← Book details Ajali Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 5

BABI NA UKU

Ajali Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

.
Ba kasafai Nazifi yake barcin rana ba, domin
kuwa ko ba inda yake da bukatar zuwa, da
wahala ka same shi a kwance da rana tsaka
kai ko rashin lafiya yake yi bai cika kwanciya a
daki da rana ba,
.
bar shi dai ya fito kofar gida ya zauna a dakali ya karanta mujallun fina-
finai ko kuma littafan soyayya. To amma
kuma sabanin wannan halayya tasa da aka san
shi da ita shekara da shekaru, kwanaki biyu
kenan Nazifi yana wuni a gida a kwance, ko
lekowa waje ba ya yi
.
Mahaifiyarsa Tabawa ta yi iyakar kokarinta
don ya fada mata dalilin canjin wannan
halayya tasa amma kuma abin ya faskara, ya
ki ya fada mata, sannan kuma babban abin da
ya fi ba ta mamaki shi ne wai a cewarsa
lafiyarsa kalau, ba inda ke yi masa ciwo. A
cikin kwanakin biyun nan ko wurin sana'arsa
ta kafinta bai leka ba,
.
wanda abu ne mai wahala ko ma kuwa menene dalilin a ce
Nazifi ya ketare rana daya bai je wurin
wannan sana'a tasa ba.
To amma kuma abinda ya tsorata Tabawa shi
ne, wani lokacin idan yana kwance yana barci
idan ta leka dakinsa
,
sai taji yana ta sambatu a cikin barci, yana fadar sunan wata yarinya
wai ita A'isha. Sannan kuma wani lokaci sai ta
same shi yana ta murmushi
.
Ko da Tabawa ta lura da wannna bakon al'amari da ya sami danta Nazifi sai ta ce da shi a fusace a wuni na biyu
.
"Haba ai ni dama na san a rina ai ga irin ta
nan kullum kwanan duniya yaron nan sai na
yi fama da kai ka rika shan maganin miyagu
da kuma na mutanen boye, amma taurin kan
tsiyarku na `yan zamani ya hana ka Nazifi, ga
shi nan ai ka yi gamo da aljana za ta sabautar
da kai a banza."
.
Tun daga wannan lokaci Tabawa ta fara
shirye-shiryen kaiwa bokanyarta ziyara,
domin kuwa ta san cewar wannan aljana da ta
cafi danta guda daya da take alfahari da shi a
duniya, duk tsiyar aljanar in dai har ta kai ta
wajen kwararriyar bokanyarta Iya mai
dogari, to ko ba ta shirya ba sai ta fice daga
jikin danta Nazifi
.
To amma kuma shi Nazifi ya san cewar ko sarakan bori na duniya ne suka taru a kan shi ba za su iya maganin
wannan matsala tashi ba, domin kuwa duk
kwarewarsu akan wannnan sana'a ba za su iya
mallaka masa masoyiyarsa da ya kamu da
ciwon so ba, wacce saura kwanaki biyu kacal a
daura aurenta da wani saurayin can daban
....
CIWON SO kenan
___________
MASOYA AKIYAYE
Izan zaka so mutum to ka soshi daidai wa daida
Haka nan yan mata kada ku dauki son duniya ku daurawa saurayi/budurwa, daga karshe kuma ku rasasu, rayuwarku ta fada cikin garari
.
Its shuraih 99%
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 8
.
Kamar kullum a cikin kwanaki biyu yana
kwance sai mahaifiyarsa ta shigo cikin dakin.
Ya yi tsammanin zancen neman maganin ta
zo yi masa, to amma sabanin haka sai ta ce
da shi.
.
"Wata yarinya ce wai ta zo tana son ganin ka,
shi ne na ce bari in zo in sanar da kai."
.
Nazifi ya mike zumbur cikin mamaki, domin
kuwa inda haka nan ne banza sai a wuni ana
fama da shi ba zai tashi ba, kai a cikin
kwanaki biyun nan har lokacin sallah sai ya zo
ya wuce yana kwance ba zai yi ba.
.
Amma yanzu daga jin an ce wata ta zo nemansa, duk da dai bai san ko wace ce ba, amma a can
cikin zuciyarsa sai ya ji ya dokanta da ya fita
din.
.
Ya tashi da sauri kamar ba shi ne ke wuni
a nannade a gado ba, kamar wanda ake yiwa
karin ruwa. Lallai dai sha'anin yaran zamani
sai dai a bar su, Tabawa ta fada a zuciyarta,
ita ma ta fice daga dakin.
.
Fitar sa ke da wuya ya cikaro da ita a tsakar
gida tana sanye da atamfa shudiya da kuma
dan fingilin gyale. Hakika zatonsa ya zama
gaskiya domin kuwa wacce yake tsammani ce
ya gani. Suka yiwa juna murmushi, Nazifi ne
ya fara yi mata magana.
.
"A'isha da ma ashe ke ce...?"
Ta jefe shi da murmushin Allah kashe ni don
dadi, sannan ta ce da shi.
"Kai da wa kake tsammani?"
