← Book details Al'ajabin Masarauta 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 6

Sashe 1

Al'ajabin Masarauta 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥
🐦‍🔥🪐 *MASARAUTA*🪐🐦‍🔥

🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸

Dr Yasmeen Ahmad😚

Autar alheri ✍️

Al'ajabi, hummm

Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI.

ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃

Book 1

Page 11 & 12

"Shidai yana isa parlor yafara cire kayan jikinshi domin hakan al'adarshi take kafin yaƙaraso bedroom kaya kaɗan ne zasu rage ajikinshi sedai duk wannan halayyar tashi baya cire boxes ɗinshi acikin bedroom harseya shiga wanka domin yarima sameer mutunne me matuƙar kunya dajin nauyi yanzu haka ko bindiga zaki ɗora akanshi bazecemiki ga yadda asalin halittarshi takeba domin bedamu dayasan yatakeba shidai muradi yayi wanka yawanke wurin kawai sabida atunaninshi kallon tsoraicinshi rashin kunyane...hakan yaƙarasa bedroom ɗin yana shiga kuwa yafaɗa wanka sabida duk agajiye yakejin kanshi....sukuwa su ameer a parlor suka zaune suna tattauna yadda tafiyarsu zata kasance agobe.

MAYE BALWA

danejo tunranarda innawuro tasha duka bata karabi takanta ba, sedai takan sakata aikin wahala wanda yafi ƙarfinta hakama bata bata'abincin daze wadaceta, kuma bata bari takwanta dawuri se salamainin dare, amma dai bata ƙara gigin dukantaba,,,sekuma abinda kebata mamaki akan danejon, bewuce yadda take ganin duk aikin data sakata bazata wuce minti ashirin ba ko talatin takama, wanda ko babbar mace ce zatayishi seta ɓata fiyeda awa biyar bata gamashiba sedai kuma dudda wannan mamakin datakeyi besa innawuro ta saurarawa danejo ba.

Tafe take ita kaɗai acikin fadamar malam baffa tadawo daga kaiwa hamma Ishaq madarar data tatso mishi, tahango wasu samari tafe maƙotan rugarsu kuma sune suke shiga lambun baffa suna mishi sata, aiko tatunkaresu wanda su ɗinma ita suka tunkaro kasan cewar ta taɓa kamasu suna satar amma bata gayawa kowaba shiyasa yanzu sukeso suyi mata gargaɗi, shikuwa jauro sonta ne yakeyi amma dalalaci bawai danya auretaba, shiyasa yakeso yahaɗu da Ita a irin wannan wuraren dabakowa. Suna zuwa suka riski juna ahanya. "Hai danejo dama nemanki mukeyi aradun Allah kika sake kika gayawa wani kinganmu a lambunku semun karyaki a rugarnan, cewar sani cikin gargaɗi..sukuwa saura duka ido suka zuba mata suna kallon zallar baiwar kyau da tsarin halittar da Allah yayi mata.

Wani banzan kallo danejo tayi musu kana tace "ai wlh baku isa kuyi mana satabq kuci bilis dama aranar nabarkune har muhadu domin bawai barinku zanyi kuci gaba da mana sataba, kuma dena tunanin wani zan gayawa dakaina zanyi muku hukunci Dede da laifinku yawwa. Taƙarasa zancen tana murguɗa baki cikin tsiwa darashin tsoro....aiko kamar jira sukeyi tayi magana ɗaya daga cikin samarin ya ɗauke ta tareda toshe mata baki suka yanki wani lungu da ita, tanata dukan bayanshi da wutsil niya da kafafunta amma yaƙi sauketa seda sukayi nisa sosai inda babu ko alamun mutun kana suka ajiyeta ita bayan sun kewayeta dukansu suna murmushi.

Ɗagowa tayi takallesu babu alamun tsoro ko ɗar aranta wani irin kallo take jifansu dashi irin na ina tausaya muku ɗinnan...suko se zabga murmushi sukeyi kafin ɗaya daga cikinsu yace "badai muzakiyiwa rashin kunyaba humm aiko sekin gane bakida wayo aradu, nidamacan haushiki nakeji agarinnan kawai ina ɗaga miki ƙafa ne amma yau tunda kika shigo gonarmu sekin yabawa aya zaƙinta, dan Allah ku tuɓe mana ita wai mikuke jiranee? Yaƙarasa zancen cikin bada umurni...cikin sauri jauro yace "amma giɗaɗo kabari nafarayi domin nine nakesonta tunda jimawa aradu kaga idan nayi sekuyi kuma. "Shikenan naji kayi da sauri kafin wani yazo wurinnan.

