← Book details Karni Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 3

Sashe 2

Karni Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarki shaibat ya juya domin ya amsa sallamar da wani mutum yayi mashi, ai kuwa sai idanuwanshi suka sauka a saitin inda Hakimi shaibat ke tsaye a can gefenshi, take yaga wayam Babu alamun shi, Batare da bari wani daga cikin jama'arshi ya lura

Bai bayyana ako ina ba sai a daf da kofar fita daga gari, kai tsaye ya durfafi kofar, yayin da dakaru suka hangoshi sai suka miƙa gaisuwa gareshi tare da yi masa sallama yana amsawa, waɗansu dakaru a gefe ya hango sun tare waɗansu samari uku da fuskokin suke ke rufe da bakin rawani suna ɗauke da waɗansu bujjuna a bisa kan amalanke.

Sannu a hankali yana takawa har ya isa gare su.

Mene ne ke faruwa ana ?

Urwat ya tambaya a taƙaice.

Wani saurayi mai tarin ƙasumba ya risina gareshi cikin ladabi ya buɗi baki Muryar na rawa yace " ya shugabana muna binciken buhhunan da suke ɗauke da sune domin tabbatar da tsaro.

"Shin baka da sanin cewa dukkan kayan daga gareni suka fi to?".

Urwat ya tambaya fuska a murtuke.

Tuba nake ranka ya daÉ—e insha Allah hakan bazai sake faruwa ba.

Badakaren ya faÉ—i.

Cikin hanzari samarin suka tura kayan suka huce gaba.

Badakaren ya bisu da kallo yana ƙarewa buhhunan kallo yana son fahimtar wani abu, har suka ɓace gareshi ya daina hangoshi.

Wata unguwa urwat ya nufa data saɓa da wacce samarin uku suka bi, da shigar unguwar ya durfafi wani gida yana isa tamkar an san da zuwanshi aka wangame kofar gidan ya kunna kai ciki.

Zaune ya isar dasu suna shan barasa suna ta ƙyaƙyata dariyar mugunta, samarin uku da ya baro a hanyar kofar gari ne

Waje ya samu ya zauna bisa wata kujera yana mai fuskantar su a lokacin da suka nutsu domin suji bayanin dazai yi musu.

Ina fatan dukkan kayan mu mun kammala yadda ake buƙata?

Urwat ya tambaya.

Wani daga cikin matasan mai yanayin shiru- shiru shine ya yiwa sauran samarin biyu Indiya ta wutsiyar idanu, da sauri suka miƙe tsaye suka nufi bangare a ɗakin sauko waɗannan buhhunan suka zo suka ajiye a daf da inda urwat yake suka buɗe buhhun.

Urwat ya ɗora idanuwashi akan buhunan domin yaga abinda ke ƙunshi a ciki.

Motsin alamun sawaye suka ji na kusanto da ɗakin, al'marin daya sanya dukkanin su sukayi turus kenan domin ganin abinda ya bayyana gare su zukatansu cike da matuƙar al'ajabi domin kuwa a iya sanin su babu wanda ya san da wannan gida na sirri face su huɗun kacal.

Wannan shi ne abinda ya wakana a ƙasar madinatul-barnawiy.

****

Al'amarin Bafade da ya tafi da kuyanga ihsan izuwa gidan 'yar mai ganye domin zartar da umarnin mai martaba na duba lafiyarta.

Lokacin da suka kaɗaita a cikin turkar 'yar mai ganye sai Bafaden ya zayyane mata dukkanin saƙon da yake ɗauke dashi izuwa gare ta daga wajen mai martaba.

Ko da jin wannan batu sai yar mai ganye ta ƙura wa ihsan idanu kuma ta hanya hannunta ta gwale idanun ta na dama, bayan ta kammala bincikenta, sai ta dubi Bafaden ta buɗi baki cikin murya mai tattare da alamun dattijantaka tace.

"Dukkanin ƙoƙarin da nayi domin na gano irin nau'in cutar dake damun ihsan hakan ya fasƙara, Kawai abinda na ɗan fahimta shine an yi amfani da sihiri ne a lalurarta.

"Ni kaina ina zargin hakan matuƙa.

Bafaden ya faÉ—i.

"Yanzu Ina ganin zan gwada yi mata addu'o'i ku Allah zai sa a dace.

