Chapter: 66
Daudar Gora Part 1 Complete Hausa Novel · about 55 min read
."UBANGIJI ya halicceki mace bayan akwai maza da yawa dake kwaikwayo son zama macen amma basu isa komawa ba. Ya halicceki kyakykyawa, bayan awai wasu da yawa da kyawun da bai kai naki ba suke fafutukar nema ta hanyar sabama UBANGIJI suna amfani da abinda yace haramunne garesu. Ya baki lafiyar jiki babu ta inda kika nakasa. Bayan ga dubunki can su nakasar itace jarabawarsu. Ya baki lafiya
matsayinki na yar adam. Bayan ga dubunki can kwance a asibitoci da gidaje basu da kudin shan magani, masu kudin ma basu isa iya sayawa kansu lafiya ba koda sun kai karuna dukiya. Ya azurtaki cikin nagartaccen addini, bayan ga dubunki can na bautar wanin ALLAH cikin batan da su a karan kansu basu san bata bane ba. Ya azurtaki da tarin dukiya. Bayan akwai dubunki da abincin yini daya ma gagararsu yake ci saboda basu da kwabo na saya. Ya azurtaki a cikin katon gidan aure dana haihuwa, karkashin kyakykyawar nasaba bayan akwai dubunki da a kan titi ko cikin bukka suke rayuwa badan kin fisu ba. Ya azurtaki da karfin iko na mulki, bayan akwai dubunki da su wanna matsayin naki suke kwadayon kaiwa, ke wasu ace ma su din hadimanki ne kawai farin ciki yake sanyasu. Ya azurtaki da ilimin addini dana zamani, bayan akwai dubunki da suke zagaye da jahilci, wasu ko suna son karatun rashin mai tallafa musu Yasa suka hakura suka zama masu aikata miyagun laifuka koda zukatansu basa so, sai dai basu iya banbance abinda ya dace da wanda zai dace da tasu rayuwar. Ya azurtaki da da daya tilo tamkar da dubu da nagartaccen mijin da duniya bazata taba mantawa da su ba, bayan akwai mata da yawa da su jarabawarsu mazajen aurensu ne da yayan da suka haifa. Duk da ya miki wadannan abubuwane badan kinfi sauran halittun duniya ba. Badan bazai dandana miki mutuwa ba. Badan bazai iya jaraftarki ki kasance su ba. Badan kinfi karfinsa ba. Sai dan kawai ya miki talala har zuwa ranar da zaki tabbatar ke din bakomai bace a cikin komai. Ke din yar adam ce, yar adam din nan da aka halitta da ga yunbun kasa, yar adam din nan mai rauni, mai barci, mai kashi, mai ciwo mai jiran kwanakin mutuwa. Badan kiyi alfahari da duk wadan nan abubuwan ba kuma ya halicceki, ya baki su ne domin jarabawaki itace su, kamar yanda ya bama wasu sabanin naki domin jarabawa suma. Dan ALLAH mi kike bukata a bayan duk wadannan? Minene burinki da fatanki da fafutukar ki da har halaka rayuwar yayan wasu ke sakaki a farin ciki amma baki son ko kuda ya rabu daya naki tilo da sunan cutarwa? Ke uwa ce, ya kamata kiyi hasashen zafi da ciwon da zaki iyaji dan akace babu wannan tilon dan naki kafin idonki ya rufe ki zama sanadin hana wasu. Ni Fhareedah bint Zayyan b yafe daukar fansa ki shaida haka, bakuma zan gajiya da fada miki na, amma ke uwa ce ina mutuntaki da wanna matsayin, dan ba'a bani tarbiyyar raina koda wanda ya girman da kwana daya ba a duniya balle ke da nasan zaki iya haihuwar wanda ya haifan musamman ace Maleek mace yazo ba namiji ba. Sannan koba komai kin haifamin gwarzo kuma barden miji da tun kan bakina ya tabbatar da alfahari da shi gabbaina isarwa suke. Shi mutum ne adali, mai addini, mai yawan bautar ALLAH da mika masa lamuransa. Baya jin wani alfahari da matsayin da ALLAH ya bashi kamar ke face takatsantsan dan yana kallonsa a matsayin jarabawarsa. Akwai tarin abubuwa masu dunbin yawa da nake bincikawa akanki da alakarki da halaka yaran mutane, idan kikace zaki cigaba da bina da izzarki why why Ammie baza'a ganeki ba. Ki bini a sannu-sannu ni zan kaiki inda kike son zuwa bake zaki kaini ba. Kamar yanda ni na kawo kaina masarautar nan bake kika kawoni ba. Kamar yanda ni nai amfani da Arshaan da Jasim da Haifah basu sukai amfani da ni ba, ke shaidace kuma ga irin makomar da suka kasance duk da somin tabi ne ma na fara musu.Kamar yanda ni na bama Shahan-shan din da kike takamar da shi garkuwa bashi ya bani ba har kike hakilo da hura hancin wai ya janyeta gareni.Kin san ALLAH kiyi maza ki dawo hayyacinki ina tsoratar miki shiga jerin mutanen da zan kwancema zani a bainar nasi cikin Masarautar nan dank kuma ya musu hukunci, kiyi azamar ajiyewa ki labe bayan mutuncin danki hukuncina ya kasance tsakanin ni da ke ne kawai. Dan saura kiris a fara bankada, idan kuma aka fara akwai gagarumar matsala, dan na fahimci ke kanki har yanzu baki gama sanin wanene danki ba da ainahinsa, kinama rogo kallon kitsene kawai, sannan kina kallon kasurgumin Zaki ne da fatar mage" ta saki murmushi tare da takawa gabanta a hankali. Hannunta ta kamo ta daura saman cikinta, "Ina tayaki murna da albishir din insha ALLAHU kafin mu dawo daga hutun in amarcinmu da iznin UBANGIJI zamu dawo da jikanki a wannan babbar garkuwar, dan haka kibar wahal da kanki akan sai Maleek ya auro wadda kike son ta haifa miki shi dole ko nisanta shakuwar iyayensa da zata zama sanadin samar da shi ta hanyar madara. Da ga kuma randa kika tabbatar da samuwarsa, ki fara irga kwanakin nadamarki da dana sani har zuwa ranar haihuwarsa. Hukunci da karfin ikon Iffah a saman naki, yanzun ne zai fara Mother in-law". Ta dan kyalkyale da dariya da sakin hannun, yako tafi yaraf alamar duk wata mahada mai motsi a jikin Malikat Bushirat din ba aiki take ba a yanzu. A hankali ta koma kasa kusa da kafafunta ta zauna, tare da hannu ta dago afar ta fara matsa mata. Zabura Malikat Bushirat tai kamar wadda aka kodama mari ko ta suma aka zubawa ruwan sanyi drum guda, sai hakan kuma yay dai-dai da shigowar Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed. Yar dariya Iffah tai kamar bata san da shigowarsa ba ta cubi Malikat Bushirat din. "Ammie irin wannan zabura haka na sake tabo wajen da yay dayin kenan?".
Idanun Malikat Bushirat ne suka sauka akan Tajwar Eshaan din dake takowa a nutse idonsa a kansu fuskarsa da dan sakewa. Sai dai kafin ta iya cewa komai da ga daurin goro ko makircin Iffah zatace mane oho Tajwar Eshaan din ya karaso yana dan gyaran murya. Dagowa Iffah tai ta kallesa har yanzu fuskarta da murmushi. Cikin yar shagwaba ta ce, "Yauwa ai garama da kazo, Ammie na nan zata kasheni da dariya, tace fa na matsa mata kafarta ya mata dan nauyi saboda zaman waje daya amma da nayi- nayi sai ta fara fadin ya isa a bari ta huta".
Wani dan moso yayi iya lips yana dauke idanunsa da ga kallon da yakema Iffah'r na kasa-kasa ya maida kam Malikat Bushirat da mamakin duniya a makircin matsiyaciyar yarinyar ke neman dauke numfashinta. A hankali
cikin dan sanyin nan nasa da kamewa ya ce,
Ammie shiyyasa nace ki dinga motsa jiki tun last year, wannan zaman waje dayan da kuke ai ba gata bane, gashi nan shi ya kashema Jaddah kafafu anata fama".
Da kyar ta iya dannewa ta dan saki murmushin karfin hali da yafi kuka ciwo ta ce.
"To ya za'ayi Saiful-malik, mizamuyi da wani motsa jiki a wannan shekarun namu?".
Kafin ya bada amsa Iffah ta amshe da fadin, "Ai Ammie kike da motsa jiki kuwa, dan motsa jikin nada amfani sosai, kuma ya kamata ko dan cikin badda kama kuna fita kwamaga yanda talakawan kasa ke yan sabgoginsu, sannan koba komai ai hakama karin imani ne da lafiyar jikin harma da ta zuciya".
Wani irin ji Malikat Bushirat tai kamar ta shako wuyan Iffah, dan ta fahimci maganace cikin ta jefa mata. Itakam ta farama tunanin anya yarinyar nan mutumce kuwa ba aljanaba a sufar mutane? Ya kamata a bincika mata kam dan al'amarin ya fara girman tunaninta. Amma a zahiri sai ta cije tai dan yake. Tajwar Eshaan da ke dan jinjina kai batare da ya fahimci komai ba shi kam a zancen idanunsa dake akan Iffah ya lumshe kadam da budewa lokaci guda. "Ammie shawaran nan nata mai kyau ne, ni kaina naso na miki tayin hakan tuni sabgogina basu barni na zauna ba. Amma Alhamdullah tunda gata yanzu bayan ni da Aunt kin sake samun diya daga ALLAH nasan zata kula mana da ke kamar mu din. Sannan kusantar al'ummar mu yanda ya kamata a zahirance zai kara saka mana son su da kaunar su a zukata kamar yanda ta fada. Zakiji dadin hakan, ki samu lokaci ki fara gwadawa koda tare da itane ni mai yarje muku ne".
"Uhm kai dai. To ALLAH ya shige mana gaba kawai".
