← Book details Bakar Sarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 2

Sashe 1

Bakar Sarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BAƘAR SARAUTA
Complete Book 1
Page 1

By
Nana Deejah ce (mrs sharif)

Ban yarda a juya mn lttfi ba

📚 JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI📚

بسم الله الرحمن الرحيم

Birnin Bahar usuƙ birni ne da ya yayi shura a arewacin kasar sin, birnin ya shahara da manyan mayaƙa sadaukai masu kifar da gari guda a lokaci daya, sannan birnin ya shahara ta ɓangaren manyan bokaye masana ilimin sihirin tsafi.

manyan sadaukan sarakuna sun mulki birnin Bahar usuƙ na tsahon shekaru masu yawa, saidai dukan su suna rasa rayukan su ne a hanyar cimma wani buri nasu guda ɗaya wanda ya gagari
kowannen su cikawa,

ganin yadda manyan
sarakunan dake mulkin nahiyar ke rasa rayukan su yasa sarakunan baya hakuri da wannan buri .

Sarki Urwat bin Shamraz shine sarki na ashirin da biyar cikin sarakunan birnin Bahar usuƙ.

Sarki Urwat ya kasance basamuden sarki ne gabjeje mai matsanancin ƙarfin damtse tare da sani akan sihirin tsafi, sarki Urwat ya gagari manya manyan sarautun dake gefe da fefen nahiyar sakamakon tara manyan sadauki dangin mutane da aljanu da dabbobi.

birnin Bahar usuƙ ya samu babbar kariya ta yadda koda dan tsako bashida ikon shigowa cikin birnin ba tare da izinin sarki Urwat ba, ƙasashe da dama sun kawo hari birnin Bahar usuƙ amma koda mutum ƙaya baya samun damar barin birnin da ƙafarsa.

angina manyan katangun birnin da jinin manyan mayakan da suka kawo hari suka rasa rayukan su.

Dan madaidaicin ɗaki ne wanda aka ƙawata shi da zallar jauhari babu komai cikin sa kujeru guda uku ta tsakiya itace babba wacce aka sana'anta ta da ɗanyan dinare sai guda biyun dake gefe da fefen wanda basu kaita girma ba.

A kan kujerar tsakiya sarki Urwat ne sanye da ƴar shara fuskar sa a buɗe kansa babu rawani fuskar sa cike da kwariji yayin da damatsan hannun sa ke a murɗe kallo ɗaya zakayi masa kaga zallar jarumta da sadaukantaka irin na manyan sarakai.

gefe da gefen sa wasu matasa ne masu tsananin kama da juna .

A gaban kujerun wani
yamutsatstsen tsoho ne ma'abocin farin gashi mai tsaho wanda ya haɗe da dogon gemun sa, kansa a ƙasa ya fara jawabi kmar haka.

""Ya shugaba kayi sani cewa wannan tsohon burin tin daga kakan ka na biyar aka ajiye shi domin kuwa daga shekara dubu uku da dari uku da sittin zuwa lokacin da aka ajiye burin babu wanda ya taɓa tinkarar cikar wannan buri ya dawo a raye.

Kafin tsohon ya rufe baki sarki Urwat ya daka masa wata gigitacciyar tsawa wacce tasa tsohon hantsilawa ya dago daƙyar jikin sa na rawa ya ce "" ka gafarceni ya shugaba na wannan buri bakomai bane face mulkin birnin kangiwa, wanda kaf nahiyoyin mu babu wata ƙasa data kaita arziki da kuma iko, kujerar wannan birni ba kmar kowacce kujera bace, ya shugaba na kabarin sarkin aljanu ne da sarkin bokayen duniya tareda sarakan yaki guda goma shabiyu aka gina shi sannan aka sana'an ta karagar akan su, ya shugaba dalilin burin mallakar wannan birni shine duk sarkin daya mallaki wannan birni to tabbas duk wasu burane dake cikin wannan duniyar zasu kasance a ƙarƙashin ikon sa sai abnda yaso za'a zartar.

