part immediately says "Uwace fah. kawai dole hakura zakayi kayi É—in koda kuwa
Qadr Part 1 Complete Hausa Novel · about 595 min read
bakaso,kwana nawane ma yarage kagama karatun baki É—aya?" dawa dannan tunanin LamiÉ—o
yayanke shawarar sauke duk wasu makamansa nason kinyi karatu tareda niyar washegari
zaigyara halinsa.
Haka ya koma zuwa makaranta as a changed person,yamadaina skipping classes bare har
yaje inda yake ɓuya Ƴan Mata da abokanan banza suzo suna tayashi zama. A ranar yaje
yasamu malaman da yayi missing test É—insu sukayi mishi makeup,damuwarshi É—aya
dukyanda yaso yamaida hankalinshi a aji don yagane abunda akeyi he always end up
sleeping kokuma yafaÉ—a wata duniyar tunani sabida tsabar ranshi bayason abun.
Kullum inzai tafi makaranta seyaje yagaishe da Umma anma bazata amsa ba hakan kuma
bazai hanashi sake gaisheta ba inya dawo. LamiÉ—o yadaina zuwa koda football É—inda
akeyi kullum yanma a unguwarsu ne,ya tsiri tayasu Jidda yin assignment É—insu na
makaranta dukdan Umma taga canzawarsa anma abanza wannan yasa hankalinsa yayi
kololuwar tashi,yashiga damuwa hakanan yadaina cin abinci sosai,duk yabi yarame
cikin sati biyu dayayi yana wannan ladabin amma Uwartasa taƙi ko kallon sa bare
yayi tunanin samun sassauci daga gareta kwana kusa. Hankalinshi bai kara tashiba
seda su Jidda sukazo sunamai kuka kan Umma tace zasu koma *Kwami* dazama karshen
watannan kuma tace dasun koma aure zatayi musu dukansu dan Allah yaje yabata hakuri
kilan taji tunda shine favorite É—inta kuma shi ya mata laifin daya jaza musu wannan
matsalar.
Adaren ranar LamiÉ—o yaje É—akin Umman nasa yazauna gefenta sekawai yafara kuka,kuka
irin me tsuma zuciyarnan datasa zuciyarta karaya lokaci guda. dole tasauke duk wasu
makaman yaƙinta cikeda damuwa tashiga tambayarshi dalilin kukan nasa tace "Kaikuma
goɗai goɗai dakai kukan mekakeyi Lamiɗo?" yanda tayimasa maganar bazata taɓa cewa
fushi takeyi dashiba,she act as if nothing happens(Uwa kenan) wanda hakan yakara
bama LamiÉ—o kwarin gwiwa hakanan bebar kukan dayakeyiba har lokacin yace "Umma kiyi
hakuri kidaina fushi dani don Allah" and she couldn't help it but to hug her only
male Son,rungumeta yayi tightly yanata maimaita faÉ—in "Umma kiyihakuri kidaina
fushi dani. Umma kiyi hakuri kidaina fushi dani don Allah. namiki alkawarin bazan
sake disappointing É—inki ba,zanyi abunda kikeso É—in" cikeda tausayinshi Umma tace
"yawuce LamiÉ—o. kadaina kukan nan ya'isa haka kada su Jidda suji Yaya babba yana
kuka" and for the first time he smiled tun bayan data fara fushi dashi.
yashiga goge hawayensa yana faÉ—in "ai in suka ga hawayennan duk sesun biyani kayana
dan nadinga zugaki mutattara mukoma Kwami kenan" dariya Amina tayi tana mai tayashi
goge gunji gunjin hawayensa tace "watodai yarannan karata suka kaiwurinka koh?"
yace "A'a Umma bawanda yakawo kararki jinayi kuna maganar" Umma na murmushi tace
"yimin shiru sekace bansan halinkuba daga kai harsu É—in" LamiÉ—o yace "toh Umma
tunda kinsan halin mu kiyi hakuri kibarmu a birni karki maidamu ƙauye" yakarashe
maganar cikin sigar shagwaba Umma tace "duk wannan zancensu ne banaka ba ni nasani.
Kai da ko acikin kogo akace kazauna so far as akwai abinci babu abunda zaihana ka
zama LamiÉ—o" LamiÉ—o yace "toh adaiyimana afuwa abarmu anan É—in Umma" Umma tayi
murmushi tana satan kallon kofar ɗakinta dantasan yaran nanan gurin laɓe sunajinsu
tace "zanyi maku afuwa amma sekasa kowacce ta ciko maka plate É—ai É—ai da abinci
takawomin nayi feeding ɗinka" aikuwa dasauri suka fito daga laɓen dasukayi suna
faÉ—in "Umma zamu kawo wallahi" daganan kuma suka ruga aguje sukayi kitchen daniyar
zuwa É—ebo abincin inda suka bar LamiÉ—o da Umman nasu namusu dariya.
Basma ce tafara kawo nata sannan Jidda sannan Salma, LamiÉ—o na kallonsu duka yace
"wato laɓe kukazo kuna mana nida Umma na koh?" Jidda tace "Yaya dolece tasamu yin
laɓen nan wallahi" Lamiɗo yace "Aiko seku shirya komawa Kwami tunda dukanku kunga
hawayena" Basma dasauri tace "nidai bangani ba Hamma" Salma tace "Nimadai banganiba
Hamma" Jidda data rasa yanda zatayi ta kare kanta tace "oh so kuke kuce nikadai
nagani kenan komi?" And they all laughed at her reaction.
LamiÉ—o yace "uwar tsarguwa kwantar da hankalinki babu mai komawa Kwami dazama sede
zuwa hutu" tuni jidda tashiga washare baki tana murna. LamiÉ—o yamaida kallonsa kan
plates har uku da duka ke makare da abinci yace "nashigesu inazankai duka wannan
abincin?" Umma tace "duka meals É—inka dakayita missing suka haÉ—o maka anan duk seka
cinyesu yau" pity face LamiÉ—o yayi yace "Umma Allah yamin yawa sede inci É—aya
yanzu, É—aya anjima, É—aya gobe" dariya Umma tayi sannan tadubi Basma tace "Basma
tashi kiÉ—auko tray mujuye duka muci abincin tare" dasauri Basma tafice a É—akin
LamiÉ—o nafaÉ—in "Daman nayi kewar cin abinci tareda ku wallahi".
Bayan sungama cin abincin ma seda yataimaka musu sukayi assignments É—insu sannan
suka danyi kallo kafin kowa yatafi makwancisa daga baya.
Tundaga nan Lamiɗo yake kokari gurin ganin baisake ɓata ma Ummarsa raiba,daman akan
karatune kuma yadaina laifuffukan daduk akace yanayi a daÉ—in. Karatunne dai haryau
bayason sa kuma baya tunanin zai taɓa sonsa arayuwarsa,yanayine kawai don ya
faranta ma Umman nasa rai dukda kuwa bayamaida hankali yagane É—in,yanadai copying
note da dictation in malami nayi sabida shine kaÉ—ai Savior É—inshi dankuwa inzasuyi
test aranar dazasuyin yake É—aukan note É—inshi yakaranta yashiga yayi test É—in,
inkuma exams ne se ana gobe za'ayi exams É—in ze É—auki littafinsa ya kakkaranta yaje
yarubuta and luckily he always pass with average scores ahaka yasamu yagama
secondary school É—in. Sanda Umma tamai maganar jamb kuwa baitada hankalin shiba dan
ya É—auka jami'ar ma kamar secondary school ne,zaiyi mata yanda yakeyi a secondary
school ayi awuce gun kawai anma seyaga abun yasha banban da yanda yake tunani daya
samu admission,yayi registration ya fara zuwa lectures. Lecture se ayini
anayi,dawannan malamin yafita wani zai shiga hakanan kowanne yazo ze dibga musu
uban handout yakuma ce sukaranta unlike secondary school dabai wuce amusu dictation
É—in pages huÉ—u ba arana na gaba É—aya courses É—in. tun LamiÉ—o naganin abun kamar
wasane daga baya zasu samu sauki anma sema abunda yayi gaba wanda hakan yasa yafara
gajiya,yaji bazai iya jurewa ba. Seyaje wannan lecture ɗin yaƙi zuwa next one
hakadai,daga bayama yazo yadaina zuwa sosai,seyayi kwana biyu bai shiga ajiba sede
dayashigo makaranta yawuce hostel É—akin wani abokin shi dake zaman hostel ya
sharara barcinsa in lokacin tashi yayi yatafi gida abunsa har akazo aka fara
continues assessment wanda se alokacin yaje yasayi handouts É—inda akayita jibga
musu. In za'ayi test se ranar daza'ayi zaikaranta kuma baya taɓa iya gama
karantawan sabida yawanshi ba iri É—aya bane dana secondary school anma ahakan
zeshiga rubuta test É—in with the hope za'ayi tambaya a Inda ya karan ta É—in anma
seyaga abunfa bahaka baneba. haka yayi tayi har aka gama test aka fara kawo scripts
duk seyaga yayi failing gashi lokacin exams yariga yazo babu lokacin yin karatu na
haikan mani'in kuma ko akwai ma LamiÉ—o baya tunanin zai iya,na secondary school da
da yake kaÉ—an ma kawai kuke zuciyar sa yakeyi yayi ahaka barekuma yanzu da abun
yafi karfin tunaninsa dole ahaka yarubuta exams É—in sukayi hutu.
Da akadawo kuwa aka manna result segashi a probation. hankalinshi ya matukar tashi
alokacin bawaidan damuwarshi Umma anma ahaka dole yaje yafada mata halin da ake
ciki anma sebata masa faÉ—a ba tace yadage kawai next time dan daman tunda yasamu
admission É—in Hajiya Hadiza tacemata course É—in nada wahala kuma ana faÉ—i sosai
shiyasa koda yayi failing tayi masa uzuri,bata taɓa kawowa ranta Lamiɗo yakoma
gidan jiya baneba tunda tana ganin effort É—inshi akullum,yana zuwa makaranta,yana
kuma tsayawa karatu har dare. wannan rashin damuwar da Umma tanuna yasa second
semester É—inma yacigaba dayin abunda yakeyi,acewarsa tunda Ummarsa ma tasan
makarantar da wahala zata cigaba dayi masa uzuri harzuwa lokacin dataga yakasa ta
haƙura tacireshi.
Suna gama session É—in farko da result yafito yaga anyi masa step down bewani damuba
sabida yasan Umma zata sake yimasa uzuri,ahaka aka dawo next session wanda alokacin
yama dena attending lectures kwata kwata,sede yashigo yagama yawonsa in lokacin
komawa gida yayi yakoma gida,haka in lokacin Test da exams yagabato seyace ma Umma
kwana zaiyi a school yayi karatu and she'll allow him wanda inyazo É—in bewuce
yayita yawace yawace da friends ba sekuma duk inda dare yayi yaje hostel yakwana
wataran kuma yagudo gida ya tsallako ta katanga yashige É—akinsa ta window yayi
baccinshi peacefully,assusuba nayi kuma zai sake ficewa batare da kowa ya sani ba
yakoma makaranta wanda ananne zeshiga neman gurayen ajinsu yaroƙi alfarmar su shiga
jarabawar tare dan ya zauna a bayansu su goyashi,inkuma baisamu ba haka zai rubuta
paper yafito abunsa with the believe cewa definitely cewa course É—in zata dawo
masa.
Atakaice dai LamiÉ—o saubiyu yayi 100 level,200level ma haka wanda seda yazo sakeyin
na biyun ne suka haÉ—u dasu Auwal suka kulla abokantaka ta dalilin Hafiz dashi daman
baisamu admission dawuri ba sabida failing jamb dayayi tayi abaya. haÉ—uwa dasune
yasa perception É—insa na akore a makarantar yafara canzawa,yaji shima bayason asake
barin shi abaya yanason gamawa tareda su yahuta da wahalar bokon tunda haryau Umman
ma batada niyar cewa yahakura da karatun. Inda kuma Allah yataimakeshi Ƴan clique
ɗin su Hafiz ɗin duk sunada ƙoƙari,basu kuma da baƙin hali sesuke goyashi subashi
amsa a hall yayi passing kamar su.
Bangaren Umma kuwa dukda shekarun da Lamiɗo ya ɓata a makaranta yana fama bata taɓa
nuna masa damuwarta ba dukda kuwa abun na matukar damunta arai,seeing his efforts,
perseverance and dedication yasa takeyi mishi uzuri akullum,she fully believe cewa
LamiÉ—o yana karatun haikan mani'an tunda yana nuna efforts É—insa a fili shiyasa
kawai takeyi mishi addu'a kawai,akullum yama ta korafin wahalar jami'a setayi ta
encouraging É—inshi dacewa wataran zaizama labari in Allah yayarda shikuma LamiÉ—o
tsoron ya ɓata matarai tayi fushi dashi irinna da yasa yakeyi mata wannan
karyayyakin batareda tasaniba. Umma a gabadaya rayuwarta flaws biyu tasani a
tattare da LamiÉ—o wanda takeda yakinin ta magance É—aya ayanzu saura É—aya. ma'ana ta
magance matsalar rashin son karatun sa saura taurin kansa dakuma rashin hakurin sa
akan abunda yakeso. LamiÉ—o inyana son abu he always go for it,he can take any risk
for what his heart desires,babu ruwanshi da consequences É—inda ke cikin abunda
yakeso É—in,babu ruwanshi da abunda mutane zasu ce,hakanan baya hana kanshi abunda
yakeso wai don yana tsoron wani. LamiÉ—o bayabin abu a saru saru,baya neman shawarar
kowa inyana son abu he just go for it,a believe É—inshi babu wanda zai iya yimashi
abu inba shiba,a believe É—inshi if you want something now just give it your efforts
and get it right instant without thinking about the negativity. yakanyi mamaki
inyaga mutane na haƙurar ma zuciyarsu abunda takeso sabida maganar mutane, sabida
consequences É—inda ke cikin samun abun,sabida negativity É—inda ke cikin samun
abun,sabida risk É—in dake cikin samun abun but to him waÉ—annan duk baswa cikin
agender É—inshi. Indai yanason abu bayama tunanin wasu risk da consequences sema
achievement ɗinda zaisamu indai ya mallaki wannan abun hakanan indai yaƙi abu toh
yakishine. His only weakness is his love for his Mother shiyass yake mata karya
akan abubuwa guda biyu,akan karatu dakuma *Maimunatu*. His only girl
friend,yarinyar da'ita kaÉ—ai ce taciri tuta cikin Mata dukda kuwa irin crushing
dinda Yan mata masu aji,kudi dasauransu keyi akasa,ita kadai yagani yaji tayimasa.
Kawar Basma ce,ajinsu daya a Islamiya kuma tana yawan zuwa gidansu gurin Basma
wanda ananne yaganta,shi babu abunda yaburgeshi a ita irin kamun kanta dakuma zakin
muryarta,mata da dama suka kalleshi susake kallo amma banda Maimunatu wanda
tunranar farko dayaganta agidansu yaji taburgeshi,bugu da Kari yazo yaji zakin
muryarta topha daganan yadaura aniyar seyayi dating dinta amma bazai taba bari
Basma tasaniba sabida yasan gulmarta da iyawarta, bakaramin aikinta bane tafada ma
Ummansu Kuma shi bayason Umma tasani tunbayan incident dincan dakuma lura dayayi
bataso yanayi mata hirar budurwa,tafison seyagama karatu shiyasa yabi tahanyaar Yar
hannun damansa Jidda,ita tayi connecting dinsu in no time suka fara soyayya suke
Kuma exchanging letters batareda kowa yasaniba.
Wannan kenan.
Dm me on WhatsApp for payment details *08147722806*
🌹 *QADR* 🌹
( _The story of Rukayya_ )
Written by *Zeeneert*💞
*Zeeneert*@wattpad
*Page Eighteen*
Last Bonus page ***
*CIGABAN LABARI*
Umma,Basma,jidda da Salma dake kwance kan cinyar Umma tana ta zuba mata shagwaɓa
sukajiyo sallamar Hafiz da LamiÉ—o daga bakin kofar parlournsu. Umma ce ta amsa
sallamar tana mamakin miye dalilin dawowan LamiÉ—on gida dawuri haka yau dan a iya
saninta indai ba lokacin makaranta ba ana hutu yakan kai goma zuwa sha É—aya na dare
baidawo gidaba. karasowa cikin parlourn LamiÉ—o da Hafiz sukayi inda Hafiz yasamu
guri yazauna yana gaishe da Umman.
Umma amasawa tayi tana tambayarshi lafiyan Ummanshi,yace "tananan lafiyanta kalau"
Umma tace "toh madallah. yaudai ansamu angama jarabawa" Hafiz yace "Eh wlhy Umma.
Sekuma aji hudu dayardar Allah" Umma na murmushi tace "Allah yabaku sa'a toh"
wannan karan dukansu suka amsa da "Amin" LamiÉ—o datunda yashigo yazo yazauna
gefenta yace "Umma zuwa nayi naÉ—auko maki Hafiz tundaga majalisa sabida yamiki
clerifying cewa Ƴar birni ba aljana baceba.
Umma da mamakinshi tace "Wai daman bamu gama maganarnan bane LamiÉ—o?" sosa kai
LamiÉ—o yashigayi yana murmushi yace "toh yazanyi Umma. kinki yarda dani shiyasa"
Hafiz dake gefe yana murmushi shima yace "Umma ba aljana baceba,kauyen da muke
saukan ma garin iyayen kakartane taje yimasu hutu lokacin anma itada mahaifinta
cikin garin Bauchi suke zama. mutanen garin nada mutunci wallahi,sanda ciwon kafar
LamiÉ—o yatashi ma agurinsu yayita zama suna bashi abinci Inmun dawo muÉ—aukeshi
mukoma cikin gari" cikeda mamaki Umma tadubi LamiÉ—o tace "ciwon kafarka yatashi
acanne dama?" LamiÉ—o yace "Eh Umma amma tun washegarin ranar ya warke" Umma tace
"dukda hakadai daka faÉ—amin. gaskiya zamu koma wurin Mallam Buzu yasake baka wancan
maganin tunda dakasha shekarun baya dasuka wuce tunda yanzu ciwon yana yawan tashi
akai akai bakamar sanda aka baka maganiba,ai wancan lokacin yajima ciwon kafar bata
tashiba" LamiÉ—o dayagama gajiya da maganar ciwon kafar yafison ayi na tafiyanshi
Babban buli yace "Umma naji saukifah basai munjeba,yanzudai maganar zuwa Babban
bulin please! tunda Hafiz ya tabbatar miki ba aljana bace kibarni inje don Allah"
Umma ta ɓata rai tace "bawani kunje kun haɗa baki awaje dai zakazo kanamin zakin
baki" Hafiz dariya yayi sannan yace "bahaka baneba Umma. Allah duk abunda nafaÉ—a
dagaske ne. mutum ce kamarmu" Umma tace "kai nayarda dakai Hafiz shidinnedai
nakeson ganin karshen naci yau" LamiÉ—o najin haka yayi sauri ya marairaice fuska
sannan yace "Umma ba naci bane wallahi. alfarma nike nema kuma tunda kinyarda mutum
ce kamar mu ki amince min inje goben Please" Umma ta hararanshi tayi tareda duban
Hafiz tace "kaji nacin nashi koh?" Hafiz dai dariya yayi baice komaiba.
LamiÉ—o yasake marairaice fuska yace "pleaseee Ummana. Agoben fa zandawo insha
Allahu" Umma tace "sede in tareda Hafiz É—in zakuje" dantasan halin LamiÉ—o indai
batabarshi yajeba yadinga mata jaraba kenan.
LamiÉ—o jin abunda Umman tace cikin sauri cikeda murna yace "Zerakani Umma. Allah
zamuje tare" Umma tace "katambayi ra'ayinshi ne dazakayi concluding" pity face
LamiÉ—o yayi yana duban Hafiz yace "Ina zaka rakani?" dariya Hafiz yayi kafin
yagyada masakai ahankali.
LamiÉ—o yamaida dubanshi kan Umma yace "kinji yace zairakani Koh? toh mushirya goben
mutafi kenan?" Umma tace "banceba ni. banida kuÉ—i tukunnan kubari zuwa jibi in
ankawomin kuÉ—in É—inki se inbaku kujeku" LamiÉ—o beso hakaba amma dayake yasan Umman
batada shi É—inne tunda har tafaÉ—i haka yasashi rungume ta yana murmushi tareda
faÉ—in "Thank you Ummana. Allah ubangiji yakaimu jibin" Umma tace "Amin" ayayinda
tamaida dubanta kan Hafiz tace "akawo maka abincine Hafiz?" Hafiz yace "Toh Umma
akawo,daman bankoma gida cin abincin dareba kinga inna cika cikina anan sede
sucinye kayansu kokuma inci dumsi gobe dasafe in Allah yakaimu" Umma dariya tayi
tace "kadaiyi hakuri kaci dumamen gobe kada Ummanka tace nahana ka cin tuwo ta"
Hafiz na dariya yace "Toh shikenan Umma" daganan Umma tadubi Basma dagabadaya
hankalinta kekan TV tana kallon Hausa Film tace "Basms tashi kizuboma Hafiz abinci"
Basma tace "toh" ayayinda tatashi tashige kitchen dan aiwatar da abunda Umma tasata
tayin.
LamiÉ—o dake zaune yana duba agogo minti minti tunbayan da'aka gama maganar tafiya
Babban Buli aka komayin na tuwon da Hafiz zai ci yace "mutumina A.P gareni
fah,gashi naga kamar zaka batamin budget wallahi" Hafiz yace "toh kajemana innagama
zanyi tafiyata karka damu" Umma cikin sauri tace "Babu inda zashi,yajeshi majalisa
ya tattagoka sannan yazo yanzu yace bazai jiraka ba dan yanada wani gurin zuwan.
tukunnan ma inane zaije dayaketa sauri haka?" Hafiz yayi dariya sannan yace
"kyaleni dashi Umma. aisai anzo tafiya Babban buli zanrama,seyagama shiri ince
nafasa. innafasa kuwa kasan gabadaya tafiyar is cancelled tunda albarkacina kaci"
Hafiz yakarashe maganar yana kallon LamiÉ—o cikeda zolaya.
wannan karan harsu Jidda seda sukayi dariya.
LamiÉ—o yace "yi hakuri oga,abun baikai nanba,zanjira ka anma kataimaka ka wurwurga
abincinnan dawuri musamu muyi gaba" Hafiz karban plate da bowl É—in ruwan wanke
hannunda Basma takawo mai yayi ya ajiyesu agabansa ayayinda yayi folding kafafunsa
sannan yasa hannu yawanke tas kafin yafara cin abincin cikin nutsuwa dukda kuwa
irin korafin da LamiÉ—o keyi masa na yayi sauri.
Seda Hafiz yagama cin abincin sannan sukama Umma sallama suka fita Jidda nasakeyima
LamiÉ—o kashedin karya manta awararta inzai dawo.
Suna fita a harabar masauratar LamiÉ—o yatsaya yana kallon Hafiz sannan yace
"Mutumina bari kaji" Hafiz yace "inajinka" LamiÉ—o yacigaba da magana yace
"kaga,wallahi sanda na jajubo ka nayi niyar maidaka inda naÉ—auko ka amma tunda ka
ɓata min lokaci kayi hakuri kakoma majalisa kaikaɗai dan kaganninan daganan hira
zantafi wurin Maimunatu"
Hafiz yace "lallaima Aiko baka isaba Mallam. kokarakani ko in fasa raka ka Babban
buli nima" LamiÉ—o ya tsuke fuska Lokaci guda yace "watoh kasamu weakness É—ina shine
kakeson yimin tsiyakoh?" Hafiz yayi dariya cikeda zolaya yace "inason insan
tsakanin Maimunatu da Ƴar birni wakafiso" tsaki Lamiɗo yayi yana sannan yace
"kaidai ba'a rabaka da shirme wallahi tallahi. ta'ina zaka haÉ—a sonda nakema
Maimunatu da Ƴar birni fisabilillahi. Maimunatu is my girlfriend and Ƴar birni is
like a sister to me" Hafiz yace "mude je zuwa" LamiÉ—o yace "kaikasani dai da
unreasonable thoughts É—inka. yanzudai yaza'ayi? wallahi tun É—azu take jirana munyi
akan karfe tara zamu haÉ—u anma gashi yanzu har tara da rabi tayi. kozamu je hiran
tare ne?"
Hafiz hararan LamiÉ—o yayi yace "inje amaidani hoto kakeson kace komi? toh badani ba
kajeka Allah yakiyaye hanya,asha soyayya lafiya" daganan Hafiz yayi tafiyarsa
LamiÉ—o namasa dariya.
***
Yau karfe tara dot Kawu Idrissa, Kawu Sani dakuma Kawu Adamu suka hallara a É—akin
da aka kwantar da Baba sunajiran É—ayan mutumin da Baba yace sujira yazo kafin
sufara magana. ba'ajima ba kuwa sega wani dattijo yashigo É—akin da sallama. kallo
É—aya namishi nasama raina wannan inba lawyer bane toh banker ne dankuwa shiga yayi
irin tasu,yana sanye da rigar ciki fara tas da'ita tasha guga se bakar suit da
wandonta sekuma black cover shoe ayayinda hannunshi ke ɗaukeda briefcase. Ƙarasawa
yayi inda su Kawu Sani suke yababbasu hannu sukayi musabaha sannan suka gaisa da
Baba,yatambayeshi yajikinsa Baba yace dasauki kafin nima na gaisheshi ya amsa yana
zolayana da "Rukyn Baba" murmushi kawai nayi dukda kuwa Ina mamakin ya akayi yasan
sunana.
Baba dake rikeda hannuna ne yakalleni yace "Mamana a Ina kuka siyo ÆŠanwaken
dakukaci ranar keda Kawunki Hassan" take nace "bansani ba Baba. Kawu Hassan ne
yasiyo" Baba duban Kawu Hassan yayi sannan yace "Hassan kuje kusiyo min ÆŠanwaken
ranar nan kaida Mamana. yaushi nakeson ci" cikeda zumuÉ—i nace "nima zanci Baba" Dan
banmanta daÉ—in ÆŠanwaken ba,harda su cabbage,salad,kwai,lemon tsami ake sakawa aciki
and it makes it more Yummy" tashi nayi daga kan kujerar dana ke zaune inacema Kawu
Hassan mutafi dan already akwai hijabi akaina ayayinda Kawu Sani yatsaidani yaciro
kuÉ—i daga aljihunsa yabamu yace musiya da kuÉ—in inda muka fice a É—akin tare
batareda nayi sensing komai ba.
***
Bayan fitan Kawu Hassan da Rukayya Mallam Umar yadubi baƙon dake ɗakin bayansu Kawu
Idrissa, Kawu Sani da Kawu Adamu yace "Barrister Bismillah kazauna mana" Mallam
Umar yakarashe maganar ayayinda yake nunama Barrister kujarar da Rukayya tatashi
daga kai bada jimawaba.
Zuwa Barristern yayi yazauna yana faÉ—in "I'm sorry nazo latti wallahi an É—an samu
akasi ne daga gida" Mallam Umar yayi murmushin karfin hali sannan yace "bakomai
Barrister Ƴan uwannawa ma basujima dazuwa nanba" Barrister yayi murmushi ayayinda
yashiga buÉ—e briefcase É—insa,yaciro wasu takardu sannan yafara magana,yace "ganan
takardun duka kadarorin dakace inkawo" Mallam Umar dake kwance kokarin tashi
yashigayi yana nishi ayayinda Kawu Adamu dake kusa dashi yayi sauri yakarasa jikin
gadon yataimaka mai yazauna kafin yasamu damar karban papers É—in daga hannun
Barrister yana bubbudewa yace "kayi transferring sunan kamar yanda nace?" Barrister
yace "Eh nayi sauran signatures É—inta" Mallam Umar yace "is it that necessary? naga
akwai nawa signature É—in dayake nuna cewa namaida komai nawa akan sunanta?"
Barrister yace "we need her signature anma still kobata saka hannunba it'll still
remain hers tunda kariga kayi stating kai" Mallam Umar yayi murmushi yace "toh
Masha Allah" kafin yadubi su Kawu idrissa yace "magana nikeson muyi daku" duka suka
ce Toh duk da kuwa suna mamakin meyakewo maganar dukiya dakuma transformation
ayanzu?anma cikinsu babu wanda Allah yabama ikonyin tambaya har Mallam Umar ya fara
magana yace "Dukanku dakuke nan are the people i'm very close to acikin family
members dinmu since childhood,munyi karatu tare, perspective É—inmu kusan
É—aya,burikan mu na rayuwa ma kusan É—aya suke and alhamdulillahi É—aya bayan É—aya
we've achieved something in life and still muna kanyi. sede inason kusan abu
É—aya,dukanmunan batare muka zo duniyarba, hakanan we just found ourselves as
siblings toh haka tafiyarma take,lokaci inyayi dole atafi. Allah baya barin wani
dan wani yaji daÉ—i sannan kowa baya wuce kaddararsa" Kawu sani datunda yaji Mallam
Umar yafara magana yaji gaba É—aya jikinsa yayi sanyi harsaida aka kawo wannan
gabar,gabar dayaga bazai iya jure cigaba dajin maganar ba cikin sauri ya tari
numfashin Mallam Umar yace "what are you saying Umar? rashin lafiyarce tasaka
kakeyin magana irin haka? meyakawo maganar haihuwa da mutuwa kuma?meyakawo maganar
kaddara kaida kake fama da rashin lafiya?" Kawu Sani yakarasa jikin gadon da Mallam
Umar É—in yake yana faÉ—in "koma ka kwanta kahuta. Koma mekake son faÉ—a kabari sekaji
sauki. dont stress yourself please" Kawu Sani yakarashe maganar ayayinda hawaye
suka cika idanunsa dashi kansa besan dalilin zuwansu ba.
Mallam Umar yarike hannun Kawu Sani dake ƙoƙarin kwantar dashi cikin rauni yace
"let me say what I want to Yaya. Inban faÉ—a yanzu ba I might never get the chance.
Every time is precious,lokaci inya tafi baya dawowa" Kawu Sani jiyayi yakasa
tsayuwa dole yasamu guri gefen Mallam Umar yazauna batareda yace komai ba.
Mallam Umar yacigaba da magana yace "Bantaba faÉ—a ma kowaba kuma ko ayanzu dazan
faÉ—a bawai ason raina nakeson faÉ—a ba sedon yazame min dole infada É—inne" Mallam
Umar yasunkuyar dakai kasa muryar shi har karkarwa takeyi yace "I'm suffe..ring
from blood cancer for more than a year now" duka yan É—akin were shocked hakanan
sunkasa koda cewa uffan ne sabida tsananin yanda maganar tazo musu abazata.
Mallam Umar daya kasa kallonsu harlokacin kansa na ƙasa yace "Nasan Kuna mamakin ya
akayi bakusaniba,nayita ɓoye muku ne sabida banason abunda zai tadama kowa
hankali,banason in É—aura muku damuwar ciwona yazame muku liability shiyasa naroki
likitana da kada yafaÉ—a muku,dukda suma asibitin nan kwanannan ne suka gano
matsalata,duk wasu gwaje gwaje dasukayi tayi kwanaki basusan asalin meyake damunaba
awannan lokacin. Even though my Doctor has been encouraging me wannan karan banajin
ajikina zantashi daga jinyarnan shiyasa nayi taking step dinnan as a Father" Mallam
Umar yayi maganar yana nuna files É—in dake gabanshi Yaya Sani da alokacin yakasa
controlling tears É—insa yasa hannu kan bakin Mallam Umar yace "don Allah kadaina
faÉ—in haka Umar, we'll Live together,keep pursuing our dreams together, raise our
children together and get them married together harma muga jikokin mu. don Allah
kadaina kirama kanka mutuwa,cuta ba mutuwa baceba" cikin ruÉ—ani Kawu Adamu dashima
yake hawayen yace "bagashi ma yafara samun sauki ba. yanzu kwanansa biyu yanata
annashuwa" Mallam Umar yayi murmushin karfin hali yana kallonsu sannan yace "I wish
I could live long too,inama duk maganganun daka faÉ—a zanyi witnessing É—insu,inama
zan samu in aurar da Rukayya dakaina inkaita gidan Mijinta dakaina,insaka mata
albarka inyi mata fatan samun Ƴaƴa na gari irinta kuma masu yawanda inta juya
tagansu bazataji irin loneliness É—inda tadinga ji ashekarun bayaba sabida rashin
Uwa da siblings" Mallam Umar yakarashe maganar ayayinda yadago yana kallon Kawu
Sani.
Kawu Sani cikin gunjin kuka yace "you'll witness it Insha Allah. Umar da hannunka
zaka kai Rukayya É—akinta insha Allahu" murmushi Mallam Umar yayi yace "kaman ta
Allah baya barin wani dan wani yaji daÉ—i? Koka tabajin masu cuta irin tawa sunada
chance É—in surviving sosai?" Mallam Umar yasauke ajiyar zuciyar araunane yace "it
rarely happens and besides kuma iyayene ga Mamana ko babuni nasan zaku riƙe ta
amana kamar yanda zaku riƙe ƴaƴanku,zaku aurar ɗa'ita kamar yanda zaku aurar da
Æ´aÆ´anku,zaku kaita É—akin mijinta kamar yanda zaku yima Æ´aÆ´anku. Banida haufi akanku
bakiÉ—aya indai tafannin tarbiyane da responsibilities"
Wannan Karan Kawu Sani kasa cewa komai yayi inbanda hawaye dayakeyi yana tuna old
memories É—insu da Umar É—in,yana tuna sanda aka haifeshi,Yana tunda sanda akayi
sunanshi suka haÉ—a party agida su siblings É—inshi,yana tuna sanda yafara wayau
dakuma rashin rowarsa tun yana karami. komi aka bashi he always shares it with his
siblings dukda kuwa wasu siblings ɗin nashi basonshi sukeba amma baya taɓa nunawa
yasani,baya taɓa banbantasu da Suwaiba. Ko gaba kakeyi dashi kaida kanka zaka sauko
dan nunawama zaiyi baima saniba, he'll talk to you nicely koda zaka kwana kana
gwasaleshine.
Mallam Umar duban Kawu idrissa dakecan jikin edge É—in bango yana hawaye yayi tareda
sakin murmushin karfin hali jokingly yace "Yaya you're the oldest. you shouldn't
cry,kaida zanbaka amanar Ƴa inkana kuka yanzu wazai lallasheta after me?" Kawu Sani
wannan karan karasawa yayi jikin gadon yarungume Mallam Umar tareda É—an makan
keyanshi yana faÉ—in "Kai Umar kayimin shiru inbazaka faÉ—i alkhairi ba" sekuma suka
saki kukan tare akarasa mai lallashin wani acikin su gaba-daya dake É—akin dankuwa
har Barrister seda yazubar da kwallah.
Mallam Umar ɗinne dakanshi daƙyar yasamu ya tsagaita kukan dayakeyi ɗin,yamatsa
daga jikin Kawu idrissa ya ajiye masa papers É—in da Barrister yabashi sannan yafara
magana yace "dukanku nan abu É—aya nake kallon ku hakanan kaunarku a zuciyata is
thesame. Sede Babba babbane ko a inane shiyasa nayi deciding baka papers É—innan
Yaya idrissa. wannan dukiyata ce bakidaya danajima Ina tarawa da zummar inbawa
Rukayya a better future,in mata auren gatan,inkaita gidan daza'a darajata sannan
inbata dukiyar da ko bayan raina nasan bazata wulakanta akan kudiba,yanda zata zama
independent sede kunsan hali na rayuwa se ahankali. tafiya mukeyi batareda munsan
final destination É—inmu ba,a kullum É—an Adam burinshi mezan zama gobe, mezanyi
achieving arayuwa without thinking cewa akodayaushe mutum za'iya mutuwa yabar komai
a duniyar. komaina were in my name before anma tunda nafara rashin lafiyar nan nayi
consulting wannan Barristern yashigemin gaba akayi transferring komai into her
name" yace "bazai yuyu in É—auki dukiya yanzu inbama Rukayya ba because she's too
young shiyasa zanbaka Yaya idrissa,ga amanar dukiyar Ƴata ahanunnka,this's all I've
in this world and they're all transferred into her name. Ka ajiyemata
agurinka,dukranda Rukayya tayi wayau,tayi aure seka damka mata ahannunta. Kace mata
it's a gift from her Father for always making him smile"
Shidai Kawu idrissa kasa cewa komai yayi still yana hawaye, Kawu Adamu kam tuni
yafice a É—akin tsabar yakasa resisting,zuciyarsa bazata iya É—aukan waÉ—annan
maganganunba. yasan Allah ne keraya mutum Kuma yaÉ—aukeshi aduk sanda yaga dama
hakanan shike da ikon lafiyar mu da rashin lafiyarmu sannan cuta ba mutuwa
baceba,it can be zafin cutace tasaka Yayansa Umar yin waÉ—annan maganganun anma for
some reason seyaji jikinsa yayi sanyi dukda kuwa jinyar da Umar É—in yayitayi
kwanaki koshi yayi loosing hope akansa anma ai É—an saukin dayasamu kwana biyunnan
is a good sign cewa akwai possibility É—in warkewarsa gaba É—aya. But why is he
saying all these things?"
Ranar Mallam Umar nalura da Yan uwannasa guda uku. sau biyar sukazo asibitin
hakanan duk zuwansu sesun É—an jima suna tambayarsa yanayin jikin nasa wanda kuwa
ada safe da dare kawai suke zuwa kuma baswa wani jimawa sosai É—an gwanda wansa Sani
ma.
***
Tunda muka dawo daga sayan ÆŠanwake nalura dawani irin extra care dasu Kawu idrissa
ke nunama Baba wanda hakan yamatukar bani mamaki hakanan yawan jeka kadawo dasukayi
tayi ranar makes me wonder what is wrong anmadai bance komai ba. Adaren ranar Kawu
Sani yazo da Aunty dasu Sadiya suka duba jikin Baba wanda wannanne zuwansu nabiyu
tunda aka kwantar da Baba a asibiti dukdakuwa Kawu Sanin yaÉ—auka sukanzo in an
kwana biyu tunda yakan barmusu sallahun suzo É—in daga gida dan wataran inyazo
dasafe zece ai Aunty ko Ummi zasuzo su anjima haka kuma har ranar takare bazamuga
koda keyarsu baneba,inzaiyi tafiya wani gari aiki kuma dayake yana yawan tafiye
tafiye saboda yanayin aikinsa yakan cemana yabar sako gun Aunty inmuna bukatar kudi
kowani abu muneme ta intazo amma har yaje ya dawo bazamuga ko keyartaba hakanan
kuɗin da akabatan yasha ruwa kenan muma kuma bamu taɓa kai kararta gurin shi ba.
Washegari dasafe kuma Kawu Sanin ya taho da Mama Hadiza dasu Zaheera dukanninsu
sanye da uniform É—in makaranta akan za'ayi dropping É—insu a school insun tashi daga
asibiti inda naji suna hirar ranarce rana ta farko daza'a kaisu makaranta da mota
da sede subi school bus shiyasa suketa murna a tsakaninsu.
Wuraren sha É—aya ma sega iyalan Kawu idrissa da na Kawu Adamu sukazo su harda kawo
abinci wanda hakan yamatukar bani mamaki anmadai shima bance komaiba. aranarne kuma
Gogode tazota tasake duba jikn Baba inda tacemin washegari su Yadikko Rahane zasu
zosu in Allah ya yarda,sunso sutaho tarema yau anma Baffa baya gida yaje can wani
ƙauye daurin auren Ƴar abokinsa bazai yuyu abar gidan bakowaba ga yara shiyasa tace
suÉ—in subari gobe swazosu.
Baba dake kwance yanajinmu yace "yauda goben duk É—aya ne ai a wurin Allah" Gogode
tace "iyi. Allah yakaimu goben" nida Baba da Kawu Hassan muka amsa da Amin sannan
nace "don Allah Gogode inkinje kisa su faru'u suciro kanya abama su Yadikko sutaho
min dashi" murmushi Gogode tayi sannan tace "toh faÉ—a musu insha Allahu".
Ranar Baba da zazzabi yakwana, zazzabin ma irin me tsananinnan dankuwa ko bacci
bamuyiba dukanmu gashi seda su Kawu Idrissa duk suka tafi sannan zazzaɓin yafara
damunshi. Washegari dasafe aka kawo abinci fankasau da miyar ganye daga gidan Kawu
Sani which was the first time dasuka kawo abinci anma Baba nayin loma na biyu
yafara kela amai dole aka hakura da takuramai da akayi yaci fankasaun yasha
magungunansa with empty stomach. yau gaba É—aya senaji duniyar tayimin zafi,banajin
daÉ—in komai sabida rashin lafiyar Baban barekuma daman kwana biyunnan daya É—an samu
sauki nasaba da walwalarsa dakuma hirarrakin damukeyi,akwana biyun dayaji sauki
hartashi dakansa yashiga bayi yayi wanka yakeyi anma banda yau dan da Kawu Hasssan
yazo zai daga shima suje ya taimaka mai yayi wankan ankai minti ashirin ana abu
É—aya. da Kawu Hassan yaÉ—aga Baba se yafara Jin hajijiya jikinsa duk yasaki seya
koma yakwanta inda daga karshema yace abarshi bazai iyayin wankan bama gaba É—aya.
***
Yau tun sassafe LamiÉ—o yagama shirinsa cikin shaddarshi milk colour daya sha wanki
da guga, Umma ne ta É—in kamai a sallar azumin daya wucennan shiyasa kallo É—aya
zakayi ma kayan kasan cewa sabone barekuma LamiÉ—o da daman baicika sa manyan
kayaba,kananun kaya daily clothes É—inshi inkaga ya saka shadda toh tabbas Friday ne
Kuma yauÉ—inma ya kasance ranar Friday and yasan kilan sallan juma'a na'iya samunsu
a can inda zasuje ko ahanyar dawowa shiyasa yayi shirin sa na juma'a baki É—aya.
Karfe bakwai da yan mintuna LamiÉ—o yafito daga É—akinshi. a parlour yasamu Jidda
nata aikin goge gogen Tv da TV stand da alama dai tagama tsaftace parlourn ne
takoma kanyin goge goge Kuma.
Tana kallonshi tace "Ina kwana Hamma? badai harka shirya tafiyanba?" LamiÉ—o
karasowa yayi inda Jiddan ke gogo gogen yace "lafiya Lau Jiddodo. Ina Umma? Yanzu
zantafi kinsan yau zamuje mudawo bamwason muyi dare bakwai mukayi zamubar garinnan
gashi har bakwai É—inma ta gota niban bar gida ba. nasan Hafiz nacan yana jirana"
Umma dake kitchen tunda tajiyo muryar jidda nama LamiÉ—o magana tayi sauri taÉ—auki
cup tashiga zuba masa koko acikin cup É—in ayayinda tadubi Basma dake harkar suyan
kosai tace "kwashe mishi kosan cikin kaskon nan a plate kibani inhaÉ—a masa da kunun
inkayi masa yasamu yaci kafin yatafi inyaso ke kicigaba da É—ana kosan" Basma tace
"Toh Umma" ayayinda takarasa inda kwando yake taÉ—auki plate tashiga kwashe masa
kosan.
Sanda kwashewa Umma tariga ta gama haÉ—a kunun ita take jira daman,sa hannu Umma
tayi takarbi plate É—in sannan tafice a kitchen É—in. harlokacin LamiÉ—o na tsaye kusa
da Jidda yana ganin Umma tafito yace "yauwa Umma. Ina kwana?" Umma tace "lafiya Lau
LamiÉ—o" ayayinda tashiga mikamai cup É—in koko da plate din kosai tace "karbi
kazauna kaci karin kumallon ka ne" LamiÉ—o da kamar bazai karba ba sabida bawani
yunwa yakejiba anma sanin cewa Umman bazataji daÉ—i ba yasashi karban abincin yakoma
kusa da É—aya daga cikin Tum tum É—in parlourn yazauna yana faÉ—in "Thank you Ummana"
Umma tace "Hafiz É—in gida zaibiyo maka kuwuce ko kai zaka bimashi?" LamiÉ—o dahar
yafara cin kosai da Kunun yace "nizan bi masa. munyi karfe bakwai zamu haÉ—u dashi
fah gashi har lokaci yawuce" Umma tanufi hanyar É—akinta tana fadin "sekaci dawuri
kada yayita zaman jiranka" LamiÉ—o yace "toh Umma".
Umma bata jima dashiga É—akinta ba ta tafito hannunta rikeda kuÉ—i,zuwa tayi tazauna
gaban LamiÉ—o dake cin abinci tamika mishi some portion of the money tace "gawannan
kuÉ—in motarkune kaida Hafiz na zuwa da dawowa" LamiÉ—o karba yayi yana murmushi yace
"nagode Umma" sauran kuɗin dayake ɗari biyar biyar guda biyu tasake miƙamai yakarba
yana sakeyi yimata godiya tace "wannan Kuma kasayama kakarta goro kona É—ari biyar
ne sauran canjin kuma kasayama yaran gidan sweet kakai musu tsaraba babu daÉ—i
kujeku hannu rabbana sannan kasake yimasu godiyan kula dakai dasukayi tayi sanda
ciwon kafarshi yatashi,kace musu mungode Allah yasaka da alkhairi"
LamiÉ—o yace "toh Umma nagode. insha Allah zanyi yanda kikace" seda yacinye kosai da
Kunun tas sannan yatashi yaÉ—auki plate da cup É—in yakai kitchen yana cema Umma da
tun É—azu takoma kitchen suka cigaba da aiki shizai tafi.
Umma tace "Allah yakaiku lafiya yadawo daku lafiya. ka gaggaishesu kuma kutaso
dawuri LamiÉ—o kada dare yayi muku ahanya" LamiÉ—o yace "insha Allahu Umma" harbakin
kofar parlour suka rakashi sunayi masa Allah yakare. Salma dayanzu fitowarta daga
É—aki tashinta daga bacci kenan ganin ana raka LamiÉ—on yasa cikin sauri takira
sunanshi tace "Hamma LamiÉ—o" LamiÉ—o juyowa yayi yana kallonta dasauri takaraso inda
yake tace "Wai har zaka tafi wurin kawartawa ne?" dariya yayi sannan ya gyaÉ—a
matakai ahankali.
Sa hannu tayi cikin hular dake kanta taciro ribom É—inda ta kama gashinta dashi
takamo hannunshi tasaka ribom É—in a tafin hannunshi tana faÉ—in "gashi kakai mata
kace mata inagaisheta and I accept her friendship shiyasa naÉ—auki favorite ribom
É—ina nabaka kabata" LamiÉ—o tsugunawa yayi yayi kissing forehead É—in Salma yana
lumshe idanu sannan yace "Ƴar birni na godiya Autar Umma" Jidda da Basma dai basuce
komaiba don duk cikinsu basu É—auki maganar Rukayya dayakeyi musu da mahimmanci ba
kamar yanda Umma ma bata É—auki maganar da mahimmancin ba dukda kuwa irin damuwa
dasu da LamiÉ—on yanuna Rukayya nayi tana kuma son suzama yayunta. Umma kuwa
takyeleshine yayi yanda yaga dama ne tunda yanuna nacinsa akan tafiyar, yaÉ—aga
seyaje.
Karfe goma da yan mintuna su LamiÉ—o suka Isa garin Babban buli. ta kofar masallacin
garin suka farabi daniyar gaida dattawan garin anma babu kowa agurin kasancewar
safiya ne kowa yatafi neman halal É—insa. Agida suka samu Gogode,tana É—aki tajiyo
sallama a kofarta wanda hakan yasata lekowa don ganin wanene,ganin Hafiz da LamiÉ—o
yasata sakan baki tace "ikon Allah. Waneke gani kamar Lamido??" Lamido yasaki
murmushi sannan yace "Nine Inna" Gogode tayi sauri tadauko tabarman dake jingine
bayan kyauren kofar dakinta tafito dashi tashimfida musu a karkashin rumfar kofarta
tana fadin "Bismillah kuka raso mana. Jabbama jabbama sannun ku dazuwa" karasawa su
LamiÉ—o sukayi suka zauna ayayinda suka shiga gaidata "Ina kwana inna?" Gogode tace
"lafiya lau" LamiÉ—o yace yace "yamuka sameku?" Gogode tace "lafiya kalau
alhamdulillah yanaku iyayen? Inafatan dai duk kalau suke" wannan Karan atare su
LamiÉ—o suka ce "lafiyansu kalau inna" Gogode tace "toh madallah" Dede lokacin Indo
tashigo kofar Gogoden gaisheda su LamiÉ—on tayi suka amsa ayayinda Gogode tadubeta
cikin yaren fillanci tace "harkin dawo daga diban kandilon?" Indo tace "eh Gogode
harnakai masu kofarsu" Gogode tace "toh sannu da aiki,kishiga daki ki dauko kwanon
sha kikawo ma su ruwa daga Randa" Indo tace "toh" ayayinda tashige dakin don
aiwatar da abunda Gogoden tasakata.
LamiÉ—o yace "aimunbi ta kofar masallacima mungaisa dasu Baffa mukaga bakowa" Gogode
tayi murmushi tace "aibazaku samesu a irin wannan lokacin ba. Kodashan dakuke zuwa
ai baswa zama iwarhaka,duka sunashan suna ayyukan gabansu se anjima zasu zasu dawo"
LamiÉ—o yace "Allah sarki. Rukayya kam takoma Bauchi Koh?" Take yanayin fuskar
Gogode yasauya tace "Rukayya takoma tuntuni. aini inaga bakuyi kwana biyu da tafiya
bama tatafi Bauchi. Babanta babu lafiya sunfi wata biyu a asibiti ma yanzu haka"
Lamiɗo dake ƙoƙarin kai kwanon ruwan da Indo takawo musu bakinshi yayi sauri yadawo
dashi ya ajiye yana duban Gogode yace "subhanallahi. meke damunshi? har wata biyu a
asibiti?" Gogode tace "wallahi yamafi wata biyu yana kwance ba Lafiya munedai
mukayita boyemata daman amma damukazo mukaga jikin yayi tsanani shine muka É—auketa
muka kaita gurinshi anmadai yanzu dasauki danko jiya danaje dubashi munyi hira
dashi sosaima" LamiÉ—o da gaba É—aya jikinshi yayi sanyi yace "Allah sarki. Allah
yabashi lafiya. daman kafin mutafi nabata lambar wayana akan intakoma can gida
gurin Baba zamuna zumunci tose naga nanne nanne haryau bata kiraniba shine nace ba
inzo nangurin ku inji ko lafiya. shirun yayi yawa" Gogode tace "Aiko ka kyauta ÆŠan
nan. Lambar wayar ka kuwa indai agarinnan kabata toh bana tunanin tatafi dashi dan
kayanta datazo hutu dasuma duk sunanan ba'a kayimata ba tukunnan" LamiÉ—o cikeda
curiosity yace "anma wani irin rashin lafiya ne haka Inna? har wata biyu yana
kwance?" Gogode tace "wallahi haryau ba'asan ainahin matsalarba,babu irin binciken
da ba'ayi ba anma ba'a gano cutar ba ninace musu sukoma gida afara neman na gida
yafi anma Ƴan uwansa sunki bada haɗin kai dayake Yan Bokon ne ke kula da harkokin
sa na asibitin" LamiÉ—o jiki sanyaye yace "toh Allah yabashi lafiya. acikin Bauchine
akayi admitting É—insa?" Gogode tace "eh nan genaran hoshbitan ba. Anan aka kwantar
dashi zakujene?" LamiÉ—o yace "eh zamubi tanan Inna" Gogode tace "toh ai ga matan
Baffan tama yanzu zasu tafi dubashi sunata shiri mezai hana kutafi tare" Hafiz da
tun É—azu baiyi magana ba yace "Kuma da hakan ma zaifi tunda su sunsan ward É—inda
yake bazamu sha wahalar neman inda aka kwantar dashiba" Gogode tace "iyi nima
abunda nagani kenan" kafin tatashi tanufi kofar su Yadikko Rahane tana cewa "ba
inji insun gama kimtsawa seku tafi taren kawai" LamiÉ—o yace "Toh" ayayinda yabuÉ—e
ledan goro da sweets É—inda suka kawo yaciro packed É—in sweets guda huÉ—u dake cikin
ledan yamika ma Indo dake rakube gefe tana kallonsu yace "gashi kuje kuraba keda
sauran yaran gidan" karba Indo tayi tana masu godiya sannan yabata ledan goron yace
"wannan kuma na Inna ne. Ki ajiyemata" dagudu Indo tabar gurin tabi bayan Gogode
tana kwala mata Ƙira.
Ba ajima ba sega Gogode tadawo tana musu godiyan tsarabar dasuka kawo tace "kukuwa
dakuke kan hanya harda wahala haka?" LamiÉ—o yace "kaÉ—an ne bayawa Inna" Gogode tace
"toh Allah yasaka da alkhairi" Hafiz da LamiÉ—o suka amsa da "Amin" kafin Gogode
tace "yanzu zasu fito seku tafi" aikuwa korufe baki batayiba segasu sunshigo suka
gaisa dasu LamiÉ—on kafin sukama Gogode sallama bayan tahaÉ—asu da LamiÉ—o tace sutafi
tare.
Abakin general hospital Hafiz yace ma mai napep yatsaya susayi fruits,da kuÉ—insa
yasaya sanin cewa ba lallaine akwai kuɗi hannun Lamiɗon ba kafin suka ƙarasa cikin
asibitin suka sauka a napep É—in suka biyashi kuÉ—inshi sannan sukafara bin su
Yadikko Rahane dakeyi musu jagora zuwa É—akin da Mallam Umar É—in yake.
****
Wuraren sha ɗaya da rabi haka inazaune kan kujerar dake kusa da gadon Baba Ina riƙe
da hannunsa nazabga uban tagumi ayayinda yake baccinda baisamu yayi daren jiyaba
mukaji anyi knocking kofar É—akin daga waje. Kawu Hassan dake zaune kan tabarman
akasa ne yace "Bismillah kushigo" buÉ—e kofar É—akin akayi wanda tunda aka buÉ—e kofar
É—akin nafarajin wani irin familiar scent,scent É—inda nasan meshi sosai anma nakasa
tuna wanene. Juyawa nayi ahankali na kalli kofar don ganin wanene anma se idanuna
suka sauka kansu Yadikko Rahane dasuke ƙoƙarin shigowa,dukda zuciyata bata yarda
cewa wannan scent É—in nasubane ba ban É—auke kaina daga kallonsuba,nasakar musu
murmushi inaganin yanda suke shigowa É—aya bayan É—aya ina gaishesu har idanuna suka
sauka cikin da LamiÉ—o.
Aibansan sanda natashi daga zaunen danakeba,nasaki hannun Baba baki sake nace "Yaya
LamiÉ—o" and he couldn't smiled dukda kuwa nagani a kwayar idanunsa yanaso yayi É—in
instead seyake min kallon tausayi wanda bansani ba kodan irin ramar danayine,kokuma
tausayin ganin mahaifina bayida lafiyane yasashi min wannan look É—in.
Dagudu nakarasa inda yake tsaye,natsaya agabanshi sekawai na fashe da kuka. Kukan
da tunjiya banyishiba sabida kada intada ma Baba hankali dukda kuwa I badly wanted
to cry seyanzu danake ganin inada mai lallashina akusa,lallashin da inada tabbacin
in akamin irinsa zuciya da ruhina zasu karbesu wholeheartedly.
Tsugunawa LamiÉ—o yayi agabana yasa fingers É—insa yashiga gogemin hawayena batareda
yadamu da kallon da daukakin É—akin keyi mana ba yace "Kukan na menene Nanah? are
you not happy to see me? koh in koma ne?" Cikin gunjin kuka nace "basabida zuwan ka
nike kukaba sabida rashin lafiyar Babane. Jiya kwata kwata baiyi bacci ba da
zazzaɓi yakwana" Lamiɗo dayagama gogemin hawayene yarike hannuna yasaka cikin nashi
yace "toh ai ba kuka zakiyiba Nanah. addu'a zakiyi masa Allah yabashi lafiya"
ahankali nace "inayi mashi ai. I just felt like crying so that someone can console
me and give me hope cewa Baba zaisamu sauki completely" wannan Karan LamiÉ—o
couldn't stop himself from smiling yasa hannu a bayana yanadan shafawa ahankali
yace "toh I console you my sister. Baba zaisamu lafiya insha Allahu" wannan karan
nima murmushin nayi masa.
Da mamakina sejin muryar Baba nayi yana faÉ—in "Wannan ne LamiÉ—on Mamana?" atare
muka juya muna kallon gadon da Baba ke kwance akai. Idanunshi biyu,ashe yatashi
daga baccin dayakeyi. cikin sauri nakarasa jikin gadon Ina faÉ—in "yaushe katashi
Baba?" Baba yayi murmushi sannan yace "tunsanda Mamana tasaki hannuna taje takama
na LamiÉ—o" Lamido da alokacin shima yakaraso bakin gadon Baban yace "Ina kwana
Baba?" Baba dake kallonshi tunda ya'iso gurin yace "Lafiya Lau 'Dana. Zauna anan
kaji" Baba yakarashe maganar ayayinda yake nuna masa gefensa abakin katifar.
Zama LamiÉ—o yayi yana tambayar Baba yanayin jikinsa Baba yace "Alhamdulillahi
dasauki" Hafiz ma yazo yagaida Baba dajiki sannan su Yadikko Rahane ma duk suka zo
suka gaidashi kafin suka koma suka zauna kan tabarmar dake É—akin.
Shiru É—akin yayi babumai cewa komai har na kusan mintuna sha biyar kafin su Yadikko
Rahane sukama Baba sallama kan zasu koma Babban Buli,Baba godiya yamusu tareda musu
fatan Allah ya kiyaye hanya. basujima da fita ba Hafiz yacema LamiÉ—o zeje yadawo
sesu wuce gaba-daya.
LamiÉ—o gyadamai kai kawai yayi batareda yace komaiba. Nidai inbanda kallon fuskar
Baba danakeyi babu abunda nakeyi. daga yanayin fuskarsa nasan cewa yanajin jiki
dauriya yakeyi kawai. Bayan mintuna kalilan da fitansu Hafiz Baba yabuÉ—e idanunsa
daya rufe tun bayan sunyi sallama dasu Yadikko Rahanen yakalleni sannan ahankali
yace "Ina Hassan?" Cikin sauri najuya ina kallon Kawu Hassan dake kwance kan
tabarma nace "Kawu Hassan Baba namaka magana" dasauri Kawu Hassan yakaraso jikin
gadon yana faÉ—in "Gani Yaya Umar" Baba yace "wanka nikeson inyi kozanji daÉ—in
jikina, gaba É—aya jikina yaÉ—au zafi,jinakeyi kamar ana tafasa ruwan zafi acikinsa"
Kawu Hassan yace "Sannu" LamiÉ—o ma dayayi shiru tundazu yana kallon kasan É—akin
yaÉ—ago yana kallon Baba yace "Sannu Baba" kafin yatashi tsaye yakoma baya yana bama
Kawu Hassan guri danya É—aga shi.
Kawu Hassan yace "zaka iya tashin kuwa?" ahankali Baba yace "I don't know Hassan.
nikawai wankan nikeson inyi da ruwan sanyi ko zanji sauki" Kawu Hassan yace "toh
ayayinda yashiga kokarin É—agashi" anma se Baban yayi sauri yakoma yakwanta yana
rimtse idanu cikin sauri yace "tsaya tukunnan Hassan" tsaya Kawu Hassan yayi Baba
dahar Lokacin bedena rimtse idanu ba yace "Inada wankakken kaya anan ne?"
Kawu Hassan yace "A'a duk suna gida daman akan Inna tafi sallar juma'a se inbi
tagidan in É—auko maka" Baba yayi wani murmushi sannan yace "toh ai nima yau dani
nakeson ayi sallar juma'an Hassan" Kawu Hassan yace "zaka iya zuwa masallacin ne
ayanayin jikinkan nan Yaya?" Baba yace "anan zanyi sallana but I want to dress like
everyone does on Fridays. Inason nima insamu ladan juma'ar tareda ku" murmushi Kawu
Hassan yayi yace "toh inje gidan in É—auko maka kayan kenan tunda akwai sauran
lokaci" Baba yace "dazaifi Kam kilanma kafin nan nadanji daÉ—in jikina se inyi
wankan anma karka Jima don Allah. I'm in so much pain from within" LamiÉ—o dake
tsaye kan Baba yace "toh kodai yayi maka wankan kafin yatafi tunda kace bakajin
daÉ—in jikinka" Baba yagirgiza kai ahankali yace "yajedai yadawo É—in. nayi wanka
babu kayan sawa ne?" LamiÉ—o yace "Toh shikenan Baba" nidai inanan zaune inata
kallon Baba hakanan inajin wani irin yanayi azuciya ta dani kaina bansaniba. Ko Ina
ajikina jinsa nakeyi yamin nauyi anma bance komaiba.
Kawu Hassan shiryawa yayi yamana sallama sannan yatafi Wanda harlokacin LamiÉ—o na
tsaye kan Baba yana kallonshi shima. kallon danaga Baba nama LamiÉ—o ne yasani
dagowa nakalli LamiÉ—on nima wanda se awannanlokacin nasamu nakarema LamiÉ—on
kallo,senaga yamin kyau,he looks more like a man in jumpa cikeda mamaki nace "Daman
kanasa Shadda ne Yaya LamiÉ—o?" LamiÉ—o daketa kallon kasa tun É—azu harsaida nayi
magana sannan yadubeni yasakar min murmushi batareda yace komaiba.
Sincerely nace "kayimin kyau. Jumpa yafi maka kyau" kafin nadubi bangaren da Baba
yake nace "Baba kaima LamiÉ—o yamaka kyau koh?" Baba yayi murmushi tareda gyaÉ—a min
kai sannan ahankali yace "sosaima Mamana" kafin Baba yamaida dubanshi kan LamiÉ—o
dake tsaye har lokacin yace "bazaka gaji da tsayuwa ba kuwa LamiÉ—o?" Baba yashiga
yimasa alama da hannu sannan yace "zo zauna akusa dani muyi hira kafin Hassan
yadawo. I want to know more about LamiÉ—on dayasa Mamana tasaki hannuna without
anyone asking her to.
Lamiɗo karasawa yayi gefen Baba yazauna. Baba yariƙo hannunsa yasaka cikin nashi
yana kallonshi yace "asalin sunan ka LamiÉ—o ne?" LamiÉ—o yagirgiza kai alamar A'a
sannan yace "A'a Baba. sunana Isma'il, Lamido inkiyace da ake kirana dashi agida"
Baba yace "Isma'il is a nice name. Mamana tacemin kai dan Gombe ne,acikin garin
Gombe kuke zamane ko a outside Gombe kuke ?" LamiÉ—o yace "Acikin Gombe,a
masaurautar Gombe gidanmu yake" murmurshi Baba yayi yana k
Jinjina kai sannan jokingly yace "kace da Sarkin gombe nike magana kenan?" LamiÉ—o
yayi dariya yana shafa sumar kansa sannan yace "Mesunan shi ne wannan Baba" Baba
yayi yar dariya yana lumshe idanunsa yace "Mamana tacemin a Gomben kake karatu
Koh?" LamiÉ—o yace "Eh Baba,munma gama aji uku zamu shiga final year insha Allahu in
ankoma hutu" Baba yace "toh Allah yataimaka" LamiÉ—o yace "Amin" Baba still besaki
hannun LamiÉ—o ba yace "Ismail thank you" dukyanda LamiÉ—o yake avoiding kallon
idanun Baba seda yaÉ—ago yakalleshi ayanzu yana mamakin godiyar ta menene.
Baba yasake cewa "Thanks for alwayls bringing a smile on my Daughters face aduk
sanda kuke tare,thanks for making her holiday in Babban buli a special one. tabani
labarin komai and tunranar da ta budi baki tabani labarinnan naji inason in kalleka
in person inyi maka godiya ashedai munada rabon haÉ—uwa" Baba yaÉ—an numfasa sannan
yacigaba da magana yace "Mamana batada wanda take Sharring happiness É—inta daduk
wasu damuwarta Irina,i'm all she's kuma koni damuke tare inban kirata nazaunar
da'ita natambayeta nace mata "Rukayya meke damunki ba" bazata taɓa bu ɗan baki
tafaÉ—a min damuwartaba,ita mutum ce me kawaici darashin son faÉ—an abunda ba'a
tambayeta ba. Tunda nake da'ita bata taɓa nunamin tana son siblings ba sabida
tasamu masu ɗebe mata kewa,bata taɓa yimin kukan rashin mahaifiyaba wanda duk
shekarun nan naÉ—auka na maye mata gaba É—aya gurbin abubuwan dabata dasu É—in
arayuwarta ashe abun bahaka bane ba because for the very first time acikin labarin
ka tafaÉ—a min cewa tace maka tanason ka haÉ—a ta da Yan uwanka,tanason ka haÉ—a ta da
mahaifiyarka tazama tata dukdama acikin labari tafaÉ—a amma ata dalilin ka nagane
cewa she's been yearning to've these people in her life batareda ta taɓa mentioning
minba. Mamana have never been fund of anyone kamar yanda take dakaiba bayan ni"
Baba yace "Isma'il bangama assuring kaina Mamana tasamu soulmate bayan niba seda
tasaki hannuna É—azu tatafi gurinka bayan taga shigowarka. I clearly saw it in her
eyes cewa tanason yin kuka tunjiya amma batayiba sabida batason tashin hankalina
but immediately after she sees you she cried, tafaÉ—a maka matsalarta amatsayin
nakusa da'ita and you console her perfectly" Baba yayi murmushi sannan yacigaba da
magana yace "dabadan you're still under your parents care ba, dabadan kar indaura
maka liability ba dana É—aura maka aure da Rukayya ayau bawai don batada masu kula
da'ita ba,bawai Kuma dan batada masu sonta acikin dangina ba sedan kawai zuciyarta
tafi aminta dakai, tafi yarda dakai zata kuma fi sakin jiki dakai"
Tunda Baba ke magana na zabga uban tagumi inajinshi É—aya bayan É—aya haryakawo kan
maganar in auri LamiÉ—o, aibansan sanda nazare idanu na ba nacire hannuna daga
tagumin danayi Ina tura bakina gaba cikeda yarinta nace "Hu'um nidai bazan aureshi
ba wallahi" Baba dake kallon LamiÉ—o jin abunda nace yasashi dawo da dubanshi gareni
cikeda mamakina yace "LamiÉ—on ne bazaki iya aureba?Akan wani dalili Mamana" Kai
tsaye nace "Baba sabida yana ƙarya. nibanason miji makaryaci" Lamiɗo da maganata ta
dakesa sosai besan sanda yafurta "Baba nima ai daman bance zan auretan ba. Nima
bazan iya auren kwailaba" LamiÉ—o yakarashe maganar yana hararana.
Lokaci guda na tsuke fuska kamar meshirin yin kuka nace "niba kwaila baceba
wallahi" LamiÉ—o ma ya kwaiwayi muryata yace "Nima ba makaryaci bane wallahi.
Circumstances ne yaja" se sautin dariyan Baba kawai mukaji wanda hakan yasamu
kallonshi atare.
Wani irin kunyane yakama LamiÉ—o dankwata kwata yama manta a Ina yake maganar gashi
yariga yayi baran barama babu halin gyara wa.
Baba seda yagama dariyar mu sannan cikeda zolaya yace "toh yanzu yaza'ayi kenan. Ke
kince bakyason aurenshi sabida makaryacine shi shikuma yace sabida ke kwailace
Koh?" shidai LamiÉ—o bece komaiba kanshi nakasa harlokacin.
Baba yadubeni yace "toh ga solution. Mamana namiki sabon Baba apart from me" cikin
sauri na tura bakina gaba nace "nikai kaÉ—ai ne Babana" Baba na murmushi yace "toh
ai zan iyamiki sabon Yaya tunda baki dashi Koh?" cikin sauri nagyada kaina.
Baba yayi dariya cikeda mamakin yarintata yace "Kinason Yaya me ƙarya kenan?" nace
"Eh ai yayu na karya nataba jin Yaya Rabi'u na karya agidan Kawu Adamu" Baba yayi
dariya sannan yadubi LamiÉ—o yace "I hope you don't mind accepting kwailar kanwa?".
LamiÉ—o dahar lokacin kejin kunyar Baba yagyada kai ahankali.
Shiru É—akin yasake É—auka harkusan mintuna ashrin babu wanda yasakeyin magana, kowa
da irin tunanin dayakeyi aransa.
Baba duban LamiÉ—o yayi yace "Isma'il karfe nawa?" LamiÉ—o yace yakalli wall clock
din dakin sannan yadawo da dubansa kan Baba yace daya da mintu uku. Baba yace "Anya
Hassan zaidawo dawuri kuwa?" LamiÉ—o yace "zaidawo insha Allahu" Baba yace "a'a
taimaka min inyi alwalan kawai lokaci na kurewa"
*Anan nakawo karshen bonus Pages da free pages. Duk mai bukatan cigaba da karanta
littafin Qadr zaibiya dari uku kacal ta account number dinnan*
08147722806.
God bless you as you patronizeðŸ˜â¤ï¸ this's just the beginning of Qadr,ba amafara
asalin tushen labarin ba.
Vote
Comment
Share!
*Page Nineteen*
Lamiɗo daƙyar yasamu ya taimaka ma Baba yatashi sannan ya riƙe kafaɗunshi suka
shiga bayin. sunfi mintuna biyar aciki kafin suka fito.
Seda LamiÉ—o yataimaka ma Baba yazauna yana fuskantar gabar sannan yakoma baya
yatsaya wanda adede lokacina aka buÉ—e kofar É—akin,Kawu Hassan ne yadawo daga gida
hannunsa riƙe da ledar kayan Baba. Sannu da dawowa muka mishi nida Lamiɗo ayayinda
ya ajiye ledan kan tabarma yana faÉ—in "Najima koh?" gyaÉ—a masa kai nayi ahankali
kafin yace "Ai harna fito zanhau machine naga ana sallah awani masallacin Æ´an izala
senace bari injona su muyi kawai yanda Inna dawo basai na sake fita ba" LamiÉ—o yace
"akwai masallacin da har sunyi sallan yanzu? karfe É—aya da mintunane fah" kallon
LamiÉ—o nayi sannan nace "masallacin unguwar mune daman sukam suna riga kowa yin
sallar juma'a. Ƴan izala ne" Lamiɗo yace "ikon Allah. mukam wataran har biyu ake
kaiwa kafin ayi sallah" Kawu Hassan yace "eyi akwai masallatan dasuke kaiwa biyun
ananma,wasu kuma É—aya da rabi. Kowani masallaci dai da lokacin dasukeyin nasu
sallar juma'an" LamiÉ—o yace "ah lallai kam" kafin yadubi wall clock É—in É—akin
yadawo da dubansa kan Kawu Hassan yana fadin "Gashi nima abokin nawa baidawo ba
bare mutafi" Kawu Hassan yace "koseya yi sallar juma'an zedawo shima?" LamiÉ—o yace
"bansani ba gaskiya dan bamuyi maganar ba anma tunda har É—aya da rabi takusa gwanda
intafi masallacin inyi sallah inyaso nadawo injirashi" Kawu Hassan ya jinjina kai
kafin yace "gaskiya kam gwanda kaje karyazo baizoba" duban ɓangaren Baba dake
sallah har lokacin LamiÉ—o yayi sannan ya kalleni yace "Nana bari inje masallaci
indawo in Hafiz yazo kice masa yajirani ba jimawa zanyiba" gyaÉ—a masa kai nayi
ahankali ina murmushi kafin yajuya yafita.
Ko seconds goma da fita baiyi ba segasu sundawo tareda Hafiz.
Kawu Hassan cikeda mamaki yadubi LamiÉ—on yace "har kunyi sallar ne?" LamiÉ—o yace
"A'a nafita kenan zantafi muka haÉ—u dashi abokin nawa. daga masallacin cikin
asibitin nan yake,wai suma harsun idar da sallah shine kawai mukayi deciding mudawo
muyi muku sallama kawai semu tafi gaba É—aya,in yaso danayi sallah acikin gari zamu
wuce tasha mukoma gida" Kawu Hassan yace "oh Allah sarki" LamiÉ—o da Hafiz suka
ƙarasa jikin gadon da Baba yake zaune akai wanda alokacin har ya idar da sallan.
Dubanshi sukayi LamiÉ—o nafaÉ—in "toh Baba muzamu koma gida. Allah ubangiji yakara
sauki yasa garkuwan jikine" gyaÉ—a mai kai Baba kawai yayi yana murmushi Hafiz ma
yace "Allah yakara sauki" nida Kawu mukace "Amin"
kafin suka dawo kan Kawu suke ce "toh mu zamu koma Kawu" Kawu Hassan yace "Allah
yakiyaye hanya. Mungode mungode Allah yabar zumunci" LamiÉ—o da Hafiz suka ce "Amin"
for some unknown reasons senaji hawaye nabin kuncina.
Baba dake lura da mood É—ina tun É—azu ahankali yace "Mamana tashi kirakasu waje kuyi
sallama seki dawo" gyaÉ—a masa kai nayi ahankali Ina share kwallana da kasan
hijabina sannan nabi bayansu LamiÉ—o da tunda yaji Baba yace inrakasu yanufi kofa
Hafiz yabi bayanshi suka fice.
Awajen É—akin nasamesu suna tsaye kuma harlokacin ina matsar kwallah.
Lamiɗo naganin nafito ya ƙaraso inda nake tsaye ya tsuguna agabana yadafa kafaɗuna
yana faÉ—in "yanzu kuma kukan na menene Nanaa?" Cikin gunjin kuka nace "Nima bansani
ba" danni kaina bansan dalilin kukan nawaba,nidai kawai nasan I don't want him to
go because seeing him around makes me believe I've someone I can count on bayan
Baba,someone I Cherish so much,someone I can share my problems with,someone that
only seeing him makes me smile koda kuwa acikin damuwa nake. Shakuwata da
LamiÉ—o,yarda dashi danayi completely,da irin yanda nakejinsa azuciyata daga Allah
ne. LamiÉ—o jin nace bansan dalilin dayasa nake kuka ba kuma harlokacin banbar kukan
ba yasashi tashi tsaye yace "Tunda bazaki daina kukan ba bari mu tafi" cikin sauri
na kamo hannunshi Ina ƙoƙarin tsaida kukana nace "Dan Allah karka tafi. Allah
nadaina" dole yasake komawa yatsugana agabana yana kallon cikin idanuna yace "Then
tell me. Why are you crying?" ahankali nace "sabida banason katafi. zanyi kewarka"
murmushi LamiÉ—o yayi sannan yasa hannu yashiga gogemin kwallata yana faÉ—in "Dole
zantafi Nanaaa. ayau nacema Umma zankoma,I don't want to fail her. koso kike
nangaba innace mata zandawo tahana ni dawowa?" cikin sauri nace "dagaske Inka tafi
zaka dawo?" LamiÉ—o yace "mezai hana? dole zandawo insake duba Baba inkuma karbi
number wayarsa inya samu sauƙi tayanda zanna haɗaki da su Jidda dasu Umma awaya.
Kokin fasa Ƴan uwantakan damu ne?" Lamiɗo yakarashe maganar cikin sigar zolaya
dasauri nace "A'a Banfasa ba" sannan nakarada "yanzu Inka tafi yaushe zaka dawo"
shiruuu yayi yana É—an tunani kafin yadawo da dubansa gareni yace "Nima bansani ba
wallahi Ƴar birni" make kafaɗa na nayi alamar banyardaba sannan nace "nidai ƙafa ɗa
kawai" yayi murmushi sannan yace "toh nanda sati biyu?" Cikin sauri nace "A'a
kadawo wani weekend dai" murmushi yayi yana kallona sannan yace "toh amma banyi
miki alkawariba but I'll surely try" stubbornly nace "nidai kayimin alkawari kawai"
Ƴar dariya yayi sannan yace "toh nayi alkawari. I'll come back next week Saturday
insha Allah" cikeda Jin daÉ—i nace "Allah yakaimu. katahomin da abun daÉ—i" LamiÉ—o
yace "me kikeso inkawo miki?" Nace "koma miyene inaso" LamiÉ—o yace "A"a kifaÉ—a dai"
kafin yafara irgamin abubuwan dayake da tabbacin za'a samu a Gombe yace "FaÉ—amin
Rake kikeso? Ko magarya? ko muruci? Ko dinya? Kogasasshen masara? Ko Dafaffen
masara?, ko yalo?,ko gauta?,ko aduwa?, kooo! dirimi?" zuba mishi idanu nayi inajin
yanda yake lissafo sunayensu funnily harya gama sannan yace "toh faÉ—amin wanne
kikeso acikin waÉ—anda na lissafonnan?" Kai tsaye nace "duka" wara idanu yayi
ayayinda Hafiz yakwashe da dariya.
Lamiɗo na kallona yace "jimin Ƴar nan daga lissafo sunayen abubuwa seki zaƙe kuma?"
dariya nayi sannan nace "toh ai naji ina kwadayinsu duka ne shiyasa" LamiÉ—o yadubi
Hafiz dake mana dariya harlokacin yace "Hafiz Nanaa dai sotake insaida shekarun
Inna insaya mata waÉ—annan abubuwan" cikin sauri cikeda curiosity nace "Daman ana
saida shekarun mutum ne?" Wannan karan dukansu dariya sukakwasheda LamiÉ—o na faÉ—in
"Zadai afara takaina tunda banida komai aduniyarnan kekuma kince sena saya miki duk
abubuwan dana lissafo" shiru nayi Ina nazarin abunda yace kafin cikin sauri nace
"A'a basai ka saida shekarun kowaba. Kasayamin rabi se Yaya Hafiz ma yasayamin
rabi" LamiÉ—o na dariya yace "ni ai ko kuÉ—in rabin banidashi kawai yasaya miki duka
seni inkawo" Hafiz yace "kyaleshi Ƴar birni wasa yake miki ninasan dukanma da
kuÉ—inshi zaisaya" nace "toh na gode" LamiÉ—o yatashi daga tsugunen dayake agabana
yace "tun ba'a kawoba kinfara godiya?" nace "ainasan zaka kawo É—in shiyasa" because
I fully trust him and I fully believe that he'll come back kamar yanda yayi alkwari
dukda kuwa nine nasashi yayi alkawarin.
Hafiz duba cikin wayarshi yayi sannan yakalli LamiÉ—o yace "har 1:40pm fah tayi
inkayi wasa zaka rasa sallar juma'a yau" cikin sauri LamiÉ—o yace "insha Allah
zansamu" kafin yadubeni yace "toh Naana koma ciki. muzamu tafi" make kafaÉ—a na nayi
sannan nace "zanraka ku waje" LamiÉ—o yace "kar Baba yanemekifa kikoma kawai" cewa
nayie "bazai nemeniba aishi yace inraka ku" LamiÉ—o yace "toh" kafin muka jera muna
tafiya tare sede wannan karan babu wanda yake magana acikinmu.
Seda mukabar ward É—in baki É—aya mukakai bakin titin dake kusa da ward É—in sannan
suka samu Napep suka tara suka shiga sannan sukacemin inkoma ciki anma banbar gurin
ba harsaida Napep É—insu ya kulemin dagani.
Juyawa nayi Ina tafiya kamar me counting steps É—ina dankuwa abunda nadinga ji
ajikina É—azune yadawomin sabo. tafiya nakeyi kamar bani ke tafiyar ba,jinakeyi
gaba-daya gabobin jikina sun sage,jinsu nakeyi kamar ba'a jikina sukeba,nikaÉ—ai
narasa meyakemin daÉ—i ajikina ahaka dai harna shiga ward É—inda É—akin da aka kwantar
da Baba yake.
Tundaga bakin kofar ward É—in naga Nurses nata kai kawo cikin sauri harna nufi
hanyar É—akin da aka kwantar da Baba sede da mamakina naga Nurses É—in ashe É—akin
suke ta shiga suna fita, gakuma Kawu Sani da Kawu idrissa daketa kai kawo abakin
kofar ɗakin ayayinda Kawu Hassan kecan jikin windown ɗakin yana leƙe fuskarsa
ɗaukeda damuwa ƙarara.
Kawu Adamu da Yaya Fahad(Babban dan Kawu Sani) da yauce rana ta farko dana fara
ganin shi a asibitin na zaune akan wasu chairs É—in dake gaban É—akin sun rabza uban
tagumi. Aibansan sanda na'isa inda suke ba da guduba Ina tambayarsu meyafaru anma
babu wanda yakulani. It seem as if baswamajin menake faÉ—a,they're totally lost in
their world of thoughts wanda hakan yasani ƙarasawa jikin windown da Kawu Hassan
yake tsaye nashige tagabanshi Ina leƙen cikin ɗakin hankali tashe.
Doctors guda biyu da Nurses nahango tsaitsaye kan Baba ayayinda naga hancinsa
daukeda oxygen dinda ko sati ba'ayi da cire masaba gakuma wani likita dake sunkuye
kanshi yana danna masa wata na'ura a kirjinsa da alama dai yana kokarin ceto
ransane,yana ƙoƙarin dawo masa da numfashinsa daidai. Wani irin kuka nasaki Ina
faÉ—in "Baba! Baba!" Kafin nabar jikin windown nanufi kofar É—akin aguje sede tunkan
nasamu damar buÉ—ewa Kawu Sani yayi sauri yakamo hannuna yadawo dani inda yake kafin
yarungume ni ajikinsa yana shafa bayana.
cikin sigar lallashi yace "kidaina kuka Rukayya. Babanki addu'arki yake bukata a
irin wannan lokacin" anma seyazama kamar ma zugani Kawu Sanin yakeyi, ƙara sautin
kukana nayi Ina faÉ—in "Yanzufah muka gama hira dashi Kawu. shine ma yacemin in
rakasu Yaya LamiÉ—o indawo" cikin shikewa nace "wallahi shine yace in rakasu
meyasameshi Kuma yanzu? miyasa likitoci suke tsatsaye akanshi? Kawu miyasa bazasu
barshi yayi numfashi dakanshi ba" na damke jikin rigar farar shaddan Kawu Sani
inamai cigaba da kuka nace "Kawu dan Allah kace musu sucire abun hancinsa subarshi
haka,in akasakamai wancan abun bayamin magana and it scares me" Kawu kasa cemin
komai yayi sema hawayen dayafarayi shima.
Haka nacigaba da kuka Ina maganganun dabakai ba gindi ni kaÉ—ai harna kusan mintuna
goma sannan mukaji an buÉ—e kofar É—akin,dasauri najuya ina kallon kofar,likitan dake
kokarin ceton ran Baba ne ɗazu yafito yana ƙoƙarin cire hand gloves ɗin hannunshi
ayayinda fuskarshi kenuna tsananin irin tashin hankalin dayake ciki.
Kawu Adamu da Kawu idrissa ne sukayi karfin halin ƙarasawa inda yake suna
tambayarshi jikin Baban but his answer was "I'm sorry we couldn't save him. Allah
yayima Mallam Umar rasuwa, accept my hearty condolences" kafin yabar gurin jiki
sanyaye. Ko ba'a faÉ—a ba shima mutuwar ta kuÉ—ima shi.
Tunda naji likita ya ambaci "we couldn't save him" nafara tunanin menene ma'anan
wadannan kalmomi dayafurta harya haÉ—a sentence dasu,jinayi kaina yaÉ—aure alokacin
sede tunma kafin nasamu yanda zanyi nayi interpreting words É—inda naji daga
bakinsa,last statement dinshi yasani kwala kiran sunan Baba ayayinda nanufi kofar
É—akin aguje kamar wata mahaukaciya.
Agaban gadon dayake kwance an rufemai gaba É—aya jikinsa da farin kyalle na tsaya
sannan cikin sauri na yaye farin kyallen daga jikinshi,idanunshi arufe kamar me
bacci wanda hakan yasani fara tabashi with the hope cewa ze bude idanunshi nace
"Baba katashi" anma shiru,nasake jijjigashi akaro na biyu ahankali Ina hawaye
nasake cewa "Baba katashi kaji abunda likita cewa. Baba katashi" nanma shiru wanda
hakan yasa sautin kukana karuwa nafara jijjiga shi dakarfi wannan karan ina faÉ—in
"Baba katashi. Baba katashi kaji wai cewa suke ka mutu bayan kuma bacci kake, Baba
katashi don Allah"
ÆŠaya daga cikin Nurse's É—inda ke gurinne tazo takama hannuna tana faÉ—in "kiyi
hakuri addu'a zakiyi mishi" kwace hannuna nayi zancigaba da tashinshi Nurse É—inda
tamin magana da wata sukazo suka kamani suna kokarin fitar dani daga dakin.
Fizge fizge nashiga yi Ina kokarin kwace kaina ayayinda nake kuka Ina Kiran "Baba!
Baba katashi zasu tafi dani, baba katashi karsu rabani dakai. Bazan iya rayuwa Babu
kaiba. Baba karka tafi kabarni kamar yanda Umma tabarmu,banida kowa aduniyar nan
saikai. Baba dan Allah katashi!" Wannan karaan nakarashe maganar harda shikewa.
Haka suka fitar dani daga É—akin ina kuka hakanan inaganin sanda suka sake lullube
fuskar Baba and that hits me cewa "dagaske fah ya rasun kamar yanda likitan
yace,Baba ya rasu ya barni a duniyar da banida kowa bayanshi,Baba yatafi yabarni
kamar yanda Umma tatafi tabarmu. shikenan banida Uwa banida Uba,shikenan banida
kowa nazama marainiya kamar yanda Baba yataba cemin seka rasa Uba kake zama maraya.
Wani irin jiri nafara ji lokaci guda gakuma dishi dishi dana dinga gani wanda
daganan kuma nasaki jiki nafadi.
Kawu Sani dake kusa da Rukayya ne yayi sauri yakarasa inda take kwance a kasa
sumamma yayi sauri yadagata. Nurse É—inda tafito daga É—akin da gawan Baba ke ciki
tayi sauri tace masa yabi bayanta. Awani É—aki daban suka kwantar da Rukayya inda
aka shiga bata taimakon gaggawa.
Dafara ruwa aka dinga shafa mata afuska anma data farfado seta sake sumewa Kuma.
Kawu Sani hankalinshi bakaramin tashi yayiba,ga mutuwar kaninsa gakuma rikidewan da
Rukayya tayi lokaci guda. hawaye kawai yakeyi batareda yamasan suna zubowaba. Dukda
irin rashin lafiyar da Mallam Umar yayi,dakuma tarasu dayayi shekaranjiya yanabar
musu wasiyya he just can't believe ya rasun dagaske,gani yakeyi kamar inya koma
dakin ze sameshi a zaune yana masa smiling kamar yanda yasabayi kwana biyun dayadan
ji saukinnan. daƙyar akasamu Rukayya tadawo daidai kafin akayi mata allurar bacci.
Bayan Nurse É—in tafito daga É—akin Kawu Sani yashiga ya duba Rukayya,seda ya
tabbatar baccin takeyi sannan yashiga ƙiran layin Uwar gidanshi da'ake Kira da
*Aunty* danyasan ko giyan wake yasha Ummi bazata zo tazauna da Rukayya a asibiti ba
hakanan bazata bar Ƴaƴanta ma suzauna da'itaba. bejima yana ringing ba taɗaga inda
dagajin yanayin muryarta yagane labarin mutuwan Umar É—in ya'isa garesu.
Gaidar dashi tayi sannan tamishi ta'aziya sannan tashiga tambayarshi karfe nawa
za'a jana'izan Mallam Umar din sannan a Ina za'ayi zaman makoki,gidanshi za'ayi
kokuma Giyade za'atafi.
Kawu Sani da maganar ma danta zame mishi dolene yace "Habiba wallahi bansani infact
I'm not with them inatarede Rukayya anyi admitting dinta Itama. Suma tadingayi
anmadai ansamu anyi mata allurar bacci,sonake inkoma can gurinsun inji me ake ciki
anma bazai yuyu inbar Rukayya itakadaiba shiyasa ma nakiraki ince miki kozaki zo
kokuma Zaki turo siyama tazo tazauna da'ita ne?" Take Aunty tace "Subhanallahi
Allah yabata lafiya badai inturo Siyaman tazo tazauna da'ita muzamuje jana'iza ai"
Kawu Sani yace "toh shikenan setazo" daganan Kawu Sani yakashe wayar ayayinda
yafara safa da marwa a dakin.
*Littafin nan na kudine duk Mai bukatar shiga paid group yana iya tuntubar wannan
layin 08147722806*
*Page Twenty*
***
Su LamiÉ—o na barin asibitin cema me Napep É—in sukayi yayi dropping É—insu aduk wani
masallacin dayasan ba'a sallar juma'a dawuri dan Allah. aikuwa ko nisa da asibitin
basuyi ba suka iso wani masallacin da aketa ƙoƙarin tada sallah wanda hakan yasa
me Napep tsayawa yadubi su LamiÉ—o yace "inkukayi sauri zakusamu a masallacin nan"
sauka sukayi daga Napep É—in ayayinda Hafiz yace "Toh mungode" ayayinda LamiÉ—o yayi
sauri yanufi taps É—inda ke bakin masallacin dan É—aura alwala yaje yajona jam'i inda
Hafiz yatsaya biyan me Napep É—in kuÉ—insa.
Allah daya taimaki LamiÉ—o ba'a tafi ruku'u ba har ya'idar da alwala yaje yajona
sahun wanda wannan dalilin yasa baiyi missing raka'a ko É—aya ba,yasamu complete
sallan. Ana idar da sallah a gaban masallacin LamiÉ—o yasamu Hafiz sannan suka
ƙarasa bakin titi suka tari mai napep sukace yakaisu tashan Bauchi. Sune two first
passengers dasuka shiga motar wanda wannan dalilin yasasu bajewa a seat É—in baya
suna hira kafin asamu passengers mota yacika sukama hanyar Gombe. Hira sukeyi akan
football sega mai tallen kayan koli yazo,tsaidashi Hafiz yayi sannan yatambayesa
koyana da wristwatch na Mata. Cikin sauri mai kayan kolin ya ajiye kayan kolinsa
kan seat É—in motar yana faÉ—in "Akwai Yallabai. gasunan kala kala sewanda kazaba"
ÆŠan kolin ya karashe maganar ayayinda yaciro agogunan yana nunama Hafiz É—in.
Hafiz zaban maikyau yayi yabiya kuÉ—in har lokacin LamiÉ—o na kallonshi bece komaiba.
Seda yaga É—an kolin yatafi sannan ya taba Hafiz É—in cikin sauri cikeda son Jin
gulma yace "waka sayama wristwatch Hafiz?" Hafiz yace "A Aminatun mu na sayama"
cikeda tuhuma LamiÉ—o yace "Anya Hafiz?" Sannan cikin sigar zolaya yace "faÉ—amin
kodai new Beb mukayine?" Hararanshi Hafiz yayi yana dariya sannan yace "Allah
dagaske a Aminatu nasayama. tajima tana damuna insaya mata writswatch kullum
mantawa nikeyi. Sannan kaima kasan banida wata Beb kuma Koda inadashi you'll be the
first to know. I've no one yet and I don't think I'll have any girlfriend soon"
Hafiz yakarashe maganar sincerely ayayinda yazura wristwatch É—in cikin aljihun
wandonshi.
Shi Hafiz gani yakeyi it's too early yafara kula mace,acewarsa there's time for
everything in life. So,yanzu gina kanshi yakeyi tukunnan,he want to finish his
studies and be a man first kafin yafara irin wannan tunanin.
LamiÉ—o dayagama sauraran maganar Hafiz É—in yakwashe da dariya sannan yace "Toh Mr
gentle Man keep building yourself kaji. mudai more rayuwar mu zamuyi aduk yanda
tazo mana" dan bayau yasaba Jin wannan maganar daga bakin Hafiz ba and to him his
thinking doesn't make any sense at all. Kuma akullum Hafiz yayi irin wannan maganar
to seya tsokane sa.
Hafiz yace "Nima ai bance maka bazan more rayuwata ba. I just believe there's time
for everything in life" LamiÉ—o yayi murmushi tareda gyara zamansa akan kujerar
yajingina da jikin seat É—in motar yana kallon mutanen dake kai kawo acikin tashar
sannan yace "And that's what differentiate us Hafiz. You plan and I don't plan. You
do everything accordingly and I do my things scatterly. You think twice before
doing things and I do anything that just come my way. You follow your mindsets and
I follow my heart desires. I know I'm a bit selfish but atleast I don't care about
worldly things,I only care about what makes me happy shiyasa da banason makaranta
nakasa takurama kaina akan senayidin, shiyasa danake son Maimunatu nayi mata
confessing and we're happily dating now anma kai ko bakason makarantar ma kariga
kayi forcing kanka sekayishi,it can be kanada yarinyar dakakeso ma anma ka danne ma
zuciyarka sabida kariga kasama ranka cewa this's not the right time" LamiÉ—o yataso
daga jinginuwar dayayi ajikin kujerar yadawo yana kallon Hafiz sannan yace "then
when will be the time you'll enjoy your life? we're 22 now,soon zamuyi 23 and
before you know it lokaci yatafi Kuma in lokaci yawuce baya dawowa,so you better
make the most of it" Hafiz dafa kafaÉ—un Lamido yayi sannan yace "is not as if I'm
not enjoying my life Lamiɗo. muna zuwa wasan ƙwallo,muna zama a majalisa,I do watch
movies during my leisure times,ina ziyara,inakuma hira da siblings É—ina. Sede komai
nakeyi a rayuwa inasaka masa lokaci sabida gudun kar inshiga lokacin É—aya daga
cikin harkokina. Something like studying is one of my biggest priorities sabida
azamanin yanzu inbakayi karatun ba babu wanda zai kalleka da idon kwalli. gashi
kuma I'm the eldest Son,I've a family to take care of in the future,I don't want to
be a liability but rather I should give a helping hand to my parents. Sometimes you
shouldn't just think about yourself,think about others,think about the people
around you and your loved ones LamiÉ—o. In yanzu iyayenmu nakula damu akwai lokacin
da karfin su zai iya karewa wanda kuma alokacinne mukuma yakamata ace munkarbi
responsibility É—in mu dawo dashi kanmu to which dole tunyanzu yakamata mufara gina
kan mu ahead of that. Shiyasa kaga Ina planning komai arayuwa,I've certain goals to
achieve insha Allah And batun kula yan Mata kuma nasan ba aure zanyi ba anytime
soon,banason inbata ma yarinya lokaci inbatama kaina lokaci shiyasa banasashi
acikin lissafina. Innazama stable and when I'm ready I'll surely find the right
women" dariya LamiÉ—o yayi sannan yace "Nice one Bro sede perspective É—ina da naka
awannan bangaren daban ne" yace "kagani,I love Umma,I love my siblings sannan
bantaba sama raina cewa Umma ne zata kula daniba har karshen rayuwata ba infact
I've a desire like yours,nima inason inzama stable,inkuma sauke mata duk wasu
nauyin dake kanta indawo dashi kaina Itama ta huta anma sede believe É—inmu ba É—aya
baneba. You believe through Western education zaka iya achieving wadannan goals É—in
naka and I believe kobanyi Boko ba zan rayu and I can take care of my family myself
Insha Allah sabida ba'akai na akafaraba and many people have lived happily and
wealthy batareda sunyi karatun bokon ba. Kowa da hanyar cin abincinsa Hafiz sannan
batun yan mata kuma,you can't just meet someone and get married to him without
knowing him sequarely, marriage is a life time something,you must know each other
first,you must know the kind of woman you're going to marry inbahaka ba you'll end
up regretting it for the rest of your life. Shiyasa kaga muke soyayyar muma,in
anfara da wannan in anga akwai mishikila se acanza dawata kuma har adace" dariya
Hafiz yayi Jin abunda LamiÉ—on yace daga karshe sannan yace
"Nagane maganarka LamiÉ—o and from our conversation I've learned something. We
shouldn't disregard others perfectives just because nasu is different from ours,we
might have thesame dreams but the road of getting there might also be different.
Like in our case,nina yarda tahanyar karatune zanyi achieving goal dina while kaika
yarda ba dole seta hanyar karatu zaka zama successful arayuwaba and many people
have thesame perspective as yours and they live happily,wasu tahanyar plantation
suke ciyar da kansu da iyalinsu,wasu tahanyar farming,wasu ta hanyar kiwo,wasu ta
hanyar kasuwanci,wasu ta hanyar talent É—in rubuta labarai and many more kuma the
most amazing thing Inka duba 99% É—insu are richer than us damukayi dedicating
almost all of our lives akan karatun bokon. But the question here is how did they
get there?ya'akayi suka samu abunda sukeyi É—in harya zame musu garkuwa?" Hafiz yace
"nidai nasan kafin sukayi É—aya daga cikin abubuwan dasukayi harya taimakesu
arayuwa,they must have prepare themselves well. Kaga kaman me aikin gona ko
plantation dole ne daman yanada gonan a ajiye inkuma bashidashi dole se inyanada
kuÉ—in saye hakanan aikin gona is not a joke. dole se yanada masu tayashi aikin
gonan dakuma abubuwan dazasu taimakamai gurin saka noman nasa yayi kyau,kaman me
kiwo kuma dole shima seyana da dabbobin in the first place kokuma dole seyanada
kuÉ—in sayan dabbobin, anmakai how are you preparing yourself against that? Did you
have any plans? No you did not.
Toh that's the difference between me,you and them.
Believe it or not LamiÉ—o. Bazaiyuyu kazauna haka kawai kace everything will come to
you ba. Komai zakayi arayuwarnan seka tashi tsaye. bakoda yaushe bane mutum yake
zama lucky and just because your Father was lucky yasamu aiki out of blue doesn't
mean your life will be thesame as his"
LamiÉ—o dakejin maganganun Hafiz É—in harya seda yakai aya sannan LamiÉ—o yayi
murmushi yakalli Hafiz right in the eyes,bravely yace "I'll be lucky insha Allah.
I've this feeling Hafiz" Hafiz sauke nannsuyar ajiyar zuciya yayi ayayinda yake
jijjiga kai cikeda desbelief. Yarasa yaushe LamiÉ—o zaizauna yayi tunani dakyau
yagane cewa not everyone is lucky ba and time have changed, nothing is like before.
we're now in a world where western education is very valued yanzu,masu kasuwancin
yanzunma most of them sunyi karatun daga baya ne suka ajiye takardar karatun agefe
suka faÉ—a harkan kasuwancin,wasu kuma seda suka fara gina kansuta hanyar aikin
gwamnatin sannan suka bari suka koma yin bussiness É—in,wasu kuma haÉ—awa sukeyi duka
biyu alokaci guda anma yasan ko kwana dubu zeyi yana faÉ—a ma LamiÉ—o irin
maganganunnan he'll never take it seriously tunda bayau suka fara argument É—innan
ba,bakuma yau yasaba kin daukar shawarar sa ba. He just hope one day he'll realize
it himself and he just hope lokacin dazaiyi realizing gaskiyar al'amarin rayuwar
will not be too late.
Sunfi awa É—aya a tashan kafin motarsu tacika sannan suka kama hanyar Gombe.
***
Ko mintuna ashirin Kawu Sani beyi da gama waya da Aunty ba Siyama ta'iso asibitin.
Batasha wahalar samun É—akin da aka kwantar da Rukayyan ba dayake tundaga gida seda
Aunty taƙira Kawu Sanin yamata kwatance sannan tataho. Knocking tashigayi a kofar
É—akin inda Kawu Sani yayi mata iso sannan tashiga É—akin bakinta É—auke da
sallama,zaune tasamu Kawu Sanin kan kujerar dake kusa da gadon da'aka kwantar da
Rukayyan. Fuska babu walwala Siyama ta russuna ƙasa kusa da Kawu Sani tareda faɗin
"Ina wuni Abba" kallon yanayin fuskarta Kawu Sani yashigayi anma sebai kawo komai
aransaba,se yayi tunanin ko Itama rasuwar Umar É—inne yasata cikin wannan yanayin.
Ahankali yace "Lafiya Lau Siyama" Siyama daƙyar tace "Ya hakuri. Kawu Umar lokaci
yayi" Kawu Sani yace "Alhamdulillah" Siyama tace "Allah yajikanshi da rahama" Kawu
Sani yace "Amin" sannan yatashi tsaye daga kan kujerar dayake zaune ada yace "Maman
kun suna gida ne haryanzu?" Siyama tace "Eh nabarosu agida anmadai suna shirin
tafiya can gidan Kawu Umar É—in,wai acan za'ayi jana'izarsa" Kawu Sani yace "waya
faɗa musu?" Siyama tace "Yaya Fahad Aunty taƙira tatambaya shine yafaɗa mata kusan
zanfitonnan" jinjina kai Kawu Sani yayi sannan yace "toh kizauna da Rukayyan bari
naje nasamosu yanzu za'a wuce da gawan can gidan nasa" Siyama tace "Toh" kafin taja
kujerar da Kawu Sanin yatashi akai tazauna ayayinda shikuma yafice a É—akin.
Sanda Kawu Sani yasamu su Kawu Adamu har anshirya gawan Mallam Umar za'a tafi dashi
gida wanda wannan dalilin yasa suka kama hanyar gidansa take. Kankacemi rasuwar
Mallam Umar yagama yaɗa Ƴan unguwansu da Ƴan uwa da abokan arziki. gida yacika
makil tunma kafin lokacin da'akasa za'ayi jana'izar tayi dankuwa an É—an jinkirta
lokacin sabida asamu mutanen GiyaÉ—e su iso. Babu wanda mutuwar bawan Allahn nan
beshigeshiba hakanan ko'ina kashiga faÉ—an halinsa na gari akeyi. Bayan sallahn
la'asar akayi jana'izar sa daya tara dimbin jama'a sannan aka kaishi gidansa na
gaskiya.
Mallam Abubakar Shattima mahaifin Mallam Umar har hawaye seda yayi dan yasan he's
lost a treasure. ÆŠan sa mafi soyuwa aransa,mafi Jin tausayinsa dakuma Jin kansa.
Bayan andawo daga jana'iza agidan akazauna zaman makoki hakanan duk baƙin dasukazo
most especially Ƴan Giyaɗe sesun tambayi inda Rukayya take amma babu wanda yake
basu takamaiman answer mekyau harsaida su Aunty suka iso sannan suka faÉ—a musu tana
asibiti kwance tunda mazan ne daman kaÉ—ai suka sani se ita Auntyn da Kawu Sani
yakirata awaya yafaÉ—a mata.
Gwaggo Suwaiba da Gogode ne suka dage sesun je wajenta sunganta wanda dole hakan
yasa Aunty taƙira wayan Fahad tace yazo yakaisu tunda shi yasan inda aka kwantar
da'ita. Cikin mintuna kalilan suka Isa asibitin.
Siyama dake zaune cikin É—akin tana karanta Hausa novel dankuwa abunda takeyi kenan
aka jajibota daga gida akace dole setazo tazauna da Rukayya shiyasama taboyo abunta
cikin hijabi tataho dashi dan ita Allah yagani bazata iya tayi hira da Rukayya ba
sabida irin haushinta datake ji tun suna yara and on top of that she don't want to
be bored. Jitayi ana knocking kofar É—akin wanda hakan yasata saurin boye littafin
datake karantawan cikin hijabinta tana faÉ—in "Come in" Gwaggo Suwaiba da Gogode ne
suka shigo wanda wannan dalilin yasata tashi tsaye ta russuna tagaidasu tareda yi
masu ta'aziya ayayinda suka amsa sannan Gwaggo Suwaiba tadubi bangaren da Rukayya
ke kwance kan gado tace "Bata farkaba haryanzu?" Siyama tace "Bata farkaba Gwaggo"
Gwaggo Suwaiba sa hannu tayi tadaga mayafinta tana matsar kwallah kafin takarasa
gefen Rukayyan tazauna tana kallonta cikeda tausayawa. Gogode ma jan kujerar dake
kusa da gadon tayi tana kwallan itama.
Itadai Siyama komawa tayi gefe tana kallonsu aranta tana addu'ar Allah yasa yanzu
zasu tafi subarta tacigaba da karatun littafinta. Anma shiru shiru harkusan awa
É—aya bataga suntashi ba kuma dai da alama bayanzu suke da niyar tafiyaba wanda
wannan dalilin yasata deciding tayi tafiyarta gida dukda babu kuÉ—in machine
ahannunta amma ai inta isa can bazata rasa mebataba. tunanin data gama yine yasats
duban su Gogode dasuka rabza uban tagumi harlokacin sannan tace "Gwaggo ku kunanan
ba?" Gwaggo Suwaiba tace "Eh zaki tafi gidane?" Siyama tace "Eh zanje gida daman
sabida bakowane agurinta kumasu Abba zasuje jana'iza shiyasa Aunty tace inzo
inzauna da'ita" Gwaggo Suwaiba tace "Toh shikenan bakomai kijeki kawai mu munanan"
Siyama tace "toh Allah yabata lafiya" wannan karan Gogode ne ta amsada "Amin"
sannan Siyama tafice a É—akin.
Tana fita a ward É—in tahangi wata mota kamar na Yayansu. Cikin sauri ta nufi motar
don tabbatar wa, aikuwa shiɗinne. da mamakinta ta ƙarasa jikin motar. yana kance
jikin seat É—in driver idanunsa a lumshe kamar me bacci ayayinda kafafunsa ke wajen
motar yakure sautin radio yanajin karatun alqur'ani cikin kira'ar Sheikh Sudaiz
daya riga yazame masa dabi'a.
Siyama Ƙiran sunanshi tayi tace "Yaya Fahad?" Fahad take kwance idanunsa lumshe
bawai bacci yakeyi ba jin ankira sunanshi yasashi buÉ—e idanunsa ahankali yaÉ—aura su
kan Siyama dake tsaye tana kallon shi batareda yace komaiba dukda kuwa yana mamakin
yaushe tazo asibitin tunda shibawai yasan yanda Kawu sani sukayi da Aunty baneba.
Siyama tace "mekakeyi anan?" amma memakon Fahad ya amsa tambayarta seya maida
idanunsa yarufe su yanamai cigaba da sauraran karatun Alkur'anin dake tashi cikin
motar tasa. da kamar bazai amsa taba dan har Siyama tacire ran samun amsa daga
gareshi amma seya buÉ—i baki yace "I should be asking you that question" cikin sauri
Siyama tace "Yaya Fahad kasan Rukayya batada lafiya ai. niike zaune gurinta" Fahad
dahar lokacin idanunshi arufe suke yace "and I brought her Grandmother with Gwaggo
Suwaiba" Siyama tace "toh ya akayi baka tafi ba?" wannan karan shiru yayi baice
mata komai ba kuma tasan dawuya yayi maganar danhaka tace "are you by any chance
waiting for them?" Memakon Fahad yabata amsa instead seya bude idanunsa yadaura
akanta wanda hakan dayayine yabata amsar cewa jiran nasu yakeyi danhaka tace "toh
ai ba yanzu zasu tafiba. Infact susuka cemin injeni gida" Fahad dake kallonta har
lokacin yace "Are you sure?" Siyama tagyada mai ahankali danhaka yatashi yazauna
dakyau sannan yafara ƙoƙarin warming motarsa. Siyama dake tsaye har lokacin tana
kallonsa cikin sauri tace "Yaya Fahad gida zakaje ne?" memakon yabata amsa sekawai
yasa hannunshi a aljihu yaciro 500hundred yamika mata and this gives her an answer
cewa bagidan zashi ba. Godiya tayi mishi tana mamakin miskilanci irin na Yayan nata
harya yaja kofar motarsa yarufe yabar gurin.
Watodai akan yatambayi su Gogoden yaushe zasu tafi ya gwammace yazauna zaman
jiransu harna morethan hour É—aya and she's sure Koda zaikai dare baze barnan ba
sede in Aunty ko Abbansune suka kira suna nemansa kokuma wani urgenty yataso masa
ne kaÉ—ai zaisa yabar gurin.
Taran napep tayi tayi wucewanta gida abunta.
***
Karfe goman dare Rukayya tafarka daga nannauyan baccin datakeyi wanda dukdan
dalilin allurar baccin da akayi matane. Karema É—akin kallo tashigayi tana mamakin
meyakawo ta nan? ya'akayi take kwance a gadon asibiti tundadai ga canular a
hannunta tana gani a yayinda lokaci É—aya kuma abunda yafaru É—azu suka fara dawo
mata a kwakwalwarta. tunawa datayi ance Baba yamutu kuma hartaje taga anmasa
lullubi da farin kyalle yasata tashi azabure tana Ƙiran "Baba!" ayayinda tayi sauri
tasauka daga kan gadon tanashirin nufar kofar sekuma tayanki jiki ta faÉ—i. Gwaggo
Suwaiba dayanzu fitowarta daga bayi tayi sauri takaraso inda Rukayyan ke zube akasa
tashiga jijjigata ayayinda Gogode dayanzu ta idar da sallah tayi sauri tashiga
bathroom É—in taÉ—ebo ruwa tazo tana shafa mata afuskarta.
Buɗe idanu Rukayya tayi tana kallonsu sekuma tasake zabura kamar ɗazu tana ƙiran
Baba anma kafin ma ta iya tashi tasake sumewa. haka tadingayi harkusan sau huÉ—u
wanda hakan ba ƙaramin tada hankalin su Gogode yayiba dole Gwaggo Suwaiba tatashi
tafita neman likita. Batafi mintuna biyar da fitaba kuwa sega ta tadawo da Nurse on
duty. Itace tazo ta dubata,tace su dagata su maidata kan gado kafin sukayi mata
bayanin abunda Rukayyan tayi tayi. Nurse É—in tace she's still in shock with the
news,inmuka cigaba da cewa dole seta farka yanzu it might affect her mental
stability. Alluran bacci kawai zansakeyi mata kafin gobe Doctor yazo yadubata.
Gwaggo Suwaiba da Gogode gyaÉ—a ma Nurse É—in kai sukayi suna hawaye, ayayinda Nurse
É—in tayima Rukayyan allura,seda ta tabbatar komai is Normal sannan tayi musu saida
safe tayi ficewarta a É—akin tana addu'ar Allah yabama patient É—in lafiya.
*Wannan littafin na kudi ne. Duk Maison shiga paid group should talk to me via this
number 08147722806*
*Page Twenty One*
***
LamiÉ—o da Hafiz isan yanma sukayi Gombe. Napep É—aya suka shigo wanda seda akayi
droping Hafiz sannan aka karasa da LamiÉ—o bakin masarautar.
Koda ya'isa gidansu sama sama suka gaisa da kannen nasa sannan yawuce É—akinsa. Umma
kam dama baisameta a gida ba,wai tashiga gidan *Galadima* dubiya karamin ÆŠan su ya
karya kafarsa awurin wasan kwallo.
Se dare suka samu zama dukansu inda Umma ta tambayi LamiÉ—o koya samu yaje gidansu
rukayyan inda atake yasanar da'ita komai dakuma abubuwan dasuka faru a Bauchin.
Umma cikeda tausayin Rukayya tace "Allah Sarki ashe rashin lafiyar mahaifinta ne
yahanata kiranka" LamiÉ—o yace "Eh wallahi Umma"
Umma tace "Toh Allah yabashi lafiya yasa kaffara ne. Inadai kasamu ka karbi number
tasa?kaga in ankwan biyu seka kira kaji yanayin jikin nasa" Umma takarashe maganar
ayayinda tamaida hankalinta baki É—aya kan LamiÉ—on.
LamiÉ—o ahankali yace "ban karba ba Umma" cikeda mamaki Umma tace "Akan wani
dalili?" LamiÉ—o yace "Babantan was in a state dabazai yuyu ince yabani numbersa ba"
Umma tace "Toh ai shikenan. Kama kanka" LamiÉ—o dai murmushi kawai yayi hakanan har
ranshi yanason yacema Umma seya koma sake duba mahaifin Rukayyan zai karbi number
anma yasan this's not the right time. Ba lallai ta amince ba dan haka yaja bakinshi
yayi shiru with a plan daga baya zaisan yanda zaiyi yayi approaching É—inta da
maganar.
Salma dake kwance jikin Umma tana kallon Hausa film tashiga tambayar LamiÉ—o
koyabama Ƴar birni ribom ɗinda tabayar akai mata.
Wara idanu yayi danshi seda tayi maganar ma sannan yatuna tabashi wani abu wai shi
sako sannan yace "wallahi namanta Salma. I put it inside my pocket shadaf namanta
inbata. Anma kiyi hakuri next time insha Allahu innaje zanbata" LamiÉ—o yakarashe
maganar ayayinda yake satan kallon Umma and her expression alone gives him an
answer.
***
Washegari Koda Rukayya tafarka thesame thing tayi tayi dayake Allah yataimaka Kawu
Sani da Fahad na gurin sunzo dubata atake Kawu Sanin yatura Fahad yaje yanemo
likita.
Fahad gyaÉ—a kai yayi sannan yafice a É—akin don yin abunda mahaifin nasa yasakashi.
Baijima da fitaba segashi sundawo da likitan. ƙarasawa jikin gadon likitan yayi
sannan yashiga tambayarsu abunda Rukayyan tayi tayi, Gwaggo Suwaiba ne tamishi
bayanin yanda sukayi da Nurse É—inda ta duba Rukayya a daren jiya dakuma alluran
baccin datayi mata.
Gyaɗa kai likitan yayi cikeda gamsuwa,sannan yashiga taɓa pulse ɗin Rukayyan,yayi
wasu gwaje gwajen sa sannan yayi rubutu jikin paper yamika ma Kawu Sani dake tsaye
kusada shi yace "kusamo waÉ—annan prescriptions É—in semuyi mata amfani dasu muga
abunda Allah zaiyi"
Kawu Sani karban papern yayi yana fadin "thank you Doctor" likitan yace "bakomai
kawai in ankawo kuyimin magana Ina office É—ina" Kawu Sani yace "toh" ayayinda
likitan yafice a É—akin. kallon bangaren da Fahad ke tsaye yayi folding hannunsa a
kirji yana kallon karfen gadon da Rukayya ke kwance Kawu Sani yayi sannan yace
"Fahad" cikin sauri Fahad yaÉ—ago dakansa yana kallon mahaifin nasa sannan ahankali
yace "Na'am Abba" Kawu Sani yashiga miƙa masa Papern hannunsa yace "Get this drugs
from chemist now please" Fahad karasawa yayi inda mahaifin nasa yake sannan yasaka
hannu yakarbi papern yana faÉ—in "toh" sannan yajuya yafita dasauri.
Sanda Fahad yadawo straight office É—in likitan yajeshi,yanuna masa prescriptions
É—inda yasiyo sannan suka nufi É—akin da aka kwantar da Rukayyan tare. Nan likitan
yakarasa dakansa yamata alluran sannan yadubi Kawu Sani yace "zuwa bakwai na dare
zata tashi insha Allahu daganan kuma se afara bata drugs É—in though I'll come back
myself and see her condition kafin mufara administering mata drugs É—in" Kawu Sani
yace "toh shikenan. Allah yakaimu lokacin Doctor" Doctor yace "Amin" kafin yamusu
sallama yafita.
Kawu Sani duban Gwaggo Suwaiba yayi sannan yace "Suwaiba kozakuje gida ku huta se
aturo Siyama tazo tazauna da'ita?" Cikin sauri Gwaggo Suwaiba tace "Bakomai Yaya
Sani. Zamu zauna tareda Rukayya harta samu sauki Insha Allah" Kawu Sani yace "to
shikenan. ita Babaan ma zata zauna kenan?" Yakarashe maganar ayayinda yake kallon
Gogode.
Gogode tace "munanan ÆŠana karka damu" duban wristwatch É—in hannunsa Kawu Sani yayi
sannan yace "Toh mu zamu koma can inda ake zaman makokin se dare zamu dawo anma
inma akwai matsala ga Fahad nan zaikawo lunch seku sanar dashi shizai kirani
yafadamin Kokuma inya koma zai sanar dani" Gwaggo Suwaiba tace "mungode Yaya. Allah
yasaka da alkhairi" Kawu Sani yace "bakomai" sannan yajuya suka fice tareda Fahad
É—in harsuka isa jikin motar Fahad É—in dayake dashi sukazo asibitin. Mazaunin driver
Fahad yashiga ayayinda Kawu Sani yashiga gidan gaba.
Tada motar Fahad yayi sukabar harabar asibitin ayayinda Fahad yaÉ—auki hanyar gidan
Mallam Umar É—in. Kawu sani yadubi Fahad yace "kunyi waya da Salim ne?" Fahad yace
"munyi jiya" Kawu Sani yace "kaika faÉ—a masa labarin mutuwar kenan?" cikin sauri
Fahad yace "I did not nasan yana jarabawa ai" Kawu Sani yace "I wonder who told him
tunda mahaifiyarsa tace ba'ita baceba ba. gashi yanacan yatada hankalin shi seyazo
gida nikuma nahanashi nace yabari se next week tunda lokacin zaigama exams É—inshi
gaba É—aya dan inyazoma mezaiyi inbanda ta'aziya tunda anriga anyi jana'iza" Fahad
jinjina kanshi yayi sannan yace "Allah yakaimu wani satin" Kawu Sani yace "Amin"
ahaka harsuka karasa wurin zaman makokin inda suka samu su Kawu Adamu zazzaune da
mutanen GiyaÉ—e da Babban buli sekuma jama'ar dake zuwa gaisuwa akai akai suna
tafiya.
***
Karfe bakwai da Yan mintuna na dare na buÉ—e idanuna inabin su Gogode dake cin
abinci akan tabarma da idanuna wanda suɗin basuma lurada cewa nafarka ba. Ƙoƙarin
tashi nashiga yi anma jin yanda kaina kemin wani irin sarawa yasani dole nakoma
nakwanta. tuno cewa da akayi Baba ya rasu nayi dakuma abubuwan dasuka faru dani
atsakanin kwanakinnan nadingayi hakanan bansan sanda hawaye suka fara bin kuncina
ba hakanan bandamu dasa hannu in gogesu ba,haka hawaye na yadinga jika katifar
danake kwance akai. I just can't believe cewa Baba is no more,gani nakeyi kamar
mafarki nakeyi,gani nakeyi kamar wasa akeyimin ba dagaske baneba,gani nakeyi kamar
Baba zezo yadubani akan gadon asibitin nan yacemin "I'm perfectly fine my Dearest
Daughter, I'm still alive kitashi mutafi gida". Juyakaina nayi daniyar kiran Gwaggo
Suwaiba da Gogode intambayesu shin dagaske ne Baba yamutu ko wasa akeyimin,kokuma
dogon suma yayi kamar yanda nayita suma tsakanin jiya dayau anma sede tunma kafin
na buÉ—i bakina nayi magana naji anbude kofar É—akin wanda wannan dalilin yasani
saurin maida idanuna kan kofar with so much expectations and it turns out that Kawu
Sani,Kawu idrissa,Kawu Adamu da Kawu Abdullahi ne sukashigo É—akin sekuma Yaya Fahad
daya shigo daga karshe hannunsa riƙe da basket ɗin abinci. Ajiye basket ɗin
hannunsa yayi kusa dasu Gogode yana gaidasu ayayinda suka amsashi Gwaggo Suwaiba na
faÉ—in "harda wahalan kawo wani abincin kuma?. Mu ko na ranan ma bamu gama cinye
shiba" murmushi kawai yayi bece komaiba ayayinda yakoma kusa da kofar É—akin
yajingina da jikin bango yayi folding hannunsa yana kallon floor É—in É—akin wanda
nalura hakan na É—aya daga cikin dabi'unsa. maida kallona nayi kansu Kawu idrissa
dake tsaye kaina suna tambayana yajiki hakanan harlokacin hawaye bebar bin kuncina
ba. Kawu Sani ne yasake tambayana yace "Rukayya yajikin naki? akwai inda ke miki
ciwone har yanzu?" memakon in amsa masa tambayarsa senace "Kawu dan Allah dagaske
ne Baba ya rasu?" Kawu Sani cikeda tausayina yajinjina min kai alamar eh wannan
Karan I couldn't stop crying my heart out loud and now I finally believe cewa
narasa Baba har abada,nazama marainiya babu uwa babu uba. nazama abun
tausayi,nazama baiwar Allah. Acikinsu babu wanda yayi yunkurin hanani kukan
danakeyi É—in har sautin muryana yazamanto baya fita sosai,nakoma ina hawaye kawai.
Gwaggo Suwaiba ce tazubamin abinci a plate sannan takaraso inda nake kwance Ina
matsar kwallah cikeda tausayina tace "kiyi hakuri kidaina kukan hakanan,kidaure
kitashi kici abinci kinji?" jijjigamata kai nayi alamar "A'a" nibazan ciba dankuwa
kwata kwata banajin zan iya cin abinci koda kuwa inajin yunwarne. Duk yanda taso
tasani inci abincin ki nayi dole sede ta hakura daga karshe ta kyaleni.
Se kusan tara da rabi sannan su Kawu Sani suka bar asibitin bayan likita yazo
yadubani,yace yanzu normal nake babukomai anma zankara kwana biyu a asibiti for
observation kafin su sallameni.
Kwana biyu nakara a asibiti hakanan banida aiki se kuka,abinci kuwa se antakuramin
sosai nike cinsa,duk na rame na kwanjame nayi wani iri tsabar damuwar dana saka ma
raina. Yau likita yazo yasake duba ni and immediately ya bamu sallama dukda kuwa
yayi complain akan rashin cin abincina,yace indage inyi hakuri Ina cin abinci inba
so nike insake kwanciyar asibitiba. Nidai gyaÉ—a mai kai kawai nayi bawai dan
maganar tasa tashigeni baneba. Awannan lokacin gani nakeyi kamar everything in my
life has stopped,farin ciki na,walwalata,burikana dakuma lafiyata duk gani nayi
basuda wani amfani ayanzu tunda banida mai supporting É—ina,banida mai bani kwarin
gwiwar cewa nidin ma mutum ce like everyone. Bayan Yaya Fahad yagama cike duk wasu
formalities muka tattara kayan mu muka shiga motar sa yawuce damu can gidanmu. Kawu
Sani besamu zuwa ba sabida yanada meeting É—inda zaiyi attending shiyasa yaturo Yaya
Fahad shikaÉ—ai.
Sanda muka isa gidan babu mutane sosai kamar ranar da akayi rasuwan,dangin Baba
matane kaÉ—ai suka rage se masu shigowa ta'aziya jefi jefi.
Ana gobe sadakan bakwai naji su Inna Lami(cousin É—in Baba) suna hirar da anyi
sadakan bakwai gobe jibi zasu koma GiyaÉ—e and I started wondering ni a Ina
zanzauna. dawa zanyi rayuwa? badai tafiya zasuyi subarni a tangamemen gidan nan
inyi rayuwa nikaÉ—ai ba?lokaci guda hankalina yatashi,kewan Baba yadawo min sabon
fil sekawai nasaki kuka ma sauti.
Dukansu juyowa sukayi suna kallona cikeda mamaki dankuwa duk kukana sede inyita
hawaye ko in kwanta inyi tagumi ina binsu da idanu,sekuma in baƙi sunzo sunmin
ta'aziyan rashin Baba toh jazaman ne senayi kuka anma kukan danakeyi ayanzu tabbas
sukansu sunsan ba Lafiya ba. Cikeda damuwa Inna Lami ta matso inda nake tana
tambayar dalilin kukan nawa,buÉ—an bakina secewa nayi "Nima zan biki GiyaÉ—en"
kallona suka tsayayi dan gaba É—ayansu sungane maganar danakeyi É—in. Se jikinsu yayi
sanyi kowa yakasa cemin komai harsaida Gwaggo Suwaiba tazo ta tarar Ina kuka
tashiga tambayar maiya faru shine suka faÉ—a mata. Zuwa tayi tazauna agefena Itama
sannan tasa hannu tashiga goge min hawayena cikin sigar lallashi tace "toh yanzu
wayace zebarki anan dama Rukayya? dole daman su Yaya suyi shawarar inda zaki zauna
sabida haka kidaina tada hankalin ki kinji? dankin rasa mahaifi bahakan yana nufin
zakiyi maraicin iyaye bane ba,ni mahaifiyace agareki,su Yaya idrissa duka mahaifa
ne agareki. Yanda Yaya Umar zai yakula dake yake miki komai muma insha Allahu bazai
gagaremu ba"
Gwaggo Suwaiba nakaiwa aya nace "Nidai Gwaggo Suwaiba ke ko Gogode nakeso inbi
muzauna tare" murmushi Gwaggo Suwaiba tayi sannan tajani zuwa jikinta ta rungumeni
tana faÉ—in "Toh Rukayyana duk inda Kika zaba nan zakijeki bari Kawu idrissa suzo
anjima semuyi magana dasu muji mezasu ce" murmushi nayi inakara shigewa jikinta
wanda inada tabbacin it's the first time danayi murmushi tun bayan rasuwar Baba.
Adaren ranar su Kawu Idrissa basu zoba se washegari daya kasance sadakan bakwai.
Anyiyyi sadaka kuma mutane da dama sunzo su sekuma saukan Alqur'ani da yaransa masu
tayasa aikin saida kayan miya sukayi. Se dare Gwaggo Suwaiba dasu Kawu idrissa suka
samu zama inda ananne tasanar dasu cewa nanuna inason bin É—aya daga cikinsu itada
Gogode. har Gwaggo Suwaiba tagama bayani idanunsu Kawu Idrissa na kaina sannan Kawu
idrissa yaÉ—an numfasa kafin yace "yanzu ke wakikeson kibi acikin su biyun?" sena
shiga kallon Gogode da Gwaggo Suwaiba lokaci guda nikaÉ—ai Ina contemplating. Nasan
dukansu love me equally but still I've to choose one tunda nini É—aya ce kuma babu
yanda zanyi inraba kaina biyu danhaka senafara tunanin yanayin gidajensu da'inda
zaifimin daÉ—in zama and I then realized I prefer staying with Gwaggo Suwaiba sabida
cikin Æ´aÆ´anta akwai sa'anni na sannan munsaba sosai,wanka,cin abinci,wasa da yawo
duk tare mukeyi a GiyaÉ—e and GiyaÉ—e yafi Babban buli akomaima nesa ba kusaba dan
haka nadubi Kawu Idrissa nace "zanbi Gwaggo Suwaiba inyaso lokacin hutu se
inazuwama Gogode hutu" jinjinakai Kawu idrissa da Kawu Adamu sukayi ayayinda Kawu
sani ke kallon mu duka harlokacin bece komaiba harsaida nayi shiru.
