Part din maji ne ba wani abin asha da akaji don bukin yaran ta neat akeyin shi cikin mutunci da sanin ya kamata.
A Lokachin Mu Ke Part 1 Complete Hausa Novel · about 467 min read
Ina rike da hannun kaunan mahaufiyata da yan uwan ubana don atare muka iso da sauran yan kawo ni daga garin mu,
Wanan kauna mamana ta dan duko tace saka kafan ki na dama ki ja basmalah kafa ashirin da daya tare da karanta, (fihizuma, wa huwa ala kulli shai in kadirr,,,, kafa ukku)
Nan mukaja muka tsaya kaman muna wani abu na karanta tace kin gama nace eh tace ubangiji Allah yasa ki shiga da kafar dama Fatima.
Mama tana jin mun shigo ta taso da kanta tazo ta tare mu ta rungumoni jikin ta tana maraba da diyata sannun ku da zuwa.
Dakin mu na shige da kawaye na na samu su maryam dakin ya cika da kawaywn ta.
Suna ganina ta saka ihu tare da shekowa ta tareni da murnan ta nan muka zube na hira ni dai ban da kuzarin bata amsa sosai a lokacin.
Zan iya cewa ni dai tunda aka fara shagalin bukin mu ban saka Amirah a idona ba har naje na dawo din ban gan ta ba ga gida ya cika ya make da mutane.
Nace niko banga Anty Amirah ba fa tace wa tana can gidan yayan mu da wasu baki ma, ana dai ince maki tana gidan ki can ta tare yau tun safe suke can da kawayen ta wai suna wa bakin shi abinci.
Kin san ita yar ba ruwan mu ne daga cikin mu adole a bayan yaya take bata san zatai kunya ba idan yaya ya shiga hannun wanan matashiyar matar tashi da nake gani.
Nace kai anty zaki fara ko tace wallahi Bintu bakiga yadda kika koma ba yau gaba daya kamar wata yar kasan etopia can.
Kin san sune yakar kyayo acikin jin sin na yan adam.
Karfe daya da rabi a kaje daurin auren yaya Ahmad wai na yaya Imirana tun bakawai na safe aka daura don su haka akeyi gidan matar shi.
Biyu da rabi aka daura auren su Anty maryam da Anty Nasmatu diyar mama, ita ba ruwan ta da sha,anin kowa a gidan mu irin masu akidar ra,ayin rikau ne ita.
Muna nan akace wai za,ai dinner da karfe bakwai zuwa takwas na dare.
Haka yasa ana idar da sallah magariba mummy tace kowan mu ta fito dama muna cikin shiri tun yamma kowa ta kimtsa tafiya gidan ta.
Nice farkon kaiwa don tare aka fita dani da maryam anty Nasmatu yan uwan uwar ta suka kaita ita ma.
Jin an dakatar da mota yadan sani bude fuskana kadan gidan da nagani sai da gabana ya fadi don zakace ba cikin garin sokoto kake ba a gidan.
Hankalina yai balain tashi ina yaya ya samu kudin da yai wanan gida haka ba dai a ball kawai.
Ina jin Inna tabawa na fadin dankari ba fashi wanan gidan haka shine dai gidan Bintu ko kuwa?
Ina makalle ga hannun kaunan mamana wacce dama ina ganin don haka yasa tazo daga bangaren mamana.
Tace idan zaki saka kafan ki akasa ki karanto fatiha kafa uku, ko wani da bissimillah.
Sai ki karanta Basmalah irin na dazun kafa ashirin da daya ki karanta falaki da nas ki hada da ikilas uku uku Allah ya sawa aure albarka ya kare muna ke daga duk wani abin ki na cikin aure.
Ina idarwa ta kama hannu na tare da rada min ki dinga karanta Hasbunallahu wani imal wakeel har mu shiga ba adadi.
Muna tafe masu guda sunayi masu suraitai nayi niko ina saman bakina har abinda batace ba idan yazo min janakeyi na neman tsarin daki.
Nan aka shiga bin gidan da kallo mun samu yan uwan mama acan sune suka tari amarya.
Muna nan dai akace afito akai maryam nata gidan ba nisa sosai don unguwa daya muke.
Wata kawar anty Amira mai makeup ce tashigo dakin bayan an watse tace amarya nazo nai maki makeup na fita dinner ne.
A hankali na kware rufin da ke kaina sai naga tare da su Amira suke da kawayen ta naji mai makeup din tana fadin masha Allahu friend wanan ce kike kira da yar kauye haba waban aiko a fashion sai haka mana.
May kuma ake bukata ga mace ga kyau ga wayewa duk a gurin nan tsoki tayi tafita daga dakin tace ma sauran su fita su bar mu.
Ta busu tarufo dakin tace na taso na saka kayan da suka shigo dashi a jikina kallin kayan nayi da mamaki nace wanan kayan zan saka tace eh shine angi ya sayo na dinner.
Ba yadda na iya dole na saka kayan hakana a jikina ba don naso ba sai da zan saka nagane akwai wani daga ciki mai tare jikin mutum.
Tana min kwalliya tana min gulma wai may yasa Amira take ta faman kusheni ne haka ita bata taba zatin haka zata ganni ba.
Don Allah kada na damu da duk abinda Amira da yan uwan ta zasuyi min hassadane kawai take gani yana damun Amira.
Nace haba anty kin taba ganin mutum yai hassada da dan uwan shi nima fa kaunan tane halinta dai ne baku sani ba amma haka take ita.
Tana min magan ganu akan rayuaan mazan yanzu abinda zakayi wanda zaka kama miji da sauri a hannun ka ni dai umhumm kawai nake ce mata har muka gama komai da ita.
Ba matar ba ni kaina nasan na hadu haduwar da ban taba sani ina da shi ba irin haka sai yau.
Sai tara da rabi akazo daukan mu zuwa gurin dinner wata irin haddan motace aka bude min baya in shiga.
Duhu bai bari mutim ya gane ko mai a ciki sai da na shiga na zauna a zatona zamu je daukan shi inda yake ne .
Sai da mota ta fara tafiya a hankali naji an matse min hannuna dana dauka kujeran motan ce na dafa.
A hankali ya kare tankware hannun nawa yace welcome to ukuba house baby Fatima.
Wani irin faduwan gaba naji amma na dake yakara cewa da fatan dai kin shirya danmaran taron abinda kika fada a shekaran jiya ko?
Nace shirye nake tsab da su don nasan cikin shi na shigo dama yace good baby good.
Haske fitilon da ya haska gurin zakace rana ne a lokacin motoci kanan duk motan dake garin aka kwaso ranan.
Zaka ji kida na tashi daga duk inda kake a farfajiyan gurin da kewayen shi.
Sai dan wani lokaci wasu mace da namiji suka zo inda muke dafa baya na gane summaiyace kawata da mukaje kauye da ita sai wani da ban sani ba namiji.
Sadauki yadan rankafo daidai kunne na yana fadin idan kika bani kunya da halinku na kauyawa wallahi nima sai na disga ki a taron nan kinji na fada maki.
Tare muka jera dasu zuwa wani dan karamin kofa shiga wani guri a hole din sai ganin maryam da Bashar din ta nayi.
Mune a gaba shiga hole din suna bayan mu naji bashar na fadin Ubangiji Allah ya sakawa maji da gidan aljanna da wanan hadin da tayi haka.
Muna shiga saida gabana ya fadi don irin taron da na gani a gurin mutane sai kace ana wani taron addinine.
Nace hasbunallahu wani, imal wakeel a hankali.
Wani haske da kamshi da wasu abubuwa ake watso muna take guri ya dauki ihu up U F kayi daidai wallahi.
Sai wani dan washe baki yake kamar da gaske yana so mun zauna aka fara event yadda akeyi a ko wani buki na dinner.
Gurin yanka cake a tare mu duka hudu muka mike ko wani ango yana rike da hannun amaryan shi,
Sai dai ni nawa angon rikon keta yai min don yatsuna duk sunyi ja saboda matsa da yayi masu na kyata.
Shine ya fara yankawa yabani ba dan guntsura kadan aka hau tafe sai ni kuma na yanko kato na kai mai a bakin shi mugun sai ya hada da hannuna ya tauna sai da nai kara aka saka ihu.
An fitar da mu wai muyi rawa ni dai ina tsaye shine dai ya dan taka kadan sai lokacin nasan wai yan kwallon su na kasa sunzo taya shi murnan aure ashe.
Nan suka zagaye mu suka fara ruwan dollars akan mu suna fada mashi wai yaya akayi ya iya zaben mata haka gani kuma very young dani.
Duk wanda yazo zai mashi farin ciki akan ya iya zaben mace komai nashi a sa,a yake shi.
Sai sha biyu da rabi nace nifa barci nake ji gaskiya zan je na kwanta ga photo da muka sha har nagaji ranan.
Hakan yace wa Bashar akai mu gida naji bashar na fafin kaifa yace yaya zan tafi nabar abokaina ka kuma san ina da bakuwa sai na lalabata fa yace kadaiji tsoron Allah wallahi.
In banji tsoron Allah ba bashat tsoron ka zanji kafasan yanzu wallahi surukin ka nake ka tuna.
Bashar yace nima ai surukin ka ne tunda kaunata kake aure kaga munyi one one ke nan ai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANI MUN BARKI DA ALLAH,,,,
A LOKACIN MUKE,,,,
Maria ta rasa may ke ma rayuwan ta dadi yanzu don gaba daya hankalin Atiku na gurin sabuwar amaryan shi da tashigo mashi da sauyin yanayin rayuwa.
Duk wani ladabi da biyayya na aure amaryan maria ta iya shi haka yasa take ta sace zuciyan Atiku don dama haka maza ke so .
Gashi da ita da dan ta abinda ya faru dashi na kaddara yaki gogewa gare su.
Kusan kullun sai yaron da akaiwa fyade ya dawo mata gida da kuka wani yai mashi gorin abinda ya samay shi.
Itama dai din idan gidan buki ta tafi ko unguwa haka mata zasu dinga cewa Allah sarki ashe itace abin ya faru da dan ta.
Abin kunya harda yan uwan ta na jini sai su dinga fadar maganan yadda hankalinta zai kara tashi taji kaman a ranan abin ya faru da Aliyu.
Ga maigidan ta da yake yawan musguna mata a gida duk abin da tayi bata iya ba yanzun gareshi.
Saboda tabon abin da ta aikatawa dan shi ya matukar tsaya mashi a zuciyar shi sosai.
Ta ramay tai baki sosai gashi sanyi ne yanzu bata cinikin ruwa ko kadan kuma ko banza bata da mai mata talla yanzu.
Wanan bakin cikin da take ciki da yai mata yawa yasa ta tafi gurin mahaifiyan ta cikin tashin hankali.
Nan uwar take ce mata ai sai ki zauna ki ta hadiyan bakin ciki, in kina fidda kudi, kije ai maki aiki ki samu kan mijin ki ki fitar idan kuma kin boye su sai dai ki zauna kina hadiyan bakin cikin da namiji kina kallo zai zama mijin ta ita kadai.
Hakalin maria yai mugun tashi da maganan mahaifiyan ta nan dai ta bata shawaran ta dawo akwai inda zata kaita don mutumin aikin shi kaman yankan yukane saboda gwanancewan shi da iya aikin shi.
Take maria taji kamar an cire mata damuwan ta don sai take gani kamar har tayi nasara ma ko a lokacin.
Ta dawo gida da farincikin ta ta samu har amaryan ta ta gyara gida sai kyali ,gidan keyi don ko yaushe a cikin gyara yake yanzu.
Tai ma Maria sannu da dawowa ta amsa mata a tatsune ta fada dakin ta don ko sallah batayi ba a lokacin.
****** ********* ******
Ina idar da sallah na fito na fara gyaran gidan kafin wani lokaci gidan ya dauki kamshi gaba daya, nan na fada kitchen for the first time don na fara girka abinci da akaina.
Kayan aikine na electronic gasu nan kala kala a kitchen din na fara tunanen wani simple abinci zan yi a lokacin.
Ina bude store din kitchen din naga kayan abinci da na,shaye, shayen, kwali da sauran duk abinci da sha tap a store din.
Na dan dade tsaye ina bin kayan da kallon mamaki don abin yayi yawa sosai a store din.
Dankalin iris na debo tare da kayan miya nai tunanen yin dan fate mai ruwa na sa naman koda dake cikin fridge din na dan yi amfani da danyen attarudu.
Sai ruwan shayin dana dafa yaji kanunfari kamshi na tashi daga cikin shi.
Ina tsaye a dining ina gyara kayan abinci naji ya shigo gidan cikin kayan motsa jiki yake.
Ban san baya gidan ba sai da naga dawowan shi daga inda nake tsaye nace mai ina kwana.
Lafiya kawai ya amsa dashi ya shige part din shi kai tsaye inda ya shiga wanka.
Nima wanka na shiga na gyara jikina ina tsaye bakin wardrobe dina da hijjab dina don sai da nai sallah walha, zan dauki kaya naji an shigo dakin.
Na juyo a firgice ina ganin shine nace cikin daure fuska don may za,a shigo min daki haka ko sallama babu kuma.
Kallon mamaki yai min tare da daure fuskan shi sai kuma naga ya dan dara yace dakin ki fa kikace yarinya?
Nace au nan din dakinkane ko kaga ni nashiga naka dakin ne da zaka ce nan din ma nakane?
Yace lalai yarinya kina da karfin hali wallahi ni da gidana kuma yau ake son kafa min doka akai.
Yace to bari na tunatar dake in har kin fara shagala kin samu gidan zama.
Ki sani duk wani abinda ke cikin gidan nan gaba daya har ke mallakana ne don baki san yadda na samay su ba.
Saboda haka ina son ki shiga hankalin ki daga yau don kada ki wani mike kafa wai ke ga maigida tunda kinga banza ko ?
Ashe shiyasa jiya nida gidana da kayana har kika sawa daki key wai ke ga mai daki ko?
Nace saukin abin dai nima ba kasuwa aka dauko ni ba dai yace towa kuma yasani sai anbincika wanan.
Raina yai balain baci nace kamar yadda kaima akwai alaman bincike akan ka dole.
Sadauki yai murmushi saboda yaba ma karfin halina yace yarinya idan zamuci gaba da haka zanfi kowa farin ciki da hakan a gidan nan.
Yace ai duk macen da zatayi abinda mijin ta ke so ana kyautata zaton samun sakamako mai kyau a gurin ta.
Don haka mu zuba dake a haka a gidan nan aga wanda zai sha wahala.
Ya fara tafiya yake cewa sai ki fito muci abinci don ban yarda dake ba kada ki kashe ma uwana ni.
Nace bazanci ba idan kaci sai ka mutu don kai ke tsoron mutuwa yanzu kuma ma na kashe ka nakai tarin zunubin ka ina ?
Yai murmushi yace ban dai yarda ba na fada maki ina jiranki a falo don nasan halin yan kauye da son banza don a gajewa uwata da yan uwana dan abinda aka gani.
Ya sa kai ya fice daga dakin yana dariyan keta raina yai balain baci haka na karasa shiryawa ina mitan maganan shi a raina.
Kaman bazan fita ba amma kuma sai tsoro ya kamani kada yazo wani abu ya samay shi ace nice nafito tare da dan saka takalmin na tare da daura dankwalin rigana ga kaina sai karamin hijjib na saka iya kafada na.
Saye nake a cikin redmaid din dogon rigan abaya maroon color nafito nima sai kamshi ke tashi a jikina.
Yana zaune yana waya yana jin motsin fitowana ya kura min ido da sauri naga ya kawar da kan shi gareni.
Ashe gaban shi ne yai wani mugun faduwa ganin yadda na sake mai a lokaci guda.
Naja kuran dake gefe zan zauna yace kaji min yar kauye yana kashe waya yake kallona yace wancan kujera zaki dinga zama mai fuskantar wanan don kada wani ya shigo ya samay ki cikin zaman kauyawa ace yar kauye na kwaso gida na.
Ban zauna ba sai jawo plate din da nayi na fara zuba mashi abinci komai da ya dace na dan zuba mai yadda muka saba zuba mai a gida.
Na koma na zauna a inda ya umurce ni yana daukan spoon yace one warning again daga yau idan ina gidan nan bana son ganin wanan takunkumin hijjabin naki kamar zaki cin kasuwan kauye dake.
Nace ai ni ba don ka na saka ba don Allah nake saka abina dama.
Yace kin makaro da wanan dakin zauna gidan ku sai kita faman saka abinki amma ba gidan Umar ba kan.
Haushi ya kamani ganin ya kura min ido yana jiran na cire hijjab din dake wuyana.
Dole na dan sa hannu na zare hijjab din daga wuya na gaba daya surana yafito a fili.
Sai lokacin naga ya fara cin abinci nikan na kasa sai naji yace may kike nufi ko dai da gaske kinyi barbaden ne a ciki wai?
Nace banda gadon wanan amma ban sani ko ku kunayi a gidan ku shiyasa kake ganin duk mata haka suke.
Dago kai yayi ya kalleni yace dakata kada wautanki ya kaiki ga zagin gidan mu yanzu na koya maki wayyo a gurin nan.
Shiru nayi don nasan zai iya idan na kara magana na fara shan dan faten da na zuba a plate a hankali.
Banyi ko rabi ba naji na koshi sai na fara juya cibin kawai ina wasa dashi a plate din a hankali.
Yana kallon abinda nakeyi bai min magana ba har yagama ci na mike zan fara kwashe kayan.
Yace shiyasa baki kiba oya maza ki cinye abincin nan kafin nazo na sure ki dashi yanzun nan.
Don bakin barna kinga banza yasa kika dafa da yawa kin san baki ci?
Na turo baki gaba nace nifa gaskiya na koshi don ban jin yunwa saboda ba abinda na hade balle yunwa ya damay ni.
Tsawa ya daka min yana fadin will you finish it my friend ?
Dole na dan fara turawa kamar zanyi amai ga nauyi da kunya da suka cikani lokaci guda.
Ganin saura kadan ya mike ya bar gurin na zaci fita zaiyi amma sai naga ya koma saman kujera three seater ya kwanta tare da dora kafan shi daya saman kan kujeran.
Kitchen na shiga na wanke kayan da muka bata na kara gyara gurin da mukaci abinci na juya zan shiga daki naji yace.
Waye dan gadin gidan ki kina daki ina falon ina maki gadin gida maza ki dawo nan ki zauna mara kunya kawai.
Nace ikon Allah nifa ba boya bace don naga kana son mayar dani kamar wata wacce ka sayo.
Yace amma ke yarinya ce karama ba,a fada maki cewa sadaki na biya bane lakadan ba bashi ba kikazo gidan nan ne ba wai.
Don haka ina da right din da sai abinda nake son za,ai min a cikin gidana idan kuma kince ba haka ba sai na kira maman naki da taci kudin sadakin nawa tazo nan tabani abina yanzu.
Don ba zan biya kudina ba don bukata na kuma a kun tata min a banza yadda nace dole shi za,ayi a gidan nan kinji na fada maki daga yau.
Haka na dawo falin na zauna ina jiran wani sabon cin mutunci daga bakin shi kuma.
Bai min magana ba sai wayan da yake ta bugawa ana kuma bugo mashi wanda akasari murna ake mashi kan auren da yayi.
Sanyin A C da yai yawa a falon yasa na dan takure a guri guda har barci ya daukeni a zaune ban sani ba.
Jin kaman nai barci a inda nake zaune yasa shi juyowa yaga ina barcin kuwa.
Ido ya kura min har tsawon wani lokaci yana bin ko ina na jikina da kallo har tatsun hannu na da kafa sai da ya kare masu kallo lokaci mai tsawo.
Nikan sai barcina nake hankali kwance jin kaman an tabani yasa ni farkawa furgigit idon shi a kaina.
Na turo baki tare da gyara wuyana da yai min tsami nace ni dai in mutum yana maita ne ko shan jini wallahi kurwa na kur akan shi.
Dariya yayi yace yar kauye kona kara maki karfin A C din ne don naga kinji dadin hakan har da sake min baki kina barci.
Nace inda bamu dashi ne a dakin uwata sai kai min gori dafin abin kafin kayi kudin ka kaganta dashi.
Yace ai nasan shi ya jawo ki yanzu tunda can kauye babu shi anzo an samu na banza ana sha nan.
Nace dakata wallahi gida gidane haka uba ubane kada ka kara zagan min gidan iyayye na nima.
Yace idan an zaga may zakiyi nace na rama aiko yayo kaina cikin tako daya duk yunkurin mikewan da nayi nagudu sai da ya cin min gurin.
Nan ya matse ni saman kujeran muna shakan nunfashin juna yace ki rama din ina sauraren ki.
Shiru nayi ina fadin ka sake ni kawai mugu sai kara matseni a kirjin shi da yayi bai sake ni ba.
Wani irin bugawa naji kirjin na yi fal, fal gashi kuma bai sake ni daga jikin shi ba.
Nace cikin karfin hali mugu kawai ka sake ni wallahi ko na fadawa mama cin amanan da kake min yanzun kuwa.
Yace go ahead kirata yanzu tunda baki da kunya ki fada mata na matse ki ko ?
Sai da ya gaji don kan shi ya sakeni daga jikin shi na tashi da sauri nai daki ina fadin mugu kawai ni bari ma na cire kayan nan don sun haramta gare ni daga yau.
Yace wallahi duk kika cire kayan nan sai na tube ki zindir a gidan nan naga tsiya.
Ke har wata mace ce can da kike ganin kamar kina da wani ajine wai?
Daki na koma na zauna a bakin gado idanuwana suka ciko da hawaye don takaici.
Nace a raina may kullun yake nufi da fafin wani har mace ce da za,a gani aji sha,awan ta ko may ?
Muryan shi naji daga falo suna gaisawa da wasu haka yasa da sauri na saita kaina nasan baki mukayi a gidan.
Ashe yan uwan mamane suka zo gaida mu da kuma yi muna sallama washe gari zasu koma gida.
Shi ya shigo yana fada min zuwan su tare da jamin kunne na saita kaina in har na bari suka fahinci wani abu har naja sukai mashi fada sai na yabawa aya zaki.
Nafito ina murmushin dole nace lah mama kune ashe sannun ku da zuwa.
Maimakon na zauna saman kujera sai na zube kasa ina gaida su a cikin girmamawa.
Masha Allahu Baba kaikan wallahi kayi dacen mata a rayuwan ka yarinya haka da ladabi, yaushe yaran yanzu masu rawan kai zasu tsaya yiwa sarakai wanan gurmamawan haka.
Baba don girman Allah ka rike matar da daraja ku mutunta junan ku, ku rufawa kan ku asiri a tsakanin ku.
Darajan miji shine na mata yadda ka mutunta matar ka haka duniya zasu mutunta maka ita.
Ke kuma Fatima don Allah basai mun fada maki ba don yaran yanzu boko yasa kun san komai na rayuwa zaman takewan aure sai dai idan kun ki amfani dashi kawai.
Don haka kin dai ga yadda uwar ku take rayuwan ta a gidan ku idan kinyi koyi da halin yayan mu da kika zauna da ita babu wani rayuwan da zai gagareki hakkuri a duniyan nan.
Don haka yi nayi bari na bari abinda duk mijinki bai so kin sani, don kun zauna guri guda gwargwado kin san halin shi yasa naki.
Gaba dayan ku idan kuka ba da kunya uwar ku kuka tozarta ita da taga dacewan hakan ta hada ku.
Komai yaya bata boye muna ba na hadin da tai a tsakanin ku kuma ku yanzu bazaku taba fahintar manufan ta ba sai nan gaba.
Don haka ku taru kuba mara da kunya ku kashe ku bisa a tsakanin ku ba komai ne ma ita yayan sai taji shi ba tsakanin ku duk abinda zakuyi ku boye sirin auren ku tsakanin ku don gujewa shigan ta wani hali.
Kai kuma Baba don Allah duk wani abin kurciya da akayi sai abarshi a matsayin kurciya ne yanzo kakai ga tara iyali nan zuwa badi war haka in Allah ya kawo rabo sai kuga mun dawo taron suna gidan nan kuma.
Nan dai sukai muna nasiha ma ratsa jiki suka zauna nan tare dani sai dare suka koma gidan mukai sallama cewa bazasu dawo ba kuma.
Har kofa na raka su suka tafi suna muna fatan alheri da samun zuria ta gari.
Suna wucewa na koma ciki wanka nayi tare da sallah ishai na zauna ina zikiri naji dawowan shi gida tare da rufe kofan gidan.
Hakan yasani sani bazai fita ba ko ina ke nan again ganin shi nayi tsaye da farar leda a hannun shi, na dago kai na dube shi ban san yaya akayi ba naji bakina yana mashi sannu da zuwa a lokacin.
Ledan ya miko min yace na dafa mashi liptop din dake cikin ledan naman kuma na kai mai falo saman dining zai fito yaci.
Inda ya aje min saida na shafa namike zuwa yin abinda ya sani na fara dafa ruwan liptop din batare da na tsaya karan ta kona maye ba.
Na fito na aje mai naman da zafin shi a table tare da ruwa da drinks mai sanyi.
Ina kitchen naji fitowan shi, falon ya zauna ya fara cin naman da na aje mashi.
Sai da na juye ruwan ga wani dan karamin flask na hado da cup na nufo falon yana zaune yana cin naman shi hankali kwance nace ga shayin na dafa.
Ya dago kai yace injin baki zuba sugar ba a ciki nace mai a,a hakana na dafa don ban san ko na may ye ba.
Da hannu ya nuna min na aje anan ina ajewa na juya zan shige yake cewa ke bazakici naman bane ?
Na koshi na bashi amsa a taikace yace may kikace ban fa son shegen gardaman nan naki kinji na fada maki.
Nace naci abinci a dasu mama na koshi dazun kafin su wuce don sai da nai masu girki sukaci da yamma.
Baice min komai ba na juya na shige na zaci daya gama zai shigane amma sai naji ya kunna TV dake falon ko da ban fita ba wasan kwallo akeyi a tv nace bissimillahi Allah nazo gidan masu yi.
Ni dai har barci ya kwashe ni ban san lokacin da ya shige ba sai tsakar dare na falka naji shiru na kara jan bargona na gyara rufe jikina da kyau.
****** ********* ******
Haka mukaci gaba da rayuwa a gidan zaman doya da manja ba wani abinda ke shiga tsakanin mu sai in yana bukatan wani abu zai shigo daki ya fada min.
Sai dai a nawa bangaren ina hankalina a tashe yake don ina ganin bazan iya cika alkawarin mama ba akan shi don a halin yanzu ban san wani rayuwa ma yake ciki ba agidan sunan muna gida daya ne kawai dashi.
Satin mu uku da aure na gama komai gashi hutun mu ya kusa karewa zamu koma school wani sati.
Sai ganin shi nayi dakin lokacin ina kwace na kifa cikina a saman gado ina sauraren kira,a a wayana kaina babu dan kwali na daure gashi na da ribon ta baya ,
Ganin ya shi ya shigo yasani saurin lalabo dan kwalina na daura akaina kallona kawai yayi ya basar kamar bai san may nakeyi ba.
Yace ke nazo na fada makine yau da dare zan koma gurin aikina don haka sai ki fada min abinda kike bukata a sayo maki idan na fita.
Nace ni ban bukatar komai sai dai Monday mai zuwa zamu fara school insha Allahu.
Yace gashi ke baki iya mota ba balle na bar maki motana kiyi amfani dashi sai kuma idan wani driver zan samo ya dinga kaiki.
Nace ai ko da kake daukata yar kauye ba wai doluwa nake ba yadda kake tunane don ni mota kuma yanzu sai dai na koyawa wani tuki.
Fatan kawai yanzu Allah ya hore min yadda ya horewa kowa na samu nawa na kaina insha Allahu.
Kallon mamaki take min kaman zaiyi magana sai kuma yai shiru kawai yafita daga dakin.
Duk da nace komai akwai shi a gidan amma sai ga kaya niki niki maigadi ya shigo dashi wanda kusan yan kayan lashe lashe ne a cikin kwalayen.
Sai da yai wanka yafito ina kitchen ina girka abincin dare ya zo bakin kitchen din ya tsaya yake ce min zancen motan da mukayi dazun na binciki maryam ta fada min ki gwane don kece ke jan ku zuwa school don haka ga motana nan zan bar maki ki fara amfani da ita kafin na duba wanda ya dace a sayo maki.
Ni zan shiga gurin maji nai masu sallama kagin dare yayi min sai ji nayi nace ni dawa zan zauna cikin wanan katon gidan haka.
Yace kedawa kikazo gidan nan dama baki san gidan yadda yake bane kika shigo kai tsaye.
Shiru nayi nace to don Allah ko na roka kanina musa yazo ya zauna dani kafin ka dawo.
Yace no kada ki fara min aanan tarkace inama laifin ki ce nace Amirah tazo ta zauna dake har na dawo.
Nace amma kana gani ita anty zata yarda tazo gidan nan saboda ni kuwa ?
Gidan ki ne ko gida na Amira fa yar uwatace kada ki man ta da hakan don haka ki barni da tsarina kawai.
Ya juya yafita na ce o Allah takawo ni gidan gwauna kaida sai dai obey the rules kawai ba jin views din mutum.
Ya samu mama zaune falo tana zaman kadaici na rashin mu tare da ita bayan mun gaisa take tambayan shi lafiya na yace ina lafiya kalau.
Tace da fatan dai ba wani matsalan komai a tsakanin ku ko?
Ya kai haba maji matsalan may kuma dai ni nama zo ne nai maku sallama yau zan tafi Spain ne muna da wasan da zamu buga har agentina zan tafi ina ganin kuma zan kwana biyu a can idan na tafi.
Da sauri mama tace ita matarka da,wa zata zauna tsawon wanan lokacin haka dake fadi?
Yace da cewa nayi ko Amirah zata koma can har na,dawo, amma ita kuma naji tana fadin wai ko za,a dauko mata kanin tane agida ?
Sai dai na kashe wanan magana don ban yarda da yan kauyen na su zo su zauna min gida ba suyi min barna.
Kana da hankali kuwa yan kauye kan tunda ka dauko diyan su ai kashiga ganin su ke nan a gidan ka.
Ina yaron kanin tane uwarsu daya kuma ba wani babba bane can fa shi yaron.
Kuma ma ita wanan malaciyar inba kwanciya ba may zata yi a gidan amma shi yaron ko wani aike ne ko aiki ai zata iya saka shi yayi mata ko ?
Kada fa kace zaka hanata zumunci da yan uwanta, tun yanzu dan sune gatan ta.
Ya ce maji ba wai zan hanata zumunci dasu bane kawai gani nayi dauko yaron kaman wani long process ne kuma yanzu.
Mama tace aa ka aje da zai kaita makaranta kuma don dazun maryam ke fada min wani sati zasu fara school insha Allahu.
Yace mun gama wanan magana ko zanbar mata motana tayi amfani dashi don ashw maryam ma ta koya mata mota ko.
Tace madallah ubangiji Allah yai maka albarka Allah ya baka zuria masu albarka da zasu tausaya maka kaima.
Yace amin maji nan ya ciro kudi masu yawa ya bata yace ta rike a hannun ta idan da bukatan wani abu a bayan shi sai ayi.
Yadda ya saba tafiya a gida ba tare da daukan kaya ba yauma haka yayi sai yar bakar jakar tafiyan shi kawai ya rataya.
Ina zaune falo don na kasa zama daki kamar mai tsoro yafito ganina zaune a falo tasa shi zama a falon shi ma yana waya ina ganin bashar ne don naji yana fadi ya biya ta gida yazo da Amira kafin ya wuce.
Sai da ya gama waya ya miko min kudi yana fadin karbi na nan nakali kudin tare da karba sai baice min komai ba.
Cikin karfin hali nace namay nene kuma yace ki rike a hannunki don amfani idan kuma ma da wani matsala bashar yana gari sai ki nemashi.
Ni gaskiya kudin nan sunyi min yawa ban da abinda zanyi dasu haka dubu biyu ma sun isheni saboda naga komai akwai a gidan ai.
Kallon mamaki yai min yace wanan kudin ne sukai maki yawa dubu darine fa kawai idan kuna son sayen wani abin fa bana gari.
Nace ni dai sunyi min yawa don ban saba kashe kudi ba komai mamane take saya muna na fadin cikin sanyin murya.
Ok sai ki aje a gurin ki idan na dawo sai na karba don ban saba alheri ba na karba ni.
Bashar suka shigo da Amirah sai wani shan kamshi take kamar an sata zuwan dole ne nake gani.
Amma tana ganin shi ta dan sake tana fadin yayana dazu shine kaje gida ina barci baka sa atayar dani ba sai dana tashi maji ke fada min kazo wai yau zaka koma.
Yace Amira ai ina ce baki gidan ne ma a lokacin da dake zanyi magana yanzun dai ga wanan nan zaki zauna min da ita har na dawo ba zan dade ba nake gani sosai sai dai kuma yadda tafiyan ya kaya min dai idan naje.
Kudi yabata itama madu yawa yace ina tsan mani akwai komai da zakuyi amfani dashi abinda babu dai ga Bashar sai ku tuntube shi kawai.
Bashar ya shigo ina gaishe shi yake fadin kaunata ashe yau wanan mayen ball din zai koma ya bar min ke ai yayi arziki hutun ku ya kare da kafanshi kafan ki wallahi.
Tsaki sadauki ya mashi yace dan Allah mu tafi ni ban iya shirmay ka da ka saba kaji.
Sai naga na mike nima da suka mike kallo na yayi cikin yanayin da bazan fahinci na maynene ba, sai suka fara tafiya daga ni har Amirah muna bayan su tafe.
Sheri bashar ke mashi wai ashe shine bakauye yana kira min kauyan ci murum zaiyi tafiya mai nisa shine zaiwa matar shi wanan sallaman haka.
Yace kai dai kasani jarababen banza ni yanzu ma har ina tausayawa maryam da wanan shegen jaraban naka da ka samo.
Yace ni matata ba irinka bane don chakwai muke abin mu ban kuntata mata bata kuntata min kaine aka bari da jan ajin banza kawai.
Suna shiga mota muna masu Allah yakai lafiya ya bada sa,an tafiya.
Sai da suka bace muka shigo ciki mai gafi ya rufe get inda suma naga ya tsaya ya basu wani abu.
Muna shiga ciki batai min magana ba naga tafara jan dan troler din ta ta nufi dayan dakin dashi nace ,a a anty ba anan zamu zauna tarw bane.
Ta wani juyo a wulakance ta dube ni tace ina ko kin mata ni bani zama da kowa daki dayane don ban son yawan takura.
Sai kawai taci gaba da tafiyan ta can kuma taja ta tsaya ta juyo duk ina tsaye ina kallonta tace Bintu kada fa ki manta gidan dan uwana ne nan ina da right din shiga duk inda naga dama batare da wani shamaki ba.
Kiyi hakkuri anty ni bada wani manufa nai magana ba gani nayi gidan nada girma mu zauna daki daya kawai shi yafi.
Tace to ba zan zauna ba sai inda naga dama zan zauna kuma kada ki kara cewa zaki min katsalandan ga al,amarina kinji na fada maki ko.
Ni dai nabita da kallon mamaki don ban san laifin da nai mata ba har muka koma haka da ita kaman wasu makiya can.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKK8N WASU PLEASE,,,,
IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYABA,,,,
Shine ya shigo gidan kai tsaye yana saye a cikin kananan kaya farare cikin mutunci musa da ya gane shi yake mashi sannun da zuwa .
Murna da yar tsalle Amira tayi sai a gaban sho tana fadin yayana ashe kana hanya shine ban sani ba tun da,safe.
Yace common yanzu ba gashi kin sani ba what else ?
Har lokacin yana tsaye daga kofa yana rataye da yar jakar shi ta maza mai dogon igiya da suke ratayawa,a,kafadar su.
A hankali na karaso garesu cikin tako daidai har na iso gare su jakar kafadan shi na sa hannu ina cirowa daga kafadan shi tare da mashi sannu da dawowa cikin wata murya sai ido ya bini dashi cikin shagala da kallo na.
Da kyat ya iya amsa min da hanya lafiya saboda hannu na da ya dan taba jikinshi ya sakar mai da wani irin kasala lokaci guda.
Daga inda Amira take tsaye tare dashi sai kallon mamaki take binshi dashi a cikin mamaki, can ta saki wani irin ajiyan zuciya jin haka yasa shi saurin juyowa gareta daga shagalan da yayi ga kallona.
Tace yaya na ko shiga baka karasa yi ba mun barka tsaye a kofa tau matar gidan ce wata barkatatta da ita can.
Ya saki ajiyan zuciya a hankali tare da lumshe idanuwan shi cikin wani yanayi yana shafo fuskan shi da hannayen shi .
Cikin falon suka karaso tare dashi inda suka zauna akan kujerun dake falon gaba dayan su har musa kani na dake tsaye daga gefe daya.
Drinks ne mai sanyi na jera a wani dan tiren silver mai ruwan golden da cups din shi ture din tafiya nake zakace wai sallon jan aji nakeyi wanda ban san dalilin kara shagalan da yakeyi ba haka.
A gaban su na girke tire din ina masu bisimillah tare samun dan guri daga gefe daya na zauna na dan zamo daga kujera inda saboda dan dukawan da,nayi gaban rigana ya baiyyana suran jikina a fili, da sauri ya lumshe idanuwan shi da sauke ajiyan zuciya a hankali,
Cup din da na tsiyayawa abin sha na dauko na mika mashi ina fadin ga ruwa mai sanyi yaya.
Yakarba ba tare da ya juyo gare ni ba nace abinci fa ko sai kai wanka ne zakaci cikin wata irin yar siririyar murya da ban san ina da ita ba a lokacin.
Ya dan girgiza kan shi tare da kara lumshe idanuwan shi sai dai fuskan shi a dauresuke mai yadda,na,saba ganin shi a koda yaushe.
Kamar da kyat ya iya furta cewa bari nai wanka idan na dawo daga sallah zanci abincin kafin na kwanta.
Yana dan kurban drinks a hankali yana wani lumshe idanuwan shi abinda ya daurewa Amira kai ke nan ta kasa fahintar yayan nata gaba daya.
Shi da kan shi yai masu bisimillah tare da cewa musa bissimila dauki mana may ma sunan kane please
Musa ya bashi amsa cikin dan murmushi da fadin musa yace malam musa ke nan naga kaman kai ustaza ne ko?
Musa dai murmushi yayi saboda ba sabawa sukayi ba bai sake jiki dashi tukun.
Dawowa nayi falon tare da dafa kan kujeran da yake zaune nace yaya ga ruwan wanka can an hada maka magariba yana kusan towa.
Duk da yana mamakin ganin sauyi a tare dani amma sai yake daukan hakan a matsayin wani sabon yaudara ne na ke kula mashi don naga Amira a gidan.
Amira bari na je nai wanka yace mata tare da kokarin mikewa tsaye daga falon zai shige ciki.
Yana shiga daki mamaki ya kara kamashi ganin yadda dakin yasha gyara ga kamahi ko ina yana tashi daga dakin.
Jiki a sabule mashi yadan bi ko ina na dakin da kallin mamaki gaba daya tarasa may nene dalilin wanan sauyin da ya gani a gare ni lokaci guda haka amma zai natsu ya fahinci may abin ke nufi ne wai.
Daga Amira ko maryam ko kuma dai akwai wani plain a kasa nake boyewa.
Haka ya shiga wanka zuciyar shi fam da tunane a cikin ta na tambayan kan shi may ke faruwa ne haka akwai yaudaran da nake shiryawa a boye.
A lokacin na juya zuwa cikin dakina na bar falon da suke zaune sai da na kwatanci ya shige bayi na budo turare a jikina, sun kai kala uku nafito falon sautin takalman dake kafana, yasa Amira saurin dago kai tabi ni da idanuwan ta.
Sai ga kamshi yana taron hancinta a lokaci guda sai taji wa ni irin wani abu ya tokare mata makoshin ta a lokaci daya.
Dakin yaya sadauki na nufa nai sa,a na samu ya shiga bathroom a lokacin cikin sauri na bude wardrobe din kayan shi, na fito mai da doguwan jallabiya fara kal mai laushi da,santsi jikin shi na bishi da turaren shi masu kamshi na fashe rigan, na aje mai wani wando gaje daga cikin kayan shi dake wanke na tafito nabar dakin kafin ya fito.
Yana fitowa kamshi ya daki hancin shi sai lokaci yaga komai da zai bukata na aje mai a saman gadon shi ko.
Musa kaje kayi alwala na fadi tare da shigewa dakina na muka barta a falon zaune ita kadai kamar manya.
Tana batun mikewa don ta gane nice silar a,watse a,barta a gurin zaune ita kadai sai taji motsin kulle kofan dakin dan uwan nata.
Da fara,a a fuskan shi yake cewa Amira kina nan zaune ne bari na dawo mosque nazo mu zauna ko ?
Tare da musa suka wuce zuwa sallah mukuma kowan mu ya,shige dakin shi a lokacin.
Wanka nayi na fito nai sallah tare da canza sutura a jikina irin da ya dace mace taiwa na miji shiga dashi da dare tankar wace zata halartan wani bukin dinner can.
Dogon rigane mai hannu kamar ta shimi za,a iya ganin hammatan mace a fili daga ciki sai zuwa kasan riga an matse shi an fitar da sharp din mace sosai wanda ko wanene yaga wanan shiga sai ya yaba da shiga na daure gashina da ya sha gyara a cikin dan kyallen riga mai kama da ribbon din daure kai.
Ba yaya saudauki ba har anty Amira da muke zama koyaushe a gida guda,
Ina fitowa falon wanda shigowan shi ke nan daga sallah nafito ina kamshi ina fadin sannun ku da dawowa tun da nake da Anty Amura babu wanda yasan cewa na iya wani yare sai yau din nan dana canza harshe da musa ina mashi yaren uban su wanda nima da karfin hali na iyaren mutanen Niger din.
Kallo biyu suke min na mamaki kwalliya na da kuma jin canza harshen da nayi wanda basu san ina da,wani yare a,harshe na ba sai yau din nan.
Inda yake zaune na nufa sai da,na kai zaune gefen hannun kujeran na fara gaidashi tare da kara mashi sannu da zuwa .
Amirah ta cika fam tun zamana a gurin ta wani hade rai hankalina ya dauke ga kallon tv gaba dayan mu duk wani film din action ake a lokacin.
Sai da aka gama gurin da ya dauke muna hankali na dan juyo gare shi cikin kwantar da murya nake cewa abinci fa yaya.
Yace kin shirya daning din din ne nace mai eh tare da mikewa yace malam musa muje muci abin ko.
Ko ba komai ni dai sai naji dadin yadda ya kula min da dan uwana batare da nuna mai yadda nazata ba daga gare shi.
Sai da suka mike da musa yake cewa Amira taso mana sister ta wani bata rai tace naga kaman ka fara mantawa danine ai yaya.
Kai haba Amira wani irin magana ke nan kuma yace mata kin taba ganin mutum ya mata da dan uwan shi ne ?
Sai bayan sun zaunane nazo na fara zuba mai abincin sai wani faman lumshe idanuwan shi yakeyi don kamshi da desire dake damun zuciyar shi.
Kujeran da yace itace nawa na zauna akai tare da dan zuba abinci kadan a plate wanda zanci .
Bai wani ci abinci ba amma yasha fruits salad din dana zuba mai sosai da ruwan kayan yajin da nai mashi drinks din hausa dashi.
Yana ci aka bugo mai waya nan hankalin shi ya dauke da hannu ya yafuto ni da alamar nazo sai na zo inda yake ya daina waya yana ce min ki dauko liptop dina ki dan dafa min kafin na kwanta zan sha.
Dakin shi na nufa naga liptop din gasu nan da yawa kala kala na dauko wani mai steberry na nufi kitchen dashi.
Musa yana gamawa ya mike tare da komawa gurin tv yaci gaba da kallon shi.
A flask na zuba mai tare da daukan cup na nufi dakin shi da ruwan shayin zalla ba madara a ciki na kai mashi.
Ban fito ba sai da,na kara gyara dakin tsab nafito don na samu kayan da yacire a,watse inda yake ajewa na feshe dakin da airfreshiner.
Dakina na koma don nagaji gani na san tunda yana gari gobe dole akwai aiki gare ni.
Sallah nayi tare da dauko rigan barci na na saka har zan kwanta sai na tuna ban sallami MUSA ba .
Nafito a cikin yare nai mashi magana cewa idan ya gama kada ya dade yaje ya kwanta yace min to Allah ya bamu alheri.
Duk da zani ne saman rigan ya san shirin da nayi alokacin na kwanciya ne.
Daki na koma ban dade da kwanciya ba naji barci ya fara dauka na gashi ban sawa kofa key ba yadda na saba sawa nufi idan na falka zanyi sallah sai na rufe kofan.
Can cikin barci naji kamar ana tsaye a kaina duk da rufe nake a cikin bargo bai hanani jin nauyin mutum aikana ba.
Da sauri na bude bargon dake rufe har kaina yana tsaye ya harde hanbayen shi biyu a saman kirjin shi ya dan jingina jikin shi da bangon daki haka ma kafan shi a harde suke mai.
Ganin shi a dakin yasa nai saurin mikewa zaune cikin dan rudewa nake cewa wani abu zan makane kuma?
Ke dakata yace min cikin daure fuskan shi tambayan ki nake son yi .
Wani muna funci kike kokarin kulla min a gidan nan kuma ?
Cikin mamaki na dago kaina tare da dan kallon shi ganin ni yake kallo ido da ido yasani dukar dakaina a kasa.
Yace tambayan ki nayi may kike kullawa akaina don ban fahinci wanan bakin ladabin shegun da naga kinayi ba tunda na dawo gidan nan.
Murmushi nayi kawai tare da kokarin mikewa zaune da kyau banyi magana ba sai da na mike tsaye da kyau tare da manta yar rigar barcin dake a jikina.
Sai da naga wani mayen kallon da yai min nai saurin koma da sauri na zauna tare da jawo zanin da ke saman gado na kara dan rufe jikina dashi.
Idanuwan shi na a lumshe yake ce min ke nake saurare zakiyi magana ko sai na saba maki yanzun nan.
Nace laifi ne kuma idan mata ta kyautatawa mijin ta ashe nace kada ka manta nauyin ka yanzu a kaina yake.
Duk wani nauyi da nasan naka yana a kaina shi nake kokarin ganin a matsayina ta matar gidan nan na sauke shi a kaina ko kuma hakan shima sabawa ne ga Allah.
Bai yi magana ba bai kuma fita daga dakin ba sai lumshe idanuwan shi kawai da yayi a lokacin.
Can naji ya furzo iska daga bakin shi yana fadin idan kika kuskura kika kulla min wani makirci har na fahinci haka wallahi sai na mugun saba maki kinji na fada maki.
Daga haka naga ya juya yafita daga dakin hakan yasa na mike nabi bayan shi na sakawa dakina key kawai.
Amirah da taga shigan shi guri na shiru shiru taga bai fito ba ta mike cikin bacin rai ta shige dakin ta sai sauke ajiyan zuciya takeyi kawai.
Tana cewa a ranta may yaya sadauki ke nufi da wanan yarinyar badai yana nufin har ya mika kan shi gareta bane mai zai gane gurin wanan bakauyan yarinyar da maji ta nace a kanta.
Tace kai yayana ban taba zaton haka ba daga gareka gaskiya kai mai tsadane kai mai daraja ne sai yar manyan mutane ta dace da irinka.
Bintu bazan taba bari ki samu farinciki ba a zuciyar yayana har abada sai dai ki zauna zaman gadin gidan nan kawai
****** ********* ******
Washe gari kafin kowa ya tashi na gama hada komai na gyara ko ina na gidan sai kamshi ke tashi na koma ciki na gyara jikina tare da saka kaya wani dogon riga Afr abaya mai simple design.
Ina zaune gaban mirror wayana yai kara na dauka ina mamakin mai kira na da safiya haka.
Anty maryam ce ina dagawa tace amarya kina kamshi fa, yaya labari.
Dan tsuki nayi nace kai anty maryam ni dan Allah ki rabani da wanan zancen kinji.
Tace cikin daga murya may kike nufi wai wallahi Bintu kiji tsoron Allah duk wanan nasihan da nai maki kina nufin baki dauka ba ko may ?
Nace haba Anty yaya kike son nayi da mutumin da baidamu dani ba zargina mafa yake wai bai yarda da sauyin da yagani gare ni ba.
Dariya naji tayi tace bashi bane ya fara kamuwa ke nan kedai kawai yi yadda na fada maki shi da kan shi zai kawo kan shi gare ki sai dai in ba mace ta haife shi ba.
Amirah ta koma ne nace tana nan what wani gulma ya tsayar da ita kuma a gidan ku amma dai Anty bata da kunya wallahi.
Yanzu zan sa maji ta aiko a dauke ta tunda ita bata san ya kamata ba don may zata zauna maku gida ta haku walawa.
Shi musa nasan namiji ne ba zai tsaya saka maku ido ba namaji yayana na fadin makarantan kwana yake so ya sama mashi nagari ya kai shi.
Wani mugun dadi naji a raina nace da gaske Anty tace wallahi jiya naji yana magana cewa yana nan yana mai process don baya son ya koma kauyen nan kuma don yaron nada kirki.
Nace wai ban ma san urin godiyan da zan ma yaya Bashar ba wallahi na dade ina tunanen mafita akan kannne na anty don haka suke zaune ba karatu wallahi.
Tace a sannu duk sai ai masu mafita yanzun dai mu samu kan wanan baudaden mijin naki tukun shine mafitan komai.
Nace nifa anty ba wai ya damay ni bane kawai ko hakan ma da muke is ok ai.
Tace kina da hankali kuwa Bintu mace baliga kamar ki zaki zauna danamiji sai kallo ni na fada maki sa ido kiyi kallon yadda zamu kamashi wallahi.
Mun dan kai wani lokaci muna waya da ita tana kara fada min abinda zanyi, mukai sallama da ita.
Muna gama waya ta kira mama tana cewa bayan sun gaisa ko anty Amira na kusa na kira wayan ta bai shiga ba tace ba tana gidan yayan ku ba ko kin manta ne ?
Tace bata dawo gida bane mai takeyi a gidan kuma bayan maigidan ya dawo ?
Yaushe ya dawo inji mama tace jiya da yamma mana ya shigo gari haba dai ita ko gidan amare mijin mutum ya dawo may zata kuma zauna yi masu a gida?
Maji tace ai yanzu zan tura Abdul ya dauko min ita bata da kunyane da bata zauna a tsakanin su ba ai.
Bayan sun gama waya da Maryam mama ta kira wayan yaya tana cewa ashe ka dawo ne Baba na?
Kunya yaji da ta fadi haka yace cikin dan kamay kamay wallahi yanzun nake shirin nai wanka nazo gida ai.
Tace babu komai ka huta abinka har zuwa yamma ka shigo ai wanda ke da iyali kuma ina zaka da dawowanka.
Sai dai ka fadawa kaunan ka ga Abdul nan zuwa yanzu ya dauke ta maza ta dawo gida.
Ban san may ta tsaya yi maku gida ba kuma bayan tasan kana bukatan hutawa da iyalinka.
Murmushi yayi kai haba maji jiyane fa na dawo ai ba komai takeyi ba zata dawo anjima idan zan zo .
A,a maza yanzu ga Abdul nan zuwa zai dauko ta dawo gida haka na ladan ya isa kuma.
Suna gama waya da mama ya shiga wanka sai da ya shirya tsab cikin kanan kaya kamar yadda ya saba shiryawa, ya fito daga dakin shi sai annuri da kamshi ketashi gare shi.
Amira ce zaune a falo nan ya zube gurinta suna gaisawa da ita sai wani shan kamshi take wai tana fushi ya shiga guri na amma shi bai ma fahinci may take nufi ba da hakan.
Yace maji tace ki shirya ga Abdul tafe yanzu zai tafi dake wai.
Bata so batace tunda safen nan kamar abin kora kuma ?
Yana zaune idon shi na akan kofana amma babu alaman fitowa na a lokacin.
Mikewa yayi tsab ya nufi dakin nawa tsaye nake ina shirin fitowa ke nan Allah ya ingizo shi dakin.
Ina ganin shi na zube kasa ina fadin ina kwana yaya?
Yace ba tare da ya amsa ba Amira zata koma gashi kayana basu iso ba har yanzu.
Nace ko zata tsaya har su iso ne juyawa yayi yana fadin umurni ne daga maji.
Ki fito ki bamu abinci kafin Abdul ya iso daukan ta mun samu bata falon a lokacin haka yasa na bita dakin ta.
Da sallama na shiga amma bata karba min ba nake cewa anty ashe yau zaki koma yanzu yaya yake fada min haka.
Tace eh zan koma nabarki kiyi yadda ranki ke so ai nasan kece da aanan kullin don na tare maki guri jarababban yarinyar kawai.
Haba anty may kika tare min aiko kina nan ba,a fasa abinda za,ayi kinga ashe zaman ki bai hana komai.
Bintu kada fa ki kawo min rashin kunya wai ke adole ga wace ta san dadin namiji ko ?
Dariya nayi nace anty aure ne fa kema idan kikayi zaki gane haka ba wai jaraba bane dadin aure ne kawai.
Lalai yau Bintu har nikikewa gorin aure har wani aure ne kikayi har kika san dadin shi ke.
Kai haba anty kema aikin gani gashi kuwa kamar har ya damay ki kullun kina magana a kan shi.
Da ki baro idan kayan yaya yazo ki karbi tsaraban ki zaifi ki koma hakana don kada mutanen gida suga kin dawo empty.
Dama sjine gurin ku ai ku mamaye komai nashi ya zama naki ke da yan uwanki kawai.
Ba abinda zaki taba sai nazo gidan nan don nasan halin yayana dole nice mai raba mashi kayan shi.
Nace da ke nan kuma anty yanzun kan ai akwai mairabo tsakanin ku ina fadin haka na fito daga dakin na barta tana yabo min magana.
Mun karya duk da a takure nake amma ban yarda Amira ta fahinci komai ba akan zaman mu dashi a gida.
Munan cikin karyawa Abdul ya shigo gidan nan suka shiga gaisawa da yayan shi ina gefe nace yaya Abdul ina kwana ya juyo gareni yace sarautan mata yaya kike?
Nace mai na zubo ma, abinci ko yace kaman kin san bar karya ba nace nasani mana yaya tunda gauro kake.
Bintu yaushe mijinki yai aure da zaki fara kira min gauro saurana fa kusan shekara bakwai ko takwas.
Kai yaya wallahi kada kaiwa kanka baki nasan komai fa ina Nadiya take da zakace haka?
Yana zaune yanajin hiran mu da yaya Abdul inda ya juya kan Amira yace kin shirya ne ku tafi ?
Yaya ko kaima kora na kakeyi ne kaman wanan mara kunyan yar kauyen dake fanin ta samu guri.
A,a Nafisa yaushe kuma kuka fara haka da Bintu ina Bintu tai kama da yar kauye ko ada can balle yanzu da ta zama wata princess can da ita.
Nace yaya Abdul fada mata dai ko zata bude idon ta tagani ni dai nasan akwai wata a kasa tsakanina da Anty kawai amma ni nasan nawaye ai yanzu.
Dariya magana ta tabashi yadda nai magana waina waye Amira tace kaiyya haka kike gani ashe ke don kinga yanzun kina rayuwa a cikin wanan gidan .
Abar rayuwan kauye ko nace kai anty ho ke manta ni diyar mamace tun yaushe mama ta mayar dani yar gatan ta.
Dama ai shine gurin ku ashigo a mamaye komai ai aleale sai yadda akayi da dangin miji ko?
Kai Amira tashi ku tafi please bani son irin maganan nan for god sake kaunan kice fa kubar wanan irin maganan mana ?
Yaya Bintu ce kaunata ko wa shiru yayi yadda na fahinci baiji dadin kalaman ta ba a gare ni.
Kallon mamaki take mashi tamike tare da shiga dakin da ta mayar nata ganin tafito da jakar tasa namike zan karba.
Tace kada ki soma taba min jakkana munafuka zamu zuba ni dake don babu gurin zama agidan nan gurin ki.
Ido muka hada yai min wani shu,umin murshi na mugunta tafita batare da tace dashi uffan ba.
Mikewa yayi yabi bayan su ina mata agaida mutanen gida.
Gurin da mukaci abinci na gyara muna tare da kawar da duk wani abinda ya dace a gidan .
Daki na koma ina zaune ban san barci ya dauke ni ba a gurin can yadawo suna falo da musa ya mike zai fita yace ina zaka tafi ustaz yace akwai inda nake fita gurin mai shago muna hira ko dasu maigadi.
Yaron nafita yaji zaman falon ya ishe shi don haka ya mike zuwa waje jin dayayi shuri ban fito ba yashiga dakin.
Dakina ya shiga ina kwance na dunkule saman gado kamar wata yar jaririya dani.
Kallon yadda na dunkule kamar mai jin tsoro yayi ya dade a kaina saida na dan gyara kwanciya tare da kara dunkulewa yabar dakin.
Ikon Allah sai gashi nai mafalki da Kabi yanace min Fatima yau ina iliminki da,wayon ki suka shiga.
Kina kokari kasa cin jerabawan ki zaki halaka kanki kin kuwa san irin dumbin masifan da zaman dakika zaba da mijin ki yake haifa maki?
Ubangiji babu ruwanshi da halin shi rayuwan biyayya da zaman takewan ku zai duba abinda yakeyi tsakanin shi da Allah shi ne.
Muddin baki bi mijinki ba Allah zai kamaki da laifin haka, kuma makomar ki shine wuta.
Fatima kibi mijin ki kinji sauda kafa don Aljananki yana karkashin kafan shi ki faranta mashi ko yaushe kinji kaunata kad ki halaka kanki.
Sai nafara kuka murmushi naga yai min kawai yajuya yafara tafiya kaman cikin wasu duhun itatuwa ya bace abinshi.
Zubur na mike tare da salati sai zufan da yafara karyo min a goshi na kawai duk da A C dake aiki a dakin.
Kabir na furta a fili wasu irin hawaye naji suna zubi min nace Allah ya jikan ka bawan Allah kila sadaka yake so nai mashi.

IDAN KIN BIYA KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH,,,
A LOKACI MUKE
Washegari kamar yadda na saba tashi na kamala muna abin karyawa ina yi ina duban kofan dakin da Anty Amirah take ciki har na gama bata bude kofa ba.
Wanka nayi na gyara jikina duk da ba wani kwaliya nayi ba amma nayi kyau zani da riga ne na atamfan super the most classic one na daura.
Falo na fito na fara karyawa sai da na kusan gamawa ne, na ji ta bude kofan ta tafito daga dakin.
Cikin murmushi nake gaishe ta, inda ta amsa min cikin ko in kulla tare da zuwa tafara bude abinda na girka muna.
Sai can bayan ta zauna take cewa yanzun duk wanan abinda kika dafa haka wa zai ci su ne wai?
Nace dani dake ne fa anty sai masu gadi da zan dibanwa nakai masu.
Humm,ummm lalai dan tallaka bai iya samun guri ba wallahi, Bintu tun ba,a je ko ina ba kin fara wanan nan irin barna haka ?
Nace haba anty ina kuma barna haka ni dana tashi gurin mama ne kuma zan ce na yi barna.
Masu gadi fa har mutum uku ne gidan nan kuma shi da kanshi yace na dinga basu abinci suna ci.
Dakata Bintu may yakawo zancen yaya a nan magana ce iya ni dake mukeyin ta ko?
Kada ki soma kice zaki raba muna zumuncin mu da dan uwan mu don tare kika gan mu ke haye kawai kikai muna daga sama.
Kodan maji ta cuce shi ta mashi wanan cushe na auren ki har kike ganin kamar ke wata tsiyace yanzu.
Bari kiji koda ace auren so kukayi da yayana wallahi ke Bintu kinyi kadan ki rabani da dan uwana ana magana kin wani kawo zancen yaya kin saka a ciki mafari ki samu wani sheri ki kulla kice nace kada kiyi abinda yace kuma.
Kallon mamaki nake mata nace haba Anty may nai maki ne haka wai yanzu kike nuna min irin wanan rayuwan a tsakanin mu nifa kaunar kice anty.
Koshi yaya din bai gwada min irin wanan kiyayyan da kika dauko gwada min .
Yar uwar wa ai dake yar uwatace da killa zan dan raga maki ta wani guri amma ina hadin kifi da kaska kuma.
Sanan shi yaya ina yaga gurin nuna maki wani abu kisa uwarshi ta tsine mashi yana zaman zaman shi akan wata banza can.
Anty nice banza kuma yau ?
Kila da hafsatu nake magana .
Cewa mahaifiya ta data haife ni wai da ita take magana na dago cikin mama idanuwa sun kawo kwalla nace nagode Anty.
Kada ma ki gode din don wallahi ki sani Bintu nifa na tsane ki a rayuwana tunda kika sa maji taiwa yayana haka.
Murmushi nayi tare da mikewa ina kokarin daukan kulolin abinci na juye wa su maigadi nake cewa nagode babu komai.
Ina juyawa naji tana fadin mace a haka ba gaba ba wani fasali na mata kamar solama dake.
Mamaki nake ina tafiya yadda cikin dan lokaci ta sake akaina gaba daya duk ta manta da rayuwan mu a baya don kawai wanan auren na dan uwan ta da aka sakaniyi bada son raina ba.
Naji tana fadin wallahi duk wani muna funcin ki ke da gwagon ki tun farko na fahince ku kwadai ne kawai yakawo ku dama cikin rayuwan mu.
Allah ne shedan hakan kuma nace mata batare da na juyo ba tace ko kina so ko baki so sai wata tashigo gidan nan yar arziki taci arzikin yadda aka iya cin shi.
Haka zaman mu da ita ya kasance a gidan ba ruwan wani da wani har zuwa karfe hudu na yamma.
Sai iko da mulki take zuba min a cikin gidan har na kwammace dama ni kadai na zauna dayafi min.
Sallama yaya Bashar mukaji a falo ganin yadda muke a zaune yasa shi fara fahintar akwai matsala azaman mu da Amira a gidan.
Jin ayi wani sallama yasa na dago da sauri anty maryam ce sai kani na musa biye dasu da yar jakar kayan shi a hannun shi.
Na rasa wa zan tara a cikin su don murna na rugumay maryam ina murna tare da fadawa jikin ta.
Itama murna da ihun ganina takeyi sai wani uban tsoki da mukaji anty taja tare da mikewa tabar falon ta dan kalle tace taufa matsalan da kuma aka kawo maki kega a gida yar uwa.
Nai murmushi nace aikin san anty hukuma ce sai lalashi don ita halinta daban yake kin san.
Na juya gurin kanina ina mashi sannu da zuwa tare da tambayan shi mutanen gida na dago kai nace wa yaya Bashar nagode yaya yace ba ni bane mijin ki ne yace na dauko maki shi ai.
Yace madam ni zan tafi sai after eight zan dawo mu tafi lokacin kun gama gulman ku.
Mukai dariya na ce yayana ai bazata fara tai min gulman ka ba nakyale ta yace haka ne fa kuma Fatima shiyasa nake yin ki.
Yana fita na kawo masu abinci maryam ta harare ni tace ko kin man ta nima madam ce yanzu sai dana girka mukaci muka fito.
Nakai kani na dakin dake farkon shigowa falon wanda ina ganin dan baki aka gina shi.
Muka koma dakina muka baje dama ta matsu ta samu abar mu, mu biyu mu wala.
Dakin tabi da kallo tace dankari gaskiya Bintu yaya yayi kokari wanan irin daulan haka gaskiya ki godewa Allah da hakan.
Nace da mama kuma ko da tai sanadin kawoni ciki ko?
Nace, anty maryam nifa duk wanan bai a gabana kawai dai ni gurina mu samu zaman lafiya a tsakanin mu.
Ta dafani tace, haba Bintu ki kwantar da hankalin ki komai zai zamo daidai a tsakanin ku da yaya.
Tun da safe fa shi ya tayar damu daga barci akan aje yau azo maki da musa tunda kince kina son yazo,
Bai dade da kiran shiba kuma sai ga maji itama ta kiramu tana fadin aje a zo maki da dan uwan ki don ta san Amirah ba zata tsinana maki komai ba.
Nai murshi kawai tace kai Bintu aure fa rahama ne wallahi, sai yanzu na gane dalilun da yasa iyayye kan damu da yarsu tai aure ashe.
Kin koga yadda yayana ke wani haba haba dani ko kuda bai son ya tabani kuma da zaran ya ga na dan shiga damuwa ya shiga tambayana ke nan may ya samay ki may yafaru kuma.
Tace kai bari ke dai yanzu ga yaya ya bata ni idan ban ji shi a jikina ba wallahi har damuwa nake shiga wallahi.
Dariya sosai tabani nace kai anty maryam wallahi baki dai barin halin ki watau, tace bari mutumiyar wallahi duk na matsu na ganki na dan baki wasu hit,.
Nan dai tata min hiran irin rayuwan dadin da suke yi da yaya bashar sai nake ji ashe ni ba ma aure nayi ba.
Jin nayi shiru sai sauraren ta nakeyi, tace yaya kuma kin barni sai faman zuba nakeyi ni kadai na san dai yaya sadauki yafi yayana waye wa.
Murmushi nayi nace anty kufa auren soyayya kukayi da yayana bashar niko da akai mashi dole akaina ina zan samu wanan daulan haka.
Allah dai kawai ya kyauta ga sabon fitina anty Amira abinda take fada min ko wanda akaiwa dole a kaina bai gwada min hakan.
Tace dan Allah fita batun ta yar bakin cikine ita da fadin rai ta dauki duniya da girma ita.
Tace ni yanzun dai na fahinci tunda kika shigo baki samu kan yaya ba ke nan ko?
Nace kamar yaya anty ni har wani kan shi zan samu can mutumin da akai mashi dole a kaina.
Tace ji nan Bintu kefa mace ce kuma ki tuna aljannan ki ta na a,karkashin kafan shi ne don haka idan zaki kama jiki ki ma gurin gyara gidan ki.
Nace anty wani gyara kullun fa sau biyu nake gyara gidan nan a wuni may kuma ake bukata bayan hakan ?
Kai amma ke ma Bintu ashe da gaskiya ke yar kauye ce wallahi.
Dalla ni ba gyaran gida nake nufi ba kinji ki saurara ki ji ba wani boyo ko kunya a tsakani na dake don ke yar uwata ce Bintu.
Da farko zaki fara shiga ta daukan hankalin shi ta yadda don ubanshi sai ya gigice a kanki badon Allah ba shifa namijine.
Namiji kuma kamar kenwa yake gurin son jiki abinci mai jan hankali zaki dinga mashi.
Sai tai shiru can tana fadin ke Bintu ke ma yar iska ce wallahi don nasan yanzun haka yar tsama kuke a tsakanin ku kuna yabawa juna magana.
Nace idan ya fada min nima ai dole na mayar mashi tace kin fadi wallahi.
Kwaran ki yake don kece da zunubi duk abinda zai fada maki ke yazama wajibi dole ki kwanta don kece a kasa.
Ladabi ya zama dole yanzu akanki idan abinci zaici ki tabbatar kina zaune tare dashi, ruwan wankan shi da suturan da zai sa duk kece da Alhakin hakan don ki sani.
Tace gyaran dakin shi duk a kanki ya rataya idan ya dawo sannu da zuwa idan zai fita Allah ya tsare ya bada sa,a.
Duk kika tsare haka wallahi ko baiwa Allah nina fada maki dole ya sauko ku daidata a tsakanin ku.
Gama sauki yanzun yadda yai tafiyan nan waima kuwa kin kirashi kuwa?
Nace ni kan ko lanban shi ban dashi tace kin shigesu wallahi Bintu wai ke kina ganin yadda yaya yake kaman ba masu son shi ko?
Wallahi ki kama jiki Bintu, don na fada maki shine kawai bai damu da mata ba in ba don haka ba da sai kin raina kanki wallahi.
Ki dinga kiran shi kina mai sannu da sauran tare da tambayan lafiyan shi idan kuma zai dawo ki bashi mamaki hada mashi abincin da kika san yana so ki gyara gida da jikin ki tsab.
Kada ki tsaya wani jan aji can ki mai kyakyawan taro sai kiga yadda zaki juya abinki cikin ruwan sanyi wallahi.
Kai gaskiya nikan bazan iya ko daya ba mutumin da ke har hasashen wai ina son na kashe shi idan nai mai girki yace dole sai naci ya gani kada na kashe shi.
Dariya tayi tace ku takon kainan ku ai daban yake Bintu don baku bari agane har afahinci komai.
Muna ciki bamu san cewa har lokacin sallah magariba ya kawo jiki ba sai jin kiran sallah kawai mukayi a masallacin kofan gida.
Mun idar kuma tashiga kara min wasu haske sai mamaki nake wai ita a ina duk tasan wanan abin haka ne wai?
Takwas da yan mintina mijinta har ya iso daukan ta baiji kunyan idanuwan mu ba yake ta faman shige mata ajiki a gaban mu nikan sai faman kawar da kaina nake cikin jin kunyan abinda sukeyi.
Yaya bashar ne yace Fatima bari na baki layin mijin ki don ya sauka kasan waje ko tun da magariba ya bugo min waya.
Mukai sallama dasu sai lokacin da suka tafi na samu ganawa da musa nan mukai ta hira dashi har gurin karfe goma da wani abu na dare muka shige don Amira tun fitan su maryan da ta dan fito bata kara leko falon ba kuma har lokacin da muka shige muka kwanta.
****** ********* ******
Kwance yake saman gadon dakin da ya sauka waya yayi da wani abokin shi dan kasan saudiya da suka shaku dashi sosai.
Yana gama wayan ya fara juyawa a saman gadon gami da zubawa wayan dake hannun shi idanu .
Saboda wani mugun takaicin Fatima da yake ji a zuciyar shi yau kwanan uku ke nan baya gida amma wanan yar kauyen yarinyar mai fadin rai ta kasa daga waya takira shi.
Gashi yana son jin lafiyan su amma sai yake ganin kirata gare shi kamar kasawa ne hakan.
Itama da take mace mallakin shi zaman shi takeyi bata kirashi ba sai shine zai kirata akan may ma wai ?
Don yasan koda ya kiratan ba wani magana bane mai dadi zai samu a gareta banda bacin rai da zata saka mashi kawai.
Ya kifa kanshi a filo yana tuna maganan Maji dazun da suka gausa take tambayan shi kana ko waya da matar ka yaba amsa da eh maji muna gaisawa ai ina tambayan ta lafiyan ta?
To yanzun idan maji din ta bugawa Fatiman waya tace bai taba kiranta ba ko sau daya yaya zata dauke shi a makaryaci mayaudari mara rikon amana zuciyar shi ta bashi amsa da hakan.
Take yai matukar tausayawa kan shi do min kuwa yasan acikin garari rayuwan shi take zuciyar shi ta kara bashi shawara ka kira ta kawai don ka kirata shine wani abu.
A haka har barci ya dauke shi bai sani ba sai dare sosai ya falka tare da jin barci ya kauracewa idon shi alwala ya mike yayi ko zai samu relief a zuciyar shi idan yai sallah dare.
Hakan ne kuwa ya kasance dashi don sai yaji shi wani wasai dashi da rana ma bai sa wani abu a zuciyar shi ba.
Satin shi biyu cif da tafiya sai zaman doya da manja muke da anty Amira a gidan gashi ta hana min dan uwa shakat a gidan.
Da yai abu kadan yanzu zatayo cikin shi da masifa da zagi yadda ran ta yaso ita ko haka abokan ta zasu shigo suyi yadda ransu ke so agidan.
Ta mayar dani kamar wata kukun ta can tace Bintu zokiyi min kaza Bintu zoki dauke abu kaza haka nake takure da ita a gidan.
Lokacin komawan mu school yayi ranan da zan fara fita shiga nayi na mutunci irin ta matan auren da suka san kan su.
Ga socks da katon hijjab na saka a jikina fuskanane kawai mutum zai iya gani a lokacin.
Na samu anty zaune a falo na gaida ita nake fada mata zan shiga school ne.
Ko adawo lafiya ban samu ba har na fara tafiya na tuna da key din motan da ya bani na koma na dauko na kara fita.
Motar dake a rufe tasha wanki tun jiya yaya Bashar yasa aka wanke ta aka kuma cika ta da mai, fam.
Ina fita ashe sai Amira ta leka tana fadin yar iska ki taki sayyada ai a kafa don sai dai kije titi ki hai taxe .
Babu uban da zai kaiki da mota in kince kwadayi kuka iya ke da uwayen ki ai kunkai karshe gurin yaya sadauki.
Lekawan da zatayi ta hago har na zauna a mota ina service din ta wani irin ashar ra mulmulo daga bakin ta tana fadin kan uban can motar yaya sadauki fa.
Ashe akwai bura ubah a gidan nan kuwa ko ni ban shiga motan shi ba balle wanan bakar jakar kauyen ta ce shi zata shiga.
Nikan har maigadi ya bude min get nasa kai ina ganin fitowan ta cikin matsifa ban tsaya ta kanta ba nafice daga gidan.
A cikin masifa ta koma cikin gida tana masifa da zage zage wai sam bazata yarda ba da hakan.
Tayi kiran layin shi lokaci yana gurin wasa wayan shi yana kashe bai shiga ba.
Maji takira a cikin fada take fadin maji kinga abinda kika jawowa yaya ko kamar Bintu zatace ta shiga motan yaya ta fita da ita?
Amira kina da hankali kuwa mata da motar mijin ta har kike fadan wai ta shiga ke kije ki shiga ta mijin ki mana.
Kashe wayan tayi don har kukan takaici sai da tayi a lokacin gashi sai faman kiran wayan shi takeyi bai shiga a lokacin.
Ina isa makaranta idanuwan mutane yayo kaina caaa suna son ganin wake cikin wanan irin motan haka kamar yadda mutane ke saka ido ga abinda bai shafe su ba yanzu.
Sai da na gama na kulle ko ina na sako kafana dake cikin takalma mai hill wanda duk kwakwan mace da wuya ta samay shi a kasan nan.
Zan iya cewa a lokaci daya muka shigo da maryam don a lokacin itama ta fito har ta rufe motar ko.
Ina tsaye ina gyara tsayin hijjab dina da ya sauka har kasa naji tace madam you are welcome to new world.
Dariya nayi nace ,a,a anty kema shigowan ki ke nan dai yanzun ko ?
Tare muka jera da ita zuwa cikin makaratan sai kowa ya nufi department din shi.
Idanuwa akan mu don komai na jikin mu sai ya koma sabon yayi kasancewan mu amare sabbin fitowa.
Ban tsaya wani gaisawa da mutane ba don gujewa sabawa Allah don balain tsoro gareni.
Ban fito ba daga class sai da lokacin sallah yayi na tafi school mosque inda muke zuwa sallah.
Maryam ce ta kirani ga waya tana tambayan inda nake wai muci abinci.
Nake bata amsa da ina mosque tace nasan dama baki wuce can ai gani kofa idan kin idar kifito ina jiran ki.
Nafito na samay take cewa ga abinci can da tazo muna dashi don tasan idan tanice bazanci komai har mu koma gida.
Nace a ina zamu zauna ya ustaziya dariya nayi nace nice kuma ustaziyan yau kuma anty ?
Nace sai dai mu shiga motar ki don gaskiya bazan zauna a fili ba can muka nufa muna ci muna hira akan matsalan anty Amira.
Sai after six na iso gida a gajiye dani nasamu musa a takure yana jirana don fitana da ya gaji da zama ga takuran anty Amira ya koma gurin su maigadi ya zauna.
Dakuma yagaji ya dan fita mike kafa yabi titi har saida ya gaji ya juyo ya dawo gida yana kofan gida zaune na shigo gidan ya taso da fara,an shi a tare muka shiga gidan .
Babu kowa a falon nan muka zauna muna dan hira dashi nace bari na dan shiga na dafa mashi abinci.
Dakina nashiga na kwabe na koma kitchen nafara dafa abinci mai saukin dafuwa don a gajiye nake a lokacin.
Ban san zuwan ta ba sai muryan ta danaji a bayana tana fadi ke mara kunya yanzu ashe harke kina ganin kin isa shine kika fita da motan yayana.
May kike nufi da hakan dakikayi don duniya tasan dake ko kuwa kinyi ne dan gadaran kan ki ?
Nace anty banda amsan baki ni amma kina iya tambayan dan uwan naki ai kiji daga bakin shi don shikeda amsan tambayan ki.
Wani tsuki taja ta jyya tana fadin zaki gane kuren ki wallahi na aikat hakan da kikayi.
Nace wai may ke damuwan anty Amira ne haka duk ta wani bi ta canza rayuwan ta lokaci guda.
Yaya sagir ne ya shigo gaida mu karan shi na biyu ke nan bayan tafiyan dan uwanshi yana zuwa duba mu a gidan.
Shima yaya Abdul yazo amma saudaya ya zo gidan ya dubamu yana min sheri wai yaga na canza may ye sirin ne dayake shi mutum ne mai son barkwanci da mutane duk inda ya ke sai anyi dariya.
Nafito muka gaisa yana tambaya na ba dai matsalan komai ko nace ba komai yaya lafiya kalau muke.
Bai wani dade ba mukai sallama ya tafi don irin sadauki ne shi miskiline bai magana sai wanda yaso yi dashi.
****** ********* ******
Duk muna falo a zaune musa da yashigo abinci yake ci yana kallo, sai wayana yai kara na duba nomba bata kasar nan bace ta kasar waje ne.
Nai matukar mamaki da tambayan kaina waye kuma ya kirani haka ne wai?
Har kiran ya katse ban daga ba naci gaba da abinda nakeyi tana zaune sai faman dakilan wayan ta takeyi.
Wayan ya kara kara sai naga ta kalleni cikin zargi yanzu tsoron ta nake ji don ta canza gaba daya.
Haka yasani daga wayan don gudun zargi kada ta kulla min sheri gashi yau nafita zuwa school.
Mai shi baiyi magana ba nake ta fadan Assalamu Alaikum amma shiru ba ai magana ba nace please don't called this nomba agai iam marriage woman.
Murmushi naji anyi yace wata irin matar aure ce da bata san hakkin mijin ta ba sai kuri fadi da baki.
Sai a lokacin nagane cewa shine online ashe cikin yar murya nai murmushi don kafe ni da idon da tayi tana son tasan dawa nake wayan.
Nace shine zaka kira mutum kaki magana ni wallahi har ka ban tsoro ma naga nomban kasar waje ban san mai ita ba kuma.
Mikewa nayi tsaye don barin gurin kada taji fitinan mu don nasan shi zamuyi tunda ya fara fadin haka ina fadin.
Yaya ina wuni?
Tabini da harara tana fadin munafuka kawai wakike boyewa maganan ku indai yayanane baki taba fari a gareshi.
Ina shiga daki yana fadin dan baki da kirki da tarbiya shine koki kira kiji yaya na isa balle yaya nake ke wai wata irin yar kauyen yarinya ce haka ?
Nace da iska zan kiraka ko da guguwan nomba zan bugo maka ?
Yace dan rashin kirkin ki bazaki iya tambayan ko Amira ta baki nombana ba ki gaidani.
Nace banga zan iya wanan ba don ba damuwa kayi da asan lafiyan juna ba ai ?
Yanzun kuma da ka damu aika kira kaga na samu lamban idan zan iya sai nakira.
Ke baki da kunya wallahi idan kika fada min maganan banza ko a waya ne wallahi gobe zan shigo garin nan naci maki mutunci son raina.
Nace kai dade idan kaso ma ka taso yau din nan ka iso anjima ba sai gobe ba dip naji ya kashe wayan tashi.
Tun ranan bai kara kirana ba nima dai haka ban kara kiran nashi ba har lokacin.
Maryam ce ta ishe ni da korafi inda ta matsa min akan sai nakirashi a gaban ta kokuma wallahi mu bata da ita.
Ba yadda na iya dole na dauko wayana daga cikin hand bag dina na kira wayan na shi a lokacin kuma shi yana zaune tare da Linda.
Sai ganin kirana yashigo a wayan shi da sauri ya dago kanshi tare da cewa hello,
Nace wa,,alaikum sallam.
Ina wuni yaya ya amsa da lafiya a takaice sai nai shiru maryam dake gefe na ta kafeni da ido don jin may zan kara fadi kuma.
Jin nai shiru yace min kuna lafiya dai ko?
Lafiya muke na bashi amsa a lokacin naji muryan mace tana tambaya cikin harshen tiranci da wa yake waya ?
Naji yace mata sister din shi ce .
Lafiya dai ko naga kin kirani yau?
Nace ai kaji matsalar sai ba lafiya zan kiraka dama ni sai anjima kawai.
Dakata sai na tsaya ina sauraren shi yace nasan wani ni yasa ki kirani dole ko?
Nace eh.
Anty maryam ce gata a zaune tace sai nakiraka ko mu bata da ita shiyasa na kiraka.
Ok
Maryam dake gefe na tace shit ta karbe wayan daga hannuna tace hello yaya ta damay ni fa da zancen ka shine nace takiraka mana taji lafiyan ka.
Murmushi yayi yace maryam kin san fa yar kauye ce bata san darajan miji ba balle ta san kiran shi taji lafiyan shi.
Daga inda nake a zaune nace, gara zama da kauyanci da hurda muranen banza ai muryan mace naji tana magana dakai yanzu.
Dariya magana ta tabashi don ya fahinci nasan kishi ke nan nima don har na kasa boyewa na fadi a fili.
Yace maryam fada mata Linda ce my wife to be nake tare da ita ba irinta yar kauye da batasan komai sai kauyanci da rashin kunyan su na yaran kauye.
Haushi naji nace komai kauyanci mu dai mun san darajan kan mu da mutuncin iyayywn mu dip maryam ta kashe wayan tana fadin.
Kinji halinki ko Bintu ke wanan bakin naki wai bai mutuwane nace cikin fada wallahi muddin bai daina kirana yar kauye ba bazamu taba shiri dashi ba kinji na fada maki.
Tace kai Bintu ada kema kice mashi kowa ma kauye ne asalin shi don mu kauyen mu fa har yanzu babu ko titin mota ba wuta ba ruwa.
Nace nagode anty aiko zai rana kanshi don daya fada zance mai munfi mutane kauyen tureta ai.
Ranan daga school maryam tace min mu tsaya salloon din dake kusa da school din mu gyara kan mu baki ba don da wuri muka tashi.
Wanke min akai akayi tare da zuba min kayan kamshin da tazo dasu masu kyau sai nace a dan gyara min kafana da yatsun hannu na haka akaimin gyara nafito wata yar birni dani.
Sai da zamu rabu take ce ban sa zamu hadu ba sai zuwa next week amma ina son ranan Friday don Allah kiyi girki mai dadi ki gyara gida da kanki sosai yadda yaya zai gane cewa yanzun ke ba bakauya bace don ina sa ran Friday din nan zai shigo garin suyi waya da yayana yace yana Abuja.
Muka rabu ina shigowa gida Amirah ta kasa boye haushin gyaran da nayi a zuciyar ta tace sai dai kikare haka Bintu miji kan sai dai kamahi shi.
Murmushi nayi a raina nace kai kodan na kure anty Amira dole nabi shawaran maryam.
Friday na yi kamar yadda tace sai bina da kallon mamaki Amirah keyi.
Kasa hakkuri tayi tace wa da ni yau wani kuma sheri kike son yi a gidan nan ne haka ko bakin yan kauyen ku zasu zo ne wai?
Nace anty ashe kin gane bakin kauyan mune zasu zo yau gidan kuma anan zasu kwana tare da mu.
Na gama komai na koma daki ganin biyar saura nan na bata lokacina gurin gyara jikina zakace wani gasan gwajin kyau zan tafi a lokaci don har musa kanina saida na bashi sabbin kayan da na,sayo mai ya saka yai aski irin ta matasa.
Falo muka dawo muka zauna ganin haka yasa Amira fitowa daga daki nasan ta hake ne taiwa bakina wulakanci a lokacin.
Bamu dade da zama falon ba da kamshi ke tashi cikin shi mukaji ana nocking din kofan shigowa don a rufe yake musa na tura ya bude kofan.
Yayin da Amirah ta sako idanuwan ta don ganin mai shigowa falon a lokacin don a shirye take da cin mutunci a ran ta.

