Gabatarwa
Aure Da Karatu Part 1 Complete Hausa Novel · about 36 min read
*AURE DA KARATU*
*RUMAISA SIDI*
Page 1 (dandano)
Kamar yanda na riga na al'adanta na gyara gidana tareda kicaniyar hadawa 'yan makaranta abin kari sauri-sauri nake komai saboda banson suyi latti har takai ga an dokesu a makaranta
Duk abinda nasan zai saka yarana farinciki har su aje hankalinsu suyi karatu inayi kama daga kan cimarsu,suturunsu( uniform) har izuwa abubuwan da zasu taimaka musu suyi karatu duk term nake canja musu uniform saboda makarantar kudi sukeyi suna ganin yanda akewa sauran yara to nima ina bakin kokarina gurin yin abinda zan iya saboda kullum ina nuna musu ba zaka taba cimma wani ba kaima wani bazai cimma ba
A kan wannan na dorasu suma akanshi suka ginu duk abinda suke so ina kokari in musu da dan abinda nake rufa ma kanmu asiri
A halin yanzu ba abinda nakeso sama da yarana su kadai ke sakani farinciki su kadai suka ragemin idan har kaga dariyata to ina tsakiyar yarana suna min labarin makaranta da kuma burikansu da kullum suke kara yawa a kaina
Yarana uku Safwan shine babba shekararsa 12 sai Aysha dake binshi ita kuma shekararta 9 sai auta Amra 'yar rigimata kenan itama shekararta 6 kuma farincikinmu gaba daya
Karfa kuga na cikaku da zancen yarana ku kosa dani ko kuyi tunanin ina b'ata muku lokaci ko d'aya labarin bazai tafi yanda nakeso ba sai yarana sun shigo a farkon labarina
Zakuce a ranku to duk wayannan yaran ina mahaifinsu?????
Mahaifinsu Lawal muhammad yananan kuma muna tare da shi har yanzu saidai.......................Jin girkina na neman konewa ya ankaraddani bayan dogon zangon tunanin da naje da sauri na hada wa kowa nashi saboda nima makaranta zanshiga saboda inada lecture karfe 10
Kukan Amra da naji yasa nayi saurin fita ganin fitowa ta yasa tayi gurina tana kara doka kafarta kasa irinna rigimammun yara
Mommy kinga Esha ta dakkomin socks ko? hannunta na rike ina karasawa cikin falon
Ina Eshar? meyasa zaki dauka mata socks?
Wallahi mommy bandauka mata socks ba kawai na duba na dau nawa shine wai tunda na taba mata abu saita rama a tawa
Murmushi nayi araina nace "Rigimammiya"
Daurewa fuskata nayi sannan na nuna Aysha "Karki kara tabawa shalelena kaya bakisan batason ana sama ta datti a kaya ba karki kara"
Kama kunne Ayshar tayi tana kunshe dariya "Am so sorry mommy bazan kara ba"
"To kowa ya zauna kuyi breakfast tun school bus bata iso ba" shayin na hada safwan ya zubawa kanshi ya zubawa Aysha ni kuma aka barni da 'yar lelena (dama aikinta sai ni)
Tsittt naji gidan yayi bayan wucewarsu zama nayi nima nayi break sannan na hada kofunan da mukayi amfani da su na wanke sannan na wuce dakina don in shirya kar inyi latti
Kallo guda nayiwa gadon da yake kwance na kawadda kaina inada tabbacin ko sallar asuba baiyi ba don yanda na fita na barshi haka na dawo yanzu ma na sameshi
Har nayi wanka na shirya yananan kwance saida na kammala komai sannan naje gefen gadon daurewa nayi na taushe abinda nakeji idan tuna abinda yamin jiya bubbuga filon na shiga yi
"Abban safwan" na shiga kiranshi a hankali kar yace na mishi ihu amma shiru Filon naci gaba da bugawa juyawa yayi yana yamutsa fuskar da har yau na kasa tantance abinda na gani gareshi da har na dage sai shi
A kufule na buge filon wannan karon sai gashi zaune tsakiyar gadon yana aikomin sakon harara " Waike wace irin matace kashemin dodon kunne za kiyi? tun safe keda yaranki kun ishi mutane da surutun tsiya yanzu kuma ke kinzo min ihu a kai"
Hadiye bacin raina nayi sanin ba abinda zai amfana min "Dama zan wuce makaranta ne kuma gidan ba kowa ba'a san mai shigowa ba"
"Yanzu dama saboda banzar makarantarki za ki hanamin bacci nasha gayamiki ba abinda ya shafeni da wata makaranta taki idan kin cika in kinje karki dawo kuma wallahi idan har kika wulakanta min aure ke da Allah"
Sauri-sauri na bar dakin ina mayadda kwallar da ke neman zubomin tare da tunatarda kaina alkawarin da na daukarwa kaina na bazan kara zubarda hawayena akan Lawal ba
Tunda na shiga makaranta na watsar da tunanin damuwata na fuskanci abunda nazo yi lecture daya ce dama 12 na fito daga makaranta inata sauri in isa gida in hadawa yarana abinci kafin su iso
Cikin sa'a kuwa muna fitowa na samu napep na shige ina yiwa abokan karatuna sallama ina jin lokacinda Nafisa ke cemin "Sai gobe uwar son 'ya'ya" haka suke cemin wani lokaci suna ganin kamar na cika son yara ina musu uzuri wani lokaci saboda basu san abinda yasa nakejin kamar nafi kowace uwa son 'ya'ya
Kamar yanda na tsammananta yana zaune akan bencin mai shagon da ke haya kofar gidanmu suna gardamar siyasa "ai wannan fagen ka kware" na fada a raina kudin mai napep din na bashi ina kokarin juyawa yaro ya iso wurina yana bani mukullin gidan "gashi inji abbansu safwan" karba nayi tareda wucewa na bude gidan na shige
Hmmmmmm salon na dabanne🥰💃
Ga sabon littafin mu mai taken AURE DA KARATU comment dinku shi zai bayyana karbuwar littafin ko akasin hakan
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI
Page 2
Gyale na na kwabe tare da wucewa daki na watsa ruwa sannan na dauko doguwar rigata mara nauyi na dora hula akai na fito
Kaitsaye kitchen na wuce na shiga hadamana abinci jallof din shinkafa na dafa da dan sauran kifin da muka ci jiya sauri-sauri nake komai kar su dawo bankare ba
