← Book details Auren Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 4

Sashe 1

Auren Kwaila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*✨AUREN ƘWAILA✨*
*Romantic and comedian story*

*Story and Written By Aunty Aisha Mamanteddy*

*Free page*
*01*

*Ga masu bukatar a tallata masu hajar su , Zaku iya tuntubar wannan number 08081202932 sannan kaman yanda kuka sani Wannan littafin na kudi ne , pages biyar kacal za muyi na free page , Don haka ga masu bukatar littafin Auren Kwaila, Regular group #500...Vip group #1000.... Special payment #1500 via 8081202932 Aisha Mohammed opay or 6037312299 Mohammed Aisha keystone bnk evidence of payment via 08081202932*

Bismillahir rahmanur Rahim

Alhamdulillah Gani tafe da Sabo mai ɗauke da Sabon Salo ,wato Auren Ƙwaila😂💃🏻 dadin wanga labarin sai Wanda ya karanta ...Kar ku manta nice dai shahararriyar marubuciyar Nan taku Wato Mmnteddy , wacce na saba kayatar daku da littafaina ....ga Kuma masu bukatar complete novels Dina zasu iya payment 👍🏻✨💃🏻 .
1)The Sexy boss#500

2)Sex before marriage #1000

3)The virgin maid #500

4)Walijaam #500

5)Y'ar Aikina #300

6)Bintoto #300

7)Kwarton manya #500

8)Y'ar tsakar gida #600

9)Fyad'e #1000

10)Mr.Romantic #500

11)Sexxies house #500

12)Y'ar waye #300

13)Rainon soja #600

14)Rainon ta zanyi #500

15)Dijama y'ar fulani #300

16)Siyasata #300

17)Gidan kwarata #500

18)Gidan zaurawa #500

19)My lady boss #500

20)Sadaka yalla #500

21)Kwaryar sama #300

22)Zuma da madaci #300

23)Y'ar maula #300

24)Tabarah #500

25)Bafullatanan Ruga #300

26)Zaki #500
Opay Aisha Mohammed 8081202932 mun GODE .
*Kaduna*

Umma Umma! Umma!!! Ta shigo gidan cikin Wani irin gudu tana kwaɗa Kiran Sunan Umma nata wacce Tayi nesa Wurin surfe Wake tana wankewa don yin Alalen yamma da take Yi da kunu na sayarwa . Umma na!! Ta ƙara Kiran sunan Umman nata a karo na biyu , Wanda Umma Ramatu ta ɗago tana cewa “ Na'am Fatiti , Fati zareriya , mene ya faru waya taɓa mun ke?? “ . Umma wai ni Ikilima Zata Yi ma Rainin Wayo , na sayar ma Yaron ta da Rake na Talatin ,wai ta dawo min dashi ba Zata siya ba ,yayi mata tsada sai na Bata kudin, ni Kuma ban taɓa amsar kudi in Mai da ba , Don haka sai Tayi Haƙuri Wallahi Ba zan Amsa ba .

Aiko Baki Isa ba ,ko sata ake Yi ba zan siya wannan Rake naki a naira Talatin ba , duk rashin kunyar ki sai kin bani kudi na eheee! . Ikilima ce ta katse Fati kamin Umma ta ce da ita Wani Abu . Aiko Wallahi bakya ba ,ko mijin naki ne Bai ishe ni ba.....Bude Baki Yan siyayyan kunu suka Yi suna mamakin Kalaman Wannan Ƴar Ƙwaila ga Matar Soja, domin kuwa Ikilima Mijin ta Soja ne, . Ke Dama Ina Jin labarin rashin kunyar ki ,Ashe Abin naki har ya tsallako zuwa Kai na?“ . To ki natsu ki San inda yake miki ciwo ,mara kunya . Haba Ikilima Kema Kya biye ma Fati da girman ki? Don Allah kiyi Hakuri ga Kudin naki amshi, Umma Tayi maganar tana Mai kwance bakin zanenta tare da kirgo Talatin tana mika ma Ikilima.

