← Book details A Wani Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 14

Sashe 8

A Wani Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Parveen a Matsayinmu nida Mahaifiyarki, Munada Daman Da zamu Zaba Miki miji Wanda Mukaga Ya Dace da Tsarin Rayuwarki, Mai Hankali da Tarbiya dan Gidan Dattaku.
Gabanta neh ya Fadi ta dake Tana Cigaba da Sauraranshi
"Dan Haka A Matsayina na Mahaifinki na Zaba Miki Miji wanda Nasan Zakiyi Alfahari dashi ko bayan bah Raina"
Kanta na Qasa Batace Komai Bah
"Ina Fatan zayi Na'am da Wannan Auren, Anma Inaso ki Fadamin idan da Wanda Kikeso. Duk da Nasan Its Too late Saboda Har an Kawo Sadaki an kuma Sa Rana Nanda Wata Daya"
Hawaye ne Ya fara Zarya a fuskanta, Qoqarin boyewa Tai Kar Ya gani..
Dan Murmushi Yayi yana Kallanta.
Bakicemin Komai bah Parveen
Kanta Na Qasa Muryanta na Rawa Tace
"Ranka Ya Dade banida Tacewa. Na Amince, Zabinka shine nawa kuma ina godiya"
Murmushi Mai Martaba Yayi
"Allah ya Miki Albarka, Tashi kije"
Ameen Tace Tareda Mikewa Tabar Falon..

Tana Fitowa Ta Fashe da wani Matsanancin kuka, Ita bah Kukan Auren da Mai Martaba Zeyi mata bneh Aa, kukan Karatunta Take. Haka Ta Qarasa Side din Umma Tana kuka Sosai, Jikinta ta xube Tace
"Umma Meh Yasa mai Martaba bazai bari na Qarasa makarantana Bah Sannan Ya Auramin duk wanda nakeso??"
Shafa Kanta Umma tai
"Kiyi Haquri Parveen, Da nan da Gidan Aurenki duk daya neh. Kamar Yanda za'a kula dake anan Haka a Chan, karki damu kanki kinji??. Maganar Makaranta kuma Za'a miki Transfer Zuwa Chan Garin Sai ki Cigaba da Abinki"
Batace Komai bah Ta mike Tana Kuka Sosai Tabar Dakin..

Kwana Tai Kuka, Kota Kan wanda Za'a Aura mata batabi Bah. Washe Gari da Safe Tanada Test Dakyar Ta Tashi ko breakfast batai bah tai Wanka Ta Tafi, Idanunta Luhu luhu. Saida Aka Gama Test din Sannan Suka Hadu da Deexa. Kallanta Tai Da Mamaki
"Meya Sameki?? Daga Ganin idanunki kinyi kuka??"
Kamar Jira Parveen take Ta Fashe Da Kuka Tana Kallan Deeza.
Hannunta Ta Deeza ta kama suka Shiga Motanta, Kuka Parveen Take Sosai Dakyar Deeza Ta lallasheta Ta danyi Shiru
"Pls Bae Banasan Ganinki cikin Wannan Halin Fadamin menene?? Ko Yariman neh kuma"
Girgiza Kai Parveen tai Hawaye na Cigaba da Zuba
"Mai Martaba neh Yakeso Yamin Aure"
Dafe Kirji deexa Tai
"Aure!? Y??"
Girgiza Kai Tai
"Nima bansani bah Deeza, Niba Auren da zaimin ke damuna bah, Karatuna. Ke kanki kinsan Yanda Naci buri akan Karatun nan, Inaso na Zama Gynecologist. Inaso na Taimaka ma Yan uwana Mata.

Dafata Deeza tai
"Wannan Bah Abin damuwa bneh Bae, Ko kina gidanki Zaki Iya Yin Karatunki indai Mijinki zai Yarda"
"Ta Yaya Deeza??, Yanda Fa Umma Kemin Bayani Ba Inan Garin Zan Zauna Bah?? Tho ya makomar Karatuna??"
Shiru Deeza Tai Tana Nazari
"Karki Damu Pls, Allah Yana Tare Dake. Ki Cigaba da Addua Kinji??"
Kae kawai Parveen ta Gyada batareda tace komae bah
Haka Tai Yinin Ranar Hankalinta ba Akwance Yake bah..

Kwanaki Sun ja, Anata Shirye Shiryen Biki daga Duka bangaren Biyu. Har Yau Parveen batasan Wanda Zata Auraba kuma Bata Tambaya bah. Iyayen neh Kawai ke Shirye Shiryensu, Yarima ko da Parveen bah abinda Suke Shiryawa Bama Kaman Parveen da Tunda Akai mata Maganan Auren Batada Aiki sai kuka Sai tunani, Makarantan ma Ta daina Zuwa, Kullum idan Deeza ta tashi makaranta Sai Tazo ta Lallasheta...