Karfe 1 dayan mintuna naji tsayuwar bus dinsu bayan na kammala hada komai Amra ce a gaba tana kwallamin kira "Mommy Mommy" tashi nayi tsaye kamar yanda muka saba kullum rungumeni su kayi su duka ukun kowa na fadin "Ni ne first, ni ce first" hadesu nayi duka ukun nima na rungumesu ina jin wata kaunarsu ta musamman tana ratsani tareda tausayinsu
Dakinsu suka wuce suka cire uniform tareda aje kayansu Aysha ta canjawa Amra ni kuma na zubo mana abinci kafin su iso yasha iska suma basu ja lokaci ba suka fito
Tsakiya na aza tiren abincin muka zagayeshi saida muka zauna na tuna da ruwa safwan na duba "Yaya dakkomana ruwa a fridge" tashi yayi ya dakkoma kowa sannan ya zauna muka fara cin abinci
Amra ce tasaka rigimar ita zata fara bani abinci wannan ka'ida ce idan muna cin abinci to kowa zai bani a baki nima in basu wannan karon ma kowa saida ya bani nima na basu bayan mun kare safwan ya gyara wurin Aysha kuma ta kai kayan kitchen
Jin an fara sallah safwan ya fita masallaci ni kuma na hadasu muka je muka yi sallah kasancewar yau alhamis ba islamiyya muka dawo falo saboda zafi gashi ba wuta system dina suka dakko suna game ni kuma na dau wayata ina duba costomers dina na whatsapp wayanda ke bukatar kaya ina tura musu suna zabawa
Na shafa'a ga mutanen arzikina har na ware ina chat da kawayena a wani group dinmu na makaranta har safwan ya dawo shima ya jone dasu Aysha suna game sam banji shigowarshi ba ganinshi kawai nayi a kaina "Wannan wane irin iskanci ne ana miki magana kamar bakyaji to yama za'ayi kiji kina hira da samarinki duk abinda kika fita kikayo bai isheki ba sai kincimin mutuncin aure a cikin gidana to wallahi baki isaba "
Kallon bangaren da yarana suke nayi suna nan zaune Safwan da Aysha sun sauke idonsu kasa amma sunbar game dinsu Amra ko kyam ta zubomana na mujiya "Safwan kuje dakinku kuyi game din" kamar mai jira suka mike
Saida naga wucewarsu sannan na maida hankalina gareshi "Haba abban safwan sau nawa zan gayama bai kamata kake fadar kowace irin magana a gaban yarannan ba ina gujema hakan ya janyo ma raini"
Kamar wanda ke jin haushina ya zaburomin "Raini na nawa kuma? bayan kingama nuna musu banida muhimmanci a garesu kina kallo nuna suke kaitsaye sun fi kaunarki a kaina kingama hore musu kunne wallahi nayi nadamar aurenki"
wani bakinciki ne ya tunzuromin nima na mike tsaye ina kallonshi cikin ido ina kara jin tsanarshi fiye da yanda nakeji "Kaine da kanka ka kada girmanka a wurin yaranka lawal kuma wallahi nafika nadama da danasanin aurenka bansan bakinciki ba saida na aure ka bansan wata cuta hawan jini ba sai a gidanka kaine..........." shiru nayi jin kowane irin lokaci kuka na iya kwacemin wayata na dauka na wuce daki shima a sanyaye ya juya yabar gidan
Da darema tare da Aysha na shiga kitchen na dafa mana abinci daidai cikinmu don alkawari na dauka bazan kara ciyadda shi ba zan nuna mishi wannan karon nima 'yar kodimo ce bazan kara daukar iskancinshi ba
Bayan mun kammala cin abinci kowa ya dakko littafanshi sukayi home work ina duba musu da inda basu ganeba ganin dare yayi nace suje su kwanta Amra tasa rigimar ita tare dani zata kwanta nace zuje su kyaleta "Ku tabbatar kunyi addu'a yaya"
Banjima ba nima na fara jin baccin tashi nayi nadauki Amra da ta dade dayin bacci dakinsu na kaita kayan wutar dakin na kashe tareda tofesu da addu'a
Shirin baccin nayi nima zan kwanciya naji yana kokarin rufe gidan na gyara kwanciyata kamar nayi bacci ya dan jima da shigowa gidan sannan ya shigo daki kamar mai tunani yayi tsaye tsakar dakin yana kallona sai can ya karaso yana buga filon da nake kwance kamar mai baccin kwarai na shiga kifta ido tare da tashi zaune "Yadai" na fada tareda dage gira ina kallonshi kame-kame ya shiga yi "Am nace MY ZEE baku rage abinci bane wallahi yunwa nakeji kuma naje gida na taradda Salma ta haihu tana asibiti to abincin duk ankai can"(salma kanwarshi ce da tayi aure shekarar da ta gabata)
Abin mamaki sai banji tausayinshi kamar lokacin bayaba da wancan lokacine da dasauri zan tashi koda abincin da zan cine to ni zan hanama cikina in bashi amma wannan karon kai tsaye na dubeshi "Wallahi babu shi duk mun cinye" daga haka na juya na gyara kwanciyata ina fatan bacci ya daukeni
Sai asuba na farka baya dakin da alama ba ciki ya kwana ba fita nayi na wuce dakin yarana na tadasu saida naga sun tashi sunyo alwala sannan na fito hangoshi nayi kan doguwar kujerar da ke falon karasawa nayi wurinshi na shiga tadashi kamar yanda ya saba kullum idan na tadashi wannan karon ma harara ya bankomin "Lafiya kuma" murmushin tura haushi na mishi sannan nace "Lokacin sallah ne yayi abban safwan nace bari in tadaka karka rasa jam'i"
Wani kallo yake bina dashi kamar ya shakeni"To ina ruwanki da sallah ta kabarinmu daya dake wai ni menamiki har haka zainab da kika bi kika addabi rayuwata ne ko so kike shima kwanan gidan in barmiki keda yaranki iye" ganin yanda yake daga murya kar ya janyo mana hankalin makwabta yasa na juya nashige daki kar in rasa jam'i wurin neman magana