"Ban yi tsammanin ki ba, domin kuwa na
dauka cewar tuni kin mance da ni A'isha."
Ta sake jifan shi da wani murmushi.
.
"In ban da abinka Nazifi ka taba ganin inda
mace ta mance da mijinta? Ko ba ka san
cewar ni a matsayin mijina nake daukarka ba,
ko ka mance da alkawarin da na daukar maka
ne in dai ina da miji a duniya ai kai ne
Nazifi."
.
Ya lumshe idanu don farin ciki, a zuciyarsa ya
ce Allah ya sa haka ya zama gaskiya A'ishata,
sannan ya ce da ita.
.
"Zo mu shiga daga ciki A'isha nan ba wurin da
za mu tattauna matsalolinmu ba ne."
Suka shiga cikin dakinsa, rufin kwano doron
zabuwa amma kuma babu silin babu komai a
ciki idan aka tsame dan tsurkun gadonsa na
katako mai kama da makara da kuma wata
kujera daya ita ma ta katako mai kafa uku da
rabi. A'isha ta yi wa kujerar kallon nutsuwa
kafin ta sami mazauni a kanta, domin kuwa
tunda suka shigo cikin dakin ta dubi
rubabbiyar kujerar ta fara zullumin cewar da
wahala kujerar ta iya daukar nauyin mutum
dukansa
.
To amma kuma cikin sa'a sai kuma
ta dauke ta gaba daya, duk da yake dai takan
nemi ta turgude a dalilin nakasar da ta yi na
gutsurewar rabin kafa guda. Nazifi ya fada
kan gadon katako
. Da farko A'isha ta yi tsammanin gadon zai baje a kasa, to amma
abin mamaki sai ta ga shi ma gadon taurin rai
gare shi irin kujerar, bai yi komai ba sai dai
burari da raki domin kuwa ko'ina a jikinsa ihu
yake yi da zarar an motsa.
.
Saurayin da budurwar suka kalli juna cikin
nutsuwa, Nazifi ya fara magana "A'isha ina
fatan ba ki samu wata babbar matsala ba a
wurin mahaifinki, domin kuwa ransa ya baci
sosai a dalilin ganina da ya yi tare dake."
.
Ta ce da shi "Kai zan yiwa wannan tambayar
ka riga ni Nazifi, domin kuwa tun rabuwarmu
nake faman zullumin ina fatan bai doke ka ba
Nazifi."
Ya yi ajiyar zuciya.
.
"Bai doke ni ba amma kuma gara ma a ce
duka na ya yi da abin da ya sanar da ni. Ya
gargade ni kada in sake kusantar inda kike
A'isha. Wannan kalami da ya yi ya sosa
zuciyata, a dalilin haka ne na sami kaina a
cikin wani hali mawuyaci. Tun wannan lokaci
ban sake fita ko waje ba kullum ina nan a
daki ina jimamin rabuwata da ke domin ni
ban ma yi tsammanin zan sake ganin ki ba
har abada, A'isha."
.
Ta yi murmushin karfin hali.
"Duk wannan bai kamata a ce sun sa ka
tsorata ba, domin ni kaina ya sha yi mini
wannan barazanar, don haka ka kwantar da
hankalinka Nazifi, aski ya riga ya zo gaban
goshi."
.
Ya dube ta cikin rashin fahimta, "Kamar yaya
ban gane ba?"
Ta sake yin murmushin. "Abin da nake nufi
shine wahalar mu ta zo karshe in dai ka
shirya, kuma da gaske kana kauna ta har cikin
zuciyarka kamar yadda ni ma nake kaunarka"
Ta dan saurara sannan ta ce da shi a sanyaye.
''Nazifi ka shirya gobe mu je a daura mana
aure.''
.
Saurayin ya ji gabanshi ya fadi ras da kalaman
suka dira a cikin dodon kunnen shi a bazata,
kadan ya rage ya fado kasa don tsananin
razana.
.
''A`isha aure fa kika ce?''
Ta dube shi har cikin idanunsa ta ce da shi.
''Aure mana Nazifi ko ba ka shirya ba ne,
dama yaudarata kawai kake son yi ban sani
ba."
.
Saurayin ya dubi kwayoyin idanin `yar
budurwar da ke zaune akan kujera ta sa shi a
gaba, ya tabbatar lafiyar ta kalau ba tabin
hankali ta samu ba, ya ce da ita cikin mamaki.
.
"A'isha kin taba ganin inda saurayi da
budurwa kawai suka ware kansu suka aurar
da kansu ba wasu shaidu ko waliyyai, sannan
kuma ya za a yi a ce gobe-gobe ba wani
shirye-shiryen komai."
.
`Yar budurwar ta ce da shi "Ni ba cewa na yi
ka sayo min akwatuna ba, sadaki kawai nake
so a wurinka, shi ma don ya zama dole ne, da
ba zan bukaci komai a wurin ka ba kuma shi
din ma sai abinda ka kawo ka ba ni. Malamin
da zai daura mana aure da shaidu, kai ko ma
mene ne ake bukata ba za mu sha wahalar
samu ba.
.
