Chapter: 83
Daudar Gora Part 1 Complete Hausa Novel · about 108 min read
…Babu wanda bai zaro ido ba a falon. Cikin bacin rai Iffah ta ce, "Na fika sanin wannan"Jikin matar na rawa ta cigaba da zayyano mata sauran. Yayinda tuni Ummu dake rude Iftihal mamuke da ita ta yunkura da niyyar zuwa ta nemi Kaka a waya, dan dazun da sukazo sun kawo mata wayarta shima Babiy yana amfani da nashi. Kin sakinta Iftihal tayi, dole sai tare suka tafi. Iffah kam juyawa tai ta dubi hadimanta da ke dauke da abincin data bada umarnin a biyota da shi, ta nuna na hannun amintacciyarta. "Ajiye musu shi suci"
Da ga Banou har abokiyar aikin nata kuka suka sanya, dan su suka san abinda suka gani a abincin. Ko kallo basu ishi Iffar ba, tana tsaye a kansu fuskarta kawai abar firgitarwa ce. Haka suka fara cin suna kuka da rokon tayi hakuri, a haka su Malikat Haseenat da akeje aka sanarmawa suka shigo hankali tashe. Dan can sun samu Malikat Bushirat tayi barcin da kyar bayan an rufu kanta da addu'oi. Kallon Iffah da su Banou din kawai suka tsaya yi cirko-cirko. Daneen Waheeda kam tuni ta koma bayan Mammah ta makale, yayinda Daneen Ammarah itama nata kamanin suka fara canjawa dan idanunta sun kada sunyi jazur. Ture abincin Iffah tai da ga gabansu, ta wani irin hankada Banou gaban Malikat Haseenat. "Jeki sakar mata kafafu!!". Cikin madaukakin mamaki Malikat Haseenat ke duban Banou da Iffah. Sai dai razananniyar tsawar da Iffahr taima Banou din ita kanta sai da zuciyarta ta shiga tsitstsinkewa. Banou dake kuka cikin rawar jiki ta kama kafafun Malikat Haseenat, wani fushin kumburi da kafafun sukai tsahon shekaru an kasa gane kansa sai gashi yau yana bajewa, Kusan minti biyu tace mata ta mike, mikewar tai jikinta sai kakkarwa yake, du da girman jikin nan nata ga tsaho amma Iffah dake yar digila gabanta ta zame mata dodo. "Na baki minti hudu, ki dakko tukunyar da kika ajiye a cikin flowers".
"Umarninki shine abin jirana ranki ya dade".
Banou din ta fada cikin sake gurfana. Suna tsaitsaye har yanzu babu wanda ya iya cewa komai sai ga Banou ta dawo da tukunyarta, A gaban Iffah ta zube, ta bude tukunyar ta shiga fiddo abubuwan da ke ciki. Abinne kamar tsokar nama, duk ta daure. Kwancewa ta shigayi tana sakinsu, firrrr suke tashi kamar tsuntsaye, wasu ko da kyar zakiga sun tashin saboda ta jima tana wahalar da su. Cikin
bada umarni ta dubi sauran hadiman ta ce, "Aje a duba duk wanda yake a halin ciwo ya mike a yanzu a kaimun shi tsakkiyar masarautar nan. Ina bukatar Ghazi guda biyu anan".
Cikin kankanin lokaci Ghazin data bukata suka shigo, su tasa suka tasa mata keyar su Banou.
*Tun fito da Hadimar da ta jibga a sashenta al'amarin ya fara zagaye masarautar. Abin mamaki sanda take fitowa su Malikat Haseenat biye da ita masarautar ta gama cika. Dan sashe-sashe an fito kamar busar kaho. Cikin kankanin lokaci duk wani mara lafiya dake gidan aka fito da shi, harma wanda ba Banou din ce ta tabasu ba. Tana kuka da faman rufe fuska ta tsatstsallakasu. Tana gamawa suma sawa tai aka daure mata su tare data farkon. Dai-dai nan su Baby suke isowa cikin masarautar. Hakama Tajwar Eshaan a rikice Malikat Haseenat tai kiransa ta sanar masa babufa lafiya a gidan da ya kamata ya
fito. Dama shirin fitowa yake, dan amintaccensa yazo masa a kidime babu dadewar nan, hakama Sayeed Fayzul-haq ya kirasa shima.
Lokaci daya wajen ya dauki shiru sakamakon fitowar tasa, dan abunne da babu wanda yay zato. Kowa a wajen sai da yay kasa da kansa har Iffah, dan a zahirinsa yake kyakykyawar fuskar nan a bayyane, sai dai fa cinkus take babu alamar wasa ko sassauci. Amintaccensa ya ajiye wata yar kujera mai kyau dake a ninke aka budeta. Sai kuma katuwar umbrella da aka bude masa duk da bawani ranar nada zafi bane dan ta la'asar ce ma dake neman faduwa. Sai dai kuma a mamakin kowa ma bai zauna ba. Sai duban Iffah da yay na kusan mintuna biyu. A hankali ya furta, "Mike faruwa". Cike da irin girmamawar dake nuni da ba ita bace ba ta kai kasa gurfane gabansa. Gaisuwa ta fara mikawa,kafin dukkan abinda ke faruwa ta zayyane masa. Idanu ya dan lumshe da sake budewa. Kamar bazaice komai ba sai kuma yay mata nuni da ta tashi, tare da fadin,"Duk da ba itace a tare da gangar jikinta ba kuskurene kai Zawjata-almilk kuma * Malikat * kasa a kowane irin yanayi a gaban al'ummar kasar ta"
Wanna furici nasa ne yasa kowa fahimtar ba ainahin Iffah'r bace iskokinta ne yau suka bayyana kansu abinda basu taba yi ba, sannan kuma maganar cikin jikinta tabbataccene tunda har shi da kansa ya kirata (MALIKAT). Neman afuwa suka shiga yi, da tsayawa tsaye akan kafafun Iffah'r. Alokacinne Sayeed Fayzul-haq ya yafito Kaka dake tsaye kawai yana murmushi. Sai da ya fara mika qaisuwa ga Shahan-shan shima sannan ya duba Iffah, kamar yanda sukaima Tajwar Eshaan bayani haka shima kakan sukai masa. Kansa kawai ya jinjina da cire jakar hannunsa ya ajiye. Ruwa ya bukata, cikin kankanin lokaci aka kawo masa. Magunguna ya fiddo da yawa ya shiga zubawa a ruwan nan. Wani irin ihu su Banou suka dingayi da rokon yayi hakuri, bama su ishesa kallo ba ya fara dibar ruwan maganin yana watsa musu. Ihu na gaske suka dinga kwallawa da surutai suna girgiza da gunji. Sai da yay musu ligif sannan ya basu umarnin bayani da bakunansu. Biyun sun tabbatar da su ba mutane bane sun rikidane kawai. Kuma a yau din nan suka shigo cikin masarautar bisa umarnin uwa da Iffah ta raunata a dazun. Banou kam mutum ce ita, sai dai akwai aljanun maita tare da ita, irin kusan duk zuri'arsu ke da shi, dan itama cikin zuri'ar uwa take. Cikin galabaita ta shiga fadin tun sanda take tare da su.
"Ni shekarata goma sha tara anan, tun bayan korar uwa da akayi da ga wannan masarauta. Ina daya daga cikin zuriarta da aka kora shekaru masu yawa da ga cikin wannan alkaryar, a da kakanninmu wannan filin masarautar shine garinsu. Amma sanda za'a kafata sai aka tashesu aka canja musu waje. Ransu ya baci matuka da wannan al'amari, dan tunda suka taso anan suka samu iyayensu da kakanni suma, nan kadai suka sani matsayin kasarsu kuma gari, ga abubuwan bautarsu masu tsahon tarihi tsahon shekaru duk an ruguza musu. Dan haka sukaji zafin tashinsu da akai da bata musu wajen bauta da abubuwan bautarsu saboda gina masarauta bayan akwai filaye da yawa da babu kowa a cikinsu miyasa baza ai acan ba. Wannan haushin yasa sukaki zama inda aka basu sukai hijira zuwa cikin jeji. A haka suka cigaba da sabuwar rayuwarsu wadda da kyar suka saba da wajen, sai ya zam duk wanda aka haifa a cikin zuri'ar mu wannan
shine labarin da za'a raineka a kansa, da kuma kiyayyar wannan gida. A haka duk muka rayu da burin daukar fansa. Mun dade da shiga jikinku muna muku illa da suffar bokanci, hatta lokacin da kuka samu ambaliyar ruwa a kusan kasar baki daya zuri 'armu ne suka balle wani yanki na kogin da ke zagaye da ku. Mu bamu taba jingina da ku domin mu taimakeku ba sai dan mu ruguzaku, a haka iyayenmu da kakanninmu suka dinga shudewa. Uwa ta kasance mafi girman hatsabibanci da yin tasiri a al'amuranku a cikin duk wanda suka zo da nufin masu taimako a gareku a cikinmu. Duk da dai akaf zuri'armu daga maye sai matsafi, kuma kowannenmu nada abinda yake yi domin ku. Jajircewar uwa da zamowarta mafi iyawa a kan iyawar kowa cikinmu yasa ta zama shugaba a garemu, kuma ita muke fata da gain ta kusa karbo mana wanna masarauta data kasance tushenmu ta koma tamu. Amma sai abubuwa suka fara canja salo a dalilin tsohuwar can (ta nuna Malikat Haseenat) ta kanainaye komai tana faman rushe duk wahalhalinmu da muke gain saura kiris komai ya kare. Dan haka mukaita kawo mata hare-hare amma bam samu nasara a kanta ba. Ana cikin hakan rana tsaka ma sai ga Uwa mun tsinta a yashe cikin mawuyacin hali anci zarafinta a dalilin wanna mutumin da mahaifinsa (ta nuna kaka). Hakan ya mana ciwo matuka, ga uwa nakan gangarar mutuwa, a take muka tattara duka karfinmu wajen cetonta, dan duk karfin dake tare da ita na tsafinmu na gado da ma wanda ta samarwa kanta wannan mutumin ya lalatashi. An bada umarnin wasunmu su sake dawowa cikin masarautar nan, duk da zuwane na kasada ni a kasance a daya da ga cikinsu. Kuma nice nan a kashe Shahan-shan Abdull-Majeed a cikin suffar maciji, dan inada maita mai karfin gaske fiye data kowa a cikin zuri'armu. Bayan mutuwarsa na cigaba da bibiyar rayuwar war masu gida, sai dai na kasa kaita kasa saboda abubuwan kanta, nadai samu nasarar nakasar mata kafafu ta hanyar ciyar da ita abubuwa a cikin abincinta. Amma tun randa na had da Zawjata-almilk abubuwa da yawa suka lalace min, dan tanada iskoki masu karfin gaske, itace ta dakusheni akan abubuwa masu yawa. Ta kuma min daurin da bazan iya barin wannan gidan ba duk da naso yin hakan tun a ranar farko dana hadu da itan. Uwa tayi iya kokarinta itama na son ganin ta fiddani amma ta gagara".
Ajiyar zuciya kawai kakeji na sauka da al'ajabin wadan nan abubuwa wai kamar wata almara. Banou da kowa ya sani mafi zama kololiwar amintacciya ga Malikat Haseenat dai, wadda inba abincin data girka mata ba batacin abincin kowa sai Daneen Ammarah. Kai to ai yanzu kowama ba abin a yarda da shi bane hatta hadiman nasu.
Kaka ya jefama Banou tambayar, "Mutane nawa kika cutar a shekarun zaman nan naki?"
"Ni ban san adadi ba. Amma na halakasu da yawa, dan akwai ayyukan da na dinga ma uwa da yarjewar wata babba a gidan nan. Sannan akwai wadanda na kashe dan radin kaina da wanda na dinga cinyewa cikinsu. Na karshen nan dana cinye shine na Jasrah a randa Zawjata-almilk bata da lafiya…..✍️
DAUDAR GORA
Book2
84
..Salati wajen ya dauka da sallami, kowa na tsinema wa da banou. Cikin girmamawa Kaka ya dubi Shahan-shan da shi gaba daya ma komai ya tsaya masa cak. "ALLAH ya karama adalin shugabanmu lafiya da tsohon rai mai amfani, a ganina barin wadan nan bashi da wani amfani, a samu dutsina a juye musu ruwan maganin nan kawai a musu rajamu anan, dan wadan nan mutane nada karfin tsafin da rufesu ko musu hukuncin zaman kurkuku bazai taba iya magance matsalarsu ba. ALLAH yasa ban shiga hurumin da ba nawa ba".
Shiru baice komai ba. Kusan minti uku sannan ya dubi Sayeed Fayzul-haq. Da ga haka ya taka a hankali gaban Iffah. "A gusa daga jikinta",. Iya abinda ya fada kenan. A take kuwa tai hamma jikinta ya saki gaba daya. Rikota yay cikin jikinsa ya rungume. A take kowa da kowa na wajen yay saurin yin kasa da kansa cikin hanzari. Shiko ko'a jikinsa ya dagata cak dagakasa kamar ya manta ma da wasu halittu a wajen yay wucewarsa.
🥱Wannan fa shine ga abin fada babu damar magana 😝
Kamar yanda kaka ya fada kuwa haka akai, tuni hadimai suka cika wajen da duwatsu, kaka ya yayyafesu da ruwan magani, Kamar jira suka shiga diba ana ambaton sunan ALLAH ana jifan su Banou.Ihu suke mai tsananin kururuwar sauti. Amma mutanen nan ko'a kwalar rigarsu. Dama wasu harda fushin Banou tai musu sanadin yaya wasu iyaye, wasu maza, wasu matansu. Dan a cikin wanda ta halakar mafi rinjaye hadimai ne. Babu wanda ya tausaya musu a haka aka jefesu har sai da suka daina numfashi.
Kakane ya ce abar gawawwakin a wajen masu su zasu aiko a debe su, dan sune aiken farko da zasu turama kabilarsu. Haka kuwa akayi, sai dai dan daukar da was samari da yammatan gidan sukayi a wayoyi suka saka a social media cikin kankanin lokaci al'amarin yay amsa kuwa. Wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam suka shiga caccakar al'amarin a bayyane ta kafafen ya da labari, kafin wasu awanni labarin ya shiga zagaye duniya, ya zama video mafi rinjaye da ke yawo kuma ake kallo.....
**
Sun iso gareta a whale, wahalar da duk wanda ke cikin wanna zuri'a sai da ya girgiza. Hakan yasa su yin cirko-cirko da zaman sauraren abinda sukazo da shi. Ita ko tana zaune a cikin kujerar tsafinta hancinta da Iffah ta gundile ya kara saka fuskar munana matuka. Hakama sauran raunikan da taji sun kumbura fuskar ta kara zama humm.
Cikin gurfana da garshekar hakin rudani daya da ga cikinsu ya shiga zayyane mata abinda ke bakinsa, "Shugaba wannan aikin yafi karfinmu, ba namu bane ba sai dai ke. Sun halaka Rudde da Zambo da Banou Sun halakasu har lahira uwarmu mai share kukanmu".
Yanda take huci har Kirjinta na dagawa sama zai baka tabbacin tafa kai kololuwar hasala. Cikin wata irin mummunar tsawa ta nuna su da yatsanta mai dauke da zurkeken farce. "Ni uwa nizan sakaku aiki ku dawo kuce anfi karfinku. Idan kun gujema mutuwarku acan anan ma ita kuka tarar. Ahamanu a daure min su, a aka angulu ta dakkomin gawawwakin su Banou!!"
"Fadi naki cikawa tawa, uwa magajiyar uwa". Wanda aka kira da Ahamanu ya fada cike da girmamawa a gareta. Cikin abinda bai wuce awa daya ba angulu ta dawo da gawawwakin su Banou, ta jima tana kallon gawarwakin guda uku da ke jina-jina da raunikan jifa,hakama sauran mutanen garin tsaitsaye suke yara da manya maza da mata. Sirkullensu a tsafi ta fara sauran suka dauka da amshi kowa ka gani ransa a jagule da bakin ciki. Bayan sun dauka lokaci sunayi ta bada umarnin daukar gawar Banou zuwa dakin gumaka. kasancewar sauran su aljanu ne dama wani ruwa kawai ta yarfa musu namansu suka shiga zaganyewa, a hankali a hankali suka bace bat.
"Lokacin da zamu shirya akin gaba-da-gaba yayi, Jajjal ne kawai ya jurema umarninmu har yanzu bai dawo ba. Na sani shi dama mai jajircewa ne da naci akan komai. Kuma duk wani dan da ya cika dan halak a zuri'armu irinsa ya kamata ace ya zama. Kuje maza kuje ku shirya yaki. Sai mun sabauta gaba daya al'ummar kasar ruman. Sai mun sake dawo musu da tarihi irin na baya koma mafiyinsa. Kuje maza kuje!!!!!"
Wani irin hun fusata suka fasa a tare ikkunansu na jujjiga irin an kada musu gangin nan. A take kowa ya nufi dakinsa na Bamboo suna kwada kiran sunan babban gunkinsu suka shiga shirin yaki. Ba wai wuka ko bindugu suke tanada ba. A tsafinsu suka shiga sake tsimawa. Shiri suke karshen shiri dan gaske. Maza da mata, yara kuwa anata faman tsumasu da abubuwa.…. Babu wanda ya sake fitowa sai cikin dare, inda aka dakko gawar Banou dake tire jikin wani katon mashi aka kafe musu a tsakkiya. An yanke wasu sassan jikinta da ke matsayin hakkin uwa, su kuma suka rufu akan gawar suka dinga yagar namanta sunaci da ihu kamar wasu kiyashi sun samu nama, suna kwala kiran sunayen gumakansu da dodanni Jejin har wani girgiza yake saboda tashin sautin muryiyinsu…..
(😱😱🏃♀️🏃♀️🏃♀️)
Washe gari an tashi masarautar a rincabe da tashin hankali kala-kala matuka. Dan haka kawai aka samu gawawwakin hadimai da Ghazi da jami'an taro sama da hamsin an musu kisan gilla a daren jiya. Ga Iffah tun fitar aljanun nan jiya da ga jikinta barci kawai take, lokacin salla ne kawai idan yayi take tashi da kyar tayita. Tana idarwa kuma zata sake komawa ta kwanta kamar wadda tasha wani abu ko batun abinci ma ba'ayi. Tashin duniya Tajwar Eshaan yayi amma taki tashi in har ba lokacin salla ne yayi ba. Ga a jiya da dare yaje ya duba Malikat Bushirat dake ta faman zabura da ihu sam batai barci ba itama jikin ya sake rikicewa. Hakama duk wanda ke zagaye da ita bai barci ba. Safiyar yau kuma kawai ta tashi da wasu irin manya-manyan kuraje masu radadin azabar zafi dana kaikayi. Kuka kawai take tana rokon a cire mata. Ga sunayen Zawjata-almilk da suka rasu sai lissafowa take daki-daki wai sunzo zasu kasheta, sun zo daukar fansa.
Gaba daya kowa ya kasa fahimtar komai da ga zantukanta, sai dai duk mai imani ya ganta sai ya ji tsoron ALLAH ya sake kamashi. Kusan a tare babban yayansu da Kaka da akaima kiran gaggawa cikin masarautar suka iso. An fara taruwa an ma gawawwakin wadanda aka rasa salla harda Tajwar Eshaan, bayan an kammala biznesu ne kuma aka rufu kan Malikat Bushirat da zuwa yanzu kurajen duk sun rure da ruwa. Duk wanda yay mata kaikayi ta sosa kuma azabace mai zaman kanta. Shiru kawai kaka yay yana kallonta, yayinda duk wanda ke cikin dakin dan yan uwanta duk sunzo kuka suke sosai. Babban yayansu da shima ke kallonta ya juyo yana duban kaka. Cike da girmamawar kasancewar ya fisa shekaru ya ce, "Baba wannan aikin jinnu ne kam tabbas. Amma miya hada Jinnu da Bushirat duk da dal an sanar min da dambarwar da ake fama da ita a gidan.
Ajiyar zuciya kawai kaka yayi kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya nisa a hankali da fadin, "Wannan al'amari ne kam da ya kamata muji a bakinta, dan babu rami babu abinda zai kawo rami kam. Ambaton sunayen wadanda suka mutu da fadin karsu kasheta da take babbar ayar tambayece a gareta Abni".
