← Book details Dr Saheeb Par 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 22

Sashe 10

Dr Saheeb Par 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daddy yace"ah'ah karkiyi kuka kukan ki akanshi ba alkhairi bane karki kuskura ki fadi abinda daga baya baza mu ji dadin shi ba nidai abinda zan fad'a Miki ki amsa phone dinta gudun kar ta Kira gida bana son kowa yasan abinda ya faru"

Mummy tace"ai dole ne wata rana ta tafi domin babu amfanin zamanta tare damu tunda ya saketa"

Maganar saki sanda yasa Abba girgiza yace"harda sakinta yayi hmmm lallai yayi kuskure,karki damu zamu rike ta kamar Iman har lokacin da zan samo Mata miji in Mata aure da kaina zanje gidan nasu inyiwa baban nata bayani Amma gaskiya ba yanzu ba maganar babu dadin ji"

Dr ne ya fito suka karasa gabanshi

Mummy tace"ya jikin nata?"

Dr yace" a gaskiya ba karamin b'arna akayi Mata ba domin sanda muka d'inketa Amma har yanzu bata farfado ba da tayi kamar zata dawo dai-dai sai kuma ta koma babu abinda takeyi sai sauke ajiyar zuciya,wanan tana faruwa ne in mutum ya Shiga shock ga kuma tashin hankali ga zafin kasanta Amma karku damu kila ta farfado zuwa gobe"

Mummy tace"mun gode Amma zamu iya ganin ta?"

Dr musty yace"eh but hajiya meya sameta ne haka waye yayi Mata wanan aika-aikan"

Mummy tayi murmushin takaici tace"mijinta d'an na shi yayi mata hakan dan ya tozarta mu"

Girgiza kai yayi yace"Allah ya kyauta"

Tura kofar mummy tayi ta ganta a kwance kan nan na walkiya kamar kwarya

Wani kuka mummy ta fashe dashi babu abinda take furtawa sai ni saheeb

Daddy ko baka iya gane yanayin da yake ciki

Drip ne a hanunta bakinta duk yayi kwanciyar jini ya taro ga shatin yatsun shi kwance a kumatun ta fuskar nan a kumbure sai wani Muni data kara wallahi bazaka yarda farida ne kwance a gadon ba

Ajiyar zuciya kawai take jerowa ummi ta d'auki d'an kwali ta d'aura Mata sanan ta kama hanunta tana Mata addu'a

B'angaren SAHEEB ko Yana barin gidan wani expensive hotel ya kama ya zauna a d'akin

Kwanciya yayi a hankali abubuwan da suka faru yana dawo me

Sai ya ji ba dadi yace"hanya abin nawa beyi yawa ba?"

Girgiza kai yayi yace"no beyi yawa ba"ai ita ta tabo ni nasan duk inda take yanzu bata haiyacinta but I most confess I enjoy the moment with her"

Gaban shine ya fadi daya tuna mummy yace"hmm bama zan kirata ba kuma ko sun Kira bazan d'auka ba sai abin ya lafa yawo kawai zanyi tayi a kasar wajen Ina hutawa dama mutum yayi needing freedom bazan dawo ba sai na samu labarin anyi sadaka da mayya nan domin itako sai sadaka"ya fashe da dariya yace"duk na kwakwale ruwan jikinta"

Da wanan tunanin ya kwanta ya biya bashin baccin da beyi jiya ba

Abu dai kamar Wasa yau kwana uku da faruwar abin tuni saheeb ya sauka a kasar lodon

B'angaren fareeda kuwa shiru bata farfado ba ba karamin tashi hankali mummy da daddy suka shiga ba kullum cikin karin ruwa ake saboda Bata farka ba balle taci abinci

Mummy tayi kuka har ta gode Allah sai dai kullum maganarta d'aya shine ni saheeb zai tozarta toh duk inda yaje Ina nan zai dawo ya sameni

