← Book details Al'ajabin Masarauta 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 6

Sashe 4

Al'ajabin Masarauta 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ido danejo tazuba Mishi kawai tana kallonshi yayinda idon ke ƙara cikowa da ƙwallah...shikuwa Ameer jin kalaman ɗan uwan nashi yasa yadubeta kana yace "please ƙanwata inaga wannan Bashine pappin dakike magana akaiba kiyi haƙuri kije gida kinji zakiga pappinki acan yana jiranki amma wannan bashi bane, yaƙarasa zancen cikin rarrashi. Ita kuwa tunda taji saukar kalamanshi idonta suka ƙara zuba tamkar panpo, cikin kukanda keson kuɓuce mata tasaki hannayenshi wanda yaji tamkar lantarki ce tarikeshi amma yanzu tasakeshi sewani zutt,zutt yakeji acikin lallausan tafin hannuwan nashi. "Ni zakace akora my pappi ni HUSNAR KA? danejo ce fa? yau nikake kora? minayima dazafi Hakan? Ni pappi? Humm sabida kaga banada kowa danake raɓa naji sanyi sekai? Karka manta pappi kaine uwata, kaine ubana, kaine yayana, kaine ƙanena, kaine abokina, amma yau kaida kanka kake korana? Hum shikenan I'm going to all your life my pappi sedai zan zauna zaman tsimayen

"When you're call me
"when you're missing me😥
"When you're coming back to me my happiness
"When you're coming back to me my everything all my life,
I'll waiting for you any time my pappi. Tana gama faɗar Hakan tamiƙe tsaye tareda saka bayan hannunta tashare ƙwallar idonta, kana tajuya kawai tabar wurin.

Sukuwa gabaki ɗaya sunyi mutuwar zaune tunda tafara magana domin sam basuyi tunanin zataji abinda princes yaceba balle har ta iya maida Mishi amsa da turanci ba, hartabar wurin basu saniba, sunlula duniyar tunanin ya akayi ƴar fillo ta iya Turanci kuma ƴar cikin ruga Fulanin jeji? Amma ba wanda ze basu amsar wannan tambayar tasu Hakan yasa suka ƙara gaskatawa ransu Cewar gamo sukayi da aljana... firgigit Hakan Anwar yayi yana kallon inda take gurfane da zimmar yabata haƙuri amma seyaga wayam bakowa Hakan yasa gabanshi ƙara mugun faɗuwa cikin kaɗuwa yake faɗar "kai ameer taɓace fa Wlh ajanace innalillahi wa'innailaihiraji'un...arazane Ameer ɗinma yamiƙe tareda riƙo hannun yarima sameer daya koma tamkar wanda aka zarewa lakka ajiki yamiƙar dashi tareda janshi suka fara tafiya gun motocinsu sedai duk yadda Ameer yaso sutaka dasauri abin yaƙi samuwa domin yadda yake tafiyarshi yanzuma Hakan yakeyinta cikin izza da ƙasaita tamkar yadda yasaba yin abarshi ga dukkan alamu dai hakanne tafiyar take bawai yanayi bane sabida kuɗi ko mulkinsu ba... hakama su imam tuni sun mara musu baya...hakimi kan se haƙuri yake basu domin ya ɗauka sun fasayin aikinne tunda yaga Manager company gini yacika bujenshi da iska, aranshi kuwa se tsinewa wannan aljanar yarinyar yakeyi...sukuwa dogaransu nahangosu tafe sukayi saurin buɗe musu motar, suna isowa suka shiga hakama excout ɗinsu suka shiga cikin sauri aka tada motocin sukabar yanki baki ɗaya.

DANEJO

Tafiya kawai takeyi batamasan ina take jefa kafartaba wani irin ɗaci takejin zuciyarta namata wanda bata taɓa jin irinshiba,,,yau ta ɗanɗani baƙin cikin dabata taɓa tunanin samuba, wai itace pappinta zece akora wai besantaba wannan wacce irin ranace me muni tazo acikin rayuwarta? tabbas wannan abin yayi mata zafi bakuma dan bata taɓa fuskantar Hakan bane a'a kawai dai ɗanta riski hakanne a inda batayi tunaniba, domin koda mutanen duniya zasu mata Hakan bazataji zafiba, amma agun pappinta kam bazata iya juraba, Hakan taketa zancen zuci harta isa gida tafaɗa babuko sallama gabaki ɗaya a hargitse take kamar wata zararriya... innawuro naganinta tataso cikin bala'i tana faɗar "ke dan ubanki nizaki wulaƙanta, tunyoshe nake jiranki amma kikayi zamanki seyanzu zaki dawomin kuma hannu rabbana, tukkunna ma ina aikenda namiki? Ko kina nufin ƙin tsayawa kikayi ki ƙarbo kika dawomin Hakan hannu rabbana? Taƙarasa zancen tana zuwa inda danejo take tsaye....Ita kuwa sema yanzu da innawuro ta tambe aikenta tatuna, dan ɗaukin Ganin pappinta yasa tayasarda saƙon.

