← Book details Birnin Sarauniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 7

BABI NA BIYAR

Birnin Sarauniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Aranar banyi cikakken barci ba duk sa'adda na rufe idona saina ci gaba da ganin damin damin wazobiya ajere reras acikin akwatin data bani
banyi barci ba har saida na tabbata na samarwa akwatin kyakkyawan maboyi acikin daren na samo wani abin cire kusa da guduma na cire daya daga cikin rubabben silin din dake saman dakina na ciccibi akwatin da karfin tsiya na taka kujera na tura ta cikin silin din sannan na mai da silin din dana barke gurin zamansu na gyara babu wanda zai iya tsammanin akwai naira miliyan uku aboye a saman dakin.

Sai bayan dana karbi kudin ne sannan naji matsaloli sun fara damuna na farko bansan yadda zanyi na sanar da mahaifina bayanin kudin ba domin na tabbata inna fadawa mahaifina gaskiyar lamarin bazai goyi bayana ba nasan sai raina yayi matukar baci kuma nasan dole ne saiya sani na maida kudin. Har gari ya waye ban cimma wata kwakkwaran shawarar abinda zanyi da kudin ba. Yau da ace iyayena zasu bani hadin kai to da da sauki to amma nasan wannan wani abune marar yiwuwa na san muddin na nuna musu kudin sai sun bukaci sauran bayani haka nayita saka ina warwarewa awashegarin ranar har kusan karfe dayan rana sannan na tashi na nufi gidan bayan na yi wanka saina sauya tufafin dake jikina da wasu wankakku sannan na dauki yan litattafaina na turanci dana lissafi don daurewa karya gindi har da karan alli guda uku na nufi gidan su Hindu El- bashir ayadda na tsara shine bayan na gama abinda zanyi agidansu Hindu daga nan saina wuce kai tsaye zuwa gidan Salma inda zamu gana da tsohon mijinta to amma abubuwa basu kasance yadda nake tsammani ba.

Unguwarsu Hindu el'bashir tana makwabtaka ne da unguwarmu ta bangaren yamma sannan dankakareren gidan el'bashir shiya mamaye kusan rabin unguwar bari na zana maka hoton gidan el'bashir azuciyarka domin ka fahimci irin tsaruwar da kuma makudan kwandalolin daya hadiye.

Lokacin daka dubi kofar gidan zakuyi ido hudu da tangamemen lambu wanda ke boye abayan doguwar farar katanga wacce keda katuwar kofa kamar kofar gari.
Ga mamakina sainaga asaman katuwar kofar lambun wacce nake tsammanin ita zata kai ka har gidan an rubuta cikin hanyan haruffa launin gwal kamar haka SALMA GARDEN

Nayi mamaki saboda ganin sunan salma ajikin kofar gidan amma daga baya saina daina mamaki ai masu suna salma na da yawa agarin nan nace cikin zuciyata.
Kamshin furanni da kayan marmari ya bugi hancina lokacin dana jera koda lambun na shiga gabana nata dar dar sassanyat iskar tsabtatacciya ta bugi fuskata gamida kamshin ganyen bishiyar lemon zaki da kashu (yazawa) sannan ne fa na fara hango tangama tangaman gine ginen alfarmar dake boye abayan shuke shuken lambun.
Wani dan siririn mai gadi fari sanye da bakaken kaya da farin rawani daya ziraro tun daga kansa har bayansa ya bayyana a gabana kamar an jefo shi.
Kai kazami ina zaka ba sallama.. Ya buga min tsawa na dubi bakin zaren ulun dake daure adan siririn wuyansa mai kamar lilo nace.
Dankerere shin mamanka hindu tana nan? Fuskarsa ta canza launi sanan idanunsa suka kada sukayi ja kafin ya yanke shawarar abinda zaiyi dani sainayi sauri nace dashi nine sabon malamin da zaike koya mata karatu shin ko kanada labarina?

Ya dubeni a yatsine yana hadiyar zuciya nayi zaton zai kawo min duka amma maimakon hakan sainga fuskarsa ta washe kaine Farisu? Ya tambayeni kwarai kwarai nace dashi yayi murmushi kayi sa'a kazami ai bangane ka bane tace idan kazo ka jirata anan zatazo ta sameka.... Kodai kaje kafada mata nazo?... Ya girgiza kai abinda tace dani kenan kazami to dankere nace dashi wannan karon baiyi fushi ba maimakon hakan ma sai ya kyalkyale da dariya sannan yace nayi mamakin ganinka da farko datace min wani sabon malaminta zaizo nayi zaton zanga abu tsaf tsaf amma saina katse. Ya isa haka in ba so kake yanzu na murde maka dankereren wuyanka ba yayi murmushi sannan ya nuna min wata kujerar katako dake karkashin bishiyar yazawa Jeka can kajirata.

