Sashe 3
Bakin Gamo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Boka Mauzaru ya kama hanya yana tafiya cikin sauri, gudu-gudu har ya iso fadar Sarki Kailubuk Hasaru. Da 'zuwa ya iske sarki tare da 'yan majalisarsa a zaune kowa ya yi tagumi ana cikin zullumi da fargaba. Koda shigowar boka Mauzaru sai kowa ya nutsu aka zuba masa ido, fadar tayi tsit kamar babu mai rai a cikinta. Mauzaru ya risina ga Sarki sannanya kwashi gaisuwa. Ba tare da bata lokaci ba ya kwashe labarin duk abin da ya faru tsakaninsa da gunki Sharkas ya sanar da su. Koda ya gama bayani sai
---
**Page 12**
wayi gari da shi."
Sa'adda Himjanatu ta zo nan a zancenta sai
Waziri Karmahan yai ajiyar zuciya, daga can
kuma sai ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar
dariya kamar ba zai daina ba. Ita kanta
Himjanatu sai da ta tsorata. Daga can kuma sai
ya tsuke bakinsa yai shiru tamkar daukewar
ruwan sama, ya juyo ya dubi Himjanatu ya ce,
"Kwantar da hankalinki ya ke matata, ki tuna
cewa ni mutum ne mai magana daya. A iya sanin
ki da ni ban taba alkawari na karya ba. Lallai zan
cika wadannan alkawarurruka guda biyu a gobe
da safe lokacin da aka zo da bakuwar mai laifi
fadar Sarki."
Cikin kaduwa da mamaki Himjanatu ta dubi
waziri Karmahan ta ce, "Ta ya ya za ka iya cika
wadannan alkawarurruka masu wuyar gaske duk
a gobe kuma a lokaci guda? Ni kam ban ga ta
hanyar da alkawarin zai iya kasancewa ba".
Koda jin haka sai Waziri Karmahan ya yi
murmushi ya ce, "Tabbas na san cewa za ki yi
mamaki, to amma kada kiyi mamaki domin duk
yadda kike tsammanina na wuce nan. Ina
tabbatar miki da cewa a cikin daren yau zan
---
**Page 13**
4KIN GAMO
gama dukkan shirye-shiryena. Lallai a gobe zan zama Sarkin birnin Daluza".
Cikina alamun kaduwa da fargaba Hijanatu ta dubi Karmahan ta ce, "Ya kai mijina ina tsoron kada duk shirin da ka kulla ya warwarc, Karshcnmu ya zo".
Karmahan ya sake bushcwa da dariya a karo na biyu ya ce, "Kada ki darnu yake matata, domin ni murucin kan dutse ne ban fito ba sai da na shirya, kuma ni hadari ne malafar duniya, duk inda na so zan sa gabana babu mai iya hanani."
Koda gama fadin hakan sai Waziri Karmahan ya fice daga cikin turakar ya bar Himjanatu a tsaye tana tararrabi.
Da fitowar Waziri Karmahan izuwa harabar gidansa sai ya kwalawa wani bawansa mai suna Zalim kira ya umarceshi da ya kawo amsa doki. Cikin hanzari Zalim ya zo da shiryayyen doki daukca da siddi da linzami. Cikin hanzari Karmahan ya kama dokin ya hayc ya sukwanc shi da gudu izuwa wajen gidan. Karmahan yai ta tafiya har ya fice daga cikin gari ya tasamma wani Karamin gari da akc kira Furus.