IDAN KUMA K8N BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA NA BARKI GA ALLAH YAR UWA,,,,
A LOKAC8N MUKE,,,
Tun ranan da wanan abin ya shiga a tsakanin mu na kasa sakin jikina a gidan.
Ban yarda mu hadu da yaya sadauki ko da a falo ne ganin na dan samu sauki yau natshi tunda safe ina son shiga school kasancewa monday ce yau din.
Tsaye nake a bakin zinc na kitchen ina dauraye kayan da akai amfani dashi daren jiya.
Ga kuma girkin dana dora ina sauri ingamawa kada na makara ko ya futo yasamay ni ban fita ba.
Jin kaman mutum tsaye a bayana yasani sauri juyowa ina kallon kofa shigowa kitchen din, .
Gaba nane yai mugun faduwa da ganin shi yana tsaye ya saka hannayen shi biyu ya raba kofan tsakiya jikin saye da kayan exercise din shi sunyi matukar yi mashi kyau a jikin shi.
Dan daburcewa nayi daganin shi bansan lokacin da nakai kasa ba a tsorace ina cewa ina kwana yaya.
Bai amsa ba,sai karasa shigowa daga cikin kitchen din da yayi gaba daya ina durkushe.
Tsayawa yayi tare da jingina jikin shi da bayan inda nake tsaye da farko yace wa kike boyewa kwana biyu a gidan nan.
Mikewa nayi don ganin bazai amsa min ga tambayan da ya jefo min kuma lokaci guda.
Fuskewa nayi nace may zan boyewa kuma ni don banda lafiya ne kawai.
Murmushi yayi yace may yasamay ki baki da lafiya kuma?
Turo baki nayi na karasa dauraye plate din dake a hannuna, na juya ji nayi ya finciko ni tabaya na.
Tsoro ne ta kamani jikina ya dauki rawa a lokaci guda don balain tsoron shi nake ji yanzu .
Idanuwa na a runtse tare da sauraren abin da zai biyo bayan rikon da yai min a lokacin.
Hannuwan shi naji saukan su a saman kirjina tare da rankofo kan shi a daidai wuyana a hankali.
Yana fadin abinda kike min rowan su ke nan gasu yau na kama su a hannuna.
Idona na ritse gam don jin abinda yaya ke min wanda ban taba ma kawo tunen hakan ba a tsakanin mu.
Cikin wata yar murya nace da kyat don darajan Allah yaya kadai na wanan abin please ?
Don Allah ka bari kada musa ya shigo ya samay mu a haka please.
Murmushi yayi yace idan yashigo and so what bada matata ya ganin ba.
Kara rintse idanuwa na nayi cikin rashin fahintar abinda yake min a lokaci zafi ne ko haushi ko ko dadi.
Da karfi na zille daga jikin shi na koma gefe ina mai da numfashi kaina a duke.
Murmushin keta yai min yana cewa matsoraciya kawai yau ina bakin naki yashiga kuma mai fadar bakat magana.
Idona da yakawo hawaye na dago kai nace don wanan cin zalin da ka dauko yi min a gidan nan bashi zai sabakina ya mutu ba ai mugu kawai mai ruwa biyu.
Murmushi yayi ganin da nayi ya juyo kamar zai yo kaina na zille akasa tare da kare fuskana da hanaye na sai naji yai dariya yace ashe bake bace ?
Har ya kao kofa ya juyo ya tsaya yace, kuma idan na kara shigo na samu kin boye zakiga abinda zan maki gidan nan.
Yana fita na sauke ajiyan zuciya tare da mikewa na karasa abinda nakeyi ina yi ina kwallon kofa kada ya dawo again.
Sauri sauri nagama komai tare da shiryawa zuwa school don lokacin har dining sai dana hada komai na fito a cikin hijjab dina kamar kullun.
Naso nafita batare da na,sallamay shi ba sai naga rashin dacewan hakan gareni don haka na nufi dakin nashi.
A hankali na tura kofan daki da yar sallama a bakina, yana kwance saman gadon shi yai rigingine fuskan shi na kallon ruffing din dakin nashi.
Daga kofa na tsaya ina fadin zan tafi school, sai na dawo.
Da kyat ya iya dago kanshi idanuwan shi kamar yafara barci ne a hakan.
Kallo na yayi tun daga samana har kasa na sai ya mayar da kan shi yana fadin akwai mai a motan, nan kuwa nace ranan da na fita last akwai mai a cikin sa sai dai ban sanar ma yau din nan ba.
Mikewa naga yayi ba tare da yai min magana ba yafita a dakin nima bayan shi nabi muka fita a tare dashi .
Motan ya bude ya shiga ya tayar da ita ya dan dade a cikin ta yana service din motan ina tsaye daga gefe ina kallon shi.
Yafito daga cikin motan bayan ya gama warming dinta tare da ce min sai kin dawo ya juya ya shige gida.
Mun hadu maryam a school duk yadda taso ta zolaye ni taji yadda muka kwasa da yaya sam naki bada fuskan yin haka.
Dole ta gaji ta kyale ni muka canza hira kan hiran matar yaya Ahmad da akace sunyi fada har da buge buge har gurin yan sanda sukaje.
Amma kuma sun dawo anshirya kamar basuyi ba nace ai dama irin su irin matan nan yan duniya ne daidai dasu.
Tace ita kuma matar yaya Imirana ance kazama ce kumai tana dan kurba syrup akai akai,
Sai dana gama saurare nace wai ubangiji Allah ya kyauta kawai zamuce ga al,amarin don yanzu abubuwa daban daban lokacin nan da muke cikin ta.
Ba mu dawo gida ba sai yamma lis after six na shigo gidan agajiye dani daki na shiga na cire hijjab dina na fito kitchen don dora girkin dare.
Misa ne yashigo yana ce min sannu da dawowa yace yanzun ko yaya ya bargidan nan yana tambayan baki dawo ba.
Nace may zan mashi idan na dawo din sallon son yaiwa mutum muguntan shi dayasaba kawai.
Kai haba anty yayane kuma mugu ni dai wallahi yana bani shawa wallahi don ba ruwan shi rayuwan shi akwai sauki sosai.
Murmushi nayi a fili a zuciyata nace baka san komai ba yaro da baka fadi hakan ba.
A gurguje na hada girki na koma dakin shi dake a hargitse na gyara mashi tare da wanko bayi na feshe ko ina da kamshi nafito nazo na samu shikafan dana dora ya tsane na tuka tare da kwashewa.
Kafin a gama kiran magariba na gama hada komai na shige dakina wanka nayi tare da dauro alwala nafito.
Ban daga ba sai da nai sallah ishai na fito tare da kara feshe falon mu da kamshi kafin ya shigo gidan.
Na koma na zauna tare gyara jikina wani riga da wando na saka daga cikin kayan lefe suke English wear ne na gyara gashina da ribon jelae shi ya sako a baya.
Dan karamin gyale na yafa ga kaina na fito falo na samu musa ya shigo nace mai ya dibi abinci yaci dare ya soma yi.
Ya dabe ya dawo inda muke zaune ya faracin abincin muna hiran mu ta zumunci labarin rayuwan garin sokoto da ya gani yake bani ina dariya.
Haka yasa bamuji shigowan shi ba sai ganin shi mukayi har ya kawo tsakar falon.
Sannu da dawowa muka fara mashi ya amsa tare da zubewa saman kujera da alaman daga gurin wasan su na ball ya fito a lokacin.
Sai ya kasance shigan da nayi na takura da zama falon dan wani kallon da naga yai min ya wani lumshe idanuwan shi.
Can ya bude bakin shi da kyat yace musa ina gani gobe zaka wuce school don an gama maka shirin komai ko.
Daga ni har musa dago kai mukayi muna kallon shi a cikin kasala yake maganan shi yace.
Ban san ko akwai wani abinda zaka bukata ba kaje cikin buth din motana ka kwaso abinda akasoyo ma ka gani idan akwai abinda zaku kara sai ku duba ku gani.
Mikewa musa yayi yafita yabar abincin don dauki sai lokacin na dago kai na kalle shi ya rike goshin shi da hannun shi daya nace yaya mungode Allah ya saka da ,,,,,,
Hannu ya daga min yace is ok please nima ai kanina ne musa.
Kara cewa angode bai yi magana ba sai mikewan da yayi ya bar falon tunawa nayi ban hada mai ruwan wanka ba a lokaci da sauri na mike nabi bayan shi.
Na samay shi a tsaye yana kokarin cire kayan jikin shi sallama nayi na shigo ya bini da kallo kawai.
Bathroom na shige tare da joner mashi heater ruwan zafin da zai yi wanka dashi.
Nafito bayan na matsa mai su maclean da subulun da zai bukata na aje mai a gefe nafito din.
Nazo zan wuce yana daure da towel iya kugun shi da sauri zan wuce naji ya finciko ni zuwa jikin shi.
Yar kara nayi nace cikin wata irin murya wayyo yaya please kayi hakkuri don Allah matse ni yayi gam yana kokarin hada bakin shi da nawa.
Sai kokarin zillewa nake don gaba daya balain tsoron shi yanzu ya cika min zuciya na don bangane wannan son yawan hada jikin shi da yake son yi dani ba akoda yaushe.
Sosai ya tsayar dani sai tsotson bakina yake cikin wani irin sallo da shi yasan irin shi.
Kafafuwa na ne naji basu dauka na a lokacin gashi ya cika min baki da harshen shi ban iya maganan komai a lokacin jikina sai kyarma yake min.
Shi kan shi yaga dama ya sake ni tare da bina da shu,umin dariya yace zamu hadu dake ai matsoraciya kawai.
Sai dana sai ta kaina a tsaye inda nake tare da bin bayan shi da zai shige bathroom.
Lokacin ne na kara sheda girman jikin yaya sadauki sosai ashe karfafan mutum ne haka ban sani ba.
Na samu musa a falon ya kwaso kaya gasu nan birjit a gaban shi.
Jakkuna na kaya guda biyu na hango sai na karasa gurin yace anty kinga abinda yaya ya sayo min haka.
Nan muka shigo budewa daga kaya sawa takalma uniform sai kayan abinci na gwagwani da na sha su madara da sauran abubuwan sha.
Kallon kayan nake cikin mamaki don ba karamin kudi ne aka kashe ba gurin sayayyan wanan kayan masu yawa haka su bucket da kulan da zai ci abinci duk an sayo mashi man shafi su maclean da sabulun wanki dana wanka da turare.
Musa yace kai yaya I love you wallahi ban ma san irin godiyan da zan mashi ba idan yafito wallahi.
Murmushi nayi kawai naji dadi kwarai a raina don nuna kaunan da yayi wa dan kanina haka.
Can yafito cikin wasu yan kananan kaya a jikin shi rigan mai dan karamin hannu iya hammata sai wando three quater da yasa fari kal dashi sai kamshi ke tashi a jikin shi.
Direct dining erea ya nufa hakan yasa na mike na nufi gurin tare da daukan flask na fara zuba mai tuwon shikafa fara da miyan water leaf yaji agushi sosai da nama.
Dan kadan na tsakurawa kaina a plate a shiririce nake ci inda ya zauna ya kwashi abincin shi sosai.
Sau biyu yake cin abinci a wuni da safe idan ya karya sai kuma da dare wani lokaci kuma fruits salad kawai zai sha yakan ce wai ina son dirka mai abinci yaci yai kiba kwana biyu ya kasa yin wasan shi.
Waya yake yi yana kallon yadda nake wasa da abincin dake gabana duk da rashin yawan da baida shi.
Da ido yai min magana alaman maza na cinye shi na make kafada na alaman banyi, sai dai ban daina cin da nakeyi ba a yangance.
Mikewa nayi tsam na fara kwasan kayan zuwa kitchen ban fito ba sai da na tsaya na wanke kayan don na rage yawan aikina da safe.
Na dawo nasamay shi da musa yana gwada mai wasu takardu a hannun shi ashe takardan addmition ne na makaran tan da zai tafi.
Zama nayi a gefe daya ina satan kallon su duk da hankalina yana gurin tv dake aiki a lokacin.
Musa ya tatara kayan shi ya kwasa cikin jin dadi zuwa dakin shi tare da muna sai da safe nasan zai tafi yyakara baje kayan ne yasake kallon su a tsanake.
Shiru falon yayi ba wanda ke magana a cikin mu sai tv dake aiki shi kadai ana ta watsa turanci ganin ankirashi a wayan hankalin shi ya dauke yasa ni mikewa nabar falon.
Bathroom na shiga da niyan nakewa sai naga kawai nai wanka na ji dadin kwanciya kawai nafito na dan shafa mai laushi tare da saka yar rigar barci na dana feshe da turare, light pink mai dagwari biyu sai dai iya cinya ya tsaya min rigar.
Ina zaune saman gado naji ya turo kofan daki sai dai ya sauya kayan jikin shi saye yake da wani wando mai laushi iya gwaiwan shi kamar three quarter da rigan shi mai kama da dinkin banga na maza.
Sau daya na daga kai na na kalle shi na dukar da kai kasa inda nake zaune a dan stoll din mirror yazo ya zauna tare tare da kura min ido.
Muryan shi naji yana fadin tashi muje mu kwanta tunda ke baki san abinda ya dace mace taiwa mijin ta ba sai an fada maki.
Na dan bata fuska tare da turo bakina nace ni anan zan kwanta murmushi naji yayi tare da riko min hannuwa na ya mikar dani tsaye.
Look at me yace, sai na dan dago kaina kadan na kalle shi amma ban iya jure kallon shi ido da ido dole na dukar da kan nawa, kasa.
Yace daga yau ban son sai na kara biyu ki a dakin ki don ko zo guri na ke baki san right din ki ba ne a gare ni.
To bari kiji bazan biya kudin sadaki na ya tafi a banza ba ni ina gabas kina yanma kudi nabiya dole kuma a bani hakkina.
Jin abinda yace yasa ni watso mashi harara au harara na ma ki keyi ko ba biya nayi ba ne ?
Cak ya daukeni kamar ya dauki babyn roba sai dakin shi ya dire ni saman gadon shi yana cewa this where you support to belong every night.
Rankwafo wa yayi tare da raba hannaye shi yasani tsakiyan shi kokari yake sai mun hada ido dashi amma na kasa lumshe idanuwa na nayi.
Yayin da naji yafara canza min sallon wasan shi a hankali yafara bin sassan jikina da wani irin romacig.
Tun ina iya daurewa har na fara dan nishi, kadan kadan cikin neman agaji sosai yake gwada min wani irin mahaukacin kauna wanda ni kaina ban iya cewa ga inda nake a lokacin.
Mun dauki tsawon lokaci dashi sai da ya gaji dan kan shi ya sarara min tare da rugumay ni a jikin shi yana sauke numfashi a hankali.
Al,amarin yau da dan sauki bisa ga daren farkon mu dashi don banyi mugun jikita irin na wancan ranan ba.
Gaba dayan mu shiru mukayi kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi a lokacin.
Ni dai tunane nakeyi anya kuwa zan iya da yaya sadauki ashe mutum haka bai da tausayin mace ko kadan.
Ko dai dama haka yake ne wai yana mu,amula da wasu matan ne acan baya.
Da sauri nai istigifari don ance zato zunubi ne koda ya zama gaskiya don haka nai saurin janye wanan tunanen a raina.
Shiko tunane yakeyi wai dama ashe abinda Bashar ke ta fihintar dashi ke nan akan mace.
Tabas yanzu ya yarda da zancen bashar da yake cewa dan hakin daka raina shike tsone ma ido ashe ni,ima da baiwane tattare da wannan yar kara mar yarinyar da ya raina a idon shi.
Bai tsan mani a rayuwa zaa samu mace haka mai tarin ni,ima da baiwa ba irin na Fatima ba yarinyar da bai taba samun wani jindadin rayuwa ba irin wanda yake tsinta yanzu a jikin Fatima ba.
A hankali ya kai hannun shi saman kaina naji yana shafa a hankali ban san lokacin da na saukw wani irin ajiyan zuciya ba mai karfi.
Ji nayi yakira sunana a hankali yana fadin FATIMA na amsa a hankali da fadin naam .
Sai naji ya rugumay kamar wani zai kwace mashi ni a lokacin yace.
Don Allah ina son kiyi hakkuri da halina kizama mai dauriya acikin duk wani al,amari na zaman takewan mu nidake.
Idan har kin min haka kin gama min komai bazan taba son na samu matsala ba daidai da rana daya da mahaifiya na koke don rayuwa a yanzu akwai akasi a cikin shi kala da kala.
Shiru nayi ina sauraren shi, yayin da idanuwana suka ciko da hawaye wanda ba zan iya fadin ga dalilin zubowan su ba a gare ni.
Kukane ya kubuce min jin yadda nake kuka yasa shi kara manna jikin shi sosai da nawa shi bai lalashe ni ba kuma bai iya furta komai ba .
A haka barci ya daukeni ban san manayi barci ba sai dai dana falko nagani a saman chest din shi kwance nayi filo dashi.
Gyara kwanciya na nayi dakyau abinda yasa shi dan motsawa ke nan ya kara jawoni zuwa jikin shi.
Da safe da kyat na mike na nufi dakina can na gasa,jikina sosai da,ruwa masu zafi haka yasa na dan samu saukin ciwon jikin da nake ji dana tashi.
Nai matukar mamaki kwarai da naga yaya yana sallah jam,i bai wuce shi duk asubahi sai naji fitan daga gidan zuwa masallacin uguwan sallah.
Ya dawo daga motsa jiki ya samay ni tsaye ina hada table din cin abinci a cikin kunyan abinda ya faru a tsakanin mu daren jiya yasani dukar da idanuwa nakd gaishe shi da kwana.
Ya kara so tare da dan rike ni daga bayan na yana cewa, ke baki gaji bane har kika tashi ki aiki haka mai yawa?
Kunyan shi nake ji ban yi magana ba sai dan murmusawan da nayi nace yanzu zakaci abinci ne?
Ba abinci nake son ci ba ke dai nake so yanzu ya bani amsa fuskan shi a daure tamau kamar ba wani magana yayi ba a lokacin.
Da sauri na kalli agogon ban gon dake falon sai na ji ya furzi iska yace zan makarar dake ke nan kike nufi ko?
Ya juya ya fara tafiya yana ffadin ok a dawo lafiya sai dai kafin ki dawo zan kai musa school din su sai kuyi sallama dashi.
Daga haka ya shige dakin shi ya barni gur8n tsaye koda na shirya nashiga yi mashi sallama na samu ya shiga wanka a lokacin.
Don haka na cire mai kaya daga cikin wardrobe din shi haka zai sa yagane na shigo dakin na juya nafita da sauri don na kusa makara ranan.
Bayan yafito kayan da ya samu na fitar ma saman gado don yasa yasa shi gane cewa na shigo dakin a lokacin sai daya gama shirin shi yafitone musa ke fada mashi nace na tafi don na makara yau.
Yana gamawa dama musa duk ya kagu su wuce don haka,basu bata lokaci ba suka fita zuwa school din da za,a kai shi na kwana.
****** ********* ******
Haka muka kasance da yaya kullun a tare muke kwana dashi yana yadda yaso dani tun ina jin nauyi da kunyan shi har na dan fara rage kunyashi da nakeyi sosai.
Yanzu yakai basai yace nazo dakin ba don kaina nake shiryawa naje don ma inhar banje ba shida kanshine zaizo ya dauke ni cak yatafi dani.
Ya gama binda yake ya koma gefe daya yana sauke numfashi a hankali tare da furzo iska daga bakin shi.
A raina nace wai dama maza basu da kunyane haka wai kamar ba shine mutumin da ke ta cika bakin shi ba abaya akan dole ne maji ta lakaka mashini.
Yanzun gashi shine harda wasu irin kalamai da ina ganin ba a hayacin shi yake fadar su ba idan mun kasance a dukule tare.
Idan kuma weekend ne zan iya cewa kusan a tare muke zama muyi shi agidan bai son fita nan da can yana nan ciki ya hanani shakat a gidan sai yayi yadda ranshi ke so zai sarara,min.
Watan shi daya cur a garin da dawowa bai fita zuwa koda Abuja bane yanan cikin gari.
Ranan ya shigo da yamma yake ce min na shirya zamu fita zuwa gida mu gaida su baba don baba bai jin dadi jikin shi ya tashi.
Na dan rude ina fadin subbahanallahi may kuma ya faru da,baba ni dai Allah yasa ba wani mugun abin aka aikata ba har ciwon shi ya tashi.
Tun karfe bakwai na fara shiryawa na saka wani atamfan super exclusive, mai ruwan yellow da zanen ganye kore zani da rigane sai gyalen da na yafa karo na farko a gidan aure na.
Takalma da handbag duk na fitar da zan saka sai wani irin mayen kamshi dake tashi ajikina na dade ina bata lokaci gurin gyara jikina kamar wacce zata gidan wani shugaban kasa.
Nasan idan na samu matsala ga shigana ba su Umma da mama ba har Amira sai na samu musguna daga gare ta.
Sai gashi ya shigo dakin yana wani kamshi dashi yai mugun haduwa don shadda ce gezenah a jikin dark blue sai wani maiko da yauki takeyi har hulla sai da ya saka yau nace dankari a raina wani abu ko sai mahaifa.
Yadda yake kallon shigana nima haka nake satan kallin nashi shigan don duk wanda ta fan mu komai bakin cikin mutum dole ya kyasa muna.
Karasowa yayi har inda nake zaune a gaban mirror ya kura min ido can naji ya numfasa yace wai ke ashe haka kike dama kike ta faman boye kanki cikin mugun hujjib kullun kamar wata munafuka can.
Nace ai dama sunana ke na a bakin ka kuma boyewan danakeyi ai ba kaina naiwa hakan ba don da baka samay ni ba kai.
Namike ina cewa dama nasani na dinga kwalliya irin na anty Nafisa tunda shina ga yafi burge mutane yanzu.
Yace dako na halakaki tun lokacin don ba zaki jawa maji zagi ba, nace ai naga shine ra,ayin ku ku.
Murmushi yayi tare da kamoni yana mikar dani tsaye yace ki tabbatar da kin rufe min wanan jikin naki da kyau don kinsa akwai kardawa a gidan .
Yayyen nawa ne kuma gardawa ashe kardawan yawa gare su bamu sani ba masu kalle surar kannen su .
Yagane maganata sai yai murmushi kawai yace ai ban kalle ba sai dai ina shirin kallo don gada wani ya bani labarin abinda ban sani ba nida abina.
Da sauri na dago kaina nace may kake nufi da hakan ya wani lumshe idon tare da furzo iska yace ma,ana har yau ban san komai ba akan matata da rana ganin dare kawai nake mata koshi ma a,wahalce ga cizo ga yakusa da zagi.
Murmushi nayi na dukar da kaina kawai don natuna first night din mu dashi yadda naitakiran shi azzalumi macuci mazina ci kawai.
Isan kin shirya sai ki tashi mu tafi kada ki bata muna lokaci don ina da abinyi ni idan mun dawo don ba wani dadewa zamuyi ba can.
Kallon mararaicewa naimashi nace tare da turo baki, ni wallahi kullun abu kullun abu ba tausayawa mutum.
Yace wani abu kuma cikin kasheni da idanuwan shi don son jin amsa na.
Banyi magana ba sai gyalena da ke tashin kamshi kawai dana yafa akaina nan na kara fitowa wata shar dani nai marukar kyau har ya kasa dauke idon shi akaina.
Yarinya ke kikace kina so dabakice kina so ba da ba,abaki ni ba, yasani gaba muna tafiya yana min waka a baya na.
Wata landdrove jeep nagani a waje dark blue sai shaki takeyi van san da ita,ba a gidan sai wanan lokaci ko ba afada nasan ansha miliyoyi a waban gurin .
Ita muka shiga shike driving kamar bai son tukin motan nace amma ya kamata mu dan sayi wani abinda zamu shigawa baba da su Umma dashi kada mu je masu hannu a sake.
Kamar baiji mai nake cewa ba yai banza dani a raina nace bahagon mutum kawai wanda ba,a gane kallan shi kaman ba shine yanzu yake min waka ba gashi mintina kadan ya wani sha toka ya murde fusaka tamau dashi.
Gaban wani katon shago ya tsayar da motar shi sai da ya kashe motan ya juyo yana ce min fito mu tafi.
Har mun fara tafiya yace gyara rufe jikin ki dak yau don kinga an fara binki da kallo kiyi shiga kamar wata budurwa can.
Gyara tsayin gyalena nayi da kyau tare da bin bayan shi munyi sayayya sosai a shagon har sai da nai mamaki leda kusan bakwai akayo muna muka nufo gida dasu.
Ina ganin get din gidan nai wani lumshe idanuwana don jin dadin ganina a gidan da nai rabin rayuwana a cikin shi cikin jin dadi.
Muna fita gab da zamu shiga gidan sai naji ya riko min hannu na kallon hashi nayi ba tare da ya kalle ni ba yace eh haka nake son maman ki ta ganmu don tasan na rike mata amana.
A haka muka shiga gidan mun fara cin karo da yaya Abdul yace tun daga nesa a,a,a Allah yayi hadi a gurin nan sai kace kuka hallici kan ku haka.
Murmushi ya sauke kawai tare da kara rike min hannu da kya yaya Abdul yace kaga zabe gaskiya kan nan ba irin wa yancan da suka zabo mata ba kamar suna barci.
Muna shiga cikin gida Rukaiyya diyar mama Asiya tana waje tsaye tana waya tana ganin mu ta wani watso muna idanuwan ta gaba daya a kan mu.
Dakin maji yace a fara shiga da kayan bayan ya cire wasu leda guda uku daga cikin ledojin da,muka shigo dasu yace min a hankali kiba wa su Umma kowa guda guda nace angode.
Dakin Umma muka faea zuwa tana zaune da yaran ta sai jin sallaman mu tayi har mun kawo kofan shiga ko duk sai ta daburce da ganin mu.
Zama yayi kan kushi na zauna kasan carpet daidai kafan shi muna gaida ita .
Cikin hali irin nata na shan kamshi take amsa muna kallo daya tai muna wani mugun hassada da bakin ciki ya darsu a zuciyar ta tace kina nan kina ta hakkuri da halin mijin naki ko don ba fasawa zaiyi ba na sani.
Murmushi kawai mukai mata don duk mun fahinci nufita amma muka kyale ta
Bamu dade ba muka mike na karasa gaban ta ina cewa mama ga wanan ba yawa dan tsara bane ta amsa a wullakance tana tabe baki tana fadin angode.
Na juya har na fara rafiya sai najuyo ina cewa yaya sagir fa idon ta nagani tana kallin kasan zanina da harara tabini ta tabe baki tace yafita dazun nan.
Dakin mama Asiya kuwa muna shiga dama Rukaiyya ta riga data fadawa mamata zuwan mu ko da ta gan mu.
Idon kyam a kaina yadda mukayi dakin mama haka mukayi a dakin ta bamu dade ba mukafito namika mata ledan tace to har da wani tsaraba can to angode.
A daiyi ta hakkuri don kin san abinda kika aura dama don haka sai a daure da hakan .
Muna barin gurin sai dakin mummy sai dai a rufe dakin yake yaran ta dai ne kawai a ciki alaman tana dakin baba a lokacin.
Yaran suka yo kanmu suna muna sannu da zuwa cikin rugumay mu Imirah yace yaya nace mummy takai mu gidan ka tace wai zamu damay ka kana hutawa .
Muma yaya kazo ka kaimu mu huta tare da kai kaji, ya shakan shi yace zanzo na dauke ku.
Yaran sukaji dadi suna ta murna yayan su yace zaizo ya dauke su zuwa gidan shi namika masu ledan tsaraban su wanda daban yake saboda akwai alawan yara acikin shi.
Sai dakin mama muka nufa kuma suna falo zaune da Amira muka shiga da sallama ina rike a hannun shi kamar wata yar yarinya can dani.
Sannu ku da zuwa mama tai muna Amira tana dago ido kallo daya tai muna naga tai sauri kawar da kan ta gefe daya tana cewa sannu da zuwa yaya.
Nace anty ina wuni ta ansa a wulakance da lafia kawai ta juya kan ta ya kalle ta yai murmushi yace sister ke nan yaya gidan gaban mama na tafi na durkusa a gaban ta nace mama ina wuni ?
Cikin jin dadi da ganin mu haka tace ashe kuna tafe ne yanzun tashi ki zauna Fatima kinji Allah yai maku albarka ai yanzu yaro yashigo da leda yake cewa kune kuka shigo.
Sadauki yace maji yaya na barku dazun haka yasa nagane cewa yashigo da rana ashe nice dai yakawo nagaida Baba da jiki ashe.
Mama tace mai lafiya muke yace to yaya jikin na baba tace a,a Alhamdullahi ai ya samu sauki sosai har ya tashi yayi sallah ko dazun.
Ta juyo gareni tana cewa Fatima kuna lafiya ko cikin jin kunya nake cewa lafiya kalau muke mama.
Tace ashe musa an tafi makaran ta saiga babana yazo dashi ya sallamay ni ranan .
Cikin jin kuya nai murmushi tare dukar da kaina kawai nace wallahi mama yaya ne yai mashi wanan kokari kuma yasaya mai komai da zai bukata acan .
Sai a taya mu godiya gurin shi mama tace ince maki sun gode kwarai Allah ya saka da alheri.
Mama tace kai haba waban ai yiwa kaine kawai wa yasan abinda zai zama watarana kuma in Allah ya raya abinshi.
Kina dai waya da su ko don ki dinga jin lafiyan su akai,akai don haka na dakyau.
Gurin da Amira take zaune ya koma ya zauna saman hannun kujera yana cewa may kikeyi ne wai kin wani fuskewa mutane haka.
Tace cikin da yake yaya kawai dai hakanaji ashe zaka dawo yace eh waccan nakawo ta gaida baba da jikin shi don dazun ya tambaye ta.
Hummm wanan muba fukar matar taka ai ta iya sace zuciyar kowa da makircin ta harda ma wanda bamu zata ba duk ta sace munafuka kawai.
Kai Amira Fatima ce kuma muna fuka munafuncin may taimaki kuma haka ne wai .
Sai lokacin ta dago kai tace humm yayya ni wallahi mamaki ma kake bani yanzu dan ban yarda amma yau na shedawa idanuna gaskiyan zargina.
Yanzu kai yaya har ka iya fito da wanan a gari a matsayin wau matar ka har kana wani jerawa da ita, kamar wata mai mukami can.
Kasa kasa suke maganan su amma duk zancen su ni yana a kunne na don ina dan kusa dasu mama ce kawai bazata ji ba a lokacin don ita sai farin ciki da murna takeyi tagan mu a cikin farin ciki a tare.
Can ya mike don ba zai jure sauraren Amiraba don tana bakanta mashi rai da zancen ta gap yake da ya dauki matakin da bata zata ba a lokaci guda.
Idan nake a zaune ya kallo yana cewa taso muje gurin baba ki dauko wancan ledan muje mashi dashi.
Yana gaba ina bayan shi muka tsaya daga kofan falon baba muna mashi sallama.
Aka ansa muna muryan mamane take ce muna mu shigo ganin mu tare yasa baba dake a kishigide ya dan dago zaune cikin fara a yake cewa,aa Fatima tare kuke ashe?
Har gaban baba naje na duka ina gaida shi shima a kasa yaa zauna kamar yadda na zauna yana gaisawa da Baba din tare da tambayan shi karfin jikin shi.
Mun dan jima zaune suna hira da baba da mummy ni dai kaina a duke banyi magana ba.
Sai can baba yace sadauki gaskiya nayi farin ciki kwarai da ganin ka haka ji yadda ka kara murjewa nasan wanan duk aikin diyata Fatima ce don tasan abinda ya dace.
Ba kamar matar wanan mahaukacin ba da tazo gaidani dazun kaga nan yana taba kujeran gefen shi yace a nan ta zauna wallahi.
Baba yace wanan irin abubuwan dole su jefa mutum a cikin damuwa yau ace irin tarbiyan da na,baku a gidan nan amma a cikin zuria ta ake samun irin haka.
Sai yai shiru tare da girgiza kan shi can yace wallahi yaran nan suna kashe min zuciya.
Baba kayi hakkuri ka daina sa irin abubuwan nan a ranka kaga ba lafiyane a jikin naka bba yanzu.
Nan dai baba ya kara dan muna nasiha mukai masu sallama don dare ya somayi sosai.
Mun koma dakin mama mukai mata sallama tana ta saka muna albarka muka fito daga gidan.

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI DA ALLAH,,,
ALOKACIN MUKE,,,,,
Tunda nai wanan mafalkin na tashi jin kaina nake yana min wa ni irin ciwo gani banda sukuni a tare dani.
Haka na daure nai muna abincin rana tare da na dare a lokaci guda sai dai ina sake sake a raina kan mafalkin kabir da nayi may hakan ke nufi ne wai?
Kudi na fito dashi da abinci nace ma musa ya bayar min da sadaka a waje ya samu karamin yaro ya bashi.
Na gama shirya dining table da kayan abincin dana girka nashege daki na kara wanka.
Dogon rigan atamface a jiki dinkin shi mai hannu daya ya matse ni sosai rigan wanan dai kan sai zaman gida don da aka kawo dinki naita fada da anty maryam akan dinkin.
Ina fitowa ban san da dawowan shi ba sai ganin shi nayi falo kwance saman dogon kujera ya sa hannun shi daya ya rufe fuskan shi dashi.
Dagani tunane yakeyi ko may yake tunane oho sai da nakai daidai kan shi na tsaya daga bayan kujeran tare da dan rakwafowa saman kujeran nace.
Sannu da dawowa yaya kamar daga sama yaji murya na sai naga yai sauri cire hannun shi firgigit da sauri yana bude ido mukai arba dashi.
Cikin mamaki ya amsa min fuska a daure yana cewa yyawa nace akawo ma abin sha ne ?
Eh kawai ya,bani amsa na juya zuwa inda fridge yake, na dauko lemon five alive mai sanyi da cup.
A kasale ya mike zaune daidai ina isowa da drinks din a hannu na sai dana aje cup na bude lemon na fara tsiyayawa a cup din.
Na dauka tare da mika mashi sai naji ya sauke ajiyan zuciya yana karba daga hannu na.
Sai da na samu kujera na zauna ya kai cup din a bakin shi ya fara dan kurbawa a hanlali tare da lumshe idanuwan sh.
Sai da ya kurba kusan sau biyu naji ya ce may ya hada ki da Amira ne wai ?
Shiru nayi ina wasa da yatsun hannu na kaina a kasa sai ji nayi yace bake nake tambaya ba ne ?
Nace wallahi yaya ni ban san wani abu ya taba hada ni da ita ba.
Kwayar idona ya daga idon shi ya kalla don tabbatar da maganan da nayi yace kin tabbatar da hakan da gaske ba abin da ya hadaku bayan bana nan ?
Kai kawai na daga mashi da eh haka ne din amsa na .
Yace shi ke nan ai idan ma wani abu kikai mata ai zanji don zan dauki mataki akan hakan.
Don ba zan yarda matar da nake aure ta wullakanta min yan uwan haihuwa na ba ko kadan.
Dan murmushi nayi nace nima ai yan uwana ne don banda wanda sukafi a garin nan yanzu don may zan mata wani abinda ranta zai baci akaina.
Wanan kuma ai matsalar ki ce ni dai kin ji may na fada maki ai sai ya mike tsaye zai fara tafiya nake cewa abin yana saman dining tun dazun.
Sai nayi sallah zanci ya bani amsa ba tare da ya juyo gare ni ba nan nabi bayan shi da kallo kawai.
Dogon mutum ne sai dai ba irin can din nan ba kuma karfafa ne mai fadin kirji ga shi da dan dogon fuska da hanci irin zubin fulananin kasan sokoto sak dashi.
Musa ne ya dawo yana cewa anty na dawo dazun na samu bakya falo.
Sai a lokacin na dawo daga tunanen wanan zaman da baudaden mijina da nakeyi.
Don nidai yanzu ban san kuma wace irin kulawa ake so na bashi ba wanda yafi wanan da nake mai yana mai dani kamar wata shakatafi can.
Na saki ajiyan zuciya a fili tare da dan murmusawa nace ga abinci can fa na zubo maka ne musa.
Yace anty lokacin sallah yayi alwala na shigo nayi naje massalaci hakan yasani mikewa nima na shiga don nai sallah.
Bayan na idar da sallah ban mike ba ina zaune a gurin da nai sallah na dan jingina jikina da gadon dakin sai tunane nakeyi.
Shine ya shigo dakin daga kofa ya tsaya yana fadin abinci fa ?
Sai da na shafa nace gani tafe har musa ma yana zaune falon nashigo.
Direct dining na nufa na fara kokarin bude kulolin abinci lokacin suka karaso suka zauna.
Sosai yake cin abincin hankali a kwance sai can ganin ban zuba nawa ba yake cewa ke bazaki ci bane nace na koshi.
Da sauri ya kara dago kai hannun shi rike da spoon din da ya debo abinci zai kai a bakin shi yake cewa.
Da kikaci may kika koshi nace breakfast din da mukayi dazun bana jin yunwa yanzu.
Tsuki yayi yace will eat now my friend ban son wasa da yunwa kada ki jawo wa mutane matsala.
Na dan turo baki tare da tabe fuskana nace ni wallahi ban jin cin abinci a koshe nake yace ko kici ko na dura maki shi yanzu kuwa.
Dole na zuba kama spoon hudu na dan fara ci sai dai kuma na kasa ci sosai don banjin ci din.
Daga inda yake zaune ya taso sai ganin shi nayi a gabana yana fadin oya open your mouth.
Wani kallo na watso mashi nace ni wallahi na koshi musa na ganin yaya ya mike ya nufe ya mike dama yagama cin nashi yafice a falon bayan ya dauke plate din.
Ganin da nayi da gaske yake zaiyi feeding dina da kanshi yasa na fara tura sauran abincin da sauri a bakina yana tsaye yana kallo na gani saura kaman spoon daya yasa shi jan tsaki yace kan cin abinci sai na saba maki a gidan nan.
Tunda na gane so kike kija min fita gurin maji tace na barki da yunwa cuta ya kamaki don sheri.
Ina gamawa na kora da ruwa tare da dan dafe kaina a hankali wanan ai cin zalin ne na fadi a hankali na dauka ya wuce ne ashe yajini.
Sai kawai naji ya kamo min baki yana fadin wanan bakin mai bakar magana da tsiwan tsiya sai na yi maganin shi.
Zan bude baki nai magana sai hannun shi naji a bakin nawa mikewa nayi don na gudu sai ji nayi ya rugumoni ta baya ya matse ni a jikin shi.
Cikin wata yar kara nace don Allah yaya ka sake ni na daina wallahi kayi hakkuri please ka sake ni.
Maimakon ya sake ni sai ji nayi ya kara rugomoni sosai ajikin nashi ya shiga bin jikina a hankali.
Kafana naji ba zai dauke ni ba a loka in don irin abubuwan da yake min a lokacin.
Sosai ya matse ni yadda ran shi ke so a lokacin kuma gashi na kasa hana shi.
Sai ganin abin nashi yana son wuce gona da iri nace cikin wata kasalaliyar murya don Allah dai yaya ka kayi hakkuri na tuba na daina zan dinga ci.
Hannun shi yakai a kirjina abinda yasani saurin zillewa da karfi nai kasa ke nan da sauri Allah yaban sa,a ya sake ni.
Wani irin numfashi ya sauke tare da shafo kan shi ya juya zuwa dakin shi ya barni a gurin a tsugun ne.
Cikin jin haushin abinda yai min naja kafana zuwa dakina saman gado na fada a rigingine idanuwa suka shiga kawo hawaye a lokaci guda.
Na furta ya Allah ka bani ikon cinye wanan jerabawan da nake cikin sa a cikin sauki.
Shima dakin shi ya shiga kwantawa yayi yana mamakin kan shi don bai san yadda akayi har kai ga taba wanan yarinyar ba haka yau.
May yake bukata gurin wanan yar kaunan bayabayan shi haka ne wai ?
Sai kuma yai murmushi zuciyar shi tace may tarasa acikin abubuwan matan da kake bukata ita .
Ba gashi yanzu yanzu kashiga wani bakon yanayi ba a zuciyar ka ka kasa controlling din kan ka akanta sai da ka dan taba ta ka samu natsuwa a ranka.
Ranan bai kara fitowa ko falo ba yana ciki a kumshe nima dai hakan ne ina dakina a kwance don yanzun haka kunya yadda zan hada ido da yaya yau nake ji.
Yadda yau ya hagula min jikina haka son ranshi yanzu a haka yana mashayi zan dinga bashi jikina yana yadda yaga dama dashi son ran shi.
Oho ni Fatima naga ta kaina zama da mashayi hada jiki dashi don raya sunnan ma,aiki don gujewa zunubi a kaina.
A hankali na lumshe idanuwa na har tsawon wani lokaci sai tunanen makomar rayuwa na ke yi kawai.
Bayan sallah la,asar naji fitan shi daga gidan haka yasani sauke ajiyan zuciya na fito falo na zauna da musa nan mukai ta hira akan matsalan mahaifin su.
****** ********* ******
Har kwana biyu ba wani abinda ke hadani dashi don tun ranan da ya matse ni ban yarda sam mu hada ido dashi bani ma fitowa sai naji baya gidan zan fito falo na zauna.
Yau tun safe sai nake jin bacin rai a zuciyana haka naje makaranta na dawo ban iya anyana komai ko a school.
Tunda na dawo bai gidan har karfe tara na dare ganin bai shigo ba ya dan sani cikin dan damuwa.
Ina son kiran wayan shi amma na kasa don gada ya dauka wani abune kuma zan tsiro mashi.
Musa yace min anty zan kwanta barci nake ji nace tun yanzu yace wallahi yau wasan kwallo nayi da yan unguwan nan kuma naje gidan anty maryam nai ta hawa keke da yaran unguwar kina school.
Ganin ni kadaice a falon yasa ni mikewa don nakashe tv dake aiki naje na kwanta.
Kofan shigowa aka turo tare da shigowa falon tafe yake cikin dan sagala corth din jikin shi ga kafa dan shi.
Kallo daya nai mashi na fahinci yau yayi halin shi na baya ke nan saboda yadda nagan shi yana tafiya.
Ban ko ce mai sannun da na saba ba yazo ya wuce ni hakana ya shige dakin shi.
Dakina na nufa raina a bace har na kwanta na tuna baici abinci ba duk yinin ranan.
Gashi nasan halin shi tun a gida baya cin abinci a waje shi duk inda yatafi sai ya dawo gida yake cin abinci.
Mikewa nayi tare da bude kofana na nufi dakin nashi a lokacin.
Ina tura kofan yadda na samay shi zube a kasa saman center carpet din dake tsakiyan dakin baki gado a kwance rigigin ne dashi.
Yadda na ganshi kwance sai tsoro ya kamani ga rigar shi ta sama ya wugar a gefe daya.
A hankali na karasa gaban shi idanuwan shi suna rufe alaman barci ne ya dauke shi a haka.
Durkusawa nayi a gaban shi idanuwana suna fitar da hawayen bakin ciki.
Hannu nasa a hankali na fara cire mashi takalman kafan shi sai socks da na fara zarewa a hankali.
Idanuwan shi ya bude a hankali ta dan kalle ni ban daina abinda nakeyi mai ba sai da na cire mai takalman da socks din a kafan shi.
Yace da kyat cikin wani murya ciki ciki leave me alone Fatima i want be alone for now.
A sanyaye nace mashi ka tashi ka haugadon ka ka kwanta please.
Ya lumshe idanuwan shi yace ki bar ni a nan iam ok here.
Nace ka tashi please ka haugado kada ka kwanta haka a kasa please sai na mika mashi hannu da niyar nakamashi ya mike zuwa kan gadon na shi.
Shima hannun ya mika min sai dai karfi ba daya ba sai maimakon na dago shi ya mikw sai jana yayi zuwa jikin shi.
Tankar na kurma ihu a lokacin don irin yadda nake jazuciya na a lokacin.
Kokarin mikewa nayi amma sai naji ya sake rike ni a jikin shi tare da fadin shiii
Idanuwa na na lumshe cikin bacin rai, don na gane may yake nufi da hakan da yace min wai nai shiru.
Yayi wani irin jan numfashi har sai da naji shi a cikin raina a lokaci guda.
Cikin karfin hali nai magana a hankali nace ka tashi ka hau gado ko kai wanka ko zakaji karfin jikin ka.
Ya kara bude idanuwan shi da kyat yace tunda kina son inyi kamani nai wanka please ?
Mikewa nayi da na samu ya sakeni na nufi bathroom na hada mai ruwa da kyat na samu ya mike yana rike da hannu na na dago shi rike da hannu zuwa kofan shiga bayin tun a gabana naga yana kokarin cire kayan jikin shi haka yasa ni komawa baya da sauri na bar dakin.
Muryan shi naji yana fadin don't go anywhere na fada maki ko na bata maki rai.
Na ja na tsaya tare da rintse idanuwa na shiga wani irin damuwa mara fasalin fadi.
Gurin wardrobe din kayan shi na nufa na ciro mashi wasu kayan barci na aje mai saman gadon shi.
Na tattara kayan da ya cire na watsa su inda yake tara kayan wankin shi.
Fita nayi zuwa kitchen na hado mai ruwan shayin da yake sa na dafa mai duk dare.
Na shigo dakin da flask da cup a hannu na yana zaune saman gado daure da towel a jikin shi iya kugun shi.
Sai da na aje flask din nake cewa ka sanya kayan ka gasu nan a gefe na aje maka.
Bai yi magana ba sai kallon kayan da na aje mashi saman gadon yayi kawai.
Na sake cewa ga ruwan shayin ka nan idan zaka samu sha yau.
Bina kawai yayi da ido kamar a ranan ya fara gani na.
Juyawa nayi sai muryan shi naji again yana cewa kada ki fita ki tsaya a nan zaki kwana.
Dam dam naji gaba ya bada na dago kai da sauri ina kallon shi.
Sai kuma naji jikina yai wani irin san yi cikin sanyi murya nake cewa zan je na kashe wuta a dakina.
Daga haka nafita daga dakin na dade zaune a bakin gadona ina faman tunane kala kala a zuciyata.
Banda yadda zanyi dole na mike na shirya yadda ya dace mace tayi idan zata turaka gun maigidan ta kwana.
Kwace na samay shi a dakin yayi dadaya a saman gado hakan yasa na gane cewa yayi barci ne a lokacin.
Duban flask din da na aje mai nayi yana nan yadda na barshi bai taba ba, a hankali na taka gefe daya na gadon na kwanta a hankali kada yaji motsina ya falka.
Nasa hannu na kashe wutan dakin na makure a gefe daya a tsorace don yauce karo na farko da zan hada makwanci da na miji.
Kuma sai gashi mijin sunnan nawa a buge yake a cikin kayan maye don dole kuma nai mashi biyayya a hakan.
Cak naji hannun shi a saman jikina tare da mirgino ya kan kamay ni a hakan.
Ji nayi duk da ina a tsorace ya sake wani irin ajiyan zuciya lokaci guda idanuwa na naruntse cikin jin kuna haka a raina.
A sannu yafara bin part din jikina yadda yake so sai runtse idanuwa nake don bacin ran dake addabana a lokacin.
Sannu sanu yake komai zakace ba,a cikin maye yake ba a lokacin, don irin yadda yake takon sallon shi a gare ni.
Duk irin yadda nai tsanmani zai kasance don a buge yake abin na sadauki ya wuce haka.
Don sosai ya canza min sallon shi a ranan wani irin mahaukacin soyayya da maza keyi ya nuna min a wanan daren don sai kusan asubu nasamu ya sarara min.
Nai kuka nayi ihu nayi yakusa duk a banza nakeyi don babu maceci a cikin wanan daren gare ni.
Haka yasa barcin dana dan samu yasa mu makara sai guraren tara na safe na falka da kyat na bude idanuwana da sukai min nauyi.
Dakin nake bi da kallo har nakai idanuwa na inda yake kwance ya kifa cikin shi daga shi sai dan towel din daya yafa daga saman shi kadan ya rufe al,auran shi dashi.
Da kyat na iya mikewa a hankali na lalubi rigar barci na dayake a kasa yashe, na nufi kofan dakin bayan na saka rigan.
Nabar dakin zuwa dakina a falo naji motsi a kitchen ashe musane yake min wanke wanke a ciki.
Dakina na shiga na fada bayi tare da sake majikina ruwan masu zafi ban san lokacin da na saka kara ba.
Sai da na gasu sosai a cikin ruwan sannan nai wanka tsarki na fito da kyat na tayar da sallah.
Haka na daure nafito na hada abin karyawa wanda dakyat nagama hadawo don zazzabin da ya rufe min jikina a lokacin.
Dakina na koma na kwanta ke nan wayana dake gefe na yai kara a lokaci daya da kwanciyana.
Maryam ce ina dauka take cewa banga kin shigo school bane yau madam.
Da kyat na iya bude bakina nace banda lafiya ne yau anty tace subbahanallahi may ke damunki Bintu?
Maimakon na bata amsa sai na sa mata kukan takaici kawai hankalinta a tashe tace kashe wayan gani nan zuwa yanzu.
Zazzabine mai karfi ya rufe ni a lokaci daya ina dunkule a cikin bargo idanuwa a rufe naji an shigo dakin.
Bai min magana ba sai tsayawan da yayi yana kallon yadda nake kaduwa a cikin bargo kawai.
Takawa yayi har bakin gadon tare da yanen bargon a hankali dunkule nake idanuwa na a rufe hannun shi yakai a saman wuyana a hankali.
Zanfin da yaji a jikina yasa shi faduwan gaba don shi kanshi yasan yadda yai min bai kyauta min ba a daren jiya din.
Dan tsuki yayi tare da daure fuskan yace ke nasan idon ki biyu may ke damun ki ne haka ?
Nikan gyara kwanciya nayi tare da kara dunkulewa dakyau guri guda.
Muryan maryam ce dakw ta kwada sallama daga kofa yashi amsawa tare da fitowa daga dakin suka gaisa yana tambayan lafiyan ta.
Tace ina Bintu take ?
Ya bata amsa da tana ciki ya wuce baiso shigowan maryam gidan ba a lokacin.
Da sauri ta karaso gareni tana cewa Bintu subbahanallahi ashe serious ne haka may ke samunki ne wai haka ?
Banda lafiya kawai na bata amsa dashi tare da kara dunkulewa kawai.
Fita tayi ta samay shi zaune yana cin abincin breakfast tace yaya an ashe Bintu bata da lafiya ne naje school ban ganta ba shine na biyo ta nagani.
Yace mata Umm kawai yaci gaba da kurba shayin shi kawai.
Ta sake cewa tasha magani ne to ?
Yace may tace maki yana damuntane ?
Batai magana ba sai dai hawayen da naga tanayi kawai a idanuwan ta.
Bari yanzu zan fita na sayo mata magani yabata amsa tace ba,a zuwa asibiti naji zafin jikin sosai ne fa.
Yace fir god sake ki barni da surutun nan kamar wata yar jarida can nace maki zan sayo mata magani yanzu idan na karya ko?
Shiru tayi ta mike zata koma dakin yaks cewa ba barci takeyi ba ki barta kawai ki tafi ai ina gida bazan tafi nisa ba .
Kallon mamaki tai mashi kamar mara gaskiya kodai yaiwa yar mutane wani mugun abune wai.
Bari nai sallama da ita na tafito ke zo ki fice min a gida ban son gulman tsiya ya fadi cikin daure fuskan shi.
Da mamaki take kallon shi batai magana ba ta juya zata fita yace ke dakata sai taja ta tsaya guri daya yace idan naji kin fadawa wani Fatima bata da lafiya wallahi sai na saba maki harda munafukin mijin ki kuwa.
Fita tayi daga gidan kamar yadda ya umurce ta gida ta koma bata koma school ba ranan.
Bashar yai mamakin ganin ta a gida yake tambayan ta ko lafiya ta dawo a lokacin .
Tace lafiya sai dai Bintu ce wallahi bata da lafiya sosai naje gidan kuma yaya ya koreni harda gargadina idan na fadawa wani sai yaci mutunci na.
Dariya taga Bashar din nayi mata yace ai maganin ki ke nan ina ke ina zuwa gidan mutane gulma kuma.
Shima fa haka yace min yace kingani tace wallahi yace kokai na fadawa sai ya saba min .
Dariya yayi yace mugu yasan abinda yaiwa yar mutane shine yake jin kunya mana kada aji.
Kallon shi tayi cikin mamaki tace may yai mata yaya yace auke kin manta da naki ke nan ko abinda akai maki da kikazo gidan nan kika lamay muna ahine shima nake ganin yau yai mata.
Sai wani shu,umin murmushi ta sake tace Allah sarki Bintu har tabani tausayi wallahi.
Amma kuma shine don keta zai hana a taimaka mata wallahi yaya sadauki mugune Allah, bakaga yadda ya sha min toka ba wai na fita na bar mashi gidan shi.
Sun kai wani lokaci da Bashar suna maganan cikin tausaya min ya fita yabar gidan.
Kiran wayan Sadauki yayi yana ina yace yana gida kuma bai samun fitowa yace gashi tafe kafin yace kada kazo har Bashar din ya kashe wayan shi ko.
Ina kwance naji yana tabani cikin barci na bude idanuwa na da kyat shine tsaye da cup din ruwa da magani a hannun shi.
Yace cikin daure fuska tashi kisha magani nace a hankali naji sauki ban sha sai ya tuna ban son shan magani dama yace idan baki sha ba wallahi zan kira ai maki allura yanzu ragguwan banza kawai.
Jin za ai min allura yasa namike da sauri ina hararan shi na karbi maganin nasha da kyat na iya hadewa.
Na koma na kwanta ina wai wai tare da kara rufe kaina gyara min kwanciya yayi ya kashe A C dake aiki a dakin.
Yafita falo ya koma ya zaina shida musa yana fada ma musa wai yau banda lafiya ne shiyasa nake kwance.
Can yaji anshigo gidan ya daga kai Bashar ne ya gani yace cikin daure fuska kai kuma may yakawo ka ne wai nace ma yau hutu nake so fa.
Yace au don nazo nayi laifi ke nan ko yace dana sani na wuce school wajen madam dina yafi min zuwa nan ai min wulakanci haka.
Ya zauna yana fafin kaunata tana school ita ma ko ?
Yace bataje bata jin dafin jikin ta yau da sauri bashar yace subbahanallahi may yasa may ta kuma ?
Sai da yai dan tsuki yake cewa fever ne kawai ke dan damun ta.
Kallon yadda sadauki ya daure fuska yayi ga dariya nadon kamashi amma ya dake inda ya yakushe shi a wuya da gefen fuska dana wuya yace subbahanallahi may kuma ya yakushe ma fuska haka kamar kayi dabe da mussa haka?
Yace kai dan iska ban sani ba mutune kaman yan jarida dakai da matarka ban san wanda yafi gulma ba wallahi.
Don Allah daka ta man kaman fa kasha yakusa nake gani jiya dakata mu gani mana.
Filon kujera dake gefwn shi ya dauka ya jefa mashi a fuska ya cabe yana cewa oho yanzu nagane kace min ka shigo gari kawai mutumina.
Fita min gida kaima watau munafukan matar ka taje ta fada maka shine kazo don ka karas da idon ka ko ?
No kadain kiramin da mata munafuka ni Maryam bata dawo gida ba tana makaranta kuma ba abinda ta fada min zuwa nayi mutafi illela gurin zancen kayan nan da zasu shigo muna.
Yace cikin taba baki ni yau ba inda zan tafi don wanan raguwar banzan ta kawo min cikas sai shegen rakin tsiya kamar wata jaririya can da ita.
Kai man wallahi ka fadi gaskiya abinda ake lalashin mace kodai kai kai mata may gaba daya ne wai ka illanta masu yarinya ga banza saboda alluran ku na yan kwallo na maka caji ko ?
Kaidai dan iska ne wallahi bashar kashe ta ma nayi ba illantawa ba bar gida don Allah naji da abindake damuna ni please.
Sai yaja tsuki yace ni wallahi maji ce bani ma son taji zancen nan Allah, bashar yace a ina zataji shi.
Gurin maryam mana bashar yace haba kai ina tana ma fara fadin wan nan magana ina bazata fadi ba zanyi warning din ta ai.
Amma sai dai sun makara don suna magan har maryam takira wayan mama tana fada mata cewa maji yaufa sai ki dafawa yarki bagaruwa don komai zam wallahi.
Murmushi maji tayi tace masha Allahu nan take cewa sai dai bata da lafiya tana can nade kuma na tafi yaya ya kore ni.
Suna gama waya mama tashirya sai gidan mu wanan ne karo na farko da tazo gidan namu tun bayan gama bukin mu.
Suna hiran su a falo suna dariya sai jin sallaman ta sukayi a falon kawai.
Damm gaban shi ya fadi ya dukar da kanshi a kasa haka kawai yaji yau ba zai iya hada ido da maji din ba karo na farko kenan a rayuwan shi.
Suna gaishe ta bata tsaya amsa masu ba da dadi take fadin ina dakin fatiman yake ne da hannu ya nuna mata.
A hankali tasa hannu ta daga bargon da nake ciki a rufe a lokacin saboda maganin da nasha har na fara zufan jin sauki fever ya dan sauka min sai dai jikin nawa akwai sauran zafi still.
Jin an tabani yasa na dan bude idona a hankali mamace na gani tsaye a kaina tace Fatima yaya jikin naki ina kokarin tashi take ce min koma ki kwanta abinki.
Kinsha magani ko nace mata cikin karfin hali eh mama ta kara min sannu da jikin na amsa da kyat tare da dan mikewa zaune na dukar da idona sam ban iya hada ido da mama din yau.
Bathroom naga ta nufa saida ta cika kwamin wankan da ruwa ta kawo wani gari ta zuba tace na tashi nashiga ciki na zauna zan dan ji daman jiki na taimin sallama ta fita abinta.
A falo ta samay sunyi zaune zugun da su sai jira yake yaji fadan da zatai mai sai dai tanafito ta dan zauna tana cewa nashigo ban tsaya mu gausa ba hankalina ya daga naga hakin da diyata take ciki.
Tace sai ai ta hakkuri da mata Allah yai maku albarka yabaku zuria dayyaba na gari masu albarka irin ku.
Ni zan koma sai anjima kazo ka dauko maku abinci kazo dashi tunda nasan bazata iya komai ba ita.
Mama ta mike ta fita tana masu sallama ta wuce zuwa gida nan ta barsu zaune cikin kunya.
Yace sai na batawa maryam rai wallahi haba dai akan may kuma may taimaka zaka saba mata kuma daga taimako
Kwarai naji dadin abinda mama ta taimaka min dashi haka yasa dana fito ban kwanta ba sai yunwan da nake ji kawai.
Shigowan shi dakin yasani saurin dukar da kaina yace yaya jikin naki da sauki nace mashi kawai.
Kin karya kuwa ya tambaye ni cikin son sani ko na karya sa safe nace a,a a hankali juyawa yayi yafita daga dakin.
Zuwa can sai gashi ya shigo dauke da cup din tea mai kauri a hannun shi daga gefe na ya zauna tare da mika min cup din.
Yana fadin ki shaye shi don ki dan kara samun saukin jikin naki wayan shi ce tai kara ya dauka sai da suke magana na fahinci da mama suke magana .
Yadda suke magana na fahinci mama tana cikin matukar farin ciki da walwala a tare da ita tana cewa ka fara ganin al,amarin Allah ko.
Nikan raina kamar an fasa min guduma tsakiyan shi nake ji don nasan dada shike nan ni tawa ta kare ke nan.
Shiko sai wani lumshe idanuwan shi kawai yake abu ya taru yai mai yawa a zuciyar shi.
Na farko tunanen irin ni,iman da ya diba daga jikin yarinyar da yake ma kallon kitse saman ruwa don bai taba zaton haka zai samu ba daga gurin Fatiman daya raina da farko .
Suranta sai gizo yake mashi a idanuwan shi ya kasa mantawa da abubuwan da suka faru a tsakanin a daren jiya din.
Idon shi ya sauke ga dogayen yatsuna dake rike da kufin da nake kurban shayi a hankali bai san lokacin da ya sauke wani irin ajiyan zuciya ba wanda har yasa na dago kai ina duban shi.
Sai kuma nauyi da kunyan yadda ya kasa sarara min har takai yai min rauni a jiki ance dama dan hakin da ka raina shikw tsona maka ido.
Nauyi da kunyan maji sun rufe mai zucita don bai taba tsanmanin cewa akwai wani rana da zaiji nauyi da kunya maji ba sai ya din nan.
Kofin nake kokarin ajewa a gefe ya kura min ido cikin daure fuska yake cewa kin shanye ne.
Na dan marairaice ina cewa, nasha yaya hannu ya miko min yana karban cup din gani sauran tea a ciki yake cewa wanan fa ?
Na dan marairai ce nace na koshi yaya please tausayi na bashi ya dauki cup din ya fita dashi.
Ba,a dauki wani lokaci ba saiga sako daga mama ferfesu ne na kaji da kayan cikin rago sunji kayan kamshi na gargajiya, sai kuma gassan naman rago mai zafi .
Da kanta ta bugo min waya akan na tashi na ci abin da akakawo tare kuma da jaddawa yaya akan ya tsare ni naci sosai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
IDAN KUMA KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA NA BARKI GA ALLAH YAR UWA,,,,
Zama muke na zaman kwari tsakanina da Amira don iyanzu takai ni inda bani son mukai tun farko da ita.
Ina zaune a dakina naui zugun ina tunanen irin wanan halin takuran da Amira take kawo min har a cikin gidana.
Sai hakkuri nake tayi ina hadiyewa don ban son mahaifiyar su su sami labarin halin da muke aciki.
Amma ranan da maryam tazo gurina ta fahinci akwai matsala a zaman mu da Amira.
Gaba maryam ta sakani sa tambaya iri nata har dai na warware mata duk irin zaman da mukeyi da kawayen ta da take kwaso wa su zo su dinga min abu isa isa a tsakar gidana.
Rayuwan maryam yai matukar baci tamike tana fadin wallahi sai tayiwa Amira magana
Amma na sha gaban ta na bata hakkuri tare da fadin idan Allah ya yarda ni da kaina zan dauki mataki a kan ta.
A kwana atashi ba wuya a gurin Allah sai ga shi yai har wata daya da kwana goma sha da tafiyan yaya sadauki.
Munan da Anty Amira muna ta kwamawa a cikin gidan don gaba daya yanzu na fitar da tsoron ta ko shakka da kawaicin ta da na ke ji da farko .
Karatuna nake don yanzu exam mukeyi hutu zamu fara next week banda wani lokaci sosai na kaina a gida gaba daya.
Tsaye yake idanuwan shi suna a lumshe dan murmushi ne ya sake don tuno da yanayin Fatima, da murmushin ta da take a boye tsiwanta da fushin ta da takeyi a lokaci daya ,
Sai dai kuma duk karancin shwkarun Fatima hangen nesa ta da kyakyawan zuciyan ta da manufan ta akan kowa haka halitta ne a gare ta.
Yana gyara tsayuwan shi yake cewa Fatima ke ba diyan masu hali ba amma kuma kina da,diyauci irin na masu halarci.
Su iso Lagos da yamma don ta nan jirgin su ya sauka Nigeria a gurin su basu dauki tafiya a bakin komai ba don haka ya tsaya yai clearing din kayan shi da ya shigo dasu.
A lokacin mun kammala exam na dawo gida satin nan ba fita duk wani motsi na da,wani taku na yana kan idon Amira da ta saka min ido a agidan.
A kullun tunanenta shine yadda zata kawo was Fatima cikas din rayuwa ta hanata jin da dadin rayuwa a gidan Sadauki.
Don ita Amira a watau ta sune yan uwanshi na jikin shi sune ya kamata suci arzikin shi fiye da,wata mace can da tashigo da sunan zaman auren sai su mamaye komai na miji ya zama na au suda yan uwan su kawai.
Shiko miji da dangin shi sai yadda akayi dasu kawai a gidan sun zama yan bi ke nan a dinga juya su yadda rai yaso,
Hakan ke matukar bankan ta mata rai ita bata kaunan ace dan uwanta sai wata ta bata doka akan shi Amira na cikin irin jinsin mutanen dake adawa da matan yan uwan su maza a duniya.
So take sai yadda tayi da shi da matar shi sai dai ta dinga bada commad ana bi kawai shine zaman lafiyan kowa da ita don bakin ran ta da yai yawa.
Takan ce dan uwa dai dan uwan tane babu mai raba shi da ita don a tare aka gan su don haka sai dai mace ta kare kutin gwilar ta tabar da dan uwan ta saboda babu wanda zai kawo wani shamaki a tsakanin su.
Haka mukai ta zama da ita a cikin fitina da gori habaici bakar magan cika baki sai dai wanda ba bu shi don duk nagani ga Amira lokaci guda.
Gashi kuma yadda take samun, gashin kanta yanzu a gidan namu tayi kiba tai fari ta kara dan girma da ita.
****** ********* ******
Suna zaune falo da kawayen tabar gazan ta wai su wayayyu su salma kubura da Fauziya sai jin motsin turo kofan shigowa falon gidan sukaji.
Idanuwan su na kan kofan don suga mai shigowa falon a lokacin don yanzu sha daya saura na safe muke ciki.
Cikin mamaki Amira tace yayana dama yau zaka dawo ashe bai amsa mata ba sai bin falon yake da kallo cikin mamaki bayan ya gama kallon fuskoki wa yanda ke zaune a falon lokacin.
Daya bayan daya yake kallon su har ya kai karshe Fatima bata falon.
Hakan yasa shi wuce wa direct dakina yagani don sai yaji zuciyar shi tana mashi wani irin kuna a lokaci guda.
Yana bude kofan zaune nake na sallamay sallah walha, ina dan jan tasbaha bayana yana jingine da fadon dakin
Jin an turo min kofa yasani saurin dago kai ina kallon kofan dakin wanda nagani a tsaye ya harde hannayen shi guri guda yana min murmushi yasani saurin dan sakin murmushi tare da yunkurawa in tashi.
Na nufoshi a a cikin fara,a ina cewa sannu da zuwa yaya yaya hanya ya can ?
Murmushi yayi tare da,ware hannayen shi na sheko da dan gudu na na shige ciki ya mayar da hannayen shi ya rufe ni dasu .
Sai da muka dan dauki lokaci a haka muna shan dumin junan namu ne yake cewa cikin wata irin shakkakiyar murya su waye nagani a falo kuma a ina suka fito hakane da au kuma ?
Nai dan murmushi tare da dan dago kaina daga jikin shi nace ban san da ga ina suke ma amma kullun dasu muke wuni a gidan nan sai dai na girka na basu idan kuma sun gama na kwashe na gyara gida idan da duk ya baci.
Yace a bisa ga umurnin wa hakan ke faruwa min a gida ban sani ba nace umurnin second command ne Anty Amira don haka sai ka tambaye ta bayanin komai.
Ina rike a hannun shi yaja hannuna zuwa falon muna shiga suna ganin mu suka sauri dawo da hankalin su a gare mu irin yadda suka gan mu a tafe ne ya kara daure masu kan su.
Zama mukayi a saman kujera daya nidashi ya dago fuskan shi dake a daure yana fadin wa yan nan kuma fa daga ina suke ne haka ?
Shiru babu wanda ya amsa ya dago kan ahi yana kallon inda nake yake yana cewa nace su wayen haka kuma don ban san su ba.
Nace ka tambayi anty Amira don tare na gan su dasu kuma ta fada min sunfini daraja a gidan nan kaga ni dole sai dai na bisu don yan uwankane na ji aiko.
Sai dana fadi haka ya dago kai ya kalli inda Amira take zaune wani irin haushin ta ne da kiyayyan ta ya darsu a zuciyar shi a lokaci guda.
Yace su waye haka kika tara min a gidana sai cewa tayi yaya sadauki salma ce fa diyar gidan baba prof da take mutuwan son ka wace nasha fada maka zancen ta tana karatu a london yanzu itama tagama ne ta dawo gida.
Wani mugun kallo ne ya watso mata yace kina da hankali kuwa Amira look kwashe min wanan mugun tarkacen da kika tara min a gida don yanzu na gama sanin inda kika dosa.
Salma da ta zage akan ta aamu shiga tunda ta samu kaunar shi nason ta sai yadda tayi dasu.
Dalilin ma da aka kitsa ke nan su dinga zuwa gidan don ta san halina da kuma yadda zata saba da gidan kafin ta shigo.
Haba UF inji salma data mike tsaye tace kaima kasan da ina son ka shi yasa kaga har nazo gidan ka kawai .
Amma daba, son ka nakeyi mai zai kawo ni wanan nan gidan nazo na zauna har wanan yar matsiyatan daka aje tace zata kawo muna raini kawai.
Don mun sauki cups din amfanin ka ta kama muna haushi ai badon Amira da ta dauki mataki a kanta ba da na so na gwada mata koni wacece.
Wani irin kallon mamaki kawai yake masu take idanuwan shi suka rikide zuwa ja kamar gauta a lokaci daya.
Yace cikin wani irin murya please get out in my house before i take a desition on you.
No no UF kada kace zakai min haka please already mun riga mun gama maganan nan da kai ko.
Tazo har inda mukw a tsaye tana cewa tare da nuna ni da hannun ta wa an yar kauyen matar taka bata dace dakai ba don tafi dace wa da masu gadin ka kawai.
Fauuuu muka ji kara mari tace ido rufe maza su kwashe subar mai gida mara sa kunya fitsararu ko mata sun kare a duniya mai zaiyi da ita mace da taje london ta gama watse wanta zai dauko ya kawo wa kanshi fitina a gida .
Tas yai masu suka fice simi simi da kunya wai su tantire sai gashi su hadu da wanda ya fisu iya fitsara yai masu tas gaban matar shi.
Wanan karon tare da tsaraban ahi ya shigo gari don koda su salma zasu wuce wata hilux data kwaso mai kaya daga airport tana sauke kayan a kofan gidan mu.
Ana shigo da kayan ciki yai tsaye yace Amira tafito ta wuce zuwa gida sai ya zo zai nemai ta a gida.
Aiko Amira ta ce yaya may kake nufi korana zakayi don munafukar matar ka tai muna hadi a gurin ka hau kazauna akai.
Babu inda zan tafi sai ka bude kayan nan a gabana kowa ya gani haka wancan karon nazo nai zaman banza komai baka ba.u ba yadda ka saba ta kwashe takai kauye inda,ba,a san darajan su ba ma.
Amira waiko anya kanki daya kuwa, ina dai gani kanki ba guda bane kawai don hakan da kikeyi abin naki ya zarce sanina gaskiya.
To bazan bude ba kuma maza ki kwaso kayan ki tun ban bata maki rai ba a gidan nan.
Idan Fatima ta kwashe abina nakine ta kwasa ko nawa ina ruwan ki da kayana Amira Fatima matatace ko kina da abinda zakiyi kan zaman ta matata.
Yaya ta furta tana mashi kallin mamaki tace kan Bintu kake fada min haka yaya Bintu fa Bintu dai.
Yace Idan na kara jin kin kira Fatima da Bintun nan da kuke kiranta dashi don rainin wayo wallahi sai kinyi mamakina Amira fito kawai ki tafi gida zan zo zamu hadu agidan ai.
Haka yai mata kora na kaskanci kan abinda tai min wanda tun yana can Bashar ya fada mashi komai duk irin halin da muke ciki da Amira a gidan, da bayana ranshi yai matukar baci shine ya zo muna a bazata batare da ya fadawa kowa zuwan shi ba.
Wanka ya shiga don ya rage gajiyan jikin shi ina kitchen ina hada mashi abinda zaici na juya zuwa dakin na shi inda na samu ya fito daga wanka na yana saka kaya a jikin shi.
Jin motsin shigowa yasa shi dan juyowa yana kallo na tare da sake murshi a fuskan shi.
Yace batare da ya dago kan shi gare ni ba mai yasa kika boye min halin da kuke ciki a gidan nan da Amira.
May yasa tun wancan zaman baki fada min ga irin rayuwan da kukayi da ita a gidan nan ba.
May yasa ki ka bari Amira ta tara yan iska suna wullakanta min ke ne haka a cikin gidana.
Ya dan dago kai kamar a fusace yake magana yace may yasa zaki boye min irin wana mugun halin da Amira taita gwada maki.
Nace yaya Anty fa yar uwatace komai tai min kanta taima bawai, ni kadai tai wa ba don wata rana zai bata mata rai yadda tai min din.
Nace yaya duk abinda Anty ke min a saboda kaine don taga ban cancanci na aure ka ba saboda matsayina bailai na hakan ba.
Sau dayawa nakan rasa laifin may nai wa anty Amira take min haka yanzu , sai da ta fada min akan gangancin da nayi na auren ka yasa take min wanan halin.
Hawaye ya gangaro min a fuskana nace yaya sadauki nasan nayi gangancin auren da matsayina baikai gare shi ba.
Haka kuma wanan ba shine irin rayuwan da ya dace dani bayar tallakawa kamata bata dace da irin ku diyan masu kudi da matsayi ba a duniya.
Ya sadauki kaima kanka kasani bankai matsayin da za,ace ka aure ni ba kasani ba irina ce ta dace dakai ba a gidan nan kamar yadda anty Amira ke fada min nima yanzu nasan gaskiya take fadi don ban kai matsayin hakan ba a gare ku.
Yaya kayi yadda yan uwanka da masoyan ka ke son ganin ka tare da,diyan attajirai irin ku masu matsayi a duniya bani yar takawan kauye ba Fatima.
Ba so tsakanina da kai sai zumunci na wa yanda suka tashi a daki daya irin na yan uwantaka kawai.
Kamata yayi ace na auri maigadin gidan ku ko wani dan aikin gidan ku wanda baida matsayi irina.
Sai faman kallona yakeyi kamar talabijin da mamaki ya lura ina a cikin damuwa da kuncin rayuwa mai yawa don bai taba ganina acikin irin wanan yanayin ba haka.
Sai na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya a lokaci guda na durkushe a bakin gadon shi ina rusa kuka.
Cikin kuka nace Allah kadai da mama suka san dalilin wanan hadin da sukai muna.
Amma da zaka daure ka auri wacce tafi dacewa da zama a matsayin matar ka hakan zai matukar saka anty Amira farinciki a rayuwan ta.
Hankalin shi yai matular tashi a lokaci guda yace tabbas Allah ba zai yafe min ba Fatima tunda nine yakamata na daukakaki a idanuwan mutanen duniya tun farko Fatima amma na kasa yin hakan.
Matsalar duk nawane da na kasa fitowa fili na nuna cewa ina matukar son matata batare da duniya na mata kallon wacce aka tilsata min da ita ba.
Dole ne komai yacanza daga gareni yadda kowa zai iya fahintar Fatima ta wuce yadda suke tsanmani a gurina.
Ahankali ya tako zuwa inda nake a tsugun ne ina kuka shima ji yake kamar ya fashe da kuka a lokacin.
Ya dago ni tare da kokarin mikar dani tsaye ya rigumay ni zuwa jikin shi muka zauna saman baki gadon shi a hakan.
Yace Fatima ki kwantar da hankalin ki ki saurare ni dagani har ke zan iya ce hada mu akayi amma kuma ba bisa kuskure ba.
Maji ta fahinci kiyayyan mu ba kiyayya bace illa kainace mai wani sabon launi ta hango abinda mu bazamu ita hango aa kan mu bane a lokacin.
Fatima komai nawa ya canza a rayuwana adan zaman nan da mukayi dake tunane yanayi da komai nawa yanzu ya canza min a dan lokaci guda.
Don haka ki fitar da zance su Amirah da wanan salman a ranki ,kimai da al,amarinki ga ubangiji don shi yafi mu sanin me ke boye yafi kowa sanin abinda bamu sani ba gaba dayan mu.
Sannan ina son ki saka a ranki daga yau ni Umar faruq sanda ina sonki Fatima, ina kuma kaunar ki fiye da tsanmanin ki Fatima ke alheri ce babba a gare don ko nina tabbatar da hakan da kaina.
Ina maki so na hakkika Fatima wanda ban taba tsanmani akwai wata mace bayan uwata da zanyi wa wanan irin son ba a duniyan nan.
Ni Umar Faruq nai alkawari har ga Allah zan rike amnan da mahaifana danaki suka bani akanki zan .
Zan taimakawa rayuwan ki naga kinyi abinda kikayi niyaryi, zan taimaka maki tako wace hanya inga burin ki yacika akomai.
Ki sani yaya sadaukin ki nai maki alkawari Fatima muddin muna a raye insha Allahu zan maki komai don wanan Umar din zuciyar shi da gangan jikin shi wanan kirjin da kike son kwanci akan sa duk nakine ke kadai Fatima zarah,.
A kullun zaki kwanta akansa kuma zan share maki hawayen ki harta inda baki zata ba Fatima.
Fatima muddin ina a raye duk abin kike so shi zan maki don haka ki share hawayenki Umar nakine ba wani wanda zai shiga rayuwanki ni da ke , sannu a hankali muddin ni mijin kine kina a matsayin matata zakiga gurinki suna cika daya bayan daya.
Yana dan buga min baya yake fadin Sadauki nakine zan maki duk maganin matsalolin ki don zan share maki hawayen ki.
A hankali na dago kaina na kara shigewa cikin jikin shi ina fadin cikin kuka nagode yaya sadauki Allah yabar min kai a rayuwana yabamu hakkurin zama da junan mu.
Yace Amin Fatima nima nagode Fatima da kika fahince ni a cikin sauki tashi muje ki bani abinci naci yunwa nake ji banci komai ba tun jiya dasafe don kawai nazo naci girki yar matata naji dadi.
Murmushi nayi tare da mikewa ina gaba yana bina a baya mukaje falon sai da ya zauna na zuba mai abincin ya fara ci.
Mikewa nayi na fara gyaran falon da suka bata kaca kaca wanda a kullun sai nayi gyaran shi fiye da sau uku suna batawa.
Yana cin abinci yana kallona a fakaice yana tinanen ashe zancen da bashar ke fada mai Fatman shi ta koma kamar boya a gidan kan abinda Amira ke fada mai.
Bayan na saka kamshi ko ina yafito neat ya mike ya dawo saman kujera yana waya.
Daki na shiga na kara wanka na gyara jikina tas nafito falon ina kamshi inda yake zaune na nufa da hannu yai min nuni da nazo saman kujeran da yake a kai na zauna.
A hankali yakai hannun shi saman jikina yana waya yana wasa da part din jikina a hankali.
Yana gama wayan yake cewa idan kin huta zuwa dare ki bude kayan nan da nazo da su, naki ne sunfi yawa daga ciki sauran zaki iya zabawa maryam da Amira sai kuma wanda kika so aba.
Nace mai mama fa yace atamfar Holland ce sunan nan zaki gan su kema ki zaba tunda naga kina son su sosai amma ki min dinki da zai fitar min da suran ki a fili.
Nace kai haba yaya abinda ake fadakar da mutane ba,a son anayin su yanzu yace ba ani zaki sawa ba ko wani ne zakiyiwa kwalliya bani ba.
Nace an gama yaya indon wannan ne kawai mikewa nayi na shiga fitar da kayan ina matukar yaba yadda ya iya zaben kaya haka kamar mace.
Gaba daya gidan su sai dana fitar wa kowa da nashi kaso har yaran mummy da suke kanana sai da suka samu tsaraba haka yasani fahintar tafiyan da yayi akwai sa,a sosai a cikin shi ke nan don haka yakeyi duk yai tafiyan da yayo nasara zamu sha tsaraba masu tsada muma a gidan.
Ranan kan naji jiki a gurin yaya sai dai daurewan danayi kawai don iyan zu na fara sabawa da halin shi ko.
Da safe bayan mun karya ne yafita zuwa kai tsaraba gida bayan na rubutawa kowa suna a nashi yadda zai gane.
Ranan kowa ya fahinci na fara jan ragamar aure na a gidan sadauki don ganin kayan kowa da sunan shi a jiki.
Dakin su Umma cewa mama Asiya tayi waiko kin gane cewa wanan yarinyar itace ta zabawa kowa kayan nan don ga suna kowa a jikin su .
Rukaiyya ta tare su da cewa amma kuma mama ai atamfan duk suna da matukar kyau wallahi don ni sun bani shawa,awa sosai wallahi.
Ke rufa wa mutane baki ke may kika sani ba sai tazabi na iyayyen ta yafi kyau ba ta bamu matasa kyau.
Kai haba mama wallahi haka baida kyau fa ina laifin Fatima gida su yaya ko tsuki sun taba kawo maku ne yakamata ku daina irin wanan halin wallahi inji yaya Sagir.
To sannu uban mu inji Umma yan uwan naka zakaiwa gori kuma don bakin kwadayi.
Mashayi dai ne ba wata tsiya ba can don har yanzu ba fasawa yayi ba ai tana cikin fadin haka sukaji hayaniya daga tsakar gida.
Nafisa ce tayo mugun sha take ta watsar da duk abinda tagani a waje da sauri suka fito hardasu mama dake dakin su cikin tashin hankali.
Ga kayan jikin ta yai futu futu sai ashar take zubawa tana fafin nagane duk munafukaine gidan nan don babu wanda ke sona.
Sai kuma tasa wani ihu kamar wata yar daji da taje farauta tace yau zan ci kazar uban duk wanda ke gidan nan munafukan banza xa wofi kawai.
Kuke nan kullun ku shige daki kuna kulla yadda zaku kashe UF ko wooo UF ko yafi karfin ku wallahi sai UF up up UF buga muje yayana ikon Allah .
Umma tafito rai a bace ta nufe ta tana fafin Nafisa abin naki kuma ya koma haukane ko may .
Tace Umma ni kika ceqa ma haukaciya yau ko zan gwada mamu ni ma ma mahaukaciyace a gidan nan saiko ta dauko tabaryan dake yashe a tsakar gida tayo kan Umma gadan gadan dashi.
Ganin da gaske zata rotsawa umma ne yasa umma juyawa da gudu saiko ta fadi kasa ku caaa gap da ta rotsa mata Sagir dake daki yafito jin yadda kowa ke ihu yayo kanta yakai mata shuri sai da ta fadi kasa takife bakinta ya fashe.
Kara dagowa tayi tana fafin wallahi yau sai na kashe ka gidan nan ni zaka daka haka ?
Nan ya samay ta yai ta jibga saida aka tare shi ganin haka yaran mummy suka sa ihu maji ta jasu zuwa dakin ta taboye su a ciki.
Yaran duk sun tsorace Umma tayi tayi ta tashi abu yaki kafa ya rike mata ashe tayi targade ne ba,a sani ba.
Ganin haka yaran ta suka saka ihu suna kuka neman taimako ga uwar su.
Mama Asiya ta bugawa Maigidansu waya yazo gida ba lafiya suna tare da sadauki dayaje gurin shi kasuwa.
Tare suka iso gidan cikin rudewa gashi an taru akan umma sai hawaye take tanaji kamar zata mutu.
Mummy ma dawowan ta ke nan ta samu wanan tashin hankalin daukan mama akayi dakyat zuwa asibiti sadauki da sagir da mama.
Yaran mummy suka fito dakin a tsorace suna ganin uwar su sukayo kanta suna kuka.
Ta rugumay su tana fafin yau kuma wanan iftila,in ne yazo muna agida haka kai Allah ya kyauta kawai.
Nafisa na cikin dakin uwarta sai ashar take ta zubawa da tonon asiri wa uwar ta.
Alhaji yana tsayevsai zufabke karyo mashi na tashin hankali mama da mummy suka nufe shi suna cewa yashiga ciki ya zauna kada kuma yajawa kan shi matsala.
Sai wani lokaci aka dawo da Umma duk ta jirkita ga uban bandejin da aka lailaiye mata kafa dashi.
Baba najin muryan su sun dawo yafito da sauri yace Atika kada ki shiga min gida dauki mahaukaciyar yar ki kubar min gidana.
Cikin yashin hankali aka shiga bashi hakkuri amma ina ya hau baji alokacin da kyat sadauki dasu mama suka samu ya koma dakin shi.
Umma tace tana kuka ai dama nasan shetine wallahi sai Allah ya isar muna duk wanda keda hannu cikin lalata min rayuwan yata.
Kai kaji kuma wani wauta wa zai tsa yiwa Nafisa wani sihiri kuma ga abin kwarai ba ai masu ba sai wanan barkatatan taki.
Haba hjy kubura a dai bar zancen ai Allah ba azzalumin kowa bane duk mai wa wani sheri ai zai girbi abinshi tun anan duniya don Allah bai barin bashi yanzu.

