Sashe 27
Narjeesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Hahhhh😂🤣 Narjeesah team kun fa sakani dariya, a page biyu, 36/40 41/45, haba dai har kun manta cewar mutuniyar taku, irin gidan da ta fito gidan mata huɗu gidan makirci? Tafa san ta kan kishi da iya zaman da mutane, kuma, cikin Shuraim shine ya saka ta, ta dawo wata irin shiru_shiru da ita, amman kowa yasan Narjeesah bata dama, haka Amrah, dan haka nasan yan zun kun gane dalilin da yasa, sukayi, acting ta maida Sunan ta NARSAL*
*Ina godiya sosai da Comment ɗin ku da sharhin ku, kuma ina ƙara godiya da addu'ar ku, sosai*
4️⃣6️⃣⏯️5️⃣0️⃣
➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Tafe muke a cikin motar Yaya Aliyu Hindu na gefen sa, nida Amrah da Shuraim muna a baya, kowa ka kalli fuskar sa, a cikin farin ciki yake.
Yaya Jafar kuma shine ke driving Humaira tana gefen sa, Baban mu da Umma da Nusaiba suna baya, kowa yana cike da farin ciki idan ka kalli fuskar sa, amman Baban mu ba zaka gane wane yanayin yake a ciki ba.
Shuraim sai surutu yakeyi, yana faɗar, "yeeee! Mun hau mota zamuje yawo, Uncle ka siya mani giwa da zaki inyi wasa dasu, mu shiga ta cikin wannan jejin muyi ta faɗa, da... Da... Dami ma ake ce masa Anty? "
Dariya mukeyi, Yaya Aliyu ya ce, "nikam ba zan iya siya maka giwa da zaki ba, amman inda kace, na siya maka doki ka hau zan iya kayi ta su guda" da dariya ya ƙarasa zancen.
Haɗe rai Shuraim yayi Hindu ta, juyo tana dariya tana kallon Shuraim ta ce, "kada kayi fushi nawan bari na anshi wayar sa na kira maka Daddyn ka, nasan shi zai siya maka su, ko? ".
Kwallar idon sa ya goge ya gyaɗa mata kai, Yaya Aliyu ya ce, "kai my boy badai kuka kake yi ba, to yi hakuri da wasa nakeyi maka, zan siya maka duk abunda kake so, kaji yaro na? ".
Maƙe kafaɗar sa yayi, mukam dariya mukeyi masu, Hindu ce, ta ɗauki wayar Yaya Aliyu ta kira number Daddyn Shuraim, ai kuwa ringing biyu, ya ɗaga suka gai sa, take sanar dashi Shuraim ke magana, ya ce, da ita "bashi wayar ki saka mashi Hans free".
Hans free ta saka mashi, ta bashi wayar, shi kuwa ya amsa, yayi kwanciyar sa, a jiki na, ya fara faɗar, "Daddy ina kwana? " dariya ya yi yace, "lafiya lau my lovely son, ka tashi lafiya ya Umma na, dafatan ta tashi lafiya da Baban mu da su Amrah da waye ma? ".
Dariya Shuraim yayi yace, "lafiya lau Daddy baka ce, da Mommy na ba, kuma muna cikin mota zamuje wani gurin, kana zuwa muzo mu tafi da kai ko? ".
Shima dariyar yayi, ya ce, "Shuraim ai Mommyn ka bata son tafiya fani, kaga bata sanar dani ba, ko? Amman zan zo yaro na dami kake son na zo maka dashi ne? "
Cikin sauri Shuraim ya ce, "Daddy zaki da giwa, da doki mai tashi sama"
Ai kuwa kowa ya saka masa dariya shi kuwa Salman ɗin ya ce, "to kai kuwa yaro na a ina ne, zaka ɗaure giwa da zakin ka kuwa san Mommyn ka tsoron su takeji ko? Kuma gashi har doki mai tashi sama, ina fatan dai zaka hau dokin".
