← Book details Bangare Nah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 3

part of me

Bangare Nah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bismmillahir rahmanir Raheem
Ina farawa da sunan Allah mai rahma mai jikai......
Wanna shafin nakune masoyan littafin BANGARE NAH.... ALLAH YABAR KAUNA AMEEN YA ALLAH........
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
{Arewa ginshi
in al'ummah}
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]
... ... ... ... 1
"BASSAM ASIM! shine sunan da taketa mai-maitawa a zuciyarta hakika abun yazo mata a bazata"
"Yaron tabbas yayi saidai kuma yarintar shi itace abar dubawa tayaya zata iya tarayyah da yaronda ta kusa haifa wannan dacewar shi Ashrab shine dai ba ni ba"
"Tayi zurfi atunani Farha ta shigo palourn bakinta dauke da sallama ta mai-maita sallamar har kusan sau uku amma hajiya salma bata ma santana yiba hakan sai ya bawa Farha mamaki matuka"
Kusa da ita takarasa tare da dafa kafadar ta mummy lafiya inata sallama amma naga kamar hankalinki yana wani gurin firgigit!! tayi ta dawo cikin hankalinta,
Na am Farha baby kin dade ne ban jiba ta zauna akusa da ita ta janyo hanayenta mummy nah lafiya? Meyake faruwa ne kinsan fah bana son damuwar ki
Hajiya salma taja dogon ajiyar zuciya tace bakomai yarinya ta damuwar tana da nasaba da office ne kada hakan yazama damuwa agareki kinji yarinyar dady takarasa maganar cikin sakakkiyar fuska tamkar ba wani abun da yake damunta.......
"Haka ta zauna cikin tunani tsahon dogon lokaci batare da ta sanarda yaranta komai ba
"BASSAM yana fita daga gidan ya kirah munubiya tana murmushin samun galaba hello tace cikin narkewar murya yace my sweet heart every things is don kuma ga alama komai zai tafi yanda aka shirya shi"
"Ta sheke da dariyar samun nasara tace dama na gaya maka ai bana tunanin dama rashin samun nasara saboda ban taba farawa nakasa karasawa ba"
"Ya lumshe idanuwan sa yace ai na fahimci ta fada fah"
Tayi dariya tace dama nasan zata fada bana tunanin akwai macenda zata kasa fadawa komar ka BASSAM kaidin na daban ne ni nasani
Saidai kuma inason kasani wannan auren na manufa ne ban amince kasaki jikin ka sosai ba dan Wallahi banida kyau kuma kai ma kasan da haka
Ya lumshe idanuwan sa kamar tana ganin sa yace kada wannan yazamar miki damuwa ai bana tunanin akwai wata matar da zata fiki matsayi a gurina"
Yanda yayi maganar har wani yarrrrrrr taji jikinta yayi ta lumshe idanuwanta ina fatar haka BASSAM saboda bazan iya sharing dinka da kowa ba kaidin na musamman ne agareni ina sonka sosai...... Ko wannan zan daure ne kawai saboda inada abunda nake nufi da hakan amma idan ba haka ba babu gangan cinda zai sanya nayi wannan danyen aikin"
tabdijam"......
BANGAREN HAJIYA SALMA
Tunani kyakkyawar fuskar shi ya gagarah barin zuciyar ta yayinda sunan sa yake yawo acikin zuciyar ta bayan ko wacce dakika kala mansa sunyi matukar tasiri azuciyar ta
Ta ja dogon hajiyar zuciya hummmmmm!!
A hankali take tambayar kanta me hakan yake nufi ya kamata ki nutsu Salma wata zuciyar take sanar da ita
Kada kyau da kuruciyar shi yayi tasiri azuciyar ki, ki ajiye wannan shirmen gefe zuciyar ta takara sanar da ita.....
Ta kwanta sosai a kan gadon ahankali tace me yake shirin faruwa dani ne ta runtse idanuwanta gam... Tabbas yakamata na dawo cikin hankalina.. Soyayya ba tawa bace abun kunyar ma da yaro sa'an kanina mtssssss taja dogon tsaki wannan ai abun kunya ne"
Har karfe 12:00am na dare tana abu daya can wayar ta tashiga neman taimako tayi matukar mamakin ganin waya awannan lokaci ta sanya hanu ta dauka number an boye ta abun ya kara daure mata kai ta share har saida ta tsinke aka kara kira karo na biyu nan ma taki dauka kirrrrrr taji shigowar sako yashigo da har ta share shi wata zuciyar tace ki duba mana ta janyo wayar ta bude
My soul shine rubutun farko a sakon
Gabanta yafadi shine sunan da Alhaji musaddiq yake kiranta dashi a mafi yawancin lokaci.
"Tunaninki yaki barin zuciyata tsahon dogon lokaci soyayyarki taki barina sukuni
Ina neman sassauci daga ma, abuciya kwarjini da kamshi hakika kedin haske ce wanda baya ta'ba disashewa
Ki tausayawa zuciyar masoyinki mai matukar kaunarki ............
Akwance take amma saida ta mike zaune ta maimata karanta sakon yafi akirga
"Kalamansa taketa mai-mai tawa taja ajiyar zuciya mai karfi na shiga uku....