Amin suka fada a tare shi da Iffah, sai dai a ransa yasan bata amshi lamarin ba. Dan haka ya basar da zance ya dakko mata na tafiyarsu.Cikin mamaki take kallonsa sai dai batace komai ba. A ranta kam wani irin zafi takeji mai kuna. Har itace sai yau Saiful-malik ke sanarma zaije Umrah, Umrah din ma na azumi baki daya. Kai anya bata fara rasa danta ba kuwa? Bata fara rasa danta daga jikinta ba kuwa? Jifa maganganun da yarinyar nan ta fada mata a yanzu, irin wanda ko mahaifiyarta sanda tana a raye bata jin ta taba fada mata su, amma shi ya hau ya zauna Kamar ma bai fahimci manufarsu ba. Tabbas akwai matsala, matsala babba da uwa sam bata lissafo ba a lissafinta. Yanda fa rawar take neman canjawa dole ne shima kidan ya canja inba hakaba zata kona Masarautar nan ne baki daya why, dan bazata dauki faduwa a saman nasararta ba. Never for ever……..✍️
DAUDAR GORA
Book 2
67
…. Suna barin sashen cikin tashin hankali tashige ciki tai kiranye uwa. Cikin kankanin lokaci kuwa sai gata ta bayyana alamar dama a kusa take. Ido rufe Malikat Bushirat ta zayyanema uwa duk abinda ya faru tsakaninta da Iffah. Yanda uwa ke huci sai ya koma tsorata Malikat Bushirat din, tuni nata fushin da harzukar suka bace. Zabura tai gefe jin sautin kakkausar muryar uwa mai tsananin amo acikin
kunnenta.
"Wannan fadan ba naki bane damu takeyi!!! Lallai damu takeyi. Ita wacece? Yar wacece? Mitake takama da shi?! Zan tabbatar da ba uwarta kawai ba, hatta dukkan ahalinta sai sunyi nadama da dana sanin kasancewarta jininsu!!!!. Wanda suka fitama sunja bata kai musu ba balle ita haihuwar jiya-jiya.".
Ta fada cikin wani irin karaji da dukan kasa da tafin hanunta, tare da rantsuwa da wani kasurgumin gunkin da take bautawa wanda sam Malikat Bushirat ita bama ta fahimta ba. Ji Malikat Bushirat din tai hatta dakin girgizawa yake, tamkar tashin guguwa uwa ta bace bat a dakin. Wani irin numfashi ta sauke mai nauyi, tare da zama jagwaf. Ta jima numfashinta na kai komo kafin ta samu daidatonsa, sai kuma ta saki murmushi mai matukar kayatarwa da dan tabe baki ta dage kamafada irin ko'a jikinta din nan,wanna kuma fadan yimata shi za'ai.
Ni dai nace, "Humm" 🥱😂🚴
*. WASHE GARI*.
Kasancewar ba' a ga wata a jyan ba basu wuce ba. Hakan sai ya saka Iffah yini a sashen Malikat Haseenat. Sai bayan sallar la'asar ta dawo. Lokacin su Tajwar Eshaan da was manyan masarautar na'a can saman ginin da agogon da duk ta inda ka bullo ta birnin Dahab City din zaka gansa da na'urorin ganin wata, Cikin amincewar UBANGIJI kuwa sai gashi an gansa, Dan danan kafofin yada labarai suka fara sanarwa da yawn Shahan-shan, dan shi da kansa yake duban wata tun hawansa mulki babu wani wakili.
Alhamdullah washe gari an wayi gar da azumin watan Ramadan a bakunan mutane. Yayinda jirgin Tajwar Eshaan da Iffah sai hadimai hudu mata shida maza. A ciki akwai hadiman sashen Malikat Haseenat da Iffah ta roka ta bata su su biyu har da hadima Banou. Lokacin da akace mata zatabi Iffah rikicewa tai harda kukanta a boye. Sal Diwa amintacciyar hadimar Malikat Bushirat ta zahri, wadda itama dai Iffah!r ce ta nema ta bata a gaban Tajwar Eshaar babu yanda ta ya ta bata, sai hiyu da suka kasance daya a cikinsu hadimar da Uwa tace zasu batane samun wanna damar yasa suka cusata a ciki.Tafiyace ta sirri dan haka babu wanda yasan da ita a Kasar, ko'a cikin masarautar a ba kowa ya san da Shahan-shan din za'ai ba. Kowa ya dauka Iffah'r ce kawai zatai gaba kafin su Malikat Haseenat da ake hasashen kila sue su samesu acan tunda suma sukanje duk kusan bayan shekara uku, tun bayan hawan Tajwar Eshaan din kuma sau daya sukaje,shiko tunda ya hau mulkin ma bai taba ma zuwa ba sai yanzu.
Lokacin da jirgi ke barin kasa wani irin kudindinewa Iffah tai a jikinsa na toro. Ta bashi dariya dan ya fahimci duk irin abubuwan nan tsoronsu takeji. Ga Elevator ma in zata shiga yanda take kasancewa balle kuma anan, tafa gwammace tabi stairs duk wahalarsa idan ita kadai ce. Rungure kayarsa yay dan su kadai ne, hadiman na nasu sashe daban. Koda jirgin ya gama dai-daita bata bar jikin nasa ba: sai ma barci da yay awan gaba da ita mai nauyi. Ajiyar zuciya ya saki yana mai sumbatar idanunta. Azuciyarsa ya ce, (Fitinanniyar yarinya nima nadan huta da surutunki) a zahiri kam sai ya gyara mata kwanciya nutsuwa na sake saukar masa. Shi kadai yasan kaunar da yakema yarinyar nan, ALLAH dai yasa karta zama ajalinsa.
😂Oh oh masoyan asali. 😉
*_SAUDI ARABIA_*
Mamaki hade da al'ajabi ne ya mamaye Iffah lokacin da suke fita a cikin jirgin hannunta cikin nasa. Wasu zuka-zukan motocine na alfarma da tawagar masarautar Saudiya, yayinda Sultan a Saudiyya ne da kansa yazo tarbar Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed Ally Qutb ba sako ba. Cikin farin ciki sarakunan biyu masu karfin fada aji a duniyar musulinci suka tarbi juna. Sam Tajwar Eshaan bai saki hannun Iffah ba har suka rungume juna da Sultan din. Bayan sun saki junan ne ta dan rissinar da kanta alamar girmamawa ga Sultan din.Fuskarsa kawance da murmushi yay mata kallo daya da musulunci ya shardanta ya dauke kansa. Ya fai mata barka da zuwa DAULAR MUSULUNCI cike da mutuntawa a gareta duk da yasan zai iya haihuwarta. Dan manyan yaranta maza twins guda biyu suma bazasu wuce 20years ba karnar Iffah'r..
A hankali ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe idanunta jin sanyin ac da kamshi mai shegen dadi ya ratsa hancinta lokacin da suke shiga daya daga cikin manyan motocin da sukazo tarbarsu. Dubanta Tajwar Eshaan yay tare da rungumota jikinsa da kyau. Tako late kamar yar mage tana shakar daddadan kamshinsa. Ashe Iffah ba komai ta gani a airport din nan ba. Sai da suka shiga babbar daular da lissafin dukiyar cikinta ma da kawatuwa bata lokacine. Tabbas tasan Daular ruman ta had, irin haduwar da babu wanda zai shiga bai yi santi ba. A tunaninta da anya akwai makamanciyar irin daularsu a duniya? Amma a yau ta tabbatar akwai, dan duk da daular Saudiyya bazatafi tasu ba, suma tasu bazata fita ba, dan nan clin ma dai badaga baya ba Dan in za'a baka zabima zaka ya kasa banbancewa ne tsabar shiga
rudani.
An musu tarba ta mutuntawa da tsantsar girmamawa, tare da masauki dan gaske da ko'a kasarsu iya abinda zasu iyama kansu kenan. Tattare suke da gajiya, musamman I/fah daba sabawa tai ba ga kuma azumi, saukin ma farkon farawa ne. Da kyar ya lallabata tal dan wanka ta kwanta. Kafin kace mi barci yay awan gaba da ita.
Bata samu kanta ba sai la'asar, shima da kyar ya tadata sanda zai wuce massalaci. Bayan ya dawo yace ta shirya zasu wuce madina ne da ansha ruwa, da ga haka ya fice ita kuma wasu mata sukazo mata da kaya inji matar sultan. Sun jirata ta shirya sukai mata jagoranci zuwa sashen matar sultan din, inda ta samu tarba ta mutuntawa da har ta dinga jin kanta ya kara girma itama a yau. Dan duk da matar sultan din ta girmeta sosai janta ta dinga yi a jikinta cike da kulawa harda cewa itafa tana so ta saki likinta da ita ne dan sun zama kawaye. Murmushi kawai Iffah tayi mai sanyi. Ta wani nutsu kamar ba Iffah'r nan mai shegen surutu ba mai addabar Tajwar Eshaan. Magana ma an koma amsata ne dai-dai cikin nutsuwa da kamewa ita a dole ga matar Shahan-shan na kasar ruman (Ashe akwai a inda bakin Iffah zai mutu haka (😂). Suna a tare har aka sha ruwa, a tare suka gabatar da sallar magrib sannan suka fito kayataccen falo karami na musamman da aka shirya musu kayan alatu na shan ruwa. Daga ita sai uwargidan Sultan da Shahan-shan din ta. Sai wani irin binta da kallon nan nasa na kasan ido yake kamar zai hadiyeta dan ta masa matukar kyau cikin kykyawar bakar abayar data haske farar fatarta ga walwalin fararen duwatsu da akai mata ado dasu. Itama dai uwargidan Sultan irin kayanne a jikinta. Haka shima da Sultan din kayansu iri gudane. Lallausar farar jallabiya mai tsadar gaske an daura bakar alkyabba da akaima adon golden da mayafi fari tas a saman kawunansu. Kamshi dai nasa ne, dan daga su sai turarrukansu sukazo kasar. An sake gaisuwa irin ta manyan attajirai masu mulki da karfin iko, sannan a nutse sukai buda baki mai sauki (ba irin na su bily ba da sai anji ciki yay nak babugurin tura kosai 🥱), Karancin lokaci ya saka sarakunan biyu mikewa zuwa gabatar da sallar isha'i. Suma kuma su Iffah suka kora bedroom din uwarg/klan Sultah suka gabatar da tasu. Suna idarwa basu zauna ba, dan tafiya tsakanin nan da Madina akwai nisan gaske, dan ma lafiyayyun motocine. Sai lokacin Iffah ta san ashe tare da Sultan din da matar tasa ma zasu wuce. Tofa wayaga in da ranka kasha kallo, dan kuwa dal acikin zukekiyar motar da zasuyi tafiyarma dai an shirya musu abincine, ga an shiryar motar daga aiki kamar wani daki ha musamman. Iffah dai da al'amarin ya zame mata sabo ga kauyanci ga son nuna class t3, haka mutunivar tamu akaita basarwa kamar komai ba komai dai kun gane ai 😉(Kuka yarda naje gurin nan alkur'an sai na nuna hali, dan kowa sai yasan Bilyn Abdull daga 9ja nazo 🤣😆🚴).
