innah kuwa, gwaggo Halima ce ta kalli su Aunty maryam da su Aunty Amina tace "yanzu ku da hankali ku da wayan ku kuke abu kamar wasu ƙananan yara, musamman ke maryam da girman ki zaki biye ma su Asma'u "
Aunty maryam tace "mi nayi kuma mama "
"ina kallon ku ke da su Asma'u  Fatima ta gaishe ku Zainab ce da Fiddausi kawai su ka amsa mata, miyasa kuke haka da hankalin ku"
"mun fa amsa baki lura bane "
tsaki ya usman ya jaya " wallahi har mamaki ki ke bani maryam ko yaro ƙaramin bazai yi abun da kike yi ba , ku kuma ku shiga hankalin ku" ya faɗa haɗi da nuna su da yatsa, mama ce ta shigo su ka gaisa da gwaggo Halima, bata wani jima ba ta koma part ɗin ta, mai aikin momy da mama ne suka shigo da manyan tray ɗauke da ruwa da lemu, bayan sun ajiye masu gaishe da su suka yi, sannan su ka fice suka kawo masu abinci da snacks .
Mansoor ne ya shigo parlorn, wuri ya samu kan sofa yana gaishe da su gwaggo uwani wacce   fito war ta kenan  daga bedroom ɗin Innah, hannu ya miƙa ma usman su ka gaisa "ya usman kwana da yawa, ka shige jos ba'ajin ɗuriyar ka"
"ba wani na shige jos, ai kai da shazim ba mutunci ne da ku ba, musamman shazim sai ya shigo jos sau ba a dadi amma ban taɓa ganin ƙeyar shi ba"
"Ka san shi da aiki ya Usman, may be shi ke hana shi zuwa in da kake"
"ba wani aiki kawai dai ba ya son zumunci ne"
gwaggo Halima ce tace"mansoor yana  ina ne   abokin naka "
"wai shazim?"
"Eh shi "
"Ina tunanin yana part É—in su,na kira maki shine?"
"a'a ƙyale shi na san zai shigo " tsaki gwaggo uwani ta ja tana ce ma mansoor "kai je ka kira shi, tun da shi ya fi ƙarfin ya shigo gaishe da mutane"
"da kin  ƙyale shi yaya, na san zai shigo zuwa anjima kuma ma duka mintin mu nawa da shigowa, ra bu da shu Mansoor ba sai ka kira shi ba  "
"haka ku ke dama ke da su yaya, yaro yaita abun da yaga dama  amma ku baku gani, da ance kaza za ku kare shi"
"ba haka bane, idan har kika ga munyi goyi bayan shi to fah yana da gaskiya, haka nan baya abu batare da dalili ba"
" haka ku kaci rani, in dai shazim ne za mu gani "
banza gwaggo Halima tayi da ita kamar ma ba da ita  take maganar ba,
Mansoor yana nan zaune  noraiz da mahmud su ka shigo, wuri suma suka samu kusa mansoor su ka zauna, gwaggo uwani ce tace " ai nayi tunanin kai ma kafi ƙarfin gaishe da mutane kamar ɗan uwan ka " bai amsa mata tambayar ta ba sai ma gaishe ta da yayi, haushi abun ya bata , ta so ya bata amsa amma sai yayi kamar ma ba da shi take ba, da lafiya ta amsa mashi
suna gama  gaishe da su , su kayi  fice war su, su noraiz basu jima da fita ba  ba mazan ma su ka  tashi har da mansoor suka fice, shi da anwar part ɗin su shazim suka nufa sauran kuma suka nufi part ɗin da aka tana da domin su, a can su saude su ka kai ma su abinci.
bedroom É—in sa suka nufa, mansoor yayi nocking har ya gaji, wayar shi ya ciro daga aljihu ta lalubo number shazim ya kira, har ta tsinke bai yi picking ba sai da ya sake kira sannan yayi picking, yana É—auka mansoor yace "kai wai kana lafiya ake ta nocking " kwance yake kan bed É—in Abdallah a gidan uncle Ahmad, É—an ya tsina fuska yayi yana faÉ—in "bafa na nan, na fita tun É—azu"
"ok kana ina ne?"
"ina wurin Abdallah "
"yaushe zaka dawo,su Anwar fa sun zo kuma gwaggo  Halima na neman ka"
"may be  sai dare ko gobe" amsar wayar Anwar yayi yana faɗin "muna gidan zaka ce wai sai gobe, wasa dai kake ko"
"Anwar ya hanya "
"Alhmdllh, ina nan ina jiran shigowar ka"
"to shikenan sai na shigo "
"ok ina zama jira "yana gama faɗa yayi rejecting kiran, barin part ɗin su kayi zuwa part  ɗin mansoor.

Sai da yamma liƙis su  Abbah  suka dawo daga wurin aiki  nan part ɗin innah su ka yada zango a parlor, suna firar yaushe gamo da ƴan uwan su,
Auny uwani ce tace" yaya ba naji kamar kace shazim da noraiz suna garinnan ba da muka yi waya da kai "
Uncle Ahmad yace "eh suna nan, basu shigo kun gaisa ba ne "
"banga ƙeyar ko ɗaya daga cikin su ba, dama noraiz me ɗan iya gaishe da mutane inya gansu, shi ko wannan uban marasa kunyar yafi ƙarfin gaishe da kowa"
Uncle Ahmad yace "haba uwani, wai miyasa a kowane lokaci kike ma shazim musammanar fahimta ne,yanzu haka baya nan ne , shi yasa baizo ya gaishe da ku ba "
"dama nasan haka zaka ce yaya, da anyi magana kan shi sai ku   goyi bayan shi "
gwaggo Halima tace"bawai an goyi bayan shi bane, kece dai baki fahimci shi ba, kuma ai noraiz ya shigo nan kun gaisa da shi "
"to naji, ai naga ke yazo ya gaishe ki ke da kika fahimci shi" girgiza kai kawai gwaggo Halima tayi ba tare da tace komi ba,
Uncle Ahmad yace
"ya isa haka, idan ya dawo zai shigo ku gaisa "
"Allah yasa "a cewar gwaggo uwani
sunjima a part innah suna fira, sai da aka fara kiraye kirayen sallar magrib su ka bar prt ɗin zuwa masallaci, su ma gwaggo Halima ta shi su kayi su ka shiga ɗakin Innah domin gabatar da ta su sallar, har sai da su kayi isha sannan su ka dawo parlor , sai bayan sallar isha kairiyya ma ta shigo gai she da su, su Aunty maryam kamar su cinye ta dan bata zo tun ɗazu ba, haƙuri ta ba su akan bata jin daɗin ne shiyyasa ba shigo ba, bata wani jima ba ita ma ta koma part ɗin su.

feenah tun korar da usman yayi mata bata sake shigowa part É—in ba sai yanzu ta shigo ita da ilham, a nan parlor suka zauna suna fira da su Aunty maryam.

Wuraren ƙarfe 9 ya motar shi ta shigo estate ɗin, a hankali yake driving  kamar baya son yi, part ɗin su ya nufa yayi parking, ya jima zaune a mota yana  waya, sai da ya kammala wayar shi tukunnan ya fito ya nufi cikin part ɗin tsit babu motsin kowa kamar ko wane lokaci, bedroom ɗin shi ya nufa, kayan jikin shi ya shiga ragewa bayan ya ajiye wayar shi da key ɗin motar da ya fita, toilet ya shiga, bayan kamar   10 minutes ya fito jikin shi sanye da bathrobe, bakin window yaje ya tsaya yana kallon   cikin estate ta baya  kamar mai tunanin  wani abu , ya jima a tsaye a wurin,daga baya ya saki curtain ya bar jikin window ya nufi clothes set ɗin shi, pajamas ya ɗauko riga da wando, wandon iya kar shi gwiwa sai riga mai garen hannun,cire bathrobe ɗin jikin shi yayi daga shi sai short, pajamas ɗin ya ɗauka ya sa, bayan ya gama sawa,cap ya ɗauko irin ta sanyi black color ya sa,fehe jikin shi yayi da turaren shi mai ƙamshi,  wayar sa da ya ajiye kan bed ya ɗauka ya zura ta cikin pocket ɗin wando, flip flops ya zura a ƙafar shi, fita yayi daga bedroom ɗin main parlor ya nufa fita yayi daga part ɗin zuwa part ɗin mansoor,yana shiga main parlor su Amina,  Asma'u da farida ya samu zaune kan sofa suna fira sai  kairiyya  da ke kwance kan sofa,ɗauke kai yayi daga kansu,  amsa mashi sallamar da yayi su kayi, gaishe da shi su ka shiga yi, ba tare da ya tsaya ba ko ya kalli inda su ke ba yace lafiya, iya abun da yace kenan ya haura sama wurin mansoor, tura ƙofar parlorn yayi ya shiga, samun mansoor yayi zaune kan doguwar sofa shi da Fiddausi suna fira ( ɗiyar gwaggo Halima ce,  ita ce budurwar shi da suke waya )  a bakin ƙofa ya tsaya yana kallon su, daga baya kuma ya shigo cikin parlorn, mansoor yace "ok ashe zaka dawo " ba tare da ya amsa mashi tambayar da yayi mashi ba, fuska a ɗaure ya kalli Fiddausi yace "ke tashi ki ba mutane wuri
Episode 34_35

Wani É—an iskan kallo shazim ke bin mansoor da shi
"kasan Allah ko ma wane irin kallo zaka man sai dai kayi amma ba in da zata, tun da ba kai ka kawo ta ba "
"ok haka kace "
"Kwarai kuwa haka nace, kayi duk abun da ka ga dama " Fiddausi dai na bayan mansoor tana zare idanu ƙes take jira ta watsa a guje, kallon ta shazim yayi yana faɗin "ke zaki zo ki wuce ko sai ranki yayi mumunnan ɓaci "
fitowa tayi daga bayan mansoor zata fice, jawo hannun ta mansoor yayi yana faɗin "in wasa da ke ne " hawaye suka fara sauka daga fuskar ta, girgiza mashai kai tayi alamar a'a, "to koma kan sofa ki zauna " ƙin komawa tayi saima sake ɓoyewa da tayi bayan mansoor ɗin, nufo su shazim yayi gadan gadan, ai ba shiri ta watsa da gudan, dan bata san mi zai yi mata idan har ya kamta,sai da ta kusa shiga parlor sannan ta tsaya kan stairs case tana mai da nufashi,  kallon ta su Asma'u su kayi, Amina tace "ke lafiya daga ina haka, sai kace wacce wani abun tsoron ya biyo " bata bata amsar tambayar da tayi mata ba sai ma binsu da take yi da idanu, sai da ta ɗan dawo cikin hankalin ta sannan ta ƙaraso cikin parlorn ta nemi wuri kan sofa ta zauna,sake tambayar ta Amina tayi "yo yana wuce ya shazim ne ya koro to" acewar Asma'u,
Amina tace "wai baza ki yi magana bane"
Sai a lokacin ta samu damar cewa "ya shazim ne ya koro ni ya mansoor yace ba inda zani, ganin yace ba idan za ni ne yasa nayi zama na, wallahi ina faÉ—a maku kaÉ—an ya hana bai make ni ba "
Asma'u tace "dama nasan za'a rina, ni narasa miyasa ya shazim yake wannan isa da mallakar, samun ya mansoor É—in yayi " Amina tace
"Wallahi kuwa rainin wayaun shi yawa gare shi, sai kace wani É—akin shi da zai wani koro ta "
Asma'u tace " samun ya mansoor É—in yayi da har zai nuna mashi wannan isa da mallakar " farida ce tace "wallahi babu ruwana kun ga tafiya ta, dan zai iya fitowa a kowane lokaci kuma kun san mi zai biyo baya idan ya kama ku kuna gulmar sa "
tsaki Asma'u taja tana faÉ—in "matsoraciyar banza da wofi kawai, yo to sai mi dan ya kama mu "
"Wallahi kun san mi zai biyo "
"duk abun da zai biyo baya bawai muna tsoron shi bane "
"ok haka kuka ce Allah ya fito da shi inga ta tsiyar cika baki " tana gama faÉ—a ta shige war ta É—akin kairiyya

*✨SHAZIM✨*

A can bedroom ɗin mansoor, bayan fitar Fiddausi da gudu, kallon shazim mansoor yayi yana faɗin "wallahi kaji kunya, sai kace kai ka kawo ta da zaka wani kore ta, idan kai baka soyayya  an gaya maka kowa irin ka ne wanda  bai san in da ke mashi ciwo ba"
"Wannan kuma ki ake ji, ko yanzu nasa ke ganin wata acikin su sai na ɓata mata rai yanda baka tunanin, inga abun da zaka iya "
"Zan kira ta sai inga abun da za kayi, mara mutuncin kawai "
"Oho dai koma mi zaka ce ka daÉ—e baka ce ba, na mamajo kawai "
"Naji ni na mamajo ne, wanda bai san inda ke mashi ciwo ba fa "
"Kai ake ji idan ma ka fita kasa kairiyya ta kawo man tea " ya faɗa haɗi  da neman wurin zama kan sofa yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya
"Wannan ne kuma baka isa ba "tsaki shazim yaja ba tare da ya bashi amsar maganar shi ba, ficewa mansoor yayi daga bedroom ɗin zuwa parlor, kamar yanda Farida ta bar su Asma'u na gulmar shazim haka mansoor yazo ya same su,bakin benan ya tsaya yana sauraron duk abun da suke faɗa, kairiyya ce da ke kwance ta hange sa ta witsiyar ido, gyaran murya tayi masu amma hakan bai sa sunyi shiru ba sai sake ba da ƙaimi da su kayi wurin yin maganar "da alama  sara kuke  baku duba bakin gatarin ku " jin haka ne yasa fahimtar akwai abun da take son su fahimta, ɗagowar da Amina zatayi karab idanunta kan mansoor daya harɗe hannuwan shi kan ƙirji yana kallon su, duƙar da kai su ka yi ƙasa  , ƙara sowa mansoor yayi cikin parlorn"sannun ku da ƙoƙari ko " ya faɗa yana binsu da idanuwa,ba wacce  ta ce ƙala a cikin su saima tashi da su kayi sumi sumi su ka bar parlorn , tashi Fiddausi tayi zata bi bayan  su , muryar mansoor taji yana faɗin "koma ki zauna " dawo wa tayi ta nemi wuri kan sofar da ta tashi, ɗuƙar da kai tayi tana wasa da ƴan ya tsun hannunta, tashi kairiyya tayi zata bar wuri da katar da ita mansoor yayi ta hanyar cewa "ki kaima shazim tea " da to ta amsa haɗi da nufar kitchen,haƙuri mansoor ya ba Fiddausi akan abun da shazim yayi mata" bakomi ai yaya " fira suka cigaba da yi ciki shauƙin soyayya, zuwa kairiyya tayi ta wuce ta gaban su zuwa sama hannun ta ɗauke da trayn da ta haɗo ma shazim tea,zaune yake kamar yan da mansoor ya barshi,ƙafa ɗaya kan ɗaya yana latsa wayar shi,   ciki ta shiga da sallama a bakin ta, sallamar da tayi ya amsa, ƙara sawa tayi cikin parlorn kan table ɗin dake ɗakin ta ɗaura mashi trayn, tnxs yace, fice wa  ta yi zuwa parlor ta wuce su mansoor zuwa ɗakin ta, shazim yana gama shan tea ɗin wayar sa ya saka cikin pocket ya nufi main parlor, kallo ɗaya yayi ma mansoor da Fiddausi dake parlorn, hararar shi mansoor yayi, ɗaga kafaɗa shazim yayi yana faɗin "aikin banza " haɗi da kama hanya ya fice daga part ɗin, yana fita a waje ya ci karo da uncle Ahmad zai shigo, gaishe da shi shazim  yayi, amsa mashi yayi yana faɗin "wai ina kaje ne tun ɗazu bayan kasan yau su uwani zasu zo, ai ko ba komi da ka tsaya kun gaisa tukunnan  " amsa shazim ya bashi da "naje wurin Abdallah ne saboda wani aiki da muke  "
"Ok to kashiga part ɗin innah  ku gaisa da su  suna can " da to ya amsa haɗi da nufar part ɗin, ciki uncle ahmad ya shiga lokacin har mansoor ya koma part ɗin shi ita kuma Fiddausi tana ɗakin kairiyya a nan zata kwana, sama ya wuce zuwa nashi bedroom ɗin.

Shazim tsayawa yayi a bakin part ɗin Innah kamar zai shiga kamar bazai shiga ba daga bi sani dai ya shiga bakin shi da sallama ciki ciki, in ba ka kalli bakin shi ba baza ka taɓa cewa yayi sallama ba,gwaggo Halima ce da innah sai Aunty zainab da ke ba yaron ta abinci sai  maryam a parlorn, amsa mashi sallamar da  yayi Aunty zainab tayi, bawai dan taji sallamar da yayi ɗin ba sai dan sanin ba zai taɓa shiga wuri  ba tare da yayi sallama ba, wuri ya samu kan sofa ya zauna, kallon gwaggo Halima yayi yace " ina wuni Aunty "da yake haka yake kiran ta
"lafiya lau shazim, ina ka shige tun É—azu nake ta cigiyar ka "
"na je wani É—an aiki ne "
"Agogo sarkin aiki, a nan É—in ma baka huta ba" murmushi yayi ba tare da yace komi ba, Innah ce tace "da yake uwar ka kawai ka sani shiyyasa ka gaishe da ita "
"to idan ban fara gaishe da ita ba ke zan gaida "
"wah ni, ai ba jiran ta ka gaisuwar nake ba "
"Koma kina so ba wai zan gaishe da ke ɗin bane " harara maryam ta maka mashi jin yan da yake  mai da ma innah magana yan da ran shi ya so
"bana ma so,  gida cike yake  da ƴaƴan albarka, kuma sun gaishe da ni, ba taka nake jira ba " har ya buɗe baki zai mai da mata martanin maganar da tayi, gwaggo Halima ta katse shi ta hanyar cewa " shazim ya su Ammyn ku da malam " tayi hakan ne dan ta hana shi ba innah amsar maganar da tayi dan tasan abun da zai fito daga bakin shi ba mai daɗi bane
"Ammy na lafiya haka ma malam "
"masha Allah "
Aunty Zainab ce tace "shazim ya kwana biyu, ya lagos "
"lafiya lau alhmdllh, ya gajiyar tafiya "
" ba gajiya" jan shi da fira gwaggo Halima tai ta yi har su ka ɗan  ɗauki lokaci, tashi yayi zai tafi, da katar da shi gwaggo tayi ta hanyar cewa " ka jira yaya ta fito ku gaisa " kallon maryam tayi "maraya  je ki kira ta su gaisa " tashi tayi ba tare da ce ƙala ba ta nufi bedroom ɗin innah, "zauna shazim kafin ta fito"
da to ya amsa haɗi da komawa kan sofa ya zauna yana amsar yaron Aunty zainab, tun da ya shigo yaron ke miƙo mashi hannu alamar ya ɗauke shi,amsar shi yayi  haɗi da tambayar ya sunan shi "gaskiya shazim mutuncin ka ra gage ne yanzu bama ka san sunan shi ba kenan "
gwaggo Halima ta ce " a'a kar ki ga laifin shi,yaron da ba'a nan kika haife shi ba, kuma ma  duka yaushe kika dawo ƙasar ne "
Aunty Zainab tace " haka ne,  sunan shi  Aayan "
" Allah ya raya " yace da Ameen Aunty zainab ta amsa,
Maryam samun gwaggo Uwani tayi kwance kan gadon innah amma ba bacci take ba, zama maryam tayi bakin bed É—in tana faÉ—in "mamy wai shazim ne ya shigo, Aunty halima tace kizo ku gaisa "
"É—an rainin hankali sai yanzu yayi lokacin zuwa kenan" maryam tace " ko dai aka ce ya zo ba "
"haka ne kuma yanzu haka wani cikin su yaya ne yace yazo ya gaishe da mu"
" ba ma mamaki " tashi gwaggo Uwani tayi tana faÉ—in "bari naje na same shi" ta faÉ—a haÉ—i da kama hanya ta fice, bin bayan ta maryam tayi.
firar suke cikin kwanciyar hankali shazim dai na sauraron ya ƙagara ta fito dan ya samu ya koma part ɗin su bacci ne cike da idanun shi.
gwaggo Uwani ce ta fito marya na bayan ta, a bakin ƙofar ɗakin innah ta tsaya tana faɗin " isashe ai nayi tunanin kafi ƙarfin gaishe da mutane "banza yayi da ita yana yi ma Aayan wasa duk da ya san da shi take ba tare da ya kalli in da take tsaye ba
"Eh dole kayi banza da ni saboda  ga mahaukaciya sabon kamu na magana "ko kallon in da take yanzu ma bai yi ba,tsaki yaja a ranshi yana faɗin "da ya san masifa zatayi mashi da bai tsaya ba " masifa take ta in da  take  shiga ba tannan take fita ba, da dai ya gaji da jin banbamin da take, ajiye Aayan yayi kan sofa haɗi da kallon gwaggo halima yace "sai da safe "
"Allah ya tashe mu lafiya " da ameen ya amsa haÉ—i da kallon Aunty zainab yace "sai da safe "
" to Allah ya kaimu " ficewa yayi yana jiyo muryar gwaggo Uwani tana zazzaga masifa kamar ta ari baki " zanyi maganin abun da yake damun ka mara mutunci "
gwaggo Halima tace "gaskiya yaya kina abun da bai da cewa, yaron nan fa har ya tashi zai tafi na tsayar da shi dan ku gaisa amma kin fito kin rufe shi da faÉ—a mara tushe bare asali "
"Ok ni zaki ce ma haka saboda wannan yaron, ai da kin sani da baki tsayar da shi ba da kin bar shi yayi tafiyar shi "
"gaskiya yaya ki chanza, dan ko ɗazu banji daɗin abun kika yima Fatima ba, ya rinya ƙarama mi tasani game da abun da kike nufi "
"Wai sadiya magana kike son faÉ—a man saboda waÉ—annan yaran ko mi kike nufi "
"ni ba magana nake son faÉ—a maki ba kawai dai ina son ki san abun da kike aikatawa bai dace ba kwata kwata "
" a'a maganar dai kike son faÉ—a man a kan yaran da ban sani miye haÉ—in ki da su ba "
"Amma nayi mamaki yaya da ilimin ki kike faÉ—in haka,bayan kin san jinin da ke yawo a jikin ki shike yawo ajikin su amma kike faÉ—in haka "
"jinin da dai ke yawo a jikin ki amma ba jiki na ba "
"Ai kuwa ko kin ƙi ko kin so jinin da ke gudana ajikin ki shi ne dai ajikin su"
"Wa ni Allah ya tsari gatari da saran suka, ni bani da wata alaƙa da su "
"Ke kuwa ke da alaƙa da su, saboda uban su da kika haɗa uba da shi "
"dan na haÉ—a uba da uban su ba ahi ke nuna cewa sun zama jinina ba"
"Wannan kuma kin faÉ—i san ranki ne "
"Wai sadiya miye ribar ki idan kin goyi bayan yarannan ne, wata riba gare ki "
"ni kuwa ke da riba, saboda zumunci Allah ne yace ayi shi kuma na riƙe shi da hannu bibiyu "
"wahalar banza kike, yau da ace uban nasu kafin ya bar duniya ya bar wani abun arziƙi to da nace kina yi ne dan ki samu wani abu a wurin su "
"ko mi nake inayi ne dan Allah, kuma maganar mahaifin su dake, ina tuna nin ko bai bar komi ba da zai rasu ina tananin sai da ya rufa maki asiri ke da Æ´aÆ´an ki da Æ´an uwanki kafin ya bar duniyar"
"Wai dakata sadiya, gori kike son yi man kan abun da sadiq yayi man "
"Ni ba gori nake maki ba saboda ba ni nayi maki ba, ina tuna maki ne da abun kika manta "
"gorin dai kike man sadiya kuma na gode "
"duk yan da kika É—auka yaya, Allah dai yasan mi nake nufi " Innah tace "wallahi kin bani mamaki sadiya, Æ´ar uwar ki kike ma gori akan abun da wani yayi mata, miye dan gan takar ki da shi da har zaki ba É—e baki kiyi ma Æ´ar uwar ki ta jini gori "
"mama sai dai ku ƙi fahimta ta amma ni ba gori nike mata ba, kuma innah ki dai na cewa ba ni da alaƙa da su, duk duniya basu da wasu da zasu nuna a matsayin dangin uban su bayan mu, muma haka kamar yan da zamu nuna su mansoor a matsayin ƴaƴan yan uwan mu haka suma dole mu nuna su a matsayin haka"
gwaggo Uwani tayi cab tace" ki dai nuna su amma ba dai ni ba, bari kiji sadiya na san ko mi yasa kike wannan faÉ—e faÉ—en "
Aunty Zainab ce tace " dan Allah mama Aunty kuyi haƙu ku dai na wannan gan ganun ba dan ni ba "
"taya zaki ce haka zainab, gara dai ta ƙarasa yi man gorin da ta fara "
"Ni dai ko mi ki kace naji, kamar yan da muke zuminci lokacin da yake raye yanzu ma bazan fasa ba "
maryam tace " haba mama dan Allah karku zama ƙana nan yara a gaban mu, mu ya kama ta ace munyi haka kunyi mana faɗa amma ba wai ku ba" ta shi gwaggo Halima tayi ta fice daga part ɗin zuwa na uncle ahmad, bedroom ɗin mama ta nufa, tsit ta same shi ba kowa mama na ɗakin abba, hasken ɗakin ta kashe haɗi da hawa kan bede ta kwanta zuciyar ta duk ba daɗi.

Lokacin da ya bar part ɗin innah part ɗin su ya nufa, a main parlor ya zauna kan sofa, gaba ɗaya ji yake zaman abujar nan kamar yana kan ƙaya yanke shawara yayi gobe ko da da yamma ne sai ya bar abuja ya koma lagos, ya ɗan jima zaune sannan ya tashi zai nufi sama zuwa bedroom ɗin shi, karab idanun shi suka sauka kan mutum dake zaune kan dinning ya duƙar da kai kan table , tashin farko bai gane ko waye ba sai da ya matsa dinning area sannan yaga ashe macece kuma fatima, ƙara sa wa yayi haɗi da kiran sunan ta amma ko motsi bata yi ba, bubbuga table ɗin yayi still bata motsa ba abun ya ɗaure mashi kai wane irin bacci ne take yi haka har bata ji kiran da yayi mata ba, gaskiya ba lafiya, hannu yasa ya ɗago da kanta, ya salam ya furta ganin ko numfashi bata yi, ruwan da ke kan dinning ɗin ya ɗauka buɗe marfin jirkar yayi ya ɗan zuba a hannun shi shafa mata yayi a fuska amma bata motsa ba, sai da yayi haka kusan sau uku sannan ta ja wani dogon numfashi "mi ke damun ki? " ya jefa mata tambaya, biji biji take kallon shi saboda nauyin da idanun ta su ka yi  mata, sake  jefa mata tambayar yayi, ware idanun ta tayi a kan fuskar shi, "da ke nake magana, mike damun ki "
da ƙyar ta iya furta "babu komi yaya, nayi dinner ne shine bacci ya ɗauke ni ba tare da na sani ba  "
"ok da man a nan kike dinner "
"a'a  yau ne nayi  a nan "
"Zaki faɗa man mike damun ki ko sai na ɓata maki "
"da gaske nake yaya ba komi " tsawa ya daka mata yana faÉ—in "ina wasa da ke ne, zaki faÉ—a man ko sai na ci mutuncin ki " fashewa tayi da kuka " Aunty Ilham ce ta mare ni "
"ta mare ki da kika yi mata mi keken "
"Wai dan momy tace na kira su su zo su ciki abinci, to shine sai tayi magana ni kuma ban ji ta ba, dan kawai nace banji ta ba shine ta mare ni Aunty feenah ta shaƙe man wuya "
"Ok shine kika zo nan kina kuka har sai da numfashin ki ya É—auke ko "
"ba kuka nayi ba, bacci ne ya É—auke ne "
"ok yayi, kinsha magani "
"Eh sa'ada ta kawo man "
" to yayi, ina so gobe tun da safe ki haÉ—a duk wani kayn ki dake can part É—in gobe zamu koma lagos ina fatan kin ji ni"
"Eh yaya naji "
"ta shi ki wuce kije ki kwanta " da to ta amsa haɗi da nufar ƙofa zata fita " ina za ki "
"zanje na kwanta ne "
"Ok shine kika kama hanyar fita "
"Zanje É—akin sa'ada ne "
" ba can zaki ba, ɗakin ki zaki wuce " da to amsa haɗi da nufar sama ta shiga ɗakin ta bata taɓa kwana a cikin shi ba, tashi shima yayi ya nufi na shi bedroom ɗin,a jiye wayar shi yayi kan bed ya shiga toilet ta ɗauro alwala, carpet ya shimfiɗa ya shiga gaba tar da nafilfilo da yake yi duk dare, bayan ya gama light ɗin ɗakin ya kashe haɗi da hawa gadon shi ya kwanta, bacci ya ɗauke shi cikin ƙan ƙanin lokaci

*WASHE GARI *

Bayan ya dawo daga masallaci ɗakin fatima ya fara liƙawa dan ganin a wane hali take ciki, zaune ya same ta kan carpet ta gama sallar subhi, gaishe da shi tayi, amsa mata yayi yana faɗin "ya kike jin jikin ki yanzu "
"lafiya lau"
"to masha Allah, ki ƙara shan maganin ki " da to ta amsa mashi, ta shi yayi ya bar ɗakin ya nufi nashi, wayar shi ya ɗauka ya kira ammay ya sanar da ita yau zasu dawo,  cewa tayi sai dai shi ya dawo yau amma ban da fatima,bai faɗa mata cewa fatimar bata jin daɗi ba ya dai roƙi ta bar su su dawo yau amma tace a'a, ganin bazata haƙura bane ya sa shi yi mata sallama, mai da akalar kiran yayi ga malam bugu ɗaya malam ya ɗaga yana faɗin "likita bokan turai ka shige abuja ba a ko jin ɗuriyar ka "
"ai insha Allah ina nan dawowa yau "
"Allah ya nuna mana "da ameen ya amsa yana faɗin "na kira ammy na faɗa mata yau zamu dawo ta ƙi amincewa wai sai dai ni na dawo ni kaɗai "
"To ai ba wani abu bane dan ka baro su can, sai su dawo da kan su "
"ba wai barin su bane matsala malam,  su gwaggo Uwani suna kuma kasan halin ta da ya ranta shiyyasa bana son su zauna musamman fatima, dan ko jiya ban san mi ya haɗa suba har sai da su ka yi sana din tashin ciwan ta"
"Subahanalilahi, yanzu ya jikin nata "
"taji sauƙi, ina tsoron abun da zai biyo baya ne yasa nake son mh dawo tare "
"E gaskiya ya kamata ku dawo tare, ku shirya ku tahu zanyi magana da Aishar "
"To shikenan malam mun gode, sai mun dawo " Allah yasa malam ya faÉ—i sallama suka yi, kiran noraiz yayi awaya yace ya same shi a É—aki, ko da yazo ce mashi yayi ya haÉ—a kayan shi yau zasu koma lagos, da fara ko uziri noraiz yafa kawo mashi akan ya bari sai gobe ko monday, ganin babu wasa a fuskar shazim ne yasa shi kama bakin shi yayi shiru.

Cikin parlorn su ka shigo hannun su É—auke da basket, dinning area suka nufa, feenah ce ta fito da flaks É—in abinci tana jerawa kan dinning
Jin motsin mutum ne yasa fatima fitowa parlorn, ganin su feenah yasa ta tsayawa a bakin ƙofar ɗakin ta, Ilham ce tace" ke zo nan " banza tayi da ita " ke bada ke nake magana ba " banza fatima ta sake yi da ita ganin bazata zo bane yasa Ilham tashi ta nufe ta " ke har ni zan kira ki kiyi banza da ni " da buɗar bakin fatima sai cewa tayi " eh nayi banza da ke ɗin sai aka yi mi " da sauri feenah ta ƙara so tana faɗin "lallai wuyan ki ya isa yanka " hannu Ilham tasa zata ɗauke fatima da mari bata kai da kai mata marin ba taji saukar lafiyyen mari a fuskarta har sau biyu, ɗago da fuskar ta tayi tana kallon shazim da ke tsaye gaban su, feenah zata buɗe baki tayi magana kenan ya ɗauke ta itama da wani a zabeben mari har saida ta dafe ƙarfen bene dan ba ƙaramin maruwa suka yi ba" ya shazim mi mukayi ka ma... " bata ƙarasa ba yasake ɗauke da mari ganin haka ne yasa Ilham watsawa da gudu ta nemi hanyar fita , magana ya fara cikin kakkausar murya "wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe  da wata banza a cikin ku zata sake ɗaga hannu ta daki fatima" yana gama faɗa ya wuce ta nan tsaye dafe da kumatu tana kuka, fatima ɗakin ta ta shige ta turo ƙofa, Ilham ce ta dawo ganin shazim ya  fita ta kama hannun feenah suka bar part ɗin..
Episode 36_37_

Ilham ce ta dawo ganin shazim ya  fita,  ta kama hannun feenah suka bar part ɗin zuwa part ɗin Innah, feenah sai kuka take kamar wata ƙaramar yarinya, gwaggo Halima su ka samu akan sofa a parlor da cup  a hannun ta tana shan kunun gyaɗa, da sauri ta juyo tana kallon feenah da ke ta kuka kamar wata ƙaramar yarinya "ku kuma lafiya daga ina haka?"
basu bata amsar tambayar da tayi masu ba, sai ma neman wurin zama da su kayi kan sofa, feenah har wani ƙara ɗaga murya take duk dan innah da gwaggo uwani su ji su fito
"wai ku ba da ku nake magana ba,ke kuma ko ki man shiru ko wallahi na make maki baki, sakar yar banza kawai" Ilham tace " mama ya shazim ne fa ya same mu yayi ta marin mu baji ba gani "
"wani iskancin kuka yi mashi ko "
"ba abun da muka yi mashi, abinci kawai muka je kai mashi shine ya haumu da mari "
"ke Ilham ƙarya kike shazim ba zai mare ku ba haka nan dole da abun da kuka yi mashi, kuma ma ko ba abun da kuka yi mashi ya mare ku yayi man dadai dan kun cancanci fiye da haka " jin abun da gwaggo Halima tace ne yasa feenah ƙara sautin muryar kukan da take, sai Aunty maryam ta faɗo parlorn kamar an jehu ta "mi nake ji, ba dai wannan mara mutuncin ba ne ya mare ku"
tsawa gwaggo Halima taa daka mata " ke maryam ki shiga cikin hankalin ki na ƙara jin kin faɗi wani abu a nan ranki zaiyi mumunnan ɓaci shashasha kawai kema"
turo baki maryam tayi tana faÉ—in
"haba Aunty mi yasa zaki ce haka, du ba fa kiga fuskar feenah duk sahun hannun shi, in ban da zalinci mi suka yi mashi har haka "
gwaggo Uwani ta fito tana faÉ—in "wallahi bai mari banza ba "
gwaggo Halima tace "yaya sai dai fa ki ga laifin shazim,  amma ko rantsuwa nayi bazan kaffara ba su ke da laifi "
"dama haka zaki ce  tunda da man ba son ganin laifin shi kike ba "
"Wai miyasa a kullum kike cewa, ina goyan bayan shi ne, ni ba goyan bayan shi nake ba kawai ina goyan bayan gaskiya"
" to ai sai ki ta goyan bayan gaskiyar, amma wallahi bai mari banza ba sai ya gane kuskuren shi "
"to shikenan in dai shazim ne ga kai ga fata "
"Wallahi Aunty laifin su " sa'ada ta faɗa wacce shigowar ta part ɗin keknan,juyawa su kayi su duka suna binta da idanu, gwaggo Uwani ce tace" munafuka ubanwa yasa bakin ki daga shigowar ki " turo baki sa'ada tayi " wallahi ba ƙarya nake ba,Aunty Ilham ce ta mari fatima kawai dan tayi magana bata jita ba, ita kuma Aunty Feenah tasa ɗan kwalinta ta shaƙe mata wuya bayan tasan tana da matsalar numfashi "
tafa hannu gwaggo Halima ta shiga yi tana salallami " yanzu da kashe ta ku ka so yi kenan, dan uban ku ku sau nawa mutum ke maku magana kunayin banza da shi bayan kuna jinshi , wallahi da ni na riƙa ku da sai kun yaba ma aya zaƙinta mutanen banza kawai "
gwaggo Uwani tace "ke yanzu kenan harkin yarda da maganar wannan shashasha yarinyar "
"dole na yarda da ita dan na san sa'ada bazata yi masu ƙarya ba"
Feenah tsagai tawa tayi da kukan da take ta kalli sa'ada tana faÉ—in "wallahi kika bari na kama ki sai kin gane baki da wayau " duka gwaggo Halima ta kaima feenah "dan ubnki idan kin kama ta kiyi mata bungun da zata kasa tashi mar mutunci, kuma wallahi daga ke har Ilham É—in sai nasa Usman yayi maganin ku "
" a kan mi zaki haÉ—a su da shi, duk wannan marin da wannan mara mutuncin yayi masu bai isa ba "
"ai mai sauƙi yayi masu, gara nasa usman yayi masu dukan da ko wani su kaga zai dake ta sa hana, bari ma kiga yanzu zan kira shi "
"a'a sadiya kar ki kira shi a bar zancen kawai ya mutu "
"idan har kinga zancen ya mutu to sai idan ita fatimar ce tace ta yafe masu "
"wallahi baza ki ja masu raini a wurin yarinya ba, tun da dai zancen ya wuce a barshi kawai "
" idan fa ba ita tace zancen ya wuce ba to fa bazai wuce ba, sa'ada kira man fatimar " da to sa'ada ta amsa haɗi da fita,ko da taje part ɗin shazim ta samu a parlor, gaishe da shi tayi, harta miƙe zata nufi ɗakin fatima yace mata bacci take saboda maganin da ya bata, koma wa tayi part ɗin Innah ,  ganin  ta dawo ita kaɗai ne yasa gwaggo halima tace " ina fatimar take "
"ya shazim na samu a parlor yace bata jin daÉ—i ya bata magani bacci take"
"to yaya kin dai ji ko, har sun kaita ga kwanciya, wallahi ko suje har part ɗin su bata haƙuri ko yanzu nasa Usman yayi maganin su "
"dan Allah dai ki ƙyale su,tun da harya bata magani zata ji sauƙi ne "
"sai fa sunje sun bata haƙuri, idan ba haka ba kuma tam"
"ba inda zasu, wai ke sadiya mi ke damun ki,  to kisa usman ɗin ya dake su " innah ta faɗa wacce shigowar ta kenan daga part ɗin uncle Ahmad
"mama dukan fatima  fa su kayi bayan sun san tana da matsala "
"koma mi su kayi mata baza su bata haƙuri ba "
"shikenan mama, amma bana jin daÉ—in abun da kuke yi "
"dallah ni yiman shiru tun da baki san ciwan Æ´aÆ´an ki ba "
"Allah ya huci zuciyar ki " kawai gwaggo halima ta faɗa haɗi da tashi ta shiga kitchen, zama innah tayi kan sofa hannu ta miƙa ma feenah " zo nan ƴar albarka dai na kuka zai gane bai da wayau, yi shiru kinji " matsowa tayi kusa da innah ta ɗaura kanta saman kafaɗar ta "kar ki damu sai yayi dana sanin marin da yayi maki har ita munafukar fatimar,  Allah dai ya kaimu anjima" lallashin feenah innah tai tayi har sai da taga ta shiru.

✨SHAZIM✨

duk wani shiri da zai masu na tafiya yau ya kammala , shi ka É—ai yake kiÉ—an sa yake rawar sa, bayan mansoor ba wanda yasan da shirin shi na tafiya yau jira kawai yake su uncle su yi taron su da yamma su kuma su wuce, fatima ce ta fito daga É—akin ta parlor ta nufo har kan sofar da take kwance, gaishe da shi tayi sannan tace mashi za ta je part É—in uncle Ibrahim ta É—auko kayanta,da to ya amsa mata haÉ—i da ce mata kar ta saki ta daÉ—e, to tace ta fice zuwa part ko da ta shiga ba kowa a parlor É—akin sa'ada ta shiga samunta tayi zaune gaban dressing mirror tana shafa powder zama fatimar tayi kan gado tana kallon sa'ada da ke kallonta ta cikin mirrorn
"Wai lafiya sister kike kallo na kamar baki sanni ba "
"Fatima ai dole na kalle ki, wai daga bari ki É—auko magani shikenan ko "
" wai dama dalilin da yasa kike man wannan kallon ne "
"Ok tambaya  ta ma kike "
ganin kamar ran sa'ada ya ɓaci ne yasa fatima cewa"sorry, ya shazim ne yace na kwana can "
"Ok ya jikin na ki "
"da sauƙi "
"Allah ya ƙara sauki, yau ɗin zaku tafi?"
"yanzu ma kaya na nace mashi zan É—auko"
"ok naso ace ya shazim ya bari ko da zuwa gobe ne "
"nima naso amma ya zanyi" fira su ka shiga yi duk akan tafiyar da su fatima za su yi sa'ada kamar zata yi kuka, anan fatima tayi wanka , bayan sun shirya ita da sa'ada sallah su kayi batan sun gama ne su ka nufi  ɗakin momy , da sallama su ka shiga momy na zaune kan carpet ta gama sallar, jiranta su kayi har ta kammala,  fatima tace "ina wuni momy"
"lafiya lau fatima, ya jikin ki "
"naji sauƙi"
"to Allah ya ƙara sauki, kiyi haƙuri kinji"
"bakomi momy"
"momy wai ya shazim yace zasu tafi, dan Allah kice ya bar fatima nan shi ya tafi "
"A'a gara dai su tafi, kuma ma fatimar ba makaranta zata fara zuwa ba "
"eh momy amma ai da sauran lokaci "
"duk da haka dai "
"momy baki son su tsaya ne "
"kinci gidan ku " turo baki sa'ada tayi tana faɗin "dan Allah idan kina so su tsaya ki roƙi ya shazim ɗin pls"
" sai kuma kiyi"
" shikenan momy tun da baza ki ba shi haƙuri ba bari na faɗama dady shi sai ya bashi, dama dady bai san zasu tafi yau ba " ( da yake suna gida shi da uncle Ahmad  ) ta faɗa haɗi da miƙewa ta nufi ƙofar fita
" kika saki ko ƙafar ki ta taka waje sai ranki ya ɓaci dan baki da hankali bai faɗama dadyn ku ba shine ke zakije ki faɗa mashi kin dawo kin zauna kafin ranki ya ɓaci "
da wowa tayi tana turo baki " momy to dan Allah ke ki bashi haƙuri ya barta "
"Kima daina yi man  magiya,gara su tafi ko itama ta huta "
ba yanda sa'ada bata yi ba amma momy tace bazata ce ma shazim ya bar fatima ba, har part ɗin uncle Ahmad su kaje nan ma sai da sa'ada ta roƙi mama kan tasa baki shazim ya bar fatima amma ita ma tace ba ruwan ta, tama fiso su tafi dan sarai tasan halin su gwaggo Uwani a ka bar fatima wahalar su kawai zata sha kafin su tafi.

Kamar yanda su uncle Ahmad su kace zasu yi meeting a yau, basu fasa ba yanzu ma haka sun hallara a babban parlorn da su ke meeting, Innah ce kawai sai su gwaggo da su uncle ba yaran, tattaunawa su ka fara daga bisani uncle Ahmad yace ayima Zainab magana tattaro kan ƙannanta, a waya gwaggo Halima ta kira ta, zaman jiran shigowar yaran su kayi,Aunty zainab ce ta fara shigowa sai Aunty maryam da Amina da Asma'u,Farida sai Fiddausi, kairiyya da su fatima ta shigo sa'ada na ɗauke da salma ƙanwar kairiyya ce,  feenah da Ilham suka shigo wuri guda matan su ka zauna sai mazan
ya usman tare ya shigo da su Anwar, Mahammad, mahmud, luqman, noraiz, faisal, mubarak, Umar, musa harda ƙananan Aliyu da Aminu duka mazan sun hallara mutum biyu ne babu shazim da mansoor, ganin babu su ne uncle Ahmad yace "usman ina sauran ƙannan naka"tun kafin yace wani abu   gwaggo Uwani tayi carabtace " na san dai mansoor zai shigo wannan mara mutunci sai dai wani daga cikin ku yaje ya kira shi amma bazai zo ba " gwaggo Halima tace " yaya baki ganin zarau sai kin tsinka, yanzu idan ya shigo ɗin batare da wani ya kira shinba fah "
ta buɗe baki kenan zata mai da ma gwaggo Halima amsa, sai ga mansoor ya shigo da sallama a bakin shi shazim na bayan shi, jikin shi sanye da baƙin wando cargo sai t_shirt fara, kallon gwaggo Uwani gwaggo Halima tayi tana faɗin "to yanzu gashi nan ya shigo " tsaki gwaggo Halima tayi batare da tace komi ba, wuri su shazim su ka samu kusa da su usman su ka zauna,uncle Ibrahim ne yace Faisal ya buɗe masu taro da adu'a, tashi Faisal yayi yayi adu'a bayan ya gama ya koma mazunin shi ya zauna,sallama  uncle Ahmad ya fara sannan ya ɗaura da nasiha , kowa ya baza kunne yana sauraron shi har ya gama nasihar da ya fara sannan yace " a taƙaice dai maƙasu dun wannan taro ba komi bane face a kan maganar  ranar da muka tsaida ce ta auran wasu daga cikin ku, tun tuni munso ace  an kammala komi ranar auran kawai muke jira, sai dai hakan bai samu ba dalilin wasu da basu shirya ba a cikin ku muka ɗaga masu ƙafa zuwa wani lokaci, wasu sun gabatar da waɗan da suke so wasun ku kuma har yanzu shiru, yanzu dai munyanke hukuncin tsaida rana ga duk kanku da wanda suka gabatar da wanda su ke so da wanda su kayi kunnan uwar shegu da maganar,dama ɗaya ce zan ba ma wanda basu gabatar da zaɓin su ba tuntuni shine yanzu su gabatar mana, idan ba haka ba zamu zaɓa masa duk wanda ko wacce ta dace "
ɗan nisawa uncle Ahmad yayi sannan ya ɗaura da cewa" shazim da mansoor sai faisal  ina magan ne a kan ku,tun a wancan lokaci na yi maku magan akan ku gabatar man da zaɓin ku amma shiru, abun da nake so na sani shine baku da raɓine ko kuwa wani abun kuke nufi na da ban, to kun daiji mi nace yanzu idan kuna da magana muna sauraron ku kafin mu zartar da hukuncin da muka yanke, muna sauraron ku " tun da uncle Ahmad ya fara magana su ka sadda kai ƙasa,  kowa dake parlorn zuba masu ido yayi domin yaji abun da zasu ce,faisal ne yace " ni ina da wacce nake so "
Uncle Ibrahim ne yace "to muna sauraron ka"
"uncle dama farida ce "  shiru su kayi basu ce komi ba,fiddausi kamar tayi kuka jin mansoor ya ƙicewa komai, shi kuwa mansoor so yake shazim ya gabatar da wacce yake so duk da yasan da wahala ,  uncle Ibrahim ne yace " muna sauraron ku kunyi shiru,ko kawai mu cigaba da abun da ya tara mu " da sauri Mansoor yace"uncle ni ina da wacce nake so" ajiyar zuciya ta sauke jin yace yana da wacce yake so
Uncle Ibrahim yace " to masha Allah kana iya faÉ—a mana wacece "
"dama uncle ba kowa bace Fiddausi ce " murna kamar ta kashe Fiddausi jin mansoor ya ambace ta
" to masha Allah"
Uncle Ahmad ne yace " to saura kai shazim muna sauraron ka "
ɗagowa yayi ya kalli uncle ahmad sai kuma ya sake mai da kanshi ƙasa, tsit kowa yayi jiran abun da shazim zai ce kawai su ke, tsawan 4 minutes shazim baice komi ba
"to idan na fahimta har yanzu baka fitar da zaɓin naka ba kenan"
sai a sannan ya buÉ—e baki yace "a'a uncle "
"to muna sauraron ka "
"ina so a ƙara man lokaci,bayan na su mansoor sai ayi nawa "
"wannan ne baka isa ba shazim,da cewa mu ƙara maka lokaci yau kusan shekara kenan, sai yanzu kuma ka sake cewa mu ƙara maka wani  lokacin abun da bazi yuwu ba kenan "
Uncle Ibrahim ne yace " to yanzu dai munji ra'ayin wasu daga cikin ku,mansoor ya gabatar da Fiddausi a matsayin zaɓin sa faisal farida, Muhammad dama tuntuni mun san ya gabatar mana da kairiyya a matsayin zaɓin sa, to sai wasu da suka nuna ra'ayin yin aure yanzu duk da munfiso mu fara gamawa da manyan su amma tun da sun nuna ra'ayin su na son yin auren yanzu insha Allah za mu yi masu yanda su ke so, kafin nan ina so na sanar da hukuncin da muka yanke akan ga duk wanda bai gabatar da zaɓin shi ba  "
Uncle Ahmad yace "shazim ina so ka sauraremu da kayau, tun da munce ka fitar da wacce kake so kaƙi, to mun yanke hukuncin haɗa ka aure da ƴar uwar ka hauwa'u "
tuna ni shazim ya shiga shin wai wacece hauwa'u cikin yaran dan bai ma san wacece mai wannan sunan ba
Uncle Ahmad ne ya katse mashi tunanin da yake ta hanyar cewa " kayi shiru banji kace komi ba " carab innah tace "yo mi zai ce, daga ma anyi mashi gata "
"duk da haka innah muna son jin ta bakin shi, ina jinka shazim " shiru kamar bazaice komi ba can dai yace
"Uncle bangane wacece kake magana a kanta ba "
riƙe haɓa innah tayi tana faɗin "lallai ɗan iskan gaye wato hauwa'un ce baka sani ba saboda ka raina ma mutane wayau ko, to ba kowa bace face takwara ta feenah ince ita ka santa " wani mumunnan faɗuwa gaban shazim yayi,a zuciyar shi yake faɗin " amma an raina mashi wayau arasa da wacce za'a haɗa shi sai wannan daƙiƙiyar yarinyar, lallai sun shiraya ganin ɓacin ranshi kenan" uncle ahmad ne yace "to ka dai ji ko wacece, mi kace a game da hukuncin " banza shazim yayi da shi kamar ma ba da shi yake magana ba, har sai da mansoor ya zungure shi yace "bro ana magana kayi shiru " ɗago da kanshi yayi idanun shi sun kaɗa sunyi jawur tsantsar ɓacin rai ne a cikin su ya wurga ma mansoor wata mummunanar harara wacce tasa mansoor kauda kai dan bai taɓa ganin ɓacin rai a fuskar shazim ba irin na yau,   mai da kanshi yayi ya  ɗuƙar, gwaggo Uwani tace "yau ga rainin wayau, yan isaka ka ɗauke mu ana magana kayi shiru "wani ɗan iskan kallo ya  jefeta da shihar sai da gabanta ya faɗi  innah tace " kayi fiye da haka ma mara mutunci, aure ne dai sai kayi " feenah dai sai zare ido take tsoron ta kar shazim yace bai son ta
ganin ya mai da su mahaukata ne yasa uncle Ahmad girgiza kai ya cigaba da faɗin"waɗan suka buƙaci a sa ranar da su "
ban da murmushi babu abun da ke fita daga fuskar luqman tun kafin ma a kira sunan shi
Uncle Ahmad yace "luqman da mahmud muna sauraron ku ku gabatar da zaɓin naku muna ji " jin uncle ya ambace su ne yasa farin cikin luqman ƙaruwa, sai da uncle ya sake magana tukunnan mahmud yace "Ilham itace zaɓin da na kawo maku "
"to masha Allah Ilham muna so muji daga bakin ki kinji abun da ɗan uwan ki yace  " duƙar da kai Ilham tayi cike da kunya  tace " uncle na amince "
"masha Allah, Allah ya nuna man lokaci " da ameen kowa ya amsa, sannan uncle ahmad yace "to kai luqman mauna sauraron ka " gyara zama luqman yayi yana kallon Innah da wani munafukin murmushi a fuskar shi yace " uncle ni ba kowa bace zaɓi na face fatima " kamar saukar aradu haka fatima taji maganar luqman, ita yaushe harma su ka samu jituwa da zai ce wai yana sonta anya ba kunnuwanta  bane suka jiyo mata ba dai dai ba, shazim mamaki abun ya bashi dan shi bai san da wani zacen soyayya ba tsakanin luqman da fatima ba kuma da ace ya sani da tuni yayi ma tufkar hanci amma ko yanzu bawai lokaci ya ƙure bane in dai da ranshi da lafiayar shi zai ga wanda zai masu auren dole, watau meeting ɗin nasu ne ma kenan  dan su aka tara wannan taron kenan maganar uncle Ahmad ce ta dawo da su cikin hayyacin su " to fatima kinji abun da yayan ki yace miye ra'ayin ki " kasa cewa komi fatima tayi sai ma kuka da ta fashe da shi " yau ga iskanci, daga tambaya sai kuka, zaki buɗe baki ki ba mutane amsar tambayar da aka yi maki ko kuwa " gwaggo Uwani ce ta faɗi haka cike da masifa, sake fashewa da kuka Fataim tayi " haba yaya kamata yayi kiji dalilin kukan ta bawai ki rufe ta da masifa ba, zo nan fatima " ta faɗa haɗi da miƙama fatima hannu ta zo kusa da ita, tashi fatima tayi ta nufe ta " yi shiru dai na kuka kinji, miyasa ki ke kuka baki son shi ne " carab innah tace " haba dai wane ita tace bata son shi, ta dai faɗi mi take ma kuka"
"dan Allah innah kiyi shiru, idan tace bata son shi ba wanda zai mata dole " acewar uncle ahmad
"idan tace bata son shi kenan biye mata za ku yi kenan, idan ba'ayi mata aure ba jiƙata za'ayi a sha " shazim dai na sauraron su dan yayi rantsuwa inda da ranshi babu wanda ya isa yayi mata auren dole kuma ma da wannan sakaran yaron
"shi na gani, wallahi ko tana so ko bata so sai ta aure shi tun ba jiƙata za'ayi ba...  " katse ta uncle ahmad yayi yana faɗin
"ke uwani kar na sake jin bakin ki a nan, kinji na faÉ—a maki "
" a kan mi zaka ce haka amadu, idan ba'ayi mata auran ba mi zata yi ma mutane " tashi fatima tayi ta fita da gudu tana kuka kamar ranta zai fita, tashi luqman yayi ya bi  bayan ta ba tare da kowa ya lura da shi ba
Shazim yace "idan bata da abun da zata yi maki ke, a kwai waɗan da suke da abunda za tayi ma su, kuma wallahi da raina da lafiya ta babu wanda ya isa yayi mata auren dole " gaban innah ne ya faɗi jin abun da shazim yace,fashewa da kuka innah tayi tana faɗin "ni kake ci ma mutunci a gaban ƴaƴana da jikoki na, saboda baka ganin darajata dan bani na haifi ubanka ba " gwaggo Halima ce tace "kiyi haƙuri mama ki daina kuka, taya zaki ce bai ganin mutunci ki saboda ba ke kika haifi mahaifin shi ba,kin kasa fahimtar shi ne amma..... " bata ƙarasa ba innah tace " yi man shiru ai duk abun da yake aikatawa na lura akwai sa hannunki mara mutunci"
uncle Ahmad ne yace " dan Allah innha kiyi haƙuri kiyi shiru "
"taya zanyi shiru kuna ganin yaro na ci man mutunci a gaban ku kun kasa ɗaukar mata ki "  
"Kiyi haƙuri dai dan Allah " ya faɗa haɗi da kallon shazim yace
"shazim mu ka ke faɗa ma haka koh, na lura ka raina innah ko,  kenan ba mu isa mu yanke hukuncin ba a kan ku kenan ba"
"uncle ba da ku nake ba, amma tun da ta nuna bata son shi a ƙyale ta kawai tun da bawai tayi girman da za'ace ta isa aure ta ƙiyi ba "
"ok kai zaka nuna mana abun da ya dace kenan ko " a cewar gwaggo Uwani,  banza shazim yayi da ita kamar ba da shi take magana ba, duk abun da ake uncle Ibrahim baice ƙala ba saboda a kan ƴaƴan shi ake magana,bazaka iya gane awane hali yake ciki ba jin su shazim sun nuna basu san ƴaƴan shi.
Uncle Ahmad ne yace "to naji ba da mu kake ba,sai ka faɗa man da wanda kake " shiru yayi baice ƙala ba ganin bazai ce komai bane yasa uncle ahmad ɗin cewa " kace babu wanda ya ida yayi mata auren dole,mi kake nufi?" yanzu ma shiru yayi baice komi ba, ɗan nisawa uncle Ahmad yayi yace "to bari kaji hukuncin munriga da munyanke aure babu fashi "
"Uncle wannan yarinyar da kuka haɗa ni da ita bana son ta,a yana yin kukan da fatima keyi alama ce ta bata son shi,   idan kuka tursasa dole sai mun bi umarnin ku komai zai iya faruwa " yana gama faɗa ya tashi ya bar parlorn, da idanu kowa dake parlorn ya bishi,tashi feenah tayi zata bi bayan shi sai a lokacin uncle Ibrahim yasa baki tsawa ya daka ma feenah yana faɗin "dawo ki zauna, shashasha banza " innah ta nufa ta faɗa kan jikinta  fashewa tayi da wani mahaukacin kuka  sai ihu take kamar wacce uwarta ko ubanta ya mutu basu taɓa tunanin shazim zai iya shuka masu rashin mutunci ba irin wannan musamman uncle Ibrahim da ya kasance ƴaƴan shi ne na cikin shi, tashi uncle Ibrahim yayi ya nufi feenah dake jikin innah ya ɗauke ta da wani mumunnan mari haɗi da jan  hannun ta ya bar parlorn, bin bayan su innah tayi tana mashi masifa dan mi zai mareta, yarinya na son shi yace bai son ta ya barta da baƙin cikin da ya ƙunsa mata..

gwaggo Uwani ce tace "yaya yanzu kenan haka za'a zuba ma wannan yaron ido yana cima ma mutane mutunci  kuma baka ce komai ba  "
gwaggo Halima tace " mi kike so yace, tunda yace bai sonta a ƙyale shi kowa Allah ya haɗa shi da rabon shi "
"dallah sadiya kiyi ma mutane shiru ke dama tuntuni nasan cewa baki tare da mu, hada ke cikin masu zuga wannan yaron "
"ni dai komi za kice kice,goyan bayan gaskiya nake, kuma tun da ya nun..... " bata ƙarasa ba uncle Ahmad yace"  dan Allah ya isa haka, kowa zai iya tashi ya tafi na sallami kowa " ɗaya bayan ɗaya yaran suka fara ta shi suna fita wasu naji haushin shazim da fatima wasu kuma na ganin yana da gaskiya duba da rashin tarbiya da feenah ke da shi, uncle Ahmad ka ɗai aka bari a parlorn yayi shiru damuwa ƙarara a fuskar shi.