Har suka wuce makaranta yau ma yana daki ni kuma ina falo ina duba abokan business dina ina yin order kayan da mutane ke bukata nishadin da nakeji ne ya jani izuwa status din jama'a ina kallo wasu hotunansu suke posting wasu kuma sana'unsu can nakai ga status din Hannatu cousin sister dina wakokin soyayyane kala-kala tayi status tareda emojies na soyayya murmushi nayi "Su soyayya manya" na fada a raina ina tuna irin soyayyar da muka buga nida lawal kamar ba gobe idan naga masoya suna zuba soyayya saidai kawai nayi dariya tareda fatan suga mai kyau don nikam ba abinda ta tsinanamin sai tarin bakinciki
Na tuna lokacin da lawal yake duke gabana yana kuka yana fadin "Ki taimakamin my zee kar na rasaki wallahi idan na rasaki to zan iya rasa raina na miki alkawarin rayuwa mai inganci nasan gidanku gani suke bazan iya rike ki ba saboda ina talaka wallahi zee indai kika aureni ko dako ne zanyi in ciyadda ke da abinda kika saba ci a gidanku"
A wannan lokacin nima zubewa nayi a gabanshi ina kuka "Ka kwantarda hankalinka Nisful ba abinda zai rabamu ni kai nakeso da kai zan zauna banajin kona second daya zqn iya kula namijin da ba kaiba na tabbata inhar na dage kai nakeso abba zai auramin kai dawowarshi kawai nake jira"
Hawaye naji suna zubomin "Allah sarki abba Allah ya gafarta ma gashi ka auramun abinda nace inaso na guji zabinka ni kuma ga abinda nake gani Allah na tuba ka yafemin"
Hmmmmmm muje zuwa dai🤔
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI
Page 3
Kuka nayi marar misali saboda tuno abinda nake kokarin mantawa taurin kai duk shi ya kaini ga fadawa halinda nake ciki a yanzu bana zargin kowa da lalata rayuwata sai ni da kaina mahaifina mahaifiyata yayyena da duk wani masoyina ba wanda bai shawarce ni akan abinda suke hangomin ba amma na take saboda wata banzar soyayya tawa banci riba ba sam ba wani amfani da hakan yamun
"Wannan wace irin mummunar dabi'ace me kuma aka miki yanzu da zaki zo kina min kuka a cikin gida ko sharrin naki ne ya tashi? to wallahi wannan karon a shirye nake da duk wani dan uwanki da zai nunamin yatsa ba wanda ya isa ya wulakanta ni "
Da kallo na bishi har ya shige kitchen hawayena na goge banjin zan iya kula shi a wannan lokacin na gaji da biyemishi duk safiya muna raba hali gyara kwanciya ta nayi kan doguwar kujera tare da saka earpiece ina sauraren karatun qur'ani ina fatan samun nutsuwa da rahama a cikin zuciyata saboda abinda nakeji kowane lokaci rashin lafiyata zata iya tashi
Dawowa yayi falon yana maganar da sam banaji saboda abinda ke cikin kunnena a hankali na sance kunne daya ina watsa mishi idanuwana da yake kira da oily eyes a lokacin da muke kan soyayyarmu yasha gayamin wani sanyi yakeji a ranshi idan ina kallonshi da su
"Ina breakfast dina fita nakeso nayi" Cikin isa yake maganar kamar wanda yasiyo komai ya aje ya zo ya taradda babu
"Hmmmm" na sauke ajiyar zuciya tareda kara kallonshi " Mun cinye" na fada kaitsaye tareda kokarin mayadda earpiece dina maganarshi ta dakataddani " bangane kun cinye ba kyaleki fa nayi ko jiya daga abincin rana har na dare ba wanda naci a gidannan yanzu ma don tsabar mugunta daga ke sai 'ya'yanki zaki cinye"
"Anzo gurin" na fada a raina " Banyi tunanin kana bukatar abinci a gidanka ba saboda duk maigidan da ke bukatar hakan fita yakeyi ya nemo ya kawo a dafa aci amma kai banga hakan a tare da kaiba kuma wannan abin da kake kiran ba'a baka ba wanda kace kafi karfin wulakanci a wurinsu ne suka aje kaga ko bazaka ci ba"
"Ai ba yau kika fara yimin gori ba Zainab ba yau kika fara nuna 'yan uwanki ke daukar nauyinki ba kuma ba wanda nace yayiwa 'ya'yana wata lalura abarsu su rayu kamar yanda nake rayuwa nima rashin sirrinki yasa kika gama zubarmin da mutunci a gurinsu shi aka nunamin tun farkon neman aurenki naki fahimta ana nunamin illolin auren 'ya'yan masu kudi amma kaddara ta riga fata don aurenki KADDARA CE"
Daga zaunen naji jiri na dibata "Lawal, Lawal ne ke kiran aurena auren kaddara? lawal din? wayyo Allah na" dishi-dishi nake ganinshi saboda hawayen da ya cikamin ido amma yanda ya bakanta min nima zan bakanta mishi gorin da yadade yana fadar ina mishi yau daya zan mishi yasan abinda ake nufi da gori " Aurena ya wuce ka kirashi na kaddara lawal idan har ni ban kira aurenka da auren kaddara ba kai kayi kadan ka kirani da hakan wace riba naci a aurenka bayan 'ya'yan da ke tsakaninmu? bayanshi ba komai kai kuma silar aurena ka mallaki gidannan da muke ciki da motar hawa kai har suturar sakawa lawal" matsawa nayi kusa dashi ina kallonshi ido cikin ido "Har abincin ci kasamu sanadina lawal nafi karfin ka kirani da auren kaddara" na karasa ina dukan kirjina jinake kamar in shake lawal sai ya daina numfashi na tsaneshi fiyeda tunaninku masu karatu
Shima cikin bacin rai idanunshi sunyi jajir ya shiga nuna ni hannunshi na rawa" Wallahi zainab ki iya bakinki kinsan dai igiya biyu ta rage tsakaninmu" tsaki na buga "to shine me? akwai wanda ke dannarka game da igiyoyin kayi yanda zuciyarka ke rayamaka akaina lawal"
A fusace ya juya ya fita daga dakin yana banko kofar kamar zai ballata jagwabb na fada kan kujera tareda dafe kaina da nakejin yana saramin kamar ana dokamin guduma har cikin idanuna nakejin ciwon da lalube na tashi na wuce daki na dakko magani na tsakiyar falon na zube ina haki dafe da kaina sunan Allah na shiga kira "Ya Allah ka kawomin dauki Ya Allah ka yafemin Allah na tuba na tuba ubangiji Allah kayi abinda yake mafi alkhairi a kaina Yarana Allah ka kawomun dauki ko saboda rayuwar yarana Allah Allah ka......." kuka ne ya kwacemin na kife kaina kan kafet inayi kamar wata karamar yarinya