Sannan yadubi Kawu idrissa yace "ni aganina Yaya be kamata ace Rukayya takoma
GiyaÉ—e ko wani gu dazama ba bayan gamunan munanan" Kawu idrissa take annurin
fuskarsa ta É—auke jin abunda Kawu Sanin yace sannan yace "Duk inda Rukayya tace
zata zauna nan zata tafi. mu bamuda wani burin daya wuce muganta cikin farin ciki
and if following Suwaiba will make her happy so be it" Kawu Sani yace "we can't
follow what she wants as of now tunda she's still a child. Rukayya tasaba da
rayuwar birni akan wani dalili za'ace takoma GiyaÉ—e bayan mu munanan. Sannan magana
tagaba yakamata muduba cewa tana makaranta and the best education she can gate is
here in Bauchi shiyasa nake ganin yakamata a ajiye batun zuwanta GiyaÉ—e. Tazauna
anan tareda mu cikin sauran Ƴan uwanta alabarshi in lokacin hutu yayi setana zuwa
GiyaÉ—e da Babban bulin hutu kamar yanda takeyi da. but I don't support the idea of
she going to GiyaÉ—e" Kawu Adamu dake gefe yace "I'm with you Yaya Sani. da'ace Yaya
Umar bayida dangi acikin garinnan ne wanna. Dole daman GiyaÉ—en zata koma anma tunda
gamu kuma bawai munrasa muhalli baneba,bakuma zamu kasa ciyar da'ita baneba komuma
zamu kasa kula da responsibilities É—inba kawai tazauna damu anan.
*Littafin Qadr na kudi ne.duk Maison shiga paid group should talk to me via this
number 08147722806*
*Page Twenty Two*
Kawu idrissa yace "kunedai kuka É—auki wannan maganar da wata manufa daban. dannidai
aganina danan garin da GiyaÉ—e duk É—ayane anma if you two really insists on this's
the right thing to do,then so be it. Shikenan tazauna anan É—in"
Kawu Sani yace "Yauwa. hakan dai yafikam" Gwaggo Suwaiba datunda Kawu Sani yayi
magana take lura da yanda yanayina yacanza lokaci guda tace "toh kodai zantafi
da'ita taÉ—an zauna acan nawani lokacine seta dawo?" Kawu Sani kai tsaye yace "A'a
Suwaiba. Babu amfanin yin hakan dan kuwa sa'anninta duk sunkoma makaranta,zango
yafara yin nisa ayayinda itako fara zuwa batayiba. Yanzu abunda yakamata muyi shine
mumaida hankali akan maganar karatunta inyaso in hutu yayi setazo GiyaÉ—en tayi muku
hutu"
Gwaggo Suwaiba da dama sabida ganin yanayina ne yasata kawo wannan suggestion É—in
tace "toshikenan. Allah ubangiji yasa hakan shiyafi alkhairi" sannan tadubeni da
dab nikeda fashewa da kuka tace "Toh Rukayya kindaiji abunda Kawunanki sukace,kiyi
hakuri kiyi zaman ki anan. danan dacan din duk É—ayane babu wani banbanci hakanan
yanda nike kanwar Yaya Umar haka suke Yayunsa sannan inada tabbacin irin kulawar
dazan baki a GiyaÉ—e suma zasu kwatanta insha Allahu" ta dafa kafadana cikin sigar
lallashi tace "ki kwantar da hankalinki. kimaida hankalinki akan karatunki na
Arabia da boko dankuwa shine jigo na rayuwar kowa azamanin mu na yanzu. Maganar
Yaya Umar kuma,yariga yatafi kuma dukkannin munnan tafiyar zamuyi,kowa lokacinsa
yake jira sannan babu gatan dazaki nuna masa daya wuce kiyi masa addu'a aduk
lokacin dakika tuna dashi dakuma duk lokacin dakike sallah"
Tunda Gwaggo Suwaiba tafara magana nakasa resisting hawayena duk da kuwa naso in
riƙe kukan nawa anma abun yaci tura. Yes mutuwar Baba is still hunting me anma
batun inzauna tareda iyalan su Kawu shiyafi tayar min da hankali ayanzu. Tunda
nasamu nabaro wannan gidan shekarun baya dasuka wuce ban taɓa tunanin ko amafarki
zankoma wannan gidan ba anma segashi rana a tsaka ana sanar dani dasu É—in zanzauna,
incigaba da rayuwa na tare dasu gashi kaf cikinsu babu gwara,babu gidan wanda zanje
ince zansamu sassauci daga kan Ƴaƴansu har Matayensu bare har inyi addu'ar Allah
yasa akaini gidan wane dan inji daÉ—i. Duka iyalansu sun tsaneni,baswa sona,baswa
kuma kaunar ganina cikin farin ciki. nikaina wani sa'in nakanyi mamakin mena tare
musu a rayuwa dankuwa aganina hujjojinsu are not enough. Dan Baba yana nuna yana
son Mama agaban kowa,yana kuma yimata duk abunda zaisata farin ciki bekamata ace
sun tsaneta ba. Mijinta ne banasuba, kuÉ—inshi ne bana wasu ba kuma shiyaga zai iya
ba'ita tasaka shiba and moreover bashi yahana nasu mazajen suyi musu ba. ra'ayin
kansu sukebi kuma kowa da irin tasa zuciyar hakanan kowa da irin nasa plans É—in
arayuwa.
Haryau Ina mamakin wannan al'amari,Ina mamakin miyasa tsanar da akayiwa Uwata
yadawo kaina dankawai ubana yana sona nima,dankawai inacikin jin dadi da walwala
fiye dasu se aji haushina ba wani dalili bayan shi? kukan danakeyi gaba É—aya seyasa
jikinsu Kawu Sani yayi sanyi dan haka cikin raunanniyar murya Kawu Adamu yace
"Rukayya kidaina Kuka hakanan. shawarar damuka yanke shine mafi a'ala
agareki,amanar ki da mahaifinki yabar mana mukeson riƙe wa kuma kobaibar amanarki a
hannunmu ba mu É—in masu rike kine insha Allahu dan tamkar iyaye muke agareki sannan
danmun hanaki binsu Suwaiba GiyaÉ—e bahakan yana nufin zamu hanaki zuwa gidan wanda
kikeso acikin muba. Kizaɓa duk inda kikeso,inma gidan Yaya idrissa ne dukda
compound ɗaya mukedashi,inma gidana ne,inma kuma gidan Yaya Sani ne kizaɓa,duk inda
kikadai ga zaifi miki daÉ—in zama nan za'a kaiki kinji?"
Cikin gunjin kuka na gyaÉ—a mishi kai sannan nace "ko'ina aka kaini ma duk É—ayane"
dankuwa bana tunanin zan iya zaɓan gidan ɗaya acikin su ukun dan babu gwara gaba
É—ayansu,nidai kawai nasan my life will surely change. From happiness to
sadness,from meaningful to meaningfulness indai har a karkashin su dakuma iyalansu
zanzauna.
Har Kawu Sani seda yatambayeni inda zanzauna anma naqi faÉ—a nace duk inda akace
inje duk É—ayane agurina dole daga karshe sukayi deciding inzauna gidan Kawu idrissa
tunda shine Babba. Sukayi kuma akan gobe dasafe zezo ya É—aukeni mutafi insu Gwaggo
Suwaiba zasu wuce GiyaÉ—e. Shidai kawai "Toh" yace musu dukda kuwa fuskarshi ta nuna
kamar baiso hakan ba amma babu wanda yayi magana akan hakan,se sukayi tunanin dan
ba'abi opinion É—inshi bane ba. Adaren ranar nasha kukana harna gode ma Allah ina
tunanin gaba É—aya ahalarin gidan Kawu idrissa dakuma halayensu,da irin zaman
dazanyi acan ahaka har baccin wahala yayi awun gaba dani. Gwaggo Suwaiba da Gogode
ne suka shiryamin kayana tsaf cikin akwati adaren ranar wanda seda na tashi
washegari na gani.
***
LamiÉ—o tunda yakoma Gombe besamu courage É—in tunkarar Umma da maganar komawa duba
mahaifin Rukayya ba gashi yau har alhamis,meaning jibi ne tafiyar. ganin yakasa
samun mafita yasashi deciding yasamu Hafiz suyi shawara. Ana idar da sallar
maghriba kuwa gidansu Hafiz yawuce tunda Allah baisa sun haÉ—u a masallaci ba sannan
yanada tabbatacin bazai sameshi a majalisa ba dan kuwa dayayi sallar maghrib
yawanci yakan koma gida yaci abinci kafin yawuce majalisa in anyi sallar isha'i. a
tsakar gidansu yasamesu shida Ummarsa da kanninsa guda uku. har ƙasa Lamiɗo ya
tsuguna yagaida Umman inda kannen Hafiz Rabi'a,Amina da Musa ma suka gaidashi da
amsa.
Hafiz dake zaune kan tabarma yanata baza loma yace "Mutumina Bismillah kazo muci
tuwo mana" LamiÉ—o shafa sumar kansa yashigayi yana murmushi sannan yace "ni É—innan
zanci abinci kuwa. I'm full alhamdulillah"
Umman Hafiz tace "ka koshi kamar yaya LamiÉ—o? ninasan ko gida baka koma ba daga
masallaci kayo nan taya zaka ce ka koshi kuma?. Kazo kajona shi kuci abinci Dan
Allah" LamiÉ—o yace "Allah naqoshi Umma" cikin sauri Hafiz yace "Bawani kaidai
fulaku kakeson kayi kuma wallahi indai bakazo munci abincinnan ba Umma ce zata zama
shaidana,bazan sake cin tuwo agidan kuba nima. haba sekace mu É—in mayune? ni inje
gidanku in takakkare inci abinci freely kaikuma kace bazaka ci na gidan mu ba
despite you being hungry. toh baka isaba wallahi" Hafiz yakarashe maganar ayayinda
yatashi yaÉ—auki karamar tabarmar dayake zaune akai yaje ya shimfida kusa da LamiÉ—o
yana faÉ—in "kahau ka zauna ba in É—auko mana abincin muci" ayayinda yakoma yaÉ—auko
kwanon tuwo da miyar kubewar da kamshinta setashi yakeyi yakawo musu ya ajiye a
tsakiyar tabarmar yazauna.
LamiÉ—o daman yunwar yakeji, tsantsan fulaku ce kawai kamar yanda Hafiz É—in yafaÉ—a
danhaka ganin Hafiz É—in ya takura kuma Umman ma ta matsa yasashi zuwa ya wanke
hannunshi sannan yazo yajona Hafiz É—in suka shiga cin abincin yanajin yanda Hafiz
da kannensa keta hirarrakinsu gwanin ban sha'awa harsuka gama cinye nagabansu.
Hafiz yace zaikaro ma Lamiɗo amma fir yaƙi dukda miyar tamasa daɗi,dazai samu
zaikara ɗin anma fulaku bazai barshi ba dole Hafiz ɗinma ya haƙura ya kyale shi.
Jin anata kiraye kirayen sallar isha'i acikin Unguwa yasasu yima Umman Hafiz É—in
sallama sannan suka fice daga gidan. suna fita Hafiz yace "Meye matsalarka LamiÉ—o?
dan nasan haka kawai bazaka zo gidanmu a irin wannan lokacin ba" LamiÉ—o ya tsuke
fuska sannan yace "mekake nufi?" Hafiz yace "nasan dai haka kawai bazakazo gidanmu
bayan sallar maghriba ba tunda dayanman nan muka rabu" LamiÉ—o yace "Kasani ko Umma
nazo gaidawa?" Hafiz dariya yayi sannan yace "aibaka zuwa gaidata se in bana gida
sede inna dawo insamu labarin kazo,wataran ma ina baroni kakeyi a majalisa katafi
gaisar da mahaifiyata nibanma saniba amma yaufa nasan kasan ina gida shiyasa kajeka
and that clearly means nemana kajeyi" LamiÉ—o yace "kaima kanayin hakan ai" Hafiz
yace "A'a kam. Mostly ni tare muke zuwa dakai" LamiÉ—o yace "Naji nidai yanzu muje
muyi sallah inmun fito daga masallaci mwayi maganan" Hafiz yayi dariya sannan yace
"nasani ai. Dole akwai wata akasa"
Suna fitowa daga masallaci LamiÉ—o yadubi Hafiz sannan yace "Hafiz I need your help.
Wallahi nina rasa ta'ina ma zanfara tunkarar Umma da batun komawa Bauchi,gashi kuma
nayi ma Yar birni alkawarin komawa ranar asabar. I don't want her to wait for
me,banason inkarya mata alkawari" kallon LamiÉ—o Hafiz yatsayayi shima,somewhat out
of option kafin yace "Kaima meyasa kamata alkwari bayan kasan it'll be very hard
Umma tabarka kakoma?" cikeda damuwa LamiÉ—o yace "Because I don't want to hurt
her,kobakaji sanda take rokon indawo very soon ba?" Hafiz yace "Naji. Anma ai babu
amfanin kabata false hope bayan kasan ba lallai kasamu kayi fulfulling ba" LamiÉ—o
yakalli cikin idanun Hafiz sannan yace "I'll fulfill it. I was very sure zancika
alkawarin dana dauka shiyasa nace mata zanjeni insha Allah" hararanshi Hafiz yayi
Jin abunda yafaÉ—a sannan yace "toh shine kuma yanzu zakawani zo nika dameni da
neman shawara? if you really have this confidence then it means you've your plan
already" ajiyar zuciya LamiÉ—o yasauke sannan yace "banida wata plan Hafiz. Abu É—aya
nasani,i'll have to go to Bauchi on Saturday no matter what. matsalar dayane
banason intafi ban karbi permission É—in Umma ba shiyasa kaga na tada hankalina"
Hafiz yace "Toh ka gwada tambayar natane?" Jijjiga kai LamiÉ—o yayi alamar a'a
sannan yace "nace maka banga fuskar tambayarba,dankuwa tunranar dana dawo datamin
tambayar miyasa bankarbi number Baba ba dakuma cema Salma danayi innakoma zankarba
ne yasa nagane ba lallai tayi na'am dazancen ba" Hafiz yace "nidai aganina kozata
maka faÉ—an mistake É—inda kayi naqin karban number she'll let you go there,ai
lalurace zesa kajeka bawai hakananba" LamiÉ—o cikeda hope yace "Are sure she'll let
me go?" Hafiz yace "I'm not sure but akwai probability É—in tabarkan. Just try and
ask semuji mezata ce" gyaÉ—a kai LamiÉ—o yayi ahankali sannan yakama hannun Hafiz
yace "muje gidan tare yanzu se intambayeta muji mezata ce" Hafiz bai musamaiba,haka
suka kama hanya suka nufi masarautar.
Basma da Jidda ne kaÉ—ai kezaune a parlourn suna kallo,sallama LamiÉ—o da Hafiz
sukayi ayayinda jidda ta amsa sannan suka karaso cikin parlourn su Jidda suka
gaisheda Hafiz sannan LamiÉ—o yashiga tambayarsu inda Umma take.
Basma ne tace "yanzu tashiga É—aki zatayi sallar isha'i" LamiÉ—o yace "kuÉ—in kunyine
dakuka zauna kuna kallo?" Jidda tace "Eh munyi Hamma LamiÉ—o. ya akayi bakadawo
munci abinci tare ba yau?" LamiÉ—o yace "naci agidansu Hafiz" ayayinda yasamu guri
yazauna yanacema Hafiz É—inma yazauna. Sunfi mintuna ashirin zaune parlourn suna
kallo ayayinda suke ɗan taɓa hira jefi jefi kafin Umman tafito. Hafiz naganinta
yatashi yazauna cikin sauri kafin cikeda ladabi yace "Ina wuni Umma?" Umma murmushi
tasaki tana faÉ—in "lafiya Lau Hafiz. Ya Umman ka?" Hafiz yace "lafiyanta kalau
Umma" Umma zama tayi kan kafet É—in parlourn tana faÉ—in "Toh madallah" sannan ta
karada "kunzo nikuma nashigayin sallah" Hafiz yace "bakomai Umma" shiru parlourn
yaÉ—auka nawurin mintuna biyar,inbanda karan mutanen dake cikin TVn babu abun
kakeji. Jin shirun yayi yawane yasa Umma tadubi Jidda dake kwance kan É—aya daga
cikin tum tum É—in parlourn tayi pillow dashi sannan tace "Jidda tashi kizubo masu
Hafiz abinci" Hafiz da gabadaya hankalinshi nakan Tv Jin abunda Umman tace yasa
cikin sauri yajuyo yana kallon Umman sannan yace "daga gida muke Umma,acan mukaci
abinci tare kafin muka taho nan" Umma tace "toshikenan. Aina É—auka daga majalisa
kuke" Hafiz yace "A'a bayan munci abinci a gida masallaci mukawuce daganan kuma
mukayo nan" Umma tace "Allah sarki" LamiÉ—o shafa sumar kansa yashigayi nervously
sannan yadubi Umma yace "Umma daman najecan gidansu nasameshi da maganar komawan mu
Bauchi ne" Umma da tunda tagansu tareda Hafiz yanata noqe noqe daman tasan da
biyune wannan zuwar tasu segashi yanzu kuma ya ambaci sunan Bauchi wanda hakan yasa
tagama daga komai anma setayi kamar bata ganenba tace "Bauchi kuma? mezakujeyi a
Bauchi?" LamiÉ—o ahankali yace "dubo mahaifin Nana. kinsan nacemiki ankwantar dashi
a asibiti,jikin nashi Babu daÉ—i" Umma tace "duba marar lafiyar kuma in akaje sau
É—aya bai isaba se ansake zuwa? Abu ba'a cikin gari É—aya ba?babu dangin iya barena
Baba?" LamiÉ—o kamar zaiyi kuka yace "Umma marar lafiya marar lafiya ne kuma aganina
dankaje ka duba mutum kasake komawa kasake dubashi akaro na biyu ba laifi banebaba"
Umma ta tsuke fuska sannan tace "ni ai daman ba cewa nayi akwai laifi acikiba
anmase mutum yaduba irin halin rayuwar dayake ciki yayiwa kansa adalci. dakasamu
dama kaje sau É—ayan dasai ka karbi number wayarsu in lallai lallai yazama dole seka
sake jin ya jikin nasa yake inyaso sekana kiransu a waya kuma inma baka da katin
wayane dandai naira dari dari biyu kasan bazan hanaka ba kasayi kati ka kirasu
anma komawa Bauchi bana tunanin zan iya sake baka wannan izinin tunda kai kayi wasa
da damarka bawani ba" ajiyar zuciya LamiÉ—o yasauke sannan cikin muryar me nuna
tsananin bukatar samun izininta yace "Dan Allah Umma kibarni injeni for the last
time. I promise you bazan sake yin wannan kuskuren ba,I promise you zan karbi
number tasa indinga ji daga garesu from here at home. Just give me this one last
chance. Pleaseeee!" Hafiz ma yakarada "Umma kiyi hakuri kiyi mishi wannan
uzurin,tunda dabakinshi yace this will be the last time dazaijeshi. Kuma insha
Allah bazai manta karban number ba kamar yanda yayi miki alkawari" Umma tace "Hmmmm
sekace bansan waye LamiÉ—o ba. yanda yazo yanamin magiya yanzu indai nabarshi yatafi
to gobe ma hakan zezo yasake yimin" cikin sauri LamiÉ—o yace "Allah bazan sake
tambayarkiba Umma" sannan yashiga nunasu Basma dake zaune parlourn yace "inbaki
yarda dani bama they should be our witness. nayi alkawari daga wannan karan bazan
sake rokon ki da maganar kibani izini inje Bauchi ba" sannan yadubi Hafiz yace
"kaima Hafiz kazama É—aya daga cikin shaidunmu" gyaÉ—a kai Hafiz yayi yana murmushi.
Umma tace "Naji kuma koda shaidu kobabu shaidu inaso wannan yazama rana ta karshe
dazaka sake zuwamin da batun zakaje Bauchi duba wannan yarinyar. danko kayima
abanza,bazan sake baka wannan damarba so inkaga dama kayi using damar taka yanda
yadace inkuma kaga dama kasakeyin kuskuren dakayi abaya" LamiÉ—o besan sanda yama
Umma wani irin wawan runguma ba hakanan cikeda farin ciki yayi kissing cheeks É—inta
yana faÉ—in "Thank you. Thank you. thank you Ummana" ture shi Umma tayi daga
jikinta tana faÉ—in "kamadaina murna. Inafatan ka tanadi kuÉ—in tafiyartaka dankuwa
nidai bazan sake baka ko kwandalaba" turuss LamiÉ—o yayi ayayinda yatsaya yana
kallon Umman,yanayin fuskarsa tacanza daga murna zuwa na mamaki lokaci guda sannan
yace "Umma dagaske kikeyi wai?" Hararanshi Umma tayi sannan tace "na taɓa yimaka
wasa ne daman? tunda ka matsu da zance zuwan kam ai na tabbatar ka tanadi kuÉ—in
tafiya" cikin sauri LamiÉ—o yace "wallahi banida shi Umma. Nida bana aikin komai
inazan samu kuÉ—i?" Umma cikeda rashin damuwa tace "Nima banidashi seka fasa zuwan
kawai" LamiÉ—o becema Umma komaiba sema tashi dayayi yafice aparlourn jiki sanyaye.
Tunanin shi ayanzu baiwuce a ina zaisamu kuÉ—in Transport É—in zuwa Bauchi ba dankuwa
har ranshi ya yarda da maganar Umman datace batada shi,toh tabbas batada shi É—inne
tunda tun tasowarsa bata taɓa gazawa gurin cika masa burinsa akan abubuwan dazai
bukata ba kozaiso indai yaga batayimasa ba toh tabbas batadashine and she'll call
him and tell him cewa batada shiÉ—inne shiyasa batayi mishi ba inda shima kuma
baitaba takura mata ba tunda yasan tana iya bakin ƙoƙarin ta sede koma ya yakeson
wannan abun haka zai haƙura harsai zuwa lokacin data samu tayi mishi,inma kuma abun
is not that important se abar maganarshi kawai,yawuce, Allah baiyi zaiyi abun
awannan lokacin bu. But today's case is different,baya tunanin zai iya fasa zuwa
Bauchi ranar asabar dan bashida kuÉ—i. Infact koda Umman tace masa batada kuÉ—i baiji
plan É—inshi yacanza ko kadanba sema tunanin yanda zaisamo kuÉ—i before
Saturday,yanda zaisamu ya'isa ga Rukayya ranar asabar.
Hafiz naganin LamiÉ—o yafita shima yama Umma sallama sannan yabi bayan abokin nasa.
Binsu da idanu Umma tayi da idanu. dagangan tacema LamiÉ—o batada kuÉ—in bashi dukda
kuwa tanadashi É—in. Tabbas batada tabbacin ko LamiÉ—o zaifasa zuwa Bauchi ko bazai
fasa ba dankuwa shiÉ—in mutum ne da inyasa ma ranshi abu saiyayi toh seyayi and on
the other hand tayarda da irin tarbiyar datama LamiÉ—o,tasan bazai taba bi tahanyar
dabai daceba yace zainemi kuÉ—i don kawai yaje ganin wata wai ita Rukayya itadai
kawai tasan kilan hanashi kuÉ—in datayi might make him realize cewa,yakamata yafara
neman nakanshi shima,it's high time yafara rage mata responsibilities É—in kanta as
her elder Son,Koda kuwa betaimaka wurin rage expenses É—inta dana kannensa ba
atleast he should be doing something for himself as of this age. tasan ita taÉ—aura
shi akan tafarkin yayi Boko yazama abun kansa,itace bata É—ora shi akan hanyar
sana'ar ba wanda duk a tunaninta zeyi yagama bokon yasamu aiki directly ne,kuma
indan naÉ—an wannan shekarun ne she's no problem with taking care of him harna
wannan lokacin amma se plans sukazo suka canza,komai yacanza,yanayin karatun nashi
yazo da tangarda wanda ayanzu yana neman shekara na shida a jami'a kaÉ—ai banda
secondary school dayayi abaya. Bazatace baya iya ƙoƙarin shiba tunda tana ganin
efforts É—insa,tana kuma appreciating tareda yimasa addu'an samun nasara but atleast
tunda ga yanda abubuwa sukazo musu,gakuma shekarunsa sunja yakamata ace shima yana
É—an taimakawa tahanyar rage mata wani nauyin,atunanin ko a hutunnan bekamata
yanazaman banza hakanan ba,kamata yayi yanemi abunyi cikin sa'o'inshi yanasamun dan
taro da kabonsa tunda tana ganin samari dadama acikin unguwar tasu sunayin hakan
despite the fact sunayin bokon at thesame time. wasu suna acaba,wasu suna aikin
napep,wasu suna aiki a shagunan ogoginsu a kasuwa inda at end of the day suke samun
É—an abinda ba'a rasaba,wasu É—inki sukeyi wanda É—aya nuna yanaso datayi supporting
É—inshi. Wasu suna koyarwa a irin islamiyar unguwarnan kuma ana biyansu dede
gwargwado dadai sauransu. Yes tasan itace bata taɓa nunama Lamiɗo yayi hakanba but
atleast shima yakamata ace yasan yakamata anma tunda shi baiyi hakan ba she'll
start by purnishing him this way and may be he'll realize it himself inma kuma
baigane É—inba itada kanta zata zaunar dashi tanuna masa abunda yakamata. Atunaninta
koda wasa LamiÉ—o bazaije yanemi kuÉ—i tahanyar da bata dace ba sabida tayarda da
irin tarbiyar datayi mashi dukda kuwa irin nacin shi akan abunda yasaka agaba
shiyasa ma tahanashi kuÉ—in,tayanke wannan shawarar.
....
Awaje Hafiz yasamu LamiÉ—o dayayi nisa cikin zurfin tunani.
Dafa kafaÉ—ansa yayi ahankali sannan yakira sunan LamiÉ—o yace "LamiÉ—o?" LamiÉ—o
É—agowa yayi ahankali yana kallon Hafiz É—in sannan ahankali yace "Na'am Hafiz" Hafiz
yace "Kai yanzu kanada kuɗin zuwa Bauchin ne?" Cije leɓe Lamiɗo yayi sannan yace
"Babu. wallahi banida ko kwandala Hafiz" ajiyar zuciya Hafiz yayi sannan yace "Nima
kuma kaga babu kuɗi agurina wallahi dasai in aramaka. Toh kai ka haƙura dazuwan
mana se Umma tasamu kuÉ—in kawai" cikin sauri LamiÉ—o yashiga girgiza kanshi sannan
yace "Noo. I've to go to Bauchi this Saturday no matter what. Kasan ni bana karya
alkwari specialy not akan Rukayya. She's very young to be waiting for me ace kuma
banyi appearing ba,I don't want to break her heart Hafiz!"
Hafiz É—an numfasawa yayi yana kallon abokin nashi sannan yace "toh yanzu menene
mafita?" LamiÉ—o yace "bansani ba Hafiz! nidai kawai damuwana Inganni a bauchi ranar
asabar É—innan in Allah yakaimu darai da lafiya which means I've to struggle kafin
jibin insamu kuÉ—in motan zuwa" Hafiz cikeda gajiya da rigimar LamiÉ—on yace "nidai
dakabi nawa daka hakura se Umma tasamu kuÉ—in tabaka sekajeka" hararanshi LamiÉ—o
yayi sannan yace "intazo tacanza ra'ayi tahana ni zuwa fah? this's my only
opportunity Hafiz sannan banason tafiyar tazo acikin satima bare har ta hanani
sabida zuwa Industrial training damuke zuwa yi. Nidai kawai kataimaka kadubamin a
bangaren ka kobaza'a rasa me kuÉ—i ya aramin ba" Hafiz yace "kaima kasan babu wanda
zan tambaya acikin abokanan mu kasamu dankuwa kowa complain É—in kudinnan yakeyi
kullum kanadai gani na recharge card ma gagarar jama'a takeyi bare har dubu biyu
sede in Umma zan tambaya maka" cikin sauri LamiÉ—o yace "Noo! Banda ita please"
danyasan definitely in Hafiz yatambaya É—in zata bayar. shi abunda bayaso wurin
mayar matane matsalar,tana iya ƙin karba kokuma yazo baisamu kuɗi dawuri ba yadinga
Jin kunyar zuwa gareta gwanda abokanansa suna iya kwasan Ƴan kallo atsakaninsu daga
baya kuma suzo su daidaita.
Hafiz Jin LamiÉ—o yace kada atambayi Ummarsa yasa shi cewa "toh nidai ita kaÉ—ai ne
daman zan iya tambaya maka kuma asamu" Jan hannun Hafiz LamiÉ—o yayi sannan yace
"muje majalisar mugwada tambayarsu ko Allah zaisa adace" Hafiz dukda he's 100% sure
baza'adacen ba anma seyace toh dankuwa bayason su tsaya suna musu shida LamiÉ—on.
Aikuwa Koda sukaje majalisar basu dacenba dankuwa dukwanda LamiÉ—on yatambaya amsa
É—aya ce yake samu "Babu" gaba É—aya seyaji dama bai tambaya É—inba dankuwa shi mutum
ne meson self respect É—insa koda acikin abokanaine barinma akan son abun mutum da
roko, yauÉ—in ma danyaga bayida Option ne and he's really in need of the money
shiyasa.
Haka yakoma gida cikeda tunanin a ina zai samu kuÉ—in tafiya Bauchi jibi,gaba É—aya
daren ranar kasa runtsawa yayi. haka yadinga saka da warwara,inya samo wannan
possibility É—in seya gano negativity É—in bin wannan hanyar dansamun kuÉ—in seyayi
cancelling É—inta hardai gari ya waye. shikanshi yarasa dalilin dayasa ya kwallafama
ransa cewa seyaje bauchin gobe and his only reason is yayi alkawari kuma yanason
yayi fulfulling É—in alkawarin to which har zuciyarshi yasan wannan bashine kaÉ—ai
daliliba inda daga karshe yakarada "kilan harda tausayi dakuma irin yanayin dayabar
jikin mahafin nata"
Koda yadawo daga masallacin sallar asubahi tunanin inda zaisamu kuÉ—in tafiya
yacigaba dayi inda daga karshedai yaga bashida wata mafita dazata ficeshi daya wuce
yafita yaje yanemi halaliyarsa tahanyar yin aikin hannu koda nayau ne kaÉ—ai. Toh
anma inya fitan ma a Ina zaiyi aikin hannun harya samu kuÉ—in? haka kawai dai bazai
yuyu yace zeyi aikin hannuba bayan bashida source É—in samun inda zaije yayi aikin
harya samu kuÉ—in. ma'ana dole se yasan wani dazai taimaka mai wurin samun inda
zaije yayi aikin hannun danhaka seya koma tunanin mutanen daya sani kuma suna aiki
acikin kasuwar Gombe kokuma sunada shaguna acan inda daga karshe classmate É—insa
*Abdulmalik* da mahaifinsa keda Babban shago acikin kasuwa yafaÉ—o mai arai. Yasan
balallai ne yace zeyi aiki a shagon mahaifin Abdulmalik ba dankuwa koyaje ba lallai
daga fara aiki ayau ace za'a sallameshi ba that's if yasamu É—inma kenan anma ai
tunda shi Abdulmalik É—in acikin kasuwan yake dole zaisan irin ayyukan dazakayi
aranar akuma biyaka aranar shiyasa yayi deciding yaje gunsa ya tambayeshi kawai.
Dukda gari haryanzu duku duku yake haka yatashi yashiga bathroom É—insa yayi wanka
yashirya sannan yafice agidan batareda yama kosu Umma sallama ba dan atunaninshi
kilan sunkoma bacci lokacin kafin dai gari yawaye atashi afara aikace aikace kuma.
Sanda yabar sashinshu shida da yan mintuna ne kuma gari yayi haske babu laifi dukda
kuwa ba'afara kai kawo sosai a cikin masarautar ba. Gate É—in fita daga masarautar
yanufa ayayinda duk inda yaga dogaraye sesun gaisa sannan yayi wucewarsa harya Isa
bakin gate É—in masarautar.
LamiÉ—o koda ya'isa bakin gate É—in masarautar seda yatsaya suka gaisa da dogarayen
dake gurin sannan yafice anma ko nisa baiyiba yaji É—aya daga cikin dogarayen na
tambayar sauran abokan aikinsa ko ansamu labarin barawon dayashigo masarautar ranar
da daddare. turus LamiÉ—o yayi yatsaya sannan yasake dawowa daf da kofan shiga
masarautar,yakai kunnensa dede jikin kofar yashiga sauraron hiran dasukeyi.
Hussaini jin silly tambayar da Zakari yamasu yasashi cewa "yanzu kai Zakari in
ansamu labarin barawon nan atunaninka bazaka sani baneba?" Hussaini yace "Zansani
mana amma dai kasan kwana biyunnan bananan naje can garinmu duba jikin innata
shiyasa banida labari" cikeda mamaki Hussaini yace "habaaa? Yaushe kaje garinku?
wallahi banma sani ba nikam" Sabi'u da Ibrahim dayanzu suka zama practicing sword
fighting se gumi sukeyi suka karaso inda Hussaini da zakarin suke zaune Ibrahim
yace "ai tafiyar zakari *Kaltungo* yakusan sati yanzu" Zakari yace "jiya satina
É—aya da tafiya kuma jiya nadawo da dare shiyasa bansamu nashigo masarautar ba seda
safennan" Hussaini yace "Allah sarki. Allah ubangiji yabata lafiya toh" zakari yace
"Amin" sannan yakarada "yanzu dai ba'asamu labarin Barawon ba kenan?" Sabi'u yace
"inafa. ba'asamuba kuma ran sarki da waziri bakaramin ɓaci yayi ba akan hakan. wai
yaza'ayi ace ankasa kama barawo É—aya duk dogaraye da mutanen dake cikin masarautar
nan" Ibrahim yace "abunkam akwai mamaki. Nikaina haryanzu Ina mamakin ta'ina yayi
escaping sannan nayi tsanmanin da Sarki yace zaibada kyautan dubu goma aduk wanda
yafiddo da barawon za'a samu wani yazo ya bayyanashi anma segashi har kwana uku da
yin alkawarin za'abada kyaunta shiru babu wnda yazo yace yasan barawon" Zakari yace
"ikon Allah. harda kyauta akace za'ayima wanda yafaÉ—i wanene barawon? Ina baisaci
komaiba?" Sabi'u yace "baisaci komaiba anma ai ya bangaje waziri yakuma rikita
jama'ar masarautar baki É—aya sabida haka nibanyi mamakiba dan ana nemanshi ruwa
ajallo harhaka" zakari yace "hakane Kuma. Allah yakyauta gaba kawai"
Duka suka amsa da Amin.
LamiÉ—o dahar lokacin yake jikin kofa yanajinsu yadaidaita tsayuwarshi dakyau yana
sauke wani irin wawan ajiyar zuciya and the thought of ance za'abada kyautar dubu
goma gaduk wanda ya faÉ—i waye barawon just make him smile feeling as if matsalar
shi na neman kuÉ—i is solved already,bama saiyaje kasuwa ya wahalarda kanshi ba
tunda ga hanyar sauki nan,inda zaisamu kuÉ—i abanza.
*Littafin Qadr na kudi ne. Dukmaison shiga paid group should talk to me privately
via this number 08147722806*
*Page Twenty Three*
First abunda yazo mishi arai shine ya zaiyi yasamu wannan kudin? dankuwa ko karen
hauka ne yacijeshi baya tunanin zaije yayi submitting kanshi dakanshi yace shine
yashigo gidan ranar da dare because inyayi hakan toh tabbas bazai samu dubu goman
ba Kuma Babu tantanma zai kirbu a hannun dogarayen masarautar bakidaya,inkuma baiyi
sa'a bama ace za'a sakashi a gidan yari. So dole wani alternative zainema,
alternative dinda yakeda tabbacin it'll not stop him from going to Bauchi gobe
dasafe but rather help him get the money he's been yearning for tun daren jiya.
Dabara É—aya ne yazo masa arai kuma yasan if he's very careful wurin aiwatar da
wannan dabarar it will surely help him achieve his goal. Anma fa tabbas kafin yayi
going through with his plan dole seya nemi taimakon wani danhaka take yayi deciding
yaje yasamu Hafiz su tattauna danyasan he's the only person that can help him dukda
kuwa shiÉ—in ma yana kokwanton kozaiyi masa abunda yakeso É—in ko bazaiyiba. Hanyar
gidansu Hafiz yanufa dukda kuwa har lokacin safiyane sosai,jama'a basu fara fitowa
daga gidajensu ba tukunnan se É—an tsirarrun mutane dake wulgawa da ba'a rasa ba.
Daman gidansu Hafiz ɗin babu katanga se Ƴar karamar kofar dazai sadaka da cikin
gidan danhaka LamiÉ—o na'isa gidan yazagaya tabayan windown Hafiz É—in sanin cewa
inyace zai bubbuga kofar tasu toh tabbas zetada mutanen gidan ne baki ɗaya. leƙa
É—akin Hafiz É—in yashigayi ta window inda ya hangoshi baje kan katifa yana sharara
bacci shida kaninshi Musa. sunan Hafiz É—in yashiga kira ahankali ko Allah zaisa
yajishi yafarka amma segashi yayi masa kira yafi goma ko gezau beyi ba. Tsaki
LamiÉ—o yasaki sannan yashiga knocking jikin windown yana kiran sunan Hafiz É—in.
Musa dake kwance gefen Hafiz ne yaji kamar ana kwankwasa musu windown É—aki. BuÉ—e
idanunsa yayi dan tabbatar da zarginsa and then he saw the glimps of LamiÉ—o,tashi
yayi yazauna daga kwancen dayake yana mutsutsuke idanun sa dan son tabbatar da
abunda idanunsa suka gane masa seyaji LamiÉ—on yasake knocking windown. Kallon
window yakumayi ayayinda LamiÉ—o yashiga yimasa alama da hannu kan yazoshi,tashi
yayi daga kan gadon yakarasa jikin windown yana kurama LamiÉ—on idanu sannan cikeda
mamaki yace "Hamma LamiÉ—o?" LamiÉ—on alama da hannu yashigayi mashi akan he should
talk softly kada yatada sauran yan gidan sannan yace "buÉ—e windown Musa" sa hannu
Musa yayi yabuÉ—e windown yana mamakin meyakawo LamiÉ—o gidansu da sassafennan sannan
yace "Ina kwana?" LamiÉ—o yace "lafiya Lau. dan Allah tayarmin da kasan can. wannan
ai se azo asaceshi ma baisani ba" dariya Musa yayi yana faÉ—in "kumafa baijima da
komawa bacciba" ayayinda yakarasa jikin gadon yashiga tashin Hafiz É—in yana kiran
sunansa.
BuÉ—e idanu Hafiz yayi rai bace Jin irin bugun da Musan keyi masa dukwai da sunan
tashinshi daga bacci fuska a murtuke yace "Wai miyene kake tashina?" Musa yace
"Hamma LamiÉ—o ne yace in tashe ka" tsaki Hafiz yayi Sannan yace "LamiÉ—o kuma da
sassafennan? Hankalin ka É—aya kuwa?" Musa yace "wallahi dagaske nikeyi Yaya Hafiz.
inbaka yarda ba ka kalli windown É—akin mu gashican yana kallon ka" kallon direction
É—in windown Hafiz yayi rai bace and then he saw LamiÉ—o waving at him,yana cemasa
yataso yazo suyi magana.
Dole yatashi yazauna dukda kuwa baccin idanunsa basu ishesa ba,amma ya ya'iya?
yasan koyace zaikoma baccinma LamiÉ—o ba barinsa zaiyiba harsai ya sauraresa dan
haka ya tashi yakarasa jikin windown yana mutsutsuke idanu sannan yadubi LamiÉ—o
yace "Wai meyafaru irin wannan sammako haka LamiÉ—o?" LamiÉ—o yace "lafiya lau kaidai
shirya kafito waje muyi magana zaifi" Jin LamiÉ—o yace Lafiya Lau yasa Hafiz cewa
"toh jirani ba'in wanke fuskana se infito" LamiÉ—o yace "alright be fast.
Inajiranka"
Cikin mintuna biyar Hafiz yashirya yasamu LamiÉ—o awaje yace "good news kakawomin
kokuma bad news?" dariya LamiÉ—o yayi sannan yace "toh dai za'a ce good news É—inne
tunda it's a way to success" Hafiz yayi murmushi yace "ansamu hanyar samun kuÉ—in
kenan?" danko tantama babu yasan maganar kuÉ—in tafiya Bauchi ne yakawo LamiÉ—on da
safiyar Allahn nan tunda dabakin shi yace masa komai lafiya Lau agida.
Excitedly LamiÉ—o yace "Exactly Hafiz" Hafiz yace "Ta wace hanyace za'a samun kuÉ—in?
dako zaka yini kanayi a kasuwa? Kokuma Bara zakaje kayi?" Hafiz yakarashe maganar
playfully,dundu LamiÉ—o yakaimai yana dariya tareda faÉ—in "bana son iskanci fah
Hafiz" Hafiz dabaibar dariya ba har lokacin yace "I'm sorry kaima kasan wasa nakeyi
maka" LamiÉ—o yace "whatever. nidai yanzu I need your help" Hafiz dahar lokacin
fuskarsa na É—aukeda annurin Æ´ar zolayar LamiÉ—on dayagamayi yanzu yace "wace irin
taimako zanyi maka? kafaÉ—a muji kozan iya" Kai tsaye LamiÉ—o yace "zuwa zakayi Fada
kace kasan barawon daya shiga masarauta ranar da daddare" ware idanu Hafiz yayi
sannan yace "bangane ba? nasan barawon neni? Kuma how does that have to do with
samun kuÉ—in ka?" cikeda kaguwa LamiÉ—o yace "mekakeji na baka na zuba? kayi hakuri
mana,zanyi maka bayanin komai ai" ajiyar zuciya Hafiz yasauke sannan yace "toh
inajinka" LamiÉ—o yace "Yauwa. katuna anyi guje guje a masarautar kan barawo yashiga
a daren dazamu gama exams É—inmu?" cikeda gamsuwa Hafiz yace "Natuna" LamiÉ—o yace
"toh ai ba'asamu ankama barawon aranar ba kuma haryau ba'a kamashi ba sabida anrasa
wanene shidin,anyi bincike anyi bincike haryau ba'a gane wanene ba shine Sarki yace
zaibada kyautan dubu goma a duk wanda yazo yace yasan waye barawon yakuma zo yanuna
shi" wani kallo Hafiz yama LamiÉ—o sannan yace "toh se mekakeson inyi yanzu?" LamiÉ—o
yace "zuwa zakayi kace kasan barawon" wannan karan harara Hafiz ya watsama LamiÉ—o
sannan yace "kafaÉ—i hakan ai yanzu. Sonake inji wakekeso inyi pointing as barawon
don kasamu dubu goman?" sosa kai LamiÉ—o yashigayi mischievously yana murmushi
sannan yace "Ni zakayi pointing" Hafiz sarai yasan abunda LamiÉ—on ze faÉ—a kenan
shiyasa tun É—azu yakeyi mashi wani kallo yanajiran yaji tabakinshi kafin ya san
irin amsar dazai basa dan haka yace "You're totally out of your mind" sannan yajuya
daniyar komawa cikin gidansu dan dagaske gani yakeyi LamiÉ—on yasamu tabin
kwakwalwa.
Cikin sauri LamiÉ—o yariko hannunsa sannan yaje yatsaya tagabanshi yana faÉ—in
"inazakaje kuma bayan bamu gama magana ba?" fuska É—aure Hafiz yace "Oh so kake
intsaya incigaba dajin useless maganganunka da babu hankali kwata kwata acikinsu?
wallahi danasan abunda zaka faÉ—amin kenan daban hana kaina bacci nazo na saurare
kaba" LamiÉ—o yace "what's wrong with abunda na faÉ—a da babu hankali aciki Hafiz? I
need the money and after you told them I can get it easily" Hafiz yace "hmmm. In
nace you totally lost it is an understatement" sannan yabuga tsaki yayi gaba yabar
LamiÉ—o agurin.
Kiran sunan Hafiz ɗin Lamiɗo yashigayi yana rokonsa yatsaya anma yaƙi yasaurareshi
kwata kwata sema shigewa gidansu dayayi yarufo kofar taciki. dafe kai LamiÉ—o yayi
ahankali. Shidaman tunkan yatunkari Hafiz da maganar yasan sesunyi rikici inma zai
yarda anma baitaba tunanin he'll react this way ba,betaba tunanin bazaima tsaya ya
saurare shi dakyau har hakaba. Ayanzu da Hafiz yaƙi bashi haɗin kai yasan bashida
wani alternative É—inda yawuce yakoma ma first option É—insa da ainahi shine dalilin
fitowarsa daga gida. Kwafa yayi sannan yashiga taku cikin sassarfa ayayinda yanufi
hanyar dazata sadashi da titin dazai kaishi kasuwa. Traking yadingayi harya isa
kasuwan kuma da ikon Allah sebeji wani gajiya ba. anma dayayi la'akari da tafiyar
dayayi yauÉ—in bekai wanda sukeyi a field work ba sebeyi mamakin rashin jin gaskiyar
tasaba. awanshi uku azaune gaban shagon su Abdulmalik É—in anma bai isoba dukdama
sauran yaran aikin mahaifin Abdulmalik É—in sun buÉ—e shagon kuma har customers
sunfara kai kawo a bakin kofar shagon. Yafi sau uku yana tambayar É—aya daga cikin
yaron shagon ko Abdulmalik É—in zai fito and he always give him thesame answer
nacewa "eh zaifito É—in amma fah bayanzu ba" dole LamiÉ—on yacigaba da zaman jiranshi
tunda shikeda tsananin bukatar ganin nasa. Se wuraren goma da rabi Abdulmalik
ya'iso shagon,bakaramin mamaki yayiba dayaga LamiÉ—o zaune akofar shagonsu.
Fuska É—aukeda fara'a yace "Aaaa'aa wanake gani kamar LamiÉ—o?" murmushi LamiÉ—o yayi
sannan yatashi tsaye sukayi musabiha yana faÉ—in "Nine Abdulmalik. Kabuya kwana biyu
shiru" Abdulmalik yace "kainedai ka buya LamiÉ—o. Mukam ai muna inda muke sede in
ba'a neme muba" wannan karan dariya LamiÉ—o yayi sannan yace "Toh ya kasuwanci?"
Abdulmalik yace "Alhamdulillahi LamiÉ—o. Ina Umma?" LamiÉ—o yace "kalau take wallahi.
tun seven nasafe nakenan inajiran ka ai,bansan bazaka fito dawuri ba dana zauna na
sharari baccina ai kafin infito nima" Abdulmalik yayi dariya sannan yace "i'm very
sorry daman bana fitowa dawuri anma danasan dazuwan ka dazan zo semu haÉ—u ai ko
ince kasameni a gida" LamiÉ—o yace "bakomai karka damu. natambayi É—aya daga cikin
yaran shagon ku ai,shi ya tabbatarmin da zaka fito shiyasama nazauna najiraka"
Abdulmalik yace "Allah sarki" kafin LamiÉ—o yafaÉ—a masa dalilin dayasa yazo
ganinshi.
Bakaramin mamakin LamiÉ—o Abdulmalik yayi ba danyasan LamiÉ—o farin sani tunsuna
secondary school,yariga yakwana da sanin shiÉ—in Umma's son ne,babu ruwanshi da irin
bige bigen nan komai sede ayi mashi anma seya boye mamakinshi sanin cewa rayuwar
tana canzawa and moreover shekaru sunja sosai,jiya ba yauba.
Yafi mintuna biyu yana nazari kafin yasake kallon LamiÉ—on yace "lallai lallai kuma
kai aikin dazaka samu kuÉ—i ayau kake nema?" LamiÉ—o yace "eh Abdulmalik. I really
need the money before tomorrow shiyasa" Abdulmalik yace "toh gaskiya ni bana
tunanin aikin dazaka samu kuÉ—i ayau zaka iyashi LamiÉ—o sauran ayyyukan kuma duk
kuɗin gaskiya daƙyar inzaka samu yau" cikin sauri Lamiɗo yace "nidai faɗamin wani
aikine zansamu kuÉ—in ayau? Koyaya yake insha Allahu zanyi so far as bukatana zai
biya" Abdulmalik yasauke ajiyar zuciya sannan yace "Dakon É—aukan kayane fah
LamiÉ—o,sekuma sauke kayan abinci daga cikin trailer ashigar dasu shago shima dakun
gama za'a baku kuÉ—inku anma inaganin kafaÉ—a min nawa kakeso kawai inbaifi karfina
ba se inbaka kaje kayi amfani dashi" Kai tsaye LamiÉ—o yace "karka damu. Indai zaka
samamin inda zan sauke kayan abincin daga cikin trailer mushigar dashi shago zanyi
babu komai" cikeda inassurance Abdulmalik yace "koka sauke musu kayan kudinfa
bawani na kirki za'abaka ba kuma ba lallai yazo ya isheka ba shiyasa nace ka
hakuran kawai" wannan karan murmushi LamiÉ—o yayi sannan yace "Don't worry just help
me get the job I'll surely manage" Abdulmalik Jin yayi insisting yasashi cewa "toh
shikenan tunda kazabi hakan" sannan yashige shagon yanacema LamiÉ—o "ba inzo se in
rakaka shagon dazakayi musu aikin danmu anriga da ankawo kayan tunjiya har
ansaukesu" LamiÉ—o yace "toh" aranshi yana addu'ar Allah yasa yasamu inda zaiyi
wannan aikin koda sau ukune ayau kadai may be inyasamu wannan opportunity É—in
zetara amount É—inda zai isheshi tafiya Bauchin. Yes he desperately need the money
and for sure har ransa yaso karban kuÉ—in da Abdulmalik yaso offering masa.
Besides,waye bayason banza arayuwarnan? sede shi nashi son banzan bekai har ya
zubar da self respect É—insa ba. Abdulmalik mutum ne meshegen son faÉ—an alkhairin
dayayima mutane ako Ina yazauna and definitely inzai bada labarin seyayi narrating
yanda komai yafaru shiyasa ma yaƙi karba,bayason azo anayi mishi kallon maroqi
cikin abokanansu,he prefer akirashi da yaje yayi dako yayi earning kuÉ—insa dakansa
than ace É—auka akayi akabashi sabida anji tausayin sa. zuwan dayayi gurin
Abdulmalik yanzunma bawai don yasoyin hakan baneba sedan bashida other option.
Abdulmalik bejima a shagon ba yadawo inda LamiÉ—on ke tsaye sannan yayimasa jagora
har shagon da zaiyi aikin. Aikuwa suna Isa shagon trailern daya kawo abincin ya'iso
gaban shagon wanda hakan yasa Abdulmalik É—in karasawa yayi cikin shagon yayi ma
ogan shagon magana sannan yayi introducing É—inshi to LamiÉ—on kafin sukayi sallama
yatafi bayan LamiÉ—o yamasa godiya.
Trailern makare take da kayan abinci acikinta,kama daga kan buhunan
shinkafa,semovita,flour,gishiri dadai sauransu. haka LamiÉ—o dawasu samari guda biyu
suka dinga sauke buhunan kayan abincin daga cikin trailern suna kaiwa cikin shagon.
Basu suka gama ba se azahar,akirawa LamiÉ—o gajiya awannan lokacin is an
understatement,tsintan kanshi yayi yana sarama duk wasu masu yin aikin hannu
dansusamu hakkinsu,tunda yake be taɓa sanin haka gumin halak yakeba seyau. gumi
kawai yaketayi. gaba É—aya rigarsa tajike julib kamar wanda akayi masa wanka da
ruwa. yaso ace yasakeyi ma wasu thesame aiki ko zaisamu kuÉ—in dadan yawa anma yanda
yagajin nan baya tunanin zai iya kara tabuka komai yau gaba É—aya barekuma daman
baici abinciba ya baro gida,hana rantsuwa dai yasan yakarbi biscuit dawata 50naira
daya tsinta cikin aljuhunshi kusan zasu fara aikin yaci.
Yanzuma zaune yake kan É—aya daga cikin dakalin dake kofar shagon yana kwankwadar
satchet É—in purewater na uku ayayinda yake jiran azo abashi guminsa yatafi gida.
É—aya daga cikin Samarin dasukayi aikin tare ne yafito daga shagon yana irga kuÉ—i.
Karasowa inda Lamiɗo kezaune yayi yana miƙa masa kuɗinsa. Kallon kuɗin Lamiɗo
yashigayi baki sake,dankuwa inba gezau idanunsa keyi masaba gudan É—ari biyu ake
miko mishi. fuska cikeda desbelief yace "kuÉ—in menene wannan É—in?" saurayin cikeda
Jin haushin silly question É—inda LamiÉ—on yamasa yace "kamanya kuÉ—in menene? kuÉ—in
aikin dakayi ne mana" karban kuÉ—in LamiÉ—o yayi yana jujjuyashi kamar wani kashi
ayayinda yakejin wani abu na tokare masa zuciya yace "É—ari biyu ne kuÉ—in duk uban
aikin damukayin nan?" wannan karan dariyan keta Saurayin yayi sannan yace "lallai
ma. daman kai atunaninka nawa za'a baka? haka ake bayarwa koda yaushe daman" LamiÉ—o
besan sanda yatashi daga zaunen dayakeba sannan yace "wallahi basu isaba. waye
yabaka kuÉ—in kabani?" Baki sake Saurayin yace "Ogansu ne yabani" fuska murtuke
LamiÉ—o yace "muje kanuna minshi dan Allah" dan harga Allah yasan Abdulmalik
yafadamai kuÉ—in baida wani yawa amma kwata kwata baiyi zatan irin biyan wulakancin
nan za'ai masaba,atunaninka zaisamu dubu daya koma fiye da haka shiyasa zaiyi sau
biyu yatara kuÉ—in motar amma baya tunanin zai lamunci wannan rashin mutuncin
shiyasa bazaiyi shiruba,se inda karfinsa yaƙare yau" Saurayi cema Lamiɗo yayi "toh"
sannan yashige gaba inda LamiÉ—o yabi bayanshi suka shige shagon. hargaban Ogan
Saurayin yakai LamiÉ—o,yacema Ogan nasu tare suka saukar dakaya daga cikin trailer.
Ogan cema Saurayin yayi yagane LamiÉ—on sannan yamaida hankalinsa kan LamiÉ—o daya
haÉ—e fuska kamar hadarin kaji yace "Koba kaine Abdulmalik yakawo ka É—azuba?" LamiÉ—o
yace "Nine" murmushi mutumin yayi dukda kuwa yanayin fuskar LamiÉ—on yasashi yaji
wani iri sannan yace "lafiya dai koh?" Kai tsaye LamiÉ—o yace "Ba lafiya ba Mallam.
naga mungama tikan aikine kuma se aka haÉ—a mu da É—ari bibbiyu amatsayin kuÉ—in
sallamar mu" still trying to be nice Ogan yayi murmushi sannan yace "Eh ai haka
kuÉ—in aikin yake. halan wannan ne zuwan ka nafarko?" LamiÉ—o yace "toh nidai gaskiya
ba'a haka nayi aikina ba Mallam. I didn't work for two hundred naira" Ogan daya
fara loosing temper É—inshi ayanzu yace "kaman Yaya?" LamiÉ—o dafa hannunshi yayi
jikin kofar shagon cike da karfin hali yana fadin "kamar yanda kaji nace" sannan
yakarada "I worked for solid three hours banzauba ba,bakuma tsaye nake aguri É—aya
ba aiki na dinga yimaka har na tsawon awowi uku kamar jaki. so I didn't expect you
to give me two hundred naira gaskiya. indai akwai adalci,tausayi,sanin yakamata
dakuma Imani acikin al'amarinnan ahhh Toh!" rai bace Ogan yace "toh haka muke
biyan kowa akodayaushe akayimana irin aikinnan sannan daman bamuyi yarjejeniya
dakai akan zanbaka abunda yafi É—ari ukuba kafin kafara aikinnan" LamiÉ—o yayi kwafa
sannan yace "That's because bansan za'ayimin rashin adalci ba, naÉ—auka kunsan
yakamata zaku kimanta kubada abunda yayi dede da gumina" Ogan nashirin sake magana
É—aya daga cikin ma'aikatan shagon dasuke kusan sa'anni yakaraso gurin yana
tambayarsa meya haÉ—ashi da LamiÉ—o dankuwa har attention É—in Jama'a yafara dawowa
kansu.
Take Ogan yayimasa bayanin yanda sukayi da LamiÉ—on. juyawa mutumin yayi yana kallon
LamiÉ—o sannan yace "kayi hakuri ka karbi abunda aka baka tunda tun asali bakuyi
yarjejeniya akan adadin kuÉ—in daza'a baka ba" stubbornly LamiÉ—o yace "wallahi bazan
karbi dari biyu intafi quietly ba bayan uwar aikinnan danaci sannan dakace bamu
kayyade kuÉ—i ba kafin mufara aikin,tunda har hakan tafaru inaganin nine yakamata in
faÉ—i abunda za'a bani tunda ninayi aikin bashine zai É—auki son ransa yabani ba"
shiru mutumin yayi yana kallon LamiÉ—o hakama sauran mutanen dake shagon dankuwa
sunsan somehow statement É—inda yayi yanzun akwai gaskiya acikinsa dukda kuwa
dukansu biyu,dagashi har ogan sunada laifi tunda shibai tambayi amount na kuÉ—in
aikinba shima kuma Ogan be faÉ—a mishiba seda aka gama yaÉ—auki kuÉ—i yabashi" wani
daga cikin waÉ—anda ke kallon dramar tasun ne yadubi Ogan yace "kaima kawai ka kara
mishi kuÉ—in mana awuce gurin" Ogan yace "bazan bashiba. Inna karamai kenan na cuci
sauran wadanda sukayi aikin tareda shi" mutumin yace "Suma seka kara musu tunda
bawai bakasan fuskarsuba,Ina Isah da Adamu ne?" stubbornly Ogan yace "nifah bazan
kara masuba,ribar ma nawa take da har zaizo yana raunana mutane wayau?" LamiÉ—o rai
bace yace "riba harnawa yake kace? Konayi rantsuwa bazanyi kaffara ba nasan cikin
trailern nan damuka sauke maka bazaka rasa riban dubu dariba koma fiye da haka so
nibanga dalilin dazaisa muyi awa uku muna sauke maka kayaba kadauki dari bibbiyu
kabamu. yanda kakeson jikinka haka muma mukeson namu sannan inba bukatar kuÉ—in
mukeyiba babu abunda zaisa muzo muyi aikinnan anma nalura ku kanku kaÉ—ai kawai kuka
sani. You never think about wahalar da masuyi muku aiki sukesha dakuma irin
tsananin bukatar dayakesasu su kaskan tar dakansu suyi muku aikin bare kuyi musu
adalci. Toh wallahi inkunayima wasu suna shiru nibazanyi shiru ba. kakaramin kuÉ—in
nan ko innemo waÉ—anda mukayi aikin dasu,inkarada masuyima other shaguna irin
aikinnan mumaida maka tsiyarka cikin trailern ka inyaso kaida yaran shagon naka
seku saukesu. And I promise you I'll make sure I convince them sutafi strike
sudaina yimaku aikin wahala kuna biyansu a wulakance harsai ranarda kukayi deciding
zakuna yi masu adalci" Rai bace Ogan yace "toh kayi protest É—in mana. Angaya maka
su mahaukata irin kane?" LamiÉ—o kafa yashiga jijjigawa yana murmushi yace "oh haka
ma zaka ce?" sannan yayi sauri yacire hannunsa daga jikin kofar shagon,yajuya yana
karema mutanen gurin kallo ko Allah zaisa yasamo samari biyun dasukayi aiki
dasu,sede tunma kafin ya kyallarosu a Inda suke tsatsaye Isah yafito daga cikin
mutanen yazo yatsaya kusada LamiÉ—o yace "Ina taredakai Bawan Allah" murmushi LamiÉ—o
yayi ayayinda yacigaba da dubawa kozaiga dayanma anma segashi shima yafito dakansa.
Daganan kuma aka fara maganganu agurin kan sunada gaskiya,daman haka akeyima
talaka,shize tiki wahala yamaka aikin dakai bazaka iyaba anma instead of ayi
rewarding É—inshi dede aikin dayayi a'a sede abiya shi a wulakance bayan kuma ansan
tsananin bukatar kuÉ—in ne yasashi yin aikin wahalar sannan ko anbiya shi a
wulakancen ba lallai yayi complain ba ahaka zaikarba sabida yana tsananin bukatar
kuÉ—in dukda kuwa har ransa yasan inza'abi gaskiya ancucesa"
Cikin mintuna kalilan LamiÉ—o yasamu kusan mutane goma Sha biyar dasuke bayansa,suke
kumada yakinin tayashi maida kayan cikin trailer daganan kuma sesukoma convincing
Yara masuyin irin wannan aikin dasu denayi harsai anfara biyansu hakkinsu dede
yanda yakamata. wasu daga cikin dattawan gurinne suka samu Ogan sukayi masa magana
cikin lalama akan ya karama LamiÉ—on da sauran biyun kuÉ—in kawai tunda sun dage
inbahaka ba hakan ze iya kawo rikici duk kuma abunda zaitada rikici to babu
amfaninsa.
Badan Ogan yasoba sedan ganin darajar mutanen dasukayi masa maganar yasashi yadubi
su LamiÉ—o dahar zasu fara É—aukan buhunan yace "su tsaya" tsayawa sukayi dukansu
LamiÉ—o na murmushi mischievously ayayinda Ogan yakaraso inda su LamiÉ—on suke
tsaye,fuska babu annuri yace "Nawa zan biya ka kaida waÉ—anda sukayi mani aikin?"
LamiÉ—o sosa sumar kansa yashigayi still yana murmushi sannan yace "Dubu bibbiyu"
wani harara Ogan yadaka masa sannan yace "baka isaba kuma wannan" É—aya daga cikin
dattawan dasuka yima Ogan magana yadubi LamiÉ—o sannan yace "haba kaikuwa yaro. dubu
biyu yayi yawa inama laifin kace dubu É—aya" duka sauran dake tsatsaye agurin suma
suka shiga faÉ—in "dubu biyu yayi yawa sede dubu É—ayan dai kam" LamiÉ—o bahaka yaso
ba danshi kawai yakayyade yafaÉ—i iya kuÉ—in dayake bukatane shiyasa yace dubu biyu
anma ganin mutanen gurin sunce yayi yawa yasashi cewa "Toh yakawo dubu É—ayan anma
fah da sharaÉ—in duk waÉ—anda zasunayi masa aikin nan dubu É—ayan zai na basu koda
yaushe. Kai bama shikaÉ—ai ba gaba É—aya cikin kasuwarnan inbahaka ba they'll still
do the protest" dattijon daya gama magana yanzu yace "Kaide karbi kuÉ—inka katafi
Yaro. Insha Allahu zamu zauna da shuwagabanni yan kasuwa ayi masu magana" LamiÉ—o na
murmushi yace "toh Baba mungode. Allah yasaka da alkhairi" kafin yamika hannu
yakarbi Eight hundred É—inda Ogan ke mikomashi yahaÉ—a da two hundred É—in dazu
yasakasu a aljihu sannan yajuya daniyar barin gurin.
Harya Kai bakin kofar shagon sekuma yadawo cikin sauri. Yatsaya agaban Ogan in a
apologetic manner yace "I'm sorry. I know you're older than me and yet I talk to
you out of respect. Wallahi rainane abace sannan this's my first time working here
shiyasa akasamu misunderstanding É—innan and moreover I was trying inkarbi hakkina
ne. Kayi hakuri ka yafemin for talking to you harshly" dukyanda ran Ogan yake abace
he couldn't help it but fake a smile,seyaji jikinsa yayi sanyi lokaci guda
sincerely yace "bakomai yawuce" rungumar sa LamiÉ—o yayi lightly sannan yayima yan
gurin sallama yatafi gabadayan su suka bishi da idanu suna yaba hali irin nasa
ayayinda masuyin aikin dako ke gode masa harcikin ransu dankuwa sunsan yanda ya
jajircedinnan yau toh tabbas za'a É—auki mataki akoma ana biyansu yanda yadace.
LamiÉ—o dede fita daga kofar kasuwa yaga me wheelbarrow É—in magarya dame rake agefe
wanda hakan yatuno mishi da maganarsu ta karshe da Rukayya ranar dazai barota a
asibiti,nacewa datayi yasiyo mata tsaraba haryayta irga mata sunayen abubuwan da
ake samu a Gombe yace tazabi wanda take so ya saya mata tace ita duka takeso.
Murmushi yayi sannan yakarasa kusa da mai magaryan yace yadiba masa na dari,yaje
gurin me raken ma yasaya,yashiga dube dube agurin ko Allah zaisa yaga wasu daga
cikin abubuwan dayamata alkawari yasaya anma babu wanda hakan yasashi komawa cikin
kasuwar dole. saida yasayi duka abubuwan daya mata alkawari sannan yatari napep
yanufi hanyar gida dukda kuwa yaso yatsaya yayi sallan azahar anma baya tunanin zai
iya yin sallah da kayan jikinsan nan dashi kanshi jinsu yakeyi wani iri ajikinsa
tsabar wahalan dayasha yau.
Yana shiga parlourn su da Salma yafara cin karo. cikeda damuwa tanufe shi tana
tambayarshi inayaje tun safe anata nemanshi.
LamiÉ—o yace "wani aiki nafita yi Salma. Ina Umman?" Salma tace "Umma taje gidan
biki" LamiÉ—o cikeda mamaki yace "biki a Ina?" danshidai as far as he could remember
basuyi maganar zataje biki wani guba kwanannan koda kuwa acikin hirane. Salma tace
"Auren Ruksaaa yar gidan Mallam Abu a Tudun wada" LamiÉ—o cikeda shakiyanci yace
"Ruksaaan hartakai aurene daman?" dariya Salma tayi batace komaiba sannan yace "toh
Allah yabasu zaman lafiya. Inasu Basma?" Salma tace "Yaya Basma na wanka. Yaya
Jiddah kuma nabarota tana sallah a É—aki" LamiÉ—o yace "toh Nima barina shiga nawatsa
ruwan nayi sallahn. In jiddah ta'idar da sallahn kice tazubamin abinci takawomin"
Salma tace "Toh Hamma LamiÉ—o" ayayinda yayi wucewarsa É—akinsa Itama takoma nasu
É—akin dan fadan sakon LamiÉ—on.
Lamido na shiga É—aki kan gado ya ajiye ledojin tsarabar Rukayya sannan yashige
wanka abunsa. yasan the battle is not yet over tunda baisamu amount É—inda yake nema
É—inba,sannan kuÉ—in daya samu yanzunma duk ya kashesu canji kalilin ne yarage anma
baya tunanin zai iya sakeyin aikin wahala irinna yau danyasamo cikaton kuÉ—in. He'll
just have to convince Hafiz akan plan É—insa na dazu no matter what.
Koda yayi wanka,yashirya yayi sallah betashi daga kan sallayar dayakeba sema janyo
pillow dayayi daga kan katifarsa yakwanta anan kan sallayar yana kissima abubuwa da
dama aransa dakuma irin wahalar dayasha yau É—in.
Idanunshi ne suka sauka kan tray É—in abincin dake ajiye kan wani stool dake cikin
dakin nashi dayakeda tabbacin Jidda ce tashigo dashi tun yana wanka,gashi ta
ajiyeshi shiyasama bailura dashiba seyanzu da idanunshi suka kai gurin. tashi yayi
cikin sauri ayayinda yakarasa kusa da tray É—in abincin yaÉ—auko yadawo inda
yakezaune É—azu,yazuba abincin yanda zai isheshi a plate sannan yashiga ci anutse.
yana gama cin abincin kuwa yasake kwanciya se bacci.
Tunda suka fito a masallacin sallar isha'i LamiÉ—o kedamun Hafiz akan yataimaka masa
yaje yace shine barawon gobe da sassafe danyasamu yasamu kudinnan yatafi Bauchi
gobe.
Hafiz yace "Bazan iyaba fa LamiÉ—o. I can't put you in danger,kamasan consequences
É—inda ke cikin yin abunnan kuwa? sunanka dana Umma baci zaiyi acikin masarautar nan
sannan kasan mai martaba bayida mutunci,yana iya É—aukan kowani mataki akanka dasu
Umma sabida haka nibazan iyaba wallahi" dafe kai LamiÉ—o yayi sannan yace "nasan
menakeyi Hafiz,kuma nasan akwai consequences aciki quit sure but I'm ready for it"
tsaki Hafiz yayi sannan yace "shiyasa nace you lost it akan yarinya Ƴar kankanuwa
you're ready to put yourself in trouble sabida kawai kaje kaganta? Toh inkaje É—inma
Kai zakabama Baban nata lafiya komi? You've tried your best wurin ganin ka koma ko
Allah ma yaga efforts É—inka so I see no reason daza kazo kana takura kanka danbaka
samu kuÉ—in zuwaba. May be rashin zuwan naka shine the best" LamiÉ—o rai bace yace
"nidai yanzu zakayimin alfarmar danake nema kobazakayiba?" Kai tsaye Hafiz yace
"bazanyiba gaskiya" LamiÉ—o yace "what if I tell you nine nashiga masarautar ranar
da dare shima bazakaje kafaÉ—i gaskiya ba?" Hafiz yace "nakwana dasanin hakan. Koka
manta ranar kaida bakinka kafadamin and besides,ba sata kashigayi ba you were
trying to find your way home sabida anrufe gate É—in masarautar so I see no reason
dazanje ince kaine barawo" cikin sauri LamiÉ—o yace "exactly my point Bro. It can be
ance wanda yaga barawon dayashigo yaje yafaÉ—a sunansa anma ai bahakan yana nufin
Satan akayiba kuma bahakan yana nufin kaixakaje kace kaga nayi sataba. Zuwafa kawai
zakayi kace tare muka dawo daga school daren ranar sabida Ina tsoron purnishment ne
yasani kin cewa abude min gate nabiyo ta katanga. Inka faÉ—i haka I'm very sure za'a
baka kyautan kuÉ—in sekazo kasameni a Tasha kabani dankuwa bazan Bari suganni ba
senadawo daga Bauchi inyaso daganan swa bani duk wata purnishment dasuka ga yadace
dani dukdama inada yakinin bazaikai yanda kai kake tunani ba" Hafiz zaiyi magana
LamiÉ—o yayi sauri yakatse shi tahanyar cewa "please do this for me Hafiz. Please!
Kasan banida wanda zanyi relying akai sekai" akafule Hafiz yace "Kai miyasa bakajin
magana ne wai?" dariya LamiÉ—o yayi sannan yace "toh yazanyi? haka nake" jijjiga kai
Hafiz yayi in desbelief sannan yayi gaba yabar LamiÉ—o tsaye gurin.
Bin bayanshi LamiÉ—o yayi still yana dariya,yasan tunda har bece komaiba toh tabbas
ya yarda ne. Majalisarsu suka nufa dankuwa se washegari dasafene Hafiz É—in ze je
fada ya aiwatar da abunda LamiÉ—on yace yayimai.
***
Kawu idrissa tunda suka rabu da Kawu Sani a kofar gidan marigayi Mallam Umar suka
É—auki hanyar gida yake tunanin ta'ina zaifara yima mai É—akinsa bayanin shawarar
dasu Kawu Sanin suka yanke na Rukayya tazauna agurinsa bayan kuma tuni suka gama
tsarinsu shida ita akan yayi ƙoƙari yasa atura Rukayya Giyaɗe yanda zatayi nesa
dasu,yanda zatayi nesa da property É—in da mahaifinta yabar masa amana ahannunshi
shi yayi badali dashi,yasamu yazama mai kuÉ—i acikin dangi shima afara bashi
Ultimate respect kamar yanda ake bama kanin shi Sani. Ada baisa rai a dukiyar
Rukayya ba koda Umar yabashi amana hakanan koka É—an tunanin cin dukiyar Rukayya be
taɓa zuwamai raiba. Infact he was willing to keep the property safely harzuwa
lokacin da Rukayyan zata girma yaÉ—auki abunta yabata anma daya tunkari matarshi da
maganar,daya faÉ—a mata yanda sukayi da Mallam Umar É—in take ta nuna mishi besan
meya keyiba tunda harzai bari dama irin wannan ta wuceshi.
Tace "lallaima Baban Rabi'u, yanzu kai ajiyan dukiya zakayi tayi harna tsawon
shekaru masu dama haka kawai batareda kai kowani ya amfana dasu ba?" ta daga
takaddun gonaki da filayen tana nuna masa yagani dakyau tace "toh wai mema Rukayya
zatayi da tarin dukiyarnan inbanda sangarta irinta Umar? Yarinyar da inta manyanta
ma gidan wani zatajeta. Kuma inma akwai adalci dasanin yakamata bekamata Umar yace
ku ajiye dukiyarnan ma Rukayya ba harsai ta girma abata. Kamata yayi yaraba muku
dukiyar a tsakaninku kaida Adamu yace kukara akan kuÉ—in kasuwancin ku inyaso se
kuna kula da duk wani expenses na Rukayya dazai taso a rayuwa tunda kune masu
ƙaramin ƙarfi acikin ku huɗun. Kuma koba komai inkuka ƙara akan na kasuwancin naku
kuma zaku samu wani alherin tayanda zaku kula damu wurin bamu ingantacciyar rayuwa.
Anma wannan abunda yayi kwata kwata baidace ba,yanuna son kai da son diyarsa kaÉ—ai
ƙarara kuma ahakan yake tsanmanin ku ki riƙeta,kukula daduk wasu bukatunta na
rayuwa. Toh nidai bazai yuyuba Baban Rabi'u. Kuma inanan dakai bari ayi sadakan
bakwai kowa ya watse cewa za'ayi ka ɗauki Rukayya ka riƙe ta agurin ka tunda kaine
Babba bayan kuma responsibilities É—in makarantar yaranmu kaÉ—ai wani sa'in se an
qoqe akesamun ayimusu komai barekuma azo ga batun abincin gida,sutura da dai
sauransu sannan ahakan za'ace kariqeta da guminka. Toh nidai dukyanda za'ayi in
akace maka kaÉ—auki Rukayya ka riqeta karka yarda,kasan yanda zakayi a turata GiyaÉ—e
tazauna acan dannasan Itama candin zaifi Mata daÉ—in zama.
Batun kuÉ—i kuma inaganin lokaci yayi dazamu cire kanmu daga Rayuwar maleji maleji
É—innan,munsha gwagwarmayar rayuwa abaya ta'isa hakanan dukdama yanzu alhamdulillahi
bakamar daba anma gaskiya lokaci yayi dayakamata muma muji daÉ—in rayuwa dagamu har
Æ´aÆ´amu,mukai matakin da ko'ina muka shiga baza'anayi mana kallon tara saura kwata
ba. Kobaka ga yanda Sani yasamu cigaba a rayuwarsa baneba?inanan muke tare dashi
ada muna fafutuka tare anma gashi yanzu ya samu gantsareriyar gida da dukiya yatafi
yabarmu hakanan cikin danginku babu wanda bayaji dashi yanzu dukda kuwa da babu
wanda ya damu dashi,kamarma anason adauki girmanka amayar mai sabida matakin
dayakai arayuwa baikai naka ba. Toh Gaskiya Baban Rabi'u kasake tunani akan maganar
dukiyar yarinyarnan zaifi" wani irin wawan ajiyan zuciya Kawu Sani yasauke alokacin
ayayinda yagama kissima maganganun matar tasa, somewhere somehow yagane maganar ta
kuma ya yarda da'ita É—ari bisa É—ari,koshi daman yanason yin amfani da dukiyar dukda
yasan baikamata ba kawai dai kwarin gwiwane besamuba shiyasa yayi deciding ajiyewan
but the idea of she saying Rukayya takoma GiyaÉ—e baiyi masaba kwata kwata.
Atunaninsa indai zaiyi amfani da dukiyar Rukayya to yakamata yazamanto shizai
riƙeta,yayi Mata komaina rayuwa yanda kowataran ance Ina kuɗin zai bugi kirji yace
dasu yamata duk wasu taimako dayayi mata danhaka yadubi matar tasa yace "nayarda da
maganganunki anma maganar insa atafi da Rukayya GiyaÉ—e ba shawara mekyau baceba.
Bagwanda in ajiyeta agurina,inriketa harta girma ba in aurar da'ita tayanda
kowataran za'ace Ina dukiyarta zan bugi kirji ince dashi nayi mata abubuwan rayuwa"
Tace "Hmmm lallai Baban Rabi'u. Toh kuwa inkayi hakannema zaka jama kanka magana.
dankuwa zai iya yuyuwa shi Umar É—in yariga yafaÉ—a mata duk kadarorinta daya baka
sannan sanin kanka ne dukiyarnan tanada yawan da yafi karfin ace yatafi a hanyar
karatunta kawai kuma what if wataran tagirma tadubi cikin idanunka tace kabata
dukiyarta fah? mezaka ce mata? Bagwanda tana nesa dakai ba inda ma bazata ganka ba
bare har tasamu damar yimaka maganar. Kuma koma tasamu damar ganin naka bazai wuce
gaisuwa bace zata haÉ—aku" Kawu Sani yace "dukda haka wannan ba shawara baceba Maman
Rabi'u. Kuma karki manta fa nafaÉ—a miki agaban su Sani Umar yabani dukiyar nan,in
ita bata tambaya ba dole wataran su su tambaya sabida haka nace miki zan riƙeta
agurina É—in kawai sabida banason abunda zeje yadawo" Tace "indai tawannan ne
ninasn inda zanje arufe musu baki dayardar Allah. Sabida haka ka kwantar da
hankalinka" murmushi Kawu Sani yayi sannan yace "Dagaske kikeyi?" Tace "dagaske
nakeyi Baban Rabi'u. nidai damuwana ayanzu baiwuce kasan yanda zakayi kar ace
Rukayya tazauna agidanka ba dankuwa shine kaÉ—ai zai iya kawo mana tangarda a
al'amarin mu" murmushi Kawu Sani yayi sannan yace "karki damu zanyi iya bakin
kokarina Inga tatafi GiyaÉ—en kawai" anma segashi yanzu komai yabaci as planned,yaso
shiyafara suggesting atafi da Rukayya GiyaÉ—e anma se itada Suwaiba suka rigashi
requesting which make him feel at ease from the start but then Sani and Adamu
ruined his plan,kuma dukyanda yaso yanuna tatafi GiyaÉ—en zaifi sunki subashi haÉ—in
kai wanda shikuma tsoron kada suyi zarginshi yasa ya amince mishi. Yanzu damuwarshi
baiwuce yanda zai tunkari Maman Rabi'u da maganar Rukayya zatazo tazauna dasu gobe
ba. How will she react? tabbas yasan bazata taɓa karbanta hannu bibbiyu ba Koda
maganar dukiya bata shigo cikin al'amarin ba sabida tsanar datajima yanajin tana
yima Umar da Matarsa Anma wannan bashine damuwarshi ba,the fact that Rukayya might
asked for her property one day inta tashi agabanshi shiyafi daga masa hankali
yanzu,dankuwa tunbayan dasuka gama magana da Maman Rabi'u yafara planing yanda
yanayin rayuwarsa zata canza in blink of an eye cikin kwanakinnan.
*Littafin Qadr na kudi ne duk maiso yayimin magana ta WhatsApp for payment details
*08147722806*
*Page Twenty Four*
Harsuka isa gida Kawu Adamu ne kaÉ—ai keta surutanshi acikin motar dankuwa Kawu
idrissa gaba É—aya yayi nisa acikin duniyar tunani. A garrage É—in gidan Kawu Adamu
yayi parking motar sannan suka fito bakidayansu,kasancewar dare ne Kuma har goma
tawuce yasa basu tsaya wani dogon surutai ba sukayi ma juna sallama ayayinda
kowannensu yawuce sashinsa.
A parlour Kawu idrissa ya tarda wasu daga cikin yaransa suna kallo ayayinda wasu
daga cikin su most especially yan pici picin duk sunyi bacci anan parlourn suma,da
alamadai suna cikin kallone baccin yayi awun gaba dasu.
WaÉ—anda idanunsu biyu harlokacin suna ganin yashigo parlourn duk suka gaidashi
tareda yi masa sannu da zuwa ayayinda É—aya daga cikin yara mazan yazo yakarbi
babban rigarsa da eyes glasses ɗinsa daya riƙo a hannu suka shige ciki. Maman
Rabi'u koda yaran suka sanar da'ita dawowan Baban nasu bataje yimasa sannu da zuwa
ba harsaida ta tabbatar tashigar da kananun yaranta É—aki tasakasu sukayi fitsari
suka kwanta sannan tafito takora Samarin boys quarters wurin Ƴan uwansu maza inda
matan kuma tace suma suwuce É—aki su kwanta dare yayi. dukda cewa Maman Rabi'u
macece me son abun duniya dakuma ruling mijin somehow,hakan besa tayi wasa wurin
bama yaranta tarbiya mekyau ba,they always respect their elders hakanan duk abunda
taÉ—aura su akai shi sukeyi. Tsaye take akansu sosai wurin ganin they always behave
wanda wannan na É—aya daga cikin abunda yasa Kawu idrissa kesonta dakuma kaunarta
daga ita har Ƴaƴan nasu.
Sanda tashiga ɗakin haryayi shirin kwanciya shikam, ƙarasawa tayi bakin gadon
tazauna tareda faÉ—in "Sannu da dawowa Baban Rabi'u" Kawu idrissa yamikar da
kafafunsa sosai akan gadonsa sannan yace "Yauwa sannu" tace "Yau naga baku dawo
dawuri ba harma nayita ƙiran layinka inji ko lafiya bansameka ba" murmushin yaƙe
Kawu idrissa yayi sannan yace "Munacan gidan rasuwar ne ana tattaunawa kan batun
inda Rukayya zata zauna seyanzu muka gama shine muka taho gida" aitunda Maman
Rabi'u taji an anbaci sunan Rukayya kuma hankalinta yakoma kan maganar dungurugun
tace "toh yanzun yakuka kare?wace magana kuka tsaida?" Kawu idrissa yace "suka
tsaida dai danni kwata kwata tunfarima ƙin ɗaukan shawarata akayi dana bada
shawara" kwafa Maman Rabi'u tayi sannan tace "Sani ne dawannan aikin koh?" Cikin
sauri Kawu idrissa yace "Aikuwa kamar kinsani. Shine yafara magana ma" Maman
Rabi'u takyabe baki sannan tace "nasan za'a rina ai. wato shi yanaganin yayi kuÉ—i
yanason yanuna yafi kowa sanin yakamata. Toh yanzun mekuka yanke? ShiÉ—in meyace
daman?"
ÆŠan numfasawa Kawu idrissa yayi sannan yabata labarin duk yanda sukayi acan gidan
rasuwar kafin daga karshe yafaÉ—a mata cewa sunyanke hukunci Rukayya zata zauna
agidan sa. aiko ko rufe baki bekai gayiba Maman Rabi'u ta katseshi tahanyar cewa
"Waaaa? Rukayyan ne zata zauna agidannan?toh wallahi bazata sabuba Baban Rabi'u!
kakuwa san mehakan ke nufi?" Girgiza matakai yayi alamar A'a sannan tace "indai
Rukayya zata zauna agidannan toh tabbas burin mu bazai taɓa cika ba danbayan fitar
ka dasafe Hajiya Jummai tazo munjemu wurin boka kuma nafaÉ—a mishi komai and he told
me bamatsala komai zaitafi yanda akeso anma karmu yadda mubarta agidanmu,inda so
samune ma karmu zauna da ita agari É—aya inbahaka ba akwai consequences. Dan akwai
wanda already yana cikin rayuwarta yanzu haka and he can go to any length for her
happiness,he's her soulmate,bashida burin daya wuce yafaranta mata hakanan babu
abunda bazai iyayima wanda yace zai kuntata mataba kuma har tambayarshi nayi akan
yaron anma seyace min daya duba fuskarshi is not visible hakanan ko iskanunshi sun
kasa gane wanene shi. Kuma mahaifiyar sa a tsaye take wurin yimasa addu'a bare suce
zasu iyayi masa wani abu shiyasama abunda bazai yuyu ba kar afarashi Baban Rabi'u"
Kawu idrissa yace "ikon Allah toh wanene wannan yaron haka damu bamu sanshi ba?"
Maman Rabi'u tace "Nima bansaniba Baban Rabi'u kuma in akwai wanda yakamata yasani
aikune tunda kukuke ganin yarinyar kullum" Kawu idrissa yace "nidai ban taɓa cin
karo da wani yaro daban dasunan yazo ganin Umar tahanyar Rukayya ba. Kuma shi bokan
bece miki acikin dangi yaron yakeba?" Girgiza kai Maman Rabi'u tayi sannan tace "be
faÉ—amin ba gaskiya" Kawu idrissa yace "toh shikenan zantambayi Adamu inji koyasan
yaron" Maman Rabi'u tace "nifah duk wannan baya gabana Baban Rabi'u. damuwana shine
asan yanda za'ayi acanza maganar Rukayya zatazo gidannan. kanadai gani tun ba'aje
ko'ina ba har kaninka yafara nuna shine sama dakai sabida yafi ka kuÉ—i. Wai dan
feleke da bushewar idanu har Sani ne zaka kawo shawara yace naka baiyiba nashine
dede" ajiyar zuciya Kawu idrissa yayi sannan yace "toh yanzudai miye abunyi dan na
riga na amince musu kan zanrike Rukayyan kuma gobe zanje in É—auketa" Maman Rabi'u
tace "kawai goben karkajeka,kosun kiraka kada ka daga" Kawu idrissa yace "ai wannan
kuma ba solution baneba dan kobanjeba za'a iya kawota har gida" Maman Rabi'u tace
"kadaiyi musu hakan insun kawota gidan seka fito barau barau kanuna kaifa bakason
riketa sannan kaja Adamu kutafi kasuwa gobe kokaturashi GiyaÉ—e yimaka wani aiki
yanda bazaisan me ake cikiba danshikam uban Ƴan tausayine yanzu seya ɓata mana
budget bayan kuma kuÉ—in nan harda shi zai amfana in akasamu cigaban tunda kominku
tare yake" Kawu idrissa yace "toh shikenan hakan za'ayi. Kawai ma zanturashi Kano
sarin kaya gobe"
Aikuwa hakan akayi. daman da É—aya daga cikin yaran shagonsu gobe zetafi Kano yi
musu sari sekawai yakirashi yace yabari kawai zai tura wani inda bayan sunyi magana
yakira Kawu Adamu awaya yacemasa ai yaron shagon nasu babu lafiya yanzu yakirashi
sabida haka yayi hakuri shiya shirya yatafi kanon gobe da sassafe In Allah yakaimu
darai da lafiya. Dukda tafiyar tazoma Kawu Adamu abazata beyi ma Yayan nasa
complain ba,aganinsa ya Isa dashi shiyasa ya aikeshi barekuma ma da abun yazo da
zancen cewa dukansune suke benefiting daga kasuwancin danhaka tun adaren yasanar da
iyalansa yakuma fara shiri inda washegari da sassafe yakama hanyar Kano.
Sorry. I know it's short but insha Allah zakujini gobe.
*Page Twenty Five*
***
Yau tunda garin Allah ya waye su Gwaggo Suwaiba keta aikace aikace acikin gidan.
daga su kimtsa nan sesu kimtsa can,seda suka kalkale ko'ina agidan yayi tasss
sannan suka tattara duka kayyakin dasukasan in an ajiyesu a afili zai iya ɓaci
kosamun mishkila kafin suka fara shirin tafiya GiyaÉ—e kuma,kowadai jiki ba daÉ—i.
Nikuwa daman tundaren jiya nace muku sun kimtsamin kayayyakina hakanan bayan Gwaggo
Suwaiba tayi wanka ta matsamin nima nayi,acewarta kada Kawu idrissa yazo É—aukana
banshiryaba. hakadai nadaure nayi wankan nashirya cikin wata kodaddiyar rigata da
yawanci daman agida nake sakashi insha iska. Koda Gwaggo Suwaiba taga irin kayan
danasaka taso tayi magana anma se Gogode ta kwabeta,tace tabarni inyi duk yanda
nakeso,i'm not In my right self,abunda yadameni ma ya'isheni. Tace "zataji da
rashin da akayi mata ne dakuma hanata binmu da akayi ne kokuma zataji da naki mitar
ne? Kowani kaya tasaka kibarta tunda ba tsirara take yawo ba kumama inbanda abunki
ba gida zatajeba? miye amfanin ace seta saka Kaya mekyau?" Itadai Gwaggo suwaiba
batakuma cewa komaiba dan koni nalura tundaren jiya Gogode a hargitse take,gabadaya
ita hukuncin da akayanke beyimata ba. Toh anma yazatayi?"
***
LamiÉ—o da plans É—insa na tafiya Bauchi yakwana arai hakanan koda yaje sallar
asubahi sedayi sporting sahun da Hafiz yazauna kafin shima yaje yajona nasa sahun
abaya dan Hafiz É—in yariga shi zuwa masallaci yau. Ana idar da sallah kuwa yadinga
lura da sashin da Hafiz É—in kezaune dankarya zo yatafi besani ba. Allah yagani kuma
bayida niyar sake wahalar zuwa gidansu yauma danhaka yanaganin Hafiz É—in yatashi
yafice yayi sauri yabi bayansa.
Awaje suka haÉ—u suka gaisa sannan LamiÉ—on yace masa sujesu gidansu,hararanshi Hafiz
yayi sannan yace "kaman ya inje gidanku? Mezanje inyi maka?" LamiÉ—o yamarairaice
fuska sannan yace "about our deal mana Hafiz" Hafiz akafule yace "toh deal É—in da
asubahin nan za'ayi shi tsantsan jaraba da takura ne kawai irin naka? Ko angayamaka
Sarkin saurarata zaiyi da asubahin Allahn Nan? Waikai miye matsalarka ne? Kabari
karfe tara tayi ashiga fada mana tukun" LamiÉ—o yace "Eh ai karfe Taran daman zakaje
Fadan but before then Inason muje gida muzauna mujira lokaci yayi dannasan Inna
barka katafi gida toh kafin kadawo ma wani aikinnne" Hafiz yasaki baki sannan yace
"toh wallahi baka isaba. Ni bacci nikeji kuma bazan hana kainayin abunda raina
yakesoba sabida kai" LamiÉ—o yace "toh ni nahanaka yin barcinka ne? Muje gidanmu
sekayi baccin acan" girgiza kai Hafiz yayi alamar beyarda ba yanashirin magana
LamiÉ—o yayi sauri yaja hannunshi yana faÉ—in "muje pleaseee! Inma katifata kakeson
inbaka kakwanta akai kai kaÉ—ai zanbaka for today dai kam" Hafiz yace "Aikuwa tunda
kafaÉ—i haka toh bazaka kwanta akai É—inba" LamiÉ—o yayi dariya sannan yace "naji.
nayarda. Mujemu" aikuwa kamar yanda Hafiz yace tunda LamiÉ—on dakanshi yace zaibar
masa katifar seya barmasa toh adole seda yasashi yabarmasa É—in shikuma yakwanta
akan sallaya. Aikuwa Hafiz yasha takura,dan minti minti LamiÉ—o ke tashin shi yana
cemasa suje su leƙa ko Sarki yafito fada.
Daga karshe dai dole Hafiz yahakura da baccin suka koma yin hira har taran safen
tayi. Tashi LamiÉ—o yayi yayi wanka yashirya sannan suka fita inda shi ya wuce tasha
ayayinda Hafiz kuma yanufi Fada don aiwatar da plan É—insu.
Sanda ya'isa Fadan Sarki bejima da fitowa ba don haka Fadawa da dagoraye basu
barshi yashigaba harsaida suka gama gaggaisawa atsakaninsu,suka É—an tattauna akan
al'amurorin masarautar sannan aka fara bama masu son ganin Sarki izinin shiga É—aya
bayan É—aya har aka iso kan Hafiz. Hafiz jiyayi gabanshi yayi wani mugun faÉ—uwa
Sanda wani dogari yazo yabashi izinin shiga yaga Sarki hakanan yakejin dama bezoba
dan seyanzu yakejin kamar he's not sure of his decision tunda baisan mai hakan zata
haifar ma LamiÉ—o ba. Anma daya tuna irin alkawarin dayamishi kuma ya tabbata by now
yanacan Tasha yanajiranshi yasa yatashi yashiga fadan kawai.
Da sallama ya ƙarasa kan shimfidar kafet ɗin da Fadawa ke zazzaune kai ayayinda
Sarki ke zaune kan throne ɗinsa,har ƙasa ya tsuguna yagaida Sarki sannan yagaida
Fadawa suma. É—aya daga cikin Fadawan ne yace "Yaya sunanka Yaro?" Hafiz kanshi na
ƙasa yace "sunana Hafiz Baba" bafaden yace "toh Hafiz,kozamu iya sanin menene
matsalarka?" cikin sauri Hafiz yace "banida matsala Baba. Labari nakawoma Sarki"
Bafaden yagyara zama tareda É—an numfasawa sannan yace "toh munajinka. wace irin
labari ne kakawo haka?" Seda Hafiz ya danyi Jim kamar bazaiyi magana ba sekuma yace
"Labari akan wanda ya shigo masarautarnsn ranar da darene,naji kunce zaku bada
kyautar dubu goma gaduk wanda yazo yafaÉ—a muku kowanene yashigo masarautar adaren
ranan" cikeda zakuwa wani Bafade apart from wanda yake tambayar Hafiz É—azu yace
"kasan Barawon ne?" Hafiz yace "nasandai wanda yashigo É—in anma ba barawo bane
gaskiya" wannan karan Sarkine yayi gyaran murya sannan yace "Wanene shi? kuma
kamarya ba barawo baneba bayan an tabbatar min da cewa tsallakowa yayi ta katanga?"
Hafiz dahar lokacin kanshi na kallon kafet yace "Eh ba barawo bane Maimartaba.
abokina LamiÉ—o ne É—an gidan marigayi Sarkin dawakai. Ranar daya diro É—in anagobe
zamuyi jarabawa ne,toh munjima a makaranta muna karatu bamumasan harlokaci yagota
irin hakaba kuma gashi babu wayoyi ahannun bare musan lokaci harsaida muka baro
makarantar sannan muka ankare da dare yayi sosai ganin babu movement acikin gari
ahakadai harmuka karaso Masarautarnan mukasamu a rufe. Toh yasan kukuma dokace
agurinku ba'a buÉ—ema kowa gate in sha dayan dare yawuce sannan yasan ba lallai
koyama dogaraye bayani sukarbi uzurinsa ba shiyasa yace zedira ta katanga kawai.
Toh Kuma jiya senaji anabatun kunsaka kuÉ—i akan anemo wanda ya shigo daren ranar
inda nikuma tsoron kada wani yaganshi ranar yazo yafada ayanke mai hukunci yasani
zuwa in faÉ—i gaskiya. Kuyi hakuri don Allah" wani Bafade yace "wannan ba huruminka
baneba tunda kazo kafaÉ—a shi LamiÉ—on inya shigo hannu zeyi bayani" Hafiz nashirin
sakeyin magana wani Bafade daban yace "tashi katafi" harya tashi ya Isa bakin kofa
zaifita Sarki dakansa yakirashi yadawo sannan yasa É—aya daga cikin fadawan yabama
Hafiz kuÉ—i.
Har Bafaden yafara korafin ai tunda ance ba sata yayi ba babu amfanin abashi kuÉ—in
anma se Sarkin yace "Eh abashi tunda su sukayi alkawarin bama kowanene yazo yabasu
labarin wanda yashigo masarautar adaren ranar" haka aka É—auki dubu goma akabama
Hafiz yayi godiya sannan yatashi yatafi hakanan yanajin sanda Sarki yake bada
umarnin aje anemi LamiÉ—o aduk Inda yake cikin masarautar a tahomai dashi.
Lumshe idanu Hafiz yayi yana tunanin ya Umma zata É—auki labarin in akaje har gida
akasameta da wannan labarin.
Ahakadai yatari napep yatafi Tasha,besha wahalar samun LamiÉ—o ba dayake straight
inda ake hawa motar bauchi yayi,nan yaÉ—auki dubu goman da aka bashi yabashi sannan
yasanar dashi yanda sukayi da mutanen Fada.
LamiÉ—o jiki sanyaye yace "thank You Hafiz and bakomai, karka damu I'll surely come
back and see them. Yanzudai damuwana shine inka koma kasanar da Umma natafi bauchi
tunda kaga sanda muka fito baswa gida suntafi islamiya dukansu kuma bamuyi sallama
ba kafin suka tafi. And please kayi mata bayani kamar yanda kama Ƴan Fada indai har
anje gida nemana. Anma karka nuna mata kaikakai karana please! Banason Umma tadinga
kallonka da abun" Hafiz yace "toh shikenan. Safe journey" 5k LamiÉ—o yacira yamika
ma Hafiz yana faÉ—in karike wannan nakane.
Hararanshi Hafiz yayi sannan yabar gurin batareda yacemai komaiba, LamiÉ—o murmushi
yayi taredabin abokin nasa da kallo sannan yasaka kuÉ—in cikin aljihun wandonsa
aransa yana faÉ—in "zama ka karba ne dole. baridai Allah yadawo Dani lafiya".
Karfe goma da rabi tagota sosai kafin motar su LamiÉ—o ta daga zuwa Bauchi.
***
Har Sha É—ayan safe babu wanda yazo a tsakanin Kawu Adamu da Kawu idrissa dasunan
É—aukana hakanan basu turo wani daga can gidansu ba. Kawu Sani kuwa tun sassafe yazo
ya sallami su Gogode yawuce office,acewarsa in Kawu idrissa ko Kawu Adamu sunzo
zamu saukesu a tasha kafin muwuce gida. Gwaggo Suwaiba dahar tafara gajiya dazaman
jira tace "toh wai meya hana Yaya Idrissan zuwa har irin wannan lokacin ne?" Gogode
tace "Allah ne kaÉ—ai masani. Kodai yamanta ne toh?" Cikeda mamaki Gwaggo Suwaiba
tace "wani irin mantuwa ne haka ni Suwaiba? toh kodai kawai zamu tari adaidaita
mubi mu ajiyeta acan gidan daganan mu muwuce Tasha kawai" Gwaggo Larai dake zaune
gefe tun É—azu batace komai ba tace "inmuka fita sukuma suka zofa?bagwanda mudan
kara jiraba" Gwaggo Suwaiba tace "toh shikenan bari mu É—an kara jiran mugani" anma
har karfe É—aya babu alaman ko É—aya daga cikin su biyu. Ran su Gwaggo suwaiba
bakaramin baci yayiba ayayinda nikuma daÉ—i abun yamin dankuwa nagama tsara plan
É—ina kancewa zanyi convincing É—insu sutafi dani kawai anma semun shiga adaidaita.
Gwaggo Suwaiba tashi tayi daga zaunen datake tana faÉ—in "toh Larai. yanzudai kam
bana tunanin zasu zo É—in,kilan aikine yamusu yawa kokuma sunmnta din kamar yanda
kukace. Muyi salla azahar kawai muje bakin titi mutari adaidaita sahu yakaimu can
gidan su Yaya idrissan mu ajiye Rukayya semu wuce tasha"
Gogode tace "hakan ma yayi"
Su Gwaggo Suwaiba sun idar da sallah kenan zasufara fidda mana kayayyakin mu waje
mukaji sallaman Yaya Fahad.
Kusan atare Gwaggo Suwaiba da Gogode suka amsa sallamar tasa. sanye yake da kananun
kaya dasuka matukar amsar jikinsa hakanan tunda suka amsa sallamartasa yashiga taku
cikin sassarfa har ya iso inda suke zazzaune kan tabarma,yatsuguna daga gefe, cikin
nuna girmamawa yace "Ina wuninku?" Su Gogode suka amsa da "lafiya lau" sannan suka
tambayeshi mutanen gidansu yace duk kalau suke daganan kuma se wurin yadauki shiru
babu wanda yakuma magana hakanan babu wanda yakuma yunkurin daukan kayan daza'a
fidda É—in. da alamadai su Gwaggo suwaiba na tsanmanin wani bayanine daga bakin Yaya
Fahad ɗin ayayinda shikuma yaƙi cewa komai inbanda shiru dayayi,yana wasa da car
keys ɗinsa tahanyar gurgurzasu a ƙasa.
Nidaman tunda yashigo nasamu jikin gini na rakube araina Ina addu'ar Allah yasa ba
É—aukana yazo yiba. Gwaggo Larai ne dataga babu sarki se Allah kumadai da alama Yaya
Fahad É—in ko shekara zasuyi zaune bazai ce komai ba yasa tace "Fahad daga gida
kakene?" gyaÉ—a matakai yayi ahankali.
Gwaggo Suwaiba tace "aikoh kayi sa'an samun mu dan harmuna shirin fidda kayan mu
wajenema" se alokacin Yaya Fahad yabuɗi baki yayi magana,yace "Ai Abba yayita Ƙiran
Kawu idrissa yaji kokun tafi baya daga wayarsa shine ya kirani yace inzo nan gida
induba ko kuntafi tunda ku babu waya ahannunku" Gwaggo Suwaiba tace "Muna shirin
fita kenan kazoka,Kawunanka kuwa babu wanda muka ga keyarsa tunsafe,daga Yaya Adamu
har Yaya Idrissan. nicewama nayi tunda basuzo ba kilan sun mantane muje can gidan
nasu mu ajiye Rukayya,muyi sallama dasu dakuma iyalansu daganan se mu wuce anma se
Suwaiba tace mudan ƙara jira kada mutafi kuma su suntahonan muyi sabani. Toh kaji
abunda yazaunar damu harwannwn lokacin inda daga karshe muka yanke shawarar tafiya
can gidan kawai tunda haryanzu basu zoba" jinjina kai Yaya Fahad yayi sannan yace
"toh yanzu muje inkaiku tashan koh? naga lokaci yanata kurewa kada kuyi dare"
Gwaggo Larai tashi tayi tsaye tana gyara daurin zaninta tareda faÉ—in "aikuwa daka
kyauta Fahad" Yaya Fahad bece komaiba sema tashi dayayi yanufi inda kayyakinmu suke
yafara fitarwa yanasakawa cikin mota.
Muna shiga mota Gwaggo Suwaiba tacema Yaya Fahad yafara kaimu gidan Kawu idrissa
suyi sallama dasu a ajiyeni seya kaisu tasha. Aikuwa inajin haka na fashe da
kuka,take hankalinsu yatashi suka shiga tambayata kukan menene nakeyi. cikin gunjin
kuka nace "Nima zan rakaku tashan" hakuri Gwaggo Larai tashiga bani ayayinda Gwaggo
Suwaiba tacema Yaya Fahad muwuce tasha kawai inyaso inya ajiyesu mukayi sallama se
yakaini can gidan Kawu idrissan tunda nace inason zuwa.
Shidai bece komai ba anmadai Naga yajuya kan motar tasa inda yaÉ—auki wani sabon
hanyar,da alamadai da harya nufi titin dazai kaimu unguwar su Kawu idrissan ne.
Dakyar Gwaggo Larai ta banbareni daga jikin Gwaggo Suwaiba sanda motar su
tacika,ita kuka ni kuka hakanan har motarsu tatashi tabar harabar tashan inanan
tsugune inda motar tatashi ina kuka me tsuma zuciya wanda nikaina nasan bana
tafiyarsu Gwaggo Suwaiba bane kaÉ—ai harda na tunanin irin sabuwar rayuwar dazan
tsinci kaina aciki. Yaya Fahad kuwa tun bayan dasukayi sallama dasu Gwaggo Suwaiba
daman yakoma can inda yayi parking motarsa yajingina da jikin motar yana danne
danne cikin wayarsa. ban ankara ba kawai sejin Karan mota nayi kusa dani wanda
hakan yasani É—ago da kaina daga cusashi danayi cikin cinyoyina inason ganin wace
motace tazo ta tsaya agabana and I saw Yaya Fahad.
Kallo É—aya yamin tunda muka hada idanu yaÉ—auke kansa dasauri sannan yabuÉ—e kofar
baya batareda yacemin komaiba. babu musu natashi nashige motar narufo taciki dukda
kuwa harlokacin banbar kukan danakeyi É—inba. Ko minti biyu baiyi da tada motar ba
naji yatsaya kuma anma sai ban É—ago dakaina ba hakanan bantsaida kukan danakeyi ba
don duk a tunanina wani gurin yatsaya zai karbi sako semu wuce yakaini Gidan Kawu
idrissa da banki akoma kiran gidan da *Prison* ba. Yes prison! Because I know for
sure ko wanda yake zama a prison seyafini Jin daÉ—i. Nanne nanne zanji Yaya Fahad
yatada motarsa anma shiru,tun Ina shesshekar kuka har muryana yadashe yadaina
fitowa nakoma ina sauke ajiyar zuciya tareda sakin hawaye anma still bamubar
gurinba wanda hakan yasa nafara tunanin ko wani gun yatafi yabarni cikin motar
nibanma saniba?. cikin sauri na É—ago dakaina daga cikin hijabina nakalli sashin
mazaunin driver and then I saw him,babu inda yaje yana cikin motar kuma da alama ba
yanzu zamu tafi ba tunda har mikar da seat É—insa yayi yakwanta yalumshe idanu
fuskarsa na fuskantar saman cikin motar ayayinda muryar Sheik sudaiz ke tashi daga
cikin radion motar yana karanta suratul Rahman.
Mamakin zaman me mukeyi nashigayi anma nasani ko karen haukane yacijeni bazanyi
gigin tambayarsa ba. Toh ma kona tambayar amsa zaibani? mutumin da magana ma wahala
take basa? danhaka nazame daga zaunen danake nakoma nayi mukus ajikin kofar motar
inamai cigaba da zubda hawayena ayayinda wani irin kewan Baba ke azalzalan
zuciyata.
Bayan mintuna kaÉ—an kuma se wayarsa tafara ringing inda naji yatashi zaune yayi
picking yana communicating dawanda yakirasan inda ananne naji har kwatancen inda
yayi parking motar tasa yakeyi ma wanda suke wayar and then I realized cewa zaman
jiran wani mukeyi kuma da alama tare zamu tafi dashi wanda mukejira É—in shiyasa
sanda zanshiga motar Yaya Fahad yabuÉ—e min gidan baya instead of gidan gaba.
bayan sungama wayar badajimawa ba naji anbude kofar seat É—in gaba wanda hakan ya
tabbatar min dacewa wanda zamu tafi dashi É—in ne ya'iso anma seban damu in san ko
wanene ba harwanda yashigo É—in yarufe kofar taciki.
Cikin sanyayyar murya naji Yaya Fahad na faÉ—in "How was the journey?" ayayinda yake
ƙoƙarin tada motar.
Sejin muryar Yaya Salim nayi yana faÉ—in "Alhamdulillahi Yaya. nasaka zaman jirako?
I'm very sorry motarmu tabaci a welcome to,seda aka nemo me gyara and i wanted to
call and inform you wurin ba network kwata kwata"
"Don't worry" shine kawai abunda Yaya Fahad É—in ya faÉ—a sannan yaja motar muka bar
haraban gurin inajin Yaya Salim na sakeyi masa ta'aziyar rashin Baba da'akayi
yakumayi mashi addu'a inda Yaya Fahad É—in ya amsa da Amin,nima na amsaa da Amin É—in
acikin raina hakanan inason ingaida Yaya Salim É—in dankuwa he's my only favourite
acikin cousins É—ina na garinnan anma sena kasa danayi tunanin ai bangaida Yaya
Fahad ba dazu dayajeshi gida toh yanzu Inna gaida Yaya Salim kuma mezaiyi tunani
kenan? Don haka naja bakina nayi shiru dukda inamai cigaba da tararradi nikadai
dukda kuwa wata zuciyar na rayamin aiko hausawa sunce gaida me gaisheka and besides
Shi Yaya Fahad ɗin wata magana ta taɓa shiga tsakanina dashine dazaiyi tsanmanin
gaisuwa daga gareni? kokuma haryau yayimin gaisuwar rashin mahaifina? Yes yana da
kirki kuma yana É—aya daga cikin mutanen dabazan manta playing important role
dasukayi acikin zamanmu na asibitin nan ba but one thing is for sure,komi yayi min
nida Baba yayine under instructions É—in Kawu Sani,biyayya yayima mahaifinsa bawai
don yanason yibane ba. Wanda zance ya jajirce tsakanin sa da Allah yayimin abubuwa
toh Yaya Salim ne,alokacin dayake gida hakanan zataho asibiti dan karan kanshi yazo
yaduba Baba yayita kuma comforting É—ina anma Yaya Fahad kam sede in turo shi akayi
kokuma in tare sukazo da Kawu Sani and moreover for once he never sympathize with
me. Sabida haka tsakanin sa da Yaya Salim akwai huge difference.
Tunanin dana dingayi kenan ahanyar mu tazuwa gidan Kawu idrissa da Kawu Adamu
hakanan inajin Yaya Salim nata zuba surutu shikadai amotar wanda gogan naku daga
yayi murmushi se ya jinjina kai baka taɓa Jin muryarsa and I'm very sure Yaya Salim
besan da existence dina a motarba danda yasani da dani za'ayi hiran tunda sarai
yasan halin Yayan nasa.
Akofan gate É—in gidansu Kawu idrissa Yaya Fahad yayi parking wanda hakan yasamin
tsananin bugun zuciya hakanan inajin Yaya Salim na tambayar Yaya Fahad É—in mesukazo
yi agidan.
Ahankali Yaya Fahad yace "we're here to drop Rukayya" ayayinda yake ƙoƙarin buɗe
murfin motarsa not minding how Salim É—in will react akan maganar tasa.
Cikeda mamaki Yaya Salim yace "wace Rukayya?" Ina gani yanuna masa bayan motar
atakaice wanda hakan yasashi saurin juyowa yana kallona,cikeda mamaki yace "Rukayya
daman kina cikin motar nan?" gyaÉ—a masa kai nayi ahankali ayayinda hawaye suka taru
cikin idanuna sannan nace "Eh. Ina wuni Yaya Salim" Yaya Salim cikeda tausayina
yace "Lafiya Lau Rukayya. Ya hakuri?" kasa amsamai nayi,se hawaye hakanan inajin
mutuwar Baban nadawomin sabuwa azuci gakuma tunanin zaman dazanyi agidan Kawu
idrissa. Shikanshi Yaya Salim É—in nasan yayi regretting ta'aziyar dayayi min É—in
because daga ganin yanayin fuskarshi nagane hakan. Sekawai naga yabuÉ—e kofar motar
yafita yazo yabuÉ—e kofar side É—inda nake zaunen yakamo hannuna yafito dani sannan
yatsuguna a gabana yashiga gogemin kwallana cikin sanyi yace "why are you crying?
kukan na menene kuma yau Rukayya?" cikin gunjin kuka nace "Babaaaa..." jiki sanyaye
Yaya Salim yace "kwanaki bana hanaki yimasa kuka ba? Kokin manta nace miki addu'a
zakinayi masa?" Girgiza masakai nayi alamar "a'a" banmanta ba sannan nace "toh ai
yanzu mutuwa yayi! yatafi yabarni,yatafi inda bazan sake ganin saba Yaya salim"
dukyanda Yaya Salim yakai ga daurewa seda idanunshi suka cika da kwallah.
Dakyar yayi Mastering courage yace "Nasani Rukayya! I know he's gone,nasan yatafi
yabarki,yatafi yabarmu duka a Inda muma bazama dauwamma anan É—inba,dole wataran
muma zamu bishi. Anma kokinsan ba'ason yima mamaci kuka? Anma ko kinsan babu
addu'ar datakai na iyaye ga Ƴaƴan su hakanan babu wanda yakai na Ƴaƴa ga iyayensu?"
YaÉ—an numfasa sannan yace "Wa Uncle Umar yake dashi bayan Baffa Mallam dayake
mahaifinshi inba keba? Inbakiyi masa addu'a ba wazai yi mishi? barema keda kikeda
kankantar shekarunki. You're very innocent, Allah Yana karban addu'an yara kanana
cikin gaggawa ko bakison ki haÉ—u da Uncle a aljanna?"
Cikin sauri nace "inaso Yaya Salim" Yaya Salim yacigaba da gogemin kwallana yana
faÉ—in "then karki sakeyi ma Uncle Umar kuka,gata É—aya zakiyi mashi shine kiyi masa
addu'a aduk sanda kika tuna dashi,kikumayi fatan Allah yahadaku a gidan aljanna"
Wannan Karan Nima saka hannayena nayi a idanuna Ina tayashi gogemin hawayena dukda
kuwa acikin zuciyata bandaina kukan ba,seda ya tabbatar nagyara fuskana nadaina
kukan sannan yatashi tsaye yakama hannuna muka shiga cikin gidan wanda alokacin
tuni Yaya Fahad yariga mu shigewa cikin gidan.
Akofar Kawu idrissa muka sameshi,yana zaune cikin main parlour É—insu shikaÉ—ai
gakuma ruwa da aka kawomai akan tray aka ajiye ayayinda akwatunan kayana ke ajiye
agefe. Tunda muka shigo parlourn hannun mu dake sarke dana juna kawai yakalla ya
É—auke kanshi wanda inaganin hakan ne yasa Yaya Salim sakin hannunawa sannan
yanunamin kujera yace inzauna sannan yaje É—ayan kujerar yazauna shima.
Munfi mintuna biyar azaune cikin parlourn kafin mukaji anbude kofar É—akin dake
sashin gabar acikin parlourn wanda inada tabbacin É—akin Maman Rabi'u ne and then my
heart starts beating so fast tunma kafin in kalleta hakanan jikina yashiga rawa
lokaci guda.
Aikuwa itanne tafito muna haÉ—a idanu ta watsamin wani uwar hararar dasaida nayi
regretting kallon direction É—in da take hakanan kan in akara naji ta dirar min wani
uban tsawan da harsu Yaya Fahad seda suka tsorata.
Tace "Keee!!!!!" Dole seda na Kuma kallonta tsabar irin firgitani da tsawan nata
yayi dukda kuwa har raina banso sake kallon nataba.
Tace "don Ubanki kujerar ubankine zaki wani hau kizauna min datsatsaman jiki?
Kokuma Ubanki ne yake biyamin masu gogemin kujerun da gyaramin parlourn? Kuma wani
gulman nema yazaunar dake kan kujerana yau bayan kinsan tunbayau ba na haneki dayin
hakan inkikazomin gida?"
Nidai kasa cewa komai nayi inbanda zamewa danayi daga kan kujerar inakokarin zama
akasa takuma sakarmin wata tsawar tace "Ai kasan ma banbaki izinin zama ba!fita
zakiyi kibar parlourn kijirasu awaje tunda babu sa'anki anan gurin" gyada matakaina
nayi cikin sauri kafin nafice a parlourn jikina na rawa.
Littafin Qadr na kudine. Duk maison shiga paid group ya tuntubi wannan layin
*08147722806*
*Page Twenty Six*
Rukayya nafita a parlourn Maman Rabi'u takaraso cikin parlourn tasamu É—aya daga
cikin kujerun parlourn tazauna sannan tadubi su Salim da gaba É—aya yanayinsu yagama
nuna ransu a bace yake da abunda tayima Rukayyan. Anma se hakan baidametaba danko
su É—inma she's ready to hurt them indai akan batun Rukayya tazauna agidannan ne toh
Babu wanda bazata iya bata ma raiba.
Salim ne kaÉ—ai ya iya yagaida ta fuska É—auke da É—an fara'a dukda kuwa ransa a
matukar bace yake inda Fahad kuwa ko kallon inda take yagaidata amma sebata
amsaba,shima kuma sebe damuba dankuwa inda sabo yasaba darashin amsa gaisuwartasa.
danne danne yakoma yi cikin wayar sa pretending as if bemasan abunda yake faruwa a
parlourn ba anma dazaka buÉ—e zuciyarsa kagani kokuma ka kalli fuskarsa closely dole
zaka gane ransa a matukar bace yake.
Maman Rabi'u ko kaÉ—an batayi danasanin rashin amsa gaisuwar Fahad daba tayiba
hasalima baya gabanta kamar yanda mahaifiyarsa bata gabanta. Koda can dasuke zaune
gida É—aya daman Ummi ce mutumiyarta dayake halinsu yazo É—aya. Kwata kwata baswa
jituwa da Aunty dukda kuwa she was the first wife. Ita tafara sani kafin Ummi anma
dayake da'ita tayi kishin balbalinta shiyasa nasu baizo É—aya ba,acewarta Aunty
macece me shegen girman kai danuna tafi kowa shiyasa basu taɓa shiriba take kuma
jin haushinta shiyasa Ummi nashigowa gidan tayi sauri suka haÉ—e kai suka zama
kawaye suna harkokinsu tare suka juyama Auntyn baya.
Amsa gaisuwar Salim Maman Rabi'u tayi Jin yagaidata sannan ta tambayesa lafiyan
kannensa sa da Umminsa inda yace duk lafiya Lau suke kafin kuma parlourn yaÉ—an
ɗauki shiru nawasu daƙiƙu.
Salim Jin shirun yayi yawa gashi Allah Allah yake ya'isa gida sabida gajiyar daya
kwaso a hanya dakuma dokin ganin iyayensa da su Zunnurain yasashi fara yunkurin
tashi tsaye yana cewa "toh Aunty. Muzamu wuce gida,daman munkawo Rukayya ne" Maman
Rabi'u zabura tayi kamarma tunda can batasan da zancen kawo Rukayya gidan ba.
Tace "wace Rukayyan? kuma awani gidan zata zauna?" Salim komawa yayi yazauna Jin
abunda Maman Rabi'u tace cikeda mamankin ta,yes yaji haushin abunda tayi yanzu
sannan yasan Rukayya ba ƙaramin wahala zatasha ba inzata zauna agidan anma bai taɓa
tsanmanin Maman Rabi'u zatayi questioning É—insa akan hukuncin iyayen
nasuba,atunaninsa tariga da takwana da sanin hakan anma Jin abunda tace yasashi
cewa "Su Abba ne suka yanke shawarar tazauna anan" dankuwa dukda Fahad befito
yafaÉ—a masa ba hakanan besan yasukayiba, he's very sure wannan É—in decision É—in
iyayensune.
Maman Rabi'u tace "Cabdi jam! Toh nidai bansan da zancennan ba kuma Baban Rabi'u
besanar dani ba inaganindai mahaifinka ne ya yanke shawarar sa shikaÉ—ai shiyasa
yace akawota nan" ahankali Salim yace "inaganin hakanne toh" Fahad dake zaune gefe
yanajinsu tundazu yadago kansa yadubi both Salim da Maman Rabi'un sannan yace "it
was not his decision. dukansu suka yanke shawarar Rukayya tazauna agidannan and
even Kawu idrissa knows about it. Infact he was suppose to pick her up from her
home rashin zuwansa ne yasa su Gwaggo Suwaiba sukace inkawotanan bayan na ajiyesu a
tasha"
Maman Rabi'u data zubama Fahad idanu tun sanda yafara magana tanajin kaman taje
tarufeshi da duka tace "komadai yasukayi can musu,atsakaninsu nidai babu ruwana
tunda maigidana baisanar daniba sannan inbanda rashin adalci da rashin tausayi
yakamata ace Rukayya tazauna agidannan nema? muma yaushe muka gama jida kanmu da
namu Æ´aÆ´an dahar za'ace za'akaro mana wani nauyin? Toh nidai ba'a gidanaba,kujecan
kunema mata wani matsugunin anma banan ba. ShiÉ—inma inaga kawai kawaici yayi ma
iyayen naku da akace yaÉ—auketa amatsayinshi na Babba anma ai Inza'a duba matsayi da
status dakuma capability na mutum mahaifinnakune yakamata yariƙe Rukayya ba Baban
Rabi'u ba,inkuma yaga shima bazai iyaba seya maida ta GiyaÉ—e wurin kakanninta ba
shikenan ba? Anma se azo ace za'a É—aurama wasu wahalanta bayan ubanta dayake raye
babu wanda yataimaka ma inbanda kanshi da Ƴar sa daya sani"
Har Maman Rabi'u ta rufe baki idanun Fahad nakanta,girgiza Kai yayi in desbelief
sannan yatashi tsaye yadubi bangaren da Salim yake zaune sannan yace "Salim let's
go" Salim cikeda mamaki yace "let's go kuma? Toh a Ina zamubar Rukayyan bayan ba'a
ƙira Kawu idrissa yamata confirming cewa anan gidan Rukayyan zata zaunan ba?" Fahad
boldly yakumacewa "I said let's go" sannan yajuya yanufi inda kayan Rukayya yake
ajiye yaÉ—auki wanda zai iya yabar sauran. Salim ganin abunda Yayan nashi yayi yasa
yama Maman Rabi'u sallama ya ƙarasa yaɗauki sauran kayan yabi bayan Fahad yanajin
Maman Rabi'u na faÉ—in "Allah yaraka taki gona"
Awaje yasamu Rukayya zaune jikin bango tanata shesshekar kuka tacusa kanta cikin
cinyoyinta da alama ma batasan har Fahad yazo yawuce ba. Ajiye kayan hannunsa yayi
sannan yakarasa inda take tsugune yashiga kiran sunanta.
Jin Ƙiran sunana da Yaya Salim yayi yasani ɗago dakaina na dubesa,ahankali yace
"tashi mutafi Rukayya" banyi mamakin kalamansa ba dankuwa duk maganganun da Maman
Rabi'u tayi aciki najisu karap acikin kunnena dakuma sanda Yaya Fahad yacema Yaya
Salim yazo su tafi but I never thought tafiyar dani za'ayi seda yayi magana yanzu
dukda kuwa naji Yaya Salim na tambayar Yaya Fahad É—in,atunanina tafiya zasuyi
subarni inyaso su Maman Rabi'un susan yanda zasuyi dani itada Kawu idrissan inya
dawo anma senaga sabanin hakan da Yaya Salim É—in yace intashi mutafi.
Tashi nayi jiki sanyaye nabi bayansa Ina tunanin ko Ina zasu kaini dasukace mubar
gidan Kawu idrissan?
Seda muka Shiga mota muka hau kan titi naji Yaya Salim na tambayar Yaya Fahad inda
zamuje.
Atakaice Yaya Fahad yace masa "we're going home" Yaya Salim yace "you mean she'll
stay there with us?" Yaya Fahad yace "I don't know Salim. Wannan decision É—inkuma
Abba ne zeyanke shi" Yaya Salim sauke ajiyar zuciya yayi sannan yace "toh Allah
yazabi abunda yafi alkhairi" sannan yakarada "anma banji daÉ—in abunda Aunty tayi
ba gaskiya. Aiko Uncle idrissa bece za'akawo Rukayya tazauna agidanan ba
aibaikamata tayi mana abunda tamana É—azunnan ba. I was very hurt by what she said
ganin girmanta kawai yasa nadanne ɓacin raina ban tanka mataba" shidai Yaya Fahad
bece komaiba haka Yaya Salim yadinga korafin abubuwan da Maman Rabi'un tayi harmuka
Isa gidansu.
Nidai ko kaÉ—an banyi murnan canjin da akasamu ba tunda har lokacin ba'agama yanke
decision É—in inda zanzaunaba,sun É—auko ni sunkawoni gidansu ne sabida anki karbana
awancan gidan Kuma nan É—inma babu mamaki aki karban nawa tunda daga nan É—in harcan
É—in babu wani banbanci.
Yaya Salim da Yaya Fahad ne suka shigarmin da kayana cikin gidan inda suka ajiyeshi
a main parlour wnda inada tabbacin rashin sanin sashin dazasu kaini ne yasa
kowannensu ajiye kayan anan parlourn. Inaganin kowannensu yanufi kofar mahaifiyarsa
inda aka barni tsaye nan parlourn kamar wata gunki. Nafi mintuna biyar zaune a
parlourn banga wulgawan kowaba. Yes yaune zuwana na biyu gidan anma a zuwa biyun
danayi gidannan nalura cewa wannan main parlourn ba gurin zaman ahalin gidan
baneba,baswa zama kwata kwata kowa sede yazauna a kofarsa tareda Ƴaƴansa. Jinayi an
buÉ—e kofa daga sashin arewa wanda hakan yasani kallon gurin. Yaya Siyama ce tafito
fuuuuu kamar an hankadota,sewani cika take tana batsewa ahakadai tawuce tanufi wata
kofa dazata sadaka dacan bayan gidan inda Kitchen É—insu yake da alamadai wani aikin
akasata ranta bayaso shine tafito cikin sauri rai abace. Wucewarta badajimawa ba
sega Sadiya kuma tafito Itama ta kofar tasu anma memakon naga tabi bayan Yaya
Siyaman senaga tanufo inda nake zaune.
ÆŠauke kaina nayi daga gareta sanin halinta sarai yayinda araina nake tunanin mekuma
zatace min? Yau Sadiya ne hartake kusantar inda nake?eh lallai za'ayi ruwa da
kankara yau. Sede tunma kafin ingama aune aunen danakeyi araina naji ansake buÉ—e
wannan kofar still and then I look at that direction.
Yaya Fahad ne yafito wannan karan kuma nalura tunda Sadiya taji yabude kofar
parlourn Aunty naga tayi sauri takaraso inda kayana suke tashiga kinkiman akwati
sabanin É—azu da dakyar take tafiyama wanda hakan yabani mamaki ba kaÉ—an ba anma
seban ce komaiba.
Ban ƙara cika da mamaki ba seda naji Sadiya na ƙiran sunana tana faɗin "intashi
mushiga ciki" dafari tsayawa nayi baki galala Ina kallonta harsaida tasakeyimin
magana akaro na biyu sannan narufe bakina natashi nabi bayanta bayan na É—auki
sauran kayana dake ajiye nan parlourn wanda alokacinne kuma naga fitan Yaya Fahad
daga main parlour ɗin hannunsa riƙe da bottle water wanda fitowarsa parlourn ne
yaÉ—auka a wani fridge dakenan cikin parlourn.
Koda muka shiga parlourn su Ba
babu kowa acikinsa inbanda TV daketa aiki shikaÉ—ai, É—akin da tashiga nashiga nima,a
tsakiyar É—akin naga ta ajiyemin akwatina tareda sakin tsaki sannan tazube kan gado
tana nishin gajiya da alamadai nauyin akwatina ne yagajiyar da'ita haryasata
behaving this way. Rashin sanin abunyi yasa nasamu kasan carpet É—in daga jikin gini
nazauna ayayinda natakure kaina guri É—aya ina karema akwatina dake tsakiyar É—akin
kallo.
