← Book details Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 3

Part din Mama ta shiga suka kule a master bedroom dinta.

Auren Huce Haushi Part 2 Complete Hausa Novel · about 202 min read

Batafi awa daya da zuwa ba, wasu Mata suka shigo gidan lokacin Ammah tana bangaren Abba.
Zilai Mai aik cei ta leko tana fadin "uwar dakina anyi baki kuwa ko Ammah zaki yiwa magana Naga bakin nata be"
Mayafi karami ta Dora a saman gashinta da tayi parking dinsa har wajen kugunta Yana reto Baki sidik dashi jikin Nan nata Kamar ka taba jini fito.
Lekowa tayi tana musu sannu da zuwa tare da gaishe su tana fadar "ku shigo daga ciki Bari na Kira Ammar".
Ta fada tana zura silifar a kafarta.
Daya daga cikin su ukun ne ta tabe Baki ta kauda Kai tana fadar "kirawo ta tazo ba sai mun shiga ba tunda ba Zama mukazo ba"
Ita dai Zahra gaba tayi yayin da su Zilai masu aiki suka zuba musu idanu suna kallon kallo ya junansu Dan daga Jin lafazinsu sun San ba abin Arziki ne ya kawosu ba.
Kafin Ammah ta fito daga bangaren Abba sahura Daya Mai aikinta ta leka ta fadawa Mama anyi baki. Da ita da Asaben suka fito Asaben na fadin "lale barhabin kushigo Mana kun tsaya daga wajen"
Wata ce daga cikinsu Bata farkon da tayi maganar ba tace "A"a Hajiya ba Zama mukazo ba munzo ne mu karbi kayan lefen da muka kawo na Sahal yace baya yi akai kasuwa".
Lafazin da Ya yiwa Ammah sallama kenan lokacin data fito Zahra na biye da ita.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"
Abinda Ammah ta fada kenan a zuciyar ta Nan da Nan wani jibi ya taso Mata.
Salatin Mama da Asabe ne ya fito da Alhajin daga part dinsa yayin da su Zilai sukayi cirko-cirko duk wuta ta dauke musu Dan maganar tasu ba karamin razani tasa a zukatansu ba.
A hankali ya karaso kusa da Ammah Yana tambayar meke faruwa ne kafin tayi magana Mama tayi tsagal tana fadin "wane irin cin mutunci ne Alhaji ba laifi tsaye bana zaune zasuzo suce a Basu lefensu Wai auren amfasa".
Ta karasa fada tana fashewa da kuka tana maganganu, ita kuwa Ammah ba abinda take sai ambaton Allah yayin da Zahra ta nemi gefen inda aka shuka filawoyi ya zauna Dan ji tayi Nan da Nan jiri Yana nema kayar da ita, itama bakinta ba abinda yake sai ambaton Allah.
Kallo Daya Alhaji Jafar yayiwa Baki ya kawar da kansa Dan da alama da rashin mutunci suka shigo gidan. Gyaran murya yayi kafin yace "Masha Allah munji sakonku Amma Dan Allah ku koma kuce musu zuwa anjima inshallah Allahu za'a dawo da duk wani Abu daya kasance nasu ne har sadakin da suka kawo Allah yasa hakan yafi Alkhairi".
Yana Gama fadar haka ya juya dakinsa ya barsu a Nan a teaye, Dan dukkansu ba karamin kwarjini yayi musu ba.
Ammah part dinta ta nufa duk kwakwar mutum baze taba Gane Yanayin da take ciki ba.Dan Allah yayi Mata wata irin zuciya Mai iya danne bacin Rai da wuya ka Gane fushinta tana da hadiye fushi sosai, dakin suka bita suna Bata magana Mama sai sharbe take tana Dan Allah wannan wane irin cin zarafi ne da tazarce ace saida komai ya kankama sannan za'a bullo da wannan cin zatafin dan a wulakanta yarinya har a ringa yi Mata wani gani -gani aga Kamar wani Abu tayi yasa aka fasa".
Sai lokacin Ammah tayi magana tana fadin "ba komai Mama Daman can haka Allah ya nufa ba mijinta bane Kuma maganar mutane su ringa ganin Kamar wani Abu marar kyau ne yasa aka fasa na barsu da Allah yayi Mani maganin komai, ba komai haka Allah ya nufa rubutaccen Al'amarine baya goguwa".
Tana Gama fadar haka ta wuce bedroom dinta sun jima a falon suna tattaunawa kafin su koma dakin mamar su Zilai kuma suka nufi in da Zahra tace zaune suka dinga Bata magana duk da Bata want rude ba a nitsenta take.
Duk wannan kwamacalar da akayi su Hameeda da Salma basa Nan sunje Aiken Mama.
Tunda Alhaji Jafar ya koma daki ya kasa zaune ya kasa tsaye Bai taba zaton karamar magana daga gida irin Honorable ba Amma ya hanasu kayan ne Dan ya tabbatar da daga Ina maganar take shin da sanin uban yaron da waliyayansa ko Babu Dan yanda sukayi komai cikin girma da mutunci ya kamata ko baza'ayi auren ba to a rabu cikin mutunta juna.
Su malam Bukar da Yayan Alhajin Wanda suke 'yan maza Alhajin ya Samu da maganar basuyi kasa a Gwiwa ba zuka nufi gurin waliyyan Sahal sai dai maganar haka take Dan sun tsame ma hannunsu daga lamarin tunda iyayensa Basu da lissafi, Wai yaron ne yace musu shi baze iya auren Zahrar ba yanzu ba wadda ya tsana kamarta duk duniya".
Lokacin da suka dawowa da Alhajin wannan labarin ransa yayi matukar baci, a ranar aka maida duk wani Abu da yake mallakinsu ne.
Sai dare Abban ya Samu kebewa da Ammah in da ya ringa tausarta da kalamai masu Dadi har ta Samu ta Samu nutsuwa Amma fa kasa kwana tayi a dakin nasa.
Lokacin data dawo daki Zahra Bata tafi nasu bangaren ba tana dakin Amma a kan gadon tayi rigingine idanuta a rife hawaye na zurarowa daga gefen idon wani Abu yake Mata yukuki a zuciyar ta.
Har Ammah ta bude kofa zahra Bata sani ba saida ta zauna a kiss da ita taji shashhshekar kukanta kasa -kasa.
"Tashi zaune magana zamuyi".
Daga sama taji maganar Sam bata San Ammar ta shigo ba.
Ba musu ta tashi zaunen tana koge fuskarta da tayi wajir.
"Meye dalilin da Sahal ya fasa Aurenki ko ya sanki 'ya mace ne".
Cikin tashin hankali marar misaltuwa Zahra ta dago ta kalli Ammah kafin ta fasa kukan da take dannewa tana na zuci. Kai ta shiga girgizawa tana wani irin numfashi nKamar wadda zata shide.
Kafin Allah ya batan ikon bude bakinta ta magantu. "Wallahi Ammah ban taba abinda kike tuhumata ba Koda wasa wallahi zan rantse Miki da Alur'an a bani zanyi Alwala in ratse, idan na taba Zina Ammah Allah ya haramtamin shiga Aljannarsa ranar Alkiyama"
Ta fada tana wani irin kuka Mai taba zuciyar Mai sauraro.
"Shitttt.....kada na Kara Jin wata magana makaranciyar wannan daga bakin ki. Ba zarginki nakeyi ba na kasa samun nutusawa ne tun lokacin da sabbin halayensa suka Fara fitowa, nake cikin zulumi da taraddadi saboda sanin yanda rayuwa ta Zama abinda ta zama, ba komai kansa yayiwa ke kuma Allah yayi Miki Albarka ya bakin Wanda yafi Sahal".
Bata iya amsawa a fill ba sai a zuciyar ta.
Tun bayan faruwar lamarin Zahra ke cikin damuwa Dan ma Haneeda tana tausarta da kalamai na kwantar da hankali. Ammah ta Kira su Ummee ta fada musu komai sun so kwarai zahrar taje Amma Alhaji Jafar yayi uwa yayi makarb'iya akan suzuzo idan hankali ya kwanta, da haka suka bar zancen.
A Dan tsakanain ne Aunty Hasana tazo, sun Sha jajantawa sosai da Ammah itama sai da ta tsare zahra da tambayoyi kala kala, daga karshe ta Kare da nasiha Mai tsoratarwa sosai.
Lokacin da zata koma Jos ta nemi zata tafi da Zahra Abban bai Hana ba Yana ganin idan tayi nisa da garin zatafi Samun kwanciyar hankali.
Zamanta a Jos Mai Dadi ne Dan daga baya ma fafutukar nemar Mata admission mijin Aunty Hasanar ya Fara ba'a samu wadda ake so ba, sai diploma ya nemar Mata a wata private school ta Fara computer science.
Hankalinta ya kwanta sosai ta cire soyayya daga zuciyar ta Sam taqi ba kowa fuska akan soyayya duk da yanda ake kawo Mata Rida.
Ranar wata litinin sun Gama lectures dinsu na safe suna zaune da wata course mate dinta 'yar kabilar Tiv suna wani Assignment jininsu ya hadu da jannifer sosai Dan har gidan Aunty Hasana tana zuwa idan zasuyi wani aikin.
Bayan sun Gama ne suka nufe caf'e na cikin makarantar a cire musu hard copy din aikin suka tarar da cinkoson mutane dole tasa suka fito waje ayi musu.
Har sun Gama sun fito suna niyyar tsallaka titi ne wata mota Mai azabar kyau ta tsaya dai dai inda suke tsaye. A hankali na ciki ya sauke tinted glass din motar, wani guy ne da gani hutu ya ratsa shi sosai, murmushi yayi musu idonsa na kan zahra
Yana fadin "sannunki"
Jannifer ce to amsa masa Dan tana Jin hausa Kamar jakar kano.
"Yauwa sannunka" ta fada.
Kofar ya bude ya fito Yana sanye da kananun Kaya,fari tas dashi kamar irin ruwa biyu din Nan half cast Dan sumarsa a nannade take kamar irin ta buzaye din Nan.
Cikin kwarewa da yadda da Kai kalli jannifer Yana fadar "Naga kawarki ne inso da fatan zakiyi min campaign".
Dariya tayi tana kallon Zahra wadda tayi kicin kicin da fuska Kamar zatace wayyo Allah.
"Gaskiya na tafi tunda Baki da aikin Yi ke saiki zauna".
Zahra ta fada tana nufar titi ganin an Sami space din tsallawa.
Jannifer da Dan jima dashi kafin ta shigo cikin makarantar, Koda ta shigo Bata yi Mata maganar komai ba har suka Gama lacture dinsu suka tashi. Direban su Aunty Hasana ya dauke su ya ajiye jannifer a hanya kasancewar su zahra sun gaba dasu Amma hanyarsu daya sau da Daman sukan tafi tare ranar da jannifer Bata zuwa shagonsu.
Ranar Saturday misalin hudu da rabi haka su zahra da yaran Aunty suna compound din gidan tana Dora Yara kan lilo marry go round suna Wasa kusan duk weekend a Nan suke hutawa da yamma tunda islamiyyar safe suke zuwa a weekend.
Mai gadi ne ya nufo gurin da suke Yana fadin Zahara'u ki fadawa yallabai Yana da bako a waje".
Auntyn ta fadawa Abban su Faruq Yana da bako inji Mai gadi.
Lokacin daya fito yayi mamakin da baiga bakon ba ya nufi gate Yana tambayar Mai gadi, shine yace "ni ne na hana ya shigo tunda yace bakasan da zuwansa ba bilhasal ma yace baka sanshi ba"
Kofar Mai gadin ya bude masa ya nufi gurin da motar take yayin da shi kuma na cikin ya fito. Da gaske baisan yaron ba, hannu ya bashi sukayi musahiha sai Kuma sukayi shiru Ya Aliyun ne mijin Aunty Hasanar yace Masa "ko kaine maisallama Dani?".
"Eh nine"sai Kuma ya danyi shiru.
Ya Aliyun ne yace "my friend pls talk feel free with me".
Nan yayi Masa bayanin yaga Zahra ne Yana sonta shine ya biyota gida, ya fada masa sunansa MUNEEB mahaifansa Kuma Alhaji Salman Mai fata. Kallonsa ya Aliyu ya karayi yayi mamakin yanda d'a Kamar na Alhaji Salman Mai fata yake da irin wannan tarbiyya ganin yanda mahaifansa yake da mahaukanta kudi Kuma yasan 'ya'yansa sosai Amma da yawansu gata yasa sun lalace basa ganin kan mutane da gashi.
Ya Aliyun yaji dadi sosai ya Kuma bashi damar zuwa gurin Zahrar sannan ya Dan fada Masa wacece Zahrar a gurinsa.
Lokacin da ya Aliyun ya koma bayani ya yiwa Aunty Hasana na abinda ya faru itama ta bada goyon baya tasan ko yanzu Zahra tayi gaba Allah ya Bata Wanda yafi Sahal Dan ba karya ba hadi a tafiyar.
Da dare Aunty ta Samu zahra da maganar da farko tuburewa tayi akan ita Bata so saida Aunty ta fito Mata ta bayan gida sannan ta fashimci abinda Auntyn take son ta Gane.
Washe gari Aunty har da ita aka hadawa MUNEEB abin tarba, Zahra ta Dade tana mamakin yanda akayi yasan gidan su Amma data Zama very curious sai ta gano duk yanda akayi jannifer ce ta bashi address dinta. Yau ma da yamma yazo, falon Ya Aliyu aka bude Masa yayin da Mai aikin Aunty shema'u ta Kai Masa abin tarba.
Wata straight gown ta saka ta atamfa glitter Mai ruwan peach colour sai madaidaici gyale kalar lemon green irin touching din jikin atamfar sai takalmi shima lemon green din plat Mai kyau. Bata daura dankwalin kayan ba. Ta fesa turenta Amber oud gold, tun kafin ta karaso kamshin ta ya fada Masa zuwanta, kofar ya zubawa idanu ai lokacin data shigo da sallama Saida ya Dan samu shock na wucin gadi Ashe ranar ba inishin Zahrar ya gani ba yanzu ne yaga zahirinta, a kasa ta zauna kan carpet tana gaishe shi kanta Yana kallon kasa. Nan ya gabatar Mata da kansa da abinda ya kawo na son aurenta, bai matsa Mata na lallai sai yaji ra'ayinta a sannan ba shima bai jima ba ya tafi, bayan ta shigo ne Mai gadi yayi knocking a kofar falon shema'u ta bude manyan ledoji ne ya Mika Mata guda biyu yace a bawa Zahara'u inji bakonta.
Tun daga lokacin Koda yaushe Muneeb yana hanyar gurin Zahra,r tun tana dari dari dashi har ta sake, shi mutum ne Mai saurin shiga Rai Yana da wasu Qualities da zasusa asoshi.
Kafin su rufe wata biyu sunyi wata irin shakuwa ta ban mamaki duk Wanda ya kwana ya tashi a family din Mubeen yasan da zaman Zahra haka itama nata sun San Muneeb Dan har Azare yaje ya gaishe su da ashirin bama sha tarabta Arziki ba,har Saida Abban su yayi Masa fada sosai akan kada ya Kara musu haka in dai Yana son su Shirya.
Sun daf da Gama diploma dinsu Iyayen Muneeb sukayi maganar aure, ba Bata lokaci aka saka Rana ba'a wani ja lokaci ba Mai tsawo ba, abu kama-kama shima Kamar na baya abun ya shashence ba wani cikakken dalili haka Nan Rana tsaka Muneeb yace ya fasa akayi juyin duniyar Nan yace shifa aure ba dai da Zahra ba komai za'ayi, dole aka hakura Dan shi cewa yayi har kayan ya bar Mata saidai abinda iyayenta Basu amince ba kenan.
Fadin halin da zahra da su Ammah suka shiga bazai misaltu ba, Dan hankalinsu yanzu yafi tashi fiye da wancan lokacin.
Ammah taso kwarai zahrar ta koma Azare Amman Maman Ya Aliyu ta roki Alfarmar zata Kai zahra gurin masu Islamic chemist a gani ko namijin Aljani ne ya aureta.
Ammah ba tayi musu ba sai godiya tayi sosai, sunje harda Aunty Hasana anyiwa Zahra tambayoyi ba alamar Aljani a jikinta sai dai sun fada musu da alamar sihiri a tare da ita Amma ba sosai ba, Nan suka bada magunguna Hajiyar ta biya suka dawo gida.
Jannifer ma tayi bakin cikin abinda ya faru taso Zahra ta Bata dama taje garinsu ayi mata wani Abu akan idan ma wani ne yake lalata lamarin auren zega abinda ze same shi. Nunawa tayi Bata so ita haka Allah ya tsara Mata wannan qaddarorin Kuma ba makawa sai sun sameta.
A haka har suka Gama diploma dinsu kafin Aunty Hasana ta mayar da Zahra Azare.
Haha rayuwa taci gaba da gudana, duk wani buri akan aure Zahra ta cire shi Bata kula kowa duk iya nacin mutum Bai isheta kallo ba, wani lokacin har fada suke da Hameeda akan rashin kula samari sai dai sau da yawa tana Mata uzuri akan irin yanda fasuwar aure take walagigi da ita.
Zama ya Mika lokacin har anyi wurin wata Tara da fasa aurenta da Muneeb. Wani yammaci suna zaune a bayan part din Ammah ita da Hameeda da Mujiba data shigo musu yawan yamma suna hira Kiran ya Abdul Hakeem ya shigo wayar Hameeda Yana tambayar suna ina ne ya shigo Bai gansu ba.
Inda suke ta fada Masa suna niyyar tashi ya zagayo bayan, a tare suka gaishe dashi ya amsa Yana gaisuwar tasu yana fadin "Congratulations"
"For what Yaya?" cewar Zahra.
Irin Brown din envelope din Nan babba ya Mika Mata Admissions letters ne guda biyu a ciki na Salma da Hameeda duk sun Sami gurbin karata a federal University Dutse jigawa state (F.U.D).
Cikin murna ta rungume Hameeda tana fadin "congratulations sister".
Kafin ta sake ta tana Mika Mata takardun, ai tana arba da wannan abin Arziki ta Diba a guje tana fadin"thank you Yaya Allah ya saka maka da Alkhairi".
Bayan ta wuce ne zahra ma ta Kara Masa godiya sosai.
Kujerar da Hameeda ta tashi ya janyo ya zauna alamun dake nuna magana Mai mahimmanci zeyi da ita.
Ganin haka yasa Mujiba tashi tana fadin "Yaya sai anjima".
"Dawo ki zauna ba Zama zanyi ba.magana zan fada Mata kawai"
A takure ta koma ta zauna.
Kan Zahra ya maida kallonsa "kina jina?" Kai ta gyada Masa alamar eh.
"Good" ya fada.
"Ina ga Nan da one month ko three weeks kema Zaki wuce Zuwa Turkey daga can Kuma idan komai ya daidaita Zaki wuce syprus inda Zaki hada a degree dinki, idan kin tuna Kamar two months da suka wuce ai na karbi komai naki to Mama Hanifa ce ta bukata a tura Mata a she makarantar zata nemar Miki taso a Samu a Nan turkey din to ba'a samu ba, ita kuma Bata son a Kara Bata lokaci, shine ta yiwa danta magana tunda a can yake aiki da ofishin jakadancin turkiyya na kasar Kuma ma Nan ne kawai Mama Hanifar ke ganin yafi kusa da istanbul din".
Ba Zahra kawai ba hatta Mujiba tayi murna kwarai da gaske gatan da za'a yiwa Zahra kenan a irin wannan lokacin na a rabata da kasar gaba daya Kota Samu peace of mind.
Godiya ta ringa yiwa ya Abdul Hakeem din harda 'yan hawayenta na Dadi.
Gashi Ammah Bata Nan taje Jimeta gurin biki, taso tana Nan ta kwanta a jikinta suyi sharing din farin cikin. Har ya Abdul Hakeem din ya kai kwanar da ze fita ya juyo Yana fadin "don't talk to anyone, keep silent pls, nasan Mujiba Bata da problem shi yasa na fada a gabanta".
Yasa Kai ya wuce.
Kallon junan su sukayi suna son banbance maganar Ya Abdul Hakeem.
AUREN HUCE HAUSHI

MAMAN FATIMAH
PAGE TWELVE (12)
__________A cikin qanqanin lokaci aka Gama yiwa su Hameeda shirye - shiryen tafiya makaranta Dan sau biyu suna Zuwa jigawar akan registration din. Sai wannan ciccira kai salma keyi tana sakin maganganu bare idan suna dakinsu su kadai ta dinga fadin magana kenan, ko ci kanki zahra Bata ce Mata sai ma wani lokacin Hameeda ke kwabawa Nan da Nan Kuma su hau sama da ita.
Ranar da zasu tafi harda ZAHRA a 'yan rakiyar, Mama ma taso zuwa Abba ne ya hanata ya Kama fadan me zatayo.
Har hostel Zahra ta rakasu Lokacin da zasu taho ne Hameeda ta Fara share hawaye itama zahra ta Kama, Saida ya Hamza yayi musu Jan Ido suka daina kukan, Yayin da Ya Abdul Hakeem yake musu dariya Yana fadar "Banda tsabar shagwaba ta lalacewa har wani kuka kuke Kamar wasu 'yan J's one".
Wani kallo ya ai kawa zahra na Baki Fara kuka ba.sai kin ganki a tsakiyar masu jajayen kunne tukunna Dan ma dai kema samman kalne ya gada a zuciyar sa.
Sai bayan magariba suka dawo gidan.
Ba'a fi sati biyu da tafiyar su Hameeda ba visa din su Zahra ta fito ita da Abdul Hakeem.
Sai ana ya gobe zasu tafi Ammah ta fadawa Mama. Ai Kuma tayi korafin abin Dan har Alhajn ta fadawa yace shima jiya yake Jin labarin tunda Saida komai ya kankama sannan suka Kira suka fada Masa Dan kada ya Hana.
Da safe Bala dureba ta dauke sai kano inda zasu tashi.
Satin Abdul Hakeem hudu a can Dan Bai taho ba Saida ya raka Zahra har syprus din a gabansa komai ya kammala ranar da ze tafi Zahra tayi kuka Kamar idonta ze fita sai a sannan taga ba karamar wauta tayi ba data yarda da wannan karatun, dadin ta daya da uncle Haisam a kasar ko banza tana da gurin zuwa a debe Mata kewar gida.
Ta Fara karatu cikin nasara Bata da wata matsala ta zahiri saidai sau da yawa tana shiga dogon tunani akan al'amuranta ta rasa Gane daga Ina ne ake samun irin wannan akasin? matsalar dai iri daya ce, Kuma salon tafiyar iri daya ce sai Dan banbancin da baza'a rasa ba.
Suna yawan waya dasu Ammah da mutanen Jordan, lokacin data Kira Hameeda mita ta ringa yi Mata akan tana boye Mata wani Abu tunda gashi Saida ta bar kasar kana ta Kira ta. Da kyar ta fashimtar da ita abun ne yazo da gaggawa itama Bata sani ba Saida komai ya Zama ready, Kuma tayi ta try din ta sameta Bata Samu ba lokacin ana fama da matsalar network a area dinsu.
Zahra najin dadin Zama a kasar duk karshen sati a gidan uncle Haisam take yin weekend din ta, sai Monday da safe motar Embassy take dawo da ita.
Tsakanin syprus science University din wadda take kyrenia city a arewacin syrups din da capital city din dake Nicosia tafiyar kilometers talatin ne, kawai daga Baya ma da uncle din cewa yayi ta baro cikin makarantar ta dawo gidansa kawai da Zama sai a ringa kaita kullum itace taqi tana ganin Kamar abun da wahala yau da gobe sai Allah daga nesa nesa dai.
Yau ma Monday da wuri motar Embassy din ta kawo ta, tayi gaba da wasu daliban zuwa mabanbantan makarantu inda suke karatunsu.Ganin da saura Kamar awa aya da rabi kafin su shiga lectures yasa ta wuce hostel Dan ta aje kayan da tazo dasu.
Tana cikin tafiya tazo gota wani hostel Kamar a mafarki sai taji Kamar ana hausa a dakin abin ya Bata mamaki tayi Kamar ta koma ta duba sai dai tayi gaba tunda bin kwakwkwafi haramun ne.
Lokacin da suka Gama lectures din Bata koma hostel ba, karatu suka zauna sunayi da wata course mate dinta 'yar kasar Lebanon Asseyeh tasu tazo daya sosai saboda itama akwai nacin karatu ga Kuma kwanyar Allah ya hore itama, uwa uba ga rikon addini tunda su dai kasar sai a hankali kawai culture din ta rinjayi addinin, Dan wasu Ma sai kaga suna sallah zaka Gane musulmi ne.
Yamma likis su Zahra suka nufi hostel, haka nan Zahra taji tana son karabi ta wurin inda taji ana magana da Hausar nan, can ta nufa bayan sun rabu da Aseeyeh.
Very lockly kuwa tayi Dace da wata daga ciki ta fito tana waya bahaushiya sosai.A shape ce a jikinta ta atamfa sai karamin hijabi a jikinta da alama Kamar fita zatayi.Dan tsayawa zahra tayi har ta karasa wayar, cikin nuna zallar farin ciki zahra ta nufeta tayi Mata sallama.
Da sauri ta juyo Jin an Mata magana da Hausa cikakkiya.
"Wa'alaiki Salam" yarinyar ta amsa Mata tana kallon zahrar da murmushi itama a fuskarta.
"Masha Allah wallahi naji dadin ganinki kema daga Nigeria kike".
Zahra ta tambaye ta.
"Eh daga Nigeria muke muna da Dan yawa zamu Kai goma".
Mamaki ne ya Kama zahra ganin Bata taba ganinsu ba Koda wasa.
"Ikon Allah! Amman dai baku Dade ba ko?"
Kai ta gyada "Mata gaskiya Kam ai ba school daya muke ba mu a Nan mu hudu ne, sauran suna different Universities ne on transfer mukazo nan daga Sudan tunda can rikici ya d'ai d'aita Qasar. Zo mu shiga ciki ki gaisa da sisters Dina kafin na dawo zan fita na samo Ko fizza ne yau bamuyi girki ba".
Ta fada tana juyawa ciki, bayan ta zahra tabi suka nufi ciki.
"Khadijah ! Fatima,! Sajida! Kuna Ina ku fito gashi mun Samu qaruwa".
Kowacce barin abinda take tayi ta nufo kofar tana fadin "Anisa menene?".
Ai kafin tayi magana Zahra tayi Arba da sajida Musa, sajidar ta ta FGGC KAZAURE.
Cikin wani irin farin ciki suka rungume juna Zahra sai kuka Dan wani abune da Bata taba zata ba robonta da sajidar tun suna cikin bala'in Sudan kafin wayar sajidar ta salwanta shi kenan suka daina Jin juma Amma kullum zahra da fargaba take kwana har zuwa lokacin da ta Samu labarin dawowar su sajidar a bakin Maryam Suraj wata kawarsu.
Kallo saiya koma sama Wai shaho ya dauki giwa ita Mai kawo bakuwa sai duk suka Zama 'yan kallo.
Hannun zahra sajidar ta Kama ta nufi bed in ta da ita tana fadin "wannan wace irin ranar farin ciki ce bestie wallahi ranar nan tana daga cikin ranekun da bazan taba mantawa dasu ba cikin tarishin zamana a syprus, pls bestie talk ya akayi haka ta faru Dan Allah kece ko gizo idona ya
ke mini ne Dan Allah kiyi magana".
Ita dai zahra ba baka sai kunne, ai ita nata mamakin yafi na sajidar sau dari idan da Wanda Allah ya yiwa gyadar dogo ai ita ce, ba zato ba tsammani Allah yayi Mata irin wannan suturar bama 'yan Nigeria ba A'a aminiyar ta sukutun ya kawo Mata kasar, ba abinda zata cewa mahalicci sai godiya take a Nan tayin sujudushshukur ga Allah. Sai da ta goge hawayenta sannan ta Samu damar magana suka gaisa da sauran yayin da Anisar ta cire hijabin tana fadin "Ai Kuma saidai kowa ya hakura da cin fizzar Dan na fasa fitar kawai ayi abinci tunda Naga bakuwar tamu ce ko sister" ta fada tana kallon sajida.
"Kwarai kuwa ai dukkanku kowa ya kwana da sanin Zahra Muhammad sani ko?".
Gaba daya suka zubawa Zahra idanu suna fadin sosai ma kuwa, niba har gaisawa munayi ba some times idan Kuna vedio call lokacin muna Sudan" inji Khadijah.
"To ai ita ce gata a gabanki zahiri"
Khadijah ta Dade tana mamakin abun ita sai taga Kamar canza Zahra akayi tasan dai yesss ba karya zahra Mai kyauce na a bugi kirji a fada, amma sai taga wannan Kamar ma Bata taba hada dangantaka da 9ja tamu ba, komai nata classic ne.
Nan suka baje hajar hirar yaushe gamo, har kusan karfe goma na agogon kasar suna tare anan su sajida suka fada Mata gwamnatin tarayya ce ta dawo dasu Nan tunda suna under scholarship ne shine aka rarrabasu kasa kasa su Allah yasa suka shigo cikin daliban da aka kawo Nan din.
Har daki suka raka Zahra a Nan ta Basu fizzar tunda Daman tazo da ita daga gidan uncle Nan ma sun jima kafin su koma.
Ai tun daga ranar wata nutsuwa da kwanciyar hankali suka Samu kyakykyawan muhalli a zuciyar Zahra, haka itama sajidar duk da Daman ita tana da masu dauke Mata kewar gida, Suma su sajidar sau da yawa suna bin Zahra a wasu weekend din zuwa gidan uncle Haisam din Amma su basa kwana duk da irin nacin da zahrar ke musu.
A haka karatunsu ya Mika har sukayi exams, Mama Hanifa taso Zahra taje Mata tayi hutu Amma Haisam yace tayi hakuri sai hutun karshe session.
A haka suka Kare hutunsu suka Dora da karatu, ba Sajida ba hatta su Khadijah suna Jin dadin Zama da zahra gashi Sam abin duniya Bai rufe Mata ido ba, Dan ta ko'ina kudi ne ke sauka a Account din ta ba daga 9ja din ba, ba daga Jordan ba, ba daga turkey ba, kowa kokarin farantawa zahra yake zuwa lokacin tayi wani irin mahaukacin kyau na ban mamaki ga wayewa da wayon zaman duniya ta Kara Zama 'yar gayu Kamar me Dan ba karya matar Uncle Haisam Yar gayu ce sosai kamar Auntyn ta Hasana tasan yanda ake tattalin jiki matuka.
Har zuwa lokacin ba ruwan Zahra da saurayi bil hasal ko aboki namiji Bata dashi, akwai wani Dan Syria Omer yaso Zahra Kamar kaddara Amma ta shafawa idanunta toka tace ba wannan maganar yace to su Zama friends Nan ma tace lah lah.
Dole ya hakura saindai duk inda zasu hadu sai yayi Mata magana idan abu ta saya duk yawan kudin shi ze biya.
Lokacin hutun karshen shekara Zahra taso zuwa Nigeria tunda taga su sajida nata Shirin tafiya, ta kwallafa Rai sosai akan zuwan Amman sai Ammah ta hanata zuwan tace taje Jordan idan hutun ya kusa karewa ta dawo Nan gurin Mama Hanifa ta karasa Abdul Hakeem zezo ya ganta. Ba haka taso ba da har tayi niyyar Kiran Abban ta fada Masa sai Kuma tayi tunanin kada Ammah tace ta Kai Kara dole ta hakura tunda Bata San nufin Ammah din ba data hanata zuwan.
Taji dadin zuwa Jordan din sosai, dan Ummee na Shirin zuwa Saudi Arabia ne ma zuwan Zahrar ne ya kawo Mata tsaiko, tare suka tafi bayan ta huta, a can suka tarar da Aunty Nawwara wadda taje zuwa na musamman tunda lokacin ana daf da bikin aurenta inda za'a kaita Bagdad (Iraq).
Sunyi sati daya zuwa suka nufi makka sukayi Umara, sosai Zahra ta mayar da hankali gurin addu'a akan matsalolinta na yanda rayuwa ke walankekuwa da ita Bata rasa komai ba Amma aure Yana neman yafi karfinta dah kudi ko kyau ke sawa mace ta auru tasan da yanzu ba wannan zancen ake ba, sai dai tasan duk Dan Adam baya wuce tasa kaddarar sai dai neman sauki gurin Allah s.w.a.
Madina suka koma da suka Gama umarar,basu Dade ba suka koma Jordan.
Lokacin da hutunsu ya taho garewa zahra ta koma syprus. Gidan uncle ta Fara Zama kafin daliban su dawo tunda ana saura one week ayi resuming ta dawo. Karatu suke ka'in da na'in ba Kama hannun yaro, amincin ta da Sajida ya Kara karfi tamkar uwa daya uba daya suke, Dan lokacin da sukaje hutu sajidar har Azare taje ta gaishe da Ammah ta karbowa Zahra sako.
Duk lokacin da za'a yaye dalibai makarantar tana hada gagarimin taro tana baiwa best student na kowane department award.
A karshe semester din ne aka hada taron Wanda ya Tara al'umma daban daban daga kasashen duniya masu Taya 'ya'yan su da 'yan uwa murnar gama karatu, celebration ne ake na gasken gaske, su zahra dai suna kallon abubuwan tunda wannan shine na farko da akayi suna Nan lokacin da akazo bada award ne ba zato ba tsammani aka Kira zahra Muhammad sani daga Nigeria aka Bata award na overall a department dinsu akan kowane subject.
Wayyo murna gurinsu ba'a magana Dan Zahra kuwa har mukan Dadi tayi data duba taga yawan daliban da suke a department din nasu Amma ace ita ta karbi best ai abin murna ne Kam. Sun Sha hotuna da mutanen mu na africa more especially 'yan Nigeria.
A ranar Zahra tayi takaicin karatun nesa da ace a gida ne da Abbanta ko Ammah ko wani daga cikin yayinta zata danqawa kyautar su sharing happiness din tare Amma Nan kuwa fa sai da friends da wasu tsirarun mutane Wanda ma ba saninsu tayi ba sukayi farin cikin, ga Uncle Haisam ma a matarsa da yaran duka sun tafi turkey.
Sai ta waya sukayi murnarsu da jama'ar gida ta tura musu hoton award din ta waya hotunan da suka dauka.
-----------------
AZAREN KATAGUM
Alhaji Jafar ne da Malam Bukar sai Habibu dan kanwar malam Bukar dake aure a suleja malam din yake rikonsa tun yana karami mahaifinsa ya rabu da mahaifiyar sa acan gida Yobe da tayi auren a suleja din ne baban Habibun yace baza'a tafi Masa da yaro gidan wani ba yayi agolanci, rigima sosai aka kwasa da shi saboda itama tace bazata bar danta a inda za'a kashe Mata shi ba. Shine mafarin malam din ya dauko shi tunda ba wasu 'ya'ya yake dasu da yawa ba, a hannun malam ya girma shi yayi karatun boko har matakin HND.
Jikamshi malumfashj zasuje Daurin Auren 'yar abokin Alhaji Jafar din sannan zasu shiga Jikamshi dubiyar malamin malam Bukar din daya kwanta kwanakin baya a Asibitin Ibadan nisa yasa shi majiyyacin ya Hana masu zuwa dubiya sai yanzu daya dawo gida ne malam zeyi amfani da wannan damar yaje dubiyar.
Tafiya ce mikakkiya Dan tsakanin Azare da malumfashi tafiya ce ba kadan ba Dan haka sukayi sakko Habibun ne ze tukasu malam Bala anyi Masa Rashi acen garinsu Itas gadau Yana can.
Cikin ikon Allah Basu rasa Daurin auren ba Dan Sha buying Mai kyau suna cikin garin malumfashin.
Basu Bata lokaci ba suka dauko hanya sun biya jikamshin sun duba malamin Alhaji yayi masa kyau ta girma.
Suka dauki hanya sosai Alhaji Jafar ya yaba da tukin Habib Dan baiyi zaton ya kware irin haka ba.
Sunzo kachako lokacin sallar la'asar yayi guri suka Sami inda akayi wani Dan masallaci dan matafiya.
Suka firfito Dan gabatar da sallar, malam ne ya Fara gewayawa yayi dahara sannan Shima Alhajin yayo sukayi alwala suka shiga sallah Saida suka Gama suka fito sannan Habib Shima ya nufi gurin you daharar Amma shi saiya nufi wani bangaren daban, Bai jima da tafiya ba sai gashi da sauri Yana Kiran" Baba malam! Kuzo ku gani". Da sauri suka nufi inda yake harma da wani mutum da suka Sami a gurin Kamar Mai kula da gurin ne Dan daga gefe da 'yar tiredar shi suka rankaya Habib na gaba suna bin shi tun kafin su karasa suka hango mutum a kwance Kamar marar Rai.
"Subhanallahi "abinda suka gada kenan suna karasawa kusa dashi sai da suka matsa sosai suka Gane da ransa Amma Yana cikin wani yanayi, dako dako sukayi aka rasa ya za'ayi dashi matashi ne ba zefi sana'an Habibun ba saidai a yanayin yanda jikinsa yake ba alamar wahala a tare dashi. Habib ne ya matsa kusa dashi sosai ya tsuguna Yana dudduba jikinsa ko akwai alamun duka ko makamancinsa amma babu komai, shawara sukayi su daukeshi kodan ceton Rai su tafi dashi idan yaso sai su dauki hotonsa a Dora a social media wata kila a Dace.
Lokacin da suka shigo Azare ana sallar insha'i directly asibiti suka nufa dashi ma'aikatan nan da Nan suka duqufa a kansa, sai gurin Sha daya Allah ya taimaka ya kawa kwakwkwaran numfashi.
Sai lokacin suka nufi gida malam ya turo dalibansa guda biyu ya fada musu dakin da aka kwantar da Wanda suka tsinta din, ya basu kudi saboda abun bukata.
Haka su Abubakar suka kwana da shi sai gurin hudu da rabi na Asuba ya bude idanunsa Yana kallon bakon gurin da yake ciki ga bakin mutane a gurinsa, yukurawa yayi ze tashi yqji ya kasa kansa Kamar an Dora Masa dutse, bakinsa ya bude zeyi magana yaji kwata kwata ya kasa yayi yayi Amma Sam maganar taki yuwuwa sai hakuri yayi ya zuwa bawa sarautar Allah ido.

