← Book details Karain Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 2

Sashe 1

Karain Inna Delu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read



ƘARA'IN INNA DELU
💄💄💄💄

NA

MAMAN AFRAH

FCW💛
ƳAR ZAMAN WANKA TA TAFI MAI ƘARA'I TA ZO😂😂😂😂😂😂

Page 1⃣➡2⃣

Zaune suke kowa yana jiran tsammani, sai dai kiran da mahaifiyar tasu ta musu ta tara su, su duka abin ya basu mamaki, dan ta ƙi furta musu komai wai har sai ƙanwarsu Maryam ta ƙaraso, wacce Inna ta kira ta a kan ta zo da gaggawa lallai akwai muhimmiyar magana da za su yi.Sallamar Maryam ita ta sanya kowa ɗagowa yana kallonta.

" Lale marhabin da autata, sannu autayye sannu da zuwa auta jaja manya, auta kin fi na fari, kin mabiyin na fari" Cewar Inna Delu tana tafa hannu har da rausaya kai. Abba da Baba sakin fuska suka yi ganin zuwan ƙanwar tasu wacce mahaifiyarsu da su kansu ke matuƙar ƙaunarta kasancewarta ƙanwarsu kuma autarsu Cikin murmusawa Maryam ta ƙaraso falon ta samu wuri ta zauna.

"A'a dawo kusa da ni ki zauna, ina mijin nawa" Cewar Inna tana washe baki.

"Ya tafi makaranta jarabawa suke" Ta faÉ—a tana samun wuri ta zauna ta gaishe da yayun nata da kuma Inna.

Bayan an gaisa shiru ya É—an biyo baya kafin Inna ta yi gyaran murya ta fara magana kamar haka.

"Dama na tara ku ne a kan in sanar da ku abin da ke raina, kun san an ce mai zurfin ido da wuri yake fara kuka, kun san dai yau da kammala takabar mutuwar mahaifinku sati biyu, Allah jiƙan Malam ya sa kwanciya hutu ce Allah dai ya sa bai sha kulkin walakiru ba" Ta kai ƙarshen maganar tana sakin kuka.

"Haba Inna yanzu fa Malam babu abin da yake buƙata sama da addu'a amma kike zancen kulki" Cewar Abba cikin ɓacin rai.

"Haba Sa'adu ni ba mugun fata nake masa ba kawai dai na san aradu ya sha cinye kaji da zabbin mutane bashi, Allah ka ɓoyi muryata ba da niyyar tone-tone na yi ba, amma mahaifinku ya ƙi jinin biyan bashi, kuma na ce zamanin annabi idan mutum ya mutu in ana binsa bashi ko gawarsa ma'aikin Allah ba ya sallata, ka ga kuwa bashi musiba ne amma mahaifinku ba ya son biya ka san shi da son nama kamar maye, ko ni nan akwai lokacin da ya karɓi wata kaza, kazar nan ina sonta saboda tana min ƙwai mai yawa amma tana cikin kwancinta ya karɓa ya yanke aka masa dabgenta, tasha kalwa amma banda kai da ƙwabri babu abin da na ci a kazar nan ya lamushe, da na san ba biya na xai yi aradun Allah da cinyoyin da ƙirji zan ci innkai masa sauran, yo har ya koma ga Allah bai b...

"Inna dan Allah ki bar tone-tonen nan ko ke mai biyawa Baba Malam bashi ne , kuma ma duk sai da muka tabbatar mun biya masa bashi" Cewar Baba Umar yana kallonta.

"Allah sarki to na yi shiru, ai da baku wahal da kan ku ba wajen biya masa bashi yo mutumin da ya daɗe da zama ƙasa da kun bani kuɗin na sayi agwagi na yi kiwo, yo shi in azabar ce ma ai an masa...

Kallon da Maryam ta mata irin na bain da kike bakya kyautawa shi ya hana ta ƙarasa maganar.

"Uhm in ji mai ciwon haƙori kai da bakin ka bawa a hanaka magana, idan ma aka so raina maka hankali a ce shiriftun tsufa ne" Cewar Inna tana taɓe baki. Ta ɗora da cewa

"Dama cewa na yi tunda na kammala takabar har na ƙara zaman kwanaki goma sha huɗu ina jimamin mutuwar Malam, a haka ma na danne na cije na kuma yi ta maza, amma da a ce ba a takaba dama tun washe garin kwana bakwai za a ɗaura mini aurena yo ai wanda ya mutu ya mutu kenan, amma da yake akwai ɓurɓushin takabarsa shi yasa na haƙura yo ai ko dan tumunin takaba na masa takaba, tunda yanzu na kammala takaba kuma zaman haka ya ishe ni, kar in ja muku gori a ke cewa uwarku bata da aure, kuma ake lissafa uwarku a cikin zawarawan unguwa shi ne na ce AURE zan yi...

GabaÉ—aya suka É—ago da mamaki a fuskarsu suna kallonta kowa bakinsa a sake

"Aure Inna?" Suka haÉ—a baki wurin faÉ—a.

"Kai É—iyan nan ku maida mamakin da na baku, aure mana ko baku ji mai na ce ba, kuke maimaitawa kamar wanda nake biya muku karatun allo, haba É—iyan nan aure fa na ce sunnar ma'aiki, ko akwai wanda zai ja da sunnar ma'aikin Allah" Ta faÉ—a tana rausayar da kai ganin kamar dai za a sha fama da su.

"Inna kin san kuwa mai kike faÉ—a, aure fa kika ce, yanzu shekara saba'in mai kuma ya rage miki sama da ki tsaya ki yi ibadar sallah da salatin annabi...