Babu wanda bai gamsu da zancen kaka ba a wajen, sai dai kuma hankalinsu ya tashi da jin abinda ya fada din. Dai-dai yana fiddo wani magani Tajwar Eshaan ya shigo dakin rike da hanun Iffah da farkawar ta kenan ta zabura. Riketa yay amma ta rokesa ya barta sashen Ammie zataje. Shima bai jima da baro sashen ba, dan tafiyarsa babu jimawa su kaka suka shiga. Zaunar da ita yayi sannan shima ya kai zaune, take aka shiga mata sannu sai dai babu wanda ta amsawa. Kaka da babban wan su Malikat Bushirat din suka sake mika gaisuwa ga Shahan-shan dan sun gaisa tun shigowarsu masarautar. Da ga haka Kaka ya bada maganin da ya fiddo yace amata hayaki da shi. Cikin sauri suka amsa aka zuba a burner da aketa bulama turaren wuta saboda kurajen Malikat Bushirat din duk wanda ya fashe wari yake yi kamar an tono rubabben nama a cikin kasa. Wani irin fisge-fisge ta dingayi da hun da ya saka Tajwar Eshaan lumshe idanu kawai idanunsa sun kada jazur abin tausayi, shi Iffah ta tsurama ido, ji take da'ace tanada damar sashi ya bar masarautar nan a yau data sakashi, dan sam bata son ai wannan tone-tonen a gabansa. Amma yaya ta iya, bazai yuwu ace a wannan dambarwar babu shugaban wanna kasar gaba daya a cikinta ba. Malikat Bushirat ta jima tana fisge-fisge gashi babu damar taba ta saboda kurajen jikinta itama in ta taba radadi take ji, dan kanta ta lafa bayan ta gama jigata. Yanda ta nutsu yasa kowa tunanin ma Kota mutu ne. A razane Jasrah ta shiga kiran sunanta tana kuka, sai da Kaka yace ta kwantar da hankalinta tanada ranta, turaren zai rage mata radadin kurajenne matuka. llai kuwa sai gashi ta bude ido. Gaba dayansu tabi da kallo daki-daki, yayinda wasu keta tofa mata addu'oi kamar yanda yayanta ya basu umarni tun dazun. Wasu. hawayene masu radadi suka shiga zaryar zubo mata lokacin da idanunta ke sauka akan Tajwar Eshaan da Iffah. Ta jima tana kallon su, sai kuma ta sake fashewa da kuka.
Yayanta ne ya katseta da fadin, "Sai hakuri Bushirat, kuka baya daya da ga cikin mafita, ki daure ki sanar mana abinda ke faruwa domin musan makamar rikewa wajen yimiki magani. Shin garin aya wadan nan abubuwan masu alaka da aljanu ke zagaye da ke? Minene kuka sani ke da Zawjata-almilk da mu bamu sani ba? Mi kuke boye mana da Jasrah har taji kuna sa'insa a shekaran jiya?".
Idanu Tajwar Eshaan ya bude da sauri ya zubama Iffah idanunsa da suka kada jazur, amma ita sam taki kallonsa ga fuskarta kicin-kicin kamar yanda tashin take, Malikat Bushirat kam kuka ta sake fashewa da shi. Kafin a hankali ta motsa lips dinta wajen fadin, "Ni na jama kaina Akhi. Ni na siyama kaina komai. Komai kuma ya farane a dalilin HAIHUWA. a dalilin neman haihuwa da tsananin bukatar samuwarta. Buri da kwadayin gani da son haihuwar magaji shine silar labarin zamana a wanna masarautar da ma duk abinda na aikata a tsahon shekaru arba'in da a yau nake girbar abinda na shuka tun daga nan duniya........
🤔Tofa UBANGIJI gagara misali, Nama rasa abin cewa.
DAUDAR GORA
Book2
85
."Duk wanda ya sanni tun a kuruciya yasan ni yarinya ce mai yawn kirinki, nayi rashinji matuka, dan a fada biyar da za'ai dani cikin yara to da wahala ka samu daya a ciki da nake da gaskiya. Tun ina karamata na kasance mutum mai son gain kowa ya zama a karkashin ikona. Hakan yasa ban yarda da abota da wanda muke shekaru daya ba ko ko sukafi gidanmu arziki. Duk kawayena na girmesu, na kuma fisu wayo, gidanmu kuma yafi nasu komai. Hakan yasa dole sukemun biyayya da bin abinda nake so koda ace su basa son sa. Mahaifiyarmu na yawan mun fada akan wannan halayyar, hakama mahaifinmu. Nakan nuna naji na dan wani lokaci amma da kura ta lafa sai na koma gidan jiya. A haka na taso da wannan rayuwar har girma. Kowa yasan Bushirat boss ce a cikin kawaye, idan kuma kana son ka zauna lafiya tilas ne kamun biyayya. Gidanmu gidane na manyan mutane, masu ilimi kuma Alhamdullah munada dukiya. Ina alfahari da hakan, amma kuma inada buri na kai da kai. Kasancewata kyakykyawa nayi samari kala-kala, duk da dokar mahaifinmu shike zabama kowace yarinya a gidan mu miji, a nawa bangaren babu wannan ra'ayin. Sai dai na shanye ban taba sanarma kowa ba. Duk wanda zai zo gurina sai nayi duk yanda zanyi na bibiyi nasabarsa da nauyin aljihunsa, idan ka kasance baka da ko sisi zan tattaraka na watsar, tare da kashedi mai girma na ka fita a hanyata. Wasu sukan barni cikin sauki, wasu ko saina yi jan ido kona hada musu tuggu a wajen yayuna sun kore su. A haka na kammala karatuna na boko, wanda na taso naga anayi a gidanmu kam shima na samu gwargwadon iko wat ilimin addini. Sai dai sam bana maida hankali garesa, dan ni salla ma sai mahifiyarmu tamun jan ido. Da girmana da hankalina nasha daukar azumi na karya batare da an sani ba, kawai dan inajin wata kaina sama can. A haka wata rana naji Akhi kazo ma da baba batun wai Miran Haysam mai jiran gadon karagar mulkin Shahan-shan ya baka zabin nema masa matar aure. Kai kuma kayi tunanin dubawa a cikin yarn gidanmu amma har yanzu baka gama yanke hukunci tsakanin ni da Hubba ba. Abinda ya girgizani shine, jin Abie kai tsaye ya furta ("Uhm-uhm Muhammad, ajiye maganar Bushirat gefe, bata jin magana, sakata a babban gida irin wannan zai iya zubar mana da kimar mu da nuna gazawar tarbiyyar da muka baku. Yarinyace mai kaudi da hange, ina tsoron al'amarinta. Akance a cikin yaya an fidda maka zakka, to tabbas Bushirat ni itace zakkata. Ka bashi Hubba kawai zamuyi alfaharin da ita") wannan bayani na Abbie ya tayarmu da hankali matuka. Dan ga koshi ga kwanan yunwa ne. Zama nai naita nazarin mafita, dan har wata zuciyar na bani shawarar kashe Hubba dan itace kawai matsalata.Naki karbar wannan shawarar, dan ko yaya ina matukar kaunar yan uwana, Haka na cigaba da saka ido a duk motsinka da na Abbie, sai dai shiru bakayi maganar ga Hubba ba balle iyayenmu mata. Dan duk da mahaifiyarmu ta rasu wajen haihuwar Jasrah bamu taba kukan rashin uwa ba ga matan babanmu, sun rikemu hannu biyu tamkar sune suka haifemu. A cikin dogon nazari dana bama kaina kwana biyu a samo mafita. Ranar na yini cikin farin ciki sosai dan inaji a raina na gama zama matar Shahan-shan. ALLAH kuwa ya yarjemin, dan a randa na gama yanke wanna shawara a bibiyar Akhi da nakeyi da Abbie na samu jin Akhi zai tura sako ga Miran Haysam ibn Abdul-majeed Aliy Qutb na zabin matar da ya nema.Tuni na garzaya na rubuta wasuka mai nutsuwa tare da saka hotunana a ciki da dama na tanada. Dakin Akhi na lallaba batare da sanin kowa ba, nai sa'a kuwa yana wajen karatu dan haka a shiga bincike dakinsa. Na samu nasarar gain hotunan Hubba da ya shirya tura masa cikin jin dadì na kwashesu na ajiye nawa da wasikar nan na sake sabon manne envelope din. Gudun a yanka ta tashi na kone hotunan Hubba a cikin toilet batare da sanin kowa ba…. Kamar yanda Akhi ya fada ya aika sakon Miran Haysam batare da sanin na canja hotuna ba. Kwana biyar tsakani sai ga masu neman aure sunzo. Hankalina ya tashi naita kaikawo da neman hanyar da zanji yaya akai amma ban samu ba. Dole na hakura har bakin suka tafi Abbie da Akhi suka shigo gidan. Cikin muryar damuwa najiyo Abbie na sanarma Ummu cewar maganar da sukayice ta taso, sai dai sabanin Hubba da su suka zaba shi yanzu ya aiko cewar Bushirat, harma sun rasa a ina ya sanni. Kokwanton da suka shiga yasa Akhi tashi da kansa zuwa masarauta dan tabbatar wa. Amma magana daya ce dai Bushirat ya zaba. Babu alamar damuwa akan fuskar Ummu tace ai duk kai da kaya mallakar wuyane ALLAH yasa haka shine mafi alkairi, dan itama dai batai magana bane kawai amma abin na damunta. Kar ace dan Hubba yarta ce aka tsallakeni aka bata alhalin nice babba. Oho ko dar banji da kalamanta ba, ni dai tunda burina ya cika damuwa ta kare. An shiga shirye-shiryen biki, yayinda niko keta nokewa kamar bana so dan harda kukana. Sai gashi su Abbie sun zubda makaman su sun koma lallashina. Da wanna salon nai amfani na cinye wasan akan bikina cikin kwanciyar hankali kowa na lallabani. An kawoni masarautar ruman masarauta mai abubuwan kawa da na birgewa. Duk da na tashi a gidanmu akwai kudi sai naga ashe muma yayan malam Shehu ne dukiya na'a inda take. Abu na farko da bai munba shine dole na zauna a kasan ikon Malikat Haseenat mai amsa sunan mahaifiya ga mijina, sai dai kuma babu yanda zanyi dan ta hakanne kawai zan samu yanda nake so. Na hakura na mika wuya anan dan koba komai tana nunamin kauna babu bambanci da yayanta. Abu na biyu shine Ashwaq a matsayin uwargidana wadda kowa ke jingina zamanta Malikat. Na shiga damuwa matuka a kanta tare da neman hanyoyin dakile al'amarin ta. Ban gama da itab ba aka auro Danish-Ara. Wannan shine mataki na farko da ya hada alakata da UWA. Dan tun sanda naji labarinta da dambarwar dake faruwa tsakaninta da Mammah a daura dammarar neman kusanci da ita. Nako sami nasara ta hanyar amintaccen hadimin Haysam, bayan na shaka masa makudan kudade amma ya nunamin har abada bazai ci amanar shugabansa ba, raina ya baci dan haka na koma barazana akan iyalansa, harma na aikata masa a aikace ta hanyar sakawa matarsa ta kawo min diyarsu daya da suka haifa sashena. Na tabbatar masa zan kasheta wanna shine dalilin amincemin badan yaso ba ya hadani da uwa. Na razana a ganin farko dana mata, dan mutumce mummunar gaske, da zaka iya rantsewa badaga yankin wanna kasa ta fito ba koma na dake zuciyata. A ranar batako kulani ba, hasalima korani tai wai ban shirya ba. Naji zafi amma na daure harda dukawa kasa ina bata hakuri akan laifin da ban san nayi ba. Bata dai kulanin ba haka na taso na taho. Na shiga damuwa dan tun daga wanna ranar bata sake yarda mun haduba har tsawon wata uku. A haduwa ta biyu ma dai bata kulanin ba sai da ta mula dan kanta sannan ta dubeni a kaskance da fadin, "Kije ki daina sallar la'asar dan kin shirya kasancewa da Uwa mai share kukan masu kuka". Na mata godiya na taso. Banyi wani tunani ba na fara bin dokarta har tsawon watanni uku. Kawai wata rana sai gata da dare ayam ta bullomin ta bango. Hankalina ya tashi na tsorata amma tsawar data mun ta sani nutsuwa. Cikin jan tsaki ta furta a haka zaki iya zama tare da uwa kina matsoraciya, Sosai na dake zuciyata wajen bata amsar ni ba matsoraciya bace. Ta sake maimaita min nima na maimaita mata nawa. Munyi haka har sau uku kafin ta kyalkyale da dariya da fadin, (Ke abokiyar tafiya ce. Mike tafe dake wajen uwa?). Cikin matukar farin ciki na qyara zama, na shiga zayyano mata haihuwa nake so, dan ina son zama Malikat bawai Zawjata-almilk ko Ameera kawai ba. Ni wannan matsayin duk yamin kankanta. dariya sosai ta shiga babbagawa har sai da na koa dan haushi amma dai na hakura na shanye. (Lallai ke abokiyar tafiya ce). Ta fada tana nunani har lokacin fuskarta da sauran daiyar. Murmushi nai mata cike da jin dad. Ta cigaba da fadin, (Nice da kaina na hana Haysam haihuwa saboda abinda uwarsa ke mun, idan tana takama ita Malikat ce dan ta haifi Miran mai jiran gado na shirya tabbatar mata komai a gidan nan sai da karfin ikona yake tabbata). Hakuri na dinga bata nidai, dan babban burina kawai bukatata ta biya nidai. Cikin tabe baki ta furta, (Ai kin wanke komai yar gari, indai zaki iya bin sharadinmu ki dauka kece Malikat a wannan karnin). Babu wani tunani nace na amince da duk wani sharadin ta tunma kan ta fada min su. Nan ma dariya tayi sosai kafin ta ajiye min wata takarda da koko mai dauke da jini wai a saka hannu da wannan jinin, itama zata saka wannan itace yarjejeniyar mu ta farko, Banji ko wani dar ba na saka ta saka. Ta bani daya ta dauki daya tana fadin, (Daga yau sunanki a wajenmu shine *_Ta-kurya_" ta kurya sa maza kurya kenan). Yar dariya nai ta farin ciki itama tana tayani. Ta wuce a ranar batace dani komai ba acewarta sai zama na biyu. Na matukar nustuwa a sati na uku da babu ita babu labarinta, dan haka na shiga bulayin nema. Harma a fiddla rai ranar kawai sai gata ayam ta kawo min ziyarar dare kamar wancan lokacin. Kafin nace komai ta tabbatar min doka ta biyu bayan suna dolene a duk sanda ta bayyana a gareni zansa gwiwuna kasa dan girmamawa a gareta, sunan da zan dinga kiranta da shi shine uwa. Nan ma babu musu na amince mata. Nanma dariya tayi kafin ta ajiye min kullin garin magani guda biyu. (Wannan sune maganin matsalarki Ta-kurya, daya zaki sha daya ki shayar da Miran Haysam. Ina mai tabbatar miki kafin watan ya mutu zaki samu ciki) na matukar kasancewa a farin ciki, sai kuma nai sansarakwai da ga baya na jeho mata tambayar to amma idan ya kasance wata a cikinsu nada ciki fa ko kuma muka samu cikin tare na haifi mace ita namiji?…✍️
DAUDAR GORA
Book2
86
-."Anan ma dai tayi dariya da fadin (Ke ta dabance ta-kurya, sannan kanki na kawo wuta fiye da yanda nake bukata). Naji dadin yabonta harda godiya ta. Wasu magungunan ta sake bani, ta tabbatar min nai duk kokarin da ya dace na shayar da Ashwaq da Danish-Ara. Na mata godiya nan ma ta sake bace mun. Na shayar dasu maganin su duka uku nima kuma na sha wanda ta umarceni, sai dai kuma washe garin da Ashwaq tasha nata akawayi gari tayi barin cikin da ni ban taba sanin da shi ba. Ranar nayi farin ciki sosai, a wani gefen kuma ina mamakin toda miye na boyewar da tayi? A nufinta da karmu taba sani sai ranar haihuwa kenan? Lallai kasancewata da uwa alkairine. Abu mafi kara sakankancewa da uwa shine bayyanar ciki a jikina kafin cikar wata gudan data fada. Nayi farin ciki nayi farin ciki, duk wani masoyina ma yayi farin ciki. Itama kanta uwa tazo ta tayani farin ciki tare da sake kawo min wasu magungunan dazan na amfani da su har na haihu. Tace kariyane ga abun cikina dani kaina. Dan suma su Ashwaq zasu iya kawoma cikin nawa hari. Na yarda da ita fiye da kowa da komai a duniya zuwa yanzu, dan haka babu wani dar a tare dani na amsa. Haka na cigaba da rainon ciki, tare da soyayyar da ban taba zato da tsammani da ga Haysam ba. Ashe haka yake tsananin so da kaunar haihuwa. Hakama mahaifiyarsa da yan uwansa su Ammarah kowa tattalin rayuwata yake yi, Masarautar ma gaba daya wani irin girmamawa akemun data kara sakamun kaina fadì da jin babu kamar uwa a tare dani a wannan duniyar. A haka watan haihuwa ya kama mun, kowa fatansa ALLAH ya saukeni lafiya, ni kuma babban fatana na haifi da namiji, dan inata fargabar tambayar uwa hakan, kar tacemun bata da tabbaci. A haka dai na wayi gari wata safiyar laraba ina nakuda a tsaitsaye, uwa ta gargadeni fadama kowa, dan haka naita dauriya sai Jasrah dake nane dani, idan taga ina murkususu taita kuka, idan ya lafamun ta sani gaba da tambaya naita dai lallabata. Har safiyar Alhamis babu haihuwa babu alamarta, ranar mana cinye wannan yinin a wannan wahalar babu wanda ya farga har dare, dan ko Ammarah dake tare dani naki barin ta sani. Sai zuwa dare da ya ke tafiya daren juma'a kenan ina tsaka da shan murkususu na sai ga uwa. Naji dadin zuwanta, dan koba komai ina saka ran taimakonta. Tako zomin da taimakon sai dai ta hanani, acewarta yau ne ranar da zata sanarmin sharudanta, idan na amince zata bani maganin da zan haihu lafiya kuma da namiji da zai zama magajin kujerar Shahan-shan, idan kuma na bijire zata barni tai tafiyarta babu kuma tabbacin zan rayu balle dan, idan kuma na rayu na haifi mace ta warware abinda taima su Ashwaq su sami ciki wata a cikinsu ta sami da namiji, dan dama dai tun farko ita ta hana Haysam haihuwa saboda abinda Mammah take mata. Cikin riko da magiya nace mata dan ALLAH ta bani, indai nice na amince, koma mi tazo da shi zan amsa. Sai da ta jadadada min sau uku nima na