Munanan zaune shiru babu wanda yacema ɗan uwansa cikanka har aka ƙira sallan
la'asar. Ina gani Sadiya tatashi tashiga bathroom É—insu dake cikin dakin ta dauro
alwala tazo tatada sallah sannan nima nashiga bayin nayi alwala nafito na jonata.
Na sallame sallar kenan ina addu'a Yaya Siyama tashigo É—akin. Turuuusss tatsaya
abakin kofar É—akin tana karema kayana dake tsakiyan É—akin kallo kafin tadubi
bangaren danake zaune kan carpet Ina addu'a sannan tamaida kanta kan Sadiya da
ayanzu takoma kan katifa tayi kwanciyarta tace "meye nake gani haka a tsakiyar
É—akin nan?"
Sadiya tace "Uhmmm kayan Rukayya ne mana" Siyama akafule wannan karan tace "bangane
kayan Rukayya ba? mekayan ta yakeyi a É—akin mu kuma inbanda neman a kazanta ma
mutane É—aki yayi ta tsami". Ta harari Sadiya sannan taci gaba da magana,tace "Wai
wani gwanin ne yashigo da kayanma tukun?" Sadiya tashi tayi daga kwancen datake
ayanzu tazauna a tsakiyar gadon sannan tace "Nina shigo dawasu Itama tashigo dawasu
kuma Yaya Fahad ne yace in É—auko mata kayanta daga main parlour inkawo su É—aki
sannan ince mata tashigo nan tazauna"
Tabbas kalaman Sadiya yabani mamaki because ko a wildest dream É—ina bantaba
tsammannin Yaya Fahad could say something like this ba. Kai bama ani kaÉ—ai ba,ama
kowa ban taɓa tunanin zai damu da al'amarin wani haryasaka baki yayi magana irin
haka ba anma seban nuna tsananin mamakina ba sabida wutar dake gabana ma ta'isa
tahanani yin wannan tunanin.
Sadiya nagama jawabinta Yaya Siyama tace "lallai kam. Toh wallahi badai adakinnan
ba. ÆŠakinsa ne koshi zaizauna mana da'ita dazai wani ce ashigo da kayanta,intaimako
yakeson yimata meyasa be É—auketa yakaita É—akinsa ba? dandai besan kazantar yarinyar
nan baneba shiyasa ya faÉ—i haka"
Sannan tadubeni fuska É—aure tace "kima tattara kayanki kinemi inda dare yamiki
dannidai bazan zauna É—aki É—aya dakeba Allah yagani hakanan kuma bazan iya tafiya
inbar miki É—akin ba" daganan tayi shigewarta bathroom tana kunkuni da mitar akan
hukuncin da Yaya Fahad É—in ya yanke.
Share hawayena nayi da bayan hannuna sannan natashi daga kan carpet É—inda nake
zaune. Nakarasa inda akwatina yake naÉ—aukeshi na fidda daga É—akin,nakoma naÉ—auko
sauran kayanma nafitar dasu yazamantoh yanzu suna ainahin parlourn Aunty,ma'ana
parlourn bangaren su Yaya Siyaman. Najima tsaye kusa da kayan nawa batareda nikaina
nasan yazanyi dasuba hakanan harlokacin banji motsin wani ko wurgawan wani a
parlourn nataba wanda hakan yasani fara tunanin ko Ina Aunty da *Safiya*( yayar
Sadiya,itake bin bayan Siyama) sukaje. Inanan tsaye har Yaya Siyama tafito daga
É—akinsu zata fita waje taganni.
Rai bace "auuuuu baki fitar da kayan ba?" kamar zanyi kuka nace "inazankaisu?"
dankuwa harga Allah nikaina bansan inda zankai kayan ba shiyasa natsaya
agurin,rashin mafita ne yasani tsaye gurin kamar wata dogara sannan aikoda tace
infidda kayan ai a É—akinsu ne tace batason ganina da kayan nawa bawai a sauran
guraren gidan ba shiyasa nayi mata wannan tambayar anma sena ga ranta yakuma ɓaci,a
hassale tace "bansani ba. Kidurasu a hanci na tunda ke dakikiyace" daganan tayi
ficewarta a parlourn tabarni tsaye.
This time I couldn't resist my tears,kobata sake faÉ—a min ba nasan bakar magana
tafaÉ—a min and she mean I should take my things out daga sashinsu baki É—aya shiyasa
kawai nashiga É—iban kayan nawa nadinga fitar dasu harna dawo dasu ainahin main
parlour. wani wawan ajiyan zuciya nasauke sakamakon gajiyar danaji nayi sabida
jigilar kayana danayi tayi hakanan so nake inzauna inhuta anma se wata zuciyar
tashiga rayamin "dakika bar kayan naki anan tsakiyar parlourn bakya tunanin nan
É—inma ana iya cewa kizo kikwashe su? bagwanda kifitar dasu gaba É—aya kihuta ba"
dawannan tunanin nakuma kinkimar kayan nawa nanufi backdoor É—inda naga Yaya Siyama
tabi É—azu dankuwa shine kaÉ—ai hanyar danake tunanin zanbi safely da kayana batareda
wani yayi min korafin na ajiye masa a kofar Saba.
Kusa da kofar fita backdoor É—in nahangi wata yar kusurwa acikin parlourn kuma an
lullube gurin da labule wanda hakan yasani ƙarasawa gurin dasauri naɗaga labule
senaga babu komai agurin. Hamdala nayi cikin raina sannan nasaka duka kayana agurin
namaida labulen narufe ina addu'ar Allah yasa kada wani
yagani yace indaukesu sannan nakoma can cikin parlourn nazauna kasan carpet
natakure kaina guri É—aya Ina mamakin miye dalilin dayasa banji duriyarsu Yaya
Zaheeera da Yaya Aisha ba tunda nazo ni gidan.
***
Tunda motarsu LamiÉ—o yabaro Gombe yake tunanin koya zata kaya tsakanin mutanen Fada
da Ummansa?. Kwata kwata bayason abunda zaitayar mata da hankali,damuwarshi baiwuce
yasamu su Isa Bauchi lafiya yaje yaga Rukayya da mahaifinta ba sannan yafara
tunanin juyowa Gombe yaje ya fuskanci koma wani irin hukunci aka tanadar masa a
masarautar.
Wajajen ƙarfe ɗaya motarsu Lamiɗo tasauka abakin tashar Bauchi. Lamiɗo nafitowa
daga motar yatari napep yace da mai napep É—in yakaishi general hospital. Ward É—inda
aka kwantar da marigayi Mallam Umar LamiÉ—o yanufa,abakin kofar É—akin yatsaya
yashiga knocking ahankali inda yaji muryar mace tana bashi izinin shiga cikin
É—akin. Tura kofar yayi bakinsa É—aukeda sallama ayayinda yashiga É—akin anma da
mamakinsa seyaga sabbin faces amaimakon su Rukayya,patient É—inda ke kwance kan
gadon ma macece ba namiji ba.
Tunani biyune sukazo ma LamiÉ—o sanda yaga babu su Rukayya a É—akin daya tabbatar nan
aka kwantar da mahaifin nata last week dayazo yagansu. Nafarko shine kilan
ansallamesune? Nabiyun kuma inba sallamarsu akayi ba toh may be É—aki aka canza
musu. WaÉ—annan sune tunanin da LamiÉ—o yayi aranshi inda lokaci guda kuma yakoma
tunanin toh tayaya za'ayi yasan wanne ne gaskiya acikin abubuwa biyu dayake
kokwanto akai? Take zuciyarshi tabashi amsar "kaje katambayi Nurses É—in ward É—in
mana" dawnnan tunanin yaÉ—aga kafa daniyar juyawa yafita yabar É—akin anma seyaga
daga patient har masu zama da patient É—in É—akin sun zubamai idanu suna mamakin
tsayuwar dayayi kansa yana tunanin duniya shikadai bece musu komai ba. Murmushi
yasaki tareda dafe kai sannan yace "Ohhh I'm very sorry. Ina wuninku?" Amsawa
sukayi da "lafiya Lau" sannan yatambayi mai jiki shima suka amsa da "dasauki"
sannan yamusu bayanin abunda yakawo shi É—akin dakuma canjin dayazo yagani. ÆŠaya
daga cikin matan dake dakin ne tace "Allah sarki inaganin ansallamesu dankuwa yanzu
munkai kwana huÉ—u a É—akin nan gaskiya" matar dake gefen wanda tayi maganar ne tace
"kokuma ancanza musu É—aki ba" LamiÉ—o yace "Nima tunanin danayi kenan anma dai bari
infita intabayi Nurses É—in dake ward É—innan may be sutaimaka min" atare Mata biyun
sukace "Aikuwa hakan yayi. Ka gwada tambayarsu kilan adace" LamiÉ—o yace "insha
Allah" sannan yamusu sallama yafice a É—akin bayan yayi wa marar lafiyar addu'ar
samun sauƙi cikin gaggawa.
ÆŠakin Nurses dake kusa da É—akin yayi knocking yashiga. gaidasu yayi tareda yimasu
sannu da aiki sannan yamasu describing Mallam Umar yakuma karada "ko last week
Friday I was here with them yanzu nadawo dubasu senaga new occupants a É—akin babu
su shine nace barinazo nan natambayeku kilan an sallamesu ne kokuma ancanza musu
É—aki"
Nurses É—inda gaba É—aya sunyi shiru suna sauraran bayanan LamiÉ—o haryakai karshe
sannan É—aya daga cikinsu tasauke wani wawan ajiyan zuciya tace "Mallam Umar kake
nufi Koh?" LamiÉ—o yace "wallahi bansan sunanshi ba gaskiya. Yarsa nasani,adalilinta
nazo dubashi" Nurse É—in tace "amma ai fulanin GiyaÉ—e ne koh?" Because she wants to
be sure,batason tabashi false news É—inda zaitadamai hankali unnecessarily.
Jin ta ambaci fulanin GiyaÉ—e yasa LamiÉ—o cewa "Eh sune" cikin sauri danbai manta
wani rana a field work É—insu da Rukayya tace masa mahaifinta fulanin GiyaÉ—e baneba.
Wannan Karan wata Nurse dabance tace "Kai relative É—insu ne?" Tunma kafin yasamu
damar amsawa Nurse É—in datake mai tambayoyi dafari tace "A'a they're not related
bakiji yace Ƴar Mallam Umar ɗin yasani ba" gyaɗa kai Lamiɗo yayi giving her full
assurance ayayinda yakejin kamar yaje yamatsa bakinsu su faÉ—i abunda sukeson faÉ—a
danshi mutum ne daya tsani ayita jan magana.
Jin nurse É—inda tamai magana tunfari tana faÉ—in "we're sorry to say aitun ranar
wannan juma'ar Allah yayima Mallam Umar rasuwa" yasa LamiÉ—o yin wani irin stand
still hakanan lokaci guda yaji duk wasu pulse dake aiki acikin jikinsa suntsaya
cak. sundaina aiki. He couldn't just believe what he heard hakanan yakejin kamar
kunnenshi ne yajiye masa ba daidai ba shiyasa yayi turuss yana jiran sakejin wani
labari game da mahaifin Rukayyan daban dawanda kunnuwansa suka jiye masa yanzu anma
har minti É—aya da wasu sakanni suka wuce besake Jin wani yafurta wata kalma acikin
office É—inba,kalmar da may be taÉ—an sanyaya masa rai inyajita wanda hakan yasashi
dole yadaidaita tsayuwarsa sannan yamaida idanunsa kan Nurses É—inda ke zauzzaune
sun zubashi idanu. So yake ya karanci wani abu a fuskarsu and may be by studying
their faces yasake samun wani sabon hope É—in but unfortunately fuskar tagama gaya
mishi komai,their faces says it all.
Daganan kuma seya tsinci bakinsa na furta kalmar "innalillahi wainna ilaihir
rajiun" ayayinda nurses ɗin suka tayashi suka ƙarasa tare.
Yafi mintuna biyar tsaye cikin office É—in bai kuma cewa komaiba tunbayan
innalillahi wainna ilaihir rajiun É—inda yafurta É—azu,tunanin Mallam Umar É—in kawai
yakeyi acikin ransa dakuma conversations É—inda sukayi wancan satin kafin yakoma
Gombe. Yatuno sanda yakecewa ayi masa wanka asaka masa wankakken kaya sabida ranar
juma'ace yanason yayi kwalliyar juma'a kamar kowa asamu lada tare dashi,yatuno kasa
hakurin jiran Hassan dayayi yace shi yamasa alwala yayi sallah lokaci yana kurewa.
Ashedai shikam shirin tafiya yakeyi,ashedai bayason tafiya da sallah akansa ne.
Lokaci guda se Lamido yaji idanunsa sun kada sunyi jazir,yaji wani irin tsoron
Allah na shigarsa lokaci guda and then tunanin Rukayya came into his mind.
"Kotana Ina yanzu? Koyataji da akace mahaifinta yarasu? How did she react? And what
condition is she in right now?"
Kawai seyaji bashida burin daya wuce yaga rukayya ayanzu, bashida burin dayawuce
yaganta,ya lallesheta yace mata dan Baba yamutu does not mean cewa it's the end of
her happiness,he's here for her and he'll always be tunda mahaifin nata dakansa
yace after him betaba ganin wanda Rukayya tayi sabo dashi har tasake dashiba
irinsa.
Motsa bakinsa yayi ahankali yace "Allah ubangiji yayi masa rahama" ganin harlokacin
Nurses É—in basu daina kallonsa ba. amsawa sukayi da Amin sannan sukayi masa
ta'aziya ganin how shocked he's ya amsa sannan yayi musu sallama yafice a ward É—in
baki É—aya. Bakin titi yaje yatsaya yatari mai Napep. tambayar inda zashin da mai
napep É—in yamasa ne ya tunatar mishi dacewa aishi bemasan gidansu Rukayyan ba
hakanan besan kowa acikin danginta dake garinnan ba. Solution É—aya ne yazo masa
awannan lokacin "Yaje Babban buli kawai" yes yasan zuwa Babban buli koma bayane.
Toh anma yazaiyi? tunda sukadai ne yakeda tabbacin zasu taimaka Mai yaga Rukayya
ayau. Don haka yacema mai napep É—in Babban buli zashi.
*Zakujini da dare insha Allahu*
Littafin Qadr na kudi ne,duk Maison shiga paid group should talk to me privately
via WhatsApp *08147722806*
*Page Twenty Seven*
Ahanyarsa na tafiya Babban buli yaga anata kiraye kirayen sallahn azahar acikin
garin Bauchin ayayinda wasu masallatan ma harsun shiga sallah wanda hakan yasa yana
isa Babban buli bezarce ko'ina ba yawuce masallacinsu. A varendern masallacin
yatarda su Baffa Ade nan yatsaya suka gaisa sukayi ma juna ta'aziyan rashin
mahaifin Rukayyan sannan yatashi yakarasa bakin rijiya yayi alwala sannan yadawo
yashiga masallaci yayi sallah duk jiki sanyaye.
Yana idar da sallah yawuce gidan Gogode. baisameta agida ba Rahane kaÉ—ai yasamu se
yaran Baffa idii dasuka shigo gida cin abincin rana kafin sukoma bakin aikinsu.
Rahanen ne ta É—auko tabarma ta shimfida masa anan tsakar gidansu yazauna sannan ta
É—ebo masa ruwa a kwanon sha ta ajiye agabansa kafin tasamu guri tazauna suka
gaisa,Itama yamata ta'aziya sannan yashiga tambayarta inda Gogoden tatafi.
Rahane tace "Aibata dawo daga can gidansu Rukayyan bama. Yaune muke tsanmanin ganin
dawowarta daman" LamiÉ—o yace "Allah sarki. Gashi nikuma bansan gidan ba bare inje
can insamo su" Rahane tace "Baka taɓa zuwa gidan ba kenan?" Lamiɗo yace "ban taɓa
zuwa ba wallahi shiyasa koda naje asibitin akasanar dani rasuwan nasa nayo nan
direct sabida bansan gidan nasuba. ananne kawai nakeda tabbacin zan samu mai rakani
can segashi kuma nazo Gogoden ma batanan ashe" Rahane tace "Ai itanma nasan bazai
wuce yanzu tana hanya ba kokuma tana shirin tahowa. daa ka jira nanda É—an jimawa
inbata zo ba se a raka ka kawai gudun karka tafi kuma yanzu kuyi sabani a hanya"
LamiÉ—o yace "tare da Rukayya ne zasuzo nan É—in?" "A'a batare zasuzo ba. Ita Rukayya
agidan Babban Kawunta zata cigaba da zama acan cikin garin Bauchin sabida
makaranta" cewar Rahanen.
Jin haka yasa LamiÉ—o cewa "toh gwanda intafi can É—in kawai yanzu. in Allah yasa
nasamu Gogoden acan semu gaisa inkuma bamu haÉ—u ba kawai kwayi mata gaisuwa on my
behalf dan ayau nikeson inkoma Bauchi. Kar inzauna zaman jiranta kuma inzo inyi
dare" Rahane jinjinakai tayi sannan tace "hakane kam. bari yaran nan sugama cin
tuwo sesu ƙira mahaifin nasu inze raka ka semuji" Lamiɗo yace "toh shikenan. Aina
É—auka ma baya gida dabanganshi a bakin masallaci ba sanda na tsaya yin sallah kafin
intaho nan" cikeda mamakin abunda yafaÉ—a Rahane tace "kana nufi baya gaban
masallaci tareda su Baffa Ade?" LamiÉ—o assuringly yace "bayanan Baffa Aden dai
dasauran dattawa suna gurin danhar gaisawa munyi dasu" Rahane tace "bedawo daga
shikin gari ba kenan. Ni da har inashirin aika masu abincinsa can" LamiÉ—o yace
"bedawo bakam" Rahane tace "toh shikenan barisu dubo Buba acan gidansa koshima
seyazo yaraka kawai" takarashe maganar ayayinda takalli bangaren dasu Faruqu ke
zazzaune sunacin abinci cikin *akushi* guda.
Cikin yaren fillanci tace "Wai baku gama cin abincin bane haryanzu?" Faruqu dake
sude hannnunsa yace "Nina gama Umma" Rahane tace "toh tashi maza kaje gidan Buba da
gudu kace yazo gida yanzunnan Ina nemansa" Faruqu yace "toh" sannan yatashi
yakarasa bakin tulunan ruwansu yabuÉ—e yaÉ—ibi ruwa yawanke hannunsa sannan yafice
agidan duk LamiÉ—o nabinsa da idanu. Seyaji tsaftar yaron ya burgesa kuma bayan
fitan Faruqun bada jimawa ba sauran Yan uwansa ma suka gama cin abinci suka kumaje
suka wanke hannunsu suma kamar yanda Yayansu yayi and then he realized cewa daga
upbringing É—insu ne,anriga anyi musu wannan tarbiyar tun tasowansu sabanin wasu
mutanen kauyen dayasha katari dasu arayuwarsa. Su da anci abinci an sude hannu
shikenan angama tsaftace hannun kenan,sede su ƙara gaba su cigaba da harkokin
gabansu hakanan. Ina kuma lokacin cin next meal É—in yayi haka za'azo azauna aci
abincin without washing the hand. Toh ashedai baduka aka taru akazama É—aya ba,duk
inda akasamu masuyin abu toh dole se ansamu masuyin akasarinsa koda kuwa waÉ—anda
sukafi yin marar kyau É—in suna dayawa ne still baza'arasa tsirarru masuyin yanda
yadace É—inba.
Jin shiru yayi yawa agurin gashi kuma Farouq É—in baidawo ba har lokacin. Kannen
sama tun bayan fitarsa dasuka wanke hannayensu suka bi bayansa basu dawoba yasashi
duban Rahane dake zaune kan wani É—an karamin dutsi tana tankade garin tuwo yace
"Ina dayar matar gidan? da kaman bayan ke da Gogode akwai wanda muke gaisuwa
da'ita" murmushi Rahane tayi sannan tace "Abokiyar zama na ce Dijeh. Batanan
tunsafe tatafi wani ruga dake dan gaba damu gurin wani wanzami. ÆŠan autanta ne yake
fama da ciwon agalawa shine sukaje karban magani" jinjinakai LamiÉ—o yayi sannan
yace "Allah sarki Allah yabashi lafiya" Rahane tace "Amin" adedenan Kuma Farouq da
Buba sukashigo.
Musabaha sukayi da LamiÉ—o,sukayima juna ta'aziyan sannan Rahanen tamishi bayanin
dalilin dayasa takirashin.
Buba yace "toh shikenan barina É—auko machine É—ina semu jemu can É—in. Sede kuma
karmuje kuma bamu samesu acan gidan ba yazaman toh munyi sabani" LamiÉ—o yace "Ina
kasan gidan kawunan nata?" Buba yadubi Rahane yace "nasan gidajensu duka anma yanzu
inason insan agidan wanne daga cikinsu zata zauna sabida karmuje muyita wahala
kuma" Rahane tace "Agidan Babban Kawunta idrissa zata zauna. hakadai Baffanku ya
faÉ—amin yau da safennan " Buba yace "toh shikenan bari muje can É—in" Rahane tace
"A'a kudai fara zuwa can gidansu Rukayyan. Inbaku samesu acan ba seku wuce can
gidan Kawun nan nata" Buba yace "toshikenan" inda daganan LamiÉ—o yama Rahane
sallama sannan suka fice agidan.
Sabani LamiÉ—o da Buba sukayi dasu Gwaggo Suwaiba,dankuwa acewar makocin gidan
Mallam Umar kominti goma su Rukayya basuyi da barin unguwar ba su LamiÉ—on suka iso
gidan. Dafe Kai LamiÉ—o yayi cikeda Jin haushin abun dan gaba É—aya yagama sawa
ranshi zai haÉ—u da Rukayya agidansu amma se gashi abu yazo baifaru as he wished ba.
Buba ganin yanda Lamiɗo yadafe kai yasashi ƙarasawa inda Lamiɗon yake tsaye ya dafa
kafaÉ—unsa cikin sigar son bashi kwarin gwiwa yace "karka damu zamu samesu acan
gidan Kawun nata ai" wani irin wawan ajiyan zuciya LamiÉ—o yasaki sannan yace "Allah
yasa" kafin suka hau machine É—in Buba suka bar unguwar suka nufi unguwarsu Kawu
idrissa sede koda sukaje can É—inma basuyi sa'an samun su ba. tundaga bakin gate mai
gadi yashiga yimasu tambayar wurin wanda sukazosu. Seda Buba yamasa bayanin abunda
yakawo su dakuma daga inda suke sannan mai gadin yace bari yaje yasanar da matar
gidan.
Yana zuwa yana sanar da Maman Rabi'un cewa dangin matar marigayi Mallam Umar ne
sukazo ganin Rukayya tace masa yaje yace Rukayya batazo mata gidaba kuma bazata zo
ba dan haka sutattari kafafunsu suja gaba. Mai gadin cewa yayi toh sannan yajuya
dan zuwa yasanar dasu Buba sakon da Maman Rabi'un tabashi hakanan yana jinta tana
ta mitar "tun yarinya batazo gidaba Ƴan uwanta sunfara dandazon zuwa barekuma
intazo aise kuma abunda Allah yayi. Inba ayi sa'a bama sesu maida mana gida gidan
tarban fulanin ƙauye. Toh bazai Sabu ba" daganan tajuya tayi shigewarta cikin gida
tana gode ma Allah da itadankanta ne tafito Jin dalilin sallamar me gadin nasu
abakin kofar parlourn su.
Toh abayan su LamiÉ—o ne su Rukayyan suka jesu gidan and she didn't bother to tell
them sabida gani take wannan É—in ba huruminta bane ba. Besides, Rukayyan wacece
dahar zata tsaya tanayimata bayanin Ƴan uwanta sunzo nemanta basu sametaba? Kenan
intayi hakan ma tadamu da'ita. Shiyasa ko maganar ma bata yiba.
Koda Mai gadi yasanar dasu LamiÉ—o yanda sukayi da Maman Rabi'u LamiÉ—o jingina yayi
da jikin machine É—in Buba jiki sanyaye. Yace "toh in banan suka kawota ba ina suka
kaita?" ÆŠan numfasawa Buba yayi sannan yace "Allah ne masani anma ninafi tunanin
sun tsaya awani gurine. Kilan agaba su karaso nan É—in" Mai gadin dake zaune yana
jinsu yace "kokuma gidan É—ayan Kawun nata suka kaita ba" Jin abunda Mai gadin yace
yasa cikin sauri LamiÉ—o yace "inane gidan É—ayan Kawun nata don Allah?" Mai gadi
yace "can GRA suka koma shida iyalansa. da anan suke tare damu ko wata uku basuyi
da komawa can É—inba inaga" LamiÉ—o yace "a GRA É—in tawajen Ina? Kayi mana kwatance
please semuje mudubo" Buba dake gefe yanajinsu yace "Bana tunanin Umma zatayi
kuskure wurin fadan inda za'a kawo Rukayya. Kuma nan É—in gidan Babban kawunta ne
shiyasa nakeda yakinin nan É—in za'a kawota kawaidai basu iso bane. Mu É—an jira
nanda wani lokaci inbasu zoba semuje can É—in mudubo" gyaÉ—a Kai LamiÉ—o yayi sannan
yasamu guri yazauna gefen maigadin. Hira suka É—an farayi a tsakaninsu wanda yawanci
hankalin LamiÉ—o baya kansu inbanda dube duben titin layin dayaketayi takowani angle
kozaiga motar dazatazo ta tsaya akofar gidan anma har wurin minti ashirin shiru
Babu su.
Duban Mai gadin yayi sannan yace "don Allah kanada agogo?" Mai gadin yace "akwai
acikin ɗakina" yayi maganar yana nuna Masa Ƴar karamar ɗakinsa da ke kusa da gate
É—in gidan. Tashi LamiÉ—o yayi yabuÉ—e kofar É—akin ayayinda yake duban wall clock É—in
É—akin. Biyu ta gota harda mintuna bakwai,juyowa yayi yakalli Buba sannan yace
"inaganin muje can É—in muduba kawai. Kasan yauzan koma Gombe banason inyi dare"
Tashi Buba yayi sannan yace "toh shikenan muje mudubo" Kwatancen gida Kawu Sani
maigadin yayi musu sannan sukayi sallama da juna suka tafi.
Basusha wahalar samun gidan ba sede kuma candinma se basuyi sa'an samun Rukayyan ba
dankuwa ko Shiga gidan basuyiba akasanar dasu batagidan. Zunnurain sukayi kicibis
da abakin gate shiyana shirin fita sukuma suna shirin shiga gidan. Gaisawa sukayi
sannan Buba yafaÉ—a masa kudurin zuwan su wanda akuma take Zunnurain yace musu ai
ba'anan zata zauna ba. Gidan Kawu idrissa zatazauna.
LamiÉ—o cikeda damuwa yace "dagacan muke yanzu. Ba'a kaita can ba" Zunnurain yace
"Kuma kunje can ainahin gidansu? Dandagacan ne za'a daukota akaita gidan Uncle
idrissan" LamiÉ—o yace "can muka fara zuwa makocinsu yace ai ko minti goma da barin
unguwar basuyi ba shine muka tafi can gidan uncle É—in naku nanma kuma basujeba"
Zunnurain shiru yayi nawasu daƙiƙu yana tuno sanda yaji Yayansu Fahad na waya da
mahaifinsu kan yaje can gidan yaduba in Kawunsu idrissa be É—auki Rukayya da su
Gwaggo Suwaiba ba shiya É—aukesu yakai Rukayya can gidan Kawu idrissan inyaso su
Gwaggo suwaiba kuma suwuce GiyaÉ—e abunsu. shikwata kwata bai É—auki maganar Abban
nasu akan za'akai Gwaggo Suwaiba tasha baneba,sekawai yayi tunanin kilan GiyaÉ—en
Fahad zaikaisu and it can be Gwaggo Suwaiba tace harda Rukayyan za'aje GiyaÉ—en
inyaso in an ajiyesu sesu dawo garin Bauchi tareda Fahad É—in danhaka yadubi su
LamiÉ—o yace "inaganin fah GiyaÉ—e suka tafi dagacan gidan nasu. daman yau su Gwaggon
mu zasu koma GiyaÉ—en. Toh may be sunje sukaisu sannan sudawo Bauchi" LamiÉ—o shiru
yayi nawasu daƙiƙu danshikanshi yarasa abuncewa hakanan yanajin sanda Buba yakema
Zunnurain godiya tareda yimasa sallama anma shi ko uffan yakasa cewa harsaida Buban
yadubeshi yace "yanzu yaza'ayi? Kozamu koma Babban buli zuwa anjima semu dawo?"
Cikin sauri LamiÉ—o yagirgiza kai sannan yace "inna koma Babban Buli najirasu kenan
babu batun komawana Gombe yau" Buba yace "toh miye aciki? basai mukwana abunmu ba
inyaso gobe seka koma" LamiÉ—o yasake girgiza kai akaro na biyu sannan yace "ai
kwanan ne bazai yuyu ba Buba. Agida cemusu nayi yau zan koma" Buba yace "toh basai
sai ka kirasu awaya kasanar dasuba?" LamiÉ—o yace "Banida waya" cikin sauri Buba
yace "Baffa Ade ai yanada ita,kwanannan yasayeta. Indai kasan number mutanen
gidanku seka kirasu damun koma" wannan karan murmushi LamiÉ—o yayi yana jinjina
mutuncin Buban aransa sannan yace "nagode da tayin dakayimin Buba. Nikaina zanso
inkwana dankuwa har cikin zuciyata banason inkoma Gombe batareda naga Rukayya nayi
mata ta'aziyar rashin mahaifinta ba anma sede akwai abu mai mahimmanci dayafimin
ganin Rukayyan yau agabana. I'm sorry I really have to go anma insha Allahu koba
kwana kusa ba I'll surely come back to see her" murmushi Buba yayi sannan yace "Toh
shikenan. Allah ubangiji yanuna mana lokacin" LamiÉ—o yace "Amin ya Allah. Don Allah
inkakoma katayani yima Inna ta'aziya,nasan by now takoma can" Buba yace "insha
Allahu" sannan yakarada "yanzu daganan Tasha zaka tafi kenan?" Wani wawan ajiyan
zuciya LamiÉ—o yasaki sannan yakalli gate É—in gidan Kawu Sanin kamar me tsanmanin
ganin wani abu kafin ya É—auke kanshi yamaida kan titin unguwar tasu yana karema
motocin daketa kai kawo kallo with thesame face expression sannan yasake kallon
Buba,feeling so dishearten and broken from within sannan ya buÉ—i baki ahankali yace
"Eh" Buba yace "toh muje insauke ka" gyaÉ—a kai LamiÉ—o yayi sannan yahau bayan
machine É—in.
Harsuka Isa tashan babu wanda ya'iya cema É—an uwansa wani abu. Kowadai da irin
tunanin dayakeyi aransa.
LamiÉ—o gaba-daya ma hankalinsa baya jikinsa. duniyar tunani yashiga,duniyar da
takunshi Rukayya da Umma kawai. 99%na zuciyar nason zama yaga Rukayya anma inya
tuna tahowar dayayi yau daga Gombe babu ko sallama,dakuma abunda yashuka kafin
yataho É—in seyaji gaba É—aya hankalinsa ya dungunzuma yakoma Gomben baki É—aya.
Tabbas inyace zaikwanan bekyauta ma kanshi ba hakanan bekyauta ma irin soyayyar
dayake ma Ummarsa ba and besides,Umma ce fah. His only support,the source of his
happiness and the backbone of his every success. Koda na second É—ayane bayason
ranta yabaci anma segashi yauÉ—in yayi abunda ayanzu yanada tabbacin she's really
hurt by it. Fatanshi É—aya Allah yasa abunda yayi É—in baishafi Umma da siblings É—in
saba. Ma'ana Allah yasa mutanen Fada basuyi involving É—insu ba. He just hope and
wish everything is fine at home haryakoma.
Yes Rukayya needs him right now but not the way he really want to see his Mother
and clear things up with her dankuwa ba mutanen Fada bane damuwarsa. Damuwar Umma
da tashin hankalinta shine damuwarsa ayanzu.
Tuno kalmar daya faÉ—ama Buba kafin su baro gidan Kawu idrissa yayi nacewa dayayi
"he'll come back and see Rukayya watarana" sekuma yatuno da yarjejeniyar dasukayi
da Umma kafin ta bashi izinin zuwa Bauchi ranan and then seyaji zuciyarshi tayi
wani irin mummunan faÉ—i,yafarajin something like fear,the fear of not seeing
Rukayya forever.
Sekuma yayi sauri yasa hannunshi agefe É—aya na kirjinshi,a Inda yakejin kirjin
nashi naÉ—an bugawa kaÉ—an kaÉ—an wanda ananne yatabo ribom É—inda Salma taba ma
Rukayya daya manta baibata ba last time dayazo. Cikin sauri yasa hannu yaciro ribom
É—in yana kare masa kallo and by just looking at the ribom seyaji wani irin hope
yazo masa lokaci guda,the hope of seeing Rukayya once again. Zuciyarshi tashiga
bashi "this's not the end there's something more insha Allah"
Yasan dawowarsa abune mai wuya kwana kusa anma for sure tunda yakalli ribom É—innan
yaji cewa haÉ—uwarsu da Rukayya wancan satin is not the last, there're more insha
Allah. Yes haduwarsun can be not tomorrow,it can be not the day after tomorrow,it
can be not next week,it can be not next month and it can even take a year kafin
susake haÉ—uwar but for sure zasu sake haduwan indai ana raye dayardar Allah. He'll
surely find a way and come back to her koda kuwa ba kwana kusaba.
Yes ayanzu kam Yana under control É—in Umma ne but for sure there'll come a time
when he'll be free,lokacin da badole seya tambayi Umma zaije guri ba. Ma'ana sanda
yazama namijin kansa,sanda itakanta Umman zata denayimasa kallon yaro takoma yimasa
kallon matashin ÆŠanta me yancin kansa.
Seda motarsu tacika ana haraman tafiya sannan Buba yatashi agefen LamiÉ—o yayi masa
sallama yajuya zaitafi. Harya hau babur ɗinsa zaitada ta Lamiɗo yaƙira sunansa
ahankali.
Tsaida machine É—in nasa yyi sannan yatsaya yana kallon LamiÉ—on da zummar jin mezai
faÉ—a. Karasowa inda yake LamiÉ—o yayi sannan yaciro ribom É—in cikin aljihun sa yace
"don Allah inba damuwa Incase kasamu lokaci koda cikin satinnan ne kaje kakaima
Nanaa wannan. Kace mata inji Salma kanwata and I came bamu haduba but insha Allah
I'll be back innasamu sarari" karban ribom É—in Buba yayi sannan yace "toh zankai
mata insha Allahu".
Murmushi LamiÉ—o yayi sannan yama Buban godiya kafin yaje yashige motar. Shikanshi
besan wani irin shakuwa sukayi da Rukayya ba dahar yakeyi mata irin wannan
tausayin. gaba É—aya yadamu yasan halinda takeciki anma tayaya? tunda dolenshi
yakoma Gombe yau.
***
Inanan zaune main parlour har akafara kiraye kirayen sallar maghriba bansake ganin
wulgawan kowaba wanda hakan ba ƙaramin mamaki yabani ba. anma kuma danayi la'akari
da irin son kallon yaran gidan se banyi mamaki sosaiba,senayi tunanin duka yaran
suna kofar iyayen su suna kallo ne ayayinda mazan kuma sukecan boys quarters.
Sekuma natuna da ganin Safiya dabanyi a parlourn Aunty ba. Sannan Itama Aunty
haryanzu banyi katari da'ita ba.
Take Kuma wata zuciyar tashiga rayamin kilan Safiya da Auntyn suna cikin É—akin
Aunty ne shiyasa bangansuba.
Yaya Salim kuwa banyi mamakin rashin ganin sanda yafita ba tunda akwai times É—inda
nayi spending adakin su Yaya Siyama and may be awannan lokacin ne yafice agidan
dankuwa nasan babu yanda za'ayi yayita zama acikin gida harwannan lokacin bare kuma
danasan shi mutum ne meshegen son tsilla tsilla. Baya zama guri É—aya. Sedanaji ana
kokarin tada sallah awani masallaci sannan natashi daniyar yin alwala inyi tawa
sallar nima. Harna nufi hanyar É—akin su Yaya Siyama sena tuna kashedin data yimin
É—azu danhaka sena fasa zuwa É—akin nasu nabi hanyar backdoor É—inda naga tabi É—azu
tareda tunanin may be akwai famfo acan se inyi alwalan nawa kawai.
Ina fita backdoor É—in hango Yaya Siyama nayi zaune gaban murhun da'aka hura a bakin
kitchen É—insu tana ta aikin rabon tuwo. ÆŠauke kaina nayi daga kallonta sannan
nafara duben duben surrounding É—in gurin kozan hangi tap and then I saw a building
dayayimin kama da bandaki dankuwa saman building É—inma babu roof kwata kwata but it
seems completed. Karasawa nayi wurin building É—in sannan nasa hannu na buÉ—e kofar
inda naga ashe bandakin ne kamar yanda nayi tsanmani.
Ciki nashiga nakama ruwa sannan nayi alwala nakoma main parlour nayi sallah na.
Inanan zaune Yaya Siyama tazo tayita zirga zirgan shigowa da kulolin abinci tana
kaiwa kowa nasu kofarsu harta gama tazo tawuce É—akinsu.
Wuraren karfe tara da rabi na dare sega Yaya Salim yashigo. dayake parlourn akwai
haske sosai shiyasa yana shigowa yaganni.
Fuska ɗaukeda murmushi yace "Aaaah Rukayya kece anan?" Murmushin yaƙe nasaki sannan
nace "eh" Yaya Salim yace "toh taho muje Abba nakiranki. Abunda yashigo dani kenan
daman" yakarashe maganar ayayinda yajuya yanufi kofar fita a parlourn cikin sauri
natashi nabi bayanshi nima.
Sashin dabaikai na matan gidan girmaba muka nufa. A parlour muka samu Kawu
idrissan,yanazaune kan carpet yana kallon *Aljazeera* idanunshi sanye da Medicated
glasses ayayinda trayn abinci ke ajiye gefenshi, plate da serving spoon É—in duk
uncleaned dasu da alamadai yanzu yagama cin dinner É—insa.
Sallama Yaya Salim yayi wanda hakan yasa attention É—in Kawu Sanin yadawo garemu.
Fuska sake yake kallona sannan yace "Rukayya" ahankali nace "Na'am?" alama yamin da
hannu inzo ni. Gyaɗa mai kai nayi ahankali sannan na ƙarasa inda yake zaune
inashirin zama agabanshi yayi sauri yakama hannuna na ƙarasa gefenshi sannan yamin
nuni da inzauna agefenshi. zama nayi sannan ya É—aura hannunsa kaina yana shafawa
yace "how are you doing?" Ahankali nace "fine" atakaice.
Ƴar dariya yayi playfully yana kallo na sannan yace "Ashe dai Ƴar tawa tanajin
turanci" Yaya Salim dake zaune ƙasa can kusa da one seater yana dariyar shima yace
"Ai Abba har gasa akan turanci Rukayya zata iyayi dakai kuma tacika" dariya Kawu
Sani yayi sannan yace "Allah Koh? Kace inzamuyi gasar bazanyi dawasaba. Dole Sena
shirya" sekuma suka saki dariya atare wanda hakan yasani sakin murmushin dole nima.
adede lokacin kuma Yaya Fahad yashigo parlourn kanshi sauke akasa.
Karasowa yayi yazauna gefen Yaya Salim sannan yashiga gaida Kawu idrissa.
Yace "Ina wuni Abba?" Kawu idrissa yace "lafiya Lau Son. Ya kokari?" Yaya Fahad
yace "alhamdulillah" Kawu idrissa yace "toh Masha Allah" sannan yakarada "kaje
kadauko mahaifiyar taka daga gidan Innan ne?" GyaÉ—a kai Yaya Fahad yayi sannan yace
"Eh Abba. Muna hanyar dawowa ne ma Salim yakirani yace kana nemana" Kawu idrissa
yace "auuu aina É—auka cemasa kayi zaka tafi daukotane lokacin ashe harkuna hanyar
dawowa ma lokacin" wannan karan gyaÉ—a kai kawai Yaya Fahad yayi.
Sauke ajiyar zuciya Kawu Sani yayi still yana kallon Yaya Fahad É—in sannan yace
"Wai kunje gidan uncle's É—inku dazu da Rukayya Koh?" ÆŠagowa Yaya Fahad yayi ya
kalli Kawu Sani Sannan yace "Eh Abba" Kawu Sani yace "Salim has told me everything
kuma nayita kiran shi kawun naku inji daga gareshi anma haryanzu baya daga wayana.
I don't really know what's wrong with his phone or what's wrong with him but I've
come to a conclusion that Rukayya will stay with us. Besides,danan dacan É—in duk
dayane ai,inma kuma daga baya yazo yace zaidauketan duk ba matsala baneba"
jinjinakai Yaya Fahad da Yaya Salim sukayi atare.
Ayayinda Kawu Sani yadawo da dubansa gareni yace "Rukayya Zaki zauna damu Koh?"
atake naji idanuna sunciko da kwallah hakanan inajin tambayartasa wani garangatsau
dankuwa ninariga dana gama sadakarwa banida yancin kaina tun bayan da Baba yamutu.
Ayanzu banida zabin kaina sede abunda aka dorani akai shizanyi danhaka Sena budi
Baki nace "toh" sannan nasa gefen hijabina inatare kwallar data zubomin and then I
found my self in Kawu sani's chest yana shafa bayana in a comforting manner wanda
hakan yasani sakin wani sabon kukan kamar wanda Daman jira nakeyi.
Seda nayi kukana mai isana cikin su babu Wanda yacemin ko kala harna sarara nadaina
sannan Kawu Sani yadago daga jikinsa cikin sigar zolaya, trying to lighten up my
mood yace "Kukan ya'isheki ne kokuma zaki sakeyin wani inmaida ki jikin Baba
kiyitayi harya isheki?" bansan sanda nasaki murmushi ba.
Da thumbs É—insa yagoge min guntun hawayena sannan ya sake yimin tambaya irin ta
dazu,yace "zaki zauna tareda mu koh Daughter?" gyaÉ—a mai kai nayi ahankali dukda
kuwa nasan wannan É—in bawai great news baneba.
Kawu Sani yacigaba da magana.
Yace "dagayau kiÉ—auko nan É—in gidanku ne,gidan Ubanki dankuwa nidin ubane agareki.
Dake dasauran Ƴaƴana bakuda wani banbanci agurina Rukayya hakama Yayunki" yayi
maganar yana nunamin Yaya Fahad da Yaya Salim sannan yacigaba.
With full confidence yace "we'll always support you. Duksanda kikeda wata damuwa
just consult any one of us kinji?" nanma gyadamasa Kai nayi ahankali.
Yace "good" sannan yamaida hankalinsa kan Yaya Fahad yace "toh Fahad yanzu yaza'ayi
da maganar karatun Rukayyan? Abokin ka daya taimaka mana akasama ma Sadiya
admission zai iya sake taimakawa Rukayyan asama mata Itama inyaso sesu tafi tare?"
Take Yaya Fahad yace "wallahi bansani ba Abba anma dai I'll call him inji ta
bakinshi" Kawu Sani yace "okay then. Call him please. Duk yanda kukayi just let me
know" gyadakai Yaya Fahad yayi sannan yace "toh" atake kuma Kawu Sani yadaga
wayarsa yakira Aunty da Mama Hadiza (Ummi) yace suzo susamesa a parlournsa Wanda
Jin hakan seda naji zuciyata tafara wani sabon race din Kuma.
Littafin Qadr na kudine. Duk maiso ya tuntubi wannan layin 08147722806.
*Page Twenty Eight*
Aunty ne tafara shigowa parlourn sannan Ummi. Ƙarara naga mamakin gani na a fuskar
Aunty sanda tashigo parlourn anma se tayi ƙoƙari ta ɓoye mamakin nata takaraso
cikin parlourn tasamu guri tazauna saɓanin Ummi da data shigo ta ganni seda taja
tunga tatsaya tana kallo na baki sake,harsaida Kawu Sani yamata magana sannan
takaraso cikin parlourn itama tasamu guri tazauna.
Gaida Kawu Sanin sukayi duka tareda yimashi sannu da dawowa ya amsa sannan yashiga
tambayar Aunty hidimar biki inda ananne nagane inda tajeta É—azun. ashe bikin cousin
É—inta data taso agaban kishiyar Inna(mahaifiyar Aunty) akeyi yauÉ—in. Sena fara
mamakin miyasa Siyama da Sadiya basuje suba despite being bikin Ƴar uwar
mahaifiyarsu. Anma ganin banida amsar dazan bama tambayar tawa yasani kawarda
zancen araina tahanyar saka ma raina cewa kilan sunada ƙwaƙwaran daliline shiyasa
basu je can É—inba.
Inanan zaune gefen Kawu Sani yafara yi masu magana akaina.
Yace "Daman nataraku ne duka dan insanar daku cewa Rukayya daga yau tareda mu
zatana zama insha Allah" saurin katseshi Ummi tayi tunma kafin yakarasa musu
bayani.
Tace "kaman yaya zata zauna anan? Ba agidan idriss kace zata zauna ba?" tabbas Kawu
Sani yaji haushin tambayar Ummin anma seya ɓoye bacin ran nasa yace "mun canza
shawara. Anan zata zauna damu kamar yanda nafaÉ—a" dan aganinshi bai kamata yazauna
yanayi masu bayanin abubuwan da su Kawu idrissan sukayiba. Wannan É—in tsakaninsu ne
su kaɗai and moreover bai tabbatar da cewa idrissa bayason riƙe Rukayya ba haryanzu
sannan yanada yaƙinin koda wasa ƴaƴanshi mazan bazasu taɓa faɗama iyayen su Mata
ba.
Salim bazai taɓa fadaba sabida sanin halin mahaifiyar sa dakuma irin ƙin Rukayya
datakeyi ayayinda Fahad Kuma daman shi ba mutum bane dayake shiga shirgin da banasa
ba. Auntyma kuma bazata taɓa tambayarsa ba dankuwa halinsu ɗaya da ɗan nata.
Harkokin gabanta kawai takeyi babu ruwanta da shiga harkan wani.
Tunbayan da Kawu Sani yabama Ummi amsa taÉ—auke kanta daga gareshi takai wani barin
rai bace tanata wani kumbura fuska ita adole bahaka tasoba kuma sotake tayi magana
anma tasani koda wasa tace zata sake furta wani kalma toh lallai Kawu Sanin ɓata
mata rai zaiyi akan wata ballagaza Rukayya shiyasa taja bakinta tayi shiru tareda
zubama sarautar Allah idanu.
Kawu Sani yace musu "Rukayya Ƴa ce agareni dankuwa abunda yayi mahaifinta shiyayi
ni sabida haka nake neman alfarmar agurin ku. kuma kuɗauke ta kamar Ƴar cikin ku,ku
riƙeta amana,kubata kulawa kamar yanda zaku bama Ƴaƴanku na cikin ku sekuga Allah
yabaku lada. besides,ÆŠana kowane. You never know wanda zai amfaneka in the future"
gyaÉ—a kai Aunty tayi ahankali batareda tace komaiba.
Haka yacigaba dayi musu nasiha akan falalar dake cikin riƙe maraya kafin daga
ƙarshe yamusu bayanin makaranta dayasa Yaya Fahad yanema min. Ananne naji yana
faÉ—in tunda ma akwai yayun mu acan baya tunanin zamu samu matsala acan and then I
realized ashe su Yaya zaheera duk sunyi resuming school ne shiyasa bangansuba. Yaya
Siyama kuwa tagama secondary school daman,kusan tare suka gama da Yaya Zunnurain
dan kusan sa'anni ne. wata uku kawai tabama Yaya Zunnurain É—in"
Sallamarmu yayi daga karshe inda ni, Yaya Salim da Yaya Fahad muka fice a parlourn
muka barshi da matayensa guda biyun dukda kuwa girkin Aunty ne yauÉ—in. Nafidai
tunanin akwai abunda zasu tattauna a tsakaninsu ne shiyasa Ummin bata fito ba.
Muna fita a parlourn Yaya Fahad yayi wucewarsa boys quarters ayayinda Yaya Salim
yatsaya mukayi sallama sannan shima yabi bayansa.
Tafiya nadingayi inajin yanda cool breeze ɗin filin gidan ke ratsa kowani ɓangare
na jikina ayayinda araina nakejin inama inada kwanciyar hankali. Inama ina cikin
farin ciki? da senafi jin daÉ—in whether É—innan,dahar guri zannema inzauna Ina
shaƙar wannan iskan me tsananin daɗin Ina feeling happiness ɗina tareda tuno
memories na farin cikin rayuwata.
Main parlour É—in nakoma anma yanzu seban zauna ba. Kwanciya nayi akan carpet tareda
lumshe idanuna dukda kuwa irin yunwar danake ji tana nuqurqusata
***
Motarsu LamiÉ—o na barin Gombe daman Hafiz yakoma gidansu LamiÉ—on dansanar da Umma
abunda yake faruwa incase ina Fadawan sun sameta a gida anma sebai sameta ba. Basma
da Jidda kawai yasamu kuma yana shiga gidan daman suka fara jero masa tambayoyin
inda Yayan nasu yake sakamakon tashin hankalin dasuka shiga tun bayan da Fadawa
suka zo sashin nasu.
Jiki sanyaye Hafiz yace "yatafi Gombe" baki sake Jidda tace "yatafi Gombe kuma?"
gyaÉ—a matakai Hafiz yayi assuringly.
Wannan karan Basma ne tayi magana tace "Anma baiyima kowa sallama,dankuwa basu haÉ—u
da Umma bama yau kafin yatafi" Hafiz trying to calm them down yace "yaso yimuku
sallamar unfortunately bakwa gida shikuma yana sauri yaje yadawo and moreover ai
sunyi maganar da Umma shekaran jiya kuma tabashi permission sannan abunda yadawo
dani yanzuma is to Inform you guys,shiyace inzo insanar daku sabida bayason
hankalin ku yatashi"
Jidda jitayi ranta yafara baci hakanan taji tanajin haushin Rukayya lokaci
guda,yanzu dai seda yatafi kenan? Wato shirin tafiyar tasane ya hanashi zuwa gurin
Maimunatu hartazo tanayi mata korafin rashin zuwan nashi kwana biyunnan hankali
tashe yau a islamiya.
Duban Hafiz É—in tayi sannan tace "Yaya Hafiz Fadawan dasuka zo kumafah? What were
they saying about Hamma LamiÉ—o?"
Hafiz wara idanu tayi sannan yace "yaushe sukazo?" Basma tace "yakai twenty minutes
haka" cikin sauri Hafiz yace "Umma tananan ne?" Girgiza masakai Basma tayi yace
"kenan basu sameta ba?" Basma tace "Eh" wani irin gauron ajiyar zuciya yasauke
feeling relieved sannan yace "Don Allah koda tadawo indai bata samu labari awani
guriba kada ku faÉ—a mata Fadawa sunzo please!" Jidda tace "toh wai me Hamman yayi
musu suke neman sa?" Hafiz yace "zanyi muku bayani Jidda anma first kuyimin
alkawarin bazaku sanar da Umma halin da ake cikiba" Basma tace "munyi alkawari" nan
Hafiz yamusu bayanin komai dakuma dalilin dayasa LamiÉ—o yayi hakan.
Jidda dayake daman tasan labarin tunda adaren da abun yafaru ma ya faÉ—a mata da
bakinsa yasa batayi mamaki ba koda Hafiz din yake basu labari. Abu É—ayane ya tsaya
mata arai yakuma bata mamaki. Risking kansa da LamiÉ—on yayi don kawai yaje yaga
Rukayya.
Rai bace tace "Sabida yana son zuwa yaga wancan yarinyar shine zeje yayi risking
life É—insa? Akan wani dalili? Itadin wai wacece agareshine haka?" tayi tambayar
cikeda curiosity.
Hafiz yace "she's nothing but a poor child Jidda. Rukayya abar tausayi ce da duk
wanda yake kusa da'ita yakumasan halin da take ciki dole yatausaya mata and LamiÉ—o
is one" Jidda rai bace tace "nidai gaskiya koma miyene banga dalilin dazaisa yaje
yayi taking wannan step É—inba sabida yaje yaganta kawai. Inyajedin undoing pain
É—inta zaiyi komi? Kokuma shine zaibama mahaifin nata lafiya? Tukunnan ma shibaya
tunanin halinda Umma zata shigane intasamu wannan labarin? kokuma damuwar Rukayya
tafi ta mahaifiyar sa yakeso yanuna ahakan? Toh nidai sena faÉ—ama Umma. babu abunda
zan ɓoye mata inyaso seyasan yanda zaiyi yamata bayani" Jidda takarashe maganar
adede sanda take ƙoƙarin barin parlourn.
Hafiz cikin sauri yace "Jidda dawonan" dawowa tayi tazauna dukda kuwa bataso
dawowan ba kawaidai batason yace tayi masa raini ne" ahankali yace "what will you
gain by telling Umma?" Basma da ranta yafara baci da behaviors É—in Jiddan tace
"Yaya Hafiz kabarta tasanar da Umman tunda ita batada hankali da tunani,kabarta
tatada mata hankali tasaka ta cikin damuwa" sannan tasaki tsaki tatashi tashige
ciki tabar Jidda da Hafiz É—in azaune. Yes abunda Yayansu yayi bekyauta ba kuma
dabadan batason tashin hankalin Umman ba Itama babu abunda zaihanata faÉ—a ma Umman
dankuwa babu wanda yakai ta kai report shiyasa ma LamiÉ—o baya sharring komai
da'ita,he prefer sharring his secrets with Jidda instead.
Toh anma komi zatayi setayi using common sense É—inta. Fatan ta É—aya Allah yasa
komai yazo musu da sauki. Acan parlour kuwa Hafiz ne yaketa ma Jidda faÉ—a kan kada
tayarda ta faÉ—a ma Umma. dakyar dai yasamu yayi convincing É—inta sannan yayi
tafiyar sa gida.
Aikuwa koda Umman tadawo babu wanda yasanar da'ita kuma da Allah yataimakesu se
Fadawan basu dawo ba tunda sukayi zuwa na biyu da azahar suka sanar dasu LamiÉ—on
yayi tafiya kuma bayau zai dawoba.
Ita Jidda daman haushin abunda yama Maimunatu ne yasata cewa zata fada É—in.
Anshiga sallar maghriba LamiÉ—o yashigo masarautar wanda hakan yasa dogaraye da
Fadawa basu ganshi ba hakanan yafi mintuna goma abakin kofar gidansu yana kokwanton
shiga ko kada yashiga sabida tunanin abunda zai iya tararwa acikin gidan.
Daƙyar dai yayi mastering courage daga karshe yashiga. irin rungumar da Salma tayi
masa sanda taga yashiga parlourn nasu dakuma amsa gaisuwarsa da Umma tayi fuska
ɗauke da fara'a ba ƙaramin mamaki abun yabashi ba. Amma seya ɓoye mamakin nasa yayi
wucewarsa É—aki donyin sallar maghriba ganin lokaci na kurewa. LamiÉ—o befito a É—akin
nasa ba harsaida yayi sallar isha'i. Bayan yafito É—inne kuma Umma tace Basma tazubo
musu abinci suci.
Like a happy family sukayi dinner É—insu dukda kuwa Umma da Salma ne kaÉ—ai keta
surutansu. gaba É—aya LamiÉ—o yarasa farin cikin menene Ummar tasu takeyi,dankuwa by
just looking at her face he can tell cewa tana cikin farin ciki da anashuwa yauÉ—in.
Atunaninshi ko haryanzu batasamu labarin abunda yayi ba yakamata ta ɓata rai sabida
tafiya dayayi baiyi mata sallama ba amma segashi yana ganin saɓanin hakan. Abunda
baisani ba shine a gidan bikin da Umman taje yau wata kawarta dasuke zumunci tazo
tabata labarin taga LamiÉ—o a kasuwa yana aiki kuma harcutansa akayi yayi fighting
for his right and the amaizing news is that bama kansa kaÉ—ai yayi fighting justice
É—inba harga ma talakawan dasuke taking part a irin waÉ—annan ayyukan.
Wannan labarin ba ƙaramin daɗi yayi ma Umman ba yau shiyasama koda tadawo gida
batasamu LamiÉ—on ba É—azu batanuna bacin ranta ba and besides tasan datana gida babu
abunda zai hanashi yimata sallama and moreover aidama tun shekaranjiya yanemi
izininta kuma tabashi izinin. Yes she might not have liked the idea of LamiÉ—o going
back to Bauchi amma ai bazatayi denying cewa adalilin nacin son zuwa Bauchin nasa
ba yau for the very first time in his entire life yayi earning kuÉ—i da guminsa and
for that she's grateful.
Ahakadai suka ƙarasa cin abincin nasu. Tashi Lamiɗo yayi yashige kitchen sannan
yafito zaiwuce ɗaki cikin sauri Umma taƙira sunansa fuska ɗaukeda mamaki.
Juyowa LamiÉ—o yayi sannan yace "Na'am Umma" Umma tace "Ba zaka fita yau baneba?"
gyaÉ—a mata kai yayi alamar eh sannan yace "Umma na gajine. zankwanta inyi bacci
kawai" murmushi Umma tayi sannan tace "toshikenan. Aikam kadebo gajiya gashi isowar
dare kukayi. Jeka hutan gobe kazo kabani labarin mutanen Bauchi" LamiÉ—o harya juya
zaitafi É—akin shi seya kuma juyowa yana kallon expression É—in fuskar Umman,the way
Umma is being nice abun yadameshi,yanason yasan dalili farin cikin nata don haka
yakarasa inda take zaune shima yazauna agefenta tareda kallonta cikeda curiosity.
Yace "Umma wai meya faru yau kiketa farin ciki ne haka?" dariya Umma tayi sannan
tace "shikenan se bazanyi farin ciki haka kawai ba? Ko so kake inta babbata rai Ina
kumbura fuska?" girgiza kai LamiÉ—o yayi sannan yace "bahaka nike nufi ba Umma na. I
want you to always stay happy but atleast when the happiness is overload aiyakamata
nima insan dalili intaya ki farin cikin koh?"
Wannan karan Jan cheeks É—insa Umma tayi tana murmushi sannan tace "Ina farin cikine
sabida kai LamiÉ—o. I'm happy because for once in your life kayi abun kanka"
takarashe maganar smiling very widely sannan tabashi labarin yanda sukayi da
kawarta a gidan biki yau kafin daga ƙarshe tajashi zuwa jikinta ta rungumeshi tana
faÉ—in "hakan bakaramin daÉ—i yamin ba LamiÉ—o. It makes me feel as if you're a grown
up now,inafatan zaka cigaba dayin haka. If not for the family then for yourself.
bakoyaushe bane zaka zauna kace komai se anyi maka. neman nakaima wani abune,kazama
mai zuciyan nema abune mai matukar mahimmanci ga kowani ÆŠa namiji"
Tariko fuskarsa da palms É—inta tace "dagangan nahana ka kuÉ—in tafiya Bauchi sabida
inason kaima kafara dogaro dakanka and alhamdulillah se gashi kagane hakan cikin
gaggawa kakumayi amfani da basirar ka kasamo kuÉ—in dazakayi amfani dashi" LamiÉ—o na
murmushi yace "and this's the reason why bakiyi scolding É—ina ba for going without
saying goodbye yauda safe koh?" Dariya Umma tayi sannan tace "Exactly. Amma hakan
bawai yana nufin na kyaleka baneba. I'll surely scold you later innagama farin
cikin nawa" rungumeta yayi ajikinshi still smiling sannan yace "A'a Umma kiyi min
faÉ—an yanzu inhuta kawai gaba daya" dundu Umma takai mishi agadon bayanshi
playfully sannan tace "bazanyiba. kaikasan laifin dakayi ai kuma Inka yarda kasake
repeating irin wannan laifin karya kafafunka zanyi" Salma ce kawai tatayasu yin
dariya wannan karan anma banda Basma da Jidda.
Sai da safe yayi musu sannan yawuce É—akinsa yana tuna irin farin cikin dayabar Umma
tanayi a parlour and then seya fara tunanin yanda zaiyi yatari mutanen Fadan
batareda sunzo gida nemanshi ba dankuwa bazai taɓa so yayi spoiling mood ɗin Umma
ba. Yes he desperately want to go out adaren nan anma inya tuna yana iyayin katari
da dogaraye ko Fadawan masarautar seyaji bazai iya fitan ba shiyasama yacema Umma
gajiya yayi ze kwanta yayi bacci a É—aki but after Sharring a little moment with
Umma dakuma irin farin cikin datake ciki seyaga babu amfanin buyan,dankuwa inyace
zecigaba da buyan nema zesa suzo gida neman shi don haka atake yayi deciding gobe
da sassafe zeje yayi summoning kansa a Fada and then he'll see what he can do wurin
ganin maganar bata yadu a masarautar ba bare har hakan yasa maganar yazo kunnen
Umma"
Yananan zaune bakin katifa yanata saka da warwarar abunda zece a Fadan gobe Jidda
tashigo É—akin nasa bakinta É—aukeda sallama amma gaba É—aya fuska babu walwala. amsa
sallamartasa yayi and by just looking at her face yasan tasamu labarin abunda
yafaru and may be ita dogarayen sukazo suka samu a gidan dasafe bayan Hafiz yabaro
Fads. But still se zuciyarshi tashiga tambayarshi miyasa Jidda zatayi acting this
way bayan tasan komai?why Jidda? In akwai wanda yake expecting yayi fushi dashi ko
ya ɓata rai toh Basma ce anma ai Jidda he's always got her back akomi yakeyi
arayuwarsa.
Tsayuwar datayi akanshine yasashi nuna mata gefenshi yace "zo zauna semuyi magana"
babu musu Jidda takarasa gefen shi tazauna dukda kuwa mood É—inta baicanza ba.
Kallonta LamiÉ—o yayi caringly sannan yace "meya faru Jiddodo na? Why are you
burning your face?kowani laifin nayi miki?" Yayi maganar acting as if bemayi
komaiba danya bugi cikinta.
Tura baki gaba Jidda tayi ayayinda take kallonshi cikeda tuhuma sannan tace "Yanzu
Hamma LamiÉ—o abunda kama Aunty Maimunatu ka kyauta kenan?" wara idanu LamiÉ—o yayi
hakanan cikeda mamakinta yace "Yanzu daman sabida Maimunatu kike fushi
dani?"dankuwa baikawo hakan aranshiba kwata kwata,yes yayi mamakin fushin Jidda
akanshi anma beyi tsanmanin it's something related to Maimunatu ba.
Jidda sake tura baki gaba tayi sannan tace "Eh mana Hamma LamiÉ—o. Nifa na haÉ—aku
kuma duk abunda zaishiga tsakaninku dole yayi affecting dina" murmushi LamiÉ—o yayi
sannan yace "toh naji. Yanzudai faÉ—amin menayiwa Maimunatun dahar kike fushi dani
haka?" Jidda tace "Yaufah kwanan ka uku rabon da kaje kaganta kuma kayi mata
alkwarin zuwa ranar da kuka rabu. baka ga yanda hankalinta yatashiba wallahi"
LamiÉ—o É—an dafe kanshi yayi sannan cikeda mamaki yace "ita ta faÉ—a miki haka?"
Gyadamasa kai Jidda tayi ahankali sannan tace "yauda safe take faÉ—amin a islamiya.
harda hawayenta fah Hamma. Wai gani takeyi kotayi maka wani abunne shiyasa kadaina
zuwa tunda baka taɓa yimata irin hakaba" Lamiɗo yace "she did nothing. Infact tana
raina wallahi Jidda. Abubuwane suka shamin kai shiyasa banje naganta ba" Jidda sake
tsuke fuska tayi sannan tace "wasu abubuwan ne suka shamaka kai dazai hanaka zuwa
ganin Aunty Maimunatu for an hour daikan?" LamiÉ—o yace "bakiji me Umma tafaÉ—a a
parlour baneba? Ko bakiji tafaÉ—i irin aikin danayi kwanannan ba?" Jidda tace "naji.
Anma ai aikin na kwana É—ayane kayi,you should've visited her the other days" É—an
ajiyar zuciya LamiÉ—o yasaki Jin yanda Jidda taÉ—au abun seriously sannan yace "Toh
Aunty Jidda. nayi laifi ayi hakuri. Ki tayani bama Auntyn ki Maimunatu hakuri,I'll
surely go and see her tomorrow" tura baki Jidda tayi sannan tace "Kadaije yanzu
Hamma. Wallahi tana cikin damuwa" wara idanu LamiÉ—o yayi sannan yace "bakida
hankali Koh? After All the situations so kike infita ayau É—innan?" Jidda tace "wani
situation?" Hararanta yayi wannan karan sannan yace "My issue with Fadawa da
dogaraye nasan kinsan komai" yakarashe maganar assuringly dankuwa in ita sabida
Maimunatu take fushi dashi ya tabbatar Basma sabida abunda yayine yasa take babbata
rai dashi tundazu sannan kuma babu yanda za'ayi Basma tasan batayi sharring da
Jidda ba.
Jin ya ambaci maganar Fadawa yasa Jidda cewa "yauwa Hamma yanzu yazakayi tackling
problem É—innan please? Kasan dai Umma batasani bakoh? Kuma bamwason tasani dan
hankalinta zai iya tashi" LamiÉ—o cikeda Jin dadin yanda Jidda takauda maganar yaje
gurin Maimunatu lokaci guda yace "I don't want Umma to Know either shiyasa nayi
deciding zuwa inje ingansu gobe dakaina kafin ma sudawo gidannan nemana" Jidda tace
"toh mezaka cemusu?" Ware hannaye yayi alamun baisani ba sannan yace "inakan tunani
dai" Jidda tace "toh Allah yadora ka akansu" LamiÉ—o yace "Amin" sannan cikeda
curiosity tace "anma abunda bangane ananba shine,why didn't you use the money
dakayi aiki a kasuwa kasamo?" LamiÉ—o yace "kuÉ—in bazasu isheni baneba Jidda and the
most annoying thing now is that namaje Bauchin bansamu naga Rukayyan ba. ankaita
gidan kawunnanta because her Father is death jiddahhh!" LamiÉ—o yakarashe maganar in
dismay.
Duk yanda Jidda takejin haushin yanda LamiÉ—on yadamu da Rukayya seda taji jikinta
yayi sanyi lokaci guda ahankali tace "Allah ubangiji yayi masa rahama" LamiÉ—o yace
"Amin" sekuma ɗakin yaɗauki shiru naɗan wasu daƙiƙu.
Jidda ganin kamar LamiÉ—on yafaÉ—a duniyar tunani yasata cewa "toh yanzu dai Hamma
inma bazakaje gurin Aunty Maimunatun ba katura mata ko letter dazai É—an sanyaya
mata raine please" LamiÉ—o dan kallonta yayi ahankali sannan yace "ta'ina zan tura
mata letter É—in? Kinsandai babu maibarin ku kufita a gidan nan dare yayi sannan
banida wayar kiran Hafiz bare har inbashi sakon yakai mata. Yauda goben duk É—aya ne
ai in Allah yayarda. I'll go see her bayan nagama solving issues da mutanen Fada. I
missed her too" yayi maganar sincerely and then se hakan yaÉ—an kwantar ma Jidda
hankali atleast she now knows cewa haryanzu Hammansu nason Maimunatu bawai fita
aranshi tafarayi ba.
***
Tunda nadawo parlour samun guri nayi nakwanta awata kusurwar da seka shigo tsakiyar
parlourn sosai tukunnan zaka ganni. Yunwa nikeji sosai dankuwa rabona da abinci tun
safe anma ko karen haukane yacijeni bazan tambayi kowa agidan abinci ba dankuwa for
sure I know the outcome hakanan tsoro nakeji inje kitchen indiba dakaina yazame min
wani matsalar kuma.
Kawai sena tsinci kaina Ina tunanin mutanen gidan baki É—aya da halayensu ko Allah
zaisa in iso kan me sassauci acikinsu and may be and may be I can rely on that
person through out my stay in the house dankuwa zama da yunwa bazai yuyu ba.
Kawu idrissa mutum ne mesanyi hali da dattaku tun acan baya danasanshi daman.
Sannan bayida nuna banbaci. Kulawar dazai nunama yaransa toh irinshi zai nuna ma
Ƴaƴan yan uwansa shidai kawai kabarshi da ra'ayi tareda yin abunda yasaka agabansa.
tunda kawunaina dasu Baba suka tare a Bauchi bada jimawa ba bayan kowa yafara
kasuwanci Kawu Sani yafara furthering education É—insa. dafarko kwata kwata cigaba
da karatu baya cikin yan kayanshi anma dayazo yafara sabawa da garin Bauchi,yake
ganin yanda mutane kesamun cigaba, dakuma irin mutanen dayake interaction
dasu,dakuma irin shawararwarin da abokanan kwarai suke bashi seyaji he needs to
achieve something more,seyaji ba kasuwanci bane kadai goal dinshiba,Seyaji yanason
yazamantoh ya kware akowani fanni,ma'ana a both kasuwancin dakuma harkar karatunsa
tayanda zai nutsa cikin gwamnati sosai wanda hakan ne yasashi fara pursuing
education É—insa. Daman diploma yayi tun asali,Kawu idrissa ne kaÉ—ai yayi degree
acikin su daman awannan lokacin.
DE yacika yanemi admission a ATBU Bauchi dayake result É—inshi nada kyau babu wani
ɓata lokaci suka bashi admission aji biyu(level 2). Bussiness administration yayi a
diploma so daya cike DE É—inma shiyasake nema and it turns out shiÉ—in suka bashi.
priority sosai yabama karatun nashi dankuwa iyalinshi bakaramin takura sukayiba
adalilin hakan dukdadai dede gwargwado yanayi masu kome,rashin godiyar Allah dakuma
hangen nasama dasune yasa suke kallon kamar bayayi masu É—in,suke ganin kamar
kuÉ—insa dana kasuwan cinsa akan karatunsa yafi tafiya.
Kawu Sani nagama degree yajona Masters bayan yagama master É—inne kuma yasamu aiki a
bank of industry as a normal employee inda acikin hakan ne kuma yakeyi PHD É—insa.
Yanda yakeda so much dedication da hardwork yasa yana gama PhD dinnasa bada jimawa
ba aka bashi managing director na bank of industry din sakamakon retire da tsohon
MDn yayi kuma shine yabada sunanshi as his candidate sekuma yaci sa'a da akayi
bincike akanshi se akaga babu wanda yakaishi deserving wannan position É—in.
Ayyuka sosai ne suka karuma Kawu Sani anma hakan kosau ɗaya be taɓa sashi Jada
bayaba kokuma nuna gajiyawarsa and besides yana earning yanda yakamata, kuÉ—i suna
shigo masa sosai fiyeda da gakuma uwa uba expenses na wasu abubuwan amfanin gida da
bank É—in ta É—auke masa. Kamar irinsu NEPA Bill,subscription na TV, biyan kuÉ—in
ruwa,petrol É—in sakawa a generator dakuma man da akesama mota na zirga zirgan both
aikin bank É—in dana gida.
Sannan ko wata uku baiyi dafara aikin ba suka bashi dankareriyar gida anan cikin
GRA dake cikin garin Bauchin wanda wannan dalilin yasashi parking shida iyalansa
suka dawo gidan. Gidan da ko kwabonsa besaka acikiba danharta furnitures Bank of
industry É—inne suka saka masa aka kuma bashi sabuwar mota dal wanda hakan yasashi
bama Fahad motar sa tada dayake fafutuka dashi inda Aunty kuma tasa Fahad É—in
yasaida wannan É—in tayi masa ciko yasayi sabuwa. Dukda sudden canjin rayuwar da
Kawu Sani da familyn sa suka tsinci kansu aciki hakan besa yamanta old self É—inshi
ba hakan kuma besa yasakar ma Ƴaƴansa maraba,acewarsa wahala yasha harya samu
yazama abunda yazama yau É—in toh sudinma hakan yakeso suyi,yanason sucigaba da
rayuwa irinta talakawa kokuma yace middle class sabida koda sun tsinci kansu acikin
wani hali in the future bazasu Sha wahalar adapting to new halin da suka tsinci
kansu acikiba,aganinsa rashin shagwaɓa yaro dakuma rashin bashi complete Jin daɗin
rayuwa shizaisa yazama abun kansa,yakumayi zuciya yayi abunda yadace shiyasa haryau
Ƴaƴansa dake primary dakuma masu zuwa Islamiya da school bus suke zuwa su dawo
islamiya kuma suje da napep sudawo da napep.
WaÉ—anda ke boarding ne kawai yafara bari akaisu da motar gida dawowan kuma Allah ne
kaÉ—ai yabarma kansa sanin zebari É—in kobazai bariba tunda tun tafiyarsu haryau
basuyi hutunba. Me aiki ma yahana a É—auka aganinsa tunda yanada gandara gandaran
Ƴan mata a gida babu amfanin masu aiki,they should learn,they should do it
themselves tunda bawai karfin yi É—inne basu dashiba bakumawai dama basu iya baneba
tunda tunda daÉ—in su sukeyi. Abunda yasa yayi hakan kuma dukwai don tunanin irin
gidan auren dazasu faÉ—a agabane,babu wanda yasan irin wanda zasu aurs hakanan babu
wnda yasan karfin family É—inda zasu tarda kansu aciki shiyasa yakeyi masu irin
wannan tanadin. Shiyasa yakeson Ƴaƴansa su taso da tarbiya mekyau tayanda ko Ina
suka shiga babu Mai aibatasu anma sede besan ainahin abunda ake toyawa agidan
ba,bekuma duba yanayin iyayensu Mata ba dankuwa dukyanda kaso gayima Æ´aÆ´anka
tarbiya dole seda hadin kan iyayensu mata sabida sune closest to them.
Anma se gashin shidin beyi sa'a ba. Dankuwa matan nashi biyu kowacce da nata
biggest flaws É—in.
Aunty itace first wife É—in Kawu Sani,she came from an extended family kuma
familynsu irin family É—innan ne dasuka yarda da dogaro dakai despite yawansu,babu
wanda yake relying akan wani sede irin É—an abunda ba'a rasaba. Kowannensu dayakai
maturity age zakaga yana da abunyi na hanyar samun É—an taro da kobo. Yes suna Boko
anma neman kuÉ—insu yafi bokon yawa,dan dayawansu kosunyi bokon toh zakasamu sun
watsar da certificate É—in sun koma harkar kasuwanci. Wasunsu kuma haÉ—awa sukeyi
duka biyun suyi lokaci guda. Sanda Kawu Sani ya auri Aunty tana level 3 ma'ana
zango nabiyun karshen gama jami'a kuma despite tafishi aji a bangaren boko hakan
bekawo wani mishikila cikin aurensu ba sabida irin sonda sukeyi ma juna kuma Koda
sukayi auren behanata cigaba da karatunta ba harta gama tunda daman tasha faÉ—a
mishi tanayin bokon ne for reference purposes kawai. Data gama kasuwanci zata
fara,Babban wansu dasuke É—aki daya yayi mata alkawarin bata jari tayi kasuwanci.
Hakan kuwa akayi dan tana karban certificate É—inta da result É—inta yayi kyau Yayan
nata yabata makudan kuÉ—i takafa nata kasuwancin.
Bussiness É—in atamfofi,laces,jakakkuna,takalma da gyalalluka tafarayi agida kuma
kan kacemi seya zamanto tana samun albarkar kasuwancin,cikin lokaci kankani abun ya
bunkasa sosai harma tafara da saida furnitures,gadaje dadai sauransu seyazamanto
she's always busy,batasa komi agabanta ba inbanda kasuwancin ta. Intana gida zaka
samu anzo duba kaya agurinta kokuma ita tafita dasu wurin masu saye danko kaÉ—an
batayi yunkurin buÉ—e shago ba. Inkuma bata gida toh ka tabbata sari tatafi yi wani
gari. Takanje cotounou,Lagos,Kano,Kaduna sarin kaya ayayinda inkuma tanason sayan
kaya a kasashen sede tabama Yan uwanta dasuke fita su saro mata dankuwa ko kaÉ—an
Kawu Sani bebata wannan damar ba itamakuma se bata damuba. Wannan rashin zaman nata
shiyasa tarbiyan Æ´aÆ´anta is somehow at stake,betafi yanda yadaceba,sukeyin duk
abunda sukaga dama agida sabida ganin batanan wani sa'in ma kotana nan É—in batacika
samusu Ido a harkokinsu ba sabida kasuwanci data sa gabanta dukda kuwa indai taga
wasu abun zata tsawatar atake.
Ko Kawu Sani yasan Aunty itace mace me hakuri tsakanin itada Ummi sannan kowani
shawara zenema itayake consulting dankuwa akwaita da hangen nesa. Abudaya tayi
lacking,rashin son zama guri É—aya dakuma rashin bama iyalinta kulawa yanda yakamata
wanda shida kanshi yayi iya bakin ƙoƙarin shi wurin ganin ta canza anma abun yaci
tura dukda kuwa bahakan bane yasashi sake aure dafari,Ummin ma ganinta yayi yaji
yanason kasancewa da'ita shiyasa ya aureta kuma daman tuncan yanada ra'ayin yin
polygamy.
Mama Hadiza(Ummi) Macece kyakyawa son kowa ƙin wanda yarasa,she came from a simple
and poor family. tayi karatu anma batakai matakin degree ba diploma kawai tayi
wanda bayan tagama bada jimawa bane ta auri Kawu Sani. Ummi Macece meson hutu da
jin daÉ—in rayuwa dukda kuwa gidansu basu dashi,kwata kwata batason wahala. Acewarta
ta wahala agidansu,tayi fafutuka da talauci bekamata tazo gidan miji tayi
encountering irin matsalarnan ba,burine da'ita sosai shiyasa koda tashigo gidan
Kawu Sani takeganin kamar ya gaza aduk wani abu dazaiyi musu,gashi ita baneman
nakai ba hakanan batada ra'ayin yin aikin gwamnati ma kwata kwata se abunda yaÉ—auka
yabata sekuma yawace yawace cikin dangi ana burgar an auri me kuÉ—i dankuwa duk
cikin Yan uwanta itace ta auri me É—an dama dama shiyasa take ganin itanma watace.
Ummi batada tsawatarwa Yara hakanan batada riƙe sirrin Mijinta,duk hirar dasukayi
da Kawu Sani kokuma magana sukayi akan abunda yashafi gidan dakuma future É—insu toh
se tazo tayi korafi ma yaran tafada musu aibun ubansu wanda hakan nadaya daga cikin
abubuwan daya bata yaran. Bata taɓa nuna musu su gode Allah a abunda suka samu
sede korafin ba'ayi musuba kuma dagangan yakiyi musu É—in. tanada zafi sosai shiyasa
tasu tazo É—aya da Mama Rabi'u kodacan dasuke zama gida daya.
Ƴaƴan Aunty huɗu Yaya Fahad,Yaya Siyama,Yaya Safiya sekuma Sadiya datake sa'ata
watanni ne kawai a tsakanin mu. Aunty tana samun tazara sosai a tsakanin
haihuwarta. Dankuwa tsakanin Yaya Fahad da Yaya Siyama yakai shekaru takwas. yanzu
haka Yaya Fahad nada shekaru ashirin da shida ayayin Yaya Siyama keda shekaru Sha
takwas tana neman sha Tara.
Yaya Safiya kuwa is just 14 sekuma Sadiya datakeda shekaru goma sha É—aya tana neman
shabiyu kamar ni. Ƴaƴan Ummi kuwa su bakwai ne, Yaya Salim shine Ɗanta na fari kuma
yanada shekaru ashirin da biyu aduniya yanzu,followed by Yaya Zunnurain dayake sa'a
da Yaya Siyama dukdama tagirme masa tahanyar bashi watanni uku.
Yaya Zaheera kebin bayan Yaya Zunnurain shekarunta Sha shida yanzu sekuma Yaya
Aisha datake sa'ar Yaya Safiya Itama watanni biyar ne kawai tsakaninsu. Sule
shikebin bayan Yaya Aisha kuma shima kusan sa'anni yake damu dukda ni nabashi
shekara guda kafin aka haifishi,se tasake haihuwan Mariya bayan Sule yanzu tanada
shekaru takwas a duniya sekuma autansu Sudaiz dayakeda shekaru shidda aduniya wanda
tunbayanshi batasake wani haihuwar ba kuma ana tsanmanin shine ÆŠan autanta inba
wani ikon Allahn ba.
Yaya Fahad yagama jami'arsa tun bara inda da result É—insa yafito yaga yayi kyau
seya wuce law school kawai dayake civil law yakaranta. Yanakuma gama law school É—in
akayi calling É—insu to bar sabida yana É—aya daga cikin waÉ—anda sukayi sa'ar cinye
jarabawarsu. Yanzu haka A *Imo* yake service É—inshi. babu yanda Aunty batayi ba
akan yanemi relocation anma Kawu idrissa yahana yace shibayason irin haka duk inda
aka tura mutum abarshi yaje yayi abunsa acan befi experience ba and moreover
inbamwa cakukudi muna ajiye kabilanci agefe yaushe kasar tamu zatazama undivided?
we're one Nigeria and we should always respect that wanda tahankan ne zamuyi yaƙi
da curruption dakuma sonkai. Yaya Fahad wani irin mutumne dazan iyacewa halin Aunty
yaÉ—auko,miskiline sosai hakanan shirgin kowa baya gabansa. Abunda yasaka agabanshi
yakeyi babu ruwanshi da shiga harkar wasu. Banbancinsu É—ayane da Aunty. Ita tana
hulÉ—a da Yan uwanta tanakuma jansu ajiki ayayinda shi kowama baya gabansa dan da
wuya kaga yana wasa da yaran gidansu.
Yaya Salim nedai dan surutu,meson mutane dakuma son gyarama mutum inyaga yayi ba
daidaiba. He always support the right party shiyasa kullum suke cikin samun matsala
da Umminsa dan ita tafison sede yayi abunda ita takeso takekuma ganin shine daidai.
Yanzu haka yana ABU Zaria yana karantar Pharmacy. Yana level three sunzo hutun
first semester da ankoma kuma za'a fara second semester daganan kuma se aji huÉ—u in
Allah ya yarda.
Yaya Zunnurain dakuma Yaya Siyama aji É—aya suke. Tare suka gama secondary school
bana daniyar shiga jami'a unfortunately se ita Yaya Siyama bataci jamb ba ayayin
shi Yaya Zunnurain yaci jamb É—in anma bayida English a result É—insa na SSCE Wanda
wannan dalilin yasa Kawu Sani nema musu remidials anan cikin ATBU Bauchi yace
inyaso next year insun samu sakamako masu kyau swa shiga jami'ar kawai.
Yaya Zaheera kuwa tana SS2 yanzu a FGC Azare ayayinda Yaya Safiya da Yaya Aisha ke
JS3 Suma anan FGC Azare É—in.
Sekuma Sadiya da akasama mata js1 acan nima kuma ake ƙoƙarin samamin mutafi tare.
Sule, Mariya dakuma Sudaiz duk suna primary school haryanzu.
Gaba É—aya yaran babumaiyina Kuma babu maisona. Bazan ce they're bad ba dukansu
dankuwa badness dinnasu akaina yawanci yake hakanan kuma ninarasa dalilin wannan
tsanar dasuke yimin dagasu har iyayensu hakanan kuma narasa wace ranar ce zandaina
ganin kiyayyata a idanunsu inkoma kallon so? dawannan tunanin bacci yayi awun gaba
dani dukda kuwa yunwar danakeji.
Karfe biyar da rabi na asubahi na farka daga nannauyan baccin danakeyi sakamakon
kiraye kirayen sallar asubahi danaji anatayi acikin unguwar tasu. Mamakin yanda
akayi nakwana lafiya a parlourn nashigayi batareda wani yazo ya koreniba dankuwa ko
ajiyan na kwanta da tunanin kilan azo ace infita a parlourn ma sabida kar insa musu
tsamin jiki anma kuma danatashi zaune nakalli yar kusurwar danayi baccin sena gane
inba mutum yashigo tsakiyan parlourn sosaiba babu yanda za'ayi yaganni and may be
that's the reason why nasamu nakwana a parlourn yau.
Littafin Qadr na kudine duk maiso ya tuntubi wannan layin 08147722806
*Page Twenty Nine*
BanÉ—akin dakenan cikin parlourn nashiga nakama ruwa sannan naÉ—auro alwala nafito
nakoma nan main parlour natada sallah. Har na idar da sallar bantashi daga position
É—inda nakeba addu'o'i nakeyi ma kaina,al'ummar musulmi baki É—aya dakuma addu'ar
Allah yasa Baba is in a better place dankuwa bazanmanta ba akwai ranar dayashigo
É—akina agida yasameni na'idar da sallah Ina addu'a a fili,seyaji ma nidashi nakeyi
ma addu'ar shine yazaunar dani yacemin inzanyi addu'a Ina haÉ—awa da duka al'ummar
musulmi baki É—aya.
I should never pray for myself alone,I should pray for everyone for Allah yafi
karban addu'a irin wannan cikin gaggawa.
Kofar É—akin sashin Aunty naji an buÉ—e wanda hakan yasani juyawa nakalli direction
É—in gurin senaga ashe Yaya Siyama ce tafito kanta sanye da hijabi sekuma sleeping
wears na riga da wando dake jikinta. HaÉ—a idanu mukayi wanda hakan yasani gaisarda
ita batareda na shirya ba.
Nace "Ina kwana Yaya Siyama" É—auke kanta tayi daga gareni sannan tace "Lafiya" tayi
wucewarta. Harta Isa kofar fita ta backdoor sekuma tajuyo takalleni adakile tace
"Ke biyoni!" gyaÉ—a matakai nayi ahankali sannan natashi nabi bayanta.
Sanda nafita backdoor É—in tana cikin kitchen danhaka nanufi kitchen É—in nima. Acan
cikin store nasameta tana É—iban Irish potatoe cikin wani try da alamadai pealing
É—insu za'ayi. Abakin kofar store É—in natsaya tareda faÉ—in "Yaya Siyama gani"
batareda ta kalleni ba tanuna min wani daro sannan tace "É—auki rubber nan kije waje
akwai tap kitari ruwa rabi seki dawo ki ɗauki wuƙa kijirani a varender ɗin kofar
kitchen ɗinnan" cewa nayi "toh" sannan naɗauki wuƙan da tanuna min nafice a kitchen
É—in nayi duk abunda tasakani sannan nazauna zaman jiranta.
Banjima zaune kan varendern ba segata tafito. Dire tray É—in potatoes É—in tayi
gabana sannan tazauna itama tana faÉ—in kisaka hannu muyi pealing dankalinnan.
gyaɗa mata kaina nayi ahankali sannan naɗauki wuƙan dana ɗauko a kitchen ɗazu dan
itama already tataho da nata. Tunda nake ban taɓa firan dankaliba arayuwata hakanan
ban taɓa ganin anayi agabana ba so ban iyaba anma ko karen haukane yacijeni bazan
iya buÉ—an baki incema Yaya Siyama ban iyaba danhaka sekawai naÉ—auki dankalin
ahannuna sannan nashiga kallon yanda take ferewan nima nafarayi ahankali. Sede duk
yanda naso Kar inci jikin dankalin seda nadinga ci gakuma wukar tayimin katuwa
ahannuna.
Yankewa kuwa seda nayanke hannuna yafi sau biyar anma ko sannu batacemin ba barema
insa ran zatace inbari kawai kuma tanaganin sanda nake yankewan dankuwa kowani
yankewa nayi sena danyi ƙara Ina washhh Allah na! anma abanza. Ahaka muka gama
firar dankalin hannnuna duk tafaÉ—i sukemin. ÆŠaukan daron Dankalin tayi sannan
tadubeni tace "jeki haÉ—a min wuta kafin inwanke dankalinnan" idanuna cikeda kwallah
na gyaÉ—a mata kai dukda shiÉ—inma ban iyaba sannan tawuce tanufi bakin tap tabarni
zaune gurin Ina kallon yanda na yayyanke fingers É—ina.
Sa bayan hannuna nayi nagoge kwallar dasuka zubomin sannan nakalli direction É—inda
murhun yake ayayinda itace,matches da ledoji ke ajiye gefe guda. ƙarasawa nayi kusa
da murhun sannan nashiga jera itatuwan ciki kamar yanda naga su Yaddiko Rahane
sukeyi in naje hutu a Babban buli. Bayan nagama jera itatuwan sena saka ledoji da
fasassun robobi asaman itacen sannan naÉ—auko ashana nashiga kyartawa dukda kuwa
yanda yatsuna ke min radaÉ—i amma seyaki kamawa.
Matches yafi ashirin na kunna suna mutuwa sabida iskan da akeyi agurin gakuma gari
yafara haske daman. Yaya Siyama data gama wanke dankalin ne tadawo taga abunda
nakeyi rai bace tace "bakida hankaline kike ta ɓata ashana haka?" Kamar zan saki
kuka nace "Inna kunna mutuwa sukeyi" harara ta watsamin sannan cikin tsawa tace
"tashi dalllahhhh! daman ansabar miki dajin daÉ—i Ina zakisan yanda ake kyarta
ashana?" Komawa baya nayi dasauri Ina miƙamata kwalin matches ɗin,wabcewa tayi
ahannuna sannan tashiga nuna ni da yatsa tace "toh barikiji ingaya miki! nanba
gidanku baneba kuma nan ba gurinda zakizo kinawa mutane kasalanci baneba. Inzaki
zage ki koyi aiki gwanda kizage kikoya dankuwa babu jakinki a gidan nan kinajinah!"
gyaÉ—a mata kai nayi Ina hayewa sannan tanuna daron dankali tace "sekije kifara
yanka dankalin ai kafin inhura wutan" sonake incemata bazan iyaba shima anma ina
tsoron outcome don haka shima dena gyaɗa mata kai kawai sannan na ƙarasa inda
rubber É—in Dankalin yake. Inasaka hannuna acikin daron naji wani irin radaÉ—i ya
ziyarceni lokaci guda sakamakon ruwan daya shiga wounds É—inda ke hannuna. Aibansan
sanda nacire hannuna daga cikin ruwan ba Ina kallon Yaya Siyama. Hararar da ta
watsamin ne yasani sake maida hannunawana cikin daron batareda nashiryaba.
Dayake Baba yana saya mana chips yasa bansha wahala wurin fidda shape É—in yankan
dankalin ba dukda kuwa inayi ina hurting kaina. Abunda dawanda baisaba ba.
Kuma koda tagama hura wutan sebata zo takarba ba. Nita bari nacigaba da yankawa
ayayinda ita take zuwa tana É—iban wanda zata saka acikin oil É—inda ke kan murhun
inyayi zafi ahaka harna gama. Ajiye wuqar hannuna nayi araina Ina cewa barkana
nagama wahala anma sede tunma kafin ingama ayyana hakan araina naji Yaya Siyama
nakiran sunana.
ÆŠaga kaina nayi nakalleta ina faÉ—in "Na'am" cewa tayi "tashi kishiga kitchen acikin
kwandon wanke wanke zakiga foodflasks É—insu Mariya guda huÉ—u kiÉ—auko min inzuba
musu abincin dazasu tafi islamiya dashi" gyaÉ—a matakai nayi ahankali sannan natashi
nashige kitchen É—in. bansha wahalar samun foodflasks É—inba danhaka na É—aukosu na
fiddo mata dasu.
Ina ajiyewa agabanta takuma cewa "indauko tsintsiya inzo insharo cikin kitchen
inagamawa kuma inzo inshare filin backyard É—in baki É—aya" Cewa nayi "toh" sannan
nakarasa inda tsintsinyoyin suke naÉ—auko guda É—aya daga cikin su sannan nazo nafara
sharan. Filin backyard É—in katone sosai ba laifi dankuwa tabbas inna share gurinnan
duka ba ciwon hannu kaÉ—ai zanyiba harma da ciwon baya wannan É—in is for sure. Haka
nasunkuya nafara sharan harnayi rabi wanda alokacinne kuma naji nagaji
sosai,karfina yafara karewa gashi kuma ban Isa ince zanhuta ba sekawai nakoma yin
sharar ahankali unlike É—azu danayakeyi with full force.
Muryar Maryama da Sule naji dagacan bakin kofar backdoor din suna faÉ—a atsakaninsu
ayayinda suke nufowa inda nake. musu sukeyi akan fitsarin kwance. Maryama tace
ba'ita tayiba shima yace bashi yayiba. sekuma cewa da kowannensu yayi bazai wanke
kayan fitsarin ba sede abarshi agurin ya rube. Ta gabana suka zo suka wuce sannan
suka nufi laundry É—inda ke can dungun gini da alamadai kayan fitsarin nasu zasu kai
can su ajiye wanda ananne nasamu nakalli bargon fitsarin dasuke rikedashi su biyu.
Wucewarda sukayi tagefena kaÉ—ai dashi seda zarnin fitsarin ya bugi hancina sosai.
Ajiyewa sukayi sukajuyo sunata cacar baki a tsakaninsu harsuka koma ciki. Basu Jima
dashiga ciki ba sega Sadiya ma tafito da nata tsummo karan fitsarin a hannunta.
Adede lokacinne kuma na É—ago daga sunkuyen danake daniyar zanje inzubar da sharan
da na tara cikin dustbin muka haÉ—a idanu da'ita sekawai naga tajuya dasauri zata
koma ciki.
Yaya Siyama ne ta daka mata tsawa cike da mamakin ta ta hanyar ƙiran sunanta sannan
tace "inazaki koma da kayan fitsarin kuma?" Tsuke fuska tayi tana kumbura baki
sannan tanufi laundry É—in kuma batareda tace ma Yaya Siyaman komai ba.
Ni abun ma dariya yaso yabani amma sena ɓoye kayana acikina. Is she by any chance
trying to hide the fact that she's bedsweating from me? toh Inkuwa hakan ne ai
aikin banza takeyi dankuwa Abunda batasani ba shine najima da sanin tanayi É—in,bama
itakadai ba harsu Yaya Aisha dankuwa suma basu Jima da denawa ba. sautari innaje
GiyaÉ—e nakanji Gwaggo Suwaiba na hirar ana nema musu maganin fitsarin kwance a
gurin masu magunguna wanda ananne nasamu labarin nima.
Kusan duka Ƴaƴan Kawu Sani babu wanda baiyi fitsarin kwance ba and most of them
sesun kai shekaru Sha huÉ—u zuwa shabiyar sannan suke denawa dukda kuwa ana nema
musu magunguna tunsuna yara kala kala anma duk baswa aiki. Abunde kamar wani wanda
sukayi gado acikin dangi.
Haka taje ta'ajiye kayan fitsarin a laundry tadawo tasake wuceni zata koma cikin
gidan.
Seda takusa shiga kofa sannan Yaya Siyama talura da'ita cikin sauri tace "Baki
wanke kayan ba zaki koma ciki" cikin kunkuni Sadiya tajuyo tana faÉ—in "Yaya Siyama
shirin islamiya fah zanje inyi. Zamuyi latti" hararanta Yaya Siyama tayi sannan
tace "tunda bakisan zakiyi lattinba se yanzu?toh kiwuce kiwanke su yanzunnan dan
bazanzo dadare inamiki hankilon kinshigo min da kaya masu zarni É—aki zakiyi
shimfidi dashiba" Sadiya kaman zatayi kuka tace "Allah inna dawo zan wanke Yaya
Fahad yakusa fitowa kuma shi zeyi dropping É—inmu a islamiyar shiyasa Aunty tace
inyi inshirya da wuri" Yaya Siyama tace "inkinga dama ma inkin dawo kada kiwanke
É—in kyanemi gurin kwana dan ba'a É—akin nanba ah toh!" cikin sauri Sadiya tace "toh"
sannan tayi shigewarta cikin gida aguje.
Sanda na ƙarasa sharan Yaya Siyama tayi shegewarta ciki. trayn dasu Mariya sukaci
Chips nahango abakin varendern kitchen ɗin ajiye kuma sun rage danhaka na ƙarasa
gurin nazauna nafara aikawa cikina sakamakon irin yunwar dake addabana tun daren
jiya. Nasan ko kwana É—ari zanyi agidan Ina jiran wani yaÉ—auki abinci agidan yabani
toh zankare rayuwana baki É—aya banci abincin ba dankuwa koda danake zuwa gidan
nakwana dasanin ba'a bani abinci sede inna koma gidanmu inci.
Dukda chips É—in beda wani yawa amma I was somehow fully satisfied. Koba komai
narage yunwar cikina, É—auke trayn nayi daga gurin nakaishi wurin wanke wanke inda
naga sun ajiye kwanuka masu datti sannan nashige cikin gidan. Babu kowa a parlourn
as usual amma sede tunda nashiga nakejin muryar Yaya Siyama tana masifar Sadiya
batayi sharan sashin su ba tayi ficewarta islamiya tana korafin Itama bazatayi ba
Sede in sadiyar tadawo tayi kayanta.
Sekuma naji muryar Aunty tana bata hakuri tareda cewa tayi sharan kawai inyaso
Sadiyan tasakeyi da yanma yanzun zatayi baƙine batakuma so suzo gidan sutarar
ko'ina kaca kaca daganankuma seban kumajin muryar Yaya Siyaman ba. Karasawa nayi
parlourn nazauna a inda nazauna jiya kenan segata tafito tanata kumbure kumbure.
Tsintsiya taje taÉ—auko wanda ahanyar dawowan natane ta hangeni cewa tayi inbiyo
bayanta. Cikin sauri natashi nayi yanda tace É—in a tsakiyar parlourn su tamika min
both tsintsiyar kwakwa dana laushi sannan tace inshare mata parlourn ayayinda
itakuma tayi wucewarta É—akin Aunty tasharo sannan tasharo É—akinsu ma wanda alokacin
harna gama sharan parlourn nakoma can main parlour É—in nasu. Acan tasamo ni
zaune,tsintsiyoyin dana baro acan tajefomin tana faÉ—in "Nan É—inkuma dakika maidashi
É—akinki wakike tsanmanin zai share miki?" tashi nayi naÉ—auki tsintsiyar batareda
nace komaiba sannan nakoma nafara karkaÉ—e jikin kujeru da labulaye Ina mamakin ya
akayi bata ce infita a parlourn ba.
Muryar tane yafiddani daga trance É—ina,cewa tayi "dakin gama share parlourn kije
can waje wurin wanke wanke kiharhada kiyi" cewa nayi "toh" sannan najuya nacigaba
da sharar da nakeyi É—in.
***
Lamiɗo ko sallar asubahi ƙin fita yayi,acikin ɗakinsa yayi sallah sabida tsoron
kada yafita yahaÉ—u dawani harma aji labari a Fada ace za'a biyoshi gida. Yafi son
yayi submitting kanshi da kanshi inyaso seyayi tackling abun alone.
Allah ma yataimakeshi yau Sunday ce,babu fita industrial training bare Umma tazo ta
addabeshi da tambayar miyasa baifitaba. Se takwas da rabi yatashi,yayi wanka
yashirya cikin kananun kayansa dasuka matukar amsar jikinsa sannan yafito parlour
yayi breakfast. Soyakeyi dayabar Fada indai everything ends well as he expected
seya wuce wurin Maimunatu,yaje yasanyaya duk wasu gurbi na zuciyarta daya
xafafa,soyake yaje yawanke laifinsa tahanyar nuna mata tsantsar kauna yau É—innan
shiyasama yayi gayu nadaban yauÉ—in. kwalliyar yau musamman na Maimunatu ne.
Yana gama cin abinci sallama yama Umma dasu Jidda sannan yafice agidan jiddah nata
zolayarshi da Ina zeje irin wannan wanka haka.
Dariya yayi sannan yace "inda Kika aikeni" ayayinda ya kanne mata ido É—aya and then
she realized cewa gurin Maimunatu zashi ayayinda su Umma kuwa suka É—auka gatse
yayima Jiddan dayace inda ta aikeshi zashi.
LamiÉ—o nafara doson Fada yaga dogaraye nata nuna shi suna kallonshi da alamadai
they were trying to contemplate ko shi É—inne ko bashi ba tunda jiya ansanar dasu
baya gari. Dayayi gaba kaÉ—an yasake haÉ—uwa dawasu dogarayen seyaga sun doso kanshi
kawai.
Tsayawa yayi yana kallonsu harsuka ƙaraso inda yake suna kare mishi kallo ayayinda
É—aya daga cikinsu yace "Daman kana gari shine mukaje gidanku akace bakanan?" LamiÉ—o
yace "I came back yesterday night" dogarin dayayi magana yace "toh muje ana neman
ka a Fada yanzu" yakarashe maganar yana nuna masa hanyar Fada.
Wani tukuki bakin ciki Lamiɗo yaji a zuciyar sa. dakyar dai ya ɓoye ɓacin ransa
sannan yace "can zani" wani dogarin ne daban yayi magana yanzu yace "toh wuce muje
mana" LamiÉ—o fearlessly yace "toh sakani agaba zakuyine?" Dankuwa ranshi yafara
baci da authority É—inda suke bashi.
Wani daga cikinsu yace "Duk yanda kaÉ—auko" karema surrounding É—in gurin kallo
LamiÉ—o yashigayi,bayaso yanemi tsokana yazamanto bashida hanyar guduwa. Wani
murmushi yasaki sakamakon idanunshi dasuka sauka jikin katangar dake barin
dama,katangar dazata sadaka da wajen masarautar daka tsallaketa sannan yaÉ—an lashi
lips É—inshi yakalli dogarin dayace masa "Duk yanda yaÉ—auka" sannan yace "toh
nikaÉ—ai zantafi Fadan inkuma kukadage sekun bini a baya kamar wanda kuka kama
barawo sede kuga babuni wallahi" wani daga cikinsu ya buga tsaki yace "toh dallah
ba barawon bane kai?" Wani murmushi LamiÉ—o yakumayi batareda yace komaiba.
Wani dogarin ne yace "Ku kuka tsaya kuna sauraron shi ma. Kamashi kawai zamuyi
mukaishi can Fadan" Amma sede tunma kafin dogarin yarufe bakinsa sukaga LamiÉ—o
yakama katanga ya haura yana tafiya.
Dagudu wasu suka bishi kan katangar ayayinda wasunsu kuma sukebin direction É—inda
suke ganin yanabi ta ƙasa. Lamiɗo ganin wasu dogaraye sun dale katanga kamar yanda
yayi kuma suna bin bayanshi yasa yafara gudu kan katangar ayayinda masu binnashima
suka fara gudun suma sede dayawansu duk faɗi sukayi a ƙasa. abunka da wanda
baisaba. daga inda suke zuwa kofar Fada babu wani nisa danhaka bejima yana gudun ba
ya Isa gaban kofar Fadan.
Tsayawa yayi naɗan sakanni yana kallon dogarayen dake ƙasa suna jiran yasauko
dakuma waÉ—anda ke kan katangar suna nufosa. Seda yaga nakan katangar sun kusa isowa
inda yake sannan yadirka dasauri and it turns out a gaban kofar Fadan yadira ma'ana
yabar dogarayen abayanshi. Cikin sauri yatashi tsaye yashige Fadan ganin sun nufo
shi.
Mutanen Fada seganin mutum kawai sukayi daga sama. Seda ya'isa gaban Sarki ya zube
sannan yaɗaga yadubesu kafin yashiga miƙa gaisuwa. Memakon su amsa se waziri cikeda
tuhuma yace "Kaine kahada commotion awaje Koh?" Cikin sauri LamiÉ—o yace "banina
sakasu ba ranka ya daÉ—e su suka sa kansu" wani irin harara Wazirin ya watsa masa
sannan yace "suka sa kansu kamar yaya?" LamiÉ—o yace "I was on my way coming here
shine suka tareni wai adole suzasu kawoni nikuma sena gudo" Waziri yace "it's their
Job you should have let them do it" sunkuyar da kai LamiÉ—o yayi kamar wani munafuki
sannan yace "Ayimin afuwa don Allah naga nan É—in zanzo toh miye amfanin sakoni
agaba kamar wanda yayi sata?" Wani irin kallo Waziri yamai yana shirin yin magana
Sarki yayi sauri ya katse shi tahanyar Ƙiran sunan Lamiɗo.
Yace "Isma'il" cikeda ladabi Lamiɗo yamaida kansa ɓangaren da Sarki yake sannan
yace "Na'am Mai martaba antashi lafiya?" Sarki yace "Lafiya Lau. Jiya na aika anemo
minkai se akacemin baka gari" gyaÉ—a kai LamiÉ—o yayi cikin sauri sannan yace "Eh
Maimartaba. Najeni Bauchi ta'aziya ne seda nadawo akasanar dani kana nema na toh
kuma dare yayi shiyasa ma nayi deciding inbari inzoni yauda safe" jinjina Kai
Sarkin yayi sannan yace "meyasa kahauro katanga ranar da dare?" LamiÉ—o sake sunne
kai yayi ƙasa tareda yin fuskar tausayi sannan yace "wallahi Mai martaba sharrin
shedan ne. Daga makaranta muka taso ranar kuma dare yayi sosai banida gurin kwana
nasan kuma danace abuÉ—e min kofar ba lallai abuÉ—e minba kuma ko anbude É—in kilan se
an hukuntani kafin abarni inshigo shiyasa kawai nayi deciding in haura ta katangar
in shigo" yayi folding hannayensa guri É—aya cikin sigar roko yace "Amma don Allah
ataimaka ayimin afuwa insha Allahu irun hakan bazai sake faruwa ba" Mai Martaba
sauke numfashi yayi ahankali sannan yace "toh dakaji ana neman wanda yayi laifin
miyasa bakazo kafaÉ—a ba? Miyasa bakazo kace kaidin ba barawo baneba kayi shiru
abunka?" LamiÉ—o yace "sabida tsoron abunda zai biyo baya Mai martaba. Atunanina
babu wanda yaganni so ko annemeni ba lallai asameni ba shiyasa but believe me I did
nothing wrong kataimaka ka yafemin please" LamiÉ—o yakarashe maganar kamar zaiyi
kuka. Sarki yace "inni nayafe maka dubbanin mutanen da ka firgitar awannan Daren
fah? Su zasu yafe makane?" Shiru LamiÉ—o yayi bece komai ba.
Sarki yakarada "toh I won't tolerate this nonsense! Yau yazamantoh nafarko nakuma
karshe dazaka sake irin wannan kuskuren kanajina?" GyaÉ—a kai LamiÉ—o yayi cikin
sauri.
Sarki yace "bagwandama ka kwankwasa gate ɗin karoƙi abarka kashigo ɗin akan ka
hauro katanga akama ayimaka kallon barawo ba yafi. Yau kaci albarkacin Ina ganin
darajar mahaifinka sannan banmanta alkhairinshi ga masarautar nanba shiyasa tunda
akace kaina na sassauta maka,nakuma hana inbanda dogaraye na da Fadawa kowa yasan
da labarin nan and moreover you're not found guilty of stealing shiyasa nayimaka
wannan uzurin! Kuma bawai hakan yana nufin bazan hukuntakaba. Punishment É—inka na
comotion É—inda ka haÉ—a awannan daren shine zakana feeding dawakai for good three
months kanajina?" Cikin sauri baki haryana rawa LamiÉ—o yace "Naji Mai martaba!
Nagode! Nagode kwarai dagaske kuma in Allah ya yarda bazan sake yin wannan kuskuren
ba" Maimartaba yace "Allah yasa" sannan yayi dismissing LamiÉ—o.
LamiÉ—o nafita a Fadan wani irin tsallen murna yasaki feeling freely and out of fear
hakanan besan sanda yashiga godema Mahaifinsa ba tareda yimasa addu'ar kasancewa a
gidan aljannatul firdausi dukda kuwa akullum yanayi mashi wnnan addu'ar inyayi
sallah. Straight gidansu Maimunatu yawuce daga masarautar,sukasha hira abunsa
harsaida yasa ta huce daga dokin fushin datahau sannan LamiÉ—o yawuce gidansu Hafiz.
Wankin kayan Umman sa yasameshi yanayi a bakin tap É—in dake kofar gidansu,cikin
gidan yashiga yagaisa da mahaifiyar Hafiz É—in sannan yaÉ—auko kujera yadawo yasamu
gefen Hafiz ya ajiye kujerarsa sannan ya zauna. Hafiz datun isowar sa ko gaisawa
basuyi ba yashiga tambayar LamiÉ—o yanda suka kareda mutanen Fada ganin bai
amsamaiba yashige ciki yasa yana dawowa yasake jefamai thesame tambaya. Murmushi
LamiÉ—o yasaki bayan yazauna sannan yace "albarkacin Baba naci Hafiz!" Daganan kuma
seyakwashe duk yanda sukayi a Fadan yasanar da Hafiz É—in.
Wani irin wawan ajiyar zuciya Hafiz yasaki sannan yace "Toh alhamdulillahi! Wallahi
bakasan yanda hankalina yake atasheba tun É—azu. Allah Allah nikeyi ingama wankin
Umman nan inje can gida ingano meyake faruwa" murmushi LamiÉ—o yayi sannan yace
"bakomai Hafiz. don't worry nagode sosai" Hafiz yace "it's okay. Anatare ai" sannan
yaÉ—ago yadubi LamiÉ—o yace "Tell me,ya mutanen Bauchi? Yajikin Baban Rukayyan?did
you get to see her? Ko an sallamesu?" Hafiz yajero ma LamiÉ—o wadannan tambayoyin
lokaci guda amma baki É—aya se yaga mood É—in LamiÉ—o yacanza ahankali LamiÉ—on yace "I
did not" Hafiz yace "kaman ya you did not? bakasamu kaga Rukayyan ba kakeson cemin
komi?" gyaÉ—a masa kai kawai LamiÉ—o yayi. Cikeda curiosity Hafiz yace "ya akayi baku
haÉ—u ba toh?" Slowly LamiÉ—o yace "Ashe tun ranar damuka baro Bauchi Allah yayima
mahaifin Rukayya cikawa" Hafiz besan sanda yasaki zanin Umman sa dayake gurjewa ba
sannan yashiga furta kalmar "innalillahi wainna ilaihir rajiun" baki sake yana
kallon LamiÉ—on kafin yace "Allah ubangiji yayimasa rahama yasa ya huta" LamiÉ—o yace
"Amin" Hafiz cikedw Jin tsoron duniyar baki É—ayanta yace "ranar ma naga yaji sauki
sosai fah" LamiÉ—o yace "Eyi Ashe saukin tafiyane" Hafiz yace "hakane Kam. Allah
ubangiji yasa muyi kyakyawan karshe" LamiÉ—o yace "Amin" Hafiz yace "toh ya akayi
kasamu labarin mutuwar tunda kace baka haÉ—u da Rukayyan ba?" LamiÉ—o yace "the
nurses at the ward told me" Hafiz yace "sekuma kai baka nemi sanin gidansu Rukayyan
ba kadawo haka? You should have gone to their house kayi musu ta'aziya" LamiÉ—o yace
"naje Hafiz. Har Babban buli naje ni jiya" se yabashi labarin komai dakuma abubuwan
dasuka faru a jiyan haryakai aya Hafiz na kallon shi.
Hafiz yace "Allah sarki. Allah beyi zaku haÉ—u ba. I just hope she'll be happy
staying with iyalin Kawun nata" LamiÉ—o yace "I hope so too even though I've to go
back and confirm it" wani kallo Hafiz yamasa sannan yace "da izinin wazakaje? Koka
manta me Umma tacemaka ne last time?" LamiÉ—o yace "ban mantaba Hafiz toh amma
yazanyi?" Cikeda Jin haushinshi Hafiz yace "yazakayi ma kake cewa? Wai tsaya! dole
ne sekaje kagantan? Zuwan dakayi jiyan ma is okay ai and I'm very sure sakon daka
bama Buba zai Isa gareta and that wouldn't make her hold grudges against you akan
rashin cika alkawari" Hafiz yakarada "abeg let go of this girl taimakon ya'isa
hakanan! Can't you see you're taking so much risk because of her? Can't you see
you're hurting the people around you because of her? Ko an gayamaka bansan
rashinzuwa gurin Maimunatu da kakeyiba kwana biyu? Ko bakasan Basma da Jidda na
fushi dakaiba? Kobakasan in Umma tasamu labarin abunda kayi zata shiga damuwa
baneba?" Hafiz yasauke ajiyar zuciya sannan yacigaba da magana yace "look LamiÉ—o.
Enough is enough now. You better focus on yourself and your family than thinking of
a way dazaka dinga zuwa ganin wata stranger É—inda banga wani amfanin datake dashi
acikin rayuwarka ba. Rukayya dakai da babu kai zatayi rayuwa tunda tunkan ka haÉ—u
da'ita she's living her life normally and even now that she's lost her Father bana
tunanin zatayi maraici tundagasu Gogode da Gwaggonta Suwaiba sannan gakuma sauran
dangin mahaifinta da I'm very sure bazasu taɓa barinta hakananba"
Tunda Hafiz ke magana LamiÉ—o zuba masa idanu kawai yayi haryakai aya. Sekawai
yasaki murmushi sannan yace "Thanks for the lectures but I want to assure you that
maganganun ka will never have impact on me. Abunda nasaka ma raina shizanyi I hope
you know that? Kuma dakake cewa dani da babu ni zatayi rayuwa nafika sanin hakan
and still after Knowing that nake sake dragging kaina gareta" Yanda LamiÉ—o yayi
maganar boldly and with utmost sincererity yasa Hafiz fara wasu tunane tunane,seya
saki baki yana karantar fuskar LamiÉ—on trying to analyze something he's suspecting
kafin yayi mastering courage yabudi baki yace "have you by any chance fallen in
love with this girl......?" memakon yasamu amsa daga bakin LamiÉ—o seyaga yakwashe
dawani mahaukacin dariya yace "You're mad Hafiz!" Sannan yatsagaita dariyar tasa
yace "Yanzu Kai atunaninka son Nanaa nikeyi sabida abubuwan danakeyi É—innan?" Hafiz
yace "inba so ba toh menene? naga abun naka naneman yawuce gona da irine" LamiÉ—o
yasake dariya sannan yace "Nanaa kamar Salma take a gurina Hafiz! yanda nake ma
Salma soyayyar kanwa haka nakejin Nanaa araina. She's nothing more than a sister
and if that's the case kasan babu Yayan dazai taɓa barin kanwarsa batareda yana
zuwa yana dubata ba" tabe baki Hafiz yayi sannan yace "kaikasani dai but I doubt
your words,gani nake kaikanka bakasan mezuciyar ka takeso ba" Hafiz yayi shrugging
shoulders É—insa sannan yace "Anyways nidai nabaka shawara Inkuma baka É—auki
shawarata ba then babu ruwana,kada kuma kayarda kace zaka sake sakani acikin
al'amarinka indai yashafi Rukayya kaje kayi abunka kai kaÉ—ai" murmushi LamiÉ—o yayi
sannan yace "insha Allah I'll never call her name infront of you let alone ask for
your help indai akanta ne" Hafiz yace "better" Kuma tunda yaji LamiÉ—on yafaÉ—i haka
toh tabbas bazai sakeyi masa maganar ba but he just hope bama ashi kaÉ—ai ba harma
akowa, Allah yasa maganar dayamasa yashiga kunnensa yakyale batun Rukayya hakanan
ya fuskanci nasa rayuwar.
***
Dayake inada nauyin jiki kuma wanke wanken nada yawa yasa bangama dawuri ba har se
wuraren sha biyun rana wanda alokacin ne kuma Yaya Siyama tafito yin girkin rana
dole tasani nasaka mata hannu muka fara aikin tare.
Muna cikin yin girkin rana su Sadiya suka dawo daga islamiya. Sadiya na cire
kayanta tazo tawuce laundry tawanke kayan fitsarin ta tashanya unlike su Mariya da
tun dawowansu ko wulgawansu bangani ba.
Ana kiraye kirayen sallar azahar Yaya Siyama tasauke tukunyar jollof É—in shinkafan
da mukayi sannan taturani kitchen tace indauko kwanukan dazata zuzzuba abincin
aciki. Cikin mintuna goma tagama rabon abincin sannan tadubeni tace inje inkirawo
mata su Sadiya.
Cewa nayi "toh" sannan nawuce cikin gidan. kusan tare muka dawo dasu. Nunama Sadiya
foodflask É—in kofarsu tayi sannan tace "É—auki wannan kikai parlourn Aunty seki dawo
kiÉ—auki namu kikai mana É—aki nima ina zuwa kinji?" gyaÉ—a kai Sadiya tayi sannan
taÉ—auki foodflask É—in tayi wucewarta ciki.
Yaya Siyama tanuna masu Mariya foodflask É—in Ummi dakuma trayn data zuba musu nasu
aciki tace suÉ—auke suma,seya rage saura plate É—inda tace Sadiya tadawo tadaukar
musu sekuma tray guda biyu dake É—aukeda foodflasks da plates da spoons da serving
spoons.
ÆŠaukan tray É—inda yafi kyau acikin biyun tayi sannan tacemin indauki É—aya tray É—in
inkai boys quarters nasu Yaya Salim ne. GyaÉ—a matakai nayi sannan naÉ—auka nabi
bayanta. Sashin Kawu Sani tanufa inda nikuma nanufi sashin su Yaya Salim don kai
musu abincin Ina tunanin nikuma Ina nawa abincin rai? Dankuwa kokadan berage a
tukunya ba. Gaba É—aya abincin ta rabe.
Kusan cin karo mukayi da Yaya Fahad a bakin kofar parlournsu shizai fita ayayinda
nikuma nake ƙoƙarin shiga parlourn. Fuskarsa da hannayensa ajike suke yana ƙoƙarin
saka wristwatch É—insa a tsintsiyar hannunsa da alamadai alwala yayi zai tafi
masallaci dankuwa naji anata kokarin tada sallah a masallatan cikin unguwa. Sauri
nayi nakoma gefe Ina faÉ—in "Ina wuni" ciki ciki yace min "lafiya" kafin yayi
wucewarsa batareda ya kalli inda nakeba. Karasawa nayi cikin sashin nasu senaga
ashe madaidaicin parlour ne dake É—aukeda kayan alatu na zamani. Har Zan ajiye
abincin a tsakiyar parlourn sena hango dinning table acan gefe guda kuma wanda
hakan yasani nufan dinning table É—in. Naje na ajiye trayn abincin nasu akai sannan
najuya daniyar tafiya sekuma idanuna suka sauka kan wata kofa dakenan ciki
parlourn. Kofar abuÉ—e take wanda hakan yabani ikon ganin view É—in gurin. Doguwar
corridor ne sekuma kofofi guda huÉ—u danake gani daga inda nake tsaye dazai sadaka
da only God knows.
Tabe bakina nayi araina Ina raya "bazai wuce É—akunan su Yaya Salim baneba" atake
kuma wata zuciyar tashiga rayamin toh ai su ukune,me É—ayan dakin kuma yakeyi.
Sekuma wata zuciyar takuma rayamin "É—akinsu Sulene mana. May be insun daina
fitsarin kwance sun mallaki hankalin kansu nan É—in zasu dawo suma" dawannan tunanin
najuya nayi ficewana a sashin nasu jin bankuma jin motsin kowa ba. Ina komawa can
main parlour lungun dana ajiye kayana na nufa,na buÉ—e akwatina naciro kayana da
inner wears É—inda zansaka sannan naÉ—auki sabulum wanka da soson da Gwaggo Suwaiba
suka sakamin cikin kayana sannan nafice zuwa can ban É—akin waje. Allah yataimakeni
akwai tap cikin banÉ—akin kuma ruwa yanazuwa danhaka bansha wahalar neman ruwan
wanka ba. Sulluka wankana nayi sannan nayi alwala nashirya nancikin banÉ—akin kafin
nafito nakoma main parlourn nayi sallah abina. Ina sallame sallan kwanciya nayi
anan kan carpet É—in and In no time baccin wahala ya É—aukeni.
Bacci nikeyi sosai hakanan bansan awannin dana É—auka Ina baccinba,kawai sejinayi
ana shanbi na. Cikin sauri nafarka sakamakon zafin danaji abayana and then I saw
Mariya,tana tsaye akaina fuska babu annuri. Tashi nayi nazauna Ina sosa inda ta
shanbeni still idanuna begama wartsakewa daga daÉ—É—adan baccin dana keyiba.
"Kizo Ummi tana kiranki" Mariya tayi maganar a dakile sannan tayi wucewarta
sashinsu,tashi nayi nabi bayanta. A parlour nasamesu duka, Ummi, Mariya,Sule da
Sudaiz duk suna kallon TV. Rabona da kallon Ummi tun daren jiya a parlourn Kawu
Sani,samun guri nayi naÉ—an rusuna sannan nace "Ina wuni Ummi" buÉ—an bakinta secewa
tayi "Daban wuni ba zaki ganni ne?" sekawai naÉ—auke kaina daga gareta namaida shi
ƙasa.
Cikin sauri tace "matsamin kusa da kujera karkisakamin kujeru yin tsami" matsawa
nayi da sauri atakekuma senaga duka yaran sunsa hannu ahanci suna tottoshewa.
Duban Mariya tayi rai bace sannan tace "meya hana kice mata taje tayi wanke wanken
dakanki dazaki wani turomin ita É—aki?" Mariya tace "Ummi Yaya Siyama ce tacemin
incemiki Rukayya ce zatayi wanke wanken nikuma nasan innazo nafaÉ—a miki zakice
inkirata dankisanar da'ita shiyasa kawai nataso ta dazan taho" tsaki Ummi tayi
sannan tace "nan gaba dai in ance itazatayi abu kawai kisakata directly banason
tana shigomin turaka! Da ganin mummunar fuskarta zanji Koda tsamin jikinta" Ummi
takarashe maganar tana yatsina fuska tareda toshe hanci kamar gaske bansan sanda
hawaye yafara bin kuncina ba.
Cikin tsawa tace "tashi kificemin a parlour joor! ana magana Kuma tana zaune tana
kallon mutane kamar wata tsohuwar mayyah! Kiwuce kije kitattara kayan wanke wanke
kiyi yanzunnan inason inzo in É—aura abincin dare kar lokaci ya kure" harna juya zan
fice tace "Tukunnan ma meya hanaki yin wanke wanken tun É—azu? bada angama cin
abincin rana akeyiba?" Mariya tayi sauri ta capa "Ummi baccima nasameta tanayi a
parlour hankali kwance" wara idanu Ummi tayi sannan tace "baccin rana agidannan? A
wani parlourn kuma?" Mariya tace "Main parlour Ummi" sakan baki Ummi tayi tayi
sannan tace "Eh lallai wuyan ki da kwari yake Ƴar nan! Anma anyi Ƴar iskar yarinya!
Main parlourn dazamuke tarban manyan baki kikeson kimayar É—akinki danke mahaukaciya
ce koh?" Cikin sauri na shiga girgiza kaina alamar a'a ayayinda l hawaye kebin
kuncina.
A harzuke Ummi tace "Auuu karya akayi maki kenan? Toh zonan dan Ubanki" tayi min
maganar tana min alama da inzo da hannun ta.
taku nashigayi ahankali Ina nufan inda take zaune harna karasa anma sena kasa
tsugunawa sabida tsoron kada takuma cewa zansa mata tsami ajikin kujerar ko carpet
anma shima seban tsira ba,rai bace tace "Auuu tsayiwa ma zakiyi akaina kenan?
sabida bakida kunya?ke dakikiya ce!" Girgiza kaina nashigayi alamar a'a sannan
cikin sauri na tsuguna agabanta batareda na shiryaba. Ban ankaraba kawai seji nayi
ta kama kunne na tana murdawa da karfi ayayinda take zare min idanu tace "ki
saurareni dakyau kiji abubuwan dazan faÉ—a miki" cikin gunjin kuka nace "toh" Ina
addu'ar Allah yasa tasaki kunnen nawa konaji sauki tsabar irin radaÉ—in dayakeyimin
anma sebata saki É—inba tace "dagayau seyau kada insake Jin labarin kinzauna a main
parlour inbaso kike kimaida shi kwatami ba kinajina?" cikin sauri nace "toh" sannan
tasakeni tace "Kuma kiwuce kije kiyi wanke wankennan yanzunnan sannan gidan nan ba
gidan daÉ—i baneba dahar zaki saki baki kikwanta kina baccin rana. Nan ba gidan
Ubanki dayagama sakalantar dake baneba ah toh! Aiki zakiyi ko kinki kokin so sabida
haka nangaba in akace kiyi aiki bakiyiba nida kene barikiji infada miki gaskiya"
gyaÉ—a matakai nayi jikina na rawa still banbar hawayeba sannan nafice a parlourn
cikin sauri.
Ni inama nasan zanyi wanke wanke daza'ayimin irin wannan hukuncin fisabilillahi?
Straight kitchen nawuce na tattaro kwanuka masu datti nakaisu wurin wanke wanke
bayan natara guntu guntun abincin da aka rage acikin kwano guda sannan nadawo
naÉ—auki kwadon dazan kifa kwanuka sannan naje nafara wanke wanke Inayi Ina kuka
nikaÉ—ai. Sona ke inci guntun abinci da aka rarrage anma damuwar danake ciki bazai
barni ba,duk yunwar danakeji É—azu senaji babushi yanzu kwata kwata. Nafi awa guda
Ina wanke wanken kafin nagama inda ananne kuma naga gari ya danyi sanyi alamar
yanma tayi sosai and then I realized cewa already la'asar tajima dayi. Cikin sauri
naÉ—auki kwandon wanke wanken nakaisu kitchen sannan nadawo naÉ—auki pots É—inda
nawanke suma nakaisu sannan nakoma bakin tap É—in nayi alwala nawuce cikin gidan
daniyar insanar da Ummi nagama wanke wanken se inje inyi sallah.
Littafin Qadr na kuÉ—i ne duk maiso should talk to this number on whatsapp
*08147722806*
*Page Thirty*
Sashinta nawuce dukda kuwa Ina fargaban shiga tace nashigo mata da warin jiki toh
anma yazanyi? Inada wanda zeje yakaimin sakon ne? And moreover inbankai sakon bama
wani laifin zai zama shiyasa gwanda nakai É—in kawai inyaso se inyi enduring koma me
zatacemin. A nan parlour inda nabarsu É—azu nasamesu,a bakin kofa na rakube kamar
wata munafuka zuciyata na bugu sannan nace "Ummi nagama wanke wanken" yitayi kamar
batajini ba harsaida na maimaita kalamaina sannan akafule tace "Naji" alamun na
dameta.