Bansan loakci ya tafiba saida naji yarana a kaina ashe wai baccine ya daukeni a hankali na bude idanuwana da sukamin nauyi na sauke su akan Aysha da ke kallona kokarin tashi zaune nayi ina tattaro sauran karfina murmushi na musu "Kun dawo? baccine ya dauke ni ashe" hannuna Amra ta rike "mommy yau baki yi hugging dinmu ba" safwan ma matsowa yayi yana taba wuyana a razane ya zare idanunshi irin nawa (inji lawal) "Mommy bakida lafiya? jikinki zafi sosai mommy" sai hawaye " to miye na kuka kuma kamar ba namiji ba dubi kannenka suka kuka zasu yi common yarana ku kwantar da hankalinku naji sauki sosai" na fada tareda hadesu na rungume
Indomie na dafa musu ganin lokaci ya tafi dayawa daurewa naci gaba dayi saboda yarana dako tari nayi zakaji suna hada baki wurin fadin "sannu mommy"
Shareshi nayi nabawa banza ajiyarshi har dare ban kara kulashi ba shima shareni yayi dukanmu muna falo har shi nidai ina harkar business dina da wayata su kuma safwan na dubama su Aysha karatunsu shi kuma yana sana'arshi ta chat da kullum ko ya rasa na pure water bazai rasa na data ba
Ganin dare yayi na kashe data ta tareda tashi na dauke yarana da bacci ya dauke anan falon kayan kallon da kunna su bayada amfani nazo na kashe ganin yana falon nabar hasken falon ban kashe ba na wuce daki shirin baccina nayi ina gaba mirrow ina kichaniyar daure gashin kaina ya shigo
Tsaye yayi yana kallonta a ranshi yace "yarinyar nan fa bata tsufa wazai ganta yace ta haifi 'ya'ya har hudu a cikinta( bayanin ta hudun yana gaba) tun lokacin kuruciya zee kyakkyawace ajin farko yar kwalisa ba wanda ya taba tunanin zee zata aure shi kasancewar ta fito daga gidan manya kuma ba wanda baisan irin soyayyar da mahaifanta da 'yan uwanta ke nuna mata ba
Karasowa yayi gaban mirrow yana kallonta ta ciki "Kinyi kyau zee" gira na dage mishi ina kallonshi ta cikin mirrow " dama can ni kyakkyawace kaima kasan wannan" daga haka ta zame tareda nufar gadon ta kwanta tareda lullubo bargon har kanta ta rufe ajiyar zuciya ya sauke "hmmmm bazata canjaba kenan" dakin ya bari ya koma falo ya kwanta
Yau bacci nasha kasancewar weekend ce suma yaran daga sallah suka koma bacci sai wuraren 11 na tashi saboda kukan Amra "mai yara baya hutu" na fada ina saukowa daga kan gadon a gurguje na watsa ruwa na fito a jikin safwan na sameta tana shesshekar kuka mahaifinsu kuma na kwance kan kujera da remote a hannunshi yana canja channel
"Me aka mata" na tambayi safwan "Wayar abba ta dauka shine garin kawomin ta fadi sai....." hannu na daga mishi saboda nasan kwanan zancen "ku je ku shirya fita zamu yi da munci abinci" ai dagudu suka ruga har amra dake kuka
Kallo daya na mishi na wuce kitchen na hada mana abinci fitowa nayi jin yara na mishi addu'ar fita kamar yanda na koya musu "Amm nace abban safwan" na dakatar da shi ganin yana kokarin fita tsayawa yayi yana kallona karasowa nayi bakin kofar nace "Dama nace zamuje da yara muje muga babyn salma daga can in wuce gida" annurin fuskarshi ne ya bace da alama ba haka yayi tunani ba "Sai kun dawo" ya fada tareda ficewa daga gidan "can ta matse ma" na fada tareda juyawa nakoma inda na fito
A kofar gidansu napep ta sauke mu na sallame shi tareda shiga gidan tareda yarana gidan cike yake da 'yan uwansu lawal duk yayunshi mata su uku da sukayi aure suna gidan gaisawa nayi da wayanda ke waje yarana ma suka shiga gaida su cikin ladabi don ba alfahari ba indai a fannin tarbiyyane banida sanya ga yarana
Dakin mahaifiyarshi na wuce inda mai jegon take sallama nayi suna dakin har mama karasawa nayi gabanta na durkusa na gaidata kamar yanda na saba kullum har gobe ina ganin kimar matar "yawwa zainab ya gidan ya kuma yarannaku" sunkuyadda kaina nayi ina fadin "Duk lafiya lau muke mama ashe salma an sauka Allah ya raya akan sunna"
"Amin Amin zainab" matsawa nayi wurin mai jegon nabar su Amra wurin mama suna zuba mata zance "Sannu salma barka da arziki" "yawwa" ta amsa a dage kamar wacca akama dole jinjirar na karba na kira su safwan suma na aza musu kowa ya dauka Amra ma ta sa rigimar sai an bata "to tara hannun na dora miki ita" da sauri ta miko hannu na doramata ba tareda na sakarmata 'yar ba
"Kinason baby gashi uwarki ta rufe haihuwar" Anty mariya (yayar lawal wacca yake bi) ta fada kai tsaye tana kawadda kanta
Sarai na jita amma sai nayi kamar banjiba hirarsu suka cigaba da yi ina jinsu amma bansaka musu baki ba babbar yayarsu ce ta shigo rike da hannun Aysha Anty A'i (wacca lawal yayiwa takwara da Aysha) "Anty ina wuni" itama kamar sauran a yatsine ta karba tana zama kan kujerar dakin
"Shekaranjiya ai nazo bansameki ba nace abu ga gidan 'yan boko lawal kawai na samu nace Allah ya maka budi kaima ka fita Allah ya rabaka da tsaron gida"
Caraf Anty mariya ta karbe "Ai anty ni ina mamakin matar da take hada AURE DA KARATU kuma tace duka zatayi wallahi ina tausayawa mijin da matarshi ke KARATU don ba wata kulawa da zai samu bare kuma lawal da yake cikin jarabawa saidai fatan Allah yasa ya cinyeta"
Mikewa nayi tareda yi musu sallama na hada kan yarana mama na samu a falo don in mata sallama "zo nan zainab" umurtarsu safwan nayi da su jirani a waje matsawa nayi kusa da ita na durgusa " ya gidan naku ba wata matsala dai ko zainab"