A yanzun kam sarakunan biyu sun baje filin hirarsu a nutse ga matansu a gefensu. Har takai ita dai Iffah ta fara ma hamma. Cikin mamaki Tajwar Eshaan yake mata kalion nan nasa na kasan ido, dan ya fara sakama yawn barcin nan nata alamar tambaya. Abu kadan ta fara hamma, yanzu zata tashi anjima kadan ta sake kwanci. Kuma bazaka taba ji tace barcin yaisheta ba. Anya kuwa? (Sa a bincika mana mai rumawaja🚴).
* MADINA BABBAN BIRNI BURIN ZUWAN DUK WANI MUSULMIL*
Duk da dare yayi kai tsaye massalacin MANZON ALLAH (S.A.W) suka wuce, inda nan ma suka samu tarbar da ga shugaban garin na Madina da tawagarsa cikin girmamawa ga Sultan din nasu a Saudiya gaba daya da kuma babban bakonsa shugaban kasar ruman. sai da suka gabatar da salla raka'a biyu sannan sukai zaman jira karasawar lokacin asubahi Basu bar mascalacin ba sal bayan sallar asuba. Yanzun ma dai wani katafaran gida aka kaisu. Gida daya amsa sunansa gida bawai muna gida ba. Gajiyar da ke tattare da kowa yasa ruwa kawai suka watsa kowa ya kwanta musamman ma Iffah dake jin kamar zatayi adungure tun a massalaci…..✍️
DAUDAR GORA
Book 2
68
...……….Lokacin da azhar ta gabato Tajwar Eshaan ya tashi yay wanka ya kimtsa babu alamar Iffah zata motsa, kwance take sharkaf tana kwasar barci kamar wadda ta mutu. Zama yay a bakin gadon ya zuba mata ido, tare da kai yatsunsa saman goshinta da wuyantan amma babu alamar wani zafi da ke nuna tana a cikin ciwo. Da kyar ya tadata tana faman tura baki gaba, ya kafeta da kaifafan idanunsan nan, sake tunzura bakin tai ta kauda kai. Sai shima ya dan girgiza kan a fusge ya furta, "Ki daina turamin wannan bakin na dinga kai azumina lafiya batare da ya raunana ba. A haka za'ai ibadan Nigar?".
Kwalkwal tai da idanunta kamar zata saki kuka tace, "Nima zuwa fa barcin kawai yake, konace bazanyi ba sai na kasa". Shi dai kallonta kawai yake zuciyarsa na raya masa abubuwa masu yawa. Amma sai bai furtaba ya ce, "Okay tashi ki shirya muje massalaci ga su Sultan na jiranmu". Babu yanda ta ia dole ta tashi ya taimaka mata ta shirya din, dan a hakan ma sai faman lumshe masa idanun take da sakin hamma. Shi dai lallabata yay suka wuce dan ya fahimci abin bana lafiya bane. Kilama Aljanun nata ne ke sakata barcin dan kar tai ibadar....
(A gurguje Please munada sauran aiki, gashi nagaji walle. Gara muyi mu gama kowa ya huta 🏃♀️).
Rayuwa a Saudiyya wani rubutaccen al'amari ne da Iffah bazata taba mantawa da shi ba a rayuwarta, dan rubutaccen labarine tsakaninta da Maleek dinta mai zaman kasan ga ma'abocin bibiyar labarinta, amma ta tattara ta killacema zuciyarta kawai kuma sai ku kiyasta da hasashenku. Duk da dai ta samu nakasun raunana a dalilin barcin da bata san kansa ba balle karshensa. Amma duk da haka tana matukar yaki da shi da ganin tayi cikakkiyar ibada. Dan abu mafi birgeta shine yanda Tajwar Eshaan ke tsaye akan kafafunsa koda yaushe babu wasa tattare da shi ko nuna gajiyawa a dare da rana. Gaba daya ya maida hankalinsa a bautar Sarkin sarakunan nan mahaliccin duniya da kayan cikinta, mai rahama da mukullin aljanna. Sarkin da babu kamarsa kai koda kwatankwacinsa ma babu. Gaba daya ya mika lamuransa garesa cikin kaskantar da kai da zubda gwiwunsa bisa kasa. A duk sanda yake addu'a zaka samesa da hawaye share-share da inba gaban UBANGIJINSA ba bazaka taba gani ba. Kullum cikin gayama ALLAH yake kan samun warwarar al'amuran da suka shige masa duhu musamman akan mutuwar yaran da basujiba basu gani ba a daliln aurensa. Duk da wannan jajircewar tasa kuma yana bata kulawa a dan kankanin lokacin da suka daukarma kansu na hutawa. Dan ko bayan kammala Umrah din su bai lamunce su zama a karkashin inuwar lalaci ba.
A gefe kuwa wata Irin shakuwace ta shiga. tsakaninta da uwargidan Sultan. Mace hamshakiya ma'abociyar kyawawan halaye da nuna tsattattacen iko saman na kasa da ita. Nutsuwa sosai Iffah tai tana koyan abubuwa, yayinda itama bata tsaya boye-boye ba ta fito tana gyarama Iffah'r duk abinda zai bata martaba da kima a wajen mijinta da al'ummar da mijin nata ke shugabanta. Dan tayi dubi ne da karancin shekarun Iffah'r da ma labarin data bata na cewar ita iyayenta basu da alakan mulki. Ba halayyar Iffah da dabi'u ba hatta jikinta wani irin gyara yake samu na musamman ga uwargidan Sultan din.
Hadimanta kam tunda sukazo bata gamsu sun ganta sau cikakken biyar ba. Hakama duk dokinta da tsammanin zal hadata da su Babiy tunkan su taho babu alamar zai yi hakan. Har magana ta masa cikin hikima amma sai baice mata komai akan hakan ba. Dole ta hadiye komai ta nuts bisa shawarar uwargidan Sultan din.
Shanyewar tai kuwa, dan yanzu Iffah an koyi halin dattako da shanye abu a ral, sai dal fa à gaban Tajwar Eshaan bakin baya mutuwa, idan kin jita shiru barci take, a lokacine kawal zai huta da tsiwarta.
Alhamdulillah yau an kai azumi na ashirin da shida, a yau ne kuma su Iffah sukayi ziyarar bankwana cikin dakin ka'aba ita da Tajwar Eshaan da Sultan na saudiya, da uwargidansa, sai wasu manyan masarautar tasu. Iffah tasha kuka lokacin da taganta cikin tsakkiyar dakin ka'aba, Abune da bata taba zaion kasancewarga ba koda a cikin matarkinta. Kal ita ketare kasar ruman ma bata taba zaton tana da rabon yi ba a rayuwarta. Amma yau sai gata da kwanaki ashirin da biyar cikin kasar Saudiyya, tare da mijin aurenta shugaban kasarta. Hannunta kawai ya rife cikin nasa alamar lallashi har suka fito, suna shige mota kuwa ta fada jikinsa ta kankamesa. Murmushi yay mai sanyi da dagota yana mata yan harara tare da lakace mata hanci. "So kike ki karyamun azumi ne?"
Baki ta dan tura tana wan kikkitata Idanun dake cike da hawaye, a shagwabe tana war idanun da yanayin mamaki ta ce, "Dama maza azuminsu a karyewa ne?". Murmushi kawal yay ya dauke kansa, sai kuma ya sake juyowa a yanayin wanda ya tuna wani abu, kallonta yay da ga sama har kasa kafin ya jeho mata tambayar data daure kanta da bata yar kunya-kunya. "Mrs Eshaan kin sha wani magani ne dan kar kisha azumi?". Da kunya-kunya mamaki-mamaki ta dubesa, sai kuma ta girgiza kanta alamar a'a. Itama kuma sai kirjinta ya shiga harbawa da sauri-sauri. To al bama watan azumi kawal ba, idan bata manta ba rabonta da ganin proud din ta fa kamar tun wanda ta gama da kwanaki kadan ya ziyarceta bafa ta sake ba. Kai kodai ta sake ta manta, to idan ma ta sake din ai a watan nan ne na Ramadan ya kamata ta gani farkonsa, juya mata kanta ya fara yi saboda neman takurama kanta da tai na sai ta tunano. "Kinga relax karki takurama kanki"., Ya fada a hankali yana kwantar da ita a kujerar.Gaba daya jiyay yama kagara su koma cikin masarauta, suna isa kuwa masaukinsu aka zarce da su. Duk da an bude mata kamar yanda aka bude masa kofa shima sal ya fito da ita ta inda ya fita, basu fi zaman mintuna goma ba doctor din da ya bukaci gani ya iso tare da uwargidan Sultan da hankalinta ya tashi da tunanin ko kukan da Iffah tayi ne ya zame mata matsala,
ita Iffah sai ma abin nasu ya bata mamaki da dariya,ta kal dubanta ga Tajwar Eshaan da yay zaman kasaitar nan tasa. Cikin langabe kai ta masa magana da ido alamar wai mike faruwa? Dauke kansa yay gefe a ransa shi kadal yasan miyake ji na farin ciki, ya kagara doctor din tace wani abu. Amma a zahiri baka isa fassara abinda ke ko"a kan fuskarsa ba balle zuciyarsa. Doctor da tai yan gwaje-gwajenta a gabansu abinka da gidan manya ta dago tana murmushi, cikin girmamawa ta fuskarci uwargidan Sultan ta mika takardar da tai yan rubuce-rubuce.
"Ya ALLAH"
Uwargidan Sultan ta fada fuskarta da kayataccen
murmushi. Ta kai dubanta ga Tajwar Eshaan da ke jin kamar ya fisgo takardan hanuntan amma ya dake a zahiri. "Ina mai farin cikin kasancewa ta biyu bayan doctor akan sanar muku samun karuwa da mukai, ALLAH ya sauki Zawjata-almilk lafiya". Wani irin lumshe idanunsa yay da sauke sassanyar ajiyar zuciya kamar wanda aka zarema numfashi. Yayinda Iffah tai fakare tana kallonsu cikin rashin fahimta sam. Dan ita kanta ma sat ya toshe kawai a wanna gabar. Har suka gara bidironsu Uwargidan Sultan ta wuce bata iya tofa komai ba..
