← Book details Iznah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 4

Part din mum asee ta wuce Dan dubo asabe dataita zaryar dubata kwana biyun.

Iznah Part 1 Complete Hausa Novel · about 162 min read

Tana shiga taji an fixgota da qarfi tareda jefota tsakiyar palon saidata bugi centr table gefen bakinta ya fashe ta 'dago da sauri taga Kamal yana wani irin huci kamar zai buga ya sake damqo gashinta dake cikin hijab da qarfi cikin 6acin Rai yace,

You ingreat bitch so nawa Zan fa'da Miki Babu shegen dazaki kula bayan ni Amma kinqi ji
Bakisan rufa Miki asiri ne zanyiba na taimaka muku keda that bastard thing you called son
Ke bandama qaddara mezanyi dake da bastard son dinki.....

Cikin baqin ciki da hasala ta katsesa tareda miqewa tsaye tace,

Karka qara Kiran yarona da shege sbd ba shege bane Dan haka ka janye tausayi da taimakonmu dazakayi ka rufa Mana asiri sbd har abada bana buqatar taimako ko tausayawa daga gareka afterall Mena sama yaci bare yaba na qasa,,,
Karka Kuma Kiran sunansa sbd inason abuna ahaka duk da Yana shege Zan iyayin komai akansa Dan kuwa dakasan yanda nasamesa naci wuya akansa na yafe gatana sunana mutumcina da iyayena akansa nazo Nan nasan zaka tabbatarda idan nace maka Zan iya komai akansa zaka yarda Dan haka karka Kuma shiga rayuwata da yarona bakasan wacece Anano ba
Yaron dakake Kira bastard yafika Dan kuwa Bai dauko halayen shegunba ko 'daya saima Kaine kakeda kaf halayensu harma.......

Hannu ya 'daga a zafafe zai wanketa da Mari mum asee ta riqe hannunsa tanabin Anano da wani irin kallo Dan dama tana palon zaune itada Kamal kafin ananon tashigo....

Lallai dama ance 'dan iska na qauye...ta fa'da cikin zuciyarta
Taji zafin maganganun ananon sosai Amma qarfin zuciyarta da iya fitsararta tareda son datace tanayiwa shegen 'danta zatai komai dominsa su zatayi amfani dasu tayi amfani da ananon ta jefi tsuntsu biyu da dutsi daya,,,ta cimma burinta,,ta wargaza ananon bayan ta sheqa shegen danta lahira..

Murmushi tasakarwa ananon bayan ta sauke hannun Kamal tareda cewa,

Bakada hankaline zaka daki mace
Kai kullum cikin zafin Rai da rashin hakuri..fice kaban guri mutumin banxa kawai.

Kallon mamaki yabi mum din dashi tamasa alamar ya wuce
Ya wuce Yana qwafa kamar zai tashi sama.

Kamo hannun ananon tayi suka zauna a kujera ta kalleta tace,

Karki saka alamarin Kamal arai haka yake kamar Mai shaqar cocaine.

Mamakine yakama Anano ganin yanda mum asee ta sakar Mata tasan akwai abunda zata qulla
koma meyene zatabita yanda takeso.

Murmushim yaqe tayi tana goge gefen bakinta da tissue dinta mum asee din ta miqo Mata tace,

Bakomai aina Saba da halinshi zuwa yanxu.

Mamakin Anano mum asee tasakeyi ganin yanda take Kai tsaye tayi murmushin mugunta tace shege baqauye...kafin ta fuskanci ananon dakyau tace,

Kince kinason 'danki,,,bakyayi Masa sha'awar kyakkyawar rayuwar hutu da ingantaccen ilmi da Jin da'din rayuwa..

Kallon mamaki Anano tayiwa mum asee

Mum asee tace,
Eh sbd naji kince zakiyi komai akansa..

Ina Masa addua da fatar hakan...

To idan nace Miki ga damafa Wadda zakiyi arziki 'danki yayi sunan Mai arziki hakama akiraki da uwar 'dan Mai arziki
'danki yayi kyakkyawar rayuwa yasamu ingantaccen ilmi...

Zaro idanuwa Anano tayi
mum asee tasaki wani shi'umin murmushi tana cewa,

Yes idan har Zaki iya tsayawa kice saheeb shine uban 'dan shegenki,
Ki tsaya kice shine yamiki cikinsa Kika haifesa.....

Miqewa tsaye tayi da sauri tsoronta na fitowa qarara Dan Bata ta6a kawo wannan shine abinda mum asee zata fa'daba..

Zaunar da ita mum asee tayi tace,

Kar kiji tsoron kowa idanhar Zaki iya nizan tsaya Miki akomai.

Tana kallon tsakiyar idanuwan mum asee 'din cikin tsananin mamaki tace,

Meyasa zance 'dana 'dansa ne...?

Sbd samun cikakken iko akan dukiyarsa...

To ai a musulunce 'dan shege baida gadon ubansa...

Ba wannan Zaki dubaba yanxu cigaban 'danki da naki Zaki Duba.

'dana bazai ta6a samun iko daga dukiyarsa ba Dan ance 'dansane tunda ba aurene atsakaninmu ba..

Aurenki zaiyi.....

Miqewa tasake yi cikin tsananin mamaki da fa'duwar gaba da zancen yasata.

Muryarta na rawa tace,

Ta Yaya?

Ta nice Zan saka ubansa yasashi aurenki Dole sbd yayi Miki ciki kin haihu...

Cikin 'daga murya takatseta da cewa,

Duk menene dalilin dazaisa ayi hakan.

Murmushi tasaki tareda miqewa tana kallon ananon da tuni zufa yafara jiqata sbd tashin hankali tace,

Dalilin hakan shine Ina buqatar takardu ahannunsa Kuma bazan ta6a samunsuba Dole saita hanyar matarsa.....

Girgixa Kai Anano tayi idanuwanta na cikowa da hawaye murya na rawa tace,

Bazan iya ba..

Zaki iya.

Bazan iyaba ki aura Masa yakurah.

Dole Sai kece zakiyi sbd 'dankine zai Zama dalilin auren.

Bazan iyaba"""ta fa'da hawayen idanuwanta na gangarowa sbd mum asee tafara wuce tunaninta.

Janyota tayi da qarfi tareda cewa,

Dolene kiyi idanba hakaba Zaki 'dauki gawar shegen 'danki da gwaggonki a hannunki Dan bazakiji sirrina abanza ba.....ta bu'de qofa ta hankadata waje da qarfi ta kife a qasa.

Qafafun mutum tagani agabanta ta 'dago da sauri gabanta na fa'duwa tayi Ido biyu da zayyan fuskarsa ta ka'da tayi jajir..
Miqewa tayi jiki asanyaye tareda sunkuyar dakai zata wuce ya sha gabanta tareda nuna Mata hanyar gym room 'din saheeb da hannu fuska.

Ganin yanayinsa ba sauqi yasa ta nufi inda yake nuna Mata Dan tsoron karta Kuma Shan azabar dazata sakata rasa idanuwanta.

Suna shiga ya rufe qofar tareda zaunawa Kan wani machine ya dafe kansa idanuwansa na qara canzawa...

Rakubewa tayi cikin tsoro duk da itama tana cikin tashin hankalin.

'dagowa yayi ya kalleta ciki wani irin yanayi yace,

Me saheeb yayi muku arayuwa dakuka za6i Zama masu farautar dukiyarsa da rayuwarsa....

Girgixa Masa kai tayi cikin sanyin murya tace,

Qaddaratace takawoni Nan Kuma nasan qaddara zata daukeni daga Nan din sbd na fado cikin mutanen daban ta6a ganiba arayuwa,,,,,

Qaddarar taimako ita tarabani da komai nawa harna kasance cikin wannan mummunan halin...

Kuka tasaki ahankali tana cewa,

Tabbas zasu kashe gwaggo da abdul matuqar banyi abinda sukaceba sbd nasan zasu iya fiyeda hakan Dan sunsha yi.

Kallonta yayi tereda matsowa ya fuskanceta yace,

Tabbas tun farko nayi zargin cikin gidannan basa qaunar saheeb sbd abubuwa da dama Amma bantaba tunanin hakanba...

Cikin qureta da Ido yace,

Waye yasa abisu Abba last time?

Kallonsa tayi da jajayen idanuwanta Dan batason shiga wata masifar bayan Wadda take ciki yanxu
Yanda ya tsareta da jajayen idanuwansa yasa ta bu'de baki ahankali murya na rawa tafara zayyano Masa komai ta 'dora da fa'din ,

Sun kashe matar saheeb da Mai aikinsu hakama Abba na cikin layi nasan zasu iya kashe gwaggo da abdul bazan iya zamaba tafiya zamuyi..

Dafe kansa yayi Yana karanto innalillahi sbd zancen ya girgixasa matuqa musamman mutuwar nafeesa.

Cikin rawar murya yace,

Idan tabbas nafeesa kasheta akayi da ciki ajikinta shima sun cire..

Dagowa tayi takallesa gabanta na tsananta fa'duwa.

Bazaki je ko'ina sbd duk inda kikaje zasu biki.

A tsorace ta 'dago hawayenta na qara gudu tana girgixa Kai tareda ficewa da sauri tana sakin sabon kuka.


Vote
Comment
Share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*25*
Zuciyarta taji tana sake kar6ar komai ta bu'de idanuwanta ahankali tareda kallon zayyan tayi shiru batareda tayi maganaba....

Shima ita yake kallon yace,
Trust me Anano I will never let anyone hurt you,,,,
I will never let any harm cme to you insha Allah....

Saheeb is my only family my only friend...
Muna secondary School na rasa both mum Dina da dad,
Saheeb shine yaci gaba da daukar nauyin karatunmu harmuka gama muka shiga military school.....
Saheeb has always been there for me harnakawo matsayin danake dashi yanxu nazamo wani.

Saheeb tun Yana yaro yataso cikin wata irin rayuwar kadaici da Rashin farin ciki sbd tsawon rayuwata da saheeb banta6a ganinsa cikin farin cikiba,,,,,
He was living a loneliness life,,,
A with no one to care or been there for him,
Tun muna yara Sam shi ko wasa bayayi sbd that witch woman tariga ta kashe Masa rayuwa and Abba is always busy he has no time for him,
Baisan damuwarsa ba,baisan buwatarsa ba,baisan ciwonsaba baisan farin cikinsa ba..

Nafeesat in his life was the only first good thing that happens to him sbd yafara hangowa kansa sauyin rayuwa,rayuwar farin ciki da iyalansa sbd samun cikinta changes alot Amma saigashi lokaci 'daya sun rabasa da wannan farin cikin, again he lost all hope haryana tunanin baya cikin masu rayuwar farin ciki a duniyar nan....

Anano Insha Allah kece hasken rayuwar saheeb daya Dade baizoba,

Kallonsa tayi idanuwanta na bushewa Jin irin rayuwar da saheeb ya 'debo shekaru yanayi haryanxu..

Share hawayenta tayi cikin wata irin murya tace,

Kamar yanda tafada Zan tabbatarmada gaskiyar hakan datace lallai 'dan iska na qauye..

Kallonta yayi ganin yanda tayi maganar koba komai tafara soye zuciyarta Wanda Dole saita cire duk wani tsoro ta qeqashe zuciyarta kozata iya hakan
Hakama Dole zata cigaba da karatu sbd samun cikakken ilimin dazata iya kane kane da dukiyar tahana kowa iko da ita sbd har Abba Dole zai shiga layi coz idan ba haka mum asee zata riqa amfani dashine tana samun yanda takeso...


Kodata suka rabuda zayyan tadawo 'daki ta 'dauki abdulshakur dake wasa  ta rungume jikinta tareda lumshe idanu tanajin sabuwar qaunar yaron nashigarta sbd taqara tabbatarda shine qaddararta tunda samunshi shine mafarin komai...

Kallo 'daya gwaggo tayi Mata ta 'dauke Kai sbd ita alamarin Ananon yadaina Bata mamaki.

Da daddare harta kwanta Amma takasa bacci
Zuciyarta takasa samun sukuni Sai azalzalarta takeyi akan tunda tana zargin zamowar Abdul 'dan nafeesat to tabbas idan batai bincike ta tabbatarba to Sam baymtayiwa Abdul adalciba..,
Meyasa tasawa Abdul suna abdulshakur sbd mahaifiyarsa ta fa'da Mata sunan mahaifinsa ne....

Tashi tayi zaune gabanta na tsananta fa'duwa tareda saukowa ta nufi akwatin kayanta ta bu'de ta fiddo komai kafin taciro wani qyalle ta warware zobenda uwarsa tabata ya bayyana..

Qurawa zoben idanuwa tayi tanajin fargaba nacigaba da shigarta ta rintse idanuwa tareda miqewa ta fito dakin ahankali...

Qurawa qofar kicin dinsa idanuwa tayi na tsawon mintuna tana qara qame zoben dunqule ahannunta..

Cikin fargaba da wasi wasi ta nufi qofar ahankali takama handle din ta bu'de tareda shigewa....

Kamal da dawowarsa kenan daga yawonsa a buge yake Amma duk da haka saidaya zagayo da niyyar nemanta cikin Daren danya lallasheta Sai kawai yaga shigewarta qofar kicin din part din saheeb na bayan....

Ransane yayi mummunan 6aci zuciya ta ciyosa ya juyo Yakoma part dinsu mum asee yaci sa'a palon ba'a saka key taciki ba...

Kicin ya nufa direct yafara 6arin Kaya gurin neman wuqa Dan ya'dau alwashin kashe saheeb yau kowama ya huta....

Yakurah cikin bacci taji 6arin Kaya ta zabura zaune gabanta na fa'duwa ta sauko gadonta ahankali tareda fitowa bedroom 'dinta ta nufi kicin din cikin san'da...

Cak ta tsaya cikeda mamaki da tashin hankali kafin taqaraso da sauri ta riqesa tana Kiran sunansa...

Zuciya a qone yace,

Wai Ina kuka aje wuqaqaen gidan Nan ne you fools..

Riqesa tayi da qarfi tareda jijjigasa tace,

Wai meyene?kafadamin saina nuna ma indasuke..

Wani mugun kallo ya watsa Mata da jajayen qananun idanuwansa cikin zafi yace,

That bastard has been seeing my girl tsawon lokaci mum tasa nay shiru and now har cikin dare Yana tareda ita Yana samun ni abinda bansamuba wlh kashesa zanyi kowama ya huta idan bamu samu dukiyarsa Yana raiba ai idan ya mutu munci gado...

Wani wawan kallo yakurah tasakar Masa tana cewa,

To idanma Dan wannan ne tun wuri saika shirya Dan kuwa bashi ka'dai zaka kasheba har mum asee sbd kuwa taha'da plan din komai na ha'dashi aure da anano Kuma cikin gaggawa batareda tayi la'akari da anano takaceba.....

Shaqota yayi da qarfi cikin zafin Rai yace,

Don't you dare say that nonsense ag.....

Daqyar ta bu'de baki tace,

Let go off m you bastard am not talking any nonsense.....

Sakinta yayi cikin hasala ganin tana neman rasa numfashinta Dan muguwar shaqa yayi Mata.

Tari tafara tana shafar wuyanta kafin takallesa da jajayen idanuwanta dasuka fito tace,

You stupid ingreat this anger will kill you one day.,

Cikinta yasake yowa aharzuqe tayi saurin ja baya tana cewa,

Karka sake gigin ta6a lafiyata Kuma wannan fushin ba'anan zaka nunaba save it for your mamah Dan idan bakayi da gaskeba kanaji kana gani zata rabakada Anano,she just don give a damn about you....

A hasale ya ture kayan dake gabansa na glass Yana fidda wani irin hucin 6acin Rana Yana cewa,

Hakan bazai ta6a faruwa ba.....

Ganin ya haukace Sai wurgi yake da kayan kicin din tayi saurin dauko wayarta ta dannawa mum asee Kira.

Mum asee cikin bacci taji ringin na wayarta ta bu'de idanuwanta Sai Kuma tajiyo kamar 6arin Kaya da sauri ta miqe tareda kallon Abba daya saki jiki Yana sharar bacci tasauko gadon ahankali riqeda wayarta ta fito 'dakin ta sauko qasa da sauri...

A palo yakurah tayi saurin tareda tana cewa,

Mum Kamal is completely crazy yanason 6ata Mana plan ne....

Kallon qofar kicin din tayi kafin ta nufa qofar tana cewa,

Bar shegen maganinsa zanyi da tosashiyar kwakwalwarsa..

Kallo daya ta Masa ta 'daure fuska cikin tsananin bakin ciki da mamakin haukardayayi akicin din duk tana tunanin a buge yake.

Gabanta yazo ya tsaya cikin zafin zuciya yace,

Duk Wanda yace zai shiga tsakanina da abinda nakeso sainaga bayansa...Dan kuwa Anano tawace Bata uban kowaba.,

Takaicine yazowa mum asee wuya sbd itadai kowa yafita samun 'da wannan toshewar kansa hartafi qarfin tunaninta..

Danne 6acin ranta tayi sbd wannan fushin nasa dashi zatayi amfani takaiga cimma auren Anano da saheeb.
Cikin kulawa takallesa tace,

Kamal wayace maka rabaka za'ayi da anano,
Ni kaina Ina tsananin sonka da ita musamman kawai Dan farin cikinka....

Sbd farin cikina shine Zaki hadata aure da bastard son dinki batareda sanina......

Karkace haka Dan kuwa a shirye nake dana tsaya nayi fito nafito da kowa akan farin cikinka Dan haka kaima nake fa'da maka karkayi Sanya ka 'daga hankalin kowa musamman abbanku kace Sam baka yardaba saheeb na nemar maka matarda kake aure Kuma ka tsaya tsayin dakan kasha kamasa Yana ja maka ita part dinsa....

Harsainayi qarya tunda dai hakan tana faruwa a idona nagani yanxu hakama tana gurinsa Nagani
I will kill her this.....

Kamosa mum asee tayi takawo har qofar Palo ta bu'de ta fitar dashi tace,

Sbd toshewar qwaqwalwarka shine kazo Nan mu zakayi Mana hauka to kaje can inda ake cin amanar taka kasamu ka'dau shaidar dazata fitarda Kai gobe Dan kuwa gobe duk ubanda ya tsaya kace baka yardaba saheeb nemarma matarda zaka aura yake.

Tana fa'dar haka kuwa takoma palon ta rufe qofar tareda yiwa yakurah kallo 'daya ta wuce sama tana jinjinawa daqiqancin da Allah ya wadatar a kwanyar 'danta.

Shikuwa a fusace yabar gurin ya nufi part din saheeb Yana fatan yatarar dasu a wani mugun yanayi acikin Daren zai watsasu a Media a qarasa kwace sauran two star dinsa kowama ya huta.


Tunda tashiga palon take takawa ahankali gabanta naci gaba da tsinkewa,,

Ahankali ta lalubo switch ta kunna wutar palon tafarabin palon da kallo ta tsaida kallonta gurin qofar datasan qila nannan bedroom din matar saheeb data rasu..

Rintse idanu tayi tareda sauke numfashi ahankali kafin ta bu'de ta nufi qofar ta riqe handle din ta bu'de ahankali tareda gabanta na fa'duwa tashiga ta lalubi switch gurin qofa ta kunna Nan take tasaki qaramar ajiyar zuciya ganin batai kuskure ba Dan kuwa Dana saheeb ne tabude batasan yazatayiba acikin Daren.

Abinda tazo nema shita hango ajiye akan bedside drowr cikin wani Dan frame Mai girma ta tsaya cak tana tsoron dubawa Sai Kuma ta nufi gurin takai hannunta dake rawa ta 'dauko hoton tareda Kai kallonta ga hannuwan nafeesar dake tallafe da kumatunta duka tana murmushi gashi hoton  ya 'dauku matuqa..

A hannuwan nafeesar takai kallonta tareda qara matso da hoton fuskarta jikinta na qoqarin saki...

Hannunta tabude takalli zoben kafin tasake maida kallonta ga yatsun nafeesat ta qure idanuwanta
Nan take tasaki hoton taredayin baya sbd shakka Babu ta tonowa kanta masifa Dan har cikin ranta Bata fatar Abdul yazamo nasu Dan batasan ita kanta yazata qare dasuba bareshi da idan sukasansa ba abinda zai Hanasu rabasa da duniya Sai Allah....

Hawaye taji sun 6alle Mata amaimakon tayi farin ciki saitaji tana danasanin dubawar duk da tana qoqonto tunda ba DNA bane Amma tabbas ba shakka abdulshakur Dan saheeb da nafeesat ne.....

Motsi taji abayanta da sauri ta juyo jikinta na rawa tanajin anturo qofar 'dakin tayi saurin shigewa cikin qatuwar wardrobe din dakin zufa na karyo mata....

Tunda yashigo ya hango hijabinta tacikin wardrobe yafito Nan take ransa yaji Yana quna sbd Sam yakasa gane inane gabas inane kudun wannan yarinyar Amma zaiyi maganinta once and for all ya huta...

Tsayawa yayi tareda qurawa hoton data yarda qasa Ido Nan take idanuwansa suka canza wani irin zafi da nauyi suka ziyarci zuciyarsa ya lumshe idanuwansa Yanajin kewar nafeesat da cikinsa na qara shigarsa....

Bu'de idanuwansa yayi tareda bu'de wardrobe din da qarfi ya fixgota notee nacikin wardrobe yariqe hijab 'dinta Amma sbd fixgar dayayo Mata Bata hankali bace Sai hijab din ya 6arke gaba daya ya maqale aciki ta fa'do Masa ya kauce da qarfi arashi  shiri Sai su dukan sukayi baya suka zube a gadon dake bayansa na dakin....

Kamal daya shigo cikin san'da ya hango qofar dakin a bu'de yaqarso da sauri....
Zuciyarsa tayi wani mugun daukar zafi ya fiddo wayarsa tareda maqalewa gefe yafara daukrsu...

Shine aqasa itace ta fa'da samansa
Doguwar Rigar bacci ce ajikinta ko hannu batada gata batada nauyi ko ka'dan Sai santsi gashi ko hula batada akai..
Shikuwa dogon wandon kayan baccine ajikinsa black da black vest data Kama qaqqarfan jikinsa...

Wani wawan turi yai Mata tafadi gefe itama batai wata wataba ta miqe tareda fisgo hijabin daya maqale tayi qofa da gudu tabar part 'dinsa gaba daya.

Dafe goshinsa yayi tareda futarda wani zazzafan numfashi yanajin wani irin tsanar zaman gidan
Dole yashirya yaje dogon hutu kozai samu nutsuwa..

Tunda takoma takasa kwanciya ta nemi guri ta zauna tareda rafka uban tagumi tana tunanin abinyi akan wannan tsaka Mai wuyar....

Cikin bacci gwaggo tabude Ido taganta zaune da uban tagumi tace,

Da wannan tagumin da tashi kikayi Kai tsayuwar dare ko Allah zai kawo nutsuwa da hankali cikin kanki Dan ni wannan alamarin naki saina hada da magungunan daji...

Tabbas gwara tayi tsayuwar dare ta roqi Allah mafita Dan kuwa tana neman mafitar..

Tunda tafara salloli Bata tsayaba saidataji anfara Kiran asuba tayi tazauna ta roqi Allah akan yasaka Mata dauriya da juriya tareda bushewar Ido akan wannan alamarin Dan kuwa matuqar ba hakan tazamo ba su mum asee zasuci galabarta Kuma Dole ta kiyaye Babu Wanda zausan waye abdul,
Bazata ta6a Bari wani yasanda wannan sirrinva har zayyan Dan kuwa ta'dau alqawarin barwa kanta zobenma tamaida can kasan Kaya ta boye....

Da safe kallo daya tawa Abdul Nan take tafara hango kamanninsa da nafeesat Bai dauko komaiba na saheeb Sai hasken fata da dogon hancin...

Rungumesa tayi ajikinta tanajin tausayinsa na qara shigarsa sbd ga iyayensa tafara ganowa Amma ba damar ahadasa da mahaifinsa sbd tarin maqiyan mahaifin nasa....
Abdul koban Kare saheeb Dan komaiba Zan tsaya na karesa kodan kasancewarsa uba agareka 'dana.

Wanka tayi tayi Masa wanka suna cikin shiri gwaggo tashigo da tea ahannunta tana cewa,

Megida zoga shayin ka..

Lafewa yayi jikin ananon Yana maqalewa gwaggon kafada..

Kajimin tsohon Dan dabara yau ni kakewa wani Jan aji Dan kaga firgitacciyar uwarka na kusa....

Karbar tea din Anano tayi tana cewa,

Gwaggo qila da zafi kike basa shiyasa..

Da wuta nake basa qarewar zafi...

Dariya tayi tareda Dan zaro idanuwa tana cewa,

Haba Gwaggo da gske wuta kike basa,
Gske dai Naga yarona Yana Zama jarumiba kullum...

Muguwar harara gwaggon tasakar Mata tareda miqewa tashige toilet tana cewa,

Shegen gorar zai zamo jarumin ne idan ya nemi nabasa abinci abaki naqi..


Qarfe Tara Kamal ya fito daga part dinsa ya nufi 6angarensu mum asee har lokacin xuciyarsa Bata saukaba danma tun jiyan ko rintsawa yakasayi yanda yaga dare haka yaga safiyar badan Yana tsoron sojojin saheeb dinba datun a Daren jiyan zai 6arkawa kowa rigar mutunci acikin gidan Amma wlh yau Sai anyita ta qare....
Mum asee takirasa da sakarai akan bazai iya daukar mataki akan alaqar saheeb da ananoba toyau zai nunawa kowa bamai Anano saishi.


Zaune suke suna breakfast a dining
Abba abincinsa yakeci hankali kwance
Mum asee cin Dole kawai take tana fatar tarkon data nadawa Kamal jiya na kunnosa Akan Anano da saheeb yayi Dan yazo yatada rigima tasamu shigowa da Tata buqatar.

Banko qofar palon yayi ya nufo gurinsu cikin zafi...

Kallo 'daya mum asee Tama yakurah
Nan take ta miqe ta nufi Kamal din tana cewa,

Kamal lafiya ku.....

Bata qarasaba ya tureta cikin bakin ciki tareda cewa,

Duk gidannan munafukaine da kafurai aciki harma da azzalumai to kowama yasani nagaji da hakuri kodai Abba yadau mataki Kona dauka da kaina.....

Da sauri mum ta taso cikin tashin hankali takamo yakurah dake kukan qaryan turan da Kamal yamata tace,

Me akai maka kaketa wannan tashin hankalin Kamal?

Karma ki tambayeni Dan wlh a shirye nakeda nayi komai agidannan..

Masifa da rashin mutumci yafara zubawa musu a palon tako ina

Abba ya qaraso da sauri shima Jin alamarin yafara tsananta Dan kuwa harda Mari mum asee ta sakar Masa...

Cikin tashin hankali Abba yakalli Kamal daya taba kumatunsa yaqara harzuqa yace,

Duk Wanda zai mutu ya mutu wlh bazan yardaba..
Abba matar danake Shirin aurece kullum saheeb ke kiranta part dinsa sunacin amanata batun yanxu nake kamasuba Amma yaqi Bari to wallahi koka dauki mataki Kona yadasu a duniya kowa yasani mutuncin gidannan ya Dade Bai zubeba matuqar ba"a dau matakiba...

Cikin takaici mum asee tace,

Kamal bance karka fitar da zancen nanba gashi yanxu kana neman zubar Mana da mutunci da 6ata Mana suna
Me kake tunanin za'a riqa kallon saheeb dashi agari ace Yana neman matar qaninsa alhalin ko gama farfadowa baiyiba daga wancan iftila'in na kwanaki......

Katseta Abba yayi cikin fargaba da mamaki da cewa,

Wace matarce wannan ni ake magana..

Anano""""Kamal yafada Kai tsaye Yana cewa,

Wllh wuta zan kunnawa motocinsa kowama ya huta....

Tsawa Abba ya daka Masa Yana kallon mum asee datayi qasa dakai cikin jimami yace,

Aseeya me nakeji Yana fa'da?

Cikin nuna takaicinta tace,

Alhaji wlh nayi iyayina gurin Hana hakan gashi shi wannan Mai zafin zuciyar Sai tashin hankali yake yanason Bata sunan gidan Nan nidai wannan alamari bansan yazamu 6ullo masaba.....wannan masifa Dame tayi Kama..

Asabe Abba ya qwalawa Kira cikin zafi yace taje takira Masa saheeb da anano harma da gwaggo..

Da gudunta taje Kiran saheeb tafadawa yaronsa daya yace zaije yanxu yasanar Masa
Taje tasanardasu Anano cikin tsananin mamaki suka biyota ba 6ata lokaci...


Suna shigowa ko gaisuwar gwaggo nai amsaba yakalli Anano yace,

Meke tsakaninki da saheeb?

'dagowa tayi da sauri Sai mum asee tayi Mata wani kallo takalli abban tareda sunkuyar dakai qasa cikin wani irin yanayi tafara hawayen data qirqiro Nan take tace,

Abba Dan Allah kayi hkr ba laifina bane shine yake kirana.....

Wani sabon mamaki da takaicine ya rufe abban kenan dai da gaskene abinda ke faruwa.....

Waya Kamal yafitar cikin takaici ya nunawa Abba hotunansu na jiya Yana cewa,

Wlh andai cuceni ancuci rayuwar yayanda Zan Haifa....

Wayar Abba ya karba tareda miqawa saheeb din daya shigo cikin fararen qananun Kaya hannu yakai ya karba wayar sbd baisan meke faruwaba

Kallo daya yayiwa hoton ya 'dauke Kai tareda tsuke fuska yakalli gefen Anano Yana watsa Mata mugun kallon tuhuma....

A zafafe Abba yace,

Yimin bayanin abinda hotunan Nan ke nufi..

Kallon abban yayi da sauri Dan Bai tsammanin Jin hakanba.

Kuka Anano tasaki harda shesheka tace,

Abba Dan Allah kayi hkr karka Hana aurena da Kamal wannan qaddarace ta gifta tsakanina da saheeb Kuma Allah nidai nayi nadama....

Cikin zafi mum asee tace,

Ba Wanda zai aureki cikin yayana sbd bazan taba yardaba kizamo matar yayanaba.....

Cikin kuka Anano ta rarrafo gaban Abba hardasu shaqewa tana cewa,

Abba Dan Allah ayimin adalci sbd bani kadaici Mai laifiba Kuma qaddarace Kuma kunada 'ya mace gatanan idan akayimin rashin adalci Allah bazai Bariba yunda mace Bata 6anna ita ka'dai....

Tabbas mace Bata banna ita ka'dai shiyasa Nima bazan bar Mai laifiba yaje abanxa
Aure kuwa tsakaninki dashi ai Dole ayi tunda haryasan ya nemi matar Da Dan uwansa zai aura ai Dole ya aureta....

Zaro idanuwa Kamal yayi tareda zaburowa Abba ya 'daga Masa hannu tareda kallon saheeb yace,

Duk Wanda na Haifa na isadashi bazaiyi magana akan wannan aurenba Kuma na rufe mgnar anan Kar akuma tadata sati biyu masu zuwa za'a daura aure...


Comment
Vote
Share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*27*
*Alhamdulillah banmasan ta yanda Zan gode mukuba Amma kusani mamuh taga qaunarku da kulawarku nagode matuqa,,,ku din nawane Nagani.. thank you so very much sweethearts more especially my wattpadians....*
*Mamuh  love you guys*.😍😍😍😍


Koda yabar palon direct motarsa ya nufa yabar gidan tareda kashe wayoyinsa gabaki 'daya.,

Zayyan Abba yakira yaqara yimasa bayanin inda zasu shida aminin NASA sbd yasani Sarai ba lallaine saheeb din yafada masaba.

Zayyan din nagama waya da Abba saheeb yakira Amma yaji suka wayoyinsa arufe
Dama yasan arina Kuma koba komai yasan zuwan saheeb din bamai yiyuwa bane yanxu
Dan haka Sai kawai yashirya shida Abu suka tafi batareda sanin abban bada saheeb suka tafiba...

Yau tun safe baqin kauye dasuka iso suka qarasa cika gidan Sai hayaniyar biki suke
itadai amarya tana 'daki tareda qawayenta Sai firarsu suke cikin farin ciki da kwanciyar hankali
Lokaci lokaci idan ta tuno dawa zata aura Kuma gobene saitaji gabanta yayi mummunan fa'duwa Dan 'yan kwanakin datayi agida jitake kamar karta koma tace tafasa
Sam yanxu batajin tsoron mum asee ko ka'dan bare na Kamal data gama rainasa kallon lusari ma take Masa Amma tsoron saheeb din acikin jininta Allah ya halitta Mata shi...

Kamar daga sama taji ana cewa ga angon Nan yazo gaisuwa
Ta lumshe idanu gabanta na tsinkewa Dan tasan saheeb bazai ta6a zuwaba Sai dai in Kamal n.....

Zumbur ta bu'de idanuwanta ta miqe Dan kuwa idan Kamal ne tonan asiri zaimusu anan kowa yagane kai da silar auren qilama har fiyeda hakan zaiyi.

Hijab ta dauko dogo tasaka tafito dakin su nusaiba suka bita da kallo
Tsakar gidan ma tana fitowa suka zubo Mata idanu ta Sosa Kai tareda waskewa ta 'dau buta ta nufi hanyar bayi tana satar kallon qofar shigowa
Cikin sa'a taga zayyan yaci ado cikin suturar alfarma yana shigowa tareda Yusuf da aliyu Dan harya gama ganinsu baffa yamusu bayanin aikine Mai qarfi yariqe saheeb shine ya wakilto shi kafin gobe suxo 'daurin aure..

Aje butar tayi tareda sakin ajiyar zuciya takoma 'daki ahankali ta zauna tareda godewa Allah ma dayasa saheeb din baixo ba.

Kudi sosai da Kayan dazata saka gurin sha'anin bikin zayyan yabayar kafin ya juya kusan da yamma Kuma harya tafi Bai gantaba tana 'daki.

