Gabatarwa
Haihuwa-Da-Hanji-Complete-Hausa-Novel · about 282 min read
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
FATIMA MUHAMMAD GURIN
*GUREENJOH*
*FREE BOOK*
*TSOKACI*
Wannan littafi nawa mai suna HAIHUWA DA HANJI ban san ta ya zan fasalta muku ba amma
tabbas yayi matuƙar shan bambam da sauran littatafai na don labari ne na wata baiwar Allah da
ya faru a gaske, kashi saba'in cikin ɗari duk ya faru sai kaɗan da za mu ƙara ta yadda zai
ƙayatar ya kuma isar da saƙon da muke buƙata ba tare da tangarɗa ba. I promise it's going to
be a hit kar ku ga don free ne yana daga cikin labaran da na jima ban rubuta irin shi ba don
haka ku shirya shan karatu domin duk wacce bata karanta ba an barta a baya.
*GARGAÆŠI*
haƙƙin mallakar HAIHUWA DA HANJI na Fatima Muhammad Gurin ne ban amince ba ban
lamunci a sauya min labari ko ta wani ɓangare ba ko a yi amfani da shi ba tare da sani na ba.
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da littafin HAIHUWA DA HANJI ga É—aukacin makaranta littatafai na.
*001*
Wani irin ruwa ake tsulawa kaman da bakin ƙwarya, kusan duka bil'adama suna kwance lub
cikin tattausan katifa lulluɓe da bargo suna bacci kaman yadda dare ya zama mahutar bawa
amma ita tana duƙe a kitchen ɗin dake tsiyaya saboda rashin kyaun kwanon da aka lulluɓe kai
da shi.
Wuta ne take hurawa Dukda bayanta dake ta jiƙewa har hakwaranta suna haɗe wa saboda
sanyin dake shigarta hakan bai sa ta damu ba sai ma ƙara mayar da hankali da ta yi ga
haurawar da bata sarara ba sai da ta ga wutar ta kama yadda ya kamata, babbar tukunya ce da
za'a iya naɗe ta a sanyata ciki kuma tsaf ya ɗauketa saboda rashin ƙiba da kumarinta ta shiga
kokawar janyowa da ƙyar ta ɗora bisa murhun kan ta nufi wani bokiti ta fara aikin ɗibo ruwa a
kimtace tana zubawa sai da ta tabbatar yayi yadda ta saba kan ta rufe ta fito, kifi É—anye da suke
sanyawa cikin ƙanƙara a wani babbar kula ta juye ta shiga wankewa don an riga an yi mata
yanka tun jiya da Magrib a bakin kasuwan, sai da ta wanke tsaf ta É—auko wani tukunyar ta zuba
su sai a lokacin aka soma kiraye-kirayen sallah daga chan nesa.
Na yi mamakin yadda ko tsoro babu a fuskarta haka take ayyukan nan cikin ruwa a take ta
sake haÉ—a wani murhun ta É—ora dahuwar miyan kifin nan, sai da ta tabbatar komai ya mata
yadda take so kan ta shiga tattaro kwanukan gidan don ta san in ta bari ma gari ya yi haske ta
shiga uku, wanke wanke take sauri-sauri yayinda ruwan da ya koma zuba chab chab ya cigaba
da jiƙata, har ta gama jikinta babu inda ba ya kakkarwa sauri sauri ta wanke shinkafa ta zuba
cikin tukunyar farko kan ta yi alwala har kuma lokacin babu mahaluƙin da ya leƙo a gidan Dukda
kuwa wasu masallatan ma har sun idar da sallah.
Akurkin ɗakin da shi ne nata a gidan ta duƙa ta shige ta cire kayan jikinta bakkon kayanta ta
janyo da kyar ta zaƙulo wata kodaddiyar doguwar riga ta saka ta janyo hijabinta ta ɗora tare da
tada sallah, ga mamakina tsaf ta gabatar da Sallar ta yadda addini ya tanadar, bata jima tana
azkar ba ta fito don gudun magana amma bata tsira ba domin a kitchen É—in ta tarar da Inna larai
da sauri ta duƙa ƙasa
"Ina kwana inna?"
Kallonta tayi ta taɓe baki ta buɗe tukwanen ganin miyan ya yi ta juyo gareta
"Uban me kika shiga ɗaki kike yi har miyan nan ya nuna saura ƙonewa baki shirya kwashewa
ba? Asara kike son ja min ko?"
"A'a inna sallah ne na je na yi"
Tsaki ta ja tare da nuna mata kular da suke kwashe miyan tallar, ta je da sauri ta É—auko inna
larai ta kwashe tsaf kan ta É—aura dumamen gidan a murhun, ita kuma ta wuce ta É—auko kular
kwashe shinkafa ta taho ta janyo ledar sugar ta buÉ—e a cikin kular kan ta shiga kwashewa turirin
na Dakar ta yana ƙonata yadda ta saba har ta gama duk sanyin da ake ta jiƙe jagwaf da gumi,
kwanukan tallarta ta cigaba da haÉ—awa a wani bokitin fenti har ta gama filate na roba da ruwa
da gutsuren dollof da take wanke plates idan ta sayar aka ci aka dawo mata dashi.
"Je ki bugawa su Iro su zo su É—aura miki a baro su kai miki yanzun nan"
Da to ta amsa cikin sanyinta ta nufi É—akin na yaran mazan ta shiga bugawa, sai da ta kwashe
sama da mintuna ashirin tana bugu da ƙiran suna kan wasu matsakaitan samari biyu suka fito
ɗayan ya sa hannu ya hankaɗeta sai da ta faɗi ƙasa.
"Don uban ki bamu hana ki wannan bugun bala'in ba? Shegiya kullum ba ki da aiki sai na
uzzurawa mutane ko wani farar safiya..."
"Ɗahiru ƙaniyar ka...! Kun wuce kun zo kun fitar min da abinci ko sai kun janyo min asara?"
Babu ruwanta da sun yi sallah ko ba su yi ba damuwarta kawai su kai mata kayan sana'ar ta.
A hankali ta miƙe tsaye tana kaɓe jikinta dama ta sani ba dai a yi musu faɗa a kan an ci
zarafinta ko an zalunce ta ba, kowa a gidan na ganinta tamkar juji da in sun kwaso sharar su
babu inda suke zubawa sai bisa kanta.
Sumsum haka ta taho suka kama suka É—ora suna ta mitar da kullum safiya sai sun yi haka har
suka fice, tana shirin fita daga gidan kenan Inna larai ta kwala ƙiran sunanta.
"Afifah Ke!"
Waigowa tayi da sauri kuma cikin sanyinta
"Saura in ga ba daidai ba wallahi sai na lahira ya fi ki jin daaÉ—i kuma kika sake kika ci kai ko lasa
kika yi Allah ya isa ban yafe ba ki je ki dawo ga dumamenki nan zan ajiye miki"
Girgiza kai tayi fuskanta É—auke da murmushi mai nauyi da ciwo ta amsa da
"Toh"
Kan ta fice daga gidan.
A inda ta saba zama gefen rumfar masu tura finafinai nan ta zauna bayan sun sauƙe mata suka
buÉ—e suka cika fillet biyu idanunta cike da hawaye tace
"Iro wallahi in..."
"Na uwarki ne ko na ta mu uwar? Ina ruwanki? Kuma wallahi ki sake ki faÉ—a mata ki ga yadda
zamu yi da ke Annoba kawai"
Da ƙarfi ta runtse ido sunan ba wai sabo bane a gareta sai dai a duk sadda aka ƙira ta da hakan
ta kan ji zafi da ciwon fiye da É—anÉ—anon maÉ—aci a kan harshenta.
"Mai shinkafa sa min na É—ari uku..!"
Haɗiye abin da ya taso mata tayi ta karɓi kudin ta saka a Jakan ƙugunta kan ta fara zuba
shinkafar kaman ko yaushe fuskanta babu É—igon fara'a ko sassauci ba kuma don komai ta É—auki
wannan mataki ba sai don kare mutuncinta.
Hakan da take ya sa maza dayawa masu kawowa 'yan mata yan tallah wargi basa samun dama
kowa ya santa duk tsiyarka tana da kwarjinin da in ta tsume hakan babu mai iya kawo mata
wargi... Saboda tsafta da kuma natsuwarta yasa dayawa suke tururuwa wurin sayan abincinta.
Ita ɗin annoba ce kaman yadda wasu ke ƙiran ta dayawa sun santa a Mayya! Dukda ita bata
taɓa sanin menene maitar ba amma ta wurin kasuwanci su kan saya abin hannunta don ko
babu komai akwai zaƙin hannu muddin ita tayi girki.
Kan ka ce awa biyu duk ta sayar da abincin tas ta janyo baro ta É—ora kulolin a kai tana jin jiri na
fusgarta saboda rabon ta da abinci tun jiya da rana gashi yanzu ana neman goma da rabi, haka
ta turo wheelbarrown ta nufi gida...
Razana tayi ta daka tsalle tayi baya sun saba yi mata hakan sai dai ta kasa sabo ita
"Ina kudina?"
Inna larai ta miƙa mata hannu a zauren wanda ko kanta bata gama sanyo wa ba, Jakan ta
sunce ta miƙa mata a wurin ta zazzage ta kirga ta ga riba yadda suka saba samu ta saɓi
kayanta ba sannu bare na gode tayi cikin gida abin ta, Afifah ta bita da kallo har ta ɓace kan ta
turo baron zuwa cikin gida ko sauƙe kwanonin bata yi ba ta nufi bakin kitchen inda inna larai ɗin
ke zaune ta duƙa
"Abincina fa inna?"
"Laaaa kin ga mun manta da ke wallahi ina fa ta zuci zucin ajiye miki"
Runtse ido tayi da ƙarfi tana danne hawayen dake taso mata idan da sabo ya ci a ce ta saba,
kusan koyaushe za su yi rabon abincinsu muddin bata gidan to za'a ce mata an manta da ita
ne, wani lokacin ma sai an sauƙe sai a aiketa kan taje ta dawo an rabar kuma a hana ta,
hanjinta har murÉ—ewa suke saboda yunwa amma ya zata yi?
Miƙewa tayi ta nufi hanyar akurkinta inna Asabe ta kwala mata ƙira daga cikin ɗakin ta
"Ina za ki da baki karɓi kuɗin nawa aikar ba?"
Bata ce komai ba ta tsaya daga kanta leda da ke kunshe da kuÉ—i ta jefa mata a fuska
"rashin kunya za ki min ki tsaya min kerere bisa kai? Kin É—auka kin wuce ko sai na tsinka miki
mari?"
Duƙawa tayi ta ɗauka ta fice daga gidan ko ɗakin bata shiga ba ta riga ta san me zata sayo, ko
kan ta dawo har inna Asabe ta gama tuka tuwon tallar tata na dare, ita ta zauna ta malmala
tana jin kanta na sarawa ayyukan sun fi karfin shekarunta amma ya zata yi? Mutum É—aya take
da shi a duniya Aunty zee ita ma kauyen gaba da su take kuma ta kan kwana biyu bata leƙo
mata ba bare ma hakkin riƙe ta na ga dangin mahaifinta ne ita kuma ga abinda Allah ya bata,
sai dai ta tashi tayi sallah har ta gama malmalar tuwon na dubu goma sha biyu kaman yadda
suka saba ta É—ora miyan ta kala biyu da Alaiyahu da kubewa, bayan ta gama ne inna Asabe ta
tarfa mata sauran ƙasan tukunyar tukun a cikin tukunyar miyan Alaiyahun da ta gama
kwashewa ganin sai kashe jiki take saboda yunwa bata son abinda ya samu kayan tallatarta
sam.
Sai da tayi wanke wanke tas har da kwanukan safe na tallar inna Larai kan ta shirya ana kiran
Magrib tayi sallah ta fice bakin kasuwa, yanzu ma bata kula kowa abincin kawai take sayarwa
har wuraren takwas ya ƙare ta tattaro ta dawo gida dama tun shidda ta sayi kifin miyan safe ta
ba almajiri ya kaiwa inna Larai za ta saka cikin ƙanƙara ji take kasusuwanta kaman ana sarawa,
kuÉ—in kawai ta ba inna Asabe ta wuce É—aki ta kwanta idanunta na kallon sama, shikenan ita
kuma a haka rayuwarta zai cigaba da tafiya? Shikenan ita kuma haka za ta ƙare? Don dai ta
san kap kauyen dutsen-wai babu namijin da zai tare ta da sunan soyayya babu kuma gidan da
za su amshe ta yadda ake ganinta annoba kuma duk gidan da ta shiga sai ta wargaza kuma sai
an yi mutuwa kan ta fita tayi zurfi cikin tunanin ta kawai taji ana dukan kyauren palangen dake
kare kofar akurkin da ɗan banzan ƙarfi sai da ta razana ta miƙe tsaye ba tare da ta sani ba.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*002*
Nannauyar numfashi ta sauƙe sai kuma ta fita daga tsoro ta shiga fargaba, kawu ne! Me ta yi?
Jikinta a sanyaye ta miƙe tsaye ta turo kofan ta fito.
"Iskancin naki ya kai ina ƙiranki kina ji na ki yi min banza ko? Ko har kin tafi meeting naku na cin
É—anyen naman mutane ne?"
Girgiza kai ta yi tana wasa da yatsun ta murya na É—an rawa ta furta
"Ka yi haƙuri kawu bacci na fara ne"
Tsaki ya ja yana jefanta da mugun kallo, babu yadda ya iya ne kawai yarinyar ke zaune gidan
shi in ba haka ba babu abinda zai sa ya ajiye makashiyar mamarshi da 'yan uwanshi har ya ke
bata abinci tabbas da ana kashe mutum a sha a banza da tuni ya yanke wuyanta ya jefar da
gawar daji tsuntsaye sun cinye, duniya in akwai wacce ya tsani ko inuwarta ya gani ya biyo
bayanta.
"Ba dai a mawankin chan za ki bar mana kwanuka su kwana ba kan safe duk shedan ya bi ya
fitsare mana kwanuka? Oh ko so kike duk ki kashe mu ne ki huta?"
Lip ɗinta na ƙasa ta ɗan datse a hankali kan ta saki ta furta
"Kayi hakuri zan yi"
Ya ja tsaki kan ya juya ya wuce É—akin inna Asabe.
Mawankin dai ta wuce akwai É—an guntun omo haka ta fara wanke wanken idanunta kaman za
su cire saboda raÉ—aÉ—in bacci har kifewa take yi bisa kwanukan tana tashi sai da kusan duk
kowa yayi bacci a gidan kan ta gama kifewa ta wuce nata akurkin sanyi kaman zai kasheta ta
shige cikin zaninta bayan ta sauya hijabi zuwa busasshe dukunkune haka tayi baccin. Kaman
jiya yau ma dai kowani É—an adam na kwance yana bacci haka ta fita tsakar gidan ta shiga aikin
abincin tallar inna larai.
Ba don ba'a sabo da wuya ba zata iya cewa wahala ya riga ya zama jininta, bata san yadda
zata fassara rayuwa ba sai dai ta san ƙaddararta mai matuƙar zafi ne da ta kan rasa sanyi ko
sama ko ƙasa a duk sadda ta rura wutar ta.
Bata da farin ciki ko É—aya bata da mai tambayar damuwarta ko ciwonta har ma da bukatuwarta
waenda suke tare da ita amfana da ita kaÉ—ai suka iya amma ita bayan mafaka da kwanon abinci
sau ɗaya a wulakance bata anfanuwa da su ko ta wani ɓangare, manyan su zaga, matasan su
daka su kuma hantara yaran su wulakantata bata da bakin magana saboda ita É—in ta riga ta
zama annoba...
Eh annoba zata ƙira kanta kaman yadda kowa ke kiranta an haife ta da rashin sa'a tunda tana
ciki watanninta basu wuci biyar ba Allah ya karɓi mahaifinta, a wurin haihuwar ta Allah ya karɓi
mahaifiyarta ta zama cikakkiyar marainiya daga ranar da ta faÉ—o duniya, kakarta ta wurin uba ita
ce ta raine ta kan madara ta bata tarbiya ilimin addini da boko har ta shekara takwas ita ta sani
a matsayin uwa kuma uba, ta samu gata na iya tsawon lokacin da tayi da kakarta har
makarantar gomnati na boko ta sanya ta kan kwatsam mutuwa ta yanke wannan ƙauna tun
daga sannan aka fara jita-jitar ita ɗin Mayya ce! Kuma duk wanda ta raɓa zai mutu.
Tsangwama ya fara yi mata yawa a hannun ƙanwar babanta da ta koma Inna Amina ta sha
baƙar wahala kasancewar inna Aminar ma cikin gidan yawa take, mijinta kuma ba wai ya karɓe
ta bane zaman dole take mishi a gida hatta abincin gidan bai amince a saka mata ba duk
abinda aka sanyawa inna Aminar suke taɓawa a tare, ta samu innar tata da ciki a lokacin
kawunta ya ƙi yarda ya ƙarbe ta tunda su uku kawai kakarta ta haifa.
Kawu ne babba sai babanta tukuna innar dole dai wurinta take lallaɓa wa rayuwarta.
Wata rana inna Amina ta tashi da nakuda babu wani cima mai kyau, babu cikakken kulawa da
ya kamata mace mai ciki ta samu, bata taɓa zuwa awo ba ana rayuwa ne cikin wahala haka ta
tashi nakudar a gida aka kira unguwarzoma ta ci azaba ko da ta haihu babu rai ita ma bata jima
ba jini ya balle mata ko kan a ce an yi wani yunkurin Allah ya karɓi abin shi, ko gawar inna da
jaririyarta ba'a binne ba aka sanya Afeefah gaba da zagi, cin mutunci, baƙaƙen maganganu
babu irin wanda ba'a jefeta ba a lokacin da take jin tashin hankali da damuwar rashin innarta
Aminan.
Ta ga mutuwar kaka amma bai kaÉ—ata kamar na inna Amina ba saboda yadda ta mutun a
wulakance cikin sakacin miji da kishiyoyi ta yi kuka kaman babu gobe, har jifan ta da dutse ake
yi in ta fita a haka kawu ya dawo da ita gidan shi tana da shekaru 10.
Matanshi basu karɓeta ba, babu wacce take yarda har yanzu ta shigar mata ɗaki ko na yaransu
dole aka buga mata keji don ba shi da maraba da keji aka sanya buhu aka bata taburma
saboda kar ta kashe musu 'ya'ya, bata sani ba ko tabbatar ta mayyar ce ta sa yanzu shekara
shidda kenan da dawowarta gidan kawu bayan ɓari da matan suke yi babu wacce ta sake
haihuwa, sun yi duka sun yi zagin duk a banza wai an tsikari kakkaura ita bata ma san ta yadda
ake yin maitar ba, wani lokaci har ta kan yi adu'ar ya tabbata ita É—in Mayya ce don tana so ta ba
su kyautar kanta duniyar bata da anfani a gareta. bata ƙara zuwa makaranta ba ko na boko ko
arabi tun bayan mutuwar kakar ta sai dai ta ga wasu da kayan makaranta, ta zama boyi boyi
abin wulakantarwa, abinci wannan da kyar ake bata a gidan kan suka fara É—ora mata tallah
ganin tana da wannan farin jinin ya sa suka dage kuma ake kishi a kanta don kaman yadda
suke raba kwanan mijinsu haka suke raba ta.
Dole kuma a rana idan ta yiwa wannan sai ta yi wa É—ayar idan ta sayarwa wannan ko kwana
zata yi waje sai ta sayarwa É—ayar kan ta dawo gidan in ba haka ba ta shiga uku, bata sani ba
zata tabbata a haka Ko wani sauyi zai iya shigowa rayuwarta? Ita É—in Mayya ce da gaske? Har
yanzu tambayar da ita karan kanta bata iya amsawa kanta ba kenan bare ta amsawa
azzaluman mutanen da suke zagaye da ita.
"Ke!!!"
A ɗan firgice ta ɗaga kai sai ta ga wani matashi na miƙa mata kudi
"tun É—azu ina ta magana kin yi shiru kaman bakya duniyar? Saka min na É—ari biyar"
Abincin ta shiga sakawa shi ne ma na karshe don wuraren sha É—aya na safe ne, bayan ta saka
mishi ya koma cikin matasan da suke tare ya shiga ci ita kuma ta fara tattare wurin cikin
natsuwa da sanyinta sai da ta gama zuba komai cikin wheelbarrown tana jiran matashin ya
gama ya bata plate sai kawai ta fara jin hayaniya na tashi, É—ago kan da zata yi sai ta ga wannan
saurayi ne dafe da ƙirji yana tari sossai da sossai har filate ɗin ya faɗi ƙasa abincin ya tarwatse
ya bi abincin yana tumurmusa a ƙasa, kan kace kobo wurin ya cike da mutane wasu na cewa ya
mutu wasu na cewa da sauran ranshi.
"Me ya ci ne? Me ya same shi?"
Abin da mutane dayawa ke tambaya kenan, ita dai Afeefah na kafe a wurin ko motsi ta kasa sai
gangar jikin da mutane suka yi wa zobe kwance ta zubawa idanu kaman daga sama ta ji Muryar
wani na cewa
"Daga fa sayan abincin yarinyar chan kun ga bai ma gama ci ba...! Ku taimaka mu kaishi asibiti
kar ya rasa rayuwarsa kumfa ne a bakin sa"
Cikin jimami ya ƙarasa
Wata murya taji tana cewa
"hohoho asshaa dama na san aje aje sai ta fara yiwa mutane dauki ɗaiɗai shiyasa ban taɓa
sayan abincinta ba, yarinyar da riƙaƙƙiyar Mayya ce an ce ma ita ce mataimakiyar shugaban
Mayu yanzu?"
Ko motsi bata iya ta yi ba taji an damketa zuciyarta kaman zai fito waje ba na tsoron abin da
mutane zasu iya yi mata ba sai na tsananin tsoron mutuwa, mutuwa na daga cikin abinda a
yanzu yake gigitata dole duk mai imani ya tsorace mutuwa a yanzu yaron nan ke mata magana
a yanzu ana cewa ya mutu? Ta yaya? Meyasa sai da ya sayi abinci a hannunta?
Wani mai ƙirar ƙarfi ya hankaɗata tsakiyar mutanen
"Ke tsallakeshi sau uku ki sakar masa kurwa yanzu wallahi ko mu sheƙa ki barzahu.."
Yayi maganan da karaji yana zaro wuƙa mutane suka fara kananun maganganu masu zaginta
na yi, wasu har labari suke bayarwa na ta kashe iyayenta ai maitar gado ne tun a ciki ta fara
kisa, hawaye masu zafi ne suka shiga gangaro mata a sadda take tsallakeshi a dole, kalaman
da suke shiga kunnuwanta sun yi mata girman da ba zata iya É—auka ba, abin tashin hankalin ma
shine yaron bai tashi ba, ya tabbata ya riga ya rasa ransa ko kan ta gama fahimtar kanta har
tayi wani yunƙuri an rufe ta da duka, ko yunkurin kare kanta bata yi ba don a yanzu ita ma ta fi
ƙaunar mutuwar da rayuwa, da kyar wasu dattijai suka kwace ta fuskanta har ya fara sauya
kamanni wasu sassa na jikinta na zubar da jini, kwanukan inna larai da kulolinta an yi daga
daga da su, ko kasheni ka É—aukanta (lalitar kuÉ—i) bata gani a jikinta ba.
Wani irin deep kuka take yi mai taɓa rai, dattijon ta kalla
"Don Allah baba ka bar su su kasheni kawai nima ina so in huta, don Allah ku bar ni su kasheni"
Abin da take ta maimaitawa kenan tana gunjin kuka ya riƙo hannunta
"Ki natsu yarinya babu mai kashe ki, shima kwananshi ne ya ƙare ya mutu kiyi hakuri ki tashi
mu raka ki gidan ku"
Cikin in-inaa take cewa
"in naje gi..gidan ma ba..ba tsira z..Zan yi ba kuÉ—in inna larai da kwanukan ta duk babu"
Ta sake rushewa da kuka, tausayinta ne ya kama su suka haÉ—u suka tasa ta gaba har gidan,
kawu suka fara nema ko da ya fito da kallon tsana ya shiga bin ta.
"Yau kuma magana kika janyo min ko? Kayan uban wa kika sata ko uban wa kika kashe??"
Dattijo É—aya daga ciki yace
"A'a malam labaran ya kamata ka fara tambayar raunin jikinta ne amma damuwarka wani abu
daban? Ka san yaran zamani da kansu a koyaushe baya gayamusu daidai akwai wani yaro da
ya sayi abincin 'yar wajenka yana cikin ci sai Allah ya turo da ajalinshi a take ya tafi shine suka
yi yunkurin kasheta a cewar su ita ce ta cinye kur..."
Tuni ya katse su
"Ai da kun barsu don ni baku burge ni ba sam, da kun barsu don ko rantsuwa nayi ba zan yi
kaffara ba ita ce nan ta kashe shi, sai ki shiga ai ki jira zuwan iyayenshi tunda ba kowani
mahaukaci bane zaki mishi asarar rai ya barki ki sha ba"
"Ashshaa amma...."
"Babu ruwanku! Tunda kun kawo ta zaku iya tafiya" ya cigaba da mita kaman zai ari baki
yarinya ba jari zata kawo mishi ba, ba auruwa za tayi ba babu wani amfanin da take mishi sai
cin abincinshi amma kullum bacin ranta ya fi na kowa a ranshi.
Dattijan suka juya suka tafi ita kam kanta ƙasa zuciyarta na wani irin karta, hawaye kuwa sun ki
kafewa a idanunta kafafunta da suka matuƙar yi mata nauyi take kokarin ɗaga wa ta shiga cikin
gidan taji an fusgo ta har tana taga taga zata faɗi wuyan hijabin jikinta aka shaƙo
"Ina kudina da kayana?"
Kakari take don ko numfashi ta kasa shaƙa, idanunta da suke manya suka sake fitowa ainun
sun rine sun chanza gabaÉ—aya.
Inna larai ganin zata yi kisa ya sa ta HankaÉ—ata bata damu da kokawar saisaita numfashin da
take tayi ba ta daka mata tsawa
"nace ina kuÉ—ina?"
"In...nn..a B..ban san ya ak...a yi ya fice daga ji..jikina B.."
Hayewa ruwan cikinta tayi ta shiga É—irkarta kaman an aiko mata ita
"kaman kuwa yadda ya fice baki sani ba haka sai na rabaki da numfashinki baki farga ba, wlh
dukan kuÉ—ina yau sai na yi miki shi"
Ko karfin kare kanta bata dashi sai da dukan yayi yawa ne kawu Labaran da ke kishingiÉ—e yana
sakace haƙorinshi ya fito ya ɗaga inna larai
"ke kar ki yi min kisa a gida"
Yana kai nan ya juya ya bar wurin ta cigaba da sababi da zage zage karshe ta tafi ta barta nan
yashe.
Yaran gidan bayan sun gama kwasar dariya kowa ya kama gabansa
Inna Asabe ma na girki tana zaginta da tsine mata don yau ta yi mata asarar tallar yamma
tunda yanzu ko ta fita ba su da tabbacin akwai mai sayan abin hannunta irin wannan suncewar
zani a kasuwa da tayi musu, ta fi mintuna goma a kwance a wurin kan da rarrafe ta shiga
akurkinta ta faÉ—i bisa taburma tana kuka kaman ranta zai fita.
Ko mintuna biyu bata yi da shiga É—akin ba tana yashe a inda take ta soma jin hayaniya tamkar
ana yaƙi, idanunta sun kumbure ko iya buɗewa da kyau bata yi, bata san ya aka yi ba sai ji tayi
an janyota tamkar tsumma an fitar da ita, sama sama take jin mutane na ta hayaniya tana
hangar sanduna da makamai na tashi sama ana ikirarin kasheta kaman yadda ta kashe musu
É—a matashi, bata san ashe rigimar har su kawu ya shafa ba don sun rantse in ba'a fita da ita ba
gidan gabaɗaya za su ƙona, tashin hankalin da bata taɓa shiga ba ta shiga a ranar, bata san ya
aka yi 'yan sanda suka iso wurin ba don ana ta janta tamkar kaya ko takarda Muryar kawu na
ihun kar su ƙona masa dukiya ita suke so don haka ga ta nan su kashe ta. Fusgar ta aka yi aka
wulla ta motar 'yan sanda suka ja suka yi ofishin su da ita...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*003*
Bayan tsawon lokacin da ba za ta iya cewa gashi ba ta ji sauƙar ruwan sanyi a kanta duk da ta
farka sai dai bata da kuzarin É—aga ko da yatsar hannunta ne.
" In ba kema da ja wa kai ba ina ke ina cin maita don janyowa mutane bala'i ki mutu a ce ai ba
ma aikinmu ne yadda ya kamata. tashi my friend"
Ya ƙarasa yana kai mata kafa.
Laluɓe take har ta samu ta miƙe zaune gajimare ya rufe mata ido bata iya ganin komai.
Maƙogoronta da ke bushe ko miyau ba ta iya haɗiyewa sai kartar ta yake da kyar ta buɗe baki
ta ce
"R..ruwa..a don Allah"
Ruwan ya tura mata ta É—auka ta afa a baki har kwarewa take sai da ta sha sossai cikinta ya
murÉ—a don dama babu komai ciki ai sai amai tana jin É—an sandan na zaginta amma ba za ta iya
tsayarwa ba ya riga da ya zo, a lokacin idanunta sun washe tana gamawa ya tasa keyarta ta
kwashe ta share wurin cikin layi.
A lungun cell ɗin ta raɓe tana ta aikin riƙe ciki saboda yunwa, ɗaya dan sandar ya taso yana
ƙare mata kallo
"Ya dai?"
"Yunwa nake ji"
Murmushi yayi yana gyaɗa kai yana sake ƙarewa halittarta kallo Dukda rama ya yi mata yawa
ainun albarkatun jikinta na daidai shekarunta ba su ɓuya ba sam.
"Zan sayo miki abinci amma kin san gomnati ta hana aikin banza ko? Nima za ki rama min"
Sam bata wani fahimta don yunwa ba ta da hankali samm kai kawai ta gyaÉ—a ya fice chan sai
gashi da filate ya miƙa mata ta fusga ta shiga ci hannu baka hannu ƙwarya sai da ta fara koshi
tukuna ma ta fahimci ashe gari ya waye kenan a cell ta kwana gashi har ana batun ƙiran sallar
azahar tsabar rashin gata babu wanda ya neme ta, ta tabbatar ko shekara zata yi nan kawu ba
zuwa zai yi ba bare ya cire kuÉ—in shi yayi belinta don sun ce sai an ba su kuÉ—in mai za su sake
ta...
Bayan ta gama ta roƙi za tayi sallah basu hanata ba ta rama duk waenda aka bi ta. A nan ta
cigaba da zama ita daya har dab Magrib wani matashin É—an sanda ne ya shigo yana dubanta
"Ya Sunanki?"
"Afeefah"
"ba ki da kowa ne da zai zo yayi belinki?"
Ta girgiza kai
"Ni marainiya ce kawu na kuma na san ba zai taɓa zuwa ba ko shekara zan yi"
'dan shiru yayi
"Afeefah za ki iya komawa gida da kan ki?"
Ta gyaÉ—a kai
"tashi ki tafi to zan biya kuÉ—in belin naki, bana so dare ya sake samunki a nan muna da
gurɓatattun 'yan sanda bare har kin bari kin ci abin hannun kopur DanJuma sai ya dawo, kuma
ba ni da ƙarfi ko ikon kare ki"
Hawaye ne suka cika kumburarrun idanunta ashe akwai masu zuciyar imani da tausayi a cikin
'yan sanda? Godiya tayi ta mishi har da kuka a lokacin da zata fita ta ce
"Menene sunanka?"
"Sa'adu. Sa'adu Rabi'u"
"Allah ya dube ka ya shiga cikin lamuranka ya dafa maka"
Amsawa yayi ta fice da sauri lunguna tayi ta bi a tsorace kar ma ta haÉ—u da kopur Danjuma har
ta isa gida.
"Uban wa yayi belinki?"
Kawu dake kofar gida ya daka mata tsawa
"Su...su suka sake ni"
Takalman shi ya wuwuro ya jefa mata
"shegiya natacciya dama shiyasa ake cewa mutum maye mana in ya cika naci, kin rantse sai
kin kasheni ko? To kafin nan sai na yi ajalinki marar anfani kawai"
Da gudu ta shiga gidan don ya miƙe ya biyo bayanta kaman zai faɗi.
Ɗakinshi ya shiga ya haɗo tarkacen da ya karɓo na kare kai daga sharrin Mayu yayi ɗakinta
dorinarshi ya samu ya rufeta da duka wai na hawan jinin da ta saka mishi jiya ta kusa ja mishi
asarar rai da dukiya babu wanda ya kula su duk ihu da neman agajinta sai da ya gaji ya kyaleta.
Ya sa aka kawo mishi garwashi ya turbune su da uban hayaƙi mai bala'in ƙauri bayan ya gama
ya tafi ya barta nan yana cigaba da sababi.
Bata san iya adadin lokutan da ta É—auka a kwance cikin yanayin ba, tun tana kuka da hawaye
har suka ƙafe sai dai zuci na cigaba da zubar da kwalla cikin ƙunci da raɗaɗin da bata san ranar
tsayuwarshi ba, yunwa ne kaman zai yi ajalinta hakan ya sa ta dole ta lallaɓa ta fito, yadda garin
yayi shiru sossai za ka san cewa dare ya riga da ya tsala murhu ta isa akwai sauran gawayi ta
dibo ruwa tana layi ta É—ora, a wurin ta zube tana kallon kicin É—in babu alamar an ajiye mata wani
abu da zata iya ci, busashen miyau da ya ƙafe a Bakinta ta lalaɓo da kyar ta Haɗiye.
Sai da ruwan ya tafasa ta juye hadari ne sossai a garin don har an fara iska da walkiya sai
dai dayake zuciyarta a kafe yake yasa babu tsoron komai cikin ranta ta shiga ta gasa jikinta
sossai ta fito, kicin É—in ta koma da kyar ta samu wani kanzo ta É—an bubbuga ta zuba ruwa yayi
laushi ta É—auka ta nufi akurkinta tana da É—an maggi da yaji da mai kaÉ—an ta saka a ciki ta ci bata
ma gama ci ba taji sauƙar ruwa kaman da bakin ƙwarya, ko da ta kwanta baccin sai ya ƙi zuwar
mata sai tunanin rasuwar yaron jiya take ko wani hali iyayenshi ke ciki? Tana kuma tambayar
kanta da gaske ita ɗin Mayya ce? Da ƙyar bacci da ya fi kowa iya sata ya lallaɓo ya sace ta...
Rayuwa ya É—auki yi mata zafi a gidan fiye da baya saboda a yanzu tallar bata yi inna larai ta yi
mugun tsanarta don ta karya mata kasuwa hakan yasa ko abin da zata ci a girkin inna larai
gagararta yake, ba'a isa a aike ta ba haka zata dawo da hawaye saboda maganganun mutane
da ma yunkurin illata ta da wasu kan yi, bautar gidan duk ya dawo kanta yanzu har girki ita ke yi
musu su zo suyi rabo kuma a hanata don daga an sauƙe za'a aike ta kan ta dawo an raba in ta
tambaya su ce sun manta da ita, ita dai gata nan amma rayuwar baya yi mata daaÉ—i ko ta wani
ɓangare.
''Ina ma mutum na da zaɓi kan rayuwarsa! Ina ma a ce bawa ke da ikon rubuta ƙaddararsa! Da
ban zaɓi maraici ba. Duk bala'i na san ko da kowa zai guje ni su ɗin ba zasu taɓa guduna ba" a
hankali take furta hakan wani irin kewa da maraici na taso mata, har ƙasan ranta bata son
yadda ta zama tamkar mujiya a cikin tsuntsaye, bata son wannan suna na Annoba da yanzu
kowa ke ƙiran ta dashi... Kanta a duƙe ƙasa ruwan hawayen da bata rabo da su na sulmiyowa
cikin ruwan kunfar wanke-wanken da take yi wani irin zafin da zuciyarta ke yi kaman zata fito
daga madaukarta
"Wai zama kika yi kina maitar da kika saba na shanye kurwuwowin mutane ba za ki yi ki kawo
mini kwanuka in raba abinci ba?"
Inna larai ta watso mata kalaman cikin hantara.
sharɓe hawayenta ta yi, cikin mintunan da ba su wuce biyar ba ta kammala.
Tattara kwanukan ta yi ta kai gaban murhu ta ja jikinta gefe ta tsaya tamkar jiƙaƙƙiyar kaza da ta
rasa mafaka yayin ruwan sama.
"Ungo sayo min kuka da daddawa."
Kuɗin da ta wullo mata a wulaƙance ta sanya hannu ta ɗauka ta juya tana jefa singallin
kafafunta masu kama da zaren lipton saboda rama tayi waje, ko da ta dawo zaune ta tadda
zuri'ar gidan suna karyawa cikin natsuwa.
"Ga shi inna larai"
Fusga ta yi suka ci gaba da kai lomar zazzafan É—umamen tuwon dake turiri ita da Inna Asabe
"Abinci...cina fa?"
Ta yi tambayar zuciyarta na rawa. Amsar da take tsoron ji ita É—in dai ce ta ratsa kunnuwanta.
"Kin ga na manta da ke a rabo, sai ki jira na rana."
Wani irin raÉ—aÉ—i ne ya ziyarci idanunta tamkar wacce aka watsawa borkono. Ba ta sauya zani
ba ba kuma ta tunanin za ta sauya É—in abu ne da ta riga ta sani a kullum idan har za a raba
abinci aka aike ta shi kenan rabonta ya faɗi ƙas.
Ita take kallo sai dai tuni zuciyarta da ƙwaƙwalwarta suka tafi nisan kiwo, hanjin cikinta jin shi
take kamar ana daddatsawa tsananin yunwar da ta kwana da ita. Ba ta da shi ba ta kuma da
wanda zai ba ta babu mai É—igon tausayinta a gidan a cewarsu mayu sun fi cinye kurwan wanda
ya ji tausayinsu ko ya taimaka musu.
Sauƙar ruwan zafin da ta ji a fuskarta yasa ta sakin ƙarar azaba a firgice ta miƙe daga durƙuson
da ta yi a gabansu tana dirza fatar inda wani irin zafi ke ziyartar ta. A take ta É—aile, daidai
lokacin inna larain take faÉ—ar
"Wallahi kurwata kur! Maye sai dai ya ci kansa."
Baya ta matsa ta sake zubewa bisa gwiwoyinta hawaye na sake tsinke mata cikin shessheƙa ta
fara roƙon su taimake ta da abinci.
"Inna don Allah ko da loma biyu ne ku taimake ni da ita, cikina babu komai hanjina murÉ—a suke,
yunwa za ta kar ni."
Kamar dabba haka ta sa ƙafafu ta hamɓare ta ba tare da ta ko damu da raunin ƙunar da ke
jikinta ba.
"Ba za ki taɓa samun nasara a kaina ba, wuce ki fara shirin ɗaura mini abincin rana."
Jiki a saɓule ta miƙe ta nufi wurin murhu, a haka cikin raɗaɗin gangar jiki da zuci ta fara aikin.
Bata yi nisa a aikin ba suka gama karyawa suka kai kwanukan mawanki kowa ya nufi É—akinsa
don hutawa. Ta rarrafa ta isa bigiren saboda ko ƙarfin miƙewa tsaye babu jikinta tsabar yunwar
dake dawainiya da rayuwarta.
ÆŠan sauran wanda suka rage take kwarfewa tana afkawa a bakin salati, ta haÉ—e da tukunyar ta
kankare ƙasan tana ci tana zub da hawayen tausayin kanta da irin rayuwar da take. Ko kula
inna Larai dake mata gargaɗin kar ta yi mata lamba a tukunya bata yi ba. Ta miƙe ba don ta
ƙoshi ba sai don babu wani abin da zata sake samu ta ƙarasa ta kwalfi ruwa ta afawa cikinta. A
gindin randar ta raɓe cike da fatan sanyin ya taimaki zuciyarta wurin kashe wutar dake ruruwa a
cikinta har take neman kai ta ga kushewarta.
"Afeefah! Afeefah!!"
Sam bata san bacci ya sure ta a wurin ba sai da ta ji ana jijjiga ta tare da kiran sunanta.
"Lafiya kike bacci a nan?"
Idanunta da ba su da maraba da na mashaya saboda gajiya da jigata ta ware tana kallon mai
maganar da muryarta yayi kama da wacce ta sani da jimawa, a hankali sanyi ya shiga ratsa ta.
Sanyin farincikin sanya mace guda da ta rage mai ƙaunarta kaf faɗin duniya a idanunta, tashi ta
yi cikin azama da 'yar fara'a ta rungume ta.
"Afeefah....!"
Kiran sunanta da ta yi tare da fincikar da tayi mata daga rungumar tana ƙarewa fuskarta da ma
jikinta kallo ne ta ji tamkar ta sosa mata inda ke yi mata ƙaiƙayi. Dama me neman kuka ne aka
jefe shi da kashin shanu. "Wa ya yi miki wannan lahanin?" Ita dai ba baki sai kunne don haka ta
ci gaba da kukanta yayin da ta shiga rarrashinta itama hawayen take zubarwa. Da ƙyar Afeefah
ta yi shiru kan matar ta buÉ—e jakar hannunta ta fiddo biredin da ta yo mata tsaraba. Kamar
mayunwaciyar zakanya haka ta afka masa da ci ba ji ba gani har tana ƙwarewa, matar ta ɗibo
ruwa ta ba ta hawaye na gangaro mata, daidai lokacin da kawu ya fito shirye da alama kasuwa
za shi..
"Labaran ka ji tsoron Allah, wallahi ka kwana da sanin kai ma ba ka fi ƙarfin ƙaddara ba.
Rayuwa da kake yi da 'ya'yanka ƙarƙashin kulawarka ba wayonka ba ne ballantana dabararka,
a yau za ka iya faÉ—uwa ka mutu, shin za ka so a yi wa 'ya'yanka yadda kake mata?"
Kanwar mahaifiyarta ta jefa masa kalaman cikin jin haushin yanayin da ta zo ta iske Afeefar
Kallon banza ya watsa mata.
"Kina da gida ko Zainabu? Toh ki tarkata ta ku tafi tun kan mu yi ɓacin ɓacina kuma ki daina
haÉ—a yarana da wannan annobar... Ni ban haifi maye ko É—aya ba, ban kuma shirya mutuwa ba.
Zaman ma da kika ga tana yi saboda ba ni da yadda zan yi ne, amma yanzu tun da ga ki Allah
ya raka taki gona...!"
Har ya nufi fita ya dawo ya sake kallon ta.
"Af! Idan ƙarshen saduwar kenan to ubangiji ya sa can ta fi miki nan."
Miƙewa tsaye ta yi a zuciye.
"Zan tafi da ita Labaran, dama rashin sani ne ya sa kaza ta kwana da yunwa a saman dami,
idan ka ga na mutu lokacina ne ya yi. Ke tashi mu tafi."
Ta watso ma Afeefahn sauran kalaman nata tana kallonta, tun farkon rasuwar mahaifiyarta
Aunty zainabu da ita kaɗai ce ƙanwar mahaifiyarta ta so karɓar ta sai dai kakarta ta ƙi har ma ya
kai ga sun yi rigimar da ta sa tayi matukar fushi, sau ɗaya ta taɓa zuwa ta duba ta a gidan
kakartata sai lokacin da take wurin innarta ma ta zo ta duba ta, haka ma tana gidan kawu ta zo
sau biyu sai dai bata taɓa wuce awa ɗaya ba tana ganinta ta kawo mata tsaraba ta tafi don wani
kauye gaba da su sossai take.
Duk da chan ta san Afeefahn na cikin damuwa sai dai bata san ya kai har haka ba, ganinta a
yanayin da ta sameta ya matukar É—aga mata hankali.
"Afeefah da ke nake yi!"
idanunta da kaman za su faɗo ta saisaita ta miƙe da sauri ta shige akurkin ɗakin nata. Wani
tunani da ya É—arsar mata ne ya sa ta nemi gefen kayanta ta tsuguna, hawaye ne ya cika
idanunta Aunty Zee ce ta shigo tana ƙarewa ɗakin kallo cike da tausayawa ta duƙa gangarta
tare da dafa kafaÉ—arta
Kaman ta karanci yanayin da take ciki da tunanin da zuciyarta ke yi.
"Sau tari ƙaddarorin da ke zagaye da mu su ke taimaka mana wurin tabbatar da imaninmu ko
akasin hakan, ina so ki zama tuwon hatsi mai yawan juriya, dukkan tsanani yana tare da sauƙi.
Mu tafi."
Taya ta tayi suka haÉ—a yar Ghana most go É—inta da babu wasu kayan kirki suka fice, bata damu
da ko sallaman su Baba Larai ba su ma kuma dariyar Allah ya tura ƙeya suka bi su da shi don
yanzu Afeefahn bata da anfani a rayuwarsu.
Tasha suka tafi suka hau mota, ita dai jikinta ya matuƙar sanyaya damuwar da ke ranta ko kusa
bai ragu ba saboda tsoron kar wani abu ya sami Auntyn nata da take ji da, ya haɗu da bata taɓa
shiga mota ba a rayuwarta don bata taɓa barin garin nasu ba wannan ne karo na farko, bata
san akwai titi kwantacce irin hakan ba sai da suka É—auki titin cikin garin Anchau daga kauyensu
chan cikin Dutsen-wai na Kaduna state, tun tana kalle-kalle har bacci ya sure ta, sai ji tayi Aunty
zainabu na tashinta tana bude ido ta ga har sun iso inda za su sauƙa ba ma su isa tasha ba don
Auntyn gidan ta na daga wajen garin Anchau duk under kubau LGA of Kaduna state ne, sauƙa
suka yi ta É—auki kayanta a kai suka gangara layin har zuwa gidan, layi ne na masu matsakaitan
ƙarfi da rufin asiri gidan Auntyn ba wani babba bane sai dai ciki biyu ne da parlor sai tsakar gida
da take da tarin shuke-shuke.
A madaidaicin parlorn ta yi mata masauki ta buÉ—e karamin frigde É—inta ta fiddo mata ruwa
"Sha ruwa bari na samu na É—ora mana wani abu ko? Sannu. Ki sake jikinki a nan babu mai
takura miki in shaa Allahu kin ji?"
Kai ta gyaɗa tana yaƙe dai, bayan ta sha ruwan ta fita zuwa kicin na tsakar gida don kamawa
Auntyn nata aikin da take yi Dukda ta ƙi tace ta je huta amma sai da ta saka mata hannun suka
shiga yi tare tare har suka gama, shinkafa fara da Miyar jajjage da tayi ta saka mata a filet
"ɗauka ki koma ƙasan mangoron chan ki shimfida taburma sai ki ci"
Yadda ta ce haka tayi Auntyn ta kawo mata ruwa again tuni ta yi nisa a cin abincin.
Aunty zainabu dai na ta kokarin haÉ—a na mijinta don ta san yana gab da shigowa shima cin
abincin ranan, dama daga ita sai shi ne gidan Dukda ta fi shekaru goma da aure sai dai har
yanzu bata haihu ba, ya sake aure bayan ita amma ba gida daya suke da matar ba itama dai
har yanzu babu wani labari na haihuwa kam suna kuma zaman lafiya sossai.
Tana ƙoƙarin kai loma yana sallama, ta amsa ya ɗan yi turus yana kallonta gabanta ne ya ɗan
faÉ—i don ganin fuskanshi ya É—an sauya ko da ta gaishe shi da kalma É—aya ya amsa kan ya nufi
ciki yana kiran zainabu...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Ba lallai ku ji ni anjima chan ba saboda wani uzuri na so pls bear with me ku riƙe wannan as na
chan anjima É—in tunda Its already friday.*
*004*
A wurin ta cigaba da zama jiki a saɓule har dai Aunty zainabu ta fito tana kallon fuskanta da har
ya ɗuri ruwa saboda ƙuna daga gefe zuwa ƙasan idanunta, Allah ya taƙaita ma bai taɓa idanun
ba ta ce
"Har kin gama ci Afeefah?"
"Eh Aunty na gama"
Ta faÉ—a a hankali don yanayin Auntyn bai mata yadda suka dawo ba idanunta kaman ta yi kuka.
"Bari na ba uncle ɗinki abincinshi sai na zo mu tafi gidan mai mazari ya duba miki wannan ƙunar
kar ya zama miki damuwa"
Daga haka ta yi kitchen, Afeefah ta miƙe ta shiga parlor zuwa ɗakin da ta ajiye mata kayanta
daidai ta sauya hijabi zata fito ta ji mijin Auntyn nata murya a sama yana magana
"Babu inda za ki da ita zainabu idan ba mayar da ita inda kika É—auko ta za kiyi ba"
Itama Auntyn a sama ta amsa shi
"sai dai kuma idan za mu bar maka gidan tare da ita Usman"
"Zainabu...!"
Da mamaki ya ƙira sunan don a zamansu ba zai ce ga sadda ta ɗaga mishi murya ba sai yau.
Kuka ta fara
"Haba Usman na fa faÉ—a maka maganan nan a wurina bashi da matsuguni, Afeefah É—iyar
yayata ce daidai take da tawa wacce zan iya haifa a cikina tana cikin matsi da takurar rayuwa
ina tsoron nima Allah ya kama ni a kan banzatar da rayuwarta don Allah ka kalleta da kyau ka
ga depression na neman kasheta tun a kananun shekaru..."
Ya katse ta
"Zainabu ba wai 'yar uwarki na tsana ba ina tsoro ne, ina tsoron abin da zai je ya zo daga nan
Anchau har Dutsen-wai babu wanda bai san da labarin yarinyar nan ba, ko kwanan nan ta ci
kurwar wani matashi a kasuwa kowa tsoron hulda da ita ya ke sai ni zaki É—auko ta ki kawo min
cikin gida?"
Tana kuka sossai tace
"Wallahi duk babu gaskiya a lamarin mutane Allah ba zan taɓa yarda Afeefah zata yi maita ba,
babu mai mutuwa sai wadda kwanakin shi suka ƙare idan ko don ka zauna da mutum kwana ya
ƙare ka zama maye ne da dukkan mu nan Mayu ne don idan baka rasa iyaye ba ma ka rasa
makusanta. Idan dai har Afeefah zata bar gidan nan zan bita mu tafi tare ba zan iya sake mayar
da ita gidan labaran ba wallahi"
Numfashi mai karfi ya sauƙe
"shikenan zainabu ai sai ta zauna, amma duk abin da ya je ya zo babu ruwana"
"Babu ma abin da zai faru sai alkhairi"
A lokacin Afeefah ta sulale ta maƙale jikin gini kamar kadangaruwa ta chusa kanta cikin
kafafunta, bata ga laifin mijin Aunty zainabu ba rayuwarsu yake karewa da ya wajaba a kanshi
amma Meyasa ita ta zama Mayya? Taya aka yi ta zama Mayya? Amsar da ta kasa ba kanta
kenan har yau bata ma san Shigowar Aunty zainabu ba sai dafa ta da tayi ta ji, ta É—ago kai
"Aunty don Allah ki yi haƙuri ki mayar da ni gidan kawu zan cigaba da juriya ni karan kaina
hankalina ba'a kwance yake ba, tsoro nake ji ina tsananin tsoron kar wani abu ya same ki ta
dalilina ba zan iya yafe wa kaina ba..."