" A'a mama ba wata matsala" numfashi ta sauke "ki kara hakuri zainab nasan kinmana kokari zama da lawal ba sana'a amma insha Allah akwai shirin da nakeyi akan hakan da anyi sunannan komai zai daidaita ki kara hakuri kinji"
Murmushi nayi "Insha Allah mama" ina ganin kimar matar sosai saboda dattijuwar arziki ce sam su lawal basuyi halinta ba "to ya karatunnaki" murmushi nayi "Karatu alhamdulillah mama wata 1 ya rage mu fara jarabawa insha Allah"
"Masha Allah to Allah yasa a kare a sa'a"
"Amin mama"
Kudi na zaro a jakata dubu 20 kamar yanda na kebesu tun gida na aje a gefen da take "gashi mama a kara ayi hidimar biki" mikewa nayi tayi saurin rike hannuna "Dau kudinnan zainab tun ban bata ranki ba duk wannan halin da kuke ciki zaki dauko wayannan kudin ki kawo"
"Wallahi ba komai mama don Allah ki karba" kudin ta dauko ta raba biyu " karbi nan na dau wannan dai mungode sosai Allah ya miki albarka"
Daga nan kofar gidanmu aka sauke mu a bakin tangamemen get din gidanmu gaida maigadinmu nayi ya amsa shima yana gaidani cikin girmamawa yana yiwa su Amra wasa
Motar da nahango a farfajiyar gidan ita ta tabbatarmin da YAYA na gidan babban yaya wanda ke taka matsayin uba a gidan tun bayan da kasa ta rufe idon mahaifinmu
Muje zuwa daiiiiiii
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI
Page 4
Bangaren mahaifiyata na wuce kamar kullum ko ina tsaf-tsaf kamar gidan sabuwar amarya to akwai masu kula da komai
Tana hakimce akan hadaddiyar kujerar dake falon cike da kauna na karasa tareda rungumeta " nayi kewarki ummi" 'yar dariya tayi irin ta jin dadi " bansan sai yaushe zaki girmaba Abun abba ke bakisan kin girma ba wani lokacin ko yaranki basa sangartar da kike yi" gyara zamana nayi tareda shigewa jikinta "karkiga laifina ummi gurinki kawai nake samun hakan a yanzu" shafa kaina tayi "Allah ya miki albarka autata"
"To ina kika baro uwayen rigimar kuma" waigawa nayi sai yanzu na lura da bama tare idanuwana sun rufe da kaunar mahaifiyata "Suna bangaren Yaya don munga motarshi a waje"
"Eh yau bai fita ba kinsan weekend ce"
"Haka ne fa" na fada ina sauke gyalena tareda ajeshi kan kujera
"Asabe Asabe" ummi tashiga kwallawa mai aikinta kira da sauri ta fito "gani um....) maganarta ta katse tana karasowa cikin falon "Ahhh anty zee sannu da zuwa wallahi banma ji shigowarki ba ina su Amra" nima murmushin na mata "wallahi munshigo anty asabe su amra suna wurinsu Nihal"
"Masha Allah" juyawa tayi wurin ummi "gani ummi" nuna ni tayi "je ki kawowa auta abinci ki zubomata farfesunnan da kika min suma yaran ki tanadar musu abinda za su ci kafin su tuna dani"
"To ummi" ta fada tareda mikewa waigowa ummin tayi tana kallona " ko akwai abinda kike bukatar asama miki" girgiza kaina nayi inajin kwalla na neman cika min ido
Allah sarki uwa duk lokacin da zanzo gidan to zakaji tana a girkamin kaza a girkamin kaza duk abinda take ganin zaimin wahalar samu a gidan mijina to kokari take ta samaminshi nida yarana
Nan take aka cika gabana da kayan abinci kala-kala da fruit fadi take "ki bude ciki kici abinci tunda ba bakuwa kike ba" abincin na diba ina ci da kanta ta shiga kitchen ta hadomin fruit salad ta kawo gabana " kifa buda ciki kici" saida ta sani gaba naci abincin sannan ta kira asabe ta kwashe kayan
"dubi yanda duk kika rame kindauki damuwa kinsawa ranki bansan randa kika koma haka ba zainab ada bakida kawa kamata amma daga lokacinda likita ya gayamana kinada hawan jini na aje wannan tunanin nasha gayamiki duk abinda kike so ki kirani ki sanarda ni ko ki kira yayanki ba abinda zaki nema a duniyannan indai akwai shi da bazamu nemo miki ba amma kullum abin inga kina cikowa kina kiba saidai kullum in ganki zuru-zuru da ido sai dogon hanci me kike tunani zainab? shin ke bazaki kwantar da hankalinki ba kodon yaranki"
Murmushin yake nayi tareda riko hannuwanta duka biyu "ba abinda ke damuna ummi duk abinda nakeso ba abinda bakumin ba kawai dai may be yawon makaranta ne yasa kike ganin hakan" ido ta zubamin kamar mai nazari irin kallon da take mana a lokacin da idan tana zargin muna boye wani abu
"Indai ko zirga-zirgar makaranta ce ta maidaki haka to zansa yayanki ya kaimiki mota daya cikin ta gidannan"
Wannan karon kasa daurewa nayi saida na rungumeta tareda fashewa da kuka "don Allah ki yafemin ummi ku yafemin abinda kuka gudarmin kenan na kasa fahimta don Allah ku yafemin" bayana ta shiga shafawa " kingani ko? kingani ban gayamiki kar ki kara zuwa kimin kuka ba zainab kodai akwai abinda kike boyemin" kaina na shiga girgizawa tareda kara shigewa jikinta "bakomai ummi wallahi bakomai"
"To karki kara kuka kinji karkisa mudinga ji aranmu kamar ba mu cika alkawarin mahaifinki ba Abbanki har ya rasu yana maimaita a kula dake a kyautatamiki ki gayamana zainab idan akwai abinda muka kasa miki don Allah"
Ganin itama ina neman sakata damuwa yasa na ware na dinga zuba mata shagwaba ita kuma sai riritani takeyi daki ta shiga ta dakkomin abayas tace gani tayi ana talla suka burgeta tasanni da son abaya ta siyamin ai kwa nahau murna nashiga gwadawa ina tsalle kamar wata Aysha
Bangaren Yaya Isma'il na shiga (shine babba a gidanmu) matarshi Anty nasma kawai na samu gaisawa muka yi cikin girmamawa na tambayeta su Safwan