Hannu Ikilima tasa tana amsar kudin tare da Juyawa tana amsar Raken Dake hannun yaronta tana mika ma Umma Ramatu .... Girgixa Kai Umma Tayi tare da cewa “ Aa Haba Ikilima, Kiba Yaro yasha rake Kya amsa a hannun sa . Allah kuwa Umma Bata Isa ba , sai ta bamu raken Nan......Fatiti Tayi maganar cike da tsiwa tana kokarin Kai hannun ta don ta kwace Raken ne Umma ta buge bakin ta , tare da cewa ’ Na hanaki Rashin kunya da Dauko mun magana ko? . Wuce ki bani .... Ikilima sai Anjima tasa me gida na ku tafi . Cike da Dan Jin kunya Ikilima ta tasa yaronta tana ficewa daga Gidan , Yayin da Zarah ta juya tana kunkuni tare da cuno Baki tana yin na daki adole tafasa sana'ar . Murmushi Umma Ramatu Tayi tana cewa “ Dama ni bani na saki ba,kan kece kika Saka kanki, Yarinya kamar wacce na haifa Cikin maza ,duk wata sana'a ta maza shi take yi😂har ta abokan hulɗar ta maza ne ko meye hakan hohoho ni Ramatu“ . Ai daga Yau an gama Sana'ar Raken,Indai ba zata nemi Wani Sana'ar ba to sai dai A bar shi , kai Ni sana'a ma Indai na Fatima Zarah ne Wallahi na yafe haka nan “ .

Dariyar Guggo Balki ne ya katse Umma Ramatu wacce take yi har tana kyakyatawa, kana tace “ Addu'a shine kaɗai zaki yi ma Wannan Yarinya kowa da Kalan Ƙuruciyar sa “. Fitowar Fatiti yasaka Guggo Balki rufe bakin ta ,tana yin shiru don Tasan halin tsiwar ta bata bar kowa ba“ .

Nufar inda Sandar Raken nata yake tayi tana cewa “ Umma bari na fita naci kasuwar yamma😹“ ...Yamma?? Aa ai Zauna Kawai Fatiti daga Yau wannan sana'ar a bar ta haka kawai na gode “. Buɗe Baki Fati tayi tana cewa “ Umma abar sana'a kika ce fa? , Aa gaskiya Ni ba mai san zaman banza ba ne!

To ai bakya zuwa makarantar naki! Guggo Balki ta katse su ,inda cike da Tsiwa Fatiti tace “ Oh to ke Guggo wa ya sako bakin ki cikin nan ? Dama Ashe idanun ki na anan ban sani ba ? , Ƙila kece kk zuga Ummana akan na bar sana'ar sayar da Rake ko?“. Aa Fatima wai ai ma sanar sayar da Rake sana'a ce ta maza ba mata ba“ .Oho to Ni kuma shi nake da Ra'ayi ....“Yi min shiru! Umma ta katse ta tare da cigaba da cewa “ Na hana wannan sana'ar daga Yau “ . Hmmmm Shikenan yanzu bara naje na Dawo? . Ta furta zancen tana Nufar Hanyar fita , a'a dawo ina za kije? Umma ta katse ta wanda kamin ta sake wata magana tuni Fatiti ta banzama ta fice tare da fadin yanzu zan dawo .

*
Tun da Ya dauko hanya har izuwa wannan lokaci bai samu damar tsayawa ba don bai san mene ya kawo sa Wannan Gari ba , parking din moton sa yayi can gyefen hanya fiye da Mintuna arba'in yana Zaune yana tunanin Rayuwar sa . Tun ina yaro na ke burin zama Soja, a nawa tunanin wannan Itace hanya mafi sauki Wurin ganin na Ɗau fansa ta , wanda na girma da Babban Ƙulli a cikin zuciya ta ,amma Sai da na zama Cikakken Soja wanda a yanzu nake da matsayin Police Army Amma duk da hakan bashi da Wata Amfani a gareni ,tun da ban dau Fansa ta ba . Kallon wannan matashin Saurayi nayi ina mai ƙara Gyara zama na domin kuwa Dabadon naji da Harshen Hausa yake magana ba ,to babu shakka sai dai nace Balarabe ne wannan Ɗan Saurayi , Fari ne tassss Ga gargaasa ta ko ina a jikin sa Alamun hutu , Wanda ba don naji yana kiran kan sa da Soja ba to da babu shakka zan kira sa da yaran da basu san ma wahalar zufar Rana ba . Idanun sa A lumshe suke da ganin su irin sexy eyes din Nan ne dashi , ga Ɗan Saje da ya kewaye fuskar sa ....motsa laɓɓan sa yayi masu ɗan tudu nan take na Hango faɗaɗan Wushiryar sa daga Sama . Lumshe idanun sa yayi yana Kallon Gyefen Windown moton inda mutane ke wucewa kowa na harkokin sa , Shi yana iya Hangosu amma su babu mai damar ganin na cikin moton sakamakon bakar gilashin Windown .

