← Book details Ajeemal Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 18

Sashe 18

Ajeemal Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ko Time d'in da aka aura masa Heelah ba waii dan ba yi da ikon hanasu ko da dakatar da su bane kawai ya kyalesune ya zuba musu ido ba wai dan ya rasa yanda zaiyi bane but hakan ba shi zai basu daman jogana masa wannan wata mace ba especially wacce baisan wacece ita ba bai kuma san daga ina ta ke ba ballai asan asalin wacce ita, turo door din toilet d'in da akayine yasashi bude ido da sauri don ganin wake kokarin shigo masa bathroom ba neman izini, Nisha ya gani ta shigo kai tsaye wacce itama da alamar ba ta lura da shi ba because toilet d'in yana da girma sosai tamakar parlourn wani gidan fiskarta dauke da fara'a takarisa gaban katafaran mirror da ke cikin toilet d'in da ya ke fara kallon mutum yayinda ya shigo tsayawa ta yi tana hango kanta ciki rabunta da ta tsaya ta kalli kanta madubi harta mance time d'in kallon kanta ta ke sosai tana karawa tare da shafo face d'inta ta jikin mirror ganin tayi har wani kumatu tayi kuma ta kara haske sosai.

tabbas itama yau tayi mamakin yanda taga yanayinta ya canza gaba daya hutu ya zauna mata haka ta dinta juya lallausan hannayenta tana kallo kamar ataba jini ya fito time daya kuma fara'a ta ta dauke face d'inta ya koma face d'in jimami saka makon tunawa da maganar salma na cewa

'duniya yayi mata dad'in da zata iya mancewa da ita'

duk da ba ta yi tsammanin wannan furcin daga gare ta ba because ita dai a iya saninta bawani jin dad'in da zata tsinci kanta aciki ta kasa tunawa da aminiyar ta kawar yarinta abokiyar cin mushe su kashe su bunne tare wasu zaffan hawayene suka gangaro mata kafin cikin hanzari ta shiga goge hawayen ta suma waige waige don fara aikin da ya kawota kar ogan nata ya zu ya taddata anan tana ta karanta wasikar jaki, wani ihu Nisha ta kawo sake tana sallati gamida rintsa idanunta because ganin Ajmal time d'in da ya mike ya na kokarin daura towel bisa waist d'insa tana kuma yin baya ganin Ajmal tsaye cikin bathtub yana kokarin daura towel bisa waist d'insa, baya Nisha ta kuma yi da sauri idanuwanta a rintsai jikinta sai k'yarma ya ke a aikuwa sai timmm kakeji ta zame santsin tailed ya zamar da ita a zafafe ta ta kuma mikewa tanufi door sai da ta bude ido kafin ta murda handle d'in tafito ta watsa aguje ta fice.

Aheel na zaune bisa dinning table yana breakfast kamar yanda Nisha ta barshi sai ganin Auntynsa yayi tafito fuuu kamar wata mota ta wuce ta fi ce da gudu daga parlourn ko waiwaye ba ta yi Aheel bin ba yanta yayi da kallo tare da kai kallonsa upstairs dan ganin mai ta ke wa gudun dan ba k'aramin tsoro ta ba shi ba sai zare ido ya ke amma ba kowa da ke biye da ita nan ya shi ga zamowa daga kujeran da nufin bin bayanta but sai ya ji muryan mom d'insa ta kira sunansa wanda ya sa ya mai da hankalinsa garaita ya shiga washe mata baki tare da kokarin karisawa gareta yayinda ta ke sakkowa ta na sanyi cikin kananun kaya wata half vest sai d'an wani gajeren wando iya gwiwa ta tufke gashinta a tsakiyar kanta sai lilo ya ke bayanta ta yi kyau da ita, Cike da murmushi ta kariso ga Aheel ta re da sa hanu ta sun kuci d'an nata tana fadi'n

"Good morning in this morning my love"

Morning Mommy Aheel ya fad'i gamida kwantar da kai jikin mommynsa

" What are you doing here" Heelah ta tambaya tana mai kallon Aheel ta na kuma kallon dining table d'in da kawata shi da kyawawan girke-girke kala-kala ta shaida wannan aikin Nisha ne nan ta shiga hararo abubuwan da ke jere bisa dining tana tabe baki nan Aheel ya shiga zamowa daga jikin mom d'insa kafin Heelah ta direshi akasa ta na kallonshi.

"Mom taho ki zauna kiye breakfast Aunty Nisha na ne ta yi mana delicious mai dadi " ta ho ki zauna ke ma " Aheel ya fad'i cike da murna yana washe baki gamida jawo mata kujera alamar ta zauna but Heelah sai Jan wani banzan tsaki tayi tana tabe baki tana kallon Aheel da ke ta rawar Kai wai Aunty Nishansa tabdi.