"Ta furta ahankali ya zanyi,..... "Yayita kira amma takasa samun sukunin dauka saboda zuciyarta tagama rauni...,,
"A nasa bangaren murmushi yayi na gefe baki yace a fili salma yanzu muka fara bazan taba kyaleki ba har sai na cika burin zuciyata akan ki"
"Soyayyar gaskiya nake miki ba wai son yarjejeniya ba dan Haka bazan taba hakura ba
tabdijam lallai akwai tashin bama-bamai kenan idan har munu tagano manufar ka".....
"Ashrab da Farha sun gama fahimtar mum dinsu tana cikin damuwa amma abun mamaki taki ta sanar dasu komai sunyi tambayar duniya amma amsarta bata wuce ba komai"
"Hakan nan suka hakura badan sun yarda ba ,.. Munubiya kuwa farinciki fal zuciyarta dama haka takeso domin kuwa hakarta ta fara cimma ruwa saida Farha tatafi school tukunnah ta nufi dakin hajiya salma, tana zaune kamar kullum tana aiki wato tunani munu tayi sallama ta shigo dakin tundaga nesa tasaki murmushi sannan ta karasa gurinta ahankali ta dafa ta mummy lafiya naga kamar kinada damuwa,..... "Ta dago tare da jan dogon ajiyar azuciya kana tace"
"Ba kama bace munu ina tare da damuwa wallahi tun lokacin da bassam ya bayyana cikin rayuwata banida sauran sukuni har yau...... Cikin rashin fahimta tace waye kuma haka mum ta dago wannan bakon mana tajim alamar tunani can tace aw wannan yaron na kwanaki ta jinjina kai shi munu...... Kece kike ganinsa yaro amma zuwanshi yana da tattare da abubuwan al-ajabi kamar yaya mum?
"Hakika yazoh da babban al-amari munu ta dago nifah ban ganeba har yanzu mum ta rigo hanunta sona yake munu.. Kalmar so da ta furta Bassam yana yimata ya yi matukar kona zuciyar munu ta rintse idanuwanta wata zuciyar tace ki nutsu munu ta yi murmushi tace....
"Ni aganina wannan ba abun damuwa bane ki amince mana inaganin yafi zaman ki ahaka kada ki manta shekarun ki karuwa suke zamanki ba miji inaga baiyi ba"
"Na sani munu ba abunda nake tunani sai ya'yanah matsalar ta yarana ce bansan ya zan sanar dasu ba abun kunyar ma ni yaron yayimun kankanta wallahi inajin kunyar sanarda Ashrab da Farha gaskiya"
"Kan uba Bassam dina ne karami ta fada azuciyar ta a fili tayi dariya tace nifa har yanzu banga wata damuwa ba inaganin ki amince kawai tunda naga kamar kina son shi,....... "Tayi shiru na yan dakiku kana tace bansani ba har yanzu ban tantanceba kaina yashiga caji na rasa tudun dafawa"
"Munu ta dafa ta tace kiyi abunda zuciyar ki ta yarda dashi kada kibari damarki ta kubuce miki yaranki bazasu zama silar rugujewar farin cikin ki ba ta mike wannan itace shawarata..... "Tana gama magana ta fice zan wuce office sai kin fito"......
"Bata samu damar amsawa ba saboda kanta ya kulle matuka ahankali tace tabbas inajin wani abu gameda Bassam tokuma ya zanyi da yarah nah,....... "Wani bangare daga cikin zuciyar ta yace ki hakura Salma inaganin zaifi kiso farincikin ya'yanki"
"Wata killa yaron yanada wata manufah akan ki KIRJINTA yayi wata mummunar faduwa RASSSSSS!!! .sai a lokacin tafara wani tunani na daban"
"To idan haka nefa ya kenan wunin ranar duka ba inda taje office dinma kasa tafiya tayi haka tayita tunanin mafita".....
"Karfe 5:00pm dai-dai BASSAM yayi parking a kofar gidan hajiya salma a lokacin baba direba yana zaune shi kadai agurin yayi mamakin ganinsa a gidan yataso saboda ya murza masa rashin mutunci yace malan dakata gurin wa kazoh Bassam ya dago cikin kallon rainin wayo yace gurin masoyiya ta Salma nazoh ko kanada matsala da hakan..... "Gaban baba ya fadi ya yadago da sauri wace Salma"
"Yace wacce kasani bani guri kajikoh kana bata mun lokaci ya bangaje baba yayi shigewar shi ciki kansa tsaye tana zaune a palourn tana kallon wata tasha kamshin sa ne yafara ziyartar hancinta ta lumshe idanuwanta a tunaninta ko gizo ne kawai batayi auneba tajiyo sallamar sa cikin sassanyar muryarsa mai dadin sauraro ta jiyo a cikin sauri sukayi ido biyu da juna"............
"Dan Allah kuyi manage dashi zaman yana bani wahala yanzu"
TAKUCE A KULLUN
LAURAT M BELLO
SHARE
VOTE
COMMENT................
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
SM-T531
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Default Paragraph Font
Table Normal
No List
Times New Roman
Times New Roman
Symbol
Symbol
Arial
Arial
Calibri
Calibri
SimSun
Cambria Math
Cambria Math
!%),.:;>?]}
$([{
060eae4880ad45438f072de6cf2c7e8b
Chapter 3 · 0% Book details