Part D
Allon Sihiri 1 To Part 9 Complete Hausa Novel · about 45 min read
Koda ya hangota sai ya mike zumbur!
Da sauri ya
tareta yana mai cewa,haba ranki ya dade,yaa
zaki
tafi cikin daji ba tare da kin sanar dani ba?
Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya Akisatul
Sauwara tayi
murmushi tace,komai akwai dalilin faruwarsa.Ka
bari
mu nutsu tukunna zan yi maka bayanin komai a
saukake.
Nan take Akisatul Sauwara ta dora ruwa a
tukunya ta kunna wuta.A takaice dai ta fara
kokarin
fisge wannan tsunstu data harbo.
Koda Lubainu yayi yunkurin taimaka mata sai ta
ki don haka sai
ya
zuba mata idanu har izuwa lokacin data kammala
gasa tsunsun sannan tayi masa tayi suka zauna
suka kama cin nama tsuntsun.
Tsawon yandakiku
suna cin naman dayansu baice uffan ba a lokacin
da
dajin yayi tsit ba a jin sautin komai face na iskar
dake kadawa.
Kawai sai Lubainu ya katse shirun ya
dubeta yace,yake wannan sarauniya mai
daraja,idan
baza ki damu ba inason ki gaya min dalilin
dayasa
kike sakin jiki dani a cikin wannan tafiya alhalin
ban
kasance muharraminki ba ko kuma amintaccenki?
Koda jin wannan batu sai sarauniya Akisatul
Sauwara ta
kyalkyale da daria sannan tace,tabbas
kayi mini tambayoyi masu amfani kuma dama ai
nayi alqawarin baka amsoshinsu a yanzu dana
sami
nutsuwa.
Da farko dai dalilin dayasa na yarda muka
kwana tare a cikin daki ina so ne na jarraba
hakurinka shin zaka kasance mai tsare
mutuncina bisa
alqawarin dake tsakaninmu na taimakon juna a
cikin wannan tafiya?
Tabbas ka kiyaye wannan
jarrabawa ka hayeta.
Dalili na biyu kuma wanda yasa
na tafi na barka a cikin tanti kana barci shine
domin
na jarraba amanarka na gani shin zaka sace
Allon
Sihiri na ne ka gudu?
Sai gashi kayi matukar bani mamaki tunda baka
sace Allon
Sihirin ba alhalin
kuma gashi na fito dashi fili karara daga cikin
kwalbar da babu wani mahaluki daya isa ya fiddo
shi.
Tabbas ka cika mutum mai amana yanzu abu
daya ya rage nayi maka jarraba akansa,kuma da
sannu zamu kai ga wannan matsayi.
Koda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a
zancenta sai
Yarima
Lubainu yayi shiru kawai yana mai kura mata
idanu.
Daga can kuma sai ya mike tsaye ya shiga
cikin tantin ya shiga cikin tantin ya shiga hada
kayayyakinsa yana zuba su acikin jakar
guzurinsa.
Itama Sarauniya Akisatul Sauwara ta mike tsaye
ta bishi izuwa
cikin tantin ta shiga
kimtsa na ta kayan.
Har suka gama kimtsa komai
basuce da junansu kala ba.
Nan take suka hau
dawakansu suka nausa cikin daji suna masu
cigaba
da tafiya.Sai da suka shafe sa'a hudu da rabi
suna
tafiya ba tare da sun yada zango ba sannan
Yarima Lubainu ya
matso kusa da Sarauniya Akisatul
Sauwara,da yake dama itace akan gaba tana yi
musu jagora a cikin tafiyar ya dubeta
yace,waishin
tafiyar kwana nawa zamuyi ne mu riski Birnin da
muka nufa?
Koda jin wannan tambaya sai Sarauniya
Akisatul Sauwara tayi murmushi tace,ni kuwa
dadina dakai
kenan ka cika zumudi da gaggawa.
Ai idan
kayi
hakuri idanunka zasu nuna maka.Koda gama
fadin
hakan sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi shiru
bata
kara cewa uffan ba har suka sake shafe sa'a
hudu
suna tafiya.
A sannan ne dare ya riskesu suka yada zango a
bakin wani
katon dutse.
Anan suka kwana
washe gari suka sake yin shiri suka ci gaba da
tafiya.Saida suka shafe kwana bakwai cur basu
riski
wani gari ba kuma basu hadu da wani mugun
abu
ba,kawai dai suna ratsawa ne ta cikin mugayen
dazuzzuka.Duk inda suka hadu da wadansu
mugayen dabbobi
ko kwaruka saidai kaga sun yi
musu kwaf! daya.Kai ko mugayen Aljanu ne suka
hadu dasu saidai kaga Aljanun sun gudu sunyi ta
kansu don sun san cewa WUTSIYAR RAKUMI
TAYI
NESA DA KASA! Kuma RUWA BA SA'AN
KWANDO
BANE.
A ranar kwana na bakwai ne da rana tsaka
Yarima Lubainu ya
hango wani babban gari a
gabansu wanda kawatuwarsa ta ninka ta birnin
Rauhul Bagadar sau uku wato birnin sarauniya
Akisatul Sauwara.Tun daga nesa Yarima Lubainu
ya
wangame baki kamar dan kauye yana kallon gine
ginen birnin cikin al'ajabi.Koda Sarauniya Akisatul
sauwara ta
lura da halin da yake ciki sai ta bushe da
dariya tace,haba ya kai Lubainu kada ka bani
kunya
mana,ai baka ga komai ba ma sai mun shiga
cikin
birnin tukunna.
Koda jin wannan Batu sai Yarima
Lubainu ya sake cika da mamaki yace,waishin
yanzu
kina nufin wannan birnin da zamu shiga shine
Birnin Kimras
inda sarki Darmanu yake mulki inda zamu
samu barin Allon Sihiri na biyu?Akisatul Sauwara
ta
jinjina kai tace kwarai kuwa amma abinda nakeso
dakai shine ka nutsu kada kayi komai da kanka
sai
abinda kaga nayi ko wanda na umarce ka dakayi
saboda Sarki Darmanu ba karamin 2shaidanin
Mutum bane.A
yanzu haka maganar nan da mukeyi nasan
yana kallonmu kuma yana jinmu,kuma zai iya yin
wani abu domin ya cutar damu,don bani da
tabbacin
cewar zai bamu hadin ka bisa bukatar da muka
zo
masa da ita.
Tabbas Sarki Darmanu ya fini karfin
Sihirin tsafi,amma fa a bangaren jarumtaka da
iya yaki KARE
JINI BIRI JINI mukeyi.
Sau tara muna
fafatawa ni dashi ba tare da wani yayi nasara a
tsakaninmu ba amma fa muna matukar jin jiki.
Bisa
sa'a ne kawai na samu na tsira daga sharrin
tsafinsa
saboda tsarin dana samu tun daga
kakannina.
Lokacin da Sarauniya Akisatul Sauwara tazo
daidai nan a
zancenta suna daf da shiga cikin
birnin ne,
Kwatsam!sai suka ga wani mutum Tsoho
tukuf ya fito dafa cikin gona goye da kara a
bayansa,shima zai shiga cikin birnin.Cikin Ladabi
Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu
suka
gaishe da tsohon.Kawai sai tsohon ya kare musu
kallo ya lura
cewa baki ne don haka saiya dubesu
yace,yaku wadannann matasa hakika ku baki ne
a
garin nan ko?
Akisatul Sauwara tace,Baba zancenka
dutse ne.Tsohon ya dubi Sarauniya Akisatul
Sauwara cikin yanayi
mai nuna tausayi yace,Yarinya bisa yanayinku da
gani kun fito
daga babban gida kuma kun sami
tarbiya mai kyau,saboda haka zan taimakeku don
kada ku fada cikin tarkon maketacin
sarkinmu.Ina
mai sanar daku cewa bisa al'adar wannan mugun
sarki namu duk bakon daya shigo garin nan
kamashi ake yi a kwace duk abinda ya mallaka a
kaishi
kurkuku a kulle ko kuma ayi masa dukan kawo
wuka sai idan yana da sauran shan ruwa a
duniya
sannan zai tsira da rayuwarsa.
Yanzu zan taimake ku
zna bi daku ta barauniyar hanya inda babu wanda
zai
ganku harmu isa gidana inda zaku kwana,in yaso
indan gari ya
waje sai ku saje da 'yan gari ku
aiwatar da abinda ya kawoku.Tsohon na gama
fadin
hakan kuma sai ya dubi Yarima Lubainu
yace,idan
sarki ya kyallara ido yaga wannan kyakkyawar
'yar
uwar taka saiya rabaka da ita har abada.
Koda jin
haka sai Yarima Lubainu ya gyada kai yana mai
jinjina
al'amarin ba tare da yace kala ba.
Nan dai
tsoho ya wuce gaba suka bishi a baya yana mai
bin
wata barauniyar hanya wacce tabi bayan birnin.
