← Book details Doctor Shazim Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 3

Gabatarwa

Doctor Shazim Part 1 Complete Hausa Novel · about 92 min read

👨‍⚕️ Doctor Shazim👨‍⚕️
     
Daga alƙalamin

KHADIJA ( M ) ABDULWAHAB

KAINAAT... ✍ 


Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ma É—aukakin sarki mai kowa mai komi da ya bani ikwan rubuta wannan littafi.
Ya ubangiji al'arshe kabani ikwan rubuta abin da zai amfani muslinci da muslmai, ka bani ikwan rubuta abun da zai amfaneni duniya da lahira 🙏

✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️

Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na littafin   nan ba ta kowace hanya, ba tare da an nemi izni a wurina ba.
idan kunne ya ji jiki ya tsira!

Wannan labari ƙagegen ne ,sannan ban rubuta shi ba da niyyar muzanta wani ko cin mutuncin wani ba,  duk   wanda ya ga wani abu yayi shige da halayyar shi arashi ne. 

Season one
Free

Episode 1_2

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ_

12 June 2003

_Ƙarfe 12:30 Am

Yanayin sanyin da gari yayi, da iskar da ke kaÉ—awa wanda ya haddasa ganyayyakin bishiyu yin rangaji, tare da ba da wata sassanyar iska.
Yadda sauran ruwan saman da ƙasa bata gama shanyewa ba, da wanda yake gudu acikin kwalbatoci zai tabattar maka da lallai damuna ta kama.

Shiru anguwar take sai kace ba kowa a cikin ta saboda yanayi na dare haɗi da damuna, duk da daman ba'a cika samun mutane na kai kawo a cikin irin waɗannan anguwannin ba ko da kuwa da rana ne, sai hasken bulbs daya haske anguwar haɗe dana street lamps  kaɗai ake gani.

Anguwace irin ta masu faɗa aji a cikin ƙasa, domin kuwa daga shahararrun yan kasuwa sai manya a gwamnati ke a cikin ta.

Motace ta shararo da gudu daga kwanar dake hannun dama a cikin anguwar, yayin da wasu ba ƙaƙen motoci guda huɗu ke biye da ita.

Gudu motar take sosai har ta fita daga cikin anguwar ta hau babban titi, still waÉ—annan moticin na biye da ita a baya
Daga irin gudun da mamallakin motar ke yi zaka san cewa yana gudu ne tsakanin rayuwa da mutuwa.
ta mirror É—in motar yake hangen fitilar motocin da ke binsa,
yana gudu motocin na bin sa har suka hau kan titin da zai fitar da su daga garin, gudu suke har suka fita daga garin,
in ban da salati da neman É—auki daga ubangiji babu abun da mai motar nan ke yi.
domun shi a yau ya san tashi ta ƙare, saboda ya galabaita a dalilin dukan daya sha, tukin neman ga garar sa yake, ƙarfinsa ya kusa ƙarewa, dubawa yayi ta cikin mirror motar amma bai ga alamun waɗannan motocin ba, tunani ya fara to ko ya tsre masu ne, amma duk da haka bai fasa gudun da yake ba, wani mummunan Bugun da yaji an kaima ma motar shi ne yasa shi fahimtar cewa kenan wata hanyar suka bi amma suna biye da shi mirror ɗin motar ya kalla, amma sai yaga ba waɗan cen motocin ba ne, wata ƙatuwa truck ce ke binsa yanzu saɓanin waɗancen motocin, ba shiri ya karya kwana ya faɗa cikin daji, gudu kawai yake amma ba wai ya san inda yake dosa ba ne, tsintar kansa kawai yayi a bakin wani ƙaton rami mai zurfin gaske, dole tasa shi taka birki ba dan ya shirya ma hakan ba sai dan baya da wani zaɓi, kawai ya sadakat kwanan shi a yau sun ƙare.
bai gama wannan tunanin ba yaji me truck É—in ya kaima motar shi wani mumunan bugu wanda ya haddasa mashi buguwar kai nan take ya suma.
Sake ja da baya me truck É—in yayi ya kaima motar wani bugun wanda yafi na É—azun, nan take motar tayi cikin ramin, ko karar faÉ—awar ta ba'a ji saboda tsananin zurfi irin na ramin .
parking me truck ɗin yayi a bakin ramin tare da leƙa ramin ta hanyar hasken motarshi daya bari a kunne.
wani irin ramine me zurfin gaske, wanda tsananin zurfin shi zai sa ka kasa ganin abunda ke ƙasan ramin.

dariya yayi me sauti da amo tare da cewa yanzu kam nasan zan samu cikwan kuÉ—ina domin wannan sai dai uwar shi ta haifi wani amma ba dai shi ba.
komawa yayi cikin motar shi, anan yasamu wayar shi na ringing  ɗaukar wayar yayi
boss  shine sunan daya bayyana a jikin screen ɗin wayar,  picking call ɗin yayi tare da sa wayar a handspree  tun kafin yace wani abu me kiran nashi yace " Ina fatan kagama dashi? "
answer ya bama boss  ɗin da cewa " ai wannan tashi ta ƙare sai dai uwar shi ta haifi wani amma ba dai shi ba,  dan a yanzu yana can ya gana da magabatan sa"
"amma naji daɗin jin haka" boss   ɗin ya faɗa .
"amma boss ya kake ganin za'ayi da matar shi da yaran shi ?" me truck É—in ya tambaya.
"Kar ka damu da wannan big boss.   zaiji da komai , yanzu dai katuraman da account number ka domin natura maka Sauran kuɗin aikin ka "
"thank you so much boss" me truck É—in ya faÉ—a. boss É—in ya ce
"don mind" Kit ya kashe wayar
account number ya turama boss tare da yima motar key ya bar wajen

WANNAN KENNAN.

🌹~ _Kainaat_ ~ 🌹

Gida ne matsa kaici shi ba ƙarami ba shi kuma ba babba ba chan sosai ɗan dai dai.
gida ne namasu rufin a siri kuma yan boko naji da faÉ—a.
Painting gidan ya kasance white and blue color ne, haka ma get É—in gidan blue and white ne.
daka shiga compound ɗin gidan zaka fara cin karo da ɗakin mai gadi daga hannun hagu Sai parking space daga hannun dama wanda ke ɗauke da rides masu kyen gaske da tsada na fashion a ƙallah za su kai guda 5 a parking lot ɗin.
Sai garden mai kyen gaske ga suke suke masu É—aukar hankali.
Sai boys quarters dake bayan part É—in masu gidan.
Masha Allah na furta a ya yin da nayi arba da parlorn gidan wanda aka ƙawata shi da furniture's masu kyen gaske da tsada, komai na cikin parlor onion and pitch color ne, daga gefen daman parlor twin up stairs ne me kyau
Sai kitchen dake gefan hagu wanda yake haÉ—e da store kusa da shi kuma dining area ne mai É—auke da chairs guda 7,Sai wani É—an corridor daga gabas É—in parlor mai É—auke da 4 bedrooms, daga chan kuma up stairs É—in ya kasu kashi 3,part É—in matar gidan dake haÉ—e dana yaranta ke hannun hagu Sai na me gidan dake hannun dama sai chan gaba na yaron gidan ne namiji. daga part É—in dake hannun hagu naji anata kwala Kiran Aaimah! Aairah!! Aairah!!!.
Wata kyakyawar mace ce tafito daga ɗaya daga cikin  bedroom ɗin  ta nufi wanda ke kallon nata ta na cigaba da Kiran
" Aaimah " da "Aairah".
Fara ce sosai tana da jiki ba sosai ba ita ba rammama ba Ita ba mai ƙiba ba a kalla zata kai kimanin shekara 50 . jikin ta sanye yake da sleeping dress riga da wando masu santsi yana yi da Pakistan dress pink color. ba ƙaramin kyau suka yima surar jikinta ba.
"Kun kuwa san ƙarfe nawa" ta faɗa yayin da take tura ƙufar bedroom ɗin ta shiga.
Masha Allah na faÉ—a domin kuwa bedroom ne me kyan gaske, komai na cikin sa ya kasan ce pink and white color ne , yaji kaya masu kyan gaske bawai cike yake da kaya ba.
bed ne sai bed side drawers, sai dressing mirror gefen shi kuwa wardrobe ne wanda clothes set ne ciki sai jikin ƙofar shigowa kuma jere suke da ƙofar bathroom sai wani ɗan corridor inda ya kasan ce laundry basket ne da shoe rag ne sai bag hanger , bags ne masu kyau na gayu dana school kowace bag set biyu ce kuma color ɗaya.
turus ta tsaya ganin ta kwance har yanzu akan bed, " Aairah lafiya kike kuwa da baki tashi ba ina Aaimah take Ita ma, ko yau baku zuwah school ne iye. "
Ƙarar buɗe ƙofar bathroom taji juyawa tayi, wata kyakyawar budurwa ce ke tsaye jikinta ɗaure da towel iya gwiwarta jikin ta sai raɓar ruwa yake, alamar wanka tayi,  fara ce Ita ma kamar mahaifiyarta sumar kanta ta sauko har saman neck ɗinta, ga matsakai tan idanu masu ɗauke da brown eyeball da zara zaran eyelashes, hancinta ma ɗan dai dai dogon bamai yawa ba sosai, ga small mouth me ɗauke da pink lips, tana da shape mai ɗaukar hankali sannan tana da tsayi amma ba sosai ba chan. masha Allah kawai zamuce, akalla zatai kimanin shekara 18 a duniya.
"Ok kin tashi kenan Aaimah ce kenan bata tashi ba."
"Wallahi mom  tunɗazu nake tashin ta amma taki tashi wai Ita batagaji da bacci ba."
"Tafi ke ki shirya, rabu da Ita yanzu ai zata tashi ba dan halinta ba " mom ta faɗa a lokacin da ta ƙarasa jikin bed ɗin , "Aaimah! Aaimah!! wake up, its time for school , ko kina so ne kuyi late ne iye autar mom . "
"Uhm uhm uhm haba mom wai miyasa kike cema Aaimah auta nifa" Aairah tafaɗa yayin da take buga ƙafa tana turo baki haɗe da rike ƙugu.
ai kuwa nan Aaimah ta tashi tana ma Aairah dariya harda gwalo, dama duk abunda mom ke faÉ—a tana ji, tashi ne kawai bata yi ba
"mom  kinganta ko dariya take man harda gwalo"Aairah ta faɗa sai wani turo baki take tana hura hanci. "Ke da'alla  rabu da Ita, ai kema autah ce"
mom ta faɗa  tana dariya ganin yarda Aairah kema Aaimah dariya harda tsalle, "oho dai ai ni aka fara cemawa" mom ta katse ta da cewa
" To ya isa haka maza kushirya
ABIE na nan yayi shirin tafiya , kunsan dai yau zai koma wurin aiki abuja."
"to shikenan mom gamu nan zuwa" har suna haÉ—a baki wurin faÉ—in haka.
fita Mom tayi daga bedroom ɗin haɗe da jawo masu ƙofa, ta shi Aaimah ta yi ta nufi bathroom tana faɗin my twin sister dan Allah kifito man da uniform ɗina kafin na fito"Aairah ta ce " to sannu mom kinji koh"
"haba twin sister dan Allah fa nace" Aaimah ta faÉ—a tana lan gwabar da kai , Aairah ta ce " hmmm sai shegen daÉ—in baki kamar ta Allah"
" Pls twinee" Aaimah tasake faÉ—a
"shikenan ba dan halinki ba"Aairah ta faɗa tana ya tsine fuska,murmushi Aaimah tayi tana faɗin "yawwa twenny Ni na san nafi kowa Sa'ar Yar uwa a duniya shiyyasa nake alfahari dake,kin kuwa san irin daɗin da nake ji Idan naganki kusa dani?" , baki kawai Aairah ta saki tana sauraron ƙaryar da Aaimah ke shirga mata. "wallahi Aaimah kin bani ki rinƙa jin tsoron Allah , ko kunyar ƙarya ba kyaji " gwalo Aaimah tayi ma ta hadi da jawo ƙofar bathroom ta shige, dariya kawai Aairah tayi haɗi da girgiza kai tana faɗin " Allah ya shirya ki Aaimah da karya"
wurin dressing mirror ta wuce Vaseline É—in dove ta shafa tare da farar powder kaÉ—an ta shafa a fuskar ta sai kwalli da ta sa ma eye's É—in ta, wurin wardrobe É—in su ta wuce buÉ—ewa tayi , kaya ne masu yawan gaske komai set biyune, wurinda hijaban su suke daban haka ma sleeping dress É—insu daban suma dogayen riguna da atamfofi wurinsu daban haka ma uniform É—in su na school dana Islamiyya,
uniform É—in school ta É—aukar masu set biyu ita da Aaimah wurin bed É—in su ta koma da kayan a hannun ta domin ta shirya.
shaf shaf ta shirya cikin uniform É—in ta, riga ce da skirt, rigar white color ce, skirt É—in wanda ya kasance iyakarsa gwiwarta pink color sai sock's fara me ratsin pink daga sama sai top wacce itama ta kasan ce pink color sai Yar baby hijab ita kuma white color ce, wurin corridor É—in su ta nufa shoes da school bags É—in su ta É—auko masu, white color ne takalman snikers sai school bag pink color.
"Sis nima kin É—auko man uniform É—in" Aaimah ta faÉ—a wacce fitowar ta kenan daga bathroom. amsa Aairah ta bata da "Eh Amma fa kiyi sauri ki shirya kona tafi wurin Abie na barki" wurin dressing mirror Aaimah ta nufa tana faÉ—in" sorry karki damu yanzu zan shirya ki bani 5 minute in sha Allah " shaf shaf itama ta shirya cikin nata uniform É—in Masha Allah
Itama ba ƙaramin kyau tayi ba,itama Aaimah kykyawa ce sosai a bun da kawai Aairah zata nuna mata tsayine shima ba wani finta tayi ba sosai ka mannin su ɗaya da Aairah tsayinne dai kawai banbancin su shima sai in sun jera zaka fahimci hakan.
Snickers É—in ta itama ta saka tare da amsar bag É—inta dake hannun Aairah
a tare suka fita daga bedroom ɗin direct part ɗin Abie suka nufa, hannun su cikin na juna suka shiga parlor  ne mai matuƙar kyau,  dan yafi na down stairs kyau da haɗuwa domin ya ƙawatu da expensive furniture's, komai na cikin parlorn sky blue ne da fari.
wani kykyawan matshin tsohone wanda Akallah zai kai kimanin shekara 60 a duniya, yana da haske shima sosai, zaune yake akan 2 siter
" abie " kenan
tea yake sha wanda mom  ta haɗa mashi, sallama sukayi tare da ƙarasawa ciki suna faɗin "abie  ina Kwana antashi Lafiya "suka faɗa yayin da suke samun wuri kusa da abie suka zauna,
"lafiya lau alhmdllh my daughters ina fatan kuma kun tashi lafiya" "Alhmdllh abie " suka faÉ—a, Abie ya ce
"to Masha Allah haka ake so"
"amma Abie zaka tafi yau shine baza ka yi breakfast damu ba" Aaimah ta faÉ—a tana turo baki
"Sorry my daughters duk da ma laifin kune tunda tun É—azu ya kama ta ace kuntashi amma ku ka yita bacci gashi ni kuma sauri nake, ai daya ke bajima wa zanyiba wannan time É—in, zandawo very soon kunji ko."
"shikenan abie Allah ya dawo da kai lafiya"da ameen abie ya amsa tare da kai cup É—in tea bakin sa.
"to uwayen surutu atashi aje ayi breakfast time na ƙurewa, abar shima abie ya samu ya gama nashi breakfast ɗin karya makara "mom  ce ke magana wacce fitowar ta kenan daga bedroom ɗin abie hannun ta riƙe da jakar kayan shi da zaiyi tafiya da Ita
"Uhmmmmm haba mom dan Allah kibari muƙara sa yin ban kwana mana" Aairah ta faɗa tana turo baki, dariya kawai Abie ke masu
"Kinci gidan ku nace, kutashi kuyi breakfast yana chan baaba larai tashirya maku,  nima abarni nayi ban kwana da mijina"
"ah mom sai kice mutashi soyayya ta motsa, to bari muyi ta kanmu," Aairah ta faÉ—a tareda yin dariya
"Kunci gidan ku ja'iran banza marasa kunya kawai"
abie ne ya faɗa tare da yi masu daƙƙuwa
dariya suka kwashe da Ita, " abari muga soyayya tukunnan sai mu tafi" Aaimah ta faɗa haɗi da gyara zama, wurin su mom  ta nufo ai bashiri suka mike da gudu suka fita daga part ɗin suna dariya.
"Kaga man ja'iran yara marasa kunya"mom ta faɗa yayin da take zama kan hannun sofa da abie  ke zaune, dariya abie  yayi tare da cewa "Allah ya shirya, dan in ki ka biye ma su Aairah sai su samaki ciwan kai" "wallahi  kuwa ai abdallah  ne kawai maganin su, yama shigo kuwa?" mom ta faɗa.

