← Book details Daga Raino Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 6

Sashe 2

Daga Raino Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi wa yan uwansa ko mahaifan sa wani abin. da ido ta bisu har suka ajiye su dada albarka ta dinga saka mai haka ma , malam da umma. ganin lokaci yana kurewa koma gobe yana da patient da zai duba kuma yana da wanda zai musu theatre. kallon jidda yayi yace, '' ki haɗa kayan ki yanzu zamu huce.,, Ihu ta saka tana buga kafar'ta nuratu minal me za su yi idan ba dariya ba dakyar dada ta lallaɓa ta , ta shirya ta fito tana share hawaye kayan ta ta dauko da yake ɗazu sukai wanki umma ta saka su, sukai ninki dan haka kayan kawai daukan su tayi a karamar Ghana most go. Nadiya amsar sultan tayi sukai musu sallama. har kofar gida dada ta rako su haka su minal sai tsokanar ta suke yi. buɗe mata gidan baya yayi ta shiga ya miƙa mata sultan ta riƙe jakar ta a boot ya saka ta shiga mazaunin direba yayi nadiya ajiyar zuciya ta sauke ba karamin dad'i taji ba da suka fito waje ji take kamar a kaya take. a hankali suka soma tafiya Sultan kwanciya yayi a jikin jidda a hankali bacci ya sauke sa. gyara mai ƙwanciya tayi itama ta miƙe kafar ta ta kwanta. ba ƙaramar tafiya sukai ba nadiya kallon sa tayi tace '' gaskiya inhar ba zaka biya mana kudin jirgi ba , bazan kara zuwa garin nan ba kalli awan mu nawa sai yanzu muka shigo. be kulata ba yayi horn a wani katafaren gida. Mai gado ya buɗe mai a lokacin kuma kissa ta , tashi zaune shaf ta manta da sultan a jikin ta aikuwa ya fado ya zunduna ihu. da sauri nadiya ta juyo tana mata faɗa daukan sa tayi tana shafa bayan sa jidda ware ido tayi ta soma kalle kalle fitowa sukai suka barta a ciki. ganin bata da niyar fitowa mansur yace'' fito mana mun zo.,, da sauri tace '' ban iya budewa ba .,, Nadiya yin gaba tayi tana jan uban tsaki zuwa azare be mata rana ba gashi ta dawo da wata bagidajiya yar kauye bude motar ma bata iya ba. jakarta ta buɗe ta ciro wani kati ta saka a jikin kofar. Budewa tayi ta shiga parlour ne iya parlour duk wani kayan jin dadin rayuwa akwai shi kujeru set uku ne a parlour. bata tsaya a ko ina ba sai a bedroom din'ta ajiye Sultan tayi, ta shiga toilet. a bangaren mansur dauko kayan jidda yayi yana gaba tana bin sa a baya har suka shigo cikin parlour. zama tayi a ƙasa ajiye mata kayan ta yayi kusa da ita ya shiga daki ganin sultan yana zaune yana kuka da sauri ya dauke sa ya fito da shi. miƙa wa jidda yayi. ina tana kalle kalle bata san ya miƙo mata ba sai da yayi mata magana da sauri ta kalle sa ta amshe shi. shiga kitchen yayi buɗe fanfo yayi ya wanke hannayen sa sannan ya buɗe fridge lemo ya dauko cake a cikin wani box me kyau fitowa yayi dashi ya ajiye a lokacin kuma nadiya ta fito daure da towel ko rufe mata cinya me yi ba amsar sultan tayi tana cewa beb tafiya nayi na watsa ruwa ga kukan da yake anya kuwa zai yarda da yarinyar nan...?'' lemo ya buɗe ya kai baki sa sannan ya ajiye yace '' yau da gobe babu abin da bata saka wa zai yarda da ita.,, Okay ta faɗa tana juyawa. Jidda kunya ce ta kama ta , tun da take bata taɓa ganin wannan rashin kunya haka ba ko matar yaya ado idan zata shiga bayi da hijabi take shiga ashe yar iska ce sai wani taɓe baki take. tana cikin wannan tunani yayi mata Magana da sauri ta ɗago tace '' na'am yaya.,, dauki kayan ki, ki shiga can dakin. tashi tayi tace '' to.,, dauka tayi ta tafi dakin da yake facing din'ta. a hankali ta tura kofar daki ne me kyau komai akwai ajiye kayan hannun ta , tayi ta kwanta akan kujera tana sauke a jiyar zuciya da yake a kwai kujera guda daya a kwai gado. mamakin dukiyar yayan nasu take , a hankali bacci ya dauke ta ba zato ba tsammani taji ɗala mata duka da sauri ta miƙe tsaye jikin ta yana rawa domin sosai dukan ya shige ta. Nadiya ce tsaye akan ta abincin hannun ta , ta ɗangwarar mata a ƙasa duk kusan rabi kantso ne kallar abincin tayi ta ɗago ta kalle ta tace '' ngd aunty.,, harararta tayi ta ajiye mata sultan tace '' dan uban ki ba zama kika zo ba kar na ƙara ganin kin kwanta a kan kujera dan uban ki a nan kika saba kwanciya ne...? da zaki miƙe min wannan bak'ar kafar taki...? idan kika ji yayi kuka kisan yadda za'a yi ki lallashe shi karki kawo min shi zan huta ne.,, Jidda muryar ta na rawa tace , '' to inshallahu bazan sake kwanciya ba kiyi hakuri.,, rankwashin