Da dare gwaggo da wata 'yar qanwar Inna suka kawo wani uban lalle daya yini a kwa6e sukace daura Mata zasuyi ta kwana dashi
Kallo daya tayiwa lallai ta kalli gwaggo tace,

Gwaggo wannan lallan idan na 'daura na kwana dashi ko kofin Dana riqe saheeb bazai sake kallaba bare yaci abin hannuna...

Baki su gwaggon suka sake Amma ita gwaggon tasan saheeb din zai iya yanda ta fa'da 'din Amma Kam yaza'akai amarya ba lalle kitso ma tun safe aka kirawo maiyi Amma ta murje idanuwanta ba kunya tace saheeb din bayason kitso.

Zama gwaggo tayi kusada ita tareda karbar robar lallen ta aje gabanta tace,

Anano Ina za'akai amarya ba lalle ba kitso saikace mugun aure..
Ki daure ko irin na 'yan gayune saiki 'daurashi kobai Kai safeba da tsakar dare saiki wanke Kinga fa kwana biyu zali tayi tana yanka Miki wannan salatif din irin zanen Yan gayu..

Kallon salatif din tayi taga yanda aka yankashi kamar za'a daura a qafar mutum biyar ta karba tareda ajewa gefenta tace,

To Zan daura da kaina gwaggo.

Suna fita ta jawo robar lallen ta daura a yatsun qafafuwanta Dana hannuwanta tana tunanin yanda komai na aurenta yazamo wani iri
Harta gama ta kwanta zuciyarta na wani iri.

Washe gari.
Tunda ta tashi sallar asuba takasa komawa ta kwanta jikinta gabaki 'daya a mace yake gashi 'daurin auren na safe ne qarfe goma..

Tun asuba gidan aka fara kaida kawon ayyuka har gari yayi haske lokacin 'daurin aure ya gabato su Yusuf da sauran samarin gidan suka shishirya tsaf
Tuni qofar gidan tafara cika da jama'ar daurin aure na qauyen.

Tunda suka hadu da Abba sallar asuba a masallaci abban cikin daurewar fuska yabasa umarnin shiri cikin lokaci daga haka ya tafiyarsa yabar saheeb din cikin wani irin yanayi...

Qarfe bakwai yamiqe yashiga toilet yayo wanka Yana cikin shiryawa zayyan tareda miqa Masa Kaya.

Ko kallon gefensa baiyiba ya wuce closet dinsa ya 'dauko wasu kayan...

Dariya zayyan yayi yace,

Banifa naKar zomonba rataya aka bani.....

Cikin milk Australian gezna yashirya tareda fesa turarensa ya fito Yana daura agogo wayoyinsa ya kwasa suka fito har lokacin fuskarsa a 'daure take..

Abba da sauran jama'arsa dama tuni suka wuce
Suna fitowa yaga motocin sojoji kusan goma ya sake 'daure fuska tareda watsawa zayyan wani mugun kallo suka shiga mota suka kwasa a guje suka dau hanya...

Kamal daya fito da gudu daga part dinsa ya daki iska cikin tsananin baqin ciki da qunar zuciya sbd tun jiya ya shirya zarewa motocinsu saheeb din burki Amma wani mugun bacci ya 'daukesa bayan yasha drink gurin mum...

Qyaci yayi cikin zafin zuciya yace,

Zaku dawo gidan daka Kai har ita idiot din zanyi maganin kowa har useless dattijon Nan daya ha'da auren har mum asee sbd bazai ta6a yafe wannan cin amanarba,,,, you'll all gonna pay for this idiots...


Qarfe goma da saura mintuna goma Sha biyu suka iso Nan qauye rikice da hayaniya sbd ganin sojoji mota mota kamar wa'inda sukazo kwantarda tarzoma...
Lokacinda saheeb din yafito yaqaraso ba baffa kawai yaji da'din ganin mijin Anano ba kaf su aliyu sunji Dadi Nan aka fara gudanar da 'daurin auren...


Tundata tayo wanka tazo ta shirya cikin doguwar Rigar wani tsadadden lace black Mai adon purple daya fitar da hasken fatarta matuqa Nan take tafito amaryarta ta shirya abdulshakur shima cikin adon sabbin kayansa da zayyan din yasako Masa shima.

Zaunawa tayi tareda 'daurasa Kan cinyarta tana basa sabuwar Madara da aka kawo Mata Tasha..

Kallonsu nusaiba tayi tace,

Anano kibani 'danki Mana kafin kugama cin amarci...

Murmushi tayi ta bu'de baki zatayi magana shigowar hamma Yusuf da goron daurin aure cikin gidan Yana fa'dar andaura ne yasa bakinta nauyi gabanta yayi mummunan fa'duwa..

Rintse idanuwanta dasuka kawo ruwan hawaye tayi
Su ubaidah kuwa fita sukayi tsakar gidan Sbd cewa da akayi ga angon Nan shigowa ya gaida iyaye Mata.

Sake rintse idanuwanta tayi lokacinda taji qamshin turarensa har cikin dakin ya shiga hancinta.,

Jiki a mace ta miqe daukeda abdulshakur ahannunta taje bakin window tana tsaya Yana qarasa shigowa tsakar gidan gabaki 'daya Kuma Kai tsaye cikin idanuwanta nasa idanun suka fara sauka...
Saurin barin bakin windon tayi zuciyarta na bugawa da sauri takoma bakin gadon ta zauna da sauri.

Cikin qarfin hali ya gaggaisa dasu yafito sbd tsananin zafinda zuciyarsa ke Masa musamman ma yanxu daya ganta itada bastard son dinta.
Sosai zayyan da Abba sukaita sakin kudi suna rabawa maroqa da Yan qauyen har aka watse suka juyo da niyar Sai washe gari za'a Aiko motar daukar amarya.

Koda suka koma tuni gyaran part dinsa yayi Nisa sbd fitar da komai da akayi akayo odar sabo bedroom dinsa ne kawai ba'a ta6aba sbd gudun laifi hakama ba laifi mum asee ta Tara jama'arta anyi taro na musamman na auren 'danta..kaman yanda take fa'da.

Baidawo gidanba Sai dare Koda yadawo angama gyaran komai part din ya canxa sosai saidai hotunan nafeesat ko daya ba'a daukeba suna Nan maqale inda suke saima gogesu da'akayi aka mayar..

Bedroom ya wuce ya shige toilet yayo wanka yaxo ya kwanta...
Asuba nayi yayi wanka ya shirya ya nufi masallaci acan yasanarda Abba tafiyarsa qarfe bakwai na safen..

Cikin sakewa Abba yayi Masa adduar Allah ya tsare Dan dama shidai burinsa ayi auren yananan..

Yana komawa 'daki ya harhada abinda zai buqata ya sake shiryawa cikin qananun Kaya black da blue leather jacket yafito daidai isowar zayyan dazai kaisa airport
Ya shiga mota suka wuce..

Jirginsa na tashi zayyan yadawo gida yahau Shirin zuwa 'dauko amarya sbd shine zaije.

Qarfe goma aka sata ta shirya baffa ya zaunarda ita yayi Mata nashiha shida gwaggo duk da da ita zasu koma
Hakama su Yusuf kowa yayi Mata tasa kalar nasihar..

Sosai jikinta ya mutu da nasihar su baffa Dan ma basusan wane irin aurene ba tayi.

Babu abinda ta 'dauka Sai kayan da zayyan yakawo Mata
Qarfe biyu zayyan ya iso qarfe uku suka juyo daga ita Sai gwaggo da nusaiba ubaida mijinta Bai bartaba Sai jafar dake gaba...

Tunda suka dau hanya jikinta ya qara saki tsoro da fargabar yanda zata ha'du da saheeb din take.

Gab da magriba suka iso Nan su mum asee da wasu baqinta suka tarbesu a aladance suka rakasu har part din saheeb har cikin bedroom din nafeesat dayake amatsayin nata yanxu..

Gwaggo 6angarenta ta nufa tareda nusaiba sbd basusan saheeb din baya gariba..

Bata tsaya wani dogon jiraba sbd tasan ba kamar kowane aurene wannanba dazata jira ango ta miqe jiki asanyaye tana kallon tsari da haduwar kayan dakin da'aka canza tana qara mamakin inda aure yakawota harta fa'da toilet tayo wanka tazo ta bu'de akwatinta ta canza Kaya tayi sallar la'asar dabasuyiba da magriba..

Tana idarwa taji ana knocking qofar bedroom din
Gabanta yayi mugun fa'duwa jikinta na saki ta miqe ta bu'de cikin fargaba.

Asabe tagani tareda wata sabuwar Mai aiki budurwa tasaki fuska suka gaisa asabe tace,

Abincine mum asee tace akawo..

Kallon kulolin hannunsu tayi kafin tace,

Su aje dining
suna ajewa suka fice ta fito palon cikin fargaba ta nufi qofar kicin tabita qofar kicin din ta fa'da dakin gwaggo..

A zaune ta tarar dasu suna hutawa tazauna gefen nusaiba tareda gyarawa abdul kwanciyarsa tana  cewa,

Nusy ga abinci acan kixo muje mudauko saimuci anan..

Muguwar harara gwaggo ta watsa Mata tana cewa,

Kedai wlh anyi gantalaliyar amarya Mara kunya,
Yanxu da ace saheeb din Yana gari haka Zaki taho kibarosa?
To Allah tsaya kiji matuqar kikace wannan zaryar gantalin Zaki riqayi zuwa Nan kayana Zan ha'da nakoma gida tunda dama Dan kina ganinane,
Abinci mun Riga munci ki tashi maza ki koma 'dakinki..

Miqewa tayi jiki a salu6e ta duqa ta 'dauki abdulshakur ta sa6a akafada ta Fice gwaggo tabita da harara ko Abdul dinma Dan taji asabe tace bayanan ne yasa tabarta ta tafi dashi.

Washe gari tunda safe nusaiba da jafar suka wuce Abu driver Abba yasa yamaidasu..

Bayan kwana biyu
Qarfe goma da rabi ta shiryo cikin wata dark blue atampar super exclusive batareda tayi kwalliyar komaiba Amma duk da haka sosai tayi kyau cikin shigar ta fito ta riqeda hannun abdulshakur dake koyan tafiya ta nufi gurin gwaggo suka gaisa tabaro abdul din ta nufi part dinsu mum asee.

Tana kaiwa qofar part din da Kamal tafaracin karo ya tsaya gabanta Yana watsa Mata wani mugun kallo zuciyarsa na mugun tafasa...

Dauke Kai tayi tareda ra6asa zata wuce a zuciye ya fixgota tadawo baya
Bata tsaya Bata lokaciba ta yanka Masa wani lafiyayyan Marin dayasa su mum asee qarasowa cikin wani mugun yanayi..

A zafafe ya 'daga hannu zai sakar Mata Marin yaji anriqe hannunsa ya juyo cikin zafi yaga zayyan tareda Ahmed zubair Barr Kuma PA na saheeb..

Kallonsa tayi cikin daure fuska tace,

Ka dawo hankalinka idanma gushe maka yayi kasan da matar babban soldier kake
Ka gode Allah baya gari da baka qara marmarin ko kallon matarsaba bare ganganci ta6awa....

Ba Kamal kawaiba hatta mum asee da zayyan sunyi matuqar mamakinta bare Ahmed daya fito da idanuwa ganin matar saheeb din ta yanxu taci uban marigayiya Dan nafeesat sanyi qalau take.....hmmm lallai akwai rigima tafe Amma Bari yagani...

Gyara tsayuwa yayi tareda kallon mum asee yace,

Mum asee dama maganar ku'din da ake bayarwane na duk wata na biyan ma'aikatan gidan da bills na gidan nakeson sanin sabon lissafinku tunda oga yayi aure yanxu Dole lissafin zai qaru.

Kallonsa tayi a wulaqance tace,

Banda wannan lokacin kaje ka qara dubu 'dari asama......

Zaro idanuwa yayi tareda gyara zaman medical glass dinsa yabude baki zaice to cikin 'daure fuska Anano ta katsesa da cewa,

Wayene Mai biyan bills din?

Oga saheeb ne madam..

Nawane?

Dubu 'dari biyu ne duk wata madam....

Sake daure fuska tayi tareda satar kallon zayyan ya gyada Mata Kai a fakaici saita juyo ta kalli Ahmed din tace,

Cancel wannan lissafin sbd nice matar saheeb nice Zan riqa bada duk wani lissafin abunda ake buqata matuqar daga dukiyar mijina zata fito daga yau kaje jibi zan nemeka idan nagama lissafin nakumayi magana baby anjima....

To yace tareda juyawa yabar gurin Yana danne tsananin mamiknsa
Zayyan ma bayansa yabi Yana jinjina alamarin....
Hmmmnn su saheeb baby manya.

Suna barin gurin ta juya zata wuce mum asee ta riqo hannunta cikin wani irin mugun 6acin rai.


#vote
#comment
#share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*26*
Hannuwa saheeb yazuba cikin aljihun wandonsa tareda yiwa anano kallo daya yabar palon Dan kuwa Sam shi baiji maganar auren ajikinsa ba sbd yasan abune dabazai ta6a yiyuwaba
Yama gama aureshi bare Kuma ace dame 'dan shege zaiyi aure tagama watsewarta atiti cikima harda qaninsa mitsw.....

Kamal na ganin Abba da saheeb sunbar palon ta saci kallon gefen gwaggo datayi mutuwar zaune cikin tsananin mamaki Dan ita Sam Bata gama fahimtar me ake nufiba da wannan taron....

Kamal dayakejin zuciyarsa zatayi bindiga ta watse tsabar baqin ciki da takaici yayo Kan Ananon
Ta miqe tsaye tareda 'daga Masa hannu tana wurga Masa wani mugun kallo take ta share hawayen qaryar datayiwa abba tace,

Karkama fara matsowa gabana kace zaka nunamin halin dabbobinka Dan kuwa yanxu ba Mai 'dauka bace wannan matar sojace kana matsowa zansa su canzamin kamanninka shashasha kawai...

Mum asee takalla tace,

Ki fahimtar da shi gskia Dan bazan juri wulaqancin duka yayanki biyuba da soldier da tantiri......

Kallon gwaggo dake qara fiddo manyan idanuwanta cikin mamaki da tsoro tayi tace,

Muje gwaggo..

Kamar wawiya haka gwaggo ta miqe suka fice mum asee da Kamal suka bisu da kallo baki sake
Musamman ma Kamal dayafi kowa qunar zuciya..

Mum asee kuwa wani shegen murmushin gefen baki tasaki Dan kuwa ba laifi qarfin halin ananon zaisa ta iya Zama da saheeb kobai so
Da alama bazasu Sha wuyar samun abinda sukesoba...

Ha'da idanu da Kamal dake kumbura tayi tai saurin barin gurin ta nufi hanyar stairs ta Haye sbd batada lokacin rashin hankalinsa yanxu....

Yakurah ce tadan matso kusadashi taci gaba da zugashi tako Ina tana qara hura Masa huta ya fice palon a zuciye Yana ayyana bala'in dazai qullowa gidan....

Suna shiga daki gwaggo ta tsaya kanta tace,

Yimin bayani dalla dalla akan abinda yafaru yanxu..

Kallon gwaggon tayi cikin marairaice fuska kalar tausayi kamar zatayi kuka tace,

Kamal ne sbd tsabar jahilcin tunaninsa yake zargina da saheeb nida duka zamana agidannan so nawama na ta6a ganin saheeb din....

Sharrr hawaye suka balle Mata cikin kuka tace,

Yanxu gashi Abba yace,

Ha'da aurena zaiyida saheeb
Yanxu me zamu cewa su baffa
Shikenan zargin da'akemin zai tabbata,,,.

Sanyi jikin gwaggo tazauna kusada ita tareda jawota jikinta tace,

Gskia Kamalu Bai kyautaba yayi Miku mummunan zargi Dan kuwa ku duka biyun Zan iya shaidarku...
Amma mu gode Allah dahaka ta faru tun yanxu Dan dakin aure kamalun yazo Yana zarginku bayan aure da Abu baiyi kyauba.....

Gskia Nima wannan magana bazan iya fadawa baffa ita Kai tsayeba cewar sbd ana zarginku tare aka hadaku aure,
Shiru zamuyi idan sunje su nemi auren kawai batareda ansan dalilin yinsaba....

Kallon gwaggon tayi da sauri tana qara matso hawayenta tace,

Ni gwaggo banason auren Nan sbd.....

Karkice haka Anano kedai ki roqi alkhairin Allah aciki sbd nikam har cikin Raina naji da'din wannan hadin duk da baixo ta hanyar da'diba.

Qasa qasa tasaki qaramin murmushi ganin ta rusga gwaggon cikin ruwan sanyi batareda ta wahalaba kamar yanda ta tsammata....

Yana fitowa Kai tsaye motarsa ya nufa soldiers dinsa suka taso yayi saurin 'daga musu hannu tareda karban key ya fa'da motar..

Jabiru na ganin haka ya zabura da sauri ya bu'de gate tunkan Rana ta 6atar Masa
Abu kuwa dama matuqar sojojin na gida baya wani dogon motsi Yana zaune abinsa saisun fita suke fira shida jabiru harda qyaqyatawa..

Direct gidan zayyan ya nufa dake cikin anguwar
Mai gadinsa na hango motar yayi saurin bu'de qaton gate din gidan..

Yanayin parking yafito ya nufi qofar palon gidan Yana kashe wayoyinsa Dan yau baya buqatar magana da kowa.

Ba kowa apalon Sai qatuwar tv dake aiki Sai sanyin AC da qamshi daya cika palon.
A doguwar kujera ya xube tareda aje car key da wayoyinsa Kan centr table..

Lumshe idanuwansa yayi maganganun Abba suka fara dawowa cikin kansa...

Cikin three-quarter na sojoji da white singlet zayyan yafito bedroom riqeda waya a kunnensa yanayi baisandashiba Yana ganinsa ya datse wayar Yana Masa kallon mamaki ya nufi fridge saidaya 'dauko robar ruwa yasha ya nufosa Yana cewa,

What's up man????? Yaushe kashigo ne.

Bu'de idanuwansa dasuka ka'da yayi kafin yatashi zaune yakalli zayyan din yace,

Zanyi doguwar tafiya...

A break?? Zayyan ya fa'da cikeda mamaki...

Wane irin break kanal ana zaune qalau,
Did sumtin happen ne?

Mayarda kansa yayi jikin kujera yace,

Abba yafara maganan aurene Kuma kaman this time ya'dau abin da zafi and nikuma banajin wannan karon zanma iya kwatanta abinda yake fa'da bare yinsa coz it's totally impossible and completely.......
Kasa qarasawa yayi ya rintse idanuwansa wani zafi yakeji Yana yawo azuciyarsa sbd ko maganan bayason tunawa bare yafada da bakinsa..

Kallonsa zayyan yayi zuciyarsa na sanyi da tausayin rayuwar saheeb din Dan yasan maganar aurensace da anano Amma Dole hakan shika'dai ne mafita Kuma kariya agaresa Kuma yariga yasan Sarai saheeb din bazai iya tsallake maganar Abba 'din ba.....

Remote ya'dauka Yana canza Tasha yace,

In that case sainace happy holiday man...

Kallon mamaki saheeb ya jefo Masa ganin yanda yayi Masa ko inkula da zancen..

Miqewa yayi ransa a6ace ya kwashi wayoyinsa yayi hanyar bedroom din yashige...

Kunna wayarsa daya yayi yakira Samuel Nan take yabasa umarnin yashirya Masa komai na tafiya Sydney Nanda kwana biyar zuwa sati 'daya...
Bai koma gidaba Sai qarfe goma saura na dare
Yana shiga harabar gidan ya hango Abba acan sama tsaye a balcony 'dinsa Yana waya kallo 'daya yayiwa gurin ya sauke Kai yayi parking yafito tareda nufar part dinsa Kai tsaye...

Washe gari da safe Abba ya aikowa gwaggo cewar su shirya abu zai kaisu gida sbd yagano musu gidan Dan jibi zasuzo neman auren dakomai kamar yanda yafada insha Allah..

Cikin farin ciki gwaggo ta ha'da musu kayansu tsaf sbd itadai tana farin ciki matuqa da wannan alamari idan harya tabbata..

Anano dai kadaran kadahan takejin kanta duk da tana tsananin son ganin iyayenta Amma batasan ya zasu karbi zancen aurenba cikin sati biyu da gaggawa haka.,
Amma dai koma meyene zata nunawa  baffa tana son saheeb din matuqa Dan tasan bazai hanaba..

Tunda suka hau hanya taji jikinta yayi tsananin sanyi sbd tasan idan Allah ya yarda anyi wannan auren Koda zata koma gidan amatsayi nadaban zata shiga gidan Kuma a muhalli na daban Wanda batasan yazatayiba Zama cikin guri daya da saheeb ba Dan kuwa tasan bazata ta6a raba kanta da tsoronsa ba Amma alqawarine ta dauka bamai sake ganin tsoronta,kukanta ko weakness dinta sbd hakan zai iya ruguzata yabada damar samun nasara akanta..

Har qofar gida motar ta Isa bayan motar tayi futik da qasa...

Suna tsayawa jafar da Usman na fitowa Nan suka qaraso cikeda farin ciki da Mamakin ganinsu suka tarbesu jafar ya kar6i abdulshakur dake hannunta daqyar ya yarda yaje gurin jafar din.

Abune ya fiddo da kayansu suka kwasa suka shiga ciki...

Cikeda farin ciki baffa ya tarbesu Dan kuwa duniya Yana tsananin qaunar 'yar uwarsa da ananonsa..

Nan da Nan suka baje a tsakar gidan Inna tafara kawo musu abinci da fura bayan hamma Yusuf yakaiwa Abu
Yana gamawa yakama hanya ya juya.

Cikin farin ciki baffa yakalli abdulshakur dake Kan cinyar Anano Yana cin dambun gyada yace,

Jafar kaga 'danku ya girma yayi wayo ko?
Cikin farin ciki yace,

Baffa ai saima ya girma yaxama soja tukuna...

Cikin farin ciki gwaggo tace,

Kamar kuwa kasan auren soja zasuyi Dan zancen nema yakawo mu Anano dai tasami miji babban mutum kuwa kuma soja ko acikin sojoji...

Baki jafar ya washe Yana kallon ananon data sunkuyar dakai su Yusuf ma duk bakin suka washe cikin farin ciki
Baffa kuwa kallon gwaggo yayi yamaida kallonsa ga ananon kafin yakalli inna dako bata fa'daba farin ciki ya bayyana afuskarta sbd kullum zancenta da fargabarta Taya Anano zata samu mijin aure tana tareda 'da ana Mata kallon ta haifi shege..

Jinjina Kai baffa yayi yace,

Hindatu waye wannan me sa'ar dayakeson auren ananon baffa.?

Hmmn aikaida baffa Anano dai Kam tayi sa'a itama Dan yaron akwai hankali da nutsuwa uwa uba sanin girma da darajar na gaba..

To hindatu yasan da maganar wannan yaron?

Yasani kuwa Dan da'aka kwantarda abdul din asibiti shiyayita Mana hidima..ataqaice dai baffa shine Wanda nake Zama gurinsa Wanda Mai 'dakinsa ta rasu...

Nan gwaggo ta 6alle tafara korowa baffa saqon Abba dakuma auren dasukeso cikin qanqanin lokaci..

Sosai baffa ya jinjina alamarin Amma dai zai jira zuwansu Abban jibi.

Da daddare haka ta saka hijabinta tai gidansu nusaiba acan sukasha firar yaushe gamo saidataga dare yayi tadawo gida bayan sunyi washe gari zasuje gidan ubaidah da'akai aurenta wata uku kenan.

Washe garima bata yini agidanba itada nusaiba suka yini gidan ubaidah Nantagaya musu duk abinda yafaru a wancan lokacin..

Da marairaice tadawo gida ta tararda abdulshakur ya daga musu hankali rashin ganinta Nan tayi Masa wanka itama tayi suka zauna shimfidar baffa daya dawo sallar magriba suka fara fira gwaggo da Inna kuwa Sai kaida kawon suyar Naman kaji da man shanu sukeyi na tarbon su Abba gobe.

Fira sukeyi sosai da abbanta anan ya tambayeta kotanason auren saheeb din ba 6ata lokaci tace eh,

Aiko washe gari su Abba da wuri sukazo Nan akai magana akakai qarshe suka bada ku'din aure da komai aka tsayar da Rana juma'a Mai zagayowa suka wuce.

Tunda aka tsaida ranar aka hanata ko fitowa tsakar gida kullum tana 'daki itada nusaiba data tare gidan har agama biki hakama ubaidah kullum tana hanya hardai bikin ya qarato daurin aure ya rage saura kwana uku..

Cikin qananan Kaya dark blue da facing cap dinsa ta soldiers yashigo palon
Kallo 'daya zakai Masa kaji yatafi da dukkanin nutsuwarka sbd yanda ya iya shiga kyawunsa da hasken fatarsa su fito sosai..

'dan risinawa yayi ya gaida Abba tareda komawa kusada mum asee ya zauna Yana kallon yanda fuskarta da idanuwanta suka kumbura sbd kuka da rashin bacci cikeda kulawa murya qasa yace,

Mum please kicire damuwar Nan indai akan tafiyar dazanyi ne.....

Cikin gatse Abba dake karatun jarida yace,

Bayan auren nakane zakayi tafiyar ko kuwa?

Qasa yayi dakai yace,

Abba gobene tafiyar.

To matar taka ya kakeso muyima da ita..?

Shiru yayi cikin wani irin yanayi Dan kuwa baya iya yiwa mahaifinsa musu sbd shikadaine garesa Wanda zaibi yasamu Lada.

cikin sanyin murya yace,

Abba tafiyar aikice ayimin afuwa..

Kallonsa abban yayi saiyaji yabasa tausayi yace,

Shikenan Amma kafin katafi kayi qoqari yau Abu yakaika kaida zayyan kuje ka gaida iyayenta sbd karsuga bakajeba Kuma bakaje daurin aurenba..

To yace tareda miqewa yabar palon zuciyarsa na wani irin quna..

Vote🤨
Comment
Share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*28*
'dan fiddo da idanuwanta tayi tareda jujuyawa ko Ina tayi qasa da murya tace,

Mum yi ahankali Kar wani yagani cikin yaran saheeb su rainani inzo inason Basu umarni suna qin bi...

Wani mugun kallo mum asee tasakar Mata Saida taji gabanta ya'dan Fadi ta ha'diye wani yawu tareda sakin murmushin qarfin zatayi magana mum asee ta katseta cikin wani irin yanayi tace,

Kibi ahankali fa karkibari rawar kanki tasaki wuce wurinki Dan kuwa bazaki Kai wani dogon labariba,,,kisan dawa kike karkiyi gangaci da rayuwarki..

Sakinta tayi ta juya ta shige palonta Kamal da tuni yayi mutuwar tsaye sbd baqin ciki gashi baiji Mai suka tattaunaba yajuya yabar gurin Yana qissima wani mummunan nufi a zuciyarsa..

Sanyi taji jikinta na nemanyi sbd tabbas tasan waye mum asee tasan dawa take dealing amma itama dolece tunda ba wata hanya ko mafita yanzu idanba wannan dinba Kuma matuqar Bata fara da hakanba bazata samu su hada duk wata shaida dasuke soba ta tona su mum din
Dan ko sunso tonasu yanxu basuda wata qwaqwaran shaidar gabatarwa...

Juyawa tayi ta jiki ba qwari takoma gurin gwaggo ta 'dau Abdul suka koma..

Abinci ta 'daura musu itada Abdul din sukaci suna gamawa yayi bacci takaisa 'daki kwantar bayan ta rage Masa qarfin ac
Takoma kicin taci gaba da ayukanta
Ta gyare kicin din tadawo Palo tazauna tana kallon tashar cwtv.

Washe gari da safe zayyan zo tareda takardunta dayasa aka kar6o Mata na gama makaranta..

Drinks din data kawo Masa ta aje tareda Zama cikin sanyin murya tace,

Mum asee tafara tambayata akan nafara gaggawar aikata abinda yasa akayi auren.

Wayarsa dake ringing ya fitar Yana cewa,

Karki damu da wannan kicigaba da yanda Kika fara dinnan sbd rashin hakuri da zafin zuciyar Kamal agurin mum ya gado abinsa coz Sam itama batada hakuri.,
Idan Kika cigaba da kunnasu cikin qanqanin lokaci zasu fara fiddo da halayensu,

Yanxu dai kishirya gobe Ahmed zaizo yakaiki siyayyar Kaya da duk wani abun buqatarki saikuma maganar jamb dinki yau za'a cika komai insha Allah..

Miqewa yayi tareda miqa Mata kwalin wayar iPhoneX yace,

Bari natafi baby saheeb ne ke kirana Kar ya hasala kinsan halinsa...

Sunkuyar dakai tayi tana dariya cikin kunya sbd tasan tsokanar zancenta na jiya ne yakeyi.

Yana fita ta fiddo wayar ta kunna tayita dube dubenta kafin ta maqala charging Dan Sam Bata iya wayarba.

Da marairaice gurin gwaggo takai abdulshakur tasamu tagama aikinta sabuwar Mai aikin da mum takawo Mata tana tayata duk da tana zargin sbd saka Ido aka kawo Mata ita.


Washe gari Ahmed yazo Koda yakirawo wayarta da zayyan yabasa number yasanar Mata ya iso
Ta shirya ta fito riqeda wayarta ta nufi part dinsu mum sbd taga motar Abba Kuma ta tabbatarda Yana gida.

Cikin sa'a kuwa ta tararda dukkaninsu a palon ta sunkuyar dakai ta gaida abban cikin girmamawa
Fuska cikeda walwala ya amsa tareda tambayarta Abdul.

Sunkuyar dakai tayi cikin ladabi tace,

Mum Ina wuni.?

Baki mum asee da yakurah suka  saki cikeda mamakin mugun ladabin data nuna,
Cikin sanyin murya tasake bu'de Baki tace,

Mum fita nakeson nayi Zanje asibiti shine saheeb yace karna kuskura nahau adaidaita....

Katseta Abba yayi da cewa,

Dama Kam ai baza'a Bari kihau napep ba ga motocin mijinki Nan aje acikin gida..

Kallon mum yayi yace,

Kwaso Mata gabaki 'daya mukullan motocin saheeb kibata ta ajiye ahannunta tunda dai yanxu itace matarsa duk lokacinda zata fita ta 'dauka drivernsa nanan.

Wani qululun baqin cikine ya danne zuciyar mum har wani 'daci 'daci ta ringa ji ta miqe taje takwasosu ta miqawa Ananon
Cikin sanyin murya tace,

Aa Abba abarsu 'dayama ya Isa..

Aa ki kar6a duka ki adana Masa sauran ai dama sbd rashin iyali ne wasu abubuwan suke Zama ahannun mu iyayensa ai tunda ya aje iyali yanxu Kam aimuma saimu huta..

Hannu biyu tasa ta kar6a tareda kallon fuskar mum asee dake turnuqe zuciyarta kuwa suya take matuqa.

Ficewa palon tayi Kai tsaye tareda zuba mukullan cikin handbag 'dinta tana sakin murmushi..

Nabeela itace budurwar zayyan dazai aura,
Kyakkyawar matashiyar datake gab da kammala karatunta a jami'a,
Nabeela ta waye sosai Amma ba irin lalatacciyar wayeba,
Hakama she's very fashionable Dan haka zayyan yasameta yasanarda ita so yake ta kusanci Anano amaryar saheeb sosai sbd so suke tazama fashion and classy ta waye sosai ta yanda zataji da'din tsula tsiya agidan.

Dan haka suna fitowa cikin wata fitinanniyar motar saheeb din black suka nufi gidansu nabeela
Tarba Mai kyau tayi Mata cikin sakewa suka gaisa da mummynta  kafin suka fito suka nufi gurin shopping.

Ahmed ne agaba da driver itada nabeela suna bayan motar harsuka iso wani qaton mall suka shiga.

Siyayya sosai sukayi Wanda duk nabeelarce Mai zaba Dan kuwa Nanda Nan ta ha'da Mata wani irin lefe guda musamman mayuka masu tsadar gske da Arabian ouds masu matuqar sanyi da da'din qamshi,

Ta 6angaren takalma kuwa kusan  gabaki 'daya hills ta 'daukar Mata wasuma tasan kawai ansiyane Amma ko sawa bazata iyaba bare tafiya,
Laces, atampopi da dogayen riguna gabaki 'daya masu tsada ta jidar Mata
Ita kuwa harda 'danta tayi siyayyar designers Kaya kafin suka gama suka fito.

Ahmed ya biya komai Yana jinjina yawan ku'din dasuka kashe duk da ko kwatan wa'inda mum asee ke kashewa basuyiba.

Daganan gurin dinki suka nufa nabeela ta bayar kafin suka koma gida Nan gurinta nabeela ta qarasa yinin suna ta6a fira har maraice kafin zayyan yazo yadauketa yamaidata gida.


Tundaga lokacin nabeela tafara qoqarin ganarda ananon komai dayake a shirye take Nan take tafara canzawa musamman hutu daya fara ratsata da lafiyayyun mayukan dasuka qara gyara farar lafiyayyar fatarta.

Gabaki 'daya suturarta kusan Babu qarama ga uwa uba mota da zayyan yasa aka duqufa koya Mata batareda sanin mum asee ba.

Sosai mum asee keson ganinta amma rashin zamanta a 'yan kwanakin yasa Bata ganinta..

Cikin qanqanin lokacin suka Saba da nabeela sosai gashi ansamu cigaba sosai Dan kuwa tuni gayu da hutu tareda class yafara hudata ga wani haske da qyalli da fatarta taqara...

Yau tunda safe mum asee ta Aiko asabe kiranta
Tana gama breakfast tabarwa nuratu Mai aikinta abdul ta tafi Kiran mum din.

Cikin sakewa ta gaida Abba dazai fito kafin tashiga suna ha'da Ido da mum tasaki dariyar mugunta cikin ranta.