Kuka ne ya ci karfinta Auntyn ta share mata hawaye
"bawa baya taɓa wuce ƙaddarar shi Afeefah babu wanda ke da ran wani a hannunshi face
ubangiji don Allah ki kwantar da hankalinki kin ji? Ba zan taɓa iya sake barinki ki zauna wurin
'yan uwan mahaifinki ba muddin ina numfashi. Tashi mu je"
Tashi tayi suka fice daga gidan suka je aka saka mata maganin ƙuna a wurin kan suka dawo.
Washegari suka sake fita dayake Aunty zainabu yar kasuwa ce tana saya da sayarwa sossai
babu wanda bai santa ba a unguwar da ma unguwannin da suke maƙotaka tana saya kuma ta
sayar, hatta kayan jikinta in zaki ce kina so ta kan iya cirewa ta sayar miki haka take bata zauna
ba, shiyasa take da rufin asirinta a karan kanta makaranta suka je aka yi wa Afeefah interview
da kyar aka barta a js2 duk da shekarunta sun wuce ajin, private ce da bai wuci dubu shidda ba
termly don haka Aunty ta karbi sample na uniform suka tafi kasuwa ta yanka mata yadi aka ba
tela akan zai É—inka kan su gama sayayya, sayayya sossai ta yi mata da saida tayi ta zub da
hawaye tana da sauran gata ashe bata sani ba soyayyar Aunty zainabu ya shige ta tamkar
yadda zata so mahaifiyarta.
Da kaya sossai suka dawo niki niki, a É—akin Aunty zainabu inda Afeefahn take suka ya da zango
nan ta sake shirya mata kayanta dama ta cire nata masu É—an dama suka tafi da su kasuwa aka
rarrage mata yadda zai ƙarbe ta duk na gidan kawu zubarwa tayi.
Rayuwa ne mai cike da natsuwa da kwanciyar hankali ta shiga gudanarwa gidan Aunty zee da
uncle usman, tun yana tsoro har ya sake barin ma da ya ga Afeefar yarinya ce mai kwazo,
natsuwa da hankali ga ibada da son karatu boko da arabi komai na gidan yanzu ita ke yi don
babu wani yawa bata bari Auntyn nata tayi komai muddin tana nan, haka a makaranta malamai
sai yabawa kwazonta suke don tana da ilimi kuma akwai saka kai, suna ganin ma a karshen
shekara za'a iya bari tayi Junior waec ta tafi ss1 in dai aka tafi a yadda take a yanzu, haka
islamiyya tana kokari sossai kusan kowa ya san ta a unguwar saboda yadda Aunty zee É—in ke
nuna ta matsayin É—iyarta.
Sauri sauri ta gama shiri don ta so makara ta fito goye da school bag É—inta, fuskanta ya fito fess
a cikin sky blue hijabin makarantar kyaunta ya sake bayyana na ainihin Black beauty, skin É—inta
har wani sheki yake na samun natsuwa, fararen idanunta take warawa ta inda za ta hango
Aunty zee sai dai bata ganta ba, a parlorn ta tsaya ko zata fito daga É—akin uncle usman ta samu
ta mata sallama sai shi ta ga ya fito ta É—an duka ta gaishe shi ya amsa cikin natsuwa
"Dama uncle ina son yin sallama da Auntina ne ko ta koma bacci?"
"Eh ai tun da ta fito ta ga kin kamalla komai tana komawa ta sake bingirewa da bacci"
Afeefah tayi murmushi
"Toh shikenan na wuce makaranta"
"karɓi"
Ta matsa ta karɓi ɗari biyu da yake miƙa mata
"Sai kin dawo a mayar da hankali"
Ta amsa tana ficewa da murmushi fal fuskarta kaman ba Afeefar da ba da take yawo da
tsananin damuwa da hawaye a ko da yaushe.
Ko a makaranta natsuwarta bai kau ba, sam ba zaka ganta tana wasa ba koyaushe littafi na
hannunta tana dubawa har ta fara presenting abubuwa a assembly da participating a wasu
programs na makarantar, bata da ƙawa har yanzu don duk ajinsu ba sa'annin ta shirin exams
ake don haka yau revision ƙarfe sha biyu suka tashi ta nufo gida cikin natsuwa.
Sai dai ta samu babu kowa, ta karɓi key a maƙota ta shiga sai da ta zare uniform ɗinta ta sauya
da wasu kananun kaya wando ne da dogon riga da ya zo mata har gwiwa kan ta É—aura
dankwalin ta fita zuwa kicin, abinci ta É—ora musu tana mamakin inda Aunty zee ta tafi don bata
ce mata za ta fita yau ba kuma kila wani abu ne dai ya taso a chan cikin dangi, ita dai ta san
suna da dangin nesa nesa ta ɓangaren mahaifiyarta amma su ma ba wani karbarta suka yi ba
ko daukar ta da muhimmanci Dukda ita kanta Aunty zee É—in ba ta su take ba abinda ke gabanta
ma ya fi karfinta.
Tana sauƙe faten doyar sai ga su sun shigo
"wannan kamshi haka me ake dafa mana ne Afeefah?"
Aunty zee ta leƙo kicin ɗin tana tambaya
Dariya Afeefah tayi
"Aunty faten doya ne fa, amma ya Naji muryarki kaman ta marasa lafiya?"
Tana zama a kujeran tsuguno ta janyo filet ta miƙawa Afeefahn, Afeefah ta karɓa ta shiga saka
mata kan tace
"Eh Afeefah ban jin daaɗi ki taya ni murna kin kusa samun kanwa ko ƙani"
Wani irin zaro ido Afeefah tayi kan ta saki ihu tana rungume Aunty zee É—in sai ta hau hawayen
murna, zuciyarta tamkar takarda haka take jinta oh ashe Aunty zee na da rabon ganin 'ya'yanta
a duniya?
Ita Aunty zee ture ta tayi tana share mata hawaye tace
"duk na murnar ne? Yanzu na gama share wa uncle É—inki da ma É—ayar Auntyn taki da suka tasa
ni gaba suna kukan farin ciki shine kema za ki fara? Oya ni sa min abinci in ci cikina kaman ana
yasa"
Tana murmushi ta ƙarasa saka mata ta dauka mata zuwa gindin bishiyar dake ba da iska mai
ni'ima, taburma ta shimfida mata kan ta ajiye mata abincin taje ta kawo mata ruwa tuni ta yi nisa
a cin abincinta.
Dukda karatu da Afeefah ta saka a gaba saboda tana son fitowa da sakamako mai kyau a term
É—in don Aunty tayi alfahari da ita hakan bai hana ta jajirce wurin kulawa da Aunty zee É—in ba, ko
tsinke in ta ga zata ɗaga za ta karɓe duk abin da take so ko a hira tayi maganan Afeefah za ta
yi kokari wurin ganin ta dafa mata shi tunda uncle usman bai Gaza da gidan ba ko ta wani
ɓangare, kishiyar Aunty zee ɗin ta kan zo sossai tun samuwar cikin itama da ita ake haduwa
ana ririta cikin Dukda Afeefah dai jininsu bai wani haÉ—u da matar ba tunda iyakarsu gaisuwa, ko
hira Aunty zee ke yi da Afeefah in dai ta sa matar bata amsawa ita dai Afeefah bata damu ba
tunda babu abin da ya haÉ—a su duk kuma a je a zo bata wuce awanni biyar zuwa goma a gidan
so bata damu ba sam.
Kaman yadda ta ci buri ranar hutu sai ga Afeefah da position 3rd ta yi murna kwarai, haka ta
dawo gidan da farin ciki. A tsaye ta samu Aunty zee tana tattare kayan da Afeefah ta wanke da
safen don shigarwa ciki sai ji tayi an rukunkumeta
"Aunty ki taya ni murna"
Result ɗin ta miƙa mata
"Masha Allah, Alhamdulillah yarinyana kai ya fara ja Allah ubangiji ya sa ki fi haka ya dafa miki a
dukkan lamuran ki, Allah ya nuna mana ranar da wannan karatu zai anfanemu ina fata za ki yi
kokarin ci gaba da tafiya a haka next term mu ga First rubuce wannan wuri"
Kai ta gyaÉ—a tana ta dariya.
****
Aunty zee ce zaune tana ta aikin kallon Afeefah dake yi musu alele don yau da sha'awar shi ta
tashi hakan ya sa tana furta wa Afeefah ta hau yi, tana aikin cike da tsafta tana kuma jefawa
Aunty zee É—in hira kaÉ—an kadan da ya shafi islamiyya da kuma boko da suka koma sati huÉ—u
kenan.
A ranta take raya abubuwa dayawa game da Afeefah ɗin tana da matuƙar buri a kan rayuwar
Afeefah yadda take very jovial bata fata nan gaba ko ma menene ya karya ta, tana adu'a yadda
ta samu farin ciki ta dawwama a haka haske ya cigaba da bibiyar rayuwarta, bata san me gaba
ya tanadar ba amma tana mafarkin ganin Afeefah a kololuwar matsayi cike da kwanciyar
hankali, danne tunaninta da ya so juyewa ta yi tana cewa Afeefah
"Wai kuwa kin san kamanninki har ya ɓaci da Yaya Aisha?"
Afeefah ta É—ago ta kalleta yau ne karo na farko da maganar mahaifiyarta ya fito daga bakin
Aunty zee É—in
"Na zaci da babana nake kama don mutane kan ce ina kama da inno(kakarta da ta rasu)"
Miƙewa Aunty zee ta yi ta shiga ɗaki ta ɗan jima sossai kan ta fito da wasu hotuna hannunta, a
lokacin Afeefah ta koma kan taburma ta zauna ta bar alelen ya dafu gefenta Aunty zee da
cikinta har ya turo sossai ta zauna.
"Jini ne kawai tsakanin ki da inno amma kamanninki tsaff Yaya Aisha ne, kin ganta nan lokacin
bikinta ne da babanki"
Karo na farko kenan da zata ga mahaifiyarta sai ta ji zuciyarta ya cika da rauni, hannunta na
ɗan rawa ta sanya ta karɓa hotunan da ne Black and White matar da ta kasance mahaifiyarta
da bata sani ba zaune sanye da zani da riga tare da Ali goggoro, hawayenta ne suka tsinke
ganin yadda matar ta zauna tamkar ta kirata ta amsa, da gaske hatta yatsun hannu da na kafar
ta irin na mamanta ne, baƙin fatarsu mai sheƙi, manyan fararen idanunsu, tsinin hancin su,
karamin bakinsu da fararen hakwaransu hatta dimple guda É—aya da maman nata ke dashi a
gefen hagu itama tana da shi.
RaÉ—aÉ—in maraici ne ya mamaye zuciyarta, in ba mutuwa ta zama dole ba wa zai so maraici?
Maraici ma irin nata marar gata da tushe? Maganganun mutane a kan iyayenta take tunawa sai
taji kaman yanzu ne ake jefanta mugayen kalamai, tsintuwa da hantara a kan waenda duk
duniya idan da za'a ce me take buƙata ayi mata ko da abu na ƙarshe ne za ta zaɓi su yi rayuwa
na har abada amma ake mata Ƙazafin kashe su, anya zuciyarta za ta taɓa warkewa? Anya za
ta iya yafewa masu alhakinta?
ÆŠago raunannun idanunta tayi ta Kalli Aunty zee
"Aunty don Allah yaya maita yake? Ya ake yi? Yaya mutanen su ke? Kila baka sanin sadda
kake yi in ba hakan ba ta ya zan zaɓi wannan rayuwa akan iyayena? Kila ko cikin fitan
hayyacine ake yi ko? Menene ribar yin? Suna yin kuÉ—i ko Aunty? To me yasa ni ban yi ba?
Yanzu wannan pure soul É—in ni na kasheta ko?"
Duk ta rikice ta rasa me zata ce, kalaman suna zuwar mata ne kawai ba tare da ta san fitan su
ba, kuka ne ya kufce mata, kukan da ke fita daga ƙasan zuciyarta na ciwo da raɗaɗi...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Ku yi ta Adu'a mu ƙare a haka ina jin karsashin typing, ina jin daaɗin comments ɗin ku Allah ya
bar ƙauna*
*005*
Hannunta ta riƙe cike da tarin tausayinta da kuma ƙaunar da take jin tana mata fiye da ƙima ta
shiga cewa
"Na san ba ki kashe kowa ba Afeefah, ƙage ne kawai da Ƙazafi irin da jahilai daga cikin
al'ummar mu, ƙarancin ilimi yayi yawa ta yadda mutane suke kasa yarda komai daga Allah ne, a
ƙarƙarorin mu ne musamman wanda babu addini sossai za ki samu ko tuntuɓe bawa yayi sai an
faÉ—i dalili da silar shi basu yarda cewa komai Allah ne yake yi ba.
Afeefah Kowacce rayuwa akwai ƙalubale ciki ke kuma ta ki kalar ƙalubalen kenan, amma fa na
faÉ—a na sake kar ki saka hakan a ranki saboda babu mai kashewa da raya wa sai ubangiji, duk
kuma wanda kika ga ya rasa ransa tabbas lokacin shi ya riga ya ƙare ne ko da sanadi ko babu
dole babu maƙawa sai ya tafi, tsakanin ki da su Adu'a ne shine zai ba su tabbacin irin ƙaunar da
kike musu. Afeefah mahaifiyarki ba za ta so ta ga kina zub da hawaye ko kin ƙuntatawa kan ki
saboda ƙaddarar da ba ke kika ɗorawa kan ki ba, kaman kowace uwa ni ma zan baki shawara
ki saka zuciyarki gaba, ki yi Adu'a ki kuma jajirce ki zama tamkar bishiyar gamji sara ko sassaƙa
ba su isa su hana ki toho ba"
Jikin Aunty zee kawai ta faÉ—a tana shesheka da kyar ta lallasheta ta bar kukan kan ta É—ago
"Na miki alƙawari in shaa Allahu Aunty za ki yi alfahari da ni nan gaba, ba za ki taɓa kuka a
kaina ba"
"Allah ya amince hajiya ta"
Dariya Afeefah ta saki jin ta kirata hajiyarta wadda babban burinta kenan ta zama shahararriyar
'yar kasuwa don tana so tayi kuɗi saboda wani dalili nata. Ƙaurin kamawar leda da suka ji ya sa
ta tashi da gudu taje ta sauke tukunyar alelenta daga kan gano tana furta
"Aunty alele na so yayi mana buƙulu"
Aunty zee na dariya tace
"Hira ta yi daaÉ—i ba, duba ki ga Allah ya sa bata yi komai ba"
Sun ci sa'a bata yi komai ba sai na ƙasan guda biyu da ledar ya ƙone nan ta zuba musu tare da
Auntyn ta zuba na uncle a kula suka zauna suka ci tare suna hirar su gwanin sha'awa bayan
sun gama ita ta yi wanke wanke, ko da ta dawo kan taburman hoton Aunty zee ta bata
"Gashi na bar miki, ki ajiye a wurinki"
Murmushi ta saki kan ta karɓa tana godiya.
Wasa wasa cikin Aunty zee ya shiga watan haihuwa, ta ɓangaren Afeefah tana nan tana
ƙoƙarin karatu ka'in da na'in don 2nd term da suka koma ita ta ɗauki na ɗaya kuma 3rd term
nan suna ƙare ta tare da ita za'a zana Junior waec ta tafi ss1, a yanzu hatta turanci ya zauna a
bakinta ba kaman baya ba da bata wani jin komai, duk wani sayayyar haihuwa tare suke zuwa
saboda a hankali ciki ya sa Aunty zee É—in ta shigar da Afeefah cikin business É—in ta, wani
lokacin ta kan aike ta ita kaÉ—ai ma kasuwa wurin customers É—inta kuma ta zo ta raba wa clients
É—inta kayan, asusu Aunty zee ta yi mata ta kan ware ladar ta na kasuwanci ta saka mata ciki
duk da Afeefah ta nuna ita bata so, tufafi, karatu da kuma cima sau uku da ake bata ya wadatar
da ita. Amma Aunty zee ta nuna hakan shine adalci kuma ko nan gaba zata iya anfani da
kayanta idan buƙatar hakan ta taso.
A yau Aunty zee take cika wata tara da kwana tara kuma a ranar ta kwana da labour mai zafi,
hankali tashe da asuba suka tarkata asibiti har da kishiyarta da ta zo ta kwanan musu
kasancewar tun da abin ya fara mijin ya ƙirata, ta fi kowa shiga damuwa an ƙarbe ta zuwa ɗakin
haihuwa sai jiran abin da hali zai yi, duk Afeefah ta fi ruÉ—ewa babu abin da take tunawa vividly
sai irin wahalar nakudar da innarta tayi ƙarshe daga ita har babyn suka koma wannan abu ba
zata taɓa mantawa ba, duk kuma ta ga mai ciki sai hantar cikinta ya kaɗa a yanzu Allah kaɗai
ya san halin da take ciki na tsoro da fargaba duk adu'ar da ta zo Bakinta ita take yi.
Sai Azahar Allah ya taimakesu midwifes ɗin da suka karɓi haihuwar suka fito suna musu albishir
na ta samu 'yan biyu mace da namiji faɗin kalar murnar da suka yi ɓata baki ne. Karo na
barkatai kenan da Afeefah ta ke kai idanunta kan yaran hakwaranta duk waje, yaran gwanin
sha'awa kaman ta HaÉ—iye su, sam bata san Aunty zee ta farka ba sai ji ta yi tana furta
"Suna ba ki sha'awa ko Afeefah?"
Da sauri ta juyo tana dariya
"Sossai ma Aunty zee, sannu kin farka? Ya jikin?"
Ta É—an saki murmushi.
"Masha Allah, jiki Alhamdulillah"
Ta furta hawaye na gangaro mata Dukda tana sauƙa sai da ta ji ɗuminsu kan wannan
wahalallen baccin ya yi awon gaba da ita amma yanzu da ta farka sai take ganin kaman
mafarki, kaman ba'a gaske ba ita ce yau da shekaru arba'in da biyu a duniya kan Allah ya nufe
ta da ganin ƙwanta? Har biyu kyautar Allah? Bata san wani irin godiya za ta yiwa mahallicinta
ba don ko yau ta faÉ—i ta mutu ta san ta bar bayan da za su iya tunawa da ita su yi mata Adu'a,
bata san daaÉ—in haihuwar ya kai har haka ba a ganinsu da take kawai ji take kaman ta rabu da
baƙin ciki har abada matukar suna kusa da ita.
A hankali Afeefah take kokarin É—aukar su ta kaiwa uwar, daidai shigowan kishiyar Auntyn
"A'a Afeefah me haka? Sabbin haihuwan kike É—aga su anyhow? Wa kika tambaya da za ki É—aga
su?"
Yadda take maganan zaka zata wani gagarumin abu Afeefar ta aikata don har ta tsorata, da ta
kurawa matar idanu sai ta fahimci kaman akwai dalilin maganar nata amma bata wani mai da
hankali ba don Aunty zee ta amsa mata
"A'a hamdiyya ai Afeefah ba yarinya ba ce da zata kada yaran baki san ko yanzu ta yi aure zata
iya haihuwa ba? Getting to 18yrs ba wasa ba"
"kin ga Aunty sabbin haihuwa ne kuma ji da abin mu muke ko kuda bama so ya taɓa su bare
wasu da idonsu idon sabon jini su ke Sha'awa"
Da sauri Afeefah ta mayar da idanunta kan matar, Aunty zee ma ta É—ago ta kalleta
"Me kike nufi Hamdiyya?"
"Gaskiya nake faÉ—a Aunty, hanyar lafiya sai a bi ta da shekara ba za mu so farin cikinmu ya
koma baƙin ciki ba"
Hawaye ne ke kokarin zubowa Afeefah da jikinta yayi wani irin sanyi, bata ankara ba sai ji ta yi
Aunty zee ta É—ora mata yaran duk biyu a kan kafafunta
"Afeefah ga su nan ƙannenki ne, ki riƙe su yadda kike so"
Juyawa ta yi ga hamdiyya
"A kan Afeefah za mu iya samun matsala da ke, ba zan taɓa zuba ido ki tozarta ɗiyata a
gabana ba, kin ga yau na haife su ko? Kuma na san daaɗin su ko? To wallahi zan iya zaɓar
Afeefah sau dubu kan in zaɓe su sau ɗaya. Ki kiyaye kan mu yi uwar watsi da ke a kan 'yata"
"Aunty ni kike yi wa gori a kan wannan mayyar?"
Ko kan Aunty zee ta yi magana Uncle ya shigo, kafin ya tambayi me ya faru Hamdiyya ta fashe
da kuka mai ƙarfi tana yunƙurin fita, da sauri uncle ya tare ta don shi mutum ne da baya son
abin da zai kawo mishi matsala da iyalanshi, yayi kokari ƙwarai wurin haɗe kawunansu ba zai
so ko ma menene ya raba su ba, ban da ma yanzu da suka soma tara zuri'a suke kuma cikin
farin ciki tsantsa.
"Me ya faru hamdiyya? Zainab me ya haÉ—a ku?"
Aunty zee dai komawa ta yi ta zauna sai hamdiyya ce ta kara karfin kukanta
"Ka yi haƙuri ni ce da laifi na zaci da ni da Aunty duk ɗaya mu ke kuma 'ya'yanta za su iya zama
nawa amma ashe na yi kuskure, in shaa Allah ba zan sake ba"
"Zainab!"
Uncle ya furta sunan cikin rashin jin daaÉ—i
"Gori kika yi mata?"
"Amma dai ka fi kowa sanin hali na Usman, ban yi mata gori ba kuma ba zan taɓa yi mata ba
don nima babu wayo na bare dabara ta Allah ya ba ni, abin da take shirin shigowa da shi ne ba
zan lamunta ba sam"
Hannunshi dake cikin nata hamdiyya ta janye
"jita-jita bai taɓa wanzuwa ba matukar babu kamshin gaskiya, an sha tare ni ana gargadina a
kan Afeefah amma na ɗauke kai saboda ganin yadda Aunty zee ke ƙaunarta, abin da nake
tsoro an ce suna kaunar sababbin jini to don na ce Afeefar ta yi haƙuri da daukar su har su yi
kwari shikenan na yi laifi...? Ku yi haƙuri bari na je gida"
Tana kai nan ta fice uncle bai ce komai ba don shima karo na ba adadi an tare shi an faÉ—a mishi
abubuwa dayawa kan Afeefah amma baya bari ya shige shi, sai dai kuma bai ji daaÉ—in reaction
na zainab ba da sai a bi abin a hankali tunda dai already akwai maganganu kan Afeefar.
"Amma ba ki kyauta ba zainab, na sani kina kaunar Afeefah kasancewar ta marainiya kuma
abin tausayi amma kuma sai ki duba kokarin hamdiyya wurin ganin ta bai wa jininki kariya, tun
fa jiya tana tare da ke ko runtsawa bata yi ba, ko da kika sauka kika fara bacci haka ta koma
gida ta dafo miki ruwan zafi ta biya ta sayo kayan tea saboda kar ki tashi da yunwa babu
abunda zai taimaka miki, ai gyara kayanka baya zama sauƙe mu raba"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Idanunta ta mayar kan Afeefah dake hawaye sossai, rabon da taji raÉ—aÉ—in zuciya tun ranar da
uncle ya amince ta zauna da su sai yau.
Yanzu ko da tana cin naman mutum wani bala'in ne da rashin tausayi haÉ—e da rashin imani zai
sa ta ci naman waennan talikan da isowarsu duniya kenan? Me zai sa ta cutar da 'ya'yan wacce
ta rungumeta ta cicciɓota ta zaro ta daga cikin bala'i da ƙuncin rayuwa?
"Afeefah..."
Auntyn ta ƙira sunanta a hankali sai kuma ta kasa magana duk suka yi shiru tsawon lokaci kan
nurses suka shigo, hakan ya tilastawa Afeefah barin É—akin kai tsaye fita tayi daga asibiti ta tsare
abin hawa ta faÉ—a mishi inda za ta, gidan Hamdiyya ta nufa don ta tabbatar a chan za ta samu
Uncle usman da ma ita karan kanta hamdiyyar.
Hasashenta ya tabbata don kuwa ta same shi tare da hamdiyyar yana ta kokarin bata baki tana
tuburewa, maganganu take gayamishi cikin ɗaci da nuna kaman shi ne ai ya zaɓi ya ba
Zainabun ciki har ta haifi 'yan biyu tana mata gori.
"Haba hamdiyya kema kin san da mutum shi ke ba kanshi haihuwa da yanzu mun tara yaran da
bakya zato saboda Zainab macece mai kaunar yara, tun aurenmu na shekara duk inda taji
magani muddin bai saba shari'a ba nema take amma da Allah bai turo ba ba gashi yanzu ta
haihun ba? Ba'a cire rai daga rahamar ubangiji kema kuma ya san dalilin da ya jinkirta naki
namu Adu'a ne kawai da neman zabin alkhairi daga rabbissamawati".
"A'a Usman ai ka fi ƙaunar Zainabun idan da Zainabun ta haihu tun farkon aurenku da baka
auro ni ba, silar rashin haihuwar ne ta saka ka kara aure ba don kana so na ba kuma ta haihun
ai..."
sallamar ta ya katse musu maganar duk suka mayar da hankali kanta.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*006*
"Uncle, Aunty hamdiyya don Allah ku yi haƙuri, ban zo da niyyar wargaza zaman ku ba, na sani
Auntyna ta faɗa miki magana ne saboda irin ƙaunar da take mini amma ni na san gaskiya kika
faÉ—a, don Allah ki koma asibitin ki cigaba da kula da ita da jariran ni zan koma gida zan cigaba
da jira har lokacin da ya kamata a ce na É—auke su É—in"
Cikin wani kalar sanyin murya take maganan, idanunta har lokacin ba su daina zubar da
hawaye ba. Uncle ɗin tausayinta ya ji yayinda hamdiyya ta taɓe baki ta ce
"Toh ai shikenan, ni ba na yi magana ba ne da wata manufa kawai dai ina kare yaran da yanzu
ne muka fara morewa wanzuwar su ba za mu juri dare É—aya a yi abincin meeting da su ba"
Uncle ne ya katse ta
"ya isa haka, ki tashi ki koma asibitin. Afeefah tashi mu je in sauƙe ki a babur na"
Miƙewa ta yi suka fice daga gidan, har suka iso gidan Auntyn nata magana bai haɗa su ba ta
sauƙa ta shige yayinda ya juya ya koma asibitin.
Bata bari abin ya cigaba da damunta ba ta kintsa gidan tamkar Auntyn na nan ta É—ora girki
marar nauyi ta ci ta zuba saura a kula kan ta É—an kwanta bacci, har ga Allah ta tsame kanta ne
saboda gudun abin da zai je ya dawo sam ba zata so wani ya yi kuka sanadin ta ba bare
Auntyn ta don haka tana ganin shawarar da ta yanke shine daidai
Sai da Aunty zee ta kara kwana biyu a asibiti saboda postpartum ciwon ciki da ya matsa mata
amma duk da haka sai damun uncle usman take akan maganan Afeefar har fushi ta yi ta matsa
a sallame ta saboda tunanin ta kar Afeefar ta ji an ware ta ko ta sanyawa kanta damuwa, duk
da sun shirya da hamdiyya sai dai har aka yi sallamar hirar arziki bai haɗa su ba don ta matuƙar
jin zafin abin da ta yiwa Afeefar.
Tana sanya kai cikin gidan ta soma kiran
"Afeefah! Afeefah!!"
Da gudu Afeefah da ke zaune a parlor tana kallo ta fito ta rungumeta tana murmushin ganinta,
Auntyn ta É—ago fuskarta sai ta sauke ajiyar zuciya
"Afeefah ni kika yasar a asibiti ko?"
"A'a Aunty ban isa yasar da ke ba wallahi, na bari ne Aunty hamdiyya ta kula da ku ni kuma sai
in kula da gida ba gashi ba gidan ma ya ji daaÉ—i, da missing É—in mu da zai yi sai yayi mishi
yawa"
Dariya Aunty zee ta yi tana girgiza kai, a parlor suka ya da masauki kan a natsa ma maƙota da
abokan arziki an fara shigowa barka tuni gidan ya soma É—inkewa da jama'a nan Afeefah ta
shiga jeka ka dawo.
Zamanta da hamdiyya na kwanaki shidda ba karamin wahala ta sha ba ta kuma danne
zuciyarta, ko Aunty bata bari ta san hamdiyyar tana matukar musguna mata ba ta yadda ko
satan kallon yaran ta yi sai ta yaɓa mata baƙar magana, har tsoron kallonsu take Dukda tana jin
son su tamkar jini da tsokarta ta sha ɓuya tayi kuka sossai na mummunar shaidar da take dashi
don bata tsira ba ranar suna har nuna ta hamdiyya ta saka ake yi saboda kananun maganganu
duk Aunty bata sani ba.
Auntyn Ta yi matuƙar kyau cikin milk leshin ta yayinda yaran suke sanye cikin kyawawan
tufafinsu pink da blue, Afeefah ma cikin leshin da Auntyn ta yi mata musamman na suna
maroon ta shirya ta yi mugun kyau Aunty zee har ajiye ta tayi ta zana mata liner a baki ta saka
ta saka kwalli ta shafa mata powder sai tayi kaman ka sace ta ka gudu, masu hidima da kitchen
ita suke kira tana miƙawa mutane abinci daidai ta zo miƙawa wasu mata kenan da yake ta
bayansu ta zo ta ji É—ayar tana cewa
"Ni kam dai ina tausayawa Zainabu saboda fa da gaske yarinyar da take riƙo rikakkiyar Mayya
ce kuma fa an ce Mayu sun fi zaluntar wanda ya ji tausayin su"
ÆŠayar ta ce
"Ni fa ban san yarinyar ba amma kuma ina da labarin tun tana ciki take cin maita, uban ta ma
bai tsira ba haka uwar da ta haife ta, aiko Allah raba mu da irin wannan iri. Haihuwa bata yi rana
ba"
Wani irin abu mai nauyi ne ya taso ya tsayawa Afeefah a kirji tana ji na ukunsu na furta
"za ki gane ta mana wata baƙa marar kiba ta saka leshi maroon, ai daga kallon idanunta da
suke manya kaman kwai kin san za'a ga kurwa da kyau... Allah dai ya hana farin ciki komawa
baƙin ciki"
Gabansu ta zagayo suka É—an sha jinin jikinsu ganin fuskarta babu É—igon walwala idanunta da
suka surke zuwa ja ta É—an zuba musu kan ta ajiye abincin ta juya ta bar wurin.
A karshe dai ba'a tashi suna lafiya ba don wata wai aljannunta sun tashi ai sai ta kashe Afeefah
Mayya ce! nan fa gidan suna ya kachame dayawa suka shiga kururuwa su ma, da ƙyar aka fita
da ita a gidan zuwa maƙota ban da kuka babu abin da take, bata san wani irin tunani zata yi ba
duk ta ji kaman ta sallamarwa duniya farin ciki da rayuwarta sai ta tuna Aunty zee da ta yarda
da ita take kuma bata kariya don yanzu ma ita ce ta nuna jan ido ta sallami kowa da abin da
za'a yi sai ya fi haka, chan kuryar maƙociyarsu ta takure tana kuka sossai bata ji Shigowar
Aunty zee ba amma ta ji hannu ya taɓa ta firgita ta yi ta miƙe tsaye tana girgiza kai
"Wallahi ni ba Mayya ba ce! Ban san ya ake yi ba don Allah ku yi haƙuri ban taɓa cin naman
mutum ba wallahi..!"
A rikice take maimaitawa da sauri Aunty zee ta rungumeta tana hawayen tausayinta
"Ya isa Afeefah! Ni ce! Auntynki ce, na sani wallahi na sani ke ba Mayya ba ce na yarda da ke"
Kuka kawai ta saki mai tsuma zuciya tana yin luff a jikin Aunty zee É—in.
Jiki a sanyaye duk suka dawo gidan, yayinda abin da ya faru a sunan ya tsayawa Afeefar ta
yadda ko kuzarin taɓa yaran bata da shi, tsoro take ji kar ta taɓa su abu ya faru haka Aunty zee
ta sa uncle usman a gaba tana kuka sossai
"Duk laifin matar ka ne usman da bata fara ba da hakan bai faru ba, yaran nan fa kannen
Afeefah ne amma ka ga yadda take baya baya da su ko taɓa su sai na yi da gaske take yi!
Haba mana ko bata duba komai ba ta duba maraicinta mana wallahi ta É—auki alhakinta dayawa
kuma ni kam ta daina burgeni sam"
Shiru yayi chan ya ce
"Ki yi haƙuri zan yi mata magana, amma ki dinga dubawa itama hamdiyyar ba don tsanar
Afeefah bane ya sa take hakan saboda kare yaran nan ne ganin tsawon lokacin da muka É—auka
kafin Allah ya ba mu"
"Wallahi na fi ƙaunarta a kan su, ta cigaba da rayuwa da wannan tsangwamar rayuwarta na
cikin haɗari don Allah zan roƙe ka Alfarma don girman Allah kar ka chanza mata kaman yadda
ka fara mata, ka dubi maraicinta ka riƙe ta kamar yadda za ka riƙe suhail da suhaila".
Hannayenta duk biyu ya riƙe
"Ban tsani Afeefah ba Zainabu, in shaa Allahu kuma zan cigaba da iya ƙoƙarina a kanta"
"na gode sossai Baban 'yan biyu"
Ya saki murmushi ita ma ta mayar masa.
Duk su biyun sun mayar da hankali kanta ta yadda hatta shi uncle É—in kan ja Afeefar jiki ko ma
ya bata babies ɗin da take matukar so ta riƙe, yau satinsu na biyu kenan a duniya.
Tsaki Aunty zee ta É—an ja kaÉ—an karo na ba adadi hakan ya saka Afeefah dake jijjiga suhaila
yayinda Auntyn ke ba Suhail Mama ta kalleta ganin tana ta yamutsa fuska ya saka Afeefar
katse shirun nasu
"Aunty lafiya kuwa?"
Ta sake jan wani tsakin karo na barkatai kan ta furta
"Wlh Afeefah ciwon ciki ne ke É—an matsa min tun haihuwar nan kullum sai na yi shi kaman
ƙa'ida"
"Sannu Allah ya ba ki lafiya, babu maganin da suka ba ki a asibiti?"
"Akwai fa ina sha amma kaman bana sha"
"Sannu"
Haka tayi ta jera mata duk ta saka kanta a damuwa domin sam bata so taji wani na ciwo a
gidan sai gabanta yayi ta faɗuwa fargaba ya bi ya rufeta har sai an furta mata yayi sauƙi.
Shigowar Uncle da karbar babyn da yayi daga hannunta ya sa ta yi musu sai da safe ta shige ta
bar su nan parlor.
Chan cikin dare sai ta ji kaman ana motsi da ƙarfi, sai kuma ta ji bugun kofar ɗakinta a razane ta
farka tana salati jin Muryar uncle ya sa ta dirko da hanzari ta zo ta buÉ—e kofar
"Afeefah ki zauna da yaran nan idan sun yi kuka ki ba su madara zan kai Auntynki asibiti ciwon
ciki ya tasar mata sossai"
Tuni ta rikice hawaye har sun fara zarya a idanunta.
"Toh uncle"
Ta faɗa tana bin bayanshi, shi ya riƙo Aunty zee da ke tafiya da kyar Afeefah na ta bin su tana
share hawaye har zuwa kan babur ya hau ta kwanta jikinshi suka fice tana ta jera mata sannu
da Allah ya bata lafiya. sai da taje ta rufe kofa kan ta dawo kan yaran ta zabga tagumi cike da
damuwar ciwon Auntyn.
Yaran sam ba su da rikici daman, tun tana tagumi har bacci ya sure ta a kansu ƙiran Sallar
farko da kukan suhaila su ne suka farkar da ita, ta tashi ta haÉ—a musu NAN1 É—in su da ake basu
saboda abinci ya ishe su, ba zallar nono Auntyn ke ba su ba, sai da ta saisaita ya zama da dumi
cikin tsafta ta fara ba su don suhailar na koshi sai suhail ma ya tashi bayan ta gama ta fice taje
tayi alwala ta zo ta fara sallah sai da ta idar tayi Adu'a ciki har da roƙon Allah ya ba Auntynta
lafiya kan ta miƙe ta bar sallayar zuwa tsakar gida.
ƙoƙarin ɗora musu breakfast ta fara a natse take aikin Dukda hankalinta rabi na ga su Uncle da
suke asibiti rabi na ga 'yan biyu kar su farka bata ji kukansu ba har ta gama haÉ—a abinda zata
buƙata ta ɗora kan ta shiga sharar tsakar gidan.
Ta gama haɗawa tana ƙoƙarin kwashewa kenan ta ji ana bubbuga kofa ba irin bugun hankali
ba, jikin kofar ta isa sai ta ji kaman surutai dai ba na mutum É—aya ba, bata buÉ—e ba ta shiga
tambayar waye ne?
"Ki buÉ—e mana ai za ki gani!"
Muryar hamdiyya da ta ji ya sa ta buÉ—e kofar sai dai me za ta gani...!
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Jama'a kuna manta cewa na rubuta True life story a jikin labarin nan, Meyasa na yi kyauta ne
kam? Saboda ina so mu ƙaru da ilimin dake ciki, na tabbatar daga page 1 zuwa yanzu kun
zaƙulo darusa masu dumbin yawa kuma ko ban kawo gyara ciki ba kun san amsar hakan.
Wallahil azeem ban ƙara komai a labarin Afeefah ba, ban ce babu ƙari ba akwai amma sai a
gaba yanzu duk abinda kuka gani a gaske ne ban chanza komai ba, please bear with meðŸ™*
*007*
Wasu gungun matasa ne ɗauke da makamai suna ƙoƙarin Hankaɗa hamdiyya su rufta mata ai
da wani irin hanzari ta mayar da kofar ta rufe jikinta na wani irin É—aukar tsuma, hankalinta sai ta
ji yayi wani irin tashi tsoro da fargaba suka rufe ta, ko kafafunta ta kasa motsa su daga inda
take tsaye... Ƙuuuuu haka cikinta yayi wani irin ƙara a sadda ta ji kukan uncle haɗi da
maganarshi daga bakin kofan
"Ki buÉ—e ki ba ni yarana...! Kin riga kin cuce ni kin raba ni da uwarsu rabuwa ta har Abada a
yanzu ba zan iya sake É—aukar raba ni da su ba, in kuma su ma kin cinye kurwarsu ne kaman
uwarsu nima duk ki haÉ—a da ni ki cinye Afeefah..."
Sossai yake gunji daga jin muryarshi zaka san baya cikin hayyacinshi ne.
Tsurewa ta yi tana jin kaman ta zauce ko kunnuwanta ba sa ji da kyau. Tamkar sauƙar aradu ta
ji wani da kaman yanzu ya iso a gigice yana furta
"Da gaske ne Usman Zainabu ta rasu?"
'Zainabu ta rasu!'
Ko kan kalaman su gama shiga kwakwalwanta sai ji tayi uncle na amsawa
"Zainabu ta tafi ta bar ni. Sai da aka gargaɗe ni amma na ƙi saurara saboda ta ba ni yaƙini a
kan yarinyar, ashe ba haka ba ne kai duniya...! Ashe wanda ya maka rana za ka iya masa
dare? Afeefah ta yi mana shigo shigo ba zurfi, lafiya ƙalau muka kwanta da zainabu daga ciwon
ciki farar É—aya muna zuwa asibiti sai ga kiran hamdiyya take sanar min ta yi mummunar mafarki
a kan zainabu, sai na sanar mata muna asibiti bata da lafiya ta tsorata tace gata nan zuwa
Dukda dare ne haka ta bi gidan wani malami ta taho da shi akan mafarkinta mai muni ne
Afeefah ta gama cinye kayan cikin zainabu ashe da gaske ne! Duk irin taimakon da malamin
nan ya so bata ya gaza haka likitoci suna gani ta ce ga garin ku..."
Hamdiyya ta chafe cikin kuka
"in ba aikin maita ba menene wannan? an riga an cinye mata kurwa, sai da na faÉ—a wlh sai da
na gargadi Aunty akan mayyar yarinyar nan.."
Gayyar mutane bayan waenda hamdiyyar ta zo da su suka sake cigaba da taruwa suna
hayaniya akan tabbas ita ce mayyar ai dama daga Dutsen-wai ma gudu wa ta yi saboda
yunkurin kashe ta da Ƴan uwan wadda ta kashe last suke kawai a kasheta.
Ƙafafunta sai suka gaza ɗaukarta, ta zube yaraf a ƙasa, hawayen da suke zuba tuntuni sai suka
ƙafe kamar rijiyar da aka yi wa yaso. Zuciyarta na raya mata cewa da gaske ita ɗin annoba ce,
da gaske ita É—in mayya ce.
Tana ji jama'a na maimaita lafiya ƙalau ta kwanta ciwon ciki ya turniƙe ta cikin dare daga isa
asibitin su sai mutuwa. Hujjar da suka kafa kenan suna ƙara tunzura shi wasu na ta faɗan
abubuwan da ita karan kanta da ake yi wa ƙagen bata san yaushe aka yi ba, ina ma da bata
biyo Aunty zee ba? Ina ma da bata zo ba! Ina ma da bata biyo ta ba!
Da gudu ta miƙe tana komawa cikin ɗaki gunjin wahalallen kukan da ta fashe da shi haɗe da
ƙara na bala'i na cika ilahirin gidan ba wai don gudun rayuwarta da mijin antinta ke ta iƙirarin ita
ma sai an kasheta ta bi matarsa ba sai don rungumar mutuwar a karan kanta, tana so a yau ta
kawo karshen komai tana so tayi mai gabaÉ—aya da rayuwarta wai haihuwa da hanji... bayi ta
shige kai tsaye babu wani tunani ko shawara ta zaro piya-piya da su ke ajiyewa saboda sauro
ta buɗe tare da kafa bakinta a kai tana kuka me tsanani da dugunzuma zuciya, ƙwatt! ƙwatt!!
ƙwatt!!! haka maƙogoronta ke ba da sauti a sadda ta ke haɗiyewa tana jin ta yi sallama da
rayuwa kaman yadda mamanta, babanta, kakar ta, innarta da ma Aunty zee suka yi.
Lallai an yi mata mummunan zato da ba za ta taɓa wankuwa ba a duniya, ta gaza! Ta kasa
rayuwa kaman kowa, a yanzu wa zai dauke ta kuma? Wa zai yarda wani nasa ya aure ta ko ya
raɓe ta? Mutuwa ita ce abu mafi sauƙi a gare ta kaman yadda ta yankewa kanta.
Kururuwa da take ji a nesa bai sa ta sauƙe kwalbar fiya-fiyan ba sai da ta ji an yi wani irin wurgi
da kwalbar ya tafi ƙasa yana tarwatsewa kwatankwacin yadda rayuwarta ta tarwatse. Dishi
Dishi take gani jiri ya diɓeta sai taji an tare ta sun tafi a tare suuuuu ƙasa.
***
A kafa su ke takawa sanye cikin uniform kasancewar assignment da aka ba su a
cikin Anchau sun gama shi kuma a lokacin ne suke shirin barin garin zuwa cikin
Kaduna, Zaratan matasa ne biyu sanye da khakin Sojoji daga yanayin tafiya da
tsarin zubin halittarsu zai tabbatar maka da waennan ɗin ko a cikin Sojoji zaƙaƙuran
ne, da wani irin ginshira suke tafiyan kowannensu na da kalar nashi kyaun, haiba da
tarin kwarjini abin da ya bambamta uniform É—in nasu abu É—aya ne, shi wadda ya fi
cin maganin fuskan nan tamau daga damtsen hannunshi akwai wani farin bandage
da aka zagaye ƙarshen uniform ɗin dashi a jiki akwai zanen plus ➕ Da jan tawada
wadda zai tabbatar maka da wannan É—in Medical soldier ne.
"Ko wanchan taron na me?"
Na gefen da bai kai haske da wani irin ƙasaitar wanchan ɗin ba ya faɗa cikin natsuwa.
A sace ya É—an kalli wurin ya watsar kaman ba zai yi magana ba cikin halinshi na i don't care ya
furta
"How would I know Saleem after all tare mu ke da kai?"
Wadda aka ƙira da Saleem ya sake kallon taron a lokacin da suka tunkaro su sossai
"Ko ma menene Rayyan ba na tunanin lafiya..."
Ko ya tanka sai ma kanshi da ya mayar ƙasa yana ci gaba da takunshi cikin ƙasaita da isa
kaman yadda yake a halittarsa.
Ihu da ƙarar da ya ratsa kunnuwansu haɗe da furta kalaman
"sai mun kasheta yau za mu ga karshen maita"
Da jama'ar wurin suke ta furta wa wasu ma É—auke da makamai ya sa Saleem taka birki yana
riƙo hannun Rayyan da yayi kaman bai ji ba.
"Guy akwai matsala, we cannot neglet our duty ba za mu ga ana shirin ɓarna mu kama hanya
mu wuce ba"
Ko ya tanka sai birkitattun idanunsa da ya kai wurin yana nazarin situation É—in fuskar nan babu
walwala ko na miskala zarratin.
Bai yi magana ba har Saleem ya isa ga mutanen, yana tsaye daga gefe da farko jama'ar sun so
yin gardama amma jin ya kira akan a turo squad kuma ya zaro bindiga ya sa aka fara watsewa
uncle da hamdiyya dai sai kuka da Allah ya isa suke yi, a mayar da maganan da ake ne ya ji
abin da ke faruwa.
"Wait here!"
Ya faÉ—awa Saleem kan ya haye katangar gidan da ba shi da wani tsawo chan chan, bai buÉ—e
kofan ba sai yayi cikin gidan yana dube dube, motsi da Sheshekar da ya ji ne ya saka shi kai
kyawawan idanunshi wurin sai suka sauƙa kan kwalbar fiya-fiya a take warin ya shige cikin
hancin shi da wani kalar hanzari ya fusgo madarar ruwa da ya gani nan cikin É—akin Auntyn
kasancewar ta mai jego ya fasa guda biyu ya isa gabanta ya sanya hannu yayi wani irin wurgi
da kwalbar ya haÉ—e da gini ya tarwatse...
Sulalewa take ƙoƙarin yi a lokacin da ya ɗago madarar yana shirin bata, bashi da zaɓin da ya
wuce ya sanya hannunshi ɗaya ya tareta suka kai ƙasa ita tana ƙoƙarin sumewa shi kuwa ya
sauƙa a kan gwiwowinshi, kanta ya ɗago da take ta kokawar numfashi ya kafa madarar tare da
matse hancinta sai da ta kwankwadi mai yawan gaske kan ta sake yunkurowa tayi gaba wani
kalar amai na kwace mata, tana gamawa ya sake dura mata É—ayar ta sake kwarara wani aman
ko idanunta bata iya buÉ—ewa alamu sun nuna ta jima da ficewa hayyacinta haka ya sanya
hannu ya É—auko ta zuwa waje, Fitowar shi da isowar motar Sojoji lokaci guda sai ciki aka sanya
ta ya shiga tare da barin Saleem wurin suka fice a guje kaman yadda suka saba.
Da gudu Uncle da hamdiyya suka shiga suka É—auko yaran da ke ta kuka suna rurrungumesu a
lokaci É—aya suna ta tsinewa Afeefah, Saleem dake tsaye ya iso gangar uncle É—in
"A komai ya kamata ku dinga adalci da tunani, ƙage ko sharri ba abu bane mai kyau shin kun
taɓa jin maita ko a addini? Ko kun taɓa ganinta ta yi maitar?"
"Wallahi billahi na rantse da Allah idona idon Afeefah sai na sa an kasheta gwara ku gaya mata
tun daga inda ta tafi ta san inda dare ya mata, sam Shigowar ta rayuwarmu bai mana rana ba"
Hamdiyya ta karɓi zancen
"ba kai kaÉ—ai ba ai gwara mata mutuwar ta da dawowa unguwar nan tsinanniya"
Juyawa kawai Saleem yayi ya bar gidan suna ta zaginta da kwashe mata albarka wasu mata na
shigowa ana ta kokarin mayar da magana ai dama an gargadesu.
BAYAN WASU AWANNI
A hankali ta shiga ƙoƙarin buɗe idanunta da suka matuƙar yi mata nauyi tana jin yadda kanta
yake wani sarawa, a tunanin ta za ta tsinci kanta cikin ƙabari ne kaman yadda ta jima da
sallamar da rayuwarta wa mutuwa sai kuma ta ga akasin hakan. Idan ma tunanin ta ya bata
daidai kaman nan ɗin ɗakin asibiti ne take ciki duba da yanayin tsarin ɗakin da kuma ƙarin
ruwan da ke shiga jikinta ta canular dake É—aure a hannunta. Tunanin dalilin mutuwar tata ne ya
bijiro mata kaman ana haska mata majigin rayuwarta...
"Aunty zee ta rasu" Daram! Haka zuciyarta ya buga zuruf ta miƙe zaune kaman ba jiri ne ke
walagigi da rayuwarta ba, hannayenta ta sa duk biyu ta toshe dukka kunnuwanta don ji take
kaman ana maimaita mata kalaman na rasuwar Aunty zee da speakern da ya fi komai ƙara a
duniya. Tamkar zautacciya haka ta saki wani irin ƙara da ya shigo da nurses har uku ɗakin da
gudu da ma an ba su aikin kula da ita kar ta farka ta sake yunkurin cutar da rayuwarta.
Shigowar su da fara fusge-fusgenta kusan lokaci guda rirriƙeta suke kokarin yi amma kaman
mai tashin aljannu sai wani irin ihu take mai tafe da gunjin kuka mai taɓa zuciyar mai saurare
don kowa ya ji kukan ya san ba na wasa bane
"Ku barni na mutu! Don Allah ku bar ni na mutu ba zan iya rayuwa ba! Ku sakeni....! Ku sake ni
na ce!"
Duk ta haukace kuma yawan su bai sa sun iya natsar da ita ba..
"Will you shut up and stay still?? Giyar wake kika sha ne?? Hauka kike yi ne??"
Kalaman suka fito cikin wani irin amo da ya amsa duka É—akin...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*008*
"Karen hauka ne ya cije ki? Ko stupid lunatic brain naki hauka yake karanto miki?? Are you
stupid?? Ki kashe kan naki oya take this..."
Muryarshi mai cike da fushi haɗe da zafi ya cigaba da sauƙa wane aradu bisa kan su ba ita
kaÉ—ai ba hatta nurses da suka san shi sai da suka sha jinin jikinsu a take, wani irin shiru ne ya
ratsa ɗakin kan takun sawayenshi suka amsa ya isa ganganta riƙe da scapel (aska irin ta
likitoci) ya damƙa mata a hannu ya fusgo ɗayan da karfi har canular ɗinta na fita daidai jijiyar
Wrist É—inta ya sa yatsarshi babba.
"Nan! Nan kawai za ki katse ki mutu idan sha'awar wutan Jahannama ne yake É—ibarki, ba
mutuwa kike ƙaunar yi kafura ki tabbata cikin azabar Allah ba? Oya yanke mana!!!"
A zaune take amma sai da tayi wani tsallen tsoro saboda tsawar da ya daka mata sai da ya
kaÉ—a 'yar hanjin ta.
"Haba Rayyan, yarinya ce don Allah ka bita a hankali mana ka ga yadda duk ka firgitata?"
