← Book details Bakar Ayah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 3

Gabatarwa

Bakar Ayah Part 1 Complete Hausa Novel · about 37 min read


____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤


Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]


*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________


*Assalamu alaikum*

Godiya ga Allah maÉ—aukakin sarki daya kawomu wannan rana na fara sabon littafi.
Dama an ce rana bata ƙaryah saidai uwar ɗiya taji kunyah. Barkanmu da wannan rana mai albarka,dafatan An wayi gari cikin ƙoshin lafiya.


*GARGAÆŠI*


Ban yadda wani ko wata ya kwafamin littafi ba ta kowacce siga,sannan akwai halayya da ɗabi'u a cikin wannan littafin wanda basu dace ba,dafatan za'a ɗaukesu a matsayin darasi mai isarda saƙo.
Sannan abu na ƙarshe ayimin afuwa idan wani yaci karo da abinda yayi daidai dashi,banyi niyyar yin hakan ba sam.
Nagode sosai ayi karatu lafiya......


Page 🖤01🖤


.........."zaki iya ki daure kinji,ki daure zaki iya,kin kusa saura kaÉ—an ,daure daure ga nan kan ina hangoshi"
Nurse É—in take fada,wacce ta haÉ—a gumi sharkaf saboda firgici.
"Nafara gajiya nurse,karfina duk ya ƙare!"
Share gumin tayi a karo na ba adadi kafin ta kalli wata wacce take gefenta,da alama tafi waccar É—in matsayi,dan kayansu ma ba iri É—aya bane.
""Ke maza hanzarta ki ƙira doctor yanzunnan,kice ana neman sa da gaggawa a labor room 24"
"Toh ranki ya daÉ—e"
Ta faÉ—a tareda zubawa dagudu. Bayan barinta wajen sake maida hankalinta tayi kan hafsa,wadda take ta nishi amma babu alama haihuwar tana kusa,gashi kuma jininta ya hau sosai babu dama suyi mata cs.
Girgiza kanta tayi cikeda tausayawa,dan duk wanda yakalleta a wannan halin yasan ba ƙaramar wahala take sha ba sosai.
"Sannu kinji,bari yazo ya duba koda akwai matsala,dan ni gaskiya bamu taba ganin irin wannan ba tunda muke anan asibitin,komai ƙalau amma kan yaron yaƙi motsi tunda yafara fitowa?"
"Nurse to ki sake yimin allurar naƙudar mana,inaga yanxun a dace wataƙil"
"Ahah kiyi hakuri,a iya daga jiya da daddare zuwa yanzu mun yi miki allura kusan biyar,bazayyi ki sake É—aukanta ba yanxu,tana da haÉ—ari sosai.
Baridai doctor yaxo muji mai zaice,inshaaallah zaki haihu lafiyah,kada ki damu,Allah yana tareda ke"
Karfafa mata gwiwa ta cigaba dayi akan lamarin,duk ita kanta ta sare da irin wannan case É—in.
Waje ta leƙa suka haɗa ido da HAJIYAH ZEENAH,wanda tun ɗazu take zirga zirga a wajen.
"Ya ake ciki nurse,ta haihu ne?"
Jijjiaga sister suwaiba tayi,shekararta ashirin kenan tana karbar haihuwa,amma wannan kam yacaza mata kai matuƙa,.
"Har yanzu dai hajiya lamarin jiya i yau,ni har na fara tsorita ma da abin,gashi tana naƙuda amma kuma babu haihuwa babu alamunta"
"Kai innalillah,ni banma san mai zanyi ba,ga IYAH SAYYADA ma,saida akayi da gaske kafin ta hakura da zuwa asibitinnan,nasan tana can ta ɗagawa kowa hankalinsa,sannan gata itama yarinyar tana shan wuyah sosai......to maizai hana ayimata cs,shi mijin baya ƙasar,amma kuma ƙaninsa yana nan ai sai ya saka hannun"
"Shima hakan bazayyi yiyu ba Hajiya,domin jininta yana at risk,a kowanne irin lokaci zai iya zama matsala"
Suna cikin maganar ne likitan ya iso wajen da coat a jikinsa,da alama zuwansa kenan.
"Ya akayi sister suwaiba,naji ance kina nemana a É—akin haihuwa,wane abune haka daya gagareki?"
"Uhm sir babbar matsalace sosai,yarinyar kwana uku kenan tana naƙuda,gashi tana last stage,amma kuma jinjirin ya gagara fitowa,idan muka saka hannu kuma saiya koma da baya,sannan da alama kaman yaron bashida rai"
"Oh to a shirya shiga operation mana,bazayyi yu a barshi a cikinta har yanzu ba ai"
"Uhm uhm sir jinin yana over tension fah,operation bazayyiyu ba shima"
"So do you like us to watch her die(so kike mu zuba mata ido ta mutu) dolene muyi wani abun,maza muje na ganta yanzunnan.
Naji kince mrs.JABEER .A.JAAN ce koh"
"Eh hakane doctor,yana shirin tahowa yanzunnan"
Juyawa yayi yana duba file É—in ta suka haÉ—a ido ta hajiya Zeena,waccce gabaÉ—aya damuwa a tattara akan fuskarta.
"Barka dai ranki ya daÉ—e"
"Yawwa barka doctor,ya kamata kuyi wani abun,idan ta kama fita da ita ne ma sai a shirya yanzunnan ta private jet"
Karki damu hajiya,zamu yi iyah koƙarimmu akan matsalar.
Daga haka suka shige site É—in da Hafsan take kwance.
Wayar tace tayi ƙara,hakan yasa ta koma inda su LAYLAH matar ƙanin mijinta (facalah)suke a zaune.
"Hello ina jinka ABDULMALEEK ya ake ciki?"
"Hmmm ummah ina hanyar zuwa asibitin,kuma tare mukeda Iyah Sayyada,tace wai dole saitazo taga jikinta,na kawota ko muyita wani wajen?"
Jan ajiyar zuciya Hajiya zeenah tayi kafin tace.
"Shikenan babu komai ka kawotan,idan ka kaita wani wajen ma,kasan bazata haƙura ba"
Sauƙe wayar tayi tana kallon Lylah wacce take danne danne a wayah.
"Lylah Iyah Sayyada tana zuwa,yakamata ki É—ora alamar tausayi akan fuskarki,inba so kike kuyi ba"
Tabe baki Lylah tayi tareda cewa.
"Nina gaji da zaman wajennan wlh,kawai akan wata zata haihu a ce saikazo ka zauna,da muka zauna É—in uwar me muka tsinana a wajennan ne,in matsalar wanine a sakoka,idan taka ce kuwa kai kake magance abinka"
"Toh yanxun wannan habaicin dani kike kokuma da mijinki dayace kizo? Bar ganin ina cikin jimami ki sami dama akaina,kinfi kowa sanin halina banida daɗi,batun zama kuma babu wanda ya riƙeki ki tashi ki bar wajen,daɗin ta ma kema naki ahalin ba ƙalau suke zaune ba,shanyayyen ɗanki ma ya isheki"
"Ehhh naki shanyayyene,amma dai surukata ai bata kashe kishiyoyinta koh,matsala kan ai tana gindinki,surukarki tazame miki alaƙaƙai,kowa shaidane ita ta kashe kishiyarta,wannan ma kar ace komai,dan biri yayi kama da mutum".............."
"Lahhhh ha ila ni Sayyada Tatin,yanzu mai zan gani,maizan gani haka,ƴar jikartawa tana ciki rai a hannun Allah,ku kuma kuna nan kuna saida hali.......ke Zeenatu,wato surukarki batada lafiya ma amma bazaki daina ɗiban rashin arziƙi ba koh......"
"Amma iyah Sayyada itah fah ta fara,kuma......."
"Dallah rufemin baki ni,saina kunyi abu nayi magana kununamin ku ƴan zamanin nasara ne,kalleku tula tula daku,ƴaƴanku na ƙasar masu jan kunne suna holewa,nikuma ƴar jikata ƙwaya ɗaya ta ni kaɗai take da,an kasa yimata gatan magani,sai paracetamal ake bunka mata dan rashin imani"
Dukkan su jugum sukayi suna jinta,ta riƙe ƴar ƙafar data ke mata ciwo tana ta zuba kaman ƴaƴan kanya,idonnnan sai fici fici nashi takeyi,kaman na ƙwarƙwata.
"Habba Sayyada kiyi shuru mana,wai bakya ganin yanda kika tara mutane sai kallonki suke ne,ni wlh dana sani dana barki kin cigaba da kukannaki ban kawoki ba"
"ABDULMALEEK ya faÉ—a yana zuya fuska"
Duka ta kai masa a gadon baya tareda cewa.
"Gyauton uwarka data ke tsayennan Audulolo,a gidan ubanwa nayi kukan,ko sharri zakamin dan ka rainani?"
Daga haka bai sake cewa komai ba ya koma gefe yana kallonsu,ta kama uwarsa ta matar baffansa sai tsefesu take a dandazon mutane.
"Mai me Kakah ma yagani ma a wannan matar ya aura har ta haifi ubanka oho,mtsww ba dama ka fita da ita saita zubarmaka da ajikinka a gaban abokanka"
Gyaran muryah likitin yayi hannunsa duk jini,ga gumi akan fuskarsa.
Sakin baki sayyada-tatin tayi tana kallon jinin dayake hannunsa,
"Kai.....É—an saurayi,yanzu wannan jinin danake gani a hannunta na hafsatuna neh,mai kayi mata kaji mata ciwo haka?"
Saurin cire safar hannunnasa yayi tareda É—orata akan tiren da nurse É—in take binsa dashi
"Ahh iyah ba haka bane,jinin haihuwa ne kawai"
ÆŠora idonsa yayi akan Hajiya zeena,tareda yimata Alamar yanason magana da itah.
"Am Iya bari muyi magana da Hajiya yanzu nan"
"Mai zaka faɗamata,faɗaminnan ni kakarta,duk nan wajen nafi kowa ƙaunar ta da son ta rayu"
"To Iyah a halin yanxu gaskiya,bamu sam mai zamuyi ba,dan wani abin mamaki ma,ta daina magana saidai bin mutane da ido,sannan gabobin jikinta munaji suna karyewa kass kass a duk sanda ta É—an motsa,da alama kuma bata cikin hayyacinta....."
"Yimin shuru haka baƙin jakada,ya isheka haka,wayyooo hafsatuna shikenan,sun haɗu sun cinyemin ita,saida nace bazan bashi ita ba matarsa mayyace,amma suka ƙeƙasa ƙasa su a dole wai yana sonta,kuma tana da hankali.
Gashi nan sun kaita wannan la'ananniyar matar tasa tacinyemin itah,bazan taba yafemuku ba wayoo ni Tateen Æ´ar mai Gaskiya"
Share hawayenta take da gefen gyalenta,tana kuka amma bakinta ya gagara yin shuru.
Buge likitan tayi tareda cewa.
"Dallah matsa na wuce naje na ganta,marasa imani kawai"
Turus tayi a bakin gadon,ganin yanda jikinta ya koma kaman babu gabobi,ta kwance take da tulelen ciki kaman gawa,dan yanxu kamma babu damar nishin da tayi É—axun.
FaÉ—uwa Sayyada-tateen tayi tana burburwa a kasan tile É—in É—akin,kaman sabuwar Æ´ar bori.
Sai ƙiran sunan LUBAN take da su hajiya zeena da Lylah tana tsine musu.
Abdulmaleek neh ya shigo É—akin tareda dafa kafaÉ—unta,suma su Hajiya zeenah shigowa sukayi suna kallon yanda kamannin hafsan suka sanja daga yanda suke.
Madeenah ce da Maleekah ƴayan hajiya Zeena mata(ƙannen Jabeer babban yayansu,sai kuma Abdulmaleek &Abdulkareem su ƴan biyune,sun gama karatunsu wannan shekarar,ABDULMALEEK engneer ne,Abdulkareem kuma doctor ne na ƙwaƙwalwa,yana housemanship a india.
Sai mai binsu Madeenah,tana 300 level a University of abuja,ita kuma Maleeka a 100 level,suna zuwa su dawo).
"Allah sarki zainabuna ma(Mahaifiyar Hafsa,kuma kanwar baban su ABDULMALEEK),haka ta mutu a haihuwa,aka haifamin ita,sai gashi itama suna so ta tafi ta barni a lokacin haihuwar"
Likitanne yashigo da sauri shida nurse din suka fara shiryata zuwa É—akin tiyata,
"Kiyi haƙuri hajiya,zamu shiga da ita tiyata,saboda mun gano abin cikinta bai mutu ba har yanzu,saidai amma kiyi haƙuri,dan iya ba lallai takai labari ba,amma duk da haka muna buƙatar addu'arku"
Dagata sukayi tareda ɗorata akan wani sabon gadon kaman gawa,suka nufi ɗakin tiyatar,suna barin wajen Sayyada-tateen ta ƙara gudun kukanta,kaman wata ƙaramar yarinya.
"Shima jabeerun sai naci bantan ubansa,dan tsabar ran yarinyar nan bai dameshi ba,shine ya É—aga kafa daga dawowarsa shekaran jiya har ya koma yau da sassafe koh hmmmm,bamai zugashi ai sai wannan mayyar kuÉ—in,a son kuÉ—i zakiyi komai"
Ta faÉ—a tana nuna Hajiya zeena,wacce ta É—auke kanta tana tabe baki,dan inda sabo sun saba ma........