B'angaren su baba ko hankalin su ya tashi domin kullum suna Kiran wayar fareedat a kashe kuma suna ta expecting ta Kira saboda sauyin mijin da ta gani shiru suke ji hakan yasa baba zuwa wajen daddy ya tambaye shi Amma baba ya tabbatar me tana lafiya tabi mijinta kasar saudiya

Haka dai baba yayi shiru badan ya gamsu ba ya hakura ya koma gida cike da tambayoyi a zuciyashi Amma ya barwa Allah komai

Koda ya koma gida mama ta tambayeshi cewa yayi yau sunyi waya da ita

Bayan sati d'aya zaune take tana shafawa fareeda addu'a a fuska kawai sai ta gan hanunta ya motsa

Cikin jin dadi tace"yauwa baby mummy bude ido ki gan sabon mummy ki"

Bude idonta tayi a hankali ta sauke kan mummy

A hankali komai ya fara dawo Mata wani ihu ta sake jikinta na mugun rawa tace"dan girman Allah kayi hakuri na tuba ka yafe min dan Allah karka saka ban tab'ayi ba"wani Kara ta saki kawai sai ta kara sumewa

Fadin tashin hankalin da mummy dake jijjigata tayi bai misaltuwa

Tace"farida bude idonki please wanan kwanciya tayi yawa ki bude dan darajar annabi "

Iman da shigowarta kenan da kullar abinci da gudu ta koma ta Kira Dr

Koda Dr musty ya zo ya gan mummy zaune tana kuka ba karamin tausaya Mata yayi ba

Karasawa yayi ya fara duba farida kallon mummy yayi yace"

Pls kuyi manaji no edition

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/6, 6:19 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄
*_DR SAHEEB*_
💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah

🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.

Dedicated to my paid groups
____________
🅿4⃣5⃣-4⃣6⃣
______________

Bismillahir Rahmanir Rahim

Dr mustapha yace"hajiya kiyi hakuri inshaallah zata samu lafiya wallahi ta mugun tsorata ne kuma abinda ya faru Yana yawan yawo a kwakwalta Wanda in bata cire shi bazata dawo dai-dai ba,wai miye takanmame abinda ya sameta? ko zan iya taimaka mata"

Iman ne cikin komai tame bayanin komai shi kanshi jijina lamarin juyawa yayi ya kalleta Wanda ta rage daga ido sai hanci

Karasawa tayi ya shafa fuskarta sai kawai ya fita cike da tausayinta shi kaidai yasan irin b'arnan da saheeb ya aikata Mata shifa har yanzu be amince shi kadai yayi ba"

Zama yayi a office yace"lallai wasu mazan rakiya sukayi"

A ranan mummy ko ruwa taki Sha washe gari ta tashi da azumi da rokon Allah

A rananma abinda ya faru jiya shi ya faru so biyu tana farfadowa sai ta Kuma sumewa

Daddy yace"a shirya duk wani abin bukata za a fitar da ita waje"domin bayan sati biyu da faruwar abu sai ta fara bleeding da mummy tayi magana sai Dr musty yace" al'ada take"sosai ta tsorata Amma ya tabbatar mata jinin zai tsaya haka ko akayi

Haka kawai Dr mustapha ya sinci kanshi da rashin jin dadin hakan sai dai bece komai ba

Haka fa ta kasance har na tsawon sati uku inda ake shirin tafiya da ita da yammancin yau

Mummy ta tafi gida shiryawa Dr mustapha ne ya shigo ward din ya zauna ya Kama hanun ta ya kalli fuskarta yayi murmushi yace"sleeping beauty"

Sunanta ya fara Kira yace"fareeda fareeda ki bude idonki bacci ta Isa haka,fareeda ki tuna iyayen ki,mama zata iya rasa rayuwarta baba ma zai Shiga wani hali saboda ke ki manta da abinda ya faru ki tashi ki cigaba da rayuwar ki"domin sanda yasan inda yayiwa Iman wayau yasan komai na fareeda haka kawai ya ji is interested a case dinta
.haka yayi ta surutai Kamar tana jin shi har ya gaji ya mike