Juyawa nayi zanbar É—akin naji cikin tsawa tace "nace miki kitafi ne?" tsayawa nayi
cikin sauri tareda juyowa ina kallonta sannan nace "A'a" harara ta watsamin sannan
tanunani da É—an yatsa sannan tace "nangaba inkikazo gurina ban sallameki ba kika
yarda kika tafi sabamiki zanyi kinajina?" gyaÉ—a matakai nayi ahankali sannan
nasauke kaina ƙasa ina zullumin miye dalilin dayasa ta tsaidani ɗin?"
Senaji tace "kiyanka min albasa guda huÉ—u manya yanzu zan fito nima" cewa nayi
"toh" anma memakon intafi sena cigaba da tsayuwa anan É—in tunda banji ta ambaci
intafi ba. Nafi mintuna uku ina tsaye sekuma naga tadawo da dubanta gareni Rai bace
tace "tsayuwar me kikeyi Kuma?" Cikin sauri nace "babu" sannan najuya nayi ficewana
inajinta tanata zagina waini mahaukaciyar wace garice tasani aiki natsaya Ina
kallonta kamar wata tsohuwar mayyah!
Dukyanda naso inyi resisting tears É—ina kasawa nayi haka nafita backyard É—in na
nufi kitchen harna isa bakin kofar kitchen sena tuna banyi sallan la'asar ba. seda
naje na sakeyin alwala nayi sallah sannan naɗauko albasa da wuƙa nafara barewa.
Nagama bare albasan kenan na wanko zanyanka sega Ummi tafito.
Kallon cikin rubbern da albasan yake ciki tashigayi baki sake sannan rai bace tace
"Baki yanka albasan ba haryanzu?" Atsorace nace "yanzu zanyanka" kamar zata dukeni
tace "mekikeyi tun É—azu baki yanka ba? zaman me kikeyi?" Murya na rawa nace "Seda
nayi sallah sannan nafara bare albasan" Ummi tace "yanzudai inyi ta zaman jiranki
kenan? Sallan la'asar É—in tun yaushe akayishi? Kumama in banda gulma da tsugudidi
keÉ—in harnawa kike dahar kika fara sallah?" Jin kalamanta dole seda na É—ago na
kalleta in shock anma ganin irin kallon datake watsamin yasani saurin sake maida
kaina ƙasa ina mamakin wannan ɗin wace irin matace? Ina shekara goma sha biyu anma
tanacemin harnawa nake dazan damu dan banyi sallahba? Sekuma natuno yanda su Yaya
Aisha sallah bata dame suba kwata kwata. Most at times tarukut salat sukeyi sabida
jarabar son kallon da insun zauna agaban TV baswason tashi harsai sunga an É—auke
wuta ko in an kashe generator Itama kuma uwartasu sebata damu data tsawatar musu
ba. wani sa'in ma harda ita akeyin hakan. wani lokacin kuma in sukaga dama ma
bazasuyin ba,in lokacin yin sallar tawuce shikenan baza'ayitaba.
Wataran baza'ayi sallar asubahi ba za'ayi azahar,ayi la'asar ayi maghrib akiyin
isha'i.
Inajinta tagama kashemin warning akan batason inahada aikinta dawani abuna,bazata
hananiyin sallah ba anma inyishi a lokacin daya dace basai tazo tana sani aikiba
infara bata excuses. nidai bance mata komai ba dukda kuwa É—azunma ai aikintan ne
yahanani yin sallar akan lokaci. Haka nakarasa yankan albasan ayayinda itakuma ta
hura wuta ta É—aura ruwan tuwo.
Bayan nagama cemata nayi nagama inda tanuna wata leather dake ajiye bakin varendern
kitchen É—in tace namane in É—auki karamar tukunya inje inwanke matashi inkawo. Sanda
nawanko Naman nakawo harta hura É—ayan murhun danhaka setace indaura,na É—aura,tace
inmiko mata albasan dana yanka shima tasaka wanda zai Isa sannan taturani kitchen
in É—auko mata su Maggi,onga dadai sauran spices nayin miya duk naje na É—auko nakawo
inda daganan kuma tacemin in É—auki É—ayan leathern dake ajiye abakin varendern
kubewa ne aciki inje inwankeshi inyanka mata.
Cewa nayi "toh" sannan na É—auka naje nawanko nazo nafara yankawa kamar yanda tace.
Yaukam hannuna yaga duniya,shikanshi hannun nawa nasan seda yashaida cewa rayuwata
tacanza bakamar da ba. Ana kiraye kirayen sallar maghriba yau aka sauke tuwo da
miya kuma already duk na kawo kwanukan daza'a zuzzuba abinci inda nan Ummi tashiga
raba abincin harta gama daganan kuma tadinga nunamin yanda zanyi distributing
abincin ma mutanen gidan. Seda nakaima kowa nasa acikin gidan yarage saura na yan
boys quarters dana Kawu Sani ne kawai agurin.
Cewa tayi inkai na Kawu Sanin parlourn ta in ajiye se indawo,cewa nayi toh sannan
na É—auka nakai nadawo kafin tanuna min nasu Yaya Salim tace Inkai musu sashinsu
cewa nayi "toh" sannan na É—auki trayn nasu nanufi boysquarters inda suke zama.
Bansamu kowa a sashin nasu ba hakanan ban haÉ—u dakowa ahanyata nazuwa sashin nasu
ba kamar yanda mukayi kicibis da Yaya Fahad É—azu anma dai kofar tasu a buÉ—e take
danhaka sena shiga nanufi dinning table É—insu na ajiye trayn abincin.
Harna juya zantafi sewata zuciyar ta rayamin intafi da tray É—in lunch É—insu dahar
lokacin yanakan dinning É—in kuma ga plates É—inda nakawo musu É—azu duk anbata da
alamadai anci abinci dasu. Sa hannu nayi najanyo tray É—in zan daga senajishi daÉ—an
nauyi wanda hakan yasani mayarda trayn na ajiye sannan na buÉ—e foodflask É—in
abincin and I saw some remaining food aciki dukdama bashida wani yawa.
Kawai senatuna ai Ummi ma batayi rabon abinci dani ba sannan banci abincin rana ba
due to abubuwan dasuka faru É—azun harnayi loosing appetite É—ina,kawai sewata
zuciyar tashiga raya min inzauna inci guntun shinkafar dasuka rage a foodflask É—in
tunda banida tabbacin za'a rage guntun abinci har insamu inci anjima.
Take kuma wata zuciyar tashiga rayamin "what if su Yaya Zunnurain suka dawo suka
sameki kinacin sauran abincinsu yazakiyi?" tura baki gaba nayi out of option dan
kwata kwata bana ra'ayin intafi da abincin can tunda inada tabbacin zan iya samun
Ummi a kofar kitchen danna barta tana wasu ayyuka agurin and may be intaganni da
abincin takarba kokuma ta tambayeni dalilin dayasa naÉ—auko ba'asakani ba.
Sekuma kunnuwa na suka jiyomin ana sallah haryanzu a masallacin dake kusa da mu
danhaka kawai senayi deciding inzauna inci dasauri intafi kafin sudawo. Jan kujera
nayi nazauna sannan nasa spoon cikin foodflask É—in nafara cin abincin cikin sauri
dukdan insamu ingama kafin su Yaya Zunnurain sudawo daga masallaci intafi.
Ban ankara ba kawai seji nayi ana ƙoƙarin buɗe kofar parlournsu,wani irin zabura
nayi tareda tashi daga kan kujerar danake zaune sannan nanufi jikin labulen dake
kusa da ni na buya ayayinda zuciyana ke dukan uku uku wanda alokacin naji harme
taba kofar yariga da yashigo cikin parlourn. Ahankali nakai idanuna jikin wasu
kananun buli bulin da akayima labulen design inawulwullah idanu kozanga wanda
yashigo É—in,can kuwa sega Yaya Fahad yazo zai wuce.
Rimtse idanuna nayi ayayinda zuciyana kekara sautin bugun dayakeyi kafin nasake
bude idanun nawa nadaura su akansa dankuwa harlokacin bebar inda yakeba,senaga yana
kallon dinning table.
Araina nashiga cewa "nashiga ukuna gashi nabar foodflask É—in abincin abude" É—auke
idanunshi yayi daga kan foodflask É—in yadan kalli labulen danake boye abayanshi
naÉ—an wasu sakanni kafin yayi wucewarsa cikin gidan kuma. Wani irin wawan ajiyan
zuciya nasauke dan sanda naga yana kallon labulennan nariga nagama sadakarwa yau
asirina tonuwa zaiyi sekuma Allah yarufamin asiri.
Seda naji yabuÉ—e kofar dazata sadashi da corridorn dazaikaishi dakunansu sannan
nafito daga boyon danayi nayi sauri nakarasa inda food flask É—in shinkafar take
nadibi loma É—aya nakai bakina kafin nayi sauri narufe foodflasks É—in sannan na
É—auki trayn nafice a sashin nasu cikin sauri har inashirin yin dungure.
Fahad tun sanda yabuÉ—e kofar parlourn yaga Rukayya na gudu zata buya abayan labule.
daya karaso gun dinning table É—inma yaga abincin data ke ci É—in,yakuma ga shadow
É—inta boye a bayan labulen anma sebai cemata komaiba,sebe nuna yamasan tana cikiba
sekawai yayi kaman yawuce ciki ne bayan kuma yana shiga corridor É—in yaja tunda
yatsaya adede jikin kofar yana lekenta and he saw everything sannan ganin yanda
tayi one loma even though she's afraid kar akamata dakuma yanda take sauri seda
hakan yaso bashi dariya anma sebeyi dariyarba seyayi murmushi kawai while on the
other hand yake mamakin miyasa tazo tanacin abinci a sashin su? Is she by any
chance staying hungry all day agidan? Ma'ana ba'a bata abincine komi?
Sewata zuciyar tashiga rayamishi cewa aitunda tazo gidanma girkin Aunty ne kuma
baya tunanin Aunty zata iya hana koda makiyinta ne abinci. Sekuma yatuna Aunty bata
taking part a harkar girki tunbayan da Siyama tagama secondary school tadawo gida
gaba É—aya. Sede ita tayi kuma kotagama É—in ita take rabawa,seya tuno tsanarda su
Siyama sukema Rukayya,rashin jituwarsu dakuma kunkunin da Sadiya tayi tayi ranar
dayace tashiga da kayan Rukayyan É—akinsu. Toh anma danka tsani mutum zaka hanashi
abinci ne fisabilillahi? abunda mukesawa a bakin salatinmu yasa murayu mukuma zama
healthy mutane?seya shiga girgiza kai in desbelief,se zuciyar tashiga rayamishi
Siyama will never do such a thing and intanayi É—in kuma toh yazama dolene ya taka
mata burki but how? Shida ko hira normal bata shiga tsakaninsu bare azo ga batun
wasa? Kowa agidan yasan halin shi na rashin damuwa da shiga harkar kowa then why
will he interfare yanzu dayazo kan Rukayya. Why? wannan shine tambayar dayama kansa
and he got no answer.
Shidai kawai yasan yanajin tausayin yarinyar tunsanda suke jinyar mahaifinta a
asibiti anma aihakan bazaisa yaÉ—auki akidarsa dakuma policy É—in saba. Koma menene
it's between her and them he shouldn't interfare. The only help he can offer shine
inyana nan he'll surely reduce food for her tunda yaga yanzu itake kawo musu abinci
takuma dawo ta É—auke kwanukan.
Ummi kam babu tantama in akace batama Rukayya abinci bazai yi mamakiba dankuwa
yasan halinta dakuma what she's capable of. dawannan tunanin yawuce É—akinshi sannan
yashige bathroom donyin wanka yaje yayi sallar isha'i inyadawo yaci abinci seya
kwanta bacci. ShiÉ—in wani irin mutum ne dake daraja lokaci sosai,kominsa acikin
tsari yakeyinsa. lokacin fitansa,lokacin aikinsa,lokacin cin abincinsa dakuma
lokacin baccin sa. He always makes sure yayi su adede lokacin daya tsara musu.
Tunda nanufi backdoor É—in gidan nakejiyo muryar Ummi tana ta aikin masifa acan kusa
da laundry itada su Mariya harna karasa bakin kofar kitchen na ajiye trayn dake
hannunta wanda alokacinne kuma Ummi tahangoni. cikin tsawa tace "ke Rukayya Zonan
don Ubanki" wani irin rass naji azuciyana kafin nashiga taku zuwa inda take tsaye.
Tana kallona tace "meya hanaki wanke kayan fitsarin nan bayan su Mariya sunce miki
kiwanke musu?" dafe kirji nayi dasauri Ina ware idanu nace "nikuma? wallahi basu
faÉ—a min ba..." Mariya da Sule dake tsaye gefe idanu wuri wuri sukace "wallahi
karya take Ummi" sannan Mariya takarada "tun safe mukace mata tawanke mana don
Allah munyi latti dan inmukace zamu tsaya wankewa Yaya Fahad zetafi yabarmu"
cikeda mamakin karyar dasuka gindayamin nasake buÉ—an baki nace "wallahi Ummi karya
sukeyi! Nibasu cemin inwanke..." Anma sede tunma kafin in karasa magana ta tayi
sauri ta katseni tahanyar yimin tsawa "Dallah yimin shiru ni. So kike kicemin
sharri sukayi miki komi? tukunnan ma ta'ina yarannan zasu iya haÉ—a karya irin haka
harsu faÉ—amin. Kede baki wanke ba shine kikeson dojewa koh? Toh wallahi baki isaba
kuma tunda har rokonki sukayi kika ƙi kiwanke don Allah ɗin toh dagayau kezakina
wanke musu kayan fitsarin nasu kullum dasafe inyaso inkikaga dama kiyitayi dan
shedan kinji?" Nidai bance komaiba se hawaye.
Tanuna min kayan fitsarin nasu dake jubge agurin cikin katuwar baho tace "wannan
É—inma kuma adarennan zakiwanke dan Ubanki! Bake taurin kaiba? har yaran masu gida
sucemiki kiyi abu ki kiyi sabida rashin ta ido. Toh wallahi sekin wanke waÉ—annan
É—in ma yanzunnan" kafin tajuya tadubi su Mariya dake tsaye suna murmushi tace "muje
inbaku klin da sabulu kukawo mata tafara wankesu yanzunnan"
Cewa sukayi toh suna murmushi sannan suka tafi abunsu,suka barni tsaye gurin kamar
wata gunki gashi gari yafara duhu sosai wai danma akwai security lights a filin
gidan baki É—aya.
Haka suka dawo suka sameni tsaye gurin Ina kuka,Mariya wulli tayi da sabulu da klin
É—in akasa cikin laundry É—in tana faÉ—in "Gashi Baba Rukayya me aiki kuma awankesu su
fita tas inbahaka ba mutum yasha duka" sekuma suka kwashe da dariya itada Sule
atare.
Nidai bance musu komaiba hakanan inajin Mariya nacema Sule seyabata sweet É—inda
yamata alkawari tunda ita takawo idea É—in suyimin sharri in order to save
themselves.
Sunkuyawa nayi naÉ—auki sabulu da klin É—inda suka wurgar akasa sannan nakarasa cikin
laundry É—in nasamu guri nazauna Ina tunanin yanda zan iya wanke waÉ—annan kayan
fitsarin. Ni wankin kanshi ban taɓa yiba hakanan bansan ya akeyiba dankuwa normal
kayana ma bansan ya ake wanke suba. Baba ne kehada kayana da nashi yawnke mana
kullum.
Hakadai nasa hannu nafara mummurzawa Ina wankewa daduka iya karfina harna gama na
dauraye na je na shanya akan igiya dukda kuwa dakyar na iya na matsesu sabida
nauyinsu hakanan koda nashanya É—in akwai ruwa sosai jikin kayan se diga sukeyi.
Seda naje nacire kayan jikina danduk sun jike julub sannan nadawo nayi alwala naje
varendern kitchen na shimfida dankwalina natada sallah danban manta hanani zaman
parlour da Ummi tayiba.
Bayan na idar da sallan karasa cin sauran shinkafar dana taho da'ita daga sashin su
Yaya Fahad nayi sannan nakoma kan shimfidin danayi,narakube guri É—aya inajin wani
irin sanyi yana ratsani wanda inada tabbacin wankin danayi da daddarennan ne
yakeson yajamin mura gakuma wani irin tsoro danakeji.
Danaji motsi kaÉ—an nadinga dube duben surrounding É—in gurin kenan zuciyana na aikin
bugu. Seda naga dare ya tsala sosai sannan tsoron nawa se karuwa yakeyi sekawai
natashi naÉ—auki dankwalina dake shimfide kasa nashige Kitchen narufe kofar taciki
sannan nasamu guri na shimfida É—an kwalina nakwanta akai tareda lumshe idanu
ayayinda wasu hawayen kebin wani.
Awannan lokacin nikaina bansan me zuciyana kejiba. Bazan iyacewa nayi bacci awannan
daren ba hakanan bazan iyacewa banyiba dankuwa dana fara gyangyadawa kaÉ—an zan buÉ—e
idanuna a firgice daganan kuma kafin insake fara gyangyadawa se anjima.
***
Salim karfe goman dare yashigo gida daga majalisa hakanan yanashigowa babu inda
yazarce se sashin iyayen nasu. Yasan by now Ummi tana sashin Abban su shiyasa ma
yayi deciding yashigo yaga Rukayya batareda yasamu wani matsala da ita ba.
Main parlour yashiga sannan yafara dube dube kozaiganta anma wayam batanan. sa
hannu yayi yanadan sosa gemunshi. For sure jiya anan yasameta tana bacci daya shigo
wuraren shadaya shima dan yaganta and somehow he felt sorry for her,ajiyan yaso
yatasheta tashiga ciki takwanta anma yasan halin Ummin sa sarai shiyasa yace bariya
bari seyau tunda yau a sashin Abban su Ummin zata kwana anma segashi yazo yanzukuma
batanan. Toh where could she've gone to? Wannan shine tambayar dayayima kansa.
Sekuma yanufi sashin Ummin. A parlour yasamu su Mariya suna kallo duban su yayi
sannan yace "Ina Rukayya?" take Sule yace "bamu saniba Yaya Salim" akafule Salim
yace "kamarya bakusani ba? bakuganta bane yau kwata kwata?" Sule zaiyi magana
Mariya tayi sauri tafaki idon Salim sannan ta mintsini Sule akafa kafin tace
"munganta Yaya Salim É—azu ma naganta a main parlour" Salim yace "toh yanzu batacan"
Mariya tayi sauri tace "kilan tana sashin su Aunty dannaji É—azu Yaya Siyama
tanacemata tatashi tashiga É—akinsu" wani irin wawan ajiyan zuciya Salim yasaki
sannan yajuya yafice a parlourn Ummin.
Sule datunda Mariya ke magana yazuba mata idanu baki sake harsaida yaga Salim
yafice a parlour sannan yace "miyasa kikayi karya Mariya?" hararan sa Mariya tayi
sannan tace "sokake incemasa tana waje yaje ya É—auko mana ita yace takwana a É—akin
mu? Toh Ummi ne tace infadi haka in Yaya Salim yazo yana tambaya dantasan zezo
yatambaya É—in tabbas" Sule yace "aibansan Ummi ne tafaÉ—a ba nayimamakin yanda kika
gindayo karyane lokaci guda".
***
Akunnena aka fara kiraye kirayen sallar asubahi wanda hakan yasani tashi na buÉ—e
kofar kitchen É—in nafice zuwa banÉ—aki nakama ruwa sannan nafito nadaura alwala anan
bakin tap É—inda akeyin wanke wanke sannan nakoma kitchen natada sallah. Bayan na
idar kayan wanke wanke na tattare nakaisu bakin famfo nayi sanin cewa koba'a faÉ—a
minba nidince dole zanyi.
Inagama wanke wanken bada jimawa ba kuma Ummi tafito nanmuka fara harkan girke
girke harmuka gama. dayake yau Monday ne babu islamiyar safe Sena yanma. Yau
makarantar Boko zasu kuma shi seven thirthy suke tafiya daman sabida ana assembly
by eight kullum kafin afara classes.
Tun muna girki su Mariya sukazo suka ajiye kayan fitsarin su sannan suka koma ciki
dansu shirya danhaka munagama ayyukan abincin bayan ankai ma kowa nashi nadawo
nanufi laundry don inwanke kayan fitsarin nasu. Inacikin wankewa sega Sadiya ma
danata memakon tazauna tawanke da hannunta senaga tazubaminsu kan nasu Mariya
sannan tayi juyawarta takoma ciki. Bance komaiba sannan tabbas nasan ajiyewan
datayi tana nufin inwanke matane kuma dolena inwanke sabida tsoron abunda zai biyo
baya dukda kuwa raina bayason wankewan. Toh haka rayuwata tacigaba da kasancewa
agidan Kawu Sani,banida lokacin zama inhuta dagana gama wannan aikin se wancan.
Kowaye zaiyi girki nizan tayasa hakanan nizanyi wanke wanken safe dana yanma inkuma
share main parlourn,inshare backyard É—insu da kitchen sannan inwanke kayan fitsarin
su Sadiya kullum dasafe. Sashin Aunty kuwa wani sa'in se Sadiya takiyi dagangan
haka Yaya Siyama zatace ni inje inshare.
Bangaren Ummi ne kawai ban taɓa sharewa ba shiɗinma itace bataso dankuwa su Mariya
sunsha attempting cewa inje inshare intasasu suyi anma danaje se tahauni da masifar
miyasa nashiga mata sashinta acewarta zansaka mata tsamin jiki da body odour. Body
odour da ahalin gida uku ne kawai Kejinshi ajikina,sukadai sukayi believing
inadashi dannidai bantaba jin jikina yana tsamin dasuke fadaba hakanan bantaba
ganin wani yana kyamatata ba.
Abinci kuwa ba'abani kasona sede in anci anrage inci dukdama yawanci na sashin su
Yaya Fahad nike ci sabida azimunne kullum sesun rage abinci wanda hakan bakaramin
mamaki yakebani ba tunda abincin bawani na kirki ake saka musu ba. Ranar laraba
Buba É—an gidan Baffa idiii yazo ganina,bakaramin daÉ—in ganinsa najiba hakanan
dagudu naje na rungumesa se hawaye. Dakyar shida Yaya Salim suka lallasheni dankuwa
da Buban yazo da Yaya Salim suka haÉ—u a waje inda shikuma yashigo dashi sashinsu
sannan yaje ya kirawoni dan inzo mugaisa sanin cewa inyakaishi sashin mu ze iyashan
wulakanci gurin Umminsa.
Munjima muna hira da Buba dan daga karshema Yaya Salim shigewa É—aki yayi yabarmu
munata yarawa da fillanci inda ananne Buban yake sanar dani ai alkawari yama LamiÉ—o
zezo yaganni yakuma bani sakon daya kawomin.
Cikeda zumudi nace "LamiÉ—o yazone daman?" dankuwa nitsabar damuwar dana shiga ma na
manta LamiÉ—o yamin alkawari zezo asabar É—innan data wuce infact kwata kwata bema
fado min raiba a Æ´an kwanakinnan dasuka wuce. ashedai yacika alkwari! ashedai inada
masu sona dahar suka É—aukeni da mahimmancin dabazasu iya saba alkawarin dasuka
yimin ba dankada suyi breaking heart É—ina.
Buba yace "Eh yazo aihar Babban buli yaje yaÉ—aukoni mukazo mukayita yawon neman
inda kike bamu samekiba" nandai yabani labarin yanda LamiÉ—on yaje asibiti akasanar
dashi rasuwan Baba dayanda yaje yaÉ—auko shi a Babban buli dakuma irin wahalar
dasuka sha shi da LamiÉ—o wurin yawon nemana hardai yahakura yakoma Gombe daga
karshe.
Sannan yaciro ribom a aljihunsa yamikamin yace "wannan shiyabani yace inbaki. Wai
inji kanwarsa Salma sannan yace in faÉ—a miki zedawo dukda ma baisan ranar dawowan
nasaba anma tabbas zaidawo yaganki" yaÉ—auki leathern dake ajiye agefenshi yabani
shima sannan yace "wannan ma shiyace inbaki Ru'eyya. Tsarabar dakikace yayomiki ne
daga Gombe. dabaku haÉ—u ba shine yabarmin yace inbaki don Allah anmafa munciye
abubuwan dazasu ɓaci sauran dai suna cikin leathern" buɗe leathern nayi Ina dariya
ayayinda hawaye kebin kuncina sannan nace "inadai kabama su Indo bakai kaÉ—ai ka
cinyeba?" Cikeda zolaya Buba yace "niban basuba nida matata kaÉ—ai muka cinye"
dariya nakumayi sannan nace "bawani nan nasan wasa kakeyi" shima yana dariyar yace
"tunda baki yarda ba shikenan"
Wannan karan murmushi kawai nasaki inajin wani farin ciki marar misaltuwa acikin
raina,senaji nasake bama LamiÉ—o wani gurbi nadaban acikin zuciyata. Something
special, something beyond the ancient feelings.
Leathern magarya na buÉ—e nadibi kaÉ—an nakai bakina Ina kissima irin farin cikin
dazanyi idan yadawo dakuma yanda zanbashi labarai,labaran dasuka sha banban danada
danake bashi. I just don't know why I feel he's the right person to know about my
happiness and sorrows all the time. I'm just free with him tun farkon sanina dashi
and wannan É—in wani ikone daga Allah. Shine yahaÉ—a shakuwata da LamiÉ—o harma
nakejin zan iya sharring komai dashi fiye da kowa.
Se wuraren la'asar sannan Buba yamin sallama yatafi sannan nakoma cikin gida. Kuma
dai bawanda yasan ma nahadu da Buba agidan inbanda Yaya Salim dankuwa wannan
lokacin I'm free kuma kowa yana cikin gida sebayan la'asar za'afara aikin girkin
dare. Kuma koda Buban yanuna yanason gaisawa dasu Ummi Yaya Salim cewa yayi
baswanan dukansu nima kuma se hakan dayayi naji yamin daÉ—i dankuwa bazanso a
wulakanta kowa nawa ba sabida ni and for sure indai Buba zai gaisa da Ummi toj
definitely seya tafi gida rai bace and may be inyaje can Babban buli ma yace ze
faÉ—a ma su Gogode wanda hakan kuma bakaramin tada musu hankali zaiyi ba inda nikuma
banason hakan tafaru. Adaren ranar Kawu Sani ya kirani yasanar dani cewa annema min
alfarmar abani admission tawurin abokin Yaya Fahad dayake koyarwa a FGC Azare kuma
shi abokin Yaya Fahad É—in yama principal É—in makarantar magana kuma ya amince akan
akaini gobe inyi pre test wanda through pre test É—inne za'agane if zasu iya bani
admission É—in kobazasu baniba tunda already anriga anyi comman entrance har results
yafito sa'annina dasuka ci suntattafi har anfara musu classes last week. Yacemin
inshirya washegari Thursday dasafe zamu tafi da Yaya Fahad zekaini inyi pre test
É—in inyaso innaci se afara yimin shiri ranar Sunday akaimu kawai tareda Sadiya
tunda Itama ranar zata tafi.
Cewa nayi "toh" sannan nama Kawu Sani godiya.
Murmushi yayi tareda cewa "bakomai Daughter. I hope litattafanki nanan gidan?"
gyaÉ—a masakai nayi ahankali dankuwa nazo da school bag É—ina dagacan gida daman.
Cewa yayi "toh seki dage kiyi karatu adaren yau and then pray muma kuma zamu tayaki
yin addu'an Allah yasa adace" gyaÉ—a kai na nayi sannan nace "Amin" shafa kaina Kawu
Sani yayi yana murmushi sannan yace "Allah yamiki albarka" "Amin" na kuma cewa
sannan yasallameni nakoma cikin gida. Inashiga main parlour class bag É—ina naÉ—auka
nanufi Kitchen, gaba É—aya daren ranar English da Maths notebooks É—ina nakwana Ina
karantawa,dana gama nazarin wannan littafin inkoma nazarin wancan hardai asubahi
tayi. Tun ina kankanuwata naÉ—auki Karatu a matsayin wani abuda ya zamamin dole
inyishi. NaÉ—aukeshi a matsayin priority a gareni shiyasa inzanyi jarabawa ko test I
always make sure I'm ready for it koda ba duka baneba toh zan tabbatar na iya 70%
shiyasa I never fail,I'm always in the average set.
Kamar kullum Ina idar da sallar asubahi natattara wanke wanke nayi wanda hakan
danake yi É—in yasa mura tayimin mummunar kamu har in ina tari zakaji kamar kirjina
ya rube ne anma yazanyi? Abunda yazamar maka dole kayishi aisede hakuri kawai.
Banjima da gama wanke wanken ba Yaya Siyama tafito dayake yau girkin su ne inda
daganan kuma muka fara aikin girki tare. Zuwa goman safe nagama aikina tsaf sannan
nashiga bayi nayi wanka sannan naje na buÉ—e akwatina naÉ—auko É—aya daga cikin sabbin
kayana tareda hijabi nasaka sannan naÉ—auki pen da pencil a class bag É—ina nasaka su
cikin envelope É—in credentials dina dana riga nadauka tundazu sanin cewa kilan a
bukacesu.
zuge zip É—in akwatina nayi namaryadashi inda yake da sannan nazuge na class bag
É—ina shima na mayar na ajiye sannan natashi tsaye envelope É—in credentials É—ina
rungume a kirjina wanda adede lokacinne kuma Kawu Sani,Yaya Fahad da Yaya Salim
suka shigo parlourn dukansu cikin shirinsu except Yaya Salim sake sanye da
jallabiya har lokacin.
Samun guri sukayi a main parlourn suka zauna Kawu Sani na kallonta yace "ÆŠaliba
Rukayya harkin shirya kenan?" murmushi nasaki inajin Yaya Salim na faÉ—in "Abba
she's fully ready for the exams fah. bakaganta harda credentials É—inta tadiba ba?"
dariya Kawu Sani yayi ayayinda nakarasa cikin parlourn na tsuguna akasa nagaida shi
sannan nagaida Yaya Salim da Yaya Fahad ma duk suka amsa.
Littafin Qadr na kudi ne duk Maison shiga paid group should talk to me on WhatsApp
through this number 08147722806.
*Page Thirty One*
Kallon envelope É—in hannuna Kawu Sani yayi sannan yace "menene acikin envelope É—in
kuma Daughter?" ahankali nace "credentials É—ina ne naÉ—auka bansani ba ko za'a
bukata" jinjina kai yayi sannan yace "kinko yi dabara abunda nazo intuna miki
kenan" murmushi kawaii nayi batareda nace komai ba.
Yace "Toh mikomin credentials É—in ingani" mika masa nayi inagani yabuÉ—e yaciro su
duka yana duddubawa harya gama yamaidomin da abuna sannan yadubi Yaya Fahad yace
"Son se tafiya koh?" Ahankali Yaya Fahad yace "Eh Abba" Kawu Sani yace "toh muje
kukama hanya nima se in wuce office" tashi Yaya Fahad yayi yana faÉ—in "toh" kafin
yanufi kofar sashin Aunty Yana faÉ—in "Bari muyi sallama da Aunty"
Bejima cikin sashin Auntyn ba segasu sunfito tare da Aunty.
Gaidata nayi ta amsa min fuska sake sannan tagaida Kawu Sani inda daganan kuma muka
fice dukanmu. harjikin mota Yaya Salim ya rakamu shida Kawu Sani Aunty kuma daman
tundaga bakin kofar fita a main parlour tayimana Allah yakiyaye hanya takoma cikin
gida abinta.
Bayan munshiga motar tada injin motar Yaya Fahad yayi still Kawu Sani da Yaya Salim
na tsaye daga gaban motan suna kallonmu.
Yaya Salim ganin Yaya Fahad yatada motar seyadubeni yace "Toh Ruky Best of luck
kinji?" Yar murmushi nasaki sannan nace "thank you" Kawu Sani yace "makesure you
compose yourself kafin kishiga test din kinji Daughter?" Shima gyada mishi kai nayi
sannan nace "toh" kafin yadubi Yaya Fahad yace "Fahad Drive carefully karkaje kana
gudu a babban titi fah Fahad" Yaya Fahad yace "insha Allah Abba" sannan yayi
reverse aka bude masa gate mukabar gida. gaban wani restaurant dake nan cikin garin
Bauchi Yaya Fahad yayi parking sannan yadubeni yace "Sauko kibiyoni" zuciyata fal
take da mamakinsa anma sena boye mamakina nakama handle É—in motan nabude nafita
danshi already haryafice a motar jirana yakeyi infita yasama motar key.
Shine agaba inabinshi abaya har muka Shiga restaurant É—in. Table me kujeru guda
biyu yasamu yaja kujera É—aya yazauna inda yanuna min É—ayan yace in zauna nima. É—aya
daga cikin ma aikatan restaurant dince tazo tayi mana sannu dazuwa sannan tashiga
tambayar Yaya Fahad abunda za'a kawo mana.
Seyace mata meda me suke dashi on ground cikin sauri tashiga lissafamasa harta gama
nidai idanuna nakan table É—in feeling uncomfortable.
Kawai sejinayi ya jefomin tambaya "what would you like to eat?" dagowa nayi cikin
sauri don son in tabbatar dani yake kobada ni ba senaga ni É—in yake kallo. Maida
kaina nayi kasa dasauri sannan ahankali nace "Anything"
Kawai senaji shima yanace ma waitress É—in "just bring anything for her" murmushi
waitress É—in tayi sannan tadawo da dubanta gareni tace "toh akawo miki chips,
plantain and egg?" GyaÉ—a mata kai kawai nayi sannan nace "toh" murmushi tayi sannan
tasake maida dubanta ga Yaya Fahad tace "what of you Sir? meza'a kawo maka?" Yaya
Fahad yace "No I'm okay kikawo Mata natan dai"
Waitress É—in nakawo min abincin senaga yatashi yafita wanda hakan yasa naci
abincina comfortably dukda Ina mamakin ya akayi Yaya Fahad yasan banci abinci ba
tundadai ai yasan anyi breakfast agida kuma harkai musu nasu nayi sashin su.
Wata zuciyar kuma seta shiga rayamin kodai Kawu Sani ne yabashi kuÉ—i yace mutsaya a
hanya inci abinci? Take Kuma É—aya part É—in zuciyartawa tayi dismissing wannan
tunanin danbaiyi making sense bama kwata kwata. Dama adawowa ne yasayamin abinci se
ince wannan Kawu Sanin ne yace yasaya min anma ayanzu kam nasan a assumption É—in
Kawu Sani nayi breakfast agida tunda basanin abubuwan da iyalin sa keyimin yayi ba.
Hakadai nakarasa cinye abincina still Ina mamakin canzawar Yaya Fahad É—in. I just
can't believe it tunda banasuba ganin yanama kowa haka ba anma sena bar abuna
acikina ni kaÉ—ai. Bansan ya akayi yasan nagama cin abincin ba kawai seganinshi nayi
yashigo entrance É—in restaurant É—in bayan nakai last spoon É—in abinci bakina.
Zuwa yayi yayi payment sannan yazo hannunshi É—auke da SWAN water guda biyu,yaÉ—au
É—aya yamika min É—aya nakarba nasha sannan muka tafi. Harmuka Isa Azare babu wanda
yayi magana cikin mu inbanda wakokin Zain Malik da Maher Zain dake tayamu hira
acikin motar inda daga karshe ma yamaidashi karatun alqur'ani. Agaban
administration block É—in FGC Azare Yaya Fahad yayi parking sanda muka shiga
makarantar. Babu laifi makarantar tayimin kyau dede gwargwado,students nata kai
kawo abunsu cikin makarantar looking very neat in their uniforms dayake lokacin
damuka isa makarantar yayi daidai da lokacin break. Office É—in abokin Yaya Fahad
muka fara zuwa. shine examination officer na makarantar baki É—aya kuma yana É—aya
daga cikin Malaman dake koyar da literature ma yaran dake *Art and humanities*.
hira sosai Yaya Fahad da abokinsa sukeyi harda dariya wanda hakan bakaramin mamaki
yabani ba dukdama yawancin hirar abokin ne ke kawota. Nidai inazaune inajinsu
dantun bayan dana gaidashi bankuma cewa komaiba.
Harsaida aka koma break É—alibai suka koma classes É—insu sannan abokin yayi mana
jagora zuwa office É—in principal É—in. I must say the principal is very nice gashi
very carefree danyanda yakeyi min magana kamar wata diyarsa wanda hakan ba karamin
daÉ—i yayimin ba. Tambayoyi yadinga min akan makarantar danayi na faÉ—a masa kafin
yakoma min oral questions a English duk ina bashi amsa inda daga karshe yasa
secretary É—insa yayo printing questions É—inda zan amsa a pretest É—in yakawo min
nafara amsawa. Daman 1hr yabani. 30 minutes for English and the other 30 minutes
for Maths.
Nikam cikin mintuna arba'in ma nagama dankuwa waÉ—anda na'iya kawai na amsa wanda
bansani ba kuma sena bar space É—in blank batareda nayi attempting ba. Principal É—in
dakanshi yayi marking scripts É—ina kuma daga ganin yanda yake jinjina kai nikaina
nasan nayi abun kirki. Yana gama marking kirana yayi inda nakarasa kusa da kujerar
sa nervously dukda kuwa nasan mena rubuta.
Scripts É—in yadankamin ahannuna yana faÉ—in "I'm really impressed by your
performance Rukayya. Congratulations you've been offered admission in to this
prestigious college" bansan sanda wani irin murmushi yasubucemin ba hakanan araina
inajin wani irin farin ciki na musamman. Yes ada naqi boarding dankuwa nidakaina
nace bazanjeni ba anma ai alokacin inada genuine reason to which yanzu reason É—in
nawa is invalid tunda shi wanda nake ƙin boarding ɗin sabida shima yatafi yabar min
duniyar baki É—aya so aganina banida wata hujjar kin boarding kuma. Yes nasan ance
ana bullying yara anma senake ganin kamar can É—in zefimin daÉ—in zama fiyeda inda
nake zaune yanzu. Atleast I'll make new friends and be doing things together wanda
agidan Kawu Sani kuma inbanda tsangwama da tsagwaran aiki babu abunda nakesha.
Abokin Yaya Fahad ne yakirani bayan Principal yabani scripts É—ina nanyakarba inda
suka shiga ganin performance É—ina shida Yaya Fahad. Inajin abokin Yaya Fahad É—in
nafaɗin ainafi Sadiya ƙoƙarin ma nesa ba kusa ba dan itakan ma daƙyar tasha. Shidai
Yaya Fahad becekomai ba inbanda murmushi dayayi. secretary É—in Principal É—inne
yamin printing admission letter daduk wasu bills daza'a biya dakuma lists É—in items
É—inda za'a sayamin inza'akawoni makaranta inda daganan principal ya jaddada ma Yaya
Fahad kancewa akawomu dawuri dan already munyi missing classes da dama.
Yaya Fahad cewa yayi toh sannan yayima principal É—in godiya shima abokin nasa
yasakeyin godiya sannan sukayi masa sallama muka tafi. Har mota abokin Yaya Fahad
yarakamu yana zolaya na da "ayi a tattaro azo makaranta afara kwanan gadon karfe"
murmushi kawai nayi bance komai ba kafin yama Yaya Fahad sallama muka tafi. Agaban
wani hadadden Bakery dakenan cikin Azare Yaya Fahad yatsaya yasayamana sponge cake
da drinks sannan mukadau hanyar Bauchi. Ledansa daban nawa daban daman haka inagani
yana cin cake É—in tareda shan ice cream while driving anma ninakasa ci sabida
nauyinsa danakeji.
Seda mukayi nisa naga babu sarki se Allah kuma tabbas innace zanbar kayan
makulashennan senaje gida dasu inci babu tantama rasawa zanyi gaba É—aya danhaka
sena É—auko leathern na buÉ—e yawuna har tsinkewa yakeyi inason insha ice cream anma
wayam babu.
Smoov ne marar sanyi sekuma sponge cake irin nasa. Cake din kawai naci na ajiye
smoov É—in araina ina ayyana "cemasa nayi banashan ice cream komi? kuma dan rashin
mutunci smoov É—inma marar sanyi!" sekuma natuno É—azuma daya karbamana SWAN water a
restaurant shinashi me sanyi ne nikuma nawa babu sanyi atake kuma nagane murar
danakeyi ne yahanashi sayamin kayan sanyin.
Nidai abun kwata kwata baimin daÉ—i ba danhaushi ma yabani. Allah yagani naso shan
ice cream ɗinnan harcikin raina. (su Rukayya iyayen zaqewa😂)
Ba ƙaramin farin ciki Kawu Sani yayiba daya samu labarin nasamu admission a FGC
Azare kuma aranar yamin alkawarin zeyimin kyauta washegari inzai dawo daga gurin
aiki. haka yatara Matansa yasanar dasu Aunty har congratulations seda tayimin
ayayinda Ummi tayi kicin kicin ta fuska takicewa komai don abun yazo mata out of
blue,itakwata kwata ma batasan banyini agidaba yau dayake yau ba girkinta baneba
kuma daman indai baranar girkinta baneba ba kasafai muke haÉ—uwa ba. Bayan Kawu Sani
yasallameni nafita a parlourn nasa seta dubeshi kamar daman jjira takeyi tace "Haba
Alhaji wani irin É—anyen hukunci kayankene fisabilillahi?" Cikeda mamakinta Kawu
Sani yace "Ɗanyen hukunci kamar yaya?" rai ɓace Ummi tace "makarantar daka sama ma
Rukayya mana. Akan wani dalili zaka É—auki nauyin sama mata makaranta me tsada kamar
na Ƴaƴanmu. baganan government schools anan garinba kusa da gida kuma duka ana
karatu mai inganci. miyasa bakanema mata nanba" Kawu Sani tunda yaji Ummi na
magana mood É—insa yacanza lokaci guda anma sebe tsaida taba sedayabari takai aya
sannan yace "Sabida haka naga dama Hadiza kuma wai saunawa zan faÉ—a miki cewa
Rukayya da Ƴaƴanmu duk ɗayane agurina babu wani banbanci atsakaninsu and I want you
to treat her thesame?" rai bace yashiga nuna Ummi dan yatsa yace "kinsanfah ni
banason kananun maganganu da yawan tada fitina Hadiza. Kudin makarantar Rukayya
nine zanbiya ba wani ba sannan she's my responsibility so I see no reason why zaki
tada hankalinki dan nayi mata abu irin na Ƴaƴanmu. Kuma bari in faɗa miki gaskiya!
Indai kinason mushirya toh dole kibi abunda nakeso" tun daganan se batakuma cewa
komai ba anma tabbas ranta yamatukar ɓaci da decision ɗin mijin nasu and no matter
what bazata taɓa bari Rukayya tazama daya da sauran Yayansu ba.
She'll make sure they have huge differences É—inda shi Kawu Sanin dakanshi wataran
zaiyi realizing cewa abunda tafaÉ—a É—in gaskiya ne. Yes yanzu tasan bata isa
tasakeyin magana ba ganin yanda ranshi yamatukar ɓaci sannan kotayi maganar ma ba
amfani zatayi mataba so action speaks louder than words!bazata hana Rukayya zuwa
boarding ba dukda kuwa bataso tajedin barinma yanzu datake ganin tasamu Ƴar aiki a
free but she'll make sure she didn't succeed! She'll make sure shiwanda yasa aka
sama mata makarantar zecireta dakansa yadawo da'ita inda ita take muradi. washegari
kuwa dazai dawo daga gurin aiki segashi da kwalayen choculates guda biyu,yaraba ma
duka yaran gidan kwali É—aya sannan yaÉ—auki É—ayan kwalin yabani yace insuna so suma
ana basu mai yawa sudage sunayin ƙoƙari a makarantar both islamiya da Boko kamar
yanda nayi koma fiye da yanda nayi. Aikuwa ko É—aya banshaba cikin chocolates É—in
dan muna dawowa daga sashin Kawu Sani su Mariya sukaje suka sanar da Umminsu yanda
akayi. Ina zaune kofar kitchen ina ƙoƙarin buɗe kwalin choculates ɗin kawai se
ganin ta nayi akaina,sa hannu tayi tawabce kwalin chocolates É—in tareda faÉ—in
"Mayyah kawai!" daganan kuma tafara masifar inni ba mayya bace miyasa zaisayamin
chocolate meyawa ni kaɗai dannaci jarabawa kawai bayan bai taɓa sayama nasu Ƴaƴan
ba insun dawo daga makaranta sun kawo result. Wai ko performance É—insu baikai
nawaba ai sundai sha wahala amakarantar danko da dukan seniors akabarsu shima abun
asaya musu gifts ne danhaka bazansha ba inma maitanci nayi nayi seducing É—in
mijinta toh bazan sha ba Ƴaƴanta ne zasu sha" nidai bance komai ba hakanan inagani
taraba musu. dama banyi mamakiba dan koda yabani agabanta daman banyi farin ciki
dan nasan za'a rina. Aunty kuwa daman ita batada damuwa! Da ansani da ba'asani a
makarantar su Sadiya duk dayane agunta. Nata idanu ne dakuma yima Mijinta biyayya
tunda ba kuÉ—inta bane zeyi aiki a harkar makarantar taawa.
Washegari da safe kuwa Kawu Sani yakira Aunty yabata kuÉ—in shopping É—inmu yace taje
tasaya mana komai nida Sadiya. A motar ta ta dibe mu muka tafi kasuwa bayan fitan
Kawu Sani aiki sabida kai É—inkin uniform. Dole se anje damu an gwadamu. babu abunda
bata sayamana ba kuma dayake Kawu yabada ishasshen kuÉ—i Kuma equally yabada na kowa
seyazamanto komi zata sayamana iri É—aya take saya mana. se bayan azahar muka dawo
gida niki niki da kaya danseda muka tsaya muka bada dinkunan uniforms É—inmu inda
tailor É—in yace aje akarba ranar asabar dayanma sannan muka dawo gida.
ÆŠakinsu Sadiya Aunty tasa aka kaimana kayayyakin da aka sai mana sannan tacema Yaya
Siyama tataimaka mana muyi arranging cikin sabbin akwatunanmu a ajiyeshi a safe
place inda itakuma tayi shigewarta É—aki. Nikam daman ina ajiye kayan hannuna nayi
ficewata a sashin ma baki É—aya nakoma kofar kitchen nayi zamana sanin cewa Yaya
Siyama tahanani zaman É—akinsu.
Banjima da zamaba sega Sadiya tazo kirana wai Aunty Siyama ke kirana. Tashi nayi
nabi bayanta,a É—aki muka samu Aunty Siyaman tana gyaran akwati É—aya tana arranging
komai in order.
Batareda ta dubeni ba tace "kayan naki dakika bari a tsakiyar É—akin wazai tattare
miki su?" Shiru nayi bance komai ba setace min "zauna kisakasu cikin akwati
yanzunnan" gyaɗa matakai nayi sannan na ƙarasa kusa da akwatin nawa nafara jerawa
kamar yanda naga tanayi ma Sadiya anma sede kafin ingama itada Sadiya suncimin
biscuits yafi shida hakanan intaga na É—auko abu double zansa a akwatina kamar yanda
aka sayama Sadiya setace inbata haka zanmika mata jiki sanyaye.
Inajin Sadiya nata mitar "ai komai equally Aunty tasaya mana kamar wasu yan gida
É—aya kuma daman taÉ—au alwashin seta karbe É—aÉ—É—aya inmuka dawo gida dan bazai yuyu
muyi kafaÉ—a É—aya da'ita ba amma tunda Yaya Siyama takarba shikenan tabar mata"
nidai bance komai ba inagama gyaran zuge akwatin nayi naje na ajiye akusa dana
Sadiya sannan nayi ficewana.
Abun mamaki ranar da yanma sega Mariya da Sule sunzo suna titsiyeni wai ina kayan
shopping É—ina,ai Ummin su tace suzo sukarbi juice da biscuits suma zasu tafi dashi
islamiya kamar yanda Sadiya taÉ—auka zata tafi dashi. Cire hannuna nayi daga cikin
rubbern danake yanka albasa sannan nanufi cikin gidan don É—aukomusu kafin Ummi
tafito tafara min masifa.
Yaya Siyama kawai nasamu a É—akin kwance tana karatun Hausa novel tana cin cheese
balls É—inda nake da tabbacin cikin namu ta É—auka dukdama bazan iyacewa nawa taÉ—auka
ba kona Sadiya. Karasawa nayi kusa da akwatina na buÉ—e anma senaga abubuwan ciki
sun É—anyi kasaa. É—auka masu komai É—aÉ—É—aya nayi sannan narufe akwatin namaida shi
inda yake. Harna Isa bakin kofar É—akin zanfice naji takira sunanaa.
Juyowa nayi ahankali tareda faÉ—in "Na'am" wani irin kallo takema items É—in hannuna
sannan tace "inazakije dasu dakika diba É—in? bana tafiya makarantarki baneba?"
ahankali nace "Su Mariya zankaima zasu tafi islamiya" Rai bace tace "akan wani
dalili?" cemata nayi "Umminsu ne tace inbasu" da hannu tayimin alama da intafi
sannan tacigaba da karatun novel É—inta hankali kwance.
Fita nayi a É—akin Ina mamakin wannan É—in wani irin haline. wato taÉ—auka na diba
zancine shine take neman ta takamin burki? wato nida abuna anma ban isa inci ba
seranarda akace inci É—in bayan sukuma sunaci despite knowing cewa na makaranta
nane. Aikuwa tundaga ranar in makaranta zasu ko islamiya se Ummi taturosu sun karba
hakanan in Sadiya zataje islamiya ma seta ɗauka nidai ban taɓa cewa komaiba kuma
koyaushe naje na buɗe akwatin senaga yayi ƙasa sosai sannan haryau babu abunda
yacanza acikin wahalar danake Sha agidan. Ayyuka kamar wata jaka haka zan yini
inayi. ga tsangwama da zagi,abu kaÉ—an zanyi yazama laifi barinma ranar girkin Ummi.
Indai girkinta yazagayo to jazaman ne senayi kuka.
Abincin ma haryau ba'a fara bani kaso na ba kuma nafi tsanmanin sunsan inacin saura
and on purpose suke ƙin bani abincin,sunfison inci sauransu tunda anmadai ni kamar
Ƴar aiki ko almajira daman anma abunda basu sani ba shine basauran tray ɗinsu
nikeci ba a almajirai nakebama sauran insun zo bara ayayinda nikuma nakecin nasu
Yaya Fahad dasuke ragewa a foodflask dankuwa jazaman ne kullum sena samu sauran
abinci shiyasa ma nadaina tada hankalina kwata kwata dan ba ayi kason abinci dani
ba.
Ranar Friday da daddare Kawu Sani yakiramu yayi mana nasiha akan yadda zamu tafiyar
da rayuwar makarantar mu sannan yaÉ—auki tellern school fees É—inmu daya biya da
pocket money É—inmu yabama Yaya Fahad yace inya kaimu makaranta yabama abokinsa
kuÉ—in ya ajiyemana inyaso duk sanda muke bukata mwaje mukarba ahannunsa,ma'ana
shizai zama guardian É—inmu kamar yanda yake Guardian É—insu Yaya Aisha.
Bayannan kuma yasanar damu gobe asabar zaitafi Lagos wani conference daza'ayi
Monday É—inda za'a shiga inda zasu tafi tareda Aunty itazata karasa cotounou tayi
sarin kaya shiyasa yakiramu ya sallame mu yau. Yace mana ranar lahadin Yaya Fahad
nezai kaimu makaranta inda daganan zaikama hanyar Imo shima dankomawa bakin aikinsa
inda yake NYSC.
Godiya mukama Kawu Sani yatambayemu in akwai matsala duk mukace babu sannan yayi
dismissing É—inmu. Dayake flight É—in yamma zasubi kafin sutafi seda Aunty taje
takarbo mana kayanmu wurin tailor takawomana gida tacema Yaya Siyama ta mana
ironing É—insu tunda bamu iyaba anma data tashi seta goge na kanwarta kawai tabar
nawa.
Nibanma bi kan kayan ba seda dare tayi dan lokacin ne nasamu lokaci. Nashimfida
sallaya kenan zanfara gugan anan main parlour dayake kowa yashiga ciki sega Yaya
Salim yashigo.
Zolayana yashigayi da "Ƴar makaranta haryanzu shirin bekare baneba?" murmushi nayi
sannan nace "gugane yarage banyiba Yaya Salim" tsayawa yayi akaina yana kallon
yanda nake shimfida trousern house wears É—ina zanfara gogowa yace "toh kin iya
gugan ne?" Sincerely nace "zandai gwada" cewa yayi "tashi in goge miki. Irin kayan
nan if you're not careful konewa zasuyi in faÉ—a miki" babu musu namatsamai yazo
yazauna yakunna socket É—in sannan yafarayimin gugan yana Jana da hira wanda duk
yawanci labarin rayuwar dayayi a boarding ne dakuma irin wuyar dayasha. Wani inyi
dariya wani kuma inyi murmushi. Yace "Ke ana jahilci a boarding Schools fah! wani
jaki ÆŠan mitsitsi kana ganin ka girmeshi anma seya rainama wayau shi adole yana
takamar yafika class" Ƴar dariya nayi sannan cikeda curiosity nace "kenan ko baka
girmi mutum ba indai yafika class dole kayi respecting É—inshi?" Yaya Salim yace
"ƙwarai kuwa sukawai they believe once someone is ahead of you a class he's your
senior no matter what dukdama majority daman hakanne anma still akwai wanda suna
shiga school dawuri wasu kuma baswa shiga da wurin shiyasa zakiga wani yafi wani
aji anma befishi shekaru ba" jinjina kai nayi cikeda gamsuwa.
Yace "kede just focus on your studies shine kawai abunda yakaiki. babu ruwanki da
rashin ji dukdamadai nasan ke ba ruwanki. Sadiya ce Ƴar kiriniya Itama gobe zanyi
mata open letter insha Allahu" Ƴar dariya nayi shima yatayani yi sannan yace "nikam
inama takene? tagoge nata kayan kuwa?" kawai cemasa nayi "Eh" yace "toh barka"
daganan kuma yacigaba da bani labaran boarding school.
Can sega Mariya tafito daga sashin su taje kitchen taÉ—auko plate tadawo takoma ciki
inaganinta harta shige parlourn su kallon mu takeyi.
Aikuwa ko minti biyu batayi da shigaba sega Ummi tafito tana kwalama Yaya Salim
ƙira. Amsawa yayi tareda kashe socket ɗin iron ɗin sannan yajuya yana kallonta.
Atsaye take bakin kofar parlournta baki sake haryajuyo sannan tace "Kwaaal Ubaa!
Salim menake gani haka?" Yaya Salim tashi yayi tsaye tareda faÉ—in "Gugan makaranta
nake taya Rukayya Ummi" wani irin harara ta watsamasa sannan tace "A'a Uwar Rukayya
kake wa guga ba Rukayya ba! yanzu yaushe rabon da kayima kannenka gugan makaranta
talk more of azo kaina anma ka iya sakan handa da kanda kanayima shegiyar yarinyar
nan guga?"
In defense Yaya Salim yace "Ummi ba Zunnurain keyi musu ba? kuma ni ai baki taɓa
cewa in goge miki kaya naqi na gogeba" dakuwa Ummi tamai sannan rai bace tace
"Auuuu sema na faÉ—a kenan! Ai itazuwa tayi ta rokeka tace kayi mata gugan koh?"
Tashiga nunashi da É—an yatsa tace "toh wallahi Salim ka kiyayeni kafita harkar Yar
iskar yarinyar nan inkanason muzauna lafiya nidakai" jiki sanyaye Yaya Salim yace
"kiyi hakuri Ummi" tsaki tasaki sannan tanunamai kofar fita a main parlour tace
"wuce katafi sashinku yanzunnan" Yaya Salim yace "kiyi hakuri inkarasa mata gugan
don Allah Ummi. Saura kadan yarage yanzu zangama intafi" Ummi takuma cewa "nace
kawuce katafi sashin ku koh?" Pity face Yaya Salim yayi tareda cewa "Ayyah Ummi
bata iya gugan ba tana iya kona kayan in aka barta tayi dakanta" cikin tsawa Ummi
tace "intaga dama ma ta babbaka kayan wannan ba damuwarka baneba. Kawuce katafi
sashin ku yanzunnan nace" gyada matakai yayi ahankali sannan yafice a parlourn rai
bace ganin yakasa convincing dinta.

via this number 08147722806
*Page Thirty Two*
Harara Ummi ta watsamin bayan Yaya Salim yafita daga parlourn sannan tanunani da
yatsa daya tace "wallahi inbaki tattare kayanki kinfice a parlourn nan ba koh
yanzunnan zanzo in tattaka ki dagake har kayan naki! Munafukar yarinya kawai"
jikina na ɓari nacire kan iron ɗin daga jikin socket sannan nakashe socket ɗin
nashiga tattara kayana cikin sauri. Sanda nagama tattare kayan hartayi shigewarta
ciki wanda hakan yasani zuwa na ajiye akwatin kusa da akwatina na kayan gida
dankuwa banason shiga É—akin su Yaya Siyama suyimin korafin natashe su suna bacci
tunda dare yayi sosai. kitchen nawuce nayi kwanciyana kamar yanda nasaba kullum.
Najima ina tunane tunane kafin nasamu bacci yaÉ—auke ni.
Washegari dasafe seda nagama duka ayyukana dasuka zamemin daily routine É—ina sannan
nashiga wanka dayake Yaya Fahad cemana yayi karfe goman safe zamu kama hanyar
Azare. Aikuwa karfe goma dot segashi yashigo sashin namu. Nidaman a main parlour
yasameni zaune nagama shirina danhaka seya wuce ciki don ƙiran Sadiya. Baiwani Jima
acikiba sega su sunfito shida Yaya Siyama niqi niqi da kayan Sadiya ayayinda
Sadiyan ke biye dasu abaya bayanta goye da class bag É—inta.
Ganin sunfito yasa nima natashi naÉ—auki class bag É—ina na goya abayana sannan na
daga akwatina nashiga ja nabisu abaya.
Afilin gidan mukayi kicibis da Yaya Salim karban akwati na yayi cikin sauri yana
faÉ—in "Rukayya akwatinnan yayi miki nauyi ai ina zaki iya jansa?" murmushi kawai
nayi sannan nace "Ina kwana Yaya Salim" shima murmushin yakeyi yace "lafiya Lau
Rukyn Abba! Yau sai kwanan gadon karfe koh?" gyaÉ—a masakai kawai nayi ayayinda muka
ƙarasa jikin motar yasaka akwatin nawa cikin boot kafin yajada baya yana karkaɗe
hannayensa. Matrasses dinmu, blanket, pillow dadai sauransu daman tunjiya akasaka
su acikin mota.
Yaya Fahad dake riƙe da murfin boot ɗinne yadubeni sannan yace "iya kacin kayan
naki kenan?" gyaÉ—a masakai nayi ahankali sannan yarufe boot É—in motar yanufi
drivers seat batareda yakuma bi takaina ba. Dafari harda ghanamostgo Aunty
tasayamin kamar na Sadiya anma raguwar provision É—ina a Æ´an kwanakinnan yasa
akwatin yayi ƙasa kuma dayake akwatin babbane sekawai nasaka komai da komaina aciki
dukdama na nade ghanamostgo É—in nasaka shi cikin akwatin shima.
Books É—ina kuwa duk suna cikin katuwar classbag É—inda ke goye a bayana. Yaya Salim
ne yabuÉ—e min gidan baya na motar yace inshiga ayayinda Sadiya tun tuni tashige
gidan gaba suna yar hirarrakinsu tareda Yaya Siyama dake tsaye kusa da windown
gidan gaban wanda duk shawarwarine take bata gameda rayuwar boarding. bayan tagama
nata se Yaya Salim ma yahaÉ—a nida Sadiyan yayi mana nasa nadihan kafin yakoma ta
barin da Yaya Fahad yake zaune yace "Toh Bro yanzu Inka tafi se yaushe Kuma?"
murmushi Yaya Fahad yayi sannan ahankali yace "Only God knows" Yar dariya Yaya
Salim yayi sannan yace "Wai me inyamurennan suke bakane? Anya Inna gama nawa
karatun bazanje nan inyi service ba nima kuwa? Inje Inga yanayin rayuwarsu?"
Murmushi Yaya Fahad yyi sannan yace "Kaje wallahi! befi experience ba ai and you'll
get to know different people from different cultures in your country" jinjina kai
Yaya Salim yayi sannan yace "You're right! baridai musamu mu gurgurda mugama
jami'ar semuga abunda Allah zaiyi" Yaya Fahad yace "Allah yabaku sa'a" Yaya Salim
yace "Amin" sannan yadan sauke ajiyar zuciya yace "anmadai bayau zaka wuce Imo
bakoh?" Yaya Fahad yace "Yeah zankwana a Abuja gidan *Uncle Bakoh* (Yayan Aunty)
inyaso gobe dasafe se inkama hanya" Yaya Salim yace "okay fine! Safe journey Bro"
Yaya Fahad yace "Thank you" sannan Yaya Salim yazuro dakansa cikin motar sosai yana
dubanmu yace "Ƴan makaranta kundai ji abubuwan dana faɗa muku ko?" gyaɗa kai mukayi
duka atare sannan yace "toh Allah yabada sa'a" mukace "Amin" kafin yaja da baya
inda Yaya Fahad yaja motar mukabar harabar gidan.
Su Mariya basusamu sunyi sallama da Sadiya ba sabida suna islamiya muka tafi
dankuwa bazance hardaniba tunda magana ta arziki bata taɓa haɗani dasu ba sede na
cin fuska da cin mutunci. Sadiyar ma bawani jituwa sukeyi ba dansau tari nakanji
suna faÉ—a anma dai hakan bawai yana nufin baswa son junansu baneba! Yes they argue
and fight but that doesn't change the love they have for each other. Makaranta tare
suke zuwa kuma har faÉ—a Sadiyan takan shigar musu idan sunnemo tsokanan wasu.
Seda muka tsaya acikin gari Yaya Fahad yasaya ma su Yaya Zaheera fruits,Bread da
kilishi,muma yasaya Mana sannan yahada yabamu duka yace inmunje mubasu nasune
Incase behadu dasuba.
Lokacin damuka Isa FGC Azare school hours bai ƙare ba shiyasama koda Yaya Fahad
yaƙira Uncle Adam awaya (abokin Yaya Fahad) sebamuyi sa'an samun sa a free
ba,cemasa yayi yana class yana ma yara lecture anma nanbada jimawa ba zaifito
kafinnan muje inda ake karban sabbin É—alibai mufara processing abubuwa kafin yazo.
Yaya Fahad cewa yayi "toh" kafin yayi hanging up call É—in yabuÉ—e motarsa yafita
yacemana muma mufito sannan ya ƙarasa gaban boot ɗin motar yabuɗe mukafara saukar
da kayanmu muna kaiwa inda ake amsan sabbin É—alibai. bamu wani samu cue sosai ba
dayake ranar ba'akawo sabbin É—alibai sosai ba,dagani,Sadiya sewasu guda uku.
Cikin lokaci kankani aka gama mana processing komai,akayi checking É—inmu in yarage
saura abamu class kuma shiÉ—inma Malamin da akayi assigning yanayin wannan aikin
baya kusa shiyasa akace muzauna mujira yazo ba nisa yayi ba zaidawo nabada jimawa
ba. Uncle Adam dakuma Malamin dazai bamu class kusan atare suka iso gaban
administration block É—in.
Bayan Yaya Fahad sungaisa da Uncle Adam seya tambayesa yanda ake ciki inda yafaÉ—a
masa munma gama saura abamu class kuma shima dan Malamin baya kusane shiyasa ba'a
bamuba harlokacin.
"Malamin dazai
basu class ai Mallam ibrahim ne kuma gashican yazo yanzu" Uncle Adam yayi maganar
yana nunamana Malamin dasukazo Admin block É—in tare wanda ayanzu yana zaune kan
protocol chair inda sauran new student É—inda akayi mana abubuwa taredasu É—azu
harsunje sunyi layi agabansa suna karban ajin da aka basu.
Dubanmu Uncle Adam yayi sannan yace "kubiyoni muje inyi masa magana yabaku ajin
kuma yanzu" cewa mukayi "toh" sannan mukabi bayansa. Munanan tsaye suka gaisa da
Malamin yamasa introducing É—inmu sannan yace aji za'abamu mu kanninsa ne. murmushi
Malamin yayi sannan yace "karya damu yanzu zaibamu ai layin ma bayawa" aikuwa
yanagama ma yarandake gabanmu yabamu class,Js1 B yabamu dukanmu biyu sannan yabama
Uncle Adam written note É—inda za'akaima form master É—in Js1 B yabamu desk É—inda
zamuna amfani dashi a class bayan yafaÉ—a masa sunan Malamin.
Uncle Adam É—inne yaraka mu mukaje akabamu desk cikin mintuna kalilan inda daganan
kuma yarakamu har class É—inda akabamu kowa ta ajiye desk É—inta sannan muka koma
gurin Yaya Fahad dakecan Admin block yana jiran mu dandaman acan mukabarshi zaune
kasancewa ba ko'ina ake bari parents and guidians dabasu aiki a makarantar su shiga
ba. Muna Isa gunsa Uncle Adam yace "toh Fahad! Yanzukam kannenka are fully our
responsibility,angama komai saura adibi kayansu akai musu hostel in closing hours
yayi inda ananne kuma house captain É—insu zata basu É—aki kuma wannan duk bawani
matsala baneba insha Allahu tundama ga Yayunsu sunanan I'm sure they'll guide them"
murmushi Yaya Fahad yayi sannan yace "Hakane. Thanks for the help Adam. Allah
ubangiji yabar zumunci" sannan yatashi daga zaunen dayake yace "barini inwuce tunda
angama komai" Abokin Yaya Fahad yace "Aaaaa kungaisa dasu Zaheeran ne?" girgiza kai
Yaya Fahad yayi sannan yace "we did not! naga school hours ne yanzu so I don't want
to distract them kagaida su kawai" Uncle Adam yace "A'a Fahad baza'ayi haka ba bari
in aika akirasu ko sama samane kugaisa kafin ka tafi" yakarashe maganar ayayinda
yashiga kwala kiran wasu students guda biyu dake kokarin shiga Admin block.
Zuwa sukayi inda cikeda ladabi sukace "we're here Sir" duban É—ayar yayi sannan
yafaÉ—a mata class É—insu Yaya Aisha dakuma full name É—inta yace taje tace anakiranta
a Admin block yanzunnan sannan yadubi É—ayar ma yafaÉ—a mata ajin Yaya Zaheera yace
Itama taje tacemata ana nemanta a Admin block yanzunnan.
Kusan atare Student biyun suka dawo anma sede babu wanda ya taho da wanda aka
aikeshi yakirayo. Da uncle Adam yatambayesu sesuka ce dukansu baswa ajinsu. Yaya
Zeheera suna chemistry lab ayayinda Yaya Aisha da Yaya Safiya kuma suke can ICT
anayi musu computer class kuma gaba É—aya Malaman sun hanasu fita sunce subari se
antashi sutafi ƙiran da akeyi musu ɗin tunda lokacima yakusa.
Wani irin wawan ajiyan zuciya Uncle Adam yasaki sannan yadubi Yaya Fahad yace "zaka
jirasu koh?" É—an kwafa Yaya Fahad yayi sannan yace "Anya zanjira mugaisa da
Yarannan kuwa? nariga nabada sakon daza'a basu Adam. 15 minutes to 1:00pm fah
kasankuma nafaÉ—a maka akan hanya nike zanwuce Abuja banason inyi dare ahanya"
jinjinakai Uncle Adam yayi sannan yace "tafiyar daren kam babu amfani Fahad anma
kasan bazasuji daÉ—iba inka tafi baku gaisaba. last week dakazoma aibaka tsaya kun
gaisa ba and they even asked me kokazo nace musu kazo kuma basu ji dadi ba from
their face expression. 15 minutes kawai yarage atashi,just wait a bit more" shiru
Yaya Fahad yayi naɗan wasu daƙiƙu yana contemplating yatsaya ko karya tsaya kafin
daga karshe dai yasauke ajiyar zuciya sannan yace "Okay Then,barina jira su fito
É—in toh" daganan seyakoma yazauna a Inda yake zaune dazu.
Aikuwa 1:00pm nayi sega dalibai sunfara fitowa daga respective classes É—insu,wasu
suyi hanyar mosque wasu kuma suyi hanyar dinning hall don jiran lokacin cin abinci
yayi sushiga suci. Can mukahango Yaya Aisha da Yaya Zaheera natahowa dukansu
jikinsu sanye da uniform looking neat and tidy.
Fuska ɗaukeda murmushi suka ƙaraso inda muke suka gaida Yaya Fahad da Uncle Adam
kafin suka dubi inda muke zaune nida Sadiya.
Gaidasu mukayi nida Sadiya suka amsa sannan suka Shiga tambayar Sadiya mutanen gida
duktace musu lafiyansu Lau sannan tasanar dasu ai Ummi tabata sakoh tun daren jiya
akanta taho musu dashi kuma yanacikin kayanta insunje hostel zata basu.
Cikeda Jin daÉ—i sukace "toh" inda daganan Uncle Adam yanuna musu kayayyakin mu dake
ajiye agefe guda yace susa akaimana hostel sukuma tabbatar anbamu É—aki kafin suwuce
hostel nasu. Jinjinakai sukayi dukansu sannan Yaya Zaheera tace "ainikam ma hostel
É—inmu É—ayane dasu kuma inashiri da house captain É—inmu sosai muna zuwa zanje
insameta tabasu É—aki" Uncle Adam yace "Fine then. If possible kiyimata magana
tabasu É—akin dakike so that they'll be under your guidance Koh?" gyaÉ—a kai Zaheera
tayi sannan tace "Toh Uncle" Yaya Fahad dakejin su tun É—azu tashi yayi tsaye sannan
yasa hannu cikin aljihun wandonshi yaciro pocket money É—inmu nida Sadiya yabama
Uncle Adam yace ya ajiyemana sannan yasake ciro wani kuÉ—i daban yabama Yaya Zaheera
da Yaya Aisha da Yaya Safiya kyautan suka yimasa godiya atake kuma Sadiya tasanar
dasu abinda yasaya mana ahanya shima sukayi masa godiya sannan yayi mana sallama
zetafi.
Har jikin mota muka rakashi seda yabar harabar makarantar sannan muka dawo gurin
kayan namu dukanmu. Uncle Adam dakanshi yakirawo mana wani tsoho mai wheelbarrow
dake harkan É—aukan kayan ÆŠalibai yana kai musu kaya hostel sannan ya nuna masa
kayayyakin mu dake ajiye kasa yafaÉ—a masa sunan hostel É—inda zai kai mana sannan
yabiyashi yaÉ—ibi kayan yatafi.
Duban mu yayi sannan yace "muje masallaci muyi sallah lokacin sallah yayi sannan
duk sanda mukeda bukatar kuÉ—in mu ko munada wata matsala muzo musameshi a office
É—inshi dakenan cikin Admin block " cewa mukayi toh sannan muka kama hanyar
masallacin dukanmu hakanan inajin Yaya Zaheera da Yaya Aisha nata hira da Sadiya
hakanan duk inda suka haÉ—u da kawayensu sesunyi introducing É—inta as Kanwar su da
aka kawo anma banda ni kuma daman ni binsu kawai nikeyi abaya dan tsron su ma da
kuma sanin what they're capable of ya hanani jerawa dasu.
Ahaka harmuka Isa masallacin makarantar inajin su suna tambayar Sadiya ya'akayi aka
kawo ni makarantar duk tafaɗa musu bata ɓoye musu komai ba harzama danakeyi
agidansu dakuma dalilin dayasa nafasa zama agidan Kawu idrissa nake zama agidansu
wanda har hakan yaso yabani mamaki dankuwa ban taɓa tunanin Sadiya tasan asali
agidan Kawu idrissa yakamata inzauna ba anma danayi la'akari da bakin Ummi baya
shiru she must've tell her children inda sukuma suka yafama ita Sadiyan danko da
wasa nasan maganar nan bazata taɓa fitowa daga bakin Aunty ba. Inama take da wannan
lokacin ita?.
Bayan tagama bama su Yaya Safiya labarin sekawai naji sun saki tsaki Yaya Aisha na
faÉ—in "nina rasa Abba wani irin zuciya gareshi wallahi tallahi. Jibifah Uncle
idrissa ma dayake Babba acikin su yakasa riƙeta sabida baƙin jini irin nata dana
Ubanta bareshi" taɓe baki Yaya Zaheera tayi sannan tace "aikuma sekiyi! wayasani ma
koh Kakarta na Babban bulin nanne tamaida asirin datama Uncle Umar É—in kan Abba
ganin ya rasu kuma yanzu Abba shine me kuɗin cikinsu. Kokin manta Ummi ta taɓa
cemana ai Maman Rukayyan ma asirce Uncle Umar É—in tayi? Hartake cemana daman
fulanin garinsu haka suke,dasunga É—an birni mesamun taro da kabo shikenan sesu
asirceshi surabashi da dangin sa yakoma yana bauta musu su kaÉ—ai" Yaya Aisha tace
"Banmanta ba! Aikuwa inde suna tunanin dukwani munafircinsu zehau kan Abba toh
wallahi mu bazai hau kanmu ba. Kuma wallahi Rukayya dajin dadi har abada dankuwa
yanda mukasha wahalar rayuwa sanda namu uban bashi dashi Itama haka zatasha ayanzu
da uban nata bayanan" daganan suka karasa bakin famfo suka jona layin É—iban ruwan
alwala.
Dukyanda naso inyi holding tears É—ina kasawa nayi gashi kuma gurin cikeda mutane
danhaka senayi sauri namatsa daga kusa da masallacin natafi can wani guri da babu
hayaniya sosai. wani gumgumen itace nagani ajiye gurin wanda hakan yasani karasawa
jikin gungumen itacen nazauna sannan nacusa kaina cikin gwiwana ina kuka mai tsuma
zuciya!
Atunani na makaranta will be easier for me anma segashi daga zuwana anfara nuna min
hali! Suda suke Yan uwana inbasu nunamin so a makarantar ba wazai nunamin
fisabilillahi? najima ina kuka hakanan dana tuno irin kalaman dasu Yaya Aisha ke
faÉ—a akan iyayena É—azu se insake Jin wani sabon kukan ya kubcemin! Nafi mintuna
goma shabiyar Ina abu É—aya hakanan harlokacin ban É—ago dakaina daga cikin cinyoyina
ba. taɓa bayana naji anyi wanda hakan yasani tsaida sheshekar kukan dana keyi anma
seban ɗago ba harsaida aka sake taɓa bayana akaro na biyu.
Idanuna dasuka gama Sanja launi nadago daga cikin gwiwana sannan naÉ—aura su akan
wanda ke tabani tun É—azu and then I saw Aziza,Aziza class mate dita danake bama
LamiÉ—o labari a Babban buli,yarinya mai shegen naci dason bako tun muna Nursery
harmuka gama primary school. Dukda halin danake ciki fuskana seda bayyana tsananin
mamakin ganinta a Inda nake zaune yanzu.
Ahankali nace "Aziza?" murmushi tasakarmin sannan tace "Rukayya ashedai keÉ—in ce"
cikeda curiosity nace "kamar Yaya? bakigane bane seda nayi magana komi?" Girgizamin
kai tayi alamar "a'a" sannan tace "bawai bangane ki baneba kawaidai nayi mamakin
ganin ki a Boarding school ne sabida tunsanda ake saida form É—in comman entrance
naji kince ke bazakiyi Boarding ba shiyasama danaganki senake kokwanto araina
kowata ce mekama dake bakeba" murmushin dayafi kuka ciwo nasaki sannan nace "Nice
anma ke a ina kika ganni harkika ganeni?" dariya tayi sannan tace "katuwar
makarantar nandake cikeda jama'a ta'ina ne bazakaga mutum ba?" sannan ta É—an
numfasa kafin tacigaba da magana tace "Kekam dai tunsanda Exam officer Uncle Adam
yakawo ku class keda wata naganki kuma alokacin nayita ƙiran sunanki sanda zaku
fita a class bakijini ba toh senayi tunanin ba keÉ—in baceba. Recently Kuma
senaganki agaban masallaci nataho zansameki inmiki magana kuma senaga kintaho nan
shine nabiyo ki abaya without knowing kinzo kikebe kiyi kukan kewan Baba ne"
takarashe maganar cikeda zolaya dankuwa yan ajinmu babuwanda baisan yanda nakeson
Baba ba. Ko acikin hirane bana magana ta minti talatin ban ambaci Baba ba infact ma
dayawansu *Rukyn Baba* sukecemin a class.
Lokaci guda Jin ta ambaci Baba senaji wasu sabbi kwallah sun taru a idanuna suna
kokarin zubowa. Cikin sauri nasaka bayan hannuna nashiga goge kwallana wanda hakan
yasa jikin Aziza yin sanyi,seta zuba min idanu batareda takuma cewa komai ba
harsaida nagama matsar kwallana sannan tace "Hakuri zakiyi Rukayya! Kowa da kike
gani a makaranta nan yana kewan gida dakuma family members É—insa kawai daurewa
mukeyi and besides inlokacin hutu yayi zamu koma gida muga iyayen mu duka,kema zaki
koma gida kiga Baba harmasai kin koshi da ganinshi kafin asake dawowa makarantar
kuma" tayi maganar calmly trying as much possible as she can to comfort me anma
sede batasan kalamanta sake famo min tabon dayajima bai warke a zuciyana tayiba.
Cikin gunjin kuka nace "Aziza Baba yarasu. Allah yayiwa Babana rasuwa kusan wata
guda yanzu" maganata bakaramin dakan Aziza yayi ba dankuwa tafi mintuna biyar
batace komai ba hakanan bata ɗauke idanunta daga gareni ba daƙyar ta'iya cewa "Kiyi
hakuri Rukayya wallahi bansani ba" gyaÉ—a matakai nayi sannan nace "bakomai kada
kidamu nasan bakisani ba shiyasa kikayimin maganar sa" jiki sanyaye tace "Rashin
lafiya yayi komi?" gyadamatakai nayi ahankali sannan nace "yamafi wata biyu a
asibiti kafin Allah yakarbi ransa" cikeda tausayina tace "Allah yajikansa.
Amakaranta kuwa babu wanda yaji labari" nace "kinsan ai mungama primary school so
ko anga nadaina zuwa zasuyi tunanin nabar makarantar ne" jinjina kai tayi cikeda
gamsuwa sannan tace "toh yanzu a Ina kike zama?" dantasan dagani se Baba muke zama
agidan mu,Tasan Mamana tarasu dajimawa.
Ahankali nace mata "Gidan Uncle É—ina" cikeda curiosity tace "kenan waÉ—anda naganki
dasu ɗazu Ƴaƴan Uncle ɗin kine?" gyaɗa matakai nayi ahankali setace "Toh anma ya
akayi suka barki kika tahonan ke kaÉ—ai?" Senace mata "Aibasu san nama taho nanba
Aziza!" Aziza tace "still yakamata ace sunemeki by now. What if Kika ɓace musu
tunda basanin kan makarantar kikayi ba?" murmushi dayafi kuka ciwo nayi sannan nace
"kikasani kosuna can suna nemana ma yanzu haka basu ganni ba tunda kamar yanda kika
faÉ—ane! Makarantar nan faÉ—i gareta and there're many people wearing thesame outfit
so it'll be difficult for someone to look for his close one" nayi maganar kaina
akasa dankarta gane halinda nakeciki. I just don't feel like sharring my pain with
her tunda ko ada bawani sabawa mukayi sosai ba.
Aikuwa ta gamsu da bayanin nawa danhaka setace "toh shikenan muje inraka ki bakin
masallaci muduba su ko zamu gansu" gyaÉ—a matakai nayi ahankali sannan natashi
mukabar gurin. babu inda bamu zaga ba a masallacin. Both in and out anma babusu
babu labarinsu senace mata kilan suntafi wani gun nemana ne shiyasa bamu gansu anan
ba.
Cewa tayi muyi alwala muyi sallah semu tafi dinning dan already har anfara shigama
inyaso inmun fito mwaje hostel munemesu. Tare mukayi sallah a masallaci kafin muka
tafi dinning hall muka ci abinci. ana fitowa daga dinning hall É—in kuwa hostel muka
wuce. har gaban hostel É—inmu Aziza tarakani inda anan naga akwatina,matrass
É—ina,pillow na,blanket,class bag É—ina dasauran kayana duk a ajiye akasa anma babu
na Sadiya.
*Insha Allah gobe zakujini*
Hope I'm not rushing things� We've a long way to go ne and I want us to reach
where the game will start as soon as possible insha Allah.
*Page Thirty Three*
*A previous page nayi mistake! Namanta kwata kwata a weekend aka kaisu Rukayya
makaranta and I make the page as if it's during week days. Hope you guys will bear
with me? Kudauka kawaicikin sati aka kaisu😠I'm very sorry*
Tsugunawa nayi gaban kayan nawa ahankali ina tattabasu sannan nace "wannan ai
kayana ne" Aziza dake tsaye akaina tace "Ina daga Admin kuka bayar ashigo muku
dashi hostel?" gyaÉ—a matakai nayi ahankali setace "toh Ina na É—ayar cousin sister
É—in naki? Koh hostel É—inku ba É—aya baneba" ahankali nacema Aziza "hostel É—inmu
É—ayane da'ita" cikeda curiosity tace "toh Ina aka kai nata kayan? kodai sunzo sun
É—auka itada Yayunkune?" tashi nayi daga tsugunen danake agaban kayana sannan
nakalli Aziza nace "Nima bansani ba Aziza" wani wawan ajiyan zuciya tasauke dukda
kuwa tana da tarin tambayoyin datake son tayimin abakinta seta riƙe su aranta tace
"toh mushiga ciki muyi tambaya kilan musamu wani da yasan É—akin da É—ayar Yayarkun
take tunda kince itama a hostel É—innan take" cewa nayi "toh" sannan muka shiga
haraban hostel É—in.
Wata muka hango zaune akan dakalin dazai sadaka da É—akunan dake bari gabar dake
cikin hostel É—in kuma daga gani zatayi kusan sa'anni da Yaya Zaheera dan haka
semuka ƙarasa inda take zaune muka gaisheta sannan Aziza tashiga tambayarta ko
tasan Yaya Zaheera awannan hostel É—in dayake tun ahanyarmu nashigowa hostel É—in
tatambayeni sunan Yaya Zaheera nafada mata.
Se mukayi sa'a tasanta,tambayar number É—akin Yaya Zalihan mukayi ta faÉ—a mana
sannan mukayi mata godiya muka tafi.
ÆŠakunan dake wannan block É—in mukayita bi harmuka isa number É—akin da yarinyar can
tabamu sannan mukayi sallama muka shiga. ÆŠakin cike yakeda occupants É—insa hakanan
kowa yana harkokin gabansa da alama ma basumasan da shigowar namu É—akin ba. Rarraba
idanu nashigayi kozanga su Yaya Zaheera anma babu su babu labarinsu.
Aziza ne ta ƙarasa jikin bunk ɗinda ke kusa da inda muke tsaye sannan tayima
yarinyar dake kwance kan bunk É—in sallama suka gaisa sannan tace mata Sister
Zaheera muke nema.
BuÉ—an bakin Yarinyar cewa tayi "Cab Sister Zaheeran nan gaskiya rabona da'ita tun
safe anma dai bansani ba kota dawo hostel bayan antashi daga classes dan nima
yanzunnan shigowana É—akin" seta dubi bunk mate É—inta dake zaune kan up bunk tana
ninke inner wears É—inta tace "Zainab nikam Yaya Zaheera tadawo hostel ne tunbayan
da aka tashi daga classes?" Zainab tace "Eh sunzo itada kannenta taÉ—auki kayanda
zatasa na tafiya evening prep sannan suka tafi. wai acan hostel É—insu Safiya zata
shirya yau" dawo da dubanta tayi garemu sannan tace "toh kunji batanan sede in
kudawo anjima" godiya mukayi masu dukansu sannan muka fice a É—akin.
Aziza dubana tayi sannan tace "Yanzu yaza'ayi? zamu É—ebo kayanki mukawo É—akin nan
ki ajiye kafin sudawo su rakaki abaki É—akin ne komuje kawai abaki É—akin kikai
kayanki can?" cikin sauri nace "kinsan House captain É—in namu ne?" girgizamin kai
tayi alaman a'a sannan tace "bansanta ba anma damun tambaya za'a faÉ—a mana É—akinta
ai" senace "toh muje abani É—akin kawai" dankuwa banason inkawo kayana in ajiye
anasu É—akin yazama abun magana tunda na leka ko'ina a É—akin banga kayan Sadiya
bama.
Komawa É—akin su Yaya Zaheera Aziza tayi takuma tambayar yanmatan É—azu É—akin house
captain É—inmu nan suka faÉ—a mata sannan muka tafi. bamusha wahalar samun house
captain ɗinba dan muna shiga ɗakin damu kayi tambaya aka nuna mana ita. Ƙarasawa
mukayi inda take muka gaida ta sannan nace mata É—aki nazo tabani, I'm a new
student.
Wani long note taÉ—auko ta ajiye kan locker É—inta sannan tashiga dube dube harta iso
wani page kafin tamikamin littafin tamin pointing inda zancika details É—ina sannan
tabani pen nacike cikin lokaci kankani namaida mata littafin ta rufe ta ajiye
sannan tafito daga corner É—inta tana faÉ—in "kubiyoni a baya" room seven takaini
tayi introducing É—ina ga yan É—akin sannan tanuna min bunk É—inda zan É—aura katifana
akai kafin tayi tafiyar ta.
Aziza ce ta tayani muka tattaro duka kayana daga wajen hostel muka dinga shiga dasu
cikin É—aki muna ajiyewa agaban bunk É—ina harmuka gama sannan tadubeni tace "Kinga
yanzu lokacin prep yakusa in kikace zaki tsaya arranging kayan ki zaki ɓata lokaci
don haka tunda akwatin arufene mutura shi karkashin gado kawai! Sauran kayan kuma
kisasu a locker É—inki se a rufe. Ina kina da extra padlock?" gyaÉ—a mata kai nayi
sannan tace in É—auko inda ita kuma ta É—aga katifa na ta É—auramin akan gado na.
Seda na ciro kayan dazan saka inje evening prep dashi sannan narufe akwatin
naturashi karkashin gado. Sauran kayana dake a ajiye agurin Kuma duk na cusasu
cikin locker narufe kamar yanda Aziza tabani shawara sannan tasani nadauki sabon
bucket dina muka fice don in debo ruwan wanka.
Wurin É—iban ruwan tanuna min sannan tayi wucewarta hostel É—insu donta dauki nata
bucket É—in Itama tazo ta diba. Bayan munrabu da Aziza taku nadingayi ahankali harna
isa bakin tap É—in. Babu mutane sosai abakin tap É—in se tsirarru wanda hakan yasa
tuni layi ya iso kaina nacika bucket É—ina naÉ—auka nabar gurin.
Harna kusa isa hostel naji ana "junior girl! Heyyy junior girl" yanda me ƙiran
junior girl ɗin take ta ƙira continuously yasa nasan dani takeyi danhaka sena ajiye
bucket É—in hannuna najuya ina kallonta don insake tabbatar wa senaga tanamin nuni
da hannu da injeni.
Dayake babu wani nisa tsakanin mu seban É—auki ruwan nawaba,anan inda na ajiye
nabarshi sannan najeni gurinta. É—aya daga cikin Buckets guda biyu dake ajiye
gabanta cikeda ruwa tanuna min sannan tace "carry this bucket and follow me" kallon
bucket É—inda tanuna min nayi sannan na sunkuya naÉ—auki bucket É—in araina ina
mamakin wannan wani irin haline? Tana ganina da ruwa a hannuna sannan kuma tasani
in ajiye inzo in É—auki nata.
ÆŠaukan É—ayan bucket É—in tayi tayi gaba senima kawai naÉ—auki É—ayan nabita abaya. har
É—akin da take zama nakaimata acan hostel É—insu sannan na fito don inje in É—auki
nawa ruwan inwuce hostel É—inmu araina Ina addu'ar Allah yasa wani bai É—auke ba.
Aikuwa Allah yataimakeni babu wanda yaÉ—auke É—in. NaÉ—auki ruwan zanwuce kenan sega
Aziza ta taho daga bakin tap Itama hannunta riƙe da bucket ɗinta dake cikeda ruwa
tace "Daman baki tafi ba? danaje bakin tap É—in bangankiba naÉ—auka harkin diba
kinwuce hostel É—inku" murmushin dayafi kuka ciwo nayi sannan nace "Bantafi ba yanzu
zanwuce dai" Aziza tace "toh amma inakikaje?dannazo nawuce tanan gurin banganki ba
kuma danazo wucewa I saw this bucket filled with water like it's right now?"
Atakaice nace mata "Aikana wata senior tayi" lokaci É—aya se Aziza ta tsuke fuska,
tace "hmmm aihaka suke! se shegen mugunta da selfishness. anganka kana naka chores
É—inma baza'a barka ba se an tareka kabar naka kayi nasu"
Nidai tabe baki kawai nayi,semuka jera muna tafiya batareda wanin mu yasake cema
dan uwansa komaiba harmuka iso kofar hostel dinmu,sallama nama Aziza zanshi ge ciki
setace "idan nagama shiri zanbiyo miki muwuce prep tare anmafa sekinyi sauri dan
ankusa fara kora" gyaÉ—a matakai nayi sannan nashige cikin hostel É—inmu ita kuma
tawuce nasu hostel É—in.
Ban wani samu layin wanka sosaiba dayake sanda nacanza kayana natafi bathroom
yawanci lokacin har É—alibai sunfara fita daga hostel É—in. Sharp sharp nayi wankan
nafito nakoma É—akin mu. Nazauna ina shafa mai kenan akafara banging gate É—in hostel
É—in namu kan ayi afita danhaka sena kara sauri wurin shirinnawa.
Nagama sa kaya kenan ina neman takalmina Aziza tashigo É—akin mu cikin sauri tana
faÉ—in "Rukayya baki gama ba?" Cewa nayi "nagama Aziza takalmin dazan saka nake
cirowa" Aziza tace "toh kiyi sauri mutafi ankusa fara taran latti abakin gate É—in
hostel" cewa nayi "toh" ayayinda na ajiye takalmana akasa nasakasu a kafafuna
sannan naɗauko class bag ɗina na goya shi a gadon bayana kafin na ƙarasa inda take
tsaye nace "nagama mutafi" gyaÉ—a min Kai tayi sannan mukajera muna tafiya harmuka
fice a hostel É—in.
Dayake luck is on our side muna wucewa akafara taran latti daga kan yan bayanmu.
Class É—inda mukaje muka ajiye desks É—inmu tareda Sadiya É—azu muka shiga.
Seda Aziza tanuna min desk É—inta dake can gaban aji sannan nawuce nawa. zama nayi
nafara kar kade desk É—ina Ina mamakin ya akayi Sadiya bata fito ba haryanzu dayake
desk É—inta ne agefen nawa kuma yanda muka ajiyeshi haka nazo nasameshi yanzu,it
doesn't look like mutum yazauna akai. Bayan nagama karkaÉ—e desk É—in sena buÉ—e
drawern dake jikin desk É—in shima na gogeshi sannan najera books É—ina aciki. Side
É—aya text books side É—aya kuma notebooks da pens É—ina.
Adede lokacin ne kuma Sadiya tashigo ajin namu tanata kukkumbura fuska tareda soshe
soshen hannu da alama dai anyi mata dukan latti ne. zuwa tayi tazauna batareda ta
goge seat É—inta ba sannan takwantar dakantar kan desk É—inta tashiga raira kuka.
Sonake in lallasheta in tambayeta dalilin kukan nata anma ina tsoron tayi vending
frustration É—inta akaina danhaka senayi shiru nakyaleta dukda kuwa inajin kukan
nata har cikin raina. sekawai najingina jikina da jikin windown ajin namu dayake
desk É—ina ajikin gini yake ina karema members na ajin namu kallo É—aya bayan É—aya.
Daga waÉ—anda suka haÉ—a gungu suna hira,se masu guje guje acikin ajin abunka da js1
disease!
Daidaikune kawai sukeyin abunda yadace acikin ajin kuma sena lura Aziza na É—aya
daga cikinsu dankuwa zaune take kan kujerar ta tana nazarin wani text book. Lokaci
guda senaji I want to be like her! I want to be as serious as she's tunda daman
abunda yakawoni makarantar kenan.
Don haka sena tashi daga kan kujerar danake zaune nanufi nata. Seat É—inda ke
gefenta babu kowa akai danhaka ina isa gurinta sena zauna anan kawai.
Tana ganina seta rufe textbook É—inda take karantawa tadawo da attention É—inta
gareni tace "harkin gama gyaran Desk É—in naki?" gyaÉ—a matakai nayi ahankali sannan
nace "anyi notes sosaifah! in kinaso se inbaki kifara copying yanzu kisamu kigama
kada abarki abaya" cewa nayi "toh" ayayinda tabuÉ—e drawern books É—inta taÉ—auko wani
note book tamikamin sannan tace "wannan English ne kije kifara copying É—insu inkin
gama seki karbi sauran" karba nayi tareda cewa "thank you" murmushi tayi sannan
tace "You're welcome" sannan takarada "Inason in tayaki anma sede nasan ke ko
assnda muke primary school bakyason anayi miki note! Kinfison kiyi kayanki ke
kaɗai" Ƴar dariya nayi sannan nace "sabida nafi gane rubutu na nikaɗai! Inwani ya
rubuta abu bancika ganewa ba innazo karantawa shiyasa I prefer to do it myself"
gyaÉ—a kai tayi cikeda gamsuwa sannan natashi nakoma seat É—ina.
Copying note É—in nashiga yi tareda tunanin may be along the way Malami ze shigo
ajin namu anma har lokacin tashi yayi babu wani Malamin dayazo. Har aji su Yaya
Zaheera suka zo suka dauki Sadiya suna lallashinta suka tafi hostel tare anma ni ko
kallo ban ishesuba barema har suyi tunanin tambayana yanda akayi nasamu hostel
akabani daki harna shirya nafito prep.
Sanda nagama copying English note É—in baki É—ayansa ajin duk anwatse,dagani se Aziza
ne kaÉ—ai muka rage. zuwa nayi nasameta a seat É—inta sannan nabata littafinta nace
mata "nagama" karba tayi sannan tace "saurankam se a night prep zakicigaba da
copying koh?" cikeda mamaki nace "da darema zamu fito ne?" Aziza cewa tayi "Eh!
Aikullum haka akeyi. weekends ne kawai ba'a fita classes da prep" cikeda curiosity
nace "toh anma banga Malami yazo yakoyar ba har aka tashi" Aziza tace "Wai kina
nufin a prep?" Cewa nayi "Eh" setayi Ƴar dariya tace "Ai prep is not meant for
lesson,lokacine da aka keɓe ma ɗalibai dan suyi revising abubuwan da aka koya masu
a aji kullum" cikeda gamsuwa nace "nagane" dariya tayi sekuma tatashi daga kan seat
É—inta tace "muje masallaci maghriba tayi ko kina da abunda zaki É—auka a hostel ne?"
takarashe maganar ayayinda take kallona.
Girgizamata kai nayi alamar a'a tace "toh muwuce mosque É—in kawai nidaman Inna fito
prep bana komawa hostel se after night prep danko mutum yakoma ma bazai jimaba za'a
fara koran masallaci and moreover yawanci awannan time É—in seniors sukafi takurama
juniors shiyasa nake zamana a aji inyita karatu in yanma tayi sosai se inje
masallaci ayi mosque sanitation dani daganan kuma muyi sallar maghriba in É—anyi
karatun alqur'ani kafin atafi dinning" jinjina kainayi sannan nace "aikuwa nima
hakan zannayi kawai dan banga amfanin zama a hostel É—in bama" murmushi tayi sannan
tarufe desk É—inta da padlock tace "kinrufe naqi kuwa?" gyaÉ—a matakaina nayi
ahankali.
Tace "Banga sisternki ba! Ya akayi batazo prep ba" cikin sauri nace "tazo fa,
É—azunnan tatafi" Aziza tace "Ayya aibanganta ba" murmushi kawai nayi bankuma cewa
komaiba hartagama rufe drawern ta muka fice a ajin tare.
Aikuwa bamu koma hostel É—inba se after night prep. kuma koda naje night prep É—in
busying kaina nayi da copying note har aka tashi. Sanda Sadiya tashigo ajinma seda
namata offering note É—ina na English dana gama copying dayanma kan Itama ta kofa
anma seta gwasaleni inda daga karshema tashi tayi daga seat É—in tana toshe hanci
tatafi seat É—in wata kawarta dasukayi primary school tare sukayita hirarrakinsu
suna dariya hakanan wani sa'in se inji ajikina kamar gulmana sukeyi suna kallona
anma senaki dagawa in kallesu.
Anatashi daga prep bamutsaya wata wataba muka wuce hostel cikin jama'a nida Aziza
sabida darene. takuramin tayi akan muje Inga hostel É—insu wanda hakan yasa nayarda
nabita muka nufi hostel É—in nasu,naga É—akin datake kafin natafi daniyar inje
inshirya locker na kafin nakwanta bacci. Abunda natarar a É—akin mu shiya tayarmin
da hankali.
Zuwa nayi nasamu su Yaya Safiya zaune kan gadona suna shiryama Sadiya lockern
ta,lockern da yake gefen nawa shine nata yanzu sannan bunk É—inda ke samana ne nata.
Inajin Yaya Zaheera na hira da wata kawarta tana tambayarta miyasa bata roki house
captain tabama Sadiya É—akin da take ba tunda taga kamar sunada extra bunk guda
É—aya. Yaya Zaheera cewa tayi "kibari kawai Meenal. Muda muka daukota memakon mufara
zuwa nan semuka wuce hostel É—insu Safiya kawai akan in andawo daga evening prep
zanje insamu house captain É—in inmata magana tabata wannan É—akin unfortunately
damuka dawo kuma nasameta da maganar setace ai har tabama wasu É—akin,harma sunyi
parking sunkoma can shine tabata nan É—akin and I know you're here shiyasa ma
banwani daga hankalina ba! Sabida haka ga Amanar kanwata nan nakawo miki" Dariya
Meenal tayi sannan tace "Bakomai karki damu. Ai bunk mate É—in nata ma Yar js1 ce
kamarta so zasuji daÉ—in zama tare" "hmmm" shine kawai abunda Yaya Zaheera tace
kafin kuma suka sauyan hiran nasu zuwa wani.
Nibanma bari sun ganni ba dan rakubewa nayi ajikin kofar dakin tunda na hangesu
nakasa shiga ciki.
Who is missing lamido? Yakamata muleka shifaðŸ˜.
Alright don't worry next page dashi zamu fara insha Allah.
*Littafin Qadr na kudi ne. Duk maiso tayimin magana tawannan layin *08147722806*
*Page Thirty Four*
Harsuka gama gyarama Sadiya gado suka tafi basu ganni ba dayake da goman dare yayi
anyi light off kuma inda na raƙube na tsaya babu wanda ya kunna Torchlight.
ÆŠakin nashiga na karasa kusa da bunk É—ina bayan fitarsu. akwatina najanyo na buÉ—e
na É—auki katon lantern É—inda Aunty tasaya mana iri É—aya nida Sadiya sannan na kunna
lantern É—in,na ajiyeshi saman locker na kafin nafara ciro kayayyakina ina jerasu
cikin locker harna gama narufe namayar da akwatina kasan gado inda alokacinne kuma
Sadiya tadawo daga rakiyarsu Yaya Safiya wanda inada tabbacin dasuka dawo tabi ta
É—akin Yaya Zaheera dan rakiya kaÉ—ai beci ace tajima hakaba. Inajinta taÉ—auki buta
tafita waje harta dawo tazo ta dale gadonta batareda tacemin komaiba takwanta. Nima
shimfida gadona nayi sannan nahau nakwanta Ina tunanin yanda rayuwata zata kasance
acikin makarantar ahaka har bacci yayi awun gaba dani.
***
LamiÉ—o tunbayan dayayi resolving issues É—insa da mutanen Fada bashida wani tunani
daya wuce yanda zaiyi yanemi alternative É—in sake zuwa Bauchi. Dukda bai furtama
kowaba anma abun naranshi yanakuma da yaƙinin zeje ɗin insha Allahu.
Sau tari yakanji kamar yanemi shawara gurin Hafiz anma inya tuna alkawarin daya
daukar ma kanshi nacewa bazai sake yimasa maganar data shafi Rukayya ba seya fasa
yimasa maganar yabar abun acikin ransa kawai. Umma kuwa ko gigin hauka yakeyi yasan
bazai tunkareta da maganar ba tunda shiya mata alkawari last time data bashi
permission É—in zuwa.
A bangaren Hafiz kuwa beyi mamakiba da LamiÉ—o yadaina yimasa maganar Rukayya don
kuwa yasan halin abokin shi sarai da zuciya,inyace bazaiyi abuba toh bazaiyinba
hakan inyace zaiyi toh seyayi. Toh anma abunda baiganeba shine shin LamiÉ—on ya
hakura da zuwa ganin Rukayyan ne kokuwa? Tunda baiga alamar yana making wani effort
nasake zuwa Bauchin ba. Seya É—auki hakan amatsayin ya hakura and then seyaji daÉ—in
hakan dukdama baifito fili yasanar da LamiÉ—on ba.
Kwatsam ranar laraba LamiÉ—o nadawowa daga companyn dayake IT se Umma tatareshi da
labarin abokinshi dayaje yasamu aiki awurinsa last weekend yakirashi awaya ta
wayarta dayake layinshi na ciki,wai akwai vacancy nawani aiki if he's interested
yaje yasameshi a shago. Take LamiÉ—o yace "Umma dakince mishi bazanyiba kawai! Last
week É—inma aidan ina bukatar kuÉ—in ne shiyasa naje nayi dakoh" tsuke fuska Umma
tayi sannan tace "agaba bazaka nemi kuÉ—i ba kenan kakeson kacemin komi? inma zakaje
gwanda kaje kaji wani irin aikine. Aibaifi rage zaman banza ba" ganin Umma tadage
se LamiÉ—on yace "Toh Umma anjima zanje shagonsu insameshi insha Allah" cikeda farin
ciki Umma tace "Allah yakaimu anjiman. Allah kuma yamaka albarka" LamiÉ—o yace "Amin
ya Allah Ummana" sannan yazauna yana kwala kiran Basma wai tazo tazuba mishi abinci
yaci.
Dayanma LamiÉ—o na fita straight kasuwa yawuce shagonsu Abdulmalik kuma yayi sa'an
samunsa a shagonsu don haka seya bashi hannu sukayi musabaha yakuma gayamasa Umman
sa tabasa sakon daya bayar abasa ne shiyasa yazo ganinsa yanzu.
Murmushi Abdulmalik yayi sannan yace "aikine akeneman masuyi shine nace bari in
faÉ—a maka tunda last week naga kazo nema,may be yanzunma kanada bukata" take LamiÉ—o
yace "A'a Abdulmalik wancan É—inma dandai Ina bukatar kuÉ—ine alokacin shiyasa nayi
amma dai faÉ—amin,wani irin aikine? may be in iya during my leisure time" se
Abdulmalik yace "Aikin transporting kayan abinci ne zuwa other states daga wani
campany dakenan garin daman. Suna neman new employees shine nace barina maka magana
if you're interested" LamiÉ—o Jin an ambaci transportating abinci zuwa wasu states
yasashi saurin cewa "wasu states za'ana kaiwa Abdulmalik?" Abdulmalik yace "inaga
Kano,Adamawa,Bauchi,Taraba,Yobe, maiduguri dadai sauransu. Kawaidai northern
states" LamiÉ—o yace "toh amma mutum É—ayane zaiyi aikin kowani state É—in kokuma
assigning mutane akeyi kowani state?" Abdulmalik yace "A'a assigning mutane
akeyi,kamar kowani daf guda mutane biyune ake assigning sannan za'a iya basu state
biyu ko uku ace sukai" cikin sauri LamiÉ—o yace "Zanyi anma fa se in state É—inda
zamuna kaiwa akwai Bauchi aciki" yanda Lamido yayi maganar seda yabama Abdulmalik
dariya,yace "Kaikuma Ina ruwanka da state dinda za'aje so far as zakasamu gumin
ka?" ÆŠan Sosa kai LamiÉ—o yayi sannan yace "bazaka gane bane Abdulmalik. Kaidai
kawai katambaya min inba'a É—auki waÉ—anda zasuna zuwa can É—inba Zanyi aikin"
Abdulmalik yace "toh shikenan zantambaya maka innakoma gida insha Allahu sannan
dukyanda mukayi dasu zankiraka infada maka" LamiÉ—o yace "a'a karka kirani wayana
tasamu matsala acikin wayar Umma nasa simcard É—ina, I'll just come here tomorrow
morning inyaso se inji yanda kukayi" Abdulmalik yace "toshikenan Allah yakaimu
goben" daganan sukayi sallama LamiÉ—o yawuce majalisa ranshi fes yana addu'ar Allah
dai yasa adace.
Washegari dasafe kuwa yakoma shagon Abdulmalik É—in and he's lucky bbu wanda akama
offering wannan job É—in,cikeda farin ciki LamiÉ—o yarungume Abdulmalik yana masa
godiya inda daganan Abdulmalik É—in yace masa yaje campanyn yasamesu sunce yaje
sunason ganinsa.
Yana barin kasuwan campanyn yawuce,anan suka gama mishi duk wani interview dadai
abunda yadace susani agame dashi sannan suka sanar dashi banda weekend mezuwan nan
wata mezuwa zasu fara fita kuma Kano,jigawa da Bauchi zasukai shida abokin
aikinshi.
Lamiɗo cewa yayi toh kuma koda yakoma gida yasanar da Umman sa ba ƙaramin farin
ciki tayiba. dukda sanda ya ambaci akwai Bauchi acikin garuruwan dazasuna kaiwa
kayan abincin seda ranta yabata da biyu yayarda zena zuwa anma sebatace
komaiba,aganinta koma miye reason É—in shi what matters here yayarda zenayin aikin
batareda yacigaba da zaman kashe wando ba.
***
Washegari Tuesday tun ana kiraye kirayen sallar asubahi nafarka daganan kuma
bansake komawa bacciba dankuwa Ina idar da sallah natafi nayi portion dina dakecan
backyard É—in hostel É—inmu. Bayan nagama Portion É—inkuma nazo na É—ebo ruwan wanka
nayi,nashirya cikin uniform É—ina sannan nafita.
Hostel É—in su Aziza nabi dandaman jiya munyi da'ita akan dukwanda yariga É—an uwansa
gama shiryawa shizai bima É—an uwansa.
Ina Isa kuwa tagama shiri kenan tana shirin fita Itama shiyasa ma ko zama banyiba
muka juya muka fita zuwa dinning. yau ba'ayi assembly ba after dinning kamar
jiya,dana tambayi Aziza dalili setacemin ainan Mondays and Fridays kawai ake
assembly unlike primary school da akeyi kullum.
Bakaramin Jin daÉ—in classes É—ina nayiba dankuwa sosai na maida hankalina kan
abubuwan da Malaman namu suke koyamana hakanan duk lokacin da yazamanto free period
ne kokuma time tsakanin fitan Malami da shigowan wani I usually use that time inyi
copying notes É—inda nayi missing hardai nasamu nayi completing É—insu duka. Damuka
fito evening prep kowa karatunsa yayi separately harsaida akatashi kowa ya watse
yarage dagani sai Aziza sannan nataso daga seat É—ina nadawo seat É—inta nace
takoyamin Mathematics classes danayi missing abaya. dayake Aziza is very good when
it comes to teaching someone yasa nagane abunda take koyamin cikin gaggawa.
Yau ma kamar jiya mukayi nida Aziza dankuwa koda muka bar Classes Area masallaci
muka wuce bamu koma hostel ba,daga masallacin kuma dinning muka wuce inda daganan
kuma muka sake komawa Classes area night prep bayan munyi sallar isha'i. Kwata
kwata Sadiya batayimin magana,nunawa ma take batasan ni ba,she's acting as if I'm a
stranger gashi ko zama a kujeranta batason yi dandazaran Malami yabar aji toh Itama
zata tashi akan kujerarta tatafi gurin kawayenta. Nima kawai sena fita harkanta
baki É—aya.
Yanzuma shigowa nayi kwanarmu nasameta tana sauya kayanta zuwa sleeping wears
dayake ta rigani isowa hostel bayan antaso daga night prep. Ajiye class bag É—ina
nayi abakin katifana sannan nasauya kayana zuwa na bacci nima. Gadona nashige
nakwanta anma abunda ya ziyarci hancina shine ya É—auremin kai,zaurin fitsari akan
katifata.
Sa hanci na nayi adede inda nakejin zaurin natashi don in tabbatar senaga tabbas
akan katifar nawane ba a wani guba.
Take kuma se Sadiya tafaÉ—o min arai,nasan ko shakka babu exchanging katifa
tayimana,tasakamin nata mai fitsari nikuma taÉ—auki nawa maikyau tasaka akan
gadonta. tabbas abun ya konamin rai anma se bance komaiba,sekawai nasama raina
washegari zan fidda katifan insaka masa ruwa yabushe arana may be yadaina zarnin
dayakeyi É—in.
Aikuwa hakan nayi washegari anma duk se ban tsiraba dankuwa dadare danadawo hostel
daga night prep daniyar É—aukan katifar inshiga dashi inshimfida akan gadona senaga
babushi,bakaramin tashi hankali na yayi ba,hakanan hankali tashe nashiga É—aki don
dubawa ko wani ne yashigar min dashi and there I saw it on my bed. Sena fara
mamakin wayene yashigo min da katifar nawa dan nasan nidai babu wanda nake shiri
dashi acikin É—akin tunda ma nazama nakeyi sosai ba anma saiban tambayi kowaba haka
na ƙarasa kusa da bunk dina nayi shirin kwanciya. Dana kwantan ne senakuma Jin
zarnin fitsari kamar jiya and I realize cewa Sadiyance ta dawo dawuri kafin kowa
tashigo da katifar,datashigo dashi É—in kuma memakon tasakamin akan gadona seta
É—auke nakan gadonta data fitsareshi a daren jiya ta sakamin itakuma tasa wankakken
akan nata still dai bance komai ba and this turn into something else dankuwa kullum
nisainayi bautar fidda katifa wanda hakan yasa akafara gulmace gulmace a block
É—inmu kan kullum senayi fitsarin kwance,wanda duk ba'a hostel kaÉ—ai yatsaya ba har
yan ajinmu seda sukaji labari dan akwai classmates É—inmu a É—akin mu kuma Sadiya ma
ta yafa ma kawayenta.
Zama a aji kuwa tuni taÉ—auke seat É—inta a gefena acewarta body odour nakeyi wanda
hakan yasa sauran yan ajinma sukayi believing inada body odour É—in,seyazamanto
anamin kallon wata solobiyo. daman gashi ni shiru shiru,bana magana da kowa a ajin
inba Aziza ba,gashi dama back bench mukasamu dayake munje makarantar late,gashi
bana participating a class sanda Malami yake koyarwa,I don't ask questions abunda
nagane nagane wanda bangane ba kuma daga baya se in tambayi Aziza.
Tabbas kallon da mutane keyimin banajin daÉ—in sa anma yazanyi? How will I prove
myself right? Inma na iya nayi proving kan nawa who will save me from su Yaya
Safiya and the rest? Shiyasama nake barin Sadiya takeyimin duk abunda taga dama.
Aganina komai mai wucewane kuma komin karya fure take bata Ƴaƴa and i fully believe
the right time will come da basainayi magana bama Allah zai bayyanar dakomai.
Aziza batajin daÉ—in abunda akeyimin a ajinmu hakama a hostel dansau tari kawayenta
dasuka santa sukan sameta suce tarabu dani,ni kazamace,banida class,daqiqiyace ni
bansan komai ba daga kauye nazo anma hakan bai taɓa nanata dakasa ba, infact she
always turn them down.
Ni wani sa'in harmamakin yanda mutane suka kasa gane cewa niba kazama bace nakeyi,
infact I don't believe basu gane É—inba kawai dai suna saka blind eye ne a al'amarin
because I always appears very neat koda yaushe,bazaka taɓa gani nasaka kaya ba'a
wanke da goge ba.
Akwai ranar da Aziza tazaunar dani tana tambayana dagaske Ina fitsarin kwance?
dandai ita tasan duk sauran maganganun da'ake faÉ—a akaina bata yarda
dasuba,fitsarin kwancen nedai she's not sure tunda ba kwana mukeyi tareba and I
just smiled.
Setace "nidai banyarda da cousin sister É—inkincan ba anma inma dagaske fitsarin
kwancen kikeyi karki damu Inna koma gida zance ma Mommy na takarbo miki magani
agurin wani Malamin daya bama kanwata *Rahama* Itama da tanayi anma tunda tasha
maganin tadainayi" murmushi nayi sannan nace "Toh Aziza nagode".
***
Ranar asabar LamiÉ—o da abokin aikinsa Kano da jigawa suka kai kayan abinci suka
dawo gida gombe inda washegari dasafe suka sakeyin lodi suka nufi Bauchi. Koda
sukaje sukakai kayan abincin zasu kamo hanyar komawa Gombe se LamiÉ—on yace ma
abokin aikin nasa yatafi kawai shizai taho daga baya. straight gidan Kawu idrissa
yafara zuwa bayan sun rabu da abokin aikinsa inda tundaga bakin gate mai gadi
yasanar dashi Rukayya aitun ranar dasukazo ba'a sake dawowa da'ita ba dayake yagane
LamiÉ—on dasuka gaisa.
Godiya LamiÉ—o yamasa sannan yakoma bakin titi yasake taran napep yamasa kwatancen
unguwarsu Kawu Sani yakaisa har kofar gidan. yauma da Zunnurain yahaÉ—u bayan
sungaisa seya tambayesa koya ganesa anma sai Zunnurain É—in yace baiganeba.
Murmushi LamiÉ—o yayi sannan yace "Yayan Rukayya ne tawurin mahaifiyarta,ranan munzo
da É—ayan É—an uwanta nemanta harkace mana suntafi GiyaÉ—e?" cikin sauri Zunnurain
yace "Awww seyanzu natuna. Ya kwana biyu?" LamiÉ—o yace "Alhamdulillahi. Ayi hakuri
kar agaji dani nasake dawowa ganinta" Zunnurain yace "wai Rukayya?" gyaÉ—a kai
LamiÉ—o yayi
sannan yace "Eh itafa" Zunnurain yace "Aitana makaranta. Inaga yanzu su Rukayyan
nan zasu kusan two weeks datafiya makaranta" gaba É—aya se LamiÉ—o yaji jikinsa yayi
sanyi dankuwa with full hope É—in ganin Rukayya yazo yau,ahankali yace "Boarding
school tatafi ne?" Zunnurain yace "Eh FGC Azare suke itada sauran kanninmu"
jinjinakai LamiÉ—o yayi sannan yace "Toh shikenan Thank you. yanzukam sesun yi hutu
kuma"
Zunnurain yace "gaskiyakam" daganan se LamiÉ—o yamasa sallama yatafi.
Har ya Isa tasha haushin rashin ganin Rukayya yau yakeji ayayinda wata zuciyar
tashiga raya mishi why not yatafi Azaren kilan he'll be lucky to see her
today,seyayi sauri yakalli agogon hannunshi,it's still morning danko shabiyu ma
batayiba dayake tahowan sassafe sukayi.
Sekawai yanufi inda ake hawa motar Azare dayake yanada ishasshen kuÉ—i,baiwani Jima
da biyan kuÉ—in motar ba motar tacika daganan kuma suka daga zuwa Azare. Koda suka
isa Azaren Lamido baisha wahalar samun FGC Azare ba anma sede tundaga bakin gate
É—in makarantar aka hanashi shiga dayace ganin kanwarsa yazoyi. Masu gadin sukace
"Ba'a zuwa ganin kanwa haka kawai,akwae visiting days da aka kebe sabida iyaye da
Yayu suzo suga kannensu inkuma sako kakawo mata shine za'a iya karba anemeta abata"
marairaice fuska LamiÉ—o yayi sannan yace "Don Allah kubarni inshigo inganta,ko
mintuna ashirin bazanyiba zan fito" É—aya daga cikin Masu gadin ne yace "Ai matsalar
ba tamu bace samari,doka ce ta makaranta kuma komun barka kashiga daganan inkaje
can ciki baza'a bari kaganta ba. Shiyasa nakeganin gwanda katafi kawai ranar
visiting kadawo"
Jiki sanyaye LamiÉ—o yace "Yaushe ne visiting day É—in?" Mai gadin yace "Every first
Saturday of the month akeyi musu visiting,kaga yanzu dai atakaice za'ace sauran
sati biyu da kwana shida" gyaÉ—a kai LamiÉ—o yayi sannan yace "Allah yakaimu lokacin"
masu gadin suka ce "Amin" dukansu kafin yajuya yatafi.
Littafin Qadr na kudine duk maiso should talk to me via this number for payment
details
08147722806
Sorry fr keeping you guys waiting,zakujini gobe insha Allahu
*Page Thirty Five*
*Avoid typing errors Please*
Haka nacigaba da rayuwana cikin FGC Azare,rayuwar dake cikeda mockery, É—aukana
ba'abakin komaiba,ganina as wawiya anma hakan kosau ɗaya bai taɓaaba hanani yin
abunda yakaini makarantar ba dankuwa Aziza da books É—ina sune abokanaina acikin FGC
Azare. tun ina damuwa da abunda mutane ke faÉ—i akaina haryazo yazamemin jiki.
Su Yaya Safiya kuwa suma kamar Sadiyar ne dankuwa ko ahanya muka haÉ—u baswa nuna wa
ma sunsanni,sautari seniors mate É—insu zasu kirani su aikeni kosu sakani É—auka musu
ruwa agabansu anma ko sau ɗaya basu taɓa yin magana ba sede ma suma su haɗa danasu.
Yaya Zaheera kuwa duksanda nake hostel babu wanda tamaida É—an aikenta irina,yi
takeyi kamar anturo ni makarantar specifically dan inayi mata aikene. Dankuwa ko a
classes area during break nitake kawowa shopping list É—inta inyo mata nakai mata
class É—insu. A hostel ma kuma ban tsira ba dan har É—akin danake take turowa a kira
ni,inda Allah yataimakeni ma daman ni I'm not fund of zaman hostel shiyasa sautari
ko ta aiko akirani ma za'azo atarar bananan sede in daga baya inji labari abakin
Ƴan ɗakin mu.
Haka ranaku suka dinga canzawa suna komawa weeks har satin visiting yazagayo.
Karkuso kuga dokin da ÆŠalibai keyima zuwan wannan rana hakanan kowa shiri yakeyi
babu kama hannun yaro,daga masuyin sabon kitso semasu saka relaxer. Harta kayan
daza'a saka ranar visiting É—inma wanki da guga nadaban akeyi mishi a ajiye. wani
kuwa daman tun dawowarsa ya ware set ɗaya yaƙi yasaka sabida yanason yasaka ranar
visiting Ƴan gidansu suganshi fes fes. Inner wears kansu sabbi akesakawa ranar
visiting indai mutum yanada shi ayayinda wasu kuma har saya sukeyi.
Cikin masu shirin visit kuwa harda Aziza dankuwa tun last week take damuna da hirar
yan gidansu zasuzo tana faÉ—amin how excited she'll be idan tagansu anma ni agurina
abun bahaka yakeba. nida za'ace za'ayi cancelling visiting day ɗinma ba ƙaramin
farin ciki zanyi ba dankuwa nasan ko anzo visiting É—in ba farin ciki zanyi ba kamar
yanda sauran yara zasuyi idan sunga yan gidan su sunzo.
Aziza har mita ta dingamin wai bana farin ciki zanga mutanen gida sede inyi
murmushi kawai ayayinda araina nake raya "Aziza bakisan gidan danake zama É—in ba ne
shiyasa kike faɗin haka. mutanen da dagasu har Ƴaƴansu basu kauna ta"
Ranar laraba adole Aziza tajani mukaje ironing clothes É—inmu a laundry dukda kuwa
baranar nasabayin gugaba. Ni a weekends nakeyin gugana every week anma seta dage da
ai na fita visiting ground zan goge ranar so inzo muje,haka mukaje mukayi gugan da
yanma inda ahanyar dawowanmu mukabi ta wani shop dake hanyar hostel Aziza tasaya
mana riboms guda biyu kala É—aya kowa É—aÉ—É—aya tareda inner wears kala É—aya shima
kowa É—aÉ—É—aya. Nibanma san harda ni tasayaba seda mukaje hostel taÉ—auka tabani nawa
sannan nasani. Kin karba nayi dafari anma dayake tafini tsiya setaje tasakaminshi a
locker na ta datse lockern da padlock wai duksanda nashirya accepting kyautar data
bani inzo inkarbi makullin a hostel É—insu.
Hakuri nadinga bata sannan nace mata nayarda zankarbi kayan datasayamin É—in sannan
tayarda tabani makullin. Godiya namata ayayinda na rungumeta inajin wani irin
kaunarta na kara samun gurbi azuciyata. She's the only friend I can always call a
real friend tunda ko ada danake da gatana batasoni kamar yanda takesona a yanzu ba.
Niba mayyar kashe kuɗi baneba sannan ban taɓa damuwa da inje inkarbi kuɗin break
awurin guardian É—inmu ba anma ganin yanda Aziza ke kashe mana kuÉ—i kuma komai
tasaya seta ce dole tare zamu raba yasa nima nazake damtse nafara zuwa ina karban
Kudi awurin Uncle Adam akai akai inayimana abu tare.
Provision ɗina kuwa haryau bai ƙare ba dan kwata kwata ma ni baswa gabana,baiwuce
incisu sau biyu ko sau uku a satiba ba sabida nafi aminta da abincin dinning.
Biscuits da drinks É—ina nedai suka kare tuni dayake innatashi fita dashi nida Aziza
nake fitar mana Itama kuma hakan takeyi.
***
Yau Saturday kuma yau visiting day ne anma dayake akwai inspection babu wanda aka
bari yafita da sassafe dan ko iyayen ka sunzo sede sujira agama inspection naduka
houses kafin abuÉ—e gate kafita kaje kasame su.
Hostel É—inmu is the last hostel da akayi inspecting kafin Malaman namu suka tafi
sannan aka buÉ—e gate akafara bari ÆŠalibai sufita can visiting ground. Bayan fitan
inspectors badajimawa ba sega Aziza tazo niqi niqi da bucket dakuma kayanda zata
saka ahannunta.
Baki sake natsaya ina kallonta sannan nace "kekuma yada kaya niqi niqi ahannu?
Bakiyi wankan baneba?" Ajiye kayan ta tayi akan gadona tana mai gyara daurin towel
É—inta take kokarin sincewa sannan tace "banyiba,zuwa nayi inyi a hostel É—inku ko
korana zakiyi?" Ƴar dariya nayi sannan nace "Nina isa in koreki? Zauna ba indebo
miki ruwa yanzu kiyi kiyi wanka kada su Mummy suzo suna jiranki" hararana Aziza
tayi sannan tace "Suzo suna jirana ko suzo suna jiranmu? kinsan Allah Mummy cewa
tayi mufita dake tare,inkuma kindage bazakijeba nima se infasa zuwa,aidaman nasan
halinki yanzu sekiki shiryawa shiyasa ma nayi deciding inzo nan mushirya tare"
samun guri nayi nazauna gefen Aziza sannan nace "Nikam ma fa library nikeson tafiya
innayi wanka dama kinyi shirin ki kinyi tafiyar ki Allah" wani harara Aziza ta
watsamin sannan tace "Uwar library zakije ba library ba" sannan tatashi tsaye
taÉ—auki rigarta tawareshi daga hadaddiyar gugan datayimasa tana kokarin sakawa
ajikinta tace "ba insaka kaya inje wurin Sir Buhari yaƙira min Mummyna incemata
sukoma kawai tunda bazaki rakani gurinsu ba" wara idanu nayi sannan cikin sauri
nasa hannu nakarbe rigar Ina faɗin "kiyi hakuri don Allah" riƙe kugu tayi sannan
tace "toh zamuje tare kobazamuje ba?" ahankali nace "naji zamuje tare shikenan?"
mischievous smile Aziza tayimin wanda se ayanzu nagane cewa wayau tamin
alokacin,inbahakaba wazai cema iyayensa sufasa zuwa masa visit sabida kawarsa tace
bazata gansu ba? Yes Mummy mutumiyar kirkice kuma tanasona sosai dankuwa duk ranar
dana raka Aziza wurin guardian É—inta Sir Buhari toh tabbas insukayi waya seta bani
ita mungaisa sannan kowani labari Aziza zata bayar seta haÉ—a dasunana wannan
dalilin yasa in no time Ƴan gidansu suka sanni sosai.
Ko wataran ita kaÉ—ai tajeyin wayar inta dawo zakiji tacemin "Rukayya munyi waya da
Mummy tace ingaisheki" kotace "Munyi waya dasu Adda Rahama, Yaya sajeed duk sunce
ingaida ki" and I'll just smile se ince Ina amsawa hakanan se indinga ji inama nima
inada nawa family É—in da sai in dinga basu labarin Aziza suma sudinga cewa suna
gaidata kamar yanda nata familyn keyimin. tare mukaje muka É—ebo ruwan wanka dayake
harda bucket É—inta tataho hostel dinmu.
Muna yin wanka muka shirya cikin gogaggun day wears É—inmu sannan narife locker na
muka fice a hostel É—in baki É—aya muka nufi visiting ground. Sadiya tunda akagama
inspection daman ta dibi kayanta tabar É—akin batareda tacemin komaiba. Koda muka
isa visiting ground É—in su Mummy basu isoba dan haka semuka nemi É—aya daga cikin
fancy chairs É—inda ke kusa da gate É—in makarantar muka zauna muna kallon motocin
daketa shigowa makarantar dakuma yanda in ÆŠalibai sunga yan gidansu suke rugawa da
gudu suje su tarbesu. Take se Baba yafadomin araina,Sena fara tunanin da yanzu yana
raye yanda nake boarding school É—innan shima haka zaizo min visit inje intarbeshi
da gudu.
