← Book details Anti Romance Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 7

Sashe 6

Anti Romance Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Nice wa?🤨”
“Kece Ɗazu kika hankaɗe Ni a hanya ...”

“Cut the story short,what brought you here? Ina da abinyi?” tana magana tana kallon agogon diamond din Dake daure a tsintsiyar hannunta.

Washe dafaffun hakoranta Dije tayi “Hajiya da dai kin daure kinyi Hausan ,nan duk ba me jin turanci ,ko ?” ta juya tana kallon ƴarta ,itama kuwa ta amsa da “Eh”

Shan ƙamshi ta ringayi tana fesarwa kamar bazata amsa su ba ,sai kuma cikin balai tace “Wa kuke nema? This is my house Kuma ban sanku ba,wajen wa kuka zo”

Laushi da Murya Dije tayi “Mai da wukar Hajiya muma ai bamu sanki ba ,Mu baƙin Ɗan lami birkila ne ,in da hali ayi mana magana dashi”

Caɓe fuska tayi cikin rashin fahimta“Ɗanlami kuma? Ban sanshi ba...Bimbo take them out!” ta bashi umurnin ya korasu waje,ta wani juya a gadarance zata shige part dinta.

“Kambu! To uban kuturu ma yayi kaɗan,in kunga na bar gidan nan to Naga ɗan lami”

“Dallah rufe muna massai(Toilet) Wai tana nufin bakin tane toilet”

“Anƙi ”

Ɗaga sanda yayi zai kwaɗa mata ,Naja taja baya ta ɗauki wani ƙwandalelen Interlocks brick 🧱 baya fashe .

“Wayyihuhu...Saini Naja ƴar Ɗan lami,Kana dukan mamana ,Kwarankwatsa saina tarwatsa kanka”

“Banni dashi Naja, Hege ɗan gidan taƙi zaman aure😱” tana magana tana tale ƙafa ,ta dunkule hannu tana shirgama hannunta ɗaya naushi,jira take kawai ya shigo ta ta far mashi da Bugu

Wangale baki Sajida tayi cikin tsorata ,wannan wasu irin gayyar jaraba ne!?

Bimbo tsalle yayi ya dawo bayan Sajida
“Dallah gafaracan sakaran banza ka koran mun su nace ! Macen ne kake jin tsoro da wannan mininiyar yarinyar mai kama da kalan hanji?”

“Hajiya kamar fa Iskokai gareta ,wannan idon ba ƙalau take ba,kinga ai banayi dambe da Aljani ba ko?”

Ɓiiiiiiiii!! Ɓiiiiii!!!

Suka farajin Horn din motocin mai gidan ,lokacin tashinsa aiki yayi.

Da gudu ya runtuma yaje ya Gwale gate,saiga motar ƴan sanda ɗaya mai jiniya ta fara danno kai ,tun kafin su isa parking lot motar na tafiya suke diddirkowa a motar hannunsu da bindigogi ,bayan motar kuma wata Hilux ne baka da Kuma Land Rover.

Wani tajin tajin gidan yayi nan da nan tsaro ya ninku kikaga ƴan sanda sun yayyaɓe Land Rover din escort ɗinsa suka fara fitowa cikin suit grey da bakaken madubin ido ,suka bude ma mai gidan gidan baya ,ya miko ƙafarsa waje ,cikin wani hatsabibin takalmi mai gigitaccen tsada ,sunkuyawa sukayi suna gaisuwa ,kana ya fito daga cikin motar gaba-daya ,nan ilahirin securities din suka daura da masa Barka da zuwa .

Dije dake tsugune kusa da kayanta jikinta ba inda baya bari ganin bindigogi a hannun jami'ai,ta sadakar kashe ta kawai zasuyi .

Fuskar wanda har duniya ta tashi bazata taɓa mance shiba ta gani cikin tsakiyar matakan tsaro.

Dafe kirji Dije tayi “Ɗan lami? Ɗan lami dama zan sake ganin ka😥? ” kawai sai ta tsage da kuka.

A dimauce ya shiga wawwaigawa yana ƙoƙarin zakado sautin matar da take kiran sunan shi ,da ya tsufa da shudewa shekaru 7 da suka wuce.

Naja dagowa tayi tana kallon mamanta “Inna meye na kuka ?”

