Gabatarwa
A Lokacin Muke Part 1 Complete Hausa Novel · about 86 min read
8/8/19, 10:30 PM - Messages to this chat and calls are now secured with end-to-end encryption. Tap for more info.
9/6/19, 10:31 PM - ~: A LOKACIN NE
1⃣
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJIN KAI,
ALLAH NAGODE MA DAKA BANI WANAN DAMA NA RUBUTA WANAN LABARIN DA KE DAUKE DA YADDA RAYUWAN ZAMANIN NAN NAMU MATSALOLI DA ILLOLIN DAKE CIKIN WANAN RAYUWAN NA WANAN LOKACIN DA MUKE CIKI ALLAH KA BAMU IKON AMFANI DA FADAKARWAN DA ZAMU TSUNTA A CIKIN WANAN GUNTUN LABARIN,,,
IDDAN BAKI BIYABA DAN GIRMAN ALLAH KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE BADA YARDANA BA,,,,,,
Zaune take saman sallaya a gurin da ta idar da sallah hannun ta ya na dauke da farar tasbaha tana ja a hankali sai dai a zahiri ne hakan a can cikin kasan zuciyar ta tunane fam a ranta tana tunanen ko a halin yanzu ina dan ta Umar ya shiga,
Kadan kadan tana daga kanta tana kallon agogon dake manne a,bangon dakin ta a hankali,
Karfe goma,sha daya na,dare saura agogon ya nuna mata a lokacin hankane ya kara sa hankalin ta, tashi sosai don tana tsoron kada ya shigo mata kamar yadda take zargin ganin shi
Tarasa gane wani haline dan nata yake kokarin jefa kan shi a ciki, ga yawan surutun kishiyoyi dake damun ta a a kullun,
Maimakon ace sun taimaka mata gurin kara bashi tarbiyan da suke ganin baida shi issashe sai kawai suka buge da gulma da kara mugun zance a kan dan nata wanan al,amarin ne ya ke kara sa jefa Maji a cikin tashin hankali, da damuwa a rayuwan ta gashi dai ita a nata fannin bata kasa da nasu yaran ba, gurin daukan su har a cikin zuciyar ta a,tsakani da Allah take masu komai,
Kara daga ido tayi takai duban ta ga agogon bangon dake manne a bangon dakin nata,
Karfe sha biyu saura yan mintina na dare ta gani haka ya kara tayar mata da hankalin ta,
Bata kai karshen tunanen taba taji an turo kofan dakin ta, da karfe inda sabo da hakan tasaba tasan ba mai mata wanan halin sai maigidan su,
Ba sallama sai cewan da yayi a hasale wai ina danki ya tafine ?
Shiru Maji tayi don ta saba da wanan kalman na danki a bakin maigidan nasu,
Kefa nake tambaya yakara fadi daga inda yake tsaye daga kofan daki rike da labulen dakin nata,
A hankali Maji ta dago kanta zuwa kalkon shi tace cikin yar murya siririya ban san ina ya shiga ba ba nima tun dazun nake zaman jiran shigowan shi don yaci abinci,
Wani wawan kallo ya watsa mata daga inda yake tsaye yace ai dama nasan da yardan ki yake wanan mugun rayuwan da take don ke ce kike daure mai gidin yake kara lalace wa ai kowa yasan hakan,
Hmmm kawai tace tare da fadin Allah ya kyauta malam amma ta yaya zan goyawa Sadauki baya ya dinga abinda yake alhalin nasan ba alheri yake koyawaba a rayuwan shi,
Wanan kuma ke kika sani don ke ce da hasara saboda ni ba shi kadai ke gareni ba ai,
Yana fadan haka ya gaura kofan dakin da karfi yafita daga dakin nata rai a bace,
A hankali maji ta sauke ajiyan zuciya, zuciyan ta yai mata wani tauri saboda kalamin da mijin ta ya fada akan dan tilon danta namiji guda da Allah ya bata a gidan sai yan kannen shi mata da ke bayan shi su uku rak Allah ya bata a gidan mijin nata,
Yayin da sauran kishiyoyin ta suke da yara fiye da nata a gidan
Maji itace mace ta uku a gidan malam habu dan kasuwa ne shi, sai uwar gidan su mama hauwa mai yara bakwai a gidan,tana aikin a women center,
