Part din Mamar suka nufa, Musaddiq ne yayi knocking har sau biyu ba'a bude ba Kuma suna jiyo maganganu da sound din tv.
Auren Huce Haushi Part 1 Complete Hausa Novel · about 221 min read
Habib ne yace "mu tafi Dan Allah yaushe zamu tsaya kamar wasu 'yan maula". Har sun sauka daga steps din balcony din sannan aka bude kofar, Asabe ce ganin Autan Ammah da mutane yasa ta fito tana fadin ku shigo Dan Allah wlh bamuji ba sai daga baya Salma ke fadin Kamar taji bugun kofa".
Habib ne yayi farat yayi magana "ai ba komai a gaishe da Hajiyar Daman mujin Zahra ne ya shigo ya gaishe ta".
Sukayi gaba suka barta a tsaye.
Ciki ta koma jiki ba kwari.
Mama ce ta kalleta.
"Wai su waye Naga kin fita Kuna magana dasu ne Kuma Basu shigo ba?"
Zama tayi kusa da mamar, "sirikin ku ne inda mukaje basa Nan yazo gaishe ki da alama Kuma sauri suke tunda sun jima a tsaye ba'a bude ba".
"Wai kina nufin Mahmud mijin Zahra?"
"Shifa sunce a gaishe ki, da alama sauri suke Dan har sun fice.
Baki Salma ta tab'e tana fadin. "saura kiris dai uban kowa ma ya rasa, ba dai kunce kun Kai turaren wutar ba, yanda aka wayi gari aka ganshi da hakoransa talatin da shida haka za'a wayi gari yayi layar zana inga ta qafafar da ake anyi aure, auren ma Dan jeka nayi ka da ba wani armashi yayi ba, Shima Abba Dan ya ganshi handsome ne ya bashi ai ko banza ance mijin agolar gidansa ne".
Dakuwa Mama tayo Mata "Abban naki kike fadawa haka? Nima da farko nayi tunanin ko wani lashi yaga yaron Yana dashi sai da na saka akayi min bincike aka tabbatar min da gidan da kayan da yake sakawa duk Wanda yakewa aiki ne suka kawo Masa Dan wasu ma ance min wannan yaron shugaban aikin nasu ne ya kawo Masa kwancensu Dan ya rinka fita kunya tunda matar tasa 'yar boko ce, shi Kuma almajiran soro ance min ma iyakarsa secondary ya Dan iya rubutu da karatu ne yasa suka dauke shi aikin nasu, har kike wani zaqewa kina sonsa ai da naji haka saina fad'i ba nauyi yo Dan kyau me ake da kyau bako sisi Allah Banda nayi Alkawarin saina Maida Zahra karamar bazawara ba, da barinsa zanyi a garin to idan nayi wannan saken kakanninta zasu iya bashi mahaukatan kudi ya nemi sana'ar da ze rike musu jika gara dai yayi gaba tazo ta zauna na Dora daga inda na tsaya".
Dariya Salma da Asabe suka kwasa Asaben ce ke fadar "Aikinki Yana kyau uwar dakina ba Wanda ze taba hasaso hakan daga bangaren ki kin kasa kin tsare duk wata kafa da wani ze fahimci da saka hannunki a lamarin yarinyar nan".
Dariya mamar tayi itama "Au da sokike na ringa nuna adawata a fill ai Ni duk ranar da tazo gidan Nan da bayanin mijin ya gudu sai nafi kowa kuka da tsine masa".
"Sai Maman mu". Salma ta fada tana kyalkyalewa da dariyar mugunta.
*********
A harabar gidan suka samu Abba Yana yiwa malam Bala direba magana, gurin suka nufa Abban na ganinsu ya nufo inda suke.
"Har kun fito"
"Eh Abba zamu koma"
Suka fada tare, takarda Abban ya mikowa Mahmud.
Hannu yasa ya karba.
"Gashi Nan ka Kara guzuri Allah ya kaiku lfy ya bada sa'a".
Godiya sukayi Masa sosai har Saida yayi fada.
Tare suka fita da Auta har gurin mota ledoji biyu Mahmud ya dauko daga seat din baya ya mikawa Musaddiq.
"Gashi naka daya na Faruq daya tukwaicin ku ne na kawo abinci".
Da murna Auta ya nufi gida Yana fadin "mun gode Uncle".
Cheque din kudi ne masu nauyi Abban ya bawa Mahmud saida abun ya Basu matukar mamaki.
Habib ya mikawa cheque din Yana fadin.
"Ka rike a gurinka kawai a sawo kayan shagon Nan dasu a Fara kasuwar tunda Allah ya kawo kawai".
"A'a baza'a yi haka ba ka tafi dasu kayi guzurin Kamar yanda yace idan Allah yasa kun dawo sai asan yanda za'ayin".
"Kayi yanda nace ba wata damuwa acan komai Yi Mana za'ayi to me zanyi dasu? ga Kuma abun bukata a gida ba gara ayi ba watakila kafin mu dawo ka koma sari na biyu".
Ya fada Yana murmushi.
Majalissar su sukaje Mahmud yayi musu sallama har salisu Yana zolayarsa akan barin Zahra da zeyi Yana tsakiyar angwancewa. Bai Dade ba ya tafi duk hanlalinsa Yana kanta yasan har ta gaji da jiransa watakila ma tayi barci.
Saida ya biya ya saya musu kaza da apple ya dauki hanya.
Lokacin Sha daya da minti ashirin da bakwai.
A hankali ya bude dakin abin mamaki Zahrar ya gani gurin fridge da glass cup a Hannunta tana Shan wani abu, Sam bataji bude kofar ba saboda tv a kunne take sannan ta bawa kofar baya, Jin kamshin turarensa yasa tayi saurin juyowa lokacin yazo daf da bayanta, juyowar da tayi sai a cikin kirjinsa.
Ledar ya saki qasa yayi Mata kyakykyawan masauki ya saka hannunsa ya talkafo bayan ta, yasa Bakinsa a dai-dai kunnanta.
"Na dauka kin wuce Kano a barcinki Ashe dai jaruma na aura wadda take iya jiran mijinta komai dare". Ya karasa fada Yana Dan hura Mata iskar Bakinsa a kunnen.
"Dan Allah ka Bari".
Ta fada tana niyyar janye jikinta shi Kuma ya Hana hakan. Dan kwabe fuska tayi, "ka sakeni toilet zani".
"Ba wani toilet idan Kuma da gaske ne muje na rakaki".
Kai ta gigiza, shafa gefen ribs dinta yayi yaji yanda rigar ta matseta komai yayi tsan-tsan. Dan sakinta yayi Yana Kare mata kallo daga sama har kasa, Dan sunan dinkin a tsokano fitina kawai, shi a dazu ai be karewa dinkin kallo ba sai yanzu a kausashe ya jefa Mata tambayar.
"Waye telan da yake Miki dinki".
Hannu yasa ba zato ya shafo gaban rigar da sauri ta saka duka hannuwanta ta tsuguna sai Kuma kasan ya baje. "Ya Salam" ya fada a hankali.
"Kinyi shiru Ina tambayarki".
"Makociyar Aunty Hasana ce take Mana dinki".
Ajiyar zuciya yayi yayi zaton namiji ne yaji ance sune ke gwada Mata idan hakan ta kasance ai an gama dashi wani ya taba Masa wannan jikin. Tsugunawa yayi ya kamota ya dago jikinsa ya maidata "ki barni naji duminki gobe ya wannan bana kusa dake Ina can na rungumi pillow, so muje muyi hirar yaushe gamo, ko Kuma ban sani ba murna kike kina Jin dadin Zan tafi na Baki space ki sake ko?"
Ya fada Yana Wasa da Dan Karamin zoben dake 'yar karamar yatsarta.
"Oya talk kinyi shiru koba haka bane daman ba kince min me naci Kamar maye na tsotseki waya sani ko maye ne ni ko Baki fada ba? Kawai Dan na koyawa bakinki ladabin magana da miji akan wannan yaron shine na samu lambar maita daga gurinki".
Sexy eyes dinta ta zaro Masa, abinda yake burgeshi yake matukar so kenan yaga ta tsorata.
"Ni nace maka maye? Yaushe akayi hakan Wana fadawa?"
"Abar maganar kawai sai ranar Dana cinyeki danya Zaki gane Ni maye ne".
"Wlh Ni ban fada ba, Toni Wana na gani da Zan Fadi haka har a Gaya maka, a kwanakin Nan ko waya ban rike ba fa".
"Naji shike Nan zo muje Naga aikin Allah yasa dai yayi kada aiki ya Koma baya"
Ledar tsarabarsa ya dauka ya jata suka nufi ciki. Gefen gadon ya zauna Yana janyo laptop din gefensa Zahrar na tsaye a dayan gefen.
"Hayo ta Nan ki bude ki nuna min aikin in gani". Ba musu tayi yanda yace Kan cinyarta ya Dora laptop din ya Dan kwanto jikinta yana ganin aikin har ta Gama nuna Masa, tab'a hannu yayi Yana fadin "inye kice idan Allah ya hure mun na samu sakatariya ta a gida basai na nema a waje ba, yanzu jeki saman fridge akwai plate biyu ki dauko kizo ki Zuba wannan" ya nuna Mata ledar daya shigo da ita.
Laptop din ta aje kusa dashi ta janyo gyalen da ta yafo zata yafa ya karbe Yana Mata wani kallo.
"Me zakiyi da shi ko akwai Wanda ba muharraminki ba a Nan da Zaki Kama rufe jiki, ok da bana Nan kin aje har Dan kwalin kina watayawa yanzu Kuma na dawo Zaki wani saka gyale tunda idan na ganki kin dauki zunubi ko?"
Shiru tayi Masa tasan idan ta magantu sai ta Kara laifi, juyawa tayi ta nufi kofa ya bita da idon Yana kistima abubuwa da yawa a zuciyarsa.
Plates din ta dauko ta kawo ta koma ta dauko ruwa roba daya da fresh milk tunda taga Kamar yafi son Shanta akan lemo.
"Dauki ki zuba" Nan ma ba musu ta bude kedar Naman wani kanshi ne ya doki hancinta har lokacin Kuma da zafinta, daya ledar ta bude apple din ta Zuba a kai, gyara zama yayi Yana nuna Mata gefen shi, Kaita girgaiza.
" Na koshi bana Jin yunwa".
"Naji ai ba abinci bane kizo kici ko nayi Miki dura da gaske nakeyi fa".
Narai narai tayi da ido, Allah bana cin Abu Mai yaji ko maiko da yawa da dare ulcer yake tada min".
Ture plate din yayi gefe ya janyota ya zaunar da ita a cinyarsa.
"Me Kika ce? Ulcer as how Kika kamu da ulcer, since when?"
"Bafa wani Abu bane tun Ina secondary ne Amma tunda aka fada min na rage cin wadannan abubuwan more especially da dare idan Zan kwanta saina daina ciwon cikin".
Plate din ya ture gefe, "tashi ki Kai fridge ki dawo".
Kallonsa tayi da alamar tambya "to Kai bazakaci ba"
"Ni saboda ke na sawo coffee ko fruit kawai nake Sha a irin wannan time din, ki wanko Mana Apple kawai ya Isa".
Saida ta wanko ta kawo sannan ta dauki kazar ta Kai fridge din ta dawo.
A Dan nesa dashi ta zauna taga alamar 'ya abun nasa Yau suna kusa.
Matsowa yayi jikinta da plate din Apple din Yana Danna waya da alama kamar Kira yakeyi Apple din ya Mika Mata Yana ci gaba da trying Kiran, sau biyu Yana Kira ba'a daga ba ya hakura ya aje wayar.
"Labarin ki Zaki bani tun daga primary, secondary Zuwa Yau din Nan da muke tare Kuma ki fada min dalilin da yasa ake fasa aurenki da dukkan Wanda sukaso aurenki laifin na waye? Ok kafin Nan Bari na tambaye ki wani abu"
Wata wayar ya Ciro daga aljihun gefen hagu na rigarsa.
Jikinta ya matso sosai Kusan Rabin jikinsa Yana cikin nata ya kanainaye ta CCTV ya kunna ya Mika Mata ya saka fullscreen gurin gate din gidansu ne Mama da Asabe ta gani tun tsayuwar motarsu har zuwa gurin Mai gadi Saida ta gama ganin komai yace "Daman Kuna abin kirki da Mama ne? Kuma wacece wannan Dan yanzu da Daren Nan da naje yiwa su Ammah sallama naganta a dakin mamar kenan daga Nan can sukayi"
Ya fada Yana tsareta da idanunsa masu razana ta.
"A'a ni bana wani good term da Mama ko kadan Dan da sam ita da Aunty salma basa yina Daman Hameeda ce tawa idan tana gurin ba Wanda ya Isa ya Fadi marar Dadi a kaina, to ita dinma bansan meya canzata ba lokaci daya tayi min cin fuska ba ko Kara gani a tsaye, ita Kuma wannan Asabe ce aminiyar Mama ce komai tare sukeyi".
"Ok ba damuwa".
Wayarsa ce ta dauki wani slow music alamar shine ringtone din wayar, dauka yayi tare da sallama.
Magana ya Fara Bai jira Wanda yayiwa sallamar ya amsa ba.
"Kazo Azare katagum local government a cikin local government ne na Bauchi state ne a duba map zakaga inda location din yake amma kada ka biyo ta jos Nissan yayi yawa ka shigo ta Kano kawai karfe bakwan safe tayi maka a garin".
Abinda ya fada kenan ya katse Kiran.
Wani Kiran ya Karayi ringing daya aka dauka.
"Bilya a canzawa Mai gadin gidana gurin aiki ya Koma Sharar compound din makarantar yaran Nan kawai" kit ya kashe Kiran duk tana binsa da ido.
Agogon jikin wayarsa ta kalla Sha biyu da Rabi.
A marairaice ta dube shi "yaushe zamu tafi nifa Ina Jin tsoron dare fa".
Kansa ya kwantar a cinyarta Yana facing din face dinta.
"A Nan zamu kwana bakiga harda jakar matafiya ba? jiranki nake ki bani labarin naki kinyi shiru kin shareni".
Dan turo Baki tayi "Toni me zance maka ai kasan komai"
"Kamar Yaya nasan komai, harda labarin da aka turo min ta msm na duk Wanda kikayi tare dashi Saida ya sanki 'ya mace yaji test din Bai Masa ba tunda kyawun iya jiki da fuska kawai ya tsaya" shima Hakan ne tunda anfada min?"
"Cikin razana ta nuna kanta da hannu.
"Ni Kuma Zina? Waye yayi min irin wannan tozarcin? Me nayi musu haka da zafi da har za'a yi min bita da kulli irin wannan?" Sai hawaye.
"Ya Ilahiy!! Ken wace iri ce daga tambaya sai kuka kewai kuka baya da wahala a gurinki Kamar wata 'yar film, tab kice na iya bakina, idan na karanto Miki sauran yau ma a Asibiti zamu waye kinga the chapter is closed labarin ma a bar shi Gama Shan apple din ki kwanta Naga alamun barci a idonki Ni aiki Zan karasa".
Cikin shashhsheka tace "basai nayi komai ba tunda banzo da kaya ba haka ma zan iya kwantawa".
Luggage din ya nuna Mata da Hannun. "Ki bude akwai komai a ciki ya janyo laptop dinsa ya Fara aiki bai Kara bi ta Kanta ba, yayi biris da ita Kamar besan Allah yayi ruwan tsirarta a dakin ba.
Nuku nukunta ta Gama sannan taje ta bude jakar kamar yanda ya fada kayansu ne ita harda sleeping dress Kusan uku Saida ta duba sosai sannan ta samu wata doguwar Riga Mai Dan dama dama ta dauka ta nufi toilet duk abinda take Yana kallonta ta gefen ido har ta shige.
Ruwan zafi ta hada ta zuba turarikan wankan data gani a gurin ajiye, shigewa tayi ciki tayi kwance ruwan Yana ratsata kamar zatayi barci ta jima sosai sannan tayi wankan ta fito, sai da ta goge jikinta ta zura rigar barcin cotton ce mai laushi ta sauko Mata har Kusan gwiwa sai da matsalar ta dayi zif akayi Mata har kasa ga saman rigar wani net aka saka transparent komai a waje yake ba wani sirri Kai kawo da dinga yi a toilet din daga karshe towel na wanka babba ta rufo a jikinta ta fito.
Dago ido yayi yana kallon ta sai Kuma ya janyesu yaci gaba da aikinsa cikin kware, idan yaci gaba da kallonta wlh wata dariya zata kubce Masa, shi dai yasan duk wayon Amarya sai an Sha manta.
A darare tazo ta zauna a nesa dashi.
" Ki tashi ki kwanta ya nuna Mata tsakiyar gadon. Jinjina Masa Kai tayi ta Haye tana Jan blanket din tana rufe jikinta. Kusan Rabin hankalinsa Yana Kanta Yana kallonta tayi Addu'ointa shafa a jiki, tun Tana Dan Jin dar a jikinta har barci yayi awon gaba da ita.
Sai gurin daya ya kammala duk abinda ya kamata ace ya gama.
Wanka yayo tare da alwala pyjamas ya saka masu kalar off-white sannan ya tada nafila raka'a hudu yayi ya sallame ya jima Yana addu'a kafin ya nufi gado dariya ta bashi blanket din daban ita daban sai barcinta takeyi cikin nutsuwa face dinta ya kurawa ido "yes she's beautiful" ya fada a hankali kamar Mai tsoron kada taji.
Kusa da ita ya kwanta kamshi turarensa Dana turaren wanka sai suka bada wani kamshin Mai dadin shaka, madaurin jikin rigarsa ya since ya zare rigar daga jikinsa ya kwanta a jikinta Bata ko motsa ba a hankali ya saka hannunsa ya zuge zif din jikin rigarta yayi mamakin nauyin barcinta blanket din ya janyo ya lullubesu da shi sannan a hankali ya mannata da jikinsa yana sakin ajiyar zuciya, a cikin barci taji Kamar hannu na yawo a jikinta a Dan tsorace ta bude idonta ga dakin ba haske so sai, Sam saita kasa gane takamaiamai a Ina take ga ta Kuma a jikin mutum ko Riga Babu.
"Wayyo Allah na!!!" ta fada jikinta ya dauki rawa..
"Shittt, cool down nine kiyi barcinki Nima barcin nakeji..
.✨✨
✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
Page 28
____Hankalin Zahra be kwanta ba sai da taji Yana maida numfashi a hankali alamun barcin ya dauke shi ajiyar zuciya ta sauke da farko Bata yarda ba da yace barci zasuyi Saida ta gani da gasken yayi barcin.
Kokarin zame kanta da yayi Mata pillow da gefen kafadarsa tayi, a cikin barcin ya kara janyo ta jikinsa yana gyara Mata kwanciyar amman idonsa dai a rufe, shiru tayi lif a jikinsa Dan Bata son ya farka su hada ido ai da kunya amma taga alama shi bashi da ita misqalazarratin idan wani ne ai zuwa yanzu Basu wani sababa yanda abun yazo musu a hagunce, ko dan shifa yana ikirarin ya santa batun yanzu ba to a Ina?Kuma waye shi?daga Ina yake? Waye sameer a zahiri shi yaron sameer ne ita Kuma a bad'ini shi yake bashi directive abin da daure Kai Kuma yace ya manta garinsu da komai nasa Amma a gurinta yana fada Mata ya tuno kakarsa har da 'yar tsamar da sukeyi.
Tunani barkatai ta dunga yi har barci yayi awon gaba da ita, karfe hudu da rabi na Asuba alarm din daya saita ya tashe su kusan lokaci daya suka farka har lokacin tana jikin shi, shiru tayi Bata nuna ta tashi ba, so take ya wuce toilet.
Addu'ar tashi daga barci yayi a hankali ya zare ta daga jikinsa kura Mata Ido yayi a cikin dimligh din dakin face dinta sai glowing takeyi ko Ina a jikin fresh sai wani sansanyan kanshi ke fita daga jikinta wanda har ya zauna a jikinta Dan duk jikinsa kamshin yakeyi, light kiss ya Bata a kumatu ya gyara Mata rufar saboda sanyin AC ga sanyin Asuba. Duk abinda yake tana jinsa bakam tayi Dan ji tayi wani irin nauyinsa ya rufeta Wai wane irin barci ne tayi har yayi sabgar rabata da rigarta amman Wai Bata sani ba, Jin karar ruwa yasa tayi saurin tashi ta janyo rigarta tana cuno Baki.
"Haka kawai duk a kalleka waya sani ma ko Abu ya saka a cikin Apple din Dana Sha shike Nan na Kama barcin asara sai yanda yayi Dani" da sauri ta ida janye blanket din tana duba jikinta Jin ba wani bakon Abu yasa taji sanyi a cikin ranta, sai Kuma abun ya Bata dariya, Jin ze fito yasa ta koma ta kwanta jallabiya ya zura ya saka tashi ka fiye naci, ya dauki tasbasha (counter( ya matso kusa da ita Dan guntun ruwan alwala na fuskarsa ya yarfa Mata kadan a fuskar ta.
"Ki tashi kiyi alwala an kusa tada sallah nasan idonki biyu tun lokacin Dana tashi".
Ya fada Yana nufar kofa zuwa masallacin cikin hotel din.
Tashi tayi ta nufi toilet din a gurguje tayi wanka ta daro alwala lokacin data fito har an idar da sallar, lotion din data gani ta shafa ta bude jakar duk wani abun da zata bukata ya sako a ciki ita mamaki take to a Ina ya Sami kayan ita dai ba nata ya dauka ba, hatta bra ma size dinta ce doguwar Riga ta cire daga leda ta saka baka Mai aikin stone, hijab ta saka ta tada sallah.
Har ta gama azkar Bai shigo ba sai gurin shida da rabi ya shigo directly inda take ya nufa.
"Barka da Asuba".
Zahra ta fada tana sadda Kai kasa, shiru yayi kamar Bai jita ba sake maiamaitawa tayi.
"Taso kiga yanda ake gaida Dear ba irin wannan local gaisuwar ba"
Sunne Kai tayi tana Dan murmushi, tsugunawa yayin daf da ita yana kallon 'yan yatsun Hannunta sumul sumul dasu kamar Bata aikin komai da Hannun, dagota yayi gaba dayan ta ya mannata a jikinsa "ji nakeyi kamar kada nayi tafiyar nan ko Kuma na daukeki mu tafi, idan na tuna zanyi nesa dake wlh wani irin rauni ne yake kamani naji kamar idan bana Nan wani Abu ze faru".
Ya fada cikin muryar karaya da gaske a 'yan kwanakin Nan Yana Jin wani Abu daya fi na da a tare dashi.
Cikin 'yar siririyar muryarta tace "ba komai kaje kawai Allah Yana tare damu ba abun da ze faru sai abinda ya hukunta a kaina, Allah ya bada nasara yasa a Dace, kawai dai Dan Allah kayi min wata alfarma kafin ka tafi".
Hijabin ya zare a hankali daga kanta ya Dora a Kan bed side kafin ya zaunar da ita a jikinsa as usual.
"Fadi wace bukata gareki".
Dan shiru tayi kamar bazatayi magana ba.
Oya fell free with me, kiyi magana Mana kinsan eight thirty nake so na wuce".
"Daman so nake na ringa zuwa Dr.sulaimanu Adamu college of Hygiene inda nayi service na ringa yin lectures ko sau biyu ne a sati".
Wani kallo yayi Mata na Amma Baki da lissafi.
"Ni matata da yawon aiki? Gaskiya A'a! Wannan bukatar Bata karbu ba, me kikeci na baka na Zuba indai aiki ne wlh sai kin gaji da yinsa, tashi daga jikina kin wani samu cinya kin dane,kada na makara nayi missing flight mu tsuguna duk dan burin bawa ya rushe".
"Yanzu Allah bazaka Bari na rinka Zuwa ba".
Ta fada a marairaice.
"Kinsan Allah wlh Zan hadaki da zayyan Dan nasan Yana daf da shigowa garin Nan ya juya min dake can kauye gurin Hajiya Inna ko banza kin tuka mata tuwon dawa kin mata shara, kinga ita gaba ta kaita balarabiya na mata aikatau ita kuwa bakar fata Kinga sai mu Dora a media muma 9ja munci gaba ana zuwa daga middle East ana Mana aikatau".
Ya karasa fada Yana Jan Dan tsinin Karan hancinta.
Tana kokarin magana wayarsa dake Kan bedside ta dauki wani kidan larabawa Mai dadi.
"Dauko min wayata Dan tsabar na Zama mijin ......, Gashi Nan ringtone din ma kidan kune na saka". Wayar ta dauko, Zayyan ta gani kwalalo idanu tayi Ashe da gaske yake da yace Shi wannan din zezo yanzu ko waye shi kuma "oho" ta fada a zuciyarta.
Wayar ta Mika masa.
"Ka karaso?" Abinda taji ya fada kenan Bata San me yace Masa ba taji yace "ok, ka shigo ciki akwai securities a kofa zasu zasu rakoka gurin da Zan ganka".
Ya kashe Kiran Yana nufar kofa, ki shirya kafin na dawo yanzu zamu wuce".
Yayi Gaga abinsa ya barta da Baki a sake "ikon Allah shi Kuma ko waye yake bada umarni cikin dare ya wayi gari da abinda ya bukata tasan ko waye daga nesa yake Dan jiya tanaji Yana fadin kada a biyo ta jos a biyo ta kano, ita duk ya Gama Dame Mata lissafi wlh.
******
A hankali yake tafiyar cikin nutsuwa Amma da gani kasan tafiyar ta ingarman namiji ce, tunda ya doso gurin Zayyan ya kafe shi da ido, take ya shiga jinjina lamarin ogan nasa wato ana zaton wuta a maqera said gata a masaqa, waze tab'a tunanin sa a irin nan yayi masifar bada kafa.
Bai Farga ya kureshi da ido ba Saida yazo daf dashi, "sorry sir" ya fada Yana sadda kai, baiyi magana ba ya mika Masa hannu wannan d'abi'ar sa ce baka Masa irin gaisawar Nan sai dai kuyi musabihwa. "Barka da Asuba ya Hanya?".
"Alhamdulillahi."
Ya fada sai da Mahmud ya zauna kafin Zayyan Shima ya koma ya zauna.
Kamar bazece komai ba gurin ya dauki shiru.
Saida yaja fasali sannan yace. "I hope ba Wanda ka fadawa munyi waya ga Kuma inda zaka sameni?"
Kai ya girgaiza "ko daya oga ba Wanda yasan inda na tafi kawai nace musu zanje gida ne na samu Kiran gaggawa".
"Good, na kiraka ne zaka zauna gidan da wife Dina take zanyi tafiya, Wanda na saka gadin Naga alamar gaskiya Bata isheshi ba, ko Kuma ze iya komai saboda kudi, zan turo maka pictures na wasu Mata koda Wasa kada kabar kafarsu ta shigar min gida shi yasa na taso ka da tsohon dare ".
Zayyan jin magwnar yayi wani banbarakwai "wife Kuma? To ta ina Hakan ta faru? mutumin da ake tunanin baya kasa sai Kuma ya ganshi a nan Yana wata irin rayuwa hankalinsa kwance, ga abubuwan tambaya Amma ba Halin yinta.
"To in Sha Allah baza'a samu matsala ba".
"Yanzu zaka shiga cikin Ibrahim ze nuna maka dakin da zaka huta daga Nan zuwa sha daya Binyaminu ze shigo kuje gidan".
Ya fada Yana mikewa.
Da kallo zayyan ya bishi har ya b'acewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauke Yana jinjina Lamarin ogan nasu wato duk yanda kasan Shi idan yayi wata bada Qafar saika rasa gane wace alkiblar ya kalla. "Wife Dina". Yanda yayi maganar kasan ba wasa cikin Yana wannan tunanin Ibrahim ya karaso Bai sani ba.
Da azama ya shiga falon a zaune ya sameta da luggage dinsa a kusa da ita tayi rolling da Veil din rigar sai tayi masa wani irin kyau, a slow ya karasa inda take zaune ya saka hannu ya dagota tsaye ya sumbaci saman goshinta.
"Nayi Miki irin gaisawar ku, Ina key din lokaci Yana ja kada da gaske nayi sakaci kija Mana, muna lallabawa, kin hakura da Zuwa makarantar naji Baki ce komai ba?"
"Bani da say, sai yanda kace haka za'ayi".
"Nace A'a! in dai Ina raye da lafiya ta bazaki nemi komai ki rasa ba Koda kuwa faskare zanyi to zanyi na samu abinda zankula dake".ya fada Yana daukar luggage din ita Kuma ta nufi kan fridge inda ya ajiye key din jiya.
A jere suke tafiya sunyi wani irin dacewa wadda dole idan ka kallesu ka qara suna kokarin fita daga reception su Zayyan suna kokarin shiga, Mahmud ya kalla da jakar matafiya a hannu Yana rike da Hannun Zahra,.
"Kam bala'i"
Yaji Bakinsa ya subuce ya fada Yana matsawa baya Kamar yanda Ibrahim yayi.
"A sauka lfy" Ibrahim din ya fada shi kuwa Zayyan kamar an saka makulli an datse Masa baki.
"Ka bashi key din dakin ka biyoni mota Zan baka sako".
Ya fada Yana duban Ibrahim, mota Zahra ta shige ta barsu suna tattaunawa kafin ya shigo ya tada motar ya nufi get din fita har yabar harabar hotel din, Zayyan na lekensa ta window sai dai yasan idan yayi magqnar Nan da wani kwabarsa ce zatayi ruwa daya fesa labari, oga da rije jikar mace uwa uba yana tukata da kansa Kai wannan abin surprised da yawa yake"Ga bikin zuwa ne babu zani.
Tafiya yake da hanzari Dan ma safiya ce sosai titin ba yawan jama'a cikin Kan kanin lokaci suka shigo unguwar, Horn ya danna da karfi da gudu Mai gadin yazo ya bude yana fadin "barka da zuwa!"
Da gudu ya Koma ya dauko sakon dasu mama suka kawo jiya Yana fadin "barka da Asuba yallabai gashi jiya bayan futarku su Hajiya Babba sukazo suka bada a ajewa Hajiya".
Ya fad'a Yana risinawa Yana mikawa Mahmud ledar.
Saida ya karewa shi da ledar kallo, sannan ya hade gabas da yamma yace ka rika idan kana so, Kuma
Ka hade kayanka in anjima kadan binyaminu ze zo da Wanda ze canjeka aikin Nan adalci daya nayi maka ban koreka ba zaka koma share-sharen makarantar Yara kawai".
Jiki na tsuma Mai gadi ya durgusa Yana fadin "Yallabai me nayi haka da zafi Dan Allah kayi hakuri wlh baza'a qara ba ka rufa min asiri".
"Iya Alfarmar kenan bana korar ma'aikaci sai lefinsa ya Kai uku to Kai daya kayi ba tare da kasan laifi bane shi yasa nayi maka uzuri bazan rabaka da rufin asirinka ba dauki kaje yanzu Zan fito". Jiki ba kwari ya dauki ledar ya juya Yana ta faman tunanin ta ina ya kuskuro yallabai jiya lafiya kalau suka rabu yau Kuma ya tashi da canjin gurin aiki da Allah ma ya dube shi da Rahama daba Kora bace days shiga uku.
Suna shiga Mahmud yayi bed room dinsa ita Kuma ta nufi kitchen ta Fara hada abu marar wahala coffee ta dafa Masa sai sandwich kawai tayi shaf-shaf a tray ta Dora direct bedroom dinsa ta nufa ya fito daga wanka Yana goge jikinsa a ranta tace shi baya mura any time wanka kamar dangin kwadi.
Sallamar ta ya amsa Yana aje towel din dake hannunsa.
"Ke! Me kikayi daga zuwan mu ba dai abinci bane ko? Ni bana cin komai a irin wannan lokacin".
Langabe Kai tayi tana dubansa kasa-kasa har Zuwa lokacin wani nauyinsa takeji. Yana ankare da ita.
"Coffee ne fa da sandwich nayi maka Dan Allah kada ka tafi da yunwa,alhalin gani a tare da Kai ai da naji kunya daga zuwa ka nemi abinci a kanon".
"Inye ashe dai ana son mamudan?".
Ya fada yana nufar inda ya aje kayan da ze saka kananun Kaya ne na kamfanin Armani ya saka bako kunya ya cire rigar wankan ya tsaya daga shi sai boxer short, da sauri ta runtse idonta Dan Bata zata zeyi irin wannan abunba Yana kallonta ya basar yaci gaba da shiryawarsa, Zama yayi Kan sofa Yana umartarta ta kawo masa coffee din nan duka ta dauko ta aje gefensa ya dauka Yana sipping Yana kallonta tana Wasa da gefen veil dinta da ya sauko, sandwich din daya yaci ya yaji ya isheshi Shima Dan kada ya watsa mata kasa a ido ne, amma Sam baya iya cin komai a irin wannan lokacin.
"Zauna muyi magana" ya fada Yana dubanta,.gefen sofar tayi niyyar Zama ya tikota "Kinga gurin zamanki Nan ya dorata inda ya Saba..
"Zan tafi Baki San cikakken asalina ba, Zan fada Miki saboda sha'anin Rai da rayuwa kona dawo ko ba na dawo ba, Ni haifaffan garin sokoto ne iyayena duka biyun sunan Nan ni dangatan iyayena ne da kakata Hajiya Inna, suna Sona yanda Baki zato yanayin rayuwa ne ya kawoni nan, duk family na ba Wanda na fadawa labarinki sai kakata ta sanki a hoto tasan wasu labaranki, kota Allah ta kasance wannan dana Kira ya zauna yayi min gadinki sunansa zayyan na fada Masa ke matata ce ze sadaki da Family na, Dan Allah kiyi min Alkawarin duk rintsi bazaki juya min Bata ba, ki rike min aurena da Kima da daraja, idan Allah yasa na dawo Zan fada Miki koni waye da duk abinda ya shafeni na rayuwata Daman taki na sani ba sai kin fada min ba,
duk abinda kike bukata ki duba waccen lokar akwai kudi a ciki bangaren abinci Kuma nabar komai a Hannun Habib, ga Kuma kudin da Sameer ya Baki ban Baki ba". Ya aje mata su a akan cinyar ta.
Jin tayi shiru yasa ya dago fuakarta da hannunsa,kukan Zuci take ba wani sound sai dai hawaye"subhanallahi kuka dai? Kona fasa tafiyar nan kawai tunda Naga hankalinki yaki kwanciya da ita"
"Ba komai kaje kawai naji Kanata nanata maganar in baka dawo ba na sani ko idan ka tafi bazaka dawon ba".
Lakuce Mata Baki yayi "ai kece bazan dawo din ba, wannan ya shafa cikinta sai kin ajiye Mana babies a ciki idan naki dawowa aini nayiwa kaina, ki kwantar da hankalin ki nema zani ki min addu'ar samun nasara".
✨✨✨
✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
Strory
&
Written
By
Maman Fateemah
Page 29
📖🖋️
_____ Sun jima a haka Yana lallashinta kafin ya dagota su tashi tsaye tare " me za'a bani nayi guzuri dashi?"
Ya tambaye ta, shiru tayi kafin ta Dan watsa hannu tana Dan kallonsa ta gefen ido.
"Ai kaga bamu kwana a gidan ba bare nayi maka wani Abu Saida idan biscuits din Nan Zan dauko maka sai ka tafi dasu na bada a sawo min wani".
Dariya abin ya bashi ita bilhaqqi da gaske take fada Wai biscuits kamar wani yaro.
"A'a niba shi nake so ba tsarabar da zan rike Ina tunawa da ita har na dawo".
"Me Kenan?" Ta tambaye shi cikin nuna rashin sani.
Jikinta ya matso sosai ya riko ta Yana kallonta da wani yanayi mai wuyar fassarawa, Bakinsa ya Kai Kan nata Dan bakin yasa Hannun ya talkafo kanta batayi zato ba tsammani taji harshensa na yawo cikin bakinta ya lalubo nata harshen cikin gentle yake tafiyar da ita ba kamar ranar nan ba, sun dauko Kusan minti biyar Yana Abu daya ji tayi kafafunta na neman gagarar daukar ta, jin jikinta na rawa yasa ya Kara mannata da jikinsa wani Nishi tayi ba Halin magana, kokarin yanye harshenta take daga Bakinsa Kai ya girgaiza Mata sai da yayi mai isarsa ya saurara Mata Kan gadonsa ta zube da gaske ya kashe Mata jiki ji take idan ta taka kafarta faduwa zatayi.
Dan rankwafawa yayi saitin fuskar ta "Haba 'yan Mata be strong Mana me akayi da maza inji karya, taso muje ki rakani idan na biye Miki labarin salo ze canza".
Ya kamo hannunta ya mikar da ita, jakar laptop dinsa kawai taga ya dauka, gyalenta wanda yake yashe a kasa ya tsuguna ya dauko Mata Yana rufa Mata a kanta.
"Zaki bani Aron motar ki naje Kano da ita? amma fa saina dawo na dawo Miki da ita a airport Zan bada ajiyarta yanda idan muka dawo saina karba kawai".
Kai ta gyada Masa alamar Eh.
*A'a magana zakiyi idan kin amince to idan Baki amince ba na nemi hanyar Tasha kawai".
"Ka dauka kaje da itan koka dawo ma na bar maka za'a kawo min wata ba kaji Abba ya fada ba".
"Ke! Kinsan kudin ta kuwa zakice kin barmin Dan ki hau Abba ya saya Miki, Aron ma Ina laifi".
Yaja hannun ta suka nufi kofar a falo ya tsaya Yana wasu 'yan dube duben da Batasan Kona menene ba sannan suka nufi harabar gidan, kasa hakuri tayi ta jefa Masa tambayar.
"Wai haka zaka tafi ba kayan sakawa da takalma da sauran abun bukatu ne?" Dan shafa gefen fuskar sa yayi ya Dan furzar da iska daga Bakinsa. "Bana tafiya da Kaya ai wahala ce nasan duk inda zani akwai na sayarwa na saya kawai, aikin gane?"kallonsa kawai batace Masa komai ba.
Saida yaje gurin Mai gadi ya bashi wata envelope sukayi maganganu sannan ya dawo gurin da take tsaye.
"Zan tafi sai Allah ya dawo Dani, ki kula da kanki bana son yawo Amma idan gidan Ammah ne ko Aunty Hasana idan Bata koma Jos ba kina iya Zuwa".
"To na gode, Allah ya tsare hanya ya bada sa'ar abinda akaje nema".
"Allahumma Amin. Allah ya tsare min ke daga sharrin mutum da Aljani da dukkan abinda yake cutarwa, ya Ubangiji na bar maka amanar iyalina ka Zama gatan mu".
