← Book details Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 72

BABI NA BIYU

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

_Da alamu Jumma'a da zata yi kyau tun daga laraba ake gane ta, sai dai zaku yi hakuri sosai domin wannan tafiyar ba kamar sauran tafiyar bane bana ce yakai Kwarkwarah ba, amma ba mamaki zai iya kunnen doki da haka tafiya ce me matuƙar tsoho da bukatar hakuri Insha Allah zaku same Ni me cika alkawarin da na dauka naso na sayar da labarin amma kuma gashi nan dai mu karanta shi a kyauta! Idan Ubangiji yayi maka ni'ima ta wani gurin kai ma sai ka gwada taka azancin da fatan zaku amshi wannan lamari da girma is FREE BOOK_

Sab'a jaririn tayi a baya, tana me ce mishi da harshen fulatanci.
"Kayi hakuri! Bawan Allah ƙaddarar kace tazo a tsakanin zukatar mugayen mutanen karshen karni, shi yasa ka fuskanci tozartawa, Ya Allah ga Al Mamoon, ka azurta rayuwar shi ta farkin da ban zata ba, ka mishi ni'ima da ilimi, ka daukaka darajar shi Ya Allah ka bashi juriya da hakurin ƙaddarar shi.

Ya Allah ka rangwamta mishi tsangwama da hantara na Al'umma, Ubangiji ka sanyawa Al'umma soyayyar shi ta yadda ba zasu guje mishi ba, Ubangiji ka sa ya zama zakarar gwajin dafi Ya Allah ka raba shi da akasin ƙaddara." Ta faɗa tana kuka, sabida Allah bai bata haihuwa ba, sai take ganin kamar sun zo kan su ne da suka wofantar da Al Mamoon, dan haka ta gyara mishi goyon shi. Sannan suka fita da mijinta.

"Yanzun kin ga na tambayi Babayo ya bani shanuna ya hanani, sai wata karsana ce ya bani. Mu dauka mushiga gari idan yaso sai na sayar na nima mana haya" ya faɗa cikin sanyin murya.
"Toh babu kome nima tun d'azun na kama dabbobina, muje na sayar da su, dan nasan Hamma Sama'ila ya tafi da shanun mu"
Haka suka hada kayan su baki daya. Suka bar rugar duk da zaman amanar da aka yi bai hana a musu koran wulakancin ba, dan har wajen rugar aka bisu, dakyar suka sami keken shanun suka hau, tare da lullube fuskar su.

  Suna fitowa wata mota kiran honda ta shiga garin garin, da gudu. Har sai da suka juya tare da kallon motar, jaririn da yake hannun Kabo ya fashe da kuka. Har da shashakewa, haka tayi ta jijjiga shi har suka bar yankin rugar Ardo bako.
Suna shiga rugar Ardo bako, suka tsaya kallonta yayi tare cewa.
"Kika ce mun iso sama a farkon gari suke."
Lumshe idanunta tayi sakamakon rungume nonuwarta da tayi har suna wani irin cika da tsirta da ruwa.
"Yaron yana bukatar ki sosai"
Kallon shi tayi cikin kuka tace mishi.
"Da fatan ba zaka tab'a juya mana baya ba, kar na dauko shi kuma kace ba haka ba, babu da Uwa bani da Uba, duk sun tafi sabida zanen ƙaddara ta, don Allah karka juya min baya, kai ne Ubana kai ne Uwata don Allah karka juya min baya."

"Insha Allah ba zan juya miki baya ba." Ya fada tare da murmushi domin karfafa mata gwiwar ta, a tare suka fito daga motar domin yara sun yanyaye motar suna kallon kansu da ihu.

   "Laaa Abuh ce! Yaran suka fada tare da watsawa a gurin, a hankali take takawa, zuciyarta yana rawa, tsoro da tararradi ya zauna a fuskarta. Tana isa bukkar Sama'ila ta samu baya nan, juyawa tayi a kidime zata nufi gidan Kabo, wata dattijuwar mata tace mata.
"Ayya ita ƙaddara sau daya takan fada maka, amma zafinta sai ta shekara dubu tana bibiyar ka, da lokacin da kika haihu kin dauki abinki bakin ki alekun babu wanda zai kuma ganin ki sai tsananin rabo. A yanzun kuwa abu biyu suka haɗu a guri daya.