Wannan alhakin ka ne ka nemo mana malami wanda zai daura mana aure
cikin sirri daga mu sai mu sai shi. Daga nan
kuma sai ka samar mana wurin zama na sirri
.
Duk wadannan abubuwan ne da ya kamata a
ce ka shirya su a gobe domin kuwa idan abin
ya wuce gobe, to mun rasa juna kenan har a
bada."
.
Shiru bai ce da ita komai ba domin kuwa
maganganun da take fada duk sun gama sa
shi tsurewa. Zuwa can sai ya ce da ita cikin in-
ina "To ai ni a gaskiya A'isha wallahi abin ne
ya zo mini duk a kurarren lokaci, kuma bayan
haka kin dai gani da idanunki wallahi ba wani
wadata ne da ni ba kuma ba wata
kwakkwarar sana'a nake yi ba. sannan...."
,
Ta katse shi cikin damuwa.
.
"Duk da haka dai na tabbatar a matsayinka na
namiji indai har ka yi niyya duk wadannan
abubuwan ba za su gagare ka ba, in dai har
kana sona da gaske to bai ma kamata ka tsaya
ka kawo mini wadanan matsalolin ba,
kasancewar dai ko rance ka nema a wurin
abokan sana'arka ba za ka rasa samu ba. Ba
wasu kudin ba ne masu yawa za ka tanada ba
Nazifi, sadaki kawai fa na ce ina bukata, daga
nan kuma sai 'yan kudin da za a baiwa
limamin da zai daura auren, don mu rufe
bakinsa kada ya tona mana asiri. Haba Nazifi
ka yi tunani fa ka gani, akwai wanda ya kashe
miliyoyin kudi a kaina, amma na ce ba na
kaunar shi sai kai Nazifi, amma kuma kana
nema ka ba ni kunya, ka kware mini baya."
.
Ya yi saurin cewa da ita "Ba haka ba ne
A'isha, ke kina ganin kamar ba na son
al'amarin ne, wallahi ina so. To amma
matsalolin da ke tattare da al'amarin nake
hangowa. Idan fa muka yi auren nan a boye,
muka nemi wurin zama dole ne a yi bincike
don a gano inda kike a garin nan, kuma abin
duniya ba ya boyuwa, dole ne asirin mu ya
tonu wata rana, don aure ba abin wasa ba
ne."
.
"To sai me don an gane daga baya in dai mun
yi auren? Ai shi kenan, ka san dai duk duniyar
nan idan an taru ba mai raba mu, tunda
muna son juna. Kuma wai kai tsoron me ma
kake ji? Sai ka ce ba namiji ba. Rigima wa ta
kashe a duniya? Mu yi auren nan shi ne mai
wahala, komai zai biyo baya ya ma biyo. Ni fa
mace ce Nazifi amma har in ce na ji na gani a
kan soyayyar mu, amma kai kana namiji ka
tsaya kana fargaba. Ni wallahi ka fara ba ni
kunya Nazifi."
.
Ta kura mishi idanu a yayin da ya yi shiru
yana mis-mis da baki, yana kokarin fitar da
tunani daya tsakanin amincewa da kuma
sabanin haka, daga nan sai ta cigaba da ta ga
bai ce komai ba.
.
"Idan kuma kana ganin ba zai yiwu ba, shi
kenan ba matsala sai in tashi in yi tafiyata, ka
nuna mini kenan da ma ba kauna ta kake yi
ba, sai in je in rungumi kaddara in auri
wancan saurayin da ba na kauna a zuciyata,
wanda shi kuma yake sona kamar ya hadiye
ni. Ba komai Nazifi, dama an ce son maso
wani koshin wahala."Ta mike daga kan musakar kujerar da niyyar
ficewa. Nazifi ya yi farat ya ce da ita, bakin sa
na rawa.
.
"Ki gafarce ni A'isha, abin bai kai mu ga haka
ba. In dai don wannan maganar ce kina
bukatar komawa ki zauna, na amince zan yi
duk abin da kika ce da ni. Ni dai a halin yanzu
ko sisi ba ni da shi a aljihuna, to amma kuma
tunda kin ce da ni rigima ba ta kashe uban
kowa, to ni ma zan jarraba yin ta, don na san
ba za ta kashe ni ba. Domin kuwa ba karamar
rigima ba ce mutum ya tunkari aure awoyi
ashirin da hudu masu zuwa sannan ya nemi
gidan haya, da kuma kudaden limamin daurin
aure duk kwana daya kacal, amma kuma bai
tanadi ko ahu a aljihunsa ba, ke ma kin san
wannan katuwar rigima ce, A'isha."
.
___________
Tab malam Nazifi kwarankwasa maganarka dutse ce,
Don da rigima na kisa, da wannan typing din bai zo gareku ba sakamakon rigimar dana jajibo ma kaina shekaran jiya, sai de dakyar na sha yayin da fuskata ta suntuma suntum, idanuwa na sukai luhu luhu, sakamakon dukan da na ci wajen .........
Kaga su o'o da o'o an kasa kunne don jin tsurku to na fasa bada labarin, its shuraih 99%
.
Chapter 3 · 0% Book details