Sashe 11
Farar Taska Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk suka zubawa Malam Audi idanu kafin su dubi mai gari cikin mamaki, ɗaya daga cikin ma'aikaciyar asibiti ta muskuta tayi wa mai gari bayanin komai tun daga farko zuwan su har kawo yanzu, kana ta ƙara da cewa saboda yaron bai isa haihuwa ba da kuma an bar ta gida har kwana biyu tana naƙuda ya saka Allah bai yi mai numfashi bane" Mai gari yace "ina ita mai haihuwa? Saratu tace" tana can kwance bata san inda kanta yake ba saboda babu jini a tare da ita, an gayawa mijin ta yaƙi ya bayar da komai sai mijina ne yaje ya siye jini aka saka mata" mai gari ya dubi Audi dake ta rarraba idanu yace "ko da ka sake ta alhakin ciyar da ita da nema mata lafiya yana kanka saboda ta dalili ka ta haɗu da wannan jarabawar, ballantana babu saki irin wannan sai na bidi'a dan haka ka biya malam wadata kuɗin sa saboda har yanzu ita matar kace" Audi ya soma ƙoƙarin tashi da gawar yaron sa yana faɗin "wannan haɗin baki ne Sam babu adalci a wannan zaman, matar da nace na sake ta kuma zaa ce na kula da ita, ta yaya ciyar da ita da nema mata lfy yake ƙarƙashi na bayan na sake ta, kai da na zo mak da zancen an kashe min magaji ka bimin haqqi Sai ka buge da wata magan can, tukunna ma waye yace ba'a saki dan tana cikin jinin haihuwa? Mai gari ya dube sa cikin bacin rai yace" ka zauna Ina magana da kai ina zaka je, nace kuɗin da Wadata ya kashe ka maida masa domin bashi yake da alhakin kula da ita ba kai ne kuma Ummy har gobe matar ka ce babu wannan sakin" ran Audi ya baci, yayi jim kaɗan kafin ya dubi mai gari yace "ina cikin wani hali na alhini saboda rasa ɗana, a bar ni naji da mutuwar a yanzu idan anyi masa sutura zan biya shi" Wadata ya muskuta kaɗan yana kallon mai gari, yace
"ranka shi daɗe maganar kuɗin saka jini a bar shi nayi saboda Allah, kawai ya bada kuɗin maganin da zaa siya mata"
Audi ya dalla masa harara yana faɗin "duk zan biya ka ragin ko sisi bana so daga gurin ka, in har da gaske saboda Allah kayi matarka bazata zo nan bainar jama'a tana maimaita mijin tane ya siye jini aka saka mata ba, dan haka zan biya gudun gorin wata rana Kuma Ummin na bar maka ita bana so" ya tashi da gawar da sauri kafin mai gari yayi magana ya fice ransa matuƙar bace, Kai tsaye gida ya nufa inda Shamwilu.
Yasira fitowar ta bayi kenan yayi dai dai da shigowar sa, ta ɗaure fuska tana faɗin "Sai yanzu kake dawowa gida? Yace
" Afuwan abar ƙaunata kuɗin ne basu samu da wuri ba, gasu da ƙyar na samu" ta fisge kuɗin daga hannun sa tana dubawa, dubu biyar ne kana ta saki fuska ba yabo ba fallasa tace " karbi kaje da su inda Azumi ka bata kuɗin zubin adashe ne da nake yi, ka tunasar da ita kada ta aiko min cewa ban zuba a wannan watan ba" ya haɗiye wasu yawu da ƙyar yace
"Wai dama yasira saboda ki zuba kuɗin adashe ne kika saka ni cin bashi har dubu biyar, ni ne zan maki zubin? Ta bata fuska tana masa wani kallon raini tace" me kake nufi, ko ban isa ka bani kuɗin ba ne? Yace "a'a yi haƙuri gimbiyar mata ki saki fuskar ki bakya kyau idan kika bata fuskar, wasa nake wallahi na haƙura" ta ja ƙaramin tsaki tana faɗin "ka da ka manta da mgnr da muka yi shekaranjiya, ka siyar da gona ɗaya ko ka karbe ta gurin Audi ka siyar ka bawa yaran nan jari za su je can kudu su yi sana'a ba aikin noma zasu zauna yi a gida ba". Yace "duk yanda kika ce haka zaa yi, ai dukiyar taku ce keda yaran ki Kinga bazan ji asarar siyarwa na biya buƙatun ku ba, zan duba naga wacce zaa siyar"
batare da tayi magana ba ta nufi ɗakin ta da hanzari ya bi bayan ta da sauri yana waiwayen bayan sa idan babu yara a gida, kafin ya washe baki ya ƙarasa shiga ɗakin, ta juyo tana kallon sa "lafiya sai bibiyata kake? Ya sosa kansa yana dariya yace" haba yasira yanzu duk wannan hidimar da nayi na bada dubu biyar na adashe bai isa ya saka nima a ɗan bani na lasa ba, ki taimaka yau kusan wata takwas kenan ina bibiyar ki kina hanamin yau kaɗai sabida Allah ki bar ni nayi". Kallonsa tayi galala baki a buɗe kafin tayi wani shu'umin murmushi tana taba hannayen ta tace