Ya fada yana nufar motar, a hankali ta biyo shi ya bude ze shiga ta riko hannunsa ta Manna masa kiss a tsakiyar hannun. "Safe journey" ta fada da wata murya Mai rauni da gudu ta juya idonta fal hawaye. Tsaye yayi Yana kallon ta har ta shige ciki, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya shiga ya tada motar jikin window ta tsaya har Saida ya fice daga gidan.
________________________
Tunda Mahmud ya bar cikin gari ya saki motar, rabon da yayi tuqi irin wannan har ya manta, kyakykyawar awa daya da minti arba'in da Tara ta kawo shi Kano, daga Hotoro NNPC sai ya shiga ta ring road ya fita 'yan kaba haka ya dunga yayyankewa har Zuwa round about na sani Baban kwari Sannan ya nufi Malam Aminu Kano international airport,Yana daf da shiga gate din ya saka face mask da glass sannan ya shiga, wayar Sameer ya Kira tana daf da katsewa ya daga.
"Kana Ina? Na shigo yanzu ina fatan komai ya dai-daita?". Dan Jim ya yi yana sauraren sa. "Ok kazo ina parking lot inda ake bada ajiyar motoci".
Ya sauke wayar Yana kalon masu Kai da kawowa.
Yana Nan tsaye har sameer din ya karaso ya gaishe da Mahmud cikin girmamawa, jakar laptop din Sameer ya karba da key din motar ya nufi inda suke da alhakin karbar ajiyar, shi Kuma Mahmud ya nufi reception din.
Sameer Bai jima ba ya dawo da takarda shedar bada ajiya, sun Dan tattauna kafin lokacin tashinsu yayi, zasu shiga screening ne Mahmud ya Kira wayar zahra, tana kwance a gado rungume da pillow bayan tayi kukanta Mai isarta ta lallashi kanta tunda Babu Mai lallashin gani takeyi shima kamar ya tafi kenan. Ringing din waya taji da sauri ta tashi Dan ita Sam tama manta da wata waya tunda ya Bata Bata karabi takanta ba, da sauri ta dauko tana duba waye ya Kira MM DANGE ta gani wani sanyi taji ya saukar mata,
Picking tayi tare da sallama, sai kuma tayi shiru.
"Zamu tafi ne nace bari na kira na fada Miki, ko zamu sake waya ze iya kaiwa jibi kada hankalinki ya tashi idan komai ya dai-daita Zan kiraki in Sha Allah".
"Tom Allah ya saukeku lfy".
"Allahumma Amin my precious, please take care bye".
Ya katse Kiran yasan idan yaci gaba kuka zata saka Masa ya rasa wane irin idanu gareta masu saurin kuka.
Sha biyu da rabi jirginsu na kamfanin air Max ya daga.
Wayar tabi da kallo kafin ta aje kusa da ita, sai Kuma ta tashi kamar wadda aka zabura. Wayar ta dauko dubawa tayi wata baguwar number ta gani batayi kasa a gwiwa ba tabi Kiran Dan missed call ne tunna jiya. Cikin kankanin lokaci Kiran ya shiga Bata jima Tana ringing ba aka daga muryar matashiyar macece daga ji tana ji da ajinta sallama Zahra tayi Mata suka gaisa sannan zahrar tace Mata taga missed call dinta ne a wayar ta.
"Missed call Dina gaskiya bani na Kira ba Amma Dan Allah wacece ke?.
Yar dariya Zahra tayi kafin tace "sunana Fatima Zahra Muhd sani Ni mazauniyar Azare ce ta jihar Bauchi".
Kit ta kashe wayar ta yunkura ta tashi, ta nufi kofa tana daf da fita taji wayar ta Kara daukar Kara ta dawo number dazu ce yi tayi kamar zata share sai Kuma ta dauka taji me zata fada Mata.
Sallama tayi daga can ta amsa sannan ta Dora da fadin "Dan Allah kiyi hakuri da farko ban ganeki bane sai da Kika fada min sunan ki wlh nice na Kira bansan yanda akayi banyi saving number din ba matar oga Mahmud ko?"
"Eh nice ke wacece?"
"Sunana Fateeha matar Sameer Babban yaron oga jiya ne ya bani number yace na kiraki na gaisheka nayi Miki Allah Sanya Alkhairi sai Kuma ba'a daga ba, an Sha sauga bamuzo mukaga daki ba gashi har sun wuce China, amma in sha Allah idan suka dawo zamuzo indai ban haihu ba har lokacin"
"Nagode kwarai da gaske,Amma naji kince China ba UK zasu Fara Zuwa ba? To can din zasu tunda kune masu tafiyar Amma na dauka da China zasu Fara tunda canne aka samu matsala sai Kuma Dubai, kinsan ogan naki ne kamar computer yake baya gajiya da aiki danma yayi wannan hutun Mai yawa sai Habibi ne yake wasu ayyukan".
"Hakane kam aiya huta yanzu sai a Dora daga inda aka tsaya".
"Ai gaskiya samun kamar oga Mahmud sai an tona".
Basu jima ba sukayi sallama. Ta Dade a zaune tana jujjuya hirar su da matar Sameer, zamewa tayi ta kwanta tana duban sama a hankali ta furta. "Ubangji ga baiwar Mai rauni ka jibinci lamarina Kasan ko waye ka hadani dashi ka Kuma sakamin nutsu a tare dashi ban tabaji bana sonsa ba Amma lamarinsa Yana bani tsora na rasa alkiblar daya duba, Allah ka Zama gata na ka jibinci dukkan lamurana Dan Isar Manzon Allah s .a.w.w.
Tashi tayi ta fita dakin nasa ta koma dauko tray din da Takai Masa break fast, duk wani Abu daya danganci kayan electronic sai ta kashe sannan ta fito tana gangarowa daga steps din corridor ne taji door bell din tana Kara alamar anyi Baki, a Kan dining table ta aje kayan ta gyara gyalenta ta nufi kofar.
Budewa tayi sai sukayi arba da zilai Mai aiki da 'yar jakar kayanta.
Cikin farin ciki Zahra ta karbi jikar kayan tana fadin "sannu da zuwa anti zilai"..
Suka shige ciki murnar Zahra taki boyuwa itama zilan ba Karamin murna tayi ba lokacin da Ammah ta fada Mata zata zo ta Taya Zahrar Zama. Nan suka shantake suna Hira har Kusan karfe dayan Rana kafin Zahra ta raka zilai dayan dakin da ba cikinsa take ba ta aje kayan ta.
Tambayar Zahra zilan tayi me zata dafa musu,
"Ki dafa komai na ni harna manta wlh ashe ko break banyi ba, ga sandwich can ki dauka kada ya lalace, Zan shiga na Dan kwanta kafin karfe biyu"
"To Allah kaimu" zahra tace "Amin"harta fara tafiya zilan Kira sunan ta tsayawa tayi har zilan ta karaso.
"Uwar dakina Naga kamar wani mutum mun gaisa dashi ko Mai gadi kuka canza". ,"Eh Mai gidan ne ya canza shi wlh jiya lfy muka fita Amma yau muna dawowa ya sallame shi, wani ya Kira ya zauna Dani kafin ya dawo.
"Wani Kuma daga Ina,?. "Nima ban san daga Ina yazo ba" Tab Allah kyauta ya kamata asan asalinsa gaskiya zamanin ne yazo da wata irin rayuwa sai godiyar Allah".
"Wannan gaskiya ne". zahrar ta fad'a. Ita nufi bed room ita kuma zilan tana nufar kitchen.
✨✨✨
✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI.
Story
&
Written
By
Maman Fateemah.
This page is deducte to the Family of late Alhaji Isah Musa bakin kasuwa kazaure.
Innalilllahi wa Inna ilaihi raji'un! Ina Mika sakon jaje da ta'aziyya ga jama'ar garin MAJIA TAURA LG bisa ibtila'in daya samesu na gobara Mai Muni sakamakon faduwar tankar man petrol, Wanda yayi sanadiyyar rasa daruruwan rayuka Allah ya jikan wadanda suka rasu,wadanda Kuma suke gadajen Asibiti Allah ya tashi kafadunsu ya Basu lafiya yasa ya zamar musu kaffara ya kiyaye faruwar haka a gaba dan darajar manzon Allah s.a.w.w
Page 30
_______Misalin karfe daya da rabi Mai a dai daita sahu ya sauke Asabe a bakin gate din gidan Zahra Dan yauma Saida taje can kauyen jama'are gurin wani mutum da wata kawarta ta tab'a fada mata shi, Nan ma ta karbo abubuwa Wanda za'a binna a gidan Wanda har abada Mahmud baze kara waiwayo garin Azare ba ko sunan jihar Bauchi ma Sai yaji ya tsane shi.
Cikin karfin gwiwa ta karaso bayan ta sallami Mai Dan sahun tunda tasan Mai gadin Dan hannu ne dubu biyu ta Isa tasa yayi musu kowa ne irin aiki ne, iyakar ta tace masa na tsarin gida ne ze binna Mata saboda yau da gobe.
Knocking tayi da Dan karfi tana mazurai ita ga uwar matar gida. Cikin takunsa na kakkarfa ya bude kofar gate Dan da hanzari tayi baya Dan ji yayi Kamar ze bangaje ta, kallo daya yayi Mata ya gane face din Dan hoton da oga ya nuna Masa yafi bada mahimmanci akanta Dan ita ce suspect dinsa ta farko, yasan da ita za'a yi amfani gurin isar da ko wane irin sako ne.
Da hargagi Zayyan ya tunkaro ta.
"Wa kike nema?"
Duk daburcewa tayi nan da Nan jikinta ya dauki rawa.
A'a Daman gurin matar gidan nazo munzo jiya ne basa Nan shine na dawo yau".
Ta fada tana rawar murya.
"Kama gabanki Nan ba wata mace a ciki gidan maza ne, idan Kuma Zaki shiga Bismillah tsuntsu daga sama gasashshe, Dan muna da kudajen da basa haram akan duk Mai tsautsayi, idan na Kara ganin giccinki a wurin Nan saina hadaki da karena yayi min fata-fata dake, wuceeee min daga nan" yayo kanta,da gudu ta kwasa ko waiwaye babu.
"Stupid! Da gani wannan tsohuwar kwarkwar ce wlh Banda oga ya hana da kinci na jaki banza wato kin samu oga a araha shine kuka Neman zaku masa shegantaka akan matarsa ni na rasa yanda akayi ma oga ya Fado garin Nan,? Kuma har ya iya Zama a haka ba wani damuwa, ko Dan meze dameshi Yana tare da wannan danyan gold din".
Ya fada Yana komawa bakin aikinsa Amma zuciyarsa fal tunanin abinda ogan nasa ya sani game da wannan matan daya turo Masa hutunan su ya Kuma shata musu dogon layi.
Asabe Bata samu zarafin tsayawa ba Saida ta dangana da wani gurin me suyar kifi a bakin titi shima gani tayi gurin da jama'a ko cimmata yayi za'a ceceta, gefe ta koma tana mayar da numfashi sai lokacin ta dubi hanyar data fito ko Mai Kama dashi Babu. Gefen wani dutse ta zauna tana tunanin to koba gidan da sukaje jiyan bane tunda ba wannan basamuden suka tarar ba Amma daga Daren jiya Zuwa yau har lamarin ya canza ita damuwarta daya shin sakon da suka bayar ya sameta ko kuma na jiyan ba shine asalin Mai gadin ba yayi musu ta 'yan duniya ya barbe kayan da kudin ya wuce nasa gurin.
Tashi tayi Kamar wadda aka tsikara ta dauki 'yar ledar data sawowa Mai gadin Dan abun tohiyyar Baki sai Kuma labarin ya canza salo. Harta dauko wayar ta Sai ta mayar idan tayi gigin fadawa Mama kwabarta zatayi ruwa Dan a yauma Saida Mana ta karo kudi masu nauyi tace a bawa Mai gadin yanda duk abinda za'a saka shi yaji baze iya gardama ba, to idan ta koma Mata da wannan labarin amshe kudin zatayi tasan halinta kayan ta, data Bata naira dubu gara ta bawa Dan tsubbu dubu hamsin, Sam Bata karuwa da ita saita wadannan hanyoyin idan ta aiketa tunda itace amintacciyarta ta Nan takeyin nata duk rintsi bazata so ta rasa wannan mafakar ba Dan Kusan da ita ta dogara gurin kwaramniyar yau da Kullum nata.
*******
Saida Zahra tayi barci Mai isarta sannan ta farka lokacin biyu har da minti ashirin da hudu, da sauri ta Mike tana addu'ar tashi daga barci tayi mamaki ita fa gani tayi kamar barcin minti goma Sha biyar tayi Ashe lokacin ya ja haka, alwala tayi tazo ta Fara sallah bayan ta idar wayar ta da dauko Ummee ta Kira cikin shauki tun dazu ta nemeta network din na garin ba kyau sai hakura tayi, Bata jima ba tana ringing aka daga ba Ummeen bace wata ce ta daga tana ta yi Mata larabcin gargal ita kuwa zahrar na language yafi kwarewa a Dan daburce tayi Mata bayini ta gane Ummeen ta fita masallacin Annabi sallah tunda har lokacin suna Madina basu tafi ba Kuma a yanda sukayi daga Saudi Arabia Nigeria zasuyo gurinta, sallama tayi wa matar ta kashe.
Number sajida ta lalubo ta syprus tasan zata Sha mita tun ranar da sukayi ways da wayar Amatu tayi Mata buyagi ta kashe Basu Kara waya ba, har tayi ringing ta katse Bata dauka ba, Bata hakura ba wani Kiran ta karayi shima Yana daf da ze katse aka daga.
"Haba bestie Ina ta kira kin shareni ko har yanzu fishin ne?"
Mai makon taji bestien sai muryar Fatima taji tana kwallawa Sajidar kira tana fadin "ku taho ga Amarya Zahra! Zahra" ta kirata da karfi tana murna kamar zata tsaga wayar, daya bayan daya suka dunga gaisawa suna ta korafin amarci Dadi ta Kama waya ta rufe wato Bata so a shigar musu rayuwa ko? Hakuri ta Basu tare da fada musu tayi missing din waccen wayar ne har sim din, sai daga karshe sajida ta karbi wayar.
"'yar duniya wato kinji dadin lamarin ko Kika wani shareni, ni yanzu ai yallabai Mahmud ya fiki kirki kinsan ya kirani Kusan sau uku? Daman ko Baki kirani ba Zan kiraki dazu wurin Sha daya ya kirani Wai na kiraki na lallasheki yayi tafiya ya baroki kina kuka?".
Ya fada tana kunshe dariyar ta.
"Malama ki fito kiyi dariyar ki sosai kada ta kume Miki a ciki,da kike wani kunsheta".
Dariyar tayi da gasken sai tayi Mai isarta tace. "Dan Allah bestie mekika bawa wannan guy din Kinga yanda yayi masifar macewa a Kanki? Wlh har tausayi yake bani Ni har mamaki nake idan ya kirani Yana min maganarki ranar Nan fa cewa yayi na bashi labarin zamanki a Nan syprus din wlh nayi zaton da Wasa yaki tunda nasan ba Karamin cajin kudi za'ayi ba. Amma haka na ware na rinka bashi labarin har na Gama ko a jikinsa, yanzu Ina aka tsaya da fatan komai ya dai daita? Dan nafi son dai dai lokacin ganawarmu muyi murna biyu graduation da naming ceremony".
"Wlh Zan kashe yaushe Kika zama haka Mai bin kwakwkwafin jama'a? to bazakiji ba an fada Miki kowa ma irinki ne ai wlh ya Abdul Hakeem ya debo ruwan dafa kansa Dan nasan Dan bawan Allah saiya rinqa guduwa daga gidan"
Wata irin dariya ta saki tana fadin "billahil Azeem gara wata wainar data wake yarinya gyara zancen ki idan ana cin baure ba'a tona cikinsa Kuma idan ana sallah ba'a magana".
"Wlh sharri zakiyi Masa Amma shi dai salihi ne".
"A inda salihai sukayi karanci ba".
"Mubar zance kawai tunda abun ya Zama haka".
Zahra ta fada tana cire hijabinta daga jikinta vest ce Fara Kal sai wando shima fari ai pink din kananun flowers gashin tayi parking a tsakiyar Kan ta kashe da band shima pink, sai fito baby sak.
Gyara kwanciya tayi, tayi ringinnine da wayar a kunnenta Hira sukaci gaba da sajida yawanci duk akan auren zahrar ne. Sun dauki lokaci Mai Dan tsawo suna tattaunawa akan bututuwa da dama kafin suyi sallama, ta nufi toilet wanka take son yi kafin ta fita cin abinci.
********
Jirginsu Mahmud a Addis Ababa Bole international airport yayi landing, daki biyu Sameer ya kama musu Nan kusa da airport din tunda a kalla zasuyi Kusan three hours.
Saida ya kaiwa Mahmud jakar laptop dinsa sannan ya nufi nasa dakin, bayan fitar Sameer Mahmud wanka yayi sannan yayi sallah maimakon ya kwanta ya Dan huta sai kawai ya bude wayarsa so yake ya ganta duk wani matsi da yayi tana manne da zuciyarsa so yake ya ganta kafin ya kirata. CCTV ya shiga ta wayarsa duk abinda akeyi ya rinka bi Yana gani yasha dariyar karon Zayyan da wannan matar wadda ko sunanta Bai sani ba, shi yasa ya dauko shi yasan shi kadai ne cikin amuntattunsa Wanda ze Masa wanna aikin ba tare da an samu matsala ba.
Saida ya gama kallon ko ina na gidan yaga ba wata matsala, sannan yayi zooming din cikin bed room dinta daga ita sai vest purple da wando skintight kanta tayi parking da purple din band sai tayi wani irin kyau na musamman, kura Mata ido yayi Kamar ya warto ta yakeji, turare ta dauko tana fesawa a jikinta. Nan ya shiriri ce Yana kallonta knocking din da akayi Masa ya katse Masa abinda yakeyi, umarni ya bada a shigo Sameer ne sai ma'aikaciyar hotel din dauke da tray na abinci sai karairaya take shi har dariya abin nata ya bashi, me Kamar zahra yaushe irin wadannan zasu burge shi, bayan ta wuce ne ya dago ya dubi Sameer "kada ka qara zuwar min da irin wannan a rinqa bawa maza suna kawo min kawai".
"Noted sir"
Ledar dake hannunsa ya Mika Masa Mai tambarin wani boutique ne, sannan ya aje Laptop dinsa a kusa dashi Yana nuna masa wasu ayyukan da ya Gama yanzu, sun jima suna aikin kafin sameer ya fita saboda lokacin tashinsu ya kusa cika shi kuma Mahmud ya ciro kayan da nufin sakawa.
Saida Zahra ta Gama feffesa turarenta sannan ta dauko after dress ta zura ta yane kanta da gyalen sannan ta nufo parlour, zalai ta samu tana 'yan goge goge duk da ba wani datti a gurin, gaishe da zilan tayi tana Mata sannu, ajiye mofar tayi "Allah ya taimaki uwar dakina ga abincin can nayi Miki abinda kikeso faten dankalin turawa da pepper soup din kifi"
Zama Zahra tayi tana fadin "Kai Amma wlh na gode kwarai da gaske shi yasa nake yinki kinsa favorite Dina wlh".
"Ai shi yasa na cewa Ammah kada a wani dauko yarinya tun daga Mubi Nima na isa na zauna dake saina kirawo Kanwata Alawiyya ta cigaba da yiwa Ammar kafin Allah yasa yallaban ya dawo, ai ni har zaman wanka ni zanyi Miki Koda kuwa bakwa garin Nan ne".
Dan smile tayi kawai bata ce komai ba saima ta canza akalar zancen.
"Ni Kuma Aunty zilai kin mikawa mutumin Nan abinci kuwa?".
"Ai tunda na Gama na zuba na hada harda ruwa da lemo na mika Masa. Naga Dan gayu ne beyi kalar masu gadi ba".
Dariya zahra tayi tana fadin "Aunty zilai kenan shi Mai gadi har Kama gareshi".
Yana da kama Mana Wai Kinga wannan din?"
Na ga wani dai dazu ban sani ko shine Wanda aka Kira jiya cikin dare".
" Cikin dare Kuma?"
Kai ta gyada "Mata kusan Hakan tunda Sha biyu ta wuce ya kirawo wani kawai umarni ya bashi yazo garin Nan da safe kinsan bakwai a Nan tayi mass nifa mutumin Nan wlh tsoro yake bani na kasa gane kansa".
Dan murmushi zilan tayi tana kallon Zahra "kiyi hakuri uwar dakina a hankali Zaki San komai a kansa badai Kuna tare ba da sannu Zaki gane shi din waye, kici abincin sai muci gaba da hirar idan kin gwma".
Bata k'i Shawarar zilan ba ta tashi ta nufi dining ita Kuma zilan ta nufi dauko Mata ruwa da mutuniyarta farm fresh, sai da ta Gama cin abincin sannan ta dawo parlourn gurin da tabar Aunty zilan sukaci gaba da hirar su, amma Kusan hankalin Zahra yana Kan Mahmud haka Nan sai taji ya fado Mata ta yarda da ake cewa sabo turken Wawa, yanzu da baya Nan sai taji duk kewarsa ta kamata, tun dazu take duba waya ko zataga kiransa Amma shiru tasan tsakanin Nigeria da inda zasu indai da gaske chinan zasu da nisa a kalla jirgin zeyi landing a Ethiopia da India yaci ace ya kirata Amma shiru har Yanzu ko lfy? ta ayyana a cikin zuciyar ta.
Ganin tunanin Zahra yayi zurfi yasa zilan ta tashi tana fadin Bari nayi wanke wanke tunda kin Gama da kwanukan"
Tayi hanyar kitchen, ita kuma ganin tunanin ze dameta yasa ta kunna tv ta kamo MBC MAX tana son finafinan su sosai,Aunty zilan ma data Gama Zama tayi sukaci gaba da hirar jefi jefi har aka Kira magariba suka shiga sallah. Tana addu'oin yaumiyya na cikin du'aul mustajaba ne kira ya shigo wayarta da sauri ta dauko tana duba Mai Kiran Ummee ta gani da sauri ta daga tana fadin "Ummeena"
Amsawa tayi suka gaisa Ummeen ke fadar an fada Mata ta kirane nan tayi Mata fadan rufe layi da tayi,nan Zahra taji kuka yazo Mata, Nan da Nan Ummeen ta rude tana tambayar ta ko tana da damuwa ne ta fada Mata cikin kukan tace "Ummee Shima fa wannan daga kawo ni gidansa ko sati daya ban rufa ba ya tafi ya barni Wai aiki zejeyi uk" shiru Ummee tayi kafin ta shiga rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali da nuna Mata ba lallai ne hasashenta ya kasance gaskiya ba, kada ta damu saboda ita har Umara tayi bayan auren tayi mata addu'oin samun nasara akan dukkan lamuranta, sannan ta yi mata fadan ta kiyayi yawan kukan Nan bashi da ma"ana, daga karshe tayi Mata albishir zawan su next week harda Mama Hanifa da Aunty Nawwara duk suna hanya Daman ko Bata sameta a waya ba zata kira Hajiya Asma'u tasa a fada Mata. Murna ta shigayi Kamar tayi me har Ummee na Mata dariya Nan da Nan ta ware ta shiga lissafo abinda takeso Wanda za"a taho Mata dashi.
Bayan maga wayarsu da Ummeen Ammah ta Kara kira lokacin tana tare da Abba.
Tana zubawa Abba Dan fruit salad wayar ta dauki ringing Abban ne ya dauko ya duba 'yar dariya yayi Yana mikawa Ammar wayar tare da fadin.
"Uwata ce ke kira". Ganin Kiran ze yanke yasa Abban karbar fruit salad din yaci gaba da zubawa Yana fadin "A dauki Kiran uwata kada ya yanke".
Daukar tayi tana amsa sallamarta da gaisuwar da take mata.
"Ammah yanzu Dan Allah bazakizo ba Kuma Aunty Hasana ma fa batazo ba fa Kuma Ni sonake na ganki".
"Ikon Allah yanzu ke saboda Allah sai a ganni a gidanki a irin wannan kwanakin ai sai a dauka ba lafiya Auntyn taku dai zatazo Daman jiya take fad'a zata shigo ta ganki tunda mijin naki baya Nan, ai Mahmud din ma ya turowa Abban ku da sako ba dadewa ta whatapp yace sun sauka lafiya, ke dai abinda nakeso ki kwantar da kiyi Masa biyyayya kinji".
Ta fad'a tana rarrashinta.
"To Ammah, daman kira nayi na fada Miki Ummee tace next week zasu shigo Nigeria nasan zata fada Miki".
"To Allah ya kaimu Daman munyi maganar shekaran jiya har take tambayar meya faru da taki wayar? Nace ta Dan samu matsala ne, ga Abbanku yace a gaishe ki"
"Lah! Ammah Daman yana Nan amma ba'a fada min ba Bashi na gaishe shi"
Sun gaisa da Abban har Yana Dan tsokanar ta, tunda a wani bangaren kakace a gurinsa, Nan yake fada Mata mijinta yace ya tafi da motarta Kano tana airport Dan haka daga nan Zuwa jibi za'a kawo Mata daya motar ta gurin Muttaka, godiya ta yiwa Abban sannan sukayi sallama.
Ta jima Bata aje wayar ba, tana juya maganarsu da Ammah Wai ya fadawa Abba sun sauka wato ita da bayaso Bata da matsayin da ze kirata ko sako ya fada Mata sun sauka, kenan Daman duk abinda yake Mata a 'yan kwanakin Nan yaudara ce Dan ya lasa Mata Zuma a baki ya gudu ya barta da kewarsa inda ta godewa Allah be lalata mata rayuwa ta gudu ya barta ba wlh duk rintsi sai ta bar Kasar Nan ta koma Jordan, Dan tasan Allah kadai yasan halin da Ammah zata shiga idan bawan Allahn Nan yaqi dawowa....
✨✨✨
✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI.
✨✨✨
✨✨✨
Story
&
Written
by
Naman Fateemah.
page 31
______________Har aka Fara Kiran sallar insha'i tana zaune tana faman tunanin makomarta, tashi tayi tayi sallah, nan Kan sallayar ta kwanta tana lazimi a haka har barci yayi awon gaba da ita.
Tun zilai na saka ran fitowa Zahra har ta hakura ta shige ciki duk da ba barci take ji ba, tun yamma take ganin zahrar wani sukuku Kamar marar lfy.
Zahra ba ita ta farka ba sai Kusan daya da kwata, tashi tayi tana mik'a tare da salatin Annabi, duk jikinta ciwo yake Mata hijabin ta cire tare da after dress din ya Zama daga ita sai vest da wandon toilet ta shiga Bata Dade ba ta fito canja kayan jikinta tayi da rigar barci ta Kashe wutar Mai haske ta kunna bed side camp tayi shiru tana istigifari ga Allah s.w.a da Salati ga fiyayyan halitta Annabin Rahama duk yanda tunani yaso ya bijiro Mata saida ta kawar dashi kawai ta fawwalawa Allah lamarinta tasan duk rintsi Yana tare da ita, a haka har barci yaci karfinta.
Da safe har zulai ta Gama share share da mofin Zahra bata fito ba ganin shirun tayi yawa yasa tayi tunanin buga Mata kofa kada ta Zama babbar banza zuwanta ya Zama marar amfani rabonta da yarinyar nan tun magaribar jiya Bata Kara sakata a idonta ba, kofar bedroom din ta nufa tayi knocking taji shiru lokacin Zahra na Wanka, Kara bugawa tayi still dai shiru taji Nan da Nan hankalinta ya tashi kada fa wani abu ya Sami yarinyar Nan ta shiga uku.
Tana Nan tana shawarwarin ta bude ta gani ko lafiya? taji alamun motsin tafiya daga ciki da sauri ta Kara knocking din, Zahra da towel a jikinta ta nufo kofar ta bude.
"A'a Aunty zilai kece? Ina kwana?"
Ta fada tana goge gashinta daya jike gurin wanka.
"Lafiya kalau, naji ki shiru ne tun daga shiga sallah jiya harna gaji da zama Baki fito ba, gashi yanzu ma naji shiru har Ina kokarin Kiran Ammah na sani koba lfy ba".
Ta fada tana kokarin barin gurin "na gode da kulawar ki Aunty zilai wlh jiya barci ne ya daukeni a nan Kan sallaya bani na farka ba sai Kusan karfe biyu na dare".
"Ikon Allah kice kwanan kasa kikayi da sanyin tayis Bai Kama ki ba, tunda Naga gidan naku ko Ina sanyi Kamar gidajen larabawa".
Sai Kuma ta rufe bakinta da hannu.
"Kin jini ba wlh na manta Ashe gidan nasu ne".
Dariya Zahra tayi "Kayya Ina wani balarabiya anan ai da uba ake ado Ni bafulatana ce kalarce dai na dauko tasu Amma idan masu abun suna yarawa wani abun sai kallo Dan ma Allah ya hadani da jarimin uba da yayi tsayin daka gurin ganin na iya yaren saboda na samu saukin mu'amala da dangin Mamana".
"Wannan gaskiya ne Allah ya sakawa Alhaji da Alkhairi ya biya Masa bukatunsa na Alkhairi"
"Allahumma Amin".
Zahra ta fada.
"Me za'a dafa miki? Mu dai nayi Mana nida bakon ku".
"Wai bakon mu wato dai bazaki ce Mai gadin ba ko?.
Dariya tayi. "Wlh baya Kama da masu gadi Kinga kuwa ai bana ce Masa ba".
"Haka ne ki dafa min indo mie da cooker oat kawai".
"To an gama sai kin fito".
Ta fada tana juyawa zuwa main parlour din yayin da Zahra ta koma ciki.
*************
DAMAGARAM NIGER REPUBLIC.
Cikin takun ta na nutsatstsiya kuma wayayyar mace 'yar gayu ajin karshe ta shigo parlourn tana sanye da doguwar rigar madam gezber kalar peach sai gyalen kalar light yellow touching din flowers din dake jikin kayan sai takalmi plat Mai azabar kyau shima light yellow din tun kafin ta karaso kamshinta ya hade gurin.
A hankali ya dago ya dubeta har ta karaso gurinsa, tattara aikin da yake yayi ya Maida hankali a kanta lokacin da take Zama a kujerar dake gefen da yake.
"Sannu da aiki Yaya barka da Asuba".
Ta fada tana sadda kanta kasa Bai amsa ba Jin shirun yayi yawa yasa ta dago kanta ta dube shi, ita yake kallo.
"Yanzu abinda Kika zaba kenan Zainab da girmanki da hankalinki ki zazzage jiki ki baro dakin mijinki kizo ki nemi guri ki zauna mijinki yayi rarrashin duniyar Nan kinqi ki saurare shi daga karshen ma Kika zabi ki dawo Nan Damagaram saboda a Yamai uncle Yousoufu ya nuna Miki rashin kyautatawar abinda kikayi shine kikayo yajin Nan ko?.Ni tunda tubus ne Bari kizo ki zauna ki Mike kafa gashi nan har an Fara kawo Miki caffar ana son aurenki idan kin Gama idda wannan arzikin ki ne?".
Ya fada Yana kureta da ido, da sauri ta cira Kai ta dube shi. "Ni Kuma Yaya ake jawo min zawarci kawai daga ganin mace sai ace zawara ce".
"Kada kiga laifinsu sun ganki yau sun ganki gobe Baki da niyyar tafiya,idan Badi'a zata fita ki wanke jiki ku kama tafiya ba dole ace Miki haka ba".
Idonta taf da hawaye ta dube shi "to Yaya ya akeso nayi kasan dai yanda abun Nan ya kasance duk yanda naso a saurareni idanuwa suka rufe ba Wanda ya kula da abinda nakeso su gane Saida suka rabani da Dana yabar gida cikin bacin Rai Wanda har gobe ba Wanda yasan inda yake, gaskiya Kuma tayi halinta yanzu za'a matsamin da zarya na fada musu niba yaji nayi ba duk ranar da yarona ya dawo Zan dawo".
"Zainab a gabana kike fadar danki, Dan farin ba zakiyi min Kara ba".
"Kayi hakuri Yaya na Bari d'anka to" ta fada.
'yar dariya yayi na nawa Kuma sai dai a koki gaba, yanzu Dan Allah Alfarma zakiyi min kiyi hakuri ki koma dakinki Suma sauran yaran suna bukatarki kusa dasu ko badan Babansu ba ki duba girman Hajiya Inna har Yamai Saida tasa aka kaita ko a jirgine dai ai tanayi dake ne amma Kika kasheta da dadin Baki akan kina tafe kikayi zaman ki karshe ma kikayo hijira daga can, duk laifin Hajja ne wlh ita an taba Mata dan 'yar so ba zaman lfy, gobe nace aje Abuja a daukeki tunda ba jirgin sokoto direct, kije kiyi ta yi masa addu'a bakin uwa Mai Albarka ne akan 'ya'yan ta muma muna tayaki nasan fushi yayi idan ya huce ze nemi gida".
Har ranta bataso wannan hukuncin ba Amma yata iya da Yaya ishaq uba ne sak tun bayan rasuwar mahaifinsu bai barsu da kukan maraici ba, duk rintsi baya Bari su koka uwa uba yanda ya janyo gudan jininta ya nuna Masa hanyar nema tun a kananun shekaru duk abinda yaronta ya zama shine sila gashi Zuwa yanzu Allah yayi Masa karfin daya fi na Yayan. Hira sukaci gaba har Aunty Badi'a ta fito itama kamar me Zuwa gasar sarauniyar kyau ita Fara ce tas buzuwa kallonta Yaya ishaq din yayi "wato ta wata fuskar naji dadin zuwanki Zainab ko banza mutuniyar ta koyi gayu irin naki da dai sai a hankali".
"Kai Yaya wlh bani na koya Mata gayu ba Daman Aunty na me class ce ko Aunty?".
"Fada Masa dai,kawai nasan dai na koyi amfani da perfumes designers dani kowa ne ma saye nake Amma yanzu tunda ta bani naji dadinsu nake amfani dasu". Dariya yayin Yana fadin .
"Ba cinya ba Wai 'yan magana sukace kafar baya, Wai yanzu Ina da kikace min zakuje? Bana son yawo har an Fara min sallama idan ta Gama idda".
Ido Aunty Badi'a ta kwalalo "sallama Kuma?.
"Wlh kuwa shi yasa nace ta tattara tayi hakuri zanyi Mata booking ta tafi kawai muci gaba da addu'ar Allah ya bayyana shi duk inda yake".
"Gaskiya kam shi yasa kenan ranar da mukaje gidan sarki kingmakers sun fito daga meeting da Mai martaba Naga ana nuna ta har wani dogari Yana kokarin Zuwa gurin mu muka tafi".
"Kinsan kuwa sakon daga fada yake".
Baki Ammi ta rike "tab gara nasan inda dare yayi min kafin wannan labarin ya Isa kunnen general".
Ta fada suna nufar kofar fita daga falon.
"Da dai kin yiwa kanki gata"
Yaya Ishaq ya fada.
*********
Tun safe su Mahmud suka fita da Sameer su shiga can su fita can duk da Sameer Kusan Dan kallo ne an Kai ruwa Rana kafin a samu ganawa da Wanda alhakin matsalar ke hannunsa Basu suka dawo ba sai dare a gajiye suka dawo Jin dadinsu daya ba a hotel suka sauka ba gida ne. Sameer yayii musu order din abincin Africa. Saida sukayi wanka sannan sukaci abincin inda Allah ya taimaka sunyi sallah a wani masallaci a hanya. Bayan Mahmud ya shiga daki wayarsa ya Ciro ya shiga ciki gurin da akayi Masa connecting da CCTV nan ya lalace gurin kallon Zahra yanda yake more kallonta yasan da ace tasan da CCTV a dakin bazata Bata sakewa haka ba tana sabgoginta. Amma ganin ita kadai a dakin take zuba yanda takeso, amma yanda ya fuskanceta kamar wani Abu Yana damunta ya Raina yanda take walwalarta, ya rasa aikin me suke ita da Mai Taya ta zama Dan gani yayi ita Mai tayata zaman ta fita waje da alama wani Abu ta sawo Dan can baya yaga ta hada wuta da gawayi akan wani Abu ta Dora tukunya Mai Dan girma, so yake yaga wace wainar zasu toya.
Dayar wayar ya dauko Yana kokarin kiranta sai kuma Kiran Mr Lee ya shigo akan Yana fada Masa kome yake ya fito bakin da zasuzo daga Thailand sun karaso shi kadai ake jira, tashi yayi Yana Kiran Sameer akan ya zama ready zasu fita.
**
ZAHRA.
Tun bayan data gama break Basu zauna ba aiki Zahra ta dauko dambun Nama take son yi yau akwai Naman da yawa sai kuma abinci shima Mai Dan yawa haka Nan taji tana son kaiwa Abban ta da Baba Malam abincin juma'a zilai ce tace a sawo kufat ayi suyar dambun a Kai tunda da yawa za'ayi ta Bata kudin aka sawo ta Dora, Basu suka Gama aikn ba sai bayan azzahar zilai ita ta mikawa zayyan bayan ta wuce ne ya bude abincin yaga irin garar da aka kawo Masa yayi ta mamakin yanda matar oga ta iya girkin hausa haka Mai shegen Dadi gashi ita Kuma ba bahaushiya bace ko Ina ya samo wannan da Kuma dalilinsa na zabar wannan rayuwar shifa ko a mafarki baiyi tunanin ogan nasa ze iya sakewa har ya Mike kafa yayi zamansa a irin wannan muhallin ba da iyalinsa, haka yayi ta sakawa Yana kwancewa.
Sai da su Zahra suka Gama Zuba komai a mazuban da suka Dace sannan Zahra ta wuce ta Kira magaji a waya akan yazo tana nemansa sannan ta shige wanka sai bayan la'asar magajin yazo lokacin ita kadaice a falon tana tulawar alqur'ani, Saida ya cika cikinsa Yana zuba Santi sannan ta bashi yace ta fito Masa na Baba Malam Dana gurinsu Ammah har ya Kai kofar fita daga parlour ya juyo Yana fadin "inyeeh su Adda Zahra an girma har an Fara aikin neman ladar tsaffi da fatan dai kin fadawa mijin naki kada garin neman lada a kwaso zunubi". Ya karasa fada Yana dariya.
"Allah ya shiryeka magaji Kai Kullum baka girma ko?"
"A'a zancen gaskiya ne Dan bawan Allahn nan baki San yanda yayi ya Nemo kudin sayen kayan nan ba Amma kin tashi kin zuba irin wannan garar Dan kawai Kinga baya gari ko?"