_*✨SHAZIM✨*_

Tun da ya bar parlorn part ɗin su ya nufa, bedroom ɗin shi ya shiga trollyn shi da ke bakin gadon shi ya jawo ya kai shi parlor wayar shi ya ciro ya kira noraiz bugu ɗaya noraiz ya ɗauka tunkafin yace wani abu shazim yace ka same ni a ɗaki ƙit ya kashe wayar, bayan kamar 10  seconds noraiz ya shigo da sallama, ko sallamar da yayi shazim bai amsa ba yace "wuce ka ɗauko kayan ka " kwata kwata babu sauƙi a fuskar shazim, da to noraiz ya amsa haɗi da ficewa ya nufi bedroom ɗin shi ya fito da trollyn shi zuwa parking lot da mansoor yaci karo zai shigo part ɗin, ba wanda yace ma ɗan uwan shi wani abu, ciki mansoor ya shiga zuwa ɗakin shazim yana shiga shazim na fitowa hannun shi riƙe da jakar laptop ɗin shi, kayan da ke jikin shi ne ɗazo a jikin shi sai p cap da yasa yanzu da baƙin glass, tsaye mansoor yayi yana kallon shi..
Episode 38_39_

Ƙarasa wa ciki mansoor yayi yana kallon shazim sama da ƙasa sanna ya fara magana
"shazim ka bani mamaki matuƙa, ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba "
"mamaki na baka ko?"
"tambayata kake ma "
"mansoor idan har baka ga laifin abun da akai man ba bai kamata ni kaga laifina ba "
"dole naga laifin ka, a gaban mu fa kake faÉ—a masu magan son ranka "
"sai dai kai ta ganin laifi na amma bazan zauna a tauye man haƙƙina inaji ina gani ba, mi fatima tayi da za'a yanke mata wannan  hukuncin kuma su rasa dawa zasu haɗa ta sai wannan ɗan iskan "
"ko da yace yana sonta kaji sun ce zasu aura mata shi ne?"
"Koma dai mi ne ne, bazan taɓa bari a ci zalinta ba, kuma ni kaga tafiya ta "yana gama faɗa yaja trollyn shi ya bar mansoor tsaye yana kallon shi, bin bayan shi mansoor yayi a bakin ɗakin fatima shazim ya tsaya tura ƙofar ya shiga tsit ya samu ɗaki alamar ba mutum a ciki, tunani yayi ko ta fita tare da noraiz, fita yayi mansoor na tsaye "wai shazim fushi kake dani ko mi " banza shazim yayi da shi ya nufi stairs case janye da trollyn shi, sake magana mansoor "magana nake maka shazim "
"inajin ka, mikake so nace maka ne "
"ok haka kace " a taƙaice yace eh, fita su kayi zuwa parking lot aminu ne ya amshi trollyn da ke hannun shazim ya sa a booth, dawowa yayi ya buɗe mashi bayan motar ya shiga rufe ƙofar aminu yayi, mansoor na tsaye bakin part ɗin yana kallon su, noraiz ne ya ƙaraso parking lot ɗin shi da mahmud, tambayar shi shazim yayi ina fatima "tana ɗakin ta "
"bata can " noraiz yace " kila tana part É—in uncle Ibrahim "
"mi take a can kuma?" shazim ya tambaya "nima ban sani ba "
"to kaje ka kira ta " da to noraiz ya amsa haɗi da juyawa ya nufi part ɗin uncle Ibrahim shi da mahmud,da sallama su ka shiga part tsit main parlorn babu kowa, bedroom ɗin sa'ada suka a bakin ƙofar ɗakin suka tsaya mahmud ne yayi nocking, zaune take bakin bed tana kuka taji ana nocking, tashi tayi ta nufi ƙofar ta buɗe mahmud ne yace " sa'ada kice ma fatima ta fito su tafi "
cikin muryar kuka sa'ada tace "ai bata nan, ina tunanin tana É—akinta " noraiz yace "bata can " maimaita maganar sa'ada tayi "bata can yaya, to ina ta tafi?"
"shine ba mu sani ba, mun ma yi tunanin kuna tare "
"ai tun da ta fita a parlor na biyo bayan ta ban san ina ta shiga ba da na zo ɗaki banganta ba  sai nayi tunanin ko tana ɗakin ta , to ko dai tana tare da Aunty kairiyya " sa'ada ta faɗa, fita su kayi zuwa part ɗin uncle Ahmad mahmud da sa'ada ne suka shiga part noraiz wurin shazim ya nufa, yana isowa shazim yace "wai ina fatimar ne kasan ƙarfe nawa yanzu "
"yaya gata nan zuwa, bata tare da sa'ada ne " ok kawai yace, gaba kusa da driver noraiz ya buɗe ya shiga, mahmud ne ya fito shi da sa'ada wurin su suka nufo tun kafin su ƙara so noraiz yace "tana ina "
sa'ada ce tace "can ma bata nan " shazim yace "bata nan" ɗaga mashi kai sa'ada tayi alamar eh, wayar shi ya ciro ya shiga dialing number ta tana ringing amma ba'a ɗauka ba, tsaki shazim yaja yana faɗin "amma sai na ci mutuncin yarinyar nan" sai da yayi mata kusan 5 missed call bata ɗauka ba, ganin dai da gaske fatima ba ɗaga wayar zata yi ba ne yasa shazim cewa "noraiz ku shiga ciki ku duba ta ko tana ɗakin ammy, ko ina dai ku duba ta " da to suka amsa noraiz ya fito su ka nufi part ɗin su, ba inda basu duba har bedroom ɗin shazim dana noraiz ɗin amma ba fatima ba dalilin ta,ne man fatima har part ɗin innah da na su Aunty zainab,su da zasu bi jirgin ƙarfe biyar na yamma sune har aka yi sallar magrib ba su tafi ba suna neman fatima,abun da ya ɗaga masu hankali ganin wayar ta da suke ta faman kira a main parlorn part  ɗin uncle Ibrahim kan sofa  sa'ada har ta fara kuka, hankalin shazim yayi ƙololuwar tashi, ina fatima taje.
duk wannan bidir da suke na ne manta babu wanda su ka faɗa ma suna ne manta, zaune suka yi a main parlorn part ɗin su shazim kowa yayi ta gumi tunanin kawai suke ina fatima ta shiga, sa'ada kuwa sai kuka take mahmud na lallashin ta,har aka yi sallar isha basu san in da ta shiga ba, tashi su kayi su ka nufi masallaci, sa'ada kuwa part ɗin su ta nufa wurin momy , ko da ta shiga samun momy tayi zaune bakin gado tayi tagumi, damuwa ce ƙarara a fuskar ta,da gudu ta faɗa saman jikin ta tana kuka, ɗago da ita momy tayi tana faɗin "lafiya ke kuma daga ina haka, mi ki ke ma kuka kuma " cikin shashekar kuka tace "momy ba'aga fatima ba " da sauri momy ta ɗago da fuskar ta tana faɗin "ban gane ba, ina ta je "
"momy tun ɗazu muke nemanta ni da su ya shazim ba mu ganta ba, muna ta kiran wayar ta ashe tana a nan parlor ta barta "  dafe kai momy tayi tana faɗin "ya salam, ina taje , kun du ba har part ɗin su innah da na su Auntyn ku?"
"eh momy babu inda bamu duba ba amma bata nan"
"har É—akin feenah kin duba "
"a'a momy ban duba ba "
"to ta shi muje mu duba " ta shi su kayi zuwa ɗakin feenah babu in da basu duba har cikin toilet sai da su ka duba babu almun ta,ɗaya bayan ɗaya duk wani ɗaki da ke part ɗin sai da suka duba amma bata ba alamar ta, dafe kai momy tayi kamar mai tunanin,girgiza kai ta shiga yi tana faɗin " ba gaskiya bane , hakan ma bazata taɓa faruwa ba, idan ko haka ne na shiga uku ni turai "
"momy miya faru, miye kuma ba gaskiya ba?" sa'ada ta jefa mata tambayar haÉ—i da tsare ta da idanu
"bakomi sa'ada,kije part ɗin su Kairiyya ku sake duba ta " momy ta faɗa tana nufar  part ɗin dady,fita tayi zuwa part ɗin su shazim yan da ta bar su ɗazu zazzaune kan sofa yanzu ma haka ta same su amma ban da shazim
"ya noraiz an ganta " girgiza mata kai kawai yayi, fashewa tayi da kuka sai kace ƙaramar yarinya, mahmud ne yace" dan Allah sa'ada kiyi mana shiru, ba ɓacewa tayi ba za'a ganta"
ficewa tayi daga part É—in.

Su Asma'u ne zaune a main parlorn part ɗin uncle Ahmad, fira su ke duk a kan meeting ɗin ɗazu da abun da shazim yayi, kowace na tofa albarkacin bakin sa, kairiyya ce ta saukko daga sama part ɗin mansoor  hannun ta ɗauke da tray da alama dinner ta kai masa ta shigowa parlor sa'ada na banko ƙofa kamar zata ɓallata ta shigo fuskarta jage jage da hawaye,da sauri su ka juyo suna binta da idanu gaban su sai faɗuwa yake jira kawai suke su ji tace ga wanda ya rasu dan duk a tunanin su mutuwa akayi , sai kuka take ta kasa cewa komi,magana su ka shiga yi mata "ke wai mi akayi ne kike kuka, wani ne ya rasu " sai jefa mata tambayoyi suke amma ta ƙice masu ga abun da take ma kuka, karshe ma part ɗin mansoor ta nufa da gudu, ta shi su kayi suna binta da idanu har ta haye sama, kallon kallo su ka shiga yi ma juna, fitowar shi kenan daga bedroom ɗin shi  yaji an banko ƙofar parlor  ɗin shi kamar za'a ballata har sai da ya ɗan tsorata da ganin sa'ada idanunta sunyi luhu luhu "ke lafiya daga ina haka " bata bashi amsar tambayar da yayi mata ba sai ma ƙara sautin kukan da tayi,  har sai da mansoor ya kwatsa mata tsawa yana faɗin "ke lafiya kike wannan kukan mi a kayi maki " cikin shashekar kuka tace "fatima ce..... " bata ƙarasa ba mansoor ya katse da "fatima ce tayi mi, kiyi magana mi ya samu fatimar " fashewa tayi da kuka tana faɗin
"tun É—azu muke nemanta ba mu ganta ba" tsaki mansoor ya ja yana faÉ—in "ina fatimar zata je, ki je dai ki sake du bata "
"wallahi yaya ba inda ba mu  duba ta ba amma ba mu  ganta ba ni da su ya shazim  " ya salam mansoor ya furta yana faɗin "an kira wayar ta kuwa "
"bata tare da wayar"  ok bari na zo mansoor ya faɗa haɗi da nufar bedroom ɗin shi  da sauri ya tura ƙofar ya shiga, wayar shi da ke kan sofa ya nufa ɗauka yayi ya shiga dialing number fatima tana ringing amma ba'a ɗauka ba kamar yan da sa'ada ta faɗa mashi kusan 5 missed call, ɗan dafe kanshi yayi yana furta "ya Allah " fita yayi daga bedroom ɗin in da ya bar  sa'ada a nan ya same ta ƙofar fita parlorn ya nufa bin bayan shi sa'ada tayi, su Asma'u har yanzu suna nan tsaye hankalin su duk a tashe, ganin ya mansoor da sa'ada da sauri kairiyya ta nu fi mansoor tana faɗin "yaya wai mike faruwa ne " ficewa yayi batare da ya bata amsa tambayar da tayi mashi ba ganin haka ne yasa ta jawo hannun  sa'ada tana faɗin " sa'ada wai mike faruwa ne "
"Aunty kairiyya fatima ce ake nema ba'a ganta ba " dafe ƙirji kairiyya tayi tana faɗin "ba'a ganta ba "
"Eh, tun É—azu muke nemanta ni da su ya mahmud amma bamu ganta ba, ko É—azu da na shigo nan ita muke ne ma"
Asma'u da Amina har haÉ—a baki su ke wurin jan tsaki da faÉ—in "aikin banza kawai saboda kawai ba'a ganta ba zaki wani shigo ma mutane kamar wacce wani nata ya rasu " mtsww su ka sake jan tsaki, kairiyya ce tace " amma nayi mamakin abun da ya fito daga bakin ku wallahi, haba Aunty Asma'u cewa tayi fa tun É—azu ake nemanta ba'a ganta ba "
Amina ce tace "ke kairiyya ki kam kan ki, ko cewa tayi ta mutu ina ruwan mu "
kairiyya tace "wallahi ku dai canza dan wannan ba rayuwa ba ce "
hayayyaƙo mata su kayi da masifa Fiddausi tace "gaskiya fa ta faɗa ko da ace ba ƴar uwar ku ba ai ita muslma ce bare jinin ku ɗaya da ita, gaskiya ku gyara "
kallon juna su kayi suna faÉ—in "yau ga Æ´an iskan yara wa'azi za ku yi mana " kairiyya tace " ba wa'azi za muyi maku ba gaskiya ce muke faÉ—a maku "
"to ba mu so " a cewar Amina, jan hannun sa'ada kairiyya tayi su ka bar part ɗin zuwa part ɗin innah wurin gwaggo Halima, ita ka ɗai suka samu a  part ɗin gwaggo Uwani da innah ba su nan, suna asibiti wurin feenah data yanke jiki ta suma lokacin da uncle Ibrahim ya fitar da ita daga parlorn da suka yi meeting ɗazu,   abun dake faruwa su ka faɗa mata,sosai hankalin ta ya tashi, wayar ta ta ɗauka ta shiga dialing number uncle Ahmad da yake shima bai nan yana tare da su innah , korma uncle Ahmad bayani tayi akan abun da yake faruwa, sosai ya nuna tashin hankalin shi, tamabayar gwaggo Halima yayi "ina su shazim ɗin su ke "
"ina jin suna part É—in su, nima su kairiyya ne suke faÉ—a man abun da ke faruwa "
"ok gani nan zuwa " ya faÉ—a haÉ—i da yin rejecting kiran.
"ga Abban ku nan zuwa,  amma da mamaki abun ina zata nufa, ku tashi muje, ke sa'ada je kikira man usman kice ya same ni a nan part ɗin  " da to ta amsa haɗi da tashi ta fita.

Lokacin da mansoor ya fita part ɗin su shazim ya nufa, noraiz ya samu a parlor mahmud ya fita, tambayar shi yayi "ina shazim ɗin" amsa noraiz ya bashi da "ya shiga ciki yanzu " ok kawai mansoor yace haɗi da nufar sama part ɗin shazim,ba nocking ba komai ya tura ƙofar da ƙarfi ya shiga
ɗago da idu shazim yayi jin yanda mansoor ya shigo kamar an jeho shi da idanu  shazim ke binshi, magana ya fara "yanzu dan wulaƙanci shazim ace kun nemi fatima baku ganta ba amma ka kasa faɗa man sai da sa'ada ta faɗa man, wai wannan haushin nawa da kake ji na minene"
"dan Allah ka barni naji da abun da yake damu na"
"ok abun da ke damun ka ko "
"haba dan Allah kaine da wata magana, yanzu fa nake shirin kiran ka sai gaka ka shigo "
"uhmm" kawai mansoor yace sannan yace "to ina ta tafi "
"nima ban sani ba, bawani wuri ta sani ba bare nayi tunanin ko tana can" dan jinjina kai mansoor yayi yana faɗin " haka ne gaskiya" can kuma ya matso kusa da shi  ya zauna yana faɗin "ɗan kira number a hashim kaji ko fatima taje gidan su" wani kallo shazim yayi mashi "  ban gane ba, mi zai kai fatima gidan a wannan lokacin "
"dan Allah dai ka kira shi "
"ni bazan kira shi ba, kai mi zai hana ka kira shi " mansoor yace 
" kai matsalata da kai kenan,  to bani wayar ka na kira shi tun da baza ka kira shi" ɗaukar wayar yayi  ya shiga kiran number A Hashim, bugu biyu yayi picking ko sallamar da yake mashi bai amsa ba yace "Fatima na tare da kai?"
"Fatima kuma?" a hasale shazim yace "taya ina tambayar ka kana tambayata"
"ba dole na tambaye ka ba, ni yaushe rabon da naga Fatima,in ba ma rainin wayau ba a wannan lokacin zaka tambaye ni fatima  " har ya ɓuɗe baki zai yi magana mansoor ya fisge wayar dan ya san abun na iya koma masu faɗa, kara wayar yayi a kunne yana faɗin "sorry Abdallah,  ka gane neman ta muke ne, an kira wayar ta bata yi picking ba  tun ɗazu mu ke neman ta , shine sai nayi tunanin ko tazo gidan uncle ne wurin Ameera"
hankalin A Hashim yayi matuƙar tashi  jin ya ce ba'aga Fatima ba, cikin tsantsan  tashin hankali yace "amma ina taje mansoor "
"wallahi shine ba mu sani ba"  Abdallah yace "ya ilahi" haka kawai ya ce haɗi da yin rejecting ɗin kiran, ta shi mansoor yayi ya fita daga parlorn ya nufi main parlor, yanda ya bar Noraiz haka ya same shi har da mahmud da ya shigo yanzu, gwaggo Halima ce ta shigo ita da kairiyya da sa'ada sai usman ,  har time ɗin kuka sa'ada keyi, kairiyya na lallashin ta, kusa da su mansoor ya matsa, haƙuri ya shiga ba ta akan insha Allah za'a ganta, fitowa shazim yayi bedroom ɗin shima ya nufo main parlor wuri ya samu kusa da noraiz ya zauna, ya usman ne yace " shazim  tun yaushe ne kuka duba baku ganta ba "
"tun fitar da tayi É—azu da ana meeting, nayi tunanin ko tana nan É—akin ta ko wurin sa'ada "
"ya salam" ya usman ya furta haÉ—i da cewa "amma ba inda kake tunanin zata "
"ina zata je yaya bayan ba wanda ta sani a abuja " kallon sa'ada ya usman yayi "ke sa'ada kin kira ƙawayen ki ko taje wurin wata daga cikin su "
"yaya ai ni bana da ƙawaye,kuma ma tun da tazo gidan su momy kaɗai muka je sai gidan uncle ɗin ya Abdallah "
"waye kuma Abdallah "ya usman ya tambaya, mansoor ne yace "wani course mate ɗin shazim ne kuma ma mun kira shi bata can "  shiru su

kayi ba wanda yasake cewa komai, kowa na tunanin inda ta shiga, shazim kuwa alƙawari ya ɗauka  duk abun ya same ta wallahi bazai ƙyale kowa dake cikin estate ɗin ba tunda ai sune silar   shigarta wannan halin har tasa ƙafa ta bar estate ɗin, damuwarshi yanzu shine ina taje awane hali take dan yasan duk in da take zai yi wuya ace ciwanta bai tashi ba, ya usman ya tashi yana faɗin "ina zuwa wannan zaman bazai mana maganin komi ba " tashi ita ma gwaggo Halima tayi "haka ne usman bazama ya kamat muyi ba " tashi su kayi duk suka fita aka bar mansoor da shazim
mansoor yace "ina mamakin inda taje, to wai mi zai sa ta bar estate ɗin nan" shazim yace " wallahi muddin wani abu ya sameta ran kowa sai ya ɓaci " shiru kawai mansoor yayi baice komi ba, can kuma sai yace "yo wai ma an tambayi security ko sunga fitar ta " sai da mansoor yayi maganar sannan hankalin shazim ya kai ga nan "hakane kuma mansoor wallahi ni duk banyi wannan tunanin ba "
"idan tafita dole zasu ganta ko da ta ƙaramin gate ta fita, tashi mu tafi  " mansoor ya faɗa haɗi da ɗaukar wayar shi su ka fita zuwa main gate da ya usman suka ci karo shima main gate  ɗin ya nufa, a tare suka ƙara sa, securityn na zaune kan benchi da suke zama,su ƙara so inda su ke, gaishe da su security su kayi a taƙaicw suka amsa masu mansoor na faɗin " tambayar ku muke son yi"
babban cikin su ne yace "Allah yasa mun sani yallabai "
a hassale shazim yace " kunga ficewar fatima "
"gaskiya yallabai ba muga fitar ta ba, motar Alhaji ce kawai ta fita shi da su innah in ba dai atare da su ta fita ba "
Mansoor yace "kun tabbata baku ga ficewar ta ba, kuma bawani driver da ya fita da mota "
"gaskiya babu, bayan Alhaji Ahmad ba wanda ya fita da mota " wuce wa shazim yayi batare da ya jira su mansoor ɗin ba, juyo suka yi suma zasu bi bayan shi sai ga mota ta nufo main gate daga waje, tsayawa su kayi dan suga waye, ɗaya daga cikin security ne ya nufi motar ba kowa bane face ya Abdallah ya kasa zama hankalin shi ya ƙi kwanciya tun da aka ce ba'aga fatima ba, izinin shiga ciki security ya bashi, ciki ya shigo ganin su mansoor ne yasa shi tsayawa wurin su sai da yayi parking sannan mansoor ya gane shi, mansoor ce mashi yayi" ya shiga ciki kawai shazim ma yanzu ya wuce" ciki ya shiga yayi parking a parking lot, part ɗin kawai ya nufa , tsaye ya samu shazim a parlor, gaba ɗaya hankalin Abdallah a tshe yake tsare shazim yayi da tambayar ina taje ne Fatimar, amsa kawai shazim ya bashi da bai saniba, gashi malam da Ammy sai kiran shi su ke yace zasu dawo yau gashi har dare yayi babu su babu labarin su. 

Sa'ada lokacin da suka fita daga part su shazim part ɗin su ta nufa, ta shiga bedroom ɗin momy ta shiga bata same ta ba tunawa da tayi ɗazu momy part dady ta nufa ne yasa fita ta nufi part ɗin dady, tunkafin tashiga ta fara jin muryar momy tana faɗin "amma ban taɓa tunanin baka da hankali ba luqman sai yau, dama ashe shashasha ne kai ban sani" muryar dady taji yana faɗin "dan Allah ki daina ɗaga murya turai "
"ok in daina ɗaga murya ko.... " bata ƙarasa ba saboda tura ƙofar da sa'ada tayi ta shiga tsaye ta samu momy da dady sai luqman da ke zaune kan sofa jikin shi sai rawa yake  kamar wanda zazzaɓi yayi ma mugun kamu,jin anturo kofa ne yasa shi tashi da gudu ya nifi bedroom dady,ganin sa'ada ce yasa shi tsayawa yana haki kamar wanda yayi wasan tsere, dady ne yace "ke kuma daga ina haka "
"dady fatima fa ake nema ba'a ganta ba "
"to naji fita ki bamu wuri"
" dady amm..... " bata ƙarasa ba ta dalilin tsawar da dady ya daka mata yana faɗin
"nace fita ko so ki ke sai ranki ya ɓacin"
ba shiri ta fita, amma sai ta ƙi tafiya ta tsaya tana sauraron mi suke cewa, bana ji mi take ji naga dai taja baya da sauri tana kallon ƙofar can kuma ta fita dagu.
Episode 40_41_

ba shiri ta fita, amma sai ta ƙi tafiya ta tsaya tana sauraron mi suke cewa, bana ji mi take ji naga dai taja baya da sauri tana kallon ƙofar can kuma ta fita dagu tana kuka, bedroom ɗinta ta nufa tana shiga ta faɗa kan bed fashewa tayi da wani matsanancin kuka, kuka take kamar ranta zai fita sai birgima take kan bed ɗin tana faɗin "wayyo Allah nah, Allah kasa abun da kunnuwana suka ji ba gaskiya bane, idan har haka ta kasance bazan taɓa yafe maka ba ya luqman " sai kuka take tana ta roƙwan Allah yasa ba gaskiya bane tashiga tashin hankali da jin abun da su dady ke tattaunawa sai ta baka tausayi yan da ta dage tana rokwan Allah yasa ba gaskiya bane,can kamar an tsikareta ta tashi ta fita daga bedroom ɗin da gudu ta nufi sama part ɗin dady har tasa hannu zata buɗe ƙofar part sai aka turo ƙofar dady ne sai momy dake bayan shi da kaganta kasan tana cikin damuwa idanun ta duk sun kumbura ba ƙaramin kuka tasha ba,tsaye su kayi suna kallonta sai kuka take dady ne yace "wai wannan kukan da kike na minene, miya dawo da ke nan ba nace ki wuce ba " ƙara sautin kukan tayi ba'a ma jin mi takecewa sosai " dady ƴar uwata "
"dan Allah kiyi haƙuri sa'ada za'a ganta yanzu ma wurin su shazim ɗin zan tafi, kiyi shiru kinji" ya faɗa cikin sigar lallashi
"to dady, amma maganar wa naji kunayi, wacce ya luqman....... "
bata ƙarasa ba dady ya katseta ta hanyar daka mata tsawa" wai ke wace irin yarinya ce sa'ada, nace maki za'a ganta kuma maganar da kike cewa munayi ba'a kanta bane, ki kwantar da hankalin ki " ya ƙarasa maganar yana lallashin ta
" amma dady dan Allah ka bari naga ko wacece pls "
"miyasa baki jin magana ne sa'ada, wuce ki tafi bedroom É—in ki ki kwanta kar ki haddasa ma kanki ciwan kai kinji za'aga fatima "
fashe tayi da kuka "ni dai dady ka bari naga ko wacece "  tsawa ya daka mata "ina wasa da ke ne, ko ki bar wurinnan ko ranki ya ɓaci shashasha"
hawayen da momy ki ɓoye wa ne suka zubu "wallahi Alhaji ina jiye maku abun da zai biyo baya"
dady yace "dan Allah turai kiyi man shiru, kija ta ku bar nan wurin "
"dole na faɗi haka Alhaji,  an cuc..... " bata  ƙarasa ba dady ya dakatar da ita ta hanyar cewa
"wai miyasa kike da taurin kai ne turai, nace ki jata ku bar nan "
jan hannun sa'ada tayi tana faɗin "zo nan kinji kiyi haƙuri ki daina kuka, kinji jikin ki harya ɗauki zafi " momy ta faɗa haɗi da jan hannunta, fisgewa sa'ada tayi ta nufi ƙofar zata buɗe, da sauri dady ya fisgota ɗauke ta yayi da wani mumunnan mari har sau biyu, tangal tangal tafara zata faɗi ƙasa, da sauri momy ta taro ta zuwa jikinta ta rugume ta tana kuka " kijata ku bar nan"
"ba inda zan kai tai, ku faÉ—a ma yara in da Æ´ar uwar su take, ko wallahi naje na kira su duk abun da zai biyo baya ya daÉ—e bai biyo baya ba "
"turai haka kika ce, kin kuwa san mi kike faÉ—a kuwa, kina cikin hankalin ki kuwa"
"cikin hankali na nake, nasan mi nake, wannan ai zalunci ne " tana gama faɗa ta ɗago da kan sa'ada tana faɗin "sa'ada tashi ki kira man mansoor ko shazim " shiru sa'ada bata amsa ba bakuma ta motsa ba, ashe tun marin da dady yayi mata momy ta tare ta suma tayi batare da sun sani ba, da sauri momy ta ɗago ta kalli dady tana faɗin " ta suma Alhaji, Innalillahi" ta faɗa tana bubuga ta tana faɗin "tashi kinji, dan Allah ki tashi " momy gaba ɗaya hankalin ta ya tashi, key dady yasa ma part ɗin shi ya rufe ya yafita ya bar momy da sa'ada durƙushe a ƙasa momy sai kuka take,daƙyar ta samu ta ɗauki sa'ada ta nufi ɗakinta da ita, kwantar da ita tayi kan bed sannan ta nufi dressing mirror ɗakin ta ɗauki robar ruwan da take ajiye wa duk dare, a hannu ta tarfa ruwan ta nufi fuskar sa'ada ta yayyafa mata sai da ta sake yayyafa mata sannnan ta ja wani dogon numfashi,Alhmdllh momy ta furta hadi da kiran sunan sa'ada, jin muryar momy ne yasa ta tashi   zambur kamar wacce aka zungura " momy ina fatima, ina ƴar uwata take, momy dan Allah ki faɗa man in da take " ta ƙarashe maganar tana kuka
"kiyi haƙuri sa'ada ƴar uwar ki bata ɓata ba kiyi shiru kijin, kar ki ja ma kanki ciwo "
"amma wacece a part ɗin dady naji kuna faɗin ya luqman yayi raping" da ta faɗi haka har sai da gaban momy ya faɗi " momy kinyi shiru,idan har ba ƴar uwata bace pls momy wacece " hawaye ne suka taru a fuskar momy, girgiza mata kai tayi " sa'ada nima ban san wacece ba, dadyn ku yaƙi bari naga ko wacece "
"momy amma a ɗakin na same ki pls momy ki faɗa man " shiru momy tayi batace mata ƙala ba, tana son kowa ya san halin da ake ciki amma ta tsoron wane irin hukunci luqman zai fuskanta, ganin tayi shirune yasa sa'ada faɗin "momy ki faɗa man, ko naje na kira ya shazim da ya mansoor su zo su ɓalle ƙofar ɗakin dady "
"sa'ada karki kira su ba fatima bace "
"idan har banga kowa cece ba hankalina bazi taɓa kwanciya ba" tana gama faɗa ta fice daga ɗaki da gudu,k'wala mata kira momy ta shiga yi tana fad'in ta dawo ,amma ina ko wai wayen momy bata yi ba , fashewa momy tayi da kuka "ya Allah ka kawo sassauci a wannan lamarin ya Allah "
sa'ada ɗakin momy ta faɗa dagu ta maida ƙofar ta rufe, wani sabon kukan ta sake fashewa da shi, sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi ta kamar wacce ciwan hauka ya kama hau buɗe buɗen drawer's tana neman extra key's gaba ɗaya ta   hargitsa ma momy ɗaki ta haukata shi kayan ta da ke cikin wardrobe duk ta watso su ƙasa,  har da su ɗaga mattress  sai nishi take ta haɗa uban gumi amma bata gansu ba, fitar da rai tayi da ganin su  sai hawaye take kayan da ta watso ta  fara kwashe wa   tana mai dawa cikin wardrobe,sai da kwashe su tasa ta maida ta rufe wardrobe ɗin, zama tayi ƙasa dirshan tana share hawayen dake ta zarya a kumatun ta, tazo tashi kenan zata  fita idanun ta suka sauka akan keys ɗin da take ta wahalar nema, ashe wajen watso kaya ta watso da su batare da ta sani ba , ɗaukar keys ɗin tayi ta fice da sauri.

Dady na fita daga part ,part d'in uncle Ahmad ya nufa ,a parlor ya same shi shida su mansoor da ya usman ,noraiz ,mahmud sai gwaggo halima da mama ,sunyi jugum jugum,kowa hankalin shi tashe yake da rashin ganin fatima, ya usman ya yanke shawarar kiran police ya sanar da su halin da ake ciki , Abba ne yace kana ganin za su zo,na ga dare yayi kuma ka san yana yin jami'an tsaron k'asar nan yan da su ke"

"haka ne Abba,ai wanda zan kira aboki na ne kuma nan kusa office d'in su yake "
"to shikenan " Abba ya fad'a,
ya d'aga waya kenan zai kira su sai ga dady ya shigo ,fasa kiran yayi,amsa mashi sallamar da yayi su kayi ,wurin su dady ya k'ara so ,Abba ne yace " wai dama kana nan?, amma dai baka san mike faruwa bane ko?"

Dady yace
"na sani ,akan maganar ne ma nake son mutattauna"

" in taso ne " da eh dady ya bashi amsa had'i da juyawa ya fita ,bin bayan shi Abba yayi, garden su ka nufa ,zama su kayi akan kujerun dake wurin ,shiru dady yayi bai ce komai ba har sai da Abba yace " kace za muyi magana mun kuma zo kayi shiru ,ina fatan dai lafiya ,d'an nisawa dady yayi  sannan  ya fara magana
"yaya kasan halin yaronann luqman bai da hankali ko ko ko alama ..." sai kuma yayi shiru, ganin yayi shiru ne yasa Abba da sauri  yace " kayi shiru kuma mi luqman yayi ,kar dai kace man duk neman yarinyar nan da ake luqman ne ya d'auke ta?"

"da ace d'auke ta yayi yaya ai da sauki , saboda bai da hankali bai san in da ke mashi ciwo ba k'okarin yi mata fyade ya so saboda kawai ta nuna bata son shi "

zanbur Abba ya mike yana fad'in "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un ,dama yaron nan bai da hankali ban sani ba ,amma Ibrahim miyasa tun d'azun baka sanar da ni ba, yanzu tana ina"

"tana bedroom É—ina, na so tun lukacin na sanar dakai ,amma ganin kuna asibiti ne yasa ban sanar da kai ba"

"haba Ibrahim idan bana nan ka kirani ai dole na dawo ,kuma ai da ka sanar da shazim ,yanzu idan ya san cewa tun d'azu tana part d'in ka ,mi kake tuna nin zai biyo baya ,kana gani d'azu cewa kawai fa yayi yana sonta amma ji irin bacin da ranshi yayi da maganganun da ya fad'ama,"

"wallahi yaya tsoron irin hukuncin da zai ma luqman ne yasa ban sanar da shi ba "

"ai da ko mansoor ka fad'a mawa shi zai iya controling d'inshi ko halima, da sai su kai ta hospital adubata  ,amma yanazu ba k'aramin kuskure kayi ba na kin fad'a tun d'azu "

"ya salam amma yaya minene ma fita "

"mafita d'aya ce a sanar da shi halinda take ciki "
"amma yaya yana iya illata luqman da duka "

"to koma mi zai mashi ai shi ya ja tun da bashi da hankali ,kuma zamu k'i  fad'a ne saboda kar ya hukunta shi, kuma idan mu kayi haka ba muyima yarinyar nan adalci ba kamar yan da luqman yake a wurin haka take a wurin mu "

"hakane, bari na kira dr sai ta zo ta du bata " dady ya faÉ—a haÉ—i da ciro wayar shi daga aljihu yayi dialing number dr su.

_*✨SHAZIM✨*_

"Shazim ni ina mamkin in da fatima zata je ,ko ina a estate d'innan kun duba kuwa " a cewar Abdallah

d'agowa shazim yayi yana fad'in
"duk in da nake tunanin zata iya shiga mun duba amma ba  mu ganta ba"

"gaskiya abun nan da mamaki ,tun da dai ba inda zata je,nifa zargi nake tana cikin estate d'innan"

d'an nisawa shazim yayi had'i da cewa" nima zargina kenan,sai dai duk inda nake tunanin zata iya shiga ko za'a iya kaita sai da na duba,dan na daina tunanin wani wuri ta tafi yanzu nafi zargin sace ta akayi "

"abun da kawai ya kamata yanzu shine mu kira police kawai dan wannan zaman da muke bawai zai amfana ma wani abun arzik'i bane ,amma ya ka gani"

"gaskiya wannan itace mafita kawai "

Abdallah wayar sa daya d'aura kan hannun sofa ya d'auka ,number wani police abokin uncle ahmad yayi dialing
Mansoor ne ya shigo part É—in wuri ya samu kan sofa kusa da Abdallah ya zauna, kallon shi Abdallah yayi yana faÉ—in " mansoor har yanzu ba wani labari "
"
"babu Abdallah,gashi tun ɗazu ya usman ya kira wani abokin shi  police amma har yanzu baizo ba, na rasa gane lamarin ƙasar nan "

"sai haƙuri, nima yanzu na kira wani abokin uncle na san shi insha Allah zai zo "

" Allah yasa " Mansoor ya faɗa, shazim dai na gefe yana jinsu baice ƙalaba wayar sa ce tayi ringing , dafe kai yana faɗin
" ya Allah, wallahi na rantse duk wanda na kama da sa hannun shi hmmm...  " kawai yace ba tare da ya ƙarasa ba, kiran ne ya sake shigowa wayar mansoor ne yace "idan bazaka ɗauka ba ka kawo na ɗauka, dan rashin ɗaukar ka shi zai ƙara jefa su cikin tashin hankali "

"idan na É—auka mi zance masu mansoor?, idan har su ka sani hankalin su sai ya fi tashi akan wanda suke ciki yanzu saboda rashin É—aukar kiran su da banyi ba "

"duk da haka shazim da ka ɗauka sai kace masu kun fasa dawowa ne yau,  amma hakan zai sa su cikin tashin hankali matuƙa "

"uhmmm " kawai yace

suna nan zaune jigum sa'ada ta bankaɗo ƙofa  ta shigo har tana tuntuɓe tana shirin faɗuwa,sai haki take kamar wacce wani abun tsoro ya biyo, fuskar ta sharkaf da zufa  mansoor ne ya taso da sauri yana faɗin "wai miyasa ba zaki zauna wuri ɗaya bane sa'ada , ji yan da ki ka shigo kina shirin illata kanki, yanzu miya ya dawo da ke nan"

sai haki take maganar ta ma da kyar take fita "yaya dama.... " maganar ce ta sarƙe mata sai sauke numfashi take
"dan Allah ki kwantar da hankalin ki kiyi man baya nin abun da ke faruwa "
bata ba shi amsar tambayar sai ma nufar shazim da tayi da sauri, keys ɗin dake hannun ta miƙa mashi tana "ya shazim gashi "
É—agowa yayi yana kallon ta "key É—in É—akin dady fatima na can " kamar saukar aradu haka su ka ji maganar ta mansoor da Abdallah da sauri suka nufe ta suna faÉ—in "da gaske kike sa'ada " É—aga masu kai tayi tana faÉ—in " eh yaya da gaske nake tana can ita da ya luqman "
"luqman kuma?, kin tabbata sa'ada? "
"yaya fatima ce fa, wallahi tana can "
"ya Allah, amma mi ya kaita can mi ta ke yi tare da luqman a É—akin uncle"
ƙarar rufe ƙofa su kaji da sauri ko wannen su ya kalli ƙofar basu ga kowa ba mansoor ne yace "shazim tashi mu je.... " bai ƙarasa ba ganin sofar wayam ba kowa, basu san lokacin da ya bar wurin ba sai yanzu su ka fahimci cewa ashe rufe ƙofar da suka ji shi ne ya fita, ba
yan sa suka bi da sauri ko da suka fita ko mai kama da shi basu gani ba a compound, zuciyar mansoor sai bugawa take yana tsoron abun da shazim  zai yima luqman,da sauri suka isa part ɗin direct sama suka nufa shazim har ya shige ya maida ƙofar da key ya rufe, bubbuga ƙofar su ka shiga yi suna kiran sunan shi amma ko motsin shi basu ji ba bare su sa ran zai buɗe masu, sai haɗa shi da Allah mansoor yake akan ya buɗe masu amma shiru.

Lokacin da ya  shiga parlorn ba kowa hakan ya sa shi wu cewa bedroom ɗin dady tura ƙofar yayi ya shiga, kwance ya hangi fatima kamar matatta an rufe mata rabin jikinta da blanket, ƙara sawa yayi bakin gadon saitin in da fuskar ta take,sai fitar da numfashin wahala take kanta ko ɗan kwali babu sumar kanta duk a ya mutse   fuskara tayi fayau da ita bakin ta ya bushe ƙamas duk ya faffashe  goshinta ma a fashe yake da gefan bakin ta   fuskar ta tayi jawur , siraran hawaye ne ke fita daga gefen idanuwanta da suka kumbura su kayi suntum,wuyan ta da ƙirjinta duk sawun ya kushi, sai jan numfashi take da ƙyar tana fitarwa, wasu zafafan hawaye ne suka taru a idon shi zuciyar shi sai tafarfasa take, hannu biyu yasa zai ɗauke ta ƙarar buɗe ƙofa da yaji ne yasa shi juyawa dan ganin wanene ya shigo, ido biyu su kayi shida luqman da ke tsaye bakin ƙofar bathroom ɗin dady daga shi sai bathrobe, tun ɗazu yake cikin toilet ɗin jin motsin mutum ne yasa shi fitowa duk a tunanin shi dady ne, ai kuwa yayi daya sanin fitowa, wani mumunnan faɗi gaban shi yayi ganin wanda bai yi tsammani ba da sauri ya juya zai koma toilet ɗin sai kafin ya ja ƙofa ya rufe tuni shazim ya cimma sa, roƙwanshi ya fara akan dan Allah yayi mashi haƙuri wallahi ba da gangan yayi mata haka ba, kuma ba abun da yayi mata " sai magiya yake mashi amma ina shazim bai ma san yana yi ba,  buga mashi kai yayi da bango nan take goshin shi ya fashe ya fara zubar da jini, wani wahalallen ihu luqman ya saki yana cigaba da rokwan shi da yayi mashi afuwa bazai sake ba,naushi shazim ya kaima bakin shi da yake rokwan nashi,naushin shi ya shiga yi ta ko ina yana buga mashi kai da bango tun luqman na da bakin bashi haƙuri har ta kai muryar shi bata fita saboda azaba.
Su mansoor na bakin ƙofar part ɗin suna aiki bugawa da roƙon shazim akan karyayi ma luqman wani abu amma ko alamar yana jin su basu jiba, hankalin su duk ya tashi akan halin da luqman yake ciki, sa'ada sai kuka take tana kiran sunan luqman da fatima, momy ma sai kuka take tana ro kwan shazim karya kashe luqman, ganin da gaske shazim ba jinsu yake ba yasa momy fita da part ɗin a hargitse ta nufi part ɗin uncle Ahmad kamar an jeho ta haka ta faɗo cikin parlorn su mama da gwaggo Halima da ya usman da sauri suka miƙe cikin tashin hankali su ke tambayar ta lafiya, momy sai hawaye take tana nuna masu bayan ta bayan nata suka kalla su basu ga komai ba, sai da ƙyar ta samu kalmomin furta " sha... zi.. m... zai ka.. sh... e luqman " ta ƙarasa maganar a rarrabe,salati gwaggo halima ta rabka tana faɗin " na shiga uku ni halima, mi ya haɗa su kuma  Innalillahi "
da sauri su ya usman suka nufi part ɗin su momyn, bin bayan su su mama su kayi momy sai sharar hawaye take, a bakin ƙofar part ɗin suka tsaya suma su ka hau bubbuga ƙofar suna rokwan shazim da ya buɗe amma ina ya usman ne yace su sa ƙarfi kawai su ɓalla ƙofar kawai dan ko zasu kwana a nan shazim ba wai zai buɗe masu bane har sai ya fitar da luqman daga hayyacin sa, haka su kai ta ƙoƙarin ɓalla ƙofar, duk wanna budirin da ake dady da Abba suna garden jiran dr basu san mike wakana ba, ba irin ƙoƙarin da su mansoor basu yi ba ganin ƙofar ta buɗu amma ina, momy ce tace mahmud yaje ya kira su  dady a kwai key a jikin shi, da sauri luqman ya tafi kiran su, su kuma su mansoor na ta aikin ɓalla ƙofar yayin da Abdallah yake sake kiran number wannan police ɗin dan yaga sun jima basu zo ba gashi ana shirin kisan kai.
sai ga dady da Abbah sun shigo hankali a tashe da sauri dady ya nufi ƙofar yana ciro key ɗin dake aljihun shi matsawa su mansoor su kayi suna bashi wuri key ɗin yasa ya shiga kiciniyar buɗe ƙofar amma ina ta ƙi buɗuwa saboda key da shazim ya bari jikin ƙofar da ya shiga, kuma yayi hakan ne dan kar ma su samu sa'ar buɗer ƙofar

Shazim  sai da yayi mashi lilis duk ya farfasa mashi goshi da bakin shi shaƙe mashi wuya yayi har sai da yaga baya motsi ko ɗan yatsa baya iya motsawa tukun ya sake shi ya faɗi ƙasa yarab ba numfashi, bai bi ta kanshi ba ya nufi gadon da fatima take hannu biyu yasa ya ɗauke ta irin ɗaukar da ake yima jarirai ya fice  da ita yana zuwa bakin ƙofar su mansoor na samun nasarar  ɓalleta suka shigo da sauri  ganin shi da fatimar ne yasa suka nufe shi sa'ada da sauri da shigo tana kuka haɗi da cewa "ƴar uwata miya same ki, ya shazim naga kamar bata numfashi " sai tambayar shi suke wane hali take ciki dan ganin fatima sun ma manta da luqman da ke can yashe a bedroom ɗin dady, dadyn kawai ya nufi bedroom ɗin da sauri har sai da gabanshi ya faɗi da yayi arba da luqman yashe  a ƙasa babu alamar ma yana numfashi, bayan shi Abba ya biyo da sauri shima ya ja burki ya tsaya yana bin luqman da ke kwance ƙasa,  kuka ne ya kubce ma dady yana faɗin "luqman dan Allah ka tashi kar ka mutum, dan Allah na roƙe ka katashi " sai jijjiga shi dady yake yana roƙwanshi da ya tashi amma ina ko motsi wannan bai yi ba Abba ne ya ƙaraso kusa da su dafa kafaɗar dady yayi " Ibrahim ai suma yayi " sai a lokacin dady ya lura da cewa suma luqman ɗin yayi.
barin wurinAbba yayi ya nufi toilet ya ɗebo ruwa yazo ya yayyafa ma shi a fuska a firgice luqman ya farka sai sambatu yake yana faɗin "dan Allah ya shazim kayi haƙuri wallahi babu abun da nayi mata, dan Allah kar ka kashe ni wallahi bazan sake ba plea.... "  da sauri dady ya kira sunan shi, zambur luqman ya miƙe zai nufi toilet dan duk a tunanin shi shazim ne tashin farko bai gane muryar dady bace sai da Abba yace "dawo luqman ina zaka ba shazim ba ne mune " sannan luqman ya tsaya yana sauke numfashi da sauri ya nufi dady yayi hugging ɗinsa fashewa yayi da kuka kamar wani ƙaramin yaro
"dady ya shazim kashe ni yaso yi, baya ƙaunata sai ce mashi nake ba abun da nayi mata amma sai da ya dake ni , miyasa ka bar shi ya shi go "

dady yace "luqman duk laifin ka ne, yanzu ai kaga irin abun da nake guje maka ko "
"dady wallahi ban yi mata komai ba, Allah bazan sake ba, dan Allah kar ka bari ya raba ni da ita wallahi ina son ta "
"kama daina faɗar haka luqman dan yanzu ko mutuwa za ka yi shazim bazai taɓa bari ka aureta ba,ba shi kaɗai ba har ita kanta fatimar da su Aisha "
"dan Allah dady"
Uncle Ahmad ne yace "ya isa haka, zo muje mansoor ya duba ka ko mu tafi asibiti goshin ka da bakin ka sai zubar da jini su ke "

"Abba banzan iya zuwa wurin ya mansoor ba nasan shima fushi yake da ni  kuma ina tsoron na fita mu sake haɗuwa da ya shazim, momy dai  ta zo nan ta duba ni " hannun shi Abba ya jawo
"zo mutafi ba abun da zai sake yi maka ai ina tare da kai "
"ni dai momy nake so ta duba ni"

"to shikenan zo mu tafi "

duk da yace haka ƙin binshi luqman yayi sai da dady yace "nima ina nan ba abun da zai maka kaji " sannan ya bi bayan su suna gaba yana baya sai zare ido yake har suka shigo main   parlor ba kowa duk su mansoor sun fita sai momy dake zaune kan sofa ta buga uban tagumi, tana ganin su da sauri ta taso tana "luqman yanzu kaga irin ta ko "
da sauri ya nufeta ya yayi hugging É—inta " momy wallahi bazan sake ba Allah "
Abba ne yace "turai kiyi mashi dressing É—in wannan ciwukan"
sai a lokacin momy ta lura da ciwukan da ke jikinshi,medical room ɗin su ta nufa da sauri zama su kayi kan sofa suna jiran ta fito, kamar daga sama suka ji ƙarar jiniyar motan ƴan sanda

Abba ne yace "Innalillahi ba dai usman sai da ya kira ƴan sandan nan ba, ya Allah  "
da sauri  luqman ya tashi  yana zazzare ido " na shiga uku dady ni su ka zo kamawa ya shazim ne ya kira su" dafe kai dady yayi
"shazim wai wane irin yaro ne yaya, yanzu duk wannan dukan da yayi mashi bai isa ba sai ya haÉ—a shi da Æ´an sanda " shi dai Abba yayi shiru baice komi ba

"dady dan Allah kar ka bari su tafi da ni, dan Allah ba dan ni ba dady" duk ya bi ya ruÉ—e jikin shi sai rawa yake
dafa shi dady yayi "kwantar da hankalin ka ba abun da zasu yi maka kaji... "

ko rufe baki bai yi ba a ka turo ƙofar parlorn aka shigo ƴan sanda ne su uku suka shigo, da gudu luqman ya boye bayan dady, Abba ne ya nufe su da sauri yana faɗin " yallaɓai lafiya?"

babban cikin su ne yace " munzo ne da sammacin kama luqman Ibrahim Nuraddeen "
Abba yace " wa ya baku izini ke nan?"