Yanzu haka shekara dubu biyu kenan ba'a ƙara samun wani sarki ko sarauniya ko wani hamshaƙin aljani ko babban bokan da ya sake hawa karagar Birnin kagiwa ba.

Bakomai yasa hakan ba kuwa face sarkin daya mallaki wanna birni na ƙarshe wani sadaukin aljani ne wato sarki Darbuza, wanda ya mallaki mutane aljanu da manyan dabbobi ya shahara a faɗin duniya yayi ƙarfin da koda tsuntsu sai yaso zai samu abinda zaici.

A lokacin sa ne duk wani boka da wani isashshen aljani saida ya kashe su ya maida sihirin tsafin kan wani kwalkwali na baar azurfa wanda yake kasancewa akan sa koda a yaushe.
Lokacin da sarki Darbuza ya tabbtar wa kansa cewa rayuwar sa ta kusa ƙarewa sai ya shirya dakaru suka ƙauki hanyar kogon Maɗaful Azab, shidai kogon Maɗaful Azab kogo ne da ta tara manyan dabbobi da aljanu, birnin yana nesa da nahiyar mu tsafiyar tsawon wata uku a ingarman doki wata shida a ƙananun dawakai, kasancewar sarki Darbuza sarkin aljanu da mutane yasa sadaukan aljanu suka kaishi cikin kwana uku,

Koda sarki Darbuza ya tsinci kansa a gaban kogon Maɗaful Azab sai ya ciro kwalkwalin dake kansa ya yanka wuyan sa da shi jinin jikin sa yayi tsartuwa ya jiƙa kwalkwalin, take jikin sa ya fara karkarwa ransa na shirin bari jikin sa, cike baƙin zafin nama ya jefa wannan kwalkwalin cikin kogon Maɗaful Azab, daga nan jikin sa ya sandare babu alamar rai a tare da shi, tin daga wannan lokaci birnin kangiwa ya kasance babu mahaluƙin da ya sake mulkar sa, badon komai ba sai don babu wanda zai iya zama akan karagar face ya je kogon Maɗaful Azab ya ɗakko kwalkwalin sarki Darbuza ya dora akan sa, kamar yadda na faɗa maka ya shugaba na tafiyar wata uku ce a ingarman doki sannan tafiya ce wacce a tarihi babu wasu hanyoyi da suke cike da azabu masifu da tashin hankali kmar wannan hanyar, sannan ya shugaba na tin daga wannan lokacin babu wani aljani dake iya tashi sama yabi hanyar saidai ya tafi da kafa ko akan dabba kaga kenan babu damar aljanu su rage tafiyar.

Sa'adda tsohon yazo nan a zancen sa sai yaja baki yayi shiru kansa a ƙasa .

Tsananin baƙin ciki da ɓacin rai ne ya ziyar ci sarki Urwat sa'adda ya gama jin labari birnin kangiwa nan take fuskar sa tayi ja iduwan sa suka furfuto kumatukan sa suka fara rawa har wani ɗaci ɗaci yake ji a bakin sa, ba tare da yace komai ba ya miƙe a fusace ya fice daga ɗakin, yayin da matasan dake tare da shi suka rufa masa baya.

COMMENT AND SHARE PLX👏🏻

BAKAR SARAUTA

P 2

NANA DEEJAH CE

JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI ALKAIRI

بسم الله الرحمن الرحيم
Cikin wani dan loko sarki Urwat ya nufa ya shigo cikin wani katafaren parlor mai girman gaske, wanda aka kawata shi da jeren silbobi a kusurwa hudun dake parlorn.
an zagaye shi da labulaye jajaye masu ratsin golden, hagu da dama na cikin parlon an jera kujeru masu zaman mutun daya, ko wane bangare guda goma sha biyu ne.

daga tsakiya dogon lallausan kilishi ne ja, a saman sa katon taburi ne na glashi wanda aka cikashi da kayan marmari tareda tambulan na lemuka kala kala.