Sai mummyn Asiya, wace itace Maji ke biwa, tana da yara biyar a gidan, tana aikin koyarwa sai amaryan su Anty Kubura da ke da yara hudu ita ma aikaciyar jinyace a wani asibitin gwaunati,
Daga cikin su maji ce bata wani aiki kwakwara don ita batai boko mai zurfi ba tana aji hudu secondary malam habu ya auro ta don haka bata da aiki sai yan buga bugan kasuwanci irin na mata da take a gida kawai,,
Da farko malam Habu yana matukar son Maji da kuma tausaya mata don bata da ilimi mai zurfi, sosai,
Amma yanzu matsalar dan ta, Umar ya wanda takewa lakani da sadauki don kasancewar shi sunan shi Umar faruk, kuma a matsayin shi na dan farin ta yasa take kiran shi da haka,
Rayuwan da Umar yake ciki a yanzu yafara kawo matsalar a tsakanin malam habu da matar shi Maji mai suna maimuna,,
Matsalar farko dai daga irin yanayin shigar shi na tufafin shi, don sam baya iya saka irin tufafin diyan hausawa na al,ada a jikin shi,
Sai kuma gashi ya bullo da dabi,ar son wasan kwallo a rayuwan shi don duk abinda yake da zaran time din zuwan shi filin wasan kwallo yayi dole yabar koma maynene zuwa gurin wanan wasan a duk safiya da marance, na kulli yaumin,
Malam habu yayi iya kokarin shi gurin ganin Umar yabar wanan wasan kwallon kafan da yake yawan fita tun yana dan karamishi,
Amma abin ya faskara duka zagi da bakar magana ga mahaifiyan shi bai sa Umar ya daina wanan wasan kwallon kafan ba da yakeyi
Yan uwan Umar duk yan kasuwa ne sai masu aikin gwaunati daga cikin su amma shi ba ruwan shi da shiga harkan kowan su
Iyakar shi yai wanka yafuta gurin abokai sai kuma zuwa wasan ball, da yake a gaban shi,
Maji tai nasihan rana taina dare amma bai sa Umar ya daina wanan halaiyar nashi ba
Fitan malam Habu daga part din Maji suka hade da Umar wanda ke shigowa gidan a lokacin wani wawan kallon da tsana ya watsawa Umar din,
Sannu Baba ina wuni yakai har kasa yana gaida mahaifin nashi a cikin ladabi da biyayya wanan gaisuwan yaran dakin maji ke da wanan tarbiyan a gidan kawai,
Uwaka na ce uwaka tare da kara mika mai dakuwa da hannun shi na dama yace yaron banza yaron wofi kawai mai ladabin shegu,
Da ban wuni ba zaka gan ni haka ina ka shige haka tun safe sai yanzu zaka shigo min gida, kana wani ladabin shegu haka dakai,
Baba bafa ko ina naje ba ina gurin training tun dazu yanzun kuma da zan dawo na tsaya gurin dantani mai shago muna hira a majalisasr su,
Training din uwar ka na ce training din tsiya jeka ai tunda rayuwan da kazaba wa kanka ke nan ni ba ruwana inka samo wahalanka kada ma kace ni Ubankane,
Umar dai yana duke a gurin da yake baidaga ba yana sauraren kalaman mahaufin nashi,
Malam habu ya wuce ciki fuuu yaba ta faman sababi da bambami akan umar din,
Daga kai yayi ya kai kallon shi ga kofan dakin mahaifiyan shi wace yasan daga gurin ta mahaifinshi yake yagama zazzaga mata tsiya ke nan a kan shi don haka yasa tafasa shigan da yai niyar yi gurin ta a lokacin,
Don yasan yanzu tana can ranta a bace akan rashin ganin shi da batayi ba yini guda zur ga kuma baba ya je yanzu ya zazaga mata balain shi da ya saba,,
Yashige part din shi ya fara dan rage kayan jikin shi, daga shi boxe din shi irin ta maza ya rage a jikin shi,
Dukawa yayi kasan gadon shi ya jawo wasu kwalabe cikin wani leda mai karfi daga karkashin gadin inda ya balli wasu kwaya dake cikin ledan ya bude wani kwalban syrup ya hade su tare ya shanye, a lokaci guda, ya fada saman kujeran shi tilo daya dake dakin,