"nine" ya ji an faɗa daga bayan su matsawa yan san da suka yi a dai dai lokacin momy ta fito hannunta riƙe da first aid box
Abdallah ne tsaye bayan su ya harɗe hannuwa a ƙirji
da mugun mamaki su dady ke kallon shi Abba ne yayi ƙarfin halin cewa "a kan wane dalili kenan, duk dukan da shazim yayi mashi bai isa ba"
Abdallah yace "pls Abba kayi haƙuri" ya faɗa haɗi da kallon jami'an tsaron da ke tsayae yace " yallaɓai kuyi aikin da ya kawo ku "
matsowa dady yayi ganin ya matsa ne yasa luqman da sauri ya nufi sama   
"dan Allah yallaɓai ku dakata dan Allah "
tsayawa su kayi suna sauraron mi dady zaice kamar daga sama suka ji ihun luqman yana kiran sunan dady a tamanin suka juya suna kallon sama, shazim ne su ka hango ya damƙi wuyan luqman ya nufo parlorn da shi ba wanda yaga san da ya shigo  part ɗin, ya gaji da jiran police ɗin ne su fito da luqman ganin sun jima ne yasa shi ya shigo shine yaji dady nacewa su dakata ya kuma hangi luqman zai shige part ɗin dady, har wurin su ya ƙara so da luqman ya miƙama ɗaya daga cikin police yace "arrest him" kama hannun luqman police ɗin yayi ya sa mashi handcuff ya fice da shi,kan sofa dady ya zube, Abba ne yace " why shazim why, yanzu duk dukan da kayi mashi bai isa ba, shima fa ɗan uwan ka ne kamar fatimar " kallon Abba  shazim yayi da idanun shi da suka kaɗa su kayi jawur tsantsanr ɓacin rai da masifa ce a cikin su hannu kawai  ya haɗa ma Abba  alamar haƙuri ba tare da yace komai ba ya fice daga part ɗin sai a lokacin momy ta fashe da kuka.
ciki mota su ka sa luqman suka tafi da shi sai ihu luqman yake yana kiran sunan dady.
Episode 42_43_

Sai ihu luqman yake yana kiran sunan dady.
Shazim ba irin haƙurin da su ya usman da su mahmud, faisal mama,gwaggo halima, har da su Asma'u da kairiyya basu bashi ba amma ko kallon in da suke bai ma yi ba sai ma kama hanya da yayi ya bar part ɗin

tare shi mansoor yayi yana faɗin " haba shazim miyasa zaka yi haka duk haƙurin da ake baka yaci ace ka haƙura,  dan Allah kar ka bari su tafi da shi, a nan ma zaka iya hukunta shi, please "
ya ƙara sa magana cikin sigar roƙo, amma ina ko kallon shi shazim bai yi ba sai ma bi ta gefan shi da yayi ya wuce, bin bayan shi mansoor yayi yana ci gaba da roƙonkwan shi amma kwata kwata babu alamar ma zai saurare shi, ko mawa yayi kan Abdallah yana faɗin " haba Abdallah miyasa zaka kira su tun da har shazim ya ɗauki doka a hannu ai da an barshi yaji da iya wannan "
"mansoor kafi kowa sanin halin luqman tun da kai ke tare da shi, ji irin abun da yayi ma fatima ace ma bai mata komai ba, halin ciwan da ya sata ya kyauta kenan "
"na san bai kyauta ba amma hukuncin zai mashi yawa "
"kai ka ga haka "
Shazim ne ya ce " ko da bai kira su ba ni sai na kira su, kuma wallahi na tabbatar da ya ci mutuncin fatima, wallahi kaji na rantse sai yayi daya sanin sani na a rayuwar shi, sai ya gommaci kiɗa da karatu daga shi har mahaifin na shi daya iya ƙoƙarin ɓoye ta dan kar wani ya sani " yana gama faɗar haka ya shige part ɗin su, mansoor yana ji yana gani ba shi da yanda zai yi haka police ɗin suka fice da luqman daga estate ɗin cikin dare,  bin bayan su shazim yayi dan ya duba jikin fatima.

kusa da dady Abba ya matsa " Ibrahim kayi haƙuri kar ka sa kanka a damuwa in sha Allah ba abun da zai faru da luqman zai dawo gobe da izinin Allah, ka kwantar da hankalin ka  "

"amma yaya mi nayi ma shazim a rayuwa da zai saka man da irin wannan abu, ai ko darajar kasancewata ƙanin mahaifin shi ya duba ya ƙyale luqman, amma saboda bai ɗauke ni a bakin komai ba bayan yayi mashi dukan mutuwa shine ya haɗa shi da jami'an tsaro, mi nayi mashi har haka "

"ka kwantar da hankalin ka ba abun da kayi mashi kawai ranshi ne ya ɓaci, amma nasan nan da zuwa wani lokaci zai huce kuma zai nemi afuwan abun da yayi maka "

"shikenan yaya, ya jikin feenah na manta tun É—azu ban tambaye ka ba "

"jikinta da sauƙi gobe da safe za su ma dawo gida in sha Allah"

"Allah ya kaimu " dady ya faɗa, da Ameen Abba ya amsa haɗi da tashi yana faɗin "ka tashi kaje ku kwanta, ka lallashi turai naga hankalin ta yayi matuƙar ta shi "  da to dady ya amsa haɗi da tashi ya nufi ɗakin momy, ficewa Abba yayi zuwa part ɗin shi lokacin da ya shiga duk sun shige ɗakunan su hakan yasa ya nufi ɗakin shi ya kwanata

Zaune dady ya samu momy bakin gado tayi tagumi sai share  hawaye take,abun zallah ban tausayi tana ji tana gani an kama mata ɗa bata yanda zata yi,  zama dady yayi kusa da ita, ɗan shiru yayi na wani lokaci can ya dafa kafaɗar ta " dan Allah turai kiyi haƙuri, ko mai zai wuce da izinin ubangiji, in sha Allah gobe luqman zai dawo kiyi haƙuri kinji "
fashewa tayi da kuka mai tsumarai dady shima kukan ne yazo mashi amma sai ya danne shi bai yi ba, jawota yayi jikin shi yayi hugging ɗinta yana ɗan bubbuga bayan ta haƙuri ya cigaba da bata har sai da tayi shiru ta koma tana sauke ajiyar zuciya, a haka har bacci ya ɗauke ta, kwantar da ita yayi kan bed haɗi da jan blanket ya rufe mata jikin, sannan ya nufi toilet ɗinta bayan kamar ten  seconds ya fito, switch ɗin ɗakin ya nufa ya kashe masu sannan ya nufi gadon ya hau sai da ya rufe jikin shi da blanket sannan  jawo ta jikin shi yayi hugging, idanu ya rufe ba bacci yake ba tunani ya shiga na abun da ya faru ya daɗe yana tunani har shima bacci yayi awan gaba da shi.

Fitowar shi kenan daga toilet ta farka a firgice tana kiran sunan shi da Ammy da malam har noraiz sai bige bige take tana ƙoƙarin cire drip ɗin da aka sa mata da sauri ya ƙarasa wurin ta yana sa hannu ya riƙe hannuwanta da take bige bige  yana kiran sunnan ta da cewa " dai na kuka gani nan a kusa da ke " jin muryar mutum ne a kusa da ita  yasa ta ƙoƙarin fisge hannun ta tana kiran sunan shazim a ruɗe  " ya shazim ka zo ka  taimake ni kashe ni ya luqman zai yi dan Allah ka taimake ni " gaba ɗaya a firgice take  ta dai ji muryar shazim amma bata san yana ina ba dan bata san shine a kusa da ita ba duk a tunanin ta luqman ne, sai ko kawa take zata ƙwace hannun ta da shazim ya riƙe jawo ta yayi jikin shi da sauri yana faɗin " kwantar da hankalin ki ni ne  a kusa da ke ba luqman ba " duk da haka bata daina yunƙurin fisgewa daga riƙowan da yayi mata ba, ganin dai da gaske a tsorace take  bazata tsaya ba ne yasa shi jawo ledar magungunan da yasa aka siyo mata allurar da ke ciki ya ciro dama ya haɗata, hakan yasa bai tsaya wata wata ba ya yayi mata allurar a damtsen hannun ta,dan danan allurar ta fara aikin ta cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauke ta, jin jikinta yayi sanyi ne yasa shi fahimtar tayi bacci, kwantar da ita yayi kan gadon ya ja mata blanket, ya daɗe zaune yana kallon ta saƙawa da kwan cewa kawai yake , muddun gwajin da ya tura asibiti  sakamakon ya fito,    abun da yake zargi ya tabbata , ya rantse babu abun da zai hana shi yin shari'a da luqman har da mahaifin shi, ya jima yana saƙawa da kwancewa daga bisani ya tashi ya nufi parlor wurin Abdallah da mansoor, zaune ya same su kan sofa kowa yayi shiru yana tattaunawa da zuciyar shi, wuri shima ya samu kan sofar ya zauna

Abdallah ne yace " har yanzu bata farka ba " ɗaga mshi kai kawai shazim yayi, yan da suka ga rana haka  suka ga dare kowannen su a zaune ya kwana, har luqman da ke station a tsaye ya kwana har gari ya waye

_*WASHE GARI*_

Haka su ka tashi da jiki su ku ku ba bu walwala, har lokacin kuma fatima bata farka ba, kowa da ke estate ɗin ya shigo ya duba jikinta har da dady,sa'ada ke zaune kusa da fatima  ta zuba mata idanu.

da safen ma ba irin haƙurin da su ya usman basu ba shazim ba akan ya haƙura a saki luqman, amma fir yace bai san wannan zancen ba dole sai anyima fatima gwaji ya tabbatar da luqman bai mata komai ba sannan,  har station ɗin suka je ko za'a basu  belin shi amma ina saboda shazim ya hana ba yanda su ka iya haka suka dawo estate suka zuba ma sarautar Allah ido, ba wanda ranshi bai ɓaci ba da shazim, shi kuwa abun da ke gabansa kawai yake, har estate ɗin ummah  matar uncle ahmad ta zo domin duba fatima kuma duk wani gwaji da shazim ke so ayi ma fatima ita tayi mata  da yake likita ce tafiya tayi zuwa hospital dan ta bicika awan da tayi ma fatima,kowa  zaman jiran dawowar ta yake da saka makon da zata zo da shi dan shazim yace  dole sai sai yaga sakamakon ko da zai yarda aba da belin luqman, shiyyasa suka zauna zaman jiran tsammani kowa adu'ar shi Allah yasa luqman bai mata komai ba kamar yanda yake faɗa, kafin  ummah ta dawo su
Innah  su ka dawo daga asibiti da feenah, ta ji sauƙi kamar ba ita ba sai dai damuwa da take ciki, kwata kwata bata da walwala,har ƴar rama tayi duk a kan shazim,  part ɗin innah su ka nufa gwaggo halima da mama ne suka shigo su kayi ma feenah ya jiki, feenah na kwance kan sofa tayi matashi da cinyar innah  , su ya usman ma sun zo gaishe ta ganin noraiz ne yasa innah cewa " ai ku nayi tunanin kun tsufa da tafiya ashe kuna nan, kenan zuciyar da uban naku hau ba wata bace" shiru noraiz yayi bai ce mata ƙala ba  gwaggo halima ce tace "dan Allah mama kiyi haƙuri daga dawowar ki " tsaki kawai innah ta ja ba tace komai ba,can kuma tace " ina su Ahmad ne "
gwaggo Uwani tace " nima dai naga ban gan su ba, kuma wai mike damun ku ne nagan ku duk sai a hankali "
"nima abun da zance kenan, sai kace kunyi zaman makoki" innah ta faÉ—a tana tsare gwaggo halima da idanu
"ba komai innah kawai saboda jikin feenah ne, amma tun gashi kun dawo Alhmdllh " shiru kawai su innah su kayi bawai dan sun yarda da abun gwaggo halima ta faɗi ba, feenah ce ta  tashi tana cema innah zataje part ɗin su dan ta watsa ruwa, da to innah ta amsa mata, tashi tayi Ilham  ta bi bayan ta, a bayan part ɗin innah su ka tsaya feenah tace " dan Allah Ilham ki faɗaman mike faruwa ne na ganku duk sai a hanli "  ɗan nisa wa Ilham tayi sannan ta faɗa mata duk abun da ya faru da basu nan, kuka feenah ta fashe da shi tana  faɗin "wai dan Allah mi yasa ya luqman bai gudun abun magana ne wani lokacin mi zai sa yayi ma fatima haka laifin mi tayi mashi har haka  "
Ilham tace "gaskiya kam bai kyauta ba, amma baki ga irin na damar da yayi ba, yayi daya sanin yimata haka "

"ba abun da dady yayi a kan ya luqman É—in "
"ba abun da yayi, domin ya shazim ya hana a bada belin shi wai har sai ya tabbatar da bai mata komai ba " 
"shikenan " feenah ta faÉ—a part É—in su suka nufa, tsit suka same shi ba motsin kowa, bedroom É—in momy su ka nufa zaune su ka same ta bakin bed ta zuba uban tagumi gaba É—aya damuwa tayi mata da bai bayi, sai sallama suke bata ma san suna yi ba tayi zurfi cikin tunani har sai da feenah ta dafa ta sannan ta san da shigowar su, ajiyar zuciya ta sauke haÉ—i da wai gowa tana kallon su, shafa kan feenah tayi tana faÉ—in " kun dawo kenan " É—aga mata kai feenah tayi " to ya jikin " da sauki feenah ta faÉ—a " momy ina dady yake "
"yana É—akin shi "

"ok, momy abun da ya luqman yayi kenan " ta faɗa idonta na tara ƙwalla  shiru momy tayi batace komai ba
"momy wai miyasa ya luqman bai jin magana, yanzu yana ganin ya kyauta, duk ya saku a cikin damuwa "
"feenah dan Allah ki bar maganar nan abun da ya faru yariga da ya faru "
" amma momy..... " da katar da ita momy tayi
" daga dawowarki  ki feenah, kar ki dawo man da abun da yariga ya wuce, in sha Allah ba abun da zai faru "
"shikenan momy, bari naje ɗakin dady " ɗaga mata kai kawai momy tayi, hannun Ilham taja zuwa ɗakin dady basu same shi a parlor ba hakan yasa feenah ta nufi bedroom ɗin shi Ilham kuma ta zauna kan sofa, a bakin ƙofar ta tsaya haɗi da yin nocking, izinin shiga dady ya bata a hankali ta tura ƙofar ta shiga tsaye ta same shi sai kai kawo yake, sallama tayi haɗi da maida ƙofar ta rufe, juyowa dady yana kallon har ta ƙaraso kusa da shi tayi hugging ɗin shi, shafar sumar kanta yayi " ya jikin naki "
"da sauki "
"Allah ya ƙara sauki " da Ameen ta amsa  sannan tace " dady yaushe za'a bada belin ya luqman "
"daga dawowar ki waya faɗa maki abun da ke faruwa, nima ban sani ba feenah, amma in sha Allah na san zuwa anjima za'a sake shi  " 
" to Allah ya kaimu " da Ameen dady ya amsa, ta ɗan jima a part ɗin dady daga baya ta fita ita da Ilham , duk abun da ke faruwa har lokacin innah da gwaggo Uwani basu sani ba har sai da ummah tazo da sakamakon gwajin da tayi ma fatima, sanna su innah suka san  abun da ke faruwa, innah tasha kuka zagi kuwa na duniyar nan ba irin wanda bata yima shazim ba, har papah dake kwance cikin kabarin sa bata bari ba sai da ta zage shi tas shi da maifiyar shi kakar su shazim, har part ɗin su taje ta samu shazim, zaune ta same shi a part ɗin su ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, su Abdallah da ummah har da Ameerah duk suna zaune kan sofa, kowa ya zuba ma shazim ido, jira kawai su ke ya gama karanta takardar dan suji minene sakamakon gwajin fatima  , kamar daga sama suka ji muryar innah tana faɗin
"dama ubanka ko kafin ya bar  duniya sai daya tozar ta man ɗana, wallahi duk abun da ya samu luqman bazan bar ka ba daga kai har uwar taka, mara mutunci kawai" masifa iri iri sai da innah ta sauke ma shazim,  zagi kuwa ba wanda innah bata sauke ma shazim ba  duk masifar da take mashi ko kallon in da take bai yi ba,takardun dake hannun shi kawai yake aikin  dubawa, gwaggo halima ce ta shigo tana bama innahr haƙuri  amma ina masifa ta rufe ma innah ido har su dady sai da suka sa baki amma taƙiyin shiru, shazim yana gama karanta takar dar gawajin , sallama yayi ma ummah da godiya, ba tare da yace ma kowa ƙala ba ya tashi ya nufi bedroom ɗin sa inda ya kwantar da fatima,sai magana su mansoor suke mashi akan ya faɗa masu sakamakon amma yayi banza da su ya nufi ɗakin shi , ummah su ka tambaya ce masu tayi itama bata karanta ba, shikenan kawai su kace, rakata parking lot mansoor da Abdallah su kayi, sai da ta tafi sannan suka dawo parlorn,

Kamar dai yanda take jiya yauma haka take kwance,goshinta  da bandage   jikinta duk a bushe yake,
sa'ada na nan zaune kusa da ita ta zuba uban tagumi, ɗagowa tayi jin shigowar mutum da kallo ta bi shazim daya shigo,ce mata yayi taje bedroom ɗin fatima ta ɗauko mashi  trollyn ta, da to ta amsa mashi haɗi da ficewa ta nufi ɗakin fatima, noraiz ne ya taso ya nufe ta yana faɗin" ya akayi naga kin fito "
"kaya yace na É—auko ma fatima da trollyn ta "
Ok kawai noraiz yace haɗi da nufar bedroom ɗin shazim ɗin samun shi yayi a bakin  wardrobe ɗin shi, sallama noraiz yayi mashi haɗi da faɗin " yaya minene sakamakon, hankalin kowa a tsahe yake kai kawai su ke jira ka faɗa masu sakamakon ka kuma taso ka shigo ɗaki.... "
"dakata man dan Allah noraiz, ka wuce ka fita yanzu zamu wuce "
"amma yay.... "
"bana son jin komai daga gare ka, kayi abun da nace kawai " da to kawai noraiz ya amsa haÉ—i da nufar bedroom É—in shi laptop É—in shi ya É—auka haÉ—i da kashe duk wani abu wuta a É—akin sannan ya fito dama trollys É—in su suna cikin mota tun jiya
bedroom ɗin shazim sa'ada ta koma da trollyn fatima da ta ɗauko, lokacin da ta shiga shazim harya canza kayan jikin shi zuwa baƙar t_shirt da cargo trouser shima baƙi da p_cap sak shigar da yayice jiya sai dai ba kayan bane wasu ne yasa irin su, a tsakiyar ɗakin ta tsaya da trollyn
"buɗe ki ciro mata doguwar riga mara nauyi " shazim ya faɗa, da to sa'ada ta amasa haɗi da ɗora trollyn bakin gadon,  buɗe shi tayi doguwar rigar abaya mara nauyi ta ɗauko mata ajiye ta tayi gefe ta rufe trollyn , kallon shi tayi tana faɗin "yaya gashi "
"ok,kina iya samata?"
"eh " ta bashi amsa, jinjina kai yayi haÉ—i da jan trollyn fatimar ya fice.
da ya  fito wata takarda ya ciro daga cikin aljihun trouser ɗin shi ya miƙama mansoor, amsa mansoor yayi yana faɗin " thank you,zan same ku kuwa kafin na dawo " ɗaga mashi kai shazim yayi, hugging ɗin shi mansoor yayi " shikenan sai na dawo bro " ok shazim yace, a tare su ka fita shi ya sa trollyn fatima a booth mansoor kuma ya shiga motar shi ya fice daga estate ɗin.

Mansoor na ficewa AMBULANCE ɗin asibitin su ummah na shigowa, ita ta turo da ambulance ɗin dan su samu sauƙin zuwa airport da fatima,tsayawa shazim yayi har sai da tayi parking sannan ya gaisa da drivern ambulance ɗin sannan ya shiga ciki yana faɗi ina zuwa da to drivern ya amsa, ha zai shiga ciki wayar shi dake aljihu tafa ringing, tsayawa yayi yana amsa kiran

✨SA'ADA ✨

Rigar ta shiga kiciniyar sanya ma fatima, tasha wahala kafin ta sama ta rigar saboda jikinta duk a sake yake kamar wacce ta mutu babu inda ke motsi a jikinta,bayan ta sa mata rigar ne ta nufi dressing mirror ɗin shazim man shafawa ta ɗauko ta ɗan shafa mata a hannuwan ta da ƙafafuwan ta saboda jikin ta duk ya bushe tana gama shafa mata ta fice zuwa waje lokacin da ta fita Abdallah da  noraiz ka ɗai ta samu su Abba duk sun fita, fita tayi itama zuwa parking lot inda anan ta samu shazim tsaye yana waya jira tayi har ya gama wayar sannan tace " ya shazim idan tafiya za kuyi, dan Allah ka tafi da ni "
" ki bari idan mansoor zai zo sai ku zo tare "
"dan Allah ya shazim, wallahi hankalina bazai kwanta ba,dan Allah ya shazim " kai kawai ya É—aga mata alamar to shikenan
"nagode sosai ya shazim ta faɗa " haɗi da nufar part ɗin su da sauri, zazzaune ta samu su Abba da su gwaggo halima harda innah,sallama kawai tayi masu bata jira sun amsa ba   ta nufi ɗakin ta da sauri, shaf shaf ta canza kaya ita ma doguwar riga ta sa,  gyalen ta kawai ta ya fa sai side bag ɗinta da wayar ta da ta ɗauka, da sauri ta fice kowa dake parlorn da idanu ya bita, gwaggo uwani ce tace " ke kuma ina zaki "
"lagos zan bi su ya shazim"
kawai tace haɗi da juyawa ta fice,da sauri feenah ta tashi jin wai shazim zai tafi, gwaggo Uwani ce ta jawo tana faɗin "dawo nan " dawowa tayi ta zauna sai turo baki take,  innah tace " amma wannan ɗiya anyi ƴar banza, kenan waɗannan marasa mutuncin zata bi " Abba ne yace " ai ba komi innah dan ta bi su, nasan tana son zama da ƴar uwarta ne har ta samu sauƙi "
"amma kuma bata ga abun da yayan yarinyar yayi ma yayan ta ba da zata wani bisu kamar wasu ƙannan uwar ta"
"kiyi haƙuri innah,shima luqman ɗin  yana da laifi "
"dama nasan bayan shi zaku bi"
gwaggo Uwani ce tace
" bansan mi yake nufi ba tafiya zai yi ba tare da yasa an saki luqman É—in ba komi "
"ke bari kiga naje na  samu wannan mara mutuncin "
innah ta faɗa haɗi da miƙewa ta fice bayanta su gwaggo Uwani suka bi har da su Abba,  tana fita shazim na fitowa ɗauke da fatima a kafaɗar shi kamar wata gawa, noraiz da Abdallah na bayan shi sai sa'ada data fito hannun ta ɗauke da jakarta da jakar laptop ɗin fatima,drivern  Ambulance ɗinne ya buɗe mashi ƙofa  ya saka fatima, zama yayi kan wata ƴar chair dake cikin ambulance ɗin,ledar magungunan fatima ya amsa a hannun sa'ada  haɗi da maida ƙofar ya rufe,wani drip ɗin ya sake sama fatima sai da yaga komai na tafiya yanda ya kamata sannan ya fito,  motar mansoor ce ta shigo estate ɗin, gaba ɗaya hankalin su kan motar ya koma har yazo parking lot yayi parking buɗe motar yayi ya fito nufo su yayi luqman  ne ya fito jikin shi duk a sanyaye har ya ɗan faɗa dare ɗaya kawai, da sauri innah ta tare shi yana ganin ta shima da sauri yayi hugging ɗinta hawaye na bin idanuwan shi , su dady ma nufo su su kayi binsu yayi tayi ɗaya bayan ɗaya yana hugging ɗin sai kuka yake, dady ne yayi hugging ɗin shi yana lallashin shi,sa'ada ƙin zuwa tayi wurin luqman haushin shi take ji, mansoor ne  ya ƙaraso wurin su shazim, hugging ɗin shazim yayi "tnxs bro " ɗago da shi shazim yayi yana faɗin "godiyar ta isa haka, yaushe za ka zo "
"In sha Allah next week zan zo"
"to Allah ya kaimu " da ameen mansoor ya amsa, raba jikin su su kayi,
"ku kuzo mu wuce " shazim ya faɗa haɗi da nufar Ambulance ɗin  da fatima ke ciki zai shiga, gwaggo halima ce ta ƙaraso kusa da shi " shazim baza ka bari ko breakfast kuyi ba sannan ku tafi "
"ba komai Aunty, idan mun isa can za muyi "
"shikenan, Allah ya kai ku lafiya, ina gaishe da Ammyn ku sai na zo "
"za taji in sha Allah, sai kinzo "
"to shikenan " ta faɗa haɗi da ko mawa wurin su innah,mama Allah ya sauke su lafiya tayi masu,dady ma da Abba sai da suka yi masu Allah ya kiyaye haɗi da adu'ar Allah ya ba fatima lafiya, ƙin amsa masu shazim yayi dan duk haushin su yake ji musamman dady  kowa sai da yayi masu Allah tsare ban da mutum uku innah, gwaggo Uwani,sai momy dake part ɗin ta bata fito ba dan bama ta san luqman ya dawo ba, sai luqman ɗin dake tsoron yazo wurin saboda shazim, amma yaso ya ga ya jikin fatima yake,mota su ka shi ga, shazim na cikin ambulance   da fatima sai mansoor da noraiz Abdallah da sa'ada a motar mansoor , kairiyya taso ta bi su amma Abba yace ta bari sai za su je sai su tafi tare, feenah taci kuka kamar ranta zai fita haukace masu tayi ita a dole sai tabi shazim  tun ana lallashin ta kan ta bari sai su dady zasu har ta kai ga ba mutane haushi dady ya wanke mata fuska da mari, Allah ya ƙara kowa ke mata. Luqman ya so ya raka su airport amma dady yace a'a.

Suna nan tsaye har motocin su suka bar estate É—in, sai da suka ga fitar su sannan kowa ya koma part É—in shi

Suna zuwa airport ba daɗewa lokacin tashin su yayi,har filin in da jirgi yake Ambulance ɗin ta shiga , shazim ne ya turo ɗan gadon da take kwance, da sauri  mansoor da Abdallah  suka fito daga cikin mota suka  shigar da ita cikin jirgin.

. Allah sarki fatima ta zo da ƙafar ta cikin ɗoki da nishaɗi amma zata koma cikin halin jinya, dama haka rayuwa ta gada in yau kai ne gobe ba kai bane, Allah ya baki lafiya mai amfani Ameen.

sa'ada da noraiz ma fitowa su kayi su ka shiga. 
Sallama mansoor yayi masu, da yake harda Abdallah zasu tafi.

Sai da jirgin su ya tashi sannan mansoor ya koma cikin motar ya bar airport  shi ka ɗai cike da kewar su.

Sai da suka isa lagos  sannan shazim ya kira malam ya sanar da shi sun dawo, faɗa sosai malam yayi mashi saboda ƙin ɗaukar wayar su da baiyi ba,duk ya bi ya tayar masu da hankali,haƙuri  ya shiga bashi ,ƙin haƙura malam yayi sai ma kashe wayar da yayi yana faɗin "zaka dawo ka same ni ne ai "
Tun kafin jirginsu ya tashi ya kira number majeed ya sanar da shi suna hanya ya turo mashi  da Ambulance suna tare da patient ne,  bai jira mi majeed zai ce ba yayi rejecting kiran yasan dole majeed zai tambaye shi waye bai da lafiya.

✨LAGOS✨

Kiran Ammy malam yayi ya sanar da ita su shazim na hanya
"amma shazim bai da hankali baba, yanzu da lafiyar su lau amma mu kai ta kiran shi baya É—aga wa"

"Allah dai ka ɗan yasan dalilin da yasa bai ɗauka  ba"
"amma ko ma minene, ai ya É—auki kiran mu idan baza su dawo a jiyan ba "
"yanzu dai sai sun shigo, kisa ilya yaje ya É—auko su dan yace sun iso" da to Ammy ta amsa haÉ—i da yin rejecting, kiran ilya tayi ta sanar da shi su shazim na hanya yaje ya É—auko su.
Suna gama waya da Ammy bai jira komai ba ya shirya ya nufi airport shi da É—ayan drivern gidan mai suna É—an Auta, shi ba kasa fai ya cika driving ba yafi yawan zaman gida.

Ko da suka isa airport ɗin su majeed sun daɗe da zuwa da Ambulance tun da shazim yace mashi suna tafe da patient hankalin shi yaƙi kwaciya sai da ya zo dan yaga waye ba lafiya, basu wani jima ba  jirgin su shazim ya  ƙaraso.

hankalin majeed yayi matuƙar tashi da yaga fatima,bawan Allah ilya har da ƴar ƙwallar shi, shigar da ita su kayi cikin Ambulance ɗin , bai ma lura da Abdallah ba hankalin shi naga fatima,  har sai da shazim yace" wai lafiya Abdallah na maka magana hankalin ka na wani wajen baka ji " sai a lokacin ya lura da Abdallah dake mashi magana, gaisawa su kayi da shi.

Mota kowannan su ya shiga, yanzu ma shazim  Ambulance ya shiga shi da Abdallah sai  majeed  da man a nan yazo,majeed na gaba shida driver yayin da Abdallah ke kusa da fatima shi da shazim, ganin duk sun shige nan yasa noraiz da sa'ada nufar motar da ilya yazo ɗaukar su, ɗan auta kuwa empty ya koma ba kowa a motar da ya zo da ita,  Ambulance ɗin ke gaba su ilya na binsu a baya.

Kasa haƙuri majeed yayi har sai da ya  tambayi shazim mike damun fatima,  duk ya bi ya damu, abun har so yayi ya ba Abdallah haushi ganin yanda majeed ya ruɗe kan ciwan fatima, amsa  shazim ya bashi da  ciwan ta ne ya tashi, tambayar shi majeed yayi miye dalilin
"majeed ka kwantar da hankalin ka,  da sauƙi jikin ta"
tsaki Abdallah yaja,shi kuwa majeed hankalin shi naga fatima bai ma san Abdallah nayi ba, shazim kawai ya lura da shi, girgiza kai kawai yayi ba tare da ya ce ma kowa komi ba
"to amma hospital za'a nufa da ita " majeed ya faɗa, tsaki Abdallah ya sake ja yana faɗin "wai lafiya majeed ka bi duk ka tashi hankalin ka, ance maka jikin ta da sauƙi, amma sai tambaya kake "
"daga tambayar lafiyar ta zaka wani ce na damu mutane jiman ƙarfin hali"
" dan Allah ya isa haka,  gida za'a kaita duk wani abu da ya dace ayi mata zan iya yi mata shi a can ba dole  sai a hospital ba" shazim ya faɗa

Majeed yace "to shikenan , Allah ya bata lafiya "
"Ameen ya Allah " shazim ya amsa, babu wanda ya ƙara cewa komai cikin su har suka ƙara so  gida, horn su kayi da sauri mai gadi ya buɗe masu, ciki su ka shiga, a compound drivern yayi parking da Ambulance ɗin, jin jiniyar Ambulance ne yasa Ammy dake parlor zaune fitowa da sauri gaban ta na faɗuwa, tana fitowa su shazim na fito da fatima, da sauri ta ƙara so kusa da su dan taga waye kuma ba lafiya, ai ko da tayi arba da fatima kwance kamar matacciya,wani mummunan faɗuwa gaban ta yayi, jiri ne ya fara kwasarta  ta tafi luuu zata faɗi  babu wanda yalura da ita sai noraiz,da wani masifafen gudu  ya ƙaraso wurin ta yana kiran sunan ta cikin ƙaraji  ganin ta tafi luuu zata faɗi,ririƙeta yayi,ƙasa suka nufa shi da ita dan tuni har ta sume,  gaba ɗaya hankalin su shazim ya dawo kanta, shazim ma a tamanin ya ƙaraso wurin su  saura kaɗan ya faɗi..
Episode  _44_45_

tallabo kanta yayi  yana kiran sunan ta

"Ammy!  Ammy!!  pls ki tashi dan Allah " sai roƙwanta yake da ta tashi duk ya bi ya firgice sai jijjiga ta yake, noraiz ban da kuka babu abun da yake, ilya ne ya shiga ciki da sauri, ruwa ya ɗauko a kitchen da sauri ya fito ya dawo wurin su, Abdallah ne ya amsa ya nufi ammy da ke kwance a jikin shazim, da sauri ya kwance marfin robar ruwan ya shiga  yayyafa mata sai da ya yayyafa mata kusan sau ukku sannan ta ja wani dogon numfashi, Alhmdllh su ka shiga furtawa, hawaye ne suka taru idanuwanta
"mi ya faru da fatima??, kar ka saki kace man ta mutu  " tana faɗa hawayen da suka taru a idanuwan ta na zuba, abun tausayi su Abdallah ma sai da zuciyoyun su suka karaya ganin yanda Ammy ke zubar da ƙwalla
"ki kwantar da hankalin ki Ammy, ba wani abu bane ya same ta lafiyar ta lau "
"taya zaka ce man tana lafiya bayan na ganta a haka "

"da gaske nake Ammy, ki kwantar da hankalin ki " ya faɗa haɗi da kallon su majeed yace " majeed ku shiga ciki da ita " da to majeed ya amsa, shi da Abdallah su ka shiga da fatima, da sauri Ammy ta tashi ta bi bayan su, bin bayan ta noraiz yayi ya na  share hawaye , shazim kallon sa'ada da ke gefe rakuɓe sai hawaye take  yayi yace " shiga ciki mana " da to ta amsa haɗi da bin bayan su noraiz ta shiga ciki,komawa yayi cikin Ambulance ɗin ledar magungunan fatima ya ɗauka sannan yayi ma drivern sallama, bai  shiga ciki ba   waya ya ciro daga aljihun wandon shi, dialing ɗin wata number yayi,wanda ya kira na ɗagawa bai ko amsa mashi sallamar da yake yi ba yace " kayi sauri ka  kawo man na dawo " yana gama faɗa yayi rejecting kiran, ciki ya nufa, bai same su a main parlor ba hakan yasa shi nufar medical room ɗin su dake kusa da part ɗin shi, tura ƙofar yayi ya shiga ciki, tsai tsaye ya same su fatima kuma na kwance kan gadon marasa lafiya gaban gadon ya ƙarasa haɗi da ajiye ledar da ke hannun shi kan ɗan table ɗin dake gefan gadon wani drip ya sake fiddowa daga cikin ledar haɗa shi yayi duk su Ammy na nan sun zuba mashi ido harya gama haɗa shi ya sama fatima, sai da ya gama daidata komai sannan ya kalle su yace "mu fita mu bata wuri "
ficewa su kayi zuwa waje, ban da Ammy matsawa ma tayi kusa da gadon ta zauna kan wata kujer ta roba  dake gefan gadon
"Ammy mu fita bata son kowa kusa da ita yanzu " shazim ya faÉ—a
"babu inda zani, ina nan har sai ta farfaɗo ta faɗa man abun da ya same ta " lallashin ta ya shiga yi akan ta tashi su fita amma ƙiri ƙiri tace bata fita, saima tsare shi tayi akan dole saiya faɗa mata abun da ke damun fatima shiru yayi yana kallon Ammy ba tare da yace mata komai ba
"magana nake maka shazim mike damun fatima ka wani tsare ni da idanuwa kana kallo na" Ammy ta faÉ—a da damuwa a fuskar ta, duk ta damu da son jin miya samu É—iyarta
"kiyi haƙuri Ammy kamar yan da nace maki ciwanta ne ya tashi "
"haba shazim sai kace dai ban san yanda ciwan nata yake ba, kuma yaushe rabon da ya tashi ina tuna nin tun tana ƙarama kuma  kai da kanka kace man ta samu sauƙi idan ba abu yayi tsanani ba ba lallai bane ciwan ya tashi"
"haka ne Ammy, amma ai bai zama dole sai abun yayi tsanani ba"
"shazim!  shazim! !  shazim!!!,  sau nawa na kira sunan ka "
"sau uku Ammy "
"to ka faɗa man mike damun ɗiyata mi ya haddasa mata wannan ciwan tun kafin ranka ya ɓaci, idan ma laifi tayi maka ka dake ta ka faɗa man dan na fara zargin laifinka ne ciwan ta  "
"Ammy kema kin sani bazan taɓa sa  sannu na daki fatima ba duk kuwa abunda tayi man"
"to naji faÉ—a man mi yasa same ta " baya son ya faÉ—a mata ne dan kar ta tashi hankalin ta sosai,
"kayi shiru?"
"zan faÉ—a maki Ammy, amma yanzu ina so na É—an watsa ruwa, zan zo part É—in ki na same ki "
"na lura dai faÉ—aman ne baka son yi "
"ba haka bane Ammy zan faÉ—a maki amma yanzu ki bari na watsa ruwan, ko fa breakfast ba muyi ba mu ka taho" jin yace ko breakfast basu yi bane yasa tace " to shikenan na ji zan koma part É—ina, amma kar ka shanya ni, zan sa Innah Asabe ta shirya maku breakfast a dinning "
"in sha Allah da na shirya zan shigo "
"to shikenan "
fita su kayi daga ɗakin, bin bayan Ammy noraiz  da sa'ada su ka yi , a parlornta ta zauna kan sofa,  kusa da ita noraiz yazo ya  zauna, sa'ada kuma kan sofa ta zauna tana faɗin " ina kwana Ammy " kwata kwata Ammy bata san da sa'ada aka zo ba sai yanzu da ta gaishe da ita sannan ta san da ita su ka zo " lafiya lau sa'ada  tare ku ke kenan "
" eh Ammy, ya gida "
" Alhmdllh, ya su momyn ku "
"suna lafiya "
"Masha Allah "Ammy ta faÉ—a
Innah Asabe ce ta shigo parlorn, gaishe da ita noraiz da sa'ada su kayi, cikin kulawa ta amsa tana tambayar ya mutanen abuja.

_*✨SHAZIM✨*_

A bakin part ɗin shi ya sami su Abdallah sun yi  tsaye, kowa da abun da ke damun shi majeed gaba ɗaya hankalin shi a tashe yake burin shi ɗaya su keɓe da shazim yaji miye ke damun ta yayin da Abdallah ke gefe guda sai cika yake yana batsewa duk dan saboda majeed dan duk ya lura da take taken shi, da kallon shazim ya bi su,  murmushin gefen baki yayi
yana faɗin "lafiya dai dakarun yaƙi, duk kun wani yi ma mutane cirko cirko sai kace wasu body guard "
majeed ne yace " dan Allah ka ajiye  wannan wasan a gefe,  ka ƙi ka faɗa man mi ke damun fatima dan na daɗe ban ganta aciki irin wannan halin ba " 
 Abdallah ne yayi saurin cewa
"wai kai dan Allah wannan damuwar ta micece ne, duk ka wani bi ka damu mutune da mike da munta sai kace in an faÉ—a maka É—auke mata ciwan zaka yi " wani É—an iskan kallo majeed ya bi Abdallah da shi can kuma sai yace
"ina abun da ya dame ka ne wai da tambayar da nake tun da ba kai nai mawa ba, wai ma miye naka a ciki ne  ina ruwan ka da ni ne ma"
"wannan kuma matsalar kace" Abdallah ya faɗa haɗi da jan tsaki ya shige part ɗin shazim, shazim dai na tsaye yana bin su da idanuwa  dariya ce ke cinsa amma sai ya ɗaure fuska bai yi ba amma a zuciyar shi dariya kawai yake masu.

Majeed ne yace " ni wallahi abun a hashim ma mamki yake bani, dan na tambayi abun da ke damun ta laifi nayi ne zai wani dage shi a dole kar a tambayi mike damun ta sai kace wani mugun abu "

Shazim ne yace " kar ka damu ranshi ne kawai a ɓace ba wani abu ba "
"dan ranshi na a ɓace shine zai ta wannan ƙarfin halin"
" ya isa dai yanzu kayi haƙuri, komai ya wuce  "
hmmm kawai majeed yace dan ba ƙaramin ɓaci ranshi yayi ba da abun da Abdallah yayi mashi,
"kayi tsaye mu shiga ciki " shazim ya faɗa, ok kawai majeed yace haɗi da bin bayan shazim su ka shiga ciki, zaune su ka samu Abdallah kan sofa ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya jin alamar shigowar su ne yasa shi zaro wayar shi da ke cikin aljihun shi yayi dialing number Abie, yana picking ya tashi ya fita zuwa waje, a bakin ƙofar part ɗin ya tsaya amsa sallamar da abie yayi yayi sannan yace " ina kwana abie, ya su mom "
"lafiya lau, ya su shazim ɗin ya kuma jikin ƙanwar tasa "
" lafiya lau abie, jikin ta da sauƙi "
" to Allah ya ƙara sauƙi, shazim ɗin na kusa "
" eh bari na bashi "
" to " abie ya faɗa, ƙofar ɗakin ya tura ya shiga ciki, zaune majeed yake yayin da shazim ke tsaye bakin fridge, ƙarasawa Abdallah yayi kusa da shi miƙa mashi wayar yayi yana faɗin  " abie ne ke magana" ok shazim yace haɗi da amsar wayar ya kara akunnen shi " ina kwana abie "
"lafiya lau shazim, ya kwana biyu, ka yada mu ko " murmushi yayi yana cewa "ba haka bane abie, ya mom "
"haka ne mana shazim,ban taɓa ganin ƙafar ka a katsina ba  idan ba abuja kaje ba nima  ina nan ai ban taɓa ganin ka ba "
"In sha Allah abie ina nan zuwa , zan maka zuwan baza ta "
"to Allah yasa, ya jikin fatima"
"da sauƙi abie "
"to Allah ya ƙara sauƙi, ga mom ɗin ku nan za ku gaisa " abie ya faɗa, to shazim yace , muryar mom yaji tana cewa "shazim ya gida "
"lafiya lau mom,ina kwana "
"lafiya lau, ya su ammyn ku "
"lafiya lau su ke "
"Ashe fatima ba lafiya,to Allah ya bata lafiya "
"Ameen ya Allah "
"Ammyn ku na kusa "
"A'a tana part É—in ta "
"to shikenan ka gaishe man da ita dan Allah "
"in sha Allah za taji "
"yawwa to nagode sai anjima " mom ta faɗa haɗi da yin rejecting,cire wayar yayi daga kunnan shi haɗi da miƙa ma Abdallah , amsa Abdallah yayi.
bedroom shazim ya shiga, kamar yanda yace ma Ammy wanka yayi jallabiya ya sa ya fice zuwa part Ammyn zaune take kamar ɗazu, sai dai yanzu ita kaɗai ce noraiz na part ɗin shi sa'ada kuma na ɗakin fatima,  zama yayi kan sofar da kusa da wacce Ammy ke zaune
"Ammy " ya kira sunan ta  a hankali , juyowa tayi tana kallon shi, magana ya soma cikin natsuwa
"Ammy kiyi haƙuri da abun da zan faɗa maki "
"ina sauraron ka shazim, haƙuri kuma ya zama dole tun da bazan goge abun da ya riga ya faru ba " ajiyar zuciya ya ɗan sauke, duk abun da ya faru a Abuja sai da ya sanar da ita har da irin matakin da ya ɗauka a kan luqman sai da ya faɗa mata, Ammy taci kuka kuma taji haushin hukuncin da su uncle Ahmad su ka yanke ma shazim dan kwata kwata bata son feenah , saboda rashin tarbiyar ta da rashin kamun kanta taso ace da kairiyya suka haɗa shi bawai da feenah ba, sannan ranta yayi matuƙar baci da luqman ta so ace shazim yayi mashi hukunci fiye da wanda yayi mashi, ta san duk abun da ya faru a kwai sa hannun innah da gwaggo Uwani
na sara miyasa innah bata ƙaunata da su shazim wai mi nayi mata ne a rayuwa, duk abun sadiq yayi mata amma da wannan zata saka mashi, ya Allah ka kawo man ƙarahen wannan al'amarin Ammy ta faɗa a zuciyar ta
kallon shazim tayi tace " yanzu yaushe su ka ce sun tsaida ranar bikin "
"ni ban san yaushe za su tsaida ba, bana ma so na san lokacin "
"shi luqman da yace yana son fatimar sun amsa cewa zasu bashi "
"a lokacin basu amsa ba, amma na san zasu amsa ne,amma ki kwantar da hankalin ki Ammy babu mai ma fatima auren dole da wannan yaron in dai ina raye"
"shazim bana son ka nuna ba su isa da kai ba ko dan Ibrahim ya kula da rayuwar ku "
"Ammy ni bazan nuna masu basu isa da ni  ba, amma bazan bari su zalinci fatima ba"
"shikenan, amma auren naka da feenah fa, na so ace da kairiyya su ka haɗa ka  ba wai feenah "
"dan Allah ma Ammy ki bar wannan zancen, ni bazan auri wannan yarinyar ba ko kuwa mi zasu yi"
"shikenan, fatima yan zu miye yake damun ta "
"jikin ta da suƙi, kawai dai alurar da nake mata ce ke sata bacci saboda firgitar da take yi ne, amma in sha Allah nan da zuwa anjima ma zata iya farkawa "
"Allah ya bata lafiya, amma gaskiya luqman bai kayuta man ba, mi yasa zai yi man haka a rayuwa"
"Ammy kar ki damu da batun luqman yanzu abun da yaso ya aikata Allah bai bashi sa'a ba ta dalilin ciwan fatimar daya tashi sai yaji tsoro bai mata komai ba,  dan haka ki kwantar da hankalin ki kawai"

_Abun da ya faru, lokacin da fatima ta fice daga parlorn da suke taro,luqman  shi kuma haushin ta nuna bata son shi ne yasa shi fita ya bi bayanta ya tare ta yana mata masifa ita harta isa tace bata son shi daga zai taimaka mata shine zatace bata sonshi, angaya mata shima son ta yake, kawai dan an haɗa shi da Allah ne akan yace yana son ta ne yasa yace yana son ta,maganar daya faɗa ce ta wai an haɗa shi da Allah yace yana son tace ta ɓata mata rai ta kai ga zazzaga mashi masifa son ranta hartana ce mashi ɗan shaye shaye, shikuma haushin rashin kunyar da tayi mashi ne yasa shi cewa yau sai ya nuna mata cewa shi cikaken ɗan iska ne,  shine ya saɓeta kan kafaɗa, tana kuka ta kai mashi duka a baya har cizon shi tayi amma ya ƙi sauke ta har sai da ya isa ɗakin shi sannan yayi wurigi da ita kan gadon shi haɗi da maida ƙofa ya rufe ba tausayi ya afaka mata,kuka ta shiga yi tana roƙwanshi daya ƙyale ta amma sam sam bai saurare ta ba,dan ma kar ta sa wani ya jisu ne yasa shi rufe mata baki da nashi,sumbatar ta ya shiga yi ba arziƙi tun tana kuka har ta kai ga fara kai mashi duka ta ko ina har da cizo da ya kushi, wani ya kushi  ne da takai mashi a gadon bayan shi ne yasa shi haɗa ta da bango har kanta ya fashe ta kifa ƙasa azabar zafin da taji ne yasa ta fasa ƙara wanda hakan ya jawo hankalin dady daya shigo part ɗaukar key ɗin mota saboda suma da feenah tayi zai kaita asibiti, kasancewar ɗakin luqman ɗin yana kusa da na shi shiyyasa yaji ihun da fatima ta tayi, har ya shiga ɗakin ya same ta yashe a ƙasa shikuma luqman tsaye yana zare ido duk ya tsorata, anan sai da dady ya wanke shi da mari kafin yasa shi su ka kama fatimar suka shiga part ɗin shi da ita duk yayi hakan ne dan kar shazim ya san abun da ya faru yayi tunanin suma kawai tayi na tsoro bai san lalurar ta ce ta tashi ba, sai da suka ya yayyafa mata ruwa ta ƙi tashi sannan hankalin dady da na luqman ɗin kanshi ya ƙara tashi
momy kuma motsin su ne yasa nufar part É—in dadyn amma sai ya hanata ganin fatimar ba irin tambayar da bata yi mashi ba dan taji ihun fatima amma dady yace ba komai, da sa'ada ta faÉ—a mata ba'aga fatima bane yasa ta zargin ko dai fatima ce_

"shikenan shazim, amma taya zan yarda bai keta man haddin yarinya ba"
"nasa matar uncle É—in Abdallah tayi mata awo kuma sakamakon ya nuna cewa ba abun da ya same ta "
"to shikenan Allah ya bata lafiya,  kaga ma ko gaisawa ba muyi da Abdallah ba nagama kamar har da Abdulmajeed ku ka shi go "
"Eh tare muke da shi "
"to bari nasa sa'ada ta kawo maku breakfast naji kace ba kuyi break ba kuka taho "
"Eh Ammy " shazim ya faÉ—a haÉ—i da tashi ya nufi part É—in shi wurin su Abdallah.

ÆŠakin fatima Ammy ta nufa, zaune ta samu sa'ada bakin gado ta zuba uban tagumi
Sallama Ammy tayi sa'ada bata amsa ba ganin kamar hankalin ta baya tare da jikin ta ne ya sata shiga ciki  kusa da sa'ada ta ƙarasa, dafa kafaɗar ta tayi tace " sa'ada lafiya kika zuba uban tagumi ina sallama bakya ji "
" ba komai Ammy "
"ya za kice ba komai bayan na ganki cikin damuwa haka, ko dai duk a kan fatima ne " É—aga mata kai sa'ada tayi alamar eh
"ki kwantar da hankalin ki za ta samu sauƙi in sha Allah "
" to Ammy "
"yawwa, zo ki je part É—in shazim ki kai masu breakfast,ke ma kizo kiyi "
"to Ammy ta faɗa haɗi da miƙewa su ka fita zuwa dinning, jera mata kayan breakfast ɗin Ammy tayi a tray, trayn ɗin bai ɗauke kayan duka ba hakan yasa Ammy cewa taje ta dawo sai ta kai masu sauran da to ta amsa har ta kama hanya zata nufi sama sai ga noraiz ya sauko amsar trayn yayi yace taje ta ɗauko sauran dan yaji lokacin da Ammy ke cewa taje ta dawo ta ɗauki sairan, " to ya noraiz " ta faɗa haɗi da komawa ta ɗauko sauran ta bi bayan shi, a bakin ƙofar part ɗin suka tsaya.

Sa'ada tayi nocking, shazim ne yazo ya buÉ—e masu, amsar trayn da ke hannun sa'ada yayi noraiz kuma ya shiga da wanda ke hannun sa, juyawa sa'ada tayi ta koma parlorn Ammy
"yawwa har kun kai masu "
"Eh "
"to kema jeki kiyi naki breakfast ɗin" da to ta amsa haɗi da nufar dinning ta zauna ,noraiz ma da ya shigo parlorn  dinning ɗin ya nufa  samun wuri yayi ya zauna , sa'ada tayi serving ɗin shi
Ammy kuma ɗakin ta ta nufa ta kira malam da ummy ta sanar da su da wowar su shazim da kuma rashin lafiyar fatima, malam ranshi yayi matuƙar ɓaci ya kuma ce wallahi babu wanda zai Aura ma  fatima luqman, idan da yayi shiru innah na abun da ta gadama akan su yanzu bazai yi shiru ba sai dai duk abun da zai faru ya faru.
"in sha Allah ina nan zuwa anjima na duba jikin fatimar "
"ai baba da kun barshi, jikin nata da sauƙi "
"A'a, sai na zo "
"to shikenan Allah ya kawo ku lafiya " da Ameen malam ya amsa,  rejecting kiran yayi.

wanda shazim ya kira a waya ne yazo, magungunan ne ya kawo mashi wanda zai cigaba da ba fatima.

sai bayan sallar asr majeed ya tafi gida, akan zai dawo da daddare ya sake duba jikin fatimar,Abdallah kuwa kamar ya shaƙe majeed haka yake ji, shima majeed ɗin haushin Abdallah yake ji dan gani yake duk wannan abun da yake yana yi ne saboda kishi, ya lura son fatimar yake
ko wannan su kishi ne ke É—awai niya da shi.

Kamar yanda malam yace da daddare su ka zo shi da ummy,  majeed  ya dawo shi da mamar shi daya faɗa mata fatimar bata da lafiya shi ne tace zata zo ta gaishe da ita, sun daɗe a gidan daga baya su ka tafi, su malam kuma shazim cewa yayi dan Allah su kwana nan,
"A'a aboki gida zan koma, ai nace sai ranar da ka zama babban mutum tukun zan dawo gidan nan "
"dan Allah dai malam  iya yau fa "
"ahab sai dai kayi kuma, komai dare sai na tafi gida fatimar dai ta farka  " ba yanda bai yi da malam ba amma yace a'a bazai kwana ba ba dan ya so ba ya haƙura, tun suna sa rana farkawar fatima har suka fara fdda rai malam ma har ya ce ummy ta zo su koma gida, Ammy ma ta so ace sun kwana Amma yace A'a gobe dai zasu dawo idan ta farka, rakiya su kayi masu har parking lot idan drivern malam yake sai da suka ga tafiyar su tukun suka koma ciki.
kowa shirin kwanciya yayi ya nufi ɗakin shi, Ammy ta so ta kwana medical room ɗin wurin fatima gudun kar ta farka cikin dare amma shazim yace ta bari shi zai kwana ɗaki ita ta tafi ta kwanta kawai, tafiya tayi amma gaba ɗaya hankalin ta na kan fatima ko da ta tafi ɗakin ta bata kwanta ba alwala tayi ta shiga nafilfilo tana roƙwan Allah ya fatima lafiya, sa'ada kuma a ɗakin fatima ta kwana.
Shazim bedroom É—in shi ya shiga yayi wanka ya canza kayan da ke jikin shi zuwa na bacci parlor ya dawo wurin Abdallah dake zaune yana latsa wayar shi shima sanye yake da pajamas, kallon shi shazim yayi yace " ka shiga ka kwanta ni zan kwana wurin fatima dan ina kyautata zaton zata iya farkawa a kowane lokaci "
"bana jin bacci, kai idan kana ji zaka iya kwanciya ni sai na zauna na jira ta farka " murmushi shazim yayi dama ya san in dai yace haka to Abdallah bazai kwanta ba
"ko ina jin bacci dole na haƙura"
"kai kana ma ji ke nan "
"na san kai ma kana ji sai dai ka ƙi kwanciya "
"to ina ji bazan kwanta ba"
"to ai shikenan " shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya ɗauki laptop ɗin shi, tashi Abdallah yayi ya bi bayan shi, medical room ɗin su ka nufa kan sofa suka zauna, shazim na aiki a laptop yayin da Abdallah ke aikin latsar waya...

