← Book details Alajabin Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 10

Sashe 3

Alajabin Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Atsiyace motocin ke darzar kwalta kamar zasu tashi sama, kafin sukaiga shiga masauratar tasu....wasu samari ne dake tsaye gefen hanya sukabi motocin da kallo kafin ɗaya daga cikinsu yace "kai jama'a ji yadda suke gudu akan kwalta kamar sukaɗaine masu ita wannan irin abu har ina? Da mamaki ɗayan yace "kai ai wannan ƙaramin aikinshine muddin yashigo gari domin daganin wannan gudun shine sabida baya tafiyar hankali akan atiti. "Waye wannan? Ɗayan yasake tambaya. "Au baka saniba? Humm *YARIMA SAMEER* kenan bakaga ga sunanshi nan ajikin nomber motarba *PRINCE S 1* da 2,3 har ƙarshen motocinshi. Dagacan gefen sukaji wani nafaɗar "babban gwaro kenan yashigo gari fari me farar aniya bangon sukari ba'ajigineka atashi abanzaba, yafaɗa cikin so da ƙaunar yariman kamar yana gaban idonshi hakan yake doka mishi kirari,,, murmushi sukayi atare kana sukaci gaba da abinda ke gabansu.

Dagudun gaske motocin ketafe akan doguwar kwaltar dazata sadasu da pert ɗin kakanni nasu, wato matan takawa, suna ƙarasawa bakin ƙofar sashe suka tsaya kamar waƴanda ake bawa umurni, kusan minti 30 da tsayuwarsu kana wani dogari yafito cikin sauri yabuɗe ƙofar ɗaya motar wadda tafi kowacce kyau da ɗaukar hankali...cikin izza da mulki wanda ke nuni da jinin sarauta na yawo ajikin kowaye zefito daga cikin motar yaziro kafarshi ɗaya aƙasa....!

Autar alheri ✍️

🪐🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥🪐

🪐🐦‍🔥 *MASARAUTA*🐦‍🔥🪐

🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸

Dr Yasmeen Ahmad😚

Autar alheri ✍️

Al'ajabi, hummm

Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI.

ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃

Book 1

Page 5 & 6

"Kusan minti 5 baya kafin yasake zuro ɗayar kana yafito gabaki ɗayanshi, wow watafarakallah bi'ahasanilhaliqeen, tabbas tsarki ya tabbata agun uban gijin talikai wanda ya ƙagi kyau yakuma ƙagi muni, haƙiƙa wannan bawa kyakkyawan mutunne mafi kyawo acikin masu kyau cikakken namiji ƙaƙƙarfa mecikar zati dakamala, wannan guy ɗin yanada kyau wanda bazan iya misilta muku shiba, farine tass afatarshi sedai lallausar suma tayiwa Fatar tashi ƙawa yadda tabi ilahirin jikinshi takwanta lubb baƙa wulik da ita, yanada dogon hanci sosai gakuma manyan idanuwa alumshe kamar na yan maye masu launin ruwan madara, eyes Ball ɗinshi kaɗai abin kallo ne, yanada wani irin baki wanda ko acikin farar fata wato turawa bakowane keda irinshiba domin bakin ƙarami ne sosai sedai lips ɗin nashine abin kallah domin kuwa daga ƙasan zagayen kowanne lips nasama dana ƙasa red ne sosai sedai daga cikin lips ɗin wato tsakiyarsu pink calor ne irin me walwali ɗinnan, bakin nashi yabada wata kalar daban, yanada kyakkyawan saje wanda ya ajiye iya kunnenshi bezagaye fuskarshi dukaba, kana ya ajiye zagayayyen gemu irinna gayu me kyau da tsari yasha gyara iya gyara abin se wanda yagani. Wannan matashin saurayin yawuce duk yadda zakuyi tunaninshi, sa'annan kallo ɗaya zaka mishi kaga yadda zallar mulki da sarauta keyawo ajinin jikinshi bugu daƙari Miskilanci ya haɗe da jinin mulki se yaya kenan 🤔

YARIMA SAMEER M HABIBULLAH MAHAR ÆŠAN FARI AGUN ALHAJI MUNEER HABIBULLAH MAHAR, JIKA AGUN SARKI MUHAMMAD HABIBULLAH MAHAR, MATASHIN SAURAYI MEJIDA IZZA DA KUÆŠI GAKUMA JININ MULKI DAKE YAWO AJININ JIKINSHI.