amsa mata sau uku. Maganin ta bani nasha kadan ta karbe abunta sai ko na samu lafawar ciwon, harna samu damar zaman saurarenta. Ta ce da ni (Bushirat ke ce kika kawo kanki gareni ban gayyatoki ba, kika kuma zo min da bukatarki ta magance miki ita?) Kai na daga mata alamar hakane, taci gaba da fadin (Gadai abinda kike nema nan kin samu, da ga yau zuwa gobe sunanki ya koma *_MALIKAT BUSHIRAT ne, zaki samu girmamawa da ga kowa. Ada nayi alkawarin hana Haysam gadar sarautar kujerar Shahan-shan, dan in har bashi da magaji ko ubansu mutuwa yay bai isa hawa ba. Amma a yanzu saboda ke na janye komai, Zan hukunta Abdul-majeed da Haseena akan laifukansu su da zuri'arsu, amma ke kam kin tsira keda danki, zan baku gata zan maidaku yan lele) godiya na mata cike da jin dadi. Cigaba tai da fadin, (Sharadina na farko bayan kin haihu zan dauke mahaifarki gaba daya, dan wanna dan kwara daya ya isheki yakar kowa a masarautar nan, sannan haihuwarsa shi kadai a nufin shine kawai magajin wanna masarauta) na amince Uwa. Na bata amsa babu wani tunani ko kyakykyawan nazari. Murmushi
tayi tamun jin jina. Ta cigaba da fadin, (Sharadi na biyu bayan haihuwarsa zakiyi yankan bakaken shanu guda goma, rakuma mata da basu wuce shekara uku da haihuwa ba suma goma zaki soke. Sai bakaken karnuka) anan ne na dani diri-diri da jin karnuka, amma sai tai saurin fadin (Karki damu su wannan karnuna zaki yankasu domin kariyar duk wani cutarwa da wani zai kawoma danki ne, dan kina haihuwar magaji tofa babu mai zama haka kuma bayanki za'aita yunkurin gani ke da dan) hakane kuma uwa. Na gane mi kike nufi na amince. Na bata amsa cike da gamsuwa da bayanin ta. Nan ma tayi murmushi da cigaba da fadin (Zaki cigaba da wannan yanka ne duk bayan watanni shida, sannan zaki sadaukar da jinin macen hadima mai dauke da ciki karami bayan ya cika wata uku, idan ya kara wata wata ukun zaki sadaukar da hadimi mai sabon aure da basu wuce wata daya ba shima) nan ma nadan shiga rudani amma ta nunamin idan bana bukata zatai gaba, ai duniya babu abinda ake iya samu cikin sauki. Sannan kuma bawai tace na kashesu bane da kaina, nawa kawai shine bata sunansu, sauran aikin nata ne) nifa matsalata kawai shine a haifi magaji, na zama abar kwatance akan karfin iko fiye dana Malikat Haseenat dan haka na amince. Ta cigaba da fadin (Saradi na biyu lokacin da yake cika shekaru goma sha biyu a duniya zakiyi kokarin a hada aure tsakanin wani makaskancin talaka da wadda kukafi shakuwa a kannen Haysam idan an samu ciki aka samu kuma mai tambarin zuri'arsu a gado bayan kwana uku zamu amshe yarinyar, inma babu tambarin ma dai ahakan zamuyi, za kuma mu kauda Abdul-majeed a doron duniya Haysam ya gajesa. Haysam zaiyi mulki na tsahon shekarun girman danki, yana cika shekarun gadar mulki zaiyi murabus ya daurasa. A ranar nadin zamowarsa Shahan-shan za'a aura masa mata hudu, matan nan dukansu zasu zama sadaukarwarmu tare da Haysam, dan in har yana raye tofa zaki cigaba da zama yar kallo ne sai abinda Haseenat tace danki ma yayi zai yi.…..) Da sauri nace na amince, dan bazan taba iya cigaba da zama karkashin ikon wata ba bayan kuma dana ke mulki. Tayi murmushi a lokacin da fadin (Shiyyasa nake jinki kamar yar dana haifa a cikina ta-kurya. Zan saki ki zama mai nasara kuwa bisa nasarar kowa. Wannan yaro da zaki haifa zai cigaba da aure muna kauda matan har sai sun cika adadin da zasu zama ginshikin rike karagar mulkinsa. Da ga karshe zamu kawo masa matar aurensa da zata zama duk wani motsinta sai da umarninki ne, koda ta haifa masa magaji kece zaki cigaba da amsa suna MALIKAT. Dan hatta shi a karan kansa ko hukunci bazai iya zartarwa ga wani ba sai da umarninki. Ki kula ki nutsu kisa hankali a jikinki a duk aure-auren sa kada ya auri wata mai alaka da zuri'arsa, idan kuma har kikai hakan to komai ya lalace kenan, duk wahalarki ta tashi a banza, mu kuma bazamu taba amsar kuskure ba, in har kika
gagara cika wadan nan sharucidan namu zaki bamu
madadinsu ne da jinin abinda zaki haifa, dan shine diyyar kuskurenki. Kuma shine hukuncinki) hankalina ya matukar tashi dan duk duniya a yanzu babu abinda nafi so kamar abinda ke cikina din, a shiga rokonta da magagiya. Ta tabbatar min itafa saina kuskure mata ne zata aikata hakan, dan bijirewar Abdul- majeed ga ayyukanta bisa shishshigin matarsa yasa zatai masa hukunci da mutuwa da mutuwar dansa (Haysam) da ya fi so, zakuma ta tabbatarma Mammah ita ba komai bace a wanna masarautar shiyyasa ta hanyar yayan da take takama da su, dan haka Ammarah ce zata zama wadda za'"aima auren sati biyu ta haifi yar da muke bukata, dama ta kashe Miran Nayyar a cikin ruwan swimming pool na gidan, Waheeda kuwa dama bawani tanada zuciya mai kyau bane kanta kawal ta sani dan haka bata gabanta, Jin wanna kashe-kashen hukunci da zatai ga zuri'ar Mammah saboda abinda Sukai mata a bijirewa yasa na karajin tsoronta, dan haka na amince ga dukkanin shardanta. Ta bani magani nasha, tare da tabbatar min zata kaworin hadimar da zata kasance amintacciyata wajen gudanar da ayyukana. Dan dolene zan boye kaina tsahon rai batare da kowa yama taba kawowa kansa nice ta-kurya ba. Koda kuwa a cikin hadiran da zasu dingamun aiki ne matsayin ta-kurya, Bayan tafiyarta haihuwa ta tashi gadan-gadan, Alhamdullah na haifo yarona namiji mai kamanina dana Haysam. A hankali, abinda duk ta fada ya cigaba da tabbata, babu wata matar Haysam da ta kara koda kwatanta samun ciki, dan haka na kara sakankancewa da ita, duk kan umarninta na fara cikasu kamar yanda ta bada, kuma komai na tafiyamun babu wata damuwa har zuwa lokacin da aka dauke Eshaan daga gabana. Ta nuna bacin ranta, kamar yanda na nuna damuwata, sai dai duk wani kokarin mu babu wanda ya saurareni, da Mammah ce ma, itama daga baya ta bada goyon bayan dauke san. Duk da tafiyace ta wani shekaru naji zafinta, sai dai bana iya cika wata guda banje na dubeshi ba. Yawan zuwana yasa Abbu (Tajwar Abdul-majeed) yayi magana a lokacin, aka kuma sakamun dokar sai bayan shekara-shekara. Naci kuka a ranar amma uwa ta kwantar min da hankali akan daukar mataki da tabbatar min ba sai yana raye dokar zatai aiki ba.Lokaci yayi da Ammarah zatai aure. Da taimakon su Miran Jasim aka cika wanna aikin, bayan wucewar su Mammah Umrah. Anyi auren Ammarah an kuma samu cikar burin samun ciki. Bayan dawowarsu an kwashi rikicin da har yay sanadin kai Jasim kurkuku. Da ga baya dai komai ya lafa Ammarah ta haihu. Bayan haihuwarta abubuwa suka nema cabewa dalilin samo wani hatsabibin mutumn, sai dai duk da haka muni nasarar mallakar abinda ta haifa da kuma kauda Abbi (Shahan-shan Abdul-majeed) nafi kowa jin ciwo da shiga tashin hankalin abinda akaima Uwa a masarautar nan dan ranar ni nasan irin kukan da naci na tashin hankali. Kwatsam bayan na gama fidda rai da rasa uwa a wata raar da Haysam ke cika shekara uku da hawa karagar mulki sai ga uwa ta bayyana.Farin cikine ma da bazan iya musaltashi ba, itama har taitamun dariya, ta kuma nuna jin dadinta da yanda na damu da rashin ta, ashe tanada y an leken asiri da ke kai mata rahoton komai a shekarun nan da bata nan…✍️
DAUDAR GORA
Book2
87
…..……….Bayan dawowar uwa al'amuran mu sun cigaba da tafiya, dukan shardanta a cigaba da cikasu, dan dama ko bayan batanan ban fasa ba, dan ina tsoron abinda ta fada akan Saiful-malik ya tabbata. Dan wannan tsoron da son cimma buri ne suka jagoranceni har zuwa wannan lokaci. Ni naita zungurar Haysam akan yin murabus lokacin da Saiful- malik ke cika shekara talatin da uku a duniya, nayi hakanne kuma bisa umarnin uwa. A duk sanda nai maganar yakan yi murmushi ne kawai, amma baya cewa dani komai, Sai hakan ke cimun rai da tunanin baya son ya sauka ya daura Eshaan din ne. Ni kuma abinda nake hange adadin shekarun da Uwa ta tabbatar min zai rasa ransa a dalilin shayin da nake shayar da shi gabatowa suke, ta kuma tabbatar min infa ya mutu ba'a daura Saiful-malik a karagar mulki ba akwai rikici sosai, domin Haysam nada kanne, shekarunsu kuma sunfi zama shekarun hankali da yan kasa zasuyi jayayya da samun rabuwar kai akan magajinsa Eshaan. Na sake takura masa da tada hankalina akan hakan har takai wata rana ya furta min abinda ya girgizani. Ya ce (Bushirat basai kinyi gaggawa akan mutuwata ko rayuwata ba. Idan kaddarar mulkar kasar ruman na rubuce a littafin kaddarar Eshaan sai yayi ko ina raye ko bana raye, abinda na sani kawai ina matukar tausaya masa, ina tausaya masa yaki na cikin gida da waje. Yakin da zai masa matukar wahala musamman kasancewarki ke wa mahaifiya da kika zamto a cikin manyan makiyansa) rai bace nace ban gane ina cikin manyan makiyansa ba? Bai sake cemin komi ba, illa murmushi kawai da ya saba mun. Maganar ta zauna min a rai matuka, har ta kaini da fadama uwa. Itama naga alamar ta girgiza, dan haka take anan ta tabbatar min dole muyi motsin da Haysam fa zai bada mulkin nan sannan mu kaudashi, dan alamominsa na nuni da akwai abinda ya sani game da ni, idan kuma har mukai sakaci wahalarmu ta baya zata zama a banza. Babu wani damuwa a raina na bata goyon baya, dan saima tashin hankali da nakeji akan cewar Haysam yasan wani abu game da ni din, ina tsoron ya fadama mahaifinmu, dan wilhy zai iya tsireni ne kawai kasancewarsa mutum mai zafi da bin dokar addini. Haka akai, ta kawo abinda naita saka masa a madara yana sha har tunaninsa ya karkata a yin murabus, babu zato babu tsammani kawai ya dawo da Eshaan gida, ya kuma tabbatar da zai yi murabus ya daurasa a karagar mulkin Shahan-shan. Kalubalen dana so fuskanta shine Eshaan da kansa, dan yaso bijirewa da cewar shifa baya son mulkin nan, bai taba ma birgesa ba, yafi son rayuwar yanci, yayi abinda yake so a lokacin da yake so, a cikin tarin burukan rayuwarsa ma babu maganar mulki a ciki. Na tashi hankalina Uwa tace na kwantar, ta bani wani turare tace na basa kyauta, in har yay amfani da shi na kwana uku sai ya amince. Hakan ce kuwa ta kasance. dan satin bai shigeba sai gashi da cewar ya amince. Uwa ta kara shiga raina da jin bani da kamarta duk duniya, zata kuma iya sakani komai nayi amma banda sadaukar mata da Eshaan, dan shine abinda nafiso fiye da komai a duniya. Anyi nadin sabon Shahan- shan tare da shagalin bikin aurensa na mata hudu, ko sau daya bai tanka akan auren ba, baice bai son su ba bai kuma ce yana so ba. Ni kuma bam ma damu da tambayarsa ba tunda nasan makomarsu. Kamar yanda uwa ta fada Haysam ya shude, matan Eshaan ma daya bayan daya sun zama labari, an cigaba da auro masa was suma tarihinsu na shudewa, a haka har nazo gab da cikar burina na gama wannan sharadin. Rana tsaka, ina gab da cimma abinda na faro kwatsam yarinyar ta shigo rayuwata. Ba kai tsaye ta shigoba, dan bana jin ma ta sanni ita. Yaki ta shirya, ya ki domin yakar Eshaan saboda rasa yayunta biyu da suka shigo cikin aikina. Itama tanada tunani ne irin na sauran mutanen kasar ruman akan Saiful-malik ne ke halaka matansa. Wanna itace mafarin matsala, dan tunkan ta shigo ita nacema uwa ta kauda min ita, dan ina a gabar da zuciyata ta gama dakewa da bushewa zuwa yanzu, hatta hadiman dake mun ayyuka da sunyi kuskure mafita daya nake hangoma kaina shine kawai na kaudasu, idan na kaudasu matsalata ta kare kenan. Da nayi din sai inga ta kare kuma, dan haka nake kallon kashe duk wanda ya shiga gabana akan cikar burina kawai na kauda san Uwa ta tabbatar min babu kaddarar mutuwar yarinyar a wannan tsakanin, sai dai mu nemo wata hanyar, a cikin neman mafitar ne muka yanke zamowarta a daya da ga cikin matansa, domin a ganinmu idan ta matso gab da mu sai munfi cin nasara a kanta. Sai dai kuma al'amarin bai kasance yanda mukai hangesa ba, dan tunda ta shigo rayuwar gidan komai ya daina yiwuwa a cin sauki. Labarin farko ya canja zuwa wanda bashi muka tsara ba. Dan hatta madarar farko da nake shayar da duk Zawjata-almilk ita kin sha tai, alkyabba da turaren da nake badawa a musu wanka da shi a sako musu tun daga gidansu shima basu akai mata ba, ban hakuraba na bibiyeta da su nan ma taki yarda tai amfani da shi, duk ta inda muka bullo sai ta waske, da ga karshe ma wata rigar da mu bamu san ta ina ta fitoba ce ta sanya, daga haka ta koma sashen Mammah da zama, ita kuma ta kaita sashen Saiful-malik batare da shawarar mu ba bayan mun yanke a yanda zamu mata rakkiya zuwa can. Dan saboda na rabota da sashen Mamma da uwa bata iya zuwa yasa na bada shawarar maidata sashen Saiful-malik ta mana bincike, amma sai Mammah ta canja shirin namu gaba daya. Wannan abu ya konamin rai matuka, ya kuma zafi zuciyata na kasance a bakin ciki. Mairakon nasara komai sai sake tabarbarewa yake, da kyar muka samu cikon ayyukan mu akan Zawjata-almilk data tarar, Itako dai ta kasa tabuwa a garemu a duk ta inda muka bullo. Tun ana yakin sunkuru har komai ya fito fili da fitar da ban san mafari ba da ga gareta, yakin ya koma na kasanni na sanka......" ta rushe da kuka mai karfi. Sai da tayi mai isarta babu wanda yace mata ko kanzil sannan ta cigaba da fadin, "Babban tashin hankali na a yanzu da jagorantar dukkan karfin halin iya maida martanina ga uwa a wannan gabar da komai na tabbatar da ya lalace shine rasa Saiful-malik, ta sake tabbatar min sai sun amshi jininsa matsayin diyyar kin cika shardansu, bana son na rasashi, shine kadai ya kuka ya sarketa ta kasa cigaba. Jasrah ma kuka take iya iyawa, sauran yan uwanta kam tagumi duk sukayi kawai. Hankalin Iffah gaba daya akan Tajwar Eshaan yake, dan tunda ya dukar da kansa da kamo hanunta ya rumtse a cikin nasa har yanzu bai ko yi wani motsin kirki ba, hannun nata kuma na rumtse a nasan duk da azabar da takeji saboda yanda yake matse a cikin nasan haka ta cigaba da daurewa tana mai ambaton addu'oi da duk sukazo bakinta. Fatanta ALLAH ya saukaka masa zuciyarsa, ya bashi juriyar dauka.
Gyaran muryar kaka ne ya katse tunanin kowa. Ya nisa a hankali tare da gyara zamansa. "Lallai kinyi kuskure, kin kuma shiga rigar yaudara irin ta wadda bokaye kanyima bayin ALLAH saboda son zukatanmu da burin gina DUNIYA mai yankewa. Wannan mushirika tai tasiri da tasirin gurbataccen burinki ne da niyyarki ta shigowa wannan gida. Amma karya take bata da alaka da samuwar cikin Shugabamu da kikayi, dan dama sanda ta baki maganin kina tare da shigar cikinsa…....
Babu wanda bai zabura ba, hatta da Malikat Bushirat din kanta. Tajwar Eshaan kam sake kankame hanun Iffah yay cikin nasa tsam-tsam fiye da farko.