Episode  46_47_

suna ɗan taɓa fira jefi jefi, har shazim ya gama abun da yake a laptop fatima bata farka ba, wajen Asuba ta fara mutsu mutsun farkawa, da sauri su ka ƙarasa wurin ta, sai kiran sunan Ammy take da shazim,sai ƙoƙarin tashe take mai da ta yayi ya kwantar "ya shazim ina Ammy " fatima ta faɗa
" Ammy tana É—aki bacci take, ya jikin naki "
"ya shazim ina nake "
"kina gida ya jikin "
"ya shazim ina ta kiran ka amma baka zo ba "
"yanzu ai  gani a kusa da ke "
"ya noor ma da Ammy duk na kira su amma basu amsa man ba, ya luqman so yayi ya kashe ni ya shazim " ta faɗa hawaye na bin idanuwan ta, sosai ran Abdallah  ya ƙara ɓaci da abun da fatima ta faɗa
"kiyi haƙuri kinji, bazan sake bari wani abu ya faru dake ba in sha Allah, ki kwantar da hankalin ki "
"dan Allah ya shazim kar ka bari su Aura man shi wallahi bana son shi "
"bazan taɓa bari su aura maki shi ba karki damu "
"yaya ina son ganin Ammy "
"Ammy bacci ta ke fatima, dare ne yanzu ki bari sai da safe za tazo kinji "
Abdallah na gefe ya ƙura mata ido ji yake kamar ya mayar da ciwan a jikin shi tsabar yan da yake jinta a cikin jikin shi
"zaki sha ruwa ne " shazim ya faɗa ganin tana miƙa hannu alamar wani abun zata ɗauka, gyaɗa mashi kai tayi
" Eh ya shazim "  hannun yasa ya ɗauko ruwan da ke kan table ɗin da magungunan ta ke kai cire marfin robar yayi da kanshi ya bata a baki, bata wani sha sosai ba ta kauda kai, ajiye robar shazim yayi yana cemata " ki koma ki kwanta " da to ta amsa haɗi da komawa ta kwanta drip ɗin da ke jikin ta ya cire mata
  "zaki sha tea ko " ya tambaye ta, ɗaga mashi kai tayi alamar eh
"Ok bari na kawo maki sai kisha maganin ki daga nan " ya faɗa haɗi da tashi ya bar gaban gadon kallon Abdallah dake tsaye ya zuba ma fatima ido kamar ya cinye ta yayi " lafiya dai ko?" ya tambayi Abdallah haɗi da tsare shi da idanu, kawata kawata hankalin Abdallah na kan fatima bai ma san shazim na mashi magana ba, har sai da shazim ya ɗan taɓa shi tukun ya dawo cikin hankalin shi, zuba mashi ido yayi yana kallon shi
"malam lafiya ka wani tsare ni da idanu " Abdallah ya faÉ—a yana wani shana mur
"kai zan tamabaya ai wannan " shazim ya faɗa yana zuba mashi harara, jin muryar  Abdallah ne yasa fatima juyowa da sauri ta kalli inda suke tsaye shi da shazim
"Ya dr " fatima ta kira sunan shi cikin muryar marasa lafiya, matsawa yayi kusa da ita yana faɗin "na'am fatima, ya jikin na ki" hawaye ne su ka taru a  idanuwan ta tace "ya dr, yaushe ka zo "
"tare muka zo da ke, ya jikin " ya faÉ—a haÉ—i da neman wuri bakin gadon ya zauna, fita shazim yayi zuwa part É—in shi .

hannun ta Abdallah ya kamo  yana faɗin  "fatima ina tambayar jikin ki kinyi shiru "
"ya dr da sauƙi "
"Allah ya ƙara sauƙi "
"Ameen" shazim ne ya shigo hannun shi É—auke da cup É—in tea sai turiri yake,kusa da gadon ya matso, amsar cup É—in Abdallah yayi yana faÉ—in
"tashi ki zauna kisha tea ɗin " yunƙurin tashi tayi, aje cup  ɗin yayi  kan table domin ya tai maka mata ta tashi  tun kafin ya ajiye shazim ya kamata ya tayar da ita zaune,
" thanks" Abdallah yace, harara shazim ya zuba mashi murmushi kawai Abdallah yayi   da kanshi ya shiga bata tea shazim kuma na duba mata magungunan da ya kamata ta sha, da ta kammala sha amsar magungunan Abdallah yayi ya miƙa mata da kanshi tasha, matsowa shazim yayi da allura a hannun shi yana faɗin " to malam matsa " juyowa Abdallah yayi yana kallon shazim dake tsaye hannun shi riƙe da allura,
"ka matsa nace bawai ka kalleni ba "
matsawa Abdallah yayi yana faÉ—in
"ka dai yi a hankali dan nasan halinka, ban da mugunta"
"ka san Allah zanyi maka ita idan baka yiman shiru ba É—an rainin wayau kawai " shazim ya faÉ—a yana nuna ma Abdallah allurar da ke hannun sa
"zaka iya" Abdallah ya faɗa haɗi da nufar kan sofa ya zauna, fatima dai sai binsu take da idanu abun ba ƙaramin burgeta yake ba,  matsowa shazim yayi kusa da ita yana faɗin "miƙo man hannun ki " hannun rigar da ke jikin ta taja haɗi da miƙa mashi hannun, a damtsen hannun ta yayi mata alurar yana tsirawa  ta rintse  ido da sauri Abdallah yace "wai Allah, dan Allah kayi mata a sannu "
"ka takura man fah, ai da zuwa kayi ka amsa kayi mata da kanka" shazim ya faÉ—a
"bana iya yi mata allura ai " tsaki shazim yaja
" aikin banza da na wofi "
" kai kaga aikin banza " fatima sai murmushi take dan ba kaɗan su ke sata nisha ɗi ba, lura da hakan ne ma yasa shazim biye ma Abdallah har sai da wani baccin ya sake ɗaukar ta tukun su ka bar ɗakin dan lokacin sallar asuba yayi, alwala su kayi a part ɗin shazim su ka nufi masallaci tare da noraiz su ka tafi, lokacin da su ka dawo Ammy da sa'ada  su ka samu a medical room ɗin tare da fatima da ta sake farkawa, gaishe da Ammy su kayi haɗi da zama kan sofar da ke ɗakin har sai da gari yayi haske tukun su ka tashi su ka bar Ammy da sa'ada Innah Asabe ma ta shigo ta duba jikin fatima,da ta tashi tafiya kitchen bin ta sa'ada tayi ta shirya ma fatima lafiyayyen breakfast, duk da bakin nata ba daɗi haka Ammy da sa'adar su ka tasa  ta gaba sai taci, ganin sun damu taci ne yasa ta  daure badan tana jin da ɗin shi ba taci   sosai sa'ada  taji daɗin ganin taci, fatimar ma daɗi taji ganin yanda kowa ke nan nan da ita ta kuma ji daɗin ganin  ƴan uwan ta a tare da ita, ko da Ammy ta kira malam ta sanar da shi farkawar  fatima hamdala yayi ga ubangiji kuma da safen ya sa driven shi ya kawo  su shi da ummy, da shazim bari yayi sai anjima yaje ya ɗauko su da kanshi sannan ya sanar da su farkawar fatimar, amma sai  Ammy ta riga shi kiran  malam  sai dai kawai ya gansu sun zo, majeed ma ya zo shi da mamar shi sun daɗe gidan sosai  sannan su  ka tafi,shazim da har ya shirya zai je Abnoor sai ga kabir ya zo duba jikin fatima,  tun jiya ya kira wayar shazim bai ɗauka ba shine ya kira noraiz, shike sanar da shi ai sun dawo da rashin lafiyar fatima, shine daya fito daga gida zai je eko ya fara zuwa nan dan ya duba jikin ta,da kabir ɗin zai wuce ne ya shirya su ka tafi tare ba yanda bai yi da Abdallah ba akan ya bishi su tafi amma yace zai tsaya idan lokacin shan maganin fatima yayi zai bata har  ce mashi shazim yayi ai Ammy na nan amma ƙiri ƙiri ya ƙi binsu, tafiya shazim yayi ya bar sa shima  bai wani jima ba ya wuce Abnoor can ma ana yi sallar asr ya dawo, Abdallah da ya zauna gida wata irin kulawa ta musamman yake ba fatima da tace kaza jiki na rawa zai yi mata shi tun yana ba Ammy mamaki har ya daina bata mamaki, dan sosai ya cire duk wata kunya da nauyin Ammy da ya ke ji ,su malam kuwa ba ƙaramin daɗi hakan yayi mashi ba ganin yanda Abdallahn yake kula da fatima a gaban su, har kiran Abie da mom yayi ya ba Ammy da malam har da ummy su ka gaisa su ka kuma yi ma su ya mai jiki,  sai da daddare su malam suka tafi akan gobe ma zasu dawo su sake duba jikin ta.
haka fatima ta cigaba da samun kulawa daga wurin kowa a cikin su har ta ɗan samu sauƙi ta ma koma ɗakin ta da  zama yanzu ba'a mata allura magunguna kawai take sha, kwanan Abdallah huɗu ya wuce katsina dan tun tuni uncle ahmad ya tafi, ya tafi ne akan zai dawo ya sake duba jikinta shi da su Abie, kamar tayi kuka da zai tafi taso ace ya ɗan yi kwana ki da yawa cematan da yayi zai dawo ne yasa ta haƙura.
Shazim kullum kafin ya tafi aiki sai ya tabbatar da taci abinci kuma tasha maganinta, noraiz ma ya fara aiki
kulawa kowa yake bata hakan yasa ta ƙara jin daɗi kuma jikin ta Alhmdllh masha Allah dan ba inda bata zuwa, kuma taji daɗin da sa'ada ta biyo ta.

Satin su É—aya da dawowa lagos su uncle Ahmad su ka zo da uncle Ibrahim, kairiyya, feenah, gwaggo Halima , luqman har da momy da mama, mansoor bai samu zuwa ba saboda aiki amma yace in sha Allah yana nan zai zo idan ya kammala, ba yanda ba su yi da innah da gwaggo Uwani ba su biyo su amma tace wallahi ita ba zata zo ba ta so ma ta hana su uncle Ahmad É—in ma zuwa amma su kace su sai sunzo sun gaishe da fatima.

Fatima gaba É—aya hankalinta tashi yayi da ta ga luqman dan ta tsorata da shi,bawan Allah duk ya
Lsha jinin jikin shi ganin yanda take ɗari ɗari da shi, ga wani kallon tsana da shazim ke binshi ga Ammy kwata kwata ta ƙi bashi fuska ko da ya gaishe da ita kadarn kadaham ta amsa mashi  ƙarshe ma tashi yayi ya bar parlorn ya nufi parking lot ya zauna a mota , haɗa kan shi yayi da siti yarin mota duk ji yayi ya tsani kan shi yayi kuma daya sanin abun da yayi mata, ganin duk ya damu ne ya kuma ware kanshi ne yasa Ammy ta ɗan saukko tanuna ba komai komai yawuce har ta sa noraiz ya kira mata shi, ko da yazo haƙuri ya bata akan abun da yayi fatima, ta kuma ce ta yafe mashi amma a zuciyar ta ɗauki alƙawarin ba zata bari ya auri fatima ba
Fatimar ma ba yanda ba'ayi da ita ba akan ko magana tayi ma luqman ɗin ko da bazata yafe mashi ba amma taƙi.

Fennah sai ƙoƙari take taga shazim ya kula ta amma ya ɗure fuska ko kallon banza bata ishe shi ba,da su uncle su ka tashi tafiya ƙin binsu feenah tayi dole ita a nan zata zauna, ganin ta dage ne yasa Ammy cewa a barta idan mansoor yazo sai su koma tare harda kairiyya ma, sa'ada daman ba mai maganar ta dan cewa tayi tun da fatima baza tai karatu abuja ba to ita zata yi lagos , ko da tace haka dady bai yi musu ba ya amince mata.
da zasu wuce sai da suka je gidan malam,su ka kuma roƙi afuwar shi akan abun da luqman ɗin yayi, ya kuma haƙura yayi masu Allah ya kiyaye hanya.

Shazim fa har su ka tafi ban da gaisuwa babu abun da ya haÉ—a shi da su har su ka bar garin.

Abdallah kamar yan da yace kwanan shi biyar da tafiya, ya dawo shi da uncle Ahmad mom da ummh, abie bai samu zuwa ba saboda wani uziri daya tsare shi, hakan yasa su ka zo su kaɗai ban da shi, Ammy taji ɗadi sosai ta kuma yi masu godiya, fatima kamar tayi mi dan bata taɓa gaini mom ba a zahiri sai dai a photo da waya sai ga shi yau taga mom ido da ido.
wani abu da na lura da shi kallon da mom ke ma ammy da wanda ammyn ke ma mom kamar sun taɓa sanin juna, sai dai sun kasa tuna inda su ka taɓa ganin juna.
A ranar su mom su ka koma katsina Abdallah kuma sai da yayi kwan biyu tukun ya koma.


_* to masu karatu kar ku manta an tafi an bar Feenah da kairiyya akan idan mansoor ya zo za su tafi tare da shi , yanzu wasan zai fara amma kafin nan ina so na sanar da ku waye shazim*_


_*WANENE  DR ABDULƘADIR ABUBAKAR NURADDEEN ( SHAZIM) *_

Dr shazim ya ka sance É—ane daga zuriar alhaji nuraddeen ahmad sharani.
Alhaji nuraddeen sharani, mutum ne mai rufin asiri, ya ka sance ɗan kasuwa ne mai sayar da kayan masarufi, alhaji nuraddeen yana zaune ne a garin kurfi dake jahar katsina, anan cikin garin yake gudanar da harkokin kasuwancin shi da ƙauyakun da ke kusa da garin kurfi.

Alhaji nuraddeen yana da mata ɗaya tilo mai suna habiba ana kiran ta da ruma,  ita ma yar cikin garin kurfi ce, barumiya ce kyakyawar gaske, shekarar su goma cif da aure Allah bai basu haihuwa ba, ruma kullum cikin tashin hankali take saboda tsangwamar da iyah ( mahaifiyar nuraddeen )  ke mata ita da ƴaƴen ta, har ta kai ko hidima suke ruma bata zuwa saboda kyara da tsangwama da suke mata, ganin yanda hankalin ruma yake atashe yasa nuraddeen ya shiga kwantar mata da hankali yana nunamata cewa Allah yana sane dasu kuma zai basu haihuwa karta damu da duk abunda ƴan uwan shi ke cewa, sosai yayi mata nasiha akan su cigaba da adu'a kawai, kwantar da hankalin ta tayi ganin mijinta bai damu da rashin haihuwar ta ba, mahaifiyar nuraddeen ta takura ma shi akan dole fah sai ya ƙara aure tunda matar shi bata haihuwa, nuna mata yayi baya buƙatar ƙara aure, indai haihuwa ce Allah zai ba ruma, sosai ran iyah  ya ɓaci jin abunda ya ce ta kuma ɗauki fushi da shi akan ƙinbin umarnin ta da yayi, har gida taje ta samu ruma tayi mata cin mutunci, duk a tunanin ta ita ta hana nuraddeen ƙara aure saboda ta shanye shi, sosai tsanar da yan uwan nuraddeen kema ruma ta ƙaru saboda ƙin ƙara aure da yayi, ruma ba ƙaramar wahala take sha ba awurin iyah , dan kusan kullum sai ta zo har gida ta ci mata mutunci, hakan yasa tayi ta roƙwan mijin nata akan ya bi umarnin mahaifiyar shi  da nuna mashi mahimmanci bin umarnin nata, da farko ƙin amincewa yayi sai da ruma ta rinƙa tasa shi gaba tana yi mashi kuka akan ya ƙara auren, haka nan  ba dan ya so ba ya amince da ƙarin auren, iyah da kanta ta nema mashi auren ɗiyar aminiyarta, ba a ɗau wani lokaci ba aka ɗaura auren nuraddeen da amayar shi hauwa'u ana kiran ta da maijidda, ranar da aka kai hauwa'u gidan shi ya haɗa su ita da ruma yayi masu nasiha akan suyi haƙuri su zauna lafiya, hakan ce ta faru dan sosai ruma da maijidda ke zaman lafiya, ruma ta ɗauki maijidda kamar ƙanwarta uwa ɗaya uba ɗaya... 
Episode  48_49_

Watan maijidda ɗaya da satittika a gidan nuraddeen Allah ya albarka ce ta da samun ciki , zo kaga murna wurin nuraddeen da ruma, da iyah  taji labarin cikin maijidda har gida ta zo tayi ta sakar ma ruma habaici tana ce mata juya, ita kuwa ruma babu abun da ya dame ta tasan Allah da ya bama maijidda yana sane da ita, sosai take kula da maijidda, cikin na kaiwa wata biyar ta hana maijidda aikin komai a gidan daga sallah sai bacci da cin abinci take yi,da  cikin ya isa haihuwa iyah  ta mai da  maijidda gidan ta, a cewar ta a gaban ta zata haihu, watan cikin  maijidda tara da kwana goma ta haifi ɗa namiji kyakyawa  mai matuƙar  kama da nuraddeen, zo kaga murna wurin angon jego da iya,  ruma ma ba'a barta a baya ba tayi murna da farin ciki sosai, da ranar suna ta zagayo yaro ya ci sunan mahaifin nuraddeen Ahmad  ana kiran shi da magaji, sai da maijidda tayi arba'in ta koma ɗakin mijinta,ruma ta cigaba da kula da ita da yaron ta har yayi ƙwari, shekarar magaji biyu maijidda ta samu wani cikin ta haifi ɗiyarta mace wacce taci sunan iyah watau maryam suna ce mata uwani haka maijidda tayi ta haihuwa amma ruma shiru bayan uwani maijidda tayi halimatu daga kan halimatu ne ta ɗan dakata bata ƙara haihuwa ba, yaranta sun taso cikin soyayyar mahaifin su da abokiyar zaman ta, sosai ruma ke son yaran kusan kullum suna tare da ita dan halimatu ma awurin ruma ta taso, haka rayuwa ta cigaba da tafiya,iyah ta tasa nuraddeen gaba akan dole sai ya saki ruma dan bataga amfanin ta ba tunda bata haihuwa, hankalin nuraddeen da ruma sosai ya tashi, amma bai saki rumar ba, ganin ba shi da niyyar sakin ruma ya sa ta sa aka kira mata shi har gida, tayi mashi faɗa sosai akan ya ƙi bin abun da ta ce har ikirari tayi mashi akan ko dai ya saki ruma ko kuma ta tsine mashi , ba shida wani zaɓi a lokacin bayan ya aiwatar da abun da mahaifiyar shi ta ce, haka ya samu ruma yace taje gida sai ya nemeta, hankalin ruma ya kai ƙuloluwar tashi da jin abun da  nuraddeen ya faɗa, haƙuri ta shiga bashi ita da maijidda, nuna masu yayi bashi da wani zaɓi ne, kuma ai ba sakin ruma yayi ba, cewa kawai yayi ta tafi gida in sha Allah zata dawo idan komai ya daidai ta tsakanin shi da iya, dole ruma ba dan ta so ba ta haɗa kayanta ta tafi gidan iyayen ta, sun sha kuka ita da maijidda san da zata tafi, haka ta tafi gida rai babu daɗi, koda ta tafi gida nan ta samu yayarta bilkisu  da ke aure cikin garin katsina ta zo, ran mahaifiyar ruma da na ƴar uwarta ba ƙaramin ɓace yayi ba akan abun da nuraddeen yayi, ko da bilkisu ta tashi tafiya tasa ruma tayi a gaba akan ta haɗa kayan ta su tafi katsina da farko ruma ƙin amincewa tayi akan zata tsaya har sai komai ya dai daita tsakanin ta da nuraddeen, hakan yasa mahaifiyarta ta yi mata faɗa sosai ba dan ta so ba ta bi bilkisu  zuwa katsina, bayan tafiyar ruma katsina nuraddeen ya zo gida wurin mahaifiyar ta ya bata haƙuri akan abun da ya faru ya kuma nuna mata bashi da yanda zai yi ne umarni ne daga mahaifiyar shi, mahaifiyar ruma ta fahimci shi ta kuma yi mashi uziri, sannan ta ce yayi ma mahaifiyar shi biyayya ka wai ya saki ruma,hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba jin tace wai ya saki ruma, ƙin amincewa yayi, sai ma haƙuri da ya ba mahaifiyar ruma. 

Sosai rayuwar ruma ta chanza a gidan ƴar uwar ta, soyayya da kulawa ta ke samu daga wurin ƴar uwar ta da mijin ƴar uwar ta, hakan ya sa ta saki jikinta sosai a gidan ga kuma yaran ƴar uwarta  da take kallo kamar ƴaƴen da ta haifa da cikin ta, ko wane lokaci tana tare da su, suma da sun dawo makaranta zaka same su manne da ita, watan ta ɗaya a gidan ta ƙara fresh tayi kyau  hasken fatar ta ya ƙara fitowa har yar ƙiba tayi,zazzabin dare ne ya taso ta gaba,sai ta wuni lafiya amma da dare yayi sai zazzaɓi ya rufe ta, ko da bilkisu ta fahimci haka sai ta ce mata ta shirya su tafi asibiti amma ruma ta ƙi, wata rana suna zaune kan dinning  zasu ci abinci daga  buɗe warmer ƙamshin abincin ya daki hancinta   tashi tayi  da gudu ta nufi   toilet,  amai tashiga ƙwarawa kamar zata amayar da ƴan hanjin cikin ta  , biyo bayan ta bilkisu tayi tana mata sannu da faɗin "nace muje asibiti amma kin ƙi saboda taurin kai, yanzu ai dole ki shirya mu tafi"
da ƙyar ruma ta buɗe baki tace " ba sai munje ba yanzu da nayi aman na samu sauƙi " ƙin sauraran ta bilkisu tayi sai ma ficewa da tayi ta nufi ɗakin ta tana faɗin " ki shirya kawai mu tafi bana son taurin kai"
tasa ta gaba bilkisu tayi  ta shirya suka je asibiti, koda suka je aka yima ruma aune aune anan likita ya shaida mata cewa  ruma na ɗauke da ciki tsawan wata uku da sati biyu, zo kaga murna wurin ruma da bilkisu, Allah sarki abun da suka da ɗe suna nema har ake mata gori  ake kiranta da juya yau gashi  Allah ya ba ta ,  koda labari ya isa kurfi sunyi murna da jin wannan labari, har gida mahaifiyar ruma ta sa aka kira mata nuraddeen ta sanar da shi, bawan Allah harda kukan shi saboda tsabar farin ciki, yana komawa gida ya sanar da maijidda, ita ma tayi farin ciki kamar mi, koda iyah ta ji labari ita ma harda kukan ta musamman da  ta tuna cin kashin da suka yi ma ruma ita da ƴaƴan ta har suke kiran ta da juya, har gida ta je ta bama mahaifiyar ruma haƙuri akan ruma ta dawo ta haihu a ɗaki mijin ta, da farko ƙin amincewa mahaifiyar ruma tayi sai da iya tai ta bata haƙuri tukun ta haƙura kuma tayi mata alƙawari akan rumar zata dawo, iyah taji daɗi kuma tayi ma mahaifiyar ruma godiya, hakan ce ta faru, bilkisu da kanta  ta shirya  ruma ta dawo da ita gidan mijinta, soyayya da kulawa iyah ta shiga bama ruma tana tattalin ta kusan kullum tana gidan nuraddeen kamar wannane jika na fari da za'a haifar mata, haka shima nuraddeen kamar ba'a taɓa yi mashi haihuwa ba ,  wani ikwan Allah maijidda sai ta fara jin haushin kulawar da iyah da nuraddeen  ke yima ruma, tana ganin kamar  sun fi son ruma akanta , ƙi ƙiri ta fara nuna hassadar ta a fili, iyah kuwa da nuraddeen basu ma san tana yi ba, da cikin ruma  ya kai watannin haihuwa  kamar yanda iyah tayi ma maijidda haka tayi ma ruma ta mai da ta gidan ta da zama, yan da iyah ke son ruma ta ke bata kulawa kamar ta ɗauke mata nauyin cikin haka ta ke ji, saboda cikin ba ƙaramin wahalar da ruma ya ke ba, kullum nuraddeen ya nan manne da ita sai dare yake koma wa gida, sosai ran maijidda ya ƙara ɓaci saboda dawowar da nuraddeen ya ke yi da daddare da kuma wunin daya ke yi wurin ruma, gani take kamar saboda cikin ruma ya banzatar da ita da yaran ta,sosai tsanar ruma ta ƙaru a zuciyar ta  duk ta manta rawar ƙafar da nuraddeen yayi lokacin da tana da cikin magaji, cikin ruma sai da ya kai wata goma da satittika bata haihu ba, hankalin nuraddeen ya tashi sosai ganin har tsawan wannan lokacin bata haihu ba, kwantar mashi da hankali iyah ta shiga yi akan ya kwantar ta hankalin shi ana samun irin haka, amma fir ya ƙi amincewa har sai da ya ɗauki ruma zuwa asibiti, ko da likita ya duba ruma anan ya gano cewa bazata iya haihuwa da kanta ba sai anyi mata cs, lokacin da bilkisu ta zo asibitin duk wani abu da ya kamata a yi na cs ɗin nuraddeen yayi har an  shiga da ita theater room, bakin theater room ɗin suka tsaya shi da bilkisu suna jiran tsammani, har kusan awa huɗu ta shuɗe amma likitocin ba su fito ba lokacin ana ta kiran sallar asr, masallaci nuraddeen ya tafi ya bar bilkisu, har ya je ya dawo ba'a fito da ruma ba likitocin ma ba wanda ya fito, hankalin nuraddeen ya kai ƙololuwar tashi, sai da wasu awannin suka shuɗe sannan wata nurse ta fito daga ɗakin hannun ta riƙe da jariri cikin towel, da sauri nuraddeen da bilkisu suka nufo nurse ɗin suna tambayar ta jikin ruma,miƙa ma bilkisu jaririn tayi tana faɗin "ana gyarata ne,idan an maida ta ɗakin hutu sai ku ganta" da to su ka amsa mata , amsar jaririn bilkisu  tayi tana kallon shi kyakyawan gaske a cikin  kamannin ruma babu abun da ya baro kamar tayi kaki, idonun shi rufe da a lama bacci ya ke, barin wurin su nurse ɗin tayi, hankalin nuraddeen duk a tashe so kawai ya ke yayi ido biyu da ruma,  sake buɗe ƙofar theater room ɗin aka yi dr ne ya fito yana cire safar hannun shi, da sauri nuraddeen ya ƙarasa wurin shi yana tambayar shi wane hali matar shi ke ciki,  "  Allah ya bamu ikwan cetan jaririn amma mahaifiyar shi ta sha wahala sosai,  yanzu dai munyi mata allurar bacci tana ɗakin hutu,ko da  za ku  ganta sai  zuwa anjima"
"to shikenan dr, nagode "ya faɗa haɗi da miƙa ma mashi hannu su kayi musaba ha, dr yace "babu komi, Allah ya bata lafiya"da ameen nuraddeen ya amsa, wuce wa dr yayi zuwa office ɗin shi,nuraddeen  komawa yayi idan da  bilkisu take ya amshi jaririn yana kallon shi, ji yake  kamar ya mai da shi ciki tsabar yanda ya ke son shi, ruma bata farka ba sai wajen ƙarfe 9, nurse ce tazo ta sanar da su farkawar ruma, ta shi su kayi suka bi bayan nurse ɗin nuraddeen har yan tuntuɓe saboda sauri.

Kwance take kan gadon marasa lafiya, jin an buɗe ƙofa ne yasa ta buɗe idanuwan ta dake rufe, binsu take da idanu ko ɗan ya tsanta bata iya ɗagawa, ba ƙaramin jin jiki take ba, zama nuraddeen yayi kan kujerar dake kusa da gadon, bilkisu kuma ta zauna kan gado, sannu su ka shiga yi mata,bata amsa masu ba sai ma hawayen da ke bin kumatun ta, hannu nuraddeen yasa yana share mata hawayen"ki daina kuka ruma Allah zai baki lafiya" jinjina kai tayi, hankalin nuraddeen duk ya ta shi ganin ko magana bata iyayi, yunƙurin tashi take zaune,pillow yasa ya  taimaka mata ta ɗan jingina da bango sannu kawai su ke mata, kiran sunan nuraddeen tayi , da sauri yace na'am, hannunta ta miƙa ganin tana son kama hannun shi ne yasa shi sauri kama nata hannun yana ƙara mata sannu, da ƙyar ta buɗe bakinta tana tamabayar ina abun da ta haifa, da sauri bilkisu ta miƙa mata jaririn da ke hannunta, amsa tayi ta zubama jaririn ido tana kallon shi hawaye na bin idanun ta, gaba ɗaya duk tabi ta karya masu zuciya da kukan da take, ta ɗauki tsawan lokaci tana kallon jaririn daga bisa ni ta miƙa ma nuraddeen shi,amsa yayi yana kallon ta, murmushi ta sakar mashi, da ƙyar magana take fita daga bakinta tace "ina so kasa mashi sunan mahaifina dan Allah, sannan  kayi man alƙawarin baza ka taɓa bari yayi maraici ba, ji nake kamar bazan tashi ba "
"dan Allah ki dai na cewa haka cuta ai ba mutuwa bace in sha Allah zaki samu lafiya "
Bilkisu hawaye ne kawai ke zuba daga idanunta duk ta karaya
"ina so dai ka ɗaukar man alƙawari "
"In sha Allah zanyi maki yan da kike so fatana Allah ya baki lafiya " nuraddeen ya faɗa,"na gode, ina so kowannan ku ya yafe man duk wani abun da nayi mashi, duk wani wanda kuka san na taɓa mu'amula da shi ina son ku roƙar man shi ya ya feman "
sai haƙuri su ke bata ciwo ba mutuwaba ne, sai dai tayi murmushi idan su ka faɗa mata haka, nurse ce ta shigo ta sanar da nuraddeen likita na son ganin shi,  tashi yayi ya bi bayan ta har office ɗin dr , wurin zama dr ya nuna mashi,  zama yayi yana zuba dr ido yana sauraron mi zaice, magana dr ya fara " da man ba wani abu bane yasa na kira ka, game da jaririn ya kamata a nemo mashi madara saboda lafiyar shi zuwa  wani ɗan lokaci sai mahaifiyar ta shi ta cigaba da shayar da shi,sannan ita ma akwai wasu  magunguna da ya kamata ita mahaifiyar tashi ta riƙa sha " dr nagama faɗa ya rubuta mashi sunan magungunan da madarar da ya kamata a riƙa ba yaron kafin mahaifiyar shi ta cigaba da shayar da shi, yana gama rubutawa ya miƙa mashi, amsa yayi haɗi da yima dr godiya ya fice zuwa ɗakin da ruma take kwance,yana buɗe ƙofa ya samu bilkisu ta kifa kai da bango sai shashekar kuka take ruma kuma jikinta rufe yake da farin ƙyalle,wani irin  faɗuwa da gaban shi yayi jikake dam dam, dafe saitin zuciyar shi yayi yana nufar gadon da take kwance hannun shi na rawa ya yaye farin ƙyale da aka rufe ta da shi, fuskarta ta bayyana idanuwan ta a rufe suke fuskarta da alamun murmushi, suma tsaye nuraddeen yayi lokacin guda ya tsinci kanshi ciki wani yanayi mara daɗi, hawaye ne suka shiga sakkowa daga idanun shi,zubewa yayi ƙasa kan gwiwowin shi  yana faɗin "yanzu shikenan na rasa ruma har abada,kai hakan bazai yiwuba " sai sambatu yake kamar wanda ya zare, jin maganganun da yake ne ya ƙara karya zuciyar bilkisu ta ƙara sautin kukan da take.

_*ALLAH SARKI RUMA UBANGIJI ALLAH YA JIƘANKI DA RAHAMA ABUN DA KIKA BARI ALLAH YA RAYA SHI*_

A wannan yana yin faɗa maku tashi hankalin da nuraddeen, bilkisu, iyah, mahaifiyar ruma suka shiga ɓata lokaci ne, sun shiga tashin hankali mara misltuwa.
bilkisu ta cigaba da kula da jaririn har aka yi adu'ar uku, sannan nuraddeen yayi ma yaron huɗu ba da suna Abubakar sadiq,ya ciki alƙawarin da ya ɗaukar ma ruma,  har akayi arba'in da rasuwar ruma sadiq na hannun bilkisu, da ta tashi komawa katsina da sadiq ta tafi har aka yaye shi, san da aka  yaye shi mijin bilkisu ya nemi  da abashi sadiq,amma sai nuraddeen yace a'a shima yana son yaron shi ya taso a gaban shi,bilkisu ta so ace nuraddeen zai bar mata sadiq a hannun ta amma bata da yan da zata yi haka ta dawo da sadiq hannun mahaifin shi,lokacin da  mijinta aka tura shi ƙasar china jakadancin nigeria, har kurfi ta zo ta sake roƙon nuraddeen daya bata sadiq ɗin ta tafi da shi, amma yace a'a idan dai sun zo nigeria zai riƙa zuwa masu hutu, taji haushin ƙin bata sadiq da nuraddeen yayi amma bata da yan da zata yi tun da ɗan shi ne dan dole ta haƙura ta tafi da kewar yaron.

Kulawa  sosai sadiq ke sa mu wurin mahaifin shi da kakar shi iyah, ganin yan da iyah da nuraddeen ke kula da sadiq ya sa maijidda ɗaura mashi karan tsana duk da yake ƙaramin yaro, ƴan uwan shi na son shi amma ta hana su ma'amula da shi, ko wasa suke ya zo wurin su sai ta sa su kore shi ko su dake shi,  tun basu ɗaukan abun da take sa su har hakan yayi ta siri da sadiq ya shiga cikin su zasu yi ta kyarar shi da hantarar shi, haka zai raɓe yana kuka ta kuma ja mashi kunne akan muddin ya faɗa ma nuraddeen sai tayi mashi dukan tsiya, bawan Allah haka zai shiru bai taɓa faɗa ma mahaifin shi ba, wani munafuncin na maijidda idan a gaban nuraddeen sai ta nuna tana tausayi sadiq tayi ta riritashi amma idan nuraddeen baya gida wahala iri-iri babu wacce bata sa sadiq har aiki wanda ya fi ƙarfin shi sa shi take yi lokacin yana da shekara shidda  amma sai ta sashi abun da ya fi ƙarfin shi,lokacin ta ƙara haihuwa yaron na da shekara ɗaya a duniya, sunan yaron Ibrahim kyankyawa ne dan yafi su  magaji kyau shiyyasa ita ma tafi son shi a cikin su,   haka rayuwa ta cigaba da tafiya sadiq ya taso cikin ƙiyayyar yan uwan shi, kwata kwata baya jin daɗin zama da su, sauƙin shi ɗaya idan mahaifin shi na gida ko kuma yaje gidan iyah ko su magaji na makaranta daya ke ba makarantar su ɗaya ba ta nan kawai ya ke samun sauƙin  wahalar da yake sha ta su magaji dan har tafi wacce yake sha wurin maijidda, wurin iyah ya koma da zama dalilin wani bugu da su magaji suka yi mashi har suka ji mashi ciwo, daya je gidan iya ya faɗa mata har gida tazo ta samu maijidda tayi mata zagin wulaƙanci akan ita ta sa su magaji su ka daki sadiq, haƙuri ta shiga bama iyah ta na cewa "kiyi haƙuri dan Allah iyah, wallahi sadiq ƙarya ya ke faɗuwa yayi amma ba dukan shi su magaji suka yi ba " ji suka yi an ce "wayyayi iyah cu yaya ne cuka buge ci" Ibrahim da ke tsaye bayan maijidda ne yayi maganar lokacin yana da shikara uku, maijidda kamar ta nutse saboda baƙin cikin abun da Ibrahim ya ce yaro ne amma sai wayen tsiya,gashi  kuma bala'in son sadiq yake dan wani lokacin idan maijidda ko ƴan uwan shi suka daki sadiq nan zai zauna yana kuka da kuma mahaifin su ya dawo zai sanar da shi, murmushi iyah tayi tana faɗin "kaga ɗan albarka, dama na  san ƙarya kike,  da ma chan na lura ba son sadiq kike ba saboda kinga mahaifin shi ya fi son shi, idan bai fi son shi ba ya ki ke  so yayi yaron nan ana haihuwar shi mahaifiyar shi ta rasu  to dan mi mahaifin shi bazai nuna mashi kulawa ba, amma kinbi kin tsani yaro kin ɗaura mashi karan tsana kin hanashi wasa da ƴan uwan shi kin sa sun tsane shi saboda tsabar zalunci, to bari kiji wallahi ki shiga hankalin ki in ba haka ba zakiyi mamakin abun da zanyi maki shashasha kawai" tana gama faɗa ta ja hannun sadiq suka koma gidan ta, haka rayuwa ta cigaba da tafiya sadiq  na hannun iya har ya kusa  gama primary school,  yan primary  5 lokacin magaji ya kammala secondary yana bin mahaifin su kasuwa ,  uwani na ss1 halimatu na jss 3 Ibrahim kuma na primary 2 Allah yayi ma iyah rasuwa sosai sadiq ya shiga tashin hankali mara misltowa ya ci kuka kamar ranshi zai fita ana bashi haƙuri, bayan an gama zaman makokin iya sadiq ya koma gidan mahaifin shi da zama, sadiq ya ga rayuwa, wahalar maijidda  yake ci sosai ba kaɗan ba  ita da uwani, saboda magaji tun da ya girma ya watsar da huɗubar mahaifiyar shi ya kama ɗan uwan shi ganin magaji yana son sadiq yanzu yasa halimatu ita ma take janshi a jiki dama shi Ibrahim baya da matsala tuna farko, uwani ce dai dama can ita bata da mutunci  sak halin maijidda gare ta, sosai sadiq ke shan wahalar ta kai sai ayi rabon abinci a manta da shi sai  dai halimatu da Ibrahim su bashi nasu a ɓoye dan idan maijidda ta sani dukan tsiya take masu shi daman magaji baya gidan yana kasuwa tare da mahaifin shi, haka rayuwar sadiq ta cigaba da tafiya kamar mara galihu mara gata, shi da gidan mahaifin shi amma bashi da sakewa  sai in mahaifin shi da yayan shi magaji na gida,  wata rana wani aminin  nuraddeen alhaji abdulƙadir wanda suka taso tun ƙuruciya,lagos yake tun bayan rasuwar iyayen shi ya koma wurin ƙanin baban shi da zama acan yayi karatun shi ko da ƙanin mahaifin nashi ya rasu bai dawo kurfi ba a lagos ya cigaba da zama , duk da yana lagos nuraddeen na kurfi tare suke  harkar kasuwanci , sai dai shi alhaji abdulƙadir yana zuwa har  ƙasashen waje ,alhaji abdulƙadir yafi nuraddeen ƙuɗi nesa ba kusa ba,   matar shi ɗaya hajiya zainab balarabiyar ƙasar  Morocco  ce, sun haɗu ne a chan ƙasar har Allah yasa suka  yi aure, shekarar su kusan goma amma basu da ɗa ko ɗaya, zainab  tana haihuwa amma ƴaƴan basu zuwa da rai,   ko da ya  kawo ma nuraddeen ziyara bai nufi kasuwa ba gidan shi ya nufa direct , nan ya ci karo da sadiq bakin ƙofar gida yana kuka,dafa kafaɗar sadiq alhaji abdulƙadir yayi yana cewa "yaro yaya sunan ka? " cikin shashekar kuka sadiq yace "sunana sadiq "
"masha Allah, amma miyasa kake kuka, ina mahaifin ka? "sadiq ya ce
"bakomi, babana yana kasuwa"
"to ko zaka iya rakani wurin shi? " da to sadiq ya amsa mashi, har kasuwa ya raka shi wurin nuraddeen, sosai nuraddeen yayi farin ciki da ganin alhaji abdulƙadir dan sun ɗan dade basu haɗu ba, gida suka koma, nan suka shiga firar yaushe gamo, anan alhaji abdulƙadir ya nuna yana son ya tafi da sadiq logas ,ƙin amincewa nuraddeen yayi, saboda ba ƙaramin son sadiq yake ba baiso ko kaɗan yayi nesa dashi, ko da ya shiga gida fuskar shi da ɗan damuwa, tambayar shi  maijidda tayi akan mike da munshi, nan yake faɗa mata "wallahi wani aminina ne yazo, to shine ya buƙaci da na bashi sadiq, to gaskiya gani nake kamar zai ƙara ma kan shi wahala ne, dan nafi shi rufin asiri ne sa ba kusa ba, to abunda ya sa ki gannin ciki da muwa ban so yaga kamar na hanashi sadiq ne saboda ni Allah ya bani , da yake shi bai da ɗa ko ɗaya " wani da ɗi ne ya rufe  maijidda tana ganin wannan ce hanya mafi sauƙi da zata raba sadiq da nuraddeen, kuma da taji mutumin talaka ne abun ya ƙara mata daɗi sai dai  bata ji daɗin ƙin amincewa da nuraddeen yayi ba , ta so ace ya ba da sadiq ɗin ko dan ta huta da ganin shi, kuma tana ganin idan sadiq ya tafi daga nan nuraddeen bashi da wanda zai so sai ƴaƴanta, haka ta shiga zuga nuraddeen akan ya ba abdulƙadir sadiq, ita duk a tuna nin ta da gaske  abdulƙadir talaka ne bai da komi,dan bai faɗa mata Abdulƙadir bane dan ta san Abdulƙadir sosai rashin faɗa mata ko waye yasa  tai ta zuga nuraddeen,kallon ta kawai nuraddeen yake, dama yace mata aminin shi ne kuma   talaka ne dan yaga mizatayi yayi ne daman dan ya gwada ta, sai kuma yaga farin cikin ta,  hakan ya ƙara tabbatar mashi da cewa da gaske maijidda bata son sadiq ko ƙaɗan,  ko da magaji yaji labari shima haɗa mahaifin shi  da Allah yayi akan ya bari a tafi da sadiq ko ba komai zai samu kwanciyar hankali, sai daga baya shima nuraddeen da yayi tunani yaga da cewar ya ba abdulƙadir sadiq, ko dan shima sadiq ɗin ya huta da tsangwamar da maijidda keyi mashi ,  dan abdulƙadir mutumne mai mutunci, yana da kirki sosai kuma zai ruƙe sadiq kamar ɗan daya haifa,ya san kuma rayuwar sadiq zata chanza, har masauki ya samu abdulƙadir   ya faɗa mashi ya amince zai bashi sadiq, ba ƙaramin daɗi abdulƙadir yaji ba ya kuma yima nuraddeen godiya sosai, sannan yace ya shirya sadiq ɗin gobe da man zai koma lagos da safe , sunjima suna fira har kusan yamma sannan nuraddeen yayi mashi sallama, yana komawa gida yasa halimatu ta haɗa kayan sadiq cikin jaka, Ibrahim sai kuka yake za'a tai mashi da ɗan uwan shi wani wuri, lallashin shi sadiq yake amma ya ƙi haƙura, ita kuwa maijidda sai jin daɗi take sadiq zai shiga cikin wahala.

Washe gari da safe wurin ƙarfe  takwas abdulƙadir yazo domin tafiya da sadiq, halimatu ce ta fito da kayan sadiq har ƙofar gida, amsar jakar  drivern abdulƙadir yayi da ga hannun halimatu ya sa a bayan mota , nuraddeen ne da abdulƙadir suka fito magaji na riƙe da hannun sadiq, bankwana abdulƙadir yayi ma nuraddeen sannan ya ja hannun sadiq suka shiga mota, sadiq na ta ɗaga ma magaji da Ibrahim da halimatu hannu, suma suna ɗaga mashi hannun har motar ta bar anguwar,kasuwa nuraddeen da magaji suka wuce halimatu da Ibrahim kuma suka koma gida, abdulƙadir koda ya kai ma matar shi sadiq, sosai tayi murna kuma ta karɓi sadiq hannu bi biyu, gata da kulawa sadiq ke samu wurin abdulƙadir da hajiya zainab, abdulƙadir ya saka sadiq makaranta,sai dai makarantar basu sa shi ajin daya tsaya ba ya fara ne daga primary 4, kuma kamar yan da ya faɗa duk akayi hutu sadiq na zuwa kurfi,  zuwan shi na farko kurfi maijidda kamar tayi huka dan baƙin ciki ganin yanda sadiq ya koma, yayi kyau yayi fresh hasken shi ya ƙara fitowa, tayi data sannin sa baki nuraddeen ya bada sadiq, nan ta nace akan idan sadiq zai koma lagos sai ya tafi da Ibrahim, sosai nuraddeen ya ci mata mutunci ya kuma ce shi ba mutumin banza bane, sadiq abdulƙadir yace yana so to dan haka bazai tura Ibrahim ba, bala'i sosai maijidda tai ta yi akan wai nuraddeen ya nuna ya fi son sadiq shiyyasa da abdulƙadir yace ya bashi shi ya ɗauka ya bashi,kullum cikin  ɗaga ma nuraddeen  hankali maijidda take har sadiq ya gama hutun shi ya koma, shekarar sadiq ɗaya a lagos  Allah ya azurta zainab da samun ciki, zo kaga murna da farin ciki wurin zainab da abdulƙadir  sadiq ma sai murna yake za'a haifa mashi ƙani ko ƙanwa, daya dawo daga school zai tasa zainab gaba yana faɗin ummy  yaushe zaki haifa man ƙani, wani lokacin idan yayi mata tambayar sai dai tayi dariya, cikin zainab na shiga watan haihuwa, ta matsa ma abdulƙadir akan dole sai ya kaita Morocco ta haihu acan, ba dan ya so ba ya kaita, sadiq ma yasa rigima akan dole sai ya bita, haka abdulƙadir yayi masu visa yakai su shi kuma ya dawo, satin zainab ɗaya a morocco ta haifi ɗiyar ta kyakyawa mai kama da ita,ba'ayi suna a morocco ba suka dawo nigeria, da sati ya zagayo  yarinya ta ci sunan mahaifiyar zainab watau Aisha, har lagos  nuraddeen yazo ranar sunan aisha, sosai sadiq  yayi murna da ganin mahaifin shi, da nuraddeen ya tashi tafiya maƙale mashi sadiq yayi akan sai ya bishi, zainab tasa ƙanwarta wacce suka zo tare da ga morocco ta haɗa ma sadiq kayan shi da zai bi nuraddeen...
Episode  50_51_

Koda nuraddeen ya koma da sadiq kurfi,  bala'i maijidda ta tada akan dole sai sadiq ya dawo kurfi da zama tun da daman dan abdulƙadir bai da ɗa ko ƴa yasa aka bashi sadiq to tun da yan zu  matarshi ta haihu sai sadiq ya dawo gida, sai da nuraddeen ya biyo mata ta bayan gida sannan ta kama kanta, sadiq bai gama hutun ba nuraddeen ya haɗa mashi kayan shi ya mai da shi lagos , a kwana a tashi asarar rai sadiq ya kammala secondry school lokacin aisha na da shekara bakwai a duniya,a lokacin tana primary 4, daya ke tun tana 4 year alhaji abdulƙadir ya sata makaranta, akwai soyayya da shaƙuwa tsakanin sadiq da aisha bacci kawai ke raba su, ko wane lokaci zaka same su suna tare da juna, musamman da yanzu sadiq yake zaune a gida yana hutu kafin ya fara zuwa jami'a, da sadiq zai tafi kurfi  kuka aisha ta sa  a dole sai ta bishi  hajiya zainab da sadiq su kaita lallashinta sadiq yayi mata alƙawarin idan zai koma bikin su halimatu zai tafi da ita  sannan ta haƙura,ko da sadiq yaje kurfi anan yake samun labarin rasuwar kakar shi wacce ta haifi ruma, yayi kuka sosai dan ba ƙaramin son tsohuwar ya ke ba saboda ita ma tana son shi,hutu na ƙarewa ya koma lagos , bai wani jima da dawowa ba ya fara zuwa school,kullum kafin ya tafi school sai ya fara ajiye aisha a school sannan yake wuce wa , da zai fara zuwa jami'a mota abdulƙadir ya siya mashi,  idan an tashe su kuwa  driver ke  ɗauko ta  ranar da bashi da lectures kuwa shi ke kaita ya ɗauko ta, haka rayuwa taci gaba da tafiya an tsaida ranar bikin su uwani ita da halimatu, bikin su na saura sati ɗaya sadiq ya shirya zai tafi kurfi maƙalewa  aisha tayi sai ta bi shi, shirya mata kayanta hajiya zainab tayi suka tafi,suna isa kurfi da Ibrahim suka ci karo zaune ƙofar gida shida abokan shi, yana ganin su ya taso da fara'a a fuskar shi yana ma sadiq barka da zuwa yayin da yake amsar jakar kayan da ke hannun shi, gaishe da shi aisha tayi, ya amsa mata da fara'a yana ce ma sadiq su shiga ciki, gidan suka nufa, suna shiga halimatu na zaune kan kujera yar tsugunno tana wanke wanke, tasowa tayi da sauri tana ma su barka da zuwa suna nan tsaye maijidda ta fito daga kitchen hannun ta riƙe da kwano, wurin su ta ƙaraso tana bin aisha da ido, sadiq ya ce "ina wuni innah, mun same ku lafiya " daga mashi kai kawai tayi tana tambayar wannan fah, sadiq ya bata amsa da aisha ce ƙanwata, fuska a ya mutse tana kallon aisha ta ce"ba shakka, sannu ko " duƙara da kai aisha tayi tana cewa ina wuni da lafiya lau maijidda ta amsa sai kuma tace" yasu mamar ki kun baro su lafiya" da fara'a aisha tace" lafiya lau suke suna gaishe da ku"
"muna amsawa "maijidda ta faɗa sannan tace ma halimatu " ki kaita ɗakin ku,  kunyi tsaye "tana gama faɗa ta juya ta nufi ɗakin ta, da kallo suka bita fuskar su da mamaki dan ba su taɓa tunanin zata yima aisha ko kallon arziƙi, kayan ta da ke hannun sadiq halimatu ta amsa haɗi da jan hannun ta suka nufi ɗakin su, sadiq ma ɗakin su suka nufa shida Ibrahim yana tambayar shi ina su baba da magaji
sai da yamma magaji suka dawo daga kasuwa shida nuraddeen, sosai magaji yaji daɗin ganin sadiq hakama nuraddeen yayi farin ciki sosai musamman da yaga aisha, kulawa sosai aisha ke samu wurin dangin sadiq mu samman halimatu dan ta ɗauki aisha kamar ƙanwarta, uwani ce kawai ba ruwan ta da aisha amma har maijidda na jan ta a jiki,  abun ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, ana  gobe ɗaurin aure gida ya cika da baƙi  alhaji abdulƙadir yazo shida hajiya zainab, tarba mai kyau suka samu wurin nuraddeen da maijidda, washe gari aka ɗaura aure aka kai amare gidajen mazajen su aisha gidan halimatu ta kwana, sai washe gari ta dawo gidan su sadiq saboda ranar zasu  koma lagos harda sadiq, da zasu tafi kiran sadiq maijidda tayi ɗakin ta akan mizai hana su tafi tare da Ibrahim tun da ya kusa gama makaranta, haƙuri sadiq ya bata yana cewa ko jiya yayi ma baban su maganar yana so su tafi tare da Ibrahim amma yace bai amince ba, haushi kamar ya kashe maijidda, gani take nuraddeen baya son ƴaƴan ta sadiq kaɗai yake so, kwantar da murya tayi tana cewa "kana jina sadiq ka rabu da maganr baban ku, da kace ma alhaji abdulƙadir kana son tafiya da ɗan uwanka nasan zai amince "maganar nuraddeen suka ji daga bayan su yana cewa "to wallahi ban amince ba , idan har kana son zaman lafiya da ni kar na sake naji kayima abdulƙadir wannan maganar kaji na faɗa maka "maijidda ta ce" wai miyasa kake haka ne, yaro na son tafiya da ɗan uwan shi amma ka hana haba dan Allah "ko kallon inda take bai yi ba yace ma sadiq "kama hanya ka wuce suna waje suna jiran ka "da to sadiq ya amsa yana ma maijidda ban kwana, Allah ya tsare kawai tace tana bin nuraddeen da kallo da zai fita, har ƙofar gida nuraddeen ya samu su sadiq yayi ma abdulƙadir ban kwana  dayi mashi godiya, da motar su zata bar anguwar  Ibrahim harda kukan shi, sannu sannu bata hana  kaiwa sai dai ajima ba'a kai ba magaji ma yayi aure lokacin halimatu da uwani na da ƴaƴa ɗai ɗai uwani na da namiji mai suna usman halimatu kuma mace sunan ta zainab.

soyayya ce ta ƙullu tsakanin sadiq da aisha hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma abdulƙadir da nuraddeen ba,  dama basu da wani buri daya wuce haka, zainab abun yayi mata daɗi dan baƙaramin so take yima sadiq ba tamkar ɗan cikin ta haka take jinshi.
da sadiq ya kammala degree ɗinshi,kullum suna tare da aisha dan har binta yake makaranta,  alhaji abdulƙadir ya ɗaura sadiq kan kasuwanci kafin ya fara aiki, sai da sadiq yayi kusan shekara ɗaya da rabi yana gudanar da kasuwanci sannan alhaji abdulƙadir ya sama mashi aiki a Abuja duk da sadiq ɗin yaso yayi a lagos saboda kwata kwata baya son abun da zai sa yayi nisa da aisha, da zai tafi kuwa aisha har da kuka  abun ma mamaki ya ba ma hajiya zainab,sadiq bai daɗe da fara aiki ba nuraddeen da abdulƙadir suka tsaida ranar auren su da aisha akan da  ta kammala makaranta za'a yi bikin,  hakan ce ta faru aisha na kammala makaranta aka fara shirye shiryen biki,ana saura wata ɗaya ƙanwar zainab tazo daga Morocco ta tafi da aisha, chan za suyi mata gyaran jiki sai ana saura sati za su dawo da ita,  ana saura  sati ɗaya bikin Aisha  ta dawo daga Morocco ita da yan uwan hajiya zainab , gida ya cika da baƙi aka fara shirye shirye an je anyi ma aisha jere gidan sadiq, shagali sosai alhaji abdulƙadir ya shirya haka ma nuraddeen ba'a barshi a baya ba, ana saura kwana uku yan kurfi suka zo part guda alhaji Abdulƙadir ya ware ma Nuraddeen ya ajiye duk wani baƙo daya zo mashi da yan uwan shi, maijidda kuwa ita da su uwani da yaran su suna part ɗin hajiya zainab , ranar juma'a aka ɗaura auren Abubakar Nuraddeen Ahamad Sharani da amaryar shi Aisha  Abdulƙadir  murna wurin ango da amarya ba'a cewa komai.
da yamma Alhaji abdulƙadir da nuraddeen suka haɗa aisha da sadiq su kayi masu nasiha,sannan suka je wurin hajiya zainab,nasiha sosai tayi masu da fatan alkairi,  aisha na kuka ƙannan hajiya zainab suka yi mata rakiya zuwa gidan mijinta, ranar lahadi yan uwa da abokan arziƙi suka fara tafiya , ƴan kurfi kuma washe gari zasu tafi litinin kenan , da yamma maijidda tasa  aka kira mata sadiq ta sake mashi maganar Ibrahim, cemata sadiq yayi "innah baba ya hana, ina kuma tsoron abun da zai biyo baya idan nace dole sai Ibrahim ya tsaya"bal bale shi da masifa maijidda tayi,  wai bai son zumunci dan yaga Allah ya ɗaukaka shi shine zai fara ƙyamar ɗan uwan shi,abun yayi mugun bama sadiq mamaki, bai taɓa tuna nin Innah za tace mashi haka ba arayuwa, haƙuri kawai ya bata, washe gari da safe sadiq yaje gidan alhaji abdulƙadir domin gaisawa da su ya kuma  yima su nuraddeen rakiya saboda da safen zasu tafi, koda ya gaishe da nuraddeen bai san miya faru kawai nuraddeen ya rufe shi da faɗa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba yana cewa "kenan ni ban isa na hana ka abu ka hanu ba ko "
haƙuri sadiq ya shiga bashi batare da yasan miya aikata ma mahaifin nashi ba, sai da zasu tafi halimatu ke bashi haƙuri haɗi da faɗa mashi abun da ya faru, wai ashe lokacin da ya bar ɗakin da maijidda ta sauka, fita tayi daga ɗakin taje har ɗakin hajiya zainab ta roƙe ta akan dan Allah tunda sadiq da aisha basu gidan yanzu za su ji duk ba daɗi mizai hana Ibrahim ya dawo gidan da zama,shine hajiya zainab ta sami alhaji abdulƙadir da maganar shiku ya samu nuraddeen akan dan Allah ya bar mashi Ibrahim ɗin, nuraddeen yayi tuna nin sadiq ne ya faɗama abdulƙadir ɗin shine ya rufe shi da faɗa, koda halimatu tagama faɗama sadiq bai ji daɗin abunda Innah tayi ba yaso ace ta bari ya lallaɓa baban nasu harya amince, amma ta ɓata mashi komai gashi baban yayi fushi da shi, kafin su wuce sai da  sadiq ya sake bama nuraddeen haƙuri,ya haƙura amma akan da Ibrahim zasu tafi daga baya sai ya dawo amma ina abdulƙadir yaƙi amincewa , ba yanda nuraddeen ya iya dole ya bar Ibrahim, maijidda daɗi kamar ya kashe ta,  nuraddeen na lure da ita bai dai ce komai ba,sai da suka isa kurfi yayi mata tatas dan ya san ita zata sa sadiq duk shirin ta ne, nunawa tayi ko a jikin ta burinta dama Ibrahim  ya zauna a lagos to burinta ya cika komi zai ce bawai zai dameta bane, watan  sadiq da aisha ɗaya  dayin aure suka wuce abuja aka bar Ibrahim a lagos saboda makaranta da ya ke zuwa, cikin ƙan ƙanin lokaci Ibrahim ya goge ya zama ɗan gayu,saboda ba ƙarmin kulawa yake samu daga wurin su hajiya zainab ba,sadiq watan su bakwai a abuja  ya nema aisha  admission ta fara zuwa makaranta, idan zai tafi aiki tare suke fita ya ajiyeta a makaranta ranar da take da lectures ɗin yamma kuma ya ɗauko ta, mota ya siya mata ranar da take ra'ayin driving da kanta sai taje da kanta ta dawo da kanta , akwana a tashi aisha har ta kai aji uku a jami'a matar magaji ta haihu ta haifi ɗa namiji  kyakyawan gaske sunan yaron mansoor lokacin Aisha tana ɗuke da ciki na tsawan wata biyar,  sosai take samun kulawa daga mijin ta da cikin ya isa haihuwa lokacin suna hutu zasu shiga aji huɗu, hakan ya sa sadiq ya ɗauki hutu wurin aiki suka tafi lagos dan ta haihu a can, cikin yardar ubangiji da komawar su ba da jimawa ba Allah ya sauketa ta samu ɗa namiji kyakyawan gaske mai matuƙar kama da ita, murna wurin sadiq ba'a cewa komai, hakama iyayen aisha da ƴan kurfi sunyi matuƙar farin ciki, da sati ya zagayo, yaro ya ci sunan Alhaji Abdulƙadir   suna kiran shi da {shazim} malam yayi matuƙar farin ciki da wannan takwara da sadiq yayi mashi,haka ma aisha taji daɗi sosai,kulawa sosai take samu wurin ummy, da tayi arba'in suka tafi kurfi ita da sadiq,Ibrahim ya so su tafi tare da shi amma makaranta ta hana saboda yana shekarar ƙarshe a jami'a,  sun samu tarba ta musamman daga wurin maijidda haka ma magaji da nuraddeen   hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma sadiq ba, matar magaji kuwa komawa su kayi tamkar ƙawaye ita da aisha, yaron ta mansoor shekarar shi ɗaya da rabi a duniya, kafin su ka koma lagos Aisha  sai da ta zaga gidajen ƴan uwan sadiq, ta kuma je gidan uwani da halimatu, suna komawa lagos basu jima ba suka wuce abuja , haka rayuwa ta cigaba da tafiya Ibrahim ya gama makaranta, sadiq yace ya dawo abuja yayi masters,  shazim ya taso cikin kulawa da soyayyar iyayen shi da dangin shi musamman Ibrahim duk abunda ya siya zai ce na Shazim ne, haka ya taso cikin kulawa da gata,da shazim ya isa yaye lagos suka kai shi wurin ummy, har sai da yayi shekara ɗaya a lagos lokacin yayi wayau sosai, ya iya tafiya ga surutu, haka zaka same shi ya tasa hajiya zainab gaba da surutu abu kaɗan yace ummy { da yake shima haka yake kiran ta saboda yaji ammyn shi na kiran ta da haka}

*_WANNAN  KENAN_*


 Ibrahim ya fara zuwa makaranta Aisha  kuma na shekarar ƙarshe, shazim nada shekara uku a duniya sadiq ya ajiye aiki ya kama kasuwanci gadan gadan riba sosai yake samu, cikin ƙanƙanin lokaci ya zama attajirin gaske ya buɗe  katafaren  company da yake sarrafa kayan masarufi musamman shinka fa, kasuwancin shi na ta haɓaka ,  ɗaura  Ibrahim yayi kan wasu harkokin kasuwancin yana kula mashi da su, gida ya gina mai girman gaske ya kuma biya ma baba, innah,  malam,  ummy makka , sai shi da aisha, farin ciki wurin su ba'a cewa komai ya sha adu'a wurin su, kafin ya tafi ya tare a sabon gidan da ya gina, da zasu tafi ya ce ma magaji ya dawo Abuja  da zama shida matar shi da  ƴaƴan shi ,   da ma gidan da ya gina yayi shine saboda su, magaji yayi godiya sosai ya kuma tattara komai nashi dake kurfi suka dawo abuja shi da  matar shi asiya, sunje sun sauke farali,  a abuja su ka sauka da ma ta nan suka tafi, sai da malam su kayi  sati shi da ummy sannan suka wuce lagos, baba kuwa da innah nan zasu zauna part ɗin su da ban, har da ibrahim da baiyi aure ba part ɗinsa da ban , innah sai nan nan take da sadiq ta ɗauki son duniya ta ɗaura mashi tun bai sakin jiki da kulawar da take nuna mashi har ya fara sakin jiki,  abun ba ƙaramin ba nuraddeen mamaki yake ba, yan da ta sauya. 