A hankali ya fara zukan syrup din har sai da ya shanye duk ruwan maganin dake cikin kwalban gaba daya, ya wurga kwalban a kasan carpet din dakin,
Nan saman kujeran ya dan fara lumshe idanuwan shi a hankali yana rufe su ko may ya tuna sai kuma ya mike daga inda yake zaune zubur ya dauke kwalban daga inda ya aje su ya mayar gurin da ya dauko su,
Nan yaja jiki zuwa saman kujeran da ya fara zama ya kara zubewa sama da karfi har saida kujerar yai, dan kara don fada mashi da karfi da yayi,
Nan barci ya kwashe shi babu bata lokaci a gurin baifi mintuna ba sai ga Maji wacce ta kasa barci ta shigo dakin ganin ko ya dawo daga yawon da mahaifin shi yace ya tafi,
Maji ta dade tsaye a kan shi tana kare mashi kallo cikin mamaki tayi tayar dashi amma bai tashi ba dole tafita daga dakin tabarshi a hakana,
Zuciyar ta fam da kunci sai kuna dan zargi da ya fara darsuwa a zuciyar ta a hankali,
A haka ta kwana ranta babu dadi a cikin sa sai faman tunanen da takeyi har dare ya raba sosai a lokacin,
****** ********* ******
Zaune take a f
gaban mahaifin ta a cikin natsuwa take sauraren shi, yana mata zance akan zuwa birnin da zatayi gur8n kaunan shi dake can tana aure don ta matsa a kan Bintu tazo mata hutu ta dan kwana biyu a gurin ta,
Sam Bintu bata,son wanan tafiyan don dai babu yadda zatayi ne da umurnin mahaifinta da gaskiya bataje ba,
Don tafi son ta,zauna a kauyen su tare da mahaifinta don koda take mace ce itace kamar jagoran gidan nasu duk da kasancewar Bintu karamar yarinya ,
Haka take yawan aikin wahala a kan su samu dan abinda zasuci a gidan su kasancewar mahaifin nata ba,wani mai abin hannun shi bane,
Itace zuwa icce itace suyan awara da rana da safe kuma tana koko da kosai kafin ta dawo zuwa makarantan bokon da yake a ranta,
Yanzu gashi gwagonta ta birni ta matsa sai tazo gurin ta wai hutu wanda ita bata san dalilin da ya sa,duk tazo sai tai zancen zuwan Bintu gurin ta hutu ba,
Yan kayan ta,already ta,shirya su a dan jakar ledan ghana most go karama duk jakar ta tsufa sosai don har ledan jikin jakar ta dan tashi ya,wani dan takure daga jikin shi,
Kudi mahaifinta ya ciro daga aljihun shi dubu daya ya mika mata tayi kudin mota dashi,
Kallon kudin take tana mamaki inda ya samo har dubu daya yabata wai tai kudin mota dashi,
Hannu biyu Bintu ta mika ta karbi kudin cikin ladabi tare da fadin na gode Baba,
Bayan ta karba ne yake cewa tau Bintu ki saurareni kiji abinda zan fada maki da kyau,
Ki sani dai rayuwar birni daban yake da,tamu irin na kauye don haka kiyi taka tsatsan da duniya ki kama kanki ,
Ki kawar da idon ki ga duk abinda,bai shafeki ba a rayuwan ki ki tsaya inda gwagon ki ta tsayar dake duk da yake ke yarinyar ce nnatsatsiya amma nasan zakiga abin mamaki da zai iya canza maki rayuwan ki a can,
Don haka kiyi taka tsatsan da duniya baki dayan ta a yanzu babu gaskiya ki tsaya a matsayin ki na yar talkawa kamar yadda kika samu rayuwar mu, aciki tun farko,
A hankali Bintu tace insha Allahu baba zan tsare kamar yadda kace zaka kuma samayni da kiyayyewa insha Allahu,
Yace Allah yai maki albarka Bintu Allah ya tsare min ke da tsarewar shi ta karba da amin Baba idanuwan ta sun kawo hawaye kamar zasu digo dag idanuwan ta,
Shi da kan shi ya rakata har tasha inda zata samu motar da zai kaita, garin Sokoto,