Aiko sunajin hakan biyu sukayi kanta domin su aiwatarda umurnin giɗaɗo na cire mata kaya kamar yadda yace, sedai basukaiga jikintaba wata irin iskar guguwa ta turnuƙe awurin wadda basusan mafarintaba kawai dai sunji tabazar dasu domin seda tayi sama dasu kana tawatsar can nesa, hakan yasa suka saki ihu atare jin sun garu dawani dutse...sekuma ta ɗauke kamar bata wanzu awurinba, hakan yabawa su giɗaɗo hango sani da gainako waƴanda guguwar tawatsar,,,,juyawa sukayi suna kallon danejo inda suka barta zaune sedai me, azaune suka ganta ko yanzu amma akan wata arniyar kujera me masifar ɗaukar hankali da sheƙi anyi mata wani matsiyacin ado na alfarma duk jikinta gwal ne da zinari ke tastas,niya sukeyi, itako se wani malalacin murmushi take jifansu dashi, taɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya.....ido kusa waro cikin mugun tashin hankali suna nunata da yatsa, kafin susamu zarafin yin magana idonsu yasauka akan kujerar datake zaune da kyau, ashe ba asalin kujera bace wani ƙaton shirgegen macijine yanaɗe tamkar kujera me hawa,hawa, danejo tazauna daga kanshi kuma yafasashi asama dashirin zara, yadda yafito tamkar kan kujerar sarki amma yana buɗar baki irinna baƙin kumurci, sekuma wasu biyu wanda basukai girmanshiba sun zagaye wurin kan nashi sunyiwa kan kujerar wani irin ado me ɗaukar hankali dajikinsu ta hanyar nannaɗewa adede kan babbansu hakan yaƙarawa kan kujerar girma da ɗaukar hankalin me kallonta tareda fiegitarwa. Daga ƙasanta kuwa wasu irin halittu ne wanda bazaka kirasu namun dawa ba kuma kai baka isa kace musu mutaneba dubada yanayin halittarsu, gasu tiƙa tiƙa tamkar samudawa sunzagaye kujerar DANEJO tamkar yadda fadawa keyiwa sarki a faɗa, se mazurai sukeyi suna kallonsu giɗaɗo da jauro wanda sukayi mutuwar tsaye tamkar mutun mutumi.

Murmushi danejo taƙarasa saki akaro na ba adadi wanda ke masifar ƙara fitoda kyawunta me firgita ɗan Adam domin ba yadda za'ayi kayi ido huɗu da ita baka alaƙantata da aljanaba sabida tsananin kyawunta koda kuwa haɗe da fuska kaganta balle kuma tana jifanka da wannan shi'umin murmushin nata me tafiya da duk wata halitta me rayuwa.

"Jauro, tafaɗa cikin sweet voice ɗinta me masifar daɗi tana kallon jauron... firgigit sukayi dukkansu kamar wanda suka suma, aka watsa musu ruwa suka dawo, se suka ƙara sauke idonsu akanta, amma abin mamaki kamar yadda suka ajiye ta zaune hakan take babu waƴannan halittun dasukagani yanzu atareda ita, tana zamanta tana murmushi...ai wani irin zabura sukayi kowanne yacika bujenshi da iska na shirin gudu sedai kuma sunkasa motsa koda ɗan yatsan sune ankafesu wuri ɗaya da shirin gudunsu sakamakon sakawa datayi aranta bataso sugudu shiyasa aka kafe matasu tun kafin tafurta abinda ke zuciyarta, anka cika umurnin zuciyar....murmushin jin daɗi tayi ganin an aiwatarda abinda takeso ta faɗa tun kafin ta faɗa ɗin kana tamiƙe tsaye tareda ɗaure fuskarta tamkar batasan minene dariyaba, kai baka isa kace itace ke doka murmushi ba ayanzu..takowa tayi har inda suke jikin kowannensu se rawa yakeyi gaya sun kasa gaba balle baya kuma ga danejo na tunkarosu aiko suka ɓare baki suka fashe da wani irin kukan ceton rai me wuyar saurara. Cikin daka tsaya tace "kumin shiru mutanen banza mutanan wofi kawai ɓata gari. Aiko sukayi ɗib kamar anyi ruwa an ɗauke. Ganin hakan yasa danejo ƙara haɗe fuska tace "kunsan Allah zan barku ne ayau domin kuhana sauran ɓata gari irinku aiwatarda wannan munanan ɗabi'un acikin rugarnan wato kune sata kuma abin betsaya isa hakanba hadda wiya ƴara fyaɗe ko? Humm to naƙara ganin wata ɓarna makamancin hakan agarinnan kugani aradu koba kubane to kune aruwa domin ku zan hukunta wannan nauyin daga yau yarataya awuyanku kubari ayi ɓarna agarinnan koku hana dabara yarage naku, tana gama faɗar hakan tajuya taɗauki ƴar tsumagiyarta data faɗi tun lokacinda suka kamota...tana juyawa sukaji kamar an sakesu, ai suka zura aguje tamkar zasu tashi sama sabida tsananin gudun dasukeyi na tashin hankali....murmushi kawai danejo tayi kana tanufi gidansu.