'yar mai ganye ta faÉ—a, gami da sanya hannunta ta buÉ—e bakin ihsan, ta shiga karanta Ayatul-kursiyyu tana Tofa mata a ciki.

Lokacin da ta kammala karatun bisa mamaki sai suka ji ihsan tayi Atishawa da ƙarfi ta buɗi baki tace "Alhamdulillah.

Nan fa Bafaden da ihsan suka cika da matukar farin ciki maral misaltuwa suka yi salati ga Annabi s'a'w domin nuna godiya ga Allah (SWT).

Su kayi sallama da yar mai ganye domin komawa ga mai martaba sarki.

Kasar Madinatul-barnawiy

Wane ne sarki Anwar ?

Kuma mene ne dalilin daya sanya Musulmi suka fara samun matsaloli a cikin al'ummar su tun daga tushe?

Dalilin haka kuwa shine kamar haka.

Sarki Anwar ɗan Adam yakasance mutum mai matsakaicin kyawu da shekaru yana tarin ilimin addini da son ganin ya kyautata al'ummarshi, bisa wannan dalili ne yasanya kowa ke zaune lafiya, manya na tausayawa ƙanana, na ƙasa na girmama manya, babu cuta babu cutarwa, kuma dukkan wani fabatake da ya shigo birni sai limamin dake yankin ya ganshi kuma ya tabbatar da cewa ga daga inda yazo domin tabbatar da tsaro.

Miji na sauƙe haƙƙin iyalanshi, mata na yin biyyayya ga mai gidanta, duk wanda ya aikata laifi tsakanin babba, Attajirai da talakawa ana yanke hukunci babu bambanci.

Bisa wannan dalili ne yasanya dukkan al'umma ke zaune cikin aminci, kwatsam sai aka wayi gari da waɗansu a yarin fatake dake ɗauke da malaman addinin Musulunci ƙarƙashin wani shehun malami mai suna sheik Habib al-attad.

Kansancewarshi malamin addinin Islama ɗaya tara ilimi wannan yasa ya samu shiga a wajen sarki Anwar har ya zama na hannun damar shi bisa wannanne ya sanya sheik Habib yayi amfani da wannan dama wajen jefa sabbin gurɓatattun aƙidoji domin kawo rabuwar kan Musulmi, saboda dukkan wata fatawa ta addini shine ke amsawa.

Kafin shuÉ—ewar waÉ—ansu shekaru yanayin al'umma ya canza al'adun su da kyawawan halaye na musulmci sun fara rabuwa dasu

Bisa wannan dalili ne yasanya matsaloli ke bazuwa a cikin al'ummar musulmi da aka kasa shawo kansu.

Wannan shi ne taƙaitaccen bayani game da sarki Anwar da rayuwar al'ummarshi a shekarun da suka gabata.

****

Lokacin da Hakimi urwat da samarin uku suka yi turus! Bisa jin wannan motsi da suka yi na takun sawaye a gidan sirrinsu.

Tsaye suka yi arba dashi fuskarshi rufe da rawani idanuwanshi kaɗai ake gani, matashi ne da shekarunshi bazasu haura ashirin da uku ba,sanye cikin sulken yaƙi.

"Assalamu alaikum".

Saurayin ya faɗi a taƙaice.

" Wa'alaika-Salam warahamatullah".

Urwat ya amsa da yawun sauran matasan dake tare dashi.

Matashin ya ɗora hannunshi akanshi ya cire rawaninhi fuskarshi ta bayyana a fili ƙarara, koda Urwat da samarin uku sukayi ido biyu dashi sai suka sakar mashi murmushi mai taushi.

Matashin ya risina ya kwashi gaisuwa gareshi sannan ya buɗi baki cikin ladabi yace"ya shugabana mun sace dukkan fataken da ka buƙata da suka tafi izuwa birnin infaƙul-Maisur domin yin kasuwanci, sai dai anyi rashin Sa'a a cikin waɗanda mukayi garkuwa dasu har da yarima Affan ɗa mai martaba sarki.

Ya ƙare batun nashi cikin alamun damuwa.

Urwat ya bushe da dariyar mugunta gami da cewa ni a wajena hakan

Babban nasara ce a garemu, domin kuwa dukkaninku kun shaida cewa babu wani mai ƙoƙarin kawowa aiyukanmu tazgaro a wannan birni tamkar yarima Affan, kun ga yanzu komai namu zai cimma nasara,

Wani abin farin ciki ma baku sani ba shine a gobe ne da safe za'a yanke hukuncin kisa ga manyan 'yan leƙen wannan birni a fada bisa laifin shirka wato (tsafi).