"Shamwilu ko na baka dubun ka biyar ne, naga sai mita kake a kansu zan iya fita naje na nema da kaina ka sani". Yace "aa babu inda zaki je neman kuɗi bayan gani, ba mitar kuɗin nake ba naga nayi abin a yaba min ne a saka min da wani abin? Tace" to ka fice min daga ɗaki kafin raina ya baci" yace "ki taimaka ko sau ɗaya ne, abin nan tana cikin yunwa idan ba wata kike so naje na nema a waje ba? wata irin dariya tayi mai cike da shaƙiyanci kafin ta juyo tana kallon sa ƙasa da sama a wulaƙance tace
" shege ka fasa, ka je ka kwanta da wata mace a waje ka dawo ka same ni gidan nan " zai yi magana suka jiyo muryar Audi Yana sallama, da hanzari ya fita baya so ko kaɗan Audi yaji suna sa'in'sa da Yasira, a zauren gidan suka yi kicibis yace
" Wai Kai da Sai ka faɗomin kawai a gida bazaka jira na fito ba, idan ka same ni akan matata fa? Audi yayi baya jiki a sanyaye yana faɗin "fito abokina fito ka ga babbar asarar da ta same ni a yau" wannan karon sai ga hawaye a fuskar sa wanda ya sanyaya jikin Shamwilu yabi bayansa ba kuzari, kallon abinda ke hannun sa yayi yana faɗin
"Audi menene ka ƙunso haka a zani, kada dai ba abin wani kaje ka ɗauka aka ganka kazo kana min kuka ba, dan Allah kada ka saka ni a matsala". Audi ya sharce majina yana faɗin
"kasani duk acikin hali na marar kyau giya ce kawai da nake sha, bana sata, bana caca da zina kuma ina sallah biyar a rana kullum ko da na buge, dana farfado nake ramakon sallah, meyasa kake bina da sharri a maimakon alheri? Shamwilu ya washe baki kaɗan yana dafa kafaɗarsa yace
" yi haƙuri aminina kasani duk duniya babu wanda zai maka shaida irin wacce zan maka, a ruɗe nake da kai ne baka saba zomin kana hawaye ba dole na ruɗe, wai menene a zanin kake boyewa? Audi ya buɗe jinjirin yana nuna masa, "yaron da ummy ta haifa ne babu rai, ka duba ka ga irin magajin da na samu sak Irina, baƙi Mai kamanni kamar ni amma sun kashe mani shi Shamwilu" (ya cigaba da zubar da ƙwallah cikin ƙunci) Shamwilu ya karbi jinjirin yana kallo, yace
"abokina tabbas ba dan ina cikin bacin rai na Yasira ba da na taya ka kukan wannan rashin da kayi, amma zuciyar tawa a bushe take yanzu saboda dukan ta na gama duk raina a bace yake, Kaga yaron sak Kai wannan zaa ce Kaine ka haife sa amma banda waɗancan matan, yanzu Ina ita Ummy? "
Audi yace" tana asibiti na sake ta". Shamwilu ya zaro idanu yana kallon sa, yace "da gaske ka saki Ummy ko wasa kake min? Yace "baƙin cikin kashe wannan yaron ya saka na sake ta, babu wani amfanin zamana tare da ita tun da bata so na da khairi, amma wancan tsohon mai gari yana cewa babu sakin wai har yanzu matata ce ita, shine na kyautar da ita ga Wadata"
Cikin ƙunar rai Shamwilu ya dube sa, yace "shi wadata ka bashi kyautar Ummy to ni menene amfani na, Ina abokin ka kaje ka baiwa wani banza gani meyasa ni baka bani ita ba sai wani shashasha".
Audi yayi Jim kaɗan kafin yace "kasan kuɗin da ya kashe na nema mata lfy Sam bazan iya biyan sa ba shiyasa na bar masa ita, kana da mata irin Yasira ina zata bar ka kayi wani aure yanzu, ni bama wannan ba, wai yanzu Shamwilu babu ta yanda zaa yi yaron nan ya tashi?
Cikin takaici shamwilu yace "ina ne ka taba jin an mutu an dawo, waye yake bayar da rayuwar idan ba Allah ba kuma ya karbe kayansa ko gurin boka kaje bazai tayar da wannan yaron ba" idanun Audi suka yi jawur ya karbi yaron yana ƙara kallon sa yana jin wani shauƙin son sa, da kyar aka rarrashe sa mutanen unguwar aka karbi yaron aka je aka masa wanka da sutura, kukan da yayi akan yaron bai yi akan rasa iyayen sa ba yanzu ne ya san zafin mutuwa, a wannan ranar yayi addu'a sosai ya saka iyayen sa tare da istighfari akan abinda ya aikata masu, yana tunanin ko haƙƙin su ne ya kama yaron, daren ranar ya nufi mashaya batare da ya ƙara waiwayar asibiti ba.
TWO WRITERS EMPIRE ✍️✍️
Ku garzayo kar ayi babu ku domin samun labaranmu guda biyu wadanda zasu nishadantar daku kuma su ɗebe muku kewa,
FARAR TASKA (600) tare da alƙalamin FATYMA XARAH
ZAMA DA MAƊAUKIN KANWA (600) daga alƙalamin UMMI A'ISHA
Dukka wadannan Labaran guda biyu zaku samesu kan naira ɗari shidda shidda, ga mai bukatar biya sai ya tura kudinsa ta 7044644433 Aisha Ibrahim Moniepoint micro finance bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko kuma recharge card na mtn ta wannan no 08169334980 da shaidar biya.
[8/3, 9:11 PM] J💕: https://chat.whatsapp.com/ER26gPFC7iT6v26Jyz8hCt?mode=ac_t
*FARAR TASKA*
Fertymerh Zarah
12