Kwana uku baya..........


🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
Æ´ar mutan jama'are


____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤


Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]


*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________


Page 🖤02🖤


Ƙwana uku baya............


________________"Ina jinka ZULUNGUM ya kake ganin za'ayi toh yanxun,nidai duk yanda zakayi kayi,kawai so nake ayi mata kisan wulaƙanci,saita ƙwammaci bata shigo rayuwar mijina ba.
Duk wata mace data rabeshi banda maƙiyiya sai ita,zan iya komai kuma domin rabashi da ita.
JABEER JAAN(JJ) nawane ni kaɗai a faɗin duniyar nan,ƙaddarar sa ce ya zauna dani ni kaɗai,duk da kuwa bana haihuwa,yanda bazanga ƙwaina ba a duniya,shima bazai taba ganin nasa ba har ya bar duniyar nan, saidai idan nina haifa shine zai gani,amma idan baniba babu wata ƴa kuma.wannan alƙawarina ne ni LUBNAH ƴar URWATU"
"Shikenan yanda kika ce aikin bazai gagara ba,saidai kafinnan zaki ajiye nairah Miliyan É—aya da rabi kafin a fara aikin,dan zubar da cikin a yanzu zayyi wuyah,saidai a bari idan yakai matakin haihuwa sai a hanashi fitowa,koya kika ce toh"
"Hmmm idan hakan zaifi ayi hakan,amma ni da son samuna ne kafin na koma gida na sameta anyi filla filla da naman jikinta,babu wani abu dazai nuna itace,vazaka gane bane boka,natsani na buÉ—i idona na ganta a cikin gidannan,da wannan tsinannan cikin tana turashi,nafiso a kasheta irinnna waccar matar,kafin ma takai ga wani samun ciki"
"Kai......!! Tsiyata dake lubna gaggawa,inkika bi a sannu,kuma kina bawa Aljanu jinin da suke buƙata,babu abinda bazaki samu ba,har matakin zaman ki na CEO ma duk zai cika nan da zuwa gaba.
Idan aka kawar da itama rufe idonsa za'a yi daga kan duk wata ƴa mace da take doron duniyar nan,ke ɗai zai dunga kallo a duk inda idonsa ya sauƙa"
"Shikenan nidai duk yanda zakayi ma kayi"
"Amma fah akwai ƙa'idoji da dole saikin kiyayesu,na farko;dolene kijata a jiki,ta yanda zata yarda dake har ki dunga sanin ya take ciki,na biyu kuma akwai wata ƴar tsana da zan baki,ki tabbatar kin saka jininta a jiki,lokacin da tazo haihuwa ki dunga karya jikin tsanar,zai zamo tamkar jikinta kike karyawa,daga lokacin da kika karyata tayi laushi,ita kuma sannan zata fuskanci tata mutuwar tareda abin cikinta"
"Naji wannan bayani naka,za'ayi yanda kace ba matsala,lokacin dazata dunga ihu sannan zuciyata zata wanke da zama min da tayi a cikin gidana.
Nagode gaskiya yau da gagarumin abinda ka bani,zan tafi,dan yau zai dawo daga taron daya tafi England"
Tashi lubna tayi daga ƙasan da take zaune tareda kaɗe zaninta tana murmushin samun nasara.
Hanyar fita daga wajen ta nufah mai matuƙar bada tsoro,amma hakan ko a jikinta,dan akan kishin mijinta babu abinda take ganin zai iya saka mata zani yarabata dashi.
Saida ta É—anyi tafiya mai nisa kafin tazo wajen inda ta ajiye motarta,Wai hausawa suna cewa SA KAI YAFI BAUTA CIWO.
Saida tayi tafiya mai nisa kafin ta shigo garin abuja,direct JAAN ESTATE ta wuce da baƙar motar ta.
Nufar babban get ɗin tayi cikeda ƙasaita da izzah,wanda hakan a jininta yake.
Titin dazai kaita apartment É—insu tabi,wanda take É—an ciki kaÉ—an da bakin babban get É—in.
Saida ta wuce nasu Hajiya Zeena kafin ta iso nasu part,shima da get É—insa mai zaman kansa,yana É—auke da part biyu,amma a haÉ—e suke ta tsakiyah,inda side É—in Jabeer yake.
Ba hanyar nata part É—in ta nufah ba,da alama wajen Hafsa zataje.
Fuskarta a murtuƙe take saboda tsanar baiwar Allahn,amma haka ta danne saboda zancen boka ta saki fuskarta kaɗan.
Da sallama ta shiga tangamemen falon,mai adon Green da purple,yayinda nata kuma yake fari da ja.
Haushi ne yakamata ganin kayan Alatun da mijinnata yasaka mata,tafison komai yazama ita kaÉ—ai take dashi bada wata matar ba.
"Assalam ƙanwata kina cikine""
Hafsace ta fito daga É—aki da doguwar riga a jikinta marar nauyi tana tura zungureren cikinnata.
Kallon Lubna take da mamaki,dam yanda taga murmushi akan fuskarta abune da bata taba gani ba a faÉ—in rayuwarta,a ranta addu'oi take jerowa duk wacce tazo bakinta.
"Lafiya ƙalau Anty lubna,sannu da dawowa ya hanya"
"Hanya ƙalau,har zan shige nace bari nazo naga ko lafiya kike,nasan babu kowa a gidan saike kaɗai,ga Honey ma bayanan,an barki ke kaɗai ga ciki"
Ƴar dariyah Hafsa tayi,har sannan bata share tantamar inaga antynnata ba lafiyar ta ƙalau ba,dan in ana neman rashin imanin matar to a tambayeta"
"Ayyah ba komai anty,akwai Alawiyyah ai ƙanwata,tana taimaka min da abubuwa,Hajiya ma kuma tana shigowa akai akai"
Mintsine bakin lubna tayi tareda cewa "munafukar tsohuwa" a ranta.
"Ohh kinga shaÉ—af na manta da hakan,dama saidai ta hakan ai,akwai abincine ki bani,yanzu na fawo gashi banci komai ba"
"Ah....ehhh barina duba kitchen É—in,ki zauna akan kujera naje na dawo"
Murmushin yaƙe Hafsan take dan kwata kwata abin bayyi mata a gaske yake faruwa ba.
Bayan tabar wajen tashi lubna tayi tana kalle kallle a cikin falon,yaune zuwanta na farkon wajen da niyyar arziƙi,saidai tazo tayi tijara ko kuma kashedi,dan haka har tazo ta tafi bata gane mai yake wakana a wajen sai yanzu.
Tana cikin kalle kallenne Hafsa ta dawo É—auke ta plate a hannunta,ta rufe da wani a sama.
Karba lubna tayi tana murmushi tareda cewa.
"Yawwa nagode ƙwanta sosai,amma zan iya tafiya dashi saina kawomiki plate ɗin?"
ÆŠaga mata kai Hafsa tayi cikin ladabi.
"Lahhh ki tafi dashi Anty babu komai"
Daga haka lubna tajuya ta fita da plate É—in abincin a hannunta.
Tana shiga part É—inta ta buÉ—e kwandon shara ta zubashi a ciki,tareda jefa plate a É—in a wajen wanke wanke tana kaÉ—e hannu kaman ta dauki kashi.