Asalin birnin Furus wasu 'yan tawaycn
---
**Page 14**
5ark1 Kailubul Hasaru ne suka ginashi, wadanda a shekaru da yawa a baya sukan kawo hari amma duk sa'adda suka kawo harin ba sa samun sa'a sai dai a kashe su ko a kame wasunsu a kaisu kurkuku a rufe bisa hukuncin daurin rai da rai. Da suka ga uwar bari sai suka hakura suka daina kawo hari. Shi kuwa Sarki Kailubul Hasaru da yake ya kasance mutum mai tausayi da adalci sam bai sa anzo an murfushe su ba, sai ya kyalesu suka ci gaba da rayuwarsu a wannan gari. Sai dai ba a huldar komai da su koda kuwa ta kasuwanci ne. A takaice dai garin Furus baya daga cikin kasar Daluza, garine mai zaman kansa.
Sarkin da ke mulkin birnin Furus wani gwarzon jarumi ne mai suna Halkum. Asalin Hulkum babban bafaden Waziri Karmahan ne kuma tun yana suarayi yake hidima a gidan Waziri har ya girma ya yi iyali na kansa. Akwai aminci da yarda mai yawa a tsakanin Halkum da Waziri Karmahan.
Lokacin da Waziri Karmahan ya 'yanta Halkum sai ya kawo dukiya mai yawa gami da bayi ya bashi, daga sannan ne ya kama fatauci ya
---
**Page 19**
4 fargabar ba?"
Koda jin wannan batu sai Sarki Kailubul
Hasaru ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ya ke
matata kiyi sani cewa ban taba yin kokwanto ba
bisa al'amarin mai girma Sharkas, amma ki sani
cwa ina shakkar waziri Karmahan. Ni na san
cewa abu ne mawuyaci ya zuba ido kawai ya ga
an fito da wannan mace da ta kashe 'ya'yansa an
'yafe mata. Ina kyautata zaton cewa ba zai kasa
yin wani yunkuri ba na tabbatar da yanke
rayuwarta. Waziri Karmahan ya cika fitinanne
kuma hatsabibi zai iya shammatar kowa ya yi
abin da ba a taba zato ba, domin yana da karfin
sihiri, sannan ina zargin yana da boyayyen shiri
a kaina domin zuciyata ta dade tana rawa
akansa."
Sa'adda Sarki Kailubul Hasaru ya zo nan a
zancensa sai Nuraiha tayi shiru tana tunani da
nazarin al'amarin har izuwa wani dan lokaci.
Daga can sai ta dago kanta ta dubeshi ta ce, "Ya
kai mijina kayi sani cewa duk cutar da ta fito fili
aka santa tana da magani, don haka yana da kyau
mutum ya yi riga-kafi kafin cuta ta same shi. Ni
ina da shawara ko in ce tunani akan wannan
---
**Page 20**
matsala, kuma ina tabbatar maka da cewa idan har
kayi amfani da wannan shawara tawa za ka sami
waraka".
Cikin mamaki Sarki Kailubul Hasaru ya dubeta
ya ce, "Mece ce shawarar taki?".
Koda jin wannan tambaya sai Nuraiha ta yi
masa rada a kunne. Koda yaji zancenta sai ya kara
cika da mamaki, ya dubeta yana murmushi da kada
kai yana mai cewa, "Hakika na gamsu da wannan
shawara taki, kuma lallai zan yi amfani da ita".
***
Tun a wannan dare Halkum da sojojin hayar
Dakaru guda dubu suka shigo cikin birnin Daluza a
sirrance ba tare da kowa ya gansu ba. Kai tsaye suka
wuce can bayan gari inda babban kurkukun kasar
yake suka 6uya akan wani dogon dutse mai yawan
ramuka da ke nesa kadan da kurkukun suka kwanta
a cikin ramukan dutse suka yi lam6o, kai kace babu
wani abu mai rai a kai.