Su kuma suka ci gaba da jan limzamin
dawakansu a
hankali suna yin tafiyar san'da suna waige waige
cikin rashin yarda da kwanciyar hankali.Lokacin
da suka yi 'yar
doguwar tafiya ya zamana cewa tsohon
yana gabansu da tazara ta a kalla taku goma sha
biyar sai Yarima Lubainu ya dubi Sarauniya
Akisatul
Sauwara yayi mata magana cikin karamar murya
yace,nifa ban yarda da wannan tsohon ba,domin
zai
iya zama dan leken asirin Sarki Darmanu ne aka
turoshi ya
yaudare mu ya cutar damu.
Koda jin
wannan batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara taji
zuciyarta ta buga da karfin gaske,take tsoro ya
baibayeta kuma taji ta gamsu da tunanin da
Yarima
Lubainu yayi,don haka sai kawai taja linzamin
dokinta ta tsaya cak!shima Yarima Lubainu sai
ya tsaida nasa
dokin suka kurawa tsohon idanu kawai
yayin da yake ci gaba da tafiya.Koda tsohon yaji
sautin sauwun dawakansu Lubainu ya dauke a
bayansa sai shima ya tsaya cak ya juyo da sauri
cikin alamun mamaki ya dubi su Lubainu yace
'ya'yana lafiya kuwa kuka tsaya a baya haka
kuka daina tafiya?
Caraf sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta
dubi tsohon ta daka masa tsawa tace,kai tsohon
banza!bakin mayaudari na gane ko kai
waye.Maza
ka bayyana surarka ta gaskiya domin mu
tattauna
bisa abinda ya kawomu birninka.Lokacin da
tsohon
yaji wannan batu na sarauniya Akisatul Sauwara
saiya bushe
da mahaukaciyar dariya cikin karfin
murya mai nuna cewa lallai ba muryarsa bace ta
tsoho.Daga can kuma sai yayi girgiza nan take
ya
rikide ya zama sarki Darmanu cikin gagarumar
shigar yaki.
Sarki Darmanu ya kasance katon mutum
mai kirar sadaukai,gashi dogo zankalele kuma
gashi kakkaura
mai murdadden jiki gami da tarin kwanji
da
jijiyoyi.
KALLO DAYA mutum zai masa ya gane cewar
ya cika sadauki mai TARWATSA MAZA.
Wadansu
bakaken kayan yaki ne a jikinsa na karfe.
Rigar dai
Farmaran ce mai budadden hannu,sai dogon
wando da
dogayen takalma duka na bakin karfe.
A hannunsa na hagu kuwa wata katuwar garkuwa
ce
wadda akayi ta da zallan dutsen lu'u lu'u mai
nauyin
gaske wacce sai kato goma sun taru suke iya
rabata
da kasa amma shi ji yake kamar takarda ya
rike.
Bayan anyi kallon kallon na tsawon dakika goma
tsakanin sarki Darmanu dasu sarauniya Akisatul
Sauwara sai Sarki Darmanu ya sake bushewa da
dariyar mugunta karo na biyu sannan ya dubi
sarauniya Akisatul Sauwara yace,ke tsohuwar
abokiyar gaba kiyi sani cewa tun kafin ku baro
birnin ki naga
duk abinda ya faru tsakaninki da
Yarima Lubainu dan sarki Sailur har izuwa
sa'adda
kuka taho izuwa nan birnina domin na baku barin
Allon Sihirin dake hannuna.
Tabbas dake dashi kuma
sami tabin hankali har da kuke tunanin zan
karbeku
hannun bibbiyu na yarda da bukatarku.
Kisa sani cewa na dade ina jiran irin wannan
rana wacce
zakuyi gangancin dauko barin Allon Sihirinki ki
taho
har izuwa birnina domin tuni nayi bincike na
gano
yadda zan iya fidda Allon daga cikin kwalbar
dakika
adanashi.Kin ga kenan yanzu na sami tsuntsu
daga
sama gasasshe tunda kin kawo kanki.Yanzu zan
hallaku na
dauke Allon Sihirin daga jikinki naje na
biya tawa bukatar dashi.
Koda gama fadin hakan sai
Sarki Darmanu yai wuf ya daka tsalle a sama
kamar
an cilloshi daga cikin baka ya kawowa Akisatul
Sauwara da Lubainu mugun sara a sama da duk
su
biyun a lokaci guda.Cikin bakin zafin nama duk
su biyun suka
kaucewa saran suka fado kasa daga kan
dawakansu,ai kuwa sai takobin sarki Darmanu ta
tsarge dawakan biyu tamkar an yanka tsakiyar
tuffa.
Take dawakan suka zube kasa matattu.Cikin
sauri da dimauta su Lubainu suka mike tsaye
zumbur suna masu zare nasu takubban.Sarauniya
Akisatul
Sauwara tayi sauri ta tofawa takobinta da
takobin Lubainu wani dalasimin tsafi sai
takubban
nasu suka kara kaifi,girma da nauyi.Koda ganin
haka
sai Sarki Darmanu ya rugo da gudu izuwa kansu
suka runtsume da azababben Yaki.
Shegen kaya Uban mayaudara Sarki Darmanu.
6 hrs · PublicALLON SIHIRI
Littafi na biyu(2)
Part E
Sannan su dauke mu mu ci gaba da tunkarar
gidan
Boka Darbusa.Yanzu ga dawakai nan guda biyu
dana
tanadar muku sai ku hau mu kara gaba.Ba tare
da
gardamar komai ba kuwa Lubainu da sarauniya
Akisatul Sauwara suka hau wadannan dawakai
suka
bi bayan Sarki Darmanu suka fice daga cikin
birnin
gaba daya.Nan dai suka nausa cikin daji suka yi
ta
tafiya ba sassauci har suka shafe sa'a goma sha
biyu ba tare da sun hadu da wani mugun abu
ba.Duk wata muguwar dabba idan ta hangosu
daga
nesa sak kaga ta ratsa ta sauya hanya,haka ma
mugayen aljanu.Yan fashi kuwa da zarar sun
hango
Sarki Darmanu tare dasu Lubainu sai kaga sunyi
ta
kansu saboda sun san cewa Bakin Rijiya ba
wajen
wasan yaro bane.Adaidai wannan lokaci ne
magriba
ta riskesu kuma a sannan ne suka shigo farkon
dajin
da wadannan tsuntsaye na sarki Darmanu
suke.Da
shigarsu cikin dajin sai Sarki Darmanu ya daga
kansa sama yana mai karanta wadansu dalasimai
na
tsafi.Faruwar hakan keda wuya sai Lubainu da
Sarauniya Akisatul Sauwara suka ji wata irin iska
mai karfin daga sama ta fara kadawa.Kwatsam
sai ga
wadansu jibga jibgan tsuntsaye guda uku sun
bayyana suna masu saukowa kasa.Duk su ukun a
gaban sarki Darmanu suka sauka suna masu
dukar
da kawunansu alamar cewa sun kwashi
gaisuwa.Nan
take sarki Darmanu ya shafa kawunan wadannan
tsuntsaye yayi magana dasu a cikin yaren
tsafi.Faruwar hakan ke da wuya sai tsuntsayen
suka
bude fukafukansu suka sake tashi sama suka
luluka
a cikin gajimare har suka bace bat tamkar basu
taba
wanzuwa ba.A sannan ne Sarki Darmanu ya dubi
Yarima Lubainu da Sarauniya Akisatul Sauwara
yace,anan zamu yada zango mu dan huta nan da
cikar kamar sa'a uku wadannan tsuntsaye zasu
dawo su daukemu mu ci gaba da tafiya.Nan take
suka kafa tanti suka fidda abincinsu na guzuri
suka
kama ci suna hira.kafin Yarima Lubainu yayi wani
abu da hannunsa tuni Sarauniya Akisatul
Sauwara ta
miko masa,ya zamana cewa tana kyautata
masa,bata son taga ya yi wani abu na wahala da
kansa face ta taimaka masa.Bayan sun gama cin
abincin ne Akisatul Sauwara ya mike tsaye ta
dubesu tace,tana son ta zagaya bayan wata
katuwar
bishiya dake can gabansu tayi bawali.Tana gama
fadin hakan sai ta juya ta nufi inda wannan
bishiyar
take.Tana isa kuwa ta zagaya bayan bishiyar ta
bace
musu da gani.A wannan lokaci ne Sarki Darmanu
ya
dubi Lubainu cikin murmushi yace,na fuskanci
cewar
Akisatul Sauwara ta kamu da matukar
sonka.Koda
jin haka sai mamaki ya kama Lubainu ya dubeshi
yace,wacce irin magana kake yi haka?Ai wannan
bayani naka daidai yake da tatsuniya a cikin
kunne
na,domin babu yadda za'a yi sarauniya Akisatul
Sauwara ta so ni saboda kwararan dalilai guda
uku.Dalili na farko shine a rayuwarta bata tabayin
soyayya ba don babu wani 'da namiji daya taba
burgeta.Dalili na biyu shine ta san cewa ni ba
cikakken namiji bane,kaga kuwa bazata so ta
auri
wanda baya haihuwa ba tazo ta rasa magaji.Dalili
na
uku shine ta fini kyau,ta fini mulki,kuma kasan su
mata sun fi son su auri wanda yafi su
komai.Koda
Yarima yazo nan a zancensa sai Sarki Darmanu
ya
bushe da dariya sannan dubi Lubainu cikin
nustuwa
yace,Lubainu kai saurayi ne matashi wanda har
yanzu yake daukar darasi a cikin karatun
duniya,sabanin magidancin mutum kamata wanda
yake da matan aure ashirin da hudu.Babu irin
soyayyar daban yi ba a rayuwata,dukkanin
alamomin
SO da KAUNA sun bayyana akan fuskar
Sarauniya
Akisatul Sauwara a gareka da kuma alamomin
kauna
a zahiri.Idan ma baka yarda da abinda nake gaya
maka ba yanzu nan gaba zaka gani a lokacin da
Kura takai bango.Ka bar ganin cewar tasan kana
da
mata a gida mai jiran ka koma gareta.Hakan ba
zai
hana taso ka ba saboda shi SO bashi da hijabi
kuma babu abinda yake iya tareshi idan har ya
yunkuro.Har Lubainu ya bude baki zaice wani
abu
sai ga Sarauniya Akisatul Sauwara ta dawo,don
haka
sai yai shiru baice komai ba yana ta nazarin
abinda
Sarki Darmanu ya gaya masa.Haka dai Akisatul
Sauwara tazo ta zauna tare dasu aka ci gaba da
hira,inda Akisatul Sauwara ta dubi Sarki Darmanu
tace,yanzu kai a ganinka ta yaya zamu jewa
boka
Darbusa?Shin zamuje masa ne cikin lumana da
nasiha ko kuwa zamuje masa ne ta tsiya tsiya?