AUREN HUCE HAUSHIN


MAMAN FATIMAH

PAGE THIRTEEN
(13)
__________Washe gari daga gidan Alhaji Jafar Abdul Hakeem da magaji suka kawowa su Abubakar abinci Asibiti, sun tausaya bawan Allah nan sosai Dan zuwa lokacin sun fuskanci baya magana Kuma jikin ma baya motsuwa yanda ya kamata, toilet ma sai da sukayi Kama Kama suka kaishi, a haka su malam suka shigo Asibitin tare dasu Malam Mudi, Basu Dade da zuwa ba likitoci suka shigo round sun tambayi menene Asalin ciwon to su dai sun fada musu Yan suka hadu dashi Dan Basu da masaniyar komai akai.
Gwaje -gwaje suka rubuta ayi Masa Dan binciken lafiyarsa.
Basu Dade ba suka koma gida saboda a ranar Alhaji Jafar ze shiga Bauchi suna da meeting da gwamna Amma ya bar kudade a hannun Abubakar saboda magani da sauran hidimar Asibitin.
Da yamma Habib ma ya shigo ya duba marar lafiyar nasu, Wanda har lokacin baya magana.
Likitoci sunyi iya nasu binciken basuga komai ba a tare dashi, sai dai rashin maganar kawai Amma Kuma Yana Jin komai da ake fada.
Bayan sun Gama bashi taimakon daya kamata suyi Masa suka sallame shi, Magaji ne ya dawo dasu gidan malam, Nan dakin malam na waje aka ajeshi tunda aka dawo dashi gida malam ya dukufa da Yi Masa addu'a Dan yayi bincike akan lamarin ya fashimci inda matsalar take, har Taraba ya tafi gurin malaminsa da yayi karatu a gurinsa ya fada Masa matsalar yaron, kwanansa biyu ya dawo Azare aka dukufa da rokon Allah da maganin hausa, haka zalika Alhaji Jafar ma Yana taho Masa dashi daga wani Islamic chemist da yayi musu bayanin matsalar yaron a can Abuja.
Cikin ikon Allah ba'a rufe wata hudu ba ya Fara magana sai dai idan yayi sau daya sai a wuni bai sake wata ba.
A haka aka dunga bashi taimakon har Allah yasa ya dawo normal Yana magana. A lokacin ne malam ya zauna dashi da Habib suka fada Masa inda suka same shi da halin da yake ciki a lokacin shiru yayi kafin yace musu shi dai yasan wata Rana Yana gida ciwon Kai ya takura masa har ya kasa fita, jzuwa dare yasha magani ya kwanta, to tun daga lokacin bazece ga yanda akayi ba shi dai ya farka ne ya ganshi a Asibiti tare dasu a hankali Kuma ya Gane a wani garin ma yake daban ba garinsu ba. Lokacin da Alhaji Jafar yazo garin malam ya fada Masa komai yanda sukayi da Mahmud din, Alhajin yasa aka Kira shi ya Kara jajanta Masa sannan ya nemi ya fadi garin nasu a mayar dashi Dan da gani Dan manyan mutanene.
Nan fa ake yinta Dan kekashe kasa yayi yace shifa ya manta sunan garin nasu akayi juyin duniya yace sai dai ko Nan gaba idan Allah ya nufa ya tuna, abinda ya tuna ma daga baya tunanin yazo Masa, haka suka hakura badan sun amince ba bayan ya tafi sun tattauna da Malam din akan lamarin inda Suke hasashen ko bacin Raine ya baro shi da gidan ya gwwmmace yayi zaman sa a Nan kafin ya huce ya nemi komawa gidan.
Nan yaci bada da Zama da Malam Yana kwasar ilimi kala kala.
Nan da Nan ya Zama Dan gida suka dinke da Habib duk da ze iya girmar Habib din da Kamar shekara biyu dan yayi Kamar sa'an Abdul Hakeem.
Bai cika wata shida ba Allah ya kawo aikin NGOs din Nan Wanda aka sakewa makarantar fasali da tsari suka sayi wani katon fili na makudan da sunan makarantar akayi gine ginen hostel din Yara suka dauki ma'aikata suka gyara tsarin karatun saboda kwazon Mahmud har co-ordinator din Shirin Muhammad Sameer ya dauke shi aika a shiyyar Katagum local government din ya Zama shine idon su a Nan, tunda ya iya rubutu da karatu. Habib ma Yana bada gudunmawa sosai a aikin duk da Shima nasa aikin da ma'aikatar ruwa ta Nan local government din tasu.
Wannan kenan.
____
Syprus.
Zuwa lokacin su zahra karatu ya Mika, tun tana saka Rai da zuwa Nigeria har ta hakura Kuma abinda ya Kara Bata mamaki sau biyu Abba da Abdul Hakeem suna zuwa ganinta idan harkar kasuwanci ya kawo sun Istanbul.Amma Koda wasa Basu taba ce Mata ga lokacin da zataje gida hutu ba.
A haka har suka hada shekara biyu a kasar, da gaske gida take son zuwa shi yasa lokacin da hutunsu ya gabato batayi shawara da kowa ba ta kama shirin barin qasar, online tayi komai Kamar su Sajida sai da komai ya Zama daidai sannan ta fadawa Uncle Haisam Shima bai hanata ba yasan tayi hakuri, Mama Hanifa ma ta waya ta fada Mata Nigeria zata wuce kawai, haka Ummee ma ta wayar itama ta fada Mata taso ta hanata Amma sai tayi wani tunani kawai tayi shiru kudade dai to tura Mata masu yawa Wanda har saida Zahrar ta Kara kiranta tana tambayar kudin ma meye haka da yawa? Tace ta turo Mata ne kawai ko idan take zatayi wani abun, godiya tayi Mata sosai hakan Kuma dabi'ar Zahrar ne komai kankantar Abu idan akayi Mata alherinsa zatayi godiya Kuma ko waye ta Bata Bata duba ai iyayene.
Kwana biyu suka Kara da akayi hutun shima visa din su Khadijah ne Bata Zama ready ba.
Lokacin da jirginsu ya dauka a Aminu Kano international airport taji ta sauko ta shaqi iskar Nigeria ji taji Kamar a Aljanna take lallai kowa yabar gida gida ya bar shi, saukar safe sukayi wurin karfe Sha daya ba yanda su zahra da Khadijah Basu da zahra ba akan ta zauna ta Dan huta kona awa daya ne a gurin sajida Amma tace A'a Azare tayi Kira su Anisa ne da Fatima suka bi Sajida Su dan huta kafin driver dinsu ya karaso tunda ba nisa tsakanin kazaure da kano, Kuma Gwammaja kan hanya ne.
Shatar taxi Zahra ta dauka ta kaita Kano line Dan direban taxi din ta tambaya Ina zata samu motar zuwa Azare ya fada Mata akwai gurare Amma ita Kano line yafi Mata kusa.
Har cikin Tasha Mai taxi din ya shiga da ita gurin motocin arear Bauchi, tayi Masa godiya sosai ta kuma Kara Masa kudi akan yanda ya bukata.
Away biyu da rabi Mai kyau matarsu zahra ta shiga Azare tun shigowa su ta Fara ganin 'yan canje canje a garin Kamar sabbin titina street light na solar sai gine gine masu kyau. Masha Allah ya dunga fada a zuciyar ta, Mai adai daita ta Sami ta fada Masa inda ze kaita, tunda suka tinkaro unguwar naji want irin nishadi ya mamaye ilahirin zuciyar ta, unguwar tasu ma an Sami cigqba sosai ga wasu gine gine sabbi masu kamar makarantar kwana har da gate a gurin gidan malam Baba gidansu ma gaba daya ya canza anyi Masa mahaukacin gyara tamkar sake sabo akayi.
Lokacin da Mai adaidatan ya sauke ta dai dai lokacin ya Hamza ya fito da alama wani gurinzeje Nan kusa.
Da madaukakin mamaki yake kallon zahrar shi dai Koda Wasa baiji ance zatazo ba Kuma yasan da ansan da zuwanta ai Bala driver ko su suje su daukota a kanon. Da sauri ya karasa Yana Mata sannu da hanya ita Kuma tana gaishe shi, shi ya biya Mai Dan sahun yace ta shiga ciki za'a shigo mata da kayan.
Tunda ta shigo gate din tasan eh lallai gidan ya lashe makudan kudin Dan gaba daya an canza fasalin gidan, tunda ta shigo gidan Mai gadin ke kallon zahra Dan shi dai sabo ne Bai Dade ba ta dai gaishe shi tayi gaba Nan ma wani mamakin ya rufe shi Jin tayi hausa radau Dan shi dai ze iya rantsuwa da abinda ze kashe shi wannan ko zo Bata sani ba da Hausa.
Ai mamakinta Bai karu ba Saida ta shiga cikin Nan dai ko rantsuwa tayi ba kaffara sabbin gine gine ne dam kwata kwata inda parts din su na da yake gurin ba komai sai filing da shuke shuken flowers.
Lokacin data shigo gidan ba motsin kowa kamar ba mutane a gidan kowa ne kofar part Yana rufe Ido ta lumshe tana shakar iska Mai Dadi ta gidan. Idonta na nufen Nan tana tsaye Dan ita batasan wane dakin zata nufa ba tunda da gaske ta Zama bakuwa a gidan, maganar Ibrahim taji Mai bin magaji Yana fadar "kai!" Da karfi ya juya a guje Yana fadin Ammah! Ammah! Kizo ga Aunty Zahra a tsaye a kofar part din Mama".
Magaji ne dake zaune a falon yana kallon wani series na 'yan Lebanon ya dago Kai da sauri daga kallon T.V Yana tsaki Yana fadin Amma Kai ba karamin soko bane dallah Banda tsabar hauka zaka wani ware murya Kama kwala Mata akan shashancin Kawai Wai zahra A'a wat......"
Maganar ce ta makale Masa lokacin da zahrar ta kunno Kai ciki da sallama a bakinta, dan a bude yabar kofar saboda zumudin ya kawo labari.
Ammah ce ta fito da sauri tana fadin Wai Kai har abada Ibrahim bazaka giirm..."
Idonta ya sauka akan Zahra wadda tayi tsaye ta langabar da Kai tana kallonsu,kafin Ammah ta dawo daga duniyar mamaki sai Jin zahrar tayi ta rugumeta ta saki shashhshekar Kuka.
"Ikon Allah!" "Ikon Allah!"
Abinda bakin Ammah ke fada kenan, ita Kuma zahra ta riketa kamar zata bace Mata.
Mamace ta shigo dakin da sauri tana fadin "Ina zahrar yanzu sahura ta shiga ta fada min taga Zahra ta shigo yanzu".
Ta fada tana kokarin Zama idanunta suna kan Zahrar.
"Wallahi kuwa Mama kin ganta Nan yanzu Ina daki Ibrahim ya shigo a guje Yana fadin gata Nan a waje nayi zaton shashancinsa ne Saida na fito na ganta kwatsam ba zato ba tsammani ba wani bayani".
Ammar ta saki da Dago kanta tana goge hawayenta tana fadin. "Haba Ammah an kaini wata uwa duniya an manta Dani idan nace zanzo ace A'a ni Kuma wallahi na gaji gida nake so shi yasa naki fadawa kowa na tasho kawai na gaji da ganinku a waya ni zahiri nakeso". Ta fada tana maida kanta jikin kafadar Ammar.
Tunda ta Fara magana Mama ta kureta da ido dan wani irin mahaukacin kyau taga Zahrar ta kara, ga wata irin gogewa da wayewa tamkar ba Zahrar data sani ba komai nata ya canza har ma salon yanda take magana.
"Ai kodai ki daina irin wannan kasadar ta tahowa daga uwa duniya irin wannan ke kadai sai ki fada ko addu'a ayi Miki sannan aje a daukoki daga Kano, Amma fa Ina tunanin a motar haya kikazo garin Nan ko?" Mama ta fada.
Kai Zahra ta gyada alamar eh, dai dai lokacin Yara suka shigo da jakunkuna ta guda biyu.
zaunawa tayi tana gaishe dasu Ammah, sannan magaji yayi Mata sannu da hanya Yana fadin "irin wannan surprised haka uktiy? kin ganki kuwa kin juye Balarabiyar ki sak kodan kina cikin 'yan uwa dangi farare irinki"
Dariya Zahra tayi Masa kawai.
Ibrahim ne ya shigarwa da Zahra jakunkunan ta dayan bed room din Ammah, ya fito ya nufi kitchen ya kawo Mata ruwa da lemo, ya koma ya dauko warmmers din abinci sai Ina yaka saka yake da zahra har Mama na Masa Dan biki.
Saida tayi wanka taci abinci sannan suka zauna da Ammah bayan sallar insha'i, hira sosai Suke Amma duk yawanci korafin Zahra ne na hanata zuwa.da Ammah tayi, a haka Abdul Hakeem ya samesu Shima yayi mamakin ganin.zahra kamar a mafarki Dan lokacin da ta dawo baya nan yaje Darazo ganin ganin wasu gonaki da Ya Hassan ya saya a can.
Sun raba dare suna Hira da 'yan uwanta a falon Mama sunyi waya ma da Abban tunda lokacin Yana aAbuja, Shima yayi fada sosai lokacin da Ammah ta Kira shi ta fada Masa ga zahra tazo.
Sai da ta kwana biyu tana huce gajiyarta, tana jikin Ammah kullum kamar kamar wata 'yar yaye, duk 'yan uwan kowa nan nan yake da ita, kowa kokarin kyautata Mata yake yi.
Sunyi waya da Aunty Hasana tace Mata tana nan tafe Jos zatayi Mata sati Amma sai Abba ya dawo, haka kusan Kullum sai sunyi waya da Hameeda.
Ranar data kwana biyar ne Ammah ta takura Mata akan ta leka makwabta ta gaishe wasu da yawansu sun shigo, wasu Kuma sun turo yaransu suyi Mata sannu da zuwa harda abin hassafinsu.
A waya Zahra ta Kira mujiba akan ta Shirya ta rakata Nan gidajen su shishhiga a gaisa.
Doguwar Riga ta saka kirar Dubai blue black Mai duwatsu tun daga sama har kasa ta saka plat she dinta fari tas ba wani makeup da tayi powder kawai ta saka sai lipsglow turarenta na Alkawari ta fesa Mai sanyi kamshi, Kota sa ko Bata Saba komai na sutarata kamshin yake.
Ta fito Kamar wani dawisu Dan da gaske zahra mai kyauce komai nata Kamar ita ta zabarma kanta. Tunda ta shiga bedroom din Ammah ke kallonta data ita sai halicinta suka San abinda zuciyar ta ke ayyana Mata a fili Kuma sai tace "Masha Allah! Har kin shirya?"
Kai ta gyada Mata tare da fadin "Eh Allah Dan dai kin matsabe Ammah Allah da Babu inda zani sai nayi sati biyu ko gate ba leka ba".
Wata leda Ammah ta Miko Mata tasa hannu ta karba tana tambayar "na waye?"
" Idan kunje gaida Baba malam saiki bashi tasa tsarabar turarika ne".
Murmushi Zahra tayi har fararen hakoranta suka bayyana tana fadar "wace irin tsaraba Kuma Ammah nida ba Hajji naje ko Umara ba daga makaranta fa na dawo hutu".
"To Miko min kije hannu sake ki gaisa ki taso tunda Zama da turawa ze saka ki koyi rowa" ta Mika Mata hannu alamum ta Bata ledar.
Dariya tayi Zahrar tana fadin "Allah ya Baki hakuri Ammah Ina ni Ina koyo rowa a garin wasu alhalin na gaji kyauta gaba da baya Allah qara lfy". Ta nufi kofa tana fadin "saina dawo"
"Allah ya tsare Kya gaishe da Malam din.
Gidan su mujibar Zahra ta Fara shiga suka gaisa da Mamanta sannan suka shishhiga gidajen suka gaisa, gidan Malam ne na karshe, a hanya Zahra ke tambayar Mujiba ginin da taga anyiwa Almajiran Baba Malam? nan ta fada Mata iya abinda ta sani akai.
A cikin rumfar canopy din da Malam yake bada karatu Zahra suka tarar da Malam din suna magana da wani matashi sukayi sallama a bakin rumfar a tare malam da Wanda Suke magana suka amsa sallamar, Yana fadin Bari naje na karbo yanzu in Sha Allah. Juyowar da zeyi sukayi ido hudu da Zahra wallahi ita dai batasan lokacin data rufe idanunta ba Dan wallahi wani Abu ta gani a idonsa Wanda Bata taba gani a idon kowa ba take zuciyarta ta wani harba a cikin girjinta. Ga wani mayen kamshi daya cika Mata hanci ita dai Bata San ya wuce ba Saida Mujiba ta tabata tana fadin ki bude idonki "Zahra menene?".
Ajiyar zuciya tayi a hankali tace "ba komai muje"
Cikin rumfar suka shiga suka zauna daga gefe suna gaida malam din.
Amsawa yayi Yana fadin Masha Allah da bakin turai ne Fatimah yaushe Kika shigo ban sani ba kodon Alhaji Yana Abuje shi yasa bani da labari".
Sunkuyar da Kai zahra tayi tana fadin.
"Ban Dade ba Baba Malam yau kwanana biyar da dawowa, Saida na huta nace Bari nazo na gaisheka"
"To Masha Allah! Allah yayi Albarka ya bada sa'ar abinda akaje nema, ai ba'a Gama karatun ba ko?".
"Eh da sauran shekara daya karatun ne da banbanci da namu na nan tunda su basa yajin aiki".
"Wannan haka yake, Allah yayi jagora ya bada sa'a"
"Amin" suka amsa tashi zahrar tayi ta karasa gaban malam din ta aje Masa ledar turarikan dake hannunta tana fadin "gashi Baba ba yawa"
Godiya yayi sosai kafin yace "ku shiga ku gaisa da zainabu batajin Dadi tana fama da masassara tun jiya".
"Allah ya sauwake"suka fada suna fita faga cikin rumfar.
Tunda suka shigo gidan suka sallama Amman gidan shiru a falon ma ba kowa uwar dakin Zahrar ta nufa tunda gidan ba bakonta bane, can tsakiyar gado ta hango Iya Abun jikinta yana ta kadawa tana ta rawar sanyi da sauri Zahra ta karasa kusa da ita tana Mata sannu Amman Sam ta kasa amsawa hannunta Zahrar ta Mika ta taba jikinta sai taji Kamar wuta.
"Ya Salam".
Ta fada tana nufar falon inda tabar mujiba tana fadar "Bari na fadawa Baba Malam jikin Kamar ya matsa gaskiya". Tayi waje ba tare data jira taji abinda mujibar zatace ba.
Tafiya take cikin sauri burinta ta Isa gurin malam ta fada Masa abinda kenan.
Ita dai Batasan yanda akayi ba sai ji tayi ta bugi kirjin mutum da kanta abinda yayi sanadiyyar ta tafi taga -taga zata Fadi taji an fusgota da Dan qarfi kafin ta Kai kasa sai ganin ta tayi rungume kane kane a jikin koma wannene an saka hannu biyu an zagaye bayanta.
Kici kicin kwace jikinta ta shiga yi data Samu ta Sami kanta coming fishing ta daga ido taga wane Mai tarar aradu da fadin Kaine ya kwakumeta haka da yammcin Allah wata'ala ta sauke Masa zallar rashin mutunci duk da ba halinta bane, tana daga Kai sukayi arba dashi ya kafeta da idanunsa masu wani irin kaifi da mugun kwarjini a cikin nata idanuwan Wanda a ganinta dashi na farko ya yamutsa duniyar ta
.AUREN HUCE HAUSHI
MAMAN FATIMAH
Page Fourteen 14.
-----------kusa da ita ya matso sosai Kamar ze Kara rungumo ta, da sauri tayi baya tare da rufe idanunta ruf zuciyarta na Kara speed, a hankali yayi magana saitin kunnanta "ki rinqa duba gabanki idan kina tafiya Mana kada kiyi Mana asara pls".
Ya fuske yayi wucewarsa ciki Bai Kara bi ta kanta ba. Nan inda ya barta Bata iya motsawa ba, wani Abu ilahirin jikinta keyi itafa ji take kamar kafarta bazata iya daukar ta ba wallahi,.shi Kuma wanene wannan a tare da malam haka? A Ina ya Samo shi Dan a gaskiya baiyi Kama da kolo ba Sam to waye shi?". Tambayoyin dake Mata Kai kawo kenan a kwakwalwarta daga ganin mutum haka kawai ze nemi yayi Mata shiga hanci da qudundune,ga wani irin kwarjini a cikin idanunsa da Bata taba gani a gurin wani namiji ba. Bata ankara ba taji maganar malam Baba Yana fadin " A'a Fatimah ya Kika tsaya a Nan ko wani Abu kike jira?"
Da sauri ta bude idanun tana kallon malam da wani yana binsa a bayan.
"A'a ba komai Daman gurinka zani jikin Iya Abun ne Naga kamar ya Dan matsa tana ta rawar sanyi".
Ta fadan kanta na kallon kasa kamar marar gaskiya, dan ji take kamar malam din Yana Jin mayen kamshin turarensa da ilahirin jikinta keyi.
"To Babu laifi muje ciki, yanzu Mahmud yaje ya dauko abokinsa don ya kara dubata tunda jiya sunje Asibiti da Halima matar malam Mudi ance zazzabin typoid ne yake damunta, to da jikin yaki Dadi ne za'a Kara bincike ko na cizon sauro ne zazzabin".. suka wuce ciki sannan zahrar tabi bayansu zuwa falon Iya Abun Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Yana tsaye daga bakin kofar ta waje ya harde hannuwansa a kirji kamar Mai tunanin.
Ganin malam din da salahuddeen sun shigo ya daga kansa Yana amsa sallamar su. Mujiba ce ta leko tana fadin" ta tashi din gata Nan fitowa".
Bai shiga falon ba Saida malam ya Fara shiga sannan suka biyo bayansa.
Sannu salahuddeen din yayi Mata ya dauki jinita take a Nan yayi Mata gwajin maleria ai kuwa ita ke damunta har ta Kai || +.
Allura ya dauko Yana fadin " malam allura za'a yi Mata emal, idan Allah yasa an dace shi kenan idan Kuma Bai sauka ba sai ayi Mata Attusunate, amma muna fatan Allah yasa a dace ma".
"Allaumma amin ya Rabb". suka fada su duka. Magunguna ya rubuta Mata na ulcer da tayi masa complain na ciwon girji da gefen kafadar ta, sannan yayi Mata Allah ya sawaqe suka fita.
Har magariba su zahra suna gidan Baba malam, tun bayan fitar su malam ba dadewa Iya Abu ta koma daki ta kwanta Zahra ta rufeta da wani qaton blanket barci Mai nauyi ya dauketa.
Nan falon suka zauna suna Dan tattaunawa da junansu, da tafiya zasuyi Majiba tace su zauna zuwa wani lokacin tunda ansan suna Nan Dan lokacin da zasu shigo mujibar taga kaninta Mubarak tace ya fadawa Mama suna gidan Baba malam.
Duk hirar da Mujiba ke yiwa Zahra Sam hankalinta baya tare da ita ta tafi duniyar tunanin abinda ya faru dazu da Wanda aka Kira da Mahmud wai ita Zahra ce kwance a kirjin wani namijin daba muharraminta ba, Kuma ba wani mataki data dauka Koda kuwa na kad'a Masa warning ne yanda gobe baze Kara marmarin rungumar wata ba, Amma Wai sai gata ta b'ige da shakkar idanunsa abinda kaf tarihin rayuwar ta hakan Bai taba faruwa da ita ba, ga wata faduwar gaba ta ba gaira ba dalili data sameta yanzu, ganin nan biyu da tayi Masa duk Abu daya takeji a kansa.
Wani wawan tsakin Zahrar tayi Wanda ya tabbatarwa Mujiba Bata tare da ita duk zubar da takeyi kamar 'ya'yan kanya.
"Keda waye kike tsaki haka kuma?".
Majiba ta fada.
"Kedai kawai bari kawai ba komai. Ta fadar tare da you kwafa ta tashi tsaye tana fadin
"Tashi mu wuce gida tunda Naga wannan barcin na Iya Abu bana Kare bane, inaga har da allaurar barci yayi Mata gaskiya".
A kofar gida suka yiwa malam sallama Yana ta Sanya musu Albarka.
Tun daga ranar Zahra Bata sake fita ba tana gida saidai lokaci-lokaci Mujiba na shigowa, a ranar data cika sati daya Abbansu ya dawo murna ba'a maganarta gurin Zahra, duk da tana ganin shi a can syprus din idan yaje Amma hakan bai Hana sun Kai wani lokaci ba suna tattaunawa irin ta d'a da mahaifi.
Saida Zahra tayi sati biyu sannan ta nufi Jos gurin Aunty Hasana.
Taji matukar dadin zuwanta Jos din. Dan har gidan Aunty Jana sukaje da Yara tunda lokacin da akayi bikin Bata Nan. Duk inda ya kamata taje taje har gidansu Mama taje haka ta kaiwa jannifer ziyara lokacin sunyi hutu tana karatu a Nan University ta Jos.
Maganar samari da gaske ta sakata side idan ka ganta tana magana Mai tsawo da namiji to ka tabbatar dan uwanta ne ko wani Mai qirma a idanunta.
Satinta daya a Jos suka taho tare da aunty Hasanar da Yara Wanda a satin sukayi hutu, bayan dawowar ta daga Jos ne su Hameeda sukazo hutun semester.
A lokacin ne Salma ta fito mata a mutum sak, ta nuna da gaske Bata yin zahra abinda yaso ya kawo b'araka Mai girma kenan tsakanin Mama da Ammah Dan da gaske an Kai hakurin Ammar karshe, maganganu Salmar ta ringa saki kamar lokutan baya, sai dai a wannan karon Zahrar ta nuna Mata jiya fa ba yau bace, idan da tayi tolerating na nonsense din ta a yanzu Kam dai dai take da ita tunda Bata Jan girmanta a gurinta, abinda ya Kara harzika Salmar lokacin da Zahra ta kalleta tayi tsaki tace "Wai wannan ce mace,kina duba mirror Kuma kina ganin kanki kuwa?gara ni da har kike min gorin ana saka aurena ana fasawa, Ina laifi tunda har ana ganina ana sona, kaddarar Babu mijina a cikin su ce take rabani dasu, kefa ko Kare Bai taba zuwa yace Yana sonki ba, baga kanwarki Nan ba Ina cewa har anzo tambayar aurenta? kije kiji da abinda ya dameki Zaki zauna kina fada da kanwar bayanki".
Tana Gama fada Mata maganar ta nufi hanyar ficewa daga dakin. Cikin fushi salmar tayo kan Zahrar ta fardota baya saura kadan ta Fadi dai dai lokacin Kuma sahura ta shigo zatayi musu sharar yamma ta tarar da wannan badakalar, da sauri ta shiga tsakanin tana Basu hakuri ta Kama salmar ta fita da ita daga dakin tana faman zagin Zahrar abinda ya janyo hankalin Amma dake main kitchen din gidan tana yiwa Abba gas meat saboda Yana sonsa sosai yawanci idan Yana gida kusan duk dare sai anyi Masa shi.
Da sauri ta fito tana tambayar "me yake faruwa ne?"
Sahura ce ta fada Mata abinda ta shiga ta gani tsakanin Zahra da salmar, juyawa kawai Ammah tayi ta koma taci gaba da aikinta Bata Kara lekowa ba tanaji Mama ta fito tana fadan daman ai ba tun yau ba ta fuskanci Zahra ta Raina Salma, Kuma komai runtsi dai Salma ai gidan ubanta ne Nan ba Mai hanata sakewa.
Zahra ce ta fito zata wuce zuwa part din Ammah,har ta gota Mamar batace komai ba, Mamar tace.
"To fiqe kafi qaya tsini da Kika Samu guri kina yanda kikeso a gidan wallahi duk rintsi bazaki Kai matsayin 'ya'yan gida ba, tunda har abada ba'a canzawa tuwo suna"
Har zahra tayi kamar ta maida Mata martani sai taji bazata iya ba babba babba ne, kawai ta shige part dinsu.
Har Mama ta juya taji maganar Ammah daga bayanta, dan harga Allah batasan Ammah ta fito main kitchen din ba, Sam duk da tana jiyo kamshi ta dauka a can part dinta take aikin.
Bata juyo ba Amman ta tsaya.
Ammar tace
"Haba Mama ban zaci haka daga gareki ba wallahi, cewa nake da Zahra da su Hameeda dauka daya ne a gurinki, ai saiki tambayi meya hada fadan?kiyi musu fadan gaba daya ba wai ki nuna Salma itace taki ba, kina fadin maganganu irin haka ai na dauka ni duk binda lauje ya yayo a gidan Nan ya kamata ki dauke shi ciyawa ne na gode amman ki sani Banda komai nufin Allah ne Zahra tafi karfin ace Mata 'yar karere tunda Mai gidan ne da kansa ya karbo rikon lokacin da aka nemi tafiya da ita kema Kuma sheda ce kinsan su waye kakanninta ba bakinki bane, dukiya idan ana gadonta kinsa Zahra 'yar mun gada ce, ko shi Wanda kike takama da dukiyar tasa yasan tazarar da nisa a tsakaninsu da kakanninta idan kina tunanin karya ne idan yazo ki tambaye shi ze Baki cikakken bayani".
Bata jira taji abinda mamar ke kokarin fada Mata ba tayi gaba abunta ta nufi part dinta.
Tun daga ranar Ammah ta daukewa Mama wuta gaisuwa kawai ke hada su, a kwana na biyu da Mama ta karbi girki ta kasa hakuri ita abin yafi damunta ta fadawa Abban Ammah Bata Mata magana, yayi mamaki matuka da gasken gaske Dan wannan shine karo na farko da irin haka ta faru da matan nasa duk tsawon shekarunsu. Bai taba rabasu akan sun Sami matsala ba Koda wasa, dan haka ya Kira Ammah a waya yace tazo part dinsa Yana son ganinta.
Batayi mamakin ganin Mama a zaune ba tasan za'a Rina tunda kaf tasan halin Mama n
a zahiri.
Gaishe da Abban tayi suka Kuma gaisa da Mama, tambayar ta Abban yayi ko akwai abinda ya hadasu da Ammah ne?.
Ba wani kwana kwana ita Daman tun can baya Bata da munafurci ko kadan. Dan haka ba wani ta fadawa Abban duk abinda ya faru tunda Saida ta tutsiye Zahrar akan ta fada Mata abinda ya hadasu da Salma da kuma abinda mamar ta fada, shi kanshi Abban yayi mamakin abinda Salma tayi sosai, itama Mamar ya nuna Mata kuskurenta na fadar wannan maganar ya Kara da cewa.
Ban tabi yiwa zahra kallon ba nine na haifeta ba, bil hasal ma shine dalilin da yasa ban aura Mata Daya daga cikin 'ya'yana ba, ita kadaice ba uwa ba uba tun batasan inda kanta yake ba, mu ta sani a matsayin iyaye sauran yaran Kuma 'yan uwanta. Idan na aura Mata wani a cikinsu ba zata Zama feel free tare da ni ba, idan damuwa ta shiga ba Wanda zata fadawa kinga ai anyi adoh badan kyau ba".
" Haka ne suka fada.
"To karna Kara Jin makamanciyar irin wannan maganar, ba Wanda ze kawo min rarraba kan iyalin gidana. Zahra 'ya tace kawai na saka sunan mahaifinta ne Dan haka shari'ar musulunci tazo dashi, badan in nunawa duniya bani na haifeta ba, a kiyaye kodon gaba".
"In Sha Allah".
Suka fada.
Bayan tafiyar iyayen yasa suka turo yaran yayi musu fada sosai sanan ya Kare da nasiha.
Tun daga lokacin abubuwa na zahiri sukayi sauki sosai.
Kusancin Zahra da Hameeda ba abinda ya taba shi saima Kara shakuwa sukeyi a kullum suna Jin dadin butun, Zahra suna waya sosai da Ummee da Mama Hanifa harma da uncle Haisam a wasu lokutan.
Lokacin da hutunsu ya kusa karewa duk sai Zahra ta nemi walwalarta ta rasa ko da yaushe kamar marar lafiya ana saura kwana biyu ta tafi Ammah ta matsa Mata taje Kiran da Baba malam yake Mata, dan sau kusan uku yana turo Yara tana cewa gata Nan Amman sai tayi burus da zancen.
Har dai ta Kai Ammah karshe tayi magana. Hameeda tace ta rakata suje tare, yau gurin malam din ba kowa ba Kuma rumfar karatu tunda ranar basa karatu. Gurin ganawa da mutane suka sameshi su Habib suna ta gyaran Shirin kantar littafai.
Da sallama suka shiga suka gaishe da malam din sannan suka gaishe dasu Habib, sai sukayi shiru.
Malam ne yace "Zahra'u Ashe lokacin komawar taki har yayi ko?"
Kara risinawa tayi tana fadin "eh lokacin yayi yayi Baba gobe zan tafi in Sha Allahu amma a Istanbul zan tsaya sai wani satin zan wuce syprus din".
"Masha Allah. Allah ya taimaka, ki Kara hakuri akan lamuranki duk wani bawan Allah na kwarai sai Allah ya jarabce shi Dan ya gwada imaninsa ki dauki abinda yake faruwa dake Daman haka Allah ya rubuta Miki taki kaddarar kada ki yanke kauna daga Rahamar Ubangiji. Ga addu'oi nan da littatafan addu'a ki tafi dasu ki ringa yinsu Kuma kada a shagala da ambaton Allah a duk inda aka Sami kai, Allah yayi Albarka ya bada nasara ya kiyaye hanya".
"Allahumma Amin suka fada a tare".
Habib malam ya yiwa magana ya Miko ledar da aka saka sakon nata, Hameeda ta karba suka Kara yiwa malam godiya suka fito suka shiga cikin gidansa Zahra ta Kara duba jikin iya Abun ta Kuma yi Mata sallama.
Basu koma gida ba, gidan su mujiba suka shiga Bata Nan ma sai Maman ta suka barwa sallahun tafiyar zahrar suka nufo gida, sunzo dai dai masallacin gidansu ne sukaga Ya Abdul Hakeem da Dodon Zahrar a zauna a kan carpet karami a gefen masallacin suna hira Kai da gani da kyakykyawar alaqa a tsakanin su.
Gaishesu sukayi suka wuce, Hameeda ce ta kalli Zahra tana fadin "Kinga wancen Guy din yanda Salma ta mutu kansa ba magana! lokacin data Fara ganinsa munzo hutu wallahi kamar zata zauce akansa sai da Mama ta taka Mata burki taci Mata mutunci akan ta rasa Wanda zata so sai Almajira Wanda ba'a San asalinsa ba, duk yanda taso ta nunawa mamar wannan da banbancin da irin Wanda ta sani amma Sam taki fahimta Dan har so tayi tayi Mata duka tana fadin Dan lalacewa ta rasa Wanda zataso sai fakiri Mai allaziwahidin Dan salon Abba yaji ya Goya Mata baya tunda Wai ance sune suka kawo shi garin bandai San kan labarin ba gaskiya". Ita dai Zahra Bata tofa tataba daga uhm sai umh umu uhm, har suka karasa gida.
A Daren sun raba dare suna Hira da Ammah a Nan ta dunga yi Mata magiyar ta daure taje gurinta ko zuwa karshen shekara ne ta ganota ba ta tura Mata Ya Abdul Hakeem ba.
Karfe shida Mai kyau sun dauki hanyar Kano ita da Ya Abdul Hakeem da Hameeda da magaji.
Nan suka zauna da zahra suna ta Hira kafin lokacin tashin su yayi, in da wani Abu da ya damu Zahra a gurin Bai wuce kallon da wani matashi ya kureta da Shi ba, duk inda zata dago Kai sai sun hada Ido dashi, Sam ya hanata sakat da idanunsa idan ba idanunta kemata gizo ba har wani lumshe ido yake da wani kankance su. A haka har lokaci ya cika aka Fara shiga jirgin hand bag ce kawai a hannun Zahra tunda kayan an tafi dasu tun zuwansu lokacin da ta juya ta Fara tafiya ba zato taji hawaye a idanunta abinda ta dunga kokarin kar tayi kenan tun daga gida lokacin da Auta Musaddiq ya fasa Kuka da suka taso Amma sai gashi ta kasa jurewa itama Saida suka zubu, juyawa tayi kadan lokacin da zata hau steps din sai taga Ya Abdul Hakeem ya Kama hannun Hameeda sun juya sun Fara tafiya tana share hawaye da dayan hannun itama ta juyo hannu Zahra ta dago Mata alamar bye sannan ta Haye zuwa ciki.
Kusa da wata Mata ta zauna da alamar kamar zatayi sa'ar Ammah, ta gaisheta.
Saida jirgin ze tashi ne taji na gefenta Yana fadin "duk tunanin gidan ne ya hanaki jin sanarwar a daura belt da ake ne?" Ya fada in a soft voice. Dago Kai tayi ta dubi Mai maganar dake gefenta, wannan Wanda ya dameta da kallo ne kafin su shigo, ita Sam batama San sanda ya zauna kusa da ita ba.
"Nagode" ta fadawa tana saka belt din lokacin da jirgin yayi balance a sama ne ta cire belt din ta bude computer dake jikin kujerar dake gabanta tana kallon location din da Suke bi tun tana Gane garuruwan data sani ko take jin sunansu har aka shigo Wanda sai dai ta karanta kawai. Jefi jefi suna Dan magana da matar dake kusa da ita. Nan kusa da ita dai Bata Kara kallonsa ba tunda taga shi kallon mutane kamar dabi'arsa ne.
Sanyi kamar tafiyar awa daya taji yana Mata magana da farko yi tayi kamar bataji ba, Saida matar dake kusa da ita tace "bakyaji ba ana Miki magana, ko kina da aurene?".
Kai ta girgaiza alamar A'a.
"To meyasa kina Jin Yana Miki magana Kika kyale shi? ba Dadi irin haka baka wulakanta mutum ba kasan gaba abinda Allah zeyi ba kinji".
A hankali take Mata maganar yanda ita kadai zata iya ji.
"Tom nagode in Sha Allah zan kiyaye". ta fada mata.
Bai hakura ba har Saida ya Sami kan Zahra duk da ba wani sakewa tayi dashi ba Amma dai hakan yayi masa.
Lokacin da suka sauka haka ya dunga bin Zahra kafa ya kafa har ta dauko kayan ta da aka gana screening suka fito, a Nan ya fada Mata sunansa Mushahu shi Dan Kano ne Yana aikin government Yana Kuma kasuwwnci yanzu ma harkar kasuwancin ta kawo shi kasar. Zahra ma ta fada Masa sunanta da inda take karatu da Dan zaman da zatayi anan kasar kafin ta wuce.
Bai bar airport din ba har Saida Mama Hanifa tazo daukar zahra, da yake Mushahun wise ne sosai ya sake da Mama Hwnifar don Basu rabu ba har Saida ya karbi address din gidanta, saida suka bacewa ganinsa sannan Shima ya nemi taxin cikin airport ya nufi hotel din da yake sauka idan yazo kasar da buri kala kala a zuciyarsa kan Zahra.
Satinta daya ata nufi syprus kafin lokacin Mushahu ya Kai Mata ziyara yafi sau hudu ba karamin samun shiga yayi a gurin Mama Hanifa ba.
Zauwanta makaranta da kwana daya Sajida da Khadijah da Fatima suka dawo Anisa ce Bata dawo ba suna Umara da Yayarta sai Kuma sukayi Dan Samu matsalar visa.
Karatu Suke ba Kama hannun yaro Koda yaushe suna busy da karatu, tunda Zahra ta rabu da Musbahu a turkey Sam ta aje batunsa a gefe duk da kusan Kullum saiya kirata sun gaisa Yana ta kafa gwamnatin sa a gurinta. Bazato ba tsammani ranar wata Saturday taje weekend gidan Uncle Haisam ya kirata da number din kasar Yana fada ya shigo kasar tayi jiransa Nan da awa daya ze shigo makarantar, ba karamin mamaki tayi ba da jin hakan, dan harga Allah batayi zaton da gaske yake ba da yace Mata Yana Nan zuwa syprus din.
Nan da Nan ta fadawa Aunty Jinan matar uncle zata koma school yau suna da wani group Assignment data manta zasuyi ta taho, Bata Hana ta ba tunda Daman uncle din baya kasar sunje wani aiki south Korea, snacks Aunty jinan ta hada Mata masu yawa ta tafi dasu. Allah ya taimaketa ta fito da card dinta na shiga bus ko train, mintina talatin masu kyau suka kawota kyrenia city.
Lokacin data shiga hostei dakinsu ta wuce ta Kara gyara jikinta.
Wani karamin basket da dauko ta zuba snacks da drinks masu sanyi, turare ta Kara fesawa har Brandy wadda Suke daki daya take tambayar ta ko zataje wani park ne ta huta yau weekend?
Eh kawai tace Mata tayi gaba ta fita daga dakin, gurin su Sajida ta nufa akayi rashin sa'a duk basa Nan sai Anisa kawai ta Samu tana sallah.
Zama tayi tana tunanin yanda lamura Suke ta juya Mata kamar a almara ko wannan din shi ya zata Kaya a kansa? Dan haka Nan taji bazata iya yi Masa rashin kirki ba Dan duk Wanda ze Bata kudinsa da lokacin sa ya biyoka har wata kasar duk da baka bashi fuska ba to kuwa Bai cancanci wulakantawa ba a gurinka.
Kafin Anisa ta idar da sallar wayar Zahrar tayi Kara alamun Kira ya shigo, number dazu ce ta daga tayi sallama, daga can ya fada Mata ya shigo ciki da inda yake.
Bayan sun gama wayar ne Anisa ta idar da sallar ta kalli Zahrar tana fadin "yaushe Kika dawo nayi zato sai Monday da safe Zaki dawo?".
"Ke dai Bari kawai wallahi guy din Nan Dana fada muku mun hadu a airport din Kano Yana kallona har ya bini gidan Mama Hanifa?"
Kai Anisa ta gyada alamar ta gane.
"To shine fa dazu ya kirani Wai gashi a kasar ya cika Alkawari zuwa anjima ze shigo Nan gurina, shine yasa na dawo yanzuma kiransa ne ya shigo Yana gurin garden din can na gurin second gate".
A gurin suka same shi Yana tsaye kusa da wani kangaroo na siminti Yana kallonsa har da kanana a kusa dashi yayi kyau sosai kamar na gaske, ya shagala da kollon har baisan sunzo gurinsa ba Saida Anisa tayi Masa sallama sannan hankalinsa ya kawo kansu. Wani irin mahaukacin kyau yaga Zahrar ta karayi a idonsa, kasa dauke idanunsa yayi daga kanta. "Masha Allah!"
Ya furta a hankali Yana fadada fara'a akan fuskarsa tare da amsa sallamarsu.
Karkashin wata bishiya Anisa ta nuna masa inda akayi kujerun sumunti masu kyau sosai, bayan sun zauna ne Anisa ta gaishe shi tana Masa ya hanya, sannan Zahra ta gaishe shi itama, duk sai taji duk wani iri saboda Sam lamarin maza gaba daya ya Gama fuce Mata daga Rai duk da bazata ce sun yaucareta ba Amman lamarin su a gurinta Mai girma ne Dan duk yanda taso ta manta abunda ya faru a baya Bata iyawa, Samun kanta tayi da wani irin Jin bazata iya watsa masa kasa a ido ba.
Sun jima suna tattaunawa da Anisa a fakaice Yana yiwa kansa campaign a gurinta, Anisar ta gabatar Masa da abubuwan da suka kawo masa, ita dai Zahra tana jinsu suna ta Hira kanta na kasa tana Dan Wasa da wani zoben white gold da Aunty Nawwara ta saya Mata lokacin da sukaje Umara.
Anisa ta jima sosai kafin tace zataje ta duba idansu Sajida sun dawo.
Bayan tafiyarta Musbahu ya yayi duk yanda zeyi ya janyo hankalin Zahrar ta sake dashi Kuma Alhamdulillahi kafin wani lokacin ta Dan sake ba kamar lokacin da suka zoba, a nan yake fada Mata shifa da gaske yakeyi yafi son kafin ta Gama makaranta a Gama komai tana gamawa kawai ayi bikin tayi service a gidansa. Saida aka dauki lokaci sosai sannan su Sajida suka karaso gurin bisa jagorancin Anisa, sun jima suna Hira sosai anan yake fada Mata Shima Dan kano ne sokoto road, ita Kuma ta fada Masa tana Jambulu Amma da suna zaune a Gwammaja ne.
Ya jima sosai kafin ya tafi,washe gari Sunday yaso su fita Amma Zahra ta nuna ba wannan maganar duk yanda yakai da naci ta Kiya har su Sajida suka saka Baki Amma ta qiya. Satinta daya ya koma inda ya sauke Mata kudaden masu yawa ya Kuma yi Alkawarin gabatar da kansa gurin iyayenta tunda bada Wasa yazo ba, itama Kuma Bata Hana ba tunda da gaske taji yes zata iya rayuwa dashi idan Allah ya amince.
Bayan barowarsa kasar da sati daya ya gabatar da kansa ga Alhaji Jafar a matsayin Mai son auren Zahra, Bai rufe Masa komai ba har zuwan da yayi syprus din,sai dai ya bashi hakuri akan zuwan daya Farayi kafin yazo gare shi, ba komai Alhajin ya nuna masa sai dai yace irin hakan bashi da kyau kodon gaba mutum yabi 'ya mace wata uwa duniyar batar da sanin magabatanta ba akwai hadarin lalacewar tarbiyya ga Wanda Allah yasa shaidan yafi karfin zuciyar su.
Alhajin yayi Masa tambayoyi sosai akan Sana'a da Kuma asalinsa, sannan ya fada Masa shima mahaifinsa ya rasu tun Yana level one hundred a jami'a, a labarinsa daya fada masa nan ya gano kanin mahaifansa sunyi makaranta tare dashi a Bauchi.
Bayan tafiyar Musbahun da Alhaji Jafar ya tada mutum takanas yaje har Kano da taimakon abokinsa Alhaji Muttaqa akayi Masa bincike kan Mushahu Kuma Alhamdulillahi ba'a Sami wani abun ashsha ba a tare dashi Dan mahaifiyar ma ta fito ne daga cikin manyan gidajen sarautar Kano.
Bangaren Zahrar kuwa kusan Kullum suna tare da Musbahun a waya Dan har ya haddace lokacin agogon kasar, tun tana daridari har ta sallama tare da karfafawar su Sajida kafin su gama semester din sun shaku dashi sosai Bata rufe Masa matsalar data fuskanta a baya ba, nuna Mata ma yayi rabonsa ne ya kawo aka ringa samun akasin na bayan ya Kuma yi Mata Alkawarin ruwa da iska ba abunda ze girgaiza tarensu bare har akai ga rabuwa Koda kuwa Aljani ne ya aurata in sha Allah sai yaga bayansa, yayi Mata alkawura da dama ya nuna Mata Babu wani abu da ze girgaiza shi koya bashi tsoro akan lamarin aurenta.
Magana tayi nisa Dan har iyaye sun shiga abinda yayiwa Ammah Dadi kenan Dan wannan karon Kam Zahra tayi Dace da Dan manyan mutane sosai, dan basu bar garin ba Saida suka shaida lokacin aure idan ta gama service da wata daya duk da sunso ayi bikin kafin tayi service din sai Alhajin ya nuna musu suyi hakuri tayi idan ta gama saita zauna guri daya ba daga kaita ba ba dadewa ta Fara fita kullum, Kuma ya Hana kayan lefe Dan Alkawari yayi ankawo biyu an karbe to kuwa ko waye zata aura sai dai ya aje Mata kayan idan taje gidan ya Bata.
Lokacin dasu Zahra suka Gama karatunsu har da Ammah da Hameeda akaje bikin graduation dinsu mutanen Jordan ma sunje har Mama Hanifa.
Bayan kammala taron sun Kara kwanaki a kasar, Zahra ta raka Hameeda kuraren shakatawa da yawa tayi kallo tayi santin inama Abba ya dawo dasu Nan Suma gashi ita har ta Gama Amma su Kullum karatunsu ba cigaba ana faman strike tunda a yanzu ma shine ya dawo dasu gida har ta samu damar zuwa itama.
Ranar da zasu taho sun Sha kukan rabuwa dasu Sajida tunda su saura shekara daya su gama.
Murna gurin Zahra ba magana ji take kamar ta sauke wani abu Mai nauyi daga kanta.
Musbahu yaso zuwa graduation dinsu Zahrar Amma lokacin Yana busy yaje wani special assignment a Kenya dole sai hakuri yayi, Amma Yana dawowa ya yiwa Azare dirar mikiya a ranar Zahra taga zallar so a gurinsa Dan ji yake kamar ya dauke ta yayi gaba da ita, itama ta bashi kulawa kamar me,Hameeda tazo sun gaisa sun Dade suna Hira dashi tambakar sun shekara da sanin juna, sunan mujiba ma ta shigo suka gaisa ba shi yabar Azare ba sai kusan magariba Dan ma Zahrar nata Masa magiyar ya tafi saboda rashin tsaro irin na kasar.
Tun daga lokacin hanya ta aure shi tsakanin kano da Azare. Mushahu na mutane ne kusan duk Wanda ya kwana ya tashi a Nan kukkuken unguwarsu Zahra yasa shi Koda kuwa ba gaisawa suke ba, wata kila ya taba yiwa wani alheri a cikin yaran gidanku Dan da gaske hannunsa a sake yake gurin Alkhairi.
Sunyi sabo sosai da jama'a a Nan har gurin malam Bukar Yana zuwa sauda dama idan ya shigo garin, wasu ma daga cikin samarin gidan malam din sunyi sabo sosai.
Lokacin da results dinsu Zahra ya fita Sam bataje ba Auncle Haisam ne yayi Mata komai Allah ya taimakeka ta fito da first class degree a akan anatomy.
Allah ya taikata da taimakon Ya Hassan aka kawota bauchi service, bayan zaman camp sukayi posting dinta Dr Sulaiman Adamu memorial college of Hygiene and Environmental health science Azare.
Ammah taji dadin hakan sosai haka shima Mushahun yaso hakan kwarai da gaske.
Zahrar najin dadin aikin sosai da sosai domin teaching Yana cikin hobbies dinta.
Bayan sun Gama ne da wata daya kamar yanda akayi Alkawari aka Fara kokarin Fara shidimar bikin ta dai dai lokacin Kuma akayiwa su Ummee rasuwa a saudiyya abinda ya Hana su zuwa kenan da har Ammah tace a daga bikin tunda rasuwar ta jikinsu ce kanin Baban Ummeen ne ya rasu,Amman sai sukace Dan me ayi idan komai ya lafa zasuzo suga daki kawaii.
A satin da za'a Fara bikin kusan Kullum Mushahu da Abokansa shakikai su Deeni da Aliyu Wanda Suke cussings suke ta zirga-zirgar ganin abubuwa sunyi yanda ake so duk wasu programs a nan za'ayi dinner ce kawai zasuyi a Kano, sun Kama dakuna uku a hotel idan zasu zauna har zuwa Daurin aure.
Saura kwana biyar Daurin auren ne wani abun al'ajabi ya faru da Hajiya Nafisa Maman Mushahu wadda suke Kira da Ammi.
Cikin dare tana barci ta farka a matukar razane saboda wani mugun mafarkin da tayi da Musbahun akan auren, addu'a tayi ta koma ta kwanta ai kamar jira ake barcin ya dauketa sai abunda ta gani a wannan mafarkin yafi wancen muni, wasa-wasa barci ya gagareta a wannan Daren kafin safe duk ta wani hargize ga wasu irin tunane tunane sun cika Mata zuciya na rashin kwanciyar hankali kafin yamma gaba daya ta Zama wata marar nutsuwa ba shiri ta Nemo kanwarta Aunty Jamila a waya Nan da Nan tazo tunda ba aure gareta ba, duk ta kwashe komai ta fada Mata akan Bata son auren Musbahun kwata kwata ita fa ko a cikin ranta ta tuna da zeyi aure ji take kamar zata zauce, da farko Aunty Jamilar ta dauki abun Wasa Amma ganin da gaske abin yake yasa ta Kira Babban yayansu Alhaji sulaiman da kanin Baban su Musbahun Alhaji isma'il, Suma da farko sunyi zaton na Wasa ne Amma da suka matsa akan ta Fadi dalilinta na Hana yuwuwar auren sai abun ya ta'azzara ya Zama kamar Mai tabin hankali, ganin abun Yana neman ya Zama wani iri ne yasa Alhaji sulaiman ya kirawo Aliyu tare da tambayar suna ina?.
Aliyun yace gasu Nan a hanya sunje Azare ne Amma har sun wuce wudil sun kusa kano ya fada Masa lallai direct su nufo sokoto road su duka.
Haka suka shigo suka tarar da wannan dambarwar ana ta fama da Ammi.
Ai tana arba da Mushahu ta Kara tuburewa tana fama fadar wallahi matukar ya kafe sai auri Zahra Bata yafe Masa nononta da yasha.
Su dai Basu ankara ba sai ganin Mushahu sukayi ya sulale ya zube a sume, da sauri Aliyu ya kawo ruwa aka zuba Masa Amma a banza ganin haka yasa suka nufi Asibitin Nasarawa dashi. Haka aka dunga juyawa da Ammi Amma ta kafe kamar kafiran farko duk Wanda ake tunanin ze kawo gyara a lamarin an fada Masa Kuma yayi bakin iyawarsa Amma ba wani ci gaba da aka nemi a Zafafa sai lamarin yaso ya koma Mata tabin hankali abinda daya tada hankalin Babarsu kenan Hajiya Yaya tace dole a hakura da auren tunda abin yazo da irin wannan lamarin marar Dadi daman tun farko ita bataso lamarin ba sai dai yaran yanzu ne baka hanasu abinda suke so, tunda Daman fa ance shine na uku a Wanda zasu auri yarinyar ana fasawa to shima gashi tun ba'aje ko Ina ba lamarin ya Zama haka.
Tashin hankali iya tashin hankali Musbahu ya shiga Dan dakyar aka Sami nutsuwarsa dan kwata kwata ya daina magana da kowa ya rufe duka wayoyinsa shima Deeni ganin kiran Zahra yasa ya rufe layin da suke wayar da ita, Aliyu ne kawai Bai rufe wayar ba Amma baya picking idan ta Kira a halin hake ne su Alhaji sulaiman sukaje Azaren da labari marar Dadi Wanda ya kawo karshen 'yar Wala walar da akeyi da Zahra akan aure ta kawo karshen duk wani makirci da bita da kulli da ake Mata na rushe aurenta idan ya taso abinda ya girgaiza duniyar Wanda suke fake suna tsula ta'addanci ta karkashin kasa.