Wani irin dagata yay bayan ficewar kowa a falon ya shiga juyi da ita. Kawal ita sal abin ma ya bata dariya ta shiga kyalkyalawa. Bai hakura ya direta ba sai da yaga ta fara date kal alamar jujuyatan da yake akwai matsala. A tare suka dinga sauke numfashi, ya tsareta da idanun nan nasa masu kaifi ga kayataccen murmushi mai matukar tada da yakan dace baka gani a fuskarsa ba, Sal dal kuma a zahirance bakin ya gagara cewa komai. Sal da ya mula dan kansa a hankali ya furta "Mrs Eshaan kin mallakeni da komal na. Da gaske fa ni din bawanki ne". Da sauri tasa hannu ta rufe bakinsa tana zaro idanu da girgiza kanta. Cikin rawar murya kamar mai shirin sake masa kuka ta ce, "Please Sultan ka daina fadar haka karma yan kasar ruman suji sumin yankan rago. Kai fa shugabana ne, sannan ashekaru ka fini, gaka mijina,uban yayana", Hawayen suka silalo mata a hankali. Hannunsa ta kamo ta daura akan cikinta. "Nagodema ALLAH da ka kasance mahaifinsu badan ya baka daukakar mulki data dukiya ba. Domin su a duniya aka samar mana da su a cikinta kuma zamu tati mu bari wataran. Ina alfahari da kai ne matsayin uban yayana saboda nagartarka da adalcinka. Tsoron ALLAHn ka da kyakylyawar zuciyarka. Maleek kai na dabanne a cikin daban. Ba yan kasar ruman bane kawal suka dace a dalm shugaba ba. Daular musulunci ma kai abin alfaharinta ne. Sannan kuma nice kololuwar dacewa da ka kasance miji gareni, Nauyin mulki bai sa ka gaza bani farin ciki da sauke duk wasu hakkokina ba. Kana samar da nishadi a tsakaninmu ka manta da kai sarki ne mai jagorantar talakawan kasa bawai jaha ko wani dan yanki ba,
Kwanciyar hankalin da nake samu da ga gareka bana jin wasu matan da mazansu basu da nauyin kowa na sarun makamancin sa. Maleek kai ne gwarzo na, kai ne Barde na, kuma kaine gagara badau dina".
Idanunsa kawai ya lumshe a zahiri, maimakon ita da ke kuka a bayyane shi a zuciya yake yin nasan. Tabbas yaga ribar hakuri, kai shi baima san mizaice da UBANGIJI ba akan kyautar wanna yarinya da ya bashi. Ita din ta dabance. Tabbas itace komansa. Tsam-tsam ya rungumeta a jikinsa na tsawon lokaci, sal da ya ji tana sauke numfashi a hankali alamar barci ya dauketa sannan ya dagota. Kwantar da ita yay a hankali ya cigaba da kalionta hannunsa saman shafaffen cikinta da kamar babu komai a cikinsa abubuwa da yawa na masa kaikawo tun daga randa ya fara ganinta soyayyar farat daya ta shigesa har zuwa yau da ajiyar gudan jininsa ke à cikin jininta…..✍️
DAUDAR GORA
Book2
69
.....WASHE GARI ta kasance ranar da zasu koma kasar ruman. Da safe bayan Tajwar Eshaan ya gama ganawa da Sultan na saudiya sunyi sallama amintaccensa da Sayeed Tasadduq-Husain da sai daga baya yazo ya samesu a saudiyyan da wasu mutane biyu suka samesa. Cikin girmamawa suka mika gaisuwa, kafin Sayeed Tasadduq-Husain ya mika ma Amintaccensa file din hannunsa. Amsa yay da sauri yaje gaban Tajwar Eshaan din shima ya ajiye.
"Wannan shine result din binciken ALLAH ya kara ma adalin shugabanmu lafiya da nisan kwana. Sannan wadan nan sune sukai binciken. Sun kuma kasance kwararrun likitoci ta wanna fanin".
Da sauri daya a cikinsu ya karbe zancen Sayeed Tasadduq-Husain din cikin harshen turanci, "Idan mukai bincike so daya ba'a samun kuskure, amma domin cire tantama sai da mukai wanna sau uku. Abu daya yake tabbatar mana shi namijin mahaifinta ne, mace kuma ba ita ta haifeta ba. Bayan muni sau uku mun sake bayarwa was asibitocin ga results din nan dai duk abu guda suke bayarwa".
Baice komai ba, sai amintaccensa ne ya amsa da
yawunsa. Da ga haka sukai masa sallama Sayeed Tasadduq-Husain yay musu rakkiya. Duk abinda akeyi Iffah na daga kofar falo na biyu ne tsaye zata fito zuwa sashen Uwargidan Sultan da zasuyi sallama. Duk da bata san manufar zancen ba sai duk taji ta tsargu, amma kasancewar yanzu an koyi wasu halaye musamman akan hadiye abu koda ta fito wucewarta kawai tavi tunda yasan da fitar tata.. Koda taje can kuma abun nata mata kaikawo har tana jin kwadayin son sanin abinda ke a tattare da file din da son sanin akan wama ake maganar da har sai anzo wata kasa za'ai binciken bayan kowa yasan kasar su suna daya a cikin masu kwararrun likitoci a duniya. Sai kuma a ka kara yin sa'a lokacin da take dawowa sashen ta samu Sayeed Tasaddug-Husain da Tajwar Eshaan din suna maganar again. Cikin kasaitar nan tasa da magana a fisge yake sanar masa. "Ayi musu komai da ya dace, nan da kwanaki biyar bayan anyi salla sai ku biyo bayanmu, dan ina son ku iso ne randa zamu koma zaman shari'ar".
"Umarninka da cikawa shine abin jiranmu Insha ALLAHU"
Iya abinda Iffah kenan ta iya ji ta shige. Lokacin da ya shigo dakin zai shirya tata fatan ya shigo da file din amma sai ya shigo babu komai. Kuma bai mata maganar ba. Amma koda suka kammala shirinsu suka fito Sultan da kansa yau ma da yayansa maza biyu da uwargidansa sukai musu rakkiya har airport Iffah harda kwallarta hakama Uwargidan Sultan abinka da sabon mata bayan shigarsu jirgi sun zauna tana a jikinsa yana lallashinta sai ga file din nan ajiye a gefensa. Ta danyi mamaki amma sai ta basar, sai dai zuciyarta na sake tabbatar mata da koma akan wa file din ya kunsa yanada matukar muhimmanci ga mijin nata. Jirginsu na dagawa babu dadewa barci ya kwasheta…...
* KASAR RUMAN
Duk da saukar dare sukai tako ina a airport din zagaye yake da matakan tsaro. Kai da gani kasan mai kasar ruman dinne da kansa zai sauka. Ta bangaren masu tarbarsu kuwa manyan masarautar ne masu fada aji. Ga wasu lafiyayyun motoci ababen birgewa ga mai kallo. Sosa barcine a idon Iffah dan yanzu kam bata da aikin da yafi wannan. Hakan yasa ta kasance a kusan rabin jikinsa lokacin da suke fitowa, Dole duk wanda ke wajen yay kasa da kansa cikin jin nauyi. Shika gogan nasu ko'a kwallar rigarsa rungume yake da ita hankali kwance yana daga musu hannu daya alamar amsa gaisuwarsu har zuwa motar da aka ajiye domin su kawai. Sai da suka shiga har aka rufe sannan hadiman da sukal masu rakkiya ke fitowa a jirgi suma. A wannan tawaga musamman ta matan Diwa ce kawai zuciyarta ke a tsarkakake game da nado labari, amma sauran duk yan daukar rahoto ne. Sai dai kuma basu samo yanda suke so ba sam kasancewar su/Iffah'r sun musu wahalar ma gani ba kamar yanda su Uwa sukai tunani ba.
Tun daga airport har cikin masarauta jami'an tsaro ne, a cikin masarautar ma tarba suka samu da taima Iffah dadi, dan harda Malikat Haseenat da Daneen Ammarah da kanta. Sal wata da Iffahr bata sani ba amma suna kama da Daneen Ammarah sosai kuma tana kama da Jaddah. Haka kawai taji a ranta itace Daneen Waheeda da aketa fada. Lokacin da take dagowa da ga rungumar da taima Malikat Haseenat zata rungume Daneen Ammarah idanunta suka sauka kan wata kyakykyawar farar budurwa sol tana balla mata harara. Bata santa ba, dan haka ta dauke idanunta ta maida hankali ya Daneen Ammarah din cikin rashin damuwa. A hankali ta saketa ta nufi Daneen Waheeda da ke tsaye tana kallonsu kusa da Malikat Ashwaq fuskarta babu yabo babu fallasa. Gabanta ta rissina ta gaisheta tare da Malikat Ashwag din. Amsa mata tai da dan murmushin yake sakamakon kallon da Malikat Haseenat ta watso mata. Sai kuma ta nufi Malikat Bushirat ta rungume, itama dai gain kallon da ake musu ne yasata shafa kanta tana yake, Jasrah kam saita boye bayan Malikat Bushirat din dan da gaske kunyar Iffah take ji. Murmushi Iffah tai itama ta rungumeta, dan koba komai kafin faruwar hakan al ta nuna mata soyayya ta gaskiya..
Tuni shi Tajwar Eshaan ya shige ciki, dan haka itama Malikat Haseenat ta kama hanunta tana facin,"Kinga zomuje kema ki huta kunyi buda baki a jirgi babu nutsuwa". Da ga haka ta nufi ainahin sashenta da ita dan an sake masa gyara na musamman. Bayan wucewarsu abubuwa da yawa sun faru a cikin masarautar, ciki hard jajircewar Malikat Bushirat akan komawar Iffah sashenta. A zahirance dai babu wanda ya kawo komai a ransa game da hakan, sai Malikat Haseenat ce ma take gain Malikat Bushirat din na son hakanne da tunanin Iffah ta kanainaye mata Eshaan, ta kuma san sai dai Bushirat din tayi ta gama Iffah da Tajwar Eshaan sun riga sun gama zama abu daya. Ga tabbaci nan ma a yau ta sake gani, dan duk mai hankali da zai kalli Iffah'r a yau yasan tana tare da juna biyu. Komai nata ya canja, ga kyau data kara da budewa. Yanzun ma Malikat Bushirat na gain sun nufi can ta saki wani lafiyayyen murmushi tana fadin, (yes) a zuciyarta alamar akwai abinda suka kulla a sashen kenan.
