← Book details Matar Yaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 20

Sashe 13

Matar Yaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kai tsaye dakin Aliyu ta nufa domain angama abin kari yatashi kada ya makara agurin aiki"Tana xuwa ta fara dukan kofar da karfi"Afusace Aliyu ya farka daga baccin da ya daukeshi'kowaye wannan da yaxo ya ktsemai bacci Cikin ba cinrai ya tashi ya nufi kofar"saida ya tambaya waye? Ya nice katashi kar lokaci ya kure ga abin kari harna gama" Aliyu da ransa yagama baci yadaka mata wata uwar tsawa" da saida ta fir gice."Da halla malama matsamin daga nan"sabida rashin hankaki shine xakixo kina bugamin kofa kamar wacca take bina bashi.
Wllh inna bude kofar nan nasameki saina kakkar yaki"juyawa tayi ta koma farlo tana kun kuni"xaune ta tadda su abba harsun fara karyawa' kujara taja xauna bata reda ta fara cinnata abin cin ba" daddy ne ya dube ta yace mamana ya akayine naga ranki abace" saida ta kuma tunxuro baki gaba sannan tace ba yaya Aliyu bane waidanna ce yaxo yayi karin ku mallo shine ya dinga xagina yana cewa saiya karyani.
To kyalaeshi xaixo yasameni"daddy na'gama magana Aliyu yashigo saida yaxauna sannan yagaida iya yannashi daya bayan daya suka amsa cikin sakin fuska"daddy ne yalura da irin kallan da Aliyu yake aikawa Ummu da shi" itama tana mayar mai" daddy ne yayi magana da cewa Aliyu meya hadaka da mamana har kake ikrarin saika karyata"saida yakuma wurga mata harara sannan yace daddy wannan yarin yar bata da hankali kwata² kawai ina Cikin bacci naji ana dukan kofa kamar xa'a karyata"wllh daddy naxa wni abunne yafaru"ashe kawai xuwatayi ta katsemin bacci da sunan ta shi" ke haka ake tashin mutum daga bacci ahaka xa'amiki aure baki iya komai ba..
Kafin daddy yayi magana Ummu tai caraf tace eyy din naji ban iyaba saika xo' ka koyamin"takarashe tare da murgu da mai baki tashi yayi xai kaimata maxga daddy yada katar da shui da cewa karka kuskura kata bata"Wllh babban banxa da akayi" ba tema kon ka akayi ba" inda bata je ta ta sheka ba aida kama kara.
Komawa yayi yaxauna yana kara hararar ta"itako sai gwalo takemai tana jin dadin yanda daddy ya tare mata"sai yanxu mommy tasa musu baki acikin maganar tasu' gaskiya dadin yara kana sankai bakaga abinda taimai ba kuma saika goyi da bayanta haka akeyi tsakani da Allah fa....
Yauwa mommy na taremin kinga daddy yafi santa ko aidama nadade da sanin daddy uafi san wacca munafukar maifuskar muna fukai kawai.yafada yana kara harar ta.kyalesu babana aisu sunfiya fiya sankai. Aukema haka xakice"daddy yafa da yana murmushi to haka suka cigaba da karinsu Cikin raha"bayan sungama mommy ta cewa Ummu ta kawai Yusip nashi abincin saida tayi kamar tayi kuka dan Allah yagani bata san xuwa gidan kodan Ubaida da mahaifiyar ta....
“Tana shiga tasamesu a farlo.slm tayi Amma babu wanda ya amsa" data'ga haka saita wuce batare da takara ce musu Uffan ba"hakan kuwa ba karamin haushi yabasu ba. sun so tayi wata mgn su fal mata.tana shiga tasa mesa" yana shirin fita'sama²suka gaisa ta bashi kulan abincin.. babu abinda yake sai aikin kala ta" itako dik ta kagu ta tafi dataga bashida niyyar cin abin cin saita cemai xata koma gida idan yagama ya kai kwanan. bai so hakan ba Amma tadage tana da aikin da xatayi..
To yace tareda mikewa yayi mata rakiya. A'ah kabarshi nagode basaika rakani ba. Ni kama saina rakaki wllh yafada yana marairaicewa"saitayi saroro tana kallan sa" da yaga kallan yayi yawa saiya hura mara iska a idonta"da sauri ta dago tana du bansa sai yanxu tagane wauwtar datayi na kuramai ido'karma yayi xargin wani abu"saita waske da narkamai uwar harara" daganan kuma suka jero suka fito gwanin sha'awa.
Sai surutu yake janta da shi amma taki kulashi.......
Ubaidace tsaye ta rikr kugu sai girgixatake tana jifansu da mugun kallo.bama susanta na yiba"tafiyarsu kawai suke harsunkai bakin kofa.. Ubaida tai kawai suke harsunkai bakin kofa.. Ubaida tai u kawai suke harsunkai bakin kofa.. Ubaida tai kukan kura ta shako wuyan Ummu'ta wanketa da mari harsau biyi"agigice Ummu ta dago tana kallan Ubaida da tarike kugu tana gir gixa"To yar gidan marasa kunya kedan bakida mutun ci shine kike wani biyoshi har cikin gida da suna kin kawomai abin ci ko" to bara kiji Wllh Yusip nawa ne kuma ke biki isa kin aureshi ba inadai ina numfashi a doran duniya"sannan xan miki gar gadi na karshe da kifita a harkar Yusip domain nawane ni kadai" Yusuf na Ubaida.bata karasa abinda take sanfada ba tahi saukar mari akun cinta harsau biyu..

More comment more typing............✍�

By
(MMN HIBBAT)

MATAR YARO!!!

Page (28/29)
Chapter 13 · 0% Book details