Ɗaya daga cikin masu aikinta ta ƙwalawa ƙira.
"Bishirahhhhh!!!!!"
"Naaama ranki ya daÉ—e"
Ta karisa magana tana zurowa da gudu.
"Gyaran gidannan bayyimin ba kwata kwata,ku tabbar kun sake gyarawa kafin magriba"
Bayan ta wuce wacce aka ƙira da bishira ta samu waje ta zauna,tareda sakin wata ajiyar zuciya,banda neman na halali mai zai sakasu aiki a wajen wannan dujal ɗin.
Bayan ta fito daga wankane taji ƙarar motoci suna shigowa cikin apartment ɗinnasu.
Shafe shafe tafarayi,dan tasan mai gidanne yadawo daga taron shekara da sukeyi da sauran companies..
Har lubna ta gama shiryawa ana ta ƙiran Sallah amma bata ga Jabeer ya shigo ba,abinne yafara bata haushi,dan tasan yanzu haka yana sashen Hafsa,saboda ita tana da ciki ita kuma batada shi.
A bangaren J.J kuwa yana fitowa daga motar muhimmin ƙira ya shigo wayarsa,ana nemansa da gaggawa,dan haka a take ya ɗau ƙaramar motarsa personal ya koma.
Bashi ya dawo gidanba sai bayan isha.
Sallama yafara a bakin falon lubnan,amma shuru bata kulashi ba har ya shigo cikin É—akinta.
A zaune take akan kujerar dressing mirror tana danna waya,tacika tayi famm kaman zata fashe.
Mamaki abin yabaww J.J,dan yasan babu abinda yayi mata kafin tafiyarsa,hasalima sanda ya fita daga gidan bata nan ta tafi gidan ƙawarta batareda yasani ba,shine ma yakamata yayi fushi,amma kuma wai itace dayin fushin.
"Lubna inata Yin sallama kinaji kaman ba musulma ba?"
"Hmmm banyi niyyar amsawa bane,dan tsabar rashin adalci wato,tun ɗazu kashigo gidan amma kana wajenta,ita gamai haihuwa koh,sai nayi magana tsofi suce banida haƙuri"
"Ke suwaye tsofin,iyayena koh? Yayi miki kyau,wai yaushe zaki sanja haline kam,dawowa ta fah kenan,yanxune ma nashigo gida,hmmm ALLAH ya shiryeki,banida lokacinki tunda lafiyarki kalau fine,na sauƙe miki haƙƙinki,saida safe"
Yana gama faɗin haka ya bar sashennasa cikin bacin rai,tasashi kuwa sarai,idan yayi zuciya da ita ta ƙwammaci ya mareta daya tura mata aniyarta,dan sai yayi sati bai kalli inda take ba.
Tsuka taja duk da taji tsoron fushinnasa,dan Allah ne kaÉ—ai yasan irin yanda take so tajishi a tareda ita,dan ita kanta shida ce shiÉ—in jarumin namijine a ta kowacce fuska,badai mace ta rainashi ba,saidai ma ta gaza.
Dama ƙarin haushinnata kenan,ba a sashenta yake ba,shiyasa take wannan kumbure kumburen.
Hafsa tana kan sallayah ya isa É—akin cikin fushi.
Sallama tayi tareda sake masa murmushi lokacin da suka haÉ—a ido.
Shima murmushin yayi mata,duk wani bacin rai da lubna tayi masa sai yaji yana sauƙa.
"Ka dawo lafiya ya hanya?"
"Alhamdulillah,ya zaman gidan da lafiyarku"
"Muna lafiya kalau,barina kawo maka abinci"
"Ahah ki barshi,barina yi wanka tukunna"
Tashi yayi ya rage kayan jikinsa tareda shiga banÉ—aki.
Kafin ya fito ta fitar masa ƙananna kaya marasa nauyi.
Da safe suna cikin yin break fast lubna ta shigo sashen riƙeda plate ɗin jiya a hannunta.
Tasha wani matsatstsen lace kalar zinare da baƙi riga da skirt,ba laifi tanada yar ƙiba,amma kuma bayada kunkumi sosai mai cika ido,sannan ba fara bace,saidai sanadiyyar mayuka na zamani,tayi fari tass kaman fatalwa.
Wani shu'umin murmushi tasake mai,dauke da ma'anoni kala kala.
Hafsa ce ta gaishe da ita tareda yi mata bismillar abinci,Jabeer kam ko kallon ta bayyi ba,sauri yake yagama cin abinci yafita wajen aiki.
"Ayya wai break fast,naga kam kuna cikin nishadi sosai,plate É—in jiya na dawo miki dashi"
Ta faɗa tamkar mutuniyar kirki. Jan kujera tayi babu kunya a kusada Jabeer ta zauna tareda yimasa kallo ƙasa ƙasa.
Hafsa tana kallonsu amma ta kawar da kanta tareda zubawa Lubna itama abincin.
Bayan kamar minti biyune Jabeer ya ɗago ya zabgawa lubna harara,saboda yanda take ɗaga ƙafar wandonsa da kafarta ta ƙarƙashin tebur ɗin.
Har ya buÉ—e baki zayyi magana ganin bata daina ba ya fasa,saboda yanda Hafsa ta ajiye cokalin hannunta tana rike cikinta.
Tun kafin Jabeer ya taimaka mata,lubna ta riƙeta tareda yimasa magana ya ɗakko key ɗin motarsa.
Cikin sauri suka nufi asibitin da itah da gaggawa,sai bayan sun isa an shiga da ita ɗakine tukunna suka samu damar ƙiran Hajiyah zeenah,wanda cikin ƙankanin lokaci ta tashi hankalinta,sai gata itada Laylah,matar baffansu ABDULLAHI. Sayyada-tateen kam ba'a sanar mata ba,saboda kowa yasan halinta da surutu da ɗaga hankali.
Safa da marwa suka fara a bakin labor room ɗin,itadai luban kallonsu kawai take,duk sanda suka nuna damuwa ƙara bata haushi suke,musamman yanda jabeer yafasa tafiya ko ina,kowa addu'ar ta sauƙa lafiya yake,ita babu wanda ya kula da ita.
Ƙara wayarta tayi a cikin jaka,wanda hakan yasa ta nufi wani dan waje gefe da inda suke tsaye.
"Hello Hajiya na É—ebi miki jinin,yanzu zan fito daga ward É—in,sai ki bini zuwa nurse section na baki"
"Okay babu matsala"
Tana kashe wayar tayi murmushin mugunta tareda kallon inda hafsan take kwance,fitowa nurse É—in tayi kanta a sunkuye É—auke da test tube na jini ta nufi sashen su,babu wanda ya kulada ita,domin kowa yayi zaton abu zata kai wani wajen.
Lubna tana ganin hakan ta bi bayan nurse din,saida sukaje inda babu kowa kafin ta tsayah,
"Yawwa gaskiya kinyi ƙoƙari sosai,ai dama yanda kika faɗa cewar kin bata maganin naƙuda tasha da safe,shiyasa na shiga sashen domin na biyosu asibitin.
Aikinki ya cika,na tura miki miliyan É—aya acct É—in yanda mukayi nagode ni barina na tafi"
Lubna ta faÉ—a bayan ta karbi jinin tasaka a jaka.
"Kwanan ki ya ƙare Hafsatuwa kema kaman ɗayar,nariga na faɗamuku,duk wacce ta rabeshi to kabarinta ta tona,koda kuwa wacece".......!!!!!