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA,,,,
A LOKACIN MUKE,,,,
Yau ya shirya unexpected ya samay ni daki bayan na dawo daga school yakw ce min zaiyi tafiya ne zuwa Mexico gurin wani taron yar kwallo da za,ayi kuma yana cikin wa yan da aka gaiytata su tafi taron.
Shiru nayi sai jin zuciyana kawai nayi ba dadi ban san har hakan ya fito a fuskana ba saida naji yana fadin baki son in tafi ke nan don engine din ko?
Ban fahinci may yake nufi ba da gakan cikin mamaki na dago kaina nake tambayan shi engine kuma ?
Yace eh mana ko karya nake yanzun ba kullun kike bukatan service ba na fahinci may yake nufi yanzu don haka najuya baya ina fadin wallahi, ni kan Allah ya kiyayye min abinda ake min a dole zaka wani ce can wai na saba ko nafiso indon tani ce wallahi mu zauna a hakana mana aga wanda zai sha wahala cikin mu.
Jinayi ya rugumoni ta baya yana fadin anki a zauna hakan sallon kijewa maman ki da kuka kice anki yi maki service kwana biyu kuma.
Allah dai ya kiyayye min wallahi kai wanan ya dama ni bai a gabana wallahi yace to tsaya mugani idan bai gaban ki da gaske din.
Gudu naje yi amma na makara nan ya samu sa,a na ya shiga aika min da sallon sakon shi.
A cikin mamakina sai gashi na zake nima yau ina mayar mashi da martani yadda yake bukata.
Mun dauki tsawon lokaci a dakin muna abu guda har sai da magariba ya kusanto sosai ya sarara min.
Rugomo ni yayi zuwa jikin shi tare da dan sinsinan wuya na yana fadin zan dauki tsawon lokaci a wanan tafiyan da zan yi don haka ki kula min da kan ki please .
Lumshe idanuwa na nayi ina sai dai a fili cewa nayi Allah ya kai lafiya ya bada sa,an tafiya.
Mun dauki lokaci ba wanda ya iya yi wa dan uwa magana a cikin mu sai can yadan min peck goshina naga ya mike ya fita daga dakin.
Maimakon na tashi daga kwancin ga lokacin sallah yayi amma sai kawai na lumshe idanuwa wani zurfafan tunane na shiga yi na yadda zan zauna kwana biyu bashi a gidan.
Irin yadda muka dan saba da juna a yanzu dashi.
Da kyat na iya mikewa na shiga bathroom don nai wanka nai sallah don har lokaci ya shige gashi takwasa zai tafi.
Ina idar da sallah namike da sauri na nufi dakin shi na samay shi tsaye yana gyara aninin gaban rigar shi.
Jin nashigo yasa shi dan juyowa gare ni cikin sakin fuska yau yake ce min ai na zata bazaki iya tasowo bane.
Karasowa nayi nake ce mashi mai za,a shirya mane wai?
Kinga ina tafiya da shirgine ni acan ina da kayan da nake amfani dasu ba sai na tafi da wani abuba daga nan.
Miko min yar hand bag dina na rataya kawai natafi don bashar yace min gashi ya taso zuwa kaini airport.
Na duka zan dauki jakar naji yana fadin wanan karon ma da Amira ke nan zaku zauna ko?
Murmushi yake nayi na karaso gaban shi nace duk yadda kace haka za,ayi yace ok zan fadawa maji ta turo ta idan nafita.
Ki dai dinga cin abinci ko zaki kara cikowa kafin na dawo nace idan haka bai maka ba sai ka karani mana.
Murde bakina yayi yana fadin wanan bakin wai yaushe ne zai mutu da bakar magana ne bari dai Allah ya dawo dani lafiya nasan maganin ki ai.
A tare muka fito falo dashi sai ga yaya Bashar ya shigo gidan nan muka gaisa dashi yana tambayana yaya kwana biyu.
Dago kai yaya sadauki yayi yace min tau ni zan tafi ke nan sai na dawo Allah yakai lafiya Allah ya sa ai nasara ga abinda akaje nema Allah ya tsare muna kai ya dawo muna da kai lafiya.
Yaji dadi matuka da addu,ana yake ce amin nagode bashar yace bakani dadin auren ba riba biyu mama tai maka ga kuma Fatima na sharto maka addua haka.
Dan bugo yakai ma bashar daga haka suka fita daga gidan ina tsaye rakube daga kofan shigowa falon mu.
Sai da naga subar haraban gidan najuya na shigo gida zuciyana a cunkushe min, fadawa nayi a saman kujera na dade zaune a guri, ina ta faman tunane kala kala ni kadai can dai ganin dare ya soma namike tare da rufo kofan gidan don ban tsan mani anty Amira zata shigo ba har wanan lokacin.
Ina shiga daki naji wayan na yana ringin da sauri na isa gurin, da wayan take shi ya kirani na dauka a kasalance ina fadin Assalamu Alaikum.
Yace wa alaikis sallam baki barci bane Fatima nace yanzun dai nake shirin yi.
To may ya hanaki yin barcin har wanan lokaci sai nace a raina kaine mana ka hanani a fili kuma sai naji yace nine ko?
Nace ni karatu na tsaya yi kawai shine ba makara don ina test da zamuyi satin nan insha Allahu
Murmushi yayi yace to ki kwanta hakana ki huta don nasan kina da gajiya a tare dake.
****** ********* ******
Ya sauka lafiya don yana isa Abuja da safe suka daga sai Mexico gurin taron su.
Yakira wayana kafin su tafi tana kashe ina cikin class ban samu magana da shi ba.
Yinin daya da sadauki yayi batare da Fatima haka yayi shi a cikin tunanen ta.
Sai a lokacin yake sanin cewa akwai wani babbban alamari a zaman ta kusa dashi ji yake tankar itace jagoran duk wani farin cikin rayuwan shi a halin yanzu.
Bai samu lokacin kiran ta ba,sai da ya dawo masaukin shi a lokacin dare yayi a can.
Yana kwance dakin shi saman gado tunane Fatima kawai ke cikin zuciyar shi har zuwa wanan lokacin.
A nan ya fara tina abubuwan da sukai ta faruwa a tsakanin su abaya.
Irin yadda yake yawan mata tsanani da hattaran ta cikin gidan su yana daukan ta a matsayin itace mai mashi gulma a gurin maji.
Sai yanzun ne yake gane cewa bata fadawa maji komai a gamay dashi sai dai nata kokarin da takeyi gurin ganin cewa ta saka mai ido ya daina shaye shayen daya ke yi kawai.
Wani irin bacin rai ne yaji sai yanzu yake gane cewa ashe son shi takeyi da,alheri take hakan gare shi.
Yana jin ciwon irin abin da yai ta aikatawa yar mutane a baya a bisa gaskiyan ta.
Haka yasa yamike ya fara dan zagaye dakin a hankali yana zargin kanshi da aikata abinda ba daidai ba akan Fatima din.
Lalai dole ne ya gyara tsakanin shi da Fatima yadda zata fahince shi ta yadda zata daina mai kallon mugun da take mai koda yaushe.
Yace in har bai gyara tsajanin su ba baiyi wa kan su adalci ba don haka zasu dinga zama suna samun matsala a tsakanin su ko yaushe.
Gurin tagan dakin ya koma tare da budewa yana shakan fresh ai dake fitowa daga window.
Ya daga wayan shi da ke a hannun shi ya kira nomban Fatima bugon farko da,wayan yayi sai da yaji wani iri a zuciyan shi .
Ina hanya zan dawo gida naji wayana na ringing, hakali na dauka na duba yaya sadauki ne a layin.
A hankali cikin wani murya bayan nayi receive din call din nace hello yaya.
Ya dan rikice da jin muryana yana cewa Fatima kina inane haka naji dan hayaniya.
Nan dan ajiyan zuciya sai nace ina hanyane yaya nafito school zan koma gida ne yanzu.
Sai nace kana lafiya yaya yaya gajiyan hanya da taro sai da yai wani lunshe idon shi ya amsa da taro Alhamdullahi Fatima mun fara yau din nan.
Allah ya bada sa,a nace mashi ya amsa da amin fatima.
Yace kiyi tuki a hankali don nasan yanzu titi ya cika da motoci yamma yayi nace mai insha Allahu.
Yace nakiraki ne naji muryan ki don na kira ki da safe wayan ki baya shiga.
Nace ina class alokacin na rufe wayana ne ya sake cewa gashi na kasa barci sai naji muryan yar kauyen matata yaya zanyi da raina dole na kira ki naji ki don mu nan yanzu daryayi sosai .
Nace shine kaki bari da safe ka kirani yace abinda ya dace ke nan nayi don na kasa samun natsuwa rashin jinki .
Kwata kwata rashin jinki a tare dani ya hanani sukuni Fatima yaya zanyi dole ne na kiraki ai.
Take zuciyana ya narke sai naji kamar na shige cikin wayan na isa inda yake din naga kyakyawan suran mijina da nai missing.
Yaci gaba da cewa Fatima ina kewan bakar maganan ki ina kewan wanan fadan namu da muka kwana bamuyi shi ba.
Murmushi nayi yace kin dauka ina wasa ne ko sai idan kinga nadawo maki don kawai muyi shi zaki gane.
Nace a hankali ina murmushi haba yaya don fada kawai zaka dawo na rokeka kayi hamkuri ka zauna har kagama abi da yakai ka.
Har nakai gida muna waya dashi inda na ke ce mai na iso gida sai da zanyi sallah mukai sallama dashi yakashe wayan.
Wayan dake hannu na dan kalla na ce ikon Allah yau kuma mai ya samu yaya haka ne ya sauya min gaba daya.
****** ********* ******
Yau kwana yaya uku da,tafiya amma Amira shiru batazo ba tun ina saka rai da zuwan ta har nagaji na,fara fitar da rai ga zuwan ta gidan.
Yaya da yakirani ya tambaye ni Amira bata zo bane nake ce mai bata iso ba tukun.
Ranan Na dawo gida da yamma a gajiye neke a lokacin sai dai ina shigowa get din gidan na hango motan anty Amira a kofan gidan namu.
Nashigo gidan da yar fara,a na a fuskana don ganin ta tazo tana zaune saman kujera tayi daidai da ita sai waya take yi abin ta.
A sanyaye nai sallama ta dago kai ta kalleni a dan wullakace nace Anty sannu da zuwa.
Hannu kawai ta daga min ba tare da ta amsa min ba taci gaba da wayan ta da takeyi.
Ido nabi ga yadda ta kaca kaca da falon da yake a gyara tas kafin na wuce da safe.
Ganun bata da niyan gama waya yasani na nufi daki na don rage kayan dake ajikina a lokacin.
Sai d nai wanka nai sallah nafito falon har lokacin tana zaune a inda na samay ta da farko.
Ina batun na zauna take cewa ke ina key din daki na yake na bude naga a rufe yake.
Nace au yana gurina anty bari na dauko maki taja uban tsuki tana fadin don isa da sa.un guri zaki kulle ma mutane daki wai ke ga matar gida ko.
Nace fita zanyi ai shiyasa na kulle ko ina na gidan kuma ma ban san kina tafe ba yau ai.
Dalla Bintu ki dauko min key ni bani son yawan zuba haka kinji.
Kallon mamaki nake mata nace yau kuma nice mai zuba anty ki dai gyara maganan ki.
Au to abin har yakai kuma zaki min rashin kunyane Bintu ?
Wanan ba halina bane anty kinfikowa kuma sanin hakan don ban tabayiwa kowa rashin kunya ba.
Kai ta gyada tare da kutawa ta dauki jakar ta bayan na bata key din ta wuce zuwa ciki ran ta a bace.
Kitchen dama a rufe yake na dauki abincin dana aje zanci idan na dawo tunda safe na shige daki da abina nace can nafito nasawa gidan key na shige abina na kwanta.
Ban fito ba sai da safe na hada breakfast na bar gidan ko fitowa batayi ba tana dakin ta kwance.
Bayan fita data gaji da barcin ta tafito ta zauna taci abincin da ta samu na aje mata.
Inda taci anan tabar min kayan sai dana dawo na kwashe su na wanke na gyara gurin.
Ban fito na girka na dare ba don a gajiye nake nashige kawai abina nai kwanciya na kawai.
Amira tafito tasamu babu komai saman tabld din tai mamakin hakan ta nufi dakina lokacin ina bathroom ban maji tana buga kofan ba har tagaji ta,wuce.
Tunda safe ina kitchen sai gata ta shigo daga kofa taja ta tsaya tace ke Bintu wai may kike daukan kanki ne halan.
Nace namay kuma anty?
May ya hana jiya ki girka muna abinci da kika dawo ki ka barni da yunwa na kwana.
Nace kiyi hakkuri anty wallahi na gajine jiya sosai kuma ga yamma yayi dana dawo.
Eyye samun guri ke nan ke ashe har kinga gurin hutu ke nan to wallahi ki kama kanki da ni.
Murmushi nayi kawai naci gaba da aiki har ta fara tafiya ta juyo ki girka abinci dasu salma don sunce anan zasuyi breakfast yau.
Yadda tace haka nayi mata na sauri na fita yadda na dawo daga gajiya da yamma haka na samu gidan sai da raina ya baci.
Ban fito ba haka nabar falon sai da safe na tashi na shiga gyaran gidan sai da nai ko ina tas har bayin falo duk sun bata shi .
Sai na dora muna girkin rana ina tsaka da yine sai ga Anty tafito ta ce yau ma su salma sunce a nan zasu wuni kiyi girki dasu.
Ina gama muna girkin na koma dakina na kwanta can na fara jin hayanin yan su har da yan ihun su.
Nace yau kuma din nan wai may ke damun anty Amira haka tana son bata rayuwan ta.
Ki fito ki gaida su salma naji muryan Amira daga sama ina kwance na dago ina kallon ta kawai.
Kamar bazan fito ba sai dai na mike na fito da fara,ana a fuskana nake ce masu sannun ku da zuwa.
A lalace cikin kallon banza suka amsa min banji dadin haka ba amna na dake na dan samu guri daga gefe na zauna.
Sai naji dayar na cewa wai ashe musty ya auro wata gajar matace can yar kauye da ita.
Ke haba inji saura tace wallahi ko kada kiso ki ganta ga gida ga komai ya hada amma ina ba matar gwadawa tsara don bakauya ce wallahi.
Sai Amira tace anyi biyu ke nan muma ga.unan da irin matsalan ai a gidan mu kin san yan kauyen nan su iya bakin asiri su mallake miji.
Yanzu bari ki gani kwana biyu idan an aaruce shi zakiga ya fara wani bakin rawan kafa bai jin kunyan kowa akan ta.
Nagane maganan ta shagube ne amma sai na dake suna sako min magana ina jin su.
Bai mata ba sai cewa tayi ke Bintu kwashe kayan nan ki girka muna indomie kubura zataci tace.
Kallon mamaki nai mata may anty ta mayar danine yar aiki ko may wai ?
Ina gama kwashe kayan sai dana wanke su na,shiga daki in fito sai naga wace tace wa Kubura dauke da cup din tambulan yaya da nake mashi amfani dashi tana shan drinks a cikin.
Kamar na wuce sai na dawo nace anty da kun canza cups don wanan din na amdmfanin yaya ne shi.
What Bintu may kike nufi lalai ma Bintu kin kai wuyan ki ya isa yanka ashe ?
To baza ,a mayar ba sai kiyi abinda zakiyi don an dauki cups din yaya ko sannu mai yaya.
May kike gurin yaya din ke nace mata a daure mata mana mai miji kuwa.
O lalai naga alama tunda har kin fara bani ansa to baza a mayar ba din tunda daga gidan ku kikazo da shi.
Nace may yai zafi haka anty harda giri da zagin gidan mu kuma haka ?
An zaga ko zaki ramane ki nuna min wuyanki yai kauri yanzu.
Nace bazan rama ba amma koda banzo dashi daga gidan mu ba nawane dai ke ma sai ki jira naki.
Aiko sai saura sukacs iyye gorin aure kuma zaki mata Bintu don ke kin samu an maki auren hadi ko ?
Nace au haka ta fada maku ashe idan yin hadi banza ne wasu suje ai masu mana mugani.
Na bada amsa haka sai na juya zan wuce ji nayi an finciko ni ta baya sai kawai naji mari kyauuu.
Cikin mamaki na dafe kumcina da ta mara nace anty abin har da duka kuma sai sauran na fadi kyale ta please kada ta kulla maki shiri kin san su da sheri irin matan nan.
Banyi magana ba na juya kawai idona tab da hawaye na,shigd daki ina mamakin wanan irin cin zarafin da Amira tai min a gaban kawayen ta haka.
Kiran yaya sadauki ne yashigo min yake kirana na dauki wayan bayan na goge fuskana.
Na amsa mashi sallama da sauri naji yace Fatima may ya samay ki ko baki da lafiya ne.
Na daure nace may ka gani babu komai yace please nace may ke damun ki ne wai ba komai nace mashi.
Baiyarda ba sai dai kawai ya kyaleni tunda nace mai babu komai ina daga kwance nake tunane dole na dage na futar da kawaici na fara gwadawa Amira nima na iya.
Bayan kaman awa daya sai gata bazaki dafa abinda nace maki kubura tana so bane ko may ?
Ban bata ansa ba na kyale ta haka suka gaji da zaman su har suka bargidan.
Da safe ma washe gari haka na gyara gidan tea na hada nasha na koma na kwanta abina.
Can cikin barci naji takai min maka a baya da gigin barci na falka ina kallon ta.
Bazaki muna abin karyawa bane yau gashi har sha daya da,wani abu na rana.
Nace bazanyi ba .
Bazakiyi ba fa kika s tsuki nayi na koma na kwanta abina sai ji nayi ta nufo zata kara kai min maka na dago ido waje nace kada ki soma kara tabani don zan rama.
Ko dazun ma arziki kikayi a gaban kawayen kine kada ki matsayi yata na disgaki a gaban su shiyasa na barki.
Yadda taga na nuna tasan za,a samu matsala sai ta juya tana fada tafice daga dakin.
Tana fita wayan yaya sadauki takira tana fada mai wai na hana mata abinci taci.
Yace ina ganin bata jin dadin jikin ta nd don tun jiya nake jin ta hakana.
Tace shiyasa ban son zusa gidan nan wallahi sai yarinya tai batun raina maka wayon ,
Kashe wayan yayi yana mamakin iri wanan hali haka da ta sakd lokaci guda.
Tun daga wanan rana ban kara girka komai ba koma nayi iya cikina nake girkawa naci

A LOKACIN MU KE,,,,
Tashin hankali a gidan su sadauki haka aka kai dare a cikin shi sai da kyat ya shiga dakin ya lalashi Nafisa dake ta faman hauka aka samu tai barci bayan irin tonon asirin da take zubawa umma da mama kawai tana kiran su da munafakai masu bin boka da malam.
Haka ya dawo gida ranan rashi a bace ina daki naji shigowan shi musalin takwas da aani abu na dare.
Nafito daga dakina saye cikin wasu kananan kayan da ya sawo min a cikin tsaraban daya zo min dashi.
Ina fitowa ya sako min mayan idanuwan shi har sai da naji kunyan hakan da yai min din.
Sannu da zuwa nai mashi idon shi na akaina ga damuwa karara a duskan shi.
Gefen hannun kujeran da yake zaune akai na zauna tare da cewa yayana may kuma ya faru ne naga kamar kana cikin damuwa.
Murmushi yayi a fili amma a zuciyar mamaki yake yadda nake saurin fahintar halin da yake ciki ko yaushe.
Yace ba komai Fatima dan matsalane kawai aka samu a gida da sauri nace subbahanallahi injin bada mama ba.
Yai murmushi ya jawoni zuwa jikin shi yana cewa don mamace kadai taki a gidan ko ?
Nace cikin murmushi ba hakana bane yaya ban dai son ace wani abu ya samu mama din ne kawai.
Yace yana sauke numfashi, Umma ce dai da Nafisa kawai ta dan shawo ne tazo gida tana hauka har ta jin ma umma din ciwo a kafan ta.
Nace innalillahi wa inna alaihim rajjiun Allah yai muna sauki wanan al,amarin kawai.
Oo ita anty Nafisa bata da ranan gyara rayuwan ta ne wai bata ganin cewa ita mace al,amarinta daban yake dana maza.
Ajiyan zuciya naji yayi yace zan samu lokaci ai na zauna da ita don na dan fahintar da ita ko Allah zaisa ta gyara halin ta amma gaskiya abin baiyi ba wallahi.
Allah ya kyauta nace tare da numfasawa na fara tunanen aanan halin rayuwan na shaye shaye gamu da acikin ta don ban sani ba ko wani hali shi mutumin nawa yake yanzu ko ya daina ko yana ciki tsunbul.
Jinayi yaja min hanci na shiyasa na sake sauke numfashi ji nayi yace kina tunanen naki mijin ko?
Murmushi nayi nace aini nawa mijin Allah ya,kawo mai sauki da sauyi a rayuwan shi Nafisa dai nake tausayawa kawai da sauran al,umma masu hali irin nata.
Idan kin gama tunanen ki nima sai ki taimaka min da dan ruwan wanka na watsa ko zanji dadin jikina.
Mikewa nayi sai naji ya kara jawoni na koma jikin nashi yake cewa amma fa zaki cika ladan ki don ke ce zaki min wankan don banjin lakkan yin da kaina ko kadan.
Da sauri na dan juyo ina kallon shi sai yake cewa eh haka na fadi ko baki ji ba nace amma yaya gaskiya sai kuma nai shiru yace to shike nan barni hakana na kwana da dauda.
Jin abinda ya fadi yasa jikina yai sanyi hakka na mike na nufi dakin nashi murmyshi ya sake tare da bin bayana da kallo kawai.
Sai da na hada ruwan wankan na aje brush din dana matsawa maclean da soso da sabulun wankan shi na fito daga bayin.
Yana zaune a ida na barshi a falon na ce a sanyaye na hada yaya yace ok sai naga ya miko min hannayen shi alaman na kama shi ya daga ke nan.
Murmushi nayi nace ni ina zan iya tayar da kato dan kwallo haka kulun cikin motsa jiki.
Dariya nabashi ya kara mika hannayen shi inda nima na kama hannayen nashi na mikar dashi din kamar yadda ya bukata din gare ni.
Amma kuma kamar ina daga dutse gashi na saka duk karfina na dago shi amma na kasa jawoni yayi na fada a jikin shi tsab ya mike tsaye dani a hannayen shi.
Bai dire dani ko ina ba sai tsakiyan dakin shi kawai ya tsaye kimkam yace sai ki fara aikin ko?
Kallon shi nayi yace uhumm bissimilah ki cire min kaya ko ?
Kallon shi nayi fuskan shi a daure dole na fara kokarin cire mashi rigan dake jikin shi.
Nakai ga wandon shi ina kokarin cire ina kawar da kaina a gefe tsaya yake kimkam dashi sai murmushin abinda yaga ina yi na kawar da kaina gefe daya.
Ina na cire wandon na kara dukar da kaina kasa, ashe akwai wani gajeren wandon maza daga ciki jin bai motsa ba yasani dan dago kaina.
Kai ya gyada min tare da kashe min ido alaman saura wanda ya rage daga ciki din .
A hankali kaina a duke na karasa cire mai wandon sai naji ya sauke ajiyan zuciya da sauri na mike na nufi inda towel yake na dauko ina mika mashi tare da kawar da kaina gefe daya.
Hannu naji yariko da kyat na iya dago kai tare da juyowa na dan kalle shi kai ya gyada min alaman bai bukatan towel din yau.
Nashiga uku na furta a raina ashe har a fili na fadi hakan ban sani ba sai naji yace akan may kika shiga uku fatima ko rabi ban bari ki shiga balle har uku.
Muje kiyi min wanka please da sauri na shige gaba tana bina a bayana sai faman kawar da kai kawai nakeyi gefe daya don ban son dago kai na kalle shi, don wani irin mugun kunyan da nake ji a lokacin.
Zama yayi a cikin bahon ruwan inda na fara yi mashi brush sai na hau yi mashi wankan idona a rufe har muka gama muka fito.
Dan towel na dauka ina goge mai jiki dashi sai faman lumshe idanuwan shi kawai yakeyi a lokacin.
Kayan da zai saka na dauko mai wani dan riga daga cikin kayan barcin shi sai wando gajere don nasan ba zai fita zuwa ko ina ba kuma.
Falo muka dawo ya ci abincin shi da ya kare ya koma saman kujera two seater ya zauna ni kuma na kama kwashe kayan nagyara ko ina tsab.
Inda yake a zaune na dawo na zauna a dayan kujeran dake daga gefen shi waya yake amma sai ya yafito ni da hannu alaman na dawo gare shi.
Abin da ya buka ta nayi inda na dawo daga gaban shi na zauna a hankali ya fara kai hanayen shi saman jikina yana aiwatar da wasu abubuwa can na ma,aurata.
Tun ina lumshw idanuwana har nima na dan fara mayar mai da martanin abinda yake, min nan muka shagalar da junan mu a falon .
Lokaci mai tsawo muka dauka a hakan cikin wani irin yanayi mai shagalar da mutun a inda yake.
Sai da ya tabbatar da kowan mu ya gamsu da dan uwa sannan ya sarara min.
Dakina na koma nai wanka na gyara jikina tare da saka rigan barci na na nufi dakin shi don nasan dai duk wani abinda zaiyi a ranan yariga yayi shi a falo ko sai dai kawai mu kwanta kawai mu huta.
Shima dai na samu yayi wanka ya kwanta a hankali na hawo gadon ta bayan shi tare da rugoma shi daga bayan shi.
Murmushi naji yayi tare da juyowa gare ni yana jawoni jikin shi nai mamaki dana ji kan shi da bakin shi a saman kirjina again.
Sai da gabana ya fadi nan ya shagala a saman kirjina tun ina rutse idanuwana har yakai nima ina jin dadin abinda yake min.
Sosai muka tsotse junan mu a karshe ta shigeni yadda ranshi ke so sai barci mai nauyi yai gaba damu.
Washe gari bamu tashi da wuri ba sai after nine na safe don haka mukai sallah a makare .
Ya ce kada na girka komai na koma na kwanta idan mun tashi zaifita ya samo muna abin karyawa.
Nan muka koma barci sai to one muka tashi wanka kowan mu yayi lokacin duk muna bukatan abinci.
Nafito falo naji ana sallama na nufi kofa naga ko waye yaya Bashar ne tafe dauke basket dauke da abinci daga gurin maryam.
Nai sauri na karba ina gaishe shi tare da bashi hanya ya shigo ciki lokacin sadauki ya fito daga daki shar dashi kayan da yasa sunyi matukar yi mashi kyau sosai.
Nan suka zauna suna hira na nufi dining da kayan na fara had gurin yadda ya kamata bayan na bude ne naga tuwo semo ne da miyan yauki.
Nace mai ga abincin can na hada mashi, a dining yace ok bari na dan ci abinci bassh.
Yace bari dai naje gida nima jirana ake muci nafito zuwa gurin ka kasan maryam yanzun ba ita kadai bace.
Ita da waye ya tambaye shi yace a anfada maka ni irin kane raggo sai iya jefa kwallo fa raga kawai amma ba ka iya jefa shi inda ya dace a jefashi ya shige.
Dariya yayi tare da kaimai nashi ya gwauce mashi yana fadin baka da kunya,wallahi wai ka manta cewa ni surukin ka ne.
Har zai fita yace kuna ko da labarin Umma bata da lafiya idan kaje ka fada mata please.
May kuma ya samay ya tambaya cikin son ji hankalin shi a tashe ya bata fuskan shi yace kawai dai dan matsalane ita da Nafisa shine ta gwauce kafan ta.
Yace mashayiyar ta shawo ke nan tazo tana hauka a gida ko yace raban ma acan na gane ta ta bugu a hanya duk dan taxes din ta tsare sai yaki tsayawa ni na daukota zuwa gida tana min tanbele a hanya.
Yafita yana maijin haushin halin rayuwa irin na Nafisa da ta jefa kan ta a ciki yanzu.
Sai wani dukar da kaina keyi don balain nauyin shi da kuyan shi nakeji yau din sam ban iya hada idona dashi.
Can yace ke na ce naam yace dago idon ki ki dube ni nan da kyat na iya daga kaina kalleshi sai nai saurin dukar da kaina kasa kawai.
Murmushi yayi yace wai wanan kunyan na may ye kuma haka ko abin bai sheki bane na kara maimata maki fiye dana jiyan ko?
Da sauri nace don Allah dai yaya kayi hakkuri kawai dai ban san yadda zan kalle ka bane dai.
Ok yanzu zan kawar da kunyan nan ai daga yau bazaki kara jin shi ba aiko da gudu na kwasa sai cikin dakina harda saka key na rufe daga ciki.
****** ********* ******
Kaya irin na marasa lafiya muka saye sai gidan su mama kwana biyu ke nan da faruwan abin amma kafan ya hau yai sundum dashi.
Tana ganin mu duk da nishin da takeyi amma bai hanata daure fuskan ta ba a lokacin.
Mun gaida ita tare da mata yaya jiki cikin daure fuska ta amsa muna Allah ya sauwaka nai mata tare da mika kayan gaisuwan da muka zo mata dashi.
Na mike na fita na barshi a dakin nasu dakin mummy na shiga na gaida ita na fito zuwa dakin mu.
Ina fita a dakin umma yaya sadauki yace ina Nafisa take ne wai ?
Umma bata amsa mashi ba sai sagir ne yace mahaukaciya tana ciki mana yar iska kawai.
Kira min ita yace wa sagir din nan ya mike ya shiga har dakin Nafisa yace tazo yaya sadauki na magana da ita.
Tafito jikin ta babu ko riga tace cikin wani yamuste fuska yaya sadauki ina wuni ya amsa mata cikin girgiza kai tare da tausaya mata.
Yace Nafisa ina son ganin ki don Allah gobe a gida na idan babu damuwa.
Tace ina ne gidan naka nema wai ?
Yai mamaki da wai batasan ma gidan shi ba yace sagir zai kawo ki idan kin tashi goben.
Tace kai tsaye niba zan shiga mota dashi ba ya illanta ni ga banza kawai mugune kagan shi nan wallahi yaya .
Tausayi tabashi don abin ya fara taba ta sosai dole ne a taimaka mata.
Ya mike yana fafin kada ki manta please sai nagan ki ko ya ciro kudi ga aljihun shi yana mika mata yace ga kudin mota ko idan zakizo.
Sagir yace kada ka bata yaya wallahi wanan shegiyar maye zata sha dashi don dama shi take nema kaga ta lafa a gida tana neman na wanda zata ware dashi idan mai shi yai sakaci.
Yace ka barta dasu ai zata zo din kasan Nafisa akwai cika alkawari tace nagode babban yaya irinka muke so ko yaushe ba masu hana abamu ba.
Amira ce kawai a falon lokacin mama tana daga ciki na gaida ita tare da mata yaya kwana biyu.
Banza tayi dani kamar bata san ina gurin ba ma a lokacin sai wayan ta kawai take dakila a hankali a lokacin.
Nace anty har yanzu kina kallon film din queen of south ko kin daina ne don shirin yai nisa sosai.
Ke Bintu kikama kanki dani wallahi don idan kikai min tsiya yanzu na lahira zaifiki jin dadi wallahi ko.
Haba anty daga tambaya kuma shine laifi Allah ya baki hakkuri nacs mata sai ko ta dago da nufin kai min duka ji tayi daga kofa yace kada ki soma wallahi yanzu zan bata maki rai sosai wallahi.
Yar kice koko kaunan ki da duk lokacin da kikaga dama zaki dinga dukata son ranki.
Duka kuma dukan wa kuma wai ban fahinci may kuke magana ba akai wa ake duka ne wai ?
Bai fasa magana ba yace kin san ina da hayshin marin da kikai mata ranan yau kuma don samun guri zaki kara dukan ta to bisimillah gaki gata shege ka fasa.
Tambayan ku nake wa ake duka ne wai yace maji rabu da yar rainin wayo yarinyar nan ban san yaushe ta zama haka ba wallahi.
Har gidana fataje ta samu Fatima da mari ta tara shegun kawayen ta a gida suna juyata kamar ta samu yar aiki.
Bai isheta ba kuma yanzun daga tambaya shine wai zata duke ta again.
Duka shin Amira ko may dukan Fatima fa akace kinyi ko may ko kin fara shaye shaye ne kema bamu sani ba?
Bata fara komai sai rainin wayyo kawai ta ji na fada mata duk ta kara dora hannun ta akan matata ko zagi wallahi sai na bata marai Allah.
Nikan mikewa nayi na cire hijjab din dake a jikina na fara gyarawa mama falon ta da duk ya wani yamutse kaman bashi ba.
Na gama na koma can uwar dakin da dama nike gyarawa nai mashi kwal na kwaso shara gudan mai yawa.
Mama tace ki duba ki gani yadda muke zaune a cikin shara haka saboda shegen son jikin ki kin kasa gyara muna mazaunin mu sai fama da dakilan waya.
Nagama na dawo na zauna yace ke in kin gama tashi mu tafi akwai inda zamu biya in mun fita.
Tun muna hanya bayan mun baro gidan su mama nake jin marana yana murda min a hankali alaman period zai zo min ke nan.
A hankali na dan ya mutsa fuska na sai kawai naji yace ba tare da yakallo niba may nene kuma ya faru.
Sai da na sauke ajiyan zuciya nace ba komai yace shine kike yamutsan fuskan ki haka kawai.
Murmushi nayi nace bakoma mun tsaya wani shago naga yayi sayaya yafito aka sa mai a bayan motan shi.
Bamu tsaya ba sai gidan Inna mahaifiyar Bashar naji matukar dadin haka muka shiga a tare mun samay ta da yaran ta zaune suna hira suna ganin mu suka shiga murna.
Nan muka zube muna gaushe ta ta matsa sai mu tashi mu hau saman kujera bamu dade ba don yamma yayi a lokacin.
Mun isa gida duk nagaji ga marana yana min ciwo sosai a lokacin daurewa kawai nakeyi.
Na shiga yin alwala naga har jini yazo min ko nan na dan daureye jikina na fito ina tunanen yadda zan fadawa yaya ina period yau.
Ban fito falo ba ina kwace rike da marana dake min ciwo yashigo dakin yasamay ni na kifa kai a filo sai nishi nakeyi.
Yake tambayan wai may ke damun kine haka kinki fada wa mutum ko so kike ki halaka kanki ne wai?.
Da kyat na iya cewa marana ne ke min ciwo tun dazun, yace shine baki iya fadi na sai maki magani tun a hanya.
Shiru nayi ba amsa yace ko period zakiyi ne wai a hankali na gyada mashi kai tare da cewa har ma yazo min ai.
Yace ashe ko da gaskiyan Bashar ni raggo ne tunda na kasa jefa kwallo a wana jan ragan naki.
Turo baki nayi yai murmushi tare da mikewa har yafara tafiya yace kwana nawa kike yi dashi ne wai ?
Nace sati daya da karfi naji yace what ?
Sati daya fa ko baki da lafiyane zaki dinga sati kina fitar da abu daya haka nan ?
Kara kife kaina nayi kawai batare da nai mashi magana ba naji da abinda ke damuna kawai.
Fita yayi zuwa can ya dawo min da magani da lemo mai bawa da sauran kayan fruits .
Sai da nasha maganin na samu ya dan lafa min na fito falo yana zaune yana kallon ball .
Guri na samu na zauna tare da gaishi shi ga kayan fruit da naman da yaci saman table a gaban shi.
Yace yaya jikin kuma nace yai min sauki sosai dana sha magani .
Zauna ki ci nama ga milk nan kuma kisha baida sanyi sosai nace na koshi yace kin koshi da kikaci may kuma ?
Banci komai ba na dai sha lemon da ka kawo min sai naji na koshi sosai.
Oya ki kara da,naman kisha milk din ko zakiji jikin ya kara sake maki ban yi musu ba na fara cin naman a hankali sai dai duk bakina ba dadi cikin shi ko kadan.
Yace kisha milk din mana ina kaiwa a baki naji kaman zanyi amai nan na cire cup din da sauri a bakina .
Na mayar da kaina baya saman kujera ina mayar da numfashi guda guda cikin wahala.
Ban san tasowan shi ba sai jin shi nayi a gaba na yace oya kwanta ki mike shi da kan shi ya gyara min kwanciya nan ya shiga dan tausa min ciki na a hankali.
Naji dadin hankan har na fara lumshe idanuwa na ban sani ba sai barci bai bari ba sai da yaga barci ya dauke ni sosai.
Sannan ya daina yadan kura min ido yaga yadda nake barcina a tsanake nan ya koma saman kujeran da ya taso kada ya tayar dani.
Mukai wani lokaci a falon yana kallon shi bai son ya tayar dani na falka daga barcin da na keyi.
Sai da dare yayi sosai ya tayar dani muka koma daki sai dai makale ni yayi haka muka kwana dashi.
Washe gari na gyara jikina nai wanka nashirya tsab nashiga kitchen hada muna breakfast, ina tsaka dayi ya dawo daga gurin motsa jikin shi.
Kitchen din ya shigo ya samay ni yana cewa har kin ji sauki ke nan ko idan bazaki iya ba ki barshi kawai sai a sayo muna muci nace zan iya ai har na kusa gamawa ko.
Yace yau fa kina da bakuwa don Nafisa zata shigo gidan nan don Allah idan tazo ba runki da ita don kin san yanzu ta burge sosai.
Sai misalin sha daya da rabi suka shigo gidan su uku ne da kawayen ta da ganin su tantiran yan duniya ne sauran don sun fita,wayewa sosai.
Da fara,a na fito daga dakina ina masu sannu da zuwa duk suka zubo min idanuwan su nan dai bayan mun gaisa na kawo masu abin sha suna godiya.
Nace gashi ko yaya ya fita ya jiraki baki zo ba yace zai fita amma ba nisa zai tafi ba.
Kada ki damu ai zan jira shi ta bani amsa nace anty may zan dafa maku ne yanzu.
No ki barshi inji wace tafi haske daga cikin su nace ,a,a Allah bari na girka maku abinci mana kafin ku wuce.
Na juya nan na barsu a zaune suna bin gidan da kallo na shiga kitchen na fara hada abinci.
Basu dade sosai da zuwa ba yaya ya dawo gidan shi da Bashar ne wanan karon.
Suka gaisa dasu fuskan yaya a daure nagan sbi nafito muka gaisa da bashar nakoma ciki.
Yaya ce wa yan nan fa tace tie friends dina ke nan yaya wanan Raiha akace mata amma anakiran ta da Rayye ne ita kuma wanan Nura ance mata Nuriyya.
Yace ok sai dayan tace amma sai naga kamar na sanka da dadewa ko sai dai in ba kai bane amma nasan wanan fuskan gaskiya.
Nafisa tace ke banza shine fa U F da kike jin ana fadi dan kwallon wasan duniya.
Yadda tai maganan kamar a buge yasa kowa yin dariya a lokacin banda yaya daya daure fuskan shi.
Nakwao masu yaya ruwan sha da drinks na aje masu nakoma gurin girki na.
Yaya yace amma ba yanzu zaki wuce ba ko don kin san nace ina son ganin ki ko.
Tace ai shine nazo mana ko don nazo da kawaye nane baka samun ganin nawa.
Yace ashe kin gane nufi na nafito masu dauke da kulan abinci da plate na aje masu tare da masu bisimillah.
Can dayan tace na tuba inda na sanka yanzu muna haduwa da can baya gurin Brosha mai kayan harka ko?
Daure fuska yayi kamar badashi take magana ba Nuriya ta jawo kula ta bude abincin dana aje masu tace wowwo kamshi ke nan aiko mu gode wallahi dama yunwa nake ji sosai.
Sam basu da kunya atare dasu ko kadan sai wani girgiza suke yi adole sunga maza mata sa yaya yace muje na sauke ka gida Nafisa ki jirani fa kinji na fada maki.
Nan muka zauna dasu suna cin abinci muna hira jefi jefi dasu dayan take tambayan Nafisa ita kadai ce matar shi halan Nafisa taba amsa da eh.
raiha tace wai amma kan zakiyi fama da arnan yaki ga mijin ki matashi kuma mai lokaci ai akwai aiki.
Sai da sukaci abinci suka koshi yaidda nai masu sunji dadi haka sosai basu boye min ba don cewa sukayi da suka gama kai amma gaskiya munji dadin yadda kika tare mu ba kamar gidan wancan yayan naku ba da mukaje suna ce muna wai yan kwaya sun shigo gidan su.
Nace subbahanallahi ai ba wanda ya wuce jerabawan ubangiji don kuma ba haka kukaso ba a ran ku.
Shiru sukayi sai Nurace ke dai ganan min hanya yar uwa ina mamakin mutane wallahi mutum na da abin fadi amma sai ya takw nashi yaje fadin nawani.
Nace Allah Allah dai ya yayewa kowa wahala kuma Allah ya kawo maku mazajen aure ku huta duniya yanzu ba tausayi wallahi.
Raihane ta jefo min tambaya halan ke yar wace garice sister kafin na bata amsa Nafisa ta ce yar uwar muce fa agidan mu ta tashi ai.
Ai ko ban taba sanin taba gaskiya nai dariya nace niko nasan ku ai yakai sau uku muna hafuwa daku ai.
Allah sarki ban ko gane kiba wallahi, tace min suka mike suna cewa zamu tafi mungode kwarai da taron da kikai muna nace kai haba ba komai aiku yan uwa na ne.
Suna fita nan Nafisa takife saman kujera sai barci koda yaya ya shigo ya samay ta tana barci sai baita da ita ba dakina yashiga ya samay ni zaune yace ita wanan barci tai muna anan.
Nace ina ruwan Anty Nafisa taci ta koshi sai barci abinci yace na bashi nabi bayan shi muka fita tare sai da ya zauna yake cewa ina ganin yau zanyi tafiya fa.
Amma sai dai yadda nagani amma iyakata Abuja zan tsaya kawai.
****** ********* ******
Bayan Nafisa ta tashi yana falon zaune ganin shi yasata mikewa zaune yace har kin gama barcin ke nan tace tana mikewa zaune wallahi fa yaya.
Yace haba Nafisa ya kamata ace yanzu kin wa kanki fada fa gaskiya baki kyauta wa iyayen mu musan man ma Umma da take mace tana zama dake a gida ko yaushe.
Shiru tayi tare da dukar da kan ta kasa yace lokaci yayi nafisa da zaki bar wanan harkan haka duk da nasan abune mai wuyan bari amma don Allah kiyi kokari ki dan rage wasu daga cikin halaiyar ki don Allah dai ba don niba Nafisa.
Abin mamaki sai gata kawai tana hawaye tace wallahi yaya nima kaina ban san may ke kaini sha ba ko naso na bari sai naji kwata kwata bazan iya ba.
Lokacin nafito falon ganin suna magana yasa na juya zan koma ciki sai yace No dawo ki zauna aikema maganan ya shafe ki tunda ya shafe ta.
Tace wallahi yaya ni ina ganin Alhakin kune da maji ne ya sauka aikaina dakin mu don irin mugun abinda Umma da mama suke shuka maku kullun tun ina karama nakejin irin tugun da suke kullawa akan maji da ku.
Dariya yayi yace kai haba Nafisa ai shi zama kishi ina ganin haka yake sai ta share hawayen tace yaya bazaka gane bane wallahi.
Amma nasan ko nayi rantsuwa ban kaffara don su Umma ne suka sa kayin shaye shaye a baya.
Na fadawa umma su bari kada Allah yajerabesu watara tundai ina suna zagin ka da mashayi dan maye mukan mata magana ni da yaya sagir amma umma bataji.
Munafukan ga mama bata bari umma tabar aikin ta yaya yaya kake ganin zan iya dainawa idan su basu daina sheri ba.
Tace umma tana sakaci da yawa tana yarda da mama asiya batan cewa muguwa bace ta karshe har yanzu bawai sun dai jifan ku bane fa.
Allah daine ke kare ku kawai amma kai kan ka da,wuya in ka daina sha yanzun haka?
Da sauri na dago kai ina kallon shi sai naga yai murmushi kawai yace Nafisa koma maynene ki sa a ranki cewa zaki daina sai kikaga kin daina din.
Ki samu miji kiyi aure koma may nene kike so ni nai maki alkawari zan sai maki duk lokacin da kika tashi aure.
Kai ta kifa tafara wani irin kuka take nima bansan lokacin da na fashe da kuka ba shima dai ina ganin kukan yakeyi a lokacin yadda na ga ya dukar da kan shi kasa.
Can ya mike ya shige dakin shi ya bar munan muna kuka tai matukar bani tausayi namike zuwa inda take na dafata.
Duk da nima kukan nakeyi amma sai na dafata ina bata hakkuri kawai sosai nake mata nasiha har nagama batace min kalla ba nace tazo tashiga tai wanka ko zataji dadin jikin ta.
Ta kalle ni da mamaki tace Bintu ke baki kyamanane yadda sauran yan gidan mu ke yi min yanzu nace kyama kuma anty akan may zan kyamace ki kina da cutane ko may.
Tace har fa ciwon aids mama Asiya da yaya Ahmad ke fadin ina dashi yanzun haka kallon mai cutar aids wasu mutane ke min.
Nikuma wallahi komai mayena ban bari mutum ya shige ni baida roba a jikin shi.
Ban san lokacin da na runtse idona ba danaji abinda tace min ba kunya take fada min tana amfani da maza haka.
Dakina nakaita tai wanka na bata wani dogon riga na mai kyau tasaka muka dawo falo nan muka samu yaya yace tazo ya sauke ta gida don can zai tafi yanzu.
Tare sukafita da ita tana min godiya nace haba anty aiyiwa kaine tausayin ta yai matukar kamani sosai.
A hanya ma sosai yaya yaita mata nasiha ya na kwantar mata da hankali na ta natsu ta daina wanan harka baida amfani don babban illa da cikas yake kawowa mutum a rayuwan shi.
Sai yamma ya dawo yake ce min tafiyan shi yana nan yace ko bazan iya zama ni kadai bane yaiwa Inna magana maman su Bashar a turo min daya daga cikin yan matan ta nace a,a zan iya zama mana yaya.
Ai yanzun na saba da gidan ban jin tsoron komai kuma kamar baya yai min sallama bayan ya shirya ya wuce Abuja .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,
A LOKACIN MUKE,,,
Suna zaune tayi murtuk da fuskan ta yarasa mai zaiyi wanda zai iya jawo hankalin ta ta sake mai fuskan ta ko zai dan ji sanyi a ranshi.
Shi dai tun auren su shi dai ba zai ita cewa ga wani dadin wanan amaryan tashi ba da yaji a zaman su.
Kullun a cikin bashi commad take yau tace wanan take so gobe tace wancan take so.
Gashi iyanzun duk dan zarahin shi ya tafi baida wani kudi da zai juya a tare dashi.
Gashi kuma a bangaren ta idan ba kudi ne ya kashe mata babu zaman lafiya a tsakanin su ko kadan.
Shi da gidan shi amma har kofa sai Jamila ta rufe mashi don cin mutunci sai ya samo mata kudin nan da ta furta mashi tana so a gurin shi.
Jin sunan shi da ta ambata yasa shi saurin juyowa da sauri a dan firgice da tace Ahmed fa dakai nake magana ka zauna kana min wani tunanen can dakai.
Kaji na fada maka dubu dari shidda nake so ina son na kai babana asibiti saura kuma zanyi amfani dashi ne akwai bukin kawata da za,ayi ina son nasai mata abu mai munhinmanci don tasan inayin ta sosai.
Nisawa yayi tare da gyara zaman shi yace Jamila wallahi ban san inda zan samu kudin nan ba yanzu don wallahi dan abinda ke hannu na kwata kwata baifi dari uku ba ma in har sunkai shine kuma nake dan juya muna.
Rufe min bakin ka kai baka ji kunyan fada min haka ba kai dan gidan Alhaji Abubakar deller shine har zaka fada min haka ?
So kake na yarda da karyan ka kana nufin haka zan zauna dakai ba wani karuwa sunan ina auren dan mai kudi ko may wai ?
Kaji na fada maka in har kana son zaman lafiyan kakan ka nemo min wanan kudin dana fada maka.
Ehe, don shine kawai kwanciyar hankalin ka don a zauna lafiya kawai kaji abinda na fada maka daga haka ta mike tashige dakin ta tare da rufo kofan dakin garam da karfi yamike yana fadin Jamila Jamila tsaya mana ki saurare ni.
Amma ina har da key taiwa kofan dakin nan ya dafe kan shi yace oh my god wanan balin na jamila da may yai kama ne wai.
A falon ya kwanta saman dogon kujeran su a takure haka ya kwana shida gidan shi ya koma kwana falo don masifa.
Washe gari ma da masifan suka tashi a gidan don yana zaune ta hado abin karyawa duk dashine yasayo amma yana zaune, yana kallo tana shan shayi da kwai a gaban shi har ta shanye tass
Ga jamila bata wasa da ci duk yawan abin nan zata iya cinye shi tas ita kadai yace a ran shi shiyasa take mulkan dan bura uban kiba haka tana curewa ita kadai.
Shi ko sai rama yake yana aje dan dogon wuya kamar matikin lema dashi ganin babu sarki sai Allah yasa shi mikewa don fita ya dan samu abinda zaiciwa ran shi tun jiya da ya karya bai ci koma ba don fitan jamila a kan shi yai yawa .
Gidan su ya nufa gurin mama Asiya don ya dan samu abin karyawa a can , duk yasan kullun yaje neman abinci sai mama tai mashi korafi kan shi matar shi da bazata girka mashi ba shi ke nan kullun zuwa gida cinye masu abincin su.
Yau ma yadda yai tunanen masifan mama hakane a kan shi don fada ta haushi dashi tana fadin sai da nai maka gudun haka amma ka dage kai sai wanan yar daban matar taka zaka aura yanzun ga shi ko abinci ba ta iya baka sai ka kama labe labe gidajen mutane.
Bai damu shi dai yace Rukaiyya ta debo mashi abinci kawai yaci nan ya hago kayan tsaraban da sadauki ya labto masu a gida.
Yace kai mama har yanzu tsohon nan yana sayo maku abinci haka mai yawa ashe.
Tace wani tsoho kanin ka dai sadauki shine ai yanzun zance mai muna sayen abinci duk wata.
Kamar Alhajin ya barshi da wanan nauyin ne kasan su da son neman suna da iyayi waishi gamai hali kowa zai gwadawa hali .
Dama ba musan uwarshi bace matsiyaciya yar taulali kawai su suka sani da shegen iyayin su wai su ga yan iyawa ke nan.
Nan dai ya kwashi abincin shi sai da yai kat dashi yana ta sake sake a zuciyan shi.
Sai da ya gama yamike yana cewa zai shiga gari yaga may gari ya waya yau kuma.
****** ********* ******
Ganin ya juya zuwa dakin shi yasani fahintar fushin abinda nai mashi na rashin nuna mashi nai wanka da yadawo yayi.
Sai da na bata lokaci na sosai gurin gyaran jikina a gaban mirror na mike ina sake sake a raina na na kashe wutan dakin da A C nafito na nufi dakin nashi.
Na samu ya kwanta ya kashe wutan dakin a lokacin jin motsina bai sa shi koda dan motsawa ba a lokacin inda na tako zuwa bakin gadon na kwanta a hankali a bayan shi.
Bai motsa ba don jina saman gadon a tare da shi ganin ba zai motsaba nakwanta a hankali tare da dora hannuna a bayan shi.
A hankali na dan fara shafa mai bayan shi amma bai sashi motawa ba sai dai ya dan sauke ajiyan zuciya kawai da naji yayi.
Ban daina mai abinda nake yi ba sai ci gaba da nayi da mashi a lokacin ina kai gayi har na kai ga,tura hannu na acikin blanket din da yake rufe a jikin shi.
Inda na sauke hannu na a kan abin shi na fara dan amfani da hannuna ina dan shafan shi a hankali tun yana daure ma abinda nake mashi sai gashi ya gyara kwanciyan shi da kyau ta yadda zaiji dadin abin da nake mashi da kyau.
Ganin haka danayi yasa na ci gaba da mai yadda yake so sai kawai naji ya rugumoni shima ya shiga mayar min da martanin abinda nake mashi da farko.
Mun dauki lokaci mai tsawo muna farautawa junan mu rai a tsakanin ni dashi har sai da naga na kawar da fushin da akeyi dani da farko.
A hankali muke sauke numfashin mu don yadda muka aikatu da junan mu.
Hannun shi naji saman kaina a hankali yake kwantar min da gashin kaina da ya tarwatse a lokacin can ya sauke ajiyan zuciya yana fadin.
Fatima may yasa kika min abinda kikai min kika hanani more abinda Allah ya halasta min a kan ki.
Shiru nayi sai da ya kara maimata min tambayan nace a hankali yaya kayi hakkuri please ni da naji ba ka tambaye ni ba shi yasa na kyale ka
kawai don na dauko hutawa ne kawai kakeyi a ran ka.
Fatima hutu,?
Hutun may zan bukata a kan ki ke fa Allah ya kawo min ke daga cikin jin dadi na don may har kike bukatan wani huta na a hankan.
Yaya don Allah kayi hakkuri hakan ba zai sake faruwa ba insha Allahu.
Daga haka yai shiru tare kankamay ni a jikin shi sai dai naji ya furzo iska daga bakin shi kawai.
Washe gari nan na barshi kwance yana barci bayan sallah asuba da mukayi nima har koma na kwanta amma ganin yana barci yasa na dan zare jikina nafita daga dakin na gyara gida tare da doro muna breakfast.
Sallaman yaya Ahmed shiya sa na je na tayar dashi daga barcin da yakeyi.
Sai da ya dan dauki lokaci ya mike yafito falon yana saye da bakar jallabiya a jikin shi mai laushi.
Yaya Ahmed yana zaune sai bin falon yake da kallo ko ina yaya din yafito bayan har na kawo mai abin sha a gaban shi.
Yaya sadauki yace Normal kai ne yau gidan namu da safen nan haka ?
Yai murmushi tare da kurba drinks din shi yace na ce bari dai nazo tunda kai ba lokaci ke gare ka ba yanzun na mutane.
Yace kai haba kaine dai kawai bamu haduwa da kai amma ai muna haduwa da surfaco yana nufin Imiran.
Sai da suka dan kara gaisawa suka dan taba hira sai dan shiru ne ya biyo bayan kuma.
Fahintar da yayi yazo da magana ne kuma yana jin nauyin yin magana yake ce mai yaya dai akayi ne Normal ?
Yaya Ahmed ya dan murmusa tare da gyara zaman shi yace wallahi abin ne duk ya jagule min UF kwata kwata yanzun harkan san,ana yana son tsaya min gaba daya.
Don dan abinda ke hannuna da nake juyawa yanzu sam kokari ma yake na koma ba komai a hannun nawa gaba daya.
Gashikasan irin matar da nake aure yanzu sai a hankali ba kirki ke ga jamila ba ko kadan.
Sadauki na sauraren shi sai murmushi yake yana dan kada kafan shi a hankali daya harde su guri guda.
Yace yanzun yaya kake so ne don ban fahince ka bane inda zancen ka ya nufa gaba daya.
Yace so nayi ka dan ranta min wasu yan kuli don na samu naci gaba da harkoki na dasu kada abin ya kwanta min.
Sadauki yace kaman nawa ke nan kake bukata yace koda miliyan daya da rabi ne koma dai dayan ne idan zan samu zanci gaba da juyasu hakanan.
Ok ba damuwa inji sadauki yanzu kabari idan na fita don tashi na ke nan daga barci amma nan zuwa two insha Allahu zakiraka kazo ka samay ni can site di na.
Zai fara godiya ke nan ya daga mai hannu yace no haba ka bari mana wanan ba komai bane ai zan kiraka anjima insha Allahu.
Yai mashi tayin ya tsaya su karya tare amna Ahmed yace sauri yakeyi ya fita da murnan samun nasara gurin dan uwan nashi.
Wanka yaya yashiga yafito cikin kanan kayan shi masu kyau yya zauna ya karya sai dai kiran wayan shi da ake tayi yasa shi barin gidan da wuri hakanan.
Zai fita ne nake cewa yaya dama nace don Allah mutanen nan naka ko zaka dan taimaka masu da dan wani abu don naga wata yai nisa kasan abu ga masu iyali.
Kallon mamaki yake min yana gyara wuyan rigan shi yace wasu mutane na ke nan fa ?
Nace cikin yar murya karama masu gadin ka tunda a karkashin ka suke da zama nagani.
Humm kawai yace min ban samu amsa ba sai ce min da yayi sai na dawo ke nan ni zan fita ki bar wanan girkin zan samo muna abinda zamuci har na dare.
Don naga kaman aiki yana son yai maki yawa zan wa maji magana ta samo maki wacce zata dan dinga taya ki aikin nan haka.
Kawai nafi bukatan ki kwanta ki huta sai dai kawai ki kula min da shimfidana da kuma na yara in Allah ya kawo su.
Nace kai yaya har ina wani aiki dagani sai kai kawai a gida in ma hakane don debe kewa kawai da a taimaka min na roko kaunata Aisha ta dawo guri na ko boko itama ta samu tayi.
Shima shiru yayi bai min magana ba sai cewan da yayi ni na fita sai na dawo ki kwanta ki huta please.
Yana fita na kammala komai da zanyi na koma dakina kaman ko yasan ina da gajiya a jikina sai barci.
Yana fita har ya tayar da motar shi abu de mai get zai fita daga gidan yaja ya tsaya da sauri musa ya iso gare shi ya sauke glass din motan yace .
Malam musa uwar dakin tace min kuna a cikin bukata na taimaka maku dashi sai dai ban da kudi mai yawa a hannuna amma ga ashirin ku raba har muga abinda zai biyo baya kuma.
Nan yaja mota ya barsu suna ta zabga mashi godiya suna muna fatan alheri.
****** ********* ******
Ban falka ba sai kusan uku na rana na tashi a gagauce ne sallah tare da watsa ruwa a jikina na fito falo ke nan ban dade da fitowa ba ya shigo gidan.
Da ledoji guda uku a hannu da sauri na mike na karbi ledojin dake hannun shi nan ya zube saman kujera yana ce wash duk nagaji wallahi.
Bude ledan nayi inda naga take away ne yayo muna hadaden fridrice ne sai drinks da kuma naman rago mai zafi sosai.
Ba mu ko je dining ba nan na dauko plate muka zauna, muka ci muka sha a tare sannan muka dan dauko hiran zancen abinda su Umma sukai wa mama Nafisa ta fada mata.
Shi ya kawo min zancen amma a karshe ni ya bari da magana don shi ba ma,abocin son magana mai tsawo bane sosai.
Muna nan zaune aka kirashi da waya yafita fitan shi bai dade ba da fita sai gasu nafisa da kawayen nan nata biyu sun shigo gidan.
Suke ce min wallahi yunwa suke ji shine sukazo su ci abinci ban tsaya ba namike zuwa kitchen na dora masu abinci dafa duka nai masu yaji kayan hadi sosai.
Sai da sukaci suka koshi muna ta hira dasu suna ban labarin wani mutum da yaso ya yaudare su duk sun tsorace dashi suka ce suna ganin kamar dai mutumin dan cult ne ma.
Nace Anty ubangiji dai Allah yakawo lokacin auren ku ku huta da wanan rayuwan haka na.
Kowan su tace min amin amin sai yamma lis suka bar gidan nai masu godiya suna jin dadi suka tafi abin su na koma ni kadai a gidan.
Har na kara komai da zanyi na shiga nai sallolin na nafito falo musalin takwasa da yan mintina a kai.
Nai kwaliya na don nasan duk inda yake bai nisa da dawowa gida a lokacin.
Shiru shiru bai dawo ba har goma ya shude nayi sa,a ina kallon wani action film daya dauke min hankalina a lokacin.
Ko da zan daga kaina na kalli a gogo har shadaya da wani abu na dare a lokaci don haka namike tare da kashe kayan kallon na koma dakina.
Ban dade da shiga ba naji horn din shi ya shigo gidan maigadi yana bude mashi get.
Shiru shiru banji motsin shi ba don nasan idan ya shigo sai ya fara leko dakina don nasan cewa ya dawo.
Jin shirun da nayi ne yasani fitowa daga daki na falon yana da dan duhu sai na nufi gurin kunna wutan falon.
Zaune na hango shi saman kujera shi kadai ya dafe kai yyai share share yana barci a zaune.
Karasowa nayi inda yake a kwance din take na fahinci yau hannun agogo ya koma min baya yayi halin nashi ke nan.
Gani haske wuta yasa shi dan bude idanuwan shi da suke mai a buge ya dan kalle ni a cikin mayen da yake.
Cikin karfin hali muryan shi kasa kasa yace min ke kashe min wutan nan please ?
Sai da na dan tsaya a kan shi na dan tsura mashi ido na wani dan lokaci na juya na kashe mai wutan na shige dakina na kwanta tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai.
Sai dai duk yadda nayi nai barci na kasa yi don hankali na yana gare shi don nasan zai iya kwana a haka idan na barshi a gurin.
Tashi nayi tare da share hawaye na na nufi falon har lokacin yana a yadda na barshi da farko a gurin.
Dan bugun kafadan shi nayi nace mai ya tashi ya shiga daga cikin daki yace ke wani daki kuma nan ma gadon ai yayi min.
Da kyata har da zagi na samu ya shiga daki ya kwanta na cire mai takalman dake kafan shi don har dasu ya haye gadon gaba daya ya kwanta dasu.
Na jawo mai kofa na wuce zuwa dakina nasaka key kawai amma barci yaki daukana sai tunane nakeyi tausayin kaina dashi ya kara kamani nan naci kukana ba mai bani hakkuri har zuwa dare sosai barci ya dauke ni.
Da asuba na tashi nai sallah na koma na kwanta don idona cike yake da barci kodana falka har naso makara zuwa school ranan.
Gashi monday ne a guguje na shirya nafice daga gidan abina na samu masu aiki suna aiyukan su a waje nan suke gashe ni da min godiya jiya maigida yai masu alheri yace daga gare ni ne sakon.
Murmushi nayi kawai na masu sai na dawo na fice gidan zuciya tab da bacin rai da bakin cikin wanan irin rayuwan da na shiga.
Ina isa school na samu har lectura mu ya shiga ko na samu yabarni nashiga na zauna.
Bazan iya cewa ranan na fahinci abinda akayi ba a lokacin don irin yadda nai nisa ga tunane.
Sai sha daya saura ya falka ganin yadda lokaci yakai yasa shi mikewa da sauri ya fada bathroom yai wanka yazo yai sallah.
Inda ya idar da sallah ya zauna yana tunanen abubuwan da zai iya tunawa a lokacin .
Tabbas yasan nasan yasha ta juya ya kalli godon nan ya fahinci ban ma kwana a dakin ba ke nan.
Hakan yasa jin wani iri bai so shan komai ba ta yadda zan fahinci akwai abinda yasha amma sai yasha dozes da yawa yadda za,a fahinta yasha din.
Baiji dafin yadda yasha har na fahince shi ba sai yaji kunyan kan shi kawai ya kamashi da wani ido zai kalle ni yau.
Yuwan da yaji yasa ahi mikewa zuwa dining yaci abinci amma ya samu babu komai ya leka kitchen din yaga ba alaman ma na leka kitchen din yau.
Dakina ya nufa yaji shi a kulle sai lokacin ne ya tuna ai Monday ce nafita gidan ke nan zuwa school.
Koda muka futo daga class sallah nayi na koma cikin motana can na zauna nai kukana mai isa na maryam tana ta nana bata samay ni ba sai da tai dabaran zuwa gurin mota ta hangoni.
Ta kwankwasa min glass din da kyat na bude mata bayan na saita kaina .
Kallin mamaki take min motan ta shiga itama ta zauna tana min wani kallon zargi.
Can tace Bintu may ke faruwa ne wai?
Babu komai na bata amsa tai murmushi tace haba Bintu babu komai zaki shige mota ke kadai kina kuka haka?
May yafaru ki fada min nace ba komai anty tace da komai kan yaya ne ko ?
Shiru nayi saida takara cewa yaya ne ko ya tayar da halin nashi ke nan ko ?
Ban san lokacin dana fashe da kuka ba itama kukan ta fashe dashi tana cewa watau ashe yaya baibar halin nan nashi ba ke nan.
Nifa kwanaki yaya ke fada min cewa bai bari ba amma yasan zaki taimaka mai ya bari insha Allahu.
Nace ni anty yaya zanyi da wanan halin na yaya may yake son nai mai wanda ban mashi da zai min wanan sakauyan haka?
So yake idan na fita mutane su dinga nunani ga matar mashayin can ko may ?
Anty bazan iya ba gaskiya duk son da nakewa yaya dole na barshi yafi min sauki wallahi.
Tace haba Bintu inkiyi haka baki kyauta mashi ba dashi da maji dama mu yan uwan shi.
Baki ganin auren ki dashi ya kawo mai sauyin rayuwan shi da dama ya canza sosai kamar bashi ba.
Hakkuri zakiyi kawai ki jajir ce mashi ke ma kinuna mai yanzun kina da fawa akan shi kamar yadda take dashi akanki.
Tana saki yana hanaki kema din nuna mashi ke jaruma ce ba wai abin hannun shi kike so ke shi kike son ya gyaru ba wai abin alatun da yake kashe ki dashi ba.
Nan dai taita bani shawara take ce min kuma zata fadawa maji halin da yake ciki don itama ta tsawata mashi.
Da sauri nace kada ki fada mata anty ki bari na gwada nawa sa,an mugani idan bai bari ba sai mu sanar da ita.
Tace to shike nan amma gaskiya badon kince haka ba dana fada mata don ta san bai dena ba har yanzu.
Sai yamma na shigo gidan na shiga dakina nai sallah nan ma kuka na zauna nayi sosai a gurin sai da naji yunwa namike don neman abinda zanci tea nasha don hanjina ya dan warwale a lokacin.
Sai da nai sallah magariba ne na zauna ina tasbihi har akai kiran sallah na mike na gabatar da ishai.
Wanka na kara yi na koma kan gado na na kwanta sai ga kiran anty maryam ya shigo min muna cikin magana da ita ya shigo dakin.
Ban ta da kai na kalle shi ba na ci gaba da wayana kawai shima bai fita ba tana tsaye ya kura min ido kawai.
Sai da mukai sallama da ita ne yake cewa kin dawo ashe ?
Umm kawai na bashi amsa dashi batare da nai magana ba na juya ina saka wayana a caji kawai.
Ganin ba zan juyo gare shi ba yasa shi cewa abinci fa naga banga komai ba a table.
Ban yi ba na bashi amsa a takaice kawai.
Bakiyi bafa kikace nace mashi eh kawai.
Ya dan tsura min ido take ya gane cewa nasha kuka yadda idanuwa na suka koma luhu luhu dasu.
To may zaki ci dabaki girka ba nace ban jin yunwa ni daga haka na mike ma nashige bathroom don ban ko son ganin shi wallahi.
Ganin nashi bathroom yasa shi juyawa ya fita daga dakin fita yayi daga gidan zuwa sayo muna abinda zamuci da daren.
Jin yafice yasani fitowa na sawa daki na key kawai na koma na kwanta abina can bai wani dade sosai ba ya dawo gidan.
Murda kofan tayi yaji shi a kulle ya kwankwasa ban bude ba ya kira wayana jin kiran shi na kashe wayan gaba daya na kwanta abina.
Ganin bafa zan fito ba yasa shi ya zauna yadanci abinda yasayo muna duk da ba dadin ci yake ji ba a lokacin.
Haka yamike yaje ya kwanta cike da tunane kala kala ta yadda zai bullowa al,amarin namu.
Yasan baida gaskiya amma haka zai daure ya dakatar da abinda nake shirin haifarwa a lokacin nan.
Don shi yana ganin don may zan so takurawa rayuwan shi kawai ina ruwana da bukatan shi may ya rageni dashi na rayuwa da zance zan hanashi nashi kalar rayuwan.
Har barci ya dauke shi bai gama tunanen abinda ya dace ya aiwatar a kaina ba hakanan.
Washe gari ma kafin ya dawo motsa jiki har na bar gidan ko na fita yai mamakin hakan shi da kan shi ya nemawa kan shi abin karyawan da zaici.
Da wuri na dawo nai girki na aje mai saman table nashige ciki abina ban kara fitowa ba.
Yana shigowa a lokacin idon shi akan table yaga abinci a gurin yakai kallon shi ga kofana yana saye yasan dai ina ciki a lokacin tunda babu inda nake zuwa.
Dakin shi ya shiga yai sa,a yau ma na gyara dakin bakamar jiya ba da na hau sosai.
Murmushi yayi kawai ya shiga wanka a lokacin yafito yasaka kayan shan iska don zafi akeyi sosai lokacin.
Dakina ya nufa don ganin har lokacin ban fito falo ba ina dakina a kwance nake kasa saman ties idanuwa na a rufe ina bin kira,an dake tashi a wayana a hankali.
Ya dan dade tsaye sai jin nauyin mutum ya shigo dakin danayi yasa ni bude idanuwa na da suke min a rufe.
Yana tsaye a kaina ya saka hanayen shi a cikin aljihun wandon shi tare da kura min idanuwan shi.
Ganin shi tsaye a kaina bai sa na bude idanuwan nawa ba sai kara lumshesu danayi kawai.
Dan tsugunowa yayi tare da rage tsawon shi ya tabo kaina da sauri na bude idona na watsa mai wani irin kallon tsana da ban masan lokacin da nai mashi shi ba.
Yace ki taso muci abinci nace akoshe nake ya mike tsaye yana cewa to sai kizo ki zuba min ai.
Nace ai banice mai zuba maka kwayan ka ba idan zaka sha don haka sai kaje mai baka kayan mayen ka ta baka amma bani Fatima ba.
Da mamaki ya kalleni yace ke kada ki soma kice zakiyi min rashin kunya wallahi.
Nace da ke nan da nake daukan ka a mutum ba yanzun da ka zube min ba.
Ke ni kike fadawa haka watau kin raina ni ko don kin ga kamar ke kin isa ko may wai.
Nace aini ban isa ba kuma ba kowa nake ba don haka kowa tashi tafishe shi kawai.
Kaman zai yi magana sai kuma ya juya yafita daga dakin ran shi a bace yana ci yana kallon kofa na ko zan fito daga dakin amma shiru har ya gama babu alamana a falon.
Gaba daya taji gidan ba dadi ban fito ba sai ma da naga tara da rabi na dare kawai na kulle kofana na kwanta kawai.
Goma da rabi ya kashe kayan kallon da komai na falon ya shiga daki sai da yasa kayan barcin shi har ya kwanta ya mike zuwa dakina ya murda a rufe kofan yake a lokacin haka ya juya ya koma don yasan bazan bude ba.
Bai taba tsanmanin cewa akwai shakuwa haka a tsakanin mu ba kuma ba zai iya daure rashi na ba a yanzu sai da yaga yai rabin kwana yana lalaban gefen da nake kwantawa bai jini ba.
Nima a nawa bangaren kusan hakane na kwana da kewan shi duk da haushin shi da nake matukar ji a lokacin.
Kowan mu da tunanen dan uwan shi ya kwana a ran shi cikin damuwa muke .
Tun da safe ina kitchen ina hada abinci yazo bakin kitchen din nai matukar mamaki da bai fita motsa jikin shi ba yau.
Kamar ban san yana gurin ba na share shi ya tako har zuwa cikin kitchen din inda nake tsaye ina motsa dankalin dake saman gas.
Ganin da yayi bazan mai magana ba yasa shi cewa kin tashi lafiya ?
Nabashi amsa da lafiya kawai.
May yasa kike rufe min kofan ki kwanan newai Fatima ?
Dagowa nayi muka hada ido kawai sai na kawar da kaina naci gaba da abinda nake yi ina tunanen watau bai masan abinda yayi ba ke nan koko tsaban rainin wayyo ne hakan ?
Ke nake tambaya ya maimata min .
Kaina na girgiza mai nace ina kwashe dankalina a tunkuya a hankali.
Nace ban da amfanin komai a gare ka don shaye shayen ka yafini daraja a gare ka nagani.
Don haka kaje kayi abinka kabarni na yarda na zama ma yar aiki kawai a gida don shine ya dace dani.
Murmushi yayi ganin zan wuce ya dan ja dabaya ya bani hanya yana fadin wanan kuma maganar kice amma ni shana baida alaka da kusantar ki a gare ni.
A ganin ka ba amma ni bazan taba mu,amula da mutumin dake a cikin sabon Allah insha Allahu.
Ido ya zuba min don jin abinda nace ya fahinci a shirye nake na zuba mai bakaken maganganun dake a bakina a lokacin.
Shiru yayi ya dan dade tsaye a gurin yana kallon yadda nake aikina a cikin tsabta da gwanewa sai ya juya kawai yabar kitchen din zuwa falo ya zauna cikin damuwa.