Na nufi kujerar da nufin na zauna sannan sainaji kamar an sokeni da kibiya su hudune daya da manjagara yana sharar matattun ganyayyakin da suke zubowa na itatuwan kayan marmari ne biyu kuma dauke da fatanya suna saran kasar gindin kananan bishiyoyin da ake reno suna gina ramin da ruwa ke taruwa dayan kuma dauke da abin ban ruwa na hudunsu dauke da katon kwando yana tsintar kayan marmari yana tarawa aciki shine yafi daukar hankalina acan cikin lambun na hango su amma kayan dake jikinsu shi yayi min tarnaki na kasa tsaye na kasa zaune kowannen su sanye yake da yankakkun wando jeans kafi shanu wuya iya gwiwa sannan kuma da bakar suwaita gumi ya lullube ni sunyi kama dasu......

Lokacin daya dago kansa sama saina gane shi lokaci guda tun kafin ma ya gama juyowa mu hada ido dashi dogon kansa mai kamar shantu ma kawai ya isa na gane shi kansa sai kyalli yake acikin hasken ranar kamar madubi dogon gemun sa mai kamar burushi ya hada gumi sharkaf muka hada ido dashi kafata na rawa sannan sainaga ya ajiye kwandon kayan Marmarin akasa ya laluba aljihunsa ya zaro karan taba sannan ya kunna mata wuta ya fesa hayakin sama yayi min murmushi da bai kai har idonsa ba sannan ya juya kan aikin sa na tsintar kayan marmari yana zubawa a kwandon a gaban rigar sa an rubuta IJAKALA

****** ******* ****** ******* ******* ******* ****

NA SHARE GUMIN DAKE KWARAROWA KAN GOSHINA...
[3/16, 5:02 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BININ SARAUNIYA-15

Sannan ya juya kan aikinsa na tsintar kayan marmari yana zubawa a kwando agaban rigarsa an rubuta IJAKALA

***** ****** ****** ***** ******** ******* *******

Na share gumin dake kwararowa kan goshina sannan jikina na rawa na juya na yafuto dan siririn maigadin nan.
Yau kam sai abinda hali yayi nace cikin zuciyata nasan na kawo kaina ga halaka.
Menene kuma nace kayi jiranta yanzu zatazo yaushe wadancan suka fara aiki agidan nan? Na katse shi maigadin yayi shiru sannan bayan ya danyi yan waige waige ya tabbata aikinsu suke ba kallonmu suke ba saiya matso kusa dani yace cikin rada jiya suka fara aiki agidan nan ita ta kori wadancan masu gadin na shekaran jiya. Wallahi nima bana farin ciki da zuwansu ni tsoro suke bani kaganta dai kyakkyawar yarinya amma halinta mummuna ne kullum saita zageni gata da shegiyar rowa bata tabayi min kyauta ba kaima ina mamakin........
Yayi shiru lokacin daya lura cewa bashi nake kallo ba daga can cikin gidan hindu ce ita da wani mutum wanda nake tunanin shine mahaifin nata suka nufo inda nake.

Koda maigadin ya fahimci abinda nake kallo sai yayi sauri ya sulale yabarni nan tsaye kamar nayi fitsari awandon don tsoro yanzu na fara gane abinda ke shirin faruwa abinda yafi sani kaduwar fiyeda komai shine lokacin danaga fuskar wanda nake tsammanin mahaifinta ne ko shakka babu shine mutumin danaga hotonsa shi da salma amakale ajikin bangon dakinta yanzu na tabbata yarinyar data nemi na koyar da ita karatu ba wata bace data wuce yarinyar datake son a hallakani don ganin ban auri matar ubanta ba wato salma. Tun daga nesa ta nuna ni da dan yatsa tace Baba gashi can sune irin barayin nan masu mana sata. Tace cikin karaji kamar da gaske. Inajin ma sune suka sace maka na'u'rorinka masu kwakwalwa na kwanakin nan sannan ta kwalla ihu kai masu gadi ku tare barawo.