Wuraren Shabiyu da rabi na rana sega motar Ƴan gidansu Aziza yashigo makarantar
namu,wani irin tsalle murna tayi ayayinda ta rungumeni tana faÉ—in "Rukayya gacan su
Mummy sun iso" kafin taja hannuna mukabi bayan motar tasu da gudu.
Acan kusa da admin block sukayi parking motarsu inda mukaje muka samosu,Mummy na
fitowa rungume Aziza tayi tana faÉ—in "Autanaaa!" Cikeda farin ciki Aziza tace
"Mummyna I missed you" kissing cheeks É—inta Mummyn tayi sannan tace "I missed you
more autanaa" daganan kuma se sauran yayunta suka shiga rungumarta É—aya bayan É—aya
inda daga karshe tashiga tambayarsu dalilin dayasa Daddyn ta baizo ba.
Mummyn ne tace "Baban ku is out of town Aziza,yatafi Abuja yin wani aiki anma yace
inbaki hakuri,he promise to visit ahanyarsa ta dawowa insha Allahu" murmushi Aziza
tayi sannan tace "Allah yakaimu yakuma dawo dashi lafiya" inda dukansu suka amsa
da "Amin" alokacinne kuma yayar Aziza talura dani danake tsaye gefe Ina kallonsu
cikeda adoration.
Fuska É—aukeda murmushi tace "Aziza wannan ce Rukayyan naki?" juyowa Aziza tayi tana
kallona sannan taja hannuna zuwa gaban Mummy tana murmushi tace "Mummy toh ga
Rukayya kawata nan" ban ankara ba kawai sejina nayi acikin jikin Mummyn tana faÉ—in
"Masha Allah. Kyakyawa da'ita" sannan taÉ—aga ni daga jikinta tana kallon fuskana
tace "Ƴan Mata yakike?" Akunyace nace "Ina wuni Mummy" ansamin tayi fuska ɗauke da
fara'a inda daganan nagaida su Adda Rahama, Adda Zainab dakuma Yayan Aziza Sajeed
dayayi driving É—insu zuwa Azare sekuma kannen Aziza guda biyu Afra da Amir dasuka
gaishe dani. Sena dinga ganinsu kamar su Mariya da Sulen Kawu Sani,halinsu ne kawai
ya banbanta. WaÉ—annan sunada tarbiya da girmama nagaba dasu while my little cousins
were no match with them when it comes to irin wannan halayen.
Katuwar carpet É—inda sukazo dashi daga gida aka shinfida anan gurin sannan kowa
yasamu guri yazauna, Aziza tashiga basu labarin rayuwarta a boarding right from day
one har kawowar yau sannan suma yan gidan nasu suka shiga bata labarin abubuwan
datayi missing agidan,kama daga kan irin episodes É—inda tayi missing a serial
cartoons É—inda suke gani agida tare zuwa irin fun É—inda akayi bata gida inda daga
karshe Mummy tasa Adda Rahama tabuÉ—e cooler's É—in abincin dasuka kawo tazuba akaton
tray sannan akace kowa yazo yaci.
Aziza ce tafara saka spoon É—inta akan trayn abincin tana lumshe idanu ayayinda take
perceiving aroma É—in abincin tana faÉ—in "Ya'ilahi Mummy I miss you cooking,nayi
kewar cin abinci daku like a family wallahi" Adda Rahama dariya tayi sannan tace
"yarinya ai yanzuma kika fara missing,anfada shekara shida wasane?" Yaya Sajeed
dake gefe yanacin abincinshi daban shikaÉ—ai yadubi Adda Rahama yace "toh sakata
kuka uwar iyayi! Kema Ina haka kikayi shekara shidan kuma bagashi yanzu yazama
tarihi ba?" Adda Rahama dariya takumayi sannan tace "toh nayi shiru, Aziza acigava
da hakurin rayuwar boarding wataran se labari insha Allah"
Dariya sukayi duka sannan suka shiga cin abincin,nidai ganinan zaune agaban trayn
anma nakasa ci danwani irin nauyinsu nidinga ji harsaida Mummy tamin magana sannan
nafara tsakuran abincin inaci kaÉ—an kaÉ—an.
Bayan mungama cin abincinne Mummy tashiga tambaya na ko Yan gidanmu sunzo su,
murmushi nayi sannan na girgiza matakai ahankali nace "A'a basuzoba" tana shirin
yimin wata tambayar Aziza takatse ta tahanyar cewa "Mummy agidan Uncle É—inta take
zama. muna hutunnan Allah yayima Babanta rasuwa mamanta kuma Aina faÉ—a miki da
jimawa tarasu koh?" Jiki sanyaye Mummy tace "Allah sarki. Allah ubangiji yamusu
rahama" ahankali nace "Amin" ayayinda nake kokarin boye hawayena,carab kuma se
idanuna suka sauka kan motar Kawu Sani daya shigo makarantar sukazo suka wuce Admin
block din. I've not decided inje ingansu ko kar ingansu anma dayake inason insamu
gefe guda inyi kukana bana so inyi agabansu senayi sauri nanuna motar Kawu Sani Ina
faÉ—in "Gama can Yan gidan mu sun iso barina je mugaisa dasu" tashi Aziza tayi
sannan tadubi su Mummyn ta tace "Barina rakata Mummy zandawo yanzu" Mummy murmushi
tayi sannan tace "toh Autaaa adawo lfy" sannan tadubeni tace "kigaishe da mutanen
gidan naku ko Rukayya?" Cewa nayi "toh" ina murmurshi sannan mukabar gurin.
Allah yagani banyi niyar zuwaba anma biyoni da Aziza tayi yasa banida wani Option
daya wuce inje insame su É—in mugaisa.
Sanda muka isa inda sukayi parking motarsu har sunyi shimfida carpet an babbaza
kulolin abinci da ledojin kayan dasuka kawo ayayinda su Yaya Zaheera suka zagaye su
suna gaisawa da su Ummi da Aunty fuska É—aukeda fara'a.
Gefen Aunty naje na tsuguna sannan ahankali nace "Ina wuni Aunty?" fuska É—aukeda
fara'a tace "Lafiya Lau Rukayya! Ya makarantar?" Cewa nayi "Alhamdulillah" se Aziza
ma tagaida ta ta amsa sannan tashiga tambayana ko kawatace.
Cemata nayi "Eh kawatace" setace "Allah sarki" sekuma tamaida hankalinta kan su
Safiya dake bada labarin JJCn da Sadiya tayi ranar da aka kawomu dakuma irin kukan
datayi dan anmata dukan latti sunata mata dariya tareda su Yaya Zunnurain dankuwa
shine yayi driving É—insu zuwa makarantar namu.
Gaishe da Ummi nayi anma setayi kamar batajini ba,sake gaisheta nayi akaro na biyu
shima shiru sekawai naja bakina nayi shiru,Aziza kuwa ko kwatanta gaisheta batayiba
nadaiga tanata harararta kuma tabbas nasan yau senasha questions akan Ummi gurin
Aziza inmuka koma hostel.
Tsuguno muka cigaba dayi nida Aziza wanda harsaida Aunty takuma lura damu sannan
tasa hannu tajanye wasu ledoji dake ajiye tace "kuzauna mana tsugunon dakukeyi
É—innan ai kafafun ku zasuyi ciwo" murmushi nayi sannan nazauna ayayinda Aziza
tatashi tsaye tareda faɗin "nikam ma tafiya zanyi gacan Ƴan gidan mu najirana"
setayi ma Auntyn sallama sannan tayimin bye bye tatafi bayan tajaddadamin da Inna
tashi tafiya inbi mata mutafi hostel tare.
GyaÉ—a matakai kawai nayi ina murmushi. Sunjima suna hira kafin su Yaya Zaheera suka
zuba abinci suka shiga ci a tray É—aya inda suka zuba masu Mariya nasu a wani plate
daban. Aunty, Ummi da Yaya Zunnurain kuwa cewa sukayi baswa Jin yunwa sunci abinci
kafin su baro gida. Seda suka fara cin abinci Aunty taga basuyimin Bismillah
ba,cikeda mamaki tadubesu sannan tace "Safiya bazaku kira Ƴar uwarku tazo kuci
abincin ba?" Danko da wasa bazatayima su Yaya Zaheera magana ba sanin halinsu
datayi,yanzu sesuyi mata rashin kunya daman tsakaninta dasu gaisuwane kawai se É—an
abunda baza'a rasa ba. Safiya daketa aikin kai lomar fried rice da cowslow baki
tace "Mama abincin ma harsai anyi mata Bismillah? Anan gurin aibabu wanda aka kira
akace yazo yaci abinci.kowa on his own accord yazo yakeci bataji yunwa baneba
datana ji zatazo taci" Yaya Aisha Jin abunda Yaya Safiyan tace take seta yatsina
fuska tace "point of correction data zuba dakanta dai. gwandama kidaina cewa zatazo
taci damu kadama tafara tunanin zamu iya cin abinci tareda ita" sekawai suka kwashe
da dariya dukansu harda Ummi. Aunty ce kaÉ—ai batayi dariyan ba.
Rai bace tace "Safiya cire hannunki acikin abincinnan kizo kizuba wani a plate kuci
tareda ita Rukayyan" yatsina fuska Yaya Safiya tayi tana kunkuni ayayinda tataso
zata zuba senayi sauri nace "karki zuba naqoshi" Aunty kallona tayi cikeda mamaki
sannan tace "kin koshi kuma? Mema kikaci?" ahankali nace "Naci abinci awurin
yangidan su kawata kafin muzo nan" se Aunty tace "toshikenan anma inkunje hostel
makesure you collect food from them kinji?" gyaÉ—a kaina nayi ahankali kafin Aunty
tadubi Yaya Safiya tace "Sauran kuma insamu labarin baki diba mataba" daganan seta
shiga yima Safiyar faÉ—a cikin yare wanda inada tabbacin duk akaina ne.
Karfe uku daidai suka shiga tattare kayansu zasu koma gida wai Kawu Sani yace kada
subari suyi dare ahanya. Kowa ledan provision É—insa da fruits,bread dana kilishi
daban haka Aunty tabimu É—aya bayan É—aya ta rarraba mana sannan tace Kawu Sani ya
turama Uncle Adam 25k ya ajiye mana,each person 5k.
Godiya mukayi dukanmu tareda cewa su isar da sakon godiyanmu zuwa ga Kawu Sanin
inda daga karshe suka shiga mota dukansu suka bar makarantar. Harsaida motar tafita
a gate din makarantar sannan nadauke idanuna daga bin motar danayi da kallo. Ina ji
su Yaya Safiya suka karasa inda muka bar ledojin kayan mu suka shiga diban
nasu,nufan gurin nayi daniyar indau nawa senaga Yaya Safiya tamika ma Sadiya ledar
bread,kilishi drinks ɗina tana fadin "Tayani riƙe wannan zan ɗauki mai nauyin. Ai
tunda tajamin faÉ—a yaudinnan toh bazatayi amfani da kayan abincinnan ba sede mu
muraba a tsakanin mu" Yaya Zaheera tsaki tabuga sannan tace "baku iyayen tausayiba
inakwanaki da'aka kawosu danace mukwace kayayyakinta kinyarda kukayi kukace
abarmata su, gashi yanzu kunfara ganin halinta na munafurci ai" kwafa Yaya Aisha
tayi sannan tace "provision dindawowa makaranta Kam za'abarmata dan muma yawa
yakeyi Mana har murasa gun sakawa anma na visiting bazamuna barmataba wallahi!
Gatan aisai yayi matayawa" Yaya Safiya tace "hmm nifa kudinta ma wallahi dandai
bansan tayaya Zan tunkari Uncle Adam baneba da tuni naje na amshe" Yaya Zaheera
tace "kedai Bari" sekuma suka nufi hanyar hostel bayan sungama tattare komai
batareda sunma lura dani danake tsaye Ina kallonsu ba,bansan sanda wasu irin
dumanmun hawaye suka shiga bin kuncina ba. I'm not hurt because sun kwace kayan
abinci na ba, I'm hurt because narasa laifin menayi musu sukayimin irin wannan
tsanar dahar bazasu iya daukana da daraja a idanunsuba bare har suga good side
É—ina. Sena tuno yanda Ummi tayita hararan Aunty É—azu datake raba mana provision
dinmu.
Sa bayan hannun nayi nashiga goge hawayena sannan nanufi hanyar hostel É—inmu.
Banmanta cewa da Aziza tayi inbi mataba anma nikaina nasan I can't go back to her
family in this condition kuma koda banshiga wannan halinba dama banyi niyar
komawanba sede muhadu a hostel kawai tayi banbaminta harta hakura ta kyaleni.
Ina shiga É—akin mu naji anfara kiraye kirayen sallan la'asar sena fara danasanin
dawowa na hostel, nashiga ayyana dama zamana nayi a masallaci nasamu jam'i anma
tunda nariga nadawo banajin zan iya sake fita kuma danhaka sena dibo ruwa a butana
nayi alwala abakin kofar dakin mu sannan nadawo ciki nashiga kwana nan na shimfida
sallaya natada sallah.
Bayan na idar da sallah hawa kan gadona nayi nakwanta bateda na ko cire kayan
jikina ba. Hostel din shiru bakajin motsin mutane duk anacan visiting ground ana
sada zumunta da yan uwa da abokan arziki. Jefi jefi zaka ji motsin mutane acikin
hostel É—in wanda it can be dalibai ne Irina dabasu da masu zuwa musu visiting din
ko wanda sukazo ajiye kayan da aka kawo musu zasu koma kokuma wadanda already har
anzo musu antafine suka dawo hostel. tunanin duniya nakeyi dakuma mutanen dake
cikinta,tunanin irin halin rayuwar dana tsinci kaina aciki nakeyi at my very young
age batareda nasan laifin danayi ba harnayi deserving irin wannan treatment din
daga gurin yan uwana ba. Sallama naji anyi akofar dakin mu wnda hakan yasani daga
kaina nakalli kofar ayayinda na amsa sallamar.
Yarinya ce karama kamar ni.
Karasawa tayi kusa dani ta tsaya ganin nikadai ne a dakin sannan tace "don Allah
nanne dakinsu Rukayya Umar Yarima?" cikeda mamaki nace mata "Eh" ayayinda natashi
nazauna daga kwancen danake Jin ni take nema.
Setace "Don Allah Ina take?" nuna mata kaina nayi sannan nace "Ganinan,nice Rukayya
Umar Yarima" cewa tayi "toh kijeki visiting ground tawurin school garden Yayanki
yazo yana nemanki" cikeda mamaki nace mata "Yayana Kuma?" gyadamin Kai tayi sannan
tace "Eh" nace "Anya bakiyi mistake ba kuwa?"
Se yarinyar tace "toh nidai tarenagansu dawata senior yanamata describing É—inki
kuma itane tace inzo nan É—akin inkiraki" sekawai nace mata "toshikenan nagode
zanjeni" dukda Ina kokwanton anya nu É—in ake nema kuwa? Take kuma sewata zuciyar
tashiga rayamin kodai Buba ne yazo ganina daga Babban buli kilan Kawu Sani yasanar
dasu yau visiting. Wata zuciyar kuma seta shiga rayamin ai dasu aunty zasu
sanardani.
Take kuma secire wannan tunanin araina danatuna cewa they're not my well wisher
tunda maganar dabata arziki bama bason yi sukeyi daniba bare har subani information
mai daÉ—i irin wannan. Buta naÉ—auka naje waje nawanke fuskana dukdan wai kar inje
yagane nayi kuka sannan nadawo daki nazari hijabina nasaka nafita dasauri Ina
addu'ar Allah yasa Buban ne because I Can't wait inji labarin Gogode da mutanen
Babban buli abakin sa. koba komai nasan zaiyi cheering mood É—ina up.
Sanda Na'isa school garden É—in Sena ga yawanci yanmata da samari ne ke hira a gurin
yawanci,ma'ana samarin da sukazo ma yanmatan visit ne yawanci ke hira a gurin
sekuma few students dasuke tareda family members É—insu. can nahango Yaya Zaheera
tazage tana hira da wani sauri fuskarta daukeda kwalliyar da adazu dasu Ummi sukazo
Babu wannnan kwalliyar,sewani dariya take tana murmushi wanda hakan ya matukar bani
mamaki anma dayake ba itane gabana ba sekawai nadauke kaina daga gareta nacigaba da
wurwurga idanu takowani angle kozan hango ta inda Buban ke tsaye and then I saw a
hand waving at me ana min murmushi wanda by just a mere look nasan ba Buba baneba,
because Buba never dresses like this, Buba ba Dan gayu bane irin wannan, Buba
baikai wannan me dagamin hannun kyau da Kamala ba.
Mutsutsuke idanuna nayi sannan nasake kallon memin waving hannu don in tabbatar
kodani yakeyi senaga still nidin yakema waving hannu. Taku nashigayi ahankali Ina
nufansa and the more I go closer to him the more nake gani kamar nasan me wannan
fuskar harna kusa karasawa kusa dashi sosai,ananne nasamu naga fuskarsa
sosai,fuskar datasani yin standstill baki sake Ina kallonsa.
Kallon dani kaina narasa shin na farin cikine kokuma mamakin irin surprise É—inda
yayimin ne?
wani irin ihun murna nasaki,baki sake nace "Yaya LamiÉ—o....?" fuskata cikeda
excitement ayayinda naruga da gudu na rungume shi without a second thought,daganan
kuma sena fashe masa da kuka.
*Littafin Qadr na kudi ne duk Maison shiga paid group should talk to me on WhatsApp
tawannan layin 08147722806*
*Page Thirty Six*
Ba ƙaramin rudewa Yaya Lamiɗo yayi da Jin kukana ba hakanan cikin tashin hankali
yashiga rarrashina tahanyar soothing bayana yana faÉ—in "It's okay! Stop crying
please. I'm here. I'm here with you Nanaa...!" and this words makes me cry even
more dukdama kukan na farin cikine,kukan cewa nidinma ashe inada wani haryanzu a
doron ƙasa dazai faɗamin wannan kalamai masu daɗin.
Sedana gama kukana nakoma ina sauke ajiyar zuciya sannan Yaya LamiÉ—o yaÉ—ago dani
daga jikinsa yana kallona da idanunsa dasukayi jazir suka canza launi lokaci guda
duma. Manyan yatsunsa yasaka a both cheeks É—ina ya gogemin hawayena tareda faÉ—in
"Toh Ƴar birni kukan ya isa hakanan. Koso kike har in tafi inyita aikin rarrashin
kuka batareda munyi hira ba?" cikin sauri na girgiza masakaina ina murmushi jin
sunan daya kirani dashi yau sannan nace "A'a" seyaja hannuna muka ƙarasa kusa da
wani fancy chair dake kusa damu yazaunar dani sannan yazauna agefena shima.
Cikeda curiosity nace "Ya'akayi kasan makarantar mu? kuma ya akayi kasan yau
visiting day ne?" murmushi yayi sannan yace "Toh uwar tambaya zaki farakoh?" tura
baki nayi gaba sannan nace "nidai kafaÉ—amin please" yace "A'a bazan faÉ—a ba semun
gaisa,inama ko gaisheni bakiyiba" yayi maganar yana É—an tsuke fuska playfully.
Ƴar dariya nayi ga yanayin dayayi da fuskarsa sannan nasa hannu a bakina Ina faɗin
"Aaawww Ina wuni?" danni nama manta kwata kwata bangaishe shiba.
LamiÉ—o yace "bazan amsaba tunda seda na roka tukunnan zaki gaidani" pity face nayi
sannan nace "kayi hakuri. Allah mantawa nayi" seyasa hannu yaja cheeks É—ina sannan
yace "I know,I was just kidding. Toh ya makarantar taku? Hope dai ana karatu sosai?
kuma injidai ba'a bullying É—inku?" yatsina fuska nayi sannan nace "makaranta
alhamdulillahi,karatu kuma anayi shima bullying É—in duka anayi dan seniors É—innan
babu abunda suka sani se mugunta,sekace susuka biya mana kuÉ—in makarantar" nayi
maganar ina sake yatsina fuska.
Seriously yace "Suwaye da waye suke bullying É—inki a seniors É—innan? FaÉ—amin
sunayensu kokuma kinuna minsu in rama miki yanzunnan" wara idanu nayi ina dariya
sannan nace "karama min kuma?" dankwata kwata banÉ—auki maganar Serious ba.
Yace "Awww baki yarda baneba? Just tell me their names kokuma kinuna minsu
inkingansu anywhere around here kiga aiki da cikawa" murmushi nayi sannan nace
"bansan sunayensu ba Yaya LamiÉ—o hakanan bansan adadinsuba kuma wasuma na manta
fuskarsu yanzu" yayi kwafa sannan yace "toshikenan sunci sa'a amma dukranar da kika
tuna just let me know kinji?" dariya nayi sannan nace "Toh" sannan nakarada "inasu
Umma da Kawata Salma? Ina Yaya Jidda da Yaya Basma?" murmushi yayi yana kallona
sannan yace "Baki manta sunansu ba kenan?" gyaÉ—a masa kai nayi ina lilo da kafana
ayayinda nakasa dena murmushi sannan nace "Nina isa inmanta su? Ko ana mutum yana
manta Ƴan uwansa ne dama?" wara idanu yayi yana mamakin kalamaina.
Tsuke fuska nayi Ina tura baki gaba nace "yakana wara idanu kuma?" Yaya LamiÉ—o yace
"yanda kikayi maganarne yabani mamaki. Sometimes you speak like an adult" senasake
tsuke fuska nace "kenan kana nufin ni jaririya ce?" dariya yayi sosai sannan yace
"jaririya kuma? Jarirai ne kaÉ—ai ba adult ba?" tsuke fuska nasakeyi ina pouting
bakina nace "Eh mana" yace "A'a Nanaaa! wannan maganar taki akwai sonkai acikinshi"
yayi maganar cikeda tsokana wanda hakan yasake hasalani.
Yace "Kefah koh É—an sweet sixteen É—in zamaninnsn bakijeba,rabinsa ma bakikai ba
anma kikeso akiraki da Adult?" nace "Eh ɗin,anma ai ni ba Ƴar baby bace dukda
bankai wannan shekarunba" dariya yake sosai yana mamakin rigimana sannan yace "toh
naji! Ke ba jaririya bace anmadai that does not mean you're an adult,dukranar da
kika zama adult I'll say it to your face proudly insha Allah"
Tsaida lilo da kafana danakeyi nayi sannan na É—ago kaina ina kallonsa nace
"really?" gyaÉ—a min kai yayi ahankali yana murmushi.
Sekuma muka mayar da kanmu muna kallon mutanen daketa kai kawo agurin kowada abunda
yake sakawa azuciyarsa.
Can se naji Yaya LamiÉ—o yace "About Baba's demise karki bari ya daga miki hankali
please! everything happens for a reason,mutuwa kuma tana kan kowa Nanaaa! Kowa
lokacinsa yake jira,dukkanmunnan inda yatafi can zamu muma. Kuma daman Allah baya
barin wani dan wani yaji daÉ—i,babu abunda Baba yake bukata agurin ki inbanda
addu'ar ki,yiwa mamaci kukama babu kyau a musulunce, addu'a shine kaÉ—ai gatan
dazakiyi masa kinji?" yakarashe maganar araunane ayayinda yajuyo da fuskarsa yana
kallona and I couldn't look at him,sena cigaba da kallon inda nake facing dankuwa
tunda yafara maganar Baba hawaye yacikamin idanuna taff.
Araunane yacigaba da magana while look at me,yace "I'm sorry that I'm not with you
during your difficult times Nana! Accept my hearty condolences please! Allah
ubangiji yayi masa rahama, Allah yasa can tafi masa nan" bakina na rawa nace "Amin.
Thaaannnnkk... You" ayayinda hawayen danake kokarin riƙewa suka shiga zubowa,dan
duk yanda naso in riƙe su kasa resisting ɗinsu nayi. Inaji Yaya Lamiɗo yamatso kusa
dani ahankali sannan yakwantar dani ajikinsa yana tapping bayana cikin sigar
lallashi. Seda nayi kukan mai isana,nagama jikamasa well ironed rigar shaddansa
sannan na daga kaina jikinsa nakoma gefe ayayinda nacigaba da kallon inda nake
kallon É—azu.
Shima seya koma kallon wannan direction É—in,mukayi shiru nakusan mintuna goma
babuwanda yakuma cewa komai dukdama ni ina sauke numfashi akai akai.
Senaji yace "How's your Uncle's place? Are they treating you well? Are you happy
staying there?" yayi maganar ayayinda yajuyo yana kallon side view É—in fuskana.
Jin ya yimin irin wannan tambayar senaji wasu sabbin hawayen suna neman su zubo
anma sena daure na gyaÉ—a masa kaina ahankali. Cikin sauri yace "Nanaa kalleni" kin
kallonsa nayi sabida nasan me kallon nasa zaijamin.
Yakuma cewa "look at me Nanaa" anma still senayi kamar banji ba sekawai naga
yatashi daga inda yake zaune yadawo ta gabana ya tsuguna yana kallon fuskana cikeda
damuwa yace.
"Are you facing any problem over there?" Girgizamai kai nayi alamar a'a cikin sauri
cike da rashin gaskiya anma memakon ya yarda dani se yace "you're lying. your face
says it all,kifadamin? wani abun sukeyi miki acan?" jijjiga masakai nayi alamar a'a
ayayinda nafara hawaye kuma.
Kama hannuna yayi sannan yace "bazaki faÉ—amin banewai? Don't you trust me?" Shima
nayi shiru bance masa komai ba,raibace yace "Inbaki faÉ—amin ba wazaki faÉ—ama
Nanaaa?" ganin yanda ranshi yafara ɓaci senace "Allah babu komai" boldly yakuma
cewa "ƙarya kikeyi inkuma bazaki faɗa min bane se intashi inyi tafiyata tunda bani
da matsayi agurinki sannan kisani indai natafi dagayau bazaki sake ganina ba and
before I disappear from your live I'll make sure na faÉ—a ma su Gogode komai" Sena
fashe da kuka mai sauti,cikin gunjin kuka nace "Sabida banida Baban da zan haÉ—aka
dashi ka haÉ—ani da su Umman ka shine kakeso katafi kabar rayuwana Koh?" wara idanu
yayi cikeda mamakin furucina sannan yayi sauri yacire hannuna danarufe fuskana ina
kuka dashi yace "Wayagayamiki haka?" cikin kuka nace "bagashi kafaÉ—a ba yanzu"
dafekai Yaya LamiÉ—o yayi sannan yace "It's not what you're thinking Nanaa. daman an
taɓa exchanging iyayene arayuwa? da Baba yananan da bayanan I want you to always
know that I consider you my Sister and if you can be like a Sister to me then
familyn ki nawa ne hakama nawa nakine. Sannan inason kisan cewa i'm stick to you
Nanaaa... bazan taɓa barinki ba, I'll always stand by you as a Brother know matter
what insha Allah" kalamansa sunyi min daÉ—i sannan yanda yake furtasu kaÉ—ai shows
his utmost sincererity anma cikeda rigima senace "bawani! Ina gashi yanzuma kace
you're leaving my life bazaka sake dawowa ba" sauke wani gauron ajiyar zuciya Yaya
LamiÉ—o yayi sannan yatashi daga tsugunen dayake agabana.
Yadawo gefena yazauna yana kallona sannan playfully yace "ooo ooohhh! So you
seriously take this into heart?" É—agowa nayi na murkuda mai baki Ina share
majinana....
Seyayi dariya yace "Darling Sis you're sticked to LamiÉ—o already barikiji in faÉ—a
miki! Kuma ko birnin sin kika tafi sena biki na nemoki" yasauke ajiyar zuciya yana
kallona sannan yacigaba da magana "wai tukunnan ma kinsan irin wahalar danasha
within this Months kafin nasamu ganin ki yau?" I couldn't stop myself from smiling
dukda kuwa halin danake ciki sannan na girgiza masakai alamar "A'a" sannan nace
"wani irin wahala kasha?" yace "Lorddd! Wahalhalun danasha Allah yayi yawa
dasu,da'ace Maimunatu nayima wannan wahalar Inna samu na aureta anrufe kofa
kenan,daga ita babu wata kuma ko yaji bazan bari tayiba dan nikaÉ—ai nasan irin
wahalar danasha kafin nasameta" tsuke fuska nayi sannan nace "Waye Maimunatu kuma?"
Yaya LamiÉ—o na murmushi yace "Budurwata" sena yatsina fuska nace "Ohhh! toh nidai
kabani labarin wahalar dakasha please" Jan kumatuna yayi sannan yace "Ohhhhh su Yar
birni Amebo" pouting bakina nayi sannan nace "Eh naji nidai kabani" dariya yayi
sannan yafara bani labarin irin wahalar dayasha kafin yasamu Umma ta amince,dakuma
irin maganganun data faÉ—a akaina,da dako dayaje yayi,da karyar dayaje yayi a Fadan
su,irin sabanin damukayi tayi,zuwanshi FGC Azare aka hanashi shigowa dakuma yanda
yasamu yazo makarantar mu yau" tunda yake banu labarin nake blushing dukda inada
tambaya guda É—aya daya tsayamin rai.
I couldn't help it but feel special, yana gama bada labarin Ina blushing nace
"Nagode" hararana yayi sannan yace "Daman kanwa tana godema Yayanta ne?" Sena sake
cewa "Nidai nace Nagode" Yaya LamiÉ—o yace "Godiyarki bata amsuba and I didn't gist
you sabida kiyi praising É—ina, nabaki labarine sabida kiyarda cewa I can go to any
length for you as a Brother! tunda na amsa cewa ni Yayanki ne then I'll always
fulfill my responsibility" still blushing nace "Thank you" sa hannu yayi yadan
murda É—an karamin bakina tareda faÉ—in "in bakinnan bekoyi denayimin godiya ba zan
yagashi" dukda zafin danaji seban nunaba, dariya nayi sannan nace "toh nadaina" Ƴar
dariyar yayi shima sannan yace "Better inbahaka ba bakinki bazaidaina shan dirzaba
harsai ya yage" dariya nakumayi sekuma natuno tambayar danakeson yimasa, ahankali
nace "Haryanzu Umma batayarda ni mutum baceba? Kace tace ko gamo kayi da aljana?"
dariya yayi sannan yace "yeah haka tace anma ninasan kawai tafaÉ—a ne bawai yakai
har zuciyartaba and Hafiz yamata confirming komai so karki damu" tura baki nayi
gaba sannan nace "I want her to love me and accept me like a Daughter sabida kaga
inbatasona ta'ina zata barni indinga haÉ—uwa dasu Salma dasu Yaya Jidda?"
Yaya LamiÉ—o yace "Don't worry! Insha Allahu namiki alkawarin kawo miki Umma har
makarantar ku taganki even though bazance miki ga ranaba but this's my promise and
for sure,as soon as taganki she'll immediately fall in love with you" cikeda
excitement nace "Really?" gyaÉ—a min kai yayi ahankali,sekuma yace "toh yanzudai
nasan kinyarda ni Yayanki ne and I want nothing but the best for you right?" gyaÉ—a
masa kai nayi ahankali.
Seyace "then tell me how they're treating you in that House Nana" take smile É—ina
yayi vernishing Jin abunda ya ambata.
Ya marairaice fuska yace "kifaÉ—amin please! Inbaki faÉ—amin ba wazaki faÉ—ama? And by
saying it out we might find a solution together right?" kallon cikin idanunsa nayi
ina contemplating in faÉ—a kokar in faÉ—a inda adede lokacin ne kuma mukaji security
akanmu yana faÉ—in "Kasamu kaga kanwartaka kenan?" Cikin sauri LamiÉ—o yakalli
security man É—in sannan yasaki murmurshi yace "Eh oga nasameta" gaisheda security
Man din nayi ganin Yana kallona ya amsa yadan zolayeni sannan yadubi Yaya lamido
yace "Kanina Visiting hours fa yakare! you should leave now kafin sauran securities
suzo su koreka" jiki sanyaye LamiÉ—o yace "toh Oga nagode sosai. Allah yasaka da
alkhairi,sewani jikon insha Allah" security Man É—in yace "bakomai yima kaine ai"
kafin Yaya LamiÉ—o yamaida dubansa gareni yace "tashi mutafi" tashi nayi muka jera
muna tafiya se alokacin naga garden É—in wayam babu Yan mata da samari dake hira
É—azu, ashe duk an korasu,sena fara mamakin miyasa security É—in was nice to us mubai
koremu ba,kuma kamar ma yasan yaya LamiÉ—o yanda naga suke magana kafin mubar gurin.
Yaya LamiÉ—o kamar yasan tunanin danakeyi seyacemin "Yana É—aya daga cikin security
guards É—inku dana samu ranar danace miki nazo,shiya faÉ—a min yaune visiting date
É—inku kuma yauma danazo banida visiting card É—in shigowa shiya taimakamin
nashigo,yace ma sauran securities É—in yasanni gurin Kanwata nazo" jinjinakai nayi
sannan nace "Allah sarki" se Yaya LamiÉ—o yatsaya ganin mun É—anyi nisa da security
guard É—in yace "tell me Nanaa? How are they treating you in that house?" jiki
sanyaye nace "Yaya LamiÉ—o it's a long story,katafi kawai kada kayi dare ahanya"
yace "Babu ruwan ki inma tafiyar tsakar dare zanyi,just tell me" nace "Allah next
time inmun haÉ—u zan faÉ—a maka,konafara baka labari securities zasuzo su koraka and
besides I'm here in school bare ace zasucigaba dayimin abunda sukeyimin agidan"
Sauke wani gauron numfashi yayi sannan yace "Okay toh yanzu yaushene next visiting
date É—inku? First Saturday of next month koh?" girgiza masakai nayi alamar "A'a"
sannan nace "time É—in muna midterm break so baza'ayi visiting ba se upper month
shikuma ze fado ne a week to za'ayi hutu kaga ba lallaine azo visiting É—in sosaiba"
se Yaya LamiÉ—o yace "toh nidai zanzo in Allah yakaimu lokacin" cikin sauri nace
"there's no need Yaya LamiÉ—o. A week to za'ayi hutune fah?" yace "toh in akayi
hutun nasan ranar dazan kuma ganin kine?" Senace "Ai zanje hutu GiyaÉ—e ko Babban
buli dan Kawu yamin alkawari kowani hutu zanna zuwa kaga innaje Babban buli basai
kazo nan muhadu ba" seya girgiza kai yace "banyarda ba. Zanzo ranar visiting É—in
kuma zanzo Babban bulinma inganki in anyi hutu insha Allah" ganin konayi masa musu
bacanza ra'ayinsa zaiyiba senace "toh Allah yakaimu"...
Yace "Amin" kuma a midterm dinma kina iya ganina agidan Kawunki. dariya nayi kawai
dan banÉ—au maganar tasa seriously ba.
Har bakin gate na rakashi Ina bashi sakon yagaidamin dasu Yaya Jidda sannan yace ma
Salma inanan Ina treasuring gift É—inda tabani kuma nima insha Allah I'll buy
something special for her.
Cewa yayi "Uhmmm masu kawaye! Ruffle É—inne harwani treasuring É—inshi kike kamar
wani gold É—inda Kika samo a field kika tona dakanki?" tura bakina nayi gaba sannan
nace "Yaya LamiÉ—o dandai bakasan how much Ruffle É—innan means to me baneba,it's the
symbol of my friendship with Salma shiyasa" dariya yayi sannan yace "toh anji zan
faÉ—a mata sakon ki insha Allah" nace "yauwa Yaya LamiÉ—o...." sa hannu yayi a
aljihunsa yaciro kuÉ—i dubu biyu yamikamin sannan playfully yace "take this,kidinga
sayan garin kwaki dashi kinasha a school shop É—inku kullum da break" make kafaÉ—a
nayi Ina dariya sannan namayar da hannuna bayana nace "A'a kabarshi nagode Allah"
tsuke fuska yayi sannan yace "nace ki karba koh?" sake makemai kafaÉ—a nayi sannan
nace "Allah inada kuÉ—i! Nada ma baikareba kuma É—azu dasu Aunty sukazo mana visit
Kawu Sani yabada 5k 5k abawa kowannen mu" Yaya LamiÉ—o yace "koma miyene dai ni ki
karba,wanda Kawunki yabaki daban nima nawa daban inkuma kinrainane toh se inje da
abuna next time se insake sanin irin shirin dazanyi na zuwa visit É—inki" cikin
sauri nasa hannu nakarba Ina faÉ—in "Allah ban rainaba. Thank you Allah yakara buÉ—i"
murmushi yayi sannan yace "Amin" sannan yakarada "akan kujerar damuka zauna kinga
wani leda koh?" gyaÉ—a masakai nayi alamar "Eh" yace "toh nakine inkinje seki É—auka
kitafi dashi hostel,bbu yawa kinsan Yayan naki talakane" seyamin bye bye kafin
yajuya yayi tafiyarsa tunma kafin in iya bude baki ince wani abu. He just left me
speechless,najima Ina tsaye Ina kallonsa harsaida yafice a gate É—in makarantar
sannan nasauke wani wawan ajiyar zuciya Ina murmushi kamar wata wawiya sannan
najuya nanufi garden É—in don É—aukan ledan dayace nawane. Aikuwa Allah yataimakeni
ba'a É—auke ledan ba,anan inda muka barta nasameta.
BuÉ—e ledar nayi senaga sponge cake ne me kala kala guda huÉ—u dayasaya a
Oasis,sekuma roasted fish dake cikin foil paper,slice bread,se irin Babban kwalin
exotic guda É—aya aciki.
Mamakin Ina yasamu kuÉ—in dayamin sayayyarnan nashigayi dan senake ga kamar É—an
aikin dayacemin yanayi yanzu baikai yasamu wannan amount of kuÉ—in ba,anma danayi
la'akari dazai iya yuyuwa yajima yana tara kuÉ—in ne seban yi mamaki ba because for
sure nasan ba sata yayiba dan nasan Yaya LamiÉ—o baiyi kama da wanda zaiyi sata ba
and from the way he's so contented with what yakedashi sanda muke zuwa field tare a
Babban Buli na tabbatar bazai taɓa yin sataba,besides i trust his intentions
sekawai naÉ—auki ledar nanufi hostel abuna raina fess kamar banine nasha kuka kala
kala ba yau.
***
Tunda nashiga gate É—inda zai sadani da hostels É—inmu nakejin hayaniya tako'ina
unlike É—azu darana dana shigo naji ko'ina shiru. Ma'ana yanzu kowa yadawo daga
visiting ground ana hirarrakin abubuwan dasuka faru acan visiting ground É—in. Ko
waÉ—anda nike wucewa a hanya yawanci hirar dazakaji sunayi kenan,daga masu bada
labarin yan gidansu semasu bada labarin sauranyinsu dayakawo musu ziyara yauÉ—in.
Nidai harna Isa hostel É—inmu fuskana É—auke yakeda murmushi hakanan duk wasu moments
É—ina da Yaya LamiÉ—o yau su kaÉ—ai keta ringing a kwakwalwana. tunaninsu yabi ya
mamaye duk wani takaici da bakin cikin da aka cusa min yau. ÆŠakin mun ma danashiga
surutu na tadda suke tayi ayayinda tundaga bakin kofa nadinga cin karo da empty
kwalayen juices, biscuits, indomie su conflakes dadai sauransu,ma'ana dayawansu
sunyi gyaran lockersu ayayinda wasunsu kuma yanzu suke kanyi.
Corner mu nida Sadiya nawuce na buÉ—e locker na na ajiye ledan da Yaya LamiÉ—o yabani
tareda kuÉ—in daya bani sannan narufe lockern nasake fita waje. Matrass É—inda bazan
iyacewa nawane kona Sadiya bane naÉ—auko nashigo dashi dankuwa haryanzu babu abunda
yacanza a abunda takeyi min game da fitsarin kwancenta haryau.
katuwar blanket É—inda na shimfida akan gadon yayi serving kamar katifa dayake
yanada nauyi nacire sannan na É—aura katifar akan gadona Ina tattaba inda na zuba
masa ruwa É—azu dasafe don jin koya bushe dakyau kobai busheba dayake yau ban
fitarda katifar dawuriba kasancewar yau anyi inspection,seda aka gama sannan
nafidda shi da Aziza tazo min dasafe. Kuma ita tanunamin dabarar shimfida blanket
É—ina akan inbar gadon empty mutane suna gani,kuma dayake katone blanket É—in seka
saka Ido sosai zaka gane babu katifa akai.
Bayan nagyara gadon na shimfida bedsheet É—ina sena É—auki buta nafita a É—akin natafi
can bakin tap É—inda ke can wajen hostel É—inmu nadibo ruwa sannan nadawo nan gaban
kofar É—akin mu nazauna nayi alwala dayake gaf ake da akira sallar maghriba. Ko
bayan dana koma É—aki bayan na'idar da alwalan kwanciya nayi akan gadona inajiran
akira sallar maghriba ayayinda nake tunanin Yaya lamido. Tunani nakeyi ko yana Ina
yanzu? Shin yasamu motar komawa ne kobai samuba? Inma yasamu motar tacikane kobata
cikaba? Kokuma kilan suna kan hanya yanzu? Ni kaÉ—ai dai haka nadinga sake sake
cikin raina har aka ƙira sallah natashi na shimfida sallaya nahau darduma nayi.
Ban Jima da idar da sallah ba naji Sister Hafsat (Room Head) É—inmu tana kwala kiran
sunana,amsawa nayi sannan natashi natafi kwanarta,plate É—in abinci da ledan fruit
tamikamin.
karba nayi duk atunanina aikena zatayi wani guri anma da mamakina setacemin "jeki
nakine" mayarmata nayi da sauri sannan nace "nagode anma a koshe nake Sister
Hafsat" tsuke fuska tayi sannan tace "Anjima zakici ai,jeki dashi babukyau maida
hannun kyauta baya" senayi murmushi nace "toh na gode" sannan najuya nanufi
kwanana,senaga few daga cikin Yan É—akinmu nata bina da kallo anma senayi kamar
banganiba harna ƙarasa kwanana.
Banyi mamakin kyautar da Sister Hajara tayimin sosaiba don daman tanada kirki kuma
she's very simple sannan duk tsanar da tsangwamana da sauran Ƴan ɗakin mu keyimin
ita batayimin kwata kwata sannan bata taɓa zagina wai Ina fitsarin kwance ba infact
sometimes intaji Ƴan ɗakin mu na gulma na har faɗa takeyi musu kotayi purnishing
É—insu. Mates É—inta nedai bata iya cemusu komai dayake batada righi É—in hukunta
su,cikinsu kuwa harda kawar Yaya Zaheera da Yaya Zaheeran tabama amanar Sadiya
ranar da aka kawo mu dadare.
Dukda ba shiri mukeyiba gaisuwa kawai ke haÉ—amu and I respect her so much.
Na ajiye plate É—in abincin kenan Ina neman wani plate É—inda zan rufe abincin dashi
kawai sega su Yaya Zaheera sunshigo corner mu dukansu huÉ—u,Sadiya,Yaya Zaheera,Yaya
Aisha da Yaya Safiya.
Akan gadona Yaya Zaheera da Yaya Aisha suka zauna ayayinda Yaya Safiya tahau saman
lockern Sadiya tazauna dayake babu wani bunk kusadamu,dagamu se kofar É—akin,sauran
bunks É—in duk seka tsallaka É—ayan side din dakin zakasamesu. abunda ke gabana
nacigaba dayi batareda na É—agoba wato neman empty plate inrufe abincin da Sister
Hafsat tabani.
Inaji Sadiya tatura ledojin kayan da aka kawomana daga gida,danasamo plate É—in nima
saina rufe abincin natura karkashin gadon mu kafin natashi tsaye daniyar infita
inbasu guri inyaso daga baya insun tafi nadawo.
Anma sede ko steps uku banyiba naji Yaya Zaheera tace "Keee! Zonan!" wani irin
rasss! Naji zuciyana yayi lokaci guda kafin najuya ahankali na karasa inda take
zaune na tsuguna sannan nace "Gani Yaya Zaheera" harara ta watsamin ayayinda take
taunar cingam sannan strictly tace "Wayene gayen dana ganki dashi a school garden
yau?" aikuwa se bugun zuciyana yakaru,Sena fara tunanin kenan "taganni da Yaya
LamiÉ—o É—azu komi take nufi?".
Wani tsawar data dakamin ne yafidda ni daga trance É—ina,tace "ba magana nakeyi miki
banewai?" bakina narawa nace "Yayanaaa ne" wani kallo takuma watsamin sannan
adakile tace "Yayanki ne?" gyadamata kaina nayi ahankali,tace "ta'ina yazama
Yayanki?"
*ah toh Zaheera Nimadai tayani tambaya.😜 Fans ta'ina Lamiɗo yazama Yayan Rukayya?"
*Littafin Qadr na kudine duk maison shiga paid group should talk to me privately
via this number on WhatsApp 08147722806 for payment details*
*Page Thirty Seven*
Avoid typing errors Please.
Ta'ina yazama Yayanki? ya akayi kuka haÉ—a dangi dashi?" inajin tambayar da Yaya
Zaheera yayimin amma senayi shiru bance mata komaiba dannikaina banida amsar dazan
bata.
Yaya Safiya dake zaune akan locker ne tace "Tawurin mahaifiyarki kuka haÉ—a dangi
dashi komi?" tsaki Yaya Zaheera tayi sannan tace "Babu wani dangin dasuka haÉ—a
tawurin mahaifiya,ke baki taɓa ganin irin dangin mahaifiyar tata bane sanda muke
zuwa asibiti duba Uncle Umar? they're typical villagers fa,Guy É—in dana gani É—azu
kuma ko kusan haÉ—a kama da kauyawa ma baiyiba" Yaya Aisha tsaki tayi sannan tace
"kyale Safiyar nan Yaya Zaheera,sekace bataji yanda su Rabia ke describing guy É—in
ba É—azu" Yaya Safiya tace "naji mana,naji yanda suke describing É—inshi anma ai that
does not mean bazai iya haɗa dangi da Mahaifiyata ba. Take a look at us,muba Ƴan
Uwan su Kawu Hassan dake GiyaÉ—e baneba? infact most of our relatives acan suke zama
kuma babu wanda zaiganmu yace mana ga asalinmu so it can be thesame thing with the
guy" sekuma maganar Yaya Safiyar tayi making sense agurinsu,se Yaya Zaheera takuma
dubana dan tayi confirming tace "Dangin Maman kine?" rashin sanin abuncewa sekawai
nace "Eh" tace "a Ina yake zama?" Nace "A Gombe suke" tace "toh ta'ina kuka haÉ—a
dangi da mutanen Gombe kuma?" senayi shiru, Yaya Safiya dakejinmu tace "tace
Yayanta ne kilan cousin Brother É—inta ne"...
Se Yaya Zaheera tace "cousin É—inki ne?" Kawai sena kuma cemata "Eh zamane yakai su
can" tace "Awani makaranta yake?" nace "Gombe state University" dankuwa banmanta
sunan makarantar tasuba.
"Wani course yakeyi kuma awani leven take?" Yaya Zaheera takuma jefomin wasu
tambayoyin dayasa nafara tunanin anya ba Ƴar jarida baceba kuwa? wannan
interrogation haka? And more over meyasa sukeson susan information akan shi? And
miyasa naji suke zancen kawayensu suna describing É—inshi anma ganin banida amsar
tambayar danakema kaina gakuma dukansu sunzubamin idanu suna jiran ansar tambayarta
daga gareni senace "Geology yakeyi kuma yagama aji uku yazu yana industrial
training É—inshi ne kafin suyi resuming yashiga final year"
Kallona juna naga suntsaya sunayi naɗan wasu daƙiƙu kafin suka dawo da dubansu
gareni wanda hakan yasani sauke kaina ƙasa da sauri.
Yaya Zaheera tace "KeÉ—in ya akayi kikasan informations har haka agame dashi?" Yaya
Safiya couldn't help it but laugh tace "mutum da Yayansu bazaisan abubuwa game
dashiba?" Yaya Zaheera strictly tace "Bawani. Yayanta najinine? He's just a mere
cousin Brother and anything can happen" sannan tamaida hankalinta gareni sosai tace
"keh! É—ago kikalleni" É—agowa nayi nakalleta kamar yanda tace sannan cikeda tuhuma
tace "kodai Soyayya kukeyine?" Aibansan sanda na ware idanuna ba hakanan cikeda
mamakin kalaman ta nace "Soyayya Kuma? Yayana nefah kawai" dannidai a iyakacin
shekaruna I don't even think yakamata tayimin maganar soyayya.
Seta cemin "tsakanin ki da Allah Yayanki ne ba soyayya kukeyi ba?" Cikin sauri nace
"Allah Yayana ne kawai" tace "toh miyasa zaizo miki visiting shikaÉ—ai?" senace
"sabida muna shiri sosai kuma baiyimin ta'aziyar rashin Baba ba shiyasa yazonan"
hararana tayi naɗan wasu daƙiƙu sekuma tatashi tsaye tanacema su Yaya Safiya
sutafi, naÉ—auka sun rako Sadiyar ne su sukoma anma senaga Itama tabi bayansu.
Nidai harsuka fita a É—akin mu mamaki nakeyi kamar mi, I'm so speechless and out of
words gashi banida wanda zan tambaya insamu amsar dalilin wannan interrogation É—in.
Fitarsu bada jimawaba sega Aziza niki niki da kaya tashigo cornern mu.
Cikeda mamaki nasaki baki Ina kallonta daga zaunen danake a bakin gadona sannan
nace "kekuma niki niki da kaya inazaki kaisu?" hararana tayi sannan tace "nikitaso
kitayani bazama zakiyi kina tambayana kamar wata Yar jarida ba" tashi nayi na karba
ina dariya sannan nace "kene harzakicema wani ÆŠan jarida? Har akwae wanda yakaiki
iya tambaya ne daman?" Aziza samun guri tayi tazauna agefena bayan mun ajiye
kayayyakin dake hannunmu tana faÉ—in "aigwanda ni inzanyi tambayar reasonable
questions nike tambaya! Kekuma naqi tambayar harda silly one's kike haÉ—awa"
hararanta nayi ina murmushi nace "Komadai menene bankaiki ba" sena canza maganar
tahanyar nuna kayayyakin data shigo dasu nace "kekuma sakon Suwaye haka kikawani
zomin dashi corner na?" Aziza tace "nawa kuwa inba naqiba? Mummy ne tace inbaki
tunda kinki kikoma kuyi sallama" takarashe maganar ayayinda ta kama hannuna tasaka
min kuÉ—i aciki tana karawa da "wannan ita tace Inbaki"
Ware idanuna nayi sannan nace "Keh lafiyarki Aziza? duk wannan uban kayan inazan
kaisu? Anya bakayan ki Kika dibo Kika kawomin ba?" Aziza seriously tace "wallahi ba
kayana baneba,kayana na hostel Mummy ne tace inbaki inkuma bakiyarda ba ranar
Monday muje gurin Sir Buhari inkirata ki tambayeta" kawai sena rasa abun cewa, I'm
so out of words and speechless...
Daƙyar na'iya uttering kayannan sunyi yawa Aziza,don Allah kiɗauko kikara akan naki
toh. I've provision yauma kuma ankaromin daga gida" harara Aziza ta watsamin sannan
tace "seki kara da wannan É—inma kumani babu É—iban dazanyi,nawama sun isheni kuma
ainaki ne banawa ba" mikamata kuÉ—in nayi dasauri nace "kuÉ—in toh kirikeshi please!
kikara akan naki inbaso kuke kuÉ—i sufara tsuro ajikina ba" dariya Aziza tatsaya
yimun sannan tace "sufara tsuron mana,aini abun murnane agareni,duksanda nikeson
kuÉ—i kawai sede inzo gurin ki in tsinka inje insayi abunda raina yakeso" hararanta
nayi ganin tamaida abun wasa anma still sebata daina zolayar nawaba.
Daga karshe dai ganin taki yarda daduk wani kudirina senace "Nagode. Allah yasaka
da alkhairi kuma don Allah ranar Mondayn zaki rakani muje ki kiramin Mummyn
insakeyi mata godiya" Aziza gyaÉ—a min kai tayi sannan tace "Allah yakaimu" senace
"Amin" ayayinda nakejin wani iri,duk senaji babu daÉ—i,ita iyayenta sunyi min
abudayawa harda wahala dani anma ni banida abunda zanbata. Gashi Ƴar provision
É—inda nake takama dashima su Yaya Safiya sunkarbe.
Take kuma se abunda Yaya LamiÉ—o yakawomin yafaÉ—o min araina,daman na ajiyene akan
setazo muci tare dasauri nasauka daga kan gadona nanufi lockerna na buÉ—e sannan
naciro ledan na ajiye agabanta sannan excitedly nace "ban faÉ—a mikibadai, Yayana
yazoshi É—azu bayan su Aunty sun tafi" sekawai naga Aziza tasauko daga kan katifana
cikin sauri tadawo ƙasa kusa dani tazauna sannan cikeda zumuɗi tace "Daman Yayan
kine yazo É—azu dagaske?" gyaÉ—a matakai nayi sannan cikeda mamaki sannan nace "Anma
Ya'akayi ke kika sani?" Aziza tace "Ai talk of the town kika zama yau a hostel
yarinya" cikeda mamaki nace "kamar Yaya?" Aziza tagyara zama tace "kekam tun ina
hanyar dawowa daga visiting ground bayan su Mummy sun tafi da yanman nan naji wasu
suna hira ahanya,wai yau wata yarinya Brothern ta yazo mata surprise visit, tundaga
nesa dakika ganshi kika kwala kiran sunanshi excitedly kikaje da gudu kika
rungumeshi kika fara kukan murna,wai su murnar dakikayi da zuwa da kikayi kika
rungumeshi dakuma haÉ—uwar gayen ne yabirgesu,kinji yanda suketa maganar kuwa? wai
he's so caring,sewani rarrashin ki yakeyi duk inajinsu dayake agabana suke tafiya
ahaka dai har muka iso wurin hostel dina nina shige inda su sukayi gaba anma me
dana ƙarasa ɗakinmu sena tarar da Yan ɗakin mu ma Thesame hira sukeyi. Ashe tunkan
nashiga É—akin Khalisat É—in É—akinmu tasanar dasu kece dayake tana gurin abun yafaru
kuma taganki shine dataji suna hirar seta sanar dasu cewa aikece dakike zuwa gurina
kullum mufita tare"
Shine fa Su Sister Salma É—akin mu dasuka ga nashiga É—akin sukayita tambayana kona
san Yayan naki ko mun haÉ—u,nace nidai bamu haÉ—u ba kumadai bansanshiba
gaskiya,shine Sister Salma tace gobe inkaiki gurinta wai itadai Allah yagani tafara
crushing akanshi dukda bata taɓa ganinshi ba.
Tunda Aziza kebani labarin nayi shiru Ina saurarenta ayayinda nake analyzing kowani
maganarta Ina assimilating É—insa,Sena tuna kallona da Yan É—akinmu sukayi tayi dana
karbo abinci a wurin Sister Hafsat,natuna interrogation É—inda su Yaya Zaheera
sukazo sukamin É—azu,natuna cewa dasukayi wata tace yahaÉ—u and then I got it cewa
Ashe har samana ido akayi a gurin mu bamuna saniba.
Araina senashiga ayyana "ikon Allah! Wai daman haka boarding É—in yake?asamu magana
É—aya aita yadashi? Masu exxageration suyi masu karyama duk sukara akai.
Maganar da Aziza tayimin ne yafidda daga trance dina bayan tagama bani labarin,tace
"ashedai dagaske Yayan naki ne? anma cousin Brother É—inkin from maternal side koh?
Because as far as I know bakida blood Yaya,you're the only child to your parents
dangin Babanki kuma ai É—azu sukazo" murmushi nayi sannan nace "Eh Aziza. Munsaba
dashi sosaine kuma baiyimin ta'aziyan rashin Baba ba shine yazo nan makarantar yau"
tsuke fuska Aziza tayi sannan tace "Shine baki taɓa bani labarin shiba koh?Ni
kullum sede inyita baki labarin close one's É—ina anma ke kwata kwata bakya bani
labarin waÉ—anda kukasaba wanda har hakan yakesani tunanin you're always tortured at
home ne" cikin sauri nace "waya faÉ—amin I don't have loved one's? I've so many of
them anma the most dear ones to me bayan Babana are three in number" na É—aga
fingers É—ina nashiga mata counting nace "Kinga Gogede Grandmother nane and she's my
role model,se Gwaggo Suwaiba,she's my Aunt but more like a Mother,i always have her
back and lastly Yaya LamiÉ—o,he's one in a million,he's my smile,my happiness and my
ultimate emotional support. banjima da sabawa dashiba anma zan iyacemiki yafimin
mutane dubbai danasaba dasu kafin shi"
Aziza data riƙe Chin ɗinta da hannunta tana kallona tace "it seems like this Yaya
LamiÉ—o dakike magana shine yazo yau?" gyaÉ—a matakai nayi Ina murmushi sannan nace
"Shine,naso ku haÉ—u anma Allah beyiba dannima bansan da zuwan nasaba,it was a
surprise visit but next time I'll surely look for you inyazomin visit insha Allahu"
Aziza setace "Allah yakaimu" dayake banagajiya da bada labari indai na LamiÉ—o ne,
because it gives me so much joy senace mata "aiyama sanki! na taɓa bashi labarin ki
kwanaki" wara idanu Aziza tayi sannan tace "nikuma?nida da bamwa wani shiri ada
labarina name kika bashi kuma?" senayi dariya nace "cewa yayi inada yawan tambaya,
I'm always curious akan koda abunda baikamata insani baneba shine nace mishi
aibankaikiba. Kema gwanace when it comes to asking questions in the class,nace
mishi har haushin ki mukeji in zakiyi tambaya a aji" dariya Aziza tayi sannan tace
"kema ai haka kike,ke kawai bakya tambaya a ajine se an fita kike damuna da
tambayoyi. dariya nayi sekuma na buÉ—e ledan naciro roasted fish dinda yakawo mani.
Nasamana akan plate mukaci da bread,muka karada abincin da Sister Hafsat tabani duk
muna hira,hiran da yawanci akan makaranta ne sekuma damuna da Aziza tayi incigaba
dabata labarin dangina wanda nasan duk bugan cikina takeso tayi,tana son tasan
halin danake cikine anma senaki bata wannan side of my story É—in,sena dinga bata
labarin mutanen Babban buli da GiyaÉ—e dasuke Sona. agidan Kawu Sani kuma sena bata
labarin Kawu sani,Yaya Salim da irin mutuncinshi,sekuma miskilancin Yaya Fahad.
ranardai atakaice Aziza a hostel É—inmu ta kwana dayake weekend ne kuma Sadiya ma
ba'a É—akin mu takwana ba shiyasa nina dale bunk É—inta nabar ma Aziza nawa gadon
tayi bacci akai. washegari ma seda mukayi wanka mukaci abinci sannan na rakata
hostel É—insu.
Ananne na haÉ—u dasu Sister Salman É—akinsu,har kwananta tajani tana min tambayoyi
akan LamiÉ—o inda daga karshe ta cemin ingaishe shi innakoma gida danta tambayeni
numbersa nace mata niban riqe ba.
Nidai harna bar É—akinsu Aziza nakoma É—aki mamakin wannan zubar da class har haka
nakeyi dukda kankantar shekaru na,ganinake ita Sister Salman harnawa take dazata
fara maganar Soyayya? nida duk a mentality na naÉ—auka a birni se angama karatu gaba
É—aya ake fara kula saurayi anma danazo boarding school senake ganin abun
differently,senake ganin kamar banbancinsu dasu Kwaidum ma kaÉ—an ne tunda su auren
akeyi musu at their young she while anan kuma yan mata kula samari sukeyi at their
young age. Natuna jiya naga Yaya Zaheera na hira,yau ance ana crushing akan Yaya
Lamiɗo kuma wani sa'in ma nakanji Ƴan ɗakinmu na hirar samarinsu atsakaninsu and
this always got me wondering.
Koda nakoma hostel kayan da Mummyn Aziza ta bata ta kawomin na buÉ—e ina gani É—aya
bayan É—aya. madara ne peack medium size na gwangwami se Milo karamin gwamgwami,se
conflakes guda biyu na kwali da golden morn É—aya,se sugar cube biyu,se packet na
detol,sabulun wanki guda huÉ—u,toothpaste,body spray,body lotion,hair cream,se
biscuits da juice half half carton se kuÉ—i 2k É—inda Azizan tabani daren jiya,ba
ƙaramin mamakin mutuncinsu nayiba ayayinda nasaka musu albarka inakuma addu'ar
Allah yakawo ranar dazanyi musu wani abun alherin nima.
Jera kayan nayi cikin locker na sannan na haÉ—a 2k É—inda Yaya LamiÉ—o yabani da 2k
É—inda Mummy tabani nasakasu can kasan akwatina daniyar zanna kashe su inyaso insun
ƙare se inkoma karban na hannun *Uncle Adam*
***
Haka nacigaba da rayuwana cikin FGC Azare,masu Sona suna Sona masu kuma tsangwama
ta sunanan sunayi haryanzu suma dankuwa nazo naci albarkacin Yaya LamiÉ—o dan
tundaga ranar dana haÉ—u da Sister Salma duk inda wata senior zata kirani ta aikeni
indai tana gurin tozata saka baki tace su kyaleni ni Kanwar crush É—in tane dayake a
SS3 take wanda hakan yasa wasu daga cikin kawayenta ma suka sanni,ko zasuyi aike
kozasu sa aiki baswa kirana su aikeni wanda hakan yasa nake respecting É—inta sosai
kuma ko'ina naganta zangaisheta,innaje É—akinsu Aziza tadinga jana ajiki kenan.
Ana saura two weeks to midterm break mukayi C.A test É—inmu kuma muna gamawa muka
tafi gida midterm break. Drivern office É—insu Kawu Sani ne yazo ya daukemu dayake
duka samarin gidan are not available,Yaya Fahad yanacan Imo inda yake service
É—insa,Yaya Salim kuma yanacan Zaria a makaranta tuni sukayi resuming ayayinda Yaya
Zunnurain kenan makaranta a Bauchi yana remedial program É—insa shida Yaya Siyama
kuma sunzo gaban yin first semester exams É—insu shine Kawu Sani yace shiya koma
hostel dazama harsai angama exams yadawo gida ayayinda Yaya Siyama kuma ya É—auke
mata duk wasu aiki datakeyi agida,yace baiyarda wani yasata aiki agidanba harsai
tagama jarabawarta. Hakan kuwa akayi dan koda muka isa gida naÉ—an kwana biyu senaga
duk ranar girkin Aunty me aikine take zuwa tayi shara,tayi wanke wanke takumayi
girki sannan tatafi kuma koda muka dawo batabaryin aikin ba duk da su Yaya Safiya
da Sadiya nanan,acewar Aunty babu amfanin ta sallameta tunda ba jimawa zakiyi agida
ba,midterm break kaÉ—ai mukazo ba normal hutuba. Hakan seyamin daÉ—i sosai dankuwa
nima aiki yaragamun sosai ba kamar farkon zuwana gidanba,yanzu inkaga na yini ina
wahala toh ranar girkin Ummi ne kuma bakaramin wahala nikeyi ba duk ranar girkinta
dukda wannan karan su Yaya Zaheera na gida tare da mu anma still baswa tayani aikin
komai,sede bada directives unlike Ummi da daman ita takeyin girkin kawai miko
wannan yanka wancan take sakani.
Daman midterm break É—in kwana goma aka bamu kuma tunda nadawo gida wani barin na
zuciyana kesaka tsanmanin ganin LamiÉ—o agidan Kawu Sani dukda kuwa sanda yacemin
zaizo gida during our midterm break da yazomin visit amatsayin wasa naÉ—au maganar
anma kuma sewani bari na ziciyana kebani zaizo kamar yanda yace zezo É—in tunda shi
mutum ne da inyace zaiyi abu toh seyayishi hakanan yanada cika alƙawari.
Anma segashi haryau satinmu É—aya agida sauranmu kwana uku mukoma bai zoba.
***
LamiÉ—o tunda yadawo daga visiting É—in Rukayya yaci gaba da aikinsa kuma bayida
matsalar kuÉ—i ko kaÉ—an dankuwa ba karamin samu yakeyi a dan aikin dayakeyi every
weekend É—innan ba,bayan biyansu da akeyi na guminsa still ana basu kuÉ—in cin abinci
ahanya na both ranaku biyun dasuke fita wanda shi bama kashewan yakeyiba dayake
seya cika cikin shi a gida kafin yafita wurin aiki. seya cigaba da amfani da kuÉ—in
kamar yanda yakeyi kafin yaje visit É—in Rukayyan kwanaki. Daman duk kuÉ—in dayasamu
every weekend farkon fara aikin nasa rabawa yakeyi kashi uku. Kashi É—aya purposely
for Rukayya yana tarawa,Kashi ɗaya nasa naɗan riƙewa a hannu,se kashi ɗayan kuma
yake using É—insa wurin yi musu cefane agida every weekend. wani sa'in yasayi kayan
miya da nama,wani sa'in kuma yasayi irinsu dankali ko doya yakawo gida dankuwa
sauran kayan abinci duka Umma tana kokarin yi,dafari daya farayi batayi masa magana
ba wai ita duk a tunanin ta na marmari ne amma dataga bayan yadawo daga Bauchin
yazo ya cigaba dayi seta zaunar dashi ta bashi shawarar daya dinga ajiye kuÉ—in yana
saving É—insu inyaso seya tada sana'a daga baya in kuÉ—in sun taru dayawa,indai
yimusu abune karya damu ai akwai gaba yanzukam itada sauran karfinta and she can
take care of her family as a whole anma se Lamiɗo yaƙi amincewa da nata point of
view É—in take,yace "Umma I don't believe on intara kuÉ—i ina ajiyesu sabida inyi
kasuwanci agaba,abunda nasamu yanzu muci shi,yanda Allah yabamu nayau i fulaku
believe zaibamu na gobe insha Allahu,kuma indai Ina raye koda karfin ki ya ƙare
banaso kiyi haufi akan komi nidin zan tsaya makowa a gidannan dayardar Allah.
Albarki da addu'an ki kawai nike nema" Umma setayi murmushi tace "to shikenan
LamiÉ—o. Allah yamaka albarka yashigamaka gaba aduk al'amuranka" yace "Amin Ummana"
seyakuma dubanta yace "Umma sede akwai abunda nake ɓoye miki da haryau bansanar
dakeba and I just hope when you find out bazakiyi fushi daniba, I'm helpless ne
shiyasa,narasa mafita shiyasa nake ɓoye miki" da mamakinsa seyaga Umma tayi
murmushi tace "ina maganar kana zuwa ganin Rukayya ne zancen dakake ɓoye min?"
gyaÉ—a matakai yayi ahankali sannan yace "Anma ya akayi kikasani Umma?" Umma tace
"Tun ranar daka sanar dani mahaifin Rukayya ya rasu nasan it was not the
end,tunranar nasan dole zaka karya alkawarin dakayimin kakoma ganinta watarana even
though you'll be helpless kumani tun alokacin nayafe maka nakuma baka izini
azuciyana. Nasan halinka LamiÉ—o,nasan yanda kake da jaraba akan abunda kakeso
shiyasa nasan konace zanyi fushi dakai ma aikin banzane and I cannot deny the fact
that because of Rukayya you're now a responsible Human being. sabida haka I'll
forever be grateful to her,fatana É—aya Allah yasa yarinya ta garice even though
inada full fate akan bazaka taɓa hulɗa da mutanen dabana kwarai ba"
LamiÉ—o rungume Umman sa yayi cikeda farin ciki sannan yace "Thank you! Thank you so
much Ummana,in Rukayya taji labarin nan ba ƙaramin daɗi zatajiba" seya bata labarin
kason kuÉ—in dayake ajiyema Rukayya,yakuma bata labarin maraicin Rukayya dakuma nuna
masa datayi tanashan wahala agidan Kawunta sannan daga karshe yace "Umma inason
insamu ladan taimakon marainiya shiyasa nakeyi mata waÉ—annan abubuwan,inajin
tausayin Rukayya and I'm afraid if she's no one close to her dazata dinga sharring
damuwarta dasu zata iya haduwa da depression kowani cuta dazaiyi affecting
kwakwalwarta at her very young age,shiyasa I want to always be there for her,inama
ta kallon su Salma ne, she's just like a Sister to me" Umma setasa hannu tashafa
fuskarsa cikeda kaunarsa sannan tace "Toh Allah yabada lada aini naÉ—auka itace zata
zama surukar tawama sabida irin wannan zumuÉ—i danaga kakeyi akanta" wara idanu
LamiÉ—o yayi sannan yakwashe da dariya yace "Habadai Umma! Wannan kwailar mezanyi
da'ita?" Umma wara idanu tayi tana dariyar Itama sannan tace "Allah Koh?
mujedaizuwa" LamiÉ—o yace "niba son Rukayya nakeyiba,inada wanda nikeso kuma very
soon I'll introduce you to her,har gida zankawo miki ita tagaisheki" Umma tace "toh
inanan inajira LamiÉ—o anmadai asamu agama karatun tukunnan kafin afara wannan
maganar,itama Rukayyar abinda yasa kaji na ambaci sunan ta nasan kozaka aureta ba
kwana kusa bane ba tunda she's still studying and kafin tagama nasan zakayi
settling by then sabida haka banason inji zancen wata ready made kwana kusa da kaji
nayi maka maganar suruka" wannan karan dariya LamiÉ—o yakeyi sosai sannan yace "Umma
ai karatunma insha Allah anzo gangara,sauran saurane yarage yanzukan" Umma tace
"adai ƙarasa ɗin asamu aikin tukunnan" seyayi murmurshi yace "Toh Umma anbar
maganar daga yanzu kuma i promise you babu wata ready made É—inda zankawo miki gida
dasunana tagaisheki amatsayin budurwata harsai nagama karatuna nasamu aiki insha
Allah" murmurshi Umma tayi sannan tace "yanzu naji bayani" girgiza kai yayi yana
dariya sannan yacanza babin hiran nasu, yace "toh yanzudai Umma yaushe zamu shirya
kujema Rukayya visit keda Ƴaƴanku? I'm very sure she'll be happy to see you all"
cikin sauri Umma tace "nidai?" marairaice fuska LamiÉ—o yayi sannan yace "Eh ke
Umma! Ko bakyason kisamu ladar faranta ma marainiyane kema?" murmushi Umma tayi
sannan tace "inaso mana amma ai this's not the only way" stubbornly LamiÉ—o yace
"toh nidai Umma wannan É—in mukeso nida Rukayya! Please kiyi fixing time" Umma dan
shiru tayi sannan tace "naji amma dai bayanzu ba gaskiya" LamiÉ—o yasake marairaice
fuska yace "Seyaushe toh Umma?" Umma tace "inlokacin yayi zansanar dakai dakaina"
dukda bahakan LamiÉ—o yasoba anma seyace "toh Umma mungode Allah yakaimu lokacin,
anmadai Æ´aÆ´an ki kam zaki bani aronsu muje tareba next time?" Se Umma tace "inkana
kuÉ—in biya musu kuÉ—in mota Allah ya kiyaye hanya" rungume Umman yayi cikeda farin
ciki yana faÉ—in "Amin Ummana! Thank You" Tura shi tayi daga cikinta tana murmushi
sannan tatashi tashige ciki. dafari bataso bin kudirinsa ba anma kuma setaji
tanason tasan Rukayyar itama and she's not ready to meet her yet shiyasa tayi
deciding taturasu Basman kawai tasan su zasu faÉ—a mata komai inyaso daga baya ita
tajemata intasamu lokaci.
Bayan aikin da LamiÉ—o yayi focusing akai baimanta lissafin kwanakin zagayowar wani
visiting day dinsu Rukayya ba. soyake yaje Bauchi washegarin ranar daya kamata
yazama visiting day É—insu tunda baisan actual date É—inda aka basu midterm break
É—inba shiyasa ma baiyi yunkurin zuwa before wannan date É—inba. Gaba É—aya yamatsu
yaganta,soyake suhadu tabashi labarin yanda ake treating É—inta agidan Kawunta dan
yataimaka mata. Aikuwa ranar Sunday sukaje Bauchin shida abokin aikinsa wanda yayi
daidai da anajibi su Rukayya zasuyi resuming school dankuwa ranar talata ne
dateline É—in komawarsu.
Seda su LamiÉ—o suka gama distributing kayan abincin dasuka kawo sannan yacema
abokin aikin nasa shiyayi gaba kawai yanada uzirin dazaiyi,inya gama kuma zai biyo
motar kasuwa yakoma Gombe anma se abokin aikin nasa yasanar dashi shima akwai
abunda zai tsayayi a Bauchin kuma indai yau zaikoma bakomai yagama abunda zaiyi
saisu koma tare dayanma kawai.
LamiÉ—o yace "toshikenan innagama a Ina zansameka?" abokin aikin nasa yace "Anan
zaka sameni inda mukayi parking motarnan. Zuwa hudun yanma nasan zangama abunda
nakeyi nima Insha Allah" LamiÉ—o yace "toh nima I'll come back by that time insha
Allah" daganan se sukayi sallama kowa yakama gabansa inda suka bar Daf É—in a
garrage É—in abokin abokin aikin nasa ajiya.
Straight unguwarsu Kawu Sani LamiÉ—o yace da mai napep É—in yakaisa kuma koda suka
isa unguwar LamiÉ—on ne yadinga ma mai napep É—in kwatance harsuka isa kofar gidan
Kawu Sani. Bama mai napep É—in KuÉ—insa yayi sannan yajuya yatafi inda shikuma yanufi
gate É—in gidan.
Knocking yashigayi dankuwa yau bai haÉ—u da kowa ba sabanin sauran zuwansa dayake
haÉ—uwa da Zunnurain. Yafi mintuna biyar yana knocking kofar kafin akazo aka buÉ—e
kofar,wani saurayi ne da kallo É—aya yamasa yasan almajirine kuma hannunsa duk a
jike da ruwa gakuma kafafun wandonsa anannade da alamadai wanki yakeyi. LamiÉ—o
mikamasa hannu yayi suka gaisa sannan yace yazo ganin mutanen gidan ne.
Sai almajirin yace "toh bismillah kashigo daga inuwa barina ƙarasa ciki insanar
dasu anyi bakoh" gyadakai LamiÉ—o yayi sannan yace "toh" ayayinda yashigo harabar
gidan,yasamu dakalin É—akin mai gadi yazauna ayayinda yake mamakin miyasa duk
zuwansa bayasamun mai gadin ba kamar can gidan su Kawu Idrissa da koyaushe kaje
zaka samu Mai gadin gidan ba. Abunda LamiÉ—on baisaniba shine Mai gadin gidan Kawu
Sani ba full time Mai gadi baneba,duty É—in overnight kawai yakeyi se in safiya tayi
yayi watering bishiyoyin gidan yatafi gurin iyalinsa,acewar Kawu Sani baiga amfanin
maigadi da ranaba,indan bude gate É—in gidanne Samarin gidan zasu iya..
Almajirin da ya zamanto me wankin duka Ƴaƴan Aunty ayayinda take biyansa every end
of the month ne ya ƙarasa kofar main parlournsu bayan yabaro Lamiɗo zaune can kofar
É—akin mai gadi dake bakin gate. Sallama yashigayi akofar main parlour É—in wanda
dede lokacin ne kuma Rukayya tafito daga parlourn hannunta riƙe da sauran kayan
wankin Safiya data bata tace takai ma Almajirin nasu can bakin tap dake kusa da
dakin mai gadi. Jin Almajirin na sallama sekawai ta ƙaraso kusa dashi tanamai amsa
sallamar nasa kafin tagaida shi sannan tace "ga kayannan inji Yaya Safiya inkawo
maka" karban kayan yayi sannan yace "toh inkinshiga kisanar dasu anyi bakoh yace
mutanen gidan yakenema" Rukayya nashirin tambayarsa Ina bakon kawai sejin muryar
Ummi sukayi abayansu tana faÉ—in "Bakoh daga Ina kuma?" Aicikin sauri Rukayya tajuya
takoma ciki inda tabar Zaheera da Ummi tsaye dukansu cikin shirinsu da alama fita
zasuyi....
Tanajin sanda Almajirin yace "gacan bakon acan bakin gate"
Se Ummi tace "kaje kace masa ya ƙaraso nan" Almajirin seyace "toh" kafin yajuya
yakoma can bakin gate ɗin yasanar da Lamiɗo dakanshi ke sunkuye ƙasa yana addu'ar
Allah yasa abarshi yaga Rukayya inyace shi ÆŠan uwan Mamanta ne.
Sanar dashi sakon Ummin mai gadin yayi sannan LamiÉ—o yatashi yanufesu,tun daga nesa
Zaheera tazuba masa idanu,sanye yake da kananun kaya yau kuma sun bala'in yimasa
kyau sosai and the more he comes closer the more take ganin kamar tasanshi hardai
ya iso inda suke tsaye anma setakasa tuna kuma inda tasanshi É—in.
Littafin Qadr na kudine duk maiso should talk to me via privately for payment
details.
08147722806
*Page Thirty Eight*
Lamiɗo ɗan rusunawa yayi yagaida Ummi daketa karemasa kallo daga ƙasa har sama
tanason taga kotasan fuskarsa. LamiÉ—o Yace "Ina wuni Hajiya" Ummi tace "Lafiya lau.
Ya aka baro mutanen gida?" LamiÉ—o yace "lafiya Lau alhamdulillah" Ummi setace "Toh
ÆŠan samari sede bangane kaba gaskiya kuma saurayincan yace mutanen gidan kazo nema.
Kozan iya sanin daga Ina kazo? Kuma wakake nema?" LamiÉ—o yace "Eh Hajiya" sannan
yatsaya dakyau yace "Daga Gombe nike. Ni ÆŠan uwan Rukayya ne from her maternal
side. I'm here to see her" lokaci guda annurin fuskar Ummi yagushe.
Zaheera kuwa tunda LamiÉ—o yace daga Gombe yake tatuno inda ta sanshi takuma gane
shiÉ—in wanene.
Ummi tsaki ta buga sannan tace "wace Rukayyan kazo nema?" Because she really can't
believe cewa wai wannan Hadadden saurayin zezo musu harcikin gida wai yana neman
Rukayya, Rukayya of all people,ita abunda yasa taÉ—an sake mishi fuska dafari ma
taɗauka sabon kamu wata daga cikin Yaran nasu sukayi tunda dai bata taɓa ganinshi
agidan ba seyau kuma dangin Aunty da customers É—inta dasuke sayan kaya yawanci
tasansu.
Lamiɗo yace "Rukayya Ƴar gidan Kawu Umar" Rai ɓace Ummi tace "sekuma akace maka nan
ɗin gidan zuwa kallon mutane ne anyhow koh?" Lamiɗo sunkuyar dakai yayi ƙasa dukda
yaji zafin maganar Ummin.
Akafule tace "toh bazaka ganta ba,Mai gidan yahana yaran gidan nan ganin gardawa
irinku bare kuma wata Rukayya" LamiÉ—o jiki sanyaye yace "Anma Hajiya I'm like her
Brother. zuwa nayi mugaisa" wannan karan dakuwa Ummi tamishi cikin hargowa sannan
tace "A'a kakanta kake ba Brother ba. Nizaka ma iyayin turanci? Nace nizaka ma
iyayin turanci? Toh bazaka ganta ba and that's final. kabari intaje kauyenku kwaje
kuyita shashancin ku acan anma ba'anan gidan ba. yarinyar tamai da mana gida kamar
na Yan karban sadaka,kowa yazo Rukayya,kowa yazo Rukayya yazo nema" Dan bazata
mantaba su Rukayya na makaranta sau biyu Buba nazuwa yana tambaya kota dawo daga
makaranta. Kawu Idii ma ya taɓa zuwa sau ɗaya kuma duk da ita suke katari.
Taceda LamiÉ—o "kajuya kafita kabar gidannan indai Rukayya kazo gani inkuma bahaka
ba se intaro maka samari suzo su fitarmi dakai dan babu mai barinka kaganta"
girgizakai LamiÉ—o yayi in desbelief, because he just couldn't believe Mata wayayya
a ido kamar Unmi could do something like this. Meyakawo wannan masifar haka? Daga
cewa yanason ganin Rukayya?.
Tabbas kalamanta dakuma yanda take behaving ya matukar bata mashi rai,so yake
yamaida mata martani,soyake yamaida mata magana anma kuma sanin darajar nagaba
dashi dakuma albarkacin Rukayya yahanashi yin hakan. He really want to reply each
an every word datayi uttering anma baisan maihakan zaijama Rukayya ba bayan
yatafi. Yana nemanta ma kaÉ—ai yazama abun masifa barekuma yace zaiyi ma matar
raini akan Rukayya?shibawai tsoron matar yakeyi ba kuma ai duk tsohon dabaiji
kunyar hawa jakiba jakin bazaiji kunyar tiko dashi ƙasa ba.
Damuwarsa halin da Rukayyan zata shiga inyace zai yi taking action dan Allah ne
kaÉ—ai yasan abunda zasu iya yi mata. Danhaka sekawai yajuya yanufi gate É—in gidan
ayayinda ranshi keyi mishi kuna sosai. He's just imagining what Rukayya must be
going through acikin gidannan.
He wish zai ganta yanzu,he wish yasan specifically inda take acikin gidan da babu
abunda zai hanashi dawowa ganinta bayan mutanen nan suntafi anma tunda baisani ba
seya hakura akan zeje yaganta a makaranta kawai kamar yanda sukayi da'ita last time
dasuka haÉ—u during their visiting day. Yanajin Ummi nata babatu da masifarta anma
ko juyawa baiyiba bare yayi acting as if yamasan me takeyi ahaka harya fice agidan.
Zaheera naganin yafita tajuya takalli Ummi sannan tace "Ummi shine yaron da muke
baki labari nida Aisha ranan. Shine yaje ganin Rukayyan a makaranta" baki sake Ummi
tace "ikon Allah! Amma ta Ina suka haÉ—a dangi da Mahaifiyar Rukayya? Nifa danginta
danasani tunsanda muke zama gida É—aya Yan Babban buli ne kawai" Zaheera ta tabe
baki tace "toh dai cousin É—intane,itada bakinta tafaÉ—a Kuma gashi yanzuma kinji
yafaÉ—a da bakinsa" Ummi tace "toh jarabar ta menene dazai biyota har gida?" Zaheera
tace "Nima bansani ba Unmi, amakarantar ma bakiga yanda yadinga rungumeta
baneba,kamar wanda suke soyayya fah" Ummi rai ɓace tace "Soyayya kuma? Rukayyan
harnawa take dazata san wani Abu waishi soyayya Zaheera? sede in kice akwai shakuwa
sosai atsakaninsu" tura baki Zaheera tayi sannan tace "Ummmm Ummi toh ba daga
shakuwar ake komawa soyayyan ba? Yanzu bakya tunanin zai iya Sonta agaba tunda haka
kawai ma yana biyota harnan gida musamman dan yaganta" tsaki Ummi tayi sannan
tafara tafiya tace "ke dallah mutafi ni Ina ɓata lokaci akan abunda bashi baneba.
Ni abu É—aya nasani ko uwarme ke tsakanin su da Rukayya nan bada jimawa ba zai
hakura ya rabu da ita barehar yayi wani zancen yana sonta. Yarinyar da take zaune
agidannan kamar Ƴar aiki,sutura maikyau ma nangaba gagararta zaiyi bare azo ga
batun tayi kwalliya tayi fasalin dahar wani zaiganta yace yanaso. Inma zaki kwantar
da hankalin ki kikwantar da hankalin ki dan baki kaini son ganinta cikin kunci ba"
Zaheera ba ƙaramin Jin daɗin kalaman Ummi tayiba dantasan tundahar ta furta hakan
she'll make sure it happens and besides yanzu hakan ma ai kamar Ƴar aikin take a
gidan nasu tunda kozaman cikin parlour ma ba'a barinta tayi bare Kuma azo ga batun
ta shiga cikinsu Yaran gidan. And this happens only because of Ummi dan inta
ɓangaren Aunty ne itaba ruwanta. Seta tuno ranar da taga Rukayya da Lamiɗo a school
garden ɗinsu,ranar ba ƙaramin tashi hankalinta tashiga ba,the thought of him
rescuing Rukayya in the future tasamu rayuwa mai inganci just bothered her so much.
Because inhakan yafaru akwai probability din tafisu Jin dadi a rayuwa and may
be,and may be she'll try to take vengeance on abubuwan dasukeyi mata yanzu shiyasa
gwanda tunwuri tazama extra careful.
Æangaren Rukayya kuwa batasan ma LamiÉ—on yazo gidanba kuma a labari batajiba.
***
Ranar Monday Aunty taje tayi mana shopping baki É—ayanmu a Kasuwa kuma koda aka dawo
ita dakanta ta rarraba mana provision É—inmu tabama kowa nashi yasaka cikin
akwatinsa anma sede wannan karan ma fah su Mariya seda suka zo suka É—auki abunda
ransu yakeso acikin akwatina dazasu tafi islamiya ranar da yanma.
Washegari Tuesday Drivern Kawu Sani yamaida mu makaranta bayan munyi sallama da
kowa dankuwa har lokacin Yaya Zunnurain basu gama jarabawar su ba kuma Yaya Fahad
da yaya Salim ma basuzo gida hutuba. ana cikin yimana checking Yayan Aziza Sajeed
ya kawota. Zokuga murna gurina da Aziza,rungume juna mukayi a visiting ground É—in
kowa na tambayar É—an uwansa mutanen gidansu. Nikam senaga Aziza tayi kiba,tayi wani
fresh abunta unlike ni da nayi baƙi na rame acikin kwanaki goman mukayo agida.
Sautari nakanji classmates dina da sauran ÆŠaliban makarantarmu suna wakar habaici
na COLEJI TAFI GIDA DADI: Semu Ƴan collegi tafi gida daɗiii! Agida duka,agida zagi,
agida ga wanke wanke ga sharan ɗaki. Semu Ƴan colleji tafi gidaa daɗi!" For sure
nasan wakar opposite É—inta ake nufi,ma'ana gida tafi colleji daÉ—i kawai dai
anarairai wakarne cikin sigar habaici but in my own case it feel as if danni akayi
wakar tunda ni agurina rayuwar makarantar tafi man na gida daÉ—i. Nuna riga da
nasan dawowarmun nan ma definitely za'ayi gulman naje gida na rame banyi kiba
ba,toh amma yazanyi? Inada bakin hanasu yin maganar ne? And besides suya dama,gani
nake rashin abunyi ne zesa ka tsallake naka damuwar kakoma kan na wani.
Haka aka gama yimana checking muka nemo me wheelbarrow yazo yadibi kayanmu muka
tafi hostel nida Aziza ayayinda take yimani hiran abubuwan datayi a hutu dakuma
guraren da takai ziyara.
Tun kafin mubaro checking ground nalura da yanda su Yaya Safiya dasu Yaya Zaheera
keta hararana ganin innata walwala abuna da Aziza anma senayi kamarma bangansu ba,i
acts as if banmasan sunayiba dukda kuwa araina ina addu'ar Allah yasa kada tsanan
da sukeyi min yashafi Aziza.
Muna shigowa haraba hostels É—inmu muka rabu kowa yayi nasa hanyar don zuwa ya
kimtsa bed É—insa yakuma gyara locker É—insa.
Da dare bayan sallahn isha'i inazaune cikin corner mu ayayinda nake haÉ—a books É—ina
cikin class bag dina kasancewar washegari Wednesday ne kuma akwai class sega Aziza
tashigo hannunta riƙe da foodflask ɗin abinci sekuma wata bakar leda madaidaiciya.
Ni kadaine daman a cornern,Sadiya tunda tazo ta ajiye kayanta tafita bata sake
dawowa ba.
Atsakiyar cornern namu Aziza ta ajiye foodflask É—inda ke hannunta bayan tashiga
cornern sannan tasamu gefena dake zaune nake abakin gado tazauna Itama. Da kallon
mamaki nabi foodflask É—inda tashigo dashi sannan nace "Aziza abinci kika shigo
dashi hostel wai?" Murmushi Aziza tayi sannan tace "Eh mana. bakiga sanda Yaya
Sajeed yabama mai wheelbarrown daya kawo mana kaya hostel aboye baneba?"
Girgizamata kaina nayi sannan nace "nagadai yana bashi leda da kuÉ—i anma bansan
menene acikin ledan ba" Aziza tace "Toh ai foodflask É—in abincin ne acikin ledan"
cikeda mamaki nace "Amma kinyi sa'a" dankuwa banmanta yanda akayi siezing na mutane
da dama agaban mu ba É—azu,kuma ciki harda nasu Yaya Zaheera da Sadiya ce tayi
sakaci aka kamasu. Yaya Safiya ne tabata jakan coolern abinci tace taje ta boye
musu abayan flowers sanda ake musu checking amma se tadinga yin abu kamar marar
gaskiya har aka kamasu shiyasa koda Azizan tace min tasamu tashigo da abinci abun
yabani mamaki.
ÆŠayan ledan data shigo dashi a hannunta apart from foodflask É—in abincine tamiko
min tana faÉ—in "Gashi Mommy tace inkawo miki" kallon ledan nayi sannan na karba
nace "Allah sarki nagode. Allah yasaka mata da alkhairi ayayinda nashiga buÉ—e leda.
Turarene hadadde se shampoo,conditioner,da hair cream duk na campanyn *Olive oil*
sekuma wani gari acikin karamin farin leda akulle.
Juya ledan nashiga yi ina mamakin menene aciki senaji Aziza tace "Maganin fitsarin
kwancen danace zan tambayar miki Mommyi ne" cikeda mamakin Aziza nace "Wai daman
dakikace zaki karbamin maganin fitsarin kwancen dagaske kikeyi Aziza?" Hararana
Aziza tayi sannan tace "akan mi zanmiki wasa. Inaso kidaina ne because I hate the
fact that mate É—inmu na mocking É—inki akan wannan abun" sekawai nayi murmushi nace
"toh thanks Aziza. Allah yasaka da alkhairi kuma don Allah ranar Monday zaki rakani
wurin Sir Buharinku in ƙira Mommy inyi mata godiya" murmushi Aziza tayi sannan tace
"Allah yakaimu" inda atake kuma tafaÉ—a min yanda za'ayi amfani da maganin fitsarin
kwancen daganan kuma semuka sauka daga kan gadon mukaci abincin data kawo mana daga
gida. Pounded Yam ne da Miyar egusin dayaji nama,su pomo,bandan kifi,stuckfish zako
zako tako'ina. Ranar naji daÉ—in sakwaran nan sosai dankuwa najima banci abincin
dayamin daÉ—i irin wannan ba.
Seda aka kusa lightout sannan naraka Aziza tatafi Hostel É—insu kafin nadawo nayi
kwanciyana. Naso bama Sadiya maganin awannan daren dan Aziza ta cemin kafin akwanta
ake jikawa da madara asha anma banason accidentally wani yaji muna maganar haryakai
ga asirin Sadiyan yatonu danhaka Sena bari akan washegari zanyi Mata maganar a aji
innasamu chance.
Washegari kuwa bayan antashi daga class da ikon Allah se Sadiya bata fita a aji
dawuriba. Kowa yafita yabarmu dagani se ita,ni inajiran Aziza tayo alwala abakin
tap É—in dakecan ss3 block semutafi masallaci danni nayi already nayi nawa tun
ɗazu,ita lokacin tana ƙarasa copying note ɗinta ne shiyasa batayi ba ayayinda
Sadiya kuma kejiran kawayenta sudawo daga tuckshop,wai sunje sayan bread zasuci da
kwababben Milo a hostel.
Daman nafito da maganin acikin jakana don haka inaganin sunfita sena É—auki maganin
nanufi inda kujerarta yake ayanzu. Zama nayi akan kujerar dake gefenta sannan na
miƙa mata maganin nace "Sadiya ga maganin fitsarin kwance nan Mommyn Aziza
tasamonin thinking that ni nakeyi,kikarba kisha may be yataimaka miki kidainayi dan
sistern ta ma shi aka bata tasha kuma tun daga ranar datasha maganin bata sakeyi
ba" memakon Sadiya ta karbi magani as expected senaga ta gallah min harara,tace
"mekike nufi? Cemiki nayi Ina fitsarin kwance dazan karbi maganinki komi?" baki
sake natsaya ina kallonta cikeda mamaki,rainamin wayon datake ƙoƙarin yine
yakuremin tunani tunda nida ita already musan meyake faruwa kuma munsan gaskiya.
Sena daure na ɓoye mamakina nace "look Sadiya, I'm here to help you,ke kinsan
kinayi kuma nima nasan kinayi so miye abun ɓoye ɓoye?Don Allah kikarbi maganin ki
gwada kozaiyi miki amfani dannidai kinga kona ajiye babu amfanin dazaiyimin" tsaki
Sadiya tasaki sannan tatashi tsaye tashiga nunani da É—an yatsa tace "in haukake
damunki gwanda kidawo cikin saitin ki. Ni babu fitsarin kwancen danakeyi inkuma
maganin infara yi kika nemo ki lanjanamin sabida muzama É—aya nidake adinga gulmar
mu acikin makaranta toh seki sani dole insha maganin" daganan tafice a class É—in
fuuuuu kamar zata tashi sama.
Nidai mamaki kamar inyi Yaya,dakyar natashi daga inda nake zaune najuya daniyar
inkoma seat É—ina and there I saw Aziza standing at the door ranta amatukar bace,by
just looking at her nasan taji komai and I now got the reason why Sadiya tadinga
pretending cewa sharri nakeyi Mata itabata fitsarin kwance.
Nufan Aziza nayi daniyar inyi mata magana kawai senaga tajuya tabar class É—in Itama
rai bace,Binta nayi dasauri Ina kwala kiran sunanta anma kota juyo ta kallene.
Daƙyar nayi gudu na kamota Ina nishi nace "Aziza kitsaya ki saurareni please" fizge
hannunta tayi tanamai cigaba da tafiya tare da fadin "mezaki faÉ—amin kuma? Mezan
tsaya in saurara bayan wanda naji yanzu Rukayya?" marairaice fuska nayi sannan
nasake riko hannunta nace "ai Allah nace miki. Kitsaya ki saurareni please!" Sake
tureni Aziza tayi tareda faÉ—in "kibarni babu abunda zan tsaya in saurara fahh kuma
wallahi yausai kowa yasan gaskiya. Inke bazaki iya fighting for your right ba ni
bazan iya zuba idanu inyi shiru ba" Jin tace zata faÉ—a ma kowa abunda yake faruwa
se hankalina yakara tashi. What if Sadiya is humiliated because of me? What if
she's tortured? For sure nasan I'll get justice here anma agida fah? Wazai cece ni
idan suna muzgunamin suda iyayen su?.
Danhaka senayi sauri nasha gaban Aziza nayi folding hannuna cikin sigar roko nace
"Kewai bakijin don Allah ne. Dan Allah kitsaya muyi magana" tsayawa Aziza tayi tana
fumming
tareda riƙe kugu sannan tace "Kona tsaya naji abunda zaki faɗama ba canzamin ra'ayi
zakiyiba ah toh gwanda makiji kisani"
Littafin Qadr na kuÉ—i ne. Duk maiso should talk to on whatsapp for payment details.
08147722806
*Page Thirty Nine*
*Avoid typing errors please*
"Cikeda damuwa nacema Aziza toh wai wazaki faÉ—ama wannan maganar? Kuma inkin faÉ—a
É—in wani riba zakici?" Wani kallo Aziza tayimin sannan tace "babu ruwanki dawanda
zan faÉ—a ma maganar riba kuma Inna fada É—in zakiga riban dazanci" seta fara cigaba
da tafiya wanda hakan ya matukar sake tadamin hankali,da sauri nasake shan gabanta
atsorace nace "Aziza you don't have to tell anyone please! Don Allah kada kifaÉ—a ma
kowa. Ni kaÉ—ai nasan what I'll go through idan kika faÉ—a É—in" cikeda mamakina Aziza
ta tsaya tana kallona dan ita aganinta taimakona zatayi by exposing Sadiya Amma
maganar danayi yanzu just confused her.
With questioning look tace "kamar ya bansan abunda zanja mikiba?" wannan karan
hawaye nafara yi,cikin sautin kuka nace "you might think you're helping me inkika
faÉ—ama wata prefect ko displine master anma kuma the truth is that bataimakona
zakiyiba Aziza,jefani awani matsalar zakiyi" Aziza tace "wace irin matsala Rukayya?
Inbaki min bayaniba yazanyi ingane?" ganin tadage seta fada É—in yasani spilling
abunda ke zuciyana.
Nace "idan kika faÉ—a anan makaranta akayi purnishing Sadiya agida she'll get back
at me itada Iyayenta" nasauke numfashi sannan nace "tsoronsu nike Aziza,banyi
laifin komai bama wahala nikesha awannan gidan balle kuma akwai dalili" senayi
folding hannuna guri É—aya guda cikin sigar roko nace "don Allah kada kifaÉ—a,kibar
maganar nan aranki and besides inna bama Sadiya maganinnan zata dena fitsarin
kwance" wanin irin kallo Aziza tayimin sannan tace "Anma dai aikina gani taki
karban maganin koh? Kuma sauran bullying É—inki da akeyi da mocking É—inki da akeyi
akan dalilin fitsarin kwancen nakifah? Kinsandai Kokin daina bakowane zaisani ba
and it will not change anything" still Ina hawaye nace "kekam karki damu,nayi
bearing dinshi abayama bare yanzu? Maganar mutane baya gabana Aziza,they should
think whatever they want to think banida damuwa da wannan. nidai don Allah kibar
maganar nan kawai" nayi maganar cikin rokon dayake nuna I'm desperate tace tafasa
faÉ—a É—in..
Kallona tayi cikeda tausayawa sannan tace "toh wai wani irin wahala kikesha awannan
gidan dahar zaisa kizabi bearing morkery É—in mutanen makaranta akan wahalar wancan
gidan" sa hannu nayi na share hawayena sannan nace "it's a long story kuma
kokinjima bawani abun zai canza ba, it'll only make you pity me more nikuma banason
relationship ɗina dake yacigaba da tafiya base on tausayi" ɓata rai Aziza tayi
sannan tace "Ina tausayinki Rukayya anma kuma bahakan ne yasani kawance dakeba,
kituna tunkafin nasan dawannan halin da kike ciki muke tare" jinjina matakai nayi
cikeda gamsuwa.
Seta kama hannuna,muka karada kusa dawani bench dake karkashin wata bishiyar
darbejiyan dake cikin harabar makarantar namu. babu kowa agurin dayake duk anbar
classes area harma anshiga dinning dan tuni aka idar da sallahn azahar a masallaci.
Zama mukayi akan bench É—in sannan Aziza tace "toh inda kinyarda I did not befriend
you out of pity then ki faÉ—amin mekike going through awannan gidan" dagowa nayi Ina
kallonta sannan nace "Zan faÉ—amin anma sekinmin alkawarin bazaki faÉ—ama kowaba"
Aziza tace "Nayi Amma se in reasons É—inki are valid" sa bayan hannuna nayi nashare
hawayena sannan nashiga bata labarin rayuwata tun bayan rasuwan Baba harzuwa yanzu
agidan Kawu Sani and I was not surprised to see Aziza shading tears for me.
Cikin kuka tace "ikon Allah wannan wasu irin mugayene? sekace baku haÉ—a dangantaka
ba?" murmushin dayafi kuka ciwo nayi dankuwa tuni nabar kukan danakeyi.
Se Aziza tace "Ammadai kema kuma kina da naki laifin Rukayya. Innine ke dana faÉ—a
ma Kawu Sani tuntuni dazai taimaka miki kuma zaisaka idanu sosai akan al'amarin
gidan amma shirun dakikeyi bakowa kike cutaba sekanki" murmushi nakumayi senace
"Inna faÉ—a mishidin ya hukuntasu aiba zama zaicigaba dayiba 24/7 agida ba Aziza. in
bayanan nasan mezasuyimin ne? Kawu Sanin da he barely spend two good weeks agida
batareda yatafi wani gari meeting ko conference ba? Kinsan masu aikin bank most
especially managers da CEOs basu cika zamaba" jinjinamin kai tayi sannan tace "but
still nidai aganina dazasu ragamiki" nace "karki damu Aziza, I'll keep enduring
everything. aidaman rayuwarnan is not a bed of roses kuma I've full fate Allah yana
tareda ni tunda bai taɓa barina ba koda na rana ɗayane ba. Insun kwace provision
kosun maida shi kaÉ—an I always have it from you,gakuma abincin makaranta ma ya
isheni rayuwa and about visiting days I've Yaya LamiÉ—o, he'll always be here to
make my visiting days wonderful insuka ɓata min" nace "agida kuma indan kwana a
kitchen ne karki damu Aziza,tun inajin tsoro ina kasa baccima harna saba,batun
abinci kuma koda suke hanani aibaswa iya cinye abincin da ikon Allah. Kullum
jazaman ne sesun rage and I always eat the remaining. Insu Yaya Fahad nanan Kuma
sauran nasuma nikece mezafi. Batun aikin da nakeyi kuma inada yakinin wataran nizai
taimaka sunedai basu gane hakan ba" cikeda gamsuwa Aziza tajinjinamin Kai sannan
tajani zuwa jikinta tarungume.
Ahankali nace "please karki faÉ—ama kowa maganar fitsarin kwancennan. Inna koma
hostel I'll convince her and give her the medicine" Aziza batacemin komaiba amma
from her reaction nasan bazata fada dinba.
Ranar dai atakaice bamu samu munci lunch a dinning ba dan sanda muka Isa masallaci
zamuyi sallah har angama shiga dinning hall tuntuni. Da muka idar da Sallah muka
fito daga masallaci kuma lokacin ne ake fitowa daga dinning ana tafiya hostel. Mu
É—inma hostel É—in muka tafi,dana Isa É—akinmu Golden morn najika nasha sannan nafara
shirin tafiya evening prep dukda kuwa ranar club activities ne bawani jimawa akeyi
a prep É—in bama,wasu ma da bwasa kowani club basu cika ma fita prep É—inba anma ni
I'm engaged in two clubs shiyasa every Wednesday bana missing fita Evening prep.
Ina cikin *Press club* da *ICPC club*.
Aziza ne tayi encouraging É—ina mushiga press club sabida muyi improving speaking
É—inmu dakuma dan insamu courage É—in magana a public dayake tasan ni da rashin son
magana acikin mutane. Press club sukanyi debate competition,presenting news agaban
assembly every Monday dadai sauransu and if you're a member dolene wataran kaima
kayi participating.
Dadare bayan kowa yakwanta bacci a É—akinmu nasakeyi yima Sadiya maganar maganin da
Mommyn Aziza takawo anma sam taki bani haÉ—in kai dole daga karshe nakyaleta na
ajiye maganin cikin akwatina anma kuma seban sanar da Aziza yanda mukayi da Sadiyan
ba dan banason hakan yakuma tunzurata. Koda tatambayeni kona bama Sadiya cemata
nayi "Eh nabata"
The following Monday we were neatly dressed in our school Uniforms dayake kowa
kayanshi yasha gugan gida ba'ajima da dawowa ba and mostly daman Mondays dressing
É—inda student keyi na daban ne because it's the first day of every week and a new
beginning to the week.
Tsaye muke a assembly ground É—in makarantar mu ayayinda kowa ke tsaye a layin yan
ajinsu.
National anthem aka farayi da school anthem sannan principal yayi magana akan
abubuwan da ba'a rasaba dayashafi activities na makarantar namu inda daga karshe
kuma aka kira Vice principal academy yazo yakira best three nakowani aji da last
three ɗinsu. daman tunda muka dawo ake rumours ɗin za'a ƙira best threes ranar
Monday and here we're za'a kiradin. ni kwata kwata bansaka abun araina
sosaiba,nidai kawai ina tsayene inajin bayanan Vice principal Academy kafin yafara
ƙira daga kan ss3 student's.
Dukwanda aka ƙira tafi ɗaliban sukeyi masa ana ihu ayayinda zeje ko zataje tahau
stairs takarbi gift É—inta har aka iso kan yan set É—inmu. Daga js1 A akafara sannan
aka iso kan ajinmu,js1B kenan. Aziza aka ƙira as first position,wani irin ihun
murna nasaki ayayinda na rungumeta dayake a row É—aya muke da ita kuma itake gabana.
Sakinta nayi tatafi stage don karban gift É—inta a hannun principal É—inmu da vice
principal academy.
Banyi mamaki ba da Aziza tazo first position tunda koda da muke primary school
wannan position ɗin natane koda yaushe, Ƴan ajinmu ma sunriga dasun sani. Koyaushe
akazo ƙiran best threes a prize and giving day tokowa yasan itane first, I'm just
happy that she's tried to maintain her position anan makarantar ma kuma babu wanda
yabugeta a ajinmu. Ina cikin wannan tunani senaji wata *Sabira* abayana tana taɓa
ni. Juyawa nayi dan inji dalilin ƙiran nawa datayi setace "bakece Rukayya Umar
Yarima ba?"Ina ƙoƙarin bata amsa senaji Vice principal academy nakiran sunana daga
kan stage,kallon shi nayi da mamaki inda alokacinne kuma Aziza tadawo row
É—inmu,fuskarta cikeda excitement ta rungumeni tana faÉ—in "kije kece 2nd position
Rukayya" baki sake natsaya ina kallonta because I'm totally shocked by her words.
Ƙiran sunana da aka kumayi daga kan stage ɗinne yasani saurin fita daga crowd ɗin
students É—in sannan nanufi stage É—in anamin tafi inajin abun kamar a mafarki.
Kallona principal É—in yashigayi sanda nahau kan stage É—in da mamaki yace "Rukayya
right?" gyaÉ—a masakai na nayi ahankali.
Yace "were you not the one that came for your comman entrance after the school has
fully resumed?" gyaÉ—a masakai nakumayi ahankali.
Seya yayi murmushi sannan yamikamin hannu alamar inyi handshake dashi ayayinda yake
faÉ—in "I'm very proud of you Rukayya. You really tried, congratulations"
Murmushi nasaki nervously sannan nace "Thank you Sir" shaking hannuna yayi sannan
É—aya daga cikin staffs É—indake miko gift É—inma principal yamikomishi shikuma yabani
ayayinda akayi mana hoto.
Haka nasauko daga kan stage É—in hannuna rungume da gift É—ina da akayi wrapping
using wrapping sheet gwanin ban sha'awa. Kwata kwata ban taɓa sama raina zansamu
wannan position É—inba,nasameshi ne out of blue and it makes me very proud of my
self. I was reading only to pass kamar yanda nikeyi back then a primary school ashe
bansan har hakan zaikaini da samun wannan achievement É—inba. Kuma koba a faÉ—amin ba
nasan zama da Aziza na É—aya daga cikin abubuwa dayasani reaching wannan step É—in
and at that moment senaji inason insakeyin gaba,senaji inason incigaba da retaining
wannan position É—in.
Haka nakoma row ɗin Ƴan ajinmu, Aziza tayimin congrats nima nayi mata. Inagani Ƴan
ajinmu natayi mana wani irin kallo most especially ni anma dukanmmu babu wanda
yadamu infact we were busy jubilating atsakanin mu. Wasu daga cikinsu sunyimana
congrats tun a assembly ground É—inma ayayinda wasu seda akaje aji.
Wasu kuwa ko uffan basuceba,wasu kuma har habaici sukeyi kan anyi cucel ko anyi
mistake ne,tayaya wawiya kamarni dako magana ma banayi a aji zanzo 2nd position.
Araina nace "watoma nisuka sama idanu? Nice marainiyar wayonsu kenan" but bance
komai ba,I act as if banmasan sunayiba. Sadiya kuwa daga kallon datakeyimin kaÉ—ai
nasan jitake kamarta kasheni kota huta.
Nida Aziza dukanmu babu wanda yabuÉ—e gift É—insa,acewarmu semunje gida munnuna
sannan zamu bude. Itazata nunama duka Ƴan gidansu ayayinda ni nakeda kudurin nunama
Kawu Sani,yes dole innuna masa tunda shike biyan kuÉ—in makaranta and he's the one
that always wants the best for me. LamiÉ—o ma yana cikin waÉ—anda zannuna ma gift
dinnawa anma shi bazai buÉ—eba,Kawu Sani will be the first to open it inyaso inzanje
Babban Buli se intafi dashi in LamiÉ—o yasamu yazo innuna masa.
Haka rayuwa tacigaba a makaranta,Adan ƙoƙarin danayin nan yasa nayi sabbin kawaye
danwasu haka kawai ma insuka ganni zasuyimin magana mugaisa,akwai waÉ—anda kuma
sunsauke Ego É—insu inbasu gane abu a ajiba sukanzo su tambayemu nida Aziza komun
iya mukoya musu. Exams nata approaching wanda sati biyu zamuyi munayin shi inda
daganan kuma zamuyi one week zaman jiran result. Wannan satinne ake kirada *Week of
Grace* mostly social activities akeyi during that period of time. Dukdama ban taɓa
experiencing abunba awannan lokacin anmadai haka nadinga ji seniors dinmu na faÉ—i.
Akuma Saturday É—inda za'a shiga satinne za'ayi last visiting day na wannan term É—in
baki É—aya.
Shiri sosai mukema upcoming exams É—inmu nida Aziza bana wasaba dankuwa munyi
dedicating almost all of our time a karatu. In bamwa library toh zaka samemu a
classes area and mind you hakan baya hanamu hutawa,komai damukeyi akwai lokacin sa
and we always use our time wisely. Lokacin hutawa da bacci zamuyi sannan lokacin
karantun ma yinshi muke haikan mani'an. mu munata shiri bamusan abunda su Sadiya
suke shirin yiba,Ashe su Yaya Zaheera sunsata tayi trapping dina ace Ina
examination malpractice batareda kowa yagane ba.
Idean na su Yaya Zaheera ne anma Sadiya da kawayenta were the ones that decides on
how to execute the plan. Nidaman mutum ce meson dictating abubuwan dana karanta a
kwakwalwana a paper,komi nakaranta nagama memorizing É—insu a brain É—ina I'll write
it down on a sheet of paper dankuwa dajimawa Baba yabani wannan tactics É—in. Yace
innayi karatu nagama I should close the book and write what I read offhead ananne
zangane karatun nawa yazauna dakyau kobai zauna dakyau ba. Innaga nakasa I should
keep trying,trying and trying harsaisa iya na rubuta É—in correctly and for sure
indai nayi achieving wannan toh a exams É—inma babu abunda zaihanani rubutawa insha
Allah.
Dawannan tactics É—in su Sadiya suka cuceni. First day dazamu fara exams É—inmu Basic
science zamu rubuta kuma papern safene shiyasa bamu Jima da baro assembly ground ba
invigilator É—inmu tazo. Dakanta tayi arranging É—inmu tasa muka barbar distance
atsakanin seats É—inmu. nikam daman back bencher ce kuma banida seatmate daman don
haka banma matsa daga inda nake zauneba.
Raba mana Question papers É—inmu da booklet É—inda zamu amsa aciki tayi sannan tace
mufara exams É—in. Questions É—in nafara karantawa duka kuma babu wanda bazan iya
amsawa acikiba dayardar Allah amma dayake anbada instruction É—in a amsa three
questions kawai yasa nayi deciding amsa first three questions É—in kawai. Na buÉ—e
booklet É—ina zanfara rubutu kenan naji anjefo min dunkulallen paper kan desk
dina,abun ba ƙaramin mamaki yabani ba,daga paper nayi Ina kare mata kallo dan insan
na menene sekawai naji Sadiya na calling attention É—in invigilator É—inmu. Tace mata
"Excuse me Ma'am, someone is doing examination malpractice over there" Sadiya tayi
maganar tana nuna bangarena and all attention were on me.
Jinayi kamar infasa ihu tsabar babu yanda zanyi in fidda kaina tunda ga paper a
hannuna. sekawai nafara hawaye.
Teachern nazuwa gabana takwace papern ahannuna ta buÉ—e shi tana karantawa,seta rufe
booklet ɗina taga handwriting ɗin iri ɗayane agun dana rubuta sunana. Rai ɓace tace
"Stand up!" tashi nayi Ina hawaye sannan nace "Ma'am believe me someone throw it on
my desk. I was not trying to steal answers" waremin idanu teachern tayi tana faÉ—in
"will you keep quiet,this's your handwriting and no one else's,so you better stop
denying if not I'll send you out of this class right now. And this clearly means
you'll not write the exams anymore" sekawai nafashe matada kuka Ina "I'm sorry
Ma'am. Sorry please" dukwanda yaganni awannan lokacin seyaji tausayina.
Rai ɓace tace "so just because you're a back bencher you decide not to read for
your exams right?" Jijjigamata kai nayi alamar a'a inamai cigaba da kukana. Tana
hararana tace "follow me jarray!! I'll see how you'll steal if I make you sit at
the front seat" nidai bance komaiba inbanda kuka danakeyi har muka isa front
seat,tatada wata *Zainab* Ƴar ajinmu tace takoma can seat ɗina dakecan baya inda
tace ni inzauna agurin. dayake daman ban rubuta komaiba sebata canza min booklet
ba,takuma tsaya akaina ta kuramin idanu nida booklet É—ina ayayinda taketa zagina da
korafin karama dani,Ina js1 amma harnasan miye satan amsa. Maganarta sunmin ciwo
and it makes me feel so embarrassed,nafi mintuna goma Ina kuka batareda nasan
abunyiba. Gashidai nasan I'm innocent but I've no way to prove myself innocent din.
Jin faÉ—an nata karuwa yakeyi sabida rashin rubutun da banayi tunda tacanza min seat
É—in yasani sa hannuna nashare hawayena.
Senaga innacigaba da kukan ma cutan kaina zanyi,Inna cigaba da zama without writing
anything nema zaisa accusations É—inda suke kaina suzama gaskiya dukda kuwa ba
gaskiyan baneba. Calming kaina nayi first sannan naÉ—auki pen ahankali nafara
answering first questions É—inda ke jikin question paper É—in and this make the
invigilator mute,setayi shiru tana kallon abunda nake rubutawa ayayinda nikuma naki
É—agowa in kalleta,haka nacigaba da rubutun harsaida nasauke aya sannan nakoma first
Page nayi crosschecking sannan natashi nayi submitting nafice a class É—in.
Harna fita a ajin I can feel her intense gaze,nasan nabata mamaki ba kaÉ—an ba.
agaban ajinmu nazauna nadinga shan kukana har Aziza tafito a class É—in tasamo ni
agurin. Lallashina tashigayi tana faÉ—in "kidaina tada hankalinki please" cikin
gunjin kuka na É—ago inaganin Aziza sannan nace "Aziza wallahi bnyi satar amsaba,out
of nowhere naga anjefomin papern akan desk É—ina" Aziza cikeda tausayina tace
"Nasani karki damu nakumasan aikin wanene yin hakan sabida haka kibar tada
hankalinki" inamai cigaba da kuka nace "toh wai menayima Sadiya dahar zata bata min
image É—ina a makarantar har haka? Abubuwan datake yimin Ina shanyewa duk basu
ishetaba?" Aziza tace "bata kyautaba and I feel like beating her black and blue
anma sede nasan komunyi hakan we'll only put ourselves into trouble. Shawara É—aya
zanbaki Rukayya. karki bari abunda Sadiya tayi yau yayi affecting É—inki in anyway
or the other kicigaba da karatunki kuma kirubuta exams É—inki without any fear Insha
Allah the truth Shall prevail soon" gyaÉ—a ma Aziza kai nayi. hakan tacigaba da bani
shawarwari kafin muka tashi muka tafi library don yin karatu. Dukyanda naso nayi
karatun kasawa nayi dan tunanin abunda yafaru yauÉ—in yagama dabaibaye zuciyana
ahaka har bacci yaÉ—aukeni agurin.
Seda lokacin azahar yayi sannan Aziza tatasheni muka tafi,Koda nakoma hostel ciwon
kaine yadameni danhaka banfita karatun yamma ba.
Inaji Yar ajinmu dake ɗakin mu na ma Ƴan cornern su gulmar ankamani Ina satar amsa
kuma Malama tasani na rubuta jarabawa a seat É—in gaba ayayinda take tsaye kaina
harnayi submitting. Inaji É—aya daga cikin corner mate É—in nata takwashe dadariya
tana faÉ—in "kice bana a last three mutumiyar zata fito kenan, nidaman nasan wannan
yarinyar dake abu kamar wata solobiyo da wuya tafito cikin best three hakanan" Ƴar
ajinmu setace "kedai bari yanzu kam ai asirinta zaitonu tunda harmun gama jarabawa
kuma thesame invilator za adinga kawo mana nasan zata saka mata idanu"..
Nidai yinayi kamar banjisuba dukda abun ya sosamin rai haka Sadiya ma ko maganar
banyi mataba.
Washegari nacigaba da exams ɗina kuma kamar yanda Ƴar ɗakinmu tace thesame
invigilator ce zata cigaba dayimata supervision hakanne tafaru kuma ko ranar akaina
ta tsaya,kuma bama a seat tabar ni nazauna ba. Akasa gaban class tabarni nazauna
ayayinda take tsaye kaina kuma kowa na kallona.
Ranar ma exams É—in baimin wuyaba dukda banyi revision ba. Haka muka cigaba da
jarabawa kuma gaban class yazama nanne permanent seat dina,tun Ina daga hankalina
harna daina nakoma normal nacigaba da harkokin gabana because kamar yanda Aziza
tace "the truth shall prevail one day insha Allah".
Littafin Qadr na kuÉ—ine. Duk maiso should talk to me via this number on WhatsApp.
08147722806
*Page Forty*
Cikin sati biyu muka gama jarabawar mu kuma kamar yau Friday mungama jarabawa
washegari Saturday ne visiting day. Yawanci bazuwa ma É—alibai wannan visit É—in
za'ayiba,muma kuma baza'azo mana daga gida ba hakama Aziza kasancewar sati guda
yarage mana mutafi gida hutu First Term. LamiÉ—o ne nake ganin tsanmanin zuwansa
dayake wancan visit É—in yacemin zaizo insha Allah.
Tunkan mugama Exams nasanar da Aziza cewa LamiÉ—o zaizo kuma zata rakani gurinshi
muje sugaisa kuma atake dana faÉ—a mata ta amince. ranar Friday bayan antaso daga
sallar juma'a muka É—auki kayan mu mukaje laundry muka gogeshi tsaf sannan muka dawo
nan kwanana muka kafa babin hira nida ita,munaji Ƴan ɗakinmu na hirar za'ayi
filmshow dadare washegari Saturday kuma ayi social night a social Hall É—in
makarantar anma kwata kwata mubamu da interest É—in zuwa dankuwa yawanci programs
É—innan zuwa ake a haÉ—u da Boys É—in makaranta ayita haukan banza dana wofi. mundaice
zamuyi attending other activities daza'ayi cikin sati mai zuwa during the
day,irinsu Games,press club day,RedCross club day,debate competition da speech
daza'ayi insha Allahu.
Washegari Saturday tun bayan inspection muka shirya muna jiran azo acemana LamiÉ—o
yazo shi anma shiru babushi babu labarin shi har azahar wanda hakan yasamu deciding
cire kayan mu mu'ajiye inyaso dayazo mwa saka mutafi. Banwani É—aga hankalina ba na
rashin ganinshi dawuri tunda last time ma bayan la'asar yazo. Aikuwa yauÉ—inma hakan
tafaru,harmunyi bacci muntashi munyo alwala zamuyi sallan la'asar kenan sega wata
Yarinya tazo nemana,ita tasanar dani Yayana yana jirana a visiting ground É—in
makarantar. Cikeda zumuÉ—i nace mata "toh mungode gamunan zuwa" Aziza dakejinmu
murmushi tayi sannan tace "ai danaga yanma yafarayima harna cire rai dazuwansa" Ƴar
dariya nayi sannan nace "Nikam bancire Raiba dayake last time ma dayazo bayan
la'asar ya'iso makarantar nan" Sena É—auki housewears É—inmu dake ajiye namika ma
Aziza nata bakinnan yaƙi rufuwa tsabar farin cikin nace "karbi kisaka muyi sallah
muje dawuri kada yayi ta jiranmu"
Cikeda zolaya Aziza tace "aikuma Yaya LamiÉ—o yazo baza'asamu kanki ba" ina dariya
nace "Kedai bari" ayayinda nake saka uniform É—ina. Cikin mintuna goma shabiyar
mukayi sallah muka ƙarasa shirinmu sannan muka fita visiting ground kuma ban manta
É—aukan gift É—inda aka baniba as the 2nd position na ajinmu. Acan school garden inda
na haÉ—u dashi last visiting muka samo shi,yauma yayi gayu yayi kyau sosai
abunsa,wani sa'in har mamakin yanda LamiÉ—o ya'iya dressing nakeyi. Walau kananun
Kaya yasaka walau manya yasaka duk amsar jikinsa sukeyi sukara masa kyau da
kamala,tunda nasanshi dede darana ɗaya ban taɓa ganinshi a hargitseba,he always
looks good and so presenting koda kuwa sanda muke zuwa field trip tareda shine.
Yau ƙanana kaya yasaka saɓanin last visit daya saka manyan kaya. yau banyi ihun
murnar ganinshi ba anmadai har na Isa gareshi bakina kasa rufuwa yayi.
Shine cikeda zolaya yace "Ƴar Birni Mobbu honduko" sekawai nakwashe da dariya Ina
kokarin rufe bakina nace "Ina wuni Yaya LamiÉ—o" playfully yace "Bazan amsa gaisuwar
taki ba tunda ajiyeni kikayi inajiranki kamar gawan shanu" dariya nakuma yi sannan
nace "Kai Yaya LamiÉ—o bamufa wani jimaba anasanar damu mukayi sallahn la'asar muka
fito kuma aikai ka Shanyamu,tunsafe muka shirya muna zaman jiranka" wara idanu yayi
sannan yace "haba?" Ina murmushi nace "Allah kuwa" seya kama kunnuwansa cikin sigan
bada hakuri yace "I'm sorry Dearest Sis,I had to finish some work acikin Bauchi
kafin nakaraso nan" cikin sauri nasa hannu nacire hannun sa daya kama kunnuwansa
dashi Ina murmurshi nace "Laaa bakomai ainasan ba lallai kazo dawuri ba daman tunda
wancan karanma iyarhaka kazo, zumuÉ—in ganinka ne yasani shiryawa dawuri" fuskar
Lamiɗon kaɗai zaka gani kagane ba ƙaramin daɗi kalamaina sukayi masaba.
Seya sa hannu a kan kirjinsa yana smiling,funily yace "Lord!!! My heart will
explode,ashedai haka nikeda importance har ana zumuÉ—in ganina" dagani har Aziza
dariya mukeyi masa ganin abunda yayi.
Aziza tace "Ai Yaya LamiÉ—o bakaji yanda Rukayya ta damu dakai baneba,kullum
setayimin hirarka" LamiÉ—o bakinnan kamar ze yage yace "Nidin É—an gatane ashe" Aziza
tace "Sosai ma. ÆŠan gatan Rukayya" wannan karan dukanmu mukayi dariya a tare
ayayinda Aziza tagaidashi ganin tunda tazo gurin basu gaisa ba,tace "Ina wuni?"
Kallonta LamiÉ—o yayi sannan yace "Lafiya Lau" sannan yadubi Rukayya yace "Wacece
wannan É—in Nana? Is she our boarding school Bestfriend?" yayi tambayar cikin sigar
wasa dankuwa tun zuwansu yaga Azizan yana tason yatambayi Rukayyan wacece ita amma
maganar dasukeyi yamantar dashi.
Murmushi nayi sannan nace "Ai a ko'ina ma itace Bestfriend É—inmu Yaya LamiÉ—o"
Lamiɗo na murmushi cikeda zolaya yace "Lord! I'm jeolous" ayayinda yake sake taɓa
gefen zuciyar sa funnily sannan yaÉ—ago yadube ni yace "But i've never heard about
her from you before? I thought you don't even have friends fah? NaÉ—auka ni kadai
Bestyn ki"
Tsuke fuska Rukayya tayi tana tura baki gaba tace "Yaya LamiÉ—o nidai kaiba Bestyna
baneba,Kai Yayana ne while Aziza is my best friend" duban Aziza LamiÉ—o yayi sannan
playfully yace "Aziza kin kwacemin Besty" dariya Aziza tashiga yi.
Funnily yasake cewa "I'm extremely jeolous, Nana tafison Besty Aziza akaina" wara
idanu Rukayya tayi sannan tace "Nifah bance hakaba Yaya,inasonka fiyeda kowa
shiyasa nace Kai Yayana ne, there's no love that can match that of a sister and her
Brother bayan iyayenta,not even a Best friend" murmushi LamiÉ—o yayi sannan funily
yace "now I feel better" yayi maganar yana lumshe idanu playfully sannan yakalli
Aziza yace "Hajiya Aziza kirike tittle É—in Bestfriend dinki nabar miki kuma,i now
prefer the Brother sister relationship " Aziza dai inbanda dariya babu abunda
takeyi,dankuwa LamiÉ—on is so jovial.
Fancy chair É—inda muka zauna ranar yace muje mu zauna dukanmu kada mugaji da
tsayuwa ayayinda nake bashi labarin Aziza,nace "Yaya LamiÉ—o zaka iya tuna watarana
dana taɓa baka labarin wata Yar ajinmu dakeda shegen yin questions agaban Malami?"
gyada min kai LamiÉ—o yayi sannan yace "Natuna? Ina ranar danace miki you're always
curious,kincika tambaya shine kikacemin bakikai Aziza ba" sekuma yayi sauri yakalli
Aziza with a smile on his face Jin yafurta thesame suna as na yarinyar dake tsaye
agabanshi yace "Wai wannan itace Azizan?" gyaÉ—a ma LamiÉ—o kai nayi ina murmushi.