Koda
jin wannan tambaya sai Sarki Darmanu yayi
murmushi cikin ajiyar zuciya sannan yace,ni ta
yaya
kuka zo mini keda Lubainu?Sarauniya Akisatul
Sauwara tace ai kai baka bari mun iso fadarka ba
tun a daji ka taremu kana mai badda kama kazo
mana a siffar tsoho don ka yaudaremu ka cutar
damu.Dajin haka sai Sarki Darmanu yayi dariya
kuma ya hade fuska yace,to kiyi zaton yaudara
da
tarkon tuggu ninki wanda nayi muku daga Boka
Darbusa tunda kin san cewa ya ninka ni sau dari
A
komai.Koda jin wannan batu sai hankalin
Sarauniya
Akisatul Sauwara dana Yarima Lubainu ya tashi
domin sun fuskanci cewar hadarin dake gabansu
na
fuskantar Boka Darbusa ba kadan bane.Kodai su
sha
wahala ko kuma su rasa rayuwarsu gaba
daya.Haka
dai suka ci gaba da hira har lokaci ya cika sai ga
wadannan manyan tsuntsaye guda uku na Sarki
Darmanu sun dawo suna masu saukowa kasa
daga
can kololuwar sama.Cikin gaggawa su ukun suka
mike tsaye suka hada nasu i nasu
su,kowannensu
ya hau kan tsuntsu guda.Sarki Darmanu ne akan
gaba,Sarauniya Akisatul Sauwara a tsakiya
sannan
Yarima Lubainu.Lokaci guda tsuntsayen uku suka
bude fuka fukansu suka tashi sama suka luluka
izuwa can sama suna masu giftwa ta gaban
Rana
wacce ke shirin faduwa ta zama ja jawur.Abin
gwanin ban sha'awa ga dukkan halittar da take
kallo
daga kasan Turba.Kamar yadda Sarki Darmanu
ya
fada haka al'amarin ya kasance wato saida suka
shafe kwana
hudu da yini daya suna tafiya a sararin samaniya
bisa
wadannan manyan tsuntsaye sannan suka hango
gidan boka
Darbusa a nesa kadan dasu.ALLON SIHIRI
Littafi na biyu(2)
Part F
Sannan suka hango Gidan Boka Darbusa a nesa
kadan dasu.Babban abinda ya baiwa Lubainu da
Sarauniya Akisatul Sauwara a cikin wannan tafiya
shine a tsawon duk kwanakin da akayi ko sau
daya
tsuntsayen dake dauke dasu basu gajiya ba,kuma
ba
a sauko kasa an yada zango ba.Haka kuma duk
su
ukun babu wanda wata bukata ta kamashi ta
bawali
ko bayan gari saidai kawai idan sun gaji da zama
akan tsuntsayen su kwanta suyita sharar barci
abinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da
fargabar
komai ba.Da yammaci ne sakaliya suka hango
wannan gida na Boka Darbusa wanda saidai a
kirashi da aljannar duniya saboda ginuwarsa da
kawatuwarsa.Tunda Yarima Lubainu yazo duniya
ko
a bakin masana tarihi bai taba jin labarin gida
mai
kyan na Boka Darbusa ba.Saidai babban abin
takaice shine a tsakiyar dokar daji aka zo aka
gina
wannan gida wanda aka bata miliyoyin dinare
wajen
ginashi.Kai da gani kasan cewa in ba rikakken
Boka
ba wanda ya cika hatsabibin gaske babu wanda
zai
iya gina irin wannan gida a dokar daji haka ya
zauna
a cikinsa.Da saukar tsuntsayen uku kusa da kofar
gidan da tazarar kamar taku ashirin sai kawai
suka
ga an bude kofar gidan wacce ta kasance
katuwar
gaske.Kofar na budewa sai sukaga wadansu
kyawawan kuyangi su goma sha biyu sun fito
daga
cikin gidan a jere a layi.Shida a hannun dama
ragowar shidan a hannun hagu.Dukkaninsu suna
dauke da wani dan karamin kwando wanda akayi
shi
da karfen jauhar.Kowanne gwando an cikashi da
wani irin jan fure mai tsananin kamshi.Gaba
dayan
wadannan kuyangin suna sanye ne da dogayen
riguna masu launin kore wadanda akayi su da
Miski.Babbar cikin kuyangin ce kadai take da riga
kala dabam mai ruwan kwai wacce akayi mata
dinki
mai siffar dawisu.Tsananin kyawun wannan
kuyanga
gami da kyawun shigar datayi dole ne ya rudi
kowanne lafiyayyen 'da namiji.Cikin tafiyar
kasaita
da karairaya tamkar macijin gona haka wannan
kuyanga da sauran yan uwanta suka iso daf da
su
sarki Darmanu suka risina sukayi gaisuwa gami
da
yimusu barkda da zuwa.A sannan ne shugabar
kuyangin ta dago kai ta dubi su Lubainu tace lale
marhaban da manyan baki na musamma,lallai
mai
girma Darbusa yana farin ciki da zuwanku kuma
yace nayi muku jagora izuwa cikin fadarsa.Koda
jin
wannan batu sai Sarki Darmanu,Sarauniya
Akisatul
Sauwara da Yarima Lubainu suka sauki daha kan
wadannan tsuntsayen.Suna sauka sai tsuntsayen
suka sake bude fuka fukansu suka tashi
sama.Kafin
kiftwar ido sun kule a cikin sararin
samaniya.Koda
ganin haka sai mamaki ya kama Lubainu da
Akisatul
Sauwara suke a cikin zuciyarsu,Wai shin su
wadannan tsuntsaue wane iri nesu?Gashi sunyi
tafiyar kwanda hudu da yini daya basu yada
zango
ba,kuma da saukarsu yanzun nan sun sake tashi
sama ko hutawa basuyi ba bare su nemi ruwan
sha
ko abinci.Anya kuwa wadannan tsuntsaye ba
sihirtattu bane?.Amsar da suka kasa baiwa
kansu
kenan.Ba tare da fargabar komai ba kuwa su
Sarki
Darmanu suka bi wannan shugabar kuyangin a
baya
suka nufi cikin gidan.Su kuwa sauran kuyangin
tuni
suna kan gaba suna zubar da wannan Jan fure
mai
kamshi a kasa su Lubainu na bi ta kansa.Da
shigarsu cikin gidan sai duk su ukun suka kama
kalle kalle da waige waige domin sun zama
cikakkun
yan kauye duk da cewar dukkaninsu sarakai ne
masu tarin abin duniya.Ba komai ne yasa suka
zama yan kauye ba face ganin kayan kawar da
idanunsu basu taba gani ba da abubuwan al'ajibi
wanda ko a mafarki da hasashe basu taba zaton
wanzuwarsu ba.A cikin wannan gida ne suka ga
wani katon Lambu wanda girmansa yafi na wani
dan
karamin garin kuma kyawawan bishiyoyin dake
cikinsa da furanni tamkar halittarsu akayi a ciki
ba
shukasu akayi ba sai kayi zaton idan kayi musu
magana zasu amsa.Barewa,tsuntsaye da kwaron
nan mai suna malan buda mana littafi kuwa gasu
nan birjik a cikin Lambun kala kala,launi launi
bazasu kirgu ba.Kai idan mutum yana kallon
wadannan Lambu da abubuwan dake cikinsa sai
ya
manta da duk wani bakin cikin duniya kuma sai
yaji
kamar shine sarkin duniyar gaba daya saboda
farin
ciki.Saida akayi tafiya dasu kusan ta rabin sa'a
sannan aka iso dasu fadar Boka
