Sashe 2
Bakar Sarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Gaba data dakarun dake birnin Bahar usuk mutane da aljanu idan ka cire dabbobi wanda basu san komai ba face kai hari hankalin kowa a tashe yake zuciyoyin mazaje sun raunana mataye na kukan rabuwa da mazajen su domin kuwa suna da yakinin wannan ita ce ranar bankwaba.
Birnin yayi tsit bakajin sautin komai sai haniniyar dawakai da sautin tsintsaye tareda kukan dabbobi yayin da jarumai na gida tare da iyalan su suna nasu kukan.
Gudu da haniniyar dawakai ke tashi cikin wani karamin daji dake nesa da birnin Bahar usuk kura ta turnuke baka ganin koda gaban ka daga can wasu fararen dawakai guda biyu suka tawo a sukwane da alama tsere suke yi daga saman kowane doki mutum daye ne sanye da riga da wando na fatar damusa takalmin kafarsu ma haka fuskokin su a rufe baka ganun komai face idanun bayan su rataye da kibiyoyi yayin da hannayen su ke dauke da kwari da baka wanda suka saita wani zomo dashi daya daga ciki ne ya samu nasarar Harbin zomon yayin da zomon ya tsaya can babu rai a jikin a hankali kuma dawakan suka rage gudu har suka karaso inda zomon yake wanda ya harba ne yayi saurin sauka daga kan dokin ya dauki zomon yana murmushi tare da kwance nadin dake kan su gaba daya kyawawan fuskoki ne suka bayyana tare da kwantaccen gashi har kugu dole mutum yayi mamakin yammatan da suka iya sarrafa dawakai kamar haka, gujr guje suka.farayi wacce tayi nasara tana yuwa yar uwar ta dariya suna zagaye jejijn, sun dan jima suna gudun cike da shaawa kafin suka ajiye zomon suka karasa wajan wata korama dake guda na a wajan tsugunawa sukayi suka daura alwala suka karasa cikin wata karamar bukka suka fito da karamin kilishi suka shimfida tare da maida lullubin su suka tada sallah.
*BAKAR SARAUTA*
P 3
NANA DEEJAH CE
JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI
بسم الله الرحمن الرحيم
Kashe gari mutanen birnin Bahar usuk sun cika makil a fada domin kuwa gobe ne ake saka ran tafiya zuwa birnin Bahar usuk.
Fadar ta cika makil ba masaka tainke sai kawunan biladama.kake gani birjik tamkar taron kiyasai, karan bugun tambura da busa sarewa da ke tasowa daga wani bangare dake cikin fadar ya tabbatar wa mutanen isowar sarki Urwat, ha tare da bata lokaci ba manyan fadawan sarki Urwat suka mike tare da baza manyan rigunan su , saida sarki Urwat ya zauna bisa karaga tareda Rakkus da Rukkas sannan suka koma mazaunan su dattijan fada ne suka fara tasowa daya bayan daya suna kai goshin su kasa suna gaisuwa ga sarki Urwat yayin da sarkin ke daga kansa shi kuma zagi yana amsawa.
Bayan gama yan gaishe gaishe sarki Urwat ya dubi jamaar dake gaban sa yace "" yaku jamaar birnin Bahar usuk kuyi sani cewa gobe itace ranar da zamu dauki hanyar kogon Madaful Azab a bisa aladar masarautar Bahar usuk baa barin karaga babu sarki a dalilin haka ni Urwat na yanke hukuncin barin waziri akan karaga ta dajin wannan batu daga bakin sarki Urwat sai mutanen da zasu zauna a garin suka cika da murma da farin cikin domin kuwa sun san waziri Larbus yafi sarki Urwat sauki da tausayin talakwa.
Suna cikin wannan farin ciki ne wata guguwa mai matukar yawa da kara tamkara zata rusa garin ta taso saida tazo kofar fadar sannan ta rikide ta koma bakin hayaki wanda ya gigita gaba daya jamaar dake fada.