AUREN HUCE HAUSHI


MAMAN FATIMAH
Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu. Dan Allah ayi hakuri da matsalar da aka samu gurin turo page fourteen sau biyu hakan ya faru ne saboda wasu dalilai Amma na karshen Wanda na turo shine cikakken fourteen din yanzu kuma na hade fifteen & sixteen guri daya na gode.

Page
Fifteen
&
Sixteen


BACK TO STORY.

________ Gurin Zahra su Sajida suka shiga tana kwance a gado idanunta a rufe tayi zurfi cikin tunanin, Sam bataji shigowar su Sajida ba Saida mujiba ta Dan zungure ta bude ido ta yunkura ta tashi zaune tana dafe kanta dake Sara Mata.
Sajida ce ta zauna kusa da ita ta Kama hannun Zahrar tana fadin "bestie Dan Allah ki rage tunani kada wani ciwon ya kamaki, ki yawaita addu'a komai yayi zafi maganinsa Allah. Kuma wani hanin ga Allah baiwa ne, ke kanki Baki taba tunanin abun ze Zama haka ba, Kuma Allah ya juya lamarin yanda yaso, to saiki gode Masa bisa ni'imar da yayi miki, Kuma nifa mujiba Ina doubting akan wannan da aka daura musu aure, Kuma ki rubuta ki aje zakice na fada Miki kije kiga gidan da za'a Kai bestie, Kuma ki duba kiga irin kayan da aka kawo yanzu kinsan duk Wanda ya hadasu first class ne a gurin gayu wallahi komai bana banza Amma Kuma Wai almajiran malam ne gaskiya I doubt much".
Ta fada tana kallon mujibar.
Ita dai Zahra ta rasa inda zata Kama komai ya kwance Mata, su damuwarsu kaya da gida, ita Kuma tata damuwar ta yanda za'ayi zaman ne, har yanzu gani take kamar a mafarki Wai wannan karon ma Saida aka samu akasi,ta rasa daga Ina matsalar take, shi kuma auren da aka daura meye ze biyo baya tasan idan ba wani nufi ba na Allah shima sai an Sami wani kalubalen a cikinsa.
A hankali ta furta "Ya Salam! Allah ka shiga cikin lamarina, wallahi bestie komai ya kwance min bani da sauran dabara,kwakwalwata ta daina aiki yanda ya kamata kinsan Allah nifa kamar ma tsoronsa nakiyi Dan tunda na Fara ganinsa naji wani irin Abu a jikina wanda ban tabaji ba a kan ko wane namiji sai shi, Kuma yayi min abinda ya kamata na dauki mataki Mai karfi amman wallahi ko magana kasayi Masa nayi, yanzu kuma a haka zan rayu dashi? Ni wallahi bana sonsa Sam Kuma fa Shima yace baya son abin yake ba kawai dai baze iya watsawa su Abba kasa a ido bane". Ta karasa fada hawaye na zubo Mata a fauska.
Lallashinta sukayi da kyar tayi shiru kafin mujiba tace "haba Zahrar ki daina kuka idan kina daga hankalin ki na Ammah ma baze kwanta ba, Kinga irin haka ba Dadi duk da an aura miki Wanda babu soyayya da shakuwa a tsaninku, ita a hakan ma yayi Mata da ace wannan karon ma an fasa aure gara hakan tunda naga alama da ita ake fadan ke kin ratso ne kawai ake fakewa da lamarin ki Dan a Hana duniyar ta zaman lafiya da kwanciyar h
nkali, Kuma Baki san dalilin da yasa Abba yayi hakan ba, kinsan dai Abba baze taba aura Miki baragurbi ba kedai kiyi ta addu'a muma muna tayaki, Bari na tambaye ki Mana idan kina addu'a bakya cewa Allah ya Baki miji na gari?"
Hannu tasa tana share guntun hayenta kafin ta harari mujibar tana fadin "Ina yi Mana kuma kawai saina yi sallah na kasa wannan addu'ar dan na Zama abinda na zama ko?"
"A'a ba haka nake nufi ba bayani zan miki shi yasa nayi Miki tambayar dai, Allah ya huci zuciyar Amarya".
"Kina jina mu 'yan adam muna rokon Allah ya zaba mana abinda yafi Mana Alkhairi Amma wani lokacin inda kake zaton alherin ne to sai kaga ba'a Nan yake ba, idan yazo ta inda baka zata ba tunda bakasan gaibu ba, sai kayi watsi dashi idan bakayi sa'a ba haka abun ze kwaranye baka mori komai ba, alhalin Kai ka roka aka baka sai kuma ka Raina abinda aka baka ba tare da kasan shine alherin ba. To Dan haka nake so ki yiwa Allah da manzonsa ki rike abinda Allah ya Baki tunda shi Kika roka Kuma ga abinda ya Baki sai kiyi ta Tahamidi ga Allah kawai, ki nemi Allah ya saka muku kaunar junanku da soyayya da jinkai. Dan kinsan dai idan ba wata kaddarar Ubangiji ba Babu abinda zesa ya rabu dake tunda ya karbi auren Nan wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba yana so, dan haka ki daure kiyi Masa biyayya shi arziki nufin Allah ne, naji ana ta 'yan kananun magamganu ki toshe kunnenki kada ki bada barakar da wani ze kushe Miki miji dan bashi da kudi, Allah ne Mai azurtawa lokacin daya so sai kiga wata Rana sai dai a tada labarin abun".
Sun Dade suna kawo Mata misalai da yawa na irin wannan auren nata daga baya Kuma ya Zama Alkhairi.
********** A matukar gajiye Mahmud ya shigo cikin gidan misalin karfe biyar na yamma tun safe ya kebe kansa a dakin daya Kama na hotel yake ta faman aiki yaso kwarai ya Gama da wuri kafin yamma amma abun ya gagara Dan da gaske aikin ya dauki hankalinsa sosai ga tafiyar dake gabansa Banda Allah yasa wasu abubuwan sun daidaita a jiya da dole tsakanin gobe da jibi dole yabar garin ko baya so. Amma cikin taimakon Ubangiji sai komai ya Fara daidaita, shi kanshi Yana Jin idan ya tsallake ya tafi daidaita wanna gabar Bai kyauta ba Sam, dan jama'a zasuga kamar ya gujewa auren gatan da akayi Masa ne ya watsa musu kasa a idon an Masa gata irin wannan sun dauki yarinyar su Mai tsada sun bashi ba tare da sun San ko waye shi ba, ko la'akari da karancin samunsa suka aura Masa.
Su Habib ya tarar a falon Yana karatun Alqur'ani, Abubakar Kuma Yana ta faman hada Nile sat.
Su duka suka amsa Masa sallamar Nan falon ya aje jakar laptop dinsa abinda bai taba kwatanta zuwa da ita ba kenan Dan duk aikin da zeyi sai dai yayi acan hotel din ya barota, amma yau dole tasa ya taho da ita nan saboda so yake ya raba dare Yana aiki shi yasa ma Kai tsaye ya nufo gidan da ita yasan bashi da matsala dasu duka biyun.
Abubakar ne ya tsaya da aikin Yana kallon Mahmud Yana fadin "Dan Allah Ina ka shiga Wai bakasan kana dagawa Baba malam hankali ba? shifa yafi son daya juya ya ganka, gashi ka Kama ka rufe wayar ana ta Kira a rufe".
Girarsa ta daman ya dan shafa kadan kafin ya zauna Yana fadin "cool down Mana my man Ina kake tunanin zan tafi? Wallahi aikine yayi yawa na wannan NGOs din bakaga har kayan aiki suka bani ba tun zuwan da sukayi wancan karon, yanzu haka ana koya min yanda zanyi amfani da ita laptop din ne yanda zanji dadin aikin, Bari nayi wanka sai muje gurin Baba malam din nayi Masa bayani yanda ze fashimta, sunce ma nan da sati daya ko biyu zasu kiramu zuwa babban taro da za'ayi".
Tunda ya Fara magana Habib ya dakata da karatun da yakeyi yana bin Mahmud da kallo haka nan kawai yaji Kamar ba gaskiya Mahmud din ya fada musu ba, Kamar yana boye wani Abu, shifa tun lokacin daurin aurensa ya lura da yanda Kamar yake baiwa Sameer umarni a wasu lokutan sai idan ya farga ne yakan yi maza ya canza taku, sannan a watannin baya ya taba jin yana waya a kusa da dakin da suke taron abinda ya shafi makaranta lokacin yana duba wasu sabbin forms da aka kawo na Enterprinuership da za'ay a gurin Sam baisan Yana ciki ba tunda kofar a rufe take ji yayi sosai Yana bada umarnin yanda abin ze kasance harda makudan kudin da za'a kashe gurin sawo kayan sana'ar da za'a koyar harda kudin da za'a participants din tunda program din harda matasan unguwa a cikinsa duk za'a Kuma bada kayan sana'ar da mutum ya koya kyauta, tun lokaci yayi masa alamar tambaya sai dai ba wata kafa daya Bari wadda za'a fashimci komai. Bai tabbatar da abinda yaji ba Saida akayi komai Kamar yanda ya bada umarnin, ga Kuma lokuta yawa sai yayi batan dabo ka nemeshi ka rasa Kuma har yanzu baisan takamaiamai Ina yake zuwa ba duk kuwa iya kwakwarsa.
Jakar ya dauka yayi gaba Yana fadin Bari na Dan watsa ruwa na fito. Da ido suka bishi har ya shige corridor din daze kaishi bedroom dinsu,kowa Yana ayyana wani Abu a zuciyarsa.
Ya dauki Kamar minti hamsin kafin ya fito cikin Riga da wando na shadda Fara tas, a gaggauce ya fito ganin lokacin sallar magriba ya kawo jiki.
Da dare Zahra tana dakin Ammah suna Hira da Inna maimuna tana Kara nusar da ita yanayin rayuwa Sajida ta shigo da waya a kunnenta ta gaishe da innar ta Mikawa Zahra wayar tana fadin "Baffan Rimi ne yake son magana dake"
Amsa tayi tare da sallama, cikin daki Inna ta nuna Mata da hannu ma'ana ta shiga ciki tayi wayar, Dan sajidar tana Mika Mata ta juya ta koma, haka Nan ta tashi duk da Bata San nufin innar na hanata waya a falon ba.
Gaishe da Baffan tayi tunda Daman ya Santa tun suna makarantar kazaure sunje masa ita da Sajida lokacin da Zahrar ta zauna a kano gidansu sajidar sanda akayi musu hutun midtrem break maimakon taje Azare sai umman sajidar ta nemi Alfarmar Ammah ta barta tayi hutun a gurinta,to kafin su koma ne sukaje Rimin sumailar gurin kakan sajidar, tun lokacin ya baiwa Zahra magunguna sosai yace tayi amfani dasu har Sajida na mita ita Bai Bata irin na Zahra ba, a lokacin murmushinsu manya yayi Yana fadin "yanda aka saka rayuwarta a gaba ke ba Wanda ya damu da taki rayuwar ita akwai tarnaki Mai yawa a kanta Kuma Naga jikin nata ba wani abun azo a gani na tsarin jiki.
Gaisuwar Baffa ya amsa Yana fadin "Ashe haka lamura sukayita faruwa ko Fadima? Dazu Babar taku tazo min da bayanin abinda ya ringa faruwa dake akan aurenki, yanzu haka tana Nan zata kwana saboda akwai abinda nasa ayi Miki gobe in sha Allah zatazo Miki dasu da yanda zakiyi amfani dasu in sha Allah ba abinda ze Kara faruwa dake, lallai akwai shedancin mutane akan lamarin Amma mu dauka Daman haka Allah yayi nufi, wanin Allah Bai Isa yayi maka komai ba face da izinin Ubangiji, ga Uwar taki ku gaisa".
Ya mikawa Maman Sajida wayar.
Bayan ta gaisheta ta Kara da yi Mata nasiha sosai itama, sannan ta fada mata gobe in Sha Allah daga Rimin Nan zasuyo ita da Babban danta Wanda some times shine direban ta idan zatayi doguwar tafiya, kafin sukayi sallama.
Dakin Ammah Zahra ta shiga ta fada Mata yanda sukayi da kakan Sajida, godiya sosai Ammah ta ringa yi tana Kara jinjina kaunar da bayin Allah nan.suke yiwa Zahra dalilin 'yarsu gashi saboda matsalar Zahrar zata taso tazo har Azare.
Washe gari tunda wuri Zahra da Sajida suka Gama gyaran dakin Ammah sukayi wanka sannan sukayi breakfast gurin karfe Sha daya Maman su Sajida da yayanta Ya Abba suka karaso murna gurin Sajida ba magana, dakin Ammah suka nufa da Maman Zahra tasonsu Fara shiga gurin Mama su gaisa Amma Sajida ta Hana tana fadin "A'a ki Bari mu shiga inda ya kamata idan min Gama abinda ya kawo ta sun gaisa da kowa so kike azo a zaune Mana a hana ruwa gudu".
Tarba ta girma Ammah tayiwa Maman Sajida itama ba wata babba bace Dan Bata Kai sa'ar Ammah ba, an sauki Ya Abba a dakin da suke sauke bakinsu yayin da magaji ya shiga shidima dashi.
Bayan Maman su sajidar ta Gama cin abubuwan da aka kawo Mata suka sake gaisawa dasu Ammah da Inna maimuna ta jajantawa Ammar abubuwan da suka ringa faruwa, ta Kuma Dora musu da bayanin da mahaifinta yayi Mata akan matsalar Zahrar inda ya bada tabbacin ko waye yake wannan shegantakar a kusa dasu yake sosai, Kuma dashi ake faduwa da tashi, kuma yace kada Wanda ya kawo wani Abu da sunan naci kona Sha yace a baiwa Zahra da sunan tsarin jiki ko na gyaran aure a barta taci sannan a kula da Koda abincin cikin gidan ne in dai ba ita Ammar ta dafa da hannunta ta Bata ba daga Nan har tabar gidan.
Wata babbar leda ta dauko wadda sukazo da ita ta bude ta Ciro jarka da ruwa a cikin Mai kalar yellow na za'afaran ta dauko wani garin magani Mai laushi ta hadasu da jarkar ta mikawa Inna maimuna tana fadar.
"Ga wanna ruwan addu'a ne da garin magarya zata dibi ruwan addu'ar ta zuba garin magaryar ta Sha ta shafe jikinta safe da yamma,wannan Kuma kafa da hannu kawai zata Riga turarawa sai Addu'oi da ya bada a Bata zata ringa karantawa safe da yamma".
Godiya sosai su Ammah suka shiga jerawa Maman Sajida Kamar ba gobe har sai da ta ringa fadin "Haba Hajiya meye amfanin taren abinda ya shafi Zahra ai ya shafi sajida wallahi shekaranjiya data Kira ta fada min hankalina ba karamin tashi yayi ba wallahi na dauka abin ya kwaranye tunda an dauki dogon lokaci kafin a Kara maganar Auren".
"Wallahi kuwa muma mun dauka na bayan da aka fasa ko matsalar namijin Aljani ne ya aureta Amma duk inda akaje da ita sai a ce ba wani iska a jikinta".
Inna maimuna ta fada.
Sun tattauna sosai da Maman Sajida Saida akayi sallar Azahar Sajida ta raka mamanta dakin Mama su gaisa, sun Sami kawar Mama Asabe sun hada Kai suna kus-kus bazaka taba cewa da mutane ba.
Sun gaisa sajida ta fadawa Mama mamanta ce, Basu jima ba suka fito Mama ta biyosu har kofar part dinta Nan godiyar ziyarar.
Sai kusan karfe uku su Maman Sajida suka juya Kano Sajida tace ita saita raka Zahra gidanta zata dawo.
Tun da Mahmud ya Kira Zahra sau daya Bai sake kiranta ba, yau yaji ya kamata ya Kira yaji lafiyar ta ko banza fa yanzu tana karkashin ikonsa ne cinta da Shanta da duk lamuranta suna wuyans Kuma ai Bai kyauta ba gaskiya ace yayi burus da lamarin ta abun sai yayi Mata yawa.
Sai gurin Tara na dare ya lalubo numbarta ya Kira, harta gama ringing ba'a dauka ba sai kawai ya share ya tura
Mata text massage ya fada Mata Daman ya kirane yaji lafiyar ta.
Tun bayan tafiyar Maman Sajida Ammah da Inna maimuna suka shiga hasashen abinda kakan Sajida ya fada na hasashen Mai yiwa Zahra bita da Killin nan duk iya nazarain su Basu gano ba sai suka.barwa Allah amma dai innar ta soke kwanan Zahra a can gurinsu tace su dawo dayan bedroom din Ammah suna wanna ita da Sajida da ita innar ya ishesu ita ko katifa sai a saka Mata a kasa ta kwanta.
Hakan akayi su Zahrar suka tattaro suka duk wani Abu na amfaninsu suka dawo dakin.
Kafin su kwanta Saida Inna maimuna ta saka Zahra tayi amfani da duk magungunan da Maman Sajida ta kawo Mata, wanna ne dalilin dayasa innar tace su dawo nan tunda komai na duniya Yana son sirri, duk da Hameeda ce kawai ke kwana a tare dasu Zahra Dan Salma tunda suka dawo ma Bata taba kwana a part din nasu ba.
Tun Hameeda na jiransu Zahra su shigo har tayi barci.
Saida Zahra ta Gama amfani da duk abubuwan da aka kawo Mata sannan ta dauko wayarta rabon data dauko ta tun bayan sallar Azahar data hau online ta duba sakonnin whatapps.
Sajida da Inna maimuna Kuma sunta hirar duniya abunsu.
Missed calls ta gani har hudu uku na mujiba ne sai Kuma wani daya number ce amma kallo daya tayi Mata ta gane ta waye, ji tayi gabanta ya fadi to neman me yake Mata da wanna tsohon Daren haka kawai ya dagula Mata sauran lissafinta. Fita tayi daga call history din sai Kuma taga envelope alama massage ya shigo budewa tayi sakonsa ta gani a hankali ta furta ta "Ya salam".
Allah da gaske fa take jin wani irin lamari a tare da shi.
Da safe ma innar ta saka Zahrar gaba Saida tayi duk abinda ya kamata kafin ta fice tabar dakin dan tun kafin ta Fara Sajida tayi waje ta Basu guri. Saida tayi wanka kafin ta fito yin break bayan sun gama ne Ammah tace Zahra taje Abbansu na kira, gyalen rigar ta yafa a kanta ta nufi gurin Abban, lokacin data shiga ya Gama break Shima, guri ta Sami ta zauna kusa da kujerar da yake Kai tana fadin "Abbana Ina kwana?"
Jaridar dake hannunsa ya aje Yana fadin "lafiya kalau uwata, Ina fatan ba wata damuwa ko?"
Kai ta gyada kafin tace "ba komai"
"Masha Allah ya fada.
Kafin yayi gyaran murya ya Fara fadin "Uwa inaga in sha Allahu jibi da yamma Zaki tafi gidanki Dan dazu ne malam Bukar ya roki wannan alfarmar saboda shi Mahmud din ne zeje wani taron da kunyar da suke aiki dashi suka shirya to Kuma yace baya son ya tafi Baki tare acan gidan ba kada abin ya Zama na magana ace ko ya gudu ne ya barki a nan, to Nima din na karbi nasa hanzarin tunda Masha Allah jikin naki yayi sauki sosai Kuma Baki bani kunya ba kin kwantar da hankalinki".
"To Abba"abinda ta fada kenan tayi shiru, Mamace ta shigo dakin itama Tasha wanka sai baza kanshi take Kamar Kullum. Da barkwwnci ta shigo tana fadin "A'a bamu Gane ba, irin wannan kebewa tsakanin 'ya da uba mu ba'a neman ayi shawara damu".
Ta fada tana fadada murmushinta.
Gaisheta Zahra tayi kafin mamar ta gaisheta da Abban tunda ba itace da girki ba.
Bayan sun gaisa ne yake fadawa mamar "Ba wani shawara muke ba wadda Bata shafeku ba Ina fada Mata ne jibi in Sha Allah zata tafi dakinta tinda Allah yasa ta warrare Kuma shi mijin nata ne zeyi tafiya shi yasa nake son ta tafi dakinta".
Nisawa Mama tayi kafin tayi magana.
"Kamar Yaya zeyi tafiya daga Kai masa yarinya basai ya tafi da ita ba salon ya cuci yar mutane ya lallaba ya budu ya barta tunda tsintacciyar mage ai Bata mage, gaskiya Abban Yara ka tsaya ka duba lamarin nan Mana kada fa azo ana Dana sani kaga masu iya magana na cewa keyace".
Abban ne yace "ba abinda ze faru sai Alkhairi Amma Jibi da izinin Allah uwata zata tafi dakinta, tashi kije Uwata Allah yayi Miki Albarka yanda Kika yi min biyayya Ubangiji ya Baki 'ya 'yan da zasu yi Miki biyayya kema".
A zuciyarta ta amsa da "Amin"
Saida Abbai yaga ta fice gaba daya sannan ya dawo da dubansa gurin Mama yace "haba Rabi'a har yaushe Zaki dinga magama irin wannan a gaban kankanuwar yarinya Kamar Zahra ai Bai kamata ba ki duba kiga yanda aka dunga walagigi akan auren yarinyar nan a baya yanzu Kuma anyi aure Zaki ringa fito da maganganun da zasu iya sakata a wani Hali ai kwantar da hankali uwata take bukata ba irin haka ba, mu bita da addu'a in sha Allahu Alkhairi na hada Wanda a gaba duka sai sun gode min koda kuwa bana duniyar ne".
Tunda Zahra ta shigo ta kwanta a kan sofa a nan falon Ammah na kallonta tasan kan zance dan tunda Abba ya dawo daga masallaci ya fada Mata, zancen da suke da Inna ma kenan ta shigo suka bar zancen.
Da hantsin Ammah ta Kira Aunty Hasana ta fada mata.
Zuwa Sha biyu tana gidan suna zaune a falon Ammah Mama ta shigo ita da kawarta ta amana Asabe wadda kwanan Nan ta mayar da gidan gurin zuwanta sabanin baya da sai a share watanni Bata zoba, Nan suka zauna akaci gaba da tattaunawa akan tarewar Zahra har Asabe ke fadin zata saka wata 'yar gusau da suke makwaftaka ta yiwa Zahra hadin kazar amare da daka shine nata Gudunmawar.
Da yamma Aunty Hasana ta umarci Sajida da Hameeda da zilai Mai aiki suzo suje gidan Zahrar a gyara abinda ya kamata tunda jeren ya dan jima da yi.
Sun fito zasu tafi ne Abdul Hakeem ya tsayar da Auntyn Yana fadin "sai Ina Kuma Aunty mu?"
"Gidan Zahra zamuje a Dan Kara gyarawa jibi Abba yace za'a kaita kaga kuwa ai dole a shiga a duba ayi abinda ya kamata".
Komai tsab suka sameshi da gani ana gyarawa Kullum dan har wani hadaddan kamshin freshner ke tashi a falon haka bedroom din Shima komai neat yake a toilet ne abin ya bawa Aunty Hasana mamaki an zuba kayan wanka masu azabar tsaba Bata Kara tsinkewa da ta janyo locker ta jikin mirror taga wasu designers din turaruka na Mata Kuma da yawa na kamfanin Al -haramain ne harda irin Wanda Zahra take amfani dasu.
Ita dai Hameeda Yar kauye ta Zama a gidan Dan ko a mafarki Bata taba kawo Wanda aka aurawa Zahra, ze Kama hayar gida irin wannan aljannar duniya haka ba.
A kitchen ma Nan Hameeda da zulai suka lalace komai na gurin saiya burge mutum, Nan ma Saida Auntyn taga wani fregde ash colour a cikin Dan ack din jikin kitchen din irin Mai kofa Kamar ta wadroof ko ba'a fada ba kasan kudi sunyi kuka a gurin.
Burner Auntyn tasa aka jona aka zuba turarikan wuta Wanda aka hadowa Zahra daga Saudi Arabia tun wancen lokacin tunda basa komai saima Kara kamshi. Basu baro gidan ba sai kusan magariba.
Aunty Hasana taso ta wuce da Zahra gidanta amman Ammah tace A'a ba inda zata so suke ace Mata tsohuwar banza idan so suke su tafi to ita zahrar ta Kira ta fadawa mijinta idan ya amince ita nata Mai sauki ne ita kuma Zahra tace lahlah a barshi kawai.
Wajen goma saura aunty Hasana ta dauki yaranta suka wuce gida. Da safe Saiga Asabe da dahuwar kazar amare da jarkar zumar Mata da ta tsimi tayiwa gidan tsinke, part din Ammah ta shigo direct, bayan sun gaisa ne ta mikiwa Ammah babbar ledar data zubo kayan tana fadin "Ina Amarya tazo gashi na cika Alkawari tazo ta cinye ta bani kashin tace a koma Mata dashi zata hada Mata wani Abu dashi. Inna maimuna ce tace "ai kuwa yanzu taci abinci ta shga daki saidai a aje zuwa anjima sai taci ko gida ne sai a aika Miki da Qashin, mun gode kwarai madallah Allah yabar zaman tare". Asaben ta amsa da "Amin ai bama sai an tashi mutum ya kaiba Nima saina jira taci din ko Nan da yamma ne" ta fada tana mikewa tayi musu sallama ta nufi dakin Mama.
Bayan fitarta ne Ammah ta dubi Inna maimuna tana fadin "nifa jikina Bai bani ba akan taci wanna abun Dan ni tunda ta fada jiya naji abin Bai kwanta min ba,mutuniyar da gaisawa ma sai ta kure akeyi da ita Amma fa ki duba sai wani rawar jiki take akan abinda Bai shafe ta ba ko alama, Kuma kar nice wani abun arziku sukeyi da zahrar Dan ko gaisawa saita kure, Amman ki duba ki gani yanzu sai haba haba take da Zahra.
Dakin Ammah aka shiga da kayan ammar tace zata cire tsokar tabar musu kashin, hakan ne ya kasance tayi komai ta baiwa auta ya kaiwa Asaben dakin Mamar.
Saida Asaben ta tabbatar auta ya fito ta kwashe da dariya tana fadin "wallahi Maman yara kinsan ta kan mugumta, yarinya har yarinya amma ta Kare a auren marar asali Wanda ko danginsa ba'a sani ba"
Kwafa Maman tayi "barni kawai Asabe wallahi tun lokacin da aka dauko yarinyar nan hankalina ya kasa kwanciya, saboda babu ta inda Allah ya rageta duk abinda ake so jikin 'ya mace to Allah yayi Mata ga uwa uba yanda mazan zamanin nan suka jarabtu da son Mata irinta nasan ba karamin mutum ne ze dauke taba Ina zaune sai dai na Zama 'yar kallo ga nawa 'ya'yan a gabana, wallahi baze yuwu ba ai hankalina Bai Kara tashi ba Saida na raka Aunty Ladi gurin wani Mutum a can jos nayi Masa maganar Asma'u to cikin binciken ne maganar yarinyar ya Fado yake fada min na kyale maganar Asma'u don ba yanda zanyi da ita jikinta a shirye yake haka Shima Alhajin ba abinda zeyi tasirin da ze rabashi da ita, Amma ga wata yarinya Nan duk gidan ba 'yar da zata wuceta a sa'ar rayuwa a gurin aure Dan mijin da zata aura ba karamin mutum bane Kuma dai..... Sai kawai bawan Allahn Nan yayi shiru da bakinsa nayi nacin duniyar nan Amman yaki karasa mana zance, haka muka tasho Aunty Ladi nata zugani kada na kuskura na Bari ta auri Mai maiko duk yanda zanyi nayi Naga hakan Bata faru ba. Nayi ta fama duk Wanda zezo gidan Nan gurin yarinyar nan zezo duk kuwa da Fadi tashin da nake akan su Salma amman a banza, maganar dai daya ce Zahra, ni Kuma nayi Alkawarin badai Zahra tayi aure ta barmin Yara a gida ba,Kuma badai ta auri Mai rufin asiri ba, gashi kuwa ta Kare a Wanda ko asalin kirki bashi dashi Abu daya ya tsaya min a Rai yanda Naga gidan da zata zauna da abin yaso razani sosai Dan ba haka na zata ba, amman duk da hakan ma yayi tunda ai gidan ma Malaminsa ne ya bashi aro su zauna, Kinga kuwa karshe sai dai a Kare a yawon haya cikin Yama yamar matan alarammomi, Kuma wannan kayan da ake qafafar an saka a gidan karshen wasu kayan saidai a sayar Dan Babu abinda za'aci dasu Dan an sawo da zimmar su tafi Abuja sai gasu sun Kare a gidan Alaramma".
Ta fada cikin izgilanci.
Duk yanda Zahra taso ta kwantar da hankalinta abin ya faskara dan da gaske zulumi takeyi na yanda zata fuskanci wannan sauyin da yazo Mata a bazata Wanda Bata tab'a tunanin hakan ba ko cikin mafarki, lallai tayi zaton daga kan Mushahu komai ya kwaranye Amma sai wata matsalar ta taso wadda tafi ta baya.
A kwance ta wuni duk ta tsangwami kanta Sajida sai tausarta take duk da itama tata zuciyar a kusa take Dan da gaske tana tausayin zahrar ba kadan ba.
Gurin karfe biyu ne sukaji alamar Kamar anyi Baki a gidan da alama ma da dan damarsu.
Sajida ce ta fito ta gaishesu zata koma cikin ne Ammah tace taje ta Kira Mama tace tazo su gaisa da Baki Iyayen Musbahu ne daga kano.
Ta fita tana mamakin to meya kawo su Kuma.
Tare suka shigo da mamar Dan sajidar na fada Mata ta nufo dakin cikin rawar jiki.
Ciki Sajida ta wuce yayin da mamar ta zauna tana gaishe da bakin nasu Kafin Inna maimuna ta Fara Mata bayanin Maman Musbahu ce tazo da 'yan uwanta ta bada hakurin abinda ya faru Wanda ita kanta Bata San yanda akayi ba sai daga baya ake fada Mata shine tazo taji ko da yanda za'ayi a gyara matsalar tunda ta dawo hayyacinta take cikin damuwa domin kwata kwata Musbahun baya cikin nutsuwarsa tun bayan samun labarin an Aurar da zahrar, ganin lamarin nasa ba sauki ne yasa suka nufo nan Ashe har da yaron sukazo sun jima a gurin Alhaji ma kafin su shigo nan din, hakuri kawai ya basu akan aikin Gama ya Gama tunda yanzu matar wani ce ita.
Kallonsu Mama ta karayi tana tambayar "Ina mamar tasa take"
Hajiya Nafisa kanwarta ita ta nuna Maman Musbahun tana fadin "gata nan"
"Ayya Allah sarki Hajiya sai hakuri Allah Bai nufa matarsa bace ba sai dai yazo ya duba wata tunda da sauran yaran a gidan".
Mama ta fada tana kafe Hajiyar da ido.
"Kayya a yanzu dai bana tunanin haka zata yuwu sai ko a gaba tunda ban taba ganin abinda Musbahu ya kwallafawa Rai ba Kamar auren yarinyar nan tunda kuwa ya rasa ta bansan Kuma lokacin da ze Kara maganar wani auren ba".
Sun Dan Jima kafin Ammah ta tashi ta shiga gurin su zahra tace ta fito su gaisa da Baki zasu tafi.
Jiki ba kwari ta nufo kofa doguwa rigace a jikinta kirar Bahrain Mai duwatsu har kasa blue black gyqlenta kwai ta Dora a kanta Dan Sam Zahra Bata fiye son saka hula ba a kanta Dan Sam santsin gashinta baya Bari hular ta zauna ta dunga zamewa kenan.
Cikin takunta na nutsuwa ta shigo falon hade da sallama Kanta na kallon kasa ta karaso cikin nutsuwa ta zauna gefen Ammah a kasa kan carpet, tunda ta shigo suka bita da idanun kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa.
"Masha Allah! tubarakallah 'yata matso kusa dani dole my son yayi kamar ya zauce da labarin rasaki ya riskeshi" abinda Aunty Nafisa ta fada kenan tana nunawa Zahra kusa da ida, jiki ba kwari ta karaso ta zauna tana gaishesu.
Suka amsa jiki a sanyaye su kansu sun San dansu yayi wani babban rashin da maida shi sai nufin Allah, tunda Daman shiya hada shi da Zahrar kuma shiya raba lokacin daya so.
Nan sukayi sallama suka fita cikin matukar jimami Dan da gaske sunyi rashin sirika.
A daki Zahra kwanciya bayi ta rufe fuskarta da hannu biyu Batasan lokacin da hawaye ya zubo Mata ba, Wai shike nan komai ya Zama past tsakaninta da Musbahu duniya ba tabbas. sajida na kallonta Bata hanata ba Dan itama Saida ta matse, lokacin zahra na falo Mushahun ya Kira wayar ta, sajidar ta dauka yanda taji maganarsa ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba kuka yake shima da idanunsa Dan abinda ya fada kawai ya karya Mata zuciya, kalamai ne na bankwana ga masoyi da da given off akan Abu, da kyar ta iya fada Masa ba zahra bace itace magiya yayi Mata dan Allah ta fito Masa da zahra yayi Mata sallamar karshe Amma hakuri kawai ta bashi tunda yanzu Zahra matar aure ce bashi da hurumin yin magana da ita.
Sun Dade a haka kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa nkafin su jiyo maganar Magaji Yana fadin "Ammah ga Ya Mushahu zaku gaisa yazu tafi ne".
Su biyu suka shigo suka gaishe dasu Ammah a nan Inna maimuna ke fadin "kayi hakuri da hukuncin Allah kaji kada kayi fushi da mahaifiyar ka itama bayin kanta bane duk uwa bataqi ace danta yafi kowa sa'ar abokiyar Zama ba, irin wannan matsalar ta Jima tana bibiyar yarinyar Nan to munyi zaton daga kanka abun ya Kare sai Kuma ya canza salo akan mahaifiyar ka, kayi hakuri ka fawwalawa Allah komai shi ze baka wadda tafi Zahra daman Allah hukunta kai ba mijinta bane ayi hakuri".
Kansa Yana kasa tunda ta Fara maganar wani Abu ya tsaya masa a makogwaro yaji Sam ya kasa magana sai Aliyu ne ya amasa da "ba komai Mama haka Allah ya nufa, Allah ya Basu zaman lafiya mu zamu koma".
"To Allah ya tsare ya baka mace ta gari wadda zata maye maka gurbin Zahara'u" Inna ta fada ita kuwa Ammah kasa magana tayi dan da gaske yaran tausayi suke Bata sun kwallafa Rai da juna Amma akayi musu karan tsaye, a zuciyarta ta ayyana "Allah ka biwa yaran Nan hakkinsu duk Mai hannu a cikin Bata lamarin Nan kayi Mana sakayya da gaggawa Dan isar Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w."
Ta window zahra ta leka lokacin da suka fito daga falon kamar ance ya juyo sai ganin zahrar yayi tana kallonsa da sauri ta juya ta rufe fuskarta da hannu ta saki wani marayan kuka ta zube a gado. Su Kuma suka fita zuciyarsa Kamar zata Kama wuta dan ganinta ba karamin fami ya zamar Masa ba, har ji yayi Yana wani layi Kamar ze fadi.
Magaji ne ya shigo falon Yana fadin "Sun tafi, wallahi Ammah naji tausayin Ya Musbahu sosai kinsan har gurin Baba malam yaje Amma magana daya dai kowa yake fada masa yayi hakuri, bayan mun fito ne yace na nuna Masa mijin Aunty zahrar na fada Masa ai shine suka Fara gaisawa dashi bayan sun gaisa da malam, shiru yayi sai kawai Naga ya dafe kansa Yana girgizawa, yace na hakura da zahra nasan wannan baze taba sakin zahra ba. wallahi Ammah sai Naga yana goge hawaye gaskiya Allah saiya saka musu wannan ai zalunci ne Kullum idan Aunty zahra ta samu miji sai an samu matsala".
Ya fada Yana Jan tsakin takaicin.
"To magaji babu yanda za'ayi haka Allah ya hukunta sai hakuri".
Bayan tafiyarsu da Kamar awa daya Abdul Hakeem ya shigo ya fadawa Ammah tazo Abba Yana kiranta.
A bedroom dinsa ta sameshi Yana tsaye ya goya hannunsa a baya Yana Dan Kai kawo a tsakar dakin.
Sallam tayi Masa ya amsa sannan ya sauke hannunsa ya nufi gefen gadon inda Ammah ta zauna tana tambayar "Lafiya kuwa Abba meya faru Naganka a haka?"
Ajiyar zuciya ya sauke Yana fadin.
"Da matsala gaskiya yaron nan ne yazo a rikice yana kuka Kamar yaro karami da kyar muka lallashe shi nida Abdul Hakeem ga mahaifiyarsa da 'yan uwanta kingansu dai nasan mazan ne suka ce ba ruwansu shine ita da kanta ta taso tazo wallahi hawaye bibiyu ta rinka yi min akan na rufa Mata asiri na warware wancan auren a maida kan Musbahu abin har abin tausayin wallahi, shi yasa na turosu cikin Dan ku Basu hakuri tunda wancen zance ya wuce Kuma ji nayi da nauyi na Kira malam wallahi tunda ganin Mahmud nake Kamar Dan cikinsa Kinga na Kira shi akan maganar ai Bai kyautu ba, to bayan sun tafi ne Abdul Hakeem ya Kira Hassan ya fada masa shine ya kirani Yana min magiyar Dan Allah a rakata dakinta yau basai gobe ba da tun farko ma ankaita da hakan Bata faru ba yasan wasu ne daga nan zasu Gaya Masa tunda Yana da mutane sosai suce ai tana gida ma yayi bata tare ba suyi tunanin ko Babu auren ne, Dan haka Nima nayi na'am da maganar tasa, kuje kuyi duk abinda ya kamata da magariba zan mikata dakinta da kaina in Sha Allah, na Kira malam ma na fada masa."
"To hakan yayi duk abinda ka yanke dai dai ne Allah ya nuna Mana lokacin".
"Amin ya amsa"....

AUREN HUCE HAUSHI


MAMAN FATIMAH.
PAGE SEVENTEEN (17)
_________ Karfe biyar mai kyau motar da Alhaji Jafar ya tuko da kansa daga shi sai Zahra a ciki daga bayansa Kuma Abdul Hakeem ne a wata motar ya biyo Abban nasu bisa umarninsa,suka dira kofar gate din gidan Zahra,sau biyu Abban yayi horn Mai gadin ya leko da yaga Alhaji ne da kansa tunda daman ya San Alhajin farin sani yayi sauri ya bude kofar suka shigo gaba daya, da sauri Mai gadin ya karaso Yana budewa Alhajin kofa Yana gaishe shi yayin da Abdul Hakeem ya budewa Zahra ta fito suka zagaya Gurin da Abban yake, Abdul Hakeem suka gaisa da Mai gadin sannan Abban ya Kama hannun Zahrar ya nufi kofar main falon da ita, tasha farar laffaya Mai adon kananan flowers pink, jikinta kamar an Mata barin turare sai tashin kamshi take Mai Dadi. A bakin kofa suka Hadu da Mahmud din ya nufo kofar da sauri Dan Yana bedroom dinsa yaji shigowarsu tun bayan anyi la'asar Baba malam yace Alhajin yace ya same shi a can gidansa da yamma za'a kawo Masa iyalinsa.
Matsawa Mahmud din yayi daga bakin kofar Yana yiwa Abban sannu da zuwa sannan ya mikawa Abdul Hakeem hannu suka gaisa, kan kujera Abban ya zaunar da Zahra sannan ya umarci Mahmud daya zauna kusa da ita shi Kuma ya zauna a kujerar dake kallonsu, Abdul Hakeem Shima ya zauna, sai falon ya dauki shiru, gyaran murya Abban yayi kafin yace "Abdul Hakeem yi Mana addu'a' bayan yayi doguwar addu'a sun shafa Abban yace "To Mahmud ga matarka nan na kawo maka bani na baka ita ba Allah ne ya baka ni nawa idawa ce, gata Nan amanace a gurinka kada ka zalunce ta duk inda yanayin rayuwa ya kaiku na baka ita ne saboda na yaba da nagartarka na Dade Ina monitoring dinka ban tabaji ko ganin abun ashsha ba a tare da kai, kullum addu'ata Allah ya bani ikon sauke nauyin marainiyar Allah dake hannuna, kuma Alhamdulillahi na sauke gata nan marainiya ce Bata da uwa Bata da uba ba wa ba kani ita kenan iyayenta duka suka rasu suka barta, kada ka zalunce ta Dan girman Allah ka tausaya Mata saboda Mai rauni ce, ka zamar Mata uwa uba abokin Shawara kuyi dariya tare kuyi kuka tare ka jibinci lamarinta gwargwadon iyawarka. Ina Kuma Kara gode maka bisa share min hawayena da kayi baka watsamin kasa a ido ba lokacin Dana baka aurenta, na gode kwarai Allah ya saka maka da Alkhairi ya yaye maka damuwarka ya kawo maka mafita a bisa lamuranka".
Suka amsa da "Amin"
Sannan yaci gaba da fadin "ke Kuma Uwata ga mijinki nan kiyi Masa biyayya abisa abinda Bai sabawa Allah ba, ki girmamawa shi ki kiyaye bacin ransa ki kiyayie mutuncinsa da rike Masa sirrinsa kindaraja mas iyayensa da 'yan uwansa lokacin da Allah ya hukunta ku hadu dasu,nkiji tsoron Allah a cikin zamanta kewarku ki saka hannu ki Barbi duk abinda ya biyo bayan aurenki dashi Mai Dadi ko sabanin hakan. Dan Allah ki kwantar da hankalinki kiyi hakuri da abinda Allah ya hukunta a kanki komai Kika gani rubutacce ne daga Allah sai dai mu 'yan adam mu karasa shi, Amma tun ran gini tun ran Zane dama haka kaddarar take, ko shi mijin naki idan yayi nazari zega wata kila wannan kaddarar auren ce ta rabo shi da asalin inda yake, to Dan haka kowa ya rike tasa kaddarar wata Rana sai labari komai na duniya Yana da iyaka ikon Allah ne kawai bashi da karshe, Allah yayi muku Albarka ya kauda fitina a tsakaninku ya tabbatar da Alkhairi a cikin rayuwar aurenku, Mahmud sai anyi hakuri da Mata su masu rauni ne kwarai da gaske".
Tunda Abba ya Fara magana yaji kamar ya dauko wani gaigimemen dutse ya Dora Masa aka.
Cikin ladabin da baisan Yana dashi ba ya furta "in Sha Allah Abba ba wata damuwa Kuma amana na karba na rike Allah ya bani ikon saukewa nike da godiya Allah ya saka da Alkhairi ya Kara Nissan kwanaki masu Albarka"
"To Masha Allah, Abdul kayi Mana addu'a mu tafi kada almuru tayi Mana a nan, Uwata ki daina kukan Nan haka bana sonsa kiyi hakuri kowa da haka ya girma Allah yayi Miki Albarka, ga makullin motarki wadda mukazo da ita takice na sai miki, kudin dayar ta wajen Abbie suna gurin Alhaji muttaka tunda aka sayar da ita nace ya juya Miki kudin zuwa lokacin da za'a bukaci wata motar Dan haka in Sha Allah cikin sati Mai zuwa za'a kawo Miki dayar ma".
Suka tashi suka fita Mahmud yayi musu rakiya har gurin mota Saida suka tafi sannan ya dawo ciki, a inda ya bar zahrar anan ya sameta ta kwantar da kanta a kan cinyoyinta tana kuka Mai tsuma zuciya a hankali ya zauna kusa da ita yasa hannu ya dago kanta daga jikin cinyoyinta idanunta a rufe sai tsiyayara da ruwan hawaye suke. Ba zato ba tsammani kawai taji ya sakata a girjinsa ya kwantar da kanta ya saka hankici Yana share Mata hawaye, daya hannun Kuma Yana tapping din bayanta kamar yanda ake yiwa yaro idan ana so yayi shiru Yana kuka, jikinta gaba daya ya dauki rawa ta taso da niyyar zare jikinta Dan wani Abu takeji duk ilahirin jikinta Amma Dan bawan Allan nan yayi kememe yaki sakinta ba arziki ta hadiye kukanta, sai sauke ajiyar zuciya kawai ba kakkautawa saida ya tabbatar ta Samu dan nutsuwa sannan ya saketa Yana fadin " sorry Baby ki daina kuka bana son kuka Sam koda kuwa na karamin yaro ne".
Hannunta ya Kama ya mikar da ita ya nufi daya daga cikin bedrooms dinta guda biyu da suke mallakinta, Saida ya zaunar da ita a gefen makeken gadon sannan ya juya ya nufi kofa Yana fadin " it's time for prayer"
Ya fice Yana ja mata kofa.
Sai ta dauki kusan minti biyar kafin ta Samu kuzarin warware Laffayar dake nannade a jikinta, doguwar rigar material ce a jikinta anyi Mata dinkin fitted gown tayi Mata kyau sosai kofar data gani ta nufa tasan toilet ne, lokacin data shiga abin ya girgizata irin kayan amfanin data gani a ciki ita ba bakuwar abin bace tasan ba kananan kudin aka narkar ba a cikinsa, abin ya Bata mamaki sosai sai dai wa zata tambaya? ta Jima a ciki kafin ta dauro alwala ta dawo dakin.
Ido ta ringa wurgawa ko zata ga sallaya tunda ita dai bakuwa ce a dakin can gefen sofa taga wani stool kamar coffee table da sallayun akai ta shimfida ta Fara sallah.
Tana cikin sallah ne taji kamar karar door bell kamar sau biyu, Saida ta idar ta tashi ta fito har lokacin tana share hawaye jefi- jefi, gurin kofar ta karasa ta bude Sajida da Hameeda da Mujiba ta gani ai batasa lokacin data fada jikin Sajida ba tana dakin kuka Mai tsuma zuciya.
Ciki suka shigo Sajida na fadin "haba bestie wallahi Dana San har yanzu baki daina kukan Nan ba da bazamu biyo bayanki ba, haba Ashe bazaki karbi kaddara yanda tazo Miki ba? ki Kuma godewa Allah a kowane Hali Kika Samu kanki, bake Kika halicci kanki ba ballantana ki tsarawa kanki yanda Zaki rayu, kin taho kina kuka duk kin dagawa Ammah hankali itama, kin kyau kenan? haba kiyi hakuri Dan Allah ki share hawayenki wallahi nasan yanzu zuciyar masu binki da mugun nufi tana can kamar zata fashe Dan ba haka suka soba duk da bansa daga Ina matsalarki take ba, ai kodan makiya kin kwantar da hankalinki ki rungumi mijinki ki ba mara d'a kunya, Amma kin tsaya kina wani Abu kamar wata karamar yarinya"
Tayi tsaki tana kallon zahrar da tayi kozai kozai ido ya kode Mata abinka da farin mutum.
Suma su Hameedar ban baki suka dunga yi Mata, da kyar ta hadiye kukan ta kallesu tana fadin "wallahi bazaku Gane bane ni kadai nasan me nakeji, komai ya kwance min Sam duniyar bata mun dadi".
"Hakurin dai zakiyi ki Kuma yawaita addu'a in sha Allah komai ze wuce kamar ba'ayi ba, muda muke son next year by now mu dawo suna".
Sajida ta fada tana murmushi.
Wani kallo zahrar tayi Mata ta juya kanta gefe tana fadar "Allah ya kiyaye min wata haihuwa can".
Mujiba ce ta kwashe da dariya tana fadar "A'a Banda cika Baki dai 'yan Mata Nan da labari yasha banban zamu tsinceki kina faman 'yan amaye amaye, lokacin ne Zaki gane Baki da wayo ko ba wata haihuwa can ba?".
Zumburo Baki tayi tana fadin "sai kiyi Kuma haka kawai Zaki jaza min, wani ciki ko dadin fada ma Babu".
Saima zahrar ta zame ta kwanta, tana jinsu suna ta faman zolayar ta har aka Kira sallar insha'i a Nan sukayi sallah kafin su shiga Kara gyara Mata Fallon da Kara masa freshner da turaren wuta Hameeda ta Kara karfin A C a falon ta gyara cutains din, bedroom din data fito suka shiga Mujiba bakinta ya kasa shiru tunda dai suka Samu zahrar ta daina 'yan koke koken sai ta balle da santin gidan Dan bayan sun idar da sallar ba inda Bata shiga ba ta leka can ta shiga can bedroom din Mahmud ne kawai Bata shiga ba tunda a rufe yake, fada take "wallahi zahra ki Kara godewa Allah, irin wannan haduwa haka wallahi ko makiyi Saida yaki fada Amma dai duk wani gata kin same shi sai dai fatan zaman lafiya kawai".
Ita dai Zahra ba baka sai kunne.Dan ita kadai tasan abinda ke Kai komo a zuciyar ta, su inda suka dosa daban ita inda ta dosa daban, ko tayi musu bayani ba ganewa zasuyi ba, domin su duka ba wadda ta tab'a shiga irin gararin data shiga, rayuwa Rumi rumi saika Gama sakankancewa da mutum Rana tsaka Abu ya lalace, uwa uba ganin da tayiwa Musbahu ba karamin famu yayi Mata ba, saboda da ta cire shi daga ranta kwata kwata ta hakura, Amma tana ganinsa komai ya rikice Mata da tana zargin kamar da niyya mamansa tayi haka saboda ya taba fada mata Maman nasa taso ya auri 'yar Yayarta shi Kuma ya ringa sharewa ana haka ne Allah ya had'a shi da zahrar abinda ya kawo karshen wancan dambarwar kenan. Amman tasowar mamansa da 'yan uwanta dashi kanshi takanas ta kano har Azaren don bada hakuri da neman gyara idan lamarin Mai gyaruwa ne, sosai abin ya tashi hankalinta, wata sabuwar soyayyar sa ce ta sake bijiro Mata idan tana tuna yanda yaci buri a irin wannan ranar da za'a kawo Masa ita a matsayin matarsa ta sunna halalinsa, irin abinda yake fadin ya tanadar Mata ita a wancen lokacin idan Yana fada kamar zata nitse kasa dan kunya Amma shi ko a jikinsa.
Wasu sabbin hawayene suka zubo Mata masu zafi tana ayyana shike nan komai ta Zama tarihi, ga inda kaddara ta kawo ta gurin da ba'asan darajarta ba ko alama sai aukin taba Mata jiki da yake Wanda ta fashimci hakan tun haduwarsu ta farko, ba kunya ya wani saka hannu ya rungumota Wama ya sani ko Dan duniya ne aka hadata dashi, tunda ance ba Wanda yasan asalin sa kuma tasan yanda yake din nan ko bashi da sisi mata zasu ringa kawo Masa rida tunda sun ganshi smart dashi.
Wani tsaki tayi tana ayyana to Ina ruwanki da wani smartness dinsa.
Mahmud Bai dawo gidan ba sai bayan sallar insha'i ganin takalma yasan akwai baki cikin gidan baya raba daya biyu 'yan uwanta ne ko kawaye, dakinsa ya wuce yayi wanka ya canza kaya ya fito falo, bai shiga dakinta ba daga inda yake yana jiyo mganganun bak'in, ita dai baiji tata maganarta ba Sam Zama yayi yana daddana wayar hannunsa.
Acan Kuma dakin Zahra Ya Abdul Hakeem ne ya Kira wayar Sajida Yana fada Mata su fito su tafi ya dawo daman lokacin daya basu kenan bayan sallar insha'i lokacin daya kawo su.
Sun fito falone suna zolayar Zahra Basu kula da mutum ba sai da suka sauko daga steps din da ze sada ka da corridor din bedrooms din suka ganshi a zaune Yana ta faman Danna waya, kallo daya Zahra tayi Masa ta kauda Kai haka kawai taji gabanta ya fadi, ta rasa wace irin masiface wannan.
Kansa ya dago yana amsa gaisuwar su Sajidar Yana fadin "har zaku koma ne?".
Hameeda ce tayi farat tace "To ba dole mu tafi ba yallabai tunda angon yaki zuwa ya sayi bakin amaryarsa ba Yana ganin Mai araha ce bai Sha wahalar komai ba aka bashi ita".
Ba Zahra da aka ciwa fuska a fakaice ba hatta Sajida da Mujiba Saida sukaji kamar kasa ta nutsa dasu a gurin Dan kunya, gaba daya suka zubawa Hameeda ido har shi uban gayyar, wani abune Wanda Zahra Bata taba tunanin Hameeda zatayi Mata ba, dan wannan cin fuska ne qarara bako kawaici a cikin maganar ko kad'an. Zahra kasa gaba ko baya tayi ta tsaya a gurin kawai, su sajida ma rasa ta cewa sukayi shi kuwa uban gayyar wayar dake hannunsa ya aje Yana kallon Hameeda direct kafin yace " waya fada Miki Mai araha ce bakiji sunanta ba? Zahra fa kinsa ma'anar sunan kuwa? tauraruwa fa a cikin taurari a gurinki take Mai araha Amma ni a gurina tafi zinari daraja, bari na baku indai abin sayen Baki ne in dai shi ne abinda ke shaida Kima da darajar mace a irin wannan ranar gurin kawayenta, ina zuwa". Ya fada Yana mikiwa ya nufi hanyar bedrooms dinsu, tunda ya wuce zahra ta juya da sauri ta nufi daki Bata yi musu ko sallama ba.
Bai jima da shiga ba ya fito da wata katuwar leda da Kuma envelope guda uku a hannunsa. Yana zuwa directly Hameeda ya nufa ya Mika Mata ledar da envelope daya sannan ya baiwa Sajida da Mujiba Suma dai dai Yana fadar "ga kayan sayen bakin Nan a cikin wannan envelope din Kuma kunsha ruwa a hanya".
Ba kunya Hameeda tace yanzu naji magana ai shi tuwon girma miyarsa Nama mun gode".
Taja katuwar ledar tayi gaba abinta mujiba ma tabi bayanta har suka fita Sajida Bata motsa ba ita kollon ikon Allah take akan Mahmud Wai wannan shine Almajirin da ake ta yayatawa a aurawa Zahra har Hajiya Mama na yiwa Abba magiyar kada ya Fara wanna danyan aikin tab wallahi da sake ita tafa abinda ta gani ga tare dashi ai da hasashe ne take yanzu be taga zahiri. Ganin sun fita yasa sajidar aje Masa envelope dinsa a gefen shi tana fadin "kabar abinka na gode, ni fatana ka rike min bestie da mutunci da amana yafi ka bani duk abinda ka mallaka, bansan Kai ko waye ba Amma jikina Yana bani kana boye wani Abu tun lokacin Danazo gidan nan da Kuma irin kayan danaga an kawowa bestie nasan Kai ba kaskantanccen mutum bane, Ina hadaka da girman Allah kada ka bautulcewa Iyayenta da suka baka ita kaji tausayinta marainiya ce, Dan Allah nasan duk inda ka fito ba karamin guri bane ka Zama garkuwarta ka zamar Mata bangon da zata jingina taji dadi duk rintsi. Dan Allah ka Bata kulawa Zahra 'yar gata ce kaddara ce ta zaunar da ita a kasar nan da Kuma kawaicin kakanninta suka hakura suka barwa Ammah ita, Dan Allah ga amana Nima na baka kamar yanda iyayenta suka baka kaji tsoron Allah a cikin zamantakewar ka da ita na San Nan gaba zaka samu zabinka ko Kuma tuntuni kana dashi Dan Allah kada ka wulakanta ta.. na rokeka ka Zama adalin shugaba a gurinta idan kaji yanda rayuwa ta dunga jujjuyata zaka tausaya Mata matuka, Dan Allah badan niba...."
Da tayi gaba ta nufi kofa Bata taji me ze fada ba domin hawayene suka ciko Mata idonta idan tace zataci gaba da magana kuka zata fasa masa ne. A bakin kofa sukayi kicibus da Mujiba wadda ta dawo kiranta ganin shirun ya yi yawa.