Tana zuwa motar ta cika suka kama hanya sai Sokoto zuciyar ta fam da kunci a cikin sa,
Sai karfe biyu suka shigo gatin na sokoto a lokacin mutane suna ta haramar yin sallah azahar a garin,
Mai yar mashin ta dauka kamar yadda akai mata kwatance tace a kaita Sama road, a bakin shagon dantani mai yar mashin ya tsaya da ita,
Shi ta tambaya gidan Gwago Asmau mai masa ya nuna mata da kwatance tabiya mai mashin kudi ya tafi ta dauki yar jakar kayan ta zuwa gidan da akai mata kwatance, dashi,
Da sallama a bakin Bintu ta shiga gidan ta samu gwago zaune a tsakar gida tana gyara kayan yin masan ta,
Tana ganin Bintu ta fara fara,a tana cewa a,a,a wanake gani yau garin namu kamar Bintu,
Maraba da yar gwago sannu da zuwa sannu da zuwa tana mata maraba cikin jin dadi da ganin ta,
Daki ta nunawa Bintu ta,shiga da kayan ta daga cikin dakin tare da,samun guri ta dan zauna a takure daga gefe guda,
Gwago ta,shigo, dakin dauke da kwanon abinci a hannun ta a rufe ta aje a gaban Bintu, tana fadin zauna ki ci abinci sai mu gaisa,
Cikin yar muryan ta take cewa gwago sallah nake son nafara yi tace tau Bintu ga bayi can jeki ki kewaya,
Sai bayan ta idar da,sallah ne ta fito inda gwagon ta take zaune tana gyaran alaihu tana kokarin karba daga hannun ta,
A,a haba Bintu jeki ki ci abinci mana daga zuwanki zaki buge ga aiki haka jeki kawai ki ci abinci kinji Bintuna,
Kamar yadda gwago tace haka din Bintu tayi ta koma daki ta zauna tare da lankwashe kafafuwanta a hankali ta bude kulan dake gaban ta shimkafane da,wake da mai da yaji a cikin kulan abincin da gwago ta aje mata,sai salad da tumatir da aka yanka daga saman shi,
A hankali take ci a cikin natsuwa har ta kare cin abincin nata wanda ko rabi batayi ba ta mayar da kulan ta rufe wai ta koshi,
Bata zauna ba a,tare sukai aikin masa da gwago ranan ba bata lokaci suka kammala komai da wuri,
Nan suka samu guri suka zauna,suka,fara hiran mutanen gida gwadabawa,
****** ******** ******
Hasken ranan da ya haska dakin ne ya haska dakin abinda ya farkar dashi daga nauyayan barcin da yake ke nan,
Zubur ya mike gami da salati a bakin shi, yana cewa subbahanallahi da sauri ya dan dago daga kwance sai dai jikin shi ya dake mai sai wani nauyi da ciwo yake mai kamar yai wani aiki,
Wanka ya fara shiga yafito da,sauri yake shiri don zuwa makaranta saboda duk abinda yakeyi bai wasa da al,amarin karatun shi ko kadan,
Yana cikin shiri yaji cikin shi yana wani irin kugi na yunwa duk yai waban shaye shayen nashi da dare haka zai wayi gari yana jin cikin shi kamar yai kwana goma bai saka komai a cikin shi,
Don haka da sauri ya shirya ya nufi cikin gida don ya dan samu abinda zai ci a ran shi don yasan cewa yanzu Maji nacan ta aje mai abin karyawan shi ko,
Yana fitowa don zuwa part din mahaifiyar nashi ne yai karo da,daya daga cikin kannen shi diyan dakin mama maimuna,
A guje yaron yake tafe bai ankara da Umar dake fitowa ba daga part din samarin gidan ba,sai ji yayi sunyi karo da junan su, ba,shiri UMAR yakai mashi nashi yana,fadin wanan wani irin iskanci ne haka zaka bangajeni ko kai makahone wai,
Yaron bai tsaya ba don sani zafin zuciya irin na UMAR don yasan idan ya tsaya zai iya shan dukan tsiya yanzu da farar safiyan nan a gurin shi,
Da sallama ya shigo falon mahaifiyar nashi Maji tana tsaye a tsakiyan falon tana magana da kaunar shi Amira,
Shigowan shi ya sa Amira,saurin cewa ina kwana yaya Umar,?