Lokacin da hayakin yazo kusa da karagar sarki Urwat sai ya jiya ya koma dan karamin mutum wanda ke zaune kan wani karamin buzu baya sama baya kasa ya dubi sarki Urwat fusk dauke da murmushi yace yakai dirkar burnin Bahar usuk hakika ka cika jarumi abin alfaharin mutanen birnin Bahar usuk saidai inaso ka sani cewa baka da damar zuwa kogon Madaful Azab domin kuwa akan hanyar ka ta zuwa Madaful Azab akwai wata babbar alkarya mamallakiyar wannan alkarya wata Sarauniyar mayu ce mai suna Zamratul Ukub ita dai wannan mayya ta kasance gagarumar matsafiya hatsabibiya mara Imani tana da dakaru wanda yawan su ya kai dubu dari biyar gaba dayan su mayu ne Basu da abinci face naman biladama kowanne daya daga cikin su yana iya cinye mutum goma ba tare da ya koshi ba su dai wadannan mayu sun kasance gabza gabza sannan kaifin takobi ko tsinin mashi baya tasiri a jikin su balle Kuma sihirin tsafi domin kuwa idan har kayi kuskuren yin amfani da sihirin tsafi a gare su to fa ni kaina bansan irin bakar azabar da zaka fada ba, Zamratul Ukub ba zata taba bari ka wuce ta garin taba har sai kazo mata da abu guda daya wannan abun ba komai bane face jaririn aljanin dan ahalin aljanin Taranzat sudai wannan aljanu sun kai su dubu biyar suna zaune ne cikin wani kauye wanda ake kira Bazzar a kullum aljana daya na haihuwa a kauyen Bazzar itakuma jaririn da aka Haifa ranar da ka Isa kauyen Bazzar shine abinda Zamratul Ukub take son yin kalaci da shi.
Su dai wadannan aljanu sun kasance ahali guda ne sannan suna iya sadaukar da rayuwar su wajan ceton yayan su sannan suna da hadin kai matuka ba zaka samu damat daukar jariri daga gare su ba har sai kayi yaki dasu kayi nasara .
Abu na gaba shine shidai wannan kauyen akwai gidaje gufa dari a cikin sa sannan a cikin gida daya ne wannnan aljanu suke dole saika nemo gidan da suke kafin nan sai ka fafata da halittun dake kowane gida saannan Mayya Zamratul Ukub zata bukaci jaririn ne kafin cikar kwana bakwai idan ya wuce kwana bakwai jaririn yayi sanyi ba taso duk wahalar da kasa idan kaje ba zata karaba ba sannan kune zaku zama abincin ta itada dakarun ta.
Saadda mutumin yazo nan a zanjen sa sai tsuke bakin sa kmar ba shine ke magana ba sannan ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa a wajan ba.
Bacewar mutumin keda wuya sarki Urwat ya dubi jamaar dake gaban sa ya ga alamun tsoro karara a tare da su duk da shima a tsoracen yake amma haka ya bude baki yace yaku dakarun birnin Bahar usuk kuyi sani cewa a tarihin masarautar mu idan muka dada bama canzawa koda zamu rasa rayukan mudon haka gobe idan rana ta fito zamu dauki hanyar kauyen Bazzar aje a fara shiri yana fadar haka ya mike samarin sa na binsa a baya suka koma ta inda suka fito.
Tin da daddre aka shirya guziri aka Dora su akan dabbobi komai an shirya lokaci kawai ake jira, kashe dari da sassafe tawaga ta hadu mutane da aljanu wadan da zaayi tafiya dasu suka shurya babu jimawa sarki Urwat tareda yaransa suka suka fito amintaccen aljanun sarki Urwat ya baza fuka fukan sa suka hau shida yaran sa ya tashi sama ya lula yayin da ragowar aljanun suka sauki mutanen da sauran dabbobin aka nufi kauyen Bazzar.
Sun dauki kwana goma sha biyar suna tafiya idan dare yayi su sauka su yada zango su kwana da safe su tashi sun hadu abubuwa kala kala kananun dabbobi sun kashe sunyi kalaci yau ne kuma suka zo gabar karshe dajin dake kusa da kauyen bazzar, sauka sukayi cikin dajin aka kafa tantina suka yada zango da nufin gobe su tinkarin kaujen Bazzar.
A madadin sarki Urwat muna gayyatar ku shiga kauyen bazzar gobe masu zuwa su taho ykmta kuyi mana kara a shiga daku🤣🤣