A zafafe yace
"Za ta ci kashi ne salim? Muddin ba za ta ci kashi ba to tabbas babu zancen yaranta a lamarin
ta sai tsagwaron iskanci da ƙarancin ilimin addini... Tana tunanin da kashe kai shi ne hukunci
mafi sauƙi ga bawa a duk sadda ƙaddara ta ruro wutarta za ta samu miliyoyin mutane a raye
ne?"
Ita dai bata san a wace duniyar take ba don tsabar yadda take kaÉ—uwa bata sani ba a farke take
ko a sume ya juyo da figitattun idanunsa da basu yi mata kala da na mutane ba ya zura mata
"To bari ki ji, idan ma ba ki sani ba ki sani idan ma kin sani danne sanin kika yi to gidahumar
kwakwalwarki ta tuna kuma ta yi hadda wutar Allah ya fi gaban wasa, kar ki zaci wannan wuta
da kuke girki da shi duk zafi da raÉ—aÉ—in na wannan duniyar, duk irin hatsarinshi da in ya É—an
taɓa ki za ki ihu sai da aka wanke shi sau dubu saba'in kan aka jefo mana"
Kanshi ya dafa yana wani jan tsaki mai tsawo saboda rabon da yayi magana haka ya manta,
amma dole ya ƙarasa don zuciyarshi a tunzure take ji yake kaman ya faffalla mata maruka wa
ta fi shiga cikin damuwa da zata kashe kanta?
"Tabbas duk wanda yana musulmi ya kashe kanshi da gangan ya fita daga musulunci kuma zai
mutu ya kuma tashi ranar gobe a kafiri... Ƙarbar kaddara mai kyau ko marar kyau na ɗaya daga
biyar É—in cikacikan musulunci. Ki yi gaggawar tuba domin a yanzu haka kin nunawa ubangiji ba
ki da cikakkiyar imani ki kuma gode Allah we were there on time Nonsense…!
Wani irin rawa da jikinta yake ya sa tuni askar ya zame ya faɗi ƙasa yana ba da sautin
kwankwataraaaan, yadda kalamanshi suke fita a hautsine cike da zafi da É—aci mai tarin zallar
gaskiya haka su ke hautsina mata 'yar hanji suna kaÉ—a hantarta kuma suna shiganta ba da
wasa ba.
Tun da idanunta suka sauƙa cikin nashi a karon farko ta yi saurin sadda nata ƙasa don ba za ta
iya ko da gangancin jurar ganin cikinsu ba, ganin tana shirin zubewa a sume ya sa salim damke
hannun Rayyan da har kaman zai rufeta da duka at any moment ya ce
"Calm down please dude"
Ya maimaita kusan sau uku don ya san hayaƙin kan rayyan ba kowa ne ke iyawa dashi ba,
hatta shi karan kanshi wani lokacin shakkar shi yake saboda wani irin kwarjini da Allah ya zuba
masa na ban mamaki, bare wannan yarinya da rubdugun rayuwa yayi mata ƙatutu.
"Sister ku taimaka mata ko da allurar bacci ne samu ta huta ta kuma samu natsuwa please"
Salim ɗin yayi directing kalaman to nurses ɗin, da sauri suka shiga ƙoƙarin aiwatarwa don babu
wadda bai san Zafin kan Surgeon General Ryan Moh'd Khamis ba, a lokacin da suka roƙi ta
kwanta ko uhmm bata yi ba ta miƙe flat zuciyarta har a lokacin tana jin shi a tsaye kyamm
tsabar tsoro.
Jan Rayyan da ke tsaye ya zubawa gini idanu yayi suka fice, haÉ—adÉ—en office ne mai cike da
ƙawa tamkar ba asibiti ba suka shiga, fasalta kyau da tsaruwar office ɗin bata lokaci ne sai wani
masifaffen ƙamshi yake fitarwa tare da sanyin Ac mai ratsa jiki. A doguwar kujera Brown mai cin
mutum uku salim ya mishi masauki, ya nufi chan dungu wurin wani tsararren frigde ya buÉ—e ya
ɗauko mishi ruwa masu sanyi ya taho ya miƙa mishi bayan ya ɓalle murfin ba tare da yayi
magana ba ya karɓa kaman faɗa ya kafa kai, sai da ya shanye tasss kan yayi wurgi da goran
"I need some space Salim"
Maganan ya fito daga chan ƙasan maƙogoronshi in ba ma salim ɗin hankalinshi na kanshi ba ba
zai taɓa cewa shine yayi maganan ba, dama kuma ya san za'a yi hakan dole ya fice ya barshi
nan yana zamewa kwance cikin kujerar Dukda tsawon shi ya zartawa kujeran nesa ba kusa ba.
Salim na fita É—akin ya koma ya janyo kujera ya zauna tare da tsura mata idanu, duk da ba zai
ƙira ta kyakyawa ajin farko ba sai dai tana da nata qualities ɗin na daban da ba kowa ke da shi
ba kuma da matuƙar wuya a same su wurin wata macen, baƙa ce amma baƙin mai haske tana
da doguwar tsiririn fuska da dogon hanci duk da idanunta ya musu kallo ne na tausayi don a
rine suke a kuma firgice zai iya ƙiransu manya kuma farare, girarta kaman ita ta zana yanayin
tsawon gashin idanunta da ma masu sheƙi irin na baƙaken Fulani dake kwance lublub bisa
goshinta za su tabbatar maka da cewa tana da tarin suman kai, bakinta kalar peach da ya ƙara
haskaka kalar skin É—inta ya amshi fuskartata.
Ta yi mishi yarinya kwarai da tunanin kisan kai, kuma ya tabbatar duk abin da zai saka mutum
tunanin kashe kan shi ba ƙarami ba, ba zai ce ga iya adadin lokutan da ya ɗauka yana
gwamutsa biyar da goma ba a kan matsalar yarinyar sai motsin ta ya ji, da É—an hanzari ya
mayar da hankalinshi kanta don dama tuntuni kallonshi na a gareta.
"Sannu 'yanmata kin farka?"
Tsura mishi idanu ta yi tana tariyo abin da ya faru a É—azu da sauri ta shiga dube dube tana jin
gudun zuciyarta na wani irin ƙaruwa ganin firgici a idanunta ya sa ya miƙe ya isa gangarta yana
furta
"Natsu 'yanmata dodon ɗazu ba ya nan, da ma matuƙar wuya ki sake ganinshi a gangarki."
Numfashi mai nauyi ta sauƙe duk da tarin tsoron da take ciki hakan bai hana kalamanshi na
ɗazu na sake bijiro mata ba, wani irin sanyin jiki da tsoron Allah na lulluɓeta a take ta fara tuba
hawayenta na ɓallewa take furta
"Allah na tuba ya Allah! Wallahi na yi nadama Allah na san kana sane dani da kuma halin da
nake ciki ya Allah ka sassauta min, Allah ka ba ni ikon ƙarbar kaddara ta a yadda ta zo min
Allah ka yafe min..."
Sossai take kuka har tana shiÉ—ewa, bai hana ta ba ya barta tayi kukan sossai har tana ajiyar
zuciya kan ya ɗauki ruwa ya miƙa mata, sai da ta jima tana kallon hannun nashi kan ta sanya
hannu ta karɓa ta sha sossai kan ta sauƙar tare da gintsewa cikin hannunta tana sauƙe
numfashi ta sake ƙura wa bango idanu.
"Ya Sunanki?"
Ta ji tambayar ya zo mata, kallonshi ta yi yana da tausayi haka yana da sanyin hali duk da
khakin sojojin da ta ganshi da shi ba irin wanchan É—ayan ba da ko a mafarki bata fata ta sake
ganinshi don kila sai ta sume.
"Afeefah"
Ta furta a hankali
"kina da suna mai daaÉ—i Afeefah".
Shiru ta yi.
"Ko za ki kwanta ki huta? Ko in samo miki abin da za ki ci?"
Nan ma shiru tayi, a hankali kuma ko me ta tuna tace
"Eh"
"Eh wa wanne kenan? Kwanciya ko abinci?"
Da wasa yayi maganan hakan ya sa ta sake kallonshi kan tace
"kwanciya"
"duk biyu dai Afeefah, yanzu kwanta ki na hutawa ni kuma zan je in samo miki abincin kin ga ina
dawowa ke kuma kin gama hutawa sai cin abinci ko?"
Ta gyaÉ—a kai
"yauwa Afeefah"
Kwanciya tayi shi kuma ya fice.
Ya fi awa É—aya da fita kan ya dawo, ya samu wani baccin ya É—auke ta yadda kuma fuskanta da
idanunta suka sake suntuma suka tabbatar mishi da ta sake wani kukan fiye ma da na É—azu.
Sossai ta bashi tausayi adu'ar samun sauƙi a ko ma menene dake damunta ya yi mata kan ya
ajiye babbar ledan da ke hannunshi ya fice, office na Ryan ya koma sai dai ya samu a rufe
girgiza kai yayi kan ya juya ya koma nurses station inda ya roki a duba mishi Drn da Ryan yayi
referring É—inta to don ya san ko mutuwa za tayi ba zai sake duba ta ba. Ganin Dr Sulaiman ya
sa ya nufi office É—in nashi.
Dukda Captain Saleem zallar soja ne na ƙasa wato land army sai dai tarensu da Ryan ya sa
kusan duk wadda ya san Surgeon General Ryan Moh'd Khamis ya san Salim, Salim shi ne
ƙwallin abokin Ryan don shi kaɗai ke iya tolerating murɗaɗɗiyar halinshi da zafin Ranshi sam
Ryan ba shi da hayaniya kuma ba ya shiri da mai hayaniya, ba ya dogon magana kuma ko da
ido yana so idan yayi magana ka fahimce shi bare kuma in ya buÉ—e baki ya furta ko za ka mutu
ba zai maimaita ba, yana da saurin fushi kullum a hasale yake ga ko in kula a koma menene
matukar ba shi ya so yin abu ba babu mai mishi dole, sarauta da ƙasaitarshi wane sarki don har
wasu kan tambayi ko shi É—in jinin sarauta ne?
A kofan office ɗin yayi knocking aka bashi izinin shiga ya sanya kai, Dr Sulaiman ya miƙe ya
bashi hannu suka gaisa kan ya zauna yana dubanshi yace
"Dr. Ka san yanayin aikin namu tafiya ce ta kama ni babu zato, zan tafi Kano kuma zan kwana
biyu ban san ko za ka iya sallamar ta a yau ba samu in mayar da ita kar in tafi kuma aiki ya
riƙeni in kasa dawowa da wuri".
Dr Sulaiman ya buÉ—e file É—inta ya sake dubawa sossai kan ya É—ago yana kallon Salim ya shiga
cewa
"A gaskiya cap. Sallama ba zai yiwu yau ba yarinyar jininta yayi ƙasa sossai matuƙa kuma ka
san hatsarin hakan, ga damuwa dake dukar zuciyarta shiyasa take ta complain ciwon kai da
kirjin dole tana buƙatar kulawar likita atleast na kwana uku zuwa huɗu".
Ajiyar zuciya salim ya saki.
"Dr Sulaiman ko za ka taimakeni don Allah ka kula da ita har na dawo?"
Murmushi Dr Sulaiman yayi
"Kar ka samu matsala In shaa Allah zan kula muku da ita, akwai wata tsohuwa dake mana aiki
gida zan É—auko ta ta zauna muku da ita har ku dawo"
Godiya sossai salim ya mishi kan ya fice.
Ko da ya koma É—akin ya samu ta farka abinci ya sa ta ci yana É—an janta da wasa yana mata hira
har ta ce mishi ya isheta bayani yayi mata a kan bayan Magrib zai bar garin akwai mai zuwa ta
zauna da ita har ya dawo in shaa Allah yana fata kan ya dawo ya samu ta yi sauƙi samu ya
mayar da ita gida Fatan hakan ba zai haifar mata da matsala ba?
Ta amsa da "uhmm" a ranta take raya a yanzu ko ɓata ta yi ɓat a duniya babu mai neman ta
bare ya damu da wanzuwar ta ko akasin hakan, yanzu haka aka tambayeta ina za'a kaita bata
sani ba don ko giyar wake ta sha ba za ta tunkari wurin uncle ba dolenta dai shi ne kawu, Nan
ma kuma bata san abin da za ta iya riska ba Shikenan ta koma Square Zero?
Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata.
"Afeefah!"
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*009*
Captain Salim ya ƙira sunan nata cikin tausasawa, ta ɗaga ido ta kalleshi.
"Akwai wani matsala ne?"
Ta girgiza kai.
"Na gode sossai Allah ya saka maka da mafificin alkhairi"
Yayi mata murmushi, bai bar É—akin ba sai ga dattijuwar matar kuÉ—i masu kauri ya fitar ya ba
dattijuwar saboda sayan abinci ya nuna mata kaya kala biyu dogayen riguna da ya siyo da man
shafawa, macline, brush, turare da soson wanka ya roƙe ta da ta kula da ita don Allah har ya
dawo, kaman kar ya tafi haka ya fice a É—akin domin haka kawai ya tsinci kanshi cikin tsantsar
tausayinta da har yana so ya yiwa zuciyarshi yawa.
Baaba jummai macece mai faram-faram da saurin sabo duk yadda Afeefah ta yi shiru sai ta
saka ta magana har da murmushi, tana kula da ita sossai sossai, bata maƙe kuɗin da salim ya
bata ba ta kan sayo musu kayan daaÉ—i ta bajo musu tana cewa
"Ke 'yannan sa hannu maza ki ga mu ci kin ga ko mutuwa muka yi yanzu za'a É—auke mu da
nishi saboda nauyin mu ina amfanin kana da shi baka ci ba? Maza-maza sa hannu"
Dole Afeefah take murmushi kuma ta biye wa Baaba ta ci sossai dare idan an gama duba
Afeefar kan su kwanta bacci za ta shiga ba ta labarin aurenta da ma rayuwar da tayi har ma da
irin kishin su na da chan baya da kissa kala kala da kan kashe Afeefah da dariya, kan kwana
biyu ya zagayo har ta fara manta tarin damuwarta, duk Sallar ta kuwa bata taɓa mance iyayenta
da Aunty zee ba ta kan kai wa Allah kukanta musamman cikin dare akan ya gafarta musu yayi
musu rahama (Tana roƙon duk wanda ya zo across wannan littafi ya nema musu rahama domin
AllahðŸ™)
Kaman yau Dukda safiya ce bayan sun gama karyawa da doya da miya haÉ—e da shayi da duk a
bakin asibitin Baaba ke sayo musu ta dubi Afeefar da ta É—an yi shiru tana tunani tsoron ta É—aya
dawowar salim ina za tace ya kaita? Ina ta nufa? Ya zata yi?
"Wai 'yannan kin kuwa san abin da ke ƙara ba ni mamaki ma a wannan zamanin?"
Afeefah ta girgiza kai tana ɗan kakaro murmushi don ta san zancen baaba bai taɓa wuce kan
taɓarɓarewar tarbiya a wannan zamani ba.
"Mu a lokacin mu ina mace ta isa ta ƙira ko mai irin sunan mijinta? Kai ko bayan ya mutu ko kun
rabu mu kam ba ma iya kiran sunan ko da kuwa da kuskure amma ki ji mace yanzu gatsal tana
cewa Ummaruuu a gaban yara ma da iyayenshi ko nata kai ko a gyalen su"
Dariya Afeefah ke yi sossai tace
"Yanzu Baaba ko sakin ki yayi ba za ki iya ƙiran suna mai irin nashi ba?"
"Eh mana! Ai da kunya 'yannan"
"Tabb baaba ba dai irin sakin wannan zamani ba, komai fa akwai silar chanzuwarshi Baaba bai
wuci mazan ma na da na yanzu ba É—aya ba ne shiyasa ake ganin bambanci"
"za dai ki kare su ni dai na faɗa miki ki kiyaye, kin ga maza suna matuƙar son a ba su girma,
idan za ki ba namiji girma toh tabbas mutuncin ki ma zai zama daban ne a idanunshi ko da
kuwa ya auri wata ne"
Tana murmushi sossai tana tuna wato gidan kawu Labaran ban da rashin tarbiya har da tarin
jahilci da suke dashi, daga mu'amalar iyayen har ta 'ya'yan gashinan dai gashi nan yo idan ta
ciwo shi ai sai dai a ji suna dambe da mata...
Fuskanta É—auke da murmushi tana sake jinjina rayuwar da don baaba jummai na sake bata
labarin yadda maƙota sai ya hukunta ɗanka baka sani ba idan ma ka sani ka je har gida ka
mishi godiya amma yaran yanzu ko kanwarka ce ka mari yaronta gabanta sai ta maka Allah ya
isa a gaban yaro to me yasa ba za'a lalace ba? Haka batun ƙarfafa zumunci Meyasa zumunci
ba zai yi ƙarancin ba yara suna 'yan pendo da ɗan kawu amma idan wanchan sun fi kuɗi sai ka
ga yana nuna bai san yayyunshi cousins ba ko ya fi karfinsu uwa kuma ta kasa kwaɓa saboda
tana ganin hakan ce daidai daga mutum mai kuÉ—i ne level nashi ya fi karfin talaka ko da kuwa
cikin umma É—aya ne.
Turo kofan yayi bakinshi ɗauke da sallama a kanta idanunshi suka soma sauƙa, ajiyar zuciya ne
ya kufce mishi ba tare da ya san dalili ba murmushi na yalwatuwa a fuskar tashi ganin ko da
suka hada idanu murmushin bai kau daga kan fuskanta ba, fara'a na yi mata kyau ya ayyana
hakan a ranshi maganan Baaba ne ya yanke mishi tunani
"Bawan Allah sannu da dawowa, lale maraba"
Ya saki murmushi ya É—an rankwafa ya shiga gaisheta ta amsa cike da kulawa tana tambayar shi
aikin da sanya mishi albarka, Afeefah ya duba da ta ɗan duƙar da kai tana kallon yatsun
hannunta
"Na shigo kuna ta raha me yayi miki daaÉ—i haka Afeefah?"
Ta É—ago tana murmushi
"Ni da Baaba ne, barka da dawowa"
Yana zama gefen gadon tuni É—akin ya cike da sassanyar kamshin shi ya ce
"Yauwa ya jikin? Hope kin samu lafiya?"
Ta gyaÉ—a kai tana dorawa da
"Alhamdulillah na gode"
Da Baaba suka cigaba da hira akan jikin nata ita dai sai murmushi bata magana har Dr.
Sulaiman ya shigo, sai da suka dan sake hira kan ya miƙawa salim takardar sallamar ta
"My patient is good to go, kawai dai ta kiyaye sa damuwa a ranta and gaskiya ku kula da ita
sossai da sossai Dukda SG Ryan yayi mugun ƙoƙari a kanta babu wani traces na guba a jikinta
amma don Allah ku sake kula, ke kuma Afeefah ki saka a ranki komai yayi zafi maganinshi
Allah. Manzon Allah S.A.W ya ce; "Wanda ya gangaro daga kan dutse ya kashe kansa, to yana
nan madawwami a cikin Wutar Jahannama yana ta gangarawa har abada. Wanda kuma ya sha
guba ya kashe kansa, to gubarsa tana nan a hannunsa yana ta kwankwadar ta a cikin Wutar
Jahannama, yana madawwami a cikinta har abada. Haka wanda ya kashe kansa da wani karfe,
to karfensa na nan a hannunsa yana ta soka wa cikinsa a cikin Wutar Jahannama, yana
madawwami a cikin ta hakan har abada. (Sahih Al-Bukhaariy: 5778; Sahih Muslim: 109)".
"Allahu akbarr" Baaba jummai ta zabga kabbara Afeefah dai kanta ƙasa zuciyarta na sake shiga
cikin tsantsar nadamar wannan yunkuri da tayi da ta mutu ta shiga ukunta.
Godiya sossai ta musu haka salim yayi wa Sulaiman da Baba godiya murmushi kawai Sulaiman
yayi yana shaida wa Baaba akwai driver waje zai mayar da ita gida sai ga Baaba na hawayen
rabuwa da Afeefah Dukda zaman nasu na kwana biyu ne amma sanin ranar sake haÉ—uwa sai
Allah, Afeefar ma sai ta kama hawaye, a duk sadda ta ga wani ya kaunace ta Saboda Allah ta
kan ji son shi fiye da yadda shi ya kaunace ta don masu hakan a gareta basu da yawa, bata yi
shiru ba ko da Baabar ta tafi sai ma zuciyarta da ya tsinke, tsoro da fargaba suka lallaɓo suka
rufe ta.
Daram! Haka zuciyarta ya buga a sadda Salim ya É—auki 'yan kayanta yana furta
"Mu je ko Afeefah?"
Jiki a saɓule ta sanya kafafunta ƙasa ta shiga takawa har ta wuce shi yana riƙe mata da ƙofa
bayan ta fita ya ja kofan a bayanta ya rufe suka jera a tare har motar shi, ya buÉ—e mata gidan
gaba ta shiga ya buÉ—e baya ya ajiye kayanta kan ya zagaya ya shiga ya ta da motar suka fice
daga cikin asibitin, cikin natsuwa yake tukin kan ya É—an kalleta
"Anchau muka nufa ko?"
Kamar mai karyayyen wuya haka ta gyaÉ—a kai gabanta na dukan tara-tara, bata fata Uncle ya
raba ta da su suhail bata fata su tashi a hannun kishiyar uwa, daga shi har yaran wani irin
tausayinsu take ji har ɓargonta bata ga laifin uncle ba don ta tabbatar dole mutuwar Aunty zee
ta jijjiga shi fiye da ƙima tana fata da adu'ar Allah ya sa ya sassauto ya karɓeta kar ya kore ta.
Salim ya gyaÉ—a kai shima, motar ya É—auki shiru na seconds kan yace
"Afeefah!"
A hankali ta amsa
"Na'am"
"Na san kowa abinda yake faɗa miki jarrabawa, kaddara haƙuri. nima ba zan chanza ba don
akan hakan Allah ya halicce mu haƙuri kuma da kaddara ibada ne kaman yadda ya halicce mu
don mu bauta masa, idan kika ga na wani Afeefah sai kin yi hamdala wani jarabawar shi
'ya'yanshi, wani za ki samu jarabawarshi Mata ne, wani talauci, wani dukiya hatta Mahaifiya ta
kan iya zama mummunar jarabawar É—a, kaman yadda rayyan ya faÉ—a kuma Sulaiman ya ba ki
har hadisi, da kashe kai shine mataki mafi sauƙi a yayin da duniya ta yi wa bawa tsanani da ba
za mu tarar da miliyoyin mutane ba a raye, akwai wani hadisi da Manzon Allah S.A.W ya tashi
tsoratar da masu yunkurin kashe kansu da ko tunanin aikata hakan ka yi to ka yi gaggawar tuba
ka tsarkake zuciyarka daga shaidan. Ban san irin naki ƙalubalen ba amma ina sake jan
hankalinki da ki kiyaye dokokin Allah ki duƙufa da Adu'a In shaa Allahu komai yayi farko yana
da ƙarshe kinji ƙanwata?"
Kai ta gyaÉ—a mishi a hankali cikin sassanyar Murya tace
"Yaya Salim hakika ba ni da bakin gode muku, kun ceceni daga azabar Allah da baku zo ba a
lokacin da ban san a yanzu wani hali nake ciki ba. Na gode Na gode Allah ya yaye maka naka
matsalolin ya saka maka da gidan Aljanna"
Ya amsa da Ameen yana É—an murmushi.
Kaman yadda ta zata isar su Anchau kai tsaye gidan uncle suka yi, ko da ya tura yaro yayi
mishi sallama da uncle ba'a jima ba sai gashi ya fito idanunshi na sauƙa kanta yayi mugu-
mugun ɗaure fuska bai tsaya ma salim ya gama bashi haƙuri da koro mishi jawabin da ya sa bai
dawo da ita kan lokaci ba ranar ya shiga karta musu rashin mutunci yana kwashe mata albarka
duk yayi wani irin susucewa, sai jefanta yake da munanan kalamai da suka zama tamkar rurin
garwashi a zuciyarta, ya shiga tuna mata Alkhairin Aunty zee a rayuwarta da mugun
sakayyarta, ya kuma yi alkawarin muddin bata bar mishi kofan gida ba wallahi shi zai kawo
karshenta yayi ajalinta.
Kokarin bashi hakuri salim ya shiga yi ganin tana wani irin kuka amma ina tuni ya soma tara
musu jama'a babu arziki suka koma mota, ta haɗa kai da gwiwa tana ƙara fashewa da wani
kukan mai taɓa zuciyar duk mai saurare.
A hankali salim ya ja motar sai da suka yi nisa sossai yayi parking tare da jingina bayan sa da
jikin kujerar ya lumshe idanu yana sauraren kukan nata da idan har ka ji ka san duniya bata
yiwa mai yinsa daaɗi. Sai da tayi ma'ishi bai ce mata komai ba da kanta ta ɗago ya miƙa mata
ruwa ta fita ta wanke fuskanta ta dawo ta sha kaɗan kan ta miƙa mishi ba tare da ta kalleshi ba
ya sa hannu ya karɓa.
"Ki yi haƙuri Afeefah!"
Ta gyaÉ—a kai
"Yanzu ina kuma kike da shi da zan kai ki?"
Hawaye ne ya sake cike idanunta a sadda take furta
"Akwai kawuna a Dutsen-wai"
Cikin dasasshiyar muryarta da ya dishe saboda kuka.
Motar ya ja tare da miƙa hannu ya kunna musu ƙira'a domin zuciyarta yayi sanyi.
Awanni kaÉ—an ya sada su da kauyen, ita tayi ta nuna mishi hanya har gidan kawu Labaran.
Yana zaune rumfar kofar gida yana cinikin Nono da wata bororuwa ganin tsayuwar mota ya sa
ya shiga shafa rantalin kanshi da babu gashi ko guda sai maiƙo yake a rana, a tunanin shi ɗaya
daga samarin yaranshi ganɗa-ganɗa da suke zaune ba aure ne domin sun rantse sai mai maiƙo
iyayensu mata kuma sun ba su goyon baya alhali gidanshi ko keken hawa mai kafa biyu babu.
Idanu ya ƙura mata bayan sauƙowarta yana tunanin inda ya santa kan ya zabura ya runtuma a
guje sai cikin gida, ganinshi da gudu ya sa mata da 'ya'yanshi kowa ya fara yin ta kanshi don
tsallake su kawai yake bai tsaya ba sai da ya dangana da É—akinshi ya zaro sandar goran shi
tare da wasu manyan layu ya zura a wuya, wasu ya saka a hannu kan ya fito ya nufi waje da
saurinshi har yana kifawa....
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*010*
"Hohohooo! Da ma an gaya min za ki dawo, za ki dawo da shirin ki da ya ci uwar na da kuma
sai ga ki, to idan ma junanki sammako ni a tafe na kwana yarinyaa! Namana guba a bakin ki
dodanniyar Mayu!"
Yadda yake maganan a kan muryarshi ya sa tuni su inna Asabe suka yo waje, abin ka da
ƙaramin ƙauye tuni maƙota ma sun fara leƙowa, daga Salim har Afeefah sun kasa ko da motsi
ne barin ma ita da wani tsoro ya sake rufe ta.
Tuni matasa suka shiga neman makami don ma kayan sojoji ne jikin salim kuma harda ƙaramar
bindigar shi a gefen ƙugunshi.
Kawu ya nufa da yake zaro maganganu tamkar sabon kamu wai enchanting words É—in kariya
yake daga Mayu ya furta
"Haba Malam! Ba ka gane ta bane? Ya duk ka firgice kaman wanda yayi karo da zaki?"
Kawu ya gyaÉ—a kai ya kuma girgiza yace
"Hayyyaa yaro yaro ne! Ni ko na santa farin sani, kai ma na tabbatar da ka san wacece ita babu
abin da zai sa ka bari ta shiga motarka. Wannan mayyar da ta cinye min zuri'a ta je ta cinye na
uwarta shine ka dawo min da ita kofar gida?"
Waigawa salim yayi ya kalleta har lokacin tana kafe kyam kaman mutum-mutumi ya waigo ga
kawu hes very confused da kalaman da ake jefa mata gwara wanchan ta ce mijin yapendonta
ne amma wannan dake wa ga mahaifinta? Ji abin da yake kaman sabon kamun hauka?
"Amma malam ka kuwa san yadda shari'ar maita take? Me yasa za ka jefeta da wannan kalma
ta Ƙazafi? Ita ɗin fa 'ya ce a gareka kuma addini kai ya ɗora wa kulawa da ita da bata kariya
tunda mahaifinta baya raye amma don Allah dubi abin da kake yi na ƙarancin ilimi, duk ka tara
mana mutane? Me yayi zafi haka?"
"Wuta! Na ce wuta ne yayi zafi, wallahi idan baka daina haÉ—a ni da wannan yarinyar ba kai ma
sai na rotsa kan ka da wannan sandar bar ganin ka da kayan sojoji, tun muna shaida juna ka
É—auke ta sawunku a likkafa ka mayar da ita inda ka É—auko ta ai Zainabun ma sai da na
gargaÉ—eta taurin kanta ya ja mata... Ni ma zaman da nayi da ita shekarun baya ban huta ba da
neman kariya da yanzu babu wanda za ka tarar anan da duk ta lashe kurwowinmu"
Ya hayayyaƙo wa salim da baƙin ciki haɗe da wani irin takaicin su ke shirin kashewa, ita dai ban
da kuka babu abin da take kaman ranta zai fita hannayenta duk biyu bisa kanta jikinta na wani
irin rawa.
Ya godewa Allah da ba da Rayyan ya zo ba yau da kuwa yanzu wani zancen ake ba wannan
ba, duk haƙurin salim sai da su kawu suka kai shi bango, ya kaɗa ya rawa a kan su karɓeta sai
dai cin mutunci kawai suka karta musu da kalamai masu zafi suka ma fara yunkurin far musu da
sunan haushin ta dama suke ji haka ya dauƙeta suka wuce suka bar garin gudun fitinar da zai
iya kunno kai idan suka ci gaba da tsayuwa.
Shiru ne ya ratsa motar sama da awa guda sai tsula uban gudu yake ita kuma tana ta aikin
kuka.
"Afeefah ya isa haka don girman Allah ki yi haƙuri, ki karɓi wannan ma a jarabawa. Akwai inda
zan kai ki kuma?"
Yayi maganan yana kallonta, É—ago ido tayi ta kalleshi sai da ya ji wani yarrr a jikinshi ganin
yadda idanunta suka koma tsabar kuka, ɗauke kai yayi har ƙasan Ranshi yana jin ɗacin da bai
sani ba baƙin cikin su kawu ne ko menene oho.
"Ba Za ka tambayi wacece ni ba? Ba ka ji kana son sanin ni É—in Mayyar ce da gaske ko akasin
hakan ba? Ba ka ji kana tsoro da shakkar taimakona ba?"
Ta faÉ—a cikin dasasshiyar muryarta har lokacin idanunta na a kanshi.
Ya samu wuri yayi parking kan ya waigo gabaÉ—aya yana kallonta
"Ki gane wani abu Afeefah, Na riga na saka a raina taimakon ki ya zama min dole. Batun sanin
ko ke wacece ba zan ce miki bana son ji ba amma ba na son tilasta ki ba ni labarinki, idan muna
tare watarana zan sani. Ba na tsoron ki don ke É—in ba Abar tsoron ba ce ba kuma na Fatan yin
da na sanin taimakon ki"
Yana kallon cikin idanunta ya ƙarasa maganar, zuciyarta ne ya sake karyewa hawayen da suka
tsagaita sai suka fara shirin dawowa sabo, kaman da wasa ta shiga sanar mishi da tarihin
rayuwarta daki-daki tun daga farko har kawo ranar da ta sha guba don ta kashe kanta.
Numfashi ta ja sam bata duba yanayin shi ba ta cigaba da cewa
"Na gode kwarai da taimakon ka da kuma yarda da ni da kayi ba tare da ka san ni din wacece
ba, ba na so in sake É—ora maka wani nauyi ko damuwa ba kuma na son wani abu ya same ka ta
dalilina. Za ka iya ajiye ni anan kawai ka bar ni ka koma gida Na gode sossai..."
Idanunshi da suka sauya sossai suka cika da tarin kwallar tsananin tausayinta da rauni ya
ɗauke bisa kanta yana lumshe su da ƙarfi, ya rasa ma kalar tunanin da zai yi wani irin
tausayinta ke bin gaɓoɓin jikinshi yana kassara su, ji yake kaman ya taya ta kukan ta ɗauki
abubuwa dayawa fiye da shekarunta, tabbas dole tayi yunkurin kashe kanta don duniyar bata
dandana mata daaÉ—i ba sai akasin hakan, hakika ya yabawa hakurin ta da tarin juriyarta da
wani ne ko guba bai kashe shi ba damuwa sai yayi bindiga da zuciyarshi.
Sama da mintuna uku ta sauƙe numfashi ta sa hannu ta buɗe kofan tana shirin sauƙa ta ji ya
kira sunanta
"Afeefah!"
Waigowa tayi tana kallonshi, ya rankwafa ya janyo murfin da ta buÉ—e ya rufe kirib kan ya kalleta
"Ba zan iya barin ki anan ba Afeefah! In na ce ma ki sauƙa anan za ki yarda?"
Ta Yi shiru ya sauƙe numfashi kan ya ta da motar yana mayar da idanunshi bisa titi ya shiga ja
a hankali.
"Sunana Salim Mahmud ni haifaffen nan jahar ne na Kaduna, ni ne É—a na farko a wurin iyayena
kuma namiji tilo ina da ƙanne mata uku Sadiqa ke bi na Dukda akwai tazarar shekaru masu
dama tsakanin mu sai Sameerah kan Auta Samha dukkansu suna jami'a ne presently. Tun
Samha na da shekaru uku a duniya muka rasa mahaifin mu ya saura daga mu sai mommy,
dangin mahaifin mu suka watsar da al'amurranmu duk da kasancewar mahaifina mai karamin
ƙarfi bai tara mai yawa ba, kuma duk yawan da zai tara akwai hidimomi gabanmu ya sa tun ba a
je ko ina ba komai ya ƙare, mahaifiyar mu ta matukar shan wahala da mu kuma ta yi ɗawainiya
mai yawa da ba don tayi karatu ba ma da bamu san halin da muke ciki ba a yanzu, bata huta ba
sai da ta ga ta kafa ni ta yadda zan iya taimakon ƙanne na. Mahaifiyar mu macece mai tausayi
sai dai duniya kuma ta koya mata son nata don bata haÉ—a soyayyar yaranta da kowa ba.
Ban sani ba ko za ki iya zama cikinmu idan kin amince zan je na roƙe ta, zan bata labarinki za
ta ji tauaayinki kuma in shaa Allah za ta haÉ—a ki da su Samha ta rungume mu cigaba da rayuwa
har Allah ya kawo miki miji ki yi aure".
Kuka take mishi mai sanyi, ashe har tana da zaɓi a yadda taken nan? Har sai ta ce ta amince
zata zauna da su ko da naman jikinta za su dinga yankewa da tayi bulayi a titi? Kalaman godiya
tayi ta jera mishi yana hana ta don gabaɗaya rauni da tausayinta sun sassara mishi gaɓoɓi da
yake jin zai iya joining É—inta su yi kuka tare.
Yamma sossai suka dawo cikin Kaduna, daga ita har shi babu mai magana idanunta zube a titi,
masu hidimar komawa gida kawai take kallo Dukda zuciyarta ya jima cikin nashi duniyar,
kwakwalwanta ya zurfafa a tunanin wani irin ƙaddara ne kuma ya dawo da ita cikin Kaduna?
Shin za su amshe ta bayan sun ji labarinta ko za su kore ta? Idan suka kore ta ina ta nufa?
Akwai mai sake mutuwa sanadiyar ta? Anya ta yi mishi adalci da ta biyo shi? Har suka isa cikin
Unguwar rimi bata sani ba, jin ƙarar horn na mota ya sa ta ɗan yi firgigit ta dawo da hankalinta
kan inda suke sai ta tsince su a wani layi mai jerin rukunin gidaje iri É—aya.
Gidaje ne masu kala É—aya kusan komai na gidajen Layin iri É—aya ne bambancin kawai lambobin
da ke maƙale gefen kyauren ko wani gida, Baƙin gate ɗin aka zuge wani matashi ya shiga yiwa
salim É—in barka da dawowa hakora a washe, Salim ya tsaya suka gaisa kan ya nausa cikin
tsararren madaidaicin gidan da ya tafi da imaninta, harabar shimfide da interlocks an ƙawata
gidan da shukoki jajaye, shudi, kore da ma wasu kalolin ma su ban sha'awa. Ginin da kaman an
zana ne ba a gine yake ba saboda yadda yayi mata kyau gidan sama ne, harabar gidan shiru
babu kowa har ya shigar da motar cikin ma'ajiyarta tsakanin wasu motoci madaidaita guda biyu.
Hamdala yayi yana zare keyn ya dube ta
"Mu je ko?"
Babu musu ta gyaɗa kai ta buɗe kofan ta sauƙa, shi ya buɗe bayan da ya fito ya zaro ledar da
'yan kayanta ke ciki suka nufi cikin gidan yana gaba tana biye da shi a sanyaye, a gaban
mashigar gidan suka dakata ya danna doorbell, babu jimawa aka buÉ—e Brown security door É—in
wata kyakyawar yarinya da za ta iya girme mata ta gani tsaye, haÉ—a idanu da suka yi da Salim
ya sa ta saki ƙarar murna kan ta sauƙo da gudunta ta faɗa mishi tana dariya sossai shima yana
murmushi ya tarbeta ya É—an yi hugging É—inta kaÉ—an ya sake ta
"Welcome home bro"
"thanks Autar Hajiya mommy"
Ta saki murmushi tare da jan hannunshi suka yi ciki tana ihun sanar da isowarshi, hakan ya sa
wasu 'yan mata biyu suka fito su ma a guje suna mishi maraba, yanayin kamanninsu ya sa ta
tabbatar da su ne ƙannenshi da ya bata labari, murmushi take saki don sun matuƙar burgeta
har tana jin ina ma da ba ita kaÉ—ai aka haifa ba, ita kam ba ta da wannan gatan Allah bai ba ta
ba bata gama tunanin ta da murmushi ba ta ga Fitowar wata dattijuwar mace da suke matukar
kama, fuskarta cike da fara'a har hakwaranta biyu na hajji na bayyanuwa, doguwa ce kaman su
salim da suke dogaye, haka ba ta da wani ƙiba don idan ba a yanayin fuska da ya bayyana
girma ba ba za ka ce ta haife su ba.
Ganinta ya sa salim ya ture ƙannenshi ya isa yayi hugging nata
"Oyoyo Mommyna"
"Welcome home my son, idonka kenan?"
Ya sake ta yana É—an shafa kai, ta saki murmushi ta san ya kan shigo cikin Kaduna amma
sungulollinshi ba ko yaushe yake bari ya ƙaraso gida ba, kusan satin shi uku zuwa huɗu rabon
shi da su sai a waya.
"Wannan kuma wacece yaya? A ina ka samo ta?"
Samha da tun bayan gama murnar su ta ƙure Afeefar kur da idanu tayi tambayar.
"Samha Afeefah sunanta, ki kaita ɗakin ki ta yi sallah ki ba ta abinci idan na sauƙo bayan isha
za mu yi magana"
Babu wanda ya sake tankawa a cikin su har ya haye sama inda nan ne sashen shi, ta duƙa ta
shiga gaishe su ɗaya bayan ɗaya sai ƙare mata kallo suke suka amsa ba yabo ba fallasa.
"Mu je"
Samha ta furta mata, ledan ta da samhar salim ya ajiyewa ta É—auka mata ta nuna mata, babu
musu ta sa hannu ta É—auka ta bi bayanta. Bayi ta nuna mata ta shige a lokacin har an fara
kiraye kirayen Sallar Magrib, Allah ma ya sa ta zauna da Aunty zee da take da 'yan abubuwan
zamani Dukda bai kai na gidan ba amma ta iya ta buÉ—e tayi alwala ta fito. Samhar na zaune
bakin gado tana latsa waya ganin Fitowar ta ya sa ta nuna mata gabas ba tare da ta bata
sallaya ko ta motsa daga inda take zaune ba, sai da Afeefar ta shimfide dankwalinta a saman
tiles ɗin kan Samha ta miƙe ta shige bayin. Afeefah na sallah ta ji samhar na wanke bayin ko da
ta idar samhar ta fito ta shimfida sallaya daga chan nesa ta tada Sallar ta, ko motsi Afeefah bata
yi ba tana ta Adu'a da roƙon Allah a kan wannan rayuwa da za ta yi a wannan gida, har aka kira
isha kan ta miƙe ta gabatar Adu'a ta cigaba da yi a kan kar Allah ya kawo ajalin wani tana cikin
gidan, tun bayan Magrib Samha ta fice daga É—akin bata wani jima da idar da Sallar ba tana
zaune kawai sai ga samhar ta turo kofa ta shigo.
Plate na shinkafa jollof ne ta ajiye mata da wani karami mai dauke da ruwan leda guda biyu.
"Na gode"
Ta faÉ—a, kai kawai ta gyaÉ—a ba tare da ta buÉ—i baki ta amsa ba ta sake ficewa.
A chan parlor kuwa bayan salim ya shigo daga Sallar isha suka ajiye mishi nashi tray É—in dake
É—auke da plate na shinkafar da wani an yi wrapping salad da wani saucer mai É—auke da pepper
chicken da ke fidda kamshi haÉ—e da zobo jug guda. Bismillah yayi ya shiga ci a natse don ya
tara yunwa sossai a cikin nashi, sai da ya gama yayi hamdala hajiyar su da tuntuni idanunta ke
kanshi ta ce
"Salim yarinyar chan da ka shigo da ita daga ina haka? Meyasa take a waje har bayan Magrib
ba za'a nemeta a gida ba?"
Ya É—an gyara zaman shi
"Wallahi Mommy yarinyar ce rayuwarta abin tausayi, na rasa me yasa mutanen mu suke haka a
wannan rayuwa ashe don ajalin bawa yayi ya amsa ƙira sai ya zama lallai lallai wani ɗan
uwansa mutum ne ya kashe shi? Duk mun manta cewa idan ajali ya zo babu mai jinkirta wa ko
da da second guda ne sai ya tafi?"
Hajiyar ta gyara zama tana katse mishi hanzari
"Hakane idan har mutum ya mutu ajalin shi ne ya riga yayi amma a komai akwai sanadi"
Ya É—an yi jimmm yana kallonta for seconds kan ya shiga magana
"Mommy Afeefah Marainiya ce! Mahaifinta ya rasu tun tana ciki, mahaifiyarta ta rasu wurin
haihuwar ta...."
A hankali ya cigaba da ba su labarin Afeefah kaman zai zub da ƙwallah har kawo yanzu, yana
sauke aya Samha ta miƙe hannunta duk biyu dafe da ƙirji idanu waje ta ce
"Mayya Yaya Salim???"
🖤Gureenjoh🖤
https://chat.whatsapp.com/Ef0BFnE69VjAhuWCV9Fxbe?mode=ems_copy_t
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Kun ga comments? To ku dage da comments za ku sha mamaki amma idan bakwa yi haka
nima zan ke shantakewa. A takaice dai ina roƙon ku da ku ba ni haɗin kai mu ga mun gama
labarin nan cikin watan nan don kowa ya sanni ya san ba na Littafi mai tsawo*
*011*
Wani irin kallo ya watsawa Samha da ya sa ta koma ta zauna sai kuma ta fara hawaye, juyawa
yayi ya kalli hajiyarsu da tunanin za ta yi mata faÉ—a sai ya ga ma kallon shi take da expression
na mamaki a fuskanta.
"Mayya fa ka ce Salim? Shi ne za ka tura ta É—akin autana ta fara da ita? Me ya hau kanka da za
ka kawo mana cutarwa gida after all faÉ—i tashi da muka sha don mu ga mun inganta rayuwar
mu?"
Kasake yayi yana cigaba da kallon mahaifiyar tashi bai taɓa tunanin zai fuskanci wani matsala
daga Mommy ba, ya zaci ta san zafin É—a kuma É—an wani ma zai iya zama nata musamman idan
ta ji cewa Marainiya ce don ta fi kowa danÉ—anar wahalar da maraici ke janyowa.
"Mommy na ɗauka Afeefah Abar tausayi ce da muddin na ba ki labarinta za ki karɓeta hannu
bibbiyu, ki rungumeta tamkar su Samha wallahi mu ma Allah zai dube mu ya ba mu ladar kula
da ita"
"Dakata Saleem! Dakata min don Allah! Ka kawo yarinya kana ikirarin danginta sun guje ta
saboda Mayya ce da tun tana ciki take cin maita ta ci har uwar da ta haife ta da ubanta ka kuma
yi expecting in karɓeta? Ta cinye min ku kenan? Ko ni kake so ta cinye maka? To ba da ni ba
salim... Ba a gidan nan ba maza maza tun dare bai ba tarkatata ka mayar da ita inda ka É—auko
ta tun muna shaida juna je ka fitar min da yarinyar nan a gida ba za mu taɓa shiryawa ba..."
Hankali tashe ya ɗan kalli kofar ɗakin Samha kar Afeefahn ta ji ya matso ya riƙe hannun
mommyn.
"Mommy wallahi ba gaskiya ba ne duk fa zargi ne da Ƙazafi irin na mutanen duniya, wallahi
Afeefah is innocent mommy ki tausayawa rayuwarta don Allah. Mu ma fa marayu ne ki saka ta
a sawun su Samha idan da É—aya daga cikinmu ne ake yiwa wannan kazafi za ki iya jura? Za
k...."
A hasale ta katse shi
"Na rantse da Allah zan tsinka maka mari salim ka sake alaƙanta yarana da wanchan Abar, eh
ku marayu ne amma da ba ku ci naman kowa ba uban wa yayi muku Ƙazafi? Bari ka ji ba'a taɓa
yaÉ—a jita-jitar da bashi da kamshin gaskiya ba. Kafin na hasala na haÉ—a da kai ka je ka fitar min
da yarinyar nan a gida..."
Samha da har lokacin take hawaye tace
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun ni dai mommy wallahi ba zan iya sake shiga É—aki na ba"
Sadiqa tace
"Ni dama daga ganinta na ji har ga Allah bata kwanta min ba, sai nuƙu-nuƙu take ashe babu
gaskiya a lamarin ta"
Sameera ta yi kwafa
"Nan ma ba ki ga idanunta bane, duk abin tso..."
"Kun yi min shiru ko sai na sassaɓa muku? Da ku nake magana ne? Ko na kira sunan dayanku
anan? Kun ga kun yi kama da waenda zan nemi izininku kafin aiwatar da abin da yake daidai?
Duk cikinku akwai wacce ta isa ta hanata zama a gidan nan ne?"
Ya daka musu tsawa Ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci duk mommy ce ta ba su wannan ƙofa amma
ya zai yi?
Gaban mommyn ya koma ya kama hannunta idanunshi kaman garwashi don saura kiris ya fara
yi mata kuka a yadda yake jin zuciyarshi ya ce
"Don girman Allah mommy kar ki koreta, ba zan iya bari ta tafi ba mommy in ta fita a gidan nan
ina za ta je? Musulma ce fa 'yar uwarmu kuma mace, ko don aikina na kare lafiyar al'umma
mommy ba zan iya tura Afeefah waje ba, Don Allah mommy ba don ni ba ki sake nazari akan
hukuncin ki kar ki saka ni yin abin da zai yi hunting É—ina for life please mommy"
Ganin zai kai gwiwar shi ƙasa yana cigaba da roƙon ta ya sa ta riƙe hannunshi suka koma
zaune, wuri guda ta tsurawa idanu sama da mintuna biyu ta sake kallonshi duk ya marairaice
yana roƙonta, Salim a yaranta yana da haƙuri yana kuma da kawaici don da wuya ya roƙe ta
abu ko ya tambayeta ko da kuwa yana matuƙar bukata ko da kuwa buƙatar kuɗi ne, yana
tausayinta ƙwarai gani yake har yanzu bata huta da ɗawainiya ba alhali, gidan gadon su ma
'yan haya ne ciki bai san ya suke kashe kudin ba a haka shi yake daukar É—awainiyar karatun
ƙannenshi da cin su, tufafin su da ma sauran hidima na rashin lafiya bai taɓa gazawa ba tun da
ya riƙe ƙasa to Meyasa za ta kasa yi mishi wannan alfarma guda? Amma kuma idan yarinyar ta
kashe mata shi fa? Numfashi mai matuƙar nauyi ta sauƙe ta ji ana cewa Mayu sun fi cinye
kurwan wanda ya taimaka musu ya ji tausayinsu kenan muddin yarinyar za ta zauna gidan sai
ta cire wa salim tausayinta? Amma ta yaya?
Ta sake jan ajiyar zuciya cikin gamsuwa da shawarar zuciyarta
"Shikenan Salim na amince ta zauna amma fa ina da sharuÉ—É—a, sharrudan da zan gindaya
maka wanda matuƙar ka tsallake Allah ya isa ban yafe maka ba"
A firgice yake kallonta, zuciyarshi kaman zai fito waje jikinshi har yana wani rawa don ba ya
wasa da Abin da ya shafe ta, me yayi zafi da Allah ya isa? Da kyar ya iya buÉ—e bakinshi da yayi
masa nauyi ya furta
"Allah ya isa mommy? Ni??"
Ta gyaÉ—a kai cikin alamun tabbatarwa tana kawar da idanunta daga kallonshi kar ma ya bata
tausayi kuma ta san muddin ya amince ba zai taɓa tsallakewa umarnin ta ba.
"SharuÉ—É—an su ne babu ruwanka da abin da ya shafe ta, za ta zauna zan bata abinci sau uku
kaman kowa, za ta yi aikin da ya kamata a ce kowacce mace na yi saidai duk wani abu da ka
ga na yanke a kanta babu ruwanka, do not question me a kan duk abin da ya shafe ta i repeat!
Magana ta fatar baki tsakanin ku in har ya wuce minti É—aya ban yafe maka ba, ni zan duba in ga
cancantar saka ta makaranta ko akasin hakan idan zaman ba na É—ore bane dole za ta bar
gidannan ka kuma yanke kowace alaqa tsakanin ku, ko da ko sannu ne"
Ya yi jimmm kanshi ƙasa duk ya damu kan ya sauƙe numfashi
"Shikenan mommy in shaa Allahu zan kiyaye umarnin ki"
Yana kai nan ya miƙe ya bar musu parlorn Ranshi na ƙuna, da yana da mata babu abin da zai
hana shi riƙe Afeefah tamkar 'yar sarki ya ba ta ingantacciyar rayuwa, a yanzu ma bai fidda
tsammani ba ya amincewa mommy ne da tunanin with time za ta sassauto daga kudurinta.
Tuni suka cika parlorn da hayaniya bayan barin shi suna uzzurawa mommyn akan me yasa ta
amince da zaman yarinyar gidan?
"ku yi shiru ku bar ni da shi, ai in bata ga wurin zama ba da kanta za ta fitar da kanta daga
gidan ba sai wani ya kore ta ba."
Ta miƙe ta nufi ɗakin Samha tana jin abin da zuciyarta ke gayamata daidai ne, duk suka rufa
mata baya wane sarauniya da fadawarta.
Suka sameta zaune inda take tun bayan idar da Sallar ta idanunta suna zube a farantin abincin
da ko loma uku bata yi ba saboda tunani da ya ci karfin kwakwalwanta, tsoro ne sossai da
fargaba suka danne yunwar da take ji don rabonta da abinci tun da suka karya da Baaba da
safen a asibiti.