Kai Kaka ya jinjina musu, "Wanna maganar da nake fada muku haka take, dama akwai cikin. Koda ace babu shi ta bada taimakon magani shi wannan maganin sai dai ya magance matsalar wani ciwo da ya zama sanadin jinkirta samuwar haihuwar bawai ya samar da dan ba. To sai a wannan labarin ma akwai samuwar cikin ma kafin ta shigo cikinsa. Rashin samuwar haihuwa jarabawace ga duk wanda baiyiba, jarabawa kuma mai ciwon gaske da radadi a zuciya, bazaka fahimci haka ba sai in ka kasance daya daga ciki. Ya halatta ka nema magani da ga kowace irin cuta a rayuwa. Sai dai fa akwai matakan da ya kamata mumini yabi wajen neman magani kowane irine balle ma akan neman haihuwa. A duk lokacin da muka rasa haihuwa idanunmu kan rufe da fadi tashin neman mafita ta kowanne yanayi. Burinmu shine kawai mu haihun. Sam babu tunanin maybe ita haihuwar ba alkairi bace a tare damu, a ganinmu kawai mun rasa shine mu nemota ta kowace irin hanya. Duk da abinda UBANGIJI ya baka ya fika sanin dalilin baka shi, idan kuma ya hanaka ya fika sanin dalilin hanaka da yayi. A rayuwa babu abinda yafi karfin addu'a, sadaka, yarda da kaddara mai kyau ko sabaninta. Idan kuma har ta kama saika nema maganin ka zama sani ba a wata gabar. A neman haihuwa wajen bokaye da malaman tsibbu zakaci karo da abu hudu in har ka samu daya da kaje nema. Na farko rasa imaninka da cire yardarka ga UBANGIJI mai badawa da hanawa, dan zaka cigaba da ji a ranka shifa wanna din nan ne ya baka wannan haihuwar (Wa'iyazubillah). Na biyu zata iya yiwuwa dan aljani ma aka samar a cikin naka batare da kasan hakan ba kai tunda kai a kai kanka ai. Na uku wasu matan ko da saninsu, ko bada saninsu ba zata iya yuwuwa bokan yay mata cikin a zahirance ko kuma ta hanyar tsafe-tsafen sa batare da ita tasan hakan ta kasance ba domin shi tsafi gaskiyar mai shine. Idan kuma ALLAH yasa dama ana a kan gabar da ALLAH ya iyakance ne dama haihuwar
tata ta kusanto gareta batare data sani ba sai a samu dai-daito da bada maganin nasa haihuwar ta samu amma zuciyarta na tabbatar mata ta sametane daga wannan bokan ko malamin tsubbun……..✍️
Mu hadu in ALLAH ya kaimu Please🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴 hannuna ya gaji😂
DAUDAR GORA
Book2
88
."Kamar dai yanda ta kasance a gareki. Ita tana da buri akan wannan masarautar, sai akai sa'a ke ma kinada naki burin da kika kai kanki gareta. Ita kuma sai tai amfani da haka kika zame mata yar aiken isar da sakonta ta yanda babu wanda zai fahimci ruhinta ya sake dawowa wanna masarauta balle ma a zargeta akan dukkan abubuwan da suka faru har a maida hankali. Wanna labarin naki yasa na fahimci maganar mahaifina da ya ce, duk saninka kankanuwar samarwace da ga taskar ALLAH da bata yankewa. Sannan haihuwar ita Fhareedah wani mashine da ga UBANGIJI da zai zama sanadin tarwatsa al'amuranku batare da kun fargaba, shiyyasa ya boyeta a cikin sirrinsa har zuwa ranar da
zata dawo gareku cikin karfin ikonsa da zai tabbatar muku babu wani karfi da ke saman nashi. Shirka babbar faduwa ce, ginshikine na gina kaskanci a duniyar bawa dama lahirarsa. A duk lokacin da ka dauki cewar wanin ALLAH a iya baka koda kariyane da ga wani abin tsoratarwa to akwai babbar matsala,dan kuwa shi wanna mushirikin zai bika mataki-mataki ne wajen kaika fie da inda bakai hange ko tsammanin zuwa ba. Kamar dai ke din nan. A matakin farko bukatar haihuwa kikaje mata da shi, sai ta ce miki kada kiyi sallar la'asar. Tayi hakane saboda kasancewarki mai bautar ALLAH, sannan kina jingine da wasu muminai da zasu iya saurin fargar dake kuskurenki kuma ki gyara. Amma data kafa miki wannan tarkon sai ta busar miki da zuciya ta yanda duk yanda za'a kiraki bazakiji wannan kiran ba, ba kuma zaki saurari mai kiran ba koda ace kin jisa. Hanaki bautama UBANGIJI itace allurar farko mai tsananin dafin data sakaki shagaltuwar da bijire mata zai miki wahala koda ace kina so. Shiyyasa maganin ayima kar a fara, tun farko ma yi kokarin yin addu'a da yakar kanka daga son zuciya ko tunanin nema daga wanin ALLAH. Miyasa musulunci ya mana gatan cewa mu tashi mu nemu na kammu? Saboda kare kammu da ga biyayya ga abinda zai iya cutar damu. Dan a mafi yawa ko nace rinjayen dan adam yana son a duk sanda ka nema daga garesa duk sanda wani abu ya taso da zaka iya masa to ya tuna maka wannan taimakon da yay maka wanda zai iya sakaka jin kunyar yimasa abun nan koda ace bai dace ba. Kamar dai cin hanci da rashawa. A duk lokacin da mai bada cin hanci ya mika ga mai karba zai iya aikata aiki komai muninsa koda ace zai iya cutarwa ga rayuwar mal karbar shi kansa ne ma. Dan haka maganin data baki a tun farko ma bashi da alaka da abinda kikaje neman. Ta baki shine domin cutar da abinda ke cikin ki data riga ta tabbatar da akwai. Sai dai ALLAH ya riga ya kaddara babu abinda zata iya yi sai ya zo duniya, dan haka ta tafi mataki na biyu wajen rabaki da mahaifarki gaba daya. Mataki na uku ta rabaki da mijinki, mataki na hudu tai amfani dake wajen gogama rayuwar danki bakin fentin da zai bakantashi ga al'ummar kasar sa da mulkinsa. Lokacin da ake ihun yay murabus badan Iffah ta shayar da shi wannan madarar mai dafin macizai ba da burinta a tsigesan, hakan yana cikin plans dinta da idan wanna baiyi tasiri ba zata tsallaka na gabansa. Da ace taci nasarar kun hada auren wadda taso ta haifi magajinsa da taci nasarar duka wasan. Dan sam wadda take burin ya aura bama mutum bace cikakkiya yar zuri'arsu ce aka raina a anan duk saboda zuwan wannan lokacin. Daga kuma sanda ta samu ciki burinta shine ta kasheki, shima ta kasheshi wanna jinjirin ya amsa suna magaji, da ga haka ta karbe mulkin ta karfin tuwo da ga wanna ahalin. UBANGIJI bai gitta rayuwar Iffah a cikin al'amurran ki da rayuwar danki ba sai dan shi tsarkakakkene mai tarin tsoron ALLAH da kiyaye dokokinsa. Ya gadar da shine da ga kyawawan halayyar mahaifinsa sabanin naki dabi' un. Addu'oin da al'umma ke masa na tasiri a tare da shi tare da yin dubi da tsarkakakkiyar zuciyar kakarsa da tai yaki da yakar mushirikai. Mutuwar mahaifinsa da kakansa tazo ne akan gaba bawai bisa karfin ikonta ba. Da ace ma tayi hakuri zasu musu, tabbas zasu mutu a dai-dai wanna gabar har su matan nasa. Amma a yanzu hakkin ruhinsu duk ya rataya a gareku ke da ita domin harda amincewarki akai komai ba tilastaki tai ba a aikace.Kaiconmu da irin wannan burin duniya, kaiconmu da irin wannan hangen da babu hango iyakar karewarsa, kaiconmu da zuciyar da ke jin hakkin wani ba komai bane komai Kankantarsa komai rashin muhimmancinsa, Wlhy duk
abinda akace maka ba naka bane sunansa ba nakan ba. Idan kuma harka taba da son zuciya ko izgili sai ka biyashi a ranar da babu kudi irin madadin a duniya. A ranar da cuniya ce zata taru, a ranar da ake biyan hakki da lada ko zunubi. Dan duk hakkin wanda ka taba zaka biyashi da ladanka, idan baka da lada za'a dibo zunubinsa a lafta maka. Shiyyasa mutane da yawa zasuje lahira da tarin lada a taskokinsu, amma yayin kammala musu hisabi sai su koma basu da korai sai tarin zunubai dan an biya duk wanda suka cima hakki da wanna ladan nasu. Haba yan uwa har wane aiki muka tara da har mukejin cin hakkin wani zai isa mu biyasa har mu sami rarar shigar aljanna da sauran. Wani ma har kaji yana izgilin shi hakkin wani ko ALLAH ya isa bata masa komal a jiki, why da tabon da zatai maka a rayuwarka gara ace a jikinka take tsirowa maybe kaji tsoron ALLAH da wuri ka sauke hakkin. Shi kuma wanda ma ya hadiye bai ce dakai komai ba yafi ban tashin hankali fiye da wanda zai furta maka maybe ka razana ka sauke. Wai miyasa bama tunanin cewar wanda muka cima hakkinsu sune masu nasara akan mu ne? Tabbas masu nasara a kammu, dan sun kasance masu ajiyewa a dauka a kuma biyasu a ranada ake farautar ayyukan cika mizani. Kawai akan son farantama was mu mu tauye kammu mu daga nasarar wasu. Wai a hakan dan wawanci murna mukeyi, farin ciki mukeyi mun karya wane, mun kaskantar da wane, mun maida wane baya, waya fada maka dariya ya kamata kayi ko kiyi?Wlhy kuka, kuka ya kamata ki fara tun kafin ganin anar nasarar mai wanna hakkin da taki faduwar,Wadan nan hakkokin da muke rainawa suke hauhawa
su gawurta su zama manyan abubuwan ruguza ayyukanmu. Kamar dai ita, ta fara ne tun a kuruciya, zalinci wancan, tirsasa wancan ana gain yarintace hakan ba komai bane amma sai abin ya cigaba da tasiri a rayuwarta har yay gawurtar da ayanzu ta fado kasan-kasan kafafun wadan da take gain ba komai ba, wanda take ganin murjesu ta taka ko cin hakkokinsu ba komai ba. Gadai shi taji dadin, tayi farin cikin, ta dauki kanta a mai nasarar, amma a karshe itace ta zama mara nasarar, mafi kaskanci.Mafiya masu cin hakki da ruguza rayuwar wasu zamu samu matasane masu tasowa, maybe batai aure ba ko baiyi aure ba, kokuma bata jima da yin auren ba,dan duk wanda, ko wanda ya kai shekaru arba'in a duniya ya zabi take hakkin wani babu babban wawa sama da shi. Amma su wadan nan masu tasowar gani suke abinda sukeyi ba korai bane, yanzu ma aka fara rayuwar. Waya gaya miki koya gaya maka ba komai bane ba. To ko kasa mutum ya gino ya tara kikazo wucewa ko kazo wucewa ka barbaza masa ai hakkine balle abinda ya killace koya nunama duniya abun nan mai muhimmanci ne a garesa koda ace kai baka ganin muhimmancin nasa. Kanada kananan shekaru kana ta daukar hakkin mutane da kake gain bamai muhimmanci ba kana tarawa yana hauhawa a mizanin aikinka yana rusaka, yana rusa rayuwar yayanka masu tasowa, yana rusa cigabanka na duniya dana lahira kai kana shirmen kana nasara akan mai hakkin. Kajifa toshewar basira, shi kana kara masa nasara ne fa, tunda dole-dole ka biyashi a inda babu kudi sai aiki inhar baka biyasa da kudin daya shardanta akan kayan nasa ba. Kamar dai ita a yau, komai yazo mata a gabar da bata da damar neman gafarar wadanda ta zalunta ta cutarma da rayuwa saboda nasararta da neman cikar burinta. Ta rasa a lokacin da su kuma suka samu, wata tayi amfani da ita dornin nasararta ta barta da katon nauyi bisa kai. Kaicon rayuwar da ba'a tuna mutuwa a cikinta. Kaicon rayuwar da ake ginata kamar bazata yanke ba. Kaicon rayuwar da ake daukar hakkin wani kamar ba hakki ba. Kaicon rayuwar da cikar buri ke jagorantar imani da tsoron ALLAH a zuciyar mai shi. Kaicon zuciyar dake bushewa da jin komai tayi dai-daine. Ya ALLAH ka karemu, ka kara tsaremu, ka tsarkake mu, ka kiyaye mu. Ka killace mu, ka karfafa mu, ka jagorance mu bisa tsoronka da tsoron shirka, da tsoron cin hakkin wani komai kankantarsa, ka kyautata neman mu da ga halak, ka karfafa ayyukanmu bisa umarninka da kiyaye saba maka badan halinmu ba. ALLAH ka shiryar da wanda suka kauce, idan ba masu shiryuwa bane UBANGIJINMU mun barka da su kafimu sanin miya dace da su. ALLAH ka rabamu da ruin duniya da kyale-kyalen cikinta. Ya rabbi ka saka DUNIYA a tafukan hannayenmu ka nisantata zama a cikin zukatanmu. Ya rabbi ka wajabta mana tsoronka, ka karfafa imaninmu. Ka yafe mana kura kuranmu, ka bamu ikon kyautatama duk wanda ka hada kaddarar zaman mu a tare ko mu'amularmu, Ya rabbi ka hana mugayen halayenmu cin nasara a kammu, kasa muci nasara akan mugayen halayenrnu da ayyukanmu".
A tare suka dinga amsawa da Amin kowa na sharar hawaye, yayinda Malikat Bushirat ke kuka mai tsananin gunji. Matuka takejin radadi a zuciyarta da azaba a cikin jikinta, So take ta kara cewa wani abu koda ga tilon danta ne da har yanzu bai dago kai a dubi kowa ba balle ita amma ta kasa hakan. Da ga karshema mikewa yay a hankali cikin tangacfin juwa hannunsa cikin na Iffah har yanzu batare daya kalla kowa ba balle cewa wani abu ya jata suka fice. Ta hanyar sirrin da suka fito ta can suka koma hankalin Iffah a tashe da yanda yake tangadì mai bada tabbacin akwai matsala….✍️
DAUDAR GORA
Book2
89
...... Suna shiga bedroom din sa ya wani irin rungumeta tsam-tsam a jikinta tamkar zai maidasu su zama abu guda. Yanda Iffah kejin gudun zuciyarsa da bugawarta hankalinta ya tashi matuka. Tayi yunkurin dagowa ta kallesa amma yaki bata koda kankanuwar dama. Sosai numfashinsa ya fara fisga, gashi ya ki sakinta balle ta bashi wani taimako, mutsu-mutsun kwatar kanta take amma ta kasa. Sai kawai ta fashe masa da kuka. Sakinta yay da sauri, sai dai bai yarda sun hada ido ba ya rabata ya wuce. Gaban window yaje ya tsaya kawai ya tsirama harabar masarautar ido. A gurin Iffah ta durkushe ta cigaba da kukanta. Tsahon mintuna goma suna a haka sautin kukanta kawai ke ratsa dakin, shiko yana a inda yake tsayen kamar gunkin da aka dasa domin tarihi. Mikewa tai itama jin jiri ya fara dibar idanunta, dan akwai yunwa tare da ita, rabonta da abinci tun jiya. A bakin gadon ta zauna jagwaf, ta dafe kanta tsahon minti daya kafin ta janye. Ciwo hannayenta ke mata sosai saboda matsar da suka sha a wajensa, har sun dan kumbura dan matsar bata wasa bace. Jin sun mata tsami babu dadi ta shiga murzasu a hankali ko zataji sassauci. Bata san sanda ya baro wajen window din ba, ganinsa kawai tai durkushe gabanta ya kamo hannun nata a cikin nashi. Kallo daya taima fuskarsa tai saurin dukar da kanta, dan idanunsa sun yi masifar firgitata. Sun yi wani irin kadawa jazur irin wanda bata taba gani ba,hakama fuskarsa gaba daya tayi jazur kuma babu alamar yayi kuka, kawai tsabar tashin hankaline ta sauya masa kamanni. Hannayen ya shiga murza mata a hankali, kafin tsahon lokaci kamar wanda aka fisgo furucin da ga halshensa ya ce, "I am sorry".
Da sauri ya dago ta dubesa, ganin yanda ya tsurama tafin hanunta idanunsa masu ban tsoro yasata jin hawaye sun sake cika mata ido. Dayan hanunta ta daura akan habarsa mai cike da lallausan bakin gashi ta dago, cikin dauriya da dakiya ta saka idanunta cikin nasa, muryarta na karkarwa ta furta, "Dan ALLAH kayi kuka koda kadanne Zakina. Kayi kuka! kayi kuka!! kayi kuka!! Zan shanye hawayen a cikina na adanasu cikin manyan SIRRIKANKA da ka bani ajiy....."
Kafin tama kai karshe sai ga hawaye sharrrrr da ga idanunsa kamar an bude fanfo, wani irin murmushi mai tsananin ciwo da kuna ya sakar mata hawayen na kara gudu. Da sauri ta tara hannayenta suka sauka a ciki, kallon tafin hannun nata da hawayen nasa ke sauka yayi, sai ya sake fashewa da kukan, hawayen na cigaba da sauka a cikin tafin hannun nata. Sai da suka taru sosai sannan tasa harshenta ta shiga lashe hawayen tana hadiye tare da fashewa da sabon kukan itama. Kansa ya daura a saman cinyarta yana zaune da ga kasan lallausan carpet din gaban gadon itako tana daga zaune a kan gadon, itama sai ta daura kan nata a kan nasa suka cigaba da kukan a haka zabban tausayi…
Bayan sallar azhar da ya kasa fita saboda zazzabin da ya rufesa mai zafin gaske itama ciwon ciki ya takurama Iffah na jin yunwa, abinka da ba ita kadai ba. Haka ya tashi cikin kakkarwar sanyi ya bata madara ta sha, tana sha ta amayar da ita, a hakan dai ya taimaka mata cikin karfin hali ta gyara jikinta, sake bata madarar yay tasha kadan, shima sai ta takura masa wai sai ya sha dan rabonsa da abincin kirki tun jiya. Kin sha yay ta sanya masa kuka, dole yasha rabin kofi ya kauda kansa, da ga haka suka dunkule waje daya kwance zafin jikinsa na matukar ratsata. Ganin zazzabin baida alamar sauka sai ma karuwar da yake yi yasa Iffah kiran Sayeed Fayzul-haq. Babu bata lokaci suka iso da Doctor Afif da ke matsayin amintaccen likitansa. Doctor Afif din kansa sai da hankalinsa ya tashi gain yanda jinin Shahan-shan din yay wata irin kololuwar hawa, ga bugun zuciyarsa har ya canja. Cikin sauri ya danna masa allurar barci mai matukar karfi dan in har aka cigaba da zama a hakan akwai babbar matsala kam. Da farko kin yarda ma yay ayi allurar sai da Iffah ta sanya masa kuka sannan ya kauda kansa kawai baice komai ba. Sai Sayeed Fayzul-haq ne yay ma Doctor din nuni da yayi aikinsa dan kauda kan nasa a nufin amincewa, Iffah dai na zaune ne kansa a saman cinyarta tanata faman sharar hawaye. Duk da karfin allurar ya jima baiyi barcin ba, dan sai da Iffahr ta hada da tofa masa addu'oi sannan aka dace barcin ya daukesa.
Haka ta cigaba da zama kansa a saman cinyarta har aka kira sallar magrib, kafafunta duk sunyi tsami,da kyar ta gyara masa kansa ya koma kan fillo, sannan ta mike ta gabatar da sallar magrib din. Alkur'ani ta dauka ta shiga raira karatu a nutse tana hawaye, bata ajiye ba har aka kira sallar isha'i nan ma ta gabatar. Ta jima tana addu'oi akan wadan nan al'amura da suka cure musu, tashinta babu jimawa Malikat Haseenat da Daneen Ammarah da Daneen Waheeda da Iftihal sukazo dubashi. Basu shigo ciki ba iyakarsu falo, Iftihal nata yan kalle-kalle dan wanna shine karo a farko a rayuwarta ma data shigo sashen nasa. Iffah na fitowa ta wani dukar da kai dan ita kam tsoranta takeji matuka yanzu. Cike da kauna da tausayi Malikat Haseenat ta rungumeta, kafin ta dagota da fadin, "Hafida-ti kema ai ba lafiyarce da ke ba ma, dan zazzabin ne a jikinki. Kin ma ci abinci. Idanun Iffah cike da hawaye ta girgiza kai da fadin, "Na koshi Jaddah".
"Bazai yiwu ba dan bake kadai bace. K Iftihal hadomin abinci mai sauki acan. Cikin rawar jiki Iftihal ta nufi dining room, har yanda tai din ya bama Daneen Waheeda haushi sai dai babu damar magana. Babu jimawa ta kawo abinci, Malikat Haseenat ta amsa da kanta ta na bama Iffah'r. Da kyar take amsa da taunawa kamar magani, batafi cokali hudu ba tace ta koshi. Lallabata Malikat Haseenat da Daneen Ammarah suka shiga yi, da kyar ta kara biyu, daga haka suka shiga lallashinta da nasihar ta kwantar da hankalinta, dan saita kwantar da hankalin natane shima zata taimaka masa ya kwantar da nasa. Ta gamsu da nasihar tasu, anan ma takejin Ummu sun wuce, Malikat Bushirat ma jikin nata ya sake rikicewa yanzu haka ga likitoci can sun kasa shiga su dubata dan kurajen jikinta nata cigaba da fashewa warin na kara karuwa. Batace komai ba illa hawaye da suka zubo mata sharr. Wanna ranar ita take guje mata, gashi tun kan aje ko' ina kuwa har tazo din. Basu wani jima a sashen ba suka tafi, haka ta koma dakin ta zauna ta saka Tajwar Eshaan gaba tana tofa masa addu'oi da fatan ALLAH ya sanya masa nutsuwa da Karfin zuciya akan al'amarin. Haka dai ta kasance bata wani samu isasshen barci ba, koda ya farka cikin dare da taimakonta ya samu yay salloli, ta debo masa abinci amma yaki ya ci, sai da ta fara masa kuka ya danci spoon biyu shima dole ta hakura ta kyalesa dan barcine bai gama sakinsa ba.Dan haka ya koma ya sake kwanciya……
Gabanin asuba wan irin ihuface-iface na tashin hankali ya farkar da ita, zumbur ta mike kamar wadda aka tsungula. hun yayi yawa matuka dan haka ta fita a razane, ALLAH ma yaso doguwar riga ce ta abaya a jikinta. Hadiman sashen Shahan-shan din duk wasu sunyi barci ma, sai jami'an tsaro dake kai kawo a ta waje da Ghazi. Sai dai duk an firgitasu ashe sune keta hun, Wani irin sarawa kan Iffah yayi, a take ta birkice alamar mutanen sun zo. Wani irin jan takobin dake a hannun masu tsaron kofar shiga falon farko na kasa Iffah tai da ga cikin kubenta ji kake wani zuuuuuu!! Sharbebiyar takobi ce mai tsananin walkiya da tada tsigar jiki, tuni tayi tsakkiyar masarautar ta wani irin karta takobin bisa kasa. Kamar yanda mafi yawan mutanen masarautar sukaji wanna tashin hankali haka sukaji karta takobin da Iffah tayi akan kasa da yin wani irin kara ji ta ce. Duk wanda ya shirya idan ya isa yazo gabanta. Saiko ga kusan mutum hudu sun bayyana gaban nata tsirara sai dan ganye a gaba suna wani irin huci da bulbulo da wutar tsafi ta baki, Juyi ta sake. yI, da wulwula takobin ta cake akan kasa, kafin tai wani irin zarota tai juyi bakinta na ambaton sunan ALLAH tamkar kyattawar ido sai ga kawunan shegun a kasa hudu reras. Zo kaga ihu, ga hadiman da duk suka farka saboda tsabar tashin hankalin firgitasu da wadan nan mutane sukayi, wanda sune a
daren jiya suka shigo sukai musu kisan gilla dama. Ba kowa bane kuwa face a cikin zuri 'ar su uwa. Tuni fa masarautar ta kara rikicewa, wanda ma bai farka ba sunata farkawa. Can sai ga Jasrah ta fito cikin kuka da kururuwar an dauke Malikat Bushirat. Ba kowa yasan mike faruwa akan Malikat Bushirat din ba sai su shakikanta, duk da dai dazun anga duk ahalinta sunzo gidan, sannan Malikat Haseenat ta fito ranta a bace da sashen ita da Daneen Ammarah. Dama Daneen Waheeda bataje ba dazun din dan haka maganar dai har yanzu bata fita akan tsiyatakun da Malikat Bushirat din ta fada ta aikata da bakinta ba. Kowa dai nata hasashe da son bin kwakwkwafin al'amarin. Masarautar ta rude gaba daya, ALLAH dai yasa itama Daneen Ammarah da nata kwankwaman a ka da kyar ta rike Iffah. Barci dai a wannan dare yara kanana ne da basu san komai ba a wannan masarauta suka yisa. Dan tuni shima Tajwar Eshaan ya farka. Tun a daren Iffah tai kiran kaka a waya, asubar fari kam a cikin masarautar ta masa. Ana idar da sallar asuba aka shiga meeting na gaggawa. Kaka, Iffah, sai manyan masu fada ajin masarautar irin su Sayeed Fayzul-haq da sauransu........✍️
DAUDAR GORA
Book2
90
.....Kaka ne ya fara magana rai bace. "Wadan nan mutanen yaki suka shirya dan gaske bawai wasan yara ba. Daren shekaran jiya sun zo sunyi kisan gilla jiya ma sun dawo harda daukar Malikat. Wadan nan da Fhareedatu ta sarema kawuna jiya bawai su kadai bane, guduwa sauran sukayi. Dolene a nemo mafita dan a dawowa ta uku zasu sake sabon shiri ne. Shakaran jiya sun kashe kusan mutane hamsin, yau ga kusan mutum tara fa, dan ma yau ALLAH ya fargar da da sai sun gama illarsu sun tafi kamar ta shekaran jiyan sannan za'a sani".
