← Book details Sirrin Zuciya Part 1 Complete Hausa NovelComplete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 3

Sashe 2

Sirrin Zuciya Part 1 Complete Hausa NovelComplete Hausa Novel · about 8 min read

Zainab:
“Ka tabbatar da cewa wannan alaka zata kasance da gaskiya, tsoron Allah da mutunta juna. Ba wasa ba nake da zuciyata.”

Faisal ya lumshe ido, yana murmushi. Sai ya ɗaga kai ya ce:

Faisal:
“In sha Allah, Zainab. Na riga na yi alƙawari da zuciyata kafin na fadi miki – ba zan taɓa wulaƙanta ki ba.”

---

A gefe guda...

Maryam na tsaye a bayan wani bango kusa da wajen da suke magana. Tana jin komai! Idanunta suka kaɗa da fushi. Sai ta juya da sauri, ta ɗauki wayarta, ta kira wani yaron da ke mata aiki.

Maryam:
“Kaje ka nemo duk wani hoton Zainab da wani ɗalibin makaranta – ko a cikin social media ne, ko a wajen taro. Ina so in ɓata sunanta a idon Faisal – nan da kwana biyu!”

Yaron:
“To Maryam, za a yi yadda kika ce.”

---

A ƙarshen babin:

Soyayya ta fara buda kamar furanni a lokacin damina. Faisal da Zainab sun fara tashi daga matsayi na abokan aiki zuwa matakin da zuciya ke shan numfashi. Amma a gefe guda, akwai hadari mai yawa da ke ƙoƙarin ɓalle musu farin ciki…

> Shin Maryam za ta cimma makircinta? Faisal zai ci gaba da kasancewa da gaskiya? Zainab fa – zata iya tsayawa kan burinta?

SIRRIN ZUCIYA

BY FATIMA BINTU HUSSEN

https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=ac_t

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

Bisimilahi Rahamanur Rahim

Page 4️⃣

Bayan kwanaki biyu da hirarsu ta soyayya ta fara bayyana a fili tsakanin Faisal da Zainab. Ba su jin kunyar faɗa ma juna nan su kalmar soyayyaa kullum, amma daga yanda suke kallon juna, dariyar da ke fitowa daga zuciyarsu, har da yadda suke sauraran juna komai na nuna cewa zuciyoyi biyu sun haɗu.

A wannan lokaci, Faisal ya fara shigo da Zainab cikin rayuwarsa. Ya fara gaya mata labarin iyayensa, aikinsa a kamfanin mahaifinsa da burinsa na gaba. Zainab kuwa, a hankali ta fara buɗewa, tana ba shi labarin wahalhalun rayuwarta da mafarkinta na tallafawa mahaifiyarta.

Faisal:
“Zainab, ke ta daban ce. Rayuwarki ta koya min darussa da dama da har ni ban taɓa fahimta ba.”

Zainab:
“Kai ma ka ban mamaki. Da farko, ban taɓa tunanin wani kamar kai zai saurari ‘yar unguwa kamar ni ba.”

Faisal ya riƙe hannunta a hankali
“Duniya na iya kallon mutum bisa waje, amma zuciyata tana kallon zurfi.”

Maryam ta samu hoton da take nema wani tsohon hoto ne da aka ɗauka a wani taron makaranta, inda Zainab ke zaune da wani ɗalibin da ake ƙoƙarin haɗa shi da ita da farko. Hoton bai nuna wani abu na lalata ba, amma Maryam ta yanke shi ta gyara shi a wayarta da wasu edits, ta haɗa shi da saƙon ƙarya kamar haka:

> "Ina tausaya maka Faisal. Ka lura da irin matar da kake soyayya da ita? Ga hujja. Wannan fa abokinta ne da suke tare tun kafin ta haɗu da kai…”

Ta tura saƙon a matsayin anonymous zuwa lambar Faisal.

Faisal na gida yana shirin karanta wani bayani da Zainab ta turo masa, sai saƙon ya shigo. Yana buɗewa, zuciyarsa ta buga! Ya tsaya shiru. Ya rasa me zai ce. Hoton yana iya ɓata mutum idan ba a fahimta ba. Amma zuciyarsa ta riƙa jayayya.