Sarki Kabeer Yasa Anata Gyaran Inda Yarima Zai Zauna da Amaryanshi, Cikin Gidan neh anma Da Tazara Sosai Tsakaninsu Da Fada Sides din fulani da Martaba. Shiko Yarima Sam Baisa Maganar auren Akaba Aikinshi Yake bah Ruwanshi. Bilal ne Kawai keta Fadi tashi akan Bikin, Duk Wanda Yakama Ya sanar Mawa duk Ya Sanar...

Ana Saura Sati Biyu aka Kawo Lefe. Lefene Nagani na fada Ko lefe Zahra buhari albarka lol, Anata Yaba Kayan Lefen Itako Parveen na daki qudundune cikin Barko sai kuka take. Ganin Batada niyar Yin wani abu lokacin Bikin Yasa Umma ta nemi Deeza, Katin Gayyata Taba Deeza Tace Ta rabama Qawayenta, Tareda Ankon da umma Tasa Akai Oder dan Rabama Yan uwa da abokan Arziki, Deeza Ce Taita Zarya na Rabo Itako Gimbiyar Tana Gida Kullum Cikin Kuka...
Fulani Tasa an Hada dinner Wanda Za'ai Washe Garin Biki Haka Umma Itama ta Shirya Events Kala Kala Tareda Taimakon Deexa.

Ana Saura Sati Daya Hajiya Shuwa daga Maiduguri Tazo dan shirya Amarya, Ansha Daga da Parveen Saida Umma Tai mata Jan Ido Sannan Ta Yarda Aka Fara Gyarata Tana Kuka Sosai. Kullum Sai an Mata Gyara Cikin kwana Hutu Ta Qara Kyau kamar ba Itaba. Ana Jibi Daurin Aure aka Fara Events Wanda Aka Fara Da Arabian Night. Da Taimakon Hajiya Shuwa ta Shirya cikin Hadadden Arabian Gown Baki, Kwalliya Hajiya Shuwa tai mata Ta Fito Sak Kamar Balarabiya, deeza Ta Shigo dakin itama Cikin shiri, ta Rike mata Hannu Suka Fito Zuwa Hall din Cikin Gidan. Suna Shiga Wajan Yadau Tafi, Sai a Sannan Parveen ta Dago, Mamaki Ne Kwance kan Fuskanta Ganin Kawayenta na nesa dana Kusa, Wasu mah Tunda Suka gama Secondry schl bata Qara Ganinsu bah, A Hankali ta Rintse ido Tareda Duqar dakai Wasu zafafan Hawaye Suka gangaro mata...

Ummy Abduol✍🏻
🏤🏤🏤👑
*A WANI MASARAUTA*
🏤🏤🏤 👑

By *Ummy Abduol*

Page1⃣5⃣

A Hankali ta Rintse ido Tareda duqar dakai Wasu Zafafan Hawaye Suka Gangaro Mata. A Haka Suka Qarasa Inda Amarya Zata Zauna. Saida Ta Zauna Sannan aka Fara Chashewa, Ganin Kawayenta da Yanuwa Yasa Tadan Saki Jiki tana Murmushi...

Haka Akaita Bukukuwa Har zuwa Ranar Daurin Aure. Parveen Ranar Daurin Aure Yini Tayi Kuka, Dakyar umma Ta Lallabata Ta Shirya Cikin Wani Hadadden Lace Light blue. Anmai Dinkin buba, Kayan sun Mata Kyau Sosai. Kana Kallan Idonta Kasan Tayi kuka, Hajiya Shuwa Ce Tai Mata Makeup ta Fito Princess Parveen dinta Sosai..

Karfe Daya da Rabi na Ranar Sati Aka Daura Auren Fardeen Kabeer da amaryarshi Parveen khaleed a Kofar Fadar Sarki Khaleed a Bisa Sadaki Dubu Dari. Daurin Auren daya Tara Manyan mutane Tun daga Kan Shugaban Qasa Har Zuwa Gwamnoni, ministers, Senators, Sarakuna. Babba da Yaro manya da Qanana. Ni Kaina Ummy Abduol Saida na kashe qwarqwatan ido na Baje kolin Hajata na Litttafai Inata Ciniki..lol chan na hango Umma Yahaya musa Da Ummiekhaleel Sunata Dambe akan takeaway..lol

Cikin gida ma Y cika maqil, Matan Manya neh anata Hidima Cikeda Farinciki, misalin Karfe Hudu Aka Tafi da Amarya Gidanta. Parveen Tayi kuka Kamar ranta Zai fita, Dakyar Ta Yarda Ta Shiga mota bayan Mai martaba ya Gama Mata Nasiha. Koda Suka Shigo garin Gombe, Gidan mai martaba taga sun nufa. A Tunaninta Za'a Kaita neh Fulani Tai Mata Nasiha, Saida Aka kaita Side din Fulani Tai Mata Nasiha Sannan Aka wuce da Ita Bangarenta. Bata Qara Tsinkewa bah Saida Akace Mata Nan neh Gidanta...