Lafiya kawai ya,ansa mata dashi a takaice ba wani dogon magana Maji dake tsaye jin muryan shi ya,sa ta,waigowa da,sauri tana kallon shi fuska a matse babu walwala, sai wani kallon takaici take mashi,
Maji ina kwana ya kara fadi cikin dan dukar da kan shi kasa cikin jin nauyin mahaifiyar nashi,
A dadare ta,amsa gaisuwa sai cewa tayi Amira dauko mashi abincin shi a kitchen kinji,
Amira ta juya zuwa dauko ma yayan nata abincin nashi kamar yadda mahaifiyar su ta umarce ta da yi,
Kujeran dake falon ya nufa don ya zauna wa saman kujera sai dai muryan Maji ne ke cewa ina ka shiga haka jiya Baba na har dare yayi sosai baka dawo gida ba alhalin kasan mahaifin ku bai son wanan bakin yawon har tsawon dare haka,
Kafin ya bata amsa sukaji muryan Mummy tana fada tanacewa ina Farukun yake ne wai wallahi bari kaji ba,zan daukan maka dukan min yara ba iskancin ka ya tsaya iya kannen ka da uwarka ta haifa amma baga yarana ba wallahi don bazan daukan maka hakan ba,
Ke kuma Hauwa wallahi kiyiwa danki fada yafita harkan yara na a gidan nan tun mu na,sheda juna dake,
Tajuya fuuu tafita daga kofan falo ran ta a,bace sai lokacin ta juya gurin dan nata tare da sauke ajiyan zuciya,
Tace Baba na kafita harkan yaran matan nan a gidan nan don ban son fitina a,rayuwana daka ganni nan,
Dukar da kai kawai UMAR yayi yana kallon kasan dakin ran shi yana kuna don wanan wulakancin da akewa mahaifiyar shi bazai iya dauka ba dole ne ya dauki mataki,
Dama yasan don dan wanan rakwashin da yai mai har uwar shi zataji haushi tazo har dakin uwarshi kafa sheda da da yai mai dan banzan dukan tsiya wallahi,
Har ya gama cin abincin shi Maji bata tanka,mashi ba saboda ran ta ya baci sosai, dashi saboda yawan maganan da yake jawo mata a gidan nan yaiyawa gaskiya,
Jin sallaman shi tayi kawai yana ce mata yatafi sai yadawo zai shiga school don gap yake yanzu da yakare karatun shi, a jamia mataki na biyu da yakeyi,
Yana fita takai kalkon ta ga kayan da yaci abinci tana matukar mamakin yadda wani lokaci yake cinye yawan abincin da take aje mashi duk safe sai dai da rana bai wanan cin abincin haka, mai yawa sosai sai da,safe,
Nan dai ta kwashe kayan zuciyar ta a cunkushe da bakin cikin dan nata, mai yawan jawo mata fitina a gida da,waje,
Jiya da dare mijin su yai mata masifa a kan shi yau kuma da safen fari kishiyarta har daki tazo tai mata still a kan shi dai din guda
Haba haba haba dai babana Allah dai ya shirya min kai kawai zan iya cewa don matsalar ka tai min yawa wallahi kowa dai kai kowa dai kai ya Allah kai min dauki akan halin wanan yaron,
Ya Allah ka,shirya min su baki dayan su ka,shiryawa sauran kullimin musulmin Allah a baki daya,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/19, 10:31 PM - ~: A Lokacin ne,,,,
2⃣
IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA YAR UWA DON HAKKIN WASU NE,,,
Zaune take a kofan dakin ta tai tagumi sai faman tunane take tana kulawa tana warwarewa ita kadai a gidan don mijin ta ya fita tun safe zuwa gurin aikin saukalen da yakeyi gurin manyan motoci ,
Sai idan ya dawo ne suke dora girkin abinda zasuci kullun a haka suke wanan rayuwan wahalan ita da iyalin ta,
Yanke shawara tayi a inda take zaune gara ta hada kayan dakin ta ta,sayar ta,dan samu koda tsohon fridge ne ta,saya tana sana,an kayan sanyi ko zata samu kobo yana dan shigo mata a hannun ta,
Ba bata lokaci da mijin nata ya,dawo gida batai nauyin baki ba tafara fada mai shawaran da ta yanke,
Shiru yayi tare da nisawa inda yake zaune saman tabarman shi, da yake shan iska a kai, yace
Halima banki shawaranki ba gaskiya amma ni a nawa tunanen da kiyi hakkuri ki zauna da kayan ki don wanan lokacin da muke ciki lokaci na lahaula ga kowa ba masu kudin ba ba tallakawan ba kowa wiwi yake yi da wanan karnin,
Koda kin sayar da kayan dakin ki don kiyi sana,a ina mai tabbatar maki rayuwa bazai bari ka mayar da ko kwatankwancin abinda ka rasa ba a baya kinga hasara da dana sani sai ya hau mutum,
Ke dai kawai ki bar kayanki tunda Allah bai hana muna dan abinda zamuci ba a rayuwan mu to ai alhamdullahi komai yanzu sai hakkuri don ba kowa ke samun yadda yake so ba,
Matar tanisa tace ni dai gaskiya nayi niyya da kabarni kawai na sayar a samu, dan gurin rage wani hanyan kuma.