“Aa ina jin baigama shirin zuwa hospital ba, nasan daya gama zai shigo muyi sallama, haka ne kuma mom ta faɗa  tare da cewa
"yanzu dai ba wannan ba yaushe zaka dawo? "
"2 week's kawai fa zanyi "
"ashe kuwa kashirya zuwa dani abuja kenan In dai 2 week's za kayi,ƙafata ƙafarka" murmushi  abie  yayi haɗi dacewa "to su fa yaran naki kibarma wa su iye"
"dan Allah kabar ma maganr yara, Sai kace wasu yan goye saunawa Nake zuwa abujar batare da su ba"

Assalamu Alaikum sukaji an faɗa,  katse labarin da suke su ka yi haɗi  da amsa sallamar, wani matashin saurayi ne wanda ko ba'a faɗa maka waye shi ba kamanin sa da abie zaitabbatar maka da cewa ɗan sa ne, DR. ABDALLAH MUHAMMAD HASHIM  kenan matashi maiji da waye wa ga ilimi both side boko da Islama, farine shi ma sosai yana da tsayi dai dai misali gashi irin mazannan ne masu motsajiki dan yana da kirar jiki mai kyan gaske ga  ƙasumba irin ta yan gayu,wacce kallo ɗaya zaka mata kasan tana shan gyara, jikin sa sanye yake da uniform ɗin  sa na  aiki hannun sa riƙe da  briefcase  ɗin  shi,  ƙarasawa ciki yayi wuri ya samu ya zauna,yana faɗin " ina kwana abie,mom ina kwana"
“lafiya lau alhmdllh suka amsa mashi abie  ya ɗaura da cewa "har anyi shirin fita aiki kenan? "
" eh abie  dayake ina da shiga Operation  ƙarfe 10:00," 
"masha Allah , Allah ya taimaka," "ameen ya rabbi , abie dawuri zaka wuce ne yau? "

"eh dawuri zan wuce saboda gobe tunda safe ina da shiga court ‍,  amma in sha Allah bazan jima ba zan dawo ina ma tunanin two days zanyi na dawo"
"to shikenan abie  Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya" da ameen suka amsa mom na faɗin
"breakfast ɗinka nachan dining,  sannan su Aairah na nan kawuce dasu school in baza kayi late ba, 
"amma mom mi ya hanasu bin school bus yau? "
" uhm kai dai bari,  shegiyar shiririta ce irin tasu , kasan halin su yanzu haka idan akace maka suna can basu kammala breakfast ɗin  su ba ba'a gardama,  narasa gane shiririta irin tasu Aaimah, wallahi yara sai kace ba masu jini ajiki ba, suyita abu kamar ba su san yi, Allah dai ya shirya su” ameen abdallah  ya faɗa  tare da cewa "bari naje nayi breakfast ɗin  sai na du basu"
"ok muma ga mu nan sakkowa"tashi yayi ya fice ya nufi  dining,  tunkafin ya isa yake jin hayaniyar Aaimah da Aairah sunata zagaye dining, Aairah ta ɓatama Aaimah baby jib da tea,ita kuma Aaimar nacewa saita rama, shi ne su ke ta zagaye dining baaba larai sai cewa take su bari amma ina kamar ƙara zugasu take.

Tsawa abdallah  ya daka masu tare da cewa "ashe ku shashashu ban sani ba,  zaku dawo ku zauna ko sai ranku ya baci,sakarkarun banza da wofi,  wallahi kushiga hankalin ku kullum girma kuke amma ɗabi'un ku sak na yara”
kowace a cikin su ta nemi wurin zama, baaba larai ce ta matso zatayi serving ɗin ya abdallah tana faɗin " abdallah  an tashi lafiya"
"lafiya lau baaba,  ina kwana," Alhmdllh tace "mizan zuba maka?"
"a'a kibarshi kawai baaba Aairah ta zuba man,"
"to shikenan ni bari nawuce kitchen"
Aairah yace ma tayi serving ɗin sa ita kuma Aaimah tayi sauri ta chanzo hijab ɗin  ta tunda sungama breakfast ɗin su , to tace haɗi da tashi ta nufi  bedroom ɗin su.

Abie  ne ke saukowa shi da mom hannun ta riƙe da  jakar kayan sa  ,  "abie  kafito " ya abdallah  ya faɗa  ayayin da yake kar ɓar jakar kayan a hannun mom,yana faɗin "abie muje koh" yayin da yake fita daga parlorn , bayansa suka bi har da Aaimah wacce sakowarta kenan daga bedroom ɗin  su da taje chanzo hijab,"adawo lafiya,  alhaji Allah ya kiyaye hanya yakai ka lafiya ya dawo da kai lafiya" "ameen ya rabbi baaba larai" abie  ya amsa, fita sukayi compound ɗin  gidan wurin motar abie suka wuce wacce bala driver  ya daɗe  da fito da ita dan har ya abdallah ya saka ma abie  kayan shi a booth ɗin  motar bankwana suka shiga yi, su Aairah har da hawaye abie  sai lallashin su yake.

abdallah ne yace" dan Allah abie  ka kyale  yarannan  sai sun sa kayi late", "kuyi hakuri bazan jimaba zan dawo may be na dawo nan da 2 days kunji" "to abie  Allah yatsare hanya"
ameen abie yace
abdallah ne yace "to kuwuce ciki ku ɗauko school bag ɗin  ku na ajiye ku a school,  abie  Allah ya tsare"  ya faɗa   haɗi da tasa keyar su Aaimah zuwa ciki, mom ce ta matso kusa da abie  tana cewa "wallahi barrister kamar kar ka tafi nake ji"
" to fah yara shagwaɓa  uwa shagwaɓa  toni wazan kama" ya faɗa  yana dariya "uhmm kaima kasan wanda zaka Kama" ta faɗa tana ɓata rai,  "yau naji,shiyyasa kenan kika ƙi magana sai da yaran na ki suka shige ciki zakiyi man adawo lafiya , ashe shagwaɓa  za'ayiman ban sani ba ", mom tace "ok hakama zakace "ta faɗa haɗi da juyawa zata nufi ciki ,  hannun ta abie  ya riƙo yana faɗin  "Sorry kubrah,  kema kinsan wasa nake , karki damu bazan jima ba zan dawo in sha Allah"

"to shikenan Allah ya dawo man da kai lafiya" ameen abie  ya faɗa  yayin da yake shiga cikin mota,back seat ya shiga   bala driver na  gaba, key yayima motar, hanu mom ke ɗaga ma abie  shima yana ɗaga mata suka nufi gate,buɗe masu gate baba mai gadi yayi yana faɗin a dawo lafiya " mom na nan tsaye har sai da motar tafita daga gidan sannan ta juya tashiga ciki , dasu Aairah tacikaro suma sun fito a dawo lafiya tayi masu tawuce ciki abdallah  ne ya sauko daga upstairs part din sa  
Yana ce masu ku wuce mu Tafi.

  🌹~KAINAAT~🌹

Fita sukayi wajen mota suka shiga abdallah  ya jasu gate suka nufa wanda tun fitar abie  baba mai gadi yabar masu shi a buɗe, gaishe dashi suka yi ya amsa  yana masu adawo lafiya da ameen abdallah  ya amsa yayin da suke fita daga gidan,
abdallah  ne yace" dama ana duka a school ɗin  ku,wallahi da sai nasa  yau anyi maku shegen duka"
"dan Allah ya abdallah kayi hakuri bazamu ƙara ba"
"kun dai ci sa'a kawai da ba'a duka da kungane kuranku yau, da daga yau baza ku sake baccin safe ba, ace wai kuna bacci har school bus ta tafi kuga yan hutu koh?"

“Kayi hakuri dan Allah wallahi baza mu ƙara ba"
"ni dallah  ku man shiru,sai bada hakuri kamar masu tuban gagaskiya  bayan nasan ƙarawa za kuyi" ya faɗa  yayin da yake hawa kan titin ring road  in da a nan ne school ɗin  su take.
A bakin gate ɗin  school ɗin  yayi parking tare da cewa "ku fito ku wuce ciki, fita su ka yi suna yi mashi adawo lafiya Allah ya sa yace, motar yayi ma key ya bar wajen tare da Kama hanyar hospital ɗin  da yake aiki...
Ep 3_4

LITTLE ANGELS PRIMARY AND SECONDARY SCHOOL. shine sunan school É—in,
Kamar yanda school uniform ɗin  suka kasance pink and white color haka fentin school ɗin  shima pink and white color ne.
Cikin school ɗin  suka shiga Masha Allah school ce mekyan gaske  ta yayan masu arziki Upstairs ce makarantar wanda ya kasan ce down na yara up kuma na manya ne, up stairs suka nufa domin an daɗe da gama  ASSEMBLY shiyyasa su ka nufi class,  S. S. 3 shine class ɗin  su , shiga su kayi ciki,master ɗin  su suka samu yana shirin fita,domin ya gama abunda ya kaishi.

"Aairah  And Aaimah   Muhammad  hashim , why are you coming late" mastern ya faɗa
“Sorry sir we have wake up too late,that the reason why we came to school late,it will never Happen again" Aaimah ta faɗa  yayin da Aairah  ke ta ɓata fuska irin tafi ƙarfin  ta bashi amma sa.

"this should be the last,  get sitet"mastern ya faɗa haɗi da ficewa daga class ɗin .

Kallan juna su kayi su na kwashewa da dariya, Aairah tace "Why are you coming late" tana kwaikwayan maganar master É—in , dariya su ka sake kwashe wa da Ita,
Aaimah tace this should be the last. wannan karan duka yan class ɗin  ke dariya.

Sit ɗin  su suka zauna suna cigaba da dariya,
"Allah ya shirya ku twins domin yanzu abun naku sai adu'a,musamman ma ke Aairah da uncle Hamza na magana sai wani harar sa kike,"
"bazaki gane bane Aeesha" Aairah ta faɗa  wacce aka kira da Aeesha tace "to ganar dani"

"Ke wallahi haushi uncle hamza nake ji,dafa Ina masa kallon mutumin arziki ashe dan banza ne, baki ji munce ya dai na zuwa gida yi ma na lesson ba, Ai korar sa ya abdallah  yayi, saboda abun da ke kai shi bashi yake yiba, Ko kunya baijiba yace wai yana son Aaimah,sai kuma yana lesson kiga yana ƙoƙarin taɓa ma mutun hannun,ai kuwa rannan ashe duk abun da yake faɗa  a kunnan ya abdallah,  shine fa ya kore shi yace karya Kara ganin sa, to Wallahi in taƙaice maki ko mu dukan da mukasha wurin ya abdallah  sai kin tausaya mana,dan Wallahi buguwa mu ka yi kamar gangar church,kuma mom tace ba ruwan ta gashi abie  baya gari, shiyyasa duk na ganshi Nake jin kamar na shaƙe sa"
Aairah  ta faɗa   tana hura hanci, Allah ya shirya sa to Aeesha ta faɗa  ,  Ameen  dai.
be silent biology teacher su ne yace haka wanda shigowar sa kenan yasame su suna ta surutu, natsuwa suka yi suna sauraron lesson ɗin  da yake masu.

_F. M. C  MEDICAL CENTER_

zaune yake a office É—in shi da ke Amenity, waya ce a kunnan sa da alama waya yake.
"haba dude ai dole nace haka tsawan shekarar mu nawa muna tare ace baka taba ziyar ta ta ba,su mom ma a suna ka ɗai  suka sanka sai waya, ai tare bata ce haka ba amma nasan maganin ka, zan haɗa ka kawai da ammy ne nasan ita zata saka kazo ba dan kashirya ba,ko nasa mom  takiraka may be kazo"  ya abdallah ya faɗa, On the other hand na cikin wayar yace “sorry my man ba haka bane, nima ina san zuwa to ayyuka ne suka man yawa shiyyasa, amma in sha Allah ina nan zuwa very soon”
“ai nima ina da tarin ayyuka amma Nake ajiye su na ziyarceka,idan kuma Sai zanyi aure zaka zo naji to, duk da in zanyi sai tare da kai, don ina samun mata zan haɗa ka da ammy  kaima ka fito da taka ko a bayar da kai sadaka"  abdallah ya faɗa  yana dariya.
"haba kaima kasan wa za'a bayar sadaka,In dai aure za ka yi bisimillah ban hanaka ba,amma ni ba yanzu ba.
"shikenan tun da kai bazaka chanza ba kullum ace mutum amsar sa ɗaya, ina gaishe da su ammy "ya abdallah  ya faɗa .
"zasuji in sha Allah nima ka gaishe  man dasu mom  kace mata ina nan zuwa very soon "
"Allah yasa domin kuwa na san halinka,"
“Karka damu dude zan zo in sha Allah, to shikenan sai anjima , Abdallah  ya faɗa ,
"ok nagode sai anjima" kashe wayar yayi, haɗi  da fita daga office ɗin zuwa dakin tiyata.
 
10:00 am
LAGOS.

_EKO HOSPITAL._

Patient ne zazzaune wanda da alama sun zo ganin likita ne.
wata  Nurse ce tafito daga Office  aƙalla za tayi kimanin shekara 25, sanye take da fararen kaya riga da wando, hulace kawai akan ta saɓanin wasu nurses ɗin  da ke sanye da baby hijab.
baƙa ce amma ba baƙi sosai ba,wurin patient din ta nufa “DR na hanya” ta faɗa yayin da take amsar Katin patient ɗin, wani dattijo ne zaune shi bai bada card ɗin shi ba da alama ma baiji mi nurse ɗin tace ba,"hey, bring your card"
nurse ɗin  ta faɗa  ganin bai ba da na shi ba "ƴata ni bana da kati,yau nafara zuwa"
dattijon ya faɗa  dakyar da alama ba karamin jin jiki yake ba,cikin harshen hausa tafara magana duk da ba ta yi kama da hausawa ba kuma bawani iya hausar ta yi ba sosai " to ya ka ke so ayi,katin ka ke so nabaka ne komi?"
"a'a naji ance  ana bada magani kyauta shiyyasa na zo" dattijon yafada, wani kallon rainin wayau take ma dattijon har ya gama magana, cikin karaji da ɗaga murya tace "hey hausa people na bani mamaki, to bari kiji nan ba charity hospital  bane, dan haka ki tashi kiba mutane wurin, in ban da abunki ta ina wannan hospital ɗin  tayi kama da charity hospital  koh ance maki irin hospital ɗin kune na Arewa??" nurse din ta faɗa  tana nuna mashi hanyar fita.
 "haba Victoria kin manta mi doctor yace ne duk lokacin da marasa ƙarfi suka zo?" wata kyakyawar nurse ke faɗin haka, chocolate color ce a ƙalla za ta yi kimanin shekara 23 itama sanye take da fararen kaya rigada wando sai farar baby hijab, zuwan ta ke nan tasamu victoria  nayima dattijo masifa Ita bahaushiya ce saɓanin victoria
"ina ruwana, ai yanzu ba ya nan sai dai in ke ce zaki faɗa  masa”
Kasa tashi dattijon yayi jikinsa sai rawa yake, tsawa ta dakama dattijo, haɗi dacewa  "I said get out from this hosp..., kasa ƙarasawa tayi adalilin saukar wani  mahaukacin mari dataji a kuncinta,ba tai aune ba ta sake jin wani marin a dayan kunchinta bashiri ta kife ƙasa, gaba ɗaya hankalin patient dana nurses ya dawo kan  wanda yayi marin.

Tsaye yake jikinsa sanye da scrub suit blue color, ƙafarsa na sanye da black din takalmi sai hannunsa dake riƙe da  briefcase da lab coat ɗin  sa,  dogone  yana da tsayi,fari ne sosai kyakyawan gaske, yana da dogon hanci sai eyes masu black ɗin  eyeball, small mouth me ɗauke da red lips, sumar kan sa wacce tasha gyara ko nace take kan shan gyara black color ta leƙo ta cikin Arab Turban ɗin dake kanshi ta ɗan sauko har saman neck ɗin shi,kallo ɗaya zaka mashi ka kira shi da balarabe ko kuma halfcast akallah zai kai kima nin shekaru 28 zuwa da 30.