Ko dar Iffah bataji da komawarta sashenta ba. Sai ma farin ciki data tsinta kanta a ciki. Ga hadimanta duk an dawo mata da abinta, a ganinta ma ita wannan wata dama ce da zatai yakinta da kyau a yanzun. Wanka ta farayi bakinta dauke da addu'a, kasancewar duk tayi sallolinta tun a jirgi shirin kwanciya kawai tai ta haye gado abinta sai ko barci.
Cikin barci take jin kamshinsa na sake shige mata hanci, a zatonta mafarki take, sai tai kokarin yin juyi abunta. Jinta jikin mutum a gaske ya sata bude idanunta da kyar. Akan kyakykyawar fuskarsa ta sauke idanun nata. Tashi tai a dan zabure ya rikota, maidata yay ya kwantar yana mai tura yatsunsa cikin gashin kanta, sai kuma ya matso da fuskarsa saitin tata ya daura goshinsa kan nata hancinsu na gogar juna.
"Yaushe kazo?"
Ta fada cikin muryar barci. Shiru kamar bazaice komai ba, sai da ya mula dan kansa sannan. "Dama zaki iya barci babu ni a tare da ke?". Kankamesa ta sakeyi tana sakin ajiyar zuciya, itama a hankalin ta furta, "Kawai dan banda yanda zanyi ne".
"Toni gani nayi yanda zanyi ai".
Ya bata amsa yana sake matseta cikin jikinsa kai kace amshe masa ita za'ai. Luf ta kwanta kuwa suna sauke ajiyar zuciya a tare. Sai kuma ya hade bakinsu a hankali. Da ga haka labarin ya sauya salo...
Karfe uku nayi ya gudu, sai farkawa tai taga babu shi a dakin. Murmushi kawai tayi ta tashi zuwa bayi tai brush da tsaftace jininta ta fito. Madara mai dumi kawal tasha matsayin sahur. Duk da barcin dake cin idanun nata sai bata kwanta ba tayo alwala ta danyi nafilfili da karatun Alkur'ani. Bata tashi a wajen ba sai da tai sallar asuba, Tana idarwa kwanciyar ta sake yi, bata tashl ba sal azhar. Tayi mamakin barcin da tayi, amma kuma sanin yanayin da take ciki da rashin isasshen barcin da bata samu a Saudiya ba yasa ta fahirci akwai ramuwa dole dama.
Tsaf tai shirinta cikin kyakykyawar abaya kamar ka sace ta ka gudu. Dama ga ko'ina ya sake fita da fitar kwarjini da kyawun haiba na ciki. Cike da girmamawa a gareta hadimanta ke zubewa Rasa gaisheta lokacin data fito. Nuni tai musu da su tashi, cikin sanyin da ciki ya haifar mata yanzu ta basu izinin mata rakkiya zuwa sashen Malikat Haseenat da ga nan su wuce na Malikat Bushirat. Da girmamawa suka arsa mata tai gaba suna take mata baya. Duk da akwal tazara a tsakaninsu bata shiga motar da aka ajiye domin ta ba tunda ta fito, A kafa ta taka hadimanta na take mata baya. Dolene ta birgeka, dan yanda ta fito da kafan ma sal ta kara kima a idanun hadiman. Ta ko'ina kuwa ta gitta hadiman ne ke zubewa mika gaisuwa, hannu kawal take daga musu fuskarta da dan murmushi dan sam bata daureta ba. Yayinda Amintacciyar hadimarta ke amsa musu da baki ita kuma.
Tun kan shigowarta aka sanar da Malikat Haseenat da ke zaune Daneen Ammarah da Daneen Waheeda tare da ita. Sai Iftihal diyar Daneen Waheeda dake zaune a can gefe tana latse-latse a laptop. A nutse ta shigo bakinta dauke da sallama. Dan haka suka dago a tare. Sai dai kuma a hankali Iftihal taja sirrin tsaki da maida kanta ta cigaba da abinda take yi. Babu wanda ya jita, sai dai Iffah kam taga kallon da tai mata sarai. Amma tai kamar ma ita bata ganta ba ta nufi Malikat Haseenat da ta bude mata hannu fuska duke da murmushi alamar tazo gareta. Ita din ta nufa cike da kunya, ta durkusa a gabanta tana murmushi da gaisheta. Cikin murmushi Malikat Haseenat ta ce, "A'a kinga Hafidah tashi ki zauna keda ke fama da kanki, ALLAH dai ya raba lafiya".
Sosai kirjin Daneen Waheeda ya buga, yayinda Daneen Ammarah ke murmushi kawai tana bin Iffah'r da kalion kasan ido, Bayan ta gaishe da su duk cikin girmamawa Daneen Ammarah ta nuna mata Daneen Waheeda. "Ga wata maman taki nan tazo kuna Saudiyya, nasan kin san dai sunanta da labarinta tun kafin yau". Fuskar Iffah cike da murmushi ta jinjina mata kai. Kafin ta kara gaishe da Daneen Waheeda din da zancen cikin nan va sata sumar zaune, cikin murmushin yake ta kai hanunta kan Iffah'r ta shafa. Daneen Ammarah ta sake waiwayawa ta nuna mata Iftihal da tai kamar ma bata san mi ake ba "Wannan yar uwarki ce ita kuma, sunanta Iftihal, itace first born a wajen mamanki. Tanada kanne maza har uku".
Murmushi kawai Iffah tai sai dai batace komai ba kamar anda itama Iftihal din ko dagowa batai ba. Yanda tai din kuma sai ya zafi Daneen Ammarah. Ita kanta malikat Haseenat dai tayi shiru ne amma fuskarta ta nuna jin zafin abinda Iftihal din tayi. Ita kam Iffah ko'a kwalar rigarta, hankalinta kwance suka cigaba da hirarsu da Daneen Ammarah da Jaddah...✍️
DAUDAR GORA
Book 2
70
....Sai da tai sallar la'asar a sashen Malikat Haseenat sannan ta baro, fuskarta dauke da murmushin abinda take kullama Iftihal. Dan ta dau alwashin sai tayi dana sanin zamanta a masarautar nan duk da gidan kakanninta ne. Da ga nan sashen Malikat Bushirat ta nufa, sai dai ta samu wai bata nan tana a sashen Shahan-shan. Hakan bai bata mamaki ba, ba kuma ta nuna ya dameta ba ta koma sashenta ita da tawagarta. Sai kusan karfe biyar ta nufi sashen Tajwar Eshaan..
***
A lokacin da Iffah ke nufar sashensa a lokacin shi kuma yake fita ta kofar sirrinsa zuwa sashen Malikat Haseenat. Cikin sa'a kuwa ya sameta ita daya a dakin. Kyawawan idanunta na tsufa ta zuba masa har ya kammala sakama kofar key ya cigaba da takowa gareta a nutse. A hankali ya kai zaune gabanta ya tankwashe kafafunsa.
"Barka da yamma Jaddah".
Ya tada a kan lips a dan fisge kamar baya so.Murmushin ta sakar masa cikin yar tsokana ta amsa da "Barkan ka dai Abbien unborn". Idanunsa ya dan waro mata na alamar mamaki, sai dai kuma bai iya cewa komai ba dan yama rasa bin fadar. Dariya Malikat Haseenat tayi mai kayatarwa, tace, "Ni dai bana fata ko mace ko namiji da za'a haifa su gado min wanna miskilancin naka Hafidi. Ace magana a bakin mutum amma furta ta ta zama aiki", Kasa ya dan yi da kansa kawai yana murmushi. Kafin cikin son kauda maganar ya ce, "Amm Jaddah! Kamar yanda kika bada shawara nayi amfani da ita. Ani musu gwaji ta wasu abubuwan hallitar jikinsu kamar gashi da yawu jini batare ma da sun san duk muni hakan ba. Ita na bada nata, Sayeed Tasadduq-Husain kuma ya samomin na iyayen nata dan kamar yanda na fada miki dama tunda na saka a kaudasu a kasar shine yay aikin kuma shi kadai suka sani ya kuma san inda suke a yanzu haka ma".
Cike da zumudi Mammah tace, "Ya ake ciki? Mi result din ya nuna kuma?"
Sai da ya dan ja iska kusan minti daya kafin ya nisa. "Al'amarin gaskiya yazo da rudani zance ne koba haka ba oho. Result din sun nuna shi Mahaifinta ne,amma macen ba itace ta haifeta ba".
"What! Kamar yaya kenan?".
"Shine na kasa fahimta why Jaddah. Tun a Saudiyya a rikice lissafina yake. A daidaiton kwanakin watan haihuwarta da na yarinyar Mamy dake rubuce kwana uku ne, sannan tambarin da ke nan a ajiye iri dayane da na jikinta, ita waccan ta mutu a randa aka haifi ita Fhareedahn. Sai nake ji kamar akwai abinda ya kamata mu sani, amma idan na auna yiwuwarsa ni a karan kaina sai naji abin yazo ba daidai ba".
"Kai mi kake tunani akan hakan?".
Nan ma sai da yay jima kafin ya bata amsa. "Itama Mammy a mata gwajin halitta tare da ita. Kinga muma sai mu samu nutsuwar yarda ba ita bace, ko itance. To amma ya akai ta samu tambarin zuri'armu bayan mahaifinta bashi da alaka da wanna masarautar? Sosai nakejin kaina a rikice a duka abinda nake tunani da fatan ya tabbata".
"Tabbas al'amarin akwai rudanin, rudanin kuma suna da yawa, dan inhar babu alaka tsakanin wannan yarinya da Arnmarah to tabbas tana da alaka da wani a wannan masarautar kuma dole ne mu sani. Sai dai dabi'un yarinyar na rikita mun lissafi Eshaan. Dan babu abinda ya banbanta da na Ammarah tana a irin shekarunta. Sai dai ni nasan diyar Ammarah ta rasu tunda da hannuna na mata wanka da hadata aka kuma kai ta aka bizne".
"Kamar yanda na fada miki Jaddah akwai abinda ke boye. Dan da gaske yarinyar nan akwai aljanu a kanta wilhy. Naga alamominsu da yawa tattare da ita, dan a wan lokacin ita kanta aljanar ma nake kallonta".
Dan murmushin karfin hali Malikat Haseenat tayi, amma a ranta fal yake da rudani... Sun cigaba da tattaunawa har zuwa gabanin magriba sannan ya baro sashen domin zuwa yay shirin massalaci…..