"Sun fita tareda abban nihal rigima suka sakamishi kan teddy shine ya kwashesu ke har yasir na hada nace duk a tafi"
"Ai gwanda da kika mika su can ko bakinki ya huta"
Sallama na mata na shiga bangaren yaya Abbas (shine kebin yaya babba) shikam yana nan gida gaidashi nayi cikin mutunci da kaunar juna itama matarshi na gaisawa mukayi ta kawomin dan abin motsa baki tareda wucewa dakinta ta barmu tare
"Yadai ZEEN ABBA ba wata matsala dai ko" murmushi nayi "ba matsalar komai yaya"
"Idan da wata matsalar kigayamin dubi yanda kika rame ko wani abun yake miki har yanzu"
"Ba abinda yakemin yaya bakomai"
"Idan har kikaga da wata matsala ki dawo gida don bazamu zuba ido ya kashe mana ke ba idan shi baya bukatarki mu muna bukatarki don haka bazamu zuba ido ya cigaba da wasa da rayuwarki ba kinji ko"
"Insha Allah yaya" tun dama can yaya mutum ne mai zuciya kuma tsayayye kan ra'ayinshi shine mutum na farko da ya fara nuna tsanar aurena da lawal tun farkon soyayyarmu baya kaunar lawal bare kuma abubuwan da suka zo suna faruwa daga baya
"Zan turo miki kudi ta account dinki ranar monday kije asibiti a duba dalilin wannan ramar"
"To yaya" na amsa cikin girmamawa
Sai la'asar nayi shirin barin gidan tareda sha tara ta arziki daga mahaifiyata da kuma 'yan uwana naji dadin fitar koba komai na kwanta jikin mahaifiyata ta kara kwantarmin da hankali
Banyi girki ba saboda munzo da abinci tun daga gida wanda ummi tasa aka girka mana na musamman saida mukayi sallar magriba sannan na zuba mana abincin
Muna tsaka da cin abincin ya shigo kallo daya yayiwa shinkafa kazar da muke ci ya kawadda kai tareda wucewa daki koda ya fito har mun kammala an kwashe kayan ina kokarin jona wayata caji ya dawo falon yana zama yaran suka dakatarda wasar da sukeyi kowannensu ya nutsu musamman amra da ta shige jikina
Kallonsu yayi " meye kuma kuka daina wasan" hannu ya mikawa amra data shige jikina "zo amra na zo inji wa ya taba ki" kafada ta make cikin shagwaba take fadin "Um um ba kaine ka dakeni ba da safe" kunnuwanshi ya kama "yi hakuri shalelen mommy zo gurin abbanki kinji"
Matsawa tayi ya dauketa ya dora akan cinyarshi wasa ya shiga yi mata tana kyalkyala dariya sakkowa yayi ya hada kan yaran duka yana musu wasa abinda na dade bangani ba sam baya cikin iyaye masu jan 'ya'yansu a jiki wani annurin farinciki nake hangowa a fuskokinsu
Iyaye kowane akwai rawar da yake takawa a zukatan yaransu basu rasa komai ba daga gareni amma kuma yau sai na hango wani bangare na farinciki a tare da su saboda kasancewar Abbansu kusa dasu kamar a mafarki na tsinci maganarshi " mama tace kunje kinkai harda gudummawa an gode sosai"
Kallo guda na mishi na kawadda kai " eh wallahi ba komai" hmmmm lawal kenan ai saidai in ba wani labarinka wallahi a wannan lokacin nasan abinda yake a zuciyar lawal na gama karantarshi tsaff kudin da mama ta rage yakeso in bashi "kaiii wallahi namiji bayada kunya"
Washe gari saiga mota ankawomin daga gida godiya nakira na musu lawal na daki naje na sameshi ina murna " abban safwan ga mota can an aikomin daga gida in rika zuwa makaranta"
"Allah ya kyauta" daga wannan bai kara magana ba jiki a sanyaye na juya na koma waje
Da motar nayi amfani na sauke su safwan a makaranta nima na wuce tawa
samuwar motar ya saukakamin sosai da ita nake kai yarana makaranta nima da ita nake zuwa
Tunda muka fito lecture muke zaune muna fira da wayanda muke tare nafisa da kuma maman ayman sai zee lawal haka muke mu hudu saboda banason tarkacen kawayennan tun dama can
Kallon Nafisa nakeyi da ta dage tana zuba kalaman soyayya a waya ko ba'a fada ba nasan Ahmad ne saurayinta ko kuma ince mijin da zata aura
kallona tayi "yadai maman amra sai kallona kike ina zuba soyayya da hubby" murmushi nayi "ai dole na kalleki irin wannan love haka amma dai da zakiji shawarata da kindan rage "
Ido ta zare "me zan rage maman amra? soyayyar? hmmm wallahi bazan iya ba don bakisan yanda nake kaunar hubby bane shima yake kaunata bazaki gane yanda nakeji ba hmmmm abin ba'a cewa komai" ta karasa fadi tana lumshe ido
"hmmm da zakiji shawarata da kin rage wannan haukar don wallahi ba abinda zata tsinana miki sai wahala kinganni nan ko alama bakiyi irin soyayyar da nayi ba amma ba abinda ta tsinanamin"
Matsowa zee lawal tayi " takwara bamu labari me yasa kike yawan nusarda mu akan soyayya"
Hmmmmmm
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI
Page 5
Murmushi nayi " nidai fatana ku hutadda zuciyarku da wannan zazzafar soyayyar da kuke dorawa kanku"
" amma ya kamata ki gayamana dalilin da yasa kike cewa hakan ko zamufi ganewa ko ya kuka ce" Nafisa ta karasa maganar tana kallonsu
Wannan karon maman ayman ce ta katse shirun da fadin " Mu bar maganar mana tunda kuka ga bata fada ba may be abinda ya shafi rayuwarta ne kuma dama ku daina tunanin samun irin wannan da kuke yi a waje a gidan aurenki"
Nidai shiru nayi ina kallon zee lawal da ke fadin " don Allah ku daina sa muna tsoron aurennan tun kan mushiga"
Wayata na duba tareda mikewa na dau jakata "Ni zan wuce gida banjin dadin jikina zan dan sha magani in gani" hada baki sukayi wurin yimin sannu maman ayman ta dubeni "kodai-kodai" saurin kallonta nayi ina kankance idona " kodai me" itama idon ta kankance kamar yanda nayi " ko ansamarwa amra kane?"