Sannan halin yanzu dukkan matasan da muka ɗauka aiki sun shirya fara aiyukan su na zartar da kisa ga dukkan wanda bai yi biyayya ga tabbatar da aƙidarmu ta mujahidul' Haƙ ba.

Koda yazo dai-dai nan azancenshi sai samarin huÉ—u suka bushe da dariyar mugunta har da kyakyatawa.

Sannan daga bisani matashi É—aya daga cikin samarin ya buÉ—e wannan buhu sai ga waÉ—ansu miyagun makamai da kwalaben barasa haÉ—e da nau'ikan kayan maye.

Koda ganin hakan sai urwat ya cika da farin ciki, sannan ya dora dacewa ku tabbatar da an bawa dukkanin matasan mu waÉ—ansu kayan maye da makaman a daren yau kafin wayewar gari.

Yana gama faɗin hakan sai ya miƙa tsaye kawai sai ya shafi wani guru a damtsenshi yakaranto waɗansu dalasiman tsafi ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba.

Wannan shi ne abin da yafaru Hikimi urwat.

Bayan ya ɓace cikin alƙalumman sihiri a lokacin da Sarki shaibat da tawagarshi zasu tafi masallaci domin sauke farali.

Madinatul-barnawiy

Kashe gari tunda duku-dukun safiya fadar birnin madinatul-barnawiy ta cika ta batse da jama'a

Kowa yayi jigum ana jiran fitowar sarki da muƙarrabanshi،Tsawon daƙiƙa talatin ana cikin wannan hali, Sai daga bisani aka hango martaba da tawagarshi sun shigo fadar ta hanyar yin sallama.

Jama'a suka miƙe tsaye domin girmama agaresu, sai da sarki da tawagar shi suka zauna bisa wajen wajen zamansu, kuma jama'a sun kammala kwasar gaisuwa ga sarki, fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta.

Sarki ya miƙe tsaye yayi gyaran murya sannan ya ɗora dacewa "Da farko ina yiwa dukkan mahalarta wannan fada rawa mai albarka Barka da zuwa, Bayan haka a yau ne dukkan jama'ata ke zuba idanu domin suga yadda za'a zartar da hukuncin kisa ga manyan'yan leƙen asirinmu, kamar yadda labarin ya wakana.

Sai a wannan karon ba haka al'amarin yake ba, domin kuwa abinda zan sanar daku zai yi matukar girgiza ku, yaku jama'ata kuyi sani cewa a daren jiya ne wani muhimmin sirri da na daɗe ina ɓoye muku zai bayyana a gareku.

Fiye da shekaru uku ina tare da Amintattun 'yan leƙen asiri a dukkan wani rukuni na al'ummar wannan ƙasa tawa, tun daga gidan sarauta, Unguwanni da kasuwa da ma manyan ƙasashen maƙiyan Addinin musulunci, kuma a kowa ce rana dukkan aiyukan da na sanya su ya kammala, ta wannan hanya ne a samu nasarar tarwatsa dukkanin shirin maƙiya.

Hanya ta biyu dana kawar da hakan shine gabatar da addu'o'i dare da rana tare da keɓaɓɓun mutane, domin kuwa babu wani abu da yafi ƙarfin addu'a, Ubangiji na iya canza dukkan abinda ake ganin ya gagara ta kowace fuska, amma sinadarin wannan canjin shi ne bin dokokin ubangiji (SWT).

Sannan wani muhimmin abu da mutane basu sani ba shine a kowa ne dare bana iya rintsawa da idanu na har sai na shiga cikin gari cikin ɓadda-kama ina mai sanya idanu akan aiyukan da na sanya shuwagabanni akansu, kamar yadda na saba wannan al'ada ne ajiya ina yin rangadi a cikin gari na shiga wata unguwa da ake ɗaukar matasanmu mayaƙan Mujahidul-Haƙ, Sai da nayi shiga da siffa irin ta Mujahidul-Haƙ sannan na samu shiga gidan sirrin inda ananne na ganewa idanuna Gaskiyar rahoton da ake bani akan Yan tawayen ƙasarmu.
Chapter 2 · 0% Book details