← Book details Karain Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 2

Sashe 2

Karain Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Kai Umaru sa idanunka cikin nawa da kyau aure na ya fi ƙarfin wai, dan wallahi ko budurwa dal a leda ba za ta cewa aure na wai ba, dan aurena dai dai yake da nata na saurayi da budurwa wataƙila ma nawa ya fi armashi da moruwa ko dan saboda tsohuwar zumar soyayyar da nake yiwa wanda zan aura ɗin, soyayya ce mai ruwa-ruwa wacce ta daɗe tana iyo a cikin gogin raina, duk ta bi ta sanya mini rauni a zuciya kunsan so da raunana zuciyar mai yinsa duk girman mutum sai ya so ya mayar masa da zuciyarsa ɗanya sharaf kamar ta jaririn da ya sunkuto daga mahaifar uwarsa yanzu...

"Inna!!!" Cewar Sa'adu da ya miƙe tsaye kamar an tsikareshi yadda furucin Innar ke masa dirar mikiya a kunnuwansa shi kansa bai sa ya tashi ba sai ganinsa ya yi a tsaye cankarkar.

"Sa'aduuuu" Ita ma ta faɗa tana miƙewa tsaye har zaninta na kuncewa ta kama ta ɗaureshi gamgam.

"Inna maganar auren nan ki daina yi dan Allah ko daɗin ji ma babu yanzu dan Allah a ce daga gama takaba da sati biyu sai ki ce wai aure za ki yi, mahaifinmu ko shekara bai yi ba a ƙasa amma dan Allah Inna da girmanki a ce wai kina maganar ƙara aure.

"HHHH na dawo in ji ɗan yawon duniya yo Umaru cewa za ka yi marigayin ubanku kuke tayawa kishi bayan yana can rufe a cikin ƙasa,Allah na tuba a nunawa na ringingine farin wata, yo kalle ni da kyau ka gani dangargar nake ji na kamar saurayi sabon balaga, amma kowa dama da kiwon da ya karɓeshi maƙocin mai akuya ya sayi kura, ni babu ni babu Malam Lawwali mahaifinku, mutuwa ce ya mutu tsakaninmu kuwa takaba ce ko a musulunci idan na gama takaba ko da kwana ɗaya ne zan iya yin aure, babu inda addini ya haramta kuma addini ba ruwansa da tsufana, ko akwai wanda zai faɗa mini inda aka haramta auren tsohuwa???" Ta jefa musu tambayar tana tsatstsare su da ido. Babu wanda ya tanka dan sun rasa bakin magana.

"Kun gani, baku da amsa to tunda ba faɗin Allah bane ba na ma'aikinsa ba babu wanda zai taka mini birki duk cikin ku, in banda ma sabo da yi gawa da gatsine ina za a haɗa wanda ke doron duniya da kuma wanda ke can ƙasa a ƙumshe ya gama zagwanyewa...

"Inna fata nagari lamiri"

"To na ji ubana Umaru in kuma duka zaka saka to aiki Maryama ta samo maka kirfo(Bulala ko madoki)"

"Ni ba haka bane amma gaskiya ki janye maganar aure dan duk wanda ma ya ji maganar nan mu za a zaga a ce mu ne Æ´aÆ´anki muna gani...

"Yo a faɗa mana zagi kuma a zageku tun da dai zagi baya fitowa a jiki,duk da an ce ba a ƙin ta mutane wai an ce wa ɓarawo ya gudu, amma ni dai na san duk wanda ma ya zage ku ya ɗauki alhakinku dan ni ce mai aure, sai ka ce wanda na ce zan fara karuwanci, to aure dai kuma babu wanda ya isa ya taka mini birki duk duniya sai dai in ni Delu bana numfashi" Ta faɗa tana bugar ƙirjinta.

"Haba Inna wai shin mai kike so mu miki? Mai kika nema kika rasa da zaki mana wannan abin dan Allah " Maryam ta faÉ—a tana sakin kuka.

"Maryama goge hawayenki kar ki yi asarar zubar da su, dan indai dan in saduda ne in ji tausayinki to ba zan ji ba tun da ni ma baku ji tausayina na luguden da zuciyata take yi ba, kullum bugawa take tana kiran Jauro, Jauro, wallahi auren ƙara'i dai tsakani na da jauro babu fashi har sai na ji an ce alfatiya, sannan hankalina zai kwanta duk wanda kuma ya ce zai hana ga wurin nan dan ta yaro kyau take bata ƙarko!"

"INNA zan biya miki umara idan kika fasa auren nan" Sa'adu ya faɗa da ƙarfin gwiwarsa dan sai yanzu ma ya tuna lagom mahaifiyar tasu, dan tana mutuwar son zuwa makka duk da ta je ta koma.

"Yanzu dai na je hajj ita ce farilla, umara kuwa zuwana ya fi a ƙirga to ko ban taɓa zuwa umara ba gwara in auri Jauro wataƙila ya mini tukuici da amarcin darenmu na farko ya biya mini umarar " Ta faɗa tana ɗan darawa

Da sauri Sa'adu ya zauna daɓas jiki ba ƙwari dan yana ganin mahaifiyar tasu ta yi nisa ba lallai ta ji kira ba!

MAMAN AFRAH😍

Masu son grp na ƘARA'IN INNA DELU👇

09030283375
Chapter 2 · 0% Book details