ta , tayi akai ta juya tabar dakin jidda daukan Sultan tayi tana shara kwallar ta zama tayi ta soma cin abincin da ta kawo mata da yake yunwa take ji tas ta cinye shi ruwan da ta kawo mata a cikin kofi ta sha tana kokarin ajiyewa ta shigo tana harararta tace, '' ki ajiye plate din da kofin a wajen ki komai da shi zaki dinga yi karki saka min cuta ni da ɗana.,, Jidda to tace mata.. kwanciya tayi a ƙasa ta kwantar da sultan a ruwan cikin ta yaron laluban ta ya fara yi yana son ya sha nono da sauri ta ɗauke hannun sa tana rarraba ido so take takai mata shi tana tsoran tijarar ta. mansur ne ya shigo da wando three quarter da riga armless ba ƙaramin kyau kayan sukai mai na milk da maroon kalar kayan ga wani farin glass da ta saka da laptop a hannun sa yace , '' ta kawo miki abinci...?'' da sauri ta tashi ta ɗaga kan'ta kwallah na taruwa a idon ta so take tace mai gida take so amma babu fuska ko dama tana shakkar sa ɓalle yanzu da ya ƙara zama kalar masu kudi komai nasa ya canza ya zama kato. bece komai ba ya juya ya fita kuka ta rushe dashi kifa kan'ta tayi a jikin gado ta fara kuka har ga Allah bata son zama a cikin gidan nan. ta jima a haka sannan ta tashi, ta hau kan gado ajiye Sultan tayi a hankali da ya fara bacci. saukowa tayi so take tayi fitsari ya matsai ta amma ta ƙasa faɗa domin bata san toilet ba ganin yana shirin kashe ta fitowa tayi bata samu kowa a parlour ba sai jin hayaniyar su tayi sama sama tafi jin Muryar aunty nadiya sai dariyar yaya da taji bata , taɓa zaton yana dariya haka ba. a hankali ta fara dube dube cikin Sa'a ta gano bayan gida shiga tayi cire pant din'ta tayi ta saki fitsari a ƙasa. Kunna fanfo tayi, tai tsarki ta fito cin karo tayi da nadiya da sauri ta ja baya muryar ta tana rawa tace '' dan Allah kiyi hakuri..,, wani kallo tayi mata ta shiga toilet din da sauri ta fito tana fusgo ta , tace '' uban waye yace miki ana fitsari a kasa salon ki saka min wata cutar.,, da sauri tace '' kiyi hakuri mu a garin mu fitsari muke yi a kasa ban san a ina zan yi ba.,, Marin ta , tayi da sauri ta riƙe kumatun ta tana kuka. Mansur ne ya fito jin maganar nadiya tana faɗa kallon ta yake cikin mamaki. dukkan su juyowa suka yi nadiya da sauri ta riƙe hannun jidda tana cewa yi hakuri kin ji kanwa'ta sweet bigewa tayi gaskiya jidda akwai shagwaɓa daga bigewa sai kuka. bece komai ba ya hau sama. tana ganin yayi nisa ta tankada jidda bigewa tayi da bango cikin tsananin tsanar jidda tace , '' saura kuma ki faɗa mai me nayi miki banza huce ki ɓace min daga gani.,, da sauri jidda ta bar gurin jikin ta yayi mugun sanyi shiga daki tayi Sultan sai kuka yake daukan sa , tayi tana rarrashin sa har yayi shiru. Study room. gaba ki ɗaya ya mayar da hankalin sa kan computer da yake dannawa a hankali nadiya ta turo kofa ɗago da kan'sa yayi ya kalle ta murmushi ta sakar mai tace , '' yallaɓai sannu da aiki ko na zo na taya ka ne...?'' murmushi yayi yace , " a'a Nagode Sultan yayi bacci ne ....? " uhmm yayi yana hannun aunty'n sa jan kujera tayi, ta zauna tana danna wayar ta. ganin lokacin sallar magariba yayi kallon ta yayi yace "sweet lokacin sallah yayi " sosai take jin dadin charting ɗin da take yi dan haka tace mai uhmm yanzu zan tashi nayi. mansur be ce komai ba ya tashi rufe computer din sa yayi ya gyara zaman takardun da suke kan table din sannan ya shiga toilet. alwala ya dauro ya fito still tana zaune tana danne dannen ta yasan ko yayi mata magana cewa za tayi shi take jira ya fito dan haka sai ya murda handle ya fita a hankali ya rufe mata kofar. cikin takun sa na isa da kasaita haka yake sauka daga kan staircase din. har ya sauka bedroom din jidda ya shiga tana zaune sultan yana kan cinyar ta jin shigowar sa da sauri ta ɗago sai dai bata iya haɗa ido dashi ba. sai tayi ƙasa da kan'ta. cikin tsare gida fuskar nan tashi ba annuri yace, " baki ji an kira sallah bane ....? " Jidda cikin sanyin murya kamar ko da yaushe tace , " yanzun nan zan yi alwala." bece komai ba ya juya ya fita jidda ajiye Sultan tayi. ta buɗe jakar kayan ta zani ta dauko na atamfar ta cire hijabin ta , tayi ta dauki Sultan ta saka shi a gadon bayan ta , ta goya shi. Hula ta dauka ta saka Sannan ya fita parlour shiru babu kowa hakan ne ya saka ta samu kwarin gwuiwar shiga toilet domin dazu bata manta abin da ya faru
Chapter 2 · 0% Book details