Sayeed Hifzur-rahaman ya ce, "Tabbas akwai matsala kam, dan da gaske suke ba wasa ba. Sai dai fa matsalar idan munce wani yunkuri zamuyi ta ina zamu kama ne?. Ku dubesu kamar ba daga jinsin mutane suke ba, ko kyawun kallo basu da. Ga su da karfin tsafin mai ban tashin hankali.....
'"Babu wanda yafi karfin UBANGIJI ai. Dan haka zamu tunkaresu gaba-da-gaba". Iffah ta fada cikin bacin rai. Duk kallon toro sukai mata, sai dai kafin wani yace komai da ga bayansu aka amsa da "Tabbas mune zamu tunkaresu kamar yanda ta fada".
A razane duk suka juya suna kallonsa. Shi din ne dai ba wani ba. Shahan-shan Eshaan Ibn Haysam Abdul- majeed Aliy Qutb. A kallo daya idan kai masa bazaka sake marmarin karawa ba dan firgicin a yanda yake yau. Cikakken GWARZON BARDE abin tsoratarwa ga duk wanda zai iya kallonsa. Karasa takowa yay cikin takun nan nasa daddaya da yau ya kara zama cikin izzar damuwa da bacin rai. Ga ido ya toshe da bakin gilashi alamar yau babu koda digon sassauci. Dole kowa ya mike cike da girmamawa a garesa.Maimakon zama tsaye yay kikam idonsa akan Iffah, cikin bada umarni ya ce, "Cigaba da bayanin ki".
Kai ta jinjina masa cikin girmamawa sannan ta dubi
kaka. Shima kai ya jinjina mata dan haka ta sake fuskantarsu. "Tunkararsu itace babbar mafitarmu kamar yanda Kaka ya fada, dan tsafinsu da wani karfin maita babu abinda zai mana da karfin tasirin UBANGIJI. Dan dole ne mu shafe babinsu gaba daya in har muna son cigaba da rayuwa cikin salama.Mataki na farko a yanzu shine Taswirar jejin da ake saka ran samunsu, sannan hada manyan baradan mayaka da ga yanzu zuwa awa biyar kacal da muke da ita….
'"Amma ranki ya dade ai bamu san jejin da za' a iya riskarsu ba. "Sayeed Aashiq-Muhammad ya fada cike da girmamawa ga Iffah'r".
Kaka ne ya amshe da fadin, "Wannan bazai zama mai wahalarwa ba, dan dukkanin abinda ke zagaye da wanna kasa muna dasu a rubuce a kundin litattafan tarihinmu. Za'a iya bincikawa tunda kabilar tasau dadaddiyar kabila ce".
Itama Iffah kanta ta jinjina da fadin hakanne kam, dan nima a karance-karancen tarihi da nai a kwanaki akwai wani littafi daya tabo makamancin dabi unsu. Dan haka muna bukatar Sayeed Aynul-Hassan shima anan".
Ba'a wani bata lokaci ba wajen kiransa, sai ko gashi da tarin littafai da wasu manyan takardun taswura da ke kunshe da gaba daya kasar ta ruman da dazukanta. Kaka ya bada umarnin tattara mayakan da ake da kyakykyawan zato a kansu, dan haka Sayeed Tasadduq-Husain ya fice domin yin wanna aiki. Sayeed Aynul-Hassan mai alhakin kula da da books room na masarautar, wanda kuma yayi rubuce- rubuce da yawa hakama mahaifinsa da kakansa a take ya bada littafin da ake kyautata zaton sune a wannan tarihin, dan bayan su din akwai dazukan da wasu mutanen daba su din ba ke zama sai dai su sun banbanta da su. An aika amintaccen Tajwar Eshaan wajen Malikat Haseenat domin amso wasu taswuriri nan ma da ke a daki littatafan sirri dake ainahin dakin karatun Tajwar Abdul-majeed. Nan take su Iffah suka shiga bincike aka kuma baje manyan taswuririn a bangwayen babban dakin meeting din. Annan ne fa Tajwar Eshaan ya bama kowa mamaki, dan ashe masanin taswurane matuka. Komai da shi akayi, kusan shine ma gaba wajen bada sirrikan dazukan, kaka da Iffah na bada shawarar yanda ya kamata a shigesu a kankanin lokacin da ake da shi suma. Suma dai sauran kowanne da irin rawar da yake takawa.
Da ga can cikin masarautar Kuwa kowa ka gani hankalinsa a tashe yake, dan hadimai masu karfin hali ne kawai suka iya gudanar da ayyukansu. Wanda aka kashe kuma anata kokarin musu sutura amma na iya cikin masarautar. Wadan da Iffah ta fillema kawuna ko ace aljanunta kam suna a nan tsakkiyar masarautar rufe yara da mata dama wasu a mazan sun zagayesu sunata kallo. Yan uwan Malikat Bushirat tuni sun iso masarautar suma hankali tashe da jin cewar wai Uwa ta dauke ta. Duk da tsiyatakun data aikata, da kuma ciwon da ke jikinta sai ya zam maganar nan ta malam ba haushe da kan ce *_DAUDAR GORA CIKI KA SHATA_*
Hankali iyaye musamman mata na masarautar bai kara tashi ba sai da suka ga ana tattara matasan masarautar ga dokuna majiya karfi ana fiddowa, Sayeed Tasadduq-Husain nata waya da shugaban sojoji na kasa ana shirya motsocin yaki da jirage uku da ya bada umarni. Hakan na nufin mataki na karshe ake shirin tunkara wato yakin gaba-da gaba da matsafan mutane irin su uwa, kafirai da basa gane komai da ga tsoron ALLAH. Wasu tuni suka fara nuna basu yarda yaransu suje ba. Amma matasan samarin nan da Iffah ta dunkule akan sakasu aikin raba abubuwan azumi dana salla sun hade kawuna akan sufa babu gudu babu ja da baya zasu kare martabar masarautarsu da sarkinsu da kasarsu ne. Duk da
basu san wahala ba, bama su taba gain yaki na zahiri ba. Gain fa abinda matasan nan sukai yay matukar burge was hadiman suma suka fito da shirinsu na kasancewa a cikinsu..
Ga al'ummar gari ma ba'a barsu a baya ba. Dan tun zuwan labarin abinda ke faruwa ta hanyar matasan nan da suka yada a social media sai ga mutane nata yo gangami musamman matasa da dama jirafa suke ace kule suce cas, Dan shi matashi a duk inda ake dan shirin a mutu ko ai rai ne, shiyyasa a mafi yawan gaba ta rayuwa inhar wani rikici ya tashi sai ka samu matasa ne sukafi zama gaba-gaba akan al'amarin.
**.
Da sauri Iffah tabi bayan Tajwar Eshaan da ya fice da ga dakin meeting din, Shigowarta dai-dai da fitowarsa da ga closet dinsa rike da sulken yaki da bata taba sanin da su ba ma a masarautar. Da ga shi har kayan takema kallon mamaki. Shiko ya dauke kai kamar bai fahimci abinda take kalion ba ya hau shirinsa. Dammarar da yake kokarin daurawa ta rike jikinta na rawa. "Maleek mi kake shirin yi ne haka?!".
"Fita bama kasata kariya mana da al'ummar cikinta, ko kina nufin zan bar yayan mutane su tunkari wannan hadarin su kadai Sohaa".
'"Ba haka nake nufi ba, sai dai ka tuna mutanen nan kai ne fa abin harinsu kai tsaye a wanna gabar shiyyasa ma suka dauki Ammie, fitarka wannan yakin akwai damuwa. Kayi hakuri ka barmu mu muje".
Ido ya tsira mata na wasu mintuna, sai kuma ya saki murmushi ya cigaba da daura dammararsa. "Ai ke badake ma za'aje din ba..."
"Saboda mi?".
Ta fada cikin tsananin damuwa. Nan ma shiru kamar bazai amsa mata ba, sai da ya mula dan kansa a fisge yace, "Saboda matata kwai ce a a hannuna, tattalinta shine abu mafi girma a gareni, kuma kin manta kinada karamin ciki ne."
"Amma..
"Shini!!!!"
Yay saurin katseta ta hanyar aura yatsarsa akan bakinta idanunsa da har yanzu suke jazur a cikin nata. Kif-kif ta farayi da nata sai ga hawaye sharrr. A hankali ta daura hanunta saman nashi da ke a bakinta ta janye, hannunta biyu ta saka ta rike hannun har yanzu idanunta dake cikin nasa na zubda hawaye. "Bazan Iya barinka ka tafi kai kadai ba".
Murmushi ya sake sakar mata yana lumshe idanunsa A hankali ya ce, "Sohaa idan mun tafi gaba daya waye zai rike al'ummar kasar? Dole kece madadina anan, roko daya zan miki koda a rasa rayuwata a wanna gabar ki zama shugaba adala, karkiyi sakaci da hakkin, al'ummar wanna kasa. Kiyi gaskiya da adalci akan masu gaskiya, ki hukunta duk wanda yay kuskure akan kuskurensa. Ki zama uwa ta gari da zata bama ya ko dan da zaki haifa mana, ki tsaya akanta ko a kansa da ilimin addini dana zamani, ki cusa masa muhimmanci tsoron ALLAH da gaskiya a zuciya.....
Kuka ta wani irin fashewa da shi ta fada jikinsa.Rungumeta yay tsam-tsam shima yana sauke ajiyar zuciya. Gangi da aka fara bugawa na umarnin fitowar mayaka ya sashi janyeta a jikinsa a hankali, shirinsa ya karasa sai gashi ya fito a cikakken gwarzon barden sa. Bai bata wata damar cewa wani abu ba ya kama hanunta kawai suka fito. Tsitt kakeji masarautar tayi da mamakin ganin har da shi za'ai fitar, sai kuma hankalin iyaye da yawa ya dan kwanta, al'amarin kuma ya kayatar da kowa. Sai da ya gama kallonsu daya bayan daya duk kawunansu a kasa sannan ya nisa yana lumshe ido da budewa. A hankali ya furta,"Kuyi hakuri! Kuyi hakuri!. Kuyi hakuri da gazawata a matsayin shugaba gareku. Ina jin ciwo fiye da irin ciwon da kuke ji, duk abinda zan iya fada muku a yanzu kun riga kun sanshi. Wanda zan maimaita kawai shine koda na rasa raina a wannan yakin MATATA itace mai gadon shugabancin da ALLAH ya daura min, inada yakimin zata samar muku fiye da abinda ni na samar muku. Idan kuma inada rabon dawowa gareku akwai abubuwan fada a bakina sosai zan kuma isar da su gareku. Duk wanda nama ba dai-dai ba a wannan hukunci ya gafarceni, ina hango muku abinda ba lallai ku hangoma kanku ba. Nagode da tarin kaunar da kuka nunamin a tsahon shekarun dana dauka matsayin shugabanku".
Hawaye kowa keyi a wajen.
Ya dan murmusa yana hadiye abu mai ciwo da ya tsaya masa a makoshi. Hannun Iffah kawai ya kama ya nufi fada, gaba daya aka take musu baya, sai dai manyan ne kawai suka shiga. Can ya dagata ya ajiye akan kujerar karagar mulkin Shahan-shan. Wani irin kabbara aka dauka Iffah kuma ta fashe da kuka. Murmushi yayi tare da kaiwa gabanta ya ajiye guywarsa kasa ya tokare kafa daya kamar wanda ke shirin saka mata zoben baiko. Hanunnta ya kamo cikin nasa ya rike tare da kaiwa saitin bakinshi ya sumbata. Cikin wata irin murya mai sanyi da nutsuwar ya ce, "Kin tuna ranar da kika sanar da Ajmaal burinki na hawa wannan kujerar? To ki dauka yau ALLAH ya cika miki, ALLAH ya baki ikon sauke nauyin hakkin al'umma My Sohaa".
Gaba dayanta ta zubo kasa ta fada jikinsa suka kankame juna. Dole gaba daya kowa ya fice kawuna a kasa…
Bayan minti kamar biyar suka fito hanunsu cikin na juna, a gaban barden dokinsa dan amana suka tsaya, kamar yanda ya saba yay haniniya tare da kwafutar kasa yay wata irin girgiza. Murmushi yayi a hankali tare da daura hannunsu dake cikin a juna akan fuskar dokin. Sai ko dokin ya kara girgiza da matsawa gaban Iffah sosai. Murmushi Iffah dake hawaye tayi, ya kalleta shima murmushin har yanzu akan fuskarsa. Dayan hamunsa yasa ya goge mata hawayen sannan yay wani irin salon tsalle na bajinta ya haye saman dokin. Take suma sauran suka haye nasu dokunan aka cigaba da buga gangi. Iffah ta kallesa ta kalli Babiy ta kalla kaka ta kalli Hanash da duk suna a cikin wanna tafiya sai kawai ta fashe da kuka..........
🚴🚴🚴🚴Basai munga yakin ba kawai a tsallake ALLAH na gaji 😫
DAUDAR GORA
Book2
91
....Sun hadu ne a mahadar shiga jejin su da sojojin kasar da suka rigasu isowa kasancewar su a dokuna ne. Shine ya fara dirgowa da ga dokin nasa. A tare sojojin suka mika gaisuwar girmamawa ga Shahan. shan din nasu. Ya amsa musu da kulawa, tare da basu umarnin mikewa. Duk mikewar sukai, sannan shugaban sojojin ya iso garesa tab…. a hannunsa ya mikama Sayeed Tasadduq-Husain dake a gefensa. Amsa Sayeed Tasadduq-Husain yayi tare da matsawa kusa da Tajwar Eshaan, shi din masanine na gaske akan ilimin sanin taswura da bibiyar waje, dan haka cike da kwarewa ya fara sarrafa tablet din cikin bibiya ya saita abinda suke bukata. Tab.. din a maidama Sayeed Tasaddug-Husain yana mai dubansu gaba daya. Kowa sake nutsuwa yayi akan kafafunsa har shugaban sojojin.
Taku daya biyu yay sai kuma ya tsaya cak hannayensa goye a bayansa. "Bazai yuwu ace mun fito wannan yakin batare da an rasa ran wani ba a cikinmu, ina fatan koza'a rasa din to ya kasance ni ne!?.……." babu wanda maganarsa bata razanar ba a cikinsu. Dan sai da duk suka zabura suka kallesa.Basarwa yay tamkar bai fahimta ba ya cigaba da fadin, "Kowanne shugaba yakanyi yaki ne domin kare al'ummarsa da kasarsa. Haka ma kowace al'umma kanyi yaki ne domin kare shugabansu da kasarsu. To a wannan gabar ina son kuyi yakine domin kare kasarmu da kayinku. Karku damu da bada kariyarku gareni zan kasance a karkashin kariyar UBANGIJINA.Mutanen da zamu tunkara duk nan mun san mutane ne masu hadari, wanda kuma bai sani ba ya sani anan sunada hadari, sannan an raini zukatansu ne da daukar fansa tamkar yanda uwa ke rainon yaronta da abincin jikinta. A mu duka da muke nan akwai masu mata da iyaye da yaya, akwai masu yaya da mata kawai, akwai masu yaya kawai, akwai masu iyayen ma kawai. Mu duka mun barsu ne suna kuka, kuka, mai ciwon shiga kila wa kala a saran dawowarmu ko mun rabu kenan. Ya zama dole musa a ranmu mun barsu da wannan tabon, musa a ramu koda bazamu dawo ba to mu kasance su mun karesu da ga sharrin wadan nan mutanen ta hanyar shafe babinsu a doron kasa na har abadan abada. Dukanmu bamu taba yaki ba a zahirance, amma sanin kowane dan kasar ruman iyayensa kan horesa da iya wasan takobi tun yana kankaninsa musamman mu maza. Wanna yasa bana jin ko dar da ga gareku jarumaina. Zamu tunkaresu da karfin ikon ALLAH, da karfin zukatanmu, da karfin kwanjinmu, da karfin horaswarmu, da karfin kare
kasarmu, da karfin kare al'ummar mu da addininmu.
Ka tuna a ranka mafifici a halitta ya yaki kafirai ne da duk wadan nan karfin ikon domin mu kasance a yau din mu cikin bautar UBANGIJI babu wani mai kuntatamu. Sai dai idan har mune muka wofantar da darajar daya sama mana tun a wancan lokacin sai mu rayu a karkashin mulkin mallakar kaskastattun kafirai. Bana fatan mu kasance hakan da karfin ikon ALLAH "
A tare sukace insha ALLAHU. Murmushi yay a karo na farko tare da duban kaka da shugaban sojoji. "Mu ukun nan mune kwamandojin wannan yakin, kar'a taba kananan yara, dan zamu iya zama jagororin canja musu alkibla bayan sun dawo hanunmu. Daga basu ba kowa abin harinmu ne. A lokacin da kuke shagalta da yakarsu, ni zan tunkari shugabar tasu ne..
Duk sun amsa da girmamawa. Daga haka aka fara nufar abin hawa. Wasu a cikin sojoji sun shiga jirage, inda aka bukaci Tajwar Eshaan shiga daya da aka kawo domin shi amma ya ce shi akan doki zaije. A dai duk cikin matasan idan da mai sha'awar haka ko rashin jimirin tafiya a doki ya kasance a cikin sojojin.Wasu sunyi hakan, wasu ko suna tare da shi a dokunansu. Bayan anyi doguwar addu'a masu bibiyar hanya ta na'urori suka fara aikinsu. Masu dokuna ne a gaba, motocin yaki na sojoji a biye da su, ta sama jiragen yaki da suka rarrabu a jejin domin sanar musu motsin komai da zai iya tunkarosu a tafiyarsu su da suke kasa musamman ma nakan dokuna. Kamar yanda Tajwar Eshaan ya bada shawara kowannensu bakinsa dauke da addu'oi..
Anan ma cikin kasa da kewaye tuni an dukufa addu'oin musamman ma cikin masarautar ruman.Yara da manya kowa ya nutsu gayama UBANGIJI da fatan kariya ga wadan nan bayin ALLAH da suke tunkaran hadarin rayuwa ko mutuwa. manyan malamai da al'ummomin yankunan su an dukufa gayama ALLAH.Yayinda mutane suka dinga cincirindon taruwa a kofar jejin ta kowacce kusurwa zaman jiran tsammani..
