← Book details Allon Sihiri 1 To Part 9 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 24 OF 25

Part C

Allon Sihiri 1 To Part 9 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Khamis Idris.
Tokusani Cewa Na Amince Za A Kaiku Izuwa Turakar Sarki Kuga Halinda Yake Ciki Amma Bisa Sharadi Guda Biyu, Sharadin Na Farko Shine Za'a Caje Kowannenku Acire Duk Wani Makami Dake Jikinsa Ko Kwagirinku Na Sarauta Baza A Barku Shiga Dasbiba Kai! Ko Tsinken Sakacen Haqori Bazaku Shiga Dashiba, Koda Kuwa Kaurinsa Bai Wuce Na Allurar Data Kasance Mafi Qanqanta A Duniya Ba, Mataki Na Biyu Kuma Shine Babu Wani Badakare Mai Tsaron Lfyr Ku Dazaiyi Muku Rakiyi Izuwa Cikin Turakar Sarki Lubainu, Cikinku Duk Wanda Ya Amince Da Wannan Sharadi Saiya Koma Can Gefe Guda, Kodajin Wannan Batu Sai Sarakunan Suka Kama Muzurai Suna Kallon Junansu Sbd Anjefasu TSAKA MAI WUYA, Domin Kuwa Duk Wanda Yaqi Yarda Da Sharadin Da Aka Gindaya Za'ace Munafukine, Shikuwa Wanda Ya Amince Zuciyarsa Zata Rinqa Rawa Yarinqa Zargin Ko Wani BAQIN TUGGU Akeso Ashirya Masa, Dadai Sarakunan Suka Ga Basuda Wani Zabi Wanda Yafi Subi Wadannan Sharuddai Sai Duk Suka Aminta Aka Cajesu Sannan Aka Tafi Dasu Izuwa Turakar Sarki Lubainu, Koda Aka Shigo Da Sarakunan Cikin Gidan Sarautar Sarki Lubainu Saisuka Rude Domin Basu Taba Ganin Anqafa Matakan Tsaro Ba Irin Wannan, Sbd Duk Inda Mutum Yaduba Acikin Gidan Sarautar Babu Abinda Zai Gani Face Dakarun Yaqi Ako Ina A Tsaitsaye Riqeda Muggan Makamai Kuma Ko Motsin Takarda Sukaji Saikaga Sunyi Harr...! Izuwa Wajen, Haka Aka Zuba Wadannan Dakaru Ako Ina Har Akan Saman Rufin Dakunan Gidan Sarautar Gaba Daya Dakan Katanga Dakarune, Wasu Sun Dana Kibiyoyi Akan Baka, Wasu Suna Riqeda Masu, Har Izuwa Qofar Turakar Sarki Dakaru Ne Ajere Sahu Sahu, Hakadai Aka Cigaba Da Yiwa Sarakan Jagora Har Aka Iso Qofar Turakar Sarki Lubainu, Anan Ne Aka Tsayar Da Sarakunan Akace Kowa Yacire Takalminsa, Nanfa Ran Sarakunan Yabaci, Suka Ga Cewa Lallai Wannan Ba Qaramin Wulaqanci Bane, Amma Dasuka Gashi Kansa Mai Ruqon Gado Sarki Zairuf Yacire Nasa Takalma Sai Suma Dukkaninsu Suka Cire Nasu Takalman, Sannan Aka Bude Qofa Suka Shiga, Suna Shiga Suka Hango Sarki Lubainu Kwance Akan Gado Bakyan Gani Kamar Kwarangwal Sbd Rama Gawani Mayaqi Tsaye Agefen Gadon Cikin Shigar Yaqi Na Qarfe Yarufe Kansa Da Hular Qarfe Idanunsa Kawai Ake Gani, Kuma A Tagwayen Takubba Saqale A Kuibin Cinyoyinsa, Take Aka Tsayar Da Sarakunan A Lkcn Da Tazarar Dake Tsakaninsu Da Gadon Sarki Lubainu Batafi Taku Goma Ba, Koda Sarakunan Suka Hango Sarki Lubainu Sukaga Yadda Yazama Sai Suka Zube Qasa Bisa Guiwoyinsu Suna Tararrabi, Jimami Da Nuna Matuqar Baqin Cikinsu, Wasu Ma Har Koke Koke Suka Kamayi Gamima Zubarda Hawaye, Duk Wannan Abu Dake Faruwa Wannan Mayaqin Make Tsaye Daf Da Gadon Sarki Yaqurawa Sarakan Idanu Yaxa Naxarinsu