Darbusa.Wangamemiyar fada ce wadda girmanta
yakai a sanya gidan sarautar Sarauniya Akisatul
Sauwara guda uku a ciki.Wannan karon sai da su
Lubainu suka rinka yin tuntube suna faduwa kasa
saboda kalle kalle da waige waige bisa ganin
kayan
kawar da yafi wanda suka gani a baya,amma
kuma
duk wannan kawa sai ta zama ta banza domin
kuwa
ba karamar razana da firgita sukayi ba
sakamakon
ganin irin fadawan da suke cikin fadar.Babu
bil'adama ko guda daya a cikin dubbun fadawan
Boka Darbusa face wadansu irin halittu wadanda
mutum bazai iya tantancewa ba yace Aljanu ne
ko
Dodonni.Wasun su rabin jikinsu na mutum ne rabi
na Aljan,wasu rabi dabbobi,rabi dodanni,wasu
kuwa
rabinsu na Aljan ne da wuta.Sun ksance manya
manya,girda girda saidai a kwatanta girmansu da
siffofin maridai ko mutanen farko.Dukkaninsu
suna
da matukar muni,kwarjini da ban tsoro,kuma suna
dauke da mugayen makaman yaki iri iri
barkatai.Wani kalar makamin ma ko a tarihi
mutum
bai taba kin irinsa ba.Wadannan dakaru sun cika
fadar gaba dayanta sai yar siririyar hanua suka
bari
a tsakiyar fadar wacce fadinta bai wuce kamu
uku
ba,kuma itace hanyar dazata kai mutum har
izuwa
inda karagar mulkin Boka Darbusa take.Koda
Boka
Darbusa ya kyallara ido yaga kuyanginsa sun
shigo
cikin fadar tare dasu Sarki Darmanu sai ya mike
tsaye daga kan karagar cikin tsananin farin ciki
ya
bushe da mahaukaciyar dariya yayita dariyar
kamar
wanda aka bashi komai na duniya.Al'amarin daya
kara razana
su Yarima Lubainu kenan sukaji a jikinsu cewar
lallai
Boka Darbusa yaudarsu yayi daya turo aka
karbesu
hannu biyu,lallai yunkurin cutar dasu zaiyi
yanzu.Bayan Boka Darbusa yayi dariyar mugunta
har
ta ishe shi sai ya murtuke fuskarsa a lokacin da
wadannan kyawawan kuyangi goma sha biyu
suka
rikide suka zama aljanun haske rike da zabga
zabgan takubba kuma suka yiwa su Yarima
Lubainu
kawanya.Koda ganin haka sai Sarki
Darmanu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima
Lubainu ma suka zare takubbansu suka jingina
da
bayansu su ukun suna jiran suga ta inda za a
kawo
musu hari.Koda gani haka sai Boka Darbusa ya
sake
bushewa da dariyar mugunta karo na biyu sannan
ya dubi su Yarima Lubainu yace,kunyi hauka
kuma
kunyi babban kuskure harda kuke yin tunanin
cewa
zakuzi wajena neman Allon Sihiri na kuma na
baku
alhalin yau sama da shekara bakwai kenan ina
son
ku kawo kanku nan fadata kun ki.Ai abinda kuka
fada gaskiya ne cewar kowa a gidansa sarki
ne.Ina
mai tabbatar muku da cewa tunda har kuka shigo
nan cikin fadata to tabbas babu dayanku dazai
fita
daga nan a raye,kuma shi kun shigo dauke da
Allunan Sihiri guda biyu.Ku sani cewa tuni nayi
bincike na gano hanyar dazan iya cire Allunan
Sihirinku daga cikin kwalaben Sihirin da kuka
sasu.Ina cirosu zan hada su da nawa.Hakan na
faruwa shike na na zama SARKIN DUNIYAr nan
gaba
daya.Duk wata halitta dake bisa doron kasa
walau
mutum ko aljan,dabba,tsunstu ko kwaro sai ya
dawo
karkashin mulkina da ikona.Yanzu zan barku da
wadannan Aljanun haske da suka yi muku
kawanya
na ga iyakar shirin ku dakuke dashi don karbar
Allon Sihirina.Koda gama fadin haka sai Boka
Darbusa ya yiwa Aljanun izinin su hallaka su
Darmanu.Nan take kuwa Aljanun suka afka musu
aka ruguntsume da azababben yaki ya zamana
cewa
Aljanun suna kai musu sara da suka cikin
tsananin
zafin nama dabasu taba gani ba.Duk sa'adda
takobin Aljanun ta hadu da tasu saidai kaga
tarwatsin wuta na tashi kuma takobin Lubainu
data
Akisatul Sauwara suka rinka dakushewa,ta Sarki
Darmanu ce kawai batayi komai ba.Haka kuma
duk
sa'adda su Lubainu suka sami nasarar sara ko
sukar jikin Aljanun saidai suji kamar iska suka
soka.Bugu da kari da kyar su Lubainu suke iya
tare
harin Aljanun saboda karfin saransu,jinsa suke
kamar katon dutse ake bugawa a kan takubbansu
wanda sai kato arba"in sun tare zasu iya
daukarsa.A
duk sa'adda takobin Aljanun ta shafi jikinsu
Lubainu
koda kuwa dan lakatarsu tayi saidai kaji sun
kwalla
ihi saboda tsananin zafi da zogon da suka ji,a
lokacin da jini je tsartuwa gami da feshi daga
jikin
nasu.Koda Boka Darbusa yaga yana samun
wannan
gagarumar nasara saiya cigaba da kyalkyalewa
da
dariyar mugunta saboda ya tabbatar da cewar
hakansa ya kusa cimma ruwa.Al'amarin su
Yarima
Lubainu kuwa suna wannan yaki ne cikin nadama
da
takaici domin sun gane cewa lallau tsautsayi ne
yasa
suka biyo Boka Darbusa har gidansa domin
karbar
Allon Sihiri.Banda Tsautsayi kuma zasu iya cewa
Ajali ne ya kirasu,domin sun san cewa babu wata
dabara dazasu iya yi a yanzu su ceci rayuwarsu
daga hannun wadannan Aljanu na haske.
SHIN SU YARIMA LUBAINU ZASU KUBUTA DAGA
HANNUN WADANNAN MUGAYEN ALJANU NA
BOKA
DARBUSA HAR SU KARFI ALLON SIHIRIN
HANNUNSA?
IDAN HAR HAKAN TA KASANCE YAUSHE NE
ZASU
ISA KOGON BAHAR IMFAL YARIMA LUBAINU YA
SAMO MAGANIN DA YA FITO NEMA?
YAYA SOYAYYAR SARAUNIYA AKISATUL
SAUWARA
DA YARIMA LUBAINU ZATA KASANCE?SHIN
ZATA
BAYYANA MASA SIRRIN ZUCIYARTA NE KUMA
YAYA
ZAI KARBI TAYIN NATA?
A WANE HALI YAZARINA TAKE YANZU A CAN
BIRNIN
ZAMRAL BISA BAKIN CIKIN RABUWA DA
MASOYINTA
YARIMA LUBAINU?
INA LABARIN YARIMA MANGUL DA MAHAIFINSA
SARKI ALKAS WADANDA SUKA KOMA CAN
BIRNINSU A CIKIN BAKIN CIKI NA SABANI?
SHIN YARIMA MANGUL ZAI CIRE SON YAZARINA
DAGA CIKIN ZUCIYARSA GABA DAYA A
MATSAYINSA
NA WANDA YA ZAMO MASAKI MAI HANNU
DAYA?
WANE MATAKI ZAI DAUKA AKAN MAHAIFINSA
SARKI
ALKASA WANDA YACE YA CIRESHI DAGA
SAHUN
'YA'YANSA?SHIN YANA TUNANIN DAUKAR
FANSA NE
AKAN YARIMA LUBAINU KO KUWA YA RUNGUMI
KADDARA?
YAUSHE NE YARIMA LUBAINU ZAI DAWO
BIRNIN
ZAMRAL HAR YA SAKE SADUWA DA
MASOYIYARSA
YAZARINA 'YAR BABBAN ATTAJIRI NA
NAHIYAR?
Mu hadu a littafin ALLON SIHIRI 3(kashi Na Uku)
don
jin ci gaban wannan kayataccen Kasaitaccen
Labari.