Faisal a zuciyarsa
“Ina iya gaskata haka? Zainab kuwa? Me zai hana in tambaye ta kafin in yanke hukunci?”

Ya share saƙon. Bai ce komai ba. Amma wata rana sai suka haɗu a makaranta...

Faisal:
"Zainab... kin taɓa soyayya kafin ni?"

Zainab ta dan tsaya kafin ta ce "Na taɓa samun wanda ya nemi soyayya ta, amma ban yarda ba. Na dinga gudu, har sai na bar batun. Na tabbata da hakan na yi daidai domin yanzu na fahimci bambanci tsakanin abu mai nauyi da wanda ba shi da tushe."

Faisal ya kalleta sosai, ya lumshe ido. Sai ya ce:

Faisal:
"Na karɓi wani saƙo da hoto, amma sai na tuna me kika ce: gaskiya da tsoron Allah. Na amince da ke. Kuma bazan taɓa yadda da kowa ba kafin na ji daga gare ki."

Zainab ta cika da mamaki da farin ciki.

Zainab:
"Na gode Faisal. Wallahi da gaske nake. Na kuduri aniyar cewa ko da soyayya ce, to sai ta kasance halal da daraja."

Faisal ya dan saki dariya, ya ce.

Faisal:
"To, mu ci gaba da gina soyayya irin wadda bata jin tsoro da boye-boye.

Wanda Maryam ta ba aiki wanda ya samo hoton ya fara jin zafin abin da ya yi. A zuciyarsa ys dame shi. Bayan kwana biyu, ya nemi lambar Zainab ta wani dalibi, ya aika mata saƙo:

> “Assalamu alaikum. Sunana Kabir. Na so ki sani cewa wata mace mai suna Maryam ce ta shirya hoto da saƙon ƙarya da aka turawa Faisal. Ni na taimaka, amma yanzu na tuba. Ki sani.”

Zainab ta karanta saƙon, sai hawaye suka cika idonta. Amma wannan karon ba hawaye na bakin ciki ba ne hawaye ne na farin ciki da fargaba da dama. Tana tunanin:

"Yanzu na tabbatar: akwai wanda ke tsare ni da gaskiya. Kuma akwai wanda ke ƙoƙarin karya ni da ƙarya…"

> Shin Zainab za ta gaya wa Faisal gaskiyar game da Maryam? Kuma Faisal fa, zai ci gaba da tsayawa tsayin daka akan Gaskiya
Please share and comment

SIRRIN ZUCIYA

BY FATIMA BINTU HUSSEN

https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=ac_t.

https://www.faceboogk.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

Bisimilahi Rahamanur Rahim

Page 5️⃣

Zainab ta zauna cikin shiru a dakin karatu, tana kallon allon waya da saƙon Kabir da ya bayyana mata gaskiyar da ke ɓoye – cewa Maryam ce ke ƙoƙarin bata sunanta. Duk da zuciyarta ta cika da zafi, ta ɗora hannunta kan kirjinta tana furta:

Zainab
"Ya Allah, Ka bani ƙarfin guiwa da hakuri… kar soyayya ta zama silar ɓacin rai."

Bayan ƙarshen darasi, Faisal ya kira ta kamar kullum. Sautin muryarsa ya kawo mata kwanciyar hankali.

Faisal
"Zainab, na rasa dalili, amma kullum da nake tare da ke, sai na fi gane kaina. Ke kamar madubi ce gare ni."

Zainab ta murmusa kadan
"Kana ji kamar madubi? To da fatan kana kallon nagartarka, ba laifukanka ba."

Faisal:
"Dukkan su. Domin ke kike koya min cewa mutum ya gane kansa shi ne farkon gaskiya.”

Zainab ta ja numfashi sosai. Ta yanke shawarar cewa lokaci ya yi da zata faɗi gaskiya game da saƙon da Kabir ya tura mata. Amma ba da zafi ba – sai da hikima.

Zainab
"Faisal, akwai wani abu da nake son gaya maka… game da hoton da aka tura maka kwanakin baya."

Faisal ya kalleta da nutsuwa
"Ina saurare ki."