Har ya bude kofa sai yaji na'urar jikinta ya fara kara

Juyawa yayi sai ya gan ta bude ido tana kalle kalle asibinti can dai kamar Wanda ta tuna wani abu sai kawai ta fara juye-juye da tsalle -tsalle a gado

Da sauri ya karasa kafin ta Kuma sumewa yace"fareeda baba ya zo"

Kallonshi tayi ta Kura me ido hawaye na bin kuncinta

Wani mugun tausayinta yaji ya rungumeta yace"you are save"

Kalle-kalle take yace"kiyi magana Mana "

Shiru tayi,kawai sai yayi murmushi yace"welcome back watan ki d'aya a asibiti"

Zaro ido tayi Amma Bata ce komai ba

murmushi yayi yace"no prob in baki son kiyi magana dani toh ko in Kira Miki Dr sahe...."

Ai be karasa ba sakamakon wani ihun da tayi jikinta na mugun rawa

Yace"Yi hakuri toh"gyra Mata hular kanta yayi domin ya tsane ya gan kanta

Jingina tayi da gado babu abinda take sai hawaye

Kallonta yayi zaiyi magana sai ga mummy

Da mamaki ta kallesu cikin farin ciki ta zo ta rungume fareeda tana hawaye

Tace"dota yaushe kika farka?"

Bud'a bakin fareeda sai Suka ji tace"a kaini wajen mamana"

Mummy tace"ai Nima maman ki ne"

Shiko Dr mustapha jin tayi magana yasa shi sauke ajiyar zuciya domin dama yana gudun kar trauma ya hanata magana"

Kuka ta fashe dashi tace"akaini gida zai kasheni yayi min fyade ya rabani da uztazu na "

Kamar Wanda ta tuna wani abu cikin kuka tace"har mafalki nayi zai aske min sumana be aske bako?"ta kare magana da tab'a kanta

Aiko taji shi sumul wani ihu ta sake tace"ya aske dan Allah ku taimakeni ku tada ni a mafalki na tuba"

Mummy ta rungumeta tana kukan tausayinta tace"

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/6, 6:19 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄
*_DR SAHEEB*_
💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah

🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.

Dedicated to my fans
______________
🅿4⃣7⃣-4⃣8⃣
_________________
Bismillahir Rahmanir Rahim

Tace"kiyi hakuri ya'ta ki cire wanan tunanin a zuciyar ki kinji?"

Kokarin tashi take son yi jiri ya kamata tayi kamar zata fadi a lokaci d'aya mummy da Dr mustapha suka riketa

Kallonshi mummy tayi domin kwayar idonshi ya gama tona Mashi asiri

Dukar da kai yayi cikin jin kunya ya janye hanunshi yace"Sannu"

Zama tayi mummy tace"me kike so toilet zaki?"

Tace"mummy Ina son in saftace bakina"

Dr mustapha yace"iam sorry I was carried away I guess shine dalilin da ya hana ki magana d'azu ko?"

Mummy ko tace"ba baki kadai ba kina bukatar wanka"

Har bakin kofa ta rakata ta shiga sanan mummy ta dawo ta zauna d'aga Kai tayi ta kalle Dr mustapha sai kawai ya Sosa kai

Murmushi tayi tace"nasan jira kake ta fito ka shafa mata mai ko son?"

Da sauri ya bar ward din cike da kunya,Yana fita tace"kayiwa kanka saheeb"

Ba a jima ba fareeda ta fito d'aure da zani a kirji

Mummy ta Mika Mata wani dogon riga tasa tace"kina ta kallona,Zaki ce waye wanan?"

Murmushi yake fareeda tayi Amma batayi magana ba

Mummy ta kama hanunta tace"ni ce mahaifiyar saheeb"ta kare magana tana kallon kwayar idon fareeda

A take fuskar fareeda ta canja babu abin da kake hangowa sai tsanan Saheeb

Mummy ma sanda ta d'anyi Jim tukkuna harga Allah taji ba dadin yanayin fareeda sai dai ya zatayi shi ya jawo

Cikin sanyi jiki tace"dear ya abin ya faru"
Chapter 10 · 0% Book details