← Book details Doctor Shazim Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 3

part biyu ne gidan , ɗaya daga cikin part ɗin  suka nufa, da sallama abakin su suka shiga cikin parlorn

Doctor Shazim Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

parlorn ne mai girman gaske  wani dattijone zaune kan carpet sai wata yar tsohuwa dake kusa da shi tana mika masa magani da ruwa.
wurin su suka ƙarasa wannan yar tsohuwar ce ta dago tana amsa ma su sallamar da su kayi, haɗi da cewa "oyoyo ango saukar yaushe" noraiz na murmushi yace "jiya" yayin da  suke samun wurin zama  kan carpet,ammy tace "ina kwana ummy, ya jikin baba"
ummy tace "lafiya lau, jiki  Alhmdllh" masha Allah Ammy tace , sannan ta kalli baba tana faɗin "ina kwana   baba,  ya ƙarfin  jiki" 
"jiki Alhmdllh da sauki,
wa nake gani kamar NURADDEEN? " Baba ya tambaya.
murmushi Noraiz yayi yana faɗin "shine mlm, ya ƙarfin jiki?"
"jiki Alhmdllh nuraddeen, saukar yaushe"
"jiya" Noraiz ya bashi amsa
"masha Allah,ya karatu?"
"Alhmdllh mlm" jin jina kai malam yayi yana faɗin "masha Allah, ina wannan ƙaton gwawron yayan na ka,mai gudun aure" murmushi Noraiz yayi yana bashi amsa da yana hospital
"Masha Allah, Allah ya taimaka" ya fada, sun jima suna fira har kusan 12  sannan Noraiz yace "malam zanje wurin yaya"
"to a dawo lafiya"
"Allah yasa" Noraiz ya fada, sallama yayi ma su hadi da nufar kofar fita daga parlorn ya fice.
kallon ammy malam yayi yana faÉ—in" jiya Ahmad ya kira ni kan maganar shazim, sun ji shi shiru, kuma suna ta kiran shi basu samu, har mansoor sai da ya kirani shima bai samun shi a waya ko da ya kira shi"
"eh haka yace man nima da ya kirani "
"kin faÉ—a ma shazim É—in?"
"eh na faɗa mashi,amma har yanzu amsa ɗaya ce,bashi da wacce yake so" ɗan nisawa malam yayi sannan yace "na lura so yake mu cire hannun mu daga maganar, mu ƙyale shi da su Ahmad ɗin, su yanke mashi duk hukuncin da suka ga dama"
"haka nima nace mashi, zamu cire hannun mu a lamarin suyi duk abun da suka ga dama"
ummy tace "ba haka za'ayi ba malam, ina ga a ƙara mashi lokaci ko da ba mai tsayi ba"
malam yace "lokaci na nawa za'a bashi zainab, tun yaushe ake bashi lokaci"
"duk da haka dai, a ƙara mashi ko da wata ɗaya ne "malam yace "to shikenan"

Noraiz yana shiga cikin eko parking yayi a parking lot, fitowa yayi ya nufi cikin hospital, da yake office din shazim chansama yake hakan yasa shi hawan elevator ta sauke shi a floor É—in da office É—in ya ke.
A bakin office din ya tsaya,nocking yayi daga ciki aka bashi iznin shiga
ƙofar ya tura ya shiga, shazim ya samu zaune yana aiki cikin laptop
sallamar da yayi shazim ya amsa mashi, wuri ya samu cikin ɗaya daga kujerun office din ya zauna
"ya aiki yaya?"
"Alhmdllh" kawai shazim yace yana yana tambayar  jikin malam
"Alhmdllh yaya,ya ji sauki" dr kabir ne ya shigo office din yana ganin Noraiz yace
"saukar yaushe Noraiz?"
"jiya Yaya, ya Aiki " Noraiz ya fada
"Alhmdllh Noraiz, ya school "
"school Alhmdllh "
"masha Allah" fira suka shiga yi ta yaushe gamo shida dr kabir shazim na sauraron su yana aikin gaban sa,  kiran sallar zuhur ne ya katse masu firar  su ka fice zuwa masallaci domin yin sallah
daga cana abnoor  shazim da Noraiz ɗin su ka wuce.