"Ya ma Sunanki?"
Mommyn ta tambaya tana sake ƙare mata kallo.
"Afeefah" ta amsa a hankali.
"Ban san wani kalar tsafin kika yi wa Saleem ba da har karo na farko ya zaɓi bijirewa umarni na
a kanki, amma bari mu ga ko ke kin san hallaci? Zan ja miki federal warning akan yarana don ni
karan kaina ban san abin da zan iya aikatawa ba a kansu, hawainiyarki ta kiyayi ramata idan
kina cin ƙasa to fa ki kiyayi na shuri wallahi ko da wasa 'ya'ya na suka yi ko da ciwon kai ne
hmmmm"
Ta kara hmm É—in da wani irin siga na razanarwa,
"ana magana ba za ki amsa ba?"
Sadiqa tayi maganan tana hankada ta da kafar ta
A É—an razane ta gyaÉ—a kai.
"Tashi in kai ki inda za ki zauna, ki É—auki farantin nan don daga yau a ciki za'a na baki abinci har
Allah ya raba mu da ke, kuma ba ki isa a saka miki abinci ki bar mana ba don a nan ba ma
almubazzaranci da gumi muke nema don haka dole duk abin da aka saka miki haka za ki cinye.
Shara, mopping da wanke-wanke su ne aikinki. Am I clear?"
Sameera tace
"Kai mommy ke ma ina wannan ina jin turanci? aka ce kin fahimta?"
"Eh na fahimta"
Ta amsa cikin rawar murya.
"Tashi mana ni ki bar min É—aki, ko za mu tsaya muna jiran ki ne?"
Dole ta miƙe da sauri ta ɗauki kayanta da plates ɗin ta bi bayansu, ta kofan baya suka fita suka
miƙa har Boys quaters jin hayaniya da hira haɗe da dariya kuma Muryar maza ya sa ta sake
tsorata, isan su varender É—in Hajiya ta shiga buga cikin aihinin main building É—in É—aya daga cikin
su ne ya leƙo ganinta ya sa ya koma da gudu ya ƙira sauran suka fito su uku. Ba manya bane
chan matasa ne duka masu jini a jika da fafutukar neman halal, Ishaq shi ne ke musu wanki da
guga sai iliya da shi ne driver sai mudi mai gadi, ganin duk maza ya sake tsorata Afeefah me
hajiyar take nufi? A sama ta ji muryarta tana cewa
"ke! Ga É—akin ki nan"
Tq nuna mata wani single room dake kan varender É—in. Da gaske a waennan garadan za ta
haɗa ta, ganin yadda suke kallonta kaman kura ya ga nama ya sa hawaye ɓalle mata a take
tana ji hajiyar na cewa
"Mudi wannan itace mai wanke-wanke da share share za ta zauna a É—akin nan kar in ji kar in
gani"
"To! To hajjaju in shaa Allah za mu kiyaye"
Suka juya suka tafi suka barta nan tsaye kyam.
"Sannu kyakyawa"
Bata tanka ba sai shige wa É—akin da aka kira da nata da tayi da gudu ta datse kofan tare da
zamewa a jikin kofan tana fashewa da kuka sossai.
Dariya suka sheke da shi don tayi mugun basu dariya suna shiga É—aki kuma suka fara gulman
kyaunta, kaman daga sama suka ga an turo kofa da ƙarfin gaske duk razana suka yi sai kuma a
take suka wani irin zubewa ƙasan ganin Saleem riƙe da bindiga muraran, fuskan nan yayi Red
babu wanda zai iya cewa ya taɓa ganinshi cikin wannan yanayin a take jikinsu ya tsume cikinsu
ya shiga ba da ƙarar tsoro suna tunanin me suka yi?
Iliya ke ta maimaita
"Yau mun shiga uku mun lalace allurar ce wallahi ta tashi a kanmu ya Allah ga mu gareka.."
Kuuuuu haka kowa cikinshi ke ba da sauti ganin ya sake haÉ—e fuskan nan tamau, ya samu
hannun kujera ya zauna tare da É—ora kafan shi daya kan kujerar ya sa bindigar ya É—an sosa
goshinshi yadda za su sake gani da kyau su tabbatar, ya sauƙar yayi kooking ta ba da sauti tuni
suka maƙale juna suna kakkarwa kaman kadangarun da suka faɗa wuta sai salati suke.
Ya ce cikin dakakkiyar murya
"Menene wannan a hannu na?"
Mudi da yake jin yana shiru saleem zai iya fashe kanshi don an sha ce musu idan allurar sojojin
ta tashi bata da hankali ana ɓata wa sojan rai sai kisa yayi carab ya ce murya na rawa
"Abin kashe mutane"
"sunanta na tambaya!!"
Ya faÉ—a a hasale da kuma gaske a mugun hasalen yake, Ishaq yayi saurin cewa
"Sunanta bindiga wallahi bindiga sunanta"
"Kun dai san ni soja ne, kuma ina da lasisin harbata ko?"
Sai kai suke gyaÉ—awa kaman kadangaru
"BuÉ—e baki za kuyi ku amsa ni malamai"
Tuni suka cika É—akin da
"Eh, tabbas! Haƙiƙa hakane!"
"To ku buÉ—e kunnuwanku da kyau ku ji ni, wannan yarinya da Hajiya ta kawo ta nan ko kallon
da ya wuce na seconds kuka yi mata bare magana ta fatar baki ba tare da kwakwaran dalili
baaaa..."
Ya miƙe tsaye ya isa inda suke ya ɗodɗora bindigar kan kowannen su yace da ƙarfi
"Toh tabbas sai ya kwana a lahira!!! Ina Fatan kuna ji na da kyau??"
Suna zare numfarfashin tsoro da kaÉ—uwa suke amsawa a tare
"Mun gane wallahi mun gane, ba za mu kuskure ba ranka ya dade yallabai"
Ya É—an matsa baya.
"Kar ku ga kaman ban cika zama ba, gidannan ko ta wani ɓangare ina da abin ɗaukar video a
ɓoye waninku ya gwada saɓa doka ta ya gani..."
Yana kai nan ya juya ya fice bayan ya sake nunnuna musu bindigar a Goshi ai da gudu iliya da
mudi suka fara rige-rigen isa bayi sai zawo...! Ko magana cikinsu babu wanda ya sake yi a haka
baccin dole ya kwashe su dukunkukune da juna.
Ya É—an jima tsaye yana kallon kofan É—akin nata bayan fitanshi kan ya wuce, yana tsaye a
balcony ɗin shi na sama ya ga isar mommy da ita wurin abin ya matuƙar damun shi, ta ya
mommy za ta haÉ—a mace da maza har uku waenda ba muharammanta ba? Tsoro ne ya
mamaye zuciyarshi ba zama yake ba yana matukar tsoron wani abu ya sameta ba zai iya
yafewa kanshi ba, wayanshi ya fitar ya kira Rayyan.
Ringing na ƙarshe ya ɗaga da sallama
"Ya aka yi ne man?"
"I need your advice, ni ne na kawo lu'u lu'u mai tsananin daraja da ƙima sai na rasa inda zan
killace hakan ya sa dole na ajiye a inda ba ni da tabbacin za ta samu tsaro da kular da ta dace
da darajar ta, ban gama nazari ba sai na kyalla ido na hango wasu kananun ɓarayi da basu kai
ko da shakar numfashi É—aya ba suna zagaye wannan lu'u lu'u da kallon da ban gamsu ba, idan
ba zan iya tafiya da wannan lu'u lu'u ba kuma dole zan tafi wani mataki kake ga ya kamata in
É—auka?"
Ryan ya É—an yi shiru na seconds kan ya ce cikin dakakkiyar voice É—in shi
"Dukkan yanki ba'a rasa ɓarayi kuma ko wani ɓarawo yana da uban gida, idan har kai ne uban
gidan wannan ɓarayi kana da dama da ikon gargaɗi mai zafi irin na asalin maza ba mata ba, ina
mai tabbatar maka daga zarar sun tsorata da gargadin ka ko kallon hanyar da wannan tagulla
take ba za su sake ba"
Lumshe ido yayi
"Na gode"
Ryan ya kashe wayanshi.
Ya É—an sake nazari kan ya saki murmushi ya juya ya je ya É—auko bindigar ya wuce sashen.
Dariya kaÉ—an yayi tuna yadda suke ta zazzaro idanu suka jike jagwaf da gumin tsoro...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Don Allah ku yi haƙuri da wannan yau ɗin nan ban zauna ba wallahi*
*012*
Ta ɓangaren Afeefah anan bakin ƙofa ta ci kukanta har bacci ya sure ta ba tare da ta sani ba,
mummunar mafarki da tayi da Aunty zee ne ya sakata farkawa a razane, fitsari ne kaman zai
zube mata hakan ya sa tayi single kofa guda É—aya da ta gani a É—akin sai ta samu madaidaicin
bayi ne, bayan ta gama abinda take ta fito ne ta fara bin É—akin da kallon tsanaki don wutar a
kunne tarrr kaman rana.
Matsakaicin É—aki ne a lailaye yake da farin tiles, fanka da bulbs duk suna aiki daga chan dungu
'yar ƙaramar katifa ce da babu ko shimfidi a kai, sai agogon bango da ɗakin ke dashi, time ta
kalla ƙarfe biyu na dare har ma da mintuna ashirin da uku, juyawa tayi ta koma bayin ta yo
alwala ta zo ta sake shimfida dankwalinta ta saka hijabinta ta tada sallah, raka'a shidda tayi a
sujadar ƙarshe ne ta saki kukan dake dukanta a kirji tana jerowa Allah kirari bayan ta jera
sunayen shi masu daraja casa'in da tara ta bi da salati annabi kan ta fara jero matsalolin ta da
neman sassauci ta yiwa iyayenta da sauran 'yan uwanta da ta rasa Adu'a ta roki Allah ya kawo
mata sauƙin rayuwa ya warware mata matsalolin ta ya kuma cigaba da bata zuciyar karbar
ƙaddarar ta a duk yadda ya zo mata. Kusan ƙarfe uku da rabi ta sake kwanciya a wurin sanyin
tiles na ratsa ta har wani baccin ya É—auke ta.
Ta makara don tana bude idanunta ta ga haske daga Window, da sauri ta miƙe ta shige bayi
tayi saurin yin alwala ta zo ta gabatar da Sallar asuba tana sallame wa bata wani zauna Adu'a
ba don tsoron laifi abincin jiya da ya ƙanƙare saboda sanyi ta cuccusa kan ta fito riƙe da plate
É—in ta nufi inda ta ga sun fito jiya.
Tsaye bakin kofan kitchen ta ci karo da mommy sanye da hijabi, duk da zuciyarta ya buga haka
ta ƙarasa ta zube a ƙasa tana gaisheta.
"Sannu isasshiya sai yanzu za ki fito? Ban gaya miki aikin ki shara da wanke wanke bane, sai
karfe nawa ake shara a gidan ku?"
Murya a sanyaye tace
"Ki yi haƙuri"
Tsaki ta ja kan ta juya cikin kitchen É—in
"Talatuwa miƙo mata kayan sharar nan da mopping ta ajiye su chan baya don bana son
kallonta gangar abincin da yarana za su ci ban san me za ta iya jefawa ciki ba ko jini ko tsoka"
Abubuwan sharan wata dattijuwar ta fito mata da su, ta karɓa ta fara share parlorn zuwa dining
area daga nan bayan ta gama ta shiga mopping da goge-goge aiki ba baƙonta bane don
wannan a wurinta mai sauki ne sossai ma, haka zagi ko hantara duk ta riga da ta saba sai dai
ba rayuwar da take fata tayi ba kenan, ba rayuwar da take buri ba kenan tana so ta ga tana
karatu tana so ta ga tana hulda da mutane kaman kowani dan Adam, tana so taga ana hira da
dariya da ita kaman yadda ta samu gidan Aunty zee, sai dai da kaman wuya wai guguwa da
auren nesa.
A gefe ta tsaya tana kallon Talatuwa dake ta aikin shirya abincin mutanen gidan bisa dining
bayan ta gama ta dubi Afeefah tace mata
"Ki zuba turarukan wuta 'yan dai-dai a cikin wanchan abin ki kunna" ta ƙarasa tana nuna mata
burner, show glass É—in ta tafi a hankali cikin natsuwa ta buÉ—e ta É—auko ta saka ta kunna yadda
aka gaya mata ta koma bakin kitchen É—in ta tsaya tana cewa Talatuwa ta gama..
"Akwai abincin ki na saka miki a plate É—inki ki É—auka kije ki ci sai yaran sun gama karyawa tass
sun wuce makaranta ake wanke-wanke"
Da to ta amsa kan ta É—auka ta fice, a hanya ta gamu da Ishaq so take ta gaishe shi amma
kaman walƙiya haka ya wuce ta, bata damu ba ta shige ɗakin da yake da sunan nata ta rufo
kofan.
Ba za ta ce rayuwa a gidan yayi mata tsanani ba, saboda kwata kwata aikinta bashi da yawan
da zai dameta, tana idar da Sallar asuba take zuwa tayi share share da su goge goge ta É—auko
abincinta daga nan ta tafi, sai wuraren sha É—aya take komawa dining ta tattaro duk abubuwan
da suka ɓata na karyawan ta fitar waje ta wanke ta kawo bakin kitchen ta ƙira talatuwa ta
shigar, lokacin ita kuma Talatu za ta fiddo mata da abubuwan da ta bata na rana za taje ta tara
su wurin wanke wanken ta rufe ta É—auki abincin ranar ta ta tafi, sai bayan la'asar za ta fito tayi
wanke-wanken haka na dare sai wuraren takwas tara. Ba Ta da abokin hira don talatuwa
tsakaninsu ki yi kaza ne kar ki yi kaza ita kuma amsar ta É—aya a komai to.
Su iliya gudunta suke bata sani ba ko sun samu labarin ita É—in annoba ce oho, bayan Hajiya da
suka gamu sau É—aya 'yan mata ukun ko ganinsu bata sake yi ba, kaman yadda bata sake saka
saleem a idanunta ba tun ranar da ya kawo ta zuwa yau da take neman sati uku.
Bata sani ba shin rayuwar zai cigaba da tafiya a haka ne ko zai sauya? Shikenan ta sallamar da
burin ta na yin karatu kenan?Shikenan ta tabbata Mayyar za ta ci gaba da rayuwa ita kaÉ—ai
tamkar a fursuna kenan? Bata da mai bata amsa.
Da misalin ƙarfe biyu na dare chan cikin baccinta ta ji kaman ana buga mata ƙofa, a ɗan tsorace
ta farka sai ta ji ana ambaton sunanta
"Afeefah! Afeefah!!"
Tun ranar da ta sanya kafafunta cikin gidan yau ne karo na farko da ta ji sunanta na fita a bakin
wani hakan ya sake razana ta, da ta kasa kunne kuma sai ta ji kaman Muryar salim a maimakon
ta ji sauƙi sai ta ji tsoro ya sake dabaibaye ta. Me yake yi a kofar ɗakin ta da wannan tsohon
daren? Ashe bai ma manta da ita ba yadda tayi tunani?
Miƙewa tayi ta nufi kofan wani zuciyar na cewa idan kuma hajiyarshi ta ganshi fa? Allah ya isa
fa zata mishi sanadiyarta, sai ta girgiza kai tana dakatawa.
"Afeefah saƙo zan baki ki buɗe don Allah, na san kina jina please buɗe ba zan jima ba"
A hankali yayi maganan amma ta ji shi tsaff kasancewar dare ne, ta gyaÉ—a kai tana ba zuciyarta
tabbacin saƙo kawai zai bata ya juya ba wani abu bane, da sauri ta je ta buɗe kofan sai suka
tsaya chakk idanunshi cikin nata yana ƙare mata kallo kusan seconds biyar bai ce komai ba sai
ita ce tayi ƙarfin halin ɗauke idanunta daga kanshi ta ɗan duka ta ce
"Ina kwana Ya salim?"
ÆŠauke idanunshi yayi ya lumshe su kaÉ—an ya saki ajiyar zuciya mai dan nauyi, matsota yayi
sossai ta matsa baya tana kallonshi da manyan idanunta, ya leƙa ɗakin kaɗan kan ya dawo
baya, time ya kalla inda seconds ke reading, babbar leda jumbo dake hannunshi ya ajiye mata
don baya so ya shiga É—akin nata ba da wannan dare ba, kai ko da rana ne ma baya jin zai iya
kebewa da ita inuwa guda ko don addini da ya haramta hakan.
"Ki kula sossai za mu yi magana"
Yana kai nan ya juya ya fice, ta bishi da kallo har ya ɓace mata kan ta runtse idanunta tana
kokarin mayar da kwallarta ta tura kofar ta rufe, ledan da ya fi ƙarfinta ta shiga ja har gaban
katifa ta barshi nan ba tare da ta buÉ—e ba tayi kwanciyar ta, sai dai duk yadda ta so baccin ya
sake ɗaukar ta baccin ya ƙi zuwa, tuni ta buɗe idanunta ledar ta janyo gabanta ta shiga buɗewa
a hankali.
Da wani bargo mai taushi ta fara cin karo kaman ya san tana matuƙar bukatar bargon don tana
shan wahalar sanyi da aka fara shiga, gashi bayin ta babu ruwan zafi wani lokacin hatta alwala
da kyar take iya yi, wanka kam ba'a magana in dai tana so tayi sai ta bar ruwan a rana wuraren
sha biyu zuwa karfe biyu nan ma da kyar za ta watsa bata gama tunanin ba ta ci karo da kwalin
heater, irin wanda ake maƙalawa jikin bokiti ɗin nan a kunna ta ɗora shi kan bargon tana ɗan
murmushi, ta sake mayar da hannunta ciki ta zaro hijabai ninkakku har kala huÉ—u kuma duk za
su iya kai mata ƙasa Brown, Ash, purple da onion colour su ma gefe ta ajiye su, ta sake mayar
da hannu ciki ta zaro kananun catons na biscuit da wasu small chops dai waenda za su dan
kwana biyu basu lalace ba daban daban masu É—an yawa, har da su five Alive kananu catons
uku. Ganin abubuwan dake ciki sun kare ta É—aga ledan domin matsarwa don ta sake kallon
sayyayarta sai taji da ɗan motsi a ciki, ta buɗe gabaɗaya ta ci karo da ƙaramin kwali jikinshi da
zanen waya, buÉ—ewa ta yi ta ci karo da karamar Villion mai kyau da tsari Dukda keypad ne
amma sossai ya mata kyau, fuskar wayan ne yayi haske alamun a silent yake saƙon akwati na
SMS ya bayyana tare da sunan.
"Saleemullah"
Sai ta saki murmushi karo na farko ta buɗe saƙon.
"Ba ki yi bacci ba?"
Numfashi ta sauƙe kan ta shiga reply don ta iya sossai a wayan Aunty zee da ma wasu 'yan ajin
su na islamiyya lokacin da take zuwa makaranta ta amsa da
"Eh, Na gode sossai da saƙon ka duk abinda ka saka a ciki kaman ka san ina da buƙatar su"
Bata ajiye wayan ba ta ƙurawa screen ɗin ido chan sai ga reply ɗin shi.
"Na kasa samun natsuwa da tunaninki zuciyata ita ta lissafo min duk abin da zuciyarki ta raya
tana da buƙata. Kin ga ko zuciya bata ƙarya"
Ta karanta saƙon ya fi sau abin da ya fi sai ta rasa amsar bashi, bata motsa ba har wani saƙon
ya sake shigowa daga gareshi.
"Na san baki jin daaɗin yadda kike zaune amma kiyi haƙuri zan yi iya ƙoƙarina in ga na yi
settling komai, za ki yi karatu har sai kin ce ya isa, ga wayan nan zan dinga yi miki saƙo ki
tabbatar kina yi min reply, duk kuma abin da kike so do not hesitate ki sanar da ni zan kawo
miki. Akwai full qur'an a memory É—in idan kin ji kaÉ—aici ki rage lokaci da shi kin ji?"
Tana murmushi a lokaci É—aya idanunta na zubar da kwalla ta rubuta
"Wallahi samun mai irin zuciyarka sai an tona Yayana, na gode na gode Allah ubangiji ya ba ni
ikon saka maka"
Ta tura tana murmushi
"Never mention my dear, ki kwanta kar ki makara da safe byeee"
Ta sake sakin murmushi kan tayi reply
"Allah ya ba mu alkhairi Soja Mai kirki"
Dariya yayi daga ɓangaren shi ya rubuta
"Au akwai marasa kirki ne?"
"Eh mana, abokin kan nan Dukda gaskiya ya faɗa amma in a wrong way, su ne suke ɓata muku
suna ake yi muku kuÉ—in goro"
Ya girgiza kai yana cigaba da murmushi
"Ryan kenan! Haka Allah yayi shi, oya sleep Good night"
Bata yi reply ba sai lumshe idanu da tayi razanannun idanunshi da yake zare mata su da sautin
dakakkiyar muryarshi suka dawo mata kaman yanzu yake yi, da sauri ta buÉ—e idanun gabanta
na faÉ—uwa ganin ita kaÉ—ai ce sai ta saki murmushi a hankali ta maimaita sunan
"RYAN" tana lumshe ido.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*013*
Sabo ne mai ƙarfi ya shiga tsakanin su ba na wasa ba ta sanadiyar wannan text message da
suke yi wa juna, yana matuƙar wuya ta sanya shi a idanu amma baya yini ya kwana ba tare da
sun É—auki mintuna masu É—an dama suna exchanging SMS ba, sai dai idan inda yake babu
network, idan kuma tana aiki ne wayan na maƙale a kunnenta tana sauraron karatun alarammar
Prof Isa Ali phantami wato sheikh Abba zari'a yana matuƙar yi mata daaɗi har ta roki Saleem da
in zai zo ma ya taho mata da alqur'ani ta cigaba da koyo don yadda yake karatun daidai da 'yan
koyo.
Yau ya kama Lahadi kusan duk iyalan gidan suna a gida in ka cire salim da rabon shi da gidan
ma an kwana biyu, da zazzabi ta tashi tana jin sanyin hunturu dake busawa na Huda jikinta,
kasancewar koyaushe hannunta na ruwa ne ko tana bakin pampo kuma sossai bazarar ya
shiga hakan ya haifar mata da mura da ta É—an kwana biyu dashi, a maimakon ya ragu ma na
safiyar yau worst ga ciwon kai mai tsanani da take fama da shi ko idanunta bata iya buÉ—ewa da
kyau, a hankali kuma karo na ba adadi ta ɗago su da kyar ta kalli agogo kusan ƙarfe tara na
safe ko shara bata yi ba gashi babu wanda ya leƙo ta bare a yi mata uzuri, lallaɓa wa tayi ta
miƙe tsaye atishawa na ƙwace mata da ƙarfi ta ja hanci tana dafe kai haka ta sauƙa ta zari
hijabai har biyu ta sanya saboda yadda a É—aki ma sanyin ya isheta bare ta fita waje, a hankali
take tafiya har ta isa main parlorn gidan daidai kofar kitchen ta hadu da Talatuwa.
"A'a yanzu kenan zan tafi biÉ—ar ki, na gama abin kari tuntuni ina son fitarwa kuma ba'a yi shara
ba. Lafiya kam?"
Ta ja hanci tana É—an dafe kanta dake juyawa
"Wallahi mura ne ke damu na sossai, kaina kaman an É—ora min dutse"
"Ashhaa! Sannu Allah ya baki lafiya, idan Hajiya ta fito ki gaya mata za ta baki magani. Yanzu ki
je ki kwanta bari ni na yi sha...."
"Ta Yi mene? Kwanciya ta zo yi gidan ne da masu gida suna kwance itama tana kwance?"
Sadiqa ta katse musu zancen da gadara.
"Wai na ga bata jin daa..."
"Kinga Talatuwa ba dake nake ba, ki je ma ki fara shirin É—orawa friends É—ina abinci za su shigo
babu jimawa, ki tabbatar abin da za ki dafa zai ishi cin mutane shidda zuwa bakwai... Ke kuma"
Ta juya ga Afeefah
"Ki wuce ki je kiyi aikin ki, kuma ki tabbatar tana gamawa ba'a ajiye mana kwanuka a mawanki
kudaje suyi ta bi ba"
Kai Afeefah ta gyaɗa bata ce komai ba ta wuce ta ɗauko kayan sharar ta duƙa don fara wa, da
ƙarfi ta runtse ido jin kanta kaman zai biyo ta ya faɗo haka ta cigaba da aikin cikin dauriya irin
nata, Sadiqa dake tsaye tana danna waya rashin maganan yarinyar ke matukar bata haushi ta
ja doguwar tsaki kan ta juya fuuu tayi É—akinta.
Afeefah ta gama sharan tana mopping kenan ta ji zuban kaya bisa saman kanta, baya baya tayi
Allah ya taimaketa ta dafe jikin dining table, ta É—ago rinannun idanunta ta zubawa Samha da ta
watso mata kayan...
"Ni ki daina kallona, kurwata kurrr... Wa ma ya sani ko naman wanda ya fi ƙarfin ki kika ci ya
tsaya miki a wuya. Ki gama abin da kike ki wanke min kayannan sameera ta aiki Ishaq kuma ina
da bukatarsu babu jimawa".
Bata jira amsar Afeefah ba ta wuce zuwa É—akin Sadiqa, dukkansu biyu suna zaune ne Samha
ta isa tace.
"Allah da gaskiyar ki Aunty sadiqa yarinyar nan ta samu wuri har wani iyayi take kaman ta Allah,
muka cigaba da zuba mata ido babu wanda ya san me gaba za ta haifar kin ga har wani fresh
tayi ta kara kyau"
Sameera tace
"Ni na fi tausayin Yaya Salim don daga ganin yarinyar nan wallahi green snake ce, bana
tunanin idan da Mommy bata É—auki matakin da ta É—auka kanshi ba zai rayu har yau, gwara mu
kasheta da aiki ta yadda zata gaji ta gudu"
Sadiqa tace
"Toh ai yanzu sai mu ci É—amarar hakan don na ga mommy ta fara mance zancenta, kin ga
idanunta kuwa? Wlh muddin yarinyar nan ta samu rana ba karamin shanya za ta yi ba".
Suka cigaba da tattaunawa akan Afeefah da idan an matse su ba za su iya faÉ—an laifinta guda a
gare su ba amma da yake amfani da zancen mutane ya riga ya zama jinin É—an Adam sai ya
zamana kawai da gaske Mayya ce a gare su kuma idan bata bar gidan ba za ta iya raba É—ayan
su da rayuwarshi, haka kuma duk wanda ya nuna mata tausayi to fa shi za ta fara lamushewa.
Zaune yake cikin mota da alama abu yake dubawa don hankalinshi duka ya tattaru ne ga
wayan hannunshi, sanye yake da wani grey trouser mai taushi ya haÉ—a ta da cream Color shirt
da yafi yanayi da gashin mage tsabar taushinsa, high neck ce wuyan don idan da zai ja daga
sama zai iya rufe har hancinshi da rigar, Dukda wani irin sanyi da hazo da ya cike sararin
samaniya motar dake kunne cike take da sassanyar iskar Ac ya haÉ—u da ni'imtacciyar kamshin
shi da ma flavours da yake amfani da su na motan suka ba da wani kamshi na musamman.
A hankali sautin waƙan Alex Warren ta ordinary ke tashi, tsaki ya ja a karo na barkatai a ranshi
yake shirin fara masifa don baya ƙaunar bata lokaci sai ga wayanshi ya shiga ƙira, Bluetooth na
kunnenshi ya É—an danna.
"Allah Saleem zan yi tafiyata ka san na tsani ɓata lokaci"
Duk da a hankali yayi maganan alamun muryarshi ya nuna ya hasala kuma tabbas zai iya tafiya
É—in don saleem ya shiga masa lokacinsa.
"Afuwan mutumina wallahi sai yanzu na tuna inda papers É—in nan suke, suna É—akina kuma
kyakyawar ɓoyo na musu babu wanda zai san inda suke ban zaci boss zai tambaya bane da na
taho da su, please help me ka je ka dubo min"
Shiru yayi saleem ya marairaice murya
"Please help a soul ba ni da mai min sai kai, ka ji Autan Mammi?"
Da magiya ya ƙarasa hakan ya sa Rayyan ɗan murmushi
"Don dai kai ne..."
"Eh taimaka pls"
Ko kan salim ya gama maganan ma ya ja motar cikin natsuwa yana sauraran kwatancen da
saleem ɗin ke mishi na inda safe ɗin da ya ɓoye confidential files ɗin yake, Saleem ya bashi
wahala don ya fi hour yana neman su a office nashi na nan head quater don mance inda ya
ajiye yayi sai daga baya ya tuna da kyar.
Daga waje Ryan ya ajiye motar shi ya sauka ya shiga cikin gidan da ƙafa cikin tafiyar shi mai
cike da ɗumbin ƙasaita wane saraki hannayenshi duk zube a aljihu, waƙa still yake ji a Earpods
É—in kunnen nashi saidai sautin na fita ne da sanyi ba mai hayaniya ba, kamar ko yaushe a
murtuke fuskar nan sai kace wanda aka zagi iyayenshi har ya shige, bai nufi ma main parlorn
ba ta kofar baya ya zagaya ya haura stairs da zai sada shi da É—akin salim, a jikin kofan ya tsaya
ya duba inda suke ajiye key ya É—auka ya buÉ—e ya sanya kanshi ciki don duk sun san inda
É—ayansu ke barin spare key incase of emergency, dulum É—akin don komai a kashe ya kunna
wuta ya wuce uwar daka direct wardrobe da ya mishi kwatance ya je ya buÉ—e, kaya ne a jikin
hangers É—in ya ware bangon ya bayyana gefe wani keypad ne da ba zaka ce akwai wani abu da
zai iya buÉ—uwa ba ko da an danna.
Wasu numbobi ya saka sai ga wardrobe É—in ya dare, ya turo wani box waje nan ma ya saka
wasu lambobin sai ya budu bai tsaya ma duba me ke ciki ba ya zaro files É—in ya buÉ—e don
tabbatar da shi ne ko ba shi ba, su ɗin ne kuwa yana ƙoƙarin scanning dilim nepa suka ɗauke.
ÆŠakin ne yayi duhu sossai ba zai iya scanning haka ba sai ya nufi balcony door yana dan tsaki
ya buÉ—e ya tsaya daga saman ya fara scanning yana forwarding to salim dake online yana jira
har ya gama, yana ƙoƙarin mayar da wayan aljihu ya ɗan ɗago sai idanunshi suka faɗa kan ta,
har ya juya ya ɗan dakata ya sake waigo wa ya kalli ƙasan ba fuskarta yake kallo ba irin aikin
da take yi a sanyin yake gani a ranshi yana raya
'Mutane are heartless'
Ya dai san babu É—iya mace mai gata da zata zauna a wannan uban sanyin tana wanki ga tarin
wanke-wanke dake jira a gefe, bai ga dacewar a ce kowa na ɗaki a ɓoye ita ɗin tana ƙasan
pampo ba, bai gama tunanin ba ta saki atishawa har huÉ—u a jere ta ja hanci tare da É—ora
goshinta a kan gwiwarta, wani iri yaji sai yaji yana son kallon fuskarta, hakan ne ya hana shi
tafiya har ta ci seconds kan ta ɗago ya ɗan ƙurawa face ɗin idanu.
Kawar da idanun yayi ya mayar hannunta dake wani irin rawar É—ari duk kakkarwa suke, sun
sandare saboda sanyi ga hijaban da ta lafta rabi a jiƙe shakaf. Tunanin inda ya san fuskan yake
sai dai ya kasa ya É—an sake kallon gashin idanunta da suka yi fari fat ya ja tsaki tare da barin
wurin gabaÉ—aya, mayar da takardun yayi ya fice daga sashen ya nufi harabar gidan don tafiya
sabgar gabanshi sai ga Sadiqa ta fito taryar Ƙawayenta da Shigowar su kenan kowacce na
ƙoƙarin sauƙa a motar ta, ganin shi ya sa ta wani zaro idanu shi kam kallo ɗaya tak yayiwa
gefen da suke ya É—auke kanshi ya cigaba da tafiyarshi with steez bai ma san su waye ba bare
ya tantance mutane ne ko aljanu.
"Ya Ryan"
Ta ƙira sunan a hankali sanin baya son ihu ko hayaniya, in ka cika ko magana da ƙarfi ne sai
Ranshi ya ɓaci kuma muddin nashi ya ɓaci kaima sai naka ya ɓaci haka yake, ya ɗan ɗago ya
kalleta a kan rigar sanyi jibgege dake jikinta ya soma sauƙe ido kan ya ɗan ja tsaki matsalar shi
kenan, da wuya ya ga abin da ke cutar da wani ya iya É—auke kai, baya son zalunci sam a
rayuwarshi Dukda ana yi mishi kallon miskilin mai murÉ—aÉ—É—iyar hali sai dai yana da tsananin
tausayi, 'yan aikin gidansu sun shaidi hakan don shi mutum ne dake so ya ga an baiwa É—an
Adam haƙƙinsa na mutum cikakke kaman yadda Allah ma ya karrama dan Adam ya kuma ba
shi daraja.
Yanzu dubeta killace cikin shigar da ba zai bar iskar bazarar cutar da ita ba amma 'yar aiki
zaune ƙasan pampo hannayenta da kafafunta duk cikin ruwa cikin halin rashin lafiya don a
matsayinshi na likita kallo daya tak yayi mata ya san bata da cikakken lafiya hakan sai ya sake
ɓata Ranshi amma sam fuskanshi na nan a yadda take bata sauya ba
"Ina kwana? Ashe ka shigo?"
Kai ya gyaÉ—a kawai ya zagaye ta ya wuce abin shi, da kallo ta bishi tana murmushi a fili ta furta
"Miskili ka fi mahaukaci ban haushi"
"Waye shi?"
Ɗaya daga cikin Ƙawayenta da duk suka bi shi da ido yuuu tayi tambayar.
"Ryan Khamis kike ji da gani, sojan da ko a cikin sojoji ake ji dashi, likitan da ko a cikin likitoci
babu kamarsa... Ga sanyi ga zafi, ganin dariyar shi ko murmushinshi sai ka yanki tikiti"
"Wow shi ne Surgeon General Ryan Khamis? Da gaske don Allah? Dama yana zuwa gidanku
haka a bati?"
Sadiqa ta saki murmushi
"Abokin yayana ne, yana zuwa sossai ma musamman idan suka samu saukin aiki saleem na
gida don ba'a raba su, mahaifiyarshi ma na zuwa har gidan nan, shine dai Ryan Khamis"
No 1 matashi ne da ake ji dashi mata suke rububinshi don duk inda ya shiga akwai masu
kyasawa amma fa shi duk basa gabanshi, yana flatforms sai dai babu wanda ya san handle
nashi don akwai handles dayawa da sunayenshi na ƙarya ana yaudarar 'yan mata, shi dai kam
kaman dutse yake mace bayan mahaifiyarshi duk a maza Ƴan uwanshi ya ɗauke su.
Da zancen shi suka shiga parlor nan aka baje ana cigaba da hiranshi kala kala da kyar suka
saki suka kama wata.
Shi kam Rayyan yana tada motar shi ya danna ƙiran Salim
"Don iskanci ko godiya ba za ka min ba ko?"
"Afuwan Ryan ka san ina gani printing kawai nayi na tafi presenting don ana jirana, yanzu
kenan fitowa ta ko wayan ban fitar ba na ji ƙiran ka"
Driving yake slowly duk zantukan Salim É—in bai tanka ba sai ya daka tsalle ya kama wani
zancen da ya kasa bari a ranshi sai yake jin kaman shima Allah zai kamashi da laifin wulakanta
dan Adam tunda ya gani bai yi magana ba
"I saw someone familiar kaman na san fuskan but i cant recall"
Salim ya É—an tafi nazari kan ya ce
"A gidan mu kuma?"
Kai Ryan ya gyaÉ—a sai kuma ya tuna voice call ne suke yi a hankali yace
"Yeah, choculate tall young lady haka"
"Afeefah ka gani?"
Salim yayi saurin katse shi, a ranshi ya maimaita sunan 'Afeefah' ba tare da yayi magana ba,
Salim ya cigaba da magana
"Ka santa mana Rayyan, yarinyar da ka ceta wacce ta taɓa shan poison a Anchau?"
Sai lokacin ya tuna inda ya san fuskar but Meyasa take aikatau gidan su salim? Ina iyayenta da
family É—inta? Kaman salim ya shiga Ranshi wai aka ce sanin hali ya fi sanin kama bai wuce
magana ne a bakinshi ya kasa fitarwa ba don haka ya shiga bashi labarin yadda ya mayar da
ita da irin wulakancin da suka sha yadda ta bashi labarinta daga farko har karshe sai da ya
gama tsaf Ryan dake parking tsakar gidansu ya ce
"Hmmm"
Ya ƙarasa yana dan taɓe jajazir ɗin laɓɓanshi ba tare da ya ce komai ba bayan nan, har salim
ya zaci ya katse kiran sai ya ji Ryan É—in ya watsa mishi tambayar
"Then taimakonta kenan ka yi to be lowly house help?"
"No! No!! Wallahi ba hakan bane a raina Rayyan na rasa yadda zan yi ne, mommy ta katange
min duk wata ƙofa da zan iya inganta rayuwarta, abin is hurting me badly... Ka kuwa san akwai
Allah ya isa a kaina muddin na yi magana da ita na fatar baki na sama da minti É—aya?"
ÆŠan zare shanyayyun idanunshi Rayyan yayi
"Wow! Why?"
"Saboda kawai sun yarda da champin mutane da ƙagen da ake yi mata" nan ya shiga bashi
labarin gumurzun da suka sha da mommy a kanta kan ma aka barta a house help É—in.
Rayyan ya É—an lumshe idanu ya buÉ—e a ranshi mamakin mutane yake yi, Sai ji salim yayi yana
cewa
"Idan bata kashe ku ba ku ai kun É—auki hanyar kasheta!"
Yana kai nan ya yanke wayar don ya gaji da magana, ɓalle murfin motar yayi ya nufi cikin gidan
cikin natsuwa da takunshi na ƙasaita haɗe da izza.
Kasake salim yayi rike da wayan a hannu yana juyawa, jikinshi ne ke bashi ba haka kawai
Rayyan yayi maganar Afeefah ba, ya kuma san a yanzu ko ya sake kiranshi ba lallai ya bi ta
kan zancen Afeefah ba kuma bare yayi mishi bayanin me yake nufi da za su kasheta?
Hankalinshi ne ya ji yana neman tashi. Allah ya sani daga lokacin da tausayinta ya yi tsanani a
ranshi ya juye ya zama mishi so ba tare da ya farga ba, har ranshi sonta yake kuma so yake ya
aureta saboda ƙaunar da yake mata not out of pity, ko da ya ajiye ta kaman yadda mommy ta
umurta yayi iya kokarinshi wurin ganin ya manta da rayuwarta ya bar wa mommy É—in sai dai
hakan ya gagara mishi dole ta sa ya waiwayeta ya dawo ya kawo mata waya don ya dinga jin
lafiyarta da bukatun ta, layinta ya lalubo ya zubawa idanu sama da mintuna uku kan ya danna
mata ƙira sai da ya jera sama da 10missed calls bata ɗaga ba sai hankalinshi ya fi na da tashi
ya tura mata text message sama da biyar ba reply.
A lokacin tana ƙoƙarin tattara kwanukan da ta gama wankewa ta kai bakin kitchen, jikinta babu
inda ba ya rawa har hakwaranta na haÉ—uwa, bayan ta ajiye ta koma inda ta tashi ta É—auki
wayan da karatun ma yau bata samu ta iya kunnawa ba ta nufi É—akin tana tafiya da kyar,
hijaban kawai ta zare ta zubar a wurin ta shige bargo tana hawayen tausayin kanta, jin kaman
vibration na wayan nata ya sa ko ido bata buɗe ba tayi picking tare da maƙalawa a kunnenta,
Sheshekarta ne ya fara shiga mishi kunne yaji wani abu ya sauka mishi har cikin zuciyarshi
hakan ya rikita masa lissafin kwakwalwa...
"Afeefah menene? Me ya sameki?"
Shiru sai kuka da itama jin muryarshi ya sa ta ƙara karfin kukan, kaman shi ma zai fashe da
kukan cikin sanyi ya shiga cewa
"Don Allah ki yi min magana Afeefah, hankalina tashi yake da kukan nan naki talk to me please,
menene?"
Sauƙe wayan yayi ya kalli time saura seconds goma
"Help me Afeefah ko ta text ne ki rubuta min Meke damun ki? Kar ki yi kisan kai ki taimaka"
Yana kai nan ya sauƙe wayan ya kashe tare da jingina kanshi jikin motarshi, ji yake kaman yayi
tsuntsuwa ya ganshi Kaduna sautin Muryar kukanta ke ta amsa kuwwa cikin kanshi...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*014*
Shigowar saƙo wayanshi ne ya sa da wani irin hanzari ya miƙe daga jikin motar yana duba wa.
"Ba ni da lafiya"
Abin da kawai ta iya rubutawa kenan, sai ya ji hankalinshi ya fi na baya tashi don bai san wa zai
kira ya taimaka mata ba, idan ma ya ƙira su Samha ya san abin ba zai yi kyau ba mommy kuma
za ta iya É—aga hankali a kan ya aka yi ya san bata da lafiya yana Maiduguri tana Kaduna?
Wani tunani ne ya faÉ—o mishi, nan ya shiga neman Layin wani friend dinshi da yake nan capital
hospital Kaduna É—in a kan ya taimake shi da Layin Dr. Sulaiman, cikin mintuna biyu sai ga Layin
a take ya shiga ƙiran Layin ringing uku aka ɗaga "Dr Cap. Saleem ne don Allah wani taimako ne
nake nema daga gareka please in ba damuwa"
Ya faÉ—a bayan sallama da gaisuwa, Nan ya yi ta mishi godiya bayan sun gama disussing, ko
gida bai iya ya je ba yana zaune ne kawai cikin motar shi cike da tsumayin sake ganin ƙiran
Sulaiman.
A chan Kaduna kuwa sallamar da ake ta doka wa ne ya sa sameera Miƙewa ta nufi ƙofan,
Sadiqa suna dining da Ƙawayenta ana cin abinci ana hira, mommy ke karyawa a tsakiyar
parlorn, Samha na wani research a system É—inta hakan shine ma ya tilastawa sameera da ke
danna waya Miƙewa tana mitar irin uban Sallamar da ake tayi, tana bude kofan ta yi niyyar
masifa ne sai idanunta suka sauƙa kan Dr. Sulaiman da ke jingine ɗan nesa kaɗan da jikin
motar shi, daga ganinshi ka san responsible matashi ne da yake kan ganiyar samartakarsa
daga yanayi shiga da kuma tsarin motar shi zaka san ko shi ba mai kuÉ—i bane daga gidan kuÉ—in
ya fito, Baaba jummai ce dake doka Sallamar ta katse ta "Har na fara tunanin babu mutane ne
gidan 'yan nan ashe kuna ciki"
Ta É—an harareta a fakaice "eh muna nan, lafiya kam?"
Ta ƙarasa tana sake kallon Dr. Sulaiman da har yanzu hankalinshi ke kan wayanshi.
"Wanchan likitan Afeefah ne mun zo duba ta da jiki"
Ta haÉ—e fuska kan tace
"Ina zuwa"
Ciki ta koma kafin mommy ta tambayi waye ta shiga ce mata
"Mommy wai sun zo duba wanchan Mayyar da yaya salim ya kawo wai likitan ta"
ÆŠan shiru mommy tayi tana tunanin Allah ya sa ba salim bane ya aiko su, sai kuma ta tuna ai
bai ma san halin da take ciki ba, kila ma ya zuwa yanzu ya mance da ita ko ma bai mance da ita
ba ta san ba zai taɓa saɓawa umarnin ta ba itama kuma hankalinta ya fi kwanciya a yadda yayi
uwar watsi da rayuwar yarinyar yake kuma mu'amala da ita da ƙannenshi lafiya ƙalau.
"Tura Talatuwa ta kai su, su suka sani"
Ta ɗan zauna kaɗan kan ta miƙe ta nufi ɗakin Talatuwa ta tura ta, Baaba jummai har ta gaji da
tsayuwa sai ga Talatuwa, suka gaisa kan tace su tafi É—akin Afeefar don yadda ta gantan nan ta
tabbatar ba za ta iya fitowa ba, Dr. Sulaiman Baaba ta yiwa magana ya bi bayansu har É—akin da
Afeefar take su biyu ya bari suka fara shiga, Baaba jummai na ta sallalamin yadda ta gantan
kan ta fito ta kira Sulaiman cikin sauri
"Alhaji ƙarami zo ka ga yarinyar nan jiki babu daaɗi sam"
Ita kaman uwa take wurinsu don gabanta aka haife shi har ya girma tana gidan su, kuma shine
babba a yadda ya ɗauke ta kaman uwa haka ƙannenshi suka tashi suka gani su ma kuma suka
yi following footsteps ɗin shi a girmama ta, shiga dakin yayi ya isa gabanta ya duƙa.
"Afeefah"
Ta amsa da "uhmm" ba tare da ta buÉ—e idanunta ba.
"Menene yake miki ciwo?"
Ta Nuna mishi kanta da kaman zai tsage.
"Akwai amai?"
Ta girgiza kai.
"Jiri fa?"
Ta gyaÉ—a kai.
"Mura fa da tari?"
Nan ma ta gyaÉ—a kai, plate na abincinta na safen da ke rufe a gefe ya buÉ—e ko spoon É—aya bata
yi ba.
Ledojin da ya shigo dasu a hannunshi ya shiga buÉ—ewa babu bukatar zuwa asibiti drip ya haÉ—a
ya É—aura mata ya haÉ—a allurai yayi wasu a jikin canular wasu kuma jikin ruwan, ya dubi
Talatuwa
"Kin san magungunan da suka shafi na mura da zazzabi da sa bacci, bare ma jininta ya yi ƙasa
sossai tana ɗan buƙatar hutu na kwana biyu ba tare da ta yi hulda da ruwa ko abu mai sanyi ba"
"Toh fa, ranka ya daÉ—e ni ma 'yar aiki ce kamar ta ba ni da ikon bata hutu da dai Hajiya da kanta
ka yi wa bayanin da sai ya fi"
Ita dai Baaba jummai ta zabga tagumi tana kallon Afeefah dake bacci ji take kaman ta yi mata
kuka ashe itama aikatau take yi gidan su Saleem É—in? Muryar Sulaiman ne ya katse ta yana
cewa Talatuwa
"ko za ki kai ni wurin hajiyar?"
Duk da basu yi haka da Saleem ba amma ba zai iya kau da ido a kan yarinyar ba she's too
young and fragile kaman she's having a lot a cikin zuciyarta.
Fitowa suka yi Baaba dai kaman ta tsaya haka take ji Don Allah ya saka mata ƙauna da
tausayin Afeefah kaman jikar ta.
Talatuwa ta duƙa gaban mommy bayan ta bar su a waje "Hajiya da ma wai likitan ne yake son
gani ki".
Kan mommy ta yi magana ma sameera tayi saurin cewa
"Ki ce ya shigo, mommy bari na ba ki mayafi"
Samha ta É—ago ta kalleta, mommyn bata ce komai ba har sameerah ta kawo mata mayafin
daidai Sulaiman ya yi sallama ya shigo.
Kamshinshi ne ya cika parlorn duk yadda mommy ta so ta kame nagartarshi da kwarjininshi ya
sa ta shiga mishi sannu da zuwa a dole, gaisheta ya shiga yi cikin girmamawa bayan sun gama
Sameerah ta shiga gaishe shi, ya amsa da murmushi saman fuskanshi dole Samha itama ta
gaishe shi itama ya amsa mata kan ya dubi mommy
"Da ma akan patient É—i ta Afeefah na nemi ganin ki Hajiya, na zo duba jikinta don ganin lokacin
komawarta checkup ya yi ban ganta ba sai na samu ashe tana kwance rip da zazzabi mura da
kuma low BP da ya addabe ta"
Mommyn ta yi kaman bata san bata da lafiya ba tace
"Asshaa ka ga aikin rashin wayaun Afeefar ko? Babu fa wanda ta sanar wa bata da lafiya,
mutum kullum a maƙale a ɗaki ya ba za'a yi zazzabi ya dame shi ba? Allah dai ya kyauta"
Sulaiman ya É—an murmusa don wannan ba hujja bace a gareshi idan kai ka kula da mutum ba
lafiya ba sai ka jira ya gaya maka ba, haka kuma idan baka ji mutum ba ana dai zaune tare kai
ke da alhakin leƙa wa ka ji shin yana lafiya?
"Ai duk alamun rashin lafiyar ne Hajiya, a likitance duk wadda ba ya son interracting da kowa ya
fi gane kaɗaici da rashin magana yana shiga ƙuncin ko damuwa duk akwai alamar tambaya
kanshi, Don Allah a taya mu kula da ita idan tana samun kulawa in No time za ta ji sauƙi ta
komawa aikinta in Shaa Allah"
Sameera ta riga mommy magana
"In shaa Allahu Dr. Za mu yi duk yadda ka ce Allah ya bata lafiya"
Yayi mata murmushi kan ya amsa da Ameen itama dai fuskar nan cike da fara'a take ta
kallonshi.
Mommy ta ce
"Ba na son ka faÉ—awa Salim, ka ga yana wurin aiki kar ya zaci ba ma saka ido ne a kanta duk
hankalinshi ya tashi, bills É—in ka dinga turomin zan ke covering"
Ya gyaɗa kai kawai yana kokarin Miƙewa Sameera tace
"Ko ruwa baka tsaya ka sha ba?"
Ya ce
"No na gode, ai daga gida na fito"
Daga an suka fice suka bar su.
Wayanshi ya zare bayan ya yiwa motar tashi key ya É—an zubawa Layin salim ido yana nazarin
abin da ke faruwa, Salim ya ce kar mamanshi ta san shi ya turo su, mamansu ta ce kar salim ya
san Afeefah bata da lafiya to me kenan? Ɗan shrugging Kafada yayi kan ya danna ƙiran salim
yana ficewa daga harabar gidan, kaman jira ko ringing na farko bai yi ba salim ya É—aga
"Ya ya jikin nata Dr.? Is it worst? Sai an tafi hoapital ko?"
"Calm down Captain jikin da sauƙi"
Nan ya shiga koro mishi bayanin yadda suka yi da mommyn. Numfashi ya sauƙe bai wani ji
damuwarshi ya ragu ba don ya san da matuƙar wuya su bi ta kanta, roƙon Sulaiman yayi da
akan ya dinga zuwa yana duba masa ita kaman yadda yayi alkawari.
Yana dan murmushi yace
"ba ka da matsala in shaa Allahu"
"Thank you so very much Doctor"
"ÆŠo not mention"
Daga nan suka ajiye wayar.
"Oh ashe wannan baiwar Allahn aiki take gidan su salim É—in?"
Baaba tayi maganan da alama dai har yanzu tana jimamin yadda suka tafi suka bar Afeefah É—in.