Mugun kallo mum Asee ta jefa Mata zata magana ananon tarigata da cewa,

Mum Ina wuni?

Sake 6aci ranta yayi xuciya tazo Mata iya wuya Amma dayake ba'a nuna Mata munafurci saita saki murmushi sbd tafara zargi tareda ganowa ananon son Raina Mata da wayo take cikin sakewa tace,

Me kikeyi akwanakin Nan ne dabakya Zama?

Murmushi tasaki tace,

Mum koyan gayu nake zuwa kafin saheeb yadawo sbd nidai duk iya tunanin yanda zanyi na samo abinda akeso nayi Amma Naga ba mafitar data wuce nakoyi yanda Zan samesa a tafin hannuna ta hanyar 'daukar hankalinsa..

Shiru mum asee tayi cikin tunanin to Kuma ai idan da gske take hakanma zaiyi...

Cigaba tayi da fadin,

Amma Kuma mum Ina 'dan Jin tsoro musamman ma idan na tuno kowane lokaci zai iya dawowa..

Katseta mum aseen tayi da cewa,

Bawai zai iya dawowa bane
Yanama Nan dawowa gobe shiyasama nakiraki Danna tunatar dake abinda yakaiki gurinsa ko kamawa tayima ki Zuba Masa guba ki Zuba Masa 'din idan har zamu samu yanda mukeso.

Sam bataji mamakin zancenba tace,

Karki damu mum Nima Dole zanyi qoqarina Dan bazan yarda nabar wannan dukiyar Dana fara lasawaba tawuceni.

Murmushin Jin da'di da mugunta mum asee tayi tanabin bayan ananon da kallo..

Tana komawa a Palo ta zube tareda dafe zuciyarta dake bugawa da qarfi Jin cewar saheeb gobe zai dawo..

Qarar wayartace ta katseta tana dubawa taga nabeela ce cikin sanyin murya ta daga.


#vote
#comment
#share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*30*
'dauke Kai tayi gabanta na tsananta fa'duwa musamman yanda ya kafeta da idanuwansa dama tanason fa'da Masa maganar abinci ne gashi gabaki 'daya ta rasa nutsuwarta tunda ya kafeta da idanuwansa.

Ganin batada niyar magana ya 'dauke kansa ya mayar Kan wayarsa Yana cewa,

If you don't have anything to say just get lost.

Ajiyar zuciya tasake ahankali tareda sunkuyar dakai ahankali tace,

Abinci ne.......

Cikin wata irin tsawa yace,

I said get lost.

Da sauri ta juya har jikinta na rawa tabar gurin ta fa'da bedroom'dinta ta rufo qofar tareda Zama bakin gado tareda dafe goshinta.

Tana barin gurin ya rufe idanuwansa ahankali Yana fa'din,

She has no manners,,,mitsw  completely shameless..

Fasa kallon yayi ya miqe Ya fice zuwa gurin mum asee yaci abincin acan.

Tanajin fitarsa ta miqe ta fito palon hakanan taji hankalinta yakasa kwanciya dayaci wani Abu a hannun mum asee
Takoma bedroom da sauri harta jawo hijab tafasa ta ajiye ta 'dauki wani qaramin gyale iya wuya ta yafo akanta tareda sake fesa turare ta  zuro  slippers ta fito tabi bayansa da 'dan saurinta.

A qofar shiga palon ta cimmasa sbd saidaya tsaya waya a harabar gidan..

Qamshin turarenta yafara iso da zuwanta ya tsaya cak hannuwansa zure cikin wandonsa ya rintse idanuwansa tareda tamke fuska ya juyo a fuska a matuqar 6ace idanuwansa suka sauka kan Kamal dake tafe bayanta Yana yiwa bayanta kallon qurulla har Yana tuntu6e jikinta ya kalla yaga fingilallen gyalan data yafo iya wuyanta gashi Riga da skirt ne na atampa ajikinta.

'dauke Kai yayi zuciyarsa na quna sbd Shi mutum ne Maison komai nasa yazamo na musamman da ba kowa keda irinsaba ko Kuma ba kowane zai samu irinsaba ciki kuwa harda matarsa zaiso tazamo tafi kowace mace Amma he endedup with this market tomatoes gashi ko acikin gidansa batada wata daraja tunda akwai tsohon Dan iskan qaninsa...

Tana qarasowa ta fuske zata wucesa harta gota taji an damqo hannunta tareda juyo da ita mummunan fa'duwa gabanta yayi da sauri ta 'dago Dan kuwa ta tsinke matuqa saitaga fuskarsa a matuqar hade Yana kallon bayanta
Cikin tsoro ta juya Dan ganin abinda yake kallo fuska a murtuqe..

Kamal'''''ta fa'da ahankali zuciyarta na sake tsinkewa gabanta naci gaba da fa'duwa Dan kuwa taga irin kallon kwa'dayin dayake Aiko Mata.

Tsayawa shima Kamal 'din yayi idanuwansa qyam aKan qirjinta dake sama da qasa sbd tsananin bugawar da gabanta keyi...

Wata muguwar matsewa taji yayiwa hannunta dake riqe ahannunsa tai saurin kallon fuskarsa idanuwanta na qoqarin danne hawayen azabar riqon  dayayi Mata taga tsantsar 6acin Rai da fusata a fuskarsa
Ya rufe idanuwansa Yana jiran Kamal ya wuce sbd idan yaci gaba da kallonsa zai iyasa ahukunta masashi Dan bazai 'daukar musu iskancin cigaba da wulaqanta igiyoyin aurensaba acikin gidansa Dole subari idan ya sauwaqe Mata suje su qarata.

Gangarowa hawayenta sukayi sbd tsananin zafi da azabar riqon dayayiwa hannunta
Ganin Kamal din Sai sake matsowa yakeyi Yana qara qure kallonsa kan qirjinta alamunsa tsaf sun  nuna a buge yake Dan haka duk yayi gangancin ta6ata....

Bata qarasa tunaninta ba ya 'dago hannu zai kamota..
Jikin saheeb tashige da sauri tareda yimasa wata kyakkyawar runguma ta rintse idanuwanta gabanta na tsananta bugawa.

Idanuwansa dake rufe ya bu'de cikin tsananin mamaki..,
Hannun Kamal ya kalla daya 'daga zai kamota kafin ya 'dago ya watsa Masa wani mugun kallo ba shiri yabar gurin duk da abuge yake Yana zage zage.

Yana barin gurin saheeb ya fixgeta daga jikinsa tareda watsa Mata wani mugun kallo ya bu'de Baki daqyar yace,

Stay within your limits Dan zakiyi matuqar mamakin abinda Zan muku time din dakukayi gangancin wasa da sadakin Dana biya.

Kallonsa tayi da sauri da fararen idanuwanta hakanan zuciyarta tayi sanyi da abinda yafada,,, at least dai ya yarda da ita matarsace.

Wani murmushin farin cikine ya kubcewa fuskarta.

Ya sake tamke fuska zaiyi magana yafasa ya wuce
Tabi bayansa da sauri tanajin wani iri azuciyarta.

Mum da yakurah ne apalon
Cikin farin ciki mum asee ta tarbesa tana cewa,

Yanxu nake cewa na aika maka abincin Dana girka maka da kaina sbd nayi tunanin ka gaji bazaka iya fitowa ba.

Murmushi kawai ya sakar Mata tareda kissing hannunta datake miqo Masa sbd tun Yana yaro yasaba da hakan.

Zama yayi kusada ita Yana 'dagawa yakurah Kai data gaidasa batareda ya kalli gefentaba.

Cikin Ido mum asee ta kalli Anano data shigo palon fuskarta qunshe da farin ciki
Taqaraso ta gaida mum din cikin ladabi Mai tsanani.
Murmushi mum asee tasaki tana jinjinawa ananon Dan tasan wannan qarin ladabin ganin saheeb ne.

Hmmmnn yarinya kina wasa da wutane Baki saniba sbd ahankali Zan maidaki abin kwatance bayan nagama anfani dake.

Amsa gaisuwar ananon tayi cikin sakewar fuska ta 'dora da cewa,

Anano sannu da qoqari kinji.

Ba komai mum""""tafada tana kallon gefen saheeb dake kallon tv.

Kallon yakurah mum asee tayi tace,

Yakurah ki kawowa saheeb abincinsa a dining yaci.

Kallon mum Anano tayi da sauri suka ha'da Ido mum ta 'dauke Kai tana sakin murmushi.

Bayan yakurah tamaida kallonta da sauri hankalinta natashi.

Tana Kai abincin tazo tace,

Mum komai is ready.

Ok yakurah,, saheeb kaci abinci inaso zanyi magana dakai.

Ok""yace tareda miqewa ya nufi dining Kai tsaye..

Bayansa tabi da kallo gabanta na tsananta bugawa
ta maido da kallonta gun mum taga mum din taqi kallonta tv take kallo hankali kwance cikin nishadi.

Yawu ta ha'diye daqyar zuciyarta naci gaba da bugawa Dan kuwa tasan Dole akwai abinda yake cikin abincin.

Zumut ta miqe ta nufi dining din tana cewa,

Nima zanci abincin mum yunwa nakeji.

Murmushi mum din tasaki tana cewa,

Saki jiki kici ai zai isheku harsai Kun rage ma.

Qarasawa tayi dining din daidai ya 'debo a spoon zai Kai bakinsa tayi saurin riqe hannunsa.

'dagowa yayi ya watsa Mata wani kallo da oily eyes dinsa

Nan take jikinta ya'dau rawa gabanta na tsananta fa'duwa ta saki wani wahallalen murmushin qarfin halin Dole muryarta na rawa tace,

Ummm""""saikuma takasa magana tasaka abincin abakinta ta ha'diye daqyar zuciyarta na tsinkewa.

Qura Mata idanuwansa yayi ya tsareta dasu
Ta aje spoon din cikin rawar murya tace,

Ummm dama zanjine ko akwai yaji sosai aci.....

Sake waro Mata idanuwansa yayi ya kafeta dasu
Ahankali tace,
Sorry ban.....

Shut up"""ya fa'da cikin tsananin tsawa da 6acin Rai kafin ya miqe yabar palon gaba 'daya Rai 6ace.

Cikin murmushi mum asee ta taso tazo gabanta takalleta a wulaqance tace,

Poor Anano,
Kinyi tunanin nasaka Masa guba ne yaci ya mutu?

Wrong,,, you're wrong sbd bazan hakan yanxuba..

Abbane ya sauko cikin jallabiya sbd yajiyo tsawar saheeb din.

Anano ce kawai ta lura dashi sbd su mum sun basa baya tasaki murmushin mugunta ta bu'de baki da sauri cikin 'dan daga murya tace,

Mezaisa nayi tunanin kin saka Masa guba yanzu tunda nasan koba yanzu Dole idan Kika gama ha'da Kan dukiyar gidan aikasa zakiyi inda kuka aika maminsa da matarsa.

Murmushi mum Asee tasaki tana cewa,

Hakane shiyasa nakeson kiyi ahankali tareda taka tsantsan Dani Dan kuwa Zaki iyabin sahu idan kikayi ganganci ko kuskuren double crossing Dina coz I won't hesitate or think twice before burying you alive keda bastard son dinki Dan kinsan Zan iya tunda kinji nakashe jininama bare ke so better be care....

Fa'duwar wayar hannun Abba da jikinsa ya dau rawa sbd jin mugun zance ne yasasu juyowa cikin tsananin tashin hankali da tsoro...

Zaro idanuwa mum asee tayi cikin wani tsananin tashin hankalin dabata ta6a shigaba.

Anano kuwa murmushi tasaki tareda gyara tsayuwarta.

Cikin tsananin zufa da tashin hankali Abba ya juya zai koma sama yaji saukar wani mummunan bugu akai Nan take jini ya 6alle ta hanci da kunnuwansa ya zube agurin Yana gangarowa.

Wani gigitaccen ihu Anano tasaki tareda Kiran sunansa da qarfi ta nufesa.

Mum asee kuwa Kamal dayayi aikin ta kalla tareda 'daga Masa Kai tana sauke ajiyar zuciya..

Yakurah kuwa cikin sauri ta qwace qaton qarfen hannun Kamal din takai bedroom dinta ta 6oye suka fara rusa ihu suna Kiran sunan abban.

Arikice yakurah ta miqe taje tafadawa saheeb dake waya aharabar gidan suka shigo cikin tashin hankali musamman dayaga jini kwance a qasa mum na kuka tana fa'dar fadowa yayi daga stairs.

Wata muguwar sarawa kansa yayi ya durqusa cikin tsananin tashin hankali shida Kamal suka 'daukesa gabaki'dayansu suka dunguma asibiti
Mum,Kamal da yakurah suna adduar Allah yasa yatafi kenan.


Sweethearts bakuda damuwa yanxu nadawo Insha Allah
I love you mah people😍😍😍😍

#vote
#comment
#share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*29*
Jiki asanyaye ta 'daga wayar
Sukai magana sama sama Nan nabeela ta sanarda ita tananan zuwa suje saloon.

Ok kawai tace tareda kashe wayar ta aje tana sake tallafe kumatunta cikin fargaba.

Tana gurin zaune tana tunanin abinda zai faru a zamanta da saheeb
Nuratu nata kaida kawon aiki har nabeela ta iso ko Zama batayiba suka fice.

A motar nabeela sukaje tunda suka fito harsuka gama abinda suke suka kamo hanyar gida batada kuzari musamman da zayyan yakira yaqara sanarda ita dawowar saheeb din.

Kallonta nabeela tayi lokacinda tagama waya da zayyan tace,

Anano wannan fargabar da tsoron saheeb dakike bazai ta6a Bari kiji da'din Zama da mijinki ba,

Karki ta6a Bari saheeb yasan kina tsoronsa sbd zakici matuqar wuyan hakan..

Cikin sanyin murya tace,

Nabeela zuciyata na matuqar fargaba da tsoronsa bansan ya....

Dolene Zaki cire tsoronsa sbd kisamu damar samun matsayin cikakkiyar Mata agurinsa.

Kallon nabeela tayi cikin marairaice fuska tace,

Bana tunanin samun hakan yanxu saidai qila zuwa Nan gaba.

Murmushi nabeelar tasaki tana cewa,
Ki qoqarta tun wuri kisamu hakan.

Yamma sosai suka dawo tun a gate ta ajeta ta juya gida sbd ganin magriba takusa.
A nutse cikin 'dan sauri ta nufi hanyar part dinsu tana adduar Allah yasa abdulshakur baiyiwa gwaggo rigima ba sbd yanxu Sam yakoyi rigima bayason tafita tabarsa ko ka'dan.

Direct bedroom dinta ta nufa tafara aje handbag 'dinta da saka wayarta charge ta nufi gurin gwaggo takarbo abdulshakur tadawo tareda nuratu.

Suna shigowa palon ta miqawa Nuratu shi ta nufi bedroom dinta sbd gabatarda sallar magriba da'ake Kira.

Tana gamawa ta fito palon riqeda chocolates din Data siyowa abdul ta zauna tareda kallon yanda nuratu ke basa abinci yanaci Yana wasa..

Murmushi tasaki cikin farin ciki tareda cewa,

My boy zo Nan naci gaba da baka abincin.

Juyowa yayi tareda baro Nuratu da gudu ya nufota sbd baisan tafito ba.

A cinyarta ta 'dorasa tareda karbar plate din tana kallon cikinsa tace,

Nuratu ai yariga ya qoshi bakya ganin yanda  cikinsa yayi qato,
Ungo mayarda abinci and ki kiyaye gaba banason ana basa abinci da yawa Wanda yafi qarfin cikinsa.

Miqewa tayi takoma bedroom dashi tayi Masa wanka ta fiddo pampas tasaka Masa ta kwantar dashi tasamu yayi bacci tafito palon taci abinci tazauna ta'danyi kallon mintuna ka'dan ta miqe ta rufe qofa ta shige bedroom tayi Shirin kwanciya ta kwanta.

Washe gari tana tashi tahau gyare gyare itada nuratu
Sun goge komai na part din sun gyare ko'ina bedroom dinsa ne kawai Bata gyaraba shima sbd is locked.

Yaronsa Samuel ne yazo yayi knocking yakar6i mukullin motar daza'a dauko saheeb din daga airport.

Abinci ta 'dora simple sbd Bata tunanin zaici Amma dai ta daure tayi suna gamawa tai bedroom Dan yin wanka tabar nuratu na wanke kayan dasukai aiki dasu tareda gyara kicin din.

Tana fitowa wanka taji dirin motocinsu sun shigo gidan Nan gabanta yasake yankewa ya Fadi ta qaraso gaban mirror jikin asanyaye ta zauna.

Daqyar ta 'dauki Mai tafara shafawa ahankali tana cigaba dajin fa'duwar gaba.

Asanyaye tamiqe taje gaban wardrobe ta dauko Riga da skirt na wata dark purple super tasaka tareda fesa turare ta nufi qofa tana dafe gabanta dake bugawa kamar zai fa'do ta rintse idanuwa tareda kiran sunayen Allah ta bu'de qofar bedroom 'din tafito palon daidai shigowarsa Samuel na biyedashi 'dauke da 'yar qaramar akwatinsa.

Cak ta tsaya tareda qaqalo wani mugun wahallalen murmushi sbd ganin Samuel muryarta na wata irin rawa tace,

Sannu da dawo....

Bata qarasa ba ya karbi jakar hannun Samuel da duk yake a tsarge yayi hanyar bedroom dinsa kyakkyawar fuskarsa data qaro kyawu da hutu a ha'de danko gefenta Bai tsaya kalloba.

bayansa tabi da kallo zuciyarta na wani irin nauyi ganin irin hutun dayai tsananin bayyana ataredashi ga wata lafiyayyar qasumba daya Bari ta qara Masa wani sirrin kyau.

Da sauri Samuel shima ya juya yabar palon Yana mamakin Ashe basu ka'dai oga saheeb kewa hakaba.

Numfashi tasauke ahankali tana qara jinjina al'amarin Dan kuwa tasan wannan auren ba qaramin galabaita zuciya da gangar jikinta zaiyiba sbd saheeb bazai ta6a kallonta da daraja ko mutumciba Dan haka gara tayi gaggawar yin abinda yakamata ta tona asirinsu mum asee takama gabanta tun kafin tarasa control na zuciyarta.

Xubewa tayi a kujera tareda dafe kanta tana Kiran sunan Allah.

Da qarfi takeson cire tsoronsa shiyasa tayi zamanta apalon taqi tafiya tafara kallo duk da hankalinta Sam baya Kan kallon gabanta Sai fa'duwa yakeyi Amma ta dake.


Zaman kusan awa uku tayi Amma Bai fitoba cire ran zai fito tayi ta miqe ahankali tareda nufar gaban kayan kallon Dan cire wayarta daga charge daidai taji an bu'de qofar bedroom'dinsa fa'duwa gabanta yayi ta 'dago da sauri sbd Bata Isa gurin ba gashi gurin hanyar bedroom dinsa ne..

Tsayawa yayi shima cikin tsananin daurewar fuska sbd ganin qofar bedroom'dinsa ta nufo,,,
E she this shameless??

Ganin irin kallon dayake Mata na qyama da yasa ta girgixa Kai tareda bu'de baki zatai magana cikin tsananin tsawa yace,

Shut up..

'dauke Kai yayi cikin takaici Yana cewa,

Daina kallona da those shameless eyes  and get out of my way.

Matsawa tayi ya wuce ta rintse idanuwanta kafin ta qarasa ta Ciro wayarta harta nufi hanyar bedroom dinta saita dakata ta nufi gurinda yake zaune Yana kunna wayoyinsa.

Nesa ka'dan ta tsaya tana kallonsa yanda yake komai cikin nutsuwa da burgewa zuciyarta na bugawa da sauri tai saurin rintse ido tareda sauke numfashi ta bude Baki zatai magana ya 'dago ya watso mata manyan white oily eyes 'dinsa tareda kafeta dasu akaro na farko tunda yadawo.

Rikicewa tayi takasa magana
Shikuwa gyara Zama yayi tareda qara sakar Mata idanuwansa danso yake yaga qarshen rashin kunyarta.


Sorry Sai Kuna manage da yanda zai riqa zuwar muku ka'dan har nasamu na kammala hidimar gabana.

Vote
Comment
Share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*34*
Zubewa tayi bakin gado tareda cusa hannunta cikin gashinta dake zube har qasan kafadunta
Hawayen datake riqewa suka gangaro Mata,
Nabeela kin gama dani,nashiga uku ya kikeson nayi saheeb kasheni zaiyi oh ni Allah.

Miqewa tayi ta 'dauko kayan data cire ta maida tana hawaye sbd tun ahanya suka dameta ta matsu tayi wanka ta curesu sbd lace ne
Duk da tsadarsa saidaya yayi nauyi shiyasa yake damunta batason Abu Mai nauyi ajikinta.

Tattara kayan tayi ta maida cikin wardrobe tasaka hijab din da nabeelar tasako Mata dogo har wasa danko qafafunta ba'a gani tayi sallah,

Tana idarwa ta miqe tana qoqarin cire hijab 'din akai knocking ta nufi qofar gabanta na fa'duwa har qafafuwanta na hardewa sbd fargaba da tsoron datake ciki.

Ahankali ta bu'de
Tana ganin zayyan tareda ma'aikatan gurin su biyu tasaki ajiyar zuciya harsaida zayyan ya gane yasaki murmushi danshi kansa yasan akwai wura idan saheeb yazo yatararda room 'daya ya Kama musu Kuma yayi magana da manager duk yanda saheeb yayi karsu basa wani 'dakin suyi tsayawarsu akan all the rooms has been occupied.

Cikin sakewar fuska yace,

Kibada order abinda kike buqarar ci ni zantafi hospital gurinsu saheeb so take care and please kisaki jikinki.

Kasa magana tayi saidai Kai data gyada Masa
Ya juya yabar gurin ta maido da kallonta ga turawan dake tsaye gabanta riqeda abin rubutu suna jiran tafadi order dinta su rubuce.

Yawu ta ha'diye tareda tattaro nutsuwa sbd tasamu ta harhado turancin gudun karta fa'da ba daidaiba duk da tasan ta iya Amma wa'innan turawane Dole nata yaci uwar uban nata.

Kallonsu tayi cikin rawar murya tace,

Menu,,

Da sauri ya bu'de file din hannunsa yaciro yabata ta kar6a.

Dubawa tayi taga batama ga sunayen abincin data sani ba bayan noodles da chicken chips Sai tea and coffee.

Noodles da tea tace sukawa Mata suka rubuta suka wuce takoma ciki tareda cire hijabin ta na'de tasaka cikin wardrobe tadawo ta kwanta bakin gado tareda takurewa sbd sanyin garin Dana ac sunyiwa qashinta tsananin qarfi Amma tsoron kashe ac takeyi karyazo yayi fa'da tunda shi a ac yataso yasaba rayuwa.

Tun tana daurewa har alamarin yaci qarfinta Nan take zazzafan zazza6inta yadawo Banda jijjiga ba abinda jikinta keyi ga amai data Riga zuwa toilet tanayi hartakai ko tashi Bata iya yi gashi dama yunwa tayi Mata mummunan cafka sbd tun jiya rabonta da abinci
qasa abakin qofar toilet ta yanke jiki ta fadi numfashinta na qoqarin daukewa idanuwanta suka rufe.

Room service tareda waitress suka zo kawo Mata abincin data buqata sunyita knocking ba amsa suka koma Dan bada wasu mintunan suka dawo sukaita knocking still ba amsa Nan hankalinsu ya 'dan fara tashi suka koma Dan qara bada time sbd qaida ne Sai anzo so uku idan still ba response saisu Kira waya kafin su bu'de room da spares dinsu.

Ana uku Koda suka dawo sunfi mintuna 30 Amma ba motsi Nan suka koma receiption aka fara neman number Wanda yayi booking room din.

Duk wani Abu daya kamata ayi na Abba a hospital din sunyi anshigardashi wani room 'din dabamai shiga saidai ka gansa ta glass harsai ranar daya fara farfadowa Dan har lokacin shida matacce banbancinsu ka'dan ne.

Fitowa sukayi Dr yasake yimusu bayanin Sai bayan kwana biyu zasu dawo sbd a hasashensu allurai da hotunan dasukai Masa Sai after two or three days suke sakaran ya farfado.

Biyan komai sukayi suna gurin biyan wayar zayyan tayi ringing,..

Qaramin tsaki yasaki sbd amatuqar gajiye yake kafin ya 'dauka.

Wat'''yafada da qarfi kafin ya'dan kalli mutanen gurin dasuka kallosa da sauri sbd yanda yayi maganar da qarfi,,,

Sorry""yace musu kafin yayi qasa da murya yace,

Wat are you saying?
Ok just wait I will be there in a minute..

Kallon saheeb yayi yaga idanuwansa a lumshe yasan Sarai Yana sauraron abinda yake fa'da.

Cikin sauri ya qarasa biyan komai suka baro asibitin ganin yanda zayyan ke gudu da motarda ko awa uku basuyi da siyanta yasa ya juyo ahankali ya kalli zayyan din ya bu'de Baki daqyar yace,

This is not an option,you know right?

Batareda yakalli gefensa ba yace,

Seriously saheeb?
Well idan kanada wani option dazaisa asan halinda 'yar mutane take ciki then tell me one,
For God sake saheeb for how long zaka cigaba da quntata rayuwarka?

Ka hanawa kanka samun farin ciki kullum sbd you never let go of the past,
Ka auri nafeesat just sbd Abba yasaka ka badan kai kasamu cigaba ba ko farinciki.,
Bayan aurenka da ita she tolerated enough and endure so much sbd she loves you dearly more than you can imagine har saidata fara kawo haske da farin ciki arayuwarka but still she died batareda kasakata farin ciki ko sau 'dayaba arayuwarta a qarshe ta bada rayuwarta sbd tsaronka da dukiyarka.,

And now this poor girl datake maka yaqi a duhu batareda tayi la'akari da ha'adarin dake ciki ba,
Ta amince da aurenka sbd mahaifinka yabata umarni
Tana zaune dakai tana qoqarin Kare maka mutumcinka da dukiyarka kamar yanda addininta ya koyar Mata
Amma you never looked bare kaga arziki da baiwar da Allah yama na samun mace Mai tsananin sonka da qaunarka fiyeda rayuwarta,
Wadda zata iya bada Tata rayuwar gurin ganin baka cutuba,

Saheeb,,
Try and forget the past and face the future sbd zaka iya rasata itama kamar sauran Wanda nasan idan harka rasata wannan karon bazaka daina regretting ba har qarshen rayuwarka,,
Sbd idanuwanka sun rufe ka kasa ganin abinda Allah yabaka,

Wannan yarinyar Amana ce da Abba yabaka tunda shine ya aura maka ita.

Parking yayi a harabar hotel din tareda bu'de motar ya fita yabar saheeb din idanuwansa sun ka'da sunyi jajir sbd maganganun zayyan din sun shigesa duk da wasu kalaman Bai gane me zayyan din ke nufi dasuba.

Fitowa yayi jiki ba qwari ya nufi ciki daidai Nan manager da wasu ma'aikatan tareda zayyan suka shiga elevator shima yashiga suka nufi sama.

Satar kallonsa zayyan yayi yaga yanda fuskarsa da idanuwansa sukai ja alamar kansa ya'dau zafi ciwo yake masa duk Sai yaji saheeb din yaqara basa tausayi.

Saida suka tsaya qofar room din suna knocking da qarfi zayyan nakira sunanta kafin ya fahimci tun farko abinda zayyan ke nufi da gudun dayakeyi.

Sake tashi hankulansu sukayi cikin tashin hankali zayyan ya kalli manager yace,

Do something, just open the damn door..

Ok ok sir,,

Ciro spare keys yayi yabude 'dakin da gudu su duka zayyan,manager da ma'aikatan biyu suka doshi shiga har suna rige rigen shiga.

Cak suka tsaya dukkaninsu cikeda mamaki sbd saheeb daya riqe handle din qofar tareda sakar musu manyan oily idanuwansa.

Zayyan da tuni ya manta da cewar matar wanice suke qoqarin shigewa basusan halinda zasu sametaba ya dafe goshinsa Yana cewa,

Oh sorry,,,,

Su manager ma cikin sauri sukace sorry sbd zayyan dayace musu matar saheeb din ce.

Juyawa yayi ahankali tareda bu'de qofar yashiga zuciyarsa na shiga wani yanayi dabaisan na meyeba.

Cikin tsananin mamaki zayyan yabi bayansa da kallo Yanason fassarawa kansa me hakan ke nufi sbd anta6a irin haka lokacin nafeesat nada ciki sunje Cyprus 'daki yarufe da ita suka bu'de Amma Bai Hana ma'aikatan shigaba tare suka shiga,,,
So meyasa yanzu.?


Saimun hade a na dare😶 may be.

Kuyi votes please 🙄
Ghost readers Allah ya shiryeku😏

#vote
#comment
And share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*32*
Kuka tasaki mai 'daga hankali sbd tsanani da mugun tsoron abinda Kamal ke Shirin yimata
Ta tattaro qarfin ta turesa yafadi gefe
Ta miqe da sauri jikinta na rawa zata gudu ya riqe qafarta 'daya tareda ja da qarfi
Tayi wata mummunar kifewa ya birkitota yashiga gaggaurawa fuskarta Mari data qi tsayawa yayi Mata kiss.,

Cikin tsananin azaba da kukanta daya fara rage fita sbd wuya dan baqaramin duka yake kaimataba,

jikinta na rawa murya na rawa tace,

Kamal Dan Allah kaji tausayina karka cutatar dani ka illata rayuwata wlh bantaba aikata abinda kakeson aikataminba,
Dan Allah kayi hkr da abubuwan danai maka karka illatani kadubi darajar igiyoyin auren 'dan uwanka dasuke kaina karkayi......

Buge Mata baki yayi da qarfi tareda sake Jan rigarta duk iya qarfinsa
Ya 6arkata
Ya damqo gashinta Yana qoqarin Kai bakinsa nata Yana cewa,

Tunda kikazo gidannan nine nafara sonki nafara kula dake da shegen 'danki ba 'dawainiyar dabanayi daku duk sbd inayiwa kaina tanadine Amma you bitch ko kiss Baki nai mikiba shine qarshe kukaci amanata,,
Yau saina nuna Miki wancan shegen Bai fini da komaiba...

Rintse idawanta dasukai jajir tayi tana girgixa Masa Kai tace,
Kamal Dan Allah kayi hkr....

Shut up bitch...yafada da qarfi Yana qara damqo fuskarta yace,

Idan Baki ta6aba shi shegen 'danki uban waye ya haifesa.....

Wlh bani na haifesaba,
Ban ta6aba Dan Allah Kamal ka....

Rufewa idanuwansa sukayi yahau shafarta jikinsa har wata rawa yake idanuwansa jajir sbd jaraba dake cinsa.,

Miqewa yayi jiki na rawa yafara qoqarin zame belt 'dinsa
Ta rarrafa da sauri ta miqe jiri na dibarta zata gudu ya damqo hannunta ya fixgota taji anriqe hannunta 'daya ta bayanta.,

Da sauri ta juyo cikin wani sabon tashin hankalin.,

Saheeb"""""tafada cikin tsananin farin ciki tareda fuzge hannunta tayo gurinsa da gudu ta fa'da jikinsa ta qanqamesa tareda fashewa da wani irin kuka jikinta na wani irin mugun rawa Dan gabaki 'daya nutsuwarta Bata jikinta ta saddaqarda Kamal ya gama lalata rayuwarta.

Idanuwansa dake Raba mutum da nutsuwarsa ya kifawa Kamal kansa na wani mugun sarawa yanda zuciyarsa tai tsinannan 'daukar zafi Dan ya 'dan jima dashigowa yatsaya kallonsune Dan yasan a ma'aunin dazai 'dora alamarin
Idan cikin son Raine fyade ne..

Rawa jikin Kamal 'din ya'dauka cikin wani mugun tashin hankali musamman kallon da saheeb din ke Masa Nan take giyarsa ta sakesa bakinsa na rawa yace,

Itace takirani tace.....

Wani mahaukacin gigitacce azababben marin dabai ta6ajin irinsaba saheeb yasakar Masa Saida ya durqushe Kan gwiwowinsa cikin muguwar qara hancinsa da bakinsa suka 6alle da jini.

'dauke Kai yayi zuciyarsa na qara qonewa sbd hukuncin dazai 'dauka bazaiyiwa kowa da'diba musamman mum.,

'dagota daga jikinsa yayi har lokacin jikinta rawa yakeyi sosai tana kuka.

Kallo 'daya yayi Mata ya rintse ido kansa na qara 'daukar nauyi sbd gabaki 'daya jikinta abayyane yake sbd yanda ya yage rigarta
Ga fuskarta data kumbura goshinta jini bakinta jini sbd maruka.

Wayarsa ya fitar ya Danna Kira idanuwansa ko gani sosai basayi sbd tsananin 6acin Rai da zafin zuciyar.

Buga qofar palon akayi yabada umarnin shigowa tareda janta yakai bedroom dinsa yafito.

Su Samuel ne tareda sauran soldiers biyu dake gadin gidan
Kamal na ganin haka cikinsa ya 'dori ruwa
Cikin tsoro da tashin hankali ya rarrafo gaban saheeb dake zaune fuskarsa kallo 'daya zakai Mata tsoro yakamaka
Ya bu'de baki zaiyi magana saheeb yayiwasu Samuel kallo 'daya
Da sauri suka matso cikin rashin tausayi suka 'damqosa suka fice dashi zuwa gym 'din saheeb dake gefen part 'dinsa.

Rufe qofar sukai suka hau jibgarsa bayan sun rufe bakinsa da salatif
Nan take kamanninsa suka sauya sbd dukan tashi kasha ruwan gishiri sukai Masa.

Ko gamawa basuyiba mota biyu da sojoji ta parker qofar gidan suka shigo aka 'daukesa kamar tsumma suka wuce dashi.