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
Æ´ar mutan jama'are


____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤


Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]


*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________


Page 🖤03🖤


Saida taje daff da inda su Hajiya Zeena suke tsaye ta riƙe kanta tareda fara layin ƙaryah.
Lylah ce ta kulada ita tace.
"Lubna kema kuwa lafiya,naga sai layi kikeyi?"
"Uhm kaina ne nake jinsa kaman zai fashe,bana jin daÉ—insa ko kaÉ—an"
"Toh ta tafi gida mana,dama waye ya riƙeta,ni nayi mamaki ma danaga tazo wajennan"
Hajiya Zeena ta faÉ—a tana binta da harara. Itama ta wata fuskar ramawa tayi,tareda yimusu sallama tabar wajen,shikuwa uban gayyar dama yayi fushi da ita jiya. Dan haka ko kallon ta bayyi ba.
Dariyah ƙasa ƙasa Hajiya Lylah tayi,da alama show ɗin yayi mata dadi sosai.
A daddafe tana nishi ta nufi motar ta,hadda tsayawa ta huta kana ta cigaba da tafiyah.
Saida tabar layin asibitin kafin ta saki shewa tareda ciro wayar ta a jaka.
"Kee Dallah ki tsaya nayi magana,nasamo mahaɗin yanzunnan,naji kincemin kinaso kiga yanda zan gama da ita,to ki hanzarta,dan ba'a son tafara naƙuda tukunna,idan ta haihu to aikin bazayyi yiyu ba"
Kashe wayar tayi tareda ƙarawa motar wutah tana waƙa.
Bata ja wani lokaci ba ta isa gida,kasancewar basuda nisa da asibitin.
A bakin ƙofar gidan ta samu motar Yaseerah ƙawarta tana jiranta,bodyguard sun hanata shiga,ta bar ID parmission dinta a gida saboda sauri.
Horn Lubna tayi musu tareda nuna musu motar Yaseerah lokacin da tazo shiga.
Tafiya take tana binta a baya har suka isa apartment É—insu.
Direct sashen Lubanan suka wuce cikwda raha da kuma shewa,tamakar tarkon su yakama Toron giwa.
"Wai dagaske kike luby,nifah har yanzu ban yarda ba irin wannanan asirin yana duniyah,kina daganan saiki kasheta hankalinki kwance?"
"Ƙawarai ma kuwa,ki zuba iso kawai kigani,lokacin dana taho bata haihu ba dan haka mu hanzarta"
"Idan ta haihu shikenan bazai aiki ba?”
"Ahah ba aikine bazai yi ba,kawai so nake na haÉ—a itada abin cikin na kashe,kingane dai koh,tunda kema Æ´ar garice ai"
Ba'a falo suka zauna ba,saboda tsaro sai suka shige É—aki.
"Wai lubby har yanzu tsoron Kucakan gidannan kike yi,i think no need,tunda kece kike aikatawa,kuma ma hakan yafi,ta hakanne kaɗai zasu ƙarajin tsoronki su daina aura masa mata,habaa mutum baza a barshi ya wataya da mijinsa ba ya more"
"Hmmm barsu mana,nafisu iya shege ai,kome suke ina daidai dasu, ko nace ma nafisu"
Tana maganar ne tana fitowa da Æ´ar tsanar daga cikin jakarta,sannan ta É—auko jinin Hafsa ma a cikin kwalba,zubawa tayi akan Æ´ar tsanar gefen bakinta yana motsawa tareda bada wani shu'umin murmushi ganin alamun samun nasara a aikinnata.
"Kinga Seerah inaga aikin yayi,saboda jinin ya tsotse a cikin dollyn,yanzu zan fara ƙiran sunanta sau uku sannan saina fara kakkaryah ta"
Tana rufe baki kuwa ta fara aiwatar abinda ta faÉ—a a aikace.
"Hafsa....hafsaaa.......hafsaaaaa,kwananki ya ƙare ganinan kema gareki!!!!!"
Ƙaƙasss tafara kakkaryah jikin ƴar tsanar,wanda duk sanda tayi hakan sai wata ƙara tafita daga jikin abin,amma hakan ko tsoro bai bata ba bare tausayi,saima wani ƙara ƙwarin gwiwa daya bata tareda nishaɗin matsalarta tana shirin kauwa daga gabanta.
Ta É—auki kusan minti talatin tana aikin,domin idan ta karyah saita jira kafin tacigaba dayi,badan komai ba sai dan tasake bawa kanta lokacin hakan.
Saida ta gama kafin ta jefar da ƴar tsanar a ƙasa tana maida numfashi,hannunta da kuma jikin tsanar dukka jinin hafsa ya bata.
"Nagama da ita itama seerah,itama ta tafi kaman yanda ɗayar ta tafi,babu wanda zan ƙyale,hakan alƙawari na ne danayi"
Ajiyar zuciya ta saki tareda komawa ta zauna a kusada seerah,kaman wacce tayi aikin daidai.
"Huh ya kike gani seerah,kina ganin ta mutu kaman yanda nake buri"
"Indai har da gaske kin yadda da aikin zulumgum,kuma kin tabbatar kinyi yadda yace,ni ina ga babu wani abin damun kai a lamarin,kinyi yadda ya dace,to yanzu yaya? Zaki kira kiji ko ta mutune ko kuma shuru zakiyi kar ace kece kaman koyaushe"
"Hmm ko nace nice ko kar nace nice dukkansu kowa yasan nice na aikata,abinda yasa kika ga banbar gidannan ba,saboda bahaka nabar mijina ba,duk aikin yasoni tamkar uwargijiyarsa bayyi aikiba,amma namasa aikin da bazai taba sakina ba,har mutuwarsa,saidai idan nice naga damar tafiyar.
Sukuwa bazasu so mutuwar ɗansu dan nabar gidan ba,dan haka a zauna a haka,su cigaba da kawo ƴaƴansu cikin gonata ina murƙushesu kaman ƴaƴan kaji"
"Heee gaskiya bakida dama lubeee,shiyasa fah a Club ɗinmu ke ta dabance,to ni kinga barina tafi,Old lady tana ta ƙirana zanje na ɗora abinci,saikinjini ko sai na jiki"
Daga haka seerah ta É—au jakarta tayi gaba.