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__ALLON SIHIRI
Littafi na uku (3)
Part AAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

__
LOKACIN da wadannan ALJANU na HASKE keta
saran
jikin su YARIMA LUBAINU,JINI na tsartuwa da
feshi,shi kuma BOKA DARBUSA nata fama rusa
dariyar
mugunta da farin ciki,sai gaba dayansu su
ukun suka zube kasa saboda jira sakamakon jinin
dake zuba a jikinsu.Har mugayen fadawan na
Boka
Darbusa sun yunkura zasu karasa kashesu suyi
musu KISAN GILLAH sai ga wani babban HADIMI
na
boka Darbusa ya shigo cikin fadar a firgice kuma
a guje har
yana tuntube,kuma yana mai kwallawa
boka
Darbusa kira.Al'amarin daya janyo hanakakin
Boka
Darbusa kenan da mugayen fadawan nasa suka
juya
izuwa kan hadimin suka kura masa idanu.Da
isowar Hadimin
sai ya zube kasa a gaban boka Darbusa
yana haki kamar ransa zai fita,sai da
numfashinsa ya
dan dawo daidai sannnan ya iya budar baki
yace,ya
shugabana ga wani takadirin MAHAYI can ya
durfafo
wannan gida naka bisa wani BAKIN DOKI kuma
sanye da FARAREN TUFAFI,ya rufe jikinsa da
fuskarsa gaba
daya,kuma yana rataye da wata
zabgegiyar TAKOBI a bayansa.Koda jin wannan
batu
sai mamaki ya turnuke Boka Darbusa,saboda a
iya
zamansa a cikin wannan DAJI babu wani
mahaluki
walau MUTUM ko ALJAN daya taba durfafo
hanyar
wannan gida nasa da tsawon kwanaki uku kafin
isowarsa ba
tare da ya sani ba,koma yasan ko wane
ne,da kuma dalilin zuwansa,sai a wannan
karon.Cikin alamun tsananin fushi da kaduwa
boka
Darbusa ya dubi wadannan fadawan nasa wato
Aljanu na haske yace ku biyo ni a baya muje mu
hallaka wannan shaidanin bil'adama daya
tunkaromu,domin
koma wane shi nasan cewa
MAKIYINmu ne.Koda gama fadin hakan sai Boka
Darbusa ya zare takobinsa take wadansu
bakaken
DAWAKAN TSAFI na haske suka baiyana a
gabansa.Kawai sai shida mugayen fadawan nasa
suka haye dawakan.Cikin gaggawa wannan
babban hadimin ya
dubi Boka Darbusa yace,ya shugabana
yanzu ya zamuyi da wadannan ABOKAN GABA
namu
su uku?Koda jin wannan tambaya sai Boka
Darbusa
ya dubi su Jarumi Lubainu wadanda ke kwance
cikin
jini,kuma rai a hannun Allah,ya bushe da dariyar
mugunta yace,ai wannan gawa ce kawai taki
rami,nan da dan
kankanin lokaci duk zasu zama
gawa tunda babu wanda zai kawo musu dauki a
cikin halin da suke ciki sakamakon wannan jini
dake
zuba a jikinsu babu wanda zai tsira da rayuwarsa
a
cikinsu.Koda gama fadin hakan sai Boka Darbusa
da
wadannan mugayen aljanu nasa sa dawakan da
suke
kai duk suka bace bat!daga cikin fadar.
Bacewarsu
keda wuya sai wanann babban hadimi na boka
Darbusa ya dubi su SARAUNIYA AKISATUL
SAUWARA ya bushe da dariyar mugunta
yace,yanzu
ku in banda wauta irin taku wane tsautsayi ne
zaisa kuyi
gangancin zuwa nan gidan domin ku dauki
ALLON SIHIRIN shugabana?
Tabbas biyu babu zakuui
yanzu babu biyan bukata kuma babu
rayuwarku.Koda jin wannan batu sai sarauniya
Akisatul Sauwara ta dubi hadimin cikin karfin
haki
tace ina farin cikin zan mutu a matsayun jarumar
data sami
nasarar shigowa har nan cikin fadar
shugabanka,kuma nayi yaki da dakarunsa,amma
ina
da wata alfarma guda daya da nake son kayi min
ita
bayan mutuwata.Ka taimaka ka matso kusa na
rada
maka wannan alfarma saboda bana son kowa
yaji.Koda sarauniya Akisatul Sauwara tazo nan a
zancenta sai
hadimin ya sake bushewa da dariyar
mugunta a karo na biyu sannan ya matso kusa
da
sarauniya Akisatul Sauwara ya tsugunna a daidai
fuskarta domin tayi masa rada a
kunnensa.Sarauniya Akisatul Sauwara ta yunkura
kamar zata gaya masa magana a kunnesa sai ta
shammaceshi
cikin bakin zafin nama ta zaro
sharbebiyar wuka a kugunsa ta cala masa ita a
KAHON ZUCIYA!!!Nan take hadimin ya kurma
uban
ihu a lokacin da jini yai feshi ta cikin kirjinsa ya
sulale kasa matacce.Koda ganin abinda ya faru
sai
ragowar dakarun dake cikin fadar suka rugo da
gudu
izuwa kan sarauniya Akisatul Sauwara,kawai sai
gani
akayi ta mike zumbur!ta yagi rigar jikinta ta
daure
babban raunin dake kan cinyarta sanna ta daka
tsalle can gefe daya izuwa inda takobinta take ta
sureta ta
sake daka tsalle sama ta dira a tsakiyar
dakarun ta hausu da SARA DA SUKA.Nan da nan
kuwa ta rinka ragargazarsu tana zubar dasu kasa
matattu.
Koda Sarki Darmanu da Yarima Lubainu
sukaga irin jarimtakar da Sarauniya Akisatul
Sauwara takeyi sai suma suka yunkura cikin
tsananin juriya
suka kama daure raunikan jikinsu
suka mike tsaye suka kaiwa sarauniya Akisatul
Sauwara Dauki aka sake ruguntsumewa da sabon
masifaffen yaki.
A¤A¤¤H¤A¤D¤A¤H¤A¤D¤A
A CAN WAJEN gidan boka Darbusa kuwa lokacin
da wannan
BAQON JARUMI ya durfafo kofar gidan sai
yaja linzamin dokinsa ya tsaye cak,sakamakon
ganin
Boka Darbusa da mukarrabansa.Nan da aka
tsaya
ana kallon kallo tsakanin Boka Darbusa da Bakon
jarumin.
Daga can sai Boka Darbusa ya budi baki
yace yakai bakon jarumi wane ne kai,kuma
menene ya kawoka
wannan daji harka durfafo wannan gida
nawa?
Koda jin wannan tambaya sai Bakon Jarumin
yayi shiru baice komai ba,kawai sai ya sauko
daga
kan dokinsa ya zare takobinsa daga cikin
kufe.Koda
ganin haka sai Dakarun Boka Darbusa ma suka
zare
nasu Takubban saboda a zatonsu yakarsu zaiyi.
Kawai sai sukaga ya kama zane akan kasa da
tsinin takobinsa ya rubuta KALMAR
SHAHADA,gami
da bayanin cewa yazo ne ya yada ADDININ
MUSULUNCI a wannan nahiya.Koda ganin hakan
sai
Boka Darbusa ya fusata ainun ya dakawa bakon
jarumin tsawaya yace kai kurmane da bazaka
budi baki kayi
magana ba,kuma mummunar fuska
gareka da harda kake boyeta?
Koda jin wannan
tambaya sai bakon jarumin ya tafa hannunsa sau
uku,faruwar hakan keda wuya sai ga wani dan
guntun mutum ya fito daga cikin daji da gudun
tsiya
tamkar tashi sama yakeyi.
Karfin gudun nasa ya cika abin al'ajabi.Da zu
wan wannan dan wada gaban bakon jarumin sai
ya
risina yayi gaisuwa yace me kake da bukata?
Take bakon jarumin yayi masa magana cikin
yaren
kurame,wato da hannu yayi masa magana.Nan
take
dan wadan ya fahimta sannan yajuya ga Boka
Darbusa yace,ni
Sunana DAZYAN kum na kasance
bawa ga wannan bakon jarumi dake gabanku!
Ku sani cewa maigidana ba kurma bane,kuma
yana
boye muryarsa da fuskarsa ne saboda wani sirri
da
ba lallai bane ba ku sanshi,amma dai kamar
yadda
yayi muki bayani mu baki ne daga wata nahiya
daban,kuma
munzo ne domin mu gabatar muku da
addininmu wanda ake kira da ADDININ
MUSULUNCI!
kuma shine ADDININ GASKIYA.Addinin daku ke
kansa na BAUTAR GUMAKA gami da ALJANU da
TSAFI duk shirka ne kuma bata ne mabayyani!!
Koda dan wada yazo nan a zancensa sai Boka
Darbusa ya tari
numfashinsa yana mai daka masa
tsawa ya dubeshi cikin alamun tsananin fushi
yace
tabbas kai da maigidan naka kun cika
wawaye,kuma
marasa hankali da tunani harda kuke tunanin
cewa
zaku zo mana da SABON ADDINI kuma mu
karbeshi alhalin
mun saba da addininmi tun IYAYE da
KAKANNI!!!