A LOKACIN MU KE ,,,,,
Ba karamin jiki umma taji ba sanadin kafan nan ta abu ga mai babban jiki irin ta.
Duk halin da take ciki bai hanata makirci ba daga zaune take kulla sheri kulun.
Ranan mama Asiya tazo tanawa Umma gulma wai taga maji da wani sabon waya tana ganin Sadauki yazo mata dashiba cikin tsaraba.
Umma tace shine mu bai bamu ba ya mayar damu mutanen kawai ko indai waya ce kowa ma na iya saye ai.
Asiya tace wallahi kona sa sace wayan ma gaba daya mu batar dashi kowa ya huta.
A dole ita yanzu ga mai da mai hali komai sai dai mu ganshi gareta ina haka ma wallahi bai yuyuwa ko alama.
But Nafisa dake daki tana shirin ta tana sauraren su tafito tace kaikayi dai koma kan mashekiya.
Kullun ku ke nan cikin kullawa matan nan sheri ita da diyan ta Allah na kareta ya na komawa kan diyan ku amma baku fasawa ku daina.
Don haka yau wallahi sai na fadawa maji wanan sherin da kuke kulla mata don ta kama wayan ta.
Yaya sadauki ya nuna min so da kauna wanda duk duniya yanzun ban da kaman shi don ni ko bai min komai ba ya bani so da kauna na yan uwan taka da ba wani dan uwa da ya taba bani shi.
In kin yi haukan e da gaske yau ina son ki gwada min kije ki fadawa Hauwau din ga abin da muka ce mata.
Murmushi tayi ta koma dakin ta kawai taci gaba da shirin ta har sai da ta gama tsab tafito tace to ni zan fita.
Ba dama Umma ta hanata ta ci mata mutunci tunda baba ba gida yake zama ba shi don shi gar yanzu tana dan tsoron shi.
Tana fita ta samu mummy da mama a tsaye suna magana kan wani makwacin su da baida lafiya suna son zuwa gaida shi.
Nafisa na fito mummy ta bita da ido caaa maji na kallon ta saudaya ta kawar da kan ta tana fadin a zuciyar ta Allah ya shirya kayan shi.
Maji sai ki kama wayan ki don gasu can ciki daki suna kulla yadda zasu raba ki dashi kowa ya rasa.
Don kin san su kullun cikin kulla sheri suke basu bari ki kama kayan ki don tun da suka ce sai sun dauke shi sai sun daka din don ba yau suka fara sheri ba.
Daga haka ta juya,ta,wuce abinta, mamaki ne ya kama su maji da mummy suka shiga magana kan Nafisa.
Mommy ne tace aiko tunda kika ji sun fadi haka wa yan nan macutan su na da niyar yin hakan don haka sai kiyi taka tsatsan da kayan ki ba waya ba komai manaki sai ki dinga hankali dashi don wa yan nan mutanen basu da imani ko kadan.
Bai wa mummy ba da baba ya dawo sai dai ta fada mai abinda Nafisa ta fada ma su.
Ran Baba yai matukar baci ya mike sai dakin Umma don a zaune take kafan ta har yanzu ba lafiya.
Yana daga labule suna zaune tare da mama daga kofan ya tsaya yake cewa to muna fukan Allah .
Duk wanan isharan da Allah ke nuna maku bai maku ba sai kunci gaba da kulla makirci don baku da imani.
Shege ya fasa sace wayan maijidda a gidan nan daga ku har muna fulan diyan ku da kuka lalata da mugun abu.
Yau gashi abin kuya ke Atika yar cikin ki da Allah ya mayar haka tazo tana tona maki asiri akan sherin ku.
A na dai kallon Nafisa haka amma ke Atika kece silar mayar da rayuwan, Nafisa haka kuma har gobe dake nake kuka a gidan nan.
Ku biyun kune silar duk wani balain da yarana suke ciki gaba dayan su don duk da hannun ku ga lalacewan su.
Allah ya isar min akan da duk wani da nawa da kuka lalata min a gidan nan kada kuce ban san duk wani sherin da kuke kullawa bane.
Wallahi nasan komai na dai barku ga Allah ne kawai ya fitar min da hakkina a kan ku.
Daga haka ya juta rai a bace yana fadin Allah ya isa tsakani na daku.
Tunda baba yafara magana jugun sukayi duk kunya da bakin ciki mamaki ya baibaye su sosai.
Yana ficewa mama Asiya tace yanzu yaya ashe saida ja,iran yarinyar nan ta fada masu zancen nan.
Amma ko nafisa takai la,ananna wallahi kidaina zaginta haka kada aji tsakanin mu idan la,anewan yafi haka kuma a kanta yaya kike son nagan ta ne.
Duk fa kece kika jawo muna wanan tsinuwar haka wallahi ina zaune zamana kika shigo min da wanan tsurkun kinga sabon waya hannun Hawau,
Ni yaya ina nasan wanan mai bakin tsiyan tana dakin bata fita aida ba zan soma maganan komai ba wallahi tun ita ta zama abinda ta zama.
Umma tace sun dai zama gidan nan waye baida abin fadi tab a tsuliyan shi sai dai na wani yafi na wani kawai.
Anan dai sukai ta yaba wa junan su bakar magana dama a haka hitan nasu ke kare a karshe kuma a dawo a samu sun shirya kafin wani dan lokaci.
****** ********* ******
Yana dai zaune Abuja ne amma kwata kwata hankalin shi yana a kan yar matan shi da yanzu yake jin ta ta zama mai wani rabin rayuwan shi.
Wata rana yankayi matukar mamakin kan shi don bai san lokacin da har son Fatima yai mashi illa ba haka a rayuwan shi.
Murmushi yayi ya mike daga kwancen da yake tare da dan murmusawa tunanen yake yadda har yanzu kunyan shi bai fita a idon Fatima ba.
Ya kamata ya san yadda ya fitar mata da wanan kunyan nata hakana lokaci yayi da ya kamata yai wani abu akan ta don kawar da kunyan dake idon ta dakuma sauran yarintan dake cin ta hakana.
Yana son mace wace ta san kan ta tasan hanyar da zatabi ta gyara mashi shimfidar shi.
Fatima zata zata iya zata iya mana, kwai dai wanan bakin kunyan nata ne ke hanata aiwatar mashi da yadda yake so da ita amma yanzun kan dole ne ya san yadda zai batar da kunyan nan nata.
Ta dawo daidai irin yadda yake son macen auren shi ta kasan ce mai a rayuwan shi komai normal.
Yana zaune sai faman tunanen al,amarin Fatima ya keyi yaji anyi nocking din kofan shi kafin ya amsa sallaman shi yaji an turo kofan dakin don dama a bude take.
Linda ce tashigo dakin abinda yasa shi saurin tashi zaune ke nan a lokaci guda.
Da sauri ya mike zaune da kyau cikin dan kaduwa don baiyi expecting din zuwan ta saboda sun dade basu hadu ba da shi, tun lokacin da ya sasanta da Fatiman shi yaji gaba daya linda tafita mashi a rai.
Linda may yakawo ki gurina again bayan na fada maki abinda nake bukatan kiyi kince bazaki iya ba.
Ta watso mashi wani mugun kallo na see you tace to maye don anzo gurin ka saboda wanan karamar yarinyar daka aura ne da batafi sixth ba.
Yace don't dear insult my wife she is part of my life now.
Ganin da gaske yake nufin maganan shi har cikin ran shi irin yadda taga ya hade rai a lokaci guda haka don tasan halin shi sarai gurin rashin mutunci idan ya tashi yi.
Ta dan marairai ce tace haba my man kada ka mance da alkawrin dake tsakani na da kai mana please.
Yace kema kin manta da alkawarin da nayi cewa idan ba zaki musulunta ba ba zan iya auren ki a haka ba.
Rashin yardan ki yasa har iyayyena sukai min zabin mace da kan su wanda yakai yanzu na gane cewa gata sukai min da hakan.
Don haka tunda kin zabi son iyayyen ki a kaina nima yanzu na zabi zabin iyayyena akan ko wace mace.
Don haka ki tashi kifice min a gida i don't want to see you again, dont ever think about me again its over now.
Linda tace my man ni kake fadawa haka akan wanan little girl dinka wai wife kake nufin kayi komay.
Ka sanni ni na wuce ka wullakantani akan wanan yarinyar don kasan asalina ka kuma san waye ubana a kasan ghana.
Amma tunda kace haka jeka zaka gane kuren ka zaka gane ni Linda ba abin wullakantawa bace a take lafiya.
Ya ja dogon tsaki tare da nuna mata hanya yace babu abinda zangani sai alheri tunda bake ce Allah ba banza dake kawai.
Kije ki rike addinin ki da iyayyen ki nima na rike nawa koba shike nan ba.
Tsayawa tayi na dan lokaci tana kallon shi babu abinda zata iya don tasan ba saurarenta zai yi ba ma yadda yayi.
Ta juya kawai tafice kamar yadda ya umurce ta da yi ran ta a bace tabar dakin nashi.
Komawa yayi ya kwanta ranshi a bace da Linda duk da yasan tana matukar son shi amma ya zama dole yanzu ya kawo iyaka a tsakanin su kawai don Fatiman shi tariga da tai masu zara ko ta ko ina.
Ya sake wani dogon tsuki kawai tazo ta bata mashi jin dadin shi da yake ciki a lokaci guda na Fatiman shi.
****** ********* ******
Nai wankan tsarki a yau don haka na baro school da wuri don ina son a wanke min kaina a gayara min shi.
Shagon da muke zuwa da maryam gyaran kai na nufa daga gyaran kai har na jiki sai da matar tai min shi ban dawo gida ba sai yamma lis na shigo gidan.
Ina farka motana sai ga mai wankin mu Atiku yazo inda nake tsaye ina kokarin rufe motar ke nan yake cewa.
Hajiya barka da dawowa, sannu da zuwa dama tun dazun nake jiran dawowan ki.
Na juyo nace a,a baba baka tafi gida bane yau yace wallahi hjy ban tafi ba na dan tsaya don naga dawowanki ne don wallahi ina da bukatane.
Shine nace bari na kawo maki koke na ko zaki taimaka min ki bani koda dubu goma ne idan anyi biya saina mayar maki ko kuma a cire daga cikin albashi na wanda dai yafi sauki daga ciki.
Wallahi matata ce amarya na ba lafiya don tana fama da laulayin ciki ina son ta tafi asibiti dana kuma Aliyu ya gama makaranta zai shiga secondry gashi har an fara karatu amma shi yana gida a zaune.
Tausayi mutumin yabani don gaskiya gaba dayan su yan aikin gidan suna da matukar mutunci sosai.
Nace mai ya bari na zo ita kuma mara lafiyan Allah ya bata lafiya mai karatu kuma Allah yabada sa,a sai na shiga.
Kudin da yaya yake bani ne bani kashewa na dauko dubu ashirin daga ciki nafito dashi.
Nabashi goma naba maigadin dare dana rana dubu biyar biyar su raba.
Atiku yace hjy nagode insha Allahu da anyi biya zan dawo maki da kudin ki da yardan Allah.
Nace haba Baba ka barshi na bakane kawai kaje kayi amfani dasu idan zai ishe ka.
Da sauri ya juyo yana cewa hjy kin bani wanan kudin haka dukka ?
Ikon Allah sai naga yakai tsugune tafara fadin Hjy nagode nagode yadda kika rufa min asiri Allah ya rufa maki duniya da lahira.
Allah yabaku zuria masu albarka a rayuwan ku, Allah ubangiji ya tare ku daga sherin makiya nagida dana waje.
Nace amin baba nagode da adduan ka baba sai ga sauran sun karaso suna min godiya da addua su ma.
Nagode masu na shige ciki don duk nagaji a lokacin wanka nake son yi nai sallah kawai sai na nemi abinda zanci a raina.
Ina shiga malam musa yace Atiku kaga ikon Allah ko yau inane baka shiga ba a garin nan dan neman rance amma baka samu ba.
Yanzu kaga ikon Allah ko yar arziki irin albarka nikan ai gobe gidana cefane lafiya na lau insha Allah.
Kai mutane mutane magindanta suna cikin wani hali yanzu na bukata saboda motsalolin rayuwa da yaiwa mutane yawa a wanan lokacin da muke ciki.
Duk yadda kake ganin kanka a cikin matsi wani nacan yafika don haka ko yayane ko ba yawa ka taimaka wa na kasa dakai don ita addua ba,a san inda take kamawa ga bawa ba.
Da wanan irin tunanen na shiga wanka nafito sai na jini wasa ina idar da,sallah naji abinci kawai nake bukatan ci a lokacin.
Don haka na fito na nufi kitchen don agazawa cikina dake dan kugin yunwa a lokacin gani ni kadai a cikin gida kamar mayya dani.
Hakan yafi min da zama cikin tashin hankali da anty Amira ke zuwa yi min wai da sunan zama.
Indomie na dafa na dan cika mai attardu nan da nan ya dafu na zauna naci nasha ruwa na kawar da kayan danaci abincin.
Kofa na rufe don karfe takwas na dare nasan babu wanda zai zo kuma gidan a lokacin.
Dakina na koma bayan na kashe duk wani kayan wutan dake falon, wanda shigana yai daidai da rurin da wayana ya soma a lokacin.
****** ********* ******
Yaya sadauki ne a layin da murmushi a fuskana na dauki wayan nace Assalamu Alaikum.
May ye hakane sai yace min babu ko dan irin honey, darling, sweet heart din nan sai ki wani ce min wai assalamu alaikum kawai ?
Nace haba yayana ni wani suna kuma kake so na canza ma,bayan wanda Allah ya dora maka a kaina na yayana.
Yace No ban yarda,ba gaskiya ni suna nake son kawai a canza min nagaji da yaya din nan kamar wani mai yaye miya yabar tuwo gaya can dani.
Ban san lokacin da maganan tashi tabani dariya ba nace kai haba yaya baka son girman ke nan kuma ko?
Yace kin daiji na fada maki ni dai ban son wanan sunan yayana din don haka yanzu basai gobe ba sai naji sunan da aka rada min din.
Shiru nayi ina tunanen ni yanzu wani suna kuma zan kirashi dashi indai ba son matsawa rai ba.
Ke fa nake saurare Fatima na nisa nace to yaya love yace daya nace my life ko?
Sai naji yai murmyshi yace to ke fa amna kamar wata tsohuwa can wai kullun yaya yadan make muryan shi yana,kwakwayona yadda nake kiran shi da sunan yaya.
Nace kai yaya nidai wallahi kana son ace min banda kuya daine wallahi amma idan akaji na canza maka suna ai za,a kalleni wata mara kunya can ne.
Yace da sauri mutane mutane su zasu hana ki dadada min zuciya ko kuwa ?
Shiru nayi yace abar wanan zancen yaya bakon ki yatafine ko yana nan ?
Da,mamaki na tambaye ina fadi bako kuma yaya ?
Waye yaya ko da wani kike magana,ne acan kusa dake ?
Nai sauri na tuna ina cewa wai yaya love wani bako kake magana ne wai ?
Wanda ya hanani farincikina da aka saba min mana, duk hakan bai sa na kawo tunane na akan period yake maganan shi.
Murmushi na dan yi a hankali nake cewa yananan har yanzu bai tafi ba da karfi yace what kina nufin har yanzun mesestration kikeyi nace eh yaya.
Shiru na dan tsawon lokaci baiyi magana ba sai can yace ok kina lafiya dai ko?
Nace mai Alhamdullahi dan hira,muka taba sama sama ya kashe wayan yana min sai da safe.
Har barci ya kwashe ni a gurin inda nake a kwance sai faman tunanen shi nakeyi ina matukar mamakin wanan sauyin nashi nace Allah ke nan mai iko yau wai ni Fatima ce yaya sadauki ke wa wanan kulawan haka yanzu.
Washe gari bayan nayi sallah na fara aikin gyaran gida da ta ko ina duk da gidan ba wani dauda ke gare shi ba sosai amma,sai kyalli gidan ke yi kawai.
Haka kawai nace bari nai girkin abinci rana mai kyau da haduwa ,sosai na zauna na girka ..
Sai da ga abincin na gama amma kuma na kasa cin komai daga ciki sai kallon shi nakeyi a gabana kawai.
Abin mamaki sai gani ina kewan ganin yaya sadauki don ina bukatan ace yanan yaci wanan girkin dana hada.
Ban kai ga karshen tunane na ba naji bell din gidan yana ringin a kasalance na mike zuwa duba wanda dake sallama a kofan gidan.
Yana tsaye rataye da coth din shi a kafadan shi sai yar jakar kayan shi dake sabale a hannun shi.
Na kasa boye farin ciki na dana gan shi a lokacin na ji kamar na fada mai a jikin shi na rungumay shi amma kuma bazan iya yin hakan ba.
Kamar wanda ya karanci zuciya ta a lokacin sai naga ya ware min hannayen shi da sauri ba bata lokaci na fada tsakiyan hannayen shi.
Ya mayar ya rufe ni dasu ina jin yadda yake sauke ajiyan zuciya a hankali kamar yadda nima ajiyan zuciyar na sauke ina cewa sannu da zuwa yayana.
Dago kai yayi tare da dan ture ni baya kadan nai mamakin hakan sai ji nayi yace niba tsoho bane da zaki dinga kirana wani yaya can na fada maki kuma sai kin biya bashin hakan da kika fasa min tunda na fada maki bana so.
Da sauri nace iam sorry my life ai min afuwan please bazan kara ba da yardan Allah.
Murmushi naji yayi tare da cewa yana tafiya ina tafe a bayan shi tare da jakar dana ansa a hannun shi.
Zubewa yayi saman kujera yana lumshe idanuwan shi a hankali dakin shi na wuce na kai jakar na dawo na dauko drink hade da cup na nufo shi.
Idanun shi suna a lumshe hannun shi na saman wuyan shi yana kokarin cire nicktie din da ya daura a wuyan shi.
Na tsiyaya mai ruwan lemo a cup tare da dago cup din ina cewa uhmm, yaya love ga ruwa kajika makoshin ka dashi ko.
Sai a lokacin ne ya dan bude daradaran idanuwan shi ya sauke idanuwan shi a kaina.
Sai ce min yayi bissimilah ko tare da gyara zaman shi yana nufin na bashi.
Gaban shi na dawo na tsugun na kadan tare da mika cup din a bakin shi a hankali yake kurbawa ina yi ina cire cup din daga bakin shi a hankali har ya sha fiye da rabin wanda na zuba mai a cup din ya daga min hannun shi yana cewa thanks.
Haka yasa nagane cewa ya koshi ke nan na aje cup din daga gefe dayan saman table din.
Nace mai abinci fa my love?
Zan so idan na samu amma bari na watsa ruwa na sauke gajiyana tukun .
Shigan da nayi yai matukar burge shi sosai don kayan sun min matukar kyau sosai english wear ne a jikina wando da riga yar rigan daga baya ne ya dan sauka min kadan amma daga gaba bude yake yana yauki sosai idan mutum ya motsa da jikin shi.
Yana matukar bukatan matar shi a lokacin amna sanin cewa tana cikin period yasa shi daurewa tare da jan guntun tsuki kawai yana kokarin mikewa tsaye.
Dakin shi muka nufa da taimakona ya shiga wanka ni kuma na kwashe kayan zuwa kaiwa mai wanki ya wanke su.
Tsab na shirya dining din na jera mai komai yadda ya dace na aje shi tare da komawa dakin nashi don nagani ko yafito daga wankan.
Na samay shi a tsaye gaban wardrobe din shi yana ciro kayan da zai saka a lokacin da sauri na kara tare da taimakon shi.
Na fitar mai da wasu masu saukin sakawa a jiki na mika mashi sai da ya shirya muka fito daga dakin a tare da shi.
Sosai yaji dadin girkin yafara ci cikin jin dadi da kwanciyan hankali sai dai yana mamakin yadda ya samu nai girki haka kaman nasan da zuwan shi garin ranan.
Sallama mukaji a tare muke kallon mai shigowa gidan yaya Bashar ne sai su maigadi dake shigo mai da katan shi har dining din yaya Bashar ya karaso yana fadin kai mutumina dama dai an san da zuwanka ke nan wanan girkin haka ?
Yai murmushi yace nima dai shine nake mamakin hakan kunyan maganan yaya bashar naji nai dan murmushi kawai.
Gyaran jikin da akaimin jiya yasa nai wani irin balain kyau sosai kurciyana ya kara fitowa fili sosai a lokacin.
Yaya bashar zama yayi sukaci abincin a tare suna hiran bayan robo a tsakanin su ganin lokacin sallah azahar yayi na sulale zuwa dakina nai sallah.
Ko da na fito na samu sun fita hakane yasani sanin sun fita zuwa sallah ne.
Bayan sun dawo a falo suka zube ranan a tare suka wuni a gidan can bashar yace kai bari na tafi gida nima gashi na hanaku walawa kaida yar kaunata.
Dan tsuki yaja yana fadin kai wani angwancewa tun tafiyana fa take zuban jini wai har yau bai tsaya ba wanan ai yazama matsala ke nan ko?
Haba wani matsala kuma kai mutumina badai har ka fara damuwa da rashin mace ba ke nan tare da kai.
Yace I dont know gaskiya amma kila hakan ne kasan ina under training din ka ne ai dole ne na ji hakan .
Kai ban son sheri kaji kai dai kawai kazo hannu ka shiga gari kawai amma ni yaushe na taba baka wani training can.
Wanda kulkun kana cikin jajayen mata da bakake kuna kallon ko wace kala har gida ake kawo maku tayi fa nasan a raha don fatin jinin ku kawai.
No no no kada kai min sheri wallahi bash ni idan ba a kan matana ba tunda nake ban taba aikata haka ba wallahi iyakata kiss kawai da mace ko shi ba wai wani can ba mai yawa.
To yanzun kan kaunata ta cira tutan ta akan haka ta kawar da wanan rantsuwan ai a zuciyar ka ko?
Ban sani ba yacd je gata can daki ka tambaye ta ina ganin zakafi samun amsanka a gurin ta.
Yace wani don Allah rufa min asiri kaji kada kasa ana daukana da daraja na koma shasha .
Sadauki yace dama may kake dan iska ita daine da bata san halinka ba take daukan ka wani kamili can.
Nafito daga daki na samay su sai kwasan dariya suke tayi sai dai wanan karon akwai hijjab a jikina kasan cewan yaya Bashar yana a gidan haka yasani rufe jikina don shi tunda ba muharamina bane shi.
Da hannu yaya sadauki ya yafuto ni lokacin zan shiga kitchen ke na hakan yasani na juyo garin su nuna Bashar yayi da hannun shi yace ga mai magana dake nan dama.
Kallon yaya bashar din nayi wanda kunya ya rufeshi sosai yace Fatima kyale shi kin ji sherin shi ne kawai na juya kawai da murmushi na bar gurin su.
Kayan tsaraba ne sosai yazo muna dasu na nan gida Nigeria daga doya manja mai kyai na kwarai irishi har buhu guda aka sayo.
Na juya naji muryan shi yake cewa cire mashi kayan su yatafi yabar mutum ya huta cikin iyalin shi.
Ni dai nabar gurin inda aka tara tsaraban na kalla gasu birjit dasu komai na girki an sayo bayan muna dashi.
Na debo wa yaya bashar da yawa nakai mashi na koma tare da hado wasu masu yawa zan fita dashi yake cewa nawaye wanan din kuma ?
Nace wai da su maigadi zanba don su suka shigo dashi gida yace yana da kyau hakan.
Murna sosai masu gadi sukayi suna ta zuka min albarka tare da godiya kamar nice na,sayo kayan.
Ban tsaya ba nafitar da namu dan kadan sauran na,shirya su na don za a kai can cikin gida gurin su mama.
Haka muka kwana bai tabani ba sai faman juyi da tsuki yakeyi shikadai a inda yake kwance.
Sai washe gari na barshi yana ta faman rankon barcin da bai samu ba daren jiya.
Haka muka wuni ya fita zuwa gida ya gaida su mama da sauran mutanen gida.
Bai dawo gidan ba sai da yamma lis bai bata lokaci ba yafita sallah
Na idar da sallah magariba ina addua ban san da shigowan shi dakin ba sai jin shi nayi yace uh,umm, haba Fatima kin fara sallah shine baki fada min ba ko yaune kika fara sallah dai.
Girgiza kai nayi yace what Fatima tun yaushe kikai wankan tsarki nace kwana biyu da ya wuce ke nan.
Wani irin kallon mamaki kaman take kuma fuskan shi ya sauya a lokaci guda sai naga ya juta ya bar dakin .

Gaba daya na daina kwaliya a gidan na daina fitowa falo yadda na saba na zauna a tare dashi, gashi wasa wasa mun fi sati daya haka sai zaman yar tsama mukeyi a tsakanin mu.
Shi kan shi har bashar ya fanhici yana da yar matsala a tare dashi sai dai bai san daga ina matsalar take mai ba.
Tunda zurfin ciki irin nashi bai bari ya fadawa kowa halin da yake ciki balle a bashi shawaran da ya dace dashi.
Zaune suke ga system ya aje a gaban shi amma ya kasa sauraren bayanin da bashar yake mashi a lokacin.
Shiru bashar yayi yana kallon shi can yake cewa wai may ke faruwa ne sadauki naga fa duk kwanan kana cikin dan damuwa.
Guntun tsuki yaja yace may ga nine wai lafiya kalau nake bashar ya hade hannayen shi biyu guri guda ya tagumi dasu ta kasan gemun shi yana kallon abokin nashi na tsawon dan lokaci.
Can yace tabbas akwai matsala a tare da dakai wanda nake gani kamar daga gida ne ko gurin kaunata Fatima?
Nace maka babu komai murmushi bashar yayi yace wallahi akwai komai kan don ni nagani kafada min may ye matsala please ?
Don nima shawarana da matsala bata wuce ka akan may kai zaka dinga boye min damuwan ka wanda a gaskiya banjin dadin hakan wallahi ko.
Kallon bashar yayi yasan abinda yafadi gaskitane har cikin ran shi ya dan ja tsuki ya mike tsaye tare da saka hannin shi a cikin aljihun shi ya nisa gurin window office din ya nufa yana kallon waje can ya nisa kadan ya juyo inda bashar yake zaune yace.
Bashar wallahi Fatima tana son jefani a cikin wani hali saboda dan dalilin ta mara amfani.
Ai tasan yadda nake ta amince ta aure ni amma kuma may zai sa yanzun sai da na yarda da ita zata bijiro min da,wasu akida nata na daban can.
Bashar ya ce tare da mikewa ya dan tako zuwa inda sadauki yake a tsaye yace ban fahinci tasan halinka ba ta yarda ta aure ka haka nan ?
Yace kai tsaye kwarai eh ai tasan koni waye tasan ina sha aiko ?
Bashar ya rintse idanuwan shi don takaici yace haba haba man kaida bakin ka har kake ikirari da sabon Allah haka why why please.
Lokaci yayi fa da zakaiwa kan fada kafin ai maka yau tun kuna kubiyu kaida Fatima inaga sai yaran sunzo an fara masu gori a makaranta akan shan ka.
Idon shi ya rutse yace kaga abinda yasa ban sha,awan auren ba hausa tun farko amma maji tanace akan wanan yarinyar sai nayi.
Ita Fatima har ta isa ta hanani abinda nakeyi ko nai niyar yi kamar ta who is she bad way ?
Itace ko wani abu don gashi saboda ita ka shiga bakon yanayi kana gani Fatima ba wata haske bace a rayuwan ka halan.
Ya dago ya kalli bashar ido da ido yace haske haske fa kace yace to haske may Fatima take a gare ni kuma?
Bashar yai yar dariya tare da dan buga kafadan sadauki yace ko wani irin haske nw a yanzu kafi ni sani wallahi.
Halan ka shawo har ta fahinta da hakan ko yace wai shine takewa fushi kwata kwata yanzu ta daina kulani har yar kwaliyan nan ma ta daina yin shi kullun tana daki a kumshe tana hadiyan bakin ciki.
Bashar yace da sauri kagani kagani zaka kashe yar mutane saboda mugun halin ka ko ?
Yace oh nima ma zan kasheta ba itace zata kashe ni ba ita da takasa bani hakkina dake a kanta.
Wallahi ta shiga hankalin ta don tasan idan yau nace zan cika uku a gida na zan iya wake da hasara ba ita ba.
Dariya bashar yayi yace wallahi da watan kunyan ka ya kama a garin nan don kafin ma ka gama zagaye dakin su ka dawo gareta gari yasan ko kaiwaye ko ?
Jeka auro mata uku yau kagani waye a matsa in ba kai ba zata kwabe mawa.
Kana zaune kalau da matar ka kai mata abinda bata so ta dauki mataki maimakon ka bata hakkuri ka lalashi abinka tunda kaine baka da gaskiya amma wao kai shine har kake neman hanyan kuntata mata Allah ya baka sa an auro mata ka tara a gida tinda kana da kudin hakan .
Wallahi batin fada maka mata da kake gani suna da nasu ranan idan kace bazaka bari ba itama rana da hanyan rama cutar ta akan ka sai ka shiga hankalin ka.
Fatima dai ce ba yadda zakayi da ita don tai maka zara a zuciya kuma muddin bakane me shiri ba har mama taji naka ya samay ka kuma ji zarayi tunda inta gidana ta samu labarin halin da kuke ciki.
Dariya yayi yace ashe kaima kasan maryan magulmaciya ce ke na kyashan ta manne da sarki.
Yace to dakata don kawai tana gyara shine zakai mata mugun lakanin suna kawai wallahi yanzu zamu saba dakai akan maryam.
Kallon bashar yake yana dariya yace kai dai ka fadi da bakin ka bashar yace ai mantawa nayi a gaban makiyin mu nake.
Yace wallahi kaje kasan yadda zaka rarashi fatima ku fahinci juna idan ma kana fasa wanan shan yafi maka alheri don ko wata mace bazata ji dadin ace mijin ta ko dan ta yana sha ba ga mata da gorin tsiya wallahi.
Sun dauki lokaci suna musayan magana kan zancen karshe bashar yai mashi sallama akan zai tafi gidan Inna ya gaida ita bai samu zuwa da safe ba.
****** ********* ******
Yashigo gida fuskan shi a sake ya samay ta zaune a falo ta kunna tv sai kida da rawa na yan iska ake a wani tasha na kasar ghana.
Zama yayi a gaji saman kujera ta watso mashi harara tace kasamo kudin ne da ka dawo min gida haka?
Kallon mamaki yai mata yace cikin karfin hali wai Jamila may yasa baki son a zauna lafiya ne ke ?
Tace lafiya kudi kaima kasan idan ba kudi ni ba zaman lafiya gare ni don dasu nasaba.
Kasan wallahi inda ba kudi kai Ahmed baka isa ka aure ni ba don kasan da wa yanda nake hurda a baya.
Murmushi yayi yace Jamila ke dai in ba kudi sam babu zaman lafiya dake ni yanzu fa ban son abinda ya taba min rayuwan yar matata don ashirye nake akan duk bukatanki ko ina zan shiga na samo maki don kiji dadi kawai.
Hararan shi tayi tace in kana son kaji dadi na mike min su kawai inji dumus sai kaji dadin nawa.
Hannu ya tura a cikin aljihun shi yana fadin angama inda za a bar ni yau na shafi wanan body da ake min kwalelen ka dashi kwana biyu.
Kudi ya mika mata da sauri ta fisgi kudin tare da sake wani murmushi tace dama nasan kana dasu ai boyewa kawai kayi don kaji may zanyi.
Ajiyan zuciya ya sauke a ranshi yace don baki san zubar da kaina danayi na samo su bane don kwadayin ki da masifan ki kawai.
Yana matukar son jamila a ranshi do ba laifi yarinyar ta iya gado sosai gurin ma irin hakane suka hadu da ita har yaji ya kamata ya aure ta kawai yanuna mata karya ya auro ta din duk da mama asiya taso kawo cikas ga maganan amma yai sa,a ba ya yarda akayi abin.
Ranan kan yasan ya kawo kudi don tun wurin suka fara harkan ma,aurata a tsakanin su duk bashin da ke kan su na kewan junan su sai da suka biyawa kansu.
Don jamila irin matan da basu iya kwana biyu ba tare da namiji bane ya kusance ta.
Tun a gaban shi bayan sun huta tafara kashe kudin gurin sayen banza da wofi yana kallo ba yadda zai yi don son da yake mata.
Ranan da dare ma tare suka fita yawo da ita ya kara kashe mata dan canjin dake hannun shi kuma.
****** ********* ******
Ina zaune a dakina kayana da aka wanke nake kokarin nikewa a lokacin don najera su a wardrobe dina.
Dakin ya shigo saye yake cikin kayan barcin shi sau daya na daga kaina na kalleshi na kawar da kaina tare da ci gaba da abinda nakeyi a lokacin
Karaso yayi bakin gadon da nake zaune yai tsaye akaina tare da kura min idon shi na wani dan lokaci.
Can naji muryan shi yana cewa kina ganin kamar wanan abin da kika zaba zai fishe mune Fatima.
Banyi magana ba illa mikewan da nayi tsaye na kwashi kayana zuwa cikin wardrobe dina dasu.
Ina ajewa na juyo ban san yana tsaye a bayana ba sai ji nayi ya rike ni kawai na dago idanuwa na da sukai ja don bacin rai nace may ye haka malam.
Oh tambaya ma kikeyi don na taba mata ta ko may ?
Zan wuce daga gefen shi sai naji ya kamoni yace ina zaki sai kin fada min may ye wai matsalar ki ne a gidan nan.
Nace cikin kukan da ya kubce min kai yaya kai kaiyaya sadauki kaine matsalata yaya.
Murmushi yayi ya jawo ni zuwa jikin shi duk kubce kubcen danakeyi sai saman gado na ya dire ne.
Nan ya shiga kokarin cire min kayan dake jikina har yai nasara rabani dakayana.
Nan ya shiga sarafani yadda yake so raina yai matukar baci tankar da dutse yake amfani a lokacin .
Har yagama abinda zaiyi ya koma gefe daya yana mayar da nufashi a hankali.
Kuka nake sosai don abinda ya aiwatar min a yanzu yai matukar bata min rai.
Nace cikin kuka abin yakai kuma har da fyede ka koma yi min kasani wallahi idan ka zalunce ni sai Allah ya isar min.
Dagowa yayi da mamaki don bai taba jin makamancin wanan kalman ba a gare shi yace.
Fatima nikike jawa Allah ya isa don na taba ki kawai ko may ?
Nace bayan na dan daga ina kallon shi da idanuwa da sukai ja nace kai bakaji kunyan tabani ba kana cikin rashin tsarki?
Nine banda tsarki Fatima nace ina kaga tsarki mutumin da ya mayar da sabon Allah abin yin shi.
Mutumin da bai tsoron haduwan shi da Allah cikin ko wani irin halin zai riske shi ko a maye ko a kalau.
Mutumin da baida mu da halinda na tare dashi suke ciki ba akan mugun halinda yasa wa kan shi don son zuciya.
Ni wallahi yanzun ko da ake cewa wai yimaka akayi kake halin nan ban yarda ba har da hali ma.
Ka cuce ni wallahi daka kusance ni a cikin rashin tsarkin zuciyan ka wama yasani ko ka shawo ne kazo min a haka tunda ba imani ke gare ku ba.
Idan kace wanan halin baza ka daina ba nima wallahi bazan iya zama da mashayi ba tubur na haifi diya ana masu gori na fita gidan buki ana zunde na nashiga mutane ana nunani.
Kuma wallahi,,,,
Ke ya ishe ki hakana nagaji da jin mugun kalamin ki a kaina haka na ko don kinga na damu dake ne zaki tsaya kina fada min magana son ranki.
Damuwa damuwa fakace yaya da kadamu dani dabakai haka ba wallahi dakaso abinda nake so maka a ranka.
Ni dana damu dakai aina fahinci abinda kake so da wanda baka so kuma na kiyayye su don azauna lafiya.
Yadda kake ganin an tursasa maka aurena wallahi nima haka aka tursasa min auren ka badon ina so ba.
Amma nai hakkuri na zauna ina maka addua a kullun na Allah ya shiryaka kamar yadda mahaifan ka suke maka a kullun.
Amma kassh kai yaya baka sawa ranka daina wanan halin mayen ba kaduba fa yadda kainan ka Nafisa maye ya mayar da rayuwan ta.
Idan badon Allah ya nufa mamatana tsaye da addua ba akan ka da yanzun ka fita lalacewa a hakan.
Nikan gaskiya ba zan zauna da dan maye ba don idan akwai abinda na tsana shine maye a rayuwana amma kuma ina kaddara ta riga fata yau gani Allah ya nufe da mai shaye shayen da baida ranan barin shi a rayuwan shi.
Yana sauraren maganan da nake fadi sai dai baiyi magana ba har lokacin karshe ji nayi barci ya dauke shi.
Har na mike na shiga bathroom nai wanka nafito nai nafila na zauna ina kara kai kukana ga Allah akan al,amarin nashi.
Nagaji na taso daga inda nake na kwanta daga gefen gadon nan nima barci ya dauke ni ban sani ba ina cikin tunane.
Da safe ko da na falka na samu yafita daga dakin bai kuma tadani ba don ganin da yayi ina barci a lokacin saboda yasan ban samu barci ba a daren jiya din.
Bayan na sallah na kimtsa jikina na shiga kitchen na hada abin karyawa na jera su atable na shige daki abina na kwanta.
Har ya gama abinda yake ba alama na a falon haka yasa shi leka dakin kwance nake rub da ciki kamar mai barci sai dai yasan ba barci nakeyi ba a lokacin.
Daga kofa yake ce min shi zai fita sai yadawo ban dago ba kuma banyi magana ba haka yasake labule yafice daga gidan.
Jin fitan shi yasani fitowa daga daki na gyara ko ina nagidan tsab na dora muna abincin rana again.
Bai shigo ba sai bayan la,asar naji shigowan shi ya shige dakin shi ina zaune ya shigo cikin shirin shi yana cewa ni zan tafi ga wanan ki rike a gannun ki sai badawo.
Da kyat na iya bude bakina nai mashi adawo lafiya yafita daga gidan ranan ban rakashi ba yadda na saba yi mai wanan abin ya kara bata mai rai.
Sai washe garine yaya Bashar suka zo gidan da maryam mun gaisa da su muna zaune tana min sheri wai na kore mata yaya a gari saboda halina.
Idona ya kawo kwalla nace cikin wata murya ta mai kararen zuciya haba anty don kawai baison a fada mashi gaskiya kawai.
Muryan bashar ne yake cewa Fatima kiyi hakkuri shi kan shi yasan bai kyauta maki ba kuma yaji nauyi da kunya da ya sani.
Hakan da kikai mai kin kyauta gara da kika rufe idon ki kikanuna mashi abinda yayi ba alheri bane.
Don idan mutum yana aikata barna a doron kasa bai samu wanda zai rufe ido ya fada mai gaskiya ba komai dacin shi sunan wanan mutum din tabbabe wallahi don baida ranan daina a rayuwan shi.
Amma kuma ke kuma kin tauye shi da yawa Fatima kin hana mashi hakkin shi bayan kin saba farauta mashi.
Kunyan maganan shi naji na saddada kaina akasa yace gaskiya kin hora min abokina wallahi.
Yace ko yar kwaliyan da kike mai da taro haba haba duk kin daina yi mashi su haba Fatima adai dan sasauta mashi mana.
Maryam tai tsagal tace akan may zatai mashi tunda shi baisan ciwon kan shi ba har yanzu ba gara ta kama kan ta ba.
Yace to gama dama ai yace shawaran ku daya da ita kece coordinater din ta.
Dariya mukayi nace babu ruwan anty kada yaga laifin ta a banza bataci batasha ba halin shi daine bai min ba yaya.
Yace to kiyi hakkuri Fatima tinda dashi Allah ya hada ki zama nifa ina ji ajikina insha Allahu zai daina nan gaba.
Tinda kinga yanzu yarage sosai inda dane ai abin ba dama wallahi don baku san irin halin da na shiga dashi bane a baya kafin ya aure ki.
Amma aikinyi sa,a ma yana shayin ki yana tsoron yayi ki gane ko ranan ina ganin akasi aka samu kawai.
Duk wanda yai mai asiri bai fasa ba mai shi yana kan yi har yanzu don dai suga ya lalace kawai a rayuwan shi.
Maryam tace ina fa suka fasa kwanaki da nafisa tai shaye shayen ta ai ta fadi amma aka mayar da abin haukan tane kawai yatashi take fadin hakan.
Bashar yace ai zan koma gur8n mutumin nan da muka taba zuwa don wallahi Alokacin ya daina kwatakwata dawowa abin yayi.
Kuma zan fada maki wani sirin shi idan yana son sha zagiga idon shi sun rine sunyi ja jajir dasu yana dafe kan shi yana dan murzawa to yana sin yasha ke nan.
Kuma ko a gidan yana da kayan maye har na shayin su da yake sa kina dafa mashi da hannunki amma ke baki sani ba.
Nazaro ido nace wallahi ko duk dare yaya sai na dafa mashi bakin shayi mara sugar da madara yasha.
Yace to sune yake sha yanzun dai kafin ya dawo insha Allahu zan koma kauyen nan naji may ke ciki akan al,amarin don idan akwai wanda zaki bashi yaci batare da yasani ba sai ki hada mai.
Nace nagode kwarai yaya yace kiyi hakkuri kinji ban son mama taji wanan zancen ko kadan don kada ciwon ta ya tashi.
Nace nima shine wallahi amma badon mama ba ranan wallahi dana gudu gidan nan yaya.
Yace no no don Allah kada kije ko ina kefa haske ne a gare shi Fatima.
Zamaki tare da Sadauki wani falala ne ga kowa ga masu gadinku suna fada min irin alherin da yake masu akan ki.
Idan kinyi haka mama bazata ji dadi ba masu hassada akan auren ku kuma zasuyi farin ciki sosai.
Maryam tace ai bata ma zuwa ko ina mutu ka raba ita da yaya sadauki sai dai yan bakin ciki su mutu.
Mun kai wani lokaci dasu suna bani shawaran yadda zan kara bullowa al,amarin.
Sukace zasu tafi don zasu shiga gaida Inna gidan ta a lokacin nai masu rakiya har waje suka tafi yaya bashar yace yace akawo maki kayan abinci sai gobe za,a shigo dasu don ina ganin zai dade a can ne.
Har ya shiga mota yake cewa kin ko kirashi kinji saukan shi na dukar da kaina ina dariya yace don Allah ki kirashi nace mashi to kawai .
Amma bazan kiraba nace a cikin zuciyata indan yadamu yakirani in kuma bai kira ba ajira har ranan da ya dawo din.
Jin za,a kawo min wasu kayan abinci na shiga kitchen na auna shinkafa da taliya don tun na garan mu sunanan ba ai komai dasu ba na kira malam Atiku na bashi kowan su leda guda guda da dubu uku uku na cefane akan Allah ya yaye mai wanan lurar tashi.
Suna ta godiya suka fice kowa yakai nashi gida don dama a bukace suke a lokacin don abin sai shukaran kawai.
Na idar da sallah la,asar naji anata kwada sallama daga kofa nafito ina karba sallah ma.
Na so sheda matar amma na manta ida na san ta a baya muka gaisa da ita cikin sakin fuska take ce min baki gane ni ba ko hajiya ?
Nace na dai so na gane ki tace Allah sarki yanzu maji tai min waya wai nazo na zauna dake don maigidan bayanan kuma tace ma zata bugo maki waya ai.
Nine Rabin dan musa uwar goyon sadauki a baya nace cikin sakin fuska Allah sarki wallahi mama ban gane ki ba saudaya na taba ganin ki ranan da kika zo gaida mama ina gida lokacin.
Na mike tare da amsan ledan bakon dake a hannun ta na shiga mata dashi dayan dakin da anty Amira ke sauka a cikin shi.
Nace mata ga daki nan inda zaki zauna mama tana washe baki tace ai da ko nan kika barni ma yayi min wallahi ko.
Nace kai haba dai nan a waje mama tace ina wajen yake nan na je na kawo mata abincin mai yawa taci sai da ta koshi tana godiya.
Mun dayi hira sai da magariba ya gabato muka shiga daki don yin alwala da sallah.
Da dare ma mun dan taba hira da ita take ta bani labarin irin zaman da akayi a baya a gidan su sadauki yadda maji tasha wuyan su Umma da mama a baya.
Sai zuwa goma mukaiwa juna sai da safe kowa yanufi dakin shi ya kwanta.
Washegari kafin duk ince nafito na samu ta gyara gidan tas ta goge ko ina tai wanke wanke nace bayan mun gaisa haba mama baki huta ba kuma wanan aikin haka tace min haba to may yakawo ni gurin ki ba don na taimaka maki ba na zauna kuma ina kallon ki haka uwar dakina.
Tun ranan itace mai gyara gida iyakata nai muna girki kawai wanda zamuci ko girkin ma tace bata iya ba da abinda mukeyi sai da icce amma in koya mata don watarana.
Shine dalin idan zanyi girki muke shiga kitchen da ita tana kallon yadda nake aiyuka na.
Yau satin shi daya da tafiya baikirani ba ban kirashi ba muna zaune a falo da Iya take ce min wai ke yar nan ni banji kuna waya da maigidan ba mana.
Sai da na kakaro murmushi a fuskana don tambayan nata yazo min a bazata lokacin .
Narasa may zance mata sai nace cikin murmushi lah iya ai shi sai tsakandare yake bugo waya kin san lokacin mu ba daya bane dasu can namuna rana sukuma suna dare ne.
Tace Allah sarki ni kan dai ince yaran yanzu baku wasa da waya da mazajen ku shiyasa na tambaya ai.
Takara cewa ba dai dan nawa yana lafiya ba dai ko nace lafiya yake yana ma yawan tambayan ki na ce mai kalau ki ke.
Tun da na fadawa Iya Rabi haka shikenan bata sake tambayana komai a kan shi ba kuma.
Abu kamar wasa yau satin sadauki biyu rabon shi da gida amma ba waya daga gare shi da farko abin bai damuna amma daga baya sai abin ya fara ci min rai kuma.
Mun shiga daki kenan munyi sallama da iya Rabi sai naji wayana yana ringing da sauri na isa furin don na dauka murja ce wata course mate dina da muka dan shaku da ita.
Nobar kasar waje ne daga US na dauka da sallama a bakina naji ya amsa sallaman nawa cikin wani murya.
Sai kuma mukai shiru gaba dayan mu can yake cewa Fatima yanzun kan na sheda dole akai maki a kaina don yadda kika nuna baki damu ba dani.
Nace dole dai akai muna da juna aikama kasan kabar mai gadi gidan ka baka damu dani ba.
Hmm naji yace yace wanan kuma mafanan ki na rasa ke wata irin yarinyace haka mai taurin kai dake.
Kina nufin idan munzuba ni dake waye zai sha wuya a cikin mu ne wai kefa mace ce ba kowa ba.
Nace oh don ina mace shine akace ban san right dina ba ko komay ?
Idan kina ganin halin da kika dauko yi min zai sa na daina abinda kike ganin zan daina sai ki matsayi ai gafili ga mai doki.
Nace ban ma son ka bari don ni ai nafison kabari don Allah da iyayyen ka da zurian ka masu zuwa.
Yace oh ashe kin sani kik matsawa wa kanki nace ni ban matsawa kaina da komai ba sai dai kawai ina tsoron mu,amulane da wanda baida tsoron Allah kawai.
Yace na gode nima haka nabashi amsa sai naji ya furzo iska yake cewa ance Rabin dan musa na gurin ki ko ?
Nace oh iyaba tananan yanzun ma ta kwanta don muna tare yace ok ina son ki kula da ita sosai don tana da mutunci sosai nace insha Allahu zanyi yadda kace.
Bashar ta kawo maki kayan abinci nace eh amma kasa akwai su dama kuma ka karo wasu shiya sa na diba wanda muke dashi na ba su maigadin ka su ma yace ok haka yana da kyau idan kuna da wani matsala dai bashar yana nan sai ki fada mai ko ma may ye.
Nace bamu da matsalan komai don iya tana da kirki matuka kuma tana debe min kewa sosai a zaman kadaici.
Murmushi naji yadan yi yace akwaita da,son hira ai sai kingaji kintashi inda Rabi ce.
Na katse shi da cewa ina fatan kana wa kanka adalci acan ka daina wanan shan mugun abin mai bata maka tunanen ka akan komai.
Tsaki naji yaja yace yacd ai da kika damu da hakan da sai ki shigo jirgi ki gani don gulma ko ?
Yace kin ga malama idan kikace zaki saka min ido haka arayuwa na wahala zakisha wallahi.
Raina ya baci da kalamin shi nace dama ai zaman wahalan aka kawo ni yi don raina yai ta baci a banza tunda ba fasawa zakayi ba kai.
Amma kin san ko ni waye kika yarda aka daura ni dake haka na ko don kin ga ban maki yadda na kulla ba shine har kike jin dadin samun gurin ke ki cutata min ko ?
Naga idan ban kashe watan ba haka zamuyi sa insa dashi akan zancen yasani kashe wayan dip na ji dul jikina ya mutu a lokaci guda.
Mikewa nayi na ahiga wanka na dauro alwala raina duk abace ina ta faman tune watau shi wanan dai bazai daina halin nashi ba ke nan yake nufi tinda da anyi zancen fitina yazo ke nan dashi.
Washe gari da safe yaya bashar ya samay mu da iya mun gaisa da yake iya mace mai fahinta sai taba guri dashi.
Wasu kulin magani ya ciro daga aljihun shi ya kashe murya yana min bayani yadda zan yi da maganin idan yadawo sosai nai mashi godiya da fatan Allah yasa mu dace gare shi yace amin ya kara jadda mi na tabbatar da na zuba mashi fa yaci sosai nace insha Allahu nai murna kwarai sai nake gani kamar har maganin yaci ko a lokacin.

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA NA,BARKI GA ALLAH,ALLAH SHI ZAI KARBA MIN HAKKINA A GARE KI ,,,,,
Saura yan kwanaki a fara azumin watan ramadan ko ina,kasa shen musulmai sai shirye shiryen taron wanan wata mai alfarma da albarka dake tafe a,wanan lokacin aketayi manya da yara da,tsofi duk farin ciki suke da wanan wata mai albarka .
Zan iya cewa rashi dawowan sadauki a cikin lokacin da nake gani kamar har za a kama a azumi bai dawo ba garin a lokacin.
Babu wani abin da na rasa,a gidan daga na ci da,sha da sauran abubuwa amma kuma sai na kasa gane may ke yawan haddasa min bacin rai haka na rasa ganewa.
Gidan baba sai abin arziki yake samu daga diya da sarakain shi da,abokan arziki na gari.
Ba kunya mama take habaici wa baba wai gashi dan na shi bai kawo ba amma fa wa yanda ba,a so sun kawo don sune ,ba,a so da alheri gashi Allah ya hore masu sin kawo mashi ya karba yana washe baki .
Kai tun abin yana damuna har yakai yanzu na daina damuwa da rashin dawowan shi wanda wata biyu.ke nan rabon shi da gida.
Sai yaya bashar mijin maryam abokin shi shine kawai ke dawainiya da mu tako wani fanni duk da,ban taba cewa muna bukatan wani abuba a gidan na rayuwa.
Maryan yanzu cikin ta yakai wata biyar ke nan a jikin ta don har ya turo sosai mutum zai iya gane haka atare da ita duk cikin mu ita kadaice Allah yabawa haihuwa.
Da kafa takan tako daga gidan ta zuwa gidan mu don motsa jikin ta idan zata koma tare muke fita har Iya mu taka mata mu rakata gidan ta don bamu da nisa sosai.
Da dare muna cikin falo zaune ni da Iyan Rabi muna hira waja jen karfe tara na dare a lokacin .
Sai jin sallama mukayi kamar daga sama muka ganshi har ya shigo tsakiyan falon a lokacin.
Sadauki ne ya shigo muna gidan da sallaman shi ya murje yayi wani kyau yayi haske kamar wani dan kwara dashi.
Cikin fara,an shi da walwala ya shigo muna a lokacin daga ni har Iya sai sannu da zuwa muke mashi a lokacin.
Ganin da nayi fuskan shi a sake yake, yasani nima taron shi a cikin farin ciki kamar babu komai a tsakanin mu can baya.
Zama yayi saman kujera tare da fadin wassh Allah Iya tace sannu na wurina da kokari andawo yaya hanya yaya aiki da sauran jaman can.
Na,dawo daga,kai jakar kayan shi daki na nufo shi tare da dan dukawa na rugumoshi ban damu da wai iya tana gurin ba shima dai rungumoni yayi zuwa jikin shi.
Iya dai kunya taji ta juya zuwa kitchen abinta tana murmushin yadda taga mun burge ta sosai a yanayin mu.
Zauna da ni yayi saman cinyan shi yana sauke numfashi tare da kai hannun shi a saman wuyana a hankali yana dan shafawa cikin lumshe idanuwan shi.
Daga inda Iyatake a tsaye take cewa uwar dakina nace ko sabon girki zamu dorawa yaron nawa ne ?
Itace tadawo muna da hankalin mu muka tuna a inda muke zaune a lokacin.
Da,sauri yace a,a kubar shi kawai zan sa,akawo abinda zanci yanzunan kafin nai wanka.
Mikewa nayi daga cinyan shi nake cewa Iya zo zauna ki huta abinki ai dan naki bai faye danuwa da abinci ba idan bashi yaso ci ba kuma bama komai ne yake ci ba shi dole yanzun sallon abincin mu ya canza ai .
Maimakon tazo ta zauna sai ta shiga dakin ta yana tambayana yaya muke yazaman mu da Rabin dan musa nace bata da wani matsala wallahi ita ai mutum ce mai dadin zama ga tsabta ga aiki bata gajiya wallahi.
Sai ganin Iya mukayi da dan jakar bakon ta tafito daga daki tana fadin uwar dakina nikan zan tafi tunda maigidan yadawo yanzu.
Da sauri dani dashi muke hada baki cewa haba dai ina kuma zaki kuma iya yace Rabi ina kike nufin zaki kuma ina anan zaki zauna gaba daya kina debe muna kewa kuma.
Tace a,a haba nawa ina zan zauna a tsakanin ku na hanaku shakakatawa kuna sabbin ma,aurata da ku.
Iya bafa inda zaki idan kika tafi dawa kike son na zauna a gidan nan idan ya fita shi ko baya garin ?
Ba sai na dawo ba idan yai tafiya din amma zan zauna na hanaku hutawa a tsakanin ku ?
Murmushi yayi tare da mikewa ya nufi inda take tare da karban ledan hannun ta yana cewa wai maji bata fada maki cewa zama zakiyi muna a gidan nan ba.
Tace zama Alhaji yace ai babu inda zaki don kinzo kenan nan zamu zauna dake gashi kuma nayi sa,a uwar dakin naki naku yazo daya da ita yanzin .
Murmushin jin dadi iyan Rabi tayi tace ai Alhamdullahi don kayi sa,an mace tagari da kowani namiji ke bukatan samu a rayuwan shi.
Murmushi yayi ya shiga dakinta ya aje mata jakar kayan ta yafito bayan yabi dakin da kallo yaga komai akwai shi dakin na rayuwa yafito bai zauna ba don ya fahinci zaman shi zai takura mata sai ya wuce zuwa cikin dakin shi direct.
Cewa iya nayi bari naje na hada mai ruwan wanka ya dan watsa yaji dadin jikin shi.
Tace afiti lafiya hajiya nabi bayan shi zuwa dakin yana duke yana cire takalman cover shoes bakaken dake kafan shi da safa.
Da sallama na shiga ya ansa min yana dagowa daga duken da yake yadda ya ansa min a cikin sakin fuska yasa na karasa gurin shi.
Cikin kwarin gwiwa ya zuba min idanuwan shi na ce yaya hanya ya gajiya kuma?
Kalau yabani amsa da hakan nakai gare shi tare da kokarin fara balle mai aninin rigan shi ta gaba.
Cikin sanyin murya naji yana cewa kin huce ke nan da mijin naki Fatima ?
Nace don girman Allah yaya ka daina wanan maganan adai gyara gaba please ?
Wallahi yaya yadda kasan mama bata kaunan wanan abinda kake yi haka zalika nima bani kaunan ganin ka cikin wanan irin yanayin don kwata kwata ban iya controlling din kaina a hakan.
Nakan jini ne kamar wata mara sa,a acikin mata don sai nake ganin kamar dunuya zata zageni a dinga nuna ni.
Wata uwar harara ne ya balla min bashiri na kama bakina na kasa cigaba da maganata.
Cikin maganan tausayi yace min don kina son na daina Fatima shine zaki dinga nisanta kanki dani ?
Saboda kin mayar dani shasha haka kike zaton kowa yana dauka na a idon shi ko ?
Na katse shi da cewa kasan halin mutane yanzu yaya bazasu iya fada maka gaskiya ba a gaban ka don abin hannun ka.
Yana da kyau kai nazari akan zance na zaka gane manufata a gare ka ba don na rainaka bane ko wani abu a,a yaya gani nayi idan ban fada maka gaskiya ba a yanzu waye zai fada maka shi.
Tsaki naji yaja yace kinga malama idan kin zo ne ki taimaka min kiyi abinda ya kawo ki .
Idan kuma har yanzu raina manin wayyo ko hankali zakiyi ki fice min daga daki rainin hankalin naki yana son yai min yawa.
Ke yarince dake zaki min wa,azin da mahaifana basuyi min ba ko may ?
Naga baki son mu zauna lafiya a gidan nan dake don nafahinci kina son ki wuce matsayinki a gare ni.
Raina ya baci nace amma yaya dama inaga dai ka yadda ka auri ni ne don ka dinga ci min mutunci ko ?
Kiyi wa Allah idan kasan bada zuciya daya kake zaune dani ba baka sona ne ka sallamay ni na tafi gidan mu ka huta dani.
Wani irin kallo yai min yace Fatima ke da bakin ki kike fadar na sallamay ki kikoma gidan ku?
Shiru nai mashi yace ok idan haka kike so sai kikoma ki fadawa wanda suka hada mu sai su raba mi tunda shi kike bukata ke ?
Naga idan na biye mai daga dawowan shi zamu sake samun matsala kuma again.
Sai nai amfani da shawaran yaya bashar da anty maryam na wuce shi zuwa bathroom na hada mai ruwan wanka tare da,aje mai duk wani abinda zai bukata na amfanin shi ciki.
Yana shiga nafita daga dakin raina a bace da yan maganganun da mukayi da shi yanzu na koma dakina na zauna a bakin gadona ina tunane.
Shima dai yana can yana wanka tunanen maganganun da mukayi dashi ne yasan ina da gaskiya na amma bai bukatan na shiga harkan shi har takai na takurawa zamantakewar mu dashi haka.
Yafito ya shiya cikin rigar barcin shi falon ya dawo sai dai babu kowa a falon sai tv dake aiki shi kadai a lokacin.
Kamar ya shiga dakina amma sai yadake kawai ya zauna tare da canza tashan zuwa na kwallon kafa.
Jin motsin shi afalo danayi na sauke ajiyan zuciya maganganun su yaya Bashar da suka fada min na dole ne sai na kwanta mashi sosai zan iya,aiwatar da,shiri na akan shi yasa na sauke ajiyan zuciya tare da mikewa na fita.
Rigan barci ke jikina alokacin sai faman kamshi ke tashi a jikina dan na gyara jikina bayan fitowa daga gurin shi nima.
Murya na yaji a bazata daga bayan shi don baiyi tsanmanin zan kula shi bakuma har yadan shiga dan damu akan yaya akayi ya bari muka dan sake samun sabani bayan yaga na sauka daga fushin da nakeyi da farko dashi.
Cewa nakeyi abincin da kace za,a kawo maka kaci fa kuma gashi baka bari mun dafa maka ba ?
Ya dan dago kai inda nake yana cewa No ki barshi kawai banjin cin komai yanzun ma zai sha drinks da tea na sai na kwanta.
Nace lokacin dana karaso inda yake a zaune yaya drinks kuma shi zai sa ka koshi yace is ok kawai.
Zan zauna yace dauko min laptop dina na duba wani abu a daki please ?
Juyawa nayi zuwa dakin nashi na dauko mai system din nashi maishegen kyau da tsada.
Mika mashi nayi na juya zuwa kitchen tare da dora ruwan tea din nashi sai dai na faki idon shi na barbada garin maganin da,akabani in bashi yasha din a ciki.
Najuyo mai tare da dauko drinks da cup har dan flaska din shayin nakawo mai.
Yace inji lemon baida sanyi don kinsan mutum bai shan ruwan zafi dana sanyi a lokaci daya don gudun cancer.
Nace baida sanyi sosai amma dai bari na zuba ma a cup sai ya huce kafi ka sha.
Dakin Iya na wuce don jinta shiru danayi yau ba hira ke nan ta boye a dakin ta don ganin shi a gida da tayi.
Na samay ta tayi barci sai rufo mata kofa tare da kashe mata wutan dakin dake a kunne lokacin.
Na samu har ya bude system din shi ya fara aiki da zaiyi dashi a kan three seat yake zaune nima saman na zauna tare da kaiwa kwance ina kallon tv dake aiki.
Can na dan ja tsaki tare da mika hannu na daga kwance na dauko remote zan canza chanel din naji yace baki son wasan ball ke nan dai ko ?
Murmushi nayi tare da kai kaina saman cinyan shi nai filo dashi nace wallahi ni ban taba fahintar may ake ba a cikin shi don ban san komai ba akai.
Dariya naji tayi yace kai amma shame on you matar dan kwallon duniya kuma bata san ball ba aiko kinji kunya wallahi.
To yaya kunyan may tunda badani ake zuwa yin ball din ba can nan kuma ina diyan hausawa yaya zan san wani ball can a rayuna.
Yace aiko ya zama dole ki sani don kada wata rana a tambaye ki mijinki dan lanba nawa ne ki kasa bada amsa naji kunya.
Duk hiran da mukeyi hankalin shi na,wurin abinda yake acikin laptop din shi lokacin baidago kan shi ba.
Muryan shi na kara ji again yana fadi amma ki saka a,ranki kulba dade kul ba jima akwai ranan da,zaji hade da yan jarida zasuyi mako inter view akaona da kan ki don har sai ki fara shitleya basu amsa da zaki fada masu.
Da sauri tare da dan dagowa daga kafan shi ina kall9n shi nace ni nidai din yaya.
Yace cijin murmushi kekuwa Fatima din nan rana da lokaci sina tafe muddin muna araye zasu tambaye ki.
Komaqa nayi na kwanta kamar yadda nake da farko tare da ajiyan zuciya nace ashe akwai aiki kuwa ke nan.
Dariya sosai na bashi yadda yake dariyan yana ci gaba da,aikin ya ban sha,awa ban san lokacin da nakai hannuna ga fuskan shi ba na shafo a hankali.
Wani irin irin ajiyan zuciya ne naji ya sauke tare da lumahe indanuwan sho gyaea kwanciya nayi akan jikin shi nace.
Basai ka fada min abinda zan fada masu ba ko kuma nace ni ban san duk wani tambayan da sukai min ba ma.
Ban san har ya rufe laptop din nashi ba sai ji nayi ya mike ya nufi gyrin tv ya kashe tare da kashe sauran na,urorin falon inda nake yazo ya dauke ni cak ya hada da computer din shi sai dakin shi.
Saman kado ya dire mu ya jaye laptop din ta fado min saman jikina yana fadin barin fada maki abinda zaki fada masu tunda shine kawai kika sani a gamay dani.
Bakina ya lalabo ya fara kai min kiss mun dade a haka can ona jin dadin abinda hannayen shi suke min sai kuma naji ya tsaya tare da zare bakin shi a cikin nawa a hankali
Ya juya yana mayar da numfashi a hankali can yake cewa sorry fa kada kuma na sake maki fyede again .
Ban san lokacin da dariya ya kamani ba nace yaushe kuma ai kasaba min yanzun ma gashi kayi min din again.
Auto ashe bari ma na karasa tinda har nayi maki ma waida kada nai lefi nake gudu nace cikin dariya ai kaf8n kai min wallahi sai na rama nima don yau nice zan maka fyede da kaina.
Kafin yasan may zanyi har na juya na haye mai ruwan cikin shi ko a hakali na cire mai rigar jikin shi bai hanani ba nan nashi ga nuna mai wani sallon da ni kaina ban ban san ina dashi ba.
Sosai muka gwadawa wa junan mu how far we miss each other a lokacin, tsawon lokaci muka shayar da junan mu zuman ma,aurata ranan masha godiya ba adadi a gurin shi kamar ba yaya sadauki bane mai izzigilancin nan.
Bayan komai ya lafa a tsakanin mu sai zancen shayin dana hada mai da magani yafado min a raina.
Gabana ya fadi kada yazo baisha ba ai hasaran maganin gashi yaya bashar ya jadda min na tabarar da yasha ahi sosai fa.
Ikon Allah sai naji yace ni wallahi har kin sani jin yunwa ma sosai wallahi nace ai ruwan shayinka na nan baka sha ba.
Yace anya yadda nake ji din shayin nan kuwa zai dauke ni a yanzu gaba na ya kara faduwa kada yazo bai sha ba fa.
Muryan shi ne yake fadin tsiyayo min insha kada kice zaki fita yin wani dahuwa da daren nan kuma.
Don keta sai da na zuba mai da yawa kuma nai sa,a duk ya shanye cup din gaba daya.
Sai da ya shanye yake cewa amma sai naji shayin ya dan canza test yau ko ya fara expire ne dai nace ko kuma don ya dade a bude yai sanyi yasa shi canza test ba yace indai a bude yake shi ya kawo hakan gaskiya.
A haka muna dan hira naji yayi shiru barci ya kwashe shi lokacin ga gajiya ga aikin magani ke nan.
Mikewa nayi nashiga bathroom nai wanka tare da dauro alwala nazo nai sallah raka,a hudu ina rokon Allah yasa mu dace ga maganin.
Muna barci can shiyoyin asuba naji cikin barci yana wani irin nishi sosai abinda ya falkan dani ke nan a dan firgice cikin tsoro yadda naga ya dunkule guri daya ya dafe cikin shi.
Cikin tsoro nake magana yayana may ya samay kane may ke damun ka kuma ?
Cikin shi ya nuna min da hannu nace a dan razane subbahanallahi ciwon ciki kuma ko may ya gyada min kan shi da kyat .
Nacw daure mu shiga bathroom kadan yi wanka ko zakaji dama sai na fita na hada ma abinci ko yunwane don kaga jiya bakaci komai ba ka kwanta hakana sai ruwan shayi .
Ban samu amsa ba sai murde murden da yakeyi a lokacin kawai na ciwon ciki na mike na shiga na hada mai ruwa na dawo ina yake kwance.
A hankali na duka cikin kunnuwan shi ina rada mai ya tashi mu shiga bathroom din yai wanka hannun shi ya miko min da taimakona muka shiga har bandakin .
Ranan dole yanayin da yake ciki na cire kunya na hada mai ruwa da kaina nai mashi wanka wankan tsarki ne kawai ya daure yayi da kan shi lokacin.
Ba laifin wankan ya sa yaji dan sauki ana kiran sallah mukai sallah ya koma ya kwanta nafito zuwa sama mai abinda zaici inayi ina lekashi dakin shi.
Ranan a daki nakai mai ya dan daure ya tsakura kadan yaci yace baijin dadin bakin shi ko kadan.
Koda Iya tafito ta samu na hada abin karyawa ko sai gyaran gida kawai tayi nafito daga dakin a cikin shirina na samay ta tana aiki muka gaisa da ita.
Tana tambayana kwanan dan ta nake fada mata wallahi Iyya yau dannnan naki ciwon ciki ne ya hana shi barci .
Tace da sauri subbahanallahi ciwon ciki kuma da sauki dai ko nace da sauki don ya ci abinci yace idan ya tashi zai sha magani .
Dakin na koma sai dai bai saman gado yana bayi ina na tsaye har zan juya sai naji yana kakar8n amai daga cikin bandakin .
Da sauri na isa gurin amai yake shekawa wani irin bakin amai ba dadin gani.
Wasa wasa amaiko yaki tsayawa sai faman sheka amai yakeyi hankalina yai matukar tashi sosai na fita na kira wayan yaya bashar na fada mai sadauki fa ba lafiya ciwon ciki da amai ya damay shi.
Yace subbahanallahi gani nan zuwa yanzun nan muna gama waya dashi nake shawaran kiran mama na fada mata .
Itama kiran ta nayi don kada taji daga baya taimin fada gata tana a cikin gari kuma.
Tana ganin wayana tunda safe haka gaban ta ya fadi ta dauka take tambayana Fatima lafiya ko nake fada mata abindake faruwa tace subbahanallahi gamu tafe yanzu.
Yaya bashar ne ya fara shigowa lokacin muna ban daki dashi har bedroom din yashigo nan yasamay shi yana wanan bakin aman nashi.
Yace subbahanallahi man may ke faruwa ne kuma yadago kai da kyat jin muryan aminin shi idanuwan shi sun canza launi sosai.
Yace wallahi ban sani ba man ciwon cikine sai kuma amai da ya biyo baya da kyat yake iya magana a lokacin .
Shi ya kamashi ya kwanta bai dade da kwanciya ba sai ga baba mama da mummy sun iso suma.
A falo suka fara zama nazo na gausa dasu suke tambayana nake fada masu abinda yakeyi ai sai aje asibiti baza a barshi a gida ba hakana bamu san may ke damun shi ba .
Naji tsoro sosai a raina kada aje asibiti ace poison aka bashi fa yaci nawa ya samay ni garin neman kiba na samo rama kuma.
Mun shiga inda yake kwance sai faman murdan ciki yakeyi sosai yana juyi mummy ta dan dubashi tare da bashi tace Alhaji aje asibiti kawai.
Ina gefe daya a rakube hankalina a tashe yace No abari kila zai bari ai baba bai yarda ba suka sashi a gaba ya tashi aje asibiti dai.
Inda nake tsaye idanuwana suna fitar da hawaye ya dan kalla yace cikin karfin hali Fatima dauko min kaya na saka.
Jin haka suka fito daga dakin suka barmu a tare sai kuka nakeyi cikin karfin hali bayan ya gama sa wando ya jawoni jikin shi yana cewa.
Ki daina kuka mana Fatima bakya son ki rasani ne ko ?
Ban bashi amsa ba na saka mai rigan tie shirt tare da dan shafawa fuskan shi dan mai sai ajiyan zuciya yakeyi sosai.
Bashar ne ya leko yake cewa yagama ne mu tafi nace mai eh a lokacin ina rugumay a jikin shi muka fito daga dakin da kyat yake tafiya.
Har sun fita bashar ya dawo cikin gida kaman zai dauki abu yace min a hankali kin bashi maganin ne nace mai eh yace ok dama ance zaiyi amai ya wahala sosai kada ki damu komai basu ganewa ai.
Shiru shiru suna,asibitin dashi muna gida da Iyya hankalin mi a tashe sosai a lokacin dashi.
Mama ce ta bugo waya tana fada min in kwantar da hankalina likitoci suna kan shi suna bincike yanzu haka.
A raina nace ina naga kwantar da hankali asirina zai tonu haka kuma daga taimako .
Sai guraren sha biyu da wani abu bashar ta dawo gidan yake fada min an bashi gado asibitin sunce wai canji ruwa ne ko kuma yaci wani abu a can wanda suke gani kamar bai dace da cikin shi ba.
Nan yake ce min mama tace yazo yaje dani yanzun don suna son zuwa gida suyi sallah su tinda yadan ji sauki .
Mun isa mun samay shi kwance yana barci har ya fada sosai bashar yake tambaya baiyi aman ba ko sukace yayi har sau biyu bayan tafiyan ka ai.
Ina tsaye kan ahi na kura mai ido ina kallon yadda ya koma a raina nake cewa wabda duk yai maka wanan asiri Allah ya saka maka.
Muryan mummy ne take fadin bari muje gida mu dawo sai azo maku da abinci nace ai da a barshi Iyya tana can tana hadawa ai.
Sun wuce aka barni da yaya bashar basu dade ba maryam suka iso da mahaifiyar yaya bashar din nan muka zauna atare dasu.
Sai dai mama tana bugo waya akai akai tana tambayan ko ya tashi a lokacin ko yana aman har yanzu ?
Nace bai kara yi ba yana dai barci ne tace Fatima kada ki yarda a cika dakinbda suruti kinji ku barshi ya huta please nace to mama.
Nan kuwa muka fara ganin yan uwa da abikan arziki harda ma wanda bamu sani ba suna shigowa gaidashi.
Mummy tagama shiryawa tace wa mama su fito su zo mama tace haba hajiya kubura kamar ban gode ma Allah ba ke nan ai.
Gaki ga matar shi da yan uwa a kan shi may kuma zan koma yi adduan mu yake bukata kuma ya samu ko?
Allah dai ya bashi lafiya sai kun dawo agaida su mummy taji dadin hakan sosai suka tafi tare da,Abdul.
Yadda yan uwa suka nuna mai yasa na gane cewa sadauki dan gatane sosai don sai ga yaya Imiran da matar shi tare da abincin sukazo muna.
Nan dai guri ya cika makil Nafisa da kawayen ta sun shigo su ma nan suke cewa yanzu Naffy ke fada muna mukace bamuga zama ba ai uwar dakin mu na cikin tashin hankali.
Kowa yai mamaki jin abinda suka fadi may ye hadina dasu kuma sai cewa Raiha tayi muna zuwa muna cika cikin mu ana muna,taron arziki ai dole ne mu zo gurin ki.
Wani likitane ta ke duba shi ko na kira P M O ne yazo da kan shi ya duba muna shine dai.
Kowa yasan zasu uya don sunyi kamari wuce pmo ma balle director gaba daya.
Yaya Ahmed suka shiigo da matar shi jamila a lokacin dressing din ta kawai ya isa mutum ya gane ko ita wacece.
Sai yatsune yatsune takewa mutane tana kallon shi tace au ashe shine ban ma taba ganin shi bani.
Sosai na mayar da hankalina gurin su Nafisa da kawayen ta muna hira maryam sai haushina suke ji da Amirah.
Suko yadda na ke tare da,su yai masu dadi sosai a ran su don sai jana suke da hira ina dan murmushi.
An cika duk yan gidan su ne gungun gungu a haraban gurin falkawa yayi da karfi yake kiran Fatima Fatima da sauri yaya bashar ya shiga dakin Abdul ne yakirani.
Na mike da sauri gabana yana faduwa idanuwa aka sako min caa da kyat nake tafiya a lokacin.
Jamila matar yaya Ahmed bata sanni ba sai ranan take fadi au matar tashi ke nan ashe ?
Ina shiga ya falka Bashar yana tsaye a kan shi lokacin na karasa gurin shi ya miko min hannun shi yana cewa zauna kija min hannu na da kafa please.
Mummy ma tashigo dakin don ganin ya falka a lokacin tana mashi sannu da jiki ya amsa mata da kyat da sauri ya dago yana son mikewa yace amai yake ji sosai da sauri na dauko roban da aka sayo don ya dinga yi a cikin shi.
Amai yayi sosai bakikirin dashi nan hankalin duk wanda ke gurin ya tashi sosai sai kawai ya rufe idon shi ya zama colarbs jiki ya sake mai da sauri na karasa ina kiran sunan shi bashar yace na fita dakin .
Don kuka yaci karfina a lokacin ganin na fito ina kuka yasa mutanen da sauri suka karaso jikin maryam na fada ina kuka tace may yafaru nace baya numfashi maryam da sauri mazan gidan su suka shiga gurin shi dakin
Ina nan naga bashar yafito da sauri ya nufi gurin likita duk wanda ke gurin hankalin shi a tashe yake sosai naji dadin su Nafisa da kawayen ta don sun nuna damuwan su sai akaina.
Likita yazo da sauri suka shiga dakin yana fadin suma yayi bayan ya duba shi ai hankalin kowa a tashe can sai ga baba da su umma sun zo.
Ikon Allah sai Nafisa ke fadin to baidai mutu ba balle aji dadi ba,azo ba sai yanzun da akaji ance baya da rai yana nan daram.
Taba wasu haushi musaman yan uwanta amma babu yadda suka iya da halinya dole aka saka mata ido uwayen dai sunji kunya sosai.
Yana falkowa yake fadin Fatima jamin hannuna da kafa please, sai da yaba kowa tausayi a dakin na koma dole dakin duk da ga iyayyen shi amma ina dan matsa mai hannayen shi da kafa a hankali.
Har dare muna tare da mummy don cewa tayi anan zata kwana amma sai yaya bashar yace duk mu tafi gida dashi da sagir da Abdul zasu kwana gurin shi.
Hakana na kwana a cikin zullumi tun da safe washegari ina asibitin gurin shi.
Ance mutum mai yawan bautar Allah yakan zama wani lokaci kamar waliyi ne saboda yawan ibadan shi.
Hakane ya faru da mama don tai sallah nafila tadan zauna tana tasbihi kafin a kira sallah asuba tayi sallah.
Nan tai mafalki ana ce mata kada ki damu taimakon shi Fatima tayi amma zai mike.
Ta falka firgigi da ita tana cewa subbahanallahi Fatima kuma haka yasa zuciyar ta zargin akwai wani abu a kasa amma koma may ye zata binciki Fatima din taji.
Sun shigo gaida shi da safe ne ta kirani gefe muka gaisai da ita can ta dafani tace ki kwantar da hankalinki insha Allahu zai samu lafiya kinji.
Can naji ta dafani sosai tace Fatima may kuka ba saudauki ya shane haka mai karfi don nagani a mafalki na yau.
Ras, ras gabana ya fadi uku uku lokaci daya nadaugo kai na da sauri na kalleta tace ba boyo tsakani na dake fada min nace cikin kuka mama yaya bai bar sha ba har yanzu.
Shine yaya bashar ganin muna yawan samun matsala ya koma gurin mutumin nan shida maryam suka anso wani wanda zai amaye abinda yasha gaba daya a jikin shi.
Ina fadin haka na dago kaina kalle ta murmushi naga tayi ta dafani tace Allah yai maku albarka Fatima kun karasa aikin dani ce ya dace nayi shi tun farko.
Kuma duk halin da kuke ciki na sani maryam ba ban sani bane amma tunda kikayi yadda nake so dake rufin asiri a tsakanin ku yasa na ja bakina nai shiru dashi.
Tace ban son jin zancen nan a bakin kowa daga Allah sai ku da kukayi don koshi kada ki yarda ya fahince ki don zai dauka wanan wahalan da yakeyi kashe shi kuke son yi ba taimakon shi ba .
Don haka ki rike wanan sirin a ranki ki boye sirin mijin ki danaki a kowa kinji Allah yai maku albarka nagode Fatima abinda nai hasashe ke nan tun farko akan ki.
Tare da mama muka dawo dakin yana zaune ya ramay ya fada sosai kamar bashine yadawo bulbul dashi ba.
Ya samu sauki don aman ya tsaya sunce har cikin dare sai da yayi aman sosai bakikirin dashi.
Yanzu sai barcine ya ke damun shi da ya dan falka sai ya koma yaci gaba da barcin shi.
A sibiti muka fara azumin wanan shekaran da wata ya kama na azumi amma ya samu sauki sosai.
Azumi uku mukayi a asibitin aka sallamashi ya dawo gida nan naci gaba da jinyan shi da kaina.