Tafiyar kaddara wacce baka iya tsayawa dole sai kayi, sai kuma akasin ƙaddara wacce idan ta same ka sai hakuri, ko minti talatin basu yi ba da barin garin nan sai wata rana." Dishi dishi, ta fara gani kafin ta ankara har ta zube a kasa, da gudu ya iso gare ta, bai tsaya ba wata dogon nazari ba ya dauke ta, suka bar garin baki daya. A mota yayi ta watsa mata ruwa bayan sun bar garin.
"Wayyo Allah na, wayyo Allah na wayyo na shiga uku, meye nayi ne haka? Meye na aikata da Ubangiji ya sab'a haduwar mu, meye yasa ban hakura na dauke shi ba, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji na tuba Ubangiji, ina son jinjirina ina kaunar jinjirina, ya Allah na tuba ya Allah na tuba, na shiga uku me yasa nayi haka? Me yasa bani da zuciya na imani, Dr Khalid bani da tausayi na rasa Yarona na barshi a hannun mujirimi, ya rabani da Uwata ya Rabani da mijin aurena, ya rabani da Ubana ya kuma rabani da Yarona Wayyo Allah Ubangiji ka tsinewa Sama'ila, Ubangiji ka hana shi jin dadin rayuwar shi."

Kuka yake tana buga kanta tare da dukar cinyarta, duk  hakurin ka sai ka zubda kwalla haka har suka iso garin Maradi, gidan Mahaifiyarshi ya kaita dama a can ya kaita. Kallon su tayi cikin tausayi tace mata.
"Kiyi hakuri  Sama'ila yayi laifi amma laifin shi bai kai naki muni ba, da yayi miki sai kiyi hakuri da shi ki dauki d'anki ki dawo."

       Dauko wata jaka tayi tare da mika mata.
"Wannan jakar Mero ta kawo ranar da abin ya faru, tace baffanki ya hana Sama'ila nisan zango dake ta hanyar da yayi amfani da ke, sai dai kabilar Bugaje basu cika zama ba suma, ba kamar Fulanin mu na yau da kullum ne ba, gashi dukiyar cikin shi sunce kiyi karatu kamar yadda kika so tunda har kinyi primary school da Secondry, since kiyi karatun da zaki amfani al'ummar Fulani, da wayar musu da kai. Domin sun tabbatar da zaki dawo, amma girman abin kunyar da ya faru dake ba zai iya sakawa su amshe ki ba, domin tunda suka ji labarin juna biyu gare ki, da shi Mijinki ya kai musu takardan sakin ki, shima yana cikin shi. Kiyi gudun abin kunya yasa suka tafi bawai basa kaunarki bane"

   Wani irin kuka ta kuma fashewa da shi, tana yi tana karawa, tare da k'amk'ame jikinta, meye yasa aka fidda al'adun da basu da tushe? Me yasa ita ƙaddara bata zab'i kowa ba sai ita? Ji take kamar an cinnawa zuciyarta wuta yake ciki. Kuka take tana kuma wa, har yamma lokacin da aka juye ruwan wankan ta nonuwarta sun kuma cika da zubda ruwa.

  Haka ayi ta watsa mata ruwan idanunta a lumshe bata buɗe ba balle kayi tsammani bata jin zafin ruwan ne kuma tana ji har cikin ruhinta da gangan jikin ta.
    ***
Damagaram.
Anan suka  fara yada zango, kuma sun ji dadin yanayin garin domin sun sayar da saniyar su, yar kudin ce, Sanda ya kama musu haya. Gidan da ya kama musu akwai mutane dayawa, musamman kabilu mabanbantar harsuna dabam dabam, yan kudin hannun su, dashi suka saka ledar tsakar daki, da kuma taburma, sai yar tukunyar da zasu amfani dashi, dan basu iya daukar wani shirgi ba, sabida fitar bata nutsuwa bace kuma ma basu san inda zasu fada ba.

Dan haka suka auno hatsi da zasu ci, dan ma sun shigo garin da yan dabbobin su. Ta watsa a tsakar gidan, bayan sun tambaya aka ce zasu iya saka kiwon su.