"Ni ma sai yau nake fahimtar hakan Baaba, kaman kuma mutanen gidan ba su É—auki
ma'aikatan su da muhimmanci ba"
Ta É—an juya kai cikin manyanta tace
"ko kuma ita Afeefar ce ba su É—auke ta mutum ba ba"
Ajiyar zuciya ya sauƙe daga nan bai sake magana ba itama haka har suka isa gida, ta sauka
kenan yana shirin ƙarasar da motan parking space ta juyo ta kira shi
"Alhj ƙarami Don Allah idan za ka koma da dare ko ban bi ka ba zan baka kunun gyaɗa ka kai
mata kila ta iya shan shi"
Ya amsa da
"Toh Baaba Allah ya kaimu dare É—in"
Ya ƙarasa da motan yayi parking kan ya nufi cikin gidan shi ma don bashi da aiki da safen sai
dare za shi asibitin ya kwana, Salim ne ya fitar dashi dole.
Da misalin ƙarfe bakwai na dare ya fito a shirye tsaf cikin kananun kaya da suka amshi kalarshi
na baƙi, skin ɗin shi da yake kalkalewa tamkar mace sai shining yake don shi mutum ne mai
tsananin tsafta, hannun shi rike da ninkakken labcoat É—in shi, mahaifiyarshi Hajiya Amina da ke
zaune cikin kujera ta É—aga kai ta kalleshi
"An fito kenan bokan Turai?"
Yayi murmushi yana furta
"Eh umma zan fara bi gidan su saleem akwai patient da zan duba kan na wuce asibitin"
"A'ah ko dai wacce Baaba jummai ke ta jajenta tun safe?"
"Ita fa Umma da safe mun fita kina bacci, ko da na dawo ban leƙo ba ashe Baaba kam tayi ta
baki labarin Afeefah"
Tana murmushi tace
"Ai ina ga zuwa yanzu kowa ya san labarinta a gidan nan, Allah ubangiji ya bata lafiya. Sai ka
leƙa kitchen ta yi mata kunu da ferfesu ka karɓa ka tafi mata dashi"
Yayi murmushi kan ya amsa yana nufan kitchen É—in baabar tana side É—in su bai neme ta bane
saboda ba gida zai dawo ba daga chan asibiti zai wuce shiyasa ma bai ba kanshi wahalar
neman ta ba don sai yayi mata dogon bayani da kyar ta fahimce shi, kwando ne mai kyau da
tsari ta shirya mata komai ciki, ya dauka kawai ya fito yana yi wa Ummarshi sallama take sanar
mishi Abban su yace ta sanar mishi lallai lallai yana son ganinshi da safe saboda kullum a
saɓani suke.
Ko da ya isa gidan su saleem a mota ya cigaba da zama yana tunanin yadda zai nemi iso don
bai ga gilmawan kowa ba, sai time yake dubawa ganin zai iya makara ya sa ya sauka ya nufi
mudi dake zaune bakin gate da iliya.
"Assalamu Alaikum warahmatullah"
Yayi musu sallamar yana sake miƙa mishi hannu duk da sun gaisa Shigowar shi
"Don Allah ku dan yi haƙuri zan shiga lokacin aikin ku, Afeefah nake son gani ko za ka min iso?"
Shiru suka yi cikin tunanin wacece ma Afeefah a gidan, a tare suka tuna ta sai suka kalli juna
suna zazzaro ido, mudi ya ce
"A'a malam sai dai ko in nema maka Talatuwa ta maka iso amma mu kam magana ma da
wacce ka ambata ya haramta tsakanin mu har Abada"
Ya ƙarasa cikin yanayin jimami da tabbatarwa iliya ma na gyaɗa kai tabbacin hakan ne.
"Magana ya taɓa haramtuwa tsakanin musulmi da musulmi kuwa Malam mai gadi?"
Yayi maganan yana É—an dariyar yadda suke reacting.
"Kai dai in ana sallah ba'a magana"
Iliya ya faÉ—a, tuni mudi ya nufi ciki ta baya ya bi ya tsaya daga kofan mashigan kitchen É—in
"Talatuwa akwai wadda ke neman iso wurin yarinyar nan mai wanke-wanke zo ki ji da shi"
Sameera da ke shigowa kitchen É—in ta É—an yi jimmm kan tace
"Talatuwa ci gaba da aikin bari na je"
Da kallo Talatuwa ta bi ta har ta ɓace, sai da ta koma ɗaki ta dubi kanta ta kuma ƙara turare kan
ta fito ta nufi waje, Sulaiman na ta bugar cikinsu don ya ji dalilin rashin mata magana kuma wai
na har abada dole ya sa suka shiga bashi labarin abin da saleem yayi musu, Sossai Sulaiman
ke dariya... Tahowar Sameera ta wani zuba mishi idanu tana tsintar kanta da murmushi.
Kallon farko da ta mishi ya tafi da imaninta, ya shiga ranta fiye da yadda tarin samarin da suke
bibiyar ta, a yanzu da ta ci karo da shi yana dariyar nan kuma sai taji tana narkewa, zuciyarta
na wani irin macewa a kanshi, ganinta ya sa ya tsagaita dariyar shi, ta shiga gaishe shi ya amsa
yana murmushi
"Whats so funny haka Dr.?"
"Ki bari kawai ni da su mudi ne, zan iya shiga?"
Ta É—an yi farrr
"Sauri kake haka?"
Ya É—an duba time a agogon dake É—aure bisa tsintsiyar hannun shi
"Kusan hakan don kaman na shiga lokacin aikina"
Ya ƙarasa yana nufar mota, ta bishi suka jera.
"Ai ma kuna ƙoƙari SLT nake karantawa amma ji nake kaman na gudu bare likitance da
aikinshi"
Ya É—an yi dariya bai ce komai ba, ta tsaya tana kallonshi har ya buÉ—e booth ya É—auki kyakyawar
basjet da Baaba jummai ta shirya mata kunu da ferfesu É—in kayan ciki da suka nuna suka yi
tuɓus cike da kayan kamshi, ganin basket ɗin sai da ya ba Sameera haushi amma ta danne, ta
sake ganin ƙatuwar leda sai zuciyarta ya shiga tambayarta Anya alaƙar nan na likita da marar
lafiya ne ko akwai abin da bata sani ba?
Amma me Afeefah take dashi da guy irin Sulaiman zai so ta? Dukda haka zuciyarta bai huta da
bugun tara-tara ba, kar dai ta faɗa soyayyar abin da ba za ta samu ba, ji tayi bata da ƙwarin
gwiwar bin shi don tabbas matukar ta bishi ta fahimci akwai alaqa tsakaninsu zuciyarta zai iya
bugawa ko ta shaƙe yarinyar har lahira, ba za ta iya bin shi ba sam bata da ƙwarin gwiwar. Ta
manta cewa kwata-kwata ma yau ne ta fara ganinshi har da zaƙewa haka, wayar ƙarya ta ƙirƙira
ya É—an kalleta
"Ka je Dr zan sameka"
Tana kai nan ta juya tana cigaba da magana a ƙarya, shi kam bai damu ba ya nufi ɗakin
Afeefah É—in a kan varender ya tsaya yayi knocking, a jiran da ya É—an yi ya fahimci maza ne cikin
ainihin Boys quaters É—in don ga wani murya na waya, kuma shine aka ajiye mace tare da su?
Sam tsarin bai mishi ba... Anan ne kuma ya shiga tuna hirar su iliya sai ya fahimci saleem yayi
hakan ne don ya bata kariya Dukda haka shi abin bai burge shi ba, ya juya ya kalli main building
na gidan, yanzu duk girman gidan nan a ce babu inda za'a ajiye Afeefah sai cikin maza?
Kimtatar lokaci yayi daga knocking da sallamar shi zuwa yanzu kan ya tura kofan ya shiga da
wani sallama again, ta lallaɓa ta tashi zaune ta sanya hijabi tana jingine da gini ƙafafunta na
cikin bargo
"Sannu da zuwa Dr"
Ta faɗa cikin sassanyar muryarta da ya ƙara ƙasa sossai.
"Sannu Afeefah ya jikin dai?"
Ya faÉ—a yana ajiye abubuwan hannunshi
"Da sauƙi"
Plate na safen nan ya ƙara gani a yadda aka ajiye da safe, wani tunani ne ya darsu a ranshi
hakan ya sa ya miƙa hannu ya buɗe ga mamakin shi abincin nan na safe ne still zaune cikin
plate É—in, bata ci ba don ko da Talatuwa ta shigo ta duba ta ta É—auka ta tafi da shi don ta kawo
mata wani mommy ta koro ta akan ba za su yi almubazzaranci ba sai dai ta cinye shi kan a
saka mata wani.
"Afeefah tun safe baki ci komai ba?"
Da É—an tausayi haÉ—e da zafi yayi maganan ranshi na sosuwa kwarai.
Ta Yi shiru
"Ina za ki samu ƙarfin jiki idan ba kya cin komai? Ai ko mai azumi zuwa yanzu dai ya sha ruwa"
Tsam ya miƙe ya nufi bayin ta, ta lumshe ido bayan ya shige chan sai gashi ya fito da bowl
haÉ—e da brush ya bata, ruwan goran da ya shigo dasu ya buÉ—e bakin É—aya ya dinga zuba mata
tana wanke bakin sai da ta gama tsaf ya mayar yaje ya zubar, ya dawo ya tsuguna ya saka
mata peppersoup ɗin da kunun ya ajiye mata a kan kafafunta ɗayar hannunta na hagu ya miƙa
mata kofin kunun ta karɓa ta riƙe idanunta na kallon cikin bowl na psoup ɗin, sai turiri da kamshi
yake fitarwa.
"Oya ci yanzun nan, ko in baki da kaina?"
Ta girgiza kai ta sanya hannu ta dauki spoon É—in ta shiga sha, da kaÉ—an da kaÉ—an yana matsa
mata har ta sha dayawa ta sha kunun kuwa sossai, fruits da ya sayo mata ya kara mata da shi.
Ta marairaice
"Zan yi amai fa idan na ci, cikina ya cika"
"kin manta kina tare da likita? Ai aman ma tsorona yake ji Harara É—aya tak zan mishi ya koma"
Ta saki murmushi karo na farko da har hakwaranta suka bayyana, ta sanya hannu ta karɓi
ayaban da ya bare mata.
Magungunan ta ya duba ya haÉ—a Allura yayi mata a canular tana ta wash wash ya ce
"Wato É—azu ma saboda bakya hayyacinki ne kika manta da raki ko?"
Ta duƙar da kai, wayanta ne yayi haske ya ɗauko ya duba
"Saleemullah ne yayi miki saƙo in karanta miki?"
Ta girgiza kai alamun A'a.
"Zan duba anjima"
Ya gyaÉ—a kai ya shiga Phone ya sanya Layin shi yayi flashing kan yayi saving da
"Dr. Sulaiman"
"karɓi, zan zo gobe da safe duk abin da kika ji kina so ko sha'awa just give me a call za ki samu
kin ji?"
"Toh Dr na gode"
Yayi saurin cewa
"Yanzu kam na wuce wannan matsayin tunda har jinyarki kika saka ni a bati"
Tayi dariya kuma da gaskiyar shi don ta mugun samun ƙwarin jiki, da Allah bai turo mata shi ba
haka za ta kwana don ba zata iya cin abincin safen ba.
Sallama yayi mata ya fice don ya makara yau kam ainun.
Sameera da ke tsaye jikin Window tun ɗazu ta ƙura mishi ido tana jin zafi a ranta, idan ta
kimtata daidai mintunanshi Arba'in da biyar a É—akin yarinyar me ya ajiye shi haka? Har zafi zafi
take ji a idanunta shi kam da bai san ma tana yi ba tuni ya shiga motar shi ya bar gidan.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*015*
Ta ɓangaren Afeefah Dr. Na tafiya ta janyo wayan, number Dr. Sulaiman shi ne number na biyu
da ya shiga wayanta murmushi ta ɗan yi bayan ta buɗe sakon Saleem. Kusan saƙon shin na
ashirin da wani abu kenan a ranar.
"Ya jikin? Kin ji sauƙi? Kin ci abinci? Don Allah kar ki zauna da yunwa ki ci ko kaɗan ne, ko
akwai abin da kike so in sa a kawo miki?"
Saƙonnin kenan masu dauke da kulawa.
A yanzu ma emphasizing yake akan ta ci wani abu cike da damuwa ƙarara a kalaman nashi duk
ya damu, rubutu ta fara a hankali
"Na Ci abinci kuma na ji sauƙi sossai ka kwantar da hankalinka ka ji Ya Saleem?"
Numfashi mai nauyi ya sauƙe a sadda saƙon ya riskeshi matsalar shi ko ya baro Maiduguri ya
dawo Kaduna a yau bashi da damar bata kulawa yadda ya dace hakan na damun zuciyarshi
ƙwarai da gaske.
"Alhamdulillah! Yanzu ni ma zan iya saka wani abu a baki na, na gode Afeefah. Ki kular min da
kan ki sossai in akwai wani damuwa kar ki yi ƙasa a gwiwa wurin sanar min"
Hawaye ne suka cika idanunta, me yasa zuciyarta ba za ta karye a kan saleem ba? Shi ne
mutum na biyu da ya karɓe ta a yadda take, bai damu da maganganun mutane ba, ya ba ta
kariya daga cutarwa ya ɗauko ta ɗaga kan titi ya kawo ta gidan su, yana iya ƙoƙarin shi wurin
ganin bata zubar da hawaye ba, bata san da me za ta saka mishi ba bata ma da abin saka
mishin da ya wuce Adu'a, har ranta take jin duk abin da mahaifiyarshi da ƙannenshi za su yi
mata in har akwai hakkinta ta yafe musu ba za ta taɓa rike su ba saboda salim ya wuce wannan
gaɓa a rayuwarta.
"Ka ci sossai har da sauran kaso na, sai da safe"
Tana kai nan ta kife wayar tare da kwanciya don da Talatuwa ta shigo ɗazu ta roƙe ta ta kawo
mata ruwan dumi tayi alwala, da alwalar tayi ta sallolinta daga zauna saboda jiri da baya barin
ta ta tashi.
Ta ɓangaren Sameera wani tsanar Afeefar ya sake cika zuciyarta, tunanin matakin da za ta
É—auka a kanta take yi, ko ta je tayiwa Afeefar gargaÉ—i akan kula Dr ne? Wani zuciyar yace
yanzu duk abin da fushi ya dibe ki kika yi mata tsautsayi ya faÉ—a kanki a bata da lafiyan nan ai
kin kaÉ—e, gwara ta warke first a haka dai da nauyin zuciya ta kwanta tana ta juye-juye cike da
haushi da tsanar Afeefah da tayi sanadiyar kasa baccinta a daren.
Kaman yadda Dr. Sulaiman ya yi alƙawari bayan ya tashi aiki da safen wanka kawai yayi ko
hutawa bai yi ba ya ɗauki Baaba jummai don yana so ta yini wa Afeefar kila jikin ya sake ƙarfi
idan ta ga mutum kusa da ita, sam baya so abin da ya faru jiya ya faru yau hakan ma ya sa
yayiwa Baaban umurnin shirya mata duk wani abu da ta san bakin marar lafiya zai so da basket
mai girma suka nufi gidan, ba su wani nemi iso ba suka zagaya zuwa sashen Boys quaters É—in
ya bar Baaba ta soma shiga.
Afeefar ta ji ƙarfin jikin nata sossai musamman da ta samu baccin dare mai nauyin gaske, ta
samu ta lallaɓa ta watsa ruwa ta ɗan kimtsa ɗakin tana sanye da peach abaya ta ɗaura gyalen
a kanta, ganin Baaba ya sa farin cikinta bayyanuwa ainun, Baaba ma tana murmushi take cewa
"Ah jiki ya yi kyau Alhamdulillah"
"Sannu da zuwa Baaba"
"Sannu Afeefah, ya jikin dai? Kin ga kan gaisuwar nan bari na shigo da Alhj ƙarami ya miki
alluranki yana sauri zai je ya kwanta idan ba haka ba yanzu za ki ga ya kama ciwon kai da baya
ƙarewa ta daaɗi"
Afeefah murmushi kawai tayi Baaba ta fice seconds kaÉ—an sai ga su, Afeefar ta warware gyalen
ta ta yafa bisa kanta, babu hula a kan hakan ya sa tsantsin gashinta ke ta zamar da gyalen tana
gyarawa, gaishe shi ta shiga yi yana amsawa idanunshi na a kanta yana yaba yadda jikin ya
fara kyau, Alluran ya haÉ—a yayi mata yau kam ma rakin ya fi na jiya, don akwai pcm kuma babu
ruwan diluting hakan ya sa yayi mata a hankali yana yi mata sannu don zafin shi.
Bai jima sossai ba ya tafi ya bar su da Baaba da ta zage ta ƙarasa gyaran ɗakin ya fita fess ta
bata abinci tana ci suna 'yar hira bayan ta gama ma ta miƙe kwance suna cigaba da hirarsu tun
tana amsawa baaban har bacci yayi awon gaba da ita.
Shi Sulaiman yana isa gida ya ga Abbanshi tsaye suna magana da mai gadi, idanunshi ya É—an
runtse gabanshi na É—an faÉ—uwa yau dai Abba ya kama shi, bai so ya dawo ya haÉ—u da Abban
ba Dukda Umma ta gayamishi Abban na son ganinshi ya dai san tatsuniyar gizo bata wuce ta
koki kuma shi kaman har yanzu bai shirya ba, haka dai ya sauƙa yana ɗan shafa kai ya matso
su suka sake gaisawa da mai gadin a lokacin sun gama magana da Abban ya juya ya wuce.
"Za ka shafa kai ai Sulaiman, wai Hausawa suka ce in kere na yawo zabo na yawo watarana
dole a haÉ—u"
"Barka da safiya Abba"
Yayi gaisuwan a kunyace yana yar dariyar maganan Abban.
"Barka dai Sulaiman ya aikin?"
"Alhamdulillah Abba"
"Toh ina magananmu ta kwana? Ka dai san na gama ɗaga maka ƙafa ko? Na fa gaji da ciyar da
tuzuru don ka fi ƙarfin gauro"
Abban na murmushi ya ƙarasa maganan
Sulaiman Dariya yayi yace
"Soon Abba in shaa Allah"
"bari na gaji da Soon É—in nan naka za ka sha mamaki, dama akwai yaran abokai da dangi da
duk na yarda na kuma gamsu da nasaba da tarbiyar su sai dai ka ji an saka maka rana, kar ka
ga ina murmushi Sulaiman wannan ne last chance É—inka, wai kai ko kunya baka ji? Kannenka
duk sun tara 'ya'ya maza da mata kana zaune abin ka?"
Har lokacin murmushi yake, ya matukar sanin mahaifinshi Alhj Abdulrasheed mutum ne mai
saukin kai da sauƙin hali Dukda tarin kudin da Allah ya bashi, ɗan kasuwa ne da har yanzu bai
daina nema ba daga shi har yaranshi suna da sauƙin hali da kyautata mu'amala da duk wanda
hakan ya haÉ—a su.
"In shaa Allahu Abba za ka ji alkhairi i promise"
"I hope so, yanzu kake dawowa daga aikin kenan?"
"A'a Abba, na dawo da wuri na É—an je na duba wata patient É—ina ne a gida na ba ta medication"
"Toh yayi kyau, a je a huta Allah ya taimaka"
Ya amsa da Ameen yana jera wa mahaifin nashi adu'ar ƙara girma da lafiya ya wuce ɗaki, haka
kawai yake tsintar fuskar Afeefah a idanunshi idanunta, murmushinta da ma sassanyar
muryarta na dawo mishi kaman a yanzu take yi mishi, lumshe ido yayi yana sauke ajiyar
zuciya...
Kaman wasa fa sabo ya fara shiga tsakaninsu da Dr. Sulaiman kachokan yake bata dukkan
kulawar shi ya kan zo kullum sau biyo har saida duka alluran ta suka ƙare, kuma bai taɓa
shigowa hannu banza ba har ta kan rasa waye ya fi wani damuwa da ita tsakanin shi da saleem
da bai taɓa hutawa da yi mata saƙo ba, ko da ta samu sauƙi ta komawa aikinta sai Sulaiman ya
cigaba da ƙiran ta tun suna gaisawa kawai su yi sallama ya fara jan ta da hira da wasa.
Yau tun safe jikinta ke a matuƙar mace, saƙon saleem ya shigar da ita rudani da damuwa marar
misaltuwa Dukda ta tsammaci hakan sai dai ya daketa fiye da zato.
Sallar asuba ta farka tana buɗe idanunta ta sauƙa tayi alwala ta zo ta gabatar da shafa'i da
wutiri kan ta miƙa sallah, tana idarwa ta janyo wayan don karatu yadda ta saba sai ta ga
pending message, buɗewa tayi ta ga ƙarfe 2 da 'yan mintuna gabanta ne ya ɗan faɗi me yasa
saleem zai mata saƙo tsakiyar dare? Composing kanta tayi ta buɗe tana karantawa hawaye na
silalo mata
"Afeefah na san a lokacin da za ki ga wannan duniyarki za ta sake shiga rudani fiye da yadda
take ciki a yanzu, na san tsoro zai mamaye zuciyarki, na san za ki yi tunanin anya saleem na
cikin hankalinshi kuwa ya turo wannan saƙo? Toh duk lafiya ta ƙalau kuma ina cikin hayyacina
hasali ma tunani da matsuwar zuciya akan fallasa sirrin ta su suka hana ni bacci har kawo
wannan lokaci, Afeefah na kasa hana zuciyata ƙaunarki... Zuciyata ta kamu da Soyayyar ki ba
na wasa ba, wallahi Soyayyata a gareki gaskiya ce, kuma ta ginu ne daga tushen tausayi
Afeefah ina ƙaunarki fiye da yadda zan furta miki"
Kuka kawai ta fashe dashi tana haÉ—a kanta da gwiwa, wani sabon al'amari ne kuma ke shirin
shigowa rayuwarta? A sadda take karanta sakon Saleem duk wani tsika na jikinta sai da ya
tashi, zuciyarta kaman zai Faso kirjinta ya fito Dukda ta jima da tsammatar hakan sai dai bata
kawo hakan kusa ba, ba tsoron ta soyayyar shi ba tsoronta danginshi ta ina za ta fara son
saleem? Ta yaya?
Ta san saleem duk inda mace take neman nagartaccen namiji ya kai har ma ya wuce abin
tambayar mahaifiyarshi da 'yan uwanshi za su karɓi uzurinshi? Ta Tabbatar muddin suka ji
cewa salim na son ta zamanta a gidan ya zo ƙarshe kenan to in sun kore ta ina zata je? Ko da
ta koshi da kukan ta fito ta ƙarewa gidan kallo sai taji ma har wacece ita da namiji kaman
saleem zai so ta? Har wacece ita da za ta yi mafarkin rayuwa da saleem? Ai ko da girgiza
kanya ta fi magarya zaƙi.
Jiki a sabule ta gama dukkanin ayyukan ta, ko da ta dawo ɗakin ta sake samun sabon saƙon
saleem.
"Afeefah na san na saka ki a rudani sai dai nima na rasa mafita ne, wallahi ban san sadda
soyayyar ki ta samu matsuguni haka a zuciyata ba, ba ni da iko da ita bare har in hana ta. Don
Allah kar ki yi kuka kuma kar ki firgita idan ba kya so ba zan tilasta ki ba don wallahi na fi kaunar
farin cikinki da nawa farin cikin, kar wannan dalili ya sa ki ja baya da ni kawai na sauƙe wani
nauyi ne da nake jin ya zame min dole na sauƙe, ina sake sanar da ke cewa Na so ki jiya, na so
ki yau, zan cigaba kuma da son ki har zuwa gobe sannan zan cigaba da son ki kowace rana"
Numfashi mai nauyi ta sauƙe hannunta har rawa yake, hawaye kuwa ya fi pampo zuba a
fuskanta, ita dai da bad luck aka halliceta mugun tabo da shaidar ta zai cigaba da bibiyar ta har
abada, a yau anan ba wani ne ya mutu ba amma tambarinta shi ya ja mata tsanar da ba zai
taɓa sanyawa mommy ta amince da ita a matsayin surka ba ko tana mutuwa tana farkawa
kuwa.
Bata san yadda yake ji a ranshi ba amma ta san abin da zai hana shi sukuni haka babba ne, ba
za ta bari salim yayi kuka saboda ita ba don haka a hankali ta rubuta
"Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alkhairi"
Lumshe ido yayi daga ɓangaren shi, shi karan kanshi tsoron yake ji, amma ya zai yi?
Kalamai ya cigaba da mata na kwantar da hankali gabaÉ—aya yinin, ganin ya damu sai ta danne
nata damuwar ta nuna mishi bata da matsalar komai kuma a shirye take da duk abin da zai je
ya dawo, ta san bata da wannan ƙwarin gwiwar amma da shi kila komai ya zo da sauƙi.
Washegari da yamma tana zaune tana karatun alqur'ani kawai ta ga saƙon shi
"Hey dear zan dawo gobe, me kike so na taho miki da shi?"
Ta karanta text message É—in ya fi sau uku zuciyarta haka kawai ya shiga bugawa amma ta dake
ta rubuta
"Ka fi kowa sanin abin da ya fi cacanta da ni, duk abin da ka kawo ba zan ƙi farin ciki ba"
Murmushi mai kyau ya saki, yana Fatan kasantuwar alaƙarsu na har Abada yana fata da Adu'a
akan muddin ya fito fili komai ya zo mishi da sauƙi don babu yadda ya iya da abin da zuciya
take so.
A Washegarin duk iyalan gidan suka shiga shirin tarbar breadwinner É—in su, hidima kawai ake
don a wannan karo ya É—an jima bai zo ba, dab la'asar ta gama wanke-wanke tana shirin shiga
wanka ta ji wayanta na ringing, ta san Sulaiman ne don shi kaÉ—ai yake kiran ta sai kuma saleem
da yake mata text message, dagawa tayi tare da sallama ta shiga gaishe shi, ya amsa cike da
wasa kaman yadda yake mata tamkar 'yar baby ya É—auke ta.
"Yau dai haka kawai na ji ina son ganinki har mafarkinki na yi fa da na yi baccin rana, zan tafi
office da yamman nan idan kin ba ni dama in biyo in kalle ki ko kaÉ—an?"
Ta ɗan sauke numfashi a ɓoye a hankali tace
"Ni na isa hana ka?"
Da É—an murmushi yace
"A'a ai na zaci za'a yi min rowan wannan beautiful and innocent face É—in ne"
Tace hmmm, wani zuciyar na ce mata kila fa shima in da ya san wacece ita ba zai raɓeta ba.
"Sai ka zo, a gaisar min da Baaba please"
"Banda ummana?"
Yayi maganan a hankali, tayi murmushi
"har da ita fa Dr. Da ma kowa da kowa"
"Toh wa zan ce mata tana gaisheta?"
"Afeefah mana?"
Ta faÉ—a tana 'yar dariya murya a karye, shi ma murmushi kawai yayi ya yanke call É—in.
Wankanta ta shiga a gaban madubi ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo, sossai ta ƙara ganin
chanzawarta ba'a tsawo ba don dama chan ita É—in doguwar mace ce, sai dai ta É—an kara kauri
saɓanin da da take lange-lange kuma fatar ta ya kara wani irin kyau da sheki, mutane dayawa
su kan yabi kyaun fatarta musamman a zamanta da Aunty zee amma bata taɓa yarda fatar mai
kyau bane kaman yanzu, ta buɗe sossai daga ƙasa sai dai saman babu wani auki tsarin jikin sai
ya bata wannan figuren da ake cewa coca-cola, a sadda take Dutsen-wai bata taɓa kawo ko a
mafarki za ta auru ba amma da ta dawo Anchau Dukda jita-jitar da ake yadawa a kanta hakan
bai hana wasu tararta da sunan So ba amsar ta dai karatu ne a gabanta, ta kuma san ko ta
amince da wuya ne a haifi da mai ido musamman ga 'yan uwa da abokan arzikin wanda za ta
amincewar, a yanzu kuwa da babu halin karatun muddin ta cigaba da zama a gidan tana jin za
ta so matsawa wani environment É—in inda za ta samu so a yadda take kuma a bata rayuwa
ingantacciya, amma Saleem shi ne namijin da zuciyarta ta fara aminta dashi don ya yi mata
abin da kuɗi ko godiya ba za su taɓa biyan shi ba.
Tana wanka haka kawai tana hawaye, tana ji a ranta matuƙar komai ya bayyana kwaɓarsu za ta
yi ruwa ba na wasa ba, kuma wa'adin zamanta a gidan ya ƙare, amma in ta saurari Sulaiman
fa?
Sulaiman bai san asalin ta ba, bai san tarihi da mugun tabon ta ba idan ya sani kila shi ma
iyayenshi ba za su taɓa karɓar ta ba. Da wannan tunani da damuwar ta fito daga wankan.
Man shafawar da Sulaiman ne ya kawo mata haÉ—e da wasu dogayen riguna inda yake ce mata
babu abin da ke karbarta kaman dogayen riguna ko don bai taɓa ganinta da lace ko atampha
bane amma tana matukar tafiya da tunanin shi in ta saka su shi ta shafa, ta É—auki wani maroon
Abaya da ya sake fito da kyaun skin ɗinta cikinsu ta saka, ta ɗan fesa turare tare da man leɓe
kaɗan, mayafi ta yafa daidai Sulaiman na ƙara kiranta a kan ya zo.
Shi kuwa Sulaiman a sadda ya gama shiryawa ya fito parlorn ya ci karo da mahaifiyarshi da
ƙannenshi.
"Sai ina Ya Sulaiman?"
ÆŠayar ta faÉ—a.
"Ina ruwan ki? Sa ido...."
Ya faÉ—a yana hararanta.
Wacce suke tsananin kama da wacce suka yi maganan da farko tace
"Sana'ar banza ba, ai yaya ka fita sabgar fa'iza ta cika saka ido. In zo in raka ka ne?"
"Kema bana so gulmatu"
Dariya suka sheke da shi ganin yadda ya ke hararinsu. Tsaki ya ja
"Umma na tafi"
"A gaishe min da surkar tawa"
Narkewa yayi
"umma wai har da ke a biye wa waennan yaran?"
Ta Yi dariya tana cewa
"Sai dai ka dawo"
Ya fice abin shi a jikin mota ya tsaya yana kokarin shiga sai ga Fauza ta miƙa mishi wani leda
wai in ji Umma ya kai mata, yayi murmushi ya karɓa kawai bai ce komai ba.
Gidansu akwai sauƙin hali da haɗin kai shi ne babba, yana da imediate kanwa da tayi aure sai
wani namiji kafin twins É—in nan mata biyu, mahaifinshi fitaccen É—an kasuwa ne inda
mahaifiyarshi ke aiki da federal government, ba su taɓa raina talaka ko ya yake musamman
Sulaiman da shi ko na kasa da shi ya kan girmama, babu mai cewa ga wani tambari nashi ko
hali marar kyau Dukda kowani mutum tara yake bai cika goma ba.
Sai da ya biya ya kara mata sayayya akan na Umma kaman koyaushe matukar zai je wurinta
bai taɓa zuwa hannu banza ba ya nufi gidan, bayan yayi parking ya ƙira ta, Bata kai ga fitowa
ba aka wangale Gate É—in gidan Motar Ryan ta kutso kai ciki a hankali...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*016*
Kaman yadda ƙa'idarsa take ba ya hanzari ko gaggawa a koma menene sai ya sha Ƙamshin
nan dai wane saraki haka a yanzu ma, sai da saleem dake sanye da khakin sojoji full 6/6 don
hatta agogon da Ke ɗaure a tsintsiyar hannunshi da ƙatuwar backpack na bayanshi duk na
sojojin ne ya sauƙo kan ya buɗe motar ya sanyo jiki.
Yau sanye yake da wata farar kaftan da aka yi wa ɗinkin zamani ya matuƙar zauna mishi kuma
farar fatarshi ya ƙara haskaka, daga takalmi har agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi
farare ne, kanshi babu hula sai kwantaccen gashin shi na ainihin Fulanin asali da ke sheƙi,
ganin Dr Sulaiman ya É—an ba saleem mamaki shi ma kuma Sulaiman ganin su ya sa ya taso
daga jikin motar shi ya isko su Saleem ya fara miƙawa hannu fuska a sake suka gaisa kan ya
miƙawa Ryan shi ma ya karɓa suka gaisa cikin 'yar nuna sanayya amma fuskar nan kadaran
hadaran.
Magana suka cigaba da yi da salim da ta shafi Lafiyar Afeefah shi dai Rayyan tun da suka gaisa
ya zaro wayanshi ya kuma mayar da hankalinshi kai don hirarsu ba huruminshi bane.
Tun da ta hango su gabanta ya yanke ya faÉ—i, abin da za ta cewa saleem ya kawo Sulaiman
gidan ke ta kai komo a ranta, tafiya take tamkar hawainiya saboda bugun zuciya, su ukun duka
kwarjininsu ya wani rufe ta tun kan ta iso inda su ke, Zaratan samarin masu jini a jika cikakkun
maza kuma kamilallu, kowanne kuma gwani ne a nashi fagen kyaun da kamala.
Ji ta yi kafafunta ba za su iya daukar ta ba a sadda mai fararen kayan ya É—ago idanu suka shige
zuruf cikin nata.
"Rayyan!"
Sunan ya yi ringing da matukar ƙarfi a kwakwalwarta, wannan idanu ba za ta taɓa manta shi ba
tuni ya mayar da kanshi kan wayanshi amma ita ta daskare ta kasa motsa kowani gaɓa na
jikinta, idanunshi sun fi yanayi da na maguna kwayar wani surkin kala ne da kan rikita lissafin
duk wadda ya zubawa su, ƙasan lid ɗin tamkar an zana mishi kwalli zirrr baƙi sidik hakan sai ya
kara saka idanun zama na daban da sauran mutane, idan idanun suna duƙe za ka zaci a rufe
suke saboda tsawon lashes ɗin sa ga su baƙake kaman gashin kansa da na girarsa.
"Afeefah!!"
Saleem ya faÉ—a da É—an karfi a karo na uku, firgigit tayi ta dawo hayyacinta.
"Ƙaraso mana kin tsaya daga chan"
Bai sake magana ba har ta ƙaraso inda suke daga shi har Sulaiman idanunsu na a kanta.
Da kyar ta iya buÉ—e baki tace
"Sannu da isowa Ya Saleem"
"yauwa Afeefah"
"Ina yini?"
Kai kawai ya É—an gyaÉ—a mata hakan ya sanar da ita cewa lokacin da ya kamata yayi magana da
ita ya wuce.
"Yaya Sulaiman ina yini?"
Muryarta da ya karye ya ƙara sanyaya yana fitowa a slow, ɗago ido Ryan yayi ya kalleta daidai
tana ce mishi shima Ina yini? Ya kau da kai kaman bai gane da shi take ba, daga shi har
saleem sun fahimci chanzawar muryarta, shi Ryan kam ma mamaki ne fal ranshi don a yanzu
abin da ya sa ya sake kallonta tuna abin da saleem ya gama faÉ—a mishi bayan ya É—auko shi
daga Airport wai son yarinyar nan yake, in ba janyowa kai raini ba shi bai ga abin ba ya tabbatar
a auren ƙauye sun kusa ajiye irin ta. Tsaki ya ja a fili yana furta
"Man we talk later!"
Ya faÉ—a cikin muryarshi mai cike da ginshira sai Muryar ya bata tsoro ta tuna ranar da yake
daka mata tsawa da hanzari ta ɗago idanu ta sake kallonshi, ya miƙawa Sulaiman tender
fingers É—in shi da kaman zai fidda jini don haske da taushi suka yi musabaha, yana kokarin
buÉ—e mota idanunshi suka sake shige wa cikin nata, daga ita har shi suka yi saurin kawar da
idanun ya shige ya ja ya bar gidan.
Saleem ya dubi Sulaiman ya ce
"Nima kaman zan shiga daga ciki jikina kaman an min duka"
Sulaiman na murmushi yace
"Ai dole, a huta gajiya mazan fama"
Suka yi musabaha kan ya nufi ciki, ya zaci Afeefah ma za ta yi wa Sulaiman É—in sallama ta biyo
bayanshi sai ya É—an waiga nan ya ga sun matsa jikin motar Sulaiman É—in yana mata magana a
hankali ita kuma tana dariya, tuni duk wani walwalar fuskarshi ta kau, ranshi ya shiga suya bai
iya ya shiga main parlorn ba ya bi ta baya ya haye sashenshi, backpack É—in kawai ya ajiye ko
zama ya kasa yi ya dawo jikin Window yana kallonsu, kusan mintuna talatin suka yi suna hira
kan ya ga Sulaiman ya buɗe mota ya fiddo wasu ledoji ya miƙa mata.
"Ga shi umma wai na kawo miki"
Tayi murmushi mai kyau cike da jin daaÉ—i tace
"Allah sarki umma, ka yi mata godiya na ji daaÉ—i sossai Allah ubangiji ya kara girma da lafiya"
Wayanshi ya zaro yana furta
"Ko kuma ki yi mata da kan ki ba"
Ido ta zaro kan ta yi magana ya shiga ƙiran ummar, bayan ta ɗaga da sallama ya ce
"Ummar mu ga Afeefah tana so ta miki godiya"
Kaman za ta nitse haka ta karɓa ta shiga gaisheta tana yi mata godiya, Albarka Ummar tayi ta
sanya mata kan suka yi sallama ta miƙa mishi wayar tana ɗan tura baki na fushin yadda ya
saka ta jin kunya, murmushi yayi
"Kar ki sa na narke fah Afeefah"
Tayi murmushi
Ya miƙa mata wani leda mai girma da farko kin karɓa tayi sai dai da ya matsa ta karɓa ɗin tare
da godiya suka yi sallama ta nufo ciki.
Da hanzari Saleem ya ɗauko wayanshi ba ta ko kai ga shiga ɗakinta ba ta ga saƙon shi
"Menene ke tsakani ki da Sulaiman?"
Muƙut haka ta haɗiye wani miyau kaman yana gabanta, da sauri ta shige ɗakin ta ajiye ledar
tare da zame mayafinta ta jefa kan katifa ta fara safa da marwa cikin tunanin amsar da za ta
bashi, sam bata so yayi fushi da ita da kyar ta iya rubuta mishi
"Babu kawai kyautatawa ce da suke min shi da ahalinshi"
Shiru ba reply, ta san ba wai ya yarda bane kuma kila shirun nan da ya yi fushi yayi, ta kasa
zaune ta kasa tsaye haka ta yi ta saƙe-saƙe ita kaɗai, ƙiran Magrib ne ya katse ta jiki a sanyaye
ta shiga bayi tayo alwala ta zo ta gabatar da sallah ta zauna nan tana karatu.
Sulaiman kasa zuwa office yayi haka kawai yake sake tariyo kallon da saleem ke yiwa Afeefah,
ji yayi ko ya je office ba zai taɓuka komai ba yana buƙatar shawara da mahaifiyarshi don tamkar
ƙawarshi haka take.
"Wash Allah na!"
Ya faÉ—a yana kwantar da kanshi a kan kafafunta, ta sa hannu ta shafa sumanshi
"Ya dai likita?"
"kawai gajiya ne umma"
"faÉ—amin gaskiya ko dai kai da surkar tawa ne?"
Ya É—an yi shiru kan ya ce
"Ina tunanin umma saleem na son Afeefah, ko dai ita bata sani ba ko kuma ta sani tana min
wasa da hankali ne"
"Saleem shi ne É—an masu gidan da take aiki?"
Kai ya gyaÉ—a mata
"Kuma Baaba ta tabbatar min kaman yarinyar tana shan wahalan gidan aiki haka ne?"
Nan ma ya gyaÉ—a kai fuskar shi babu walwala
"Kaman saleem É—in ne kawai yake taimaka mata, kuma kaman ba ta da kowa don dole ne
kawai take zaune gidan"
"Ka kwantar da hankalinka Sulaiman, kila ba soyayyar ba ce tsakaninsu sai kyautatawa don ya
na tausayinta, kila kuma yana son ta É—in amma yana tsoron bayyana mata don iyayenshi, zai
ma iya yiwuwa ya sanar mata ɗin amma ta ƙi bashi haɗin kai don babu macen da za ta yi
kuskuren jefa kanta inda ta san ba'a ƙaunarta ko kuma inda za ta sha wahala"
Numfashi ya sauƙe
"Umma haka kawai nake jin kaman ba zan sameta ba"
"Ka cigaba da kyautata mata domin zuciya tana son mai kyautata mata, idan har matarka ce za
ka aureta, ni ma zan so ka sameta don na tabbatar wacce ta iya mallake zuciyar My Son ba
ƙaramar nagartaccciyar mace ba ce"
Ya miƙe zaune yana murmushi
"Umma za ki fara taya autocinki zolaya ta ko?"
"Ai gaskiya ne sabon shiga, duk ka bar komai obvious sai gano ka muke yi dubi duk yadda ka
ruÉ—e daga sanin tana da wani saurayin"
Ta ƙarasa da dariya.
"Duk ba za ku gane bane umma ni dai na yi nan"
Yana ji tana cewa
"Toh zo ka ganar da mu mana"
Yayi murmushi kawai. Allah ya gani shi karan kanshi ba zai ce ga sadda ya fara jin son Afeefah
a ranshi ba, kawai dai ya san ta yi mishi kyau ranar da ya fara ganinta, sanyin muryarta idan
tayi magana sai yake jin tamkar ƙanƙara ake zuba mishi. Ko da ta bar asibitin bai wani sa hope
É—in sake ganinta ba amma daga ranar da ya je ya isketa cikin fitar hayyaci sai ya ji tamkar an
soki zuciyarshi da mashi barin ma da ya gama fahimtar tana shan wahalar rayuwa a gidan,
sannan ya san babban burin ta a rayuwa shi ne ta yi karatu ta zama wata public figure da za'a
yi alfahari da ita, kaman tana da wani ciwo ne da take jin ba zai taɓa warkewa ba har sai ta yi
nasara a duniyar ta, ba ya jin zai iya bar wa saleem ita za su buga wasa ne duk wanda ya iya
allonsa ya wanke.
A daren da misalin ƙarfe tara ya ƙira layinta, ta gama wanke-wanken dare kenan da yau yayi
yawa sossai saboda abincin da aka yi kalolin daban-daban, sai duba wayan take ko za ta ga
saƙon saleem don gabaɗaya ranta babu walwala, ko da suka haɗu ko kallonta bai yi ba kuma ta
sake mishi saƙo babu reply.
"Assalamu Alaikum warahmatullah"
A natse ya amsa
"Wa'alaikissalam gimbiyar mata"
Tayi ignoring sunan da ya ƙiratan
"Ka koma gida lafiya?"
"Da an damu da ni ai da an neme ni, ni da ya zama dole na ba gashi na kira ba. Ya kike?"
Har za tayi magana ya katse ta
"Wait!! Kina lafiya ko? Ya na ji muryarki duk cike da damuwa da rashin Walwala ba yadda na
bar ki ba?"
Ta É—an ja numfashi tana tafiya kwance daga zaunen da take jingine da gini.
"Kaina ke É—an ciwo"
"Eyyaa so sorry, kina da ORS?"
Ta girgiza kai tana amsawa da
"A'a"
"Ki sha pcm da safe zan zo in auna jinin ki sai in taho miki da ORS É—in, ciwon kai bashi da daaÉ—i
musamman ga ke da jininki sauƙa yake kuma kin san ya fi high BP hatsari"
Idanu kawai ta runtse bata san me zata ce ba tunda ta riga ta yi suɓutar baki ta ce kanta na
ciwo zuwa kam sai ya zo to kuma saleem da har yanzu bai sauko daga fushin É—azu ba fa?
"Kina ji na kuwa Afeefah?"
"Eh ina ji, na ce da ma ka barshi in na yi bacci zai daina"
"hmmm ke dai kawai in na zo ɗin zan ƙira ki, kwanta ki huta Allah ya baki lafiya"
Yana kai nan ya katse wayan ba ya so ta hana shi zuwa haka tayi ta juye-juye har bacci ya sure
ta.
Washegari tana gama goge-goge ko ɗaki bata koma ba sai ga ƙiran shi, gate kawai ta wuce
don ta karɓa da sauri kan saleem ya tashi ya ganta
"Sannu da zuwa"
"kin tashi lafiya?"
Yayi tambayar yana ƙare mata kallo, ita kam ko me ta saka kyau take mishi
"Alhamdulillah ya su umma?"
"Umma na gaishe ki da jiki ta ce in miki sannu"
"Na gode sossai"
Leda ya fitar ta zare ido, ko kayan jiya bata buÉ—e ba saboda damuwar fushin saleem da ita
yanzu kuma ya sake ciko leda? Shi kam ba ya gajiya ne?
"Hidimarka na yawa a gareni Dr. Na kan rasa kalaman godiya a gareka, wani lokacin sai in ji
tamkar ba na kyauta maka don ka fara ƙaunata tun ba ka san wacece ni ba! Ban san ya za ka
karɓeni ba a duk ranar da wani ya tare ka ya ce maka Afeefah annoba ce!"
Kallon bana fahimtar zantukan ki yake mata daidai saƙo ya shigo wayar ta sanin saleem ne ya
sa dole ta buɗe tana ta ƙoƙarin haɗiye kukan dake zuwar mata
"Ki sallame shi za mu yi magana"
Ta É—ago ta kalli Sulaiman da har lokacin idanunshi ke kanta.
"Zan shiga ciki za mu yi magana"
"Saleem É—in ne ya ce ki sallameni?"
Ya faɗa cikin wata murya yana ƙara tsare ta da idanu.
Ba Ta yi magana ba ta mayar da kanta ƙasa kawai.
"Ya za ki saka ni a duhu kuma ki tafi ki bar ni ciki? Me kike nufi a tare ni a ce ke annoba ce?
Mutum ya taɓa zama annoba ne Afeefah?"
Muryar ta na rawa tace
"Kwarai Dr. Sulaiman da za ka iya da ka yi tattaki zuwa Dutsen-wai ka tambayi wacece Afeefah
kamal ina da tabbacin bayan nan ko mai sunana aka ƙira maka za ka gudu! Umma ta karɓe ni
ne domin itama bata san wacece ni ba don babu uwar da za ta karɓeni matsayin surka muddin
tana ƙaunar ɗan ta"
Ranta zafi yake mata, tana maganar ne tana tuna mahaifiyar saleem da kyamatarsu gareta ta
wani ɓangaren kuma bata ga laifinsu ba don ba laifi bane mutum ya kare abin da yake so.
"Ka yi haƙuri ka tafi Dr. bana so sai ka zurfafa kasan ni wacece in karya maka zuciya, na tafi
ciki"
Tana kai nan ta nufi ciki ta bar shi tsaye, hawaye take zubarwa ba wai duk cikinsu babu mai
nagartar aurenta bane sai dai tana ji babu inda za'a karɓeta matuƙar an san wacece ita!
Taɓon nan da bata san mafari ba ba zai taɓa goguwa a tarihin ta ba, tabo ne mai raɗaɗi da har
Abada za ta cigaba da rayuwa cikin gangar jikin da ruhi mai tarin buruka suka mutu... Da
saleem ta ci karo a sadda ta shawo kwanar É—akinta ido kawai ya zuba mata ko da ta zo bata
tsaya ba kawai ta wuce shi yayi saurin shan gabanta.
"Afeefah saboda Sulaiman kike ɓata rai da ni?"
Hawaye take yi wadda ta kasa sarrafa su cikin rabuwar murya tace
"Ba saboda shi bane yaya saleem"
Ta sake yunkurin wucewa ya sake tare ta
"Ban gane ba bayan ga idanunki nan suna zubar da kwallah Afeeefa?"
Cikin Muryar kuka ta shiga cewa
"Ina kuka ne saboda na gaji da yaudara ta da zuciyata ke yi na cewar zan samu farin ciki, ina
zubar da hawayene saboda na farka daga mafarkin da bashi da tabbas"
Shesheka ta ja tana kallon cikin idanunshi
"Ka gaya min Yaya saleem a cikin ku biyu da waye zan dogara? Da Kai da mahaifiyarka ta yi
Allah ya isa muddin ka yi min maganar da ta wuce ta minti É—aya ko da Dr. Sulaiman da bai san
wacece Afeefah ba?"
Wuce shi kawai ta yi don ta san ba zai amsa ba saboda minti É—ayan ya riga ya wuce hakan ya
kara rura wutar zuciyarta ƙarfin kukan ya ƙaru, jakar hannunshi ya bi ta har cikin ɗakin ya ajiye
ya tsaya ya zuba mata idanu yana jin kukanta na sukan zuciyarshi, idanunshi suka sauya
sossai tausayinta da ƙaunarta suka ninku a cikin ranshi.
Samha da ke tsaye jikin pampo ta sake hanci da baki tana kallon su ta kwasa da gudun tsiya ta
kamo hannun mommy
"Mommy zo zo zo ki ganewa idanunki wallahi Ya Saleem ne É—akin Mayyar chan..."
Mommy har tana tripping garin sauri suka nufi bayan a lokacin suka hangi bayanshi ya fito ya
nufi hanyar waje, duk su huÉ—u suka nufi É—akin kowa da bala'in da ke cin shi a rai...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*017*
18hours Earlier
Kanta a ƙasa tun da Sulaiman ya fita daga gidan tana tsaye ne jikin taga tana kallonsu tun
Shigowarshi da ma isowar su saleem da tafiyanshi bayan ya ba Afeefar Abu a leda, bata taɓa
sanin haka so yake ba sai da ta faÉ—a komar Sulaiman zuciyarta yayi mata wani irin nauyi,
tsananin haushin Afeefah take ji kaman ta samu bindiga ta harbeta kowa ya huta, a yanzu ma
bata san hawaye na zuba mata ba sai da ta ji an dafa ta.
Ɗago kai tayi ta kalli Samha sai ta duƙar da kan again tana share hawayen fuskarta
"Sameera me ke damun ki haka? Menene ya sameki kike kuka?"
"Babu Samha"
"A'a Sameerah ina fa lura da ke kwana biyun nan duk kin chanza kaman ba ke ba, kullum kina
cikin damuwa 'yar faÉ—an nan da kike biye ni muyi tayi duk yanzu bakya yi walwala ta kau daga
fuskanki har mommy É—azu maganan take yi, in baki faÉ—a min ba wa za ki faÉ—awa Sis?"
Kuka kawai ta sakarwa samhar, sai da tayi mai isarta kan ta É—ago ta kalleta
"Samha ko na faÉ—a ma ba ku da maganin damuwata"
"Ko Adu'a muka taya ki ai mun taimakeki bare kila akwai shawarar da zan iya baki, idan ba kya
son kowa ya sani ne ma i promise ba zan faÉ—awa kowa ba".
"Samha na kamu da Soyayyar Dr. Sulaiman"
Tsayuwa tayi tana tunanin waye Drn Sulaiman sai da yayi clicking a brain É—inta kan ta yi saurin
cewa
"Wannan likitan dake zuwa duba Mayyar chan?"
Kai ta gyaÉ—a a sanyaye
"Samha kaman soyayya suke da ita"
"Amma Sulaiman É—in bai santa bane ba ko? Ina nufin bai san wacece ita ba rufe shi take
kokarin yi ta nuna mishi ita 'yar gidan nan ce?"
Samhar ta fada har yanzu tana mamaki, Afeefah ta kai Sulaiman ya ce yana so?
"Da alama kam"
"Toh me kika yanke?"
Ta É—ago jajayen idanunta tace
"Dole su rabu idan na cigaba da kallonsu tare zuciyata zai iya bindiga Samha, dole ko in sakata
ta rabu da shi ko kuma in san hanyar da zan bi gidansu su san wacece ita! Ko yana sonta ai ba
shi zai aurar da kanshi ba ko?"