Harararsa tayi "To nayi kayan nan dai nawa ne mijina ya aje min Bai Kuma yi min iyaka ba duk abinda nakeso zanyi dasu idan bazaka Kai ba dawo ka aje min sai Aunty zilai ta Kai ko naje da kaina". Ta taso ta nufo inda yake da sauri yayi gaba Yana fadin.
"Allah ya huci zuciyar uwar gidan Mahmud tuba nake".
"Dan rainin hankali shi dai gurinsa ya saka mutane magana".
Aunty zilai ce ta Bata amsa Sam Bata lura da fitowarta ba.
"Kema uwar dakina Kamar kin manta halin Mai sunan Alhaji ai shi burinsa Ke nan yayi jan magana".
"Ai sai yayi tayi tunda halinsa ne"
Abincin zilai ta kawowa Zahra Nan cikin parlour some times Bata fiye son zaman dining ba, kitchen zilai tayi niyyar komawa Zahra ta Hana "ki zauna a nan muyi lunch din Ina Zaki kuma koni bafulatana bana irin wannan d'abi'ar".
Sun Fara cin abincin kenan door bell din tayi k'ara zilai ce ta tashi taje ta bude Mujiba ce tare da wata yarinya Sa'ada 'yar makotansu.
"Kai! Kai!! Kai!!! Tab amma dai batan hanya kikayi Mujiba, yanzu Alkawari da amana sunce haka? Yaushe rabonki da gidan Nan?"
Dariya mujibar tayi tana fadar "eh lallai da sauranki irin wannan Baki zai- zai, Kuma shike Nan daga kawoki saina dunga sunturi a gidanki ai Mai gidan saiya saka Mai gadi ya hanani shigowa tinda Zan zamar masa matsala, Wai ke tsaya waye a gate din gidan nan daya tsaremu da dogon turancin daga Ina zuwa Ina me mukazoyi ke tambayoyi dai gasu nan kamar zanga Mrs president".
Ta fada Tana Zama a kujerar dake kusa da zahrar Sa'ada ma ta zauna.
Spoon din hannunta Zahra ta aje "Bari kawai Muji wlh Nima haka na ganshi haka Nan Rana tsaka ya canzawa Mai gadin gurin aiki ya mayar dashi makarantar gidan Baba Malam ya ringa share share ya kirawo wannan bansan ko daga Ina ba yanda aka wayi gari da Mahmud shima haka aka ganshi nifa lamarin yafi karfin tunani na kawai na saka ido ne Naga karshen film din".
Ta fada tana Dan tab'e Baki.
"Amman wlh Baki da kirki auren naki kike cewa film dan bawan Allah ya biya sadaki ya daukoki daga gidan ku ya killace ki guri daya ya Baki ci da Sha amma ki Kira Masa aure Shirin film humm zakiyi bayanin film da alama komai normal yake tafiyar Miki ko Aunty zilai?"
Dariya tayi "A'a babu ni a cikin wannan maganar kunga tafiya ta".
Ta wuce kitchen da plate din abincin ta.
" Kinga Sauko kiyi serving din ku, ni ban iya abinda Kika iya ba ku Kenan bakinku ba kintsi ku dunga sakin magana irin haka Ina Dadi Kinga kin Kori Aunty zilai daga wurin".
Tasowa tayi ta sauko kusa da zahrar tana fadin "lallai kina Jin Dadi irin wannan garar haka sauko sa'ada Wai Ina Mai gidan na Dan kwana biyu ban ganshi ba?"
Plate din ta ture gefe ta dauko tissue tana goge bakinta.
"Yayi tafiya jiya baya Nan".
Tsayawa mujiba tayi da cin abincin. "Bayanan Kamar ya?"
"Kamar yanda na fad'a Miki yaje taron gamayyar Qungiyoyin da suke taimakawa ilimin makarantun government Dana allo a Nigeria da wasu kasashen Africa, to a Nan zone din namu na north east shine aka dauka a Bauchi state, a jigawa da Kano ma duk suna da nasu wakilan tunda state uku suka dauka".
"Masha Allah kice wata Rana ku sai turai tunda Mai gida ya Fara irin wannan babbar harka ai ku hannu sama chololo lallai mutuniyar kinzo da goshi".
Tsaki tayi wlh ki raba kanki da camfi Wai nazo da goshi to tun kafin nazo yake aikinsa Kuma tafiyar ma dagawa sukayi tun ba labarina a rayuwarsa zasuyi abarsu Nima da abinsa na same shi sai yanzu ne dai ta Kara tasowa.
Haka suka dunga Hira har Kusan magariba sannan suka tafi Zahra ta Basu kilishi da biscuits masu yawa.
Saida magaji ya Fara Kai sakon Baba Malam sannan ya karasa gida, yauma aikin Ammah ne lokacin daya shiga parlourn ta ba kowa sai Alawiyya tana saka turaren wuta da freshner tambayarta yayi Ina Ammah? Tace Masa taji dakin Abbansu can ya nufa da basket din da ledar knocking tare da sallama a kofar falon Mamace ta amsa Masa ya bude ya shiga da alama wani Abu suke tattaunawa.
Gaishe da Abban yayi sannan ya gaishe dasu Ammah Yana aje basket din da ledar Naman da aka kunshe cikin poil paper.
"Abba gashi inji Adda Zahra tace a kawo maka".
Mama ce ta taso tana fadin"Kai Masha Allah lallai wannan 'yar tana ji da Abbanta". warmers din ta Fara cirowa tana bude miyar falon ya cika da kamshi Curry da spices.
"Abban ne yace "magaji sannunka Kaima lallai uwata ta haifu Allah ya yiwa wanna aure Albarka ya tsane idon makiya wlh naji Dadi kwarai da gaske a Miko min nan Naga abinda uwata ta kawo min".
Ya fada Yana mik'awa magaji bugun Abuja biyar zuwet.
"Na gode Abba, Kuma ta bada an kaiwa Baba Malam ma ya fada Yana nufar kofa.
"Masha Allah nasan uwata zatayi abinda yafi haka".
Cikin rawar jiki mama ta kinkimi basket din ta Kai gurin da Abban yake zaune ta dora akan coffee table, sannan ta dauko ledar, ledar yace ta bude lafiyyayan dambun naman rago ne yasha kayan Hadi ya sayu jawur dashi sai Kamshi ke tashi, Dina yayi yakai Bakinsa ya tauna Yana fadin "Masha Allah uwata ta Gama min komai wlh har Raina Ina son yarinyar Nan bilhaqqi uba ta daukeni sak duba ki gani Rabi'a ga Asma'u a zaune amma Ni ta yowa wannan garar Kai madallah, Yau abincin ki sai dai yayi hakuri na uwata zanci".
Ya fada yana kallon Ammah. 'yar dariya tayi Ammah tana fadin "Ana ta sabon d'a wa yake ta tsohon da inji barmani choge".
"Gaskiya kam, ai Babu Mai shafewa Zahra Zane a gurin Abba"
Mama ta fada.
"Ki Fadi ki Kara Zahra yarinya ce mai tsananin yi min biyayya ki duba yanda lamarin auren Nan ya kasance Amma tunda tayi 'yan koke-kokenta ta hakura ba Wanda ya Kara Jin kanta, duk da mijin nata Mai Karamin karfi ne akan wadanda suka nemi aurenta Allah be nufa ba da Kuna duba da inda ta fito da Kuma uwa uba dangin mahaifiyar ta Amma tayi zaman ta Ni kuwa ba abinda bazan yi Mata ba matukar baifi karfin arzikina ba".
"Wannan gaskiya ne duba da yanda ta waye tayi karatu Mai zurfi ai ba wata ce bijirewa zatayi ayi ta Kai ruwa Rana"
Mama ta fada.
Yar dariya kawai Ammah tayi duk Dadi ya cikata Bata taba tunanin Zahra nada wayo haka ba tasan dai abun duniya Bai rufe Mata ido ba.
✨✨✨
✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
✨✨✨
✨✨✨
Maman Fateemah.
Page 32
_______Qaran alarm din daya saita ne ya tashe Shi sallar Asuba, duk da bai kwanta da wuri ba Dan sai Kusan karfe biyu na dare suka shigo gidan, meeting din nasu sun jima suna tattaunawa akan sabon kafanin da zasu bude a jihar kebbi na shinkafa, masallacin da suke sallah da gidansu akwai tazara sosai shiyasa ya saita kafin sallar Asuba da kamar hour daya, sai da yayi yaqi da Shaidan sannan ya samu ya sauko daga gado Bai jima a toilet ba ya fito sanye da bathrobe Fara tas Mai jikin towel. Jallabiya ya saka yayi raka'atanul fajri sannan yayi waje a Yana niyyar yiwa Sameer knocking ya bude ya fito.
"Barka da Asuba" Sameer ya fada yana mikiwa Mahmud hannu sukayi musabaha,
"Ashe ka tashi ai nayi tunanin saina shafa maka ruwa sannan ka mitsa".
'yar dariya Sameer yayi Yana fadin "irinku da kuka San inda kuka dosa Kuna dagewa da mujahada to mu ta Yaya zamuyi kwance muna barcin asara ai sai lalacewa tayi yawan".
"Kayya Kai dai Allah ya datar damu kawai"
"Allahumma Amin"
Sameer ya fada lokacin da suka jero suna Kara tattaunawa akan harkokin yau da Kullum, Sameer ne yaja musu motar suka fice daga gidan, bayan sunyi sallar zama sukayi akayi karatu Kusan masallacin mahadar 'yan Africa ne mazauna can Kusan duk Wanda yake a kukkuken gurin Baya Bari khamsu salawat ta wuce shi, sai da gari ya waye sannan suka nufo gida.
A hanyar ne Sameer ke fadawa Mahmud sunyi waya da Habib jiya a kan training din da za'ayi na matasa maza da Mata na koyon sana'a.
Har suka zo gida suna zancen, yaso yayi barci amma ya fasa, so yake ya Kira Nigeria baze iya mazewa ba Kamar yanda yayi niyya Bai gane shi Mai rauni bane sai akan yarinyar nan,sai da yayi Mata nisa ya gane shayi ruwa ne, duk da Bata shigo rayuwarsa da Wasa ba kafin ya hadu da ita shi jarimi ne sannan shi baima fa San yanda kake kwana da Abu ka Kuma tashi dashi, shifa idan ya tunata har wani ji yake zuciyarsa ta harba, yaso ya dan Bata iska, so yake ya fahimci shin ta karbeshi da zuciyarta da gangar jikinta ko Kuma har yanzu tana zaune dashi ne by force na iyayenta, amma idan ya kalli kwayar idanunta Yana hango wani Abu na daban a cikinsu Kuma uwa uba yanda sukayi rayuwa a Dan zaman da sukayi da ita.
Bayan sun shiga gida kowa nasa gurin ya dosa Dan shi dai Sameer barcin ya kama, shi kuma daya shiga wanka ya sake, shifa idan ze wuni Yana zubawa jiki ruwa bashi da damuwa. Sai da ya gama komai ya Haye gado daga shi sai singilet Fara sol da boxer short.
Wayar ya dauko dauko cikin ikon Allah yaga Zahra online ji yayi wani Dadi yaji ya rufe shi, vedio call ya Kira daya wayar Kuma ya bude connection din CCTV.
Tana cikin charting da Aunty Nawwara kawai kiran nasa ya shigo Yana kallon yanda ta kwalalo Ido waje abin har yaso bashi dariya, hijabin da tayi sallah ta dauko ta rufa kirjinta sannan ta daga Kiran suna hada Ido taji gabanta ya Fadi ji tayi abun Nan na da ya dawo Mata.
Sallama yayi mata da husky voice dinsa wanda ya saukar Mata da wata muguwar kasala, a hankali ta daga idonta ta kalleshi cikin murya Mai rauni da rashin karsashi ya amsa Masa sallamar, kuri yayi da idon Yana kallonta yanda tayi Masa wani irin kyau Kamar shi gani yayi a tsakanin jiya da shekaranjiya Kamar an Kara Mata kyau.
"Ki bude Ido ki kalleni ki bani labarin abinda ya faru daga tafiya ta Zuwa yau, kuma wlh ki cire hijabin nan tunda ba sirikinki bane Ni da Zaki dauko hijabi ki Kama rufe jiki wato Ni ban cancanta Naga abinda yake halalina ba ko?"
Kai ta girgiza tana masa kallonsa a shagwabe.
"Nifa tunda nayi sallah nake sanye da abuna bawai saboda Kai na saka ba nida bansan zaka tuna Dani bama ballentana ka kirani, nifa na dauka Kama shafe babina tunda baka nemana wanda ka damu dasu kake nema".
Ta fada tana juya sexy eyes dinta wanda Bai sani ba ze dauka da niyya tayi Hakan.
Ajiyar zuciya yayi Yana Hadiyar yawu shifa ganin Nan da yayi Mata ta jangwalo masa wata fitinar da sai Allah kawai.
"Ki cire hijabin Nan Allah kona Baki mamaki". Kafada ta make tana kallon gefe Dan wani fitinan nan kallo yake Mata.
"Dan Allah ka dena kallona".
"Ikon Allah wato naje nayi ta kallon Mata a titi kenan ba ruwanki ke ko irin 'yar kissar Nan ta Mata Ni baza'ayi min ba tunda ni ba Mai aji bane banyi boko mai zurfi ba ko
"Ni kuma? Yaushe nace bakayi karatu Mai zufi ba?"
Yar dariya yayi irin ta kana cikin ?nishadi din nan.
"Wato wayo zakiyi min na bar maganar hijab wlh ki cire Kona biyo dare nazo Nigeria na....
"Dan Allah ka Bari wlh Zan cire kada ka fada".
"Ki Bari kiji mezance Mana my previous".
Ya fada Yana Kashe Mata ido.
Itafa mamaki yake Bata idan Yana fadar wasu kalmomin turanci sai taji Kamar zurfin iliminsa ya wuce yanda ake fada, ta ko Ina a waye yake ga wata irin tsabta ta ban mamaki itafa idan ba karya idonta yayi Mata ba sai tace Bata taba ganin ya Mai maimaita Kaya ba idan ya saka Bata qara ganinsu a jikinsa.
"Wlh kiyi abinda nace kona baro Miki aikin da Baki shirya Masa ba, 'yar yarinya dake kin hana zuciyarta sakat tunda na Dora idona a kanki komai ya kwance min duk, akanki na iya tsayawa nayi doguwar magana na iya ja in ja akan Abu duk soyayata da Hajiya Innata saida mukahau sama da ita mukayi uwar watsi nayi Mata yaji Kuma haka kawai Allah ya dubi diminiya ta ya tausayawa Dan malam kiyi min rowar ganin halalina, wlh Zan fadawa oga Sameer ayi min afuwa na dawo gida na fasa attending din meeting din a saka wani na dawo na rungumi 'yan kayana".
" Wai Kai baka jin komai idan ka Fadi magana! Dan girman Allah kayi zamanka kayi abinda ya kawoka in dan hijab bari ba cire. Amma Dan Allah ka Bari na saka riga Allah ba kaya a jikina sai vest".
Wani kallo ya jefeta dashi na Amma kin Raina ni.
"Dan Allah, wlh kunyarka nakeji da gaske"
Ta fada tana sunkuyar da Kai kasa.
"Kunyata ni Kuma wlh immediately kuwa Zan cire kunyar Nan aini cutuwa zanyi, To wai tsaya na tambaye ki yaushe Hakan ta faru? Ko bayan na baro kasar ne ki? amman ai bakya jin kunyar kallon tsabar idona ki tarewa wani Kato fada Dan nace masa lusari kika Kare min tas har kina fadin na Kama ki na runguma ko kina min kallon Dan duniya ko? humm Ashe ma duka nine lucky din a cikinsu dama na San abin nawa ne Aida saina dama daddawata da moda a lokacin Dan wlh a Ranar sai da na Raina kaina Banda mutum besan gobensa ba Aida saina Yi wandaqata a lokacin" fuskarta ta rufe da tafin hannunta dayan, da gaske so yake ya koya Mata fitsara taga alama shima ba kyalle bane cikakken zani ne. Idonsa ne ya sauka q gurin data cire hijabin.
"wow!! Masha Allah! Koke fa Amma da kin zumbuda hijabi Kamar wata matar liman ai yanzu hirar zatafi Dadin yi ki kawar min da tunani kowa daga zuciyata sai naki, Baki fada min abinda kukayi jiya ba Naga harda spare girki a waje" .
Zaro ido tayi tana dubansa "waye fada maka nunyi wani Abu a gudan?
"Nina gani kinsan nabar idona daya a Nan na taho da daya, ga Kuma Dan gidana magaji shine yayi min voice note ya bani labarin selfishness din da kikayi na kawai su Abba Kika garar arziki ta juma'a Kika ware min iyayena Mata, shi yasa Kika saye zuciyar su Abba da Baba malam kenan,? Kullum maganar daya ce ga amanar yarinyar Nan ka kula da ita Ashe dai tushiyar Baki kike bayarwa".
"Kai wlh ba haka bane ai gani nayi idan na kaiwa Abba Kamar na bawa Ammah ne, haka Baba malam ma ai Iya Abula na bawa koba haka ba"
"Eh kusan Hakan ne amman dai da gyara, Kuma kike wani cewa Abula ko 'yar Karar Nan Babu nifa sunan tsohuwata ne,amma kici gaba da fada wata Rana kunya zakiji idan Kika fada a gabanta tunda bakinki ya Saba fada kinsan dai mu mutanen karkara bama Raina abun fada can zakiji zance ya zagaye cikin kauyen mu ace Mamuda ya auro 'yar birni ko sunan Inna Bata sayawa gatsau take fada".
Kai ta Dade tana tadan turo Baki irin na sakatattun yaran Nan tana fadin "Nifa ban sani ba Ina janta ne tunda sunan kakata ne babar su Ammah zakace min waye waye nima ai Mamana ce ba taka bace Kai kadai yanda kayi kutse a gurin Amma Nima haka zanyi a gurin Mamana harda Hjy Inna".
"Kice nayi celebration ana son da Ammi, inye matar Mahmudun ba, fada min wace addu'ar kike min Dana kasa kallon ko wace mace da sunan so tun bayan kin shigo rayuwata, da dai bana musu da kowa Amma a kanki humm har bore Saida na koya, oya fada min sirrin inji?"
Shiru tayi saboda ji tajeyi kamar zir take a gabansa, Amma ta lura shi ko a jikinsa kamar ma be damu da yanda take din ba.
"Kinyi shiru ko abun sirri ne baza"a fada min ba?"
"To me kake so na fada maka".
"Komai ma, me kike fadawa samarin ki idan sunzo zance? Nima yau zancen nazo Wanda ban samu damar yi ba a baya shine yanzu nike qara'i".
Batasan sanda tayi dariya ba "Au dariya ma na baki ko? Shike nan wlh nifa a kanki na iya zance me yawa da mace ada daga Ammi sai Hjy Inna kawai nake doguwar Hira sadu, nasan duk ranar da Hjy ta ta ganki sai tayi Miki ciwon Baki tace dan kwali yaja hula kinsan meta fada lokacin Dana fada Mata mgnr ki?" Girgiza kai tayi alamar A'a.
"Cewa tayi idan na cika cikakken namiji na shiga duniya na nemoki, Ni kuma nayi wani Alkawari daga ni sai Allah saina bata mamaki wlh".
Kama Baki tayi tana Dan Zuba masa sexy eyes dinta wadan da ke rikita Masa lissafi.
"Kakar taka zaka bawa mamakin duk soyayyar da kake yi Mata kace za'a ganku a rana?".
Kai ya gyada Mata yana gyara kwanciyarsa.
"Yes ai kece mahadin aikin da zanyi na Bata mamakin ko bazaki tayani ba?".
"Ni kuma meya hadani da dabin ku?"
"Kina son sani na fada Miki?"
"Uhm".
Karan doorbell ne ya dakatar dashi daga kokarin bayanin da ze Fara mata.
"My precious Afuwan naji ana bukatar shigowa Bari naje I will call you later, take care by".
Ya tura mata wani hot kiss Yana kashe Mata ido ya sauka daga online din.
********
DAMAGARAM.
Waya ce a kunnenta tana magana cikin tsantsar ladabi kamar tana gaban Mai magabar, cikin ladabi ta Fara fadin "wlh Hajiya ba haka na fada Masa ba cewa nayi kada ya tura kowa Abuja nayi booking din flight ne daga Abuja Zuwa sokoto, tunda Yaya ishaq jirgin Abuja ya yi min booking Kuma nace masa ko nazo sokoto bana son a turo min kowa yanda na fita Ni kadai haka bake bukatar dawowa ni kadai kinji yanda mukayi dashi ai nace masa Zan dawo Amma gani yake kamar gaba zan karayi"
"To ai yanda Kika gindaya Masa dokar ne yake tantamar hucewar taki, kiyi hakuri Zainab anyi Miki ba dai daiba Amma ki zama mai yafiya akan laifin da akayi Miki kema sai Allah ya yafe Miki naki kura kuran, ki Kara godewa Allah kece karama ke Kuma Allah ya daukaki naki Dan fiye da kowa a dangi ki dauka abinda ya faru jarabawarsa ce tazo a haka,Daman Allah swa yace shin bana jarabceku ba? to ki dauka hakan rubutaccen al'amarine daga Allah idan aka daure wata Rana sai labari, shi ba yaro karami bane da za'ace ya bata kawai yayi Mana fushi ne inaji a jikina Yana kusa da dawowa garemu da izinin Allah, ai kawunsa mustapha yace min ba abinda ya tsaya a harkokinsa Dan yana bibiyar lamuransa a yanar gizo yaga komai yana tafiya daidai".
"Nima Ina bibiyar lamarin nasa Hajiya Amma abinda yafi damuna koni bai taba kirana ba ko sau da har zuwa Yau".
"A'a Zainab mu duka masu laifine lokacin daya kamata a saurare shi kowa baya ya juya masa, Banda Mai biyaya bane yanda Allah ya daukaka shi ko ganinsa basai yayi Mana wahala ba? Amma yaro Mai ladabi da biyyayya mun taru mun yi masa naqi ba dole yayi nesa damu ba".
Saita balle da kuka, da kyar Ammi ta lallasheta tayi shuru. Sannan tayi mata sallama tana Kara jaddada Mata zuwan tare da fadin ta turo direbanta ya daukota Dan gidanta zata sauka tunda anan tabar motar data zo gurin Hajiyar da ita a Ranar data wuce YAMAI.
Aunty Badi'a ce ta karaso kusa da Ammin tana fadin "ina ganin soyayyar uwar miji da matar d'a amma ban taba ganin irin taku ba inaga yanda Hajiya Inna ke sonki ko Yallabai Bata so haka gashi ta kwallafa rai kan Mahmud kamar me"
Zama sukayi a Kan sofa daya dake cikin dakin.
"Wlh Ni kaina Aunty Ina jinjina yanda Hajiya ke Sona da dukanin yarana shi yasa sau da yawa idan wani Abu ya taso a gidan bana Bari taji ko labarin sa Dan nan da nan zata tashi hankalin gidan sai Kuma abun ya Zama wani Abu daban Dan Kullum gani sukeyi na Gama da kowa a gidan ballentana abinda ya biyo bayan rigingimun da akayi wanda suka saka na baro musu gidan,sai Abun ya Kara zafi ganin irin tujarar da general yayi da irin hukuncun daya yanke".
Dan nisawa Aunty Badi'a tayi kafin tace. "Abinda dai baiyi tsabta ba Kam sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba, Daman shigowa nayi muyi magana akan hukuncin da Zaku yanke ne hada Mahmud Aure da 'yar aminiyarki matar takawa, tun a jiyan naso mu tattauna sai nayi Baki sauka cinye lokacin, me ze Hana ki Bari aga dawowar tasa tukunna sannan kiyi masa tayin yazo yaga yarinyar idan Allah yasa tayi masa a irin matar da yake ra'ayin ta Zama iyalinsa Kinga shike Nan idan Kuma an samu sabainin haka Daman ba'a amsa ba bare zumuncin ku ya samu matsala ko ya Kika gani?".
Shiru Ammi tayi tana nazarin maganar matar yayan nata Kuma 'yar uwa abokiyar shawara.
"To ai abin dubawa Aunty kada fulani taga ban kyauta mata ba tayi min na huce ace na buda Mata kasa a ido bazan iya ba, idan Allah ya dawo dashi mijin mace hudu ne idan Yana da wadda yake muradin aure ya Kara da ita Dan nasan bazeki Haura'ul Insiyya ba, duk abinda ake nema ga Diya mace Allah yayi Mata ga uwa uba nasaba".
"Haka ne Allah ya dawo Mana dashi lfy ya Kuma zaba abinda yafi Alkhairi, Amma dai in ina Raye wlh ba Mai yiwa yarona dole ba ruwana da Amincin ku can tsaninku"
Baki Ammi ta Kama tana Fadin "Tofa kaji masu 'ya'ya wato kin nuna side ko?"
"Ki fadin koma meye Amma dai a barmin yaro ya samu peace of mind gaskiya, shi bashi da idon ganin matan ne? Ina cewa kasashen duniya yake yawo Kinga kuwa wane irin Mata ne be gani ba, Kuma da bakinki kike fadin yace shi da wadda yake so daman biyayya ce kawai zeyi ya karbi auren da aka bashi Amma komai Daren dadewa zeyi wani auren to ki cire kanki a cikin jerin masu tilasta 'ya'yan su auri abinda sukeso, ki bishi da addu'ar Allah ya hada shi da abokiyar Zama ta gari kawai, se kimarki ta karu a idanunsa ki Zama abokiyar Shawarar sa babu abinda ze rufe Miki Amma kina shigo Masa da irin wannan zance ze Miki wani aji na daban, baze saki jiki dake ba balle kisan menene matsalarsa, ki tsaya kiyi nazarin abin nidai shawara ce na baki"
Tunda Aunty Badi'a ta Fara Kora bayani jikin Ammi yayi sanyi saboda suk abinda Aunty Badi'ar ta fada gaskiya ne, nisawa Ammin tayi "haka ne Aunty wannan observation ne me kyau hakan zanyi Daman fulanince ta Fara kawo maganar Naga Kuma ya dace na Bata goyon baya, Amman in Sha Allah zanbi Shawarar ki...✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
✨✨✨
Page 33.
MAMAN FATEEMAH.
________Zahra ta Dade a kwance tana sakawa da kwancewa, wani irin yanayi takeji a jikinta ita abun har mamaki yake Bata "Wai menene hakan" tayi tambayar da ba Mai Bata amsa. abinda takeji wani Abu ne na daban Wanda Bata taba Jin irinsa ba akan kowane da namiji ba, cikin kankanin lokaci ya cika Mata zuciya ita abun har kunya yake Bata,ta gama bore harda su somewa dasu wunin Asibiti Kuma yanzu a wayi gari a ganta dumu dumu cikin soyayyarsa ai da kunya wlh.
Wani tunanin ta qarayi Bata San lokacin data rufe idonta ba tana ambaton "Ya Ilahiy wlh abun da matukar Allah ka agajeni gaskiya idan hakan ta kasance naji kunya".
Ta fada tana qara qanqame jikinta.
Saida ta Kusan Bata minti talatin tana abu daya sannan ta yunqura da kyar ta tashi,wanka tayi ta shirya cikin English wears yellow irin shaking material din Nan sai sukayi Mata wani irin kyau Karamin mayafi ta rufe gashinta dashi black Mai shara shara ana kallon bakin gashinta Mai santsi da laushi ta cikin gyalen, sama sama ta fesa turarenta ta fito parlourn ba kowa sai kamshin freshner da turaren wuta kawai sai Kuma sanyin A/C daya ratsa ko Ina,cikin takunta na nutsuwa ta doshi kitchen inda take jiyo motsin zilai a cikinsa.
Sansanyan kanshi ta ya Fara shiga hancinta zilan kafin ta karasa shigowa.
"Masha Allah! Uwar dakina dawisu sarkin ado, Allah ya barki gidan Yallabai muhmudu, ubangji ya kawo Mana kazantar daki Amma Bata shara ba".
Dan murmushi Zahra tayi tana Fadin kin jiki Aunty zilai ni kibar wannan maganar gaskiya, Ina kwana".
Ta fada tana komawa parlour biyota zilan tayi tana Fadin "yau fa abinda kikafi so nayi Miki" ta fada tana kokarin bude warmers din abincin,waina ce manya irin tasu ta Bauchi sai Kuma pepper soup na cow leg da kunun gyada Wanda yaji Madara.
"Wow! Amma aunty zilai kin gama min komai na gode" ta fada tana janyo plate din da zata Zuba, zilan ce ta karba da sauri tana fadin "haba dai gani a tsaye Zaki Zuba abinci da kanki to meye amfanina".
Rike plate din Zahra tayi tana fadin "Dan Allah kada muyi haka dake Ina laifin dafawar ma ai dadin sai yayi min yawa, Ina kwance Ina barci kina ta faman dawainya sannan Zuba abincin ma Sai anyi mini".
"To menene ai aikina ne".
"A'a wlh ba Aikinki bane a Nan cewa akayi ki tayani Zama kwarai".
Ta fada tana bude abinci akan dole zilan ta hakura ta koma kitchen inda take wanke waken alale zatayi musu cikin abincin Rana.
Bayan ta Gama yin break din parlour ta dawo ta kunna tasharta mbc max tana kallon wani film da sukeyi, tana Nan zaune taji karar door bell ta tashi ta nufi kofar ta bude yara ne kamar 'yan sheka sha uku haka suna rike da manyan ledoji kowa guys biyu a hannunsa.
Cikin girmamawa suka gaishe da Zahra tare da fadin "gashi inji Baba Malam yace a kawo Miki Kuma Yana gaishe ki".
Suka fada a tare, hanya ta Basu suka shigo da kayan ciki sai raba Ido suke suna kalle-kalle.
"Sannunku ku aje ku zauna, na gode kwarai da gaske Allah ya saka da Alkhairi, a me kukazo ne?". Dayan da yafi magana yace "Yaya Habibu ne ya kawo mu Yana kofa gurin wancen mutumin" ya fada Mata.
"Masha Allah". Ta fada tana Kiran zilai, da sauri ta fito tana fadin. Gani uwar dakina".
"Kaya ne Baba Malam ya Aiko aka kawo min".
Gurin da kayan suke ta karasa tana fadin "Masha Allah 'yar gatan Baba malam, an gode madallah sai a Basu tukwaici". Zilan ta fada tana kokarin bude ledar dake kusa da it's.
"To Bari na dauko musu ki shiga da kayan ciki sai ki zuba musu abinci a robobin nan na take away Wanda aka kawo saboda zuba kayan gara Dan kada su zauna yau Ranar wanki da 'yan aikace aikacensu ne," ta fada tana yin gaba.
Bedroom dinta ta shiga ta duba Sam ba kudi a gurinta, Dan Jim tayi sai Kuma ta bude bedside locker ta dauko keys din dakin Mahmud daya Bata.
Kamar' Mai tsoron wani Abu kada ya kamata ta bude dakin, komai tsab hatta kamshinsa Yana dakin kamar yanzu ya fesa yabar dakin,limshe ido tayi tana shakar kamshi, komai na dangin electronic a kashe yake a dakin a hankali ta ratsa ta nufi inda ya nuna Mata yace idan bukatar wani Abu ya tashi ta dauka, locker din ta janyo 'yan dari biyar ne da dubu dubu ko wanne rapper uku uku 5k kawai ta Ciro daga cikin 'yan 1k din ta mayar ta rufe tana tunanin Kiran magaji yazo ya Ciro Mata kudin saboda irin haka Bata bukatar komai tunda ba abinda ba'a aje Mata ba wani abun ma Sai a shekara Bata nema ba.
Bayan ta kawo musu sukayi gdy suka fita, gurin Aunty zilan Zahra ta shige.
***********
Karfe biyar na yamma jirginsu Ammi ya sauka a sokoto, lokacin data fito Harabar da masu jiran saukar 'yan uwansu suke,Habu direban Hajiya Inna ne ya nufo Ammi da sauri Yana fadar "barka da sauka Hajiya, nine Hajiya Inna ta turo nazo na tare ki".
Ya fada Yana karbar karamar luggage din dake hannunta .
"To sannu da kokari nagode kwarai".
Direct gidan Hajiy innar ya nufa da ita da yake unguwar mabera, duk yanda Abban su Mahmud yaso ta zauna part dinta daya Gina Mata Amman ta nuna tafi son daga nesa dai.
Har kofar falon Hajiya Malam Habun ya kawo ta bisa umarnin Hajiya, lokacin da ze tafi dauko ta fada masa ya kawo Mata ita har kofar parlour.
Kafin ta fito Yara qananu guda biyu suka fito da gudu daga parlour wanda yayi dai dai da fitowar Ammi daga mota da gudu suka karaso, suna fadin ga Ammi! Ga Ammi" suka fada jikinta a tare suna fadin "Ina kikaje Ammi Baki tafi damu ba mukayi ta kuka".
Kansu ta shafa tana fadin "sorry My babies ba gashi na dawo ba, ai kuka Kuma ya Kare"
Hannunsu ta rike ta nufi kofar da suka fito, sun riketa ram kamar zata gara guduwa ta barsu.
A zaune Ammi ta samu Hajiya inna tana lazumi, gurinta ta nufa cikin takunta na nutsuwa tana fadin "Hajiya barkanmu da yamma".
.
Ajiye tasbahar dake hannunta tayi tana kallon Ammi wadda tayi wani tas da ita, bazaka taba cewa ta aje kamar' Mahmud ba, idan aka jera su mafi yawan mutane zasu ce yayarsa ce. Gefen Hajiyar ta zauna daga kasa wannan d'abi'ar ta ce Bata taba Zama a kujera matukar Hajiya na Kan kujera, cikin ladabi irin na D'a da uwa Ammi ta gaishe da Hajiyar Tana fadin "Masha Allah zainabu kin cika Alkawarin da Kikayi min Koda kuwa ba a lokacin bane nagode kwarai da gaske Allah ya Albarkaci zuciyar ki ya Baki rinjaye akan duk masu son su tagayyara Miki zuri'a, ki Kara hakuri akan Wanda kike yi lallai duk Wanda akace yayi hakuri an Bata masa ne, Allah yayi Albarka yanda kike min biyayya kema Allah ya Baki surukar da zatayi Miki fiye da yanda like min, Wai kin samu yin magana da mutumina kuwa bayan munyi wayar nan?".
"A'a har yanzu be nemi kowa ba ina ganin ko ba lafiya ba dai shirun tayi yawa ya Kamata ace zuwa yanzu yayi hakuri ya huce ya dawo gida".
Ammin ta fada cikin damuwa.
"Ba komai in Sha Allah lfy na fada Miki yanda mukayi da mustapha kema kince kina bibiyarsa ayi ta addu'a Allah ya sassauto da fushinsa ya waiwayo gida wallahi ko cikin dare yaron Nan ya Fadi min a Rai to barcina ya Kare Kullum ta Allah sai anyi mini saukar Alqur'ani akan Allah ya bashi kariya a duk inda yake wallahi nayi Dana sanin fada masa maganar da nayi danasan maganar tawa ze dauketa da zafi wlh da bazan fada masa ba yana cikin zafi".
Hawaye ne ya balle Mata kamar lalataccen famfo har da shashhshekar ta.
"Dan Allah Hajiya kiyi hakuri wlh ba maganar ki bace tasa yabar gida nakin dai yazo Kan gab'a ne kawai".
"A'a keda Baki Nan mukayi yazo Nan Yana ta huci Dan motar dazo a ciki ma ko kashe ta baiyi ba ya fado min Kamar an jefo shi, Yana huci Yana Fadi wlh duk duniya ba Wanda ya Isa yasa ya auri safna Koda Matap sun kare shi Daman koya aureta biyayya ne zeyi Yana da wadda yake da muradin aure, ni kuma a lokacin bani da cikakken masaniyar abinda yake faruwa kinja layin kada a fada min gaskiyar maganar,Ina bude Baki sai ce Masa nayi idan ya ciki shi d'ane na halali ya shiga duniya ya Nemo min yarinyar da yake maganar a kanta Wanda take ganin darajarta tafi ta zuwairiyyar, wlh shiru yayi a inda yake tsaye kasa cemin komai yayi Kusan tsawon minti biyar, kafin ya kalli idona yace min wlh zakiga cikakken Dana halak, ki rubuta ki aje idan kin qara ganina a sokoto ba tare da ita ba to kuwa shege ne ni,idan Kuma ban sameta nida sokoto har abada ya juya ya wuce ko motar Bai kalla ba Kuma tun daga Ranar har Rana Mai kamar ta yau ban Kara saka mahmudu a idona ba, sai dai Babban yaronsa Yana zuwa ganina Yana kawo min duk abinda Mahmudun yake kawo min ciki kuwa harda magungunan da nake sha na hawan jini".
Ammi tayi mamakin Jin Sameer na zuwa gurin Hajiyar koda Wasa Bata taba Jin haka ba, Kenan wato kafa ya bawa mutane Yana cikin Nigeria din kenan bawai inda ake zaton zashi ba.
"Allah kyau Hajiya ki daina damun kanki, jikina Yana bani Yana cikin kasar Nan Kuma Yana da labarin komai tunda kikace min Sameer na zuwa, duk inda yake ya sani ya hana shi ya fada ne kinsan halin kayanki dai".
Mardiyya da Urat Hajiyar ta kalla Tana fadin "yan nema kunki iyayenku sai uwar wasu tun barinki garin Nan yaran Nan suka tare a Nan Wai saina kaisu Yamai gurinki tunda aka fada musu naje suka tada hankalin iyayen sai su dawo Nan idan Zan koma na tafi dasu, Kinga mardiyya jiya da Iyayen sukazo daki ta gudu ta rufe Dan ma kada su tafi da ita, ko makaranta sai dai direban ya biyo ya dauke su anan ya dawo min dasu Nan".
Kansu Ammi ta shafa tana fadin rigima ta kare tunda ga Ammin ku ta dawo ko?".
Kai suka gyada Mata a tare.
Masu aikin Hajiya ne suka shigo ta kofar baya daga kitchen suna fadin "lale marhabin da Ammi barka da zuwa".
Gaisawa sukayi a mutunce tana tambayar su iyalansu.
Abinci na musamman masu aikin suka gabatarwa da Ammi Wanda Hajiya ta hanasu sakat tun safe ake saukewa da dorawa da gaske Babu Mai shafewa Ammi Zane a gurin Hajiya tana sonta kamar me.
Sai bayan insha'i Ammi ta kwashi su Urat ta nufi gida cikin motar data Bari a gidan Hajiyar. So take ta bada mamaki yanda ta fice batare da sanin kowa ba a wayi gari a ganta batare da kowa yasan sanda ta dawo ba, duk gidan amintacciyar Mai aikinta kawai ta Kira ta fada Mata tana Nan Zuwa garin yay ko su Abeeda ba Wanda ta fadawa tasan zumudin su ze saka kowa ya sani.