Deeza dake kusada Ita Ta Kalla Idonta cikeda Kwalla, Deeza Wanene Mijina?? Shiru Tai Nayan Seconds Sannan Tace
"Nima Bansani bah Parveen"
Qara Kallanta Parveen Tai Cikeda Mamaki
"Nanfa Gidansu Yarima Fardeen neh, Meh Nakeyi a Nan??"
Shiru ne Ya biyo baya. Ganin Deeza batada Niyan Magana Yasa Parveen ta Sulale ta Kwanta Kan Gado Tareda Lumshe Ido. Shin wa Zata Tambaya??

Yarima Fardeen koh Babban riga Yasa Fari Kar, Kayan Sun Amsheshi Sosai. A Wajan Daurin Aure sai Washe Baki Yake Yana Gaisawa da Mutane Kamar da Gaske. Shiko Bilal Har Ranar Mamaki Yake Wai dagaske Yarima Neh kuwa Yau Ya Yarda Zeyi aure?? Ana Gama Daurin Aure ko Walima Yarima bai Tsaya bah Ya juyo zuwa Gida. Yana Tsa Gida Ya Chanza Zuwa Black Trouser da White T Shirt ya Fito. Matan dake Haraban Gidan Sai mai Tsiya Suke, Murmusawa Kawai Yake Yahau motarshi yabar Gidan, wani hadadden Gida Ya nufa Wanda tun dawowanshi Ya Siya. Horn Yayi mai Gadi Ya bude Ya Shiga Yayi Parking ya fito. Cikin gidan ya Nufa Kai Tsaye, A Hankali ya bude kofan falon. Wata Kyakyawar Budurwa ce Daga Gani bah musulma bace Ta Taso ta rungumeshi Tana Mai murmushi, Shima Murmushin yake Mata Ya Dagata chak Sai Bedroom din dake Falon..

Fardeen bai dawo gidan bah sai washe Gari da Safe, Fulan ta tareshi rai bace.
"Daga ina kake Yarima??"
Sosa Keya yayi
"Wallahi Na...Umm Naje wajan mahdi neh jiya da Daddare Sai Barci ya kwasheni a Chan"
Kallanshi kawai Fulani tai tareda Girgiza kai
"Shiknan jeka. Ka Shirya Anjima Akwai Dinner"
Dan Tsuke Fuska Yayi baice Komai bah Yabar wajan
Mamaki neh Sosai a fuskan Fulani. Binshi tai da Kallo tai Har yabar Wajan Sannan Ta Wuce...

Amarya Nachan Side dinta ita da Qawayenta da Yan Uwanta. Fulani ce Tareda Kuyanginta Sukai Sallama, Duka mutanen Falon Suka Amsa, Gaidata Sukai Ta amsa Fuska A sake Sannan ta Nufi inda Amaryan Take.
Kwance ta Sameta, Qawayenta Sun Zagayeta, Tanajin Muryan Fulani ta mike ta zauna. Saida Suka Gaida Fulani Sannan Suka bar dakin. Fulani Ta Matso kusada Ita Tana Murmushi
"Amarya Kinsha Kamshi"
Turo Baki Parveen Tai
"Nifa Fulani Har Yanzu ban Gane bah"
"Menene Baki ganebah??"
Tsintan Kanta tai da Kasa fadama Fulani Rashin Sanin waye Mijinta
Fulani ta kalleta
"Ina jinki"
Shiru Parveen tai ta Dukar dakai tana wasa da zoben zinarin dake Hannunta..

Cikin Tsa Fulani Ta soma kiran Kuyanganta
"Ladi! Ladi!!"
Ta amsa ta shigo dasauri dauke da Wani Hadadden Trolly. Ajiyewa tai ta Fita
Fulani Ta kalli Parveen
"Anjima Akwai Dinner, Wannan Kayan nakeso kisa Kinji my Daugther??"
Kai Parveen ta Gyada Sannan Tace
"Nagode Fulani"
Shafa Kanta Tayi tana Murmushi
"You dont hav To"
Itama Murmushin Tai. Fulani ta mike ta mata Sallama Tabar Dakin...

Karfe Bakwai da Rabi dai dai Aka Gama Shirya Parveen Cikin Hadadden Gown. Kwalliya Aka Mata Ta Fito tai Kyau Sosai, Deeza Dake gefenta Sai Kodata Take. Parveen Koh Sai Bata Fuska Take Kamar zatai Kuka...
Chapter 8 · 0% Book details