✨ Aairah ✨

dawowar su kenan daga school dan ko uniform basu cire ba suka haye bed saboda ba ƙaramin  gajiya su kayi ba ' dan Aairah da wani irin zazzabi ta dawo 

Mom ce ta shigo É—akin tana cewa "lafiya kuke, ko uniform ba ku cireba kun kama bacci"
"wallahi  mom mun gaji ne sosai shiyyasa, kuma ma Aairah bata jin daɗi,zazzabi ne a jikin ta"
"wani aiki ku kayi ne a  makarantar" mom ta fada yayin da take ƙarasawa  kan bed,  hannunta ta ɗaura  saman wuyan Aairah "ya salam" mom ta fada saboda jin zafin dake fita daga jikin Aairah "mi ke damunki?"
"zazzabi ne da ciwan kai"
"ok yaka mata ki tashi ki cire uniform ki  watsa ruwa, bari naje na dauko maki magani kafin yayan ku ya dawo" tashi tayi zaune mom tace ma Aaimah ta shiga bathroom ta hada mata ruwan wanka, to tace hadi da nufar toilet, ficewa mom tayi daga daki 
Uniform ɗin jikinta ta cire  ta daura towel,  Aaimah ta fito tana cewa sister kishiga ga ruwan chan " to nagode  sister" ta fada tana nufar toilet ɗin
kayan jikinta ita ma ta cire Aairah na fitowa ta shiga
bed Aairah tahau tana jan blanket,wani irin sanyi take ji saboda wankan da tayi.
Mom ce ta shigo hannun ta ɗauke  da tere wanda ta haɗa ma Aairah abinci 
"wai kwanciyar kika sake?" wurin ta mom ta nufo,  table ɗin  dake ɗakin  ta jawo ta daura tray da ta shigo dashi,  hawa tayi kan gadon tana fadin "tashi ki ci abinci ga maganinan"
tashi tayi zaune "baki sa kaya ba kenan?" mom ta fada tana nufar wardrobe din su, riga mara nauyi mom ta dauko mata
"tashi kisa" mom ta fada yayin da take mika mata rigar,
amsa tayi tana tashi ta sanya rigar sannan ta dawo kan gadon ta zauna abincin da  ta haɗa mata tamika mata
tana gama ci mom ta bata magani tasha sannan ta koma ta kwanta blanket Mom taja mata
ta haɗa tiren da Aairah taci abinci ta fice da shi yayin da take cema Aaimah inta gama shiri ta fito taci abinci ita ma 
shaf shaf Aaimah  ta shirya sannan ta dawo kusa da Aairah
"sister ya jikin naki"
"da sauki " Aairah ta fada
"ok Allah ya kara sauki, bari naje naci abinci na dawo "
gyada mata kai Aairah tayi alamar sai kin dawo
ficewa Aaimah tayi daga bedroom din , parlor ta nufa Mom ta samu kan dinning ita da abie 
ƙarasawa tayi wurin su tana cewa "ina wuni abie"
"lafiya lau,yanzu Mom din ku ke fada man Aairah ba lafiya,  ya jikin nata?"
"da sauki abie "
"to Allah ya bata lafiya, Idan Abdallah  ya dawo sai ya duba ta,in ma taka ma ayi mata allura, koh mi kenan dai " abie  ya fada, Aaimah a jiye spoon din dake hannun tayi tana dariya hadi da fadin "kace yau akwai daru,Aairah za a yima allura?, tashin hankali kenan"
"ka jita sai kace ba jirgi daya ya kwasu ku ba,  kema son  allurar kike ne?" Mom tafa hadi da mangare mata kai, sosa inda Mom ta mangareta tayi tana turo baki da fadin "Allah gara ni da Aairah Mom" 
"Bawani nan" Mom ta fada,suna gama cin abincin abee ya mike yana cewa "bari naje na duba jikin ta" ya fada  yayin da  yake nufar dakin su, samunta yayi kwance kan gado kamar yanda Aaimah ta fita ta barta, duk ta rufe jikinta da blanket har fuska, ƙarasawa  gaban gadon abie  yayi yana kiran sunanta "Aairah"
"na'am abie" ta amsa mashi tana É—anjan blanket din ta fito da fuskarta
" ya jikin naki?"
"da sauki abie"
" to Allah ya ƙara  sauki, Idan Abdallah  ya dawo sai ya duba ki kin ji" zanbur ta tashi daga kwance tana fadin
"amma dan Allah abei idan ya dawo dan Allah karka bari yayi man allura, yaba ni mgni kawai" tuni fuskarta ta koma kalar tausayi "to shikenan kwantar da hankalin ki magani kawai zai baki, kinji koma ki kwanta "
" to abie "
" Allah ya baki lafiya  " abie  ya fada hadi da nufar kofa ya fice....

✨SHAZIM ✨

Sai bayan da akayi sallar magrib  su ka bar abnoor shi da Noraiz , direct gidan malam suka nufa domin ammy na chan har da fatima wacce daga school  chan ta wuce
Suna shiga gidan parking su kayi sannan kowanen su ya fito daga motarshi saboda  Noraiz da motar shi yaje eko  wurin shazim
Chapter 2 · 0% Book details