Shekarar shazim 5  sadiq ya sa shi makaranta shi da mansoor  aisha ta sake haihuwar ɗa namijin mai matuƙar kama da sadiq, sosai sadiq ya yi murna haɗi da gode ma Allah da kyautar daya bashi, ranar suna yaro yaci sunan baba watau nuraddeen suna kiran shi da { noraiz}  baba yaji daɗi,satin noraiz uku da haihuwa asiya ta haihu ita ma ɗa namiji sunan shi mahmud,  Ibrahim ya samu mata yayi aure sunan matar turai, yar kano ce amma iyayen ta anan abuja suke da zama, shekarar ta ɗaya ta haifi ɗa namiji mai suna luqman lokacin noraiz da mahmund nada shekara ɗaya da kusan rabi,  shazim shidda mansoor  bakwai faisala ukku ƙanin mansoor, wani abun mamaki tun da matar Ibrahim ta haihu innah ta ɗauki karan tsana ta ɗaurawa aisha da asiya  kamar sunyi mata wani laifi, duk da wannan chanji da take nuna masu hakan bai hana su kyautata mata ba, kuma kan su haɗe yake dan matar Ibrahim ba ruwanta hakama yaran su kansu haɗe yake ko wane lokaci suna tare da juna musamman shazim da mansoor dan ko school tare zaka gansu da ƙanansu faisal da yake ansa shi makaranta shi ma , noraiz ne dai da luqman sai mahmud  ba'a kai da sa su ba , sai daga baya aka sa noraiz , luqman da mahmud   makaranta, shazim da mansoor kullum sun part ɗin baba kakansu wani lokacin har da su noraiz kullum haka suke in basu part ɗin baba suna part ɗin papah { sadiq} ko hutu shazim zai je lagos tare suke zuwa shida su mansoor luqman ne dai bai taɓa zuwa ba.

_*WANNAN KENAN*_. 

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau daÉ—i gobe akasin haka
sadiq ganin duk abokan shi sun tsunduma a cikin siyasa ne ya shi samu baba da batun yana so ya shiga shiyasa ƙin amincewa baba yayi hakan yasa abokan sadiq su kayi zuga suka zo wurin baba dan su roƙe shi akan ya bar sadiq, ai kuwa faɗa sosai baba yayi ma sadiq ya ce kenan dama su suka hure mashi kunne ya ke son  shiga shiyasa,dole ta sa sadiq haƙura ganin baba yayi fushi sosai, lagos yaje ya sanar da malam abun da ke faruwa, hakan ya sa malam wanke ƙafa yazo har abuja wurin nuraddeen, tattaunawa suka yi malam kuma ya roƙe shi akan ya bar sadiq ɗin, ba dan hakan ya kwanta ma baba arai ba ya amince,sosai sadiq yaji daɗi, da  matakin ɗan majalissa ya fara ,cikin ikwan Allah ya samu,shekarar su uku da fara mulki ya ida ginin estate ɗin daya fara  opposite da gidan shi, suna gab da sauka daga mulki  da jam'iyar su zata tsaida  ɗan takarar shugaban ƙasa suka tsaida shi, ƙin amincewa yayi dan shi baya da burin yin muƙami mai girma irin wannan,matsa mashi suka yi ba dan ya so ba yace "to shikenan,  amma sai yayi shawara da iyayen shi, duk abun da suka ce da shi zaiyi amfani ", ko da ya samu malam da baba da maganar  cewa suka yi yayi haƙuri ya yi, ai abu ne mai kyau in sha Allah zasu taya shi da adu'a, yaji daɗin hakan da suka ce ya kuma samu ƙwarin gwiwa, cikin ikwan Allah ana zaɓe sadiq ya samu,daya ci zaɓe sai Ibrahim da magaji suka koma estate da zama,sadiq ya so  malam ya dawo abuja da zama lokacin daya zo yi mashi fatan alkairi daya ci zaɓe amma ƙiri ƙiri malam ya ƙi amincewa, baba ma da farko cewa yayi sadiq ya bar shi anan gidan shi amma sadiq ya ce a'a ya fi so ya zauna tare da shi yanda zai riƙa bashi shawara, sadiq ya fara mulkin shi cikin adalci mutane na jin daɗin mulkin shi,aiki ya nema ma Ibrahim da magaji dan tun dawowar shi abuja sadiq ya ne ma mashi admission ya jona karatu sai dai iya kar shi degree  saɓanin Ibrahim da ke da master's  ,business ɗin shi kuwa ya ɗaura wani aminin shi  daya ke da amana,  lokacin daya kusa gama zagayen farko na mulkin shi , Allah yayi ma nuraddeen rasuwa mutuwar da ta girgiza ahalin ga ba ɗaya musamman sadiq ya fi kowa fita hayyacin shi, sun shiga alhinin mutawar nuraddeen kamar mi, malam yaji mutawar aminin shi kamar mi, lokacin da aka yi  adu'ar bakwai maijidda tace zata koma estate da zama wurin su magaji, ba yanda sadiq bai yi da ita ba amma ta ƙi zama ko da takaba ta gama amma ina  ba dan ya so ba ya sa aka kaita, time ɗin da akayi arba'in ɗin nuraddeen matar Ibrahim ta sake  haihuwa ta samu ɗiya mace kyakyawa mai suna hawa'u innah kenan suna kiranta da feenah,innah taji daɗi da Ibrahim yayi mata ta kwara ai kuwa ta ɗauki son duniya ta ɗaurawa feenah,bayan haihuwar feenah da sati biyu asiya ma ta haihu, ita ma ɗiya mace ta haifa  mai suna kairiyya,   watan nuraddeen tara da rasuwa za'a sake  sabon zaɓe sadiq ya bar gidan gomnati  ya koma gidan shi inda ya fara zama, awannan zaman ana saura sati ɗaya zaɓe Allah yayi mashi rasuwa, ta dalilin haɗarin mota, sunje wani ƙyauye ne a hanyar su ta dawowa su kayi haɗari wasu a nan take suka mutu sadiq kuma sai da yayi jinyar kwana biyu sannan Allah yayi mashi rasuwa ,mutawar sadiq ta girgiza dan gin shi kamar mi, aisha ta shiga tashin hankali mara misltowa da rasuwar sadiq hakama ƴaƴan ta sunci kuka kamar ransu zai fita duk da bawani wayaune da su ba sosai har dama dama shazim, kusan zaucewa aisha tayi, malam ma ya shiga  alhini wanda ya fi na lokacin mutuwar nuraddeen , ummy taci kuka kamar mi dan ba ƙaramin son sadiq take ba tana mashi kallon babban ɗanta.


A estate akayi zaman makokin shi har aka yi kwana bakwai,  laulayin ciki Aisha ta fara na tsawan wata biyu sai bayan rasuwar sadiq cikin ya bayyana , ta sha kuka kamar ranta zai fita, tana tausayin abun da zata hai fa zai taso batare da ya san waye mahaifin shi ba, ko da maijidda taji labarin cikin aisha baƙin ciki kamar ya kashe ta,  ta fara nuna ma aisha tsana da tsangwa ma, hakan ne ya sa aisha ta ce zata koma lagos da zama, amma si malam da ummy suka ce ta bari ta gama takaba sannan, haka ta haƙura har ta kammala takaba, amma da zata tafi sai Ibrahim da magaji suka roƙeta akan dan Allah ta zauna har sai ta haihu sannan saita koma lagos ɗin, hakanan ta haƙura ta zauna ba dan ta so ba, dan kwata kwata yanzu bata jin daɗin zama da innah, ta ware ta  su asiya kawai take  so su da ƴaƴan su ta ɗauki karan tsana ta ɗaurama su Shazim ba hali su shiga cikin ƴan uwan su ko su je part ɗin ta tafara kyarar su kenan da hantarar su, ta kuma sa su mansoor tsanar su babu hali su raɓu da juna, tun abun bai damun Aisha  har ya koma yana damun ta, har ta kai da samun innah dan ta bata haƙuri ko tayi mata laifi ne batare da sanin ta ba , amma sai innah ta rufe ta da masifa wai tayi mata rashin kunya, haƙuri kawai aisha ta bata, lokaci ya shuɗe har cikin aisha ya shiga watan haihuwa, a lokacin ma ta so ta koma lagos ta haihu a chan amma ƙiri ƙiri innah ta ce bata isa ba sai dai ta tsaya ta haihu a nan in ya so daga baya bayan ta yaye abun da ta haifa sai ta tafi tabar masu ƴaƴan su, maganar innah ta girgiza Aisha  ba kaɗan ba tun tana boye ma malam da ummy irin zaman da suke yi ita da innah har ta kasa haƙuri ta kira ummy tana kuka ta zayyane mata duk abun da ke faruwa tun daga mutuwar sadiq har zuwa yanzu, abun yayi matuƙar ba ma ummy mamaki dan ita bata san halin innah ba kallon mutuniyar kirki take mata ashe ba haka take ba, ko da ta sanar da malam shima abun ya bashi mamaki dan bai taɓa tuna nin haka daga wurin ta ba, haƙuri suka bata akan tabi komi a sannu in sha Allah komi zai wuce kuma baza su bari a rabata da ƴaƴan ta ba, Ibrahim yana bata kulawa sosai , hakan ya sa ta kwantar da hankalin ta taciga da kula da ƴaƴan ta , shazim tun da ya lura  da innah bata son shi da mahaifiyar shi, kuma su mansoor ma basa son su yanzu   sai kawai ya yanke shawarar fita harkar kowa dake estate ɗin , ko part ɗin su ya dai na zuwa, da tare su ke  tafiya makaranta dasu mansoor amma ganin yan da suke takura mashi shi da  noraiz ya sa ya dai na tafiya tare da su, yasa ammy ta ba ɗaya daga cikin drivers ɗin gidan makullin motar ta yana kai su, abun yayi matuƙar bata ran  innah, ta tasa aisha da bala'i tana son raba zumunci, ta kuma amshe makullin motar daga hannun drivern,  ran shazim ya ɓaci da abun da innah tayi,  ai kuwa  har part ɗin ta yaje ya ɗauke key ɗin motar lokacin tana cikin toilet wanka su mansoor kuma na parlorn zaune  dama cikin drawer ta sa shi,innah na fitowa feenah ta faɗa mata shazim ya shigo mata ɗaki kuma ya ɗauki key,mamaki abun ya ba innah ba shiri ta fice sai part ɗin Aisha  tun daga bakin ƙofa ta fara masifa tana zage zage aisha na zaune kan kujera ita da mai aikin ta tana matsa mata ƙafafunta dake ciwo  ta ji haya niyar innah, ta na shirin tashi innah ta shigo ta hau bala'i tana zagin ammy, haƙuri ammy ta shiga bata dan bata san mi tayi mata ba, suna nan sai ga shazim ya shigo innah na ganin shi ta shaƙo wuyan rigar shi tana faɗin

" ɓarawon banza ɓarawon wofi,bani key ɗin da ka ɗauko ɗaki na munafuki"

gaban ammy ne ya faÉ—in jin abun da innah tace, shazim kuwa cike da masifa ya ce

"wallahi ni ba ɓarawo bane, kuma key bazan ba da  ba tun da ba naki bane "

suman tsaye ammy tayi jin rashin kunyar da shazim ke ma innah, mamaki da tsoro ne ya kama innah jin abun da shazim ya ce mata, yaron da ko yatsa kasa mashi a baki bazai tauna ba amma shine yau yake faɗa mata magana cike da rashin kunya, katse mata tunani yayi ta hanyar figewa daga riƙwan da tayi mashi ya nufi up stairs ya haye, bin shi kawai tayi da kallo har ya ɓace ma ganin ta, ammy tace
"dan Allah kiyi haƙuri innah zan amshi key ɗin na maido maki"

fashe wa da kuka innah tayi tana faÉ—in

"munafuka nasan ke zaki zuga shi yayi man rashin kunya, kuma wallahi ki sani dani kike magana"
tana gama faÉ—ar haka ta fice daga part É—in...

Episode  52_53_

Innah na fita ammy ta wuce bedroom ɗin ta, noraiz ne ya shigo yana kuka, har zai nufi ɗakin ammy sai ya fasa saboda maganar shazim daya ji yana ce mashi"lafiya kai kuma kake kuka,  waya dake ka ?  " cikin muryar kuka noraiz ya ce "su  ya mansoor ne da luqman " balbale shi da masifa shazim yayi danmi zai tsaya luqman ya dake shi bayan ƙaninshi ne, shiru noraiz yayi, tsaki shazim ya ja haɗi da cewa "suna ina? " noraiz ya bashi amsa da "part ɗin uncle Ibrahim  "    shazim bai ce komi ba ya kama hanyar fita daga part ɗin ya fice, yana fita part ɗin uncle Ibrahim ɗin ya nufa, luqman da feenah ka ɗai ya samu zaune a parlor suna kallo, bai yi wata wata ba ya hau luqman da duka sai da yayi mashi jina jina sannan ya kyale shi yana kuka,  feenah ce ta miƙe tana faɗin "ya shazim dan mi zaka dake shi" buge mata baki shazim yayi yana faɗin "rufe man baki koke ma na haɗa da ke " kuka ta kama yi tana faɗin Allah ya isa ban yafe ba kuma sai na faɗa ma dady da innah"

kwata kwata feenah bata da kunya ko ko ko alama, kuma hakan ya samo asali daga wurin innah saboda mugun son feenah take kamar mi, ita ta shagwaɓata, ta kuma zugata akan duk wanda ya dake ta tace bata yafe ba idan bazata iya ramawa ba, hakan ya sa ta taso a sangarce ga rashin kunya iri iri feenah ta iya ta , abu ƙaɗan tace innah ko faɗa dadyn ta yayi mata tana kuku zata faɗa ma innah, ita kuma tai ta bala'i,saɓanin kairiyya da ba ruwanta, kuma tana son su noraiz dan kusan kullum tana part ɗin ammy,ita ba ruwanta shiru shiru ce,   mari shazim ya   kaimata ta ruga da gudu tana kuka ta shige bedroom ɗin momyn ta,yazo fita yaci karo da mansoor da faisal zasu shigo part ɗin, cakumo wuyan rigar mansoor yayi, faɗa sosai ya kyaure tsakanin su har sai da momy {turai}  ta fito ta raba su,  mansoor na kuka saboda ciwan da shazim ya ji mashi, wuce wa shazim yayi zuwa part ɗin su, yana tura ƙofa yaci karo da ammy tsaye , "daga ina kake? " shine abun da ammy tace, shiru yayi bai bata amsa ba,jin yayi shiru ne yasa ta sake mashi tambayar,  shiru ya sake yi ,  saukar mari kawai yaji a kumatun shi, abun da ammy bata taɓayi mashi  ba, rufe shi tayi da faɗa sosai,tana gamawa ta juya,   yana dafe da kumatu yace "dan Allah ammy kiyi haƙuri " wuce wa tayi batare da ta kalli inda yake tsaye ba, binta yayi har ɗaki yana bata haƙuri sai da ƙyar tace ta yafe mashi kuma ya ɗauko key ɗin daya ɗauko ɗakin innah ya kawo mata,  da to ya amsa haɗi da ficewa ya bar ɗakin, key ɗin ya ɗauko ya bata, ƙarar buɗe main  ƙofa sukaji da ƙarfi, sai kuma hayaniya, fita ammy tayi zuwa parlor, innah suka gani ruƙe da hannun feenah  su luqman na bayanta tana ta zazzaga masifa,  uncle Ibrahim ne ke bata haƙuri yana faɗin
" dan Allah innah kiyi haƙuri"
"wlh ba zan haƙura ba, yan da ya dake su wlh sai na rama masu "
ammy ce tace "mike faruwa ne? "
tun kafin ya bata amsa innah tayi saurin cewa " munafuka annamimiya, kina iya cewa baki san mi wannan fitsararen É—an naki yayi ba, bayan ke kika sa shi munafuka kawai "
muryar shazim suka ji yana cewa "gaskiya innah ki dai na ce ma ammy na munafuka dan ba munafuncin da tayi maki, dukan noraiz su kayi ni kuma na rama mashi, kuma wlh suka ƙara dukan shi sai nayi masu mafiyin haka tun da ba jakin su bane "
tsawa uncle Ibrahim ya daka mashi yana cewa " kai baka da hankali ne shazim, innar kake faÉ—a ma wannan kalaman, kar na sake jin bakin ka "
innah tace "ai da ka barshi yayi man abun da uwar shi ta koya mashi, na san nan gaba har duka na tana iya sa shi tun da ba sona take ba"
uncle Ibrahim yace "kar Allah ya nuna mana hakan, dan Allah kiyi haƙuri ki koma part ɗin ki"
tasa ƙeyar su feenah tayi zuwa part ɗin ta tana tafiya tana zagin shazim,Aisha  tayi tsaye ta kasa ko motsi,
uncle Ibrahim ne yace "dan kiyi haƙuri da halin innah, karki sa abun a zuciyar ki kinga dai halin da kike ciki,ce mashi ta bakomi nagode haɗi da nufar part ɗin ta, faɗa tayi ma shazim har da duka, tana faɗin saboda zuwa makaranta yayi abokai marasa kunya shine zai zo gida yana ma manya rashin kunya, ta kuma gargaɗe shi kar ta sake jin yayi faɗa da wani cikin estate ɗin,
cemata yayi to, bawai dan hakan ya shigeshi ba, ya zame ma yaran gidan abun tsoro dan ko kallon da bai yi mashi  ba kayi mashi to zai hauka da duka ne ba ruwanshi, tun ammy na mashi faɗa har dai ta zuba mashi ido tana adu'a Allah ya shirya shi, dan komawa yayi mar kunyar ƙarfi da yaji har jira yake wani ya tsokane shi ko noraiz, dole tasa yaran tsoron shi.

Wata  rana wasu mutane suka zo da ga  hukumar efcc, har part ɗin ammy wai ana zargin marigayi Abubakar da satar kuɗin gomnati,dan haka ammy ta tattaro duk wani takardun dukiyar sadiq ta basu tun daga kan filaye har zuwa na company,  abun yayi matuƙar bama ammy mamaki haka ma su uncle Ibrahim,ai kuwa kaca kaca ammy tayi masu ta kuma ce "babu wanda ya isa yasa ta bada koda allura ce daga cikin dukiyar sadiq, mutumin da yake hukunta duk wanda aka samu da laifin sata shine zaku ƙullama wannan sharrin , kuma abun ta kaici bayan ba ranshi, wallahi Allah bazai bar kuba"
wani daga cikin mutanen ne yace " hajiya ki kwantar da hankalin ki, mu bamu zo dan rigima ba aikin mu kawai muke yi, muna so ki fito mana da duk wani takarda daya shafi Abubakar in ba haka ba zamu sa jami'ai su duba mana"
ammy ta ce" sai dai kuyi duk abun da zaku yi amma ni bazan ba ku komai ba, tun da na san ƙarya kuke munafuncin ne kawai "
ganin dai da gaske bazata yi masu abun da suke so ba ya sa suka miƙe suna faɗin " to shikenan tun da haka kika ce, Ibrahim mu zamu wuce, amma bawai hakan na nufin baza mu sake dawowa ba " suna gama faɗar haka suka fice da harara ammy ta raka su, har inda suka yi parking Ibrahim ya raka su sannan ya dawo part ɗin ammy, magana ya fara yi ma ammy yana cewa "ina so ki fahimce ni "
"ina sau raron ka "ɗan nisawa yayi sannan ya ce " ina so ki gane cewa tun da ki kaga an turo su to daga hukumar su ne, kuma ba sharri zasu yi ma yaya ba dole akwai abun da mu ba mu sani ba, amma ina so kiyi haƙuri mu bi komi a sannu ko dan halin da kike ciki, in sha Allah komi zai dai dai ta " ko mi akayi sai yace saboda halin da take ciki bai da wata magana bayan wannan
"to shikenan Allah ya shige mana gaba kuma zan yi magana da lawyern sadiq, tun da a high court yake aiki " uncle Ibrahim ya ce "hakane ni da kaina  zanyi magana da barrister, ba sai kin kira shi ba " sun ɗan jima suna tattaunawa ta yan da zasu ɓulloma al'amarin, uncle Ibrahim na barin part ɗin ya kira barristern sadiq ya faɗa mashi duk abun da ke faruwa,sannan ya samu uncle Ahmad  ya faɗa mashi  lokacin da suka zo baya gida,  ammy ma ta kira su malam ta sanar da su,lallashinta su kayi,ko da su uncle Ibrahim suka sanar da innah abun da ke faruwa cewa tayi to sai mi su ɗauki haƙƙin mutane su ba su mana , sadiq ɗin waliyyi ne shi da bazai iya satar ƙuɗin mutane ba , abun yayi matuƙar basu mamaki dan basuyi tsammanin jin haka daga wurin ta ba, kwana uku da zuwan efcc ammy ta haihu ta haifi ɗiya mace  kyakyawa mai matuƙar kama da noraiz, farin ciki wurin ammy ba'a cewa komai dan tana matuƙar san ɗiya mace,kwanan ammy biyu da haihuwa turai ita ma ta haifi ɗiya mace kyakyawa, farin ciki wurin uncle Ibrahim ba'a cewa komai, duk wani abu da uba zai yima ɗiyar shi sai da yayima babyn ammy da tashi,da ranar suna ta zagayo aka sama babyn ammy fatima babyn turai kuma sa'adatu suna kiranta da sa'ada.

Shiru har tsawan wata uku efcc basu dawo ba kuma basu shigar da ƙara ba.
watan fatima da sa'ada biyar da haihuwa kwatsam sai ga sammaci kama uncle Ibrahim  da ga court  efcc sun shigar da ƙara, hankalin kowa  yayi matuƙar tashi musamman uncle Ibrahim da akayi arresting, Innah sai kuka take tana ma ammy masifa uncle Ahmad  na bata haƙuri akan tayi shiru , amma ina sai zagin ammy take tana cewa
mijinta yaje yayi sata shine zata liƙama ɗan ta, wallahi duk abun da ya samu Ibrahim sai ta gane bata da wayau
Allah sarki ammy ban da kuka babu abun da take,noraiz ma sai kuka yake ganin mahaifiyar shi na kuka shazim kuwa in ban da haɗiyar zuciya babu abun da yake, zazzaɓi ne ya rufe ammy bayan ta shiga part ɗin ta,wayar ta shazim ta ɗauka ya kira malam ya faɗa mashi abun da ke faruwa, hankalin malam yayi matuƙar ta shi sosai, ya kuma cema shazim in sha Allah suna nan zuwa shi da ummy.
innah taci kuka kamar ranta zai fita ta tsine ma ammy yafi aƙira akan laifin da bana ta ba, takuma ƙara jin tsanar ta, turai ma sosai taji zafin ammy in ta tuna saboda laifin sadiq aka kama mijin ta duk da bata nuna mata a zahiri ba,kwana biyu da kama uncle Ibrahim uwani da halimatu suka zo daga kurfi su da ƴaƴan su , har suka yi kwana ɗaya da zuwa ammy bata san sun zo ba, dama halimatu ce mai zuwa wurinta to innah ta hana, sai washe gari da safe ta shigo part ɗin ammy suka gaisa, sai a sannan ammy ta san da zuwan su, daga ranar kullum sai halimatu ta shigo sun gaisa saboda tun da abun ya faru ammy ta dai na fita tana part ɗin ta koda yaushe ita da ƴaƴan ta, ta ɗan samu natsuwa saboda kullum sai malam da ummy sun kira ta sun kwantar mata da hankali sun kuma faɗa mata sunan zuwa hakan yasa ta dai na damuwa sosai taci gaba da adu'a, kullum lawyern  sadiq sai ya zo har aka tsai da ranar shiga court, ana gobe za'a shiga court malam da ummy suka zo amma basu sauka a estate ɗin ba sai suka sauka a gidan da sadiq ya fara zama , can ammy taje ta same su ita da su noraiz, anan suka kwana, washe gari da zasu tafi court gida aka bar su shazim tare da mai aikin ammy, suna isa court ba'a daɗe ba alƙali ya zo aka fara gaba tar da ƙara, da lawyer ya fara gabatar da ƙara abun yayi matuƙar ɗagama ammy hankali jin anƙara akan abun da efcc suka faɗa time ɗin da suka zo gida,an mai da zargin kan ana zargin sadiq da cinye hannun jarin abokanan kasuwan cin shi, sannan gomnati na zargin shi da satar maƙudan ƙuɗin da sunan aiki, an kuma kama container biyar da kayan maye da sa hannun shi, alƙali ya buƙaci ganin abokan kasuwan cin sadiq da wanda sune maƙa sudin shigar da ƙarar, abun yayi matuƙar ba ma ammy mamaki , saboda waɗan da suka shigar da ƙarar abokai ne ga sadiq na ƙut da ƙut  wasu daga cikin su tun kafin ya shiga shiyasa yake tare da su, haka ƙara ta ciga ba da tafiya duk yan da lawyer sadiq ya so kare sadiq abun ya ci tura dan mutanen sun gabatar da hujuji masu ƙarfi, ammy na ji na gani aka ɓata sunan mijinta bayan ranshi kuma aminan shi,duk wani company  na sadiq sai da kotu ta amshe har da wasu gidajen shi, a taƙaice daga  gidan shi dake lagos sai estate ka ɗai kotu ta bari, rayuwa tayi ma ammy zafi, taci kuka kamar ranta zai fita, sai da malam da ummy suka yi ta bata haƙuri da nasiha, malam yace ta yita yi ma mijinta da ƴaƴenta adu'a,sun kwantar mata da hankali sun kuma nuna mata mahimmanci haƙuri da ƙaddara, hakan ya sa ta ɗanji sauki a ranta,amma abun na damun ta  ba ita kaɗai ba har da  malam da su uncle Ahmad  dan sun san  wannan duk sharri ne, innah kuwa kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha saboda tsabar  jin daɗi   an saki uncle Ibrahim,kwata kwata bata damu da halin da Ammy take ciki ba,  yanke shawara ammy tayi idan su malam zasu koma lagos ƙafarta ƙafarsu kuma da ƴaƴen ta zata tafi komi innah zata ce sai dai tace dan a yan da take ji har kotu tana iya kai ta idan tace zata amshi ƴaƴen daga wurin ta,ko da ta faɗa ma su uncle Ibrahim shawarar data yanke, haƙuri suka shiga bata har da halimatu amma ina, sunyi sunyi amma taƙi haƙura, har zuwa su kayi wurin malam ko zai sa baki ta zauna amma sai yace shima yana buƙatar ta a kusa da shi, ya dai yi masu alƙawarin zata dunga ziyartar su in sha Allah ita da yaran,sun so ko noraiz a bar masu amma malam yace a'a,ba yanda suka iya haka suka haƙura, tsab ammy ta haɗa duk kayanta dana yaranta dake part ɗin su, duk wani abu da tasan tana so sai da ta ɗauka sannan ta fitar da wanda zai lalace taba ma'aikanta estate ɗin sannan ta kashe duk wani abu na wuta, har part ta samu innah tayi mata ban kwana tayi tunanin innah zata ce wani abu amma sai taga saɓanin haka, turai da asiya sun sha kuka da ammy  zata tafi ,maƙalewa kairiyya tayi akan dole sai ta bi ammy, haƙuri ammy taita bata, mansoor  ma sun shirya da shazim shima har da kukan shi  innah har gida ta samu su malam tayi masu sallama, tun da safe suka kama hanyar lagos cike da kewar mutanan abuja.

Tunda suka koma lagos malam da ummy suke bama ammy kulawa ta musamman dan ganin ta kwantar da hankalin ta,hakan baƙaramin  kwantar da hankalin ammyn yayi ba ta rungumi ƙaddarar ta,  kullum cikin yima mijinta adu'a take da ƴaƴen ta, malam ya saka shazim da noraiz makarantar boko da islamiya,shazim na jss one noraiz kuma primary two, makarantar su ɗaya, su noraiz ƙarfe 12 ake tashin su amma noraiz baya komawa gida sai an tashi su shazim 2:30 pm sannan su tafi tare, da sun dawo wanka suke su ci abinci sai su wuce islamiya, malam ya tsaya tsayin daka akan rayuwar su duk wani abu na rayuwa wanda uba kema ƴaƴen shi malam na masu shi,hakama ummy babu abun da ba ta masu, uncle Ibrahim da uncle Ahmad ma suna matuƙar ƙoƙari akan su  sosai su ke basu kulawa duk da basa a tare da su, kuma lokacin bayan lokacin uncle Ibrahim yana kawo masu ziyara har lagos,   haka suka taso cikin soyayyar kakannin su da mahaifiyar su,
malam ya so ammy ta ƙara wani auren musamman da uncle Ibrahim ya nuna yana ra'ayin aurenta, malam ya so tayi ko da ba uncle Ibrahim ɗin ba,mutane sun sha zuwa suna nu na ra'ayin aurenta amma tace a'a tafi son ta zauna tare da su malam da ƴaƴen ta, ƙyaleta malam yayi sai ma nema mata aiki da yayi, da farko ƙin amincewa tayi da aikin sai da malam ya zaunar da ita yanuna mata amfanin yin aikin sannan ta amince tafara aikin.
haka rayuwa ta cigaba da tafiya ammy na zuminci sosai  da su asiya, suna waya time to time, lokacin da turai da asiya suka haihuwa har abuja taje ita da fatima bata tafi da su shazim ba saboda makaranta.

Akwana a tashi shazim harya kammala secondry school lokacin noraiz na jss one fatima kuma na nursery one, uncle Ibrahim yazo lagos ya roƙi ammy da ta bashi shazim yayi karatu a hannun shi tare da su mansoor,  ƙin amincewa ammy tayi da zaman shazim a abuja saboda innah, tana tsoron zaman su tare saboda ta lura kwata kwata innah bata ƙaunar shazim,   da kuma shi kan shi  shazim ɗin ta san bazai taɓa raga ma innah ba tana tsoron abun da zai biyo baya, babu yan da uncle Ibrahim bai yiba amma tace a'a,ganin bazata amince bane yasa ya sanar da malam da ummy, faɗa malam yayi ma ammy dan mi zatace a'a, Ibrahim ba uba ne a wurin shazim ba yana da ikwan da zai iya mai da shi wurin shi da zama bama karatu ba, ba dan ammy ta so ba ta haƙura,sosai uncle Ibrahim yaji daɗi da ta amince kafin ya tafi sai da ya amshi takardun shazim duka, ko da ya koma abuja addimission ya nema ma shazim da mansoor cikin ikwan Allah suka samu,
kiran ammy uncle yayi ya sanar da ita ya kuma faɗa mata time ɗin da  zasu fara lectures, malam ta samu ta sanar da shi yaji daɗi ya kuma kira uncle Ibrahim yayi mashi godiya, ya kuma ce mashi in sha Allah ana saura sati biyu su fara lectures ɗin shazim zai zo,hakan ce ta faru ana saura sati biyu su fara lectures ɗin shazim ya shirya ya tafi abuja, da zai tafi noraiz harda kukan shi, ko da ya isa abuja mansoor ne yazo har airport shi da driver ɗaukar shi, farin ciki sosai  mansoor  ya nuna na zuwan shazim ɗin da kuma kasancewa da zasuyi a tare,ko da suka isa estate ɗin tarba ta musamman   shazim ya samu daga wurin uncle's  ɗin shi da matan su,  sosai suka nuna farin cikin zuwan shi har da yaran su,  feenah  ce dai da  innah sai luqman  ko a jikin su, lura da hakan da shazim yayi ne yasa ya ɗauke kan shi daga innahr yayi kamar ma bai san da zamanta a estate ɗin ba,  feenah kuwa ko kallon banza bata ishe shi ba daga ita har luqman ɗin dama ba son rainin wayau yake ba kuma ita da ma yar rainin wayau ce ga  rashin kunya, da zasu fara zuwa makaranta uncle Ibrahim ya sai masu motoci masu kyan gaske, sunyi farin ciki sosai, da farko shi da mansoor kowa tafiyar shi yake shi ɗaya har da haɗi da  ba department ɗin su daya ba shazim na karantar medicine and surgery mansoor kuma yana karantar medicine,abokin shazim ɗaya a department mai suna  A hashim,shaƙuwa ce sosai tsakanin shazim da A  hashim, mansoor kuwa yana da abokai ba laifi ,  sai  daga baya mansoor ya ce mizai hana su dinga tafiya tare, da ƙyar shazim ya amince da su rika tafiya tare, ta dalilin haka shaƙuwa sosai ta shiga tsakanin su kowane lokaci suna tare da juna ko a school ko a gida, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma uncle's ɗin shi ba dan dama burin su yaran su haɗa kan su, innah ce kwata kwata hakan bai mata daɗi ba dan ba haka taso ba, har kiran mansoor tayi tana mashi faɗa dan mi zai shige ma shazim, shazim ɗin da ba son su yake ba san da suna yara, shikuma   ya ce mata ko ada laifin  su ne , su suka nuna ba ss son shi shiyyasa shima ya nuna bai son su, ba ƙaramin haushi maganar mansoor ta ba innah ba hakan yasa ta ƙara jin ta tsani shazim musamman ma yanda yayi fatali da ita a estate ɗin, dan sai ayi sati bata sa shi a ido ba kuma kullum sai mansoor ya zo gaishe da ita da safe amma bata taɓa ganin shazim ba, har ƙararshi ta kai wurin uncle ahmad akan bai zuwa yana gaishe ta, kiran shi uncle ahmad yayi yayi mashi faɗa da nuna mashi hakan bai dace ba, haƙuri ya bashi ya kuma yi alƙawarin gyarawa, tun daga ranar kullum da safe idan mansoor zai je gaishe da ita tare suke zuwa, kullum kuma yaje gaishe da ita ta rinƙa faɗa mashi baƙaƙen maganganu kenan, in tana yi yi yake kamar ma bai san mitake yi ba, hakan kuwa ba ƙaramin haushi yake bata ba, sai daga baya daya lura abun nata ba mai ƙarewa bane yasa in tace mashi A to sai ya kai mata har Z, bata yi mamaki ba tun da daman tasan halin shi tun yana yaro ba ragamata yake ba, wata rana suna dawowa daga makaranta mansoor ya ce suje su gaishe da ita ko da  suka je gaishe da ita basu same ta ba tana part ɗin uncle Ibrahim sai su feenah da kairiyya suka samu a part ɗin suna kallo, gaishe da su kairiyya tayi amma feenah mansoor ka ɗai ta gaida, dama tun da shazim ya zo kowa na gaishe da shi amma banda ita, lura da bata gaishe da shi ba ne yasa mansoor rufe ta da faɗa maimakon ta gaishe shi sai tashi tayi tafice tana ƙunƙunai, a kwai wata rana da uncle Ibrahim ya kira shazim part ɗin shi daya je part ɗin ba kowa a parlor sai ita kaɗai da yayi sallama ta ƙi amsawa sai ma ɗago da kai tayi ta kalle shi ta kauda kai tana jan tsaki , abun yayi matuƙar bata ran shi ya tsani rainin wayau da rashin kunya  hakan yasa ya ɗauke ta da mari har sau biyu har sai da ta duƙe saboda zafin da taji ai kuwa ba shiri ta nufi ɗakin momyn ta tana kuka, da ta shiga ko da ta sanar da momyn ta taso ƙeyarta tayi har parlorn ta bashi haƙuri, dan dole ta bashi haƙuri tun da ga ranar kuwa ta dai na yi mashi koda kallon banza bare aje ga tsaki.

Lokacin da su shazim su kayi hutu da zai tafi lagos tare suka tafi da mansoor har hutun su ya ƙare suka dawo, haka rayuwa ta cigaba da tafiya shaƙuwa ce sosai tsakanin shazim da A hashim dan A hashim yana yawan zuwa lagos wurin shazim hakan ne yasa kowa ya sanshi tare da shazim musamman fatima ba ƙaramin son a hashim take ba idan ya zo lagos  to tana nan maƙale da shi, tun wata rana da noraiz ya ji ciwo yayi mashi alura shine ta tambaye shi daman ya iya alura kamar ya shazim sai yace mata eh ai su doctors ne tunga ranar ne ta sa mashi suna ya dr.

Cikin ikwan Allah   sun kammala degree za suyi joining masters,maganar aure su uncle ahmad suka yi masu amma sai suka ce su ba yanzu ba sai sun kammala masters sun fara aiki tukunnan, ko da suka ce haka su uncle ahmad sunyi na'am da hakan, tunga time ɗin basu sake masu maganar auren ba sun barashi a sai sun fara aikin,business malam yace  shazim ya fara kafin su fara masters, da zai fara malam ya bashi jarii, cikin ikwan Allah lokacin da za su tafi business ya haɓaka Allah ya sa ma abun albarka,da zasu tafi malam ya samo  wani yaro mai gaskiya da ruƙwan amana ya ɗaura shi akan business ɗin kafin  shazim ɗin ya kammala karatu,cikin ƙanƙanin lokaci business ɗin ya ƙara haɓaka,saboda   yaron na kula da business ɗin shazim cikin aminci ga gaskiya da ruƙwan amana,
lokacin da suka kammala master business ɗin shazim ya haɓaka sosai dan malam na kula da komai ga kuma hameed hakan yasa business ɗin haɓaka.
lokacin da suka kammala  masters lokacin su noraiz shi da mahmud da luqman suna aji biyu a jami'a.
Basu jima da kammala masters ba suka samu aiki su duka,har da A hashim,  uncle Ibrahim ya so shazim yayi aiki a abuja amma yace ya fi son lagos saboda business ɗin daya ke hakan yasa uncle Ibrahim haƙura,shazim yana aiki awata babbar asibiti dake nan garin lagos, haka rayuwa ta cigaba da tafiya shazim yana aiki hameed na  kula mashi da  business,yanke shawarar yin phd yayi, ko da ya sanar da uncles ɗin shi da malam goya mashi baya su kayi ,amma sai malam ya bashi shawarar yin phd ɗin ta online, sosai hakan yayi mashi daɗi ko ba komi zai samu ya dinga zuwa aiki wani lokacin yana kuma kula da business ɗin shi,cikin ikwan Allah yana kula da aikin shi da business ɗin shi ya kammala phd,ƙarin girma ya samu a wurin aikin shi  bayan nan kuma yana visiting wasu hospital ɗin,ganin komai na tafiyar mashi dai dai yasa ya yanke shawarar buɗe privet hopital, daya  samu malam  da maganar , sosai ya bashi goyan baya, ya kuma taimaka mashi da wani abun wurin gina hospital ɗin, cikin ikwan Allah aka gama gina hospital ɗin , ammy ma ta tai maka mashi da wani abun da zai zuba kayan aiki, sosai yaji daɗi ya kuma yi ma ammy godiya,kayan aiki masu inganci ya zuba, sai da komi ya kammala sannan ya ɗauki ma'ikata,ya kuma ɗaura wani abokin shi mai suna majeed wan da su kayi islamiya ɗaya,daman yayi karatu a harkar  lafiya hakan yasa shazim ya ɗauke shi aiki ya kuma ɗaura shi  a matsiyin MD na Hospital ɗin,shi ke kula da komai ko da shazim ɗin na nan...

Episode  54_55_

Uncle Ibrahim da uncle ahmad tasa shazim da mansoor gaba suka yi akan su fito da mata suyi aure, amma sai su kace  ba yan zu ba, faɗa suka yi masu sosai suka kuma ce sun basu nan da wata huɗu ko dai su fito da mata ko kuma su zaɓa masu da kansu
ganin haka ne yasa mansoor ya gabatar da wacce yake so amma shazim shiru ta business É—in shi kawai yake dan ya ma manta da wata magana ta aure.
ganin mansoor ya gabatar da wacce yake so amma shazim shiru yasa uncle Ibrahim  shiryawa yaje har lagos ya samu malam da batun, ya kuma sanar da shi sun yanke shawara ko dai ya fito da mata yayi aure ko kuma su aura mashi duk wacce suka ga dama, malam bai  bada goyan baya ba akan  hukuncin da suka yanke  yace su bar shi da shazim ɗin shi da kansa zai sa ya fito da matar , kwata kwata ba haka uncle Ibrahim  ya so ba yaso ace malam ya goyi da bayan su, ba dan ya so ba ya amince ya koma abuja, koda ya koma ya sanar  da uncle ahmad yan da suka yi  da malam faɗa ya kama yana cewa  kenan malam ke goya mashi baya shiyyasa da suka yi mashi magana yayi kunnen uwarshegu da su, ya kuma yanke hukuncin dole tare za su yi mashi aure shi da mansoor da su feenah dake shirin kammala makaranta, {su noraiz su gama masters kawai suke jira} ko yana so ko baya so, sosai uncle Ibrahim da innah suka amince da hukuncin da uncle ahmad ya yanke, uncle ahmad da kan shi yakira malam ya sanar da shi cewa sun ƙarama shazim ɗin wata biyu kacal ko dai ya fito da mata ko kuma su aura mashi duk wacce ransu ya so,abun yayi matuƙar ba malam mamaki yan da suka ɗau abun da zafi sosai har haka, shima yana so yaga shazim ɗin yayi aure amma ya fiso abi komi a sannu gudun dana sani.

Ammy da ummy malam ya kira ya sanar da su abun da uncle ahmad ya ce, suma basu ji daÉ—in hukuncin da suka yanke da zafi haka ba,suma babu abun da suke buri sama da shazim É—in yayi aure.

Kiran shazim malam yayi ya sanar da shi hukuncin da uncle ahmad ya yanke,sannan yace mashi komi yake ya fito da mata suma sun fi son yayi auren tunda dai dai dai gwargwado Allah ya bashi rufin asiri, to sai ya godema Allah shima yayi aure ya tara nashi iyalin, cewa yayi in sha zaiyi ƙoƙari ganin ya fitar da mata yayi auren, malam yaji daɗi da ya amince zai yi auren ya kuma yi mashi adu'a Allah ya zaɓa mashi mata tagari.

Tun ranar da su kayi magana da malam har tsawan wata biyu shazim bai kawo matar ba bai kuma sake maganar ba, tun su uncle ahmad nasa idon ya zo  yace ga wacce yake so  har suka gaji,su kai fushin har suka gaji ganin wanda suke yi dan shi bai ma san suna yi ba.

gajiya malam yayi da shirun nashi ya sake mashi maganar, ko da yayi mashi maganar sai cewa yayi gini yake yanzu so yake sai ya kammala tukunnan,malam yace to ya kamata ya kira su uncle ahmad ya sanar da su, da to ya amsa, ya kuma kira su ya sanar da su, balbale shi da faɗa uncle Ahmad yayi dan mi bazai sanar da su ba tuntuni sai yanzu da lokacin da suka bashi ya ƙare, haƙuri ya bashi ya kuma sanar da shi ya kusa kammala ginin ai saura ka ɗan , jin yace hakane yasa uncle ahmad haƙura ya ƙara mashi wasu wata uku, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma shazim ba dan shi kwata kwata bai shirya yin aure yanzu ba neman kuɗi kawai yasa a gaban.
tun da uncle ahmad ya amince da maganar gini daya ce yana yi yasa ya fake da ginin har akayi shekara ɗaya bai ce ya kammala ba bai ce ga mata ba, sai da malam ya tasa shi gaba da faɗa sannan ya kammala,gida ne mai girman gaske kusan part uku ne gidan,  kuma yana kammalawa yace su koma gidan da zama, malam cewa yayi sai dai shi da ammy da fatima su koma(da yake noraiz na makaranta shi da su mahmud)  amma shi ba yanzu ba sai yayi aure sannan zasu dawo shi da ummy, ba yanda bai yi da malam ba amma ya ƙi amincewa dole tasa shazim haƙura suka koma shida su ammy duk da da farko da malam yace bazai koma ba ammy itama cewa tayi bazata koma ba sai tare da su malam amma sai malam yace ta koma suma sunan za su dawo.

_*CIGABAN LABARI*_

Aunty safiya ce tsaye bakin ƙofar parlorn mus'af tana nocking amma ba'a buɗe ba , ba kuma a bata izinin shiga ba, da dai ta gaji da tsayuwa ne yasa ta fara kiran sunan mus'af ɗin tana faɗin " wai lafiya kake ne? , ana nocking amma kayi shiru ka kuwa san ƙarfe nawa yanzu kowa na waje kai ka ɗai ake jira "
daga ciki mus'af yace " gani nan zuwa, ina gama shirya wasu kayan ne "
"amma kai ko anyi shiriritacce, yanzu da baka gama shirin ba kenan,  yayi maka kyau, to kayi sauri ina nan ina jiran ka "
zaune yake bakin gado sai dialing number Aairah yake amma bata picking ga umma dake bakin ƙofa tana faɗa mashi shi kaɗai su ke jira, ganin dai da gaske ba ɗagawa zata yi bane ya sa shi haƙura da kiran ya miƙe trollyn shi da ke bakin gadon ya ja haɗi da sanya wayar cikin aljihu, da kaga fuskar shi zaka tabbatar da cewa yana cikin damuwa,kwata kwata ba walwala a fuskar shi duk dan saboda kiran Aairah da yayi bata picking, da ya fita tsaye ya samu ummah tana jiran shi ya fito, da kallo Aunty safiya ta bishi " wai mus'af  mike damunka ne,  tafiyar ce baka son yi ko mi"
"a'a ummah "

"idan ba ita bace ba ka son lyi ba, ace tun last month kasan da wannan tafiyar amma ace har yau baka gama shirin da zaka yi ba "

"kiyi haƙuri na gama yanzu " 

gaba tayi tana faÉ—in "ka taho mu wuce kowa na waje yana jiran ka "

bin  bayan ta yayi, a compound su ka samu abba da su najma su kawai su ke jira, suna isowa wurin su ba ɓata lokaci kowa ya shiga mota su ka fice faga gidan zuwa airport, mus'af duk a takure Aairah  taƙi kiran shi, bini bini ya duba waya amma shiru har su ka iso airport  tun yana sa ran ganin kiranta har ya fidda rai, parking su kayi a parking lot ɗin airport ɗin, fitowa su kayi su ka ɗunguma zuwa ciki, saura 25 minutes jirgin su ya tashi, zama su kayi kan chair's ɗin da aka tana da domin zama, mus'af gaba ɗaya ya kasa sukuni sai zuba idon ganin Aairah yake amma shiru har dai Abba da ummah su ka lura da halin da yake ciki, Abba yace " lafiya dai ko mus'af"
"lafiya lau Abba "
"A'a ba dai lau ba, ko a kwai wanda ka ke jiran zuwan shi ne " girgiza ma Abba kai yayi alamar a'a, har lokaci ya rage saura  15 minutes jirgin su ya tashi Aairah bata kira shi ba ba kuma ta zo ba, sai da ana saura 8 minutes sai ga su sun zo ita da Aaimah harda mom ya Abdallah ya kawo su, sunje gidan  mai gadi yake sanar da su ai sun tafi airport ɗin tun ɗazu, shine su ka biyo bayan su, mus'af har wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke ganin Aairah,da sauri ya nufe ta ganin mom da ya Abdallah ne yasa shi waskewa ya nufi mom ɗin, murmushi Aairah tayi dan ta san wurin ta ya nufo ,so yake su ƙeɓe domin suyi ban kwana amma  Abdallah ya kasa ya tsare,sai dai kowannan su ya ƙurama ɗan uwan shi ido ba yanda su ka iya dole su kai ban kwana kamar  kowa,kowa da kewar ɗan uwan shi, jirgin su na ta shi kowa ya nufi mota, mom bin su Aunty safiya tayi zata je gidan granny, da mom zata tafi Aaimah  ba yan da bata yi ba akan tana son su bi mom gidan granny amma ya Abdallah ya hana, Aairah daman bata tanka ba dan ta mafi so su tafi gida,suna isa gida parking yayi a parking space,yana gama parking ko kashe motar bai yi ba Aairah ta buɗe ta fice, bedroom ɗin su direct ta nufa,tana shiga ta faɗa  kan bed fashewa tayi da wani kuka mai tsuma zuciya sai kace wacce akayi ma wani abu, a haka Aaimah ta shigo ta same ta, kallo ɗaya Aaimah tayi mata haɗi da taɓe baki tace " amma wallahi kin haɗa kanki da aiki, daman wannan cika da batsewar da kike yi a mota kuka ne kike ɓoyewa ashe, ah lallai sannun ki " banza Aairah tayi da ita sai ma ƙara sautin kukan ta da tayi, tun Aaimah nayi mata iya shege har dai ta koma lallashin ta " dan Allah Aairah kiyi haƙuri in dai ya mus'af ne zai dawo ki kwantar da hankalin ki, karatu kawai fa yaje ba wani abu ba " haka Aaimah tai ta lallashin ta har ta sa mu ta ɗan yi shiru sai sauke ajiyar zuciya take.