“Naja ga babanki ɗan lami can ,yau Allah ya nuna mun shi kin huce gori” ta nuna mata kyakyawar mutum cikin danyar filtex cream ,ingarman Namiji Mai cikakkun damatsa basai an tambaya ba ,yana jimming sosai , exercise sun ratsa shi.

Naja cikin zumudi ta kwasa a guje ko ganin matakan tsaron da yake tsakiyar su suna sallama batayi ba taje ta rungume ƙafafuwarsa

“Oyoyo Babana!”

Oum Aphnan
09065990265
[2/10, 11:15 PM] Chuchu👻: ANTI ROMANTIC
Page G

______
Ɓiiiiiii
Horn ɗin mota daga wajen Gate ɗin shi ya dawo da bimbo attention dinsa ya falla da gudu yaje yana tale Gate.
Caɓe baki dije tayi, taja siririn tsaki, ta sauke ɗumamen tuwon su dake ta zaɓarɓaka cikin miya, ta ɗauko yajin daddawa ta baɗe kan tuwon .

“Uhum ayi bismillah” taba Naja umurni daga nan kuma ta fara soka ma bakin Naja danƙwala²n loman ɗumame a baki , itama tana cin nata joyfully da goran ruwan da suka ɗebo a burtsatse suna korawa, sanyin bishiyar na masu daidai.

With bouncing Salim ya fito daga cikin motar ƙirar camry fari tar.
“Barka da Isowa yallaɓai”
Salim da bai wuce shekaru 31 ba, kallon bimbo yayi kana yaja belt din wandonsa da ya zazzago ƙugu.
“Oh thnk you, and what's this for? ” ya nuna su Naja dake sanƙarar tuwo a gaban itace sai bulbula hayaƙi yakeyi.

Dukan hannu yayi irin na munafukan masu gadin nan “Oho wai su baƙin oga ne”

Ɗage giran sama yayi “Oh really? ”
“Oho, sanin gaibu sai Allah, Madam tace in kore su saidai ga dukkan alamu sun saba da tuwon dawa ƙarfi garesu kaga kar su je su sabauta ni”

“Mtsew kai gafara can, sam baka cancanci zama mai gadi ba, macen ma tsoron ta kake ji inaga ɓarayi?! ... Abeg moveeee!! ”
Ya taka a nitse zuwa gaban su Naja.

Daga ɗan nesa ya ɗaga mata hannu “Assalamu Alaikum✋🏽” kallon sheƙeƙe dije tayi masa ta ƙara danna ma ƴarta loman tuwon a baki

“Nace ba? ” daidai nan ya ƙaraso gabansu
Dunƙulo wani rafkeken loman tuwo tayi ta dangwala a cikin miya. Ta tsaya tana kallon sa rike da loman tuwon kamar ta ɗauki dutse, kana ta saki wani wawiyar gyatsa irin na wullayen ƙauyen nan

“Hwarrrrrrrr”
Da sauri Salim yakai hannunsa kan hancinsa yana doɗewa. Ai kuwa a fusace Dije ta wullo masa rafkeken loman tuwon nan da ta dangwala masa miya, da gudu yayi baya ganin zata ɓata masa farin shirt dinsa da yayi odarsa daga UK.

Dukda gaggawar matsawa da yayi amma bai nasara ba saida ta wulla masa a ƙirji
Cikin tashin hankali ya buɗe baki zai magana, amma kafin yayi magana ta sake karyo wani tuwon ta sake jefo masa, itama kuwa Naja ganin uwarta na cilla ma mutum loman tuwo itama ta fara dangwalo miya tana wulla masa.

Ai a guje yabar wajen
Fashewa da dariya bimbo yayi, ba kace na Faye surutu ba, Sune daidai daku mutanen gidan nan... Ahayye yaseen na huta kallon film a waya .

***
“Kalleni nan, nikam kaga ban damu da waye ita ba, ko kuma da wacce take tare ba, kawai I want them out of my house this minute” Sajida ta bashi amsa a fusace ta hangame kofa zata fita daidai nan Salim ya fado dakin kamar an jeho shi, kayan shi, jagaje jagaje da miya.
A tsorace ya makale a kofa ya bata hanya ta fice a fusace.