LamiÉ—o cikeda mamaki yace "But you never said you two were this close,infact yanda
kike maganarta ranar I thought bamwa kwa magana" dariya nayi sannan nace "Da bamwa
magana sosai da mukazo nan ne muka daba,yanzu komai tare mukeyi" kallon Aziza
LamiÉ—o yayi sannan yace "Masha Allah. It's nice to meet you Aziza" Aziza na
murmushi tace "Thank you. It's nice to meet you too" playfully LamiÉ—o yace "Hope
dai bakya cika Malamai da questions time É—in break ko in an tashi har Kanwata
tarasa abinci ko sallan azahar?" Aziza dariya tayi sannan tace "Nina isa,tambaya ai
se Rukayya yanzu" hararanta nayi playfully sannan nace "wallahi bankaikiba kumani
ba Malami nike tambaya ba ai ke nike tambaya" Aziza tace "toh aidaman nidin nike
nufi kuma tambayoyin da kikemin yafi wanda nakema Malami" LamiÉ—o dake dariya yana
kallonmu yace ma Aziza "I agree with you on this,Rukayya da tambaya......"yakarashe
maganar yana riƙe haba irinshi neman tsokanar nan.
Tsuke fuska nayi take sannan nace "nidai bankaitaba kumama nafasa nuna maka abunda
nayi niyar nunamaka tunda bayanta kake goyo" nayi maganar Ina ƙara rungume gift
É—ina cikin hijabina.
Dakyar Lamiɗo yatsagaita dariyarsa sannan cikin sigar lallashi yace "Haba Ƴar
birni! wasafah mukeyi miki fah" sake tura baki nayi tareda juyamai baya ni adole
nayi fushi.
Inaji Aziza na tambayar Lamiɗo waye Ƴar birni anma seyamata alama da tayi shiru da
finger É—inshi wai zai faÉ—a mata daga baya, yanzu fushi nikeyi suyi rarrashi.
Marairaice fuska yayi sannan yace "Toh kiyi hakuri bazan sake goyon bayanta ba
kinji" make kafaɗa na nayi Ina murmushi ƙasa ƙasa ganin bani suke kalloba.
Aziza ne tazo tagabana tana kallona tace "kiyi hakuri Allah wasa mukeyinmiki" ganin
kamar taÉ—auki maganar dagaske senayi sauri nasaki fuskana nace "Nima fah wasa
nikeyi muku kisaki fuskanki" murmushi tayi sannan tace "toh nuna masa gift
dinnaki" juyawa nayi ina kallon LamiÉ—o sannan naciro gift É—ina namika masa ina
faÉ—in "Yaya LamiÉ—o kaga kyautar da akabani" karba yayi yana murmushi sannan yace
"kyautar menene haka?" Cikeda zumuÉ—i nace "Best threes aka kira na C.A test dinda
mukayi a Term É—innan and I'm the 2nd position in our class" fuskar LamiÉ—o cikeda
excitement yace "alhamdulillah! Alhamdulillah. Congratulations Nana,so zama da
Aziza yasa kinzama guruwa?" dariya nayi sannan nace "toh ya na iya,but I love
reading now and I want to maintain my position" playfully LamiÉ—o yace "Yarinya ai
gwanda dabaki gajeniba,insha Allah you'll maintain it,just keep striving for it.
Allah yabada sa'a" senace "Amin" sa hannu yayi zaibude ayayinda yake faÉ—in "Ba Inga
kyautar da aka bamu indauki rabona" sauri nayi nakarba a hannun sa Ina faÉ—in "A'a
karka buÉ—e,I want Kawu Sani to open it first" seya gyaÉ—a min kai yace "Okay then
anma promise me zaki kawomin Babban buli ingani bayan yagani?" nace "insha Allah"
yace "toh good"
Tunawa nayi ban tambayesa labarin su Umma ba tunda yazo danhaka senace "laaa munata
surutu bantambaye ka su Umma ba,ya suke? Ina Yaya Jidda, Yaya Basma da kawata
Salma?" Murmushi LamiÉ—o yayi sannan yace "Lafiyansu Lau suna gaidaki,infact I
wanted to come with them anma senaga kamar zakifi Jin daÉ—in ganinsu idan nakawo
mikisu sanda term yafara ba ankusa tafiya gidaba shiyasa nabari se next visit É—inku
inkun dawo insha Allahu" cikeda farin ciki nace "Wai dagaske kake?" LamiÉ—o na
murmushi yace "Allah kuwa?I asked Umma kuma tayarda" nace "I can't wait to see
them,harda Umma kuma?" nayi tambayar cikeda Curiosity.
Seyace "A'a Umma tace bayanzu ba tukunnan su Basman dai sufara zuwa" dukda naso
zuwan harda ita anma seban nuna komaiba nace "Allah yakawo ranar dazata zo É—in"
yace "Amin Nanaa" nace "Bari Inna koma hostel zanzauna infara counting how many
days yarage next visit inmun dawo,I just can't wait" dariya Aziza da LamiÉ—o kema
excitement É—ina.
inacikin zumuÉ—in kuma natuno da alkawarin dayamin wancan visiti É—in kan zezo gida
during our midterm break kuma baizo ba,tura bakigaba nayi nace "Yaya LamiÉ—o nayita
jiranka lokacin midterm break kazo bakazoba bayan kacemin zakazo" take senaga
yanayin fuskarsa tacanza, ahankali yace "I went to your house two days to kuyi
resuming but I couldn't get the chance to see you" naso intambayeshi meya hanashi
ganina É—in anma yanayin fuskarsa says it all, yajene anhanashi shiga shiyasa yanzu
dana tado da zancen ranshi yabaci.
Senayi sauri nacanza hiran tahanyar bashi labarin mun gama exams É—inmu kuma muna
cikin week of Grace É—inmu,nabashi labarin programs É—inda za'ayi duka ayayinda Aziza
ketayani yin hirar.
Nasan LamiÉ—o kawai jinmu yakeyi dankuwa tunda na ambaci beje gida ganinaba naga
mood É—insa yacanza baki É—aya and this only shows cewa anyi masa wani abu dayajeshi
gidan Kawu Sanin,nasan soyake yayi magana dani Privately anma kuma Aziza na gurin
nima kuma seban bashi fuskaba because Adan maganarnanma ranshi ya dagule barekuma
Inna bashi labarin halin danake ciki awancan gidan yazaiyi reacting? Danhaka koda
Aziza tanunamin tanason tafiya hanata nayi. Not today,banason yatafi gida rai a
dagule nafison semun haÉ—u a Babban buli inbashi labarin komai.
Se after 5 LamiÉ—o yamana sallama yatafi bayan yabani Leda da kuÉ—i wanda inada
tabbacin kayan makulashe ne acikin ledan da É—an abunda ba'a rasaba. Kafin yatafi
seda ya tambayeni sanda zantafi Babban buli hutu amma senace masa bansaniba,infact
bansani ba ko Babban buli zani hutun kokuma GiyaÉ—e dukdama nafison inje Babban
bulin sabida in haÉ—u dashi anma tabbas GiyaÉ—e yakamata inje wannan hutun tunda last
time a Babban buli nayi hutuna.
Koda muka koma hostel duka abubuwan da LamiÉ—o yakawomin rabashi biyu nayi nabama
Aziza rabi inda abubuwan ci kuma damukasan zai iya baci muka cinyeshi aranar. KuÉ—i
ma biyu naraba nabata rabi naɗauki rabi,dafari ƙin karba tayi anma danace indai
taƙi karba nima nangaba in Mommyn ta ta aikomin kuɗi kowani abu bazan karba sannan
tayarda ta karbi abubuwan dana batan cikin sauri.
Sauran kwanakin dasuka rage mana a makarantar kafin mutafi gida karasheshi mukayi a
harkar games,debate,speech,club activities,filmshow dakuma social night ayayinda
Malaman mu kuma were busy compilling our results on the other hand.
Ana gobe zamutafi gida kusan kwanan zaune dayawa daga cikin ÆŠaliban makarantar
sukayi,daga masuyin lalle se masuyin kitso sekuma masu arranging kayansu,sekuma
waÉ—anda suka raba dare suna hira tareda jiran gari ya waye tsabar zumuÉ—in tafiya
gida hutu. Nikam baccina nayi hankali kwance dukda kuwa kafin nasamu baccin
yaÉ—aukeni najima ina tunanin gwagwarmayar dazanje in tarar a gidan Kawu Sani in mun
koma.
Washegari Friday tun karfe huÉ—un asubahi natashi sakamakon karafniyan da aketayi
acikin hostel ɗin namu, inbanda surutan yan hostel ɗin da ƙaran akwatinan da ake
jansu akan varender ana fita dasu daga hostel din babu abunda kakeji. Dole na
natashin nazauna daga kwancen danake Ina mika bawai don baccin ya isheni ba, sedan
nasan konace zankoma baccinma surutan jama'a da karafniyansu bazai bari nayiba.
Juyawa nayi ina karema Yan É—akinmu kallo jin suma suna nasu babin karafniyan inda
anan naga wasunsu sunyi wanka sun shirya ayayinda wasu kuma suna ta shirin fidda
kayansu suma.
Inanan zaune kan gadona ban motsa ko'ina ba sega Aziza tashigo cornern mu dasauri
tana ƙiran sunana,kallonta nayi da mamaki sannan nace "Ke kuma lafiya da asubahin
nan?" tace "lafiya Lau Keee,tashi zakiyi mufidda kayanmu can kusa da gate É—in
makaranta" cikeda mamakinta nace "Akan wani dalili? bagwanda mubari inmuntashi
tafiya gaba É—aya ba semutafi dashi" Aziza tace "A'a idan mukabari se time É—inda
zamu fita hanamu tafiya dashi za'ayi idan prefect suka fara taran latti,cewa zasuyi
se after assembly sannan mudawo mu É—auka shiyasa gwanda mukai yanzu kawai, bakiga
yawanci kowa yanzu yake fidda nasa ba?muma mukai namun can bakin gate kawai yanda
da angama assembly basai mundawo hostel ba wucewa gida kawai zamuyi in anzo É—aukan
mu" senace mata "anma bakya tunanin za'a iya sace mana kaya Aziza?" cikeda kaguwa
Aziza tace "ke Wallahi kincika tsoro Rukayya. Waye zaisace bayan kayane sunanan
dayawa kuma ai kowa yasan nashi" senace Mata "toh shikenan" sannan natashi naÉ—auko
hijabina nasaka kafin najanyo akwatina da Ghana most go É—ina dake karkashin gado
because nikam tuni nagama parking kayana.
Haka muka fidda kayayyakin mu can kusa da gate É—in fita daga makaranta nida Aziza
kamar yanda rabi da kwatan ÆŠaliban makarantar sukayi sannan muka koma hostel donyin
portion É—inmu daganan muyi wanka mushirya kafin lokacin dinning da assembly yayi
afara kora. Karfe takwas daidai Principal da staffs suka iso Assembly ground wanda
mu tuntuni muna tsaye agurin munajiran isowarsu,daga yanda ÆŠalibai keyima Principal
da School Staffs É—in wakar welcome kaÉ—ai zakasan cewa they're so overjoyed,haka da
akazoyin National Anthem ma on top of our voice mukeyinshi cikeda farin ciki. Bayan
angama National Anthem É—in Principal yayi addressing É—in mu,yabamu shawarwari akan
bawai muna murnar zamuje gida ba atleast inmunje É—in muna duba books É—inmu koda sau
É—aya ne a sati,we should try and read ahead our teachers yanda in an dawo anayi
mana bazamuga wahalar abunba,yakuma bamu shawarar we should be respectful to our
parents at home,muyi kokari muna taya iyayenmu aiki agida for there's so much
reward in doing that,in sun aikemu ma mujemu sannan musan inda zamukai ziyara
dakuma irin mutanen dazamuyi mu'amala dasu most especially friends. bayan nan se
aka ƙira senior boarding House Master na boys Hostel da Senior Boarding House
Mistress nanamu Hostel É—in Mata suzo sufadi wasu Hostels guda uku ne sukafi tsafta
overall throughout the term dakuma Hostel É—inda yazo last. Inaji yan ajinmu nata
mitan ayi agama assembly susamu sutafi gida shine damuwarsu ba abunda ake faÉ—a ba
ayayinda wata Khadija a ajinmu naji tana nuna ma Kawarta motar gidansu da already
yana cikin haraban makarantar yanzu, Yan gidansu sunzo É—aukan ta suna jiranta. Ba
Motar gidansu Khadijah kaÉ—ai bane acikin makarantar,parents dadama sunzo É—aukan
Ƴaƴansu,jira kawai sukeyi agama Assembly ɗin Yara su karbi results ɗinsu sesu tafi
gida. Nidai bana wani murna infact jinakeyi kamarma ayita prolonging assembly É—in
har time yayi ta tafiya.
Bayan angama ƙiran Hostels ɗinda sukafi tsafta akabama House masters ɗinsu da House
Mistresses É—insu gifts,inda na karshe kuma aka basu shawarar su dage next term se
aka kira Vice principal academy da yazo yakira best three na kowani class kuma.
Daman munsamu labari ranar hutu ake kiran na term gaba É—aya abada gift kafin atafi
gida.
Dagakan SS3 aka fara wannan karan ma kuma kowani aji se an ƙira best three da last
three É—insu kamar yanda akayi na C.A test anma kuma sede wannan karan harda overall
Three na kowani set gaba É—aya ake kira abada gift.
Haka aka dinga kira har aka iso kan set ɗinmu,sanda aka gama ƙiran na js1A za'a
fara namu inaji wasu a bayana Yan ajinmu na gulmar zasuga waza'a ƙira wannan karan
tunda asirina yatonu angane Satan amsa nakeyi Kuma exams agaban class narubuta kowa
yana ganina. nidai bance komaiba sema focussing danayi akan abunda VP academy É—inda
nayi. Wannan karan ma Aziza ce first position a ajin mu and I'm the 2nd. ba ƙaramin
mamaki Ƴan ajinmu sukayi tayiba suna bina da kallo ayayinda naje na karbi gift ɗina
akan stage nadawo ƙasa. Inaji Aziza nacema Ƴan ajinmu dake gulmana ɗazu "Yanzukam
ai bakin ku yarufe,yanzukam ai nasan everyone of you has fully believed cewa
Rukayya has never cheated a test da exams É—inda mukayi. She did it with her brains
and someone trapped her on purpose sabida yanayi mata bakinciki da hasssada anma
dayake Allah baya bacci gashi kungani da idanunku" Babu wanda yayi magana cikinsu
harta gama addressing ɗinsu ƙasa ƙasa tsabar kunya ayayinda nikam ko kallo basu
isheni ba.
Da aka gama nakowani class se aka koma overall,ananma Aziza ce first position
sewani yaro 2nd and I was the third position.
Sanda nahau stage nakarbi É—ayan gift É—ina zan sauko sega Malamar da tayi mana
invigilation tataho kan stage É—in fuskarta É—aukeda so much regret ta rungume ni
sannan ta É—ago dani daga jikinta tace "Congratulations Dear" kawai sejin hawaye
nayi sunfara bin kuncina da kuwa nasan she's here to fight for me tunda naji tayi
congratulating É—ina.
Cewa nayi "Thank you Ma'am" kafin takama hannuna muka koma kusa da Principal sannan
tace abata mike tanason tayi magana please.
Vice principal bata mike ɗin yayi sannan taje gaban Ɗaliban tana riƙe da hannuna
tace "Good Morning Staff and Students" duka aka amsa Mata da "Good Morning Ma'am"
sannan tace "I want to share a hearttouching story here with you guys" aka gyaÉ—a
matakai duka sannan tadubeni kafin takuma maida kanta ga ÆŠaliban baki É—aya,tafara
basu labarin zuwanta na farko ajinmu dakuma incidence É—inda yafaru,dayanda nayi
trying nayi defending kaina anma taƙi yarda dani,dayanda tayita zagina a aji tana
disgracing É—ina a gaban mates É—ina and how she was shocked data maidani seat É—in
gaba taga Ina rubutu wanda by just reading one paragraph from my writing tasan cewa
i was writing something sensible Amma still sebata nunamin komai ba because if her
assumption is right tanason Ƴan ajinma su shaida shiyasa tamaidani nake zama agaban
aji washegari inda daga karshe tace "And on this stage,at this right instant this
girl has proven herself innocent. I was willing to meet their form master in order
to see her result and present it to her colleagues next semester but even before
that time this girl has proven herself innocent" tajuyo tana kallona tace "My Dear
I'm sorry for saying all those Ill things about you. Forgive me please" cikin
hawaye nace "it's okay Ma'am" setace "Thank you" sannan ta juya tanuna musu regret
É—inta,takuma ce by abunda yafarunnan tayi learning wani abu guda É—aya,bawai daga
angaya maka abu koka ganiba kace zakayi judging mutum directly,try and
investigate,try and listen to what that person is saying because by just listening
to his words,by just looking at his reaction you might find out if he's guilty or
not" tace "I fully believe this girl was trapped by someone among her classmates.
I'm very sure there's someone that don't want to see her success and we'll surely
find that person and punish him" Principal da is so emotional yanajin abubuwan da
Teachern ke faÉ—a seya matso kusa da'ita yace "Madam you said one of the students
was the one that called your attention that time right?" cikeda ladabi Teachern
tace "Yes Sir" se Principal yace "do you know her name? Or can you remember her
face? because I don't think something is right with her" se Teachern tace "I don't
know her name Sir but I can vividly remember her face" Principal nashirin yin
magana sega muryar wasu daga cikin Yan ajinmu na faÉ—in *Sadiya! Sadiya* Despline
Master ne ya ƙarasa gurin yace suyi shiru ayayinda Principal yace mutum ɗaya yayi
magana acikinsu. Aziza ne ta É—ago hannunta sama cikin sauri kan tanaso tayi magana
inda aka bata permission. tace "Sir we were trying to tell you the name of the
student that accused Rukayya of cheating the other day" Principal seyace "okay.
What's her name? And where's she?" Aziza tace "Her name Is Halimatu Sadiya Sani
Sir" Despline master dake tsaye kusa da Yan ajinmu bebar gurinba harlokacin yafara
Ƙiran full name ɗin Sadiya.
Kin fitowa tayi harsaida Principal dasu VC sukasaka baki sannan tafito jikinta na
rawa wanda hakan kaÉ—ai zai nuna maka cewa bata da gaskiya. Hawa kan stage É—in tayi
duka idanun kowa nakanta. cikeda tuhuma principal yadubeta yace "How did you know
that Rukayya was cheating during exams that day?" Jikin Sadiya narawa tace "Sirr...
believe me I saw her cheating during the exams......." Wannan Karan Teachern ne
tadaka mata tsawa sannan tace "You're lying...you idiot! By just looking at how
you're stammering right now,it's evident that you were the one that put your
colleague into this mess" Sadiya na hawaye ayayinda jikinta ke rawa tace "I'm sorry
Ma'am" duka se akatsaya ana kallonta.
Rai ɓace Teachern tace "this means you're guilty?" dankuwa daman ta tsoratatane
danta faÉ—i gaskiya and here she's ba'aje ko'ina bama tatonama kanta asiri,Daman
Sadiya shegen tsorone da'ita kamar farar kura. GyaÉ—a kai tayi jikinta narawa
ayayinda take hawaye tana kuka.
Ran principal bace yace Akira Masa Sargent yakawo masa koboko,shida hannunsa ma zai
zaneta inda daga É—aya bangaren kuma Sauran malaman ketayi Mata faÉ—a suna Allah
wadai da abunda tayi. Sanda Sargent yakawo koboko principal karba yayi yamata 5
strokes of cane,VC academy ma yamata 5 inda daga karshe Teachern ma tayi mata biyar
daganan kuma akace tabani Hakuri.
Jikinta narawa tadubeni tabani Hakuri sannan akace tasauka akan stage din taje tayi
kneeldown agaban kowa. Principal duban Sauran students yayi yayi warning dinsu da
cewa duk Wanda aka kama da irin wannan halin will be severely punished,inbazakayi
kokari kayi reaching stage É—in successful ones ba then don't envy them,kada kayi
musu bakin cikin,keep yourself the way you're. Atake kuma yayi declaring punishment
É—in Sadiya,yace after angama hutu zata kara one week agida as her suspension days
sannan inzata dawo dole tazo da parents É—inta kuma bayan parents É—in nata sundawo
da'ita she'll have to serve her punishment in the school sa well. sati guda zatayi
tana wanke school toilets na classes area inda daganan kuma sukace inkoma cikin
colleagues É—ina.
Ina Isa layin Yan ajinmu Aziza ta rungume ni cikeda farin cikin tana faÉ—in "Mena
gayamiki? Aidaman nace Miki insha Allahu the truth shall prevail" nidai faking
murmushi kawai nayi dankuwa ni kaÉ—ai nasan irin disaster É—inda abunda yafaru yauÉ—in
zaijamin. Dayawa acikin Ƴan ajinmu hakuri suka dinga bani tunma kafin mubar
assembly ground É—in ayayinda wasunsu kuma agurin karban result suka dinga bani
hakurin bayan anyi dismissing É—inmu daga assembly ground.
Ina gani Yaya Zaheera tazo ta karba ma Sadiya result É—inta wurin form master É—inmu
suna harara na wanda hakan yasa gabana faÉ—uwa. Suna yake kira inkaji naka sekaje ka
karba katafi,Aziza was the first kuma dayake already Yayanta Sajeed yazo É—aukan ta
yasa tana tayimin sallama tatafi,Sadiya ma ankira sunanta kafin ni wanda ananne
Yaya Zaheera taje ta karba Mata sannan takama hannunta tana kuka sukabar gurin.
Sunana ne 2nd to the last,ina karban result É—in kuma nayi sauri nanufi gate É—in
makarantar sabida gudun kada innashiga mota suyi korafin na ɓata musu lokaci dan
inada yakinin by that time yakamata ace su Yaya Safiya ma sunriga da sun karbi nasu
result É—in sun haÉ—u guri É—aya. Inda kayana yake naje naÉ—auka sannan nafita a gate
É—in makarantar dankuwa tun ina tahowa nadinga dubawa kozanga motar Kawu Sani
bangani ba and last time da driver yazo É—aukan mu dazamuje midterm break ma awaje
yayi parking shiyasa nayi deciding naje can wajen kilan insamesu. Aikuwa Ina fita
na hangi motar nasa kuma su Sadiya duk suna cikin motar har angama saka kayansu.
ganin karamin figure danayi a driver's seat kuma he's busy yana lallashin Sadiya
dake gaban mota yasana kurama cikin motar idona sosai don Inga wanene and then I
saw Yaya Zunnurain.
Wani irin dum naji zuciyana yafarayi lokaci guda sannan naÉ—aga kafafuna nashiga yin
sauri sabida kada injama kaina faÉ—a da zagi anma sede da mamakina naga Yaya
Zunnurain yana kokarin tada mota. Gudu gudu nafarayi Ina dagama su Yaya Zaheera
hannu dasuke baya akan sucemasa yatsaya anma senaga sun daka min wata uwar harara
itada Yayaa A'isha ayayinda Yaya Safiya kam ko kallo ban ishetaba. Inagani Yaya
Zunnurain yatada motar yayi yayi reverse sannan yajuya kan motar yabar gurin aguje
duk baiganni ba dankuwa gaba-daya attention É—insa nakan Titi.
Tsayar da sauri sauri da gudu gudun nakeyi nayi ganin ko ihu nayi a yanzu ba lallai
yajiniba ayayinda wasu irin dumanmun hawaye suka shiga bin kuncina batareda na
shirya ba.
Littafin Qadr na kudine duk maiso should talk to me privately via WhatsApp for
payment details.
08147722806
*Page Forty One*
*Avoid typing errors please*
Najima tsaye Ina kuka kafin naja akwatina nakoma jikin wata bishiya dakenan gaban
gate din makarantar na ajiye akwatin nahau kai nazauna narabza uban tagumi with the
hope cewa may be Yaya Zunnurain yajuyo motarsa yadawo yadaukeni,may be tozarta
kawai sukeson suyi shiyasa sukayimin haka. Inba haka ba wani marar imanin ne
za'aturoshi daukan kannensa a makaranta yabar daya agurin Kuma bawai Dan ya manta
ba.
Haka nacigaba dazaman jira inayi Ina leken takowani angle kozanga motar gidan Kawu
Sani anma sede babu shi babu labarinsa gashi har anfara watsewa,tsirarrun student
ne suka rage agurin Kuma Suma anata zuwa daya bayan daya ana daukarsu,gashi Naga
Rana yafito kwatsa kwatsa da alama dai Sadiya tawuce sosai. Banida agoge inakuma so
insan lokaci don innemi stand dina danhaka senatashi daga kan akwatina Dana zauna
nakarasa can wurin wasu group din students dake zaune suna hirarrakin su na
tambayesu kosuna da agogo. Senayi sa'a daya daga cikin su tanadashi,tambayar ta
lokaci nayi inda tace min ai shabiyu da rabi ne lokacin. Zuciyana seda
yabuga,shabiyu harda rabi,Awa na nawa anan kenan Ina jira? dan tun after nine aka
sakemu daga assembly ground. daurewa nayi namusu godiya kafin nakoma kusa da kayana
natsaya Ina tunanin abunyi. Ayanzu Kam nasan insu Yaya Zunnurain Basu Isa gida ba
toh sauransu kiris. Wasu irin hawayene suka tahomin lokaci guda,niwana sani yanzu
dazai taimakamin?
Take kuma se commercial car yafado min arai,nafara ayyanawa ko inbi commercial car
ne? anma Sena tuna banida kudi,bankarbi kudina agurin Uncle Adam ba dukdama tun
shekaranjiya ya kiramu duka kan zai raba mana yabamu namu ninaki karba. Nace Masa
ya ajiyemin kawai se andawo hutu nacigaba da amfani dashi dankuwa alokacin gani
nikeyi kudin bazaimin amfanin komai agidaba tunda bawani abun zance zansaya ba Kuma
konace zansaya din ai sede inci aboye kowani abudai haka. Regret din rashin karban
kudin seyahau kaina dankuwa dana karba dayanzu zaiyimin amfani.
Take kuma sewata zuciyar tashiga rayamin kode inje cikin makarantar induba office
din uncle Adam dinne inkarbi kudi yanzu may be inyi sa'ar samunshi. At first naji
tsoron zuwa sabida kada yayi questioning dina dalilin dayasa aka tafi aka barni
amma danaga banida wani mafita daya wuce wannan sekawai nayi deciding inje din.
Harda akwatina nadauka nanufi cikin makarantar dashi dankuwa banason wahalar dawowa
nan indai har nasamu nakarbi kudin tunda commercial cars dinda makaranta take
kawowa acikin makaranta suke diban dalibai,masu gadi seda sukayimin tambayar
dalilin dayasa zan mayar da kayana cikin makaranta sekawai nace musu staff quarters
zankai.
Koda na'isa gaban admin block sebanga commercial car ko daya ba,duk sun tafi
dajimawa. daman Naga sanda suke fita a gate din makarantar anma ai banyi tunanin
duka suka tafiba. Anan gaban admin block na ajiye kayana sannan nashiga cikin admin
block din nanufi office din uncle Adam Ina addu'ar Allah yasa insameshi inyaso Inna
karbi kudin basai inhau napep intafi Tasha in hau motaba. Anma sede banyi sa'a ba
dankuwa office dinma agarke take gabadaya gashi admin block dinma shiru duk yawanci
malaman suntafi. Tashi hankalina yakumayi ayayinda nakoma gurin kayana,najima zaune
gurin Ina ganin yanda ake zuwa daukan wasu dake cikin makarantar Basu fita gate ba
sunajiran azo adaukesu harya rage saura Mutum biyu. Ananne tsoro yakara kamani,Sena
fara tunanin insuka tafi suka barni anan akazo akasaceni fah? Kokuma in Allah
yahadani da mugayen mutane fah? Dankuwa naji ance maza nayima Mata fyade most
especially agurin da babu crowdness,agurin da kikayi ihu babu Mai taimakonka.
Wannan tunanin danayi ne yasani tashi dasauri nadauki akwatina nanufi wurin
masallaci. Acan tambayan masallaci inda baza'a ganni ba na ajiye akwatina sannan
naje nadauro alwala nazo natada sallah sanin cewa azahar tawuce.
Koda na'idar da sallahn anan cikin masallacin nacigaba da zama Ina kuka na tareda
neman dauki gurin Allah anma har la'asar tayi tawuce babu wanda yazo to my rescue.
Infact makarantar tayi shiru sosai,sallah ma ba'a zuwa Yi a masallacin danake ciki
dayake masallacim student ne se in sunanan ake Jam'i aciki ayayinda lokacin hutu
Kuma malaman dake zama a staff quarter's sesukeyin sallarsu acan masallacin dake
kusa da staff quarters din. Allah yataimakeni ma ba'akai ga rufe wannan masallacin
ba anma nasan may be zuwa dare ko gobe dasafe zasu rufe danbazasu taba barinshi
haka Kara zube ba.
Yanma ne yafarayi sosai wanda hakan yasa hankalina yakuma tashi,nigashi bani da
gurin zuwa gakuma banida kudin dazai taimaka min inje wani guri shiyasa ma nake
tsoron sake fita daga masallacin,shiyasa nacigaba dazama anan Ina neman mafita
gurin ubangiji.
****
Bakaramin dadi su Safiya sukaji ba da maganganunsu sukayi tasiri agun Yayansu
Zunnurain,daman can Sunshanshi da zuciya da mugunta shiyasa suna shiga motar suka
dinga kunnashi suna bada labarin abubuwan dasuka faru a Assembly ground din,suka
hada karya da gaskiya duk suka cakuda su. Sukace ai Rukayya ne tatona ma Sadiya
asiri tafadi abunda tayi mata shiyasa akayi disgracing dinta. Hakan yayi matukar
bataran Zunnurain,jiyadingayi kamar yaje yashake Rukayya ya daketa Amma seya daure
zuciyarsa kasancewar yasan muddin yadake ta gaban jama'ar makarantar dole za'ayi
questioninng dinta,but one thing is for sure bazai taba bari tashiga motarsa yayi
driving dinta har gida ba bayan abunda tayi ma kanwartasa. He's not her driver and
he'll never be,tanemi hanyar komawa gida dakanta and after that he'll deal with her
sequarely inta iso gidan. Shiyasa sanda yaji su Safiya nacewa Rukayyan nazuwa kawai
seyadaina rarrashin Sadiyan yaja motar suka bar makarantar ranshi nayi mishi Kuna
da zafi. Daddyn su baya gari shiyasa kobai koma da Rukayya ba intabi motar kasuwa
ba lallai labari ya Isa gareshiba shiyasa ma ko kadan baiyi tunanin akwai
consequences acikin abunda yayi dinba.
Karshe shabiyu da Yan mintuna suka Isa gida,Bayan Zunnurain yayi parking se kowa
yakwashi kayanshi yayi cikin gida cikeda murna inda kowa tayi kofar uwarta. Sadiya
da Safiya basu samu Aunty agida ba Wai taje can family house dinsu yini. Siyama ce
kadai adaki tana karatun hausa novel dinta na jaraba dayake sungama exams alokacin
se zaman jiran result.
Siyama naganin kannen nata tashi tayi ta rungume su cikeda Jin dadin dawowartasu
dankuwa the house has been Boring da baswanan,koba komai intana tareda su zasuyi
hira irin ta yayu da kanne dukda kuwa majority fada sukeyi akan Dan abunda ba'a
rasa ba even though that doesn't change the fact that they love each other truely.
Kallo daya tama Sadiya tasan tasharbi kuka bayan tasakesu daga rungumar datayi
musu. Cikeda damuwa takama hannunta tashiga tambayarta ko lafiya. Nan take se
Safiya tabata labarin abubuwan dasuka faru dakuma barinta amakaranta da Zunnurain
yayi.
Ran Siyama yabaci sosai amma seda hankalinta yatashi Jin Zunnurain din yabar
Rukayya a makaranta. Tace "Kaman ya yabarta? Waye zaije yadaukota toh? Ko ta
yarinyar Nan zatasan hanyar dazai kawota Bauchi fisabilillahi? Shibaya gudun
maganar Daddy ne kokuma baya gudun abunda zai iya samunta?" Tsaki Safiya tayi
sannan tace "Adda Siyama matsalata dake kinada son daura makanki damuwa akan abunda
baikai yakawo ba. Rukayya bayau tasaba shiga motar kasuwa ba tunda ko kaita hutu da
Uncle Umar yakeyi zuwa Babban buli da GiyaÉ—e ai motar kasuwar sukebi so yanzunma
nasan shidin zata biyo tadawo gida" Siyama setace "Anma ai wadancan din tariga data
saba zuwa kuma ba'ita kadai take zuwa ba" Sadiya daranta yafara baci dayanda
Siyamar tadamu setace "Ai acikin makarantar ma akwae commercial cars zata iya vinsu
basai taje tashaba" sauke ajiyar zuciya Siyama tayi sannan tace "Toh Allah ubangiji
yasa ta iso gida lafiyan Kam" daga Sadiya har Safiya babu Wanda yace Amin sema tabe
baki dasukayi suka kama harkokin gabansu. Can bangaren su Aisha kuwa koda sukabama
Ummi labarin abunda yafaru suda Zunnurain Ummi praising dinsu tadingayi tana cewa
sunkyauta. "Shine daidai da'ita dan ubanta. aini dakun karbe gifts dinda akabata a
makarantar kun yayyaga tareda sakamakon da akabatan yanda kotazo gida batada abun
nunawa" Dan cizan yatsa Aisha tayi sannan tace "Kumafa hakane Ummi. Wallahi wannan
tunanin bezo manaba kwata kwata" Zaheera tace "Kuma wallahi indai har tazo dashi
gidannan tabbas Daddy yayi praising result dinta,harma kilan yace zaiyi Mata kyauta
mukuma ko oho" Aisha tace "basai mukwace ba data iso gida. Kinsan sai bazata taba
yin magana tace muneba sede duk abunda muka fada tabishi ahakan" Zunnurain yace
"kuyi fatan Allah yasa sufadi ahanya ma kawai" sekuma suka sheke da dariya inda
suka koma plan din yanda zasu kwace result din da gifts dinda aka batan. Maganar
parent din Sadiya yaje da ankoma Kuma tuni Ummi tace itazata je danko Aunty bazasu
Bari tasamu labariba. Because indai labari yaje kunnenta,toh tabbas kamar yaje
kunnen Kawu Sani ne inya dawo and that'll surely reveal their secret na gift din
Rukayya. Shiyasa gwanda suyi covering up a tsakaninsu.
Daga baya kowa harkokin gabansa yahau yi agidan batareda wani yakuma bi takan
zancen Rukayya ba koya tambayi ba'asin dalilin dayasa Bata isoba har ukun yanma.
Alokacinne Kuma Salim ya diro gida dankuwa shima tun jiya dayanma yagama exams
dinsa inda yau yayi sammako yakamo hanyar gida daga Zaria. Fahad ma na hanya daga
Imo,tunjiya ya iso Abuja yakwana inda yake hanyar tahowa daga abujan yau.
Bakaramin farin ciki Yan gidan sukayi daganin isowar Salim dinba,barinma uwarsa da
kannensa bakidaya. Haka kowa yazo yayi masa oyoyo Yana rungumarsa kasancewar shidin
Daman Mai saukin Kai ne da faram faram,Kuma tuncan yakanyi Wasa da kannensa shiyasa
baswa shakkunsa suke shiga jikinsa sosai. Kowa seda yabashi tsarabar daya kawo
masa,su Mariya da sule chocolates da sweets yasaya musu ayayinda daga kan Sadiya
yayi sama yasaya ma kowa popcorn a Kano kowa daidai banda Ummi dankuwa tsarabar
tayara ce kadai. Yajima zaune parlourn su Ummin suna hira,seda yaji ana kiraye
kirayen sallahn la'asar sannan yamusu sallama zeje masallaci daganan kuma seya huta
anan sashin su. Da ledar popcorn guda daya yafito a hannunsa,Wanda yakeda niyar
bama Rukayya dankuwa yabama kowa nasa natane dai bai bataba Kuma abunda yasa
baibama Yara su kaimataba sabida gudun maganar Ummi ne. Basai angaya mishi inda
takeba yasan by now tanacan baya tana Taya masuyin girki aiki kowani Abu tunda
that's the place dayake yawan ganinta a gidan Koda yaushe darana danhaka seya nufi
cndin cikin sauri dankada ma yajima har Ummin tafito tasameshi. Tunda yafita
backdoor din yaketa leke leken ta'inda zai hangeta anma babu ita babu labarinta,ya
leka kitchen batanan,ya leka bathroom shima nan batanan.
Juyawa yayi yakoma main parlourn gidan inda yanufi kofar su Sadiya daniyar
yatambayesu kotana can tunda tabbas yasan Bata side dinsu Kuma ko Karen hauka ne
yacijeta bazata taba zuwa side dinnasu ba. Anma sede tunma kafin ya Isa kofar su
Sadiyan sega su Mariya sun fito daga kofarsu itada sule. Alama yamusu da hannu
suzo.
Karasawa sukayi inda yake sannan sukace "Gamu Yaya Salim" Salim yace "Ina Rukayya
take? Kunga inda tayi? Kowani ya aiketane?" girgiza masakai sukayi dukansu biyu
atake sannan Mariya tace "aibata isoba" cikeda mamakin maganarta Salim yace "Kamar
ya Bata isoba? daga inane Bata isoba?" Wannan Karan sule ne yayi magana,yace "Daga
makarantar su. Ba su Yaya Zunnurain Basu taho tareda itaba sabida Dukan dataja
akama Adda Sadiya" hankali tashe Salim yace "Kuna nufin Zunnurain baidauko Rukayya
daga makaranta ba dayaje daukarsu duka?" gyadakai sukayi dukansu ayayinda yayi
Sauri yashige parlourn Ummin yana huci cikeda bacin rai because he just can't
believe abunda su Mariyan suka fada Amma sede yasan bazasuyi Masa karyaba,yasan
haka kawai bazasu kirkiri labari su Fadi abunda baifaru ba. Sanda yashiga parlourn
Zunnurain yatashi kenan daniyar yatafi masallacin shima Jin anata kokarin shiga
sallah a masallatan unguwar tasu. Tsayawa yayi yayi turussss ganin Salim din yayo
kansa rai bace yana mamakin meya faru haka anma sede tunma kafin yasamu amsar
tambayartasa seyaji Salim din yajefo masa tasa tambayar.
Yana huci yace "Ina Rukayya take?" Cikeda rashin gaskiya Zunnurain yace "Nima
bansani ba" Rai bace Salim yace "dagaske a makaranta kabarota?" Zunnurain yace
"bakasan metayi bane shiyasa kake tambayana Yaya Salim" a harzuke Salim yace "I'm
asking you a question Man! Dagaske a makaranta kabaro Rukayya?" tsuke fuska
Zunnurain yayi yanata wani muzurai sannan kamar Wanda batason ya motsa bakinsa yace
"Eh" saukan Marin dayaji a fuskarsa ne yasashi dafe kuncinsa ayayinda yake kallon
Salim din Baki sake anma sede tunma kafin ya Isa sake cewa komai Salim din yakuma
wanka Masa wani Marin tadaya gefen kumatunsa.
Yace "Bakada hankaline? Are you insane?Kai wani irin mahaukacine? Kai wani irin
dakikine Zunnurain?" Zunnurain daranshi yagama baci yace "Yaya Salim akan Rukayya
ka mareni?" Salim yace "Na mareka din and if you dare ask me again,wani Marin Zan
Kuma saukar maka tundakai dakikine bakasan Ina hankalinka yakeba" Zaheera daketa
batarai Wai Dan anmari Zunnurain setace "Yaya Salim bakatsaya kaji me Rukayyan tayi
bane ba shiyasa kake Marin shi" wani harara da Salim din yadaka ma Zaheera seda
Tasha jinin jikinta,yace "My friend! Will you get out of this room kosaina hada
dake naci Miki mutunci?" Jiki na bari Zaheera tatashi tashige dakinsu,Aisha ma
datake sallah anan parlourn Salim din yashigo tana sallamewa tatashi tabi bayan
Zaheeran sumui sumui zuciyarta na bugawa,tasan Salim Sarai bayida fada Amma Randa
ka tabishi toh ma kaguji zuwa inda yake.
Salim bayan fitarsu Zaheera a parlourn seyamaida dubansa kan Zunnurain,yace "Where
are the car keys?" Zunnurain yace "mezakayi dashi?" Salim Rai bace yace "Auuu
tambayana ma kakeyi? I said where are the car keys?" Zunnurain na huci yace
"Sunanan" Mika Masa hannu Salim yayi sannan yace "Bani" Zunnurain jiyakeyi kamar
yakama Salim din da duka tsabar bakin ciki,he just can't believe wai Yayannashi
tafiya dauko Rukayya zaiyi. Sa hannu yayi yaciro Masada makullin batareda yamika
masa bayace gashinan.
Salim yasake mikamasa hannu yace "Aicewa nayi kabani bawai karikesu ahannunka kamar
wani kayan kwalliya ba" stubbornly Zunnurain yace "There's no need for you to go
there, she'll find her way home" wannan Karan ran Salim yayi matuka gurin
baci,cikin tsawa yace "zaka bani makullin ne kosai na fara ball dakai adakinnan ko
Yaya?" mikamasa makullin Zunnurain yayi ayayinda Salim din yakarba Yana fadin "And
mark my words,if anything happens to this girl ranka inyayi dubu sai yabaci,just
pray that she's safe and sound sannan inaso ksaka ma ranka cewa kamar maganar Nan
yaje kunnen Daddy inya dawo" daganan Salim yanufi kofar fita daga parlourn Ummin
Amma sede tunma kafin yayi stepping kafarsa out,Ummin tace "da izinin wazaka tafi
daukota din?" Juyowa Salim yayi yana kallon mahaifiyar tasa batareda yace komai ba.
Ummi Rai bace tace "nace da izinin wazakaje daukota?" Salim trying to assimilate
his anger yace "Ummi I don't think I need anyone's permission,the girl might be in
danger" dakuwa Ummi tayi mishi sannan tace "Uwar danger ba Danger ba. Inma mutuwa
zatayi Ina ruwanka?" Salim zaiyi magana Ummi setayi sauri tadaga Masa hannu Rai
bace,tace "Banason Jin komai,kadawo ka ajiye makullin Nan babu inda zakaje inda
Nina haifike" tace "Har Kaine yau zaka daga hannu ka Mari kaninka sabida wata
ballagaza Salim? Harkaine zaka wanka ma Zunnurain mari sabida Rukayya? Toh wallahi
indai Nina haifeka bazakaje daukar taba" Salim kamar zaiyi kuka yakarasa inda Ummin
take,cikin sanyin murya yace "Ummi don Allah kisaurareni! What if wani Abu yasameta
fah? What if Daddy yadawo yana questioninng dinmu mezamu cemasa?" Dauke Kai Ummi
tayi sannan tace "bana tunanin bazata iya dawowa dakanta ba Kuma koma bata dawo
dinba mukam ai hutaroron mu ne sannan zamusan abunda zamu fada ma mahaifin naku
tunda batada say ita" Baki sake Salim yatsaya yana kallon mahaifiyar tasa,tsabar
bakin ciki seya kasa cewa komai dukda he desperately wants her permission anma
yasan komi zaiyi bazata yarda ba tunda har tsanar datake ma Rukayyan yakai haka,
yakai har in Rukayya ta Bata ma Bata damu ba. Yanajinta tagama kashe mishi warning
akan taji yace seya fada ma Babansu abunda Zunnurain yayi,toh Bata yarda ba Allah
baiyarda ba inkuma yace seya fada dintohi da'ita ne. Kafin daga karshe takarbi car
key dinda ke hannunsa tace Kuma inyayarda yace ko motar kasuwa zaibi yaje yadauko
Rukayya Bata yafe masaba.
Shidai baice komaiba haka yafice a sashin nasu hankali tashe Kuma ranshi a matukar
bace, tunanin wani hali Rukayya take cikine yasaka shi agaba,gashi duk wani
possible way dazai iya bi dan yasamu ynda zaiyi yaji daga gareta Ummi duka ta toshe
wadannan hanyoyin. Anan dakinsa yayi sallah dan masallaci ma kasa fita yayi,Yajima
Yana tunane tunane,yakulla wannan ya saka wancan anma duk bbu wasu possibilities
dankuwa ko hauka yakeyi bazai bikan maganar uwarsa yaje yayi abunda yakeso ba. No
matter what Uwa,uwace kuma dole yayi Mata biyayya. yananan zaune gefen gadonsa Sega
Kiran Kawu Sani yashigo wayarsa. Jiki sanyaye yasa hannu yadauki wayar sannan yayi
picking din tareda yin sallama.
Daga daya bangaren Kawu Sani ya amsa sannan Salim din yace "Ina wuni Daddy?" Kawu
Sani yace "lafiya Lau Salim! Ya hanya?" Salim yace "Alhamdulillah. I'm home already
ma nikam" Kawu Sani yace "Masha Allah harka Isa gida kenan?" Salim cikeda ladabi
yace "Eh Daddy wuraren three na iso" Kawu Sani yace "gaskiya kunyi sauri, I've been
trying to call you dasafe naji wayarka bata shiga daganan kuma munzo munshiga
meeting, yanzu fitowarmu nace barina kiraku kaida Fahad inji ya hanya" Salim yace
"Allah sarki. Inaga sanda kakira dasafen muna inda ba network ne don fitowar
sassafe mukayi" Kawu Sani yace "May be" sannan yasauya maganar zuwa kan Fahad yace
"Shi Fahad din Kuma fah? Nakirashi shima wayarsa Bata tafiya? Ya iso gidane?" Cikin
sauri Salim yace "no bai iso ba tukunnan Amma inaga yakamata yakusa dan bamu Jima
da kamo hanya ba yacemin shima lokacin zaitaho" se Kawu Sani yace "toh shikenan
I'll keep trying his number kaima kana gwadawa. Allah yakawo sa Lafiya" Salim yace
"Amin" cikin sauri danbashi da burin daya wuce yagama waya da Kawu Sanin yafara
neman Fahad din awaya dankuwa yanaji Kawu sanin ya ambaci Fahad idea tafado Masa
lokaci guda,Yasan ayanzu Fahad shine kadai zai iya taimakonsa da maganar Rukayya.
In Ummi tahana shi zuwa takuma hanashi fada ma mahaifin su aibata hanashi nema Mata
taimako agurin wasuba and moreover Fahad will surely back him yasani Sarai, sunayin
sallama da Kawu Sanin seya shiga Kiran layin Fahad anma sede Kiran yaki tafiya
kamar yanda Kawu sanin yasanar dashi. Haka yacigaba da Kira babu kakkautawa dukda
yayi attempt yafi talatin duk amsa daya ake bashi anma ai ba a cirerai ga rahamar
ubangiji? Moreover akan hanya yake, anytime zai iya Isa guri Mai network yasameshi
suyi magana.
Har karfe biyar ta gota Salim baidaina trying number Fahad akai akaiba Wanda har
hakan yasa charging din wayar shi tasauka sosai harma tafara nuna Masa danger,gashi
basuda wuta agida,gashi ba'a kunna gen agidan se after sallar maghriba.
Trying number Fahad din yakumayi Yana addu'ar Allah yasa yasameshi kafin wayartasa
ta mutu and he's lucky enough sega wayar tafara ringing,wani irin hamdala yayi
aransa lokaci guda. ji dayayi Fahad din yayi picking call dinyana fadin "Hello"
"Hello" ne yasashi fadin "Yaya Fahad kana inane please?" Dankuwa aganinshi bashida
lokacin gaisuwa tunda anytime wayartasa zata iya mutuwa.
Daga daya bangaren Fahad yace "Ina cikin gari,yanzu shigowana Bauchi zankaraso gida
insha Allah" "innalillahi wainna ilaihir rajiun" shine abunda Salim din yafadi
ayayinda yadafe kanshi dankwata kwata baiyi tunanin Fahad din ze iso dawuri haka
ba,a plan dinshi invai wuce azarai ba zece Masa yatsaya a makarantar su Rukayya
yaduba kota taho. Jin abunda Salim din yayi se Fahad yace "Lafiya? wani abunne
yafaru?" Cikeda damuwa Salim yace "Rukayya Yaya Fahad" lokaci guda hankalin Fahad
yatashi Jin Salim ya ambaci Rukayya, arikice yace "meya faru da'ita?" Wanda har
yanayin voice din Fahad din seda yabama Salim mamaki dankuwa yasan Yayan shi,he
cares for no one,he never cares akan abunda baishafeshi ba anma seya boye mamakinsa
yace "We don't know Where she's" hankali tashe Fahad yace "Kamar Yaya bakusan inda
takeba?" Salim yace "They left her in school while coming back,so we don't know
she's still there ko ta tataho. All I know is she's not yet home and I'm worried
Kar wani Abu ne yasameta dankuwa tun safe aka basu hutu" burki Fahad yataka ma
motarsa ayayinda yayi parking gefen titi,wannan karan shine yashiga furta kalmar
innalillahi wainna ilaihir rajiun dinda Salim keyi dazu anma sede yalura Salim is
not on the call anymore dantun dazu wayar ta katse,he tried calling him back
danyaji Karin bayani anma wayartasa a kashe.
Reverse yayi yayi U~turn ayayinda yakejin wani irin fear nashi garshi,the fear of
loosing little Rukayya. hanyar azarai yadauka without thinking twice hakanan yake
sharara gudu kamar ba gobe,yaso yakira mutanen Giyade yatambaya kocan tajeta anma
dayayi tunanin zai iya tada musu hankali sebai Kira din ba, seya hakura akan seyaje
makarantar inbai sameta ba seya kirasu ya tambayesu. Tunani kala kala yakeyi akan
hanyar sa ta zuwa azarai,tunanin inbaisamu Rukayya a makaranta ba,invai samu
labarinta a Giyade da Babban buli ba where could she've gone too? Allah ne kadai
yakaishi azarai lafiya.
Alokacin daya Isa har dare yayi dan gari yayi duhu sosai. Agaban gate din
makarantar yayi horn ayayinda daya daga cikin guards din yazo yana tambayarsa koshi
wanene. Bayani Fahad yamasa W
wanda hakan yasa guard din shiga tashin hankali,cikeda damuwa yace "Anya akwai
dalibar data rage acikin makarantar nan kuwa?Dan kaga yanda muke zaune abakin gate
dinnan babu inda muka motsa seda muka tabbatar kowani dalibi yatafi gida" sauran
guards din Jin abunda abokin aikin nasu ke fada yasa sukasan ba lafiya ba,danhaka
sesuka taso suka taho gurin motar Fahad din dukansu suna tambayar meya faru. abokin
aikin nasu ne yamusu bayanin komai inda suma shiga jimamin abun.
Daya daga cikin su yakuma maimaita abunda shina farkon yace,se na farkon yace
"Abunda nagama gayamishi kenan. Har kowa ya watse duk munanan" wani acikin su yace
"Daman bazuwa daukarta akayi ba motar kasuwa tabine?" Fahad yace seyace "Eh kawai"
don bayason dogon bayani,se guard din yace "Anmadai ba motar da aka kawo cikin
makaranta tabi ba Koh? dankuwa duk malaman dasuka raka dalibai garuruwansu da
commercial car sundawo dazu sannan kowa ya Isa gidansu lafiya" Fahad akafule yace
"Bansani ba Mallam! What matters here is she's missing and we've to look for her
within the school premises ko za'a iya samunta kafin kuma ace za'aduba wasu
guraren" jinjina Kai sauran guards din sukayi ayayinda daya daga cikinsu dabaiyi
magana ba tundazu yace "Amma fah wani hanzari ba guduba,nina ga akwatin wata daliba
data manta a kusa da masallaci dazu,harma nadauke nakaishi security office dinmu
sabida may be zatazo nema daga baya" cikin sauri Fahad yace "Ina akwatin yake?
Innaga akwatin ta zangane" se guard din yace "Yana security office muje innuna
maka" cikin sauri Fahad yafito a motar ayayinda suka dunguma sukayi hanyar security
office tareda sauran guards din makarantar.
Littafin Qadr na kudine duk maiso should talk to me privately via WhatsApp
08147722806
*Page Forty Two*
Suna isa security office ɗin guard ɗin ya ƙarasa ciki yaɗauko akwatin daya ɗauka
abakin masallacin yafito musu dashi. Fahad nagani yace "Shine! Akwatintane wallahi.
A Ina kasamu?" dankuwa bai manta kalar akwatin ba tunsanda yakawo su ranar da akayi
admitting É—insu a cikin makarantar.
Security Guard É—in seyace "Acan kusa da masallacin hostel É—in Mata nasamu a ajiye
kusa da varendern masallacin. ni duk a tunani nama wata daga cikin ÆŠaliban ne
tamanta dayake wasu sukanyi misplacing kayansu ranar hutu kokuma sumanta shi inda
mukuma inmuka gani semu É—auko mu ajiyeshi agurin mu yanda in andawo masu shi sunzo
sunyi claiming semu basu" Fahad yace "wannan kam akwatin Kanwata ce,muje muduba
gurin may be musameta" jinjina kai sauran sukayi sannan suka nufi masallacin
ayayinda security guard É—inda ya tsinci kayan yake faÉ—in "Nidai banga alamar akwai
ÆŠaliba agurin ba" wani acikin su yace "kasani ko tana cikin masallacin? mujedai
muduba anything can happen".
***
Zama na cigaba dayi anan cikin masallacin har aka fara kiraye kirayen sallar
maghriba duk a kunnena. tashi nayi nafita daniyar yin alwala inzo inyi sallah,anan
bakin tap na tsuguna na É—aura alwalana,natashi kenan zankoma cikin masallacin
senaji kamar motsin mutum. Hakan ba ƙaramin tsorata ni yayi ba,lungu nasamu na buya
cikin sauri ayayinda zuciyana ke bugu,seda nadaina Jin foot steps É—in dana dinga ji
sannan nafito daga lungun dana buyan,nashiga leken hanyar dazanbi inshiga
masallacin inda annanne nahango É—aya daga cikin Security man É—inmu É—aukeda akwatina
ya nufi security office dashi. zare idona nayi cikin sauri ayayinda nadaga kafana
daniyar infito fili in tsaida shi ince mishi nawane anma take sewata zuciyar ta
haneni dayin hakan dana tuna cewa "No one is to be trusted and Some Men take this
kind of advantages suyi ruining rayuwar Ya'ya Mata,yanzu a tsakiyar makarantar nan
da duhu yafarayi innace zanmishi magana yazo yamin wani abunfah? Wazai zo yayi
rescuing dina? don haka sena hakura dayi masa maganar nayi sauri nashige masallaci
Ina addu'ar Allah yasa baijuyo yaganni ba kokuma Allah yasa baiji karar rufe kofar
masallacin danayiba dukdama i was very careful wurin rufewan. I badly wanted my
Box back sabida akwai abubuwa da dama dazan bukata aciki kafin gobe anma na
gwammace in yita zama ahaka akan inbi bayanshi,na gwammace inzauna a duhu batareda
nayi using lantern dinaba don ganin haske dankuwa babu hasken koda security light
ne acikin makarantar kasancewar daman lokacin hutu yanke wutar akeyi harsai ÆŠalibai
sundawo sannan adawo musu dashi.
Gaba É—aya a tsorace nayi sallan maghriba,inayi zuciya ta na bugawa hakanan inaji
kamar security É—in zaidawo yayimin wani abu,bayan na idar da sallah can dungun gini
nakoma na rakube agurin kamar wata meshirin shiga ginin ayayinda zuciyana ke dukan
uku uku. Nafi mintuna talatin acikin wannan fear É—in,fear É—inda bana tunanin zan
iya mantashi a rayuwata. Surutun mutane danaji dakuma footsteps dana keji suna
tahowa towards masallacin ne yasa nasake mugun tsorata,bugun zuciyana yakaru gashi
kuma muryar maza nikeji,hawaye nafarayi babu kakkautawa ayayinda nake kokarin
holding kukana dan kada yafito fili har su jini,addu'a kuwa babu wanda banyishi ba
alokacin,harda na shiga banÉ—aki seda nadinga yi tsabar kidima.
Inaji sukazo kofar masallacin,senaji wani acikinsu na faÉ—in "Aikuwa ga takalmin ta
nan" wani irin danasani ne yashigeni lokaci guda,Sena fara danasanin barin
takalmina awaje. Cusa kaina nayi cikin cinyoyina dasauri ayayinda zuciyana kecigava
da bugu,nikam nasan yau tawa yakare shine abunda nake ayyanawa araina ayayinda naji
ambude kofar masallacin. Haska Torchlight É—inda aka shigayi acikin masallacin
takowani angle har ya iso kaina babu wanda hakan yasani É—ago da kaina daga cusashi
danayi cikin cinyana.
Inaji suna faÉ—in gatacan,muryar Yaya Fahad danaji Yana faÉ—in "Rukayya" ne yasani
É—agowa dasauri cikeda mamaki and there I saw him coming towards me. Dasauri natashi
Ina hawaye nakarasa inda yake nafaÉ—a jikinshi se kuka. Tsugunawa yayi agabana ya
rungume ni dakyau yana shafa gadon bayana batareda ya iya ya ce komai ba.
Seda nayi mai isana sannan ya É—ago ni daga jikinsa,Yana Fallon fuskana daya canza
launi cikeda damuwa yace "Are you okay now?" gyaÉ—a masakai nayi ahankali dukda I'm
not normally okay, I'm still in fear dukda kuwa he's come to my rescue. Da mamakina
senaga yasa thumbs É—insa yashiga gogemin guntun hawayena ayayinda yatashi yakama
hannuna yana faÉ—in "Let's go home" jinjinamasakai nayi alamar toh ayayinda yajuya
ga securities É—in,yace "thank you so much. Mungode Allah yasaka da alkhairi" cewa
sukayi ba komai kafin É—aya daga cikin security Man É—in yadubeni,yace "Keh yanmata
anma tun É—azu kina cikin masallacin meya hana dakikaji naÉ—auki akwatinki baki fito
kinmin magana ba?" Cikin sauri nace "bananan sanda kaÉ—auko,seda nadawo naga
babushi" wani daga cikinsu daban seyace "Amma meya hanaki tafiya gida bayan kinsan
za'anemeki agida?" shiru nayi bance komaiba, Yaya Fahad dake kallona harlokacin
seyace musu "Kuyi hakuri mutafi yanzu, she's stressed out now ba lallai kusamu
amsoshin tambayar ku yanda yadaceba" É—aya daga cikin security guard É—in yace
"toshikenan kujeku anmadai nangaba karta sake irin wannan garajen,it can risk her
life,inma wani Abu yafaru tayi reporting a makaranta and we'll always be there for
her" gyada kai Fahad yayi ayayinda nima na gyaÉ—a musukai sannan Yaya Fahad É—in
yakuma cewa mutafi.
ÆŠaya daga cikin security Man É—inne yataimaka yakaimin akwatina mota yasamana a boot
sannan mukabar gate É—in makarantar. A cikin gari Yaya Fahad yatsaya yayi sallar
maghriba da Isha'i a masallaci,kuma daya tashi tafiya garkameni yayi acikin motar
tawaje sekace wanda nace masa guduwa zanyi. Acan kusada wajen gari yatsaya awani
bakery yasaya mana snacks da Ice cream sannan yadawo cikin motar,Kuma ko awannan
lokacin ma dazai fitan seda ta garkameni a motar tawaje. Ba ƙaramin mamaki nayiba
dayabani Ice cream yau and then I realized cewa Yaya Fahad can be a *Taciturn* but
atleast he cares from within,kobai fito ya faÉ—a ba actions É—insa suna nunawa. Wato
ranar abunda yahana shi siyamin sabida yaga Ina murane badan wani abuba. Haka muka
É—auki hanyar Bauchi wuraren takwas na dare kuma yau banji kunyar cin abinci akusa
dashiba dayake darene and moreover koba daren bane cin abuna zanyi tunda inajin
wata irin uwar Yunwa daban taɓa jin irinsa ba dan rabona da abinci tun bread and
egg É—inda naci a dinning yau da safe. Hakanan tunda muka dau hanyar Bauchi babu
wanda yace da wani kala acikin mu tun bayan godiyar danayi Masa sanda yasayomin
snacks da Ice cream yabani. inbanda sanyin AC daya haÉ—u da sanyayyar turaren Yaya
Fahad babu abunda ke tashi a motar. Sekuma wakokin colum Scott daketa yi cikin
radion motar tasa. A É—an sanin danama Yaya Fahad bayaga yawan Jin karatun alqur'ani
yanason foriengn songs sosai dankuwa Inka shiga motarsa inba wakar Westlife
yakejiba ba toh zakasamu na shyneward ne ko colum Scott dadai sauransu.
Yaudai na colum Scott É—in yadage daji kuma nalura guda É—aya ya kulla mawa,tunsanda
muka bar gari dan har inwakar takare se inji yasake maidata baya tafaro daga
farko,tun inajinta wani iri a kunnena harnaji wakar tafara yimin daÉ—i nima,wakar
*You're the reason Why*
🎼 "You Are The Reason" 🎼
There goes my heart beating
Cause you are the reason
I'm losing my sleep
Please come back now
There goes my mind racing
And you are the reason
That I'm still breathing
I'm hopeless now
I'd climb every mountain
And swim every ocean
Just to be with you
And fix what I've broken
Oh, cause I need you to see
That you are the reason
There goes my hands shaking
And you are the reason
My heart keeps bleeding
I need you now
If I could turn back the clock
I'd make sure the light defeated the dark
I'd spend every hour, of every day
Keeping you safe
And I'd climb every mountain
And swim every ocean
Just to be with you
And fix what I've broken
Oh, cause I need you to see
That you are the reason
I don't wanna fight no more
I don't wanna hide no more
I don't wanna cry no more
Come back I need you to hold me
(You are the reason)
Come a little closer now
Just a little closer now
Come a little closer
I need you to hold me tonight
🎼I'd climb every mountain
And swim every ocean
Just to be with you
And fix what I've broken
Cause I need you to see
That you are the reason🎼
Akai akai dai nakanji sukanyi waya da Yaya Salim yana tambayar sa ya hanya bayan
yaƙira da fari yasanar dashi yasame ne.
Wuraren goma muka shiga garin Bauchi kuma inaganin munshiga garin Bauchin senaji
hankalina yafara tashi kuma,Sena fara tunanin abunda zanje in tarar a gidan,sena
tuna abubuwan dasuka faru yauda safe a assembly ground É—in dakuma abunda abun
yafarun yajamin. jina dingayi kamar ince ma Yaya Fahad karya kaini gidan nasu
yawuce dani Babban buli kawai anma nasan ko karen haukane yacijeni bazan iya buÉ—an
baki ince masa hakan ba. Ahaka muka ƙarasa gida yayi horn akofar gate ɗin gidan
inda mai gadi yazo ya buÉ—e mana yashigar da motar yayi parking a harabar gida.
Shiya É—aukar min akwatina dakanshi yashigar min dashi main parlour ayayinda nabisa
abaya da class bag É—ina goye agadon bayana. nayi tunanin anan zai ajiyemin anma
senaga yanufi kofar su Aunty dashi,alokacin ne ma na tuna ashe su basumasan a
parlour nake ajiye kayana inkuma kwana a kitchen ba. banyi niyar binsa abaya
ba,nayi niyar in wuce matsuguni nane anma dana tuna taimakon dayayimin yauÉ—in
dakuma irin mutunci mahaifiyar sa senaga bai dace in tafi banje nagaishetan ba.
Danhaka sena bishi abaya muka shiga parlourn Aunty.
Safiya ce kaÉ—ai kwance a parlourn tana kallon Zeeaflam kuma tana ganin Yaya Fahad
É—in yashiga parlourn tayi sauri tatashi tazauna tana gaida shi,ba tareda ya amsa
gaisuwar taba yanuna Mata akwatina dake ajiye agabansa yace "Take this to your
room" take naga ta murtuke fuska tanamin wani irin kallo ƙasa ƙasa kafin kuma ta
ƙarasa taɗauki akwatin tayi shigewarta ciki. Dede nan Aunty tafito daga ɗakinta
tana faÉ—in "Fahad seyanzu? Ya akayi kayi dare haka?" Samun kasan carpet yayi
yazauna sannan yace "Ina wuni Aunty" Aunty tace "Lafiya lau. Ya hanya?" Fahad yace
"Alhamdulillah" Aunty na kallonshi tace "Wai nikam motar matsala tasamu ahanya ne
komi?" cikin sauri Fahad yace "No Aunty" Aunty setace "toh ko katsaya awani gurin
ne?" Nanma girgiza Mata kai yayi alamar A'a.
Baki sake se Aunty tace "Toh wai wani irin tafiya kadin gayi haka? Sekace wanda
yataho daga Lagos? Ina tun sassafe kabaro Abujan?" Fahad cewa yayi "Eh Aunty"
sannan ya kara da "wujajen five na'iso garinnan fah,I just had to go back to Azarai
shiyasa nayi dare" Aunty data kasa ɓoye mamakinta tace "Azare kuma? Mekajeyi a
Azare kuma?" Memakon yabata amsa seya kalli Rukayya dake rakube ajikin É—aya daga
cikin one seaters É—in parlourn ayayinda class bag É—inta ke É—aure akan cinyarta.
Aunty bin inda Fahad É—in yayi da kallo tayi sannan tace "Rukayya?" Ahankali nace
"Na'am Aunty. Ina wuni?" Aunty tace "Lafiya Lau. Yanaganki da uniform da jakar
makaranta haryanzu baki cireba kuma?" Shiru nayi bance ma Aunty komaiba. Yaya Fahad
ne yamaida dubansa gareta sannan yace "yanzu naÉ—auko ta daga makaranta Aunty.
Itanakoma daukowa" zare idanu Aunty tayi sannan tace "Kamar Yaya?" Fahad seya bata
labarin yanda sukayi da Salim awaya sanda yashigo gari.
Cikeda Mamaki Aunty tace "Toh anma ya akayi ni banida labari? Shi Zunnurain É—in
hankalinshi É—aya dazaibar kanwarsa a makaranta fisabilillahi?" Sekuma tashiga kwala
ƙiran sunan Sadiya da Safiya,cikeda rashin gaskiya suka amsa dankuwa tun daga ɗakin
sunajin zancen dasu Auntyn suke maidawa.
Harsaida Aunty tayi musu kira akaro na biyu sannan suka fito a É—akin,irin kallon da
Fahad É—in kebinsu dashi kaÉ—ai seda yasa suka sha jinin jikinsu. Bakin Sadiya narawa
tace "Gamu Aunty" Aunty zuba musu idanu tayi cikeda son karin bayani sannan tace
"Wai meya faru har Zunnurain yabar Rukayya a makaranta?" Safiya ce tayi sauri tace
"Muma bamu saniba Aunty" Fahad dakebin Sadiya daketa rawarr jiki da kallo strictly
yace "Sadiya meya haÉ—aku da Rukayya a makaranta dahar yasa Zunnurain yabarta?" Dan
for sure yasan koba hannun Safiya a al'amarin toh akwai na Sadiya sabida yanda take
trembling kaÉ—ai zaisanar da mutum komai and moreover yasanya Sarai,yasan intana da
gaskiya inma batada shi dankuwa tsoron ta ke tona mata asiri akoda yaushe.
Baki na trembling Sadiya tace "Babu fah Yaya Fahad" cikin tsawan da Fahad baitaba
yimasu irin saba yace "You're lying My friend!" Kafin yayi sauri yaja igiyar
charger dake jikin extension wire É—in TV yashiga nuna mata yana faÉ—in "Zakiyimin
bayani ne kosai na faffasa mikijiki yanzunnan?" Aituni Sadiya ta rude tafara kuka
ayayinda ko Ina ajikinta ke aikin yin rawa,cikin in Ina tace "Zanfada! Wallahi
zanfada Yaya Fahad! Karkaaaakarka dakeni don Allah zanfada" tsaki Fahad yayi sannan
ya ajiye igiyar chargern yana mamakin tsoro irin nata yace "inajinki toh"
Baki na rawa Sadiya tashiga bashi labarin abubuwan dasuka faru a makarantar dukda
kuwa irin hararar da Safiya take tayi Mata nakar ta faÉ—a É—in anma tsoron Yaya Fahad
É—in dakuma dukan dataga yake shirin yi mata bazai bari ta iya yin shiru ba.
Tanakaiwa aya Aunty tafara sallallami baki sake,rai bace tajawota takwada Mata Mari
tana faÉ—in "Sadiya tarbiyar danayi Miki kenan? How can you stoop this low? Is this
how I raised you?" Sadiya dai Inbanda Kuka babu abunda takeyi tana bada hakuri.
Aunty jibgarta tashigayi tako Ina tana zaginta rai ɓace,tace "Kinason kicemin
Hassada kikema Ƴar uwarki komi? Sokike kicemin you're not grateful with your
performance dahar sena wani ya tsole Miki idanu? KeÉ—in meya hanaki yin zuciya kiyi
karatu kici dakanki harsai kinyi ma wani bakin ciki danya fiki" Baki na rawa Sadiya
tace "Aunty wallahi su Yaya Safiya ne suka zugani inyi" wani kallo Aunty Tama
Safiya dake gefe tace "Abunda kuke koyamata a boarding din kenan koh? Toh bari
Babanku yadawo duk zakuyi masa bayani dan nasan komi zanmuku bazan huce takaicin
abunda kukayin nanba" cikin sauri Fahad yace "And before Abba comes back I'll deal
with them first" Rai bace Aunty tace "Dakoh kayimin daidai" fuska daure Fahad
yadubi Safiya yace "jeki kiramin Aisha,Zaheera, Zunnurain suzo yanzunnan dukansu"
gyada kai Safiya tayi sannan tatashi tafice cikin sauri hartana tun tube.
Littafin Qadr na kudine duk maiso should talk to me via WhatsApp through this
number 08147722806.
*Baza kuna samun long page kamar su RAYUWAR BINTU ba tunda za munayi kullum insha
Allah. Nasan nayau yayi kadan anma insha Allah zan nayin kokari inyi like 5 to 6
readmores insha Allah*
*Page Forty Three*
Bayan fitan Safiya se Aunty tadubeni cikeda tausaya wa tace "Babu dai wanda kika
samu matsala dashi a makarantar da aka barki koh?" GyaÉ—a matakai nayi ahankali.
Tace "toh yanzun kinci abinci ne?" nanma gyaÉ—a matakai nayi sannan nace "Yaya Fahad
yasayamana ahanya" Aunty jinjinakai tayi sannan tace "toh tashi kikai class bag É—in
naki cikin É—aki sekiyi sallah ki kwanta ki huta Koh?" gyaÉ—a mata kai nayi sannan
natashi ahankali ayayinda nasaci kallon Yaya Fahad dake danne danne cikin wayarsa
kafin najuya nayi shigewata É—aki inaji inama abunnan yatsaya hakanan basai anyi
furthering dinshiba because the more su Sadiya will be purnished the more nima
nasan zansha wahala arayuwa,toh anma inada bakin cewa kar a hukunta su É—inne?
Banidashi shiyasa nayi tafiyana kamar yanda Auntyn ta umarceni hakanan inaji Sadiya
tanata sheshekar kuka anan tsakiyar parlourn
***
Safiya nabarin parlourn Auntyn kuwa straight parlourn Ummi tawuce. Aisha,Zaheera
dasu Mariya kaÉ—ai tasamu a parlourn dankuwa Ummi bata jima da shiga yin sallar
isha'i ba dan saida takalli wani Series sannan tashiga ciki kuma tunda tashiga bata
sake fitowa ba. Su Zaheera naganin Safiya tashigo parlourn daman suka tashi sukayo
kanta dan Sule daman yakai musu gulmar yaga sanda Fahad da Rukayya suka shigo dazu
suka kuma zo sukaji kukan Sadiya wanda hakan yatada musu hankali yasa su fara
tunanin ko asirin su ne ya tonu.
Aisha ne takalli Safiya sannan tace "Ya naganki wani iri? Meyake faruwa newai?"
Safiya tace "Hmm atakaice dai yau kashin mu yabushe kawai shine abunda zan iya ce
muku. Kuzo Yaya Fahad na kiranmu duka yana parlourn Aunty" a kidime Zaheera tace
"Akan wani dalili yakeneman mu?" Safiya tace "sabida yasamu labarin abunda muka ma
Rukayya. infact shiyaje ya É—auko ta ma,tare suka dawo badajimawannan ba" seta juya
cikin sauri tana faÉ—in "nidai kunga tafiyata,zanje inkira Yaya Zunnurain mu haÉ—u
acan parlourn Auntyn kawai kada Yaya Fahad yazo yaci ubana yace nabata masa lokaci"
daganan Safiya tayi ficewarta a É—akin jiki na rawa. Kallon juna Zaheera da Aisha
sukayi akidime kafin Zaheera tayi sauri tashige É—akin Ummi tana kwala mata kira.
Bin bayanta Aishan ma tayi, Ummi dayanzu ta'idar da sallahn tana ƙoƙarin ninke
sallaya ahassale takalli Zaheera da Aisha dasuka shigo É—akin kamar wanda aka jefosu
daga sama sannan tace "Wai wannan uban kiran na menene haka sekace bakusan inda
nakeba?" Zaheera a rude tace "Ummi Yaya Fahad ne ke kiranmu" harara Ummi ta watsa
mata dukda tayi mamakin wai yau Fahad ke kiran kannensa anmaseta ɓoye mamakin nata
tace "Daya kirakun kuma se akayi Yaya? Kuje mana kukasani ko tsaraba yayi muku"
Aisha kamar zata fashe da kuka tace "Ba tsaraba yamana ba Ummi. Cin ubanmu zaiyi
wallahi" wani kallo Ummin tamata sannan tace "Cin ubanku kuma? Akan wani dalili?"
Aisha tace "Sabida yasamu labarin anbaro Rukayya a makaranta. Shida kanshi yaje
yaÉ—auko ta" Baki sake Ummi tace "Wace Rukayyan kuma?" dandai ita hartagama
lissafinta akan Rukayya, gaba-daya a tunaninta tunda taga dare yayi Rukayya
batadawo ba toh tawuce Babban buli ne Koh GiyaÉ—e wanda har hakan yasa tariga tagama
kissima abunda zata faÉ—ama Kawu Sani inya dawo baisamu Rukayyan agida ba.
Aisha tace "Wallahi kuwa Ummi! Yanzunnan ya Aiko Safiya takiramu kuma daman bayan
shiganki É—aki yin sallah bada jimawa ba Sule yace mana yaga sanda suka shigo ranshi
a bace kuma muna parlour ma munji kukan Sadiya daman" Ummi setace "toh shidin waya
faÉ—a mishi?" Zaheera kamar zatayi kuka tace "Oho" se Aisha tace "Hmmmm yawuce
Rukayyan ne taje tasamu Uncle Adam tasanar dashi shikuma ya kirashi yafaÉ—a masa
tunda daman abokin sa ne" Zaheera cikin sauri tace "I doubt zata faÉ—ama wani
kobakiga irin yanda take tsronmu baneba?" Aisha tace "toh ya akayi yasani inba faÉ—a
É—in tayiba?" Se Zaheera tace "sede in sun haÉ—u ne kotaje karban kuÉ—in mota kan
anmantata a school shine shikuma ya kira Yaya Fahad É—in ya faÉ—a masa" Aisha tace
"toh ya akayi yasan meyafaru har yake neman mu?" Tsaki Zaheera tayi danta fara Jin
haushin silly questions É—in Aishan sannan tace "koma wayene yafaÉ—a mishi shouldn't
matter right now. Damuwar mu ayanzu shine musan yanda zamuyi mufidda kanmu acikin
maganarnan" wani kallo Aisha tama Zaheera sannan tace "Ah tunanin ki zamu iya fidda
kanmu ne wancan matsoraciyar tana gurin? Ai wallahi tonama kowa asiri Sadiya zatayi
I'm very sure about that" cije lebe Zaheera tayi sannan tadubi Ummi with pity face
tace "Ummi yanzu yazamuyi don Allah" tsaki Ummi tasaki sannan tace "Yakoh zakuyi
dayawuce kuzuba ma sarautar Allah ido. Koh da atunaninku barin shi zanyi ya hukunta
ku inyi shiru batareda nace komai ba?toh wallahi yayi karya yakwana da yunwa.
Yadaki kannen nasa wannan damuwarsa ne anma kukam bazai taɓa ku inkyaleshi akan
wata shegiya Rukayya ba" take se su Zaheera suka fara murmushin Jin daÉ—i,Ummi tace
"Kuyi gaba ganinan biyoku a baya kada ma kuwani tada hankalinku" Ummi ta karashe
Maganar ayayinda ta ajiye sallayar datagama ninkewa akan bedside É—inta sannan
tashiga ƙoƙarin cire hijabin dake jikinta zata sauya kayanta.
Aisha da Zaheera gyaÉ—a matakai sukayi sannan suka fice a É—akin nata suka nufi
parlourn Aunty.
Yaya Fahad,Aunty da Sadiya dake ta aikin kuka a tsakiyar parlourn kaÉ—ai suka samu
agurin,ma'ana Safiya da Zunnurain basu isoba. Samun guri sukayi suka zauna kamar
wasu mutanen kwarai tareda gaishe da Aunty,amsawa Aunty tayi ciki ciki sannan suka
gaida Fahad dako kallon inda suke baiyiba barema susa ran zai amsa musu gaisuwar
tasu. Zaheera ce tayi karfin hali tace "Yaya Fahad gamu wai kana kiranmu" nanma
shiru kakeji baice musu komaiba.
Sekawai taja bakinta tayi shiru,not long after shigowartasu kuma sega Zunnurain da
Safiya sun shigo. Ciki ciki Zunnurain É—in yagaida Aunty yanata wani kumbure kumbure
ta amsa sannan yagaida Fahad dako kallonsa baiyi ba bare yasa ran amsa gaisuwar
tasa. Sunfi mintuna uku zaune a parlourn shiru kafin Fahad É—in ya ajiye wayarsa
dake hannunsa agefe,ya daga ya kalli Zunnurain sannan politely yace "Meyasa kabaro
Rukayya a makaranta da aka turaka kaÉ—auko su?" Fuska murtuke Zunnurain yace "Yaya
bakaji abunda tama Sadiya baneba" cikin tsawa Fahad yace "Is that a genuine reason
dazaka bar Ƴar mutane a makaranta? What if something bad had happened to her mezaka
cema Abba?" Zunnurain yace "I thought she'll know the way home tunda tasaba shiga
motar kasuwar shiyasa namata haka" Rai ɓace Fahad yace "Watasani a Azare? Kota taɓa
zuwa garin ne dazakace zatasan hanyar gida? Anya kanada Imani Zunnurain? How can
you do this to a small child like Rukayya?" Cikin tsananin ɓacin rai Fahad yace "I
thought you're sensible and mature by now but I was very wrong,dagakai harsu
Safiyan bakuda banbanci. Shekaru kawai kafisu anma hankalin ku duk É—ayane" shidai
Zunnurain baice komaiba kanshi nakasa yanajin faÉ—an da Fahad É—in keyi masa.
Yace "instead of you to purnish the right person anma sekake purnishing innocent
Rukayya! Well you might think this's love,you might think you did the right thing
by purnishing Rukayya akan laifin da batayi ba dan karama ma Sadiya abunda tajamata
but believe me you're ruining your own fleshy bloods future,you're ruining Sadiya,
Safiya,Aisha and Zaheera. You're putting them on the wrong track sabida abunda kayi
dashi zasuyi koyi dashi. If you're backing them a irin abubuwan dasukeyi dinnan yau
in akace babu Abba,Babu ni Babu Salim waye zaiyi musu gyara? Waye zaiyi musu
tarbiyar dazasu shiga ko Ina dashi batareda sun tabe ba Zunnu?" Fahad yasauke
ajiyar zuciya sannan yace "Kai bazanyi purnishing É—inka dakaina ba kamar yanda
zanyi masu" yayi maganar yana nuna su Zaheera,sannan yakarada "I'll leave that to
Abba anma one thing is for sure dole kabama Rukayya hakuri and if you decide not to
ananne zakayi forcing É—ina inyi overlooking shekarunka inyi maka hukunci yanda
yadace dakai" seya juya yakalli su Zaheera dasukayi tsuru tsuru da idanu yace
"watarku tashiga É—aki ta kiramin Rukayya" jikina bari Zaheera tatashi tashige É—akin
dasauri. ba'ajima ba sega su sunfito tareda Rukayyan.....
Seda suka zauna sannan Fahad É—in yadubi Zunnurain yace "Oya apologize" Zunnurain
fuska murtuke kamar bayason yin magana yace "I'm sorry" batareda yadubi Rukayya.
Nidai bance komaiba inbanda bugu da zuciyana keyi,inaji Yaya Fahad yakoma kansu
Zaheera yace suma duk subani hakuri kuma duk sesukayi kamar yanda yace É—in batareda
sunyi masa musu ba dukdama fuskar su kaÉ—ai yanuna hakurin dasuka bani É—in bawai
yakai har zuci baneba inda daganan kuma yadubi Zunnurain yace "You may leave" take
Yaya Zunnurain yayi fuskar tausayi sannan yace "Yaya don Allah kada ka faÉ—a ma
Abba" harara Fahad ya watsa masa sannan yace "Kasan kana tsoron Abban kayi abunda
kayi?" Kara marairaice fuska Zunnurain É—in yayi sannan yace "Nidai kayi hakuri don
Allah. Wallahi bazan karaba" sesu Zaheera ma suka shiga taya Zunnurain É—in bada
hakurin kada a faÉ—a ma Kawu Sani. Tsawar da Yaya Fahad ya musune yasasu yin shiru
lokaci guda,yace "Will you all be Quite! Kune zaku faÉ—amin abunda zanyi dawanda
bazanyiba?" gabadaya sesukayi shiru, Yaya Zunnurain sumui sumui yatashi yafice jiki
sanyaye ayayinda Yaya Fahad yadubi su Yaya Zaheera yace sutashi suyi tsallen kwado
kowa 20×,up and down ma 20×.
Babu wanda ya iya yakuma cewa komai sema yin abunda Yaya Fahad É—in yasakasu take
dankuwa yanayin fuskarsa kaÉ—ai yasanar dasu babu wasa a tattare da lamarinsa.
Nidai inagani zasufara serving punishment ɗin sena fara ƙoƙarin tashi zantafi anma
kuma sega sallamar Ummi abakin kofar parlourn Aunty.
Aunty ne ta amsa mata sallamartata ayayinda tashigo parlourn,zubama su Yaya Zaheera
daketa tsallen kwado idanu tayi sannan tasaki baki tace "Menake gani? Kukuma yada
haka? Punishment É—in makarantar bata isheku bane kukazo kukeyin wani agida kuma?"
Aunty murmushi tayi dankuwa tabbas tasan Ummin tasanda labarin shiyasa tabiyo bayan
Ƴaƴanta inbahakaba yaushe take shigo mata sashi haka kawai? anma seta boye sanin
datayi ɗin,tace "bismillah ki ƙaraso mana Ummin Mariya. Laifi sukayi ake hukunta
su" cikin sauri Ummi tace "wani irin laifine haka dahar za'ayi musu irin wannan
horon?" Wani murmushin Aunty tasaki tareda girgizakai sannan tace "Kanwarsu da
Yayansu sukayima laifi!" Ummi seta dubi Zaheera kamar gaske tace "Ke Ƴar nan
mekukayi?" tsayawa Zaheera tayi tana nishi kamar meshirin yin kuka sannan tabama
Ummi labarin komai kamar wanda daman Ummin batasa komai ba tun asali.
Ummi salati da sallallami tafarayi sanda Zaheera tagama bata labarin sannan tace
"Toh yanzu fisabilillahi ku miye laifinku anan dahar za'a hukunta ku? In akwai
wanda yakamata a hukunta ai Rukayya ce sabida itace munafuka. ataimakeki arika ki
agida sannan kice zakifi karfin Yaran masu gida? Allah yagani nidai banga laifin
Yarannan ba,abunda sukayi ba karamin burgeni yayi ba kuma da inada hali ma kyauta
zanyi musu"
Baki sake Aunty tace "Basuyi laifi bafa kikace Ummin Mariya?" gyara tsayuwa Ummi
tayi sannan tace "Eyi! Yoh Ina laifin anan? Nemafa suke sukare soyayyar ubansu
garesu dankuwa wallahi insukace zasuyi wasa shedaniyar Yarinyar nan kwace musu
ubanma zatayi gaba É—aya!" Ummi tayi tsaki ayayinda tazuba ma Aunty idanu tace "Wai
ke sekace bakisan waye matar Umaruba? Sekace bakisan irin asirce uban Yarnan
datayiba tunma kafin suyi aure? Toh yanda take haka Rukayyarnan take kuma wallahi
indai yaranmu damu bamu tashi tsaye ba wataran zamu wayi gari megidannan yazabeta
sama dasu shiyasa gwanda tun wuri muhadu muyiwa tufkar hanci" Aunty data kasa ɓoye
mamakinta tace "Anma Ummin Mariya kinbani mamaki da maganganunkinnan! Yara sunyi
laifi ana musu gyara anma ke kina faman ki goya musu baya? Aiko mi Mahaifiyar
Rukayya tayi abaya baikamata suyi abunda sukayi yaudinnan ba dankuwa wannan É—inba
tarbiya baneba ba. Kuma a Ina Kika taɓa gani laifin wani yashafi wani
fisabilillahi? Dukdama nidai ban taɓa yarda daduk wani kazafi dakukeyi ma ita
marigayiyar ba" taɓe baki Ummi tayi sannan tace "Uhmmm kekam daman ina zakiga
metayi tunda ba yini kike tareda itaba barehar kiga abubuwan datayi tayimana É—in
daga ita har Mijinta. Batun laifin wani baya shafan wani kuma bekamata ma akawo shi
cikin zancennan ba dankuwa gashinan ƙarara Rukayya tayi ma Yara laifi tunda tana
ƙoƙarin shiga tsakaninsu da ubansu" Aunty dai tsabar mamaki kasa cewa komai tayi
inbanda kallon Ummin data tsayayibaki sake.
Ummi kuwa nagama bama Aunty amsa seta dubi su Zaheera daketa up and down danhar
sungama tsallen kwandon tace "ku kubar punishment É—innan kuzo mutafi,bakuyi laifin
komaiba sabida haka bamai hukunta min ku! Zakuji da huce wahalar dakuka shawo a
makaranta ne kokuma da serving wani wahalar kukazo yi agida. Yara Basu huta a
makaranta ba yanzu sundawo gidanma baza'a barsu suhuta ba"
Aunty da abunda Unmin tayi yamatukar batamata Rai setace "Anmadai Ummin Mariya
bekamata kice subaryin abunda Yayansu yasaka suba. Wannan tsakaninsu dashi ne be
kamata mu manya mushiga ba" taɓe baki Ummi tayi sannan takalli Aunty tace "Waye
Yayan nasu? Wannan Yayan nasu kike nufi?" Ummin tayi magana tana nuna Fahad datunda
tashigo É—akin kansa ke sauke akasa.
Rai ɓace Ummi tace "Ina yanaganina nashigo dakinnan gashi har Ina shirin fita ko
gaidani baiyiba. Dabaiga darajana ba ta'ina zance Ƴaƴana suyi masa biyayya? Akan
wani dalili?" seta maida dubanta gasu Zaheera akafule tace "ku kuzo kuwuce mutafi
nace koh! Kudai danahaifa dakaina ina da iko daku kuma inada ikon hanawa ayi muku
abunda baigamsheni ba nake kuma ganin zai cutar daku sabida haka maza kuwuce
mutafi" kallon Fahad Zaheera da Aisha sukayi cikeda tsoro batareda sunyi abunda
mahaifiyar tasu taceba harsaida takuma daka musu wani tsawa tace "Wainikam ba
magana nakeyi muku baneba?" Cikin sauri sesuka fice a É—akin inda tabi bayansu
tanata masifa.
Fahad daranshi yagama mugun ɓaci seya tashi zaifita adakin. Cikin sauru Aunty tace
"Fahad koma kazauna?" Fahad yace "Aunty I'm not following them. Sashin mu zantafi"
Aunty na kallonshi tace "Nasani! Still kakoma kazauna" komawa yayi yazauna ayayinda
yakejin zuciyar shi nayi mashi Kuna,wannan na É—aya daga cikin abubuwan dayasa baya
shiga harkar yaran gidan baki É—aya sabida dukyanda kaso kayi gyara se ansamu wani
babba yaja maka raini gurin yaran. Dubanshi dakyau Aunty tayi sannan tace "Meya
hanaka gaishe ta datashigo?" Fahad kamar bazaiyi magana ba sekuma tace "Aunty yaune
fa kaÉ—ai bangaidata ba and nasan abunda zai biyo bayakenan shiyasa ko kallon inda
take banyiba datashigo" Aunty setace "Komadai menene bekamata kaki gaidataba! She's
like your Mother and she deserve some respect no matter what Fahad. So dagayau
karka sakeyin irin haka" gyada kai Fahad yayi sannan yace "Insha Allah" Aunty seta
karada "And about what she did kayi hakuri! Insha Allahu in Abban ku yadawo nida
bakina zan faÉ—a masa inyaso shi seyayi addressing issue din! Shikam ai bata Isa
tajada Shiba nasani" shindai Fahad baikuma cewa komaiba se tashi dayayi yafice a
parlourn bayan Auntyn ta sallameshi dukda kuwa aranshi yagama rayawa zaisamesu ya
kashe musu warning akan insuka karama Rukayya abumai kamarhaka he'll not hesitate
to deal with them sequarely.
Bayan fitan Yaya Fahad Aunty seta dubi su Yaya Safiya tayi musu faÉ—a sosai da
nasiha kafin tasallame mu baki É—aya tace mushiga ciki mukwanta dare yayi. Nidai
gaba É—aya atsorace nike kuma dabadan Aunty tayi kane kane a parlour taki shiga
É—akinta ba babu abunda zaihanani fakan idonta intafi inda nasaba kwana.
Muna shiga samun guri nayi a jikin bango nazauna na takure guri É—aya kamar munafuka
ayayinda nasauke kaina kasa,harlokacin Sadiya batabar kukan dataketa aikin yiba tun
É—azu,Yaya siyama dake karatun Hausa novel ne tadago tashiga kallon mu baki É—aya
kafin tadubi Yaya Safiya daga karshe tace "Wai meya farune naji anata hayaniya a
parlourn Aunty?" taɓe baki Yaya Safiya tayi sannan tace "maganar jakar yarinyar
nanne mana akeyi" É—agowa Yaya Siyama tayi takalleni ayayinda Safiya tanuna matani
kafin tasake maida dubanta ga Yaya Safiyan tace "yanzun meya faru? ba tacemin Yaya
Fahad ne yadawo da'ita ba? What's the commotion all about kuma?" dankuwa tun
shigowana É—akin nafarko É—azu tatambayeni sanda nadawo inda nace mata Yaya Fahad ne
yaÉ—aukoni and from then seta cigaba da karatun littafinta batareda tasake bitakaina
ba harna sake fita zuwa parlour da Yaya Safiya tazo ta Kirani sanda Yaya Fahad ya
aikota.
Yaya Safiya labarin abunda yafaru kaf tabama Yaya Siyama kafin daga karshe tadubeni
rai bace tace "ke! Barikiji kadama kiji da wai ance mubaki hakuri munbaki kice zaki
farayi mana tsifiri da iyayi! Wallahi mark my words abunda kika jamana yau insha
Allahu wataran semun rama! dankuwa bazan taɓa mantawa da ranarnan a tarihin
rayuwataba" inaji Yaya Siyama tace "Yadai wuce yanzu! Duka kuyi hakuri kunemi guri
kukwanta dare yayi" se Yaya Safiya tayi tsaki tace "ta Ina mutum zai iya baccI!
Bayan tunyanzu kafafuna sunfara yimin tsami" Sadiya dake sheshekar kuka tace "nikam
gaba É—aya jikinama ciwo sukeyimin wallahi! Ga dukan da aka min a makaranta gakuma
punishment É—inda mukasha yanzu. Allah yataimakemu ma Unmi tazo tatsaida abun"
Safiya tsaki takuma saki sannan ta karasa kusa da wordrob tashiga cire kayan
jikinta tasauya zuwa kayan bacci da alamadai haushin Sadiyar ma takeji. tana gama
canza kayan kuma senaga ta nufi kofar É—akinsu tashiga leke ahankali.
Wani tsaki nakumaji ta buga sannan tajuyo takalleni strictly tace "Daman Aunty
Nashigewa É—aki kisan inda dare yayi miki dakeda tsummokaran kayanki dan bazamu iya
kwana É—aki É—aya dakeba kimaji kisani" gyaÉ—a kaina nayi ahankali ayayinda naji wasu
hawaye nashirin zubomin. Nikaina bason kwana dasu É—in nikeyi ba daman dankuwa
kwanan kitchen É—in yafiye min kwanciyar hankali akan inkwana dasu Ina tararradi
tareda tunanin kowani numfashi zanyi a tsorace zanyi sa. Inagani Sadiya tasauya
kayanta zuwa na bacci sannan ta shimfida karamar katifarta da ledan fitsarinta
asama sannan tahau takwanta ayayinda Yaya Siyama da Yaya Safiya kuma ke kwance kan
gadonsu.
Haka nadinga leken kofa akai akai ko Auntyn zatabar parlourn insamu intafi amma har
shabiyu ta gota batabar gurinba dankuwa daga karshe ma Jakarta ta É—auko da takardun
kasuwancin ta tazauna a parlourn tana lissafe lissafe abunta. Bacci nikeji bana
wasa ba anma tsoron kar inkwanta baccin inkasa tashi har asubahi tayi su sameni a
É—akin yasa nakasa yin baccin nacigaba dazama inajira Aunty tatashi a parlour
infice. Se wuraren É—aya naji tana rufe kofar É—akinta,seda nabari kamar bayan 5
minutes da shiganta sannan natashi nafita a É—akin nabar sashin nasu baki É—aya.
Gurin kayana na gida dake main parlour nanufa nacire uniform É—ina nasauya zuwa
kayan gida sannan natafi can kitchen É—in wajen nayi shimfida nayi kwanciyana.
Najima Ina tunanin me Yaya Safiya zasuyimin dabazan taɓa mantawa dashi a rayuwana
ba kamar yanda tafaÉ—a É—in?dankuwa nasan kamar yanda tafada É—in toh tabbas haka take
azuciyar yan uwan natama. They'll surely take vengeance. Ni damuwana ma baiwuce
faɗama Kawu Sani da Aunty tace zatayiba,ninasan hakan ba ƙaramin sake hura ma abun
wuta zaiyiba even though bansan wani irin mataki Kawu Sanin zai É—auka akansu ba.
Daƙyar nasamu nayi bacci ranar inda anayin sallar asubahi kuma natashi nahau yin
aiki kamar yanda nakeyi da danake gidan. Girkin Aunty ne dankuwa daga kwanukan da
akaci abinci jiya nagane hakan. nasan danazo midterm break akwai Mai aiki anma ai
yanzu munyi hutu,banida tabbacin ko an sallameta ko ba'a sallametaba shiyasa ma
nayi deciding yin aikin kawai. Ina cikin yin wanke wanke kawai Sega Yaya Salim nan
yazo,daga yanayinsa nagane daga masallaci yayo Nan ko sashin su baikoma ba dankuwa
haryanzu gari baigama yin haske ba.
Dafari dana hangoshi bakaramin tsorata nayiba dankuwa har tashi nayi zan ruga
dagudu wanda hakan yasashi saurin cewa "Rukyn Baba Salim nedai" komawa nayi nazauna
Ina sauke ajiyar zuciyar. Karasowa yayi inda nake yanayima tsorona dariya ayayinda
yake girgizakai sannan yace "Wai daman kema kinada tsoro Rukayya? I thought you're
a brave girl keba irin Sadiya baceba" murmushi nayi sannan nace "Yaya Salim aigari
baiyi haske ba shiyasa na tsorata. Nadauka ghost ne" dariya yake sosai wannan
Karan,dakyar yatsaigata dariyar tasa ayayinda yazauna agefena Yana fadin "toh Wai
dakika tashi Zaki gudun Ina zakije?" Ina dariyar Nima nace "cikimana zangudu"
playfully yace "se akace Miki ghost din kuma bayabin mutum harcikin gida" nace
"Nidai bana guduba! I was just running for my life" yakumayin Yar dariya sannan
yacanza topic din zuwa wani.
Yace "yanzun kinyi sallah ne dakika zauna zakiyi wanke wanke?" gyaÉ—a masakai nayi
Ina murmushi,seyace "Still it's too early Rukayya,dakin bari se gari ya waye. Mura
Yana iya kamaki" yayi maganar cikeda care.
Nace "Bafah wani sanyi Yaya Salim!" seya É—auke idanunsa dagakan kwanukan wanke
wanken yamaida kaina,in a low tune yace "Kindai dage sekinyi wanke wanken yanzu
kenan?" dariya kawai nayi bance komaiba ayayinda naÉ—auki cup É—in da ke gabana na
fara wanke shi. Da mamakina senaga yazuro da kafafunshi cikin gurin wanke wanken
sannan yamatsa É—ayan side É—in yana fadin "toh tunda bazaki hakura ba barina tayaki
muyi tare mugama da wuri" ware idanu nayi dasauri sannan nace "Yaya Salim don Allah
kabarshi zanyidai" memakon Inga ya hakura kawai senaga yasa hannu yakarbi cup É—in
hannuna dana wanke yashiga daurayewa. Hankali tashe nace nayi sauri nakarbe cup É—in
a hannun sa ina faÉ—in "Don Allah katashi anan gurin Yaya Salim" dankuwa ni bawai
tayani dayace zaiyi bane damuwana. Damuwana kada wani yazo yaganshi yana tayani
wanke wanke hakan yajamin wani bala'in Kuma.
Littafin Qadr na kudine duk Maiso should talk to me via WhatsApp for payment
details through this number 08147722806.
*Page Forty Four*
Amma da mamakina se naga yasake karban cup É—in ahannuna yacigaba da daurayewa. Yana
murmushin danasan baikai har zuciba yace "Nasan kina tsoro kada Ummi tafito taga
Ina tayaki aiki ne kokuma su Mariya su fito suganmu suje su faÉ—a Mata Koh? but
believe me Ummi bazata fito yanzuba sabida yau ba girkinta baneba. Su Mariya Kuma
incase insun fito I know how to handle them" Jin abunda yace É—in senaji nazama
speechless gaba É—aya, senaji jikina yayi sanyi saka makon irin tune dayayi using
wurin furta kalaman sa. It clearly shows shima bahakan yakesoba.
Sekawai na sunkuya na É—auki wani cup nafara wankewa ahankali batareda nace masa
komai ba. Haka mukayi shiru harna kusan mintiuna goma,inbanda karan kwanuka bbu
abunda kakeji. Can senaji ya ƙira sunana.
Ahankali yace "Rukayya" É—agowa nayi na kalleshi sannan nace "Na'am Yaya Salim"
ajiye plate É—inda yagama daurayewa yayi cikin basket É—inda muke kifa kwanukan
sannan yamaida attention É—insa kaina baki É—aya,cikin sanyayyar murya yace "I'll
like to apologise to you on my Mom and siblings behalf akan abunda yafaru jiya. I
know you're going through alot because of them anma inason kisan cewa they're not
that bad you might think they're,they just've wrong impression about you and your
Mother from the very beginning shiyasa" yasauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya
sannan yace "Kiyi Hakuri Dan Allah. Kikuma cigaba da Hakuri for insha Allah wataran
komi zaizama tarihi" murmushin dayafi kuka ciwo nasakarmasa sannan nace "Bakomai
Yaya Salim karka damu. I'm absolutely fine" dukda kuwa araina Ina tunanin yaushe ne
ranar dazai zo har komai ya wuce gaba É—aya,har su Yaya Zaheera sudaina yimin irin
tsanar dasukeyi min yanzu? Har komai dayake faruwa acikin Rayuwata yanzu yazama
tarihi? Yaushe ne wannan ranar zatazo?
Seya kawar da zancen tahanyar yimin hira yana bani labarin jami'a dakuma irin
wahalhalun dasukesha wurin lecturers É—insu har muka gama wanke wanken Wanda
alokacin kuma har gari yafara haske sosai. kwandon wanke wanken yaÉ—aukamin yakaimin
kitchen ayayinda nabishi da tukwanen dana wanke ahannuna inayi mishi sannu da aiki.
Yace "Kimadaina yimin sannu Rukayya! In akwai wanda yakamata ama sannu aikene. Nida
ɗauraya kawai nike tayaki" Ƴar dariya nayi sannan nace "toh ai shima aikine" Yaya
Salim yace "Aganin kiba anma nidai aguna bawani aikin azo agani baneba" Ƴar dariya
nasakeyi sannan nace "Toh na gode" senaga yabata rai lokaci guda,yace "Godiyar ta
menene kuma bayan yanzu nagama cewa niba aikin komai namikiba" sekawai na
girgizakai in desbelief Ina murmushi batareda nakuma cewa komaiba.
Yananan tsaye kaina harnagama jera tukwanen dana shigo dasu a ma'ajiyinsu sannan
natashi tsaye Ina faÉ—in "Alhamdulillah nagama" Yana kallona yace "Seme zakiyi
next?" sincerely nace "Sharan backyard zanyi kafin afara maganar girki" cikin sigar
zolaya yace "toh muje intayaki" wara idanuna nayi sannan nace "Medin!!!" yanda nayi
maganar a firgice ba ƙaramin dariya yabashiba. Dakyar ya tsagaita dariyar tasa yana
faÉ—in "Rukayya Uwar tsoro. I was just kidding dannasan konace zantayaki dagasken ma
bayarda zakiyiba" cikin sauri nace "Bazan yarda bakam Yaya Salim. wanke wanken ma
danba yanda na'iya ne yasa nabarka katayani so kayi tafiyarka kaje ka huta. It's
still early in the morning" still yana dariya yace "Auuu yanzu kuma korata kikeyi
kenan?" Cikin sauri nace "A'a ba korarka nikeyiba nagadai kamar kagajine" seyayi
murmushi ayayinda yajuya yana fita a kitchen É—in yace "Toh Ruky ayi shara lafiya
tunda kinki intayaki" Murmushi namasa ayayinda nabishi da idanu Ina faÉ—in "A huta
gajiya".
Seda ya kulemin dagani sannan najuya naÉ—auki tsintsiyar dazanyi shara dashi nafita
a kitchen É—in nafara sharan Ina mamakin ya akayi su Safiya basu É—auki hali irinna
Kawu Sani dasu Yaya Salim ba. Ina cikin sharan backyard É—in kuwa sega Mai aikin
Aunty tazota, gaisawa mukayi inda take tambayana yaushe muka dawo daga makaranta
nace mata jiya.
Tace "Toh sannun ku da dawowa Yan makaranta" Ina murmushi Nace "Yauwa Sannu Iya"
karasowa tayi inda nake shara tamika min hannu wai inbata tsintsiyar tacigaba da
sharar ayayinda take faÉ—in "Aidama baki fara sharan ba waifa inata sauri inzo
inyine" Ƴar dariya nayi sannan nace "Karki damu ainama kusa gamawa" ganin naki
mikamata tsintsiyar setace cikin sauri "Toh bani tsintsiyar inkarasa" sunkuyawa
nayi nacigaba da sharar sannan nace "Kibar shi kawai Iya, zankarasa aisaura ma
kaÉ—an" Tace "Allah kikawo zanyi! Aikinma yi kokari" girgizamata kai nayi ayayinda
nacigaba da sharan danakeyi É—in Ina fadin "zankarasa karki damu. Kikama yin wani
aikin kawai" ganin nadage naki nabata seta hakura takyaleni takama harkar É—ora
abinci kuma. Inaga already tunjiya ansanar da'ita meza'ayi a breakfast.
Daman tunsanda nafara sharan backyard É—in su Mariya da Sadiya suka fiddo da kayan
fitsarinsu wanda hakan yasa Ina kammala sharan naje nawanke su tas nashanya sannan
nadawo Ina taya Iya aikin abinci. Bayan mungama ita taraba abincin inda nikuma
nakaima kowa nasa daga karshe kuma nadawo mukaci abincin tareda ita dankuwa yau
kason abinci harda ni akayi wanda inaga shine ranar farko da akayi hakan tunda nazo
gidan. Tunda lokacin damuka zo midterm break ma bawai wani taya Iyan aiki nakeyiba
itakuma inta tashi yin kason haɗawa takeyi danawa acikin nasauran Ƴan gida. Yau
É—inma tambayana tayi zanci yanzune shine nace Mata tazuba mana muci tare inbahaka
ba da haÉ—awan zatayi kamar kullum.
Adaren ranar Aunty tafita a girki inda Ummi tashiga wanda hakan yasa hankalina
yatashi dannasan it'll be very hard yin aikin dasu,dama yaya bare kuma yanzu nayi
laifi. Washegari bayan na idar da sallahn asubahi sena tattara wanke wanke zanyi
kamar yanda nayi jiya anma sede tunma kafin infara sega Yaya Salim yazo shi,
naÉ—auka yauma cewa zaiyi zai tayani wanke wanken dankuwa har na gama shirya abunda
zan faÉ—a masa anma da mamakina bayan mungaisa seya shiga tambayana kosu Yaya Aisha
sun fito. Girgiza masakaina nayi ahankali alamar A'a kawai senaga yanufi cikin gida
ta backdoor rai bace. Ashe tunjiya yamusu Assembly ya kashe musu warning akan
sudaina barmin aiki nikaÉ—ai,suna fitowa munayi tare.
Bayan kamar mintuna goma sha biyar segashi yasako su Yaya Zaheera agaba sunata
kumbure kumburen fuska. Akusa da inda nake wanke wanke sukazo suka tsaya sannan
yakalli Yaya Zaheera yace "Aiyukan miye da miyene yakamata kunayi kullum daman?"
Fuska murtuke Yaya Zaheera tace "shara,wanke wanke da girki ne" Yaya Salim yace
"Good! To dagayau keda kike babba kezakina yin girki, Aisha tayi shara inyaso ita
Rukayyan setanayi maku wanke wanke kunajina?" Cikin sauri se Yaya Aisha takalli
Yaya Salim Jin yace wanke wanke kaÉ—ai zannayi,tace "Wanke wanke kaÉ—ai fah kace
zatanayi Yaya Salim?" wani kallo ya watsa mata sannan strictly yace "Eh haka nace
ko kinada Jane?" Shiru tayi batace komai ba seya Yaya Salim yakarada "And innaji
wani Abu yacanza agame da rabon aikin danayi mukunnan kokuma innaji labarin
maganarnan yakoma kunne Ummi, believe me I'll surely deal with you sequarely Kuna
jina?" gyaÉ—a kai sukayi dukansu kafin yajuya yayi tafiyarsa yabar gurin.
Seda sukaga yatafi sannan suka fara kunkuni da mita! Yaya Aisha ta watsa min harara
tareda faÉ—in "Shegiya mayya kawai! Tukunnan ma wayasaki fitowa kiyi wanke wanke da
sassafe inbanda kilibibi da iyayi? gashi kinsa an katse ma mutum baccinsa yana
zaman zamansa!" Yaya Zaheera ma seta watsa min nata series of hararan,tace
"Munafurcin kuma wazaiyi mata! Taga shekaranjiya taci galaba akanmu wato shine
yanzu ta fito da sabon tsirin haÉ—amu da Yayunmu" seta zare min idanun ayayinda
tashiga nunani da yatsa tace "Toh wallahi kibar ganin kowani Munafurci kikayi kina
succeeding,akwai ranar kin dillanci and we'll surely take vengeance" daganan seta
juya tanufi kitchen afusace.
Yaya Aisha seta matso kusa dani sosai,tace "Keee! Juyo kikalle dakyau" da idanuna
da tuntuni suka fara zubar da kwallah najuya nakalleta,seta nunani da É—an yatsa
tace "Bawai dankinji yace kiyi wanke wanke kaÉ—ai ba kice shi kaÉ—ai zaki dingayi!
Sharan bayan nan kezakinayinshi haka ma main parlour dankuwa niba jakarki bace
dazanyi miki sharan inda kike yawan zama" gyaÉ—a matakai nayi ahankali, strictly
tace "And yes! Bawai Kuma nace kiyi sharaba sekinga yazo sannan ki tsiri yi
danyamin magana! I swear inkika yarda yaganki kina shara koda na rana É—ayane kikayi
putting dina a trouble toh ki kuka da kanki dakanki kafin ma mukoma makaranta" Yaya
Zaheera datagama debowa dankali tafito yanzu tana zaune abakin varender xata fara
fita tace "Kuma kiyi sauri ki ƙarasa wanke wanken nan kizo muyi aikin girkin tare
munafuka algunguma kawai!" gyaÉ—a matakai nayi ahankali ayayinda najuya nacigaba
dayin wanke wanke na.
Inajinsu itada Yaya Aisha, Yaya Zaheeran na rokon Yaya Aishan da tazo tatayata
firan dankalin kafin nagama anma setaki,tace bacci bai isheta ba komawa zatayi
takwanta seta tashi zatayi aikin da akace dole su zatanayi.
Niduk sena gwammace ma da Yaya Salim É—in baiyi musu maganaba,daya barni zannayin
abuna miyene aciki? Ina wataran sai labari? Kuma innayi aikin ai bawani abubane
zairagu a jikina ba. Haka nacigaba dashan tsangwama gurin su Yaya Zaheera dankuwa
mistake kaÉ—an zanyi suhauni da masifa da zagi,wani sa'in ma abun ba mistake É—in
baneba anma se anyi twisting É—inshi anmaidashi wani abu dukwai don su kuntata min.
Wannan hutun is like living in hell dan kallon banzan dasukemin kaÉ—ai inmuka haÉ—a
hanya ma ba ƙaramin firgitani yakeyi ba barekuma azo ga batun tsangwama. Bangaren
su Yaya Safiya ma basauki dan hardasu akemin tsangwamar dukdama su ranar girkinsu
bawani wahala nikeyiba tunda Aunty nada Mai aiki! Sharan É—akinsu dana Aunty kawai
nikeyi kuma duk a tunanin Aunty yanzu a É—akin su nake kwana tunda bazama takeyi
sosaiba,kullum dadare kuma sena tabbatar tashiga takwanta sannan nake barin É—akin
intafi makwanci na.
Satin mu É—aya da dawowa Kawu Sani yadawo daga Abuja,cikin yaran inaga Mariya da
sule ne kaÉ—ai ke farin ciki dankuwa gaba daya sauran a tsorace suke,tararradin
abunda Kawu Sanin zaiyi musu idan yasamu labarin abunda sukayimin sukeyi. Isowar
dare yayi wanda hakan yasa zuwa kawai mukayi muka gaisheshi mukayi Masa sannu
dazuwa sannan kowa yakoma É—akinsu.
Aunty ma batasanar dashi komai ba dukda kuwa ranar girkinta ne yadawo, inaga tayi
hakan ne sabida ganin irin gajiyar daya debo ahanya ne dankuwa na tabbatar data
sanar dashi aranar zaiyi addressing É—in abin anma from yanda yaketa sakarmana
murmushi damukaje yimashi sannu dazuwa dakuma yanda ya amsa gaisuwar mu faran faran
washegari dasafe daya shigo sashin namu kaÉ—ai zaisanar dakai baisamu labarin ba
tukunnan. Adaren washegarin ne nida Sadiya muna parlourn Aunty muna kallo ayayinda
Yaya Siyama da Yaya Safiya ke É—aki sega Auntyn tashigo wai Kawu Sani yana kiranmu
duka,yace kowa yaje da result É—inshi.
Cewa mukayi "toh" ayayinda nafita a parlourn don in É—auko nawa inda Sadiya kuma
tashige É—aki donta É—auki nata takuma sanar dasu Yaya Safiya sakon Kawu Sanin.
Result É—ina kawai naÉ—auka dan tun bayan abunda yafaru É—in naji kuma nuna ma Kawu
Sani gifts É—inda akabani a makarantar ma yafita araina. Kuma da da halima dakuma
inada yanda zanyi incire position É—inda akasakamin ajikin result É—in wallahi cirewa
zanyi.
Nina fara Isa sashin nasa inda nasamesu shida Aunty da Ummi azazzaune,tsugunawa
nayi nagaida su duka cikeda ladabi wanda Aunty da Kawu Sanin ne kaÉ—ai suka amsa
ayayinda Ummi inbanda uwar harara babu abunda take bina dashi....
Kawu Sani bayan mungama gaisawan yana murmushi seyace "Ina sauran Ƴan uwan naki
kuma?" Ahankali nace "Suna zuwa" seya kalli hannuna yace "Toh kawo muga result É—in
naki infara gani kafin su ƙaraso" Yakalleni playfully sannan yace "Hajiya Rukayya
kodai ba'ayi abun kirki bane naga kina ta rungume result din a kirji kamar bakyason
bayar wa" girgizamasa kai nayi Ina murmushi sannan naje nabashi result É—in. Aunty
dake dariya Jin abunda Kawu Sanin yace setace "Alhaji stop being judgemental so
easily kada kasha kunya yanzunnan" Ƴar dariya yayi ayayinda yake buɗe result din
nawa yana faÉ—in "Allah Koh! Tayi abun kirki kenan?" Aunty na murmushi tace "kadai
bude kagani da idanunka" Baki yasaki yana murmushi from ear to ear sakamakon abunda
yagani a result É—in nawa sannan excitedly ya dago yana kallona yace "Rukayya wannan
ai kincinye komai ma!" nidai murmushi kawai nakeyi dukda baikai har zuciba.
Yasake maida idanunsa kan result É—in excitedly yace "A's keta flying fah!" Aunty
dake ta murmushi tace "Wai baka duba possition É—in baneba?" yana murmushin yace
"ina na duba natsaya ina ganin excellent from A~Z ba amma ba induba yanzu" Aunty
juyowa tayi ta kalleni sannan tace "Ina kyautar da akabaki a makarantar? Ya baki
kawo yagani ba?" ahankali nace "namanta ne" Aunty kallona tayi naÉ—an dakiku kafin
tace "toh kije kidauko dan sarai tasan bamantawan nayiba, tsoro ne yasani kin
daukowa" gyadamatakai nayi sannan natashi zantafi anma senaji Kawu Sanin na faÉ—in
"Come here Daughter! Zokibani hug because I'm very proud of you today" karasawa
nayi inda yake nayi,seyajani zuwa jikinshi yarungume Yana faÉ—in "I'm so impressed
by your result Rukayya! Congratulations and keep it up" Ina murmushi nace "Thank
you" sakina yayi daga jikinshi sannan yace "Oyajeki dauko gifts din ingani kafin
nima inzo inbaki nawa kyautar" gyadamasakai nayi sannan nafita a parlourn cikin
sauri inata murmushi dankuwa dukyanda naso kar inyi farin cikin kasawa nayi yanzu
kuma.
A kofar parlourn na haÉ—u dasu Yaya Zaheera zasu shiga parlourn Kawu Sanin,kallo
É—aya nayi musu nagane gabadaya a tsorace suke anma senayi sauri naÉ—auke kaina nayi
gaba abuna.
***
Kamar wasu munafukai haka suka ƙarasa cikin parlourn Kawu Sanin,kowaccensu sewani
Jada baya takeyi bataso ace itace agaba. Aunty ne tafara lura dasu,fuska É—aure tace
"Yakuke ta wani nuku nuku? Ku ƙaraso mana" gyadakai sukayi ahankali atare sannan
suka karasa cikin parlourn suka samu guri suka zauna. Kawu Sani da tunda Aunty
tamusu magana yake binsu da idanu yace "Meya Faru naganku wani iri?" Aunty se ta
taɓe baki tace "duk rashin gaskiya ne yaja hakan" Kawu Sani da kanshi ya kulle yace
"Rashin gasjiya kuma? Mesukayi?" dankuwa kwata kwata baima sama ranshi cewa basuyi
ƙoƙari baneba tunda They're always average student,dukda yaso sudinga fita da
flying colours basu taɓa fita dashi ɗinba atleast they always try their best wurin
passing duka subjects É—inda sukeyi koda da credit ne duka and everytime suka kawo
sakamakon su encouraging É—insu yakeyi dasu sake dagewa.
Aunty Jin abunda Kawu Sanin yace setace "Katambayesu zasu faÉ—a maka" kallon su yayi
dukansu wanda hakan yasasu saurin sauke kansu kasa kowa bataso ace ita tayi magana.
Kawu Sani dayamaida full attention É—insa kansu yace "Laifin me kukayi ma Auntyn na
ku kuma?" Ummi data kasa yin shiru tun dazu tanata taɓe baki setace "Uhmmm bafa
wani laifin dasukayi! Wai danbasukai Rukayya yin ƙoƙari ba shine akeso amaida
maganar wata aba daban Kuma" Kawu Sani sauri yayi yaÉ—aga ma Ummi hannu alamar tayi
shiru dankuwa daga yanayin yanda take maganar kaÉ—ai yasancewa akwai wani abu a kasa
da take kokarin ɓoye masa. Yasake maida dubansa kan Ƴaƴan nasa wannan karan
strictly yace "Laifin me kukayi?" nanma shiru babu wanda yace komai..
Aunty tace "Bazaku buÉ—i bakii kufada ba kenan? Toh ni bari in fada masa tunda
bakina ba ciwo yakeyiba" Sadiya da already tafara kuka tace "Don Allah Aunty kiyi
hakuri" anma sede Aunty ko kallon inda take Auntyn batayiba,haka tashiga zayyana ma
Kawu Sani abunda sukayi É—in É—aya bayan É—aya! tunda take mishi bayani yadinga ji
ranshi nayi mishi wani irin kuna tareda Jin zafin abunda yaran nasa sukayi!
Tanakaiwa Aya kuwa Sega Rukayya tashigo Niki Niki da gifts É—inta a hannunta.
Dubanta yayi sannan yace "Rukayya ajiye abun hannunkinnan kikoma kije kikiramin
Zunnurain sannan kice yaciro tsumagiya yatahomin dashi yanzunnan"
Jin abunda Kawu Sani yace inyi kawai se jikina yafara rawa, daƙyar na iya na ajiye
gifts É—inda akabani a makarantar sannan nafice dan in aiwatar da abunda yasaka ni
inyi,sashin su Yaya Fahad na nufa Ina tunanin dawani idanu zan kalli Yaya Zunnurain
dankuwa tunranar da abun yafaru kallon dayakemin kaÉ—ai nasan cewa bakaramin zafi
yaÉ—auka ba and there's something behind that evill look! definitely yanason yimin
abunda zai huce takaicinsa anma something is really stopping, something dani kaina
banida tabbacinsa dukda nafi saka ran yana tsoron abunda zai biyo bayane inyamin
wani abu kokuma an kashe mishi warning ne. Sanda na'isa sashin nasu Yaya Fahad
kaÉ—ai nasamu a parlour yana zaune kan three seater ayayinda yaÉ—aura kafafunshi kan
stool inda ke ajiye agaban kujerar ayayinda kan cinyarsa kedauke da System yana
danne danne cikinsa. Sanye yake da Sandy brown jallabiya data matukar amsar
jikinsa,gashi gashinnan agyare tsaf yakwanta se sheki yakeyi kamar nawani ba indiye
ko balarabe. Sallama nayi bayan narufe kofar parlourn,banji sanda ya amsa min
sallamar ba anma motsin danaga bakinsa yayine yasa nagane ya amsa sallamar tawa
ciki ciki danhaka sena ƙarasa cikin parlourn,kusa da kujerar dayake zaune naje
natsaya sannan ahankali nace "Ina wuni Yaya Fahad" batareda ya kalleni ba yace
"Lafiya Lau" sekuma narasa mezance masa,sekawai nashiga wasa da fingers É—ina ina
kallon yanda yake aiki cikin system É—insa cikeda kwarewa da nutsuwa,gakuma
sanyayyar kamshin turarensa daya haÉ—u da sanyin Acn parlourn yagama gauraye ko Ina
gaba-daya yabada wani irin special scent nadaban. Contemplating nakeyi akan inwuce
ciki innemi Yaya Zunnurain É—inne ko in fara tambayarsa ko yananan.
Ɗagowa dayayi yakalle ni Jin nayi shiru ne yasani saurin sauke idanuna na ƙasa
nervously. Cikin sanyayyar muryarsa naji yace "Do you need anything?" girgiza masa
kaina nayi ahankali sannan muryata na É—an stammering É—inda bansan dalili ba nace
"Daman Yaya Zunnurain nake nema" still bedauke idanunsa daga kaina ba yace "What
about him?" ahankali nace "Kawu Sani ne yace inkirasa" sekawai yajefomin da
tambayar data bani mamaki. Yace "Waye Kawu Sani?" Wani irin wara idanu nayi
ayayinda na É—ago nakalleshi Ina faÉ—in "Ehhh?" Irin banji maganar tasa dakyau ba
kuma konajin ma ban fahimci tambayar tasa ba.
Anma sebe sakeyimin tambayar ba,kuma bai É—auke idanunsa daga gareni ba,ma'ana yasan
naji abunda yace and he want an answer from me. Rasa abun cemasa nayi danhaka sena
shiga rarraba idanu a parlourn kamar wata munafuka. Nafi mintuna uku Ina abu
É—aya,daga inraba idanu anan se in jefashi acan hakanan Ina ta wasa da fingers É—in
hannuna nervously kuma inajin intense gaze É—insa akaina,nikuma ba abun intafi ba
tunda baicemin ga inda Yaya Zunnurain É—in yakeba,baikuma bani permission É—in intafi
ba.
Can Sena tsinci muryarsa ahankali yana faÉ—in "It's Abba not Kawu Sani" dagawa nayi
nakalleshi dan in tabbatar shiyayi maganar koba shiba anma senaga yamaida
hankalinsa kan aikin dayakeyi É—azu yacigaba,wallahi dabadan nasan muryarsa baneba
dakuma ace akwai wani acikin parlourn bayan nidashi cewa zanyi bashine yayi maganar
ba. Ganin shirun bazai amfane ni da komaiba kuma su Kawu Sani sunacan suna jirana
sekawai na buÉ—i baki zansake tambayarsa inda Yaya Zunnurain É—in yake incase yamanta
ne anma sede tunkan inyi uttering wani word É—in seshi yarigani yin magana. batareda
yakalleni ba naji yace "Kije Yana zuwa" sekawai na gyaÉ—a mai kai ahankali sannan
najuya zanfita. Senaji kuma yakira sunana,yace "Rukayya....!" juyowa nayi
nakalleshi sannan nace "Na'am" anma senaga bani yake kalloba,aikinsa yakeyi
haryanzu.
Ahankali yace "KiÉ—auki Trayn abincin can kitafi dashi" gyaÉ—a masakai nayi batareda
nace komaiba sannan na nufi dinning area É—insu, É—aukar trayn nayi Ina mamakin
miyasa koda yaushe innazo É—aukan kwanukansu nake tararwa ba'a yi amfani da plate
guda ba,kuma koda yaushe abincin mutum É—aya seya rage wanda hakan kesani tunanin
wanene bayaci acikinsu. Nasandai ba Yaya Zunnurain baneba tunda shi sanda baswanan
ma inakawo Masa abinci nakanzo indauki empty foodflask ma. Atsakanin Yaya Fahad da
Yaya Salim ne to which I don't know wanene acikinsu. Take kuma se zuciyarta tashiga
rayamin "Kika Sani Koh a plate É—aya suke cin abinci kuma basuda wani ci sosai
shiyasa suke ragewa" taɓe bakina nayi Jin amsar danabama kaina ɗin be gamsheni ba
Kuma. ÆŠaukan trayn nayi nanufi kofar fita a parlourn ayayinda naji Yaya Fahad na
waya da Yaya Zunnurain yana sanar dashi sakon Kawu Sani. Ta backyard nabi naje na
ajiye trayn abincin a kitchen sannan najuyo nanufi sashin Kawu Sani,kusan zanhau
varendern Kawu Sani senaji an buÉ—e kofa daga can sashin su Yaya Fahad É—inda nabaro
bada jimawannan ba. Juyawa nayi dan Inga wanene senaga Yaya Zunnurain ne ke fitowa.
Sauri nayi nahau varendern Ina mamakin wai daman yana cikin sashin nasu anma Yaya
Fahad É—in yahana ni zuwa kiransa sannan shima kuma suna sashi guda suke Makinng
phone call? Girgizakaina nayi Ina mamakin abun ayayinda nashiga parlourn Kawu Sanin
inda nasamu su Yaya Zaheera duk suna kneel down,Koda Kawu Sani ya tambayeni Yaya
Zunnurain senace yana zuwa. Aikuwa ko mintuna biyu banyi da zamaba segashi
yashigo,Rai bace Kawu Sani yace "Ina tsumagiyar danace ace maka ka tsinko min?"
Yaya Zunnurain seyace "Ba'a fada min ba" strictly Kawu Sani yace "toh yanzu ai
nafada maka! Jeka ciro kadawo" juyawa yayi yafice dasauri ayayinda nakejin bugun
zuciyana nata karuwa akowani dakika,ni kwata kwata nama manta ance in ce yaciro
bulala Kuma Koda banmanta dinba ta Ina zansanar dashi tunda ogan naku baibari nama
hadu dashiba.
Yaya Zunnurain baijima ba yadawo,yanabama Kawu Sani tsumagiyar yace shima yajona su
Yaya Zaheeran yayi kneel down din. Fada yashigayi musu sosai akan abunda sukayi
din,yace "Wannan É—in wani irin shashanci ne fisabilillahi! kurasa wazakuma Hassada
se Yar uwarku? Kurasa wazakuma bakin ciki se Yar uwarku? Kuda yakamata inwani yayi
Mata abunda kukayi din ku shige Mata gaba anma seyazamanti kudin dakuke natan ne
kukeyi Mata bakin ciki? Inbaku so junanku tun yanzu ba ta Ina zumuntar ku zaizauna
bayan bamwanan?" Yadan numfasa sannan yace "in mutum yanason kaiwa wannan matsayin
shima seyadage yayi karatu kamar yanda tayi bawai Kai kakiyiba kakuma ce zaka yima
wani Hassada. Toh ni bazan lamunci irin wannan shashanciba! Inzaku hada kanku guri
guda kuhada kawunan ku kuso juna. Inna kuskura nasake Jin wani Abu kamar haka
yafaru toh ba karamin Saba muku zanyiba Baki dayanku Kuna jina" jikina rawa suka
gyadamasakai lokaci guda kafin daga karshe yama kowannensu bulala goma goma,Sadiya
biyar akayi Mata wai ita tunda tasha bulala a makaranta sannan ya kashe musu
warning yace insuka yarda wani kamar haka yasake faruwa saiya bata musu rai fiyeda
yanda yake tsanmani inda daga karshe yace subani hakuri dukansu. Haka suka bani
hakuri atake,shima yabani hakuri sannan yakarbi gifta dina yakalla yayi
congratulating Dina sannan yace "infada masa duk abunda nikeso zaisaya min" nidai
alokacin cewa nayi "Babu kawai" playfully yace "kodai hutu kikeso kije Babban
buli?" Aibansan sanda nagyada Masa kaina atake ba.
