← Book details Taki Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 3

Gabatarwa

Taki Zaman Aure Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

✧✦ 𝐓𝐀 Ƙ𝐈 𝐙𝐀𝐌𝐀𝐍 𝐀𝐔𝐑𝐄 ✦✧


𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲


*©️®️Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye ⚠*

SHIMFIDA...

“Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min liyi, yadda alƙalamin ya zana dole haka zanbi...
Daga lokacin da na fahimci haka, sai tsoro da fargabar me zai faru a gaba ya fice a zuciyarta. Tafiyar da babu dawowa ta zama dakuna...”

TA ƘI ZAMAN AURE...
Share fagen wata tafiya ce mai sarkakiya da daure kai. Wata kalar kaddara ce mai rikitarwa, shimfida ce dake lalaye tafiyar wasu daidaikun mata....

Tafiya ce ta irin matan da duniya ta canja musu zane, suke da wani rufaffen sirri a zuciya! Sai dai kadan daga masu ilmi ke fahimta. A cikin rayuwa akwai mutuwa haka ma a cikin mutuwa akwai rayuwa shim kun ankara da haka?

Mabudin kowace kofa makulli ne sai dai wannan kofar a balleta ne ta kasa, sai shigar cikinta ta kasa yi ma mai dakin dadi.
Al'umma sun kasa yi mata uzuri iyayenta  sun kasa fahimta, mazajen kuma sun kasa riko...! Uba na gari jigo, sai dai ita bata dace ba, miji na gari gimshiki a nan din ma dai bata dace ba, kuma duka laifin yana komawa zuwa gareta ne.... Duniya ta yi mata juyin masa, ta yadda ta kasa banbance fari da baki, ji da gani sun mata nisa,  albishin daya take jira... mutuwa...!

Masoyana Assalamu Alaikum Khadeeja Candy ke muku sallama tare da fatan na same ku cikin aminci da kwanciyar hankali.
         Gani dauke da wani sabon labari kuma ina fatan zai kayatar da ku fiye da sauran. Labari ne akan NOOR da rayuwarta da iyalan gidanta.
Labarin nan kirkiren labari ne idan yayi daidai da rayuwar wasu ko wata to arashi aka samu. Za ku fi samunsa a AREWABOOKS @KhadeejaCandy

Ranakun posting. Monday - Friday
Chapter 1 · 0% Book details