AUREN HUCE HAUSHI

PAGE EIGHTEEN
STORY
AND
WRITTEN
BY
MAMAN FATIMAH.
_________ Bayan wucewar Sajida Mahmud ya Dade Bai tashi ba, kwarai yarinyar ta burge shi matuka, da gaske take son Zahra domin furucin da yarinyar can tayi yayi touching dinta sosai, lallai ya tabbatar son da take yiwa Zahra bana Wasa bane shi tun lokacin da Magaji ya fada masa ta baro syprus Dan kawai ta halarci bikin zahrar ya jinjina Mata duk da suna hutu Amma yasan irin wadannan daliban ba kowane hutu suke zuwa gida ba sai dai idan iyayen sun sunci sun tada Kai.
Envelope din data aje masa ya kalla yayi wani killer smile ya zurata a aljihun Wando Yana Kara wani murmushin Wanda shi kadai ya barwa kansa sani.
Yaso ya shiga dakinta sai ya share kawai Dan yasa baya raba daya biyu kuka take Dan da gaske koshi baiji dadin furucin da akayi Mata ba Kai tsaye bako rusunawa a ciki.
Lokacin da Abdul Hakeem ya Parker mota
r a parking lot na gidan Sajida ce ta farkon ficewa daga motar zuciyar ta na Mata wani zafi Dan da gaske idan ta tsaya zata shatawa Hameeda rashin mutunci ne na karshe Wanda zata Dade Bata manta ba, dan da gaske an shirya ne kawai dan a tozarta Zahra a gabanta mijinta, shi yasa kenan lokacin da zasu ltafi ta shiga part din Mama Kiran Hameedar akan ta fito suje, taji Salma na fadin saura Kuma ki kasa fada ki dawo Mama ta tumurmushi banza, ita Sam Bata kawo komai ba kawai dai ta dauka wani abune can tsakaninsu saida hakan ta faru ta Gane me ake nufi da waceccen maganar. Tana jin Mujiba na kwala mata Kira lokacin data nufi karamin gate wanda ze sada ta da cikin gidan, batabi ta Kanta ba tayi wucewarta ciki ta kyalesu.
Koda ta shigo part din Ammah directly bedroom din da suka kwana ta wuce tana yiwa su Aunty Hasana sannu har ta shiga ta fito tana fadin "Aunty Dan Allah idan su Hameeda sun shigo kice su raba kayan su biyu kwai Banda ni". Ta koma da sauri Dan tana jiyo maganar su a kusa alamar Nan suka nufo.
Tun shigar Zahra bedroom din Nan ta kwanta rub da ciki take risgar kuka Kamar ba gobe, Hameeda ta Bata mamaki Bata taba zaton irin wannan ranar ba a tsaknainta da Hameeda cewa take ko kowa ya nuna Mata naqi a bangaren Mama ita kadai zata tsaya a bayanta duk runtsi duk wuya saboda a baya ba Mai cin fuskar ta a dakin Mama makukar tana gurin Koda kuwa mamar ce, Amma yau Hameeda da bakinta Kuma a gaban idonta take fadar magana irin wannan, to meya canzata daga Hameedar data sani Mai sonta da kaunar ta da Bata kariya da kulawa a kowane janibi. Saida tayi Mai isarta har ta baiwa uku lada, sannan ta hakurkurta da Kanta ta tashi zaune. Kanta taji ya Sara Mata a hankali ta furta "Alhamdulillahi ala kulli halin. Allah na gode Maka duk abinda kayi nufi a gareni na karba ka bani ikon cinye jarabawar Nan dan isar Annabi Muhammad s.a.w.w".
Hannu tasa ta dafe Kanta dake matukar Sara Mata, wannan wace irin rana ce a gareta? ranar da duk wasu masoya keda tarin burika a Kanta Amma ita ranar ta ta farko ta kasance ranar cin fuska daga inda Bata taba zato ba, ba tarairaya duk burin da suka dade sunaci na irin wanna ranar ya tashi a banza. "Astagafirullah Ubangiji ka yafe min zunubina daya janyo min irin wannan rayuwar Mai tarin qalubale a cikinta".
Ajiyar zuciya ta sauke tana Kara dafe Kanta da gaske jinsa take Kamar ze rabe gida biyu, ba zato ba tsammani taji an bude kofa Bata daga Kai taga ko waye ba dan kamshinsa kadai ya Isa ya fada Mata Mai shigowar, Kuma ma waye ze shigo haka Kai tsaye a irin wannan lokacin, sallama yayi Mata Amma Allah baisa ta amsa Masa a fill ba ta dai amsa a zuciyar ta.
Takowa yayi a hankali har zuwa inda take zaune, har lokacin Kuma Bata daga Kai ta dube shi ba farar ledar dake hannunsa ya aje kusa da ita ba tare daya tanka Mata ba ya juya ya nufi kofa yana juya baya ta dago da sauri ta kalli bayansa kananan Kaya ne a jikinsa sabanin dazu da yake sanye da wani lallausan yadi fari tas da hula, sai taga Kamar yafi kyau yanzu akan dazun, kananun kayan sunfi karbarsa akan manyan da yake sakawa, hannun daya saka ya Kama handle din kofar idonta ya Kai taga hannun wani fresh dashi Kamar Mai rayuwa a kasashen sanyi. Ganin Kamar ze juyo ne yasa tayi saurin kauda Kanta Dan kada ya kamata da wadannan idanun nasa tana kallonsa. Kofar tabi da kallo bayan ya fice a hankali ta sauke ajiyar zuciya da gaske fa mutumin Nan yana Mata wani irin kwarjini, ga wani tsare gida naba gaira ba dalili da yake saiya karta Abu ya wani maze Yana Shan kamshi.
Karan bude kofar ne ya dawo da ita daga tunanin data shiga na wucin gadi, kusa da ita ya zauna daf da daf dan ji tayi Kamar numfashi daya suke sharing dashi, a hanakli yasa hannu ya dago fuskarta data Kama idon ta rufe, a zuciyar ta tace "na bani ni Fatima shi Kuma kome faskar Nan tawa tayi Masa? shi dai ya taba jikina kawai ya sani, muryar shi ta jiyo cikin deep voice yana fadin "Pls open your eyes and look at me mana".
Kai ta shiga girgiza Masa alamar a'a.
Shi abin nata ma mamaki yake bashi, a ranar da suka samu wannan arangamar da ita soron gidan Baba malam yaga ta rufe idanu ya dauka ko tsabar razanar zata fadi ne. Amman sai yaga abin na neman ya Zamar Mata jiki indai zata ganshi to kuwa sai ta rutse idanu Kamar taga wani abun tsoro, a haka zasu rayu da ita ai baze yuwu ba gaskiya dole yayi wani abun daze cire koma meye yake haddasa Mata hakan a tare dashi.
"Ok Ashe zamu kwana a haka kenan tunda bazaki bude idanun ba, ko Kuma wallahi na shayar dake mamaki yazun nan".
Shiru tayi Masa kirjinta Yana fat, fat da sauri kusancin yayi yawa duk ya kanainaye ta.
Batayi zato ko tsammani ba taji harshensa akan fata idonta Yana lasa yana busa mata iskar bakinsa kamshin Lister mint mouthwash Yana dukan fuskarta ciki Shirin fita hayyaci tayi baya da sauri ta fada kan gadon da baya idanun nata tar akan fuskarsa da yana mata wani Yana Mata wani kallon kasa - kasa nan da Nan taji tsikar jikinta tana tashi sai hawaye zurrr...
"Why! meyasa? Ai da sai ki barni na kwashe abinda yake hanawa kina kallon nawa Mana, oya tashi abinci zakici bazaki kwanta da yunwa ba kisa na Fara karya Alkawarin dana daukar Iyayena na kula dake,dan kowa amanarki yake bani da jaddadda min na rikeki da amana da gaskiya cikinsu harda bestien mu kuwa".
Ya fada a kasalance Yana kashe Mata ido.
Sai Kuma ya dan zamo kadan ya dauko plate Wanda ita Sam Bata San lokacin daya ajesu a gefenta ba, ledar ya bude wani kamshi ne ya doki hancinta Mai shegen Dadi kaza ce wani irin gashi akayi Mata Kamar na tsire da vegetables a ciki ya juye Yana fadin.
"Oya tashi kici kafin ki kwanta kinsan yunwar dare tana kawo ciwon ulcer,kada ta kamaki ace Ina barinki da yunwa ni d'an malam gara na Kara kiwataki duk wanda ya ganki ace Masha Allah! Kamar ba matar Almajirin Baba malam ba".
Ya fada da alamar zolaya a karshen maganar tasa. Itafa Yana Bata mamaki wallahi zata iya rantsewa idan aka saka Masa hannu a Baki baze ciza ba amma dubi yanda ya wani zage yana magana Kamar bashi ba.
Ganin da gaske zata Bata Masa lokacin shi Kuma Yana da abinyi da yawa yasa ya matsa sosai kusa da ita ganin Yana nema Kara mannata a jikinsa yasa tayi saurin tashi zauna tana kikkibta idanu tana kallonsa. Da hannu ya nuna Mata plate din, cikin Rashi kuzari a maganar tata tace Masa "na koshi bazan iyaci ba kaina ciwo yake".
Ta fada murya a shagwabe ga daman tasha kukanta.
Sai yaji ta Kara bashi tausayi abun ne yayi Mata goma da ashirin.
Cikin sigar lallashi yace.
"To kici ko kadan ne saina kawo Miki magani kisha kinji"
Ya fada yana Kara nuna Mata plate din da idonsa, kadan taci duk a takure shi har mamaki take bashi a yanda yake ganinta ai ta wuce ace tana jin irin wannan kunyar ko tsoron irin haka, tunda da gani wayayya ce ta ajin karshe, ga Kuma yanda ta ringa ta'ammali da samari kala kala, a yanda yaji labari fa sau uku ana fasa aurenta Wanda ba Wanda yasan dalilin hakan, yasan kawai rainin hankaline irin na Mata, yanda zamanin ya Zama abinda ya Zama Amma dai ai gaskiya zatayi halinta komai daren dadewa.
Ba laifi ta danci tace masa ta koshi tana kokarin fitar da kwalla. A zuciya yayi yana jinjina saurin kukanta Kamar wata 'yar goye Sam yaga kuka ba wani wahala yake Mata ba, tana kuka tun abun kukan Bai Samu ba to idan ya samu yaya za'ayi kenan?.
Kwashe kayan yayi ya fita dasu Bai jima ba ya dawo da p.c.m tablet a hannunsa da ruwa marar sanyi, farm fresh yogurt ya Fara zuba Mata ta karba Tasha sosai dan tana sonta sosai lokacin tana Jos har kamfanin take zuwa ta sawo musu, tayi Mata Dadi sosai sanyin moderate ba Mai cutarwa ba.
Saida ya tabbatar da tadan samu relief kafin yace Mata.
"Ki tashi ki canza kayan jikinki ki kwanta idan kikayi barci kan ze daina ciwon, in Sha Allah, Kuma na fada Miki tun kina Asibiti ki rage damuwa Bata maganin komai sai Karin matsala Amma idan Kika hakura komai Mai wucewa ne Zaki sameni fiye da yadda Kika tsammmata kiyi hakuri komai da Kika gani hukuncin Allah ne ba Wanda ya Isa ya canza idan Ina tunani akan kaina na duba yanda connection din ya faru nasa ba Wanda ya Isa ya tsara haka sai Allah Dan haka ki Barbi abinda ya Baki Koda bakya so kinda ance wani hanin ga Allah baiwa ne tunda gashi ya Baki Dan malami sukutum ai tsakaninki da Allah sai godiya". Ya fada Yana kafeta da idanunsa masu sakata ladabin dole.
Kai kawai ta gyada Masa, ba baka sai kunne, mikewa yayi da cup da robar farm fresh din a hannunsa ya nufi kofa a hankali ya juya very lockly suka hada ido kashe Mata ido daya yayi Yana Dan murmushi Wanda Batasan Kona menene ba, sannan yace Mata "good night".
Yaja kofar wasu sabbin hawayene taji Kuma ita harga Allah bada niyya ba jinsu kawai tayi hakika tana tausayin kanta, da gaskiyar masu iya magana da suke cewa cusa Kai ba kwarjini yawa ne yau ta gani ganin idonta Wai ita Amarya ce wadda zayati kwanan farko a gidan miji.
"Ya illahiy!!! Wannan wace irin ranace haka? Yanzu da Musba.... Astagafirullah".
Ta fada da sauri tasan tunanin wani irin haka haramun ne da aure a kanta.
Ta jima a gurin tana sakawa da kwancewa Amma dai duk inda ta juya amsar daya ce aikin Gama ya riga ya gama sai hakuri da zubawa ikon Allah ido Dan shine alimil gaibi.
Tunda Mahmud ya shiga nasa bedroom din ya kasa samun nutsuwa Banda yayi namijin kokari ya kauda kansa da lallai sai ya rage zafi gaskiya idan yayi haka baimata adalci ba. Dan shi a nasa bangaren kamai ya gama zamar Masa daidai, saidai ita uwar gayyar batasan wainar da yake toyawa ba dan idan da abinda shi Kuma Bai lamunta ba yayi Mata dole yafison komai Daren dadewa taso shi da muradin kanta yafi son ya koyar da ita yanda zata soshi fiye da kowane da namiji data taba so a rayuwarta, ba Kuma ya son tasan koshi waye bama ita ba kowa ma dake tare dashi a nan, yafi son ya Gina kanshi a gurinta a wannan matsayin na yanzu.
Wanka yayi ya saka pyjamas dinsa farare sol nasu laushi, yana jinsa cikin watan irin nutsuwa, maimakon ya kwanta sai ya dauko laptop dinsa ya dosa aiki sai gurin biyu da kwata ya ture computer din ya tashi ya nufi kofa ya fita dakinta ya nufa dakin zahrar yana zuwa yana turawa yaji kofar a bude Kuma dakin da haske yayi zaton ko barci ne ya dauketa tabar wutar Mai haske a kunne. Yana turawa ya ganta akan sallaya tayi sujuda Amma shashhshekar kuka take Allah kadai yasan abinda take roko tsakaninta da mahalicci ya jima a tsaye kafin yaja Mata kofar ya fita jikinsa a matukar sanyaye dan ba karamin qima ta kara a idonsa ba ya Kuma Kara godewa Allah da yayi Masa kyauta da wannan yarinyar yasan Allah sami'uddu'ai ne yasha raba dare Yana rokon Allah ya bashi mace ma'abociyar addini, sai gashi a inda Bai taba zato ba Dan gaskiya Bai taba kallonta a wata mujahida ba yafi Mata zaton bokon ya rinjayi bangaren islamar ta.
Koda ya koma shima Bai kwanta ba Saida yayi nafilfili sannan ya kwanta da tunani kala-kala a zuciya.
Hudu da minti arba'in ya farka ka'idarsa kenan ta tashi sallar Asuba, wanka yayi ya saka jallabiya milk colour ya bude kofa har ze wuce sai yaga Bai Dace ba gara ta tasheta ta.
Sanda ya tura kofar har ta Fara raka'atanul fajri ta Riga ta tashi, lallai ya jinnina Mata gurin ibada sai yaji ya qara samun wata nutsuwa a tare da ita da sauri yaja Mata kofar ya nufi falon jin za'a tada sallah.l


AUREN HUCE HAUSHI


MAMAN FATIMAH

PAGE NINETEEN
(19)
AssalamuAlaikum warahamatullahita'ala wabarakatuhu.
Ina mika sakon jaje gan Alummar maiduguri bisa ibtila'in daya samesu na karyewar Alo dam, Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya Wanda Kuma suke gida da Asibiti Allah ya basu lafiya, abinda aka rasa na dukiya Allah mayar musu da ninkin abinda suka rasa.
_______________Mahmud tunda aka idar da sallah Bai shigo gidan ba sai kusan karfe shida da rabi, ya Dan jima da Mai gadi kafin ya shiga ciki dakin Zahra ya nufa a kwance ya sameta akan sallaya da gani batasan lokacin da barci ya dauketaba yasan kusan kwanan zaune tayi, a hankali ya matsa daf da ita Yana karewa fuskarta kallo idanunta sun dan tasa alamun kukan da tasha da Kuma rashin barci, wayarta ce a gabanta a kunne tsugunawa yayi ya dauka Qur'an ya gani tana karantawa barcin yayi gaba da ita, baiyi tunanin tashin taba kada ya katse Mata barcinta.
Kan stool na madubi ya zauna da wayar a hannunsa Yana dubawa haka nan yaji Yana son ya shiga ya duba received calls da missed calls nata, a hankali ya ringa bi Yana dubawa yawanci kawayenta ne sai Kuma Ummee da ya gani har ze aje sai yaga Kamar number din guyn da zata aura Dan lokacin daya tafi da wayarta ya canza mata wayar da sim card din a Nan ya haddace number din tasa sai Kuma yanzu daya ga Kiran jiya dai dai lokacin suka bar gurin Baba malam, Nan da Nan yaji ransa ya sosu duk da Kiran daga gurinsa ne ba daga gareta ba.
Tashi yayi tsam yabar dakin da wayar a hannunsa shima kwanciyar yayi, can cikin barci yaji alamun ana Danna door bell da kyar ya tashi ya nufi kofa, Musaddiq ne da Faruq din Aunty Hasana suke kawo break fast cikin ladabi suka gaishe dashi ya amsa yana Basu hanya suka shigo da basket din dake hannun Musaddiq ya Dora akan dining table.
Musaddiq ne ya juya ya nufi kofa yayin da Faruq yayi tsaye, har Musaddiq yakai kofar fita daga falon ya juyo Yana fadin "Faruq me kake jira ne ka tsaya? kasan driver Yana jiranmu fa"..
"Taya zamu tafi bamu gaishe da Aunty Zahra ba?".
Mahmud ne yace "Faruq Auntyn barci take sai dai zuwa anjima sai ku dawo kaji".
Cikin damuwa da matsanancin tashin hankali Mama ta tashi, tunda garin Allah ya waye ta tasa kayan da Hameeda ta shigo dasu jiya a leda da envelope din kudin da mijin Zahra ya Basu a gaba ko bakasan kayan kwalliyar Mata ba kaga wadan Nan kasan ba Karabiti bane ga uwa uba kudin daya lafta musu ita abin har ya Fara Bata tsoro, dan a zahiri kowa yasan fakiri ne wanda Bai ajeba bai bada ajiya ba amma a badini abubuwan da yakeyi suna da ban mamaki.
Wayar ta ta dauko tayi dealing din wata number ba'a Dade ba aka daga Bata koyi sallama ba ta Fara magana "Asabe kome kike kizo anjima da matsala babba komai Yana neman ya dagule fa kizo kiga abinda wancan tsintacciyar magen ya baiwa su Hameeda jiya harda fadin magana dan Hameeda ta fadin maganganun danace ta fada wallahi Ina kokonto akan lamarin yaron nan Dan jiya da dare Dana Kira malam na BANDE cewa yayi Wai mun kuskure wani abu shi yasa har Alhajin ya iya daura mata auren Kuma yayi duk iya yinsa ya kasa ganin komai akan mijin nata sai wani haske kawai yake gani".
Daga can taji magansr mamar ta amsa da "hakane ba damuwa sai kinzo din ta aje wayar tana jan karamin tsaki ta tashi ta shiga toilet.
A bangaren Ammah kuwa bayan Sajida da zulai sun Gama aikin break fast din da aka Kai gidan zahra, sajidar wanka tayi ta Shirya kafin ta fito falo su karya, bayan sun Gama ne ta kalli Ammah tana fadin "Ammah in Sha Allah yau an tafi gida Ina son na wuce school ne daman na jira ne saina raka Zahra gidanta tun last week muka Fara lactures".
Ta fada a ladabce.
"To Babu laifi hakan Allah yayi Albarka, sai Magaji ko Malam Bala wani ya Kai ki mun gode madallah, kunyi sallama da mutuniyar tun jiya kenan!" Ta tambaye ta.
Kai ta girgaiza tana fadar "A'a sai anjima zan shiga muyi sallamar".
Zahra Bata tashi ba sai wurin takwas da rabi tayi Mika gami da salati tana Kara ware idanu tana kallon dakin da alama kamar ma ta manta inda take Sai a hankali ta dawo cikin nutsuwarta "ya Salam".
Ta furta hankali tana ware sexy eyes dinta, wallahi Sam ta Manta da waifa a dakin gidan aurenta take ba a dakin Ammah ba, tashi tayi zaune kan sallayar tana Kara kallon Kanta har lokacin hijabin da tayi sallar ne a jikinta.
Toilet ta shiga duk jikinta ya Mata wani irin nauyi Sam Bata jin dadin jikin nata ruwa Mai dumi ta hada ta shige ciki tayi kwance tana shakar kamshin turen wanka data zuba ta jima sosai a cikin ruwan kafin tayi wanka ta fito sabon towel ta dauko mai kalar purple Babba ta daura ta fito gurin mirror taje lotion ta dauko ta shafa a jikinta, tashi tayi ta nufi gurin wata jaka kayan gyarab gashinta ta dauko, zuwa tayi ta zubesu yanzu da a gida ne da Ammah ce zata gyara Mata tsab ta hade shi guri daya, tana kiciniyar daureshi taji alamun bude kofa da sauri ta kalli gurin, Mahmud ne cikin shigar kananan Kaya yayi wani irin fitinannan kyau, hannunsa ya nade a kirji ya jingina da kofar ya zuba Mata idon dake figitata, shi be shigo ba shi be koma ba ya kafeta da idanunsa.
Tunda suka hada ido dashi tayi saurin sunkuyar da Kanta jikinta na wata irin rawa duk ji tayi ta rasa yanda zatayi daga ita sai towel din Nan a jikinta, gashin ta saki ya bazu har gadon bayanta ta matse hannunta a kijinta, sun Kai kamar minti uku a haka Yana Kare Mata kallo son ransa a cikin zuciyar sa Yana tsarkake sunayen Allah da yayi Masa kyautar bazata da wannan kyakykyawar halittar dake gabansa a matsayin matarsa ta sunna halaliyarsa wadda ba wani shamaki a tsakanin su.
Cikin takunsa Mai Cike da karsashi Amma a nutse, ya doso inda take tsaye Yana zuwa ba zato ba tsammani taji ya saka hannu Yana tattaro gashin daya bazu a kafadarta yana fadar "Bari na gyara Miki tunda Naga yana neman gagararki".
Bata iya ce Masa komai sai jikinta daya cigaba da tsuma, tsab ya hade ya saka ribom din daya gani a kusa mayukan gashin brush comb ya saka ya Kara gyara shi sannan yayi baya a hankali ya zauna akan sofa Yana fadar "ki shirya kizo muje ki bamu break fast gashi can Ammah ta aiko tun wurin 7:30 su Musaddiq suka kawo".
Bata amsa ba Kuma ta dago kalle shi ba, d'an gunguni ta fara kasa kasa "kawai ka zauna mun a daki kana kalleni kaki fita a gabanka kake son na saka kayan ko me?".
Yana kallonta gefen ido tana magana a ciki baya raba daya biyu yasan complain take akan zamansa. Tashi yayi Yana fadin "idan kin Gama kiyi min magana Ina aiki ne".
Ya juya ya fice.
Wata ajiyar zuciya ta sauke tana fadar "innalillahi ni Fatima Naga ta kaina Wai shi wannan waye shi? Nifa wallahi lamarinsa sun fara bani tsoro gaskiya" ta fada tana cuno Baki, sai Kuma tayi sauri har towel din jikinta na neman faduwa key ta sawa kofar, a gurguje ta saka doguwar rigar lace peach colour Mai touching din flowers green Bata daura Dan kwalin kayan ba saita rufa gyale green,Sam batayi wani make up ba powder kawai ta shafa sai lips glow turarenta ta fesa ta nufi kofa ta bude ta fice tsaye tayi a cikin corridor din saita rasa a wane bedroom din yake.
Ta jima a tsaye tana saka yanda zata tunkari dakinsa Kai tsaye, cikin yin shahada ta nufi inda take zaton nan ne bedroom din nasa a hankali ta murda handle din ta tura kamar wadda za'a cewa ket ta ruga, wani sanyi da kamshin turensa Dana freshner ya shiga hancinta dakin ba wadataccen haske duk curtains din windows a sake suke can kan sofa ta hango shi da laptop a gefen sa yana ta faman daddanabawa tsaye tayi ita Bata shiga ba ita Bata koma ba, yana kallonta ta gefen ido Amma sai ya basar kamar bai ganta ba.
"Assalamu Alaikum".
Ta fada a darare, Bai kalleta ba Amma ya amsa sallamar.
Dan Jim tayi kafin tayi karfin halin cewa "na gama shiryawar".
Kansa ya dago ya kafeta da idanunsa da yake razanata dasu kafin yace "idan bazaki shigo kije kawai an fada min Ina cinye mutane ne da Kika tsaye a nan".
Dan cuno Baki tayi ta saki handle din ta shigo a nutse Amma fa Babu nutsuwa Kota sisin kwabo a zuciyarta ta ayyana "waya sani ko mayen ne tunda abune a duhu".
A tsakiyar dakin ta zauna an carpet Kanta na kallon tace Masa "barka da Asuba".
Shiru yayi kamar Bai jiba Saida ya Mula dan kansa yace "Lafiya ya kwanan bakunta I hope ba wani damuwa ko?".
Kai ta gyada masa alamar eh.
Yace "good Bari na karasa wani dan aiki muje muyi break ko?"
Ya fada Yana kallonta.
Ganin tayi shiru yasa yaci gaba da aikinsa ita Kuma tana zaune duk sanyin dakinsa ya Mata yawa, tana son sanyi amma sai taji na dakin yana neman ya sakata rawar jiki.
Baifi minti biyar ba ya rufe laptop din ya Miki, gurin da take zaune ya nufo yana zuwa ya Dan tsuguna kusa da ita Yana fadin "taso muje kada nabar 'yar amanata da yunwa na amsa query a gurin su bestie ko?"
Ya fada Yana murmushi.
Hannunta ya kama ya dagota tsaye suna shakar numfashin juna Amma ita kanta yana duban kasa, dayan Hannun yasa ya dago fuskarta as usual yanda ya saba.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali Amma bata rufe idon ba kamar yanda ya hanata a jiya Bata manta ba amma ta kauda Kai gefe dan da gaske Bata iya had a ido dashi.
Dan kwanto da ita yayi jikinsa Yana juyo da fuskarta yana fadin.
"Wallahi kada ki rusa min budget dina kisa na kwashe kunyar nan daga idanunki tun banyi niyya ba matukar zakici gaba da irin wannan dabi'ar".
Das das girjinta ya kara bugawa akan wadda yake, tana fadin "oh ni Zahra tawa ta sameni shi Wai wane iri ne haka? sai yayi ta sakin magana ko kunya babu".
Saida ya matsa mata taci abincin kirki bayan sun Gama ne suka dawo parlor suka zauna Sam Babu sabo ko kalilan a tsakaninsu kallo ya kunna a Nile sat ya kamo super support suna kwallo live.
Ganin ita ba wani gane kan ball din take ba yasa ta Mike zata koma daki ta kira Sajida taji ya maganar tafiyar Dan tun jiya da Abba yace a jiya zata tafi gidanta sajidar tace itama sai gida ta.
Takunta biyu taji ya janyo ta ta fada jikinsa ba Shiri ta zaro ido waje hura kata iskar bakinsa yayi a fuskarta dalilin yasa ta rufe idonta kenan a hankali yace "Ina Zaki ki barni a zaune alhalin saboda na tayaki Zama yasa naki fita ko ina".

AUREN HUCE HAUSHI

PAGE TWENTY
(20)
_______"ya Salam". Zahra ta fada a hankali jin yanda yake hura mata iskar bakinsa a fuskarta, yasa hannuwansa duka biyun ya tallabo fuskarta yana kallon face din very cute da ita, shifa baya gajiya da kallonta komai nata burgeshi yake yi Dan bakinta ya kalli 'yan kyawawan lips din ta pink, gdy yake yiwa buwayi Gagara misali daya mallaka masa ita a lokacin da bai taba zato ba, tunda ya kafeta da ido Bata yarda sun hada ido ba, ba Kuma tayi gigin dogowa ba.
Qaran da door bell din tayi shiya kawo karshen 'yar tutsiyen da yayi Mata wani soft kiss ya yiwa gefen wuyanta Wanda har Sai da ta zabura tana fadin "wayyo Allah!".
A shagwabe ta janye jikinta daga rikon da yayi mata, shi Kuma ya tashi ya nufi kofa, Bata jira taga waye ba tayi wuf ta nufi ciki jikinta kamar mazari.
Tana shiga ta zube a gado tana fitar da numfashi da sauri da sauri kamar wadda tasha gudu, jin alamun bude kofar yasa tayi saurin duba gurin Sajida ta gani tsaye ta tsura Mata ido tana Mata wani kallo cikin mutukar tsantsar farin ciki zahrar ta taso tana fadin "haba bestie kin wani tsareni da ido kina min kallon qurillah irin wannan ko Kinga wani abu a jikina ne?".
Ta qarasa fada tana karasowa kusa da ita 'yar madaidaiciyar ledar hannunta tana fadar "Wai meye Kika wani yi shiru kina kallona ne Dan Allah talk to me Mana pls".
Biyo bayan zahrar tayi har gefen gadon kafin ta samu kuzarin fadin "Bestie Kinganki kuwa just one day Amma har kin Fara canzawa, Fadi min meye sirrin gaskiya, na tafi jiya da zulumin ki a Raina yau kuma nazo na sameki haka kin wani Kara Zama fresh dake".
"Bestie tsakanin mu harda 'yar zolaya zakice Wai na Kara zama fresh?"
Zama tayi gefen zahrar tana fadin "wallahi I am serious kin canza a idona gaskiya Kinga ai dole na fada ko?".
"To shikenan kin fada bazan hanaki ba, wai da gasken yau Zaki wuce?"
Kai ta gyada Mana kafin tace "In Sha Allah meya rage kuma ai gara naje na fuskanci karatun ko tunda na samu nutsuwa kin shigo gidan ki. Alhamdulillahi, ga sauran abubuwanki na wajen Baffan rimi kici baga da amfani dasu dazuma munyi waya da safe yace na bawa Ammah abinda ya Aiko dai ya Kara jardada Mata na a fada Miki kada wani ya kawo Miki abu kici Kuma yace a tura a karbo Miki sako Nan da sati daya".
Dan langabar da Kai tayi tana Kara ganin kimar Sajida ta dauki matsalar nan tata bada wasa ba.
Godiya sosai Zahra ta yiwa Sajida akan abinda suke mata, sun Dade sajidar na yiwa Zahra nasiha akan ta rike aurenta da kyau ita bataga wani abun ashsha ba gurin Mahmud idan. Nan da Nan idon Zahra ya kawo ruwa ta shiga sharewa da hannunta tana fadar "wallahi bestie na rasa dalilin da yasa nake jin wani abu a tare dashi tun ranar Dana Fara ganin shi naji abun ko kallonsa fa nayi sai naji gabana Yana faduwa heart beat Dina Yana karuwa, kinsan ma inda matsalar take?"
Kai sajidar ta girgaiza tana fadar "sai kin fada".
"Kinsan haduwar mu ta farko rungumeni fa yayi a cikin jirjinsa tsam kamar.wata baby amman Kamar an dinke min Baki na kasa ko fada Masa magana ne saima wani azababben kwarjini da yayi min harda fadar na ringa kula kada nayi musu asara'.
Ai Sajida Bata San lokacin da wata dariya ta kubce Mata ba tana fadar.
"Babbar magana kice da wata tsumammiya a tsakani ku tun tuni har kika dauki alhakina gurin hanani kwanciyar hankali tun jiya Allah barci ma ban samu na kirki ba Ina zulumin abinda kaje yazo, Dan ba kowa bane za'a aje masa mace kamar ke ya iya kauda Kai gaskiya"
Wani duba zahrar tayi Mata tana fadin "ban Gane ba me kike nufi da maganganunki?.
Wata dariyar tayi tana fadin "A'a ba mefa nake nufi kawai dai...... "
Sai tayi shiru.
Wani zancen ta dauko Tana fadin "Zahra ki tsaya ki nutsu a gidan aurenki ki gyale kowa duk wanda ze raina Miki miji kada ki amince ko waye kuwa Koda ni da nake Miki wannan maganar, Kuma game da Hameeda ki kula sosai Dan a jiya ta nuna Miki jiya ba yau bace, jini kuma yafi ruwa kauri, Koda ta dawo tana neman Kara shiga jikin ki da wata manufar tazo, Dan Allah kiba marada kunya duk yanda ake son ganin lapses dinki kada ki bada damar hakan".
In Sha Allah zan kula nagode Bestie Allah yabar zumunci. Zahra ta fada
"Ameen" sajidar na ta fada, suna cikin hira akayi knocking din kofar ba'a bude ba Zahra ce Mike tana fadin "ina zuwa, tana kokarin yafa gyale ta rufe gashinta Sajida ta warce ta aje gefen ta tana fadin "haba ke kamar matar liman a daki na da Bata ja ba tayi gaba saboda an Kara buga kofar, budewa tayi Mahmud ta gani Yana tsaye ya canza kaya ya saka Riga da wando na wani yadi light brown dinkin buda yana baza kanshi sa na ibada.
Matsawa tayi daga jikin kyauren ganin alamar shigowa zeyi Amma fa Saida yadan shafi fuskarta kadan sannan ya ida ahigewa ciki, tsaye tayi tana binsa da ido tana ayyana "Wai meye ne yake faman shafa mata fuska har a gaban mutane ko kunya bayaji tasan wlh sarai Sajida ta gani sai dai ta basar kawai gashi ta wani rike mata gyale ta wani barta tsurarta".
Direct gurin mirror ya nufa ya zauna a Kan stool, Yana fadin "Bestien mu zuwa nayi muyi sallama naji Abdul Hakeem yana maganar Zaki wuce yau ko".
Ya fada Yana murmushi, itama murmushin tayi masa tana fadar.
",In Sha Allah yau sai kano tunda Allah ya cika min burina Zahra ta shigo gidanta fine".
"To mun gode kwarai Allah ya saka da Alkhairi sai munzo visiting idan madam zata dauki nauyin zuwan mu Kinga Nima sai Naga duniya ko madam?" Ya zubawa Zahra narkakkun idanunsa Yana Mata wani kallon qasa qasa.
Shiru Zahra tayi tana yafa gyaren a kanta, Sajida ce tace "gaskiya Kam haka za'ayi".
Tashi yayi ya Dan tako kadan zuwa gaban Zahra kamar ze hadeta da jikinsa da sauri tayi baya tana turo Baki yi yayi kamar Bai gani ba, envelope ya Mika mata Yana fadin ki Bata sskonta ne na jiya data Bari nayi niyya bazan canza ba sai dai idan bataso ta bayar, nizan shiga gurin su malam".
A hankali tace "an gode madallah a dawo lfy".
"Amin to bestie sai munzo ko".
Bai jira abinda zata ce ba yayi ficewarsa.
Ajiyar zuciya Zahra ta sauke tana Zama kusa da Sajida Mika Mata envelope din tayi tana fadin "yaushe ya Baki kikace bakya so?".
"Jiya Mana lokacin da zamu tafi sanda wannan jikar marokan ta zubar da darajarta ta rokeshi, yanzu Dan Allah me Hameeda ke nema? wane irin rufin asiri ne Allah Bai mata ba. Amma ta lalace gurin roko? shi yasa na aje masa kudin sa nayi gaba kayan ma nace bana so su rike".
Dan murmushi Zahra tayi tana fadin "Saji danger wato halin na Nan ko? To nidai gashi nan tunda a gaban ki ya bayar saiki karba".
"Bude mu gani to"
Sajidar ta fada.
Stalling founds ne na ingila musu yawa a ciki kallon kallo sukayiwa juna kafin Sajida tace wallahi bestie akwai kukus a shinkafa zakice na fada Miki, Wai kuwa kin tsaya kin Kare guyn nan kallo kuwa?". Kinga ya Miki Kama da Wanda baida abinyi ko wanda ya tashi a cikin rashin wadataccen ilimi da mugu? Dubi muhallin daya ajeki, ance malam ya bashi gidan sai kungiyar da yakewa aiki sukayi renovation din gidan ki kiyasta nawa yaci gurin aikin kinsan da an kashe abinda yafi kudin ginin duk yi Masa akayi? Ki tuna Nan fa ba garinsu bane ance bako ne kuma yaki fadin garinsu anyi magana ance yace ya manta komai sai a hankali idan ya tuna hankali ze yarda da hakan? Kuma kina tunanin Abba ze daukeki ya bashi ba tare da yasan wani Abu a tare dashi ba? Kiyi nazarin abin Mana ni dai ina fada Miki kibi komai a hankali kuma yanda na fashimci wani Abu a maganar da Kika fada min kinfa kamu da son guyn Nan tun sanda kuka hadu ba tare da kin sani ba, Kuma Shima Naga yanda yake shige Miki ko kunya ta Bai jiba kinsan sai a hankali kawai kwanan Nan labarin ze sauya irinsu basayi da wasa fa".
Ta garasa fada tana dariya kasa-kasa.
Suna cikin tattaunawa Kira ya shigo wayar sajida "Ya Abdul Hakeem ne" ta fadawa Zahra kafin ta daga.
"To"
Kawai tace ta kashe Kiran tana fadin.
"To bestie ya Abdul Hakeem Yana jirana Wai a she shine ze Kaini nifa daya fada na dauka da Wasa yake lokacin da Ammah tace Magaji ko Malam Bala dureba zasu kaini sai kawai yace su Bari Shima Yana son yaje kanon Sai ya tafi Dani".
Dariya Zahra tayi tana fadin "idan tayi wari munji batun, yanzu ba fa Naga Ya Abdul Hakeem Yana dama dama dake ba bai fada min ba Amma zakice na fada Miki Ina ga target dinsa kenan yau yake son ya yad'a manufarsa shi yasa yayi Riga malam masallaci yace Wai daman kanon zaya".
Kin magana sajidar tayi sai murmushi kawai. Zahra tace "bestie ko dai komai ma ya kankama ne ban sani ba Ina shirme?".
Kafin sajidar ta Bata amsa wani Kiran ya shigo da sauri ta dauki jakarta tana fadin "To bestie sai gani na gaba Allah ya bada zaman lafiya ya kade fitina, sai anyi ta hakuri kafin komai ya dai daita ki kwantar da hankalin ki zakiji dadin Zama dashi in Sha Allah".
Har gate ta rakata babbar ledar dake hannunta ta Mika mata tana Mata addu'ar sauka lfy. Amsa tayi tana Mata godiya ta bude gate din ta fita, ya Abdul Hakeem Zahra ta gani a mota a zaune cikin mamaki tace.
"Ya Abdul Hakeem daman kana Nan waje Amma baka shigo ba?".
Fitowa yayi ya karaso gurinsu Zahrar ta gaishe shi, sannan ta juya ta koma ciki duk zuciyarta ba Dadi Kamar ta Hana sajidar tafiya amma ba hali.
*********
Mahmud Yana fitowa direct Famfon shanu ya nufa tunda lifan din Habib a gurinsa ya kwana, tun jiya daya karba da yamma Bai koma unguwar ba.
Lokacin daya karasa yayi arba da motar Sameer wani murmushi yayi Yana fadin. "magulmaci kawai".
Kafin ya shiga Saida suka dinga gaisawa da jama'a anata Allah sanya Alkhairi, Binya ya tambaya Ina Habib yace yaje Kai wani sako da malam ya tura shi ya Kai gidan sarki.
Gurin Malam din ya shiga shi dasu Sameer ya samu suna magana da malam din Yana shigowa da sallama mlm din yace.
"Yauwa Dan halak yanzu nake cewa bazaka jima ba zaka shigo, mutanen ku ne sukazo da wasu ayyuka gasu nan dai zasuyi maka bayani. Ya wajen iyalin naka!?"
Dan sosa kansa yayi Yana Dan sadda shi qasa yace "Lafiya kalau tace a gaisheka" .
"Masha Allah. Allah yayi Albarka"
Gurin su Sameer ya juya suka gaisa, kafin suka fita zuwa inda suke meeting.
Stepdown training zasuyi da school base management committee Basu tunda tsarinsu ya koma sun bin tsarin makarantun government ne sai kuma officially da suka gayyaci Mahmud zuwa gurin taron da zasuyi a Lagos nan da kwanaki biyar masu zuwa. Bayan Gama taron Sameer ya dauki Mahmud a mota suka fita hotel din suka nufa a hanya Sameer ya kalli Mahmud Yana fadin "yallabai meye labari naga text dinka komai an sawo zuwa anjima motar zata karaso amma sai nake ganin kamar kayi tafiyar nan da ita tunda zaka jima a can Kuma kaga duka kwanan ta nawa zaka tafin baka ganin abin ze iya Zama na surutu ko ace ma guduwa kayi amma dai ya kake gani?".
Dan Jim yayi kafin yace.
Tafiya da ita ba shine solution ba na dauketa na kaita Ina ko Kuma nace Mata wanene ni Nan nace Lagos zani can Kuma taga sabanin hakan ya kake tunani ka tuna fa she's educated, zatayi saurin gane komai ni kuma nafi son na Gina soyayya ta a zuciyarta ba tare da tasan who I am ba, I hope you understand?".
Kai ya gyada Masa alamar eh.
Sun Dade suna tsaya yanda program din ze kasance da abinda za'a batar da abinda za'a kashe a makarantar zuwa lokacin da zasu dawo suna cikin aikin direban daya dauko kayan ya Kira Sameer ya fada Masa ya shigo Azaren ya fada Masa inda yake tattara komai sukayi suka wuce gurin da direban yake, Sameer din ne ya shiga gaba direban na binsa a b
aya har zuwa gidan Mahmud din.
Mai gadi ya taya direban sauke kayan, kayan abinci ne da sauran tarkacen girki hatta nama da kifi daga can aka kawo kayane masu matukar yawa.
Ciki Mahmud din ya shiga tararwa ya yi tayi Baki har su zulai da sahura, a tsaitsaye suka gaisa yayi gaba zuwa bedroom dinsa.
Ganin idon su zilan yasa zahra mikewa tabi bayansa dai dai lokacin Kuma Yara suka Fara shigon kayan masarufin da aka kawo, ganin zahrar Bata Nan yasa su sahura shiga dasu store din kayan abincin suka hada da wanda Abba yasa suka kawo dazu da kayan gara su gireba dasu dublan da alkaki.
Sunyi mamakin yanda yara ke shigo da kayan abincin basu Kara Shan mamaki ba Saida aka Fara shigo dasu Nama da kifi ga drinks Nan ko ba'a fada ba Wai ance ido ba mudu ba amma yasan kima sun San kayan na manyan kudi ne, ko wacce da magana a bakinta Amma bata furta ba.
Zahrar na shiga corridorn ta waske zuwa nata dakin.
AUREN HUCE HAUSHI