Kai na girgiza "Allah ya shiryaki"dariya suka sa gaba daya dan sukayi
takomin suka yi na shiga mota na dau hanyar gida a hanya naga mai kwa-kwa na tsaya na siya wa su Aysha da ke sonta
Hamdala nayi bayan na kashe motar na fito kofar falon na taba najita a bude abinda ya tabbatar min yana gidan sallama nayi yana kwance a kan kujera da waya a hannunshi banga alamun amsa sallama akan labbansa ba
Wuceshi nayi na wuce dakina jakata na aje tareda zare dankwalin kaina gefen gadon na samu na zauna ina sauke numfashi ina bukatar ganin likita kwanannan ciwon kannan ya matsamin mikewa nayi na wuce toilet in samu in watsa ruwa ko zanji sauki
Bandau lokaci ba a toilet din nafito jikina na tsane da towel turare kawai na goga a jikina kallon kaina nayi a madubi inaso inga ramar da mutane ke fadar nayi bazan musaba domin ko bakincikin da nake kwankwada a gidan lawal ya isa ya ramadda ni riga na samu mara nauyi na zuba na dora hulata
Har yanzu yana falon dama ina zaije kullum muna tare idan baya cikin gida to yana waje idan baya waje yana gidansu ko ni da nake mace bazan iya wannan zaman ba amma shi ko a kwalar rigarshi
Kujera na samu na zauna ina sauke numfashi " kamin izini gobe inje asibiti banjin dadi" kallo daya yamin ya cigaba da latsar wayarshi ya dau lokaci sannan yace " Kinyi marmarin tonamin asirine shiyasa zaki koma asibitin ace kinada wata cutar 'yan uwanki su sakani gaba" kallonshi nakeyi kamar wata sabuwar halitta " wai lawal meyasa abin fada bayada kadan a gurinka fisabilillah yaushe maganar nan takai ka maidata haka maganar lafiyata nake maka fa kuma ko wata cutar akace ta sameni to ko wannan karon kaine silarta lawal"
Kaina dake sarawa na dafe " wai me kakeson maidani lawal me kake nufi dani ne? na gaji wallahi nagaji" na fada hawaye na silalomin gabadaya abubuwannan sun isheni wani lokacin idan na zauna ina tunani sai na dinga jin inama ban hadu da lawal ba? inama bantaba saninshi ba? kai inama banyi aurennan ba (Astagfirullah) na shiga istigfari ganin damuwa na neman tabamin imani
Har dare ina fama da ciwon kan ko abinci su safwanne suka girka sosai nakejin ciwon ina kwance ya shigo yarana na zaune tare da ni kusa dani ya matso "zainab ko zamuje asibitinne" harara naso ballamishi to amma idanun sunki bada hadin kai dakyar na bude idona na dubi yarana "kuje ku kwanta na samu sauki" ina kallo suka fita suna waiwayena tausayi suka bani to yanzu idan mutuwa ta dauke ni ya zasu yi? anya kuwa wannan shakuwar baza ta zamo cutarwa a garesu ba lokacinda kasa za ta rufe idanuna? saboda yanzu na fara gazawa zuciyata ta fara nauyi komai yana nema ya kawo karshe
Cikin taushin murya ya sake fadin "ki daure muje asibitin ban dauka abin ya kai haka ba" ya fada yana kama hannuna ya shiga jeramin sannu da lallabani muje asibitin wata kila yana tsoron na mutu ace shi ya kasheni
"Mu bari dasafe sai muje idan Allah yasa zan kai safen"
Ban runtsaba saboda halinda nake ciki ga zuciyata da takemin zafi abin mamaki shima bai yi bacci ba duk lokacinda zan motsa to zanji yana jeramin sannu da safe ma shiya hadawa yara abin kari yace na shirya ya aje yara sai mu wuce asibitin saida ya sauke su muka wuce yana ta min iyayi nidai shiru nayi don ko magana nayi ba dadi
Kaina na sunkuyar ganin irin kallon da anty hauwa wacca take matsayin yayata saboda 'yar gwaggona ce kuma itace likitar da ke dubani tun daga kallon da take min nasan akwai matsala
"Ka jira ta a waje" ta fada batare da ta kalli lawal ba mikewa yayi tare da fita ta maida hankali gare ni mikewa tayi daga kan kujerar da take ta dawo wadda ke fuskantata (wadda mara lafiya ke zama) hannuwa na ta riko duka biyu tana kallona " Zainab dubi idona kiyi magana dani as your sister ki gayamin gaskiya zainab me kuma ke damunki yanzu da kike neman janyowa kanki wani ciwon? ki gayamin zainab wace damuwa ce wannan zainab? jininki ya hau sosai zainab sannan halinda kika jefa kanki ko wane lokaci za ki iya kamuwa da ciwon zuciya haba zainab akan namiji? namijinma lawal da ba wani abun kirki da za'a so shi saboda shi ki tuna yaranki zainab Ummi da mu 'yan uwanki wani hali za mu shiga idan wani abu ya sameki to gaskiya na gaji zanje in sami ummi kawai a raba wannan auren bazaiyu muna kallo rayuwarki ta salwanta saboda wani banzar lawal ba wannan karon dole ayita ta kare"
Hannuwanta na jimke ina zubarda hawaye " don Allah kiyi hakuri anty hauwa na miki alkawarin cire kowace irin damuwa a raina bazanso aurena ya mutu ba anty idan lawal ya sakeni to yarana ya rayuwarsu za ta kasance? wazai rike su kinaji lokacin yanda yaya abbas yayi rantsuwar baza su zauna gidanmu ba itama maman lawal din tace duk ya sakeni bazata rika mishi su ba to ina zan barsu? don Allah karki gayawa kowa na miki alkawarin daina tunani da kowace irin damuwa"
"Kinji abinda ke cutar da mata har su jefa kansu a wahala daga mace ta haihu da namiji to gani yake dole ta zauna da shi kodon wa'yannan yara akwai mata da yawa da ke fuskantar irin matsalarki a gidajen aurenki amma sun boye saboda tunanin makomar yaransu karki kashe kanki akan wannan zainab wannan karon ki yaki matsalar lawal daga zuciyarki"
Na sha fama kan na shawo kan anty hauwa so tayi in kwana asibitin na lallabata nace ta bani magani kawai ta bani magunguna tare da shawarwari
Kallonshi nayi "kaina na ciwo please" daga haka yayi shiru har muka isa gida bai kara magana ba
Ayi hakuri da wannan mura🤧
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI
Page 6
Wani tattali na ke samu daga lawal kulawa yake bani ta musamman nida yarana nidai nawa idone kawai da kuma tsoron abinda zai biyo bayan kulawar hmmm Lawal ne fa lawal bazaimin haka a banza ba dole akwai wani abun
Su kansu yaran sunga canji daga gareshi kai maganar gaskiya lawal ya iya kulawar da zata sa ka manta dukkan sharrin da ya maka Allah ya bashi baiwar tsara zance da wannan ya dinga amfani wancan lokacin yana kassarani