Cikin tsawa taji saukar muryar innawuro tana faɗar "wai badake nake maganaba kinwani shareni sekace wata sa'ar uwarki....ɗib tayi tare da haɗiye sauran kalamanta Ganin yadda danejo taɗago azabure tana watsa mata waƴannan idanuwan nata dasuka gama komawa abin tsoro sabida ɓacin rai wanda yanayinta yamaidata aljanar ƙarfi dayaji. Tsorontane yashiga innawuro lokaci ɗaya Hakan yasa tazuba mata ido kawai tana kallonta domin inda ada ne dasedai taji saukar ruwan duka tako'ina ajikinta amma yanzu kam tana shakku...iskace tafara kaɗawa tayi baya da sumar kan danejo tana kaɗata sama, Hakan yaƙara ta azzara sauyawar halittarta daga mutum zuwa siffar aljanu...dasauri innawuro tanufi ɗakinta tareda maida ƙyauren tarufe gam tana faɗar "aikin banza wannan yariya ko dangin ibilisai ni wuro inaganin jarabawar duniya mlm yaɗauko mana jaraba dabe ɗauko uwar aljanar nanba daba abinda zesa tazame muna fitina kataɓa ta kuma wani bala'in yabiyo baya, Hakan innawuro keta mitarta ita kaɗai acikin ɗakinta.

Danejo kuwa nasu ɗakin tashiga tareda zubewa akan katifarta tana rushewa da matsanancin kuka metaɓa zuciya, sam takasa danne abin aranta

Wani irin ɗaci ke taso mata azuciya, tarasa ina zata saka kanta, taɗauki tsawon lokaci tana kukan kafin taji ana shafa lallausar sumar kanta....dasauri taɗago tana kallonshi cikin mamaki domin tasan dudduniya mutun ɗaya kemata Hakan kuma sam batayi tunanin ganinshi ba yanzu..aiko sukayi ido huɗu dashi yana sakar mata lallausan murmushi wanda yaƙara fitoda asalin kyawun fuskarshi ga dimple ɗinshi duka biyu sun lotsa abinda ke bala'in ɗaukar hankalinta gareshi kenan...dasauri tajuye fuskarta tana turo baki gaba kawai taƙara rushewa da matsanancin kuka.
"Ya salam shine abinda pappi yafurta ahankali yaname dafe kanshi, kafin yariƙo hannunta cikin sigar rarrashi yake faɗar"please my husnah stop crying mana, sata kigayamin miyasaki kuka, yafaɗa cikin Cool voice ɗinshi sak irinna yarima sameer domin basuda banbanci ko ƙwayar zarra ne tsakaninsu daga murya har kamanni na fuska da jiki har yanayi komai nasu iri ɗaya ne. Hakan yasa danejo keyiwa yarima sameer kallon pappinta. Shiru tayi taƙi Magana kusan minti ukku, kana tabuɗe baki cikin muryar kuka take faɗar "nikatafi bayan ɗazu ka wulaƙantani kakoreni daga wurinka dan kawai kana tareda wayancan mutanen shine yanzu zakazo min, haba pappi miyasa zakamin Hakan dan Allah? Karka manta fa Kaine ummana yayana kuma malamina idan kagujeni yazanyi? Tafaɗa tana ƙara sakin wani sabon kukan me tsima zuciyar mesauraro.

Tunda tafara magana yake kallonta tamkar yasamu tv aranshi yana ayyana Cewar ta haɗu da princes Sameer ne kenan duk yadda akayi domin duk faɗin Afirca shine kawai keda kama dashi wanda za'a iya gani ayi tinanin shine, bece mata komaiba harta gama zancenta taɗora da kuka..hannunta kawai yariƙa tareda hura mata iskar bakinshi a ido domin bayaso wani daga cikin gidan yazo yaji abinda suke magana akai, aiko suka ɓace bat kafin su bayyana bakin wani ƙaton teku, buɗe idonta tayi taga inda suke, amma batace komaiba kuma bataji tsoroba kasan cewar sun saba irin wannan tafiyar da pappi, kusan minti 15 suna ahakan kafin yajiyo gareta cikin tausasa harshe yace