A tsanake Dije ta fara hade kwanukan da sukaci.
“Kinaji ko Naja, bari in hada maki kwanukan nan ki zo ki wanke su ”

Ɗannn Naja ta ɗane bayan Dije “Ni sai kin yi mun bambu to” tana magana tana harba mata ƙafa a ciki kamar dai ta sama dokin gaske.

Cikin kwarmato take balbaleta da masifa “Ke Naja sakko, ki sauka nace ko? Naki in yi maki goyo goyon”
Dukda masifan da takeyi amma bai sa Naja ta tsorata ba, kenan inda sabo ta saba da jarabanta.

Fakam fakam sai ga Sajida tazo ta tsaya a gaban su
“Excuse me foolish woman, kindly pack all your nasty gabages, ki fice mun a gida yanzu yanzun nan... Oya Oya tattare ƙazantarki ki fice! ”

Wani galala da fuska Dije tayi mata kamar doluwa sai dai kuma bata ce komai ba ta cigaba da magana da ɗiyarta.

“Oho ƴar iska kika maida ni ko me? Ina magana kina mun banza!? Zan maganinki ne.... (Cike da jaraba ta ƙwalla ma mai gadin kira) bimbo Bani bulala ko lalataccen wayan wuta in akwai a dakin ka”

Haba ai Dije najin haka tai zumbur ta Mike ta dirke Naja a bayanta ta yayibo dankwalin da suke zaune a kai ta ci ɗanmara dashi.

“Ahayyyeee 😳Ni zaki duka? Kar shirun da nayi maki ya baki damar neman kawo mun hauka... Wabillahillazi hauka na ya girmi na uwar ki... ” Ɗaga hannu tayi zata mareta, ai kamar kura ta cafki wuyar hannunta, ta matse gam!

“karki kuskuren taɓa jikina, don zai zamo kuskuren ki da zaki yi na karshe a duniya... " A fusace ta watsar da hannunta a iska

Da sauri ta rike hannunta da take jin kamar an tunɓuke mata daga jikinta.

“Ni kike nemar nakastawa? ”

“kash, na lura damben nan dai kike so ayi ni kuma tausaya maki Nike, don kwarankwatsa yanzun nan lahira zatai baƙo, yoo wani ma yayi rawa bare ɗan makaɗa! Ni da na saba shan ɗamara in dambe da maza majiya ƙarfi????! ”

Da gudu ya ƙaraso gabansu har yana tuntuɓe da gima gimandutsen murhun da ta kafa masu a tsakar gida sai hayaki yake

“Na shiga uku sajida me kike yi haka? ”

Dije ɗaga yatsa tayi tai tsalle ta dungure ma shi goshi ba tareda ta dubi girman darajan sa ba

“Ɗan lami, kaine rikaƙƙen munafukin, mugu kawai mumugunci, Saida ka ɗirka mun ciki, sai ka gudu ka barni shekara 7 yunwa da fatara na ƙoƙarin kashe mu .... Humhun Ji inda kake rayuwa kana jin daɗin ka!! Wallahi Allah ya Isa..... To duk ma ba wannan ba ina binka a saffa saffa wannan matar mai ruwan karas zubin zabiya da ban sani ba matarka ce ko wacece wai har zata zo tace mun in fita... Halan baka bata labarin Dukiyar da kake tunƙaho dashi ba NAWA NE! ”

Ras!!! Gaban Sajida ya faɗi “Ke ke kin ga dakata karki ci ma mijina fuska, waye ke”

“Mijinki ko mijina, Sannan na faɗa dukiyar nan nawa ne ni Dije ba nashi bane, bare kuma ke da kike wani gwalangwalaso har kike cewa in fita a gidan, kece zaki bar gidan nan DUN UBAN KI!!!”

TOPAH KAJI ZAGIN MAGUZAWA😆
MUJE ZUWA AKWAI TARIN CAKWAKIYA A LITTAFIN NAN, WANDA NASAN DOLE KI YI NISHAƊIN KARANTA SHI

WANNAN KUMA SHINE FAJIN KUSA DA KARSHE NA KYAUTA, DAGA PAGE NA GABA NA KYAUTA YA KARE.

KI BIYA KUƊIN KI TA WANNAN ASUSUN
7782217014
MOHAMMAD HASSANA
FCMB
Chapter 6 · 0% Book details