Masu iya magana sun ce da dan gari akan ci
gari. Hakika wannan magana gaskiya ce, domin
babu abin da zai bawa mutum mamaki face yadda
wadannan dakarun sumame suka sami damar
---
**Page 21**
shigowa cikin birnin Daluza ba tare da asirinsu ya tonu ba. Yadda abin ya faru shi ne, a daren aka yi wasa da hankalin masu tsaron kofar birnin aka shagaltar da su ta hanyar kawo musu kyawawan 'yan mata daga cikin gari gami da lafiyayyen abinci da abin sha suka yi ta budurinsu har dakarun suka wuce ta gabansu cikin tafiyar ruf da ciki da sanda ba tare da sun sani ba. Kuma daya daga cikin 'yan matan da aka kawo ne ta bude musu kofar birnin bayan an shayar da masu tsaron giya sun bugu sun fara fita daga haiyacinsu. Tabbas an dafe ana shirya kaidi da makirci ta hanyar amfani da giya da mata a duniya, don haka wadannan abubuwa biyu suka zama abin tsoro, ya zama wajibi mutum ya nisancensu ko dan ya baiwa kansa kariya daga sharrin makiya,
Ya yin da gari ya waye sarai har rana ta hudo sai aka je aka fara kofarin bude katuwar kofar kurkuku. Koda jin haka sai dakarun sumame suka kara nutsuwa kuma suka gyara zaman makaman jikinsu. Dama yadda suka ga rana haka suka ga dare, kuma ko alamar barci babu a idanunsu, domin sun sha wani magani wanda ke hana barci. Su dai wadannan dakaru sun kasance karfafa kuma masu karfin sihi. Shi kansa Sarki Barzufa yana alfahari da su domin bai tafa turasu yin wani aiki ba wanda ya
---
**Page 22**
igaqresu.
Ita dai kofar kurkukun birnin Daluza ta kasance gabjejiya mai tsaw o da fadi, kuma an yi ta ne da wani murtukeken lailayayyen kafre wanda koda mutum zai kwana yana saransa da gatai ba zai iya huda shi ba. Shi kuwa ginin kurkukun gaba dayansa an yi shi ne da dutsen wuta. A tarihin wannan kurkuku tun da aka gina shi sama da shekaru dari da ashriin baya ba a tafa kaw o fursuna ya sami damar guduwa daga cikinsa ba. Wannan katuwar kofa kuwa tana da manyan sakatu guda tara, kowacce sakata daya sai kato ashirin sun taru suke iya zareta.
Tun da aka fara zare sakatar sai Dakarun sumame da suka yi lambo a kan dutse suka nutsu sosai suna kirga iya sakatun da ake zarea domin an sanar da su cewa guda tara ne cif. Koda aka gama zare sakata ta tara sai gaba dayan Dakarun suka fara fitowa daga cikin ramukan da suka bu66uya suka ci gaba da tafiyar jan ciki a kasa suka durfafi inda kurkukun yake. Wata hikima da dakarun suka yi shi ne, hatta tufafin jikinsu ya saje da kalar ciyayin da ke kan hanyar zuwa kurkukun, don haka da zarar sun baje akai sai aga kamar babu komai a wajen sai ciyayi kawai.
Bayan an zare sakata ta tara sai kofar kurkukun
---
**Page 23**
ta budc gaba daya wan-war, sai ga Dakaru guda dari sun sawo wata mace a tsakiyarsu wacce ta sha daurin sarkofi a hannu da kafafunta har da wuyanta. Sabo da kaurin sarkofin da nauyinsu da kyar take iya tafiya. Nan take dogaran Sarki suka tusa keyar matar izuwa hanyar cikin gari, kowannensu na rike da zabgegen kulki da sandar karfe mai kama da mashi.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai dogaran nan suka ga dakarun sumame kimanin mutum dubu sun yi musu kawanya.
SHIN . ZA SU SAMI NASARAR KWACETA?
WANNE MATAKI SARKI ZAI DAUKA IDAN YAJI LABARIN AN KWACE WACCE ZA TA ZAMO GARKUWA A BIRNINSU?
Mu hadu a littafi Bafin Gamo kashi na biyu.
Daga mai debe muku kewa
ABDUL’AZIZ SANI M/GINI
---
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,