Good morning sir, nurses É—in suka shiga gaishe da shi, hannu kawai yake É—aga masu yana kiran security,
ƙarasowa  security ɗin  su ka yi suna gaishe da shi cikin girmamawa, amsa masu yayi yana  nuna masu dattijon ya
ce su shigar mashi dashi office ɗin shi yayin da yake ba ɗaya daga cikin securityn key din office ɗin  shi,  kamashi su ka yi suka ɗaurashi akan wheelchair wannan nurse ɗin ce wacce tayima victoria magana ta matso kusa da shi, hannu ta mika zata anshi briefcase ɗin dake hannun shi  dakatar da Ita yayi,  magana ya fara cikin harshen turanci nurse "hidaya me nace ne gameda masu zuwa neman taimako? "
" kace duk wanda yazo neman tai mako ah EKO aturashi ABNOOR,  kuma itama nurse Victoria ta sani kuma sai da nasake faɗa mata da tana ma datijjon faɗa"
"shikenan koma dai miye Wannan yazama nakarshe, in dan kuwa ba haka ba dukkan ku sai ranku ya ɓaci "ya fada haɗi da nufar office ɗin  shi

    🌹~ KAINAAT ~ 🌹

Tasowa victoria tayi daga duƙewar da tayi domin ta maru, haryanzu bata dawo dai dai ba,  masifa tafara yima nurse Hidaya akan Ita ta  haɗa ta da dr haryayi mata wannan marin,  "to bari kiji Victoria garama tun wuri kifita daga harkata,basai da na gargaɗe ki ba, amma mikika ce ke kina ganin dr  shazim bazai iya yimaki komai ba ke yar gaban goshi,  ke dai kawai za fin mari ne yasa zaki sauke a kaina mizai hana shi dr bazaki bishi office kiyi mashi masifar ba "hidaya ta faɗa   tana dariya sauran nurses ɗin  ma dariya suke saboda  sun san magana  ce hidaya ta faɗa ma victoria  saboda  ba ƙaramin  so take ma DR. SHAZIM  ba,  mutsww victoria taja tsaki saboda haushin dariyar da suke mata ta kuma gane miyasa su dariya wuce wa tayi office ɗin  dr  saboda  itace ke tura mashi da patient, 
Shiga tayi cikin office ɗin  haɗi dacewa,  good morning sir  zaune yake yana rubutu ajikin file wanda da alama na wannan dattijon ne yayin da dattijon ke kwance  bisa gadon marasa lafiya a office ɗin , ko kallon inda take bai yi ba,sake gaishe da shi tayi,  kira man nurse hidaya abun da kawai ya ce mata kenan, hakuri ta shiga bashi dan bazata iya daina aiki dashi ba domin in har chanzata zaiyi da nurse hidaya to sai dai tabar hospital ɗin saboda  bazata juri ganin shi tare da wata ba,   tsawa yada kamata domin yaga bata da niyyar fita daga office ɗin yace " get out from my office" ya na nuna mata hanya,  fita tayi daga office ɗin  zuwa office ɗinsu  na nurses,tana shiga ta  fashe  da kuka,  tana faɗin  bazai yuwu ba wlh dr  shazim  nawa ne ni ka ɗai, babu wacce ta isa ta raɓesa sai ni,taƙara fashewa dawani kukan,  wata nurse ce tashi go office ɗin wacce itama daga ganin ta ba muslma bace tana cewa , "ai yanzu kika fara kuka victoria, tadama ba sai da na faɗa  maki ba kitashi tsaye  amma kika ƙi ji,wanda kuwa duk yaƙi ji ba yaƙi gani ba, to wallahi  Idan ba kiyi wasa ba kina nan sake da baki hidaya zata kwace shi, sai dai  kizama ƴar kallo"
"haba destiny yaza ki man wannan mummunan maganar,   kisan kuwa yanda nake son dr shazim kuwa,da kinsan yanda nake son shi da baki ce haka ba"
" victoria kenan ina ga bakisan halin hausa peoples bane, zaki sha mamaki in kika tsaya wasa domin kuwa Ita hidaya yarensu ɗaya bayan nan religion ɗin  suma ɗaya kina ganin zai kula ki ne yana ganin hidaya, kawai kitashi tsaye"
"to ya zanyi ki bani shawara pls"wani munafukin murmushi destiny tayi haɗi  da cewa yanzu dai kifara kira mashi hidaya tukkun nan zuwa anjima sai muyi magana"
" haba destiny  yaza ki ce nakirata, sai dai yaji haushi amma ni bazan kira taba wlh" "kaji sakarya,idan baki kira mashi ita ba taya zai gane kintuba, kuma itama hidayan ki roketa akan ta tayaki bashi hakuri nasan zatayi,"
"uhmmm shikenan ta faɗa  haɗi  da barin office ɗin  domin kiran hidayar, dariya destiny ta kwashe da Ita haɗi da cewa "zaki gane baki da hankali Victoria, zaki san cewa ni ba kanwar lasa bace, yanda ki ka ƙi brother samuel to haka zaki rasa shazim  shima sakarya kawai" .

wurin su hidaya Victoria ta nufa,tana zuwa ta tsaye tayi tana riƙe da ƙugu tace
"kizo dr nakira” tana faɗa ta juya kai gefe "wakenan acikin mu?" wata a cikin nurses ɗin  dake zaune  ta faɗa , "tasan kanta ai"acewar Victoria, sarai sun gane hidaya take nufi saboda sun San tana yar tsama da Ita amma sai suka nuna basu gane ba "hidaya kinsan fa ke nake nufi amma kinyi kamar baki ganeba zanje na faɗa  masa bazaki zoba"
" ke jiman Victoria da karfin halin, kin faɗi sunanta ne daza kice ta ƙizuwa"
"ah to gane mana hanya sister maryam" acewar wata daga cikin nurses ɗin  "haba Victoria ni na rasa me hidaya ta tare maki a hospital ɗin nan,ai ko bakomi ƴar uwarki ce tawurin aiki,  amma ace kullum baki da abokiyar faɗa  sai Ita"
"karka faÉ—a man mgnr banza mana Joseph ina ruwanka" victoria ta faÉ—a tana wani huci
 "sorry shawara ce" barin wurin yayi wanda aka kira da Joseph
"mike faruwa ne anan cewar destiny wacce isowarta kenan, a'a hidaya Victoria bata faɗa  maki dr na kira ba nagan ki zaune ko har kin dawo daga wurin shi ne??"
"A'a destiny yanzu zanje"ok destiny ta faɗa haɗi  da cewa "kefa Victoria naga kinyi tsaye ku tafi mana" bin bayan hidaya destiny da Victoria su kayi suna ɗan yin nisa da sauran nurse's ɗin  destiny ta ɗan taba Victoria alamar ta roki hidaya akan ta taya ta ba dr  haƙuri, ganin baza tayi ba ne yasa destiny dakatar da hidaya tana cewa "kiyi hakuri hidaya akan abun da Victoria tayi maki,haushin dariyar da kuka yi mata ne ɗazu yasa tayi maki haka,  amma kiyi hakuri"
"shikenan bakomi, ni da man ba waina riƙe ta ba ne" "shikenan amma ki taya ta ba ma dr hakuri pls karya cireta daga cikin nurses ɗin  dake tura mashi patient pls" a ranta take faɗan"ok shiyyasa kenan tazo ta ciman mutun ci"amma  a zahiri sai tace "bakomai yawuce in sha Allah zan taya ta" thanks Victoria ta faɗa  yayin da suka kawo office ɗin  shiga ciki su ka yi sallama hidaya tayi yayin da Victoria ke bayan ta
“good morning dr" hidaya ta faɗa
"morning,ki saka patient a layi amma mutum 15 kawai zan duba  sauran kiturasu office ɗin  DR KABIR" Dr shazim ya faɗa ba tare da ya ɗago ya kalle su ba
 "sorry sir  ni ina iya tura su" a cewar Victoria data ga yayi kamar bai san tana wurin ba,  "this should be the last day da zaki Ƙara zuwa office ɗina, I hope you understand"
“ a fuwan sir,kayi mata haƙuri  bazata ƙara ba" hidaya ta faɗa  gaban ta na faɗuwa tsoron kar itama ya koreta
"nagama magana get out'
zubewa Victoria tayi akan gwiwowinta tana ci gaba da bashi haƙuri  harda kuka
“I said get out from my office" ya faɗa  da tsawa yana nuna mata hanyar fita,  fita tayi tana kuka kamar ranta zai fita "kema zaki iya tafiya" Ok sir hidaya ta faɗa  fita  itama tayi wajen office ɗin  ta samu Victoria da destiny suna ganin ta suka nufe ta rokonta suka shigayi a kan ta taya victoria ba ma dr haƙuri  " shikenan in sha Allah zan taya ta kar ku damu" hidaya ta faɗa tana sharema Victoria hawayen dake fuskarta tana cigaba da kwantar mata da hankali godiya su kayi mata sannan su ka koma office ɗin  da suke zama ita kuma ta wuce wurin patient domin tura ma dr su .
haka ya cigaba da ganin patient shi kuma wannan dattijon ruwan da aka sa mashi  na ƙarewa  yasa driver ya mai dashi ABNOOR aka bashi gado ,  bashi ne ya bar EKO ba sai wurin 12:30 sannan ya wuce ABNOOR nan ma yaga patient dayawa saboda yafi jimawa a nan a kan eko ,  abnoor  hospital ɗin  sane halak malak Ita kuma eko  aiki yake a chan,  sau biyu   yake zuwa eko  a sati idan yana lagos  saboda yana visiting wasu Hospital ɗin  ,  kuma in yaje 2 to 3 hours yake yi yaje abnoor    ,  amma  standard in da yafi zama abnoor  ne saboda chan har ranar Saturday yana zuwa in yana lagos  ,sai  wurin 6:00 ya tashi daga aiki dan har an fara kiraye kirayen sallar magrib masallacin hospital ɗin  ya nufa domin gabatar da sallah sai bayan angama  tukkun yanu fi gida,

horn yayi a bakin wani katafaren gida naji da faɗa  dake Victorian Ice land , gida ne har gida wanda daga gani ba sai an faɗa maka ba kasan cewa an narkar da dukiya wajen ginasa, me gadi ne ya buɗe masa gate, ciki ya shiga   ya nufi parking space da ke chan cikin gidan,ɗakin mai gadine farko daka shigo gidan sai boys quarters daga chan gaba sai kayi ƴar tafiya sannan zaka iso part ɗin  masu gidan sai parking space dake gefe sai wani katon garden dake bayan part ɗin  masu gidan,ride's ne gasunan kala kala a kallah zasu kai 6 a parking space ɗin , parking  yayi, cikin gidan ya nufa,tura ƙofar shiga part ɗin  yayi bakinsa ɗauke da sallama,parlor ne me kyan gaske komai na cikin sa ya kasan ce golden and white color ne royal sofas ne masu kyan gaske set biyu sai wani ƙaton dining table mai chairs guda 10 , sai wasu bedroom guda 3 dake hannun dama sai kitchen da store atare, wani corridor ya nufa inda yana shiga nan ma wani madaidaicin parlorn me dauke da sofa a set 1 komai na cikin sa golden color ne sai dining mai dauke da chairs guda 5 sai two bedroom, daya daga cikin su ya nufa bakinsa ɗauke  da sallama, wata kyakyawar mace ce zaune a kan sallaya itama farace sosai suna Kama da dr  banbanchi Ita mace ce shikuma namiji zata yi kimanin shekara 50  , sanye take da hijab hannun ta reke da chasbaha tana ja , da alama sallah  ta gama, sallamar da yayi ta amsa mashi yayin da yake ƙarasa wa inda take zaune,wuri ya nema ya zauna  "an wuni lafiya ammy,  ya gida"ya faɗa ,  amsa mashi tayi da
"lafiya qlu Alhmdllh,ya aiki, ya  fama da patient kuma??" "alhmdllh ammy"
"Masha Allah" ta faɗa  haɗi  da cewa "ka tashi ka shiga ciki domin kasamu ka huta zansa fatima ta kawo maka dinner ɗinka" shi dama ba ma'a bocin cin abinci a dinning bane
"to shikenan ammy bari na wuce ciki" fito wa yayi daga bedroom ɗin  ya nufi stairs dake parlor wani  part ya shiga wanda da alama nasa ne tura ƙofar  yayi haɗi  dayin sallama, ya kutsa kai ciki parlor  ne shima madaidaici me kyan gaske komai na cikin sa ash and black ne ,bedroom ya nufa wanda shima bedroom ɗin  kayan cikin sa ash ne hatta da furnitures ɗin  dake ciki ash ne ɗan corridor ya nufa clothset ne sai gefe  laundry basket,  kayan jikin sa ya shiga ragewa ya koma daga shi sai boxer  bathroom yanu fa domin watsa ruwa after 15 minutes ya fito jikin sa sanye da bathrobe, wurin clothes set ɗinsa ya nufa jallabiya ya saka ajikin sa bathroom ɗin ya koma domin ɗauro  alwallah saboda time ɗin  sallah isha yayi
masallachin gidan ya nufa dan gabatarda sallah anagama sallah part ɗin  sa ya koma a parlor  ya zauna kan sofa  bai jima da zama ba yaji ana nocking  tambaya  yayi waye ne " fatima ce Yaya"
"ok shigo" ya faɗa turo ƙofar  tayi ta shigo bakinta ɗauke  da sallama kyakyawar matashiyar budurwace da aƙalla zata kai kima nin shekaru 18 zuwa 19 a duniya fara ce itama tana kamada ammyn su amma ba sosai ba dr dai shine ke kama da Ita sosai
"ina wuni Yaya, andawo lafiya?"
"lafiya lau"
"dama ammy ce tace na kawo maka dinner ɗin  ka"
"ok,zaki iya ajiyewa kan table" gyaɗa kai tayi tana ajiye mashi,ficewa tayi daga parlorn, jawo table din yayi , serving ɗin  kanshi yashiga yi, yana kammala cin abincin bedroom ɗinsa  ya koma laptop dinsa ya jawo dake kan bedside  aiki yashiga yi.

KATSINA.

Su Aaimah ne zaune a falon mom suna kallo, sanye suke da pajamas sky blue,   mom ce ta fito daga bedroom ɗin  ta,  ita ma sanye take da pajamas purple color,  waya ce kare a kunnanta da alama waya take, wuri tasamu kan sofa ta zauna tana cigaba da wayar 
"mom abie  ne Aaimah ta faɗa  yayin da take matsowa kusa da mom" daga mata kai mom tayi alamar eh
"mom dan Allah kice muna gaishe shi munkira shi bai ɗauka  ba"
"to kaji Wai twins ɗinka  nagaishe da kai, wai sun kiraka baka ɗauka ba" mom ta faɗa,mika ma Aaimah wayar tayi da a lama cewa yayi a basu wayar, amsa tayi tana faɗin " inawuni abie  ya Abuja, ya kuma aiki?" on the other hand abie  yace" lafiya lau Alhmdllh, ya gida ya kuma school"
"Alhmdllh abie"  ta bashi amsa
"abie  ko ka ce ina nake Aaimah ka ɗai  kasani" Aairah ta faɗa wacce ƙarasowarta kenan "afuwan yanzu zance kina ina sai kuma gaki,ya gida ya school?"
"Alhmdllh abie,  yaushe zaka dawo"
"jibi in sha Allah zan dawo"
"to Allah ya kaimu abie" ameen ya faɗa   sun jima suna waya  sannan suka yi sallam,  bedroom ɗin su  suka nufa domin bacci dan mom ta daɗe dashige wa nata bedroom ɗin.
Ep 5_6

FRIDAY.

sauko wa yake daga stairs jikin sa sanye da baƙaƙen suit hannun sa riƙe da briefcase, ammy ce zaune kan sofa ƙaraso wa yayi kusa da ita
"Ina kwana Ammy, ina fatan kin tashi lafiya?" ya faÉ—a yayin da yake samu wuri kusa da Ammy ya zauna
"lafiya lau Shazim har ka fito?"
"eh ammy ya bata amsa
"ga breakfast din ka nan kan dinning"
"to ammy,kin kuwa yi waya da NORAIZ?"
( kaninsa mai bimasa yayan fatima da yake baya nan yana kasar portland yana masters) ya fada yayin da yake nufar dinning
"eh, naji yace yana nan zuwa ranar sunday ( lahadi ) ammy ta faÉ—a " eh ammy haka ya faÉ—a man jiya"
"to Allah ya kaimu lafiya,Jiya uncle É—in ku ya kirani, yace kai ka É—ai suke jira"
shiru yayi baice komai ba sai da ammy ta sake cewa "da kai fa nake magana, ni ban san mikake nufi ba , da anyi magana sai kayi shiru, tun yaushe ake abu É—aya sai yawo ka ke ma mutane da hankali"
"kiyi haƙuri ammy, wallahi ban gama abun da nake ba, kuma ni fa bani da wata wacce zance ina so, nafi son su bar na samu wacce nake so"
"to bari kaji na faÉ—a maka ni ba ruwana daga yanzu bazan sake shiga maganar ba, duk hukuncin da suka yanke akan ka ba bu ruwana"
shazim yace "dan Allah ammy kar kice haka, idan kika zare hannunki innah zata iya zuga su su yanke man hukuncin da duk su kaga dama"
"to idan har baka son haka ta faru to dole sai ka nema ma kanka mafita"
"in sha Allah ammy"
"to Allah ya yarda"
"ameen ammy "

fatima  ce ta fito daga bedroom dinta dake kusa da na Ammy, sanye take da uniform , dinning ta nufo Ita ma domin breakfast
"Ina kwana Yaya, an tashi lafiya"
"lafiya lau" ya bata Amsa, yana gama breakfast ya mike yana daukar briefcase É—in shi "Ammy ni zan wuce, to a dawo lafiya,Allah ya bada sa'a" "ameen Ammy" fita yayi zuwa parking lot, gaisawa ya tsaya yi da masu aikin gidan tun daga kan maibama flower ruwa Har izuwa kan maigadi sannan ya fice daga gidan, ABNOOR ya nufa domin yau baya zuwa EKO.