Dariya Kawu Sani yashigayi sannan yace "toh kifara shiri zuwa weekend se akaiki"
cikeda farin ciki nace "toh nagode" Yana murmushi yace "Anma fah sati guda zakiyi
kidawo because I want you to join islamiya like your other siblings kinji" dukda
banji dadin sati gudan da akace zanyiba anma sebance komai ba danko ba komai
dawowan nawa will be of my benefit,I really missed islamiya and I'm sure yan ajinmu
sunyi nisa sosai yanzu a karatu ni anbarni abaya Wanda inada tabbacin da ace yau
wannan islamiyar za'a kaini sede ayimin repeat dansu baswa son wasa da karatu anma
nasan bacan din za'a kainiba. Islamiyar su Yaya Zaheera za akaini.
Haka taron ya watse Ummi dai sai cika take tana batsewa wai Kawu Sani baibari
yatsaya yaji opinion dinta ba,dankuwa tunyana cikinyimana magana taketa son saka
baki anma yadinga hanata.
***
Tunranar da Kawu Sani yasanar dani zanje Babban buli hutu a weekend nashiga irgen
kwanaki,kamar yau in gari ya waye se ince saura kwana kaza inje Babban buli! Haka
gobe ma,haka jibima, haka gata ma har dai ranar alhamis ta zagayo. Tunda na idar da
sallar asubahi na tattaro kayan dattina tareda É—aya daga cikin guntun sabulun
danataho dasu daga makaranta nawuce laundry na cancada wankina dayake ranar ya
kasance girkin Aunty ne,banida wasu ayyuka dayawa akaina. Iya mai aikine keyin
yawancin ayyukan,nikawai tayata nikeyi daman dukda ma sau tari hanani tayatan
takeyi. Dayanman bayan nagama taya Iya tankade garin dazatayi tuwo dashi sena nufi
igiyar shanya nashiga tattare kayana É—aya bayan É—aya Ina ninkewa ina É—aurawa akaina
dayake duk sun bushe tun tuni.
Yaya Salim ne yazo backyard É—in yana kwala kiran sunana wanda hakan yasani juyawa
Ina kallon kofar mashigan main parlour É—in ayayinda nakemai cigaba da ninke kayan
dake hannuna. Ƙarasawa yayi inda nake fuskarshi ɗaukeda murmushi ayayinda yake
faÉ—in "Ruky yau wanki akayi kenan" murmushi nayi sannan na gyaÉ—a masakaina,nace "Eh
Yaya Salim. Ina wuni" cewa yayi "Lafiya Lau" ayayinda yasa hannu yadebe kayan dana
É—aura akaina ya rungumesu akirjinsa yana faÉ—in "Yanda kika dorasu akankinnan aizasu
iya zubewa kiyi aikin Baban giwa" dariya nayi sannan nace "Aikayan basuda yawa"
doramin kayan yayi kan wani protocol chair dake gurin sannan yace "Koma menene dai
gwanda ki ajiye É—in yafi akan kidaura akanki" Sena gyaÉ—a masakai nace "Toh"
ayayinda nake murmushi.
Seyasa hannu yaciro wata paper acikin aljihun wandonsa yace "Karasa ninke kayan ki
ajiye kizo muje kicike form É—innan" bin form É—in nayi da kallo sannan nace "Form
É—in menene?" Yaya Salim yace "Na Islamiya ne Abba yace inkarbo miki kicika ranar
asabar zakije interview insha Allah" wara idanu nayi sannan kamar meshirin fashewa
da kuka nace "ranar asabar kam ba Babban buli zani ba?" dariya Yaya Salim yayi
sannan yace "wayace miki asabar zaki tafi Babban buli?" tura bakinayi gaba sannan
nace "Kawu Sani ne yacemin a weekend É—innan za'a kaini" Yaya Salim dariya yakeyi
sosai yanzu,yace "Toh ai weekend yace Miki ba Saturday ba and Saturday ba'ita kaÉ—ai
bace ranar weekend harda Sunday" nidai fuska murtuke nace "toh yanzu yaushe zantafi
kenan?" Cikin sigar zolaya Yaya Salim yace "Ai maganar tafiya kam babu ita yarinya.
Koh bakiji nacemiki zakije interview islamiya ba? Kuma da anmiki interview anbaki
aji zaki fara zuwa ranar Sunday" kawai sejin nayi hawaye sunfara bin kuncina.
Sakan baki Yaya Salim yayi cikeda mamakina ayayinda yayi sauri ya ajiye form É—in
islamiyar akan kayana dakekan protocol chair sannan yakaraso inda nake dasauri,yace
"Kuka kuma Rukayya? Rufamin asiri don Allah wasa nakeyi Miki" kamar wata wawiya
kuma Sena daina hawayen,Sena zuba masa idanu nace "Dagaske wasa kakeyi?" kallo na
yatsaya yi shima da mamaki kafin yakwashe da dariya yana fadin "Amma lallai agaishe
ki Rukayya! Daga ance bazaki Babban buli baseki fara hawaye?" Jan numfashi nayi
sannan nace "Ina kewar su Gogode shiyasa,najima bamu haduba" hanky yaciro a
aljihunsa yamika min sannan yace "karbi kigoge kwallarki ranar lahadi zakije Babban
buli insha Allahu" bansan sanda nafara murmushi ba hakanan cikin sauri nakarbi
hankyn nashiga goge guntun hawayena. Shidai sai kallon mamaki yakebina dashi.
Daman riga gudace tarage ban ninkeba danhaka senayi sauri na ƙarasa ninkewa na
ajiya kafin muka karasa kan dakalin laundry da form din islamiyar ahannunsa yanamin
tambayoyi Ina amsawa yana cikewa cikin form din harmuka Gama inda daga karshe yace
min ranar asabar dasafe inshirya inzaikaisu Yaya Zaheera islamiya dasafe za ajedani
inyi interview.
Cemasa nayi "Toh" tareda yimasa godiya kafin yatafi da form din ahannunsa. Aikuwa
ranar asabar din tare muka tafi dasu Kuma har office din Headmaster Yaya Salim ya
rakani akayi min interview inda take akabani aji biyu,ajin su Mariya. Sunso infara
attending islamiyar aranar ma anma se Yaya Salim din yace A'a subari sewani sati
insha Allahu zanfara zuwa kafinnan andinka min uniform. Muna barin islamiyar kasuwa
muka wuce,yayankamin yadin islamiya muka Kai dinki sannan yasaya min books da jaka
kafin muka komo gida. Aranar da dare Kawu Sani ya aika aka kiramu duka yaran gidan.
Muna zuwa yashiga tambayana Kona shirya kayana.
Gyadamasakai na nayi sannan nace "Eh" seyace "Toh masha Allah. Gobe seku da sassafe
in Allah yakaimu" cikeda Jin dadi nace "Toh nagode" inda daganan Kuma seya maida
dubansa gasu Yaya Siyama yace "Kuma kushirya seku rakata Koh? Inyaso se Zunnurain
yatafi daku kuwuni acan dayanma kudawo" tabbas basuso suggestion dinba amna babu
bakin cewa bazasujeba,haka suka amsa da toh kafin ya sllame mu muka tafi. Aikwa
nasha mita da tsangwama ranar,Babu irin zagin da Kauyen Babban buli da mutanen
cikinsa Basu shaba. Mita suka dingayi akan wai miyasa za'ace su rakani,kumawai
bayan ance surakanin ma har wuni akeso suyi.
Nidai jinsu kawai nadingayi harsu ka Gama korafin su suka gama. Washegari karfe
takwas Yaya Zunnurain yadebemu a mota yayi Babban buli damu dankuwa Kawu Sani cewa
yayi shizaikaimu dukda dafari Yaya Salim yaso kaimu dakanshi. Yace Kuma kaima yinin
zakayi,kaje kaga kauye,kaga mutanen cikinsu,kaga yanayin yanda suke rayuwa dadai
sauransu banason kudawo gidannan se shidan yanma tayi.
Yaya Salim dariyar mugunta yadinga musu kasa kasa alokacin ayayinda yakebi É—aya
bayan É—aya yanayi musu Allah yakara. Se kunkuni suke kamar zasu shakeshi. Sanda
muka Isa Babban buli zokuga murna,da gudu nashiga gida na rungume Gogode Ina ihun
farin ciki inda sedaga baya su Buba suka biyoni dakayana dakuma bakin Dana manta da
kashin su awaje tsabar zumudi. Sanda suka shigo fada Kawu Idii yashigayimin Wai
Nazo da Baki Kuma nayi tahowana nabarsu. Hakuri nabasu ayayinda Gogode dakanta
tadauko musu katuwar tabar ma tashimfida musu akarkashin runfarta tace suzauna.
Tarba babu irin wanda basu gani ba ranar. Haka aka ciga gabansu da dammammar fresh
fura da nono dakuma hadaddiyar Dambun daba'a Jima dasaukeshi daga kan wuta ba. Yaya
Zunnurain kuwa tuni Buba yajashi suka fita can gidanshi Wai dagacan inyasha nashi
fura da nonon sesu wuce yawo......
Bakaramin daÉ—in yanda basuyi kyamar su Gogode dakuma nuna musu dabasuyuba nayi
dankuwa sundan saki jikinsu, Sunsha fura da nonon da aka kawo musu. Dambun nede
sukaki ci, Sadiya ce kadai taci Itama kadan taci. Kwaidum dasu Hari sunajin labarin
na dira agari sukazo gidan Gogode suka samoni. Rungume su nayi muna farin cikin
sake ganin juna inda daganan Kuma muka kwasa muka tafi yawo tareda su harma da
Indo. Nayi wa Sadiya tayin tabimu anma setaki.
Damuka fita yawon ne indo kefada min ai Lamido yazoshi satin daya wuce dincan Yana
tambaya Kona zo hutu. Excitedly nakalli Indo sannan cikin yaren Fillanci nace
"Allah yagongai?(Allah dagaske kikeyi)" seriously Indo tacemin "Allah emi
gongai,daga pinde muwari se alasara mahoti (Allah dagaske nikeyi,dayazo tunsafe ma
baitafi ba seda yanma tayi) Ina murmushi senace "Allah sarki! Kuma bece zaidawo
ba?" Indo tace "Wallahi mi'anda bananan yatafi lokacin natafi debowa kandilo anma
kigwwada tambayar Gogode inmun koma" senace "Toh shikenan Zan tambayeta. Allah
yasadai yadawo din" "Amin" suka amsa minda duka.
Sebayan azahar sannan nakoma gida inda anan nasamu anyi masu Yaya Zaheera
lafiyayyar kunun hatsi da biski miyar taushe,basuwani ci sosai ba dayake bazaka
taba hada taste din abincin birni dana kauyeba dukda kuwa su ahakan sunyi musu iya
kurewar medadi kenan. Seyanma lilis suka tafi bayan ancikasu da kayan arziki akace
sukai gida,kana daga kan kalwa ne,kukane,tsintsiyane har fura da nono. Bayan
tafiyarsu dadarene Sena samu Gogode nayi Mata maganar Lamido inda ananne take sake
jaddaddamin yazoshi Kuma yace nace Masa zanzo hutu inda sukuma sukace Masa Basu
sani ba kozanzo kobazan zo ba tunda basu hadu daniba dukdama they were planning to
go and see me.
Akagare "Toh Gogode bece zedawo baneba?" Girgiza min Kai Gogode tayi sannan tace
"Gaskiya baifadamin ba" Sena tura baki gaba kamar me shirin yin kuka ayayinda
araina nake addu'ar Allah dai yasa yadawo kafin wani sati inkoma Bauchi. Haka
nacigaba da hutu agarin Babban buli cikeda Jin dadi da nashadi,Babu takura,Babu
tsangwama kowa Sona yakeyi Yana Kuma yin nannan Dani. Daga muje surge
dasafe,wataran muje kiwo,wataran muje diban Karan daza'ayi girki sekuma muje
dandali wasa da dare inda dana dawo Kuma zanzo intarar da tsarabana da ake kawomin
daga cikin gari kullum, either tsire da bread,ko doya da kwai,ko awara,ko kilishi
kokuma wani Kaya makulashe dai haka. Kullum dai shine aikin. Adan kwananin Nan Sena
gane cewa living a life of luxury bashine kadai happiness ba,the people around
you,how they treat you and how comfortable you're with them shine farin ciki,shine
kuma Jin dadin rayuwa. Yau asabar Kuma gabadaya yau very moody natashi dankuwa gobe
zankoma Bauchi gashi haryau Kuma Lamido besake zuwa ba wanda hakan yasa nakejin
kamar bazan samu ganinsa ba har in koma gobe din.
Littafin Qadr na kudine duk maiso should talk to me privately through this number
on WhatsApp 08147722806 for payment details.
*Page Forty Five*
*Avoid typing errors please*
Brush da maclean naÉ—auko a É—aki sannan nafito naÉ—auki buta naje nadibo ruwa
acikinsa daga randa sannan nazo naÉ—auki kujera nanufi can kusa da hanyar banÉ—aki na
tsuguna ina brush. Ina cikin yin Brush É—in Indo tafito daga É—akin Gogode tana kwala
Ƙiran sunana. amsawa nayi ayayinda nujaya Ina kallonta,ɗauke take da kwarya a
hannunta wanda inada tabbacin tagama shirin tafiya surfen hatsine.
Dubana tayi sannan tace "Zakije surfene?" girgiza matakaina nayi ahankali ina
yatsina fuska danni gaba É—aya yaujina nake banajin daÉ—i sabida gobe zankoma cikin
gari. Cemin tayi "toh shikenan" sannan tayimin sallama tayi tafiyarta. Bayan nagama
brush wanke fuska na nayi nakoma É—aki gurin Gogode.
Da mamaki tadubeni tace "Daman baki ta fi surfen ba?" gyaÉ—a matakai nayi ahankali
sannan nace "Eh Gogode. Yaukuma naji banason zuwa" jinjinakai tayi sannan tace
"Niko harnake cewa dagacan seki wuce gurin Innan Kwaidum tayi miki kitso tunda gobe
zakikoma cikin gari" batarai nayi take sannan cikin sauri nace "Bazanyi kitso ba"
Gogode tace "Kunada masu kitso a unguwarku kenan?" Senace Mata "Eh". Gaba-daya su
Gogode basusan halin danake ciki agidan Kawu Sani ba,infact a tunaninsu ana
treating ɗina very well agidan tunda Buba ya taɓa zuwa mungaisa bannuna masa
komaiba gakuma dazanzo anhadoni dasu Yaya Zunnurain sunkawoni. Dukda bayan
tafiyarsu Gogode tasha tambayana ko akwai matsala anma kullum amsar babu nakebata
sabida banason abunda zaitada Mata hankali,most especially awannan shekarun nata.
Ranar har azahar babu inda naje ina kwance adaki.
Ƴan gidan kowa yajini shiru seya leko ɗakin Gogoden yana tambaya ko lafiyata Lau
inda zance musu kalau nike,kawai dai yauÉ—in banjin fitowan ne. Wuraren ukun yanma
Ina kwance a É—aki ni kaÉ—ai Ina karanta wani story book danataho dashi acikin kayana
naji andoka sallama a sashin Gogode É—in. Tsayawa nayi da karatun ayayinda na
tsurama kofar É—akin nata idanu dukda akwai labule dan in tabbatar sallamar akayi
dagaske kokuma imagination É—inane. Wani sallamar aka kuma yi wanda Jin kamar nasan
me muryar yasani saurin tashi nazauna ina murmushi kamar wanda akamin kyautar
kujerar makka,sallaman daya kumayi akaro na ukune yasani fitowa daga kan gadon
kaina ko dankwali babu nafito dagudu Ina faÉ—in "Waalaikumus Salam" ayayinda na daga
labulen kofar. Yaya LamiÉ—o nahango tsaye jikin katangar data raba sashin Gogode
danaso Yaddiko Rahane.
Wani irin lallausar murmushi yasaki sakamakon ganina dayayi sannan cikin sigar
zolaya yace "Yakika tsaya kamar statue? Toh ki karaso mugaisa mana. Koh baki farin
ciki da ganina ne inkoma" yayi maganar ayayinda yake kokarin juyawa wai zai koma,ai
cikin sauri nasaki labulen Gogode nanufesa da É—an gudu gudu Ina faÉ—in "Wallahi
inayi Yaya LamiÉ—o. mamakin ganinka ne yasani tsayawa guri guda" Yana murmushi
tajuyo gareni sannan yace "Miye abun mamakin? Didn't I promise you that I'll surely
come and visit you inkukayi hutu?" tura Ƴar karamar bakina nayi gaba sannan nace
"You promised to come and danazo ancemin you came last week bananan shiyasa nayi
tunanin bazaka sake dawowa ba" seyasa hannu cikin lallausar gashina yadanyi
stroking É—insa yana fadin "Ai indai banganki ba toh I won't rest until I get to see
you" washare bakinayi cikeda Jin daÉ—i sannan nace "Really?" gyaÉ—a min kai yayi yana
murmushi,senace "Kana nufin dakazo wannan satin baka sameni ba wani sati ma zaka
dawo?" GyaÉ—a min kai yakumayi still looking at me while smiling.
Cikeda Jin daɗi nace "What if har hutu ya ƙare banzo Bafah?" Seyasa hannayensa a
kirji yayi folding yana kallona,yace "then I'll surely go to your Uncle's House
inganki kafin kuyi resuming" bansan sanda nafara blushing ba,nace "Inkuma ba'a
barka kashiga ba fah?" Boldly yace "I'll surely find the way no matter how insha
Allah" senace "But why will you go to this length kawai danka ganni? Ai akwai
komawa makaranta and you promise to always visit lokacin visiting days" LamiÉ—o cire
hannayensa yayi a kirjinsa ayayinda yamaida su cikin aljihun wandonsa yasauke wani
sanyayyar ajiyar zuciya sannan playfully yace "Yarinyar nan you can ask questions
for Africa" Ƴar dariya nayi sannan nayi pouting bakina nace "Nidai kafaɗa min don
Allah" Kama hannuna yayi muka nufi rumfar Gogode ayayinda yake faÉ—in "because I've
so much to discuss with you dayake ta damuna for months now while kekuma gudun muyi
maganar ma kikeyi and secondly nayi miki alkawarin zuwa inganki so I'll make sure
nacika wannan alkawarin because I don't like breaking promises,most especially
indai akanki ne Nanaaa!" Yakarashe maganar slowly ayayinda yasaki hannuna,yaja
kujera yazauna yana faÉ—in "Tunda ba'acemin inzauna ba ba inzauna dakaina dannagaji
da tsayuwa" Ƴar dariya nayi sannan naja ɗayan kujerar nazauna nima Ina faɗin "Ina
wuni?" Yaya Lamiɗo yace "Lafiya Lau Ƴar Birni" tura bakina nayi gaba sannan nace
"Wai bazaka manta sunan nanba" Ƴar dariya yayi sannan yace "Akan wani dalili zan
manta? Kokin tashi daga Ƴar birni kinkoma Ƴar kauyene?" Tura baki nayi gaba sannan
nace "Ni ba Ƴar kauye baceba" dariya yayi sosai wannan karan sannan yace "Toh kuma
sekice kar acemiki Ƴar Birni?" fuska tsuke nace "Nidai banaso,haka ranar ma kafaɗa
agaban Aziza. Allah yataimakeni hankalinta baya kan sunan sosai dayanzu tamaida min
suna yakoma Ƴar birni" wannan karan Lamido dariya yake sosai harda riƙe ciki,
dakyar ya tsagaita sannan yace "Kice dana kwabsa" hararanshi nayi playfully inabata
Rai.
Seya yi serious face,yace "Okay fine! I'm sorry bazan sake ba" É—auke kaina nayi
daga gareshi namayar gefe batareda nace komaiba.
Ahankali yakuma cewa "I'm really sorry. Allah bazan sakeba" cikin sigar shagwaba
batareda na kalleshiba nace "Bawani nasan zaka sakeyi wataran" seya taso daga
zaunen dayake yazo gabana ya tsuguna,sake É—auke kaina nayi zuwa wani gefen daman
kuma,wai ni adole nayi fushi dagaske.
Fuskar tausayi yayi sannan sincerely yace "Allah bazan sakeba" Jin irin tune É—in
dayayi using sena kalleshi,yana kallon cikin idanuna yace "I promise bazan sake
cemiki Ƴar birni ba" bansan sanda nasaki wani lallausar murmushi ba.
Shima murmushin yasaki sannan yace "Kin hakura?" gyaÉ—a masa kaina nayi ahankali,
stroking lallausar gashina yakumayi sannan yace "Ina ÆŠan kwalin ki?" daga idanuna
nayi sama kamar wanda zan iya kallon gashin nawa danni kwata kwata nama manta ban
fito da dankwali ba inba yanzu dayayi maganar ba, senace Masa "Yana É—aki" Yaya
LamiÉ—o yace "Toh jeki É—auki kirufe gashin kizo mutafi yawo" wara idanu nayi
ayayinda natashi daga zaunen danake sannan nace "Ina zamuje?" shima tashi yayi
tsayen yana faÉ—in "kedai kije kiÉ—auko dankwalin ki zaki gani" gyaÉ—a masakai nayi
sannan nashige É—aki dagudu.
Dankwalin kawai naÉ—auka nafito nasameshi,senace "Mutafi" jerawa mukayi muna tafiya
ayayinda muka nufi kofar fita daga gidan Ina tambayarsa dalilin dayasa baitambayeni
Gogode ba inda ananne yakecemin ai yasan batanan,sun haÉ—u a hanya zataje gidan
*Innaru* kawarta kuma sungaisa,itane ma tace masa Ina gida.
Damuka iso sashin su Yadikkoh Rahane senace "Su Yadikko Rahane fah?kungaisa ne daka
shigo?" Jinjinamin kai yakumayi sannan yace "Seda na tsaya muka gaisa a kofarsu
sannan nakaraso gurinki" jinjinakai kai nayi ahankali sannan muka fice agidan baki
É—aya. Tafiya mukeyi Ina wasa da karan hatsi a hannuna ayayinda yake bani labarin su
Umma da Salma bayan na tambayeshi lafiyarsu. Ƙarƙashin bishiyar dana fara ganin
yadiro washegarin dasuka fara zuwa field trip yakaini sannan yanuna min wata Yar
karamar dutsi dake gurin yace "toh zauna" Ƴar murmushi nayi sannan nazauna Ina
faÉ—in "Daman nan zaka kawoni?Aida nataho da kwallah nadibar ma Indo kandilo inzamu
koma gida yanda basai tasha wahalar zuwa ba kuma anjima" zama yayi kan wata Yar
karamar dutsi dake gefena sannan yace "Wai a Ina ne kuke diban kandilon ne!" Garken
shanun dake opposite inda muke zaune nanuna mishi ayayinda yake jinjina Kai.
Nace "tacikin nan nafara hango ka the second day damuka haÉ—u zuwanku garinnan" yayi
murmushi sannan yace "Ranar dakika fara gane ni makaryacine kenan?" Ƴar ware
idanuna nayi sannan nayi sauri na sunkuyar dakaina a kunyace sannan nace "Ai
lokacin bansanka sosai ba shiyasa nace haka" dankuwa seyanzu nake ganin
wautana,dubanshi danayi cikin Ido alokacin nace masa shi makaryacine. Dariya Yaya
LamiÉ—o yayi sannan yace "You don't have to feel Bad Nana. Dagaske nayi karya
alokacin,I truely lied and that was the reason why you addressed me with that name"
senace "Eh nasani anma ai kayi karyar ne sabida kayi protecting kanka" wannan karan
dariya yayi sannan yakalleni yace "Wani protection anazaune kalau? Rashin
jidai,tsantsan rashin jinane yasani yin karyar" Yar dariya nayi sannan nace "Koma
miyene dai ni bazan sake cemaka makaryaci ba" Yana dariya yace "I've proved myself
worthy kenan?" gyaÉ—a masakai nayi Ina murmushi sannan nace "Yes! You've proved
yourself so many times not even Once" seya dawo da dubansa gareni bakidaya,Yana
kallon cikin idanuna yace "And I promise to always be a worthy Brother Nana. I just
need you to trust me and nothing else" ahankali senace "I trust you completely Yaya
LamiÉ—o,batun yau nayarda dakaiba and bana tunanin kuma akwai abunda zaizo yayi
breaking wannan trust É—in danake yi maka agaba" expression É—in fuskarsa kaÉ—ai
tanunamin irin daÉ—in da kalamaina sukayi masa,seyasa hannu yakamo hannuna guda
yasaka cikin nasa sannan ahankali yace "Then share your pain with me,ki faÉ—amin
damuwarki Rukayya, kifaÉ—amin halin da kike ciki agidan Kawun ki and may be I'll be
able to help you out" Jin abunda yafaÉ—a din take senaji gabadaya mood É—ina yacanza
lokaci guda,senaji gaba É—aya zuciya ta ta bijiro dawannan feelings É—inda nakeji
aduk sanda nike gidan Kawu Sani,take kuma se idanuna suka tara kwallah.
Ahankali nace "Kona faÉ—a maka bazaka iyayin komai ba Yaya LamiÉ—o. My story will
only hurt your feelings" ahankali yace "Inma bazan iya komai dan incanza yanayin
Rayuwarki ayanzu ba ai I can share your pain Right? I can console you right?"
gyadamasakai na nayi ahankali.
Cikin sanyin murya dakuma nuna damuwarsa akaina yace "Toh ki fadamin" wannan Karan
already harna fara zubar da hawaye, ahankali nashiga bashi labarin asalin irin
yanda dangin Baba basusona most especially waÉ—anda mukayi rayuwa dasu,nabashi
labarin yanda akazo inzauna agidan Kawu idrissa bayan rasuwar Baba dakuma abunda
Matar da tamin ranar da su Yaya Fahad suka kaini gidan,nabashi labarin yanda nake
zama a gidan Kawu Sani yanzu da irin maltreating ɗina da akeyi,Babu abunda na ɓoye
masa and by just one look danayi masa bayan nagama basa labarin nasan cewa he's in
great pain,abun ya taɓa shi sosai dankuwa idanunshi gaba ɗaya canza launi
sukayi,yace "Why can't you stand for yourself toh Nana?why can't you tell your
Uncle duk abubuwan dasukeyi Miki bayan kinsan he'll surely take vengeance for
you?" cikin gunjin kuka nace "Tsoron su nikeji Yaya LamiÉ—o, I'm afraid of abunda
zaije yadawo bayan na haÉ—a su dashi tunda shibamai zama baneba,nafi zama dasu fiye
dashi kuma nafi kowa sanin halinsu dakuma what they're capable of shiyasa gwanda
inbarsu kawai,gwanda inbari sucigaba dayimun abunda sukeyi din. Wataran zaizama
tarihi Insha Allah" rai bace se Lamido yace "Toh zanfada masu Gogode inyaso su
saisu dau mataki" take Sena rude Masa nafara rokon da da kada yafada musu don Allah
inda dakyar yayarda sannan cikin sanyin jiki yasauko daga kan dutsen dayake zaune
yakaraso gabana yatsuguna sannan yajani zuwa jikinsa ya rungume yana soothing
bayana batareda yace komaiba. Nikuwa Sena samu daman sakin kuka mesauti a jikinsa.
Munjima ahaka,seda nayi kukar me isana,seda naji Dan dama dama sannan nasake shi
and for some reason danayi Sharring labarina da Yaya Lamido,senajini wani irin
sakayau,senaji kamar nacire wani gyambo dayajima Yana damuna acikin zuciyata. Sanda
nacire kaina daga jikinsa sa palms dinsa yayi yakama fuskana sannan yana kallon
cikin idanuna,with utmost sincererity,with a look that looks like a dare,with a
tune that sound like a promise yace "Insha Allah! Insha Allah everything will come
to an end soon Nana,insha Allah I'll bring you out of this mess very soon" Gyada
masa kaina nayi ahankali Ina murmushin dole dankuwa senaji kamar yamin alkawarin
cire duk wata sorrow acikin rayuwana ne.
Haka muka koma gida shiru babu maice da wani uffan,kowa da irin tunanin dayakeyi
aransa.
Ni tunanin yanda zankoma rayuwa awannan gidan gobe nakeyi ayayinda nasan bangaren
Lamido kuma bazai wuce tunanin irin abubuwan da akeyimin din bane yadameshi
azuciya. Sanda muka Isa gida Gogode harta dawo daga gidan kawarta dataje,samu
mukayi tana dama Fura da Nono.
Da murmushi tadubemu sannan tace "Ina kuka shigane haka? Yanzu nakeson intura Indo
tanemo min ku kazo kasha fura da nonon Nan tunda fasalinsa" Lamido murmushi yasaki
sannan yakarasa kusa da ita yana kujera yazauna ayayinda yakarbi ludayi da kwaryar
nonon yacigaba da damawa kamar yanda yaga tanayi sannan yace "Yawo mukaje Inna!"
Yar dariya Gogode tayi sannan cikin sigar zolaya tace "Kodai albarkatun kasan kuka
sake zuwa gani wannan karanma?" Nida Yaya Lamido dariya muka saki atare sannan Yaya
lamido "A'a Inna! Meyakaimu mukuwa,wancan dinma Aidan yazamemin dolene" Gogode tayi
dariya tace "Nasani! Tunda Kanwarka naso" kallona Lamido yayi sannan yace "Do you
still want to explore the rocks?" Ina dariya nace "Inaso Mana Amma komunje kaima
basani kayi ba bare kamin bayani" wara idanu yayi yana dariya ayayinda yakai hannu
gejen kirjinsa Yana tabawa funnily,yace "Nashigesu! Wannan downgration haka Nana?"
Tura Baki nayi gaba Ina Masa dariya nace "Toh ai kaida bakinka kake cewa bakasansu
ba sanda muke zuwa field" jinjinamin kai yayi sannan yace "And that's the fact. I
know nothing about Geology sabida banida interest akai,Ina karanta shine Dan anbani
shine as course of study kawai,Ina karanta shine sabida inyi earning certificate na
degree kawai kamar yanda Ummi take burin gani bawai don ya amfane niba" cikeda
Curiosity senace "toh Kai mekakeson zama?" wara hannaye yayi yana murmushi sannan
yace "I don't know really! Duk inda Allah yajefani kawai" Gogode dake Jin zancenmu
setace "Anmadai yakamata ace kafara plans tunyanzu,inma kasuwanci zakayi,Inma wani
abunne you should first plan ahead the future" jinjinakai Lamido yayi sannan yace
"Hakane Gogode,baridai mugama degree din tukunnan semuga abunyi" murmushi Gogode
tasakar mai sannan tace "Allah yayi jagora" Lamido yace "Amin ya rabbi Inna".
Tareda shi mukasha fura da Nonon dankuwa yanagama damawa nadauko wani ludayi nazo
najonashi munasha suna Hira shida Gogode, bakaramin mamakin irin sabon dasukayi da
juna nayiba,Ashe Wai yakanzo sugaisa once in a blue moon inyazo Bauchi hakanan duk
Wanda suka shigo gidan se Inga suna gaisawa dashi harma Sudan taba hira kamar Wanda
sukajima da sabawa, Lamido yazama kamar wani Dan gida a Babban buli dankuwa koda
zaitafi dazan rakashi haka yadinga sallama da dayawa daga cikin mutanen Kauyen.
Ahanyane nasanar dashi washegari Nima zankoma dayacemn may be next week
zaidawo,cikeda mamakina yatsaya yana kallona yace "Komawa Kuma? Mezaki koma kiyi
hutu baikare ba?" ahankali nace "Kawu Sani ne yace inkoma sabida zuwa islamiya.
Yanzu haka inata missing classes ma already dantun last week naje akayimin
register" sauke nannauyar ajiyar zuciya Lamido yayi sannan yace "toh shikenan
anmadai kidaina sa damuwa aranki kinji?" Gyadamasakai nayi ahankali Ina
murmushi,yace "insha Allah wataran komai zaizama labari! I'll make things right for
you,I promise you this Rukayya" gyadamasakai kawai nayi dukda Ina mamakin menene
zaiyi yayi Making komai right acikin rayuwata anma kuma se Allah baiban ikon
tambayar tasaba.
Haka nadinga rakashi,seda ya tursasamin inkoma gida sannan nahakura najuya nakoma
gida.
Washegari Sunday Yaya Zunnurain yazo yadaukeni yamaida ni gida cikeda tsaraba daga
mutanen Babban buli dankuwa bayan tsarabar dasuka bayar aka kaima su Aunty last
time dasu Yaya Zunnurain din zasu tafi ranar dazan koma dinma seda akasake bani
wani nakai musu. Aunty cema kadai tayita godiya dana bata nata tsarabar ayayinda
Ummi ko kallon inda nake batayiba bare ma insa ran zatayi godiyar,nadai barmata su
anan parlourn ta wanda bayan andan kwana biyu kuma naga tana amfani dasu daddawa
dasu kukan acikin abincin da akeyi anan gida.
washegarin dana dawo nafara fita islamiya taredasu Yaya Zaheera dayake lokacin
hutune so islamiyar safe ake zuwa,lokacin makaranta nedai akeyin ta yanma.
Yaya Salim kullum shiyake kaimu islamiya yakuma dauko mu yadawo damu gida sannan a
hutunnan bakaramin Sabo muka sakeyi dashiba dankuwa sau tari in Ina zaune a
backyard zezoshi yasameni yayi ta damuna da surutai,tun Ina noke noke inayi inajin
tsoro harna daina nasaki jikina sabida Yaya Salim always make sure baizo at the
wrong time ba,seyayi timing yake zuwa gurina. In zaune nake shiru yatayani
surutu,in aiki nikeyi nanma tayani yakeyi,inkuma karatun islamiya yazo yasamu inayi
toh shima taimaka min yakeyi yanayimin gyara a Inda nike da mistake wanda har hakan
yasa wataran in Abu yashugemin duhu ma koban ganeba dayazo nake tambayarsa dakaina.
Sau tari Kuma idan an aikeni agidan, either Ummi kosu Yaya Siyama sun aikeni shago
saya musu Abu toh dana fita indai Yana zaune awata Yar kwarya kwaryar majalisa
dasukeyi da abokanansa acan kofar gidan makotan mu toh haka zaitashi ya rakani muje
mudawo tare,barin ma da dare dankuwa Ummi tatsiri aikena dadare wani shago dake
gaba damu kadan. Ranshi yakan baci inya ga nafita aike da dare haka kullum indai
nafitan seya tambayeni waye ya aikeni nikuma koba Ummi bace ta aikeni cewa nakeyi
itane sabida nasan innace su Yaya Zaheera kosu Yaya Safiya ne toh tabbas he'll get
back to them.
Haka hutunmu yakare muka koma makaranta mukacigaba da school activities dinmu yanda
yadace. Wannan Karan andan rage tsangwama ta dakuma wani irin kallo da sauran
dalibai sukeyi min,infact dadama munkoma muna shiri dasu ayayinda wasu har
respecting dina suke suna ganina da mutunci. The only problem danake facing yanzu
shine bullying dinsu Yaya Zaheera dakuma fitsarin kwancen da Yan hostel dinmu suke
ganin inayi.
Su Yaya Zaheera haryau basu daina bullying dinaba,infact abunma karuwa yayi bayan
munyi resuming,in diban ruwane nizasu aika akira inje inyi musu,wanki nizadubama
inyi musu,a class during break nizasu aika akira inje school shop inyo musu sayayya
Wanda wataran harma break din yawuce bazansamu insaya dawuri ba sabida layi.
Gabadaya sun kullamin dukansu,kwata kwata banida sukuni indai suna guri. Aziza
tashamin fada akan inyi reporting dinsu anma se inki wanda wataran harcewa take ita
zataje takai karar su anma se in hanata inyi threatening dinta da inta kuskura
tafada toh tabbas zamu bata ne da'ita, Babu ni babu ita. Dole ahaka tahakura
takyaleni tazubama sarautar Allah idanu.
Lamido kamar yanda yayi alkawari first visit damukayi bayan dawowarmu yakawomin
Yaya Basma,Yaya Jidda da Salma,ranar murna kamar inyi Yaya,tsallen nadingayi harda
rungumesu and they were happy seeing me too dukdama nalura Yaya jiddan kamar
batawani Sona sosai kamar Salma da Yaya Basma. Salma is so friendly while Yaya
Basma is a genuine Sister,su biyunne suka dinga bani labarin yanda Yaya lamido
yadamesu da labarina dakuma damunsu dayayi saisunzomin visit even though ita Salman
dama has been dying to come.
Alokacin dariya nayi sannan nace "Ai yanzukam ma kowani visit zakuna zuwa Koh?"
wara idanu Yaya Basma tayi sannan tace "Iyeeeeyyy! wazai barmu? Aikece zakizo next"
pity face nayi sannan nace "Inason zuwa anma ba kwana kusaba dannasan baza a barni
agidaba" Yaya lamido dake gefe yanajinmu seyace "Toh yaushene zakizo din agaba
tunda baza'a barkiba?" Pouting bakina nayi sannan nace "Innayi aure" dukansu
zaremin idanu sukayi da mamakina suna dariya.
Yaya Basma tace "inkikayi aure fah kikace Rukayya!" gyadamatakaina nayi Ina
murmushi, Yaya lamido Baki sake yace "Lallai yarnan. Wato harma kinfara maganar
aure a shekarun kinnan?" Tura bakinayi gaba ayayinda nayi pity face sannan nace
"Bahaka bane Yaya lamido,kawai dai nasan bamai barina inje dinne harsai nasamu
yancin kaina ko innayi aure mijina yakaini" Yaya Basma dake dariyar yarintata seta
jinjinakai tace "toh Bari muyi sauri mufiddo miki miji kawai ayi auren kwana kusa
because I can't afford to miss you anawa auren,I want you to attend every bit of it
insha Allah" Yar dariya nayi sannan nace "Niba yanzu zanyi aureba" sekuma sukayi
dariya dukansu, Yaya Basma nafadin "Kinason kice bazakizo bikina dana Yaya lamido
ba kenan?" cikin sauri nace "Zanzo Mana" Yaya Basma tace "Ta'ina tunda baza'a barki
agida ba?" Senace "indai a makaranta muke seyazo ya karba min pass,inkuma Ina gida
ne zansan yanda zanyi abarni inje Babban buli daganan seya daukeni yakaini" Salma
setace "Perfect Idea" daganan Kuma semuka canza babin hirar tamu zuwa wata.
Itadai Yaya Jidda batawani surutu,sedai tayi murmushi kotayi dariya and nidai
batamin kama da wadanda baswa magana ba and besides Yaya lamido yasha bani labarin
tanada surutu,nakuma Sha Jin suna waya dakuma yanda take ta mishi zuba shiyasa nafi
alakanta rashin surutun nata dasuka zo din da rashin Sona,kamar batayi na ne kawai.
Haka Rayuwa tacigaba da tafiya cikin amincin Allah. tunda nashiga FGc azarai nafara
fitowa cikin best three toh haka nacigaba da retaining positions dina dankuwa sosai
namaida hankalina kan Karatuna nida Aziza. Magana in public kuwa shima gradually
nazo nafara iyawa dankuwa press club dinda na shiga bakaramin taimakona yayiba
dayake muna debate within club members din,mukanyi presentation da speeches hakadai
Wanda daga cikine ake selecting Wanda zasuyi a wani program na makarantar kokuma
daza'aje ayi awasu schools din. Dukda ba ataba zabana ba but l alwalys participate
sabida compulsory ne ga duk wani dalibi yayi indai Yana cikin club din. gakuma
encouragement din da Aziza kebani akullum Wanda hakan nadaya daga cikin abubuwan
dayake karamin karfin gwiwar expressing kaina din ako ina, because Ayanzu har
inbangane Abu a ajiba Ina iya tashi in tambayi Malami yakuma bani amsa. Ayanzu in
akayi tambaya Ina iya tashi Inbada amsa Inna sani kokuma inyi attempting wanda ada
bana iyawa kwata kwata. ayanzu malamai da dama sunsanmu nida Aziza sosai most
especially wadanda suke koyardamu kuma ji suke damu sosai sabida irin kwazon mu.
A fannin islamiya ma inmukayi hutu bana Wasa da karatuna,dagewa nakeyi kamar yanda
nakeyi a boko Wanda hakan yasa shima nake fita da result mekyau Masha Allah,a
islamiyar ma Kuma inada kawaye sosai hakanan muna shiri da malamai sabida kwazo na
da jajircewana. Kowa Sona yakeyi,kowa yina yakeyi except Yan uwana dasuka fi alaka
Dani. Ayanzu banida wata matsala dayawuce irin tsanar da iyalin Kawu Sani sukeyi
min suka Kuma tasani agaba da wannan tsanar daban San ranar goguwarsa ba dankuwa a
abubuwan dasukemin haryau babu abunda yacanza sema abunda yake karuwa kullum.
*2 Years Later*
Acikin shakaru biyunnan abubuwa da dama sun faru acikin tarihin rayuwata wanda bana
tunanin akwai Wanda Zan iya mantawa dasu aciki,I went through alot kamar yanda
nakeyi tun farkon rayuwata agidan Kawu Sani,infact hardships din akullum karuwa
sukeyi anma hakan baitaba hanani gode ma ubangiji na ba because no matter how the
circumstances are I'm still blessed,i'm blessed educationally and I'm blessed with
so many loved once da in Ina tareda su Koda na awa gudane suna fadin away bad
chapters na rayuwana. Dankuwa kowani hutu senaji hutu,innaje Babban buli wannan
Karan to next Giyade zanjeni dukda kuwa ba gabadaya hutun Nike spending acanba but
atleast I got to spend some happy moments with them. Lamido kuwa acikin shekaru
biyunnan Dede da Rana daya baitaba skipping visiting days dinaba,kowani visit
seyazo yaganni hakanan sau uku Yana zuwamin dasu Yaya Basma sekuma nakarshen dayazo
da Salma ne kadai yazo sudun Basu samu zuwa ba Wai suna bikin kawarsu awannan
satin. Haka lokacin hutuma indai Ina Babban buli toh seyazo yaganni kafin
inkoma,inkuma Giyade nake toh zai Bari Sena dawo gida yabiyo dare yazo yaganni
kafin yatafi.
Acikin shakaru biyunnan kowa yasake girma,kowa yasake manyanta dayin wayau ayayinda
kuma kowa yayi stepping forward arayuwa most especially a fannin karatun mu. Ayanzu
Ina js3 first term inda mukesa ran damun gama term din zamu to hutun JSCE inda
daganan Kuma semu shiga senior class. Yaya Zaheera tagama secondary school dinta
tun karshen last year Wanda kusan zamuyi resuming new session dinnan ma admission
dinsu yafito kuma tana daya daga cikin wadanda suka samu damar shiga jami'ar ATBU
dake nan cikin garin Bauchi inda tajona su Yaya Siyama suke karatun tare dansuma
tunsanda suka gama remedial dinsu suka samu admission yanzu harsun shiga year
Three. Yaya Aisha da Yaya Safiya kuwa suna Ss3 yanzu,ma'ana su za'ayi graduating
bana insha Allahu.
Sabona da Yaya Salim kuwa Sena abunda yakaru dankuwa cikin shekaru biyunnan dasuka
wuce bakaramin shakuwa mukayiba,komanshi Rukayya haka nima komaina Yaya Salim.
Aziza harzuwa tayi daga baya tafara tambayana Wai tsakanin Yaya Salim da Yaya
lamido wanafi sabo da,wanafi Kuma so and I'll just laugh,se ince Mata dukansu
sunada special place azuciyana,dukansu are playing important roles in my life
dukdama deep down ninasan Wanda nafi jidashi,deep down nasan Wanda zuciyata tagama
relying on dakuma Gama ragama Masa sabida babu wani obstacle daya shiga tsakanin
mu. Yaya Salim yagama karatunsa na pharmacy shima Kuma yanzu Yana internship dinsa
anan cikin garin Bauchi. Sekuma Yaya Fahad ogan yan miskilanci,I can't say much
about him sabida yanzu baicika zama agidaba,zuwa gidanma yarageyi sosai dankuwa
baifi yazo sau daya ko sau biyu a shekaraba Wanda mostly ma mukanyi sabani,koyazo
Ina makaranta kokuma inyazo natafi hutu kokuma wani sa'in inyazo Ina gidanma
baiwuce muhadu sau daya kosau biyuba shima se innaje Kai musu abinci ko innaje
daukowa like always. A Abuja yake aiki yanzu acan Federal high court dinsu wanda
tun bayan gama service dinsa Kawu Sanin yasaka Baki akasama Mai aiki acan din.
Baiyi aureba haryanzu Kuma shikadai yake living rayuwar sa a Tantamemen gidansa
dake Nan cikin garin abujan dankuwa su Sadiya suntaba zuwa sunsauka agidan sa
dasuka je bikin wata cousin dinsu tareda aunty wnda bayan dawowarsu ne naji sunata
Wasa kyawun gidan dakuma gulmar Aunty da danginta sunfara yimasa fadar ya fidda
mata yayi aure hakanan shekaru se tafiya sukeyi. Nidai alokacin danaji suna zancen
tabe bakina nayi inda araina nake raya "Ta'ina zai samu matar bayan shiko kalloma
kannensa Mata basu ishesa ba barekuma azo ga batun wasu Mata daban,mutumin da
aikinsa ne kawai agabansa. Bazaka taba ganinshi Yana Wasa da dariya ba kokuma Ace
yanadan wani having fun haka. He's always working or doing something mature. Toh
wannan inyayi auren ma wani farin ciki zaibama matar? Aisaidai suyita kallon juna
kawai. ni gani nakema indai shi zai fidda Mata toh su Aunty zasujima basu ga yayi
aurenba, solution kawai su sunema Mai acikin dangi su hada su auren kawai taje
tayita hakuri da halinsa.
Littafin Qadr na kudine duk maiso should talk to me privately on WhatsApp
08147722806 for payment details.
*Page Forty Six*
***
Dawowana kenan daga Game field É—in makarantar mu kasancewar yau Thursday ne,ranar
da akezuwa games kowani sati a makarantar mu. Akan gadona na zube sakamakon irin
gajiyar dana É—ebo,gaba É—aya natsani Thursdays sabida gajiyar danake deba wa kowani
sati indai naje Games din jarabar nan,gashi baka Isa kace bazakajeba,it's
compulsory kuma har attendance prefects suke É—auka. Ni Abunda yasa banason zuwa
Games É—in ma badan komai bane sedan irin gajiyar da mutum yake debowa agurin
wallahi. Asaka kayita tsalle tsalle kamar wani inji,gaba É—aya karfin ka yakare
kadawo kanata nishi da zufa da gumi. Anma ahakan wasu so suke, abun birgesu yake yi
unlike me da baya gabana.
Seda naji ana ƙoƙarin kiraye kirayen sallar maghrib sannan nasauko da lazy kafafuna
daga kan bunk É—ina,nacire kayan jikina naÉ—aura towel sannan na É—auki bucket nafita
a É—akinmu daniyar in É—ebo ruwa inyi wanka kafin nayi sallah dankuwa jinake inbanyi
wankan ba bazan taɓa Jin daɗin jikina ba. Koda nayi wanka nayi sallah shiryawa nayi
nafice zuwa hostel É—insu Aziza dan insameta muwuce dinning hall tare inda daganan
inmunyi sallar isha'i kuma se muwuce night prep. Bayan munfito a masallaci muna
hanyar tafiya class nida Aziza seta dubene tace "Rukayya gobefah Friday gashi
haryau baki kira Yaya LamiÉ—o kintuna masa batun visit É—inmu ba?" murmushi nasakar
Mata sannan boldly nace Mata "Basai na tuna mishi ba Aziza. I know he'll surely
come insha Allah" Aziza setace "Dadai kikirashi ɗin,kinsan Ɗan Adam da mantuwa" Ƴar
dariya namata sannan nace "kin taɓa gani Yaya Lamiɗo yamanta dawani abu game dani?
He's never done that kekan ki shaida ce" dariya Aziza tayi sannan tace "Nasani and
everytime I asked you to remind him of a day like this kema Thesame answer kike
bani and baya taɓa mantawa ɗin kamar yanda kike ikirari anma ni Ina tuna mikine
sabida ɓacin rana" jinjina matakai nayi cikeda gamsuwa sannan nace "toh naji Aziza
gobe semuje gurin Sir Buharin ki in kirashi" Aziza tace "Allah yakaimu. Nima
daganan zan kira Mommy inji karfe nawa zasuzo jibin" tayi maganar excitedly. Nidai
murmushi kawai nasakar mata Ina jijjiga kaina in desbelief,wani sa'in zumuÉ—in da
Aziza keyi in za'ayi visit har mamakin ta nakeyi. nothing has changed from her
behavior haryau tunda mukazo FGc Azarai,when it comes to her family members jinta
take kamar wata yar karamar baby and nima bana ganin laifin ta dankuwa irin
soyayyar dakuma shagwaɓa ta da yan gidan nasu keyine yake sawa take ganin kamar
bata girma.
Washegari Friday bayan antashi daga class straight wurin Sir Buhari muka wuce nida
Aziza inda muka gaisa dashi,tace ya ƙira mata su Mommy,yakira suka gaisa
tatambayesu time É—inda zasu zo gobe asabar É—in sannan tashiga irga musu abubuwan
dazasu kawo Mata inzasu zo visit É—in wanda inada tabbacin wannan É—in shine time na
yafi a ƙirga data faɗi thesame thing,bayan sungama waya da Mommyn seta bani muka
gaisa da'ita kafin mukayi sallama. Haryau Mommyn su Aziza nasona sosai dankuwa
jidani takeyi sosai,intazo visiting tadinga nan nan dani kenan hakanan kowani visit
seta kawomin abu inkuma za'ayi resuming ma toh saitabama Aziza wani abun takawomin.
Tun Ina feeling awkward inajin wani iri harma nasaba naÉ—aukesu kamar family yanzu.
The only problem am having with Aziza yanzu shine hanata zuwa gidanmu danakeyi
dakuma rashin zuwa nasu da banayi,tadai taɓa zuwa Babban buli sau biyu a wasu hutu
damukayi a baya. Nafarkon a sessional hutun mu na JS1 ne ayayinda É—ayan kuma a
hutun 2nd term É—in mu na js2 ne tajeta. Sau tari kafin atafi hutu takan tambayeni
address É—in gidan Kawu Sani anma se inki bata sabida banason taje a wulakanta min
ita,batun zuwa gidansu kuma gani nakeyi bamai barina inje ni dukda dazan iya sa'a
in tuntunbi Yaya Salim may be yayi finding way yakaini anna in magana tadawo kunnen
Ummi fah? How will she react to it? Shiyasa ma nakebama Azizan hakuri kullum. Data
takuramin a hutun session dinmu na JS1 shine nace mata zanje Babban buli muhadu
acan kawai.
Ranar datazo Babban buli tayi tayi inbita muje gidansu anma naki dayake tazo very
late kan washegari zankoma Bauchi. Zuwanta na JS2 kuma itane ta kwana biyu a Babban
buli tareda ni inda takoma gidansu bayan nan,wannan É—in ma ta matsa muje gidan nasu
anma senaki kasancewar lokacin Ina expecting zuwa Yaya LamiÉ—o. Banason yazo
baisameni ba muyi sabani inkoma cikin Bauchi bamu samu munga juna ba. Nikaina nasan
bana kyautawa,bana acting like a genuine friend kamar yanda Aziza takeyi but
circumstances ne sukasa hakan and from that very day data tafi gida naga yanayin
yanda bataji daÉ—in abunda nayi mataba nariga nasama raina the next time dazata nemi
inje gidan su insha Allah ko akwai abunda yasha min gaba I'll surely leave it and
go with her because tanamin kokari,samun kawa irinta se an tona,bakowani zaisoni
kamar yanda take Sona ba despite me being no one,ni ba yar kowa ba,marainiyar Allah
dani. Aziza Son fisabilillahi takeyi min Kuma tunda yau nasan hakan ba shiyasa
danaga kamar ni bana reciprocating nayi deciding canzawa for better anma segashi
haryau muna JS3 first term bata kuma zuwa Babban bulin ba,bata kuma sake yimin
maganar inje gidan nasuba dukda ma hakan baicanza kokadan daga cikin alakar dake
tsakanin mu ba wanda nafi alakanta hakan da tayi zuciyane tazuba min idanu taga
gudun ruwana. inda nikuma ayanzu nagama kudurta ma raina a hutun JSCE É—inmu Insha
Allah zanyi ƙoƙarin in goge laifin nawa baki daya.
Dayake Sir Buharin nada number Yaya LamiÉ—o kasancewar gurin sa nake communicating
da LamiÉ—on tun bayan da yayi waya yabani numbersa yasa Aziza tace yakira minshi
zamuyi magana Dan Allah. Take kuwa yakira danshi duk a tunanin shi LamiÉ—o Yayana na
jinine. Anma se bamuyi sa'aba,har Kira biyu yayi masa baiyi picking ba.
Banwani damuba haka muka wuce masjid sanitation kafin lokacin sallar juma'a tayi
because I've full faith LamiÉ—o will come for my visit daman dan Aziza ta ta kurane
kawai yasa nayarda muje mukirashi É—in. And batun rashin picking call kuma nafi
alakanta hakan da baya kusa da wayar ne and for sure dayaga missed call he'll call
back kuma nasan Sir Buhari zai fada Masa sakon zuwa visit ne.
Washegari Saturday as usual muka shirya muka tafi visiting ground,Aziza akafara
zuwama kamar koda yaushe dankuwa Yan gidan su dawuri suke zuwa kuma su yini tareda
ita se yanma sutafi inda daga baya kuma su Aunty suka zomana suma. kamar dai every
visit haka yauÉ—inma takasanceda Yan gidan namu,ankawo mana kayan abinci da
kuÉ—i,munci abincin dai tareda su anan visiting ground sabida gudun idanun Aunty
inda bayan tafiyarsu Auntyn kuma suka haÉ—a harda kayana sukayi tafiyarsu dashi. Ni
yanzu harma nariga nasaba da halinsunnan dankuwa damun raka su Auntyn sun tafi
banama sake bi takan kayan abincin da aka kawo mana da provision tunda sunriga
sungama maida rabona mallakinsu. Abunda aka kawoni dashi tun farkon term nike
managing dukda shiɗin ma kafin nataho daga gida se ansa mishi rani,sekuma Ƴar
tsarabar da Yaya Lamiɗo keyimin every visit, Mummyn Aziza ma tana ƙoƙarin yimin
provision dede gwargwado dukdama bakoda yaushe bane take sayamin kayan abincin,wani
sa'in irin toiletries da turarrruka kokuma É—an kayan makulashe dai haka. Bayan
tafiyarsu Aunty wurin Yan gidansu Aziza nakoma muka cigaba da hira dasu har bayan
la'asar wanda alokacin ne kuma nake saka ran ganin Yaya LamiÉ—o yazo shi because I'm
sure visit É—innan shi kaÉ—ai zaizo tunda last one ne sukazo da Sadiya kuma daman
inshi kaÉ—ai zaizo mostly se bayan sallahn la'asar yake zuwa shiyasa ma da banganshi
dawuri ba seban wani tada hankalina ba. Bayan na idar da sallah la'asar can school
garden natafi nazauna zaman jiransa anma nanne nanne zaizo shiru har biyar da rabi
babu shi babu labarinsa. I was beyond shocked hakanan with every passing minutes
nadinga ji jikina yana sanyi tareda Jin fear É—in meya hana Yaya LamiÉ—on zuwa
dankuwa koda na minti ɗayane ban taɓa kawo ma raina bazai zo min yau ɗin ba,se
hakan yasa nake tunanin kodai wani abunne yafaru dashi. Inacikin wannan halin Aziza
tazo tasameni,har Yan gidansu sun tafi. Yanayin data ganni acikine yasa tatsaya ta
tsuramin idanu tana kallona sannan tace "Rukayya lafiya? Ina Yaya LamiÉ—on?" Sekawai
nafashe da kuka kamar wanda daman jira nakeyi,cikeda mamaki Aziza tatsaya tana
kallona sannan hankali tashe tace "Meya farune Wai?" Cikin gunjin kuka nace
"Baizoba" Itama bakaramin mamakin rashin zuwar nasa tayiba because fuskar ta has
said it all,tace "Baizo ba Kuma?" gyadamatakaina nayi Hankali tashe Ina rera kuka.
Shiru tayi naÉ—an wasu dakiku kafin can tace "Toh miye abun kukan Rukayya? kikasani
ko wani aikin ne yahanashi zuwa?" Cikin sauri na girgizamatakaina sannan nace "Aiki
bazai hana Yaya LamiÉ—o zuwa ganina ba Aziza inda kuma aikin yazama dole yahanashi
zuwa ganin nawa I'm very sure he'll let me know before yau,dabazai ma bari insaka
raina ba,dabazai ma bari har inzo inazaman jiransa ba" nakarashe maganar cikin
sautin kuka. Aziza jiki sanyaye tace "Nagane maganarki Rukayya anma rayuwarnan
akwai certain abubuwan dasuke tasowa out of blue dayazama dole muyi attending to
them,bakoda yaushe bane komanmu yake tafiya as planned. Kiyiwa Yaya LamiÉ—o uzuri,
I'm sure something must've stopped him from coming and he'll surely call and
explain why nasani" senace "Nasani Aziza, I'm just afraid of miye dalilin daya
hanashi zuwanne" cikin karyayyar murya nace "I'm just afraid Kar wani abune yafaru
dashi dayahanash...." Cikin sauri Aziza tasa hannu tarufe bakina tana jijjigamin
kai alamar Indaina wannan tunanin sannan tace "Rukayya kidaina irin wannan tunanin
please! Insha Allah nothing bad has happened to your Yaya LamiÉ—o" senayi shiru
kawai bankuma cemata komaiba dankuwa nidai gaba É—aya hankalina yakasa kwanciya,I
just don't believe lafiyar Yaya LamiÉ—o zaibarni haka baikirani koda awaya bane
yasanar dani dalilin rashin zuwansa.
Hakuri Aziza tabani sannan tace intashi mutafi hostel dan already har angama kora
visiting hours yakare,harma anrufe gate É—in makarantar baki É—aya. Ahnyar mu
nakomawa hostel É—in senace Mata muduba ko Sir Buhari yananan inkira Yaya LamiÉ—on
inji,batayimin musuba haka muka nufi admin block dukda dagani har ita munriga da
munsan abune Mai wuya musamu Sir Buhari awannan lokacin. Aikuwa bamusame shin ba
setace inbari washegari musake dawowa tunda yana shigowa school Sundays kasancewar
yana É—aya daga cikin Malaman dake attending MSSN da akeyi every Sundays ma ÆŠalibai.
Ranar dai kwana nayi cikin fear,fear É—inda bantaba jin irinsa ba a fadin rayuwata.
Babu irin tunanin dabanyi ba duk ni kaÉ—ai, hakanan kowani juyi nayi tunanin wani
hali Yaya LamiÉ—o yake ciki dakuma dalilin daya hanashi zuwa É—inne a raina. because
I just have full faith in him, I've full faith that in lafiyarsa Lau bazaikai har
wannan lokacin bainemeni yasanar dani dalilin rashin zuwan tasa ba. Awannan daren
jina dingayi kamar gari bazai waye ba hakanan koda garin ya waye senake ji kamar
lokacin baya tafiya kasancewar se goman safe ake fara MSSN program É—in. Tun seven
nashirya naje na addabi Aziza tashirya muka fita school area.
Ranar dinning ma banshigaba,can kusa da masallacin mukaje mukazauna muna jiran
isowar Sir Buhari. Seda aka fara MSSN program ma sannan yazoshi danhar officials
sunkora mu cikin masallaci dukdama seda nasan yanda nayi nazauna akusa da kofa
inayi Ina leken isowartasa. Inaganin yataho natashi naja hannun Aziza muka fita a
masallacin bayan munyi karyar fitsari zamujeyi dan haka kawai ba'a bari ayita
roaming about awaje in aka fara MSS program É—in. Kusan zaishiga masallacin nida
Aziza muka tareshi da gaisuwa.
Juyowa yayi yakallemu jin munmasa magana,fuska É—aukeda murmushi yace "A'a Aziza da
Rukayya ne?" gyaÉ—a masakai mukayi sannan muka sake cewa "Ina kwana Sir" Sir Buhari
yace "Lafiya Lau Yakuke?" Atare muka ce "Lafiya Lau alhamdulillah" seya maida
dubansa ga Aziza cikin sigar zolaya yace "Jiya su Hajiya sunkawo miki abubuwan
dakika lissafa ɗin dai Koh?" Ƴar dariya mukayi nida Aziza sannan Aziza tagyada
masakai tace "Eh sunkawomin Sir. Sunata tambayarka ma,Mommy tace in gaisheka tunda
basu samu kun haɗu ba" Sir Buhari na Ƴar dariyar yace "toh yayi kyau,Ina amsawa
nima naso inshigo makarantar mugaisa ai da su dasauran iyayen Yara anma se ayyuka
suka shamin kai wallahi,se bansamu nashigo ba kuma" Aziza tace "Allah sarki" gyara
tsayuwa Sir Buhari yayi yana duba agogon hannunsa sannan yace "Ya akayi kukayi
latti haka yau? naga har anfara MSSN program É—in tun dazu kukuma yanzu ma kuke
zuwa" danshi gaba É—aya yaÉ—auka muma zuwan mu kenan,munga Yana tahowa ne shine muka
tsaya gaidashi.
Aziza ce tace "ai tundazu mukazo Sir,muna ma cikin masallaci damuka ganka ne muka
fito gurinka" Sir Buhari seyayi murmushi yace "Allah yasadai ba laifinayiba"
girgizakai mukayi nida Aziza sannan Aziza tace "Sir daman wayarka mukeson ka bamu
zamuyi kira" Sir Buhari yace "Wazaku kirakuma?" Cikin sauri nace "Yaya LamiÉ—o zaka
kiramin Sir" kallona yayi sannan cikin sigar zolaya yace "Rukyn Yaya LamiÉ—o
ganinshi dakikayi a visit bai isabane? Mezaki Ƙira kice Masa?" kamar meshirin yin
kuka nace "Aibaizo visiting É—inba" fuskar Sir Buhari cikeda mamaki "Haba?Meya
faru?" cikin sauri nace "Nima bansani ba! Shine nakeso inkira inji Koh Lafiya" Sir
buhari seyace "Nina É—auka ma yazomiki dayake usually in Kika kirashi yakan kirani
back Incase bakusamu kunyi magana awannan lokacin ba. Danaga baikiraba ranar senayi
tunanin kunriga kunyi magana dashi awani wayan" girgiza masakai nayi sannan nace
"bekiraka ba kenan?" GyaÉ—a min Kai yayi ahankali senace "Nima Kuma bankirashiba tun
bayannan" nayi maganar ayayinda naji hankalina yakara tashi,because by just hearing
what Sir Buhari yace senaji gaba É—aya something is really wrong dan Yaya LamiÉ—o
bazaiki calling back haka kawai ba.
Sir Buhari ƙiran layin Yaya Lamiɗon yayi yasaka a handsfree anma se mukaji wayar
akashe,sau uku yana trying amma everytime akashe akecewa inda daga karshe yace min
Inyi hakuri may be wayartasa bayada charging ne but he'll keep trying insha
Allah,inyasamu sukayi magana zenemeni yafada min yanda sukayi. Nidai gyaÉ—a
masakaina nayi kawai ayayinda Aziza tajani muka koma cikin masallaci.
Har aka Kare MSS program É—in bazance ga abu guda dana tsinta kona koya ba. Gaba
É—aya hankalina baya garesu,negative thoughts and all have you shine kawai araina.
Muna fita a masallaci seda nasake takurama Aziza muka koma gurin Sir Buhari
yakiramin Yaya LamiÉ—o anma still har lokacin wayarsa akashe. Haka muka koma Hostel
jiki sanyaye dukanmu Dan Aziza kanta tarasa bakin comforting dina. Harsaida taga
nakicin abinci,nakwanta zazzabi ya rufeni sannan tafara min faÉ—a akan indaina
negative thinking,inkwantar da hankalina Yaya lamido is in good health and
condition kuma inma wani abunne yafaru dashi ai za'azo afadamin abun bazai buyaba.
Jin kalaman Aziza kawai Se hankalina yakuma tashi,take sena fashe da kuka because
by just saying za anemeni afada min inma wani Abune yasameshi Kara tadamin hankali
tayi because for sure nasan abunda tafada din bahaka baneba,kafin asanar dani
aisaina wahalar,cikin raunanniyar murya nace "Aziza bakisan asalin dangantaka ta da
Yaya LamiÉ—o ba neba shiyasa kike faÉ—in haka. To me and him we're so important to
each other,we're so attached and connected to each other da munsan dole muyi
sharing komai tare like siblings,like Brother and sisters relationship,like a
friend and his/her Bestfriend,like soulmates anma inason kisan cewa bakowane zai
É—auki wannan mahimmancin relationship dinnamu kamar yanda mu muka dauka a tsakanin
mu ba,because in reality we're not connected by blood,we only build that relation
upon our selves and dagani saishi ne mukasan irin ultimate value dinda muka bama
relationship din namu" na share hawayena sannan nakalli Aziza dakyau,cikin
karyayyar murya nace "Aziza yau in akace wani abu yasamu Yaya LamiÉ—o his family
will never think of informing me first because to them I'm just a mere orphan,a
mere orphan da ÆŠansu yakejin tausayi yake kuma taimako. Shiyasa kikaga hankalina
yatashi dabanji daga gareshi ba,because indai har wani abunne yafaru dashi toh I'm
sure I'll be the last to know bayan kuma jinake babu wanda yakaini damuwa da shiga
tashin hankali da al'amarinsa"
Dukda Aziza batagane kan maganar nawa sosaiba anma sebata tsawalla bincikeba ganin
halin danake ciki É—in,seta Jani zuwa jikinta tarumgumeni tana bani ban Baki. Tace
"koma miyene dai tunda bakiyi confirming komai daga gareshi ba baikamata ki É—aga
hankalinki irin hakaba Rukayya. Kiyi zato maikyau,pray that he's safe, pray that
he's perfectly fine wani abun daban ne yahanashi zuwa da neman ki awaya" shiru
kawai nayi ayayinda nacigaba da sheshekar kukana acikin jikinta.
Bayan É—an jimawa kaÉ—an kuma se bacci yaÉ—aukeni,baccin danasan na zazzabi da ramuko
ne sabida rashin baccin dabanyiba adaren jiya. Babu yanda Aziza batayi dani Inci
abinci ba anma naki ci har dare which clearly means 24hrs rabona da abinci kenan
dan tuwanda naci a visiting ground dasu Yaya A'isha bankuma ci ba bayan nadawo
hostel jiya. datakasa shawo kaina seta kira room head É—inmu ta haÉ—a ni
da'ita,Sister Maryam room head ɗinmu nazuwa tana taɓa jikina tace a ɗaukeni akaini
clinic hankali tashe.
Dukda raina bayaso haka suka tursasa ni muka tafi,muna zuwa akasakamin drip. In
short a clinic É—in nakwana ranar, Aziza da room mates É—ina se zirga zirga sukeyi
wurin zuwa dubani anma Yan uwana na jini,the people that are really my own ko
keyarsu bangani ba dukda inada tabbacin Sadiya tasani kuma kilan tafaÉ—a ma su Yaya
Aishan tunda haryau É—akin mu É—aya da'ita,ba'a rabamana É—aki ba because she always
makesure an haÉ—a mu bunk É—aya koda fitsarin kwance ta danake taimakonta dashi Ina
Mata rufa rufa.
Aziza ce takwana dani a clinic ranar inda washegari da sassafe tatafi hostel don
shiryawa bayan tamin alkawarin zataje gurin Sir Buhari in an gama assembly dayake
Monday ne tarokeshi yasake gwada Kiran layin Yaya LamiÉ—o koza'a sameshi. Tunda
tatafi nake zuba idanun ganin dawowarta,kodayaushe idanuna nakan kofar É—akin clinic
É—in. barin ma da akagama assembly students masu zuwa duba friends É—insu da aka
kwantar a clinic da masu zuwa karban drugs suka fara shigowa akai akai. Can kuwa
segata tashigo,cikin sauri nashiga ƙoƙarin tashi zaune Ina kallonta ayayinda tayi
sauri ta ƙaraso tataimaka min nazauna dakyau tana faɗin "Be careful" batareda na
damuda abunda taceba nace "kinsamu kinje gurin Sir Buhari?" kallona tayi sannan ta
girgizakai alamar "A'a" jiki sanyaye nace "Bezo makaranta bane yau?" Dannasan haka
kawai Aziza bazata ki zuwa ganinsa ba barin ma yanda taga nadamun nan anma da
mamakina senaji tace "Yazo mana,yau assembly ya Isa yace bazaizo ba" senace "Toh
hanaki yin wayar yayi?" Nayi maganar dukda nikaina Ina doubting sir Buhari inzai
iyayin hakan.
Se Aziza tasake girgizamin kaina alamar a'a bahanata yayiba,Ina shirin yin magana
setayi sauri tanuna min direction din kofar with a smile on her face.
Tace "Look who's here Rukayya" kallon direction É—inda ta nuna min nayi ahankali
without a second thought and there I saw Yaya lamido. Looking as healthy as
ever,looking as handsome as ever anma kuma baya murmushi,damuwace karara a fuskarsa
na irin halin dayaganni acikin. Sa hannu nayi na shiga murza idanuna wai dukdan in
tabbatar ba mafarkin nakeyi ba and then I'm fully assured shiÉ—in nedai agabana,Yaya
LamiÉ—on danake ta tsumayin ganine bawani ba. Yana sanye da kayan NYSC dasai da nayi
masa kallo na biyu sannan ma na lura.

08147722806 for payment details. God bless you as you patronize my work.
*Page Forty Seven*
Avoid typing errors Please
Taku yashigayi ahankali har ya iso gaban gadon danake zaune ayayinda nikuma nakasa
É—auke idanuna daga gareshi sabida jinake kaman dana É—auke idanun nawa akanshi,he'll
surely disappear. Akwai wata Yar karamar drawer agefen gadon danake kwance wanda an
ajiye drawern agunne purposely for saka drugs kokuma file É—in patient É—inda is on
admission awannan bed É—in. Asaman drawern Yaya LamiÉ—o yazauna sannan ahankali yace
"How are you feeling now?" gyaÉ—a masakaina nayi ahankali ayayinda wasu hawaye suka
shiga bin kuncina,nace "Am fine. Kai inaka shiga Yaya LamiÉ—o? I've been trying to
call you hankalina duk yatashi" cikin rauni Yaya LamiÉ—o yace "I'm sorry..." danna
tabbatar yarasa abun cewane,abunda nayi has made him speechless.
Cikin rashin gane inda yadosa nace "Sorry for what?" Yace "For Making you go
through this Nanaa..." cikin sauri na shiga girgiza masakaina sannan nace "I'm not
in this condition because of you" Yana kallon cikin idanuna yace "You're. basai kin
ɓoye minba Aziza tariga tagaya min komai and it's only my fault,I wanted to
surprise you without thinking of yazakiji inbaki ganni ba" cikin muryar datake nuna
tsantsar damuwarsa akaina yakuma cewa "I'm sorry for not coming on Saturday and for
making you go through alot,kiyi hakuri don Allah" cikin sauri nace "Yawuce" seyace
"But please dagayau karki sake tada hankalinki akan silly abubuwa irin haka. I'm
perfectly fine,i just wanted to surprise you and nothing else Rukayya. Anma ke duk
sekika bi kika tada hankalinki?Why?"
Batareda nagane wani irin surprise yake nufiba nace "Wani irin surprise kakeson
kayimin?" dandai nasan bazuwan dayayi yau bane surprise É—in tunda yanada
opportunity ɗin zuwa on Saturday ɗin yaƙi zuwa.
Nunamin kayan jikin shi yayi sannan yace "I'm going to serve in this school" wara
idanuna nayi with a grin on my face, bakina gaba É—aya yakasa rufuwa nace
"Really...?" gyaÉ—a min kai yayi ahankali sannan with a serious face yace "Amma
nafasa tunda,zanje insake neman relocation kawai tunda rashin lafiya nake saki"
cikin sauri murmushin dake kan fuskana yayi fading away nakoma nayi fuskar
tausayi,kaman meshirin yin kuka nace "Kayi hakuri don Allah" girgizakai yayi sannan
yace "A'a basaikin bani hakuriba. Nina saka kaina Kuma na janye dakaina tunda
matsala zamana a makarantarnan zeja miki dahar dan baki ganniba zaki bi ki É—aga
hankalinki" sekawai nafara hawaye,nace "Don Allah kayi hakuri Yaya LamiÉ—o" kayana
kallona yace "zanyi anma sekinmin alkawarin bazaki sake daga hankalinki akan abunda
baikai yakawo ba,sekin min alkawarin bazaki sake tada hankalinki akan abunda bakida
tabbacin yafaru kobai faruba" cikin sauri nace "Allah nayi alkawarin anma kaima
please kada kasakeyimin irin surprise É—innan,I hate this kind of surprises because
kafin surprise É—in I'll go through alot" gyaÉ—a min kai yayi sannan yakuma cewa "I'm
sorry" murmushi nayi sannan nace "I'm sorry too"....
Aziza dake kallon mu tana murmushi tace "toh maza tashi mutafi aji tunda kinsamu
Lafiya" dagani har LamiÉ—o dubanta mukayi tareda sakin dariya sannan LamiÉ—o yace
"Haba Hajiya Aziza,ayimata uzuri nayau mana" Aziza tashi tayi tsaye sannan tace
"Toh shikenan anyi Mata tunda ka roka Mata alfarma. Barina tafi class nasan yanzu
kilan anshiga first period ma" gyadamatakai mukayi sannan namata godiya tana harara
na tafice a clinic É—in.
Yaya LamiÉ—o dawowa da dubansa gareni yayi sannan yace "Did you have your
breakfast?" jijjiga masakaina nayi ahankali,seyace "mezakici?" ahankali nace "zasu
kawo abinci a clinic din ai nan bada jimawa ba" seya duba wristwatch dinda ke
hannunsa,yace "Zaki iya cin abincin nasu ne toh!" Yar dariya nasaki sannan nace
"Mezai Hana? I've been eating their food for three years now" Yaya lamido yace "you
really tried,gani nake bazan iya cin abincin suba. abincin gidan bikima Yaya barena
dalibai dasuka fi dubu yawa" senakuma sakin murmushi,nace "Ai munasa yaji ko Maggi
aciki" Yaya LamiÉ—o yace "still it won't be as delious as home made food"
jinjinamasakai nayi ciki da gamsuwa sannan nace "Gaskiya Kam" adede lokacin ne kuma
Nurse on duty tashigo wanda gabadaya clinic din yayi shiru yanzu,ma'ana ankori
dalibai,masu karban drugs ma duk sun karba sun tafi.
Mu ukune a dakin kuma gadona ne nafarko daka shigo dakin,karasowa tayi kusa dani
ayayinda nagaidata ta amsa sannan Lamidon ma yagaisheta ta amsa. Tana kallonsa tace
"Are you her guidian?" gyadakai Lamido yayi sannan Yana murmushi yace "Yes! You can
say that anma I'm her Brother" jinjinakai matar tayi sannan cikin sigar zolaya tace
"Yan Mata kekuma da ciwo zakiyi welcoming Brothern naki?" dariya mukayi nida LamiÉ—o
sannan tadubi LamiÉ—on,tace "Inba damuwa kaje waje zasuci abinci se susha drugs
dinsu su huta" cikin sauri Lamido yace "I'll go out anma se after taci abincin
tasha maganin please" irin fuskar tausayin dayama matarne yasa batace komai ba.
Already tun daren jiya aka cire drip É—inda akasaka min daman danhaka seta zubamin
abinci a plate (jollof sphagetti) ta ajiyemin akan cinyana,tayi prescribing ma
LamiÉ—o drugs É—inda zansha sannan ta ajiyemin ruwa guda É—aya tace innagama cin
abincin insha maganin dashi. Cemata nayi "toh" sannan tawuce taje tazuba ma sauran
patients É—inma abincin anma sesu bata basu drugs É—inba tace idan sungama zata dawo
tabasu dakanta sanin halin marasa Lafiya dakin shan magani. Ni É—inma sabida LamiÉ—o
nanan ne yasa ta bani lokaci guda.
LamiÉ—o dakanshi yadinga bani abinci abaki muna hira gwanin ban sha'awa inda ananne
na tambayeshi yanda akayi yazo zeyi service a makarantar mu. Because it does not
look like a coincidence. Dariya yayi sanda nayimai tambayar sannan yace "Yarinya
bakisan wahalar danasha ba kafin nasamu akamin relocation É—innan" nace "Kenan
dagaske zuwan naka ba coincidence baneba?" jinjinmin Kai yayi ayayinda yakai wani
spoon É—in abincin bakina,yace "Uhmmm I decide to serve here sabida ke. Inbadan keba
mezai Kawoni makaranta, makaranta ma wai teaching! Abunda nafi tsana fah kenan a
rayuwata" yayi maganar yana ɗan yamutsa fuska Ƴar dariya nayi Jin abunda yacesannan
nace "Tunda bakaso aida baka taƙura kanka ba" Yace "Uhmmm i've too ne ai shiyasa"
da mamakin sa nace "Why?" Yaya lamido yace "Sabida inason inaganin ki kullum. I
want to protect you" yakarashe maganar with utmost sincererity.
Bansan sanda nayi blushing ba,nace "Ina aka turaka da fari? And ya akayi kasamu
relocation?" Yaya LamiÉ—o yace "Toh uwar tambaya. Zaki fara koh?" dariya muka saki
atare sannan yace "Enugu suka turani" wara idanuna nayi cikeda mamaki Ina maimaita
kalmar Enugu,nace "Enugu!! Can kasan inyamurai fah kenan?" dariya Yaya LamiÉ—o
yakumayi sannan yace "Eh fah can suka turani. Anan nayi camp dina kuma muna camp
dinne nanemi relocation and alhamdulillahi with the help of mahaifin Auwal nasamu"
nace "Kana nufin harkaje Enugu kadawo bansaniba?" Yaya lamido yace "Eh. Bayan mun
ravu a Babban buli dana koma gida washegari result din mu yafito and I pass the
course danayi failing so immediately nayi registeration na NYSC Because it was on
process Daman" yadago takalleni dakyau sannan yace "I wanted to tell you badly
about it Nanaaa sabida nasan sanda yakamata inyi graduating nazo banyiba nayi
failing course daya you sympathize with me,you were very sad even though ni I was
not,I know how much you want me to succeed like everyone anma alokacin nasan
kinkoma gidan ku tunda munyi daman washegari Zaki koma and namiki alkawarin bazanje
neman ki acan ba so I had to keep my promise. Banwani Jima da Komawa Gombe ba akayi
posting É—ina Enugu even though Bauchi was my choice anma basu bani ba so I was
advised by Auwal muje camp É—in kawai meanwhile munemi relocation dan shima Enugu
aka turashi. Kinsan na taɓa cemiki besamu yatafi service last year ba even though
baida matsala a result É—insa,rashin lafiya ne yakwantar dashi wanda yahanashi zuwa
din se bana" jinjinakai nayi ahankali sannan nace "Yanzu kunsamu relocation É—in
kenan?" Murmushi LamiÉ—o yayi sannan yace "Eh munsamu" nace "Yaya Auwal É—inma nan
aka turo shi?" gyaÉ—a min Kai Yaya LamiÉ—o yayi sannan yace "Uhmmm mahaifin shine
yataimaka mana. He's at the admin block right now nasan ma bazai wuce yanacan yana
nema na ba dan anatashi daga assembly bayan anyi introducing dinmu Aziza tazo
tafada min halin da kike ciki shine direct muka taho nan" Ina kallonshi adoringly
nace "Thank you" last spoon din abincin yakaimin bakina nakarba Yana fadin "Rike
godiyan ki bana so" sekuma muka saki dariya atare.
Seda yabani maganina nasha sannan yace min bariya shiga makarantar gurin colleagues
dinsa yaji yaza'a raba musu ajin dazasuna koyarwa kada ayi dismissing É—insa tundaga
day one. Bayan tafiyarsa bada jimawa baccin me daÉ—i yaÉ—aukeni bani natashi ba seda
yanma kuma Ina buÉ—e idanuna suka shigo É—akin shida abokin shi Yaya Auwal wanda
kallo ɗaya nayi Masa natuno fuskarsa dukda naga ya ƙara manyanta,yakara kyau fiye
da last time dana haÉ—u dashi a field trip. He's the serious and delligent Auwal
dana sani tun can baya. Bayan mungaisa dasu se Yaya LamiÉ—o yazauna agefena yana
faɗin "Yarinyar Nan baccin ki yaso tsoratani fah" Ƴar dariya nayi sannan nace
"Kaman Yaya?" Sakan baki yayi yana kallona sannan yace "Tunfah safe kike bacci. Kin
masan lokaci yanzu kuwa?" innocently nashiga girgiza kaina sannan nace "Uhm Uhm
bansani ba" É—aga idanu Yaya LamiÉ—o yayi yakalli wall clock É—in dake É—akin wanda
hakan yasa nakalli gurin Nima. Ganin 4:30pm danayi jikin agogon ne yasani sauri
dawo da dubana garesu da mamaki.
Nace "4:30pm?" Ƴaƴa Auwal da Yaya Lamiɗo gyaɗa min Kai sukayi cikeda assurance.
Baki sake nace "Banyi azahar ba" Yaya LamiÉ—o na kallona yace "Bakici lunch ba" se
Yaya Auwal yakarasa da "batayi la'asar bama kuma ba" pouting bakina nayi ayayinda
nadafe kaina sannan nace "Anma ya akayi nayi bacci sosai haka?" Aziza dayanzu
shigowanta É—akin daga bakin kofa tace "Tayaya bazakiyi bacci har haka ba bayan
rabonki dasamun bacci me kyau tun ranar asabar" tura bakinayi Ina hararanta
playfully batareda nace komaiba. Alokacinne kuma Nurse tashigo taganni tareda su
muna wannan conversation din.
Sallama na tayi atake wai ai nasamu sauki tunda har Ina hada mutane muna surutu,in
tattara inkoma hostel. Bakaramin dadi sallamar nawa yamin ba haka muka tattara muka
tafi hostel nida Aziza inda Yaya Lamido da Yaya Auwal suka fita a makarantar wai
zasuje gidan wani Uncle din Yaya Auwal
su dawo. Ranar ban fita night prep ba dukda kuwa naso zuwa anma se Aziza tahana ni
wai inyi zamana a dakin metron dinmu for ranar inkara Jin karfin jikina. Danace
Mata inason inyi copying notes É—inda nayi missing ranar setace zata kawomin har
hostel inyi tunda banason wani yayimin note. Aikuwa hakan akayi, kafin lokacin
night prep taje class tadauko min books Dina da nata takawomin hostel kafin tatafi
inda mukayi akan da andawo zatazo tayimin explaining abunda bangane ba.
Da aka taso daga Prep segata da written letter,gasasshen barooo da Bread wai Yaya
lamido yazo nema na a aji baisameni ba shine yabata sako ta kawomin. Aida sauri na
amshe ledar sabida kamshin Naman baroon daya bugi hancina. Tare muka ci da bread
din kafin daga karshe takoyamin Maths dinda akayi ranar takomayimin explaining wasu
abubuwan daban ganeba a other subjects kafin tawuce hostel dinsu dataji anata
kokarin rufe gates na hostels din. tattare books dina,ledan naman da bread É—inda
muka gama ci nida Aziza nashigayi don insamu inkwanta bacci inda ananne Naga letter
É—in da LamiÉ—on yabama Aziza tabani. Cikin sauri naÉ—auka nashiga budewa,ni kwata
kwata nama manta tabani letter tsabar kwadayin nama Wanda seyanzu nagani abun
yafadomin arai.
Karantawa nashigayi ahankali bayan nagama warware takardan,ga abunda sakon ya
kunsa.
_Hey Nanaaa_
" _I just want to order you something. Are you getting well soon or not? _ "
" _If you are not getting well soon,Then I am coming and hitting you hard_ "
" _Ok don't get scared ya..I was just kidding..._ "
" _Wish you recover too fast and join the school activities along_ ".
Hope you know that you are pretty strong?So get well soon.
And yes...
*Good night* bansan sanda wani dariya ya kubuce min ba ayayinda nadan bugs tsallen
farin ciki akan gadon nawa wanda har hakan seda yasa dabata Jima da shigowa Bayan
fitar Aziza lekowa tana kallona. Sauri nayi na boye lettern Jin motsinta ayayinda
nakwanta naja bargo na lullube kaina Ina blushing nikadai.
***
Washegari Tuesday tunda muka fara first period bamusamu free period ba harlokacin
break yayi dankuwa kaf Malaman sunzo sun koyar a lokacin period dinsu. Hakanan akai
akai Aziza takan taba ni tanuna min windown class din namu inda nake hango Yaya
lamido daga waje yana leken cikin ajin namu, zuwan shi uku amma duk bai samu ganina
ba. Haushi kamar inyi yaya,gashi ba abun indauki excuse ba awuceni a explanation.
Aikuwa inaji anyi ringing bell din break nahau murnar Teacher zaifita yabarni inje
Inga Yaya lamido anma da mamakina senaga Teachern yaki fita yacigaba da koyarwansa.
Tsabar haushi ban San sanda na galla masa harara ba dukda kuwa aikin banza nayi
tunda attention dinsa bayakaina. Ashe Aziza tana ganin duk abunda nakeyi,mintsinina
tayi ta kasan bench wanda hakan yasani kallonta cikin sauri ina fadin "Auccch!!!
Miye hakan" matsowa tayi kusa dani sannan teasingly tace "Tambayar ki nakeson yi ko
akwai abunda baki ganeba intambaya Mana Malam Babagana inya gama explanation"
harara na watsa mata sannan ahankali nace "Seki tambaya din ai mugani" Yar dariya
tayi sannan tace "kidai Kara hakuri yanzu zai fita nasani and besides Yaya Lamidon
ma baisake zagayowa ba,ba lallai kisamu ganinshi ba may be se an tashi a class
tunda zamuje saya ma kanmu da Ill mannered sister's dinki abincin break" yatsina
fuskata nayi ina shirin yin magana se muryar Mallam Babagana Islamic studies
teachern mu ya katseni,tambayar Yan ajin yake yi koda akwai wadanda suke da
question din tambaya. Aziza daga hannunta tashigayi ta karkashin bench tana teasing
dina wai zatayi tambaya akara delaying time. Sauri nayi nadanne hannunta tareda yin
pity face Ina fadin "Don Allah save your question for next class" Aziza na dariya
tace "Wasa nike Miki. I'm fed up with his class too. ga wata uwar Yunwa danakeji"
tayi maganar tana taba cikinta.
Malam Babagana ganin Babu Wanda yakeda tambaya seyace "We now call it a day"
ayayinda yadebi teaching materials dinsa yafice a ajin. Maida books dinmu mukayi
cikin locker muka rufe sannan muka tashi zamu fita Aziza na mitar ita tagaji dazuwa
karban kudin break dinsu Yaya Aisha danakeyi,shima yana Kara Bata Mana lokaci wurin
sayan kayan break kullum.
Nidai hakuri nashiga bata ayayinda muka nufi kofar fita a ajin,inda sabo nasaba.
Dan Kullum Aziza setayi mita da korafi akan thesame Abu and I don't blame
her,gaskiya take fada toh amma yazanyi?. maganan ganin Yaya lamidon kuwa bancire
ganinshi araina ba kamar yanda tabani shawara,infact nayi niyar inmuna dawowa daga
tuckshop zan roketa mubi ta admin block mudubashi tunda shi yazzazzo dazun ganine
baisamu yayi ba.
Jinayi na bugu da mutum abakin kofar fita a class din namu Wanda hakan yasani
saurin jada baya Ina fadin "Ya ilahi" ayayinda nadaga idanuna dan Inga wanene. Yaya
lamido ne,shima jayayi da Bayan Yana fadin "Ya ilahi. Nanaa zaki fasamin ciki"
sekawai nasaki dariya sakamakon yanayin yanda yayi maganar sannan nace "Sannu"
wucemu yayi nida Aziza yakarasa saman desk Dina yazauna yana fadin "Ko inama kuke
shirin tafiya kuyi hakuri kudawo kuzauna inyaso Inna tafi kwatafi. First it was
your old fashioned and punctual Teachers and now ku zaku tafi yawo" binsa mukayi
abaya muka koma kusa da seat din namu, Aziza nafadin "Bafah yawo zamujeba Yaya
lamido. Tuckshop zamutafi sayan kayan yin break" daga mana wani leda yayi Wanda se
alokacin ma muka lura dashi sannan yace "I bought it already"
cikeda farin ciki Aziza taje kan seat dinta tazauna tana fadin "Thank you. Yau mun
huta da wahala" Baki sake nace "Aziza Yakika zauna? Kizo muje mu don Allah"
batareda Aziza tabi takaina ba tashiga kokarin bude ledan da Yaya lamidon yakawo.
Wani kallo Yaya Lamidon yashigayimin,kike "what's wrong with you dinnan" anma
senayi kamar bangani ba,zama nayi a seat dina ayayinda naja ledan dake kan desk din
Azizan nadauki baked meat pie da lacasera dinda yasiyo Mana koya daidai nashiga ci.
Inajinsu sunata hira shida Aziza anma gabadaya ni hankalina baya kansu,tunanin su
Yaya Aisha nacan suna jirana kawai ke yawo a kwalkwalwana,innace zanyi wani yunkuri
Kuma Yanzu Aziza setace zata fada ma Yaya lamido don bataba sanar dashi aikena
dasukeyiba da maganar fitsarin kwancen Sadiya and indai maganar taje kunnenshi
he'll surely make mountain out of a mall nasani.
Footsteps dinda mukaji ne yasamu juyawa Baki daya muka kalli kofar ajin dankuwa
Daman mukadai be acikin class din,tunda Malam Babagana yasake mu duk kowa yatafi
neman abunda zaisa ma cikin sa Kuma haryanzu basu fara dawowa ba dayake yaudin
bamufita break dawuri ba. Junior dinmu ce Yar dakinsu Yaya Aisha tashigo ajin namu.
Seat dinmu ta karaso tana kallonmu tace "Ina wuni Sister Rukayya da Sister Aziza"
amsawa mukayinda "Lafiya" atare sannan tagaida Yaya lamido. Ya amsa shima kafin
tadubeni tace "Yaya Rukayya su Yaya Aisha ne sukace inkiraki" Daman nasan za'arina
don haka senace "kije kice Ina zuwa" gyadamin Kai tayi sannan tajuya tafita
ayayinda Yaya lamido ke tambayana waye "Aisha" ajiye meatpie dinda ko rabi bankai
ga ci ba nayi sannan natashi tsaye Ina fadin "Room dinmu daya da'ita. Sako zanbata
yanzu zandawo" Aziza cikin sauri Rai bace tacema Yaya lamido "She's lying Yaya
lamido. Daya daga cikin cousin Sister dinta ne Aisha" wani kallo na watsa ma Aziza
anma sema tayi kamar Bata San inayiba,tana kallon Yaya lamido tace "Sunga bataje
takarbi kudin yimusu break a tuckshop bane shine suka aiki wannan yarinyar
takiraya" da mamaki Yaya lamido yace "Kamar Yaya? Ita takezuwa saya musu Abu
kullum?" Aziza tace "Eh fah. Tun js1 ake abudaya. Kullum mu muke zuwa musaya musu"
cikin Jin haushin abunda Aziza tayi nace "Karyane! She's lying sako zanbasu Allah"
kafin nayi sauri najuya Zan nufi kofar fita a ajin anma senaji Yaya lamido yariko
hannuna.
Juyowa nayi zanyi magana anma ganin yanayin expression din fuskarsa yasa nakasa
cewa komai .
Strictlya yace "Dawo kizauna" tsabar irin kwarjinin dayamin bansan sanda nakoma
nazauna ba. Meatpie dinda na ajiye yadauka yabani sannan yace "Eat" idanuna cikeda
hawaye nace "Nakoshi" strictly Yaya lamido yakuma cewa "Eat...!" dole nashiga ci
Ina hadawa da cold drink din babu kakkautawa ayayinda yasa hanky yasharemin guntun
hawayena dasukayi slipping akan cheeks dina. Inajinsu shida Aziza suna hirar
makarantar mu inda yake fada mata ajin dazai dinga dauka.
Ss3,ss1 da ajinmu
Wai ss3 da ss1 din Geography zena koya musu ayayinda mukuma English zenayi mana
sabida Malamar English dinnamu zatayi tafiya hutu shine zaiyi taking over kafin
tadawo.
Ahaka har Yan ajinmu suka fara dawowa aji daga tuckshop hakanan kowa yashigo seya
dinga mana kallon mamaki,daga masu kus kus semasu saka Mana idanu anma Yaya lamido
ko akwalar rigarsa,seda akayi ringing bell sannan yatashi daga saman desk
dina,yasunkuyo kusa da kunnena, ahankali yace "Don't
be afraid Nanaa. No one will dare touch you when I'm around" bansan sanda nakalli
cikin idanunsa ba,idanunsa dasuke cikeda promises da dama dabasai ya furta ba nake
ganesu.
Jinjinamin kai yayi yana murmushi sannan yama Aziza sallama yatafi. Wata Zuwaira da
seat dinda ke bayan namu tana ganin Yaya lamido yafita tayi sauri tataso tazo seat
dinmu tana tambayarmu inda muka sanshi. Aziza ne tace Mata ai Yayana ne aikuwa Sega
seat mate din Zuwairan Asma'u tataho seat dinmu Itama tana fadin "Bana fadamaki ba.
Shine Wanda yake zuwa Mata visiting dinnan" fuska daukeda murmushi Zuwaira takalle
ni sannan tace "Lord... I envy you Rukayya. Inama duka Yayun duniya haka suke"
yatsina fuska Asma'u tayi sannan tace "kibari kawai Zuwaira. Kiganshi very handsome
and caring,bedamu da abunda Yan ajinmu ketayi ba fa tun baywn shigowarsu dasuka
ganku tare. Da Yayana ne take serving a makarantar nan ninasan nunawa ma zaiyi
baisanni ba in public sabida zece Zan iyaja Masa raini gurin dalibai" Zuwaira tace
"Uhmm keda kikeda Yayan ma kenan. Ni nice Yayar kaina" Aziza tayi dariya tace "Ke
first born ce kenan?" gyadakai Zuwaira tayi sannan tadubeni tace "Kiyi hakuri I
judge things without knowing. Wallahi yanda Naga Yana Miki nadauka saurayin kine ba
Yayankiba shiyasa ma naita musama Zuwaira da muke maganar tare harnace Sena
tambayeki" murmushi kawai nasakar ma Zuwaira bance komai ba.
Malamin Basic science É—inmu dayashigo ajinne yasa Zuwaira da Asma'u komawa seat
dinsu dasauri ayayinda Sauran Yan gulma dake eardropping akusa damu duk suka koma
seat dinsu Suma. Har closing hours yayi tsananin ganin su Yaya Safiya da Yaya Aisha
nakeyi,nadauka zasuzo sucimin mutunci sabida banje nasaya musu break ba dasuka
kirani ma Kuma banje ba anma da mamakina sebasu zo dinba. Sena dauka zasu nemeni a
hostel anma Koda muka koma hostel dinma se basu neme ni ba,Kuma da Sadiya tadawo
batakawomin uniform dinsu Yaya Aishan da socks dinsu dasuka saba Bata kullum after
class takawo min in wanke ba. Nikadai se jimamin abun nakeyi araina, dana fita
diban ruwa ma banhadu dasuba bare subani daukan ruwa inkai musu hostel dinsu. Ahaka
nashirya Aziza tabiyomin muka tafi Evening prep,bamu Jima da Isa class ba sega
descipline Master da Yaya lamido sun shigo ajinmu. Tashi mukayi duka muka gaidasu
sannan descipline Master din yadubeni nida Aziza yace mubi bayansa. Take jikina
yafara rawa ayayinda tsoro Mai tsanani yashigeni Danni gabadaya abunda nakawoma
Raina shine students sunkai karar muna Hira da corper a aji shine akazo aka dibemu
za'a Mana hukunci.
Admin block muka nufa zuciyata nata racing gashi Yaya lamido betsaya yakalleni
koyamin wata maganar dazata sa tsoron nawa yadan sassauta ba. Infact Hira sukeyi
shida descipline Master din. Cikin staff room muka shiga inda nahango Yaya Aisha da
Yaya Safiya suna kneeling hannunsu dage sama kuma dukansu biyun babu wanda tacire
uniform din jikinta,ma'ana basu koma hostel ba. Muna Isa gabansu descipline Master
yadubeni sannan yace "They've been bullying you for three years right?"
Zangirgizakaina alamar a'a descipline Master din ya katseni da cewa "Don't be
afraid. Your brother has told us everything da close friend dinki tafada Kuma Suma
seniors din naki sunyi confessing laifinsu. Makarantar nan babu wanda za'a zalinta
bamubi Masa hakkinsa ba. Kidaina tsoron kowa dukwanda yamiki laifi so far as yafita
a rules and regulations na makaranta kizo admin kifada Mana kinji" jiki sanayaye
nagyada masakai na.
Dubansu Yaya Aisha yayi sannan yace "Apologize to her" wani kallo suka bini dashi
Wanda harsaida yakuma maimaita kalmar "Apologize to her" din sannan sukace "Sorry"
kamar wasu masu ciwon baki inda daganan Kuma Desplinee Master din yashiga kashe
musu warning. Yace "Makaranta bata Hana seniors aiken junior dinta ba,hakanan
makarantar Bata hana senior purnishing student intayi mata laifi ba,do it in a
proper way anma bazamu taba accepting a situation whereby Wani zaisaka wani agaba
Yana cin zalinshi ba,bazamu saka idanu muyi shiruba muna gani ana maltreating
students dinmu in a wrong way. You girls are all here to learn, you're all here to
have so many experience not to make someone feel like he's in a prison or any other
enemy's home. This's a college,we're here to interact,learn and support each other
bawai muyi making life din wani miserable ba. It doesn't matter if you're related
or not,be like a family,love each other like one big family sabida Kuma ayi
treating naku family members din well somewhere out there kunajina" girgizamasakai
sukayi kamar gaske,muma Kuma seya dawo kanmu yashiga yimana fada nida Aziza akan
bawai don Yana purnishing dinsu a gaban mu ba kuma muce zamu rainasuba,laifi sukayi
yake hukunta su daidai da laifinsu and if we dare do thesame abunda yafi nasuma
zaiyi Mana. Daga karshe yace suje suwnke duka toilets din classes area insungama
suzo sukirashi yaje yagani shine purnishment dinsu.
Mukuma ya sallame mu muka koma ajinmu. Nidai narasa farin ciki zanyi ko bakin ciki
hakanan narasa shin godiya zanma Yaya lamido ko sabanin haka. For sure nasan komi
yayi yayine sabida ni,he want me to be happy anma nikuma nikadai nasan menake
hangowa shiyasa tun fari banaso yanasanin halin danake ciki din.
Da dare during night Prep muna answering wani PQ na Mathematics nida Aziza muka ji
Yan ajinmu na gaisuwa,daga wa mukayi atare dan muga wanene and there I saw Yaya
LamiÉ—o and Yaya Auwal. Sune suka shigo kowanne da dorina ahannunsa sunzo patrol na
night prep. Yaya lamido nasanye da Ash pajamas ayayinda Yaya Auwal kesanye da Farar
jallabiya. Seat dinmu Yaya lamido yakaraso ayayinda yasunkuyo kusa dani ahankali
yace "Did they trouble you again?" kallon cikin idanunshi nayi sannan na girgiza
masakaina alamar a'a. Wani sanyayyar ajiyar zuciya yasaki sannan yayi murmushi,yace
"Inkun tashi kisameni abakin masallaci, I've something for you" gyaÉ—a masakai nayi
dukda Ina mamakin menene kuma miyasa bazai bani anan ba but I trust him,koma minene
inmun hadun zanji ai. Ana tashi abakin masallacin muka samesu shida Yaya Auwal.
Bakar leda kawai ya mika min sannan sukayi mana "Saida safe muka tafi".
Doya ne me manne da kwai me shegen daÉ—i Kuma lokacin dayabanin akwai dumi
sosai,muna Isa hostel mukaci nida Aziza sannan tawuce hostel dinsu. Washegari two
period to lokacin break din time din English ne. Seda first period yawuce har
anshiga wani sannan Yaya lamido yazoshi. Dayawa a ajin namu harsun cire Rai
baza'ayi class din bama danbasusan ancanza Mana teacher ba,nida Aziza ne kawai muka
sani and she's always punctual,in batazo lokacin da time dinta yayi ba toh bazata
zo ba gabadaya Kenan. Surutu sosai Yan ajin namu keyi,masu Hira nayi masu iface
iface nayi anma Yaya lamido na shigowa kowa yashiga taitayinsa yanemi guri yazauna.
Nihar mamakin yanda shida Yaya Auwal students basuyi musu haukan dasukema duk wasu
sabbin corpers da ake kawowa makarantar ba.
Littafin Qadr na kudine duk Maison shiga paid group should talk to me privately via
WhatsApp 08147722806 for payment details.
*Page Forty Eight*
Avoid typing errors please.
Yana shigowa bezarce ko Ina ba se gaban desk dinmu nida Aziza. Akan desk din Aziza
ya ajiye teaching materials dinda yashigo dasu sannan yadubi entire class din yace
"Good morning class" da turancinsa da is very clear and fluent sannan ga ascent din
fillancinsa daya karama yanayin turancin nasa gardi.
Gabadaya Yan ajin amsawa mukayi da "Morning Sir" kafin Yaya Lamido yace "let me
start by introducing myself first" seyadan numfasa kafin yafara introduction
din,yace "I'm Isma'il Yusuf Kwami From Gombe state, Kwami local government. I
finished all my studies within Gombe state. And Alhamdulillah I'm now fully a
graduate in BSC Geology. I'm here for my NYSC program and within my entire NYSC
program I'll be taking you guys English Language in the absence of your Teacher.
She'll be out of the college for few months due to some personal issues" jinjina
kai mukayi duka sannan yakarada "I hope you guys will cooperate with me for a
better understanding?" "Yes sir" shine abunda duka Yan ajin muka fada.
Sekuma yace muma muyi introducing kanmu one by one sabida yasan kowa.
Dagakan first row akafara inda kowa zaifadi full name dinsa,state of origin dakuma
local government dinsa hakanan he somehow makes the class lively tahanyar tsokanar
yaren mutum kokuma inkayi kama da masu yaren ko bakayi kama dasuba. Ahaka har aka
iso kan row dinmu wanda mune a seat din gaba nida Aziza dankuwa tun js2 dinmu muka
Zama seatmates,ita yafara tambaya tayi introducing din kanta tagama Wanda ni
atunanina nice next anma da mamakina senaga sabanin hakan. Tsallake ni Yaya Lamido
yayi tahanyar nuna Zuwaira dake bayana.
Binsa nayi da idanu baki sake jin ya tambayi Zuwaira sannan cikin sauri nace "Yaya
Lamido ka tsallakeni baka tambayeni ba" ni gabadaya ma na manta position dinsa
awannan lokacin dakuma inda muke,naga ana tambayar kowa ankuma tsallakeni shiyasa
nayi magana dankuwa har rehearsal din yanda zanyi introduction din nagamayi a
Raina. Dariyar danaji wasu daga cikin Yan ajinmu nayine yasani sauri gane
baranbaramar danayi, sauri nayi nasa palms dina a bakina Ina wara idanu ayayinda
nakalli Yaya Lamido nace "Sorry Sir" anma memakon ya kawar da zancen tahanyar
karban tuban nawa seya dubeni with a smile on his face yace "Mezan tambayeki
Nanaaa? Is there anything new that I need to know about you?" Shiru nayi bance
komai ba,seyayi dariya, yace "I'm asking those that I don't know kekam aisede ma
atambayeni Abu game dake" sekuma yamaida hankalinsa gakan Yan ajin.
Yace "Don't mind her. She's my sweet little Sis,nema kawai take tatadamin hankali
babu gaira Babu dalili" dariya Yan ajin sukayi inda daganan kuma aka cigaba da
introduction din har aka gama. Tambayar mu yayi topic dinda muka tsaya muka fada
mishi,seya koma farkon topic din yadan sake briefing dinmu akan topic din kafin
yashige next topic dazamuyi maisuna "CLAUSES". Yafara mana introduction kenan
lokacin break yayi. Aikuwa yanajin anyi ringing bell yarufe teaching materials
dinsa yadubi Yan ajin namu yace "it's time for break,so let's just call it a day"
gyadakai mukayi duka inda mukace "Okay Sir" cikeda farin ciki anma memakon
yatattari takardunsa yafita yabar ajin sekawai yahau saman desk dina yazauna yana
fadin "How do you see me teaching today?" murmushi nasaki sannan nace "Bravo alaik.
you did well! Like very very well Yaya lamido. Bantaba tsanmanin you can teach well
like this ba" nayi maganar sincerely.
Dariya yasaki Jin abun da nace sannan yadan sassauta muryarsa,in a funny manner
yace "Ke karfin haline fah kawai and moreover it's English,naci ubana gurin Aunty
chioma dole bazan mantashi ba" dariya nida Aziza mukayi inda Aziza tace "wacece
kuma Aunty chioma?" grinning Yaya Lamido yashigayi sannan playfully yace "Aziza
yakaman kema kinason kizama Miss curious kamar kawarki neh?" Sekuma yayi sauri ya
juya yana karema class din kallo tako Ina,duk yawanci anfita break,mutum dayace a
ajin,Itama kuma tanacan baya zaune kan seat dinta wanda hakan yasashi yin kasa da
murya yace "warning Zan muku. nasan ku da shegen tambaya,toh wallahi kurufamin
asiri kada wataran kujefomin tambayar datafi karfina a ajin ku inkasa amsawa insha
kunya" dariya muka saki nida Aziza harda nikam harda rike ciki.
Aziza tace "A'a Yaya Lamido zama ka iya amsawa Insha Allah. We fully trust you"
cikin sauri Yaya lamido ya girgizakai,yace "A'a fah,ajiye batun trust dinnan agefe
yarinya. Sabida English ne yasa kuka ga hakan ma and all thanks goes to Aunty
chioma my lesson teacher tun Ina karami,ita tayi coaching dina tun Ina karami and
that's the reason why harna iya tsayuwa agabanku yau na koyar daku. Dan wallahi da
ace dan attending school danakeyi ne kawai wallahi da babu abunda zan iya koyar
daku" cikeda curiosity nace "Seniors dinmu da zakana ma Geography din kuma fah
yazakayi dasu Yaya lamido?" yace "yarinya jiya nayi first class dina dasu, note
kawai nadinga dirka musu suna dictating. nakuma ki bama kowani dan air fuskar yin
tambaya" dariya muka sake saki nida Aziza Ina girgiza kaina in desbelief.
Daga idanun dazanyi kawai sena hango Yaya Aisha da Yaya Safiya sun shigo ajinmu.
Zuciyana dukan uku uku yashigayi lokaci guda ayayinda nakasa dauke idanuna daga
garesu. Tsinkayar muryarsu nayi suna gaida Yaya lamido ya amsa nidai duk bance
komaiba amma kuma azuciyana mamakin meya kawosu nakeyi.
Sekuma naga yaciro kudi a aljihun wandonsa yabasu yanayi musu lissafin abunda zasu
suyomai a Tuckshop haryagama suka juya suka fita. Dawo da dubansa yayi gareni yace
"Koh bazakuci eggroll ba?" wara idanu nayi sannan nace "Daman namune?" yace "Uhmm
mana kona miki kana da secondarian mecin breakfast yakuma zo yaci break irin ku?"
tura baki nayi gaba sannan nace "toh ai da ka bari zamuje musiyo dakanmu" Kai tsaye
Yaya Lamido yace "Banyi niyaba,sunayi niyar aika" Aziza kuwa se farin ciki takeyi
hardacewa "Wallahi Yaya Lamido ka burgeni. Koba komai kana raama ma Rukayya
abubuwan dasukayi Mata" Yar dariya yayi sannan yace "Yauwa Yar gari,that's exactly
what I'm doing" tsuke fuska nayi lokaci guda Jin abunda suka ce din sannan nace
"Nikam basai an ramamin ba nayafe musu duk abubuwan dasukayi min" hararan wasa Yaya
Lamido ya yimin sannan yace "toh holy holy,inke kinyafe mu bamu yafe ba" Aziza tace
"Wallahi kuwa Yaya lamido. Nimadai banyafe ba kuma wahalar zuwa shop dinnan hardani
akeyinta kullum" harara na watsa ma Aziza Jin tana kokarin rura wuta a abun sannan
na maida dubana kan Yaya lamido na tura baki gaba,cikin sigar shagwaba nace "toh ai
ina makaranta ma tariga da ta hukunta su tun jiya" Yaya Lamido yace "sekuma kiyi
ai,Makaranta daban ni daban,purnishment dinda school tabasu sukayi daban haka nima
nawa punishment din dazan basu daman" kamar zanyi kuka nace "Don Allah nidai
kabarsu kawai. Allah komai yawuce agurina...." tabe baki yayi sannan yace "Sekuma
fah kiyi ai"
Ganin dagaske yakeyi senayi shiru bankuma cewa komai ba gashi Yan ajinmu sunfara
dawowa daga break lokacin,inaji su Zuwaira dake bayanmu sunata kokarin su shiga
conversation dinda Yaya lamido keyi da Aziza anma duk seya gwasalesu yayi kamar ma
besan sunayiba harsuka hakura sukayi shiru.
Seda aka kusan kada kararrawa sannan su Yaya Aisha suka kawo kayan break dinmu da
Yaya Lamido ya aike su saya,karba yayi yabamu agabansu sannan ya sallamesu suka
tafi. Inaganin yanda su Yaya Aisha keta kumkumbura fuska wanda hakan yakara haddasa
min tsoro araina,naso kin karba tun sanda yabani anma babu dadi,zezama kamar na
kaskantar dashine agabansu bayan kuma abunda yakeyi sabida ni din yakeyinshi
dukdama yakasa ganewa abunda yakeyi din kamar son sake jazamin wani wutan yakeyi.
Seda na tabbatar sun fita a ajin sannan namayar masa da ledan kayan break din nace
"Gashi" kallona yatsaya yi da mamaki sannan yace "Mezanyi dashi?" Tsuke fuska nayi
sannan ahankali sabida kada su Zuwaira dake bayanmu suji nace "Bazanci ba nakoshi"
shiru yayi yana kallona nadan wasu dakiku kafin yatashi daga zaunen dayake ya
tattari books dinsa yace "inbaza kici ba seki zubar dasu" kafin yajuya yafita yabar
ajin batareda yasake waiwayena ba. From his tune nasan baiji dadin abunda nayi
masaba. Toh anma yazanyi? Taya zanbari yacigaba da kwatar min yanci anan bayan
nasan innakoma gida I'll surely pay for each and every abunda su suke going through
anan din....
Aziza ma bataji dadin abunda nama Yaya lamidon ba,tanaganin yafita tajuyo tana
kallona tace "Rukayya wai menene hakan kikayi yanzu?" Bansan sanda hawaye yafara
bin kuncina ba, ahankali nace "Aziza toh yazanyi? It's not as if I'm not grateful
ga abubuwan da Yaya Lamido yakeyimin. Nasan taimakona yakeyi anma sede shi baisan
taimakon dayakemin anan din ba might lead to another disaster for me Inna koma gida
and besides komi su Yaya Aisha sukayi min yariga da yawuce,in hukuncine anriga da
anyi musu there's no need yace shima seya hukunta su kamar yanda sukayi min" Aziza
rai bace tace "koma miyene baikamata ace yayi putting alot of effort ya aika
asiyomiki abinci kidubeshi kice bazakiciba. You should have explained politely
sekada yasake" senace "Hmmmm Aziza kenan. Haryanzu bakisan waye Yaya Lamido ba.
Inyayi niyar abu seyayi,tunda namishi magana yanuna bazai bariba inban nuna bacin
rainaba nasan bazai bari din ba and karki damu bawai wani fushi yayiba anjima zai
sauko" jinjinakai Aziza tayi sannan taja ledan kayan break din tana fadin "toh
nikam bani inci tunda bansamu naje na sayaba. Allah yagani yunwa nikeji bazan iya
da wannan rigimar takuba" nidai bance matakomaba sema mikamata ledar danayi dankuwa
kotaci kobata ci ba shi yasan bazan taba ciba tunda nace bazan ci dinba.
I thought zanga Yaya Lamido a evening prep yazo nemana tunda bandauka fushin gaske
yakeyi ba anma shiru babu shi babu labarin shi,haka night prep ma bezoba har muka
koma hostel wanda hakan yasa naji hankalina yatashi dankuwa yanzu na tabbata fushin
yakeyi dagaske. washegari ma kwata kwata banganshi ba dayake bamuda English
ranar,daman during break ne nayi tsanmanin zuwansa anma shiru babu shi babu
labarinsa nanma. A break din Kuma segasu Yaya Aisha ma sunzo nemansa cemasu mukayi
baizoba inda naji Yaya Safiya nacema Yaya Aishan suje staff room suneme shi kada
kin nemanshin yazame musu wani laifin kuma. Ananne nagane Ashe cewa yayi kullum
suna zuwa suna samunsa a ajinmu during break and if that's the case kenan yayi
niyar Yana zuwa guna kullum lokacin break toh amma segashi yaudin bezoba,ma'ana
fushin dai yakeyi.
During prep ma bangashi ba harmuka koma Hostel.
Arana na ukunne mukeda English first two period,ranar har Allah Allah nadingayi
time yayi yazo muhadu Intabbatar dagasken fushin yakeyi kokuma shurgullah ne
yahanashi zuwa gurin nawa dukda nafi zaton fushin yayi danhaka kawai Yaya Lamido
bazai ki zuwa ganina ba and besides wani aikine zaimishi yawa? Bayan ba kullum bane
yakeda class da students dinshi and moreover shi mutum ne da baya takurama kanshi
akan harkar karatu. Seda first period yawuce gabadaya sannan yashigo ajin namu
kamar yanda daman hakan yace zenayi duk ranar damukeda shi.
Yau manyan kaya yasaka dayake Friday ne kuma kayan ba karamin amsar jikinsa yayiba.
Bakin yadi yasaka dayasha aiki gakuma wanki da guga da akayi masa mai kyau. hular
kansa ma baki haka ma cover shoe dinda yasaka bakine. Sajen nan yakwanta luf luf
gwanin ban sha'awa,yafito fulanin sa sak. Akan desk dina ya ajiye books dinsa daya
shigo ayayinda duka Yan ajin muka gaida shi ya amsa sannan yafara mana koyarwa
cikin nutsuwa da kwarewa hakanan yanayi yana making funny funny jokes tayanda hakan
yayi making class din lively. Gashi baya tsatsaura bayani,cikin sauki yakeyinshi
tayanda kuma kowa zaigane.
Aranar yagama mana "clauses" sannan yabamu excercises dinda ke karshen topic din a
text book dinmu yace mu amsa su acikin mintuna goman dasuka rage time dinshi
yakare. Nidai kallon shi kawai niketayi inaso yakalleni,inaso yamin magana amma
kuma kwata kwata shiyaki yarda muhada idanu tunda yashigo ajin dukda kuwa be matsa
daga gaban seat dinaba. Sena tsiri kinyin excercise din dayace ayidin kozai yimin
magana yatambayi ba'asi amma shima shiru becemin komaiba,inagani Aziza tayi nata
tabashi yaduba yace tayi daidai inda daganan kuma yashiga zagayawa yana duba na
wadanda sukace masa sungama nasu a ajin.
Ganin haka senima nayi sauri nafara amsa nawa wai dukdan inyi ingama ince masa nima
nayi yazo yaduba nawa insamu yamin magana. But I was not lucky dankuwa yanacikin
duba na wata class mate dinmu acan baya akayi ringing bell,haka yabar natan ma be
karasa dubawa ba yafice wai yana da class da Yan ss1,yace next class zekarasa
dubawa which is next week Tuesday. Inaji yan ajinmu nata yaba method of teaching
dinsa anma ni wani irin kututun bakin cikine naji ya ziyarceni,senaji I feel so
low! Senaji inajin haushin shi nima inbahaka ba wani irin laifine namishi mai
tsauri dahar ko kallona bayason yi? Dan kawai nace bazan ci abincin daya sayaba? I
don't think this's a genuine reason. Sonake inyi kuka anma sena daure sabida
banason abunda zaijamin attention acikin ajinmu and moreover nasan sunanan daman
suna kus kus dinsu a tsakanin su ganin yau bamuyi magana da Yaya Lamidon ba.
Yana fita wani Malamin yashigo mana don haka senayi kokari namaida gabadaya full
attention dina kan abunda Malamin yake koyamana a ajin dukda kuwa abun yanacina
arai. Seda akatashi a makaranta sannan mukasamu magana da Aziza.
Tambayana takeyi wai nahadu da Yaya Lamido ne kwana biyunnan dasuka wuce,tsabar
takaici bansan sanda nace mata "Bansani ba Aziza" sakan baki Aziza tayi tana
kallona sannan cikin sigar tsokana tace "Bafah ni nakar zomon ba Rukayya. daga
tambaya se cibi yazama kari?" Rai bace nace "Kema kinsan ai banhadu dashiba kike
min tambayar rainin wayau" Aziza setace "Nasani koya nemeki sanda bamwa tare?"
Tsaki nayi sannan nace "Yaushe ne bamwa taren, we're always together Aziza so
kimadaina min irin wannan tambayar please..." Aziza tace "not all the time.
Inmunkoma hostel ai kowa hostel dinsa yake tafiya,nasani ko awannan tsukukin
lokacin yazo yanemeki kun hadu" ganin Aziza bazata hakura tabar min musuba sekawai
nace "Toh bamu haduba shikenan?!" Aziza cikin sigar zolaya tace "toh koh kefah,
abunda nikeson ji daga bakin ki kenan anma daga tambaya sekihau yimin bala'i" nidai
bankuma cemata komaiba sema tafiya na danacigaba dayi dadan sauri.
Kama hannuna tayi cikin sauri sannan takalleni dakyau,wannan karan with serious
face tace "Anmadai kinsan fushi yakeyi dake koh?" fuska daure nace "Basai yayi
tayiba" sakan baki Aziza taykumayi cikeda mamakina tace "seyayi tayi Kuma? Hakuri
yakamata kibashi Rukayya. Dan abunda kikayi kema kinsan baki kyautaba" nace "Nidai
bazan bashi hakurin komaiba danni banga laifin danayi anan dahar zaisa yadauki irin
wannan zafin ba. daga nace Bazanci abincin daya sayamin ba? Koh ana dolene daman?"
Sauke numfashi Aziza tayi sannan tace "Nima bandauka zaiyi fushi hakaba,I thought
ma yadanyi tafiya na kwana biyune shiyasa bamwa ganinshi amma the way he was acting
towards you yau is evident cewa fushin yakeyi and fushin nashi is justified so
kibashi hakuri kawai awuce gurin" kwace hannuna nayi daga cikin na Aziza ina fadin
"Nifah bazan bashi hakuri ba wallahi,so inzakima daina bata yawun bakinki gwandama
kidaina" daganan nayi gaba nabarta tsaye kamar gunki tana kallona. I'm sure I made
her speechless, she's never notice this side of me seyau.
Haka taboyoni tacigaba dayimin wa'azinta anma ko uffan bankuma cemata ba harta
hakura takyaleni.
Masjid sanitation mukaje mukayi daganan akayi sallar juma'a sannan muka nufi
dinning hall. Layi muka tarar sosai agaban dinning din wai kuma abunda yaja layin
ba komai bane illa seka mutum ya nuna spoon din cin abincin sa kafin abarshi ya
shiga dinning hall din. Damanhaka wasu prefects din suke,they're very strict kuma
inranar duty din irin su yazagayo toh yara sun badekasu kenan,shiga dinning na
sewanda yashirya. Dolen ka sekabi rules and regulations na school. Class bag dina
nashiga dubawa kozanga spoon dina anma babushi babu labarin shi. Ni se alokacinma
natuna ashe jiya da nasha cornflakes dashi da dare kafin nakwanta banmayar dashi
cikin jakana ba dana gama. Yau da safe kuma bread and egg akabamu so balallai seda
spoon zaka shiga dinning ba.
Aziza ganin nagama searching jakana banfiddo spoon ba setace "Badai kinmanta a
hostel ba?" frowning fuskana nayi sannan nace "Namanta wallahi! jiya danaci abinci
dadare namanta banmaida shi cikin school bag dinaba seyanzu na tuna" Aziza tace
"toh yanzu yaza'ayi?" Wara Mata hannayena nayi alamun bansani ba dukda kuwa har
raina inason cin abincin. Rice and stew da fish za'aci ranar and it's always my
favourite.
Aziza setace "toh yanzu yanda za'ayi barina shiga seki zagaya tabaya inmika miki ta
window seki shigo" cikin sauri nace "A'a kije kawai, I'll wait outside in an fito
semu tafi hostel" dannasan it's very risky abunda tace zatayi din, prefects na iya
kamata suyi punishing dinta a banza da wofi.
Bayanda batayiba inyarda naki daga karshe setace Itama tafasa shiga toh. Ganin
inban yarje mataba zamuyi two zero sekawai nayimata wayau nace tashiga
din,zanzagaya in karba.
Aikuwa tana shiga nanemi guri agaban dinning hall din nazauna dan nasan koda wasa
babu mai barinta tafito tunda tariga da ta shiga. Inanan zaune agaban dinning din
har aka gama shiga yarage semu dabamufi 15 ba da bamuda spoons ba abarmu munshiga
ba. Inaji akayi ringing bell din serving abinci acikin hall din duk Ina zaune daga
gefe agurin ayayinda Sauran ma duk suke zaune a different places na harabar gaban
dinning hall din. kamar ance indaga idanuna karaf segasu cikin na Yaya Lamido
dasuke tahowa dinning hall din shida su Yaya Auwal da Mallam Babagana Islamic
studies Teachern mu.
Sauri nayi nadauke kaina daga garesu ayayinda na hade girar sama data kasa dukda
kuwa race dinda zuciyana keyi. Ahaka harsuka isa kusa da wasu dalibai dake kusa
dani.
Inaji Mallam Babagana yashiga tambayar su meya hanamu shiga dinning din inda sukace
masa spoon ne bamu dashi shiyasa prefects on duty suka hana mu shiga,budan bakin
Mallam Babagana secewa yayi "Serves you right. Ai kunsan ga curriculum din
makaranta anma bazakuna bin dokaba. Simple instructions you can't follow" yayi
maganar Rai bace ayayinda yayi gaba ze shiga dinning hall din batareda yasake bi
takanmu ba.
Binshi Yaya lamido yayi harsuka wuceni kadan yanacewa "Anma Mallam dan yara basu da
spoon is it right ace za'a hanasu cin abinci?" In an I don't care manner Mallam
Babagana yace "That's the rules Isma'il, besides su sukajama kansu,aisun sani bawai
basu saniba suka ki zuwa dashi din" cikin sauri Yaya Lamido yace "But I don't think
this's fair to the student" tsaya wa da tafiyar da Mallam Babagana yakeyi yayi
sannan yajuyo yana kallon Yaya lamido,yace "how's it not fair?" Gyara tsayuwa Yaya
Lamido yayi sannan yace "Mallam aganina bekamata ayima dalibai horo da abinci ba no
matter what. Yes agreed you might think they've provision in the hostel zasu iya ci
anma inaso katuna bakowa bane yakeda abunda zaisama bakin salatin sa inya koma
hostel din,not everyone has the provision because akwai wadanda iyayensu basuda
karfin yimusu,akwai wadanda kuma sunzo dashi yakare,meaning they now only depend on
abincin dinning din kawai. Toh in akace acikin wadannan yaran da aka Hana shiga
dinning din karban abinci akwai wadanda suke cikin wannan situation din ai anshiga
hakkinsu kuma haka zasu yini da yunwa and it can be dadaren ma susake shiga thesame
situation" Mallam Babagana da gabadaya attention dinsa nakan Yaya Lamido seyace
"Maganar ka akwai ma'ana toh anma fah kasan halin yaran Nan,ba'ayi musu wallahi
yanzu da ance za'afara favoring marasa shi toh dayawa zasu daina zuwa dashi
dagangan ma" Yaya lamido seyayi murmushi yace "I know and nima bangoyi bayan adinga
barin daliban dasuka karya doka hakanan ba. I'm just trying to point out cewa
hukuncin da kuke dauka din baiyi daidai ba. Inyaro baizo da spoon ba baikamata
ahanashi shiga yaci abinci ba but rather let him In and later punish him for his
mistake wanda ni inaganin zema fi Jin tsoron punishment din harma yadinga tunawa da
zuwa da spoon din fiyeda hana shi shiga daza'ayi yatafi free" yace "We should not
make eating food a choice for them but rather make it a priority"
Mallam Babagana jinjinakai yayi cikeda gamsuwa sannan yace "shawarar ka mekyau ne
and insha Allah zansamu prefects da dinning hall master muyi magana dasu se acanza
tsarin" murmushi Yaya Lamido yayi sannan yace "Thanks for considering my advice
Mallam" Mallam Babagana yace "Bakomai ai shawarace mekyau kakawo" Yaya Auwal dake
tsaye agefensu shima dashi ake zancen seyajuyo yana kallon mu yace "Wadannan
dinkuma yaza'ayi dasu?" Mallam Babagana cewa yayi "Yakuwa. Yaukam ai ya wuce sede
kuma gaba danko anbarsu sunshiga yanzu basamun abincin zasuyiba danhar students
sunriga sunyi serving kansu" Yaya lamido seyayi Yar dariya yace "Baza ayi haka ba
Mallam. baridai mutmbaya muji in akwai yanda za'ayi dasu din first" Yaya lamido
yakarashe maganar ayayinda yajuya yana kallon kofar dinning din. Ast. Dinning hall
prefect dinmu dake tsaye abakin hall din yashiga yima alama da hannu kan tazota.
Karasowa tayi kusa dasu cikeda ladabi tagaida su suka amsa sannan Yaya lamido
yashiga tambayar ta ko akwai extra abinci. Cemasa tayi bari taje ta duba inda
daganan tajuya tashige hall din. Ba tawani Jima ba segata tadawo tace musu akwai
pots biyu dasuka rage.