Ahankali yashiga tako ɗaya bayan ɗaya cikin izza da mulki dogarai natake mai baya har yaƙarasa cikin babban parlor daze sadashi da kowanne sashen na matan sarki habibullah, ɓangaren dama yanufa inda ze sadashi da pert ɗin mebabban daki wato uwar gidan memartaba kenan dattijuwar tsohuwa me dattako da jijidai gakuma tujara domin bata ɗaukar reni, yana isa bakin ƙofar parlor ta dogaran suka tsaya abakin ƙofar shikuwa yaƙarasa ciki,,,,,zaune yasameta akan kilisa kuyangi kusan huɗu sun zagayeta suna mata tausa wasu na yanka mata kayan marmari

Dasauri hadima uwani tarussuna tana faɗar "lale marhabin da yariman mahar ɗan zakin zakuna jikan sarki giwa me tafiyar ƙasaita ko acikin dawa se,anraɓe, bangon sugari kowa yaraɓe seya lasa, sannun dai da sarkin gobe. "Hannu yaɗaga mata alokacinda yake zama ƙasan kafafunta mebabban ɗaki domin Allah yasani shi bayason wannan ihun dasukeyi idan sun ganshi acewarshi, humm aiko doli ka haƙura yallaɓai tunda kafito a jinin sarauta 🤷

Ahankali mebabban ɗaki tamiƙe zaune kana tadafa kanshi, "sannu dazuwa yarima sameer sannunka da dawowa cikin mahaifarka ina Fatar wannan lokacin zaka ɗan jima muna anan kafin kakoma domin yadace kaɗan fahimci wani abun acikin sha'anin mulkin garinnan. Taƙarasa zancen fuskarta ɗauke da murmushi.....shirune yabiyo baya dudda yaji abinda tace kusan minti 15 kafin yabuɗe baki daƙyar kamar bayaso yace "ina fatar nasamu uwar gidan Muhammad habibullah lafiya, mebabban dakin masauratar mahar. Ɗan shiru yaƙarayi kana yace "banajin zan jima mebabban daki domin wani aikin kawai zanyi nakoma, yafaɗa kamar bayaso..tunda yafara magana nakebinshi da kallo domin kuwa yadda yake juya bakinshi yana fidda haruffa ɗaya bayan ɗaya abin gwanin sha'awa gawani irin sihirtaccen daɗi dake fita a sassanyar muryashi kamar ana busa sarewa.

Murmushi me babban ɗaki tayi kana tace "dudda hakan inason ganin yarima sameer acikin yan uwanshi kamar yadda nasan suma suna buƙatarka atare dasu, gakuma abbanka kullun zancenshi kaine Indai mutum naso yaga far'a a fuskarshi to yazo masa da labari me daɗi akan ɗan lelenshi, shin kodan Abdullah bazaka zauna nawani ɗan lokaci ba. Taƙarasa zancen tana kallon jikan nata.

Shikuwa shiru yayi bece komaiba se lumshe kyawawan idanuwanshi dayayi yanajin yadda zuciyarshi ke dokawa tabbas yasan abbanshi nasonshi fiyeda komai aduniya kuma shima yana sonshi amma bayajin ze iya zaman masarautar tasu mecikeda abubuwan bantsoro da ruɗani. Kusan minti 30 yakwashe a pert ɗin me babba ɗaki batareda yace mata komaiba...itama bata ƙarayimai maganaba domin tasan iya wannan dasukayi idan zasu kwana ahakan baze ƙara cewa komaiba, wannan halin nashi kuwa baƙaramin ƙonawa wasu daga cikin family nasu rai yakeyiba domin idan kana taredashi ze iya mako ɗaya bakinka danashi be haɗu ba koda kai kemishi maganar balle kace jirakakeyi yayima.