Kai Samha ke gyaÉ—a wa
"Wannan haka yake, shawarar nan yayi kuma ki sameta ki ja mata warning mai girma ta tsaya
matsayin ta"
A hakan suka yanke don har ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi da Afeefah da safe kuma
tana tashi bacci wanka kawai tayi ta fito kaman an ce ta leƙa waje ta hanjeshi tsaye da ita, ko
abinci bata ci ba ta zauna parlor tana jiran Afeefar ta dawo don ta lura abin nasu gaba yake,
bata gama tunanin ba sai ga Samha da gudu ta ƙira su suka nufi ɗakin Afeefar...
***
Tana zaune kanta haɗe da ƙafafunta tana aikin zub da hawaye kawai ta ji an banko ƙofan
ɗakin, suka tsaya suna ƙarewa ɗakin kallo kan Sadiqa ta nufi wayanta da ke zaune gefenta
"Kutt! Yaushe kika yi waya? Na dai tabbatar ba da ita kika zo gidannan ba"
Kayakinta Samha take dagawa tana cewa
"Mommy yau dai kam Yaya da kike yabo ya watsa miki ƙasa a idanu duk wa zai saya mata su
bargo har da su heather in ba Yaya ba? Dubi ƙwalamar dake ɗakin nan? Mommy anya ba
asirce shi tayi ba?"
Ita dai tana tsaye tana kallonsu duk da zuciyarta da ke dukan sakwara ta kame bata firgice ba,
Sameera ta je ta fusgo ledojin da Sulaiman ya kawo mata tana zazzage kayakin ciki idanunta
cike da kwallah.
"Shikenan wallahi tambaÉ—e mana take shirin yi a gida, wani namijin ne zai na kashewa mace
kuÉ—i haka ba tare da ta bashi komai ba?"
Sadiqa ce tayi maganan tana ganin turaruka da dogayen riguna masu tsada da mahaifiyar
Sulaiman ta bata.
Sameera ta katse ta
"Ko dai asiri ta yi musu ba yaya sadiqa in tambaÉ—e wa ne kenan har da Yayanmu kalli wayan
nan kalar text messages dake ciki na tsantsar soyayya don tsabar rashin kunya da nuna cewa
ta isa dashi ma kin ga sunan shi gatsau tayi saving saleemullahi"
A fili ta fara karantowa mommy wasu inda yake tabbatar mata da zai iya jurar komai a kanta
kuma zai jajirce har sai ya ga sun samu cikar burin su na kasancewa karkashin inuwa daya.
"Ya isa haka sadiqa"
Mommy ta faÉ—a jiri na kwasarta ta samu wuri ta zauna, har Dishi Dishi take gani saboda yadda
kanta ya sara ashe salim zai iya tsallake maganar ta? Yanzu idan da basu lura da wuri ba tayi
amfani da wannan dama ta kashe mata shi fa? Da gaske maita na tafiya da aljanu? Ai kuma
duk inda Aljanu suke akwai asiri kenan dai tun farko ma asiri ta mishi ta sa ya kawo ta
matsuguninsu?
"Lallai saleem! Ni yaron nan zai nunawa É—an yau ne shi? A kan mace? Macen ma Mayya marar
galihu da tushe haÉ—e da asali mai kyau? Allah ya isa na a banza ya É—auke shi? Ni saleem...?"
Sai ta kama hawaye, hankalin Afeefah ne ya tashi ganin mommyn na mishi hawaye bata son
masifar hawayenta ya taɓa shi ko ta wani ɓangare da sauri ta isa gaban mommyn ta zube a kan
gwiwowinta
"Don Allah Hajiya ki yi haƙuri kar ki mishi kuka, wallahi yana jin maganarki yana kuma tsoron
fushinki, Ni ce mai kuskure ni ce na nemi ya sayamin kar ki yi fushi da shi domin fushinki bala'i
ne a tare da shi..."
Tauuuu sadiqa ta É—auke ta da mari
"Kin san hakan amma kike hure masa kunne ya saɓa mata? Kin san abin da ɓacin rai daga
gareshi zai iya ja mata?"
Samha da ta janyo jakar da saleem É—in ya shigo ya ajiye mata ta zazzage komai na ciki tana
cewa
"Wallahi yarinyar nan so take ta raba mu da É—an uwanmu Mommy, kalli uwar tsarabar da ya
kawo mata a ɓoye ko ke bai kawo miki irin hakan ba bare mu... Farraku take shirin yi mana
daga karshe ta sa ya kora mu daga gidan nan"
"ƙira min saleem sadiqa"
Da wayan Afeefar ta ƙira shi, ringing ɗaya ya ɗaga a hankali ya kira sunanta sai ta duƙar da kai
hawaye na gangaro mata jin muryarshi.
"Yaya Salim Sadiqa ce Mommy ke son ganinka"
Runtse ido yayi da ƙarfi gabanshi na faɗuwa, bai shirya ba! Bai shirya tashin hankali a yanzu ba
ba yanzu ba da yake jin son Afeefah yayi mishi yawa a zuciya.
Da sauri ya juyo kan motar dama bai yi nisa ba ya dawo wani irin parking yayi ya sauƙa ya nufi
sashen Boys quaters É—in yana Adu'ar Allah ya sa kar mommy tayi mata wani abu, sai kace-
nace ya same su suke yi ana ta maida magana, Afeefar na tsugune kaman mai neman gafara
tana kuka.
Gaban mommyn ya je kusa da Afeefar shima ya duƙa kawai ba tare da ya furta kalma ko guda
ba.
"Saleem"
Ta ƙira sunanshi ya amsa ba tare da ya kalleta ba
"Ɗago saleem ka kalleni, ka ɗago ka tabbatar min da kai ke tura duk wani saƙo da na gani
wayar yarinyar nan, da gaske kai ne kake son wannan marar cikakken asalin?"
Ya runtse ido wani irin nauyin Afeefah yake ji kaman yayi yaya, baya so baya kaunar ta ke jin
furucin ɓatanci daga ahalinshi zuwa gareta musamman mahaifiyarshi.
"Mommy ni ne, Son ta nake kuma aurenta nake Son y...."
Wani irin mari ta É—auke shi da shi, karo na farko kenan da ta kai hannunta jikinshi don shi yaro
ne mai tsananin biyayya a gareta.
"Maimaita!"
Ta daka mishi tsawa ya sake cewa
"Mommy ina ƙaunarta, kuma aurenta nake buri"
Wani marin ta sake dauke shi da shi, ba shi kaɗai ba har su sadiqa sun tsorata basu taɓa
tunanin za ta iya kai hannunta jikinsu ba don ita Allah yayi ta da tsananin son yaranta, hawaye
take yi ta sake cewa saleem ya maimaita
"Mommy... Mommy da gaske zuciyata ta kamu da Soyayyar Afeefah da ba na tunanin ko wani
hukunci za'a yi min zai sa ta fita daga ciki, mommy kila sai kin cire zuciyar gabaÉ—aya daga
kirjina za ki daina jin harshena na furta kalmar ƙauna zuwa gareta..."
Wani irin kuka Sameerah ta fashe da shi, a yanzu ta yarda ta yarda ba wani asiri don tabbas
abin da take ji a kan Sulaiman shi ke azabtar da Saleem tunda har zai iya mayarwa mommy
magana sau uku, Mommy ta sake ɗaga hannu zata mareshi sadiqa ta riƙe hannun tana hawaye
"Mommy ba shi za ki daka ba ga Mayyar da ya kamata ki kassara chan, wallahi Afeefah sai kin
bar gidan nan ba za ki tarwatsa mana gida ba"
Afeefah dai ta rasa yanayin da take ciki, wani irin ƙauna da tausayin saleem ne suka sake
mamaye zuciyarta ko tunanin inda za ta nufa in sun kore ta bata yi, damuwarta saleem idan
suka raba su basu mishi adalci ba, shi ya cancanci bautar ta na aure har mutuwa.
"Saleem!"
Mommy ta kira shi karo na ba adadi muryarta har yanzu da wani irin mamaki, idanunshi da suka
sauya ainun ya É—ago ya kalleta tamkar ba soja ba wani irin rauni ya bayyana karara a fuska da
idanun nashi.
"Saleem!!"
Ya amsa a hankali
"Saleem!! Sau nawa na kira ka?"
A hankali yace
"Uku"
"Wannan ba aikin hankali bane na asiri ne, amma ko da asirin ai ka san matsayi na a wurin ka
ko? Ka san ni wacece ko?"
"Mommy ke mahaifiyata ce kina da darajar da babu wanda yake dashi a wurina duk faÉ—in
duniyar nan. Kin isa da ni kuma na san za ki so farin cikina! Mommy a yanzu ba na jin ina da
wani buri da zai haifar min da farin ciki kaman Afeefah, ban san sadda sonta yayi min wannan
kamu ba don ba ya shawara kan ya shiga wallahi ina sonta! Ba zan iya rarrashin zuciyata ba
don so bai san rarrashi ba..."
"Afeefah Allah ya isa tsakanina da ke! Allah ya isa"
Mommy ta faÉ—a tana kuka. A lokacin hawayen da saleem ke danne wa suka gangaro ya É—ago
ya kalli mommyn zai yi magana ta daka mishi tsawa a kan ya mata shiru
"Aure kake so zan É—aura maka aure da yar É—an uwana Sabreena da take sonka tun bata san
kanta ba, amma soyayya, magana ko zancen aure tsakaninka da wannan yarinya saleem har
Abada, ko bayan raina ne Allah ya isa ban yafe ba! Wallahi wallahi sai na iya tsine maka ka
sake shiga huldar yarinyar nan ko a hanya kuka haÉ—u ban yafe ba ka mata ko da sannu ne... In
har ni na haif...haifeka Saleem sai dai in kana da wata uwar za ka iya"
A razane yake kallonta, ta share fuskanta ta dubi Samha
"Je É—akina ki É—aukomin akwatin da ya fi kowanne girma"
Da sauri ta tafi, Sameera zuciyarta ne ke tsitsinkewa a yanzu tsoro ne ya rufeta, wlh tana iya jin
irin abin da saleem da idanunshi ke runtse yake ji a yanzu, gabaÉ—aya jijiyoyin kanshi sun
mimmiƙe girgiza kai take yi
"Mommy don Allah ki dakata! Ki tsaya kar azabar yayi mana yawa... Ki barta don Allah ko bai
aureta ba ta z..."
Sadiqa ce ta kai mata duka
"Kema asirce ki tayi don ƙaniyarki? Wallahi ta gama zaman gidan nan"
A lokacin Samha ta shigo da wani cream trolley.
Mommy ta karɓa ta jefa mata
"Na tsani ganin ko inuwar ta ne, ku gaya mata ta tattari duk taeukucenta ba na son ganin ko
ƙyallenta a gidan nan kar ma ta dawo cikin dare ta kama wani biya... Har Abada ko magana ta
yi wa dana sai na tabbatar ta kare rayuwarta a gidan yari"
Ko gwada roƙon su bata yi ba don ta san ko sama zai haɗu da kasa a yanzu mommy ba zata
amince da hakurin ta ba, kuka mai sauti take yi jikin saleem ne ya fara rawa, ba zai cigaba da
sauraron kukanta ba ba zai iya ganin tafiyar ta ba, zuciyarshi tamkar zai fashe saboda tsoro da
fargaba in ta fita ina za ta je? Wa ta sani a duk faɗin Kaduna? A hankali ya miƙe jiri na kwasar
shi a dafe da gini ya cigaba da tafiya har ya bar É—akin zuwa lokacin da gaske yake hawaye,
hukuncin Mommy tamkar zare mishi farin ciki tayi a wannan rayuwa, tamkar ta kulle shi ne a
magarƙamar da ya fi kowani magarƙama duhu da azaba.
Afeefah ta haɗa komai nata, wayar da saleem ya saya mata kawai ne ke riƙe hannun mommy
kan suka tasa ta gaba har wajen gate, ta jima tsugune a wurin tana kuka kan ta miƙe ta share
fuskarta ta ja akwatin ta fara tafiya.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel...! Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Abin da take ta nanatawa kenan tana share hawaye ta yi tafiyan da bata san adadi ba har ta fito
wani babban hanya dake dauke da ababen hawa fiye da cikin unguwar da ta bari, nan ma
miƙawa kawai tayi ta cigaba da tafiya ko biyar babu a hannunta, ta fi awa biyu tana tafiya janye
da trolley É—in lokaci lokaci ta kan share hawaye masu zafi dake zuba mata, a daidai wani wurin
ba da hannu ta tsaya ta É—aga kai ta kalli garin, mutane ne ke ta hada hada kowa harkar
gabanshi yake yi, daidai wutan ya nuna ja motoci suka tsatsaya wani daga gaba yayi kokarin
kin bin doka sai hatsari ya faru a wurin tuni go slow ya wani irin haÉ—uwa.
Tana tsaye har lokacin rike da akwatinta kamkam sam bata san me za ta yanke ba, bata san ya
za tayi ba kaman an ce ta É—aga kai sai idanunta da suka zama wasu iri tsabar kuka suka shige
cikin nashi daidai yana sauƙe glass, kallon seconds biyar suka yi wa juna ya ɗauke kanshi ya
mayar gaba yana tsaki, ita kam bata dauke kai ba sai take jin kaman ta je ta roƙe shi ya taimaka
mata ko da ya haÉ—a ta da Sulaiman ne, amma kuma Sulaiman ai bai san wacece ita ba idan su
ma suka kore ta fa? Innalillahi wainna ilaihi rajiun ta sake faÉ—a hawaye na silalo mata daidai ya
sake kallonta idanunshi suka sauƙa kan hawayen a lokacin suka samu hanya ya ja motar ya bar
wurin.
Juyawa tayi ta cigaba da jan trolley É—in dama ta sani bashi da kirkin saleem, babu mai kirkin
saleem ma a duniyarta shi kaÉ—ai ta sani mai kirki, daidai ta zo gaban galaxy mall da ta gani
rubuce sama za ta wuce sai tayi karo da wata mata, baya baya matar tayi za ta faÉ—i Afeefar tayi
hanzarin sake akwatin ta riƙe ta
"Subhallah! Ki yi haƙuri"
Ta faÉ—a cikin dasasshiyar muryarta, sai ta ga matar ta kasa tsayuwa numfashinta na ta kai
komo ga ta dai cikin shiga na alfarma har da jaka a hannunta
"Lafiya Aunty? Ko baki da lafiya ne?"
Take ta tambayar cike da damuwa matar ta kasa magana.
Hankalin Afeefah ya tashi, kar ta mutu yanzu ma a ce ita, ya zata yi? Ba Za Ta iya barin ta a
nan ba a haka yadda take duk ta fice hayyacinta ta jike jagwaf da gumi Dukda sanyi ake. Wani
tunani ne ya faÉ—o wa Afeefah ta yi hanzarin karbar jakar matar tana cewa
"Aunty taimakon ki zan yi ba sata zan miki ba bani da ko biyar da ba zan taɓa jakanki ba"
BuÉ—ewa tayi ta samu É—ari biyar bata tsaya tunani ba ta tari abin hawa ta sanya matar a ciki
itama ta shiga mai machine É—in ne ya dauka mata akwatinta tana ce mishi
"Asibitin dake kusa don Allah"
"Sannu, Sannu"
Take ta maimaitawa matar gwanin tausayi sai taji tana yi wa Allah godiya da ya barta da
lafiyanta ko ba komai ta tsira da shi, a haka suka isa wani private hospital ya shiga da su har
ciki aka dauƙeta emergency zuwa lokacin bata numfashi.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*018*
Sai da ya bar gida da motar ya fahimci gas din Ac ɗin shi ya ƙare, hakan ya ɓata mishi rai don
baya son buɗe glass na mota yana tuƙi, a haka ya tafi Asibiti yayi abin da zai yi a ranar wuraren
sha biyu ya bar asibitin ya nufi gida, a daidai babban titin da zai É—auki hanyar cikin unguwar su
na Barnawa hold up ya riƙe shi, a dole ya sauƙe glass saboda zafin da yake ji.
Karon farko da idanunshi suka sauƙa a kanta bai gane ta ba sai da ya ɗan yi focusing na
seconds kan ya gane ta, wannan yarinya ce da ya taɓa ceta from poison, wannan yarinya da
saleem ke so, sam bai yi tunanin wani abu ne ya tsayar da ita a wurin ba sai a karo na biyu da
ya mayar da idanunshi wurin suka sauƙa a kan trolley dake gabanta, idanunta ya sake mayar
da ido sai ya fahimci ta yi kuka sossai, horn ake ta danna mishi hakan ya sa ya ja motar yayi
gaba wayanshi ya zaro ya shiga neman Layin salim sai dai har 2missed calls ya mishi bai É—aga
ba shi da ya tsani kira sau biyu ya kan ce ai duk uzurin da mutum ke yi in ya zo ya ga na farko
zai bi ba sai ka ta jera kira kaman marar aikin yi ba, a kira na uku saleem ya É—aga sai dai ya
kasa magana.
"Saleem are you Okay? Whats wrong with ur voice?"
Saleem ya kasa magana don shi kaɗai ya san me yake ji, Ryan bai taɓa jin Muryar abokin nashi
a haka ba, dole ya nemi wuri yayi parking
"Saleem Mommy ce?"
Yayi uttering
"Uhmm Ryan Mommy ta kori Afeefah ban san wani irin hali za ta faÉ—a ba, mommy tayi
alkawarin tsine min na sake ko da magana da Afeefah ne bare yunkurin taimako aure ko
soyayya, she's too young Ryan she's too young! Na san tana chan all alone, scared and
disturbed idan wani abu ya same ta fa? Its all my fault da na fara son ta Its my fault..."
Hawayen da yake yi ne ya sa ya datse lips ɗin shi da ƙarfi sai kawai ya katse wayan.
Kunna motar rayann yayi yana jin wani abu a ƙasan ranshi, tausayin Saleem ya rufe shi haɗe
da damuwan jin halin da yake ciki bai taɓa jin abokin shin haka ba, saleem da ko haɗe rai baya
yi. Fuskarta yake gani a idanunshi ashe kallon taimako take mishi, steering ya É—an buga da tafin
hannunshi yana zagayowa inda ya barta sai dai neman duniya bai ganta ba, har parking yayi ya
sauƙa yana takawa da kafa ya zazzaga bata nan. Bakinshi ya ɗan taɓe kaɗan yana shirin
juyawa wayanshi yayi ringing.
Zarowa yayi sai ya ga Driver É—in Mamminshi ne, dagawa yayi
"Ado ya aka yi?"
Ya fitar da maganan yana lumshe ido sam ba zaka san yana da damuwa ba ko hankalinshi ya
É—an tashi don fuskar bai nuna ba ko da wasa.
"Oga akwai matsala ne, Hajiya ce!"
Tuni ya ware idanun a take suka sauya ya fara nufar motanshi yana ji Ado na mishi bayani wai
ya kaita sayayya kuma yayi ta jira bata fito ba ya shiga ciki kuma yayi neman duniya bai sameta
ba.
"A ina ne?"
"Galaxy mall"
Yana kusa da wurin ƙarasa wa kawai yayi
"Ka ƙirata?"
Ya jefawa Ado tambayar Ado yayi saurin duƙar da kanshi don ya san fushin Rayyan a take sai
ya haukace, idanunshi sun yi mishi kwarjinin da ba zai iya kallon cikinsu ba
"Ban fito da waya ba"
Wani irin kallo ya watsa mishi lip É—in shi ma sun yi nauyin buduwa bare su sake furta ko da
kalmar A.
Wayanshi kawai yake dannawa ya shiga ƙiran layinta sai dai ringing na duniya ba'a ɗaga ba,
tracker ya shiga na Find my Iphone tuni ya ga location da take, a maimakon hankalinshi ya
kwanta sai hankalinshi ya sake tashi ba za ka sani ba amma in ka ƙura mishi ido zaka ga
hannayenshi har rawa suke idan kuma ka taɓa za ka ji sun yi sanyi tamkar ƙanƙara to baya
cikin lafiya kenan.
Mota kawai ya shiga ya ja tafiyar mintuna goma ya isar da shi asibitin yayi rough parking ya
sauƙa ya nufi ciki, a gaban nurses station ya tsaya
"An kawo wata elderly woman yanzu! Where is she?"
Da É—an karfi yayi maganan don ya ga mace É—aya ce kawai ta mayar da hankali kanshi tsawar
da yayi ya sa duk suka juyo, kofan emergency kawai ta nuna mishi ya nufi wurin kawai ya tura
ya shiga.
"Excuse you! Baka san ba'a shiga nan bane?"
Id card ɗin shi ya fitar ya nuna musu idanunshi na kan Mammi da suke ta ƙoƙari wurin ganin
sun ceceta ya furta a hankali
"The patient is experiencing end-stage renal disease(ESRD) nd she's diabetic i hope ba ku yi
kuskuren komai a kanta ba"
Ja da baya wanda ke rike da drip yayi don ba ruwan masu sugar bane, Id card É—inshi kuma ya
tabbatar musu da waye shi. A tare da shi aka cigaba da ƙoƙarin ceton Mammin kusan awa ɗaya
da wani abu kan suka fara fitowa aka barshi shi kaÉ—ai.
A kan kujera ya zauna ya sa hannu ya riƙe nata ɗaya ya gimtse a duka hannunshi biyu ya ɗora
goshinshi a kai yana jin jininshi na cigaba da tsitstsinkewa rauni mai girma ne da ba zaka É—auka
irin shi mai dakakkiyar zuciya zai nuna ba bayyane a fuskar shi da ma idanunshi, ƙiran sallah ne
ya sa ya É—ago a hankali ya zuba mata idanu sama da mintuna uku kan ya mayar da hannun a
hankali ya ajiye mata ya miƙe ya fito Fuskarnan babu ɗigon walwala, a kan trolley idanunshi
suka fara sauƙa ya ɗan kalli Ado da ke maƙure gefe kaɗan kaman zai yi magana kuma sai ya
fasa yayi gaba, sallah yaje yayi bayan ya idar ya dawo yana shigowa reception É—in tana É—agowa
suka haÉ—a idanu, handbag É—in hannunta ya É—an kalla kan ya nufeta.
Yana matsowa dukar zuciyarta na ƙaruwa gabanta sai dukan uku uku yake tamkar za ta rasa
numfashinta take ji don bai daina kallonta ba kuma bai daina nufarta ba kamshinshi ya riga shi
isa, ko kan ya iso aka ƙira shi
"Sir the patient, ta farka"
Numfashi kaɗan ya sauƙe ya juya ya nufi ɗakin, bata san ta kama numfashi ba sai da ya ɓace
mata taji tana kokarin mutuwa ta sake shi da ƙarfi tana dafe kirjinta, Allah ya gani tsoron shi
take bata sani ba ko tun ihun da yayi mata ne tayi developing wannan tsoro ko yaya amma
muddin ya sauƙe ido a kanta sai ta ji wani tension na building inside her.
Idanu kawai ya zuba mata ta ɗago ido ta kalleshi cikin ƙarfin hali ta sakar mishi murmushi tare
da miƙa mishi hannunta, ya taka a hankali yaje ya kama yana zama
"Mammi..."
Sai yayi shiru ta sake yin murmushi mai kyau
"Saraki na ji sauƙi ka kwantar da hankalinka, sannan am sorry na ji ina son ɗan shan iska ne ya
sa na fita not knowing hakan zai faru am sorry na É—aga maka hankali"
"Mimmi stop it please, am sorry i wasn't there to take you out myself da kin faÉ—a min zan bar
duk abin da nake zan zo na kai ki na kula da ke har mu koma, Its my fault da nake emphasizing
akan zaman gidan am sorry you get bored"
Hannunshi ta ɗan matse tana murmushi har lokacin, ɗago ta yayi ya buɗe ruwa ya bata ta karɓa
babu musu ta sha sossai kuwa don masu ciwon su na buƙatar enough ruwa a jiki.
Basu wani jima ba suka fito yana riƙe da ita, har lokacin in har ka san shi sosai za ka hangi
akwai damuwa a fuskar shi, Afeefah da har lokacin tana zaune a wurin tayi saurin Miƙewa ganin
su tare, dama ya san matar?
Menene alaƙarsu? Ta ya aka yi ya san tana nan? Su ne tambayar da ta tsaya yi tana daga
tsaye tana kallon su.
Idanun Mammi ne ya kai kanta, sai ta dakata tana tunani ga jakanta dai hannun stranger a
hankali take tuna abin da ya faru yarinyar ce ta taimaketa, ta yi mamaki ƙwarai ganin yarinyar
har lokacin kuma riƙe da jakanta da alama ko ajiye shi bata yi ba, tana tuna kalaman yarinyar
na ban haƙuri a sadda ta ɗauki ɗari biyar ciki.
"Saraki wanchan yarinyar ita ta taimakeni ta kawo ni nan, da ban san me zai faru ba"
Kaman bai fahimta ba ya sake kallon Afeefah, chan ƙasan ranshi ya ji daaɗi kuma ta samu wani
ƙima a idanunshi saboda duk wadda ya kaunaci Mammi ko da bai kaunaceshi ba shi ya bashi
daraja na musamman, sai dai har lokacin fuskar shi bai nuna ba sai nufanta da Mammin ta sa
suka yi, ita abin da ya kaÉ—a ta ma tahowarsu tare, ita dai ta rasa wannan irin razani da take
shiga da kwarjinin wannan bawan Allahn, ko da suka tsaya gabanta sai ta ga ya cike wurin
gabaÉ—aya, kuma kallonta yake don Mammi ta sake shi ta kama hannunta.
"ÆŠiyata yaya Sunanki?"
"Sunana Afeefah, Aunty ya jikin ina fata komai lafiya?"
Tayi maganan kaman mai tsoron wani abu zai kama ta
"Alhamdulillah Afeefah, na gode ƙwarai da kyakyawar tunanin ki ba kowa ne zai iya irin
taimakon da kika yi min ba, Allah ya saka da alkhairi"
Afeefah tayi murmushi
"Babu komai Aunty, ga jakarki ki yi haƙuri na cire ɗari biyar a ciki mun hau adaidaita saboda ba
ni da ko biyar"
Murmushi Mammi ta saki ta É—an kalli Rayyan da bai ce komai ba ya zuwa yanzu ya kawar da
kai daga kallonta sai dai yana sauraren su.
"Gaskiya samun irin ki a wannan zamani sai an tona"
Idan ta tafi da jakar nan ba karamin abu za ta samu ba don bata tantama har zobunan
gwagwalanta suna ciki amma bata ko buɗe ba bare tayi tunanin yi mata sata, hakan ya matuƙar
burgeta.
"Saraki mu kai ta gida ko? Ina so in ga gidansu in yi ma iyayenta godiya kuma in basu hakurin
rashin ganinta kan lokaci"
Ta kalleshi shima ita ya kalla bakinshi ne yayi mishi nauyi, kuma ba ya son dogon bayani sai ya
kalli Afeefar da kanta ke ƙasa kaman daga sama ta ji ya ce
"Kina da gida?"
Yayi maganan yana É—age gira É—aya.
Mammi ta Harare shi
"Wani irin tambaya ne wannan akwai wanda ya faÉ—o daga sama ne?"
Ita dai tambayar ya zo mata wani iri sai hawaye suka cika idanunta a lokacin ta tuna ashe bata
da inda za ta je, da alamu kuma ya sani don maganar shin ya fi yi mata yanayi da gatse, a
hankali ta kalli Mammi
"ba sai kun kaini gida ba Aunty, kina bukatar hutu saboda jikinki daga nan zan koma da kaina"
Tayi saurin juyawa amma duk da haka ya ga hawayen da ya silalo mata, Ado ya kalla
"ÆŠauki akwatin nan mu tafi"
Yana kai nan ya fara kokarin kama mammin
"She has No where to go, for now za mu tafi tare"
Cike da tausayi Mammi take kallonta, so take ta ji karin bayani me ya sa bata da inda zata je?
Ina dangin ta in bata da iyaye? Amma sanin duk ba yanzu bane lokacin maganar ta saki
Rayyan ta riƙo hannun Afeefar galala yayi yana kallonta ko ta tsaya don ta san rigimar shi, haɗe
fuska yayi sossai ya biyo bayansu.
Sanin halinshi ya sa Mammi ta zauna gaba Afeefah ta shiga baya, ya ja motar a hankali ya fita
daga asibitin, Ado ma ya bi bayanshi har yanzu zuciyarshi bai dawo daidai ba yana tantamar ko
Rayyan ya barshi ko sai ya É—auki mataki a kanshi don abin da duk ya shafi Mammi baya wasa
da shi sam kaman yadda ita ma bata da kaman Rayyan a duniyarta.
Shiru motar yayi don Mammin na buƙatar hutu so ganin ma kaman ta gaji da zaman ya nemi
wuri yayi parking, ya É—an koma baya ta yadda ya sake birkita Afeefah dake zaune saitin kujeran
shi ya sa hannu ya kwantar da seat É—in mammin a hankali, ta buÉ—e ido ta kalleshi ta É—an yi
murmushi kawai ta sake lumshe ido ya furta
"Sannu"
Cikin tsantsar kulawa, sai kallonsu Afeefah take yi. A iya zaman nan ta fahimci matar tana da
matuƙar muhimmanci a rayuwarshi Dukda bata ga kama ba don matar baƙa ce kaman ita shi
kuwa farin shi har ya ɓaci, ba zaka taɓa cewa bai hada dangi da Larabawa ba barin ma
kasumba da gemun da ya ajiye ɗan daidai da shi baƙi sidik.
Motsin kirki bata iya yi kamshin motar har yana hawa mata kai a haka suka isa wani tsararren
unguwa shiru ne unguwar kaman ba titin da suka baro ke É—auke da hayaniya da jama'a ba, nan
É—in gidajen manya manya ne, sai dai ka hangi su dawisu da su jimina a gidajen da gininsu ma
na zamani ne, gaban ko wani gida kuma akwai securities zaune kusan kowanne sanye da
uniform ko yellow ko blue, a hankali ya gangara gaban wani golden gate mai girma fuskar sai
sheki take horn yayi, sai gashi an leƙo wannan ɗin ma na sanye da blue riga da bakin wando,
Gaisuwa ya shiga miƙawa Ogan nasu ya ɗaga mishi hannu kawai don Window na sauƙe
saboda rashin Ac. Tamfatsetsen gida ne don yayi na su Saleem sau uku ko biyu da rabi, gidan
tamkar ginin sarauta saboda fari ne kal an mishi ado da golden paint har kwanon golden Color
ne, harabar na shimfide da interlocks É—auke da shukoki masu tsananin kyau da É—aukar ido,
Dukda akwai parking lots har uku jere da motocin alfarma bai yi parking a ciki ba sai da ya je
dab kofar shiga yayi parking ya sauƙa ya zagaya ya buɗewa Mammin kofa.
Ita dai Afeefah na ta mamaki don bata zata akwai wanda wannan mai zafin ran ya dauka da
muhimmanci ba haka, bata taɓa zaton zai iya buɗewa wata macen kofa ba kila dai
mahaifiyarshi ce, kila kuma kamannin mahaifinshi yayi shiyasa basa kama ko ta wani ɓangare.
"Afeefah sauƙo mana kin zauna ciki"
Ta faɗa a hankali, buɗe murfin tayi ta sauƙa tana jin kanta dake sara mata na ƙaruwa saboda
tsabar kukan da tayi yau, kunyar hijabin jikinta take don onion colour ne kuma duk gaban da ya
jike da hawaye ya bushe sai yayi wani jirwaye jirwaye,
A baya ta bi su har suka shiga cikin tsararren parlorn mai girman gaske sanyi ne ke ratsa ko ina
ga kamshi, parlorn kal kal kaman a zuba maka abinci a ƙasa ka ci komai na parlorn royals ne
golden and milk, tana kuranta kyaun gidan su saleem wannan gida ya fi nasu tsaruwa nesa ba
kusa ba.
A cikin kujera suka samu wata budurwa ganin Mammi ya sa ta tashi da gudu ta nufeta sai dai
hararar da Ryan ya sakar mata ya sa ta fasa isa da gudun ta É—an natsu
"Mammi are you Okay? Me ya same ki? Na dawo daga school wai kin fita Mammi jikinki yayi
kyaun da za ki fita? M..."
"Will you shut up and let her rest?"
Ya faÉ—a ba da tsawa ba sai dai ba kuma da wasa ba, mammi ta É—an yi murmushi
"Abeeha ga Afeefah ki kai ta É—aki na musamman a kai mata abinci tayi wanka ta kwanta ta huta
sossai please she's exhausted daga alamunta"
Kallon Afeefah Abeeha tayi sai ta juyo zata fara jero wa Mammi tambayoyin ina ta samo ta sai
suka haÉ—a ido da Ryan tuni ta wuce ta kama akwatin da Ado ya shigo da shi suka yi wani
ɓangaren daga cikin parlorn.
A hankali suka isa wani matakala uku suka hau zuwa wani corridor da ya ji interior kan suka
shiga wani parlor madaidaici kuma tsararre grey ne da Black colour, bai barta nan ba sai da ya
sadata da cikin bedroom É—inta duk ko ina suka bi kalkal yake gidan kaman kullum ake
wankewa, a bakin gadon da shima Grey ya ji shimfida White ya ajiye ta ya buÉ—e wani frigde
dake gefe ya fiddo ruwa marar sanyi sossai ya bata ta sha sossai kan ta É—an kwanta
"Sannu Saraki Allah yayi maka albarka"
Idanu ya lumshe ya buÉ—e tuni suka É—an sauya, a hankali ya amsa da Ameen kan ta É—an kwanta
tana sauƙe numfashi.
"Mammi ki huta sossai please, bana so in tafi in barki amma Saleem bashi da lafiya i need to go
and see him, ba zan jima ba zan dawo"
Tayi murmushi
"Su fa Maryama suna nan kar ka damu take your time, kuma ma Abeeha ba ta dawo ba na san
tana gamawa da Afeefah zata zo"
"Ta ishe ki da surutu dai"
Yana kai nan ya miƙe tana mishi sai ya dawo ya gaishe mata da saleem ya fice.
Wani motar daban ya É—auka mai Ac ya fice daga gidan bayan ya umurci Ado da ya fita da
wanda ya dawo ya kai a saka Gas na Ac, kai tsaye gidan su Saleem ya nausa bayan ya isa ya
bi ta baya ya haye saman zuwa É—akin saleem É—in komai a kashe ya samu kaman ba mutum,
hasken ya kunna ya nufi cikin É—akin sai ya samu saleem lullube da bargo, kanshi ya nufa ya
janye bargon ya sa hannu a goshinshi ya janye
"Subhallah! Saleem you are burning up tashi mu tafi hospital"
"Ryan Afeefah, ban san wani irin hali zata faÉ—a ba am scared kar Allah ya kama ni da laifi...
Please help me find her please"
Da kyar yake maganan saboda zazzafar zazzabi dake kassara gaɓoɓinshi.
"Za mu same ta, In shaa Allah i will find her lafiyarka First ur temperature is very high"
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Ku min uzuri da rashin amsa comments please matsalar wayata ta saka sai na nemi wani
wayan nayi connecting hotspots saboda gidan sim din ta ƙi gyaruwa, please bear with me idan
na tara comments ina bi in karanta na gode sossai da sossai. Anjima zan samu in duba idan na
ga an zuba yadda ya kamata in shaa Allah za ku ji ni da dare*
*019*
Ko sanar da mutanen gidan bai yi ba suka tafi asibiti kai tsaye Amenity ya sa aka kai shi ya fara
bashi taimako saboda abin ya Buge shi sossai, tausayin Saleem É—in ne ya rufe shi mahaifiyarshi
bata yi mishi adalci ba amma uwa ce ya suka iya?
A chan gida kuwa Mudi ne ya shiga ya same su duk suna zaune a parlor fuskokin su babu
walwala.
"Hajiya Oga saleem ne..."
Da sauri Sameera ta katse shi
"Yayi me?"
"Babu lafiya yanzu Oga Rayyan ya fita dashi jikin dai babu daaÉ—i ban gan ku ba nake tunanin
baku sani bane"
Samha ta ce
"Mun shiga uku, duk akan Afeefar ne?"
Shi dai mudi shiru yayi karshe ma ya bar parlorn, Sameera ta É—auki mayafi tana kallon mommy
dake zaune har lokacin, sadiqa da Samha ma suka miƙe Sameera tace
"Mommy ki tashi don Allah mu je muga ya jikin nashi, mommy kaman ba a yi mishi adalci ba
wallahi..."
"Ba zan je ba ki ja ni ki kai ni, babu inda zan je ya gama ciwon ya dawo ya same ni, ba dai a
kan wanchan Mayyar ba ce? Zai yi ya gama Rabuwa kam sun rabu na har Abada"
"Amma mommy ya kamata dai ki je ciwo ai ya kore komai"
Sadiqa ta faÉ—a, Samha tayi fuskar tausayi bata san haka abin zai kasance ba da bata janyo
wannan rigimar from First place ba, suna son dan uwansu basa son ganinshi cikin wani hali.
Duk yadda suka yi da mommy akan ta je ta ƙi haka suka tafi su uku, suna ficewa ta sabi gyale
itama ta dauki mota ta bar gidan.
Tafiya mai nisa tayi kan ta iso inda ta nufa, wani gida ne tayi parking gidan dai daga gani Talaka
ne mamallakinshi don ya tsufe har ya gaji, ta sauka ta shiga ciki da sallama.
"Ah Hajiya Hussaina ce tafe? Maraba sannu da zuwa sannu da zuwa"
Matar da daga ka ganta ka san suna cikin wahala daidai gwargwado ta faÉ—a tana É—auko
taburma sabuwa ta shiga shimfida mata zama tayi suka shiga gaisawa, bayan sun gama tana
É—an kallon cikin gidan tace
"Yaya fa? Allah ya sa dai bai yi nisa ba"
Tace
"Yanzu kuwa ya fita amma babu jimawa zai dawo don abu ya je karɓo wa nan kusa da mu"
"Ina yaran? Ina sabreena?"
"Duk fa sun tafi Allo, ita sabreena suna bukin ƙawarta ta fita"
Bata gama magana ba kuwa sai ga Yayan ya shigo.
"Hajajju ke ce a gidan maraba sannu da zuwa"
Gaisawa suka yi Dukda yayanta ne sai dai shi ke bata respect duk saboda kuÉ—i masu gidan
rana.
"Ina soja marmari daga nesa? Sati biyu kuwa da ya shige ya aiko mana da kayan abinci wane
Allah dai yayiwa rayuwa Albarka ya cigaba da buda mishi"
"Ameen yaya, dama maganan da ta kawo ni kenan ma akan shi... Ka san akwai batu a kanshi
da sabreena da take ta mutuwar sonshi shi kuma yana nuna baya so, to yanzu zancen da nake
maka wata yaje ya É—auko chan wani kauye ta asirce shi tun kan ma ayi auren sai maganarta
yake ji yanzu haka saboda na raba su yana chan kwance gadon asibiti"
Gaje da Yaya suka hada baki suka ce
"Eyeee ka ji min yaran zamani ki samu mutum da uwar shi ki so raba su? Amma Saleem dai
yayi ragon azanci ina shi ina irin waennan matan?"
"Shiyasa nake so a tado magananshi da sabreena da na É—auka wata mai hankali zai É—auko
mana ashe dai shima hankalin bata ishe shi ba, na kuma ga gida bai koshi ba ai ba za'a kai
waje ba, idan ba damuwa ma bana son auren nan ya É—auki lokaci ko wata bana so ya rufa ta zo
tayi jinyarshi"
Gaje ta washe baki, Yaya dai ya É—an yi shiru kan yace
"Toh ai wani hanzari ba gudu ba, kin san bamu ajiye komai ba na shirin aurar da sabreena"
"Yaya duk wannan ba komai bane, ni ce nan uwarta ni ce ubanta ita kaÉ—ai nake so"
"Toh ai shikenan Allah ya shige mana gaba"
Suna cikin maganan sai gata ta shigo sanye da hijabi har ƙasa ganin mommy ta tsuguna
"Sannu da zuwa mommy"
"Sabreena ba zan amsa ba, yaushe rabon ki da gidan mu? Tun su Samha na jaje har suka gaji"
Baki ta ɗan taɓe tana ayyana su kuma dayake basu san inda nake ba ba, ai ina sane da
kyamar gidan mu suke ji shiyasa basa zuwa.
"Mommy islamiyya ne duk ya riƙe ni kin san muna ta shirin sauƙa"
"haka ake so ai Allah ya taimaka"
Daga nan bata wani jima ba tace zata tafi suka raka ta har mota kan suka juyo gida.
Wani irin guÉ—a gaje ta saki
"Malam!!! Kukanmu ya kusa yankewa nesa ta matso kusa"
Shi dai wani kalar murmushi yake, Sabreena ta cire hijabin jikinta ta jefar
Sanye take da wata fitted gown na lace da aka yi wa arniyar É—inki da ya bayyana komai nata,
kanta attach ne da ya zo har duwawu ta ja tsaki.
"Ke 'yar gari ya aka yi kika ankare tana nan?"
Gaje ta faÉ—a tana kai mata duka kamar kawarta
"Motar ta na gani nayi maza na shiga makota na ari hijabi na wanke fuska na cire eyelashes da
nails É—ina gashi a banza bata bani ko biyar ba mata sai makon bala'i"
"maganar aurenki ya kawo ta, nima zan so a zo ayi saboda na gaji da gani gani da ake yi min a
unguwar nan, ita kuma Hussaina a zaton ta banza ya faÉ—i ne zata É—auka bata san ta daukawa
kanta wuta ba... Ai yadda uwata bata taɓa kaunar nata uwar ba nima ban taɓa ƙaunarta ba
kuma ita ma haka da tana ƙaunata da bata barni nan cikin wahalar talauci ba"
Haka suka dinga tattauna yadda za su ci arziki don mommy ta jima da tsaya musu a wuya
kaman kashin kifi, don ma saleem mutumin kirki ne mai son zumunci baya wata bai turo musu
wani abu ba amma ita kam bata tunawa da su sai in bukatarta ne ya tashi, ta watsar da dangin
tamkar kashi an ɗauki Ƙawaye masu kuɗi an manna a jiki har kunyar nuna su take.
Sabreena dai da farko yarinya ce natsatsiya amma zamani ya zo mana da wani abu, iyaye ba
ruwansu bane yaro ya tsaya yayi karatun islama ko kar yayi, damuwarsu dai a nema ko ta wace
hanya, babu kwaba babu cikakkiyar tarbiya, tun tana dai yin abin saffa saffa yanzu babu wanda
bai san Sabreena 'yar karya ba, barta da son karya yau wannan saurayi gobe wanchan don
tana da kyau kuma suna kashe mata amma dai ita ta riga ta saka saleem ne mijinta tunda
iyayenta suka kwadaita mata hakan a ganinsu duk samarin ta ba zata yi mai kudin saleem ba.
Ita kuwa mommy tana shiga mota tayi murmushi
"Gwara ka auri wacce ko kwanciya na ce tayi in bi ta kanta zata kwanta, wacce dole ku haÉ—u ku
bi umarnina tare akan ka kwaso wacce zata raba ni da kai ko ta hanyar soyayyace kuwa bare
uwa uba asiri"
Daga haka ta ja motar ta bar unguwar tana kwafa.
****
Afeefah kam suna shiga É—akin da Abeeha ta kaita ta tsaya tana karewa É—akin kallo, É—akin yayi
kyau kwarai kuma full furnished don kayan É—akin milk da gold a gyare yake kaman akwai
mutum ciki alhalin ba mai zama É—akin tunda mai dakin tayi aure.
"Feel free Afeefah ki yi wanka bari na sa a kawo miki abinci, in kin ci sai ki hau gado ki huta
ko?"
Ta kalleta sai taga murmushi take mata saɓanin ranar da ta fara haɗuwa da Samha ta tuna har
wanke bayi Samha tayi da sunan tana kyamarta don kawai ta shiga tayi alwala, murmushi ta
mayar mata tace
"Na gode"
"Mind not"
Ta faɗa tana ficewa, a ƙasa Afeefah ta zauna tana dafe kanta da kaman zai faɗi, ta fara tunanin
halin da Saleem ke ciki sai dai kuma tayi tunanin ba zai damu sossai ba idan Ryan ya faÉ—a
mishi tana gidan su, jiri sossai yake damunta a haka ta lallaɓa ta miƙe ta shige bayin, wanka
tayi tana raya a komai ma fa gaba da gabanta tana tunanin abubuwan bayi da ƙawa na gidansu
saleem ne ƙarshe bata san akwai irin wannan ba, sai kuma ta fara tunanin kila suma akwai
wanda ya fi nasu shiyasa Allah ma da ya tashi bai yi yatsun hannu daidai ba kowa da
matsayinshi.
Amma me yasa kirkin waennan ya bambanta da waenchan Dukda waennan sun fi su dukiya?
Bata da amsar wannan tambaya ta wani ɓangaren kuma tana da shi don uwa nagartaccciya da
suke dashi ya gama amsa mata komai, dafe da gini ta fito riga kawai ta saka ko abincin da aka
kawo mata ta fito ta samu shirye a babban tray bata iya ta bi ta kai ba ta hau gadon ta
dukunkune, zazzabi ne ya saukar mata ciwon kai da jiri kuma suke contributing.
Kusan awa biyu tana cikin wannan yanayi tana ta hawaye, hawayen tunanin saleem bata san
itama tana jin wani abu a kanshi ba sai da suka rabu, ko babu komai shine mutum na farko da
ya bata dukkan kulawa da lokacin shi, ya nuna mata itama mutum ce kamar kowa, tana kukan
maraici da tsananin kewan iyaye saboda shi ne sila tun farko.
Knocking aka yi mata sai aka turo kofar da sallama aka shigo Abeeha ce
"Afeefah"
Ta ƙira sunan tana zagayawa ta kanta, ganin halin da take ciki ya bata tsoro
"Subhallah! Baki da lafiya ne? Sannu bari na faÉ—awa Mammi ta kira Ya Rayyan ya zo ya duba
ki"
Bata jira amsar Afeefah ba ta fice da sauri.
ÆŠakin Mammi tayi ta shiga da sallama ta samu mammin ta idar da la'asar tana zaune ne kawai
tana lazimi a hankali.
"Mammi Ya Rayyan bai dawo ba? Ko za ki kira mana shi?"
"Me ya faru? Ke fa kin iya rudewa a karamin abu"
"Mammi wannan yarinya da kuka dawo tare Afeefah kin ji jikinta? Kaman wuta sai kuka take yi
tana bukatar a duba ta ko mu tafi hospital?"
"Subhallah! Tashi mu je in ga jikin"
Har sun miƙe Mammi tace
"Taho min da wayata"
Taje ta É—auka a bedside suka fita, a ta babban parlorn nan suka yi sashen da take É—in wanda na
'yan matan biyu ne Jannah da tayi aure bai jima sossai ba sai Abeeha su suke rayuwa anan.
Suna shiga Mammi ta hau gadon da taimakon Abeeha suka É—aga Afeefar Mammi ta jinginata
da kafaÉ—arta tana yi mata sannu cikin kulawa, wannan dumi na jikinta da kulawar sai ya sake
karya zuciyar Afeefah tana tsoro! Tana tsananin tsoron su san tarihin ta suma su guje ta, tana
son wannan dumi da kauna a tare da ita in ba haka ba kila mutuwa zata yi kawai sai ta fi
hutawa, ta gaji haka zuciyarta ya fi glass tarwatsewa a yanzu haka.
"Kira min Yayanku"
Layin shi ta nemo a wayan mammin ta ƙira ringing na farko ya ɗaga da sallama.
"Mammi jikin ne?"
"No Saraki! Na ma ji ƙarfin jikin ka san abin kaman tashin aljannu yanzu sauƙi anjima babu
sauƙi sai na Allah, ya jikin saleem ɗin?"
Ya amsa cikin muryarshin nan
"Ya ji sauƙi though he's still on admission, amma komai zai daidaita in shaa Allah"
"Toh Allah ya bashi lafiya, ina so ka zo ka duba Afeefah fa ashe itama bata jin daaÉ—i jikin nan
rau sai kuka take"
Shiru yayi for seconds kan yace
"Mammi bai wuci yunwa ba and stress she should just eat nd get enough sleep"
"Ta ya mutum zai iya bacci with this temperature? Idan ba zaka zo ba in É—auki mayafi in kaita
asibiti"
Zaune ya miƙe daga kishingiden da yake a office nashi yana wara ido, yaushe Mammi ta san
yarinyar nan da har take mishi irin maganan nan a kanta? Yamutsa fuska yayi ko dai da gaske
asirin take yiwa mutane da har ta asirce mishi Mamminshi?
"Ina zuwa"
Abin da ya fada kenan da kyar, Mammi ta kashe wayan Abeeha tace
"Lallai Mammi kina so Ya Rayyan ya tsani yarinyar nan, tabbb he sound upset fa da yadda kika
mishi maganarta yo ko mune bamu da lafiya ba sai ya gama shan kamshin shi yake duba mu
ba, wani sa'in ba sai dai mu haƙura mu tafi asibiti ba ma"
"Abeeha yarinyar nan haka kawai nake jin she gets special place in my heart, kin san taimakon
da tayi min?"
Nan Mammi ta shiga bata labarin abin da Afeefah tayi mata
"Mammi wlh har Naji ina sonta sossai nima, to ina 'yan gidansu ina parents É—inta?"
"Ina ga sun yi magana da Saraki while i was unconcious don shi ya ce min bata da kowa"
Afeefah dai na jinsu, tunda Mammi ta kira Rayyan tsoro ya rufeta, gashi ya ji haushin yadda
mamanshi ta mishi magana a kanta kar ya zo ma yayi mata allurar da baƙar mugunta ita dai da
an barta kawai.
Suna É—akin suna ta hira kadan kadan don Abeeha bata son zama baki shiru har Afeefah na
mamaki kaman ba ƙanwar Rayyan da magana ke mishi wahala ba, ita ma dai bata ga
kamanninsu ba sai dai Abeehar kyakyawa ce kuma ta fi Mimmi haske amma ba ta kai ko farcen
Rayyan ba, bata gama nazarin ba ya shigo É—akin hannunshi rike da karamar Red briefcase.
Dammm haka gabanta ya buga, ya kalli Mammi da har lokacin Afeefah ke kan kafaÉ—arta ya
wara kyawawan idanunshin nan kan ya ce
"Me wannan? Mammi yaushe kika yi lafiyar daukar wata? Watan ma stranger?"
Da sauri Afeefah ta miƙe zaune jiri ya kwashe ta ta koma jikin gadon ta jingina idanunta a
lumshe zuciyarta na harbawa da tsoro.
"Haba Saraki ji yadda ka tsoratata?"
Ganin sossai ranshi bai mishi daaÉ—i ba yasa bata sake cewa komai ba, ya dubi Abeeha
"Wawuyar banza come on raka Mammi É—akinta she should be resting ba stressing kanta ba"
Tura baki tayi ya nufeta ta miƙe da gudu ta koma kusa da Mammi sai Harare Harare yake.