"ni banga abun da zai sa ki tashi hankalin ki ba Aairah, in dai ya mus'af ne zai dawo karatu ne ya tafi ba wani abu ba "

magana Aairah ta fara cikin muryar kuka
"ni fa ba tafiyar da yayi bace ta sani kuka ba "

"idan ba ita bace to minene ya saki kuka ana zaman lafiya?"

"ya Abdallah fa shi ya hana mu muyi bankwana, ya tsare mu da idanuwa ni na rasa mi yasa baya son soyayyar mu ni da ya mus'af, shima abie baya goyan baya"

dafa kafaɗar ta Aaimah tayi "sister ba wai baya son soyayyar ku bane, kawai dai abun da nake tunani ya na ganin ƙanƙantar ku ne ku duka "

"amma idan haka ne miyasa mom da Aunty safiya da Abba basa gani sai shi da Abie kawai "

"to Allah ka É—ai ya san dalilin su, amma tabbas na san ba wani abu bane "

"Allah yasa haka, amma wallahi ina matuƙar ƙaunar ya mus'af ban san ya zanyi ba idan su abie su ka ƙi goya man baya ba, ina son shi sosai "

"ki kwantar da hankalin ki in sha Allah ma za su amince,amma ki ta adu'a  Allah ya zaɓa maki abun da yafi zama alkairi, nima zan taya ki da adu'a "

Kwantar da kanta tayi saman kafaÉ—ar Aaimah tace "Ameen sister nagode"

mangare mata kai Aaimah tayi haÉ—i da cewa tace" dama a kwai godiya tsakanin mu "
murmushi Aairah tayi tana shafa inda Aaimah ta mangare ta  " sorry my lovely twiny"

Aaimah tace " sister ni fa ko na ƙagara mu samu addimisson mutafi makaranta na gaji da zaman gida "
"nima Allah na gaji, ai naji ya Abdallah yace cikin satinnan za su fara bada addimisson"
"Allah ya kaimu, har na ganni a school nama so ace a hostel zamu zauna  amma abie yace A'a "
"ni daman nafison gida, ko ƙarfe nawa zan kai gida dai zan dawo " a cewar Aairah
"gaskiya na fi son zama hostel dan sai na fi karatu a can "
"ko a gida idan ka sa kanka zaka yi ai "
"ki kace koh, amma ni nasan sai na fi jin daɗin yi a hostel " sun jima suna firar sai daga baya su ka nufi main parlor Abdallah su ka samu kwance kan sofa da waya kare a kunnan shi, raɗa Aaimah tayi ma Aairah a kunne tana faɗin " ina fa zargin yaya buduwar yayi, any time yanzu cikin waya yake"
jinjina kai Aairah tayi haÉ—i da cewa " ni ban ma lura ba "
"kice jirgi ya bar  ki tasha, wallahi tun da ya dawo daga abuja ya koma waya kowane lokaci  "
"ah lallai kam jirgi ya bar ni a tasha "
Aaimah tace " wallahi kuwa, zan so naga wacece yaya yake kashe ma murya hak..... " bata ƙara sa ba ta dalilin make kanta da aka yi Aairah tun kafin taga wanene ta watsa dagu sai kitchen sai da ta shige ne tafara leƙen parlorn, ya Abdallah ta hango riƙe da kunnan Aaimah yana mata ƙoso a kai sai faɗin " dan Allah yaya kayi haƙuri wallahi da zafi " ta ke
"amma gulma bata da zafi ko "
"wallahi yaya ba gulma muke ba kuma ba da kai muke ba labarin school nake bata "
"Allah ko " Abdallah ya faÉ—a, É—aga mashi kai tayi cikin sauri tana faÉ—in
" ka tambaye ta kaji "
tana faɗin haka Aairah da ke leƙen su da sauri ta koma cikin kitchen haɗi da turo ƙofar ta rufe, abun ma har so yayi ya ba Abdallah dariya, sake jan kunnan Aaimah yayi yace " daga yau idan na sake jin kuna maganar wani ko da ba tawa ba sai nayi maganin ku"ɗaga kai Aaimah tayi kamar ƙadangaruwa tace
" wallahi baza ma mu sake ba dan Allah kayi haƙuri dai " mangare mata kai yayi yana faɗin "wuce ki bani wuri " yana sakar mata kunne da gudu ta nufi up stairs tana sosa kunnen ta, Aairah dake cikin kitchen jira kawai take taji ana nocking ta shige store.
mai da wayar yayi a kunnen shi yana faÉ—in " hello Æ´ar qanwer ta"
daga cikin wayar fatima tace "ya dr kai da waye naji kamar kana magana da wata "ta faɗa cikin muryar da ke nuna bata ji daɗin jin yana magana da wata ba,  duk abun da yake faɗa ashe duk tana jin shi ,up stairs ya nufa yana  murmushi haɗi da cewa
"ba nace maki ina gida ba"
a shagwaɓe  tace " eh haka kace, amma wacece kuke magana "
"to ai sai ki tsaya na faÉ—a maki, wata younger sister na tace"
"twins?" ta fafa cikin sigar tambaya
"eh É—aya daga cikin su ne "
"yaya yaushe zaka basu waya mu gaisa "
"yanzu bana kusa da su amma ki bari zan kira ki sai na ba su"
"shikenan yaya, yaushe zaka zo "
"very soon zan zo " sun jima suna waya daga ƙarshe su kayi sallama

*_✨SHAZIM✨_*

Zaune yake a office ɗin shi dake eko yana aiki a laptop , wayar sa ce ta fara ringing, hannu yasa ya jawo wayar yana ganin mai kira yayi tsaki haɗi da yin rejecting ya cigaba da aikin da ke gaban sa,wani kiran ne ya sake shigowa ,banza yayi da wayar aikin dake gaban sa kawai ya ke ,haka wayar taita ringing mai kiran bai daina kira ba shi kuma bai yi picking ba ,message ne  ya fara shigowa ba k'ak'autawa,papers d'in dake gaban sa ya ture da laptop ɗin.
dafe kansa yayi yana fad'in "da alama yarannan so su ke na koya ma su hankali " ya fad'a had'i da jawo wayar  yana shirin kashe ta wani message d'in ya shigo wata number ce daban buɗe message din yayi ya fara karantawa

_GM dr da fatan ka wayi gari cikin ƙoshin lafiya, a ko da yaushe dai ina k'ara miko ƙoƙon barata fatan zaka amshi tayi na wata rana ,ka huta lafiya daga ni masoyiyarka 🌹.._

yana gama karantawa ya ja wani dogon tsaki yana ,a zuciyar shi yana fad'in " dole nayi maganin ki yau" yana gama fad'a ya jawo landline din dake kan table din,dialing wasu numbobi yayi ,ana picking ko sallama da na cikin wayar ke mashi bai amsa ba yace
"Am waiting for you" yana gama fad'a yayi rejecting had'i da tashi daga kan kujerar da yake zaune ya koma kan sofa.
bayan kamar 5 second akayi nocking k'ofar office din ,izinin shigowa ya bada ,turo k'ofar tayi ta shigo ,kamar ko da yaushe sanye take cikin  uniform din ta farare ,sallama tayi had'i da cewa "dr gani "
batare da ya amsa sallamar da tayi ba yace
"ina wayar ki take " gaban ta ne yayi wani mummun faɗuwa ,da sauri ta d'ago tana kallon shi ,cikin in ina tace " wa...ya.. ta ...kuma d..r? " ta k'arasa maganar cikin sigar tambaya , jifar ta yayi da wani sakaran kallo haɗi da cewa  "A'a tawa"
"dan Allah kayi hak'uri dr mi zaka yi da wayata?"

"bana son jin wata magana ,zaki bani  wayar ko saina b'ata maki rai "

_abun da hidaya bata sani ba tun lokacin da ta amshi number shi a hannun dr kabir ta fara tura mashi messages yasan cewa ita ce ,dan  dr kabir ya kira shi ya fad'a mashi cewa zata kirashi ta damu akan yanayin da ya bar hospital ranar ,saboda  yasan zai yi wuya idan ta kira shi ya ɗauka dan ba kasa fai yake d'aukar baƙuwar number ba_   

hawaye ne ke sauka kan fuskar ta ,hannu tasa cikin aljihun rigar ta ta fiddo da wayar hannun ta na kyarma ta mik'a mashi ,amsa yayi ,number ta da ke cikin wayar shi yayi dialing tana fara ringing ya ɗago da kanshi ya na kallon ta ,duƙar da kai tayi tana share  hawayen da ke bin kumatunta, magana ya fara da kakausar murya
"kema ashe baki da hankali ban sani ba, ina maki kallon wacce ta san ciwan kanta ashe ba haka ki ke ba, daga yau kar na sake ganin ƙafar ki acikin office ɗina "
wasu zafafan hawaye ne suka sake wanke mata fuska, cikin muryar kuka tafara magana " dan Allah kayi haƙuri kar kace ka kore ni, wallahi kuskure ne bazan sake ba in sha Allah.... " tsawa ya daka mata
"fita ki bani wuri tunkafin ranki yayi mummunan ɓaci " kuka sosai hidaya ta fashe da shi tana bashi haƙuri, amma kwata kwata bai saurare ta ba, haka ta ja ƙafarta ta fice daga office ɗin ranta duk a jagule sai data sanin biye ma shawarar maryam da tayi take, da ta san wata rana zai ganota kuma har ya koreta da bata biye mata ba, tana fita daga office ɗin da dr kabir ta cikaro tsaye bakin ƙofa ya harɗe hannuwa a ƙirji, da alama ba tun yanzu yake a bakin ƙofar ba kuma yaji duk abun da ya faru tsakanin ta da shazim, dagama yanyin kallon da yake mata ta san cewa ba abun da baiji ba...
Episode  56_57_

Fuskar shi a murtike yake  bin ta da kallon ƙasa da sama, idanuwan shi sun ƙaɗa sunyi jawur,tsantsar ɓacin rai ne a cikin su, bi tayi ta gefan shi zata wuce, da sauri ya fisgota, har sai dai da tayi ƴar ƙara saboda zafin da taji, janta yayi har office ɗin shi suna shiga ya yarfar da hannunta har sai da ta kusa faɗuwa , magana ya fara cikin kausashiyya murya dake nuna tsantsar ɓacinran da yake ciki

"dama duk abun da ke faruwa saboda shi ne, duk irin wulaƙancin da kike man dama duk  saboda shi ne?,  amma  kinyi matuƙar bani mamaki,banyi tunanin haka daga gare ki ba,mi nayi maki da zaki yi man haka, da me ya fini da har zaki zaɓi zubar da mutuncin ki na ƴa mace a idanuwan shi, why !  why !! why hidaya  "

ya ƙarasa maganar da wata kalar murya da ke nuna ya karaya,har ya buɗe baki zai sake faɗin wani abu  sautin kukanta daya karaɗe office ɗin ne ya dakatar da shi, matsawa yayi kusa da ita, ɗurƙushe take a ƙasa sai zubar da hawaye take,tausasa murya yayi yace
" saboda na nuna ɓacin raina ne kike wannan kukan, ko dan saboda ya nuna baya sonki?? "
shiru tayi bata ce ma shi ƙala ba, sake kwantar da murya yayi yana faɗin
" da ke nake magana kinyi shiru, idan ma dan nayi maki faɗa ne kike wannan kukan kiyi haƙuri, dole raina ya ɓaci ina ta fama da ke akan ki ƙarɓi soyayyata ki so ni ko da bai kai kwatan kwacin  yanda nake sonki ba amma kin ƙi, ashe duk wahalar da na ke baki gani, miyasa kika yi man haka, ko ina da wani haline wanda bai yi maki ba, idan har ina da wani abu wanda baki so ki faɗa man zan daina amma dan Allah ki rabu da shazim, shazim bazai so ki ba yasan cewa ina sonki kuma  gani yake soyayya rashin aikin yi ce, kuma zuwan da yayi abuja uncles ɗin shi sun zaɓa mashi matar da zai Aura yanzu haka tana gidan su "

Gabanta ne yayi mummunan faɗuwa jin furincin shi na ƙarshe, da sauri ta ɗago tana kallon shi da rinanun idanuwanta " ya kabir da gaske kake?" jinjina mata kai yayi alamar eh , fashewa ta sake yi da wani kukan, da sauri  ta tashi ta bar office ɗin da gudu, da sauri shima ya tashi ya bi bayan ta,ko da ta fita bata tsaya ko ina ba sai bakin gate ɗin  hospital   ɗin tana fita tayi sa'a samun abun hawa, lokacin da dr ya ƙara so bakin gate ɗin har mai adaidaitan daya ɗauke ta  yabar wurin, dafe kan shi yayi yana faɗin
" wai mi kike so ne hidaya? dan Allah kar ki zautar da ni " haka yayi ta sambatun shi shi ka ɗai a bakin gate da dai ya gaji, komawa yayi cikin hospital ɗin direct office ɗin su ya nufa, a bakin ƙofa ya samu maryam ta fito, tsaida ta yayi yana faɗin
"please maryam kayan hidaya za ki É—auko man "
"dr lafiya dai, mi ya samu hidayar, yanzu muke tare da ita dr shazim ya kira ta  "
"ba komai ki kawo man ina office" yana faɗa ya wuce office ɗin shi 
ok kawai tace haÉ—i da komawa cikin office ta tattaro kayan hidaya ta nufi office É—in dr kabir da wayarta a hannun tana dialing number hidaya amma bata shiga.
Tana yin nocking yana buɗe ƙofar, miƙa mashi jakar hidayar tayi tana faɗin " dr gashi, amma mi ya sameta ina ta kiran wayarta bata shiga "
Amsar jakar yayi yana faÉ—in " bata jin daÉ—i ne ta tafi gida"
"dr ai da kabari sai na tafi mata da kayan "
"A'a ki barshi kawai zan kai mata kafin na wuce gida "
"to shikenan Allah ya bata lafiya " da ameen ya amsa, wuce wa yayi ya barta anan tsaye sai mamaki take azuciyar ta tana faÉ—in
" mi ya samu hidaya yanzu yanzu, Allah dai yasa ba wani abu bane ya haɗa ta da dr shazim ba dan ta san abun da zai sa hidaya tafiya a wannan lokacin dole yana da alaƙa da shazim tun da shine ya kirata" 
A zahiri kuma tace "Allah dai yasa lafiya " office ɗin su ta koma tana cigaba da dialing number hidayar amma har yanzu bata shiga daga ƙarshe ma jin wayar tayi a kashe, hankalinta ya ɗan tashi jin wayar a kashe kuma
"tao wai mike faruwa da hidaya ne?, amma zanje gidan inji ko lafiya nake kiranta bata É—auka" haka tai ta jefa ma kanta taambaya tana haÉ—a kayan ta ita ma.
Da ya bar hospital É—in wani shopping mall ya nufa,parking yayi ba tare da ya shiga ba wayar ya fiddo yayi dialing wata number wanda ya kira na picking sallamar da yayi kawai ya amsa ma shi sannan yace
"ina waje "
shine kawai abunda   yace yayi rejecting kiran, bayan kamar 5 seconds sai ga wani matashi ya fito hannun shi ɗauke da wani madaidaicin kwali ya nufo motar dr kabir, yana iso wa dr kabir ya buɗe mashi gefan shi , saka kwalin yayi ya maida ƙofar ya rufe, zagayowa yayi wurin dr yace
"a sauka lafiya ranka ya daÉ—e"
da Ameen dr ya amsa haÉ—i da yima motar key ya bar harabar wurin.
A bakin gate ɗin gidan yayi parking, fitowa yayi haɗi da zagayawa, jakar  hidaya da kwalin daya amso ya ɗauka ya nufi gate ɗin, ƙofar da ke jikin gate ɗin yayi nocking, mai gadi ne ya buɗe ƙofar, kallon dr kabir yayi yana faɗin
" ranka ya daÉ—e barka da zuwa, an wuni lafiya, ai da kayi horn sai na buÉ—e maka "
"lafiya lau, kar ka damu wuce wa zanyi,  dan Allah wannan saƙon nake so ka ɗan miƙama hidaya"
"to shikenan yallaɓai,amma da ka shiga "
"karka damu , yanzu dai amshi kayan ka kaimata "
ya faÉ—a yana nuna ma maigadin jakar, amsa mai gadin yayi yana faÉ—in
"shikenan  ranka ya daɗe sai anjima" hannu yasa a aljihu ya ciro  5k ya miƙa ma mai gadin yana faɗin sai anjima, hannu mai gadin yasa ya amsa yana yi mashi godiya.

Wurin motar shi ya koma ya shiga,reverse yayi ya bar anguwar, a hankali yake tuƙi har ya kawo wani ƙaton gida yayi horn a bakin gate, maigadi ne ya leƙo yana ganin motar ya koma da gudu haɗi da buɗe mashi gate ɗin, ciki ya shiga da motar a compound yayi parking,yana gama parking ya fito ba tare da ya kashe motar ba a buɗe ya bar ƙofar haka ma key a jiki ya bar shi ya nufi main entrance ɗin gidan.

Gida ne bani da gida ba, babba ne sosai dan ya fi gidan su shazim girma nesa ba kusa ba, part part ne gasu nan bila adadin, tsayawa faɗa maku yana da gidan yake ɓata lokaci ne.
Ma aikatan gidan ne su ka shiga gaishe da shi, hannu kawai yake É—aga masu, dan a yanayin da yake ciki ba zai iya magana ba.
Da sauri wani matashin saurayi ya nufi motar ya kashe  haɗi da buɗe back seat ya ciro mashi briefcase ɗin da laptop, key ɗin ya zare ya rufe motar da sauri ya bi bayan shi.
parlor ne ƙato da royel sofas a ƙalla za su kai set huɗu milk color.
Up stairs ya nufa  matashin saurayin nan na biye da shi da kayan shi da ya kwaso masu, suna zuwa wani ɗan corridor matashi saurayin ya ɗan da kata yana faɗin
" ranka ya daɗe ina zan kai maka kayan? " 
"main parlorn na" shine kawai abun da ya faɗa yayin da yake tura wata ƙofa da ke cikin corridor,juyawa saurayin yayi ya nufi wata ƙofa dake can ƙarshen corridor ya shiga wani parlor,ba laifi yana da girma kamar dai yanda main parlor yake,komai na cikin shi brown color ne, ya tsaru iya tsaruwa, kan tow seater saurayin ya ajiye mashi kayan ya fice.

Ƙaton parlor ne sosai dan da ƙaɗan parlorn da suka fara shigowa zai nuna mashi girma da tsaruwa, wata ƙofa dake facing ɗin shi ya nufa haɗi da tura ƙofar ya shiga,nan ma wani parlor ne ɗan madai daici, lab coat ɗin dake jikin shi ya cire ya yi wurgi da ita kan sofa sannan ya cire top ɗin da ke jikin shi ita ma yayi jifa da ita ya koma daga shi sai dogon wando da riga long sleeve, wani ta ƙofa ya nufa tura ta yayi ya shiga ciki, masha Allah nace da ganin wani danƙareren bedroom dake ɗauke da royel bed mai kyan gaske, komai na cikin bedroom ɗin white color ne, faɗawa yayi kan bed ɗin yayi kwanciyar rub da ciki, ya rasa mike mashi daɗi a duniyar  nan, gaba ɗaya ji yake ya tsani kan shi, magana ya shiga yi da zuciyar shi " miyasa hidaya zaki yi man haka,gaba ɗaya kin gama  zubar man da mutunci, dan mi zaki ƙi ƙarɓar soyayya ta kice wai  shazim kike  so, wai da mi shazim ɗinnan ya fini ne da har zata iya cewa tana son shi amma ni ta ƙi ƙarbar soyayya ta" haka ya cigaba da saƙawa yana kwance wa, daya juya ƙaɗan ya buga tsaki.
turo ƙofar bedroom ɗin akayi wata mata ta shigo, sanye take da less ɗin kin doguwar riga, hannun ta riƙe da kayan shi da ya zubar a parlor, bakin bed ɗin tazo ta tsaya
"Auta mike damun ka ne ka zubar da kaya a parlor sannan ka zo nan ka kwanta, lafiya dai ko?? "
shiru yayi bai ce komai ba, bai kuma juyo ba daga kwanciyar da yayi, kayan da ke hannun ta ta ajiye gefan bed É—in, sannan ta hau kan bed É—in, hannu tasa ta shiga shafa sumar kan shi, cikin lallashi ta fara magana

"wane mai tsautsayin  ne  ya taɓa ɗan gidan momy yau ya kwana a kulle, faɗa man wanene yanzu na ɗau mataki a kan shi kaji ɗan gidan mama,ko na kira yayyen ka ne " shiru yayi nan ma baice mata komai ba

"yanzu Auta har  akwai ɓacin ran da zaka shiga kayi fushi da momyn ka tana magana kayi banza da ita" sai a lokacin ya ɗago da kanshi ya kalle ta ba tare da yace komai ba, murmushi tayi tana faɗin
"mike damun bugun zuciyata ne,faÉ—a man naji yanzu nayi maganin sa?"
hawaye ne suka kwararo daga idon shi, ɗuƙar da kai yayi ƙasa, da sauri ta sa hannu ta taro fuskar shi tana

" ya salam Auta mi zan gani haka, waye ya ɓata maka rai ne har haka yasa ka zubar da hawayen ka,  maza ka faɗa man ko waye yanzu na ɗau mataki saboda saman auta koka da yayi "  faɗawa yayi jikinta yayi hugging ɗinta so tightly, fashewa yayi da kuka kamar wani ƙaramin yaro, shafa bayan shi ta shiga yi

" dan Allah ka dai na wannan kukan ka faÉ—an man abun da ke damun ka, ko so kake nima ka sa ni kukan,kasan kukan ka tashin hankali ne a gare ni"
ajiyar zuciya ya shiga saukewa, cikin muryar kuka ya fara magana ba tare da ya raba jikinshi da nata ba
"momy ashe wahalar banza nake bani take so ba " yana faɗin haka ta fahimci akan hidaya yake magana dan komai na shi na rayuwa ta sani ko shawara zai yi da ita yake yi babu wani sirrin shi da bata sani ba, ba ya iya ɓoye mata komai.

"ban gane ba, itace tace maka bata sonka?"
raba jikin su yayi , komawa yayi ya kwanta ya É—aura kanshi saman laps É—inta, shafa sumar kanshi ta shiga yi
" ka kwantar da han kalinka babana nasan tana sonka, babu wata ƴa mace da zaka ce kana so a duniyar nan ta ƙi amincewa da kai,in sha Allahu hidaya matar ka ce bata da wani miji a duniyar nan bayan kai"

"to ai momy yau da kunne na naji bani take so ba "

"ba kai take so ba, to wa take so?"
"momy shazim wai take so bani ba "
"shazim dai "
"Eh momy, shi tace tana so "
"tofa ana wata ga wata, to shi shazim É—in yana son ta ne"
"A'a momy, ai ya san ina sonta kuma ma anyi mashi mata a familyn su "

"to ai ta kwana gidan sauƙi tun da shi ɗin ba wai yana sonta bane kuma har kace an yi mashi mata "

"amma momy ta zubar man da mutunci, kullum faÉ—i nake tana da kamun kai tana da natsuwa amma ta buÉ—e baki tace ta son wani bani ba "

"kar ka damu ina tuna nin bata san kana sonta bane ai baka faɗa mata ba  "
"momy na faÉ—a mata kin manta ne "

"yanzu dai ka kwantar da hankalin ka, ni zan san yarda zanyi zan sanar da dadyn ku , in sha Allah za ka Aure ta kar ka damu kaji " ta faɗa tana share mashi hawayen da suka ɓata mashi fuska, murmushi tayi haɗi da jan gemun shi tace

"babana kafa girma ka rage wannan yarintar ko so kake ɗiyar tawa ta raina man kai ne " ta faɗa haɗi da   lakuce mashi hanci, murmushi yayi haɗi da cewa
"momy ai bazan yi a gabanta ba, ke kaÉ—ai zan mawa tun da daman ke maganin kuka na ce"
"duk da haka dai, kar ka haifa man jikoki masu kukan banza kamar kai "
murmushi yayi
"momy har kin fara maganar jikoki, duk wanda ke a gaban ki "
"to babana idan ban yi maganr su ba maganar mi ka ke so nayi, jikoki kuma ai na babana na da ban ne  "
"haka ne my lovely mom"
" ta shi kaje ka watsa ruwa, abinci na nan kan dinning yana jiran ka "

"momy ni a nan zanyi" 

"to shikenan tashi kaje kayi, amma ka kusa daina shigar man toilet "

"kai momy, saboda mi?"
"saboda ka girma, ka kusa aje iyali "
ta bashi amsa haɗi da miƙewa ta bar bedroom ɗin, tana fita shima ya tashi ya nufi toilet ɗin, bayan kamar 15 minutes ya fito jikin shi sanye da bathrobe.
Ficew yayi daga bedroom din yanufi parlor ,zaune ya samu momy ita da su ya mustafa ( yayyan shi, su ba kwai  ne y'ay'an momy ,maza biyar mata biyu ,dr kabir shine karamin kanin su shi ka dai ne bai yi aure ba ,ya mustafa shine babba sai umar,khalid,aliyu,safeenah,
azeema sai dr kabir,duk acikin gidan  maza suke zaune da matan su   )
binshi da kallo su ka yi , ya mustafa ne yace " yau ina ganin ikwan Allah ,wai kai da man har yanzu baka girma ba ,wanka a bedroom din momy ko kunya "
  turo baki yayi gaba yana fadin
" wallahi da na san kuna nan da ban fito ba ,haka nan ku hana mutum saket "
rike baki ya umar yayi yana fadin " Allah ya shirye  ka junior"
( da yake haka su ke ce mashi  )
"Ameen" ya ce yana murguÉ—a ma ya umar baki kamar wata mace ,tsaki ya khalid ya ja ba tare da yace komai
ya aliyu kuwa cewa yayi "gaskiya ku kyale shi ya huta,idan bai ma momy da mu  ba wa zai mawa ,ku barshi ya shana wata rana sai labari"
Matsowa kabir yayi kusa da Aliyu yana fadin
"yawwa ya Aliyu shiyyasa nake sonka"
"mu kuma baka son mu ko saboda muna fada maka gaskiya  " ya khalid ya fada
Ya mustafa yace " ai shima jirgi daya ya kwaso su shi da Aliyu,dama ce kawai shima bai samu ba"
"fadi kanka tsaye ,da ace ni ne shi sai nayi abun da yafi wanda yake yi Allah" ya Aliyu ya fada ,momy dai na gefe sai murmushi take tana kallon su.
Ya Aliyu ne yace " kaji Autan momy ta shi kaje ka sa kaya ka dawo na san baka ci abinci ba ,kazo da kai na zan baka a baki "
"Allah dai wadaran naka ya  lalace ,yanzu wannan katon zaka ba abinci a baki amma dai gaskiya kaji kunya Aliyu "
"A'a ya khalid bari ,wane irin naji kunya ba wata kunya da naji kanina ne fa  ko ba haka ba momy " ya fada yana kallon momy dake bin su da ido
"rabu da shi Aliyu na lura adawa yake da babana"
"haba momy wane irin adawa ,wannan katon ne zai ba abinci a baki "
"Ai ba haramun ba ne ,idan kai bazaka bashi ba ,sai ka bar mai bashi ya bashi "
"Allah ma ya kiyaye na zauna ina ba junior abinci a baki sai kace ban da aikin yin "
"to ni zan bashi idan kai bazaka iya ba,je ka sa kaya kaji Autan momy  " ya Aliyu ya fada yana kallon dr kabir

gwalo dr kabir yayi ma ya khalid ,tsaki ya khalid din yaja yana fadin

" wallahi kaji kunya kato da kai kana abu sai kace wata mace "
Dariya su ya mustafa su kayi suna fadin

" da gaske dai adawa kake da shi "

Tsaki ya khalid yaja ba tare da yace masu komai ba ,kwata kwata baya son ganin kabir na taɓara  abun haushi yake bashi .

Shaf shaf ya sa kaya ya dawo parlorn samun su yayi zaune a dinning su duka har da dady wanda shigowar shi kenan ,kusa da dady yaje ya zauna ,shafa kanshi dady yayi yana fadin
"likita bokan turai yau da wuri aka dawo kenan? "
"Eh dady"
"sannu to ,ya aikin?"
"Alhmdllh dady"
"to masha Allah" dadyn ya fad'a
"juyo na baka abincin kar ya khalid yaji dadi"
ya Aliyu ya fada yayin da yake d'ebo abincin a spoon ,bude baki  kabir yayi ya Aliyu na ba shi a baki dady ma na bashi sai murmushi yake yana ma ya khalid dake jifan shi da harara  gwalo ,karshe dai daya gaji da ganin abun kunya  jifan shi yayi da spoon da sauri ya duke yana fadin " wayyo Allah dady zai cire man ido "
"wallahi zan sa k'afar wando d'aya da kai khalid idan baka fita harkar junior ba "
"haba dady baka ga yanda ya  k'ara sangar cewa ba kuma fa duk dan kuna goya mashi baya ne "

"An goya mashi bayan " momy ta fad'a ,shiru khalid yayi bai sake cewa komai ba, dr kuwa sai murmushi yake  kamar wani zautacce

Haka suka cigaba da lunch suna fira cikin ni sha di ,da suka gama ma kan sofa su ka koma momy ke sanar da dady maganar hidaya, haƙuri ya ba dr ya kuma ce in sha Allah zaiyi iya bakin ƙoƙarin shi ganin ya amsar mashi auren hidaya, da dady ya faɗi haka da sauri ya rungume shi yana faɗin
"na gode sosai dady " saboda sangarta da rashin kunya har da su rawa.
Su ya mustafa nayi mashi dariya, ya khalid kuwa ban da tsaki babu abun da yake.

Wannan ahali akwai nisha ɗi a tattare da rayuwar su, Allah ya dawwamar da farin cikin a gare su, hidaya ina taya ki murna idan kika shigo wanna ahali mata ga junior ɗan gata momy da dady da su ya khalid 😜.
Haka suka cigaba da fira cikin nishaÉ—i sai da lokacin sallah yayi tukun suka nufi masallaci.

_*✨HIDAYA✨*_

"Wai hidaya zaki buɗe ƙofar nan ne ko sai ranki ya ɓaci"

zuwa tayi ta buɗe ƙofar idanuwan ta duk a kumbure alamar taci kuka, tana buɗe ƙofar ta koma ciki, bin bayan ta ummah tayi tana faɗin
"yanzu abun da ki ka yi kina ganin shi ne dai dai ko, wai zaki faÉ—a man abunda ke damunki ko sai na kira Abban ku"

"Ummah kai na ne ke man ciwo "

"Ƙarya kike hidaya,har ni zaki ɓoye ma damuwar ki  "

"umma ki yarda da ni kaina ke man ciwo "
Shikenan shine abun da ummah ta faÉ—a
"kije to ki watsa ruwa kizo ki ci abinci ki sha magani " ummah na gama faÉ—a ta fice ta bar bedroom É—in, komawa tayi ta kwanta a rigingine kanta na kallon ceiling , tayi shiru gaba É—aya ta rasa mike damunta, dagaske dr kabir yake anyi ma shazim mata a familyn su,hawaye ne suka gangaro mata daga cikin idanuwanta, hannu tasa ta share
turo ƙofar ɗakin akayi, tsaye tayi tana binta da kallon daga baya ta shigo, zama tayi kan bed ɗin, ta dai ji almar shigowar mutum amma bata san waye ba duk a tunanin ta umma ce, sai da taji shiru ne yasa ta tashi daga kwanciyar, zuba mata ido maryam tayi tana kallon ta
"lafiya kike man wannan kallon " ta faÉ—a cikin kasalalliyar murya
"idan ma da akwai abun da yafi kallo kin cancanta hidaya,yanzu kan dr kike son sama kanki ciwan da zai zame maki masifa a rayuwa, miyasa bazaki rabu da shi ki kama wanda ke sonki naga dai ba wani abu da dr shazim zai nuna ma dr kabir, kuma tun da ki kaga kina roƙon Allah a amma kuma baki samu abun da kike so ba, ki haƙura mana inaga haka shine mafi alkairi a rayuwar ki "
"maryam amma kin fi kowa sanin yanda nake son dr, mi zai sa kice in rabu dashi "

"idan baki rabu da shi ba ya zakiyi hidaya, bafa a so dole kin sani, tun da ki ka ga ya nuna baya ra'ayin ki ki haƙura mana ko dan ki samama kanki sauƙi"

"ni dai shawarar da zan baki shine ki fitar da shi a zuciyar ki,ki roƙi Allah idan har dr kabir alkairine a rayuwar ki Allah ya tabbatar maki amma idan kinji "

"maganar gaskiya ina son dr so mai ƙarfi wanda nake jin bazan iya daina son shi ba "

"to aikuwa kina da aiki mai girma a gaban ki"

"ba wani aiki,in sha zan cigaba da roƙon Allah wataran na san zai so ni "

"gaskiya hidaya baki cikin hankalin ki, naga Allah kika roƙa akan idan shi ba alkairi bane a rayuwar ki ya sauya maki da alkairi, yanzu ga alkairin ya zo amma kin kasa fuskantar gaskiya "

"bazan ɓoye maki ba maryam wallahi bana son dr kabir  idan nace na amince da soyayyar sa zan cutar da kaina ne kawai tunda bana son shi "

"ba cewa nayi ki amince da shi ba, A'a ina son ki fitar da tunanin dr shazim a zuciyar ki ki roƙi Allah idan har dr kabir alkairine Allah ya tabbatar maki, amma kina ɓata lokacin ki ne akan shazim "

"bazaki gane yanda nake jinshi bane a raina maryam"

"bazan gane ba ko dai bazaki gane ba " 
Haka suka cigaba da magana a tsakanin su  kowa so yake ɗan uwan shi ya fahince shi har dai ummah ta shigo ta same su, tana shigowa su kayi shiru binsu da idanu tayi daga baya tace,
"maryam É—an bamu minti biyu babanta na san magana da ita " da to maryam ta amsa, kallon hidaya ummah tayi tace

"ta shi ki wuce Abban ku na kira"  gabanta ne ya faɗi , yanzu idan Abba ya tambayeta mike damun ta mi zata ce mashi

"ummah nace maki fa kaina ne kawai yake ciwo "

"zaki tashi ki wuce ko kuwa " tashi tayi ta nufi ƙofa ta fice zuwa parlorn Abban ta zaune ta same shi kan carpet yana duba jarida, sallama tayi ta shiga ciki, amsa mata sallamar yayi yana nuna mata wurin zama, zama tayi inda ya nuna mata kusa da shi, gaishe da shi tafa ra daga bisani tace "Abbah gani ummah tace kana kira na"

"miyasa kika dawo gida yau da wuri,  sannan mi ya sameki a wurin aikin na ku da har yasa kika dawo gida kina kuka, sannan miye haɗin ki da kabiru ɗan gidan minister mai wada daya kawo maki jakar ki sannan wannan kwalin na minene ??? " ya faɗa yana nuna mata jakarta da wani ƙaton kwali  da ke gefan shi.

gabanta ne yayi wani mumunnan faÉ—uwa jikake daram, a zuciyar sai faÉ—in " mi ya kawo dr gidan nan sannan wannan kwalin na minene " katse mata tunani yayi ta hanyar cewa
"da ke nake magana kinyi man shiru "

"Abbah bana jin daÉ—i ne kaina na ciwo shine na dawo gida"

"to shi wannan kwalin na minene??, hidaya kin san dai bana wasa da ke ko? "

_lokacin da dr kabir ya zo ashe Abba na bayan shi harya bada jakar da kwalin, da ya tafi ne ya tambayi mai gadi kayan miye kabir ya bashi, a nan ya sanar dashi cewa hidaya yace a ba_

"Eh Abbah da gaske nake maka bana lafiya ne shine ya ɗauko man jakata wannan kayan kuma na maryam ne  "

"Yau kika fara rashin lafiya ne da zaki kama kuka "  shiru tayi

"idan kika bari na bincika na gano ta ƙamaimai abun da ke damunki baza kiji da daɗi ba "

" da gaske nake Abbah "

" shikenan É—auki jakar ki da kwalin ki wuce"

da to ta amsa haɗi da ɗaukar jakarta da kwalin  ta fice, da ummah taci karo zata shiga part ɗin Abbah , fuskarta  a ɗaure  babu alamun sassauci, fasa shiga tayi tace " biyo ni ina son magana dake " kawai ta faɗa, ajiye kwalin tayi a main parlor ta  bi bayan ummah har bedroom ɗin ta, tsaye ta samu ummah a bakin gado, kallon ta ummah tayi tace.
" hidaya miye haÉ—in ki da kabir yaron mai wada?"
" ummah ba komai "
" kar kiyi man ƙarya hidaya,  maryam ta sanar dani duk abun da ke faruwa"
"ummah maryam ƙarya take"
"ƙarya?  , maryam ɗin ce zata yi maki ƙarya "
"A'a ummah"
"ki shiga hankalin ki dani hidaya kinji na faÉ—a maki "
"to ummah "
"tafi amma ba wai mun gama maganar bane kina jina ko "
"eh ummah " ta faÉ—a haÉ—i da kama hanya ta fice, da idanu ummah ta bita hara ta fice.

ɗaukar kwalin tayi da jakar ta ta wuce ɗakin ta, zaune ta samu maryam kamar yanda ta bar ta ɗazu, mai da ƙofar ɗakin tayi ta rufe, tana zuwa tsakiyar ɗakin tayi jifa da kwalin harda jakar ta, da sauri maryam ta kalleta tana faɗin

" ke kuma lafiya miya same ki ki ke jifa da kaya"
"Ki barni kawai maryam, wai ashe dr gidannan ya zo har Abba ya ganshi " wani wawan tsaki maryam ta ja tana faÉ—in
"aikin banza da wofi, shine zaki shigo kina wannan jifar da kaya, wai dan Allah miye laifin wanda yace yana sonka ne, kuma kema kin sani in ban da so na so ba wallahi bazai ce yana sonki ba dan kin fi kowa sanin shi ba sa'anki ba ne,kawai dan Allah ya jarabce shi da son ki shine zaki riƙa yi mashi wannan wulaƙan cin"
"maryam na lura bazaki taɓa fahimta ta ba "
"in dai akan wannan haukan da kike yi ne bazan taɓa fahitarki ba, kuma ki sani zan sanar da ummah duk abun da ke faruwa tsakanin ki da dr shazim kin dai san abun da zai biyo baya idan taji kin buɗe baki kince kina son wani ɗa namiji "
" maryam bana son irin wannan wasan, ke yanzu sai ki faÉ—a mata "
"kina wasa ne ki cigaba da wulaƙanta dr ki gani idan ban faɗa mata ba, ke  har ma abun da bakiyi ba sai nace kinyi wallahi"
"komai zakice sai dai kice, amma maganar gaskiya bana jin son dr a zuciya ta "
"zaki ma koya ne malama, kwalin minene wannan da ki ka jefar " maryam ta faɗa yayin da take nufar kwalin da ke ƙasa yashe, ɗaukar shi tayi ta buɗe,  wani kyakyawan teddy bear ne pink sai heart fari a gaban cikin shi   an rubuta am sorry dear da baƙin fenti, kwashewa maryam tayi da dariya tana faɗin
" soyayya ruwan zuma, lallai dr " ta fa É—a haÉ—i da sake buÉ—e kwalin ta fito da sauran kayan da ke ciki, sweet ne da uban chocolate masu É—auke da sorry a jikin ledojin su, ba maryam ba har ita kanta hidayar sai data dara.
Episode  58_59_

"Amma fa dr na matuƙar son ki hidaya " maryam ta faɗa yayin da take buɗe wani chocolate ta kai baki, taɓe baki hidaya tayi
"ke ki kaga haka "
"wai ke haryanzu kina a kan bakanki na baki son shi "
Kwanciya tayi haÉ—i da juya mata baya batare da tace komai ba, binta da ido maryam tayi tana faÉ—in
"karki fasa zaki sha mamakin abun da zanyi maki kuwa "
"ke maryam kin daÉ—e ko mi za kiyi ana so dole ne "
"haka ki kace? "
"eh haka nace "
tashi maryam tayi zata fice, da sauri hidaya ta riƙota
"wai ke Æ´anzu ko kunya bakiji sai kije ki faÉ—ama ummah "
"sakar ni" maryam ɗin ta faɗa taba fisgewa daga riƙon da hidayar tayi mata ta nufi ƙofa, a sukwane hidayar ta rigata isa bakin ƙofar, abun ma dariya ya so ba maryam amma sai ta ɗaure fuska bata yi ba tace " ki matsa man a gabana "
"wallahi bazan matsaba tun da ke baki san wasa ba "
"wasa ko zakiga wasa " maryam ɗin ta faɗa tana ƙoƙarin janye hidaya
"dan Allah maryam kiyi haƙuri wasa fa nake "
"Ina ruwana da wasanki ni bani hanya na wuce " haka su kai ta jayayya har ummah tayi nocking ta hidaya sai roƙon maryam take akan dan Allah kar ta faɗa ma ummah, gajiya ummah tayi ta sake wani  nocking ɗin tana faɗin
"wai lafiya kuke da baza ku buɗe man ba " da sauri hidaya tasa hannu ta buɗe tana yima maryam alama da da ido akan dan Allah kar ta faɗa ma ummah, ummah na shigowa kallon su tayi tana faɗin "ku lafiya  naga duk kunyi wani tsaye cirko cirko " hidaya ce tayi carb tace
" ba komai ummah magana muke"
"maganar ce har sai kun zo bakin ƙofa? "
maryam tace " tafiya zanyi ne daman"
"tun yanzu zaki tafi maryam?, ga abinci can a dinning, ki bari sai kinci sai ki wuce gida "
" naci abinci ummah kafin na fito daga gida  daman saboda naga ta dawo ne da wuri kuma ina kiranta bata ɗauka ba  yasa nayi tunanin ko lafiya "
"to shikenan, ki gaishe da mamar ku "
"za taji insha Allah " jinjina kai ummah tayi haÉ—i da ficewa ta ba É—akin
"shine zaki wani ce zaki tafi "
"idan ban tafi ba mizan yi maki ne, ko so kike na zauna ki cigaba da ɓata man rai "
"haba dan Allah wane irin ɓacin rai kuma "
"koma dai minene ni tafiya zanyi "
"Amma ai kin tsaya na baki wancan kayan "
"bana so" shine kawai abun da maryam ta faɗa ƙofar ta nufa ta buɗe bin bayan ta hidaya tayi tana bata haƙuri amma taƙi sauraronta,ba yanda ta iya haka maryam ta tafi ba tare da ta amshi chocolate ɗin ba ko ban kwannan arziƙi ba su yi ba, juyawa tayi ta koma ciki dinning  ta nufa wurin ummah .

_*✨KATSINA✨*_

Abie ne da uncle Ahmad da uncle mustafa zaune a parlorn suna magana

Uncle mustafa ne yace

" yaya yanzu yaushe zaka tafi kenan"
Amsa Abie ya bashi da

"da wannan week É—in nace amma yanzu ina jin sai wani week É—in saboda safwan da za su zo gobe "

"to shikenan Allah ya kaimu " da Ameen abie ya amsa,

uncle Ahmad ne yace

" wai yaya idan sun zo su safwan É—in anan za su zauna?"

"eh mana Ahmad idan ba nan ba ina zasu zauna "
"a gaskiya yaya da zaka ji shawara ta da ba su zauna anan ba "
"saboda mi? "
"yaya bawan Allah rayuwar shi tana cikin hatsari, sai nake ganin zaman shi a nan kamar akwai gangance "
"Ahmad bawani gangance nasan da lilin da yasa nace ya zauna nan "
"to shikenan yaya,bawani abu Allah ya bashi lafiya "

"Ameen shi ne kawai, yaushe zaka koma Abuja ne " abie ya tambaya
"tunani nake ranar friday zan tafi "

"ok Allah ya kaimu, wai addimisson É—in su Aaimah shiru "

Uncle Ahmad yace
"Inajin fa basu fara ba dawa ba kuma kaga late aka nemar masu addimisson É—in Amma na san bazai wuce wannan week É—in ba tun da makarantar next month su ke fara lectures "
"to shikenan Allah ya kaimu " da Ameen su ka amsa su duka, dadi ce ta fito ta zo wurin su ta zauna kan sofa gaishe da ita su kayi, amsa wa tayi da kulawa a fuskar sannan tace
" mi ake tattaunawa ne tun É—azu? "
uncle Ahmad ne yace " magana muke ta yanda zamu nemo maki yaron ki "

"mai makon naji kunce kun nemo shi sai kuce magana ku ke ta yanda zaku nemo shi, na lura so kuke mu sa ƙafar wando ɗaya da ku kafin ku nemo shi "
Abie ne yace
"ba sai an kai ga haka ba"
"to yauahe zaku kawo man shi gidannan? "
"in sha Allahu nan bada jimawaba, da wannan satin zan tafi kadunar to amma saboda zuwan su safwan yasa na fasa sai wani satin"

"Allah sarki gobe ne kenan zasu zo, to Allah ya kawo su lafiya "
"Ameen " su ka amsa su duka, fira suka shiga yi cikin nisha É—in har sai da lokacin sallar zuhur yayi sannan suka nufi masallaci dadi kuma ta nufi É—akin ta.

_*✨SHAZIM✨*_

Lokacin da hidaya ta fita daga office ɗin shi bai wani jima ba shima  ya nufi Abnoor 
Aiki yayi sosai sai daga baya yanufi office ɗin majeed,bai same shi a ciki ba hakan yasa yayi tunanin ko yana duba patient ne  zama yayi kan sofa yana jiran ya dawo, wayar shi dake ringing ya jawo duba mai kiran yayi, Mansoor ne, picking kiran yayi sallama yayi, amsawa mansoor ɗin yayi yana faɗin

"kai dai babu ruwanka da neman mutane, idan mutum bai nemeka ba shikenan kai ba ruwan ka da shi "
É—an yatsine fuska yayi yace
"kai ai na lura neman mutanen kake yi "

"gashi kuwa na neme ka "

"to naji,  yaushe ne ma kace zaka zo "
"ok ka ma manta yaushe nace zan zo, nalura kamar baka son zuwana saboda zan zo na É—auke maka habibtyn ka "

"wait mansoor idan ba so kake nayi maka rashin mutunci ba to ka daina haÉ—a ni da wannan sakaryar yarinyar"

"lallaima shazim sakaryar kace?"
"ƙwarai kuwa ba sakayar bace, ni da zaka taimaka wallahi da zuwa kayi yau ka tattarata ka mai da ma iyayenta ita dan nagaji da zama da muke yi a gida ɗaya "
"Amma nayi mamaki shazim ko da ace yau baka san taba ai baka faÉ—i haka ba, bare ma tana Æ´ar uwar ka "
"ni dai da zaka taimaka da kazo gobe ka tafi da ita "
"bazan zo ba É—an rainin wayau, idan da gaske ne ka gaji da zama da ita ka dawo da ita da kan ka"
"bana da wannan lokacin kuma "
"to nima bana da shi "
"Alright haka kace "
"Kwarai ma kuwa " yana faÉ—ar haka yayi rejecting kiran, murmushi gefan baki yayi haÉ—i da cire wayar daga kunnan shi, kwanciya yayi kan sofar latsar wayar shi ya shiga yi, anan majeed ya shigo ya same shi, zama yayi yana faÉ—in
" yaushe ka shigo?"
hannu ya miƙa mashi su kayi musabaha
" tun É—an É—azu na shigo "
"Ok naje duba patient ne, lafiya dai ko"
" lafiya, maganar waÉ—an nan kayance nake so muyi "
" ok , wanda ke hannun mu ko wanda kace a tura "
" eh wanda nace ku aika "
"anyi kamar yanda kace"
"yawwa nagode sosai "
"Amma shazim baka gani gara mu miƙa kayan nan hannun ƙungiyar drugs Abuse"
"a'a majeed, idan mu kayi haka kamar mun ba masu kayan kayan su ne, kasan yanda cin hanci yayi yawa a ƙasar nan muna bada kayan nan masu su za su fito ne su bada cin hanci su amshi kayan su "
"haka ne, amma to idan mun bar su nan mi za muyi da su"
"ba abun da za muyi da su, kawai ina son yin amfani da su ne wajen gane mai kayan daga nan sai na ɗauki matakin  da ya dace akan shi "
"to shikenan, amma a canza masu wurin zama daga store "
"ka jika da wata magana, idan ba nan ba ina zamu kai su, a nan zamu bar su har Allah ya toni asirin masu su"
"shikenan " majeed ya faɗa canza firar su kayi zuwa wata, ana kiran sallar asr su ka fita su ka nufi masallaci, da suka gama sallah majeed office ɗin shi  ya koma shazim kuma yace mashi briefcase ɗin shi kawai zai ɗauka gida yake son ya koma saboda fatima, sallama su kayi majeed na faɗin yana gaishe da fatimar.

Yana shiga office ɗin kamar yanda yace briefcase ɗin kawai ya ɗauka ya rufe office ɗin, motar shi da yayi parking a parking lot ya nufa, shiga yayi yayi mata key haɗin da yin reverse ya nufi gate , mai gadi na ganin shi  da sauri ya tashi ya  buɗe mashi gate ɗin , yana ɗaga mashi hannu har ya bar hopital ɗin.
yana fita wata ɓakar jeep ta fito daga bayan Abnoor, ta mirror ya hange ta abun yaso ya bashi mamaki saboda ya san bawani titi ko wani gida da mota zata iya fitowa daga wurin, tuƙi yake yana kallon motar  da farko yayi tunanin hanya ce ta biyo da ita may be ko matsala ta samu ne yasa ta tsaya a bayan Abnoor ɗin, sai da yaga ya bar titin abnoor ɗin ya hau wanda zai kai shi gida yaga motar tana nan tana binshi, tafiya ya fariyi a slowly abun mamaki sai kawai yaga mai motar yayi parking,murmushi ne ya so kufce mashi dan abun yayi matuƙar bashi mamaki, key yayi ma motar ya cigaba da tafiya, shima mai jeep ɗin key yayi mata ganin haka ne yasa shi yin kwana ya sauka daga titin da zai kaishi gida, shima mai motar canza hanya yayi zuwa wacce shazim ɗin ya bi, yanke shawara kawai shazim yayi daya tsaya ya ga ko waye ke binsa a baya, gangarawa yayi bakin hanya yayi parking kashe motar yayi ta zare key ɗin motar ya fito, mai motar na ganin ya fito da sauri yayi reverse ya a wani irin masifan gudu ya shiga wata kwana, jinjina kai yayi yana faɗin "ƙaramin ɗan iska ai da ka tsaya sai naji dalilin bin nawa da kake " komawa yayi cikin motar ya kama hanyar gidan malam, yana isowa horn yayi mai gadi ya buɗe mashi, ciki ya shiga , parking yayi sannan ya fito ya shiga ciki, parlorn ummy ya fara zuwa zaune ya sameta ita da mai aikinta tana ɗan daddana mata ƙafa saboda fama takeyi da su kwana biyu, ƙarasawa yayi ciki bakin shi ɗauke da sallama
Amsa sallamar da yayi ummy tayi tana faɗin " lale marhabun da bokan turai "  wuri ya samu kan sofa kusa da ita ya zauna, mai akin ummy ce tace " ina wuni "
"lafiya lau "
ya amsa mata haÉ—in da kallon ummy yace

"ina wuni ummy, ya ƙafafun "
"da sauƙi ya aiki "
"Alhmdllh"
"ya fatima da jiki "
"Alhmdllh taji sauƙi sosai "
"to masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi "
"Ameen "  sun ɗan jima suna taɓa fira da ummy kafin daga bisani ya nufi part ɗin malam

Samun shi yayi a kan carpet yana duba wani littafi,sallama yayi mashi haɗi da ƙarasawa ciki ya samu wuri ya zauna kan carpet ɗin, amsa sallamar malam yayi sannan yace
"daga ina haka da yamma "
"daga Abnoor nake, shine nace bari nazo na duba ku kai da ummy "
"ai kuwa ka kyauta,ina nuraddeen da fatima "
"Fatima dai na gida, noraiz kuwa yana mall kasan yanzu noraiz an daina zaman banza"
murmushi malam yayi yana faÉ—in " haka ne kam aboki na an girma yanzu ba'a zaman banza, to Allah ya taimaka"
"Ameen "
"fatima jiki yayi sauƙi ko "
"ta samu sauƙi ba inda bata zuwa yanzu "
"to Allah ya ƙara sauƙi"
"Ameen "
"yaushe zata fara zuwa makaranta? " malam ya tambaya
"in sha Allah nan da wani watan zasu fara karatu, da yake makarantar basu jima da bata addimisson ba "

"Ah abu yayi kyau Allah ya kaimu nan da wani wata "
" Ameen malam"
"ya wajen su kawun ka sun sake kiranka kuwa "
"A'a ba wanda ya kira ni cikin su " ya faɗi hakan kawai saboda bai son malam na mashi maganar yayi haƙuri ya ƙyale su
"shazim kenan,  ina so kasa haƙuri a zuciyar ka, ko jiya Ahmad ya kirani yace suna nemaka ba su samun ka, abun da ya faru shazim yariga da ya faru tun da yaron nan yayi nadamar abun da yayi kayi haƙuri mana, yanke alaƙa da su bai da amfani su ɗin jinnin ka ne "
"amma ai malam su basu ganin haka"
"wayace maka basu gani sun sani kuma duk wani abu da kaga suna yi maka suna yi ne dan suna sonka a matsayin ka na É—an É—an uwan su "
"malam kai kaÉ—ai kake fahimtar haka, amma su ba haka bane a ransu"
"idan zaka biye wannan tunanin naka bazaka taɓa fahimtar abun da nake so ka fahimta ba"
" malam na fahimce ka kuma nasan mi kake nufi"
"da ka fahimta da baka É—auki wannan fushin da kake yi da su ba, ko ka manta lokacin da kana yaro miye wanda uba ke yima Æ´aÆ´anshi wanda Ibrahim bai yi maku ba"
"malam baka san waye uncle Ibrahim ba shiyyasa kake cewa haka, kawai yayi ne saboda wani dalilin shi "

"hmmm lallai shazim,duk da ban zauna da Ibrahim ba sosai amma ina tabbatar maka da cewa mahaifiyar shi da yayan shi kaɗai za su nuna man sanin Ibrahim,suma sai dai su nuna man wani amma Ibrahim na san shi sani bana wasa ba, a halayen shi babu wanda ban sani ba, ko ƴan uwan nashi basu san shi da shi ba, tun da kaji nace kayi haƙuri ka maida komai ba komai ba kayi hakan kawai"

"shikenan malam,  amma wane hali ne nashi wanda ka sani har kake cewa ƴan uwan shi basu san shi da shi ba?"