Tabbas kun kawo kanku GIDAN
MUTUWA,kuma bama ku ba hatta ire irenku ma
sai
sunyi nadamar zuwa wannan nahiya tamu,kuma
yanzun nan zansa a yi muku kisan wulakanci irin
wanda ko a tarihi ba'a taba yin kamarsa ba a ko
ina a cikin
wannan duniya.Koda gama fadin hakan sai
Boka Darbusa ya dubi wadannan Aljanun haske
dake
kewaye dashi yayi musu wata inkiya.Nan take su
duka suka sakarwa dawakansu linzami suka
zaburesu da gudu izuwa kan Dazyan da
maigidansa bakon
jarumi.Koda Dazyan ya hangosu sun yiyo
kansu sai ya daka tsalle sama ya dane kan wani
bishiya mai tsawon gaske yana mai motsa
bakinsa
alamar cewa yana karanta wata addu'a ne ta
neman
tsari.Shi kuwa maigidan nasa bakon Jarumi sai
ya
daka tsalle sama ya haye kan dokin nasa tamkar
daukarsa kayi
aka ajiyeshi akan dokin sannan ya
daga takobinsa sama yana mai kwallah
KABBARA ya
tunkari aljanun.Ai kuwa tun kafin ma su hadu
aljanun hasken da dawakan nasu suka firgice
suka
razana ainun saboda tasirin wannan kabbara da
bakon jarumin yayi.Ai kuwa suna haduwa aka
ruguntsume da
AZABABBEN YAKI mai tsananin tayar
da hankali,sai gashi bakon jarumin yana tsarge
wadannan aljanun haske da dawakan nasu suna
zubewa kasa matattu sun kamawa da wuta su
kone
kurmus,saidai kaga iska na diban tokarsu.Koda
Boka Darbusa yaga yadda Bakon Jarumin yake yi
masa
mummunar barna sai ya fusata ainun kuma
yasha
JININ JIKINsa ya tabbatar da cewar lallai
wannan
bakon jarumi ba kanwar lasa bane,tsafi bazaiyi
tasiri
akan sa ba.Amma da yake Boka Darbusa ya
yarda
da kansa akan jarumtakarsa da KARFIN DANTSE
Sai kawai
shima ya zare takobinsa kuma ya sauko daga
kan tsafaffen dokin nasa take dokin ya bace bat!
shi kuma sai ya falfala da gudu izuwa kan bakon
jarumin.Koda ya rage baifi saura taku goma ba
tsakaninsu sai Boka Darbusa ya daka tsalle sama
tamkar an cillashi daga cikin Baka ya kaiwa
bakon jarumin
mummunan sara a wuya da nufin ya cisge
masa kai.Cikin tsananin bakin zafin nama Bakon
Jarumin ya daga tasa takobin ya kare
saran,amma
saboda karfin saran saida ya kusan tuje rawanin
bakon jarumin.koda ganin haka sai bakon jarumin
ya fusata ainun kawai sai shima ya daka tsalle ta
baya akan
dokin yayi wata irin alkafira ta ban
al'ajabi.Hatta wannan dan wada nasa wato
Dazyan
daya buya a can sama bishiya bai san sa'adda
yayi
masa tafi ba saboda ganin irin wannan
gagarumar
BAJINTA da yayi.
Bakon jarumin ba sama shima ya
maida martanin saran da Boka Darbusa ya kawo
masa
adazu.Sai gashi shi nasa saran ma yafi na
Boka Darbusa nauyi da karfi,don har saida Boka
Darbusa ya durkushe kasa bisa gwiwarsa guda
kuma
sai da kaifin takobin ta farka rigar Boka
Darbusa.Al'amarin dayasa Boka Darbusa yayi wuf
ya mike
tsaye kenan yana mai gyara tsayuwa yana
mamki saboda tunda yake GUMURZU da
MANYAN
MAZAJE bai taba haduwa da mai karfin damtse
da
iya yaki kamar wannan bakon jarumi ba.Saidai
wani
abu ya jefashi cikin wasi wasi ba komai bane ya
jefashi cikin wasi wasin va face duk sa'adda ya
dubi wannan
bako jarumin sai yaga surar jikinsa tana
kama data MATA,amma kuma idan yayi la'akari
da
irin zafin namansa da kuma KARFIN DAMTSENsa
sai
yaga cewa babu yadda za'ayi ya kasance 'YA
MACE.Nan take Boka Darbusa ya aiyana a cikin
ransa cewa duk yadda zaiyi sai yaga fuskar
wannan bakon
jarumi ko da kuwa bazai sami nasarar
hallakashi ba.Bayan anyi kallon kallo na tsawon
yan
dakiku tsakanin Boka Darbusa da Bakon Jarumin
sai
suka rugo da gudu a lokaci guda izuwa kan
juna,suna haduwa kuwa suka ruguntsume da
azababben yaki na gaban kwatance ya zamana
cewa
suna kaiwa junansu sara da suka cikin zafin
nama,juriya da jarumtaka.
Saidai suka shafe kusan
rabin sa'a suna wannan BAKIN ARTABU ba tare
da
dayansu ya sami nasara ba.
Koda bakon jarumin
yaga Boka Darbusa na neman bata masa lokaci
sai ya sauya
salon fada ya hada da kai naushi da bugu
ta ko ina kuma yana tsalle tsalle da kwance
kwance.Ai kuwa nan da nan ya rikirkita Boka
Darbusa har ya sami nasarar gabza masa
mugayen
naushi guda uku a fuska.take Hancin Boka
Darbusa
da bakinsa suka kama yoyon jini,kuma idanunsa
suka kumbura
sukayi suntum!Haka suka ci gaba da
kwabsa wannan masifaffen yaki mai tsananin
muni
da tayar da hankali a tsakaninsu,tun Boka
Darbusa
yana iya kare naushi da bugun da bakon jarumin
yake kawo masa har ya gaza balle ya samu
damar
mayar da martani.
Ana cikin hakane bakon jarumin ya shammaci
Boka Darbusa ya
daka tsalle masa ya
doki fuskarsa da kafa.Saboda karfin dukan saida
Boka Darbusa yayi katantanwa sau uku a tsaye
kuma
take hakorinsa guda na sama ya
yi fitar burgu daga cikin bakinsa tare da Wani
GUDAN
JINI,saboda tsanani zafi da zogin dayaji
saida yaga taurarin wuya a cikin idanunsa a
lokacin
daya kife kasa,kuma yaji kansa ya kara girma
yana
neman rinjayar gangar jikinsa.
Koda Boka Darbusa
ya
tabbatar da cewar wannan bakon jarumi ya fishi
karfin damtse
nesa ba kusa ba,kuma yafi shi iya
yaki,sai ya mike tsaye zumbur,cikin matukar
karfin
hali da numa 'ki fadi,kamar cigaba zaiyi da
yaki,amma sai ya juya da baya ya falfala da gudu
izuwa cikin daji kamar dunduniyar kafarsa zata
tabo
keyarsa saboda karfin gudun.Koda ganin abinda
ya faru sai
dan wada Dazyan ya sauko daga kan
doguwar bishiyar da yake kai ya ruga izuwa
gaban
bakon jarumin ya shiga yi masa kirari yana
cewa,Ga
'ki gudu maganin sa gudu!!Ga mai dogaro da
Allah,dodon kafirai.Koda jin wannan kirari sai
bakon
jarumin ya dagawa Dazyan hannu yana mai yi
masa nuni da yai
shiru,kawai sai ya nufi cikin gidan Boka
Darbusa da sauri,shima Dazyan sai ya bishi da
sauri.
Nima ganin Boka Darbusa ya gudu,sannan Bakon
Jarumin ya nufi gidan Boka Darbusa yasa nima
nabi
bayansa.
Zan dakata anan dafatan yayi.
pls Like nd comments idan naga yamin Anjima
sainayimuku post din 3b
7 hrs · PublicALLON SIHIRI
Littafi na Uku (3)
Part B
A CAN FADAR Boka Darbusa kuwa bayan an
shafe
kusan rabin sa'a ana gumurzun yaki tsakanin su
Yarima Lubainu da dakarun dake cikin fadar,su
Lubainu nata samun nasara suna ta ragargazar
dakarun saida suka karar dasu gaba daya.A
lokacin
ne suka gaji likis don haka sai suka zube kasa
suna
haki da numfarfashi kamar ransu zai fita.Faruwar
hakan keda wuya sai suka ji takun sawaye da
yawa
daga can wasu bangarori na gidan da yawa ana
rugowa izuwa inda suke.Al'amarin dayai matukar
firgitasu kenan suke mimmike tsaye a
tsorace,kafin
suyi wani yunkuri sai ga wadansu samudawan
dakarun mutane masu kirar MUTANEN
FARKO,rike da
mugayen makamai suna ta tuttudowa cikin fadar
ta
gabas da yamma,kudu da arewa,su da yawa ba
adadi.Nan da nan suka yiwa su Yarima Lubainu
KAWANYA.Koda ganin haka sai Sarauniya
Akisatul
Sauwara ta yarda takobinta,ta dubi sarki
Darmanu da
Yarima Lubainu cikin alamun karayar zuciya
tace,ai
shike nan kuma tamu ta kare,domin babu yadda
zamu iya kare kanmu daga sharrin wadannan
dakaru
a wannan yanayi da muke ciki.Babu wani karfin
dantse ko na Sihiri dazai cecemu.A yanzu duk
burinmu ya rushe,kuma karshen rayuwarmu
yazo,saidai mu rungumi kaddara.Idan muka ce
zamu
yaki wadannan dakaru ma zamu bata karfinmu
ne a
banza ba tare da mun samu koda nasarar sisi a
kansu ba.Koda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo
nan
a zancenta sai jikin Yarima Lubainu dana Sarki
Darmanu yayi sanyi,take shima Sarki Darmanu ya
yarda takobin hannunsa,shima Yarima Lubainu
har
ya yunkura zai yarda takobinsa sai ya fasa yace
kai!