     Wani abinda ya Kum burge su da gidan akwai rijiya da wata tsohuwar turmi, dan haka ta nemi Izni gurin daya daga cikin matan gidan zata yi daka. Cikin kallon tsoro ta nuna mata inda turmin yake, ta wanke hatsin sannan ta zuba ta fara dakawa, ta surfe shi tass, sannan ta kuma wankewa har ya tsane ta koma ta dake shi sai da ya zama gari, lokacin Sanda ya shigo, da sauri ya amshi Jaririn bayanta.
"Kabo bana son haka, taya zaki zo kina daka da goyon dan luɗi a bayanki, idan tabaryan ya fado daga hannunki fa?"

"Kayi hakuri mai gida" ta faɗa cikin wani irin farin cikin, sabida yadda ya nuna kulawa kan Al Mamoon, yayi mata dad'i. Haka ta gama dakar tazo dakin ta same shi.
"Ki dama mana kunu mana tunda na samo mana madarar Rakumi shi yafi yawa a garin nan"   "toh me gida,"

   Haka ta fito tana kallon yadda suke ta harkan gabansu.
"Iya isuhu kunyi bakin Bororoji ne?" Matar da aka kira Iyar isuhu tace.
"Eh wallahi, d'azun suka zo"
"Toh kuyi a hankali" matar ta faɗa dake tana saman katanga ne, jikin kabo ne yayi sanyi, ta koma daki.
"Maigida bari su gama nasu sabgar idan suka gama na fita nayi mana" dake shima yaji abinda aka fada, bai takura ba, haka  suka zauna a dakin shiru, suna tarerayyar  Almamoon.

      Sai da suka ji tsakar gidan shiru ya fito ya fara kokarin niman abinda zata hada wuta, sai da tafita ta sayi itaccen tazo ta haɗa musu wuta aka daura kunun nono. Bayan ya gama ta wanke jikin tukunyar ta itaccen.
Komawa daki tayi, suka zauna tare da shan abin su. Tana jijjiga yaron su.
            Hakuri yayi ta bata taɓa gaya mata abinda suke so, rayuwar Yaron shine kan gaba,  dan haka ba zai yi kasa a gwiwa ba, Insha ALLAH sai yaron su ya taka muhimmiyar rawa a duniya...
     **
Duk inda take tsammanin ganin Sama'ila da Aminatu bata same su ba,haka ta dauki kudin tai ta bin ƙauyuka da wanda suke iyakar Nijar da Najeriya, haka tayi ta b'atar da kudin ta, ta lalace sosai, bata da aiki sai na kuka, idan ta zauna kuka da kaunar danta take, yau ma tun sassafe take shirin fita Dr Khalid ya hana a barta ta fita. Yana sane da jininta yana yawan hawa.

"Khalid me yasa ka hana Musa ya barni na fita?" Kallonta yayi sannan yace mata.
"Sabida ina son na kilace ki daga fita ko ina, so nake na kuma sabunta rokon ki akan na baya. Ina son aurenki, kuma ba wasa nake miki ba, wancan ranar da kika tawo har kika kwanta a kasar bishiya, ba dan Allah ya nufa zan tafi niman ko zan ganki ba me kika san zai faru dake? Don Allah ki taimaka min aurenki zanyi ba wani abu ba, idan muka zauna a inuwa daya Insha Allah Ubangiji zai kuma baki wani Yaron ki duba lamirina."

   Hawaye na zuba mata ta kura mishi ido, tun lokacin da suke shigowa gari da nono yake Bin ta yana Sonta amma take gaya mishi ita tana da wanda zata aura, zama tayi dab'as tare da fashewa da kuka. Ta rarrafa gaban shi tare da rike kafarshi.
"Don Allah karka manta ka tayani niman  Yarona wallahi ina son shi"
.d'ago ta yayi tare da cewa.
"Insha Allah zan tayaki niman Yaronki Insha Allah."

Da wannan shawaran ya sami mahaifiyar shi, dake itama dattijuwar arziki ce mai kaunar Ƴaƴan wasu da nata, tace mishi.
"Allah ya tabbatar da alkhairi"
     Dan haka a cikin satin aka daura auren Zainab Hamza Bugaje, tare da Dr Khalid Agla, akan sadaki CF dubu arba'in da biyar.

      ***
A hankali zaman garin Damagaram yake niman fin karfin su, kasancewar yadda mutane suke tsoron su. Yasa suke dan fuskar halin rayuwa.