ABDULƘADIR   ABUBAKAR NURADDEEN PRIVATE  HOSPITAL ( ABNOOR ).

Direct office din sa ya nufa briefcase din sa ya aje akan table, zama yayi haÉ—i da buÉ—e laptop din sa, aiki yafara kafin time din daya ke duba patient yayi.
sallama a kayi haÉ—i da turo kofar,wani matashin saurayi ne wanda zasu yi sa'anni da shazim É—in.
Amsa mashi sallama yayi, shigowa yayi daga ciki, hannu ya miƙa ma shazim suka yi musabaha , sannan ya zauna kan  kujerar dake gaban table din
"shazim  amma yanzu ka shigo, dan na zo baka nan?"
"eh shigowata kenan nakama aiki"
"ai ku manya ne agogo sarkin aiki"
"haka dai ka ke gani majeed,  karfin haline kawai"
"wlh kuwa ai kana ƙoƙari"
"to ya za'ayi,dole a nema"
"hakane dama maganar kayan da suka kusa ƙarewa ne"
"kai ai kuwa gara daka tuna man,dan har na manta, zanyi magana da su yau in sha Allah"
"to shikenan,ni bari nakoma office"
"to shikenan nima yanzu zanje duba patient in sha Allah, saboda da time din sallah nayi zan tashi sai kuma gobe Idan Allah ya kaimu"
"ameen" majeed  ya fada barin office din yayi, shi ma shazim bai jima ba ya fita, dakin marasa lafiya ya nufa, sai 12:10 sannan ya dawo office, yana shiga ba wani jimawa yayi ba ya haɗa kan kayansa ya fito direct gida ya nufa bedroom din ammy ya fara zuwa gaisawa kawai su kayi ya nufi part din sa. bedroom din sa ya nufa kayan jikin sa ya shiga ragewa ya nufi bathroom after 10 minutes ya fito kugunsa daure da towel dressin mirror ya nufa mai ya shafa mai dankaran kamshi, comb yasa ya shiga combing din kansa sannan ya shafesa da man aloe da hair spray, clothes set ɗinsa ya nufa shaf shaf ya shirya cikin wata shadda ƴar ubansu milk color ba karamin
kyau yayi ba,hula ya dauko ya daura brown color, feshe jikin sa yayi da turare mai ƙamshi,sannan ya nufi  shoe rag dinsa, takalmi ya dauko me kyan gaske shima brown color. masha Allah kawai zamu ce dan ba karamin kyau yayi ba,wayoyin sa dake bedside ya dauka fita yayi daga bedroom din sai zuba kamshi yake,down stairs ya nufa parlorn ammy,a zaune ya sameta tana karatun Qur'an.
tana kai aya tace "sai masallaci kena"
"eh ammy" ya bata amsa
"to shikenan a dawo lpy nima zanje gida domin na ƙarasa  duba jikin baba"
"to saikin dawo, Allah ya bashi lafiya, nima in sha Allah yanzu daga masallaci zan biya na gaishe shi,saina dawo" ya faɗa haɗi da kama hanyar fita,Ammy na cewa a dawo lafiya, da innah  asabe ya cikaro ( mai Aikin su) zata shiga wurin Ammy, gaishe da Ita yayi ta amsa mashi da ita
"lafiya lau Shazim,har za'a tafi masallaci kenan?"
"eh" ya bata amsa haÉ—i da ficewa daga falon ya nufi parking space motarshi ya shiga,mai gadi ya buÉ—e masa gate ya fice.

_KATSINA._
AIRAH

Zaune take bakin gado jikinta daure da towel da alama wanka zatayi .
"sister gaskiya kiyi sauri ki fito nima nayi wanka, kin san yau abie  zai dawo kuma mom tace muje gidan granny mu gaishe ta,har so nake muje gidan aunty safiya ( kanwar Mom wacce suke uwa daya uba daya) mun kwana biyu ba muje ba"
Aairah ta fada.
fitowa Aaimah tayi daga bathroom jikinta daure da towel "ba wani nan sis, zaki ziyara ne ko dai za kije ganin ya MUS'AF dan nasan halinki sarai"
"Amma wlh Aaimah kin bani da sharri,yau she nace maki saboda  shi zanje gidan ni dai ziyara zani bawai saboda  ya mus'af ba,dan wallahi ki bari kar ki jaman ya Abdallah yaji wannan maganar"
"ai kuwa saina fada masa,nace ba kiji gargaɗin da yayi maki ba, ni wallahi har mamaki ki ke bani,kirasa dawa za kiyi soyayya sai ya mus'af , harka duk ta yarinta" "eh naji matar babban mutum, sai mi ko da ace na girmi ya mus'af  ina ruwan ki" Aairah ta fada tana hura hanchi
"Allah ya baki hakuri Aairah  ni nayi nan" Aaimah ta fada tana nufar dressing mirror bathroom Aairah ta shiga shaf shaf Aaimah ta shirya cikin atamfa super Red color ɗinkin riga da skirt,tana nan tsaye tana fesa turare Aairah ta fito sai ɓata rai take.
shiryawa itama tayi cikin atamfa color daya data Aaimah tana gamawa ba tai ma Aaimah magana ba taka ma hanyar fita daga bedroom din, murmushi Aaimah tayi tana cewa " kina fa iya cewa kinji haushi" bata bata amsa ba sai tsaki da taja
"haba twin sis kiyi hakuri, bazan sake ba kinji ta ya mus'af,  sorry pls" Aaimah ta fada tana matsowa kusa da Aairah sake bata hakuri tayi tana cewa "haba abun gidan ya mus'af  kiyi dariya mana dan Allah" tafa da tana langwaɓar da kai, murmushi kawai tayi tana cewa "wallahi Aaimah ki daina kushe man ya mus'af,  In dai kina so mu zauna lafiya da ke"
"kaina bisa wuya na daina in sha Allah" Aaimah ta fada tana jan hannun Aairah su ka fita,bedroom din mom su ka nufa, samun ta su ka yi a zaune gaban dressing mirror tana saka sarka a wuyanta sanye take da wani hadaden less brown color ta sha daurin ture kaga tsiya hannunta ya sha adon ɗan hannu da zobe kalar sarkarta, har suna haɗa baki wurin faɗin masha Allah Aaimah ce ta ce "kice yau an tashi rikita mana abie  kenan,wannan kwaliyya haka mom,ai sai ya ka sa gane ki, yayi tunanin sabuwar amarya aka kawo masa"
Aairah tayi charab tace "ba ki ga harda ture kaga tsiya ba,  lallai duk wanda ya ture ya taro match ba yan ball" murmushi  kawai mom tayi tana cewa "kun rainani ko, na lura ni kuka maida granny da dadi"
Aa wane mu kawai dai munga kin hadu kar abie  ya rikice" "Allah ya shirya ku" mom  ta faɗa da ameen suka amsa, Aairah tace "daman mom  daga gidan granny  zamu wuce gidan aunty safiya  dan Allah"
"shikenan Idan kunje kuce ina gaishe ta"
"to shikenan mom  za taji In sha Allah amma sai abie  ya shigo sannan zamu tafi"
"to shikenan mom  ta fada..

Ya Abdallah ne ya shigo bedroom din sanye yake da shadda maroon color, sallama yayi hadi da shigowa, gaishe da shi su Aairah su kayi sun ficewa zuwa falo, zama su kayi kan sofa suna kallo.
a chan kuma bedroom din mom  gaishe sa Ita Abdallah  yayi, amsa mashi tayi tana cewa "har ka dawo daga masallachin?"
"eh mom"  ya bata amsa "abinci fa, a kai maka part dinka ko za ka sauko kaci a dinning"
"a'a a barshi nan zan sauko Idan abie  ya shigo sai muci tare da ku,nayi waya da shi da ina kan hanya wai ashe ya dawo yana gidan dadi  (kakar su ta wurin uba mahaifiyar Abee) amma yanzu zai baro gidan"
"to shikenan bari nasa ajera abinci kan dinning sai muci tare da da shi,dama nayi tunanin basu kusa isowa ba" "to shikenan mom ni na wuce part dina kafin ya kai da shigowa" ya faɗa yana ficewa itama mom  fita tayi direct kitchen ta wuce a chan ta samu baba larai na zuba abinci cikin warmers "yawwa baba kice harkin kwashe kafin na zo,  halan kinga najima ban dawo ba sallah nayi sai nace bari kawai nayi har da wanka tun da nasan lokacin da zan dawo na san a bincin ya nuna kuma barrister na hanya shiyyasa" "A'a nima sai da nayi wankan da naga baki sauko bane kuma ya nuna sai nace bari kawai na kwashe, to shikenan bari na jerasu a dinning" mom  ta faɗa tana daukar warmers din ta nufi dinning bala  driver ne ya shigo hannun sa dauke da kaya suna cikin gaisawa da mom  su ka ji sallamar abie daga bayan su, saukowa su Aairah su ka yi da gudu jin sallamar abie,  nufar sa su ka yi da gudu, hugging din su yayi yana murmushi sun bi sun makalkale shi mom  ce ta matso tana cewa 'ku sa ke sa mana,  kunbi kun makalkalesa"
"mom  kwana biyu fa baya nan"
"to ko baya nan fa , ya kwaso gajiya shine zaku kara masa wata, ku sake sa nace" sakin sa su ka yi kan sofa suka  zauna,  shi kuma up stairs ya haura shi da mom , bala ne ya sake shigowa da wasu kayan na abie,   jakar kayan abie  kadai bala ya kai sama sauran kayan kuma kitchen ya nufa dasu .
AFTER 25 minutes......