Aida dai na mutu RAGO gwara na mutu
JARUMI,tsakanin mutum da sa'a da rabo,mutuwa
ce
don haka dole ne na jarraba sa'ata.Yana gama
fadin
hakan sai ya daga takobinsa sama ya riketa da
hannu biyu.Koda ganin haka sai shugaban
dakarun
ya bushe da dariyar mugunta yace,kai yaro
hakika
ganganci ne ya kawoku nan gidan domin babu
abinda zaku samu face AJALINku.Koda gama
fadin
hakan sai shugaban dakarun ya daga hannunsa
sama ya bayar da inkiyar a afkawa su Yarima
Lubainu.Kafin daya daga cikin dakarun nasa yayi
wani yunkuri sai aka jiyo KABBARA ta cika fadar
gaba dya.Take kowa ya waiga baya izuwa inda
sautin kabbarar ya fito,kawai sai aka hango
BAQON
JARUMI rike da takobinsa ya falfalo da
azababben
gudu,tazarar dake tsakaninsa da wadannan
dubban
samudawan dakaru yakai taku ashirin amma
daua
daka tsalle guda daya sai gashi ya fado a
tsakiyarsu
ya hausu da sara da suka.Nanfa ya tarwatsasu
shi
kadai ya zame musu GUGUWAR ANNOBA.Da
zarar
sun yunkuro da nufin su yanyameshi sai kaga ya
tarwatsasu yana filfilawa a kasansu da samansu
tamkar katantanawa ake murza wa,kuma duk
inda
yakai sara guda sai dai kaga Mazaje sama da
arba'in sun zube kasa Matattu.Koda su Sarauniya
Akisatul Sauwara sukaga wannan gagarumar
jarumtaka ta ban al'ajabi wacce tafi gaban
hankalinsu da tunaninsu sai suka cika da
tsananin
mamaki suka zazzaro idanu suka zubawa
sarautar
Allah idanu kawai.Nanfa YAKI ya kara TSAMARI
ya
zamana cewa dakarun sun fusata ainun suna
dada
afkawa bakon jarumin ta ko ina da dukkan
karfinsu
suna kai masa sara da suka,duk da cewa
ragargazarsu bakon jarumin yake,JINI na feshi da
fantsama kuma sassan jikinsu na yawo a sama
yana
zubowa kasa suna ihu da kururuwa suna zubewa
kasa.Saida aka shafe sa'a biyu da rabi ana
wannan
mummunan azababben yaki daya daga cikin
dakarun
bai sami nasarar koda kwarzanar jikin bakon
jarumin ba,kuma basu ga ya gajiya ba.Cigaba
yake
da ragargazarsu kawai amma saboda tsananin
yawansu sai kaga kamar karuwa sukeyi.Duk
wannan
abu dake faruwa dan wada Dazyan ya shige
karkashin wani tebur ya buya yana morewa
idanunsa kallo,kuma yana karanta addu'ar neman
tsari don kada tsautsayi ya haushi domin shi a
rayuwarsa ko rike takobi bai taba yi ba bare ya
iya
yaki ko ya kare kansa.Haka dai aka cigaba da
wannan mugun azababben yaki har aka sake
shafe
wata sa'ar gudu,a sannan ne fa samudawan
dakarun
suka gane cewa SHAYI RUWA NE!Domin tuni
bakon
jarumin ya gama kashe kaso biyu cikin kaso
ukinsu.Wadanda basu mutu ba kuwa sun zama
nakasassu,wasu sun rasa kafafu,wasu
hannaye,aki
wasu ma sai kaga an zabtare rabin
kafadarsu,tsabar
taurin rai ne yasa basu mutu ba.Koda ragowar
samudawan dakarun suka tabbatar da cewar
lallai
bazasu iya kashe wannan takadirin jarumi
ba,kuma
indai aka cigaba da wannan yaki sai ya karar
dasu
gaba dayansu sai suka ciki wandunansu da iska
suka bar ragowar nakasassun a wajen.Nan take
fadar tayi tsit,tamkar babu wani mahaluki mai
numfashi a cikinta,kuma sai aka fara kallon kallo
tsakanin bakon jarumin dasu Yarima Lubainu.Shi
kuwa dan wada Dazyan ya fito daga inda yake
boye
ya tsaya a bayan bakon jarumin yana murmushi
gami da karkade kurar jikinsa sakamakon kurar
data
baibaye masa jiki saboda a lokacin da bakon
jarumin yake yaki da wadannan samudawan
dakaru,sun ragargaje duk wani abu mai amfani
dake
cikin fadar an tashi 'kura mai yawa.Bayna anyi
kallon kallo tsakanin bakon Jarumin dasu
Sarauniya
Akisatul Sauwara sai Sarauniya Akisatul Sauwara
ta
tako kafafunta ta matso kusa da bakon Jarumin
ta
dubeshi tace wanene kai kuma menene dalilin
dayasa ka ceci rayuwarmu?Koda jin wannan
tambaya sai bakon jarumin ya dubi Dazyan shi
kuma sai ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara ya
risina a gareta cikin alamun girmamawa
yace,yaku
wadannan jarumai guda uku,kuyi sani cewa
shugabana baya magana ba don ya kasance
kurma
ba,kuma ya rufe fuskarsa ba don bashi da kyau
ba,saboda wani babban sirri ne yasa yake aikata
hakan da fatan bazaku damu ba.Kuyi sani cewa
mu
baki ne daga wata nahiya dabam,kuma munzo
nan
nahiyar ne
domin mu gabatar muku da Addinmu wanda ake
kira
ADDININ MUSLUNCI!ADDININ MUSULUNCI shine
ADDININ GASKIYA,don haka duk wani addini da
kukeyi walau na BAUTAR GUMAKA ko RANA ko
WATA ko ALJANU duk bata ne mabayyani!!!Tsafi
shima shirka ne babba saboda haka muna kira
agareku daku tuba ku bar wadannan addinai naku
ku karbi namu.Ba komai ne yasa shugabana ya
ceci
rayuwarku ba face saboda ya fahimci cewa
wannan
Boka da kuke yaki dashi AZZALUMI ne kuma
mushriki.Shin yanzu zaku karbi wannan Addini
namu ne ko kuwa zaku bijire masa?Koda jin
wannan
batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima
Lubainu da Sarki Darmanu suka dubi junansu
sukayi
shiru aka rasa wanda zaice kala.Daga can sai
Sarauniya Akisatul Sauwara tayi gyaran murya
sannan ta dubi dan wada Dazyan tace,yakai
wannan
gutun mutum..."Koda jin haka sai Dazyan ya
turbune fuskarsa kuma ya tari numfashin
Sarauniya
Akisatul Sauwara yace ke yarinya kada kici min
fuska ko kiyi min rashin kunya.Ki sani cewa na
haifi
kamarki don haka bai kamata ki kirani da dan
guntu
ba!!!Koda jin haka sai Sarauniya Akisatuk
Sauwara ta
risina cikin biyayya tace,k gafarceni amma
bansan
sunan da yakamata na kiraka dashi bane.Dan
wada
Dazyan yace sunana na yanka shine DAZYAN!