"abun da ya wuce shazim ya riga da ya wuce sai dai kuma mu fuskanci gaba "
"Amma malam da ka sanar da ni "
"ka kwantar da hankalinka, idan akwai ƙaddarar ka sani zaka sani, amma karka sama ranka wani abu ba komai bane fatana kawai ka daina wannan fushin mara amfani da kake yi da su "
"shikenan malam in sha Allah zan dai na"
"kaji É—an albarka ko kai fa " malam ya faÉ—a yana shafa kan sa, canza firar suka yi zuwa wata, ya jima sosai a gidan,sai bayan da yayi sallar magrib sannan yayima malam da ummy sallama ya kama hanyar gida,
yana shigowa layin su ya hangi wannan baƙar jeep ɗin tayi parking a ƙofar gidan su mai gadi na tsaye bakin motar da alama magana su ke da mai motar, ƙarasawa yayi bakin gate ɗin, mai gadin na ganin shi da sauri ya nufi gate ya buɗe mashi, ko kallon inda jeep ɗin nan take bai yiba ya shige ciki, yana shigewa mai gadi ya maida gate ɗin ya rufe, parking yayi a compound kashe motar kawai yayi ba tare da ya ɗauki kayan shi dake ciki ba ya fito ya nufi mai gadi dake ƙoƙarin ficewa zuwa wurin wannan mai jeep ɗin, da hannu ya dakatar da shi,alama yayi mashi da ya zo, da sauri   mai gadin ya nufo shi,yana isowa yace " barka da dawowa ranaka ya daɗe "
ba tare da ya amsa mashi ba ya jifa mashi tambaya
"wanene a bakin gate da na ganku a tare? "
"wani mutumi ne"
"wani mutumi? kana nufin baka san shi ba"
"eh ranka ya daÉ—e "
"ok, maganar mi na hango ku kuna yi? "
"tambaya ta yake wai da yaushe zaka dawo gida, to shine sai gaka ka dawo "

"shine kawai abun da na hango ku kuna tattaunawa " da sauri mai gadin yace
"eh shine ranka ya daÉ—e"
"am wama kake da suna ina fatan kasan halina, ka faÉ—a man maganar da kuke tattaunawa da shi karka bari nayi bincike na gano gaskiya"

"yallaɓai dai Allah kayi haƙuri, wallahi ina tsoron matakin da zaka ɗauka a kaina, amma maganar gaskiya ya tambaye ni ne akan   wai kai ke da asibitin abnoor, nace mashi eh naka ne to shine yace wai mahaifiyar shi ce bata da lafiya wai yaji ance a asibitin ka kuna duba marasa lafiya a kyauta wai bai san ta yanda zaiyi magana da kai ba shine yake so wai dan Allah na bashi wani haske ta yanda zai samu ayi ma mahaifiyar shi aiki"
"wane kalar haske kenan"
"wai so yake na haÉ—a shi da Ammy, to dana ji yace haka ne sai nace yaje asibitin ya kai ta za'a du bata ba dole sai Ammy ta sa baki ba, shine yace wai zai bani dubu É—ari dan na haÉ—a shi da Ammy "
"sai kace mashi mi kenan"
"zan bashi amsa ne sai gaka ka dawo"
"ok shine kawai abun da kuka tattauna"
"shine kawai ranka ya daÉ—e"
"to amma mi yasa naga kana ƙoƙarin komawa wurin shi "
"zan koma nace mashi ne idan da gaske yake ya zo ya sameka kuyi magana, "
"zaka iya tafiya, amma ba sai ka koma wurin shi ba  "
"to shikenan nagode" mai gadin ya faɗa haɗi da komawa bakin ƙofar ɗakin shi ya zauna .

Ciki shazim ya shiga,ba kowa a main parlorn , sama ya nufa zuwa part ɗin shi, yana tura ƙofar ya shiga wani ƙamshi ne ya bigi hancin shi,ba irin wanda ya saba ji a ɗakin , wani irin ƙamshi ne gashinan dai, bin ko ina na ɗakin ya shiga yi da kallo sai gani yayi kamar an canza mashi fasali , azuciyar shi yace
"wannan wane irin ƙamshi ne haka" ya faɗa  haɗi da nufar   bedroom ɗin  shi nan ma  ƙamshin yaji irin na parlorn, mai da ƙofar ɗakin yayi ya rufe , gaba ɗaya ƙamshin ya addabe sa dressing mirror ɗin shi ya nufa inda yake ajiye room fresheners ya jawo ƴar locker room fresheners ne iri iri a cikin locker, daya daga cikin su ne ya ɗauka haɗi da maida locker ya rufe, fesa room freshener ya shiga yi  sai da ya tabbatar ya canza ma ɗakin iskar shaƙa tukun ya maida turaren wurin zaman shi, kayan jikin shi ya shiga ragewa, toilet ya nufa bayan minti biyar ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani a hannun shi yana goge  kanshi, ajiye towel ɗin yayi daya gama guge kansa,zama yayi kan kujerar dake bakin dressing mirror ɗin nan ya shiga shafe shafen shi sai da ya ɗauki kusan minti biyar zaune yana abu guda daga baya ya nufi corridor da wardrobe ɗin sa take,ash ɗin jallabiya ya ɗauko ya sa, komawa yayi bakin dressing mirror ya feshe jikin shi da turare, yana shirin barin wurin yaji anturo ƙofar bedroom ta ciki mirror ya zuba ido dan   ganin wanene wannan da ya fi ƙarfin yi mashi nocking, a iya sanin shi dai ko Ammy bata shigar mashi ɗaki babu nocking, turo ƙofar tayi ta shigo hannunta ɗauke da tray data shirya mashi abinci, zuba mata ido yayi yana kallonta ta cikin mirror har ta gama shigowa ta nufi ɗan table ɗin dake tsakiyar ɗakin ta ajiye mashi juyowa tayi tace " dinner ne na kawo maka " banza yayi da ita kamar ma bai san da zamanta a ɗakin ba, matsowa tayi kusa da shi kamar zata shige jikinsa tana faɗin " ya shazim wai minene matsalar, ina sonka kuma kaima nasan kana sona,so banga wani abu aciki ba da zaka rinƙa wulaƙanta ni " baƙaramin ɓaci ranshi yayi ba wai yau wannan yarinyar ce ta samu power har ta iya tsayawa a gabanshi tana faɗa mashi waɗannan maganganun, bai gama fita daga mamaki ba yaji ta kai mashi runguma ta baya.
Episode  _60_61

"Please duk ka ajiye wani fushi a gefe da kake yi dani,abun da ya wuce ai ya riga da ya wuce " ta faɗa tana wani ƙara manne mashi ajiki haɗi  da  zagayo da hannunta tana shafa ƙirjinsa,wani irin mumunnan ɓacin rai ne ya rufeshi har bai san lokacin da yayi wurigi da ita ba, bata faɗa kan komai ba sai kan table ɗin dake tsakiyar ɗakin gaba ɗaya ta kifa kan tray da tashigo da shi,kafa abinci ya zube ajikinta, azabar zafin abincin  da taji ne yasa ta fasa wata uwa ƙara gashi hannunta ya bugu sosai, bata gama dawowa hayyacin ta ba ya ɗago da ita wanke ta yayi  da lafiyayyun maruka har sau huɗu tangal tangal ta shiga yi juwa ta kwashe ta sai ƙasa jikake tim ta faɗi ba ƙaramin buguwa ƙugunta yayi ba, fashewa tayi da wani matsannancin kuka tana faɗin " wayyo Allah nah momy zai kashe ni, na bani innah ki zo ki taimake ni ya ɓallaman ƙugu "
tsawa ya daka mata yana faɗin " tashi ki fita ki bani wuri  kafin ranki ya ɓaci" wani kukan ta sake fashewa da shi dan bazata iya tashi ba dan ba ƙaramin azaba take ji a ƙugunta ba gashi idanuwan ta bata wani gani sosai saboda marukan da yayi mata har jini ya kwanta gefan indonta na hagu,ganin bata da niyyar tashine yasa shi jan hannunta data bugu ƙiyyy ya jata har bakin ƙofa yana zuwa yayi wurgi da ita wani ihu ta kwala zaiyi wuya ace su Ammy basu ji ta ba, dan kware baki tayi sai ihu take tana ta bani ta lalace hannunta ƙugunta,maida ƙofar bedroom ɗinshi yayi ya rufe nan ya barta sai kuka take tana kiran su Kairiyya su zo su kawo mata ɗauki.
Noraiz ne ya shigo a sukwane jin ihun mutum,  bai ɗauki murya ba ya dai ji ihu da koke koke  sunyi yawa kuma a part ɗin yayan shi, hakan ne yasa shi shigowa a guje,a nan durƙushe ya sameta sai kuka take
"wai wacece ke wannan ihun lafiya?,mi ya sameki?"  bata bashi amsar tambayar da yayi mata ba sai ma sake fashewa da wani kukan da tayi, su fatima ne suka banko ƙofar ɗakin  har rigen rigen shigowa suke Ammy na bayan su, noraiz sai magana yake mata, amma taƙi shiru gashi bai gane ko wacece a cikin su ba  bare ma ya san minene ke damun ta, sai da ya ga shigowar su kairiyya sannan ya fahimci cewa ita ce,tsaki yaja haɗi da cewa
"yo wai ashe ke ce ki ka wani addabi mutane da ihu, ai ba wani ya aiko ki part ɗin nasa ba koma mi yayi maki wallahi Allah ya ƙara " abun da yasa ya faɗi haka yasan dole ita da  shazim ne wani abun tayi mashi har yayi mata
"wane irin sakarci ne wannan noraiz, bakaga halin da take ciki ba kake mata Allah ya ƙara,kenan ma kasan abun da ya sameta?" Ammy ta faɗa yayin da take matsawa wurin feenah da kairiyya ke ta ƙoƙarin ɗagawa amma ta kasa saboda data ɗagota take komawa saboda bata iya tashi
"yana wuce wani abu tayi ma ya shazim, tun da daman ya hanata shigo mashi part, amma da yake ba jin magana take ba ai gata nan ta shigo "
noraiz ya faɗa yayin da yake ƙoƙarin juyawa ya nufi ƙofa, da katar da shi Ammy tayi ta hanyar cewa
"na ga kana shirin fita ina zaka ko bakaga halin da take ciki ba ne,kuma yaushe shazim É—in ya shigo gidan "
"na gani Ammy mi zan yi mata?"
"tambayata kake?"
"A'a Ammy mi zan yi mata to"
"kira man shi yayan naka da ya yi mata hakan, ai sai ya zo ya san yanda zaiyi da ita idan ma hospital zai kaita"
"
to noraiz yace haɗi da nufar ƙofar bedroom ɗin shazim ɗin yayi nocking shiru ba'a bashi izinin shigaba ba kuma a buɗe ƙofar ba,Ammy tace
"lafiya?"
"da alama dai baya ciki, dan ban ji motsin shi ba "
kallon feenah Ammy tayi tana faÉ—in " wai ma mi ya sameki, da nayi tunanin ko ke da shazim ne?"
"Ammy shi ne ya mare ni ya kuma haÉ—a ni da table É—in bedroom É—in shi ko nan shine ya jeho ni "
sai da tayi magana tukun Ammy ta lura da jinin daya kwanta a gefan idon ta, ga sawun hannuwan shi nan a fuskar ta raɗau, mi noraiz zai in ba dariya ba jin tace wai ya jehota, sa'ada ma ɓoyewa tayi bayan fatima tana dariya, daƙuwwa Ammy tayima noraiz tana faɗin
"ya jeho ki dai ?, sai kace wasu kayan wanki " wata dariyar noraiz ya sake kwashewa da ita yana faɗin " kayan wanki fa ki ka ce Ammy " wani ƙululun baƙin ciki ne ya tukare feenah ganin yan da noraiz ya dage sai kwasar dariya yake yana mata Allah ya ƙara
"Noraiz wallahi zanci mutuncin ka kai da sa'ada, ku wane irin mutanene wai,  tana wani hali kuna mata dariya saboda rashin  tausayi  "
"Ammy kina ji fa tace a bedroom É—in shi ya mareta, in ba tsabar iskanci irin nata mi ya haÉ—ata da bedroom É—in shi" noraiz ya faÉ—a
tsaki Ammy taja haɗi da nufar bakin ƙofar bedroom ɗin shazim, nocking ta shigayi tana kwala mashi kira amma babu alamun ma yana ɗakin,
kallon feenah tayi tace " ko fita yayi? " girgiza mata kai feenah tayi tana faɗin " yana nan ciki, daya jeho ni waje mai da ƙofar yayi ya rufe " dariyace ta kusa kufce ma noraiz jin ta sake cewa ya jehota, da sauri ya sa hannu ya tushe bakin sa haɗi da sadda kai ƙasa
"shazim kana jina shine kayi banza dani ko saboda tsabagen rainin wayau" Ammy ta faɗa yayin da take sake nocking ɗin ƙofar still shiru babu alamun zai zo ya buɗe mata, ganin dai da gaske ba zuwa zai yi ba ya buɗe mata ba ne yasa tace su Kairiyya su kama feenah, haka su ka talallabata kamar kayan wanki da take faɗa su ka fice noraiz na bayan su yana dariya mara sauti dan gudun kar Ammy ta ji shi, haka su ka saukko da ita daga saman stairs un expected su ka hangi shazim kwance saman sofa three seater ya ɗaura hannun shi na dama saman kanshi yayin da hannun shi na hagu yake saman cikinsa da alama ma bacci yake jallabiyar da yasa ce ɗazo a jikin shi , abun har so yayi ya ba feenah tsoro tun da ita dai  ta san lokacin da ya fito da ita bedroom ɗin shi ya koma abun mamaki kuma gashi a parlorn Ammy, Noraiz ne yayi surin cewa "to ga ya shazim a parlor  kin gani kenan ƙarya take da tace shine ya mare ta Ammy " zuba shazim ido Ammy tayi baccin shi kawai yake kwasa abun shi hankali kwance,zama kusa da shi Ammy tayi tana kiran sunan shi haɗi da bubbuga hannun sofar, duk abun da ke faruwa idon shi biyu yana jin su, sai da Ammy ta sake kiran sunan shi tukun ya buɗe ido yana kallon ceiling sai da ya ɗauki sakanni sannan ya mai da duban shi ga Ammy
"lafiya na ganka nan kwance?" Ammy ta jefa mashi tambayar, ɗan ya tsine fuska yayi haɗi da yun ƙurawa ya tashi zaune
"kai na ne keman ciwo shine na sha magani na kwanta "
"Amma shazim mi feenah tayi kayi mata haka?"
"wacece kuma feenah?" ji wani tambayar rainin wayo nan wurin shazim
"ok baka ma santa ba "
"Ammy naji kina wata magana ne bayan ni tun da na dawo ina nan kuma ni banga kowa ba, shiyyasa na tambaye ki "  fashewa feenah tayi da kuka tana faɗin
"wallahi ya shazim mun haÉ—u ba dinner naje kai maka ba kuma ma ai tray yana bedroom É—inka" hannu Ammy ta É—aga ma feenah tana faÉ—in "ya isa haka feenah, yanzu kai ai sai kaje da ita medical room ka du ba hannun ta"
tashi yayi yana faÉ—in "Ammy cewa fa nayi kaina ke man ciwo, bazan iya duba kowa ba a yanayin da nakeji kai na, noraiz ya kaita asibiti " yana gama faÉ—a ya kama hanyar barin parlorn
"tafiya ma kake?,ka yima yarinyar mugunta sannan  kace baza ka duba ta ba "
waigowa yayi yana faɗin "bana jin daɗi ne Ammy kuma ni ban ma san akan mi kike magana ba" yana gama faɗa ya haye sama, da kallo kawai Ammy ta bisa tasan ƙarya yake shine ya dake ta amma zai ce wai bai ma san akan mi take magana ba
"Kairiyya ku ka mata zuwa waje noraiz ya kaita asibiti, kai kuma maza ka É—auko key ka kaita asibiti " ammy ta faÉ—a tana kallon noraiz da ke tsaye, turo baki yayi yana faÉ—in
"Ammy ni bacci nake ji " ko kallon shi Ammy bata yiba tace "ku fita da ita kunji, gani nan zuwa"
da to su ka amsa haÉ—i da nufar waje da ita, Ammy kuma bedroom É—inta ta nufa , ganin shirin É—auko key take ta kai feenah da kanta yasa noraiz bin bayan ta yana faÉ—in
"dan Allah kiyi haƙuri zan kaita da kai na "  ko kallon shi bata yi ba ta shige bedroom ɗin , wardrobe ɗin ta ta nufa buɗewa tayi ta ɗauko hijab sannan ta koma wurin dressing mirror ɗinta locker dake jiki ta jawo key ɗin motar ta dake ciki ta ɗauka,
"Pls Ammy wallahi zan kai ta " roƙonta ya shiga yi sai da ƙyar ya samu ta bashi key ɗin , tana bashi ya fita a tsaye ya samu su fatima riƙe da feenahr sai ruri take tana kuka yan ƙarasowa wurin su yace
"Allah ko kiyi mana shiru ko wallahi na koma, ƴar rainin wayau kawai wani ya aike ki ɗakin shi da zaki ta wani cika ma mutane kunne " ya faɗa haɗi da nufar motar Ammy da ke parking lot, da harara feenah ta raka shi duk buguwar da tayi bai hanata rashin kunya ba, fito da motar yayi zuwa compound in da su ke tsaye sa'ada ce ta nufi motar ta buɗe ƙofar baya su Kairiyya su ka shigar da ita, kairiyya ce ta zauna a baya tare da feenah fatima kuma ta shiga gaba, sa'ada ta koma ciki dan ɗauko masu hijaban su saboda duk cikin su babu mai hijab sai fatima ita ma gama sallar ta kenan taji ihun feenah,bayan kamar 1 minutes sa'ada ta fito hannunta riƙe da hijab ɗin kairiyya da ta feenah,miƙa masu tayi su ka amsa sannan ta koma ɓangaren da feenah take ta shiga, zama tayi suka sa feenah a tsakiya ita kairiyya, reverse noraiz yayi ya nufi gate da tun fitowar shi ya sa mai gadi ya buɗe masu, ficewa yayi daga gidan hanyar Abnoor ya ɗauka idan su ka zo in da za su sha kwana da mugunta yake shan kwanar dan duk ya sha kwana sai fennah ta saki ƙara, sa'ada dariya kawai take kwasa a zuciyar ta tana faɗin

"Allah ya ƙara maganin mai shishigi kenan, mutum yace baya so to ina dalilin maƙale mashi, in dai ya shazim yanzu kika fara gani "
haka tai ta ma feenah dariya da Allah ya ƙara har su ka iso Abnoor, horn noraiz yayi mai gadi ya buɗe mashi ya shiga da motar ciki,parking yayi yana gama daidaita parking yace su sa'ada su kamata su shiga ciki, fitowa su kayi har da fatima su ka kamata sai ɗangesa ƙafa take har su ka shiga ciki yayin da shi kuma yake bayan su, sun shiga nurses ɗin dake night su ka amshe ta,noraiz ne yaje office ɗin majeed ya sanar da shi abun da ke faruwa da yake yau bai tashi da wuri ba,
"Ya salam " majeed ya furta haÉ—i da cewa " shazim baya gida ne?"
" yana nan baya jin daÉ—i ne shiyyasa bai duba ta ba"
"amma wane irin rashin jin daÉ—i ne wannan da har zai hana shi duba patient " abun da yasa majeed ke faÉ—in haka noraiz ce mashi yayi faÉ—owa tayi daga bene koma yana zargin ta karye shiyyasa duk hankalin majeed ya tashi.
"muje na ga jikin nata" majeed ya faÉ—a yayin da yake tashi daga kan kujerar da yake, fice wa yayi noraiz ya
biyo bayan shi har inda feenah take sai uban kuka take kamar yarinyar goye, nurses ɗin da ke wurin kamar su maketa haka su ke ji abunda kawai yasa su kayi shiru su ka ƙyaleta tana cika masu kunne saboda kawai sun ganta tare da masu asibiti amma da ta sha masifa
majeed na ƙarasowa tambayar ta ya shiga yi mike damun ta ina da ina ne ta bugu , bata bashi amsa ba sai sake ɓare baki da tayi tana wani kukan , noraiz ne yace
"dallah malama an magana, idan kuma ba inda ke maki ciwo mu tashi mu koma gida "
"da kata noraiz saboda mi zaka yi mata ihu bakaga sai kuka take ba dole akwai inda ke mata ciwo kuma ka ce faÉ—owa tayi daga bene ba "

"haka ne faÉ—owa tayi " ya faÉ—a fuska a É—aure shi a dole gaskiya ya faÉ—a, jin abun da yace ma majeed ne yasa feenah buÉ—e baki tace

"wurgi ya shazim yayi da ni har na faɗa kan table hannuna ya bugu da ƙuguna amma ba faɗuwa nayi ba "
norai a ranshi yace " shashasha ana so a rufa mata asiri amma da yake bata san ciwan kanta ba, take tona ma kanta asiri sai kace wani abun arziƙi ne dan ta sanar da ya majeed ya shazim ne ya ji mata ciwan"

tsaki yaja  sannan a zahiri  yace " ka rabu da ita kawai ya majeed ka duba ta ka gani ko ta samu karaya a ƙugunta dare yayi " ihu feenah ta sa jin noraiz na faɗin ko ta samu karaya, abun ma har so yayi ba majeed dariya, in ba sharri irin na noraiz ba yaushe daga wannan faɗuwar zata karye kuma a ƙugu

"ya isa haka dan Allah noraiz " nurses ɗin dake wurin yasa su ka kamata zuwa emergency room,cikin ƙanƙanin lokaci majeed ya shiga dubata daya kama hannunta sai ta fashe da kuka,hakan yasa ya gane cewa ta samu targaɗe ne a hannun,wurin gayran targaɗen sai da ta so ta tara mashi mutane, da dai ya gaji tsawa ya daka mata yana faɗin wallahi ko dai tayi shiru ko kuma ya ƙyaleta da ciwan,  nurses ɗin dake ciki suna taimaka mashi tsaki kawai su ka ja duk ta ba su haushi sai kace ba mace ba wata cewa tayi
" zanga ranar da ki ka zo haihuwa,ƙila ranar mutuwa zaki dinga yi kina dawowa"
"ai kam dai" harara kawai feenah ta maka ma su
"yo ashe abun iskanci ne tun da har kina da idon hararar  mutane "

"ya isa haka " majeed ya faÉ—a

Sai da ƙyar ya samu feenah ta tsaya ya gyara mata targaɗen sannan yayi mata allura,magunguna ya ɗauko mata a pharmacy  wanda zata sha  har da wanda zata shafa a fuskar ta da hannun ta  da na ɗigawa a ido saboda jinin daya kwanta mata  sannan ya sallame ta,

fitowa tayi sai ɗangesa ƙafa take hannu ya sha uban ɗauri, duk sai ta ba su fatima  tausayi idan ka cire sa'ada da noraiz dan su ko kaɗan ba su ji tausayin ta ba, sai ma Allah ya ƙara da su ke mata suna faɗin gobe ma idan halinta ne ta sake komawa part ɗin shi.

Godiya noraiz yayi ma majeed sannan suka nufi hanyar fita, tsaida fatima majeed yayi yana tambayar ta ya ƙarfin jiki da bata haƙuri na rashin zuwa kwana biyu da bai yiba ya duba ta
"babu komai ai ya majeed naji sauƙi sosai "
"to shikenan Allah ya ƙara sauƙi, amma duk da haka zan zo har gida na sake duba ki "
"to shikenan ya majeed sai na ganka "
"ok in sha Allah " ya faÉ—a
har in  da noraiz yayi parking su ka yayi mata rakiya lokacin da su ka iso har su Kairiyya sun shiga cikin motar ita kawai suke jira, sallama tayi ma majeed sannan ta shiga ciki, tsaye yayi har sai da ya ga ficewar su sannan ya koma ciki ya haɗa kayan shi ya bar asibitin.
Lokacin da suka iso gida tuni baccin wahala ya ɗauke feenah sai da kairiyya ta tashe ta tukun ta san sun iso gida, fitowa su kayi su ka shiga ciki a parlor su ka samu Ammy tana jiran dawowar su, wurin ta su ka ƙaraso,

"ya jikin feenah?" Ammy ta tambaye ta, amsa ta bata da
" da sauƙi Ammy "
"Allah ya ƙara sauƙi, ki tafi ɗaki ki kwanta " da to ta amsa haɗi da nufar ɗakin da suke kwana ita da kairiyya kusa da ɗakin fatima.
"noraiz mi majeed yace ya samu hannunta na ganshi a É—aure?" Ammy ta tambaye shi
"targaɗe ne wai ashe,  dan ni har nayi tunanin karyewa tayi jin yanda take neman fasa ma mutane kunnne"
"ban san shashancin banza noraiz"
"to Ammy ga key ɗin ki nan sai da safe" ya faɗa haɗi da miƙama Ammy key ɗin motar ta ya nufi sama zuwa bedroom ɗin shi Ammy ma cewa tayi suma su fatima su wuce suje su kwanta dare yayi da to su ka amsa mata haɗi da wucewa ɗakunan su, kairiyya ɗakin su ita da feenah ta nufa da ledar magungunan feenah,tura ƙofar ɗakin tayi ta shiga ciki.
Masha Allah É—akin ya haÉ—u sosai family bed ne acikin sa mai girma wanda mutum huÉ—u za su iya kwanciya ba tare da sun takura ba, dan gadon duk yafi na É—akunan su Ammy girma da faÉ—i.
Zaune ta samu feenah kan gado sai zuba uban kuka take tsaki kairiyya taja dan   tun abun bai bata  haushi har abun ya fara bata haushi, ciki ta ƙarasa kan  dressing mirror ta ajiye ledar magungunan feenah ta nufi toilet, alwala ta ɗauro ta zo ta gabatar da sallar shafa'i da wutri da ta saba yi duk daren duniya, har ta kammala sallar ta canza kayanta zuwa na bacci feenah bata bar kuka ba,da abun ya ishe ta cewa tayi

"wannan kukan da kike yi ki sani bawani amfani da zai yi maki ba, dama kinyi shiru kin kwanata dan zai fiye maki, komai ma ya sameki feenah laifin ki ne kin san halin ya shazim sarai ba sai an baki labarin shi ba,tunda kika ga baya ra'ayin ki inaga da  haƙura kika yi da shi kika fita batun shi amma duk wannan shishige mashi da ki ke yi bazai amfana maki komai ba face ma kiyita shan wahalar sa,kina dai gani yau da da tsautsayi da tuni ya karya ki, shawa..... "

bata ƙarasa na feenah ta daka mata tsawa tana faɗin

"dallah dakata mana kairiyya, dama ba tun yau ba nasan cewa ke ƴar baƙin ciki ce , kina bakin ciki na samu ya shazim, to wallahi aniyar ki ta biki,dama sai da innah tace mana kema son shi ki ke damace kawai baki samu ba shiyyasa ki ke man baƙin ciki, to wallahi kiyi ki gama ni da ya shazim nan gani nan bari ɗumaman mayya ehe" ta ƙarasa maganar haɗi da dallama kairiyya harara kamar idanuwanta zasu zazzago ƙasa, abun yayi matukar ɗaure ma Kairiyya kai wai ita feenah ke ce ma tana mata baƙinci kuma wai innah da bakinta ta ke ce ma feenah wai tana mata baƙin ciki tun da take bata taɓa tunanin wani cikin su zaiyi tunani makamanci haka ba,
"Allah ya tsare ni feenah da yi maki baƙin ciki,gaskiya ce nake faɗa maki
"to bana so kitsaya a matsayin ki kawai ban son gaskiyar taki"
"haka kika ce?"
"eh haka nace, gaskiya ko in dai da ga wurin ki ne bana so na ya fe "
"shikenan wahalar ya shazim kuwa yanzu kika fara shanta" kairiyya ta faɗa haɗi  da jan blanket ta juya mata baya
ta rufe jikinta ruf, tana jin feenah na faÉ—in
" aniyar ki ta biki, ni da ya shazim sai alkairi duk baƙin cikin mutum wallahi sai dai ya mutu"
tana jin ta amma tayi banza da ita kamr ba da ita take magana ba, itama da ta gaji da banbotan kwanciya  tayi.

_WASHE GARI_

zaune su ke kan dinning suna breakfast, kowa nacin abinci amma ban da feenah da bata iya ko da É—aga hannunta balle ta samu taci lura da hakan ne yasa Ammy cewa

" feenah lafiya kowa yana breakfast amma banda ke "
Kwalla ce ta taru a idanuwan ta tace "Ammy bazan iya ci ba saboda hannun" ta faÉ—a hawayen da ke idanunta na zubowa
Sai da ta faÉ—i haka sannan Ammy ta tuna da cewa tayi fa targaÉ—e a hannunta,
"taso ki dawo kusa da ni sai na baki, ke sa'ada koma in da ta taso " Ammy ta faÉ—a, turo baki gaba sa'ada tayi tana faÉ—in
"Ammy tana fa iya ci da kanta"
"kinci gidan ku zaki tashi ko sai naci mutuncin ki, wai ku wane irin mutane ne wai" miƙewa sa'ada tayi haɗi da ɗaukar plate ɗin da take cin abinci  ta koma in da feenahr ta tashi
"wallahi Ammy ke ki ke ƙara biye mata wani bata iyaci da kanta sai kace wacce ta karye, ai da karyewa ki ka yi ƙila komai sai anyi maki k....... "
kasa ƙara sawa yayi ya duƙe ƙasan table da sauri sakamakon jifar shi da Ammy tayi da spoon, dariya ce ta kubce ma fatima dama haushin abun da yake ma feenah tun jiya ta keji , yana a ƙasan table bai ɗago ba yace
"na rantse da Allah na kamaki fatima sai ranki ya ɓaci zaki san ni ki ke ma dariya "
hannu ta sa ta toshe bakin ta tana faÉ—in
"A fuwan ya noor bazan sake ba "
"kima sake yarinya , dan Allah Ammy kiyi haƙuri "
Ya faÉ—a ba tare da ya É—ago ba, tsoro yake ya É—ago Ammy ta sake jifan shi
"Ammy kinyi shiru baki ce kinyi haƙuri ba " sai kace wani yaro
"Sai baƙin tsoro ga jan faɗa " Ammy ta faɗa, jin tace haka ne yasa shi  fahimtar  cewa ta haƙura, ɗagowa yayi yana zuba ma fatima harara, tsit wurin yayi baka jin motsin su sai na cokulan da suke cin abinci, shazim ne ya shigo daga motsa jiki,wurin su ya ƙara so Ammy kawai ya gaida ya nufi sama daman tun da su feenah su ka zo ya daina breakfast a dinning dama can ba gwanin zama dinning  ba ne, suna kammalawa fatima ta shirya mashi na shi a tray da zata kai mashi noraiz cewa yayi mi zai hana ta ba feenah ta kai mashi, cika feenah tayi ganin da gaske noraiz bazai barta ta zauna lafiya ba shikenan ya samu abun da zai riƙa tsokanan ta.
Shazim bayan fatima ta kai masa breakfast É—in shi yaci shirya wa yayi ya wuce EKO.

Su hidaya ya samu zaune a reception, gaishe da shi suka yi amma ba wacce ya amsa mawa acikin su gaba yayi abun shi, victoria ce ta taɓo destiny tana nuna mata hidaya kwashewa su kayi da dariya ashe duk abun da ya faru tsakanin ta da shazim sun sani wani munafukin aka samu ya sanar da su shiyyasa yau suka zauna a reception kawai dan su sa mata ido, abu kaɗan su saki dariya, tun hidayar bata gane da ita su ke ba har ta fahimci cewa ita su ke ma dariya, gajiya tayi da dariyar da su ke yimata tashi tayi ta nufi office ɗin da suke zama,wata dariyar shaƙiyyanci suka ƙara kwashewa da ita, abun yayi matuƙar ɓata ran maryam aikuwa ta tashi tana faɗin
"Amma dai wallahi wasu anyi dabobi,ku wani tasa mutane kuna yi masu dariya sai kace wasu mahaukata,Allah dai wadaran wanda bai san ciwan kanshi ba " nurses ɗin da ke wurin har haɗa baki su ke wurin faɗin " ke dai bari maryam wasu mutanen dai basu san ciwan kan su ba" tsarguwa su ka yi ganin kowa sai faɗin abun da yazo bakin sa yake yasa victoria miƙewa tan faɗin
"kushiga hankalin ku dan naga take taken ku, dan duk wacce tace zata zage mu sai ta gane bata da wayau"
"wai dakata victoria ki ke ko wa, wai ma wakike faÉ—a ma wannan maganganun "
"da uban da ya tsargu nake "
"ai fa kaji matsalar bamuguje" maryam ta faɗa haɗi da kwashe da dariya dan ta san victoria bata san mi kalmar bamaguje take nufi ba sauran ma dariyar su ka kwashe da ita, haka su kayi ta jefa ma victoria baƙaƙen magamganu da hausa ganin bata fahimtar mi suke cewa, baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshi nan ta shiga zunduma masu zagi da yaren su, banza su kayi da ita kowa ya kama harkar gaban sa su ka barta ita kaɗai sai ɓaɓatu take kamar wata mahaukaciya,  destiny ce tace "haba victoria sun maida ke mahaukaciya,amma baki gane ba sai wani gazi ki ke "  da yaren su tayi maganar dan kar su maryam su fahimci mi take faɗa mata amma abun da bata sani ba daga yana yin yanda victoria tayi shiru su ka fahimci cewa wani abun ta faɗa mata, jan hannun ta destiny tayi suka bar wurin zuwa office ɗin su da suke zama samun hidaya su kayi tana karatun alqur'ani mai girma,zama su kayi suna sauraron ta  wani abu na Allah kamar tace su zauna suyi shiru, haka suka zauna sai satar kallon ta su ke bata ma san da zuwan su ba, karatun ta kawai take, wayar ta ce dake cikin jaka ta fara ringing,sai da ta kai aya tukun ta buɗe jakar ta ciro wayar duba mai kiran tayi , dr kabir shi ne mai kiranta, latse wayar tayi ta sata a silent  ta cigaba da karatun ta, haka yayi ta kira ba tare da tayi picking ba.
Zaune yake a office ɗin shi abun duniya duk yabi ya ishe shi sai kiranta yake Amma taƙi ɗauka kuma ya san taga kiran shi ɗauka ne kawai ba zata yi ba,sai dai daya juya yace "wai hidaya kashe ni kike sonyi ne, mi nayi maki ne dan Allah da ki ka zaɓi ki azabtar da ni" haka yake ta sambatu bawan Allah duk ya zama abun tausayi ƙarshe dai kiran Momy yayi tana picking ya fashe da kuka yace "momy so take sai zuciyata ta buga momy bata sona ban san mi nayi mata ba "
"ya Allah Auta ba dai acikin hospital É—in kake man wannan kukan ba "
"momy a nan ne mana gaba É—aya so take ta zautar da ni ban san mi nayi mata ba"
"yanzu dai daina wannan kukan da kake yi kamar wani yaron goye"
"to momy na dai na, amma dai yau dady zaije wurin baban ta ko"
"eh yau zai je in sha Allah ka kwantar da hankalin ka, idan kana saurin karaya bazaka iya shawo kanta ba, ka daina saurin karaya ka sama ranka ƙwarin gwiwa, ka nuna mata soyayya na san zata so ka my Auta"
"to shikenan momy na dai na "
"yawwa, yanzu tana ina tana gida ne ko ta zo hospital É—in"
"momy nima ban sani ba ko ta zo ba "
"ai kai kana hospital É—in ko?"
"eh momy "
"to kaje ka du bata mana"
"to momy" ya faÉ—a haÉ—i da yin rejecting kiran, ta shi yayi ya fice daga office É—in ya nufi reception,gaishe da shi su maryam su ka shiga yi amsa masu yayi sannan yace
"maryam ina take,ko bata zo ba yau?" tun da ya faÉ—i haka maryam ta gane hidaya hake nufi
"tana office, a kira maka ita ne"
"a'a bari naje da kaina " ya faɗa haɗi da nufar office ɗin na su, binshi da kallo nurses ɗin su kayi kowa da gulma a bakin shi, maryam duk ya bata tausayi yana matuƙar son hidaya kuma shi ba ruwanshi ko a ina nu na sonta yake ba ruwan shi,jin nurses ɗin na ta ƙusƙus ne yasa maryam cewa " to uwayen gulma za ku fara, abun nema ya samu "
"daga faÉ—in alkairi sai abun ya zama gulma" wata ta faÉ—a
"eh, ai idan kayi maganar mutum ba tare da ya sani ba gulma ce"
"to munji ba sai kin yi mana wa'azi ba"
"ba ku son gaskiya na lura" maryam ta faÉ—a.
Yana zuwa bakin office ɗin  ya jiyo  muryar ta tana raira karatun alqur'an, ajiyar zuciga ya sauke yana faɗin
"ya Allah ka mallaka man wannan baiwar taka" ya faɗa haɗi da tura ƙofar da sallama a bakin sa,ɗagowa su victoria su kayi su ka kalle shi, abun ya basu mamaki mi ya kawo dr kabir office ɗin su, gaishe da shi su kayi,hannun ya ɗaga masu ba tare da ya amsa ba, jin suna gaishe da shi ne yasa hidaya ɗa gowa ta kalle shi, da sauri ta duƙar da kai, kallon su victoria yayi yana faɗin
"Please excuse us"
ta shi su kayi su ka fita, amma sai su ka laɓe bakin ƙofa dan son jin mi zai ce mata 
matsawa yayi ya samu wata kujera ya zauna kusa da wacce take zaune,binta kawai yake da kallon sai wasa take da ƴan yatsun hannun ta,  cikin ƙasa da murya ya fara magana
"beb wai mi nayi maki ne,Please idan da abun da nayi maki wanda baki so ki faÉ—a man kinji zan daina"
kanta na a duƙe tace "babu abun da kayi man"
"to amma mi yasa kike man wulaƙanci, ko dai baki sona har yanzu shazim kike so " girgiza mashi kai tayi
"magana nake so kiyi man, hidaya ki fahimce ni ina sonki tsakani na da Allah ne, ina son ki fahimce ni please"
har ga Allah bazata ce  dr kabir baya birgeta  ba, amma son da take ma shazim ne na daban ne wanda take jin bazata iya haƙura da shi ba har ta so waninsa ba,
"ya kabir maganar gaskiya bazan ce baka burge ni ba amma ina so ka fahimce ni ya shazi.... " tsawa ya daka mata yana faÉ—in
"dan Allah dakata man hidaya shazim ne dai ko to ga shazim nan" yana gama  faɗar haka ya tashi ya fice daga office ɗin,ya tsani maganar shazim da take yi mashi
duk sai taji ba daɗi amma ba zata iya haƙura da shazim ba, ta shi tayi ta bi bayan shi.

_*✨KATSINA✨*_

Su Aairah ne ke ta gyaran part ɗin da ke kusa da na Abie saboda zuwan su safwan, tun safe su ka tashi da shirye shiryen tarbar su Abie ma na gidan dadi saboda zuwa da za suyi su ɗauko su a airport shi da su uncle mustafa da Abdallah, mom da matar uncle Ahmad suna kitchen suna shirya masu abinci da ƙarfe huɗu na yamma jirgin su zai sauka.

_Episode  62_63_

Hidaya lokacin da ta bi bayan dr kabir,ko da ta fita bata ganshi ba hakan yasa ta bi shi office ɗin shi, zaune ta same shi kan sofa ya ɗaura hannun shi na dama saman kai, idanuwan shi a lumshe  ya rasa mi ke mashi daɗi a  duniyar nan, ƙarasawa tayi wurin shi
"Dr are u ok" banza yayi da ita duk da ya gane ita ce tunaninta bai ji ta ba ne  hakan ya sa ta sake kiran sunan shi,
"Please hidaya leave me alone" ya faÉ—a da É—an É—aga murya
"kayi haƙuri, na san abun da nayi maka ne ya ɓata ranka,dan haka nake haɗa ka da Allah da kayi haƙuri "  hannun shi daya ɗaura saman kanshi ya cire duk a tunanin ta ya haƙura ne Amma sai ganin shi tayi ya kama hanyar ficewa daga office ɗin
"ba dan halina ba kar ka fita, idan nice baka son gani zan fita amma dan Allah karka fita" ta faɗa yayin da take miƙewa ta nufo ƙofar, tsayawa yayi cak shi bai fita sanna kuma bai dawo ba,zuwa tayi har gaban sa tana faɗin " ina so ka fahimce ni Please, duk abun da ka ga ina faɗa maka ina faɗa maka tsakani na da Allah ne"
"naji hidaya, ai na ce maki kije gaki ga shazim ba shikenan ba"
"amma dr.. "
"please ya isa haka bana son jin komai  daga bakin ki"
" saboda mi"
"saboda duk abun da zai fito daga bakin ki ba alkairi ba ne a wurina, dan haka ni kawai ki fita,ki barni da abun da ya ishe ni Please" ya ƙarasa maganar haɗi da haɗe hannuwan shi wuri ɗaya,kan sofa ya koma ya zauna
"shikenan zan fita na baka wuri" tana faɗa tabuɗe ƙofar office ɗin ta fice,  wurin su maryam ta nufa , tun kafin ta ƙara so  maryam ke jefan ta da harara
"lafiya wai ki ke hararata?" hidaya ta faÉ—a yayin da take samun wurin zama ku sa da maryam É—in
"kinfi kowa sani"
"ni babu wani abu da na sani "
"yayi kyau " maryam ta faɗa, fira su ke ɗan taɓawa jefi jefi, suna nan zaune har aka fara kiran sallar zuhur, dr kabir ne ya fito daga office ɗin shi ya shiga na shazim, yana shiga ya same shi yana tattara files ɗin da ke kan table ɗin alamar ya tashi sai kuma wani lokacin.
Sallam kabir yayi mashi haÉ—i da shiga ciki, kallon shi shazim yayi yana amsa mashi sallamar
"Autan momy lafiya dai?" shazim ya faÉ—a dan ganin kabir da yayi duk sai a hankali ga idanuwan shi a kumbure kamar na wanda ya sha kuka
"lafiya lau,  mi ka gani?"
"bakomai" shazim ya bashi amsa
"mu tafi ko" shazim ya faɗa saboda ya gama haɗa duk wani kayan shi, gaba kabir yayi shi kuma ya bi bayan shi su ka nufi masallaci, da aka gama sallah shazim sallama yayi ma kabir saboda shi zai wuce Abnoor kabir ma cewa yayi shima da anyi sallar asr  gida zai tafi  hakan ce ta faru ana gama sallah bai daɗe  ba shima ya kama hanyar tafiya gida.

_*FEENAH*_

zaune take bakin gado a É—akin su ita da kairiyya, wayarta da ke kan bedside drawer ta É—auka number innah ta shiga dialing bugu biyu innah ta É—auka tana faÉ—in
"sai yau ki ka yi lokacina?"
"kai innah daga kiran ki zaki fara da complain"
" ni ki ke cema haka ko"
"innah ai ke ce daga kira sai ƙorafi"
"to naji , mi yasa ki ka kira ni dan na san ba dan Allah ki ka kira ni ba"
"haba dan Allah innah"
"ba wani haba, ƙarya na faɗa tun da nake da ke kin taɓa kirana haka nan kawai da sunan ki gaishe ni tun da kika kama ƙafa kika koma lagos da zama "
"naji ni dai innah, kima tsaya ki saurari mi ke damuna amma sai wani faÉ—a kike man"
"to naji, yanzu faÉ—a man mike damunki da yasa kika kirani "
"dama ba komai bane, yaushe su Abbah su ka tsaida ranar Auran mu da ya shazim, dan ni nagaji da wulaƙancin da yake man ga wannan munafukar kairiyya a gefe "
"wannan ko Æ´ar banzar yarinya, a nan É—in ma sa maki ido take ke nan "
"Ai wallahi innah sai ma abun da ya cigaba jiya har da wani tsare ni zata yi man wa'azi saboda naje part É—in ya shazim ya mare ni "
"mi?, mari fa kika ce?"
"eh kawai dan na taɓa shi, fuskata fa duk ya kumbura man ita, hannuna har da targaɗe kuma da Ammy tace ya duba ni ƙinyi yayi, shiyyasa na kira ki kisa su Abbah su tsai da ranar Auran mu nasan dai ya Aure ni ƙarya yake yace zai dake ni "
"amma kin bani haushi feenah, bana hanaki taɓa sa ba ke mi yasa baki jin magana ne, yanzu da ya illata ki da ya kenan, shi bai da asara saboda daman ba sonki yake ba"
"ai bazan ma ƙara ba, dan wallahi ba ƙaramar azaba na sha ba jiya da ana gyara man hannuna "
"to da dai ya fiye maki, dan shi ba ruwan shi dan ya yi maki illa"
"to innha yanzu yaushe zaki sa a sa ranar bikin mu "
"kar ki damu ki barni da su ni na san mi zanyi "
"yawwa innha ta shiyyasa nake sonki "
"kar ki ji komai, kawai ki bi abun da na ce maki "
"to insha Allah "
"sai anjima, na manta in faÉ—a maki mansoor na nan zai zo nace ya barki ya dawo da su sa'ada amma na san halin shi duk yanda zai yi karki saki ki biyo shi kinji na faÉ—a maki "
"in sha Allah innah bazan biyo shi ba"
"yawwa, sai anjima "
innah ta faÉ—a haÉ—i da yin rejecting kiran
faÉ—awa tayi saman gado tana faÉ—in
"yawwa innah shiyyasa nafi kowa sonki don baki bari na zubar da hawaye "

✨KATSINA✨

Abdallah ne ya shigo wurin su mom dake  kitchen ita da ummah da baaba larai ya nufa, da sallama a bakin sa ya shiga kitchen ɗin, amsa mashi mom tayi tana faɗin
"wai da kai baka bi su abie É—inka ba?"
"eh naje na dawo ɗaukar takardun su Aairah ne , makarantar ta fara ba da addimisson yanzu wani  abokin uncle Ahmad ya kira shi yake sanar da shi  Ameerah ta samu , shine uncle Ahmad yace na zo na ɗauki na su Aairah  na tura ma Abokin na shi wanda ya duba ma Ameerah sai suma ya duba masu suma"
"masha Allah kace Æ´an biyu na sun kusa tafiya school hankali ya kwanta, kullum na huta da mom wai yaushe ya Abdallah yace za'a fara ba da addimisson kullum maganar su kenan"
Ummah tace "ai  gara su da Ameera, yanzu hankalina ya kwanta tunda Allah ya sa an samu addimisson yanzu hankalina zai kwanta "
"ai yaran nan idan ka bari su ka tasoka gaba kaga ta kanka" mom ta faÉ—a
Ummah tace " Allah dai ya shirye su " da Ameen su ka amsa Abdallah ya ce
"ni zan wuce"
Mom tace
"yaushe Abie É—in naku yace za su iso"
"sai É—an anjima ka É—an yanzu ma ni su ke jira "
"Ok sai kun dawo, su kuma Allah ya kawo su lafiya"
"Ameen, sai na dawo" ya faÉ—a haÉ—i da ficewa ya bar kitchen É—in.
Su Aairah ne su ka shigo da gudu daga garden  Ameera na riƙe da wayar Aairah, Aairah na biye da ita tana faɗin
"wallahi Ameera ki bani waya ta kafin ranki ya ɓaci "
"wallahi ban badawa kin bi duk kin ishi mutane,ban badawa idan kina da ƙarfi ki zo ki karɓa " Ameera ta faɗa tana ma Aairah gwalo, sai zagaye parlor su ke Aaimah na tsaye tana masu dariya tana faɗin
"wallahi karki bata "
"Aaimah ban san wulaƙanci dan mi zaki ce karta bani "
"ai wallahi ko bata ce haka ba bazan baki ba, dama kin daina bi na" Ameerah ta faÉ—a sai haki take, awannan yanayin ne Abdallah ya fito daga part É—in shi ya gansu, tsawa ya daka masu yana faÉ—in
"wai ku wane kalar yara ne, kun girma amma kwata kwata baku san ciwan kanku ba, wallahi ko ku natsu ko ranku yayi mumunnan ɓaci sakarkaru kawai "
"yaya wayata fa ta amsa Aaimah na ce mata wai karta bani "Aairah ta faÉ—a tana turo baki
"na dai faɗa maku " Abdallah ya faɗa haɗi da ficewa ya bar parlorn , suna ganin ya fita kamar yace su cigaba sai kace ƙananan yara haka su kai ta zagaye parlor duk sun cika gidan da hayaniya.

_*✨Airport✨*_


motar su Abie ce ta shigo cikin Airport ɗin Abdallah ke driving motar da su Abie suke ciki yayin da uncle mustafa  ke driving motar shi, parking lot su ka nufa haɗi da yin parking su ka shiga fitowa,  Abie da uncle Ahmad  ne su ka fara fitowa sai uncle mustafa  sai ya Abdallah, cikin Airport ɗin su ka nufa abie da su uncle Ahmad suna ɗan fira sama sama, wani ƙyatattce wuri su ka nufa, zama su kayi kan chair's ɗin da ke wurin , su abie kaɗai ne su ka zauna ya Abdallah kuma can gefan su ya samu wuri ya zauna wayar shi ya ciro yayi dialing number fatima,bakin ta ɗauke da sallama tayi picking call ɗin tana faɗin
"ni nayi fushi,sai yanzu daga bari na dawo "
"da ya dr ki ka yi fushi?" ya faÉ—a cikin sigar tamabaya
"ai duk laifin shi ne, ya bar ƙanwar shi tana ta jiran shi" a shagwaɓe tayi maganar
"kin san dai idan ba wani abu ya tsare ya dr ba bazai bar ƙanwar shi tana jiran shi ba ko?"
"shikenan tun da haka kace "
"haka ne fah ba wai nace ba "
"kana ina yanzu?" fatima ta tambaya
"ina airport"
"ya dr ba dai wani wuri zaka je ba?"
"zanyi tafiya ne, kina so na zo maki da wani abu ne"
nan take yana yin muryarta ya canza, rai a ɓace tace 
"bana so, sai ka dawo"  ta faɗa haɗi da yin rejecting kiran, murmushi ne ya suɓuce mashi yana faɗin
"fatima manya" tashi yayi daga inda yake zaune ganin su Abie sun ta shi,bin bayan su yayi.
Wani kyakyawan matashin saurayi  ne ke saukowa daga mata ƙalar benen jirgin da ya sauka, fari tas da shi  hannun shi ɗauke da madai daicin trolly sanye yake da baƙin cargo trouser  sai t_shirt wacce ita ma ta kasan ce baƙa da p_cap red color da ɓakin glass, ba ƙaramin fito da kyawun shi da na fatarshi kayan su kayi ba,saukowa yake cikin natsuwa   yayin da wani dattijon mutum ke bayan sa  jikin sa sanye da kayan mu na hausawa riga da wando na yadi mai taushi.
shima fari tas kyakyawan gaske za su yi sa'annin juna da uncle Mustafa duk da yawan shekarun shi haka bai hana kyauwun shi fitowa ba, tafiya su ke shi da matashin har su ka iso inda mutane ke tsaitsaye.

Abie ne ya ƙara so da sauri wurin su  fuskar shi ɗauke da tsantsar farin ciki,su uncle mustafa na bayan shi, yana ƙarasowa yayi hugging ɗin wannan dattijon yana faɗin " masha Allah, barkan ka da zuwa ƙasar ka,  barka da  dawowa " murmushi shima dattijon yayi yana faɗin "nagode" raba jikinsu su kayi su uncle Ahmad ma matsowa su kayi kusa da shi, hannu suka miƙa mashi su ka yi musabaha, suna mashi barka da zuwa, ya Abdallah matsawa yayi wurin wannan matashin yana faɗin
"safwan manyan ƙasa yau dai gaka a nigeria,ina tsoron naka ya tafi"  
murmushi safwan yayi haÉ—i da cire glass É—in dake idon shi yace
"Abdallah ka raina ni, wani ya ce maka ina tsorone"
"sosai ma kuwa tsoro kake, in ba tsoro ba mi ya hanaka zuwa tun tuni sai yanzu"
"saboda kai ma baka zuwa "
"ba wani nan tsoro ne ya hanaka zuwa " 
"haka ka ce "
"eh haka na ce "
"zamu gani ai ni da kai wake tsoron" safwan É—in ya faÉ—a haÉ—i da matsawa wurin Abie ya shiga gaishe da su.