abie  ne da mom  ke saukowa daga up stairs abie  har ya chanza kayan jikin shi da alama wanka yayi dinning su ka nufa, tasowasu Aairah su kabyi su ma suka nufo dinning din
"Aairah maza kije ki kira yayan ku" mom ta fada, tashi Aairah tayi direct part din ya abdallah  ta nufa tsit parlorn  shi yake ba ko wa sai kamshi kawai dake tashi ya hadu parlorn  golding color ne komai na ciki , bedroom din sa ta nufa nocking tayi tambaya yayi waye
"Aairah ce yaya, mom ta ce ka sauko abie  ya dawo"
"ok gani nan zuwa" yace fita tayi daga part din ta koma wurin su mom
"ya ce ga shi nan zuwa" ta fada yayin da take samun wurin zama, serving din su Aaimah ta shiga yi sai ga ya abdallah  shima ya sauko jikin sa sanye da jallabiya,ƙarasowa yayi yana gaishe da abie  da gajiyar tafiya, amsa mashi abie  yayi tare da tambayar  shi ya aiki,amsa ya bama abie  da alhmdllh shima serving din sa Aaimah tayi , abinci su ka shiga ci ba magana sai dai karar spoon  dake tashi,  su Aairah su ka fara tashi
"ba dai har kun ta shi ba?" abie  ya tambaya  yana binsu da idanu
"eh abie,zamu je gidan granny ne shiyyasa kuma fa mun koshi"Aairah ta bashi amsa
"to shikenan sai kun dawo kar dai ayi dare , a dawo dawuri kun ji"
"In sha Allah abie  baza mu kai ba"
Allah yasa, ameen suka fada su na nufar up stairs , abie  su na gama cin abinci kan sofa su ka koma suna fira shi da ya abdallah ,mom  kuma tattare dishes din da su kayi amfani dasu tayi ta nufi kitchen, baaba larai ce ta fito daga corridor din da da kinta yake wurin su abie  ta nufo hadi da gaishe da abie  tana tambayar  shi ya gajiyar hanya amsa mata yayi da, "lafiya lau alhmdllh,  ya gida ya kuma muka same ku"
"Alhmdllh mu ke, naga saƙo nagode,Allah ya saka da alkairi" ameen nagode  bakomi abie  ya bata amsa ( nasan masu karatu zasu ce godiyar mi baaba larai ke yi ma abie , kudi ya ba ma mom  ta ba ma dukan hadiman gidan dama ya kan yi haka duk In zaiyi tafiya.) Kitchen ta nufa anan ta samu mom  na wanke dishes din da suka ci abinci "ah hajiya dakin bari na zo na wanke ai, A'a bakomi  baaba kema ki huta mom  ta bata amsa, to shikenan bari mu yi tare" in ji baaba larai, "A'a da kin bar shi Allah, kinga na kusa gamawa ai"
" to shikenan" su Aairah ne su ka sauko sun sha jalbab har kasa sai bag kalar ta kalmin dake kafarsu,karasowa su kayi wurin su abie  hadi da cewa sai mun dawo,abdallah ne ya ce" mudi na nan waje shi zai kai ku" to suka ce suna nufar kitchen wurin mom sun cewa sai mun dawo a dawo lafiya tayi masu , ficewa su ka yi zuwa harabar gidan,  a nan suka samu mudi na jiran su , motar su ka nufa,  shiga su kayi,  key yayi ma motar suka fice da ga gidan dama me gadi ya bude masu gate labari kawai Aaimah da Aairah keyi shi dai mudi nashi saurare har suka isu gidan granny horn mudi yayi a bakin gate din gidan,bude masa gate din a kayi ya shiga daga ciki, ya na parking su ka fito gidane dan dai dai me kyau cikin gidan suka nufa wata kyakyawar tsohowa ce suka samu zaune a parlor  tana kallon SUNNAH TV ( granny kenan mahaifiyar mom  ce) sallama su ka yi da gudu suka nufi yar tsohuwar,  granny tace "karku kuskura ku fado man,salon kawai ku ida kara sa man yan kafafun da nake fama dasu" Aaimah ce tace "haba granny daga munyi murnar ganin ki sai kice zamu ida karasa maki kafafun"ta fada  tana turo baki, Aairah ce tace " shiyyasa yau zan zuga tsoho yayi maki kishiya tun da baki da kafafu" granny tace
"sai dai ke ayi maki kishiya,  amma ba dai ni ba,  saboda  ni ba wacce zata iya kishi dani, in kuma kece kishiyar in ji tunwuri" dariya su ka kwashe da Ita su duka Aairah tace
"wah wai ni , ai kuwa da kin sha kwarkwasa da kisisina" murmushi kawai granny tayi hadi da fadin Allah ya shiryeki yan biyu ( dayake haka take ce masu ko kuma Hassana da hussainah) gaishe da Ita su kayi suna tambayar  tsoho na nan, ( wato mijin granny) granny ce ta basu amsa da "yana parlor da yake ganin daliban sa, inajin ma karatu suke saboda  yau juma'ah ( malamin addini ne shi duk da ya tsufa hakan bai hana shi koyar da daliban sa ba) Aaimah tace" to shikenan granny bari muje gidan aunty safiya  mu dawo,  kilan time din ya gama, to sai kun dawo ku gaishe man da ita" granny ta fada Aairah ce tace "za ta ji in sha Allah" fita su ka yi harabar gidan nan suka samu mudi zaune kan benchi suna fira da me gadin gidan, gannin sun fito ne yasa shi tasowa Aairah ce tace "kabar shi kawai ba nisa za muyi ba, gidan aunty safiya za muje"
to ya fada yana komawa kan benchi ya zauna,su ku ma fita su kayi daga gidan,  tafiya su kayi a kafa ba mai nisa ba su ka iso gidan, tura yar kofar dake gefen gate su kayi su ka shiga gidan,  gida ne mai girma ba laifi dan har ya kusa girman gidan su,  part din masu gidan suka nufa da sallama a bakin su suka shiga parlorn,  yan yara su ka samu na wasa a parlorn  mace da namiji a kalla za suyi kimanin shekaru 10, suna jin sallamar su suka nufo su da gudu suna masu "oyoyo aunties ya gida, ya mom" su Aaimah su ka ce "lafiya lau hisham sai ku ka dai a parlor  kai da hibba" wata matashiya ce ta leko daga up stairs jin hayaniyar yaran zata yi sa'anni dasu Aaimah tana ganin su Ita ma da gudu ta sauko tana fadi "oyoyo lovely sister, da ku ka ce kun fasa zuwa" Aairah ce tace "ke dai bari najma,  dafa har mun fasa saboda  abie  zai dawo yau, to da muka koma gida daga school mom  take ce ma ai yama kusa isowa, to shine fa muka shirya yana dawowa muka ta ho" najma  tace "gaskiya  naji dadi, da Allah har nayi fushi"
Aaimah tace "yanzu dai ba wannan ba naji banji mutsin Ummah ba ( Aunty SAFIYA suke cema Ummah saboda su najma  ) ko bata nan ne , tana dakin Abba  najma  ta bata amsa hadi da jan hannun su tana cewa "mu tafi part din Abban daga nan sai ku gaisa da shi ko"
"ok muje"  part din abban su ka nufa, sallama su ka yi yayin da suke shiga cikin parlorn  zaune suka same su kan sofa, amsa masu sallamar su ka yi aunty safiya  tace "ah lallai yau ina da manyan baki" abba yace " lallai kam yau muna da man yan baki, ya mom din ku da abie  ya kuma school, alhmdllh abba suka amsa mashi, to masha Allah abba ya fada najma  ce tace " to ku tashi mutafi daki, da to suka amsa mata hadi da mikewa suka fice direct bedroom din najma suka nufa suna shiga suka yada zango akan bed din ta Aairah ce tace " wai nikam ina Yaya mus'af  ne najma" wani kallo Aaimah tayi mata
"uhmm dama nasan hali,har ni za kiyi ma bariki wai ziyara za mu zo bayan nasan ƙarya ne"
"eh din naji komi za kice kice Aairah ta fada tana murguda ma Aaimah baki ,najma  ce tace" ya Isa haka in kuka fara sai ku ba mutun haushi wallahi, ya mus'af  ne dai ko, to yana part dinsa bari nakira maki shi a waya ko ke ki kira shi ba shikenan ba" Aaimah tace "aikin san wasa nake maki ko rabin rai"
niban wani sani ba Aairah ta fada, to yanzu kinsani shikenan ko ta wuce, bari ni na kira maki shi da kaina a cewar Aaimah hadi da ciro wayarta tayi dealing number sa kiran na shiga ta mikama Aairah wayar picking call din yayi hadi da ce " Assalamu Alaikum"
"Waalaikassalam" ta amsa mashi sallama da ya yi
cewa yayi" Aaimah ya ki ke,ya gida yasu mom  da ya Abdallah,ina kuma sweetie nah take" bubbuga kafafu ta shiga yi tana turo baki hadi dacewa" haba Qalbei nice kenan ma baka gane ba"su najma  mi za suyi inba dariya ba,suna cewa "ashe soyayyar bata kaiba da har ake kasa gane muryar juna" fashewa tayi da kukan shagwaba tana faɗin"ka gani koh Aaimah da najma  nayi man dariya, on the other hand yace " sorry sweet heart nayi tuna nin Aaimah ce,  kinga ai numberta ce amma kiyi hakuri kinji my, najma na gidan kune?"
"Aa fa, kai da na zo dan nayi surprise din ka,  amma sai ka bata komai baka gane ni ba" Aairah ta fada"sorry kinji tawan faɗa man kina ina kin ji" turo baki gaba tayi hadi da cewa " Ina bedroom din najma"
"am coming sweetheart" ya fada hadi da kashe wayar,ajiye wayar tayi Ita ma tana yima su najma gwalo "oho dai ke da ba'agane ba najma ta fada su na tafawa ita da Aaimah" nocking su ka ji ana yi da sauri Aairah ta nufi kofar ta bude,wani matashin saurayi ne tsaye jikin sa sanye da jeans da T-shirt na kamfanin Gucci kyakyawa ne ba laifi a kalla zai yi kimanin shekaru 20 a duniya murmushi Aairah ta sakar mashi shima martanin murmushi ya mayar mata, gaishe da shi Aaimah tayi, ficewa su kayi daga bedroom din,  su Aaimah kuwa fira kawai suke har aka kira sallar asr, sallah su ka tashi su kayi a lokacin Aairah itama ta shigo domin yin sallar Aaimah na ce mata "ai nayi tunanin nisa ku kayi da naga kun fita ashe kuna kusa" banza Aairah tayi da ita ta nufi bathroom  domin yin alwala, basu ne suka bar gidan ba sai wajen 5:00 sannan suka koma gidan granny najma  da Aaimah na gaba yayin da Aairah da mus'af ke bayan su , suna shiga gidan granny tace "ashe za ku dawo harna yi tunanin kun wuce gida, ashe kuna nan" kallon mus'af tayi tana fadin "kai kuma lafiya kayi man tseye a kai , aure ne dai bana yi ehe" dariya mus'af yayi yana faɗin "sai mi,  dama ni yarinya nake so me jini a jika ba tsohuwa ba" dariya su ka kwashe da Ita su duka, "haba kai dai kawai dan ba za ka samu bane , ya safiyar take ina su Hibbatu da hisham"
"lafiya lau suke granny" fira su ka shiga yi da granny tana tsokanar su a nan tsoho ya same su,  gaishe da shi suka yi , dashi suka taru suna ta firar ba su ne suka bar gidan ba sai kusan 5:50 sannan mudi ya mayar da su gida duk da mus'af ya so mai da su,  amma suka ce ya barshi tun da da driver su ka zo ,da shigar su gida bedroom  suka nufa domin time din sallar magrib ya kusa kayan jikin su suka cire suka sanya ma rasa nauyi, saukowa su kayi down stairs direct kitchen suka nufa wurin mom da baaba larai dake shirya dinner , kama masu aikin su kayi har suka kammala kowa ya nufi bedroom dinsa domin gabatar da sallar magrib wacce ake kira.

KAINAAT

_Lagos....._

Innah asabe ce a kitchen ita da fatima suna girki kiran sallar da a ke yine yasa fatima cewa "Innah kije kiyi sallah zan karasa aikin, to amma kefa, karki damu Innah kitafi kawai ( da yake tana fashin sallah ne) To shikenan, fita tayi daga kitchen din ta nufi dakin ta, shazim  ne ya shigo cikin gidan jikin sa sanye da farar jallabiya da alama daga masallachi yake parlorn Ammy ya nufa bai isketa ba sai ya wuce bedroom din ta, nan ma bata nan fitowa yayi daga part din ya nufi main parlor  fatima ya gani ta fito daga kitchen hannun ta rike da food flask " Ammy bata dawo bane,eh bata dawo ba , ok ya fada hadi da komawa part din sa, lokacin da Innah asabe zata koma kitchen har fatima ta gama komai da yake sai da ta jira aka kira sallah isha tayi, kama mata kawai tayi suka gyara kitchen din,  falo fatima ta fita kiran daya daga cikin ma aikatan gidan tayi a waya domin yazo ya daukar masu a binchin su, sallama a kayi daga kofar falon haɗi da turo ƙofar, fateemah ce tace yawwa ilya  tana shiga kitchen,fitowa tayi hannun ta ɗauke da food flask din masu aikin mika mashi tayi , part dinsu ita da Ammy ta nufa bedroom din ta ta shige kayan jikinta tacire towel ta daura bathroom ta wuce domin yin wanka 10 minutes ta fito daga bathroom din dressing mirror ta nufa mai kawai ta shafa ta nufi clothes set dinta, dama ta sanya pad tun a toilet shiryawa tayi cikin pajamas lemon green ta yafa mayafi white mai dan girma feshe jikinta tayi da turare mai dadin kamshi fita tayi daga bedroom din a falon Ammy ta zauna kan sofa wayarta dake charge tacire ta shiga chatting wurin 9:00 sai ga Ammy wacce shazim  ya dauko falo  ta tsaya shi kuwa up stairs ya haura sai 9:30 fatima da Ammy su kayi dinner dan shi shazim  cewa yayi takai masa part din sa,suna kammalaawa fatima ta kwashe kayan da su ka yi amfani dasu ta kai kitchen nan falo ta zauna suna fira da Ammy sai wuri 10:00 su katashi kowa ya shige bedroom dinsa
zaune yake kan sofa dake bakin bed dinsa yana aiki a laptop dinsa sai wurin 12:00 ya rufe laptop din toilet ya nufa bayan  5 minutes yafito jikin sa da damshin ruwa da alama alwala yayi, wardrobe dinsa ya nufa sallaya ya fito da Ita ya shimfida shafa'i da wutiri yayi,ya jima kan sallayar yana adu'oi sannan ya niketa ya maida ta cikin wardrobe,  bed dinsa ya nufa hadi da kashe bulbs din dakin ya kunna bedside lamp, zama yayi daga bakin bed din adu'a yayi ya shafa a fuskar sa sannan ya ida hawa kan bed din kwanciya yayi hadi da jan blanket yarufe iya kugunsa.

Washe gari.......
Zaune Ammy da fatima suke kan dinning suna breakfast, shazim  ne ya shigo jikin sa sanye da jogging suit black color sai p-cap  white hannun sa rike da water bottle wurin su Ammy ya nufa " ina kwana Ammy fatan kin tashi lafiya ya fada Ammy tace "lafiya lau alhmdllh, yau baka zuwa abnoor  ne,  amsa ya bata da " A'a Ammy zanje, ok naga har 10:30 tayi Ammy ta fada , " eh wallahi nayi late wurin tashi daga bacci,amma yanzu zan shiga ciki nashirya In sha Allah"
"to shikenan sai ka shirya ga breakfast dinka nan na jiran ka a dinning, to Ammy ya fada hadi da nufar part din sa.

✨ _Victoria_ . ✨

Anguwace ta christianity irin ta masu kara min Karfi, destiny naga ni ta fito da ga wani gida ta nufi wan da ke opposite din in da ta fito jikin ta sanye da gown iya gwiwarta purple color kanta da kitson kalaba na attachment ka farta sanye da flat shoe, gidan dan karami ne, ko ina ya sha cement dakuna biyu ne a gidan nufar daya daga cikin kofofin tayi knocking tayi hadi da cewa" excuse" daga cikin dakin naji ance "come in" tura kofar tayi hadi da shiga Victoria ce acikin
dakin tana ta faman jan straight gown taki shigar ta destiny ce tace " lallai Victoria a she bakima shirya ba, kin kuwa san nisan da wurin ya ke da shi,sai fa mun fita Lagos kuma fa kinsan yau ana zuwa church da yamma, sorry destiny yanzu zan shirya mu tafi, abun da yasa ma nayi late bari nayi sai momy ( mahaifiyar ta ) ta tafi market sannan domin in tasan inda zamu ba zata bari mu tafi"
"Ok kiyi sauri gaskiya" Victoria na ga ma shiryawa su ka fita gidan tafiya su kayi sai da suka hau kan titi tukun suka tsai da mai mashin suka hau,  tafiya su kayi mai dan nisa sannan suka kawo wani dan karamin kyauye duk duwatsu suna kawowa inda mashin bai wuce wa suka sauka,  kudin sa suka bashi su kuma suka cigaba da tafiya nanma sai da su kayi tafiya ba laifi tukun suka kawo wata yar bukka ita kadai a wurin sai mutane dake a jere a bakin bukkar, suna karasowa suma suka bi layi, sun jima a tsaye layi bai zo kansu ba, victoria harta gaji da tsayuwa ta duƙa, lokacin da layi ya zo kansu shiga su kayi tare cikin  bukkar,wani mutum ne zaune, gaban sa wasu irin ƙahuna ne sai ƙoƙunnan kan mutane,jikin sa sanye yake da jajayen kaya fuskar sa duk ta sha ɗiɗɗige ɗiɗɗigen fari idanun sa a kewaye su ke da bakin fenti,gaishe dashi su kayi da wani irin yare mara dadin ji, kwashewa yayi dawata irin dariya mai firgitarwa sannan ya tambaye  su meke tafe dasu, destiny ce ta kora masa bayani a kan abun da yake tafe dasu, dariya ya sake kwashe wa da Ita sannan yayi yan surkullen shi wani magani ya dauko cikin wani bakin tulu ya ba destiny tasa hannu ta karba ita kuwa Victoria sai zare idanu take kudi suka dauka masu yawan gaske suka ajiye a gaban bokan sannan suka fice daga bukkar ta hanyar da suka biyo ta nan suka bi sai da suka kawo cikin kyauyen tukun suka samu wani mashindin ya dawo dasu gida,   gidan su destiny suka wuce dan lokacin kafe 4:15 dakin destiny suka nufa zama su kayi suna huce gajiyar tafiya destiny ce tace" ina zuwa" tana fada ta fice daga dakin, ba tafi 1 minute ba ta dawo da kwano a hannun  ajiye shi tayi gaban Victoria fita ta sake yi sai gata ta sake shigowa hannun ta rike da pure water guda biyu zama tayi,bude kwanon ta yi sakwara ce da miyar okra ( kubewa) suna cikin ci saiga wani saurayi ya shigo dakin sanye ya ke da crazy jeans sai singlet gashin kansa kuwa yasha dada ( yanda yan iska keyima gashin su ya koma kamar lagwani ) kallo ɗaya zaka masa ka san a buge yake, ya na ganin Victoria ya kama washe baki   daure fuska Victoria  tayi tana ganinsa , kusa da Ita ya matso kamar zai yi hugging din ta ba shiri ta mike tsaye hadi da daka mashi tsawa tana cewa
"which kind of this nonsense samuel"
"bangane wulakanci ba Victoria,you are my wife" ya fada yana washe baki, destiny dai na gefe tana kallon su bata ce masu kala ba sai da taga Victoria na niyyar fita da ga dakin sannan taba Victorian hakuri shi kuma Samuel ce mashi tayi ya fita ya basu wuri tun da shi ba shi da hankali , Victoria tace bata son shi to mi yasa zai ta kura ma rayuwar ta,  Komawa Victoria tayi ta zauna sai wani cika take tana batsewa, suna kammala cin a binci fita su kayi bakin wani fanfu suka wanke hannu Victoria ce tace "destiny zan tafi gida domin nayi shirin zuwa church din kuma kin ga momy bata san nafita ba, kar ta dawo bana nan
"kawai dai kina son zuwane amma aikin san bata dawo ba, da ta dawo da mun iske momy ( mahaifiyar destiny ) a gida, tun da wurin business din su daya" kuma tare su ke fita su dawo tare"
to kawai Victoria tace,  komawa su kayi dakin,  destiny  tace "kin san Adu'a da nake kuwa Victoria?"
"Aa sai kin fada" Victoria ta fada tana sauraron mi destiny zata ce
"so nake wannan wawuyar hidaya ta taya ki bama dr  hakuri kamar yarda da tace, a samu sa'a ya haƙura kuma ya maida ke bakin aikin ki,uhmmm zata sha mamakin abun da zamuyi mata,dan sai munrabata da eko  ma gaba daya yanda ba zata sake ganin dr ba"
"nima haka nake buri, zata sha mamaki In dai ya mai da ni wuri na,sai tayi data sanin sani na a rayuwarta" dariya su kayi harda ta fawa suna nan suna shirya yan da za su yima hidaya mahaifiyar destiny ta shigo gidan ,suna jin shigowarta su ka fito daga dakin gaishe da Ita su kayi yayin da destiny ke amsar kayan da momynta ta shigo dasu, Victoria ce tace "ni na tafi"
"to saina shigo gidan" destiny ta fada, ficewa victoria tayi daga gidan, gida ta shiga momynta ta samu a dakin zaune" good afternoon momy"
"afternoon daga ina ki ke na shigo baki nan momyn tafa da?"
"ina gidan su destiny ne momy" ok kawai momyn tace, wurin 5:00 suka shirya domin zuwa church ( suna zuwa church su duk ranar Asabar domin gyaregyre sbd lahadi ) gidan su destiny , Victoria taje daga chan suka wuce church din....