**
Sun nausa matuka cikin jejin da bakajin motsin halitta irin ta mutane sai tsuntsaye nau'i-nau'i,yayinda a farko-farko suka dinga wuce kauyuka. Duk kauyen da suka gifta aka sanar da Shahan-shan ne da kasan sai kaga matasan kauyen sun daura dammarar bin bayansu suma. Dan sunfi kowa sanin dazukan wajen da abinda ya kunsa. Ga sojoji ta sama suna isar da sakon duk inda suke tunkara. Tafiyar awanni biyu cur ta iso da su gab da bataliyar sansanin da su uwa suka kafa gari. Anan suka taka birki bisa umarnin Shahan-shan aka gabatar da sallar la' asar, yayinda jiragen sojoji keta kai kawo da sake bincike jejin ta yanda su Uwa bai zama lallai su fahimta ba a tunaninsu.
Sai dai kuma abinda basu sani ba su Uwa nada yan leken asiri a wasu kauyuka, hakama sunada na hatsabibanci tsaface-tsafacensu da suka kafa domin shirin kota kwana a irin wanna yanayin. A yanzu haka ma yan leken asirinsu sun isar musu da sakon shigowar su Shahan-shan din. Jin harda Tajwar Eshaan wata irin kyalkyalewa da mahaukaciyar dariya uwa ta shiga babbakawa da dukanin budaddiyar muryarta, sautin yay wani irin karade dajin. Sai da tayi mai isarta sannan ta bada umarnin kowa ya kasance
cikin shirinsa. Dandanan suka fara shiryawa mazansu da matansu, masu hayewa kan bishiyu nayi, masu hawa kan dunitsina nayi, yaran aka tattaresu cikin wani kogon dutse gaba dayansu dake nan jikin kauyen.
Dai-dai nan jiragen sojoji suka mamaye garin ta sama. Dabbobin da su uwa ke kiwo kawai suka iya gani, dan haka suka sanarma da Tajwar Eshaan akwai matsala fa. Dan kauyen babu kowa cikinsa sai dabbobi. Da mamaki yace,
"Kamar ya babu kowa?".
Shugaban sojoji ya ce, "Wlhy babu kowa sai dabbobi”.
Yanke wayar Tajwar Eshaan yayi, kaka dake kusa da shi duk yaji komai, murmushi kawai yayi, kansa a kasa batare da ya kallesa ba ya furta,"Babu inda sukaje ranka ya dade, hakan na nufin sun san da zuwanmu zuwa yanzu. A sanar musu kar jirgi ko daya ya sauka kasa har sai mun fara shiga".
Sayeed Tasadduq-Husain Tajwar Eshaan ya mikama wayar, dan haka shi yay kiransu ya sanar musu.Shugaban sojoji zaiyi gardama Tajwar Eshaan ya sake amsar wayar, babu alamar wasa tattare da shi ya furta, "Kuyi yanda akace". Cikin girmamawa yay saurin amsawa. Daga haka suma suka hau dokunansu, kaka ya juya yana kallonsu, "Kowa ya kasance bakinsa da addu'a, duk abin tsoron kuma da za'a iya bude maka do da shi karka razana. Kar kuma mu yarda addu'a tabar bakinmu dan itace babban makamin da zai iya rusa wadan nan mutanen bakwai makaman hannunmu ba".
Duk sun amsa da girmamawa garesa, da ga haka Tajwar Eshaan ya yunkura. Shi da Kaka sune a gaban,sai tawagar masu dokunan biye da su, sai motoci sojoji da duk wanda bazal iya tafiyar kan doki ba. Har suka iso tsakkiyar garin suma basuga komai ba sai farin dabbobi. Shiru sukai tsaiwar shirin kota kwana suma da baza idon son gain ta inda wani zai fara bullowa. Mintuna uku shiru sunata ambaton ALLAH sudai, sai jirage da ke ta kai kawo ta sama.
"Kodai zamu sauka mu bincika ne?".
Daya da ga cikin samarin ya fada. Alamar yay shiru kaka yay masa. Kai ya jinjina masa. Cikar minti daya da hakan bai karasa ba dajin ya dauki wani irin sautin kuka mara dadin ji. Hatta wanda ke cikin jiragen sal da zukatansu suka shiga bugawa da sauri-sauri. Sai dai kowa yayi tsam bakinsa da addu'a. Kukan sake cika musu kunnuwa yake da tunkarosu, hakan yasa kowa sake shiri. Wasu inn halittune masu ban tsoro da rashin dadin kallo suka zagayesu. Cikin dakiyar zuciya Kaka ya furta. "Kar wanda ya firgita". A zahiri dai kowa ya amsa masa da to, amma a zukatansu wasu dai kam sun razana. Amma sai ambaton ALLAH da sukeyi ya saka musu wata jarumta da jin karfi, kafin ma halittun sun yunkura su sun yunkura a dokunan batare da jin zasu gagaresu ba duk da yawansu. Na cikin motoci ma duk sun fito, haka ma wanda ke cikin jirage, jirgin na daga sama suka dinga silalowa ta sama sai ya zamto sunma halittun kawanya. Su Tajwar Eshaan a tsakkiya, sai halittun,sojoji a karshe. Cike da jin karfin zuciya Tajwar Eshaan ya fara ketawa cikin halittun sai ga kawunansu yana saukewa da takobin hanunsa shi da kaka. Gain hakan yasa a cikin samarin ma wasu suka afka sura. Tuni halittun suma sun fara tsalle a kawunansu, sai kusan uku su taru a kan mutum daya, cikin dai amincewar UBANGIJI suka gama kaudasu a abinda bai wuce mintuna ashirin ba. Da yawansu sun jijii musu ciwuka da farautansu. Ganin haka su Uwa suka sake turo wasu. A yanzu kam kaka ne yay wani irin dirowa daga saman dokinsa. A kausashe ya dubi halittun da suka sake zagayesu da fadin, "Ku kananun hatsabibai, idan har baku kasance matsoratan kafurai ba ku bayyana kayinku mana mushirikai. Ko kun tsorata ne? Nace ko kun tsoratane Uwar gijiyar taku ta reneku da tsafine kawai amma babu karfin zukata
da jarumta!!!".
Tabbas wadan nan kausasan maganganu na kaka sun matukar musu dacin, dan kuwa jikin uwa da ke a dakin gumakansu ga Malikat Bushirat shimfide sun zagayeta cikin wata kaya da kayan tsafi rawa ya kamayi, cikin wani irin kara ji da mummunan sauti ta ce, "Ku fito ina bukatar kan shugaban nasu a gabana. Kuma ina bukatar karagar mulkin ruman a gabana a yanzun itama tare da kan tsohon nam dana matar shugaban nasu da ya bari gadin gida"….✍️
DAUDAR GORA
Book2
92
-.Maganarta ta zama tamkar busa musu kaho da kada musu gangi ne. Dan saukar kibau kawai su ka fara ji shuuuuuu daga sama. Da sauri Sayeed Tasadduq-Husain yace,"Garkuwa sojoji masu karfi da karfafawar ALLAH!!".
A take suka dunkule waje daya suka zagaye Tajwar Eshaan ya koma tsakkiya tare dama kansu garkuwa kibiyiyin suka dinga sauka akan saman garkuwar karfen hannayen nasu. Da wanna damar yan kabilar su uwa da ke saman bishiyu da duwatsu fara dirgowa kasa suka zagayesu. Sanda suke janye garkuwar bayan gama saukar kibau din sun gama zagayesu. Ko kadan hakan bai razanasu ba, dan kowa a fusace yake da jin tsanar wadan nan kafirai. Sannan sunyi alkawari duk rintsi bazasu bari a taba musu Shahan-shan din su ba. Tuni sukai wata irin rabewar da kaka duk ya tsara musu. Su kuma gain hakan sai sukai tunanin tsorata sukayi ne suka afka kai tsaye da tunanin korar su. Wannan itace damar farko data basu nasara akan wadan nan mutane, cikin kankanin lokaci kura ta tashi waje ya hargitse. Kabilar uwa sunyi shiri ne irin shirin da wuka ko bindiga bazata ratsasu ba. Yayinda Kaka ya bada shawarar fara tunkararsu da wuka sai sunzo hannu ai amfani da maganin daya tanada wajen karyasu su da karfin yakin nasu. Gurin na cakudewa kam wadanda zasuyi feshin maganin ta sama da ga cikin jirgin sojoji suka fara. Tun anan fa ihu-da-ihu ya hargitse, suka fara kaiwa kasa samarin nan a gille kawunansu. Yayinda kabbara ke tashi da amsa kuwwa a cikin jejin. Cikin abinda bai wuce awa uku ba an gama da kaso biyu da rabi bisa uku a cikinsu. Zuwa yanzu fa hankalin uwa da ke kwasar dariya ya fara tashi. A take ta bada umarni ga wadanda ke zagaye da ita fara aiwatar da shirinsu akan Malikat Bushirat. Dan hakanne plan c dinsu, plan b shine wasu kason mutanensu da ke can masarauta dakko karagar mulkin Shahan-shan..
** MASARAUTA **
Kukan da taci ya haifar mata da matsanancin ciwon kai, duk yanda taso kin kwanciya sai da Malikat Haseenat ta takura mata. Kwanciyar tayi, sai dai bata
rufa mintuna ashirin cikakke ba ta tashi a matukar firgice. Hankali tashe Malikat Haseenat da Daneen Ammarah sukai yunkurin riketa amma ta girgiza musu kai. Sun fahimci tabbas akwai matsala, dan haka Daneen Ammarah ta ce, "Mammah barta. Barta kawai akwai matsala ne".
Hankalin Malikat Haseenat tashi ya karayi, dan tuni itama Daneen Ammarah din ta birkice a cikin kankanin lokaci. Dai-dai nan ko Amintacciyar hadimar Malikat Haseenat ta shigo hankali tashe, cikin hakki take sanar musu babu lafiya, ga was irin mutane nan da ba'asan ta inda suka shigo masarautar ba sun zagaye ko ina. Wasu a cikin jami' ai sun fara harbinsu amma ko gezau da alama ma bindigar bata kamasu. Wasu kaso a cikinsu kuma sun nufi fada ne inga karagar mulki take.
Kafin ma takai karshe Iffah ta fice, Daneen Ammarah biye da ita. Gaba daya masarautar ta gama harmutsewa. Tuni kowa ya fara gudun ceton rai.Yayinda jami'an masu karfin hali da Ghazi da wasu a cikin hadimai da samari da aka bari sunata kokarin kai musu hari amma mutanen nan babu alamar razani a tare da su, saima wani irin dariya sukeyi cike da karfin iko na ko gezau. Ai babu wanda yasan ta yaya, ta ina
ma, kawai saukar kawunansu aka fara gani bisa kasa. Hankalin Ghazi ya tashi, ganin SARAUNIYA Iffah ce da kanta ba sako ba. Tare da Daneen Ammarah da a yau kowa ya shaida eh lallai ba ita kadai bace itama da nata ifiritan aljanun bisa kai.
Duk wanda ya tunkari Iffah kai kawai take sauke masa ta matukar fita a hayyacinta da canjawar kamanni. Suko hatsabiban wani irin bulbulo wuta suke ta bakunansu suna kokarin tunkarar fada da tuni aka rufo ruf. Masarautar tayi masifar rikicewa, mata da yara kuka kawai suke. Hakama wasu a cikin mazan tuni sun nema wajen buya. Hatta su Miran Jasim da ke a cikin kurkuku sun tabbatar yau gidan babu lafiya kam......
**
*
Su uwa na tsaka da zagaye Malikat Bushirat da aka gama jikewa da ruwan tsaffi a tsakkiyar gumaka Tajwar Eshaan ya fado musu. Da wani irin jarumta dokinsa yay haniniya mai razanarwa kawai yay kansu.Daga dokin har shi Tajwar Eshaan din gani sukai sun koma musu wata halitta daban. Yau sai ga uwa tsaye akan kafafunta ta mike da ga kujerar tsafinta cikin matsanancin tashin hankalin gain dokin nan fa babban gunkinsu ya nufa. Kafin tai wani yunkuri yay ma butum-butumin gunkin wani irin duka da dukan karfin kwanjinsa shi da dokinsa sai gashi tarwatse a kasa. Ai ko kashin hannunsa yay wata irin karar masifa da ke tabbatar da yaji ciwo a cikin kashi. Hannun yay kokarin rikowa da dayan Hannunsa dake rike da linzamin dokinsa yaji saukar kakkaifar wuka a cikin damtsen hannun.
"Ya Arrahaman!!"
Ya ambata da dukkan karfin murya dana jiki da ya masa saura. Dan wata irin azabar zafi ce ta ratsasa har cikin kwakwalwa, Dai-dai juyowarsa kan wanda ya sokesa da wukar a dartsen hannun ya sauka kasa. Babiy ne da ya biyo bayansa, dan tun barowar Shahan-shan din a cikinsu ya farga yay azabar biyo bayansa. Bummm!!!! Shima Baby uwa ta sauke masa wani mulmulen ice saman kai, kara ya saki shima cikin ambaton ALLAH ya dafe kansa da jini ya balle, luuuu ya tafi kan dokinsa zai zubo cikin karfin hali Tajwar Eshaan yay wani irin juyi ya tallafosa. Gaba dayansa ya dago ya ajiye saman dokinsa. Kafin ya fisgo sarkar da suka shirya rataye Malikat Bushirat a ciki ya watsata, cikin amincin UBANGIJI ya samu nasarar sarko wuyan uwa da ke kokarin zare wata takobin tsafi da ga jikin wani gunki. Razananninayar karar data fargar da wanda ke waje ta saki, dan sarkar ta tsafi ce, amma cikin amincewar UBANGIJI shi Tajwar Eshaan din sai bata masa komai ba. Duk da da yawansu an musu jina-jina haka suka dinga dannowa dakin dan zuwa yanzu suma sun gama da wanda suke wajen, wadan da suka rage kuma an kamesu an daure bisa umarnin kaka.
Cikin tashin hankali suka nufi Shahan-shan, amma sai ya girgiza musu kai alamar su barsa. Da kansa ya dirgo kasa, su kuma suka kama Baby da babu numfashi tare da shi suka sauke aka fita da dokin Shahan-shan. Shi da kansa ya daure uwa da sarkar nan tare da bama matasan sa umarnin rushe gumakan: a gabanta, rushewar kam suka farayi itako tana kukan bakin ciki da wata irin jijiga a cikin sarkar da ya dauretan.
Shi kam takawa tay a hankali gaban Malikat Bushirat. Hannu ya kai ya yaye jan mayafin da suka. lulluba mata, dai-dai nan ta bude idanunta sai ko a cikin nasa, kallon juna sukai na kusan sakkani goma. Shi ya fara janye nashi da sukai wani irin jazur cikin lumshesu da budewa. Batare da ya yaye farin mayafin dake a kasan jan ba yasa hannayensa biyu ya dauketa duk da yanda hannunsa a haggu da yaji ciwo ga wuka a ciki jini na zuba ke masa azaba da rawa. Wasu irin hawaye ne masu zafi suka shiga rige-rigen sakko mata, dan su kadaine ke aiki a jikin ta, amma su Uwa sun sandarar mata da jiki gaba daya babu abinda ke aiki tare da ita sai kanta da idanun.Duk yanda ta kuresa da ido shi yaki yarda ya kalletan.Cikin sauri masu bada taimakon gaggawa da aka taho
dasu cikin sojojin suka nufosa da gadon daukar marasa lafiya. Amma bai daurata ba har sai da yaje ga jirginsu na sojoji da suka sauka. A hankali ya shimfidar da ita, sai da ya tabbatar ya gyara mata mayafin da take ciki dan tsirara take sannan ya dubi matukin jirgin yana lunshe ido. Ya fahimci abinda yake nufi, dan haka ya kame jikinsa tare da salute nashi.
A gaban su kaka ya tsaya ya wani rumtse danunsa da daura hannunsa saman wukar nan dake kafe a jikinsa zai fincike kaka yay saurin dakatar da shi. "A'a ranka ya dade, hakan da zakai matsalane, dan wukar ba wuka bace takai tsaye kamar saura akwai dafi tare da ita. Kawai ka shiga jirgi dan bai kamata ka koma damu ba a doki".
Bai cire din ba, sai dai ya bama kaka amsa da cewar"Tare da ku zan koma Jaddi".
Murmushi kawai kaka yayi shi da Sayeed Tasadduq- Husain, dan yau ne karo na farko da Tajwar Eshaan din ya kira shi da kaka. A dai-dai nan aka fito da Uwar dake daddaure cikin sarka. An tsareta da tambayar ina yaran garin suke amma taki fada, sai ma dariya data sanya musu da cewar, "Bazan fada ba, bazan taba fada muku ba. Dan ku tabbatar karar da mu iyayensu kamar kashe maciji ne baku sare kansa ba hahahahaha!!!!!".
Babu wanda ace da ita komai saboda isowar jiragen sojoji da shugaban sojoji ya bada umarnin a karo, dan yanda suka jigata din nan babu mai karfin iya komawa ta mota ko doki. Ga wasu shimfide babu alamar rai ma tare da su. Wasu kuma sun jigata matuka da ko yatsansu basa iya dagawa ma. Kin fadar inda yaran suke yasa sukai tunanin ko sun dauke su ma daga jejin ne gaba daya yasa shugaban sojoji bada umarnin ana gama kwashe su a sakama garin wuta kawai. Uwa bataji wannan furuci ba, kasancewar an tisa keyarta ita da sauran mutanensu ashirin da daya daba'a kashe ba cikin motar yaki.Hakama sauran mayakan duk an sakasu a jirage su, marasa lafiya sune farkon wucewa domin zuwa a basu taimakon gaggawa. Kaka da Tajwar Eshaan da Sayeed Tasaddug-Husain da shugaban sojoji sune karshe, za'a warema Tajwar Eshaan jirgi ya dakatar dasu.
Tuni sauran sojojin da aka bari suka sakama garin wuta gaba dayansa bayan an tabbatar da babu wani kauye a kusa da su da wutar zata iya shafa. Dan su tsabar bakin hali ma basu yarda yin makwaftaka kota kusa da wasu kauyukan ba. Wannan wuta itace ta dinga wasar kogon dutsen da suka boye aransu zafin ya dinga ashes batare da an san anan din suka boyesu ba.
*
Abinda ya far a cikin masarautar ya sasu iske cikin Dahab City a hargitse. Dan jiragen a inda suka dauke su farkon jejin dole anan suka dakata aka dinga kwasarsu a motoci. Nan din ma cike suka samesa da jama'ar gari ga yan jarida. Jinin da Tajwar Eshaan ya rasa sakamakon sukar wukar da aka masa mai dafi a hannu dama ga kananun raunuka yasa idanunsa har sun fara rinjaya, dan sal da taimakon shugaba sojoji da kaka aka fito da shi aka daura a gadon marasa lafiya zuwa mota Hankalin mutane ya tashi matuka dan sun fahimci Shahan-shan dinsu kenan gariin yanda sojoji suka zagaye gadon, hakama da aka saka shi a motar an zagaye motar da uban tsaron da korna miye ya gitta zal iya zama gawa ne….✍️
DAUDAR GORA
Book2
93
……..Cikin masarautar ma a hargitse suka sameta,dan tuni an is da Malikat Bushirat da aka fara tahowa da ita. Ga Iffah da jini ya balle mawa ta yanke jiki ta fadi itama aka shiga da ita ciki har yanzu likitocin da ke kanta basu fito ba. Tashin hankalin hakan yasa ko wanda suka sarewa kawuna ita da Daneen Ammarah bama a janye ba. Ba'a bari kowa ya ga halin da Tajwar Eshaan ke ciki ba aka shige da shi sashensa. Hakama sauran mayakan da sukaji munanan raunika aketa nufar cikin clinic da su duk da kukan da iyayensu keyi ba'a bar kowa matsowa kusa da su ba, wanda sukaji kananan raunuka ne dai aka zube a harabar masarautar suma ana basu taimakon gaggawa na ruwa da magani. Ga magrib ta gabato. Amma burin kowa dai yaji yaya Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb yake. Yanda suka tada hankalinsu yasa dole sai da Sayeed Fayzul-haq ya fito yay magana da yan jarida akan kowa ya kwantar da hankalinsa Shahan-shan na nan raye, sai dai yana bukatar addu'oin Su...