Yaya Auwal ne yajuyo yadubemu yace gaba dayanmu mutaso ayayinda Mallam Babagana
yacema Ast. dinning hall prefect din takawo masa dorina wai seyayi mana 3 3 stroke
of canes shine punishment dinmu for not coming with spoon. Inaji sauran duk suka
tashi suka nufi kusa da su Yaya Lamidon anma ninaki tashi nacigaba da zamana
dankuwa na gwammace Kar inci abincin da ayi min bulala guda uku and moreover
awannan lokacin nariga naji abincin ma yafita araina gabadaya,gakuma Daman Ina
fushi da wanda yamana dalili aka barmu zamu shiga hall din.
Mallam Babagana ne yashiga min magana da mamaki ganin bantaso ba,yace "Hey Student"
dagowa nayi Ina kallonsa dukda inajin intense gaze din Yaya lamido akaina,nace "Yes
Sir" fuska daure Mallam Babagana yace "Why are you still seating there?" Da kamar
bazanyi magana ba anma sena daure nace "I'm not hungry Sir" aikuwa dakuwa yamin
take yana hararana sannan a harzuke yace "will you stand up and join the cue my
friend..." Sekawai naji hawaye sun cika min idanuna tsabar takaici,senaji nasake
Jin haushin Yaya lamidon dandabaiyi magana ba dabazai jamin duka da humiliation ba
yanzu ba.
Tashi nayi naje nayi joining cue din fuska daure wanda alokacinne kuma Yaya Auwal
yama lura dani,da mamaki yace "Rukayya waidaman hardake?" Ashe shi kwata kwata
baima lura daniba.
Gyadamasakai kawai nayi Ina faking murmushi sannan nace "Ina wuni..." cewa yayi
"Lafiya" sannan yajuya yana tsokanar Yaya lamido da "Mutumina nidai naga andage
anata preaching,Ashe da biyu kayi" dundu Yaya lamidon yakai ma Yaya Auwal playfully
yana fadin "bawani da biyu. You know me well and you know what I said was right"
cikin sigar tsokana Yaya Auwal yace "nidai banyarda ba,mutum inzai fito yayi
accepting gaskiya yafito yayi accepting" sekuma Yaya Auwal din yadubeni yace "Koh
ba hakw ba Rukayya" faking murmushi kawai nayi bance komaiba hakanan ko kallon
barin dasuke banyiba. Se Yaya Auwal yashiga tambayana ya akayi banzo da spoon
ba,fada masa dalili nayi inda daganan kuma se yakoma yin wata hirar da Yaya Lamido
Wanda inbanda eh,Uhm ko a'a dayake cemishi banajin komai. It just seems like
bashida interest a conversation dinda Yaya Auwal dinkemasa, it's as if his mind is
somewhere else.
duk maganganun dasukeyi din kasa kasa sukeyinshi,nikadai danake karshe a cue din
nakeji dayake daga baya baya suka tsaya ayayinda Mallam Babagana kecan gaba yana
yin bulalar dayace seyayi mana kafin mushiga hall din. Ahaka har aka iso kaina,haka
akamin bulala uku masu zafi sannan nashiga hall din ashake.
Muna shiga sauran daliban suka fara fita danhar su sungama cin abincinsu. Table
biyu aka bamu kowanne da pot din rice daya dana miya akai inda akace muraba a
tsakanin mu. nidai tsabar takaici kwanciya nayi akam desk din dinning din kawai
batareda nasake bi takan abunda sukeyi a table dinba. Sonake intafi anma banason
Mallam Babagana yaganni abakin kofa yadawo dani. Inaji suka gama serving abincin
suka turomin plate dina gabana anma duk bandago ba haka nacigaba da kwanciya na
agurin. After like twenty minutes haka sena dago kaina,ananne naga yawanci wanda
akahadamu cin abinci tareda su din harsun gama suntafi,wata yarinya ne kadai tarage
itama kuma takusa karasa cinye abincin nata. dinning hall dinma shiru ba dalibai
sai matan dasuke mana girki dasuka shigo suna tattare pots da plates dinda akayi
amfani dasu. Tashi nayi daga zaunen danake sannan nanufi exit din dinning hall.
abakin kofar fita muka kusan cin karo da Yaya Lamido,ni Ina kokarin fita shi kuma
yana kokarin shigowa ayayinda yake Making phone call.
Jinayi yana cema wanda suke wayan "I miss you more Moon. Anma karki damu yaune
kawai,gobe iyar haka Ina gida and we'll see each other tomorrow night insha Allah"
karaf idanunsa cikin nawa sanda yakarasa last statement din nasa,jinayi kamar
ancaka min wani abu a kirjina,sauri nayi naja da baya sannan naratsa tagefenshi
zanwuce anma seyayi sauri yarike hannuna still bebar wayar dayakeyi da Aunty
Maimunatun ba dankuwa tabbas nasan itace,itace kadai yake kashema murya haka,itace
kadai zakaga yana murmushi nadaban insuna waya,itace kadai yakefadama dadadan
kalaman danaji yanayi mata yanzu. For the past three years tunda Yaya Lamido yayi
waya yasha yin waya da'ita agabana,walau yazo visit kokuma yazo Babban buli and
sautari yakan hada mu ma mugaisa dan Itama tasanni anma hakan betaba sani Jin wani
iriba, infact I'm always excited ingaisa da budurwar one and only Yayana, I'm
always excited in anshi sakon gaisuwar ta daga gareshi inyazo gurina kokuma
intafada ma su Yaya Jidda sugaidani but for the very first time yau naji inajin
haushinta,haushi nakeji yabata min rai amma yaje ita yana faranta Mata. Bansan
sanda na galla mishi harara ba bayan yakama hannuna sannan na kwace hannun nawa
daga cikin nashi nayi gaba nabarshi tsaye kamar wani gunki yanabina da kallo.
Aikuwa Ina Isa hostel na fashe da kuka,kukan da nikaina bansan dalilin sa ba.
Seda nayi kukan me isana sannan nahau yin bacci kasancewar Friday ne babu evening
prep se night Prep. Koda Aziza tazo tadinga min mitar nasata wahalar nemana a wurin
window banshiga ba hakuri nabata nace Mata ainazo nashiga daga baya haduwane kawai
bamuyiba. damukaje night prep da dare kwata kwata bansa ran ganinshi ba yau tunda
ya kauracewa zuwa kwana biyu kuma koma yazodin nariga nasama raina baya gabana,it
doesn't make any difference to me. Aikuwa ba ajima da fara prep dinba segasu sunzo
su shida Yaya Auwal. yana shigowa ajinmu straight seat dinmu yanufa,seda suka gaisa
da Aziza yatambayeta ya karatu sannan yasunkuyo kusa dani, ahankali yace
"Naanaaa..." yanda yafurta sunan nawa seda naji kamar zuciyata zatayi exploding
anma senadaure naki kallonsa,senayi kamar ma banjishi ba nacigaba da nazarin
textbook din Basic Technology dake ajiye agabana.
Seda yasake Kiran sunan nawa akaro na biyu sannan nadaga nakalleshi,shima bawai don
inasoba sedan kada Yan ajinmu suyi tunanin wani abu.
Yana kallon cikin idanuna pleadingly yace "Don Allah in antashi kitsaya zamuyi
magana" dauke idanuna nayi daga nasa namayar kan littafina sannan nace "Okay" kamar
wanda aka tursasani dukda kuwa har raina banida niyar tsayawa muyi maganar koda
antashin,nafadi hakan ne kawai don ya kyaleni. Toh Wai mema zaicemin? Ba fushi
yakeyi daniba? Yacigaba dayin fushin mana.
Littafin Qadr na kudine duk maiso should talk to me privately via WhatsApp through
this number 08147722806 for payment details.
Kuna comments please. Wallahi shikeban kwarin gwiwar yin typing.
*Page Forty Nine*
Haka Ina ganinshi se safa da marwa yake a block dinmu dan baya minti ashirin
bezagayoba har aka tashi a prep din. Sauri nayi nadauki class bag dina na saba a
baya nafice a ajin batareda natsaya jiran Aziza ba, cemata nayi fitsari nikeji
muhadu a hostel kawai ko kuma se gobe in Allah yakaimu mwahadu. Kiran sunana
tadingayi tana kokarin tsaida ni wai injjrata tarufe locker dinta anma Ina...
Tuni ninayi gaba,banason intafi cikin tsirarrun mutane tayanda zaiganni harya
tsaidani shiyasa nafita da sauri dan intafi cikin crowd in bata a rigar tsakani
anma duk abanza.
Na iso wurin JS3 block kenan kawai senaji ankama hannuna,ware idanuna nayi arazane
ina shirin sakin ihu yayi sauri yasa palms dinsa a bakina ahankali yace "ke nine
karki yi ihu" inda daganan kuma yajani muka hau js3 block dinda Already duk dalibai
suntattafi. wabce hannuna nayi daga cikin nasa sanda muka shiga js3A sannan najuya
zantafi batareda nace komaiba.
Cikin sauri yasha gabana,cikin marairaicewar murya yace "Wai where are you going
ne?" akafule nace "Hostel Manaa" Ahankali yace "Amma banace miki kitsaya zamuyi
magana ba in an tashi?" shiru nayi bance komaiba inata huci nikadai,seya matso kusa
dani sosai,kamar wani maraya yace "Why are you ignoring me Nana...?" Bansan sanda
namasa wani kalloba,nace "Nine ma nake ignoring dinka?" yace "Eh mana. Nazo ajinku
dazu baki kulani ba,munhadu a dinning ma bakice min komaiba even though I tried to
stop you in order to make a conversation" wani kututun bakin cikine yaziyarceni
lokaci guda,waima ninake ignoring dinsa.
Akafule nace "Kai fa kafara ignoring dina baniba" sekuma nafashe da kukan da bansan
dalilin sa ba. Take Yaya lamido ya rikice, hankali tashe yace "Kukan na menene kuma
toh? daga na kiraki muyi sulhu seki hau yimin kuka?" cikin sigar kuka nace "Wani
sulhu zamuyi bayan kadaina Sona! bana gabanka! Aunty Maimunatu da Aziza kadai kake
kulawa yanzu" dukda rashin hasken dake ajin seda naji fitar sautin murmushinsa
dankuwa security light din wajene yakedan haskowa kadan,wutan ajin Already Yan ajin
sun kashe kafin sufita.
Cikin sigar zolaya yace "Wayace miki nadaina sonki?" Wannan Karan tura baki nayi
gaba,nace "Aibasai kafito kafada ba. Action speaks louder than voice,da baka daina
Sona amatsayin Kanwarka ba babu abunda zaihana ka kin nemana harna kwana uku,kazo
kagannin ma kuma kaki ka kulani" nakarashe maganar cikin shesheka, because the
thought of it hurts so much.
Nace "Aini namanta I'm just a Sister by name,namanta alaka na da naka ba irin naka
danasu Salma bane in reality. Batun Aunty Maimunatu kuma I can't even match myself
with her sabida itadaman mahadin Rayuwarka c..." Sauri yayi yasa finger dinshi akan
lips dina,cikin muryar datake nuna baiji dadin kalamaina ba yace "Enough...ya Isa
haka Nana..." sa hannu nayi nature hannunsa daga kan bakina ayayinda najuya fuska
na gefe guda Ina hawaye.
Yaya Lamido yace "Don Allah dagayau karki sake hada kanki dawasu Nanaa... I mean
stop comparing the love I've for you with the one I've for the people around
me,kowa da irin gurbin dana basa azuciyana. Gurbin danabama su Salma daban,wanda
nabama Maimunatu ma daban hakanan kema naki daban and only me know how much each
and everyone of you means to me. I can't tell you about them sabida ba maganarsu
mukeyiba,maganar nida ke mukeyi yanzu and inkuma akan abunda nakeji game dakene
then I want you to be rest assured cewa babu abunda zaicanza game dake a
zuciyana,komi rintsi komai Zakiyimin you'll still be my sweet little Sister. Yes I
can be angry with you and I can decide to ignore you for days but believe me you'll
always be in my mind and my love for you will never fade away! Never...." yayi
maganar cikeda utmost sincererity.
Yadan numfasa sannan yacigaba da magana,yace "Kwana biyun dasuka wuce kikaga bana
yi maki magana ma fushi nayi,I was angry with you and I wanted you to realize your
mistake kizo kineme ni kibani hakuri anma bakiyi hakan ba harna gaji da rashin
ganinki,nagaji dayin fushin nazo dakaina wai Inga kozakiyimin maganar in kika ganni
anma nandinma se kikayi fuska and then I decided to start a conversation first a
hall but you still went away without saying a word,kika kwace hannunki kika
gallamin harara dukwai akan laifin dabani nayiba ke kikayi shi. I know I play with
you,I know that I care for you too much Naanaa but atleast that should not give you
the right kidinga yimin magana any how,that should not give you the right to be
behaving anyhow with me ako ina. I can decide to tolerate and ignore it anma
banason hakan yajamin raini wurin sauran dalibai kokuma kawarki shiyasa ranar
dakika min hakan naso innuna miki kuskurenki" Jin abubuwan dayace din se jikina
yayi sanyi, take senaga wautana da rashin kyautawa na. He's right komai yamin I
need to give him all the respect he deserves,Dan yana sakemin fuska yana wasa dani
baikamata ince zan rainashiba. Nikaina I don't know what has gotton into me kwana
biyunnan, it's unlike me kuma wannan baya daya daga cikin tarbiyarda Baba yayimin.
I was just angry for no reason wanda nafi alakanta hakan da samun gurine
kawai,inbahaka ba na Isa inma wani Dan ubana?take sena marairaice fuska,nadawo da
dubana garesa daga juyamai keyar danayi dazu,nace "Kayi hakuri don Allah. I'm
really very sorry Yaya Lamido" murmushi naji yasaki ayayinda yasa hannu cikin
aljihunsa yaciro handkerchief da wayarsa kirar black berry *bold two* da ake yayi
awannan lokacin,kunna hasken screen din wayar yayi yashiga haska fuskana ayayinda
yakai hankyn yashiga gogemin kwallana yana fadin "Zanyi hakuri anma saikin daina
kukannan" karban hankyn nayi daga hannunshi nacigaba da goge hawayen nawa Ina fadin
"Aina daina" seyace "Yanzu mun shirya kenan?" gyadamasakai nayi ahankali.
Yace "toh kiyimin alkawari bazaki sakeyin irin wannan fushin ba haryakai ga kidinga
kin kulani" ahankali nace "wannan dinma aikai kafara" seyadanyi dariya yace "toh
bazan sakeba,nangaba in kin mun abu I'll just bulaleyi you and punish you
immediately" yanda yayi maganar seda nayi dariya nace "Nayarda ko dukan zaisani
kuka bazan damu ba kamar yanda idan kadaina kulani" I can see him blushing asanda
muka fita a ajin muka nufi hanyar hostel.
Sekuma yashiga tsokana na yana imitating yanda nace yana kula Aziza da Maimunatu ni
baya kulani,yace "Yarinyar nan bakaramin kishi zakiyiba. Mijin ki yaga takanshi"
tura baki nayi gaba Ina dariya nace "Bafah kishi baneba" kallona Yaya Lamido yayi
sannan yace "Toh menene?" wara hannayena nayi alamar nima bansaniba.
Wayarshine yashiga ruri,dago wayar yayi yana kallon screen din wayar,Aunty
Maimunatu ce takira. dagawa yayi sukayi gaisuwa irinta masoya sekuma naji yanacewa
"Gatanan. Yanzunnan muka gama sulhu" kallonshi nayi da mamaki anma kafin in iyacewa
komai seya miko min wayar,yace "Maimunatu wants to talk to you" karba nayi nakai
kunnena with a smile on my face nace "Ina wuni Aunty Maimunatu" daga daya bangaren
tace "Lafiya Lau Rukayya ya karatu?" ahankali nace "Alhamdulillah. Ya mutanen
Gombe?" Tace "Duk lafiyansu kalau" sekuma tacanza babin hirar,cikin sigar tsokana
setace "haka akeyi Rukayya? kawai sekika hau fushi da Yaya kuma?"
take senaji kunyarta yakamani dukda ba'agabana takeba,senace "aikomai yawuce yanzu
nasauko" Yar dariya tayi sannan tace "toh barka danda baki sauko bama dungumowa
zamuyi muzo Bauchi mubaki hakuri dakanmu nida su Umma" dariya kawai nayi Ina
mamakin kirki irin nata daganan kuma seta hau yimin nasiha tace "Karkina cewa zaki
dauke ma Dan uwanki magana no matter what,you can get angry with him but never stop
a conversation. Keeping malice is not a good habit,it ruin relationships kinji?"
gyadamatakai nayi kamar wanda tana gabana sannan nace "Aunty Maimunatu shiyakamata
kifadawa haka aishi yafara" Yar dariya tayi sannan tace "Karki damu zanfada mishi
anma kema inkinga yayi irin haka sekarki biye Masa" Ina murmushi nace "toh nagode"
daganan mukayi sallama namika Masa wayar sukadanyi magana sannan sukayi sallama
bayan yace mata zaikirata inya koma gida.
Agurin masallaci yatsaya mukayi sallama bayan nagama korafin miyasa yafada ma Aunty
Maimunatu.
Yace "A'a nibani nafara fadaba,tambayana tayi ke wai baku gaisa ba tunda nazo shine
nace mata aima fushi kikeyi dani" tura baki nayi gaba sannan nace "Mukayi da juna
dai" Yar dariya yayi sannan yace "toh naji,mukayi da juna shikenan?" Dariyar nima
nasaki sannan nace "Kuma munsauko a tare ba" girgizamin kai yayi yana dariya yace
"A'a nidai nafara saukowa" sekuma ya kalli wasu students dake diban ruwa abakin tap
din masallaci yace "kije kibi wadancan kutafi hostel tare naga hanyar ba mutane
sosai yawanci duk an wuce hostel" gyada masakai nayi sannan nace "toh Saida safe"
kafin najuya nafara tafiya.
Harna danyi nisa sekuma nadawo da gudu ina kiran sunansa,bebar inda nabarshi tsaye
ba daman yana jira sena tafi sannan shima yatafi.
Cewa yayi "Na'am" ayayinda na karasa kusa dashi,da fuskar tausayi nace "Don Allah
kakyalesu Yaya Aisha hakanan. Don't ask them for anything anymore Allah komai
yawuce agurina nikam" cikeda mamakina yace "abunda yadawo dake kenan?" Gyada
masakai nayi ahankali with a pity face inasake fadin "pleaseeee..." jinjinamin kai
yayi sannan yace "Toh bazan sake yi masu maganar ba Insha Allah" cikeda farin ciki
nace "Thank you" yace "ba thank you ba,if they try something stupid again I'll
surely deal with them" Ina murmushi nace "bazama su sakeba" kafin najuya nanufi
hanyar hostel da gudu ina fadin "Good night Yaya Lamido".
Ranar bacci mai dadi nayi, baccin da nakwana biyu banyi irinsa ba. Washegari da
gyare gyaren hostel muka tashi kasancewar Saturday ne kuma akwai inspection. Se
after 10 akagama inspection din inda daganan kuma muka dunguma mukayi dinning hall
don yin breakfast. tunda muka doshi dinning din nahango Yaya lamido,Yaya Auwal da
Mallam Babagana suna tsaye agaban hall din,da alama dai sune suka karbi duty jiya.
bansan sanda murmushi ya kubuce min ba sakamakon ganin Yaya Lamidon danayi,yau
shigan kananun Kaya yayi dasuka matukar amsar jikinsa. Without a second thought Ina
isa gaban dinning din naje nagaida su duka,Yaya Auwal na tsokana na da "Hajiya
Rukayya yau ba'a manta spoon ba kenan?" dariya nayi sannan nace "Jiyan ma akasai
aka samu ai" cikin sigar zolaya Yaya Lamido yace "kedai kawai kinsha bulala bakyaso
yauma kisha wani shiyasa baki manta ba" tura baki nayi gaba Ina fadin "Allah bahaka
baneba Yaya lamido" Mallam Babagana dayagama waya dandaman nazo nasame shi yana
making phone call seya dubeni yace "Wai daman Rukayya na cikin wadanda basuzo da
spoon ba jiya?" Yaya Auwal ne yace "Eh itace wanda kace tataso tayi joining cue
daga karshe ai. Kanwar Isma'il ce" kamar gaske se Mallam Babagana se yace "Au haba?
ni ai banma lura da ita ba. She's my student inadaukan su Islamic studies and I'm
always proud of her,Ashe Kanwarka ce?" Yaya lamido na murmushi yace "Eh Mallam"
nidai ko kallon inda Mallam Babaganan yake kinyi nayi dan nasan tambayar rainin
wayau ne kawai,haka Mallam Babagana yake,BS BS ne dashi when it comes to rashin
mutunci. Jiya yaganni sarai kuma yagane ni anma dayake yana mood din muguntarsa
seya nuna kamar baisanni ba. Mallam Babagana tafiya yayi yanufi gaban dinning hall
din ayayinda muka shiga hira nida Yaya Lamido inda yake sanar dani zaije Gombe
ranar.
Banyi mamakiba tunda daman naji yana fadama Aunty Maimunatu jiya da rana damukayi
kicibis dashi a hall.
Senace "Yaushe zaka dawo Inka tafi?" Yaya Lamido yace "gobe Sunday insha Allah"
senace "Allah yakaimu" yace "Amin. Tsarabar meza'akawo miki?" Yar dariya nayi
sannan nace "Koma minene ma. Kawaidai kowa yabada nasa tsarabar akawomin,na Umma
daban,na Yaya Basma daban,na Yaya Jidda daban,na Kawata Salma ma daban" nayi
maganar Ina counting masa using my fingers.
Yar dariya yayi sannan yace "Sekuma nawa?" shiru nayi inadan nazari kafin kuma
Aunty Maimunatu tafado min arai,cikin sauri nace "Yauwa dana Aunty Maimunatu" Yaya
Auwal dakejin mu yace "dakuma nashi Oga kwata kwatanba" Yaya lamido seya harari
Yaya Auwal din playful yace "Ai kuma wannan basai kafada ba yaro" dariya nayi
sannan nace "Yaya Auwal kaima zakaje gidanne?" Seyace "nida gidanmu yakenan
inazani? Ai anan nike da zama" Sena danyi grinning fuskana sannan nace "hakafa,Aina
manta" Yaya Lamido yace "Anma ai we're going together" Yaya Auwal seyace "well
gidanmu tatambayeni zanjeni nace Mata anan garin niike. Binka dazanyi ai ziyara
zanje" Yaya Lamido yace "bawani kaidai bakaso ace kakawo tsaraba ne kawai yasa kake
dodging" dariya Yaya Auwal yayi sannan yace "Allah ya shiryeka toh Lamido kuma
inbanda abunka nida zanje bakunta inani Ina kawo wata tsaraba" Yaya Lamido
stubbornly yace "Koma Ina ne zaka indai kai matafiyine it's expected kakawo tsaraba
inzaka dawo gida ko zakaje sabida haka kaima seka sayama Nanaa tsaraba. Inbahaka ba
kuma musamaka suna me rowa" kallona Yaya Auwal yayi irin I should back him dinnan
anma senaki,cikin sigar wasa nace "I'm with Yaya Lamido".
Yaya Auwal yace "toh ai shikenan kunrufemin baki gabadaya" dariya muka saki duka
ayayinda nayi musu sallama nanufi cue din shiga dinning din ganin layi yakusa
karewa bayan munyi zamu hadu muyi sallama in an tashi a hall din.
***
*GOMBE*
Isan yanma Lamido da Auwal sukayi Gombe sannan suna sauka a Tasha basu zarce ko'ina
ba se Fadan Gomben inda sukayi gidan su Lamido din. Umma bakaramin farin ciki tayi
da ganinsu ba even though daman tana tsanmanin isowar tasu dayake Lamidon yariga da
yasanar da'ita a waya. anan parlourn Umma da ayanzu ansaka musu sabbin kujeru dede
talaka na zamani masu kyau unlike shekaru uku dasuka wuce da Tum tumne kadai azube
a parlourn. TV stand dinnata ma ancanzashi zuwa modernized one dukda Tv dinkam
haryanzu nada dinne.
Seda suka gaisa da Umman,su Basma ma dasuke gida duk suka fito suka gaisar da Yayan
da Auwal inda Auwal din keta zolayarsu dasun sake zama Yan Mata inda daganan kuma
suka danyi hira irin ta Yan uwan juna ayayinda daga kan Umma harsu Basma suka dinga
tambayar Lamidon Rukayya wanda hakan yabama Auwal mamaki dankuwa shi kwata kwata
yadauka bawanda yasan Rukayya a gidansu Lamido,all he thought was coincedence ne
yasake hada Rukayya da Lamido a FGC azare,yasandai yajima yana nazarin miyasa
Lamidon yadage se FGC Azare zaiyi service dinsa anma baitama kawo hakan nada alaka
da Rukayya ba tunda koda wasa dasuke camp bai taba sanar dashiba,yanason yanemi
ba'asi amma yasan wannan bashine lokacin dayakamata yayi tambayar ba,danhaka seyayi
shiru kawai. Abinci Umma tasa aka kawo musu,abincin da specifically tagirka da
kanta kasancewar Lamido yace Mata zaizo gida shida Auwal. Haka suka shiga cin
abincin anutse Auwal nata santin yayi missing girkin Umma dayake sanda suke jami'a
sukanzo gidansu Lamidon suci abinci daga makaranta. Umma cewa tayi cikin sigar
zolaya "Toh Auwalu kodai zaka tattaro kazo kanemi aiki agarinnanne muyi zamanmu
inayi maka girki harka samu Mata" dariya Auwal yayi sannan shima cikin sigar wasan
yace "Kumafa wannan shawara ce mekyau Umma. baridai inkarasa service dinnan kigani"
Lamido daketa zuba loma danshima yayi kewan girkin Umman yace "kamar gaske" Auwal
danhararanshi yayi sannan yace "oh wai kadauka wasa nakeyine?" Lamido yace "nida
nasan hali. Dayaya muka samu kagama jami'ar anan dinma?"...
Bayan sungama cin abincin kuma sesuka nufi dakin Lamidon dansu huta ananne Auwal
din yadubi Lamido yace "Man dama Yan gidanku sunsan Rukayya?" Yar dariya Lamido
yasaki Jin abunda Auwal din yace sannan yace "Eh mana. Bakaji dazu tana bada sakon
gaisuwa abasuba" Auwal yace "Naji tana fada anma nadauka duk cikin wasane,I thought
labarin su kawai datasani ne tunda ashe suma sunsanta" Lamido yace "Eh. Aihar visit
suna zuwa Mata. Rukayya is like a family now" Auwal cikeda curiosity yace "Anma if
I can clearly remember a Babban buli kukafara haduwa sanda mukaje field trip?"
Lamido seyagyadama Auwal kai,yace "sure. Acan muka fara haduwa inda daganan kuma se
muka cigaba da communication" seya shiga bama Auwal din labarin haduwan dasukayi
tayi da Rukayya, da rasuwar babanta and all his efforts kafin daga karshe yace "I'm
serving in FGC Azare purposely sabida Nanaaa nagurin ne" Auwal jinjinakai yayi
cikeda gamsuwa sannan yace "Amma do you think you're doing all this sabida kawai
kataimaki Rukayya ne? I mean you still believe kawai sabida shakuwa da tausayinta
ne yasa kake duka wadannan abubuwan?" Batareda Lamido ya kalleshiba yace "Off
course yes Auwal,what could be the other reason if not this?" hararanshi Auwal yayi
sannan yace "I don't believe you!" Because daga yanayin maganar Lamidon kadai yasan
akwai abu akasa,fada ne kawai bayason yi.
Dariya Lamido yayi sannan yace "Kaikasani nidai nagaya maka wannan shine kadai
dalilaina" daganan kuma seyayi sauri yatashi yashiga bathroom daniyar watsa ruwa
inda yabar Auwal din yana binshi da kallo yana dariya kasa kasa shima.
Seda akayi sallar isha'i sannan Lamido da Auwal suka samu rankaya wa gidansu Hafiz
da already sunkirashi sunsanar dashi zuwansu. Seda suka shiga gidan suka gaisa da
Umman Hafiz sannan suka fito gaban gidan suka zauna kan wani bench suna hirar
yaushe gamo,barinma Auwal da Hafiz dinda tunda sukayi graduation baifi a kirga ba
suka hadu seyanzu. Hafiz yacema Lamido "Mutumina ba karamin taimakawa kayi ba
dakatafi service Bauchin nan. Koba komai ka hankado mana keyar marasa zuwa ziyara"
dariya Auwal yayi sannan yace "Kaidai Hafiz ba arabaka da mita. Kaima ai kasan
sabida rashin lafiyar danayi ne shiyasa" Hafiz yace "Bawani. Kafin kakwanta rashin
lafiyar kuma fah? dakuma recent months dakake da lafiyar kafin kafara service
dinfah? Zuwana gurin ka Azare musamman sabidakai sau uku anma kai this's the first
time,first dinma nasan seda Lamido ne ya matsa maka sannan kayarda kuka taho tare"
Auwal yace "Toh tunda nayarda nazo din ai shikenan nagoge laifuffukana" Hafiz na
dariya yace "bawani,kadai fara gogewa anma baka gamaba har seka cigaba da zuwa akai
akai sannan zaka goge sauran laifuffukan naka"......
Daganan kuma sesuka koma hirar wahalar samun aiki,Hafiz yace "Aini jinake kamar
inkoma insake service dinnan wallahi. Koba komai kanayi din kana samun allowance
anma yanzu shirunefah. Aiki ya gagara samuwa,Helter skelter kullum Ina cikin yawo
da CV daga wannan branch din zuwa wani anma shiru babu labari" Lamido seya saki
tsaki yace "Shiyasa gabadaya Inna tuna irin wadannan abubuwan abaya se indinga
ganin miye amfanin bokon ma tun asali? Tunda gashi irinku dakuka gama karatun da
grade mekyau ma bakusamu aikin ba baremu kinja alaye" Auwal yace "abun ba'anan
yakeba Lamido. Sa'ane kawai fah yanzu sekaga shi baisamu aikin ba kai kariga shi
samu dukda yarigamu gama service din dukdama bamwa fatan hakan tafaru" tabe baki
Lamido yayi sannan yace "nifah kwata kwata bansamaraina samun aikin gwamnatiba
dakuka ganninnan bare yadameni. Aikin danakeyi da campanyn kayan abincin shizan
komayi dana gama service dan already ma sunsan zankoma and they're willing to
promote me,abunda zasuna biyana komin kadan dinsa ma Allah ya amfana" Auwal yace
"Amin. Lamido bazance karka koma aiki agurin can ba tunda atleast suna biyan ka
dakyau kuma yafi zama babu abunyi din but while kanayi din seka nemii aikin
gwamnatinma kilan adace,gurin da kake magana din ba lallai subiyaka mekyau yanda
idan kasamu aikin gwamnati" Lamido seyace "Toh wai innace zannemi aikin gwamnatin
dawani kwakwalwar zan je inyi aikn? You know I know nothing about Geology.
Certificate din kawai gareni shiyasa ma ni kwata kwata kaga nake cire raina a abun"
Dan numfasawa Auwal yayi sannan yace "Yanzu yau in akace akwai hanyar dazakabi
kagyara mistakes dinda kayi abaya zakabi kagyara su?" ahankali Lamido yace
"probably" se Auwal yace "Then when you're moving forward don't look back,karka
bari past dinka yayi haunting present dinka but rather look for a way dazakayi
brightening future dinka tayanda wataran koka tuna bayan ma bazakayi regretting ba.
You hated school back then,I know studying was not part of you abaya anma presently
yanzu nasan daza'ace kakoma baya kagyara wasu abubuwa a Rayuwarka you'll have
surely done that,baka fito kafada ba but your action shows it, you're just giving
it up ne sabida kana ganin kamar bakada solution daya wuce kayi giving up din bayan
kuma bahaka baneba" Auwal ya dafa kafadun Lamido yace "I know you now know how
important it's to have knowledge akan field dinda ka karanta Koda kuwa bawannan
bane hanyar cin abincin ka,asan yanzu kasan amfanin karatu bawai don anemi aiki
bane kadai akeyinsa,it also makes you look different and outstanding,it also
differentiate you with others,it makes your thinking different from wanda basuyi
dinba and to hold the certificate and have the knowledge is also something else.
Moreover inkanada ilimin Kuma babu inda bazaka shigaba arayuwarnan with your head
held high. Toh you're not too late Lamido,you can start afresh bye
correcting your mistakes koda daga Rana maikaman nayau ne"
Jiki sanyaye Lamido yace "but how?" Dankuwa maganar Auwal din gaskiya,babu tantama
acikin sa, shikanshi yasan dayau za'a maida hannun agogo baya da he'll have changed
so many things dasuka faru arayuwarsa,irin time dinda yayi wasting dakuma irin
kudaden daya bari sukatafi a banza batareda yayi cherishing dinsu ba toh Amma ganin
babu mafitar ne yakesashi cigaba da having old beliefs dinsa batareda yabari abun
yadameshiba.
Auwal yace "Geology is more about practical aspect you know! anan kasarne kawai
mukafi bama theoritical aspects kaimi sosai sabida bamuda capability din fita field
din koda yaushe anma ai koh bature kanshi yace 'Seeing is believing'. Inkaje kaga
Abu da idanunka akayi maka bayani akansa ba lallai kamanta shi ba akan wanda za
anuna maka a littafi ko amaka describing dinsa ace shine abu kaza and this's
exactly the reason why must of us fail,anmana bayani bamu ganeba sekawai muyi
deciding muhaddace shi in an tambaye murubuta mubayar bawai don mungane dinba sedan
kawai abamu marks dinmu muyi passing bayan the real actual knowledge dinda akeson
musamu akan abun bamusameshi ba. If you want while muna NYSC dinnan we can start
going for field work Lamido. Bauchi state has so many Geological Terrains likewise
Gombe. Semuyi fixing time like kamar ko a weekends se muna zuwa inayi maka bayani
with the little knowledge I've,abunda bansani ba konake kokwanto akanshi we can
snap it with our camera inmundawo gida muyi consulting daya daga cikin lecturers
dinmu,in ma akwai features dinda mukeson gani babu a state guda biyunnan we can
also fix date and time semuje wasu states din like kamar a hutu haka koya kace?"
Auwal yakarashe maganar yana kallon Lamidon.
Murmushi Lamido yayi sannan yace "I'll surely be glad indai you're willing to help"
Hafiz yace "Nima zanna binku, atleast befi revision ba and I'll surely learn new
things ma" Auwal yace "You'll surely learn new things danhar Ina planning muyima
like irin waterboards magana,kokuma masu zuwa quarry,da masu minning kokuma
extraction na minerals duk inmun samu convinient time muna zuwa muna ganin aikin
dasukeyi kafin muga abunda Allah zaiyi" Hafiz yace "A very good suggestion" Auwal
yace "Allah dai yamana jagora kawai. inkace zaka zauna kajira se anbaka aikin
kakoya shima wani aikinne. Gwanda inkana putting alot of effort may be tahakan aga
hardwork dinka da capability dinka a daukekan and nidama dana gama service dina
meanwhile Ina abubuwan nan indai bansamu aikiba I'll just pursue my Masters" cikin
sigar tsokana Lamido yace "toh uban son Boko" sesukayi dariya dukansu Auwal nafadin
"I'll surely inspire you both Dan ubanku. Masters dinnan tare zamu farashi insha
Allah"
Lamido na dariya yace "A'a kadaiyi abunka kai kadai,mu degree din ma ya ishemu"
wayarsa daya shiga rurine yasa yasaka hannunsa cikin aljihun gaban rigarsa
yaciro,Maimunatu ce ke kira. Dafe kai yayi dasauri sannan yace "oh shirt...
Yarannan kunsa nama Gimbiya laifi. Allah dai yasa kwalliyar datayimin baigogeba"
Lamido yakarashe maganar ayayinda yayi picking call din yakai kunne yana sunne
murya.
Binsa da idanu abokan nasa guda biyu sukayi suna mai dariyar shakiyanci,Maimunatun
tambayar shi tayi dalilin rashin zuwansa harlokacin inda yashiga bata hakuri wai
gashinan zuwa Hafiz ne yarike shi kafin sukayi sallama. Hafiz yace "Nidai adaina
yimin sharri ban rike kowaba" dariya Lamido yayi sannan yace "inba rikenin kayiba
mekayi? Kasandai da majalisar mu mukaje bazan manta cewa zanje gurin ta ba Koh?"
Auwal dake jinsu seya dubi Hafiz yace "Hafiz nidai katayani yimai wa'azi yadaina
saka confusion azuciyar Yara Mata" Hafiz da ke dariya da mamaki seya dubi Auwal din
Jin abunda yace,yace "Kaman Yaya? Badai Yan Mata yaje yayi a makarantar dakuke
koyar wanba?" Danshi dai as far as he knows budurwa Lamido kwara dayace,wato
"Maimunatu" kuma tunba yauba suke tare.
Auwal yace "A'a fah in tara Yan matan yakeyi aida sauki, atleast za'asan shi player
ne kosu Matan bazasu daura high hope dinsu akansa ba anma the way I'm seeing things
now za'a iya samun matsala agaba" Hafiz dakanshi yadaure yace "go straight to the
point Auwal. I don't get you" Auwal seyayi murmushi yace "Zaka iya tuna wata
yarinya damuka hadu da'ita a Babban buli lokacin field work dinmu na aji uku?"
Cikin sauri Hafiz yace "kana nufin Rukayya?" Auwal yace "Exactly. He's still with
her,infact yana serving a FGC Azarene sabida yarinyar and here he's telling me wai
kawai tausayinta yakeji" Hafiz da tunda Auwal din yayi magana yasaki baki yana
kallon Lamido yace "Wai daman Lamido haryanzu kuna haduwa da Rukayya?" dariya
Lamido yayi sannan cikin sigar zolaya yace "Meza'a fasa?" Hafiz yace "I thought
tunsanda mukayi magana dakai kadaina zuwa gurinta fah danaji baka sakeyin
maganartaba" Lamido mayar da wayarsa yayi cikin aljihun rigarsa sannan yatashi
tsaye yace "kaifa kanuna bakason magana akan al'amuranta shiyasa nima nadaina
yimaka maganarta gabadaya. But we're still together,infact our bond is better than
before" Auwal yacema Hafiz "Kajiba" Hafiz yace "aibasai najiba Auwal. Nizan baka
labarin alakar Rukayya da Lamido dankuwa three years back nima seda akayi zirga
zirga dani dana mishi wa'azi shine yadainamin zancenta. Back then nakwana dasanin
indai suka cigaba da alaka definitely wannan abun zai rikide yakoma soyayya anma
danadauka sun rabu senayi tunanin everything is over, Maimunatu ce kawai agabanshi
ashe abun bahaka baneba,ni ansaka ni a duhu Ina zaune bayau da baki anan.
Relocation dinda yayi ashewai dukdan Rukayya ne nibansaniba" Hafiz yakarashe
maganar cikeda jimami.
Girgizakai Lamido yayi in desbelief yanama abun nasu dariya kafin yace "nikunga
tafiyata kar insakeyin wani laifin" saurin riko hannunshi Hafiz yayi yadawo dashi
yanafadin "wallahi baka isaba yaro. Dawo kafada mana. What's going on on your mind?
Shin wai Rukayya kakeso ko Maimunatu?"
Dariya Lamido yakuma saki sannan yadubi Hafiz yace "inkuka Sani din mezakuyi?"
Auwal yace "aimun ma riga damunsani munadai son mutabbarar cewa kaidin kasan abunda
zuciyar ka takesone ko bakasani ba semu baka shawara" se Lamido yace "inkuma
zuciyar tawa duka abu biyun takeso fah?" Wannan karan Hafiz ne yayi sauri yace
"Impossible! Yes zaka iya son Mata biyu anma dole son daya seyafi na dayan
yawa,dole akwai wanda tafi kwanciya maka arai" komawa Lamido yayi yazauna ganin
maganar nasu bana kare bane sannan yajinjina kai yace "You're right but that
doesn't mean sabida nafison dayan inyi ignoring daya tunda zuciyata tanason duka
abu guda biyun and she'll surely be happy staying with them both" shekewa da dariya
Auwal yayi sannan yace "Mutumina polygamy zamuyi kenan?" Dariya Lamido yasaki yana
fadin "nidai bance makaba" Hafiz dabai dauki abun amatsayin wasaba yace "Joke apart
Lamido. anmadai kasan bayanda za ayi kace zakaso Mata biyu lokaci guda koh?" Lamido
dahar yanzu yakasa dena dariya yace "gashi kuwa inakan yi?" Hafiz yace "Then you've
to stop" cikin shakiyanci Lamido yace "Why? Is it a sin? Kokuma addini ya hana son
mace fiyeda daya lokaci guda?" Hafiz seyace "kodaya. Addini bai hanaba inkaga
damama zaka iya Aurensu rana daya anma fah se inkana da halin rikesu kana kuma da
halin yin adalci a tsakaninsu" Lamido cikin shakiyanci haryanzu yace "toh aini
bance lokaci guda zan auresuba,zanfara da Babba se incika da karamar agaba" wannan
karan dundu Hafiz yakaima Lamido ganin haryanzu shi a wasa yadauki maganar.
Yace "Haba Man let's talk to seriously mana" dakyar Lamido yatsagaita dariyar
dayakeyi sannan yace "toh wai mekakeson ince maka?" Hafiz yace "Sonake inji
tsakanin Rukayya da Maimunatu wakafi so" plainly Lamido yace "off course Nanaaa
mana" wani harara Hafiz yqsakar mai sannan yace "shine kuma kake yaudaran
Maimunatu?" Se Lamido yayi serious face yace "I'm not decieving her Hafiz,I care
for her and I'll willingly marry Maimunatu indai she's ready to do thesame,indai
she can wait for me zuwa sanda zanzama stable nafara aiki har in riketa. Zankuma
aurenta ne bawai don wani dalili ba sedan inasonta,nakuma yarda da tarbiyarta
nakuma san she'll surely be a great wife and a good Mother to my children" Hafiz
seya rabza uban tagumi yana kallon abokin nasa,yace "itakuma Rukayyan fah?" Lamido
seyayi murmushi,yace "wannan ai constant ce. She's my dream wife and my future
insha Allah. Yes at farkon haduwana da Rukayya banda sabo damukayi babu abunda
nakeji game da'ita,sekuma nazo tausayi yashiga ciki wanda tun ranar da tasanar dani
halin datake ciki a gidan Kawunta dana dawo gida nadinga kissima mezanyi dan
intaimaketa,Mezanyi dan in cireta daga wannan kangin rayuwar? and I see no solution
than marrying her wanda nasan alokacin konace zan aureta din babu Mai bani aurenta
tunda ni bakowan kowa baneba,Umma ma bazata goyamin bayaba sannan alokacin mema
Rukayya tasani dazan bijoro Mata da maganar aure dasunan taimako? shiyasa kawai
nabar abun araina with the niyyar I'll continue helping her harzuwa sanda zata gama
secondary school wanda alokacin kuma nasan nima I'm stable se in tunkareta da
maganar,se in aureta indauketa daga wnnan gida me ukuban. But the more I spend time
with her,the more I get to see her,the more I get to know her senafara ganewa she's
the one,she's the one zuciyata da gangar jikina keson kasancewa tareda ita har
karshen rayuwana and I'm now looking forward to the time dazan mallaketa insha
Allah. I'm looking forward to see the day that I'll be her only source of
happiness,the day when she'll look all around her and feel nothing but joy,the day
when she'll be secured,the day when she'll look at me with a pure look tacemin
batada wata sauran matsala arayuwarta se farin ciki"
"you're confusing me Man" shine abunda Hafiz din yafada bayan yagama Jin abunda
Lamidon yafada.
Dariya Lamido yayi sannan yace "The truth is that Nanaa is the only woman I love
and I want to spend the rest of my life with Hafiz,yau daza'ace inzabi guda daya
acikin su babu tantama Nanaa zan zaba sabida ita tun asali daman I see a future
with her. Maimunatu kuma bazan cemaka banasonta ba tunda munyi soyayya abaya muna
kuma kanyi haryanzu dukdama asali wani abuntane yake burgeni(Muryarta) haryajani
zuwa gareta muka fara soyayya and as time goes on mukayi sabo muke kuma claiming
muna son juna. Rukayya kuma soyayyar danakeyi Mata daga Allah ne,yau inzaka yanka
ni bazan iyacemaka ga dalilin dayasa nakeson Rukayya ba bayan tausayinta danakeji.
Bazan iyacemaka Dan kyaunta nake sonta ba dankuwa tun kafin ma ace takai mizanin da
kyaunta ze fara fitowa nake jinta araina Kuma haryau dakake gani Rukayya is still
young,bazan iya cemaka sabida halin ta baneba kokuma wani ilimi nata. I just found
myself in love,in love with Nanaaa and I just believe in every situation kuma Koda
ace tanada wani flaws my feelings for her will never change. Anma kokasan haryau
nida Maimunatu bamu taba maganar aureba? yes Rukayya ma banmata maganar
aureba,infact bantaba nuna mata asalin abunda ke cikin zuciyana ba kuma nasan Itama
bataasani ba and itan I've a reason,she's just 15years,she's still young for
that,I'm still nurturing her,inajiran ta mallaki hankalin kanta dakyau kafin
infurta mata abunda keraina. Anma Maimunatu fah? Shekaru fiye da uku muna tare
inbanda hiran hauka babu abunda mukeyi"
"ko sau daya maganar yanda zamuyi rayuwar aure da kuma yanda zamuyi future tare
baitaba shiga tsakanin mu ba. Bata taba tada maganar ba nima kuma bantaba yiba.
Kumadai nidakai duka munsan Maimunatu is not only seeing me,tanada wasu samarin
wanda inada tabbacin may be akwai wanda take ganin future dinta taredashi" Lamido
yasauke ajiyar zuciya yace "I might be handsome and good looking but I can't deny
the fact that I've nothing,I earn nothing, I'm poor,Yar buga bugan danakeyi ayanzu
bekai har in iya rike Mata kwana kusaba and may be this's the reason why Maimunatu
is holding back bata taba yimin maganar aure ba dan bazan ce bata Sona ba,tana Sona
for sure anma ai ba lallai ta iya jiran sanda zanzama stable ba,if she's willing to
wait kuma toh iyayenta ma ba lallai su bariba. Shekaru tafiya sukeyi,ita macece ba
namiji kamar niba shiyasa nima bana daga hankalina gurin tambayarta,bankuma yi
kokarin inyi ending komaiba sabida banason yazamanto kamar kasawan daga gareni
ne,banason yazamanto ace ninayi breaking heart dinta kowani Abu. We'll keep going
like this,along the line intasamu miji tayi aure I'll wish her well and happily let
her go inkuma zata jira insamu aiki inzama stable then I'll surely marry her and
make her my wife inta yarda bayan nan Kuma se in auri Rukayya even though auren
Mata biyu baya cikin agender na anma ai bazan cuci wata sabida inason wata ba Koh?
Bayan may be tagama saka trust dinta da yardarta akaina"
Auwal seyace "Hmm! You've a heart of pure gold Man. Yarinyar da bata taba nuna
tanason aurenka ba kake cewa zaka aura if she's willing to wait? Ni I'm very sure
she's only staying with you sabida kyawunka,ranarda tasamu mijin aure sede kaji
andaura kawai" Yar dariya Lamido yayi sannan yace "Nima ai inada laifi. As a man
niyakamata infara Mata maganar aure ba itaba so if we both keep it to ourselves it
means dukanmu yaudarar junanmu mukeyi shiyasa nace muje ahakn kawai. If it's meant
to be it'll surely be" Hafiz yace "hakane amma ita Maimunatun tasan alakan ka
Rukayya?" Wara idanu Lamido yayi sannan yace "Tasan Nanaaa,I gist her alot about
Naanaaa har gaisawa sunayi, jiyama nahadasu a waya sungaisa and I'm sure if she's
sensible yakamata ace tagane inason Rukayya. I just believe she's pretending not to
know ne kawai" Auwal yace "toh wallahi yarinyar nan ba aurenka takeda niyar yiba"
dariya Lamido yayi sannan yatashi daga zaune dayake yana fadin "in bata aureni ba
ba hutarorona ba? Kaga shikenan Naanaaa na will have me to herself all alone. daman
nalura zatayi danbanzan kishi" dariya sukayi duka kafin yamusu sallama wai zaije
gurin Maimunatu yadawo sesu wuce gida da Auwal.
*Shin kuntaba experiencing masu soyayya irin ta Lamido da Maimunatu? I mean masu
soyayya without a plan,masu soyayya sabida kawai su debe ma juna kewa dansu kansu
sunsan yin rayuwa tareda da juna abune me matukar wuya?*
*Littafin Qadr na kudine duk Maison shiga paid group should talk to me privately on
whatapp 08147722806*
*Page Fifty*
*Avoid typing errors please*
***
Yaya Lamido ranar Sunday dinda yace zaidawo yadawo makarantar tamu kuma adaren
ranar seda yanemeni yabani tsarabana,tsarabar da seda aka kawomin nakowa kamar
yanda na bukata. Yaya Auwal ma yabani nashi playfully yana fadin "gashi dukdama dai
tsarabar dole akasani nayi" nidai dariya kawai nayi sannan nayi masa godiya.
Tun matsalar damuka samu dashi mukayi resolving bamu sake samun wani matsalar ba.
infact wani irin sabo da shakuwa ne yasake shiga tsakaninmu,babu wanda baisan Yaya
Lamido Yayana bane awannan lokacin dan kullum semun hadu,either during break kokuma
after night prep kafin muwuce hostel hakanan babu ruwanshi gaban kowa nunawa yakeyi
I'm very special to him wanda hakan yasa ko seniors shakkun tabani sukeyi kosakani
aiki. Barinma wadanda suka samu labarin abunda akayima su Yaya Aisha. masu crushing
akanshi kuwa shisshigemin sukeyi suna Jana ajiki anma duk abanza dan gabadaya baswa
gabanshi.
Akwai lokacin da wata Sister Kaltum ta dameni kan insama Mata number shi dannikaina
ban rike ba tunda ba wayane daniba banikuma da wanda zaibani wayarsa inkira sa koda
ina gidane,a Babban buline kawai zan iya kira da wayan Buba shima kuma already
yanada number wayartasa saved acikin wayarsa,Inna tashi kira kawai searching
sunanshi zanyi inkira. Alokacin da Sister Kaltum tadameni da batun Yaya lamido
cemata nayi yanada budurwa anma dukda haka seta dage sena samo mata number nasa.
Yakan bani wayarsa inyi game inmun hadu,most especially during the weekend
inyashigo dadare anma banason in dauki contact dinshi without his knowledge
shiyasa nayi deciding in tambayar mata anawa wautan.
Yaya Lamido baya taba shiga abunda zaiyi affecting karatuna. Kamar during prep
inyazo sede kawai mugaisa yawuce hakanan during classes ma inba sako zaibani ba
banma cika ganinsa ba. Zuwa dayakeyi during break kullum farkon zuwanshi makarantar
tun bayan abunda yahada munnan yazo yadaina zuwa. In kaganshi during break a ajinmu
toh ranar munyi class dashine Tuesdays and Fridays kenan. In yagama mana lesson
toseya jira munyi hira kafin yatafi,sauran ranaku kuma sede muhadu after evening
prep ko night prep kokuma insuke on duty na zuwa hall muhadu in an tashi ko kafin
ashiga.
Yau Wednesday kuma anatashi daga night prep nasabi jakana nafita a ajinmu
kasancewar nasan Yaya Lamido nacan gurin masallaci yana jirana. Sonake inje inbashi
sakon Sister Kaltum kamar yanda nayi mata alkawari ranar shiyasa ma bantsaya jiran
Aziza ba,nace tasamoni acan kawai semu wuce hostel tare.
Yana ganin nakusa isowa gunshi Ina murmushi shima yataho muka hadu a hanya,yace
"Nana murmushin yau dinnan na menene haka?" Yar dariya nayi sannan nace "Babu" Yaya
Lamido yamin kallo a darare sannan yace "Anya kuwa? Anya bawani abu muka samu ba"
Ina dariya nace "Allah bakomai Yaya lamido" Yaya lamido yace "Toh ya karatu? Hope
you had a good time reading?" Gyada masakai nayi ahankali sannan nace "Yau banga
kazo patrol night prep ba" dan yatsina fuska yayi sannan yace "wallahi kuwa. I'm
having headache tun rana yanzuma nafito ne sabida banason kizo kiyita jirana" sad
face nayi take Jin yace bayida lafiya sannan ahankali nace "Sorry. Allah ubangiji
yakara sauki,Aida kayi zamanka" playfully yace "Na'isa? Inyi kwanciyana gobe inji
ance gaki a gadon asibiti?" Tura baki nayi gaba tareda sakin dariya sannan nace
"Banasooo Yaya Lamido" yana dariyar shima yace "Aigaskiya nafada. I don't want to
cause you any problem Kuma"....
Jinjinakai nayi cikeda gamsuwa sannan nace "toh ka wuce kawai nima zantafi Hostel"
folding hannayensa yayi a kirji sannan yashiga girgizamin kai kamar wani karamin
yaro, sincerely yace "Bangaji da hira dakeba. Innatafi yanzu I'll miss you
soon,gwanda mucigaba da hirar lokaci yasake tafiya ynda I'll get to see you
tomorrow dawuri" blushing nayi sannan nace "Toh inkaje kakira Aunty Maimunatu kuyi
hira you'll not miss me" sake girgizamin kai yayi sannan yace "aike zanyi missing
ba itaba,so Kona kirata tunanin ki bazai bar rainaba" tura baki nayi gaba sannan
nace "toh yaza'ayi?" yayi Yar dariya yace "mucigaba da tsayuwa for a little longer
tunda students ma basu gama tafiya hostel ba yet" Gyada masakai nayi ahankali
sannan nanufi dakalin masallacin nazauna Ina fadin "muzauna anan kada kagaji da
tsayuwa" zuwa yayi yajona ni muka zauna sannan mukayi shiru nadan wasu dakiku babu
maicewa komai,se wulgawan student dasuke tafiya damukeyi. Mu muna ganinsu anma su
inba mutum ya lura ba bazai hangomuba.
Take Kuma se sakon Sister Kaltum danayi niyar fada masa ya fadomin a raina,cikin
sauri na dubeshi nace "Yauwa Yaya Lamido Ina wayarka?" Ba musu yasa hannu cikin
aljihun sa yaciro wayar yamika min yana fadin "Yaukuma game kikejin yo dadarennan?"
dan yasan bancika karbar wayarsa inyi game ba after night prep,mostly a weekends
nake karba sabida munfi jimawa tare awannan ranakun dayake ba'a zuwa night prep.
Karbar wayar nayi na bude ta ina fadin "uhm uhm. Ba game zanyiba,number ka nikeso"
kallona Yaya Lamido yayi da lumsassun idanunsa sannan cikeda mamaki yace "Number
na?" Gyada masakai na nayi ahankali sannan nace "Uhmmm" cikeda curiosity yace
"finally kinyarda zaki rike number kenan basai kinyi naki wayarba?" danyasha cemin
irkarbi numbersa in haddace sabida Zan iya bukata wataran anma se in gwasaleshi
ince "Uhm Uhm senayi wayarkaina zan haddace Kona haddace yanzuma banida wayar dazan
na kiransa,se shima kuma betaba takura min akan dole sea rike dinba" cikeda yarinta
nace "Ba rikewa zanyiba, Sister Kaltum tace inkarba Mata" Damamaki yace "Waye
Kaltum?" Nace "She's my Senior. kana koyar dasuma,wai burgerta kakeyi tana sonka"
Plainly Yaya Lamido yace "bakice Mata inada budurwa baneba?" tura bakinayi gaba
sannan nace "nafada Mata mana anma ahakan still tace tanaso" wannan Karan murmushi
yasaki sannan yace "shine kekuma kikazo zaki karba Matan? Bakya taya Aunty
Maimunatun ki kishi me?" Tura baki nayi sannan nace "toh yazanyi? Tadameni ne and
she's my Senior, she's always nice to me kartaga kamar inakin karba matane da
gangan" Yaya Lamido seyace "toh kice Mata tazo tasame ni takarba dakanta kuma
dagayau duk wanda yake damunki akaina just ask him to meet me personally" wara
idanu nayi sannan nace "insuka zo gurin naka mezaka musu?" Yar dariya yayi sannan
yace "Abunda sukeso Mana?" Take na tsuke fuska nace "Soyayya zakayi dasu kenan?" se
yayi dariya yace "Innayi soyayyar dasu haramun ne?" Kara tsuke fuska na nayi nace
"Aunty Maimunatun fah?" seyace "ita tagida ce ai sukuma wadannan na makaranta
ne"....
Tashi nayi daga zaunen danake ina fadin "cab aikuwa sena gaya Mata" tashi yayi daga
zaunen shima yana fadin "kiyi hakuri kurufamin asiri karki fada,wasa nakeyi miki"
kallonshi nayi sannan nace "toh mezakayi musu idan sukazo gurinka?" Zuba min idanu
yayi sannan yace "Don't you trust me?" ahankali nace "I do" Seyace "Then do as I
say" gyadamakai nayi ahankali,adede lokacin ne kuma Aziza ta iso gurin. Gaisawa
sukayi da Yaya Lamido ya amsa yatambayeta ya karatu kafin mukayi mishi sallama muka
tafi hostel bayan nasake yimasa Allah yakawo sauki.
Aikuwa washegari nasamu Sister Kaltum nafada Mata sakon Yaya lamido,at first she
was very happy harda rungumeni tana min godiya anma dataje tasamu Yaya lamidon
tadawo se labari yasha banban,kirana tayi tadinga min mitar miyasa nace ma Yaya
lamidon ita tace insamo Mata numbersa,ita ai cewa tayi insato bawai inkarba a
hannunsaba.
Hakuri nidai nabata inacewa "aibansaniba nadauka cewa tayi inkarba Mata" bayan kuma
tabbas nasan sata Matan taso inyi,Satan dabazan iyayi bane yasa na tambayashe.
Bansan yasukayi dashiba but for sure it's not something good shiyasa ranta yabaci.
aranar damuka hadu da Yaya Lamidon ma seda yatambayeni ko Sister Kaltum tamin
magana anma senace Masa batayimin bama kwata kwata sabida banason infada mishi
injaza Mata wani abun kuma dan tabbas Yaya Lamido bazai yi shiru ba indai nace Masa
gayanda mukayi. Tundaga ranar bawata Senior ko colleague dina data sake tambayana
number Yaya Lamido ko in hada ta dashi.
Haka rayuwar mu tacigaba a FGC Azare,days are turning into weeks har satin visiting
yazagayo.
Kowa shirye shiryen visiting yakeyi anma ni gabadaya I'm not excited tunda daman
murnar visiting dinda nakeyi ada can dan Yaya lamido da yan gidansu zasuzomin ne.
Toh wannan karan kuma already muna tare Koda yaushe buguda kari kuma abunda
yahanani yin zumudin shine rashin yini dayakeyi a makaranta during weekends dankuwa
tunbayan dawowansa daga gida kowani weekend sesun fita field work shida su Yaya
Auwal,either within local governments na Bauchi state kokuma suje Gombe. In within
Bauchi ne aranar yake dawowa makaranta washegari susake fita Amma indai gombe toh
Friday yake tafiya yadawo Sunday evening. toh Daman wannan satin insukayi mapping a
Bauchi the other week Gombe zasuyi. Satin dayakama visit dinnamu Gombe yakamata
yajeshi shiyasa ma gabadaya jikina yayi sanyi.
Gashi abu bashi kadai yakeyiba,tareda abokanansa sukeyi bare ince mishi yafasa
shima kuma benuna min yana son fasawan ba,infact yanda yakeyi kamar ma baisan satin
za'ayi visiting dinmu ba nima kuma sai bandamu intuna mishi ba dukda nafi tunanin
yasani din kawai bayason adago da zancenne tunda Aziza tasha yin maganar visit
agabansa.
Ranar Friday koda yagama mana lecture betsaya munyi surutun damuka sabayi ba cemin
yayi zaije hostel yayi parking kayansa baishiryaba kuma Hafiz nahanya already daya
iso zasu dau hanyar Jos. Da mamaki nace "Me Yaya Hafiz zaizo yi kuma? Ba wannan
satin Gombe zakuje ba?" girgizamin kai Yaya lamido yayi sannan yace "We're not
going to Gombe,already mungama mapping Gombe so Jos zamuje wannan satin" jiki
sanyaye nace "Toh shikenan" dukda araina naji wani iri,naji haushin miyasa baifada
min ba Gombe zasuje ba se ranar dazasu tafi. Haka yatafi staff quarters cikin sauri
danko wanka baiyiba yazo yayi mana lesson ranar to which I don't know why hakan
tafaru dankuwa Yaya Lamido baya taba zuwa aji ba'a shiryeba hakanan kowani Friday
inzai shigo makaranta tunsafe yake shigowa school premises da shirin juma'arsa. ko
sallar juma'a kasa tsayawa nayi ranar,hostel nayi tafiyana na tattara wankina
nahauyi.
Nagama wankin kenan Ina shanya akan line din dake gaban dakunanmu wata yarinya tazo
nemana wai Yaya lamido nakirana insameshi a staff room. Cemata nayi toh kawai
ayayinda nakarasa shanyar danakeyi din sannan nashiga daki nasaka house wears dina
nanufi admin block,sanda na'isa agaban admin block naga Yaya Auwal da Yaya Hafiz
suna zaune suna hira. Gaidasu nayi inda sukacemin Yaya Lamidon nacikin staff room
inkarasa,cemusu nayi toh sannan nanufi staff room.
Ina shiga staff room din nahangoshi zaune kan table dinshi,shikadaine babu kowa
dayake anriga antashi a school sauran Malaman kowa yakama gabansa. Yanzu sanye yake
da ash colour shadda daya matukar amsar jikinsa unlike dazu dayake sanye da kananun
kaya. gashinnan yasha gyara akwance luf luf gwanin ban sha'awa dankuwa yacire hular
tana ajiye akan desk dinsa. Bankai ga karasawa inda yakeba naga yatashi tsaye anma
as soon as mun hada idanu seya koma yazauna yana fadin "Aaaa ashe ma kin iso,aiihar
inashirin tafiya neman ki. I thought sakona bai Isa garekiba" faking murmushi kawai
nayi ayayinda nakarasa kusa da desk dinsa ahankali nace "Anfada min" folding
hannayensa yayi duka biyu guri guda Yana kallona sannan yace "What took you so long
toh?" Nace Masa "wanki nikeyi mesakon tazo tasanar dani" seyace "Tafiya zamuyi naga
bamuyi sallama ba and I looked everywhere after prayers bangankiba shine natura
akira min ke" jinjinakaina nayi ahankali sannan nace "Allah yakiyaye hanya" yana
kallon fuskana yace "Amin. Thank you" sekuma yatashi tsaye yadauki hularsa yasaba
akansa datasake fidda kyawun sa sannan yafito daga gurin desk dinnasa.
Yakaraso gabana yatsaya with a smile on his face yace "Tsarabar mezanyi mekike so
inkawo miki daga jos?" trying to hide my pain nayi sauri na girgizamasakai sannan
nace "Babu" wara idanu yayi da mamakina sannan yace "Babu Kuma Nanaaaa?" danyasan
betaba tambayarta mezai kawomin inzai yi tafiya ince "Babu" sede ince "koma miyene"
inbanida abunda nike marmarin yakawomin. Gyada masakai nayi ayayinda naki bari in
kalleshi sabida irin hawayen danaji suna kokarin zuba daga idanuna. sa hannu yayi
yadago chin dina ahankali yana fadin "look at me Nanaa" anma still naki kallonsa.
Ahankali yace "badai tafiyarne bakyaso inyi ba?" kawai sai hawayen suka fara zuba
kuma hakanan without a second thought najuya nafice daga staff room din Ina
shesheka. Inajin shi yanabina abaya yana kiran sunana harna fice anma ko tsayawa
banyiba. haka nakoma hostel nashakari kukana daganan bacci yayi awun gaba dani,ni
haushina bawai tafiyar dazaiyi baneba rashin min maganar visiting day dakuma rashin
nuna yasan bazan ji bayanan bane yasani Jin takaici.
Dayanma sega Aziza tazo da letter wai Yaya lamido yace tabani. Ina Karbar lettern
jefashi nayi cikin locker na inda daganan kuma bansake bi takanshi ba sabida
banajin ma inada ra'ayin son Jin me letter ta kunsa. I just believe tunda yatafi
jos din mekuma zaicemin? haka tadinga damuna wai muje muyi guga bayan tabani letter
din anma naki nace taje tayi abunta kawai. Dole haka ta hakura daga karshe tatafi
abunta itakadai.
Washegari visiting as usual Mummynsu Aziza ne suka fara zuwa bayan naje mungaisa
dasu mungama cin abinci kenan nahangi shigowar motar gidan Kawu Sani,fadama Aziza
dasu Momky nayi mutanen gidan mu sunzo sannan natashi natafi. Sanda na'isa inda
suke harsun shimfida darduma su Yaya Aisha sunzozzo anata gaisawa. Ummi ce kadai
tazo visiting din se Yaya Zunnurain dayayi driving dinta yakawota wai Aunty sunyi
tafiya da Kawu Sani Lagos,shiyaje conference meeting inda itakuma zata karasa
cotonou tayi sayayya kafin yatashi dawowa. Tunda naga ba Aunty agurin daman bugun
zuciyana ya tsananta,naji hankalina yatashi fiyeda wanda nake ciki ada anma ahakan
nadaure nakarasa bakin tabarmar na tsuguna kusa da Ummi nace "Ina wuni Ummi?" Ummi
ko kallona batayi ba,seda nagaida ta a karo na uku sannan ta watsa min harara,rai
bace tace "ke dallah kin isheni! Cemiki nayi inason gaisuwarki? Kokuma daban wuni
ba Zaki ganni anan?" adan tsorace nace "kiyi hakuri Ummi" tsaki Ummi tasaki tana
fadin "Yarinya sekace mayyah haba....!!!" Yaya Aisha dake zaune gefen Ummi tanata
min kallon banza tace "Ummi wannan ai in akwai abunda yafi mayyama toh dashi za'a
kirata" se Yaya Safiya tace "Nina rasama meya kawota nan gurin!" Kafin takalleni
adakile tace "ke yanzu bayan abunda Kika jaza mana Harkina da guts din zuwa inda
muke?" Ummi Jin abunda Yaya Safiyar tace setayi sauri takalleta,tace "Meta jazamuku
Kuma?" Yaya Safiya cikeda takaici tace "Hmmm Ummi Aisha tabaki labari" kallon Yaya
Aisha Ummi tayi cikeda son Jin abunda yafaru tace "Wai meyafarune kifadamin Mana?"
Yaya Zunnurain dake danne danne cikin wayarsa shima seyabar abunda yakeyi din
yazuba ma Yaya Aisha idanu yanason Jin mezatace...
Nidai awannan lokacin har jikina yafara rawa tsabar tsoro.
Yaya Aisha tace "Ummi kintuna saurayin da muke baki labarin yana zuwamata visiting
tun zuwan mu makarantar nan?" cikin sauri Ummi tace "Natuna shi,kice min
fitsararrren yaron can dayataba zuwa gida Wai yanason yaganta kawai" Yaya Aisha
tace "Eh toh shi Ummi!Ashe duk abunda mukayi ma yarinyar nan zuwa take ta kwashe
mashi shine yanzu yazo Yana service a makarantar nan. Bakiga cin uban mu dayayi ba
a satin zuwan shi nafarko kadai,gashi yamaida mu boyi boyinshi duk ranar damuke
dashi,mune goge blackboard,mune copying masa note,mu yake jefama questions dukyanda
yaga dama a aji dukwai akan shegiyar Nan" Yaya Aisha tayi maganar tana nunani da
dan yatsa.
Yaya Safiya tace "Ummi babu fah Wanda ya Isa yataba yarinyar Nan yanzu a makarantar
nan. Tazama celebrity,tazama gwal kowa jiyake da'ita,kanwar sir Isma'il,kanwar sir
Isma'il...yenyeyygme" Yaya Safiya tayi maganar rai bace.
Yaya Zunnurain dabai gane kan komaiba seyace "kumin bayani in detaiils" aikuwa take
suka shiga bashi labarin komai har karshe,suna sauke aya Ummi tace "kan ubancan!!!!
shidin dan gidan uban wayene dazai sa a hukunta mana Ya'ya? Shida ku wayafi kusanci
da'ita dan ubansa?inma aikinne Baku Isa kusata bane a matsayin ku na yan uwanta"
Sadiya da tun dazu batace komai ba tace "Ummi har ajifah yakezuwa suyi hira kullum
kamar wasu masoya" Ummi seta rike haba tana kallona tace "sede Yan iska ba masoya
ba" kafin tazare min idanu tace "Yanzu Kedin harnawa kike dahar kika san yanda ake
hira da saurayi?" nida already nafara hawaye alokacin bakina rawa nace "ba
saurayina bane Ummi" dakuwa Ummi tamin rai bace sannan tace "inba saurayin ki bane
Ubankine?" girgizamatakai nashigayi dasauri sannan bakina narawa nace "Yayana ne"
Ummi tace "Yayanki agidan uwarwa? ta Ina kuka hada dangantaka don Ubanki!" wannan
Karan kuka nakeyi sosai..
Inaji Yaya Zunnurain yashiga calming Ummin down yana fadin "kubar maganar Nan Ummi
kina janyo Mana attention" Rai bace Ummi tace "aitunda itabatasan halalciba,aitunda
ita tazama Yar iska har take Kai Karan Ya'yan da iyayensu suka rufa Mata asiri suke
rike da ita wani Dan iska can Yana hukunta su toh wallahi batanemi zaman lafiya ba.
Miyasa shi abokin iskancin nata baidauketa yakaita gidansu ba harzai wani zo
yanacimin zarafin Yara? Toh wallahi bazai yuyu ba! Maganar Nan ai har gaban
makarantar zataje. Zamuje yamana bayanin ta inda yahada dangi da'ita dahar zai
dinga shiga tsakanin ta da Yan uwanta danmudai bamusanshi ba" Yaya Zunnurain hakuri
yadinga bama Ummi tanata babatu Yana cemata kaiwa gaban makarantar is not a
solution,hakan kawai zaisake zurma su Aisha a case ne and this might call the
attention of Kawu Sani. Subari kawai suyi handling dinshi in their way.
Dakyar Ummin ta hakura tayi shiru daganan kuma takoreni wai intafi Inbata guri inba
so nake tayi loosing temper dinta ta kakkaryani gaban mutane ba. Allah yataimake mu
ma inda muka zauna babu mutane dab damu yasa attention din mutane bezo kanmu ba da
Ummin keta magana tunda tadaga muryar ta dafari Yaya Zunnurain din yamata magana.
*Sweet and Long chapter tomorrow insha Allah*

this number 08147722806
*Page Fifty One*
Tashi nayi nabar gurin jiki sanyaye Ina hawaye ayayinda nanufi hanyar Hostel.
Bankoma gun Aziza ba dukda nasan zatazo nemana dankowani visit tana zuwa sugaisa
dasu Ummin acewarta Ummin tanacin albarkacin Aunty ne da babu abunda zaina kawota
gaishe su. Most at times ma tare muke zuwa in Yan gidan Kawun Sanin sunzo su.
Yaudin sanda suka iso tana waya da Abbanta shiyasa ninayi gaba,seyanzu ma nake
godema Allah da banzo tareda itanba dan nasan inda tana gurin bazata kyaleba kuma
koda takyale batace komaiba toh tabbas labarin nan se yaje kunnen Yaya Lamido. Ina
shiga dakin mu gadona nahau na takure guri guda ayayinda nashiga rusa kuka mai
tsuma rai,kukan dana jima banyi irinsa ba ayayinda kalaman Ummi dasu Yaya Aisha na
dazun keta lingering akaina.
What have I done? Yaushe ne ranar dazasu fahimce ni sudinga daukana kamar mutum?
wadannan sune tambayoyin dayake yawo acikin kwakwalwana. Gashidai yanzu shekaru
sundan ja,shekaruna uku dasu anma har rana maikaman tayau babu wani improvement
azamana dasu sema abunda ya karu akan nada din.
***
Can bangaren su Ummi ko bayan da Rukayya tatafi Ummi batadaina masifaba,korafi
takema su Zunnurain wai da sunbari takai karar makaranta zaifi kawai......
Zunnurain yace "A'a Ummi muddin kikace zaki kai karar yarinyar nan gaban makaranta
su Aisha ne zasu kwana aciki. Tunda ita Rukayyar tanada shaidu" tsaki Ummi tasaki
sannan tace "Basai mu nada mata sharrin tana iskanci dashiba kawai kuma mu
bamusanshi ba
mune danginta" Aisha cikin sauri tace "Ummi cikin makarantar nan fah daidaikune
basusan su tareba. Har Malamai sunsan cewa ita kanwar sane,ko Ina yashiga fada
yakeyi kuma ako ina suna magana irinta ya da Kanwa" Ummi yace "toh Amma ai mahaifin
ku baisani ba" Zunnurain seyace "Meya kawo maganar Abba kuma cikin zancennan Ummi?"
Ummi tace "Ina nufin idan shi muka fada mishi ga abun da Rukayya takeyi a makaranta
tana kula samari suna claiming shi Yayanta ne zaizo yayi magana yadau ki mataki.
Daganan kuma kinga mun karyata su daga ita harshi,za'a tsaneta,za'a hukuntata daga
ita harshi akan abunda sukeyi bayan sunsan they're not related" sauke wani irin
gauron ajiyar zuciya Zunnurain yayi Jin bayanan Ummin sannan yace "But they said
they're related in real life" Ummi tace "tawurin dangin mahaifiyar taba,kuma ai
sukadai sukasan kayansu mu bamusan komai gameda alakar tasuba so inmukayi haka
mundauresu" Aisha tace "Ummi bakya tunanin Abba yariga dayasan da Sir Isma'il
dinnan kuwa?" Cikin sauri Ummi tace "baisanshi ba,dayasan shi koda sau dayane
zakiji yayi bayaninsa" wannan Karan Safiya ce tayi magana tace "Kai koya sanshi
kobai sanshiba wannan ba solution baneba. Wallahi sir Ismail is very clever,Shiba
Rukayya bane daza'ayi abu yayi shiru batareda ya tsaya makansa da'ita ba. bazai
taba bariba harsai yakawo shaidu ninasan wannan" Sadiya tace "I'm with you Yaya
Safiya adai nemi wani abunyi din anma banda wannan dan akwae probability din daga
karshe mune zamu kwana aciki" tsaki Ummi tayi sannan tace "toh yanzu miye abunyi?"
Zunnurain yace "karki damu Ummi. We'll see what we can do. For now muyi hakuri
muzuba ma sarautar Allah idanu. Our time will come,the very perfect time dazaiyi
favouring dinmu even though I'm eagerly waiting for that very day dannima inacike
da Rukayya,haryau banmanta abubuwan datajamin ba and I'll never forgive her for
that. I'll surely take vengeance,surre!!!!" Zunnurain yakarashe maganar har
jijiyoyin wuyarsa natashi because the more he remember that incident dayafaru
shekaru uku dasuka wuce the more he gets agitated.
***
Har azahar tayi Ina kwance kan gadona Ina kukan zuci nikadai. Dakyar na iya natashi
nadauro alwala nazo nayi sallahn azahar,koda na idar da sallahn bantashi daga kan
sallayar danakeba,kwantar dakaina nayi abakin gadona dayake dab da gadon na
shimfida sallayan.
Kaina wani irin sarawa yakeyi sakamakon irin kukan danasha. muryar Aziza danajiyo
tundaga kan varendern dakin mu ne yasani daga kaina daga jikin gadon nawa nakoma
Ina kallon kofar dakin mu batareda nace komaiba. Shigowa tayi dakin tana fadin
"Rukayya! Rukayya kina inane wai?" Excitedly. Budan baki nayi zan amsa kiran sunana
datakeyi anma wanda nagani abayan tane yahanani furta koda kalma gudane.
Salma ce biyeda ita abaya,Salma kanwar Yaya Lamido.
Da mamaki natsaya Ina binsu da kallo harsuka iso cikin kwanana, Aziza tasako salmar
agaba tana cewa "look who's here" bakina rawa nace "Salmaaaa....?" dariya Salma
tasaki sakamakon yanayin yanda nayi maganar kafin takaraso inda nake tafada jikina
tana fadin "Kawataaaa...." Rungumeta nayi cikeda farin ciki sannan nace "Yaushe
kikazo? Keda waye haka?" dagowa tayi daga jikina tana kallona da mamakin tambayar
tawa tace "Yaya Lamido becemiki zamuzo baneba?" girgizamatakai nayi sannan nace
"befada minba. Nadauka bazakuzoba sabida yanzu yana koyarwa a makarantar nan bare
kuce zaku biyoshi" Salma tace "Cabdi aitun zuwanshi gida two weeks back yace
visiting dinku yazo in satin yazo zezo yadaukemu muzomu toh kuma se tafiyar su Jos
tatashi shine yakira awaya yace mutaho kawai" tunda Salma take bayani inbanda
tunanin Yaya lamido ba abunda nakeyi,so daman bai mantaba,so he's plan alot
surprising dina yakeson yi?"
Senace ma Salma excitedly "Ina su Yaya Basman toh?" Salma tace "Suna visiting
ground nima dakyar akabarni nabiyo Aziza hostel kinsan securities dinku se
ahankali" gyada matakai nayi cikeda gamsuwa sannan cikin sauri natashi na ninke
sallaya na nace mutafi dayake daman banma cire day wears dinaba.
Haka muka nufi visiting ground mu uku muna tafiya munata hirarrakin mu wanda har
hakan yasa naji wasai araina nafara manta abunda yafaru tsakanina da yan gidan Kawu
Sani dazu. Ahaka harmuka Isa gurin da muka saba zama dasu kowani visit idan sunzo
su. turus nayi natsaya sanda muka isa gurinsu ganin ba su Yaya Jidda bane kadai
akan darduman dasuka zo dashi,harda wata Mata in her late forties za'ace hakanan
kallo daya zakayi Mata kaga irin tsantsar kamar dasukeyi da Yaya Lamido dasu Yaya
Jidda. Dana ganta babu abunda yazomin araina face cewa itace Umma anma dayake
banida tabbacin hakan,it's my first time seeing her senayi sauri najuya nakalli
Salma dake gefena with a questioning look dake cikeda hope.....
Salma na dariya mischievously tace "Umma ce...." aikuwa kamar wanda dama jira
nakeyi sekawai nadaka tsalle nafada jikin Matar cikeda farin ciki Ina fadin
"Ummmmma......" rungumeni Umman tayi tana dariya haka su Yaya Jidda ma. I know she
felt awkward at first danbatayi tsanmanin haka daga gareni ba anma sebata nuna
ba,nima kuwa I was not acting straight,I was just do excited,Matar danajima inason
gani taazomin alokacin da banyi tsanmani ba ai dole inyi farin ciki.
Munjima rungume da juna sekuma nayi sauri nadago daga jikinta tunawa danayi ai
Salma bata fadamin tareda Umma sukazo ba tundaga hostel. Kallon Salman nayi inada
hararanta playfully nace "Wato shine kikaki kicemin tareda Umma kukazo Koh?" Salma
Yar dariya tasaki sannan tace "Nifah nadauka kinsan da zuwanmu wallahi ashe Yaya
lamido baifada mikiba,shiyasa ma dakika nunamin baki sani ba se na boyemiki kawai
sabida banason inyi ruining surprise dinda Yaya lamido yayi niyar yimiiki" tura
baki nayi gaba nace "Anma ai kincemin kunzo dasu Yaya Basma Umman nedai baki fada
ba" Salma tace "su ai nasan babu yanda za'ayi ince miki banzo dasuba kiyarda tunda
daman tuncan tare muka Saba zuwa" senayi dariya nace "Toh kin kyauta dagake har
Yaya Lamidon" sekuma namaida dubana ga Umman,nazauna dakyau agefenta kamar wata
meshirin shigewa jikinta nace "Ina wuni Umma?" Umma na kallona da murmushi tace
"lafiya Lau Rukayya ya karatu?" Nace "Alhamdulillah. Ya hanya?" Umma tace
"alhamdulillahi" gabadaya bakina yaki rufuwa tsabar farin ciki nace "Masha Allah.
yaude gani ga Ummana" dariya Umma tayi sannan cikin sigar wasa tace "Nima yau gani
ga Rukayyan Lamidona" sekuma muka saki dariya dukanmu Yan gurin.
Bansan miyasa ba haka kawai Allah yasaka min son matar tunma kafin insanta and here
I'm feeling so free and normal with her. Jinake kamar Ina zaune da mahaifiyata na
gaskene,jinakeyi kamar daman tuncan munsaba,babu wani Jin nauyi ko awkwardness haka
and even though ita nalura tanadan Jin nauyina dafari anma ganin yanayina seta
ajiye awkwardness din agefe tana biyeni Itama. haka muka gaisa dasu Yaya Jidda muna
tambayar juna karatu aikuwa sega kiran Yaya Lamido yashigo wayar Umma. Picking call
din tayi inaji suka gaisa,yatambayeta kosun sameni tace eh muna ma tare gani a
gefenta.
Take seyace abani wayar, Umma mikomin wayar tayi tace "Ga Yayanki zakuyi magana"
make kafada nayi sannan nace "Umma kikyaleshi fushi nakeyi dashi baicemin zakuzoba
harsaida nagama shan kukana" Umma setadanyi dariya tamayar da wayar kunnenta tace
"toh kaji wai fushi ake dakai. Ashe har kuka kasakamin Diya?" bansan meyacema Umman
ba setasake mikomin wayar tace "Yi hakuri kikarba wannan yaron jarabane dashi
inbaki Yi magana ba bazai barni inhuta ba" Karbar wayar nayi Ina murmushi sannan
nakara a kunne na Ina fadin "toh Umma Yaya lamido yaci albarkacin ki" dagacikin
wayar senaji yace "Naaanaaa?" tura bakinayi gaba nace "Bazan amsaka bafah. Banace
fushi nakeyi ba" Yar dariya yasaki sannan yace "Anma ai kince naci albarkacin Umma
Koh?" nace "Eh ai wannan na amsar wayar inji mezakacene bawai inyi maka reply ba"
seyayi murmushi yace "Toh hear me out" senayi shiru bance komai ba Ina sauraronsa.
Ahankali yce "I'm sorry for making you cry yesterday" make kafada nayi kamar wanda
Ina gabanshi ne sannan ashagwabe nace "Naqi" cikin rada yace "Bazakiyi hakuri ba
kike nufi?" nace "Uhmmm banace maka banason surprises ba anma still seda kayimin"
sassauta murya yakumayi kasa sannan yace "Ai it's no longer a surprise tunda nafada
miki tun jiya" wara idanu nayi sannan nace "Yaushe kafadamin Yaya lamido?" Yace "I
sent you a letter yesterday. Baki karanta baneba?" niseda yayi maganar ma na tuna
da letter, ahankali nace "I didn't read it,I was angry sanda aka kawomin kawai sena
jefata cikin locker" Yaya lamido yace "oh shirt.... I'm sorry,at first I wanted to
surprise you about zuwan Umma sabida nasan kinjima kina son zuwanta anma jiya
danaga kintafi kina kuka,you didn't even hear me out senaji tsoron kada abunda
yafaru last time yasake faruwa garin son yimiki surprise" yayi maganar cikin sigar
zolaya sannan yace "Sena tuna kuma kince bakyason surprises shine naturomiki letter
nayi ruining surprise din ashema baki karanta ba?" Se Yace "Wai Nanaa kindauka
namanta visiting day dinku? Kindauka bazan San how much you'll need someone by your
side ba bayan filty dangin Babanki sun kuntata miki? I've been planning to make
your first visiting day with me in your school a special one tunbayau ba, I've been
planning to see your smile,your face expression in Kika ga Ummana for the very
first time a irin zumudin da kikeyi da bakisanta bama anma Allah baiyiba. Professor
dinda muka samu zemana field lecture a Jos is fleeing to UK cikin satin daza'a
shigannan kuma bamusan ranar dawowansa ba, it's an opportunity that we can't afford
to miss shiyasa Kika ga natafi da babu abunda zaisani tafiya,da normal field work
ne canceling dinta zanyi"
Take senaji jikina yayi sanyi ahankali nace "Shine bakayimin bayani ba?" Yaya
Lamido yace "banfada miki bane sabida surprise dinda nayi niyar miki,I thought ba
amfanin fada din tunda su Umma zasuzo Miki inyaso Inna dawo semuyi maganar but
believe me jiyaafter seeing your tears I wanted to tell you everything kafin
intafi,rashin tsayawar dabakiyi bane yahana ni yimaki bayanin" nikaina bansan Ina
blushing ba hakanan inaji hawayen farin ciki nason zubowa anma nayi kokari na
rikesu, ahankali nace "thank you Yaya lamido" daga daya bangaren yace "How do you
like my surprise?" Ina murmushi nace "Amaizing. you never cease to bring smile on
my face" I can hear him chuckle,yace "Umma fah? Is she nice to you?" cikin sauri
nashiga gyada kaina kamar wanda Ina gabanshi nace "she's so nice Yaya Lamido
daganan kuma sena shiga bashi labarin yanda encounter dinmu ya kasance da'ita da
irin murnar damukayi inda daga karshe nace "She's the best and Beautiful just as
Handsome as you're" seyayi dariya yace "So I'm handsome?" Sena ware idanu da
mamakinsa nace "Oh bakasani ba?" Yaya Lamido yace "Uhmm.... toh bansaninba za'ace"
seyayi kasada murya yace "Fadamin,am I really handsome?" budan baki nayi zanyi
magana carab muka hada idanu da Umma dake kallona tana ta murmushi adoringly....
Aibansan sanda nacire wayar a kunnena ba Ina mika ma Umma kamar wata munafuka
dankuwa senaji nakasa basa amsar kuma,Umma na murmushi tace "kungama maganar ne?"
gyadamatakai nayi ahankali Ina smiling.
Setakai wayar kunne inajin Yaya Lamidon cemata yayi bamu gama magana ba senaji
tanacewa "toh ita tace kungama" daya dameta setace "Kai waini mune mukazo Mata
visit din Koh Kai? In magana kakeson yi da'ita meyasa baka fasa tafiyar taka ba?"
daganan seta kashe wayar tana murmushi tadubeni,tace "kyale Yayan kinnan. Inkika
biyeshi ko abinci bazakiciba" dariya nayi bance komaiba haka Umma tasa Yaya Basma
tazuba mana abinci a tray mukaci dukanmu anata hira cikin raha. abincin ba karamin
dadi yaminba wanda har hakan yasani kasayin shiru nace ma Umma "Umma gaskiya
wataran zanzo koyon girki gurin ki" dariya Umma tayi sannan tace "Allah yakawo ki
Rukayya" Yaya Basma dake jinmu setace "Kamar gaske,kedin yaushema kika yarda
kikazoma mutane ziyara bare azo ga batun harkizo kijima kikoyi giki. Aisede inmun
auroki munkawoki gida ki koya" murmushi nasaki sannan nace "Allah bahaka bane Yaya
Basma" Salma kuwa dariya ta kwashe da ayayinda tadaura hannunta a chin dinta
dreamily tana fadin "Wayaga suruka na koyan girki gurin suruka" harara Yaya Jidda
tawatsa musu duka lokaci guda da alama dai bataji dadin zancen nasuba,tace
"meyakawo maganar aurowa akawo gida dakuma surukan taka tsakanin Rukayya da Umma?"
Yaya Basma zatayi magana senayi sauri na katseta,cikeda curiosity nace "miye
ma'anar surukantaka?" dankuwa harga Allah bansaniba,infact it was my first time
hearing the word.
Wara idanu Salma tayi da mamakina tace "Wai dagaske bakisan ma'anar surukantaka
ba?" gyadamatakai nayi ahankali sannan nakuma cewa "miye ma'anars" Salma tace
"Lallai kawata bakiji hausaba... Surukantaka na nufin... " Sauri Umma tayi takatse
ta da "Wai abinci kukecine koh surutu kukeyi?" Salma na Yar dariya tace "duka Umma"
dakuwa Umma tayi mata sannan tace "toh azabi daya kuma abinci nazaba aci sabida
haka banason insakejin wani yayi magana cikinku" aikuwa duk semukayi tsit muka
cigaba da cin abincin mu dukda kuwa kowa da abunda yake sakawa aransa,ni ma'anar
surukantaka nikeson sani wanda shikadai ne zaisa ingane sauran maganganun su Yaya
jiddan Amma sede bansamu amsar tambayar tawa ba harsuka tashi tafiya ranar dankuwa
da muka gama cin abincin wani hirar muka hau yi,Sena manta shadaf da batun kalmar
*Suruka* hakanan bantashi tunawa ba se washegari da Yaya Lamido yadawo da dare muna
magana.
Provision kuwa daidai gwargwado dede karfinsu suka kawomin dukdama naso inki karba
dafari harsaida ran Umma yabaci tace kenan ma bandauketa amatsayin Ummana ba kamar
yanda nake fada indai bazan karbi abunda takawomin ba. Abinci kuwa seda na ture har
washegari dasafe akwai saura. Nasan tabbas anyomin aike daga gida anma Koda Wasa
nasan su Yaya Aisha bazasu baniba,yazama nasu kenan kuma nima banwani damu kaina ba
tunda bayau sukafaraba and moreover gashi nasamu na Allah da annabi sunkawomin
nima.
Washegari Sunday a sallar maghrib naga Yaya lamido inda ananne nasan yadawo aikuwa
ana idarda sallar nafita waje nasameshi.
Fuskarshi daukeda murmushi yace "Aiyanzu zan tafi nemanki ashe Kinganni" Yar dariya
nayi sannan nace "ta Ina zaka iya nemana acikin crowdness din dalibannan?" Yar
dariya yayi sannan yace "I'm a Teacher Sis,yarinya daya kawai zansa taje tanemo
minke kuma dolenta tayi" Jinjina masakai nayi cikeda gamsuwa sannan nace "Ina
wuni?" Yace "Lafiya lau watoh jiya muna magana Kika mayar ma Umma wayarta Koh?" Yar
dariya nayi sannan nace "kayi hakuri Yaya Lamido. tana gabana ne fah?" Yana dariya
mischievously yace "And then?dan tana gabanki shine ni baza'acemin kyakyawa ba?naga
kema Umman kice" tura baki nayi gaba nakumacewa "kayi hakuri wallahi kawai muna
hada idanu da ita senaji maganar taki fitowa" wannan karan dariya yasaki sosai
sannan ya tsaya daga tafiyar dayakeyi dandama mundauki hanyar classes area
ne,juyowa yayi yana kallona wanda hakan yasani tsayawa nima ayayinda yayi folding
hannayensa a kirji yazuba min idanu.....
Yace "Toh yanzu ai gani gaki seki bani amsa,am I really handsome?" without a second
thought nace "Yes You're Yaya Lamido. bantaba ganin kyakyawan namiji irin kaba" I
can see him blushing,seya lumshe idanu yanadan dafe kirjinsa in a funny manner yace
"oh Handsome me...." dariya muka saki duka sannan na canza zancen tahanyar
tambayarsa Ina tsarabana.
Yace "Cabdi. Wace tsaraba kuma? Bakince bakison tsaraba ba?" tsuke fuska nayi
lokaci guda sannan nace "Ni bance banaso ba" wara idanu yayi yana dariya yace
"bakice bafah kikace?" tura bakinayi gaba sannan nagyada masakainace "Aikaima kasan
inaso kawai dan raina a bacene yasa nace banaso din" Yana dariya yace "ni Ina
nagane" fuska tsuke nace "Nidai Ina tsarabata" seyace "Yi hakuri anfito dashi ba.
nabarshi a staff quarter's Inna koma zan dauko miki Insha Allah" take kuma se
fuskana tayi wasai cikeda farin ciki nace "Nagode" daganan kuma semuka koma hiran
su Umma da visiting din jiya inda acikin conversation din namu nema na tuna da
kalmar *Suruka* aikuwa cikin sauri senace "Yauwa Yaya Lamido nikam miye ma'anar
suruka?" tsayawa yayi yana kallona nadan wasu dakiku kafin yace "waya fada miki
kalmar?" Innocently nashiga bashi labarin yanda mukayi dasu Yaya Jidda da abunda
Umma tace kafin daga karshe nasake cewa "Kafadamin meaning din"...
Yana murmushi yace "Zan fada miki anma bayau ba" cikeda mamaki nace "miyasa?" Yaya
Lamido yace "just don't ask me why Nanaaa... Kede nace zanfada miki wataran insha
Allah" senayi pouting bakina nace "toh seyaushe kenan zaka fada min?" Yaya Lamido
yace "I can't tell you the exact time either,just promise me bazaki tambayi kowaba
harsai kinjira ranar dazan fada Miki dakaina" gyadamasakai nayi Ina mamakin menene
ma anar kalmar haka dahar aketa boyeta anmadai koma minene I'll do as he says.
Ranar banshiga dinning ba haka mukayita hira dashi,seda lokacin night prep yayi
sannan yatafi staff quarter's nikuma nawuce aji akan zamu hadu after night prep
yabani tsarabana.
***
Bangaren Umma kuwa tun saura sati biyu visiting daman Lamido yadameta da maganar
taje taga Rukayya yarinyar has been yearning to meet her,alokacin cemasa tayi a'a
anma seya tuna Mata da alkawarin datayi nacewa wataran zataje taganta shekarun baya
dasuka wuce yakuma nuna Mata yanda Rukayya ta daukaki alkawarin,yabata labarin
halin da Rukayya take ciki agidan kawunanta filla fillah yakuma nuna mata how much
it means to Rukayyan tasamu soyayyar uwa daga Umman. Umma har hawaye seda tayi
tawaya da lamidon yabata labarin and from that very moment setaji wani irin
tausayin yarinyar yashigeta sosai,setake tambayar kanta shin miyasa wasu mutanen
basuda Imani ne kwata kwata?ita ai Bata taba tsanmanin abun haryakai hakaba danhaka
seta yarda zatazo taga Rukayya and datazo taga Rukayyan setaga so many things are
missing in her life,she might not say it out but her eyes dayanda tadinga yin
abubuwa yasa tagane cewa tabbas Rukayyan nacikin hali na rashin kulawa. Inba rashin
mafadi ba,inba rashin dangi masu sonka ba yaushe har wasu bare dabakasan su
ba,bakataba sanin inda muhallinsu yakeba kakarbe su hannu bibbiyu kamar naka?
yaushe har zaka dauki wani namiji daban dabaku hada dangin iya bare na Baba kamaida
shi wanka kuma babu Wanda yataba kwabarka akan hakan and you never feel it's wrong
to do that....
Setaji tana tausayin yarinyar,setaji tana son taimakon ta dankuwa she's a pure soul
datake Karbar soyayyar mutane batareda tayi tunanin koya intention dinsu
yakeba,itakawai tayarda suna sonta for real sabida kawai tana tsananin bukatar irin
wannan kulawar. Irin Rukayya ne yanzu in Lamidonta ba mutumin kirki bane seyayi
taking advantage dinta harsu saba yayi seducing dinsu into doing something bad
bayan tagama yarda dashi....toh anma alhamdulillahi tunda tafado hannu
nagari,tafado hannunda za'abata soyayyar datake nema din batareda annemi wani Abu
in return ba,sedema asota don Allah,sabida humanity dasanin darajar dan Adam. Umma
setaji she want to fully make her Daughter bawai a fadan baki kawai ba,bawai ya
tsaya a tsakanin su kadai ba kowa ma ya shaida. Kowama ya shaida daga ita har
Lamidon sunada right akan ita yarinyar shiyasa tana Isa gida takira Lamido adaren
tace sati mezuwa yazo gida yasameta akwai maganar datakesonyi. Magana akan solution
dinda take ganin shine kadai zai cire Rukayya daga cikin kangin datake ciki.....
***
Satin daya zagayo Lamido yatafi Gombe kamar yanda Umman ta umarce shi dayi kuma
dayake daman shima tunda yadawo Rukayya tayi masa maganar da tayi da kannen nasa
seyaji shima yanason yaje gidan yayi addressing dinsu akan miyasa zasuyi using irin
wannan kalmar ga Rukayya? What if ace tasan ma'anar kalmar how would she have
reacted? Shikanshi bazai iya dukaken matakin da Rukayyan zata dauka ba but one
thing is for sure, she's still young,she can act anyhow dazai iya ruining tsakanin
sa da'ita wanda tsoron hakan yasa bayason tasan manufarsa akanta yanzu, yafison
seta Kara girma,yafison se ita dakanta tagane cewa relationship dinsu is boyond
that of a brother and a sister dakanta sannan ya tunkareta da maganar alokacin
dayake da tabbacin zatayi amanna dashi takuma yi understanding dinsa,takuma zabi
abunda zuciyar ta da gangan jikinta keso.
Ayanzu duk maihankali inyaga irin alakarsa da Rukayya dole zaisan akwai soyayya mai
tsafta a tsakaninsu dankuwa hardayawa daga cikin abokanansa Malamai dasuka Sansa da
Rukayya sukanyi masa tambayar nan and he never hide anything,he go straight to
point yace musu "Eh yanason Rukayya, soyayyar aure bayan na Yan uwan taka dayakeyi
mata and he's hoping to have a future with her even though itan batasani ba
haryanzu"....
Wuraren shadaya da rabi na safe Lamido ya Isa gida dayake tafiyar safe yayi bana
yanmaba
Umma kadai yasamu a gida zaune parlour tana kallon wani Hausa film dayake yasamu
akwai wutan lantarki ayayinda gabadaya kannen nasa kuma duk suna islamiyar safe
basukai ga dawowa ba,daman se shabiyu ake tashi in akafara tun karfe takwas na
safe. Anan parlournsu yayada zango ko dakin shi baishigaba inda suka hau hira da
Umman.
Suna cikin hirar ne su Basma suka dawo daga islamiya.
Da fara'a suka karaso parlourn sukagaida Lamido dasuka ganshi sunayi mishi ya hanya
duk ya amsa. Basma ce tafara nufan hanyar dakinsu daniyar taje tacire kayanta
seyayi sauri yatsaidata yace "Basma dawonan" dawowa Basma tayi tana mamakin yanayin
tune dinda Lamidon yayi magana sannan tace "Gani Yaya Lamido" nuna mata kasa kusa
dashi yayi sannan yace "Zo zauna anan" Zama tayi kamar yanda yace din,Jidda da
Salman ma duk seyace suzo suzauna agefen Basman. Seda suka zauna suka nutsu sannan
yadubesu calmly yace "what was the meaning of abubuwan dakukaje kuna fada agaban
Nanaaa ranar visiting?" Basma ne tayi sauri ta kalleshi tace "Me mukace kuma Yaya
lamido?" danharga Allah ita tadauka ma wani laifin sukayi daban but as far as she
should remember basu fadama Rukayya kalma koda guda daya dazata batama Rukayyan
raiba. And why will they even use harsh words on her bayan she's the most innocent
and sweetest girl they've ever known" batareda Lamido ya tsaya wani boye boyeba
yace "maganar suruka thing dakuka je kunayi Mata. Meya kawo wannan maganar? Why
will you use that word?" se Basma tayi dariya tace "Wai dama Maganar surukantakar
damukayi kake nufi?" harara Lamido ya watsa ma Basma ganin batadau maganar serious
ba sannan yace "watoma abun ma dariya yakoma koh?" Still Basma na dariya tace "Toh
Yaya Lamido mufah duk cikin wasa mukayi maganar nan bada wata manufa ba" Lamido
yace "karyane!" Basma dake dariya har lokacin tace "toh karya mukayine Yaya?
ninasan ko ba dade koba miji Rukayya ce zata zama surukar mu insha Allah" Lamido
yace "koma dai menene wannan kuma ba hurumin ku bane yanzu,seku Bari intazama
surukar taku kufara irin wannan zancen da'ita" Basma ganin dagaske Yayan nasu yadau
zafi setace "toh kayi hakuri Yaya Lamido insha Allahu baza'a sakeba" Lamido yace
"Better" Jidda dake jinsu tundazu seta tabe baki tace "Ainima seda nayi musu magana
akan subari Yaya Lamido. Daga taimakon yarinya se awani fara lakaba maka ita anace
mata surukarmu" Basma tsaki tasaki Jin abunda jiddan tace sannan tadubeta tace "Toh
ai yanzun ma bakiji yace bayason auren Rukayyan ba kuma Jidda bari kiji,dukda boye
boyen dakukeyi dagake har Yaya Lamidon dakuma ita Maimunatun babu abunda bansaniba.
Kuma nasan dalilin dayasa kike kin karban gaskiya gameda alakar Rukayya da Yaya
Lamido. kinayin hakan ne sabida kina ganin kamar in Yaya Lamido yazabi Rukayya sama
da Maimunatu yacuceta and you'll be held responsible sabida ke kika hada su anma
abunda bakisani ba anan shine daga ke har Yayan naki yaudararku Maimunatu
takeyi,Maimunatu bazata taba auren Yaya Lamido ba sabida anriga anyi mata
miji,auren hadin gida za ayi Mata dawani cousin Brother dinta dukdama tana boyewa
sabida ku karkuji anma nasamu labari gurin kawayenmu. January za'ayi auren insha
Allah dukda ba'asaka specific date ba" Baki sake Jidda tace "kamar Yaya?" Basma
tashi tayi daga zaunen datake tana Yar dariya sannan tace "kamar yanda kikaji nace
so inzaki sa ranki a ruwan sanyi kikarbi abunda zaiyuyu gwanda ma kiyi dan nasan
shikanshi Yaya lamidon yasan aurensa da Maimunatu abune me kamar wuya" daganan
Basma tayi shigewarta ciki bayan tasaci kallon Yayan nata......
Kallon Lamido da fuskarsa is expressionless Jidda tayi nadan dakiku kafin tatashi
tabi bayan Basman akafule tana kwala kiran sunanta dan Allah yagani takasa yarda da
abunda Basman tafada...
Lamido kuwa even though maganar Basman baizo masa abazataba danyasan babu yanda
za'ayi all this while batasan suna da alaka da Maimunatu ba, infact atunaninshi da
shekaru sukaja Maimunatun zatafada ma Basma din kuma koda Basman bata taba nuna
masa tasan meke tsakaninsa da Maimunatu ba baiyi tunanin sabida Maimunatu bata fada
mata baneba yyi tunanin sabida shibai fada Mata bane shiyasa bata tada maganar ba
anma the fact yau tafito tace Maimunatun ma boyemata takeyi suna tareda Lamidon
haryau has shocked him to the core and what shock him even more is maganar aurenta
wai January. Wata hudu agaba fah kenan yanzu. Kuma Maimunatu has never for once
feel it was right tace zata fada masa. Yes Dan Maimunatu bata aureshiba ba matsala
baneba,dan Maimunatu zata auri wani akan ra'ayinta is a relief cewa shibai
yaudareta ba anma for some reason he felt heartbroken,he felt heartbroken for kin
fada Masa datayi,for cigaba da wasting time dinshi da takeyi bayan Kuma tasan aure
zatayi. Ina laifi danta fada mishi?ai ko wishing dinta well yayi sekuma sucigaba da
zumunci but by keeping and hiding things from him hakan yarage Mata kima da
darajarta a idanunsa.... Kuma har yaushe take tunanin zata boye mishi? Badai tana
nufin sede yaji labarin aurenta kawai ba?
Tashi yayi daga zaunen dayake daniyar yatafi daki because awannan lokacin jiyayi
bayida bukatan komai daya wuce yaganshi a daki shikadai. Anma sede Umma da abun
yafaru akan idanunta she's not willing to let him go just now sabida tanason Karin
bayani Itama. tanason Jin miye ra'ayin dan nata dankuwa wannan shine dalilin dayasa
tace yazo gida yasameta tun asali.
Ahankali tace "Lamido Ina zakaje?" ganin yatashi zaibar parlourn.
Juyowa Lamido yayi ahankali shi se alokacin ma yatuna da ita a parlourn kuma wai
agaban ta komai yafaru,ahankali yace "Daki zanje indan kwanta Umma" Umma setace
"Dawo kazauna muyi magana tukunnan" Lamido kamar yace "Umma kibari anjima muyi
magana" anma bazai iya yimata musuba danhaka seyakoma yazauna kamar yanda tace
yayidin.
Wani nannauyar ajiyar zuciya Umman tasaki tana kallon Lamido sannan tace "Naji
kamar su Basma na zancen Maimunatu,Wai wace Maimunatu ne?" Ahankali Lamido yace
"Kawar Basma Umma" da mamaki Umma tace "Daman haryanzu kana tareda yarinyar nan?"
danda jimawa tasan da alakar tasu anma tayi tunanin tunbayau ba suka rabu,soyayyar
yarinta ce kawai.
Lamido dukda yana mamakin ya akayi Umman tasani seya boye mamakin nasa araunane
yace "Umma yanzukam everything is over ai tunda zatayi aure" Umma tace "Dadai
yafikam" sekuma tamishi kallon tuhuma tace "Ita kuma Rukayya daman amatsayin me ka
ajiyeta atsahon shekarunnan dakake tareda Maimunatun?" dagowa dasauri Lamido yayi
yakalli Umma Jin abunda tace din sannan yace "Na'am Umma?" dankuwa baigane inda
maganar tata tadosa ba. Umma tace "tambayarka nake miye matsayin Rukayya agurinka?
daman can ba Sonta kakeyiba duk cikin taimako da tausayine kawai abubuwan dakakeyi
mata?" girgizakai Lamido yashigayi sannan yace "That's not the only reason Umma. I
love Rukayya and I'm willing to make her mine insha Allah" Umma seta tabe baki tace
"kaida Maimunatun yaudarar juna kukayi tayi kenan?" Lamido yace "bahaka bane Umma"
Umma tace "Komadai menene yanzu an ajiye maganar Maimunatu agefe. What are your
plans gameda Rukayya?" Lamido yace "Aurenta zanyi indai kin amince Umma" Umma tace
"Yaushe?" Lamido seyadan Sosa sumar kansan nervously yace "Umma kema kinsan seta
gama karatu ai" cikin sauri Umma tace "wani karatun? Secondary ko jami'a?" Lamido
yace "secondary,intagama secondary zanmata maganar aurenmu inyaso tacigaba da
karatun ta agida na"......
Se Umma tace "wannan kuma ba shawara bace Lamido. Bakace wahala takesha gidan Kawun
taba?" gyadakai Lamido yayi,se Umman tace "Toh nidai aganina indai kanasonta
dagaske kana kuma son taimakonta baikamata ace abari harzuwa wancan lokacin ba.
tunda kasanar dani labarin Rukayya dallah dallah damukayi waya dakai satin dazamuje
visiting naji tausayin yarinyar yashigeni sosai,ada dakake fadamin sama sama
bandauka abun yakai har haka ba seda mukayi magana ranar and from that very day
naji inason ganinta,naji inason taimakonta and danaje visit naganta ananne nagane
how innocent and sweet she's,ananne nagane she's a lonely child that need
love,comfort and peace....."
"Yanda ta rungumeni ranar visiting dayanda tadinga farin ciki yasa nagane she's
lonely and it's the happiness of having a family datayi lacking muka bata ranar
wanda hakan yasa takasa boye farin cikinta,takasa boye maitarta a fili" Umma tace
"Tunbayau ba nasan kanason Rukayya Lamido anma ita zaman awanni kawai nayi da'ita
nagane cewa itadin batasn irin soyayyar datakeyi makaba,tadaukeka ne amatsayin
Uba,uwa,aboki dakuma wanda she can always rely on,tadauki family dinka amatsayin
nata kamar yanda kace mata tayi and she's sincerely doing that. Nikaina zanso
Rukayya tagama karatu kafin azo ga maganar aurenku tunda kaima you're not stable
toh Amma inason inrike Rukayya, inason incireta daga kumcin rayuwar datake ciki
agidan Kawun ta kuma indai zanyi hakan dole tahanya dayane,tahanyar kai kanemi
aurenta yanzu ne" Lamido besan sanda yadaga yakalli Umma ido budeba.
Umma ta jinjina masakai tace "Eh auren Rukayya nikeson kanema" dukda yaji dadin
amincewar Ummin dakuma nuna son Rukayya a fili seyace "Tayaya Umma?" dankuwa yasan
abune mekamar wuya abashi auren Rukayya a kankantar shekaruntan nan and moreover
bayason ya zamantoh yashiga hakkin Rukayya,komi zaiyi yafiso yayishi da izinin ta
dakuma yardarta. Umma da tambayar tasa tayi mata kamar ta rainin wayau tace "Ta Ina
ake neman aure? Dan murmushi yayi sannan yashiga shafa suman kansa yace "Umma Ina
nufin ba lallai abani aurenta haka kawaiba! she's still young zasu iyacewa abari
setagama makaranta and moreover Rukayya batasan Ina sonta ba,kallon Yaya kawai
takeyi min toh yau innaje nanemi aurenta dawani idanu Zan dubeta?"..
Umma tace "Babu Mai katse Mata karatun ta ananma zatayi karatunta kamar yanda
kannenka dakai kanka kukeyi. dandai mutum daya kamar Rukayya kam nidakai bazamu
gagara riketa ba. batun batasani ba kuma seka sanar da'ita,kayimata bayanin dayasa
kakeson aurenta,knuna mata kanason tsamo ta daga wahalar wannan gidan ne. She'll
surely accept you koda bata karbe ka ta sigar soyayya ba. Yarinya ce datake neman
rangwame da sauki bana tunanin zataki amincewa kuma da ace tunbayau ba nasan da
asalin abunda yarinyar nan ke going through da matakin dazamu dauka kenan" Lamido
yace "Umma bakisan wacece Rukayya ba kenan" Umma tace "Komadai menene ninagama
magana na. Indai taimakon Rukayya kakeson yi then go straight to the point kayi shi
tun yanzu inkuma bahaka ba kafita a rayuwarta kadawo gida kakama harkokin gabanka
danbazai yuyu kaje kana kula yarinyar mutane a boye kana claiming ita Kanwarka
bane batareda marikan ta sunsaniba" Lamido yace "Umma dangin mahaifiyar ta sunsanni
fah" Umma tace "Anma ai na mahaifin ta basusanka ba bayan kuma a hannunsu take
dazama" gyadakai Lamido yayi cikeda gamsuwa.
Umma tace "When you want to build a relationship with someone be open in and out!
Karka tsaya kana boye boye so far as your intentions are clear because anything can
happen Lamido. You might have your reasons for doing that anma in abu yazo ya kwabe
ba lallai mutane su tsaya sauraran uzurinka ko su fahimce ka ba" jinjinakai Lamido
yayi yace "Hakane Umma the reason why I'm holding back is because Rukayya bataso
asani. Ita tasani yimata alkawarin bazan fada ma kowaba shiyasa nayi deciding yin
shiru harzuwa lokacin dazata gama karatu in aureta indauketa agida. Umma Nataba
attempting Zan fada ma maternal grandmother dinta tahana batun zuwa gidan kuwa
konaje bazasu barni inshiga inga itakanta Rukayyan bare har azo ga batun kawunta
yasanni" Umma rai bace tace "Yanzu kai fisabilillahi Lamido se abunda Rukayya tace
kayi zakayi? Ashema ba taimakon nata kakeson yiba indai ra'ayinta zakabi. Rukayya
yarinyar ce data taso da tsoron mutanen nan aranta dole daman inkace zaka fada ta
hanaka sabida tana tsoron miye zaije yadawo,sabida tana tsoron kilan da'ita zai
kwabe a karshe so kama bar maganar bin ra'ayinta indai taimakon ta kake da niyar
yi. maganar ajira tagama makaranta ma duk ba hujja bace Lamido,kasan wani irin hali
mutanen gidannan zasu jefata Nanda shekara ukun inta cigaba dazama tareda su?
Yarinya da kankantar shekaruntan batasan miye dadin rayuwa ba?" Umma tadan numfasa
tace "Nabaka nanda zuwa lokacin hutun makaranta megabadaya na term dinnan kasamu
Rukayya ku daidaita a tsakanin ku inyaso in anzo hutu se mu tura iyayen ka suje
suga nata iyayen ayi tambaya ahada auren ka dana Basma dankasan Itama yaron yanata
so yaturo iyayensa itanema take tsaida shi,inma sun nuna karatu takeyi bazai yuyu
ba se a fito afada musu halin da yarinya take ciki inshi Kawun nata zaitsaya akan
iyalansa toh fine seka bari Inta gama karatun inkuma bazai tsaya ba yabaka auren ta
muda mukasan darajar Dan Adam muka kuma damu zamu kula da'ita insha Allahu"
"Inma shibai bada hadin kaiba akwai sauran Yan uwan iyayenta dasuke kauye Kuma kosu
sukaji labarin abunda sukeyi mata acan gidan nashi inma basu baka aurenta ba toh
zasu dau mataki"
*Ayimin afuwa bancika alkawari ba jiya*😰
Littafin Qadr na kudine duk maiso should talk to me privately on WhatsApp for
payment details.
08147722806.
*Page Fifty Two*
Lamido jinjinakai yayi Jin bayanan Umman sannan yace "Hakane" Umma tace "tashi
kashiga ka huta Allah ubangiji yazabi abunda yafi alkhairi" "Amin" shine kawai
kalmar da lamidon ya'iya furtawa kafin yatashi yanufi dakinshi yana kissima
maganganun Umman nashi aranshi daya bayan daya. Tabbas yasan gaskiya tafada and
he'll be more than happy in aka bashi auren Rukayya tabar gidan Kawun ta tazo tana
rayuwa dasu anan toh anma matsalar tayaya zai tunkari Rukayyan dawannan maganar?
will she be angry with him?will she accept him easily batareda takai shekarunda
tasan miye ma'anar soyayya ba?" Wandannan sune abubuwan dasuka dinda damun ransa
baki adaya ranar.
Maimunatu kuwa kiranshi tadingayi awaya tanason taji ya ya iso gida ganin cewa
shibai kirataba anma sede babu daya daga cikin calls dinta daya daga.
Daga karshe Basma takira taceda ita tanason magana da Jidda,tabe baki Basman tayi
don ko ba afada mataba tasan maganar Lamido zasuyi. Mikama jiddan wayar tayi wanda
Jiddan dafari kin karba tayi dan'ita hat tajona layin yan fushi da Maimunatun kamar
yanda Lamidon ma yakeyi. haushi takeji akan miyasa Maimunatun tayaudaresu itada
Yayanta bayan tagama basu full trust dinta,harsaida Basma ta takurama jiddan
tahanyar yimata Ido sannan takarba tana kunkuni. Daga daya bangaren Maimunatu tace
"Jidda yakike?" Jidda tace "Lafiya Lau" Adan dake wanda hakan yasa jikin Maimunatun
yin sanyi dankuwa tasan bahaka Jidda tasaba amsa mataba,da on Normal circumstances
nema ita zata fara gaidata....
Maimunatun seta daure tace "Bakida lafiya ne?" Jidda tace "Lafiyata kalau. Mekika
gani?" Maimunatu dukda taji amsar jiddan banbarakwai sets daure tace "Naji muryarki
wani iri" Jidda tace "Ayyah I'm fine" wanda wadannan kalaman susuka sake sa
Maimunatu tabbatar wa ba lafiya ba,dole laifi tama Lamido kuma koma wani irin
laifine jiddan tasani shiyasa take fushi da'ita itama.
Setace "Daman tambayarki zanyi Koh Yaya lamido yadawo? Inata Kiran layinshi baya
picking" Jidda atakaice tace "Yadawo" Maimunatu tace "toshikenan thank you kilan
yana bacci ne shiyasa baiyi picking ba" Jidda tace "may be" sekuma Maimunatu tayi
mata sallama ganin bata samu fuskar dama zata iya neman taimakon tahada ta dashi
tawayaba...
Jidda tsuka tasaki bayan sungama wayar sannan tayi wulli da wayar tana fadin
"wallahi Yaya Basma dandai kince inyimata shiru ne dasaina amayar mata dana cikina
yau" Basma tace "kidaiyi hakuri shida akama abun yadau mataki. Yanzu seke kidau
zafi shibai daukaba yamaje susha soyayyarsu kisha kunya" Jidda wani kallo tama
Basma sannan tace "Cabdi.... Yaya Lamidon? Wallahi ninasan yagama da Aunty
Maimunatu kenan har abada. Kokin manta shi mutum ne dayatsani karya,yatsani aboye
masa abu no matter how little it's barekuma maganar aure da bana wasa ba"
jinjinakai Basma tayi cikeda gamsuwa sannan tace "Hakane Kuma. Allah dai yasa
yakyaletan" Jidda tace "Amin. Aiko bai kyaleta ba mu zamu zugashi" dariya Basma
tasaki sannan tace "kintashi a Team Maimunatu kenan" Jidda yar dariyar tasaki
sannan tace "Daman can dinma kaddara ne yabarni acan"...
Girgizakai Basma tashigayi in desbelief tana fadin "Bakida dama wallahi Jidda".
Haka Maimunatu tacigaba da kiran Lamido babu kakkautawa ganin batada wani mafita
daya wuce wannan,Lamido dafari yayi niyar shareta ne kawai harta gaji takyaleshi
anma ganin taki barin kiran nashi yasa yagane baza fa takyaleshin ba inba nuna mata
yayi yasan komaiba and moreover shiba ita baneba,he can't just be out of her life
without unspoken words,bayason yayi holding grudge,abunda akayi zaifito yafada
baiji dadinsaba.
Danhaka dakanshi seya kirata da dare,ko ringing din farko begama ba tadaga call din
kamar wanda daman jiran kiran nasa takeyi.
Hankali tashe tace "Wai Ina ka shigane Yaya lamido? I've been trying to call you
baka picking" batareda ya amsa tambayarta ba yace "Are you home?" jiki sanyaye tace
"Eh" yace "Then I'm coming tonight. Akwai maganar dazamuyi" daganan baijira
cewartaba ya katse call din ya wullar da'ita agefe.....
Ana idar da sallar isha'i ya yada zango akofar gidansu Maimunatu. yaukam agaban
gidansu ma yatsaya bakamar da datakece mishi suje bayan layinsu ba sabida kada
agansu agida ayimata fada ace tacika fita hira,shigabadaya seyau ma yagane ashe
hakan datakeyi din dukdan kada ayi mata fada agidane tana kula wani bayan anbada
ita kokuma dan kada wani yaganshi yafesa masa labarin daga baya. Shi kwata kwata be
taba fassara abunba dayake tun farkon fara soyayyar tasu haka sukeyi wanda adadin
sunayin hakan ne sabida sunyi kankanta alokacin anma yanzu fah? Shibai taba
tambayar kansa miyasa basu canza dabi'a ba bayan shekaru sunja kuma yanzu lokacin
sune seyau daya tsinci kansa a kofar gidan nasu komai yake dawo masa cikin
kwanyarsa yana bashi explanation dede da tambayar sa. Da hijabi tafito as usual
kamar kullum hakanan tadanyi simple makeup daya kayata fuskarta,Maimunatu kyakyawar
budurwace da babu abunda tarasa a irin suffoffin da akeson mace maikyau ta kasance
tanada shi. Bakaramin mamakin ganinshi a kofar gidan tayiba danyawanci inyazo can
yake wucewa direct itakuma taje can tasameshi.
Ahankali takarasa inda yake tsaye tace "Ina wuni Yaya lamido?" Lamido yace "lafiya
Lau" Maimunatu setadanyi murmushi tace "yau yanaga katsaya anan? Ko kewana kakeyi
dayawa dabazaka iya jira har in isoba?" tayi maganar cikin sigar tsokana dukda kuwa
tasan ba lokacin tsokanar bane yanzu.
Murmushin yake Lamido yasaki sannan yace "A'a kodaya. nanma ya Isa,yau anan nakeson
muyi hirar" nervously Maimunatu tace "Kaman ta dalilin mu na rashin tsayuwa ananne
wai?" dankuwa Allah yagani tsoro takeji wani agidansu yazo yaganta
taredashi,barinma *Yaya khalipha(mijin dazata aura,cousin Brother dinta)* da takeda
tabbacin yana iya zuwa kowani lokaci daga yanzu tunda yana gari. Lamido yace
"Ganinayi mungirma,shekaru sunja so our relationship should be uplifted too. We
can't keep going like this,doledai inson juna muke tsakani da Allah iyaye ma susan
da alakar mu" take se jikin Maimunatun yafara trembling...
Duk kuma Lamidon na lura da yanayinta,yace "koya kika gani?" ahankali Maimunatu
tace "Ina ganin kabari seka samu aiki kafara zama stable tukunnan mufara kai wannan
gandun" wannan karan murmushin takaici Lamido yasaki,wato bazata fito tafada masa
gaskiya ba, she'd rather continue giving him false hope? She'd rathe continue lying
to him and leave him heartbroken in the end" Araunane yace "Atunanina badole sai
ansamu aiki akefara neman aureba Maimunatu and besides baturowa gidan ku
zanyiba,adai dinga ganina asan da zamana yana da amfani wanda wannan dinne kadai
zai nuna seriousness dina akanki yazamanto bawai yaudaran juna kawai mukeyiba"
Yadan numfasa sannan yace "Nibanga amfani kin barina Ina zuwa kofar gidanku hiraba
ayanda nike yanzunnan tunda son tsakani da Allah mukewa junan mu. Sede indama can
ba aurena ke kikeson yiba,sede indama can kinada wanda kikeso kunyi alkawarin aure
dashine" Lamido yayi maganar cikin tune dinda ke nuna karaya.
wannan ran Maimunatu kuka tafashe da,kukan da itakanta tarasa na farin cikine kona
bakin ciki,wai yau for the very first time Lamido yanuna yanason aurenta,yanuna
yanason relationship dinsu tayi gaba kamar na kowani irin masoya anmu kuma sede
itakanta tasan he's late,he's too late dankuwa baifito yafada alokacin da take
tsananin bukatar irin wadannan kalaman daga gareshiba. Lokaci guda se taji bazata
iya cigaba dayi masa karyaba,cikin rawar murya tace "Kayi hakuri don Allah" Lamido
jiki sanyaye yace "it means my assumptions are right?" girgizamasakai Maimunatu
tashigayi cikin sauri sannan tace "bahaka baneba" Lamido yace "toh menene?" Cikin
kuka Maimunatu tace "Ina sonka wallahi... Kuma kana daya daga cikin mutanen dabazan
taba mantawa a rayuwa naba koda kuwa awani hali na tsinci kaina hakanan mutuncinka
da kimarka bazai taba gushewa a idanuna ba. Banki ace kazama mahadin Rayuwanaba
Yaya Lamido anma sede dagani harkai bamu taba irin wannan maganarba,dagani harkai
mundauki soyayyar mun bata wani ma'ana daban ne dukdani u wanted it further anma
amatsayina na mace senake ganin kamar baikamata infara yimaka maganar aureba bayan
kai baka taba yimin ba,na biyu tsawon shekarunnan karatu kakeyi baka ma gama ba
bare ayi batun samun aikinka harma ka iya rike Mata while on the other hand kuma ni
macece,iyayena sun matsamin da maganar infidda miji tunbayauba wanda hakan yasani
fara kula wasu tunda banida tabbacin inda nawa da naka alakar suka dosa. Acikin
wadanda nike kulawan ne Yaya Khalipha yakwanta min arai kuma yanada duk wasu
qualities da kowace mace zata so ace Mijinta yanadashi arayuwa. Innace maka Banason
Yaya Khalipha nayi maka karya Yaya Lamido dankuwa zuciya tanason me kyautata matane
kumani babu abunda yarageni dashi kamar yanda kaima baka rageni da komaiba. We've
been dating for two years with him kuma tun farkon fara soyayyar mu yaso yaturo
gida anma nadinga delaying abun with the hope cewa wataran zakayi hobbasa,wataran
zaka fara yimin maganar auren mu harma insamu courage din iya rejecting wanda
yakeyi dagaske anma har rana maikaman tayau bakayimin ba wanda hakan yasa nabama
Yaya Khalipha dama yaturo gida kuma yanzu har ansaka ranar auren mu dashi, January
za ayi insha Allah" Maimunatu tadago a raunane takalli Lamido da idanunsa suka
canza launi tace "Nasan bankyautaba na yaudareka,nasan bankyautaba naqi insanar
dakai anbadani inacigaba da kulaka despite knowing that but believe I'm feeling
guilty from within, tsoron kada kayi misunderstanding dina yasa naki nafada maka
even though bawai inada niyar boyemakan bane har abada, I'm just trying to install
some courage and moreover I'll miss you,rabuwa dakai will not be easy for me
shiyasa zuciyata takasa aiwatar dakomai! Don Allah kayafemin" Maimunatu tayi
maganar tana kuka maitsuma zuciya, Lamido duk seyaji jikinsa yayi sanyi,dukseyaji
wani haushinta dayakeji yaragu because he can understand her pain,he can understand
what she's going through and moreover shima da nashi aciki,he never make an effort
which was why she's holding back too ..
Ahankali yace "kidaina kuka don Allah" batareda tabar kukan ba takumacewa "I'm
sorry please...." Lamido yace "Yawuce... Kidaina kukan hakanan don Allah" dankuwa
in akwai abunda yatsana a rayuwarsa toh yaga mace tana kuka. Sa hannu Maimunatu
tayi tashiga goge hawayenta hartagama duk Lamido na kallonta.
Seda Lamido yaga tadaidaita kanta dakyau sannan yace "mucigaba da maganar ananne
komu koma can?" ahankali Maimunatu tace "mujecan anytime Yaya Khalipha na iya zuwa"
gyadamatakai yayi ahankali sannan yajuya yafara tafiya inda tayi sauri ta Isa inda
yake suka shiga jerawa tare ahankali batareda kowa yace da dan uwansa wani abuba
ahaka harsuka Isa inda suka saba hira acan bayan layinsu Maimunatun kan wani
dakali. Zama sukayi dukansu sannan Lamido yace "Naji bayanan ki and I understand
you Maimunatu. anma sede inason kisan cewa you've hurt my feelings by hiding things
from me, Atunanina nidake munzama abu daya,Atunanina bamuda abunda zamu boyema juna
amma still Kika boyemin maganar aurenki,sede naji labari awaje which is the worst