   "Iyar Mamoon, naga kin iya surfe da daka ko zaki mana mu biya ki"
"Kai Iyar isuhu zan yi mana," ta faɗa tare da amsar hatsin, kafin awa daya tayi musu daka cass, ta kuma daka musu. Ta tankad'e musu. Sannan ta basu,

       "Laaa. Iyar isuhu kiga yadda yayi laushi. Nima Iyar Mamoon zaki min" take mata suka shiga kawo mata surfe, matan maraya suna da banbanci da matan karkara, sabida matan karkara suna juran aiki, matan maraya kuwa basa iya juran ire iran wannan aikin.

        Shi yasa har makota kawo mata surfe suke, tare da bata aikin.

      Aminatu tana da mugun hakuri, ga dauke kai akan abubuwan da suke faruwa, idan yaron ta yana kuka zata goge shi. Du buga surfen su.

     ***
Tunda aka daura auren kawai yasan da auren ne amma babu wani abu na auren sai yawan rikicin da take mishi dan haka ya shawarci mahaifiyar shi zasu bar kasar. Bata ki ba tayi musu addu'a, dan haka ya haɗa mata kaya suka nufi Faransa,. Zuciyar ta cike da kewar D'anta. Ranar da zasu bar garin Maradi, kuka tayi ta yi tana kallon yadda tayiwa kanta iyaka da D'anta ko iyayenta basu dame ta ba karma yadda tayiwa kanta iyaka da D'anta.
   Wannan shine sanadin Kenan da ta bar garin Nijar.
***
2011/August/04
Idan kace rayuwa tabbas Aminatu da Sanda sun ganshi,kuma suna kan ganin shi. Duk wani abin da zasu yi domin amfanin Almamoon suna yi, kuma Alhamdulillahi.
Yaron ta taso babu tashin hankali, sai dai idan ka tsokane shine fa bai iya fada ba kamar kurma.

       Shi yasa yaran da suke gida daya dasu basa fada dashi sai dai idan an fi karfin su, shine zai shigar musu. A wannan yanayin har suka saka shi a makarantar boko, da arabiyya dan ma yana karatun Alqur'ani a gaban Baban shi Sanda yayi nisa.

    Almamoon  Allah yayi mishi baiwar Ilimi, tun yana shekara biyar ya fara shiga musabaka, kuma yana lashewa, gashi da wani banzan hali shine karka nuna mishi ka damu dashi domin da wannan yanayin yake iya saka damuwa, idan kace kana son shi da abota, wayyo Allah..ka shiga uku domin zai ta baka wahala ne, yana share ka.

         Gashi da farin jini idan turawa yan yawon bude ido suka shiga makarantar su, har rige rigen daukar hoto ake dashi sabida bakin fatar shi, wanda idan ya shiga rana har wani kyali yake, idan ka cire kwayar idanun shi da hakoran shi sune fararre tass a jikin shi sai harshen shi ja, bayan nan babu wani abu da zaka ce fari ne a tare da shi..

Yanayin fatar shi ta janyo mishi soyayyar mutane, sai dai abu daya yake mugun bawa kowa haushi a tare shi a yanzun yana da shekara goma a duniya idan ya yab'a maka bakar magana sau ka rasa inda zaka saka kanka.

A yanzun haka yana tare da wasu yan ajin sune. Amadu Bukar sai Salihu Muhmuda jarabawar suke ta gama primary.

      "Mamoon don Allah taimaka min da amsar nan mana?" Inji Amadu Bukar, Banza yayi dashi. Can Salihu Muhmuda ya taba shi.
"Don Allah taimaka mana abokin mu"
"Ai kusan ni na kawo ku makaranta shi yasa zan baku satar amsa," ya faɗa mu....
8/19/21, 12:42 PM - My Mtn Number: I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx
     ```Zaku iya samun kayan mu daga turaren zamani na wuta, shu'umar humra, dambun nama na mata, tsumin. Da sauran su kayan mu ba irin nasu bane sai an gwada akan san na kwarai..... Akwai haɗin kayan amare da na uwargida...🗣️🗣️Friday  Promo!!! Buy 13pcs @15k only : Turaren wuta 5pcs, humra 3pcs, Turaren tsugunno, shu'umar humra, mopping and toilet perfume, curtains and carpet parfume &kasko💃🏻💃🏻```

🐂🐂BOROROJI🫀🫀 
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
Littafi na D'aya...

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris

_🙄 Daga farawa naga yadda kuke sakawa Dan baki namu ido fa😛🤭 Wallahi ko hmm_
Chapter 2 · 0% Book details