_Katsina._

Mom ce zaune a main falo suna fira da baaba larai, Abdallah ne ke saukowa daga stairs case jikinsa sanye da jallabiya, wurin su mom ya zo yana faÉ—in"cewa fira kuke ne nagan ku a zaune"
"ai kuwa, sai ina haka naganka da jallabiya"
mom ta fada amsa ya bata da cewa "zan ɗanje wani wuri ne daga can zan tsaya sai an kammala sallah tukun zan dawo" mom  tace "ah kace wurin ɗiyata zaka, amma sai ka je mata da jallabiya sai kace wani limami"
murmushi kawai yayi yana cewa "mi za ki yi da wata ɗiya, ke da ki ke da yan biyu duk mata a gaban ki" wanj kallo mom ta mashi " duk da ina da su ƙari ai ba ya ƙin daɗi koh baaba larai?" ta faɗa tana kallon baaba larai
"haka ne kuwa hajiya” baaba larai ta bata amsa, Mom ce ta kuma cewa" ni dai yau she zaka kawo man surukata gidan nan" murmushi abdallah  yayi yana faɗin" kar ki damu mom dana samu wacce ta dace dani zan kawo maki Ita har gida"
"hmmm Allah ya shirye ka Abdallah, watan kana nufin har yanzu baka samu wacce ta dace da kai ba ko, nasan maganinka ai, xan sa abie  din ku ya zabo maka mata tun da kai ka kasa"
"haba mom kamar ni za'a zaɓa ma mata,ai kuwa dana faɗo,yo ai sai abokaina su yi man dariya"
" to in dai baka son auren dole ka fito da mata kayi aure,kai ko kunya baka ji shekara kusan 30 amma ace baka da mata haba ina amfani"
"dan Allah mom kibar batun auren dolen nan,In dai aure ne very soon zanyi in Allah ya yarda"
"Allah ya yarda" mom ta fada, "ni na wuce sai na dawo" ya fada hadi da nufar kofar fita, a dawo lafiya mom ta fada, fira mom suka cigaba Ita baaba larai suna a nan zaune su Aaimah suka shigo da
alama daga Islamiyya su ke, sanye suke da hijab blue color  gaishe da su mom su kayi sannan su ka nufi bedroom din su, wanka su kayi tare da alwallar magrib,kaya marasa nauyi su ka sa, a daki suka zauna har sai da su kayi sallah isha tukunnan su ka fita falo,fira su ka ke ɗan taɓawa akan Islamiyya anan mom tasa me su har da abie  wanda baijima da dawowa daga masallachi ba, zama su ka yi Abie na tambayar su ya islamiyya,da Alhmdllh su ka amsa mashi har 9:00 suna parlorn zaune,sannan su ka tashi su ka nufi dinning dan gabatar da dinner,bayan da su ka kammal ne kowa ya nufi ɗakin sa bayan sun yi ma mom da Abie sai da safe
su na shiga daki wayar Aairah na ringing,dauko wayar l dake ajiye kan bedside tayi tana sakin murmushi ganin mai kiran nata, Aaimah ce tace
"halan ya mus'af   ne?" a cewar Aaimah,ɗaga mata kai Aairah tayi
"to sai da safe,domin nasan ke ba yanzu ba" Aaimah ta fada tana nufar bed ta kwanta, blanket taja, Ita kuwa Aairah zama tayi bakin bed ta cigaba da waya, ba Ita bace ta gama wayar ba sai wurin 10:55 pm tukun ta kwanta bayan tayi adu'a ta shafa hadi da shafa ma Aaimah sannan taja blanket Ita ma bayan ta kashe bulbs da bedside lamp.
Ep 7_8


_Washe gari........_

Zaune suke kan sallaya suna adu'a da tasbihi, tashi Aaimah tayi daga kan sallayar ta nufi  in da suke Ajiye Alqur'ani ,  ɗaya ta ɗauko,  kusa da Aairah ta dawo ta zauna tana miƙa mata" sister amsa in karanto maki haddar da nayi, in da nayi kuskure saiki gyara man,"
"to in dan na  gama maki nima sai ki amsar man" da to Aaimah ta amsa
karatu ta fara cikin ƙira'a mai daɗi ,Aairah na sauraron ta   in da tayi kukure sai  ta gyara mata,  sai da suka gama amsar ma junan su hadda tukun su ka mai da qur'anan wurin da su ke a jiye su , fita su ka yi daga bedroom saboda gari ya yi haske sosai, lokacin Ƙarfe 7:00  na safe,   main parlor  su ka nufa a kitchen su ka samu mom da baaba larai suna hada breakfast, gaishe da su su kayi ,cike da kulawa su ka amsa masu su Mom na faɗin" ina fatan dai kungama hardar ku ta yau, eh mom,to masha Allah,Allah ya taimaka"
baaba larai  tace " kace muna da bikin hadda dana kammala makaranta gagarumi gidan a nan, to Allah ya taimaka ya nuna mana lokacin lafiya" har hada baki suke wurin cewa ameen, kama masu aikin su k ayi har su ka kammala, su Aairah su ka jera kan dinning,  bedroom din su su ka koma domin shirin zuwa Islamiyya  ( Islamiyyar harda suke, in suka tafi tun safe sai yamma duk ranar weekend, Idan kuma ba weekend bane karfe 2:30 suke zuwa su taso da yamma,  amma ban da ranar Friday in kuma an yi hutun school to kullum ne  ban da friday .)
Aaimah ce ta fara shiga toilet domin yin wanka ita kuma Aairah uniform dinsu na Islamiyya ta dauko masu tare da bags dinsu ,  Aaimah na fitowa itama ta shiga, shaf shaf Aaimah ta shirya cikin uniform din, Lokacin da Aairah ta fito har Aaimah ta gama shirin ta ita ma cikin kankanin lokaci ta shirya suna gamawa suka fice zuwa main parlor, dinning suka nufa domin yin breakfast, suna gamawa part din abie  da na mom suka nufa domin su ka yi masu sallama,a dawo lafiya suka yi masu , fita su kayi harabar gidan anan suka samu mudi na jiran su dan shine ke kaisu, sai wurin 10:00 su mom su kayi nasu breakfast din kasancewar weekend ne..

✨  _SHAZIM_ ✨

Yau ta kasance sunday baya zuwa aiki , kwance yake kan sofa  a bedroom din sa ya baje papers da laptop din sa yana aiki,tun da ya gama sallar asuba ya ke nan wurin yana aiki har bacci yayi awan gaba da shi,sanye yake da jallabiya, ya ajiye wayarsa saman cikin sa yayin da ya sa ɗayan hannun sa ya rufe fuskar sa, wayar sa dake saman cikin sa ce ta fara ringing, hannun sa dake kan fuskar ya zame yana ya tsina fuska alamar an katse mashi baccin sa , daukar wayar yayi "Brother" shine sunan daya bayyana akan screen din wayar picking call din yayi hadi da Kara wayar a kunne " hello  Yaya" na cikin wayar ya fada, "ba zaka chanza ba ko noraiz , ina amfanin wani hello kana ɗan musilmi"
 "a fuwan big bro" noraiz ya fada
"Allah ya shirye ka" kawai shazim É—in ya faÉ—a
"ameen,Yaya  ka tashi lpy yasu Ammy da fatima?"
"duk su na lafiya,kaifa,Ina fatan kai ma kana lafiya??"
"ina lafiya Yaya"
"Masha Allah shazim" ya fada hadi da cewa
"ya maganar dawowar ka yau, domin da na ga kiranka nayi tunanin za kace man ka iso dan na san halin ka da chanza lokaci idan za ka dawo"
"A'a ba haka bane Yaya ina nan zuwa yau In sha Allah,  kawai dai ban samu biyo jirgin safe bane shiyyasa na kira ka na faɗa maka sai dai da yamma in sha Allah"
"ok Allah ya kawo ka lafiya" "ameen Yaya sai an jima"
ok kawai shazim ɗin ya ce yana rejecting kiran ya ajiyeta kan center table,  sai da yayi  5 minutes a kan sofar tukun ya tashi,papers din da ya baza ya kwashe da laptop ya saka cikin briefcase ɗin shi, cire jallabiyar dake jikin sa yayi ya koma da gashi sai  short,toilet ya nufa, ya ɗan jima a toilet ɗin tukun ya fito ya nufi dressing mirror ɗin sa,anan ma ya ɗan jima yana yan shafe shafe kai kace mace ce, bayan daya.kammala ne ya nufi clothes ɗinsa shiryawa yayi cikin jeans da T_ shirt, ficewa yayi daga bedroom din zuwa part din Ammy,
a parlor  ya same ta Ita ka dai,  fatima na Islamiyya,  gaishe da Ita yayi , amsa mashi tayi wuri ya samu ya zauna kusa da ita,  Ammy  tace " ga breakfast dinka chan kan dinning, tun ɗazu har nayi tunanin yau ba ka fitowa a daki za kayi weekend"
"wane ni Ammy, kina a gida na zauna a daki,  ai dole na fito na tayaki fira,tun da auta na Islamiyya kuma rigimenmen ki baya nan duk da yau zai dawo"
 murmushi Ammy tayi tana cewa "ka yi waya da shi ne, naji yace da safe jirginsu zai taso"
"kin dai  san halin kayanki Ammy da chanza lokaci in zai dawo,wai kuma yanzu sai yamma tukun" girgiza kai Ammy tayi
"Allah ka shirya mai babban suna,Allah ya kaimu yamma lafiya"
ameen Ammy ya fada yana tashi ya nufi dinning,  warmer din dake kan dinning din ya shiga budewa yana duba abun da ke cikin su. cup ya dauka ya hada tea sannan ya zu ba arish,  wurin Ammy ya dawo ya zauna,suna  fira shi da Ammy yayin da shi kuma yake cin abincin duk ba wani sosai yake magana ba,sun jima suna fira har lokacin sallar zuhur yayi,tashi Ammy tayi ta nufi dakinta shi kuma ya nufi  part din sa domin yin alwala...

✨ _HIDAYA_ ✨

 Flat house ne me kyan gaske Masha Allah na masu rufin asiri kutsa kai nayi cikin parlorn  gidan wanda komai na cikin sa brown color ne,  hidaya naga ni zaune kan dinning tana lunch ita da  mahaifiyar ta wacce kallo ɗaya zaka mata ka gane kamaninta hidaya ta biyo,  tashi hidaya tayi,kallonta mahaifiyar tata tayi tana faɗin" mi ki ke nufi ne,naga kin tashi?"
"na ƙoshi ne mama"
"wai ni kuwa hidaya mi ke damunki ne, a ce kwata kwata mutum baya  son cin abinci,  ko baki da lafiya ne?"
"lafiya ta kalau mama,dan nayi breakfast a makare ne yasa bana jin yunwa sosai, amma lafiya ta lau"
"to shikenan" mama ta faɗa bedroom din ta ta nufa,  kayan jikin ta ta cire ta shiga   toilet,ta dan jima sannan ta fito jikinta daure da da towel,  dressing mirror din dake dakin ta nufa simple make-up tayi sannan ta nufi  wardrobe din dake kusa da dressing mirror din,  gwon  ta dauko ta  atamfa da mayafi,  shiryawa tayi cikin kayan Masha Allah dan bakaramin kyau kayan sukai ma fatar taba,hidaya chocolate color ce,ita ba faraba sannan ita ba baka ba,  wayarta  dake kan bed ta dauka da jaka wurin da takalmanta suke ta nufa ɗan flat shoe ta dauko tasa , fice wa tayi daga bedroom din ta nufi na mamar ta, zaune ta same ta kan gado, sallama tayi tana faɗin" mama zan tafi gidan su maryam" mama tace "to shikenan sai kin dawo ina gaishe da hajiya lubabatu,  sannan kar ki bari yamma tayi baki dawo ba, kinsan dai Baban ku yana gari"
"in sha Allah mama bazan jima ba zan dawo"
"to sai kin dawo" to tace tana ficewa daga ɗakin, a  bakin gate  ta tsaya tana neman abun hawa, bata jima ba ta samu adaidaita shiga tayi sannan ta yima mai adaidaita din kwatancen anguwar da zai kaita, tafiya su kayi mai dan nisa kafin su ka iso wata anguwa, a bakin gate din wani gida tace da mai adaidaita yayi parking,fita tayi ta bashi kudinsa ya wuci ita kuma ta nufi gidan,  mai gadi ta samu zaune akan ɗan benchi,  gaishe da shi tayi, ya  amsa mata yana faɗin "yasu maman ku, suna lafiya?"
"duk su na lafiya"
da alama ya santa shiga tayi cikin gidan,part biyu ne gidan daya daga ciki part din ta nufa, shiga tayi, tsit ta samu parlorn gidan kamar ba kowa wani dan corridor ta nufa ɗakuna ne kusan guda hudu  ƙofofin su na kallon juna, wanda ke farko ta shiga bedroom ne mai  kyau , bed ne  sai wardrobe  da toilet da dressing mirror,  ba kowa a dakin sai karar ruwa daga cikin bathroom alamar a kwai mutum a ciki, wuri tasamu  gefen bed din ta zauna batajima da zama ba sai ga maryam ta fito daga bathroom daure da towel "a she dai zaki zo"  maryam din ta fada "wallahi kuwa zan zo ya ki ke, ya gida,ya su mama?"
"duk su na lafiya" maryam ta fada hidaya  tace " ba kowa ne gidan sai ke ka dai?  " 
" A'a suna nan , kawai dai suna É—aki ne"
"ok,  naji shiru ne da na shigo"
"A'a suna nan bari dai nasa kaya dai" maryam ta fada tana nufar wardrobe,kaya ta dauko riga da skirt na martial , shaf shaf ta shirya sannan ta dawo wurin hidaya ta zauna tana fadin "wai ni kam sister ya kuka kare da Victoria kinsan tun ranar da ku ka yi fada da ita bamu sake wata magana  ba, ya kuka kare naga dr  ya mai da ki wurin ta, kin kuwa san dadin da naji, domin nasan in sha Allah burinki ya kusa cika"
"bakomi,ba mu sake wata magana da ita ba da sunan sa in sa, dan har roƙuna su ka yi ita da destiny akan na taya ta  bama dr  hakuri ya maida ta wurin ta"
"to ke sai kika ce mata mi?" Maryam ta fada ta na tsare ta da idanu
hidaya  tace " mi zan ce kuwa maryam,  tun da ta roƙe  ni  mi zai hana"
"amma wallahi  hidaya baki da hankali,sai kawai kije kice ma dr dan Allah yayi ma Victoria hakuri koh,hmmm ko dai yanzu kin haƙura  da shi ne  ba ki son sa  yanzu??" Maryam ta jefa mata tambaya  hidaya tace "wallahi maryam bazan boye maki ba ina son dr har zuciyata"
"to amma shine zaki taya ta kuma kinsan cewa son shi  take,dama kawai take jira ta raba shi da kowa"
"to ya zanyi maryam,ko mi tayi dan kanta tun da har ta roƙeni zan taya ta mana"
maryam tace "hmm sannu uwar masu tausayi,tun da  ta rokeki ai sai ki  bashi haƙurin, wallahi ke ba kisan wacece Victoria da destiny ba,su kan su munafuntar junan su suke yi  in ma baki sani ba to ki sani, ita kanta destiny din son dr take muna funtar Victoria kawai take,shiyyasa kike fadan haka ni da na daɗe  dasu ni zan baki labarin ko su su waye su, garama tun wuri ki mai da hankalin ki a kan dr ki kyale wata Victoria da destiny chan,amma fa in kinji shawarata,dan wallahi  kika tai make su,sai kinyi dana sannin haka,amma fa in kinji"
"shikenan nagode sosai da shawarar ki,amma  sister sai nake ganin kamar dr bazai soni ba, kina ganin in ya shigo hospital duk matan dake hospital din bamu ishe shi kallo ba, amma zan ciga ba da rokwan Allah in har shi alkairi ne a rayuwa ta  Allah ya tabbatar man"
"to ameen,amma ya ka mata kisanar dashi cewa kina son sa,ko ba komai zai san ke masoyiyar sa ce,ko ya ki ke gani"
"zanyi ƙoƙarin haka in sha Allah,amma gaskiya ina tsoron abun da zai biyo baya,  karma ya zo ya da katar dani kamar yan da yayi ma Victoria,abun da bazan soba kenan"
Maryam tace " to idan baki fada masa ba taya zai gane kina son shi ,  ki fada masa kawai in sha Allah ba abun da  zai biyo baya sai Alkairi, kuma in sha Allah zan taya ki da adu'a"
"Ameen sister nagode  sosai Allah ya barmu tare"
"ameen,karki damu" maryam ta fada, canza firar su ka yi zuwa wata suna nan zaune har a kayi sallar asr , sallah suka tashi su kayi sannan suka fita daga dakin suka nufi parlorn gidan

Wannan kenan..........