Bayan yafito daga part ɗin me babba ɗaki yasake shiga motocinshi suka nufi ɓangaren yamma ɓangaren gidan ƴaƴan sarki habibullah wato iyayenshi. Wani tangameme parlor yashiga inda yasamu wata mata hakince akan ɗaya daga cikin manyan kujerin parlor hadimai kusan Shida nagefenta kowacce da abinda takeyi....suna ganinshi suka Miƙe dasauri suna kwasar gaisuwa sukabar pert ɗin...cikin tafiyarshi me ɗauke da ƙasaita yaƙarasa gun matar kyakkyawar mace masha allah, yana zuwa ya russuna agabanta tareda kawo fuskarshi dedetata ya manna mata kiss agoshi da gefen kumatunta kana ya rungumeta ajikinshi yana sauke ajiyar zuciya...wani ƙaya taccen murmushi taƙara saki tana shafa bayanshi ahankali kana tace "sannu dazuwa Muhammad sameer ka zo lpy? Tunda tafara magana yake lumshe ido yana sakin ajiyar zuciya kafin yasamu zarafin buɗe bakinshi daƙyar yace "lpy qalau mammi, ina Fatar nasameki lafiya. "Lpy qalau Muhammad kowa yana lafiya ƴan uwanka nacikin kaɗaicin rashinka ko ɗazu ameer da anwar dasukazo yin lunch se da sukayi zancen dawowarka nasan baka gaya musu zuwanka ba ko? Tatanbaya tana shafa kanshi...bece komaiba kusan minti 5 kafin yamiƙe kawai yanufi matakalar benen dake parlor cikin tafiyarshi me ɗauke da izzar mulkinshi...da kallon sha'awa mammi tabishi harya ɓacewa ganinta kafin tasauke ajiyar zuciya tanajin son ɗan nata harcikin ɓargon jikinta.....!

Autar alheri ✍️

🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥
🐦‍🔥🪐 *MASARAUTA*🪐🐦‍🔥

🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸

Dr Yasmeen Ahmad😚

Autar alheri ✍️

Al'ajabi, hummm

Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI.

ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃

Book 1

Page 7 & 8

"Ajiyar zuciya taƙara saukewa akaro na biyu tareda ɗauke idonta daga wurinda ya wuce kana tamiƙe zuwa wani bedroom dake nan ƙasa.....shikuwa yana hawa saman tun a parlor yafara cire tsadadden agogon hannunshi, yana shiga bedroom ɗin yaƙarasa cire kayan jikinshi gaba ɗaya kana yafaɗa bathroom wanka yayi tareda brush sa'annan ya ɗauro alwala yafito sanyeda rigar wanka, mirro yanufa tareda janyo kujera yazauna, hakan yariƙa ɗibar mayuka kala,kala yana shafawa ajikinshi kowanne pert danashi kamar wata mace, yaɓata kusan minti 15 awurin kafin yamiƙe yasaka kayanshi inda yasaka farar riga da farin wando 3kwata, kana yafeshe jikinshi dawani mayen turare me masifar daɗin shaƙa, seda yagama duk abinda yakeda buƙata kana yaɗauki wayoyinshi yanufi parlor cikin tafiyarshi me ɗauke da ƙasaita...yana fitowa parlor yayi arba da ameer zaune akan ɗaya daga cikin kujerun parlor yana danna wayarshi, yanajin motsin fitowar yarima Sameer yamiƙe dasauri yazo yarungumeshi yana faɗar "I miss you so much my bro saukar yoshe bako sanarwa? Se yanzu mammi takirani tana sanarmin zuwanka, yaƙarasa zancen yana ɗan sakinshi daga rungumar dayayi mishi...kallon Ameer yayi da shanyanyin idanuwanshi kana yaɗan shafa sajenshi batareda yace komaiba yariƙo hannun shi suka zauna, kusan minti 5 bece komaiba, ganin hakan yasa ameer cigaba dayi masa fira domin yasan tabbas bazeyi maganaba tunda har yazauna beyiba, sunjima ahakan ameer ne keta famar surutunshi, sedai idan yafaɗi wani abin yaɗago kawai ya kalleshi wani kuma yalumshe idonshi shine kawai amsar, suna nan zaune aka kira sallar la'asar hakan yasa duk suka Miƙe domin zuwa masallaci bayan ameer yayi alwala anan cikin bathroom ɗin dake parlor kana suka nufi masallacin.

Maye balwa
Chapter 3 · 0% Book details