*WASHE GARI*
Alhamdullah an wayi gari da dadin rai, dan su Babiy duk sun farfado. Hakama Tajwar Eshaan kaka ya saka masa magani an kuma masa na asibiti da dorin karayar sai dai ace Alhamdullah. Itama dai Iffah an samu nasarar tsayar da jinin kuma cikin da aketama damuwar zai iya lalacewar dai yana nan. Malikat Bushirat ce dai idanun nan da kai kawai ke aiki, sai dai duk abinda za' a fada tana ji. ALLAH sarki Jasrah bata gazaba a yi mata hidima. Jama'"ar gari dama na masarautar da basu san komai akan al'amarin nata ba sunata tausayinta da gain Uwa ta tsafeta ne saboda cikar burinta. Was har addu'a suke mata na samun lafiya. Gawarawakin dangin uwa an tattaresu anyi rami acan daji an biznesu, wanda kuma suka rage tare da uwa an zubasu a kurkuku har sai ALLAH ya bama Tajwar Eshaan lafiya.
Tako ina labaran abinda ya faru a kasar ruman dinne ke yawo a duniya, wasu na caccakar Shahan- shan akan abinda akai bai dace ba suma mutanen nada yancin kansu, wasu ko na ganin hakan da akai shine dai-dai. To koma dai yaya ne yan kasar ruman sudai hakan da akai yayi musu. Dan babu wata kasa da zata so rayuwa da masu bakin kafirci irinsu uwa.Masu ganin ba'a musu dai-dai ba ma son zuciya ne kawal.
Lokacin da Iffah ta tartado taci karo da Tajwar Eshaan jikinsa ta fada kawal ta fashe da kuka. Ya rungume kayarsa yana murmushi shima idanun nasa dai sun kada. Sai da tayi mal isarta sannan ta dago, babu zato kawai yaji ta manne lips dinsu a waje guda. Idanu ya zaro itama sai ta zaro nata tare da janyewa tana dariya. Da sauri ya rikota da hanunsa mai lafiyar ya maidota jikinsa yana murmushi.
"Wannan ai mugunta ce a lasama mutum zuma a baki a gudu". Ya fada cikin rada a kunnenta. Dariya ta shigayi a hankali tana boye kanta a cikin jikinsa, da ga haka ya canja wasan a yanda yake bukatar kasancewarsa, duk da kuwa komai da yake na karfin hali ne kawai, dan sam zuciyarsa babu dadi, shi kadai yasan halin da yake ciki akan mahaifiyarsa. Amma yanata kokarin dannewa da gayama ALLAH kukansa.
Lokacin sallar azhar domin sake Kwantan da hankalin mutane ya fita sallar cikin karfin hali duk da
hanun nasa an masa dorin karaya ne. Ga yankan wukar nan da yay matukar shiga jikinsa sosai, saukin ma dal anyi maganin dafin. Bayan anyi salla an fito ya dan gana da manema labarai da yasa a tara masa. A nan yay ma al'ummar kasarsa godiva da fatan alkairi bisa kokarinsu da addu'oinsu. Ya kuma sake jaddada Iffah matsayin SARAUNIYARSU har yanzu dan bazai amshi mulki ba sai ya samu lafiya. Babu wanda yay jayayya da wannan al'amari. Sai ma Tajwar na jihohi da manyan kasar dake ta layin zuwa dubashi tako ina, tare da sauran mutanen da suka fita wannan gumurzu. Musamman yan kauyukan nan da Hadimai da wasu a jama'ar gari da suka taimaka musu anhadasu da manyan kyautuka, hakama itama SARAUNIYA Iffah ta bisu su dukansu da manyan kyaututtuka da ya sakasu a farin ciki, dan ita dukansu ta hada har matasanta.
Lokacin da don Malikat Bushirat ke gain bayanin Shahan-shan akan Iffah zata cigaba da rike matsayinsa har sai ya samu lafiya, da lokacin da ake nuna Iffah'r akan karagar mulkin Shahan-shan din randa take zartar da hukuncin kyautukan da ta bama wanda sukaje yakin a matsayin Sarauniya kuka ta dingayi, kuka mai zafi da tsananin kona zuciya. Sosai takejin radadi matuka a cikin kirjinta, ji take inama kafin zuwan wanna ranar ta mutu ta huta. Bayan tasha kukanta ta godema ALLAH ta cema Jasrah a cire mata tvn daga dakin. Jasrah har ta amsa da to Malikat Haseenat ta ce kar a cire. Dan tsaf ta fahimci manufar Malikat Bushirat din. Tana ammakin taurin zuciyar matar nan, ace duk wadan nan abubuwan daka gani basu isheka izna ta saraya ba. Ko dan data haifa ta kasa neman gafararsa ma balle su. Kai ALLAH ya rabamu da irin wanna mummunar zuciyar ta kafuran farko,
Kullum sai Tajwar Eshaan yabi ta barauniyar hanyarsa dubota. Zasuje da safe shi da Iffah da an idar da sallar asuba. Zakuma suje bayan sallar isha' i. Da ga gaisuwa da tambayarta yaya jiki bai iya kara sake cewa komai. Sai ma ita Iffah'r ce kan dan mata addu'a ta tofa mata, duk da dai kaka nata kokarin bada magani ana mata ko za'a dace. Haka zatayi ta kallon Tajwar Eshaan tana hawaye, amma shi daga kallo daya na gaisheta baya sake yarda ya kalleta har yabar dakin kansa a kasa yake.
**.
Bayan kwanaki bakwai abubuwa da yawa sun dai-data, musamman masu kananun raunuka sunji sauki sosai, sai wanda suka jigata ne sosa ke cigaba da karbar magani. Baby ma dai da yake buguwace Alhamdullah jikinsa da sauki, dan haka Tajwar Eshaan yace kawai Daneen Ammarah ta tare haka nan. Duk yanda taso zamewa sai da aka shirya wani dan kwarya-kwaryar walima data kayatar. Dan anyita ne irin ta manyan mata masu aji da ilimi. Zuwa dare aka shirya mika amarya dakinta, Iffah kuwa ta dage sai taje. Sai da aka tuna mata itafa SARAUNIYA ce a yanzu, babu yanda ta iya dole ta hakura, amma tanata ima Mamyn (Daneen Ammarah) tabarar wai shikenan ita haka kowa zai tafi ya barta. Ita an kawota gidansu ita kuma za'a maidata gidansu. Itakam data san hakane kawai kowa yay zamansa gidansu. Dariya sosai Malikat Haseenat da Daneen Waheeda keyi da drama din tasu. Dan wata shakuwace ta musamman ta sake shiga tsakanin Iffah da Mamyn (Daneen Ammarah) taja yarta jikinta sosai da sake tabbatar mata da kaunar da take mata dabance a rayuwa. Haka itama Iffah'r tana kaunar mahaifiyar tata matuka duk da bata rayu da ita ba. Sannan tana kaunar Ummu dinta da Baby. Hanash Akhi kam ai shi na musamman ne gareta da Kakanta abin alfaharinta. Kullum cikin lallabasa take shi da lyyani su dawo cikin masarautar da zama ko zata dan ji saukin kewarsu da tayi. Shi dai ya nuna bazai dawo ba. Amma Tajwar Eshaan ya ce ta kawantar da hankalinta zai dawo mata dasu, Ba karamin farin ciki tayi da hakan ba.Dan shima Babiy an gyara masa gidansu sosai dan bazai iya barinsa ba saboda gidan gonarsa.
Lokacin da za'a wuce da Daneen Ammarah sai gashi tana kuka, ta rungume Malikat Haseenat da Iffah sunata kuka. Da kyar Daneen Waheeda da Malikat Ashwaq suka rabasu aka fita da ita. Yau kuma sai dakin mijinta ban yarta.
Tarbace ta mutuntawa suka samu da ga su Ummu, kowa halayen Ummu na birgesa, dan mace ce data amsa sunanta cikakkiyar mace jaruma abin koyi da nunawa a duniya ga kowa, Yan kawo amarya basu wani jima ba suka wuce abinsu. Lokacin da ango zai shigo Ummu da kanta tayo masa rakkiya cakin amaryarsa. Zata gudu Daneen Ammarah tace saifa ta zauna sunyi hira. Babu yanda Ummu ta iya dole ta zauna. Sai dai hirar ma dai duk akan rayuwarsu ta bayace data shude. Kuruciyar Iffah da su Arfa Daneen Ammarah har kuka tayi, ta jinjinama hakuri irin na Ummu. Ta kumayi alkawarin kyautata zamansu tamkar yan wan juna har abada. Zasu zama aminan juna bawai kishiyoyi ba. Ganin dare yaja da wayo Ummu ta tattare kwanikan da sukaci abinci ta gudu. Dama shi Hanash Akhi yana can masarauta Iffah ta rikesa wai shine amintaccenta, nan ko duk wayone dan taita gain dan uwanta ne. Dan babu wani abu da yake yi sai idan sun dan shiga fada zatai wani zama mai muhimmanci da manyan masarautar ya kasance a gefenta. Hakan sai ya saka mata zaman lafiya da Tajwar Eshaan sarkin kishi, dan tana ambata maganar Hanash Akhi dinne zai kasance amintaccenta harda kyauta sumba aka bata. Wai hakan shine dai-dai.
Ummu na fita Babiy sauka yay kasa gaban Daneen Ammarah ya zabga tagumi ya wani zuba mata idanu. Murmushi tayi da jan mayafin jikinta ta rute fuska cike dajin kunyarsa. Ya lumahe idanu da budewa yana murmushin shima, Kafin ya mike tsaye ya yaye mayafin gaba daya ya kama kafadunta ya mikar da ita ya rungume abinsa. A tare suka dinga sauke ajiyar zuciya, sai kuma hawaye na tsananin kewa da tuna baya.
"ALLAH na gode maka daka maimaitamin wannan rana a rayuwata. Ka gamamin komai UBANGIJINA daka bani mafi tsadar nan a cikin mata matsayin matata"
"Ni zan godema ALLAH da samunka matsayin miji kuma uban yayana Zayyan. Tare da yar uwa jaruma Saliha irin Jumaymah. Yanda kuka sharemin hawayena, da zama silar canja labarin da ban taba tunanin zai canju daga kaddarata ba kuma ALLAH ya share naku hawayen. ALLAH ka hana shaidan shiga tsakaninmu. Nayi alkawarin in har inada rabon sake haihuwa a duniya zan malakama Jumaymah (Ummu) yayan nan har abada".
Cikin rada-rada a kunenta ya furta, "Insha ALLAHU a yau din nan zan dasa kwam Arfa da Fariha gimbiyata." cike da jin kunyar furicin nasa ta wani kankamesa da boye kanta a jikinsa. Wani irin rungumeta tsam-tsam Baby ya sakeyi shima yana dariya, tare da bata sumbata tako ina a jikinta harya sauke akan lips dinta, Jin tsaiwar na neman gagararsu ya dauke abarsa tsamm suka shige daga ciki, dama dai ga Daneen Ammarah yar dum-dum kai kace bata wuce talatin a duniya ba. Jin an rufo kofa harda murza key nayi baya dan wanna fagen na manya-manya ne ba gain kanana irimmu ba 🥱😉😂🚴
* BAYAN WATANNI SHIDA DA FARUWAR YAKI TSAKANIN SU SHAHAN-SHAN DA SU UWA
Kai kawo yaketa famanyi a cikin bedroom din nashi bakinsa dauke da addu'a. Duk ko yanda waya ta motsa sai ya daga da tsammanin su Malikat Haseenat ne. Babu abinda yafi burin ji a wannan gabar kamar ace ALLAH ya sauki Sohaa dinsa dake nakuda tun a daren jiya lafiya. Duk yanda yake da tarin ayyuka a fada ya kasa fita. Su Sayeed Fayzul-haq ma sun hakura da fitowar tasa yau tun sanda labarin nakudar Iffah'r daya iso kunensu. Sai kowa ya koma fatan saukarta lafiya.
Daga wayar da tai dai-dal da bugawar agogo karfe sha biyu dai-dai na raar litinin din ya wani irin sauke ajiyar zuciya da zama cikin kujerarsa a hankali. Murmushi ne mai sanyi ya subuce ma kyakykyawar fuskarsa. A hankali ya motsa lips dinsa ya ambaci "Alhmdullah"., Sai kuma hawaye suka dan ciko idanunsa. Shi Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb ne yau ALLAH ya azurta da kyautar yayan har guda biyu mace da namiji daga jikin yar uwarsa kuma matarsa, farin cikinsa Fhareedah bint Zayyan. A take bakin ciki da kuncin dake tare da zuciyarsa a cikin watanni shidan nan yaji ya wani fada masa daga makoshi zuwa cikin ciki. Babban yatsarsa ya kai a idanun nasa a hankali ya dauke hawayen da sake furta. "Abbie an haifo maka jikoki har guda biyu a rana daya, lokaci daya da ga tilon danka. Insha ALLAHU za'a sake haifo maka wasu biyun kamar haka har sau hudu Abbie na. ALLAH ya gafarta maka, ALLAH ya yafe maka kurakuranka kai da Jaddi da ma duk zuri'ata data musulmi baki daya. Kai da Jaddi da Jaddah ne abin AL'FAHARINA ABBIE NA"……✍️
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (94)
*_MAAB LUXURY HOME._* _Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini. Ina uwar gida da Amarya, Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*._
_____________________
.........Cikin ƙanƙanin lokaci zancen haihuwar Iffah ya karaɗe ƙasar ruman baki ɗaya. Tuni farin cikin kowa ya bayyana, tare da addu'oi ga waɗan nan jinjiraye da ga bakin al'umma. Yayinda Tajwar Eshaan daya matsa a kai masa su ke can rungume da kayansa tsam-tsam a jiki. Jinsa yake a yau ɗin kamar wani sabon mutum, final shima dai ya zama Abbie. Ga yaran sun ɗakko kamanninsa sosai musamman ma mace kamar an tsaga kara an karya da shi, gara namijin yafi rinjaya da Iffah shi kuma. Da kansa ya tauna dabino ya basu tare da musu huɗuba.
Duk yanda yaso ganin Sohaa ɗin sa hakan bata yuwuba sai bayan la'asar tai barcinta ta huta sannan. Murmushi ta dingayi kanta a sinne saboda irin kallon nan na ƙasa-ƙasa da yake faman binta da shi. Duk sai taji kunya ta lulluɓeta. Har ya ƙaraso gaban gadon bata yarda ta ɗago ɗin ba sai da ya zauna a kusa da ita ya ɗago fuskar tata da kansa. Bai tsaya wata wata ba kawai ya manne lips ɗinsu waje guda. Sai da yayi yanda yake so da ita ya barta dan kansa sannan ya rungumeta yana jero mata daɗaɗan kalamai masu sanyi da ratsa zuciya da bata san yayi nisa a sani ba har irin haka. Jitai kawai idanunta sun cika da ƙwalla. Dan ita kanta bata san adadin ƙaunar da takema wannan bawan ALLAH ba zuwa yanzun. Tana jinsa daban a cikin daban a duniyarta. Shi ɗin na musamman ne a gareta fiye da yanda yake jinsa na musamman...
Lokacin da aka kaima Malikat Bushirat da har yanzu ake nan yanda ake babu abinda ke motsi sai kai da ido Jasrah baiwar ALLAH nata wahala da ita kuka sosai ta fashe da shi. Suko yara kamar sun san inda aka kawosu suka wani dage da tsanyara kuka tsiyau-tsiyau kamar ƴaƴan magena da yau mukasha bikin sunansu (Na manta ban faɗa muku ba magena ta haihu ƴaƴa hudu kowa sai ya kawo kayan barka haihuwar fari ce babu ɗaga ƙafa😂🚴🥱) kuka sosai suka dingayi har abin ya bama kowa mamaki, ana fita da su sukai shiru kuma kamar basu ba. Koda aka maidasu anan bama Malikat Haseenat da Iffah labari murmushi kawai Iffah tai batace komai ba. Garama Malikat Haseenat tsohuwar ƙwarai ta tofa kaɗan.
A can ko jikin Malikat Bushirat rikicewa yay sosai. Dan har sai da takai an kira Shahan-shan da Malikat Haseenat. Al'amarin kam yau dai bana wasa bane. Dan doctors da suka rufu a kanta ma dai sunyi iya ƙoƙarinsu amma bata bar jijjigar da ta dingayi ba, daga baya ma sai ga aman jini. Hankalin kowa ya tashi musamman Tajwar Eshaan, dan da kansa ya hau gadon ya rungumeta jikinsa ta dinga bulesa da aman jinin nan. Addu'a ya dinga tofa mata, ganin fa tafiyar mai tsaho ce Malikat Haseenat ta fara maimaita kalmar shahada ko za'a dace Malikat Bushirat ɗin ta karɓa. Hakan yasa suma sauran jama'ar dake a ɗakin suka dinga maimaitawa, Jasrah dai kuka take kamar ranta zai fita. Sai dai kuma ita rayuwa duk yanda kaso, bai zama lallai abinda kaso ɗin ya kasance a yanda kaso shi ba. Dan kuwa dai Malikat Bushirat ta koma ga UBANGIJI batare da ta iya neman gafarar koda ɗan cikinta tilo data jefa kanta a halaka domin haihuwarsa ba. Tayi mutuwa mai ban tsoro da tashin hankali, dan kuwa maimakon kalmar shahada da suka so ji daga bakinta sunan UWA ne ƙarshen ambaton ta cikin wani irin gurnani mai ƙarajin gaske daban tashin hankali. Wannan al'amari ya matuƙar kiɗima Shahan-shan. Dan jikinta na gama saki shima ya kife kansa akan fuskarta. Tsahon lokaci bai ɗago ba har sai da kowa ya fita a ɗakin Malikat Haseenat tazo tana lallashinsa. Sannan aka samu ya ɗago idanun nan nasa jazur matuƙa abin tausayi, sai dai baiyi kuka ba, ya jima yana kallon fuskar mahaifiyar tasa abubuwan data lissafa ta aikata na dawo masa tiryan-tiryan kamar yanzu take yinsu....
Masarautar gaba ɗaya ta gama rikicewa. Dan mutuwar nan kam ta daki kowa musamman da Malikat Bushirat ta zama tamkar wata tauraruwa a zamaninta a cikin gidan. Sai dai yanda mutuwarta tayi dai-dai da mutuwar kaf mutanen nan ƴan ƙabilar uwa abin ya bama kowa mamaki. Dan kamar waɗanda aka shayar guba kawai aka samesu duk a mace su kusan goma sha uku. Dama wasu sun ɗan mummutu ɗaɗɗaya. A yanzu dai kam Uwa kawai ta rage a raye. Itama ɗin dai sai a hankali dan duk ta ƙara wani irin yamushewa na tashin hankalin faɗuwa ƙasa da tai. Wai yau itace mai zaman kurkuku a cikin masarautar ruman kuma da ranta da lafiyarta tsahon watanni shida. Ai ko'a iya haka aka tsaya ta gama kunyata a wannan duniya.
Jasrah ce ta mata wanka tana kuka abin tausayi ita da yayarsu Badiha. Bayan an mata sutura aka fiddota Tajwar Eshaan ya jagoranci sallatarta tare da miƙata gidanta na gaskiya aka barta da halinta kuma. Dan ya rage ita da UBANGIJINTA. A yanzu kam. Wannan itace ranar da ya kama kowa ya kasance yana gudu a rayuwarsa. Dan ko kaƙi ko kaso sai tazo. Ko kai mutumin kirki ne kona banza ne ma dai sai tazo. Ko shekara dubu bisa dubu zakayi a duniyar sai tazo. Koka shirya ko baka shirya ba sai tazo. Yau dai gashi Malikat Bushirat ta tafi tafiya ta har abada. An shafeta an shafe babinta dama iyakarta kenan akan duk wani abin kirki ko ɓarna da zaka shuka a duniyar....