•••••••BACK••••••••

"Innalillahi innalillahi innalillahi..........".
"To sai salati kike kamawa amma bakya ƙarisawa,nasan yanda kuka shaƙu da hafsa Madeena,amma addu'a zaki mata ita take buƙata a yanzu"
Abdulmaleek ne yafaɗa cikin tausayawa,dan kowa yasan Madeenah batada wata ƙawa bayan Hafsan,kasancewar tare suka tashi,kuma kansu ɗaya.
"Yah Abdul kana gani fah,kalli yanda take shan wahala,jikinta duk ya lanƙwashe,shikenan fah bazata tashi ba"
"Am sorry sis ki dunga yi mata addu'a kinji,ikon Allah sai kiga ta tashi da ƙafafunta,komai nufine na Allah"
ÆŠaga kai tayi Alamar taji abinda yace,bayan suÉ—in babu wanda yake magana a wajen,sai Lylah abu kaÉ—an taja tsuka ta turo baki,ita a dole an sakata zaman wajen babu yanda zatayi.
Hajiya zeenah ce ta juya ta rafka mata harara,har zatayi magana ko mai ta tuna sai kuma tayi shuru tareda minding nata business din.
Ƙarar ƙofar dakin tiyatar ne ta ankarar da dukkansu,inda kowa ya juya yana kallon waye zai fito daga ɗakin.
Doctor Basheer É—inne ya fito É—auke da hankerchip a hannunsa yana share ruwan gaban goshinsa.
Kallon su yayi da alamar bayason faÉ—amusu abinda yake kan fatar bakinsa.
"Am sorry munyi iya ƙoƙarinmu amma.........."
Abdulmaleek ne ya katseshi tareda cewa.
"Uhm doctor duk wajennan nine namiji,shin ko zamu iyah yin magana dakai a office tukunna,kafin saina faÉ—amusu,bai kamata ka dunga faÉ—an magana a waje ba irin wannan ,musamman da iyah a wajen"
Kowa na'am yayi da maganar abdulmaleek din,inda doctor yashige office shima ya bishi.
Ya ɗau kusan miniti talatin kafin ya dawo inda su hajiya zeenah suke,duk da yanda yake ƙoƙarin saita Yanayin fuskarsa,amma kana gani kasan ba ƙaramar magana bace a bakinnasa.
"Am sorry to said,she's gone,Allah daya fimu sonta ya karbeta Iyah,please dan Allah karki saka damuwa a ranki sosai kinji,ki É—auka cewar Hakan shine abinda yafi mata Alkhairi akan rayuwar da take ciki."
ÆŠan ja da baya Sayyada tatin tayi ta zauna a akan kujerar da take bayanta,saida ta saita ta kwantar da hankalinnata da taimakon Abdulmaleek kafin ta É—aga kai ta kalleshi.
"Toh...toh ina yaron naji ance yana da rai kafin ayi mata tiyatar koh?"
"Ahah iyah,an fitar dashi da rai,amma kuma yabi bayanta bayan mintuna da yazo duniyah,saboda shima abin ya shafeshi sosai,bai daÉ—e ba ya koma ga mahaliccinta"
"Naaaa shiga uku shikenan jinin zainabuna ya ƙare a duniya,wacce nake ganin zata maye min gurbinta itama ta bi bayanta,hadda ɗan dazan riƙe naji daɗi shima ya tafi,yanxu wannan tantiriyar mayya mai yasa zata min haka mai yasa zata lagarta min rayuwar iyali.......yanzu........"
"Dan yarasulullahi Iyah sayyada ki taimakemu kiyi shuru,Hafsa Addu'a take nema a halin yanxu,naƙira baban su Abdul da kuma Abba ƙarami,dukkan su suna hanyar zuwa inshaaallah"
Hajiya zeena ce tayi maganar tana share ƙwallar da take idonnata,ita ba komai ne yasake girgizata da mutuwar ba sai yanda taga ci taga rashi,burin wannan ɗa yazo duniyah amma sai gashi wata ta kasheshi tun kafin ta ganshi.
Wani tirurine da kuma bakin ciki tareda muradin ɗaukar fansar jikanta suka turnuƙe a cikin ƙirjinta.
Babu abinda take ambata sai sunan Lubnah a zuciyarta.
Suna cikin tsaye xugum zugum Alhaji Abdullahi ne yashigo shida Jabeer,wanda kana ganinsa kasan abun ba ƙaramin dukan ƙirjinsa yayi ba sosai.
Bai taba zaton zai rasa hafsan ba inaga kuma ÆŠannasa dayake jinsa tamkar tsoka É—aya a cikin miya.
Tunda yazo wajen bayyi magana ba,banda rawa babu abinda jikinsa yakeyi,duk yadda Mutanen wajen suka kai ga jin haushinsa saida ya basu tausayi,duk da shi mutum ne mai sanyin rai,amma kuma da wuyah mutum yaga Lagwonsa ya karye kamar haka.
ÆŠakin da hafsan take ciki ya nufah jiki a salu'be.
A kwance take akan gadon tiyatar an rufeta da farin kyalle,gefe kuma jinjirinne shima an naÉ—eshi da farin kyallen.
Kallo ɗaya yayiwa inda jinjirin yake ya ɗauke kansa,dan baya fatan ma ya buɗe yaga menene a ciki,saboda yasan hoton bazai taba barin zuciyarsa da tunaninsa ba,ya dunga farautarsa kenan har ƙarshen rayuwarsa.
Hannunsa yasaka na dama yafara yaye farin kyallen dayake kan hafsan,duk da yanda hannun nasa yake rawa amma yana iya koƙarinsa wajen ganin yayi mata kallon karshe,macen da duk namiji zayyi mafarkin samu a rayuwarsa,hankali,tunani,tausayi,uwa uba sanyi rai da sanin yakamata.
Ko mutum bai taba zama da itaba yasameta yasan sai ya ratsa duniyah kan ya samo irinsu,to inaga shikuma da dama yana cikin duhun rashin sa'ar samun mata,kwatsam lokaci É—aya hasken yazo masa yafara haska duniyarsa....kashh sai kuma gashi ya É—auke ya barshi a duhunsa wanda yafi ma na baya,saboda a da bai É—anÉ—ana hasken yaji ba,yanzu kuwa daya É—anÉ—ana yaji saiya ke ji tamkar duniyah sun taru sun juya masa baya.
Jajayen fatar bakin sa da suke rawa saboda tashin hankali ya fara motsawa tareda son furta wata kalmar.
"Meyasa meyasa.........lokacin da ban shirya ba......"
Ƙwallah ce ta ɗigo daga idonsa zuwa kan goshin matacciyar da take gabansa a kwance.
"Ki jirani nima ina nan zuwa wajenki kinji,banga laifinki ba da kika tafi,domin babu komai a duniyar sai rashin daɗi,kece kika fara nunamin ba yanda na ɗauketa take ba,saidai kuma yanzu dakika tafi nasan babu wanda zai sake nuna min yanda kika nunamin......ALLAH YA JIƘANKI HAFSA"
Yana gama fadin hakan yasaki mayafin yamayar mata kaman yanda ya ganshi,daga nan yafice daga É—akin yana share hawayen daya taru a idonnasa.
A zaune take tasaka riga rabin ciki,da wando matsatstse,head phone akan ta,da kuma cocumber akan idonta tana jijjiga kai.
Da alama yanayin yanayi mata daÉ—i sosai.
Bishira ce tashigo falon jikinta har rawa yake domin da isar da saƙon da take ɗauke dashi.
"Hajiya hajiyah hajiya...."
Saida tayi ƙira sunfi biyar kafin Lubnah ta cire cocumber dake kan idonta ta kalleta.
"Menene kuma yanxu kike buƙata kika zo kika durkusamin kaman mai neman gafara,mayu kawai."
"Uhm hajiya dama .....wani labari naji wai Hajiya hafsa ta rasu a asibiti dazu"
"Oh an faÉ—i ta mutun,yaya hadda É—an cikin suka rasu ko ya?"
Abin yaɗan bawa bishira mamaki amma ta danne,dan dama ko karen gidan ma aka tambaya ai yasan itace ta kasheta,to amma wazayyi magana,duk yanda gidan suke ji da taƙama da kuɗi,amma bazasu iya shari'a da lubna ba,saboda baban ta shine Chief private lawyer da abuja take ji dashi,kuma lubna ita kaɗaice ƴar sa mace,zai iya komai dominta.
Musamman daya zamo basuda hujjah bayananniya cewar an ganta ta kasheta,shiyasa take kashesu da boka take cin karenta babu babbaka.
"Eh hajiya naji ance wai harda yaron duk suka mutu,ana tahowa da su gida ma ayimusu sutura a binnesu"
"Huh naji daÉ—in wannan labarin naki"
Ta faɗa tana murmushi,gefenta ta juyah ta ɗauko dubu biyar ta miƙawa bishiran,dan dama dansu ta kawo mata labarin,duk da zagin data sha bai dameta ba tunda an bata kuɗin.
"Nagode nagode hajiya,zakuwa kijini da wani labarin idan nasamo"
Daga haka taja dabaya ta fita daga falon jikinta har rawa yake don son kuÉ—i.


🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
Æ´ar mutan jama'are


____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤


Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]


*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________


Page 🖤04🖤


Ƙarar jiniyar motar asibiti ce tafara amsa kuwwa a gidan,wanda hakan ne ya shaida alamar shigowa da gawar Hafsa tareda jaririn yaronta cikin gidan.
Bayan motar asibitin ta shigo sai kuma motocin su Jabeer suma suka biyo bayanta.
Kowanne idan kaga fuskarsa kasan mutuwar ta shigeshi,yanda suke fitowa daga motar jiki a sanyaye.
Sashenta aka nufa da ita domin yi mata sallah a É—akinta,duk abinda ake Lubna bata fito ba,bare tazo wajen yin suturar.
Sai bayan an tafi da ita kafin tafito da jumbulelen hijabi a jikinta fari tana rarraba ido.
Babu abinda kakeji a wajen sai kukan Sayyada-tateen,wacce babu yanda ba'ayi da ita ba,amma taƙiyin shuru sam,kowa tausayinta ne ya kamashi,saboda babu wanda baisan shaƙuwar da sukayi ba da hafsan.
Bayan dawowa Daga binnetan aka cigaba da karbar gaisuwa,Saidai duk wanda yazo yiwa Jabeer gaisuwa sai a ce bayanan.
Abinne ya É—aurewa abokinsa kai Khaleel,wanda hakan yasashi shigowa cikin gidan nemansa.
Da madeena suka haÉ—u a hanyar shiga sashensu zata kaiwa Æ´an uwan Hajiya zeenah Abinci.
"Am Madeena ina kuwa JJ( Jabeer Jaan) banganshi ba,gashi ana ta zuwa yimasa gaisuwa a waje"
Alamar mamakine yaÉ—an hau kan fuskarta,dan itama batasan inda yake ba,sannan babu wanda yaga shigowarsa,sashensu ma mutanene a wajen sosai.
"Ahah Banganshi ba,bansan inda yayi ba,kuma ina kyautata zaton baya Sashensu ma,dan wajen akwai mutane sosai. Amma ka ƙirashi mana kaji inda yake"
"Tun ɗazu nake ƙiran wayarsa switch off,tabbas mutuwar Hafsa ta girgizashi,amma bai taba yin haka ba ya kashe waya dukka,kuma a irin wannan yanayin da mutane zasu nemeshi sosai"
Dukkan shuru sukayi kowa yana tunanin shin a ina zasu ganshi,can bayan shurun nasu madeena tace.
"Uhm barina tambayi ummah kota san inda yake "
Daga haka ta wuce tabar Khaleel a tsaye,yana jiran fitowarta.
Wasa wasa anyi sadakar uku amma babu Jabeer babu Alamarsa,kowa yayi ta mamakin ina yashiga,anyi zaton ma ko ya bar garin.
Sai washagarin kwana uku mutane sun fara raguwa sannan yashigo gidan da motarsa.
A hankali yafito daga motar yana jefa ƙafa kaman mai koyon tafiyah,idanuwansa sunyi luhu luhu sai lumshesu yake kaman wanda yayi maye,kallon mutanen da suka kewayeshi yayi,amma babu wanda yayi wa magana,har hajiya zeenah wacce ta kafeshi da ido,da alamar tambaya a kallonnata.
Hanyar sashensa yayi kansa a sunkuye,bai juyoba har ya shige ya turo ƙofar.
Bai cire takalman ƙafarsa kana bai fasa tafiya ba har ya shiga cikin ɗaki.
Kan luntsumammen gadonsa ya faÉ—a a haka yana jan gwauron numfashi,tareda fesar da iska mai zafi.
Runtse idanuwansa yayi na tsawon sakanni kafin yafara buɗesu yana sauƙesu akan farin POP ɗin ɗakin.
Hawayene sirara suke bin gefen idanuwansa suna zuba akan zanin gadon,bai damu daya share su ba,haka yabar su suka cigaba da zuba har na tsawon wani lokaci.
Wayarsa ya fitar daga cikin Aljihun wandonsa ya kunnata.
Kaman jira kuwa takeyi,tafara amayar da saƙon da aka zubo mata lokacin da take kashe.
Ƙuramusu ido yayi suna ta shigowa,saidai ko kaɗan bai nuna alamar ma zai buɗe ko ɗaya daga cikiba,shidai yana kallonsu kawai.
A jiyeta yayi a kan drawer gadon ya shiga banɗaki,har sannan wayar bata daina ƙarar shigar massage ba.
Ya daɗe a wankan kafin ya fito sanye da towel a ƙugunsa,ɗaya kuma akan sa yana tsane ruwan jikinsa.
Farine ba sosai ba,sannan yana ƙirar jiki,da alama ba haka aka bar jikin ba ana motsashi.
Yanada baƙin gashi sosai,amma daga ganin yanayinsa kasan bashida laushi a nature sa,ana amfani da manyan mayuka ne wajen bashi gyara na musamman.
Kallo É—aya yayi kansa a madubin dage gabansa yayi saurin É—auke kai.
Da alama bayason kallon ramar da take kwancene a kan fuskarsa,kana da kuma launin idanwansa wanda har yanzu basu dawo da haskensu ba.
Riga da wando yasaka marasa nauyi yafita daga ɗakin da sauri,jin alamun ana buga ƙofar falon da ya sakawa key shigowarsa.
Da Madeenah suka haɗa ido lokacin daya buɗe ƙofar itada Maleekah,ɗauke da kulolin abinci a hannunsu.
Ganin kallon tuhumar da sukewa idanuwansa ne yasashi saurin É—auke ido tareda komawa cikin falon ya barsu a tsaye.
Suma basu damu daya ce musu su shigoba suka biyo bayansa,dan sunsan ko za'ayi shekara bazai faÉ—a ba É—in ba.
A jiye kayan abincin sukayi a kan center table ɗin dake gabansu, Madeenah ce tayi ƙarfin halin faɗamasa saƙon da aka aikota dashi.
"Uhm ummah tace idan ka gama tana nemanka a sashen Abbah"
Bayyi magana ba duk da tasan yaji abinda tace,dan haka kowa ke fama da halinsa na rashin magana shida Maleekah.
Har takama handle ɗin ƙofar zata fita taji muryarsa ƙasa ƙasa,inda akwai surutu a wajen ba lallai taji mai yake faɗa ba.
"Lubna tana nan?"
Haushine ya turnuƙeta sosai,bayan kwana uku daya ɗauka bayanan,ana nemansa an damu dashi,amma yana dawowa bai tambayi kowa ba sai wata Lubna.
"Bansani ba"
Shine amsar da Madeenah ta bashi a daƙile,kafin tayi wuff tabar sashennasa,kar ya huce akanta.
Fitowa yayi daga sashen ya nufi hanyar na Lubna.
Ga hasashensa kuwa bata nan kaman yanda yayi zato,ina taje oho.
Tun halinta yana bashi mamaki yanzu abun har ya zame masa jiki,lokacin da ake wani abin daya girgiza kowa a gidan,ita sannan zata shirya tabar gidan,ko kunya ma da kuma bakin mutane bata ji.
Jawo ƙofar yayi ya nufi Apartment ɗin iyayennasa.
A zaune yake mahaifinnasa kaman kullum akan Wheelchair,shekararsa uku kenan akai tunda ya samu paralyse na Accident,a lokacinne Jabeer ya karbi kujerar CEO na Companyn.