PAGE TWENTY ONE
(21)
...............
... Sai da su zulai suka gyara Mata komai yanda ya kamata sannan suka gyara parlourn,lokacin da Mahmud ya fito bedroom dinta ya nufa baiyi wani knocking ba ya tura kofar a gaban gado ya ganta ta cire bedsheet din ta zubo da pillows din da alama wani Abu take nema sallama yayi mata cikin muryarsa Mai nutsuwa yana kallon ta, cikin takunsa na cikakken namiji ya karaso Yana tambayarta "lfy me kike nema ne haka Kika birkita gurin haka?".
Jiki sanyaye tace Masa "wayata nake nema tun safe banganta".
Dan matsowa yayi kamar ze tayata dubawar Yana fadin "Kuma tun safe Baki ganta ba Kuma Baki nema ba sai yanzu, to su waye suka shigo dakin ne?".
"Shiru tayi kawai tunda tasan daga ita sai sajida ne a dakin Kuma tun bayan tafiyar ta ko Baki ne 'yan ganin daki Bata ahigo dasu Nan Dan gani take yaushe za'a dinga shigo da jama'a har dakin barcin mutum su dai dayan tunda ba a ciki take ba.
Dagowa tayi ta Dan kalli gefen shi da gani wanka yayi ya canza kananun Kaya tana mamakin sa ita tunda take ganinsa Bata taba ganinsa da shiga irin wannan ba Kullum manyan kaya ne Amma daga jiya zuwa yau ya zamar Mata wani daban, Sam ba wancen bane take gani.
Kamar ze wuce ta bayanta sai Jin Hannun Mutum tayi ya zagayo ta cikinta ya manna bayanta a kirjinsa ya kwanto da kansa dai dai saitin kunnenta iska yadan hura Mata kadan tare da hucin numfashinsa kafin yace.
"Ki daina wahalar da kanki tana gurina tun safe na dauka, nayi mamakin da baki nemeta ba sai yanzu? Na cire sim din saboda Naga wani sakarai ya kiraki da number din to nasan ze iya bibiyarki tunda naga bashi da taushidi ko kankani Bai hakura ba da hukuncin Allah so yake da karfi saiya kwato abinda ya kubce masa".
Kasa ko kwakwkwaran motsi tayi sanda yake jero Mata maganganun. Amma jin ya Kira Musbahu da sakarai marar taushidi yasa taji Zuciyarta ta wani baci, idan beji tausayinsa na abinda ya faru ba ai baze Masa bita da kullin irin wannan maganar ba, shida ya tsunci dami a kala har ya samu bakin magana irin haka. Nan da Nan taji ta samu wani courage wanda Bata San tana da shi ba, cikin muna bacin rai ta fara kokowar raba jikinta da nasa tana fadin.
"Wallahi Musbahu ba sakarai bane, ba Kuma marar tauhidi bane,dan ya biyo abinda yake halalinsa amma kasan dai Banda qaddara ba abinda ze rabani dashi, dashi muka tsara planning na rayuwarmu Amma lokaci daya ka rusa Mana budget din mu ka yarda da aurena da aka baka Kuma wallahi tunda nake dashi bai ko taba rike ko hannuna ba, amma Kai kuwa fa ranar Dana fara ganinka a duniya dame ka Fara min bada rugumata ba?" Kai kenan baka da aikin yi sai tabawa mutane jiki ......
Bata karasa fadar abinda tayi niyya ba taji ya hade bakinsa da nata cikin zafin nama Yana ladabtar da bakin nata da harshensa, dayan hannun Kuma yayi Mata wani irin riko bana Wasa ba dayan Kuma yana yawo dashi a ilahirin jikinta cikin wani irin sarrafawa Mai zafi.
Wata irin tsuma jikinta ya kama ga hawaye kamar na lalataccen famfo sai zuba suke ba bakin kuka sai mutsu mutsu take Amma ko a jikinsa wajen sau uku ana Kiran wayarsa tana tsinkewa, yayi biris da Kiran Kumar baya ji, sai da ya tabbatar da ya ladabtar da ita yanda yake so ya saketa, kan bed ta fada tana shashhshekar kuka hannunta daya yana Kan lebenta dake Mata zafi haka ma kirjinta zafi yake Mata ga gaban rigar ya farke Mata ita.
Kafarsa daya ya doro Kan gadon dayar tana kasa ya Fara fadar maganarsa hankali kwance kamar bashi bane ya Gama yamutsa Mata jam'iyya yanzu ba cikin mugunta.
"Wallahi na Kara Jin wannan sunan a bakinki ko magana makamanciyar irinta saina shayar dake ruwan mamakina, an fada Miki ni lusari ne da har Zaki tasani gaba kina fada min rubbish ne? an rusa muku budget din sai kuyi duk abinda zakuyi, an fada Miki Nima son abin nakeyi ne? da har Zaki tsaya kina min rashin kunya akan wannan lusarin Mai karairaya kamar mace,ke yanzu wannan har wani namijin arziki ne da ze iya dake? wallahi da kinyi tsautsayin aurensa da kin Gane Baki da wayo, idan Kika Kara gigin fada min magana makamanciyar irinta zan Baki mamaki wallahi, , har kike wani zakewa kina fadawa mutane magana, kice tak akansa billahil Azeem sai kin Raina kanki a dakin Nan saina banbance Miki tsakanin namiji da muna maza".
Yayi tsaki ya juya abinsa cikin takunsa na ingarman namiji ya fice daga dakin zuciyarsa kamar zatayi bombing.
A yanda su zulai sukaga ya fito Saida abin ya Basu tsoro kallon kallo suka shiga yiwa juna, sahura ce tace.
"Zulai bakiga yanda Mai gidan nan ya fito bane? Allah yasa ba mutuniyar taki bace ta taboshi Kinga ai ba haka ya shiga ba".
Zama zilan tayi tana fadin "waya sani sahura muna Nan tare dake, nifa shi yasa nace ba zanzo ba yau amman Ammah ta matsa akan sai nazo na Gane mata lafiyar ta,tun safe wayarta idan an Kira Bata shiga".
"To Kinga kuwa dole ki dubota ki gani ko Lafiya ya fito a haka kofa a dawo lfyr mu bai amsa Mana ba".
Jiki ba kwari zulai ta nufi bedroom din Zahra ganin zilan ta shige cikin corridor sahura ta Ciro wayarta Nokia ta Kira Mama. Ba bata lokaci ta dauka kamar jira takeyi ta shiga labarta mata abinda ta gani tun daga kan kayan da suka Zuba store har fitowar Mai gidan yayi da alamun bacin Rai a tare dashi, to kawai sahurar ke fada alamun wani Abu mamar take fad'a Mata sannan sukayi sallama.
Sai da ya fice harabar gidan ya Ciro wayar daga aljihun wandonsa ganin Sameer ne yasa ya Maida wayar ya nufi inda Sameer din yake zaune cikin mota, Bai Masa magana ba, zagaya yayi ya shiga motar yana fadin "let's go"
Ganin yanayin daya fito ya hana Sameer din korafin barinsa a waje baice ya shigo ba, dan kwantar da kujera Mahmud din yayi ya kwanta yasa hannu ya dafe kansa da gaske Sara Masa yakeyi lokaci lokaci Yana Dan Jan tsaki, Sameer dai be tanka Masa ba yasan a kusa yake, sai da sukayi nisa da gidan Sameer din ya Dan juyo yana tambayar.
"Ina muka nufa yanzu nifa na gaji ga yunwa Ina ji kace muzo gida muci abinci Kuma ka watsar dani a mota inaga ma sai da ka rage zafi ni in Nan Ina hamma ka shanyani".
Ya fada Yana Maida hankalinsa a titi.
Tsakin ya Kara yi Yana dagowa daga kishingidar da yayi Yana duban Sameer din "Allah ya shiryeka ka dauka kowa ma irinka ne Wanda baya iya kauda Kai a Kan Mata? Muje can hotel din kayi order abinci kaci tunda bani na gayyato ka ba cewa nayi ka dorowa mota kayan Kai Kuma sai gurin jibi kazo, to bansan wane kinibibin ya kawo ka ba ka bar yarinyar mutane da ciki kana gantali".
Ya karasa maganar Yana hararar Sameer din.
Dariya yayi Yana "fad'in easy man bani na kar zomon ba rataya aka bani, waya fada maka lamarin su da sauki? bakaji abinda Abbanta ya fada maka ba? ai da yace sai ana hakurin da gaske ne Zama dasu Saida hakuri".
Wani sakaran kallo Mahmud din ya aikawa Sameer da shi.
"Ka wani zaqe kana ta zuba wani Abu nace maka tayi min ne? da kaketa faman fadin maganganu haka tsabar saka ido kawai, gobe ka tattara ka koma inda ka fito tunda ba gayyato ka nayi ba da zaka dameni da kananun maganganu zan shigo da kaina kanon ba ai ba bakuwa ta bace ba".
Ya fad'a da gaske Yana Bata rai.
Shiru Sameer din yayi ganin da gasken koma Nene yayi touching dinsa sosai.
Suna shiga harabar hotel din kafin Sameer ya Gama parking a parking lot Mahmud ya bude ya fice abinsa Yana picking din wayarsa da aka Kira.
******Tunda zulai ta doshi kofar bedroom din Zahra take jiyo Kamar shashhshekar kuka, hannunta har rawa yake gurin bude kofar Dan ba maganar knocking, rubda ciki ta sameta tana faman shashhshekar da sauri ta mayar da kofar ta rufe ta karasa gurin zahrar da sauri tana Fadin.
"Subhanallahi uwar dakina me zan gani haka me kikayi masa? Dukanki yayi? Dan Allah kiyi magana Kona Kira Aunty Hasana ne sai ki fad'a mata ko na Kira Miki Ammah".
Kai ta girgaiza mata alamun a'a, "to ki fad'a min ko zan iya yi Miki wani abun Mana".
Saida kukan ya lafa Mata sannan ta yunkura ta tashi zaune ido zulai ta zuba Mata ita ba yarinya bace kallo daya tayi Mata tasan da wata a kasa ganin yanda take a yamutsa ga labbanta sunyi jajir abinka ga farin Mutum ga gashin kanta duk gyaran ya turje. Zama tayi kusa da ita sai a lokacin taga gaban rigarta a yage Hannun bra dinta guda a tsinke.
Kai kawai zulai ta dafa tana Fadin "mezan gani haka ni zulaihatu! Haba Zahra'u me yayi zafi haka ai sai kisa ya illataki a banza, gardama kika yi Masa yayi Miki haka?"
Cikin shashhshekar kuka tace "A'a maganar Musbahu yake min shine ya Fadi Abu marar Dadi a kansa shine kawai Dan na mayar Masa da amsa Nima yayi min haka". Ta karasa fad'a tana kuka.
Kasake zilai tayi tana duban zahrar kafin tace
"Haba Zahra'u da wayonki da hankalin ki Zaki rinka irin wannan abun har yaushe Zaki ringa maganar wani namiji a gaban mijinki har kiyi ikirarin fad'a Masa magana marar Dadi akan shi ai yayi Miki kadan wallahi idan wani ne yau basai gobe ba saiyayi Miki kaca-kaca yanda ko sunansa ba Zaki Kara fad'a a gabansa ba, kada ki kuskura ki Kara irin haka Zaki ragewa kanki kima da daraja a idonsa, duka yaushe akayi daren da shashshawa zata Bata,Ina cewa jiya aka kawo ki amma ace an Fara da haka kinga abin baiyi kyau ba ko kadan, yanzu ki tashi ki shiga kiyi wanka da ruwan dumi zanje na cewa sahura kina wanka ne, mu tafi kawai tunda nasan halinta Abu kadan zata fara yaya tashi tunda nasan badan Allah ta biyoni ba dan Saida na fito harabar gidan ta biyoni.
Sallam zulan tayi Mata Tana Kara tausarta akan ta ringa tauna irin maganar da zata ringa fada masa.
Cikin karfin Hali ta Mike ta nufi toilet da gaske ya tsumama mata jiki ta jima a toilet din tana kuka maganganunsa sun Mata ciwo matuka har wani gori yake Mata Shima ba sonta yake ba, to an fada masa ita son nasa take har yake wani Mata wulakanci, ita ta rasa a Ina ta kuskuro ne take haduwa da fitintinu daga wannan sai wancan? "Astagafirullah".
Ta fada a zuciyarta, alwala ta dauro ta fito ba wani kwalliyar azo a gani tayi ba duk ranta a cunkushe ga 'yar wayar da zata debe mata kewa ma ya dauke, a ranta tace "mugu kawai wani sumumu kasam dashi Kamar na Allah Nan kuwa dan duniya ne Mai lasisi".
Tana cikin saka kaya taji karan bell alamun Baki a gurguje ta ida yafe gyalen rigar ta dan fesa turare tayi gaba.
*****
Sai Bayan sallar magriba su zilai suka karasa gida dai dai lokacin Magaji ya fito da manya warmers a hannunsa sai Autan Ammah da basket a hannunsa Shima, zasu kaiwa zahra abincin dare.
Suna shiga zilai ta wuce part din Ammah ta fada Mata sun dawo ita Kuma sahura ta nufi nasu bangaren sai da zulan ta shige part din sannan sahura tayi wuf ta shige sashen Mama.
Salma kawai ta samu a falon tana kallon series na India ko arzikin amsa sallamar sahurar Bata samu ba sai wani kallon banza tayi mata tana Fadin "lafiya Kika wani shigo afujajun haka?".
Kafin sahura ta samu zarafin Bata amsa Mama ta fito daga bedroom din ta tana Fadin Kamar maganar sahura nakeji?"
Cikin azarbabi tace "nice Mama mun dawo".
Ta fada tana Zama a kasa kan carpet.
Cikin kwarewa da munafurci ta shiga korawa mamar bayanin abinda ta gani harta Kara da cewa.
"Anya Mama yaron Nan kuwa Babu abinda yake boyewa kin ganshi kuwa? Gaskiya wallahi baiyi kama da fakiri Mai neman abincin yau da gobe ba, kayan abincin da muka zuba a store din wallahi ni wani abin ma ban taba gani ba hatta madara wannan manyan gwangwwnaye sunfi ashirin Nama kuwa na kaji kawai sun Kai hamsin Banda na rago Banda na shanu Banda kifi Allah Mama Saida muka cika freezer din cikin kitchen din ga lemuka da ruwa Kamar banza ga......
Bata Bari ta garasa ba ta daga mata hannu "bar shi kawai jeki zan nemeki".
Mikewa tayi tana Fadin "a huta lafiya Bari naje nayi sallah naji ana Kiran insha'i". Ta fice.
Tunda ta fita Mama ke jijjiga Kai tana kwafa, Sam hankalin salma na can gurin kallon ta Bata damu da abinda su mamar suke ba, Saida mamar ta Kira sunanta sannan hankalinta ya dawo Kan mamar tasowa bayi ta dawo kusa da ita tana fadin.
"Mana menene Naga kamar ranki a bace,?".
Tsaki tayi tana fadin.
"Anya Abbanku da Asma'u ba ninkeni sukayi a baibai ba kan auren yarinyar Nan? ni daman tunda naga daga b'angaren Asma'u da 'ya'yan ta da 'yan uwa ba wata turjiya nasan da abinda suka taka bakiji labarin da sahura tazo min Rashi ba?".
Kai salmar ta girgaiza alamar bataji ba, Nan Mamar ta shiga fad'a mata abinda sahurar ta fada Mata, Nan da Nan hankalin salma ya tashi ta shiga fadar "ai laifinki ne Mama Nan nazo na fada Miki naga wani inaso a gurin Baba Malam Kika dinga zagina duk yanda naso ki fashimceni shi ba irin wanda kike tunani bane ni naga abinda na gani Amma Kika shafawa idanunki toka kikaki saurarena ai gashi nan duk fafutukar ki ta tashi a banza ko yanda kika fada min gidan yake ai kinsan da wata a kasa".
Ta fad'a tana share hawaye, Nan da nan hankalin Mamar ya Kara tashi idanunta sukayi jajur, cikin kaushin murya ta Fara fadar.
"Ni za'a yiwa haka wallahi sai dai kowa ya rasa Dan wannan auren sunansa matacce dole ya saketa ko baya kaunar Allah ai indai Ina raye yarinyar Nan sai dai kyanta ya Kare a banza ba dai tayi aure inda zata huta ba ita da hutu sai dai tayi nata gaji da aiki, duk wani haske na rayuwarta saina dusashe shi Bari ma ki gani".
Ta yunkura ta Miki ta nufi bed room dinta tana lalubar wayarta.
Ayi hakuri ba editing Naga kwanaki wata na fadar kada a karanta rubutun ba kyau.

AUREN HUCE HAUSHI

Story
&
Written
By

Maman Fatimah.