Jabiru Mai gadi Yana ganin haka ya sulale yashige 'dakinsa sbd ganin yau sojojin ashirye suke suci uwar duk Wanda yayi gangacin shiga gabansu.
Suna barin gurin su mum asee na dawowa tabi motacin da kallo sbd ganin yanda suke gudu motoci na kauce musu.

Rintse idanuwansa yayi tareda dafe goshinsa,
Tabbas bashida rabon farin ciki arayuwarsa Dan kuyaushe yasamu hanyar farin ciki saiya rasata.

Sarawa kansa yake matuqa ya miqe ya nufi bedroom dinsa,

Tsayawa yayi bakin qofa tareda 'dauke Kai ganin yanda jikinta ke tsananin rawa sbd zazza6in Nan take na wahala daya rufeta idanuwanta ko bu'dewa basayi.

Hanyar toilet ya nufa yashige
Ta bu'de idanuwanta daqyar tafara rarrafawa ta Fice bedroom'din ta shige nata.

Yaji fitarta shiyasa ya watso ruwa ya fito 'daure da towel ya zauna bakin gado tunanika da dama na shigarsa.


Washe gari ko yatsanta Bata iya 'dagawa sbd tsanani da jikinta yayi tayi kuka har idanuwanta basa iya fidda hawaye sbd kumburinsu.

Nuratu taje tafadawa gwaggo batada lafiya
Nan gwaggo tazo ta dubata tana adduar Allah yasa laulayine.

Tunda yafito yaje asibiti zayyan yagane akwai wata sabuwar damuwar bayan ta Abba saidai kawai yayi shiru sbd saheeb din ba Wanda ake tambaya bane yabada amsa.

Suna fitowa daga asibiti cikin mota ya fiddo wayarsa yakira Ahmed
Ahmed din na dauka Kai tsaye yace,

Ayimata kamai na passport anemi visa da ita
Da ita za'aje.

Am um sir wa kenan?

Katse wayarsa yayi Dan baida time 'din basa amsa.

Wani kallo zayyan dake driving yajuyo yayi Masa cikeda mamaki Dan yasan Anano yake nufi.

Wani dadine ya ziyarci zuciyarsa sbd dama yanada niyar Dole Sai anje da ananon sbd su samu time acan su fara fahimtar juna Dan kuwa matuqar ba canza salon Anano tayi saheeb yafara sontaba yanada wuya zuwa gaba Kota tona asirin su mum asee ya yarda Amma da zaran akwai so to zai yarda da abinda zata fa'da.

Don't forget to,
#vote
#follow
#comment
#and
#share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamhugee_


*_ina ganin comments dinku sosai Kuma Ina matuqar yabawa_*
*_ONE LOVE MY PEOPLE_*💋


*33*
Tsananta tamke fuskarsa yayi sbd ganin yanda zayyan ke son jeho Masa tambaya and shi bazai iya fadawa wani abinda Kamal yayiwa matarda aurensa yake kanta.

Mum asee tun jiya rabonta data saka Kamal a idanuwanta ta aika akirasa yakai so hudu asabe na dawowa tace bayanan,
Wayarsa taketa Kira baya 'dagawa ta aika yakurah still dai bayanan.

Da farko Bata damuba Saida taga marairaice yayi bashi ba labarin inda yake gashi yakurah ta 'dauko wayarsa data tarar a palonsa tanata ringin.

Jabiru mum takira ta tambayesa yaushe Kamal ya fita?

Yawu ya ha'diye cikin fargaba da tsoro murya na 'dan rawa yace,

Hajiya tun jiya da daddare bayan fitarku ya fita.

Kallonsa tayi da kyau tace,

Da qafa ya fita ko kuwa da mota akazo 'daukarsa tunda dai ga motarsa Nan a gida Kuma nasan Kamal bazai ta6a iya fita da qafa bada motaba.

Washe baki yayi gudun karta ganosa Dan gwara wahalarta da Wadda zaisha hannun mazaje wato sojojin oga saheeb yace,

Wani abokinsa ne daya Saba zuwa Nan gurinsa Naga yazo ya rakasa waje to bansaniba koshi yabi Dan zagayawa bayi nayi bansan barinsu ba.

Dafe goshinta tayi tareda sakin Dan qaramin tsaki Dan kuwa hankalinta yafara tashi da wannan alamari
Gashi Abba baya Nan bare ta 'daga Masa hankalin saiya Nemo Mata 'danta.

Kallon jabiru yakurah tayi tace,

Kaje idan dai yadawo kace yazo mum na nemansa.

Da sauri ya fice Yana adduar Allah yasa yaran oga saheeb sudawo dashi da wuri.


Ba laifi ta 'danji sauqi sbd wankan datayi da ruwan zafi sosai taci abincinda gwaggo tasa nuratu ta girka Mata na faten dankali da Naman kaji
Ga zayyan daya kirata ya sanarda ita Kamal na hannun yaransu meya faru?

Shiru tayi kafin ahankali tace,

Shigomin yayi.

Wat yafada cikin takaici,
Lallai Dole ne saheeb bazai iya fa'dar wannan abinba.
Kashe wayar yayi ya nufi light room 'din da aka Kai Kamal yasa aka tsananta Masa.

Batasha maganiba sbd Sam ta tsani magani arayuwarta
Fuskarta daice still a kumbure sbd marika da buguwar datai.

Wayarta ce tayi ringin ta miqa hannu daqyar ta jawo ta taga nabeela ce
Murya can qasa ta 'dauka suka gaisa ta sanarda ita gatanan zuwa.
Tom kawai tace tareda aje wayar takoma ta kwanta.

Ko mintuna goma basuyi da Gama wayarba ta iso cikeda tausayawa take Mata sannu da yimata jajen abinda yasamu abba.

Sama sama suke fira da nabeelar Dan har lokacin batada qarfin jiki ko ka'dan.

Wayar nabeela ce tayi ringin tana gani tasaki murmushi tareda 'dauka cikin laushin murya tafara magana sbd zayyan ne.

Wat""tafada cikin farin ciki tana dariya kafin tace,

Yanxu kuwa my man.

Aje wayar tayi tareda dawowa kusada ananon dake kallonta tace,

Ki tashi tun wuri kisamu qwarin jiki sbd man Dina yace na tayaki parking qarfe Tara da safe jirginku zai tashi mijinki yace dake zai tafi.

Lumshe idanu tayi duk da tasan nabeela Bata Mata qarya Amma zancen Bai shigetaba saheeb ne zaice zaije da ita bayan abinda yafaru jiya tasan yaqara tsanarta ma sbd zarginsa ne ke tabbar Masa.

Ganin Bata yardaba yasa nabeela miqewa ta bu'de wardrobe ta shiga xabar Mata Kaya ta shirya cikin qaramin akwati sbd tasan tafiyar maza basason Kaya da yawa musamman ma irin saheeb.

Murmushi tasaki lokacinda tagama saka kayan taga irin kayan data saka ta rufe akwatin ta aje gefe tadawo ta zaune gaban mirror ta 'daukar Mata abubuwan buqata na cikin handbag tasaka Mata kafin tazauna tana cewa,

Anano please idan kinje karki dawo saida little feenat or junior abbah ko kuma....

Wani kallo Anano ta watsa Mata tana miqewa zaune tace,

Wlh idanma da gske kike ni banason zuwa sbd bazan iya Zama dagani Sai saheeb ba Kuma ba ranar dawowa....

Katseta nabeela tayi da cewa,

Karkice haka nidai Ina Baki shawarar kiyi amfani da wannan damar ki daidaita komai da kanki,
Saheeb namiji ne kamar kowane namiji Dan haka idan kinso wannan damace dazaki samu gurbi a zuciya da rayuwar mijinki.

Shiru tayi sbd ita kanta zataso hakan Amma gani take kamar da wuya.

Har dare asanyaye ta yini sbd fargaba ko abinci takasa ci,
Kayan Abdul kuwa gabaki 'daya ta kaiwa gwaggo tunda agurinta zasu barshi
Itama gwaggon gurinsu baffa zata tai hutu kafin sudawo.

Ta 6angaren mum asee kuwa tuni tafiya da ita ta fasu sbd dai Kamal ya tabbata ya 6ata
Duk inda hankalinta yake yakai qololuwar tashi ga saheeb yakama wayoyinsa duka ya kashe yaqi dawowa gidan Sai cikin dare duk da haka saidata kirasa ta 'daga hankalinsa da kukanta.

Kallonta yayi tareda riqo hannunta ya zaunar da ita tareda cewa yakurah takawo Mata juice.

Cikin baqin ciki da takaicinsa takalli juice din wato Dan ubansa Dan ya Rainata 'danta ya 6ata shine zai Bata juice,
Lallai saita 'dandana Masa baqin cikin dayafi wannan.

Bu'de Baki tayi daqyar yabata juice din Yana rarrashinta kafin yace ta kwantarda hankalinta zaisa yaransa zuwa gobe su nemosa za'a dawo dashi gida insha Allah.

Kai ta gyada kafin yatashi ya fice.

Tana tashi sallar asuba tayi wanka ta shirya ta zauna jiran tsammani duk da uban zazza6in dake damunta Amma tsoron laifi take abu 'dayane ya kwantar Mata da hankali da nabeela takirata tafada Mata tareda zayyan zasuje.

Knocking qofarta akayi ta miqe jiki asanyaye ta nufi qofar ta bu'de
Kodata bu'de harya bar bakin qofar ya nufi qofar fita.

Samuel ne yashigo 'daukar jakarsa yace ta miqo Tata
Taje ta 'dauko takawo Masa ta fito 'daukeda handbag 'dinta tabi ta kicin taje gurin gwaggo.

Fa'da da Yar nasiha gwaggo tayi Mata kafin suka fito nuratu na riqeda abdulshakur suka rufe ko'ina tabawa gwaggo keys suka nufo harabar gidan.

Da sauri Samuel ya bu'de Mata gefe 'daya na bayan motar tashiga gabanta na fa'duwa ya rufe Yakoma yashiga da sauri ya tayar suka fice.


Cikin rawar murya qasa qasa ta gaidasa tana satar kallon gefensa.

Qananun kayane ajikinsa black Sai shades na warby parker Wanda ta lura black is his favourite colour sbd kalar na matuqar yima farar fatarsa kyau,

Wayarsa yacigaba dayi batareda ya kalli ko gefenta ba bare tasaran ya amsa gaisuwarta.

Ahankali yake waya kamar mace har suka Isa gidan zayyan Samuel na parking Yana fitowa gidan Sbd already saheeb yakirasa
Da sauri Samuel yafito ya karbi jakarsa yasa boot shikuma yashiga gaba suka nufi airport cikin gudu sosai sbd sabo ne agaresu basa tafiya Sai gudu.

Suna Isa saura mintuna qalilan jirginsu ya tashi Dan haka Kai ba 6ata lokaci suka shige jirgi sbd already motar asibiti takawo Abba Yana ciki Nanda Nan jirginsu ya 'daga.


Zuru tayi hankalinta a tsananin tashe sbd Bata ta6a shiga ko babbar motaba idanba yanxu datake Hawa motocin saheeb ba bare jirgi ko acikin jirgin vip.

Kallon gefen zayyan tayi taga Yana Shan tea hankalinsa kwance
Ta maido da kallonta Kan saheeb taga wasu takardu yake karatu fuskarnan a tamke saidai hakan Bai Hana annuri fita acikintaba.

Kwantarda kanta tayi jikin kujera tareda lumshe ido tana tunanin irin rayuwarda zatayi dashi awata qasar.

Tun tana tunani har bacci ya dauketa batasan iya lokacinda ta 'daukaba saida aka iso.

Manyan motocin hotel din dasuka Kama a online sukazo 'daukarsu saheeb motar asibitin da'aka kawo Abba yabi ita Kuma tareda zayyan sukabi motar hotel din sbd zazza6inta daya dawo sosai sbd yunwa da gajiya tareda mugun sanyin qasar Miami din daya fara shigarta.

Suna Isa zayyan yayi musu komai aka wuce da kayansu 'dakunansu dake can fifth floor
Shi room 316 sukuna room 319
Shigar da kayansu akayi har cikin wardrobe kafin ma'aikatan suka fice.

Kallon 'dakin tayi cikin fargaba mamaki da tsoron yanda zasu zauna saheeb acikin dakin har tsawon lokaci.

Makeken lafiyayyan gadon takalla taga tasan lallai honeymoon suite ne aka Basu sbd yanda room 'din yake kusan a qawace.

Toilet ta nufa ta tube tayo wanka jikinta na mazari sbd rawar sanyin zazza6in daya fara cin qarfinta.

Ko Mai Bata tsaya shafawaba ta bu'de akwatinta Dan saka Kaya Amma me?
Gabaki daya Babu kayan arziki aciki Banda hijabin sallah 'daya.

Hannu ta 'dora akai idanuwanta na cikowa da hawaye tace,

Nabeela kin kasheni.


Votes sunyi qasa fa😏


#vote
#comment
#share#
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*31*
Mugun gudu yakeyi Wanda ya matuqar 'daga hankalinsu mummunan yanda sukaga fuskarsa Nan hankalinsu yaqara tashi musamman Kamal dake ganin Bai shirya mutuwaba yanxu.

Anano kuwa abdulshakur taje ta 'dauko takaiwa gwaggo shi tasako hijab ta fito tareda nuratu Samuel ya nufi asibitin dasu
Har lokacin jikinta rawa yakeyi idanuwanta Basu daina zubada hawayeba sbd tabbas tasan itace taja Masa Dan datun farko data gansa ta nuna Yana gurin dabazaji komaiba bare suyi Masa wannan mummunar illar.

Adduarta 'daya Allah yasa baisamu matsala akaiba.,
Kuma batasan wane Hali saheeb zaishigaba idan yarasa mahaifinsa Dan kuwa shika'dai ne yarage Masa yanzu Sai abdulshakur dabai masan alaqarsa dashiba.

Cikin gaggawa aka kar6i abban akai cikin emergency dashi Dan harsuka iso kansa Bai daina jiniba.

Tun acikin mota takira zayyan tasanar dashi abinda ke faruwa
Shiyasa kusan atare suka iso asibitin dashi hankalinsa shima atashe.

Gurin saheeb dake zaune bakin 'dakin ya Isa tareda zama kusadashi cikin tsananin jimami 'dan daki kafadarsa yace,

I'm really sorry saheeb
Insha Allah nothing will happen zaiji sauqi komai zai daidaita.

Bai amsa ba sbd bayajin zai iya magana sbd yanda kansa yayi Masa tsananin nauyi.

Asanyaye ta matsa gurinsa har lokacin takasa daina hawaye ta zauna 'dayan gefensa tanason tai Masa magana Amma bazata iyaba Dan ita kanta tana cikin tsananin tashin hankali bareshi da idanuwansa ne ke nuna tsantsar tashin hankali da damuwar dayake ciki.

Shiru sukayi Banda kukan mum asee dake tashi ahankali yakurah na rarrashinta Sai Kamal dake tsaye gefe shima cikin fargabar kada Allah yasa
Abban ya tashi
Koda yatashi Allah yasa ba qalau ba.

Tun suna tsammanin fitowar doctors harsuka dangana sukai jugum jugum
Suna jiran tsammani.

Agogon dake saman gurin mum asee data matuqar gajiya da kuka takalla agalabaice cikin tausayawa kanta Dan kuwa tuni kunnuwanta da kanta yafara ciwo sbd kukan qaryar gashi har kusan 1:30 na dare Babu wani bayani.

Doctors biyu ne suka fito lokaci guda 'dayan naqara yiwa 'dayan bayani akan lalurar abban.

Saheeb Dr yakalla cikin kulawa yace,

Well kanal I'm really sorry bazamu iya cewa komaiba yanxu akan alhaji kawai dai mun samu mun tsayarda bleeding din tareda yimasa 'dinki sbd ba qaramin buguwa kansa yayiba Wanda shine ya haddasa Masa fita hayyacinsa.,
Yanxu dai ataqaice duk abinda yakamata muyi munyi result dinmu Sai zuwa gobe mugani musan idan bawata matsalar.
So you'll have to wait till tomorrow....

No problem doc,I just pray and hope that Allah yasa ba wani abinda zai samesa.

Ba'a barsu sun gansaba sbd Sam baya cikin yanayin daza iya Barin kowa ya yadubasa shiyasa Dole suka tarkato suka dawo gida bayan zayyan yakira soldiers biyu dazasuyi gadin room 'din gudun su mum asee su sake want abin.

Motar saheeb zayyan yasa Anano tashiga su mum asee suka shiga ta Samuel shikuma yashiga tasa suka fito suka nufi gida.

Ahanya Banda rawa babu abinda jikinsa keyi sbd gabaki 'daya jiyake Yana tsananin buqatar fitarda damuwarsa Amma baida Wanda zai iya fadawa damuwarsa..

Ganin yanda jikinsa ke tsananta rawa har motar na lilo a titi
Ta 'dago cikeda tausayawa ta kallesa hawaye na ciko idanuwanta cikin sanyi da tsananin tausayinsa ta 'daga hannunta ta 'dora Kan nasa.

Burki ya taka da qarfi tareda rintse idanuwansa.

Bu'de motar tayi ta fito ta zagayo gefensa ta bu'de tareda kamo hannunsa
Baiyi musuba ya fito Dan bashida wani kuzarin hanawa.

Zagayo dashi tayi ta zaunar dashi tareda rufe Masa qofar ta zagaya tazauna mazaunin driver ta tada motar suka nufi gida ahankali.

Harsuka iso gida Rabin hankalinta nakansa sbd halinda yake ciki Yana qara raunana zuciyarta.

Suna Isa gida tayi parking tazagayo ta bu'de Masa still saidata kamo hannunsa suka nufi part dinsu.

Suna shiga Palo ya zube akujera tareda tallafe fuskarsa cikin tsanani.

Bedroom ta nufa jiki asake itama ta zube bakin gado tareda tallafe fuskarta hawayen tausayin saheeb da gangaro Mata.


Qarfe bakwai na safe yabar gidan Yakoma asibiti
Taji motsinsa kodata fito palon harya fice
Tsayawa tayi tareda dafe goshinta tana qoqarin maida hawayenta sbd tabbas tarigada tasan matuqar Abba ya rasu saheeb will totally break,
Zai shiga mummunan quncin dayafi Wanda yake ciki,
Rayuwarsa zata qarasa shigewa duhu.


Bedroom takoma tafada toilet tayo wanka tana fitowa ta shirya cikin doguwar Rigar maroon atampa ta jawo gyale da wayarta Sai key ta fito ko gurin gwaggo Bata shigaba ta fice.


Tana Isa asibitin daidai qofar room din shikuma yafito tareda Dr suka nufi office 'din Dr
Ta ra6e suka wuce
Kallo 'daya yayi Mata ya 'dauke Kai suka wuce soldier 'daya na bayansa.


Shiga 'dakin tayi ta tararda nurses uku maza da Dr 'daya a 'dakin
Cikin sanyin murya ta gaishesu kafin tamaida kallonta ga abban taga gabaki 'daya ya sauya kamanni cikin dare 'daya gashi ko numfashi bayayi Saida oxygen baisan waye akansaba.

Zama tayi Kan kujera tana ayyana abubuwa da dama akansu mum asee.

Zayyan ne yashigo jikinsa asanyaye fuskarsa cikin wani mugun yanayi ya kalleta.

Fa'duwa gabanta yayi cikin sanyin murya ta gaidasa tareda cewa,

Me Dr yace akan Abba.

Girgixa Kai yayi cikin tsananin damuwa yace,

Wata jijiyar kansace ta katse Wanda ta jawo Kwakwalwarsa ta ha'de da jini sosai,,,,
Ba hope Anano, saheeb na cikin wani irin tsanani.,
Dole za'a fita da Abba waje zuwa jibi.


Hawaye masu dumine suka gangaro Mata ta share hannunta na rawa kafin ta miqe asanyaye tafuce Dan Bata iya tsayawa ganin halinda saheeb ciki.


Gida takoma tashige bedroom ta zauna tafara kuka cikin tsananin tashin hankali Dan yanxune taqara sanin su waye mum asee.


Yinin ranar ko Palo Bata fitoba idanuwanta sunyi tsananin kumbura Dan har wani sarawa kanta yakeyi.

Da daddare su gwaggo dasu mum asee gidan dai duka suka 'dunguma zuwa asibitin ita ka'daice ta rage a gidan ta miqe ta fito Palo ahankali jiri na 'dibarta ta nufi kicin ta 'dauko ruwa tadawo Palo.

Daf dazata shiga bedroom dinta taji anfuzgota da qarfi.

Cikin tashin hankali da tsoro ta bu'de baki zata kurma ihu ya toshe Mata baki Yana sakin Wani shi'umin murmushi sbd Yana sane yatura su mum asee asibiti da gwaggo Dan yasamu yau yacire kwadayinsa.


Zaro idanuwa tayi cikin wani mugun tsoro da fa'duwar gaba tahau qowarin qwace kanta.

Kasa qwacewa tayi ta daddage tasakar Masa wani mahaukacin cizo

wata irin qara yasaki tareda tureta da qarfi saida kanta ya buge da bango Nan take goshinta da bakinta ya fashe
Bata tsayaba ta rarrafa zata gudu yasake fuxgota Yana yarfe hannu yaga yanda haqoranta suka fito ahannunsa ya wanka Mata wani gigitaccen Marin daya kuma sata kifewa bakinta na qara fashewa.

Jawota yayi da qarfi tareda sa qarfi ya 6arka doguwar Rigar baccin dake jikinta Yana cewa,

Yau sainayi maganin duk wani iskanci da kike jidashi keda good for nothing bastard mijinki.


#vote
#comment
#share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*35*
Turo qofar yayi bayan shigarsa ya tako ahankali har tsakiyar room 'din sbd yanada girma sosai,
Tsayawa yayi lokacinda ya hangota hanyar toilet zube kamar ba Rai ajikinta
Maganar zayyan ta fa'do Masa itama zata iya mutuwa kenan tabarsa kenan.....

Nufarta yayi zuciyarsa na nauyi da tunanikan da maganganun zayyan dasuke dawowa suna amsa kuwa a kunnuwansa.

Duqawa yayi ya 'dauketa cak saidaya rintse idanuwansa sbd Yana 'daukarta tarayyarta da Kamal tafado Masa ya bu'de idanu da sauri kafin ya nufi gado ya kwantarda ita tareda jawo duvet cover ya rufeta ya zauna bakin gadon tareda Kiran wayar zayyan

Jiki na rawa zayyan din dasuka matsu suji abinda ke faruwa ya 'dauka.,

Zasu iya shigowa yace Kai tsaye tareda kashe wayarsa ya rintse idanuwa sbd har lokacin zuciyarsa takasa samun matsaya.

Jiki asanyaye suka shigo suna ganin halinda take ciki zayyan yakalli manager yace,

Hurry please and call any dr...

Yes yes""""yace da sauri Yana Ciro wayarsa sbd Shi duk sun rikitasa yakasa gane komai.

Ko mintuna goma ba'ayiba Dr ya iso cikin gaggawa yafara dubata bayan dukkaninsu sun fita Banda saheeb din dake zaune still agurin idanuwansa a rintse kansa tsananin Sara Masa yakeyi.

Duk abinda yakamata Dr yayi yagama dubata yayi Mata allurai tareda aje magunguna,

Juyowa yayi yakalli saheeb yayi gyaran murya,

Ahankali ya bu'de idanuwansa ya zubawa Dr din,
Dr yayi Masa bayanin magunguna ya 'dora da fa'din arinka Bata abinci akan time sbd harda yunwa.

Dr na fita ya lumshe idanu tareda juyawa ya budesu akanta
Akaro na farko daya qure kallonsa akanta batareda tsana,baqin ciki ko takaiciba.

She's very young,

Face 'dinta yakalla zuwa jikinta bai qarasa qirjinta ba yayi saurin 'dauke kansa tareda miqewa ya fito.

Bai jimaba tareda zayyan yadawo yabada order abinci yakalli gadon yaga har time din Bata farkaba ya saki qaramin tsaki sbd atakure yake Sam shi bai cikason Zama ko kwana da wani aroom ba
Ko lokacin nafeesat ba kullum suke kwana a daki dayaba,

Tu6ewa yayi ya nufi toilet yashige.

Wanka yayo Yana fitowa ya shirya cikin kayan bacci black ya nufi qofa ya bu'de sbd knocking da'akai.

Abincin dayayi order ne ya karbo ya ajiye,
Tea kawai yasha da toasted bread ya kashe wayarsa sbd mum asee data hanasa sukuni da koke koken rashin ganin Kamal har yanxu.

Ahankali ta bu'de idanuwanta dasukai Mata nauyi ta 'darasu akansa.

Zaune yake bakin gadon yabata baya ya cusa hannuwansa cikin gashin kansa Sam zuciyarsa takasa samun nutsuwa jin maraicinsa yake matuqa Yana shigarsa akaro na farko dayaji hankalinsa na tashi kamar zai rasa wani Abu.

Qoqarin tashi zaune tafara sbd jikinta ba qwari duk da taji sauqi ba laifi.,

Motsinta yasashi juyowa ahankali idanuwansu suka ha'du cikin na juna
Duk da tana cikin Hali na ciwo sosai taji hankalinta yatashi sbd ciwo da tsananin damuwa data gani qarara a idanuwansa,

Sunkuyar da kanta tayi tareda matsawa gefe ta sauka gadon cikin sanyi da 'dan jiri ta fa'da toilet.

Wanka tayo sbd ajiqe take sharkaf da zufa Kuma wankan ya taimaka Mata matuqa Dan taji qwarin jikinta.

Daqyar ta iya danne kunyarta ta fito toilet din 'daure da towel Sai ta rufo jikinta da wani towel din.

Kasa 'dago idanuwanta tayi ta nufi wardrobe jikinta na rawar sanyi ta jawo doguwar Riga red Mara hannuwa tasaka sbd amatse take data saka koma meyene tunda batada want za6in.

Miqewa yayi ya nufi bakin window  ya tsaya Yana kallon waje ta cikin glass hannuwansa zube cikn aljihun wandon kayan baccinsa.

Mayarda towels din toilet tayi tadawo tana tafara qoqarin komawa ta kwanta sbd sosai takejin sanyi Dan rigar jikinta ba abinda ta Hana ko takare Kan sanyi.

Gyara tsayuwa yayi batareda ya juyoba yace,

Kici abinci akwai maganin dazaki Sha.

Shiru tayi tareda 'dagowa ta kallesa duk da Bai juyo taga fuskarsa ba taji da'din kulawar daya nuna Mata.

Murmushin dabatasan dashi bane ya kubce mata ta sauko gadon ta nufi gurinda abincin yake ta ha'da tea tafara Sha tanajin wani sanyi na shiga zuciyarta.

Tana gama Sha ta 'dako takalli gefen dayake idanuwansu suka ha'du sbd ya Jima da juyowa ya qura Mata oily eyes dinsa yanason gano abinda yakeji gameda ita,
Meyasa yakejin zafinta akoda yaushe Dan yakasa yakice tarayyarta da kamal Wanda hakan ke qara hura wutar Jin zafinta dayake.

Sunkuyar dakai tayi bazata iya jurar kallon idanuwansa ba sbd zata iya fallasa dukkanin sirrikanta idan tana kallonsu.

Takowa yayi ahankali yazo ya zauna kusada ita
Cikeda tsoro da mamaki ta 'dago suka qara hada idanu tai saurin mayarda kanta qasa gabanta na tsananta fa'duwa.,

Maganin ya 'dauka ya cicciro ya miqa Mata
Sake 'dagowa tayi still idanuwansa kafe akanta
Hannu ta miqa ahankali ta kar6a ta bu'de baki cikin sanyi tasaka tareda daukar ruwa tasha still idanuwansa kafe akanta.

Miqewa tafara qoqarin yi ya 'dauke kansa ta ra6a ta wuce sum sum tana satar kallon gefensa cikin rashin sa'a suka sake hada ido
Tayi saurin qarasawa gado zuciyarta cikeda mamakinsa yanda ya iya tsare mutum da idanuwansa kamar yasan idanuwan nasa rikita Mai kallonsu suke.

Jawo bargo tayi ta dunqule tareda rufe idanuwanta duk da Sam bataji alamar ma barci zai iya zuwar Mata ba sbd rashin sukuni da yanda gabanta ke fa'duwar kasancewarsu zasu kwana guri 'daya abinda Bata ta6aba arayuwarta.

Tun tana jiran Jin ya motsa harta daina bacci ya 'dauketa.

Cikin tsakar dare zazza6inta yadawo sosai Nan tafara rawar sanyi tana hawaye.

Zaune yake akan sofa ya 'dora qafafunsa akan table din gabansa idanuwansa a rufe,,
Ahankali sautin kukanta yafara fita Yana shigarsa ya bu'de idanuwansa ahankali ya kalli gadon yaga yanda take jijjiga.

'dauke Kai yayi tareda rufe idanuwa Amma saiyaji yakasa samun nutsuwa da sautin kukan ya sake bu'de idanuwa ya miqe cikin nutsuwa ya Isa bakin gadon ya zauna batareda yayi maganaba yayi shuiru cikin tsananin damuwa da takaicin abinda Dole shine zaiyi Dan taimaka Mata.

Rigarsa ya cire ahankali ya
Hau gadon tareda yaye bargon wani zazzafan hucin zafin jikinta ya bugesa
Ahankali yakai hannuwansa ya tada ita zaune tareda shigar da ita cikin jikinsa ahankali ya rungume Yana rufe idanuwansa.

Ahankali zafin jikinta ke shiga jikinsa tareda wani irin yanayi dabaisan meneba Dan bazai kirasa da sha'awaba.

Tun yanajin numfashinsa na toshewa sbd yanda ta narke sosai ajikinsa dakuma rashin sabo sbd baya kwana haka Sam da mace
Har yaji numfashin nasa na tafiya daidai still idanuwansa arufe suke
Kamar ha'din Baki kusan atare bacci ya 'daukesu.


Qarfe bakwai suka tashi kusan atare
Shine yafara bu'de idanuwansa ya qurawa face 'dinta ido ko qyaftawa bayayi.

Tana bu'de nata idon Sai acikin nasa Tai saurin mayarwa ta rufe gashi still tana cikin jikinsa maqale.

Sakinta yayi tareda zamewa ya miqe ya nufi toilet Yana yamutse fuska
Mitsw Meyasa nake yawan kallonta?

Alwala yayo yana fitowa ya tada sallah ko gefenta Bai kallaba.

Itama jiki amace ta shiga tayo alwala tazo gefensa ta tayar.

Yana gamawa ya fice zuwa gym.

Bakin mirror ta tsaya tana kallon fuskarta data kasa 6oye farin cikinta jitakeyi duk wani ciwo da zazza6i yabar jikinta ataqaice ma qamshin da jikinta keyi yafi komai sanyata farin ciki.

Toilet ta fa'da tayo wanka hankalinta kwance tafito tazauna gaban mirror tayi shafe shafenta ta miqe tana bu'de wardrobe ta tuno da batada kayan arkikin sawa
Tadawo bakin gado ta zauna tareda lalubo wayarta ta kunna tana cikin neman numbern Nabeela saiga kiranta yashigo ta 'dauka tana cewa,

Dole ki kirani ai kiji yanda naci gidanmu tunda kin kaini kin baro..

Dariya tayi tana cewa,

Haba Mrs saheeb wane ni nakaiki na baro nadai yiwa aure gyarane.

Numfashi ta sauke cikin sanyin murya tace,

Maganar gaskiya nabeela banason Jan hankalinsa ta hanyar nuna Masa jikina ko kwa'daita Masa kaina sbd hakan aganina bashine soyayya ko zaman aureba,

Inason saheeb so Mai tsanani Wanda zanso idan har zai Soni to yazamto ba son sha'awa zaiminba,.

Cikin Jin da'din abinda ananon tafada nabeela tace,

Hakane Amma ba duka matane suke gane hakanba Wanda wasu sun 'dauki sha'awa itace aure ko soyayya Wanda aure da dama ya mutune Kan angina rayuwar auren ne bisa sha'awa Babu soyayya.

(marubuta ku kiyaye ba duka sha'awa ke jawo soyayya ba sa6anin nunawa da kuke dazaran ta nuna Masa jikinta zai sadu da ita shikenan Sai soyayya,
Sam wannan bashine soyayyar aure ba
Karkuji zafina tunatarwace nayi.)


#vote
#comment
#share
And
#follow.
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamhugee_


*36*
Suna Gama waya da nabeela ta miqe ta lalubo wata doguwar Riga maroon iya gwiwa Mai dogon hannu tasaka tareda gyara fuskarta ta gyara gadon tadawo ta zauna tana kallon tv.

Qarfe tara ya dawo Yana knocking ta miqe ta zura dogon hijabinta ta nufi qofar ta bu'de,

Tare yakeda zayyan ganin hijabinta yasa ya ra6ata ya shige da dafarko yayi wani bake bake abakin qofar
Shi zayyan abinma dariya tabasa yadai qyalesa ne kawai sbd yanxu ya gano inda ya dosa.

Cikin girmamawa suka gaisa da zayyan yayi Mata ya jiki ya wuce room dinsa sbd daga gym suke.

Rufe qofar tayi bayan zayyan ya wuce ta juyo ahankali tadawo sofa ta zauna tana tareda bu'de baki cikin sanyi tace,

Ina kwana?

Ruwan daya Ciro a fridge ya zuba a cup tareda gyada Mata Kai batareda ya kalli gefen datakeba.

Yana gamasha toilet ya fa'da yayo wanka Yafito daureda towel
Kallo 'daya tayi Masa gabanta yayi mummunan fa'duwa ta 'dauke Kai da sauri sbd lafiyayyan mur'daden jikinsa data gani musamman ma kafadunsa kamar 'dora masasu akayi.

Shi kansa kasa sakewa yayi yasaki qaramin tsaki tareda 'daukar kayansa Yakoma toilet Yana yamutsa fuska ya shiryo yafito.

Zayyan ne yayi knocking Yana bu'dewa ya sanardashi su sauko suje suyi breakfast a qasa cikin restaurant.