************
Safa da marwa take tun bayan gama wayarta da Aunty Ladi ranta idan yayi dubi a bace yake Wai shi wannan yaron wane iri ne aiki akeyi a kansa Amma Kamar ana zubawa a teku wannan guri na uku ne da Aunty Ladi taje Mata a Jos Amma amsar daya ce wannan yaron yafi karfinta, Mata ne guda biyu a teaye a kansa da addu'a sannan yana da tsarin jiki na ban mamaki Nan kusa ba abinda zeyi tasiri a kansa sai ikon Allah.
Wayarta ta dauko Asabe ta Kira cikin k"an k'anin lokaci ta daga Kiran "kizo ina jiranki yanzu". Ta kashe wayar tayi wurgi da ita Kan gado.
Cikin abinda bai wuce minti Sha biyar ba Asabe ta shigo gidan ko part din Ammah Bata shiga ba kamar yanda ta Saba direct ta wuce gurin Mama.
Parlourn ba kowa ganin haka yasa ta wuce bedroom dinta a tsaye ta sameta tana kaiwa da kawowa Ido yayi Mata jawur kamar na tsohon mashayi.
Ko sallamar ta Mama Bata ba ta amsa ba ta, fara fadin "Ina ne garin da kikace min 'yar dago kawarki ta fada Miki da wani shahararren mutum Mai aiki kamar yankan wuka?".
Shigowa tayi ta zauna tana kallon mamar "Wai lafiya na ganki haka?"
"Ina fa lafiya! Aunty Ladi ce ta tasheni daga barci take fada min taje har guri uku ba sa'a, Wai yanda suka fada Mata yanzu ne ma Zahra ta gamu da Wanda ake ta fada Mana a baya bawai wadanda mukayi ta aiki a kansu ba, Kuma Shi wannan din duk ya fisu Shirin jiki Dan da alama yanda sihiri baya tasiri a jikin ita yarinyar shima baya yi a jikinsa, Wai wasu Mata ne guda uku a da maza biyu tsaye a kansa duk juyi sihirin baya kaiwa inda yake, yanzu Kiran da nayi miki ina son Jin tabbacin kin koma kin tabbatar da Mai gadin ya saka wannan abubuwan da Kika bashi?".
Dan murmushi tayi irin na kwararrun 'yan duniya din Nan kafin tace "Haba Hajiya shekara nawa muna tare ban taba ha'intarki ba sai yau an aiwatar da komai sai jiran sakamako kawai ai wannan yaron bama Azare ba Kasar Bauchin ma gaba daya shi da ita har abada, Kuma malamin da 'yar dagon ta fada min a wani gari yake cikin kasar katsina ana ce Masa Bakiyawa tace idan na shirya zata rakani garin iyayen mijinta ne daya rasu". Hake sukayi ta kullawa da kwancewa,Asabe nata Kara zugata akan ko nawa zata kashe kada ta Bari Ammah da 'yar zumunta su fisu komai, tunda ta Nan take samun nata rabon a jikinta idan Bata encouraging dinta itama zata rasa income nata.
**
Tun bayan ganawa da Bakinsa Mahmud ya shige bedroom ya Haye gado yaso ya Kira Zahra suci gaba da Hira Amma saiya fasa Dan yasan yanzu gari ya waye sosai a 9ja Bari ya kyaleta sai dare hirar zatafi tafiya yanda yake so. Bai tashi ba sai lokaci sallah, wanka yayo ya saka kananu Kaya yayi sallah yana cikin addu'a yaji ana knocking din kofa umarnin shigowa ya bayar Sameer ne ya shigo Bakinsa yaki rifuwa.
"Barka da Rana". Sameer ya fada Yana mikawa Mahmud wayar hannunsa.
Hannu yasa ya karba yaga menene yasa shi irin wannan murmushin.
Wani fine Baby ya gani nade cikin farin towel na jarirai fari sol.
Kallon shi Mahmud yayi Yana neman Karin bayani.
"Takwaranka ne madam ta haihu jiya cikin dare".
Cikin madaukaikin mamaki Mahmud ya kalli Sameer "are you serious?"
Kai ya gyada Masa Yana Fadin " yes sir".
Mahmud sai juya wayar yake Yana Kara kallon babyn.
"Masha Allah, my friend Allah ya Raya mana, amma me yasa ka taho ka baro yarinyar mutane a watan haihuwarta ai sai iyayenta suga rashin kyautatawar ka ga 'yarsu".
Shafa Kai yayi Yana Dan murmushi "ba wani Abu,idan na zauna me zanyi musu duk abinda ake bukata nabar musu".
Wani kallon baka da lfy Mahmud yayi Masa "an fada maka Bata bukatar kulawar ka ne a irin wannan lokacin?" wlh Dana San lokacin haihuwata yayi ba inda zakazo Kuma yanzu ka nemi visa ka koma gida daman Nan anyi clearing din komai U A.E din naji da komai kawai, naji kace takwara na nayi zaton sunan Abban koko za'a saka masa?".
"Ai umarninsa ne yace nayi masa huduba da sunan ka".
"To Masha Allah! Godiya ta har gida zanje na yiwa Abban tafi karfin ta waya Allah ya Raya Mana Mahmud yayi Masa Albarka, kaje ka Fara shiri tun yanzu ka shiga kasuwa kayi musu abinda ya Dace".
"In Sha Allah".
Godiya Sameer yayi ya nufi kofa Yana fita alarm na shigo Masa Wanda Saida ya girgiza shi baya yayo yana Murda kofar ze dawo ya jira yayi locking dinta, dariya yayi Yana Fadin "manya gatan Wasa, Allah ya biya maka bukatunka na Alkhairi".
A Ranar cikin dare suka bar Kasar su duka Sameer yayi Nigeria shi Kuma Mahmud ya nufi U.A.E .
✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Page 34
AssalamuAlaikum warahamatullahita'ala wabarakatuhu.
'yan uwa muna barar addu'oin ku bisa rashin abokiyar aiki da mukayi ECCD co-ordinator ta KIRIKASAMMA LOCAL GOVERNMENT JIGAWA STATE muna rokon Allah s.w.a ya jikaanta yayi Mata Rahama yasa Aljanna makomarta tare da Iyayen mu da sauran Al'ummar musulmi Baki daya ya Raya abinda ta Bari ya Albarkaci bayanta.
______ Misalin karfe uku da rabi jirgin sun Mahmud ya sauka a DUBAI INTERNATIONAL AIRPORT (DXB) cikin amincin Allah, yana cikin kusan rukunin mutanen karshe a fitowa, yana sanye da suit ash colour na kamfanin Armani hannunsa sanye da ogogo Rolex, baya tare da komai sai jakar laptop dinsa a hankali yake gangarowa cikin takunsa na cikakken namiji me ji da lafiya da karfi, direct gurin da taxin airport suke ya nufa, baya bukatar asan yazo garin so yake ya tantance wata jimurda da aka hada, taxin ya shiga saida sukayi balance a titi sannan ya fadawa direban ya kaishi JW moritte marquis hotel cikin harshen larabci,sunyi tafiya mai tsayi kafin su karaso hotel din, bashi da matsalar kama daki dan tun yana china yayi booking din dakin ta online, katin dakin kawai ya karba ya koma waje yin 'yan uzurirrika daga baya ya nufi ciki, wanka ya fara kafin yayi order abinci, sai da ya gama komai sannan ya kwanta dan yayi matukar gajiya, yaso kwarai ya kira 'yar gidansa amma yana son su tattauna sosai, sai yanzu yake jin haushin wani ra'ayin nasa badan haka da suna tare da ita suna hutawarsu, yanzu kadaicin rashinta da be dameshi ba, wlh da beyi alkawari ba da visa zesa ayi mata ta sameshi a nan saboda hotel din yayi masa, yana daga cikin lattest hotels na duniya be taba sauka a wani hotel ba a dubai sai BURJ AL ARAB JUMAEIRAH dakinsa parmanent ne duk mai hulda dashi a dubai nan suka sani, duk da yana da gidaje a kasar shi be fiye son yakai abokanin bussiness dinsa gida ba. Wannan shigar ta sirri ce shi yasa ya canza sheka baya son asan ya shigo kasar mamaya sake son yakai wasu gurare, yanda har ya gama abinda yake yabar kasar wani be sani ba duk da abune mawuyaci hakan ta faru.
Barcinsa yasha sosai dan har akayi sallar magariba be sani ba, lokacin daya tashi ana gab da kiran sallar insha'i, a gurguje yayi wanka ya zura sabuwar jallabiyar daya saya cikin kayansa a kasar, a cikin dakin yayi sallar magariba ya fito yabi lifter zuwa masallaci,koda suka idar da sallah be dawo daki ba a nan harabar hotel din ya Zauna da gaske yanayin gurin ya burge shi sosai, coffee yayi order ba'a jima ba wata matashiyar balarabiyar yarinya ta kawo masa coffeen sai yaga kamar 'yar gidansa, nan da nan yaji duk rintsi ita yake muradin gani number dinta ya lalubo ya kira duk ba baya son kira direct yafi son ta Whatsapp.
Suna zaune a parlour ita da zilai tana Shan mutuniyar tata farm fresh, Kira ya shigo a wayarta dake kusa da ita, tayi mamakin ganin code din Dubai har sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka, batayi magana ba Shima baice komai ba, ganin shirun yayi yawa yasa zilan Fadin "naji kinyi shiru koba Kira bane".
Karamin tsaki Zahra tayi "wlh na daga amma naji shiru inaga ko wrong number ne dan code din na Dubai ne ni kuwa waye ze kirani daga Dubai da dai Aunty Nawwara Bata saudiyya da saina dauka ko sunje ne da mijinta tunda business man ne, Bari na kashe wata kilama ba'asan an Kira ba"..
Kafin ta dauke wayar daga kunnen ta taji yayi magana cikin husky voice kada ki kashe min waya, ki bude data zamuyi magana". kit ya kashe Kiran wayar tabi da kallo a zuciyar ta tana Fadin "ikon Allah shine Kuma a Dubai ya illahiy, to Wai wannan Dan talikin waye shi lamarin fa Yana neman Zama abin tsoro fa, yace Yana yiwa kungiyoyin waje aiki ita Kuma a gefe guda wani Abu yake yi irin na Mai bada umarni Kuma bataga yanayi gaban kowa ba sai ita, kamar Ranar da taji yana Kiran zayyan da umarnin daya Bashi akan lallai ya sameshi da safe Kuma Bai karya Umarnin ba"
Wayar ta kalla tana mikiwa zuwa bedroom dinta Saida ta shiga ta duba data idan Babu ta saka tunda Sam Bata taba saka data ba tunda ta Fara amfani da wayar datar data gani tayi bala'in Bata mamaki 4.5 BT ta gani sub din shekara daya ne.
Cikin sofa ta zauna Tana juya wayar Bata bude datar ba, wani Kiran ne ya sake shigowa still dai nashi ne, dagawa tayi tana fadin Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, meya hanaki bude datar danace a bude?"
Shiru tayi ta kasa magana,.
"Wai ko sai nayi ramuwar sayen bakin da banyi bane ake min jan aji irin haka. Dan Allah kimin magana kona samu nutsuwa wlh ji nakeyi Kamar na gudo tun ba'a gama ba duk kin mamaye ko Ina na kasa komai sai tunanin ki, Ni danasanin zuwan ma nakeyi gashi sun rarraba mu wasu suna London mu kuma suka kawo mu hadaddiyar daular larabawa, shine nace Bari na kira na fada Miki Koda abinda kike bukata na taho Miki dashi tunda da kudinki a gurina"
"Kudina kuma? Name nene kuma yaushe na baka".
"Bake Kika bani ba ke aka bawa na manta na Baki Sai a Nan na tuna danaga Kaya irin naku na 'yan Mata".
Ya fada Yana dariya.
"Wai 'yan Mata".
Ta fada tana Dan turo Baki irin bataji dadin Nan ba.
"Au ashefa an wuce wannan stage din ko?"
Ya fada da alamun zolaya.
"Wato kinki bude data sai kin cinye min 'yan canjin da aka saka Mana kinsan dai ni ba iya saka Kati zanyi a kasar Nan ba, pls Dan Allah ki bude datar na ganki kona samu nutsuwa nayi aikin daya kawoni, naso ace kina gefena a wannan gurin Kinga dakina kuwa? da Hali gareni anan zamuyi honey moon irin Wanda naji su Habib suna fada idan ana hira ko Zaki biya ki taho ki sameni?"
Ido ta ware kamar Yana kallonta.
"Na biyoka nayi maka menene?"
"Kiyi min abinda mace take yiwa mijinta ai kin gane?".
"Ya Salam haba Ya Mahmud menene haka kaifa yayana ne".
Wata dariya ce ta kubce Masa "A yaushe na zama Yayanki? Ki gyara zancen niba Yayanki bane, haka kawai ki haramta min abinda Allah ya halasta min idan Zaki Ware ki Dan ina dawowa labarin ze canza salo gara mu fuskanci juna ki tausaya min Kinga Sameer fa ya Zama Daddy madam dinsa ta haihu sunyi min takwara,ai gara muma mu zage dantse ko?"
Dokin haihuwar da aka fada Mata ita ta Hana ta gane inda nasa zancen ya dosa, cikin nuna farin ciki tace "Dan Allah da gaske yaushe Fateehar ta haihu? Masha Allah! Allah ya Raya kace mu sai Kano ko Yaya?".
"Allah bakinki ya kiyayi fada min yayan Nan tsabar kinibibi kawai yau Kika tashi dashi Wai wani Yaya kamar a kauye, kibar 'yan garinmu su Fadi Amma Banda ke wato Ni da yake ba Dan bokon kirki bane ba baza'ace min sweetie ba ko irin su my love ko Dear, saboda almajirin soro ne ni ko?"
"A'a wlh ni ban fada ba, kawai dai Naga abokin Ya Abdul Hakeem ne kai ai kaima yayan ne".
"To anki wayon, Kuma da kike cewa Zaki Kano ganin yaro keda wa zakuje kuma waye ze kaiki Kuma kice Mata wacece ke".
"Address zata turo min Mana, Kuma maganar kaiwa sai Malam Bala direba kaimu nida mujiba wuni daya dai, Kuma nace Mata matar yaron mijinta ce ko ba haka ba?
"Yayi Kam Amma saina dawo ki rakani muje tare anfi saurin ganeki ga kafarki ga tawa, kice na sawo Miki kayan baby na zuwa barka kenan? ko kema a hado Miki kayan naki babyn? tunda da karfina Zan dawo wata kilan ni double shoot ma zanyi tunda Nima Dan biyu ne Ina da twins sister Aishat".
"Twins sister da gaske?"
"Kin taba ganin nayi Miki karya? wlh mu biyu Ammin mu ta haifa first born dinta, mun B'ata ne da ita shiyasa bakisanta ba. Amma nan gaba zaki santa ne Amma fa Zaki Sha surutu Dan sister Aishat parrot ce".
"Amman laifin me tayi maka da zafi haka? Mu namu twins din basa doguwar batawa gaskiya gashi kaima Ammin irin na Ammah tayi mace da namiji".
"Ki Bari kawai labarin da tsawo sai na dawo ai nace Zaki San duk labarina kaf ba abinda Zan boye Miki tunda kin sarkafo min zuciya tun kina free matured dinki Kika Hana duniyata zaman lfy,da farko na dauki irin mutum ya burge ka ne Ashe diban Karan mahaukaciya Kikayi da gudan tsokar kirjina".
Dariya maganarsa ta bata.
"Au dariya ma kike min ko? bayani zakiyi da yarenki, yanda nayi ta fama da garari saina fanshe kayana tas idan Zaki shirya ki shirya".
Cuno Baki tayi kamar tana gabansa ta Fara turza kafa tana fadin "Ni yaushe kaga Ina maka dariya kawai dai... ni banyi maka dariya ba kaifa yayana ne koka manta my big bro....." Ta wani ja cikin salon da ita kanta Bata San tayi ba.
"Ya salam" ya fada a hankali Dan yanda tayi magana har cikin bargonsa.
"Kinaso ki karya min budget ko?"
Ya jefa Mata tambayar.
"Wane irin budget Zan karya maka kana Nan Ina Nan".
"Idan kina min irin haka ai sai kisa na saki layin Dana hau na tattaro ya nawa ya nawa ko komo gida ko ba'a gama ba".
"To me nayi daga magana tom shike Nan sai anjima".
"Wlh Kika kashe min Kira sai kinzo Dubai ko a kafa ne kuma saina yi Miki abinda bazaki manta ba Dan tarihi me kyau Zan kafa Miki ki kashe ki gani, muna hira kina bani nutsuwa Zaki gudu nida ake yashewa Yan canjina Baki tausaya min ba shine Zaki tsere ki barni da Mata masu farauta ta ko? Yanzu haka guda uku tun dazu suke shawagi a gabana suna tunanin irin nasu ne Dan hannu".
Gyara Zama Zahra tayi kirjinta ba dukan tara tara bama uku uku ba.
"Mata kace ko me?"
"Eh Mata Mana bake kina min rowar ganin halalina ba to gashi Nan free sai Wanda yayi maka ka zabi son ranka, ba nace ki bude data na kalli kayana ba Amma kika Kiya Kinga kuwa yanzu saina duba na darje na zaba ta rage min dare, koya kikace my previous?"
Ya Dana Mata kiss ta cikin wayar ya kashe abarsa.
Yana fadin gobe ma idan bace ki bude datar ki qiya, saina kowa Miki kishina ba gaske kafin na kaiki Ina zakiyi da hujja Amma ki shiga yanzu ai Africa ce da sauran gyara.
AUREN HUCE HAUSHI
MAMAN FATEEMAH
PAGE 35.
________Yana katse Kiran ya tashi tsam ya nufi masaukinsa laptop dinsa ya janyo ya shiga aiki sai kusan karfe daya ya kwanta lokaci bayan lokaci sai yayi murmushi idan ya tuno yanda suka rabu da 'yar gidansa yayi zance mata tana neman tikitawa kanta lissafi Wai ita me miji, kamar ta wani san dadin mijin,Saida yayi wanka yayi nafila sannan ya kwanta.
*
Zahra kasake tayi da waya a hannu kamar itace Mahmud din "me yake nufi da zasu rage Masa dare kenan neman Mata yajeyi?"
Take wata zuciyar tace Masa A'a Yana zolayarki ne da manemin matan ne koda karfin tuwo saiya nemi wani Abu a jikinki, kauda wannan tunanin tayi daga zuciyar ta tasan zato zunubi ne, parlour ta koma gurin zilai sukaci gaba da hirarsu sai kusan Sha daya suka shiga ciki.
Washe gari Zahra Bata tashi da wuri ba sai kusan Sha daya, tun cikin dare bata Jin Dadi wata irin murdawa mararta ke Mata, tana samun irin wannan pain din duk karshen wata idan zatayi period Amma wannan yanda yake mata yayi tsanani sosai tun wurin karfe ukun dare ciwon ya tashe ta farka a gigice, inda Allah ya taimaketa Bata sakaci ta rasa maganinta duk rintsi Yana tare da ita, a lokacin ta sha cikin ikon Allah lokaci kalilan ciwon ya lafa ta koma barci da Asuba ma data tashi sallah da sauki sosai sai Kuma yanzu data farka taji Yana neman dawo Mata, da kyar tayi wanka ta sake inner wears ta zura rigar matarial marar nauyi ta koma ta kwanta idan tana wannan yanayin ko turare Bata so sai guda daya kawai body mist ne na strawberry shi ta fesa ta koma ta kwanta Dan abinci dai baya ciyuwa a irin wannan yanayin.
Ganin Sha biyu tayi Zahra Bata fito ba yasa zilai nufar bedroom din nata ta gani anya lafiya kuwa?
Knocking tayi taji Shiru ta qara you taji Shiru Bata kara ba uku ba ta tura kofar a can tsakiyar gadon ta ganota a kudundune, da sauri ta karasa gaban gadon tana ambatar sunan ta "Zahra kafiyarki kuwa har Sha biyu ta gota Baki tashi ba abin Karin ki har ya Fara sanyi?"
Da kyar ta dago ta kalli zilan cikin miryar marar lafiya tace Mata "bana Jin dadi tun cikin dare marata take ciwo".
"Subahaballahi Kuma Kikayi Shiru Baki fada ba idan haka ne bani da amfani Kenan ace tun cikin dare kina fama da ciwo ki kasa fada mini, ina maganin da kike Sha yake na dauko Miki Ni wlh cewa nake tunda ance idan Kikayi aure ze dena, to na dauka kin rabu dashi yanzu, ai haka wannan likitar ta fada Miki zuwan mu na karshen ko?".
Kai Zahra ta gyada Mata kawai alamar Eh Dan ita kadai tasan azabar da takeji.
"Fada min Ina maganin yake na dauko Miki"
A hankali tace mata "Na sha".
"Kin sha Kuma marar Bata Dena ciwon ba?"
"Eh" ta fada tana runtse ido saboda azabar ciwo.
Fita zilai tayi da sauri ta koma dakin da aka sauketa ta lakubo keyboard dinta ta lalubo number Ammah, lokacin tana tare da Abba suna maganar komawa makarantar Imam Kiran zilan ya shigo.
"Abba Bari na daga Kiran Nan Zilai ce naji ko lafiya".
"In Sha Allahu ma lfy".
Abban ya fada.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu"
Ammah ta fada bayan ta daga wayar daga can zilan ta gaishe da Ammah sannan ta Dora da fadin "wlh Ammah jikin Zahra ne ba Dadi tun cikin dare ciwon mararta ya tashi Tasha maganin Kuma a banza shine nace Bari na Kira na fada Miki Koda abinda zakiyi mata tunda kema Aikinki ne ko Kuma a turo Mana malam Bala ya kaimu Asibiti taga likitar ta" .
"Ikon Allah! Yanzu ina zahrar?".
"Tana daki tana faman mukususu kamar me nakuda wlh abin gwanin ban tausayinsa".
"To shike Nan ki dubata za'a San yanda za'a yi ki jira".
Ta kashe wayar ta dubi Abba Wanda Shima itan yake kallo, kafin tayi magana ya rigata.
"Meya samu Uwata naji Kuna magana Bata da lfy ne?"
Ajiyar zuciya Ammah ta sauke "wlh ciwon mararta ne Wai ta tashi tun cikin dare Tasha maganin da take Sha Amma ba wani cigaba shine zilan tace ko Asibiti zasu koma suga likitar da take gani Dan munyi expecting idan tayi aure zasu rabu to Kuma a yanda zilai ta fada min kamarma yafi na baya zafi".
"Ikon Allah! Allah ya saukake Bari a tura musu magaji ya kaisu Asibitin tunda duk sauran basa Nan sai mu bisu daga baya mu kuma, ai hakan yayi ko?".
Kai ta gyada Masa tana kokarin tashi da nufin tafiya, riko hannunta yayi ya mayar da ita inda ta tashi dayan Kuma Yana Kiran wayar magaji.
"Ka dauki mota kaje can hayin banki zaka Kai uwata Asibiti".
Ya kashe Kiran yana kallon Ammar.
"Ina zaki Kuma Kika tashi? Ki kwantar da hankalinki in Sha Allah ba wata damuwa Kika sani ko jika zamuyi kwanan nan"
Ya fada Yana dariya irin tasu ta manya.
Itama Dan murmushi tayi tana fadin Allah yasa".
"Amin yauwa kokefa dauko gyakenki mu bisu wata Kila muje tare tunda gani a gida araha sai nayi aikin bariki tilas ne".
Zilan Ammah ta Kira ta fada mata su shirya ga magaji Nan ze kaisu Asibitin, Suma zasu samesu a can..
Dakin Zahra zilan ta koma yanda ta barta haka ta sameta, kusa da ita zilan ta matsa tana fadin na hado Miki ko ruwan shayi ne kisha Asibiti zamu".
Kai ta girgaiza Mata alamar bazata Sha ba.
"Ki daure ko kadan ne Dan Allah Kinga wata Kila ayi Miki allura gara kici ko kadan ne".
"Cornflakes".
Abinda ta iya fada Kenan ta koma ta kwanta.
Ba laifi tasha cornflakes din da Dan dama, rolling kawai tayi suka nufi parlour zilai na rike da ita. Basu jima ba sukaji dirin mota alamar magajin ya karaso Kenan, zilaice ta bude kofar tun Bai karaso ba direct inda zahrar ke kwance ya nufa akan two seater.
"Sannu Adda ya jikin naki?"
Da kyar ta cira Kai ta dubeshi tana fadin "da sauki".
"Allah ya Kara sauki, kamota muje kada Rana ta karayi yanzu twenty five minutes to one fa".
Zalai ta riketa tana tafiya da kyar suka fito compound din Zayyan yana zaune Yana game a waya tunda bashi da aikinyi a Nan sai zama,ba zato yaga an fito da Zahra haka, da sauri yayi wurgi da wayar Allah ya taimake kan jacket dinsa ta fada da sai dai wata ba ita ba, ya nufo gurinsu Yana tambayar "Lafiya meya faru? Oga kuwa ya sani? sannu" duk a lokaci daya yake jero wadannan tambayoyin da gani a rude yake.
Magaji ne ya nufi inda yake suka Kara gaisawa Yana farin.
"Ba wani abun damuwa bane Bata Jin Dadi ne zamuje Asibiti kada ka damu".
Zilai magajin ya duba "kun fadawa mujinta kada mu tafi babu sanin sa".
"A'a bamu fada Masa ba ai ko daga bayane an fada Masa yanzu dai muje Asibitin wannan ma wani Bata lokacin ne".
Da sauri Zayyan ya bude musu gate suka fita yayin da Zayyan din ya dauko wayarsa Yana Kiran Mahmud.
Ya kirawo shi Amma Sam taqi shiga sai text kawai Zayyan ya tura Masa ya koma ya zauna yana mamakin ogan nasa na neman gurin Zama a wannan Dan gurin shi ko takura ma yaga alama bayayi wata sabuwar rayuwa yake shimfidawa cikin kwanciyar hankali.
Direct A&E magaji ya nufa zilai ce ta taimawa Zahra ta fito daga mota suka shiga ciki shi Kuma magaji ya nufi inda ze karbo file.
Ba jimawa yazo ya kawo file din, bayan duguwar tambayar da wata likita da take on call tayi Mata ta rubuta Mata magunguna da allurai da drip ana cikin saka Mata ruwa su Ammah suka shigo dakin, ma'aikatan da masu jiyyar suna ta gaishe da Abba, gaban gadon Abban yaje ya tsaya sunan ta Abban ya Kira ta bude Ido ta kalli Abba tana kokarin tashi zaune "A'a uwata koma ki kwanta ya jikin naki?"
"Da sauri Abbana, Ina kwana?"
"Lafiya kalau".
Ammah ce ta matso tana fadin "sannu Ashe ciwon cikin ne ya tashi?"
"Eh Ammah wlh har yafi Wanda nakeyi kamar Zan mutu".
Ta fada tana goge hawayen daya zubo Mata.
"A'a uwata Banda kuka ai kin girma".
Abba ya fada Yana dariya. Itama Zahra dan murmushi tayi ta juya Kai kunya ta kamata ta.
Abba Bai bar Asibitin ba Saida aka Maida Zahra Aminity ward.
Tun bayan tafiyar su Zahra Zayyan ya kasa tsaye ya kasa zaune, ya nemi number Mahmud tafi cikin carbi amsa daya balarabiyar da akayi linking da computer ke bashi wadda ba fashimta yake ba, sai dai hasashe kawai number Bata tafiya take fada Masa.
A gida Abba yayi sallar Azzahar bayan an fito ne ya fadawa Baba malam Zahra tana Asibiti Bata Jin Dadi.
Cikin nuna jimami Malam yace "tun yaushe take Asibitin ba'a fada min ba, kuma menene yake damun diyar tawa?".
"Wlh ciwon cikin ne take fama dashi tun cikin dare shine dazu Mai Taya ta Zama ta kita Asma'u ta fada mata, sai nasa magaji ya Kai su Asibitin sai suka Bata gado Wai zasuyi Mata hoton cikin da sauran gwaje-gwaje don su fadada bincike akan ciwon tunda ta jima tana fama da lalurar".
"Ikon Allah! Allah ya Bata lfy yasa kaffara ne, ai da anyi magana tun a bayan da an Nemo Mata taimakon ciwon Amma yanzu ma Bata baci ba, idan anyi binciken an gano wane irin ciwo ne a fada mini akwai magungunan ciwon cikin Mata da yawa a gurina in sha Allah koda tsiron mahaifa ne da sauransu in Sha Allah zasu narke Koda na aikine zebi jinin al'ada ya narke ya zube".
"To in Sha Allah Zan fadawa Asma'u kome Kenan Zan fada maka".
Sun jima a harabar gidan Abban kafin suyi sallama.
Bayan sallar la'asar malam yasa Habib ya tukashi zuwa Asibitin lokacin da sukaje Zahra tana barci sun gaisa da Ammah Malam ya jajanta Mata Habib ma ya jajanta Mata jikin Zahrar Basu dade ba suka tafi.
****
Tun safe da Mahmud ya fita tare da daya daga cikin amuntattun hadimansa na kasar suka fice sun Kai ziyarorin bazata Dan tono wasu laifuka da ake son binnewa, ya dakatar da mutum hudu ya sallami mutane biyu wadanda sukayi sama da fadin maqudan kudade tun bayan rashin sanin inda Mahmud din yake ganin tafiya tayi nisa Kuma baya bibiyar su Sam sai kawai suka tsunduma cikin dukiyar sukayi dumu dumu a ciki, zuwan Sameer ne ya bankado badaqalar wadda tafi karfin shi wadda tasa dole Saida Mai takanas din ya taso, China Kuma issue ne na rufe musu kamfanin laces da materials da akayi Wanda suke zargin ba'a biya kudin harajin kasa ba a tun farkon bude kamfanin, Mahmud yayi kokarin tura duk evidence dinsa ta wibeside nasu Amma sunqi yarda Wanda dole tasa Saida yazo da kansa sannan lamarin ya gyaru.
Sai dare sosai ya dawo masaukinsa yaso ya fita ya dan shaqata beach Amma yayi matukar gajiya sosai Koda yayi wanka coffee kawai yayi order da snacks, tunda garin Allah ya waye Bai samu kanshi ba sai yanzu wayarsa ya dauko ya kunna Dan rabon da ya kunna ta tun jiya, sakonni ne suketa shigowa rututu, amma na Zayyan da Habib su sukafi daukar hankalinsa lfy? Ya tambayi kansa.
Sakon Zayyan ya fara budewa ai baisan lokacin daya Mike tsaye ba duk gajiyar dake tare dashi Nan take tayi nata guri, cikin tashin hankali ya Fara lalubar number din Zayyan cikin kankanin lokaci Kiran ya shiga, Bai saurari gaisuwar da yake Masa ba ya Fara fad'in "wace irin magana kake min haka? Ashe ajiyekan da nayi bashi da anfani,tun safe Amma kaqi fada min halin da yarinyar mutane take ciki sai yanzu da tsohon Daren nan? Kana son ace ban damu da halinda 'yarsu ke ciki ba tunda throughout yau ban kirata ba nayi busy sosai".."sorry oga wallahi tun lokacin nake neman wayar ka Bata shiga kwata kwata shine nayi make text".
"Oh shit! Wlh ban bude wayar ba sai yanzu, yanzu ina zahrar?"
"Wallahi Yallabai bansan inda take ba tunda suka fita ban Kara samun wani information akan komai ba".
Tsaki Mahmud yayi ya datse kiran. Habib ya lalubo ai sakonma bai tsaya dubawa ba ya Kira shi.
"A gaggauce ya amsa sallamar da gaisawar da Habib din yake Masa.
"Wai meke fatuwa ne da Zahra?".
"Wallahi Nima bani da masaniyar takamaimai kawai dai bayan anyi sallah baba Malam yace na kaishi Asibiti ya gano jikinta sai a lokacin na Sami labarin Bata da lafiya ance ciwon ciki ne, lokacin da mukaje tana barci Amma idan an jima zan koma na qara dubota kome kenan Zan fada maka ka kwantar da hankalinka naji Abban su Yana fadin Daman tana fama dashi ne Saida na yau yafi zafi fiye dana bayan gaskiya Dan har hoto da gwaje-gwaje zasuyi Mata inga in Sha Allah ba wani damuwa kome ake ciki Zan sanar da kai Allah ya Bata lafiya".
"Allahumma Amin".
Ya fada jikinsa a mace da duk ya shiga cikin damuwa.
Number zahrar ya Kira tana ta ringing Amma ba'a dauka ba tsaki yayi tunda yaji haka yasan wayar na gida Basu dauka ba.
A karo na farko ya Kira wayar Ammah lokacin wayar na hannun Auta Wanda ya biyo mama da Asabe Asibitin, Dan lokacin da su Ammah suka taho mamar Bata Nan Wai taje duniyar kanwar Babar su Asaben, shine da suka dawo.Abba ke fada Mata Zahra ba lafiya suka taho harda Auta, Autan dake kusa da Mama da wayar Amman a.hannu Yana game na football Mamar dake kusa dashi ta karbi wayar ta mikawa Ammah, batare da Ammah ta duba wayar ba ta daga tana fadin.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
Cikin girmamawa Mahmud ya fara gaishe da Ammah, ita har ga Allah Bata tab'a kawo Mahmud ze Kira ba.
Dan Jim yayi Yana Jin nauyin tambayar ta Zahra, Jin shirun yayi yawa bayan gaisuwar yasa Ammar fadin "wa ake nema ne".
"Ammah nine na kirane naji ya jikin Fateemah? wlh ban sani ba tun safe ban bude wayar ba muna aiki sai yanzu dana bude ake fada min Bata da lafiya Kuna Asibiti, Dan Allah ayi hakuri in Sha Allah hakan bazata fatuwa ba".
Ammah ji tayi kamar ruwa ya cinyeta Ashe sirikinta ne wlh Sam bata Gane shi ba.
Ciki Jin kunya da Kara Ammah tace Masa "ba komai ai jikinta da sauki yanzu ma barci takeyi, ya akayi suka fada maka haba ka kwantar da hankalinka Daman takanyi irin wannan ciwon lokaci lokaci sai dai wannan ne ya Dan matsa Mata sukayi admitting din ta zasu bincike a Kai".
Ammar ta fada tana dan jin nauyinsa.
"To Ammah nagode in Sha Allah da safe Sameer ze shigo zasuje Kano Nan Aminu Kano zasu dubata sosai tunda suna da Gynecologist consultant Ina ga kamar hakan zaifi can suna da kayan aiki na zamani, Zan Kira Abba da Baba Malam muyi maganar, na gode Allah ya Bata lafiya".
"Allahumma Amin, Allah ya bada sa'a yayi Albarka".
Sukayi sallama.
Bayan sunyi sallama Ammah wayar tabi da kallo tana mamakin yanda yake magana da ita tamkar mahaifiyar shi, ya kama sunanta radau.
Mama ce ta kalli Ammah tana fad'in "ko mijin nata be? Naji kina masa bayanin yanayin ciwon nata gashi abin takaicin tun ba'aje ko Ina ba ya tsallake ya bar yarinya da wahala, Allah dai yasa ba juduwa yayi ba ya barta da jangwam yanda aka Fara 'yan ciwace ciwacen Nan ai karshen maganar ace ciki ya bayyana shi Kuma yayi masa wuri tunda Daman tsintacciyar magen ce Bata mage ya sulale yabar gari naji ance harda motarta ya tafi Kinga ribar kafa Kenan".
Duk surutun da Mama keyi akan Zahra ko kallon ta Ammah batayi ba Dan tasan tana fada ne dan ta Bata Mata Rai kawai, Zilai ma Mai aikin su tana tsaye kusa da Zahra tana gyara Mata hannunta da aka saka mata drip, itama ko tari be kunce Mata ba bata tofa tata ba, to me zata ce maganar ba ta ta bace.
Jin ba Wanda ya tofawa Mama ko A a cikin maganarta yasa Asabe cewa.
"Wallahi kuwa mama Allah abin tsoro mutum abin tsoro daman nasan in ba wani ikon Allah ba yaron Nan guduwa zeyi yayi gaba kinsan irinsu Yan hujja ne ba wani Zama zeyi na din-din-din ba a garin Nan, abin gudun ma ya jonawa yarinya ala kakai ya tafi ya barta da 'ya'ya, Kuma ki duba kiga yaro Nan a wanke yake Kar bashi da duhun jahilci ko kauyenci ko qanqani haka kawai ya jonawa yarinya alakakai ya gudu ya barta, idan tafiya ta Mike wata Ranar har azo ana yiwa yaro gorin mahaifi ga babu jinjinan dangi kana ji a sheganta yaro
ko yarinya".
Har Zilai ta baro bakin gadon da zimmar maida martani, sai maganar Zahra suka juyo suka juyo tana kallon Asabe Tana fad'in "lafiya kalau muka rabu, bai Kuma bar garin Nan ba Sai da ya fada min salinsa da iyayensa daga karshe ma mutum ya aje min saboda yana yin rayuwa koda ta Allah ta kasance shine ze kaini har dakin mahaifiyar sa Kinga kuwa ai bani da damuwa a Kan lamarin".

Page 36
______Zahra tana Gama fadawa Asaben abinda ke cikinta ta juya musu baya, ko banza bazata kwana da fushin zuciya ba, dan tasan idan ba ita tayi magana ba Babu abinda Ammah zata ce Dan sau da yawa idan irin haka ta faru ko kallon Mama batayi sai dai ta bawa banza ajiyarta.
Daga Asaben har Mama ba Wanda ya Kara magana,haka Ammar ma da Zilai ba Wanda ko tari ya kuncewa, Auta kuwa wayar mamar ya dauka yaci gaba da sha'aninsa.
Shiru dakin ya dauka kamar mutuwa ta ratsa, sallamar Abdul Hakeem da Abba ta katse shirun cikin nuna tsantsar duniyanci Mama ta tashi da sauri tana fadin "Abba har kun karaso sannu da Zuwa" tana gyara Masa kujerar kusa da gadon.
Sai da ya zauna sannan ya amsa gaisuwar dasu Zilai da Asabe ke Masa suna jajanta masa, suka gaisa da Abdul Hakeem sannan suka fice daga dakin.
Mama ce ta Fara gaishe da Abban kafin Ammah ma ta gaishe shi, sannan Abdul Hakeem ya gaisu dasu Ammar Yana tambayar Mai jikin.
Zahar ce ta juyo tana fadin. "Abbana sannu da Zuwa, ina yini?".
"Yauwa uwata lafiya kalau Alhamdulillahi jiki yayi kyau".