Mammi tayi dariya
"Zan je in huta Saraki don Allah ka yi mata a hankali, she's suffering"
Ta dubi Abeeha
"kin ga kama ni mu tafi tunda overprotective Yayan naki ya kore mu"
In ta shi ne fa tafiya ma zai iya yi mata, itama kuma son da take mishi bata hada da kowa ba,
kuma babu wanda ya kaita saninshi don ko kallon abu yayi ta san ma'anar kallon, Dukda
fuskarnan ya fi zama a haÉ—e amma ita tana gane idan yana cikin farin ciki, damuwa ko bakin
ciki, yanzu haka ta karanci akwai 'yar damuwa a ranshi sannan har da rigima irin tashi don baya
so yaga tana fifita wani a kanshi, su Jannah kan ce Ya Rayyan idan ya samu wacce yake so
kamar rai za'a ga kishi kamar hauka.
Bayan fitan su É—akin ya zama shiru sai su biyu kawai hakan ya kara tsinka Afeefah.
"Kwanta"
Ta ji muryarshi ya daki dodon kunnenta duk da ba da ƙarfi ko tsawa yayi maganan ba.
Da sauri ta kwantan tana kara jan bargo, hannunta dake kan cikinta kawai taji sassanyar tafin
hannunshi mai taushi ya kama babu shiri ta buÉ—e idanunta sai suka faÉ—a cikin nashi da shima a
lokacin ya kalleta...
****
Ta ɓangaren Sulaiman yana ta gwada Layin Afeefah don ya ji ya jikinta har yamman ya kasa
samunta, ya ajiye kila network ne don haka ya cigaba da huldar gabanshi har Magrib baya
samunta, yana gama shirin asibiti ya nufi gidan don ya ji ko lafiya baya samunta haka bayan ya
isa suka gaisa da su mudi.
"Don Allah ko za ku dubo min Afeefah?"
Iliya ya ce
"Ai Afeefah bata gidan nan, ina zato ma ta barshi gabaÉ—aya don da akwati ta fita tun safe"
Gabanshi ne ya faÉ—i
"wani irin tafiya ba dawowa? An taɓa tafiya haka babu shiri? Gida ta koma ne?"
Mudi yace
"Wallahi bamu sani ba amma dai kaman gidan dai ba lafiya dai, don Oga saleem ma yanzu
haka yana kwance Hajiyar na a hasale, 'yan matan kuma sai kuka Toh ita ma Afeefar da ta fito
a chan ta tsuguna ta ci kukanta isashe kan ta tashi ta tafi"
Sossai damuwa ya nuna a fuskanshi, idan tunanin shi ya bashi daidai Saleem ya faÉ—awa
Afeefah yana sonta mamanshi ta ji shine suka kore ta, godiya yayiwa su Mudi ya juya ya nufi
gida, kila ta koma kauyensu yana ji a ranshi da sauƙi ma tunda har ta faɗa mishi sunan kauyen
kan su rabu da bai san inda zai sa kanshi ba, dole ya je ya neme ta.
Gida ya dawo Umma na ganinshi tace
"Ah Sulaiman ina asibitin? Me ya faru na ga kaman kana cikin damuwa?"
"Umma su saleem sun kori Afeefah a gidansu, mamanshi ta kore ta ta koma kauyensu dole
gobe in nemi leave in je in sameta ban san ya take ba kuma wayanta baya shiga"
"Wacece haka?"
Suka ji Muryar Abba!
Umma ce ta mishi bayani yana murmushi yace
"Toh ai Alhamdulillah! Dama da niyyar aura maka mata na dawo a yau na gama maka uzuri
goben da su Yaya Zubairu za ku tafi a yi maka tambaya gabaÉ—aya tunda Allah ya sa ka samu
wacce kake so kuma mahaifiyarka ta gamsu da tarbiyar ta"
Murmushi ya saki yana jin sanyi a ranshi Dukda ta wani ɓangaren yana tunanin kar Afeefah taji
ba daaÉ—i tunda bata sani ba kuma ba wai soyayyarsu yayi zurfi bane ita ke ture shi yana sa kai
amma dai ya ji daaÉ—i don da farin ciki ya koma asibitin da bai yi niyyan zuwan ba ya tafi saboda
ya samu leave a gobe É—in don su tafi Dutsen-wai.
A waya Abba ya sanarwa yayyenshi biyu akan za'a je wa Sulaiman tambayar Na gani ina so a
kauyen Dutsen-wai, basu wani damu ba don duk su burin su ba su hada zuri'a da masu kuÉ—i ba
sai su hada da gidan mutunci gidan tarbiya da sanin ya kamata shi ne abin da suke dubawa.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Gobe in muna raye sai dare za ku ji ni da yardar Allah*
*020*
Harara ya sakar mata da sauri ta mayar da idanun ta rufe ruff tsaki ya ja a fili, ya fara ƙoƙarin
neman vain É—inta... 'Asshh' ta faÉ—a a hankali jin ya soka allurar sai ta fara kokarin janye hannun.
"Kina janye hannun nan sai na wanka miki mari akwai wanda yace ki yi ta tuna samarin ki kina
kuka har ciwo ya kama ki?"
Tsit tayi bata kuma motsan ba, kila Rayyan shine ajalinta wa ya sani don tunda ya daka mata
tsawar nan ko numfashi mai kyau ba ta iya ja har ya gama É—aura mata drip É—in, bata ji fitan shi
ba ita kam tun tana pretending har baccin gaske ya É—auke ta a haka, don dama jiya ba baccin ta
samu ba na kirki gashi yau ta yini a kan hanya tana galantoyi.
Sashenshi kawai ya miƙa daga nan don ya matuƙar gajiya hutu kawai yake buƙata, wanka yayi
ya fito da alwala ya zo ya shirya cikin wani morrocon jallabiya baƙi sidik mai sheki wanda ya fito
da ainihin kyaunshi fatarshi ya haska jallabiyar, masallaci kawai ya wuce bai dawo cikin gidan
ba sai da yayi isha, time ya kalla ya É—auke ido ya nufi cikin main parlorn kai tsaye É—akin da take
ya wuce, ta miƙe zaune bayanta jingine da jikin gadon kafafunta na cikin bargo, idanunta sun
kara girma sun dan sauya saboda kukan da ta yini yi ga kuma bacci da tayi tayi, hulan kanta ya
zame sosai ya bayyana rabin gashinta mai sulbi, tunani take ya zata yi in ruwan ya ƙare sai taji
an yi knocking seconds uku zuwa huÉ—u ya turo kofan ya sanyo kai da sallama wadda iya shi
kaÉ—ai ya san yayi kayanshi.
Kanta tayi saurin mayarwa kasa Alamu sun nuna bashi da niyyar magana don har ya zo ya cire
ruwan da ya ƙare ya bare wani allura ya fasa yayi mata a canular bai ce takk ba itama bata ce
ba, kamshinshi duk ya cika É—akin har ya gama ya juya zai fita ta furta
"Na gode"
Bai ce komai ba ya fice daga É—akin, kai tsaye wurin Mammi yayi, tana daga parlor a zaune cikin
kujera abinci ne a gabanta wanda ta gama ci yanzu cikin kula sossai da cimar tata É—in don
professional cooker ya samo mata wacce take kulawa da zallar abincinta kuma take da karatu
na musamman akan cimar da ake ba wa masu ciwon ƙoda da kan tafi da diabetes, ba'a so ta ci
late kuma da ta gama ta sha magani tana so ya É—an saketa sai taje ta duba Afeefah.
Bai yi magana ba kawai ya zo ya zauna gefenta, ta kalleshi tayi murmushi
"Gajiya ne a jikinka sossai Saraki, ka ci abinci sai ka je ka huta"
Kai ya gyaÉ—a kawai don bashi da niyyar magana, da intercom tayi amfani ta kira su a kitchen a
kan a kawo abincin Saraki, simple abinci ne marar nauyi yake ci da dare suka kawo suka jere a
gabanshi, har lokacin yana kishindige kusa da ita idanunshi a lumshe.
"Tashi ka ci kar yayi sanyi babana ko in baka?"
Ya buÉ—e ido a hankali ya É—an yi murmushi kaÉ—an sai wani sirrin kyaunshi ya bayyana Dukda
murmushin bai jima ba sai dai tabbas duk wanda yayi wa irin murmushin zai jima bai manta ba.
Itama murmushi tayi don ita kam akwai fara'a masha Allah, abincin ya É—an ci kaÉ—an ya kalleta
jin tana cewa
"Ina zuwa zan duba Afeefah"
Da Kai ya amsa ta fice, ta samu Afeefar ta idar da sallolinta tana kokarin cin abincin da aka
shigo mata dashi Abeeha na zaune cikin kujera daya daga cikin huÉ—u dake gefen É—akin tana
danna waya ganin Mammi ya sa ta taso
"Afeefah É—iyata ya jikin?"
Murmushi ta saki a kunyace tace
"Alhamdulillah da sauƙi sossai Aunty na gode"
"Bana son sake ji kin ce Auntyn nan baki ji Abin da su Saraki ke faÉ—a bane?"
Murmushi tayi.
"Abeeha ki kula da ita har tayi bacci zan je Saraki na jirana in na sha sauran magungunan kuma
kin san bana iya taɓuka komai sai da safenku"
"Toh Mammi sai da safe Allah ya kara sauƙi"
"Allah ya baki lafiya sai da safe Mammi"
Afeefah ta faÉ—a ta amsa da murmushi kan ta fice.
"Na ga dai baki da niyyar sa abincin nan bari na zuba miki"
Abeeha ta faÉ—a tana zuba mata Afeefar ke cewa yayi amma sai da taji ya mata a ranta kan ta
bari kuma tace sai Afeefar ta cinye, sossai moment É—inta a gidan na yan awannin nan yayi mata
daaÉ—i in ka cire arangamarsu da Rayyan amma Mammi da Abeeha mutanen kirki ne da suka yi
ƙarancin samu a wannan zamani.
Mammi na komawa ta samu ya gama, É—aki ta shige ta fara shirin kwanciya cike da dauriya take
komai fuskarta dai baya nuna wa amma ita ta san me take ji, sai da ya bata mintunan da yake
da tabbacin ta gama yayi knocking ya shiga É—akin tana zaune bakin gado sanye da doguwar
rigan bacci har ƙasa mai kauri, frigde yaje ya ɗauko mata ruwa tulin magungunanta da suke
cikin wani basket guda mai kyau ya ɗauko ya zaɓi na daren ya bare ya sanya mata a tafin
hannunta, babu musu ta sha yadda ya buƙata kan ta kwanta, ya ja mata bargo ya zauna daga
gefenta tare da riƙe hannunta ɗaya.
Adu'a yayi ta mata tun tana kallonshi tana danne hawayen da suke ta yunkurin zubo mata har
tayi bacci, idanunshi da suka rine ya É—an rintse yana jin azaban da zuciyarshi ke yi, da yana da
yadda zai yi ya mayar da ciwon Mammi jikinshi da bata shekara takwas tana fama da kidney
failure ba, da kuÉ—i za su yi mishi maganin ciwon Mammi da ko zai yi yawo tsirara sai ya samar
mata lafiya, sai dai yana roƙon Allah a koyaushe yadda aka bata wa'adin watanni uku za ta
mutu amma yanzu shekara har bakwai da abin ya san ba yin su bane ba kuma dabararsu bace
Allah ne mai yadda ya so, sai dai a tsananin tsorace yake hakan ya sa sadaqa da duk adu'ar
shi yake kan Mamminshi itama saboda rage mishi damuwa take danne wani abin.
Sai da ya tabbatar komai intact kan ya fice daga ɗakin yayi Sashenshi, Saleem ya ƙira da har
lokacin yana asibiti yana samun kulawa
"Har yanzu babu labarin Afeefah ko Rayyan?"
Ajiyar zuciya Rayyan ya sauƙe
"Na ce ka daina É—aga hankalinka za mu same ta, ina kan bincike dai in har tana cikin Kaduna
ba zata ɓace ba just focus on your health"
Kai saleem ya gyaÉ—a sai yake ganin kaman Rayyan bai yi niyya bane, da yayi niyya ba zai kai
zuwa lokacin bai same ta ba, damuwarshi ya zata kwana? A ina zata kwana? Me ta ci? Duk ya
kasa kwantar da hankalinshi a gefe ga damuwar rashin ganin mommy Dukda ta mishi abin da
ya zama gyambo a zuciyarshi sai dai uwa ce babu yadda ya iya kuma yana ƙaunarta bata da
mahadi a wannan duniya.
A É—an sanyaye yayi sallama da Rayyan, Rayyan ya bi wayan da kallo baya jin zai gaya mishi
inda Afeefah take saboda yana son Saleem É—in ya manta da ita once and for all yanzu in ya san
tana nan zai cigaba da sa hope a kan samunta alhali mahaifiyarshi bata É—aura wannan damara
ba na mallaka wa yaron nata cikar burin shi hakan ya sa ya ɓoye mishi wanzuwar Afeefar a
gidansu.
Su Samha ko da suka zo sun ƙaraci zamansu ko ci kanku bai ce musu ba sun gaishe shi ma
bai amsa ba, wani irin zafin su yake ji a lokaci ɗaya yana mamaki bai taɓa sanin inhumanity
É—insu ya kai haka ba, suka gaji suka tafi.
****
Washegari
Da misalin karfe bakwai na safe Sulaiman ya fito shirye cikin manyan kaya, sallama yayi wa
umma tana ta adu'ar dacewa Baba Jummai ma Adu'a tayi ta mishi har ya fice. Gidan Yaya
Zubairu ya fara zuwa ya É—auke shi kan ya wuce gidan babban Yayansu Abban Yaya Ummaru,
dattijai ne masu mutunci da kamala kuma duk suna da dukiyar su daidai gwargwadon.
Anan suka kama hanyar kauyen su Afeefah yana ta Adu'a da Fatan ya same ta chan Dukda bai
yi ma tunanin rashin samunta ba don ina zata koma in ba gida ba? Tafiyan awanni kadan ya
kawo su kauyen yana jin hirarsu Yaya Zubairu da suke zaune a baya, sai da suka É—an shiga
cikin garin kan ya ɗan tsaya jikin wani shago matasa ne zaune su wurin huɗu ya sauƙe glass
"Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka"
"Barka dai Alhaji"
"Don Allah tambaya nake yi"
"To Allah ya sa mun sani"
"Gidan su Afeefah kamal"
Tsittt suka É—an yi wannan ya kalli wanchan wanchan ya kalli wanchan..
"Kai ko me zaka yi gidan su Mayyar yarinyar nan? Ai Annoba za ka ce sai mun fi gane ta"
"Annoba"
Ya maimaita sunan, abin da ta faÉ—a mishi kenan me yasa ake ce mata annoba? Dan kallon su
Yaya Zubairu yayi duk fuskar su ya É—an nuna mamaki.
"Gidansu nake nema"
Ya faÉ—a ba tare da ya ji daaÉ—in furucin su a kanta ba.
"Ka ga kara gaba sai ka tambaya a chan, ba mu san ko laifi ta muku ba kun zo yi wa kawunta
tijara abu ya shafe mu lalala bamu shirya rigimar Labaran ba"
Babu wanda ya tanka a cikinsu har ya ja motan suka yi gaba, wasu yara 'yan daidai ya samu ya
kira su su biyu
"Gidan su Afeefah kamal nake nema"
ÆŠayan ya É—an kalli É—ayan
"Mayyar nan fa suke nema ta gidan su Auwalu"
ÆŠayan ya zaro ido
"Wacce ta cinye Amadun gidan malam yahaya ta gudu duniya?"
"Eh ita ce..."
Sai É—ayan ya gyaÉ—a kai ya juya ga Sulaiman da kanshi ya sake mugun É—aurewa.
"Idan kayi gaba ka É—auki Layin hagu gida na biyu in baka gane ba ka ce gidan su Annoba kake
nema ajalin duk wanda ya raɓeki"
Suna kai nan suka gudu.
"Sulaimanu a wani irin gida ka nemo aure? Wace irin yarinya ce wannan bata da shaida mai
kyau?"
Shiru yayi shima amsar yake nema don kwata kwata ya kasa fahimtar komai.
Gaba yayi don clearing doubt ya sake tambayar wata mata a yanzu annobar shima ya faÉ—a
yana runtse ido aiko ta nuna mishi, Da gaske ne ko wasa? Ya kasa ba kanshi amsa, kaman
mafarki yake kaman kuma duniyar halluscination ya shiga don abin ya fi yanayi da almara,
wacece Afeefah?
Tarin mutane da suka gani kofar gidan kawu ne ya É—an basu mamaki, bayan yayi parking suka
fito su uku suka tsaya suna kallon abin mamaki, dambe ake ci da Kawu da inna larai har kofar
gida duk ana tsatsaye ana kallonsu don su in suna yi ba'a raba su in ma ka shiga karshe kai za
ka ji kunya, kuma ba karamin dukan ta yake ba, Bakinta ya ƙi shiru duk yaransu na zagaye
suna kwasar kallo.
"Wani irin tsantsar jahilci ne wannan? Sulaiman a nan gidan ka É—auko aure? Anya da
hankalinka?"
Kawu Zubairu yayi maganan kaman ya rusa kuka.
Kawu Ummaru ne ya je ya janye kawu Labaran daga riƙon da yayiwa larai ya ce
"Haba malam baka san wannan abin da kake yin ya saɓa shari'a ba? Musulmi ne fa kai sannan
mutum ba dabba ba wannan ai É—abi'ar dabbobi ne, ba matarka bace ta sunna?"
"Kyale shi ai ni wandon roba nake daidai da kugun kowa, wlh ba zan yi wahala in nemi kudina
Labaran ya dinga bin dare yana sace min ba shi ba ciyar da mu yayi ba kuma muyi wahala mu
samu ya zama ɓera, Toh ni ba Asabe bace da ka gama kassarata ta koma cima zaune babu
abin da take ba, kuma wallahi sai ka biyani kudina"
"Ni kike cewa ɓarawo? Yau sai na ci ubanki Larai sai na zubar da hakwaran rashin da'ar nan
Malam Sallau shi zai raba mu"
Babanta yake nufi, ganin za su cigaba da rigimar su kawu Ummaru ya ja shi gefe.
"Ashe baka san Annabi yayi mana hani da dukan matan mu ba? Yanzu kai ba abin kunya bane
yaranka gode-gode suna tsaye suna kallon ku ba? Dambe har kan layi? Subhallah"
Kwarjini mutumin ya mishi da sai ya yanko mishi magana amma sai ya Buge da cewa
"Waye kai? Me kake so? In baka da abin faÉ—a zan kama gabana don ina da abin yi"
Girgiza kai Kawu Zubairu yake Sulaiman kam ya mayar da kanshi kasa yana jin yadda
zuciyarshi ke cigaba da tsitstsinkewa don tabbas da matukar wuya Su kawu su bari su yi
surkuntaka da mutum irin kawu, yanzu wannan baban Afeefah ne? Innalillahi wainna ilaihi rajiun
ya maimaita ya kai sau biyar.
"Sunana Umaru Malami zuwan namu ya shafi 'yar wurin ka Afeefah"
Zaro ido kawu yayi
"Ba dai a yawon tambaÉ—arta ba ne ta kashe muku wani kuka zo nemanta? Ni fa na jima da
yanke alaqa da yarinyar chan ba zai yiwu a dinga zuwa ana É—aga min hankali akan kashe-
kashe da take ba"
"kashe-kashe?"
Kawu Zubairu ya maimaita
"Wai baku sani ba? Ai rikakkiyar Mayya ce da ta addabi al'ummar garin nan a ƙarshe korinta
muka yi ta shiga duniya"
Jiri ne ya kwashi Sulaiman yayi baya baya ya dafa mota, zuciyarshi na harbawa da karfin gaske
tuni idanunshi suka sauya, kwalwarshi ya nemi tsayawa da aiki amma sai ya tuna farkon abin
da ya kawo Afeefah asibitin su ta sha poison ne don ta kashe kanta! Afeefah tana da tarin
damuwa da yake haddasawa jininta sauƙa sossai zuciyarta kuma na ta kokarin samun matsala,
me kenan? Menene ke kunshe a rayuwarta haka? Duk ya rikice amsa yake buƙata sai dai ba
daga bakin wannan kaskantaccen mutumin da ya kira kanshi kawunta ba.
"Toh mun gode ko, sai anjima"
Juyawa kawu yayi ya kada rigar shi yayi gaba.
"Sulaiman wannan ƙasƙanci har ina? Yanzu inda ka zabi neman aure kenan? Toh ba'a zuriyar
Malami ba"
Kawu Zubairu ya faÉ—a yana bude mota ya shiga, kawu Ummaru ma ya shiga Sulaiman da kyar
yayi composing kanshi ya zagaya ya shiga ya tada motar a hankali yace
"Don Allah ku yi haƙuri kawu ku yi min uzuri, wallahi Afeefah ba haka take ba ita nake so ba
kawu..."
"Sulaiman ko Afeefah ta fi kowa musulunci a duniya ba za mu nema maka aurenta ba, ba
za.mu taɓa hada zuri'a da irin mutanen nan ba, ban damu don an ce mata Mayya ba duba da
irin kauyen da tarin jahilci ya musu yawa amma a yadda ta shiga duniya danginta suka watsar
da ita har suke ikikarin yanke duk alaqa da ita, da kuma yadda muka sami wannan gida ba
gidan aure bane, kana da tarin mata masu nasaba da asali cikakku waenda suke gaban
iyayensu zaune don haka ka tabbatar baka kara tado zancen wata Afeefah ba, a yau ka fara
dubawa cikin sauran yaran da iyayensu suke maka tayin auren su za'a hada aurenka da Munir"
Kawu Ummaru yayi maganan.
Muryar shi na rawa ya ce
"Amma ka..w..."
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Ina so na yi addressing wani issue, na yi kokari in share in yi kaman ba komai amma dai na
kasa, wato muna zuwa wani mataki da za'a iya fara cewa Gureenjoh na wulakanci ban damu ba
saboda Allah ya gani ba wulakancin nayi ba, babu yadda za'a yi na fara littafi na yi nisa ki zo ki
ce in tura miki na amsa na kuma tura miki zuwa inda na tsaya, muna groups dayawa dake da
nake posting a maimakon ki cigaba da tarawa ko ki cigaba da bi baki yi hakan ba bayan kwana
biyu na sake yin nisa ki sake dawowa ki ce in kara tura miki daga inda na tura miki last zuwa
inda na tsaya wallahi ba zai yiwu ba, ba zaman banza nake ba wani lokacin ni na san yadda
nake squizing time É—ina ina typing, wallahi ba zan tura ba idan za ki jira na gama na haÉ—a
document na tura groups ki gani ki karanta fine, idan ba za ki karanta ba duka a wurina daidai
ne*
*jama'a kuyi haƙuri da Page nan guntu ne pls, idanuna rufewa su ke da kyar na kai inda na kai
saboda gajiya da bacci*
*021*
"Sulaiman?? Har za ka ja da maganan Yaya a kan yarinyar? Aaa lallai, yo ko mahaifinka ya isa
ya sauya maganan nan?"
Kawu Zubairu ya katse shi a hasale.
Shiru Sulaiman yayi sai dai idanunshi tamkar garwashi, zuciyarshi yake jin ya wani matse ya
mishi nauyi wane dutse aka É—ora mai, kawai don kawu bai da hali sai a hana shi auren Afeefah?
Me laifin ta? Ita me tayi? Har suka shigo Kaduna bashi da natsuwa, da kyar ya kai kowannensu
gida suna ta kushe wannan neman auren nashi haka ya nufi gida ko da ya shigo a parlor ya
samu Umma, ganin yanayinshi kaman zai faɗi ta miƙe da hanzari ta riƙe shi
"Sulaiman! Menene? Lafiya kake kuwa? Ko wani abin ne ya samu Afeefar?"
Girgiza kai Yayi yana neman inda zai zauna ta ja shi kujera suka zauna tare, Baaba jummai ma
da tun safe take ta adu'ar dacewa ta fito, ruwa ta je ta É—auko mishi Umma na tsaye kanshi tana
ta tambayar shi duk ta rikice ta sanshi da masifar migrine in ya fara kuma baya jin magani,
ruwan ya karɓa ya sha sossai tamkar zai fasa ihun kuka yace wa Umma
"Umma wai su kawu ba za su nema min aurenta ba, wai ba za su hada zuri'a da ita ba, Umma
idan kenan kawunka bashi da halin kirki sai aka ce kaima haka kake? Me Afeefah tayi na kin
aurenta? Don Allah ki yiwa Abba magana ya samu Yayanshi zan nemi Afeefah! Zan neme ta
duk inda take ni dai don Allah ya bar ni in aureta a haka nake son ta"
Duk sun kasa gane inda ya dosa, Abba da shigowan shi kenan ya ce
"Ba da Miyau na ba kam, sai dai kuma idan kai zaka nemawa kanka aure wannan kam zaka iya
amma tunda har Yaya ya kirani ya tabbatar min gidan chan ba gidan neman aure bane ba zan
taɓa sake tado maganar ba don na san ba karya ya yi ba, da kai aka je ai ba da wani ba kuma
kaima shaida ne"
Idanun da suka sake rinewa sossai ya zubawa Abban yace
"Abba ita wallahi ba haka take ba, nitsatsiya ce kuma tana da tarbiya daidai gwargwado, Abba
aka auri karuwa da ta tuba ma bare Afeefah? Abba ko ladarta ba za ka bari na samu ba?
Korinta fa suka yi bayan sharri da ƙage da aka lankaya mata a garin"
A yanzu kam hawaye sai da suka zuba mishi.
"Ko ma menene Sulaiman ba a zuri'ar mu ba, ban taɓa saɓa maganan Yayana ba kuma ba zan
fara a kan ka ba Sulaiman, ku fara shirye-shiryen auren shi za'a hada da na Munir"
Umma ta É—ago da sauri ta kalleshi
"Alhj wata É—aya fa kacal ya saura na Munir yaushe ya gama warke wannan ciwo da zai yi
aure?"
"Ke kenan kike goya mishi baya yayi abin da yake so ko? Toh shikenan kar yayi"
Yana kai nan ya wuce abin shi.
Baaba jummai kam har hawaye take yi, bayanin abin da duk ya faru yayi musu bayan ya gama
ya kama hannun Umma
"Don Allah umma ko auren za'a yi min ki taimaka ki saka baki a hada da Afeefah wlh ina son ta,
tausayinta kuma yanzu ya sake kama zuciyata har ina jin kaman zai fashe"
Duk sun tausaya mata, Baaba jummai ta sha kuka sai Allah ya isa take yi a madadin ta, abin da
ya dame su ma kasancewar yanzu ba'a san inda ta dosa ba.
"Yanzu ka je ka sha magani ka huta sai ka je ka nemo mana ita in har muka sameta komai mai
sauƙi ne, rayuwar 'ya mace a haka hatsari ne komai zai iya faruwa, imma a yi mata mugun abu
ko kuma ta jefa kanta halaka"
Duk sun gamsu, Miƙewa yayi ya nufi Sashenshi cike da tunanin ta ina zai fara nemanta?
*****
Saleem a Washegari aka sallameshi ya koma gida, shi ne ma ya matsa saboda ya damu da
halin ko in kula da Mahaifiyarshi ke mishi, ƙannenshi kam ba ya kula su bayan ya dawo wanka
yayi ya fito, har kicin ya shiga Talatuwa ta bashi abinci ya zo ya ci kan ya nufi É—akin Mommy,
sossai yake kokarin danne damuwar da yake ranshi saboda Rayyan da yayi ta ƙoƙari wurin
ganin ya manta Afeefah ya cire ta a rayuwarshi.
Zaune ya sameta bakin gado tana danna waya, sallamar shi kawai ta amsa amma ko É—ago ido
bata yi ta kalleshi ba, a gaban kafafunta ya je ya zauna
"Ban taɓa tunanin akwai ranar da zai zo da zan yi rashin lafiya har in kwanta na tsawon kwana
daya gadon asibiti Mommyna bata zo ta duba ni ba, na san na miki laifi mai girma ne shiyasa na
kasa bari in samu lafiya na nemi a sallameni don in zo in nemi yafiyarki, kiyi haƙuri in shaa
Allahu na cire Afeefah daga raina..."
Ya faÉ—a a raunane
"Duk kuma abin da kike so zan cigaba da so matukar bai saɓawa shari'a ba ko da kuwa zai
cutar da ni ne, ki yi haƙuri Mommy"
ÆŠagowa tayi ta kalleshi sai zuciyarta ya karye, wani sashe na cewa bata yi mishi adalci ba, wani
kuwa na bata ƙwarin gwiwa a kan abin da ta aikata ɗin ai taimakonsu ne gabaɗaya.
"Zan yafe maka in manta irin rashin kunyar da ka yi min matuƙar ka bi umarnina na karshe a
gareka"
Ta faÉ—a cikin tabbatarwa.
"Mommy ko me kike so ki faÉ—a ni kuma zan cika miki ko da bana so"
"Zan aura maka Sabreena nan da wata guda"
Da sauri ya É—ago ya kalleta amma sai harshen shi ya mishi nauyi, uffan ya kasa cewa sama da
mintuna uku kan ya ce da kyar
"Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi"
"Ita ce ma Alkhairin naka"
Kai kawai ya gyaɗa ya miƙe ya fice fuskar shi babu walwala sam, a parlor ya ga Sameera na
zaune, ido ya É—an zuba mata ganin ta mishi rama kuma ta yi zuru zuru ga damuwa nan fal a
fuskarta, kaman zai yi magana kuma sai ya wuce abin shi.
****
Ta ɓangaren Afeefah ta tashi Washegarin jikin da kwari sossai, wanka tayi ta saka kayanta ta
samu wuri ta zauna don bakunta ne fal cikinta da kuma tsoro, har yanzu Mammi bata san
wacece ita ba shin wani abu zai chanza in ta san wacece ita? Anya shi ma Rayyan ya san
wacece ita kuwa? Tunanin da yake ta kai komo kenan a ranta har ta ji an tura kofan an shigo.
ÆŠaga kai tayi tana amsa sallamar Abeeha.
"Alhamdulillah jiki yayi sauƙi sossai Aunty Abeeha"
Ta amsa mata bayan ta jefa mata tambayar yaya jiki, Zaro ido Abeeha tayi
"Lallai Afeefah ni ce Auntyn taki? Kin ga kirani Abeeha na bana wani son Aunty na san ko da
zan girme ki ba zai wuci da shekaru biyu ba"
Afeefah ta É—an yi murmushi
"Toh ai ko da kwana É—aya ne kin cancanci na ce miki hakan bare har shekaru biyu"
"Ni dai bana so na bar miki"
Ta faÉ—a da dariya, Afeefah ma tayi murmushi
"Kin karya kuwa?"
Abeeha ta tamabaya don ita ta tafi lectures 6 yanzu kenan dawowanta 9 É—in nan.
"Eh sun kawo min har nan na karya, ina dai so in je in duba jikin Mammi ne kuma ban san ta
inda zan ganta ba"
"Nima chan nayi daga nan, na fita duk kuna bacci. tashi mu je"
Miƙewa Afeefah tayi Abeeha na cewa rigarta ya mata kyau tayi murmushi tana mamakin saukin
halin Abeehar da saurin sabon ta.
Sai kallon gidan Afeefah ke yi tana ƙara yabawa abin da ya fi burgeta yadda ko ina kalkal sai
kamshi da sanyin Ac ke tashi, ga nan chandliers design daban daban masu kyau kowanne da
kalar hasken shi da tsaruwarshi, silifas É—in kafafunsu mai taushi kaman ka nitse ciki take ta jin
daaÉ—in shi don duk basa yawo kafa banza a cikin gidan da lofas É—in su masu kyau itama kuma
har É—aki aka kai mata saboda sanyin tiles, É—akin Mammin suka tura da sallama suka shiga.
A kan kujera suka samu Mammi gabanta fruits ne masu low potassium tana sha shima kuma in
portion ne akwai yawan da ba zai yiwu ta sha ba, Daga kan gadonta Rayyan ne yana cikin
bargo Dukda ba bacci yake ba idanunshi lumshe yana tunanin maganan da Mammi ta gama
faɗa mishi yanzu, numfashi ya ɗan sauƙe ya buɗe idanunshi ya kalli inda suke a lokacin
Afeefah ta kai ƙasa Mammi na ce mata
"Tashi! Tashi a ƙasan nan Afeefah ga kujera zauna ko ki zauna bakin gado ina ke ina zaman
wannan sanyin"
A bakin kujera ta É—an dosana tana gaishe da Mammin, Mammin ta amsa cike da kulawa tana
tambayarta jiki ta ce ta ji sauƙi, Abeeha ma ta gaisheta tana tambayar karfin jikinta duk adua
suka dinga yi wa Mammin tana amsawa, sam Afeefah bata kula da Rayyan ba Mammi da ta
kosa ta ji Afeefar daga ina take kuma ina danginta tace
"Afeefah ki yi haƙuri da tambayana, ba wai zan tambayeki bane saboda mun gaji dake ko muna
so ki tafi ba, yana da kyau ne tambayar saboda mu san asalinki mu san me ya rabo ki da
danginki, in kika duba yadda wannan zamani ya zama har wasu tsoron taimakon suke saboda
dayawa an fi janyo su inuwa su tura mutum rana. Idan har baki shirya sanar da mu ba kuma za
mu hakura mu cigaba da zama dake har ki ji kin gamsu kina son sanar da mu É—in. Na yi ta
tambayar Saraki bai ce min komai ba"
Afeefah ta É—an muskuta gabanta na tsananta faÉ—uwa ta ce
"Mammi don Allah ki daina ba ni haƙuri, ya zama dole in sanar da ku wacece ni! Ina tsoron saka
ki cikin damuwa alhali ba lafiya ce ta ishe ki ba don labarina bashi da daaÉ—i, bashi da abin
burgewa ko karsashi, babu abin da ke ciki sai tarin baƙin ciki, kuka da damuwa, Mammi Sunana
Afeefah kamal na buÉ—i idona ne kawai na tsince ni gaban kakata wacce ta haifi babana...."
A hankali ta cigaba da basu labarinta tun daga farko har ƙarshe, ta gaji da kuka a kan labarinta
hakan ya sa a yanzu ta danne kwarai bata yi kukan ba sai idanunta da suka rine matuƙa gaya,
bayan ta gama ta É—ago ido tana kallon expression na su Mammin gabanta na faÉ—uwa zuciyarta
na duka da ƙarfin gaske....
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*22*
Ga dumbin mamakinta dukkansu biyu kuka suke yi, Abeeha kam ma da sauti yayinda Mammi
ke zubar da hawaye, ko kan tayi wani yunkuri Mammi ta miƙe ta iskota ta ɗago ta sai ta sanya
ta jikinta ta rungume tana shafa bayanta, wannan dalili! wannan É—umin jikin shi ya saka Afeefah
fashewa da sassanyar kuka mai sauti.
Sun fi mintuna goma a haka tana wannan kukan, tuna komai take yi tamkar yanzu ne ya faru ji
take duk mace-macen yanzu ne suke dawo mata sabo, taji tana kewar mahaifiyarta da Aunty
zee, wannan tausayi da kauna da ta gani daga Mammi sai ya tsaya mata a rai ta ji itama tana
ƙaunar matar tamkar mahaifiyarta.
Rayyan da tun kan tayi nisa ya lumshe idanunshi bai buÉ—e ba sai da ya ga kukan na yawa, duk
tsikar jikinshi jinshi yake a tashe, ko da ya miƙe zaune sai da ya ji kanshi ya sara ya ɗan runtse
idanunshi ya buÉ—e kan ya ja tsaki ya sauka daga gadon, ya taka ya dafa kafadar Mammi da har
lokacin take rike da Afeefah.
Mammin gabanta ya faÉ—i tuna yana É—akin ta tuna labarin Afeefah sai tayi sauri ta saki Afeefah ta
waiga tana kallon yanayinshi, idanunshi ya sauƙe kasa a hankali yace
"Mammi please ki bar kukan nan, you are sick already kukan nan bashi da amfani, dole ne sai
mutum ya rayu da dangi? Dole ne sai sune kaÉ—ai za su baka farin ciki da kulawa? Na Allah na
nan dayawa Mammi..."
Yankewa maganan yayi ya ɗago garin kaucewa idanun Mammi sai nashi suka sarƙe cikin nata,
sama da seconds huÉ—u yana kallonta kan kawai ya juya ya bar É—akin.
"Saraki.! Saraki....!!"
Bai juyo ba ya fice, ta duƙar da kanta tana ambatar sunan Allah... Chan ta sauƙe numfashi ta
waigo ga Afeefah da tunda taji sauƙar muryarshi da yadda yake magana da amo kukanta ya
tsaya chakk, haɗa idanun da suka yi ya matuƙar Dakar zuciyarta idanunshi abin tsoro ne a
gareta amma a yanzu sai taga ya zama wani iri duk yadda zata fassara ma'anar kallon nashi ta
kasa, maganan Mammi ne ya dawo da ita tunaninta.
"Lallai Afeefah kin ga rayuwa, haƙiƙa na kaɗu da labarinki abin mamaki kika iya daurewa kika
cije kika tsallake wannan jarabawa duk da kananun shekarun ki, Afeefah rayuwar nan duk
jarabawa ce kuma ko wani lokaci yana da karshen sa, za mu yi ta shan wahala a duniya amma
sakamakon yana hannun Allah kuma ya fi jarabtar wanda ya fi kauna daga cikin bayinsa,
Afeefah ina so ki san idan dai har ni, Abeeha, jidda ko Saraki muna raye a wannan duniya kin
gama kuka, zan cigaba da rikeki har karshen numfashi na haka zan yi musu umarnin cigaba da
kula da ke da baki kariya har nasu karshen numfashin, in shaa Allahu kin gama zubar da
hawayen baƙin ciki Afeefah... Sannu! Sannu da juriya"
Sabon hawaye ne suka cigaba da silalo mata ta sake rungume Mammi tana fashewa da kuka,
Abeeha ta taho ta ɗago ta tana riƙe hannunta
"In shaa Allahu ba za mu taɓa kyamatarki ba Afeefah ai duniya ce idan wani ya ƙi ka dole wani
ya so ka haka Allah yayi rayuwar, ni na yarda ki ƙirani Addah don ko kowa zai guje ki in shaa
Allahu ni ba zan taɓa gudar ki ba"
Sossai take kuka, a ranta Adu'a take tana tuna irin kaunar da Aunty zee ta nuna mata a ƙarshe
ta tafi ta barta, anya ta zama mai adalci? Anya zamanta a gidan zai haifar da É—a mai ido?
Karshen wahalar kenan ko kuma akwai saura? Duk ta bar wa Allah.
Sossai suka rarrasheta ta natsu kan Mammi ta miƙe tayi sashen Rayyan don duk yana cikin
ranta tun É—azu, a kwance ta same shi hallau dai idanunshi a lumshe, kai tsaye ta je ta sa hannu
a goshinshi ganin jijiyoyin kanshi raÉ—a-raÉ—a a waje, jin hannunta ya sa ya buÉ—e idanun da suka
sake sauyawa ya zuba mata
"Saraki ciwon kai ne? Ko za ka je asibiti?"
Girgiza kan yayi kaÉ—an yana yamutsa fuska
"Ba sai na je ba Mammi"
"Saraki in na barka haka dare ba zaka iya bacci ba, ka taimakeni ka je ka ga psychiatrist din ka"
Shiru yayi bai ce komai ba. Ta sauƙe numfashi ta fara duba wayanta cikin mintuna kaɗan sai ya
ji muryarta tana magana da likitarshi, buÉ—e ido yayi ya kalleta bata damu ba har suka gama
wayan.
"Za ta zo, don Allah ka tashi ka saka wani abu a jikinka mu je parlor"
Ta faÉ—a cikin kulawa kaman yadda yake damuwa da ciwo da damuwarta, shi ma bai san yadda
zai yi bane, bai san ya zai yi ya hana kwakwalwarshi tsayar da tunanin baya ba, bai san ya zai
yi ya cire tsananin nauyi da damuwar da ke kwance a ƙasan ranshi ba, a duk lokacin da ya
samu sassauci to fa a tsakanin da yake ganin farin ciki da walwala a fuskar Mamminshin ne
saboda baya so yake sakata cikin damuwa amma yaya zai yi?
"Zan zo!"
Ya faÉ—a a hankali.
Ta juya ta fice da damuwa a fuskarta, bai yi bacci ba a daren jiya dama ya saba da rashin
isashen baccin dare, tun tana kwana dashi har taga yayi girman da bai kamata su cigaba da
kwana ba amma ko bacci take tana tunanin yadda yake tafiyar da nashi daren, ba'a yi mishi
adalci ba amma kuma to ya suka iya ne?
Da kyar ya miƙe ya saka armless vest mai fadi da three quater da ya kai mishi gwiwa, a bakin
gadon ya zauna yana dafe kai har lokacin fuskarshi jazir babu É—igon fara'a a kan fuskar tashi,
ba'a jima sossai ba sai ga Mammin ta dawo ta kama hannunshi suka fito, a zaune kan kujera ya
ga Dr. ÆŠin tashi macece babba da a haife zata haife shi, ganin sun haÉ—a idanu ya sa tayi mishi
murmushi ya É—auke idanu, ajiyar zuciya ta sauke har ya zauna ya kishingida ya É—aura kafa daya
kan daya Mammi ta fita bata ce komai ba.
"Malam Rayyan! Barka da warhaka"
Ido ya É—an buÉ—e ya kalleta kan ya amsa.
"Whats happening? Na zaci mun wuce wurin nan duka..! Mafarkin ne?"
Shiru yayi chan dai ya gyaÉ—a kai
"Am having a sleepless night for almost a month now"
"Me ya faru? Are you taking your pills?"
Gira kawai ya É—aga don kan ya mishi nauyin da ba zai iya dagawa ba.
Ba don ma ya san darajar likitar ba ba zai kula ta ba, tayi ta janshi da magana dai har ya É—an
sake ta bashi magani cikin kulawa da kwarewa a aiki.
"Mammi wants me to get married, tana tsoron ta mutu...." Ya É—an yi shiru zuciyarshi babu daaÉ—i
sam kan ya cigaba
"ba ta so ta bar ni ni kaÉ—ai ba tare da mata ba and i hate the idea... Me yasa take yawan zancen
mutuwa? Yana damun zuciyata da kwakwalwata kina tunanin zan rayu bayan bata nan?"
Idanu ta zura mishi, Rayyan a cikin patients É—inta da take gani sama da shekaru talatin yana
daga cikin na daban da take jin damuwarshi tamkar É—an cikinta, tana tsananin tausayinshi gashi
kuma Allah sai ya sake aiko mishi wata jarabawar akan wata na rashin lafiyar Mammi da
fargabar mutuwar a kowani lokaci, sam bata so Mammin tashi take kawo mishi zancen tunda a
ranshi ya riga ya san kowa zai mutu idan ajalin shi ya zo amma kuma ta taya ta duba raunin da
yake danne wa a cikin zuciyarshi he was already traumatized, yana fama da insomia for so long
ciwon Mammi kuma ya haifar mishi da anxiety tsoro da fargabar barin shi da zata iya yi.
Lallaɓa shi tayi tayi har ya ɗan sake, maganin da ta bashi kuma ya taimaka mishi don kafin ta
tafi ma yayi bacci a kan kujerar, Mammi ta samu
"Don Allah Maman Rayyan ki taimakeni a kan Rayyan, ki daina mishi maganganun da zai ji a
ranshi kaman wasiyya ne, kin san matsalar shi kin san da ya ya girma in ba Allah ba babu mai
iya kawo Rayyan matakin da yake kai yanzu"
"Dr. Ya zan yi ne? Ina faÉ—a mishi hakan ne saboda ya shirya, ya kamata ya shiryawa hakan
dole zata kasance amma bana Fatan hakan ya kasance bashi da wani kafaÉ—ar, bana Fatan
hakan ya kasance ba shi da inda zai iya bayyana damuwarshi shiyasa nake so yayi auren"
"Amma kin san matsalar da niyyar auren nan ya jawo a baya, a maimakon ya gyara sai
tabargaza da yayi mana har ya zama for months Rayyan baya aiki baya kuma fita ko ina, bakya
tsoron abin da ya faru ya sake faruwa?"
Shiru Mammi tayi itama duk damuwa a kan fuskanta kan ta ce a hankali
"Zan san yadda zan yi likita, na gode sossai da taimakon ki ina fata zai É—ore ko da bana nan"
Murmushi kawai tayi ta taso ta dafa kafadar Mammin ta É—an bubbuga kan ta fice bata iya ta ce
komai ba.
Hawaye ne ya silalowa Mammin, ita kadai ta san me take ji, ita kaÉ—ai ta san tsoro da fargabar
da bawa kan shiga a duk sadda aka ce maka ga wa'adin mutuwarka Dukda bata yarda ba
amma hakan ya tsaya mata a rai tun shekaru bakwai baya, Dukda ta wani gefen hakan ya
matuƙar bata kusanci da ubangijinta sai dai tsoronta yadda zata tafi ta bar Rayyan, bata jin
yaranta matan saboda basu da matsalar komai amma Rayyan fa? Raunin shi sabo zai dawo
bata son hakan bata Fatan hakan don haka dole ne a gareshi ya nemi abinda zai tallafeshi a
bayanta.
****
Ta ɓangaren Dr. Sulaiman neman duniya ya saka an yi wa Afeefah sai dai babu ita babu
alamunta, police station har uku daban daban ya kai report sai dai babu ko duriyarta.
Tun yana ciwon kai a tsatsaye har sai da ya kwanta don da gaske ya matuƙar damuwa, a
ƙarshe haƙuri umma tayi ta bashi akan ya fawwalawa Allah ya karɓi auren da aka bashi don
Abba ya nuna mishi babu gudu babu ja da baya.
A dole daga ita har ƙannenshi suka fara shirye shiryen auren tunda sati biyu kachal ya saura a
yanzu.
****
A ɓangaren saleem ma duk ya ƙare a tsaye saboda damuwa da tunani, a kullum adu'ar shi a
kan Afeefah ne Allah ya tallafeta ya hanata faɗawa halaka Allah yayi riƙo da hannayenta ya
bata uwar ɗaki na ƙwarai, har yanzu iya gaisuwar ƙannenshi kawai yake amsawa wanda abin
ya dame su sossai ya zura musu ido kawai musamman mommy da ke ta shirye-shiryen aure
ka'in da na'in ita uwar amarya kuma uwar ango.
Sameera na zaune a kan plastic chair a wurin parking lots saleem ya shigo da motar shi ya zo
yayi parking ya sauƙa, bai mata magana ba don ta gaisheshi da safe kuma ya amsa har zai
wuce tace
"Yaya!"
Ya juyo ya kalleta duk tayi wani iri da ita
"Yaya don Allah kayi hakuri da abubuwan da muka yi maka, wallahi na gane kuskurena tun da
jimawa na tuba don Allah"
"Me kuka yi min Sameera? Ai ni dan uwanku ne ba zaku iya min komai ba ko? Sai bare ne zaku
iya yi wa... Babu komai Allah yana gani"
Kuka sossai take yi.
"Allah ya riga ya nuna min iyaka ta ko a haka na gane kuskurena, Yaya in na tuna abin da muka
yi wa Afeefah sai Naji tamkar jayayya muka yi da ubangiji... Za ka yi mamaki yaya idan na ce
maka na san abin da kake ji a ranka, na san zafi da raÉ—aÉ—in rashin masoyi domin Allahnta ya
saka mata, a sadda take nan ina samun sauƙi ne kawai da kallonshi amma a yanzu ko arzikin
kallon babu tunda Afeefah bata nan haka kawai ba sakayya bane?"
Idanu ya zura mata duk ta zama wani iri ta rame,
"Sameera wa kike so? Rayyan?"
Ta girgiza kai
"Sulaiman?"
Tayi shiru ya É—an yi jimmm, kan ya matso ta.
"a haka kawai Allah ya barki ya rama mata, ba yafiyata za ki nema ba ita za ki nema ta yafe
miki"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Ta saukar da kai tana hawaye, tana bibiyar Sulaiman sossai Dukda bai sani ba a haka ta san
auren shi wadda hakan ya sake daga mata hankali amma ya zata yi? Jarrabawarta kenan, ashe
Afeefar ma ba laifi tayiwa ubangiji ba ya zaɓi jarabtar ta ta hanyar da ya so, ba zata taɓa cewa
Sulaiman tana son shi ba amma zata yi Adu'a Allah ya sassauta mata ya kawo karshen shi.
****
Rayyan yayi kwana biyu yana jinya kan ya É—an sake Dukda ba sossai ba, sam ko a hanya basu
sake haÉ—uwa da Afeefah ba don bata zauna ba shima kuma ba shiga mutane yake yi ba idan
bashi da lafiya, Abeeha ta É—auke ta suka yi sayayya sossai wadda Mammi ce duk tayi mata,
suka je aka sama mata makaranta sun ma ƙi karbar ta sai da kyar aka barta SS1 za ta yi waec
kawai SS2, idan tace hankalinta ya taɓa kwanciya irin na kwana biyun nan tayi ƙarya, wani irin
so da kulawa suke nuna mata.
Bata aikin komai don gidan ma'aikata har sun yi yawa sai ka ga daman zuwa kitchen, uniform
da ake jira É—inka mata bai samu da wuri ba saboda uniforms É—in school din ba'a Kasar nan ake
yi ba kuma tsakiyar term ne ya ƙare already wanda suke dashi ba'a kawo wani ba, don haka
kullum suna tare da Abeeha kusan duk wanda ya san Abeeha sai ya san Afeefah matsayin 'yar
uwarta.
Gidan Jannah suka je suka sha yinin su itama bata da damuwa kaman dai Abeeha don duk sun
samu nagartaccciyar tarbiya daga mahaifiyarsu.
A yau monday Afeefah ta fito sanye da uniform É—inta mai dauke da bajin KIS(Kaduna
international school) tayi kyau sossai a uniform din sai kuma tayi kankanta, murmushi ne sossai
fuskarta tana yiwa Mammi sallama Abeeha ce zata sauketa in an tashi sai Driver ya je ya É—auko
ta, har tana shirin fita Mammi tace
"Afeefah kin mance lunch box É—in ko kunyar dauka kike?"
Abeeha tace
"Ana kunya da ciki ne? Oya maza yi sauri ki sameni a mota"
Da sauri ta juya bata ankara da akwai mutum ba kawai ta ji ta buga goshinta a kan kirjin shi,
kamshin turarenshi ya sanar da ita waye tun bai É—ago ba a razane tayi baya baya tana É—ago ido
sai suka sarƙe cikin nashi fuskar nan tamau, uban Harara da yake zabga mata ya sa ta nemi
rikecewa...
"Ba ki da hankali ne? Ko ba kya abu da natsuwa ne?"
Dakakkiyar muryarshi ya sauka a cikin kunnenta ai sai....
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*23*
"Ba ki da hankali ne nace!"
Ya sake faɗa da ɗan ƙarfi, in za ta iya tunawa kalaman shi na farko kenan a gareta, kila to bata
da hankalin ne don yanzu ma rikice wa tayi ta rasa me zata ce Bakinta ya kasa furta ko A sai
baya baya da tayi da sauri idanunta da suka firfito farare tass a kanshi.
Ganin Hararar da ya watsa mata yana cewa
"Daina kallona!"