Batareda ya kalletaba yace ta taso suje
Ta taso riqeda wayarta suka sauka zayyan na qoqarin janta da fira
Tanason sakewa suyi firar tana tsoron yanda taga saheeb din ya ha'diye fuska.

Vip suka shige suka'daine gurin ya tsaru matuqa Nanda Nan akazo aka kar6i order dinsu
Tana fira da zayyan ahankali
saheeb Kuma Yana waya da 'daya daga cikin doctors din Abba.

Cikin kwanciyar hankali sukai breakfast duk da dukkaninsu bamai cin abinci sosai.

Sosai yake kallon yanda tasake take fira da zayyan kamar wa'inda dama sunyi shekaru da sanin juna
Musamman yanda take Masa firar nabeela.

Qurawa qaramin bakinta dake magana Ido yayi Yana kallon yanda lips dinta ke motsawa batareda tasaniba
Shikuwa zayyan Yana luredashi saiya qara qaimi gurin janta da firar nabeelar.

Shidake kallonta yafi shagala akan ita dake firar,

Ganin kamar dogon hijabinta yafara damunta yasa yakira waitress dinsu 'daya tana zuwa ya miqe tabi bayansa saida yakusa Kai qofa ya juyo tareda sakar Mata wani miskilin murmushin daya kusan Raba Anano da numfashinta sbd akan idonta.,,

Jitayi qirjinta yayi mugun nauyi idanuwanta taji na neman kawo ruwa tai saurin 'dauke Kai tareda sunkuyarwa,

Murmushi zayyan yasaki sbd yaga halinda tashiga duk da dai yasan ba abinda saheeb zaiyi da baturiyar.

Sunanta yakira cikin son ya mantarda ita komai
Tana 'dagowa kafin yayi magana waitress 'din ta iso gurinsu tareda kallon zayyan tace,

Sorry sir but i need to take her somewhere.

Kallonta sukayi kafin suka kalli juna
Ta miqe jikinta na qara saki suka bi wata qofa sukabar restaurant 'din.

Cikin wani qaton lafiyayyan boutique taga sun fa'da tana 'dagowa sukai Ido hu'du dashi
Ya 'dauke Kai Yana fiddo wayarsa.

6angaren dogayen Arabian,Kuwait and Turkish gowns takaita tareda fara jidar matasu
Itadai komai takasa yi Sai waiwayen gurinsa takeyi zuciyarta na qara cika da tsananin qaunarsa.

Suna gamawa aka saka kayan a jaka suka fito ta rakota har qofar room 'dinsu takoma.

Zubewa tayi bakin gado fuskarta cikeda farin ciki tareda murmushi,,
Lumshe idanuwanta tayi tana tunano murmushinsa da fuskarsa ahankali tace,

Mrs saheeb abdallah.

Miqewa tayi fuskarta kunshe da farin ciki tafara kwada kayanta.

Kwanansu biyu kenan cikin asiri da rashin sani sun fara sabo duk da Babu wata magana dake shiga tsakaninsu bayan gaisuwa Sai idan zasuje cin abinci,

Hakanan yakejin wani yanayi Mai da'di nashigarsa ko yaushe sukaje cin abinci idan tana fira da zayyan saiyaita kallonta Wanda ita batamasan yanayiba.

Yaune zasu koma asibiti tunda wuri suka shirya,
Doguwar Kuwait gown dark blue tasaka tareda rolling qaramin gyalen rigar ko handbag Bata 'dauka Sai waya kawai suka fito.

Tunda yatashi ta lura da damuwa Sosai a fuskarsa duk Sai itama jikinta yayi sanyi
Suna shiga mota ta juyo ahankali takallesa gabanta na fa'duwa ta dake cikin tsananin kulawa tace,

Karka damu insha Allah Abba zai samu lafiya.

Juyowa yayi ya kalleta da oily eyes dinsa dasuka fara canzawa sbd tension baisan sanda ya gyada Mata Kaiba ya tada motar suka wuce sbd zayyan already ya fice wani gurin dagacan zai wuto asibiti.


Mummunan tashin hankali shine ya kutso Kai cikin rayuwar saheeb lokacinda likitoci suka sanar dashi qwaqwalwar Abba tayi damage Sai anyi Masa aiki Wanda suna fatar Allah yasa adace.

Ka'dawa idanuwansa sukayi Nan take jajir,
Hawaye yaji na neman taruwa a idanuwansa akaro na farko arayuwarsa tun wayonsa,

Ganin mugun halinda yashiga yasa hankalinta tashi hawaye suka 6alle Mata batasan sanda ta riqo duka hannayensa biyuba ta ha'de da nata ta damqe tana kallon cikin idanuwansa alamar lallashi.

Zayyan na isowa ya tarar da mugun labarin Nan take shima hankalinsa ya tashi
Dole shine yaje ya qarasa formalities 'din daza'ayi aikin gobe.

Tunda suka dawo ya zauna a sofa tareda rintse idanuwansa har lokacin hannuwansu na damqe Dana juna sbd sosai ta lurada Yana tsananin buqatar kulawar wani awannan lokacin sbd tabbas idan yarasa Abba yarasa kowa kenan,.

Da daddare duk yanda taso yaci wani Abu 'daure fuska yayi yaqici itama saitaqi cin komai ta zauna kusadashi.

Gyagyadi tafara harta zame ta fa'di jikinsa bacci ya dauketa,,

Qurawa face 'dinta idanu yayi yaga tayi wani pale da ita saiyaji zuciyarsa tayi sanyi da tausayinta sbd yau itace Rana ta farko arayuwarsa da wani ya hanawa kansa sukuni da qin cin abinci akan damuwarsa,

Yau itace Rana ta farko da wani ya nuna Masa kulawa Akan damuwarsa,

Yau itace Rana ta farko daya hango damuwarsa afuskar wani bashi ka'daiba,

Yau itace Rana ta farko dayake cikin tsananin damuwa ya wuni cikin kulawar wani ba kamar ko yausheba da shika'dai kecin damuwarsa hartai Masa illa ta Gama.

Hannu yakai akaro na farko ya shafo fuskarta cikin tsananin kulawa da tausayinta sbd Sam itama ko ruwa takasa sawa cikinta sbd ganinsa cikin damuwar mahaifinsa,

Gyara Mata kwanciya ajikinsa yayi tareda kallon Abincida tayi order yasan ya huce ya jawo waya yasake bada order coffee da noodles.

Cikin qanqanin lokaci akai knocking ankawa.,

Kallon yanda take bacci hankali kwance ajikinsa yaji yakasa miqewa yabada umarnin shigowa.

Har gabansa aka aje abincin Kan table kafin ta fice.

Bu'de abincin yayi ya 'dauko da hannu 'daya yakai hannu 'daya zai tadata
Sai kuma ya dakata ya kalli hannunsa Yana tunanin kansa,.

Qamshin noodles 'din yashiga hancinta cikin bacci taji yunwarta ta motsa ta bu'de idanuwa ahankali tana lumshewa,,

Tsikar jikinsa yaji ta tashi akaro na farko arayuwarsa baisan sanda ya lumshe ido ba shima.

Cikin shirmen bacci ta bu'de Masa Baki tana cewa,

Yunwa nakeji.

'debowa yayi da spoon ahankali yakai bakinta ta cinye tareda lumshe idanu,

Gyara kwanciya tayi jikinsa yaqara 'debowa yabata tanaci.,,

Saidata kusa cinyewa ta 'dago ta kallesa ta kar6e plate 'din da spoon ta 'depo ta nufi bakinsa still idanuwansu cikin na juna.

Bai ta6a cin noodles ba arayuwa sbd baya cinta ya kwata kwata Amma tana 'dora spoon din bakinsa ya bu'de ahaka ta ringa basa Saida suka cinye tasa ta 'dauki ruwa tabasa yasha kafin itama tasha takoma jikinsa tayi lafewarta.


*Maganar gskia inajin da'din comments dinku,*
*Kun nunan qauna Kuma nagode matuqa...*

*Musamman my wattpadians and my group members*
*I love you guys so much so keep the doing the good work.*


#vote
#comment
#share
#and follow.
#vote
#comment
#share
#vote
#comment
#share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@muhgee_


*37*
Baccine yakuma 'dauketa ajikinsa
Ya qurawa 'yar qaramar face 'dinta idanu tsawon lokaci kafin ya lumshe idanuwansa ahankali ya rufe damuwa shimfide cikin ransa.

Qarfe shida ta bu'de idanuwanta ahankali cikin bacci
Suka sauka kan fuskarsa da idanuwansa idanuwansa suke rufe dukda ba bacci yakeba.,

Qarasa bu'de idanuwanta tayi suna qoqarin cikowa da hawaye jikinta yaqara sakewa sbd tsananin gajiya da damuwa data hango qarara ataredashi Dan har fa'dawa yayi cikin daren guda.,

Jin kamar ana kallonsa yasa ya bu'de idanuwansa dasukai Masa nauyi ahankali ya xuba cikin nata idanun data kafesa dasu.

Ganin yanda idanuwansa sukai laushi yasa hawayenta gangarowa tareda 6allewa sunta saukowa.,

Hawayen nata dake gangarowa ya mayarda kallonsa kafin yakuma kallon idanuwanta ya bu'de Baki akasance cikin wata irin murya Mai sanyi yace,

What is it....Bai qarasaba ta fashe da kuka ahankali harda shesheka,,

Baisan me zaiyiba Sai kawai ya mayarda ita cikin jikinsa ya rungume batareda yace komaiba sbd ko Baki bayason motsawa.

Saidatai shiru kafin ya dagata ya miqe ya nufi toilet yayo alwala Yana fitowa itama ta shiga kusan atare sukai sallar
Gari na qarasa wayewa shiya fara shiga wanka yashirya kafin itama tayi ta shirya cikin doguwar Rigar Morocco coffee brown
Wayarta kawai ta 'dauka suka fice.

Wani babban restaurant ya biya da ita  breakfast Wanda shi komai baiciba sbd azumi daya wuce dashi,
Itama dai milkshake kawai Tasha Sai cookies suka fito suka nufi asibiti.

Suna Isa acan suka tararda zayyan fuskarsa kawai ta qara tabbatar musu da Babu wani sauqi Sai abinda Allah yayi.

Fuskar saheeb takalla tareda dafa hannunsa ta gyada Masa Kai alamar yabarwa Allah komai insha Allah za'a dace.

'dora hannunsa yayi Kan nata batareda yace komaiba.

Duk wasu shirye shiryen aikin anyi angama qarfe Tara suka shiga dashi aka fara.


Zaune yake fuskarsa ta ka'da sunyi jajir kasancewarsa fari musamman idanuwansa da sukai laushi sosai,
Kallo 'daya zakai Masa jikinka yayi tsananin sanyi duk da saheeb din namijin gske ne baka gane damuwarsa,6acin ransa,fushinsa ko farin cikinsa.

Zayyan madai cikin tsananin damuwar yake sbd rasa Abba a rayuwar saheeb ba qaramin tarwatsewa zaiyiba Dan kuwa yasan barin qasar zaiyi tunda dama sbd abbane yake zaune anan idan abba yatafi zai tafiyarsa su mum asee zasu samu yanda sukeso su lalata arziqinsa gabaki 'daya.

Zaune take kusadashi idanuwanta sunyi jajir sbd yawan hawayen datake
Addua take Allah yatashi kafadun Abba yasa adace Kar wata matsalar tabiyo baya.


Tun suna sakawa kansu juriya gurin jira harsuka fara katsewa sbd ganin an 'dauki awonni.

Cikin tashin hankali wasu nurses suka fito da gudu,

Atare dukkaninsu suka miqe Amma nurses din ko gefensu Basu kallaba sukaje suka 'dauko wasu abubuwa suka dawo suka shige,

Suna shiga wata nurse takuma fitowa cikin sauri takirawo wani Dr cikin sauri shima ya qaraso Yana gyara kayan tiyatar daya sako cikin sauri ba daidaiba.


Innalillahi wa'innaalhr raji'un,,,
Kullu nafsin za'ikatul maut
Haqiqa kawanne Rai saiya 'dandani mutuwa
Abba dai Kam lokaci yayi ya rasu batareda ankammala aikinba,

Cikin tsananin damuwa suka qarasa abubuwan dasuka kamata suka kashe komai tareda qarasa rubuce rubucensu suka fito.

Zufa babban doctorn yasa handkerchief ya goge tareda signing papers din fitowa aiki da nurse ke miqo Masa ya miqa Mata ya juyo ya fuskancesu.

Kallo 'daya saheeb yayi musu wani irin jiri ya 'dibesa cikin tashin hankali Anano tayo kansa tareda taresa suka zube a kujerar dake gurin ta rungumesa ajikinta da qarfi sbd tuni Dr yakorowa zayyan bayanin abban ya rasu.

Kuka tasaki Mai tsuma zuciya tana qara qanqamesa sbd ganin yanda jikinsa ke wata wata irin rawa..

Tsoro rawar da jikinsa keyi tafara Bata cikin kuka ta'dago kansa sukai Ido biyu da sauri ta rintse idanuwanta tareda sakin Wani sabon kuka sbd ganin wani masifaffen rinewa da idanuwansa sukayi ga jijiyoyin kansa dasuka matuqar tashi
Cikin kuka ta qwala Kiran zayyan daya shiga 'dakin da gawar take yafito idanuwansa shima jajir bakinsa abushe.

Da sauri ya qaraso tareda riqosa zaiyi magana yasan saheeb zai iya miqewa ya nuna zai iya jurewa Wanda dukkanin alamu sun nuna Yana buqatar kulawar likitoci.

Miqewa yayi da sauri yakira doctor da nurses biyu suna zuwa sukai Masa wata irin allura kafin yayi wani yunquri aka kawo gado aka dorasa sukai wani room dashi Nan take idanuwansa suka rufe jikinsa yasaki.

Kukan tashin hankali Anano tasaki hartana shaqewa sbd yau ta tabbatarda mijinta da 'danta sun Zama marayu,
Abba ya rasa ransa ta sanadin naso fallasa sirrinsu mum asee,
Abba yarasa ransa ta hanyar kisar azaba Mai tsanani sbd Allah ne kawai yasan halinda yashiga na tsananin azabar dayasha kafin Allah yadauki ransa,
Mutane nawane su mum asee zasu kanshe dan cika qaramin burinsu?

Sun tarwatsa rayuwar saheeb sun hanasa farin ciki tun tasowarsa yataso cikin rayuwar ka'daici,rashin nuna qauna ko kulawa tareda tsananin duhun qunci.,
Sun kashe Abba yanxu gaba wa zasu kashe?
Zai iya yiyuwa saheeb, abdulshakur, gwaggo,zayyan kokuma ni kaina.

Cusa Kai tayi tsakanin qafafunta kukanta na qara tsananta tanaji aranta lokaci yayi daza'a takawa su mum asee burki Babu 6oye boye zata zayyanewa saheeb komai sbd bazata iya jurar su kashe Mata waniba Nan gaba,..

Tashin hankalin zayyan qaruwa yayi ya zauna tareda dafe kansa dayakejin kamar zai rabe sbd azabar ciwo da nauyi,
Saheeb kawai ya kalla yaji hankalinsa yaqara tashi sbd badan wannan allurarba zai iya collapsing.
Ga 6angare 'daya kukan tashin hankalin da anano ke risga.

Bai Bari sun qara kwanaba yafara musu shirye shiryen tafiya
Cikin qanqanin lokaci yagama komai aka sako musu gawar Abba da saheeb jirgi suka nufo gida.

Tunda suka koma hotel ta hado musu kayansu kukanta ke qaruwa harsuka shiga jirgi jirginsu yatashi..

Koda suka sauka Nigeria tuni labarin rasuwar ya kara'de ko'ina ta hanyar labarai.

Motocin sojojine birjik sukazo daukarsu suka tunkaro gida lokacin anyi sallar asuba gari yafara haske,

Har suka Isa gida saheeb Bai farfado ba sbd ba qaramin qarfine da allurarba,
Anano kuwa ko gani sosai batayi sbd kuka
Koda suka iso gida tuni gidan yake cike ana jiran isowarsu

Mum asee kallo 'daya zakai Mata tabaka tausayi sbd kuka dakuma uwar ramar datai badan mutuwar mijintaba saidan 'danta daya 6ata saidai abin mamaki kafin isowarsu zayyan din aka kawosa qofar gida
Yaci duka yayi mugun baqi da Rama yafice hayyacinsa matuqa yaja qafafuwansa dasukaci uban duka sukai mugun tsami ya shige 6angarensa batareda kowa ya gansaba.

Gwaggo ma tunda asubahin ranar suka dawo itada baffa dasu Yusuf Inna ce kawai ba'azo da itaba.

Ana gab da kammala suturta abban
Ya farfado tareda dafe goshinsa sbd tsananin nauyi da kansa yayi masa.,

Yana ganin inda yake yasan allurarda zayyan yasa akai Masa
Yafara qoqarin tashi zaune.

Zaune take cikin mutane acan part dinsu mum ta miqe ahankali ta fito ta nufo part dinsu sbd ta dubosa koya farka sbd awannin da'a diba sunyi..

Tana shiga bedroom din Yana kawowa bakin qofa cikin sauri ta riqosa sbd jiri Bai Gama sakinsaba.

Zafi taji sosai jikinsa yayi takallesa idanuwanta cikeda hawaye zatai magana akai knocking qofar Palo.

Kasa sakinsa tayi ta juya ta nufi qofar tana riqeda hannunsa tana bu'dewa taga zayyan ne cikin damuwa yace,

Dama angama komai nazo naji koya tashine..

'daga Masa Kai tayi sabbin hawayenta na gangarowa ta matsa yashigo palon

Yana kallon saheeb din yaji zuciyarsa na neman karyewa sbd yanda idanuwansa sukai jajir.

Alwala takaisa har toilet yayo suka fito zayyan yabi bayansa suka fice zuwa gabatarda sallarsa daza'ayi.


#vote
#comment
#share
#and follow.
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*38*
Lokacinda saheeb yayi Ido biyu da gawar mahaifinsa wani sabon nauyin qirji ya danne zuciyarsa jijiyoyin kansa suka sake fitowa
Nan aka fitoda abban dubban jama'a sukai jana'izarsa aka tafi aka kaisa makwancinsa aka dawo.

Har maraice anata kar6ar gaisuwa Sai bayan sallar isha'i yashigo gida bayan kowa ya watse itama tana fitowa tareda nabeela daga 6angaren mum wucewa part dinsu tayi sbd duk baqin mum 'din dasukazo gaisuwa daga wasu garuruwan Sai dangin abban duk Nan zasu kwana.

Saidata biya gurin gwaggo ta dubo abdulshakur kafin ta fito.

Wanka tayi sba kanta dayake tsananin ciwo ta saka rigar bacci Mara nauyi harta hau gado
Taji zuciyarta takasa nutsuwa batareda tadubosaba
Ta sauko ta saka hijab ta fito palo.

Kicin ta nufa ta ha'da Masa tea tareda dafa indomie ta jero a qaramin tray ta nufi bedroom 'dinsa.

Cikin fa'duwar gaba ta tura qofar tashiga tareda siririyar sallama.

Kwance yake bakin gado ya takure sosai kamar maijin sanyi ko lullu6i baiyiba.

Ga wutar 'dakin akashe bedside lamp ce kawai a kunne.

Wani sabon tausayinsa da tsananin sonsane yasake shigarta ta qaraso idanuwanta na cikowa da hawaye ta aje tray din Kan bedside drower ta durqusa gabansa saitin fuskarsa.

Bu'de idanuwansa yayi ahankali ya kalli fuskarta
Ya qurawa hawayenta Ido nauyin zuciyarsa na qaruwa..

Hannu ya 'daga cikin sanyi ya share Mata hawayen,

Cikeda tsananin mamaki ta kallesa hawayenta na qara gangarowa.

Cikin sanyi da rawar murya tace,

Ga abinci.

Tray 'din ya kalla kafin ya maido da kallonsa kanta yaga yanda tai wani zuru zuru fuska akumbure jajir.

Ahankali ya tashi zaune tareda nuna Mata kusadashi batareda yayi maganaba.

Tashi tayi ta tazauna kusada shi tareda jawo tray din ta 'dauki cup din tea ta miqa Masa tana kallon fuskarsa.

Kallon face dinta yayi kafin ya kar6i cup din tareda kaiwa bakinta
Ba musu ta bu'de Baki ta kur6a ahankali.,

Indomin ta 'dauka tareda debo kadan a spoon takai bakinsa ya girgixa Kai
Ta qyafta idanu hawaye suka gangaro
Ya bu'de Baki ya karba.

Ahankali suka ringa cin indomin suna Shan tea har suka cinye kusan duka duk da ba maganar data shiga tsakaninsu saidai saqonnin idanu.

Suna gamawa ta fitarda kayan dagacan ta wuce bedroom 'dinta ta kwanta jiki amace zuciyarta cikeda damuwa da tausayinsa.

Daqyar bacci ya iya 'daukarta
Cikin Tsakiyar dare taji kamar motsi a Palo
gabanta yayi mummunan fa'duwa ta miqe zaune tareda saukowa gadon ta fito palon ahankali saita jiyo kakarin amai bedroom dinsa
Tsinkewa gabanta yayi ta nufi bedroom din da sauri batareda takoma ta sanyo hijab ba.

Cikin toilet yake yanata yunqurin amai fuskarsa tayi jajir jikinsa ba inda baya rawa.

Da gudu ta qarasa tareda riqosa ya 'dora idanuwansa dasukai ja daqyar kanta.

Idanuwanta na taro hawaye ta kallesa kafin ta zuba Masa ruwa Yana wanke fuskarsa ahankali
Yana gamawa suka dawo bedroom ya kwanta tajawo duvet cover ta rufesa ta rage sanyin AC dakin tadawo bakin gadon ta zauna tareda qura Masa Ido tana qoqarin mayarda hawayenta ganin yanda jikinsa ke jijjiga sosai Yana fitarda wani hucin zafi.

Ganin yayi bacci yasa ta kamo hannunsa ahankali ta riqe sonsa na qara karya zuciyarta.

Kyakkyawar farar fuskarsa ta qurawa idanu ganin ta fa'da sosai tayi jajir cikin kwana 'daya da yini da rasuwar abban.

Gab da asuba zazza6in ya'dan sakesa ya farka
Yana bu'de idanuwansa Sai Kan fuskarta data kwantar bakin pilonsa bacci ya 'dauketa
Da alama shitake kallo baccin ya 'dauketa sbd har numfashinsu Sosai yake ha'duwa.

Hannunsa ya motsa zai gyara Mata kwanciya sbd aqasa take zaune kantane kawai a gadon yaji hannunsa maqale da nata ta riqe Gam.

'dayan hannun yakai ya shafo fuskarta ahankali sbd baida qarfin jiki.

Bu'de Ido tayi Sai kawai tasamu kanta dajin tsananin kunya ta rintse ido tareda qoqarin miqewa taji yaqara damqe hannunta da nasa yake ciki.

Sunkuyar dakai tayi tana qare damqe idanuwanta xuciyarta na harbawa da sauri.

Jawota yayi yakai fuskarsa daf da Tata zaiyi magana Bata Bari taji Mai zai fa'daba ta qwace ta Fice 'dakin da gudu.

Bayanta yabi da kallo da oily eyes dinsa dasukai mugun laushi suna lumshewa.

A daddafe yayi sallar asuba yakoma ya kwanta yanaji zazza6insa na dawowa Dan yanda kansa ke Masa nauyi.

Tana Gama sallah ta fito ta nufi kicin ta ha'da Masa 'dan simple breakfast takoma 'daki Tai wanka ta fito ta 'dauka cikin qaramin tray ta nufi bedroom din.

Bacci yake Dan haka saita aje abincin ta matso bakin gadon takai hannu ta ta6a goshinsa
Nan taji zafi sosai
Ta 6ata fuska kaman zatayi kuka ta fito takoma bedroom dinta ta dauki wayarta takira zayyan cikin tsananin damuwa tafada Masa halinda saheeb din yake ciki.

Ba'a 'dau lokaciba zayyan ya iso da Dr daqyar ya iya fitowa bedroom Dr yadubasa yayi Masa allurori tareda rubuta magunguna masu kyau ya wuce.

Abinci takawo Masa ta ajiye gabansa Kan table 'din dake tsakiyar palon tana qin kallonsa sbd lurada yanda yake qureta da kallo Wanda tuntuni tagano hakan yafara zama 'dabi'arsa.

Zayyan dake kallon ikon Allah yayi gyaran murya tareda miqewa Yana cewa Bari naje daga can harabar gidan Sbd masu zuwa gaisuwa sunfara zuwa.

Yana fita takoma bedroom ta sanyo hijab'dinta tabi ta kicin tai gurinsu gwaggo ta tararda gwaggon zata wuce gurinsu mum suka wuce tare tana riqeda hannun abdulshakur.

Kwana uku akai zaman gaisuwa aka watse Kuma tun lokacin take noqewa ganinsa saidai idan dare yayi ta lalla6a taganosa Wanda duk zuwan datake idanuwansa biyu Amma Bata saniba.

Mum asee kuwa tunda taga yanda 'danta yakoma yakuma fa'da Mata abinda yafaru ta qara ninninka mugayen burikanta akan saheeb din wannan karon harda Anano Dan kuwa ta hangowa kanta masifa a idanuwan saheeb gameda Anano.

Tun bayan rasuwar rayuwarsa taqara canzawa miskilancinsa da shirunsa rashin son maganarsa ya qaru,
Gashi har lokacin lafiyarsa taqi dawowa gabaki 'daya.

Zayyan takira tayi Masa bayanin rashin lafiyar saheeb din Nan take yayi Masa booking appointment na ganin doctor 'dinsa dake new York yafara nemar musu visa.

Ita kanta Bata saniba Sai abakin nabeela dake tsokanarta tana cewa,

Honeymoon 'dinnan fa Yana burgeni musamman yanxu danasan Sai ranarda muka ganku tunda dama saheeb sbd Abba ne yake Zama anan.

Kallon rashin fahimta Anano tayi Mata tana cewa,

Honeymoon ana zaune qalau nida Zan fara zuwa makaranta tunda komai ya kammala registration kawai zanyi.

Miqewa nabeela tayi tana bu'de wardrobe dinta tace,

Kinyarda na qara shirya Miki kayan tafiya?

Da sauri ta taso tana cewa,

Aa banyardaba indai irin na wancen Karan ne.

Dariya tayi tace,

Amma dai koba komai na taimaka ko?

Harara ta watsa Mata tana cewa,

Eh ba laifi Amma dai kinsan ra'ayina.

Bata yarda da tafiya zasuyiba Saida zayyan yakirata yasanarda ita washe gari zasu wuce.

Shirya kayanta tayi zuciyarta na Mata tunanin 'danta sbd har cikin ranta tana tsananin buqatarsa kusada ita saidai Kuma batason Yana kusantuwa sosai da saheeb yanxu tafison Sai komai ya daidaita sbd tayi alqawarin insha Allah dasunje zata fadawa saheeb komai gameda su mum Asee
Saita fara ganin yanda zai kar6i zancen kafin ta sanar dashi maganar nafeesat da abdulshakur.

Gurinsu gwaggo tayi kusan Raba dare kafin tadawo tayi wanka Tai Shirin kwanciya.


#vote
#comment
#share
#and follow.
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*39*
Shirin kwanciya tayi harta kwanta Sai Kuma ta taso ta fito Palo ta nufi bedroom dinsa ahankali ta murda handle ta tura qofar tana kallon cikin 'dakin sbd duhu ko Ina.

Cikin san'da ta Isa gurin switch ta kunna wutar 'dakin
Zaro idanuwa cikin wata matsananciyar kunya biyu sbd ganinsa zaune a sofa idanuwansa qyar akanta
Dama yasan zatazo shiyasa,

Cikeda kunya tayi qasa da kanta ai kawai saitaga kayan baccin dake jikinta a firgice ta 'dago takallesa taga oily eyes dinsa qur akanta da gudu tayi hanyar barin 'dakin cikin rashin sa'a ta bu'de qafarta da wardrobe tasaki qaramar qara tareda durqushewa cikin tsananin zafi.

Akaro na farko dayayi murmushi bayan tsawon shekaru Wanda har nafeesat tayi rayuwa dashi ta rasu bata ta6a ganin murmushinsaba.

Sam baisan sanda murmushin ya kubce Masaba Dan ta matuqar basa dariyar yanda tashigo da yanda taji kunya.

Tasowa yayi ya qaraso gabanta saiyaga hawaye na gangaro Mata Sai kawai abin yaqara sashi murmushi

Duk da tana cikin azaba hakan Bai Hana tsantsar mamakinta bayyanowaba karo na farko arayuwarta dataga murmushinsa
Tasaki Baki tana kallonsa..

Hannu ya miqa Mata daga tsayen
Ta Kama ta miqe har lokacin Bata daina kallonsa ba cikeda mamaki Dan har lokacin murmushin Bai gushe daga fuskarsa.

Bakin gado suka qarasa suka zauna tare ya juyo ya kalleta ganin takasa daina kallonsa.

Ahankali ya bu'de Baki murya akasance yace,

Kina mamaki ko?

Kai ta 'daga sbd bakinta ya mutu bazata iya maganaba.

I'm also surprised, after so many years I've found my smile again,.

Sunkuyar dakai tayi batareda tace qalaba sai qafarta datake tabawa gurinda ta buge.

Kallon qafar yayi yakuma 'dauke Kai sbd ganin fararen santala santalan cinyoyinta a fili sbd rigarta iyakacinta kwatan cinyarta.

Lurada hakan yasa ta miqe ahankali cikin sanyin murya tace,

Saida safe.

Miqewa yayi tareda miqa Mata hannu ba musu ta miqa Masa suka fita tana 'dingisawa ya rakota har qofar bedroom'dinta ta shige ya juya Yana mamakin kansa.

Washe gari Sai qarfe takwas ta fito Palo taci adonta cikin Riga da skirt na turkie brown da lopas coffee brown ta nado gyalansu akanta Kar itama 'yar turkie dince.

Shida zayyan ta gani a palon suna maganar wasu takardu da ake buqatar saka hannunsa.

Gaisawa tayida zayyan yana tambayarta abdulshakur.

Mummunan fa'duwa gabanta yayi kusan atare suka saci kallon saheeb

Nantake taji hankalinta ya tashi da yanayin dataga fuskarsa tayi sum sum tabar gurin tabita kicin tafada gurin gwaggo.

Rungume abdulshakur tayi ajikinta tanajin qaunarsa data mahaifinsa na qara shigarta.

Koda mum asee ta Aiko Kiran saheeb fuskewa yayi yace ace yariga ya fita sbd yasan maganar Kamal ce zatai Masa wanda ita agurinta ba hakan bane wani mugun magani ne tasa aka kawo Mata daga nijar wanda zai ringa qone jininsa ahankali batareda kowa ya ganeba harsai yabi uwarsa da ubansa sbd yanxu shikadaine yayi saura Wanda yayi Mata shamaki da samun cikar burinta.

Da gwaggo kawai tayi bankwana taqi zuwa gurin mum sbd zayyan yafada Mata mum batasanda tafiyarba sbd zata iya Hana saheeb tafiyar.

Tunda suka ha'du da safiyar fuskarsa ta canxa jiyake zuciyarsa da kansa kamar zasu tarwatse sbd maganar 'dan da zayyan yayi Mata.

Koda suka shiga jirgi harsuka Isa fuskarnan a tamke take ko alamar fara'a Babu.

Already zayyan yayi musu booking komai motar hotel dinsu tazo 'daukarsu takaisu hotel din.

Lafiyayyan honeymoon suite aka Basu
Shiyafara yin wanka yayi sallolinsa yasaka kayan Shan iska ya kwashi wayoyinsa ya fice zuwa ganin Dr sbd a Daren ne yakeda appointment dashi.

Wanka tayi itama jiki asanyaye tareda yin sallah tasaka rigar baccinta ta kwanta Nan take baccin gajiya ya 'dauketa.

Bai dawoba Sai tsakar dare 'daukeda ledojin snacks da pizza daya siyo musu.

Jikinsa yaji ya mutu dayaga yanda tayi bacci atakure fuskarta na bayyana damuwar data kwanta da ita.

Ajewa yayi tareda qarasowa Bakin gadon ya shafa fuskarta ahankali.

Bu'de idanuwanta tayi cikin nutsuwa ta 'dorasu akansa suna cikowa da 'kwalla.

Tayarda it's zaune yayi Yana kallon cikin idonta ta rintse idanun
Ya jawo pizza ya bu'de tareda Ciro 'daya yakai bakinta.

Ba musu ta ringa ci haidaida taci slice uku kafin ta girgixa Masa Kai ya Bata ruwa tasha.

Tana zaune tana kallonsa yaci uku shima yatashi yaje yasako wanka da brush
Yana fitowa Tai saurin rufe idanuwanta.

Yana Gama shirinsa ya hawo gadon ya kwanta Yana kallon idanuwanta dake rufe dogayen eyelashe dinta daya kwanta.


Ahankali wani irin sabo da shaquwa yafara shiga tsakaninsu musamman yanda ta sake take kula dashi sosai
Nan take rayuwarsa tafara canxawa sbd yanxu ko abinci sukeci sunyi sabon ciyarda juna,

Gurin kwanciyama tun ana kwana kowa gefensa Amma su farka sukagansu maqale da juna harsun fara sabawa.,

Abu 'daya data lura yafiso shine tsananin kulawa da riritawa tareda son rayuwar yanci kamar turawa kotace yatashi ciki yanason rayuwar
Saita tattara ta lalace gurin riritashi da basa wata irin kulawa ta musamman
Ga yawo da kullum suke fita yi idan ka gansu zaka dauka masoyan asaline..

Haryanxu baisawa zuciyarsa Wai sone yayi Masa mummunan kamuba sbd baitaba Jin wannan feelings din akan kowaba.,
Abu 'daya yasani zuciyarsa ta yarda da ita,

So da dama tanason sanar dashi komai sai Kuma taji batason 6ata Masa 'dan farin cikin dayake ciki zata Bari Sai sun dawo Nigeria...