"Eh Abba Daman Kai nake jira kazo kayi musu magana su sallameni mu tafi Nina warke na gaji da Asibitin tunda sunyi min hoton da gwajin da safe mun dawo mu karba bana son kwanan gurin Nan".
Ta fada tana hade rai.
"Eh Nima abinda ya taso ni Kenan maganar tafiyar taku gidan ne Dan yanzu haka daga office din doctor din muke sun bamu referral Zuwa Aminu Kano kamar yanda mijinki ya bukata yace da safe zaku tafi kiga gynecology doctor ayi bincke tunda ance kin jima kina fama da matsalar".
Kafin Ammah tayi magana Mama ta rigata.
"Wane irin Kano Kuma ana zaune lafiya, Wai ciwon har ya Kai haka ne idan Asibitin ake son canzawa aje Bauchi Mana Amma har kano akan ciwon mara kawai".
Dan murmushi Ammah tayi Bata ce komai ba.
Abban ne yace. "Yanzu kina nufin na Kira shi nace masa abinda ya fada baze yuwu ba Kenan ko Kuma Yaya kike son ayi?".
Shiru tayi Bata ce komai ba. Ammah ya kalla "kinyi Shiru ko kema hakan ne nufinki".
Kai ta girgaiza tana fadin "A'a tunda ga yanda ya fada ai shike da iko da matarsa ita da waye zasu tafi kanon?".
"Yace Sameer ne zezo sai zilai ta rakata haka dai ya fada min yanzu da Daren nan"
" To Allah ya kaimu yanzu tafiya zamuyi ke Nan?".
"Eh haka ne, ku kuje Abdul Hakeem ya mayar daku gida kafin ya dawo ruwan ya Kare sai na raka uwata gida" ya fada Yana murmushi.
Sororo Mama tayi Jin Abba da kansa ze maida su Zahra gida.
Badai ta tofa ba Amma a ranta taji ba dadi. Tun kafin Ammah ta dauko hand bag dinta Mama ta fice daga dakin.
******
MAHMUD
Bayan sun gama waya dasu Abba, Sameer ya Kira harta katse ba'a dauka ba sake Kiran yayi tana Fara ringing ta dauka.

Ya fada Yana Zama kusa da Fateeha tana shayar da jaririn su.
Daga can Mahmud ya amsa sallamar ya Dora da fadin "gobe in Allah ya kaimu ka shiga Azare ka taho da madam zataga doctor a Nan kanon na Kira doctor Haseena za'a kawo patient dina".
"Doctor Haseena fa! ita zata duba maka madam din?".
"Eh Mana ko da matsala ne?".
"A'a gani nayi kada taga anyi Mata cin fuska".
"Ba wani damuwa kawai,do what I said".
"Ok. In Sha Allah".
"Kada ka kaisu gidanka a kaisu gidan dake Nan DAWAKI ROAD su zauna har su Gama abinda zasuyi su koma".
"Kana ganin Bai musu girma ba kuwa? dana karkasara aka kaisu yafi kusa da Asibitin ma akan na Nasarawa GRA".
"A Nan nake son ta zauna kake maganar girma har wani babban gida ne ka barta ta saba da Zama a irinsu tun yanzu Kai dai kasan kuma abinda zaka fada Mata, a Kai musu duk abinda ya kamata sai dai na fada ba kayi komai kawai, ka fadawa momi ta Basu house maid daya su hadu da tata sai su ringa aikin tare, kayan sakawa dai nasan ba matsala ka Kira Rukayya ta duba abinda ya kamata sai taje ta sawo, ka Bata card din master bedroom na kasa ta sauka a nan.
"Shike Nan za'ayi yanda kace, amma baka tunanin taga wata shaida data danganceka a gidan?"
"Gaskiya bana tunanin akwai wata alama dake alamtani da gidan".
"Anyway, Allah ya kaimu goben, takwaranka na gaisheka".
"Oh sorry a shafa kansa sai nazo ganinsa, kaina ne ya dauki zafi".
Dan murmushi Sameer ya kashe Kiran Yana kallon Fateeha dake Masa kallon Karin bayani.
"Oga ne, Kinga yanda ya shiga damuwa kuwa nifa Banga abinda oga ya damu dashi ba irin yarinyar Nan idan Kika cire Iyayensa to ba na biyunta, ai ban Gama sarewa da lamarin sa ba saida ya nemi guri ya zauna a dakin kofar gida na almajirai duk da gurin bashi da wani aibu". Baki bude Fateeha ta bi Sameer da kallo "dakin Almajirai fa tace shi ogan da kansa? Tab lamarin Azimun ne, Allah ya bamu ko Rabin yanda tayi sa'ar sace zuciyar jarimi kamarsa Wanda Mata ko kallo basu isheshi ba".
Lakuce Mata kumatu yayi Yana fadin.
"Waya fada miki ba'a Miki so irin Wanda ake mata?" 'yar dariya tayi kawai tasan zance ne inji 'yan magana
*******
Lokacin da Ya Abdul Hakeem ya dawo ruwan ya qare har an cire Mata.
Cikin marairaita Zahra ta kalli Abban da Ya Abdul Hakeem.
"Dan Allah Abba ka tafi Dani gida wlh jiya nasha wahala gashi ba kowa a kusa dani kada na mutu Ni kadai a daki".
Saita saka Masa kuka.
Baki Ya Abdul Hakeem ya bude alamar mamaki.
"Ke! Amma wallahi wannan dai abun kunya ne ki wani kama kuka, kin manta yanzu ba da bane kema fa soon Zaki Zama uwa".
"Ungo Abdul uwata kake fadawa haka a gabana? Fita ka Kirawo zulaihatu ta tattara musu magungunan Nan sai mu tafi can din"..
Dariya yayi ya fice Yana mamakin Abba yanda yake nunawa Zahra soyayya fiye da kowa.
Ba zato ba tsammani Amma taga zilai ta shigo da Kaya a hannu Zahra na biye da ita.
"A'a ku kuma ya haka Naga Abba yace ze rakaki gida sai Kuma gaku a nan?"
Maganar Abban Ammah taji a bakin kofar parloun.
"Ni nace ta taho gida tunda batajin dadi Kuma gida su kadai, gashi Mai gidan nata yace goben zasu wuce kanon gara su kwana a Nan kawai tunda ke dai ba can zaki bita ba gara su tafi a gaban ki".
"Ok, ai ban sani ba nayi tunanin ko gaban kanta tayi nasanta da kulafucin gida ganin ta samu dama zata iya fakewa da haka ta taho kaima Abba kasan halinta"..
D'an Bata fuska tayi "Kai Ammah Dan Allah fa....."
"Kinga uwarta wuce ki kwanta ki huta Keda Baki da lafiya gida dai ai na danki ne, ba Mai hanaki shigowa Zan Kira shi Mahmud din na fada masa ".
"To Abba na gode".
Ta fada tana shigewa cikin Zilai ta bita da ledar magungunan ta.
Abban Bai jima ba ya fice saboda ya baro mutane masu son ganinsa da yawa a kofa.
A bakin kofar bedroom din Ammah suka had'u da zilai tana kokarin fitowa.
"Ku kuma sai koyo gudun hijira bakwa tsoron maganar mutane masu jiran k'iris su karawa miya gishiri?".
"Kayya Ammah idan za'a biyewa maganar mutane ai ko ruwa ruwa ka shiga sunce ka tada k'ura, Kuma ma waye ya ganta Kuma gobe da safe zamu wuce Kano idan Allah ya dawo damu ta wuce dakinta".
Zahra na shiga ta fada toilet Dan babu abinda take bukata sama da wanka du ji take jikinta na warin Asaibi.
Ta jima tana zubawa kanta ruwa kafin ta fito, sabuwar rigar barci ta dauko cikin kayan Ammah ta saka, ta dauko zumbuelen hijabin Ammah ta Fara sallah.
Ammah ce ta shigo dakin lokacin Zahra ta Idar da sallah Tana addu'a, sai da ta shafa sannan ta juyo tana fadin.
"Sannu da dawowa Ammah".
"A'a ke za'a yiwa sannu, ya jikin naki?".
"Da sauki sosai nifa da Abba ze fada Masa bama sai munje wani Kano ba, na warke tunda Daman na Saba duk wata inayi wannan ne kawai ya matsa min sosai".
"Kamar Yaya Abba ya fada Masa shi wa za'a fadawa?".
Ammah ta fada tana kallon zahrar, Baki ta turo tana fadin. "kema Ammah kin sani fa kowa nake nufi".
Dan murmushi tayi kawai.
"Ki Kira ki fada Masa bazakije ba Mana sai Abba ne ze Miki tafinta, tunda yace ga yanda yake so ai haka Zaki hakura kuje a duba ki tunda Naga alama Nan din be kwanta Masa ba, Kuma dazu naji kina maidawa Asabe har da Mama magana tona Hana kada na k'ara Jin makamanciyar magana irinta daga bakinki, ki bar mutum da halinsa kedai ki Zama me kauda Kai kawai ki Kuma rike Addu'a takobin mumuni ce kuma hassada ga Mai rabo taki ce".
"Kiyi hakuri Ammah in Sha Allah bazan Kara tankawa kowa ba,gani nayi basuji kunyar maganar a gabanki ba shi yasa na rama Nima".
Knockig da Sallamar Abdul Hakeem ce ta dakatar da abinda Ammah zata fada. Ammah ce ta amsa sallamar ta bashi uzinin shigowa.
Sannu da dare ya Kara yiwa Ammah sannan ya mikawa Zahra wayarsa dake Hannunsa da alama vedio call yakeyi, Yana fadar "gashi Mahmud zeyi magana dake".
A d'an kaikaice ta kalli gafen da Ammah take kafin ta Mika hannu ta karbi wayar.
Tana karba Ya Abdul Hakeem ya juya, Ammah tabi bayansa tana Masa maganar danyar Madarar da akace ya Aiko da ita da yamma lokacin tana Asibiti.
Saida Zahra ta tabbatar sun fice gaba daya daga dakin sannan ta dubi
Screen din wayar fuskarsa ta gani Yana kallon ta sai taga yayi wani zuru-zuru kamar Wanda yayi ciwo sai hancinsa ya Kara fitowa zuwat dashi hakensa ma ya qaru.
"A hankalin tayi masa sallama tana fadin "Ya M baka da lafiya ne Naga ka rame?".
Bushashshen lebensa ya da tura cikin Bakinsa ya lumshe idanunsa tun lokacin da aka fada Masa Bata da lafiya bai samu peace of mind ba sai yanzu daya ganta. Dan ita ke ciwon Amma shi keda zulumin da ramar Dan tun daga lokacin zuwa yanzu daya ganta Baya Jin yaci wani Abu na kirki a cikinsa.
A hankali ya bude idonsa ya Dora akan tata fuskar dake kallonsa, wani yarrrr taji da suka hada idon.
Cikin tsantsar kasala da jigata ya bude Bakinsa a hankali yace.
"My previous hankalina ya tashi, wallahi gani nakeyi kamar Zan rasaki, ya jikin naki? Kuma tun yaushe ciwon ya kamaki Baki fada min ba? sai Zayyan ne yayi min text Wai an wuce dake Asibiti, kinsan kuwa yanda hankalina ya tashi? Daman kina yin irin hakan ne ko yanzu ya Fara Miki?".
Dan walainiya tayi da idanunta tana fadin " Naji fa sauki Daman inayi kawai wannan ne yayi min tsanani sosai, amman tunda akayi min allurai da drip na warke, kaga ai ba sai munje Asibtin Malam din ba ko?". Wani kallon Baki da lissafi yayi Mata, shi Yana can ya kasa tsugun da ransa ita Kuma tana fada masa wani shirme.
"Zuwa can ba fashi, kuma da izininwa Kika taho gida jinya kin tambayeni Zaki zo gida?" Narai narai tayi da Ido abinda ke tsuma shi kenan yaji Yana neman sakin layi.
"Kai Yaya wallahi na fada maka Zanzo gurin Ammah Kuma ka amince kace nazo koka manta Ranar da zaka tafi?" Ta fada a shagwabe tana zubawa Masa sexy eyes dinta da suka Kara wani hasken wahala data Sha.
"Kawai dai kin min wayo tunda kin fini sanin takan duniya kin fini ilimin boko me zurfi shine zakiyi min education, haka ake cewa ko?".
Shiru tayi Masa.
"Kiyi magana Mana nifa bana son Shiru sai Naga kamar jikin ne"
"Nifa na fada maka na warke sai wani jikon Kuma".
Zaro Ido yayi Yana Mata kallon mamaki.
"Sai wani jikon kamar Yaya? Kenan har kina tunanin Zaki qara fuskantar wani ciwon bayan wannan?".
Kai ta gyada Masa alamar Eh.
"Pls talk ki bude Baki kiyi min bayani as how kike expecting Zaki Kara irin wannan ciwon?".
Sai da ta kauda kanta ta daina kallonsa sannan tace Masa.
"Nifa each and every month sai nayi wannan ciwon".
Ta fada tana Kara juyar da kai.
Cikin damuwa yace. "Pls juyo muyi magana Ina son sanin yanda ciwon yake ne Zan fadawa wani doctor Kinga ai saina San komai kafin na fada Masa yanayin ciwon"
Cikin Jin kunya da nauyinsa tace. "Nifa idan zanyi period ne nake yin ciwon cikin Baya sauki sai anyi min doclofenic injection yake denawa".
"Ok, to idan period din yazo Kuma shike nan baya Kara ciwon?".
Kai ta gyada masa. "Ki cire hijabin Naga yanda Kika rame tunda Nima daba ciwon nayi ba na rame lokaci daya dubi yanda nayi Rama? a lokaci aiki ma zanyi amma na kasa tabuka komai".
Rufe bakinta tayi cikin mamaki tace.
"Dan Allah ka daina haka ka manta a dakin Ammah fa nake idan ta shigo fa ta ganni a yanda nake me kake son na fada Mata?".
"To ya za'ayi Kenan Ranar data ganki da ciki Kuma a jikinki tunda kina kunyar taga muna video call ba hijabi kamar Wanda ta aikata alfasha Allah idan na dawo dole asan abinyi na Fara gajiya gaskiya sai ragaita nake kamar marayan da bashi da uwa, alhalin Allah ya Gama min sutura, koba haka ba?".
Shiru tayi Kamar ruwa ya cinyeta idan ta biye masa kunya ze Bata tunda taga alama Yana neman fitsare idanunsa.
Jin tayi Shiru yasa Shima ya bar zancen ya koma Kan batun tafiyar su Asibiti.
"Goben idan Allah ya kaimu magaji ya kaiki ki dauko wayarki tunda tana gida ki dauko Yan abun bukata tunda sai kun Gama komai kafin ku dawo wata Kila zaku dauki lokaci ba'a Gama gwaje-gwajen da zasuyi Miki ba, itama wannan Matar ta dauki abinda ya Kanata nata saiki fada Mata".
Sun Dade suna wayar har Ammah ta wuce part din Abba Basu Gama ba, sai kusan Sha daya ya hakura sukayi sallama.
Da safe tunda wuri Ammah ta saka magaji yakai Zilai gidan ta karkashe kayan electronics, ta cire duk abinda ake ganin ze iya lalacewa ta Mika gidan maman junior bisa Umarnin Ammah.
Karfe bakwai da rabi Mai kyau su zilan sun koma gidan Ammah da kayan Zahra a jaka set biyar da sauran tarkace na bukatar yau da Kullum.
Sam Mama Bata da labarin kwanan zahrar a gidan Sai da zilai ta shigo da Kaya a hannu magaji Kuma karamar luggage a hannunsa da sauri ta aje bowl din dake hannunta ta nufo Zilai tana fadin "lafiya kuwa daga Ina haka zilai?"
Gaishe ta zilan tayi tana fadin "munje mun daukowa Zahra kayan sawarta tunda Bata koma gidan ba Nan muka kwana daga asibitin gida mukayo". Ikon Allah wallahi ban sani ba, Babu Wanda ya fada min tun daren, Bari na shiga Naga jikin nata".
Suka nufi part din Ammah.
✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
✨✨✨
MAMAN FATEEMAH.
Page 37.
_______Cikin wani irin takun Jin Dadi da karsashi Mama ta shiga parlourn Ammah tana fadin "Ina patient din take? Ashe nan Kuka kwana jikin ne yaqi Dadi bayan mun taho? wlh ban sani ba sai yanzu da naga zilai ta shigo da kaya ta fada min". Ammah ce ta fito faga kitchen din part din ta tana fafin "ko daya sangarta ce kawai Wai kada ciwon ya tashi cikin dare, kamar an fada Mata a Nan din ciwon baze tashi ba".
Dan murmushi Mama tayi "ai kinsan yanda take da son gida ai inaga idan sun dawo ma saita zauna a nan din tunda ba'a San ranar da mijin nata ze dawo ba gara tana kusa tunda Naga alama ba wani iya riqeta zeyi ba da farawa da iyawa, Allah ma yasa Bata da juna biyu ai da abun yayi yawa ga zawarci ga goyo".Dan Jim Ammah tayi Dan da gaske maganar ta doketa wane irin mugun fata ne haka bako kawaici gurin fadin maganar.
"Allah ya rufa asiri, duk abinda Allah ya tsarawa zahra Zan karba da hannu biyu ba komai, idan Allah ya hukunta Mata rabuwa dashi bani da tsimi bani da dabara,kinsan shi dare ga Mai rabo hantsi ne, fatan da muke dai Allah ya rabata da wannan ciwon me bibiko".
Zahrar ce ta fito Shar da ita cikin doguwar Rigar material Baki da pink din flowers manya ta saka gyale medium a kafadarta tana baza kanshi kamar anyi barin turare a jikinta a hankali ta shigo cikin takunta na rausaya tana amsa wayar sajida wadda ta kirata tana dubata da jiki.
"Ke kuma waya fada miki bani da lafiya?" Zahra ta fada tana Zama kusa Auta da yake breakfast ze tafi school.
Tunda zahrar ta shigo idanun mama ke bin zahrar da kallo.
Wayar taci gaba da amsawa tana fadin "jikin fa da sauki kawai shine yake ta bankama abun kema fa kinsan ciwon tun Mana kazaure shi ne fa yaketa faman tsallen tsinka tsimma akansa".
Ta fada tana dariya kasa kasa.
"Amma Baki da kirki mijin naki ne me tsallen tsinka tsimman? Saura kadan nayi Miki tawaye bestie irin wannan cin fuska haka?".
"Sai anjima Zan kira".
Ta fada a hankali duk da Daman idan ba Kuna kusa sisai ba bazakaji abinda take fada ba.
Sai da ta kashe wayar sannan da dubi inda Mama take zaune ta Dan rankwafa kada daga zaune tace
"Mama Ina kwana?"
Ba yabo ba fallasa ta amsa tana fadin "ya jikin duk da dai ba alamar ciwo a tare dake, Banda son yawo Ni banga abin tafiya har Kano ba akan ciwon mara na Mata".
Badan Ammah ta jawa Zahra layi ba da Babu abinda ze Hana ta bawa Mama amsar maganarta ba to ba Hali sai zilai ce ta magantu "To Mama tunda yace taje a duba lafiyar ta ai dole taje tunda da gaske Yana cikin damuwa".
Dan tabe Baki tayi tana fadin. "Ai kam sai kuje nasan dai rabe-rabe zakuyi a gidan uban gidan nasa".
Duk abinda ake Ammah najin su amma ko kallon su batayi ba, haka zilan ma Bata Kara fadin komai ba ta fice daga parlourn.
Hamza ne ya leko parlourn ya gaishe da Ammah tunda sun gaisa da Mama, Zahra ta gaishe shi Ya amsa yana fadin "ya jikin naki? Ku fito inji Abba zaku wuce kanon".
Ta amsa da "to Yaya, jikin da sauki nafa ware wlh, kawai dai".
"To Allah ya Kara lafiya".
Ya juya ya koma.
Zilai ce ta shigo da sauri tana "Ammah zamu tafi ayi Mana addu'a".
Dan murmushi tayi "Allah ya tsare ya bada lafiya".
"Allahumma Amin".
Gurin Ammah Zahra ta karaso a hankali ta rungumeta kamar zatayi kuka, zamu tafi Ammah saina Kira idan munje kada ki Kira Aunty Hasana tunda Bata Dade da tafiya ba, Allah yasa ma gobe zamu juyo gida wallahi bana son zuwa nifa".
Bayan ta Ammah ta Dan shafa tana fadin "kuje ba komai In Sha Allah za'a dace a gano menene matsalar tunda suna da Qualified Gynecologist doctors, Allah ya tsare hanya".
Kai ta gyadawa Ammar ta saketa ta koma ta dauki hand bag dinta sai lokacin tayiwa Mama kallon Ido cikin Ido.
Zamu tafi Mama sai Allah ya dawo damu". Tayi gaba tana rike da hannun Musaddiq sukayi waje, Bata bi takan abinda mamar ke fada ba, da sauri mamar ta rufa musu baya ko sallama batayiwa Ammah ba, wani lokacin Ammah tana mamakin yanda Mama ke nuna tsana da hassada akan Zahra idan abin ya taso Mata Bata iya hiding dinsa dole saita nuna an gane.
"Allah ya raba na gari da mugu li'ilafi quash".
Ammar ta fada tana komawa kitchen inda take kokarin hadawa Abba break fast.
Zahra na rike da hannun Musaddiq suka fito compound din.
Mama na fitowa sukayi kicibus da sahura da sauri ta kyara Mata tabi Zahra a baya, ta nufi part dinta ita Kuma sahurar tabi Zahra da sauri.
Ganin Abba a harabar gidan ya hana sahura garasowa gurin zahrar dole taci burki a gefen second gate din. Zahra gurin Abban ta nufa Yana ganota ya Fara fadar "Masha Allah! Uwata jikin yayi kyau, ya kika kwana?".
"Da sauki Abba, Ina kwana?"
Ta fada tana tsugunnawa kusa dashi.
"Lafiya kalau Aina leka dana dawo daga masallaci akace Baki tashi ba".
"Eh Ammah ta fada min, nifa Abba dama hakuri akayi da zuwan Nan nafa warke ba inda yake min ciwo yanzu".
Sameer ne ya shigo da alama daga wurin Baba Malam yake Dan harda Habib suka shigo, gurin Abba suka nufo Habib ya gaishe da Abban sannan Zahra ta gaishe su shida Sameer din suka dubata, mikewa tayi suka nufi inda Malam Bala direba yake jiran Auta su tafi makaranta, sai ya shiga ya zauna sannan Zahra ta bashi 1k, tace ga kudin chocolate Nan idan ka dawo Ammah zata baka wasu na saka Aunty zulai ta debo maka".
"Nagode Aunty Allah ya sauwaqe Miki Zan Miki addu'a idan nayi sallah, malam Bala ne ya karaso suka gaisa da Zahra ya tada motar suka fice Musaddiq Yana daga Mata hannu.
Ta juyo kenan ta hango zilai da sahura sun nufi gurin su Abba suna gaishe su sannan Habib ya karbi key din motar suka zuba kayan dake hannun su.
Sallama su Sameer sukayiwa Abban suka nufi gurin motar, zahrar ce ta dawo gurin Abban tana fadin "zamu tafi Abbana ayi Mana addu'a"
"Allah ya tsare hanya uwata ya Baki lafiya yasa daga wannan zuwa Asibitin a samu warakar wannan ciwon".
"Amin Abba nagode mun tafi sai nu dawo" ta juya ta nufi motar.
Har gurin motar Abban ya karaso Yana musu Addu'a da fatan sauka lafiya.
A hankali Sameer yayi kwana ya nufi gate din fita Abban Yana daga musu hannu, haka ma Ya Hamza shima Saida yaga ficewarsu sannan ya koma side dinsu, sunzo fita Sameer ya dunkulo kudi yaba Mai gadi cikin murna ya Fara jero Masa Addu'oi da fatan Alkhairi har yayi Dan nisa suna jiyo muryarsa.
A wurin gidan sarki Habib ya sauka, sukayi sallama da Sameer yayiwa zahra sallama da fatan samun lafiya Mai dorewa, yayi gaba zuwa ina zaya.
Sun mika a tafiyar sosai Sameer ya Dan juyo kadan Yana fadin.
"Madam tun jiya nake Kiran wayar ki ba'a dauka".
Dan kwantar da Kai tayi jikin seat din tana fadin. "Wallahi rabona da wayar tun jiya da safe a gida na barta lokacin Ina Zan iya tunawa da wata waya Ina tunanin ko ranar karshen ce tazo, sai dazu da Aunty zilai ta dauko min nabi wasu missed calls din kafin na Kira taka number din ya Hamza ya shigo yace kazo mu fito, na gode kwarai da kulawar ka Allah ya Raya Mana babyn mu". Ta fada tana Dan murmushi.
Shima murmushin yayi tana fadar "wato baby kadai Zaki tambaya Banda mamansa wato saboda sunan mijinki ne son Kai ko?.
Hannunta ta saka ta rufe fuskarta.
Dariya zilai tayi tana fadin tuba muke Yallabai ai baza'a Fara haka ba, gani tayi baby shine bako".
"Kin Kare ta dai kawai Aunty".
Tafiyar awa biyu da minti Arba'in da biyar suka shigo Kano.
Suna area mariri Sameer ya lalubo Rukayya.
"Da fatan komai yayi yanda akeso ya zama ready ko?"
Sauraren amsar da take fada Masa yake, kafin yace "ok mun shigo ki Kira mommy tasa salmanu ya kawo iya Rahane yanzu".
Bai jira abinda zata fada ba ya kashe Kiran.
Wani Kiran ne ya shigo masa, shima dai yana da alaqa da zuwan nasu duk dai zahrar naji tayi mamakin Yanda Sameer yake magana cikin ladabi irin haka to shida waye yake wayar Wanda ya jibinci lamarinta haka? Wata qila inda sukeyiwa aiki ne suka dauki nauyin zawa Asibitin nata, haka ta ringa sakawa da kwancewa, shi Kuma Sameer shiga can kurda can har suka shigo Nasarawa G.R.A sultan road.
Tunda suka shigo Kano zilai ke baza idanu, Tana bawa idonta abinci, ita fa zilai duka zuwanta Kano baifi sau uku ba,
Shima Ammah take yiwa rakiya idan wani uzurin ze kawota.
Gidaje ne na garari take gani da ban mamaki yinsu ake kamar baza'a mutu a barsu ba, tana ganin gidajen da take mu'amala dasu sun Kai sun kawo Amma yanzu sai take ganin tamkar akurki ne kan wadan da take gani Bata gara sarewa ba Saida taga gidan da Sameer ya dosa, take hantar cikinta ta kada, innalilllahi takeyi a zuciyar ta, Nan da nan jibi ya Fara karyo Mata Daman tana mamakin gidan da zahrar ke ciki na can Azaren to kuma saiga wani, duk da Bata San mamallakinsa ba, wata Kila karar kwanace tasa ta biyo zahrar irin wannan gidan da sai ayi dambun Naman ka na waje baiji ba.
Kofar wani mahaukacin gate ya tsaya yayi horn sau biyu aka bude suka shige.
Ba zilan ba ita kanta Zahra ta sare da lamarin gidan Dan tasan yes Sameer masu kudi ne ko kungiyoyin su suna sakin kudaden aiki kamar ba gobe amma Bata taba tunanin ya mallaki irin wannan mahaukacin gidan ba. Dan da gani ba tambaya mamallakinsa yaci ya tada Kai. A kofar parlourn ginin da yafi ko wane tsaruwa da kyawun gani ya tsaya yana hamdala ga Allah s.w.a.
Wata matashiyar buduruwa ce ta fito daga parlourn cikin rigar atamfa fitted tana takun yanga da gayu ta nufo motar tana fadin "sannunku da zuwa, Amma wallahi I am very surprised Dana ganka yanzu".
"Rukayya Kenan kin dauka Ina Miki Wasa ne idan Kinga banyi driving ba nine bansa kaina ba".
Dariya tayi "ai na yarda Kuma nasan wannan assignment ne me mahimmanci a gurinka".
Fitowa yayi Yana fadin "yauwa sannunki da kokari, kuma haka ake tarar Baki a garin ku? kinzo kinata surutu kin tare Mata kofar fita".
"Oh! Sorry" ta fada tana budewa Zahra kofa duk da Bata ganinta sosai saboda tintac glass ne a motar.
Dan matsawa tayi ta bude Mata kofar, kanshin da yayi Mata sallama ne yaja hankalin Rukayya ta kalli kofar lokacin Zahra ta sako kafarta daya Kan fuskar zahrar idanun Rukayya suka sauka.
"Kam bala'i"
Rukayyar ta fada a zuciyar ta "wacece wannan din Kuma? Tun jiya lokacin da ya Sameer ya aiketa shopping na abubuwan amfanin gida da kayan Mata ready made take Masa kwawar ya fada Mata na waye? sai dai yace Mata wata ce Zaki ganta yarinya ce ko sa'ar ki Bata kai ba yayanta ne ya hada su ya kawota Asibiti, sai oga yace a sauketa a gidansa har su gama da asibitin.
Rasa wane yare Rukayya zatayi Mata tayi saboda tasan wannan ko zo da hausa Bata sani ba duk da shigarta ta hausawa ce. Aunty zulai ce tayi magana lokacin data fito "haba yallabai Ina laifinta gashi ta fito ta tarbe mu".
Dan murmushi zahra tayi lokacin data fito daga motar gaba daya ta kalli Rukayyar tana wani smile Mai daukar hankali tana fadin "sannu Aunty mun gode" ta fada tana mika Mata hannu, ba Karamin mamaki Rukayya tayi ba Jin zahrar na zazzaga tsantsar hausa bako gargada. Bangaren Sameer zahrar ta kalla tana fadin "Haba oga Ina laifin Aunty na ko wannan fitowar da tayi ai shima Yana cikin entertaining ne mun gode".
Ta fada lokacin data rike hannun Rukayyar.
Sai lokacin zilai ta Dan samu Peace of mind ganin Rukayya tasan dai da alama gidan bana macuta bane duk da ba tana zargin Sameer bane,yau din ce wata iri baka saurin amincewa da mutane.
"Sannunku da hanya".
Rukayyar ta fada tana kallon Zahra, yayin da Sameer ya shiga motar ya nufi parking lot ya ajeta.
"Yau Aunty mun gode"
Zulai kuwa sai kalle kalle take tana jinjina girman gidan Dan wasu gine - gine take hangowa na Alfarma ga shuke-shuke Nan sai wani sanyin kamshi ke tashi a gidan ko Ina Kuma tas ba alamar datti a cikin, dukiya dai Mai sunan dukiya an kasheta a gidan Nan.
Ita tunda uwarta ta kawo ta duniya Bata taba shiga irinsa ba, sai yau da dalilin uwar dakinta Zahra ya kawo ta.
Maganar Rukayya ce ta dawo da ita cikin hankalin ta.
"Bismillah mu shiga daga ciki".
Rukayyar ta fada tana nufar kofar parlourn numbers ta daddanna ta bude musu kofa ita dai zilai yau jinta take kamar ba cikin kasar take ba.
Lokacin da suka shiga parlourn ba zilai ba kifin rijiya ita kanta zahrar sai da wani shock ya shigeta na wucin gadi, badan Zahra tana fita waje ba Kuma kakanninta masu dashi ne kuma tayi zaman syprus taga guraren hutawa da yawa da gidajen Alfarma da Babu abinda ze Hana ta zabga kauyanci, dan Babu karya naira tayi kuka a cikin parlourn Nan tamkar fadar sarauniyar ingila komai na ciki off-white ne da sirkin ash colour ba tarkace da yawa sai dai an kawata shi da wasu irin cutains masu azabar kyau dan shi kadai abin kallo ne, sai fremes masu kyau da tsari da wasu irin flowers, sai wani special kamshi daya hadu da sanyin A/C ya bada yanayi Mai dadi, sai plasma kusan bango guda.
Zilai dai 'yar kauye sak ta koma ko Zama kasayi tayi sai da Rukayya ta juyo tace Mata Bismillah ki zauna Mana ku Sha ruwa".
Ta fada tana yin gaba ta nufi wani steps gurin dining table ta shige wata kwana.
Zahra zilai ta kalla "Wai Ina ne Nan din Kuma gidan na wanene nifa duk a rude nake na kasa samun nutsuwa ko kadan, irin wannan gidan ai sai sarki ko wani gagarimin Mai kudi".
Da watsa hannu Zahra tayi.
"Toni Ina nasan amsar tambayar taki, Nima duk daya muke dake bansan komai ba, nasan dai yace zamu zauna a Nasarawa GRA kawai ba wani Karin bayani da yayi min". Rukayyar ce ta shigo dauke da babban tray da robobin farmfresh dasu ruwa da Shani na gwangwani, sai fruit fresh ones.
"Bismillah kusha ruwan sai muje ku huta sai kuci abinci".
Sannu Zahra tayi Mata, itama zilan tayi mata, Sameer ne ya shigo da wani matashin saurayi da luggage din Zahra da 'yar madaidaiciyar jakar zilai a hannunsa ya gaishe su ya aje ya koma.
Rukayya ce nufo inda Sameer din yake tana fadin "Ya Sameer Dan Allah ka jirani Zan bada sako gurin mommy ka taho min dashi"
"Kefa Ruky kina da damuwa kiyi Abu Mai mahimmanci sai ki tsaya kina Wasa".
"Allah Yaya da gaske nakeyi ka taimaka min".
"Ok"
Gurin su Zahra ya duba Yana fadin "sannunku madam kun sha hanya ki huta zuwa dare zamu fita Asibitin doctor tace mu hadu da ita a Nan Asibitin Nasarawa zataga patient yau a can da dare saita dubaki idan yaso sai mu hadu da safe a malam din".
"To ba damuwa in Sha Allah Zan shirya da wuri nagode".
Ya juya ya fice daga parlourn.
Zahra tayi mamakin ganin favourite drinks dinta da aka kawo, more especially farm fresh Amma Bata kawo komai ba ta dauki abin arashi ne kawai.
Bayan Sameer Rukayyar tabi suka fice daga parlourn.
Saida suka sauka daga steps din gurin sannan Rukayyar ta dubi Sameer tana fadin "big bro Dan Allah wacece wannan din? Meye matsayinta a gurin Ya Mahmud nasan wlh ba banza ba yace a bude Mata wannan apartment din nasa".
Tsaki Sameer yayi "na dauka want important Abu Zaki fada min Ashe tsabar gulma ce a cikinki, ba abinda yayi Miki zafi a lamarin yarinyar Nan yanda Kika ganta haka Nima na ganta bansan ko wacece dinsa ba tunda baiso in sani ba, Dan haka kada rawar kanki tasa ki fadawa Dr Haseena wani Abu Koda zata tambayeki kice Baki San komai ba".
Tunda ya Fara magana Rukayya tayi zuru tana kallonsa yanda ya kiciccife yasa tayi masa alamar (?) Tasan there's something behind.
Amma fadan dayafi karfinka sai ka mayar dashi Wasa.
Dan jinjina Kai tayi tana fadin shake Nan Bari na koma kada suga an barsu su kadai".
Ta juya ta koma Zuciyar ta fall da tambayoyin da Babu Mai Bata amsarsu.
Lokacin da ta shigo sun gama suna Dan hira.
Cikin bada uzuri Rukayyar tace "kuyi hakuri na barku ku kadai Bari na Fara rakaki naki masaukin kafin na dawo na rakaki Aunty ta fada tana kallon zulai".
"Babu komai muje na shigar Mata da jakar kayanta.
Rukayyar ce a gaba su Zahra suna bayanta, saida suka wuce parlour uku kowanne Yana wane na Bata zulai da abin harya daina Bata tsoro tunda taga abin bana karewa bane, wani corridor ta nufa suna biye da ita wasu steps suka gangara suka shiga, wani parlourn suka shiga Mai azabar kyau fiye Dana baya, kofofi biyu ne a cikin wani arc suna kallo juna, kofar hannun dama Rukayyar ta nufa saka Kati ta bude kofar tana tana fadin Bismillah". Tana murmushi.
"Mu shiga Mana". Zahra ta fada.
"A'a iyakata Nan, dakin na manya ne bani fa hurumin shiga ciki".
Jin haka yasa zilai Jan burki, itama jagabar da tasan ciki da Bai na gidan tana fadin haka inaga ita 'yar karere.
Aje luggage din tayi tana fadin. "A fito lafiya uwar dakina".
Suka juya Rukayyar na fadin Bari muje sai kin fito.
"Ok, nagode.
Zahrar ta fada tana janye da luggage din ta murda handle din da siririyar sallama a bakinta. Bata iya karawa ba taja ta tsaya tana waro idanu waje na mamakin abinda idonta yayi arba dashi...
AUREN HUCE HAUSHi.
MAMAN FATEEMAH.
Page 38.
A hankali ta ringa tafiya kamar wadda ke tsoron kada a kamata, abinda ta gani ne ya Bata matukar mamaki wannan bed room din tamkar an dauko na can Azare na Mahmud an aje a Nan, hatta da curtains din windows din iri daya ne ba banbanci, Abu daya wannan yafi wancen shine girma wannan yafi balance akan wancan, Amma tamkar an dauko shi an aje, ita abin da farko tsoro ya bata hatta kamshin turarensa taji a dakin jiki ba kwari ta dosana ta zauna a gefen bed din tana Kara karewa dakin kallo tabbas a gizo idanunta ke Mata ba abinda ta gani haka yake, bata Kara tabbar da kamshin Mahmud takeji ba Saida ta zauna kamar lokacin ya saka ya fita daga dakin.
Dan dam tayi Jin ta Fadi sunan Mahmud fatsal sai taji wani bambarakwai a bakinta duk sai wani irin Abu ya darsu a zuciyar ta.
A shagwabe kamar tana magana da wani ta Fara fadin "to me ma zance masa ne? Kuma Wai Nan din dakin waye da suke kamanceceniya da nasa har kanshin ba banbanci?.
Ba Mai Bata amsar tambayar Dan haka ta Dan zamo kadan tana janyo luggage dinta tana fito da abinda ke ciki,wanka take sonyi duk jinta take a takure indai tana period sai a hankali sam Bata da sakewa ko misqalazarratin, Banda dole Babu abinda ze sakata barin gida a irin wannan condition din.
Luggage dinta ta janyo a hankali ta Fara fito da abinda ke ciki, na Kan mirror ta Fara diba ta nufi inda yake lokacin data karasa ba karamin mamaki tayi ba ganin irin kayan shafar da take amfani dasu har da wasu daga cikin irin turarukanta ta gani Banda su freshner na fesawa.
Bata fasa aje na hannunta ba, gurin kayan ta dawo ta bude cloth set din data gani tana budewa tayi arba da kayan Mata Babu abinda Babu, harsu shoes da bags, dasu inner wears.
Mayarwa tayi ta rufe ta dawo da kayan a hannu ta mayar inda ta dauko su.