Godiya da yabo sun tabbata ga Allah s.w.a, salati da daukaka da Amincin su tabbata ga shugaban mu Annabi MUHAMMAD s.a.w.w.
Page twenty two. ( 22)
________Mahmud Bai bar cikin hotel din ba Saida yayi sallar insha'i, cikin gari ya koma gurin malam lokacin sun Fara karatun dare da maza manya Kamar Yanda suka Saba, shima littafin ya dauko na Riyadussalihinp ya zauna daukar karatun sai gurin takwas, bayan jama'ar sun watse ya rage daga malam din sai Mahmud da Habib.
Ganin Mahmud din ya zauna malam yasan da magana, Saida Habib ya gama gyara littatafan kusan aikinsa ne shida Abubakar, bayan fitar Habib din kusa da malam din Mahmud ya matso Yana Fadin Baba barka da dare".
Cikin sakin fuska malam ya amsa Masa Yana Fadin.
"Ya akayi ka zauna har wannan lokacin baka koma ba kasan ba sabawa tayu ba itama ya kamata a ringa kula". Kai yadan Sosa Yana Fadin in Sha Allah yanzu zan tafi daman na tsaya ne Ina son muyi magana".
"To Babu laifi ina saurarenka".
Qara sadda Kansa yayi Yana Fadin.
"Daman game da maganar tafiyar da zamuyi ne nace ko za'a samu wadda zata zauna da yarinyar Nan ne?".
Gyaran murya malam din yayi kafin yace
"Eh hakan yayi dai dai saidai ka tuntubeta kaji nata ra'ayin tunda Naga gidan nasu da wadatar juma'a ko wata zata tayata zaman tunda kasan sha'anin yau sai a hankali kada a Kai Mata wadda za'a samu matsala".
Tunda baba malam ya fara Kora bayani Mahmud ke gyada Kai sai da ya Kai Aya sannan Mahmud din yace. "haka ne in Sha Allah zan nemi shawarar tata duk yanda mukayi zan fad'a maka, na gode" Ya fada kafin su fad'a wata hirar akan wani sabon project da suka samu daga usaid karshi gwamnatin jihar Bauchi da sukazo musu aikin plane na shekara bakwai. Bashi ya bar gurin malam ba sai wurin Tara da rabi, daya fito ma majalissar su ya nufa gurin su salisu Nan suka dunga yi masa chari akan ya zagaye ya tafi gidansa bai nemi rakiyar kowa ba ko rowar ganin Amarya yake musu, shi kuma ya Kare kansa da hujjar Shima be San da zuwenta ba kawai da yamma Baba malam yace yaje can gidan ya jira Alhaji Jafar Yana son ganinsa, Yana zuwa kuma ya ganshi da zahrar ya kawota da kansa, to wa zaya Kira Kuma ihu bayan hari.
Sunyi masa Allah Sanya Alkhairi da Alkawarin zuwa su gaida amarya sai goma ya karbi lifan din Habib ya nufi hayin banki.
Lokacin daya shiga falon shiru ba motsin komai sai ni'imtaccen kamshin turarukan wuta 'yan asali da kuma na roomfreshner masu dadin kamshi lumshe ido yayi Yana shakar kamshin.Nan da Nan yaji wata irin kasala ta rufe shi ga wani mahaukacin feeling yana bijiro masa tun bayan barinsa gidan yake fama da wani irin tunanin ta duk motsin da zeyi sai ta fado Masa,moment din yake tunawa duk da ba cikin dadin Rai yayi ba Amma ya tsaya Masa a zuciya sosai Kamar magnet haka ya d'afe Masa.
A hankali ya taka zuwa tsakiyar falon komai tsab Kamar wani mahaluki Bai shiga falon ba, harya Fara Hawa steps din da zasu sada shi da bedrooms nasu hankalin sa ya Kai wurin dining din manyan warmers ya gani a hankali ya sauko ya nufi gurin abinci ne mai rai da lafiya sai Kuma pepper soup na cow tail da hadin salad da alama na ba'a taba ba yasan aikin Ammarta ne kada kai yayi Yana fadin "wato abincin ne bazataci ba ko me take nufi? baiwar Allah ta Bata lokacinta ta bada a kawo Amma ba za'aci ba"
Dakinta ya nufa Yana zuwa ya kama handle din yaji ta a rufe, shiru yayi wata zuciyar na cewa yayi knocking wata Kuma na kwabarsa, juyawa yayi ya koma gurin dining din shi dai baze iya cin abinci Mai nauyi ba, abincin ya dauka yabar pepper soup da hadin salad din tinda bashi da yawa.
Gurin Mai gadi ya nufa yana Fadin "Ga abincin nan a samu ayi amfani dashi yayi yawa".
Da hanzari ya taso Yana fadin "To yallabai ai dazu ma Mai gidan ta Aiko dashi har Saida na bawa wasu Yara ma sauran, wannan kuma Bari na kira Mustapha yazo ya kai musu can gida madallah dai an gode da dawainya".
"Haba ba komai gashi idan yazo sai ya biya mashin dasu". Ya aje Masa 5k akan warmer din ya juya yabar Mai gadin Yana sheka Masa addu'a da fatan Alkhairi.
Saida yayi wanka sannan ya dawo dining din yaci iya Yanda yake ganin ya isheshi sauran ya Kara kaiwa Mai gadin sannan ya koma daki.
Kan kujerar desktop computer ya zauna Yana kunnawa da ita akayi masa connecting din CCTV din dake gidan, a hankali ya fara watching Yana kallon duk wani abinda ya faru a gidan wani irin murmushi yakeyi lokacin daya ke kallon dabin su da ita da yadda tasha kukanta, wani Abu daya ja hankalinsa shine yadda yaga su zilai da yadda yaga sahura tayiwa zilai dabara ta turata ciki gurin zahra, ita Kuma tana waya bayan ta gama Kuma yaga ta shiga store ta fito tana kudundune Abu a cikin hijabinta wanda be San ko menene ba, take a Nan ya Dora mata question mark.
Saida ya Gama ganin komai Dan yanzu ma littafi ne take karantawa har lokacin daya murda handle din kofar da Yanda ta wani zaro sexy eyes din ta Kamar zasu Fado kasa saboda razana, murmushi yayi Yana fadin "matsoraciya kawai wannan za'a Sha drama da ita Dan Naga alama shagwaba tabi jikinta Bata San wahala".
Zahra kuwa tunda ta shige ta rufe kofarta tayi duk abinda zatayi na al'adun kwanciyar ta, sai ta dauko littafin ta du'aul mustajaba tana karanta addu'ar barci, bayan ta Gama ta shafa shiru kawai tayi tana tunane tunanen zuci ba, memories na abinda ya faru tsakanin ta da Mahmud ya shiga dawo Mata, Dan guntun tsaki tayi tasa hannu a kirjinta data wuni suna Mata zugi, a hankali ta Fara magana Kamar Mai gudun kada wani yaji ta.
"Jarababbe kamar maye duk ya cinye min labba da harshe ya shafeni tas yana wani gurnani kamar na zaki, da wasu idanunsa da gani na fitinannu ne! Ni Zahra na gamu da gamona na shiga Tara bama uku ba, shikenan na Zama nama sai Yanda hali yayi". Hawaye ne sharrr suka zubo Mata duk lamarin ya cud'e Mata ta rasa mafita, alwala ta shige ta dauro tana ayyana gara ta kaiwa Wanda baya barci wani abu Kuma Bai taba boyuwa ba a gurinsa kukanta tasan shine sami'uddu'a.
Sallah tayi raka'a hudu ta zauna tayi istigifari da hailala da salati ga fiyayyan halitta Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w har Saida taji zuciyarta ta samu nutsuwa kafin daga karshen ta daga hannuwanta sama tana Fadi cikin raunin murya da Qasqantar da Kai ga Allah s.w.a
"Ya Ubangiji Kaine mafi sani ga abinda yake faruwa Dani, wani Abu Bai sameni ba sai da izininka na gode maka a duk halin dana samu kaina a ciki, ka zama gata na,ka lullubeni da bargon Rahamarka, ka suturtani da suturarka, ka rufa min asiri da rufin asirinka, kada ka barni da iyawata ka iya min da iyawarka, Ubangijina ga wannan bawan naka Nan kasan ko waye shi lamarinsa Ubangiji ka sani ba boyayye bane a gurina Idan Yana da wani kaidi kada ka Bari yayi tasiri a kaina Dan isar Annabi MUHAMMAD a gurinka. Ubangiji kajikaina ka duba raunina ka tausaya min kada ka Bari makiya suga wallena ka bani rinjaye a kan dukkan al'amurana".
Duka hannuwanta tasa ta rufe fuskarta kamar me shafa addu'a Amma kuka ta saki Mai tsuma zuciya tana ayyana "Wai fa ita Amarya ce wadda ya kamata ace a irin wannan time din ana can ana riritata kamar a hadiyeta dan so da kauna da tarairaya da kulawa. Amman nata da haka yazo Mata, Astagafirullah Ubangiji ka yafe min zunubina daya janyo min irin wannan gararin rayuwar".
Ta dauki dogon lokaci tana shashhsheka a haka barci yaci karfinta ta sulale a gurin yayi awon Gaga da ita.
Bata farka ba sai kusan biyar da rabi cikin sauri ta tashi tana fadin "subahanallahi!"
Da sauri ta nufi toilet tana addu'ar tashi daga barci, a gurguje tayi uzurinta tayi alwala ta fito sallah tayi ta zauna yin Azkar da karatun qur'ani har gurin takwas na safe.
Mahmud Bai dawo gida ba daga sallar asuba gurin Sameer ya wuce, so yake yi suyi duk abinda ya kamata a Nan tunda kwaso jiki ya taho, shi yasa jiya yaqi yin komai yayi kwanciyarsa kawai.
Ba karamin mamaki Sameer yayi ba ganinsa da yayi a irin wannan lokacin to ai ko lokacin da taye single baya Masa sakko haka. Amma sai gashi shida yake expecting dinsa gurin one-two haka shine ya ganshi haka kamar an koroshi.
Cikin zolaya yace "My man ya naga haka ka duba time kuwa? Ka fito kabar 'yar mutane ko dai da matsala ne na fadawa Babanka manya su shiga ciki, sun baka yarinya girma -girma kana neman ka bada musu yaji a ido duk Wanda ya ganka a irin wannan lokacin daya Kamata ace kana can kana Shan kafi tea, ai sai mutane su dauka fanko aka kawo maka, gaskiya ka yiwa Allah ka koma ni zan shigo mu karasa aikin a gidanka daman meke kawo mu Nan? ba bukatar privacy ba? to yanzu muna dashi kaga no need sai munzo Nan Kuma kasan yanzu ba da bane ".
Ya fada ba alamar zolayar yanzu, ikon Allah Mahmud ya tsaya yana kallo kafin yace "ka Gama Alhaji muhammadu tunda Naga alamar roll din tsohona kake playing, to Wai Ina ruwanka da harkar Nan Ina cewa Mata dai tawa ce yanda nayi ra'ayi haka zan tafiyar da abina, ai dalilin daya kawoni kenan kazo mu ida duk Wani aikin da zamuyi kaje kayi sallama da malam ka kama gabanka".
Ya zauna Yana dauko laptop din Sameer Yana operatin dinta.
Kusa dashi Sameer din ya zauna Yana fadin "Allah ya huci zuciyarka angon Zahra da Safnah....." wani kallo Mahmud ya watsa Masa wanda yasa Sameer yayi shiru ba Shiri, shi kansa baisan sanda bakinsa ya furta sunan safna ba ko alama.
AUREN HUCE HAUSHI
Story
Written by
Maman Fatimah.
Page twenty three
(2 3)
________Zahra ba ita ta farka b sai gurin bakwai da rabi, sai lokacin ta tuna ta cewa Musaddiq ya fadawa Ammah ta bar kawo abinci zata dafa tunda ba komai take ba, toilet ta fad'a ta Dan sakarwa kanta ruwa Bata jima ba ta fito Riga da Wanda na Pakistan ta saka tayi rolling da gyalen ta saka plat shoes na daki ta nufi falo Amma zuciyar ta tana ta dar- dar kada suyi arangama da Dodon nata, falon ta shigo shiru sai sanyin A/C da daddad'an kamshin da yake ga curtains din duk a sake ga fitilu masu qarancin haske a kunne saiya bada wani irin yanayi Mai saka nutsuwa.
Dan waige-waige ta Fara Kamar tana neman wani Abu gurin sai Kuma ta nufi gurin tv ta tsuguna tana hada socket din adapter din tv ta kunna ta kamo tashar Almajid, kokacin sun saka Qira'ar Muhammad Saddiqul minshawi a cikin suratul ISRA'I sai da ta dai daita volume din sannan ta nufi kitchen din a nutse da takunta Wanda da yawa suke ganin yangace da jiji da Kai alhalin ba haka bane naturally haka Allah yayi ta.
Kitchen din ta shiga Kusan shigowarta ta uku Kennan, lokar da taga kayayyakin aikin ta bude ta dauko roba mai Dan Fadi ta nufi store ta debo Irish ta fito wanke shi tayi ta fere ta zuba a tukunya ta kunna gas, sai kuma ta dauko kaza guda ta yanka ta wanke ta zuba seasoning da spices ta rufe, ta jona egg boiler ta zuba kwai hudu a ciki.
A gefe kuma ta dauko attarugu da Albasa ta yanka kananu ta aje a gefe Irish din ta Fara dubawa taga yayi ta sauke ta zuba a container Mai zurfi tasa fork ta murje ta dora frying pan ta zuba Mai kadan ta saya attarugu da albasar ta zuba a Kan irish din ta zuba magi da curry ta fasa ta yanka dafaffen kwan a ciki sannan ta fasa danye ta zuga ta juya ta aje ta duba kazar itama tayi Nan da Nan ta hada pepper chicken sannan ta jona tanda electric ta Fara zuba hadin Irish din Nan tana soyawa Kamar masa, tana gamawa tayi pepper chicken. Dora ruwa tayi a karamar tunya kafin ya tafasa ta dauko madara ta bude ta diba a wani bowl ta dama sannan ta dama corn flour a cup, jikin kitchen cabinets din ta tsaya tana bin karatun da yake shigowa daga parlour har sun kai suratul D'AHA.
Madarar ta zuba taci gaba da tafasa sannan ta zuba corn flour din ta daure da yayi dai dai yanda takeso ta sauke ta Kara Masa condensed milk a cikin ta juye, hadesu tayi a babban tray tayi ta nufi falon, Nan akan dining table ta jero komai sannan ta koma ta dauko sauran tarkacen su cups.
Kitchen din ta koma ta gyara gurin tas, sannan ta koma daki wanka ta shiga, tana fitowa ta shafa lotion dinta tayi simple makeup ta saka saka turarikanta na jiki dasu humra Nan da Nan jikinta ya shiga fitar da wani fitinan Nan kanshi, doguwar rigar Dubai Mai kananun stones pink mai duhu ta saka rolling tayi dan Vail din
rigar milk colour sai ta fito balarabiyarta sak Dan idan ba kaji tayi maka Hausa ba bazaka taba cewa tasan ko zo da Hausa ba, tayi kyau matuka yarintarta ta fito sosai idan ka kalli fuskarta very cute sai wani annuri take fitarwa.
Parlour ta fito gurin dining din ta nufa cikin takunta das das. Tana mamakin Ina ya shiga Dan ko motsinsa babu har yanzu ita kuma bazataje bedroom dinsa ba, idan ya gaji da zaman dakin ya tunda ba yaro bane yunwar cikinsa ta fito dashi. Kunun madarar ta zuba da masar Irish din kwara biyu kawai ta dawo main parlourn ta zauna tana ci tana sauraren karatun, sai da ta gama ta Kai kayan kitchen ta wanke sannan ta dauko Wanda ta zubawa baba Mai gadi ta nufi kofa a hankali take tafiya a cikin harabar gidan iskar bishiyoyin da sauran shuke shuken suna kadawa gwanin sanyi can gurin gate taga baba Mai gadin ya nufa da sauri da alama budewa zeyi.Dan tsayawa tayi daga gefe idonta Yana kan gate din Dan taji dirin mota zata shigo cikin kankanin lokaci motar ta shigo ido cikin ido sukayi da shi shine yake driving din gabanta ne ya bada ras ras Kuma ya kafeta da fitinannun idanunsa cikin gwaninta ya nufi parking lot, Sameer kuwa Kamar wani sakarai haka yake kallon zahrar Yana tsarkake suna Allah a zuciyarsa ya ganta har kusan hudu Amma da alama ganin tsoro yake Mata sai yau yaga zahirin zahrar, da sauri baba Mai gadin ya karaso yana gaisheta ta Mika Masa Dan Karamin basket din ta juya da sauri ta nufi kofar falon har Kamar tana dan sassarfa ta shige ciki, harta wuce idanun Mahmud suna binta Nan da Nan yayi kicin-kicin da fuska daman ga Sameer ya tabo shi ga itama da kalar nata shirmen, cikin zafin nama ya kashe motar ya Kama kofar ze bude Sameer ya kamo hannunsa ya rike Yana girgiza masa Kai kafin ya dungule dayan hannunsa irin na roko din nan yace.
"Pls Dan Allah cool your temper kada kaje mata a haka kayi Mata uzuri Batasan Kai ko waye ba, Kuma infact ma laifinka ne ka tafi ka barta a gida har zuwa wannan lokacin Kuma tana ganin hakan da tayi shine dai dai koni nayi supporting dinta hakan shine dai dai ta nuna maka tasan haqqin abinda ka bar mata amana" .
A Dan fusace ya kalli Sameer.
"Nine na Bata amanarsa da izuninwa ta fito nan wato. ya kalleta yanda yakeso ko? Matata take kaiwa Mai gadi abinci wannan wane irin zubewar aji ne a gurina? Dubi fa yanda ta fito? Ko baka gani ba?"
Ya fada yana kallon Sameer.
"Ni banga wani Abu na rashin kyautatawa ba a shigarta, kawai dai idonka wani Abu ya nuna maka na daban gaskiya".
Hannunsa ya zare daga cikin na Sameer din ya bude kofar a hankali ba Kamar dazu ba zagayowa Sameer yayi ya rufe motar yabi bayansa Dan Idan ya Bari ya shige irin na jiya ze masa ya ajeshi a waje, kofar ya bude wani sanyi da kanshin girki Dana turarikan daki sukayiwa Sameer sallama Bata Nan sai tv a kunne ana karatun har lokacin.
Direct gurin dining Sameer ya wuce yana fadin Bari na Fara da Nan Idan na gama ma gaisa tunda ba bako nake ba ya Fara budewa Yana kallon Mahmud Yana fadin.
"Tab da alama Allah ya tarfawa garinki nono irin wannan delicious".
Gaba Mahmud yayi Bai tanka Masa ba ya shige ciki.
Kofar bedroom dinta ya kalla har dariya take bashi bilhaqqi da gaske tsoransa takeji bare Kuma da jiya ya Dan motsa mata Jamiyya.
Ta Dan Dade a bedroom din nata daga baya ta bawa kanta kwarin Gwiwar ta fita ko banza bazata bada kofar da wani na waje ze gane da 'yar tsama a tsakaninsu ba Kar a Raina Mata wayo, fuskarta ta Dan Kara shafawa powder kadan ta Dan Kara fesa mouth freshner Mai kamshi apricot ta nufi kofa tana budewa saura kadan yau ma suyi karon, da sauri taja Baya. Shigar kananun Kaya yayi as usual dan zaman da sukayi ta fashimci kamat ya samu wani freedom ne na sakewa, trouser black da milk T-shirt ne a jikinsa hannunsa daure da agogo sai waya a hannunsa. Baya tayi da sauri tana Dan zare idanu Dan ba Karamin tsoro taji ba, Shima kallon ta yake Kamar ya rungumota ko yaji relief na abinda yakeji a zuciyarsa, amma sai ya share ya Mika hannunsa ya kamo nata ya natso da ita kusa dashi Sosai Yana Fadin "kin tashi lfy?".
Ya shafi gefen fuskantar, cikin siririyar murya tace masa
"Ina kwana? Shiru yayi Kamar beji ta ba, ya janyo ta suka Fara tafiya a cikin corridorn, sai da suka Fara gangara steps din taji yace waya Baki izinin fita gurin watchman din can?"
Ya Dan matse hannunta dake cikin nasa.
"Wash!!! Allah ta fad'a ba tare data shirya ba. Dan da gaske matsewar ta shigeta dago Kai tayi cikin narke fuska Kamar zatayi kuka dai dai lokacin Sameer ya dago Kansa daga daddana wayar da yakeyi Jin maganarta Sam beji tahowarsu ba wani irin perfect match couples ya gani sun masifar dacewa da juna ya Dade bega ma'auratan da suka burge shi kamar su ba, a zuciyarsa yake Fadin.
"Masha Allah".
Zahrar Tace masa.
"Ba kowa, Dan Allah ka sakar min hannu wlh zafi...."
Ta fada cikin shagwabar da Bata San tayi ba.
Murmushi Sameer yake ta saki daga inda yake Dan ba karya yasan muhmud yayi dacen da Basu zata ba abun kamar a film yake ganinsa. Dan lokacin da suka Fara ganinta da Kuma furucin da shi Mahmud din yayi ashe Allah ya karbi addu'ar.
Dan gyaran murya Sameer yayi Yana kallon Mahmud din tare da fadar.
"Yallabai a bar madam ta karaso mu gaisa Mana ni ba mazauni babe gaba nayi daga Nan"
Ya fada da sigar zolaya duk yaga har yanzu kamar Yana Jin zafinsa tun maganar da yayi masa na Safnah.
Sassauta rikon hannaun yayi suka ida gangarowa directly dining area ya nufa yana zuwa ya ja Mata kujera ya zaunar da ita sannan Shima ya janyo ya zauna.
Gurinsu Sameer ya karaso daga inda yake zaune Yana fadin.
"Madam barka da Asuba kingan ni sai yau ki?".
Ya fad'a yana Zama kusa da Mahmud.
A kunyace ta amsa da "lfy kalau Ya Sameer ya kaje gida? Ina madam?"
"Komai lfy ya hakuri damu?".
'yar dariya tayi kafin ta Mike ta Fara bude abincin Wani daddad'an kamshin ne ya doki hancin Mahmud har Saida ya lumshe idonsa, Dan kallonsa tayi sannan ta kalli Sameer tace "me za'a zuba?".
Kai Sameer ya girgaiza Yana fadin "ai ni na riga ku ci tun shigowarmu naji bazan iya jiran masu gidan ba saina shide Ina jin kamshin delicious Amma ace saina jira".
Ya fad'a Yana dariya.Dan murmushi Mahmud din yayi.
"Wato ko Ina saika nuna halinka ko?".
"Pls zuba min kawai".
Kallonsa tayi kasa-kasa, tace "Toh"
Masar dankwalin turawan ta zuba sannan ta zuba pepper chicken din ta tura Masa sannan ta zuba kunun Madarar sannan ta koma ta zauna a darare.
Wani cup d
in ya zuba kunun Madarar ya dauko da fork ya matso kusa da ita da plates din abincin yace.
"Oya saka hannu muci".
Ya wani hade gabas da yamma alamun ba wargi Kai ta shiga girgaizawa alamar ta koshi Shima ture abincin yayi Yana duban Sameer.
"Muje kawai"
Ya fad'a yan Jan kujerar baya.
"Zanci".
Ta fada a gajarce.
Komawa yayi ya zauna Yana fadin "fine tunda zaki
i gara Idan mutuwar zamuyi mu mutu tare Dan naga abinda Mata suke yayi kenan Idan aka Basu Wanda ba shine zabinsu ba su kashe shi su auri wanda sukeso".
Tunda ya Fara Kora bayani Zahra tayi masa kur da ido tana Mai maita.
Kai Sameer ya shiga girgaizawa Yana mamakin wani sabon hali da Mahmud din ya tsira, yaga alama nema yake ta Hana yarinyar Nan sakat.
Ita Kuma tunda ta furta zanci Bata Kara tofa ko kalma daya ba, sai kawai ta dauki fork ta cako Irish din ta Kai bakinta ta tauna ta hadiye, pepper chicken din ta dauka taci ta dauki kunun Madarar ma ta Sha duk Yana kallon ta shi kuwa Sameer Yi yayi Kamar Allah Bai halicce shi a gurina ba.
Tana gamawa ta tura kujerar da take Kai baya sannan ta dubi shi ido cikin ido tace.
"Gashi naci idan kana tunanin zan zuba maka poison a abinci kayi kuskure lalacewar tawa Bata Kai haka ba, Idan na kasheka wace riba zanci? wato ka tafi lahira free ko? duk lodin zunuban daka dauka niga sakarai na lodawa kaina, to Bari na fad'a maka ba saina aikata zunubi irin haka zan rabu da Kai ba A'a salin alin kowa ze kama gabansa ni da Kai tunda daman masu iya magana na cewa tsintacciyar magen Bata mage nasan komai Daren dadewa zaka koma inda ka fito".
Ta fad'a Tana wurga masa harara ta wuce ta kyalesu batabi ko takan Sameer da yake fadin "Allah ya huci zuciyar amaryarmu".
Da ido Mahmud yabi Zahra har ta bacewa ganinsa "Wai shi yarinya kamar wannan zata saka shi gaba ta fada Masa son ranta amma yayi shiru Yana kallon ta".
Sameer ne ya katse Masa tunanin da yake.
"Dan Allah kada ka koya matsa tsiwa wlh da gani Bata Saba ba, bakaga jikinta har rawa-rawa yake ba".
Ya fad'a Yana kallonsa.
"Jikinta na rawa kenan Kare mata kallo kayi har kaga jikinta na rawa ni ban gani ba?".
"Subhanallahi! Wace irin magana ce haka wlh ba haka nake nufi ba, Bari naje kawai sai munyi waya".
Ya Mike Yana aje rafar dari biyar guda biyu Yana fadin "A bawa madam ace Mata na wuce tunda ka Hana muyi sallama".
Ya biya Kan center table ya dauki keys dinsa yayi gaba tunda yasan ba magana Mahmud ze Masa ba Dan da gaske yazo wuya yanda yanayin fuskarsa ta nuna.
Bayan fitar Sameer, Mahmud kasa ko motsin kirki yayi wai shine tsintacciyar magen? Da gasken gaske maganar ta dokeshi kwafa yayi Yana fadin zakiga tsintacciyar mage iya ganinki sai kin gane bakin rijiya ba gurin wasan makaho babe".
Ji yayi kwata kwata abincin ya fice masa raga Rai duk yanda yake jin yunwa ture abincin yayi ya Mike ya nufi bedroom dinsa Bai jima ba ya fito cikin shigar yari filtex fari dinkin boda da farar hula a Kansa Yana baza qamshinsa na Ibada, yayi waje.
Tunda Zahra ta Fadi maganar dake ranta taji zuciyarta wasai, gefen bed dinta ta zauna tana mita.
"Haka kawai saika wani ringa sakarmin magana ba control duk abinda yazo bakinka saika fad'a mini, Wai na saka wani Abu girkinma ba saina Kara yo da Kai ba sannan na Zama suspect daman saboda A kashedin Ammah ne yasa nayi, kwana biyu amma kamar na shekara duk ka matsa min ka karbe min waya nayi Shiru na Zuba maka ido Naga gudun ruwanka, na fita mikawa bawan Allan Nan abinci kace da izininwa? Haka kawai ka zamar min karfen kafa".
Ta fad'a Tana kwafa.
Tunda gari ya waye Ammah Bata zauna ba shirye-shiryen tafiyar Inna maimuna take wadda zata tafi yau, cikin Shirin fita unguwa Mama ta shigo lokacin Ammar na zubawa innar kilishin da Abba yasa akayi Mata zaunawa tayi tana Fadin "Inna yau zakiyi Mana ta Baki wlh ba dadi".
"Kayya Hajiya Rabi banda abun yazo da sammazi Aida na jima da tafiya gida daga zuwa biki na share our na zauna kinsan da Ardo Yana Raye hakan ba zata faru ba yaushe ze Bari".