A Nigeria kuwa tunda mum asee Kamal yasanarda ita tafiyarsu saheeb da ananon bindigewa ne kawai zuciyarta bataiba sbd baqin ciki da tsananin 6acin rai Wanda tayi alqawarin magance komai lokaci 'daya dasun dawo.


Yau watansu 'daya a qasar
Dukkaninsu sun sauya matuqa musamman mashi dahar wata lafiyayyar qasumba ya aje data qarawa lafiyayyar farar fuskarsa kyau da aji ga wani haske sosai daya qara.

Ita kuwa girma da cikowa ta qara tareda qarin wayewa tazamo mace Mai cikakken class musamman hips 'dinta dasuka baje daidai.

Tsaye take gaban mirror 'daure da towel fari tana waya da nabeela tana combing dogon gashinta Dan handsfree tasaka wayar ta aje gaban mirror.

Suna cikin wayar ne yashigo 'dakin sanyeda jallabiya fara qal da hular larabawa dawowarsa kenan daga sallar isha'i.

Kallonta yake Yana qarasowa gaban mirrorn.

'daukar wayar tayi tareda cire handsfree ta 'dora a kunne tace,

Nabeela gobe zankiraki.

Aje wayar tayi ta 'dauki comb zata cigaba ya riqe hannun Yana kallon cikin idanuwanta ta cikin mirror.

Sunkuyar dakai tayi sbd yau tun safe take ganin sauyi ataredashi Wanda hakan ba qaramin tayar Mata da hankali yakeba,
Har cikin ranta batason wani Abu yashiga tsakaninta da saheeb Dan zai gano Bata ta6a sanin wani 'da namijiba kenan Dole zai tsareta saita fa'da Masa abdulshakur 'dan waye.

Zame hannunta tayi tareda miqewa zata nufi wardrobe ya birkitota tareda matsota Yana jifanta da wani irin kallo daya karya dukkanin garkuwar jikinta.

Rufe idanuwanta tayi ahankali numfashinta na fita da sauri qirjinta na sama Yana komawa.

Qirjin nata ya qurawa Ido Nan take yaji abinda baita6a jiba na yawo cikin jininsa
Yakai hannunsa 'daya ya dafe Mata qirjin 'dayan hannun kuwa ya riqo qugunta yaqarasa matso da ita cikin jikinsa
Still idanuwansa dasukai wani laushi suna kanta
Ta qara rintse idanuwanta tana jan 'dauke numfashi.


#vote
#comment
#share
#and follow.
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*41*
fasa wucewa gurinsu gwaggo tayi ta nufi part dinsu tana cigaba da dialling numbern zayyan
Yana dauka cikin sanyin murya suka gaisa ta sanardashi abinda yafaru na takardun hannun kamalu data gani yana boye matawanda ta tabbatarda na wani mugun qullin ne.

Kwantar mata da hankali yayi yace tabari zaiyi gaggawar bincikawa yagano kona meyene.

Suna gama wayar kiran saheeb yashigo wayarta gabanta yadan fadi ta qurawa screen  'din wayar ido tana kallon sunan data sakawa numbersa kkewarsa da marmarin ganinsa na shiga jikinta tana qara ratsa koina nata.

Cikin sanyi da taushin murya ta 'daga
Qasa qasa tajiyo muryarsa yana mata magana
Nan take taji tsikar jikinta ta tashi
Jikinta na sake mutuwa tace,

Kana lafiya kuwa?

Numfashi ya sauke mata cikin kunne ahankali sbd tsananin kewarta dake tsabanin cin ruhi da jikinsa yace,

I'm not Okay,i want to be home.

Murmushi tasaki tana zamewa ta kwanta kan kujera tayi qasa sosai da murya itama tanacewa,

Then come back soon coz the home is already  missing you so badly..

Da wata irin murya yace,

Are you sure?

Yes hundred percent sure.

Sun dauki tsawon time suna waya batareda sun ankaraba har lokaci yaja kafin suka kashe.

Tundaga ranar basu sake wayaba sbd sunfara aikin daya kaisa tuquru ko waya bai kunnaba sbd kai yadau zafi.

Ta bangaren school kuwa tuni aka gama komai tafara zuwa hankali kwance tana karantar medicine ,
Zayyan kuwa duk yanda yaso gano wani abu kan takardun datace na hannun kamal yayi amma yakasa samun damar samun yin binciken yanda yakamata dole dai saisun samu sun sato takardun sungani kona meyene.

Yau tunda tadawo school  da yamma taga fitarsa kuma batareda motarsa ya fitaba da motar mum yafita saitaji tanason dubawa motarsa kozataga takardun.

Wanka kawai tayi ko abinci bata tsaya ciba ta lallabo ta nufi motarsa sbd duhun magriba dayayi dan anmashiga masallaci.

Cikin saa tana bude motar tajita abude tayi saurin shigewa ta rufe tafara duddubawa cikin sauri.

Cikin dashboard taga wasu takardu cikin file anyi musu kyakkawan boyo tabudesu da sauri jikinta na rawa tafara dubawa amma sam bata gane kona meyeba saidai ta tabbatarda sune taga kamal na boyewa ta rufe dashboard  din da sauri tafito ta nufi part dinsu ta shige.

Hotunan takardun ta dauka ta turawa zayyan cikin sauri kafin takirasa ta sanar dashi.

Cikin tsananin mamaki da tsoro yaqara zooming din hotunan bayan ta turo masa sbd ganin takardune na mallakawa wani dukiyarka da kadarorinka  gabaki 'daya,

Sunan wanda za'a mallakawa dukiyar gabaki 'daya yaduba yaga baa riga ansa sunanba
da sauri yana zufa ya kalli gurin sunan mai bayarwar yaga sunan saheeb 6aro 6aro.
Gabansa yayi mummunan yankewa cikin kidima yakira ananon yayi mata bayani nan hankalinta yatashi jin kakaf dukiyarsa da kadarorinsa harda gadonsa ko mota 'daya bazaa bariba kenan wulaqanci da tozarci suka shirya masa.

Miqewa tayi jikinta na rawa takoma ta mayar zuciyarta na tsananta quna,
Tabbas lokacin tonuwar asirinsu mum yazo dan kuwa ta hanyar takardun nan zata tona asirinsu
Tonon asiri irin wanda basu taba zatoba ko tsammaniba,..

Kwana biyu dayin haka taci gaba da zuwa makarantarta amma duk wani motsinsu tanasa ido idan tana nan duk da dai har lokacin mum asee taki nuna mata komai duk yanda taso taji plans dinsu mum taqi sake mata shiyasa take zargin zuwa yanxu mum asee tasan ina ta dosa.

Satinsu biyu da kwana biyu suka kammala abinda sukaje yi kuma aranar yakira yasanarda dawowarsa washe gari.

Aranar itada nabeela sukaje saloon ta gyaro kanta tareda gyara qafafuwanta akayi mata jan lalle a fararen faratan hannuwanta.

Yau tunda ta tashi take aikace aikace
Da kanta tayi gyaran koina har bedrom 'dinsa da toilet  saidatayiwa tsaf qamshi da sanyin ac sai tashi yake koina.,

Abinci lafiyayye ta girka masa tana gamawa tabarwa nuratu kicin din tagyara itakuma ta nufi daki riqeda hannun abdul sukai wanka
Shi tafara shiryawa tabasa abinci yaci yaqoshi da gudunsa yayi gurin gwaggo.

Zaunawa tayi gaban mirro tafara shafe kowane lungu da saqo na jikinta da arabian oud masu sanyin qamshi
Kafin ta tsara yar simple kwalliya ta miqe ta ciro wasu riga da skirt na wani tsadaddan drylace maroon daya mugun fito da kyawun hasken farar  fatarta da hot red lipstick din data shafawa lips  dinta.

Daure gashinta tayi ta yafa dan qaramin siririn gyale iya wuya sbd dankwali bai cika damuntaba kuma shima kansa ta lura yafison ganinta bada dankwaliba.

Tana cikin fesa turare taji knocking qofar palonsu gabanta ya fadi duk da bataji dirin motocinsuba tasan sune suka iso.

Nuratu ce tabude qofar tana ganin samuel riqeda jaka tayi saurin matsawa tana musu sannu da zuwa.

A palo ya aje jakar ya juya daidai shigowarsa cikin wasu darkblue qananan kaya dasuka tsananin fidda hutu da lafiyarda farar lallausar fatarsa ta qaro,

Gaidasa tayi da sauri tareda barin palon tayi gurin gwaggo itama.

Ahankali ta bude qofar bedroom din tafito cikin yar kunya sbd yanda taci uwar kwalliya.

Kallo 'daya yayi mata yakasa dauke idanuwansa saima qara kafeta dayayi dasu ta tako ahankali ta qaraso gabansa murya qasan maqoshi a tausashe tace,

Welcome..

Bakinta yakalla shima can qasan maqoshi yace,

Is that all abinda zan iya samu?

Murmushi tasaki tareda Sunkuyar dakai tana wasa da hannuwanta,

Kallon faratan nata yayi yaji sun balain burgesa sbd lallan datayi
yakamo hannuwan ahankali tareda nufar bedroom  dinsa.

Suna shiga ya aje wayoyin hannunsa ya juyo da ita cikin nutsuwa ya shigar da ita jikinsa ya rungume.,

Kusan atare suka sauke ajiyar zuciya taqara sa hannuwanta ahankali ta qanqamesa.

Saida dukkaninsu suka samu nutsuwa kafin yasaketa yana zama bakin gado idanuwansa akanta yanajin wani irin yanayi na shigarsa gameda ita coz zai iya cewa abinda yakeji akanta zai iya rasa kansa duk ya rasata kota kubcewa rayuwarsa sbd koma meyene jinsa yakeyi har cikin jini da numfashinsa.

Hannu ya miqa mata yana kallon cikin idanuwanta dake cikeda kunya da tsoron daren na yau sbd tasan sai allah
hannu ta miqa ta kama nasa daya miqo mata yajawota ta zauna cinyarsa
Kunnenta yakai bakinsa qasa qasa yace,

Wannan kwalliya da adon fa?

Rintse idanuwanta tayi da sauri tareda tura kanta cikin qijinsa

Ya qara qasa da murya yace,

Nawane right?

Kai ta daga ahankali...

Yace,
I really love this,,yana nuna lips dinta da tsadadden jambakinta na oriflame daya.zauna daidai.

Zamewa tayi ganin yanda yake kallon lips  din nata idanuwansa na shigewa ta fada toilet  ta hada masa ruwan wanka takoma palo.

Yana fitowa cikin qananun kaya ya shirya nashan iska ya fito palo nan takama hannunsa har dining ta zuba masa abinci kusan itacema tabasa sbd ta lura yana tsananin son hakan qila sbd baisamu hakan bane tun tana yaro.
yana gamawa office ya wuce yakai wasu takardu yadawo.

Baidawoba sai magriba nan yayi alwala ya wuce masallaci yana ftowa gurin mum yayi acan ya zauna har lokacin sallar isha yayi yakoma masallaci.

Yana shiga masallaci zayyan yazo cikin gaggawa ya bata wasu takardu cikin file yace idansu mum sun kawo masa waincan takardun karta bari yasa hannu ta canza da wainnan na shaidar cewane har abada dukiyarsa tasace bazaiba kowaba.

Girgixa kai tayi cikin gamsuwa tace insha allah zata saka shi yasaka hannu.

Yana wucewa itama ta kai rakardun ta boye a bedroom  dinta.

Wani irin murmishin farin ciki dajin dadi mum asee tasaki lokacinda kamal ya sanarda ita plan dinsu na tafiya daidai sbd zarginsu ya tabbata zayyan yazo yakawo wasu takardun kamar yanda suka tsammata.

Dariya tasaki cikin qwarewa da iya mugun abu tace,

Tabbas adaren yau komai zai lalace tsakaninsu dan kuwa wlh ni nasan gobe qauye zatai baqi.,

Wasu takardu ta daga ta miqawa yakurah tace,

Kaiwa nuratu yanxunan ita tasan sauran abinda zatayi.


Sorry sweetheart kwana biyu ina fama da mura but alhmdllh naji sauqi insha allah.

And sorry idan kunga typing error ba editing ne sbd mura ba dadi wolla.

*_EZNAH_*🌹
_wattpad @mamuhgee_


*42*
Wanka tayo tazauna gaban mirror jikinta duk amace hakanan takejin faduwar gaba
Amma tana danganta hakan da yanda taga yanayin saheeb na buqatuwa.

Turaruka tabi jikinta dasu ta miqe ta dauko doguwar rigar bacci red qarama mai qaramin hannu da santsi tasaka tareda daure gashinta tsakiyar kai yana lilo.

Bedroom slippers tasaka tareda zura hijab ta dauki abdul dake bacci tabi ta kicin takaisa gurin Gwaggo.

Tana fita nuratu tafito dakinta tashige room din da sauri tafara duddubawa cijin saa bata wahalaba taga takardun da zayyan yakawo ta cire tareda saka wainda yakurah takawo tafito dakin da sauri tana fadawa dakinta ananon na dawowa ta nufi bedroom tashige.

Zama tayi bakin gado tareda cire hijab din taqara gyarawa ta miqe tana tunanin yanda zatayi ta canxa takardun su mum da wainnan na hannunta.

Fitowa tayi ta nufi kicin ta hado masa milkshake cikin cup ta doro a qaramin tray ta nufi dakinsa gabanta naci gaba da faduwa.

Tura qofar tayi ahankali tagansa zaune daure da towel yana aiki da laptop da alama wanka yayi niyar shiga ya tsaya aikin.

Dagowa yayi ya yakalleta sbd qamshinta daya raunana kuzarin jikinsa da aikin dayake,

Hannu daya ya miqo mata ta qaraso ahankali ta aje tray din kusadashi tareda miqa hannu takama nasa ya zaunar da ita kan cinyarsa yana cigaba da aikin dayake yi a laptop qamshinta na shiga hancinsa tareda tayar da duk wata tsigar jikinsa,.

Cup din ta zura hannu ta dauko tana basa abaki yana cigaba da aikin ganin yafara shirme a aikin sbd nutsuwarsa data fara barin jikinsa yasa ya aje aikin tareda fuskantarta yana kallon qirjinta daya fito sosai acikin rigar baccinta gashi kalar dayafi so ce matuqa ajikin mace wato red colour  sbd tana matuqar daukar hankalinsa,,,

Hannu yakai ahanakali ya zame band din data kame gashinta dashi
Gashin ya zuba kafadunta
Qamshin oil din Olive&aloe na gashin yashiga hancinsa ya lumshe ido sbd duniya yanason qamshi gashi ita kuma komai nata ya taba saiyaji qamshinsa.

Cup din datake basa milkshake ta aje tareda shafo gefen fuskarta cikin langabar dakai tace,

Wanka zakayi fa..

Bude baki yayi zaiyi magana wayarsa tayi qara yasaki qaramin tsaki tareda kai hannu yadauki wayar cikeda mamaki yakira sunan mum afili.

Faduwa gabanta yayi takallesa da sauri tareda kallon wayar zai dauka tayi saurin riqe wayar..

Kallon mamaki yasakar mata ta saki wayar cikin fargaba tace,

Umm me zai hana kabari idan kafito wanka saika kirata...

Wani kallon yakuma sakar mata cikeda mamaki ganin yanda take maganar hanakalinta ba kwance ba ga kamar rashin gskia atareda ita,.

Murmushin qarfin hali tasakar masa ganin kamar yana mata kallon tuhuma ta miqe tsaye tareda fuskantarsa da kyau gabanta na faduwa hannuwanta na dan rawa cikin rawar murya tace,

Mum ba yanda kake tunaninta.takeba,,

Wani kallon yasake jifanta dashi batareda yama fahimci meta fadaba.

Durqusawa tayi tareda riqo dukkanin hannuwansa biyu tana kallon fuskarsa tace,

Mum asee da kamal rayuwarka da dukiyarka suke hari....

Zame hannuwansa yayi tareda miqewa tsaye yana mata wani wawan kallo,

Tashi tayi da sauri tareda sake kamo hannuwansa ya janye tareda kallonta da kyau fuska ba wasa yace,

Karna sakejin zance mai kama da wannan abakinki...

Sake ringin wayarsa tayi ya dauka cikin 'dacin zuciya sbd zancenta na neman dagula lissafinsa wannan zance kai tsaye haka ba wani abu..

Daga wayar yayi kafin yayi magana mum tace ga kamal nan zata aiko da saqon takardun yanxu takeson yasa hannu yabayar.

Kashe wayar yayi tareda zura jallabiya yafito palo daidai kamal na knocking  ya bude fuska a daure.

Zama kamal din yayi a daya daga kujerun palon cikin ladabi ya gaidasa kamar da gske
Shikuma bedroom takardu yakoma kai tsaye da file din riqe a hannunsa
yana shiga ya aje file din a gado ya nufi toilet
Tayi saurin shan gabansa cikin qoqarin son fahimtar dashi tace,

Dan allah ka tsaya kafahimci abinda nakeson kasani nasan komai na abinda yake faruwa.....

Daga mata hannu yayi tareda rabata ya wuce toilet..

Dafe goshi tayi hankalinta na tsananta tashi abinda tai gudu kenan tun farko ba lallaine saheeb dama ya yarda kai tsayeba idan tafada masa..

File din takalla taga shine wanda tagani a mota batareda tasake dubawaba ta fice da sauri zuwa bedroom  dinta ko kamal dake zaune palo bata luradashiba ta dauko waincan takardun da sauri tadawo room din ta cire waincan tasaka nata kenan yana fitowa daga toilet

Ya tsaya cak yana kallon takardun hannunta dan tabbas yaga canje ne tayi.

Ganin yana kallon hannuwnta cikieda tuhuma da zargi hakama tuni tafara hango canji a fuskarsa ta hadiye yawu cikin dakewa tace,

Abinda nakeson fahimtarda kaine ka kasa fahimta shiyasa bazan bariba acutatarda kai..

File din ta dauko tareda biro ta miqa masa tace,

Gashi kasa hannu tukuna sainayi ma bayani.

File din datake miqo masa yabi da kallo takardar dake sama yakalla abinda yagani yasashi karbar file din idanuwansa na kadawa lokaci daya hannuwansa har wani rawa suke sbd kishi da baqin ciki..

Ganin halinda yashigane yasata karbar takardun dan sake dubawa
Idanuwanta sukai mata mugun gani sbd takardune na transfarring komai na dukiyarsa da kadarorinsa zuwaga danta abdulshakur salis danja.

Kallonsa tayi cikin sauri tana girgiza kai idanuwanta na cikowa da hawaye arikice murya na rawa tace,

Meye wannan..ban fahimci mai suke nufiba,
Wlh takardune suka kawo dan mallake dukiya da kadarorinka,
Mum ta aiko dasu ne dan kasaka hannu da gaggawa....

Wuceta yayi cikin wani irin yanayi ya saka doguwar riga tareda ficewa dakin yanayinsa na qara canxawa.

Hijab ta zura da sauri tabiyosa duk inda hankalinta yake yayi mumman tashi..
Cak ta tsaya ganin kamal tsaye a palon tai saurin shan gaban saheeb hawaye na ciko idanuwanta tace,

Wlh wainnan mutanen basa qaunarka dukitarka sukeso
Mum asee bata taba qaunarkaba
Sun aikata laifuka da dama dan ganin sun cimma burinsu,
sune suka kashe......

Saukar Wani gigitaccen mari yasa zancenta katsewa
Ta dago a rikice idanuwanta suka sauka kan mum asee,

Juyowa tayi ta kalli saheeb taga idanuwansa sun qara canzawa sbd halinda yake ciki data kasa tantance kona yarda da itane kina akasin hakan.

Cikin sanyi da nuna zallar baqin ciki mum asee ta kalleta tace,

Tuntuni nasan badan allah kike zaune damu ba sbd alamomi da dama sun nuna kwadayinki da budewar idanuwanki kan dukiya,

Kin gama yaudarar kamal yayita dawainiya dake da shegen danki duk baki tsayaba idanuwanki nakan dukiyar saida kikayiwa saheeb qazafi abbansu yasa ya aure sannan yanxu kice mune muke bin dukiyarsa...

Wani banxan kallo anano ta watsa mata cikin takaici da baqin ciki tace,

Qaunarsa kike amma shine kikeson mallake dukiyarsa da kadarorinsa,

Takardun hannunta ta daga tareda miqa masa cikin son ya yarda da ita tace,
ka duba kagani takardune na mallake dukiyarka shiyasa sukeson sa hannunka..

Kamar wani wawa ya miqa hannu ya karbi takardun yana karantawa yaga takardune na komawa makarantar kamal qasar germany sukeson yasa hannu.

Kuka mum tasaki ahankali tace,

Saheeb kaine dan dana fifita fiyeda dan dana haifa,
na qaunaceka fiyeda komai,
Takardun komawa makarantane na kamal shine kanaji matarda bayan dukiyarka ba abinda take hari take ikirarin nason mallake dukiyarkane...

Zaro idanuwa anano tayi hankinta na qara tashi ta fuxgo takardun daga hannunsa ta duba jikinta na rawa taga tabbas na makarantane suka kawo ba wainda ta tsammataba,,

Wainda zayyan yakawo mata ta duba taga na mallakar dukiyane zuwaga abduk dinta
Badai zayyan haintarta yayi yabata su sbd sakata cikin.

Mum ta nufa jikinta na rawa cikin baqin ciki tace,

Mum kinsan nasan me canxa wainnan takardun suke nufi sbd saheeb yasan bazan taba kwashe dukiyarsa nabawa abdul ba,

Saheeb wlh mum itace ta kashesu abba...

Wata gigitacciyar tsawa kamal ya daka mata tana juyowa afusace tasakar masa wasu lafuyayyun marika guda biyu ajere
Sbd idsnuwanta sungama rufewa da bacin rai da baqin ciki.

Juyowa tayi gurinsa ta riqosa tana jijjigawa tace,

Saheeb please ka yarda dani wlh bansan da wainnan takardunba daaka saka sunan abdul.

Rintse idanuwansa yayi sbd sunan abdul dinma datake kira qara qona ransa yake sbd shi gabaki daya takasa fahimtar inda zancensu ya dosa abu daya ya fahimta shine takardun dayaga ta canxa sune na mayarda dukuyarsa ga danta,,
To sauran maganganun kuwa sun masifar daure kansa..

Mum asee kuwa kuka tasaki sbd ganin saheeb din na Na wasi wasi bakuma hakan takesoba so rake yadau mataki mai zafi nan.

Riqosa tasake matsowa tayi yayi baya tareda watsa mata wani mummunan kallo ya nufi bedroom  dinsa kansa na mugun sarawa,

Zubewa tayi qasa hawaye na balle mata sbd bata tsammaci hakaba.

Cikin tashin hankali da takaici suma suka kalleta sbd basu tsammmaci duk abin zai birkice musu hakaba dan basu tsammaci zata iya fadar abubuwanda tafadaba.

Cikin tashin hankali suka fice sbd sunsan sarai saheeb zai dasawa maganar ayar tambaya.

Suna fita tasaki kukan datake dannewa
Saidatai mai isarta ta miqe ta nufi daki tadauki wayarta jiki na rawa danna kiran zayyan sbd bazata iya kwana batareda takirasaba taji dalilin qulla mata wannan cutar.


Vote
Comment
Share
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamugee_


_karku damu da typing error banyi editing ba_..


*43*
Qoqarin kiransa take kukanta na qaruwa amma wayarsa takasa Shiva saima akashe take jinta tai wurgi DA wayar tareda zubewa qasa kukanta na fita ahankali zuciyarta na tsananta quna DA karyewa,

Tunda take kallon alamarin bats tabs tunanin zai juye hakaba amma saheeb yakasa tsayawa ya fahimci bayaninta DA inda zancen ya dosa.

Washe gari Kida gari ya waye ta fito palo KO gani sosai batayi sbd kumburin idanunwanta data kwana tana kuka..

Zama tayi palon jiran fitowarsa amma shiru har kusan awa ko motsinsa batajiba ta miqe ta nufi bedroom din tabude tashiga.

Duddubwa tai had toilet bayanan ta fito harabar gidan taga motarsa daya batanan kenan fita yayi.

Dafe goshinta tayi xuciyarta na qara karyewa sabbin hawaye suka gangaro Mata ta share tareda kallon part din mum ta nufa cikin zafi DA qunar rai.
Har zata shiga ta tsaya bakin qofa tareda kunna video recording tariqe wayar ahannu tashiga.

Cikin saa azaune ta tarar DA dukkaninsu apalon fuskokinsu ba walwala Dan kuwa ba qaramin ruwa ananon ta ballo musuba data Fa  a tona asirinsu duk DA basusan a wane ma'auni saheeb yadauki zancenba amma hankalinsu baa kwance yakeba Sam shiyasa tadau alqawarin yau din sai anano tabar gidan kafin ta jawo musu wani balain dayafi wannan asirinsu ya tonu.

Cikin qasqanci take kalll8 ,su tana qoqarin ware idanunwanta dasuka qanqance sbd kuka zatayi magana mum ta tareta DA cewa,

Karkiyi saurin cewa komai Dan gwara kije ki hada kayanki Dan wannan alqawarine na daukar miki bazaki kwana agidannan yauba sai qauye gidan tsoho..

Idan wannan shine alqawarinki
Ninayi miki alqawari ayau kafin natafi ko bayan natafi din saina bankade duk wani mugun sirrinku dake 6oye..

Murmushi mum din tasaki tareda tasiwa ta tsaya gavanta tace

Yaro man kaza,
Kinyi kuskuren wasa Dani tun farko sbd bakisan da balain dakike wasa ba,

Nuratu tasanardani zuwan DA zayyan keyi gurinki da wasu daga cikin maganganun dataji kunayi.,

Naso nayi amfani DA hakan gurin saheeb dan yakalli alamarin kamar nacin amana amma sainaga Bari nayi muku yanda zakufi ganewa,

Tabbas munyo takardun mallakar kadarori DA dukiyar saheeb saidai tunda wancan mai qwaqwalwar kifin yacemin kunyi Karo sun zube agabanki nasan wlh saikinyi zargin wani Abu kuma saikinyi bibiyarsu yasa nuratu tasaka ido sosai akanki tagano kinanan kina bibiyar kamal Dan ganosu
Shiyasa mukabar motarsa abude
Kuma abinda muka hasasa yafaru Dan kuwa kingani kinkira zayyan agaban idanuwanmu yazo yakawo miki wasu
Nuratu itace ta xanza wainda yakawo miki tasa wainda saheeb yagani
Mukuma kina tunanin zamukai na mallake dukiya saimuka canza namu zuwa na makarantar kamal.

Anano so DA Dama kina qoqarin ganin kin kare saheeb Wanda bazaki iya hakanba tunda bazai taba yarda dakeba kamar yanda ya yarda Dani,

Yes nice na kashe mamarsa,
Nasa su kamal yasa su bullet suka kashe mana matarsa
And kamal shine sanadin mutuwar abbansu but anaki daqiqin tunanin kina zaton idan kinfada masa Kai tsayene zai yarda?
Zance fa ake na kisa amma kina fada Kai tsaye kamar zancen tadi kuma kiyi tunanin ya yarda Kai tsaye..hmm anano kinyi kuskure babba.

Dafe kujera tayi sbd jiri dayaso dibarta jin nuratu ce take musu aiki tana munafuntarta aboye,
Tagode Allah dayasa network yaqi Bari tasamu zayyan ajiya DA yanxu ta zargesa tagaya masa maganganu marasa dadi da komai ya ida lalace Mata kenan.

Dagowa tayi idanuwanta jajir da tsananin bacin ran datake ciki tace

Tabbas nayi kuskure babba Dana yarda da nuratu hakama nayi kuskure babba danayiwa saheeb zance bada shaidaba amma zancena nagaba dashi inada qwaqwaran shaidata cikakkiya.,

Kinsan menene idanma saheeb ya yarda dhe dukiyarsa zanyi nabawa Dana wannan ba laifi bane sbd Abdul din dansane,
Koyaushe kuna kiran yarona shege
Ina tabbatarda banice nafara abin kunyaba sbd alamu da yawa sun nuna kamal shine asalin Wanda yadace da sunan Dan 'da na halak bazai aikata abinda yayiba kenan kafin ni mum kema kinbawa bariki Dama..

Afusace kamal da zuciya tagama cinyesa ya daga hannu ta watso masa wani mugun kallo sbd idanuwanta sun gama rufewa da masifa da baqin ciki dake cinta tace,

Karka kuskura kafara Dan yau ko mahaifiyarka wannan hurumin yayi mata yawa,

Cikin qunar zuciya mum tace,

Dukkanin alamadai yanxu gashinan kin bayyana kanki,
Dama na Dade da zargi tareda wasi wasin kinada saka hannu a kisar nafeesat sbd KO jabiru cewa yayi cikin wainda suka wurgo gawarta bakin gate mace ce agaba kenan kece kika kasheta kika sace abinda ta Haifa kika kawo kanki gidan gashi yanxu kinfadi gskia cewa danki Dan saheeb ne duk wannan sbd kwadayin dukiya harki raba uwa da danta,
Ki raba mace da rayuwarta wannan ba aikinki ne kekadaiba dole dasa hannun tsoho......

Hannu ta daga cikin rufewar idanu da tsananin bacin rai na sunan baffa data sako zata sakar Mata wani wulaqantaccen Mari taji anriqe hannunta
Ta juyo a fusace sukai ido biyu da saheeb.

Qwace hannunta tayi sbd masifar dake cinta Dan ranta yariga yagama 6aci t bude baki zatai magana ya daga Mata hannu ransa amatuqar bace fuskarnan ba kyan gani.

Gyara tsayuwa mum tayi zuciyarta fes sbd tun lokacinda tace Abdul dansane yashigo tana lure dashi shiyasa ta canxa akalar zancen amma matuqa da girgixa da Marin da ananon tai niyar sauke Mata tabbas yarinyar Nada zuciya.

Kuka tasaki ahankali tareda durqushewa tana fadin yau itace matar 'danta zata Mara Dan tasan ba itace ta haifesaba..

Rungumeta yakurah tayi tana lallashi itama tana hawayen munafurci.

Damqar hannunta yayi ya fito da ita bai tsaya koinaba sai tsakiyar palonsu da ita ya wurgar cikin quna da karyewar zuciya ya bude baki zaiyi magana ta katsesa sbd tasan gida zaice taje,

Karkayi saurin yanke hukunci da abinda idanuwanka suka gani da ji batareda kaji yanda zancen yakeba tun farko,

Wayarta ta daga tareda Fara nemo daukar datayi ta miqo masa wayar ya daka Mata wata irin tsawa tareda wucewa bedroom dinsa Dan kuwa duk wani burin samun farin cikinsa da soyayyarsa ya karye...

Bayason wainnan abubuwan dasuke faruwa dole yana buqatar sanin komaiyanda yake saidai tashin hankalinsu yaqi Bari gashi zayyan na Lagos gurin saka ranar aurensa da akayi da nabeela.

Dole zai tura anano gida kafin zayyan yadawo baisan zancen wa zai daukaba and sam yakasa gane inda zantukan nasu suka dosa yana buqatar Wanda zai zauna yayi masa bayani yanda zai gane.

Kasa danne kukanta tayi da baqin cijinta tayi zafi bibbiyu kenan tayi Dana sanin cewa Abdul dansabe duk da basu San gskiyace tafadaba amma sun juya zancen kanta.

Maganar Samuel taji tana dagowa tagansa bakin qofa cikin ladabi ya gaidata yace oga yace za'a kaita gida.

Rintse idanuwanta tayi hawayen ciki sabbi suka gangaro ta tashi tashige bedroom ta hada kayanta Dana Abdul cikin akwati biyu tana share hawaye.

Handbag dinta da dauka tafito Samuel din yakarbi akwatinan yayi waje dasu

Gurinsu Gwaggo tanufa idanuwa suntum Allah yasa sunyi wanka harsun karya suna zaune,

Kallo daya Gwaggo tayi Mata ta miqe tana tambayarta lafiya tasaki wani sabon kuka hartana shaqewa.

Gwaggo na ganin haka tayi hanyar fita tai saurin riqota cikin dasashiyar murya tace,

Gwaggo karkije gurinsa yanxu ransa amatuqar bace yake kibari idan ya huce yanxu ni gida zanje tareda Abdul.

Cikin jimami Gwaggo tace,

Gida zaki KO gida zamu,
Bari ba hada kayana na tashi.

Cikin qanqanin lokaci suka dau hanya nan tafadawa Gwaggo takardun dukiyarsa yabata ta 6atar sbd batason zancen yafita yanxu ba'akai matsayaba.

Ba qaramin tashin hankali da damuwa su baffa suka shiga jin abinda Gwaggo tafada baffa ya Dora Mata da fada sosai ganin yanda take kuka ba qaqqautawa yasa suka saurara Mata.

Da dare kodata nemi wayarta bata gantaba sai lokacin ta tuna tabarta apalo lokacinda yayi Mata tsawa ta fadi.

Videon data dauka ta tuna saikuma ta tuna da baida amfani tunda saheeb din bai yarda da itaba ya korota su mum ya zaba ya yarda dasu Wanda hakan yayi Mata zafi matuqa ya daki zuciyarta fiyeda yanda take tsammani.

Da zazzabi ta kwana sbd kukan dataita dirza tun jiya har yinin yau.

Koda gari ya Waye sosai su baffa sukaji tausayinta sbd har lokacin takasa daina hawaye ga zazzabi mai zafi atareda ita nan aka Fara lalla6ata gashi atunaninsu tanada juna biyu.

Kwananta biyu agida duk tayi wani irin anyi KO abinci bataci sosai su Gwaggo sunyi sunyi sun kasa Dole suka qyaleta.