Wanka ta shiga Nan ma wata duniya ce aka hada, ta jima tana gasa jikinta Dan idan Tana irin wannan condition din Bata kaunar abinda ze hadata da ruwan sanyi ko kadan.
Bata wani Bata lokaci ba gurin shiryawar ta saka doguwar Rigar atamfa glitter purple, Rigar tayi Mata das a jiki mayafi light brown ta saka touching din jikin atamfar sai takalma suma light brown din plat, haka nan taji tana son saka turarensa Mai sanyin kamshin Nan dauka tayi ta fesa ta nufi hanyar ficewa daga dakin.
Saida ta fito yanzu ta karewa wannan parlourn kallo yafi duk Wanda ta gani a baya tsaruwa kunjerun dake ciki ko rantsuwa tayi bazatayi kaffara ba Bata taba ganin irinsu ba duk kuwa da gidajen Alfarma data shiga ta bangaren Ummee.
A hankali ta ratsa ta wuce tabi hanyar da suka biyo suka shigo.
Ba kowa a parlourn lokacin data shiga sai dai tana jiyo Dan Karan plates haka kamar ana wanke-wanke.
Zama tayi taga ta inda wani ze gitta tunda ita dai ba sanin Kan gidan tayi ba. Wata Mata taga ta fito daga wajen dining ta wata kofa da manya food warmers a hannunta,ta aje a kan table din har zata juya ko jijinta ne ya Bata da mutum a gurin yasa ta juyo tana duban cikin parlourn, Ido suka hada da Zahra da sauri matar da gangaro daga steps din dining din tana fadin "Masha Allah, ko surukar tamu ce ta fito?".
Ta fada tana nufo Zahra dake zauna tana murmushi, itama iya Rahanen murmushi take har ta karaso gurin zahrar.
"Sannu Mama Ina yini"
Zahrar ta fada.
"Yauwa sannu yarinya ya kukazo?"
"Lafiya kalau Alhamdulillahi".
"To Masha Allah, sunana iya Rahane nice mommy ta turo na zauna dake kafin ki gama abinda ya kawoki".
Ta fada tana Dan tsugunnawa a gefen zahrar.
"To Mama na gode, Amma Dan Allah ki daina tsuguna mini kinyi jika Dani idan Ni ban Baki irin wannan girman ba to kema bai kamata ki bani ba, Dan Allah ki tashi"..
"A'a 'yata Allah ne ya Baki Dan na tsuguna Miki Babu laifi".
Kafin zahrar ta samu zarafin Mai da Mata amsa Rukayya ta fito daga inda iya Rahane ta fito ganinta da Zahra yasa Rukayyar ta karaso gurin su tana fadin "har kinyi me?"
"Harna fito Ina Zan iya Zama a wancan lungun Ni kadai kamar mayya ai Naga kokarin matar gidan nan data iya zama a cikinsa, Daman jiranki nake dakin da Kika rakani na matar gidan ne gara ki hadani da zilai mu zauna tunda duka kwana nawa zamuyi mu tafi kada a samu matsala kinsan halinmu Mata da zargi naje na manta wani Abu daya danganci namu na Mata a samu rashin yarda a tsakanin masu gidan Dan na bude cloth set Zan zaka kayana saina tarar da kayanta a ciki Kinga ai Bai kamata na shigar Mata dakin ba ya Zama Bata da sirri kenan".
"Wannan gaskiya ne ranki shi Dade kinyi tunani me kyau a kam".
Iya Rahane ta fada.
Zama Rukayyar tayi gefen zahrar tana fadin ai gidan Mai shi ko auren fari baiyi ba, kayan da kika gani duk nakine bana kowa bane Dan ya Sameer ya bani kudi nayo siyayyar jiya Dan a Nan na yini nida su suhaila Dan furnitures din dakin ma jiya aka sakasu Ina ga ba wata macen data taba zama a cikinsa Banda Mai gidan to kece ta biyu da Kika zauna, bama a dakin yace a sauke kiba dayan yace sai Yaya Sameer yace na Baki wannan ya wadatar kawai.
"Iya aje a fito da sauran abincin sai muje kiyi lunch din tun, shigarki ciki ya Sameer ke kirana Wai kinci abincin Baki da lafiya na tabbar kin Sha magani ni har mamakinsa nakeyi Bai dauki lamarinki da Wasa ba gaskiya".
Iya Rahane ce tace "Haba Rukayya yaushe Alhaji karami Zeyi wasa da lamarin iyalin Mahmud, Nima da Mommy ta kirani Saida ta Kira shi ta fada Masa nice zanzo ya amince kafin Nazo, ya jaddad min na kular Masa da ita yanda ya kamata, Kinga kuwa ai baiyi laifi ba ko?".
Kai kawai Rukayyar ta iya gyadawa mamakin duniyar Nan ya gama kasheta a zaune "matar Mahmud? Haba biri yayi Kama da mutum, tasan ba banza ba ya Sameer keta rawar kafa ya kasa tsaye ya kasa zaune akan lamarin, Kuma da alama itama yarinyar ninketa sukayi ta bai-bai Dan da alama batasan waye hakikanin mijin nata ba, gaskiya ta tayata murna dan ta zama Mai sa'a duk da shima Saida ya dauko diamond a cikin zinarai, Dan Daman wannan irin matansu ne.
Gurin dining din Rukayya tayi Mata jagora suka nufa tana fadin "kice min matar big bro ce Amma nayi mamaki gaskiya sun lullubeni Amma ki Bari kawai bazance naji ba Naga iya gudun ruwan ya Sameer sai wani cewa yake kanwar abokinsa ce".
Ita da zahra Dan murmushi take tunda ba gane Kan zancen tayi ba.
Abinci ne yakai kala biyar Rukayya ce ta bubbude wa zahra tana fadin "Auntyn mu ki zabi Wanda kike so a zuba miki".
"Kaji Aunty ni basai kin zuba min ba haba dadin sai yayi min yawa hakan ma na gode, ina Aunty zilai tazo muyi lunch din".
"A'a nan naki ne ke kadai na Kai Mata nata dakin ta tun dazu".
********
Knocking din kofar akeyi a tana zaune ta Sha uban gayu kamar wadda zata wuri dinner ta biki sai kanshi ke fita a jikinta Mai Dadi tana rike da wayar ta tana addu'oin yaumiyya na cikin du'aul mustajaba.
Umarnin shigowa ta bayar tana kallon kofar, Basira ce yarinyar dake aikin shara da goge-goge a bangaren ta, tsugunnawa tayi tana fadin "barka da Asuba Ammi".
"Barka kadai Basira har kin fito da wuri haka, lafiya dai ko?"
"Lafiya kalau Ammi Daman Hajiya Inna ce tazo ita da Abie".
Littafin ta aje akan bed side tana fadin "Hajiya Inna kuma"?"
Kai Basira ta gyada alamar eh.
"Kije gani Nan fitowa in Sha Allah".
Ta nufi clothset dinta ta dauko gyale mahadin shaddar ta fito daga bedroom din.
A hankali take saukowa daga stairs din shar da ita tun kafin ta karasa saukowa kamshinta yayi musu sallama, cikin takunta na nutsatstsiyar mace Mai aji da yarda da kanta ta da tarin ilimi Hadi da wayewa, sallama tayi musu tana nufar gurin Hajiya Inna ko inda general yake Bata kalla ba.
Kusa da Hajiyar ta zauna lokacin da take amsa sallamar tata.
"Ina kwana Hajiya".
Cikin nuna kauna da kulawa Hajiyar ta amsa tana tambayar ta Ina su uratu Ammin tace Basu tashi ba tunda yau ba zuwa school.
Ammin ta Dan juya bata yarda sun hada Ido dashi ba tace Masa. "Barka da Asuba".
Shiru yayi Mata kamar beji abinda ta fada ba, itama Bata kara bi takansa ba, Hajiyar na ankare dasu.
Ammin ce tace "Hajiya me yasa Kika fito yanzu da sassafe idan kina son ganina basai ki turo nazo ba basai kin taso da kanki ba Dan Allah kiyi min wannan alfarmar kada wani Abu ya taso nason ganina ki taso ki taho saboda ni".
"To in Sha Allah hakan baze Kara fatuwa ba nima ba zuwan kaina bane jiya Muhammadu ya sameni da dare yake fada min wata maganar da banji dadin ta ba, shin da gaske ne bakije inda yake ba tunda Kika dawo? Idan ya Kira wayarki bakya dauka, yazo da kansa yafi sau biyar kin rufe kofa?".
Shiru Ammi tayi shi Kuma general kamar ya rungumeta a gaban Hajiyar haka yakeji Dan gani yayi ta wani Kara yin fresh da ita bazaka taba cewa ita ta haifi wadannan yaran ba, ta koma masa danya sharab da ita ga uwa uba ko runhu ka rike Kan sakko bazaka taba ganinta a hargitse ba ta San kanta sosai yanda ya kamata, da kyar ya iya saita kansa a gaban Hajiyar.
"Kinyi Shiru zainab kenan abinda ya fada gaskiya ne?"
Sadda Kai ta Karayi kasa sai Jin shashshekar ta sukayi.
"Subahaballahi haba zainab ko lokacin da lamuran suka jagule Baki zubar da hawaye ba sai yanzu, kiyi hakuri na fada Miki duk Wanda za'ace yayi hakuri to an zalunce shi ki yafewa mijinki wallahi rashin samun kulawar ki tasa ya runtse ido ya iya fada min abinda Bai kamata na sani ba, na roqi arziki ki dubi girman Allah da manzonsa ki rungumi mijinki da 'ya'yan ki kiyi boyayyiyar aure yanda Kika saba".
Sai da tayi kukanta Mai isarta sannan ta share hawayen ta sai lokacin taji wani gululo ya fice daga kirjinta.
"In Sha Allah ya wuce Hajiya har abada ki tayani bashi hakuri hakan baze qara faruwa ba".
Dan karamin tsaki Hajiyar tayi "Babu hakurin da za'a bashi, shida ya shuka rashin kirki, kece dai da hakurin ai cewa nayi bana zuwa shi daya Bata yaje ya gyara kayansa tunda Allah yasa kikazo gidan Nan Baki taba kawo min qararsa ba sai shine gemai gemai dashi ze dauko jiki ya kawo korafi ashe Babu dadi king...
Dan gyaran murya yayi "Hajiya kiyi Shiru komai ai ya wuce basai kince komai ba, tunda dai nayi abinda takeso ai shike Nan kowa ya ganni a Nan da ranar Allah na taso tsohuwa ta gaba ta min biko".
Ammi dai Shiru tayi Bata tanka ba sai Hajiya Inna ce tayi dan murmushin su na manya Wanda suka San jiya suke ganin yau. Ammi duk sai taji wata kunya ta lullubeta, wani lokacin maza kunyarsu kadan ce wallahi duk girmansu idan sukayi wani abun sai kaji kamar kananun yara, kome ya fadawa Hajiya ya taso ta da wannan safiyar?.
"To shike nan sai ka bamu guri ko tunda Allah yasa taga girmana ta yafe".
"To shike nan yaushe Zaki koma gida?".
Kafin Hajiyar tayi magana Ammi ta rigata.
"A Nan zata wuni da magari ba za'a maidata gida".
",To kaji sai ka tafi naka uzurin tunda 'yata ta yanke hukunci".
Baice komai ba ya nufi part dinsa da yake bangaren ta, harya danyi nisa ya juyo Yana kallonta ido cikin Ido da wani yanayi a tattare dashi.
"Kuyi breakfast Dani a kawo min ciki".
Kai ta gyada masa ya wuce ciki.
Yi Hajiya Ina tayi kamar bataji me yake fada ba ta cewa Ammi.
"Muje ki bude min dakin ko lazimi ban Gama ba yaje ya daukoni Dana ce yaje za'a kawoni ma cewa yayi A'a".
Ita dai Ammi ba baka sai kunne tare suka shiga dakin da Hajiyar.
*******
A qalla sun dauki minti kusan Sha biyar kafin Zahra ta Gama. Parlour na biyu Rukayyar taja Zahra suka shiga Bai Kai na farkon girma ba Amma ba karya Shima ya hadu kamar jira ake su zauna wayar zahrar ta dauki sansanyan kidan ringtone din ta.
"Amma"
Ta fada tana picking din Kiran sallamar Ammar ta amsa tana fadin "kiyi hakuri Ammah wallahi yanzu na fito daga wanka naci abinci, yanzu nake son kiranki na fada Miki mun sauka lafiya".
Daga can Ammar ta amsa Mata da "babu komai da fatan dai komai lafiya ba wata damuwa? zilai ce taso daga min hankali Wai wani gida aka kawo ku gari guda bata taba shiga ko kwatankwacin irinsa ba kamar Kuna wata kasar ita tsoro takeji".
Dariya sosai zahra tayi Jin yanda zilai ta nadi zance ta fesawa Ammah.
"Kai haba Ammah kyale Aunty zilai rudunta ne kawai, gidan Dan babba Kam babba ne Amma komai normal Ina Jin gidan wani friend din oga Sameer ne aka kawo mu, Kuma momin su oga Sameer ma Saida ta turo Mai aikinta daya da kanwarsa daya Aunty Rukayya gata ma nuna tare ku gaisa".
Wayar zahrar ta mikawa Rukayya suka gaisa da Amma, godiya Ammar ta dinga yiwa Rukayyar har kunya ta kamata tace Kuma ta bawa Zahra number din mommy ta kirata tayi Mata godiya.
Sallama sukayi da Ammar suna kashewa Kiran ya shigo international tana gani tasan shine.
Dagawa tayi tana masa sallama Jin muryarta ba kamar jiya ba ya sauke ajiyar zuciya a hankali da Bai yarda ba da Sameer ya fada masa kamar batayi ciwo ba sai yanzu da yaji muryarta tana fita ba kamar jiya ba.
Sallamar ya amsa Yana fadin "my previous...".
Wani deeply saida tsikar jikinta ta bada wani yarrr. "Wash" ta fada.
Kara Kiran sunan yayi a hankali ciki wata murya Mai tada zaune tsaye "me ya faru ne to jikin ne"?".
"A'a ba komai" ta fada a shagwabe.
Rukayya na ganin haka ta Miki tana nuna Mata tana zuwa Dan ta barta ta sake yanda ya kamata.
"Alhamdulillahi haka nake son ji, ya ciwon ya daina ko yanayi kadan kadan".
"Ya M na warke yanzu ba wani Abu da yake damuna dama mu koma gida kawai tunda ya wuce, kawai naje Naga baby muje mu gaishe da mommy da Umman sajida zuwa jibi mu koma, Dan Allah kace to kaji Kuma fa kaga gidan da oga Sameer ya kawo mu gaskiya ka fada Masa ya mayar damu gidansa ko gidan mommy wallahi yayi girma Ni tsoron inda aka kaini nakeyi gurin yayi nisa da main parlour Kuma wani abin mamaki kasan funitures din dake dakin irin na dakinka ne na Azare komai da komai".
Dan Jim yayi kafin yace irin nawa Kuma wace unguwa ya kaiku?".
Dan Jim itama tayi. "Ina ga ko Dawako Road Nasarawa G.R.A.
"Ok nasan gidan na wani friend dinsa ne, wane bedroom din aka Baki?".
" Bangaren dama daga can ciki sosai".
Shiru yayi wato Sameer be bude Mata master bedroom din ba kenan.
"Precious ki hakura a duba min ke kinsan kuwa tension din dana shiga akan ciwon nan naki? kiyi hakuri ayi bincike akai kawai sai nafi samun kwanciyar hankali, gida Kuma nasan shi Baki da matsala dashi Dan cike yake da tsaro ba wata kafa da za'a shigo cikinsa".
"Baka Gane ba nifa ni kadai ce bazan iya kwana a gurin ba sai dai Aunty Rukayya tazo mu kwana".
Ta fada kamar zatayi masa kukan shagwaba.
"A'a ban Amince ki kwana da kowa ba, ba abinda ze kamaki matsoraciya kawai kice na shirya nida nake fatan Allah ya hore min nayi Miki Wanda yafi wannan girma yanda Zaki sake ki walwala keda yaran mu, to kina tsoron wannan ma inaga Wanda nake fatan ajiye sarauniyar Mata a ciki Zahra fa kike ko cikin taurari keta dabance, haka kawai ki janyo min wata ta hanani rawar gaban hantsi da dare so nake ki ragemin zafi idan da wata a dakin ai kin sabautani ko baza'a taimawa dan malam ba?".
Ya fada cikin wata irin kasala wadda ta saka Zahra Jin wani irin Abu a jikinta. "Ya Ilahiy Ajib"
Ta fada cikin kasakalliyar murya.
"Yan Mata yaya dai Kona gudo ne kina bukatata a kusa"
Ya fada Yana huro Mata iskar Bakinsa ta cikin phone din, da sauri ta cire wayar daga kunnanta, Dan da gaske sakon yaje inda aka aike shi kashe Kiran tayi bako sallama.
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Page 39.
________Wurin karfe takwas Sameer ya shigo gidan, wayar Rukayya ya Kira yace su fito doctor tana jiransu, lokacin suna bedroom din da zahrar take suna cakusawa da Zahra akan wata Rigar shadda 'yar Mali da Rukayyar ta daukowa Zahra cikin kayan da Sameer ya bada ta sawo haka Nan Rukayyar taga zata Dace da zahrar shi yasa ta nace akan ta sakata ita kuma tana ganin tayi Mata girma da yawa, Jin Kiran Sameer yasa ta hakura ta saka sai gashi tayi Mata das kamar an gwadata aka Dinka.
Shar ta fito kamar ka dauke ka buye saboda kyau sai yarintarta ta Kara fitowa, dauri mai kyau Rukayya tayi Mata tunda ta kware har makeup din amare takeyi, light makeup tayi a fuskar ta sai ta fito kamar amarya ranar a yini.
"Masha Allah" kadai Rukayya ke fada ba karya kyau daban yake ko ita mace zahra ta tafi da imaninta to yayi namiji Kuma? Bata yarda da kyau idan yayi yawa hadari bane sai yanzu da Zahra ke gaban ta Dan babu namiji da ze ganta Bai Kara kallonta ba.
Kasa hakuri Rukayyar tayi Saida ta magantu.
"Allah yasa kiyi ta haifowa big bro Yara masu Kama dake gaskiya Ya Mahmud ya Dace ai shi wallahi gaba ta kaishi gara da aka samu wannan incidence din da Bai faru ba yaushe ze gano Mana ke".
Ita dai zahra murmushi kawai takeyi, amma Kasan zuciyar ta tambayoyi ne fal, Ta Ina Mahmud ya zama big bro din Rukayya da alama akwai wata dangantaka Mai karfi a tsakanin Sameer dashi bawai aikin NGOs din Nan bane gaskiya.
A haka suka fito main parlour suka tarar da Iya Rahane da zilai suna kallon Arewa 24 suna program din mata a yau.
"Masha Allah, Allah ya kade mugunji da mugun gani".
Iya Rahane ta fada tana kallon Zahra.
"Allahumma Amin. Allah ya tsare uwar dakina ya Baki lafiya yasa a dace".
Zalai ma ta fada, Rukayya tace "Allahumma Amin, sai mun dawo".
Suka nufi hanyar fita, a cikin mota suka iske Sameer, gaba Rukayyar ta shiga ita kuma zahra ta shiga back seat.
Basuyi wata tafiya Mai nisa ba suka shiga cikin Asibitin, bayan sun fito daga motar number Dr. Haseenar Sameer ya Kira, saiga wata sub-staff da wayar a hannunta tana fadin "sunnunku da zuwa doctor tace na tafi daku office dinta tana zuwa suna wani aiki ne"
"Ok mun gode".
Rukayya ta fada.
Har cikin office din ta kaisu ta fita Nan Sameer yabar su yace zeje yaga wani friend dinsa Dr. Sulaiman.
Bai jima da fita ba aka turo kofar su duka suka juya suna kallon Mai shigowa macece wankan tarwada Mai matsakaicin tsawo fuskarta doguwa ce da maidadaicin idanu da hanci tana sanye da doguwar Rigar material coffee Mai haske tayi rolling da milk din veil fuskarta fal fara'a ta shigo tana fadin " wa nake gani kamar Rukayya a office dina rabon daki tako Nan harna manta Sai dai a waya".
Dariya Rukayyar tayi tana fadin "Ina laifin Kiran wayar ma Shima zumunci ne yafi ace ba'ayin ko daya".
Direct gurin da suke zaune ta nufa " Kinga kin dauke min hankali Ina ta zuba ban yiwa bakuwa ta sannu da zuwa ba, sorry na barku a zaune ta fada tana kallon zahra"
"Lah haba doctor ba komai yanayin aikinku ne hakan".
Zama tayi kusa da Rukayya tana maida hankalinta akan Zahra.
Patient din dangen ce?"
Ta jefawa Rukayya tambayar, da alamun mamaki a fuskar ta.
Kai Rukayyar ta gyada mata.
"Anyway Bismillah ta fada tana tashi daga gurin ta nufi table dinta.
Zahrar ta Mike tabi bayanta.
Tambayoyi sosai ta rinqa yiwa zahrar wasu har kunya take kamata ta kasa Bata amsa, tambayar data fi Bata mamaki shine inda take tambayar ta meye tsakanin ta da Mahmud Dange?"
Kafin zahrar tayi magana Rukayya ta rigata "sister din abokinsa ce daga Bauchi, kuma matar aure ce Dan naji Baki tambqyeta ba, ita Kuma Bata fada Miki ba".
Wata ajiyar zuciya ce ta kubcewa Dr Haseenar har Saida Zahra ta kalleta.
"Ai ban sani ba Ruky Naga DANGEN yayi matukar damuwa ne ko yanzu kafin na shigo saida ya kirani yana fada min Kuna Nan Kuna jirana na dubata sosai".
Dan smile zahra tayi kawai ita Kuma Rukayya tace "kinsan halinsa baya Wasa da rashin lafiya komai kankantar ta, kinsan suna China Aunty Fateeha ta haihu sending Ya Sameer yayo Nigeria shi ya wuce Dubai".
Dan murmushin itama Dr din tayi "zeyi abinda yafi haka in dai Dange ne yanda ya damu Zaki dauka matarsa ce wallahi duk yafa rikice kamar ba dangen da Mata ke fada a kansa ba ko kallo basu isheshi ba Sanda muna school a UK da yawa mutane sunyi mamakin yanda muka Dade dashi ba wani matsalar data faru fatana ya dawo su hadu da Daddy ayi a wuce gurin kawai, kinsan halinsa tunda aka samu matsala Nima fa ta shafeni tunda lokacin da abun ya faru munje gida sokoto shiya Hana ayi abinda za'ayi ta fice yabar kasar Kinga Banda case din Nan ta sister din friend nan tashi Bai Kara kirana ba wlh na tura Masa sako ta email dinsa Amma ba reply".
Ita dai zahra ba baka sai kunne wata magana sukeyi wadda ta jefata a kogin tunani akan Mahmud abinda kunnen ta keji daban abinda yake nuna mata daban.
"Hum lamarin big bro sai a hankali kin sanshi da zuciya kafin dai yayi fushin ana dadewa Amma idan yayi jam'i yakeyi gurin yanke hukunci sai hakuri komai ze Zama normal".
Rukayyar ta fada.
Forms ta cikewa Zahra ta test-test Wanda za'ayi Mata ta Mike ta fito daga mazauninta tana fadin kuzo muje ayi wannan testses din Sai Kuma muje ayi scanning mu gani akwai abinda nake tunanin yana kawo matsalar Amma bazamu tambbatar ba sai mun duba.
"To Allah yasa a Dace" Rukayya ta fada.
Sai da suka Fara zuwa lab sannan suka nufi radiology department inda za'ayi hoton cikin.
Dr karima ce tayi mata scanning din tambayoyi ta Riga yiwa Zahrar harta gama.
Basu jira karbar result din ba, da safe doctor Haseena zata shiga dasu can Asibitin malam Aminu inda za'a mata saura gwaje-gwajen Nan sun Dan rage ne saboda cunkoson can din.
Har gurin mota doctor ta rakasu suna 'yar tsama da Sameer, sannan sukayi sallama Sameer na Mata godiya saboda taki yarda ya biya ko sisi tace patient din DANGE nata ne, itama Zahrar godiya tayi Mata Rukayyar ma haka.
Har Sameer yayi ribas doctor Haseena ta daga Masa hannu alamun yazo gyara parking yayi ya fito ya nufo inda take a gefen baranda.
"Yana zuwa Bata jira komai ba ta Fara tambayarsa cikin nuna damuwa Dan idanunta har Dan ruwa ya taru a ciki da gani tana cikin damuwa da tashin hankali.
" Wannan yarinyar wacece a gurin DANGE?"
Iska ya Dan huro daga Bakinsa ya hade hannuwansa a kirji Yana kallonta kawai.
"Me yasa Kika yi min wannan tambayar?"
"Just pls answer me who's she?"
"Abinda ya fada Miki da farko yanzu ma dai shi zan maimaita Miki, kanwar friend dinsa ce daga Bauchi sukazo Kuma matar aure ce abinda na sani kenan".
"To Amma me yasa ya shiga damuwa akan lamarin ta ya hanani sakat Ni Kuma nasan wannan ba d'abi'ar DANGE bace".
"To ki Kira shi kiji gaskiyar magana daga Bakinsa Mana".
Ya fada Yana kokarin barin gurin.
"Kada kaji haushina na kasa samun nutsuwa ne"
Bai tsaya ba Dan da gaske nema take ta karya Masa gwiwa har yayi abinda baze musu Dadi ba, gara taji daga baya a bakin wani ba shi ba, Daman yasan za'a Rina dole ta kawo wani Abu a ranta yanda ya nuna damuwa akan lamarin Zahrar.
Jiki ba kwari ya dawo motar ya tada yabar gurin, har lokacin tana tsaye Bata bar gurin ba. Shi kansa yaji Babu dadi a ransa yanda Haseena ta mace akan Mahmud tun suna UK yasan idan taji yayi aure ba Kara min tashin hankali zata shiga ba.
Sai da sukayi nisa da Asibitin sannan Rukayya tayi magana "Dan Allah Yaya kaimu murtala Muhammad way zanyi sayayya a Nameer Sale".
Tsaki yayi kadan da gani ranshi ba dadi, "nifa baba son yawo kinga ai saimun koma baya, me yasa Baki fada min ba tun kafin mu fito nasan da zuwan".
"Kayi hakuri mantawa nayi Amma muje gobe in Sha Allah naje kawai".
Bai Kara kulata ba haka zahra Bata tofa tata ba.
Yana zuwa round yayi ya dawo ya nufi murtala Muhammad way din, tare suka shiga da Sameer din yace zahra ta duba abinda take so, har Rukayya ta Gama daukar abinda tazo nema zahra Bata dauki komai ba, ganin haka yasa Rukayyar ta daukar mata kayan shafa dasu turarikan gashi Dana wanka shi Kuma Sameer ya daukar Mata dangin su wafer da ice cream, a hanya hira sosai Rukayya keyi musu Amma ita Zahra hankalinta Yana Kan maganganun doctor ita fa abin yafi karfin tunanin ta ke nan da lauje cikin nadi, shin waye uban gidan wani tsakanin Mahmud da Sameer idan ba kunnenta ne baiyi daidai ba taji Rukayya na cewa Mahmud ya Turio Sameer gida daga China ya wuce Dubai zance yayi dai dai Dana Fateeha matar oga Sameer lokaci tafiyar su.
Har suka shigo unguwar hankalin ta baya tare da ita tayi zurfi cikin tunanin makomarta kodai yanda ya taba fada Mata Yana yaudarar matan ne ya gudu dasu tunda yanzu yasa an dauko su ba Wanda yasan inda ya kawo su daga Rukayyar har Sameer din ba Wanda yasan takamaimai Ina ne asalinsu an kawo su ita da baiwar Allah an killace su a wannan uban gidan kamar resident na matar shugaban kasa.
Sai da Rukayya ta Dan tabata lokacin da suka tsaya a kofar parlourn Dan da gaske tayi mugun zurfi a tunanin Dan zabura tana Fadi. "wallahi har naji tsoro".
"Ai ke dince Ina ta magana Amma kinyi Zurfi a cikin tunanin, ki rage yawan tunani saboda lafiyarki kinsa Yana shafar lafiyyar Dan Adam".
"In Sha Allah Zan Dena na gode".
Ta yungura ta fito Bata jira ba ta nufi kofar shiga tana fadin oga Sameer sai da safe kaina yake Dan Sara min a shafa min Kan Abeed"
Dariya Sameer.
"Zeji in Sha Allah Banda mamansa ko?"
"Kaina bisa wuyana na Isa ayi min gaisuwa, zanzo muyi jegon tare".
Wani kallo Rukayya tayi Mata tayi wani killer smile ta matso daidai kunnen ta "saurin me kikeyi in dai jego ne kamar yaune kinsan Yayana ba rago bane daina gaigaye zakiçi tumo".
Tayi gaba abinta kamar Bata Fadi komai ba. Ido Zahra ta zaro tabi bayanta da kallo, ta fuske kamar ba ita ta Fadi maganar ba.
Ganin haka yasa Sameer ma ya basar ya dauko wasu ledojin yabi bayan Rukayya data dauko wasu.
A Nan parlour sukayi sallama da Sameer ya tafi, su zilan Basu tashi daga kallon ba suka Yi musu sannu da zuwa tare Da tambayar ya jikin nata, bata jima ba ta dauki kedar cosmetic din da robar ice cream Daya da biscuits da chocolates ta nufi hanyar masaukinta tunda yace Mata ba komai a gidan da tsaro sosai ta Sami kwari gwiwa da kwanciyar hankali, tana barin gurin ta dauko wayarta ta kasheta gaba daya tana fadin.
Wallahi kwana kusa ba zasu gaisa ba tunda shi wani irin mutum ne marar Alqibla. Kuma tafiyar ta zatayi ta koma inda ta fito haka kawai Kullum ita kenan cikin matsala gara ta koyi jajurcewa itama kowa ya samu dama saiya ringa dokata kamar wata ball impossible wallahi".
Ta fada tana zura katin bude kofar ta shige ciki, a Kan sofa ta zube kayan ta shiga cire kayan jikinta Daman duk sun dameta, wanka ta shiga Dan wallahi barci takeji, barcinta zatayi tasan mutum Bata wuce kaddararsa.
******
A gajiye ya shigo masaukinsa yau throughout bai samu hutu ba, hankalinsa gaba Daya yayi gida so yake ya ganta ra'ayal ain bawai ta wayar ba yaji dumin jikinta ya tarairaiyi kayarsa suyi barci tare su tashi tare ya gaji da watangaririyar Nan gara ayi wadda za'ayi kawai game din ya Zama over.
Saida yayi wanka yayi order coffee sannan ya janyo wayar ya shiga nemanta da gaske yayi kewarta ba kadan ba, shifa yana ganin yarinyar Nan itace weakness dinsa duk inda take tana manne a kirjinsa ko barci yake itace a cikin barcin idan ba ganinta yayi ba ko yaji muryar da da akwai damuw, yaga alama any nan gaba ze iya kulla wani abun arziki kuwa? tun yanzu da gishiri bai Sha Kan kazar ba yana jinsa haka Yaya idan labarin ya sauya salo?
Abin mamaki wayar switch off.
Zuru yayi Yana kallon wayar "me kenan?"
Yasan dai ba matsalar charge bane, Sameer ya Kira, duk da basu Dade da Gama waya ba.
Sameer yayi mamakin ganin wani Kiran nasa.
Kafin Sameer ya Kai ga magana Mahmud ya Riga shi.
"Meya faru ne a Asibitin naji wayarta a rufe ko jikin ne ta tashi da akayi Mata gwaje-gwajen?"
"A'a gaskiya normal muka dawo har muka biya nan Murtala Muhammad way sukayi sayayya Kasan Rukayya bataso a zauna lafiya,idan tajita da kudi ba zaman lafiya. Dan Allah ka daina turo mata kudi har madam tabar garin nan, kasan Ruky da yawo Kullum aka fita saita qirqiro zuwa wani gurin, wani Abun ne ya faru yanzun ?"
"A'a ba komai, kada ka manta da maganar kayan da za'a sauke gobe a Nan kanon a turasu can Azaren munyi magana da Habib dazu".
"Ok in Sha Allah".
Sukayi sallama, ji yayi baze iya fada masa komai ba. Wayar ya aje kusa dashi wani tunani yayi sai yaji dariya ta kubce masa "zakiyi bayani da yaren garinku yarinya duk yanda akayi taji wata maganar yanzu a Asibitin yasan Haseena farin sani yanda yaji ta damu da sanin relationship din dake tsakanin sa da zahra yasan zatayi duk yanda zatayi ta shigo da wata maganar wadda zatayi touching dinta tunda shekarun da wayonsu ba Daya bane.
Itama Zahra kasa cin komai tayi fridge ta bude ta saka ice cream din da chocolates tayi kwanciyar ta bayan tayi Addu'a, amma barcin Kuma yace baisan zancen ba, tashi tayi zaune a tsakiyar gadon tana tariyo rayuwarta ta baya "ko yaushe Zan Zama stable a rayuwata? sai hawaye suka zubo Mata "Ubangji ka hanani ganin bakin cikin gidan Aure, lamarin Yana neman yafi karfina ka jibinci lamurana Dan isar fiyayyan halitta Annabin Rahama Muhammad s a w.w.
Bansan ko waye ba wannan bawan naka, kafini saninsa ka amintar Dani a cikin lamarinsa daka barni na tozarta, ka kareni daga dariyar makiyana Ubangiji kasan ko suwaye suke mini yankan Bata a cikin lamarina, kayi min kariya ka bani juriyar abinda ka jarrabeni dashi kasa ya zamar min kaffara.
Tasa tafin hannunta a fuskarta taAUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Page 40.
______ karfe takwas saura Zahra ta fito cikin shigarsu ta asali doguwar Riga baka Mai aikin zare maroon sai kananan stones har kasa,tayi rolling da maroon din veil, cikin takunta na rausaya take gannaro steps din, tana baza sansanyan kamshi, ba kowa a parlourn sai wani sanyi da kamshin freshners ke tashi, Dan Jim tayi tana tunanin ta koma kota zauna sai Kuma ta jiyo alamun motsin kwanuka a kitchen gurin da taga suna shiga ta nufa tunda ba sanin Kan gidan tayi ba, tunda ta shigo iyakarta Nan sai Kuma bedroom din da take, tana dosar gurin wani kamshin girki yayi Mata sallama, babban kitchen ne na zamani Mai kunshe da na'urori birjik kamar a wani babban Hotel ko irin modern restaurant din nan iya Rahane ta gani tana yanka wani Abu yayin da zilai ke tsaye tana duba wani abu a tukunya.
Sallama tayi musu tana fadin "Ina kwanan ku".
A tare suka juyo suna amsawa tare da fadin "ya Kika kwana da jikin?".
Dan juya Kai tayi tana fadin. "Nifa Babu abinda ke damuna kawai dai Dan a dunga yawo ne da Bata lokaci, wallahi har kunya nake ji" .
"A kul Kika Kara fadar haka tunda mijinki yace Kizo a duba aga menene matsalarki kada ki watsa Masa qasa a Ido ki sage Masa gwiwa akan kokarinsa, kije idan Allah yasa Babu komai shike Nan idan Kuma anga abinda ke kawo ciwon a magance shi".
"Wannan gaskiya ne".
Zilai ta fada tana sauke girkin.
"To in Sha Allah na daina iya".
"Yauwa kokefa fa ai idan Kika Fara da haka ko lalular da tafi haka baze Maida hankalinsa ba duk da ba fata ake ba".
"Dan Allah Aunty zilai bani wayarki na Kira Ammah tawa tun jiya ta kashe kanta taki kunnuwa".
Ta fada tana istigifari a zuciyar ta Dan tasan karya ta shara.
" To Bari na dauko Miki tana can a daki"
Ta wanke hannunta ta nufi kafar fita Zahrar tana biye da ita, sai da suka fito zilan ta kalli Zahra "uwar dakina Dan Allah Wai Kinga kuwa dakin da aka ajeni a ciki Dan Allah muje kiga wannan duniyar da aka sakani kamar dakin gidanki,to acan dai bana Hawa gadon Amma wannan akai na kwana har naso in makara Allah yasa ita Iya Rahane Bata makara ba".
Dariya Zahra tayi tana fadin "daina fada Aunty zilai sai a Raina mu wallahi, muje Naga dakin naki Daman ban San inda kike ba Koda tsoro ze kamani sai nayo gudun hijira".
A parlour na biyu suka shiga wani corridor bazaka taba cewa da dakuna a gurin ba steps ne kamar goma suka haura sama Nan ma wani parlourn ne da two three bedrooms biyu suna kallon juna sai Daya daga gefe.
"Masha Allah" Zahra ke fada a zuciyar ta tana mamakin gidan Wai wane irin gida ne wannan gari guda compartment guda kawai ya hada irin wadannan mahaukatan falukan da bedrooms din Nan to yaya sauran parts din suke?.
Dakin dake hannun hagu ta nufa ta bude, daga inda Zahra take ta hango wani Royal bed milk Mai azabar kyau, Bata Kara gaskata maganar zilan ba Saida ta shiga ciki, a gefen bed din Zahra ta zauna tana fadin "Bari na Dana gadon Aunty zilai".
Dariya sukayi su suka "kin gani ko wallahi nifa a jiya da kyar nayi barci duk zulumi ya isheni ji nayi Ina tsoron gidan yayi girma da yawa, na jinjinawa matar gidan".
"Wai Mai gidan Bai taba aure ba a gaba dai ze kawo matar".
Baki zilai ta Kama tana fadin "to shi wane irin kudi ke gareshi da ze Gina irin wannan gidan Yana saurayinsa".
"Bani wayar Aunty zilai wannan hirar ba karewa zatayi ba kada lokaci ya kure yau daga Asibitin cikin gari zamu gidan su oga Sameer na gaishe da mommy". Wayar ta Bata suka fito tare ta Kira Ammah suka gaisa sun jima tana fada Mata abubuwan da akayi mata jiya da Kuma komawar da zasuyi yau, karfafa Mata gwiwa itama Ammar tayi tana fada mata ta kwantar da hankalinta In Sha Allah ba komai.
Lokacin da suka fito har Iya Rahane ta shirya table din Rukayya ma ta fito.
Kallon su Rukayyar takeyi ganin daga bangaren da suka fito.
"Aunty Rukayya Ina kwana?"
Zahra ta fada.
",Lafiya kalau matar big bro, ya Naga kin fito daga bangaren mu".
"Au kema a can Kika zauna kika ki zama a dayan dakin kusa Dani".
Baki ta bade tana kallon Zahra. "Na shiga dakin Mai gidan na zauna tab ai wannan part din sai ku".