IDAN KUMA KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH,,,
Mun kai wani lokaci mai tsawo tare da yan uwa ana ta yaushe rabo a tsakanina da su wanda yawanci duk wasan su akaina ne su na min wasan kanin miji.
Ganin yai shiru nasan halin abina bai faye son surutu mai tsawo ba shi sai dai a dan yi ai shiru yasa na fahinci taron hayaniyan ya dan ishe shi ke nan a lokacin.
Na dan mike zuwa gaban shi nace tare da dan rakwafowa gare shi yana zaune ya rike goshin, shi da hannu daya yana dan murzawa a hankali idanuwan shi a lumshe gaba daya.
Jin muryana kusa dashi ina magana ina cewa yaya may za,a zuba maka ne kaci ?
Bude idanuwan shi yayi ya sauke a fuskana da nake duke gap dashi na kara cewa may zakaci ne yaya?
Ya dan sauke min murmushi yana fadin duk abinda kikaga ya,dace dani ki zubo min.
Gurin dinin na tafi na fara hada mai abincin gargajiya wanda mun dade bamu ci shi ba sai yau da muka dawo gida.
Tare da zuba muna ferfesun kayan cikin rago dana danyen kifi manya masu tsoka sosai.
A plate daya muka ci abincin da yake ba,a saman table bane kowa yana kasa nan kowa ya fara diban abinda yake so muna ci muna hira tsakaninn mu.
Nice na fara mikewa tare da dan fuskan tar yaya nace zan dan shiga ciki na kewaya wai irin kallo yai min wanda yasa dul wanda idon shi ya kai ga kkallon a lokacin sai yaji wani iri.
Don da ido yai min magana na taimaka mashi shima na shige dashi a cikin dakin shi.
Hannu na mika mashi ya kamo tare da mikewa tsaye muka shige daki dakin shi muka fara shiga sai da ya shiga wanka na fito zuwa dakina wanda nai watanni ban a cikin shi.
Wani kamshi ne mai tuna min da abubuwan da suka shude a baya da dama kamshin dakin nawa ya,tuno min.
Maryam ce ta biyo bayana muka zube tare da su a dakin nan na shiga wanka na shirya cikin wani riga dogon milk color mai guntun hannuwa.
Na mulke jikina da kayan kamshi masu kyau da tsada na gyara na fito inda kowa yake bayan nayi sallah.
Mazan sun fita zuwa masallaci mu matane muka rage a cikin gida sai ga Nafisa da kawayen ya sun shigo taron mu.
Da murmu muka tari juna da su kowa yana mamakin dalilin shakuwa na da su darrr ake zaune dasu kamar ana ga masu cuta a jiki ko kuma masu wani aikin kissa.
Sun fahinci cewa kowa yana jin haushi zuwan su gidan a lokaci da yake basu da kunya sai cewa Nafisa tayi ni dai ba gurin uban kowa na taho roko ko maula ba gidan dan uwana ne nazo dole kuma nayi yadda kowa keyi.
Nam suka so kaurewa da maryam da ita dama ba shiri tsakanin su tun gida Allah ya kawo yaya ya daka masu tsawa tare da masu fada suka daina.
Kamar yadda Nafisa tace yadda kowa yayi haka zatayi don gidan dan uwan ta ne hakane kuwa tayi.
Don mikewa tayi ta kwaso abinci gudan mai yawa ita da kawayen ta komai na gurin sai da ta debo masu shi duk an saka masu idanuwa na ce su zo muje dakin Iyya can muka zauna tare da ni dasu da ma maryam din .
Karshe suka shiga bamu dariya tun maryam na daure fuska har ta shiga dan murmusawa hiran da sukeyi mun dauki lokaci da sune sukace zasu tafi ina tsaraban su don shi ne sukazo tun yau kada a wawashe a barsu.
Nace tsaraban ku ya na hanya sai zuwa ranan Thursday ku shigo na baku naku
Raina tace kai uwar dakin mu walleh kada ki sa muyo tahiyar banza mu taho bamu ga yan, kudin man, mu kuma bamu ga tsaraba.
Nace shim banita nice ku taho ba walleh na,sayo maku tsaraba tun can da sunan ku na sayo shi .
Wani ihun dadi suka yi suka tafa tare da shewa shiya sa muka son ki uwar dakin mu don ke dauki duniya simple ba ruwan ki da wani jiji da kai ko kyamatar halin mu gare ki.
Nace kai amma dai anty akwai ku da wani irin magana lalura ta Allah shi yaye maku ita bayan ita minana gare ku na kyama tunda dai nagani da idona kuna sallah to miyarage kuma watan azumi anan kuka daukan abin buda bakin ku to mi aka so.
Nan dai mukai sallama dasu na fito na raka su har bakin kofa na juyo muna dariya.
Yaya Sagir yace Fatima ina kika kwaso wanan gayyan tsiyan haka,wa yan nan mu,amula dasu ba alheri bane fa .
Yaya bashar yace ai kuma kaji matsalan mutanen mu ke nan wallahi sai a dinga gudun mutum shi ke kara jefa su ga halaka sosai wallahi .
Yanzu yadda kaga Fmta sake da Fatima haka duk yadda ta juya ta zata bi don bata kyamace ta ba kaga zata iya mata nasiha har yai tasiri a kanta idan ma wani magani ne yadda da shakuwa zai sa ta yarda tasha koma may nene.
Shiru Sagir yayi yana sauraren maganan bashar yace bai kamata ace kuna nuna mata kyama haka ba kujawo abinku ga jiki da sannu kuna mata nasiha kuna bata taimako har ta gane gaskiya idan tana da rabon dainawa.
Amma gaskiya nisan ta kai daga mai shaye shaye yana kara jefa su ne a cikin halaka kawai.
Shi kan shi yaya Sagir maganan tayi tasiri sosai a ranshi sai yake ji daga lokacin zai yi kokarin ganin ya jawo Nafisa a jikin shi ya taimaka mata.
****** ********* ******
Washe gari muka tafi gidan su mama muka gaida su suke cewa ai da mu bari suzo su samay mu su tare mu .
Yaya yace haba kai ai mune masu neman albarka a gurin ku dole muzo inda kuke mu nema.
Mummy tazo dakin mama ta samay ni nan muka zauna ana hiran tafiyan mu tare da mukayi a saudiya.
Duk hiran mu Amira na gefe a zaune mugun halinta yana cinta a lokacin bata saka bakin ta ba.
Mummy da ta fahinci haka tace aike Fatima sai ki godewa Allah don Allah shi ke azurta bawan ya duk sanda yaso.
Yau ga shi kece a wanan kasashen duniya ga yaran gidan mu da suka tashi a cikin daula wasu ko Abuja basu sani ba balle wanan irin kasashen da kika shi ga haka.
Maji tace ai ubangiji miskarraziratin ne shi ke yin da yaso da bayin shi a duk inda yaso.
Yanzun baga shi ba hajiya da gidan wani akakai wanan auren ai wani abin sai dai mu hanga a cikin gari ko a makwabta kawai.
Amma yanzu kinga hikimar manya da mijin da matar komai gida,yake dawowa gaba daya shine ai ake cewa duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau sama baya hango shi.
Yaya sadauki dake gurin Baba tun shigowan mu yana mashi bayani akan tafiyan mu irin nasarorin da yayo a gurin wasu masananta da ya saka hannun jari acikin su a waje.
Yace to ke tashi mu tafi hakana ko mun bar iyya gida ita kadai mama tace yanzu yarinya na zaune tana hira zakace wai ku tashi ku tafi.
Mummy tace yanzun fa ya san dadin iyalin shi bai son zama inda muke kuma .
Yai murmushi yace wallahi mummy ba hakana bane kawai da Iyya Rabi da muka bari a gida ne ga kuma mutane suna zuwa taron mu har yanzu.
Mummy ai da zaku bamu daki a gidan nan sai munfi jin dadin zama a kusa da ku dariya sosai yaba mummy har saida tayi tagaji don kan ta.
Mama ta saki ajiyan zuciya daga inda take zaune bayan mummy ta fita daga falon tace Allah sarki ubana har na rasa farin ciki da jin dadin da zan nuna dana gan ku a gaka wallahi.
Yace kai haba maji falalar adduan ki ne fa yakaimu ga haka baki dayan mu ko Amirah yana takalar Amira da yaga ta cika ta batse da shi.
Mama tace kai amma babana baka da zuciya duk wanan iskancin da take shukawa mutane don taga ta samu guri.
Amma katsaya wani kulata can wallahi Amira da kake gani na kusa fita bayan ta muddin bata fitar da miji tai aure ba mu huta da bakin iya shegen nan nata.
Sadauki ya kwantan da muryan shi kasa cikin sanyi yace maji kiyi hakkuri don Allah nima wanan karon na dawo da wanan kudirin a raina ina son naga tayi aure itama ta kama dakin ta hakana ta huta da fadan ki.
Damu da ita dukkan mu dole ne muyi maku biyayya kada ki damu maji zata fito da miji itama tai aure badadewan nan ba zamu sha buki insha Allahu.
Mama tace Allah ya bada ikon yin hakan ga maryam har tana batun haihuwa ita ko ajikin ta.
Sai wanan lokacin Amira tai magana tace ikon Allah maji gama wanda suka aure basu da komai saini da ko auren banyi ba ake min gori.
Wani iri naji a raina da magansn da tayi nasan ni takewa gori a fakaice naji sadauki na fadin lokaci ne baiyi ba Amirah wata rana sai labari.
Kiyi hakkuri gaskiya ake fada maki ba wai ba,a sonki bane aure shine darajan diya mace zan zo mu zauna dake sai muga may yadace ayi.
Baba ya aiko akira mashi sadauki yafita yakoma dakin baba din ina zaune nai shiru don gaba daya jikina yai sanyi da maganan Amira.
Don na fahinci so take ta jawo min wani sabon matsala a rayuwa na ganin yadda nai shiru cikin damuwa yasa mama kokarin sani magana tace.
Waiko Fatima na kin ko ga yadda kika koma kamar wata diyar larabawa dake can aini da a hanya nagan ki bazan gane ki ba gaskiya babana ya iya kiwo sosai wallahi haka duk uwa ke son ganin diyan ta a cikin farin ciki.
Sai aita hakkuri da rayuwa don hakkurin bawa bai taba tashi a banza insha Allahu.
Amirah ko maganan mama bai mata dadi bane sai mikewa tayi kawai tashige ciki abinta tabar mu inacewa mama.
Mama insha Allahu kuma yaya baida matsalan komai wallahi don duk wanan halaiyar nashi ina gani kamar yanzun duk ya kawu.
Sanan mama irin mutanen da yaya yake zama dasu abune mai wuya mutum bai fada cikin halaka irin tasu ba.
Amma sai naga shi yana kokarin yaga ya kare hakkin addinin shi a cikinnsu da muka je can.
Mama taji dadi tace masha Allahu Allah na gode ma abinda nake matukar son ji ke nan Fatima nan mukaai ta hira iina bata labarin tafiyan mu har haduwan mu da Linda a can da mahaufin ta.
Sadauki yana shiga gurin baba ya samay shi zaune yadda ya,barshi da carbi a hannun shi yana tasbihi jin sallaman dan nashi ya dago kai da sauri ya kalli dan nashi mummy tana daga gefen shi a zaune.
Yace na manta na fada maka cewa muna umurah an shigo dakin nan nawa an min barna wallahi.
Da sauri sadauki yace subbahanallahi baba yace wallahi an kwashe min duk agogaiya na masu tsada dama wasu yan abin amfani na bazan ma iya cewa ga iya abinda aka dauka ba ciki.
Sadauki ya saki ajiyan zuciya yace amma baba sai naga kamar barawon waje zai iya shigowa gidan nan kuwa ashe ?
Babada mummy sukace ba daga waje bane koma,waye a cikin gidan nan yake daya daga cikin yaran nan ne yai min wanan aikin.
Sadauki ya kara ajiyan zuciya yace indon agogo ne aida ka fada min tun muna can da an sayo maka wasu daga can munzo maka dasu ko yanzu naga kamar Fatima ta sayo ma agogo guda biyu a Dubai masu tsada da kudin da abokaina suka bata can.
Baba yai murmushin jin dadi yace ikon Allah kaga hukuncin ubangiji ko ?
Yace Allah yai maku albarka yabaku zuria masu albarka a rayuwanku.
Mummy tace nifa abinda yafi tayar min da hankali shine takardun gidan nan da ba a gani ba har yanzu wallahi.
Sadauki a razane yace subbahanallahi may kuma za,ayi da takardan gida da za,a dauka ?
Baba yace nayi zaton ko suna ganin kamar takardan wani abune suka hada hardashi akwai dai abinda sukazo nema a gidan nan.
Sadauki yace insha Allahu zan sa aimin bincike a tsanake ko za,a gano wanda yai wanan aikin haka.
Sun jima suna maganan shida baba da mummy ya kwantar wa baba da hankali yai masu sallama yadawo dakin mama.
Nan yasamay mu yake cewa mama ashe abinda ya faru ke nan bayan tafiyan mu anshigawa baba dakin shi.
Mama tace ni ina ganin yaran gidan nan ne sukai wanan aiki Allah dai ya shirya ko wanene abin baiyi dadi ba wallahi don ta gurin A C din shine suka shiga yadda ba wanda zai gane an shiga dakin.
Muna hanya yake cewa kai gaskiya ko waye yai wanan abin bai kyauta ba takardun da aka dauka yafi tayar min da hankali wallahi.
Nace Allah ya tsare kada mai shi yayi wa baba bar na da takardan yace nima shine damuwa na wallahi.
Har muka kawo gida ba wanda yai magana a cikin mu kowa da abinda yake tunane a zuciyar shi.
****** ********* ******
Sai bayan kwana hudu kayan mu suka shigo gari nan na fara rabawa kowa tsara ban shi har gida sai da na aika masu kuma nace zan tafi amma sai yaya ya hana yace na bari sai an kwana biyu don zamu koma school lokacin.
Maryam ta gama karatun ta saura ni na rage yanzu don haka na koma ni kadai ce ke moving a makaranta.
Ga idanuwan mutane a kaina duk da ina kokarin kama kaina a matsayina na matar aure kuma musulma.
Amma sai kaji ana gulmana wai suturun danake sawa da motan da nake shiga ya zarta na sauran mutane.
Kullun fa a cikin hijjab nike amma mutane saboda sa ido har suna fahintan may ke cikin jikina.
Dole ne don duk wanda ya sanni a baya babu mai ganina yanzu bai san akwai canji a rayuwana ba.
Banda matsala don ina maida hankalina sosai ga karatuna ba sai na tsaya wani loveying ba akan makin dina.
Na dawo a gajiye daga school da wuri na shigo gida don yau Friday na idar da sallah ina kwance saman sallayan da nai sallah hannuna da carbi ina ja.
Ya shigo dakin nawa yana saye da farar shadda tasha aiki a jikin ta sosai sai maiko take yi.
Na dago kaina a hankali na kalleshi yadda na ganshi na fahinci bai cikin dadin rai a lokacin .
Mikewa zaune nayi da kyau ina mashi barka da jumma,a ya amsa min tare da zama a bakin gadona.
Inda yake zaune na tako na zauna daga gefen shi na kalleshi cikin natsuwa na sakan mai lalausar murmushi don in isar ma zuciyar shi da sako.
Nace wa ya taba min sadaukina kuma yau haka zai bata muna jumma,an haka ?
Ya dan kakaro guntun murmushi tare da dan jan guntun tsuki yana cewa .
Fatima al,amarin yaran gidan mu ne yake bata min rai wallahi yanzun ace duk yadda Baba yai kokarin ganin ya inganta rayuwan mu amma babu wanda ya mayar da hankalin shi ga abinda ya koya muna.
Nace yaya ai yan uwanka duk yan uwan ka ne don haka ni sai naga kaman yanzu abinda ya dace shine ka taimakawa yaya Sagir da yaya Abdul su da ke tasowa yanzu ko Allah zaisa a dace ta gurin su.
Murmushi yayi tace tunanen mu yazo daya danaki ke nan abinda na dade ina kudurtawa a rayuwana ke nan a kan su.
Zan dauko sagir na saka shi a jikina sosai yadda zan samu Allah yasa muna hannu ko za,a samu dama ga al,amarin.
Don kinga yanzu ni nan da wasu shekaru dole na bar zancen buga ball din nan da nakeyi don in girma ya kara kama ni ba zan dawma ga wasan ball ba.
Shiyasa yanzun ma nake ta kokarin ganin na samu inda zan kafu da kafana koda na daina wasa ya kasance ina da wani madogara da zamu ci musha a cikin shi.
Tausayi ya bani don nasan yaba da nauyi da yawa yanzu a kan shi don duk wani lalurar gidan su shine maiyin a yanzu.
Nace bayan duk munyi shiru ba dan lokaci mai dan tsawo kowa na tunane a ran shi.
Yaya yan uwaka ne na jini dukkan su kuma bakai kade suke yan uwanka ba a yanzu nima sun zama yan uwana na jini.
Duk abinda su Umma suke gwada maka kan su,suke gwadawa, abinda basu so su gani yau Allah ya yayi suna gani da idon su.
Kaine kuma mutum mafi daraja a cikin gidan mu a yanzu don haka saka masu da,alheri sai aniyar su ta koma masu.
Nakai kaina saman kafadan shi tare da dan shafo fuskan shi nace sai kai tunanen inda ya dace ka saka su.
Rugumoni yayi zuwa jikin shi tare da sauke ajiyan zuciya yace maganan ki Fatima ya bani kwarin gwiwa a yanzu sosai zanyi yadda ya dace dasu din zuwa wani sati zajiji may muka shirya akai idan naga bashar.
Nace nagode yaya aikin na Alheri allah ya kara daukaka shi akoda yaushe Allah kuma ya tsare muna kai daga duk wani abinnki.
Ba mu sake junan mu ba ina makale a jikin shi ina shakan kamshin jikin shi maidadin amowa.
Sannu a hankali bayan ya dan samu natsuwa naji yai dan gyaran murya a hankali ya soma yi min magana yana cewa ina ta kokari naga kin fara sana,a Fatima.
To amma kuma bazan iya bari kina fita ba akoda yaushe don sana,an mata abune dake yawan dauke masu hankali ga harkokin su na cikin gida.
Bazan so hakan ya kasance dake ba Fatima nafi son kalar sana,an da kina gida kudin ki suna shigo maki ga account din ki kawai.
Wani irin sanyi ya sauka min cikin raina nai maza nace mashi nima yaya ba zanso abinda zai sani na raja,a da bautan Allah na ba ko kadan.
Cikin zuciyana naji kanar nace mai to ko muyi sanan kayan dakin mata show room.kawai sai da ma,aikata maza kawai su zauna a gurin.
Amma sai naji tsoron fadin hakan don ban san irin tanadin da yai min ba a zuciyar shi.
Yana makale dani a jikin shi yake cewa zan kara dubawa nagani idan akwai wani harka mai sauki da zai yiyu.
Amma don Allah koma may nene za,ayi ki yi kokari kiyi adalci tsakanin mu kada ki so kanki da yawa a ciki.
Nace mashi insha Allahu yaya bazan raja,a ba ga son duniya akan ka yaya sai naji yayi murmushi kawai alamar yaji dadin a ran shi.
Sai da ya mike har ya fara tafiya yake cewa yau fa ina ganin mutumiyar ki kamar tana labor ne don nakira wayan Bashar dazun yake ce min wai suna asibiti da ita tun safe.
Da sauri nace anty maryam Allah sarki nan na fara murna da adduan Allah ya raba lafiya .
****** ********* ******
Bai dade da fita ba sai ga wayan ta ta bugo min tana fada min ta sauka lafiya nan na yanka wani ihun murna na nufi falo da zuman fada mai yana zaune ya cin fruit don yanzun ya rage yawan cin abin sosai kamar baya sai dai fruits da yan sauran abubuwan gina jiki kawai.
Murmushine a fuskan shi na iso da murna na nace yaya yace kun zama su mama yau ko nazauna ina fadin wallahi fa.
Nace yaya na tafi asibitin ne na dubo ta yace dauki bai bari ki tsaya mu tafi tare ke nan ko?
Naji kunya nace sorry barin tsaya kagama mu tafi, nasan zolayana yake yana ta shiririnta ci har yagama muka kama hanya zuwa asibitin da ta haihu din.
Nice nai driving din mu yana gefe zaune sai waya yakeyi yana fafin sister shi ta haihu ta samu baby boy.
Muna shiga dakin muka samu yan uwa da abokan arziki harda mummy a gurin don itace tazo daga gidan mu.
Yaron yana nade a cikin showel a,saka mai rigan sanyi sky color mai kyau ta jarirai a jikin shi.
Ita ko maryam tana kwance saman gado sai murmushi takeyi na karbi yaron na mikawa yaya shi ya dan kalle ni yace Fatima ban fa iya daukan yaro ba fa.
Na gyara mai tare da nuna mai yadda za rika yaron ana muna dariya yaya idan naku yazo yaya zakayi inji sister din Bashar nace ai shine fadila
Inda maryam take a kwance ya taka yana ce mata sannu yar gidan maji yau kan kin san kin shigo duniya ko?
Murmushi tayi cikin jin kunya tace kai haba yaya dama ban san nashigo bane yace to yaya jikin naki normal dai kike ko don naga dan nawa so health dashi.
Murmushi kawai tayi tace ummhumm yaya Bintu over to you now ko ni kan na sauke na huta .
Ke ban son Bintun nan na fada maku ku daina kiran ta da aanan sunan kauyawan hakana please mutum da sunan shi mai kyau kuna bata mashi da,wani Bintu can.
Kai malam yayane kuma mutum yayi fitan kutsu haka shine zaka kama min mata da fada tana kwance a gadon asibiti.
Kai dan iska wallahi jawa matar ka kunne duk ranan da naji sunan nan haka a,bakin ta ba hauhuwa tayi ba ko duniya ta haife ranan sai na nashi shegen bakin nan nata.
Aiko da sai fada kawai za,a raba mu dakai donbda sai na rama mata yace ga Fatima zaka ramay ko ankan wa .
Bashar yace akan ka dai kaida kai min laifi ba kaunats da bataji tagani ba yace ko zaka gwada ne yanzu Baba.
Tun da kaga yau ka zama Baba kana gani kamar karfinka yazo ke nan ko yaro.
Yaro fa kace min maye kagani anan kuma ni yanzu ai sai dai baba kawi aka bushe da dariya a gurin.
Naso yaya ya barni gurin Maryam amma yace mu koma gida gobe zai kaini na wuni a can yanzu mutane sunyi yawa sosai.
Haka na tafi gashi muna son kebewa da maryam nasha labarin abinda tasha.
Muna hanya yana waya ina tuki ban yi magana ba saida ya gama waya ya furza iska nace kana can kana fada ga abinda ya dace kaiwa fada akan shi.
Yace may ke nan fa ?
Nace kiran mamana da Majin da kukeyi mana don Allah ua kamata ku canzawa mama suna hakana please.
Kuma fa yaya duk kaine ka saka mata wanan sunan don Iyya ta fada min wai baka iyannkiran ta maijidda da baba ke kiran ta shi ne ka dafa mata wai maji can.
Mirmushi yayi ya shafo kan shi yace na dai ganecwallahi Iyya Rabi tana min tonon silili a gidana .
Nace lah may ye laifin iyya yaya don ta ban kado min sirin baya tafa fada min irin yadda kai ta wahal da su mama wallahi.
Yace hummm yai shiru tare da kwantawa da kyau saman kujeran mota ya rufe fuskan shi da hular kan shi kawai.
Mun kusa shiga kwanan layin mune naji yace Fatima cikin wani irin murya nace na,am yaya yace wallahi yanzun ban san may yasa ba ina matukar son baby nima sosai wallahi tun dai yanzu dana ga na maryam din nan.
Please Fatima will you give my baby too please Fatima ina son naga nima na haihu wallahi.
Idanuwana na lumshe cikin wani irin yanayi da tausayin kan mu don ya fadi ne a baki amma ni na riga shi furta hakanna raina.
To waye mai laifin a cikin ni dashi da muka kasa samo ma kan mu farin ciki irin haka ?

IDAN KUMA KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI DA ALLAH YAR UWA,,,
Ya ramay sosai sai dan wuya da ya aje a lokacin ga wani irin barci da ko ysushe yakeyi ni da iya ne kawai muke azumi don shi bai iyawa a lokacin.
Abinci ma sai da kyat nake samu ya dan tsakura yaci yasha magani.
Yau hudu ga watan azumi ya fito falo ya kwanta tun safe yake kwance a falon sai shige da fice masu zuwa dibiya sukeyi a gidan zuwa azahar bayan a watse ba kowa a gurin shi gurin da ya idar da sallah yake zaune.
Nafito zan shiga kitchen gurin da iya take a zaune ta na fere dankali na nufa sai ji nayi ya kira suna na a kasalance da Fatima.
Na amsa tare da juyowa gare shi kan shi na a,saman kujera baida lakka da gani a jikin shi.
Na karaso tare da zama a saman kujera da kanshi yake sama gyara kan nashi yayi tare da dora kan shi saman cinya na da kyau.
Yace wai may ake cikine ban ji kin ce min komai ba ba hannuna na dora saman kan nashi dake saman kafafuna na a hankali ina shafa mai kai dashi.
A hankali naji ya sauke ajiyan zuciya tare da lumshe idanuwan shi ya kara sako min nauyin shi a jikina.
Nima lumshe idanuwa nayi a lokacin nace yaya love kamar may fa ke nan ?
Yace may za,a ba mutane ne na azumi don na dawo da niyar na tambaye ki naji yaya za,ayi ne may ya dace aba mutane na azumi.
Na lumshe idanuwa again nace yaya bazaka bari kaji sauki ba sai ayi maganan ?
Murmushi naji yayi yace ai naji sauki mana ya kamata ayi wani abu don lokaci yana ja gashi ina son zuwa umurah cikin watan nan.
Nace to Allah ya kara baka lafiya yaya yanzu may kake ganin za,ayi ne ke nan ?
Naci gaba da cewa su baba ma nasan kaine mai tallafa mashi yanzu gashi kuma lalura yazo ya gifta akai.
No ki bar zancen na su baba da mutanen Rabah na riga nai masu tana din nasu ko yanzun dai ina son ki taimaka min ki yi list din mutanen da kika ga yadace aba wani abu sai na gani nace to bari na dauko pepper da biro sai na fara a gaban ka ko ?
Sai dana je gurin Iyya a kitchen na bata hakkuri taci gaba da aiki zan dan yi wani abu yanzun ne.
Tace haba hajiya dama dai aike ce baki zama amma komai da kuke bukata ai na iya yanzu wanda ban iya ba zan kiraki ki duba min .
Na dawo gurin shi ida na fara rubuta sunayen makwabtan su na can gidan baba.
Inayi ina lissafo mashi wa yanda nake rubutawa har na kawo gurin na ugun da muke zaune a yanzu shine ma yake kara tuna min da wasu gidajen idan na manta.
Yace banji kin sa sunan mutanen ki ba mana suwa ke nan yaya na tabaya cikin sonji su ?
Yace masu gadin ki mana nace Allah sarki wallahi har na manta dasu nan rubuta sunayen su ciki.
Nace shike nan ko ina ga an gama ya dan dago kai yana kallo na, yace kin san ban san mutanen arzikin ki na can gida ba fa ?
Murmushi nayi nace har dasu yaya za ,a rubuta yace ki rubuta su mana su ma.
Mutum kusa goma na rubuta mai yan uwana dana mamana har da yayan mama tabawa ciki.
Yace motan da nai odan kayan sun shigo sukace don haka bashar zai zo sai a bashi list din kinga ga musa ya dawo sai yakai na mutanen ku shi da driver ko ?
Yadda ya fada haka akayi washegari nan gida ya kace may su yaya Sagir yaya Abdul da yaya Jibrin kannen shi sai yaya bashar da wasu ma,aikatan su ne sukai ta faman rabon wanan kayan shi yana daga ciki tare dani ina kula dashi sai dai duk wanda ke son ganin shi yaya Bashar ya hana a shiga gidan sai da shi da kannen sadauki kawai suke shigowa gidan.
Take labari yakai ko ina sai ga al,uma bayin Allah masu bukata sun yo caaa a gidan.
Nan yace ma bashar da ya shigo ya fada mai araba masu sauran sai a karo buhu hamsin a hada masu dashi.
Ba karamin mamaki nayi ba da irin wanan abin alherin da yaya sadauki yayi ba koda yake ba mamaki don yagaji alheri ga uwa da uba ne.
Ankai kayan azumi a gidan mu ida abin ya zama abin magana a gari ashe ya ba da buhu biyar na shimkafa yace a rabawa mutane gari kuma ban sani ba sai da musa ya dawo ne yake fada min.
Nai matukar mamaki duk da ba,a mamaki da ikon Allah wai a kwallon kafa ne yaya sadauki ya samu wanan kudin haka.
Ikon Allah ke nan yau sadauki ne da,wanan irin alheri ga al,umma haka ubangiji Allah ya kara albarka.
A kwana na shidda ne da azumi yace zai tashi da azumin naso yadan kara sha amma yace zai gwada ya gani.
Lafiya yakai azumin shi ranan haka yaci gaba da azumin shi kuma yanzun yana fita zuwa site din su ya dan duba su.
Ranan ya dawo da dare bayan mun gama buda bakine yake cewa ina fatan kin fara shirin tafiya ko ?
Nace zuwa ina yaya ?
Yace umurah mana daga can kuma zamu wuce chaina akwai wani aiki da zanyi don ina son bude kamfanin karfe anan sokoto insha Allahu.
Ban san lokacin dana fada jikin shi ba na ma manta da wata Iyya Rabi a gurin lokacin.
Shima rugumoni yayi yana murmshi yace cikin harshen turanci kin san dama fa bamuje honey moon din mu ba kin ga sai muyi shi acan tunda kuna hutu.
Dan jaye jikina nayi tare da cewa kai haba yaya wani honey kuma bayan wanda ka lashe a nan cikin gidan ka yace to bari kigani idan mun tafi ai.
Koda na farga ashe iyya dake zaune tana kallon sallah a kasar makka ta bar falon .
Nace lah ashe iyya bata falon nan ban ma san tashin taba wallahi kaga ka koreta ko yaya ga Iyya da son kallo wallahi.
Yace kin dai koreta ke bake ce kika rugumay ni a gaban ta ba ya kamata fa ace an saka tv a cikin dakunan nan don kallo kinga ko musa na lura idan ina falon nan kamar ina takura mashi shima.
Washe gari kuwa sai ga masu hada starlight sunzo gidan suka hada ako wani daki na gidan kowa da nashi receive din a dakin shi.
Nan naita faman koyawa iyya yadda zata dinga kamo tashan da take so a dakin ta ita kadai.
Ashe tafiyan har su babane da su mama za,ayi shi sai da tafiyan ya matsone saura kwana biyu mu tafi naga ya shigo da passport din masu tafiya.
Daga iyya sai Musa na muka bari a gidan na fada mata don Allah kada a manta da masu gadi gurin girka abinci idan sunyi.
Naje gidan gurin su mama na samay su suna shiri gaba dayan su ban fita ba sai da na gyara mata kayan ta da daki da yake wuni zan dayi masu a gidan take ce min ai gwagona ce zata zo ta zauna mata daki da Amira don bata tafiya ta barta ita kadai a gida hakana.
Anty Amira sama sama muke don haushina da take ji babu abinda ya canza a ciki sai ma ince ya karu ne kawai yanzu.
Sai bayan la,asar na bar gidan zuwa gidan anty maryam can muka lalace da ita wanda hiran namu akan mazajen mu ne mukayi shi.
Na dawo gida na samu Iyya ta gyara ko ina ta gama komai yadda ya kamata sai bayan sallah magariba ya shigo gidan.
Muna falo gaba dayan mu sai mashi sannu da shan ruwa mukeyi a kasalance ya zauna don har yanzu ba wai karfin jikin nashi yake ji ba sosai.
Nan muka shiga jera mai kayan buda baki a gaban shi bai ci wani abu ba sai kayan fruits din da ya sha kawai ya kai kwance fuskan shi yana kallon tv ana sallah asham a saudiya tv.
Yace iyya Rabi gobene fa tafiyan mu insha Allahu zamu tafi mu barki da Musa sarkin son yawo kingan shi kada ki bari ya wuce takwas bai shigo gida ba kun rufe don tsaro.
Tace insha Allahu nawaje na za,ayi yadda kace yace kai kuma kaji may nace ko?
Musa yace naji yaya ai ba inda zan tafi ga tv nan muna kallo ai da rana ne kawai nakan dan fita can bakin shagon.
Daga haka yai shiru idanuwan shi suna a lumshe sai da akai kiran sallah suka fita tare da MUSA.
****** ********* ******
Washe gari da azahar muka bar garin sokoto zuwa sadauya mun sauka da dare inda akai muna screening motan da ke jiran mu muka shiga sai wani hotel nan muka kwana a jidda sai da safe muka wuce zuwa madina.
Ibada sosai mukeyi ba kama hannun yaro har su umma da mama sun bani mamaki sosai yadda naga suna ibadan su sai dai bawai sun bar halinsu bane ko acan.
Adduoina sun fi yawa ne akan Allah ya shirya min yaya sadauki da samun zuria masu albarka dam yan uwa musulmai da suka fada cikin irin wanan halin .
Sai dai a can ni da mummy muka zama kamar kawaye sai mama da muke tare da ita wani lokaci don mama bata da time din wasa ko kadan ko yaushe cikin ibada take .
Mun bar madina mun nufi makka a can mukai kwana goma muka fara shirin dawowan su gida mu anan zamuyi sallah two days after sallah zamu wuce chaina din.
Ana gobe zasu tafine ina makale da mama da mummy da wani iri shakuwa ya shiga tsakanin mu yanzun da ita.
A can nice mama take sakawa na zaba masu abubuwa ni da mummy wanda kusan sayayan na Amira ne da naji ance wai zatai aure bada dadewa ba.
Har gado nice yaya yasa a gaba na zabi gadaje har guda biyar masu kyau.
Da,safe mukai masu rakiya suka tafi muna tsaye muna kallon su ba yadda zan yi ban san lokacin da hawaye ya zubo min ba.
Muna motane yai dan murmushi tare da rungumoni zuwa jikin shi na langabe kaina ina share hawaye a hankali yace baki son rabuwa da mama ko?
Ban yi magana ba sai ajiyan zuciyar da nayi kawai muka kai masaukin mu wanka mukayi muka nufi masallaci gurin sallah sai dare sosai muka dan huta kwana biyu duk a cikin masallaci mukayi shi.
Ranan sallah na saka wani dogon rigan mai tsananin tsada da ya sayo min a wani katon shago na kayan mata.
Rigan da gani ta matan manya ce irin tasu sai wace ta isa take sayanta
Na yafa mayafin rigan take na koma kamar irin matan manyan larabawan da muke gani ko kuma matar wani kusa a kasan mu.
Ga zubbunan gold da na saka guda biyu a yatsuna wuyana kuma Diamond ne kiran Dubai sai takalma mai tudu da yar karamar jakan takalma dana rika a hannu na sai wani kamshin turaren larabawa ke tashi a jikina.
Yana falo zaune na fito a cikin shirina wani irin mugun kishina ne ya darsu a zuciyar shi.
Na karaso inda yake zaune shima kayan maza yasa na larabawa masu tsada na karaso inda yake zaune cikin wani takon da ban san inayin shi ba.
Wani kamshi ne ya daki hancin shi har ya saukan mai da kasala a lokaci daya.
Ya sake idon shi yana kallona har na karaso gare shi tare da,dan fadawa jikin shi ina cewa yayana barka da sallah.
Yace Fatima anya kuwa kece haka ko dai an canza min matane nace bari ka tabbatar da ni dince to na dan kai mai wani guntun cizo a kunnen shi ya dan saki wani dan kara yace muguwa.
Na mike ina dariya yace Fatima kinyi kyau kinyi kyau sosai wallahi ban san may yasa duk dogon rigar da zaki saka sai naga tai matukar karban ki kaman don ke aka dinkata ba ?
Gaskiya kafin mu bar garin nan sai na kara saya maki irin dogayen rigunan nan da yawa koda mun koma gida ki dinga min kwaliya haka dasu.
Nace kai haba yaya kaface da tsada ka,sayo su fa ai biyun nan ma sun isa haka please.
Yace Fatima shigan ki a cikin suturun alfarma shine mutunci na ga idon idon jama,a shigar ki shine zai nunawa duniya ni Umar ina sauke hakkina akan iyalina.
Ya jawoni da hannu daya na fada a jikin shi yace bakin san ko waye mijin ki ba ko bakin U F ba ko Fatima ?
Nai dariya tare da dan shafo fuskan shi da hannu daya yai murmushi nace niko nasan waye mijina don ni nasan kayana.
Yace to ki godewa Allah daya baki Umar a matsayin mijin auren ki uban diyan ki nan gaba kuma.
Yace Fatima mijin ki mai tsada ne mai daraja kuma a idon jama,a sai dai a idon mutum biyu zuwa uku ne kawai yake mai rauni.
Dariya nayi nace idona dana mama ke nan na ukun ne ban sani ba yace na ukun shi ne baba.
Kai yaya kada kaiwa baba haka wallahi tun haihuwan ka har yau baba baida wani da dayake ji dashi kamar ka a duniyan nan.
Iyya fa ta fada min irin son da baba ke maka tun haihuwan ka har ya kai su Umma suna kishin ka tun kana karami har yanzu.
Murmushi yayi tare da jawoni jikin shi yana sinsina na kamar ya samu handkici mai kamshi yacs nasani Fatima nima nasani wallahi.
Iyya Rabi batai karya ba son da baba ke min yasa su imma suka sakani a gaba da horo tun ina karami ga mamanki da shegen hakkuri duk abinda akai min kona fada mata bata cewa komai sai dai tace min inyi hakkuri kawai.
Ya kara motsoni a jikin shi yace kin san may fatima nace ,a,a yayana yace watarana har nakan zargi su Umma a raina akan da hannun su a cikin lalacewa na a baya.
Sai dai zato zunubine koda ya zama gaskiya Astagafullah amma yadda suke gwada min bana jin dadi Fatima.
Sun hana diyan su hurda dani sun hana mutanen shiya ma hurda dani haka yasa na kasance ban da aboki sai bashar.
Bashar yai min kokari a rayuna na Fatima banda kamar bashar a duniyan nan kuma na san har gobe banda kaman shi wallahi.
Yace humma Fatima idan ina tuna wasu abubuwa bazan iya koda gaisawa da Umma da mama a duniyan nan.
Yace akwai lokacin da maji tai tafiya wallahi abinci hana min shi sukayi haka nake takawa da kafa har gidan su bashar a can zanci insha sai dare zan kamo hanya na dawo gida da kafa.
Wata rana ruwa ya hana naje gidan su bashar cin abinci na shiga gida ko zan samu wanda ta tausaya min cikin su ya bani ga abinci ina gani amma sukace min wai na Ahmed ne da Imirana.
Nadawo dakin mu da yuwa sai ga Bashar cikin ruwan nan ya aro mashin din makwabcin su bai ko iya tuki sosai ba yakawo min abinci shi naci har dare na kwanta.
Ga maji bata dawo ba aai ashe tayi yaji ne ta tafi gida ban sani ba lokacin tana goyon Amirah.
Kin san may nacece mai a,a lokacin duk jikina yai sa yi ga labarin da yake bani yace wallahi a lokacin ne na fara shaye shaye tun ina da fifteen year Fatima.
Idanuwana na runtse don jin abinda ya fadi nan yai ta bani labarin irin musguna mashi dasu Umma sukai tayi har mama ta dawo.
Yace ni mummy batai min komai ba wallahi don daidai da rana daya duk da nasan itama tana kishina kan wai baba yafi so na da diyanta amma tana boye zafin kishin ta akaina.
Don Allah Fatima duk zafin kishin ki a kaina kada ki mu,amula da masu sihiri bala,i ne da fadaqa halaka ga mai irin wanan halin daga karshe.
Kara shigewa jikin shi nayi nace kada Allah ya bani kwandalan zuwa gidan boka ko malam wanda zan illanta rayuwa wani bawan Allah.
Munje sallah idi muka dawo bamu sake fita don ansha ruwa ba azumi muna gida muna farautawa nunan mu rai.
****** ********* ******
Mun sauka a China inda na kara tsinkewa yaya ke nan irin abokan da nagan shi da su can har sun so sufi na saudiya ma don ko a can naga yadda yake hurda da yaran masu kudin kasan ga kyautan dana samu har tsoro abin ya bani.
Mun tafi wani katafaren hotel mai shigen tsawo da kyawo sosai kauyanci kan wallahi nayi shi sosai na lumshe idanuwa na daga inda muke zaune a bayan mota nace Alhamdullahi Ala Kulli Halin.
Yace jawoni yace may kikace Fatima nace godiya nake mikawa ga uban gijina da ya nufe ni da hakan .
Tsayawa bada labarin hotel din zai bata muna lokaci amma gaskiya nasha kallo Allah ya horewa mijin kowa yakaita kashen duniya tai kallon abin mamaki a can.
Munga karamawan ta ban girma a gurin abokan shi na can nikan sai faman godiya nake ga Allah da ya daukaka min rayuwana haka.
Ina rungumay a jikin shi muka bar gurin haraban hotel din zuwa masaukin mu a tare muka zube agado dashi.
Na lumshe idanuwa na tare da ajiyan zuciya yace yaya akayi ne Fatiman yaya ?
Nace ni may ma zance yaya dariya naji yayi yace kice kina son U F dinki sosai Fatima .
Ki dinga gyara min kanki ina kallo ko yaushe gadona yazama ready ba sai na nema ba abani idan kin min haka kin gama min komai Fatima a rayuwana.
Murmushi nayi nace ai baka da matsalar haka din ko yanzu yaya .
Yace umm haka din ne amma ba sosai yadda nake so a raina na ba jinayi ya shiga zuge min zif din rigar dake jikina a hankali tare da fada min wasu kalamai da bazan iya fadin su ba anan.
Nace ko wanka ba zamuyi ba yau kuma yace wanda mukayi kafin mu fita may mukaci dashi kada fa ki manta honey moon dina nake yanzu.
Rugumashi nayi nace ai kayi abinka tin a gidan ka na sokoto sai dai ka dora inda ka tsaya kawai.
Yace hakan za,ayi ranan kan nafitar da duk wani kunyan shi a idanuwana na nuna mashi nifa ba yar kauyen da yake kirana da ita bace.
Rayuwa sosai na jin dadi mukayi da yaya a kasan China satin mu biyu a can ya sanya hannun jari a kamfanin yin karafuna da yake son yi a sokoto.
Mun dan kara kwanaki muka wuce har Hong Kong nasha mamaki sosai yadda yaya yasan kasashen duniya haka da mutane kuma cikin yan shekarun kwallon shi.
Daga karshe muka dira a Dubai a lokacin banda matsalan komai a raina ban da na tuhumar ko yaya yabai daina sha ba har yanzun .
Don wanan irin mutanen da naga yana hurda dasu haka dole ne idan mutum.baikai zuciyar shi nesa ba ya yi aikin sabawa Allah.
Amma sai naga shi akan ibada baida wasa ko kada ko wani kasa yana da time din sallah su ko baya gida zai bugo min waya yace lokacin sallah yayi na tashi nai sallah.
A kasan Dubai kan kamar a gida Nigeria muke don yan Nigeria dake kasan maza da mata gasu nan manya da yara kana gani.
Nan naga matan manyan kasan mu yadda suke hurda da matasa ko ina zai tafi tare muke zuwa yana nuna masu ni a matsayin matar shi.
Mutane da yawa suna cewa basu taba tsanmanin yai aure ba ma a rayuwan shi don basu ji ba ana fadin zancen auren shi akasa ba.
Akwai wata hjy wai shi take so ranan da ta ganmu mun fito gurin wani shakatawa sai da ta girgiza da ganin mu.
Nagane hakan a fuskanta tun da muka hadu gasu su uku hamshakai sai wani shakiyancin duniya sukeyi wai su karuwai.
Bayan mun rabu dasu ne naso na tambaye shi ko su waye su amma sai kawai na basar da zancen su.
Shi da kan shi naji taja tsaki yace rabu da mahaukaciya wai a haka sona takeyi bata san ni ba irin shashan matasan nan bane masu kwadayin tsofin mata ba.
Ni yanzu ko budurwa bata gabana balle wata tsuhuwar kwama can na banza.
Har Lindan shi sai da muka hadu da ita a Dubai wai tazo tare da mahaufin ta wani business nace tir da kafurci ta sa ni dan skirt dan mitsitsi iya cinyar ta kawai duk komai nata a fili.
Ita kanta Linda ranan da ta ganni sai da ta girgiza sosai don yadda taga nai mata kyau ga dress din jikina ya karbe ni nan tasan dole ne U F ya manta da wata Linda can.
Tasan lalai yanzu Fatima ta sace zuciyar U F din ta don babu ta inda za a kwata mu da ita gashi kuma addinin mu daya dashi gamu yan uwa kishi ya rufe ta taji kawai tasakawa ranta hakkuri ga tunanen zai dawo gare ta wata rana.
Daga ita har mahaifinta da muka hadu wanda yasab soyayyan su da yaya sai da suka bimu da wani irin kallo .
Mahaifin Linda yake tambayan wanan ce matar shi daya aura din linda tace ita ce dadd.
Yace so young pretty how are you tare da mika min hannun shi na girgiza kaina nace mashi dai yana lafiya tare da tambayan family din shi.
Yaji dadi yai murmushi yace sorry na manta addinin ku ya hana hakan nan ya shiga muna murnan aure ya dafa yaya yana cewa kinga shi nan ki rike mijin ki da kyau don mijin ki big man ne sosai yana cikin lokacin shi.
Dariya mukayi a tare har dan dimple dina ya dan lutsa kadan .
Linda taja tsuki tace ai dole ne UF ya rikice dadd a kan wanan karamar yarinyar ji yadda ya mayar da ita kamar wata queen can .
Ta juya tabar gurin ya ce don't mind her she is jealous of you taga kin fita komai baby ki rike mijin ki kinji yarinya.
Nai mashi godiya ya bani kyautan wasu irin mahaukatan kudi kamar bau san zafin su ba.
A mota hanyan mu na dawowa ne na ciro kudin ina bawa yaya yace na may ye fa nakine fa kece akabawa don haka kibar abinki gurin ki.
Tsaraba kan nasha shi gurin yaya don bai bari na kashe koda kwandala ba daga cikin kyautan da nake samu.
Mun baro kasan mun dawo gida Nigeria don hutuna da ya kare ba don yaya yaso yakare din ba don bai gama morewa ba can.
Sai da mukai kwana uku a Abuja san nan muka ahugo jirgi zuwa sokoto birnin shehu cikin jin dadi da walwala muka iso gidan mu.
Nai mamaki kwarai yadda muka samu yan uwa sun cika muna gida gurin taron mu.
Anty maryam na ganina lokacin cikin ta ya tsufa sosai ya kara girma tazama wata mama da ita.
Muka rugumay juna muna murna daganawan mu again ta sake ni tace wai ko Fatima don Alkah kece haka kodai yaya yakaiki cikin injin ne please.
Na dan shafo cikin ta nace masha Allah ubangiji ya raba lafiya ya bamu mai albarka.
Nan muka samu yan uwa sun cika falon sai faman sanu suke muna kowa kallon mamaki yake min don ganin yadda gaba daya na sauya na koma,wata yar larabawa dani abu ga dana,asalin buzaye.
Mun samu a girka abinci kala kala wanda nasan aikin maryam ce haka na.
Ban lura da Anty Amira a falon ba sai da naji yace mata haba sweet sister ba ko gaisuwa ne ?
Sai lokacin na dago na dubi inda yake kallo tana zaune ta yi irin zaman dacta saba yi ta dunkule saman kujera sai chatting takeyi abinta.
Ashe tun shigowan mu ta daga kai ta kalle mu taji wani abu ya tsaya mata arai irin yadda gaba daya taga na koma wata matar manya ko diyar manya can dani sai kamshi da annuri ke tashi gare ni.
Gani cikin wani irin dogon riga kore yaji duwatsu tun daga sama har kasan shi hannayen rigan shara shara na yafa mayafin rigan a kaina ina rataye da jakka ja da takalma mai duwatsu kamar na rigan.
Ga yan uwan su sai haba haba sukeyi dani mu kamar sunga wata basarkiya can daban.
Haushi ya kumay ta tace wai wanan Bintun kauyen ne yau ta murje ta zama haka da ita kai kai maji why please maji taja wani dogon tsuki tamike tana fadin ita zata tafi gida ke nan.
Nace a,a haba Anty Amira yanzun nan da shigowan mu hatta hausana ya sake ba sakwatancin nan sosai a cikin shi .
Tace a,wulakance wani abun kuma zan tsaya nai maki bayan naga kun sauka lafiya ko so kike na tsaye ina,fadanci a kanki kuma ?

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYABA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKIN MU AKAN KI,,,
Maganan yaya yai matukar tsaya min araina nace a raina wanan kuma matsalar Allah yasan dalilin shi amma har yaushe ma mukai aure da za,a dinga damuna kan haihuwa hakane wai ?
Ban fito ba ina dakina don abin yadan damay ni a raina sai nake jin ba dadi a tare dani kawai.
Kira,an sheck Ahmad suluiman kano na saka a wayana shine yake tashi ina zaune ina bi a hankali nai makari da gadona ta baya kadan.
Dakin yashigo yana saye da doguwar rigar jallabiya a jikin shi yake ce min lafiya kike kuwa ?
Dan murmushi ne na kakaro a fuskana nace lafiyata kalau kawai dai sai naji nagaji ne.
Yace ok ni zanje gida naga baba nakuma yiwa maji barka daga can don yar gaban goshin ta ta haihu nasan tana can tana murna yau.
Nace ba dole ba duk wanda nashi yai ciki kuma ya sauka lafiya ai abin farin ciki ne haka sosai.
Nace adawo lafiya yace baza,a sayo komai ba ko idan nafita ?
Nace yaya ai akwai komai nake gani adai dawo lafiya muna gaida su kafin na shigo nima.
Koda yafita yaje gida bai samu komai ba sai bacin rai kawai don yasamu mama da Baba suna jidali akan Ahmad.
Wai yana zuwa duk abinda aka sayawa mama yana koshewa yakai gidan shi shi da matar shi mara kunya suci.
Yaya ya samu dakyat yaba Baba hakkuri sai cewa baba keyi idan saye yana da dadi shi ya dinga saya suna amfani dashi mana can.
Aishi yace yaji yagani ita yake so ga Imirana nan da lalacewan shi da komai yana fita yana samun nakan shi ai.
Amma shi sai darga da rikicin kayan mutane da yasawa ran shi yakeyi duk ya zubar min da mutunci ga mutanen arzikina.
Shine yau zuwa gurin wanan gobe yana gurin wancan yana bakin roko da yaudaran daya saka kan shi ciki.
Umma dake daki tace ai babu dan kwarai a gidan nan yanzu sai dan son ka don shine mai abin hannun shi.
Dama Atika aike butulu ce baki da godiyan Allah yanzu in ma don abin hannun shi ne ai tare dai dake muke cin komai ko ?
Yaya ya samu baba ya shiga dakin shi da kyata ya kwanta da murya yana bashi hakkuri sai faman fada yakeyi.
Yana cewa nai nadama da zama da matan a rayuwana ni nasan iya tsawon rayuwan da nayi suna,wahal dani suna cutar dani da sauran iyalina a gidan nan.
Bai dade ba gurin baba yafita zuwa gurin maji dake zaune falon ta duk abinda akeyi sunaji ita d Amira.
Ya gaisa da ita tare da mata barkan haihuwan maryam tace ni wanan gidan fitinan shi yana bani tsoro wallahi.
Kullun ba,a san an girma ba sai anyi jidali a tsakani kuma na rashin gaskiya.
Karo na farko maji taji yakira ta da mama yace mama hakkuri zakuyi kawai don kowa da irin halin da ke gare shi dashi kuma ake zama da mutum.
Nan dai suka dan taba hira kan zancen yadda gidan ya koma yanzu yace shi zai tafi don dare yayi a lokaci.
Ko da ya dawo ya samu nayi barci a lokacin ina kwance a dakin shi bai ta daniba shima ya kwanta sai da dare dana falka nagan shi kwance yana barci.
Da Asuba yafita zuwa masallaci nikuma na koma part dina nai sallah na kara nadewa a gado na nakoma barci don weekend ne yau.
Ya dawo daga masallacine ya samu wayan shi tana ringing a daki da sauri ya daga wayan mamace a layin take kiran shi.
A ranshi yace lafiya kuwa maji take kirana da safe haka ?
Ya dauki kiran da,sauri yana sallama yana fadin maji lafiya dai ko ?
Tace lafiya lau babana na idar da sallah ne nace bari na kiraka naji yaya jiya ka koma kafita da bacin rai a gidan.
Yace a ran shi Allah sarki maji ashe takwana tana tunanen shi ke nan tunda ta kurashi da safe haka.
Yace lafiya na isa mama tace nima ina zaune ne ina addua akanku Allah ya kara tsare min ku yabaku saukin rayuwa da haske ga,al,amarin ku.
Don na fahinci har yanzu su yaya basu san Allah ne mayin yadda yaso ba ga bayin shi.
Ya saki ajiyan zuciya yace mama ki kwantar da hankalin ki ai tunda basu iya komai damu muna kanana ba ko yanzun ma Allah bai basu sa,a .
Tace kaga kwanaki haka Alhaji sani yazo gidan nan yai min kaca kaca wai ni na hanaka hurda da kowa a cikin yan uwa sai yan uwana dana matanka kawai yanzun ka sani.
Don wai yaji labarin irin abin arzikin da kake tura masu a can kauyen su nan kabarsu hakana.
Kai maji ni har yaushe ma nakewa iyayyen Fatima ma,wani abu mutanen da ma nake matukar jin kunyan su sosai ban fako je ba tunda mukai aure.
Dasu da baba tsoho wallahi suna a raina ina son mu samu lokaci na ziyar ce su.
Baba tsohon da yake nufi mahaifin mama dake zaune a Niger state shi da sauran iyalin shi noma ya mayar dasu can sun zama yan kasa yanzu ko.
Yace amma zan ga baba sani din sai asamu abinda akai mai bashi ke nan ba.
Mama tace kaifa baka da zuciya babana duk wanan abinda sukai maka shi da su yaya maganan su fa daya ne
Yadan kwantar da murya yace maji kiyi hakkuri don Allah don kin ga akanki suke sauke haushin su ko yaushe don haka zan masu yadda yake so a zauna lafiya.
A hankali mamatace Allah yai maka albarka ya baka ikon kyautata masu ko yaushe.
Yace amin maji tace ina fatima yace ta koma barci yau weekend bata fita tace yana dakyau ta dan huta don nasan anjima kadan yau gidan maryam zasu dire.
Yace kaman ko kin sani mama aini dai yanzun nasan ni da samun kanta,sai sun gama bukin nan kan.
Tace kaima ka sani tsakanin maryam da Fatima ai sai Allah yace da yake muna fukai ne ba sun hade wa sister na kai su biyu.
Ba wani hadin kai halinta dai ne sai ita Amira tafita daban a cikin ku sai kace diyar umma.
Dariya tabashi cewan da tayi sai kace diyar umma take yace itama dai zatai auren ai ta huta da fadan kowa hakana.
Dadai yafi mata alheri taje kowa ma ya huta da bakin halin ta hakanan.
Suna gama wayan da mama sukai sallama kowa yana cikin farin ciki duk kan su.
****** ********* ******
Sai da nai barci na mai ista na tashi batare da ya tayar dani ba nata shi wanka na fada nafito ne ina zaune ina shafa mai ya shigo dakin.
Shima yai wanka don a shirye yake a lokacin idanuwan shi a kaina yace ashe barcin ba mai nisa bane inace ko sai biyu zaki tashi.
Nace cikin murmushi da yau anty maryam ta yankani ai tun fa safe take kirana a waya.
Sai da na shirya duk yana zaune a bakin gadona yana dakilar wayan shi tsab na gama nace mashi nashirya yaya.
Yadago kai yana kallona yace au yaune zakuyi bukin ke nan da sauri na,ware idanuwana nace yau kuma yaya ?
Yace to wanan uban kwalliyan haka dana ga kinyi aina dauka zumudi zai sa kuyi shagalin bukin ne yau ?
Yamike yana cewa ni dai yanzun nasan ba a da time dina sai dai yadda Allah yayi dani kawai.
Nace haba dai yaya yanzun ne ma fa zan bar gida to eleven fa yanzu ake nema kamata yayi ace ina gidan tun bakwai ai.
Eh tunda gaki ungwazoma ba sai kije bakwai kiwa jariri da uwar shi wanka ko.
Dariya nayi kawai nace tau ni fa ai yanzun komai zanji amma bazanyi fushi ba tunda ina son abar ni na tafi.
Shi yajamu zuwa gidan ya sauke mu a kofan gidan ni da iya don maryam tana dakin ta bata koma gida ba.
Uwar mijin ta daine tadawo gidan nasu da zama inda yake zaine na dan kalla tare da gyara tsayin mayafina don gyale na saka yau nace sai mun dawo ke nan yace four zan dawo na dauke ku fa.
Kaina na langabe nace haba yaya four fa inace ko sai magariba yace idan kika bata min rai wallahi yanzun zaki shiga ki fito mu wuce nace da sauri iam sorry sir don nasan karamin aikin shine hakan.
Ko don ya batawa maryam din rai na bude mota zanfita naji yace ban son fitina fa da kowa kuyi lafiya a watse lafiya nace insha Allahu yaya.
Nafita ina cewa mun gode sai ka dawo yaja mota yanajin dadi komai kankantan abu sai nayi godiya akan shi.
Ya furta a fili simple life .
Muna shiga gidan tun a kofa muke jin hayaniyan mutane yan uwan yaya bashar sun cika gida sai surutu sukeyi.
Nai sallama iya tana bayana nagaidasu ina fadin to abani ruwan zafin ajuyo nai mata wanka duk aka kwashe da dariya.
Inna dake gefe tana gasa jariri tace hai Fatima kwana nawa ance ma maye ga nama.
Daga daki maryam ke fadin ki koma ban so tunda bakiyi farin ciki da zuwan baby naki ba sai yanzun ne zaki zowa mutane.
Na daga labulen daki tana zaune da cup din kunun kanwa a gaban ta sai zufa takeyi tako ina nace bura uban nan wani abu ko sai haihuwa wallahi anty kece haka kace kace cikin zafi.
Na zauna saman gado ina cewa wayyo Allah na wallahi duk na gaji sai kace nice na haihu wallahi.
Ta kurba kunun tare da lumshe idon ta tace da waye ya haihun bake ba ni sunan nai cikine kawai ai dan nakine.
Nace kada ki sa na gudu dashi fa yau gidan mu tace aida yayan ki ya tare maku a gida kinko ga jiya da kyat inna ta samu yatafi ya kwanta ya barmu wai shi anan zai kwana nace Allah yabaku maryam.
Ke da yaya wallahi kuna sha,anin ku harara ta kara watso min tace kunan daban ne Bintu ?
Tace wai da sauri na manta ina gadon asibiti ma nace Bintu ance za,a balbalani balle yanzu ina dakina zaune.
Wanan dan rikici halin shi sai shi wallahi yanzun ma cewa yayi wallahi idan nai tsiya dani dake yanzun zamu shiga mu fito tace dako na hada shi da maji wallahi.
Nace kina hada shi da ita nabi mijina don ban son fadan nan dakike sa ana mashi ko yaushe.
La la la Bintu ni kike fadawa haka yau kan yaya eh lalai kan mage yaji gishiri kuwa.
Waya na jawo na fara dan dana nomba sai ko naji ya dauko yana fadin hello na,shake muryana nace yaya love kaji anty maryam tana ce min Bintun daka hana ko.
Ya ko hau fada maryam wallahi zan zo na balbalaki tace iyye watau karana kika kai ma ke nan lalai Bintu wai Fatima wuyan ki yai kauri ashe.
Nace sorry yaya ta gyara yanzu tace Fatima din kayi mata hakkuri tsuki yaja yace mashiririta kawai kuka sani nace asauka lafiya na kashe wayan.
Tace yar iska ke dai kin kirashi da,wayyo kiji muryan shi kawai ba,wani kai karana da kikayi.
Indai yayane wallahi naga take taken shi yarinyar har tausayi kike bani don nasan baki da hutu.
Nace abu cikin duhu sirine ne tace kwarai kuwa nayarda sirine don nagani yanzu a zahiri.
Sai lokacin Iyyan Rabi ta leko dakin tana gaida maryam din na tuna nace Allah sarki iyya na manta fa kina waje kiyi hakkuri kinji.
Muna nan dakin sai hira mukeyi shigowan matan yaya Imirana dakin shine yasa muka kwasa muka yo waje can sai ga wasu yan school din mu da suka kare da ita sun shigo.
Wasa wasa gida ya fara cika iya ta mike zuwa inda ake aiki takama masu aiki.
Shigowan matar yaya Ahmad tanbele ya tashi sai hira take muna ana kwasan dariya wanda hiran nata duk kusan batsa take yi wai ita hira ke nan.
Sai ga Umma da mama sun shigo barka da wata kawar mama makwabciyar mu nan muka shiga gaidasu sai dai yadda Jamila matar yaya Ahmed tayi masu banji dadi ba.
Don ta nuna rashin da,a sosai a gare su kamar bata san sune ba abin duk ya bamu mamaki ganin su baisa ta fasa abinda takeyi ba sai ma ci gaba datayi da abinda takeyi.
Basu dade ba sukai sallama suka tafi har kofa muka rako su ni da matar yaya Imirana Hadiza wace ke da dan matashin ciki yanzu.
Gani bai sa umma ta fasa fadin abinda tai niya ba don cewa tayiwa Hadiza ki yi haraman komawa gidan ki don banga abinda kukai wani taruwa nan kunayi ba kamar haihuwan gidan sarki.
Tace ai shine zai zo ya dauke ni yace tace to kindai ji na fada maki ki maza ki koma gidan ki ban son irin shige shigen nan.
Sai da muka dawo cikine take cewa sai mutum nason ya shigo yan uwan shi amma aita hanashi .
Jamila tace walleh ke an nan nikan anso akawo min wanan control din amma tuni na wuce gurin don ban yarda uwar miji ta hanani shakat.
Hadiza tace nikan sai lokacin da yazo zan tafi mutum yana cikin yan uwa yana dan walawan shi amma sai duk a takura maka.
Jamila takara cewa yanzun dadafa ke akaji inda tsofin gana walleh har yanzu su kishi sukai harda diyan su kosu kegane su kaman kan su a hade walleh cin kan su suke tsakanin su.
Kowa gulman dan uwane yakai idan daya baya kusa ni jiranakai watarana su shiga gonana nai masu tas wallahi.
Nidai da maryam bamuyi magana ba muna jin su don da mun tanka namu ne zai fita nasu ya boye.
Nan dai muka wuni anata faman shiririta irin na matasan mata idan sun hadu zallansu.
Sai naji ranan naji dadin haduwan mu haka saboda bamu taba haduwa haka ba tsakanin mu sai bayan sallah la,asar muka fara watsewa daya bayan daya nikan yaya yai min halarci sai yamma lis yazi daukan mu muka koma gida.
Yace ma Iyya kada ta damu kanta da zancen girki zai sawo abinda za,aci da dare.
A gajiye nake don kai da komon da mukayi a gidan maryam wanka nayi nai sallah muka fito falo yana dawowa shima wanka yayi yafita gidan.
Nan muka zauna da iyya muna hira tsakanin mu tana bani labari akan matar yaya Ahmed bata da mutunci ko kadan bama wanda ya zaci har zasu kai wanan lokacin dashi ai.
Iyya ta dan tausa muryan ta kamar wani na jin mu tace ke irin su Nafisan Umma ta fa duk harkan su guda.
Nace Allah mai iko watau kowa dai Allah ya bashi a dakin shi ke nan ba mai fadawa wani kuma.
****** ********* ******
Sannu sannu suna yana matsowa sai shirye shiryen bukin suna akeyi inda yaya sadauki yaiwa maryam duk wani nauyi da iyayye suke dauka na yar su.
Nice mama tasa a gaba akan na auwatar da komai daya dace da shirin sunan.
Haka yasa ban zaunu ba don ma na samu iyya tana da kokari itace na samu take yawancin zirga zirgan na komai a gidan.
Komai mun hada Alhamdullahi ranan suna yaro yaci sunan mahaifin uban shi wanda dama tun kafin suna Inna ke kiran shi da Alhaji karami.
Cikin yan uwan Inna da sukazo ne nazo zan wuce naji wata na fadin wai ba Fatima bane nan najuyo na kalli matar naga kamar na san ta.
Sai dai nace mata nice batare dana gane ko wacece ba sai cewa tayi halan baki ganeni ba dai ko nace gaskiya ban gane ki ba.
Tace Asmau matar marigayi Kabir da kika tashi aure nace Allah sarki ankoyi haka wallahi.
Nan na tsaya muka gaisa da ita na tambaye ta yaran ta tace sunan lafiya sun girma yanzu suna makaranta.
Tace min ai tayi sabon aure ta auri wani miji amma dan sanda ne tana nan cikin gari yanzu.
Nace ina anty tace itama tayi aure anan gari tana auren wani malamin yan izala masu da,awa tana zaune a arkilla ne.
Nan nakawo mata abubuwan abinci dana buki na karamata sosai takuma ji dadin haka tace nai mata kwatancen gida na zata zo.
Nawuce ina tunanen duniya matar da da take jin kan ta wani abu yau itace takoma haka kai duniya abin tsoro ne wallahi Allah dai yasa mu gama da duniya lafiya kawai.
Anci ansha maijego tafito yadda ya dace duk
wanan abin da mukeyi zakace Amira ba yar uwar maryam bace tana tsabare abinta ita dai haka Allah yayi ta kawai nake gani.
Munyi photuna sai da mutane da sukazo sunan inda aka hada walima wata malama tai wa,azi akan hakin iyayye ga yayan su dakuma hakkin diya ga iyayyen su.
An raba gift na robobi da yan wasu kayan sha taro ya,watse lafiya akabar mu mu zalla yan gida da dare bayan na idar da sallah maryam tana zaune tana shayar da yaron ta na kura mata ido ina tunane.
Tana tambaya ko an aikawa makwabtanta da abinci gidajen su banji may take fadi ba sai da take ce min wai may kike tunane ne haka Fatima ?
Na lumshe idanuwana nai murmushi tare da sauke ajiyan zuciya nace wallahi ba komai anty tace ba komai kike zurfin tunane haka.
Nace maryam yaya ya fara min zancen haihuwa fa tace to may ye abin damuwan kai ciki.
Ya baki mana yagani in baki dauka ba wayasani ko lefin shine banaki ba kadama ki damu kan ki da wanan har yaushe akai auren da za,a fara wanan magana haka.
Ba kowa ya zuga shi ba nasan Nafisa ce tun ranan naji tana ce mai wai ita yanzun baby din shi kawai take jira suzo don ita sune yaran ta.
Kuma nasan tana fada mai hakane kawai don ya maryar da hankalin shi ga zancen.
Idan ma yai maki magana kice mashi yabaki aiba kece zakiba kanki bako ?
Maganan ta yai min dadi sai da na shirya mata komai sanan na kirashi yazo ya dauke ni tace na dauki duk abinda nake so daga cikin abinda ta samu.
Dariya nayi nace haba dai anty aiko da ban gode ma Allah ba yanzun haka fa ina da turamay sunkai ashirin da ban dinka ba aje.
Tace kaji masuyi don jallah inda nice ai ban iya ganin turumi ban din ka ba tace da tuni nagama dasu.
Na dan bata rai nace kin san halin yaya shifa yafi son ko yaushe ya sayo min dogayen riguna irin na kasashe da yake zuwa kuma yafin yaga na sasu.
Tace kuma wallahi suna maki matukar kyau ko dazun naji wasu na gulman ki ai wai duk shigan da kikayi kamar kece kika halicci kanki.
Nace kai kaji mutane da gulma kuma ina ruwan su dani tace wallahi Fatima kin dace da Allah yasa yaya yazama mijin ki da bakece matar shi ba da sai dai muyi taganin abu a gidan wasu.
Allah yana da hikima da basira kila dalilin hakane ya jefo rayuwan ki a cikin mu fa?
Nai murmushi nace sanin gaibu sai lillahi anty amma gaskiya yaya baida matsalan komai inba wanan shan ba kuma yanzu sai nake gani kamar yama daina yi.
Mun ware turame wasu umma da Inna harda iyyya Rabi saida maryam tace aba turmi daga ciki da kannen mijinta su sahura su biyu.
Sai goma yazo ya dauke ni muka bar gida zuwa namu gidan kowan mu har iya duk mun gaji a lokacin.
Wanka mukayi don kowa a koshe yake sai kwanciya ba school yasa na kwanta washe gari bamu fito ba sai after eleven muka fito daga daki kowa agajiye yake.
Nan muke falo ranan bai fita zuwa ko ina ba sai dai wayan da yake ta faman bugawa kawai.
****** ********* ******
Ranan bayan suna da kamar sati biyu wanda bai zaunu ba don ginan sabon site din su da akeyi ya mayar da hankali sosai ga aiki.
Ya dawo da la,asar don ya huta yace yabajin kan shi na mashi balain sarawa a lokacin.
Sai wayan shi yai kara Baba sani naji yace yadauka suka gaisa dashi baba din ke fadin yana son ganin shi da dare anjima ya amsa da to Baba ina nan zuwa insha Allahu.
Magani na kawo mashi cikin wani dan karamin plate da ruwa a cup ya hadiye maganin.
Can naji yaja tsuki yana fadin ko kuma yau mai baba Sani ya samu yake nemana a gidan shi.
Mutumin da abaya ya tsane ni kamar may ko gidan shi cewa yayi bai son yana gani na,shida baba Shaibu ni tun lokacin suka fita raina wallahi.
Zancen auren Raiya ne ma da baba ya matsa lokacin sai anyi yasa nake dan zuwa kada ran shi yabaci idan yaji banzuwa.
Amma haka idan naje kiranta zasu yi tamin wullakanci yara da samarin gidan suna cewa ga dan wiwi din nan yazo.
Na dan yi murmushi don nasan cikin bacin rai yake magana nace ba babanka bane yaya duk abinda sukayi ai don kan su wallahi.
Kadai je kaji may yake neman ka dashi yafi kada yace kuma yakiraka kaki zuwa kiran nashi.
Yace ai zan tafi naji may yake nemana dashi kuma ne wai kwanaki fa da haihuwan na na maryam sai da maji tasani gaba na basu yan kudade duk kan su har gwagwanin mu.
Nace Allah ya saka da,alheri ai duk yiwa kaine hakan ma.
Sai da yai sallah ishai ya shirya cikin wani shadda mai ruwan maku dinkin garen hannu haka ma rigar iya cinya akayi mai shi, ya nufi gidan baba sani ban kawo komai ba tun da kanin mahaifin shi ne.
Yana isa ya buga waya yace gashi kofan gida ya iso baba yace ya iso mana yashigo yana falo zaune.
Yasamay shi zaune tare da matar shi ya gama cin abinci suka gaisa duk cikin kyankyamin yadda falon ya koma yake.
Ya tambaye shi harko ki shi da matar shi yace duk Alhamdullahi.
Can baba yace dama ba wani abu bane yasa na kira sai akan zancen ka da yar uwar ka Raiya ne naga gara kawai ace anyi abin nan tunda dai ita ba wai auren tayi ta kuma gama karatun ta bana.
Dama dai can kuna son junan ku dan matsalane aka samu na munafunci ya shiga tsakani.
Ba karamin mamaki Sadauki yaji ba yadda baba yau ya murje idon shi ya iya mai wanan magana.
Ya manta yadda yaci wa mahaufin shi fuska yana kirarin wai zai bawa yar shi mashayi dan wiwi dan giya.
Ya kuma tuna Irin halin da maji tashiga a lokacin irin cin fuskan da akayi mashi kan wanan auren hadin da akaso yi bayan tun Raiya tana karama duk sallah sai ankai mata kayan toshi.
Itama kanta Raiya din sai da taci mai fuska daya buga mata waya lokacin da yaji labarin sai ce mashi tayi.
In aure ka in kaika ina kama big girl ace na tsaya auren wani mashayi wanda baida aikin yi sai shaye shayen tsiya kada ka kara kirana daga yau na fada maka .
Yana tuno haka ya dago kai yai murmushi yacd Baba naji abinda kace amma na farko kasan nayi aure ko.
Nabiyu kuma ita Raiya fa ta bude bakinta tace min bata sona bata kaunana idan na haihu cikin maji kada na kara kiranta.
Don haka Baba don Allah abar zancen da yawuce yawuce kawai Allah ya bata mafi alheri a gareta ni yayan ta har gobe najini zanyi duk wani abinda duk wani yaya yakewa kaunar shi.
Mama suwaiba tace haba Umar ai kasan halin yarinta har nawa Raiya take hakkuri zakayi tunda kuna son juna.
Yamike yana cewa gaskiya Baba abar wanan zancen ba zai yuyu ba tun da tun farko an fara shi da tsegumi masuyi kuma ba fasawa sukayi ba.
Baba yace dakai da Raiya duk daya kuke a gare ni don haka ina da ikon yin komai akan ku murmushi kawai yai masu yace shi zai koma ayi hakkuri.
Raiya da yan uwan ta suna labe sunajin yadda akayi sukace kingani kin wa kanki tace aiko yaki ko yaso sai na shiga gidan nan wallahi koda tsiya ne.
Jifa irin kafirar motar da ranan mukaga matar shi naja dayan tace kice dai ta koma kamar diyar wani presedent da ita.
Dan iska kudi yake samu har na tsiya wallahi ba ance albashin su ma,wai yafi na wasu gwaunoni ba kudi.