Washe gari Alhamdulillah na samu sauki sosai ina jin lawal yana kiciniyar shirya yara "nanny lawal" na fada ina sauka kan gadon na shiga toilet wanka nayi nima don inason in daure in shiga makaranta
Bakin gadon na sameshi zaune bayan na fito daga wanka kallona yayi yana murmushi "Lallai my zee jiki yayi kyau" nima murmushin na mishi "naji sauki sosai" mikewa yayi yana nufar mirrow ya dau key din mota " zan aje yara makaranta" sauri na kara wurin shafa man a jikina ina fadin "don Allah jirani in karasa shiri nima zan shiga makaranta"
Kamar wanda na fadi mugun abu ya waigo da sauri " ba inda za kije sai kin kara jin sauki ko gobe ba zakije ba ko makarantar ai zaki karo ciwon kai ki bari sai kin kara samun sauki" daga haka ya juya ya bar gidan shiryawa nayi nafito falon nadau abin karin da suka ragamin a raina nace " lawal anga banza" har da su kwai aka soya
Gidan naji yamin shiru ba dadi in shiga daki in fito in shiga kitchen na rasa aikin da zanyi gaskiya lawal na kokari na zaman gida ina kitchen ina goge plates dina naji sallama fitowa nayi ina amsawa da fara'a na karaso falon maman haidar ce makociyata ta amana " maman haidar ce a gidannamu" itama da fara'a take kallona "ai dole kice haka tunda ke kin gujeni yaushe rabon da ki lekamu nima shiyasa na daina shigowa sai jiya haidar ke gayamin sun hadu da safwan a masallaci ya gayamishi bakida lafiya"
Zama nayi kusa da ita " wallahi banida lafiya maman haidar amma yanzu na samu sauki" gyalenta ta kwabe ta aje kan kujera kallonta nake ganin irin ramar da tayi "bakida lafiya ne kema" na tambaya ganin wata irin rama da tayi murmushin karfin hali tayi "A'a nikam lafiyata kalau me kika gani"
"Kamar ya lafiyarki kalau wai kinga ramar da kikayi? sannan zaki cemin lafiyarki kalau" hawaye naga sun cika mata ido sannan ta dubeni " ina cikin damuwa zainab na rasa wanda zan gayawa naji sanyi ina cikin damuwa zainab" ta karasa tana barkewa da kuka kyaleta nayi tayi kukan ko zata sami saukin abinda takeji a raina nace " kenan bani kadai ce keda damuwa ba" saida naga tayi kukan sannan na lallasheta " kiyi hakuri bilkisu wallahi yanzu rayuwar nan sai a hankali damuwa yau akwai ta cikin zukatan kowa" hannuna ta rike " damuwata ta banbanta da ta kowa zainab banida wanda zan gayawa damuwa ta zainab banida kowa garinnan ki taimaka ki gayamin abinda zanyi" duk na rude bantaba ganinta cikin wannan yanayin ba kullum zakaganta cikin fara'a sabanin ni da kullum da sabuwar chapter da zamu buga da lawal
Mijinta yana kaunarta wanda baya boye hakan a gaban kowa ko zaman minti 2 kayi dasu zaka shaida hakan "meke damunki bilkisu meya sameki"
"Zainab ke kinsan banida kowa garinnan in ba abban haidar ba ni 'yar kano ce aurene ya kawoni sokoto ba yanda amma bai dubi wannan ba tun bayan haihuwar khairat na fuskanci Kasim ya canja ya daina dawo mana weekend sai ya kwashe wata 2 bai dawo ba kuma idan ya dawo ba alamun wata damuwa a tare da shi na yayi kewarmu ko wani abu ina shan wahala zainab saboda ya riga ya sabamin da kulawarshi nashiga damuwa sosai da wannan sauyin nashi sai a 'yan watannin nan na fahimci wani ya daina damuwa dani sai yayi wata 2-3 bai damuba idan ma ya dawo bayada lokacinmu ta wayarshi kawai yake baya bari in taba wayarshi idan ma ya dawo baya wuce kwana 3 ya koma wai ashe wata yake tareda ita acan din na fahimci hakanne ranar da yabar wayarshi ya shiga wanka zuciya ta dinga tunzurani na duba naga abinda yake boyewa a wayar nayi nadama nayi danasanin duba wayar saboda na shiga tashin hankali a wannan ranar munyi rigima sosai dashi tsorona kar abinda yakewa 'yar mutane nima wata rana ayiwa 'yata amma sai ya shawo kaina da min alkawarin ya daina na yarda ganin irin rantsuwar da yake min ashe karyace bai dainaba kwatsam shekaranjiya na fara rashin lafiya shiryawa nayi naje asibiti ana dubani akace ina fama da infection wato ciwon SANYI fadar damuwar da nashiga bata bakine zainab na tabbata shi ya kwasomana wannan abun ina shan magani zainab amma ba wani sauki har yanzu ga mahaifiyarshi da ta sawoni gaba ta hanani zaman lafiya gani take kamar na mallakeshi haka take fada kullum to nagaji da bakinshi ya gayamin bazai iya rabuwa da yarinyar ba aurenta ma zaiyi na yanke shawarar kawai ya sakeni bazan zauna da shi ya kassaramin rayuwa ba ya sakeni kawai inje in nemi magani"
Dankari wato dai matsalar nan kowa da tashi "kiyi hakuri bilkisu ki daina kuka kasim bai kyauta ba kuma dole ki shiga damuwa insha Allah zamu samo maganin sanyi ba matsala bace zan gayamiki abubuwan da zakiyi amfani dasu amma ki dakatar da maganar saki yanzu har ki samu lafiya musan mafita mikewa nayi nashiga daki na dakko papper da biro na bata "Ki rubuta abubuwan da zan gayamiki yanzu shine maganin sanyi"
Ku biyoni a page na gaba don amfana da abubuwan da ke maganin sanyiâœï¸âœï¸âœï¸âœï¸
AURE DA KARATU
NA
RUMAISA SIDI
Page 7
INFECTION
Da farko dai kisani yar uwa ciwon Sanyi ciwone da bawata ya mace face tana tattare dashi , ko tasani koma bata Sani ba
Don haka ke mace kece ke janyo bayyanarsa a jikinki ko Kuma ki kwanta dashi yar uwa Mai daraja.
ABUBUWANDA KE HABAKA CIWON SANYI
1- Yawan tunanin saduwa
2-yawan amfani da Pant kala Daya ko shearing dinsa da wata
3-yawan saka Dan yasa ga al'aura yayin tsarki ko wankan haila
4-fara wanke Kashi kamin tsarki
5- Yawan tsarki da ruwan Sanyi
6-saka unders da sanyinsu
7-yawan shan yaji
8-saduwa lokacin fushi
9-fitsari a ban dakinda kowa kan shiga
10-yin amfani da hannu domin biyawa Kai bukata
KASHE - KASHEN CUTAR SANYI
1- Mai saka kai-kai ga al'aura
2-fitar wasu ruwa ga al'aura
3- Mai sanya warin al'aura
4- fitar wasu ruwa bayan kammala period
5- fitar wani gari ga al'aura
6- fitar kuraje ga al'aura
MAFITA
kisani cewa idan cutar tayimiki katutu to takan sa miji ya rinka tsanarki kila ma har yakai ga rabuwar aure (wa iyazu billah)
MAGANI
1-kisamu bawan lemun Yami , yabushe ,amma bushewar daki bata Rana ba
2- kisamu garin Dan Sudan
3-kisamu garin Jan goro
4- kisamu ruwan tumfafiya
5-kisamu zuma maras hadi
Duka kihade garin guri Daya kiyimasa Kashi biyu