Zainab
*Wani yaro ne ya aiko min da saƙo. Ya ce Maryam ce ta shirya hoton da aka yi maka forwarding. Kuma da gangan ta so ta ɓata sunana."

Faisal: (ya dan juya kai, ya nisa)
"Na zarga hakan tun farko, amma na kasa yarda... na san Maryam tun muna yara, amma ba zan iya fahimtar yadda zuciya zata juya haka ba. Zainab, ki yafe min idan na taba yi miki shakku."

Zainab
"Ba komai Faisal. Kai ka fi kowa yarda da ni fiye da kowa. Wannan ya isa alfarma."

Faisal
"Na rantse da Allah, zan kareki daga kowanne irin zargi ko kage. Maryam za ta fuskanci gaskiya ko da hakan zai ɓata tsakanina da ita har abada."

Maryam na zaune a cikin gidansu mai ɗaki uku, tana jiran amsar Faisal bayan yunkurinta na baya. Har yanzu ta kasa hakura da yadda Faisal ke ƙara shiga cikin Zainab. Amma ran wannan rana, sai ta karɓi saƙo daga Faisal:

> Faisal:
“Maryam, na san komai. Na san ke ce kika tura min hoton nan, kuma na san ba gaskiya ba ne. Ban taɓa tsammanin za ki iya hakan ba. Ki daina shiga rayuwar Zainab – tun kafin abin ya kai inda ba za ki iya jurewa ba.”

Maryam ta karanta saƙon da rawar hannu. Idanunta suka kaɗa da hawaye – amma ba hawaye na nadama ba, sai na cin kishi da ƙi.

Maryam:
“Faisal ya fi ni Zainab? Shi ke nan kenan? Za ka zabi ‘yar talakawa akan ni?”

Tana jin zuciyarta na ƙonewa da shashasha

Soyayyar Faisal da Zainab na ƙara ƙarfafa bisa dogaro da juna da gaskiya. Makirci ya fara rushewa, amma zuciyar da ta cika da kishi kamar Maryam – ba zata hakura da wuri ba.

Zainab ta shiga sabon mataki na soyayya amma wannan soyayya zata fuskanci sabbin jarabawa...

> Shin Maryam za ta sake tashi da wani salo? Kuma Faisal zai iya tsayawa kan burinsa na kare Zainab duk da matsin lamba daga gida?

SIRRIN ZUCIYA

BY FATIMA BINTU HUSSEN

https://chat.whatsapp.com/LZtufHUnlqUFvnBvvoUWs3?mode=ac_t.

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

Bisimilahi Rahamanur Rahim

Page 6️⃣

Ranar Lahadi ce. Gari na daɗaɗɗen sanyi, rana na fito da sauƙi. Faisal ya shirya ya kai Zainab wani wuri ba wajen shakatawa ba, sai dai muhimmin wuri gidansu.

Zainab ta firgita da farko.

Zainab
"Faisal… ka tabbata lokaci ya yi da zan sadu da iyayenka?"

Faisal
"Zainab, na yanke shawarar gaya musu komai. Ba zan ɓoye ki ba kamar wata sirri. Ke ce gaskiyar zuciyata."

Sai dai zuciyar Zainab na ƙoƙarin kwaɗayi da tsoro. Ita da mahaifiyarta sun saba da tozarta daga masuy kudi. Amma saboda soyayyar da take gani cikin Faisal, sai ta haɗiye damuwa, ta amince.

A GIDAN FAISAL...

Gidan na alfarma ne, mai yalwa da nutsuwa. Sai dai fuskar mahaifiyarsa, Hajiya Nafisa, na nuna tsattsauran ra’ayi tun daga shigowar Zainab.

Bayan sun zauna suka gaisa, Faisal ya bayyana gaskiyar:

Faisal
"Mama, wannan Zainab ce. Yarinya ce mai tarbiyya, ilimi da kwazo. Ni nake son ta. Kuma da izinin Allah da yardarki, ina son ta zama matata nan gaba."

Hajiya Nafisa ta kalleta daga ƙasa zuwa sama, sannan ta ce da kakkausar murya.

.
"Yarinya, daga ina kike?"

Zainab
"Daga Rigasa, Hajiya. Ina zaune da mahaifiyata."
Chapter 2 · 0% Book details