Ranar data tafi aranar yabar garin shima ya wuce Australia sbd sosai yakejin zuciyarsa da qurjinsa na ciwo baisan yazaiyiba baida ko Wanda zai masa sannu su mum hakanan yakejin KO fuskar daya daga cikinsu baison gani.

Zayyan baidawoba sai bayan kwana biyar da faruwar alamarin.
Samuel yasanardashi anano na gida hakama oga baya qasar.

Tunda safe washe gari Yakama hany  qauyen zuciyarsa ba dadi sbd baisan abinda yafaruba.

Koda ya isa su aliyu ya tarar a qofar gidan cikeda sakewar fuska suka tarbesa nan suka shiga ciki dashi.

Gwaggo na ganinsa tasaki fuska tana masa sannu da zuwa Abdul dake kan qafafun anano tana basa madarar shanu yatashi da gudu yayi gurinsa sbd yasaba sosai dashi.

Cikin sanyi ta gaidasa ya amsa yana gaida Inna data fito daki lullube da qaton mayafi.

Furar sabuwar madara aka kawo masa yasaki jiki sosai yasha suna fira dasu Yusuf dasu Gwaggo har baffa yadawo nan suka gaisa shima aka kawo masa furar suna cigaba da firar.

Saida sukayo sallar la'asar yasanarda baffa anano yazo dauka sbd makaranta suna gab da Fara jarabawa.

Da farko baffa baiso bariba yaso ace saheeb din ya sauka takoma gabaki daya amma sbd jarabawar da zayyan din ya nace saiya yarda ta zauna gidansu nabeela shidima saida Gwaggo tasa baki tace tasan nabeelar sosai.

Gab da magriba suka baro qauyen suka Kama hanya.

Cikin kulawa ya tambayeta nan tazayyano masa abinda yafaru alamarin ya juye.

Recording din datayi ya tambaya tace tabaro can.

Shiru yayi cikin mummunan yanayi Dan bai tsammaci hakaba kwata kwata gashi duka wayoyin saheeb din ba'a samu amma tunda anyi haka ai komai azo qarshe sbd yatabbadarda itama mum din tanacan hankalinta ta tashe sbd dole komai yafara fitowa saheeb kuwa yasan dole next week zai dawo sbd aurensa dazaai next week din.

Tunda tadawo gidansu nabeela damuwarta tadan rage sbd kullum bata zama tana school idan tadawo kuma shiri suke sbd bikin yagabato sosai Dan Lagos za'a wuce can za'ayi bikin adauko amarya adawo da ita,
Tun bata Saba da zama gidanba harta Fara sabawa saidai haryanxu saheeb da abinda yamata na maqale cikin ranta ga wata irin fitinanniyar kewarsa dake damunta.

Dinkuna sukai sosai na manyan laces marasa nauyi ta bangare daya kuma anata shirya amarya kusan komai tareda ita mummy kesawa ayi
Shiyasa nan take suka canza musamman ma ita dayake farace sosai tafi nabeelar haske.

Ana gobe zasu wuce Lagos akai musu qunshi da komai
Suna isa Lagos aka Fara sha'anin biki Kai tsaye.

Tunda sukazo garin tafara ja baya tana nonneqewa sbd jikinta na bata KO saheeb bai isoba yana gab da isowa garin.

Kusan satinsu uku kenan da rabuwa tasan har lokaci bai isa buqatar dawowarta ba qilama rabuwar kenan.

Yau Daren daurin aure kuma aranar ake dinner
Batai niyar zuwaba shiyasa tayi wankanta ta kwanta.

Nabeela nafitowa wanka taga sauran friends dinta duka suna next room ana musu kwalliya ita kadaice kwance
Ta qarasa gaban mirror tana goge jikinta da qaramin towel fuska a daure tana cewa,

Sometimes ba abinda ke wahalardamu Mata sai Barin damuwarmu tana fita harta sakar mana rauni.,

Nasan kina cikin damuwa amma atleast karki bari damuwarki ta fito kusamu rauni sbd mutane zasusan halinda kike ciki afterall nasan na cancanci ki danne damuwarki ta Dan wani lokaci kitayani farin cikin wannan ranar after all Wanda zaki qi zuwa dominsa haryanxu bai isoba so Idan kinason amarya taje just kwashi kanki kije kishirya.

Murmushin qarfin hali tasaki sbd zancen nabeelar ba qarshe kafin ta tashi sbd tabbas nabeelar ta cancanci ta danne damuwarta Dan tayata farin cikin aurenta.

Fitted gown din wani tsaddaden drylace tasaka dark blue Wanda dinkin yayi masifar yimata kyau ya zauna jikinta sbd kudinda suka narkar gurin biyan kudin dinkunan itada nabeela.

Simple makeup akai Mata saidai duk da haka ba qaramin fitowa kwalliyar tayiba sbd kalar kayansun karbi fatarta sosai.


Tunda jirginsa ya sauka a lagos Samuel yazo daukarsa sbd tun jiyan su Samuel suka iso Lagos din bikin oga zayyan.

A babban hotel din daya Saba sauka Lagos suka nufa already yanada permanent room daba'aba kowa nan aka Kai kayansa
Samuel harzai fita yatuna da wayar daya tsinta Palo tun ranarda saheeb din zai tafi dayazo daukar kayansa zai kai mota ya ganta Palo ya dauka yama dauka ta ogance yakai mota ya ajemasa sai bayanda jirginsu yatashi yaganta ya tuna tun lokacin ya kashe ya aje masa.

Ciro wayar yayi cikin ladabi ya aje masa wayar ya fuce batareda yace komaiba.

Sosai yayi Rama yatara qasumba sai wani irin haske daya qara idanuwansa har wata qanqancewa sukai sbd damuwa da ciwon dayake fama dashi tsawon lokaci Dan sai yanxu yake tabbatareda wata mutuwarma hutuce ga bawa.

Wanka yayi yafito cikin sanyi ya shirya cikin wani fitinannan tsadadden filtex dark blue dayayi masa sanyin kyau ya fesa turarensa ya zauna bakin gado yana saka takarmi idanuwansa suka sauka kan wayar daba tasaba.

Cikeda mamaki yakai hannu yadau wayar tareda kunnawa sbd ganin kamar wayar anano.

Nauyi qirjinsa yayi sbd tunota da irin illarda rashinta ke masa ya rintse ido zafin ciwon qirjinsa na qaruwa Dan kuwa yasan rashinta qila shine ajinsa.

Hoton Abdul yagani gaban wayar ya rufe idanu tareda aje wayar zuciyarsa na bugawa da qarfi.

Maganarta ta qarshece tafado masa lokacinda takeson nuna masa wani Abu awayar.

He can still see the pains in her eyes cikin zuciyarsa haryanxu.,
He want to believe her but zancen yayiwa qwaqwalwarsa girma.

Sake daukar wayar yayi yaduba,
Akaro na farko daya kalli Abdul din ya qura masa ido numfashinsa na fita da sauri
Saurin batar da hoton yayi sbd fuskar nafeesat yake gani tsaf a fuskar yaron kodai maganar mum gskiya ce.

Shiga wayar yayi qirjinsa da kansa na daukar zafi.

Wani hoton Abdul din yakeson gani sbd sake tabbatarwa yana shiga hotuna da yaci Karo da hoton takardu..
Harya wuce yadawo dashi yaduba
Akaro na farko dayaji gabansa yayi mummunan faduwa harsaida kansa ya sara,,
Baya yadawo cikin SAA videon datayi ranar yashiga.

Naga comments dinku wasu sunyi dadi wasu kuma ba laifi saidai inason KO yaushe fa qarya bata take gskia saidai idan lokaci baiyiba.,
Masu cewa KO awaje baa haka tokusani Allah yafi yuwa munafukai da mushrikai talala.,kudai Ku roqi tsarin Allah daga munafukai.

Allah ya karemu yayi mana tsari daga muna fukan fili Dana boye...amin.

*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*44*


*_One love my people_*😍😍😍
*_Sbd qaunarku da kulawarku tana fa tasiri sosai akaina,,,,nima I love u guys morethan yanda anano keson baby saheeb_*😃😃


_*Ina kike UMMI AISHA wannan nakine sbd qaunarki na nan cikin raina bata gusheba...ina yinki*_😍


*_Aunty Sis keda zuwairat ummumaryam ina miqa godiyata_*😍


Kallon videon yake duk da bai 'dauku sosaiba sbd rawa da motsin da hannunta keyi lokacin 'daukar amma tiryan tiryan yake sauraron abinda mum din ke fada,,,

Qasa qarasa sauraron recording yayi lokacinda takai ayar kashe kashen datai.....

Rawa jikinsa yake sosai yana jijjiga sbd ciwon qirji da zuciya daya taso masa nan take...
Bai taba tunanin shiba jarumi bane sai yanxu sbd yanda jikinsa ke rawar sanyi...

Cikin nutsuwa samuel yasake dawowa dakin yana ganin halinda yake ciki ya qaraso da sauri cikin tashin hankali sbd numfashinsa dake qoqarin daukewa kamar mai asthma..

Waya yaciro jiki na rawa yakira wayar oga zayyan,

Yana dauka cikin tashin hankali da raka'di yafara ihu yana cewa,

Oga please come quickly oga saheeb is having an heart attack and....

Wat,,,,yace da qarfi tareda kashe wayar yana kallon naseer abokinsu dake driving dinsu zuwa gurin dinner hankali tashe yace,

Muje five star please speed up saheeb is having an attack....

Nabeela dake gefensa tai saurin kallonsa amma ganin tashin hankalinda yake ciki yasa tai shiru cikin fargabar halinda anano zata shiga idan taji haka.

Anano da wasu abokanan nabeelar biyu suna cikin motar bayan tasu nabeelar sukaga sun Kama wata hanyar
Cikin qaramin tsaki mai tuqa motar yaciro wayarsa yakura naseer yaba dagawa yace

Which road are thinking of taking kuma??

Wat,heart attack kuma at his age?
Meyayi zafi haka dashine?
Saheeb is unbelievable wlh.......

Mummunan yankewa gabanta yayi tadago cikin rawar murya tace,

Wane saheeb ne heart attack yakama?

Abdulshakur saheeb...

Bata bari ya qarasaba cikin rawar mrya jikinta na rawa tace,

Kiramin zayyan yanxu please....

Miqa Mata wayar yayi ganin kamar zata kwace zayyan kuma bai dauki wayarba sbd bayajin zai iya daukar wayar kowa yanzu daga ita harshi adduarsu Allah yasa ba wani abun su mum suka samu damar yimasaba.

Cikin sauri tace,
Please kabisu da sauri baya daukar wayar.

Juyowa tayi gurin Sarah qawar nabeela murya na rawa tace,

Kiramin nabeela da sauri please.

Ringin daya ta dauka cikin tashin hankali tace,

Nabeela please ba zayyan inason naji meyasamu saheeb din,
Da gske heart attack ya...

Cikin sigar lallashi tace,

Anano please ki kwantarda hankalinki ba abinda zai samu mijinki insha allah.

Jin cewar mijintane yasashi qarawa motar gudu nan take suka isa kusan taredasu zayyan din.

Yana tsayawa ta bude motar da sauri ta fita tabi bayan zayyan daya shige tareda naseer tun cikin lift hawayenta suka kasa tarewa suka Fara sauko Mata
Arayuwarta bata taba tunanin zata so Abu yanda takeson saheeb ba,
Bata taba tunanin sonda take masa yakai hakaba Dan bazata iya kwatanta Rayuwa babusaba.

Suna fitowa lift suka nufi room dinsa zayyan kasa tafiyama yayi da gudu ya qarasa room din.

Zaune suka tarardashi ya takure har lokacin numfashinsa bai koma daidaiba jiknsama bai daina rawaba
Gabaki daya fuskarsa tayi jajir jiniyoyin goshinsa duk sun fito.

Kallo daya zayyan yayi masa yasan wani babban alamari yasameshi...

Cikin tsananin fargaba ta sawo Kai 'dakin tareda kiran sunansa ahankali cikin tsananin fargaba.

Daqyar ya dago jajayen idanuwansa suna hada ido da ita hawaye suka sauko fuskarsa akaro na farko arayuwarsa tun girmansa.

Ganin hawayensa ya matuqar sanyayata tareda karya duk wata garkuwar jikinta.

Ganin irin kallon dayake matasa yasa ta qarasa gabansa ta durqusa baiyi wata wataba ya fada jikinta tareda qanqameta hawaye na qarasa 6alle masa.

Samuel na ganin haka jiki na rawa ya fice hakama zayyan
Naseer Dama a qofa ya tsaya.

Kuka yake sosai Wanda hakan yayi mugun tayarda hankalinta itama tafara kukan sbd bata taba ganinsa cikin wannan tashin hankalinba ko lokacin rasuwar Abba.

'Dagosa takesonyi amma ba qaramar damqa yayi Mata ba sbd yana tsananibuqatar wani atare dashi musammanma ita yafi buqata yanxu fiyeda kowa.

Zazza6i mai zafine ya rufesa taso tashi takira zayyan ya sake qanqameta takai hannu zata dauki wayarsa takira taga wayarta cikin sauri takallesa
Tabbas dole yashiga wannan halin idan har yaga videon wayartane..

Da wayarsa takira zayyan suka kirawo Dr nan yadubasa yayi masa allurai sbd gadan gadan zazzabin yayi masa mugun shiga lokaci daya.

Dr na fita lokacin baccin wahala ya daukesa ta kalli zayyan cikin sanyin murya tace,

Kakoma tunda mutane nacan suna jira insha Allah Zan kula dashi.

Girgiza Mata Kai yayi yana cire hularsa
Ta dage daqyar tasamu ya yarda suka tafi duk da Sam hankalinsa yariga yatashi ganin abokinsa haka sbd yanxu nasuda kowa sai junansu da matansu.

Dawowa tayi ta zauna bakin gadon tareda riqo hannunsu zuciyarta na qara narkewa da sonsa da tausayinsa.

Anan gurin bacci ya dauketa tana riqeda hannunsa gam.

Qarfe 'daya da Rabi ta farka sbd jin motsinsa
Tana bu'de idanuwanta suka sauka cikin nasa daya farka kusan mintuna biyar dasuka wuce ya qurawa fuskarta I do abubuwan dasukaita faruwa na dawo masa.,,
Tabbas yaga jarabawar Rayuwa sbd abubuwan dabai taba tunani ko tsammaniba sune suke faruwa dashi batareda saninsaba.,

Mum asee tayi babban kuskuren amma bazai bari wannan abin ya ta6a rayuwarsaba,
Itace ta kashesa amma ya yarda da lokacinda Allah ya dibar musune a duniya ya qare Dan haka bazaiyi yunqurin daukar fansaba sbd zataci darajar kasancewarta qanwar mahaifiyarsa kuma matar mahaifinsa,
Duk abinda ta aikata zata girbi abinta sbd Allah baya barin haqqin wani akan wani,,abu daya yasani shine bai yafe masu haqqin ran iyayensa da matarsaba harma da dansa ko 'yarsa.

Qaqalo murmushi yayi tareda shafo fuskarta da har lokacin kwalliyarta nanan ras saidai head dinta daya zame.

Dafa hannunsa daya 'Dora kan fuskarta tayi tareda lumshe idanu ahankali tace,

Kabani tsoro matuqa sbd nasan bazan iya kwatanta rayuwata bakaiba.

Lumshe idanuwansa yayi sbd ba qaramin shigarsa zancen yayiba.

Hannuwansa ya miqa Mata da niyar tazo ba musu ta hawo gadon.

Rigarta ya tayata zamewa daga kwancen sbd har lokacin murus yakejin kansa.
Kwanciya tayi ya 'Dora kansa saman qirjinta ta data kansa ahaka bacci ya sake daukarta shikuwa lumshe idanuwansa yayi ra'da'din maraici da rashin iyayensa tareda matarsa na ruruwa cikin ransa,
Tabbas yana cikin qunci da damuwa amma zai danne bazai bari hakan yashiga cikin haqqin ananoba sbd itace gabansa itace bayansa,
Itace rayuwarsa,itace farin cikinsa..,

Sonta daban yake cikin ransa bazai ta6a ha'da soyayyarta dayakejiba data kowa arayuwarsa,
Baisan zafi da 'dacin rabuwa da farin cikiba sai a kwanakin nan dayayi babuta ataredashi.,
Ba tantama ita haske ce arayuwarsa.

Har akayi sallar asuba idanuwansa biyu ya zame ahankali cikin rashin qarfin jiki ya nufi toilet.

Alwala yayi yafito yayi sallah yana 'daga hannu zaiyi addua yaji wani irin kuka ya kubce masa ya sunkuyar dakai kukan nafita ahankali.

Sheshekar kukansace ta tayar da ita ta sauko gadon ahankali tareda tareda zaunawa gabansa tana kallonsa cikin tsananin tausayinsa idanuwanta na cikowa da hawaye.

Shiru yayi badan yaji sassaucin komai a zuciyarsaba saidan ganin yanda itama ananon ke kuka ya dago yakalleta tareda jawota jikinsa ahankali ya share Mata fuska yana nuna Mata toilet da ido.

Miqewa tayi tashiga tayo alwala tasanya jalla biaMarda daya tai rolling gyalanta tayi sallah.

Tana idarwa takoma gado ta zauna kuasada shi ya zame ya kwanta tareda 'Dora kansa kan cinyarta ya lalibo hannunta ya damqe cikin nasa murya akarya yace

Forgive me my wife....

Rufe bakinsa tayi da hannunta 'daya tana girgixa masa kai.

Cikin sanyin murya yace,

Please karki rabu Dani ki juyamin baya sbd Zan iya daukar rabuwa da kowa amma bazan iya jura ba I can't imagine living a life without you,,.

'Daga masa Kai tayi tana shafa kansa
Dukkaninsu sukayi shiru zuciyar kowanne ba dadi.

Bacci ne yasake daukarsa ta qurawa fuskarsa ido tana kallo harsaidataga lokaci yaja ta same ahankali tafada toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin rigarta ta jiya tana gamawa yana farkawa yabita da kallo ya tsayar da idanuwansa kan fuskarta dayafiso fiyeda komai duniya yanxu.

Qaramin murmushi tasakar masa tareda qarasowa gabansa ta tsaya cikin murmushi tace,

Gud morning..

Lumshe idanuwa yayi yabudesu akanta cikin wani irin shauqi yace,

Come here""yafada yana miqa Mata hannunsa idanuwansa kan fuskarta.

Matsawa tayi ya tashi tareda 'dorata kan cinyarsa yana kallon yatsunta dasukaci adon lalle.

Murza yatsunta yayi yana kallonta murya qasa qasa yace,

I like this.

Murnushi tayi batareda tace komaiba.

Wayarsace tai ringing yashare itace ta lalubo masa tana dubawa taga zayyan ne ta miqa masa ya kar6a cikin sanyin murya sukai magana nan yasanardashi gashinan zuwa dubasa tareda sauran friends dinsu,,

Kallonta yayi kafin yacewa zayyan din kada suzo shizaizo daurin auren yanxu.

Sakinta yayi yatashi ahankali ya Kira restaurant yayi masu order breakfast kafin yashige toilet.

Yana fitowa wanka Ana kawo breakfast din shiya bude ya karba ya aje.

Da kanta ta takura masa taringa basa haryaci kadan yasha magani ya shirya cikin wata dakakkiyar Australian gezna shadda black data fito da haskensa da kyawunsa matuqa.

Yana 'daura agogo ta qura masa ido ganin yanda yayi Rama lokaci 'daya,
Tabbas badan hausawa nacewa matar mutum kabarinsa tasan saheeb yafi qarfinta amma Allah yayi itace matarsa shine farin cikinta.

Juyowa yayi yakalleta tareda miqa Mata hannu takama yayi kissing din hannun yace,

Am going..

Are you sure you're ok?"""tafada tana kallon fuskarsa gefe 'daya kishin fitarsa haka takeji.

'Daga Mata Kai yayi ya fice batareda yadau wayarsa KO 'dayaba sbd soyake da'an daura auren yadawo sbd badasu za'a koma Kai amaryaba sai hankalinsu ya kwanta.


Vote
Comment
Share
And follow.

*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


_*my xinnie this one is for you sweetheart*_😍😍


_*maganar gskia masu canza number pages suna jawa mutane rai banajin dadin abun matuqa Dan haka kudaina sbd kuna ru'dar min da masoya*_,
_*na roqeku please Ku daina Dan hakan na 6atamin rai matuqa*_😠😡


*45*
Yana fita ta Zauna kan sofa ahankali tana bin qofar daya fita da kallo.,
Batasan wani irin so take yiwa saheeb ba sbd zuciyarta tariga tayi raunin dabatada za6in son wani Abu bayan sonsa.

Breakfast 'din tajawo gabanta tafara cin chips ahankali tanajin saura Abu daya ya rage mata ta sanar dashi waye Abdul.

Tana gamawa room service tazo ta gyare koina ta fice.

Wayarta ta dauka ta danna kiran nabeela nan suka sake sukai magana cikin tsokana nabeela tace,

Ciwon miji ya hana awaiwayomu sai jira muke amma shiru.

Murmushi tasaki tace,

Nabeela wannan bakin naki Allah yasa zayyan ya saita manashi yau.,

Dariya sosai nabeelar tayi kafin tace,

Allah yasa adaidaita manashi tare dan naga alamar saheeb angwancewa zaiyi tun 'dazufa ya aiko Samuel ya kar6i kayanki duka ni nasanma saikun dawo kozamu ha'du.

Yanxu dai ba wannanba nakirane naji andaura auren?

Eh andaura zaki zone?

Wlh zanzo nazo kafin Ku wuce amma bari idan yadawo naji koxai bari..

Dole yabari ma tunda munem mukazo dake kiran swty zanyima nace allah karya barki tunda gurin baffa yaje da kansa ya kar6oki saheeb yabari idan mun maidaki yaje ya 'daukoki.

Qaramar dariya tayi tareda kashe wayar Dan tasan nabeela zata iya fiyeda haka indai itace.

Miqewa tayi tareda bude wardrobe ta 'dauko charger saheeb ta maqala wayarta charging takoma ta kwanta kan sofa tana kallon TV bacci ya sake 'dauketa.

Da qyar yasamu ya zame bayan an 'daura auren an watse Samuel ya jasa suka nufi masaukinsu.

Ahanya suka tsaya wani qayataccen restaurant yasa Samuel yayo musu order kafin suka wuce.

Tun ahanya yakejin farin da kwanciyar hankali na ratsashi
Hasalima jin yake kamar shine aka 'daurawa aure sbd ko zayyan bai kaisa farin ciki da 'dokin son kasancewa da matarsaba koyace amaryarsa.

Saidaya tsaya qofar room din ya sauke numfashi ahankali kafin yayi knocking ahankali.

Cikin bacci taji ana knocking ta tashi zaune tana kallon agogo kafin ta sauko ta nufi qofar tana yamutsa fuska sbd doguwar rigarta dake damunta sosai Dan Dama ita ba gwanar son kaya masu nauyi bace

Tana bude qofar yabita da wani irin kasalallan kallo ganin yanda tayi masa kyau matuqa ta burgesa cikin yanayinta na mai bacci.

Shigowa yayi tareda rufe qofar ya aje kayan hannunsa tareda qaramin akwatinta dayasa Samuel karbowa gurin nabeela.

Akwatin ta kalla tareda maido kallonta kansa tana murmushi qasa qasa tace,

Wannan kamar kayana ko?

Zama yayi tareda jawota ta fa'do jikinsa ya matseta ahankali yana kallon cikin idonta zuwa bakinta qasa qasa yace,

Kayanki ne dazaki kar6i punishment akansu.

'Dan bude ido tayi cikin sigar 'daukar hankali tace,

Punishment for what mistake?

Cikinta dake lafe ya shafa yana cewa,

Da izinin wa kikazo nan 'din uhmmm?

Murmushi tasaki tareda zamewa ta miqe tana cewa,

Laifin zayyan ne amma zankirasa yanxu nace yaxo sutafi dani ya maidani inda kace natafi tun farko....

Rungumota yayi ta baya cikin kunnenta yace,

Mutuwace kawai ta isa tayi wannan yanxu sai kuma ubangiji daya ha'da.

Murmushi tayi sbd taji dadin abinda yafada har cikin ranta.

Wanka yayi yayi sallah yashirya cikin qananun kaya itama wankan tayi bay an tayi sallah ta canza kaya zuwa qaramar rigar shan iska.

Murmushi tayi lokacinda ta bude akwatinta taga sabbin 'yan iskan kayan bacci aciki tasan sarai aikin nabeela ne amma duk da haka ta gode sbd dama duk kayan baccin dataxo dasu daga gida masu nauyi ne sbd ba tsarinta bane saka sexy kayan bacci cikin mutane ba.

Mayarwa tayi cikin akwatin ta saka cikin wardrobe.

Zama tayi kusadashi ya bude abincin dayazo musu dashi nan sukaci suna gamawa ta 'dauko magani ta miqa masa ya kar6a yasha yana kallon rigar jikinta data fiddo santala santalan fararen cinyoyinta waje sbd iyakacinta cinya.

Tattara gurin tayi suka zauna yana waya da zayyan dake sanar dashi yanxu jirginsu zai tashi.

Ahankali bacci ya 'daukesa kansa na kan qafafunta.,

Ahaka itama bacci ya 'dauketa sai maraice suka farka
Sallar la'asar sukayi ya fita zuwa wani guri.

Wani qaton shopping mall yaje yayi siyayya daganan yasa Ahmed dashima yazo 'daurin aure bai komaba yayi musu arranging tafiya Cyprus.

Baidawoba sai bayan sallar magrib lokacin tana wayada nabeela dasuka isa tun 'dazu tana gidanta kuma bayan 'yar aiki ba'abar kowaba duk suna gida gurin mummy.

Kashe wayar tayi tareda tasowa ta kar6i kayan hannunsa tana masa sannu da dawowa.

Aje kayan tayi tareda juyowa ta kallesa ganin ya tsaya inda yake yana kallonta kamar zai cinyeta..

Da ido ta tambayesa ya akayi
Murmushi yayi tareda qarasowa ya zauna yana cemata ta basa milkshake din daya shigo dashi.

Budewa tayi ta miqa masa tareda bude pizza daya shigo daita suka ci.

Yanka 'daya taci ta miqe sbd sukuni data rasa na tsoro da fargaba ga qarin mayen kallon dataga yana binta dashi.

Toilet tashige tayo alwala sbd kiran sallar ishai da'aka fara,
Shima alwalar yayi ya fice zuwa sallah.

Kafin tayi sallah ta tattara gurin ta qara gyare room din tareda qara sanyin ac.
Tana idar da sallah yana shigowa yasata sukai nafila tareda kaiwa Allah kukansu dakuma gode masa.

Suna gamawa ya miqe a sofa yana waya da wani abokin Abba daya kirasa kan wasu maqudan miliyoyin kuda'de da abban ke binsa yanaso yabayar.

Ganin hankalinsa ya 'dauku sosai gurin wayar ta ta6e ta fada wanka tana fitowa yana gama wayar shima yashige toilet 'din.

Jiki asanyaye take shafa mai tana gamawa ta fesa body pray na haramain madina ta fesawa gashinta hair spray mai qamshi na aloe ta tattarasa ta 'daure da qaramin banda.

Bude wardrobe tayi tana tunanin saka kayanda nabeela ta sanyo Mata amma bazata iya sawaba sbd kunya
Tafara lalubar Nata amma bata gansu
Dafe goshi tayi tana cewa,

Not again nabeela.

Jitayi an rungumota ta baya tai saurin rintse ido gabanta na tsananta faduwa ga sanyin ruwan jikinsa na wanka daya ratsata.

Juyo da ita yayi yana shaqar qamshinta yace,

Nabeela nacan tareda mijinta yanxu why are you calling her name uhmmm?

Kasa magana tayi sai qoqarin zamewa datake sbd hankalinta daya qara tashi ganin qaqqarfan mur'da'dan jikinsa na majiya qarfin abayyane Dan towel ne kawai iya qugunsa.
Ya 'dago fuskarta ya kalla ganin yanda duk ta daburce kamar yau zata fara kwana dashi 'daki 'daya.

Wani malalacin murmushi yasaki tareda janta zuwa gaban mirror yace,

Look,,,

Mirron ta kalla tai saurin qasa da idonta
Ya sunkuyo daidai kunnenta yace,

Mijinki ya canxa miki ne?

Rufe ido tayi tareda 'dauke numfashi sbd saukar hannunsa kan wuyanta zuwa qirjinta,

Hannu 'daya yakai cikin nutsuwa ya zare band 'din data Kama gashinta dashi gashin ya zubo
Ya shaqi qamshin gashin tareda lumshe ido murya qasa qasa yace,

I love this hair wifeyy..

Mutuwa jikinta yayi murus jin muryar dayayi amfani da ita gurin magana gashi hannunsa 'daya na cikin gashinta 'daya na kan towel 'din jikinta.

Birkitota yayi yana kallon idanuwanta dake rufe da idanuwansa dasuka fara canxa launi.,

Zame towel 'dinta yayi cikin nutsuwa
Kallo 'daya yayiwa kakkyawar surarta idanuwansa suka qarasa birkicewa
Cikin kunnenta yakai bakinsa a wahalce yace,

Can i.....

Fa'dawa jikinsa tayi tareda qanqamesa cikin tsananin sonsa,buqatarsa,kunyarsa dakuma son faranta masa.

Ha'duwar jikinsu ba kaya yasa numfashinsa kusan barin jikinsa ya cirata gabaki 'daya ya 'dora gado yana ha'de bakinsu guri 'daya...

Asubar farko ta farfa'do daga qaramar sumar datayi sbd baqar wuya da azabar datasha ahannun qaqqarfan soldiern daya tunkareta da qarfinsa sbd sanin ita 'din ta ta6a haihuwa saigashi alamarin yazo masa a bazata shiyasa taci wuya matuqa.

Tunda yasamu kansa ya zauna tsaronta sbd zuciyarsa data kasa sukuni da sabuwar soyayyarta da tausayinta dakuma farin cikin babu Wanda ya ta6a sanin masa Mata
Hakan yaqara tabbatar masa da ita 'din tasace shikadai.

Abu na biyu daya hanasa sukuni shine Abdul,
Waye shi?
'Dan waye?
Meyasa take tsananin sonsa kamar itace ta haifesa.

Tana tashi ya matso jikinta tareda qara shigarda ita jikinsa ya lumshe ido yanajin yanda soyayyarta keson hana numfashinsa fita.

Shafo fuskarta data kumbura sbd kuka yayi cikin tausayi yace,

I'm sorry wifeyy..

Sabbin hawaye suka gangaro Mata na farin cikin 'darenta na farko da namiji mafi soyuwa a rayuwarta Wanda tasamu shine Wanda yasamu damar kar6ar budurcinta Wanda Allah yayi danshi aka yosa tunda shine ya kar6esa
Kuma duk da baqar wuyar datasha taji sirrikan zuciyarsa akan irin matsayi da soyayyar dayake Mata.

Share Mata hawayen yayi cikin qaramar murya yace,

Not now please baby.

Toilet yakaita da kanta tayi wanka ta fito ahankali ta sanya doguwar riga da qaramin hijab sukai sallar asuba,

Suna gamawa takoma ta kwanta sbd ciwon Kai da zazza6in datake ji na shigarta.

Kasa kwanciya yayi sbd zuciyarsa 6angare 'daya data kasa nutsuwa akan son jin waye abdul agurinta.

Yana zaune cikin wasi wasi yana kallon kyakkyawar fuskarta dayakejin yafiso fiyeda duk abinda yatara duniya har qarfe Tara ta buga kafin ta motsa ahankali ta bude ido ta saukesu fes akan fuskarsa.

Murmushi yasakar Mata yana shafo fuskar yace,

Good morning love..

Murmushi tasaki tana tashi zaune ya matso kusada ita yana janye Mata gashin daya zubo fuskarta yana kallon qirjinta dasukai jajir sbd murxa ta cikin fingilaliyar rigarta.

Kwantawa jikinsa tayi cikin kunyar kallon dayake mata.

Da kansa ya cire Mata Riga ya 'dauketa suka shiga wanka.,
Daqyar ya iya controlling kansa gurin wankan sbd yasan taji jiki matuqa saidai yayi wasanninsa sukai wanka suka fito.

Cikin qananan kaya dukkaninsu suka shirya yayi musu order breakfast daqyar ya lalla6ata Tasha tea da naman rago dayasa aka gaso yanxun.

Suna gamawa ta bude wardrobe ta jawo handbag 'dinta taciro wani tana juyowa yana bayanta ya riqo hannunta suka zauna bakin gado ya 'dago fuskarta ya kalli cikin idanuwanta a tausashe yakira sunanta,,

Kallonsa tayi jin he sounds so serious..

Riqe hannuwanta yayi gam cikin nasa yace,

You're my wife,,
My life,,
My happiness,
My Savior,
My present, my future, the mother of my kids insha Allah,
The woman I want to spend all my life with,here and life after.,
Kinsan komai gameda ni harma abinda ni kaina bansaniba,
Kallon cikin idonta yayi yana sake damqe hannunta yace,

No more secrets tsakaninmu Dan haka nakeson sanin gaskiyar 'danki,
And when I said gaskia ina nufin everything about him.,

Sanyi jikinta yayi gabanta ya tsananta bugu ta kallesa murya a kasalance tace,

Abdulshakur 'Dana ne da mahaifiyarsa tabani kyautarsa lokacinda yafado duniya batareda ko kalar fuskarsa tasaniba,
Ina tsananin qaunarsa fiyeda farin cikina Dan Zan iya fuskantar kowane Irin qunci da qalubale akansa,
Abdul shine qaddarata,
Abdul shine sanadin samun farin cikina,
Na kasance ina jinsa tamkar 'Dan Dana Haifa da cikina,
Da farko ina mamakin irin qauna da son danake masa sai daga bayan nan nagane son mahaifinsane da Allah ya halitta cikin jinin jikina tun kafin nasansa kona gansa......