Sosai, Ashe A Cikin Hulaqar Qarfen Daya Kwama A Kansa An Sanya Gilashin Hangen Nesa Akan Idanunsa Don Haka Yana Iya Hango Idanun Sarakan A Kurkusa, Bawani Bane Acikin Wannan Shiga Ta Kayan Yaqi Ba Face Jaruma Suhailat, Kuma Nan Take Tarinqa Ganin Abin Mamaki, Domin Dayawa Daga Cikin Wadannan Sarakan Koke Koke Qarya Suke Sbd Dazarar Sunkalli Junansu Sai Kaga Suna Yin Murmushin Mugunta Gamida Yaqen Farin Ciki, Daya Bayan Daya Saida Jaruma Suhailat Ta Shaida Sarakan Ta Tabbatar Dacewar Bazata Mance Da Kamannin Fuskokinsuba, Nan Dai Sarakunan Suka Nuna Alhininsu Sannan Suka Tashi Suka Fice Daga Cikin Dakin, Acan Fada Ne Sarki Zairuf Ya Sallamesu Suka Watse Kowa Yatafi Izuwa Qasarsa, Tafiyarsu Keda Wuya Sai Sarki Zairuf Yakirawo Sarkin Yaqin Qasar Wato Qanin Mahaifinsa Tareda Dukkan Manyan Gwarzayen Mayaqan Kasar Wadanda Ake Taqama Dasu Suka Shiga Taro Na Gaggawa, Bayan Kowa Ya Hallara A Dakin Taron Sai Sarki Zairuf Yadubesu Gabadaya Yace, Yaku Yan Uwana Mayaqa Inaso Kusani Cewa Ban Karbi Wannan Matsayin Dukiya Ko Karaga Ba Face Don Kishin Qasata Da Jama'ata, Ban Nemi Abani Wannan Matsayiba, Sarki Ne Dakansa Yaga Na Cancanta Shiyasa Yabani, Amma Niba Haka Nasoba, Sonayi Sarki Ya Kyaleni Nabi Dangin Mahaifiyata Qabilar Banu Zahar Ma'abota Rayuwar Farauta A Daji, Kubar Ganin Cewa Wannan Mugun Ciwo Yakama Sarki Niban Fidda Ran Cewa Sarki Zai Iya Tashiba Farat Daya Akoyaushe Kamar Yadda Ciwon Yayi Zafi Farat Daya.Ban Taraku Anan Domin Komai Basai Sbd Muyi Shawara Akan Yadda Zamu Tsare Birninmu Da Jama'armu Daga Sharrin Abokan Gaba Sbd A Halin Yanzu Da Sarki Ke Cikin Wannan Hali Maqiyanmu Ko Ince Maqiyan Sarki Zasu Iya Amfani Da Wannan Dama Sukawo Mana Hari A Koyaushe, Sbd Suna Ganin Cewa Shine Kadai Kariyarmu Tsawon Shekaru, Yanzu Wacce Shawara Ce Ta Farko Dakuke Da'ita Dangane Da Wannan Al'amari? Kodajin Wannan Tambaya Sai Gaba Dayan Mayaqan Suka Yi Shiru Suka Kama Kallon Junansu Akarasa Wanda Zaice Qala, Daga Can Sai Sarkin Yaqi RAMAZAN Yayi Gyaran Murya Yace, Nitawa Shawarar Itace, Kawai Daga Yau Mukulle Qofofin Shiga Garin Nan Ya Kasance Bashiga Bafita Har Izuwa Ranar Da Sarki Yasami Lfy Yamiqe, Sannan Kuma Azuba Dakaru Yan Leqen Asiri Akan Iyakar Kasarmu Su Zuba Ido Domin Dazarar Sun Ga Alamun Za'a Kawo Mana Harisu Garzayo Sukawo Mana Rahoto Kodajin Wannan Shawara Sai Gaba Dayan Mayaqan Sukayi Amanna Da Ita Suka Kama Cewa Lallai Abinda Yakamata Ayikenan, Koda Ganin Haka Sai Sarki Zairuf Yadaga Hannu Kowa Yaishiru