"Haka ne Kam Allah yayi musu Rahama".
"Amin" su Inna suka amsa.
Leda mamar ta aje kusa da innar tana Fadin.
"Gashi Inna ba yawa Allah ya kiyaye hanya ni fita zanyi unguwa nasan kafin na dawo kin tafi".
Gdy innar da Ammah sukayi Mata ta tashi tana yiwa innar fatan sauka lafiya.
Sai bayan ta wuce ne innar ke tambayar Ammah ina Hameeda ne Naga tun she jiya da safe bata qara ganinta ba.
"Jiya kina barci tazo Nan Wai ta tafi Jos gurin yayar mamansu larai".
"To ba laifi hakan ba laifi daman shekaranjiya ne da dare na fita zanje can inda na baza ganyen yandi Dana shanya naji uwar tana surfa Mata zagi ban dai San dalili ba Amma naji ita yayar tata tana Fadin sai kije kiba Zahra hakuri Mana tunda kanwar uwarta ce ni dai Nan na barsu Dana dauko shanya ta".
"Allah ya rufa asiri kowa yayi nagari Kansa ya yiwa kuma sharri Dan aike ne duk inda ka tura shi ze dawo, bansan abinda yarinyar Nan ta tsare musu ba, bana raba day biyu da abinda sukasa Hameedar tayi inaga daga baya ta gane Bata kyauta ba shine tayi magana uwar ke zaginta".
Sun Dade suna tattaunawa.
Gurin Sha Sha daya da rabi magaji yazo ya dauki Inna maimunar zuwa gidan Zahra.
Zahra na barci Dan batasan lokacin da barci yayi awon gaba da ita ba, cikin barcin taji alamar bell din kofa ta yunkura ta tashi ta yafa Veil din rigar saman gashinta.
Tana budewa taga Inna maimuna da magaji, jikin innar ta fada kawai sai ta saki kuka Wanda ita kanta bata San kona menene ba.
" Ke matsa can da Baki rabuwa da shiririta saboda Allah menene abin kuka magidanciya dake, Dan Allah duba min Nan Mai sunan malam wannan ai rashin wayo ne koba haka ba?"
Ta fad'a Tana kallon magaji, duriya yayi Yana fadin "kumfi kusa Inna na bankwana ne tunda Idan Kika shige wannan lungun Sai baba ta gani, ni Naga ma kinyi Rana gaskiya har yanzu Baki tafi ba".
"Ai a Gombe zanyi kwana biyu gidan Dan aminiyata da nayi rainonsa to nayi Masa Alkawarin zuwa idan zan tafi".
Ita dai Zahra tunda ta kwantar da kanta a cinyar Inna maimuna Bata Kara dagowa ba, jinta a jikin innar sai takejin wani sauki da nutsuwa suna saukar mata.
Gashin Kanta innar ta Dan shafa inda gashin ya fito tana Fadin shi dai wannan gashin baisan kitso ba Kullum Yana Nan a nannade kamar gammo".
Dan turo Baki tayi tana Fadin
"Ya zanyi kinsan ba kitsuwa yake ba ko anyi idan ya Dade kwana biyu ne kawai ga zafi".
"Allah ya kyauta kawai dai 'ya'yan zamani Amma har yaushe za'a yita Zama da Kai haka? Yau Wai uwar taku tace meya samu wayarki ko an Kira Bata shiga? tasan ba rashin caji bane tunda ance Kuna da wannan abar Mai amfani da hasken Rana"
Dan Jim Zahra tayi tace ya karbe wayar ai hakan be dace ba, Sai kawai tace.
"Nima bansan meye matsalar ba kawai rufewa tayi taqi kunnuwa".
Magaji ne Wanda yaketa faman cakular waya dago Yana fadin dauko mugani ko abun minor ne".
"Bata gurina tana gurinsa ban sani ba ko dubawa ze bada ayi".
"Shu wa?"
Ya fad'a da sigar zolaya, banza tayi masa kamar bataji ba.
Tashi daga jikin innar Zahra tayi tana Fadin Bari na dawo wlh murnar ganinki ta mantar Dani ko ruwa ban kawo Miki ba". Tayi gaba innar na Fadin "dawo Zahra'u nida ba bakuwa ba".
Gaba tayi abunta.
Saida ta ciko tray babba da dangin Zaki da sanyi har sauran pepper chicken din ta zubo musu, tunda ta aje innar ke binta da kallo tana jinjina abin wannan cimakar bata mai Karamin kafin bace ko ance gida tallafin qungiya ya samu har abinci ci susuka dauki nauyin bashi?"
Ita dai shiru tayi Bata tofa ba Amma a kasan zuciyarta da maganganu fal Wanda zasu tattaunawa da 'yarta.
Ware ciki magaji yayi ya kwashi gara har Inna na Masa Dan biki.
Wayarsa Zahra ta barba ta Kira Ammah ta gaisheta itama abinda ta fadawa innar ta fada Mata game da wayar lokacin data sauke wayar harda share 'yan hawayenta, magaji Yana Mata tsiyar shatwabarta tayi yawa ita Batasan ta kusa Zama uwa ba,Inna na Taya shi.
Sai da Innar ta Gama sannan ta tambayi Zahra.
"Wai Ina Mai gidan nawa ne banji motsinsa ba tunda nazo?"
Kafin Zahra ta lalubo abin fad'a magaji ya rigata Yana fadin.
"Ai kin baroshi can a unguwar mu gashi nan suna magana da Ya Abdul Hakeem a kusa da masallaci har suka daga Mana hannu".
"Awoh to ai kasan ban waye dashi ba sai a hankali".
Nasiha Sosai da ban baki Inna maimuna ta Kara yiwa Zahra tare da kara jaddada Mata mashinmancin biyayya ga miji.
Kaya Zahra ta zubawa inna a wata babbar leda harda atamfa dasu turaruka taba Magajin ya rike mata.
******
Tafiya ce miqqqqiya daga Azare zuwa Babban mutum ta Babura jihar jigawa, direban daya dauko Mama da Asabe ya Dan juyo yana kallon Asabe wadda ta maida hankali gurin cin doyarta da kwai da suka saya a kanya babba yace ",munzo Babban mutum fa Ina zamuyi kinyi shiru alhalin kece idona tunda wannan ba yanyata bace".
"To na manta wallahi kasan da Dan Habu muke zuwa na zata shine ita dai Mama Bata cewa komai Dan niqab nema a fuskarta badan ta matsu da son ganin malam na bande din ba da ba yanda za'ayi tayi wannan kasadar Dan yanda ta fadawa Abban Itas/gadau zasu wata dubiya Alhajin yaso Bala direba ya Kaita ta nuna Masa da kawarta matar tshon Ambassador zasuyi tafiyar abinda ya Hana Bala direba kaita kenan, hanyar tinkin ta nuna Masa alamar Niger zasu shiga.
"Yanzu ke Asabe a she Niger zamu shiga shi ne kikace min kauyen Babban mutum wlh da bani da takardar ecowas da Saida na zubeku ku nemi wadda zata karasa daku kinsan kuwa yanda suke da doka da order?".
Tafiya ce miqqqqiya daga Babban mutum zuwa bande, sun Sami tarba Mai kyau daga yaran malam na ciki suna fitowa su Asabe suka shiga malam din yana zaune akan buzu da wani zabgegen carbi a hannunsa ya amsa musu sallamar su suka zauna suna gaishe shi.
Asabe ya dago kai kalla.
"Baki fad'awa Hajiya sakona ba?"
"Allah ya taimaki malam na fad'a Mata cewa tayi na kawota gurinka tazo taji Koda yanda za'ayi lamuran ne suke neman canza fasali".
Carbinsa ya Fara ja yana girgiza Kai yayi hakan kusan say uku kafi ya sauke wani dogon numfashi yana Kara girgiza Kai.
Mama cikin kidimewa ta furta.
"Da matsala ko malam?".
"To da matsalar Amma Abu mafi ban mamaki shi yaron har yanzu bana ganin komai akan Lamarinsa kwata-kwata sai yau Naga wasu mutane a Kan lamarinsa da Kuma itama yarinyar an tasa ta gaba da dafa'i shiri Kuma na gasken gaske sai dai naga wata tafiya a gaban mijin nata da alama Kuma tafiyar da Alkhairi q a cikinta sai dai idan dauke hankalinsa za'ayi daga garin kwata kwata, idan ya tafi ya kasa ko tunanin garin bare ya dawo, idan ba haka akayi musu ba ba makawa sai kin Zama 'yar kallo a gidan dan duk yaran gidan Mata ba wadda tauraruwarta ta kama kafar tata da gaske haka Allah ya yita da madaukakin Alkhairi".
Zuru Mana tayi ta kasa magana, maganar dai ita kenan Zahra tafi nata 'ya'yan.
"Malam ayi duk abinda ya Kanata inda hali ma ya rattaba Mata saki kafin yabar garin".
""Abinda ban gani ba kenan a cikin auren nasu Dan Idan shi ne ze saketa to inaga sai dai ta mutu da auren Dan Banga hakan ba a tare dashi,ni a yanda na gani a istiharata ma ya Santa batun a Nan garin naku ba Kuma da soyayyar ta Mai karfi a zuciyarsa wadda har abada baze iya rabuwa da ita ba, ayi dai hakan yanda Idan iyayenta suka gaji da jiran dawowarsa Bai dawo ba su raba auren da Kansu". Bayanin ya kwantawa da Mama hankali, ya kawo abubuwa ya bata har Wanda za'a hada da tuaren wuta a bawa zahrar Idan harta turara Mahmud ya shaqa shida Azare har abada.
Kudi masu kauri Mama t


AUREN HUCE HAUSHI


MAMAN FATEEMAH


PAGE TWENTY FOUR (24)


_____ Tun bayan tafiyarsu Inna da magaji sai gidan ya zamar Mata shiru Bata Dade a parlourn ba ta koma ciki, da taga tunani yana neman ya dameta saita dauko qur'an dinta ta Fara karatu Saida taji Kiran sallah ta aje taje tayo alwala.
Bayan ta gama sallar ta Haye gado ta Kara A/C tayi kwanciyar ta ba tafi minti talatin da kewnciya ba taji alamar Baki ana Danna bell, tashi tayi ta nufi kofar da gaske dai bazata samu barcin na kirki ba,Kofar ta bude a hankali su Amatu ita da Aunty safiyya ne guri daya suka zauna a Dr sulaimanu Adamu model school of Hygiene inda tayi service, su Kuma permanent lecturers, rabon ta da Amatu tun ranar daurin aurenta dan lokacin da zata wuce jama'are garinsu Bata biyo ta gidan Ammah ba daga gidan Aunty Hasana ta wuce kawai. Cikin nuna tsantsar farin ciki Zahra ta rike hannun Amatu tana fadin "wlh nayi fushi Amah Ina nan Ina jama'are? Amma kikaqi dawowa ni Aunty safiyya zanyi welcoming kawai Amma ke kam dai sai a hankali kawai, Aunty sannu da zuwa". Ta fad'a Tana Basu hanya tare da karbar yaron Aunty safiyya dake hannun Amatun.
"Hakan ma na gode tunda an karbi Auntyn ai shike nan tunda ita ta gari batayi laifi ba saini da nake can kauyen mu".
Ta fad'a Tana Zama a cikin one seat dake kusa da ita.
"Eh wlh Aunty tana da excuse a gurina tunda nasan Bata Nan taje gida sokoto Amma ke kuwa ko waya fa Baki Kira kinji ya ake ciki ba".
"Kice dai ban Kira ba. Amma tambayi Sajida kiji na kirata yafi sau ashirin ma ke dince lokacin Kiran baze yuwu ba Sai ki qara narkewa".
Dariya suka saka su duka harda Aunty safiyyar.
"Wlh Amah saina rama kinci bashi, Wai na narke kamar wani danyan tuwo".
"To da mecece? mutuniyar dake somewa Kikayi fa dif kika dauke wuta".
Kyale Amatu Zahra tayi ta karasa kusa da Aunty safiyya ta zauna ta Dora Shureem a Kan cinyarta tana Fadin.
"Aunty sannu da zuwa Ina yini?"
"Lafiya kalau Amarya ya Amarcin Naga ya barbeki kanwata Masha Allah".
Dan sinne Kai tayi tana Fadin "Kai Aunty Ina wani Amarci a Nan kawai dai".
"Gulmammiya Kinga yanda kikayi wani mahaukacin kyau kuwa? Ai da gani Amarci ya tabbata a gare ki,wa Zaki kife a baibai yarinya Kar nake kallonki fa".
"Allah ya shiryeki tunda haka Kika zama, Bari ki gani".
Ta Mike da Shureem a hannunta ta nufi kitchen, saida ta Zuba musu kayan garar a plate ta dauko musu ruwa da drinks ta dauko plate ta fito tana Fadin "Amah shiga ki dauko dayan Dan Allah".
Sai da suka Gama sannan Zahra tace su shiga suga gidan, ko Ina suka shiga Fadi suke Masha Allah! a gurin fridge din dake cikin Dan Arc din dake tsakanin kitchen da dining area ne Aunty safiyya ta kasa hakuri Saida ta magantu lokacin data Kai hannu ta bude tana fadar.
"Yau ne ganina na biyu da fridge din nan naso shi kamar qaddara Amma da aka fad'a Mana kudinsa Saida na Raina kaina"
"Kai haba Aunty bakiyi niyyar saye bane".
Zahra ta fada.
'yar dariya Auntyn tayi. "Bazaki gane ba Idan ci baizo daya ba ai koshi ma baya zuwa daya".
"Haka ne kam Aunty".
Amatu ta fada, suka nufi bedrooms dinta ko Ina dai maganar daya ce Masha.
Amatu ce ke fadar "Allah ya mayar damu danshinki".
"Amin. Amma Banda kalubale irin nawa, ba Dadi Amah har gobe abun Yana damuna bani da nutsuwa ko Kankani wlh duk lamurana sun tsaya cak bani da wani karsashi irin na amarya a gidanta, komai ganinsa nake Wai banbarakwai kamar a mafarki haka".
Sai Kuma idanunta ya ciko da hawayen da taketa kokarin kada su zubo.
"Ayya haba Zahra kiyi hakuri Mana, ai zuwa yanzu yaci ace kin hakura da koke-koken Nan tunda Mai abkuwa ta abku ai sai hakuri ki rungumi abinda Allah ya Baki ki dangana wata Rana sai labari".
Aunty safiyya ta fad'a.
Parlour suka dawo sukaci gaba da Hira, rabi duk ban Baki ne Aunty safiyyar kewa Zahra da nuna Mata ribar hakuri a cikin hirar ne Amatu take fadawa Zahra sakon Sajida na tana kiran wayata Amma Koda yaushe switch off.
Dan lumshe ido tayi sannan ta bude tana kallon Amatun.
"Matsala wayar ta samu shi yasa ba'a samuna Amma in Sha Allah soon zan sayi wata, yanzu bani taki na kirata".
Wayar Amah ta Mika Mata tana dialing din number ta.
Tana dauka ta Fara mata tsugudidi.
"Yau wacce Rana Amatu ta kirani".
"Assalamu Alaikum ayi sallama Mana bestie".
Ta fad'a tana murmushi.
"Kai!!! wa nakeji haka bestie, haba Dan Allah kin kyauta kenan ba waya ba wasika kin barni a tunani kala-kala Sam na kasa samun nutsuwa". Tashi Zahra tayi ta shige ciki tana Fadin "Bari kawai bestie guy din nan ya fa karbe wayar tun ranar da Kika tafi ya dauketa da safe daya shigo, shine fa daya shigo ya tarar duk na hargitse gado ina neman ta yace tana gurinsa, ya kama min wasu zantika akan Kiran da Musbahu yayi ranar ni kuma na kasa hakuri shine yayi min Rashin mutunci Kuma ya hanani wayar".
Ta fada kamar zata fashe Mata da kuka, tambayar ta tayi yanda abun ya faru Bata rufe Mata komai ba ta fada Mata. Bata katse Mata hanzari ba har ta gama.
"Amma ban taba sanin Baki da wayo ba sai yau, Gaskiya Baki kyauta ba ko alama Ina hankalinki ya tafi kada ki Kara Koda Wasa saboda wani ki ciwa mijin aurenki fuska ai wallahi jarimi ne daya iya hadiye fushinsa bakiji a jikinki ba".
Ta fada a kufule, kit ta kashe Kiran.
Ajiyar zuciya Zahra ta sauke tana kallon wayar a zuciyarta tana fadin ji a jiki na nawa Kuma ba ze fadu bane shi yasa.
Lokacin da zahrar ta fito wasu bakin ta tarar sun shigo su biyu har Amatu ta kawo musu ruwa da drinks suna hira dasu Aunty safiyya, sallama tayi musu sannan suka gaisa Nan Amatu tace musu "ga matar gidan nan".
"Masha Allah"
Suka fada a tare sannan babbar wadda zatayi kamar sa'ar Aunty safiyya tace "mune makotanki da hannun dama sunana Hafsat Amma ana kirana maman junior, wannan Kuma kanwata ce Nuratu da take karatu a Nan Abubakar Tatari Ali polytechnic (ATAP) aiki ne ya kawo Mai gidana mu 'yan Taraba ne".
"Masha Allah! Allah ya taimaka ya bada sa'a".
Suka fada.
Sun Dan jima ana hira dasu sannan suka tafi har gate Amatu ta rakasu da ledar kayan garar biki.
Suma mikewa Aunty safiyya tana goya Shureem da yayi barci, Dan langabar da Kai Zahra.
"Wai har zaku wuce ne Kuma Aunty?".
"Eh mana zan shiga gidan fachalata data haihu bana Nan".
"Amman Banda ke dai Amah gaskiya tunda nasan kina garin Nan sai karshen wata keda jama'are".
Aunty safiyya ce ta tari numfashin zahra
"Ai ita ke driving dinmu ya zan barta a Nan ta dawo Miki special ko weekend ne".
Alamar bude kofar da akayi ne yaja hankalinsu, Mahmud ne ya shigo Yana musu sallama da katuwar leda a hannunsa, tunda ya shigo Aunty safiyya ke kallonsa ita dai tasan wannan fuskar amma ta Yaya za'ayi haka ko Kuma kama ce kawai.
A cikin takunsa na cikakken namiji ya shigo, da sauri Zahra ta nufo gurinsa tana Fadin.
"Sannu da zuwa". Tana Mika hannu zata karbi ledar.
"Da nauyi bazaki iya dauka ba".
Ya fada Yana kallon ta.
Har cikin kitchen ya shiga da ita sannan ya wuce bedroom.
Amatu ce ta zunguri zahra.
"Ke! meye hakan Kuma? Kika wani sharesa Kada dai kice min sokoncin da kike bazawa a gidan kenan ko Kuma Dan kin gammu ne kikayi wani biris dashi".
"Gaskiya Kam ki dage ki Kama mijinki irinsu tsada suke".
Aunty safiyya ta fada tana nunawa Zahra hanyar daya bi.
"Kai! Aunty Kuma ......"
Bata karasa ba Amatu ta Kama hannunta ta nufi steps din tana Fadin "kije kawai tunda daman tafiya zamuyi saina shigo Saturday in Sha Allah".
Dan raurau tayi tana kallon Aunty safiyyar.
"Na gode Aunty ku gaida gida saina zo har gida ban gajiya".
Dariya Auntyn tayi.
'Haba dai sai dai mun dawo, wannan turaren kada kiyi Wasa dashi tun daga besse na taho Miki dashi kakata ta wurin Babana take haduwa da Kanta Yana da matukar kyau sosai ba sai fada Miki ba da kanki Zaki nema".
Dawowa tayi Saida ta rakasu har gurin mota duk da mitar da Amatu ke mata, ta hadasu da kayan garar fal ledoji biyu dasu bokitan roba da mug masu kyau da plates Wanda Aunty Hasana ta bada aka kawo mata saboda Baki masu zuwa.
Saida suka fice daga gidan sannan ta dawo ciki.
Bata shiga ciki ba a parlourn ta zauna tana mitar. "Idan na shiga me zan Masa wanda yake ganina a wata Mai neman rayuwarsa".
Saida Amatu ta dai daita a titi sannan da Dan dubi gurin da Aunty safiyyar ke zaune tana rungume da Shureem.
"Aunty nifa wani Abu ya bani mamaki da daure Kai"
"Kamar me fa?".
"Duk gari ya dauka an aurawa zahra Almajiri k'olo saboda ita ba 'yar Alhajin bace, surutu dai gashi nan, ni Kuma yanzu Naga sabanin abinda ake fada, yaushe Zaki kalli wannan kice Yana Qasqantacciyar rayuwa irin wadda ake fada?".
"Ni Nama fiki mamaki Dan ni dai Idan ba gizo idona yayi min ba ko Kuma kama ce ta halitta tunda ance kowa Yana da Mai Kama dashi a wani gurin, da sai nace Miki M.M DANGE na gani".
"Waye hakan?".
Amatu ta tambaya.
"Bazaki gane ba Amatu wasu Family ne a sokoto masu mahaukanta kudi Nima fa sau daya na taba ganin M.M DANGEN a bikin wata cussing Dina zainab data auri Dan Family din, Kai gaskiya bashi bane inaga Kama ce kawai, amma Kuma kamar harta baci sai dai ba yanda za'ayi DANGE ya iya rayuwa a nan".
"Kamar Yaya Aunty?"
"Tab kinsan kuwa waye shi? ai inaga kaf ba Wanda ya mallaki abunda ya mallaka a duk Family din, gashi yaro matashi Kinga gidansa na sokoto ma kuwa? Banda na Abuja da sauran garuruwa, to in kuwa shine me zeyi da Dan wannan gidan ai ji zeyi kamar Yana rayuwa a kurkuku ne, bama shi bane shifa ko bodyguard dinsa abin kallon ne Suma sun Zama done fa"
Ido Amatu ta zaro.
"Kikace wannan gidan kamar kurkuku? Duk yanda na ganshi Aljannar duniya".
"Naki wasane Amatu. Allah ya kawo dalilin da Zaki shiga ko gidan daya daga cikin families din DANGE ne kiyo kallon duniya me Kika gani a Nan kedai Allah ya Kai damo ga garawa kawai, Dan dai a wannan zuwan da nayi sokoto naje yiwa zainab din barka naji wasu a cikin family din sunata hirar MM DANGEN Wai ko ya bar kasar ya koma turai tun bayan samun wata matsala Mai zafi a cikin family din wadda ta tada kura har rayuka suka baci".
Da ire-iren hirarrakin suka karasa gidan barkar.
Tana zaune a Nan parlourn ya fito cikin kananun kaya da karamar leda a hannunsa direct inda take ya nufo ji tayi gabanta ya Fadi.
"Ya Ilahiy" ta fada a zuciyarta.
Gefenta ya zauna Yana Fadin
"Wash!! I am tired wlh samo min ruwa Mai dan sanyi".
Yayi maganar yana dan matsowa jikinta. Da sauri ta tashi yabi ta da kallo Yana kissima abubuwa da yawa a kanta kunyar ta tayi yawa yasan sai yasha fama kafin ya rabata da ita yanzu dai most important thing ya samu shakuwa da ita sosai.
Ruwan da farm fresh yogurt da snacks ta bawo Masa, idonsa a limshe Kamar me barci Amma Yana kallon ta yanda take tafiya kamar me counting steps sai rausaya take.
Table coffee ta janyo ta Dora tare da bude Masa ruwan ta Zuba duk Yana kallonta.
Ajewa tayi ta juya zata wuce taji hannuwan mutum duka biyun ya zagaye k'ugunta ya mannata a jikinsa ta baya, yayi Mata bazata Dan ko motsin mikewarsa bataji ba ko alama, a tare suka sauke ajiyar zuciya juyota yayi gabadayan ta suna facing din juna Yana Mata wani duban kasa-kasa.
Narke fuska tayi Kamar zatayi kuka tace Masa.
"Menene Kuma? gafa ruwan Nan na kawo maka".
Fuskarsa ya matso da ita dai-dai tata yace.
"Haka ake tarbar miji? Ki bani abincin yunwa nakeji fa, tun safe banci komai ba tunda kika tada min hankali abincin ya fice min daga Rai, waini Kika kalli kwayar idona Kika gasa min maganganu son ranki ko?".
"Ni me nace, cewa fa kayi zanyi poison dinka ni banji haushi ba sai kai, kisa fa? To me kayi min, ni na daina abincin ma ba shike nan ba ban dafa ba bare na zuba maka guba".
Ta fada tana kokarin zame jikinta, Kara gyara rikon da yayi Mata yayi ya nufi two seat da ita a jikinsa kan cinyarsa yayi Mata masauki, ya Kai hannunsa daya ya zame veil din da tayi rolling gashin ya shiga shafawa yana fadin.
"Nifa da Wasa nake Miki dazun bada niyyar na bata Miki rai ba na fada, so I am very sorry Baby in Sha Allah bazan Kara fada ba, na Saba haka nake yiwa kakata Hajiya Inna a irin wannan lokacin na break shine na tunata da ita na fada Miki kema Ashe lefi zanyi, yanzu muje na tayaki ki Samar Mana light Abu muci bana son cin Abu Mai nauyi sosai da dare nasan kafin mu Gama anyi magariba ko"
Ita dai tayi tsumu tsumu duk ta takura fatan ta ya saketa ta fece tunda Allah yasa yanzu ba 'yan tabe taben bane a Kansa a iya gashi kawai aka tsaya.
Dagota yayi daga jikinsa ya rike hannunta kamar wata 'yar baby suka nufi kitchen, ledar daya shigo da ita ya dauko ya Dora a Kan cabinet din kitchen din Yana Fadin "zo ki cire wadan Nan daga ciki.
Kayayyakin amfanin gida ne masu yawa harda su biscuits su chocolate, sai da ta saka komai a muhallinsa sannan ta Fara hada abinda zatayi, kujerar kitchen ya samu ya zauna Yana kallon movement dinta friend spaghetti Mai vegetables tayi sai tayi gasmeat.
Lokacin data Gama komai an Fara Kiran sallah.
Tare suka fito ya mannata da jikinsa a haka ya nufi bedroom dinsa da ita suna shiga ya zaunar da ita Kan sofa ya wuce toilet.
Sai daya rufe kofar sannan ta tashi ta wuce nata dakin wanka take sonyi.
Koda ya fito Bai ganta ba beyi mamaki ba yasan za'ayi haka, lokacin daya leka ya fada Mata ya wuce masallaci tana toilet.
Saida yayi insha'i sannan ya shigo gidan abincin Mai gadi ya dauko ya futa ya Mika masa, daya dawo be nemeta ba,sport news ya kamo yana kallon labarun wasannin da akayi Bai gani ba.
Zahra Kuma da tayi sallah saita zauna tayi Azkar na yamma da Bata samu tayi ba, data Gama tayi shafa ta saka riga da siket English waars combination din milk da maroon tayi rolling da milk veil tayi kyau kamar ka dauke ka boye body mist kawai tayi amfani dasu kusan kala uku cikin Wanda ta gani a cikin locker din mirror dinta sai kamshin ya Bata wani irin Dadi Mai kwantar da zuciyar me shaqarsa.
Plat shoes tasaka a kafarta ta nufi falon,jin gidan shiru batayi tunanin Yana Nan ba Saida ta shigo sosai ta ganshi a kishingide da remote a hannunsa Yana kokarin canza tasha.
Tashi yayi daga kishingidar ya zauna sosai Yana binta da wani mayen kallon, tunda suka hada ido sau daya Bata Kara yarda ta kalleshi ba.
"Zo ga wayar ki Nan tunda Naga itama kinyi zuciya da ita kin bar min".
Ya fada yana Mika Mata hannunsa alamar tazo ba musu ta nufo shi cikin takunta na nutsuwa, shi komai yarinyar Nan tayi burgeshi takeyi ga uwa uba Kuma ya fuskanci tana da tarbiyya da biyayya sabanin yanda yake kallonta, Bai zaci zata kwantar da hankalinta haka ba sai yaga ta tattara komai ta aje gefe abinda ya fuskanta kawai dai Bata daukar raini.
Tana karasowa saita zauna kusa da kafafunsa a kasa taki zuwa gurin hannunsa da yake Miko Mata. Dan murmushi yayi Shima ya sauku Yana facing dinta da karamar ledar dake hannunsa, Mika mata yayi."Gata Nan ayi hakuri ki hada ta batirin ma yana da full charge da sim a ciki, duk numbers dinki important suna ciki.
Wayar ta bude sabuwa ce Kar jujjuyata ta Fara tafi wadda ya Fara Bata tsada nesa ba kusa ba kallon tuhuma ta Farayi Masa tana girgiza Kai tare da Mika masa wayar tana Fadin.
"A Ina kake samun irin wadan Nan wayoyin na mahaukatan kudi wlh ba ruwa na ka rike kayanka bana so ka maido min tawa ta asali kawai".