Amma
ana kirana da ABUL YAZRIN.Sarauniya Akisatul
Sauwara tace,daga yau nayi alkawarin zan rinka
kiranka da Abul Yazrin don girmamawa.Ka
gayawa
mai gidanka cewa muna bukatar cikakkiyar hujja
wacce zata sa mu gamsu da cewa lallai wannan
addini dakukazo dashi shine ADDININ
GASKIYA.Baya
ga haka kuma muna bukatar muyi nazari da
shawara
domin mu sanar dakai abinda muke ganin zaisa
mu
sami nutsuwa da yarda akan wannan sabon
addini
naku.Koda jin wannna batu sai Bakon Jarumin ya
dubi Dazyan yayi masa zance da hannu.Dazyan
ya
dubi Sarauniya Akisatul Sauwara yace maigidana
yace yaki bayananku,kuma ya aminta da duk
uzurin
dakukazo dashi amma kuma yana son yasa abu
guda biyu a tare daku.Abu na farko da yake son
sani shine shin me ya kawo ku nan gidan har
yaki
ya barke tsakaninku da wannan Boka?Abu na
biyu
kuma shine yana son yasan iya tsawon lokacin
dazaku yanke shawara da kuma abinda kuke son
yayi muku wanda zaisa ku gamsu cewa addininsa
shine ADDININ GASKIYA?Ya ce na gargadeku
akan
cewa ku tabbatar da cewar duk abinda zaku fada
masa ku fadi iyakar gaskiya,in ba haka ba kuwa
bazai sake taimakonku ba kuma zaku iya zama
ABOKAN GABA a gareshi!!Kuma yace a sanar
daku
cewa har yanzu fa baku tsira daga sharrin
wannan
Boka ba,domin ba mutuwa yayi ba guduwa
yayi,babu mamaki ma yana nan a labe wani
wurin
yana fakonku.Koda Dazyan yazo nan a zancensa
sai
Hankalin Yarima Lubainu,Sarauniya Akisatul
Sauwara
da Sarki Darmanu ya dugunzuma ainun,sukayi
tsuru
tsuru suna kallon junansu suka kasa cewa
uffan.Kawai sai Sarauniya Akisatul Sauwara taja
su
izuwa can gefe daya inda su Bakon Jarumin basu
ji
abinda zasu tattauna ba.Cikin nutsuwa Sarauniya
Akisatul Sauwara ta dubi Sarki Darmanu da
Yarima
Lubainu tace me kuke ganin ya kamata muce da
wannan hatsabibin bakon jarumi?Kowannenmu ya
ga irin tsantsar jarumtakarsa ta ban
al'ajabi.Tabbas
idan muka yi kuskuren yi masa karya ko yaudara
zamu iya yin nadama.Koda jin wannan batu sai
Yarima Lubainu ya numfasa yace ai dama tun
kafin
na baro gida na dauki alkawaron cewa bazanyi
karya
ba,kuma bazanci amana ba,sannan zan zamo mai
cika alkawari saboda haka idan kun amince zan
wakilceku naje na yiwa wannan bakon Jarumi
bayanin komai bisa gaskiyar al'amarin kuma mu
nemi taimakonsa bisa hada wannan ALLON
SIHIRI
tunda a yanzu haka bamu san a inda Boka
Darbusa
ya boye nasa ALLON SIHRIN ba kuma bamu san
irin
tsaron da ya bashi ba bare har mu iya
daukoshi.To
amma fa akwai matsala guda daya,a tsakaninmu
mu
ukun nan babu wanda yasan abinda kowannenmu
ya
shirya a zuciyarsa.Babu mamaki bayan an hada
ALLON SIHIRI dayanmu ya shammaci sauran ya
cutar dasu ya gudu da ALLON SIHIRIN don cika
burinsa shi kadai tunda dole dai mutum daya ne
daga cikinmu zai iya cika burinsa a lokaci
guda,kuma dole sai yana tare da ALLON SIHIRI
zai
iya kammala sauran aikin cikia burin
nasa.Lokacin
da Yarima Lubainu yazo nan a zancensa sai
Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu
suka
dubi juna kowannensu yai shiru aka rasa wanda
zaice kala.Daga can sai Sarki Darmanu yace kai
yaro
ne tayaya zamu hadu da mutum a yau dinnan
rana
daya jal,kuma mu saki jikinmu dashi har mu gaya
masa sirrinmu?Shin baka tsoron cewa zai iya
cutar
damu ko kuma yayi amfani da sirrin namu sami
Damai-Akala?Kawai muyi amfani dashi wajen
cika
burinmu in yaso mu a tsakaninmu mu sasanta
yadda kowa zai amfana.Koda jin haka sai
Sarauniya
Akisatul Sauwara tayi murmushi tace tabbas
kazo
da shawara mafi alheri,shi kuwa Yarima Lubainu
sai
ransa ya baci ya dubesu su biyun yace,ni kam
daga
yanzu na fita daga cikinku domin bazan iya baku
yarda da amanata ba,tunda har zaku iya yin
karya
da yaudara,gwara na baiwa wannan bakon
jarumin
amincina saboda akwai alamun cewa zaifiku iya
rike
amanata.Koda gama fadin hakan sai Yarima
Lubainu
ya juya ya bar wajen su Sarki Darmanu ya nufi
inda
Bakon Jarumin da dan wada Dazyan ke
tsaye.Koda
ganin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta
ruga
izuwa gareshi tasha gabansa tace haba yakai
wannan dan Sarki,ka tuna irin halaccin danayi
maka
lokacin dakazo gareni bisa neman taimakona.Ka
tuna yadda na dauko ALLON SIHIRI NA kuma na
biyoka a cikin wannan tafiya mai hadarin gaske
don
kawai na taimake ka ka sami nasarar samo
lafiyar
jikinka ka koma ga matarka kuma masoyiyarka
YAZARINA?Idan ka tarwatsa mini nawa shirin
saboda
cikar burinka kaci amanata kuma ka nuna mini
cewa
kai
ba dan Halak bane!Koda Sarauniya Akisatul
Sauwara
tazo daidai nan a zancenta sai Jikin Yarima
Lubainu
yayi sanyi kuma hankalinsa ya dugunzuma har
idanunsa suka dan ciko da kwallah,amma daya
sake
tuno da nasihar da aka bashi kafin ya baro gida
ta
rike gaskiya,amana da alkawari sai ya dubi
sarauniya Akisatul Sauwara yace,kiyi hakuri akan
fadin gaskiay saidai kice naci amanarki.Yana
gama
fadin hakan ya tunkari bakon jarumin gadan
gadan
yana shirin ya isa daf dashi sai dan wada Dazyan
yai
sauri ya shiga tsakiyarsu ya dubeshi a fusace
yace,doka ta farko ba a kusantar maigidana don
yin
magana dashi.Na gaya muku cewa ba kurma
bane
ba,don haka ko daga nesa zaka iya fadin duk
abinda
kakeson fada masa.Koda jin haka sai Yarima
Lubainu yayi murmushi yace hakikanin gaskiya ni
neman magani ne ya fito dani daga kasarmu.Nan
take Yarima Lubainu ya kwashe labarinsa kaf ya
zayyane bai boye komai ba harda batun
soyayyarsa
da YAZARINA wacce ta haddasa gaba a
tsakaninsa
da abokinsa YARIMA MANGUL har sukayi gasar
neman aurenta ta hanyar yakar juna ya cirewa
Yarima Mangul hannun daya shi kuma yayi masa
asiri ya kashe masa Mazakuta.Yarima Lubainu ya
cigaba da bayani akan fitowar da yayi don neman
ALLON SIHIRI ya karantashi don ya gano inda
KOGIN
BAHAR IMFAL yake yaje cikinsa ya tsinko dan
itaciyar da zata warkar da wannan cuta tasa
domin
ya koma gida a matsayin Namiji lafiyayye yaci
gaba
da ZAMAN AURE da masoyiyarsa
YazarinaLokacin da
Yarima Lubainu yazo nan a labarinsa sai bakon
Jarumin da Dazyan suka ji sun kamu da tsananin
tausayinsa.Bakon Jarumin yayi shiru yana tunani
da
nazari izuwa tsawon dan dakiku kadan sannan ya
dubi Dazyan yayi masa zancen kurame.A Sannan
ne
Sarki Darmanu da sarauniya Akisatul Sauwara
suka
taho garesu da sauri domin suji abinda bakon
jarumin zaice.Dazyan yayi gyaran murya sannan
yace,yakai wannan dan sarki kayi sani cewa
shugabana yace inda zaka yi imani da
UBANGIJIN
MUSULUNCI ka karbi addininmu zaka iya samu
lafiyarka a rana guda a cikin dakika guda daya
ma jal
ka yankewa kanwa duk wahalar dake gabanka.To
amma ya fuskanci cewa zuciyarka da ta
wadannan
Abokan Gaba tana da rauni akan yin imani da
ubangijin musulunci saboda kun yarda da Addinin
iyayenku da kakanninku,kuma kuna gani kamar
addinin naku shine addinin gaskiya,saboda kuga
zahiri kuma ku gamsu cewar addinin musulunci
shine na gaskiya mafin inganci da daraja akan
naku,shugabana ya amince zai ci gaba dayin
wannan tafiya tare daku amma duk inda akaje zai
barku ku jarraba kafin sihirinku da na damtsenku
wajen ganin cewa kun kawar da kowacce irin
masifa
da aka riska sai bayan kun kasa sannan shi ya
kawar da masifar da taimakon ubangijin
musulunci,amma fa sai idan kun dauki alkawarin
cewar bayan anzo karshen tafiyar zakuyi imani
da
addinin musulunci,idan kuma baku yarda ba da
wannan sharadi ba,to zai cigaba da binku kawai
a
cikin wannan tafiya ya zaman dan kallo ba tare
daya
taimaka muku da komai ba.Koda Dazyan yazo
nan a
jawabinsa sai hankali Sarki Darmanu dana
Sarauniya
Akisatul Sauwara ya dugunzuma ainun fiye da ko
yaushe suka rasa abinda yake musu dadi a
duniya,shi kuwa Yarima Lubainu sai farin ciki ya
lullubeshi ya dubi bakon jarumin cikin murmushi
yace tabbas ni na yarda da wannan sharadi
naka.Koda jin hakan sai Bakon Jarumin yayi
maganar kurame ga Dazyan shi kuma Dazyan sai
ya
dubi Yarima Lubainu yace mai gidana yana
murna
dajin bayaninka.Dazyan ya juya ya dubi Sarki
Darmanu da Sarauniya Akisatul Sauwara
yace,maigidana yace ki kuma fa menene
ra'ayinku?
Cikin rawar murya da tuntuben harshe Sarauniya
Akisatul Sauwara tace babu matsala muma mun
amince da sharadin maigidanka to amma yanzu
yaza ayi akan batun ALLON SIHIRIN Boka
Darbusa
wanda mukazo nema a cikin gidansa?
pls Like nd comments
15 hrs · PublicALLON SIHIRI