Cike da jin haushin su, na ce, "ai da yake shi mutum baya tsoron zakin dolene a cikawa mutane baki, kuma kada a sake sakoni a cikin shirmen ku ehe! ".
Dariya yakeyi ta cikin wayar, haka su Amrah, Shuraim ne ya ce, "Daddy ka kawo mani mage ƙarama mai kyau ".
Da sauri na ɓalla masa harara, na ce, ki nemi gidan uban da zai kai maka ita, ku ajiye, kai wallahi kun fa fara cika ni, zan baku mamaki, idan baku fita hanya taba".
Yaya Aliyu ne, ya ce, "to ke Narjeesh wannan faɗan kuwa, kamar yana a gaban ki, firar suce sukeyi a tsanin ɗa da mahaifin sa, sai kuma kiji haushin su? "
Ni kuwa na ce, "to baka jin sune suke sako suna na a cikin zan cen su? To kayi masu magana mana su dai sakani a harkar su, ehe! "
Dariya sukayi shi kam firar shirmen su sukeyi kuma duk abunda nake faɗa, a kunnen sa, ne yaƙi magana sai ma cewa yayi, "Shuraim ka kirani da wayar Mommy ka yan zun sai muyi firar mu ko? Ka baiwa Uncle wayar sa kaji yaron kirki? ".
Dariya yayi ya baiwa Hindu wayar ta kashe suna dariya, kallona ya keyi yana son na bashi wayar amman na ɗaure fuska, kuka ya saka, na kallesa, na daka masa tsawa, "rufe mani baki daga nan ko yan zun nayi maganin wannan rashin kunyar, anƙi a baka wayar, tunda da kuɗin ku na siya, ko kuma ta mutum ce, na ɗauka dole sakani abunda banyi niyar aikata wa ba, kuma ba zaka kira shi da wannan wayar ba, sai dai ku zauna kurame ni babu ruwa na, a ciki" ina zare masa ido.
Ai kuwa cikin jikin Amrah ya faɗa ya saki kuka yana kiran "Dadd... Daddy", share sa nayi kamar bana a kusa.
Amrah ce ta shiga lallashin sa, da taga yaƙi yin shirun ne, ta rasa ya zatayi, zuwa can tayi kamar zatayi kuka, ta ce, "Anty Narjeesh dan Allah ki aro muna wayar taki, mu kira masa Daddyn nasa, tunda ba kece zakiyi maganar ba, kinji Anty Narjeesh wallahi har jikin sa ya fara zafi".
Shareta nayi, itama tayi shiru Hindu ta ce, "shima dai Salman yaso ya haɗa wannan rigimar ne, yasani sarai, Narjeesh ba zata bada wayar ta ba, amman ya saka Shuraim a ciki dan ya fahimci rigimar sa, ke kuma dan Allah ki basu aron wayar tunda ba cinye wa za suyi ba".
Kamar nayi kuka na zaro wayar a jaka ta na bashi, ai sai kukan ya dawo dariya idon sa da hawaye amman dariya yakeyi.
Suma ajiyar zuciya suka sauke suna dariyar, Hindu ce ta anshi wayar ta saka number ta kira, ta saka murya ta bashi da farin ciki ya amsa, ya fara magana amman bayaji saboda munzo gurin da service yake rawa, dole ya haƙura, zuwa can yayi bacci, sai a lokacin ne Yaya Aliyu ya ce, "Narjeesah wai miye ya saka kika saka yaron nan kuka kuma ba zaki lallaba sa ba, kodai irin yanda Umma takeyi maki zaki yi masa ne? ".
Na ce, "to ya zanyi masa, ai dai kasan ni bana son lambar wayar wani ta shiga cikin waya ta, sabo bana buƙatar ya takura ni, tunda ba shine ya siya mani wayar ba".
Ya ce, "amman kin san zai iya siya maki wadda tafi wannan ko? "
Na ce, "aa ni ban sani ba dan ban buƙata ba, kuma ban roƙa ba".
Hindu ta ce, "hahh wata rana zaki buƙata Miss Salman Allah dai ya ƙara danƙon soyayya dan wannan zazzafar soyayyar tana tafiyar dani ne fa".