"My husnah kitsaya kinutsu ki saurareni kinjiko..kai kawai taɗaga Mishi amma batace komaiba...Hakan yasa yaci gabada faɗar"kiyi haƙuri abisa korarda yarima sameer m habibullah yayi Miki, domin banine na korekiba yarima sameer ne, Shima kuma ba'ason ranshi yakorekiba sedan kasan cewarshi yatsani mata suraɓeshine da irin halayyar Ameer M habibullah yakeda Ita sam baze korekiba sabida Hakan kidena fishi da pappinki kinjiko ƙanwata, yaƙarsa zancen cikin kwantarda kai yadda zata fahimta....amma ina tun lokacinda yace bashi bane yakoreta ƙwaƙwalwarta tadena gane komai, tunani kawai take aranta to bashi bane waye? Waye takeda kama irinta pappinta? tayaya mutun biyu zasu kasance iri ɗaya? Kodai su ɗin twins ne? To koma twins ne aikamarsu tayi yawa kuma miyasa shi batasanshi ba se pappi kawai? Miyasa kuma bayason mace taraɓeshi? Miyasa ze koreta bayan ita batasan ba pappinta bane? Kuma tayaya ma zata yadda ba pappi bane? Hakama tayaya zataƙi yadda bayan pappinta betaɓa mata ƙarya ba...duk acikin ranta take jerawa kanta waƴannan tambayoyin da batada amsarsu, sedai abinda batasaniba afili take zancen zucin nata kuma koda azuci tayi pappinta ze iya sanin abinda take saƙawa....muryarshi ce takatse mata tunani inda yake fadar "duka zaki samu amsoshin wannan tambayoyin naki my husnah sedai bayanzuba dasannu Zaki fahimci komai, abu biyu saki sani ayanzu sune na ɗaya muba ƴan biyu bane hasalima bajinsinmu ɗaya ba inafatar kinsan Hakan, Sena biyu zaki bawa zuciyarki nutsuwa da bani bane kika gani ɗazu sabida zankaiki har inda yake kiganshi amma bazan bari yagankiba kin yadda? Yaƙarsa zancen yana kallonta...kai kawai ta iya ɗagawa amma takasa cewa komaiba sabida mamaki da al'ajabi. Sunjima aruwin yanata rarrashinta kafin yasamu zuciyarta taɗan nutsu yamaidata gida.

MASARAUTAR MAHAR

Sedare lis suka dawo garin MAHAR sedai agajiye liƙis suka dawo domin daga Adamawa ko ina basu tsayaba se masarautarsu, motar data ɗauko imam ce kawai tatsaya taraba ta ajiye shi kana suka ƙaraso..suna fitowa daga cikin motocin kowanne pert ɗinsu yanufa domin dare yayi sosai, koda yashigo general parlor gidansu bakowa kuma duka ankashe fitilun parlor, Hakan yasa ya haura kawai pert ɗinshi batareda yanemi mammi ba, yana shiga tun a perlor yafara fatali da kayan jikinshi harya shiga bedroom ɗin ƙarasa cirewa kawai yayi yafaɗa bathroom yasakarwa kanshi ruwa tareda lumshe kyawawan idanuwanshi, sedai arazane yabuɗe su jin saukar sweet voice ɗin danejo inda take fadar "kaine uwata, kaine ubana, kaine yayana, kaine ƙanena, kaine abokina, amma yau kaida kanka kake korana daga gareka,

"when you're coming back to me my everything.
Wani irin mugun faɗuwa gabanshi yayi yana ƙara ganin kyakkyawar fuskarta me ɗaukar hankali a ƙwayar idonshi, "hasbinallah "innalillahi wa'innailaihiraji'un wannan wacce irin yarinya ce ? Yafaɗa asaman lips ɗinshi kafin yayi sauri yayi wankan shaf'shaf yafito, kayan bacci shi kawai yazura taredayin addu'a yakwanta, sedai baccin yaƙaura cewa idonshi sam muryarta kawai yakeji tana mishi gizo idan kuma yarufe idonshi ita yake gani, yaɓata tsawon lokaci ahakan yarasa abinda yake mishi daɗi daƙyar bacci ɓarawo ya ɗauke shi, sedai ko minti 40 beyi dayin baccinba yafarka arazane yana salati, saka makon danejo dayariƙa gani acikin baccin shi tana kuka kamar ranta ze fita akan korar daya saka ayimata ɗazu, cikin wani irin yanayi yadafe kanshi yana maimaita....!

Book ɗin AL'AJABI Paid book ne akan 1k kacal zaki iya tura kuɗinki ta wannan account ɗin 👉2276776261 sha'awanatu ƙasim UBA bank, kana kitura Shedar biyanki a wannan nomber 👉 07037092176 on whatsapp.

Autar alheri ✍️

🪐🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥🪐

🪐🐦‍🔥 *MASARAUTA*🐦‍🔥🪐

🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸

Dr Yasmeen Ahmad😚

Autar alheri ✍️

Al'ajabi, hummm
Chapter 4 · 0% Book details