✨ _Ammy_ ✨

Zaune take kan sallaya a bedroom dinta bata jima da gama yin sallah ba wayar ta da ke kan dressing mirror ce tayi ringing hannu tasa ta dauko wayar murmushi tayi hadi dacewa "Allah sarki mai babban suna ina jin ya kara so"
picking call É—in tayi tana Kara wayar a kunnenta yayinda take sallama fuskarta É—auke da murmushi, on the other hand na cikin wayar yace "wa'alaikissalam my Ammy ya gida"
"lafiya lau Alhmdllh mai babban suna ya hanya, ka iso ne?"
"Alhmdllh ammy,yanzu zamu ta so,in sha Allah nan da Karfe 5:30 mun iso,shiyyasa na kira ki fada ma ilya  yazo ya dauke ni na kira Yaya bai dauka"
"may be baya kusa ne" Ammy ta fada "to Ammy ki fada ma ilyan"
"yanzu kuwa Allah dai ya kawo ku lafiya"
"Ameen Ammy wallahi harna ƙosa na ganni kusa da ke" "Allah dai ya dawo da kai lafiya" ameen  ya fada,  kashe wayar tayi , mikewa tayi daga kan sallayar,parlor ta nufa a kan sofa ta zauna  , number ilya ta shiga nema cikin wayar ta sai ga fatima ta dawo  daga Islamiyya wurin Ammyn ta nufo tana cewa  "barka  da gida Ammy,  mikike yi zaune ke ka dai a parlor?"
ta fada yayin da take samun wuri kusa da Ammy ta zauna, amsa Ammy ta bata da "number ilya nake nema saboda  zai dauko mai babban suna"
"ya noor ya dawo ne" ta fada tana mikewa harzata nufi upstair Ammy tace " dawo uwar zumuɗi  cewa nayi zai dauko shi bawai ya dawo ba" dawowa tayi tana  turo baki gaba tana faɗin"to Ammy ƙarfe  nawa  zai dawo , Ammy tace"zuwa ƙarfe 5:00 in sha Allah jirgin su zai sauka,  shiyyasa yace a kira mashi ilya yaje ya dauko sa"
"Ammy dan Allah zanbi ilya in zai tafi"
cewa Ammy tayi" to shikenan maza kije " bata ma tsaya sauraron mi Ammy zata ce ba ta nufi dakin ta da sauri, wanka ta fara shiga bata jima ba ta fito sanye da bathrobe shaf shaf tashirya cikin doguwar riga abaya tayi rolling da gyelen  a kanta,  wayar ta kawai da jaka ta dauka ta fice daga dakin inda tabar Ammy nan ta sa meta,   ƙara sowa fatima tayi wurin ta tana fadi "yawwa Ammy na shirya, kin yi ma ilyan magana?"
"A'a bari nayi sai kin shirya tukunnan,ai a kwai sauran lokaci,duka  yanzu ƙarfe  4:00 kuma kinga cewa yayi sai 5:30 jirgin zai sauka"
"Ammy ai da kin yi mashi magana,kinsan fa a kwai nisa Airport din,zamu yi kusan 20 to 30 minutes bamu kai ba fah, kuma ga go slow" Ammy tace "haka ne nasha'afa ne shiyyasa,amma bari na kira ilyan ya fitar da mota sai ku tafi" ta fada yayin da take kiran ilya a waya yana picking  tace " ilya ka fitar da mota za ku je Airport kai da fatima domin dauko mai babban suna yana hanya"
"to Ammy in sha Allah yanzu kuwa zan fito da ita" ilya ya fada da yake shima Ammy yake cewa
"to shikenan ga fatimar nan fitowa" Ammy ta fada hadi da rejecting din kiran, mike wa Fatima tayi tana cema Ammy sai sun dawo
a dawo lafiya Ammy tayi mata sannan ta tashi ta nufi , kitchen innah Asabe ta samu a kitchen din tana gyarashi domin fara shirye shiryen dinner , Innah asabe na ganin ammy  tace " barka da fitowa hajiya, da yawwa Ammy ta amsa mata" kina bukatar wani abune ? Innah asabe ta fada saboda  ganin Ammyn da tayi a kitchen a wannan lokaci " eh kinsan mai babban suna na hanya to shine nake son a daura dinner tun yanzu , kuma shima shazim bai ci komai  ba ya fita ga fatima ita ma kuma,  kinga in aka gama da wuri zai fi ai" innah asabe tace"ah yaufa muna da babban bako,shiyyasa naga fatima ta wuce da gudu dan bata ma lura da niba" Ammy tace "kin san halin Fatima da zumuɗin,ai ina ce mata yana hanya duk tabi ta rude tana can tabi ilya Airport" dariya Innah Asabe tayi hadi dacewa" Allah dai ya kawo shi lafiya"ameen Ammy tace shirye shiryen daura dinner suka shi ga yi..

✨ _SHAZIM_ ✨

 shigowa yayi main parlor bakinsa dauke da sallamada alama baya cikin gidan daga waje yake, su Ammy dake kitchen su ka amsa mashi sallamar, fitowa Ammy tayi daga kitchen din tana cewa
"kai ashe baka gidan, ka kuwa yi waya da ƙanin ka?  ya ce man ya kira wayarka baka dauka ba?"
"Eh na ɗan fita ne tun dazu har bedroom din ki nazo na same ki kina bacci, wayar na silent ne sai daga baya naga kiran sa,  yace man ai kunyi waya akan ki tura mashi ilya ya dauko shi"
eh Ammy ta fada tana komawa kitchen din shi kuma part dinsa ya nufa,bedroom dinsa ya wuce kayan jikin sa ya rage ya nufi toilet  bayan kamar  15 minutes sai gashi ya fito sanye da bathrobe dressing mirror dinsa ya nufa, zama yayi kan stool din dake gaban mirror din, ya jima yana yan shafe shafensa sannan ya nufi wardrobe , shiryawa yayi cikin kana nun kaya riga da wando,wandon baki ne iyakar sa gwiwarsa sai rigar fara mara nauyi mai gajeran hannu, wurin dressing mirror ya koma  feshe jikin sa yayi da turare sannan ya fita  daga bedroom din ya nufi  down stairs parlorn Ammy, dinning ya nufa  ya ga bakomi,  fita yayi daga parlorn ya nufi kitchen wurin su Ammy yana shiga yace "Ammy akwai abinci kuwa?, yunwa nake ji"
"gashi nan ana girkawa saura ka dan mukarsa" Ammy ta faÉ—a
"gaskiya  Ammy bazan iya jira ba, sosai nake jin yunwar babu wani abu ko da mara nauyi ne?"  Ya tambaya
Ammy ta ce" bari na yanka maka fruit" ta fada tana bude fridge ta dauko fruit ta wanke, yanka mashi tayi ƙanana  ta zuba mashi a ɗan bowl ta mika mashi amsa yayi yana faɗin "nagode sosai Ammy" ficewa yayi daga kitchen din,  main parlor ya koma TV ya kunna yana ɗaukar remote ya chanza channel zuwa TVC news,  zaman shi yayi kan sofa  yana shan fruit yana kallo

🌹~ _KAINAAT_ ~ 🌹

_MURTALA MUHAMMAD INTERNATIONAL  AIRPORT

Mutane ne ke daban daban a cikin airport din wasu najiran time din da zasu hau jirgi yayi yayinda wasu kuma sun zo daukar yan uwan su ne, wasu na a parking lot cikin mota wasu na zaune akan chairs din da aka ta nada domin masu zama.
Motar su fatima ce ta kara so cikin airport din parking lot din dake wurin ilya  ya nufa parking yayi, fatima ce ta fara fitowa sannan shima ya fito, cikin airport din suka nufa in da mutane ke zaune fatima ta nufa, wuri ta samu ta zauna ,  wayar ta da ke cikin bag ce ta fara ringing fito da ita tayi "YA DR" shine sunnan daya bayyana akan screen din wayar, picking call din tayi hadi da sallama,on the other hand na cikin wayar ya amsa mata sallamar " ina wuni ya dr,ya gida ya kwana biyu?" "lafiya lau Alhmdllh Bintalo" turo baki Fatima tayi cikin shagwaba tace" haba Yaya nace fa bana son sunnan, amma ka ƙi ka daina ceman" ta fada tana dan bubuga kafafu, dariya na cikin wayar yayi, ai kuwa nan tashiga yi mashi kukan shagwaba tana cewa "dariya ma na baka koh"
"sorry fatimaaaaaa" ya fada yana jan sunan,Uhmmm kawai tace
sake magana nacikin wayar yayi "bana ce kiyi hakuri ba, ai duk laifin ki ne nace ki bar ceman ya dr nan da kika ƙware wurin kirana da shi, shiyyasa nima nace maki haka, kinga nima na rama kenan,amma kiyi hakuri bazan sake ba kin ji" "shikenan Yaya ya wuce"
"Yawwah koke fa, yasu Ammy kina ina ne haka naji hayaniyar mutane?
amsa ta bashi da " Ina airport,munzo daukar ya noor ne "
" ok yau zai dawo kenan, kice ina gaishe dashi ina mashi ya gajiyar tafiya "
" to zai ji In sha Allah yaya "
"ok take care of your self for me pls, bye" ya fada,itama bye masa hadi da rejecting  call  din, game ta shiga  bugawa a wayar tana a nan zaune aka fara sanar da iso war jirgin 5:30 tashi tayi ta koma inda mutane ke tsai tsaye domin tarbar yan uwan su passengers ne suka fara ɓullowa ta wata kofa da aka rubuta EXIST da manya harafi wacce domin su aka tana de ta,ta kai 5 minutes a nan tsaye, mutane da yawa na rugawa da gudu suna tarbar ƴan uwn su, ita dai sai zare idanu take so kawai take taga ta ina ya noor dinta  zai bullo.  Wani matashin saurayi ne ya ɓullo,sanye yake da ƙananun kaya jeans da T -shirt na company gucci,yana rataye da ɓaksr jaka a kafadar a jikinta anyi rubutu da manyan harrufa in da aka rubuta ADIDAS  da farin fenti, riƙe yake da trolleyn sa yana ja, P-cap ce a kansa sai face mask,Akallah zai kai kimanin shekaru 25 a duniya.
Fatima ce ta rugo da gudu tana fadin ya NOORRR tana nufar wannan saurayin, sakin trolley din dake hannun sa yayi, fa dawa tayi jikinsa tana dariya haÉ—i da cewa " shine kawani boye fuskanka dan kawai nasha wahala wurin gane ka koh" janye ta yayi daga jikinsa yana faÉ—in
"Autar Ammy ke dai har yau Allah baisa kinsan cewa kingirma ba koh" fatima tace "haba ya Noor haka ma za kace koh, shikenan tunda baka yi farin cikin ganina ba" ta faÉ—a tana juyawa zata bar wurin, hannun ta ya riko yana cewa "sorry my yar qanwerh, wasa fa nake maki, kema kin san nayi farin ciki ganin ki autar mu" ya fada yana jan kumatunta, dariya ta saki "koke fah " ya fada yana cire facemask din da ke fuskarshi MASHA ALLAH na fada daganin wannan kyakyawar fuskar ta Noraiz kamannin sa daya da fatima , dan dai shi namiji ne ita kuma mace.
ilya  ne ya karaso in da suke yana washe baki Noraiz  yace "kice tare kike da ilyan Ammy" ya fada yana mikama ilya  hannu domin su gaisa
"ina wuni,ya hanya, ya aka baro mutane turai " iliya ya faÉ—a,dariya fatima da Noraiz su kayi jin ilya yace wai ya aka baro mutanen turai, amsa mashi Noraiz yayi da
"Alhmdllh ilya,ya gida?" amsawa ilya yayi da "lafiya lau" ilya ya faÉ—a yana É—aukar trolley din Noraiz suka bar wurin, parking lot su ka nufa booth ilya ya bude ya saka trolley da jakar Noraiz,shiga su kayi cikin motar Noraiz da ilya na gaba ita kuma fatima na baya, key ilya yayi ma motar su ka bar airport din, hanyar gida su ka nufa suna tafe suna fira Noraiz ne yace
"wai ina ya shazim fatima?" amsa ta bashi da "may be yana gida,dan ni ban jima da dawowa daga Islamiyya ba na biyo ilya"  ok kawai Noraiz yace,daga nan bai sake ce mata komai ba har su ka iso  anguwar su horn ilya yayi a bakin gate din gidan, megadi ne ya bude masu gate din, ciki ilya ya shiga, parking space ya nufa parking yayi, fitowa su ka yi daga motar suka nufi cikin gidan, ilya na biye da su a baya hannun sa dauke da trolley da bag din Noraiz.
Shiga su ka yi cikin gidan bakin su dauke da sallama
da sauri Noraiz ya nufi shazim dake zaune kan sofa, hugging din sa yayi yana faÉ—in "nayi missing É—inka yaya sosai"
shafa kansa shazim yayi kamar wani karamin yaro yana cewa " to ai yanzu komai ya wuce tunda gaka ka dawo"
"haka ne kuwa yaya" Noraiz ya fada
Ammy ce ta fito daga kitchen ita da Innah Asabe wurin su su ka nufo Ammy na faÉ—in
"oyoyo mai babban suna" tashi Noraiz yayi ya nufi Ammy,hugging É—inta yayi yana cewa "nayi kewar ki sosai Ammy nah"
"nima nayi kewar ka mai babban suna" Ammy ta fada,  Innah Asabe ce ta matso tana cewa "marhabun lale da babban mutum,ya hanya, ya kuma karatu??" Amsa ya bata da "Alhmdllh" ƴan gaishe gaishe suka shiga yi da firar yaushe gamo,sama ilya ya haurawa da kayan Noraiz zuwapart din sa,bai jima ba ya sauko yana sanar da Noraiz ya kai masa kayan part ɗinsa.
godiya Noraiz yayi mashi, ficewa ilya yayi ya koma bakin gate wurin mai gadi dama nan yake zama.
tashi Noraiz É—in yayi yana faÉ—in"zan shiga na watsa ruwa na fito,naga time din sallah magrib ya kusa" ya faÉ—a yayi da yake haurawa upstairs.
Ammy ce tace  "shazim   abincin fa, ko ba yanzu ba?"
"A'a Ammy sai anjima in mun dawo sallar magrib"
"to shikenan" Ammy ta fada tashi yayi ya nufi upstairs shima
Ammy ma da Innah Asabe na su bedroom din suka nufa aka bar fatima ta gyara kitchen da jera abinchi kan dinning tana gama wa itama ta nufi nata bedroom ɗinta,wanka tashiga ( idan tana period takan yi wanka sau uku har huɗu a rana)

✨_NORAIZ_✨

Fitowa yayi daga bathroom sanye da bathrobe   (  part din sa shima ya hadu sai dai bai kai na shazim girma ba, amma dai masha Allah yayi kyau ) dressing mirror  ya nufa,mai kawai ya shafa ma jikin sa ya nufi clothes set dinsa,jallabiya ya dauko black color yasa, wurin kayan sa da ilya ya kawo masa ya nufa, turare ya dauko cikin jakar sa ya fesa ya mai
Ficewa yayi daga part din dama yayi alwala tun a toilet ,  part din shazim dake ku sa da na shi ya nufa.
yana shiga shazim din na fitowa daga bedroom
shi ma sanye yake da jallabiya.
Ficewa kawai su ka yi,masallachin dake can main gate din gidan su ka nufa, ba su ne suka dawo cikin gidan ba sai da su kayi har isha tukun su ka dawo
A parlorn Ammy su ka yada zango,fatima kaɗai su ka samu zaune a parlorn,su na  zama Ammy na fitowa, wuri ta samu ta zauna tana faɗin
"to a tashi ga abinci can najiran ku"  to su ka cemata su na tashi suka nufi dinning Fatima ce tayi serving din su.