Yanzu ne na fahimci abinda take nufi so take tayimin kamun barawo idan yan ta'addar da ta dauko amatsayin masu aiki sun kasheni to sun kashe barawo kenan.
Na zubar da litattafaina da karan allina guda biyu na zura aguje domin tserar da kaina na tabbata babu abinda zai fitar dani daga sharrin datayi min idan na tsaya kuma nasan sakamakon abinda zai faru.

Ijakala ne yafara fitowa ya biyo ni da adda tsirara ahannunsa sannan sauran suka rufo masa baya da gudu yakawo min sara da adda amma bai sameni ba sannan muka cigaba da gudu duk kokarin da nake shine nakarasa kofa nasan indai na fita daga gidan shikenan banajin zasu iya biyoni waje.
Ku tare barawo hindu ta sake kwalla ihu adaidai lokacin dana kusan karasa kofar gidan ba zato ba tsammani sai ga dan kereren mai gadin nan yashiga gabana alokacin ina kokarin kaiwa ga kofar nayi kan maigadin da gudu ashirye nake na banke shi domin tserar da rayuwata.
Na runtse idanuna na banke maigadin adaidai lokacin da Ijakala ya kawo min sara da addarsa.
Banke maigadin danayi shiyasa ni tuntube dashi na fadi fuskata ta daki kofar gidan ji kake gau gau naji wani radadadi ya soki kaina har wani kara nakeji a kunnena wur wur wur abin tsautsayi faduwar danayi ita ta cece ni cikin nufin Allah sai addar ijakala ta sauka awuyan maigadin nan take anan maigadin yafadi kasa yana shure shure tuni jini yayiwa rigarsa wanka.

Ganin abinda yafaru shiyasani mantawa da nawa ciwon nayi zumbur na tashi sannan Ijakala yakawo min sara da addar na sunkuya ya sari kofar gidan sannan yayi sauri ya tsare kofar da adda a hannunsa tsirara tana walkiya
ku gama dashi mana ya bugawa yaran tsawa daya daga cikinsu ya daga manjagaran dake hannunsa sama da niyyar ya sauke min shi a tsakiyar kai ganin cewa sauran basu karaso ba sai nayi amfani da damar na shige shi kafin ya sauke min manjagaran na daki ruwan cikinsa abinka da wanda yake gudun ceton rai dukan danayi masa shiyasa ya jefar da manjagaran gefe guda shi kuma ya durkusa nan rike da cikinsa nayi sauri na rarumi manjagaran daya yar.

Ijakala ya sake kawo min sara nasa manjagaran na kare ji kake kal! Hakora uku na manjagaran suka balle adaidai lokacin dayake shirin sare min kafata ne naji an tika min wani abu abaya dam nafadi agurin ina murkususu azatona kashin bayana ne ya karye daya daga cikin yaron Ijakala na tsaye akaina hannunsa rike da dankareren icen bishiya yayi yani atsaye azatona irin icen da ake tashen zan buge dashi ne.
Mai dogon gemun ya sake kawo min sara wannan karon kuwa saina sa hannu na kare saboda radadin dukan da akayi min bazaisa na kauce ba.
Addar tasa ta tsarga min hannu jini yayi tsartuwa sannan ya sake daga addar nayi zumbur na mike adaidai lokacin daya sake sauke min ita agadon baya nayi sa'a bata sameni ba adaidai amma ta tsarga min riga nayi taga taga kamar zan fadi amma na cije domin nasan idan na sake na sake kaiwa ga faduwa kasa to ni shikenan tawa ta kare.

Suka rufa min baya don tsabar sharri irin na mace su suna kokarin halakani ita kuma tana faman kururuwa wai barawo barawo nasan nufinta so take ta janyo hankalin sauran mutanen unguwa suzo su karasa ni.

Nayi cikin shuke shuken gidan da gudu ina cikin gudu sai kayar bishiyar lemon tsami ta rike min riga nayi nayi na kwace amma......
[3/16, 5:02 PM] Abubakar Saleh AlQuyraeme: BIRNIN SARAUNIYA-16

Nayi cikin shuke shuken da gudu ina cikin gudu sai kayar bishiyar lemon tsami ta rike min riga nayi-nayi na kwace amma abin yaci tura gashi kuma Ijakala na biye dani ko wannen su dauke da makami. Shi da adda wani da manjagara dayan kuma da katon itace shikuma na cikon hudun dauke yake da dagi na hakar kasa. Ku rike shi na soke shi!! Yace dasu ijakala cikin karaji.
Chapter 6 · 0% Book details