"Mu suwa daga zuwa bakunta sai mu zaqe Ina laifin can din wallahi transfer zanyi, Ina dalili Ni kadai kamar mayya kufa Nan ku uku ko ihun neman taimako kayi an taimaka maka amman Ni kuwa ko kasheni za'ayi sai dai a dauki gawar da safe".
"Tab wallahi ba inda Zaki zauna a Nan ba haka big bro yace ba,a can yace ki zauna Dan haka Babu Mai canza wannan Umarnin".
Dan turo Baki tayi "Ni na taba ganin haka mutum ya ringa saka doka a gidan mutane inaga baisan girman gidan ba shi yasa yake bada wannan Umarnin, gaskiya da sake".
Time Rukayya ta duba a waya kizo muyi break yanzu zakiga ya Sameer yazo tunda da wuri za'ayi Miki sauran gwajin".
Suna cikin break din Sameer yazo Saida ya jira a mota suka Gama sannan suka tafi, a ANC department suka samu doctor Haseenar sun awon ciki.
Ba yabo ba fallasa ta tarbesu ba kamar jiya ba ko yanda suka ringa Yi jiya da Rukayya yau ba haka bane daga gaisawa Bata Kara cewa komai ba, itama Zahra saita Kama kanta Rukayyar ma haka. Gwajin jini ta Kara tura Zahrar ta hadasu da wata ma'aikaciyar su ta rakasu main lab aka dauki jinin.
Lokacin da suka dawo sun Gama ante-natal din gwajin jira ta dauko da scanning din ta Kira Sameer tana fadin mu hadu a office dina".
Ta kashe tana fadin Bismillah Ruky muje office dina tunda mun Gama da Ante-natal sai zuwa anjima zamu Fara gyne".
A kofar office din suka samu Sameer din ya rigasu zuwa.
Sai da suka zauna sannan suka gaisa da Sameer din, bayani ta farayi Masa na gwaje-gwajen jinin jiya "a cikin jininta ba wata cuta ko kadan kawai scanning ne ya nuna Mana akwai matsala a mahaifarta ta fibroid amman be wani girma sosai ba za'ayi aiki a cire mata tun kafin ya girma Amma zamuyi admitting dinta zuwa one week tana karbar magani kafin ayi surgery din, Dan haka sai ta Kira mijinta ta fada masa yazo da mutane muna son jini leda biyu, zamu jira results din Nan ya fito total blood count za'ayi Mata".
Rukayya ce tayi farat ta tambayi doctor Haseenar "yanzu dole sai tiyata baza'a iya Shan magani ba a warke?"
Kallon tsab Dr Haseenar tayi Mata kafin tace "hanya mafi saukin rabuwa dashi ta sai dai aikin gaskiya".
Tunda doctor Haseena ta Fara bayani gaban Zahra ya yanke ya Fadi idan da abinda taki jini a rayuwar duniyar Nan to tiyata ce.
Nisawa Sameer yayi kafin ya samu karfin halin fadin.
"Thank you so much doctor kome kenan zakiji idan munyi communicating da mijinta saina kiraki later"
"Ok.ba damuwa Allah ya sauwaqe".
"Amin".
Rukayya ta fada Dan zahra ba bakin magana har suka shiga mota tana cikin tashin hankali, kuka takeyi irin na zuci din Nan sai dai hawaye kamar an bude famfo.
Saida suka fita daga Asibitin har sun shiga court road sannan Sameer ya Dan juyo, Madam kiyi hakuri in Sha Allah ba wata matsala idan Allah yasa yin surgery din ne yafi Alkhairi ayi kawai Kinga kema saiki huta da zulumin ciwo duk wata".
Rukayya ce juyo tana fadin "gaskiya kada ki yarda a yanka ki haka kawai Ni banma yarda da maganar Haseena ba, kawai ta jawo Miki wahala Ni Daman da anyi shawara Dani da Babu abinda zesa Haseena ta duba matar big bro haka kawai taje ta jawo Mata matsala da gangan bakaga yau sai wani share mutane takeyi ba, wani ya Hana big bro din ya aure ta".
Wata uwar harara Sameer ya zubawa Rukayya "Billahillazi Zan saukeki a Nan ke wace irin mutumce da bakinki bashi da controlto me kikayi ke Nan? wannan ai shashanci ne keda Zaki kwantar Mata da hankalinta shine Kika sokawa zancen wuqa".
Ita dai Zahra maganganun Rukayya sun daga Mata hankalin kenan da wata jikakkiya a tsakanin wannan likitar da Mahmud.
Wallahi ko likitoci sun Kare wannan ba zata Kara dubata ba shi yasa Kennan jiya ta damu da sanin waye mijinta da dangartakar ta da Mahmud.
Tunda Sameer ya yiwa Rukayya buyagi Bata kara magana ba har sukazo junction din gidan shatima. "Wai yaushe mommy taje gidan Hajyr makwararin?".
"Dazu da safe na kaita Wai zasu karbi lefen mujahida".
"Ok Allah ya Sanya Alkhairi. Dan Allah ya Sameer Zan sayi alawar Madara idan ka tsallaka Zan kaiwa Hajiyar makwarari".
"Kice dai Zaki saya bawai Zaki sayawa Hajiyar makwararin ba".
"Allah tana son shi sosai"
A kofar gidan Hajiyar yayi parking Babar mommy ce.
Da karadi Rukayya ta shigo gida yayin da Zahra da Sameerke biye da ita a baya, suna runfa ana hira da kunnen Rukayya da 'ya'yan dangi da mommy masu karbar lefen basu Fara zuwa ba gaishe dasu yaran sukayi suka fice, sukabar mommy kawai. Cikin nuna kulawar mommy ta kalli Rukayya dake gaba. "Ba dai har kun gama da asibitin ba?"
" Mun Gama kin ganta Nan Wai doctor Haseena tace zata yankata tayi Mata tiyata Dan nace ban yarda da ita ba shine ya Sameer yake ganin bekena".
Sallama Zahra tayi tana Dan tsugunnawa tana gaishe da mommy cikin muryarta Mai sanyi da nutsuwa da Kuma alamun tasha kuka.
Mommy kallonta tayi tana fadin "Masha Allah tabarakalla sannu ya jikin naki?"
Da sauki sosai".
To Allah ya Kara lafiya naji Rukayyar na fadin tiyata za'ayi Miki".
"Eh haka suka fada"
Hajiyar makwararin ce ta fito tana fadin "wa nakeji kamar Rakiya a gidan nan waye ba lafiya naji ana magana tiyata".
" Kin ganta Hajiya, matar Mahmud mutumin ki ce".
Mommy ta nuna zahra.
" Wai Amaryar ce? Sannu kinji menene ya sameki?"
Rukayya ce ta fada Mata.
Mommy ta kalla "Ni Zan hada Mata maganin wannan lalurar ba sai anyi Mata aiki ba, ki huta Rukayya ki shiga Nan kurmi ki sawo min abin hada maganin a Nan na hada Mata insha Allah sai dai ya narke yabi jinin al'ada.
"Amma gaskiya ba wanda ze yanka ta Kamar kabewa ku 'ya'yan zamani komai a yanka ta haka ne daji yake shiga ai ta fama da rai idan yazo da karar kwana kiga an mutu, daina kuka, samiru kiwawo min mijin nata na fada Masa da bakina Babu me yi Mata danyan aiki ko haihuwar fari Bata yi ba a jawo mata tsuguniya mazan yanzu marasa hakuri".
Ta fada tana nufar uwar dakanta.
Ita dai mommy Shiru tayi Saida Hajiyar ta shige sannan ta dubi Rukayya "Wai Ke Sai yaushe hankali ze Gama Miki jiki? Kinzo kin kwatsa zance gashi Nan kin tubzura Hajiya Mai hanata hada maganin Nan sai Allah, itama Kuma Mai lalurar maimakon ki kwantar mata da hankalinta A'a tashin farko kin sokawa zancen wuka, ai kin kyauta".
"Wallahi ba haka bane mommy Kinga dai muna good term da Haseena amma wallahi yau kamar ma Bata taba gani na ba sai cin magani take yiwa mutane da dacin rai want ya Hana Ya Mahmud din ya aureta taga yarinya ta gigice zatayi mata illa haka kawai".
Maficin dake kusa da ita Mommy ta jefawa Rukayya tana fadin fita ki bani guri tunda kin Zama babbar kwabo kin tasa yarinya gaba kina fadar abinda be Dace ba".
Wata uwar harara Sameer ya saukewa Ruky ji yake kamar yayi Mata duka duk ta cakude lamarin tana kokarin ta saka jinin yarinyar mutane ya hau, tun sassafe Mahmud ya Kira shi Yana fada Masa ya kira Rukayya yace ta fadawa Zahra ta bude wayarta ya manta shaf sai fa yanzu ya tuna.
Wayarsa ce ta Fara ringing "shine ya kira" ya fadawa mommy.
"Ka dauka kayi Masa bayanin halin da ake ciki".
"Nasan Haseena ce ta fada Masa shine ya Kira yaji".
Wayar ya saka a speaker yanda zahrar ma zataji.
Bai jira komai ba ya Fara fadin "Sameer wace magana naji Haseena tana fada min? kada ka Bari su taba min yarinyar nan Zan kaita inda ya Dace, naji tana fada min wasu nonsense wallahi idan na shigo saina Bata Mata rai, ita harta isa ta fada min son ranta who is she? Yanzu ina ita zahran take? Tun jiya jikina ya bani an samu problem wayar ta fa ta rufe ta Hana nayi magana da ita fa".
Tashi Sameer yayi tsam ya fita ya cire wayar daga speaker saboda kada yayi katobara.
"Gamu Nan a makwarari gidan Hajiya Zahrar sai kuka takeyi,ita Kuma Ruky sai tinzira ta take kada ta Bari a yankata har Hajiyar makwarari taji tayi tsallen Albarka tace bata san wannan magana ba, ita zata hada Mata maganin hausa Wanda ze narke ciwon, wallahi sun caza min kai har na rasa yanda zanyi da rigimar Hajiyar, yanzu haka kasuwar kurmi zata aiki Rukayya ta sawo Mata mahadin maganin da zata hadawa zahrar".
"Yanzu dai bazan Gane kome kake fada ba hadani da Zahrar muyi magana"
"Ok Bari na kira ta dakin mujahida Naga ba kowa a ciki ka kwantar Mata da hankali duk ta shiga damuwa sosai sai kuka takeyi"
Rukayya dake zaune a tsakar gida ya yiwa nuni data Kira Zahra, lokacin da suka fito Yana tsaye suna ciga da maganar.
Wayar ya Miko Mata ya nuna Mata dakin mujahida yayi nufi waje.
Tana shiga cikin dakin tana Jinsa Yana faman hello, hello tayi shiru karshe ma ta sakata wayar a flight mood tayi kwanciyarta a katifar mujahadar tana goge hawaye.
"Me kake son fada min Kuma? naji komai me Za'ayi bazan zauna a garin Nan ba wallahi, gida Zan tafi kuma idan ma ciwon ne ai Ina da inda za'ayi min maganin ba sai Nan ba, da gata na da komai na zauna sai watangaririya nake yi Dani".AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Page 41.
📖🖋️
________Wani irin barci me nauyi yayi awon gaba da zahra, sai da Sameer ya shigo yace Rukayya ta duba Masa Zahra oga ya Kira yace Masa da matsala.
Dakin Rukayya ta shiga ganin Zahrar tana barci ga wayar Ya Sameer a gefen ta, daukar wayar tayi tana dubawa a airplane mode taga wayar 'yar dariya tayi tana fadin "good yarinya kinsan kanki kenan ai Ina bayanki ki tsaya tsayin daka akan wannan mijin naki idanun Mata a kansa suke kinyi dai-dai wallahi".
Wayar ta cire daga flight mode din tayi waje da sauri tana fadin "gashi ya Sameer wallahi barci takeyi" .
Wayar ya Karba Yana dubawa gashi Nan a kunne take haka datar itama ba wani matsala.
Tsaki yayi kadan Yana fadin "duk nema suke su dagulamin lissafi wallahi har na rasa Yanda zanyi" .
Rukayya najinsa tayi Shiru haushinsa takeji tun buyagin da ya yi Mata dazu,waje ya juya ya fita Yana kokarin Kiran waya.
Hajiyar makwarari ce ta fito daga daki da manyan tabarmin roba a hannu tana fadin "zo Nan Rakiya ki shimfida su cikin baranda kafin mutane su Fara taruwa".
Zuburo Baki tayi "Allah ki daina fada min sunan nan ni sunana Rukayya haka a ringa batawa mutum suna".
Ta taso tana karbar tabarmin.
"Gidanku, nace Rakiya ba sunan ki bane, Kizo ki shiga kurmin ki karbo min masoro gurin Alhajin Baba nayi na hadawa yarinyar Nan magani na Bata tun yau ta Fara amfani dashi ba'a bori da sanyin jiki".
Saida ta Gama shimfidar ta shiga gurin Hajiyar cikin falonta suna duba kayan da za'a bawa masu kawo kefen robar da aka zuba chicken pepper ta bude tana fadin "bari na dauki Daya naji kamshin yayi min Dadi".
"Ki rufe wannan gashi can a kitchen a waje ki diba harda snacks din duka, Amma ki Fara karbo Mata sakon a kasuwar tukunna kuje da sadiya ta rakaki ku shiga a dai daita tunda ba nisa ga cunkoson cikin kasuwa Kuma kinsan Sameer baze Baki motarsa ba, wadda mukazo da ita Kuma Aliyu yayi nasa gurin da ita".
Basu dauki minti talatin ba suka dawo da sakon har lokacin Zahra barci take sai da jama'a sun Fara taruwa a gidan duk dangi need sai dai-daikun Yan uwan mahaifar mujahidar.
A blender hajiyar taba mommy ta nika Mata masoron ta juyo mata shi a cikin robar da Hajiyar ta bada a zuba a ciki.
Lokacin da mommy ta kawo Mata Hajiyar da kanta ta nufi dakin mujahidar tana fadin "Ina matar Mahmudun take?.
Barcinta take sadidan Dan tabata Hajiyar tayi tana fadin. "Tashi 'yar nan ga maganin lalurar ki da izinin Allah".
Tashi zahrar tayi tana bin Hajiyar da kallo lokacin data aje robar kusa da ita.
"Bude ki gani sai nayi Miki bayanin yanda za'ayi dashi".
Batayi musu ba ta bude robar taga garin masoron.
"Kina jina? Abinda za'ayi dashi ki ringa diba Kashi Daya bisa hudu na karamin cokalin shayi kina zubawa a ruwab zafi tafasashshe cikin kofin ok ki barshi yayi minti ashirin a ciki sai ki tace ki Shanye ruwan,haka Zaki ringa yi har ya Kare in Sha Allah ze narke yabi jinin al'adarki ya fice, ki rabu da wannan shirmen komai ace za'a yanka mutum kamar kabewa"
'yar dariya Zahra tayi tana fadin in Sha Allah zanyi na gode madallah Allah ya saka da Alkhairi".
"Allahumma Amin. Allah ya Baki lafiya,ayi ta hakuri irin mijinki Mata Ido rufe suke nemansu sai kin kauda Kai zakiçi ribar zaman aurenki. Amma kada ki kuskura ki yarda a nuna Miki San iyawa akan mijinki, ki kula da sukarki Bata da damuwa ko kalilan ki girmama Masa danginsa da kakarsa jiya ya wannan suna gidan Nan sunzo ganin Mai sunan mijinki na wurin Sameeru, Ni cewa nake can wurinku zasu sauka ma sai naji Sameeru na maganar su fito zasu koma a jiyan kinsan sha'anin tafiyar iska, ba wani nisa ke gareta ba".
Ita dai Zahra Jin Hajiyar take Dan ba komai ta fashimta ba.
Rukayya ce ta shigo da Abinci dasu snacks a babban tray tana fadin " Ai tunda naji shiru Hajiya Baki fito ba nasan kin hanata barci kawai wallahi ke idan Kika so Abu ba sauki saina Allah idan kinyi hakuri zata tashi ki bata".
"Ke tafi can waya fada Miki ana bori da sanyin jiki Baki San hadarin wannan abun bane baya barin haihuwa fa ba dole a tari abun ba tunda wuri, wannan yarinya tubarakallah haka ai ba'aso a samu abinda ze kawo Mata cikas a zaman aurenta ba, ni tunda na ganta ta kwanta min har maganin tsarin jiki Zan karbo mata a Sanka, nan babban gida".
Baki Rukayya ta rike tana kakabin Abun "Ikon Allah to ke Hajiya fada Miki tayi tana son na tsarin jikin? Da kike faman fadin Zaki karbo Mata".
Kafin Hajiyar ta Kara magana Zahra ta rigata.
"Haba Aunty Rukayya Ina laifin Hajiya kuwa tunda na sako Qafa gidan Nan Bata huta ba hidimata takeyi".
"Eh haka ne kam tunda har kasuwar kurmi ta aikeni, da girnana da komai nace bazanj ba tace nayi mata kiwa dan rabon da naje cikin kurmi tun Ina secondary Dan ma ban manta shogon ba"
Ficewa Hajiyar tana fadin kyaji dashi idan Kaya ne".
Tashi zahrar tayi tana fadin Bari na dawo, ta fice daga dakin.
Toilet ta shiga ta Kara gyara Kanta, lokacin data fito dai dai lokacin masu kawo lefen suka karaso suma Nan da nan gudan ya dauki jama'a Dan makota ma Wanda suka makara suka ringa shigowa.
Ganin gidan ya kacame da jama'a yasa Zahra tayi amfani da wannan damar ta nufi hanyar soron gidan, a soron ta tsaya ta Ciro wani face mask da yake cikin jakar ta da eyeglasses dinta ta saka ta fice daga gidan.
Ba Bata lokaci tana fita Dan sahu Yana kawo Kai, ta dafe shi ta shige, tana fadin "Janbulo zaka Kaini".
"Hajiya sai dai drop gaskiya Dan hanyar ta baude ni rimi na nufa".
"Muje Zan baka kudin drop din".
Ta fada tana Dan leken gefenta kamar narar gaskiya, hankalinta be kwanta ba sai da taga sunyi nisa da unguwar, ajiyar zuciya ta sauke tana "na barka da Dr Sai ku cinye kanku haka kawai za'a sabautani saboda Kai,Wanda har yanzu bansan daga wace bahiyar ka bullo ba, ayi min sakiyar da Babu ruwa a cuceni a cuci rayuwata shi yasa na taho da hirina idan tayi ruwa rijiya idan batayi ba ta Zama Masai"
Kafin su karasa layin su Ssjida tacewa Mai adaidaita din ya taya gurin me P. O.S zata ciri kudi.
Har kiofar gate din gidan ya kaita 10k ta bashi, cikin mamaki ya dubeta "Hajiya kudin sunyi over dari bakwai ne kudin, Hala ke bakuwa ce?"
Gaga tayi Tana fadin na sani kaje kawai nagode Allah ya tsare".
"Na gode Allah ya rufa asiri ya kara Miki daukaka".
Tana tafiya tana fadin. "Allahumma Amin".
Ta shige gidan shi Kuma ya juya Kan mashin dinsa ya wuce Yana Fadin "Bari na koma na sallami gidan sai na Kara fitowa".
***********
Bayan tafiyar masu kawo lefen an baje anata kallon kayan arzikin da suka kawo Masha Allah kayansu sunyi kyau sosai Dan akwatuna set hudu suka kawo da manyan jakunkuna uku har da adudu biyu.
Saida komai ya lafa sannan hankalin Rukayya ya dawo jikinta ta shiga neman zahra, abin mamaki ba zahra ba alamarta Abu kamar Wasa ya Zama gaske Nan da Nan tashin hankali ya wanzu a gidan Dan mantawa akayi da murnar wani lefe Nan da Nan Rukayya ta Fara share hawaye.
Mommy ce ta Farayi Mata fada "Haba Rukayya menene haka Zahra Karamar yarinya ce ku shiga makota Mana ko taron jama'a ne bataso ta shiga can ta zauna ba kince toilet tace Miki zata shiga ba? Kafin ta fito Kuma bakin sun shigo?"
"Eh haka ne Amma Naga fitowarta harta tsaya a can daga Nan mutane sukayi yawa ban sake ganinta ba".
"Ke Zubaida maza ku shiga gidajen kusa ku duba ko can ta shiga ku kirawota".
"To mommy". Ta fada sukayi waje su uku.
Hajiyar makwarari kuwa cewa take "Ina yarinyar nan ta shiga ko masu kawo kayan tabi suka tafi".
Wani kallo Rukayya tayi Mata "kaji Hajiya da wani zance kamar wata 'yar baby ce zahrar da zatabi wasu mutane".
"Ungo Nan".
Abu kamar Wasa karamar magana tana neman Zama babba, duk kukkuken babu it's Babu dalilinta komai Kama da Zahra Babu.
Mommy da Kanta ta Kira Sameer tace duk inda yake yazo yanzu tana son ganinsa.
Daman ba nusa yayi ba Yana tare da abokansa na unguwar Dan a hannun Hajiyar ya girma harya Gama secondary school dinsa.
A tsakar gida ya samu su mommy anyi cirko-cirko.
"Gani mommy lafiya na ganku haka?".
Hajiya ce ta Fara fadar "Ina fa lafiya ba'aga matar Mahmudu ba har makota anbi baku ko alamarta".
Mommy ya kalla. "Kamar ya ba'a ganta ba? To Ina ta shiga?"
"Allahu A'alam, da farko abin ban dauke shi haka ba sai yanzu da naga da gaske ne yasa nace Bari na Kira ka".
"Ok, Bari naje Nan Ina zuwa"
Ya juya ya fice da sauri, cikin tashin hankali me ze fadawa Mijinta Ina ta tafi?.
Tambayar mutanen kusa masu sana'a a kofar gidan ya rinka yi, har ya juya sai wani Mai sayar da Mai yace yaga fitowarta da face mask da glass a Ido ta hau a dai- daita sahu sunyi hanyar nan ya nuna hanyar gidan shatema.
Dafe Kai yayi cikin tashin hankali, "wannan wace irin masifa ce haka kawai an tadawa yarinya hankali har ta yanke Shawarar tayi tafiyar ta, to tana Ina? Ina ta tafi? Ba wani ta sani a garin Nan ba ga Babu waya a hannunta, Saida ya fada masa ya fito Mata a mutum sak a wuce wannan wasan yaran ya kaita inda ya Dace a duba Masa ita amma ya gano ya yiwa Haseena waya ta a duba Masa ita yasan karshen film din ba Mai kyau bane"
Jiki ba kwari ya koma ciki..
***** ***** *****
Hankalin Zahra be kwanta ba so sai Saida ta ganta a cikin falon gidan su Sajida, Mai aikinsu ta bude Mata parlourn tana fadin "A'a marhabin maraba da Amarya sannu da zuwa".
Ta fada tana murmushi, tare suka shigo ciki.
"Yauwa Mama Hauwa sannu da gida, ya naji gidan naku Shiru ko su Mamar basa nan ne?"
"Wallahi sunje Rimin sumaila duba kanin Baffa bashi da lafiya,a nan ya kwanta a Asibitin Murtala to shine sukaje su Kara duba shi da jikin".
"Allah sarki ko kawu Musa?"
"Shine Ashe kin sanshi".
Eh nasan shi Mana, har a gidansa mun kwana lokacin da mukaje da sajida. Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne"..
"Allahumma Amin, Bari na bude Miki dakin mutuniyar ki shiga na kawo Miki abinci can, inaga sai dare zasu dawo tunda suka Kai har wannan lokacin".
Wanka ta shiga ta Dade a toilet din kafin ta fito tana tsane jikinta da towel, lotion ta shafa ta dauko Rigar material marar nauyi ta saka a cikin kayan sajida.
Jallop din kuskus aka kawo Mata wadda Tasha kayan lambu da pepper soup na kayan ciki da kunun aya Mai sanyi da ruwa.
Abincin taci ta koshi ta dora da kayan sanyi tayi hamdala ga Allah ta kishingida jinta take fresh idan Allah ya kaimu safiya ta karawa motarta Mai, ganinta a araha yasa ake garata kamar kwallo.AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH
Page 42.
_______Abu kamar Wasa har kusan karfe taran dare ba zahra ba labarinta, iya Rahane mommy ta Kira tana tambayarta kosu Rukayya sun dawo? Dan bazata fada ba direct tace ana neman zahrar hakan dabara ce ta tambaya a fakaice.
Amsar data Bata ita ta Kara tadawa kowa hankali cewa tayi "Basu dawo ba tun fitar safe da sukayi ga zulai ma duk ta shiga damuwa tace tun yamma Ammarta ke Kiran wayar zilan tace wayar zahara'un Bata shiga".
"Yanzu ya za'ayi kenan?"
Rukayya ta tambaya.
"Ni damuwa ta Daya kada ta fada mugun hannu Dan ma dai ba lallai ansan matar waye ba Amma yau abin tsoro ce kiransa zanyi kawai na fada Masa halin da ake ciki ko yasan wasu 'yan uwansu a nan kanon, tunda barin Kashi a ciki baya maganin yunwa gara ya fada kawai asan Yanda za'ayi tun guri be kure ba.
Number dinsa yayi ta try Amma amsar Daya ce a rufe take.
Da kyar ya mayar dasu mommy gida har Rukayya a gidansu ta sauka, to ta koma tacewa baiwar Allah da sukazo tare zahrar ta Bata ko me?"
Duk wani lissafi ya gama suncewa Sameer, duk wannan Abu be tashi faruwa ba Saida sukazo gidan kakarsa, ita kanta Hajiyar makwararin tashi Dan kukanta tana mitar yarinyar Nan Bata kyauta Mata ba ta rasa a inda zatayi irin wannan shegantakar sai a gidanta.
Jiki ba kwari Sameer ya shiga gidansa, sau Daya Fateeha ta kalleshi ta dauke Kai ta cika fam da fushi tun safe Daya fice Bata Kara sakashi a idanunta ba, ta kirawo shi ya Kai sau biyar sai dai yace Mata gashi Nan Amma bezo ba sai yanzu wurin Sha dayan dare.
A kusa da ita ya zauna ta kauda Kai, hannu yasa ya dauki yaron a Kan cinyarta, yasa hannu Daya ya tallabota ta hada da babyn ya rungumesu, Jin ajiyar zuciyar da yake saukewa a jajjere yasa Fateeha ta gane da matsala.
"Wai menene?"
Ta fada cikin damuwa.
"Bari kawai wlh hankalina a tashe yake, tun bayan Azzahar Zahra ta fice daga gidan Hajiyar makwarari bamu San inda ta nufa ba, duk inda muke tunanin zataje munje Bata nan".
Itama mantawa tayi da fushin da takeyi dashi ta Fara sallallami "Yanzu Ina ta tafi? Kadafa wani Abu ya sameta kasan mutane yanzu gaskiyar su kadan ce".
Dafe kansa da yake Sara Masa yayi "Bana tunanin haka gaskiya da Kanta ta fita ta tafi kawai dai an Bata Mata Rai ne ban Kuma yi tunanin abin yayi Mata zafi haka ba da bazan barta a gidan Hajiyar ba, amfani tayi da masu kawo lefen mujahida ana can gurin karbar lefe ita Kuma ta fice daga gidan Dan akwai Wanda ya fada min Yanda ta fito nasan da niyya ta fice abunta".
Zuru Fateeha tayi tana sauraren mijinta.
"Ka Kira ka fada masa?"
Kai ya girgiza Yana fadin na kasa samunsa nafi one hour Ina nemansa ban same shi ba".
*** *** *** ***
Karfe Tara su Umman sajida suka shigo gidan lokacin Zahra na parlour suna hira da Mama Hauwa, turus Maman tayi ganin zahra ko rantsuwa tayi Babu kaffara, wannan ba zuwan arziki bane amma sai ta share tana fadin "wa nake gani haka?"
Dariya Zahra tayi tana fadin "Umman mu sannunku da hanya".
"Yauwa sannu,aike za'a yiwa sannu kin sha doguwar tafiya".
Shiru zahrar tayi batace komai ba, kannen Sajidar ne suka Fara gaisheta suna fadin "Aunty kin rigamu zuwa munata cewa idan Ya Abba ze Kai Miki sakonki da Baffan Rimi ya bada a Kai Miki zamu bishi sai gashi Kuma kinzo"
Karamar kanwarsu ta janyo tana fadin "ai zakuje ko mutuniyar tunda anyi min Alkawarin zuwan".
"Eh zamuzo Aunty zahra".
Nusaiba ta fada suna Zama kusa da zahrar, yayin da Maman su ta wuce bedroom dinta tana cike da tunani barkatai a zuciyar ta.
Tana shiga jakar hannunta ta zuge ta Ciro wayar ta, Ammah ta Kira Dan bazata Zama uwar banza ba da alama gudowa yarinyar Nan tayi.
Lokacin da Kiran ya shigowa Ammah tana duba wasu kaya da Hajiya kaltume ta Aiko Mata dasu ne.
Ganin Umman sajida ne yasa ta aje kayan ta dauki wayar tare da sallama.
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
"Hajiya ya gida ya wajen Amare? Ina ta son na Kira mu gaisa Allah Bai nufa ba sai yau, itama zahrar mun kwana biyu bamu gaisa ba".
"Wallahi kowa lafiya, Amare Kuma suna nan kusa daku Bata jin dadi ne mijin ya matsa suzo Nan Kano a dubata ni tun safe da muka gaisa da wayar zilai ban Kara samunta ba, na Kirawo zilan ma tace min har yanzu Basu dawo ba duk ta tada hankalin ta, nace ita da ba ita kadai ta fita ba tare suke da amininsa da kanwarsa, Kinga duk inda suke ai suna tare".
Shiru Maman tayi kenan hasashenta ya kusa Zama gaskiya Kenan.
"Hajiya ga zahrar a gidan nan,yanzu muka dawo daga Rimi Sai na tarar da ita Ina ganinta nasan ba lafiya ba Ashe garin sukazo ta kawo min ziyara".
Jim Ammah tayi tana jinjina lamarin.
"Anya kuwa ki dai saka Mata Ido zuwa safe kome ke nan sai ki fada min idan anzo daukarta to da sanin mijin tazo idan Kuma tace zata tafi ki hanata ki fada min na gode kwarai Allah yayi Mana jagora ya Raya Mana zuri'a".
"Allahumma Amin". Sukayi sallama.
Zuciyar Ammah sai bugawa takeyi a hankali ta furta "meke Nan Kuma? Ni Asma'u Allah ka taimaki 'yar marainiyar Allah, matsaloli daga an toshe wannan sai waccen ta bulle Allah yayi Mana maganin wannan matsaloli yanzu kuma ko menene damuwar datasa ta tsallake tabar inda suke gashi ta Kama wayar ta rufe Dan ma kada a San inda take,ai kuwa zamu gauraya bazan dauki shashanci ba".
Ta hada duk kayan ta zuba a ledar da aka kawosu ta fice daga dakin ta nufi dakin Abban Yara tunda ita keda girki.
Saida Umman sajida tayi wanka tayi sallah sannan ta fito har lokacin suna falon da yaran direct dining ta nufa taci abinci sannan ta dawo falon.
Gaisheta zahra ta Karayi tana tambayar ya Mai jikin,
Dasu Baffa.
Sun dauki lokaci suna hira kafin Ummar tace "Wai daga Ina kikazo ne daga can Azaren ne ko Kuma kinzo nan garin ne?"
Shiru zahrar tayi kafin tace "ganin likita nazo akan wannan ciwon marar da bakeyi duk wata".
"Ikon Allah kuma ke kadai Kika taho ganin likitan kamar marar gata".
"A'a bani kadai nazo ba tare da Aunty Zilai Mai aikin Ammah mukazo tana can a Nasarawa G.R.A".
"Ok, to mryasa baku taho tare ba Nan din".
Shiru tayi Bata ce komai ba, ganin da Yara yasa itama ummar tabar zancen.
Kafin kowa ya tashi Zahra ta tashi tana fadin "Umma Bari naje ba kwanta barci nakeji"
"To Allah ya tashemu lafiya.
Basu Dade ba Suma suka shige daki Daman duk sun gaji.
Lokacin da Ammah ta shiga dakin Abban samun Mama tayi kane -kane tana ta zuba zance da kudi a hannunta masu Dan yawa da gani a gurin Abban ta Karba, cikin alamun rashin gaskiya mamar ta Fara fadin. "Aina leka parlourn ki naji Shiru nayi zaton kina Nan wallahi Ashe Baki shigo ba"
Fuska ba annuri Ammah tace. "Eh ban shigo ba idan kin gama na dawo ta juya har Takai kofar ficewa Abban yayi gyaran murya Yana fadin "dawo ki zauna Ina Kuma Zaki ita ta tashi ta tafi tunda ta gama abinda ya kawo ta"
Jiki ba kwari Mama ta tashi tana fadin "ai Kam na Gama Allah ya tashemu lafiya nagode Allah ya Kara arziki".
Ta nufi inda Ammah ke tsaye tana fadin "mu kwana lafiya ki tayani yiwa Abban yara godiyar abin arzikin Daya bawa Najjahi na kudin registration".
"Masha Allah! An gode Allah ya bada sa'a".
Ta fada fuskar ta Babu walwala ko alama, da gaske ta kule Abun Yana so ya Zama rainin hankali tayi noticing dinta duk ranar girkinta sai ta dunga Karakaina a part din Abban Amma idan tasan wata ai Bata San wata ba.
Dawowa tayi ta zauna kusa dashi "meya Bata Miki Rai ne Kika juya Zaki bar dakin?"
"Ba komai".
Ta Bashi amsar in short.
Haka Nan yabar zancen badan ya gamsu da abinda ya fada ba.
"Neman izinika na shigo zanje Kano gobe in Sha Allah"..
Saida ya Kare Mata kallo tsab sannan yace. "me akeyi a kanon da zakije?"
Kai ta girgiza ba komai zanje barka ne na yaron nan Sameer ranar da yazo daukar su Zahra yake fadawa magaji anyi Masa haihuwa an samu takwaran mijin Zahra".
"Kai Masha Allah, ai ban sani ba da nayi Masa barka ranar da yazo".
Tashi tayi zata fice Abban ya mayar da ita "Wai me yake faruwa ne Naga ranki a bace tun shigowar ki".
"Ba komai zanje na dawo ne yanzu in Sha Allah".
Ta Mike ta nufi kifar ficewa, haka Nan yayi Shiru badan ya yarda da ba yasan da abinda yake damunta taqi fada Masa ne kawai".
Ammah na shiga part dinta ta Kirawo Abdul Hakeem, lokacin Yana kofar masallaci tare da Habib.
A parlour ya samu Ammar ta zuba tagumi.
Saida yayi sallama biyu sannan taji.
"Wa'alaika Salam".
Ta fada tana kallon Abdul Hakeem din, kusa da ita ya zauna Yana fadin "lafiya kuwa Ammah Ina sallama bakya jina?"
Ajiyar zuciya ta sauke tana fadin "yanzu ba dadewa Umman Sajida ta kirani waiga zahra taje Mata zata kwana a can Kuma ita kadai ba tare da zilai ba, na Kira zilan tace min tun fitar safe Basu dawo ba har dazun, ka Kira Sameer kaji shin yasan da tafiyar ko Kuma wani Abu ya faru tayi musu yqji nasan halin kayana zatayi abinda yafi haka ma in dai zahra ce, Dan haka ka kwana da Shirin Kano sakko zamuyi ko Abban KU ban fada Masa wannan maganar ba ina tsoron ta fito duk da nasan ba lallai ta fito din ba amma sha'anin mace da miji sai Allah"
"Allah ya rufa asiri".
Abdul Hakeem ya fada Yana Kiran Sameer duk da lokacin ya ja Sha Daya ta gota.
Ringing Daya saneer ya daga kafin Abdul Hakeem ya Fara magana Sameer ya rigashi Dan ko sallama Babu ya Fara fadin "Abdul Hakeem zahrar tazo Nan ne?.
"Easy my man! Tana Nan Kanon a Janbulu gidansu Sajida, yanzu Umman su sajidar ta Kira Ammah ta fada Mata saboda hankalin ta be kwanta da ganin zahrar ba duka yaushe akayi Abu da zata wani zo yawon ziyara tasan da wata a kasa, shine ta Kira zilai ta fada Mata tun fitar safe baku dawo ba".
Ajiyar zuciya ya sauke, sai Yanzu ya samu nutsuwa dan Yanzu suka gama wayar da mommy akan ko akwai wani cigaba? Yace Mata Babu Kuma tun lokacin da abun ya faru yake ta kokarin ya Sami Mahmud Abun ya faskara.
"Na gode kwarai Abdul wallahi muna nan hankalin mu a tashe tun bayan Azzahar muke Abu Daya, Dan Allah kayi min godiya gurin Ammah, kace Kuma tayi hakuri ba sai tazo ba Dan Allah ga mommy ta Isa tayi komai ka fada Mata laifi akayi mata amma in Sha Allah hakan baze Kara faruwa ba wannan ma tsautsayi ne".
Kai kawai Ammar ta gyadawa Abdul Hakeem ya gane me take nufi tunda handsfree ya saka wayar".
"To ba damuwa tace ayi maka godiya da kwaramniya"
"Ba komai yiwa Kaine ka turo min da address din gidan Yanzu na gode".
Sukayi sallama ta kashe Kiran Yana Maida hankalinsa a Kan Ammah.
"Ammah lokaci yayi daya kamata a zauna da Mahmud asan who's he? Aure ba Abun Wasa bane asan asalinsa Kinga muna tare sosai wallahi be taba fada min asalinsa ba kawai dai nasan he's educated fiye da tunanin mu badai ya nunwa ne kawai anyway kome Kenan dai kiyi abinda ya kamata kawai".
*** **** ***
Suna Gama waya Sameer ya lalubo Number Rukayya tana dauka yace ki fadawa mommy gani Nan zamuje mu taho da Zahra tana janbulo gidansu friend dinta".
Bai jira tayi abinda zata fada ba ya katse Kiran ya saka jallabiya ya dauki key din motar yayi waje.
A kofar parlour ya tarar da Rukayya da Mommy.
Fitowa yayi yana fadawa mommy Yanda sukayi da Abdul Hakeem da Ammah.
"Dan Allah ki zauna mommy muje da ya Sameer kawai ana ganin mu dake za'a San ba lafiya ba Kinga ai itama zato takeyi kawai muce Mata ya Mahmud ne ya dawo yace muzo mu taho da ita tinda da saura lokaci".
"To shigo mu tafi tsari mistress".
Saida suka dauki titin rijiyar zakin sannan Sameer ya mikawa Rukayya wayar da address din da aka turo Yana fadin " duba ki gani ko kinsan laying kune masu yawo lungu da sako na garin nan".