✨ _KATSINA_ ✨

Zaune suke kan dinning suna dinner su duka gidan baka jin ƙarar komai sai na plate da spoon ɗin da su ke cin abincin
Su na gamawa abie  da  Abdallah da Mom suka koma kan sofa yayin da su Aairah ke gyara dinning din, suna gamawa wurin su abie su ka dawo,zama su ka yi abie  na tambayar su yaushe zasu fara exam din SSCE "saura 3 weeks abie " su ka bashi amsa "to Allah ya bada sa'a" da Ameen suka amsa  "abie  wace school  zaka kaimu  in mun gama" Aaimah  ta faɗa "ban gane inda zan kai ku ba,ku da ku ke da school a cikin grinku,ai ba sai kun je wani gari ba" abie  ya fada yana tsare su da idanu "A'a gaskiya abie,mu yi primary school da secondary school a nan sannan kuma ace munyi high school a nan, dan Allah abie a canza mana"
"to sai kun gama exam din tukunnan"
"to shikenan abei" chanza firar su kayi zuwa wata, sai kusan 9:30 sannan su Aairah su ka nufi dakinsu saboda sun fara karatun exam ga kuma zuwa school gobe
suna shiga bedroom din su wanka su kayi su ka sanya pajamas din su,books din su su ka É—auka,sai a round 12:00 sannan su ka yi bacci.
9_10

Sanye suke da uniform din su na school, ko wacce rataye da school bag din ta,  ficewa su kayi daga bedroom din su ka nufi main parlor ,su Mom suka samu kan dinning  suma basu jima da zuwa dinning area ba, gaishe dasu su kayi hadi da samun wuri kan dinning din suka zauna,  abie  ne yace " yau yan biyu an shirya dawuri kenan " amsa suka bashi da " eh abie  "
"to Allah ya taimaka ya ba da sa'a"
da ameen suka amsa, mom  ta miko masu tea  data hada masu godiya su ka mata suna sa hannu suka Karba, basu fi minti 10 ba su ka tashi suna goge bakin su da tissue paper,sallama su ka yi masu, a dawo lafiya su ka yi masu, fice wa su ka yi suna fadin Allah yasa.

Suna ficewa daga gidan school bus É—in su na shigo anguwar,har bakin gate in da su ke tsaye Bus É—in ta zo tayi parking, kofar bus dince ta bude shiga su kayi daga ciki su ka nemi wuri suka zauna kusa da wannan friend din ta su Aeesha
Aeesha tace "twin friends yau wace rana kun fito da wuri, kun samu bus first round " ta fada  da  murmushi a fuskar ta " ke dai bari kawai Aeesha sa'a ce kawi yau " Aairah ta fada Aaimah kuwa cewa tayi
"sai kace kema kullum da wuri ki ke zuwa Aeesha " dariya Aeeshar tayi tana faÉ—in "ai wlh duk da haka gara ni dai "
"bawani nan, wlh kema muguwar let comer ce " Aaimah ta fada lokacin da bus din ke shiga cikin School É—in,
bus stop bus din tanu fa parking tayi aka bude kofar student nata fita suna nufar assembly ground
Inda ss 3 ke tsayawa nan su Aairah suka nufa annan suka samu sauran yan class din su wanda su ka zo dawuri, gaisawa suka shiga yi.
bayan 30 minutes aka gama assembly kowa ya nufi class din su

✨SHAZIM✨

Saukowa suke daga upstairs shi da Noraiz parlor Ammy su ka nufa,a dinning suka same ta ,  gaishe da ita su kayi Noraiz yace  "ammy ina fatima, naganki ke kaɗai a dinning?"amsa  ta bashi da
"Fatima ai ta wuce school"
"kai!,na manta fah, amma Ammy yaushe take gama wa ne"
" tace man dai next month zasu fara exam,  daga wannan week din ma ta gama zuwa school sai kuma exam"
"Allah ya taimaka ya bada sa'a, yaya" Noraiz ya kira Shazim dake zaune yana sauraron su, da na'am ya amsa mashi  , Noraiz yace "amma dai yaya  fatima a abuja za tayi  university kamar yanda take buƙata idan ta gama secondary school " sai da yayi kusan 5 seconds sannan yace "A'a a nan za tayi  school kusa dabammy" ya fada fuskar sa babu a lamun wasa, hankan yasa dole Noraiz ya kama bakin sa yayi shiru,amma baiji dadin shawarar da yayan nasu ya yanke ba,  saboda  fatima ta ƙwallafa rai akan zuwa abuja saboda sa'ada
"Allah ya taimaka " kawai yace yaci gaba da breakfast din sa,  Ammy duk da  ta fison fatimar  tayi karatu kusa da ita amma sai tace "wai shazim mi yasa ka ke haka ne, tun da kai ka janye jiki da abuja, mi yasa suma ka ke son dole sai sun janye jiki da abuja ne wai, miye ai bun dan tayi karatu a can, duk da ni ma nafi son tayi kusa da ni amma zamanta can zai ƙara maku kusanci da dangin mahaifinku" ɗan nisawa yayi sannan yace "ammy ni ba haka nake nufi ba,kwai naga zaki yi kaɗaici ne,ke kaɗai fa a gida"
katse shi ammy tayi da cewa "in dai dan ta nine karka hanata zuwa abuja, idan bata nan baga ku nan ba kai da noraiz "
"ammy mu ba zama muke ba, idan muka fita tun safe sai dare fa muke da wowa"
"to naji sai dare kuke da wowa, itama idan ta je makaranta ba sai da yamma zata dunga dawowa ba?" ta ƙarasa faɗa da sigar tambaya tana tsare shi da idanu
"ammy dan Allah kiyi haƙuri tayi karatun ta nan, itama sai ta fi jin daɗi karatun, chan haya niyar innah kawai ta ishe ta" uhmm kawai ammay tace ba tare da ta sake cewa komi ba
Ba wanda ya sake magana cikin su har suka kammala  breakfast din , shazim ne ya fara ajiye fork din da yake cin arish,hannu ya mika ya yagi tissue din dake kan dinning ya goge bakinsa sannan ya dauki robar ruwa ya sha,mikewa ya yi ya nufi sofar da ya ajiye briefcase dinsa ya na fadin "Ammy ni zan wuce" cup din tea din da ta kai baki ta janye tana fadin "a dawo lafiya , Allah ya  ba da sa'a, an jima ka dan zanje gidan baba,may be baza ka same ni ba lokacin da zaka dawo, dan zanjima kilama sai dare ma zan dawo "
"Allah ya kaimu anjmar lafiya, ina gaishe da malam,  sai na dawo" ya fada yana nufar ƙofar ficewa daga parlorn, Noraiz  yace "a dawo lafiya Yaya, Idan na ajiye ammy gidan malam zan zo wurin ka in sha Allah "
"Allah ya kawo ka  lafiya " kawai ya fada yana ficewa, parking lot ya nufa motarsa wacce yasa aka wanke masa ya nufa, bude kofar motar yayi briefcase din sa ya aje da lab coat, sannan ya zagaya driver seat ya zauna , key yayima motar ya nufi main gate , gaisawa yayi  da ma'aikatan gidan sannan ya fice daman mai gadi yariga da ya bude masa gate,eko  ya nufa yana tafiya yana sauraron karatun alqur'ani a mota...

✨HIDAYA✨

Tsaye take gefen titin anguwar su  tana jiran  abun hawa, kusan 5 minutes tana nan bata samu abun hawa ba, wata bakar motace ta shigo anguwar tasu, tunda motar ta shigo anguwar tasu take ma motar kallon kamar tasan mamalakinta, motar na ƙarasowa  kusa da ita tana rage gudu,  kallon motar kawai take sai da ta kawo dab da ita sannan aranta tace"wannan ai kamar motar dr kabir" parking motar a kayi hadi da sauke glass din motar, kyakyawan saurayine fari amma ba sosai chan ba, akallah zai yi kima nin shekara 28 zuwa 30, sanye yake da scrub suit blue color fuskar sa manne take da glass, hidaya  tace" ina kwana dr" amsa mata yayi da " lafiya lau , mi ki ke yi tsaye anan?" amsa ta bashi da "ina jiran abun hawa ne dr"
"ok to shigo ciki mu wuce "
" A'a dr ka tafi kawai zan samu abun hawa in sha Allah" hidaya ta fada,  glass din dake fuskar shi ya cire yana cewa "to fah, hidaya ko dai kina tsoron  na sayar dake ne iye " murmushi tayi hadi da cewa "A'a ba haka bane "
ajiyar zuciya ya sauke
"to inhar ba haka bane, to kishiga mu wuce " to kawai tace hadi da zagayawa ta shiga ciki, key yayima motar yana cewa "wallahi kina bani mamaki hidaya, sai kace wata ƙaramar yarinya in ki ka yi wani abun" murmushi kawai tayi masa ba tare da  tace komai ba, haka su kai ta tafiya yana janta da fira har suka iso  eko,parking lot din asibitin ya nufa yayi parking, har tasa hannu zata bude kofa ya da katar da ita yana cewa "wai hidaya tsorona ki ke ji ne, naga har wani sauri kike ki fita"
"A'a " kawai tace mashi tana duƙar da kanta ƙasa, "shikenan bakomi kina iya tafiya" ya fada, ficewa tayi daga motar shikuma ya tsaya tatara kayan sa dake back seat, tana fitowa motar shazim na parking, dr kabir ne ya fito hannun sa riƙe da  tarkacen sa yana cema hidaya su tafi,tafiya suke sun kusa kawo inda motar shazim take sai gashi ya fito,miƙa masa hannu  dr kabir yayi  suka gaisa,hidaya ma gaishe da shi tayi, da lafiya kawai ya amsa mata , wuce wa tayi tabar su shi da dr kabir tayi cikin asibitin, office din su da nurses kezama ta nufa, ba kowa ciki sai friend ɗin  ta maryam da alama wanda su ka zo duk sun fita.
"lafiya  yau ki ka yi late ? " maryam ta tambaya , ƙarasowa  inda take hidaya tayi tana cewa "ke dai bari,  banyi bacci bane jiya dawuri shiyyasa nayi late" dafa kafadar ta maryam tayi tana cewa "kingama yanke shawara yan da zaki tunkari dr da maganar koh"
"a'a gaskiya,  maryam ina jin tsoro ne, ban san ya dr zai dauki maganar tawa ba " hannun hidaya maryam taja suka zauna sannan tace " ki kwantar da hankalin ki hidaya In sha Allah alkairi ne zai biyo baya,  kinji" ajiyar zuciya hidaya ta sauke tana cewa "to Allah yasa haka maryam" da ameen maryam ta amsa mata tana cewa "tashi mu fita" ta fada tana jan hannun hidaya, fice wa su kayi suka nufi inda yan uwansu nurses suke, gaishe da junan su  suka shigayi , office din dr Shazim hidaya ta nufa tana cema maryam " sister bari naje office din dr na dawo"
"ok  sai kin dawo " maryam ta fada, office din hidaya ta nufa hadi da tura kufar ta shiga  bakinta ɗauke  da sallama.
amsa mata sallamar yayi, sannan tace "dr asa patient a layi " amsa ya bata  da" eh " har zata  fice sai kuma ta dawo sai da tayi 2_3 seconds sannan dai ta daure tace "afuwan dr dama ina so ne muyi wata mgn" ɗago kansa  yayi daga aikin da yake ya tsare ta da idanu alamar ina sauraronki,  magana  ta fara "dama dr maganar  Victoria ce" ɗaga mata hannu yayi alamar ya isa haka "wannan ya zama na ƙarshe  da zaki ƙara man maganar ta   a nan, in ba haka ba kema zaki bita , fatan kingane"
"ok sir in sha Allah bazan sake ba" ta fada tana ficewa daga    office din , direct wurin patient ta wuce,  ta shiga aikin ta ,a haka Victoria da destiny suka same ta,  wuri suka samu suka zauna kusa da ita , gaisawa su kayi sannan Victoria tace "hidaya ya maganar  mu ne" ajiyar zuciya hidaya tayi sannan tace "gaskiya kiyi haƙuri  Victoria, ko yanzu daga wurin dr na ke nayi nayi ya haƙuri  amma yaki,  dan har cewa yayi kona daina masa magnar ki ko nima ya koreni " wani kallon banza  Victoria tayi mata sannan ta ce "munafukar banza, wannan nasan duk shirinki ne, to kisani kamar yanda kika rabani da dr nima sai na rabaki dashi" mikewa hidaya tayi tana cewa "ki je kiyi duk abun da za kiyi Victoria, tun da ke baki da mutunci" faɗa ne ya kaure a tsakanin su har Victoria na neman kaima hidaya duka,  destiny na jenyeta,   su maryam ne suka zo wurin saboda hayaniyar Victoria data jawo hankalin su, nan suka shiga cewa gaskiya baki da mutunci Victoria, komawa Victoria tayi kansu tana ce masu munafukai tasan ai da hadin bakin su, ai kuwa abun yayi masu zafi nan suka shiga maida mata da martani.
hayaniyar su ce ta damesa harta na neman haddasa masa ciwan kai hakan yasa shi ajiye abun da yake yi,  landline din dake office din ya dauka, dialing numbers yayi ana picking call din yace
"ka same ni a office dina" yana gama faÉ—a yayi rejecting kiran bayan kamar 30 seconds sai gashi anturo kofar, wani security ne ya shigo gaishe da shazim yayi yana faÉ—in "dr gani"
"wai hayaniyar mi nake ji ne?" "afuwan dr bari naje na duba "ok" kawai yace masa, fita security yayi inda su Victoria su ke ya nufa nan ya same su har lokacin basu dai na fadan da suke,  hidaya sai kuka take saboda a rayuwarta ta tsani fitina,  su maryam ne ke maida ma Victoria martanin, ɗaya daga cikin nurses ɗin  mata security ya tambaya   mike faruwa amsa ta bashi "zuwana kenan na same su suna hayaniya ban san miye maƙasudun faɗan na su ba "
"to shikenan" shine kawai abun da security ya faɗa ya  komawa office ɗin  shazim  ya sanar dashi cewa "sir su nurse Victoria ne ke hayaniya, ina jin dai wani abun ne ya ha dasu"
"Mtssww"shazim  yaja tsaki  a ranshi yace "nonsense kawai dasu,zasu wani tada ma mutane hankali,sakarkaru banza "
achan kuwa waje dr kabir ne ya fito daga office ɗinsa  ya nufi in da su Victoria suke  shima hayaniyar su ce ta dame shi, yana isowa wurin dukan su su kayi shiru tsaki yaja hadi da cewa"wallahi kun bani mamaki matuƙa,ashe baku da hankali ban sani ba" ya fada hadi danuna hidaya ya na cewa "wacece nan,mi kuma akayi mata take kuka" da yake a duƙe take shiyyasa bai gane ko wacece ba, maryam  tace "nurse hidaya ce" matsowa yayi kusa da ita yana fadi "mike da munta ne " amsa maryam ta bashi da cewa "Victoria ce ke ci mata mutunci,ita kuma bata iya ramawa,shine take kuka, mukuma..." hannu ya daga ma maryam yana cewa"ya isa haka, oya tashi " yace ma hidaya,  mikewa tayi  fuskar nan duk tayi sharkaf da hawaye "wuce muje" yace,  binsa tayi a baya har office ɗinsa , toilet ya nuna mata "shiga ki wanke fuskar ki" shiga tayi ta wanke fuskarta sannan ta fito
wuri ya nuna mata kan sofa da ke cikin office din,
zama tayi tana sauke ajiyar zuciya
ita bakomai yafi bata haushi ba wai a ce daga taimako Victoria zata yi mata haka, gyaran murya dr kabir yayi haɗi da zama kan sofar yana fuskantarta "hidaya nasan wannan ba halinki ba ne, miyasa ki ke biye ma mutane irin waɗanna,  ke da ita bafa ɗaya ba ne, al'adar ku ba ɗaya ba kwata kwata ita batasan kunya ba saboda ba'a koya mata ba, amma ke duk wanda ya ganki zai yimaki kallon wacce bata san mutuncin kanta ba,please hidaya karki sake"
"in sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba nagode"
"bakomai karki damu, tashi ki tafi ki cigaba da abun da ki ke"
"ok" ta faɗa hadi da mikewa ta fice, wurin patient ta koma  ta cigaba da turama dr su.

✨noraiz✨

Parlorn ammy ya shigo jikinsa sanye da kananu  kaya farar riga da bakin wando, yana shigowa Ammy na fitowa daga bedroom dinta sanye take da hijab har kasa
"yawwa Ammy harkin shirya kenan?" "eh" Ammy ta fada, ficewa su ka yi,  parking lot suka nufa wurin wata baƙar mota ƙirar rang rover,back seat ya bude mata tukun ya zagaya driver seat ya zauna hadi da yima motar key ya nufi gate, megadi ne ya tashi ya bude masu gate, gaishe da Ammy yayi, amsa mashi tayi cikin kulawa sannan Noraiz yayima motar key su ka fice daga gidan.
tafiya su ka yi mai É—an nisa, a bakin gate É—in wani gida Noraiz ya yi horn.
ƙofar dake jikin gate din gidan aka bude,wani mutum ne ya leƙo yana ganin motar Noraiz ya koma da sauri
gate din gidan  aka bude ciki Noraiz  ya danna kan hancin motar, parking lot din dake gidan Noraiz ya nufa ya yi parking, fitowa su ka yi shi da Ammy suka wuce cikin gidan
Chapter 1 · 0% Book details