Zame hannuwansa yayi cikin Nata ahankali idanuwansa na xanxa launi zuciyarsa na bugawa da qarfi sbd zafi da ciwon data Fara yimasa sbd baita6a tunanin akwai Wanda takesoba bayanshi....
Fuskarta data sunkuyar ya kalla murya a karye yace,

Kinason mahaifinsa haka..?

Ina sonsa fiyeda kaina,
Ina qaunarsa fiyeda numfashina,
Ina burin da fatan kasancewa dashi har qarshen rayuwata....

Miqewa yayi tsaye yana rintse idanuwansa sbd zantukanta ba qaramar illa sukewa zuciyarsa bazai iya cigaba da jiba ya juya jiki amace zai wuce ta riqo hannunsa ya tsaya cak numfashinsa nason sarqewa.

Zagayowa tayi gabansa tareda bude masa tafin hannunta zoben data 'dauko a handbag 'dinta ya bayyana...

Qurawa zoben ido yayi..,
Tace,
Aranar Dana kammala karatuna na secondary aranar na hadu da qaddarar rabuwa da abokanan tafiyata na fado daji,
Acikin Daren acikin dajin na hadu da mahaifiyarsa tana Neman ceto daga hannun 'yan ta'addar da'akasa su kasheta sakamakon ru'di na dukiya da duniya,
Allah ya ha'da qaddarata da tata shiyasa ta haihu a hannuna bayan harbi na bullet biyu dasukai Mata da duka sosai tsohon cikinta Wanda qarshe acikin rami ta haihu bayan azaba da tarin baqin ciki da damuwa ta rasu tabarni da jaririn 'danta data bani wannan zoben ta fa'damin sunan mahaifinsa abdulshakur......
Kallon da'akemin na nahaifi shege yasa 'yancina da karatuna tareda mutumcin iyayena ya katse aka raboni da gida inda na tararda masifar datafi wadda na baro..

Sarawa kansa yayi yai masa wani irin nauyi jiri yaso 'dibarsa yayi saurin zubewa qasa Dan shi yama kasa fahimtarta daidai..
Kar6ar zoben yayi jikinsa na makyarkyata bazai ta6a manta zobenba sbd shine da kansa yasiyowa nafeesat shi a qasar mexico dayaje..

'Durqusawa tayi tareda dafashi idanuwanta nacigaba da zubo hawaye tace,

Bullet shine sunan shugaban 'yan ta'addar da mum asee tasaka suka kashe mahaifiyar abdul,
Sune tasaka suyi kidnapping Abba wancan lokacin,
Mum itace tasa kamal ya Saki information 'Din aikin office 'dinku wancan lokacin.,
Kaine mahaifin abdul da rayuwata take ha'de da taka tun kafin na ganka..
Kaine nakeyiwa son daya shafi abdul bansaniba tun Kafin nasanka..

Sassauta kukanta tayi tace,

Ka yafeni nasan cewa abdul 'dankane ban fadamabane sbd karesa daga farautar rayuwarsa daza'ayi idan aka gano asalinsa saidai zanso ayi gwajin jini tsakaninku dan.......

Fadawa jikinta yayi tareda qanqameta hawaye da siririn kuka na 6alle masa..


#Vote
#Comments
#Share
#And follow.
*_EZNAH_*🌹
_wattpad@mamuhgee_


*46*
*_LAST PAGE_*


Rungumesa tayi hawayenta na tsananta itama sbd har tsakiyar ranta takejin kukansa sbd tasan tabbas ba qaramin alamarine zaisa jarumin soja kamarsa kukaba,

Saida sukai iya iyawarsu Sukai shiru suna sauke ajiyar zuciya kafin ya tashi tareda kallonta duk wani matsayi datake dashi agurinsa saiyaga tama wuce nan,
Kamo fuskarta yayi ya ha'de bakinsu ahankali cikin nutsuwa yafara kissing 'dinta harsaida tayi laushi ahankali murya a dashe  yace,

Kece rayuwata,
Kamar yanda nafeesat tabaki Abdul nabakishi nima har abada Abdul 'dankine...

Kwantawa tayi jikinsa cikin farin ciki tace,
Nagode dad Abdul..

Wani wanka suka sakeyi kafin suka koma baccin gajiya sai ajiyar zuciya suke saukewa,

Basu tashiba sai qarfe biyu
Sallah sukayi sukaci abinci zuciyoyinsu fes cikeda farin ciki da tsananin shauqin juna..

Da daddare duk yanda yaso dannewa kasawa yayi sbd wata fitinanniyar rigar bacci datasa da wani irin qamshi dake tashi cikin sanyi ajikinta,

Kwanansu hu'du suka wuce Wanda tuni suka saki jiki suna kwasar amarcinsu hankali kwance musamman yanda ta lafe tasakar masa jiki yana yanda yakeso,
Baisan cewa shi lafiyayyen mabuqacine ba sai yanxu sbd koyaushe suna naqale da juna gashi dasu zayyan kawai suke waya dayake suma su zayyan 'din suna Vegas sai kawai suka yanke shawarar ha'duwa dasu acan sukoma Nigeria tare.

Ranar dazasu wuce Vegas da ciwon kai ta tashi ya ru'de cikin kulawa ya jawota jikinsa ta lafe
Ya shafo wuyanta yana kallon idonta yace,

Missty are you sure zaki iya tafiya nan kodai mubari zuwa jibi saimuga Dr yau..

Langa6ewa tayi tana sake shigewa jikinsa tace,

No zan iya kawai dai inajin sanyi ne sosai.

Sake shigar da ita qirjinsa yayi ya rufe da hannunwansa yana cewa,

I love you baby..

Da kansa yayi mata wanka suka shirya cikin qananun kaya
Ita blue pencil jeans da maroon half long sleeve sai black kimono da black Vail,
Shima blue jins ne ajikinsa da black shirt da black armani jacket da black shade suka fito.

Har airport hannunsa na maqale da ita sai suna isa jirginsu ya tashi.

Zayyan da nabeela ne da Kansu sukazo 'daukarsu
Suna ganinsu kowanne yakalli 'Dan uwansa sbd mamakin canxawar da kowa yayi,
Su su nabeela suna mamakin ganin canzawarsu suma su saheeb 'din mamakin sauyawarsu suke musamman ma yanda nabeela tayi qiba shikuwa zayyan yayi haske,

Saheeb kuwa haskensa ma tuni ya zarta na ananon yatara wata irin lafiyayyar kyakkyawar qasumba data fitarda hutun daya samu sosai.
Anano kam haske kawai tayi sai wata irin cikadatai a kirqi da hips..

Zamewa tayi daga jikinsa ta rungume nabeela cikin farin tana gaida zayyan.

Amsawa yayi yana miqawa amininsa hannu cikin tsananin farin cikin ganin kwanciyar hankali da farin ciki shimfide a fuskarsa.

Kama hannun matarsa yayi ba ruwansa shikuwa zayyan Dama tuni matarsa takoma jikinsa suka 'dunguma mota.

Wani lafiyayyan suitee suka kama rooms 'dinsu maqale Dana juna.

Saida sukai wanka suka huta kafin dukkaninsu suka fita gurin cin abinci.

Abinci sosai nabeela taci Wanda yabawa kowa mamaki banda mijinta dayasan da wannan canjin tun watan farko bayan aurensu..

Anano saheeb ya kalla cikin marairaicewa ya nuna mata plate da kwalin shawarmar da nabeela ta cinye sbd ita kuma Sam batason cin abinci yanxu sai dai fresh laban ko coke idan ya matsa matane takecin slice 'daya na shawarma..

Langa6ewa tayi cikin shagwa6ewa tace,

Please baby karka farama I cant eat all that,,

Hannunta ya riqo cikin tsananin sonta yace,

Yes but atleast you can try koda quarter of it 'din ne please missty..

Dariya zayyan yayi yana cewa,

Yes mrs saheeb please try atleast,,,kar abokina yafara mana hawaye anan dan naga alamar he's not the old soldier we all knw...

Nabeela dake laluba aljihun dogon parazo trouser 'dinta zayyan ta kalla tace,

Love, i cant find my chewing gum kuma zuciyana tashi take.

Hannu yasa cikin aljihun three quarter dinsa ya zaro chewing gum kusan biyar ya miqa mata ta zari 'daya tana cewa,
Thanks love.

Shidai saheeb daqyar yasamu taci pasta kadan da vegetables.

Daganan gurin cin popcorn suka wuce sbd nabeela keso,,

Basu koma ba sai magrib suna isa tayi wanka tayi sallah ta sulale jikinsa ta kwanta sbd bacci takeji.

Gyara mata kwanciya yayi yana cigaba da aiki a wayarsa..

Ganin baccin ya 'dauketa ya qurawa fuskarta ido har zuwa qirjinta daya ciko sosai yakai hannu ya shafa aransa yana cewa,
I love you wifeey.

Washe gari beach suka nufa cikin shigar qananun kaya Dama tuni su su saheeb suka maida Kansu turawa sbd tun a Cyprus sun saba shigarsu suke Lamar turawan su fita damashi saheeb rayuwar acikin jininsa take.

Lokacinda saheeb ya ke6e da zayyan yafada masa komai har matsayin Abdul agurinsa
Mamaki da farin ciki matuqa yayi ya 'Dora da qara sanar dashi irin wahalhalun da ananon ta fuskanta kansa musamman lokacinda yakusa rasa aikinsa Dama rayuwarsa.,

Cikin sanyi yace,
Yanxu wane irin hukunci ko mataki zaka 'dauka akansu mum?

Numfashi ya sauke tareda gyara tsayuwarsa ya kur6i Drink 'din 'din hannunsa yace,

Mummy,nafeesat da abbah duka lokacinsu ne yayi,
Allah yabasu sa'ar kashesune sbd time dinsu ya riga yayi,
A qarshe allah bai barsu sun samu nasarar samun abinda sukeso,
Allah yabani kariya akansu batareda nasan abinda suka 'debi shekaru suna ginawaba,
Allah yabani matar danake so fuyeda komai hakama yabarni da 'dan da banta6a sanin da akwaisaba
Dan haka zan barwa allah wannan alamarin sbd shine yasan abinda ya tanadar musu akan abinda suka aikata,
I'm living a very happy life now so suje zasuga ribar abinda suka aikata may now,later,here or life after.

Jinjina kai zayyan yayi cikeda jinjinawa abokinsa sbd allah ne wato yaga zuciyarsa yake kare bawansa.

Satinsu uku agarin suka fara shirin dawowa sbd anano data fara damunsa akan 'danta tanason takoma tagansa da baffanta.

Siyayyar kusan hauka tayiwa Abdul saida ya riqeta da kansa yana mrmushi yace,

We are starting to get jealous of little abdulshakur..

Juyowa tayi tana kallon fuskarsa ta sargafo hannuwanta wuyansa tace,

We..?

Yayi qasa da murya yana kallon tsakiyar idanuwanta dake gigita nutsuwarsa ya zura hannuwansa cikin qaramar rigarta yana 'dauke gira 'daya yace,

Yes,,me and my upcoming little soldier..

Kallonsa tayi da sauri ya 'daga mata gira 'daya tareda 'dora hancinsa kan nata yana kallon yanda ta zare idanuwanta yace,

Me kike tunani ko do you want doctor's prove uhmmm..

Lumshe idanu tayi ahankali sbd jin yanda yake shafar cikinta zuwa qirjinta,

Bakinsa ya 'dora kan nata tareda zura mata halshensa ahankali sbd lurada yanxu tanason hakan fiyeda komai
Nan kuwa ta kar6a tana tsosa idanuwanta na qara lumshewa cikin jin dadi da farin cikin abinda tasamun.,

Anan tsakiyar room 'din suka zube yana zare musu kayan jikinsu.

Washe gari qarfe shida na yamma jirginsu ya sauka Lagos saida suka kwana 'daya suka sake hawa jirgi suka nufi gida.

Motocin sojojine hudu sukazo daukarsu tunda suka kamo hanyar gida take kallon fuskarsa taga sai annashuwarsa yake ba abinda ya canxa masa
Ganin kallon yayi yawa ya waiwayo ya kalleta tareda kamo hannunta yace,

Babu wani Abu dazai canxa walwalata at you by my side so just chill babyy.

Murmushi tayi tareda sunkuyar dakai.

Jiki na rawa cikin tsananin farin ciki jabiru da Abu suka bude gate motocinsu suka shige aguje kamar koyaushe nan take sojoji suka zagaye gate taciki da waje.

Samuel ne yashiga da kayansu Palo yafito.

Kallon palon tayi fes dashi saidai qura dayayi ta rashin mutane.

Shiya shigar musu da kayan cikin bedroom ya zaunar da ita sbd yanda jiri keson dibarta
Ya gyare musu koina ya kunna ac tareda dawowa bedroom lokacin harta Dade dayin bacci.

Zare mata kayanta yayi ahankali yakaita toilet yayo Musu wanka suka fito.

Shiryata yayi tayi sallolin da'ake binta

Shikuma yana shiryawa ya fice zuwa masallaci.

Zaune take duk yanda take tunanin alamarin zaizo taya wuce tunaninta babban abinda yafi 'daga mata hankali shine kamal dayazo ya sanar da ita duk watannin nan da saheeb bayanan Ashe yana tareda matarsa..
Kallon yakura daketa faman cin gasashen kifi tayi taji ranta yayi mummunan 6aci
tananan tana tunanin masifar dake shirin 6allo musu shegun yaran ko ajikinsu..

Kasa hakuri tayi ta aika asabe kiran saheeb 'din amma kai tsaye sojoji suka koroto
Ta miqe da kanta taje suka sawa idonsu toka suka hanata ko isa qofar part din tadawo xuciyarta na tafasa lallai gwara su harhada abinda zasu sata su bar qasarma gaba 'daya kafin asirinsu yatonu dan tsaf wainnan sojojin zasu daddatseta su watsar shara...

Koda yadawo daga masallaci Samuel yakawo aiken dayayi masa ba dinner dayayi order
Daqyar yasamu ya lalla6ata taci kadan takoma ta kwanta jikinsa.

Washe gari ma duk yanda taso ganinsa bata samu ba
Sukam suna shiryawa suka fito Samuel yayi gidansu zayyan dasu
Breakfast kawai sukayi suka kama hanyar zuwa qauye.

Sosai zazza6inta Keson dawowa sbd gajiyar tafiye tafiyen datai kwanakin ba Hutu.

Suna isa taji ta'dan wartsake tafito da saurinta ganin Abdul a qofar gida gurinsu jafar da baffa yana wasa hankalinsa kwance yaqara girma da wayo..

Yana ganinta ya taso aguje yana cewa,

Mommahna tadawo baffa...

Cikin tsananin farin ciki ta yunqura da sauri ya riqe hannunta batareda yadamu dasu baffa qasa qasa yace,

Easy ma'am,,,

Zame hannunta tayi tana harararsa tace,
Abinda ke hannuna shine nawa Wanda banganiba bazai hanani murnar ganin na hannunaba,
'Daukesa tayi sama tareda qanqamesa tanajin qaunarsa har cikin ranta.

Cikeda farin ciki jafar yataso shida us man suka tarbi su saheeb 'din suka qarasa gurin baffa dake zaune yana gyarawa Abdul tsohuwar keken daya siyo masa a kasuwar dataci satin daya gabata.

Baffa baki har kunne yake kallon ananonsa cikin tsananin farin ciki Mara misali yana amsa gaisuwarsu..

Su Yusuf ma cike sukeda farin cikin ganin kwanciyar hankali tareda farin ciki atattareda qanwarsu.

Zama sukayi su saheeb itakuma tayi cikin gida tareda nabeela da Abdul dayaqi ko yarda ya sauka jikinta
Saheeb kuwa kasa 'dauke idonsa yayi kan yaron har suka shige
Jin zuciyarsa yake sayau sbd rashin damuwar komai da farin ciki.

Gwaggo na ganinsu farin cikin duniya yacikata musamman data qyallo qaruwa atareda dukkaninsu su biyun
Sun murje sai qyallin Hutu da kwanciyar hankali suke.

Inna madai bata 6oye farin cikintaba nan aka hau 'dawainiyar hidima dasu.

Baffa nashigowa tareda gaba 'dayansu bayan sunyi sallar azahar nan aka shimfida tabarma babba guda biyu kowa ya zazzauna takoma kusada baffanta sbd daga ita harshi sunyi tsananin kewar juna.,

Abdul daya maqale mata takalla cikin kulawa tace,

Abdul baka gaida daddy zayyan ba ga kuma dadynka maza jeka gaishesu.

Qin tashi yayi daga jikinta kwance yace,

Daddy ina kwana.

Dariya kowa yayi banda saheeb daya qurawa abdul din ido zuciyarsa da gangar jikinsa nason jinsa cikin jikinsa.

Abinci kowa yaci banda ita data kasacin komai sai fura datasha kadan
Ido ya kafeta dasu tasan meyake nufi ta marairaice fuska tareda 'daukar part 'daya na kaza takai bakinta,
Nabeela kuwa nik tayi hankinta kwance musamman ma dambun dayaji zogala yayimata dadi sosai.

Bayan sungama ne zayyan ya zayyanewa su baffa komai nan mamaki da tsoron allah suka kamasu sosai
Tausayin ananonsu da saheeb din suka shigesu musamman idan suka tuno zargin dasuka runga binta dashi lokacinda tazoda abdul yana jinjiri.

Sai kusan magriba suka baro tareda gwaggo da abdul Wanda har lokacin baije gurin saheeb ba yana jikinta shikuwa bakinsa da jikinsa duk amace suke saidai ido dayake binta dasu duk motsinta itada abdul.

Suna isa wanka kawai sukayi suka kwanta ya jawota jikinsa tareda sakin ajiyar zuciya.

Washe gari da kanta ta ha'da breakfast takoma tayo wanka suka fito Palo..

Bedroom takoma 'dauko wayarta daidai shigowar abdul da gudu.

Ahankali ya rankwafa ya 'daukesa tareda yimasa kyakkyawar runguma zuciyarsa na tunano masa nafeesat.

Dawowa tayi daidai lokacinda ya ajesa kan cinyarsa yace,

I wish your mum is here to see how quick you grw.....

Kanta idanuwansa suka sauka yaga yanda yanayinta yaso canzawa..

Dining ta nufa yayi saurin riqo hannunta zaiyi magana ta girgixa masa kai idanuwanta na cikowa tace,

Sorry.

Jawota yayi ya 'dora a cinyarsa 'daya yace,

You're the only one, and you'll forever be the only one..

Abdul dake kallonsu ta kalla qasa qasa tace,
I know..

Breakfast sukayi a dining yau dole saidataci chips sosai sbd shida abdul suka data gaba sunata bata harsuka gama.

Hayaniya suka jiyo a harabar gidan ya miqe ya nufi qofa tana biyedashi riqeda abdul hankalinta na tashi.

Mum asee ce keta zubawa sojojin fada sbd dukan dasukaiwa kamal daga ta aikosa kiran saheeb
Sukuwa umarnin ogansu sukebi daya basu damar cin uwar duk Wanda ya 'daga musu murya agidan har mum 'din bai cireba.

Tana ganinsa ta qaraso gabansa cikin tsananin 6acin rai tace,

Kaine kabawa wainnan umarnin hanani ganinka kome?

Rintse idnuwansa yayi ahankali sbd bayason 'daukar zafi ko fansa akanta sbd allah ne zai tsaya masa saidai ganinta na matuqar qona zuciyarsa da hakurinsa tareda tunku'do zuciyarsa gason 'daukar mataki.

Anano na ganin halinda yashiga tayi saurin matsowa ta riqe hannunsa
Ya bude ido yana ganinta yaji zuciyarsa ta sauka ya fiddo wayarsa zai sake kiran zayyan saigasu sun shigo harabar gidan shida Ahmed.

Komawa Kansu kallo yayi suka qaraso gaban saheeb 'din
Ahmed ya miqa masa takardun dayasashi kawowa safiyar yau daya kirasa.

Kar6ar takardun yayi ya budesu 'daya bayan 'daya ya karanta kafin ya juyo gurin anano da duk jikinta ke sanyaye ya kamo hannunta tareda saka mata Biro ciki ya'daga takardun yace mata,,
Sign..

Kallonsa tayi hankalinta na qara tashi ya tsuke fuska yakoma saheeb 'dinsa na da yace,

Sign..

Hannunta na rawa kamar yanda idanuwan mum da kamal ke rawar son ganin takardun meye..

Signing tayi a inda taga subayenta ta miqa masa biron.

Bin takardun yayi yai signing ko dubawa bayayi yana gama signing ya jawo hannunta har gaban mum ya 'daga takardun yasaka cikin hannun anano murya a karsashe yace,

Agaban lawyer na da aminnina tareda yarana ni saheeb na mallakawa matata da 'dana jinina dukiyata da kadarorina gabaki 'daya kona mutu babu Wanda yakeda gado da ita....daga yanzu abinda zancigaba da mallaka sune nawa Dana 'yayana masu zuwa.

Kusan atare mum da ananon jiri yayi musu muguwar 'diba ya tareta tareda kallonta yace,

Yes and ban amince kiyi ko kalma 'daya akan hkanba..

Mum kuwa yakurace tai saurin tareta sbd ganin yanda zufa ya yanko mata lokaci 'daya ya jiqata sbd masifar bala in da taji saheeb yafada,.

Kamal kuwa wani irin juyawa yaji kansa na masa tsabar baqin ciki nan take qwayar dayakesha tafara motsa masa cikin kai...

Wasu takardun Ahmed takuma miqo masa ya kar6a ya yaduba ya miqawa mum yace,

Wannan sune takardun gadonki keda 'danki wainda Alqali da lauyoyi suka raba
Nibazan iya cin rahamba dan haka gasunan zaku iya tafiya sbd har hankalina bazai ta6a kwanciyaba idan kuna kusada iyalina.,
I cant ensure my family safety with you people around so please mum...

Qurawa abdul ido tayi zuciyarta na kumbura

Ganin irin kallon datakewa abdul ko qyaftawa da motsi takasayi zayyan ya matso yace,

Yes 'dansa da nafeesat ta Haifa tabari shiyake nufi......

Kawai ganin sukayi ta yanke jiki ta fadi asume
Ihu yakurah tana kiran sunanta cikin tashin hankali ita yanxu idan mum ta mutu batada madafa tunda dai basu karbo dukiyarba bare tasamu.

Kamal kuwa takardun hannun anano ya damqo tareda kaimata mugun naushi aciki ya tureta baya da qarfi ta bugi qarfen rumfar motocin dake gurin da qarfi ta sulale ta zube gurin jini biyo doguwar rigar jikinta.
Arikice Gwaggo da asabe sukai kanta suna salati,

Gate ya nufa da mugun gudu
Cikin zafin rai da qulewar zuciya saheeb ya kar6e bindigar hannun yaronsa 'daya kusan atare shida zayyan da samuel tareda soldier biyu suka sakar masa harbi a qafa,

Bullet biyar suka shiga qafafunsa lokaci 'daya nan take ya zube agurin yana shure shure.

Arikice yayo kanta yana kiran sunanta daqyar ta bude idanuwanta ta mayar ta rufe jikinta yasaki.

Ruwa yakurah ta lemawa mum
Mum din na tashi taga kamal cikin jini yana shure shure a haukace ta miqe tayi gurinsa tana ihu kamar mahaukaciya,

Dama akwai key hannun yakura suka ciccibesa suka saka mota aguje mum takar6i key tashiga ta tayar..

Gurinsu saheeb dake 'daukeda anano zai saka mota da abdul a gefe ta kalla taji zafin zuciyarta har abada bazai gusheba matuqar bata raba wainnan ukun da duniyaba.

Giya tasa tayi cikinsu a tsiyace da motar zayyan da Samuel ne suka turesu gefe harsaida goshin abdul ya fashe.
motar tayiwa rumfar aje motoci mugun bugu saida rumfar ta karye qaton qarfe yafa'do kan motor ya sai cikin tsakiyar kan kamal ya rabe biyu.

Ihu tasaki tafito hartana faduwa tana dubawa taga kan kamal ya tarwatse sai kawai ta zube wasa Rabin jikinta ya shanye sai shure shure take.

Zaburowa su Samuel sukayi zayyan ya 'daga musu hannu yace,

Kawai dai Ku fitar dasu ko jininsu karkubari saheeb yazo ya tarar Ku wanke.

Saheeb kuwa koda suka juyo tuni yayi asibiti da matarsa da 'dansa.

Kamar kayan wanki ba tausayi haka su Samuel suka kwashesu harda gawar kamal suka kaisu bolar gefen tasha suka watsar suka tafiyarsu.

Zagayesu akai anata kallo wasu su tausaya musu wasu su tsine musu sbd sunsan abinda yasa akai musu haka ba qaramin mugun Abu bane.

Ganin yanda quda suka suka fara binsu yasa yakurah ta zari takardun gadon da saheeb yabayar ta lulale tabar mum nata wani irin shure shure har lokacin ta nufi hanya tana waiwayen mutanen dasuka fara biyota dan ganin meta Zara a jikin mum
Gurin waiwayensu tai titi wata babbar mota takawo aguje tabi ta kanta ta wuce kuma drivern yaqi tsayawa
Takardun tareda jini da kwanyar kanta mota ta markade.

Ganin gawa biyu lokaci 'daya yasa mutanen gurin suka 'dauki gawarwakin suka kai daji suka zubar dan Dama duk gurin 'yan tasha ne,


Asibiti kuwa suna isa aka kar6eta saidai cikin ikon allah da yardarsa cikin bai tsayaba ya 6are Wanda alamarin ba qaramin ta6a zuciyarsa yayiba matuqa dan saida su zayyan da Gwaggo suka tausaya masa.

Lokacinda ta farka taga halinda yake ciki tasan cikin ya 6are saidai ta sakawa kanta juriya sbd karta qara masa damuwa saidai daga baya tayi kuka kamar me
Lokacinda yazo da safe yana kallonta yasan tayi kuka ya qarasa kusada ita ya zauna tareda riqo hannuwanta ya damqe cikin nasa
Batasan sanda kukan yadawo mataba ta fada jikinsa ya rungumeta yana shafa kanta danshima zuciyarsa na cikin zogin rasa gudan jininsa.

Kwananta 'daya aka sallemesu suna dawowa su baffa da inna dasu Yusuf gabaki 'daya na isowa Samuel yaje yadaukosu umarnin ogansa.

Cikeda tausayawa suke mata sannu da ya jiki
Nan su asabe da nabeela suka girka abibci kala kala.
Ganin yanda kowa yadamu yasa ta 'dan sake tanuna tacire damuwar komai.

Aranar su baffa sukaso komawa saheeb ya hana sbd Dama niyarsa sune zasu dawo nan gidan suci gaba da zama shikam da matarsa da 'dansa sabon gida zasu koma inda bazai ringa ganin komai yana tunasu mum ba.

Daqyar su baffa suka amince shidinma saida anano tace yannanta ta za6a su kular mata da dukiyarta.

Tafiyar sati biyu yayi kafin yadawo su tare gidansu.

Tun bayan tafiyarsa mummyn nabeela da Gwaggo harma da nabeela suka duqufa gyarata nan take takoma shar Lamar budurwar larabawa.

Ranar dazai dawo tana sane ta gudu gidan nabeela daga aje abdul school.

Bajewa sukayi suna fira a palo sai qyalqyala dariya suke hankali kwance..

Tun a airport zayyan yafada masa anano na gidansa dan haka kai tsaye can suka nufa.

Zayyan ne yashigo yashige bedroom 'dinsa tareda kiran nabeela aka barta ita 'daya ta fiddo wayarta akaro na ba adadi dan duba ko misscall dinsa amma still babu ta turo baki tana gyada kai.

Tsayawa yayi daga nesa tareda qura mata idanu yana qare mata kallo
Sonta na qara karya kuxarinsa.

Juyowa tayi da niyar kallon agogo idanuwansu suka hadu da juna wani irin sanyi da farin ciki ya ratsata amma saita 'dauke kai tana qowarin miqewa.

Gyara murya yayi yace,
Da zarar kin bar palon nan ba abinda zai hanani komawa inda na fito.

Shagwa6e fuska tayi tana kallonsa tace,

You know this is not fair right?

Murmushi yayi tareda nuna mata qirjinsa ta nufesa tana jujjuya ido tun bata qarasoba ya fixgota ya rungume suka saki ajiyar zuciya kusan tare ta qara shigewa jikinsa tana qara qanqamesa.

Dago fuskarta yayi yace,

Lets go home missty..

Murmushi tayi tace,.
Yes baby.

Batareda ko masu gidan sun saniba tabi mijinta suka wuce warsu a motarta.

Sabon gidansu direct ya nufa da ita takallesa zatai magana ya 'Dora hannu a bakinsa yana kallon cikin idonta yace,
You're my wife i can take you anywhere anytime i want OK?

Da kansa ya bude mata mota ya riqo hannunta suna shiga ga mamakinta taga asabe nata aikin kaida kawon Girki koina sai qamshi da sanyin ac ke tashi.

Bedroom dinsa suka yada zango yana shiga wanka ta sulale ta fito sbd hayaniyar abdul da'aka kawo data jiyo.

Qaton lafiyayyen 'dakinsa dayaji adon komai na yara takaisa ta cire masa uniform tai masa wanka ta sako masa kayan shan iska suka fito Palo daidai fitowarsa da gudu yayi gurinsa yana tambayarsa yaushe yadawo suka nufi dining suka ci abinci,
Suna gamawa tayi masa shirin islamiyya Abu yatafi kaisa ita kuma tayi sallah suka fara shirya abincin dare.


Kwanan mum asee biyu agurin wani 'dan qwaya yazo da qaramin baronsa ya kwasheta yasaka ciki ya dinga bara da ita yana samun kudi
Id an dare yayi duk inda yasamu ya zubeta nan saida safe yazo yakuma 'daukarta sbd yunwa da wahala ga shanyewar jiki da dau'da ta nanna'de takoma kamar wani tsumma.

Tsaye take gaban mirror tana qoqarin 'daure gashinta da band ya riqe hannun yana qarewa rigar baccin jikinta kallo tacikin madubin sbd da ita da babu duk 'daya
Ya birkitota idanuwansa na sauyawa murya a shaqe yace,

This dress is making me loose my mind,,,

Shafo wuyanta yayi tareda zura hannunsa 'daya cikin rigar
Taja wani irin numfashi tareda kamo fuskarsa ta hade bakinsu tana lalubo harshensa
Shikuma ya cirata ya kwantar agado yabita.

Washe gari daqyar ta iya fitowa ta shirya abdul ya wuce school sbd taji jiki matuqa kamar Daren farkont.

Koda abdul ya wuce tana dawowa suka sake lulawa soyayyarsu hankalinsu kwance...

Da daddare sukaje gida ya gaidasu baffa itadai kasa sakewama tayi sbd kun ya.

Cikin qanqanin lokaci tasamu wani cikin Wanda yafi na farko laulayi sosai qarshedai saida suka dangana da barin qadar yakaita ganin Dr a madina daganan sukai zamanso suna shan love sbd cikin maitar ubansa aka saka masa kullum suna maqale abinsu.

Watansu biyu acan nabeela ta haifi baby girl 'dinta suka dawo dole yarinya taci sunan Fatima wato mum 'din zayyan.

Tunda cikinta itama ya tsufa taso takoma gurinsu Gwaggo kai tsaye yaqi dole sai gwaggonce tadawo gidansu.

Zuwan Gwaggo da sati 'daya ta haihu a asibiti bayan uwar wuyar datasha itadashi sbd kasawa yayi ya tsare kamar zaiyi hauka shima sbd ganin halinda tashiga kodata haihu ita sharkab da gumi shima sharkaf.

Baby boy tasamu Wanda yayi saheeb Zak bai bar komaiba.
Ranar suna yaro yaci sunan Abba suna kiransa da saheeb junior.


ALHAMDULILLAH.

Nan nakawo qarshen labarina na eznah Wanda yayi nuni da shi aikin alkhairi kokuwa sharri binka yake basai Wanda aka cuta yadau fansaba,,

Arayuwa karkazamo mai sonkai da qyashi tareda zalama dan kuwa sune suka kai mum asee da tawagarta ga wannan mummunan qarshen,,
Su nuratu da bullet kuwa koba'a fada qarshensuba kunsan bamai kyau bace sbd shi mugun abu shukace girbarsa ake dan haka allah yasa muyi aiki da darasin dake ciki kuma mu watsarda illar dake ciki....amin.
Kurakuren ciki allah ya yafe mana dani Dana rubuta daku masu karantawa.


Karku ce bai kamataba ace novel yaqare anan sbd banga amfanin jansaba bay an Riga an isarda saqonda akeson isarwa jansa ba abinda zai qarar sai rage dadinsa.


Godiya ta musamman ga dukkanin groups danake ciki dan bazan iya lissafosuba amma kadan daga ciki sune,

Mamuhgee's novella,
Mamuhgeee fans grp 2 to 3
Masoyan mamuhgeee
Zauren biebie isa
Biebiedee fans grp
Khadijatus crew
Ummu subay'a fans grp
Realhausa Fulani
Duniyar marubuta
Hausa novels palava
Faeamgnovels
Sophy novels,
Members na kundin qaddarata fans grp
Musan kanmu marubuta,
Aysha sada machika fans grp,
Aufana fans grp,
Lubbies crew
Meesharh lurv fans
Dokin karfe association
Dandalin raheenat

Kai im really sorry I can't name all amma dai ngd duka har wainda ban zayyanoba.,


*Thank you my wattpadians i love you guys morethan you guys can imagine...*

Thank you,
My momy Aysha hassan
My zinnie,
Balkeey shuwarh
Aunty sis
Ummumaryam
Splendid
Ag💞💞💞💞💞
Anfa
Sisin mama
Real maidambu
Mum subay'a
Biebiedee
Raheenat Niamey
Faeamg
Dadah
Sameera ilyas

Uhhhmm im sorry nanma i cant name them all
Thank you all allah yabar qauna saikun jini gaba.
Vote
Comment
Share
And vote.

#vote
#comment
#share
#follow

Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
Chapter 4 · 0% Book details