A bangaren Iffah kam data nufi sashensa kai tsaye kitchen ta nufa, inda masu kula da abincinsa ke ta kaikawon lissafin abinda zasu shirya masa na buda baki. Tana shigowa duk suka zube kasa suna kwasar gaisuwa. Hannu kawai ta daga musu, kafin tai zaran bibiyar duk abinda suke shirin yin da kallo. Duk lissafinsu sal da ta wargaza ta shimfida nata, karshe ma ita ta koma shirya abincin da taimakonsu. Wannan al'amari ya matukar basu mamaki kam, dan ko'a tarihin masarautar basu taba jin a inda wata Zawjata- almilk ta shiga kitchen girka abinci ba koda na Shahan-shan ne kuwa. Sai gashi a yau Itfah ta ajye tarihin,
A matukar gajiye suka kammala aikin, tayi tibis da ita saboda a yanayin da take, duk da dama cikin nata nada saukin laulayi da tsurfan abinci. Sannan ita dai bazatace ga wani waje na mata ciwo ba mai jigatarwa. A dining room din ma tana tsaye suka shirya komai, aka kara turaren wuta ko ina ya dauka harami. Bayan duk wucewarsu bedroom nashi ta nufa, ta dinga binsu daya bayan daya tana lekawa har sai da ta shiga a inda ya kwana. Kamar ko yanda tai hasashe ba'a gyarashi ba, tunda ita da kanta ta hutar da amintaccensa tun kan su wuce. Duk da yanda take jin kanta haka tai dauriyar gyarawa, sannan ta shiga toilet din tayo wanka shima bayan ta tsaftacesa Bata da matsalar kaya anan kam tunda tasan tabarsu tunkan su tafi ba, tako shirya cikin wandon jeans 3quater blue da karama roga mara nauyi fara tas, sai hoton heart da akayi babba a gaban rigar. Kayan sun mata kyau. Tana barbaza gashinta da haushi na rashin son a taba mata shi ya shigo dakin da sallama. Dan turus yayi yana kallonta irin na rashin tsammani. Dan a yanzu haka da yake shigowarnan da ita a ransa ya shigo, kewarta yake ji sosai, dan duk yau bai ganta ba, rabonsa da ita tun daren jiya da ya kai mata ziyarar sirri sashenta.
A hankali ya cigaba da takawa cikin dakin yaje gabanta ya tsaya. Jitai kawai an tura mata yatsu cikin gashi. A firgice ta dago dan ko kadan bayaji motsin shigowar tasa ba. Cikin juna idanunsu suka shige, kowanne cike da kewar dan uwansa kamar sun hada watanni basu hadu ba. Itace ta fara janye nata a slowlv. kamar mai in kunvarsa ta maida kanta kasa ta dukar. Numfashi ya dan furzar kadan, tare da dukowa
ya zare ribbon din hanunta ya saka cikin tsintsiyar nasa hannun kamar maisa bangles, sai kuma ya maida duk hannayen biyu saman kanta ya tattaro gashin a tsakkiya ya dare mata.
"Thanks you".
Ta fada cikin siririyar muryarta da ke ratsa masa jiki, yasan tsaiwarsa a wajen bazata hafar masa da da mai ido ba. Dan haka ya rabata ya wuce cikin tafiyar tasan nan daddaya dan azuminsa ya isa lafiya. Da kallo ta bisa har ya shige bayi, sai kuma ta saki sassanyar ajiyar zuciya ta mike. Closet dinsa ta nufa kasancewar akwai finger print dinta yanzu akai itama. Lallausar jallabiya kalar maroon ta zaba masa, tare da alkyabba irin ta sarakan saudiyya. Fitowarta dal-dai da tashi. Kallo daya ta masa ta dauke kai dan har yanzu ta kasa sakewa da kalion wanna jikin nasa. Kanta a kasa ta karaso gabansa, karamin towel da ke hannunsa ta amsa, babu musu ya sakar mata, sai da ta lumshe idanunta sannan ta fara tsane masa jikin. Dan garetan murmushi ya saki idanunsa kan kyakykyawar fuskarta harta kammala. Man da yake amfani da shi ta ajiye zata gudu ya rikota a slowly yaNmaidota baya. Sai da ya gama kare mata kallo da gaNsama har kasa sannan ya dire kan fuskarta da idanun ke lumshe. A can kasan makoshi ya furta, "Shi man wazai shafa?". Batare data bude idon ba ta ce, "Ka tayani".
"Naki wayon".
Ya bata amsa yana maidota gabansa da kyau. Dan murmushi tai zatai magana ya ce mata, "Shilli!!!" Shiru tai ta hadiye abunta. Shi kuma ya daura mata man a kan hannu. "Oya zan makara sallar magrib". Babu yanda ta iya dole ta shafa masa. Kirjinta sai bugawa yake da sauri-sauri dan da gaske jikin nan nasa toro yake bata. Ta rasa mike birge maza suke maida kansu haka ita kam. Rashin mafita ya sa dole har shiryawa sai da ta taimaka masa wajen yi. Tana kammala saka masa turare ya kamo fuskarta cikin tafukan hannunsa ya sumbaci goshinta da idanunta da karan hancinta, sai kan habarta. Sassanyar ajiyar zuciya ta dan saki. Bata ankara ba kawai ta gansa duke gabanta ya dan daga rigarta ya sumbaci cikinta. Da ga haka ya wuce abinsa cikin dakewa kamar bai aikata komai ba. Da kyar ta iya bude ido ta bisa da kallo, dai-dai zai fice ya dan tsaya a jikin kofar tare da juyowa suka hada ido. Kauda nata tai da sauri, shi kuma ya dan sakin murmushi a iya lips da fadin, "Idan kika bar sashen nan kafin na dawo sai na hukuntaki". Da ga haka ya fice ya barta da murmushi a fuska..
Bai shigo gida ba sai da aka idar da har sallar isha'in da asham, dan bayan idar da sallar magrib ya sha ruwa da dabino a can. Da ga haka yay zaman karatun Alkur'ani. Kowa yasan hakan yake yi a duk shekara, dan baya shigewa sai bayan an kammala salla baki daya kamar yanda yake yi idan ba'a azumi sai ani har sallar isha'i. Bisa rakkiyar su Sayeed Fayzul-haq ya dawo sashensa. Hadiminsa kam tun da yaji a bakin masu girki Zawjata-almilk tazo itamace taima Shahan-shan girki da kanta baiyi gigin biyosa har nan ba sai ya lake a 3 floor din. Babu kowa a faion sai sanyin ac da kamshi mai dad ba irin wanda ya bari ba. Bedroom ya nufa domin rage kaya, zuciyarsa na raya masa tama gudu kenan bataji gargadinsa ba. Sai dai yana murda handle din kofa itama tana budewa, kusan cin karo sukal da juna ALLAH dai ya kiyaye taja baya da sauri, sai kuma ta kusan faduwa sai da ya rikota jikinsa. A jiyar zuciya ta sauke cike da shagwaba ta ce, "Thanks you"
Maimakon amsa. mata godiyar cak ya dagata bisa kasa suka koma dakin. Tana watsal-watsal da kafafu da rokon ya sauketa ita yunwa takejl bai ma saurareta ba sai da ya direta inda yake bukata ya rufe bakin tsiwar dan iya yaren da zuciyarsa da kwakwalwar ke bukata kenan kawai…….✍️
DAUDAR GORA
Book2
71
_..Taji a jikinta kasancewar da gaske yunwar take ji,dan itama ruwan kawai tasha da dabino sai dan madara mai zafi da take matukar so a yanzu tunda akasha ruwan. Ta hakura ne tai salla dan tasan in har taci abu da yawa to tabbas bazatai sallar ba barci zatai. Duk yanda take wani tuttura masa baki na shagwaba bai kulata ba, da taimakonsa sukai wanka a tare sannan suka fito daning room din. Sai da ta tabbatar ta gam harare-hararen kwanikan abincin tsaf duk da tasan bayan sun ajiye babu mahalukin da ya sake shigowa nan sai shi bata aminta ba kai tsaye. Komai a tare ta hada musu, hatta shayi a kofi daya ta zuba duk da kasancewar dan mitsitsin nanne na larabawa. A haka suka dinga cin abincin kowa na ciyar da dan uwansa har sukaje iya inda suke bukata. Falo suka dawo, yana kokarin kuna Laptop din tasa ta fama ta je ta haye cinyarsa tana tura baki.
"Wai nikam kodai computer din nan kishiyata ce?".
A yanda tai maganar ma sai abin yaso bashi dariya. Amma dai ya gimtse bai yi ba ya dai tsareta da idanunsa kawai. Lumshewa yay ya dan bude tare da tallafo fuskarta cikin tafin hannunsa. A kasalance ya furta, "Ko dai ke ce ke kishi da ita".
'"Ai dai banyi laifi ba".
Murmushi kawai yay dan bashi da abin cewa kuma.Sai kawai ya dauka remote ya kunna musu television ya kamo babban gidan tvn kasar. Basu fara labarai ba, sai wani shiri mai suna * ZAUREN MUSULUNCI_*. sannin muhimmancin shirin yasa bai canja ba ya bar musu nan, itako harda gyara kwanciya a jikinsa ta lafe kamar wata mage. Shima sai ya gyara mata yanda zataji dadì sosai hannunsa saman cikinta da duk duniya a yanzu babu abinda yafi so da bukatar gani kamar girmansa da haihuwarsa. Koda wani takaici ya tuno a ransa daya tuna Iffah'r sa nada cikin gudan jininsa sai yaji nutsuwa ta saukar masa..
*
-*
Washe garin aka tashi da fatan gain watan salla,Iffah na zaune tana karatun Alkur'ani bayan idar da sallar asuba Tajwar Eshaan ya dawo da ga massalaci. Komawa yay ya dan kwanta dan barcine a idonsa sosai. Ta idar itama tana shirin hawowa gadon yake sanar mata sakonta ya iso yanzu Sayeed Fayzul-haq ke sanar masa. Fasa kwanciyar tai cike da doki ta mike ta hau shiri, shi dai kallonta kawai yake dan ya santa da barcin tsiya amma da ga cewa sakonta ya iso ta fasa yi. Ganin sauri-saurin nata yay yawa a hankali ya furta, "Madam a hankali karki jamin asara abuna baiyi kwari ba fa".
Ita kunya ma maganar ta bata, dan haka ta juya masa baya tana rufe fuska. Shima sai ya dan murmusa kawai ya lumshe idanunsa. Kirtsawa ta karasa yi ta zo gaban gadon ta manna masa sumba a goshi. Hannu ya kai zai damkota ta zille. Murmushi yayi da kara gyara kwanciya yana fadin (Fitinanniyar yarinya) a zuciyarsa…..