"Ungo nan Sa'adu" Cewar Inna tana watsa masa yatsunta biyar alamar daƙuwa da sauri ya sunkuyar da kansa ƙasa

"Yau na ga abin da ya turewa buzu naɗi, ni Delu yanzu Sa'adu ni kake cewa ban san abin da nake faɗa ba, wato ga mahaukaciya mai taɓin hankali, wato shekara saba'in mai ya rage mini sai sallah da salatin annabi yo ce maka aka yi bana yinsu ai ko auren ma ibada ce mai zaman kanta Allah na tuba da in zauna in mutu bazawara ai gwara in mutu a ɗakin mijina ko ruwan wanka da na alwala nake kai masa bayi mai na manta, ai ya fi dai a ce zaune nake ba miji, kai in taƙaita muku wallahi ko tsarkin kashi ya ce in masa tatas zan wanke masa mazaunansa yo ai duk a cikin soyayya da ibada ne, bare ma ku ne kuke mini kallon na tsufa, amma ni nan da kuke gani wallahi da saurana babu abin da ba zan iya ba a gidan aure, daga sama har ƙasa ban tsufa ba yo Allah na tuba ai ni irin matan nan ne da ake kira DAKI BARI...

"Haba Inna me yasa kike haka dan Allah mu fa Æ´aÆ´anki ne me ya kawo maganar daki bari kamar wata atamfa"

"Yo Maryama da bakina ba ɗinke min aka yi ba a hana ni faɗar gaskiya ko ku ƴaƴana ne ai ina da ƴancin faɗar abin da ke raina, gani na yi ana mini kallon na yi tsufan da bani da mamora, har kya yi maganar atamfa ma wacce shekara uku ta mutu, amma ni nan shekarata hamsun da bakwai ina gidan ubanku amma yanzu nake son ƙara aure kin ga luwa ubanku ya daka ya bari Jauro ma zai ɗora daga inda ya tsaya, dan ni na san kamar yadda ƴar shekara ashirin za ta moru a wurin miji a gidan aurenta ta kowane ɓangare haka ni ma zan moru, aradun Allah Maryama ku yarda dani da saurana, zamzam nake wallahi abin da na sani makusa a jikina wallahi ɗiyar nan mashaya ce (Nono) Amma mafitar ɗa (HQ), yana nan tsut a tsuke kamar ba ni na haifeku ba, mashayar ce dai ni kaina na san akwai matsala yo dama nono ba kwalifi gareshi (quality) Abu ne ya jagule yanyi jalele kamar alalar gero, duk ya tauye ya yamutse amma Allah na tuba mai gyara ya bari har mafitar ɗan ma sai a nemi abin gyara yo na san dai kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan kwano, tuni Maryam kina rakani kasuwar kayan gyara muka samo maida tsohuwa yarinya na gyara ko ina daga na shiga ɗakin mijin kirif za ki ji an rufe bakinsa yp gyara mai ya bari komai yana so gyara, yo ango ɗiɗif zai yi, ya ji abu zamzam" Cewar Inna tana murmushin tare da ɗan kauda kai tana ɗan sussunkuyarwa ita ala dole ta ɗan ji kunyar furucin da ta yi.

"INNA!!!" Cewar Maryam da takaici ya hana ta magana ga kunyar yayunta Abba da Baba da suke zaune, jin nauyin maganar Inna ya sanya sun yi É—if kamar ruwa ya ci su.

"Allahu akbar kabiran wallahi Maryama sai yanzu na ankara, duk sai na ji kunyar ku ta baibaiyeni, yo kin san ni ƴar gaskiya ce kuma an ce in zaka faɗi faɗi gaskiya, kuma dai da na ga auren nan ba haramun bane, kuma kuna kawo ƙauli da ba a di kinga sai na zage dantse na muku biyani yadda zaku fahimta, kin ga kuwa dole na yi iya yina na fahimtar da ku da akwai mamora a tare da ni, kuma dai kun ga ni ma zan so in ƙara muku ƴan ƙanne tun da ku uku rak na haifa bare ke, ke kaɗai ce mace kina buƙatar abokiyar shawara, tun da auren nan ma'aikin Allah S.A .W ya ce mu yi aure dan mu hayayyafa domin ya yi alfahri da mu"

"Wai Inna me kike nufi ne?" Maryam ta tambaya kamar za ta yi kuka.

"Ka ji ja'irar yarinya, da hausa fa nake magana sai wani hanya -hanya kuke kuna kaucewa to tun da haka kuke so bari na muku gwari-gwari a harshen hausa da aure kowa ya san mai ake nufi da shi tun da kaf ɗinku babu wanda bai san auren lanjane na yi da mahaifinku ba, dan auren marigayin ubanku sunansa kaɗan ya fi zawarci, kun san dai Jauro shi ne zaɓina....

"Inna" Cewar Umar fuskarsa na nuni da tsantsar jin haushin abin da Innar ke faÉ—a.

"Na'am Umaru faɗi ina jinka, dan wallahi faɗarka ba faɗar annabi bace tuni zan saka ƙafata na yi fatali da kai da maganarka matsawar dai ba baya za ka goya mini in yi abin da raina ke buri ba, yo ƙarya zan muku abu da auren dole ne aka laƙaba mini uban naku tun yana almajirci bai zama Malam ɗin ba" Ta faɗa tana kallonsa ido cikin ido dan kar ma ya yi zaton za ta ji kunyarsa ta ɗan fari ta fasa kudurinta na auren ƙara'i

"Inna a kan maganar wai auren nan da kike faÉ—a haba dan Allah...
Chapter 1 · 0% Book details