AUREN HUCE HAUSHI


Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah s.w.a, salati da daukaka da Aminci su tabbata ga Annabin Rahama Muhammad s.a w.w.

Page 25
________Dariya ya kama harda hawaye abinda bata taba gani ba.
Sororo tayi tana kallonsa, ita bataga wani abin dariya ba a maganarta, hannu ya Mika ya karbi wayar kunnawa yayi ya Mika mata Yana kashe Mata ido tare da d'age gira.
"Kina son kisan inda nake samun mahaukanta kudaden Nan ne?".
Kai ta gyada Masa.
"Good ki Bari sai ranar da Kika Zama ni na zama ke na mallaki kayana, a ranar nayi Miki Alkawarin sanin komai nawa na duniyar Nan, Idan Kuma yanzu you are ready za'a taimaki Dan Malam a lullubeshi da bargon ni'ima to? yanzu kuwa kisha labari har wanda Baki nema bama zan fad'a Miki, tunda ke inda nake samun kudi kawai Kika bukata baki son sanin waye ni?daga Ina nake?meya kawoni garinku? Gasu nan rab'ab'a da yawa, to ki rubuta ki aje har abada ni Mahmud bazan tab'a ciyar dake ko shayar dake ko wani Abu na jindadin rayuwa da haramun ba, duk abinda na Baki ki tabbata da gumin halalina na nema, kinga wannan wayar da kudina na saka na saya Miki,wato kina tsoron kada na Sato kayan mutane na kawo Miki ko?"
Kai shiga gigizawa.
"Ni ba cewa nayi kayi sata ba, gani nayi kana ta abubuwan da sai Mai wadata ne ze iya yinsu Kai Kuma Naga...." Sai kuma tayi shiru tana kallonsa.
"Oya continue Mana,kinyi shiru wato Kinga bana aikin komai ko?".
Shirun tayi Bata Kara cewa komai ba.
"Tashi ni ki bani abinda zanci idan na biye Miki da wannan yarintar taki sai yunwa tayi min illah kisa a Fara gulmarki ace kina barina da yunwa, ganshi kin sani azumin da Babu lada".
"Ba Kaine kayi zuciya ba ka tafi kabar abincin"
Ta fada a shagwabe.
"Ki tashi ki bani kada lissafin ya canza fa"
Ya fada yana matsowa jikinta sosai, da sauri ta Mike ta nufi dining inda ta jera abinci.
Table mat ta shimfida a Kan carpet din sannan ta dauko abincin ta aje.
Plate biyu ta dauko dayan ya janye.
"Ki Zuba Mana a plate daya ya Isa ai Kuma indai Ina gida plate din mu daya tunda Kika yimin horon yunwa yau daga Wasa Dan kawai kewar Hajiya ta ta kamani shine Kika horani duk ranar dana kaiki gabanta saina fada Mata tasan irin zaman da zatayi dake, ni Dan gata ne a gurinta bana laifi zakiga yanda take sona".
"Ko?" Ta fada tana zuba abincin a plate, Dan tura Masa plate din tayi kusa dashi "Gashi Nan ni bana Jin yunwa".
"Ashe zan Miki dura wlh, sai kinci kuji min yarinya da kinibibi Wai so kike da karfi sai kin koya min surutu ne? Kin iya kalato abin magana da wani bakinki chut".
Ya fada yana shafo pink din lips dinta.
Taci Amman ba wani na kirki ba da gaske abinci Bai dameta ba barta dai da 'yan ciye-ciye.
Bayan sun gama ne ta kwshe kayan ta gyara gurin duk Yana kallonta komai tayi kyau yake mata gata ba wata babba ba sai dai akwai Sama da kasa masha Allah.
Lokacin data gama ne ya yafito ta da hannu,a hankali ta nufo shi kamar me counting steps sai rausaya take, wani yawu ya hadiye, Dan risinawa tayi a gabansa duka hannuwanta ya kamo ya zaunar da it kusa dashi.
"Zaki rakani unguwa?"
Ya fada Yana zame Mata veil din da tayi rolling gashinta ne ya bayyana biki sidik dashi sai walqiya yake yasha gyara ga kamshin hair spray Yana tashi.
"Eh zani Bari naje na shirya".
ta fada Tana kokarin zare jikinta daga nasa. Duka hannuwansa yasa ya riko kugunta ya hade ta da jikinsa.
"Ina zaki?wane irin Shiri zakiyi kinsan inda zamu ne kike sauri?".
Lakwas tayi a jikinsa da karfi da yaji so yake ya Saba mata da Zama a jikinsa gashi baya ko Jin jauyin taba Mata jikin sai dai idan Bai soba.
"Bazaki tambayi inda zamu ba, kina Neman sake canza Kaya".
"Nasan gida zamuje Mana".
"Ai kece gidan, kinaji da so nake muje gidan da gaske mu roki alfarmar a bamu aron me aiki daya Wadda zata zauna min dake kafin na dawo".
"Kafin ka dawo? Ina zakuje?".
"Au Ashe ban fada Miki ba, aikin NGOS din Nan ne ya taso suka gayyace mu zuwa meeting da zasuyi a UK Kinga ai bazan zauna ba da dollars ko stalling founds suke biyan mu, idan Allah yasa na samu da Dan auki Kinga na Kara jarina tunda Naga Nima Ina sha'awar siyar da materials har munyi magana da Abba yace ze bani rumfa daya a Muda lawal market na gwada ko ina da nasibi a cikin sana'ar, sannan Habib ma munyi magana zamu Fara siyar da spare parts na motoci a nan Muda lawal market din dai".
"Allah ya bada sa'a, Kuma idan ka tafi sai yaushe zaka dawo? Ko kaima shike Nan abinda yake faruwa Dani ze faru a kanka kaima, kada ka tafi ka barni Dan Allah tunda nasan ba Sona kake ba baka ni akayi sadaka, Dan Allah ka taimaka ka kaini Jordan tunda Ina kudin flight kawai ka taimaka ka fitar Dani daga kasar da sunan Kai zaka tafi dani, bana son Ammah ta qara shiga cikin damuwa a kaina wlh Batasan tashin hankali ba Sai Dana isa aure Kullum idan kaga Ammah a cikin tashin hankali to a kan lamarina ne ni Kuma yanzu bana fatan na qara ganinta cikin bacin rai ta dalilina, kaje ka fada musu zaka tafi Dani ko Kano ne ka Kaini na zauna gidan su bestie kafin na samu visa, nagaji da Kasar nan wlh Ina da gata Amma sai walagigi rayuwa ta takeyi anan Dan Allah kayi min wannan alfarmar Koda ita kadai zakayi min ta karshe a zamana da Kai".
Ta kifa kanta a jikin kafad'arsa ta saki wani kuka Mai tsuma zuciya.
Bai hanata ba ya dai Kara matseta a jikinsa Yana shafa bayanta yasan abin Yana cin zuciyarta ne bata rasa komai ba amma an dabaibaye Mata Jin dadin rayuwa kamar yanda Baba malam ya fada masa. Sai da tayi Mai isarta ya dago kanta daga jikin kafadar tasa.
"Kiyi hakuri kowa da irin tasa jarabawar ke taki a haka tazo, Kuma waya fad'a Miki zan tafi na barki bazan dawo ba? Waye kuma yace Miki bana sonki? Kinsan tun tsawon lokacin da nake dakon soyayyarki kuwa? Tun Baki san meye son bama yarinya share hawayen ki Mahmud naki ne har abada, dole kije Jordan ke me gida sukutum a can.Amma yanzu kiyi hakuri nema zani idan Kuma na zauna bakya son tafiyar saina fasa Sameer yayi komai kawai nace madam ta Hana".
"Kaje kawai idan baka dawo ba nasan abinda zanyi".
"Keh! kina da hankali kuwa me zakiyi wlh zan turaki gurin Hajiya Inna duk da ban shirya zuwa yanzu ba kawai ki Kira min ruwa, zaman Allah nakeyi zamanki nakeyi badan ke ba Dana Dade da barin garin Nan".
" Ni Kuma?"
"Off cours
Ya fada da karfin gwiwa.
"As how?"
Share ta yayi kamar bai jita ba.
"Tashi ki rakani kada dare yayi, dauko Mana key din motarki na dana kada na tafi ban Sanya albarka ba, ki canza shiga kada a kalle min kayana" fada Yana mikar da ita daga jikinsa.
Duk kin haye min cinya kinsa sai ciwo take min".
Ya fada Yana Mata wani smile.
Bata kula shi ba tayi gaba abinta duk zuciyarta ba Dadi sannan tana jujjuya maganganunsa a zuciyarta, kinsan tun lokacin da nake sonki? Danke nake zaune a garin Nan gasu Nan dai da yawa.
Saida ta sakarwa Kanta ruwa sannan ta shirya agurguje ta saka wata Riga da siket na atamfa super dinkin ya zauna das a jikinta ta saka mayafin da yayi matching da atamfar ba tayi amfani da turaren kaya ba body mist kawai tayi amfani dasu a jikinta kusan kala uku, sai ya bada wani sansanyan kanshi Mai dadi. Tana gyara gyalen ya shigo dakin tsayawa tayi tana kallonsa shida yace unguwa zata raka shi sai gashi da Riga armless da wandon ta farare tas na kamfanin Adidas sai taga kwata kwata ya canza Mata ya koma irin 'ya'yan hutu din Nan na gaske wadanda Jin Dadi ya gama ratsa su yayi wani irin fresh da shi.
Matsowa yayi kusa da ita Yana Dan watsa hannu irin dai na isassun yaran. Mayafin ya kama ya ida rufa Mata a kanta.
"Kallon fa na menene? Kona canza Miki ne?".
Kai ta girgiza Masa.
"Baba son body language fa ki bude Baki kiyi min magana".
Yana janyo ta jikinsa.
"A'a kawai dai da naji kace unguwa zan rakaka kuma na ganka da......"
Sai tayi shiru.
"Karasa Mana sai Kika ganni da shigar nigas ko?"
Shirun dai tayi.
"Idan Ina tare da iyalin dole na sake, kema da nace ki canza ai na Shan iska nake nufi ba Wai irin wannan ba, zo muje ki canza yawon Shan iska zamu ki min hira ki bani labarin ki tunda ke bakya bukatar nawa ki bani happiness a wannan Daren yanda duk inda nake na rinqa Tino da abubuwan su zamar min kamar kina kusa Dani".
"Ni dai Dan Allah ka barni haka muje kawai"
"Dauko key din to muje dare nayi Kuma Ina son ganin Baba malam da Abban mu, ko ba namu bane?"
Ya fada Yana kallon ta, an samu cigaba, tunda ko banza tunda ya mamnatse ta take iya kallon idanunsa ba kamar da ba da Bata yarda ta kalleshi.
"Namu ne". Ta fada a hankali, badan Yana very closer to her ba da ba lallai yaji me take fada ba.
"Oya let's go".
Ya fada Yana nufar kofa, saida ya kashe electronics na gidan sannan suka fito Yana time da karamar luggage a hannunsa,Kati ya curo daga cikin wallet dinsa ya saka a kofar ya rufe, daga nesa Mai gadi ya hangesu sun nufi parking lot din gidan inda motar daya take ajiye, a ransa yake fadar "duk inda wannan Dan ya fito Dan mafita ne ba irin yaran Nan bane lalatattu kamar yanda aketa surutun abun masu kushe da ganin rashin kyautatawar su Alhaji nayi masu gani kyautatawar nayi".
Yana can Yana tunani Bai ankara ba yaji Karan Horn alamun har sun karaso Yana can Yana nashi zarafin.
Da gudu ya tashi Yana fadin Ayi hakuri nayi zurfi gurin tunani ne, a dawo lfy Allah ya tsare".
Horn ya yi Masa suka fice daga gidan.
Suna barin gidan sun hau babban titi sosai motar su mama ta doso kofar gidan. Dan saida suka hada turaren wutar ya kammala aka zabga Masa turarika masu mahaukatan kanshi da mazubai Wanda dole yayi attracting mutum.
Daga Dan besa direban ya tsaya Mama da Asabe suka fito Asabe na rike da ledar Mai tambarin gurin Saida turarukan wutar dasu humra suka nufi gate din gidan, Asabe CE tayi knocking ta 'yar karamar kofar jikin gate din ya leko ya gane Mama tunda ya jima a unguwar sai dai ita ba lallai yasan shi ba.
Da sauri ya bude kofar Yana fadin. "Hajiya kune haka barka da zuwa ina wuninku".
Ta rusuna ya gaishe su.
'yar dariya Mamar tayi tare da amsawa kafin tace masa.
"Munzo Kara duba Zahra ne tunda tazo ban samu mun shigo ba sai yau"
Cikin nuna girmamawa malam Sani yace. "wallahi kuma anyi sabani yanzu ba dadewa suka fita da Mai gidan da kun lura ma inaga kunyi kiliya dasu a lokacin da zaku shigo su Kuma sun fita".
Turus sukayi wannan ta kalli wannan.
"Ina suka fita daga kawo yarinya ko sati Bata rufa ba?" Ta fada da alamun bacin rain a maganar ta ta.
"Wlh nima ban Sani ba tunda ba hurumina bane sanin hakan ba, sai dai ko Zaki Kira ta a waya idan basuyi nisa ba sai su dawo".
Mama Bata taba danasanin rashin karbar number zahrar ba irin yau.
"Ba komai ga sako Nan ka aje mata idan Allah ya kaimu gobe Asabe zata dawo tayi Mata bayaninsa"
Ta fada tana kallon Asaben, Wadda ledar ke Hannunta, da sauri ta mikawa Mai gadin tana fadar "in Sha Allah zan shigo Amma a fada Mata".
"In Sha Allah za'ayi fada kin gaida gida".
Ya juya da ledar a hannunsa, want abu Asabe ta radawa Mama a kunne tayi saurin tsayawa tana duban kofar da Mai gadin ke kokarin turowa.
"Malam Bismillah".
Ta fada Tana komawa tare da dauko Abu a cikin Jakarta.
Dawowa yayi Yana Dan sadda kai, kudin da Bata San ko nawa bane Mika masa.
"Ga wannan ba yawa Dan Allah a tabbata sakon ya shiga Hannunta komai dare"
"In Sha Allah Hajiya da shi zata shiga ciki, Allah ya Kara sutura na gode madallah".
Ya fada Yana qara gyara rikon ledar da kyau.
"Hajiya ta haka akeyi Nan gaba ko wani aikin kike bukata da gudu zeyi Miki kinsan su bugun Abuja ba bayanin da basa ganewa in dai kina ungo to zance ya Kare Abu sai dai in Baki nema ba, ai Nima goben da sako zan taho Masa Naga alamar kamar zeyi son abin duniya jifa yanda yayi caraf ya karbe kudin daman kamar jira yake.
Dariya sukayi gaba daya harda tab'awa, suka nufi motar data kawo su.
******
Tafiya suke yi Yana rike da Hannunta da nasa dayan, dayan Kuma Yana tuki cikin kwarewa lokaci lokaci Yana Dan matse hannun, ganin sun dauki hanyar barin garin yasa Zahra ta Dan dube shi.
"Wai Ina zamu ne?".
"Siyar dake zanyi, kinji yanda nake samun makudan kudina cikin sauki, duk garin da naje haka nakeyi na duba kyakykyawar mace na aura idan an sake Dani sai nabi dare na gudu nabar garin daman ba Wanda yasan daga inda na fito, bare ke yanda Allah ya surantaki da sura ai ke sai nafi samun alheri a jikinki".
Ya fada Yana wani daure fuska.
Zuruzuru Zahra tayi ganin fuskarsa ba annuri ko misqala zarratin Nan da Nan jikinta ya dauki rawa, duk sanyin ACn dake motar Saida gumi ya rufeta, kallonsa ta Karayi still dai fuskar kamar bai taba fara'a ba a duniya.
Jikinta tsumar ya karayi kamar ana kada Mata gangi, cikin sarkewar murya ta Fara magana bakinta Yana rawa.
Me nayi maka zaka cutar Dani?".
Rage gudun motar yayi cikin duhu, a hankali ya tssyar da motar, Zahra rufe idonta tayi take hawaye suka wanke mata kumatu.
AUREN HUCE HAUSHI
Maman Fateemah
Page 26.
________Sai da ya gangare sosai sannan ya kashe motar, chak ya daukota kamar 'yar Baby ya rungumeta, dai dai kunnenta ya kai bakinsa ya hura Mata iska duka tsikar jikinta ta tashi duk da tana cikin halin rudu bai Hana sakon zuwa ba.
"Ki rufa min asiri ada ace satoki nayi Nan da Nan kin rikice nayi Miki Kama da masu irin wannan d'abi'ar? Wlh zolsyarki nakeyi haka Zaki shide min ki Kira min ruwa daga fita unguwa mu bige da kwanan Asibiti cool down idan na sayar ai Nina kashe kaina".
Ba zato taji ya saka harshensa Yana lashe hawayen Yana Wasa da harshensa a saman idanunta, qanqameshi tayi, "Dan Allah ka bari".
"Na bar me?"
"Hakan ba Dadi".
"To da cewa nayi kiji Dadi? Ni nasaka kukan Kinga ai shanye hawayen ya kamani kada muje inda zamu a juya min baya".
Ya fada yana shinshinar gefen wuyanta.
" Kiyi hakuri bazan Kara ba tunda wannan idon naki Mai arahar kuka ne Ni zanga yanda za'ayi idan abin kukan ya samu".
"Cewa fa kayi ka Saba halinka ne ka Saba yin hakan Kuma fa fuskar ka ba Rahama a ciki kamar Mai tsaron gidan wuta".
"Kai innalillahi! Mai tsaron wuta ni din?" ya fada yana fiddo idanu waje
"A'a ba Kai nace ba kamar nace".
"Ba cinya ba kafar baya"
" Nifa nayi ne Dan Naga idonki, idan kina cikin halin tsorata yana sakani nishadi".
Wayar sa ce ta Fara vibration a jikinsa, Dan zameta yayi daga jikinsa ya dauko wayar ya duba tsaki ya d'an Yi.
"Dan matsala kawai".
Ya fad'a yana saka wayar a handsfree.
"Ya akayi Hayatu".
Dariya ce ta kwacewa Sameer Wadda Bai shirya Mata ba.
"Wlh zan kashe, wato abin dariyarka na Zama ko?".
"Sorry sir wlh ji nayi gaba daya tazo min, Kuma ko sallamar da nayi baka amsa min ba".
"Ka Fadi abinda zaka Fadi Kona kashe da gaske Kuma sallama na amsa Kaine dai bakaji ba, duk safiyar Allah baka tashi kirana ba sai yanzu da tsohon dare salon ka Hana mutum rawar gaban hantsi, na fada maka idan Ina bukatar Abu ni zan nemeka Amma tsabar saka ido sai ka kirani ni, to fad'i meya faru? Ina jinka".
Ya fada Yana maido ta jikinsa.
"Game da maganar tafiyar Nan ce anya zanje kuwa wlh jiya danaje sokoto daukar wadannan hardcopy din na shiga gurin Hajiya Inna muna cikin magana saiga uncle Mustapha ya shigo a sukwane bansan wane minafikin bane ya fada Masa nazo garin ba tunda bana zuwa lokacin da suke gida, ya tasani gaba da sababin nasan inda kake ina kallon su suna walaqiqin nemanka Amma nayi mirsisi naki fad'a musu komai, Ni Ina ta faman lallaba mutuniyar taka amma Saida Uncle mustapha ya Bata lamarin Dan wlh kuka take da hawayen ta bibiyu tana fadin Dan Allah na fada Mata idan mutuwa kayi saita hakurw tasan ita kadai zata nesanta ka da ita, wlh yanda ta bani tausayi da bude aiki kawai zanyi sai Kuma na tuna da warning dinka kawai na fasa, Kuma wlh yanda uncle yayi ba abinda ze Hana shi bibiyata ta karkashin kasa ban sani ba a gida da waje amma ya kake ganin za'ayi? Numfashi ya sauke me karfi yana Kare matse zahrar a jikinsa har Saida tayi 'yar karar Jin zafi.
"Karar me nakeji a kusa da Kai ne?".
"Ina ruwanka tsabar saka ido, to madam ce a kusa Kona baka ita kaji for confirmation, a'a Barta a gaisheta".
Tana jinka a speaker wayar take, ka Bari kawai Zancen baze yuwu ta waya ba idan Allah yasa na shigo sai mu tattaunawa Kuma ka tabbata komai ya kammala kafin na shigo goben in Sha Allah"
"Noted, in Sha Allah a gashe min da ita sosai a fada mata Batool tayi ta kiranta dazu ba'a dauka ba".
"Ina ga a gida ta baro wayar ka ganta Nan sai rigima take zabga min irin tasu ta shagwababbun 'ya'yan larabawan" ya fada yana dan matse dantsen Hannunta kadan.
"Wash Allah na da zafi fa".
Ta fada tana Masa wani kallo Mai ma'anoni kala kala.
"Allah ya bamu Alkhairi"
Sameer ya fada Yana kashe wayar Bai jira yaji abinda Mahmud din ze fada ba.
"Kinga kinja ya katse Kiran bamu gama bayani ba irin wannan Abu haka ai sai ayi zaton muna hanyar shuga wata nahiyar ne".
Sunne Kai tayi a jikin kirjinsa, "Dan Allah ka Bari ni me nayi,".
"Ba komai".
"Bayani zakiyi da yaren garinku yarinya".
Gurin zamanta ya maida ta sannan ta tada motar suka koma kan titi, tunda zahra ta koma gurin zamanta take Masa kallon tukuma da neman Karin bayani.
Amma saiya fuske abunsa kamar be gane ba, Yana ta faman tukinsa ko a jikinsa. Zaranda hotel taga sun shigo, kallon mamaki tayi Masa a kasan zuciyarta tana tunanin me kuma za'ayi a Nan shida yace unguwa zata raka shi to Wai mema ya hada shi da hotel ne? Gurin da aka tanada don parking ya nufa ya kashe motar.
Fitowa yayi ya zagayo kofar da tare zaune ya bude ya Mika Mata hannunsa ta Kama ta fito.
Kulke motar yayi ya jata suka nufi ciki, a Hanya suka hadu da wani security da gani akwai sabo sosai a tsakaninsu.
"Ranka ya Dade an shigo lfy?
Ya fad'a Yana kallon Zahra a kaikaice.
"Lafiya kalau Ibrahim ya aikin?"
"Lafiya kalau yallabai".
Ya fada Yana niyyar wucewa yana Kara kallon Hannunsu dake sarke Dana juna.
" Ibrahim gafa madam Dina Yau na kawota taga mafakata".
Ya fada Yana Dan murmushi.
Dawowa yayi Yana fadin.
"Masha Allah yallabai Allah ya bada zaman lfy, ai Dani aka daura Auren babban masallacin juma'a, madam sannu da zuwa gurin namu".
Ta amsa ta gaishe shi ya amsa yana Mata Allah Sanya Alkhairi sannan sukayi gaba, dakin da yake kusan mallakinsa ya bude musu suka shiga lumshe ido Zahra tayi Dan wani special kamshi da sanyi A/c ne ya bugeta, yanayin ba Karamin Dadi yayi Mata ba, direct kan sofa ya nufa da ita tare suka zauna har lokacin Bai sakar Mata hannu ba. Falon tabi da kallo ba karya komai yaji Dan an kawata shi sosai.
"Wai me zakayi a nan?"
Ta fada tana masa kallon ido cikin ido.
"Me kikeci na baka na Zuba? ai dai muna tare dake ko! zakiga abinda zanyi yanzu ki zauna ki dan tayani aiki kafin naje unguwar ku gurin iyayena sallama".
"Dan Allah kaje Dani "
"Kai ! Naje dake Ina? Lallai kina so na amsa tambayoyi kenan kwanan ki nawa rabonki da gidan? Kawai na kawoki Nan ne kisan dakin yana cikin abubuwan da suka zamar min abin tunawa a zamana na garin Nan kinsan saboda ke na kama shi ya Zama permanent dakina tsawon shekara kusan biyu da nayi a garin nan?".
Galala take kallonsa.
"Saboda Ni kamar Yaya?".
Wani kallo yayi Mata Yana Dan taune gefen lips dinsa na kasa.
"Naki Wasa ne yarinya,Wai kin zata daga cewa an bani Mata saina karba kawai? Niga sarkin tausayi ko to Daman Nima Ina son kayana kawai dai kinfi karfina ne na mikawa Allah kukana Ina zaune Kuma ya juya lamarin gareni tunda shiya hadani dake a inda ban zata ba ya cusa min soyayarki lokaci daya nasan baze Bari na shiga gararin rayuwa ba, duk rintsi ze kawo min mafita sai gashi ya kawo min lokacin da har nayi given up Ina kokarin barin garin idan na shaida dauri Aurenku, amma fa da Allah kadai yasan meya faru yanzu to Sai ya taqaita cikin shikimarsa".
Agogon hannunsa ya duba, Zahra tana kokarin magana ya katseta.
"Adana tambayar saina dawo Kinga idan na biye Miki ba inda zan fita, a 'yan kwanakin nan kin mayar Dani wani parrot sai magana nakeyi ba comma ba full stop, wlh kin canzani kwata-kwata da Hajiya Inna zata ganni Ina zuba haka hum..".
Ya fada Yana daukar luggage din daya shigo da ita da dayan hannun dayan Kuma ya mikar da ita tsaye.
"Zo muje ki tayani shiryawa".
Nokewa tayi tana Dan ware idanunta. Shiryawa kuma? Kaje kawai Ni ina nan".
Gaba yayi yaga alama da gasken ze iya shashancewa a gurinta.
Komawa tayi ta zauna tana jujjuya lamarin bawan Allahn nan sai wasu maganganu yake fada Mata ba tare da fashin baqinsu ba.
Kamshinsa shiya fada Mata wanzuwarsa a falon, a hankali ta dago Kai ta kalleshi "Masha Allah" ta fada a hankali Dan ba lallai yaji ba.
Gurin da take zaune ya Dan tsuguna a gabanta ya Dora Mata laptop din dake hannunsa da wasu takardu da list na sunan mutane kusan dari da ashirin da biyar daga local government hudu Alkakeri, Jama'are, Zaki da Dass, karkashin makarantun Allo zasuyi step down training a Nan Azaren schedule ne na aikin da payment dinsu.
Ta dago zatayi magana ya Dora Mata yatsa a biki "kiyi kawai idan na dawo kin tambayeni duk abinda kike bukatar sani bana son nabar garin Nan aikin Nan Bai kammala ba".
Ya Mike fuskarsa ya kawo dad da tata ya Bata light kiss a gefen kumatunta, saina dawo take care". Ya nufi kofar da sauri da key din motar a hannunsa.
Harya rufe kofar Bata dauke idonta daga gurin ba, ita fa mutumin Nan ya Fara Bata tsoro mutane suna daukarsa wani Abu daban ita Kuma tana ganinsa wani Abu daban.
Ta Dan jima Tana sakawa da kwancewa daga karshe ta watsar da komai ta dauki laptop din ta shige cikinki bedroom din ta Haye lafiyayyan gadon ta bude ta shiga aikin inda Allah ya taimaketa yaci karfin aikin karasa Masa zatayi.
*******
Lokacin da Mahmud ya fito Ibrahim da wani sulaiman ya Kira ya Basu aikin kula da dakin da Zahra ke ciki duk da yasan suna da matakan tsaro sosai Amma hankalinsa Bai kwanta ba sai da ya Kara Mata da nasa, gurin motar ya nufa bayan ya zauna ne ya Ciro wayarsa ya bude ta haka Nan ya shiga CCTV da akayi connecting da wayarsa.
Hotunan ne suka fito rababa na dakinta yayi zooming qura Mata Ido yayi lokacin data fito daga wanka tana daure da Karamin towel fararen cinyoyinta sunyi wani sambal dasu ta Kai ta kawo Yana kallonta harta gama, tunda ya Fara kallon yake sakin wani Nishi kadan kadan Dan da gaske ta yamutsa Masa tunani ji yake kamar ya zubar da Alkawarin daya daukarwa kansa a kanta, komawa yayi baya na kofar gate ya dauki hankalinsa ganin wata mota mata sun fito sun dauko wani Abu a Leda sun nufi gate din gidan full screen yayi da gurin da suke ya waye da mama amma Asaben
e bai ganeta ba yana kallon duk abinda sukayi har Zuwa lokacin da Asabe tayiwa Mama rad'a a kunne ta Kira Mai gadin ta bashi kudi suka juya
da yanda suke kwasar dariya har da tabawa kamar yara sai abin ya bashi mamaki, meya kawo su gidan su kadai ga Kuma motar da gani ta commercial ce, girgaiza Kai kawai yana tunanin abinyi.
Da gurin malam ya fara zuwa ya Dan jima tare dashi kafin ya aje Masa Alkhairi yayi Masa sallama, Yana Kara yi Masa addu'ar samun nasara a tafiyar da godiyar Alkhairnin daya bashi, Habib ne ya Dan kalli Mahmud din bayan sun fito Yana tambayarsa..
"Da gaske baka fad'awa Baba malam ba inda zakun kada fa yaji daga baya yayi fada yace ka tsallake kasa baka fada Masa ba.
Kafadarsa ya dafa.
"Kada ka damu da kaina Zan fada Masa in sha Alllah".
Tare sukaje gidansu Zahra inda suka Dace suna kokarin yin knocking sai magaji ya fito, daga gani wani gurin zaya yanda yayi Shar dashi.
Gaggaisawa sukayi kafin Magajin yayi musu jagora zuwan gurin Abban nasu. Anan falon ganawa da bak'insa suka sameshi, sun gaisa Sosai a Nan Mahmud ya fada masa tafiyar da zeyi, Abban yasa Albarka soshi.


AUREN HUCE HAUSHI.

MAMAN FATEEMAH


Page 27


_____Dan Jim Mahmud yayi kafin ya Dan muskuta kadan ya Kara sadda kansa kasa.
"Abba Dan Allah ko za'a taimaka a bamu Aron daya daga cikin masu aikin Nan Mata su tayata Zama kafin Allah ya dawo damu". Ya fada a ladabce
Dan gyaran murya Abban yayi Yana fadin "Hakan babu laifi kayi tunani Mai kyau baza'a bar yarinya ita kadai ba gara da babba, ba komai kome kenan da safe za'a turo wadda zata zauna da ita, Allah yayi Albarka ya bada sa'a"
Sun jima suna Hira da Abban har suke fada Masa harkar kayan spares na kayan motocin da zasu ringa saidawa, Albarka ya sanye musu sannan sukayi Masa sallama, har sun Kai kofa Abban yace Bari ya fadawa Ammah ku shiga ku gaisa, a waya ya kirata ya fada Mata sannan yace su karasa ciki.
A kofar gate na shiga ciki suka samu Musaddiq Yana jiran su, cikin ladabi ya gaishe su Yana tambayar Mahmud Aunty Zahra, hannunsa Mahmud din ya Kama Yana bashi amsa har suka shiga part din Ammar.
Sallama sukayi tana zaune a parlourn, sallamar ta amsa tana fadin. "Su Habib ne sannunku Bismillah".
Ta fada tana nuna musu gurin Zama.
Basu zauna a kujerar ba sai suka zauna a Kan carpet.
"Ina yini?"
Suka fada a tare, "lafiya kalau ya wajen malam?"
"Lafiya kalau yace a gaisheku".
"Masha Allah muna amsawa, Allah yayi Albarka, yayi muku jagoranci cikin dukkan lamuranku, ayi ta hakurin Zama da yara".
Ta fada a kunyace Dan har ga Allah tana Jin nauyin yaron da kaunarsa saboda karamcinsa da halin fattako daya nuna lokacin da aka bashi Auren zahra da Rana tsaka ya Kuma sa hannu biyu ya karba.
"Amin na gode ba komai, zahrar tace ma a gaisheku, kuma nazo ne nayi muku sallama zanyi tafiya ne amma in Sha Allah bazan jima ba, na fadawa Abba a samu wadda zasu zauna tare kafin Allah yasa na dawo".
"Masha Allah. Allah yayi taimako hakan baze gagara ba ko can gida Mubi Sai a samu wadda zatazo su zauna tunda akwai yaran sosai ba sai an dauko bare ba tunda yau din ta Zama wata iri Amma kafin tazo sai su Fara Zama da zulai tunda Bata da matsala"
"Godiya muke Allah ya kara sutura" Habib ya fada, suna mikewa har lokacin Autan Ammah Yana jikin Mahmud a zaune. Addu'a Ammah take musu har suka fito Nan da nan wani rauni ya shigi Mahmud haka tasa Umman take Masa a duk lokacin da ze shiga wurinta bakinta baya gajiyawa da Yi Masa addu'a, duk kewarta sai ta rufe shi, "kaimu gurin Mama mu gaisa".
Mahmud ya cewa autan Ammah.
Chapter 2 · 0% Book details