Daga karshen dakin wata hadaddiyar kujera ce ja wacce akayi mata ado da zallar gold.

hannun sa ya goya a bayan sa ya fara zagaye a cikin daki daidai tsakiyar dakin ya tsaya ya bude tafin hannun sa ya kura masa Ido kamar mai nazarin wani abu yace "" na rantse da girman kujerar birnin kangiwa saina mallaki birnin nan koda za'a rasa rayuwan da ba zasu kirgu ba, koda dukkan nahiyar nan zata jike da jini, saina binne gawarwaki wajan gina katafariyar masarauta ta.

Zaka iya ya kai baban mu muma mun yanke shawara akan yadda zaka mulki birnin kangiwa cike izza ya juyo a nutse ya sauke idon sa akan kyawawan yaran sa guda biyu ya fadada murmushin ba tare da yace komai ba

Daya daga cikin mai suna Rukkas ya dubi sarki Urwat yace yakai abban mu kayi sani cewa zuciyoyin mu cike suke da takaicin tare da bakin cikin kasancewar mu anan bayan manyan sadaukai sun shude wanda har yanzu tarihin sadaukantakar su bai gushe ba wanda suka amsa sunan su maza ba mata ba nida dan uwa na Rakkus mun yanke shawara tafiya kogon Madaful Azab domin neman kwalkwalin sarki Darbuza ya baban mu kayi sani cewa Koda bamu dawowa zamu wanzu cikin tarihin jaruman da suka rasa rayukan su a hanyar kogon Madaful Azab wanda ba kowanne jarumai ke ita tinkarar sa ba.

Koda jin wannan batu daga bakin Rakkas sai ran sarki Urwat ya cika da alfahari da farin ciki bakin ciki dake zuciyar sa ya yaye kishin mazajen dake ransa ya kauce karfin zuciya da fatan zama sarkin kangiwa ya kara mamaye zuciyar sa.

A hankali ya fara takowa gare su ya shiga tsakiyar su ya dafa kowannen su day hannun sa ya ce "" yaku ababen alfahari ne hakika yau kun cika zuciya ta da farin cikin kun sawa zuciya ta yakini dakuma yadda da irin jarumtar da baya na ke da shi na tabbata koda bayan raina mulki na bazai gushe a wannan birnin ba saboda haka inason sanar daku cewa na shirya tsaf domin tinkarar kogon Madaful Azab a sanar da sarkin yaki ya shirya mayaka nan da kwana uku zamu kama hanya.

Lokacin da sakon sarki Urwat ya isa wa Ramwal kafafun sa ne suka fara rawa zuciyar sa ta fara tsinkewa domin shi ya jima da sanin labarin kogon Madaful Azab nan take marar sa ta fara kullewa fitsari ya fara jika masa wando, a tarihin sarkin yaki Ramwal bai taba girgiza don ganin tawagar abokan gaba ba Koda kuwa jinsun aljanu ne a tarihin birnin Bahar usuk shine sarkin yakin dake jagorantar tawagar mayakan aljanu zuwa kowane irin fafatawa shine sarkin yakin dake dakawa aljanu gumba a hannu kaf mutane da aljanun dake zagaye da birnin Bahar usuk suna tsoron gabza yaki da birnin ne saboda sarkin yaki Ramwal shine jarumin da yake saka kansa gaba cikin mayaka saidai kaga kawuna suna zuba a kasa kamar ana sassabe a gona ba tare da an samu wanda ke iya lakutar koda jikin sa ba zafin nama garshi tamkar wanda aka cudanya naman sa da zaki duk sadaukantaka irin ta sarki Urwat bai kai sarkin yaki Ramwal ba saidai ya fishi kwarijini da dabarun sarrafa makiyi.

Jiki a sanyaye sarkin yaki Ramwal ya koma gidan sa cikin zuciyar sa yana lissafa adadin kwanakin da suka rage wa rayuwar sa idanun sa ne suka furfuto sukayi ja tamkar ruwan hawaye zasu zuba daga gare su saidai wannan ba halin jaruma Ramwal bane .
Chapter 1 · 0% Book details