Sashe 1
Daga Raino Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
DAGA RAINO Episode 1 AZARE Yara ne suka zagaye motar suna taɓa wa nadiya guntun tsaki taja ta gyara zaman sultan da yake cinyar'ta. Dr mansur kallon ta yayi yace '' are you okay...?'' bata ce mai komai ba ta buɗe kofar ta fita Sultan ta saka a kafaɗar ta , tana jin tsanar garin na ƙara rufe ta ban da ta matsa sai ya zo ita kuma bata so su rusa mata shirin ta da ba zata taɓa barin sa ya zo gurin mahaifar sa. wani durkusasshen gida ne na laka. kofar gidan almajirai ne zaune wasu na rubutu wasu na biya karatu. Wani dattijo ne zaune da Kur'ani irin bugun falle falle din nan na da, a hankali ya ɗago sosai yayi mamaki yau mansur idon sa yake gane masa. Yaron da yafi wata biyar ba kira ba aike farin glass din sa ya dauko ya saka domin a ganin sa ba daidai idanuwansa suke gane masa ba. Dr mansur Suleiman azare ƙara sowa yayi ya ɗurkusa har ƙasa ya gaishe da Malam babba me allo kaf fadin azare kana fadan wannan suna gurin sa za'a kawo ka malami ne babba wanda ake ganin girman sa. kan'sa a ƙasa yace, '' malam ina wuni.,, ajiye kur'ani yayi yace, '' mansur lafiya qalau yau kai kake tafe..?'' kan'sa a kasa yace, '' eh wallahi na same ku lafiya...?'' Alhamdulillah kowa lafiya qalau. ya faɗa yana daukar Kur'anin sa. mansur ɗago kan'sa yayi ya kalli nadiya da ta tsaya a can gefe da ido yayi mata alama tazo. Ranta idan yayi dubu ya ɓaci haka ta ƙara so ina wuni. Malam cikin fara'a yace '' mun wuni lafiya ya jikan nawa...?'' Alhamdulillah lafiya qalau ta faɗa tana kawar da kan'ta gefe hannu ya saka ya karbi Sultan yaron kallon sa yake yana mai dariya da yake masha Allah akwai fara'a. tashi mansur yayi, itama tashi tayi ba ƙaramin hakuri nadiya tayi ba ganin malam ya dauki wani ruwa a kofin silver ya bawa sultan yaron ne yake ta kallon lokacin da yake basa ruwa shi ne ya dauki ruwan ya basa. suna shiga soran gidan ta ja tunga ta tsaya tace '' sweet gaskiya ka karbo min yaro na ko baka ga ruwan da malam ya bashi ba kar wata cutar ta kama shi...?'', haɗe rai yayi yace '' nadiya me kike nufi mahaifina zai bawa sultan abin da zai cutar dashi ne...? Me ya saka kike haka ne ...? Wannan ruwan da kike gani shi nasha na girma har kika gani kika ce kina so na na aure ki.,, yana gama fadar haka yayi gaba takaici hana ta magana yayi, ɗage abayar ta tayi tana jan karamin tsaki. gidan duk kwata dakyar kake samun hanyar shiga cikin gidan. sallama yayi Dada ta take tsakar gida a zaune ta kunna Radio da sauri ta washe baki tana cewa miji na yau kai ne a gari... matar ta tuba bata rasa miji da nayi fushi har ina cewa na sake ka saki tara yanzu kuwa na komar da kai. dariya yayi yace , '' dada kenan daman ni nasan ba wanda ya isa ya raba mu.,, Hakane kishiya ta ta kike rabe rabe zo ki zauna anan ta nuna mata , tabarmar kaba. zama tayi tana yatsuna fuska kan'ta yana ƙasa tace '' ina wuni.,, Dada tace '' lafiya sumul qalau ina Sultan yake badai ya isa yaye ba...?kin baro shi a gida.,, a'a tare da shi muka zo mansur ya bata amsa. Dada tace '' maman taku tana daki ku shiga kwana biyu bata jin dad'i alhamdulillah yau jikin ta yayi sauki maharazu ya siyo mata magani tana surfe turmi ya fashe ya bugar mata kafa wallahi shikkenan take ciwo.,, tun kafin dada ta ƙara sa ta miƙe ya shiga daki jikin sa yana rawa tausayin umma ne ya kama shi umma uwa ta gari umma da take kin ci take kin sha duk ganin yayi karatun boko da yake so yayi ta siyar da kayan dakin ta yau shine ya samu abin duniya ya bar ta a haka ina hankalin sa yake me yake damun sa anya kuwa be zalinci kan'sa ba. ɗurkusawa yayi ya shiga dakin tana kwance sai numfarfashi take domin kafar'ta ta takura mata. dafa ta yayi yace '' umma.,, a hankali ta ɗago kan'ta bakin ta narawa tace '' Mansur kai ne...?'' ta faɗi haka cikin rauni da son tabbatar da abin da take gani a zahiri domin ta jima tana mafarkin ya zo lokaci ɗaya suka dena samun sa a waya kullum sai ace musu user busy. a hankali ta , tashi zaune ta cire mayafin da ta rufe kafar ta dashi kafar ta kumbura sosai. Mansur ƙasa yayi da idon sa ya riƙe hannun mahaifiyar sa yace '' umma ki yafe min. ,, dafa kan'sa tayi tace '' Mansur ko sau daya ban riƙe ka a cikin zuciya ta ba kullum addu'a nake maka babban buri na ka samu ka ciyar da iyalan ka ni basai ka bani ba , nasan idan