Ɗunguma su kayi zuwa parking lot in da su kayi parking ɗin motocin su, safwan shi da Abdallah su ka shiga motar shi yayin da Abie da uncle Ahmad  su ka shiga motar uncle mustafa, barin airport ɗin su kayi ba su nufi ko ina ba sai gidan Dadi.
Horn su kayi a bakin gate ɗin gidan dadi, mai gadi ne ya buɗe masu ciki su ka shiga,parking lot su ka nufa haɗin da yin parking, fitowa su ka shiga yi ɗaya bayan ɗaya bayan sun gama fitowa ciki su ka nufa, abie gaba ɗaya a cikin farin ciki yake da zuwan wannan bawan Allah, da sallama a bakunan su suka shiga ciki, parlorn tsit yake kamar ba kowa, Aunty Rabi ce zaune kan sofa tana karatun qur'ani mai girma,sai da ta kai aya sannan ta tsaya haɗi da  amsa masu sallamar da su kayi, ciki su ka ƙara sa haɗi da samun wurin zama kan sofa's su ka zauna, gaishe da wannan dattijon ta  yi tare da yi mashi barka da zuwa ,cikin kulawa ya amsa mata, da fara'a a fuskar safwan ya gaishe da ita, amsa mashi tayi tana faɗin "safwan yau dai gaka a nigeria,ya gajiyar hanya "
"lafiya lau Alhmdllhl" safwan ya faÉ—a
"masha Allah , ya ka baro momyn ka "
"tana lafiya tace a gaishe da ku"
"muna amsawa"
abie ne yace  " ina mama, ko tana ɗaki?"
"eh yanzu ta shiga bari naje nayi mata magana"  ta faɗa haɗi da tashi ta nufi ɗakin dadi,wannan dattijon ne ya kalli abie  yace
"sai dai ban gane nan ina ne ba?"
"nan gidan mama mahaifiyar mu"
"oho Allah sarki " mutumin ya faÉ—a
Aunty Rabi ce ta fito ita da dadi,ƙarasowa wurin su su kayi wuri dadi ta samu kan sofa ta zauna tana kallon wannan mutumin, ta sowa yayi ya dawo kusa da ita yana faɗin " mama ina wuni " wani iri dadi taji jin ya kirata da mama, duk sai ya bata tausayi, shikenan waɗannan mutanen sun cuce shi yanzu baya iya tuna komai da ya shafi rayuwar shi,ya manta ko shi wanene ya manta iyalan shi da ƴan uwan shi.
Kallon Abie yayi yace "naji tayi shiru ko ba ita bace mamar ba?"
"ita ce bata ji ka bane" abie ya faÉ—a
"lafiya lau nake, ya hanya" dadi ta faÉ—a fuskar ta da É—an murmushi wanda da ka ganshi kasan na dole ne
"Alhmdllh " mutumin ya faɗa, fira suka shiga taɓawa shi da dadi kamar ɗan da ta haifa da cikinta, tun bata saki jiki da shi ba har ta saki jiki su ka sha fira duk da firar ba wata bace tambayoyi ma da yake mata duk sunfi yawa.
Aunty Rabi ce ta kawo masu ruwa da lemu, sun jima a gidan sannan abie yace su tafi can gida amma sai wannan bawan Allah yace bazai je ba shi yana nan tare da mama, abie ne yace mashi ai idan sun je za su dawo,dadi ma tace zuwa za kuyi ku dawo sannan ya yarda ya bisu suka tafi.

Lokacin da suka isa gida su Aairah na nan zaune a main  parlor suna kallo, jin sallamar abie ne ya sa su tashi da sauri suka nufe su,  suna faɗin
"oyoyo ga abie"
haÉ—i da gaishe da su uncle Ahmad, ciki su Abie su ka shigo abie na faÉ—in
"ina su mom É—in ku sai ku ka É—ai a parlor "
"yanzu su ka shiga ciki" Aaimah ta faÉ—a
Abie yace "ba kuga uncle sadiq ba" ya faɗa yana nuna wannan mutumin, da sauri su ka nufe shi suna faɗin
"uncle sannu da zuwa, ya gajiyar hanya "
"Alhmdllh, ya kuke "
"lafiya lau mu ke"
"masha Allah " ya faÉ—a
Wuri su ka samu kan sofa su ka zauna yana tambayar su Aairah ya sunan su, É—aya bayan É—aya suka shiga faÉ—a mashi sunayen su yan jinjina kai.
Ameera ce ta tashi ta tafi kiran su mom , ba ta daɗe da tafiya ba sai gata tare da su mom,ƙarasowa su kayi ciki, nan suka shiga gaishe gaishe, abie na nuna ma uncle su da sunayen su, sun jima anata fira har sai da aka fara kiraye kiyaren sallar magrib sannan su ka tashi su ka nufi masallaci, su mom ma da su Aairah ɗakunan su suka nufa domin gabatar da tasu sallar, bayan sun kammala ne mom tace su je su jera dinner kan dinning,tafiya su kayi su ka jera komai da ya kamata sannan suka koma kan sofa suna cigaba da kallon da suke ɗazu, su abie ba su dawo gidan ba sai bayan da su kayi sallar isha tukun su ka dawo,  suna shigowa dining su ka nufa,su Aairah mom tace suje suyi serving ɗin su,su kuma su kawo masu na su abicin nan kan carpet saboda dining ɗin da yayi masu ka ɗan.
bayan sun kammal serving É—in su,kamar yan da mom tace kan carpet su ka kawo masu na su abicin su ka ci.
Bayan sun kammala dinner a nan mai parlor su ka zauna suna ɗan taɓa fira amma banda su Aairah da suka gama dinner bedroom ɗin su suka nufa, Abdallah ma da safwan part ɗin Abdallah su ka nufa su ka bar su Abie ka ɗai a parlor suna fira.
Sai wurin ten uncle mustafa ya tafi gida uncle Ahmad kuma ya tafi part É—in da su ka sauka shi da ummah,abie kuma shi da uncle sadiq su ka tafi part É—in shi.
bayan sun shiga part ɗin abie, wani bedroom abie ya kaisa wanda ke kusa da nashi, da suka shiga ciki pajamas abie  ya ɗauko mashi sannan ya nuna mashi wani corridor da wardrobe ce ciki yace ya shiga ya canza kayan jikin shi , bayan ya canza abie yace ya shiga toilet yayo alwala, da to ya amsa mashi haɗi da nufar toilet ɗin ɗakin bayan kamar 1 minute ya fito jikin shi da danshin ruwa.
Nuna mashi bed abie yayi yace ya zo ya kwanta, matsowa yayi ya hau gadon zaman abie yayi shima kusa da shi sannan yace" zan riƙa karanto maka adu'ar kwanciya bacci sai ka maimaita" to ya faɗa
nan abie ya shiga karanto mashi shi kuma yana maimaitawa har abie ya gama karanta mashi, sannan yace ya kwanta, kwanciya yayi abie yaja mashi blanket sannan yayi mashi sai da safe haɗi da nufar ƙofa ya kashe mashi light ɗin ɗakin tare da jawo mashi ƙofa, cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba da shi..
_Episode  64_65_

Abie ɗakin shi ya koma, shima alwala yayi sannan ya zo ya gabatar da safa'i da wutiri sannan ya kashe light ɗin ɗakin ya  kwanta, duniyar tunani ya shiga, yanzu baya da wani buri face yaga Allah ya toni asirin mutanen nan, ya jima a kwance yana saƙawa da kwancewa  batare da bacci ya ɗauke shi ba, sai da dare ya raba sosai sannan  bacci ya fara kama idon shi,ta shi yayi yaje ɗakin da uncle sadiq yake a bakin ƙofa ya tsaya, leƙashi yayi, hango shi yayi ta hanyar hasken bedside lamp dake kunne  yana ta sharar baccin shi  hankalin shi kwance, mai da mashi ƙofar abie yayi ya rufe, bedroom ɗin shi ya koma kwanciya yayi dan da nan bacci shima yayi awan gaba da shi..

_*WASHE GARI*_

Masallatai na fara ƙwala kiran sallar asuba abie ya farka,toilet ya nufa  ya ɗauro alwala sannan ya dawo ya canza kayan dake jikin shi zuwa jallabiya, fita yayi ya nufi ɗakin da uncle sadiq yake ciki, lokacin da ya tura ƙofar hango shi yayi a zaune a bakin gado da alama ma har alawala yayi saboda danshin ruwa dake jikin shi, da sallama Abie ya shiga , ɗagowa uncle sadiq yayi yana kallon abie, yace" yawwa harka tashi kenan"
"eh" uncle sadiq ya bashi amsa
"ta so to mu tafi masallaci " abie ya faÉ—a haÉ—i da kama hanyar fita, bin bayan shi uncle sadiq yayi, a main parlor su ka samu uncle Ahmad da su Abdallah,
ficewa su kayi zuwa masallaci,lokacin da su ka dawo abie da uncle sadiq a parlorn abie suka zauna abie na koya mashi karatun qur'ani mai girma, sun jima abie na koya mashi, har sai da gari ya waye sosai tukkun su ka ajiye karatun, uncle Ahmad ne ya shigo parlorn da sallama a bakin shi, amsa mashi sallamar su kayi, wuri ya samu kusa da abie ya zauna yana faÉ—in " ina kwana yaya, fatan an tashi lafiya " amsa mashi abie yayi da
"Lafiya lau Alhmdllh" sannan uncle Ahmad ya kallin uncle sadiq yana faÉ—in " ina kwana, an tashi lafiya"
"lafiya lau Alhmdllh " ya amsa shi ma kamar yanda yaji abie ya amsa, fira su ka ɗan shiga taɓawa,nocking ɗin ƙofar parlorn a ka yi abie ne ya  ba da izinin shigowa, turo ƙofar su Aairah su kayi su ka shigo bakunan su ɗauke da sallama hannun su ɗauke da manya tray da mom ta shirya ma su abie breakfast ɗin su, amsa ma su sallamar su abie su kayi, table ɗin da ke tsakiyar parlorn su ka nufa, trays ɗin su ka sauke su ka ɗaura kan table ɗin haɗi da gaishe da su,cikin kulawa su ka amasa ma su musamman uncle sadiq,tsayawa su kayi sai da su kayi serving ɗin su tukun su ka nufi hanyar fita, parlorn su ka nufa wurin su mom da ke zaune kan dinning suna breakfast, dinning ɗin su ka nufa har sun ja kujeru za su zauna mom tace " yayan ku fa, kun kai mashi abinci ne "
"mom bari mu kayi sai mungama, ba su isa tashi ba yanzu " Aairah ta faÉ—a
Carab Ameera ta ce " ba su tashi ba fa mom" daƙƙuwa ummah tayi ma Ameerah, mom na faɗin " kunfi kowa sanin halin Abdallah, kar Allah ya sa ku kai masa zai fito ne ya same ku "
"mom Allah ba isa tashi ba yanzu"
"ku dai kuka sani,amma ni ba ruwana ya fito ya same ku ba ku kai ma shi abinci ba"
Ameera cewa tayi " ni dai Aairah ta so muje mu kai masa wallahi ina tsoron abun da zai biyo baya "
"sai kin dawo, gaskiya ni yunwa nake ji"
"ok haka kika ce ko "
"eh" Aairah ta faÉ—a yayin da ta ke kai bread a bakin ta
hanyar kitchen Ameerah ta nufa tana faÉ—in

"wallahi idan baki zo mun tafi ba saina cema ya Abdallah ke akace ki kawo masu ki kace baki zowa "
É—an É—aga murya Aairah tayi tana faÉ—in
"idan kin fasa, uwar yan jan sharri " daga kitchen Ameerah tace
"wallahi zaki san ni kike cema uwar Æ´an jan sharri "
"eh ɗin in sani, ai na san dalilin da yasa kike son jaman sharri kuma ko mi zakiyi bazan ba da ba ehe " ɗaga murya Ameerah  tayi yan da Aairah zata jita sosai tace
" wannan kuma ke kika sani kar Allah yasa ki bada Æ´ar rainin hankali " gwalo Aairah tayi mata sai kace tana gaban ta tace
"oho dai, ban ba dawa " Ameerah na jin ta amma tayi bazan da ita,
Aaimah dai na jin su bata ce ƙala ba, sai zuba ma cikin ta abinci kawai take, Ameerah ce ta fito hannun ta ɗauke da trayn da ta shirya masu breakfast, zata wuce kenan Aaimah ta dakatar da ita tana faɗin  
" kawo na É—aukar maki naga kamar kayan sun yi maki yawa, ke kuma wallahi Aairah sai kin gane baki da wayau "
"dan Allah ku rabu da ni, zuwa dai ne nace bazanyi ba koma mi zaki faÉ—a kin daÉ—e"
"haka kika ce " Aaimah ta faÉ—a, amsa Aairah ta bata da
" sosai ma kuwa, duk abun da zaku faɗa mashi kun daɗe " ta ƙarasa maganar tana murguɗa ma Aaimah baki
"haba yarinya kamar a gabansa kika yi haka"
"dan Allah ya isa haka, ke Aairah tashi ku tafi ko gaisawa ai kunyi da safwan"
"mom zanje idan na gama " Aairah ta faÉ—a, kallon su Aaimah mom tayi tana faÉ—in " to ke wuce ku tafi ba dole sai kunyi zuga ba, ke da Ameerah ma ai ya isa "
"mom ai ta je ta gaishe da ya safwan ko "
"za taje ai tace idan ta gama, maza ku wuce ku" da to su ka amsa haɗi da nufar part ɗin, suna tafe suna surutun da suka saba amma fa acewar Abdallah, suna isowa bakin part ɗin Ameerah ce tayi nocking har ta ɗaga hannu zata sake wani nocking sai gashi an buɗe ƙofar, safwan ne tsaye jikin shi sanye da ɓakar jallabiya, da fara'a a fuskar Ameerah tace
"ya safwan ina kwana, fatan an tashi lafiya" fuskar shi shima da fara'a yace "lafiya lau,ina su ummah"
"suna main parlor suna breakfast, ga naku nan kai ma mun kawo maku kai da ya Abdallah " murmushi yayi a zuciyar shi yace " Ameerah ba dai surutu ba,  Aaimah ce tayi gyaran murya tana faɗin
"to ni dai a bani wuri na wuce dan na gaji da tsuyuwa" girgiza kai safwan yayi da murmushi a fuskar shi yace
"Aairah uwayen ƙorafi, zo ki wuce kar ki faɗin ƙasa " ya faɗa haɗi da matsa mata hanya, ciki ta shige tana faɗin " wai dan Allah mi yasa ya safwan kake ce man Aairah ne, ba fa ita bace wannan Aaimah ce " ta faɗa yayin da take ajiye tray ɗin kan carpet, Ameerah ma bayanta ta bi ita ma ta ajiye wanda yake hannun ta
"to naji ina ita Aairah take na ganku ku ka ɗai, ita bata zuwa a gaisa" 
"tana parlor wurin su mom " Aaimah ta faɗa yayin da take nufar ƙofa
"to ki kira man ita Please" da to Aaimah ta amsa haɗi da nufar ƙofar fita su ka fice,  tana zuwa wurin su mom tace "Aairah ki je ya safwan yana kira" ɗagowa Aairah tayi tana faɗin ni kuma
"A'a ba ke ba ni " Aaimah ta faÉ—a yayin da take jan kujera ta zauna
"dallah daga tambaya zaki wani mai da man da baƙar magana "
"an mai da maki, dallah malam idan zaki tashi kije ki tashi idan kuma bazaki tashi ba kiyi ta zama Æ´ar rainin wayau, wai ke A'a ni " Aaimah ta faÉ—a tana kwai kwayon yanda Aairah tayi magana,
Aairah tace " mom kina jinta ko,daga maganar ariziƙi sai ta tsiya "
dafe kai mom tayi tana faÉ—in
"ya Allah, ke Aaimah kar na sake jin bakin ki ke kuma Aairah tashi kije kira da yake maki " 
tashi Aairah tayi tana hararar Aaimah, taɓe baki Aaimah tayi tana faɗin
"inga sun zazzago ƙasa  sannan zan san kina harara"tsaki Aairah taja haɗi da wuce wa ta nufi  part ɗin Abdallah, girgiza kai ka wai mom tayi ba tare da tace ma su komai ba.
Nocking tayi, izinin shiga aka bata, tura ƙofar tayi ta shiga, zaune yake kan sofa  kamar yanda su Aaimah su ka barshi hannun shi ruƙe da cup ɗin tea sai turiri yake,yayin da Abdallah ke zaune kan carpet yana haɗa breakfast fitowar shi kenan daga bedroom ya samu an kawo masu breakfast, safwan  ɗago da fuskar shi yayi ya zuba mata ido haɗi da amsa mata sallamar da tayi, gaishe da su tayi tana faɗin " ya safwan gani,Aaimah tace wai kana kira na " amasa mata gaisuwar yayi yana faɗin
"dama ba wani abu bane, kawai naga baki zo bane shine na ce su kira man ke mu gaisa tunda ke baki zo ba "
"zan zo ya safwan breakfast nake ne shiyyasa "
" ok yayi kyau, kin tashi lafiya"
" lafiya lau "
" masha Allah "
" ina iya tafiya " ta faÉ—a dan duk ta gaji da tsayuwa da kuma kallon da yake mata
" eh kina iya tafiya dama kiran kenan "
"to sai anjima " ta faɗa haɗi da ju yawa zata wuce Abdallah ne yace " ki dawo anjima ki kwashe wannan kayan " ya faɗa yana nuna mata kayan breakfast ɗin da ke gaban sa, da to ta amsa haɗi da kama hanyar ficewa, idanu safwan zuba mata har sai da ta ɓace ma ganin sa tukun ya janye idon sa, karb su ka haɗa ido da Abdallah, hararar shi yayi yana faɗin
" lafiya da wannan kallon malam " taɓe baki Abdallah yayi yana faɗin
" aiki ya zo ga ma iya "
" Æ´an sa ido ba " safwan ya faÉ—a
" mi zan sa ma ido a nan, Allah ya kiyaye " Abdallah ya faÉ—a yana mai da kanshi kan breakfast É—in da yake yi
"Ohon maka kuma  wannan " safwan ya faɗa shima yana kai cup ɗin tea dake hannun shi baki, babu wanda ya sake cewa komai cikin su.

_*✨LAGOS✨*_

Zaune yake a office É—in shi yana aiki, files ne gaban shi na patient yana duba wa, wayar shi ce ta fara ringing, hannu ya sa ya É—auko ta, du ba mai kiran shi yayi, privet number shine abun da ya gani, tsaki ya ja haÉ—i da yin rejecting kiran ya cigaba da abun da ke gaban shi, wani kiran ne ya sake shigowa, ko kallon inda wayar take bai yi ba haka taita ruri har ta gaji tayi shiru alamar mai kiran ya gaji
sai ga message ya  shigo, ɗaukar wayar yayi dan ganin wanene ya turo mashi message, baƙuwar number ce ya gani kuma da alama bata nigeria ba ce, buɗe message ɗin yayi ya fara karan tawa kamar haka

_DR ABDULƘADIR ABUBAKAR NURADDEEN,manya yan aji bakwai ba'a ɗaukar baƙuwar number,ganinka  kuma sai an cika form,wow i like your style  keep it up na san nan gaba zai yi maka amfani, ba komai bane ya sa nake neman ka ba face ina so na sanar da kai illar dake cikin yaƙin da kake son  jefa kanka aciki,manyanka ma sunyi ba suci riba bare kai ƙaramin alhaki, ko da yake hausawa na cewa barewa baza tai gudu ɗan ta yayi rarrafe ba malam Abdulƙadir o afuwan dr Abdulƙadir, kar kace na mai da kai malamin makaranta 😊, ya ta kwaranka kuma kakan ka,mun kwana biyu ba mu gaisa ba amma da alama yanzu na lura  kana so mu dawo da zumunci dake tsakanin mu , fatan yana lafiya shi da hajiya zainab ina nufin ummy????, 
Abdulƙadir ina mai baka shawara idan har kana son zamanka lafiya a duniyar nan to ka tsame hannuka daga abun da kake shirin aikatawa gudun aikata abun da zai jefa ka cikin matsala kai da iyalanka, fatan zaka ɗauki shawarata duk da na san kai mai taurin kai ne, amma ina mai baka shawara._

Wani wawan tsaki shazim ya ja lokacin da ya kawo ƙarshen message ɗin yana faɗin " aikin banza matsoracin banza da wofi kawai, mu zuba mu gani ni da kai da duk wani mai hali irinka shege ka fasa " ya faɗa yana
maida kanshi yayi kan abun da yake, wani tsakin ya sake ja yana sake faÉ—in " aikin banza matsoracin banza da wofi kawai "

Ƙofar office ɗin yaji an turo an shigo, majeed ne ya shigo a uzirce kamar wanda aka jeho, wurin shazim ɗin ya matsa yana faɗin " amshi shazim ka gani " ya faɗa yana miƙa ma shazim wayar shi, amsar wayar shazim yayi yana duba abun da majeed ɗin ke nuna mashi, text message ne shima aka turo mashi da irin number da aka turo ma shazim yanzu, karanta message ɗin shazim ya shiga yi

_ABDULMAJEED MA'ARUF WAKILI,na san za kayi mamakin wanene ni da kuma sunan ka da na ambata, kar kayi mamaki yanyi ne ya zo da haka.
a taƙaice dai abun da ke tafe da ni,  ba wani abu bane face ina so na ja maka kunne kai da  abokinka, ku rufa ma kanku asiri ku fitar da kanku acikin yaƙin da  iyayen ku su ka kasa,idan kuma ba haka ba zaku sa kanku cikin bala'in da ba kuyi tsammani ba ku da iyalanku, shawara ce idan kun  ɗauka  ku zata yima amfani idan kuma kun ƙi to duk abun da ya biyo baya  kuyi kuka da kanku._

Tsaki shazim yaja yana miƙa ma majeed wayar shi, amsa majeed yayi yana faɗin
" ni dai shazim a ganina mu fitar da kan mu a wannan matsalar ko dan su Ammy "
" tsoro kaji ne wai majeed?"
" dole naji tsoro shazim, barazana fa yake mana, ni abun da nake ganin zai fi shine kawai kayan nan mu miƙa ma hukuma su "
" to dan yana mana barazana sai mi, ya isa yayi mana abun da Allah bai nufa ba ne, sannan kaya da kake cewa mu miƙa ma hukuma su tamkar munji tsoron ne, kuma Allah zai kama mu da laifi duk wanda ya cutu a kan kayan "
" bai  isa ba shazim,kuma Allah bazai kama mu da lafin wani ba tunda hukuma muka ba kayan kuma muna kyautata zaton tayi adalci ne"
"majeed ina so ka fahimci wani abu a lamarin ƙasar nan cin hanci yayi yawa muna ba da kayan nan zai ba da cin hanci ne a bashi batare da tausayin bayain Allah ba da aka ɓata ma rayuwa ba, yau da ace ƴaƴansu zasu ba da bazan da mu amma inaji ina gani bazan bari a cuci al'ummah ba "

"haka ne shazim, amma duk da haka mu miƙama hukuma ko dan su Ammy dan  gaskiya ina jin tsoron abun da zai biyo baya idan muka cigaba da riƙe waɗannan kayan "
" to idan kana jin tsoro ka kira shi kace kai ba ruwanka, Amma ni ba gudu ba ja da baya " shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi wata ƙofa dake kallon in da yake zaune, tashi majeed yayi yana faɗin " miyasa zaka ce haka shazim, ko da naji tsoro ai bazan iya tsame hannu na ba na barka "
Shigewa ciki yayi ba tare da yace mashi komai ba, bin bayan shi majeed ɗin yayi, tura ƙofar ɗakin yayi ya shiga, ma daidai ci ɗaki ne mai kayan gaske harda ɗan madaidaici family bed a cikin sa da sofa masu kyau guda, tsaye ya hango shazim bakin wani ɗan ƙaramin fridge ya na ɗauko robar ruwa, sofa dake ɗakin ya nufa haɗi da samun wuri ya zauna, shima zama majeed yayi yana faɗin " Please shazim ina so ka fahimce ni ne, bana so mujefa wani daga cikin ahalin mu acikin matsala ne shiyyasa na ce haka" ajiye robar ruwan shazim yayi yana faɗin " majeed akwai wani ɗan adam daya isa yayi ma bawa abun da Allah bai ƙaddara ba "
"A'a shazim "
"to inaso ka fitar da wannan tsoron a ranka ka fuskanci gaskiya, duk wani barazana da zai yi mana yana yi ne dan muji tsoro "
"to shikenan, yanzu ya zamuyi "
"karka damu zanyi shawara komai na yanke zan sanar da kai "
"to shikenan bari na koma office na barshi ba kowa "
"to shikenan, ka ja man ƙofar idan ka fita" shazim ya faɗa, tashi majeed yayi ta fita haɗi da rufe mashi ƙofar kamar yan da yace.
Zamewa yayi ya kwanta kan sofar, idanuwan shi ya rufe  kamar mai bacci.

Duk  yinin ranar a wannan ɗakin yayi shi ko sallah a nan yayi ta, sai da yamma bayan sallar asr ya tashi ya koma cikin office ɗin kayan da ke kan table ɗinshi ya tattara ya zuba cikin locker sannan ya ɗauki briefcase ɗin shi da wayar shi ya fice zuwa parking lot in da ya ajiye motar shi, briefcase ɗin ya fara ajiye wa sannan ya zagaya ma zaunin driver ya zauna, key yayi motar haɗi da reverse ya nufi gate, da katar da shi mai gadi yayi ta hanyar ɗaga mashi hannu, parking yayi a bakin gate ɗin yana ce ma maigadin " lafiya dai ko?"
"lafiya lau ranka ya daÉ—e, dama wasu mutanen suka zo neman ka É—azu"
"Suna ina?"
"ban barsu sun shigo ba yallaɓai sun tafi "
"saboda mi mudi, nan fa asibiti ce dan mi zaka hana su shigowa idan suna tare da patient ne fa "
"yallaɓai abun da yasa na hana su shigowa shine basuyi kama da marasa lafiya ba yallabai wallahi da ƴan dambe su kayi kama duk sun wani sha baƙaƙen kaya kamar sheɗanu "
"mi suka ce maka da suka zo?"
"wai maigidan su ne ya aiko su wurinka,daga ganin ba su da gaskiya shiyyasa ni da su isya muka hana su shigowa "
"koma dai minene, daga yau idan su ka sake zuwa ka kirani ka faÉ—a man kaji ko "
"eh naji ranka ya daÉ—e, insha Allah su ka sake zuwa zan kiraka na sanar da kai "
"to shikenan, buÉ—e man gate na wuce"
"to yallaɓai " mudi ya faɗa haɗi da nufar gate  ya buɗe mashi, ficewa  yayi ya daga Asibitin ya hau kan titin da zai sada shi da  gida.

Wayar shi dake ciki briefcase É—in shi ce ta fara ringing, banza yayi da wayar dan ya san bazai wuce wannan shashashan mutumin ba ne, wani kiran ne ya sake shigowa, tsaki yaja yana faÉ—in
"sai kuma kayi ta yi"
Kira ne yai ta shigowa ba ƙaƙautawa amma ko kallon briefcase ɗin bai yi ba bare ya ɗauki wayar har ya iso gida, horn yayi a bakin gate mai gadi ya buɗe mashi, ciki ya shiga yayi parking a parking lot ya jima a motar bai fito ba wayar shi ya ciro cikin briefcase ɗin dan ganin wane mahaluƙin ne yayi tayi mashi wannan kiran duk da yana da ya ƙinin waɗannan mutanen ne sai dai kuma da ya duba mai kiran nashi number mansoor ya gani da ta Ammy sai noraiz da fatima, faɗuwa gaban shi yayi yana faɗin
"Ya Allah,  mike damun su Ammy su ke man wannan kiran" a hanzar ce ya buɗe motar ya fita ko briefcase ɗin shi bai ɗauka ba ya fice zuwa cikin gida yana shigowa main parlor tsaitsaye ya samu su Ammy har da mansoor wanda zuwan shi kenan, sallama yayi ya nufi Ammy yana faɗin "Ammy lafiya mike faruwa ne ??"

"Feenah ce ta fita tun ɗazu da safe tace man zata je gidan su ummy to shine tun ɗazu bata dawo ba da muka yi waya da  ummy nake ce mata feenah wai yaushe zata dawo naga yamma tayi ko nan zata kwana shine take ceman wai wace feenah ita duk yau bata ganta ba,  na kira wayarta ni da su fatima yafi a ƙirga amma a kashe kuma ka san bata da lafiya  "
A jiyar zuciya  shazim ya sauke  yana faɗin " wallahi Ammy ba kuji yan da kuka tayar man da hankali ba, yanzu duk dan wannan yarinyar ta fita ne kukai ta man wannan kiran kuma kuka tashi hankalin ku"
"shazim ba asan inda taje ba fa nace maka kuma an kira wayarta a kashe  amma kake faɗin haka "
"Ammy ina wannan yarinyar zataje da  har zata ɓata, kawai dai taje yawan banzan ta da ta saba amma kina nan zata dawo da ƙafar data fita "

ran mansoor ne ya ɓaci jin abun da shazim ke faɗa ya rasa miyasa shazim bai ƙaunar feenah , amma sai yayi shiru baice komai ba

"haba shazim ya za kace haka, feenah fa yarinya ce ina zata je a garinnan da bata sani ba,dama a abuja ne sai nace taje gidan su mahaifiyar ta ko gidan ƙawayen ta "
"Ammy ki kwantar da hankalin ki in dai akan wannan yarinyar ne ba in da zata shige a garin nan ta ɓata,  tana yawan da ta saba ne amma ba ɓata tayi ba  "
"wai shazim minene matsalarka da feenah duk kabi ka tsani yarinya kawai dan ta nace tana sonka shine zaka riƙa jifar ta da waɗannan kalaman " slowly shazim ya juya yana kallon mansoor dake tsaye bayan shi  fuskar shi a murtuke,tsantsar ɓacin rai ne a idanuwan shi, side smile shazim ya saki yana faɗin " kai kuma saukar yaushe?"
" ban sani ba " shine kawai abunda mansoor ya faÉ—a
" to fa daga tambaya "
"ka riƙe tambayar ka bana so" murmushi shazim yayi wanda ya bayyana kyawawan haƙuran shi
"wai wannan fushin duk na minene ƙarya na faɗa,bata yawan ne " shazim ya faɗa yana ɗaga mashi gira
"kanka ake ji kuma " mansoor ya faÉ—a
"dan Allah ya isa haka, ya muna cikin wani hali ku kuma daga haÉ—uwar ku zaku kama yi ma mutane jaraba " Ammy ta faÉ—a
mai da kallon shi yayi ga Ammy yana faɗin " kar ki damu fa Ammy zata dawo ne dan kanta " yana gama faɗar haka ya nufi sama zuwa part ɗin shi da kallo kawai su ka bishi, sun rasa wace irin tsana ce shazim ke yima feenah da har bai damu da ɓatan ta ba kuma ya san bata da lafiya.

Zaune su kai a parlor ko wa yayi shiru suna jiran tsammani har akayi sallar magrib ba feenah ba labarin ta, wasa wasa dai har tara na dare feenah bata dawo ba kuma duk in da suke zargin za su ganta sun je amma ba labarin ta, fidda rai su kayi da zata dawo, mansoor ne yace su tashi kowa yaje kwanta idan bata dawo ba gobe za su je police su  shigar da ƙara kawai, kowa ya aminta da maganar mansoor haka ne yasa su ka tashi kowa ya nufi ɗakin baccin shi.
Ammya na shiga ɗaki wayarta na fara ringing, abun yayi matuƙar bata mamaki ganin number feenah bayan yanzu ta gama kira a kashe, picking call ɗin tayi da ko sallamar da feenah keyi bata amasa ba tace " feenah ina kika shige duk kin bi kin tayar mana da hankali " daga cikin wayar fashewa da kuka feenah tayi tana faɗin " Ammy ni bana son na koma abuja "
" haba feenah idan baki son komawa sai ki faÉ—a man, amma ba wai ki bar gida ba, yanzu kina ina?"
"ina gidan su wata class mate É—ina , dan Allah karki bari ya mansoor ya tafi da ni "
" shikenan bazan bari ya tafi da ke ba amma kar ki ƙara irin wannan shashancin kina jina"
" to Ammy bazan sake ba in sha Allah "
" to shikenan, gobe ki dawo da safe "
" to Ammy "
" yawwa sai da safe " ammy ta faɗa haɗi da yin rejecting kiran, fita tayi zuwa part ɗin shazim,nocking tayi mansoor ne ya  zo ya buɗe mata, a bakin ƙofa ta tsaya, mansoor yace" ki shigo mana Ammy "
" A'a ba sai na shigo ba, feenah ce ta kirani yanzu "
da sauri mansoor yace " ta na ina Ammy?"
"tana gidan wata ƙawar ta" 
Shazim dake zaune kan sofa taɓe baki yayi a zuciyar shi yana faɗin " ni ai na sani "
" amma feenah bata da hankali shine bazata faÉ—i ba zata tayar ma mutane da hankali dan sakarci"
" kai dai ka bari kawai mansoor, wai abuja ne bata son komawa shine tayi tafiyar ta "
" lallai ma yarinyar nan, zata dawo ai ta samu mutane " a zuciyar shi kuma yace  " na san ba kowa zai sata ba sai Innah "
"idan zaka tafi  ita ka barta nan ɗin tun da tana son zama"
"Amma Ammy gata ga sa'ada abun zai yi yawa. "
"haba mansoor wane irin yawa ana zaman lafiya, idan ita ma Kairiyya bazata bika ba ka ƙyaleta lokacin da su ke san komawa sai su koma"
" shikenan Ammy" mansoor ya faÉ—a
" yawwa, sai da safen ku " Ammy ta faɗa haɗi da ja masu ƙofar, sai da safe su yayi mata, bedroom ɗin shazim ya nufa dan shi har ya shige.
Episode  66_67

Kamar yanda Ammy tace ma Feenah  tun da safe ta dawo, sosai mansoor yayi mata faɗa kamar ya daketa,arziƙin Ammy kawai taci ya rabu da ita, washe gari da zai tafi ma faɗa yayi mata sosai akan ta kama kanta, in dai ta bari yaji ta aikata wani abu to zai zo ne da kanshi ya tafi da ita komai kuwa zatayi, ce mashi tayi inasha Allah ta bari  bazata yi wani abu ba, noraiz da fatima da sa'ada su ka raka su airport shi da kairiyya dan shazim tun faɗan da su kayi ba su wani shirya ba shiyyasa bai raka shi ba.

_*✨KATSINA✨*_

Addimisson ɗin su Aairah abokin uncle Ahmad ya amso,  sai dai kuma ba anan branch ɗin su dake abuja ba su ka basu Addimisson, branch ɗin su dake lagos su ka tura su,ko da uncle Ahmad ya sanar da abie cewa abie yayi baza su tafi lagos ba sai dai ya nema masu wata school ɗin anan katsina amma baza su lagos ba saboda shi baya son su zauna a hostel, mom ma da taji cewa tayi gaskiya sai dai suyi a nan amma bata bada goyan bayan suje lagos ba,su kuma suna so ba yanda ba suyi da abie ba akan ya amince yace A'a, sai ma kiran wani abokin shi yayi da ɗiyar shi ke school of nursing yace idan ba su gama bada addimisson ba yana so zai sama ma su Aairah.
" gaskiya ina tunanin sun gama É—aukar É—alibai amma zan bincika naji"
" to shikenan, komai kenan sai ka kirani ka sanar dani "
" to in sha Allah " abie ya faÉ—a haÉ—i da yin rejecting kiran
" haba yaya miyasa zaka ce haka, tunda dai suna son makarantar yaya ai banga aibu ba, kabi su da adu'a kawai in sha Allah babu abun da zai faru da su har su gama " uncle Ahmad ya faÉ—a
" Ahmad ni bazan bar yarannan su zauna a hostel ba, ko da ace a cikin garinnan ne bare ba nan ba can wata uwa duniya,  gaskiya bazan iya ba "
"yaya wai mi kake tsoro ne aciki, tarbiyya dai daidai gwargwado suna da ita nasan baza suyi abun da za muyi da mun sani ba, dan Allah ka bar yarannan suyi karatun su inda su ke so, ka bi su da adu'a kawai "
"dan Allah abie ka bar su, in sha Allah wani abu bazai faru da su ba sai alkairi " Abdallah ya faÉ—a wanda zuwan su kenan shida safwan yaji uncle Ahmad nama abie magana akan makarantar
"Ai kai daman bakin ku É—aya da su "
"ba haka bane abie, tunda suna so kuma kai kan ka ka yarda da nagartar makarantar ka barsu kawai dan Allah"
"yaya idan kana tsoron rayuwar da za suyi ne, ni ina da wani aboki dake cikin makarantar a nan yake zaune da iyalin shi sai kawai su zauna a gidan shi amma dan Allah karka hana su "
"Yanzu dai sai Alhaji umar ya kirani na ji, idan an samu nan É—in to nan kawai za su yi idan ba'a samu bane to"
"dan Allah dai ka bar su kawai suyi karatun su a inda su ke so "
"Kaga wanda kake magana abokinka ne kar mu takura mashi "
"Idan kana ganin haka yaya to su zauna a hostel ɗin shi sai ya riƙa lura da duk wani shigi da ficen su "
"abie wallahi ina mamakin yanda kake ko kwanto akan su Aaimah"
"dole nayi kokwanto Abdallah, yara ne yanzu ka haife su ne baka haifi halin su ba "
"haka ne abie, abun da nake gani kawai mizai hana su zauna a gidan su shazim,dama fatima a can shazim ya nema mata addimisson kaga kawai sai su riƙa zuwa tare suna dawowa tare, hankalin ka ma sai ya fi kwanciya "

"to zan dai fi yarda da hakan, amma kana ganin baza'a ta kura su ba "
Uncle sadiq dai na gefe yana sauraron su kamar yana fahimtar mi suke faɗa, safwan ma sauraron na su yake amma baice ƙala ba

"haba abie wane irin takura kuma shazim fa nace maka ba wani ba,yanzu idan yaji kace haka ai bazai ji daÉ—i ba"

"duk da haka Abdallah, ka san halin su Aairah ba jin magana su ke ba kana gani a nan idan iya shegen su ya motsa yanda ake fama da su"

"wannan abie duk rashin aikin yi ne ke damun su, Amma da sun fara zuwa makaranta za su daina wasu abubuwan "

Fitowa su kayi daga cikin gidan
Aairah na ɗauke da tray wanda snacks ne a ciki, Aaimah kuma ruwa ne acikin trayn dake hannun ta yayin da Ameerah  bowl ne babba a hannun ta  yanka kun kayan marmari ne a ciki, wurin su abie su ka nufa dake zaune  a garden, ƙarasawa wurin su su ka yi,ya Abdallah ne ya nufe su trayn dake hannun Aaimah ya amsa safwan kuma ya amshi na hannun Aairah yana ce mata " sannu da ƙoƙari "
Yawwa tace tana ya mutse fuska
"to fa ni da yake bani da galihu shiyyasa ba'a amshi na hannu na ba " Ameerah ta faɗa, dungure mata kai Abdallah yayi yana faɗin "bani nan uwar yan ƙorafi " turo baki tayi tana faɗin " yo ai dole nayi magana ya Abdallah an amshi na hannun su amma ni ban da ni "
"to naji Abdallah ya faÉ—a yana ajiye bowl É—in da ya amsa a hannunta kan table É—in da ya ajiye saura kusa da su abie.

"to oya a koma ciki" Abdallah ya faÉ—a, juyawa su kayi su ka nufi cikin gidan
wurin su abie ya koma,zama yayi kan kujerar da ya taso É—azu yana faÉ—in
" abie babu wata matsala za su iya zama a can "
" amma Abdallah baka ganin za'a takura su, ni dai da ka bari kawai na nemar masu wata a nan"

" abie babu wani takura, amma idan baka son zaman su a can to dan Allah ka bari su zauna hostel,babu abun da zai faru da su in sha Allah, Amma na san Ammy bazata ji daÉ—i ba ace tana garin su zauna a hostel "

"A'a gaskiya ba za su zauna a hostel ba "
" to shikenan ka bari kawai nayi ma Ammyn magana "
" to shikenan, kira ta ni sai nayi mata baya ni da kaina"
to Abdallah yace yayin da yake zaro wayar shi dake cikin aljihu yayi dialing number Ammy, tana picking ya miƙa ma Abie tana faɗin gashi abie, amsa yayi haɗi da kara wayar a kunne, muryar Ammy yaji tana sallama haɗi da faɗin " Abdallah "
"bashi bane abie É—in sa ne, an wuni lafiya "
" lafiya lau Alhmdllh, ya aiki"
" Alhmdllh, ina su shazim "
" suna nan lafiya, ya su hajiya kubrah da ƴaƴa na, har yau dai sunƙi zuwa ko daya ke ba'a kawo man su ba zance ?"
" suna nan lafiya saboda su ne ma yasa na kira "
" to, Allah yasa lafiya?"
"lafiya lau, maganar makaranta ne mun nema masu makaranta ne a abuja to da suka basu addimisson sai suka tura su branch É—in su dake nan lagos, bana son su zauna a hostel ne saboda yara yanzu suna gaban ka ma sai a hankali bare ace basa gaban ka,shine nake son su zauna nan sai su dunga zuwa suna dawowa "
" Amma gaskiya banji daÉ—i ba,yanzu akan su Aairah har sai ka ka kira da kanka, haba dan Allah "
" ba wani abu bane, faÉ—in ai yana da daÉ—i "
"duk da haka dai banji daÉ—i ba "
" to ayi haƙuri "
"shikenan ya zanyi tunda anriga an gama, yanzu yaushe za su fara lectures?"
" nan da sati uku ne "
"to Allah ya nuna mana lokacin, nan ai gida ne,ko da kama barsu a hostel naji labari bazan bar su ba "
"to shikenan nagode "
"wane irin godiya kuma"
"to shikenan sai sun zo É—in "
" to Allah ya kawo su lafiya "
"Ameen ya Allah " abie ya faɗa  sallama su kayi ammy na faɗin tana gaishe da mom, miƙa ma Abdallah wayar  abie yayi , amma bai san yana yi ba saboda hankalin shi ba anan yake,
_har wani ajiyar zuciya  ya saki daya ji ammy tace ko da sun zauna a hostel zata dawo da su ne gida, yanzu ko ba komi ya samu kafar da zai riƙa zuwa lagos ba tare da wani abu ba_

zaungurin shi safwan yayi cikin magana raÉ—a raÉ—a ya ce
" hankalin ka yanzu ya kwanta ko"
"sosai ma kuwa " Abdallah ya faÉ—a a hankali yanda su abie baza su ji ba "
"Amshi wayar ka na ce " abie ya faɗa yana sake miƙo mashi wayar, amsa yayi yana faɗi
"ka gani ko Abie, na san ma bazata ji daÉ—i ba "
"duk da haka dai tunda an faÉ—a mata ai shikenan nan "
murmushi uncle ahmad  yayi yana faɗin "yanzu sai da ka samar ma su idan ka fi yarda sannan hankalin ka ya kwanta yaya"
"bazan ɓoye maka ba gaskiya sai yanzu naji zan iya bari suyi ne sa da ni "
"to ai shikenan tun da ka amince "

Cikin gida su Abdallah su ka nufa shi da safwan, suna shiga main parlor da hayaniyar su Aairah su ka fara cin karo suna ma Ameerah dariya  tana kuka saboda ba su samu addimisson a abuja ba, ta so suyi makaranta tare amma Allah bai nufa ba shine suka tasa ta gaba suna mata dariya.

"ku har gobe baza kuyi hankali ba, ai gara ma da abie yace anan za kuyi karatu saboda baku da hankali "
tsit su kayi, Ameerah kuma bata bar kukan da take ba tsawa Abdallah ya daka mata yana faɗin " billahil'azim ko kiyi man shiru ko ranki ya ɓaci " shiru tayi amma hawaye basu daina zuba ba, tsaki yayi ya nufi part ɗin mom, safwan kuma zama yayi kan sofa Aaimah tace "dan Allah ya safwan da gaske abie bai amince ba " ɗaga mata kai yayi alamar eh,ɓata fuska Aaimah tayi tana faɗin
" Amma miyasa abie zai ƙi amincewa "   dariya Ameerah ta kwashe da ita " wallahi Allah ya ƙara naji daɗi da abie ya ƙi amincewa "
"yar baƙin ciki in sha Allah zai amince ne"
"bazai amince ba in sha Allah" 
tashi safwan yayi yana faÉ—in
"Aairah ki kawo man tea please " turo baki tayi tana faɗin to, dama tun da ya zauna wurin bata sake cewa ƙala ba, haka nan ita fa shishige matan da yake yi ba burgeta yake ba,tashi tayi ta nufi kitchen ɗin shaf shaf ta haɗa mashi tea ta nufi part ɗin Abdallah, nocking tayi, da kanshi yazo ya buɗe mata ƙofar matsawa yayi gefe yana faɗin ki shigo ciki
" mom ke kirana " ta faÉ—a so kawai take ya amsa ta gudu, amsa yayi yana faÉ—in" to muje can main parlor sai na sha a can idan kin dawo daga wurin mom sai ki zo" to tace haÉ—i da yin gaba yana binta a baya har main parlor, kan table ta ajiye mashi ta nufi É—akin
mom  da Abdallah ta ci karo zai fito,  yana ganin ta yace
"harkun biyo ni kenan"
"yaya ba kai na biyo ba wurin mom na zo "
" ba wani " ya faɗa haɗi da ficewa, ciki ta ƙarasa tana faɗin
" mom kinji dai ko abie bai amince ba"
"to ya za kuyi sai haƙuri "
" ya muka iya tunda bai amince ba " ta faÉ—a kamar zatayi kuka bed É—in mom ta nufa ta kwanta, murmushi mom tayi " yanzu fa kina iya kuka "
" A'a mom ba kuka zanyi ba"
" ai nayi tunanin shi za kiyi, to wasa yake abie É—in ku ya amince "
" dan Allah mom da gaske "
" A'a da ƙarya "
" sorry mom, farin ciki ne yasa nace haka, amma naji daɗi da abie ya amince " tana gama faɗa ta fice ta nufi parlor wurin su Aaimah, dariya ta fara yima Ameerah kafin ta sanar da su abie ya amince,ƙululun baƙin ciki kamar ya kashe Ameerah, saboda dariyar da Aairah ke yi mata.
Aaimah kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha da Aairah ta sanar da ita abie ya amince, haushi da takaici kuwa wurin Ameerah ba'a magana.
_Wannan kenan_
Lokacin da Ammy  su ka gama waya da abie,parlor ta fito wurin su fatima take sanar da fatima zuwan Aairah, fatima kamar tayi hauka dan daɗi da ma ta jima tana son ganin su har cewa take idan su ka samu hutu sai taje katsina ko dan taga waɗannan yan biyun na su ya dr, yau gashi burin ta na ganin su zai ciki har ma za su zauna tsawan wa su shekaru,taji daɗi sosai da wannan labari da Ammy ta sanar da ita Ammy na barin wurin ta ɗauki wayar ta ta kira Abdallah dan sake ji daga bakin shi, ƙara tabbatar mata yayi da sunan zuwa nan da three weeks.
"ya dr dan Allah su zo next week, wallahi na ƙosa na gan su "
"one week da three weeks ai duk É—aya fatima, in dai da rai da lafiya za ki gansu har ma sai kin gaji "
"duk da haka dai ya dr"
"to ni dai babu ruwana hukuncin abie ne wannan "
"shikenan Allah ya kaimu, ka basu wayar to mu gaisa "
"sai dai na tura maki number Aairah ko ta Aaimah"
"kai ya dr, to naji ka tura man duka "
"to shikenan zan tura maki "
"yawwa ya dr nagode bye "
"Wait naga sai wani rawar ƙafa kike, karfa su zo ni ki share ni kuma dan saboda ke nasa abie ya amince za su zo dan nima na samu damar ganinki" ya faɗa yana ɗan murmushi, rufe ido fatima tayi ita a dole kunyar zancen shi taji
"kinyi shiru idan haka ne gara tun wuri na sani "
"haba ya dr dan Allah ka daina faÉ—ar haka, kaima ka san babu abun da zan samu da zai É—uke man hankali har na share ka "
"na sani, nima wasa nake maki, naga dai kina ta rawar ƙafa ne "
"na ƙosa na gansu ne"
"very soon zaki gan su "
"to shikenan, katuro man number"  to ya faɗa haɗi da yin rejecting kiran, bayan kamar minti ɗaya sai ga number ya turo mata duk da ta Aairah da Aaimah,ko kiran shi tace taga number bata yi ba saboda zumuɗi, number Aairah tayi dialing, da sallama Aairah a bakinta tayi picking kiran, a hanzar ce fatima ta amsa mata sallamar tana faɗin
"sister ya kike, ya gida "
"lafiya lau, pls wake magana " Aairah ta faɗa, murmushi fatima tayi sannan tace " na san bazaki gane ni ba, fatima ƙanwar ya shazim abokin ya Abdallah"
"ooo Allah sarki, ya kike ya su Ammy "
"lafiya lau su ke, yanzu take faÉ—a man zaku zo lagos ke da Aaimah"
"Eh"
"dan Allah kuce ma abie ya barku ku zo next week ba dole sai nan da sati ukku ba pls "
abun mamaki ma ya ba Aairah ganin yarda fatima ke zumuɗin zuwan su duk da ba su san juna ba a zahiri, hakanan taji fatima ta kwanta mata arai ita ma taji ta ƙagu da taganta
" shikenan in sha Allah zan roƙe shi ni da Aaimah "
"yawwa nagode sosai, ina Aaimah take?"
" tana wurin mom "
" ok dan Allah ki bata mugaisa harda mom É—in "
" to shikenan, kashe idan naje wurin su sai na kiraki "
" to " fatima ta faÉ—a haÉ—i da kashe wayar.
Wani wawan tsaki feenah taja, dama tun da taji Ammy ta faɗin zuwan su Aairah taji ranta ya ɓaci hakanan taji ta tsane su duk da bata san su ba amma taji  bata ƙaunar su zo
" haba ya feenah miye abun tsaki kuma?"
" dole nayi tsaki, saboda ke shashasha ce baki san mutane ba amma dagaji za su zo sai wani zumuÉ—i kike "
" bangane bata san su ba, ke dai idan baki san su ba to kiyi shiru amma ita ta san su ko nima nan da kike gani na san su " sa'ada ta faÉ—a tana hararar feenah
"ƙannan uwarki ne su da zaki ce kin san su,kuma wallahi na kama ki zaki san ni kike harara"
" ba ƙannan uwata ba ne, amma ai su muslmai ne kuma muslmi ɗan uwan muslmi ne, to wai ma ina ruwanki idan sun zo ke dai ba a kanki za su zauna ba kuma ai dai inji nan ba gidan dady bane bare har sai kin zaɓi wanda zaizo kema kara ki akayi " sa'ada ta faɗa tana miƙewa tsaye dan ta san abun da zai biyo baya tsakanin ta da feenah ba mai kyauba ne, tashi feenah ita ma tayi ai tana gani haka ta kwasa da gudu sai ɗakin Ammy tana faɗin " Allah yasa idan su ka zo su koya maki hankali, tunda ta ƙamarki yi ma mutane wulaƙanci sai kace ma nan ɗin gidan ku ne "
"ai da kin tsaya inji uban da kike faÉ—a ma wannan maganganun " gwalo sa'ada tayi mata tana faÉ—in
"da karyeyyen hanun " ta faɗa tana langabar da hannun ta irin ciwannan taji  tana faɗin " wayyo Ammy wurgi ya shazim yayi da ni "
A harzuƙe feenah ta bi bayan ta, da gudu sa'ada ta shige ɗakin Ammy jikake garam ta banko ƙofa ta rufe da key, bubbuga ƙofar feenah ta shiga yi tana faɗin
"wallahi sai na ci ubanki na kamaki "
daga cikin É—akin sa'ada tace
" ki kashe ni idan kin tashi "
" zaki san da ni kike magana feenah ta faɗa haɗi da barin bakin ƙofar, ta koma cikin parlor, samun fatima tayi tana   waya da mom da Aaimah, haushi kamar ya kashe feenah, ta shima tayi ta nufi bedroom ɗin ta da take kwana, wayarta ta ɗauka tayi dialing number Innah, tana picking ko sallama bata ti ba ta zayyane mata komai dan gane da zuwan su Aairah har da ƙari
Baƙin ciki da takaici ne ya cika Innah ƙala bata ce ba ta kashe wayar, haushi kamar ya kashe feenah jin innah bata ce komai ba.
Shazim da ya dawo gida Ammy ke sanar da shi zuwan na su, Allah ya kawo su shine kawai abunda yace.
A kwana a tashi babu wuya wurin ubangiji yau ya rage saura kwana biyu su Aairah su zo lagos, duk wani shiri da za suyi sun kammala, ranar da zasu tafi kawai su ke jira, Abdallah ne zai kai su, sai ya gama su komai a school sannan zai dawo.

Ameera sun koma Abuja tun last week, ta sha  kuka kamar mi bata yanda zata yi dole ta haƙura, taci ƙurin suyi school tare amma bai nufa ba.

Washe gari ranar da za su tafi har gida su ka je su ka yi ma dadi sallama, sannan su ka je gidan granny da gidan Aunty safiya, najma ma kamar ta haɗiye zuciya dan baƙin ciki za su tafi su barta, saboda ita dadyn ta a nan ya samar mata da school, sai da dare sannan su ka koma gida...

_WASHE GARI_

_SEASON TOW KENAN, MU HAƊU A SEASON TOW DAN JIN YARDA ZATA KAYA ZAMAM SU AAIRAH A LAGOS, GA FEENAH YAR BAƘIN CIKI_

_SHIN WANENE SU SHAZIM SUKA RIƘE MA KAYA YAKE MA SU BARA ZANA, YA MAGANAR AURAN SHAZIM DA FEENAH DUKA WANNAN AMSAR TANA CIKIN SEASON TOW_

_ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFIN DOCTOR SHAZIM SEASON ONE_

_GA MAI SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN DOCTOR SHAZIM 500 NE BA YAWA_

_9131306012 MUKHTAR HADIZA OPAY BANK_

_SAI A TURA SHAIDAR BIYA TANA WANNA NUMBERS 09131306012 KO 08133650574_
'
Chapter 3 · 0% Book details