Maganinsa Hajiya Zeenah ta balla ta miƙa masa,tareda kofin ruwa.
Sallama Jabeer yayi a hankali can ƙasa ƙasa yanda za'a jishi amma kuma bada sauti sosai ba.
Hajiya zeenah ce ta waigo ta kalleshi daga haka da maida kanta wajen mijinnata.
Gaisawa sukayi da mahaifinnasa kafin daga bisani ya tambayeshi jikinsa.
"Jiki Alhamdulillah Jabiru,Naji ummanka tace kwana uku baka gida sai yau ka dawo?"
"Eh Abba dama......dama...."
"Bakomai nasan yanda kakeji a ranka,rashin mata da kuma É—a,musamman a yanayinka abune da yakamata ayi maka uzuri,sannan kuma a jajanta maka.
Allah yabaka ikon yin haƙuri da kuma tawakkali,sannan kuma ka dage da addu'a da miƙa lamarinka ga Allah,watarana zai wuce sai labari"
"Inshaaallah,nagode Abba"
"Tabbas ansan anyi maka mutuwa,amma bai kamata ka kashe wayarka sannan kuma tafi batareda ka sanar da inda kake ba,Abokan kasuwancinka jiya suka zo daga india yimaka gaisuwa,sai tafiya sukayi basu sameka ba........"
Shuru Jabeer yayi yana jinta,yanda take faÉ—an baya nan,badan ta damu dashi ba sai dan ta damu da yanda aka zo ba'a sameshi ba,shikansa wani lokacin yana zama yayi ta tunanin shin Hajiya zeenah ce ta haifeshi,saidai ga sauran Æ´aÆ´an ma haka takeyi,wanda yake nuna zai fiddata kunyah yayi kuÉ—i shine a gaban goshinta,gaba É—aya batasan nuna soyayya ga É—anta tsakani da Allah ba,saidan wani abun duniyar.
Haka ta horar dasu tun suna yara,burinta su zamo sunfi kowa,indai har wani ya fisu to anan zasuga bacin ranta a fili.
Shiyasa takeji da Jabeer saboda yana matakin farko a compayn nasu,abu ɗaya ne yake cimata tuwo a ƙwaryah,shine mata marar arziƙi da Allah ya haɗashi da ita,saikuma rashin haihuwa da bai samuba.
Lokacin daya auri hafsa ta samu ciki,tafi kowa farinciki,itama zata samu jika a daina yimata habaici,saidai kash Yanda taso bai yiyuba. Wannan dalilinne yasa ta ƙunshe vaƙin cikin Lubna a cikin zuciyarta.
"Haba Zeenatu wai meyasa kike hakane,yaronnan fah Matarsa ce ta rasu da kuma É—ansa,kuma kinfi kowa sanin yanda waÆ´annan mutane suke a wajensa,dan yatafi yabar gida,daga dawowarsa ki fara wai abokan kasuwancinsa sunzo bayanan basuji daÉ—i ba?"
Jumburo baki tayi tareda hararar Jabeer ɗin ta ƙasa ƙasa,
"Haba Alhj yanzu kai baka ga maganata akan gaskiya,yanzu daya tafi da wani muhimmin aiki ya taso fah,yakake ganin za'ayi,kuma dazakace haka duk waye ya jawo komai idan bashi ba,da bai auro waccar masifarba aida komai bai faruba. Hmmm ai bari ayi sadakar Arba'in,takardarta zai bata ya auri Æ´ar mutunci wacce zata haihu,ba ita ba juya"
"In kina so ma kice yasaketa yanzu,ai duk É—aya ne tunda kin faÉ—i Abinda ke bakinki,ki dunga sararawa zuciyarki dai,kina yayyafa mata ruwan sanyi,dan yanzu girma yafara kamaki,inba so kike ciwon zamani ya kama ki ba"
Shuru sukayi dukkan su babu wanda yasake cewa komai,kana ganin Hajiya zeenah kasan da maganganu a ranta fal,ganin idon mijinnata ne yasata yin shuru badan ta haƙura ba.
Shikuwa dama Jabeer duk maganar da suke a iya zuciyarsa yake saƙasu,ko ɗago da kansa bayyi ba.
Alhj Aliyu ne yakalleshi cikin tausayawa tareda cewa.
"Tashi ka tafi Jabeer Allah yayi maka albarka,sannan yakamata ka É—au hutun Aikin kaje wani waje nesa da gidan kaÉ—an huta na wani lokaci"
"Toh Abbah"

Alhaj Abdullahi ne ya fito daga mota ransa a bace ya nufi bangarensu.
Sauri yake zubawa kaman zai tashi sama,dan dama irin mutanennnan ne masu firitt jiki da kuma sauri.
Bai samu kowa a falon ba, dan haka ÆŠakin lylah ya nufah.
A zaune take tana bawa Haneef Abinci a baki,wuyansa sai gilu gilu yake da ƙyar yake karban abincin.
Tsayawa yayi bakin ƙofa batareda yayi ƙyakykyawan motsi ba yana kallonsu.
Tunani yatafi yanda rayuwar su take kasancewa shida matar tasa,shekararsu sha shida kenan da aure,babban É—ansu haneef mai shekara Sha biyar,Allah ya jarabceshi a Lalura,ko kansa baya iya tsayarwa bare yayi wa kansa wani abun.
Saurna yaransu kuma huÉ—u dukka matane,shikaÉ—aine dansu namiji saidai dashi gwara babu a wajensu.
Yanada shekara É—aya a duniyah yakoma haka,har yau babu wanda yasan meyasa ya koma haka,anyi na gargajiya anyi na asibiti amma abu yaci tura.
Haneef É—inne ya juyo yakalli mahaifinnasa dake bayansu,aikuwa ya wangale bakinsa yawu yana zuba,alamar yana masa dariya.
Itama lylah juyowa tayi ta kalleshi tareda cewa.
"Ahh yaushe ka shigo,amma lafiya na ganka da wuri haka ka dawo,É—azu fah kake cemin yau sai dare ka dawo"
"Hmmm kedai bari laylah,ni narasa yanda zanyi da wannan yaron,nine nafara sanin companynnan kafin yasani,amma dan tsabar babu wanda yake ganina da daraja a gidannan,wai aka ɗau kujera mafi matsayi aka damƙa masa.
Project É—in danacemiki zan jagoranci aikinsa,saida suka zo yau da suka ga Jabeer baya nan wai bazasu yadda na jagoranci aikin ba,tunda hutu yatafi kuma ya kusa dawowa to zasu jirashi ya dawo"
"Kutt to miye dalilin daya saka bazasu baka ba,ba kaine Defuty CEO ba,duk wani aiki dayake ai kai yakamata kayi in bayanan.
Hmmm dama na daɗe da faɗamaka ai cewar duk gidannan ƴan baƙincikine,babu wanda yadamu da rayuwarmu a cikinsu,in ina faɗamaka kana ganin banason yan uwanka,yanzu ai gashi ka gani da idonka"
"Nagani kam,duk wani aiki danayi a companynnan banida daraja a cikinsa,yau inna faÉ—i na mutu babu abinda iyalina zasu tsira dashi,dolene na É—au mataki akai"
"Hmm hakane kam,yanzu inka yarda a É—au mataki to kabar komai a hannuna,nikuma zan saita komai yanda ya kamata,buÉ—ar idonka kawai zakayi ka tsinci kanka a matakin CEO na JAAN company"
"Na baki dama kiyi komai ma yanzu,nima yanzu bazan saurara ba,dole na ƙwaci haƙƙina a ciki"
Wata dariyah gefen baki laylah tayi tareda kanne ido guda É—aya.
"Ka zuba ido kaga aikin laylah masoyina,bazan baka kunya ba"


🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
Æ´ar mutan jama'are


____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK1_ 🖤


Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]


*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________


Page 🖤05🖤


"Ke Madeena zoki rakani gidan Hajiya ladi,na daÉ—e banje ba,kullum cikin samun abin tashin hankali muke"
"Kai ummah Binciken semina fah nakeyi,maleeka ta rakaki mana"
Haɗe girar ƙasa da sama tayi,tasani sarai babu wani bincike da takeyi,dan tana jin ƙarar game ɗin candy crush a wayar tata,Kawai dai dan kar tajene su haɗu da Al'ameen a gidan,Babban ɗan Hajiya ladi wanda suke son haɗata dashi,shi yana so,amma madeena kam kwata kwata bayyi mata ba.
"Banason shashanci dallah sanjo kayanki kizo mu tafi,yara ana nuna muku abinda zai taimakeku kuna wani abun daban"
Cikin zumbura baki babu yanda zatayi ta sanjo kayan harda guntun hawayenta.
Tasan badan komai mahaifiyarta take son haÉ—ata dashi ba,saidan yanada kuÉ—i,ita kuma wanda takeso bashida kuÉ—i,tunda ummannata taji zancen a wajen Maleekah tayiwa tufkar hanci,a cewarta Æ´aÆ´an ta bazasu auri talakawa ba.
Tafiya suke a motar Madeenah tacika tayi fam,babu abinda ma yafi bata haushi kaman yanda yadunga yi mata izzah,dan yasan mamuƙata ake a wajensa,kawai dan yasameta mai sanyi bata mayar masa magana.
Basuyi tafiya mai nisaba suka iso gidan Hajiya Ladin,shima gidane tankatsetse naji da faÉ—a,kana ganin tsarin gidan kaga jiji da kan yaran gidan,kasan sunayi ne da dalili.
Wanda hakanne yasa su Madeenah jin haushin Æ´aÆ´an aminiyar uwartasu.
Suna fitowa daga mota ,wata mata tayi musu iso zuwa ainihin falon hajiya ladin,ba wanda take tarbar mutane haka ba.
A zaune take a falon suna taÉ—i da Æ´ar ta guda É—aya mace JAWAHEER,wanda bazata wuce sa'ar Madeenah ba,dan set É—in su É—aya ma,saidai ita Business Admin take karanta,irin na Jabeer.
Dukkan ahalin guda biyu babu wanda baisan yanda ake muradin haɗa jabeer da Jawaheer aure ba,saidai kash lubna tayi musu cikass,tazame musu kaɗangaren bakin tulu,har kawo yanxu babu abinda basuyi ba,amma su kansu sun tabbatar Asirin lubna yafi nasu ƙarfi,babban tsoron su kar Jabeer ya aureta a yanxu itama ta kasheta.
Sakalci take zubawa son ranta,ita kuma hajiya Ladi tana shafa mata kai,wanda yake kan cinyarta,duk da shigowar su hajiya Zeenah ma hakan bai sa ta ɗago ta kallesu ba,saima ƙarawa abinda take ƙaimi.
Hajiya ladi ce ta kalli Jawaheer tareda cewa.
"Kai mana Baby waike ko kunya bakyaji yin fitina a gaban mutane,kuma hadda maman yayannaki koh,ki tashi ki gaishesu mana,sannan ki kawo musu ruwa"
"Toh amma ruwa kam su jenifer suna nan su kawo musu mana koh momy,kinji fa nace miki jiya jikina tsami yayi dana tashi a bacci"
Ƴar dariyah hajiya zeenah tayi,tareda cewa.
"Ohhh lallai Jawaheer É—in mama,har yanzu dai kece da cinya koh,saiki sha magani ai ki huta"
Sakin baki Madeenah tayi tana jin abinda ummanta ta faɗa,tsamin jikine zai hana mutum kawowa baƙi ruwa,kuma ji abinda suke faɗa.....anya kuwa ba asiri hajiya Ladi tayiwa uwartasu ba,inba haka ba wannan ai ya wuce ɗaukar tunani.
Harara Madeenah ta gallawa Jawaheer,wanda itama ta rama a take,kaman ba itace take sakalcin Æ´an shekara biyu ba,gaisuwar da akace tayin ma batayi ba ta tashi ta tafi. Half vest ce a jikinta sai bom short,su a dole suna kwaikwayon turawa,ko mahaukaci yagani yasan abin bayyi tsari ba,amma Hajiya zeenah idonta ya rufe akan mutunin nata (kuÉ—i) kwata kwata bata ga hakan ba.
Har taje bakin ƙofar fita daga falon ta juyo ta kalli Madeenah.
"Ahh Madeenah zamuje ciki mana na rakaki sashen Yah Ameen"
Kallon ta Madeenah tayi babu yanda ta iya tabi bayanta,saboda kallon da Hajiya zeenah tabita shi,na gargaÉ—in karta musa.
Itakuwa tasani sarai ba abin arziƙi bane yasaka Jawaheer ƙiranta,dan tafi kowa sanin wacece Jawaheer ɗin.
Kaman kuwa dama jira suke,Madeenah tabin bayan Jawaheer hajiya zeenah ta matso gefen Hajiya Ladi.
Labarin abinda ya faru tafara zayyane mata na mutuwar hafsa,kasancewar basu samu tattauna hakan ba ana abin mutuwar.
Wani murmushin ciki ciki hajiya ladi tayi,koba komai taji daÉ—in hakan,duk da taso lubna ce ta mutu,in suka tashi hafsa bazata yimusu wahalar kawar wa ba a cikin tsarin.
"Toh naji mai kikace Zeenatu,amma ya kike ganin zamuyi yanxu toh,wanann idan muka barta bamu san wani irin barazana zatayi ta kawowa ba,sannan gaskiya bazan yadda Jawaheer tazama surukarki ba wannan matar tana gidan"
"Nasan da haka,abin da yafi mu zauna a mukawo shawara kawai,ni burina shine ta fita daga rayuwar É—ana,yazamana cewar inada iko dashi yanda naga dama"
"Plan biyu zamuyi yanzu,na farko shine ki ƙirasu dagashi har matar tasa,kafinnan ki tabbatar yasha wannan maganin a abinci tukunna.
Komin asirin dayake jikinsa to a take zai daina aiki na minti talatin,a lokacin saiki umarceshi da yayi mata saki uku,kinga koya dawo asirin dai aikin gama ya gamu.
Idan kuma wannan bayyi aiki ba,to inaga wata matar zamu aura masa,mu nuna mata muna tareda da ita,ta dunga yin duk abinda muka ce,idan tayi nasara akan Lubnah itama saimu kawar da ita,idan kuma batayi nasara ba itama ta kasheta,shikenan kinga dai ba Æ´ar mu bace dai abin ya faÉ—a kanta ba"
"Wanann aiki yayi,kai ai ƙawance dake Hajiya ladi nasara ce,da duk ban tuno haka ba......."
Suna barin falon sashen Jawaheer suka nufa.
Chapter 1 · 0% Book details