kana dashi sai inda karfin ka ya ƙare duk rintsi duk wuya karka ci abin da bana ka ba duk inda halak take ka neme ta domin inhar ka fara cin haram ka lalata kan'ka da zuri'ar ka wallahi dakin nan da yana magana sheda ni kullum cewa nake Ubangiji ya yafe maka ni bakai min laifi ba Allah ya yi maka albarka kai da yan uwan ka karkai sakaci da ibadah.,, duk dakiya irin tasa sai da yaji kwalla ta , tarar mai a idon sa umma ta cika uwa ta gari duk irin abin da ya faru ita kawai babban burin ta ya bawa iyalinsa ita basai ya bata ba ajiyar zuciya ya sauke yace '' ya jikin naki...?'' da sauki yanzun nan ne ma ta dan tayar min. ta faɗa tana kallon kafar tata. Mansur yace '' umma ki dena wannan surfen da kike yi ga yaran nan nan idan ma ya zama dole kiyi balle insha Allahu ba zaku ƙara sake shiga wani hali ba Allah zai rufa asiri.,, umma tace '' mansur kenan zama guri ɗaya ba dad'i yaran da suke da son jiki musamman ma nuratu bata son ta daga ko tsinke ne dan ma ina mata jan ido.,, Mansur yace '' to har da nake cewa son tafiya da ita , kinga nadiya aiki take fita sai ta dinga dan temaka mata da wani abun zan saka ta a makaranta ga rainon Sultan ita kinga aiki take tafiya....,, Umma tari ne ya tsarke dakyar Muryar ta , take fita tace '' a'a ba zan baka nuratu ba ga jidda nan ka dauke ta shikkenan mu cika alkawarin da mukai wa shatou.,, gaban sane ya faɗi shifa shaf ya manta da wannan maganar danne fargabar sa yayi yace , '' to shikkenan ba damuwa .,, yauwa Allah yayi maka albarka kai da yan uwan ka yau zaka tafi ko sai gobe...?'' Mansur yace '' yau inshallahu.,, Umma jin jina kai tayi a hakan ma taji dad'i ganin sa da tayi. nadiya ce ta shigo a can gefe ta zauna ta gaishe da umma amsawa tayi cikin kulawa. tana tambayar ta ya iyayen nata alhamdulillah lafiya qalau tace musu. umma kin ga nuratu ta hana ni daukan sultan ko, wata yarinya ba zata huce shekara goma sha ɗaya , ba ta shigo tana fadar haka. Ganin yaya da matar sa da sauri ta gaishe da su amsawa yayi kan'sa yana kan wayar sa jidda zama tayi tana cewa umma kice ta bani shi gata can ta , tafi gurin dada dashi. Umma tace, '' ki kyale ta ke da riƙe shima sai ya ishe ki tare zaku tafi.,, da sauri ta zaro ido lokaci ɗaya nadiya ta ɗago ita da gidan ta shi ne zai dauko wani be faɗa mata ba ai ita ce me gidan tun da dai ta haifi da namiji yanzu duk rabin dukiyar mansur tata ce. Mansur ganin yadda take kallon sa sai yayi sauri ya rubuta mata message kamar haka nasan Sultan yana hanaki fita aiki da wuri da shirin sa shi ne nace a bani ɗaya a cikin kanne na su dinga temaka miki kinsan ni bana son yan aiki ga kanne'na nan suna bukatar temako. ajiyar zuciya ta sauke ta zata haka kurum yace zasu tafi da ita da yaga tashin hankali ita bata bukatar kowa daga dangin mijin ta ya rabe ta. Jidda tashi tayi, ta fita ta zauna a kusa da, dada tace '' umma tace zanbi yaya dan Allah ki ce tayi hakuri ni wallahi bana son binsa .,, Ungo dan uban ki kaf cikin ku, ki godewa Allah shi ne za kiyi mai butulci birni fa zaki tafi Abuja garin shugaban ƙasa.,, hawaye ta share dan da gaske bata son tafiyar nan. dada shiga daki tayi ta dauko nono me kyau fari tas dashi a cikin kwarya da ludayi fefe ta saka ta rufe nonan tace '' maza tashi ki kai mai.,, turo baki tayi ta dauki ƙwayar ta shiga dakin ajiye mai tayi s gaban sa bata ce komai ba ta juya ta fita idon ta duk kwallah ta taru. budewa yayi sosai yaji farin cikin kawo mai nono da Dada ta yi daukan ludayi yayi, bismillah yayi ya kai bakin sa. Jidda dawo wa tayi ta ajiye wa nadiya a kusa da ita nadiya tace '' dauke alhamdulillah na koshi.,, domin ko taba kwaryar ba zata iya ba wallahi. to tace ta ɗauka ta kai wa dada. tace '' tace ta koshi.,, Dada ta ɗaga murya tace '' ke bana son ki dauke mu a matsayin surukanki ki sakata ki bararraje nan ma kamar gidan ku ne.,, Nadiya tace '' wallahi da gaske na koshi.,, to ai shikkenan cewar Dada. Malam ne fa su maharazu suka shigo kara gaisawa suka yi. Mansur fita yayi shi da maharazu. Nadiya ba ƙaramin takura tayi ba fitowa tsakar gida tayi kamar ance kallo hanya ganin maharazu da wasu yara da kwalayen macaroni taliya shinkafa buhu uku ta gani. ta shiga uku shikkenan shirin ta ya lalace shi ya saka tayi blocking din su, suka dena samun sa innalillahi wa'inna ilaihir raji'un babban bakin cikin'ta tagan sa