Duk da safiya ce sosai tuni kayan da aka shigo da su cikin manyan motoci kusan goma masarautar ta dauki dumi. Kowa jira yake ya ga da umarnin wa aka kawo kayan, dan abune dai sabo da ba'a san da shi ba, ga kuma wasu kayan da suka dan fitgito sun nuna suturu ne ma. Tuni fitowar Iffah da ga sashen Tajwar Eshaan Sayeed Fayzul-haq da amintaccensa biye da ita kallo ya koma sama, sal kuma ga tawagar matasan masarautar da ta saka suka mata aiki a wancan karon ma sun fito, a gabanta duk sukal rankwafawar gaisuwar girmamawa. Ta amsa musu itama da kulawa fuskarta da murmushi har da yar tsokanarsu wai kwanan nan zata fara saida form din aurar da samarin masarautar ta ga sun fara yawa. Dariya suka shigayi da barkwancin nata. Harda Sayeed Fayzul-haq da ke jin kaunar yarinyar, gata dai karama amma da halin manya, manyan ma sai an tona. Haka ma amintaccen hadimin Shahan-shan na jin kima da girmanta, dan yanda take kula da shugabansa kawai da sakasa farin ciki ma abin a jinjina mata ne. Shi baya ma ganin karancin shekarun sam sal wata kimarta da girma irin wadda yake kalion Shahan-shan da ita.
Ta musu bayani akan kayan suma da za'a rabasu kamar yanda aka raba kayan abincin azumi ne. Akwai kuma kaji da shanu suma zuwa yammaci zasu isa. Sai dai su baza'a kawosu nan ba a kowace jaha aka samar da masu kiwonsu aka siya idan kowane wakili yaje inda zai raba kayan da aka bashi zai amsa. Sai kuma wanda za'a rabama hadiman masarautar suma da nasu daban, sukam harda kudi wanna kuma Sayeed Fayzul-haq ne zai bada su sakone da ga Shahan-shan da kansa
Abdul-Shakhur in Khairul-Bashar shugaban tawagar ya share kwallar da suka ciko masa ido. Cike da girmamawa a gareta ya ce, "Lallai ke alheri ce garemu gimbiyarmu. Ke haske ce mai haskaka fararen fitulun da ke zagaye da daular ruman. Kasancewarki damu sake buda mana sanin wanene adalin shugabanmu yake da kyawawan halayensa a koda yaushe. ALLAH ya kara miki daraja, ya albarkaci rayuwarki data shugabanmu, ya zagayeku da kariyarsa da ni'imominsa. Yay riko da hannayenku ya baku ikon sauke nauyin al'umma da adalci. ALLAH ya bamu ikon muku biyayya ya karemu zaginku koda a bayan idanunku. ALLAH ya karya makiyanku koda jininmu ne ya azurtaku da zuri'a masu irin kyawawan halayarku da dabi'unku. ALLAH ya jika magabata, wanda suka rage ALLAH ya rabaku da su lafiya...
Haka ya cigaba da jero addu'oi sauran a amsawa da Amin tare da hadiman da suka zagayesu cike da farin ciki. Iffah kam sai taji har hawaye na ciko mata idanu. Tabbas babu abinda ya kai kyautatawa dad da soyayyar mutane. Da ace dan adam ya gane da ya kasance mai kyautatama mutane sabanin munana masu. Kyautatawa na bada muhimman abubuwa uku a lokaci guda. *_DARAJA. SOYAYYAR MUTANE.
SANNAN LADA A WAJEN UBANGIJI_* Cikin kankanin lokaci masarautar ta harmutse, bakin kowanne hadimi ka kalla a washe da farin ciki musamman idan ya kama yan kudadensa da kayan sakawa kusan kala biyar uku a hannu. Ga iyayen kaji da shanu an zube musu na girkin salla. Ga albishir na basu damar yin shagalin bikin sallarsu kamar yanda kowa keyi. Harda damar yin gyaran jikinsu matsayinsu na mata Iffah tabama matan, dama albishir din kawo masu gyaran jiki €ikin masarautar saboda hadimai matan kawai. Kai jama'a harda masu kuka, kaunar Iffah kam da Shahan-shan din kansa ba' magana a zukatansu. Sai sukejin kamar an yanta rayuwarsu ne da wani haske na musamman a yau din.
Ba cikin masarautar ruman kawal ba. A cikin al'ummar. kasa ma duk wanda ALLAH ya tsaga da rabonsa a kayan' nan ya tsinta kansa a farin ciki mara musall. Badai ta wadata kowa da kowa ba. Amma ta ragema was radadin talaucin da suke ciki. Ta faranta
ran marayu marasa iyaye. Duk da alkairi ne na sirrince da akaki bama yan jarida damar sani sai gashi ya fita karar wata amsa kuwwa a katafen yada labarai, Ya koma latest topic na wanna ranar harma da washe gari. Dan cikin aminci, UBANGIJI a ranar akaga watan salla washe gari aka tashi da farin cikin zagayowar wanna rana. Inda karfe tara dal-dai Shahan-shan da Kansa ya jagoranci sallar idi a massalacin Masarautar da mutane kasar suka ziyarta ta ko'ina a jar, harma abin ya bada mamaki, dan duk da ana cikashi dama duk shekara sai gashi a wannan shekarar ya ninka da ninki mai ban mamaki,. Talakawa da yawa sunzo cikin Dahab City yin salla domin kawai suga Shahan-shan.(Haka rayuwa take, duk kasancewarka mai mugun hali ko wanda za'a gogama bakin fenti da kayi alkairin da yay shura tsakaninka da ALLAH badan duniya ta gani ta fada ba ko a yaba maka sai kaga ALLAH ya saka soyayyarka a zukatan wadan nan mutanen dake aibantaka da kyararka a baya. Yan uwa mu dage da alkairi domin ALLAH, idan ka cire Naira dari a cikin dubu da ya baka sai ya sakama sauran albarka ya kuma daga darajarka. Dan shi alkairi da gaske danko ne baya faduwa kasa banza inji hausawa. Dan ko yayan cikinka kaima shi sake kaunarka suke, hakama iyayenka)
Tajwar Eshaan yayi addu'oi masu ratsa zukatan bayan idar da salla. Hakama lokacin khuduba kalamansa masu ratsa zukata ne da hikima a cikinsu da mutare duk jikinsu yay sanyi da yanda suke kallonsa a baya. Bayan kuma kammala addu'oin yay wani dan gajeren nasiha da Fatan alheri ga kasarsa da ma al'ummar kasar da musulman duniya baki daya. Ya rufe da musu Barka da shan ruwa.
Wannan jawabi a Tajwar Eshaan Ibn Haysarn Abdul-majeed Ally Qutb shine ya dinga amsa kuwwa a kafafen yada labarai, masu fashin baki nayl talakawan kasa da basu samu halarta ba nayin nasu suma,
*Duk gayun da Iffah taci domin kayatar da zuciyar Maleek dinta bata samu ganinsa ba har sallar zuhur. Bataji haushi ba, sal dal ta kagu su hadun. Duk da itama da kanta tai masa shirin fita sallar. Yayi matukar kyau kamar wani dan saurayin dawusu (lols 😉😂)) harda fada masa ita why kamarma ya fasa kishin fitarsa a kalle mata shi takeyi haka. Amintaccensa da ke jinsu (okacin da take bashi shayi sai kasa ya karayi da kansa kawai yana murmushi.
Bayan ta idar da sallar azhar ta fito domin zuwa gaida Jaddah da Malikat Bushirat da ya kasance dole tayi. Sai lokacin ta fahimci yanda masarautar ke cike. Ashe dole ne duk wani Tajwar a sauran jihohi sai yazo a yau din yayma Shahan-shan barka da shan ruwa, Hakama manyan attajirat da masu fada ajin kasar da dattijai. Zasuci abincin salla da Shahan-shan su kuma tattauna matsalolin kasa da shawarwarin magancewa. Gaba daya sai Iffah taji ta Kara tausaya masa. Dan lallai mulki ba wasa ba, yanda ta sanshi bal son hayaniyar nan yana can cikin takura ne.
Sashen Mallkat Bushirat ta fara nufa yau tawagarta zagaye da ita. Kowa ya kalleta sai ya sake kallo dan kyawun da tai cikin walliyar sallar tata mai tsananin kayatarwa da daukar idanun mat kallo. Ga kyawu da cikin jikinta ya sake sakatayi kamar ka saceta ka gudu. Tako ina hadimar da jami'an tsaron masarautar gaisuwa kawai suke mikawa. Itako fuskarta kawace da murmushi mai sanyi da ke sake saka kaunarta a zukatan talakawan nata masu jin yanzu kam babu kamarta a cikin masarautar bayan Malikat Haseenat da itama ta kasance adalar shugaba…..✍️
DAUDAR GORA
Book2
72
.....Cike Iffah ta samu sashen Malikat Bushirat da danginta da sukazo mata Barka da salla. Hakan ya mata dadi, dan duk wani wanda ke da alaka da Tajwar Eshaan a rayuwa tana ganinsa da kima da mutunci. Cikin mutuntawa suka tarbeta, dan sakonta da na Tajwar Eshaan yaje garesu har gida a jiya. Duk da suma sun kasance mafi yawansu basu nema komai na rayuwa sun rasaba. Amma alheri dadine da shi, musamman da ya kasance wani abu bai taba zuwa garesu ba ace daga dan yar war tasu kuma Shugabansu. Abinda ya basu mamaki da tabbatar da an samu sauyi yar uwar tasu ma sai da suka zo yanzu duk suke mata godiya har tasan Tajwar Eshaan din wai ya musu aike suma. Murmushin yake kawai ta musu, dan tun jiya dama a tunzure take da abinda Iffah'r tayi. Koda Iffah'r ma ta gaisheta cikin yake ta amsa gain yan uwanta duk sun zuba mata ido.Amma zuciyarta tafasa take da yanda suke ta sanya albarka da yaba abinda Iffah'r tayi, tare da tabbatar da shugabansu kuma dansu yayi dace da mace ta gari mai buda masa hanyar alkairi. Sukam suna farin cikin shigowarta cikin ahalinsu. Wasunsu harda kiranta gagara badau wadda tafi karfin duk wani shedanci a azzaluman masarautar.