MASARAUTAR MAHAR

Tafe take tana sauri kamar zata kifa tana tafe tana wai wayen bayanta kallo ɗaya zaka mata kaga alamun rashin gaskiya atare da ita, ahakan harta ƙarasa pert ɗin matan sarki kaitsaye tawuce wanda ke yamma da sauran. Hakince tasamu wata kasaitacciyar dattijuwa akan kilisa tareda ciroma mubarak wato abba ciroma, wasu hadimai biyu na ɓare musu ayiba sunaci suna fira dagani kasan ɗa ne da uwarshi dudda kuwa taɗan manyanta amma mulki da sarauta sun hana manyancinta bayyana. Sallama tayi tashigo parlor tareda zubewa aƙasa tana faɗar

"Allah yaƙarawa Fulani daraja da nisan kwana gaisheki nakeyi Fulanin memartaba tantabarar masauratar MAHAR. Murmushin fuskar Fulani abu ne ya faɗaɗa, kafin tagirgiza kanta alamar ta amsa kenan. Ganin hakan yasa wannan hadimar juyawa ga babba ciroma tana faɗar "Allah yaƙarawa ciroma girma da daraja ɗan sarki jikan sarki kuma sarki uba ga sarkin wata rana barka da wannan lokacin. Ahankali abba ciroma yace "yawwa barka laraba. Daga hakan yamiƙe yana yiwa mahaifiyar tashi sallama yafice...ita kuwa mayarda hankalinta tayi kan baiwa laraba tana faɗar "laraba Mike tafe dake hakan domin naga alamun akwai magana abakinki. "Hakane ranki yadaɗe a yau ne wannan yaron yashigo masarautar nan wato yarima sameer kuma sun shiga wajen memartaba shida yan uwansa shine nace barana garzayo na sanar muki domin ƙila bakisan da shigiwarshiba Allah yaƙara miki daraja...ɗan shiru Fulani Abu tayi tana nazartar kalaman baiwa laraba kafin tanisa tace "aiko dai nasani domin sun shigo nan shida ƴan uwanshi,, kuma ina ta jan kunnenki laraba akan banason gulma da dakawomin zancen da ban tambekiba amma ƙinƙi kidenako? Tafaɗa cikin tuhuma..dasauri baiwa laraba taduƙarda kanta tana faɗar"tuba nakeyi uwar gijiyata amin aikin gafara. "Humm kawai Fulani abu tace kana tajanyo wata salka dake rataye agefenta ta fidda wata ƴar batta aciki tamiƙawa baiwa laraba, tana faɗar ga wannan kozakiyiwa yara anfani dashi. "Jikina rawa baiwa laraba takarɓa tana zuba godiya kamar zatayiwa Fulani abu sujjada takwashi tarkacenta tabar parlor aranta tanajin daɗin kyautar Fulani abu domin hannunta asake yake itada mebabban ɗaki domin duk sunfi Fulani huraira alkhairi.....itako Fulani abu da kallo tabi baiwa balaraba harta ɓacewa ganinta kafin ta girgiza kanta afili tace"gidan sarauta gidan gulma da munafunci kome hakan ze anfaneta dashi datazo zuwa gayamin oho? gaskiya bayi nada matsala sabida wannan gulmar tasu tayi yawa, tana gama faɗar hakan tamiƙe zuwa turakarta.

Washe gari
Chapter 1 · 0% Book details