Tajwar Eshaan bai samu hawayen dake riƙe da maƙoshinsa sun zubo ba sai da yaje ya rungumi ƴaƴansa da matarsa sannan. Kuka yayi sosai Iffah na tayasa. Sai da sukayi mai isarsu abin tausayi. Ranar ma har zazzaɓi yayi dole Iffah ta kwana tare da shi da ƴan yaransu da sukaci sunan Ajwaad da Ajwaa (Dan su bawani al'adar suna a sati ɗaya suke ba ba irin ƴan 9ja bane😝). An dai yankama yara raguna da shanu akai sadaka a washe gari tunda ranar mutuwar Malikat Bushirat ta hana. Gida kam ya cika maƙil, ƴan gaisuwa da taya murnar haihuwa ta ko ina ketowa suke. Su Mamy (Daneen Ammarah) sun zo suka kwana itama da cikinta ɗan watanni biyar da wasu kwanaki. Da alama dai zancen Babiy ya tabbata. Ita da Ummu idan ka gansu abin sha'awa kamar yaya da ƙanwa. Sai ma shirye-shiryen bikin Hanash da sukeyi dan shikam ya koma ɗan ɗakin Mamy, Iffah dai na nan ƴar gaban goshin Ummun ta kuma autarta. Dan duk ƙurarta idan ta yaya Ummu dai, itace abokiyar shawararta itace abokiyar sirrinta. Sai an gama Mammy kanji da Babiy. Iyakarsu dariya idan na dariyane. Idan na fatan alkaicine kuma suyi addu'a. Iyyani da kaka kuwa ai dama tuni sun dawo cikin masarautar. Ko yaushe zaka sami Iyyani tare da Malikat Haseenat ne da ƙanwarta Yamma. Tsaffin sun matuƙar haɗe kansu sun zama iyayen kowa. Hakama Kaka da su Sayeed Fayzul-haq sun zama aminan juna dattijan ƙwarai kuma a masarautar kuma iyayen kowa har shi kansa Shahan-shan ɗin....
*_BAYAN WATTANI UKU DA HAIHUWAR IFFAH DA MUTUWAR MALIKAT BUSHIRAT (BIKIN AL'ADA)_*
Kamar kowacce shekara a wannan karon ma tarin al'ummar ƙasar ruman da kewaye sun cika birnin Dahab da akafi sani da DAULAR RUMAN tako ina domin gudanar da bikin wasan al'ada. Kowa ka kalla a wannan karon yasan wasan na musamman ne sannan ana gudanar da shine cikin tsafta da nutsuwa. Duk wani wasan ganganci da za'a iya rasa rayuka an kafa masa doka, hakama matakan tsaro tako ina an baza domin kare kowa da kowa. Duk wani boka ko ɗan bori ko malamin tsubbun an hanasu yin kowane motsi a yanzu. Dama yanzu kam dokane, in har aka kamaka to hukuncin kisa kawai ake yanke maka.
A yau kam Iffah taga mutane da yawa da suka kawoma Shahan-shan gaisuwa. Ciki harda Sir Fawzan da tuni yay aurensa. Tare da yaran Shahan-shan su Azaan da a yau kam sukaita faman sinne kai na kunyar abinda ya faru tsakaninsu da ita a shekarun baya. Ita dai murmushi ma ta dingayi, shi kansa uban gayyar Shahan-shan murmushin yaƙe yi dan kawai ba'a ganin fuskarsa ne. Su Ajwaa da Ajwaad sunsha addu'oi yau a wajen mutane. Duk da ma bawai kowa ake bamasu ba. Yaran sunyi ɓul-ɓul abinsu gwanin sha'awa. To mi yafi ransu suna samun kulawa da tattali da soyayyar iyayensu. Dan zuwa yanzu ma dai kam Iffah ta tattara inata-inata ta koma sashen Shahan-shan ɗin gaba ɗaya ita da yaranta. Dan yace shikam babu wani sashen matarsa da ban nasa daban. Idan ka ganta a sashenta sai in tayi baƙine ko yin wani abun dai tunda babu mai hurumin zuwa sashen Shahan-shan ɗin sai ita. Hatta da amintaccensa ma zuwa yanzu iyakarsa hawa na na uku ne kawai, idan ka gansa a hawan ƙarshen sai ƙwaƙwƙwaran dalili.....
★Alƙawarin ALLAH ya cika akan zartar da hukuncin su Miran Jasim da Miran Arshaan a yau. Dan kuwa wanda ya kashe dole ne a kasheshi. Hatta da malikat Bushirat Tajwar Eshaan ya gama yanke hukunci a yau ɗin zai zartar da hukunci a kanta irin hakan sai ALLAH kuma ya ɗauki ranta kafin zuwan yau ɗin. Sosai al'amarin ya girgiza kowa matuƙa, musamman ganin iyalan Miran Jasim ƙalilan ne a cikinsu suka koka saboda wahalar daya basu a rayuwa. Shi dama Arshaan ba'a ajiye kowa ba. Amma duk da haka Jasrah mai karyayyar zuciya sai da tai kuka. Al'ummar ƙasa sun taru wajen nema musu afuwar ƙarƙashin cigaba da zama a cikin kurkuku tsahon rayuwa. Hakan yasa duk sai jikin Tajwar Eshaan ɗin yay sanyi, dan shima yanajin ɗaci fiye da irin ɗacin da kowa ke ji kasancewar su kaɗai ne Uncle's nasa makusanta da mahaifinsa da suka rage a duniya sai mata. Ganin dai jama'a sun dage ɗin kuma harda iyalan Sayeed Khairul-Bashar da kansu dana Sayeed Hifzur-rahaman ɗin suma yasa aka maidasu cikin kurkukun a bisa sassaucin ɗaurin rai da rai. To saima dai ta ALLAH dan shi Miran Jasim ma bawani cikakkiyar lafiya ce da shi ba. Hatta Miran Arshaan ɗin kansa kawai dai a rufe rufau ne.
Uwa kam da aka fiddo cikin sarƙa cike da ƙarfin iko kowa ke shelanta a kasheta!! A kasheta!!! A kasheta!!!. Kallonsu kawai take tana kuka da dariya da kiran sunayen gumakansu duk a lokaci ɗaya. A haka aka ɗaureta jikin ƙarfen. Mutane zasu fara jifanta da dutsina aka dakatar da su. Dan wannan aikin ba nasu bane na mai gayya da aikine da kansa tare da matarsa. Bayan lafawar kowa fiye da yanda ake buƙata Shahan-shan ya fito hannunsa na dama riƙe da na Iffah, na haggun rungume da Ajwaa da aka canjama gayu ita da Ajwaad. Da shi kuma ke a hannun Iffah. Masha ALLAH aka shiga ambata, dan a zahirinsa ya fito ga mutanensa babu wani shamaki yana son su gansa ya gansu. Haka itama Iffah duk jikinta a rufe amma fuskarta a bayyane ga al'ummar ƙasarta. Bayan sunyi gaisuwa ga al'ummar ƙasar su da fatan alkairi aka kawo kwari da baka na tsire Uwa da zasuyi. Iyyanni da Malikat Haseenat ne da ke tare da su suka amshi twins, yayinda Tajwar Eshaan ya kamo hanun Iffah a hankali cikin nasa yana kallonta ƙasa-ƙasan nan nashi ya tsayar da ita gabansa. Matsawa yay ya jingina jikinsa a nata tare da kamo duka hannayen nata biyu cikin nashi ya saka mata kwarin tare da ɗaga hannayen nasu a tare ya daidaita su sannan ya daidai mashin da zasuyi amfani da shi cikin bakar saitin manya-manyan idanun nan na uwa da ke kwasar dariya da kuka kamar sabon kamu...........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (95 END)
______________
*_MAAB LUXURY HOME._* _Duniyar kayan Kitchen da decoration din gida na keta raini. Ina uwar gida da Amarya, Ku ziyarci shagon mu dake No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook @maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya *08034631010*_.
__________________
..........Wata irin mahaukaciyar razananniyar ƙara ta saki lokacin da kibiyar mashin ke sauka a cikin idonta ɗaya. Kafin ta gama dawowa cikin hayyacin azabar data shigeta suka sake soke ɗayan ma. Tuni jikinta ya shiga matsanancin karkarwa ta cigaba da ihun ambaton gumakansu. Na uku kama sai da suka saita maƙogwaronta sannan suka sakeshi. Kakari ta shigayi irin na mai fitar rai. Yayinda al'umma ke ta faman kabbara. Gaba ɗaya Iffah ta juya ta rungume Shahan-shan tsam-tsam ta fashe da kuka. Hannu biyu ya amshi abarsa ya rungume ko tuna ɗunbin mutanen dake a zagaye da su ma bayayi. Ai tuni jami'an tsaro da Ghazi dake zagaye dasu suka musu zobe, yayinda ƙatuwar umbrella ta musu runfa daga sama. Ganin wannan damar ta samu Shahan-shan ya ɗago fuskar sohaa ɗinsa ya manne lips ɗin sa a kan nata cike da ɗunbin so da ƙauna. Murmushi mai sanyi da ƙayatarwa kawai Malikat Haseenat tayi ita da Iyyani....
Shike nan kuma an shafe da babin Uwar mushirikai itama. Wanda mutuwarta itama kuma yay dai-dai da haihuwar Daneen Ammarah ta samɓalo ƙyaƙyƙyawar ƴarta mace mai kama da babiy. Ai sai bikin al'ada ya cigaba dana murnar haihuwa, yarinya taci suna Arfah. Zo kaga farin ciki wajen Iffah Nina Arfa ɗin ta ta sake dawowa. Daneen Ammarah kuma ta cika alkawari, dan a ranar a gaban kowa ta damƙa Arfa ga Ummu. Ummu tasha kuka matuƙa Mamy na tayata. Daga ƙarshe ta dawo mata da Arfa akan ta bata shawayarwata har yaye. Babiy da Kaka dai nasu murmushi ne hakama Hanash da shima matarsa ɗauke take da ƙaramin cikin itama dan tanata fama ma da laulayi.....
*_BAYAN WASU SHEKARU_*
Abubuwa da yawa sun faru, wasu masu daɗi wasu marasa daɗi. Wasu a tuna wasu baza'a ma iya tunawar ba. Haka rayuwa ta gada dama. Zuwa yanzu kam zamu iya cewa hankalin Iffah da Tajwar Eshaan ɗinta ya kwanta sosai, dan manyan matsaloli dai sun ɗan ragu musu musamman wanda suka shafi tsafe-tsafe da sauransu. Amma na maƙiya kam har goben-gobe a kwaisu. Dan duk inda bawa yake, komai ƙyautatawarsa ya sani akwai wanda su burinsu kawai cin dunduniyarsa. Ƴar uwa karki damu, kamar yanda Bily bata damuwa. Dammu masoyanmu sun wadatar damu😘. Haka dama rayuwar take dole ka kasance a zagayen abu biyu, (Masoya da maƙiya) idan ka kwantar da hankalinka duka sai su amfanar da kai. Idan har MANZON ALLAH da yafi kowa a halitta, ɗan gatan ALLAH zai fuskanci ƙalubale na maƙiya, masu hassada da kushen abinda yazo da shi daga umarnin UBANGIJI kai waye da bazaka samu kanka da irin waɗan nan mutanen zagaye da kai ba. Kai dai kawai yi abinda zaka iya, kuma ƙyautatama duk wanda ke tare da kai maƙiyi ko masoyi duk zakai alfahari da hakan wataran. Wannan shine abinda su Iffah da Tajwar Eshaan suka haƙƙaƙewa rayuwarsu da zukatansu suka zauna lafiya. Sun ajiye komai, basa ganin komai sai kansu da masoyansu. Sun fi kallon masoyansu fiye da tuna maƙiyansu, suna shimfiɗa mulki a tare cikin gaskiya da riƙon amana, randa suka sami saɓani kuma sukan binne a tsakaninsu suyi haƙuri dan yau da gobe sai ALLAH. Duk inda zo mu zauna take sai ka samu zomu saɓa.
Iffah ta ƙara haihuwar ƴarta mace taci suna *_Bilqeesa_* (Dan bazanyi a banza ba sai na ma kaina takwara a ƙasar ruman ehe🥱😂). Ajwaa da Ajwaad sun girma abinsu masha ALLAH. Yara ƙyawawa da ke samun soyayya ga mutane, wasu ko basu da wanda suka tsana kamar su a yanzu musamman ma Miran Ajwaad da kowa kema kallon magajin mahaifinsa. Sai dai kuma babu abinda suka isa yi dan tun ran gini tun ran zane.
Burin Iffah ya cika akan karatu, inda a yanzu haka ta zama cikakkiyar ƴar jarida koma muce shugabar gidan jaridar nan na *African eye* da mijinta ya kafa. A zahirance dai kamar yanda yake ɓoye kansa a baya itama haka take ɓoye kanta a yanzu. Sai dai rubuce-rubucenta da zaƙule-zaƙulen sirrikan munafukai na matuƙar tada hankalin wasu. Dan a duk lokacin da tai wani rubutu game da wata ɓarnar da akeyi koma ta fitar da muryar wasu da abin ya shafa kusan duniya ɗauka take aita cecekuce musamman da ya kasance bayan kafofin yaɗa labarai a yanzu social media ma na taka rawar gani akan yaɗa abu cikin sauri. Sai ta gama zaƙulowa da tallace mutum mijinta kuma gwarzonta ya zama gaba-gaba wajen hukunta mai laifin idan a ƙasar sa ne. Idan ba ƙasarsa bane zai yi duk yanda zai yi ga shugaban da ke shugabanta ƙasar da mai laifin ya fito dan ganin an hukuntashi, cikin ƙananan lokaci sunan da take amfani da shi yay wata irin amsa kuwa, mutane har zalamar jiran fitar wani abu da ga African eye sukeyi, dan sun san mai amfani ne kuma na gaskiya ne. Takanyi ayyukanta a gida, idan kuma fitar sirri ta kama sukanyi ita da Mijinta harma subar ƙasar batare da wani ya sani ba koda a masarautar ne kuwa.
★★...
Ƙoƙarin kamota yake tana zillewa, ya kwaɓe fuska da ɓata rai kamar gaske. Gwalo ta masa da ga inda take tana cigaba da dariyarta mai narkar da shi.
A hankali ya furta, “ALLAH Sohaa karki bari na kamaki, kizo nan na yarda zamu raba 50-50”.
Kafaɗa ta maƙe masa tana mar-mar da idanu da tura baki gaba. Fuskarta a shagwaɓe ta ce, “Naƙi wayon sai dai na baka 30 na ɗauka 70”.
“Tunda na fara jin tsoronki ko?”.
Ya faɗa cikin ɗage gira sama. Baki ta ɗan murguɗa masa itama. “To dama ai tun tuni tsorona kake ji”. Murmushi ne ya suɓuce masa, shi baima san yanda zaiyi da tsiwar yarinyar nan ba. Fitinanniyar yarinya ce ta bugawa a jarida, yara uku har yanzu bata san ta girma ba. Hannayensa ya tura cikin aljihunsa wandonsa har yanzu fuskar tasa da murmushi ya nufeta. “Okay shikenan na yarda 30-70 ɗin, sai dai yanzu yarana najin yunwa zo muje a fara cin abinci amma da sharaɗi”.
“Nami?”.
Ta tambaya tana matsawa da baya-baya. Tana ganin ya kusa isa inda take tai yunƙurin sake zurawa da gudu. Wani ɗan tsalle yayi ya cafkota, bai saurari ɗan ihun da take masa na taɓara ba ya murɗe hannun ya amshe ɗan box ɗin dake cikin hannun nata. Cak ya ɗagata ta shiga watsal-watsal da ƙafa. Dariya ya shigayi ganin yanda take kukan taɓara da faɗin ita sai ya bata abunta. Sai da ya zauna akan kujera ya ɗaurata a kan cinyarsa sannan ya dungure mata kai da faɗin, “K yarinyar nan rigimarki tayi yawa, wai nida abuna”.
Da sauri tace, “Nawa dai, dan 30 ne naka a ciki”.
“Tun kan kiji sharaɗin nawa ma kin yanke hukunci”.
“Ka faɗi sharaɗin mana banga wanda bazan iya ba”.
“Okay haka kika ce?”.
“Eh”.
Ta faɗa cike da ƙarfin gwiwa. Murmushi yayi ya ce, “Okay muje a fara cin abinci mu dawo zamu gani ai”.
★Kamar ko yanda ya faɗa yaransu na zaune a falo zaman jiran fitowarsu. Balqeesa dake tsalle-tsallenta ita kaɗai da gudu ta nufesu, a hankali ya kai duƙe fuskarsa da ƙayataccen murmushi dan a rayuwarsa yana matuƙar ƙaunar yaransa, bai haɗa su da komai ba. Hakan kuma bai hanashi tsayawa akan tarbiyyarsu ba. Mulkin al'umma kuma bai hanashi shaƙuwa da su ba, rungumeta yayi tare da miƙewa da ita a hannunsa duk da kuwa takai shekaru shida a duniya. Cikin ƴar muryarta ta ce, “Abbie ina sonka kai da Ammie”.
Idanunsa ya lumshe fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce, “Muma muna sonku mai gadon zinari na”.
Sosai yarinyar ta ƙanƙamesa tana dariyar jin daɗi. Kallon juna sukai shi da Iffah suna murmushi. Dai-dai nan Ajwaa da Ajwaad suka iso garesu suma. Yara masu nutsuwa da shiru-shiru kamar mahaifinsu. Suma hannu ya miƙa musu alamar suzo garesa. Fuskokinsu ɗauke da murmushi suka rungumesa. Baki Iffah ta zumɓira ita a dole taji haushi. Murmushi yayi itama ya mata alamar tazo. A hankali ta matso jikinsu tana murmushi ya haɗesu gaba ɗaya ya rungume........✍️
*_🥱To nima dai na haɗaku gaba ɗaya na rungume masoyan albarka ababen alfahari. Alkairin ALLAH da rahamarsa da ni'imarsa sukai gareku ku da zuri'armu baki ɗaya._*
*ALHAMDULILLAHI🙏*
_Ya rabba na gode daka kawoni wannan rana badan iyawata ba ko dabaruna. Ina roƙonka ka yafemin kurakuraina, abinda ya kasance dai-dai a cikin wannan ɗan littafi ya rabbi ka haɗamu a ladan. ALLAH ka amfanar damu amfanin cikinsa, wanda ya kasance mai cutarwa ALLAH ka hanashi tasiri a zukatanmu.🙏_
Bazan gaji da faɗa ba. Rubutun nan nishaɗine. Fadakarwa ce. Wani lokacin ma harda ban haushi. Wasu abubuwan akan saka ne kawai domin ayi nishaɗi. Ina roƙonku yin watsi da duk abinda bamai amfani ba a ciki.
_Mungode! Mungode!! Mungode masoyan Zafafa. Alkairin ALLAH ya kai gareku, yanda kuka kasance damu kuma ALLAH ya kasance daku cikin rahama da amincinsa. Yanda kuka somu domin ALLAH kuma ALLAH ya soku haka❤️❤️🙏_
*_Yanda muka fara lafiya muka kammala lafiya ALLAH ya haɗamu ana gaba cikin lafiya da nutsuwar zukata. Wanda duk naima kuskure ko ba daidai ba dan ALLAH ya yafemin a yayin wannan rubutun ajizanci ne banda burin ƙuntata kowa koda da magana ne🙏. Ngd Ngd sosai masoya ƴan DAUƊAR GORA CONVERSATION, ku ɗin na dabanne a cikin daban gareni. Alkairin ALLAH ya kasance daku a duk inda kuke. Ku na dabanne a zuciyar Bilyn Abdull 😘😘Nikam kune Sohaas ɗina TAURARINA⭐._*
*Bilyn Abdull ce 😘😘🙏*
*_ƙaunarku nake irin trillions ɗin nan🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰😘😍😘😘_*
_🙈🙈Yau sunan magena har yanzu banga kun fara kawo kayan Barka ba 😂😂 fa. Bye bye idan na mutu da ga nan kowa ya yafe min🙋🏻♀️🙋🏻♀️🙋🏻♀️😭🙏🏻_