Dakin Taron Yayi Tsit! Sarki Zairuf Ya Numfasa Yace, Yaku Yan Uwana Mayaqa A Matsayina Na Shugabanku Ayanzu, Kuma Qaramin Cikinku, Ban Amince Da Wannan Shawara Ta Ubana Sadauki Ramazan Ba, Kuma Yanzu Nan Zanfadi Hujjojina Naqin Amincewa Da Shawaran, Dafarko Dai Idan Muka Rufe Qofofin Gari Muka Hana Shige Dafice Tamkar Mun Karya Tattalin Arziqin Kasarmu Ne, Domin Kasuwanci Zai Raunana A Birninmu, Hakan Zai Iya Haifar Da Talauci Acikin Qasa, Haka Kuma Idan Muka Aika Da Dakarun Leqen Asiri Izuwa Ga Iyakokin Qasarmu Za'a Iya Mamayar Dakarun Liqen Asirin Duk A Cafkesu Ko A Hallakasu Batare Da Munsaniba, Kuma Akawo Mana Harin MAMAYAR BAZATO Acimu Dayaqi, Shin Idan Hakan Tafaru Megari Ya Waya, Ina Hikimar Turasu, An Yi Biyu Babu, Babu Su Babumu! Sannan Abuna Gaba Danake Son Tabbatar Muku Dashi Shine, Shikansa Rufe Qofofin Gari Alamace Dazata Tabbatarwa Da Maqiyanmu Cewar Mun Tsorata Bazamu Iya Kare Kanmu Daga Sharrinsu Ba Tunda Babu Sarki Lubainu, Adalilin Haka Zasu Iya Yin Gagarumin Shiri Akanmu, Wataqilama Suhada QARFI DaA QARFE Su Da Wadansu Sarakan Suzosu Murqushemu Su Kwace Qasarmu, Koda Sarki Zairuf Yazonan A Jawabinsa Sai Jikin Gaba Dayan Mayaqan Yayi Sanyi Suka Rude Dafadin Cewa, Kwarai Wannan Gsky Ne, Cikin Fishi Sadauki Ramazan Yadubi Sarki Zairuf Yace, Ai Saika Fadamana Taka Shawarar Wacce Kake Ganin Cewa Zata Fisshemu, Amma Dai Ina Mai Tabbatar Maka Dacewa Sarki Lubainu Shine Babbar Dirkar Datake Kare Wannan Qasa Tamu Daga Sharrin Dukkan Maqiya, Yanzu Kuwa Tunda Yafadi, To Ina Tabbatarmaka Dacewa Itama Dirkarmu Tafadi, Kodajin Wannan Batu Sai Sarki Zairuf Yamiqe Tsaye Zumbur! Afusace Yadoki Saman Teburin Dake Gabansu Yadubi Sarkin Yaqi Ramazan Cikin Tsananin Fishi Da Fusata, Lkcn Da Sabon Sarki Zairuf Yadoki Teburin Dake Gabansa Cikin Fishi Da Fusata, Sai Yafara Magana Dacewa, Yanzu Shikenan Sbd Babu Sarki Lubainu Saimu Zauna Maqiya Suzo Su Kashemu Sumaida Matanmu Da Ya Yanmu Bayinsu? Sbd Kawai Babu Sarki Lubainu Samu Zamo Karnukan Dabasu Iya Cizon Kowaba? Da Yawanmu Fa Anan Zakwaquram MAYAQA Ne Wadanda Suka Sukayi Suna Amma Muna Neman Mukarya Zuqatanmu Da Kanmu, Toku Saurareni Dakyau Kuji Shawarar Dazan Bamu Wacce Nake Da Yaqinin Cewa In Dai Mukabi Ta Saimun Sami Nasarar Kare Qasarmu Da Jama'armu Daga Dukkan Sharrin Maqiyanmu, Kuma Saimun Sami Nasarar Ganin Bayan Duk Wani Maqiyinmu Adoron Qasa, Mataki Na Farko Dazamu Dauka Shine, Zamu Zabi Zakwaquran Dakaru Mayaqa Guda Hudu Daga Cikinmu Wadanda Zasu Jagoranci Dakaru Kimanin Dubu Arba'in Arba'in Suje Iyakokin Qasarmu Guda Hudu, Gabas Da Yamma, Kudu Da Aremu Su Yada Sansani A Can Cikin Shirin Kota Kwana, Duk Baqinda Zasu Shigo Cikin Birninmu Sai Sun Cajesu An Tabbatar Dakosu Suwaye Da Kuma Abinda Zasu Shigo Dasu Cikin Qasarmu, Bazamu Taba Yarda Ayarin Dayafi Adadin Mutum Dari Biyar Ba Su Shigo Cikin Qasarmu Ba Dauke Da Makamai Koda Kuma Sun Kasance Fatakene, Wannan Shine Babban Matakin Tsaro Da Zai Hana Maqiya Samun Damar Kawo Mana Harin MAMAYAR BAZATO, Domin Kodasun Kawo Kafinsu Gamada Dakarun Dake Wajen Tuni Lbr Ya Riskemu Munyi Shiri,
[2/16, 6:42 AM] ∂Ѧη ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: ALLON SIHIRI
Littafi takes 8
Chapter 24 · 0% Book details