"Come and seat Mom" Aheel ya kuma fad'i yana kallon mom d'in nasa wacce ke ta faman hararo shi da shi da table d'in gaba daya tana fadi'n

"Kai da Allah rabu da ni mai zan zauna na ci a wannan tsiyar Allah kaidai yasan hade haden da ta ke cikin girke-girken nan da ta ke tana jan hankulanku da tunanin ku ku ke ta wani ribibi a kanta ta ga ma siye zuciyoyinku da yin nasara a kanku to nikam na fi karfinta ta Allah ba ta mutum ba muna fukar banza kawai Heelah ta karisa fad'i hadai da jan wani dugun k'wafa zuciyarta ta sai zafi ta ke ita ta rasa ya zatayi da wannan yarinyar gaba daya ta shige mata hanci da k'udunduni juya baya tayi yayinda ta hade hannayenta a k'irji ta na kada kai ta na tunano irin hanyar da zatabi da Nisha, shikuwa Aheel shiru yayi jikinsa duk yayi sanyi ganin yanda mom d'insa ke ta surfa masifa akan Auntynsa duk da baisan inda zantukan na ta suka do sa ba baikoma fahimce ta ba.

Shiru yayi ya na ta kallon mom d'insa da ke tsaye ta na ta kaiwa da kawowa ta kasa zama gefe guda kuma ya hangi papansa wanda ya ke sakkowa daga upstairs yana sanye cikin kyakykyawan black suit and black shoes sai bakin glass da ya sanya ya tushe idanuwansa, da gudu Aheel ya taho ya d'ale jikinsa time d'in da ya gama karisowa, cike da murmushin nan na shi Ajmal ya dago Aheel ya sunbaci kumatunsa kafin ya sauke shi kasa karfin Aheel ya ja hanun papansa suka zauna bisa dining table Ajmal ko kallon inda Heelah ta ke baiyi ba ballai ya San da tsayuwarta ya nemiguri ya ya zauna,

Heelah tunda ya sakko ta ke binshi da kallo harya karisa dining ya zauna kafin ta tabe baki gamida matsawa kusa da shi ta ja kujera ta zauna ta na fad'in

"good morning dear"

"Morning" Ajmal ya amsa cikin cool voice na shi ya na mai kokarin kai hanu dan serving din kanshi cikin hanzari Heelah ta a ga je shi ta shiga serving d'insa shikuwa bai dakatar da ita ba because ya na bukan hakan , tana gama serving d'insa itama tayi serving kanta ta zauna ta tusa plate agaba tana ya mutsa fiska sai ka ce wanda aka ce ta ci dole gefe kuma Ajmal breakfast ya ke cikin kwanciyar hankali yayinda Aheel ke gefe shima sai kada kai ya ke time din da ya ke shan daddad'an yoghur fruit ya na santi wayar Ajmal ne ya shiga ruri alamar Kira wanda ya sa shi dakatawa daga breakfast din ya kai kallonsa ga phone din ya kalli screen din wayar dan ganin mai kira, sharewa yayi ya ci gaba da cin abincin sa Heelah sai mika wuya ta ke tana kokarin hango sunan da ke makale jikin screen din wayar dan ganin wanda ya uzura da kira haka shikuwa Ajmal ya ki kula wayar tana a jiye saman table daga karshe ma silent ya sanya wayar ganin an matsa da k'iran, Ajmal mikewa yayi gamida goge hannayenshi ya kamu kan Aheel ya sunbaci goshinsa yana fadi'n

" take care of yourself bye yana fadi'n haka ya dauki phone d'insa tare da key din motarsa cikin hanzari ya fi ce daga parlourn Heelah har ya gama ficewa daga parlourn ya kurewa ganita binshi ta ke da kallo tana tab baki , shi kuwa Ajmal yana fitowa direct parking space ya nufa ya shiga mai gadi ya na ganin fitowar da rawar jiki ya tashi yabude masa gate haka Ajmal ya zo ya sa kai ya fice mai gadi sai daga masa gaisuwa take

Guraren4 yamma wasu kyawawan mota guda biyar duka danno kai cikin gidan time din da mai gadi ya bude gate motar ga ba Daddy ne aciki sai kammala da ke driving dinsu sai yan rufa masu baya mota guda 3 suka karisa shigowa su kayi parking daidai parking space daga nan Daddy da Kamal suka fito daga bisani sauran security gidan suka shiga yayiwa Daddy sannu da isowa daga haka Kamal ya karbi dan madai daicin troler ya karisa shiga masa da shi, yau gurinsu fareeda murna ba a magana Daddy ya dawo duk ida yau anacikin murna duk da tafiyar tashi ba wani jimawa yayi ba but kowa yayi kewarsa sosai kasan cewar Daddy mai yawan wasa da dariya wanted sa'in harda tsokana, awanan rana ammi ta kasa tsugul sai da ta zaiyyane masa duk wani abunda ya faru bayan ta fiyarshi wanda abun ba k'aramin mamaki ya ji ba jin har suma Nisha ta yi ta kwanta rashin lapia ga kuma soyayyarsu da Kamal wanda basu san da shiba nan ya yanke
Chapter 18 · 0% Book details