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKIN MU AKAN KI
Tukin mota yake yana tunanen wanan hali na Baba sani wanda ya rasa gane kan shi.
Son kaine ko kuwa rashin tunanen may yadace ne don yai matukar jin wanan magana daga bakin Baba Sani din.
Ko da ya iso gida ya samu har nayi barci ko shima sai da ya gama duk abinda zaiyi ya hawo gadon ya kwanta.
Inda nake kwance ina barci ne ya kalla kamar ya tayar dani sai kuma ya fasa ya dan kura min ido yana kallon yadda nake barcina a tsanake.
Tausayi yaji na bashi yasan dani da iyayyena sun mai komai yadda suka dauke ni suka bashi .
Bayan nashi jinin sun kyamace shi sun ki shi saboda halaiyan shi da sukace baida kyau.
Amma kuma shine yau kuma da ake ganin kamar ya zama wani abin kwarai zasu dawo suce wai dashi zasuyi.
Kai wai mutanen duniya ne suka lalace koko duniyan ce ta lalace haka da kan ta.
Yanzu shi Baba Sani har ya manta da cin fuskan da sukaiwa mahaifin shi shi da matar shi ne da zasu dawo suce shi ne kuma suke son ya auri yar su ko may ?
Da kyat dai ya samu har barci ya dauke shi yana cikin tunanen irin halin Baba sani da wasu mutanen da basu san kunya ba.
Da safe koda muka tashi ganin shi nayi kamar wanda baijin dadi don yau ko fita judging bai samu yi ba na safe.
Har nai wanka na shirya nafito naji shi shiru a daki na nufi dakin nashi na leka shi.
Yana kwance a saman gadon shi ya kifa cikin shi alaman motsin da naga yanayine yasa na gane ba barci yakeyi ba a lokacin.
Na nufi bakin gadon nashi ina fadin ina kwana yaya love?
Sai lokacin ya dan dago kai ya juyo gare ni har na kawo bakin gadon na dan zauna daga gefe tare da tokaro hannu na daya ta baya saman katifa na sa shi a tsakiya.
Yace yaya dare naga jiya kin samu barci sosai baki ma san dawowa na ba.
Murmushi nayi tare da dan dukar da kaina daidai saitin fuskan shi nace nima wallahi ban san yadda akayi har nai barci ba haka da wuri daga fa wai na dan jiraka kadawo shine barci mai nauyi ya dauke ni hakana.
Nace tashi kai wanka ka karya yaya yace ki tayar dani to duk banjin dadin jikin nan nawa yau.
Da sauri nace subbahanallahi yaya may ya samay ka kuma maimakon yabani amsa sai ya jawoni zuwa jikin shi yana sauke numfashi a hankali.
Can naji yace Fatima na amsa na,am yaya yace tunda kun samu hutu sai ki shirya nakai ki kiga su mama duk da ba haka naso mu tafi masu ba don akwai dan planing din da nake son yi a kan su.
Wani irin sanyi naji ya sauka min a raina ina fatan zaki je ki dawo batare da wani matsala ba dai.
Nai maza nace mashi matsalan may kuma yaya bayan gida na tafi gurin su mama.
Yace to fada min inji da kanki kwana nawa zakiyi a can idan kin tafi don inji ko kina da adalci .
Shiru nayi ina nazari nace nace ko nace sati uku don na samu na zagaye dangi da yan uwa da abokan arziki.
Sai kuma nai tunane ko a gidan baza su amince min nan da Rabah nai wanan kwanakin ba haka.
Amma a fili cewa nayi ko kwana nawa kace nayi ai zanyi ne na dawo , yadan shafo fuskana da hannun shi yace.
Ai ni nace ki fada don idan kin wuce nima zan tafi ghana ne akwai kayana da suka makale a can nake son zuwa na duba su.
Don haka ki fada naji sai dai kada ki manta duk hukuncin da zakiyi a tsakani na dake na rokeki kar ki so kanki a kaina da yawa kiyi tsakani da Allah.
Dariya maganan shi tabani don yasan na dade ina binshi kan ina son zuwa gida na duba su Baba amma ya hanani zuwa.
Yace No na san kin sani bayau ba kike min zancen zuwa gida ina basar dake kada yanzu kiji nace ki zaba kimin rashin adalci.
Kin san dai ina son ki Fatima kuma ko ban furta maki ba ke kin sani don kinga alama yafi a kirga.
Don haka ina kara jaddada maki ina matukar sonki a rayuwana Fatima fiye da duk yadda zaki tsammani gaba daya fatana da buri na shine bai wuce na nuna maki ba a kullun irin halarcin da kikai min ba.
Nace yau kuma duk may ya kawo hakan ne don zancen tafiya gidan ne ko dai baka da sha,awan ina raban iyayyena ne yaya ?
Yayi murmushi yace haba haba subbahanallahi ko daya wallahi bandai son kiyi nisa danine ko kadan yanzu Fatima.
Nace to nayi sati daya idan na tafi ko ?
Naji yayi murmushi tare da dago kai ya kalleni yace har sati Fatima sati daya fa kika ce.?
Nace a hankali to ka rage yaya idan yayi yawa ne, yace zaki iya yin kwana biyar ko nasan zai ishe ki kiyi duk abinda kike sonnyi can.
Nace to na gode yaya nagode yaji dadin hakan yana mikewa zaune na gyara mashi ya zauna da kyau.
Yace sai ki fara shiri don ni na gama maki shirin tafiya ko gobe insha Allahu zan kaiku ke da musa idan kuma iyya Rabi tana son tabiki ne sai ku tafi tare idan bazata ba sai ta tafi gida har ki dawo a rufe gidan.
Murna da dadin jin gobe zan tafi gida duk ya cika min zuciyata ina matukar kewan mahaifiya ta dana dade ban gan ta ba ya cikani.
Yace ni in nai wanka zan fita zuwa gida sai na fadawa mamanki zaki gida gobe goben idan mun shirya zamu wuce sai na biya dake ki sallamayta.
Nace nagode nagode yaya ya mike yana kokarin shiga bathroom don yai wanka.
Na juya zuwa dakina sai ma dadi ya kasa barina nasan may zanyi akai lokacin.
Wardrobe dina na bude tare da jawo troler dina na fara zaban kaysn da zan tafi dasu.
Idona yakai ga kan atamfofina da suke ajere ban faye amfani dasu ba nan nashiga zabo masu saukin dinkin da nasan mamana zata iya sawa na tara a gefe na.
Wanda nai yan matanci dasu kuma na jawo wani ghana most go na loda a aciki inkai a rabawa mutane shi.
Inda turamay suke na bude akwatin na fitar da wasu masu kyau suma na tara guri daya.
Ina tsaka ga aikin ne ya shigo dakin tare da bin kayan da kallo yace duk wa yan nan kayan fa haka ?
Ba dai duk na tafiyan bane sai nai mashi bayanin manufa ta dasu yai yar murmushi ya karaso inda nake a zaune saman godo yace No bazaki kai wa maman mu tsofin kaya ba Fatima ki bari a sayo mata nata kawai da zaki mata dasu idan nafita ban mashi musu ba sai nuna farin cikina da nayi.
Da zai fita ne yake cewa sai kiwa Iyya magana muji ko may ye ra,ayin ta ita kuma ga tafiyan.
Nace ok yanzu zan fita naje gurin ta naji yadda za,ayi akai.
Yana fita na samu iya a kitchen nake fada mata yadda mukayi da yaya din da kuma tambayanta may ta yake shawara akai.
Tace haba uwar daki na idan ma na zauna a garin may zanyi ai kafarki kafata tare zamu tafi dake nace Iyya na gode da wanan karamcin da kikai min.
Itama nan ta fara shirin tafiya na bata atafofi guda uku masu kyau tana ta godiya da jin dadi.
Tunda yaya ya fita gidan da safe bai dawo ba nima a cikin zumudi na wuni.
Ya shiga gidan su ya gaida mutanen gidan yadawo gurin mama suka gaisa da ita.
Yace bayan sunyi dan shiru gobe ne nake son Fatima ta tafi gida ta duba su insha Allahu.
Cikin mamaki mama tace gobe goben nan dai shine bamu da labari kan tafiyan sai yanzu zamu ji may kake so na hada mata na zuwa gida a matsayinta na karon farko kenan da zata ganin su.
Yace nima jiya ne naji ya kamata su tafidon dan hutun da suka samu din nan sai taje ta gan su ai ba dadewa zatayi ba,kwana biyar zasuyi ta dawo.
Baka dai kyauta min ba kama yayi naji da,wuri na dan hada mata tsaraba taje dashi mana.
Yace ai babu komai maji za,ayi abinda ya dace ayi kafin su wuce din nima zanyi tafiya zuwa ghana inshs Allahu.
Sai dan shiru bayan tai mai adduan Allah yakai lafiya a dawo lafiya da tace mai.
Lafiya kake kuwa yai dan murmushi yace lafiya nake maji tace naga kamar kana da damuwa a ranka yace ba komai maji.
Can yace Baba Sani bai zo gidan nan ba gurin Baba ?
May kuma ya faru mama ta tambaye shi da sauri yace jiya ya kirani da dare naje gidan shi.
Shine yafito min da zancen wai yana son a tayar da zancen aure na da Rahama.
Da sauri mama tace ba zai yuyu ba wallahi ko alama.
Shi yanzu baiji kunya ba da har zai fito maka da wanan zancen yanzu don yaga Allah ya mayar da kai mutum ko ?
May yasa mutane basu da ta idone wai haka ?
Idan ma kai ka yarda ni wallahi ban yarda ba da wanan zancen ko alama hakan ma ai tatsuniya ne.
Yanzu ko da yaga Allah ya daukaka shine har ya manta da irin cin mutuncin da sukai muna ya kalli idon Alhaji yace ba zai aura wa yar shi mashayi ba.
Kaje duniya tana da yawa ka samu irin ka yar shaye shaye ka aura shi yafi ma.
Shine yanzun don baida kunya zaice wai wani a tayar da zance to nima yanzun nace ban yarda ba duk abinda zaiyi yaje yayi amma wallahi baka auren Rahama.
Wa yanda sukaje suka bata ka garesu ai suna da diya yaje ya aura masu ita mana.
Wai ko akan zancen kake son tura Fatima gidane wai ?
Yace wallahi mama ban son Fatima ma tasan da wanan zancen shi yasa nace zan tura ta tafi ni kuma sai na tafi bashi ke nan ba.
Idan Fatima ta samu wanan labarin nasan akwai rikci sosai a tsakanin na da ita wallahi.
Bata ma komai amma baza,ayi ba na fada maka yace nima maji yanzu ba ida zan kai Rahama kuma don ta fita raina kwatakwata wallahi.
Don dai ka fadawa Fatima zancen tafiyan ne wallahi da ba inda zaku shi din may wai da har zaka gujeshi ?
Idan ma kun tafi ai dawowa zakuyi dole tunda ba inda zaku sai gida tun wuri zan ma Alhaji magana kada ma a soma zancen.
Nan dai sukai ta maganan yafito tare da mata sallama akan gobe zai kawo ni nai masu sallama kafin mu wuce.
****** ********* ******
Sai bayan la,asar ya shigo gidan yace kun shirya dai ko?
Nace mashi eh tafiya kawai ya rage muna gobe insha Allahu.
Yace kunyi magana da Iyya din ko ?
Nace eh tace tare zamu tafi da ita sai yai dan murmushi yace dama nasan bazata zauna ba ai.
Yace komai an shirya don na dan yi maki tsaraba sai dai basu da yawa sosai suna a cikin motan da zamu tafi dashi akwai kaya nanan na Baba ne sai wanda zaki kaiwa mama din.
Idan na kaiku na dawo Hamza zai samay ku can da motan da zakiyi amfani da ita har ku dawo.
Nace na gode yaya Allah ya kara daukaka ai mai yawa ke nan don kai baka kyauta kadan nasani.
Yace min karbi wanan ki saka a kayan ki idan kinje ki zauna da mama kuyi magana ki samu wanda ya dace kiba da aikin gidan su a fitar mata da plan yadda take so idan bai isa ba sai muyi waya a karo maku.
Ban san lokacin da nace yaya na ina son ka ba wallahi ban ma san bakin da zan maka godiyan hakan ba.
Yai murmushi ya kamoni zuwa jikin shi yana cewa wani godiya zakiyi min bayan yau ki barni nayi na ban kwana kwana biyar aiba wasa bane.
Nai dariya nace kai yaya kai baka da magana sai na wanan zancen kawai yace a,a toke in banda abiki ina dan kwallo inbayi wanan ba may zanyi tunda ina jin lafiya ajikina.
Nan dai ya zauna bai kara fita ba muna ta shiririta a gida sai zuwa yamma ne naji baba sani ya kirashi a waya.
Nai mamaki danaga ya mike zuwa dakin shi amma abin da da mahaifi nasan kila wani maganan siri ne zasuyi sai da,ya shige ne naga ya bar A T M din shi a falo na dauka nabi shi ina shiga dakin naji yana fadin.
Kada kaga laifin maji baba na fada maka tun jiya bazai yuyu ba taje Allah ya ,,,,
Sai gani ina nuna mai katin daya bari a falo din yace sorrya tare da mika min hannu na bashi na mika mai na juya nabar dakin.
Bai fito ba sai da magariba yafita zuwa maslaci yai sallah nima ina daki naji fitan shi .
Hakama da dare muna tare sai hira,akeyi yana waya yana fadin gobe insha Allahu tafiya zai yi zuwa waje.
Har dare yayi muka kwanta ranan kamar ba zamu sake haduwa ba again sai da ya gaji don kan shi ya barni.
Da safe bayan mun karya akafita muna da kayan mu zuwa waje aka loda su a cikin mota.
Kwalliya sosai mukayi daga ni har shi har su iya da zasu rakani ita da musa na.
Sai bayan nafito ne naga ashe da mota biyu zamuyi tafiyan danashi da hilux din shi sabuwa dal da ita.
Dani dashi da iya da musa a mota daya sai wancan dayan motan dake da kaya naga mutum biyu muka gaisa dasu naiwa su maigadi sallama muka kama hanya.
Kafin mu isa gidan su mama ne na kira maryam ina fada mata zancen tafiyan don jiya zumudi ya hana nakirata.
Ainan ta hauni da masifa inda take shiga ba nan take fita ba sai dai hakkuri kawai nake bata.
A gidan su mama ma tayi nata korafin na samu ta hada min nata tsaraban su sabulu man shafa clean parket parket tace na rabawa mutane mukai mata godiya nafito na sallami sauran mutanen gida.
Mummy takawo turare mai kyau da,tsada tace nakaiwa babana turmi naba mama.
Nai godiya mukai sallama muka kama hanya mun dan sha kwanan kadan dagida ya jawo hand bag dina dana aje a gefena ya ciro kudu masu yawa ya zuba aciki wanda ban san ko nawa bane a lokacin.
Ya mikowa Iyya da musa yan dari bibiyu yace su rika acan ko saga abin saye su saye.
Tuki yake a hankali bai wani irin sharara gudun nan da ya taba yi da mu ba a baya daya taba zuwa ya dauko ni ba.
Nakalle shi naga yadda yake tuki a tsanake naji dadi araina ganin irin natsuwan da yake ciki a yanzu.
Gashi mutum mai cikakken halita ga iya kwaliya da tsabta ga kwarjin shi ya kara fitowa a fili sosai.
A hankali na lumshe idanuwana tare da mayar da kaina kan seat din motar ina sauke ajiyan zuciya.
Bai juyo ya kalle ni ba sai cewa yayi yaya akayi ne yan mata ?
Nadan bude idanuwana a hankali tare da dan sauke numfashi again nace babu komai.
Na dai kalli irin haduwan mijina ne da Allah ya mallaka min shi a matsayin uban yayana nan gaba.
Watarana insha Allahu idan zamu irin tafiyan ga killa a full family zamu tafi da yaran mu.
Shiru yayi sai dan murmushin da yayi kawai yace hummm a fili .
Can naji cikina yana murdawa zuciyana yana tashi take na tuna idan na shiga mota amai nakeyi dama.
Aiko nan dana amai yazo min da sauri na jawo leda a jakata na fara amai.
A rude yaya yace ko na tsaya ne wai cikin karfin hali nace mai mu tafi babu komai zai tsaya.
Sosai nai amman sai da Iyya ta miko min goro tace na saka a bakina sai naji aman ya dan tsaya min.
Sai dai jikina da yai dan nauyi a lokacin kaina yana sara min sosai kamar zai tsage min a lokacin.
Tafiya mukeyi ba wanda ya kara magana a cikin mu sai tunane nakeyi cikin al,amarin aure na dashi kawai.
Auren da daga farko kowa ke hango min zaman ukubar da zanyi a gidan shi wanda nima kaina nasan zaman ukubane kawai zanyi a lokacin.
Tunane nayi sosai irin yadda Allah da ikon shi yau gashi ya mayar da,sadauki wani kamilin mutum bawan Allah wanda kowa ke sha,awan zama irin shi a rayuwa.
Yau dubi irin abin arziki da ya labto min nakai wa iyayyena duka a gidan mu da yan uwana.
Aman ya kara yunkuro min na danyi kadan nakoma na kwanta saman kujera sai faman sannu yake min yace wai kodai mu koma ne a fasa tafiyan nan ?
Nace da sauri haba yaya kayi hakkuri please mu tafi ai zai tsaya min nakoma na kwanta naci gaba da tunane na danakeyi akan shi.
Gaskiya yau sadauki ya gwada min shi din na miji ne cikakke mafi darajan mutum da nake ji dashi a zuciyata da ruhina.
Nasihan mahaifiya ta ne lokacin da zamu rabu ya fado min a,raina yau gashi maganan ta dutse hasashen mama ya zama gaskiya ke nan.
Muryan shi ce ta katse ni da yake cewa idan kinje ne zaki zo da yarinyar da kikace din .
Da sauri na juyo ina kallon shi nace wa Sa,ade ?
Yace sunan ta ke nan ko ?
Nace to ai ban fadawa mama ba kafin na wuto kada ta ganni da yarinya haka kawai ga kuma musa already a guri na.
Yace ina ruwan maji may zasuyi mata tunda ba,a gida daya muke dasu ba.
Nace to sau naje naji yadda zamuyi da mama din akan magana zan buga na fada maka komai.
Yace gurin mama ke nan yau zaku fara sauka ko?
Nace haka nake so muyi kwana uku sai mu dawo gurin baba mu karasa kwana biyun mu kafin mu dawo.
Haka muka karasa tafiyan ina jigibce sai faman sannu kawai suke tayi min dukan su.
****** ********* ******
Mun isa gida lafiya nan mutane ke bin motan da kallo suga gidan da za,a sauka sai kofan gidan mijin mamana muka tsaya.
Abin mamaki sai gashi yana ganin mu ya fara murna da fara,a hardashi ake shigo da kaya daga cikin gida.
Dakin mama muks shiga gaba dayan mu har yaya sadauki din da Iyya data rakoni.
Mama farin ciki ganin mu duk ya kashe ta ta rasa inda zata saka mu don ganin bazata ne tai muna a lokacin.
Mijin mama duk ya rude sai cewa yakeyi kai musa je wajen Isa mai shago kasamo maku ruwan sanyi.
Yaya ce No abarshi kawai ai da ruwa ma a motan sai bin gidan yaya yake da kallo yana tunanen yadda zan yi kwanaki acikin wanan irin gidan haka ?
Yadago ya kalleni yaga ni sai masha,ana nakeyi kawai ba abinda ya damay ni da komai bai jima ba yace zai koma don yai zai bar garin shima.
Namike na gyara mayafin jikina nabi shi a baya a kofan gidan muka tsaya dashi yake cewa tau ni zan tafi Fatima sai in Allah ya dawo damu ke nan ko nace to yaya Allah ya tsare na gode yace ki dai sha magani idan kuma kinga jikin zai matsa maki sai ki buga waya Bashar yazo yaje dake ko ?
Nace kai yanayin tafiyane kawai dana dade banyi ba kasan dama ina amai a mota ai.
Yace niko na sani nida kikaita ma amai a mota sai da nima naje gida naita shararawa har da ciwo sai da kika sani.
Nace kai yaya banda sheri yamiko min kudi yace kiba mijin mama wanan idan na wuce don tausayi wallahi mutumin yake bani.
Murmushi kawai nayi nace angode ni haushi yake bani ba tausayi ba abu tunda kurciya gashi yanzu har yafara farin gashi amma bai daina halin shiba na kurciya.
Suna wucewa na koma ciki kaina yana damuna da ciwo naki fada agaban shi kada hankalin shi ya daga yace mu koma.
Na dan kwanta sai barci ya dauke ni bamu ko gaisa da mama ba ban falka ba sai da akai kiran sallah azahar na tashi nai sallah na samu angyara dayan dakin.
Amna wanan karon mu a dakin mama zamu zaune mijintane zai zauna dayan dakin da musa.
An dafa abinci amma,banci ba nace hura zan sha shi aka,sayo iya ce ta dama min na dan sha jin zuciyana yana tashi na ture kwanon gefe daya.
Sai lokacin ne muka samu kebewa da Mamana tace ashe kuna tafe bamu da labari bamu shirya ma zuwan naku ba.
Banji dadin yadda mijin ki yazo bai sha ko ruwa ba ya koma hakana da yunwa.
Cikin dan murya nace haba mama ai ba komai koma an dafa bazaici ba nasani don ba komai yake ci bashi sai abinda yaso.
Tace wani irin tsaraba kukayo muna haka mai yawa yar baba nace wallahi mama ni sai ma yanzun da aka sauke nagani tsaraban yayane duka.
Nace sai su baba da in zan tafi za,a ware masu nasu muje masu dashi tace har can zaku isa ke nan nace ba dole ba mama.
Kada baba yace na fara gudun shi yanzu kuma don naga nayi aure.
Mama ta tabe baki tace aiba gudun shi kikeyi ba halin matar shine baida kyau kuje dadi dadi a kare da,tsiya kuma.
Nace nikan insha Allahu lafiya zamu rabu ai yanzu na riga na gano takon ta sai a zauna lafiya.
Ranan har dare muka raba da mama muna hira sai da dare ne nake fada mata sakon da yaya sadauki ya bayar akawo na gyaran gida.
Mama ta saki lalausar murmushi tace oh ikon Allah ni Amina yau ke da,wanan babban sa,an haka ?
Nikan banda abinda zan sakawa hajiya da zurianta sai addua da fatan gamawa da duniya lafiya nagode nagode bari wanan baudaden ya,shigo muji yadda za,ayi amma bazan nuna mashi kudin yana nan tare dake ba,sai dai naga yaya salisu asan abinyi dasu.
Don har yanzun da kikaganshi nan ga girma yazo amma bai fasa halin shi ba ni kadai nasan irin kuncin rayuwan da nake ciki a gidan nan ke dai.
Shiya sa tunda kika fada min zancen mijin ki ban sake rufe idona a gidan nan nayi barci ba gayawa Allah nake matsalan mu.
Nai murmushi nace da alama kuwa yanzu mama Allah ya karba muna rokon ki.
Don yanzu gaskiya ko yanayi ba irin nada can baya ba kamar farko sai dai kila aboye idan yanayi din.
Mama tace Allah dai yasa ya bari kwatakwata a rayuwan shi.
Yau gashi wanan hadin na hajiya da kike gani kamar son kai tayi maki ya zama aure mafi daraja da ko wace uwa ke mafalkin samun shi a rayuwa.
Dukar da kaina nayi don jin nauyi maganan da tayi tace ga sako da ake aiko muna dashi ta hannun mahaifin ki duk da nasan ba duka yake kawo muna ba.
Nace kai haba mama yaya baba zai rage maki sakon ki kuma tace ai bashi ba wanan munafukar matar tashi dai itace zata rage su.
Cikin natsuwa nace mama tabawa zata iyashi mama don bs imani ne da ita ba wallahi.
Haka muka kwana muna hira harda Iyya da,ta kwanta waje da,farko har barci ya dauke ta nasan tai hakane tabamu guri mu zanta ni da mamana.

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKIN MU AKAN KI,
Yana isa zuwa yamma ya bar garin ya wuce zuwa lagos inda zai tafi ghana daga can gurin business din shi.
Yana can ya bugo min washegari lokacin na tashi nai wanka ina shiryawa wayan shi yashigo na dauka tare da gaidashi yake tambayana jikin yayi sauki ko nace na samu lafiya sosai.
Dama ai idan na shiga mota ne kawai nai tafiya mai nisa nake jin haka.
Mundayi hira yana tambayana mutanen gida nace duk suna lafiya yace nagaida su nai mai Allah ya tsare yaba da sa,an tafiya muka kashe waya.
Sai dana shirya ne mama tashigo dakin tana ce min karyawa fa nace mata da,dai akwai dumamay tuwo ne shi nake son ci.
Tuwon aka dumamon an saka mai man shanu shi na danci kadan still ina jin tashin zuciya har lokacin.
Nan mama take tambayana yaya za,ayi da kayan da mukazo dashi nace a fitar wa Baba na da nasu sai su raba sauran amma sabulu da clean abawa makwabtan su.
Yadda nace haka mamana tai rabo na adalci don har na Baba na yafi yawa sai da nazo nagani nace a,a daidai za,a raba ita dashi.
Mutanen da aka kai ma tsaraba sukai tashigo yi muna sannu da zuwa naji dadin yadda mutane sukai ta nuna min karamci haka.
Ice dake gidan mama a karkashin shi muka mayar gurin zaman mu ni da iya sai dare muke shiga daki don rana haka na wuni kwance rijib ba lafiya.
Iya ta matsa wai na fadawa maigida banda lafiya asan abin yi nace mata haka nakeyi dama idan nai tafiya.
Sai mama ne da iya dake taya ta aiki suke ta faman kai kawo a tsakar gida kawuna yazo amsa kiran mamana da ta aika tana neman shi.
Nan suka kebe tai mashi bayanin komai kuma ta kawo kudin aikin ta damka mashi don shi a garin yake zaune dama gurin shi tazo har mijinta ya ganta ya aureta.
Sun gana da maigidan mama da kawu yace aiba matsala wanan taimako ne ai akai mashi da yamma kuwa sai ga masu aiki sun shigo gidan suka fara awon yadda za,a fitar da plan din ginan.
Dakuna guda biyu na mama ciki da falo dayan kuma single ne sai wasu biyu a gefe daya su ma sai na samari washe gari yan aiki suka fara aiki akan idona akafara komai ga katan aiki kawu har ya sawo an fara aiyuka ko.
Da dare daga ni sai mama na a daki Iyya na waje kwance wai zafi take ji.
Nace mama dama ina son mu samu lokaci in fada maki wani magani da aka anso muna naba yaya yasha wanda ina gani shine sanadin barin shan abin maye da yakeyi.
Nan dai nai mata bayani da kuma garin don ba nisa tace tagane mutumin ai dan uwan mahaifina ne tace insha Allahu zatayi kokari taje gurin shi.
Muna cikin hirane yaya sadauki ya kirani muka gaisa yana jin murya na yace Fatima na amsa may ke damun ki nace may kagani ne yace you sound like baki da lafiya na kakaro murmushi nace daga barci na tashi yanzu barci na somayi kata dani.
Ina ganin bai yarda ba sai naji yace humm kawai yace ina mama nace gata tare dani barin bata ku gaisa dama tana son maka godiya.
Yace No No godiyan may kuma don nayi wa mamana alheri haba kada ma ki bata idan hakane kice ina gaida ita nace to ya kashe wayan.
Koda ya kashe wayan hankalin shi bai kwanta ba yadda yaji muryana sai hankalin shi yai matukar tashi.
Amma kuma baida yadda zaiyi tunda nace mai lafiya nake da ance sokoto nake da ya zo gobe gobe taga yanayin da nake ciki.
Dole jiki ya matsa min ban samu tafiya ba ranan da muka ce zamu tafi sai da dare ya samu time ya bugo min waya yana tambayana mun sauka lafiya da kyat nake magana don da zazzabi na wuni.
Yake tambayana ko mun sauka lafiya yaya baba nace cikin karfin hali ban samu wucewa ba yau yaya.
Ya rage fara,anshi yana tambayan saboda may nai mai shiru yace baki da lafiya ko Fatima ?
Shine kika shige kauye kika zauna da ciwo yana cin ki ajiki haka.
Watau ke kin samu su mama kin manta da lafiyan ki ko ?
Na rasa abinda zance sai da ya kara tambayana may ke damun ki ne ma wai ?
Na rasa abinda zance mai sai can nace zazzabine amma naji sauki shine mama tace na bari sai gobe mu tafi idan na kara jin sauki.
Yace a zaune zaki ji sauki bakiga likita ba ko may nace nasha magani ai na samu sauki yace ina Iyya take ne wai nace tafita.
Yace gobe goben nan ki koma sokoto zan ma bashar magana yazo ya kaiki asibiti idan kun isa kafin na iso.
Gabana yai matukar faduwa gashi banje gurin babana ba kuma yasan munzo.
Na marairaice nace don Allah yaya kayi hakkuri naje gurin baba nai kwana daya jibi sai na karasa gida.
Bai jira may zance ba ya katse layin bayan dan tsokin da yaja.
Mama dake zaune gefe na takale ni a tsorace tace so yake ki koma gida baki isa can ba ?
Na bata fuska tare da jan tsuki nace wai haka yake nufi ni kuma ba zan koma ba banje gurin baba tunda ba bari yake nazo ba.
Tace a,a yar baba kirashi ki roke shi idan ya yarda sai ki karasa gurin su idan kuma yace lalai sai ki koma gobe din sai ku shirya ku koma din.
Na dai daga wayan badon naso ba ga mama ta tsareni da ido na kirashi na zaci ba zai daga wayan ba dana kira.
Amma sai naga ya dauka yace yaya akayi kuma ?
A hankali na ce mai kayi hakkuri yaya don Allah naje gurin baba gobe nai kwana daya sai na dawo kada yace ko gudun shi na soma yi na rike uwata.
Yace as you wish ai jikin ki ne nace kadai yi hakkuri please gobe da safe zamu karasa can mu kwana da safe sai mu taso.
Yace na fada maki da kun kwana daya ki dawo gida kije asibiti aduba lafiyan ki nace insha Allahu jibi da safe zamu taso da yarda ubangiji.
Yace is ok Allah ya sauwaka nace nagode muka kashe wayan mama tace ai kinga haka yafi da ran shi ya baci yakawo ki cikin dadin rai kuma akoma ana haka baiyi ba gaskiya.
Nai mamaki irin tsaraban da mama ta hada muna mu tafi dashi wai kaji, man shanu fura da nono kwakwamayti kuka daddawa da kuli kuli da kwanzabbi mai yawa.
Mijin mama ma yabani mamaki rago yasa akayanka aka,soya shi sai da ya cika bucket din penti yace nashi tsaraban ke na da mazzakwaila mai yawa.
Tun da safe mukai masu sallama na wuto da kauna ta Sa,ade muka bar Asma,u tana kuka nai mata alkawari itama zan dawo in dauke ta ai tai makaranta haka yasa tai shiru.
Sai kauyen mu nan na samu baba bai gida da farko kamar mama tabawa bazata karbe mu ba amma tana ganin an fara jido kaya ana shigowa dashi tafara washe bakin ta tana cewa sai yau Hjy maryam tun fa shekaran jiya akace muna kina Rabah.
Nai dariya nace wallahi mama munje daniyar nai kwana biyu nazo nan nakarasa kwana uku sai ga ciwo ya rike ni acan.
Tace assha subahanallahi inji da sauki dai ko nace naji sauki mama.
Nan muka basu tsaranan su na aika,wa kakanina da nasu sukai ta godiya.
Da baba yadawo shima na bashi nashi sakon yai ta saka albarka kwanan mu daya tunda safe muka kama hanya sai sokoto.
Rijibb na iso garin na kwanta bamu jima dashigowa ba wayan yaya ya shigo yana cewa yaya kun taso ko nace gani dakina kwance yace ki shirya bashar yazo yanzu kuje asibiti.
Ba adade ba bashar yazo muka wuce asibiti ganin likita duk a lokacin na jigaye na wahala sosai.
****** ********* ******
A gurin da zanga likita ma sai dana dan kwanta kafin shiga ya kawo kaina banda kuzari sai yawan jin kasala dake damuna ko ruwa nasha sai na fitar dashi san nan naji shakat a raina.
Nan yakira wayana nace gamu asibiti muna jiran layi yazo kan mu ne.
Yace wai may ke damun ki ne Fatima haka ?
Na lumshe idanuwa na nace ban sanni ba yaya komai naci dai sai na amaye shi kuma banjin kuzari a jikina ina dai ganin maleria ne yai min yawa a jikina.
Yace bari a shiga gurin likita muji may ke damun ki haka kilama ruwan kauyen ku ne bai karbe ki ba kike wanan wahala haka ?
Mun shiga gurin likita yai min yan tambayoyi irin nasu ina bashi amsa can dai yajefo min tambaya yaushe rabona da period ne ?
Gabana ya fadi sai lokacin na tuna zancen wani period can nace gaskiya ina ganin kamar yakai kusan three month yanzu sai dai koda nake gida ai nakan yi irin haka din.
Test akai min cikine dani har wata uku da kwana takwas nan dai suka rubuta min magani tare da,son na samu hutu don nayi weak da yawa.
Kunyane ya rufe ni da akewa yaya bashar din bayani tun nan yaya bashar yake min congrats.
Muna fitowa wayan sadauki na shigo mashi yace wai may ake cikine kunga likitan.
Yace eh mungan shi gashi mun fito zan da tsaya na sai mata magani ne mu koma gida.
Yace may sukace yake damun ta yace may ko zasuce banda cutar daka zubawa yar mutane mugu kawai.
Gaban sadauki ya fadi shidai yasan baida wani cuta a tare dashi asalima shiba mane min mata bane balle.
Yace for god sake may ya samu fatima din Bashar wani cuta ke gare ni da zan zubawa Fatima shi ?
Yace kaiko keda cuta gatan kana kayan shi cikin wando kullun kana durawa yar mutane wahala.
Nan yake ta tsokanar shi har yagane ciki yake nufi ke gare ni yace don Allah da gaske kake yi ko shirmay ka bashar ?
Lokacin yake shigowa mota yake ce min karbi wayan maryam ki fada mai da kanki tunda ni ya mayar dani makaryaci yanzu.
Kuma ka shirya tukwaici na wallahi don wanan ba karamin albishir bane nai maka.
Yamiko min wayan yace ga fitinanen mijinki kiyi mashi bayani da kanki ko zai yarda murmushi kawai nayi mashi.
Na dauki wayan cikin sanyin murya nake cewa hello yaya.
Bai amsa ba sai cewa yayi wai wanan munafikin maganar gaskita yake fada min ko wasa yakeyi nace uhumm kawai tare da murmushi na mikawa yaya bashar wayan shi.
Nan sukaci gaba do zolayan kan su har muka isa gida yaiwa iya bayani kan ance ana son in samu hutu sosai don haka kada ta bari inyi aikin komai please.
Barci ne ya dauke ni mai nauyi ban falka ba sai misalin karfe takwas na dare koshi amai din ne ya tayar dani a lokacin.
Sai dana natsu na jawo wayana kirane ciki barkatai na mutane nashi yafi yawa amma.
Ban kirashi ba don yanzu ko hayani kwarai ban so sosai na shiga whastff nan naga yayi posting din suraitai barkatai na farin ciki.
Ban dade ba nafita na kwanta sai ga Iyya tashigo dakin take min yaya jiki nace mata naji sauki sosai.
Tai min tayin abinci nace tea nake so na ruwan liptop kawai ba madara ba sugar tace ikon Allah shi ta hado min na zuba zuma ciki dan kadan nasha shine har naji dan dadin bakina nai sallah na kara kwantawa.
Da safe kiran mama ne ya tayar dani daga barcin tace Fatima ashe kin dawo kuma ba lafiya nai dan muushi nace wallahi mama.
To yaya jikin da sauki yanzu ko nace naji sauki sosai mama tace shima yace insha Allahu yau zai dawo zuwa yamma don yana abuja babu jirgin safe yau.
Nace Allah yakawo shi lafita tace amin ki kula da kanki kinji Fatima Allah ya inganta banyi magana ba don kunya.
Falo na fito na samu Iyya da Saade azaune suka gaishe ni tare da min Allah ya sauwaka.
Can nace Iyya afito da tsaraban nan kiraba abawa mutane nasu tace to nace man shanu da nama akai wasu mama shi idan kin dibi naki tunda munan akwai nama su zai masu a.fani suna da yawa can nasa ta diban ma anty maryam nata da Inna mama bashar kwai nace akaiwa mummy ta soyawa yaran ta.
Yadda nace haka iya tayi kayan miyane kawai tabar muna don muna da bukatan su sosai.
Iyya ce da kanta takaiwa kowa nashi mama tai matukar jin dadin yadda nayi don Iyya ta labarta mata komai kwai danace akawo wa yaran mummy da kwakwamayti ya matukar burgeta har mummy din suka ce suma suna nan shigowa su gaidani.
Nan mama ta debarwa ko wani daki ta aika masu tana fadin ga tsaraban Fatima nan da ta dawo dashi suka karba suna gyatsire fuska kuma suka shiga ci.
****** ********* ******
Bayan sallah azahar mama da mummy suka shigo tun a kofa mummy take fadin ina yake tun bai fito ba na kwali kan na yana wahalar min da yarinyana haka ?
Kunya naji sosai na dan dukar da kaina,a kwance suka samay ni saman dogon kujera na mike da kyat muka gaisa dasu nan mummy take fadin tun da dare sadauki yakirani yake fada min ai ban san lokacin da nai ihu ba har Alhaji saida yafito.
Mama tace kai in ma ba abin kurciya ba yaya mutum zaiyi ciki har wata uku ba,a sani ba tun fa tafiyan su ke nan ta dawo da cikin nan amma haukan shi bai bari ya sani ba.
Taron dai kurciyane hajiya inbashi ba ai ko ita zata gane tana da ciki a jikin ta ma kawai dai duk kan su kurciya yana cin su ne.
Mummy tace mazajen ki na gaishe ki sunce sunga tsaraba sun gode sunace suna murna wai yayan su ya samu baby Banan da haukan ta wai nazo da ita ta dauki baby.
Murmushi nayi nace lah mummy shine baku zo min da ita ba tace ban iya kiriniyan ta barta can suzo idan yayan su yadawo yakai su yawo ai yasaba da kwaram din su shi.
Mama tace a,a Sa,adatu din ke nan ai ni dani kuka ba ita ta debe min kewan ku wallahi gata kamar ku daya wallahi nace mama ai munfi kama ko da Asmau sosai idan kingata kaman mu yayi yawa tana can mun barta tana kuka wai ita ma sai tazo mukai mata wayo nace zanzo na dauke ta daga baya yanzun ba wuri.
Amma ko Fatima baki kyauta ba kikabar min Asmaun nawa kaunata ce ina ji da ita duk cikin kanne na wallahi.
Bari ya dawo ai zan sashi ya tura azo min da ita tunda ku baku son zama da ita nan.
Naji dadin jin haka kuma haka nake so don ina son yaran su fito suyi karatu itama mama ta dan huta yawan iyali.
Idan kuma ta zauna gurin mama zata sha dadi sosai a gurin ta don mama uwace bata fada ba.
Basu wani dade ba sukai muna sallama suka tafi akabarni da Iyya da Sa,ade a gida musa ya fita abin shi.
Sai da dare ya shigo garin ina,falo kwance na dunkule yashigo gidan Sa,ade naji tana mashi sannu da zuwa don tare muke zaune Iyya tana kitchen.
Yashigo idanuwan shi na akaina har ya karo inda nake kwance ina kokarin mikewa zaune daga kwancen da nake.
Yace No don Alla kwanta abinki yazo ya zauna bakin kujeran da nake kwance haka yasa Sa,ade mikewa ta nufi kitchen gurin iya tana fada mata dawowan shi.
Ya dan kai hannu shi a saman wuyana yana tabawa a hankali yaji ba zafi sosai yace how the you feel now ?
Nace a hankali da sauki ya daga hannuwana ya rike a cikin nashi gama yace I dont know what to say but nagode Fatima na gode kwarai da wanan babban kyauta da kikai min.
Na lumshe idanuwa na a hankali tare da kwantar da kaina ga jikin shi nace yaya I miss you.
Yai dan murmushi ya shafi fuskana yace kina hakan da fa fushi nake dake da kikaje kika zauna da ciwo a kauye kamar wacce bata san zafin kanta ba.
Amma yanzu kin wanke kanki ko gare ni komai ya,wuce ko yake cewa yanzun may kike ji kuma ne wai ?
Nace ba komai yaya bandai jin karfin jikina ne kawai sosai kamar farko yace ina zakiji dadin jikin ki kina haka Allah dai ya rabaku lafiya kawai.
Wanka ya,shiga yafito ya dawo falo inda muke don ni na kasa tashi ma,a lokacin sabada jiri dana ke ji.
Da dare ma dai haka muka kwana dole washe gari aka sa min ruwa don amai yai min yawa sosai.
Wani irin ciki ne wanan kuma bai bani wahala ba da farko sai yanzu gashi yana son kawo min cikas ga karatuna.
Haka nake daurewa na je lectures na dawo gida a,wahalce yau ciwo gobe lafiya.
****** ********* ******
Wasa wasa baba sani ya saka sadauki a gaba da zancen Rahama duk da mama tace bata yarda ba ita.
Ido da ido sukayi da baba Sani take fada mashi indai ita ta haifi sadauki wallahi ba,a auren nan sai dai in bayan ranta za,ayi shi.
Tace yanzu kasan suna da zumunci kamanta lokacin da kaiwa mutane cin mutunci kace dan shaye shaye ne shi baka aura mashi yar ka naje cikin dangina na nema mashi.
To na nema mashi din kuma yanzun sai hassada da kyashi ya biyo baya nace ba ayin auren idan kuma ka isa sai ayi mu gani.
Yace ke wallahi hauwa baki isa ki raba muna zumuncin ba sai dai ki mutu amma sai anyi wanan auren muddin ina raye kuwa .
Mama tace to ayi mugani idan kaika haifa min dan dakace na bari ya baci da shaye shaye saboda sakaci na a baya.
Sai da baba ya tsawa ta masu yace subar zancen zai yi tunane yaga mai yadace yasan maji na da gaskiya kuma baitaba ganin ta rufe ido tayi sa,insa da wani ba haka sai ranan.
Takira sadauki tun a waya ta falfalleshi so sai har hankalin shi ya daga tace katatake mutanen da basu kaunar ka da alheri su shiga cikin jikin ka.
Yar matar ka kuna zaune lafiya za,a shigo a tarwatsa maku farincikin ku da tsagumi yace wallahi maji ni wanan magana ma bai gabana don na riga na fada mai gaskiya ko.
Ana haka ma tafiya wasan su ya taso ban tashi ji ba sai bayan tafiyan shi da Nafisa tazo take ce min .
Ke ashe wanan munafukan wai yanzun kuma yayana suke so ya auri Rahama bayan sun gama ciwa mutane mutunci.
Gaba na ya fadi nace wata Rahama kuma ?
Nan dai tabani labarin abinda ya faru da Baba Sani da mama ranan a gidan su tace wallahi maji tabani sha,awa yanda ta mayar mai da amsa son ranta.
Munafukin mutum ne fa tare suke makircin su dasu Umma kullun akan yayana ko yanzun ma kila wani makirci ne suka kulla suke son ayi hadin.
Duk da hankalina ya tashi ban nuna mata ba sai cewan da nayi kai anty baba kikecewa muna fuki kuma ?
Au ke baki san munafuki bane dama mugune wallahi duk shi ya cinyewa baba kudin shi haka suke so kuma yanzu su shigawa yaya su cuce shi shida yaya Imirana kuma fa duk su Umma ke turasu don basu da tausayi dakika gan su nan.
Tausayi tabani nan ta kwanta tai barci ta tashi tace tana son shan tea ni da kaina ba hado mata tea din da nai mata hadin da bata sani ba acikin shi.
Tana gama sha tace zata tafi nakawo alheri dana saba mata idan tazo nabata dubu biyar da su man shafa da turare tai min godiya ta tafi nace Allah yasa a dace .
Aiko da dare tafara gala baita hankalin uwar ta yai matukar tashi sosai a ka kwasheta sai asibiti ranan can aka kwana da ita hankali a tashe.
Sai da tai kwana biyar tana abu guda a asibiti aka gaji aka sallamota.
Ko yaushe muna makale da waya da yaya muna hira akan dai zancen ciki yake min surutun shi sai nagaji nace zan kwanta.
Da safe ma,shi zai kirani ya tayar dani yana min yaya jikin haka na zan shirya na tafi makaranta da alolayi .
Ranan nakewa maryam magana kan zancen Rahama tai mamaki inda na samu labari tunda mama tace kada abaru na san zancen ina cikin lalura haka.
Ban fada mata inda naji ba sai dai cewa danayi ni ba wai shigowan ta nakewa tsoro ba wullakanci nake gudu tunda ita yar gida ce ni bare.
Tace yar gidan wa Fatima don Allah ki daina kiran kan ki da bare a cikin mu please.
Tace balle ma may yaya zaiyi da,wata Rahama can bakiga yadda takoma bane yanzu fa yan wahala wai harda ranon anko sukeyi fa.
Nan naji hankalina yai matukar tashi sosai ranan har saida jikina ya tashi cikin dare dole aka kaini asibiti a can na kwana kwanana biyu Allah ya taimakeni anyi hutu sai mama tace a wuto dani gidan ta tunda dai jikin yakiya kuma shi bai gari.
Daga ni har Iyya da Sa,ade muka koma gurin mama can gidan su amma ina matular jin jiki.
Maryam ke fadawa mijinta har da zancen Rahama da nasawa raina ke kara damuna.
Yakira sadauki ya fada mashi suna kashe waya sai ga kiran shi yake cewa uban wa ya fada maki zan auri wata Rahana can da zaki tayar da hankalin ki haka kina batun kashe kanki Fatima ?
Murmushi nayi nace haba yaya akan Rahama zan kashe kaina don may zanyi kishin yar uwar ka ce fa ba,a aure ka aure ni ni ?
Yace waya fada maki auren Rahama zanyi ne wai Rahama may ce ni bata ko a cikin lissafina wallahi.
Sai da ya gama fadan shi yake tambayan jikina nace mai naji sauki yace kina cin abinci kuwa nace eh mama tana saka ni gaba na sha koko.
Yace kokon may kuma can Fatima koko abinci ne da zakice kina cin abinci.
Zan wa maji magana ta saka ki gaba sai kin dinga cin abinci sosai na dan marauraice nace ko naci wallahi bai zama a cikina wahala kuma yake sakani.
Ya kashe wayan nace namiji ke nan kamar badashi ake wanan zancen ba ji wau Rahaman may can kamar ba a baya sun sha soyayya tare ba.
Yadda ma nake jin labari duk abinda ya samu su yake kaiwa ita da uwarta shi yasa bai kawowa maji komai a lokacin.
Amma da suka tashi bashi baya suka rufe ido sukai mashi cin mutunci ta uwa ta uba.
Baba da kan shi yake zuwa har dakin maji da safe ya duba lafiyata wanan abin yana matukar ciwa su Umma da mama rai sosai.
Sunyi gulma har sun gaji sun kyale shi suna zunde wai don ina matar dan son shi ne yake min haka.
Ya bugo min waya muna zaune da mama da Iyya yake ce min gashi wani shago yazo shopping din kayan jarirai wani iri zai zabo antambaye shi yace a bari ya tambaya.
Sai naji yace Fatima mace ce ko namiji a cikin ki innalillahi na furta da sauri suka kallo ni mama taju tsoro ta karbi wayan a hannu na lokacin da ya kara tambaya yana cewa fada min mana please.
Mace ne ko namiji ba ance kuna ganewa ba idan mace tana da ciki don in san wanda za zaba.
Mama tace to mara kunya ita ba irin ka bane mara ta ido kai kasan wanan ita batasan shi ba kada Allah yasa ka sayo din insai tafada maka abinda ta kumsa.
Kaida kaicikin bakasan ko wani iri bane ka saka mata a cikin sai itace zata sani mara hankali kawai.
Amira da ke zaune ko kallo bamu ishe ta ba tai tsuki tace maji tambaya fa kawai yakeyi killa yana son sayo kayane a can.
Shidai yana jin fadan mama ya kashe wayan yana dariya kawai.
Wani irin mahaukacin sayayya yayi kamar bai san zafin kudi ba yadda ya kashe su akan kayan baby kawai.
Har su kayan wasan yara saida ya sayo sukekuna da gadaje ya hada da kayan uwar jego gaba daya, ya sako su a jirgi kaya guda dasu.
Sai da dare ya kirani yana cewa watau dazun kika hadani da maji ko don kina muguwa na dauka abin siri ne tsakani dake amma kika mika mata waya don keta.
Nace to naga sune manya su suka san abinda ya dacs asaya shiyasa nabata wayan ta fada maka abindake cikin.
Kai dan kwallo dai bai jin wahalan kashin kudi kodan samun shi sukeyi any howa balle shi dayake ya,shara dan kwallon duniya ne shi yanzu kasa kasa ana hayan shi ya buga masu wasa.
Don nan yanzu sun dauko sheri wa yaran musulman mu sai su hana su buga masu wasa idan za,a tafi.
Haka yasa yanzu yai watsi da yan Nigeria yake bugawa wasu kashe she sai daga baya kuma suke son wai ya dawo masu yanzu ya dinga buga masu.
Amma shima yaja masu aji ayace yabarsu can inda yake sunfi sanin darajan su suna biyan su da tsada fiye da nan da,ake masu kyat.
Yayi kudii fiye da tsanmani don dai yana,bogon kurwa ne ba,a gane yawan kudin shi sai wanda yasan kan abin.
Yana can yana gina gida a abuja wani irin maithigh house na gani na fada ba wanda ya sani sai yaya bashar da Baba kawai da mama.
Don gudun yan baki irin su Umma don gujewa sherin su da munafunci don zasu iyacyin komai suga bayan shi.
Zaman mu gurin mama yakaiwa Anty Amira ko ina don yadda mama take ririta sai take jin haushin hakan a ranta.
Cewa takeyi wai shagwabane nakeyi ba wani ciwo dake damuna don dai naga kawai ana kulla min ne.
Sai ranan da dare fever ya rufe ni sosai taga an rufa min bargo amma jikina sai shocking yake ina rawan sanyi
Shine washegari har na samu sannunta take min yaya jiki yaya Sagir ne ya kai mu asibiti ni da mommy muka tafi akece wa fever ne na masu ciki yakamani.
Kila sauro ya cije ni ne sadauki yana ji yaturo bashar a gyara AC a canza fanka a saka neat a window mama da kofa.
Amira tace lalai ashe abin nayi ne wai duk a bintu ake wanan abin haka wani aiki kan sai malam.
Ina jin ta nai murmushi nace lalai kam malam yai aiki saura biya tace Allah dai na ganin ki wallahi idan ma daure min dan uwa kukayi ke da mai masa dama ta iya bakar shige shige ai wa mutane balle nata.
Nace ai wanda tayi ma saka ta akayi tayi din ba yinkan ta bane tayi don haka ashe masu ahige shige suna da yawa.
Aiko tace wai na zage ta nai mata cin mutumci nan tafara min masifa mama tashigo tasamu tana min zari tace a,a ashe rashin tausayin naki yakai haka yarinya bata da lafiya mijin ta bai gari kice zakiyi mata rashin mutunci.
Ke na gaji da wanan bakin halin naki wallahi Amira nan gidan su Bintu ne tunda gidan mijin tane kema kije ki nemi uwar mijin ki can ku karata can da ita.
Amma baki zuwa ki saka min yarinya haka a gaba bata da lafiya kin isheta da masifan tsiya haka.
Haka taita tunzura ta kwashi fushin ta tashige daki itama maji tafice zuwa waje.
Iyan Rabi tace kinyi daidai wallahi wanan yarinyar kamar ba hajiya ta haifeta ba wallahi mugun halinta yayi yawa Allah.
Nace haka take ita bara da,son jama,a yaniyin take tunda tace kai dan Allah wallahi dai halinta baiyi ba.
Mutum bai da lafiya ace kuma bakai mashi sannu ba sai bakar yadiya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BA KI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA PLEASE DON HAKKA CIN AMANA NE MUN BARKI GA ALLAH,,,
Zamana a gidan su mama yasa na dan kara walwalewa na dan samu sauki sai dai har yanzun ba dama naci wani abu a ciki.
Don da zaran naci yanzun zan shiga na mai ke nan sai kunu kawai zan dan sha ya zauna min a cikina.
Ana cikin haka yaya saudauki ya dawo daga tafiya da tarin abin arziki don kusan watan shi biyu ke nan a can gurin tafiyan da yayi.
Sai da yaje gida ya,shirya ya tafi inda muke a lokacin ya dawo ya samu matar yaya Imiran ta haihu ta samu diya mace.
Muna zaune a falo mama gaba dayan mu mama da Iyya suna hira ni kuma ina dunkule saman kujera na nade kaina har kafa a cikin hijjabina.
Anty Amira da,wayan ta a hannu tana chatting sai Sa,ade da ta kurawa tv ido tana jallo don ita kallo baya isan ta.
Da,sallama ya shigo falon gaba dayan mu muka mai da hankalin mu a kan shi.
Duk da dare ne mutum zai iya ganin canjin da ya samu a tare dashi sosai a lokacin daya haka.
Zama yayi suka gaisa da kowa dake cikin falon tare da mashi yaya hanya suna mai fatan alheri.
Sa,ade ta mike har gurin da yake tana gaida shi yace a a wa nake gani haka kamar yar kauye don yanzu sunana a kanta ya koma kuma.
Daga inda mama take zaune take cewa ,a,a kabar kira min yarinyata da yar kauye don yanzun ta waye kai ma nake jira kadawo kakai muna ita makaranta gata sai zama gida ba karatu.
Yariko hannunta yana cewa mama wanan bakauyan zata iya karatu ne a haka ?
Kaita a gani mana inji mama ta bashi amsa tare da cewa kai yaya akayi ka iya ba koyo kayi ba kaima.
Ita dai Sa,ade sai murmushi takeyi kawai don bata sake jiki dashi ba har lokacin duk yana dan mata wasa jefi jefi.
Gurin da nake zaune ya kalla yace madam yaya kuke wai har yanzun dai jikin ne haka ?
Ya mike zuwa inda nake zaune bai damu da akwai mutane a falon ba ya zauna a bakin kujeran da nake a kwance tare da dan shafo fuskana a hankali.
Wani irin mugun zafine yaji jikina dashi yace kai maji haka jikin nata yake da zafi ko yaushe?
Su ka dan kallo mu tare da saurin kawar da idanuwan su don ganin irin zaman da mukayi dashi a lokacin.
Mama tace aima jikin yai sauki yanzu gata har tana dan fitowa falo yanzu aida ko yaushe tana daki a dunkule.
An ko koma asibiti da ita kuwa ya tambaya ?
Yau sati daya ke nan da aka kara mata ruwa da magani ai abin yazo mata da akasi wallahi haka nan nai cikin maryam kusan duk sati biyu uku sai na sha ruwa ga zafin jiki da ciwon kai duk na kare a lokaci sai dana haihu kamar anzare min kaya naji komai ya wuce.
Iyya tace hjy ashe maishi ya biyo gwagon shi ke nan da ga jini wani ciki kara gare shi sosai wallahi.
Ya mayar da hankalin shi gare ni tare da tausa muryan shi yana tambayana may nakeji ajikina ne wai ?
Nace ba komai yaya ai naji sauki nace mai yaya hanya yace cikin bata rai Alhamdullahi.
Sannu yaya jikin to yanzun kuma nace da sauki yaya.
Maji ko zan fita da itane waje idan nan basu gane may ke damuwar ta ba ?
Dariya sukayi mama tace ji shirmayn ka ciki may ye bai zuwa wa mace dashi kowa da kalar daukan cikin ta ai.
Yadda ya mai da hankali akaina muna magana kus kus yasa Anty Amira jin haushi matuka tana gani idan da dane daya dawo itace yar gaban goshin shi amma yanzu tunda ya shigo hankalin shi yana a kaina baima ko yi mata wani magana ba bayan gaisuwan da sukayi kawai.
Mikewa tayi tare da tsuki tabar falon daidai lokacin da yake tambayan ina kuwa cin abinci yaga duk na ramay gaba daya haka,?
Baima san tanayi ba tashige tana gunguni wai an asirce shi yanzu bai ganin kowa da gashi sai ni da yan uwana kawai.
Mama tace mai bata cin komai sai ruwan kunu kaganshi nan a gefen ta aje koshi bai ludayi uku ba idan ma tasha din ke nan ai.
Nan ya fara tambayana zakici abu kaza ko na sayo maki kaza ne nace yaya ban son komai Iam ok haka ma na koshi.
Ya dan tsuki tare da kura min ido yana tausayawa halin da nake ciki sosai can mamatace mai.
Matar dan uwanka fa tana gidan nan kasan na fada ma ta haihu banda gobe suna.
Yace au a gidan nan take zaune ne mama tace eh daga asibiti uwar su tace a kawo ta nan.
Yace amma naga maryam ita a dakin ta ta haihu ai bata dawo gida ba ?
Mama tace kasan kowa da irin ra,ayin shi nata ra,ayin ke nan yin haka din Alhaji ma ido yasa masu don yasan ba a wanyewa lafiya indai yaya ne.
Sun dan yi hira ya mike zuwa cikin gida dakin Umma idan ya duba jaririya.
Ya samu su umma da uyalin ta a falo yai masu barka suka tambaye shi hanya yace Alhamdullahi.
Da zai tafi bayan maijego tafito sun gaisa da ita yakawo kudi masu yawa ya bata yace ta sai wa yarinya sabulu dashi.
Yana fita yaji Umma tana tambaya nawane halan ya basu ta nuna masu raffan yan dari biyar sabbi tace akawo a kara ga laluran buki dashi.
But Nafisa dake daki tafito tana cewa a,a Umma ki bar mata kudin ta don Allah don dai ita aka ba itama ai tana da abin da zatayi dasu ko?
Umma tace kada ki kawo min diban albarkan ki da kika saba yiwa mutane wani lalura gare ta wanda yafi namu kuma ?
Ita dai Shafa,tu mikawa Umma kudin tayi amma sai Nafisa ta rike tana cewa wallahi ba,a bayarwa tunda ita akaba.
Ai ya ganki baice maki gasu ba ya mika mata idan yabaku naku da ita zaku raba ta shige cikin daki da kudin a hannun ta umma tana kwalla mata kira amma ta kyale ta.
Nafisa ke kan ke kan wallahi Allah ya waddaran hali ir8n naki na tir da Allah waddai tace daga ciki ban dai bayarwa wallahi.
Bai dade ba yace zai tafi ya kwanta don a gajiye yake lokacin mukai mai sai da safe ya fita daga gidan.
Ji nayi kamar na bi bayan shi da zai fita sai dai babu halin yin haka dole na zauna a gurin mama don nan ya samay mu.
****** ********* ******
Kwanan shi biyu da dawowa sai faman sintiri yakeyi bai gidan mu baya gidan maji gurin mu.
Yau an tashi da bukin sunan matar yaya Imirana inda yarinya taci sunan Umma kowa na kiran ta da Ummi don sunan ta na Umma da taci.
Sai naji kawai ranan ina marmarin alale na gwangwani don haka na fadawa Iyya Rabi abinda nake son ci.
Baita kasa a gwiwa ba ta shiga shirin yi min alaila ta samo gwagwani gurin wani mai shayi a unguwan ta hauyin alalen da nake son ci.
Ba bata lokaci ta gama min ina daki ina shiyawa zan fito falo yau na kokarta na yi dan kwalliya a jikina don jama,an da suka cika gidan.
Cikin atamfar super nake dark blue dinkin shi mai shara sharan hannuwa half gown na daura dan kwalin kayan a kaina.
Cikin dake jikina kayan yasa yafito don lokacin ya kai wata shidda a jikina sai dai ba kowane zai iya ganewa ba sai wanda ya sanni da farko.
Nafito falo na zauna Iyya Rabi tace yauwa yanzun nake batin kiran ki kifito kici shi da dan zafin shi kada kuma ya fita ran ki.
Zama daidai da shigowan maryam gidan da ita da kannen mijin ta da suka rako ta gurin sunan.
Suna dauke da danta a hannun su sai wata makwabciyar ta data rakota kuma again don ita tana hurda da makwabtan ta sosai.
Suna zama aka kawo alalen da ita muka hada hannu muna ci a plate daya naji dadin shi sosai muna ci muna hiran yaronta irin yadda yake yawan alolayi sosai.
Muryan Baba mukaji a tsakar gida yana kwalawa matan shi kira cikin tashin hankali.
Gaba daya suka fito daga dakunan su sai gidan yai tsit kowa nason jin kiran don daji bana lafiya bane.
Mama Asiya tana fitowa ya kalleta yace Asiya kuncuce ni kunci amana keda dan ki bazan taba yafe maku ba a rayuwana.
Mummy ce cikin karfin hali yadda taga Baba a rude take cewa wai may yafaru ne Alhaji kuma ?
Yace Ahmed ya sayar da gidan nan yau wata uku ke nan ban sani ba ashe ?
Salati kowa ya saka sai ihun mama Asiya kawai mukaji daga waje abinda yasa mu fitowa ke na daga dakunan mu duk wanda ke gidan sai da yafito don tashin hankali.
Baba yaci gaba da fadin yanzun haka wanda yasai gidan yana waje yace yazo ne yabamu notice din tashi don anyi dashi nan da wata uku zamu bar gidan wai .
Lokaci daya aka saka salati masu kuka sunayi masu salati da tir sunayi a lokaci daya.
Sai ganin kawai akayi Baba yai suuu zai fadi da sauri mama da mummy suka tare shi bai kai kasa ba sai dai ba rai.
Idanuwan shi a waje inna lillahi wa inna alaihim rajiun,,,
Ihu da tashin hankali a ranan mun gane shi a gidan da gudu wasu suka kwasa zuwa kiran maza a waje.
Yaya saudauki yana tare da yaya Bashar suna hanya kiran maryam ya shigo wayan shi .
Yace kai munafukan matar kace fa ke kirana yanzu, bashar yace wa maryam lafiya kuwa ya dauki kiran tana kuka take ce mai yaya don Allah kazo gida Baba.
Cikin wani irin murya yace Baba may fa ?
Sai kuka takeyi tace don Allah yaya kazo Baban mu ya rasu inna lillahi wani irin burki ya taka da ya daki motar dake kusa dashi.
Ga you turne din sokoto da tsawon tsiya haka ya kwashe su da gudu Allah dai ne ya tsare su sai gida cikin yan mintina suka kawo.
Irin mutanen da ya hango sunyi cincirindo a kofan gidan su cikin tashin hankali ne yasa hankalin su ya kara dagawa sosai.
Wani irin mugun parking sukayi ya bar mota a bude ya nufi cikin gida da gudun shi irin na yan kwallo bashar tana bayan shi.
Sai wani yaro makwabcin su ne ya kashe motan ya gyara parking gefe yana shiga get su Sagir sun dauko Baba ya tare su tare da kamashi suka fita zuwa waje da shi sai asibiti cikin tashin hankali.
Suna zuwa emergency aka nufa dashi nan aka samu da kyat ya farfado duk ilahirin iyalin shi suna gurin sai yaya Ahmed ne kawai da matar shi basu gurin.
Koke koke kawai ke tashi tashin hankali ne ga duk fuskan wanda ka kalla a lokacin.
Muna tsatsaye tare da su anty maryam da anty Nafisa don tare muka zo asibitin da su.
Wani iri nake ji dole ssuka samomin guri na zauna ga alalen da naiwa mugun ci sai taso min yakeyi ina jin zanyi amai a lokacin.
Maryam ce ta dafani take cewa Fatima ko zaki koma gida ne kinga baki da lafiya fa a jikin ki gaki da lalura kada tashin hankali ya kamaki kuma ?
Nace ba komai ai anty aiko sai aman da nake taushewa ya taso min nan na duka naita sharara shi hankalin mutane kuma ya dawo a kaina.
Daga cikin daki da Abdul ya shiga inda su yaya suke a kan Baba da ake neman jijiyan shi yake cewa ga kuma Fatima can wallahi ita ma a waje sai a hankali sai amai take shararawa kawai.
Da sauri suke cewa harda ita da bata da lafiya tazo ne yaya sadauki ya dago rai bace yace may yakawo ta ita da bata da lafiya kuma ?
Bashar ya fita da sauri halin da ya samay ni ciki yace su maryam su kamani muje gurin likita.
Muna zuwa likita mace ce muka samu tace ina bukatan bedrest a lokacin nan nima aka kwantar dani asibitin.
Dole rabin yan uwa suka dawo gare ni barci ya dauke ni mai nauyi sosai har ban san inda nake ba ma.
Da kyat aka samu baba ya farfado tana kiran Ahmed Ahmed ka cuce ni wallahi ka cuci iyalina Ahmed.
Nan sadauki yake cewa haba Baba yi hakkuri a samo lafiyan ka tunkun na koma may nene please.
Sagir ne ya jashia gefe daya can kusurwan gadon da Baba yake kwance yace yaya sadauki baka san may ke faruwa bane ko ?
Yace may kuma ya faru ne Sagir ?
Sagir yace wai yaya Ahmed ya sayar da gidan mu shine ya jawowa Baba wanan matsalar haka.
Cikin wata murya sadauki yace what Ahmed ya sayar da gida fa kace nan dai Sagir ke fada mai duk yadda abin yake don a gaban idon shi akai komai.
Yace mai gidan yazo da bukatan yana son a kwashe a bashi gidan shi don wa,adin aka bayar ya cika.
Innalillahi sadauki yace may yasa Normal yai wanan mugun aika aikan haka da lafiyan shi kuwa ?
Waye ya sayi gidan ya tambayi Ahmed cikin dago kai da idanuwan shi suka kada sukai ja a lokaci daya.
Nan Bashar ya shigo yanayin da ya gansu ne ya tayar mai da hankali ya karaso yana fadin may ke faruwa ne kuma man ?
Yace humm bari kaidai man wani sabon labari nake ji wai Normal ya sayar da gidan baba ga wani mutum.
Yace what da dan karfi yace no warder ake ce min yanzu anga yana bushasha da kudi ya samu lafiya.
Kai amma guy din nan baiyi ba wallahi wanan ne ya jawo wa Baba matsala ke nan ko ?
Bai bashi amsa ba sai cewa yayi yaya ita Fatima din kuma take yanzun ?
Yace itama an bata gado tana bukatar bedrest wai sukace .
Yace o my god wata sabuwa kuma again Allah gamu gareka yace a zuciyar shi amma a fili cewa yayi tana ina yanzun kuma ?
Tana gany room a can suka kwantar da ita har tayi barci shine na fito zuwa nan don gaskiya tana jin jiki sosai wallahi.
Sai da yaga komai ya saitu wa baba ne ya fito zuwa dakin da nake kwance ina barci maryam da Nafisa sun sakani a gaba suna kallo na.
Shigowan shi yasa suka juyo suna kallon shi tare da tambayan shi jikin bana yanzu.
Yace masu ya farfado idanuwan shi a,kaina ya kura min ido ina barci cikin wahala ga ruwa daure a hannu na lokacin.
Takowa yayi zuwa bakin gadon ya dan tabo fuskana ban ma san yanayi ba don nai barci sosai.
Ya dade a tsaye baiyi magana ba ya juya tafita daga dakin ya nufi gurin Baba shima barcin yakeyi yasa shi fitowa don likita yace kada a shiga dakin abarshi ya huta haka yasa akabar su mama da umma da mummy kawai.
Fita sukayi daga asibitin shi da bashar bai mashi magana ba shine dai ya karbi key yajasu barshar din.
****** ********* ******
Ina muka nufa yake tambayan shi kai tsaye yace kaini gidan Normal please inji daga bakin shi.
Sai gidan yaya Ahmed bashar ya tsaya suka fita gidan yana a rufe amma akwai mutum don kara kidan disco daya karadw erea din a lokacin daga gidan.
Nocking din kofan gidan sukayi kusan sau uku kamar baza,a bude ba can jamila tabude kofan gidan.
Tana cikin wani matsatsen wandon jeans da ya matse ta da wani dan riga ja mai guntun hannu a rubutawa rigan crazy girl.
Tana ganin shi ne tace up UF yau kaine gidan da kanka cikin wani yanayi na farr da idanuwan ta.
Yace mai gidan fa a taice ?
Baka ma bari mu gaisa sai tambayan dan uwaka watau shi ka sani kawai ko ?
Yace please ina Normal yake nake tambayan ki ?
Normal kan baya kasan ya tafi kwatano dauko mota tabashi amsa ganin da tayi ba wasa a fuskan shi.
Ok kawai yace ya juya yabar gurin bashar yabi shi a baya mota suka shiga suka bar unguwan .
Baiyi magana ba da suka fara hanya sai sa hannu yayi ya dafe goshin shi da hannun shi daya kawai.
Zuciyar shi tana mai wani irin suya don bacin rai hankalin shi a tashe yake lokacin.
Bashar ne yace yanzu kamata yayi mu nemi mutumin mu fara jin yadda sukayi dashi first.
Yace wa yasan mutumin sai bashar yace bari mu nemo Sagir ko yasan labarin mana ?
Asibiti suka dawo har looacin Baba yana kwance sharkaf dashi sun dan dade a kan shi ba wani motsawan da yakeyi sai dai numfashi kawai da zai nuna ma yana raye.
Fita yayi ya kira yaya Imiran da Sagir din shima Abdul ya biyo bayan su dashi da bashar.
Yace wani mutumine ya sayi gidan baba din hannun Normal Sagir ?
Gaskiya ban san shi ba sai dai ina gani a GRA kamar nake ganin motan shi idan naje gurin aboki na dake can.
Abdul daga bayan su yake cewa wanan guy din da suka zo dazun yace eh shi yace dan masani ne mana guy din nan mai sayen gidaje dake GRA ko ?
Mota biyu suka tafi dashi gidan mutumin sai dai baya nan ance masu yafita cikin gari .
Yanzu yaya kuke ganin zamuyi ke nan ?
Bashae yace lauya zamu fara nema mana shine farko don nasan dole abin sai ya hada da lauya ai.
Wani lauya kake gani duk garin nan zamu iya samu ya tsaya muna kan wanan magana don ba karamar case bane fa ?
Nan suka fara kawo sunayen lauyoyi da suka san cewa yakai lauya da zai iya tsaya masu karshe dai suka tsaya akan barister Nuraddeen mohammed moroki dake zama a gusau zamfara state.
Shine zai tsaya masu a matsayin lauyan su matashine wanda yasan aikin shi da sanin darajan tallakawa akan aikin shi sosai.
Sun samu lamban lauyan inda suka kira shi tare da mashi bayanin komai dake faruwa shima yana tambayan su wasu abubuwan da ya dace ya sani daga cikin maganan.
Haka aka shigar da kara a koto ranan basai ma gari ya waye ba don da zafi zafi ake buga karfe.
An aikawa dan masani da sammacin sayen gida ba bisa kan kaida ba a hannun dan maigida da yayi.
Yana karantawa yai dariya yace shi may ye nashi sana,anshine ba yau aka fara irin wanan ba ai Allah ya kaisu kotun lafiya.
****** ********* ******
Falkawana yai daidai da su Mama suna dakin lokacin ma magariba ya gabato sosai na bude idanuwa na a hankali.
Sai naji suna sannu Fatima yaya jikin naki nace a hankali da sauki na daga ido na kalli gurin daki ne na asibiti ashe nake ciki a lokacin.
May ke damunki yanzun Fatima mummy ta tambaye ni ?
Da kyat na bude baki nace mata juwa nake ji tace bari a kira likitan ya dubaki.
Likita sun dawo tare da su yaya nan suke gaishe mu likita yace su dan rage daga dakin nan aka barmu ni da yaya da likitan kawai.
Bayan yan tanbayiyi idanuwa na suna a lumshe yai yan rubuce rubucen da zaiyi ne yake cewa dole sai nayi bed rest a cikin asibiti don yana gani baby dake jikina yayi weak sosai zai iya fitowa indan an matsa mai wanda hakan babban hatsari ne sosai gare shi.
Idanuwan shi ya runtse tare da tausaya ma halinda nake ciki lokacin nan dai aka yanke shawaran zan zauna asibiti har wani lokaci a gani.
Iyya Rabi ce zata zauna a tare dani don dama tare muke itace ke ta fama da lalura na ko a gida.
Hankalin kowa a tashe don yadda baba yake matukar jin jikin shi ko matsi bayayi sai na,uran taimako da,aka saka mashi ke aiki.
Zancen karan da akayi an tsayar da magana dole sai anga Ahmed anji ta bakin shi za,a,san yadda za,ayi.
Gashi har lokacin bai dawo garin ba kullun akaje gidan baya gari Jamila take fadi.
Ashe ta dawo ya samu labari gurin wani abokin shi shine yake boyewa kada su ganshi.
Sai dare sosai yake komawa gida ya kwanta tun da safe ya bar gidan ya koma maboyan shi ya boye.
Duk wani dan gidan hankalin shi a tashe yake yadda baba ake hasashen ya samu faralazy ne barin shi guda na dama.
Gashi har zuwa lokacin yana unconscious bai san inda yake ba sai cewa likitoci keyi akwai improvement ga lafiyan shi.
An yanke shawaran za,a fita dashi waje wani abokin sadauki likita yace a kawo shi gurin su su duba shi a Germany.
Komai an cika na tafiyan su waje da baba lokaci kawai ake jira na fita da mummu kawai sai shi sadauki da,Sagir aka shirya tafiyan da za,ayi.
Ina zaune Iyya tana tsaye a kaina ta wade min lemo zan sha ya shigo dakin zai min sallama.
Tana ganin shi ta fara gaudashi tare da mashi yaya maijiki yace Alhamdullahi Iyya zamu tafi yau da,daren nan lagos gobe da safe zamu daga dashi.
Iyya tace kai duniya gaskiya wanan yaron wallahi bai kyauta muna ba wallahi wanan sallon yaudaran nashi yayi yawa ina zai kai alhakin wanan bawan Allah da,sanadin shi ya mayar haka ?
Ya tako zuwa inda nake ina tsotson lemun da Iyya ta wade min a hankali yace yaya jikin naki Fatima ?
Nace naji sauki yaya yaya jikin baba din yake ya dan lumshe idanuwan shi a hankali yace yaji sauki yau insha Allahu zamu tafi.
Ki kula da shan maganin ki Fatima kin dai ga yadda kike fama ban how long zaki yi ba anan yadda likita yai min bayani zasu dan rike ki suga yadda jikin naki zai kasance kafin su sallamay ki daga nan.
Idanuwana na lumshe ina jin wani ba dadi yace naso mu aikawa mutanen gida don su san halin da kike ciki amma maji ta hana tace kada mu tayar masu da hankslin su suma.
A bari har aga yaya jikin naki zai kasance tukun sai a fada masu amma ni naso su sani kila za,a samu wanda yazo daga can ya zauna dake.
Shiru nayi ban da ta cewa sai dai naga aiko yayane ya kamata a basu hakkin su a matsayin su na mahaifa na.
Don idan sunji bazasuji dadi ba daga baya sai dai banda yadda zanyi don ban da tacewa ni yanzu.
Muna tare muna hira jefi jefi dashi wanda na lura bai a cikin hankalin shi a lokacin.
Yace zai tafi gida ya shirya ya bar zancen makarantan Sa,ade a hannun bashar yana ganin zuwa wani Monday za,a kaita makaran ta.
Musa ma Bashar zai kula da zuwa mai visiting kamar yadda ya saba zuwa mai.
Nace na gode a hankali ya mike yace zai tafi ya dawo idan ya kimtsa nace Allah ya tsare ya fita.
Da yamman ne wani abokin bashar ke fada masu cewa yaga yaya Ahmed yana garin don sun hadu dashi da rana a,wani shago yana sayayya.
A gida kuma mama Asiya da yan uwanta suna cikin matukar tashin hankali sosai don tana gudun wani abu ya faru da mijinsu a sanadin dan ta.
Wanda tasan ba zasu yafe mata ba don halin da danta ya jefa gidan ko yanzu bata da shakata a gidan kowa sai zagin su yakeyi tanaji tana gani babu yadda zatayi akai sai hakkuri.