Tafiya take bazar bazar bazar , hannun ta dauke da bakar ladar wanda yake dauke da kayan yin Kalallaɓa wainar fulawa . Tun kamin ta iso layin su take yin tallah yau zata fara kalallaɓa har ta iso dab da gidan su tana tsayawa a bakin titi tare da kallon ƴan samarin dake zaune wasu cikin napep wasu kuma na zaman majalisar bayan la'asar....Garba yau zan fara kalallaɓa ashirin Ashirin . Yanzu zan shiga gida a ƙwaɓa mun zan fito da Murhu da Kwanan suya . Aaaahh haba Fatiti a soya mun ta ɗari kuwa . Juyawa tayi tana ce ma sauran mutanen ku fa?“ . Ai muma a fara suyan zamu siya .... Murmushi tayi tana Nufar napep inda Bello suke tana cewa “ Bello yau da kallaɓa da yamman nan , ta nawa zaka siya?“ . Murmushi Bello yayi yana cewa “ Fatima manya , A soya mun ta Ɗari biyu , Sai dai matsala na dake kin Fara girma amma bakisa Hijabi..... Harara ta zabga masa tare da cewa “ Ina ruwan ka dani naga wannan bai shafe ka ba , Uhmmmm! Kai dai naka siyan Kallaɓa ka Ajiye mun kuɗi na“ . Murmushi Bello yayi don da sabo ya saba da tsiwar Fatiti “ . Har ta wuce Motan sai ta dawo tana cewa “ A'a wannan fa moton tun wurin ƙarfe biyu take anan , Kuma a gaba na ta tsaya ban ga kowa ya fito daga ciki ba , Tabbas dai kowa ye a ciki yanzu yana bukatar Abin taɓawa Bara ka gani..... Maganar tayi tana kai hannun ta tare da Bubbuga glass windown , Wanda a hankali y fara saukewa yana bin ta da kallo ....Turusss Fatiti tayi tana tunanin Ko dai Balarabe ne wannan anya kuwa yana jin Hausa ..... hmmmm numfasawa tayi tana cewa “ Mene Sunan ka? .

Bin ta da kallo yayi kamin a taƙaice yace “Jibo Saleem Fahad.....🙀Jibo!!! Ta furta tana buɗe Baki cike da mamaki ,kana tace “ Ikon Allah, yanzu duk kyawun nan naka a rasa sunan da za'a sanya maka sai Jibo? Hmmmm ba Wannan ba aƙwai kalallaɓa naga tun ina sayar da Rake ka tsaya baka fito ba ,nasan dai yanzu ko wata irin Hanji ne da kai yanzu zata buƙaci Abinci “ . Ta nawa zaka siya???????😹😹😹😹😹“ .

Masu karatu muje zuwa , wai shin ya labarin take ne??? Waye Wannan Jibo saleem Fahad, Wanne ne sunan sa na yanka a ciki? SALEEM ne? , Ko JIBO ne , ko kuma FAHAD ??? muje zuwa me labarin ya kunsa ? Ni dai ku cigaba da biyo alƙalamin Mmnteddy......

*Kar ku manta free page 5 kaɗai zan yi ,ga masu bukata zaku iya fara biyar kudin littafin AUREN ƘWAILAH .*

*Regular group #500*

*VIP group #1000*

*Special payment #1500*
Chapter 1 · 0% Book details