Iffah da mur mushi kawal ta dingayi kasa-kasa. Tayi zaman kamar awa guda sannan tai musu sallama akan zuwa anjima zata aiko azo da su su gashe da Shahan-shan. Wannan zance nata na karshe ta sakasu sake shiga jin dadi, dan a cikinsu ma akwai wanda rabonsu da Tajwar Eshaan din tun kan a bar kasar da shi, Kuma uwa daya uba daya suke da Malikat Bushirat din, Sun baje babin hira da sanya albarka ga Iffah Jasrah ha kara basu labarinta. Babbar yayar su Malikat, Bushirat din da suke kira Akia Badiha cikin nuna jin dad) ta furta, "Al ni babban abinda ma ya sakani farin ciki fiye da komai wannan cikin na jikinta, dan zamu samu tsatson alkairi a zuri'armu, ALLAH dai ya raba lafiya".
Kusan a tare duk suka dubeta. Malikat Bushirat da ke kishingide tana shakar iska da fesarwa harda zabura. Jasrah ce tai karfin halin fadin, "Akia wal waye mai cikin? Kin samu a rudan!" Baki ta Kara washewa, cikin barkwanci ta ce, "Aw to tunda baku ramfo ba ku bada goron albishir tukkanna. Kudi sabbi kal-kal Jasrah ta sauke cikin tafin hannun Akia Badiha, cike da zumudi ta ce, "Muna saurarenki".
"Uhm wadan nan din ma babu laifi, sai dai da kanku ma zaku karo idan kunji. Insha ALLAHU muna gab da samun Miran, ko Daneen a wannan masarautar. Dan da alama Zawjata-almilk tana tare da shigar ciki".
"Whattt!!!!!!".
Suka fada cikin hada baki da hun murna. ALLAH ma ya sosu hadimai yau an basu freedom din kansu sai dai-daiku dakan dan shigo dan an bukaci ganinsu. To su sunama a falon Malikat Bushirat din nacan ciki ne iya su dan yau ranar baje kolin hirar zuminci ce. Wani irin diff-diff kirjin Malikat Bushirat keyi, zuciyarta kamar zata faso ta fito. Ga kanta da yay wani irin azababben sarawa, sai ta fara ganin falon na juya mata da su da ke ciki. Tashi tai da sauri ta nufi daki ta kulle kanta. Tana gama sakama kotar key ta daura goshinta jikin kofar tai wani irin fashewa da kuka mai tahowa irin gaba dayan nan mutum yaji kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa..
Bama su fahimci halin da take cikiba su balle tashinta, sunata murnarsu, sai da mai bima Malikat Bushirat din ta juyo tana magana idonta ya sauka a wajen zamanta wayam. Bata kawo komai a ranta ba a tunaninta duk murnarce ta kebe yin abunta dan sun san yar war tasu da shegen kasaitar son mulki kamar itace Shahan-shan din ba matarsa ko uwa ba…..
*A bangaren Iffah kam tana sashan Malikat Haseenat, taso ta samu Iftihal dan yau tayo mata tanaji sai dai aka samu rashin sa'a wai ta fita ita da Husam babban dan Miran Jasim. Anan ma Iffah ta jima sai bayan sallar la'asar ta baro, sunata shan hirarsu ita da Mammah da Mammy. Daneen Waheeda dai bata saka baki sai lokaci-lokaci...
Tattauna zancen cikin Iffah ga zuri' ar Malikat Bushirat ya sa ya fito har ya fara yawo a cikin masarautar. Dan danan fa aka fara wani karamin bikin murna da sam Iffah da Tajwar Eshaan da sai da akai sallar la'asar ya samu kansa basu sani ba. Hasalima suna can manne da juna abinsu hankalinsu kwance da jin tamkar suma kadaine a cikin duniyar (Su bily duk an mutu ashe 😏🤔👹). A kankanin lokaci zancen ya cigaba da shiga lungu da sako. Da ga masu shiga farin ciki sai masu shiga rudani da tashin hankali dan abune da basuyi zato ba...
"Aiko lokaci yayi da zaki bijiro da zancen auren nan Waheeda".
Malikat Ashwag ta fada cikin tashin hankali bayan gama sauraren Daneen Waheeda. Daneen Waheeda da gaba daya ita tasan kunar da zuciyarta ke mata ga rikicin Iftihal taja numfashi mai matukar zafi. "Hakane Ashwaq, amma kin san kafiyar Mammah, ga shi Ammarah sam nunawa ma take tafi son yarinyar nan sama da Iftihal din, taya kike ganin hakan zai yiwu cikin sauki?".
"Yuwuwarsa daya ce, mu nema su Sayeed Tasaddug-Husain da zancen shi da su Sayeed Hifzur-rahaman, da Sayeed Fayzul-haq tunda sune dai iyaye a gidan nan, duk da yake shugaba suma ai sama suke da shi, kuma dama a duk aure-auren nasa ai sune dai Mammah ke sakawa gaba ko da su Jasim".
"Eh hakane, kema kin kawo shawara mai kyau.Yaushe kike gain zamu samesu?".
"Ko zuwa anjima dan ba'a bori da sanyin jiki. Bara na kiga mu nema ganawar sirri da su, da ani ishan'i insha ALLAHU sai kawai mu zauna"...
(To koyaya zata kasance,Iffah'r mu ga Abar nan na tunkaro ki ki hira 😝😢)
Su Malikat Ashwaq sun gana dasu Sayeed Fayzul. haq, sun kuma tattauna sosai da sauraren abinda Daneen Waheeda tazo da shi, shi dai Sayeed Fayzul- haq ma baice komal ba. Garama Sayeed Hifzur- rahaman yace su basu lokaci zasuyi magana da Mammah a kuma jira Sayeed Tasaddug-Husain ya dawo daga Umrah gobe insha ALLAHU. Daga haka suka rabu.
A lokacin da suke tasu tattaunawar Iffah na can taima yan wan Malikat Bushirat rakkiya ga Shahan- shan da ya sakko hawa na biyu. Ya nuna farin cikin ganinsu shima, dan bai taba zama irin wanna dasu ba tunda yasan kansa, ballema yanzu da yake a shugaba. Suma duk wanda ka kalla zaka fahimci tsantsar farin ciki a tare da shi. Sun kuma ji dadin yanda ya dan sake dasu yay hira duk da maganar daya biyu ce dai. Sai dai abu mafi kayatar da su yanda ya girmamasu ya mutunta su. Sai kuma komi yake idonsa aka matarsa Iffah. Kusan zaman awa daya da rabi sannan sukai masa sallama...
Bikin sallah ya cigaba da gudana masu ziyara nata zuwa gaishe da Shahan-shan. Yayinda Malikat Bushirat ke a birkice, gaba daya Jasrah tama kasa gane kanta. Tayi kiranyen uwa har ta gaji amma taki zuwa. Sai taji komai ya karasa kwace mata. A kwana na uku da salla sai da doctor ya dubata. Jasrah dai tai
shiru da bakinta babu wanda ya sani gudun kananun maganganu. A washe garin cikar sallar kwana hudu Maganar komawa zaman kotu taje kunnen kowa, dan haka wasu suka kasance cikin zullumi da tsoron karfa garin tone-tone ga su Miran Jasim suma tasu allurar ta tone galma..
* KOTU*
A yanda zaman shari'ar ma ya cika yau sai ya baka maraki. Dan tarin matasan nan a yanzu da Iffah ta dunkule waje daya bisa jagorancin Sayeed Fayzul- haq kaf dinsu sai da sukazo. Abinda basu taba yi ba tunda ake zaman shari'ar. Hakama wasu a mata da mazan masarautar sun karu. Kotu dai ta cika tai hani'an masha ALLAH.
Tsabar yau Iffah da jin kai ta shigo da yafi na kullum ma Shahan-shan ya rigata zuwa. Dan kusan itacema karshen shigowa da hadimanta. Nana kowa ya zuba mata ido harda uban gayyar ta cikin glasses din da ya boye idanunsa. A ransa kam kara jinjina fitinar yarinyar nan yake. Tafa rigashi kammala shiryawa amma tsabar taso neman magana sai ta gudu sashenta har sai da ya rigata zuwa kotun. Yau ma sai da taje ta gaida Malikat Haseenat da su Daneen Ammarah. Hakama Malikat Bushirat da tai wani irin ramar fita hayyaci da mai lurane kawai zai fahimta, dan abin dariya yau harda eyeglasses a idonta itama, da alama akwai abinda take boyewa. Hannu kawai ta dagama Iffah a maimakon amsa mata gaisuwa, ko a kwalar jikin Iffah tama mike abinta tana takun nan nata na neman magana.
Bayan nutsuwa kotu yanda ya kamata aka shigo da su Miran Arshaan. Sunyi duhu sosai sun rame. Ba duka ba zagi babu harara zaman duhun nan kawai da suka saka Iffah ciki a wancan karon da bakin cikin kamar su a cikin kurkuku ya maida su haka. Yan kananan magana ne suka fara tashi a kotun har sai da aka tsawatar. Ameera Haifah dai sai faman rufe fuska take da mayafi, gashi yau kuma harda iyayenta itama a kotun dan habanta yazo akan maganarta tun washe garin rufesu amma bai samu gain Tajwar Eshaan ba.
Bayan kotu ta sake nutsuwa Sayeed Hanifud-Din ya karanto karar haka. "Har yanzu dai muna kan zaman shari'a ne akan Miran Jasim da ya bada madara mai dafi ga Zawjata-almilk ta shayar da wanda suke son halakawa. A wancan zaman kotu ta bada damar kawo bokansu a zama na gaba, sai kuma aka samu wani al'amarin akan Miran Arshaan da Ameera Haitah, wanda yay dalilin kaisu kurkuku suma, zaman makwaftakar Miran Jasim da Miran Arshaan ta zakulo wasu sabbin abubuwa masu ban mamaki da ya karata ace an fara saurare a wannan shari'a kafin a cigaba da yinta. Idan adalin shugabanmu ya bada damar hakan to".
Hannu Shahan-shan ya daga a hankali da yin alamar an baka dama. Godiya Sayeed Hanifud-Din yayi sannan ya kalla shugaban jami' an tsaron. Mikewa shugaban jami 'an tsaro yayi, yayinda Miran Arshaan da Miran Jasim ke kallon juna a rikice, dan sun dai san karn kalar tabargazar da sukaira juna da tone-tonen tsiyatakunsu a cikin kurkukun. A hankali Iffah ta
saki wan irin sassanyan murmushi. Cikin Sa'a kuwa sai a idon su Miran Jasim din kamar an kirawosu su dubeta........✍️
😂Gaskiya Iffah virus ce 😆🚴🚴🚴🚴
DAUDAR GORA....!!