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BAKI GA ALLAH YA SAKA MUNA AKANKI YAR UWA,,,
Ya dawo acikin shirin shi ina kwance Iyya tana kokarin fita da ta gan shi yace, Iyya ni zan tafi don Allah mutumiyar ki a kulla da ita sosai naso ace ina garin don na bata kullawa sai dai hakkan baisamu ba.
Nasan ban da matsalar hakan don ke da maji kuna kusa da ita bana son tana wanan rashin cin abincin da batayi yana matukar damu na sosai ko ba dadi abata koda kadan ne please.
Iyya tace uban dakina kada ka damu tsakani da Allah nake zaune tare da ku zanyi wa Fatima duk abinda kasan zan iya yiwa yar cikina shi insha Allahu.
Ya ciro kudi masu yawa yabata yace ga wanan ki rike a hannun ki ku dinga lalura dashi a nan din.
Tai mai godiya ta fita daga dakin ta barmu mu biyu dagani sai shi a dakin.
Isowa yayi inda nake kwance yana cewa na,shirya zamu tafi yanzu bakin gadon da nake kwance ya zauna ya kamo hannuwa na.
Yana fadin Fatima don Allah ki kula da kanki ki tausayawa abinda ke a jikin ki please.
Idan baki ci abinci ba yaya zaki samu kuzari har baby na ya samu shima please ki tausaya min ko ba dadi ki dan dinga cin yan abubuwan gina jiki don kuzarin ku.
Kune rayuwana Fatima kune zan kalla nayi farinciki don kune jindadin farin cikina.
Nasan bakya jin dadi amma ki kara tausayawa kanku please badon ni ba for the sake of our baby please.
Idanuwa na na dago sun ciko da hawaye nace yaya ina son ci amma ko naci din fitina yake zama min nai ta amai sai na fitar da abinda naci nake dan samu lafiya.
Ya dora kanshi saman goshina ta yadda muke iya shakan nufashin junan mu.
Yace sorry my baby nasan kina wahala wallahi dada halin karban ciwon nan a hannuki da na karba maki kin huta ke ma.
Hawayen da nake dannewa ne suka silalo daga idanuwana a hankali.
Yasa hannu ya goge min yace ko bakya son na tafine Fatima?
Sai na barsu mummy da sagir su tafi su kadai na zauna nai jinyanki da kaina.
Nace cikin kada kai tare da bude bakina da kyat nace no yaya Baba yafi bukatan ka a hanlin yanzu.
Tausayin ka kawai nake jin irin yadda rayuwa yazo muna cikin wanan dan kankanin lokaci haka komai ya jagule a lokaci daya.
Yace cikin dan murmushi tare da rugomoni zuwa jikin shi da kyau yace duk bawa yana da tashi kalar jerabawan a kullun don haka wanan wani sabon gwajin Imanin bawa ne yazo muna.
Ki kula da rayuwan ki don likita ta fada min kina matukar bukatan hutu sosai saboda kalar mahaifan ki ba mai daukan wahala bace haka.
Nace insha Allahu yaya zanyi yadda kace Allah ya tsare min kai a duk inda kace yace amin cikin dadin rai.
Yace Fatima wanan baby ya wahal da maman shi da yawa udan yafito ashe bazan yi punished din shi ba kuwa?
Dariya nayi dama shi yake son ji gare ni kafin ya tafi nace ni har cewa nake a cire min shi na huta wallahi.
Sai naga ya sake ni ya lame kwance saman gado yana fitar da numfashi tare da furzo iska daga bakin shi.
Yace Fatima ko bakya son nawa ne da gaske da har kika iya furta wanan kalman haka a gabana ?
Nace haba yaya kaima ai kasan ina son ka wahala dai ne yai min yawa wallahi yaya.
Yace to kiyi hakkuri please ki haife min shi nai maki alkawari baku kyakyawan kulla dake da ko maynene a tare da ke insha Allahu nace naji yaya.
Kudi ya ciro masu yawa yabani yace karbi wanan ki boye a gurin ki don ban san abinda baya zai yi ba.
Nace ni may zan saye anan wanda akace zai kwana biyu a cikin asibiti yace karbi dai ki rike a hannun ki in case zai maki amfani.
Ya rugomayni na dan tsawo lokaci ya mike yana cewa zamu tafi nima kokari saukowa nake daga saman gadon da nake kwance.
Ina kuma zaki tafi na dan marairaice nace ina son ganin tafiyan baba ne yaya.
Ido ya kura min kamar zaiyi magana sai kuma ya mika min hannun shi alaman nazo mu tafi tare muka fito bayan na saka dan silifas a kafana tare da saka hijjib dina.
Tare muka fito daga dakin yana rike da hannuna nan naga kowa na gidan mu yana gurin maza da mata manya da yara.
Idanuwan su akaina har muka karaso suna gaisawa dani bai saki hannu na ba har lokacin muna tare muka shiga inda Baba yake kwance harkaf an shirya shi kamar ace ya tashi ya tashi.
Har bakin gadon muka karasa yaya yadan duka daidai kan shi yace Baba ga Fatima tazo tai maka sallama.
Yadan jawonin zuwa kusa da Baba nace Baba Allah ya tsare hanya Allah ya baka lafiya ka dawo cikin mu lafiya.
Ikon Allah sai kawai baba ya dan bude idanuwan shi a hankali wanda sunce ya kwana biyu bai bude idon shi ba.
Yana bin mu da kallo a hankali na kara cewa Baba Allah ya baka lafiya ka dawo ka dauki jikan ka da hannun ka.
Sai ya dan sake murmushi a hankali wanan yasa kowa dake gurin jin dadi sosai har likitan dake tsaye yana gyara shi yace gaskiya da za,a samu irin wanan da yake so a tare dashi ko yaushe za,a samu improvement sosai ga lafiyan shi.
Nace muyi addua kafin a wuce nan na gyara na dinga kwararo mashi adduoin samun lafiya ana karbawa da Ameen.
Muna tsaye aka fito dashi aka saka shi a ambulance din asibiti zuwa airport.
Sai da aka rufe motar yaya ya dawo har inda nake bai damu da,wai mutane suna gurin ba yai hugging dina a jikin shi yana dan bubuga min baya kamar yana lalashi na tace be strong Fatima Allah ya baku lafiya.
Ya juya ya tafi kowa sai kuka yakeyi don yadda aka fita da baba ko mutum baida Imani sai ya tausaya mashi.
Da gata na kwato bawa daga hannun Alah da gata ya kwato Baba cikin wanan halin rayuwan da yake ciki a wanan lokacin.
Gaba daya diyan shi yan uwanshi abokan arziki jikoki saraikai duk suna gurin tsaye cikin tashin hankali a lokacin.
Rahama tana gurin da iyayyenta a gaban idon ta komai yafaru tana kallo.
Wani kishi ya rufe mata idon ta don ganin yadda yaya yake wani jiji dani kamar diyar wata da wani.
Tace sai tayi magani na sai ta mayar da wanan son tsakanin mu ya koma kiyayya watarana a cikin ranta take zancen ta.
Uwarta ma kishine ya rufe mata ido suna hanya take magana cewa jifa yadda yaron nan yake wani jiji da yarinyar nan.
Ai don dai baki tare dashi ne idan kina gidan wane ita yar talkawan tsiya kawai.
Baban yace ai barshi da gaiyya zan daura masu aure inga yadda zai yi da ita idan nakai mashi ita gidan shi.
Muna kallo suka fice daga asibitin suka barmu nan aka fara watsewa daya bayan daya ana mai fatan samun lafiya.
Na kalli duk taron nan watsewa zasuyi su tafi su barni a cikin asibitin ni da Iyya kawai .
Sai naji wasu hawaye sun zubo min Nafisa ta kama min hannu tace kada ki damu matar yayana Allah na tare da ke.
Tare da ita muka koma dakin da nake bayan nayi sallama da mutane mama da maryam da mijinta ne suka biyo ni zuwa dakin.
Sun dan jima a gurin mu sukace zasu tafi sai dai da safe idan sun dawo kuma insha Allahu.
Nafisa tace ita yau a gurina zata zauna mama ta zaci wasa takeyi sai da tace Allah maji yau a nan gurin Fatima zan kwana na debe mata kewan yayana.
Nan mama ta tafi tabarta sai dai mama bataso haka ba don tasan halin Nafisa na watsewa.
Amma batai komai ba wallahi sai hiran da mukeyi akan matsalan baba kawai da zamu kwanta ta hau dogon kujera iya tasa bargo a kasa ta kwanta sai safe.
Washe gari da muka tashi Nafisa bata tsaya an kawo abin karyawa ba ta wuce gida.
****** ********* ******
Sun isa Germany da baba lafiya an kuma duba lafiyan shi har ana samun sauki sosai suna isa yaya yake kiran layina tare da tambayana karfin jikina.
Ganin an wuce da baba yasa yaya Ahmed fitowa daga maboyar shi ya na komai nashi normal.
Sun buga suna fadawa sadauki fitowan shi yace abar case din har ya dawo don kotu ta fadawa dan masani cewa bai da hujjan tayar da maigida a gidsn shi sai ya samu lafiya an yi sharia.
Sadauki baya son ayi maganan kan zancen sayar da gidan nasu na gado da akayi duk da zancen ya karade gari anji labarin abinda Ahmed yayi wa mahaifin shi.
Mama Asiya hankalinta yai matukar tashi yadda taga kowa gidan ya tsane ta ita da danta.
Don laifin Ahmed ya shafe laifin duk wani laifin yaron dake gidan gashi Alhaji bai ko yarda ya gaisa da ita a waya.
Ko yana waya akace ga mama zata gaida dashi zai kashe wayan yaki dauka.
Balle ga mummy kusa abin nema ya samu dama ba shiri a tsakanin ta dasu ko kadan.
Duk da baba yana asibiti cikin halin lahulai amma idan mutum ya shiga gidan zai ga kamar hankalin su a kwance yake.
Irin yadda suke busha shan su agidan ba wani damuwa a tare dasu a lokacin.
Ga wani shakuwa da yashiga tsakani na da Nafisa yanzu don ko wani lokaci tana gurina a asibiti muna tare.
Wani lokaci anan kawayen ta ke samun ta nan zasu wuni suna debe min kewa.
Banda matsala dasu wani lokaci idan suna hiran busha shan su a gabana nakan ce haba anty kamata yayi ace cikin maneman ku ku cafke daya ku aura.
Nura kance ke kaunata nifa mijin ki nake so na aura nakance aiko danaji dadi anty idan har zakiyi aure ki zauna ba sai mu zauna lafiya ba.
Kin sanni na san ki kinga ba fada a tsakanin mu sai so da kauna mu rike mijin mu tsakani da Allah.
Nuriya wallahi idan kina wanan maganan zamu sami sabani sosai wallahi Raiha ke fada mata haka duk lokacin da tai irin wanan magana.
Nafisa kuma takance may zaiyi da honko haka may ya rage jikin ki baya cus kin sha burga kamar rijiyar kwakwara da ke.
Nace ba komai zamu gyara ko anty Nura ai mace mai gyara bata baci ko ?
Raiha takan sha toka tace please abar wanan zancen bata so su ko watace sukaji mijina yana nema sai inda karfin su ya kare akai.
Tace Fatima kin muna fa wata matar aure ce zata sake jiki damu haka abinda ake gwada muna kyama keko kin muna rikon tsakani da Allah kamar wasu yan uwan ki naji fa kika mayar damu.
Yan uwan mu ma naji yanzun haka basu hurda damu don kaaai wanan halin da muka tsunci kan mu a ciki.
Mutane suna manta cewa ko su Allah yana iya jarabtan su a kan haka?
Duk lokacin da ya tashi yin ikon shi a kan mutum na tabbatar da yan gulma suna fadawa mijin ki kina hurda damu haka amma sanin koke wacece yasa bai damu ba duk dai yana halarci ne akan yar uwar shi dake cikin mu amma duk da haka Fatima kunyi muna wallahi.
Nan zamu wuni da su ai ta shiririta suna matukar bani tausayi ina yi ina masu gyara.
Yau ma sunzo mun jima muna hira dasu sosai har barci ya kwashe ni na barsu da Iyya suna hira sun sayo nama mai zafi da drinks sun baje suna ci.
Amira ne tashigo dakin da nake kwance wanda yanzu ya zama min dakina na komai.
Suna gaida ita amma,sai wani basar dasu takeyi sukaci gaba da harkan su kawai.
Bakin gadon da nake kwance ta karaso tana tayar dani daga barcin.
Iya da Raiha ke cewa haba kin san tana son hutu barta mana tai barcin ta kada ki tayar da ita.
Tace waye zai hanani tayar da ita Rabin dan musa ko wa wai takai hannu ta tabani na bude idanuwana.
Ina kallon ta nace anty kin shigo ne ashe tace a wulakance may wa yan nan sukeyi a nan ne haka ta nuna su a wulakance.
Sai sha,anin su sukeyi kamar basu san da ita ba afurin ko tanayi ma ba wanda ya kulata.
Na dan kakaro murmushi a fuskana nace anty kawayen anty Nafisa ne fa.
Tace and so what Nafisan may can kuma wai kinga bani son na kara ganin su a tare da ke kinji na ffada maki ko?
Tace sai dai ban sani ba ko kema harkan taku dayane dasu don banza bai kai zomo kasuwa.
Wasu hawaye suka zubo min nace haba anty cin fuska baida kyau haka wani abu mukeyi banda mutunci da zumunci kawai.
Tai mun wani kallon wulakanci tace zaki gane wallahi Nafisa tace Amira wallahi yadda kike da Fatima nima haka nake da ita don haka baki isa ki rabani da ita ba don bakece kika hadamu ba.
Tace yanzu ko da yake ba mamaki tunda naga yazama dan uwanku don abin hannun shi ai.
Tajuya tare da yi min wani kallon mamaki na wullakanci tafita daga dakin.
Tana futa tun a haraban asibitin ta kira dan uwanta cikin fada take mai batanin karya da gaskiya.
Yace Amira badai zuwa kikayi kika tayarwa Fatima da hankali ba tana fama da kanta ba nan tace don may zata dinga tara wa yan nan yan iskan haka tare da ita.
Yace kin san halin Fatima fa Amira bazata taba bari tayi wani abin asha ba insha Allahu a rayuwan ta.
Kuma ai don Nafisa suke zuwa tace min nafusa ko yaushe tana gurin ta tana debe mata kewa ke da baki son su zo may yahana ki tare a gurin su.
Lalai ma yaya dama ba yau ba nasan cewa Bintu ta gama dakai gaba daya baka son a fadi abinda tayi don ta shanye ka.
Baiyi magana ba don ranshi yakai kololuwar baci mama ya kira yana fadin daga yau kada Amira ta koma gurin mamatata don bata san zafin ta ba.
Don may zataje ta tayar mata da hankali bayan ta san irin yanayin da take ciki likita yace a bata hutu.
Kai wai may ke faruwa ne haka wai nan dai ta kwashe yadda sukayi da Amira ya fadawa mama komai.
Mama tace ji mahaukaciya kawai Nafisan da koda Fatima ke a gida tana nan like da ita ko yaushe a dakin nan.
Ko ranan da kuka wuce fa a gurin Fatima Nafisa ta kwana tace bazata dawo gida ba zata tsaya ta debe mata kewa.
Yace balle zaman Nafisa da fatima Allah ne ya hada su ai maji.
Mama tacs kuma tun yayatana fada har ta gaji yanzu ta daina ta saka masu ido tsakanin su don waya sani ko hakane zai zama silan shiryuwan ta ma ?
Nan dai sukayi magana sosai ta kashe wayan tana jiran dawowan Amira gidan.
Mummy dake kusa dashi taji fadan da yakeyi tace kai Amira ma dai ita fa bazata iya tsayawa tayi yadda ya dace ba Fatima da yanzun take son wai raba tsakanin Nafisa da Fatiman.
Zaman Fatima da Nafisa fa yakawo sauyi sosai yanzu a rayuwan Nafisa fa don yanzu kan zaman Fatima a gida zata iya kwana barkatai bata fita waje ba.
Aiko wanan abin sai ace abune na dubawa sosai wallahi tabar irin wanan cin fuska haka baida kyau ga dan adam wallahi.
Baba ta najin su wanda yanzu bakin shi ya dan fara budewa yake cewa Fatima Fatima ai alheri ce a cikin zuria ta wallahi.
Amira na shigowa gida zata fara fadawa maji mama tai cikin ta da fada sosai har sai da ta raina kan ta a lokacin.
Ta shige tana cewa indai kan Bintu ne wallahi bazan sake saka kaina ba a al,amarinta da yardan Allah kuwa tashige ciki abinta.
****** ********* ******
Amira na fita wasu hayen bakin ciki suka zubo mata nace yanzu ni may laifina kuma?
Idan naki Nafisa kuma zagina za,ayi ace bani son dangin mijina balle ni Nafisa tsakani na da ita yanzu sai hamdala kawai.
Duk da ta girmay ni amma idan nai mata magana takan daina abinda takeyi a lokacin.
Amma may zai sa Amira tace wai kila harkan mu daya dasu bayan ta san koni wacece takuma san halina din.
Yayan ta ma ya ganni dasu bai ce komai ba don shine ta jawota gare ni .
Allah sarki yaya sadauki mutumin kirki mutum mai adalci wanda ta san ya kamata .
Muryan su naji suna fadin sister indai don muna hurda dake zamu jawo maki matsala zamu daina zuwa gurin ki gaskiya.
Nace akan may anty wanda ya ajeni baiyi bakin ciki da zamana da ku ba sai don anty tazo da wani zancen ta can na daban.
Nace ba inda zaku idan dai ba maigidan da kanshi yace min bai son hurdana da ku ba.
Wayan shi ne ya shigo a lokacin jin ina kuka yasa shi cewa Amira tazo ta bata maki rai ko?
Yace ina Nafisa take nace mai gata nan yaya yace bata waya na mika mata wayan nace yaya yana magana da ke anty.
Ta karbi wayan daga hannu na yan uwan suka tsura mata ido don son jin may zai fada mata a lokacin.
Mun dai ga tana cewa ai ba komai yaya duk abinda tai min yar uwata ce ita tace ba komai komai ya wuce ai don badon ta muke zuwa ba ai dama.
Sukai sallama ta miko min wayan ya tambayi jikina nace naji sauki ni so ma nake a sallamay ni na koma dakina wallahi.
Yace sallama Fatima likita yace min sai kin haihu zasu sallamayki fa don bazasu bari ki fita asibitin nan ba hakana.
Banji dadin wanan zancen ba ina cikin asibiti har tsawon wani lokaci ni wani irin ciki ne dani haka wai ?
Gashi muna batun fara exam haka nake karatu a asibiti sai idan lokaci yayi zasi yarda na tafi na zana koshi tare da wata nurse zamu tafi suka ce.
Yadda suka fada ko hakane haka zan shirya da safe yaya bashar yazo ya dauke mu zuwa school dani da,wata nurse da aka dauka haya don dubani ba dama nayi wani dogon motsi dana gama zamu juyo zuwa asibiti tare da ita a sauke mu.
Bai tafiya gida sai yaga anbani magani na kwanta zai bar asibitin har na kare exam dina da mukayi.
Gaskiya yaya bashar mutum ne don yana bani duk wani kulawan da ya dace wanda zai sa banji kewan mijina ba gurin kula.
Haka zai kawo min maryam mu wuni da ita muna hira sai dare sanan yazo ya dauke ta.
Mama ma takanzo sosai kuma abinci dare da rana yana saman hanya ana kawo muna duk abinda muke so.
Ba laifi don yanzu da cikina yake wata shidda da yan kai saura kiris ya cika wata bakwai ina dan iya cin abinci kadan.
Sai dai ba mai yawa ba don idan har naci mai yawa ranan sai na fadawa aya zaki gurin wahala.
Haka dai nake zaune Iyya tayi min halarci matuka a rayuwan na don komai itace ke min shi iyakana naiwa kaina wanka kawai.
Bayan shi duk wani abin bukata na itace mai aiwatar dashi da kan ta zatai min komai.
Yan uwa sai faman zarraiya suke zuwa gurina duba ni zuwan Baba na biyu yana duba lafiya na a,asibitin.
Haka ma a bangaren mamana saida sukayi mota daya ita da abokan arzikin ta da yan uwa sukazo duba ni.
Don haka ban da wani damuwa a tare dani sai na kadaicin mijina a kusa dani kawai zance yana damuna.
Acan ma Germany ya wuce gurin buga wani wasa da akayi mai zafi inda kuma team din su na basilona da yai ma,wasa yai nasaran lashe wasan da suka buga.
Ba karamin kudi ya kwaso ba sai dai bai dawo gida ba ya koma gurin su baba asibiti.
Baba yanzu ya dan samu lafiya don likita yace zasu iya dawowa dashi nan da sati biyu masu zuwa idan an tantance lafiyan jikin nashi da kyau.
Sai kuma ga,wasa ya taso mai zai tafi arabian kingdom ya bufa,wasa wanda ake tsanmanin zasu samu makuddan kudi idan har sunyi nasara ga wasan da zasu buga.
Jirgi ya samu ya kammala komai akan tafiyan su Mummy da baba sai yaya sagir da zasu dawo gida.
Ya basu kudi kowa ya sawo tsaraban da zai zo gida dashi inda,zasu dawo tare suka fita dashi ya kaisu sukai sayayya inda yaya sagir ya kwaso laptop da kudin shi zaizo dasu ya,sayar itako mummy kayan yaranta da,wasu abubuwan anfanin ta ne ta sayo acan kasan.
Ranan da zasu dawo kowa yana cikin farinciki da dawowan su gida anshirya ma dawiwan baba din sosai yanzu.
Muna asibiti labarin dawowan shi ya riske mu sai dai ance bari dayan baba bai aiki gaba na ne ta yanke yafadi ras.
Amma Rukaiyya tace min sai dai gaskiya idan kin ganshi ya samu lafiya sosai wallahi.
Tun bayan fitanta nake jin marana yana dan yanka min kamar zanyi period nake ji.
Sai ban damu ba don nasan tunda ina da lalura mai zai tayarwa kaina da hankali dashi.
Wasa wasa ban daina ji ba har cikin dare sai barci ya gagare ni ina kallon iyya da ta samu barci tana barcin ta hankalinta a kwance abinta.
Jin mara din ya matsa min ne na mike zaune aiko zama yace bai sanni ba can da naji wani iein ciwo na sauko na kama karfe gadon na dan nisa tare da murde bakina don dan zafin danaji a lokacin.

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YA SAKA MUNA,,,
Kukan dan jarin da ya fado ne ya saka Iyya dake kwance dan bude idon ta a hankali.
A lokacin da nake fadin Iyya Iyya tashi ki gani abin cikin cikina ya fito Iyyah ko na haihu ne ?
Tamike tana fadin subbahanallahi ikon Allah uwar dakina kin sauka ne ?
Sai kuka yaron dan karami dashi sosai yake tsalawa duk Iyya tabi ta rude taje inda ake kunna wutan dakin ta kunna tana cewa.
Kinko haihu wallahi uwar dakina amma sai dai killa bakwaini ne kika haifa don yaron yai kankanta da yawa.
Ta dan taba yaron yakara tsala ihu tace namiji ne sai dai bakwaini ne da sauri tafita daga dakin zuwa inda nurses suke kwana ta kira su.
Sai gasu da saurin su sun shigo tare da ita taimakon gagawa suka fara ba yaron nan suka rabashi da uwar tafiya Allah yasa akwai reza da na anty Raiha ta sayo min sai ta sayo parked din shi gaba daya.
Dayar nurse din taje dakin doctors takira likita mace wacce tai adimin dina a,asibitin ranan ita ce akan duty.
Tana zuwa ta danyi dube duben da zatayi ta tambaye ni banjin komai na fada mata komai bana ji.
A cikin daren akaiwa yaron wanka nima nai wanka Iyya tace a kira gida ne a fada masu nace tabari harda safe sai a kira gida don yanzu kowa yayi barci hankalin su zai tashi tunda ina lafiya.
Sosai likitan taita gwada yaron tace min lafiya yake sai dai premature baby ne idan da rabo zai rayu insha Allahu.
Nace daga inda nake zaune a bakin gado anty zai rayu kuwa ?
Tace insha Allahu zai rayu ai seven months ne yanzu kike da kwana biyu.
Sai dai da,safe zan so muyi shawara muji idan zai yuyu sai a dan saka shi a kwaba yadan kara tasawa tukun.
Bamuyi barci ba sai da,asuba muka dan runtsa kadan shigowan nurse din dakin ya,samu falkawa Iyya ta tafi sallah ni kuma ina kwance ina kallon yadda sukewa baby din.
Bakwai da yan mintina Iyya tashigo dakin nace ta bani wayana , numban mama na fara kira har ya kusa tsunkewa ta daga da,sauri ba ko gaisuwa hankalinta ya daga don ta ga ban kiran ta da farar safiya irin haka.
Tace Fatima lafiya dai ko ?
Nace a hankali mama na haihu ne.
Cikin wani murya tace kinyi may fatima nace na haihu ne mama.
Sai naji ta kashe wayan maryam na nema tana barci wayana ya tayar da ita na fada mata na haihu sai Nafisa.
Koda na kira nafisa ina jin muryan mutanen gida a na yaya nasan zancen ne mama ta fada masu a lokacin.
Kafin wani lokaci naji kiran sadauki ya shigo yace batare da gaisuwa ba Fatima is that true o you are joking yanzu bashar ya kirani.
Kafin na bashi amsa yaron da nurse din ta daga ya dan yi kuka na kara mashi a waya yaji.
Yace it means yaron yana da rai har yanzu ke nan nace mai eh kawai sai aka turo kofa su mama ne da mummy da mama Asiya suka shigo dakin a rude.
Idon su akan nurse din dake shirya yaron za,a kaishi pediatric asaka a kwalba.
Gurin nurse din suka nufa suna kallon yaron dan karami dashi a cikin zani na da aka nade shi.
Muna kallo suka fita da yaron mummy da,su sagir suka bi bayan su harda mama Asiya.
Sai lokacin mama ta karaso inda nake zaune a bakin gado take cewa Fatima lafiya dai kike ko ?
Na kakaro murmushi don hankalina a tashe yake nake cewa lafiya kalau nake mama.
Tace to ki kwantar da hankalin ki idan yaron Allah yayi shi rayayye insha Allahu zai rayu.
Nakoma a hankali saman gado na kwanta na lumshe idanuwa na shigowan su maryam ne yasa na bude idanuwana a lokacin.
Maryam tana fadin tare da,waige waige ina yaron yake maji ?
Tace sun tafi dashi nan tafada masu komai basu tsaya ko a gaisa ba suma suka bi bayan su da sauri.
An saka shi a cikin wani dan karamin gado mai naurori tare da saka mai wani dan rigan sayi a ciki.
Kafin likita ya shigo dakin sun fada min zan tashi daga wanan dakin da muke na gany room zuwa maternity room.
Sai da,aka gyara komai suka mayar damu dakin lokacin yan uwa da,abokan arziki sun cika a dakin ko.
Sai hira ake yayin da niko zuciya na duk a cunkushe yake min ban majin farin ciki ko kadan ni.
Duk da kowa yazo fadin yake ai anyi arziki wata bakwaine insha Allahu zai iya rayuwa da yardan Allah.
Barci ne ya dauke ni a lokacin mai nauyi sai mama Asiya ne naji tana tayar dani wai na tashi na sha tea da aka hada min.
Na mike zaune ta miko min tea din yana wani irin tururi tace na kafa kai nasha shi hakanan.
Har na daure na kafa kai zafi ya konani nai saurin cire bakina daga cup din ga tea din gudan mai yawa dashi.
Lokaci daya suke ce min a,a a Fatima anya kuwa kafa kaifa zakiyi ki shanye shi duka yanzu.
Nace a dan marairaice mama duka fa wallahi akwai zafi mummy tace kin manta cikin ki akwai miki a cikin shi maza shanye shi don Allah kinji.
Haka na shanye tea din ina zufa take naji bakina ya dauki zafin kuna sai dai tea din yana shiga cikina naji wani irin dadi a jikina da nake jina yau kamar banawa ba.
Ban dade ba na koma barci mama Asiya da mummy sukace a dan rage a dakin don na samu barci.
Barci nayi sosai sai zuwa sha biyu da rabi na rana wata nurse tashigo dakin wai na tashi naje naba yaron nono.
Tare muka tafi da maryam da Nafisa da mummy a ka dauko shi na zauna na fara bashi nono sai dai bai iya kamawa.
Mummy ce ta gyara shi da dan kyau ya dan tsosa kadan ya koma barci don ba komai a nonon ma lokacin.
Likita ya shigo yana cewa sannu madam ashe haka abin yazo muna kuma dai.
Allah ya raya muna,shi ga baban shi yace yau yana da ball da mungashi yazo.
Haka muka wuni yan uwa da abokan arziki sai zuwa suke gaishe ni allura akai min sai magani da,suke bani kawai.
Bayan shi ni banda wani matsala a tare danj gaskiya mama ta bugawa iyayyena waya ta sheda masu yadda haihuwan yazo min haka.
Sai dare aka rage a gurin mu inda aka barmu da Iyya sai mama Asiya da tace itama zata tsaya wai.
Nafisa bata bar gurin mu ba sai zuwa sha dayan dare wani yazo ya dauke ta tafi.
****** ********* ******
Bayan kwana biyu da haihuwa ne likita yace zasu iya sallamana na koma gida sai dai zasu bani time da zan dinga shigowa ina bawa yaron nono.
Karfe biyar na safe , tara na safe sha biyun rana karfe biyu na rana zuwa hudu sai shidda na yamma kuma zuwa takwas na dare idan da hali sai na dawo da,sha biyun dare ko sha daya da rabi.
Yaya bashar yace insha Allahu za,a kiyayye zan dinga zuwa ina bashi nono din.
Haka na dawo gidan don da aka bugawa sadauki waya cewa yayi na koma gidan shi kawai tunda ance lafiya na kalau.
Gwagona ta zauna dani tare da Iyya a gidan tana min wankan jego gadai jego ina yi haikan amma babu baby a gida.
Sai time yayi yaya bashar zaizo ya dauke ni ya kaini asibiti aba yaron dake karkashin kulawan likitoci nono ya sha.
Satin mu daya Alhamdullahi yaron yana ta kara murmurewa sosai don yana samun kulawa gashi ba,a barin kowa ya dauke shi sai ni idan zan bashi nono ko ganin shi ba,a bari yan uwa suyi yana ciki a rufe.
Kwanan mu goma da haihuwa yaya sadauki yashigo Nigeria da,tarin arzkin da yasamo a rayuwan shi sosai.
Don andage suna sai yaron yayi kwari sosai zaa saka lokacin yin suna bisa shawaran da likita ya bayar ayi.
Koda ya,shigo sokoto ya samu ina shiri ina jiran zuwan yaya,bashar don time din zuwan mu ba yaron nono yayi lokacin.
Ina saye cikin atamfa zani da riga don nafi jin dadin ba yaro nono hakanan.
Yana rataye da corth din shi a kafadan shi daganin shi a gajiye yake a lokacin.
Direct dakina ya nufo da ya,shigo ina zaune a bakin gado nayi kyau dani don jego ya karbi jikina sosai a lokacin..
Jin shigowan shi dakin ne yasani daga idona na kalle shi shima dai ido ne ya,tsura min a lokacin yana takowa zuwa inda nake zaune.
Sai da ya karaso inda nake nake ce mai sannu da zuwa yaya.
Yace aikece da,sannu Fatima ya kai zaune gap dani yana cewa yaya kike nace lafiya kalau yayana.
Yace yaya baby din yake kuma yanzu nace lafiya yake yanzun ma can zamu tafi bashi nono yaya nake jira yazo.
Yace to na tashi mu tafi tare dashi nace bazaka huta ba tukun yace ina zan huta banga baby na ba Fatima.
Tare muka tafi dashi da yaya bashar daya ja motan ranan an barsu sun shiga don shi.
Shiya fara daukan yaron da muka samu idon shi biyu a lokacin sai watsalniya yake da kafafuwan shi.
Ya dade da yaron dauke a hannun shi yana mashi addua ga sauran yara a gurin kwance suna barci zasu kai su biyar a lokacin.
Mun ba yaron lokaci sosai muna tare dashi muna kallon shi muka aje shi ba don mun so ba muka fito daga dakin.
Haka na dinga zuwa yaya ya na kaini har akai wata daya yaron ya dan yi wayau sosai a lokacin.
An saka mai sunan Baba watau Abubakar an yanka rago da shanu anyi sadaka da naman wa mabukata.
Likita ya bada shawara da yaron ya kai wata takwas akan zamu iya tafiya dashi gida a lokacin.
Ranan da muka dawo gida da yaron naga dan mutum sosai a gidan masu zuwa min barka aka saka suna sati mai kewayowa za,ai taron suna irin na al,ada hausawa musulmai.
Sai faman shirin suna akeyi Jamilan yaya Ahmed da ita ake komai a taron wanda mama ce ta saka ta yin haka dole.
Don su taushi zuciyar sadauki akan maganan gida dake aje a kasa ba,a tayar ba tukun don wanan al,amarin sunan dake gaban shi.
Ranan suna gidan ya cika makil da jamaa masu zuwa taron suna wanda na sani da ma,wanda ban sani ba yazo gurin taron sunan.
Anyi walima sosai tare da ciye ciye da lashe lashe yan uwana sun zo da yawa sosai gurin sunan.
Yan uwan mama ma sun zo da yawan su daga Niger state dasu akai sha,anin bukin sunan yaron wanda muke kira da Amir.
Yai wayo sosai amma gwago bata bari ana daukan shi kamar yadda mukeyi ranan suna duk wace tazo sai ta dauki yaron ta ganshi.
Likita ya hana haka yasa itama gwago ta hana a dauke shi yana gurinta a wani dakin da suke kwance a saman gado.
Duk wace tace ina yaro sai dai ace mata yana lafiya yana can gun kakan shi anyi rabon kayan buki masu armashi da tsada aka saka acikin ko wani jakkan da za,a ba mutum.
Zuwa yamma Nafisa suka shigo gidan da mutanen ta nan kallo ya koma kan su kuma sai gulma ke tashi a kan su.
Kuryan daki suka kutso anan muka zauna dasu wanda hakan yai masu dadi sosai don ni bani nuna masu kyama ko kadan.
Don nasan Allah ne ya jarabce su da yin hakan kuma muna rokon Allah ya yaye masu hakan a rayuwan su.
Basu dade da shigowa ba sai ga tawagan Rahama da kayen ta sun kai su goma suma dai sai a hankali wallahi.
Su ko suna ganin burgewa ne hakan suna jaye da troler har kuryan dakina inda nake suka kutso kai.
Sai dai suna shigowa ganin tawagar Nafisa tab a dakin yasa jikin su yai sanyi akan wulkancin da suka kullo suzo suyi a gidan.
Don sun san gaba da gaban ta wa yan nan yan daban da suka gani sun cuna masu gurin iskanci sau milayan albarka .
Don su basu tsoron ta kwana balle ta bare masu ko kadan sun saba da casa juna a daba ko.
Daya daga cikin su tace ga kayan yaron Rahama nan takawo mai aita saka mai har kala ashirin ba dai.
Daga cikin yan daban Nafisa daya ta cabe da cewa kai amma kuma ta makara don tasamu har uwar yaro da uban yaro sun saya mai kaya na kasan waje masu tsada ba yar sokoto central ba.
Sai ta koma da abinta ko ta samu cikin dangi a basu su suka don shi wanan yaro ko ta sunan shi mai tsadane balle suturan shi.
Ke kuma a suwa gayyan na anya waya gaiyato ki nan yar daba mai arna dubu.
Tace yanzu dani dake aga wanda aka gaiyato wanda ke tsaye ko wanda ke zaune kafin ai haka ashe Nafisa ta mike sai ji mukayi kawai ta kwashe Rahama dake gefe tsaye da mari kayau.
Abin nema ya samu kafin haka su Raiha da Nuriya har sun mike tare da sauran su sai ko daki ya rude da danbe in bakaci bani guri na sudade na bar dakin ina haki nagudu dakin dasu gwago suke zaune.
Take gida ya cika harda maza sunyiwa su Rahama kaca kaca da suturun su duk anyayaga masu shi.
Sadauki yana site din shi mummy takirashi a waya sai gasu gidan yazo a hasale tsawa daya yai masu kowa yaja ya tsaya.
Yace maynene haka wai please may kuke min haka a gidana ne wai wata mata tace muna aha,anin mu na lafiya wai ko yan kungiyar Rahama sukazo muna da fitana duka da zagi da habaici wai gida nasu ne sunzo ne kuma ba,wanda ya usa ya kore su a gidan.
Idon shi ya runtse yana maijin takaici yace ma Sagir dake bayan shi ya kira mai mobil police yace kuma a rufe gida ba inda zasu.
Take tan sanda suka shigo aka kwashe su sai police station aka rufe su kan tuhumar sunkai mai fada a gidan shi sun tayarwa mutane da hankali.
Baba Sani ranan kamar zaiyi hauka gashi ya kira wayan sadauki yafi a kirga amma wayan a kashe take wayoyin shi duk ya kashe su.
Yaje police station ance baza,a bada bellin su ba sai sadauki yazo da kan shi.
Har dare ba wanda yasan inda yake ashe yana can sabon gidan shi da yake ginawa gaba kadan da inda muke duk dai a unguwa daya ne da inda muke yanzu.
Baba Sani yaje gida duk da Baba baida lafiya amma haka yai ta yankar kauna da tashin hankali yana zagin Nafisa da kawayen ta.
Ranan munsha zagi don har dani sai da Baba Sani ya hada ya zage a cikin fadan shi da yakeyi.
Har yayi ya kare ba wani mataki da za,a dauka don ba,aga sadauki ba sai cikin dare lokacin mutane sun rage ya shigo gidan ya wuce dakin shi ya kwanta bayan ya fadawa masu gadi kada a bude wa kowa gidan.
Baba ya zo da wasu makwabtan shi amma masu gadi suka ki bude mai gida.
Haka ya hakkura ya koma da tarin takaici fam a zuciyar shi ba yadda zaiyi.
Asuban farko yazo gidan da masifa inda yake shiga ba nan yake fita ba yana fadin don sadauki na ganin yana da dan hali shine har yake gani zai iya taka kowa ya zauna lafiya.
Dama ba yau ba yasan cewa shi shedanin yaro ne shiyasa al,amarin shi bai mashi ba.
Duk hayaniyar da yakeyi bai san yanayin gidan bai bari a sani ba a banza yake ihun shi a,waje.
Na shirya a cikin wani dogon riga tare da daukan Amir a kafadana muka nufi dakin shi mu gaida shi.
Na samay shi a tsaye yana saka aninin dogon rigar shirt da ya saka a jikin shi jin shigowan mu yasa shi juyowa gare mu yana murmushi a fuskan shi.
Na karaso inda yake tsaye nace yaya na ina kwana yace maman Amir an tashi lafiya ko yaya gajiyan jama,a dai ?
Jama,a sunyi dadi sai dai abinda ba,a,rasa ba kawai da kaje ya dawo na halin taro.
Nace gaskiya yaya jiya banji dadi da kasa a rufe su Rahama ba kuma kai tafiyan ka Baba har dare yana zuwa gidan nan neman ka ba,a ganka ba.
Yace ko yanzu yana a,waje ya tafi can gida jiya ance yaiwa baba tas da mutanen gidan.
Amma kina nufin kinji dadin irin wullakancin da sukazo har cikin gida su sukai min ko ?
Nace ayi hakkuri son kane ya rufe mata ido har ta aikata hakan ba wani abuba.
Kuma aiko banza Rahama yar uwar kace yaya sai hhakkuri kawai wallahi amma basu kyauta ba gaskiya.
Nifa shigowan ta baidamuna sam don a tare na ganku gidan ku daya yar uwan kace Rahama ta jini.
Hannun shi ya mika yana son karban yaron sai bai iya ba don bai kan dauki yaro shi sam.
Zama yayi bakin gado yace min zoki gyara min shi please ban iya daukan yara ni.
Na zauna gap dashi ya tsurawa yaron dake barci nade a ciki a
showel a hannun shi.
Na zauna ina cewa ai yanzu naga zaka fara dauka tunda dai Amir din badani yai kama ba.
Dawa yai kama ya tambayeni cikin dago kan shi yana mai kura min idon shi.
Ina dariya nace ai kaima kasani ni bai biyo ni ba,duk kaine ko yaya sagir ne ko yaya Ahmed oho ?.
Da sauri yace Ahmed kuma Fatima please ki bar hada min yaro na da,wanan mara mutuncin mutum wanda bai san Allah ba.
Nace hakkuri za,ayi yaya tunda ya riga da ya aikata yanzu baba ne abin tausayi wallahi don na san har gobe koda yake haka abin yana damun zuciyar shi.
Yace ai Monday zamu shiga kotu dama zancen ne na suna ya hanani sukuni don naga mutumin da yasai gidan baida mutunci ko kadan wallahi.
Yadda naso mu rabu dashi lafiya hakan baiyuyuwa sai anyi rashin mutunci dashi za,a wanye lafiya.
Don kamar ma da gaiyya ya,sai gidan don Sagir yace min wai yaji yana fadin zai saka a rushe gidan yayi maikatan shimkafa ne a gurin don idon gari gidan yake.
Nace ikon Allah kada Allah ya bashi ikon yin haka a,rayuaan shi da ya barwa mutane abin gori har tarihi.
Nace amma yaya yanzu mama Asiya tayi matukar sanyi sosai sai neman shiri takeyi da mutane.
Ko dana haihuma tare da ita fa muke kwana a,asibiti har aka sallamay ni.
Yace wanan dadin bakin sai tai maku kuda bakusan halinta ba ai kaikayine ya koma kan mashekiya.
Don ni suka so na lalace na aikata hakan uwana tashiga balai Allah ya karw ni.
Ya mike yana fadin barin fita zuwa wajen wa yancan marasa mutuncin inji yaya zamu kare da su.
Nace suwa ke nan fa ?
Yace Rahama da kungiyar ta na yan iska mana da tazo min da fitina gida.
Nace sai anyi hakkuri suma basu zaci cewa al,amarin zai kai haka ba ai, sunzo ne suyi son ransu suyi muna iskanci su tafi.
Sai Allah yafisu suka samu wa yanda suka fisu balai a gidan suka jamay dasu.
Wai ki fada min gaskiyan yadda abin ya faru don in san abin fadi a can.
Tsaba na mayar mashi da komai yadda akayi akai fadan yace ai bari zanyi maganin su don zan masu kashedin shigo min gida watarana ne wallahi.
Nace amaryan naka zakaiwa wanan furucin haka kasan fa itama nan gidan ta ne tana da ikon da zata shigo ko ina take so a gidan.
Harara ya watso min yace a,a kila dai kece zata aura bani ba dai kan don ni wallahi har gobe na tsani mutanen nan marasa mutunci.
Jiya wata matace ra rufe ido take fada min abindaya faru ne haka naso nagane ta amma ban gane taba.
Nace ai matar Atiku mai wanki ne mana matar da kullun take godiya kan taimakon da kaiwa dan ta a baya Aliyu mana.
Yace Allah sarki itace wallahi gar gobe ina son in taimaki yaron ya zama wani abu idan ya girma don na wanke mai wanan bakin tabon a rayuwan shi.
Allah ya nufa nace mashi yace sai ya dawo nai mashi Allah ys tsare yafice daga gidan.
Yana fita ya samu mutane cinjim a kofan gidan shi iyayen yaran da Rahama ta, gaiyyato su rako ta nan suka shiga bashi hakkuri akan ya jaye maganan don yan sanda sunce wai kotu za,a kaisu.
Sai ga Baba sani da motar shi ko kashe motar baiyi ba da kyau yafito cike da masifa babban riga yana jan kasa.
Yace ashe baka da mutunci haka sadauki ban sani ba kai har ka isa kasaka a kule muna yara su kwana a caji office.
Sadauki yai murmushi yace amma Baba kaji irin rashin mutuncin da,suka zo gidana sukayi ko?
Kai har ina gidan yake da kakewa mutane wanan wulakancin haka kan shi akan wanan yar matsiyantar matar taka kake son wullakanta muna yara kamar wata mai asalin kwarai can.
Baba maganan ya tsaya iya ni daku kada ka hada da yar mutane please ?
Ko nima zaka saka a kulleni ne idan na zageta din ?
Bai mai magana ba don yasan dalili yake nema kawai ya shiga motar shi ya nufi police station din inda ya samu su Rahama sun ji jiki sosai dan kwana dayan da sukayi a rufe.
Nan yasaka akai masu warning akan kada su kara shiga mai gida gaba dayan su idan ba haka ba zai yi karan su again a kulle su kuma.