Dubawa tayi tana fadin " Nasan gurin layin gidan su saliha sani Musa ne tare mukayi Excel da ita".
Cikin ikon Allah suna tsayawa a kofar gate din motar ya Abba ta shigo shida Abie dinsu sun dawo daga kwangwalam bodar NIGER inda sukaje gaisuwar mahaifar amininsa data rasu jiya, sun biya ta kazaure gurin wani abokin aikinsa daya kwanta a Asibiti Shima a Nan sukayi dare.
Ganin mota a kofar gidan yasa Abie yace Abba ya tsaya yaje yaji ko lafiya Yana fita Mai gadi ma ya fito Yana ganin Abba ya karasa gurin da sauri, fitowa Sameer yayi ya tarbesu Yana Mika musu hannu sukayi musabaha Yana fadin "Ayi hakuri munzo cikin dare ba sanarwa,Daman munzo mu tafi da zahra ne tun Rana tazo Bata Fadi zata kwana ba sai Yanzu mijinta ya dawo gashi ba waya a hannunta, ganin da sauran daren yasa muka biyo samunta".
,"Ok. Ba damuwa muma Yanzu shigowar kenan munje unguwa tare muke da Abie".
"To mu karasa Mana na gaishe shi ya juya yabi bayansu suka nufi gurin Abie din, Rukayya gani tayi kamar akwai rashin kyautawa ace tana kallo aje a gaishe da babban mutum tana zaune sai kawai ta fito ta rufa musu baya.
Cikin girmamawa Sameer ya gaishe da Abie din sai Jin muryar Rukayya sukayi daga baya tana gaishe da Abie din, hankalin Ya Abba biyu ya kasu ga wata murya data fizgeshi lokaci Daya ga Kuma bayanin da yake yiwa Abie.
""Ba wani Abu Bari a Kirawo Umman tasu saita fada Mata ta fito wannan ai shashanci ne ya za'a bar yarinya ta nemi gurin kwana da mijinta da komai".
Sameer ne ya Dan shafa Kai.
"Ayi hakuri Abie mijin ne baya Nan sai yanzu ba dadewa ya shigo kasar".
Mazaunin direba Abban ya koma suka nufi ciki tunda Daman Mai gadi ya bude gate Yana jiran su shigo.
A waya Abie ya Kira Umma har lokacin idanunta biyu da wuya tayi barci matukar tasan mijinta baya Nan da sauri ta dauki wayar tana Masa sannu da zuwa.
"Yauwa ya amsa a takaice Yana fadin. "ki taso bakuwar da kikayi a gidan mijinta ya dawo gasu Nan a gate". Ya kashe Yana nufar part dinsa.
Shiru tayi waye ya fada masa da bakuwar a gidan jiki ba kwari ta nufi dakin sajida, barci ta Samu tanayi sadidan kamar Nan duniya Bata da damuwa Kota sisi dakin ta shigo tazo bakin gadon ta tsaya tana Kiran sunan ta a hankali, tana fadin "tashi ki kimtsa ki fito ga Mai gidanki can zaku tafi gida". Idanun tadan zaro tana fadin "wallahi bazani ba Umma kice musu bana nan
sai hawaye"..
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Page 43.
_______ kuka zahra keyi ba kakkautawa a hankali Umman ta zauna kusa da ita, ki daina kukan Nan kiyi hakuri ki tashi ku tafi, kiyi ta addu'a Allah ya kawo Miki saukin ko menene damuwar, kada ki Kara tunanin yin irin haka idan Abu ya dameki ki tafi kibar gida ba shine maslaha ba kinji, tashi ki cire Rigar barcin ki canza suna jiranki Kinga dare ya farayi inaga tun Rana suke bulayin nemanki sai Yanzu suka samu inda kike".
Kai ta gyada tana goge hawayenta, Bata taba tunanin yau zata koma gidan Nan ba Dan ita a budget dinta daga Nan gaba zatayi Dan kasar tayi niyyar tsallakewa tayi gaba abunta tunda passport dinta yana jaka, to Wai ta Yaya suka gano tana gidan Nan Wama yasan gidan a cikinsu, to shi yaushe ya dawo?
Haka zuciyarta ta dunga sake-sake.
Fita Umma tayi ta Bata guri ta canza Kayan, jiki a mace ta fito ta iske Umma da Ya Abba a parlourn, gaishe da Ya Abban tayi ya amsa Yana fadin "wallahi kin wahalar da mutane da wannan Daren Kika sakasu fitowa har da mace Ina jinma mijinta ne"
.ita dai zahra Shiru tayi Masa ta nufi Hanyar fita daga parlourn tana fadin "ummah na tafi Saida safe".
Ta fada tana yin gaba "to Allah ya tashemu lafiya kiyi hakuri da safe idan Allah ya kaimu ki bude wayar zamuyi magana".
"To Ummah in Sha Allah Zan bude". Suka fice daga Fallon. Ya Abban Yana biye da ita tun kafin ta karaso Rukayya ta taho cikin sassarfa ta ringume Zahra tana fadin "wallahi kin dauki alhakina da Hajiyar makwarari Kinga kukan da muka Sha yau? Tambayi Ya Sameer kiji duk kin tashi hankalin mu".
Wani sanyi ya ratsa Ya Abban Jin Rukayya ta ambaci Sameer da yayanta, daman Kuma yaga Kama ta zahiri duk da dare ne Bai Hana shi ganin kamannin nasu ba.
Shiru zahrar tayi Mata ita sai Yanzu taji wata kunya duk ta rufeta, me kenan tayi? Shike Nan zasu dauka fa tayi yaji ne dole ta magantu.
"Wai Dan Allah Aunty Rukayya ku kasa barina nayi kwana ko Daya ne a gurin Ummata nifa bada wata manufa ba na taho kawai dai nasan idan nace zanzo ba Bari Oga sameer zeyi ba zece saina nemi izinin....."
Sai tayi Shiru.
"Izinin wa za'ace ki nema?".
Gaba tayi kawai ta nufi gurin da Sameer yake tsaye jikin kofar driver, da wannan damar Ya Abba yayi amfani ya matso kusa da Rukayya yana fadin "Ashe Aunty tasha kuka zanso Naga kina matse hawaye".
Kallonsa tayi haka nan taji yayi Mata kwarjini.
'yar dariya tayi tana fadin "Ina yini?"
"Lafiya kalau beauty, ki saka min number ki Zan kira naji ya kukaje gida tunda sister Zahra har wayar tayiwa tawaye".
Ya karasa Yana murmushi itama murmusawar tayi tana karbar wayar, number ta saka Masa ta Mika Masa wayar tana fadin "bari na wuce ya Sameer Yana jirana"
Tayi gaba.
"Ok saina kira shima gurin Sameer din ya nufa sukayi sallama, ya leka ta window Yana yiwa Zahra magana.
Tunda suka dauki hanya ba Wanda ya Kara magana sai ajiyar zuciyar Zahra ke sauka kadan- kadan.
A hankali zahra ta bude Baki tace "Dan Allah oga sameer kayi hakuri na Bata maka Rai bada niyya nayi ba kawai dai Ina son Naga Ummah ne Naga kuma kamar bazaka yarda naje na kwana ba".
"Ba komai kawai, Daman Yanda su mommy suka tada hankalin su ne ya daga min hankali nasan ba Bata zakiyi ba tunda da kafarki Kika fice".
Shiru tayi tasan magana ce ya fada Mata a kaikaice, tasan a kule yake da ita kawai dai Batasan dalilin Daya hana yayi Mata buyaji ba, Dan taga alama ya iya tijara Yanda ya karewa Rukayya dazu ko shi yasa taja bakinta tayi shiru Yanzu.
Sha biyu da minti goma yayiwa Mai gadin gidan horn Saida ya leko shima Sameer din ya fito Yana ko waye sannan ya bude.
Yana shiga da motar Maimakon yaje kofar main parlourn sai taga yabi ta baya ya nufi wani gani Mai azabar kyau ko Ina tar kamar dauko ginin akayi aka aje ga wata 'yar baranda data hade ginin biyu an saka glass anyi kamar katanga da wasu irin flowers masu kyau a jere ana ganinsu gurin yayi matukar kyau da burgewa a kusa da steps din da ze sadaka da
Main parlour, Zahra ba tayi kokarin bude side din da take zaune ba, dan juyowa Sameer yayi "Dan Allah kada maganar nan ta fita kawai da safe ki fada musu mun Dade a Asibitin ne yasa Kika bamu dawo da wuri ba sun kulle, kiyi using da Nan kawai ki barsu su a can, Rukayya zata kawo Miki kayanki da safe kiyi idan Allah ya kaimu".
"To nagode".
Abinda ta iya fada kenan, ta bude ta fita Rukayya man ta fito tana fadin " Bismillah kizo muje na rakaki".
Tare suka jera suka hau zuwa kofar, ita Kanta kofar abin kallo ce ita Yanzu zahra abin har ya daina Bata mamaki so take taga iya gudun ruwan bayin Allah nan Kullum lamarin su ba baya yake ba gaba yakeyi daga Nan sai can suna shiga ta Kara jinjina girman lamarin Wai shi wannan abokin nasu wane irin kusancin ne a tsakanin su da za'a dunga sauke ta a duk inda akayi ra'ayi. Wannan part din yafi wancan komai parlour sun Kai hudu, a cikin parlour na uku ne suka taka steps ya Kai shida sannan suka shige want korido ko Ina tadal sai wani special kamshi ke tashi bedrooms ne guda biyu a jere, Rukayyar ce ta Dan juyo tana murmushi "to madam gasu Nan saiki shiga Wanda kike so ki kwanta, tunda kin samu muna yawon dare kamar marasa gaskiya, Zan Baki shawara sai kin Zama jaruma fa a gidanki Dan Ya Mahmud wallahi Mata rubibinsa suke, idan kikace Abu kadan Zaki fece kece ki tafi kece a kwana Dan idan yayi wata tafiyar sai ki kwana hamsin Baki saka shi a idonki ba, pls you have to be very strong gaskiya kada ki yarda a gano Ina kike da lapse akwai damuwa kwarai ki rike mijinki da kyau ki mutunta shi ki girmama iyayensa zakiji dadin Zama dashi in Sha Allah, zabi na rakaki dakin na wuce barci Kuma nakeji tunda Allah yayi Mana gyadar dogo ya rabamu da kwanan zaune to matar big bro ta Bata Ina Ni Ina barci ai sai kwana sallah".
Ta fada tana 'yar dariya.
"Ki sakani kowanne Wanda za'a sanwa ya taba cewa way gutsiri nan? Duka zaman na yau zuwa gobe ne Dan gida zamu koma bana son wani surgery a Nan idan ma yimin din za'ayi ba wannan Mai fuska kamar Jan karas din zatayi min ba muma muna da qualified a can Dan dai kada nayi musu dashi ne kawai".
"Kinga mu Shiga na koma dare Karayi yakeyi gara naje na kishingida".
Dakin da yake facing dinsu ta bude MashaAllah" ta fada Tana karewa dakin kallo sannan ta juyo tana fadin mu kwana lafiya"
Kallonta Zahra keyi tana son tayi Mata tambaya Amma ta rasa ta Ina zata Fara, Dan Yanda tasan gudan Nan da Yanda take fadar wasu abubuwan akan Mahmud ga Kuma abinda Hajiya kakarsu ta fada Mata dazu maganganun suna kamanceceniya da juna amma Bari ta Adana tambayoyinta da sauran lokaci.
"Nagode Aunty sai da safe, Amma fa Ina Jin tsoron gurin nan fiye da can din wallahi, Kinga Nan ba kowa. Allah mu kwana tare ko kin tafi bazan iya barci ba".
Dan Jim tayi tana tunani ita Kanta Bata San dalilin Ya sameer na kawota Nan ba, amma tasan dole da dalilinsa nayin hakan.
"Ok ba damuwa Bari naje na dauko sleeping dress Dina da naki saina dawo"
"Ok, yauwa Aunty ki taho min da phone Dina tana cikin bedside".
Ta nufi Hanyar fita, wayarta ce ta dauki ringing number ce tasan Wanda ya Karba ne dazu a ta daga da sallama suka Kara gaisawa ya tambaye ta ya suka zo gida ta fada masa lafiya kalau sukayi sallama ta fice.
Kofar ta rufe ta farko tayi gaba tana fadin "kamar wata Rukayyar mahaukata na shigo wannan part din na kwanta a can ma naki kwana ballentana a Nan yarinya Allah ya kawo mijinki ki tarairayi kayanki kuna gefe Naga alama sai nayi Mata budedden karatu sannan zata gane mace har Mace ta fita kunya Amma ki tsaya kina Wasa da damarki".
Ta wannan barandar Mai glass ta Shiga Daya part din da yake tasan wanancin lambobin kofofin tunda duk sati suke zuwa da sauran yaran gidansu suna gyara bedrooms din kawai sauran Kuma da masu aikin da sukeyi dakunan kwanan ne dai Batasan dalili ba masu aiki basa shiga.
Ko Ina tsit a gidan baka Jin komai sai kukan kananun kwari da dai daikun tsuntsaye ta gefen inda zahrar ta kwana ta wuce da gaske ko ita data Saba da Shiga gidan wani lokacin tsoron Yana kamata bare a irin Nan da sauri ta shige parlourn na uku ta wuce corridor da za sadata da dakunan.
Tana bude dakin zilai ta bude ta fito tana fadin "sannunku da dawowa, Dan Allah lafiya kuwa tun rana sai Yanzu sha biyu ta wuce?'.
"Lah ba wani damuwa munje unguwa ne motar ta samu matsala sai dazu muka shigo garin muka biya gidan mommy a can muka Shantake Sai Yanzu ya Sameer ya kawo mu".
Wani sanyi zilai taji a ranta, "to ai shikenan Allah huta gajiya da ko barci na kasayi ina ta tunani barkatai".
"Kai haba ba komai Allah ya tashe mu lafiya ta bude kofar ta shige itama Zilan ta Koma ciki.
Tun bayan fitar Rukayya zahra ta dosana gefen ta zauna ta zabga uban tagumi, da sauri tashi ta fito ta dauko handbag dinta ta biyo Hanyar da suka shigo kofar fitar ta murda tajita bam ko motsi batayi, tayi tayi taji kamar tana taba dutse, hakuri tayi ta juya sai lokacin tsoron ya rufeta da gudu ta shige dakin tana turo kofar, dube-duben makulli kofar ta Farayi ita dai bataga gurin wani key ba har zata hakura taga wasu numbers a jikin wani Abu kamar switch din kunna wuta numbers din ta Danna Yanda suke a jere taba taba ta karshe taji want Dan sound daga jikin kofar handle din ta Kama zata bude taji ta rufe gam, sai lokacin ta Dan samu peace of mind, ta nufi gadon ta aje jakar a gefe ta nufi toilet dole saita sake gyara jikinta. Tana Shiga ta cire rogar material din sajida data sako ta taho da ita ruwan zafi ta hada tayi wanka ta fito da towel a jikinta sanin ba wasu kayan sakawa a Nan yasa ta Haye gadon daga ita sai towel ta rage hasken dakin ta janyo lallausan bargo ta rufe jikinta sai fuskar kawai ta Bari a hankali ta Fara Addu'oin kwanciya barci, kafin ta Gama barcin yayi awon gaba da ita.
Karfe Daya da rabi daidai jirgin Max air ya sauka da duban jama'a daga kasahe daban daban na duniya, cikinsu harda Muhmud Muhammad Dange, a hankali yake tako stairs din jirgin sanye yake da kananun Kaya Ash T- shirt da black jeans a jikinsa sai jakar laptop dinsa a kafadarsa.
Yana karasa saukowa wani matashi fari marar jiki ya nufe shi Yana fadin "barka da sauka yallabai, ga key din motar Nan a hannunta oga yace na kaika gida, sai Balarabe ya bimu da wata motar sai mu dawo tare dashi".
Hannu ya mikawa Mai bayanin Yana fadin "bani key din kawai kace masa na gode kwarai da kulawasa, zanyi driving da kaina".
Mika masa Yana fadin "Allah ya tashemu lafiya kayi min godiya sosai ya Ciro kudin America ya mika Masa sannan ya bar gurin.
Lokacin Daya fito daga airport din Daya da minti ashirin da bakwai, tuki yake cikin nutsuwa sau biyu kawai ma'aikata suka tsayar dashi, har yazo gate din gidan ba Wanda ya Kara tsayar dashi, sau Daya yayi Horn Mai gadin ya falfalo da gudu yana leken waye a Nan baisan motar ba Dan haka ya koma ya dauko abinda ze Bashi kariya.
Kafin ya bude ya fito, Mahmud ya fito ya harde hannusa a kirjinsa ai Mai gadin Yana ganinsa yayi sauri ya koma da gudu Yana Fadin "barka da sauka fari Mai farar Aniya Allah ya Kare gabanka da bayanka baya Mai goya marayu"
Dan murmusawar Mahmud yayi Yana fadin "wani Abu sai Malam Musa shi Babu ruwansa da dare". Ya fada Yana kunna Kai harabar gidan wadda take kamar rana, mutane hudu ne suka bullo daga mabambantan gurare. Parking lot suka nufa sun San Mai gidan ne tunda suka jiyo hargagin Malam Musa. Shima da gudu ya karaso gurinsa Yana cigaba da Yi Masa kirari.
Sun gaisa sosai dasu har kusan minti biyar sannan yayi musu sallama Saida safe ya nufi babban part din, Murtala ne yayi sauri ya sameshi "yallabai Ina ganin madam din kamar tana can sabon gurin can Dan Nan Naga Sameer ya ajesu dazu ita da Rukayya kanwarsa, can ya nufa Yana mamakin me yasa Sameer ya kaita can alhalin yace a barta a tsohon part din.
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Page 44
_________ kamshinta ya Faraji Yana shigowa parlourn, wani limshe idanu yayi Yana ayyana abubuwa da yawa a ransa, direct ya wuce bangaren bedrooms din Yana jinsa cikin nishadi, wato Sameer Yana expecting dinsa ne a kasar shi yasa ya bude Mata nan kenan, a hankali ya taba handle din kofar farko ya jita a bude Shiga yayi komai tsab, iska ya huro daga Bakinsa ya aje jakar laptop dinsa a Kan sofa da take dakin, ya zauna a gefe Yana cire takalman kafarsa, wanka yake son ya Fara kafin ya Shiga gurin waccen danger girl din "yar yarinya ta Hana shi sakat duk ta birkita Masa Lissafi" ya fada a fili Yana rage kayan jikinsa.
Wanka ya shiga bai wani dauki dogon lokaci ba ya fito saboda dare ya Fara nisa ga gajiyar zaman guri daya, pyjamas ya saka masu kalar sky-blue ya fesa turarensa ya dauki wayoyinsa ya fice daga dakin ya nufi dakin da zahrar take, wani Abu ya taba mai Kama da socket din electric na kunna wuta sai kofar ta bude,a hankali ya shige Yana Jin kamshinta yanda ya cika dakin, shi dai yawanci duk matan da suka zamar Masa dolensa suna bala'in son kamshi, yana ida shigowa kofar ta rufe Kanta Wai Abu ya taba ba Wanda zahra ta taba ba, yayi gaba Yana nufar gadon inda ya hangeta ta kudundune cikin bargo, da gani a tsorace tayi barcin, wayoyinsa ya aje a Kan bed side ya zauna a gefen gadon Yana Kare Mata kallo, shifa duk hankalinsa ba a kwance yake ba tunda aka fada masa matsalar dake damunta yaji ba shida sauran nutsuwa idan ba zuwa yayi ya ganta ba, Kuma Dole ma yasan abinyi akan ciwon Nan ko ana Wasa da wasu lamuran Banda lafiya baik'i tasan kowaye shiha a wannan lokacin dole ya dauketa ya kaita inda za'a dubata Masa ita duba na gaske.
Remote din AC ya dauka ya rage gudunta dakin yayi sanyi da yawa duk da Yana son sanyi amma wannan yayi yawa, a hankali ya saka hannu ya janye bargon daga fuskar ta barcinta takeyi shower cap din dake Kanta ta cire sai gashi Baki sidik Yana ta walqiya a cikin Dan hasken data Bari a dakin, Kara zame rufar yayi har zuwa kirjinta jikin sai wani glowing yakeyi Jin sanyi Yana shigarta yasa ya juyo da fuskar ta inda yake zaune "ya Salam". Ya fad'a a hankali, gani yayi ta Kara yi Masa wani kyau na musamman, Kare mata kallo yayi yaga daga ita sai towel a jikinta, murmushi yayi da gani Batasan da Kaya a dakin ba.
Kayan jikinsa ya cire ya Zama daga shi sai boxer short ya shige jikinta ya janyo lallausan bargon ya rufesu Yana sauke ajiyar zuciya, a cikin barci taji an rungumeta gaba dayanta jikinta ne ya dauki rawa shikenan tasan tata ta Kare shi yasa suka nemota da tsohon dare suka kawota Nan Yan ko wane irin ihu zatayi ba Mai jinta, cikin murya Mai rauni tana cracking ta Fara farin "innalilllahi na Shiga uku wayyo Allah na....
Bata katasa fadin abinda tayi niyyar fada ba taji yace "shittt...Ni ne fa cool down precious ba abinda ze sameki a cikin gidan Nan sai ikon Allah, akwai kyakykyawan tsaro".
sansanyan kamshin turarensa ne ya shiga hancinta, kokarin kwace jikinta takeyi Dan yayi Mata kane-kane so take taga zahirinsa Amma ya Hana hakan, ita mamakinta Daya yaushe yazo garin kuma ta Ina ya shigo Dan ita dai tasan ta rufe kofar nan. Dai dai kunnenta ya saka Bakinsa "ki kwanta muyi barci na gaji da yawa kin hana duniyata kwanciyar hankali kina min kisan mummuqe ko wayar ma kin haramta Mana yinta, tunda Naga alama Nima Mai laifi ne". Ya fada yana shafa gashin kanta zuwa bayanta, hannu Daya yasa Yana zare towel din data daura a jikinta da sauri ta rike tana girgiza Masa Kai.
"Dan Allah ka Bari bafa kyau muyi barcin to".
Wani guri ya taba a jikin gadon wasu irin fitilu suka Kama kamar star masu haske sosai, Bata ankara ba ya fizge towel din gaba Daya daga jikinta Yana Mata wani mayen kallo hannu tasa ta kare kirjinta cikin matsananciyar kunya tace Masa "Dan Allah ka kashe hasken Nan wallahi kunyarka nakeji".
"Ni kike Jin kunya?"
Kai ta gyada Masa, 'Well done Yanzu kuwa Zan cire kunyar nan daga idonki".
Wani bed sheet data gani a gefen gadon ta janyo da sauri ta lullube jikinta dashi tana Kara sadda Kai kasa Dan da gaske ya saka taji kunya sosai.
Wutar ya kashe ya matso sai Jin mutum tayi ya shigo cikin Bedsheet din data rufa dashi ya hanye shi ya maye gurbinsa da lallausan bargon.
"Ki hanani Zama a gurin neman abincina sannan na dawo ki Kama guduna, ai impossible wallahi muyi barcin da safe mayi bayanin".
Ya Kara mannata a jikinsa suka samu body contact da kusancin zahiri.
Sun jima yana sarrafata.Tayi laushi iya laushi dan da gaske da kishirwarta ya shigo garin tamkar mayunwacin Zaki badan tana cikin rashin tsarki ba da Babu abinda ze Hana labarin sauya salo, dan tuni ya wani manta da Alkawarin da ya daukarwa Kansa, Saida tafiya tayi nisa ya ji abinda yayi Masa cikas Dole ya saurara Mata, sun kai kusan karfe uku da rabi a haka shi Mai fad'ar barci ya keji sai gashi ya bige da Hana Mai barcin yin Bata barcin.
Sai sauke ajiyar zuciya suke su duka har lokacin hannunsa Bai daina shafe shafe ba, wani irin yanayi jikinta keyi har mararta ciwo ta Dan Fara Mata cikin dashashshiyar murya mai dauke da salon shagwabar da Batasan iya ba,ta kankame Shi jikinta na wata irin tsuma muryarta ta dishe tamkar me yin mura ta Fara magana.
"Dan Allah ka bari wallahi marata ciwo takeyi...".
Baiyi magana ba sai kakkameta da yayi kamar ze shige jikinta shima ya hade bakinsu Yanda ba Yanda za'ayi ta iya furta wata maganar ba, hannunsa ya tura Yana shafar marar ji yayi tadan tasa kamar ta Dan kumboro, hannun ta rike tana girgiza Masa Kai.
Zare hannun yayi ya dawo dashi sama yaci gaba da sabgarsa ya Kuma ki sakin bakin da zatayi korafin, suna haka har wayarsa ta Fara rera kiran sallah.
A hankali cikin muguwar kasala ya saki bakinta yana Maida numfashi da sauri da sauri gefe ya margina Yana dafe da tasa marar idanunsa a rufe, Zahra naji ya raba jikinsu ta Kara takurewa a cikin bargon wani irin tsoro ne ya lullube ta da gaske yazo Mata da wani lamari Mai girma, ita ai ko idanu bazata yarda su hada ba ai da kunya wallahi duk yabi ya tsorata tas ya lalube ko Ina na jikinta, Ashe can baya Wasa ne kawai yayi Mata yanzu ne ya nuna Mata true colour dinsa tana ganinsa salihi Dan bawan Allah Ashe shima guda ne ba gyale ba, kirjinta sai zogi da ciwo sukeyi mata yayi son ransa da jikinta.
Tana jinsa ya tashi ya shige toilet ya jima tana jiyo motsinsa, sannan taji ya fito alamun tsayuwarsa taji a Kanta,a hankali ya saka hannu ya janye bargon kankame jikinta tayi Dan daga ita sai pant Kare Mata kallo yakeyi take yaji alwalarsa na neman warwarewa, laimar hannunsa ya Dan yarfa Mata a jikinta "wash...Allah na!".
Mayar Mata bargon yayi ya shige clothset din dakin jallabiya ya sako Fara tas da hula mahadinta raka'atanul fajri yayi, jikin gadon ya matso ya Dan zauna "zanje masallaci".
A dawo lafiya tayi Masa tana kudundune Yanda take, tanaji ya fice daga dakin.
Sai ta tabbata ya Kai masallacin sannan ta yunkura ta tashi ta nufi toilet, tsabtace jikinta tayi sannan tayi wanka ta fito,lotion din data gani ta shafa sai body mist na itacen sandal wood Dana oud ta hada ta fesa kayan da zata saka ne ya zama cikas Dan bazata iya mayar da Wanda ta cire ba Kuma bazata Kuma Zama da towel ba tunda taga abinda hakan ya janyo Mata, Shawarar duba clothset din tayi idan taga Kaya sabo Kona waye zata saka, tana mamakin ace Mai gidan Nan bashi da Mata Kuma ya sakarwa abokai irin haka baya gudun a ring aikata fasadi a cikinsa, were Dan wannan sai ka shekara a ciki ba'asan kana nan ba.
Ba karamin mamaki tayi ba ganin kayan Mata masu yawa har Sunfi na wancen apartment din ba wani d'ar undies ta saka ta saka doguwar Rigar material Bata daura Dan kwalinba wasu hulina na Mata ta gani da yawa ta duba kalar ash irin flowers din jikin material din ta saka a Kanta, barci takeji sosai Dan tunda Allah yasa ya tasheta da aalonsa Bata Kara rintsawa ba shiko gogan Allah besa an raba barcin jiya dashi ba.
Harta juyo zata bar gurin taji tana son ta bude dayan side din, kayan make up ne dasu turarika shoe and bags turaren ta dauka tana dubawa duk yawanci irin nata ne sai wasu irin nasa ga Kuma kayan maza nan Lodi Lodi dasu underwears tana tsayen tana dubawa taji kawai an rungumota ta baya, ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe ido Sam bataji alamun bude kofa ba ko takun tafiyarsa, Kansa ya Dora a kafadarta Yana Dan hura Mata iskar Bakinsa a kunne "Good morning my previous".
"Morning Yayana".
Ta fada da wani salo, juyo da ita yayi suna facing din juna.
"Bude idonki ki kalleni ki fada min waye yayan naki? Wato har yanzu da sauran Rina a kaba kenan ko? Nifa bazaki tauyeni ba Ni ba wani Yayanki bane a bani special name Dina, kodan kinga mu 'yan gargajiya ne "ya'yan Alarammomi Malam soro, bamu da wayewa irin taku ko?"
Batasan lokacin data sauke ifanunta a Kan nasa ba, tana jinjina maganarsa.
"Wayewar saita kasheku".
Tayi subul da baka ta fada harga Allah a zuciyar ta tayi niyyar fada bakinta ya subuce ya fada.
"Kai! Nine wayewar saita kashemu to nida waye zata kashe din?"
Kauda Kai tayi tana Jin kunyar maganar.
*Ni ba haka nake son fada ba Bakina ne ya furta hakan".
*Ok, zomu kwanta barci nakeji tunda kin hanani barci da fitinarki".
Rigar ya zuge zif din ya cire mata ita ya barta daga ita sai undies kawai ya dauketa can ya nufi bed din da ita tana mutsulmutsultun ya sauketa ya kiya Saida ya dangana ta da saman bed din, shima jallabiyar ya zare ya janyota ya lullubesu da gaske barcin za'ayi Dan tunda ya sakata a jikinsa Bai Kara yi Mata komai ba.
*** *** ***
Tunda Ammi tayi sallah Bata Koma barci lazimi ta zauna tana yi amma zuciyar ta Babu dadi kwanan nan kusan Kullum sai tayi mafarkin Mahmud da wata yarinya budurwa Yana rike da ita da hannu Daya dayan Kuma Yana ta faman fada da wasu irin halittu mara kyawun gani, to yau ma shita Karayi Saida taga wasu mutane dattijai guda biyu sunzo sun Taya Shi kashe wadannan halittun sun tasa su shida yarinyar har wani gida sai da suka shige sannan suka juyo suka tafi.
A haka Mai gidan ya sameta Saida ya zauna ya Kare Mata kallo yasan da akwai damuwa a tare da ita sai dai tana kokarin biyewa.
"Ammin Yara me yake damunki duk kwanakin Nan Baki da walwala Sam ko kula dani ma tayi baya ko Baki huce bane har yanzu?".
Kai ta girgiza "A'a kawai dai lamari Hussain ne yake damuna kofa da Rana Daya Bai taba kirana ba ko sako ta email Bai taba Yi min ba, gashi a kwanakin nan sai wasu irin mafarkai nakeyi dashi marasa dadi abinda yafi tsaya min a Rai Kullum da wata yarinya budurwa kamar 'yar India nake ganinsa da ita Ina tsoron wani Abu wallahi na rasa yanda zanyi Dan Allah kayi wani Abu akai".
Sai hawaye sharrrr.
"Subahaballahi! Haba zainab ya Zaki ringa yi Masa kuka kinsan masifar zubarwa da d'a hawaye kuwa ko wani abun yake aikatawa ai saiya karu idan kina Masa kuka, addu'a zamuci gaba da Yi Masa nifa jikina Yana bani Yana Dubai Dan last week na samu leakage akan Yana can din Dan yayi wasu ziyarorin bazata a can harya dakatar da wasu ma'aikatansa sai dai duk kokarin a gano min masaukinsa sabo hakan yaci tura Dan ba'a inda yake sauka ya sauka ba tunda gudun hijira yayi".
Hawayen ta goge ta tashi tana ninke sallayar ta zauna kusa dashi. "Shikenan Allah ya shiga cikin lamarin ya kureshi daga sharrin zinace zinacen zamani wallahi badan komai nufin Allah bane Wanda yaso yake bawa kyautarsa danace dama bashi ya samu wannan budin ba da kananun shekaru to yanda yaso haka yake tsara kayansa, Amma ga yayunsa Nan ba Wanda ya takura musu Suma ai suna da wadatar,tunda Allah yayi muku karfin arziki waye talaka a cikin family din nan?".
Dan murmushi general yayi Yana kallon yanda take fadin magana abinda ba halinta ba inda akan twins ne sai dai wani yayi magana Amma ta zage tana fadin son ranta.
"To ya zamuyi da hukuncin Allah shi yaso ya daukaka a cikin zuri'ar da Wanda ya Isa yace a'a Ina cewa Alhaji Ishaq ne ya bashi jarin Daya Fara sana'a dasu tun Yana hannun Hajja, Amma yanzu zaki hada arzikinsu ko kusa ko alama Babu Hadi,.koni Dana haifeshi ya mallaki abinda bani da kwatqnkwacinsa, Keda Kika haifeshi kin mallaki abinda yake dashi? To kiyi istigifari ga Allah tunda shine yace Yana azurta Wanda yaso ba tare da hisabi ba,ai kin gane?".
"Na gane Allah ya Zama gatansa a duk inda yake,Amma fa yarinyar Nan ta tsaya min a rai idan Yana kusa da wannan ai zai manta da kowa ne tunda cikin bacin rai yabar gida ga Kuma kudi a tare dashi kaga sai Allah kadai ze kare shi".
Dariya ta bashi sai da yayi sosai kafin yace.
*In Sha Allah in dai Zina gado ce to Alfarmar Manzon Allah s.a.w.w zuri'ar mu bazasuyi ba Ni ba mazunaci bane haka kema ba ita bace in Sha Allah.Allah baze jarabcemu da ita ba, Kika sani ko bushara ake Miki ke uwa kin samu sirika".
"Haba dai har abun ya Kai haka yayi aure ba sanin iyayensa ai kuwa da lamarin ya lalace".
'yar dariya yayi.
"Kedai kije ki shirya min breakfast daurin Aure zamuje kabba na Dan gidan sanata Abdul Aziz"
"Ok.bari na shiga kitchen din"
Ta tashi ta fice tana baza kamshinta as usual.
******
Tun idar da sallar Rukayya ta taso ta nufo part din da zahra ta kwana,abin mamaki an canza pin kofar dan ta kwada yafi sau goma Amma taki budewa. Nan da Nan taji hankalin ta ya tashi me Kenan badai wani bane ya shigewa 'yar mutane ba gashi jiya Taki Kai Mata wayarta da ba saita kirata ba, gudun kada tace sai sun kwana ya hata ta Kai mata.
Number ya Sameer ta lalubo lokacin Yana barci,
Yana dauka ko gaishe shi bata tsaya yi ba ta Fara fadin "Ya Sameer ka taimakeni wallahi tun sassafe bake kokarin shiga part din da zahra take Amma kofar kofar kamar an canza pin din na saka yafi sau goma Amma yaki budewa".
Tsaki yayi "Waike Dan Allah Ruky yaushe Zaki girma ne? to oga ne ya shigo cikin dare Nima da asuba naga text message dinsa Dan haka ki Zama ready idan na shigo saimu wuce tare Amma yanzu kada kuyi komai za'a kawo abinci".
"To ai su Iya Rahane har sun kusa gamawa baka fada min ba tun dazu".
Ok, ba komai sai a hada tunda gidan da jama'a, yauwa zuwa an Jima ki bude musu part din Nan na kusa da parking lot sai su zauna a nan tunda shima ogan Bai san ze shigo kanon ba harsu Gama su koma to matsalar madam din ce inaga ta caza Masa Kai Wai cewa fa yayi daina amsa Masa waya tayi".
"Kamar ya Bata amsa masa waya? Batasan kowaye bane da zata ringa yi masa haka?"
"Eh kusan hakan ne gaskiya"
"Allah ya rufa asiri" ta fada.
Sukayi sallama ta kashe Kiran tana dariya "su oga anzo hannu ana walagigi da rayuwar 'yan Mata gashi kaima kazo hannun yarinya tana juyaka son ranta, nasan bana raba Daya biyu saboda shi ta rufe wayarta jiya, taki magana dashi a wayar Ya Sameer karshe ma ta sakata jirgi, yes! Haka nake son irin matansu su kasance, idan suka samu wadda ta mace a kansu ta Zama sorry Amma wannan ta shuka mulkinta yanda takeso tunda Batasan waye shi ba".
Ya juya ta koma kitchen inda tabar su zilai suna aiki, tana shiga zilan tace Wai ni lafiya yarinyar Nan? naji shirun yayi yawa ko dai rakani zakiyi na gano lafiyarta kada na Zama babbar kwabo an hadoni da yarinya nayi wasarere da lamarinta".
'yar dariya. Rukayya tayi "gaskiya kinaji da matar big bro irin wannan shiga damuwa jiya fa ko barcin kirki bakiyi ba kina zaman jiranmu yau ma tun Asuba kike ta nemanta, ki kwantar da hankalin ki Aunty sirikinki ne ya taho ba Shirin wannan 'yar taki tsaye ce taki saurarensa ko a waya dole ya tsallake hidimominsa ya nufo Nigeria".
Iya Rahane ce ta aje Wukar hannunta tana duban Rukayya "kikace uban gidan mu ya shigo garin?"
"Kwarai kuwa iya jiya cikin dare ya shigo Kinga kuwa sai ki fadawa Aunty ta kauda Kai kawai gurin son ganin 'yarta ba yanzu ba gaskiya, Dan haka da an gama aikin Nan zamu bar Nan Bangaren mu koma wancan".
"Wannan gaskiya ne inba tayi dalili ba yaushe zamu shigo wannan guri harda kwana a cikinsa, Amma dalilin uwar dakinmu mun dangwali arziki ai wannan ba komai bane akan gidan da aka sauke mu a sokoto, Kai Naga inda arziki ya amsa sunansa wannan yaro uwarsa tayi farar haihuwa wallahi Nan kusa Banga mutane masu karamcin su ba, uwarsa yarinya karama sai halin girma".
Ita dai zilai sai ta rasa Wai wannan maganar dawa ake ne waye suke zance a kansa ne ita fa maganar Zahra take musu su Kuma sun kamo wata tashar Ina hadin zahra ba Wanda suke magana a kansa ko dai Mai gidan ne ya dawo Basu gane me take nufi ba, ita Zahra matar Almajirin Malam Bukar Wanda gidan zaman ma na Baba Malam ne mutanen da yaje yiwa aiki turawa suka gyara Masa shi, to Ina shi Ina wannan Aljqnnar duniyar suda aka kawosu zaman 'yan kwanaki na ganin likita.
Cikin nuna mamaki zilan tace "ikon Allah ai ban sani ba kice da anyi uwar banza gara da Kika fada min kada naje nakai kaina girma ta Fadi".
"Ai Koda kin shiga basa Nan ba a nan suka kwana ba".
Wayar Rukayya ce tayi qara ta dauka ta fice daga kitchen din shine abinda ya Hana zilai fadar abinda tayi niyyar tambayarki Rukayyar.
Hira iya rahane taci gaba da yiwa zilai a Kan Mahmud amma ko Daya zilan Bata gano ainishin waye take magana a kansa ba.