Ya sa tayi saurin É—auke idon, Mammi ce ta ceceta
"Haba Saraki! Bata san kana wurin bane za ka tasa ta gaba kana zazzare mata ido, kayi haƙuri"
Mammi yake kallo, itama Afeefah jin abinda Mammi tace ya sa tayi ƙoƙarin har haɗa kalaman
haƙuri tace
"Ka..yi haƙuri"
Tsaki ya ja ya wuce ta ya barta da fitinannen kamshin shi, kitchen ta wuce ta É—auko lunch box
É—in mai kyau dashi ta fito a sanyaye tacewa Mammi
"Mun tafi Mammi"
Daga haka ta fice a parlorn da sassarfa don tana fitowa ya zuba mata ido, tsaki ya ja bayan
fitan ta ya dubi Mammi
"Meyasa kuka sakata makarantar da ba'a sa hijab kamar ba musulma ba?"
Mammi ta kalleshi
"Yanzu menene aibun uniform din nan?"
Sky blue shirt ne da navy blue blazer da skirt Dukda a gwiwa ne sai dai ta saka socks da ya
haura mata har cinya, cover shoe Black ne kafafunta sai navy blue cap da ta rufe kanta kirip
dashi, neck tie ne me layi layi sky nd navy blue sun yi mata kyau kayan kuma babu inda ke
bude jikinta banda hannayenta da fuskarta.
Baki ya taɓe bai sake cewa komai ba, abin kari mammi ta kira aka kawo mishi ya fara karyawa
a hankali, bayan ya gama ya dube ta
"Mammi auren salim next week friday"
"toooh aure haka kwatsam babu sanarwa babu shiri?"
"Nima jiya ne yake faÉ—a min"
"Toh Allah ubangiji ya sanya alkhairi ya sa da mu za'a yi"
Ya amsa da Ameen.
Daga nan wani hirar ta shiga yi mishi yana bata amsa a hankali hankali har suka gama ya miƙe
ya bar gidan.
Ƙarfe biyu sai ga 'yan makaranta an shigo, bata samu Mammi a babban parlor ba kawai sai ta
shige É—akinta tayi wanka ta sauya kaya zuwa doguwar riga Abaya onion colour mai kyau, hula
ta saka ta fito ta nufi É—akin Mammi jinta take very fresh nd healthy, wani sa'in ta kan tuna salim
da halin da yake ciki sai kuma tace kila ma ya manta da ita, Sulaiman ma kan zo mata rai ko
yaya yake oho bata sani ba.
Da sallama ta tura parlorn Mammi ta shiga ta sameta zaune gabanta abinci ne, farin shinkafa ce
basmati aka dafa amma dibawa aka yi kaman na jinjiri da alama ma da measurement cup aka
gwada don ba zai wuce 1/2 cup ba, sai wani wake green, akwai salad É—an kaÉ—an shi ma daga
lettuce sai cucumber da lemon tsami, kaza ce gasashiya 'yar kaÉ—an itama a gefe sai ruwa.
Murmushi Mammi ke yi tana amsa sallamar
"Barka 'yan makaranta an dawo?"
"Eh Mammi mun dawo, ya jikin?"
"Alhamdulillah, Ki karɓi abinci ki ci sai ki huta ko?"
"Toh Mammi"
Abincin Mammin ta zubawa idanu sama da seconds biyu kan tace
"Mammi idan ba damuwa zan iya tambayar me yake damun ki?"
Mammi tayi murmushi tace
"Babu damuwa Afeefah, ciwo biyu ne ke damuna an haifeni da diabetes na gado don tun ina
shekara biyu aka gane cewa na gaji ɓangaren mahaifina ne da ciwonsu na sugar, matsalar
ciwon sugar idan yayi tsanani yana iya affecting koda to wannan dalilin ne ya janyo na samu
damuwa da koda shekaru tara zuwa goma baya, an ma yi min aiki an chanza duka ba'a dace
ba Afeefah har ma an ba ni wa'adin wata uku shine ƙarshen rayuwata sai kuma gashi da yardar
ubangiji na shekara bakwai bayan nan"
Afeefah damuwa ne sossai ya nuna a fuskarta tace
"Toh Mammi shi ciwon ƙodar yaya yake? Ba'a warkewa ne?"
"Allah ya halicci mutane da koda biyu, wani halitta ne kaman wake akwai wasu ma da suke da
É—aya jal kuma suke iya rayuwa amma kowa biyu Allah yayi mu da su, waennan kodar
amfaninsu kuma su tace jininmu ne idan ruwa yayi yawa su cire ta ta hanyar fitsari, suna
taimakawa wurin hana jini ya hau sannan suna kuma sake wasu kwayoyin halitta na hormones
su hana ƙarancin jini suna kuma haɗa vitamin D dake ƙara karfin ƙashi. Akwai abubuwan da
suke kashe koda ba sai ciwon sugar ba wani ma abu mai sauƙi kan iya janyoshi kaman rashin
shan isashen ruwa, riƙe fitsari ki ga mutum yana jin fitsari ya matse shi sai lokacin da ya maka
tukuna zaka tafi da gudu, yawaitar shan pain killers baya na É—an ciwo a sha diclofenac, wani
yatsa ma na ciwo ki ga an apka feldin yawaitar shan su akai akai to su suna zuwa ne su rufe
jijiyar da yake kaiwa koda jini, a cikin jikin mu kuma koda na daga cikin organs da suka fi
kowanne bukatar jini, Sai kuma hawan jini ya fi yawa ma a ƙasar mu yana taimakawa sossai
wurin kashe koda waennan dalilan bayan ciwon sugar su kan iya haifar da ciwon ƙoda, a kan
iya chanzawa a dace amma ni an chanza min duk biyu ba'a dace ba yanzu haka ina zuwa
dialysis ko wani wata."
Tamkar Afeefah za ta zubar da hawaye take juya maganganun Mammin
"Mammi Allah ya baki lafiya ya sa kaffara ce duk kika yi ta yi"
Mammi tayi murmushi tace
"Ameen, kila Allah ya ajiyeni ne don ƙaddarar haɗuwarmu kila alkhairi zai haifar, bana fita
kwata-kwata sai da Saraki ranar kawai na ji ina son fita ashe da rabon mu haÉ—u ne"
Afeefah tace
"Na ga Yaya..."
Sai ta kasa cewa Rayyan a hankali tace
"Ya Saraki! Ya damu sossai da rashin lafiyar naki"
Mammi ta É—an murmusa Allah ya sa kar Rayyan ya ji tana ce mishi Saraki don baya so, shiyasa
ko su Abeeha ma Ya Rayyan su ke cewa
"Afeefah ba zan iya misalta miki yadda hankalin Saraki ke tashi a kan ciwo na ba, ko kin san
hatta me dafa min abinci ta karantu ne sossai akan cimar masu ciwon mu? Saraki ya tafi yayi
courses akan likitanci ne bayan ciwon sugar na ya haifar min da wannan ciwon ƙodar in ba
haka ba burin shi ya zama soja ne kawai ba Army medic ba, duk don ya san irin taimakon da
zai bani a cikin gida ba sai mun yi ta zarya asibiti ba sanin bana so"
Jinjina irin kaunar da yake mata take yi, lallai Rayyan na son mahaifiyarshi.
Cigaba da mata hirar irin gudumawar da Rayyan yake bayarwa a rayuwarta take yi. A yadda dai
ta gansu kaman babu wani namiji a gidan bayan Rayyan to mahaifinsu rasuwa yayi? Bata da
wannan amsar sai dai ta san idan har tana gidan za ta sani ne.
Abeeha ce ta shigo
"'yan makaranta ashe an dawo?"
Tayi maganan tana zama hannun kujerar da Afeefah take
"Na dawo Adda Abeeha, makarantar akwai daaÉ—i they are all nice to me basu yi min dariya ba"
"Ai na faÉ—a miki babu mai miki dariya, wasu da girman da suka fi naki ma suke zuwa suyi karatu
bare ke da jikinki ba nuna girman yake yi sossai ba"
"Aikam na gani kuma na ji daaÉ—i, ga malaman sun iya karantarwa komai fa fahimta nake kaman
na sani tun da chan"
Mammi da Abeeha suka murmusa, za ta sake magana kenan Ya shigo parlorn da sallamar da
shi kaÉ—ai yake sanin yayi kayanshi.
Kai tsaye kusa da Mammi yaje ya zauna, da ita da Abeeha suka haÉ—a bakin ce mishi
"Sannu da dawowa"
Kai ya É—an gyaÉ—a bai kalli kowaccensu ba, mammi ma ta mishi sannu da dawowa yake
tambayarta ya jikinta ta amsa da da sauƙi.
"Yauwa Mammi É—azu na haÉ—u da Samha a school ashe auren ya salim wani sati?"
Abeeha Tayi maganan da É—an mamaki, Dukda da ta kalli Samha sai da ta tuna abubuwan da
suka yi wa Afeefah kuma haushin su take ji har ranta ko da samhar tayi mata magana da kyar
ta daure ta amsa, wurin kokarin janta da hira ne take sanar mata auren salim É—in kuma suna
gayyatarta.
Wani irin faÉ—uwa gaban Afeefah yayi
"Aure Ya Saleem zai yi?"
Bata san a fili tayi maganan ba sai da ta É—ago idanunta suka faÉ—a cikin nashi da a lokacin ya
É—ago ya kalleta jin furucinta, da sauri ta É—auke ido gabanta na dokawa sam bata son suna haÉ—a
ido bata san me yasa ba, sai dai yanzu maganar auren saleem É—in sai ta ji shi wani iri duk ta ji
babu daaÉ—i, Abeeha ma sai da tayi maganan kan ta tuna da Afeefar.
Mammi ce tace
"Eh aure zai yi Afeefah wani sati, kar ki wani sa damuwa a ranki in shaa Allahu Allah zai
musanya miki da abin da ya fi alkhairi"
Kunya ne ya rufe ta sai ta duƙar da kai tana kallon yatsun ta sautin tsakin shi ne ya shiga
kunnenta, Mammi ta fara mishi faÉ—a akan yawan tsakin kaman wani tsaka, Abeeha ce ganin
yanayinta ta ja Afeefar akan su je su ci abinci suka fice daga parlorn.
****
Hidima fa ya kankama ɓangaren Amarya sai shiri ake wane, tun saura sati aka fara bikin 'yan
karya don Mommy sossai ta ajiye musu kuÉ—i Dukda ma angon ya ja mata gargadi akan duk abin
da za su yi kar su sake su saka shi, bai ma je gidan ba ko sau É—aya sai ranar da suka yi
kauyawa bayan Magrib yana zaune harabar gidan su da dangi suka cika, shiru kawai sam ba ya
jin daaÉ—in komai kuma komai ba ya burgeshi kaman daga sama ya ji Muryar Mommy.
"Saleem yanzu ka rantse sai ka nunawa duniya duka ba ka son auren nan dole na maka ko?".
Shi bai san me yayi ba, kaman zai yi kuka yace
"Me nayi kuma mommy?"
"Ko sau daya ka je kofar gidan su Sabrina da sunan zance? Ko ita ba mutum ba ce? Ka hana ta
saka ka cikin duk hidimar ta da kyar ma na bugi cikinta ta nuna min kai ne baka so ba ba bata
sanar da kai bane, baka bata komai ba haka ake yi?"
"Amma mommy ni nace tayi wani hidima ne?"
"Au in kai kana ƙunci da baƙin hali a kan wata chan da na tabbatar yanzu ta rabarwa maza
kanta sai aka ce ita ma ta biye ka kuyi ƙuncin tare?"
Runtse ido yayi ya buÉ—e tuni suka sauya Meyasa mahaifiyarshi ke yin abu kaman bata je
islamiyya bane? Ya subhallah maganar da ta faɗa ya mugun ƙona mishi rai amma ya zai yi ne?
Uwa uwa ce.
"Zan je, zan ba ta kuÉ—in"
Abin da kawai ya iya faÉ—a kenan ba tare da ya kalli mahaifiyar tashi ba, sai da ta wuce ya bita
da kallo yana jan Astagfirullah don yana tsoro, 'ya'ya mata ne garesu yana tsoron Allah ya
hukunta mahaifiyar tasu da daya daga cikin yaranta, yana tsoro ta fahimci kuskurenta in a Hard
way.
A lokacin ya miƙe ya nufi mota kan ya shiga aka wangale Gate, motar Rayyan ne ya shigo cikin
gidan dole ya fasa tafiyar sai ya nufi wurin Rayyan É—in suka gaisa.
"Fita za ka yi ne?"
"Eh wai zan je ne in ba Sabrina kudaÉ—en da ya kamata su yi hidimar bikin"
Kai Rayyan ya gyaÉ—a yana furta
"zagayo mu tafi"
Zagayawa yayi ya shiga motar, shiru yayi dama shi ne mai hirar muddin suna tare da Rayyan to
shi ma baya cikin yanayin hiran, hakan kuma sai yake sa Rayyan ke jin wani iri sai ya ga kaman
bai kyauta mishi ba ɓoye mishi da yayi Afeefah na gidan su amma zaman lafiyanshi kenan
tunda mahaifiyarshi ba amincewa zata yi ba ko ya faÉ—a mishi É—in.
Har suka isa unguwar da saleem ne ke ta mishi kwatance hira ba sossai ya hada su ba, a cikin
Layin aka yi kauyawan ana ta shirye-shiryen kiran sallahn isha su kam suna nan suna chasewa
'yan mata sai zuba rawa suke, Rayyan ya samu wuri yayi parking yana kallon arean da abin da
suke yi a ranshi ya ja tsaki yayi dubu, auren saleem ne ake yi ake wannan haukan? Babu
natsuwa a lamarin nasu babu kama kai, ba'a hana hidima ba amma sai a yi shi da tsari ba irin
wannan ba ko daga rawar da ake ka san an zubar da mutunci.
Wayanta ya shiga kira ringing na karshe ta É—aga
"Hello Ya Saleem"
Ta faɗa da ɗan ƙarfi saboda kida dake tashi
"Ki zo ina daga bayanku kaÉ—an"
Babbar kawarta ta janyo jiki na tsuma suka nufi motar, baya suka bude suka shiga suna gaishe
su.
"Amma mun yi fushi sai yau abokanan ango ke neman mu?"
Ci kan ku Rayyan bai ce ba, arzikin kallo ma basu samu ba yana wurin ne kawai saboda
Saleem ne da wani ne waennan É—in sun mishi kaÉ—an ya haÉ—a numfashi da su a mota guda.
Bundles na 'yan dubu dubu guda uku ya buÉ—e dashboard ya fiddo ya ajiyewa saleem a kan
kafafunshi dole ya ɗauka ya juya ya miƙa mata
"Ku yi hidima."
Jiki na rawa suka karɓa sai kamshi kudin ma ke fitarwa na sabunta.
"Akwai wani abu?"
Ya tambaya saboda kawai mommy ta mishi dole
"A'a ya saleem wannan ma ya isa mun gode sossai"
Daga nan suka fice don shi maganan soyayya ma ba wai hada su yake da ita ba.
"Ka ga abin da mommy ta ja min ko Rayyan?"
Saleem ya faÉ—a bayan sun fice daga unguwar.
Hakika shima ya ga wautar mommy, da ya ga yarinyar sai ya hasko Afeefah a idanunshi ko a
kusa bata da abin da za'a haÉ—a ta da Afeefah bai ce komai ba dai har ya mayar da saleem gida.
Su Gaje sun yi shiri matuƙa na wannan aure, yayinda amarya tayi shagali sossai kuma ta kullaci
kannen angon da babu wanda ta gani a hidimar ta har aka É—aura aure ranar Juma'a, Dukda
aure ne da babu wani sanarwa ko hidima saleem ya ga mutane kwarai an mishi kara, saboda
shi ma na jama'a ne Rayyan na a gefenshi yana yi ne kuma saboda saleem ne don baya son
harkar hidima da hayaniya har aka ci bikin aka watse, amarya dai ta tare a sashen saleem na
gidan inda duk mommy ce ta tsara hakan sai fatan Allah ya basu zaman lafiya.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*24*
Da misalin ƙarfe ɗaya na dare ta jefar da mayafin kanta tare da dira daga saman gadon tana jan
tsaki, me salim ke nufi ne? Babanta ya tabbatar mata shirin da aka yi akan shi ba mai sauƙi
bane da zai iya resisting amma me ya faru har yanzu bai shigo ba? ÆŠaukan maganin da Gaje ta
bata a gefen bedside tayi ta jujjuya
"To bai ma zo bama bare in sha wannan ɗin" ajiyewa tayi ta janyo wayanta kaman ta ƙira su
Gajen kuma sai ta fasa ta nufi parlor, kasancewar sashen nashi É—aki daya ne da parlor sai
kitchen in har dai ya shigo to ba zai wuce yana parlorn ba sai dai idan a waje zai kwana.
Shi kuwa salim tun karfe tara ya shigo gidan yanayinshi baya mishi daaÉ—i sam, fuskarshi babu
walwala haka ya tura kofan da sallama ya shigo, yana taka door mat É—in ya ji kanshi yayi wani
diimmmmm jiri na shirin kwashe shi a hankali ya furta
"Subhallah!"
Ya tsaya a wurin sama da mintuna biyu kan ya sauƙe numfashi ya nufi three seater ya kwanta
hannunshi dafe da goshinshi, duk yadda zai yi ya samu sauki ya yi sai dai wani irin tension yake
ji, sai juye juye yake Sabrina da a chan ƙasan ranshi ya san bai damu da ita ba sai kai komo
take yi a ranshi, bai san adadin lokacin da ya dauka ba shi ba mai bacci ba shi ba ido biyu ba,
ko matse shi zaka yi ba zai ce maka ga abin da ke damunshi ba sai jin Fitowar ta yayi.
Ganinshi ya sa ta nufe shi.
"Ya salim dama ka shigo? Shine kayi kwanciyarka anan ina chan duk tsoro ya rufe ni?"
Bai ce komai ba sai ido da ya É—an zuba mata.
"Ka tashi mu je ka kwanta a ciki idan baccin ne ma"
Ta faɗa tana riƙo hannunshi, kasa mata musu yayi haka ya bi bayanta kaman rakumi da akala,
a bakin gado ta ajiye shi ta shiga rage mishi kayakin jikinshi, wani sashi na zuciyarshi tsantsar
mamaki yake na wannan bushewar idon wani sashen kuma na faÉ—a mishi ba laifi bane, har ta
gama cire mishi kayan shi dai bai tanka ba kuma bai motsa ba, hannunshi ta ja wai tunda ba ya
jin daaÉ—i su je ta mishi wankan, tana tura shi bayi ta dawo da baya ta sha wannan maganin da
gaje ta bata don ta tabbatar mata yana kusantarta da maganin babu kuma wani abu da zai
gane, babu wacce zai gani nan duniya bayan ita.
Tun daga chan cikin bayin zancen ya sauya, ita ce ke jan ragamar komai kaman ba amarya ba
har dai ta samu nasara a kanshi Dukda ita ce tayi kidinta kuma tayi rawanta abinda zuciya bata
so gangar jiki ko an tilasta ta ba zata ba da abinda ake so É—in É—ari bisa É—ari ba, shi dai ya san
bayan nan bacci mai nauyi ya É—auke shi tana kwance jikinshi tana zabga murmushin nasara.
Washegari da kyar ya iya tashi yayi sallah a makare, yana zaune kan sallaya idanunshi na zube
a kanta tana ta baccinta, duk ya rasa me yake tunani ko me yake ji kaman an yi blocking
kwakwalwarshi da daidaitacciyar tunani, knocking da ake ta yi shi ya É—aga shi daga wurin ya
nufi kofan ya buÉ—e Samha ce.
"Ina kwana yaya?"
Kai ya gyaÉ—a bai ce komai ba.
"Gashi in ji Mommy wai in kawo muku"
Karɓa kawai yayi ya juya ya koma, ta tsaya tana kallon kofan for seconds kan ta tafi.
Shirya abincin yayi kan ya nufi cikin É—aki ya nufi bakin gadon ya shiga bubbuga hannunta.
"Sabreena! Sabreena!!"
"Uhmmmm"
Ta faÉ—a cikin baccin tana haÉ—awa da tsaki
"Wai menene?"
"Kin yi sallah?"
Ta sake jan tsaki kan ta buɗe idanu tare da Miƙewa zaune
"Ka san gajiyar da nayi? Ai koyaushe na tashi zan yi Sallar yanzu ka tashe ni sai in yi ciwon kai
ai"
Da mita tayi maganar.
"Ai in sallah bai tashe ki ba yunwa zai tashe ki, ga abinci chan ki fito mu karya"
Yana kai nan ya miƙe ya fice yana ji kawai ya gamsu da something is off with him amma ba zai
iya pointing menene ba.
Sama da mintuna arba'in sai gata ta fito shirye cikin wasu riga da wando masu fadi, yana zaune
yana jiran ta ganinta sai ya fara kokarin sanya musu abincin bata hana ba ya saka plate É—aya
zai saka wani ta riƙe hannunshi
"Wannan ma ai zai ishe mu Ya salim mun riga mun zama É—aya ai ko ba haka ba?"
Kai ya gyaÉ—a yana zame hannun nashi ya É—auki spoon ya saka, ita ta haÉ—a musu tea tana wani
irin murmushi.
Tun daga wannan rana saleem sai da ya kwana bakwai bai fita ko ina ba yana tare da ita, wani
lokacin haka za su yini duk abinda tace zai gyaÉ—a kai kuma zai iya yi mata amma ba zai yi
magana ba, itama kuma tana abunta da taku ne, ko sau É—aya basu sauka sun gaida Mommyn
ba suna gida É—aya abinci kuwa safe rana dare daga wurin mommyn ake turo musu, wayanshi
ma kashewa tayi kar ma a kira shi don dama ya É—an samu hutun aiki.
Yau mommy na zaune a parlor tana mamakin wannan sabon hali na Saleem kasa shiru tayi ta
kalli Sadiqa tace
"Yayanku kam duka cikin daaÉ—in auren ne za'a kwana bakwai muna gida É—aya bai iya lekowa
ya gaishe ni ba? Daga shi fa har Sabrinar tunda aka haura da ita ban ga keyarsu ba"
Sadiqa tayi murmushi
"Ai za ki musu uzuri Hajiya mommy kin san sabon shiga, amma na san dai duk yadda ake ciki
yau kam kila su sauƙo kin san har da gajiya duka na hidima ya tarar musu"
Samha dai bata gamsu ba amma ganin mommy bata sake cewa komai ba sai itama ta share.
"Amma mommy ba kya tunanin akwai abin da yake damun Sameera? Yarinyar nan duk ta zama
kaman ba ita ba don damuwa?"
"Toh Sadiqa ya zanyi? Na yi tambayar duniya ta ce babu komai kila ku in kun saka ta gaba zata
faÉ—a muku damuwarta"
Sadiqa tace
"Wlh ni dai ta ƙi faɗa min ban san ko Samha ba"
"kawai karatu ne fah! Kin ga tana ta shirin shiga final year abin babu sauƙi"
Ba wai sun yarda ba suka bar maganan, Sameeran ce ta fito ta zauna za tayi magana suka ji
motsin takowa kaman ana saukowa daga stairs duk ido suka zubawa staircase É—in sai ga
Sabrina da Saleem suna jerowa idanunshi na kallon ƙasa yayin da take murmushi mai faɗi har
tsakiyar parlorn suka zo bai ɗago ba, ganin zai fice mommy ta miƙe tsaye
"Saleem"
Waigowa yayi ganinsu ya É—an shafa kai
"Oh mommy ashe kuna nan, barka da safiya"
Speechless ta zama ta kasa furta ko A, Sabrina ta kalleshi
"Kayi sauri don Allah Ya Saleem idan ka dawo za'a yi gaisuwar"
Ba musu ya juya ya fice, ta juyo tana murmushi ta zo ta samu kujera ta zauna
"Mommy barka dai Fatan kina lafiya?"
Ido kawai suka zuba mata, da kyar mommy ta kawo musu uzuri a ranta ta zauna tana cewa
"Lafiya ƙalau ɗiyata ya zaman sabon wuri?"
"Lafiya ƙalau mommy ai ba wani sabunta da yake duk gida ne kuma yayan yana kula da ni
yadda ya dace"
Kai mommy ta gyaÉ—a, samha da Sabrinar take sa'a da ita tace
"kin tashi lafiya?"
Murmushi tayi
"Lafiya ƙalau ƙanwar mu"
Harara ta maka mata Sabrinar tayi wani murmushi tana kallon su sadiqa tana jira su gaisheta.
Mommy ce ta musu ido duk suka gaisheta ta amsa kuwa hankali kwance ita matar yayansu
"Mommy kin ga ya fita yana sauri ko? Wlh Gaje ce bata ji daaÉ—i ba kuma Bakinta babu taste
kwadayi take ji shine na ce ya je ya sayi kayan kwalam sai ya kai musu gidan ya kuma bata
kudin magani"
Mommy da kanta ya sake É—aurewa tamau ta zubawa Sabrina ido sabon salo wai gada a kotu
yaushe kuma aka fara hakan?
"Ah yayi kyau"
Abinda ta faɗa kenan, Sabrina ta miƙe
"Bari na koma ciki"
Tana kai nan ta haura saman ta Barsu da tunanin me ke faruwa? Sai dai babu wanda ya je da
nisa saboda mommyn na mata uzuri kuma tana son ta da Saleem É—in sai suka kama wani hirar
daban.
****
Yau sunday tun safe Afeefah ke tare da Mammi, hira suke yi kaman 'ya da uwa kafafun
Mammin na kan cinyar Afeefah tana É—an matsa mata take cewa
"Mammi yau ƙafafunki sun kumbura dama yana miki haka?"
"Yana yi Afeefah, ni kam me ba na gani ne? Yau kam ma na tashi jikin sai a hankali ai ni kaÉ—ai
na san me nake ji"
Tayi maganan da 'yar haki tana kishingida.
"Sannu! Ko zaki ƙara magani?"
"Kayya bar zancen maganin nan Afeefah, je ki kira min Yayanku nayi ta gwada layinshi bana
samu tun bayan asuba da ya shigo nan muka gaisa ban sake ganinshi ba"
Idanu ta ɗan waro gabanta na faɗuwa, Dukda ta san ta inda Sashenshi yake amma bata taɓa
gigin shiga ba to me zai kai ta? Yanzu ɗin ma jiki a sabule ta miƙe ta fice daga ɗakin, Abeeha
bata nan tun safe taje gidan jiddah za ta raka ta asibiti wai bata jin daaÉ—i da ko ita zata iya zuwa
amma ita har yanzu ganinta baƙuwa a gidan take, ko ba ma haka ba ina zata iya da wannan da
ba'a mishi gwanintar? Mutum sai faÉ—in rai da masifa... Da kyar ta É—aga hannu tayi knocking
kofan parlorn sai dai shiru babu amsa, ta sake yin knocking karo na biyu nan ma shiru, a
hankali ta tura kofar da sallama a Bakinta ta shiga yana kishindige very relaxed a cikin kujera,
parlorn da hasken shi ba sosai chan chan ba sai tashin kamshi yake, kaman waya yake yi
amma ba da wayar da ta saba ganinshi dashi ba gabanshi system ne shima a kunne kaman dai
aiki yake yi ya tsaya amsa wayar.
Daga ɗan nesa ta tsaya kanta a ƙasa tana jin yadda yake magana wane wani sarki, murmushi
tayi a chan ƙasan ranta take raya dole Mammi ta kira shi Saraki don shi komai nashi ya fi yanayi
da jinin sarauta, bayan ya gama wayan ya É—an kalleta ba tare da ya ce komai ba ya É—auke
idanu itama jin shiru ya sa ta ɗago ganin ya gama wayan ta ɗan ƙara taku biyu sai ta rasa me
za ta ce.
Da kyar ta iya haÉ—a kalmar sunanshi akan lips É—inta
"Yaya Saraki..."
ÆŠagowa da yayi ya kalleta ya sa maganar datsewa, bai san ya É—ago É—in ba don yadda ta kira
sunan sossai ya dake shi, bayan Mammi bai yarda ya ji sunan bakin kowa ba amma jinshi a
Bakinta sai ya rasa me yake ji ma, haushi ne ko takaici ko bacin rai? Tsam ya miƙe ya nufo ta.
Idanu ta shiga zarewa takunshi na tafiya da bugun zuciyarta har ya matso dab da ita yace
"Maimaita abin da kika ce?"
Shiru tayi ta kasa magana idanunta da suka yi raurau alamun kuka ko wani lokaci ta É—auke
daga kanshi jikinta na tsuma ta ciki, kusan seconds huÉ—u kan ya ce
"Allah ya so ki, da kin maimaita sai na fasa miki baki ke Mammi ce da za ki kira ni Saraki? Wani
Yaya Saraki...!"
Ya sake maimaitawa yana É—an harararta.
"Me?"
Ya faÉ—a yana dan gyara tsayuwa idanunshi tsamm a tsaye a kanta ko a jikinshi.
"Yaya..."
Wlh sai ta kasa cewa Rayyan É—in tayi tsai tsammm sai ma ta fasa kiran sunan da É—an saurin
baki tace
"Mammi ce wai ka je!"
Ta juya za ta fice yace
"Tsaya!"
"Ba ni da suna ne? Ko da gini kike magana?"
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."
Ta faɗa kaman za tayi kuka chan ƙasa, sarai ya ji ta
"Ga musiba tsaye gabanki ko?"
Girgiza kai tayi, tsaki ya ja yace
"Bar nan"
Da sauri ta fice.
Sai da ta ganta tsakiyar babban parlor kan ta dafe kirjinta tana sauƙe numfashi, Rayyan na son
kasheta da ranta, yaushe ya iya ma dogon magana haka bata sani ba, shi da komai ko oho ne
me yasa zai saka ta a gaba yayi ta razana ta!
Jiki a sabule ta ƙarasa wurin Mammi
"Wai yana zuwa"
Zama tayi kawai bata sake cewa komai ba, mintuna basu wuci uku ba sai gashi gaban Mammin
kawai ya ƙarasa ya fara taɓa temperature ɗinta, numfashinta baya fita yadda ya kamata
hankalinshi tashi yayi, a take yace su tafi asibiti duk yadda Mammin za ta ƙi ya nace ya dubi
Afeefah yace ta É—auko mata mayafi, da sauri taje ta É—auko duk sai ta shiga damuwa ganin
yadda hankalinshi ya tashi, kuma dai a fili Mammin bata yi tsananin da ya kamata ya É—aga
hankalin nashi haka ba, bata zauna ba itama gyalen da ta É—aura a kanta na Jersey ta warware
ta yafa akan doguwar rigar atamphar dake jikinta ta bi bayansu, a gaba ya saka mammin ta
buÉ—e baya ta shiga suka fice daga gidan.
Tafiyar mintuna ashirin ya kai su asibitin shi ya sake kama mammin suka yi inda za'a duba ta
don ya riga yayi call, tuni suka karɓeta don a yi mata gwaje gwaje a tabbatar da babu abin da
ya sake tsananta ko chanzawa.
A reception ta zauna idanunta na kan yatsun ta sai adu'ar samun lafiya take yiwa Mammi mata
mai kirki da mutunci, macen da ta zame mata uwa kuma garkuwa a yanzu.
"Afeefah...!"
Da É—an karfi ta ji an kira sunanta har bata san ta É—ago a razane ba sai...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*25*
Sulaiman kaman zai kama hannunta haka ya tsaya gabanta yana kallonta.
"Da gaske ke ce? Ashe zan sake ganinki Afeefah? Ina kika shiga? Kin san irin neman da na
miki?"
Idanunta na sauƙa kanshi ta miƙe tsaye, ganin irin kusancin su ya sa ta ɗan yi taku biyu baya
fuskarta a sake tace
"Ina nan Dr. Allah ya haÉ—a ni da mutanen kirki"
"Afeefah me yasa ba ki zo office na ba? Me yasa ba ki neme ni ba da mahaifiyar saleem ta kore
ki?"
Idanunta ne suka cika taf da kwallah a hankali tace
"Ban san inda zan sameka bane ban san sunan asibitin ku ba ko in ce ban riƙe ba, ko ma na
riƙe ba ni da ko biyar da zan hau abin hawa in ce a kawo ni"
Idanu ya ɗan runtse kaɗan ya buɗe da sauri sai ya ga kaman za ta iya ɓace mishi any moment
"Ina kika shiga to? Waye ya taimake ki?"
"Na haɗu da mutanen kirki sun tallafeni daidai lokacin da na buƙata kuma suna riƙe ni tamkar
É—aya daga cikinsu yanzu haka ina makaranta"
"Alhamdulillah!"
Zama yayi saboda a lokaci ɗaya daaɗi da baƙin ciki duk suka haɗu mishi, itama ta zauna a
hankali ya ce
"Afeefah har Dutsen-wai na je nemanki"
Da sauri ta É—ago ido suka haÉ—a idanu ya gyaÉ—a mata kai alamun tabbaci.
"Gidan kawu ka je?"
Kai ya gyaÉ—a cikin nuna damuwa ya ce
"Abin da muka tarar ba karamin tsoro ya bamu ba Afeefah, ban so ba, ban san hakan zai
kasance ba da ban yi ganganci da kuskuren tafiya da manya na ba"
A lokaci daya ta zama very confused sun je gidan kawu? Me suka tarar? Me yasa yaje da
wasu?.
"ko da ban furta miki ba kin dai san Sonki nake ko Afeefah?"
Lumshe ido tayi kalamar na sauka mata wani iri a zuciya.
"A lokacin da na samu labarin tafiyar ki i was very disturbed na É—auka chan gida za ki koma, ko
da na koma gida na samu mahaifiyata da labarin ban gama bata ba Abba ya shigo ya ji zancen,
dama ya matsu kuma da maganan aurena dole ya haÉ—a ni da Yayyenshi kuma ya kafa hujja ne
da cewa a musulunce ma bai halatta namiji ya fara taran mace ba tare da sanin iyayenta ba..
Dole ta sa muka tafi tare da su ba don na so ba"
Hawaye ne ya zubo mata a kan fuska ta ɗan yi murmushi mai yanayi da wani ciwo a ƙasan rai
ta ce
"Sun ji kunya ko? Na tabbatar ba su amince maka ba kuma ba za su taɓa amince maka ba..! Ka
yi haƙuri, da na san za ka aikata hakan da ni da kaina na faɗa maka wacece ni kafin ma ka je"
Ya É—an haÉ—iye wani abu mai ciwo a hankali yace
"Afeefah sun yanke min hukunci mai girma a yanzu haka ina da aure, an É—aura min aure last
week saturday amma har yanzu zuciyata ke take so, ke take marararin rayuwa da ba wata ba.
Na haƙura na karɓi auren ne saboda ban san inda zan ganki ba ban san inda zan sameki ba, a
ina ne gidan da kika koma? Idan kin ga da takura za ki iya dawowa wurin Umma na tabbatar ita
me riƙe ki ce tamkar ɗiyar da zata haifa a cikinta"
Rayyan ne ya fito sai idanunshi ya faɗa kan su, a kan hawayen dake bin ƙuncin ta ya ɗan tsayar
da idanun kan ya É—auke kai ya zo ya wuce su kaman bai gane su waye ba, Afeefah da suka
haÉ—a ido ta sa hannu ta share hawayen fuskarta ta dubi Sulaiman
"Zan tambayi Mammi zan zo in gaishe Da Umma! Amma batun soyayya don Allah ka ajiye shi a
gefe Dr. Kai fa ka gayamin irin abubuwan da Kawu ya muku na ba da kunya, taya za ka yi
convincing iyayenka su sake komawa irin gidan chan?"
"Zan iya Afeefah kawai ki ba ni dama!"
Ta girgiza kai
"Aurenka fa?"
Zai yi magana ta ce
"Ka yi haƙuri Dr. Yanzu ba lokacin wannan maganan bane marar lafiya muka kawo"
Shigowar Abeeha da Jannah ne ya sa ta ƙarasa share fuskarta ta ƙirƙiro murmushi ta saka,
suka ƙaraso kusa da ita
"Afeefah ya jikin Mammin?"
Ta ce
"Da sauƙi sossai amma tunda Ya Saraki ya shiga da ita ba'a fito da ita ba"
"Amma Yaya Rayyan É—in yanzu muka wuce shi a waje yana waya"
"Eh shi kadai ne ya fito"
Gaisawa suka yi da Dr. Sulaiman yana mamakin jin ana ambaton Rayyan, gidan su Rayyan ta
koma?
"Afeefah ko zan iya samun Layin da zan yi magana da ke?"
Ya faÉ—a yana kallonta, kallonta Abeeha tayi sai ta É—an yi murmushi tace mata
"Dr. Sulaiman kenan!"
Shima ta juya tace
"Yayyena ne Addah jannah da Adda Abeeha"
Murmushi yayi lallai Afeefah ta samu wurin zama idan har ta sake da ahalin haka sun zama
tamkar jininta ya tabbata ba zata iya barin su ta dawo wurin ummanshi ba yadda ya ci buri.
"Dr bamu natsu ba har yau bamu samu mun je mun sayi waya ba, bari na baka layina za ku iya
dinga gaisawa kan ta samu nata"
Godiya sossai yayiwa Abeehar, ta bashi contact É—inta ya tafi da sauri ta juyi wurin Afeefah tana
murmushi sai ta ga damuwa a kan fuskarta, dafa kafaÉ—arta tayi
"Ya dai?"
"Adda wai Shima aure yayi last week saturday"
Duk sun ji maganar wani iri amma sai suka dinga nuna mata babu komai kila ba rabonta bane
ko kuma Allah ya kaddara za ta zama matarshi ta biyu bata san ta cewa Abeeha ba
"A yaushe kenan? Aure last week Adda Abeeha kina tunanin ko shekara daya ne zata amince
ya mata kishiya a kusa haka?"
"Duk ba mu san tsarin Allah ba, mu yi Adu'a kawai duk abinda ya kaddara daidai ne"
Ta gamsu amma har lokacin ranta na suya da abinda kawu ya aikata, kenan akwai É—an sunnar
da zai aureta a duniya kenan? Waye zai yarda É—an shi ya auri irin ta matukar za su bincika asali
da tushenta?
Bata san Rayyan ya dawo ya wuce ba chan sai ga shi sun fito da Mammi, duk Miƙewa suka yi
suna mata sannu tayi murmushi
"Duk rigimar Saraki ne amma jikin nan bai kai zuwa Asibiti ba, Jannah ya jikin naki?"
"Da sauƙi Mammi, sannu Allah ya baki lafiya"
Ta gyaÉ—a kai.
Idanunta ta kai kan Afeefah dake ta murmushin yake
"Afeefah kina lafiya? Na ga damuwa a fuskarki"
"Babu komai Mammi sannu da jiki"
Kai ta gyaɗa ba wai don ta yarda ba suka nufi mota, ƙin shiga motar Rayyan tayi don wlh tsoron
ko motsi take a gabanshi, motar Jannah ta tafi suka haÉ—u su uku suna hirarsu har gida.
A babban parlor suka yi masauki don Rayyan ya riga su isa kuma ya shigar da Mammi ciki ko
da ya fito a babban parlorn ya tsaya yana nuna su da yatsa
"Ba ku parrots ba? To in ga watan ku ta shiga ciki tana damunta da surutu ko wata taje tana
saka ta gaba da kukan banza ku ga abin da zai faru"
Yana kai nan ya wuce abin shi basu motsa ba sai da ya ɓace Abeeha da Jannah suka tafa suna
sheke wa da dariya, Afeefah na murmushi.
"Mutum yayi ta muzurai kaman a filin daga yake"
Jannah ta faÉ—a, Abeeha tace
"Ai ke baki ganin komai tunda yanzu kin bar gidan nan da sauƙin ki"
Jannah ta girgiza kai
"Kema kin san babu wani sauƙi wlh sai dai in ban yi wani abin ba Ya Rayyan bai game shi ba ya
je har gidan auren nawa ya zane ni tsaff"
Ita dai Afeefah bata ce komai ba idanunshi kawai take gani, a hankali ta É—an yi murmushi tana
girgiza kai.
Jannah bata tafi ba sai dare, sun sha hira sun ci sun sha, kuma sai da suka cika Mammin da
surutu don yana fita daga gidan suka yi É—akin suna bata labarin gargadinshi tana dariya ta dubi
Afeefah
"Afeefah ke ce me kukan banza kenan? Me aka yi miki za ki zo ki min kukan?"
"Ba ayi komai ba fa Mammi"
"Afeefah ki faÉ—a min damuwarki wlh ina hangar damuwa a tattare da ke"
Kanta ta duƙar Mammi ita uwa ce, uwar ma ta wannan baudadden mutum ai dole ta san
expression na kowa.
Abeeha tace
"Mammi Dr. Sulaiman yayi aure shima ashe"
Mammi ta kalli Abeeha kan ta kalli Afeefah tace
"Auren ne ya dame ki É—iyata? Kin ga fa duk abin da Allah ya hanaka ba rabonka bane wanda
kika ga kin samu shi ne rabon ki, in shaa Allahu za ki samu miji na nunawa sa'a"
A hankali tace
"Mammi ba auren shi bane damuwata"
"Toh menene Afeefah?"
"Mammi bana tunanin zan auru, Musulunci ya yarda a auri mace don kyaunta, dukiyarta ko
nasabarta, sannan bincike a aure kaman dole ne a musulunci akwai dangi na ƙwarai da za su je
bincike a kaina su yarda su bar É—an su ya aureni? Mammi kin ji abinda su Sulaiman suka samu
kawu suna yi a kan layi? Kin ji abinda aka fada musu a kaina daga shigar su kauyenmu?"
Hawaye ne ya tsinke mata ta fashe da kuka tana jin ciwon Taɓon ta da bata tunani har Abada
zai gogu.
Jannah da Abeeha har sun fara tayata hawaye don idan ka ji yadda take maganan za ka san
abin na mata ciwo kwarai da gaske..
"Afeefah zo nan"
Mammi ta ƙirata, Miƙewa tayi ta isa kusa da ita Mammin ta ɗora ta akan kafaɗarta tana shafa
mata kai.
"in shaa Allahu Afeefah sai kin auri mijin da kowa sai ya ji sha'awar kasancewa ke, nagartaccen
namiji kuma mai tarin ilimi da baiwa na musamman, kawunki ko mutanen garinku ba su isa sun
shafe abin da Allah ya rubuta ba, ko kin manta Allah da kanshi ya faÉ—a mana yana fitar da
mummuna cikin kyakyawa ya kuma fitar da kyakyawa cikin mummuna? Ba fa a suffa ko sura
ake magana ba ana magana ne akan hali da ɗabi'a. To ki sa a ranki mijin da Allah ya zaɓa miki
yana nan kuma idan lokaci yayi za ki aure shi ba makawa kar ki wani damu kanki kin ji?"
Kai ta gyaÉ—a cike da gamsuwa
"Na gode Mammi"
"na ƙara ji sai na Buge bakin godiyar"
Murmushi duk suka yi don da wasa tayi maganan.
*****
Hajiya Hussaina tun fa tana tunanin abin na Saleem da Sabrina wasa ne har ta fahimci da
gaske ne, domin yau tana zaune a parlor Sabreenar ta sauƙo ta ɗan kalleta tace
"Sannu Mommy"
Bata jira ta amsa ba ta wuce kitchen ta samu Talatuwa na aiki, ta ce
"Talatuwa me kike dafawa?"
"Tuwo ne da miyar egusi shi mutanen gidan suka ce a dafa musu"
"Toh bari ki É—ora min fried Rice da kaji iyayena za su zo ganin É—akina ba zan tarbesu da tuwo
ba"
"Amma S..."
"Kin yi abinda nace ko sai na bi ta kanki? Har kin isa ja da ni typical 'yar aiki? Toh wallahi ki
kiyaye ni"
Sadiqa da ke shigowa ne tace
"Haaa me ke faruwa da ihu haka?"
Talatuwa ce ta mata bayani sadiqa ta kalleta sama da kasa
"Amma ba ki da hankali yanzu su Gajen ne baƙi da har za'a dafa musu kaza da wani fried Rice?
Dama shi suka saba ci a gida?"
Sabreena ta riƙe baki tana kallonta na seconds kan tayi wani murmushi kawai ta juya fuuuuu ta
fice.
Mommy na nan zaune tana tunanin wannan lamarin da bata gane kanshi ba bare ƙasan shi ta
ga wucewarta kamar iska, ba'a fi mintuna biyu ba sai Ga saleem rike da belt nashi na sojoji ko
mommy bai kalla ba ya shiga kicin ya ya kuwa samu Sadiqa ya rufeta da dukar kawo wuka....
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
*FREE BOOK*
*Ku lallaɓa wannan kaina ciwo wallahi kaman zai faɗi*
*26*
Ihu take yi sossai na neman agaji, shi kuwa tamkar wanda ake zuga shi dukan ta yake kaman
an aiko shi cike da wani haushi nasu da dama yana kwance ƙasan ranshi, Mommy da ta shigo
da gudu ne ta riƙe belt ɗin a tsorace take cewa
"SALEEM! SALEEM!! Me haka? Me ya hau kanka? Sadiqa fa kake yi wa wannan duka kaman
wanda ya kama ɓarawo? Sadiqa fa ba sameerah ko Samha ba?"
"Na kula rainin sun ya fara yawa ne, kuma wallahi kaÉ—an na mata ko kallon banza ta sake yiwa
Sabrina ta gani bare zagin iyayenta sai na yi ƙasa ƙasa da ita, marasa kunyar yara kawai..."
Yana kai nan ya wuce fuuuuu mommy dake tsaye kaman an dasa ta jiri ya kwashe ta ta tafi
zaune.
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun me ke faruwa?"
Sadiqa da baƙin ciki kaman ya kasheta tana dukunkune gefe tana kuka sossai don ba laifi ta
bugu ta ce
"Me kuwa mommy? Duk wa ya ja mana? Wlh babbar alamar tambaya ne akan yarinyar nan
dama ni ba sonta nake ba kika saka shi dole aurenta yanzu wa gari ya waya? Tun fa ba'a je ko
ina ba mommy wlh ba zan iya zama da yaya a wannan gida ba, ni zai daka? Akan Sabreena da
take ƙanwar ƙanwar bayana?"
Samha ta je ta kama sadiqa a tsorace take don jikinta duk rawa yake, ita dai Sameera bata ce
komai ba ta juya ta fice, zuciyarta rawa yake kuma a cunkushe yake tana ji Mommy na fashewa
da kuka tana tambayar me ke faruwa ita ta kasa gane komai me ya hau kan É—an ta? Ko ci
kanku bata ce ba.
Samha ce ta taimakawa sadiqa da ruwan zafi yayinda ta dawo parlor wurin Mommy ta zauna
suka yi shiruuu ita mommy tana tunanin me ya kamata tayi? Me yake faruwa ita bata gane
komai ba, Sabrina ta sauƙo tana waka ta wuce su zuwa kitchen ta tabbatar Talatuwa ta ɗora
mata abinda tace kan ta dawo ta haura ko kallon su mommyn bata yi ba.
"Ashe yarinyar nan macijin sari ka noke ce?"
Mommyn ta faÉ—a cikin mamakin duniya da ya rufe ta. Ina hijaban? Ina ladabin?
"Mommy me ta yiwa yaya saleem? Ki dubeshi a kwanakin nan kaman ba shi ba duk ya zama
wani iri ga faÉ—a da masifa ga saurin duka mu da tun muna kanana ma bai dake mu ba sai
yanzu?"
Samha ce me maganan zuciyarta har lokacin yana bugawa
"Nima na kasa ganewa Samha kaina ya kulle tamau, kwakwalwana ba ya tunani daidai... Amma
bari iyayen nata su zo mu ji me kenan?"
A parlorn suka cigaba da zama chan kuwa sai ga Gaje da Yaya sun shigo, yanayin shigar tasu
ma ba yadda suka saba zuwa ba a raɓe a raɓe a baya suna tsoro kar su yi ma mommyn ba
daidai ba, kai tsaye suka zauna cikin kujerun parlorn yaya yana cewa
"Hajiya Hussaina ashe ana nan, barka da gida"
"Sannunku da zuwa"
Ta faÉ—a tana ta kallonsu kaman sabbin halitta yadda suka shige cikin kujera duk ba haka suke
yi a baya ba, bata gama mamaki ba sai da Sabreena ta zo da gudu ta rungume Gaje tana musu
oyoyo
"Masha Allah, Amarya kin sha kyau da kamshi"
"kai Gaje, Baba sannu da zuwa"
Ta faÉ—a tana daga jikin Gaje dake ta riritata.
"Barka dai 'yar arziki irin albarka, ya sabon wuri? Babu takura ko?"
"Ah baba wa ya isa ya takura ni ni da gidan mijina"
Suka yi dariya.
"Yana zuwa ya gaishe ku, sa kaya yake yi"
"Ah ba komai ai muna nan"
Mommy tana zaune tayi tsamo tsamo kaman ruwa ya daki babban zakara har Saleem ya sauko
ya zo ya tsuguna suka gaisa da su Gaje sai albarka suke sa mishi kan ya miƙe ya kalli
Sabreena yace
"Na fita"
Da sauri ta miƙe ta bishi muryarta na fita a lokacin da take cewa ka zo min da... Sai dai bata
ƙarasa da karfi ba, bayan ya fita ta dawo ta saka su Gaje gaba banza suka yi da su Mommy
kaman Allah bai halicce su a wurin ba, wasu irin hawaye ne ke zubowa Sameera tana ambaton
sunan Allah kan ta tashi ta shige É—aki tana fashewa da kuka.
Samha dai da mommy sun kasa magana, suna kallo har ta musu iso dining suka ci suka yi nak
suka dawo parlorn, mommy ta kasa shiru tace
"Yaya...!"
Kallonta yayi
"Menene yake faruwa ne? Na rasa gane kan Sabrina tunda aka yi auren nan, É—azu fa har sa wa
tayi Salim ya daki sadiqa abin da ba halinshi ba, ba haka na saka shi ya aureta su zauna ba ba
zan zuba idanu mu cigaba da tafiya a haka ba, Salim ko kallon mutunci ya daina min daga
aure? Me hakan ke nufi?"
"Hajiya Hussaina ke fa kike É—aukar abu da zafi, yaro yayi sabon aure ai ba za'a saka musu ido
ba, tarbiya daidai gwargwado mun ba Sabrina kuma idan Sadiqa tana mata gani gani da a
matsayin ta na yayarta yanzu yayansu take aure ya kamata su san maganan da za su dinga
faÉ—a mata ina ga hakan sai a zauna lafiya"
Mommy ta saki baki da hanci tana kallonsu. Sabrina tayi murmushi tace
"Abin da mommy ta kasa ganewa kenan, mu ajiye batun nan ku tashi mu je ku kalli sashena"
Basu bi ta kan 'mommy ba suka bi bayan Sabrina, numfashi ne taji bata iya ja da kyau Samha
ta riƙe hannunta
"Mommy...! Mommyyyy!!"
Hankali tashe take kiranta kiran ya fito da Sadiqa da Sameera ruwa suka dauka suna shafa
mata a fuska har ta Fara sauƙe numfashi da ƙarfi, me su Yaya suka yiwa yaronta? Sai yanzu
tunanin za su iya cutar mata dashi ya zo mata innalillahi kawai take ta maimaitawa a tsananin
tsorace.
Su kam suna hawa Sabrina tace
"kun yi min komai iyayena, ba ni da abinda zan saka muku kun ba ni wannan daula da dukiyar
sai yadda naga dama zan juya shi, a yanzu ma ina ragarwa uwar ne saboda wani dalili nawa
amma itama nan kusa za ta gane ta É—auki goruba ne ta damkawa kuturuwa don kwace saleem
a hannuna sai mutuwa"
Dariya suka sheke dashi Gaje tace
"Ke gidan nan fa duk na mijin ki ne kina da ikon yin yadda kike so, sai na ga kaman wannan