IDAN KIN BIYA KIKA,TURAWA WANDA BAI BIYA BA DAKE DA ALLAH,,,
Munyi arbain yaro yayi matukar kyau dashi gashi sai kara murjewa yakeyi yana kara haske da kiba sosai.
Ga sadauki yanzu sai ahari,a akan gidan su sukeyi da dan masani wanda yaja sosai a kan zancen.
Anyi nasaran kama yaya Ahmed an kulle shi a cewar Baba ma kada a sake shi a rufe shi don matsayin shi daya da barawo a gare shi.
Tunda gidan shi ya shigo mai ta dakin shi ta baya ya fasa ya shiga ya kwashe mai duk wani abin kwarai nashi a lokacin.
Don haka sata yazo yai mai a gida kuma ya kwashe mai takardu da ga baya yazo ya kwace mai gida.
Hankalin mama Asiya yai matukar tashi sosai jin irin hukuncin da baba yace a yankewa yaya Ahamed.
Sai gata a gidan mu tunda farar safiya ta sallama muna lokacin na gama shiri na tsab nayi kwalliya Iyya tayi wa Amir wanka takawo shi ya sha nono.
Don shan nono kawai ke kawo Amir gurina da ya gama kuma zata goya shi sai idan ya falka ko tana daki su kwanta tare.
Haka nake fita na barsu zuwa school don ina semester karshe yanzu ga karatuna.
Sallaman mama yasa mu fitowa daga dakina ina rike da yaro a hannu ina bashi nono muka fito falon.
Mama Asiya ce zaune saman kujera ta rafka uban tagumi cikin damuwa take.
Nace a,a mama sannu da zuwa ashe kece mama shine kika zauna a falo baki shigo ba.
Tace Fatima ba zama nazo ba mijinki na zo gani Allah dai yasa yana gida bai fita ba ?
Nace yana nan mama tace yi min magana dashi don Allah Fatima kice gurin shi nazo.
Na nufi dakin tabini da kallon yadda na koma wata fresh dani sosai kamar ba Bintu ba can.
Yana kwance ya kifa ciki yana barci na,shigo dakin na samay shi a hakan .
Sai da na zauna bakin gado na dan fara taba shi a hankali ya bude idon shi ya dago kai yana kallo na.
Ina zaune ina kallon shi ina gyara yaron a nono nace ina kwana ina dare da fatan an tashi lafiya ?
Ya dan goga kan shi a filo ya gyara mirginowa yana kallon mu yace my friend har ja tashi kai wanka ni ina kwance ko ?
Nace tuni mukai wanka kaima ka tashi kai wanka sai ka karya sai dai mama tana falo tana jiran ka.
Yace mama tare da kallon agogon bangon dakin shi da ido yace wata maman ke nan ke jira na kuma ?
Nace mama Asiya ce mana Asiya kuma may kuma ya kawo ta nan gidan ko dama takanzo ne wai ?
Nace gaskiya bata taba zuwa haka ba babu wani dalili sai yau kawai tazo ya ja tsaki ya mike zaune da kyau sai da ya shiga bandaki yai brush yafito daga dakin.
Ya karbi Amir a hannu na ya fice da shi ina bayan ta jin motsin fitowar mu daga dakin ta dan gyara zama da kyau tana cewa kafitu Sadauki ga mamakin shi sai yaga yau itace ma mai gaisheshi kafin ya gaida ita.
Yace lafiya dai mama naganki da sasafe hakan ga ko wani abu kuma ya faru ne a gida.
Maimakon mama tayi magana sai kawai ta fashe da kuka mai tsuma rai sosai.
Yace haba mama may yafaru ne ban son wanan kukan da kikeyi ni fa dan ki ne mama don Allah may ke faruwa ne please.
Mama ta dan tsagaita kukan ta tace sadauki nazo gurin ka ne neman taimako akan dan uwanka da ke a tsare.
Don Allah sadauki ka saka baki wa baban ku ya dan sasauta kalamin da yayi akan wai a daure Yaron nan da yace.
Yace mama amma dai kin san Ahmed bai kyauta wa Baba bai kuma kyautawa mu yan uwan shi ba.
Babu abin kunyan da yafi ace wai dan uwanka yasayar da gidan ku na gado ga kuma mahaifin ku da rai.
Tace na sani sadauki yaron nan bai kyauta ba ba ku kadai yaiwa tozarci ba har ma dani mahaifiyar shi tunda ina a cikin gidan yanzu.
Tace kaiwa Allah ka taimaka a tsare shi a lalabeshi ina sauran kudin suke aji idan yaso idan zai biya sauran da gabaya ne sai muji yadda za,ayi.
Sadauki ya gyara rikon yaron dake a hannun shi yana cewa mama ai antambaye shi babu kudin a hannun shi yanzu yace yayi sayayan kayan part da yake sayarwa saura kuma matar shi ta sai abubuwan bukatan ta.
Tace da karfi dama na,sani aidama nasan wanan shegiyar matar tashi yarinyar banza itace ta saka shi a,wanan halin.
Sadauki yarinyar nan tun farko na fadawa yaron nan ba matar auren shi bace ita yarinyar da ta san kaduna tasan lagos itace zata zauna zaman aure agidan wani.
Ko fa,abinci bata iya yi mashi gashi nan kullun cikin yawon zuwa saye ko yazo gurina yaci sai Alhaji yai mai fada yanzu ya bari.
Idan dai tace ga abin da take so duk inda zai shiga ya samo shi sai ya shiga ya samo mata shi ake zaunawa lafiya in ba haka ba ko ba,su da zaman lafiya ita dashi ke nan.
Yace kai amma gaskiya bata kyauta ba wanan aiba so bane kamar ba auren soyayya sukayi a tsakanin su.
Mama tace soyayyan may can kuma dama aiba son shi takeyi ba karya yai mata shi mai kudi ne kuma dan mai kudi.
Kakaga ko akwai karya acikin wanan yanayi koba gaskiya ba .
Yace Allah ya kyauta mama tace amin cikin damuwa tare da nisawa takara fadin yanzu don Allah jika kaida Fatima gwanin ban sha,awa da ku ga zuria Allah ya fara baku a tsakanin ku.
Kowa yaga yadda zaman ku yake sai yai maku sha,awa sosai don ga yi nayi bari na bari ba irin wancan mai bakin auren tsiya ba da duk ta halakamai rayuwan shi ko.
Mama yanzu ki koma gida naji bukatan ki insha Allahu zan san abinda akayi abin yazo da sauki ai Ahmed dan uwana ne najini ba zan so naga ya,wullakanta ba nima.
Godiya sosai mama tai mashi har da saka mai albarka da fatan gamawa da duniya lafiya (kudi ke nan)
Nan dai ya mike itama ta mike yai mata rakiya har kofan gida ta,shiga motar ta wanda ya fara jin jiki yanzu sosai.
Sai da yaga fitan ta daga gidan ya sauke ajiyan zuciya ya tsaya suna gaisawa da su maigadi har suna tambayan lafiyan Amir dake a hannun shi.
****** ********* ******
Mama tana komawa gida dakin maji ta shiga ta samay ta,a zaune tana karyawa ganin ta a,shiri kamar fita zatayi yasa take kallon ta da mamaki.
Sai da ta samu guri ta zauna take cewa daga gidan sadauki nake yanzun haka.
Gidan saudauki maji ta tambaya tace eh na tafi na samay shi ne kafin ya fita akan zancen yaron nan.
Don ya taimaka Alhaji ya jaye zancen daurin da yace sai anyi mashi nasan yayi laifi mai muni amma sai ina ganin daurin da yace aimashi kamar zai iya kara jefa shi a cikin fitina kuma ya kara hinjirewa yafi haka.
Don Allah idan sadauki ya shigo ki ka taimako na hjy maijidda kiyi mai magana duk da dai yai min alkawari akan na kwantar da hankalina zai duba al,amarin da idon basira in Allah ya yarda.
Maji tace ai tunda kin mashi magana zai duba din da ke dani ai duk daya muke a gare shi don duk uwanshi muke Ahmed kuma ai dan uwan shi ne.
Tace amma zan kara mashi magana nima akan magana don ya duba al,amarin.
Tace nagode tare da mikewa tana fadin barin tafi na duba yaran nan na barsu basu ko tashi ba na fita daga gidan.
Allah ya sauwaka mama tace mata tace Amin tana tsaye take cewa aini godiya na ga Allah shine sadauki yana da abin hannun shi da zai iya taimakawa dashi.
Hakane inji maji tace da yanzu ai duk munsan inda muka nufa tunda mai gida yace yana bukatan gidan shi da,wuri haka.
Sai da ya gama abinda yake ya shirya ya fita daga gidan ya nufi gidan su ganin iyayyen shi.
Ya samu mama a dakin ta suka gaisa nan take cewa dashi sai ga hjy Asiya kun gani da sassafe haka yace eh tazo dazun itace ma ta tayar dani daga barci ai yau din nan.
Nan yake fada mata yadda suka kwashe da mama din tace tunda taje har ta ganka sai kasan yadda zakayi da shi yanzu.
Kayi kokari ka taushi mahaifin ku yayi hakkuri akan maganan da yayi yace ai babu damuwa maji.
Ya nufi gurin mahaifin su don ya gaidashi ya samay shi zaune a keken dake taimaka mashi ga tafiya wanda shi sadaukin ne ya kashe kudi masu yawa ya saye shi don baba din ga shawaran da likita ya bashi a can.
A mutunce ya durkusa ya gaida baba din sanan ya tambayi lafiyan jikin shi ?
Baba yace Alhamdullahi can baban yace yaya zancen kotun naku yakaya ne cikin maganan shi da ba fita yake sosai ba.
Kan shi ya dago yace Baba ai mun yi magana ta fahinta da mutumin yace a jaye karan idan har zan biyashi kudin shi na,kara mai riba a sama.
Baza,a kara mai ba inji baba aiko shi mai laifi ne don ba gaskiya bane yasan ina a raye ya sai mingida ga hannun dana.
Sadauki yace hakane baba ai yanzu shi lauyan tanan ya bullo mai shine yasa hankalin shi ai ya tashi sosai.
Don da da farko yana ganin zaici riba ga maganan amma yanzu jikin shi ya fara sanyi kan case din.
Ance halinshi ke nan ko mutuwa akayi sai ya kwace gidan marayu ya,saye a araha ya cuce su.
Baba yace shine ni bai jira na mutu ba yazo cin nawa ko?
Kayi hakkuri baba kaddarane duk haka ba kyau ma gana tuna aanan zancen a zuciyar ka don kara tayar ma da hankali kawai maganan zaiyi.
Insha Allahu gidan ka har yanzu yana a matsayin naka illa iyaka mubashi kudin shi daya,bashi Ahmed din shike nan a zauna lafiya.
Shiko Ahmed din ku kulle dan banza can yayi iya rayuwan shi a gidan yari don banga amfanin haihuwan shi ba ni.
Hakkuri dai za,ayi baba ai yanzu shima a cikin tashin hankali yake ko yaushe.
Wanan yarinyar da ya,aurace ke kaishi ga halaka akace don ba yarinyar kirki bace wallahi.
Bashi ya aurota ba inji baba sadauki yai dariya yace baba kaine fa ka,yarde mai bayan mama ta hana abin .
Shiru baba yayi yana daya sani a,ranshi don yai nadaman zaman Ahmed da,wanan yarinyar mara mutunci da ita.
Yana fita gurin baba bayan sun gama magana dashi kotu suka nufa shi da yaya bashar sun samu danmasani ya ce idan zai samu kudin shi ya janye maganan shi.
Ba bata lokaci sadauki ya saka hannu akan zai ba mutumin kudin shi miliyan bakwai da Ahmed ya karba a hannun shi.
Nan aka zauna ranan ya biya kudin a ka rufe case din tare da sako yaya Ahmed yakai shi har gidan shi gurin matar shi ya nufo gida don lokacin har duhu yafara yi ko.
Bai shigo gida ba sai da aka sallamay sallah yashigo gida agajiye dashi.
A sanyaye ya samay mu a falo muna hira Amir yana hannun Sa,ade tana mashi wasa.
Sannu muke mashi yana karbawa da kyat ya fada saman kujeran dake kusa da wanda nake zaune.
Na kalle shi yadda na ganshi a wahale dashi nace ko zakai wanka ne ka ji dadin jikin ka ?
Yace shine daidai tun safe muna koto ana zirgazirga kan zance yanzun dai mun samu ankashe case din mun karbi takardun mu ko.
Nace masha Allahu yau baba idan yaga takardan shi a hannun shi kila hankalinshi zai kara kwantawa hakanan.
Ya lumshe idanuwan shi yace ban tafi na,kai mai ba,sai da,safe idan Allah yakaimu.
Nace Allah ya kaimu na mike na nufi dakin shi na hada mai ruwan wanka a can kafin ya taso yayi.
Sai washe gari ne ya shirya tafi gurin baba ya kai mai takardan gidan nashi da,aka anso gurin mutumin da ya sai gidan hannun Ahmed din.
Sai da baba ya tara kowa diyan shi da matan shi da,aka kirasu a,waya yake cewa dama akan zance gidan nan ne gashi yau Allah yayi Sadauki ya karbo gidan a hannin azzalumai macuta.
Don haka daga yau ina son ku sani gidan nan ba gida na bane gidan sadauki ne da uwarshi don haka ko bana raye kowa ya rike wanan zancen a ran shi.
Duk suka dago kai suna kallon baba da mamaki don jin abinda yace wai gida na sadauki ne da uwar shi yanzu.
Sadauki ya tare baba da cewa haba baba gidan nan na kowa ne baba tunda gida nakane har yanzu ni bawai na karbo bane don ya zama nawa ba.
Baba ya daga mai hannun shi da kyat yana cewa wanan magana danayi ba fashi a cikin shi sadauki gida nakane yanzun ba nawa ba.
Idan kuma kana,son ganin bacin raina ne a yanzu sai ka matsa da magana mu gani.
Dole yaja bakin shi yai shiru yana gudun yai magana wani matsala ya faru da baba.
Baba yace Ahmed dai yanzun sai kuyi kuka dashi da uwar shi don shine yaja ma kowa wanan bani ba.
Don ni Allah ta gani nayi yadda ya dace nai maku muhalli wanda ko bayan raina iyayyen ku daku zaku iya zama a ciki am.a ya,sa kafa ya take tausayin kowa dani daku yasayar wa banza irin shi macuci.
Don haka yanzu na fada maku gida yana a zaman sadauki ne bani Abubakar ba kuma.
Sai kowa ya,watse na gama magana na ke nan ya juya inda mummy take zaune tai tagumi sai sauraren shi ta yake yace ke turani ki maidani dakina nagama maganan da zan yi kenan.
Mummy ta mike duk jiki ba kwari ta fara turashi zuwa uwar dakin shi cikin rashin kuzari.
Nan ya barsu a,zaune kowa jikin shi ya mutu ana shigewa dashi Nafisa ta fara mikewa tana fadin yau dai shi ke nan tafaru ta kare kurun kus kan kutsu sai kowa ya fara neman madafa.
Maganan ta yai matukar ba kowa haushi uwarta ta kalle ta tace ke kan anyi sakariyar yarinya wallahi nan.
Ke kan baki san ciwon kanki ba ko kadan yau wanan abin tashin hankalin da may yai kama harda kike fadin wai takare.
Takare mawa ke nan kike nufi yanzu mu ko ku da baku da madafa kamar kowa.
Ai mu muna da gidan iyayye sai mu koma can mu zauna ku kuwa ina zaku kuda baku da gidan uba.
Mu dai wallahi ancuce mu anzalunce mu sai dai muce Allah ya isar muna kawai ancuci na kauye.
Saboda hainci da zalunci dan gidan ma da za,a tsira dashi akama a sayar wa mutane su rasa matsuguni sai rabe rabe.
Sadauki ya mike tsab ya fara fita daga dakin bayan fitan Nafisa yabi bayan ta.
Sai mama da Amira da maryam suka mike suma suka fice daga dakin ran su a bace.
Lokacin Umma ke fadin muna fukai kawai kun kai ga yadda kuke so ai dama gurin ku su ke nan duk su mamaye gidan to gashi Allah ya cika maku ai gida ya zama naku.
Sagir dake zaune kasa saman carpet yace haba haba Umma yanzu may yw laifin yaya sadauki a gidan nan.
Mai laifi daban wanda bai da laifi ya taimake mu ya raba mu da gararanba a saman titi kuma za,aga laifin shi a banza.
Gaskiya wanan ba adalci bane kuyi wa kanku nasiha ku san may ke a gaban mu ba,wai mu zauna kuma muna cusa kiyayyan junan mu ba a haka.
Ya mike yafita daga falon shima,ranshi a bace ya,saka takalman shi ya bar falon.
Nan dai sukai ta watsewa daya bayan daya a falon kowa jikin shi ya mutu don basu taba zaton wanan hukuncin baba zai iya yankewa akan su ba.
****** ********* ******
Da,sannu yau Allah yayi mun gama exam din final din mu gaba daya sai dai fatan alherin Allah ya ba da sa,a kawai wa kowa daya zana exam din shi a matsayi finalist.
Muna gamawa da sati biyu muka daga zuwa waje da yaya sadauki inda ni kaina ban san tsawon lokacin da zamu dauka a can ba indan mun tafi.
Mun fara zuwa kasar hongkong, inda muka share kusan wata daya a kasan muna hutawa kawai.
Dani dashi sai dan mu Amir da yanzu yayi wayo sosai zakace watan nin shi ya zarta ya kai shekara ma.
Sosai nake jin dadin yadda muke rayuwa a wanan kasan a tsakanin mu ukun nan inda sone da kauna tsantsanta ake gwadawa junan mu.
Don kowan mu yana son dan uwa mun shaku da juna fiye da tsanmani komai a tare mukeyin shi.
Zai kwashe yai ta yawo da mu muna ganin gurare tare da yin photuna masu kyau.
Mun bar kasan zuwa kasar Beselona inda zasu buga kwallo da,aka dauke shi wani contarack mai tsada da kudi masu yawa.
Ina zaune ina kallon shi yana shirin abubuwan da yake bukata da zamu tafi dasu a gurin wasan
Can ya dago kai ya kalle ni ya sake min laulausar murmushi ya ce kina kallon yadda mijin ki ke fita,gurin neman kudi halaliyar mu ko ?
Tsab ya,shirya cikin wasu kananan kaya sai ga wani abokin shi Daniel yazo dashi zamu tafi na,dauki dan jakkan da na saka kayan mu a ciki muka kama hanya sai gurin da za ai wasan ball din.
Muna isa ranan naga inda,akasan muhinmancin wasan kwallon kafa don naga taron dan mutum da ban taba gani ba a duniya.
Wata baturiya ta karbi Amir a hannu na da sauri tace nima na biyo ta nan muka shiga wani daki ta miko min riga mai tambarin yan wasan inda shima Amir din ta saka mai rigan yan kwallo na yara mai tasu tambarin.
Hijjab ne a jikina irin dan karamin nan ta karba taje ta sa aka buga mai tambarin su nasaka rigan saman dogon rigan dake a jikina tare da hijjab din na take na saje da duk wanda yake a gurin.
Suka miko min wani dan abin wasa kamar hure wai na rika nikan na samu abin yiwa Amir wasa dashi.
Muna fitowa a wani guri da,sai wanda aka yarda dashi zai shiga gurin nan naga yan wasan kwallon duniya birjit dasu suna ta mota jikin su kafin a,shiga filin.
Can na hango sadauki rana,na,farko dana fara ganin shi saye da kayan su na yan kwallo yana ganina ya bar abinda yakeyi yanufo ni yana murmushi.
Nan sauran abokan shi ke tambayan shi wai matar shi ne da dan shi yadda ya rugumay mune ya tabbatar masu da amsan da suke son ji daga bakin shi.
Don hada kaina da nashi dana,Amir yayi guri daya a hankali yake fadin kiyi min addua Fatima Allah ya bamu sa,an wanan wasan da za,a buga a yau.
Nace yaya Allah ya tabbatar da alheri yasa a,dace da abinda akazo nema ta hanyan alheri.
Yace amin nan yan jarida da sauran median suka shiga daukan mu hotuna kalakala.
Kyau, kudi, ilimi yanzu duk Allah ya bani don haka gwargwado zan iya gogaiya a cikin wa yan nan mutane.
Muna sahun gaba cikin officials muka fara fitowa bayan yace wa matar nan ta kula damu amana please.
Muna futowa guri ya kaure da wani irin ihu wanda yasa na daga kai na kalli fadin gurin sai da gabana ya fadi sosai naga gurin yana juya min.
Kujeru aka bamu muka zauna bamufi minti biyar da zama ba suka fito a jere dasu ana taken team din su.
Sai flowers ake watso masu ta ko ina can na hango wasu da irin furen da aka bani a hannkali nakewa dana wasa dashi yana dariya.
Sai daukan mu hutuna akeyi tako ina nan bayan sunyi taken kasan tasu aka fara shirin fara wasa.
Wasa yakai wasa guri ya rude sosai mutane sai faman ihu suke inda sai ranan nan nasan muhinmancin kwallon kafa da kyau.
Tun ina kallo ban damu ba,sai gashi da,wasa yai wasa da kaina nake daga Amir ina nuna mai wasan .
Wanda idan mutum.ya gani zai dauka cewa wani wasan jin dadi nake mai a lokacin.
Har aka tafi half time suka dan huta suna dawowa wasa ya tashi sosa kafin atashi wasan sai da sadauki da wani farin fata suka ci cibiyu babu ko daya .
Haba aiko guri kaure da ihin murna nan muka kutsa muka shiga filin akai ta muna hutuna tare dasu suna ta daukan Amir kowa da kalan maganan da yake idan ya dauke shi akai masu photo suna kiran shi little UF.
Washegari Naga karamawa ranan sai shaye shaye da lashe lashe da tsotson juna akeyi.
Abinda yaban mamaki shine ina zaune na dawo a gajiye wayana ya nuna min sako yashigo.
Ina dubawa yaya sagir ne ya turo min da photuna da akai muna a gurin kala kala wasu ma ban san anyi suba ni.
Yana tayani murna na mayar mashi da amsa dana gode yayana kawai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
I'mIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH,,,,
Washegari aka hada lifaya, don taya murnan samun nasaran da sukayi akan wasan su da suka buga na kwallo.
Mun sha kwalliya sosai a lokacin in cikin wani dogon riga mai launin dark blue wanda yaji duwatsu a jikin shi sosai.
Nai rolling din kaina da dan kwalin shi wanda shima yana da duwatsu da aka jera mai a jikin bakin shi.
Ga zobunan gold sun cika min yatsu na dama duka hudu, daya sayo min wuyana saye da English gold.
Na saka wani takalma mai dan tudu akafana sai yar karamar jakar hannu dana rike.
Shigar tawa duk wanda ya ganni sai ya yaba da ita shi kan shi sadauki dana fito sai da ya kasa boyewa a ran shi ga kamshi dake tashi na jikina saboda mayukan danake amfani dasu a can yanzu.
Haka Amir shima yaji kwaliyan shi irin ta yara maza mai tsada sosai tare da saka mai hula irin ta yaran turawa.
Wayan shi ya dauko ya fara daukan mu hoto dashi, yana yaba kyawon mu ni da yaron.
A cikin wata irin dirkekiyar mota muke tafe dagani sai shi sai Amir wanda yake rike a hannun mahaifin shi yana waya.
Muna Isa gurin munga karamawan ban girma a gurin mutanen da muka samu suna jiran isowar mu gurin.
A gaskiya wanna mutane suna matukar girmama yan was an kwallon a rayuwan su.
Yana fitowa ya zagaya a bangaren da nake zaune ya bude min motar da kan shi yayin da idanuwan mutane yake a kan mu caaa.
Wasun su da yawa a gurin basu san cewa sadauki yana da aure ba don su ganin su a gurin su shekarun shi yai karami da aje iyali haka.
Hannun shi harde acikin nawa muka shiga babban holl din wanda yake makil da jinsin mutane kala kala.
Duk wanda yake da iyali acikin su tafe yake da iyalin shi a gurin.
Nan aka shiga gaisawa da mutane ana introducing din juna ga manyan masu kudin kasan turawa.
Inda matan dake gurin suka shiga kallon kalar shiga ta wanda ke baiyyana musulunci a fili.
Don haka aka shiga gimamani don suna matukar daraja matan musulmai sosai.
Ga wasu flowers da ake watsowa daga sama sai shagali suke suna shaye shayen su irin na al,adan su.
Nan sadauki suka hade da wani balarabe mai kudi dan kasan Dubai mutum ne mai tsananin arziki da tarin dukiya acikin nahiyar Arab side.
Gaba daya shine mutum na farko da yazo na daya a duk duniya arziki da tarin dukiya.
Gashi da ra,ayin son wasan kwallon kafa don matashi ne shima haka yasa ya kyasa taimakawa yan kwallo musanman matasa musulmai irin su sadauki.
Yana kuma da kamfani na kera gwala gwalai da diamond nashi na kanshi ga rijiyoyin mai da yake dasu kasa kasa na duniya.
Yana da kamfanin kera jiragen sama da na ruwa wanda yake mallakan shi na kansa.
Hannu Abu sufiyanu ya mika ya karbi Amir dake a hannu na ya dan yi mashi wasa tare da sumbatar yaron.
Cikin wasa yake cewa sadauki ya bashi Amir don yaron ya shiga ranshi.
Sadauki yake cewa ya bashi yace ya gode tare da kissing din yaron inda ya juya gurin na hannun daman shi yai mai magana.
Mutum ya amsa da insha Allah.
Nan yaja hannun sadauki wanda nake biye a bayan shi sun dan jima suna magana irin ta Siri a tsakanin su.
Wanda ashe alakace ta business suke kullawa a tsakanin su a lokacin, mutane da yawa sun San ba kebewar banza Abu sufiyanu yake da sadauki ba a lokacin.
Da hannu ya yafito na nufin na karaso inda suke a tsaye, yake ce min nai wa mutumin godiya.
Duk da ban San ko na may ye ba amma nai mashi godiya irin ta addinin musulunci wanda ya kara sawa mutumin jin dadi a ran shi.
Don shi mutum ne wanda yake son mutane masu yi mashi godiya da nuna farin cikin su gare shi.
Nan dai sukai ta gaisawa da mutanen arziki na duniya kala kala ina rike a hannun shi har taro ya fara watsewa.
Muka Fara ficewa daga sahun farko muka bar gurin don a lokacin a gajiye nake sosai ga Amir da nauyi ba kadan ba.
Muna a mota ya dan sasauta tie din wuyan shi yana juyowa inda nake zaune yana cewa my queen kin gaji ko don nasan baki saba irin wanna kwaram din namu ba ke.
Idanuwana na Dan lumshe nake cewa nauyin daukan wanan din dai ya isheni .
Yace Kai ni dake son na samu ma yafi haka girma idan son samu ne a gurina.
Nace kai Yaya idan Amir yafi haka kiba kuma ai sai dai na dinga barin shi a zaune guri daya don ina zan iya daukan wanda yafi wanna girma haka.
Yanzun ma a Yaya nake iya daukan shi balle ya kara yafi nan kuma ?
Ya dan juyo a mamaki yace Queen baban nawa zaki bari a zaune don tsaban mugunta kuma ?
Nace ai nima babana ne ko ko kamanta nima shi ya haife ni ne wai ?
Nace sune fa gata yanzu a duniya don sune sillar wanna rayuwan da nake a ciki yanzu.
Murmushi yayi don jin abinda na fada yasan ba karya na fadin ba haka zancen yake ko yaushe Ina matukar godewa mama da baba din.
Yace tare da kwantar da kanshi saman kafada ta nauyin ya karu min biyu wanda a lokacin ba nauyi naji ba sai wani sanyin dadi da naji a raina kawai.
Don farin cikina yanzu karuwa yake a kullun Ina mai godewa Allah na da biyayyan da yabani iko nai wa Maji ban butulce mata ba ga bukatan ta a gare ni na auren dan ta da duniya kewa kallon lalatace.
Matsalata daya yanzu shine ban gama tantace ko sadauki ya daina halin shi ba ko yanayi har yanzu.
Haka ne yakan rage min jin dadina a kullun na tuna da wanna rayuwan nashi na shaye shaye.
Ai fa tuni idanuwana ya ciko da hawaye yana magana jin nai shiru yasa shi dago kanshi daga kafadata ya kalleni.
Ganin da yai min a cikin rashin walwala komai ma na duniya yafita min arai a lokacin.
Da sauri ya Kara dagowa yana kallona acikin mamaki tare da kamo hannuna ya rike gam a cikin nashi yana tambayana may kuma ya faru haka queen ?
Na sauke ajiyan zuciya tare da zubo hawayen dake a cikin idanuwana kasan fuskana.
Yasake maimaita tambayan shi da wai may ya faru bana son ganin ki ko kadan a cikin damuwa queen.
Na sauke ajiyan zuciya tare da mayar da kaina ga nashi kafadan ina sauke ajiyan zuciya a hankali a karo na biyu.
Da sauri ya kara jawoni a jikin shi ya rugumay mu yana cewa kada kimin haka Fatima kinsan kwanciyan hankalinki shine nawa yanzu.
Na dauka yanzu zakifi kowa farin cikin gani da idon ki da kikayi na irin baiwan da Allah yai ma mijin ki.
May ye kuma ya samay ki a lokacin da nake tsanmanin farin ciki a gare ki Kuma ?
Na goge kwallan da suka fara zubo min a idona nace Yaya love tunanen bayane yazo min kawai.
Maganan tawa ta doke shi har ciki ranshi yace tare da riko min hannayena duka biyu.
Yace kiyi hakkuri Fatima nasan cewa na bata maku rayukan ku sosai a baya dake da iyayyena wanda nima a yanzu idan na tuna wanna rayuwan bana jin dadin shi a raina ko kadan.
Ki daina damuwan kanki da yawa don sai ma ince ki godewa Allah saboda na San kece sillar daina duk wani mugun rayuwan da nayi a baya Fatima.
Ni kaina nasan har abinda ke kanki baki san kina yi ba akaina don wanna rayuwan da nayi a baya yana bata maki Rai sosai da sakaku kunya ga jama,a.
Fatima nasan kina son na fiye da son da Maji take min a baya wanda a baya nake ganin babu wani mai sona bayan maji da mahaifina da yan uwana biyu da Allah ya bani.
Amma sai haduwana dake Fatima na fahinci cewa Allah kan jefo wasu mutane a rayuwan bawan shi don kawai su taimakawa bawan shi a wani halin taimakon dayake bukata a rayuwan shi.
Hakane Fatima ke alheri ce a rayuwan mu gaba daya don a sanadin ki Abubuwa da dama nawa sun gyaru Fatima ta sanadin ki a rayuwana.
Most especially zan iya ce maki ibadana gaba daya a sanadinki Allah ya nufa na gyara shi.
Kin min Abubuwa da dama wanda ke baki San na San dasu ba a rayuwana Kuma bawai kina son na sani din bane kinyi ne kawai don ki taimaka min kawai.
Wanna maganan da yayi itace mafi girma da tsoro danaji don ban San may yasani wanda nai mashi a rayuwan shi ba.
Nace Yaya love idan abin da naima ya bata ma rai a lokacin ka yafe min don Allah don ba a cikin hankalina nai maka ba.
Ya langabe kan shi tare da girgizawa yace Fatima bata taba yi min abinda ba daidai da rayuwana ba dana sani.
A lokacin motar mu ta tsaya a kofan hotel din da muka sauka a ciki ya karbi Amir daga hannuna muka fito daga motan.
A gajiye muke don ba karamin gajiya muka kwaso ba daga inda muka fito nace ya kawo Amir din na kama mai don nasan shi ba gwanin rikon yara bane sosai.
Yace ki barshi don nima in son ya saba dani ko kin manta da sunan wanda yaci ne a gurina.
Ya ce don haka ke kuma sai ki dinga kokarin kina Sanya mu a cikin farin ciki da ni,imar ki.
Kina kashe Muna kishin ruwan sha,awan mu daga ni,imar da Allah ya tana dar muna a gareki.
Kunya ya kamani daga maganan da yayi haka yasani dan murmusawa kawai Ina biye a bayan shi.
Duk da gajiyan da muka debo Bai hana mu kasancewa a tare ba a daren wanda sai faman sanbatu yake akan irin ni,imar da Allah yai min a jikina.
Har muka bar kasar na yoghuslabea bai barni na huta daga jikin shi ba ga sabon kasalan da ke yawan taso min wanda nake gani sabon yanayin jin dadin da na samu ne hakan.
****** ********* ******
Watan mu cikin na uku ke nan yanzu rabon mu da gida ga wani irin mahaukacin soyayya da so da kaunan da yake gwada muna ni da Amir din.
Abin har yana bani tsoro irin yadda ya ke kashe muna kudi haka har sai da yakai nace mai yayana kayan nan fa sun Isa haka.
Sai dai ya girgizawa min Kai kawai yace Queen idan ban kashe maku ba na kashewa wasu wa kudi haka a rayuwana.
Nikan ban da tacewa dole na saka mai Ido na bishi da kallon mamaki don sai nake gani kamar ba Yaya sadauki dana sani a baya bane .
Wanda tsaraba ma idan ya sayo babu rabo na a cikin sa sai idan mamana tai min ci da karfi nake samu daga gare shi.
Allah mai iko sai gashi yau nice dungurungun a gurin sayan kayan baki daya.
Haka Amir yasha kayan wasan yara su kekuna da jirage teddy ga abin koyon haruffa na English da Arab kala kala ko wani da kalan sautin sa.
Bayan yasan cewa akwai su a gida wanda ya sayo tun yaron yana cikin ciki.
Kafin mu bar kasan ya turo da kayan gida ta hannun Yaya Bashar kayan zasu fada .
Wayanda na sani kenan wanda ban sani ba sai idan mun Isa zan gansu a can idan Allah ya Kai mu.
Daga can bamu nufi Dubai din ba wai suna da meeting a US da zasuyi acan na yan kwallo.
Sai da muka share wata daya a kasan inda ya kara hada business da wasu turawa na kasan don ya saka hannun jari atare da su.
Nan ma bai barmu hakana ba sai da yai min sayayya kamar wanda zai hada kayan lefe.
Suturu na alfarma da atamfofi masu tsadan gaske ya saya muna anan kasan.
Ni kaina a lokacin nasan na zama wata daga cikin matan manya a kasata ke nan.
Gashi nai wani irin kyau fatana yai wani irin lub lub dashi tankar dai irin matan, larabawan Pakistan din nan hakan ni da kaina nasan na samu canji a rayuwana.
Mun shiga kasar Dubai wanda a lokacin watan mu hudu rabon mu da gida kenan har na Fara kewan gida da yan uwana.
Duk da Ina waya da duk wanda nai kewan shi a raina amma duk da haka Ina son gani na a gida.
A kasan Dubai naga mata kasa she masu ji da kansu duk da na taba zuwa amma sai wanan zuwan ya zama min kamar na farko a rayuwana.
Ga matan Nigeria Nan zakace tankar a gida Nigeria kake Nan na Dan sake jiki naji Dan sauki shaukin gida da nakeyi a raina duk da irin kullan da muke samu a gurin shi.
Sam sadauki baya yarda nai hurda da matan hausawan da muke haduwa dasu a can acewan shi Bai yarda da hurda da irin wa ya Nan matan ba dake baro gida su zuwa wata uwar duniya da sunan neman kudi ba.
Gashi suna son yin hurda dani amma sai yace masu ni matata boye ta nakeyi don matar kulle ce ita.
Mutum zai yi mamaki yadda matan manyan kasar mu suke acan birjit dasu zakace a gida Nigeria ne mutum yake ganin su ba wani boyewa ba ne kamar nan da ba,a ganin su sai da ticket.
Gashi da farin jinin jama, a a tare dashi duk kowa na son shi wanda hakan ne muma iyalinshi ya shafe mu don mutane suna haba haba da mu a can.
A nan nuna min halarci so sai a kasan don sun it's taron bakin su dake zuwa masu ko yaushe. wani buki da aka shirya na yan kasan Nigeria inda akai ma Naira kaca kaca a gurin.
Don ko a can sai wanda ya Isa zai halarci wanna taron da aka shirya ida yan bussines din kasan mu suka baje nairan su a gurin.
Shiga sosai ta alfarma mukayi wanda nan ma wani dogon riga na saka mai balain kyau kamar alkyabba rigan take.
Bayan na saka wani English wear daga ciki na kawo rigan daga sama na dora akai.
Alkyaban irin mai tsananin tsadan nan ce ta matan manyan ko manyan ma sai wace ta isa take saka ta don yakai jarin wata a kudi.
Hular rigan yai min wani irin rufi yana rike da wani dan mayafi da yake like a jikin rigan Idan kinga dama zaki iya Dan zarga shi akai shi ma.
Sai ki koma kamar kin yafa idan kuma baki ra,ayin haka zaki sake shi ya biyo bayan alkyaban ne.
Haka na dan yafo shi yai min matukar kyau sosai ajikina kamar wata yar labawa masu fada aji.
Wuyana Kuma diamond necklace dan Kiran Dubai sai su awarwaro da zubbuna masu tsada na saka.
Yaya sadauki yake cewa gaskiya da nasan haka rigan nan yake da kyau da akwati daya zan saya maki nashi.
Nace Kai haba dai Yaya har guda biyar fa ka saya min su duk da tsadan dake gare su.
Yace Queen ba tsada ba shagarki na fada maki shine mutunci na a idon jama,a da kuma matan abokaina.
Ina amfani mijin ki yana rike makudan dollars haka amma babu fitan kwarai ga iyalin shi ai sai duniya ta zage ni kamar ban godewa Allah ba ke nan.
Nafi son duniya su San cewa ke mai tsadace dariya ya bani nace to nagodewa Allah da irin baiwan mijin da ya bani yace to ke fa.
Isowan mu yaja hankalina mutanen dake gurin fitowan mu ya mayar da hankalin mutane sosai a kan mu don shigan mu ko makiyi dole ya kyasa muna ga Dan mu a hannun shi ya dauka a kafanshi Wanda barci yakeyi shi yaron duk da yasha kwaliyan shi sosai.
Matan da basu San mu ba sai tambayan sukeyi halan matar waye wai shin wanna guy din dan Nigeria ne wai ?
Aka fada masu Dan wasan kwallon duniya ne da ake Kira UF Dan jahar sokoto din nan da matar shi.
Lalai yayi abinshi don su keda lokaci gaskiya inji wasu Mata dake zaune saman wasu kujeru dayan tace matar shi yar wanene a Nigeria ita Kuma ?
Dayan tace ba yar kowa bace diyar tallkawa ne auren hadi ne ma akai masu shi ya mayar da ita haka da kike gani.
Kalleta cikin shigan matan manyan duniya kamar diyan wani hamshaki can da ita.
Matar dayan tace gaskiya ba laifi don first class ce gurin gwadawa tsara wanna don bata da makusa ta ko Ina gaskiya dubi dan data haifa mai mai dan karen kyau da shi don Allah.
Wata daga ciki taja tsuki tace kalli yadda yake wani tarairayan ta kamar diyan wani can.
Dayan matar tace ke ko aita isa yai Mata haka don gaskiya ba laifi akanta gara yai haba haba da abinshi don akwai muggan tsofi a gurin nan kema kin sani.
Gaskiyan shi kan gara ya kula da abinshi don tsofin nan da kike gani basu da dama gurin mace maikyau balle suna ganin ta haka yarinya danya da ita.
Dayan kuma tace ke ko ai mace rahamace fa ga mijinta gara yaji da abinshi kowa ya gani a fili.
A gaban matan dake gulman mu muka karaso suka shiga daga muna hannu muma hakan mukai masu muka wuce zuwa inda aka tanadar muna mazauni.
Sun bimu da kallon rigan dake jikina yasha jinin jikin su sosai wanda ko shagon sayar da irin su basu iya shiga don tsadan gurin.
Amma gashi a jikina Kuma mai high quality din na saka a jikina a lokacin.
Sai yatsune fuska suke su na rayawa a ransu dama sune a wanna matsayin haka ko diyan su a haka.
Don haka aka shi ga girmama ni a gurin don matsayin baiwan da Allah yaiwa mijina kawai don sun san ni din nashiga cikin sahun matan manyan yanzu.
Ganin saukin kan dake gare ni yasa wasu suka sauke girman kansu suna zuwa muna gaisawa dasu cikin mutunci.
Bamu wani jima agurin sosai ba don dare ya soma yi muka koma masaukin mu sai dai nayi kawaye da suka nuna ra,ayin su akan hurda dani duk da Yaya ya hade rai bai son hakan dani.
Washegari a masaukin mu sabbin kawayena suka kawo min ziyara nan muka sha hira dasu suna ta yaba irin kyawon da nayi a daren jiya gurin waliman da akayi.
Tare dasu da wasu abokan Yaya mutum uku muka Kai ziya gurin Abu sufiyanu daya gaiyace shi da kan shi.
Karban girma akai muna a gidan nashi inda muka samay shi don suna da appointment da Yaya da suka aje kan tana son ya dora shi jagorantan wani company da yake son yi a Nigeria na mai.
Da sunan zuwa yini muka shiga gidan sai gashi munyi kwana buy a tare dasu cikin kullawa da mutunci.
Ya dankawa Yaya duk wani abinda ya dace na mallakan company da yake son yi a Nigeria din.
Don ya zamo masu babban wakili a can idan min koma gida Nigeria don samun nasaran shi.
Taron nasu ya samu halartan wasu manyan engineers yan Nigeria wanda wanda shi halinshi ne ya daukaka matasa na kasashen duniya don ci gaban su da kasan su.
Mutane sunyi murna da wanna anin alherin da sadauki ya jawo wakasan mu Nigeria.
Gashi matashi mai tashen zamani sun San matasa zasu samu aiki da dama a wanna harkan insha Allahu.
Ga kyauta na alfarma da sukai muna nagani a fada bamu ba harda su Salma kawayena dasu ka raka mu sun samu alheri sosai a gurin su.
Haka yasa na tuna da masoyiyata yar uwata Maryam wace nai alkawari a raina duk abinda na samu nima tare da ita zan raba shi.
Don Maryam ta nuna min so da kaina da bazan iya mantawa dashi ba a rayuwana don itace silar komai da nake ciki a yanzu.
Ba don ta gwada min so da kaunan ba da ban Kai haka a gidan su ba da tuni na gudu na koma kauyen mu duk da halarcin da mama itama take nuna min.
Idan da ban jin dadin zama da Maryam indon ta Amirace kawai ba zan iya zama na tsawon lokaci ba a gidan.
Na samu kyautar mota daga matar maigidan irin da matan su ke yayi a lokacin.
Tare da wani dan karamin kit wanda ke dauke da gwalagwalai a cikin sa Kiran kamfanin su ta alfarma wanda sai wanda ya Isa ne zai saye su a nan Dubai din ma.
Ranan da zamu bar gidan matar tana rike da hannu na tana yabawa da halaiyar mu na kirki don har su Salma da muke tare da su sai da ta yaba da halinsu.
Kwanan mu biyu a masaukin mu na Dubai din muka dunguma zuwa airport inda zamu biya kasar saudiya muyi umurah a can kafin mu dawo gida Nigeria.
Mun Isa kasan muyi ziyaran fiyayyen halitta manzon rahama, a Madina muka dan fi dadewa acan din.
Ranan jumma,a muka shiga garin makka muka fara umarah tare da sallah jumma a.
Adduoin danayi a can sun fi yawa akan samun shiryuwa da kariya na zuria da neman zaman lafiya a gidan aure na tare da mijina da sauran yan uwan shi.
Muna Shirin dawowa ne zazzabi da nake fama dashi ya tsanata a kaina wanda dole muka tafi asibiti ganin likita a can din.
Bamu sha wahalan ganin likita ba sosai kasancewa da wani abokin wasan su sadauki dan kasan muke tare.
Nan a ka shiga min duk wani test da binciken da ya dace ai min a lokacin inda a take results yafito cikine a jikina Dan wata uku Kuma again.
Ya kara auna ni tare da min wasu binke komai nawa normal yabamu shawara Alan Amir da zaran ya dan Kara shan nono na wata daya mu cire shi daga nono.
Yabamu magani na yara da zamu dinga bashi Yana sha kafin a yaye shi daga nonon.
Muna barin asibiti masaukin mu muka koma inda sadauki ya rugumoni zuwa jikin shi yana murna tare da fadin my queen ban San irin godiyan da zan maki ba a rayuwana ba.
Don kin min komai a rayuwana gashi a Dan kankanin lokaci zaki wadatani da zuria a gidana kyawawa abin son kowa.
Nan ya nemo bakina muka mannewa junan mu sai kalman godiya yake sako mun tare da kara manne ni a jikin shi.
Bamu dauki lokaci ba dana ji sauki sosai muka dawo gida Nigeria cikin yan uwan mu tare da tarin arzikina alheri mai yawa da muka dawo dashi a gidan.
Mun kwana bit a garin Abuja kafin mu Kama hanya zuwa sokoto birnin shehu inda yan uwa da abokan arziki muka samu suna jiran mu a airport din.
Yawancin masu taron mu yan zuwa taya shi murnan samun wanna babban nasara ne na shugabancin wanna babban kafanin da zai jagorantan a kasan mu Nigeria.
Mun sauko daga matakalan jirgin cikin shiga irin ta alfarma dana saba yi a yanzu don fitar kunya.
Idanuwan mutane Cass akan mu wanda nai mamakin ganin wanna taron da akai muna a gurin.
Yana sabe da dan shi a kafadan shi yayin da nake biye a bayan shi Ina saukowa a hankali daga matakalan jirgin.
Nan aka shiga watso muna wasu flowers masu kyau da kamshi ana ta muna sannu da zuwa.
Acikin taron nan haka Maryam ta kutso kai naji ta rungumay ni ta baya take muka rungumay junan mu a cikin murna da saukin ganin junan mu.
Dan wani lokaci kadan ta sake ni tare da dagowa ta Dan kalle ni tana cewa wai Fatima kece haka ko dai mafalki nakeyi.
Nace kai haba anty na bagani a gaban ki ba tace kin koga yadda gaba daya Kika koma kin zama wata irin big madam dake Fatima.
Murmushi nayi na Kara jawo ta nai hugging din ta tare da rada mata cewa aikin yayan ki ne haka yar uwa.
Muryan shine a cikin taro yana fadin ke uwar surutu agajiye take please ki barta ta huta tukun kin wani tsare ta da gulman ki.
Nace haba Yaya baka ko tausayin mu yaushe rabon mu da ganin junan mu ne wai?
Ya jawo hannuna tare da watsa mata harara yake cewa kwayi gulman a gida idan kin hadu a can.
Gaba daya da masu taron mu muka wuce zuwa gidan mu sai dai nai matukar mamaki da ganin an canza hanyan da na sani zuwa gidan namu.
Inda naga an shiga wani irin mamakeken gida mai wani irin katon get ginin gidan ba sai na tsaya fadin shi ba don har da bene a gidan.
Nan ma yan uwane Mata dam a gidan a hankali ya rada min cewa welcome to our new house queen.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , ,
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH, , , ,
A hankali na sako kafana waje wanda don samun daula yai wani lub lub dashi fari fatte gwanin ban sha, awa.
Yan uwane da abokan arziki birijit a gidan ba masaka tsinke a ko ina na gidan sai motoci xa suka haraban gidan da wajen gidan.
A hankali ya zagayo inda nake a tsaye ban yi aune ba sai ganin yan jonarlist nayi a gaba da kayan aikin su.
Nan suka fara jero min tambaya ina rike ga hannun sadauki daya makale ni.
Sun fara da tambayana suna na da alkata dashi na fara da sallama irin ta addinin musulunci wanda ni ban san ma wai hausa ya canza salo ba inji mutanen dake gurin.
Nace sunana Fatima Abdullahi mata a gidan Umar faruq da ake kira da UF dan wasan kwallon kafa na international.
Sukace hajiya wani irin farin ciki zaki nunawa mutane a wanan tafiyan da duniya ke ganin kunyi da maigidanki mai tarin nasarori a cikin sa.
Nace to Alhamdullahi don gaskiya bazan iya nuna farin ciki da dadin da naji ba a cikin wanan yanayi da muka samu kan mu a cikin sa ba.
Sai dai kawai nace nagodewa Allah ubangiji da yakai mijina a cikin wanan matsayin tare da kara godewa Iyayyen maigidan nawa wanda da taimakon adduan da iyayye ke muna muka kai ga wanan matsayin da muke ciki a yau.
Nace ina matukar alfahari da godewa Allah da kasancewa mijina a cikin wanan matsayin da ubangiji ya nufe shi da zama a yau.
Ina ma kowa fatan alheri a rayuwan shi da fatan kara samun nasara ga duk wani abin alheri da wani ke bukatan yi a rayuwan shi.
Mutanen da suka zo taron mu kuma ina mika godiya na a gare su akan lokacin su da suka bayar gurin nuna muna farincikin su a gare mu Allah ya mayar da kowa gidan shi lafiya.
Nan suka juya zuwa gare shi suna tambayan shi nashi farin cikin da zai nuna shima.
Mai interview din yace Umar faruq Abubakar kayi namijin kokari sosai gurin haska muna kasan mu ga idanuwan duniya a matsatin ka na babban da wasan duniya da ake ji dashi a wanan lokaci tare da kuma jawo wa kasan mu nasarori gurin harkan ci gaban ta.
Wanda a yanzu babu abin da zamu ce sai mu maka godiya don wanan halakar nasarorin da kajawo wa kasa zata kawo ragewan zauna gari banza ga matasan da suka gama karatu babu aikin yi a tare dasu.
Yace insha Allahu haka nake fata don wanan kamfanonin da za, a bude zai bukaci ma, aikata kimani dubu ashirin da biyar a ko ina na sassan kasan nan maza da mata indan har mutum yana da takardun da muke bukata a gare shi.
Dama wanda baiyi zurfin ilimi ba za, a samu daidai dashi asaka shi a inda ya dace.
Mai tambayan yace masha Allahu mujin dadin jin wanan dibin nasaran da kasan mu ta samu ta dalilin ka wanda muke fatan samun haka ga sauran matasan kasan nan masu kishin zuci kamar ka nan gaba.
Sai dai baza mu barka haka ba ko zaka iya fadawa duniya da masu sauraren mu ko shekaran ka nawa a yanzu.
Sai da yai dan murmushi tare dan jawoni a jikin shi kadan yace yanzu shekarana talatin da daya cif insha Allahu.
Yace yayan ka nawa matan ka nawa ?
Yai dariya tukun yace matata daya gata nan a kusa dani kana ganin ta sai yaro na daya Amir wanda yaci sunan mahaifina watau Abubakar.
Yace itace matarka ta farko ko akwai wata a gaban ta?
Yayi murmushi yace itace mata ta tafarko kuma ta karshe .
Don yar uwata ce aure mukayi na zumunci da ita wanda ta zama muna aure na soyayya daga baya.
Hakan yasa mutanen dake tsaye suna kallon interview din wasu suka numfasa daga gefe don jin abinda yace .
Mai tambayan yace daga karshe wani irin godiya zaka mika ga mutanen da suka taru a nan saboda kai.
Ya dan murmushi tare da daga kanshi ya kalli inda mutane suka taru don shi yace ni Umar banda abinda zance wa tan uwa da abokan arzikin da suka taru a nan don ni kawai da iyalina.
Sai dai nace inawa kowa fatan alheri a rayuwan shi kamar yadda suma suka taru anan don ni da iyalina.
Ina ma kowa fatan alheri shima mutumin yace na gode da lokacin ka da ka bamu shima yace ya gode.
Nan suka jaye kayan aikin su suka bamu guri inda muka shiga gaisawa da mutane dake jiran mu a haraban.
Can na hango anty Amira da wani dogon mutum a tsaye daga gefe daya na zare hannuna daga rikon da sadauki yai min na nufi gurin ta.
Da dan sauri na na rugumota a jikina itama dai ba laifi ta riko ni din tana dan murmushin yake a fuskan ta.
Nace anty nayi missing din ku mun samay ku lafiya tace mun dai yi missing din dan uwan mu kawai Bintu.
Nasan magana ta fada min don tana fadan haka bata tsaya ba ta wuce zuwa gurin sadauki mutumin yabi bayan ta tabar ni a tsaye nan.
Naji an dafa kafada na ina juyawa anty maryamce tace kada ki damu don ko kin saba da halinta yanzu ai.
Shigowan su Nafisa ya katse muna zancen mu nan suka rugumoni da farin ciki suna fadin kai matar yaya kin bamu kewa wallahi sosai.
Barin Nafisa da mutumin da take tare dashi wanda ta gabatar mai a matsayin wanda zata aura wai.
Yayi ya nufo inda nake tare dasu nafisa nan suma suka shiga gaidashi tare da mashi sannu da zuwa suna mai taya shi murna samun karuwan da yayi.
Hannuna ya kama zuwa kofan shiga gidan namu wanda yake a rufe a lokacin don za, abude shi da addua don shiga ciki.
Malaman da aka gaiyato ne suka bude gidan da addua tare da fatan gamawa da duniya lafiya.
Mun shiga gidan da farinciki gaba daya mutane sai yaba kyau da tsarin gidan suke yi.
Abincin da aka girka don taron mu aka shiga ci kowa sai da ya wadata yaci ya koshi zuwa yamma mutane suka dinga watsewa daya bayan daya kowa a cikin farin ciki.
Ganin an dan rage yawa sai yan gida tsiraru suka rage ba yawa yasa na juya gurin anty maryam nace zan dan shiga ciki anty .
Tare da ita muka shiga dakin da yake a matsayin mallakina wanda yasha kayan alatu sosai na zamani don komai daga waje aka shigo dashi a gidan.
Yana zaune tare da Amira da Bashar dasu yaya sagir da yaya Abdul suna hira.
Muna mikewa ya bini da wani irin kallo na so da kauna yana cewa maryam ki barta ta huta please koma may ye ai zata labarts maki idan kun natsu.
Don nasan bakunan nan naku tab yake da gulman da kowan ku ya tara ya tsiyayawa dan uwa.
Nace kai haba dai yaya kana iya raba anta da jini ni da anty maryam sai Allah fa.
Yace ai na gani na kuma sani don gashi ta haki zaki barni a nan ni kadai.
Kai kade kuma yaya inji Amira yace kin san na saba da matata yanzu bamu raba second a tare.
Amma wanan da kike gani naga yau tana son nisanta ta dani idan ban yi niya ba.
Amira ta kawar da kai gefe daya don ta fahinci i yanzu ba karamin ji dani yaya sadauki yake yi ba har bai iya boye feeling din shi a gaban kowa.
Ga wani irin kyau da haske dana kara tare dani ga wani annuri da take gani yana fita tare dani.
Lalai kam Bintu tayi sa, a da dace a rayuwan ta na jajircewa da tayi ta mallaki zuciyan sadauki da ma ruhin shi a baki daya.
Lalaikam shima din yayi dace samun Bintu a matsayin matar aure a gare shi don mace mai kyau da addini rahama ce ga namijin daya samay ta.
Kalli yadda ta koma yana wani ji da ita da dan shi wanda ko dan kukan yaron bai son ji komai nasu gwanin burgewa.
Gaskiya yayi sa, an samun mace mai kyau a rayuwan shi da Rahama ce ai bazai wani jin dadin nunata haka ba a duniya.
Ba Amira ba kowa ya kalle mu zancen zuci yake a kan mu don ko mun dace da junan mu sosai.
Don sadauki za, ace mutum ne mai sa, a a rayuwan shi ga dukiya mai tarin yawa Allah ya daukaka shi dashi.
Ga mace ya samu mai kyau da tarin addini tare da ita ta gyara mai rayuwan shi don duk wanda ya ganshi yasan ya watsar da halaiyar shi ta da can baya.
Hassada dangin shedan tuni Amira ta mike tana fadin ita zata tafi gida sai anjima kuma.
Sadauki yace haba Amira tun yanzu ki tsaya mana har ayi sallah sai ki tafi gida tunda ba koranki ake ba?
Tace no bari kawai na tafi don naga kamar kana son hutawa ne da iyalin ka tafice tana cika tana batsewa a ranta.
Ya gurgiza kan shi yabita da kallo don yasan abinda take nufi akan Fatiman shi ne take wanan cikar haka tana batsewa ita kadai.
Sun dan jima suna hira akai kiran sallah suka mike zuwa sallah nikan muna dakina mun baje da maryam muna hiran yaushe rabo da ita.
****** ********* ******
Bamu samu jan mu ba sai bayan karfe tara kowa ya watse yarage daga mu sai iyya a gidan da take ta faman gyaran guri.
Ya fito daga dakin shi a cikin jallabiya baka mai gajeren hanni yace haba iyya wanan aikin yai maki yawa fa gaskiya.
Nace a nemo muna wasu masu taimaka wa agidan mutum biyu aikin ki kawai ke yanzu shine kula da Matar gidan da yara ba ruwan ki da wanan aikin kuma haka.
Tace haba Alhajina har ina aikin yake a nan ai ba sai an nemo wasu ba zan iya ko ni kadai.
Yace a, a iya na gama magana ko gobe ne insha Allahu masu aikin zasu fara zuwa sai ki gwada masu komai daya dace suyi.
A lokacin na fito ina saye da wani dogon riga dinkin shi simple ne irin na zama gida mai launin jikin kura, kaina da hula dana daure gashina a cikin sa.
Nan nake cewa , a, a iyya baki huta ba hakana har yanzu don Allah ki huta kibar aikin nan haka har da samay ga Amir kuma goye a bayan ta tare dashi take aikin.
Tace wai na dan rage kayan nan kafin safe kada gurin ya kwana haka da kazanta.
Badai tsabta ba kan Iyya don mace da bata haihuwa dama ance tsabta gare ta sosai haka ne ya kasance ga iyya din don yar ta daya a duniya.
Kima tayi aure sai dai ba wani dadi a gidan auren don wahala take sosai sunan ta suwaiba.
Yatana da yara uku ga mijin bai wani aiki sai dan buga bugan da yakeyi kawai iyya tasha min magana akan wanan zaman na Suwaiba haka nan.
Haka yasa na sa a raina zan wa yaya magana akan wanan matsalan don ya kamata a taimaka ma rayuwan su don Iyya gaskiya ba laifi mace ce mai rikon gaskiya da amana.
Fruit muka zauna muka dan sha muna hira yaso fita da daren zuwa gida don yaga iyayyen shi sai dai yana tare da gajiya.
Waya naji sunyi yana ba baba hakkuri sai da safe zai shigo ya duba su insha Allahu.
Bamu jima ba muka shige ciki muka kwanta iyya ta bukaci na bar Amir a gurin ta wanda naji dadin hakan.
Don ko banza an kunsa yaye shi ma a lokacin don haka yana bukatan dan jayewa daga gare mu.
Don ya manta da nono da sauri a cikin sauki batare da ya wahala ko ni na wahala ba.
Washegari ma masu zuwa muna sannu da zuwa sun kara cika muna gida ba wani hutu sosaia lokacin don jama, a kada su ce ina masu fadin rai
Kowa haba haba nake da zuwan shi don duk abu daya ne ya kawo su da mai kudi da tallaka sunzo ne don nuna farin cikin su gare mu.
Na fahinci mutane mu suna a cikin wani hali na haula, i don wahalan da ya ishi mutane haka yasa duk wanda yazo naga yana da dan rauni nake taimaka mai wasu zan basu sabulai da kudi wasu kuma sun fi karfin karban kudi a gurina sai dai na basu tsaraban abinda ya dace dasu wanda ankawo min abubuwan da zan rabawa mutane dake shigowa taron mu.
Sai bayan kwana biyu da dawowan mune na fahinci an canza muna ma, aikatan mu dana saba dasu abaya.
Ma, ana anbarsu a tsohon gidan mu da muka taso haka yasa banji dadi ba nai magana da yaya yace zai duba al, amarin.
Da yamma kuwa sai ga Atiku da iyalin shi sun zo taron mu na tare su da farin ciki nake tambayan su yaran su sukace suna lafiya.
Tare ma suke da maigidan su yana waje nace a, a shine zai tsaya a waje ku shigo dashi mu gaisa mana.
Amaryan shi ta fita ta shigo dashi nan muka gaisa nake tambayan shi mai yasa bai dawo nan inda muka dawo ba.
Yace hajiya ance nan kayan aikin ku duk yanzu na naura ne bazan iya aiki dashi ba nace haba haba basai a koya maka ba.
Gaskiya daga gobe gaba dayan ku har su baba musa duk a nan zaku dawo da aikin ku sabbin a kai su wancan gidan.
Nan ya shiga min godiya nake tambayan shi Aliyu fa suke ce min yana nan gida kudin makaranta yai tsaye tunda maigida baya nan.
Banji dadin jin haka ba nace gobe yazo da yaron za, a san abinda za, ayi akai insha Allahu.
Nakawo tsaraba da kudi na basu shi kuma mijin na bashi kudi ga sayi shinkafa dashi.
Nan ya dukar da kai sai hawaye ya fara zubo mai yana cewa hajiya ban san irin godiyan da zan maki ba keda maigidan ki akan irin taimakon da kuke muna a rayuwan mu ba.
Ga yaron nan Aliyu maigidan ki ya taimake mu a baya an mashi aiki ance da ba, ai aikin ba haka zai koma dan luwadi shima don abin zai ta damun shi idan bai yi ba.
Yanzun ko kinga zancen ya koma tarihi a sanadinku ke da maigidan ki da kuka taimakawa rayuwan mu.
Nace haba malam atiku babu komai ai duk yiwa kaine may ye amfanin kana tare da mutum baka taimaka mashi ba.
Munyi sallama dasu zasu tafi sai ga maigidan ya dawo nan suka tsaya suna gaisawa dashi.
Yace malam Atiku hajiya tace sai a dawo daku gidan nan ko nai magana da Bashar yace duk zaku dawo nan da aiki daga gobe insha Allahu.
Nan ya shiga godiya nace ai na manta maman Aliyu don Allah ina son kuyi min wani taimako keda abokiyar zaman ki.
Sai gaba daya hankalin kowa ya dawo a kaina nace ina son don Allah duk safe a dinga dama muna koko da kosai ana kaiwa makaran tan dake da almajirai sadaka da yamma kuma ina son duk ranan jumma, a a dinga dafa shimkafa da wake buhu daya ana kaiwa sadaka a wanan makarantan.
Don haka sai kuyi min lissafin abinda kuke bukata daga kayan aiki da kulan da za, a dinga zubawa sai naji na aiko maku da kudin.
Kara zubewa sukayi a gurin suna min godiya cikin jin dadin wanan ci gaban da suka samu na rayuwa.
Tunda dama manejin rayuwa ne sukeyi ba wani sana, an da sukeyi yanzu zaune kawai suke a gida dan abinda mijin su ya samo ake amfani dashi.
Munyi sallama dasu akan zanji sako daga gurin maigidan su idan ya zo gobe aiki.
Suna fita sadauki ya juyo inda nake zaune yana sauke ajiyan zuciya yace wanan sabon hikimar kuma ta maynene queen ?
Nace godiya da neman kariya ga ubangijin mu yaya na kasan duk wanda Allah yai ma baiwa ya kamata ya gode masa.
Sai nake ganin yaran almajirai masu bara a titi zamu taimaka da dan abinda zasu ci suji dadi a ransu muma muji daga ni, imar su.
Yace haka yana da kyau sai kuma may kike gani ya dace ayi don kudin kwallon da na samu wanan karon ina son inyi amfani dashine a sadakatuljari,a
Nace akwai magidanta mabukata yaya da abinda zasu ci da iyalinsu yake masu wuya akwai kuma marayuwa da ke neman taimako don Allah ya kamata ayi awani abu akai yace insha Allahu angama queen.
Na kuma gode da wanan shawaran taki zan duba nasan abinda za, ayi na taimako ga alumma daya dace ayi.
Sai da mukai kwana uku na shirya na tafi gaida su mama don lokacin mutane sun dan tsagaita shigowa muna sosai gaida mu.
Wanda wasu gulma ne kawai ke kawo su gidan don suga yadda gidan namu yake ne.
Shiga nayi na alfarma dagani har Amir da Iyya muka tafi gidan namu sadauki ne ya jamu a mota.
Mun samu su lafiya sai dai gaskiya duk akwai sauyin canji a tare dasu mama ce kawai zaka kalla kasan bata da wani matsala a tare da ita.
Amma sauran gaba daya duk sun wani jemay kamar basu ba Umma duk kiban nan nata yanzu ya tafi tsufa ya taso mata sosai tare da ita.
Ga furfuran dole daya bata masu kansu ita da mama Asiya yanzu kana ganin su kasan suna cikin wani bakon yanayin da basu saba ba a baya.
Mama tai matukar farin ciki sosai da ganin mu ta shiga haba haba damu a gidan.
Kaunata dake gurin ta ta murje tayi kyau da ita sosai harda tsayi naga ta kara min da haske ga sabon da naga sunyi da mama sosai yanzu.
Itako yar bakin rai na kusa awa daya a dakin bata fito ba tana can tana ji da kanta a daki don suna da wata yar dattijuwan da ke masu komai a shiyan su basu ko kauda kara sai matar ce mai aiki.
Can tafito tana wani cika tana batsewa nace a, a anty Amira ai na zata kin fitane ban san kina ciki ba wallahi.
Ta zauna tana cewa ina ciki na kwanta ne ina jin shigowan ku bandai fito bane kawai.
Nace Allah sarki mun samay ku lafiya tace Alhamdullahi a takaice inda Amir yake zaune yana wasa ta kalla tace my boy kaine wai kazama wani bulele haka dakai?
Nace anty aiko yama ramay sosai don tun shekaran jiya da muka dawo bai faye lafiya ba baya son cin abinci sosai sai anyi da kyat yake dan shan tea.
Ai dolr kuyi kiba kuna cin gashin kanku kun manta da kowa kina kokarin raba muna dan uwa damu.
Nace kai haba anty ni na ma isa na rabaki da yayan ki kin dai fada ne kawai ra,ayinki.
Amma ai tsakanin ki da yaya sai Allah tace lalaikan gani nan bari nan takalmin kaza.
Murmushi yayi daga inda yake zaune kusa da mama yace wai ke yaya zance da mukayi ne na ma,aikacin bakin da kikace min kin samu.
Ta wani lumshe ido tare da bin lafiyan kujeran da take zaune akai tace yana nan yaya.
Naga baka da lokaci ne ai sai na matan ka yanzu shi yasa ban fito ma da zancen ba ranan da kazo.
Yace kin san Fatima yanzun queen ce lalaba abata nakeyi a hankali don banson ganin bacin ranta akan komai.
Haka kuma duk wanda yai niyar bata mata rai wallahi sai inda karfina ya kare akan mai shi don bazan dauki rozarci akan iyalina ba ko kadan.
Tasan da ita yake wa warning don haka taja bakin ta tai shiru tana sauraren shi har ya kare zancen shi.
Yace mata ki fadawa mutumin yazo mu gana gobe da dare karfe takwas don kafin aiki ya taso min idan son samu ne ma har aurwn nake son ayi akafin lokacin.
Sai ya mike tsaye yana fadin shi zai fita nace don Allah yaya rogo nake so da zogala na dade ina son cin sa tun muna turai nake kwadan shi wallahi.
Na juya gurin mama ina cewa mama akwai man shanu ai ko ?
Tace akwai shi fatima yace yau kuma abinda kuke son ci ke nan kuma kayan yan kauye.
Abinda aka samu a turai ina shi ina kwadayin abincin yan kauye kuma maimakon yai kwadayin kayan sanyi.
Mama tai murmushi don sai yanzu ta fahinci wanan mugun kyau din da nayi bana banza bane ashe dama tai hasashen hakan amma sai taga ai Amir ko shekara daya bai kaiba watan shi ma na takwas ke nan da haihuwa.
Ko iya sai lokacin tagane ciki gare ni tace kai masha Allahu uwar dakina Allah ya raba ku lafiya yasa wanan karon ba dan zama asibiti bane kuma aka samu kamar maigidana cewa Amir.
Au ita yanzu cikine kuma da ita ina ruwan naga banza wai kina nufin kiyi saurin cika gida da diyan ki kafin wata ta shigo ko may?
Banza kuma Amira wai ke wata irin shashan yarinya ce mara wayo haka dake ?
Abin arziki ya samu maimakon kiyi farin ciki da karuwan da aka samu amma mugun halinki yakaiki ga hasashen banza kuma.
Kai maji nidai ba dama nai magana akan Bintu sai an zageni don tabi ta hada mutane da ku baku ganin kowa sai ita haba maji.
Nace nima anty wallahi ban so cikin nan yanzi ba Allah dai ne ya kawo shi don ban manta da wuyan da nasha ba gana wanan din.
Amma to yaya zanyi Allah ya riga da ya kawo shi basai na yi hakkuri ba da ikon Allah.
Amira kada fa naji kinzo kina karamin murya naba yara suzo maki weekend na hanaki kice zakiyi fushi ya fada mata hakana.
Komai Amira tai mai yana kokarin shanyewa ne don ya fahinci ita haka Allah yayita da bakar magana.
Shi kadai ne kawai nasu ke zuwa masu daya koshi don baya biye mata ne kwai suke zaunawa lafiya amma ita haka take da kowa ba dadi nata kalar rayuwan ke nan kuma ita.
Shi dai ya fita da yaji fadan mama ya tsanan ta akan Amira din yana cewa haba mama kiyi hakkuri da yar sister na ta dai kusa wucewa tabar maki dakin ki itama ta huta hakana kamar kowa.
Bai dade da fita ba sai ga yaro da rogo cike da zogala nan na zauna da kaina na shiga gyarawa hankali kwance kowa sai da yaci banda Amira da take ta faman fushi ita kadai.
Mukan sai faman hira muke da mama da su iyya da yar aikin mama din don mama bata dauke ta wata yar aiki ba can.
Ina basu labarin abubuwan mamaki da na gano a tafiyan mu da irin daulan da na gani a gidan Abu sifiyanu mai kudin duniya.
Duk sun natsu ina ta basu labarin irin daukakan da yaya sadauki ya samu a duniya ta wasan kwallo.
Tsukin Amira mukaji ta mike fuuu ta shige ciki cikin bacin rai dama kuma don ta kule ne nake kara bada labarin tunda na gane ita yar hassada ce a rayuwan ta.
Don maganan da tayi kan cikin dake jikina ya bata min rai dakewa kawai nayi kada mama ta fahince ni ta kara mata fada.
Baba ya aiko yana kirana nan na mike na saka gyale na nufi dakin shi nan na samay su zaune da mummy kusa dashi.
Na shiga da sallama na tare da gaishe shi yake cewa yanzu kubura take fada min cewa kun shigo ina barci nace takiraki mu gaisa.
Nace eh baba ance ka samu barci shine nace a barka tunda anan zamu wuni mun samay ku lafiya ko ?
Yaya karfin jikin naka kuma yace Alhamdullahi Fatima ai iyayyen ki gasu nan suna bani kulawa sosai wallahi.
Kinga ita wanan ma yanzu ta aje aikin ta don lalura na itace take min komai ita da hauwau.
Jiki kan naji sauki sai dai tafiyan da ban iya yi ne kawai har yanzu matsala koshi likita yace insha Allahu da sannu zan dan iya fara takawa.
Nace Allah ya nufa baba ya amsa da Ameen Fatima yaya maigidan naki kuna dai lafiya ko?
Nace lafiya muke baba ai tare ma muka shigo dashi ya tafi ys dawo ne yabar mu anan.
Fatima Allah yai maku albarka a rayuwan ku ina mai alfahari da kasancewar ki mata a gurin sadauki.
Don nasan wani abin tare da taimakon ki ne yake yin shi a rayuwan shi yasa Allahda Annabinsa sukace ku auri mataye na gari don ku sama ma diyan ku uwaye na gari a rayuwan su.
Ke alheri ce sosai Fatima a rayuaan dana wanda ina matukar alfahari da hakan ko yaushe kasancewan shi tare dashi yasa sadauki gaba daya ya sauya daga sadaukin da muka sani a baya.
Duk wani mumunan halaiyar shi yanzun yazama tarihi a gurin mu da bakece ya aura ba da sai dai muce Allah ya kyauta kawai.
Gashi natashi kudi suna shigo mai ta ko wani hanya may zai sashi tunanen gyara wani mugun halaiyar shi can na baya da basu da kyau da ai saidai kawai yaci gaba da gurbatacen rayuwan shi babu mai kwabon shi a kai.
Amma duk irin kokarin da kikeyi a kan shi ina da labarin komai a kunne na Fatima.
Allah dai yai maku albarka yasa ku gama da duniya nan lafiya yabaku zuria dayyaba masu maku biyayya kamar yadd kuke muna.
Na amsa cikin kunya da Amin baba na gods nima da kuka mai da rayuwana haka don kune silar komai da nake ciki a yanzu.
Yace kai haba dai Fatima ai mune dai da godiya a kanki yadda kikai muna biyayya haka yau gashi ya zama muna alheri ga baki dayan mu ko.
Haka dai nabar gurin baba yana ta saka muna albarka da fatan gamawa da duniya lafiya a rayuwan mu kamar yadda ko wani da ke bukatan addua ga mahaifan shi kullun.
Sai dare ya dawo ya kwashe mu muka bar gidan zuwa gidan mu cikin farin ciki a ran mu yadda iyayyen mijina suke zuka ma rayuwan mu albarka haka.
Muna hanya nake cewa ashe mummy tabar aikinta ne akan rashin lafiyan bab ?
Yace wallahi fa haka sagir ya fara fada min da kuma naje gun baba din shima yake fada min haka din.
Nace ai ko ta kyauta wallahi don haka shine zama tare yace ai zan duba akan al, amarin don asan abin da za, ai mata akan haka din.
Nace yaya bafa mummy ba kawai dukkan su sun bukatan taimako wallahi don alama ya nun sun a cikin wani hali wallahi ba dadi da ganin su.
Yace nima nai tunanen hakan amma banji kince komai ba shi yasa nai shiru nima.
Nace kai haba yaya nice kuma zanyi magana akan taimakon iyayyen mu yace bakece P A ba ke ce ya kamata ki tsara abinda ya dace a kan su ai.
Nan na shiga zaiyano mai abinda ya dace ai masu din don a taimakawa rayuwan su har muka kai gida kowa ya shiga part din shi don watsa ruwa ajikin mu ko zamuji dadin hakan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,
IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA IDAN KINYI HAKA MUN BARKI GA ALLAH.
Alheri sosai ya tanadarwa su Mama da Umma da mummy har motar shiga sai da ya canza masu tare da gyara masu dakunan su tsab.
Wanan ya zamo karo na farko da sukaji dadi a ransu abinda taya sadauki yake masu na alheri wanda hassada baya bari suga irin alherin da yake masu abaya.
Yanzun ko abu yakai babu gare su duk yadda mutum yai masu alheri komai kankantan shi suna godiya sosai.
Don yanzu wanda suke samu gurin shi watau baba shima ta kanshi yake yi baida komai duk diyan su sun wawashe mai shago baida wani abin hannun shi kuma inba gonan da sadauki ya saya mai ba farkon fitan shi wasan kwallo da yafara zuwa.
A takure suke komai da suka fi karfi a baya yana basu sha, awa yanzu shi yasa suke ganin wanan kyautan na baya yazo masu kamar kyauta na farko da ya taba masu.
Har daki mama Asiya ta samu mama tana mata godiya wanda mama ma a lokacin bata san da wanan alherin ba inba yanzu da mama Asiya tashigo mata da zancen ba.
Mama tace ikon Allah wallahi yaya banda labarin wanan zancen yanzun ma nake jin shi a gurin ki.
Godiya dai ta karayiwa maji tare da fatan alheri tana ta saka albarka wanda maji ke gani yau kamar a mafalki.
Mama Asiya ce sakawa dan ta albarka haka akan alherin da yai mata don jin dadin zuciyar ta.
Mama Asiya tana fita har tsakar gida tana godiya Nafisa ta gamu da ita dakin su tashiga gurin mahaifiyarta tana cewa kina nan zaune halan may ya faru naga mama tana ta godiya a waje tafito dakin maji.
Umma tace nasan taje godiya ne godiya akan may kuma Umma ?
Tace yanzu Sagir ya samay mu da kyautan alherin da yayan ku dan kwallo ya aiko muna dashi mu uku motace ya sake muna da kujerun daki da gadaje sai kudi wai mu saka mai a mota da kayan abinci.
Nafisa tace tirkasa amma ko Allah ya saka mai da alheri wallahi to umma shine kike zaune ke baki zuwa kiy godiya?
Koda yake yadda naji kina magana kamar har yanzu kin saura hassadan abinda yafi karfin ki fada.
Dadai kin sakawa ranki ruwan sayi kibi kici arziki dayafi maki wanan hassadan da kukeyi shekara da shekaru yaki kare.
Ga yar uwar munafuncinki ta sulala taje tayi godiya tabarki nan kina hassada ga banza.
Kallon takaici taiwa yar tata da suke dauka a matsayin mara hankali ga maganan ta da dabiun ta amma kuma gaskiya ai Nafisa ta fada mata don tasan mama Asiya yanzu tana zare jikin ta tana hurda da al, amarin maji da yayanta.
Nafisa kan dakin ta tashige takwanta abinta yanzun ta daina sha sai dai bata bar harkan bazan ta ba da ta saba.
Sagir ya shigo ya samu umma zaune tayi tagumi ganin shi ya dan sata sake jikin ta tana mashi tayin abinci.
Yace Umma na fada maki yanzu a gidan yaya sadauki muke karyawa ni da Abdul komai dare sai Fatima ta kira mu muzo muci abincin mu yana aje haka ma dasafe.
Umma taji wani iri a ranta ba dadi tasan cewa ko ba komai anyi hadin zumunta a gurin kafin takai karshen tunanen ta taji muryan shi yana cewa.
Wai ko Umma kin san wani abu fatima fa tai muna kanfen gurin yaya ga sabon gurin aikin da za, a bude a abuja nasu.
Shi da kanshi yaya sadauki din ke fada muna cewa wai yar uwar mu ta nuna son kai ta matsa ita sai dai muma a nema muna babban gurbi a can mu kama aiki dasu ko kuma wanda ke nan sokoto.
Umma wallahi yadda suke gwada muna halarci irin haka ni abin ma har kunya yake bani yadda a baya mukai ta gwada masu kiyayya a filin Allah .
Amma sai gashi yanzu da ya samu mune na farko samun alherin shi harda mota fa yace zai saya muna wallahi.
Bamu kadai ba har dasu yaya Imiran naji ana magana a kansu suma za, a basu appointment a gurin.
Tace kai amma ko da ya kyauta muna wallahi don zaman banzan nan na Imiran ya fara ista wallahi.
Umma yanzun dai jekiyi naki godiyan kafin wani lokaci kuma kin san irin wanan alherin na bazata shi ake kira da kyautan dan aljanna.
Kyantan da zaizowa bawa a lokacin da bawa yake a bukace da wani abu a rayuwan shi dubi fa wa yan nan kujerun yadda suka koma kamar tsunma ni har kunyan nake jin azo agansu a dakin nan haka wallahi.
Bai bar dakin ba sai da yaga Umma ta mike yaga ta nufi dakin maji hankalin shi ya kwanta.
Don bai zai yuyuba ana masu alheri irin haka amma ace su har yanzu basu daina hassadan su ba da sukeyi.
****** ********* ******
Allah mai iko a yanzu ankai duk inda sadauki ya sa kafan shi yana tare da manyan body guard masu tsaron lafiyan shi dana iyalan shi wanda goverment da kansu suka bashi su don tsaron lafiyan shi.
Saboda gashi karamin matashi amma yana daya daga cikin manya masu shigo da manyan ababen amfani daga kasashen duniya.
Haka yasa ya zamo abin kula sosai a gurin manya na kasa da suke fada aji.
Saboda ya zamo daya daga cikin yan kasa masu kishin kasan su don sun cigaban matasa.
Gashi akan kamfanin da suke son kafawa har guda biyu na mai dana manyan jiragen ruwa da zasu dinga shigo da kaya daga waje.
Ga manyan injima na haska wutan lantarki da za, a shigo dasu kasa don amfanin kamfanonin da za, a gina nan n
Nageria.
Ban fita sosai zuwa yanzu don cikina da yai matukar girma don ko a wanan ma likitoci sun kara bani bedrest sai dai ba kaman wancan na baya ba danayi na Amir din.
Ina kwance saman dogon kujera a falo na dan mike kafafuna na da sukai min nauyi.
Yashigo gidan a gajiye dashi su Sagir suna take mai baya shi da Abdul dauke da dan briefcase din takardun shi da laptop dinshi a cikin case din.
Ya zauna yana cewa kai nagaji da yawa wallahi nazaci a nan idan na dawo ko zan huta amma gashi duk ba wani hutu da mutum ya samu tare dashi.
Na dan lumshe idona tare da kokarin mikewa zaune don na karbi case din zuwa dakin shi.
Yace da sauri No No kwanta abinki ki huta barshi idan zan shiga zan shiga dashi ai.
Bayan ya karasa kaiwa zaune ne yake cewa duk rashin samun hutu ya saka har kirjina yana min ciwo wallahi.
Da sauri na dago ina kallon shi nace amma gaskiya tunda ka fara jin haka ya kamata ka samu hutu ka zauna a gida koda na kwana biyu da zaifi ma.
Yace na kwana daya dai Fatima kwana biyu yai min yawa ga mu da tulin aiki mai yawa a gaban mu.
Idan ba naga angama gina muna komai ba hankalina bazai taba kwanciya bane ai kinga dukiyar mutane ne nauyin shi ya hau kaina dole na kula masu da abinsu ko?
Nafisa ce tashigo gidan da alamun damuwa a fuskanta nan muka zauna da ita ana hira suko abinci suka wuce ci a dining.
Yana gamawa ya shiga ciki ya dan jima bai sauko ba yana sama koda zai fito ya sauya kaya jikin shi a lokacin.
Tun bai kai zaune ba ya soma magana yana cewa gaskya kauna ya kamata ace kifito da miji hakana kiyi aure na hada ku da Amira dama yan sa, a daya kuke kinga kowa sai ya huta abar Rukaiya har su karasa nasu karatun.
Cikin wani langabe kai tace ni yaya wama zai aure ni kawai ni na fitar ma da rai ga wani aure can
Da sauri nace haba anty ce astangafurullahi mana yaya zaki magana kamar ba musulma ba dake.
Tace to madam wakike gabin zai aureni a haka yadda nake duk masu zuwa gurina ba da sunan aure suke zuwa min ba sai dai da tasu bukata kawai.
Gaba dayan mu tausayi tabamu ga maganan ta don mun san cewa gaskiya ta fada maganan ta.
Amma kuma ai abin Allah ba a yanke kauna a gare shi nace anty gaskiya yaya ne ki natsu ki rage wasu halaiyar ki ko Allah zai tausaya maki.
Don kinga ai Allah miskaraziratin ne ba abinda ya gagari ubangiji sai kinyi mamakin irin mijin da Allah zai kawo maki idan kin natsu.
Kafin tabani amsa wayan ta yai kara jin sunan wace ta kira da Raye yasa na gane da Raiha take waya a lokacin.
Tambayan ta tayi tana ina tabata amsa da cewa gani nan gidan su madam ina shan sanyin A C.
Tabata amsa da gata nan tafe tana gamawa yake ce mata kinga ni maganan ki bawai ya karbu bane gareni fa kiyi tunane a kai ki gyara halaiyar ki Nafisa .
Mace fa dan guntun lokaci ke gareta tun anayi daku watarana masu neman naku gudu za, suyi su koma ga
wasu yan matasan
Ta amsa a marairaice da tau naji yaya insha Allahu zanyi kamar yadda kace amma zaka dinka min hijjabbai na fara sakawa ko?
Murmushi yayi yace gatanan yana nufin ni zata dinka maki ko guda nawa kike so kaunata.
Nidai kawai ki natsu ki daina wanan halin please.
Shigowan Raiha ne yasa muka daina zancen suka gaisa da shi ya mike zuwa babban falon shi na waje da yake taron baki a cikin sa yabar mu nan zaune a na cikin gida da waya a hannun shi yanayi.
Nan muka fara hira dash nake tambayan Nuriya suke ce min wai tabi wani saurayinta dan Ibo sun tafi lagos tare.
Banji dadi ba na kasa boye bacin raina nake cewa haba dai haba ace kuma mutum yana hurda da harda wanda ba musulmi ba kuma ai abin yayi muni gaskiya.
Raiha tace madam kawai dai Allah ya gafarta muna zamuce don dai gaskiya nima yanzu da hankali yafara zo min na gane hakan ba daidai bane.
Ni yanzu fatana kawai Allah ya kawo min miji wanda zai soni tsakani da Allah wallahi ko yaya yake zan zauna dashi na natsu bakiga yadda al, amarina har yasakawa iyayyena cutan hawan jini ba.
Tace to mazan ne yanzun sai a hankali wallahi na rasa wanda zaizo ma da tsigar so na gaskiya bada bukata ba.
Nafisa tace maganan da muka gama ke nan da yayana kafin ki shigo abinda na fada mai ke nan kema yanzu sai gashi kinzo dashi.
Tace wallahi muna son auren bawai bamu so bane to amma wazaka aura shine matsalan.
Istigifar bai bar komai ba ku koma ga Allah kwana biyu kuga ikon Allah wallahi bana jin dadin irin wanan rayuwan da kukeyi yanzu ya kamata ace kunyi wa kan ku fadan hakan.
Shi yasa nake son ki madam wallahi kece kawai zan iya cewa a yanzu kina tsayawa ki nusar da mutum hanyan alheri bayan kowa ido yakawo ya saka muna.
Ana jiran da garin Allah ya waye kai wani abin asha asakaka ga faifai a tallata ka.
Yaya sadauki ne yashigo yana ce min sai ki shirya don muna da bakin da zasu duba gurin da za, a gina kamfanin shimkafa a garin nan
Gashi sunce min ba, a hotel zasu sauka ba anan gidan zasuyi masauki don haka sai ki samo wanda zasu yi aikin abinci idan kuma bayarwa zakiyi ai masu duka daya.
Kafin ma ya karasa zancen shi sai cewa Raiha tayi bagamu ba yaya aikin may mukeyi dabaza mu yi ba mu.
Baiyi magana ba don na lura hankalinshi bai kwanta da al, amarin Raiha din ba wanda shine bai fahince ta ba sauki kaine da ita sosai.
Amma shi yana ganin sune suke jefa yar uwarshi a cikin wanan mumunan harkan da sukeyi tare.
Bai san tafi su zama shedaniya ba don ita ta hure fitillar ta sosai ma fiye dasu.
Mun jima dasu muna tatauna abinda ya dace muyi da wanda zamu saya na bukatun mu.
Har sai bayan sallah magariba suka tafi mukai sallah suna cewa idan an shirya na kirasu.
Bayan yashigo gidane yake fada akan cewa may zaisa na yarje ma wa yan nan mashiririta suyi mai aikin abincin bakin shi yaushe ma suka zauna balle su san yadda ake girki su.
Nace haba yaya sai kace ba mata ba su gani kuma ga iyya a gurin ai zamu taimaka masu da wani abin.
Yace da sauri No no kada ki soma cewa zakiyi aikin komai kin dai san yadda condition din ki yake please kada ki fara ki taba komai idan ma bazasu iya ba sai a kira wasu suyi final nace ballema insha Allahu zasu iya duk abinda suka lissafo zasuyi din.
Bai kara magana ba haka muka bar zancen don yaga na aminta dasu sosai yasa ya kyale badon yaso ba.
Izuwa yanzu alherin da sadauki yaiwa iyayyena bazan iya lisfoshi ba don muna waje sun tafi sun sauke farali ga gyaran gida da abin sana, a da ya sayawa kowan su a sanadiya na iyayyena da yan uwana sun fita a cikin talauci yanzu wanda hakkurina da biyayyana ne yajawo muna wanan alherin haka.
H
Yan uwa dama yan garin mu sukan zo neman alheri a gurina wanda nakan yi masu shi gwargwadon halina.
Lokacin zuwan bakin shi yayi bayan sati ya zagayo yabani kudi masu yawa akan abubuwan bukatan su.
Ban masu kyata ba na ba kudi fiye da wanda za, a kashe sosai suma su karu daga ciki suka shiga kasuwa saywn abubuwan bukata duk da wasu muna dasu a gida.
Ranan har anty maryam da Rukaiya sai da suka zo da mummy tare akai aikin komai dasu na fita kunyan baki yadda ya dace sai da aka hada abinci kusan kala goma sha biyu nau,i daban daban suka kara gyara katon falon muna na baki an saka kamshi da komai a falon yadda ya dace ayi.
Bakin basu shigo gida ba sai misalin karfe uku na rana dirin motocin da mukajine yasa muka gane cewa gidan mu ya dauki manyan baki yau don har dasu jiya da alaman akwa wasu manyan kusa a cikin su ke nan.
Nan aka shiga fito da kayan ci dasha bayan wanda aka kai masu da farko wa drivobin su.
Gida ya rude da hayaniya sai kai da komo su Anty Nafisa sukeyi a gurin ana yaba aikin da sukayi.
Allah da ikon shi a wanan sanadin Allah ya hada su da masu son su a gurin sukai wa yayan su magana kan ya basu kannen shi din nan yace yabasu.
Wasa wasa magana ya zama babba don ita Nafisa ta hadu da wani ustazune manager din wani babban company dake garin Abuja.
Ita ko Raiha wani sojane babba wanda gwaunati ta turo shi as a security guard na kasa ya kyasa mata.
Amira da mama tace tazo ta taya mu aiki tace ita ba yar aikin kowa bane ba inda zata tafi nan mama ta ganta ta kyaleta.
Amma daga baya da taji sun ba da tukwaicin dubu dari biyar wa masu aiki sai kuma ta shiga fada tana ganin laifina
Wai dama ni yar bakin cikine shiyasa na gaiyato yan iska su cika min gida shiyasa ita bata tafi ba.
Karshe kuma sai ga zancen auren Nafisa da Raiha da taji Allah ya hadasu da wasu manya sai dai ba yara bane su.
Nan kuma ta shiga zage zage kamar mahaukaciya wai ta yarda ni yar bakin cikine ta karshe sosai don ban son ta da arziki nafi bukatan komai sai a gani a gurina kawai.
****** ********* ******
Bukin anty Amira ya taso sosai ba kama hannun yaro don haka muke ta zirga zirga ba hutu don mu ke gudanar da komai akan bukin duk da gwatsale ni da takeyi tana nuna bata bukatan saka hannuna acikin al, amarinta sam.
Hakan bai sa na daina duk wani abinda nake da niyar yi ba don ba don itace nakeyi ba dama don Allah nakeyi da mijina da kuma mahaifan su.
Bata san ina da rana a gare ta ba sai da masu zuwa ganin dakin da za, a saka mata kaya sukaje suka dawo da labari mara dadi don ashe a family house za, a aje ta.
Kuma ga dakunan ba wasu dakuna bane maigirma a jere suke ita da uwargidan ta wace yar uwace ga mutumin da zata aura.
Da labarin yazo ba karamin tayar da hankalin ta tayi ba sosai nan ta tuburewa mutane akan Ibrahim ya cuce ta don cewa yayi gida zai kama mata haya don may yazu zaice a gidan su zai aje ta.
Sosai ta tayar da hankalinta akan bazatayi auren ba ta fasa hankalin mama yai matukar tashi gashi an gama komai akan shirin buki ga yan uwa na nesa har sun fara hallara a gurin bukin.
Kuka wiwi takeyi akan ita kan wallahi ta fasa sai dai akai wata ba ita ba don bazata wanan gidan da ake bada labarin shi ba babu tsari.
Mama kuma da yan uwa sun kafe kan lalai sai anyi auren nan sai dai ta mutu idan an kaita don bazata basu kunya ba.
Ganin matsalan yai yawa ga tashin hankali ga fuskan kowa idan ka duba ya sa na tashi daga inda nake zaune lokacin cikina yai girma sosai wata bakwai saura kwana goma nake.
Dakin da take na shiga na samay ta ta kifa kai ga filo ita kadai a cikin dakin tayi buji buji da ita kanta duk a hargitse dashi.
Zama nayi bakin gadon don bazan iya tsayi tsaye ba a yadda nake lokacin don karfi hali kawai nakeyi da kaina.
Duk da taji anshigo dakin bai sa ta dago daga yadda take a kwance ba cikin yanayin tashin hankali.
Cikin yar siriryar murya nace Anty Amira ki tashi muyi magana musan mafita akan wanan al, amarin don kuka ba shine mafita yanzu tunda kinga mama ta kafe akan sai anyi auren nan ba fashi.
Jin muryana yasa ta dago kai a cikin fushi tace Bintu for god sake ki barni naji da abinda ya damay ni please ke har wani taimako zaki iya yi min ?
Wani matsayi ke gare ki da har zaki dauka zaki iya taimaka min dashi a matsayinki ko don kawai kinga kina auren dan uwana kina juya shi yadda kike so to ni ba shi bane ko maji ki sani.
Murmushi nayi kawai nasan ban taba fari a gurin ta amma ni don Allah kawai nai niyar taimaka mata.
Nace a fili ba matsala anty ni don Allah nazo gurin ki don mu san mafita kawai idan kina da lokaci ki tashi muyi magana dake mu san abinyi tun ba, a kai maki kayan ki ba a wancan gidan yawan.
Wani kallo ta watso min kafin tace ina sauraren ki nace nagode naci gaba da fadin nasan bawai baki son Ibrahim bane a yadda nasan kun dade tare dashi kuna soyayya.
Kawai dai wanan matsalace ta gurin zama yasaki bacin rai irin haka sai nake gani idan yace zai canza maki gurin zama duk wanan matsalan zai iya wuce a tsakanin ku tunda soyayya ce ta hada ku ba kiyayya ba.
May kike fadi mutumin da ya kafe akan shi baida kudin da zai karasa ginan shi kuma baida wanda zai iya kama min hayan irin gidan da nake so a yanzu.
Nace insha Allahu anty idan don gurin zamane na rokeki Allah ki kwantar da hankalinki ayi wanan bukin cikin farinciki.
Yadda kowa yazo lafiya don farin ciki ya koma gida da farinciki a ranshi anty baku gaji yin kunya ba a rayuwan ku balle kuji kunya don Allah ni dai yanzu abinda nake so shine ki kwantar da hankalinki ki koma kamar babu abinda ya faru a baya don marasa da suyi kunya don yanzu kinga ido aka sakawa mama aga yaya zata kaya ana farin ciki zaki shiga gida mai kuntatawa.
Wani kallone takara watso min tare da cewa wanan shine dama maganan da zaki fada min din.
Nace eh anty don Allah tunda kuna son juna da Ibrahim kiyi hakkuri ki daure ayi wanan abin cikin rufin asiri insha Allahu bazaki zauna a wanan gidan ba.
Tsuki taja tare da marya da kanta a saman filo tace na zaci wani shawaran arziki kikazo min dashi har na bata lokacina a kanki haka.
Na dade a zaune ba tare da tajuyo gare ni ba ga wayan ta dake ta verviration taki dagawa.
Wanda nasan ba kowane ke kiranta ba a lokacin sai angwan ta wanda yake a cikin tashin hankalin kan cewan da tayi bazatayi auren ba ta fasa.
Nagaji da zama ina batun tashi anty maryam ta shigo dakin kallon mamaki tai min ganina da tayi a zaune ga maidakin ma kamar bata san ina zaune a gurin ba.
Tace ke kuma may kikeyi anan ina can ina neman ki mama tace wai wanan kayan kitchen din da aka fitar a mayar dasu a kwali tunda babu inda za, a saka su a gidan.
Tajuyo cikin zafin rai daga inda take a kwance idanuwan ta sunyi ja jajir dasu don kukan da tasha sosai.
Tace sai naga iban da akewa shirin auren da har ake maganan rage wasu kayan daki can akai badai ni ba.
Nikan da kyat na mike tsaye muka fita maryam tana mata dariyar mumuke muka fice.
A gajiye na bar gidan don dare yayi a lokacin yaya Sagir ne ya kaimu gida da kan shi don ban driving saboda matsalan cikin dake jikina.
Sai da nai wanka nafito falo na samu Iyya tana gyaran abin da zamu karya dashi tana kwaba abin da zatai muna sanasir dashi.
Ina zama ana kirana ga waya yaya sadauki ne wanda bai ma kasan yai tafiya a lokacin.
Mun gaisa yake tambayana ko mun dawo gida ko muna can gidan su mama har lokacin .
Nace mun dawo tun dazun har munyi wanka gani a falo ma zaune zan sha magani na kwanta.
Yace maji ta kirani tana fada min iskancin da wanan mara hankalin kewa mutane tun jiya wai ta fasa auren ko ?
Nace yaya bafa fasawa tayi ba kune dai baku fahince ta ba bawai bata son Ibrahim bane a, a gidan da za, a kaita ne bai bata ba don a cikin family house din su ne inda uwargidan shi take zaune.
Kaga kasan halin anty Amira da tsandan mutane bata son yawan hayani ita tafi son ta zauna koda yaushe silent bata son yawan hayaniya.
Ya karba kafin naci gaba da fadin don taita mugun hali ko?
Nace haba yaya ya kamata a taimakawa anty please bai kamata abar rayuwan ta a haka ba don Allah.
Yace ok yanzi so kike nima na biyewa haukan ta nace a fasa auren taita zaman gida ko?
Nace ba nufina ke nan ba yaya abinda nike nufi shine ka taimaka da baiwan da Allah yai ma na falala ka sama mata inda zata zauna don wanan auren nata yai karko kamar na kowa please ?
Ban fahince ki ba Fatima kima nifin nine zan bada gurin da Amira zata zauna da mijin ta ko may ?
Nace ai ba mijin ka zakaiwa ba yar uwar haihuwan ka zaka taimaka kamar yadda Allah ya taimake ka kaima ka sama mata gurin zama yadda take so.
Don yin haka kawai shine shedan dan uwata ya samu kuma mai taimako ne ga jinin shi don kaga ba Amira ba kawai wallahi har mama hankalinta a tashe yake akan wanan magana daurewa kawai mama keyi don ta bata karfin gwiwa amma ran mama baiyi dadi ba ace a wanan gidan za, a kai Amira gaskiya.
Yanzun dai na fahince ki yace nine zan aurar da ita kuma na bata gurin da zata zauna kamar na matsu da ita a gida ko ?
Nace wallahi yaya ba haka nake nufi ba ni nufi na shine kawai ka taimakawa rayuwan su tunda Allah ya hore ma abinda zaka iya yin haka din.
Idan kai haka ba karamin lada zaka samu ba har a gurin Allah don shine shedar zumunci yanzun fa kaine uwar mu kaine uban mu gaba dayan mu har kai.
Amira ba ko Nafisa ce da irin wanan matsala din zaka iya taimaka mata idan kaso saboda Allah.
Ji nayi ya katse layin tare da jan guntun tsoki haka yasa banji dadi ba a raina nasan bai yarda da shawaran da nake gani shine a matsayin mafita ba ni.
Bayan mun gama waya nasha magani na mun dan taba hira da Iyya akan zencen tana fadin ahi yasa ba, a son mutum ya faye bakin hali wallahi don karshen shi baya kyau.
Yanzu ga irin ta nan ai tace ita tafi kowa bata ganin kowa da daraja kamar ba mamace ta haife ta ba tafita daban a cikin yan uwa.
Nace Iyya kin san kowa da kalar halin shi ita nata rayuwan ke nan haka Allah yayi ta daban.
Ai ba za, a biye mata ba idan ana son auren yai karko sai a taimaka mata anyiwa banza ma balle ita.