Tsaki kawai na sakar masu ban sake bin ta kan su ba, tafiya kawai mukeyi , amman mun tsaya a hanya munyi sallah munci abinci mun riƙo wani, na guzuri sai gab da magriba muka iso garin namu, ham dala muka shiga yi mun shigo garin dutse, a wani hotel muka sauka, muka kwana, tun da safe muka ɗauki hanyar shiga garin gumel, mun iso cikin garin gumel lafiya muka ɗauki hanyar shiga ƙauyen mu.
Tafe muke wasu zafafan hawaye ne, suka shiga zubo mani, ina tuna irin fitowar da mukayi a lokacin, kallon Amrah nayi naga tana wani makirin murmushi, ta ce, "Alhamdulillah Allah mun bar garin nan da far gaba da tashin hankali da tunanin makomar gurin da zamu sake sabuwar rayuwa, sai gashi yanzun zamu shiga garin nan da ƙarfin mu, kuma cike da farin ciki, da tarin nasa rori".
Kwatan ce hanyar da zasu bi Amrah takeyi, har muka iso ƙofar gidan mu, mukayi parking, duk muka furta "Alhamdulillah",
Bamu fito ba muna daga cikin motar, kusan mintina biyar, idon mutane, yana akan mu, Yaya Auwal ne ya fito daga cikin gidan yana kallon motocin, a kuwa nida Amrah da gudu muka buɗe ƙofar motar muka fita da gudu muka faɗa jikin sa, muna hawaye, cike da mamaki da farin ciki ya ce, "Alhamdulillah Alhamdulillah Amrah Narjeesah kune nake gani da ido na? Ina Umma ina Auta Nusaiba ina yaron nan Shuraim? ".
Yaya Aliyu ya ce, "to taya zasu iya amsa maka duk wannan tambayar lokaci ɗaya, ka bari ku shiga daga ciki ku zauna mana ".
Dariya Yaya Shuraim ne ya ƙaso gurin yana faɗar "Mommy waye ya dakeku kuke kuka, na kira Daddy na, nasar dashi yazo da Bindigar sa ya rama maku? ". kamar zaiyi kukan shima
Da sauri Yaya Auwal ya janye mu daga jikin sa, ya matsa, ya ɗauki Shuraim yana dariya yayi cikin gidan dashi, mutane kuwa tuni labarin zuwan mu ya riski kowa.
Inno ce ta fito tana gyara ɗaurin zanen ta, ta ce, "dama nadan duk daren daɗewa zaku dawo, toni yan ban zanga kuzo na rungume ku mana".
Ai da gudu mukayi kanta har da Auta da ƙaraso gurin mu, rungume ta mukayi, kuka ta fashe dashi taja hannun mu kukayi cikin gidan, kallon gidan mukayi duk an sauya masa tsari icce dalbejiyar mu yana nan, amman ɗakin Umma babu shi kwata_kwata wasu ɗakuna ne akayi daga baya, a tsakiyar gidan cikin inuwar icce inno ta saka akayi muna shimfiɗa muka zazzauna, Shuraim ne suke fira shida Yaya Auwal yana bashi labarin Daddy sa, suna dariya Inno kallon mu takeyi ta kalli Shuraim.
Ta ce, "wai nikam Amrah yaron nan ne yayi wannan wayon haka? "
Dariya mukayi Yaya Aliyu ne ya ce, zan je nadawo Shuraim kayi mani rakiya mani"
Da sauri ya tashi yana murna, Inno ta ce, "kuce ɗan naku swai_swai ne jirgin yawo to ayo muna tsara dai".
Dariya mukeyi Shuraim ya ce, "zanyo maki tsaraba mai yauwa ko Uncle? "
Dariya yayi masa ya shafa kansa, Inno ta ce, to da kuɗin waye zakayi mani wannan tsabar mai yauwa, dan nasan kai dai ba kuɗi ne da kai ba, baka da ko naira". Tana yi masa dariya