Ya fahinci bazata dauki shawaran shi tayi hakkuri da jarabbatar talaucin da suke ciki ba don haka sai ya kyale ta tayi yadda take so kawai.
Don yanzu ba matan birni ne kawai ke bijirewa girmama wa dokan mazan su ba har ma da matan kauye haka suke don yadda zamani ya juya a lokaci ne muke ciki,
Bai gida washe gari baya gida takira dillaliya sukai cinikin kayan dakin ta tazo ta kwashe akan dan kudi kalilan tabar mata su,
Ba bata lokaci ta hada kudin tana jiran dawowan maigidan ta ta fada mai ya barta taje ta dan samu abin da tai niyar saye da kudin,
Bai mussa mata ba don yasan kudin ta ne don haka ya kyale ta tayi yadda take so da abinta don yana gudun yai magana ta ga kamar yana son wani abune daga cikin kudin, nata.
Bata tsaya bayan sallah magariba ta shirya sai gidan wata dillaliya mai sayar da kayan hannu, inda tai sa,a tasamu fridge har guda uku a gidan da akasa a kasuwa nan sukai ciniki ta samu dan babban wanda bai tsufa ba sosai ta saya da kudin nata,
Suna barin gidan ta turo mai baro ya daukan mata shi zuwa gida zuciyar ta fam da farin ciki a ran ta,
Da mijin nata,ya,dawo yai mata fatan alheri da,daukaka a cikin al,amarin.
Tun daga wanan lokacin ne tafara dan sana,a da fridge din nata tana dan samun kwabon kashewa ta fannin ta ita ma,
Hakan ne ya kawo mata saukin yan damuwan yau da kullun da take ciki don tana dan samun kudin kashewa a wanan fannin nata.
****** ********* ******
Safiyane duk jama,an gari sai faman zirga zirga suke kowa harkan ga ban shi yake yi ba mai kama hannun yaro daga cikin su.
Sai faman sallama ake a gidan gwago Asmau da manyan kuloli gurin sayen masan da take soyawa tun da farar safiya.
Gwago Asmau taji dadin kasancewar Bintu da ita a yau din don ba karamin taimaka mata takeyi ba.
Komai cikin natsuwa Bintu takeyi ga tsabta sai ta wanke hannu da da kayan aiki kafinta taba shi,
Sannu sannu tafara gyara ma gwago aiyunkan ta sabanin yadda take aikin ta a baya in local way,
Bintu taba gwago shawaran cewa ta mayar da masan ta na zamani don yanzu akasarin mutane suna fama da lalurar ciwa gyambon ciki watau ulcer,
Gwago Asmau tai mamakin yadda Bintu karama da ita tasan wanan dubara gashi kuma daga kauye take zaune,
Don Bintu ta bata shawaran cewa yanzu da safe zasu dinga kai nika kuma su toya shi, a lokacin,
Gwago Asmau tace kai haba Bintu ni kada ki jawo min hasaran kudi yaya zaki ce na kai nika ranan kuma na soya masa a ranan,
Bintu tace wallahi gwago ki gwada masan ki zata samu karbuwa sosai wallahi don duk masu tsoron cin masa don tsamin shi zakiga sun fara sayen shi,
Gwago tace yaya zan yi wanan aika aikan haka Bintu na,
Bintu tace gwago zamu wanke shimkafan mu fara sai mu barta a jike cikin ruwa ta kwana da safe zamu tsamay mu hada da dan falawa dai yadda muke son shi sai mu hada da dafafan shinkafa da yis da baking powder,
Sai a kai nikan shi ayi muna kullun shi na ruwa amma kada a cika ruwa da yawa gurin nikan shi idan an dawo sai k8 dan kara gurorin dafafan shikafa da kaurin shi yadda kike bukatan shi,
Sai kawai a fara soyan shi kamar yadda ake masa a koda yaushe,
Kai yan nan akwai ki da dabara kamar wata babban mace ke a ina kika koyo wanan masan kuma,
Bintu tai murmushi har dan dimple din ta ya lutsa kadan tace nima a gurin wata makwabciyar mu dake masa a bauchi sukai zama, naga tana hakan.
Yadda Bintu ta fada hakan sukayi sai dai gwago Asmau sai Allah Allah take kada abin ya bashe su sai da taga zubin farko masa yafito da kyau hankalin ta ya kwanta,
Nan da nan masa ya kare masu washe gari masu sayen masa sai yaba dadin masan jiya sukewa gwago Asmau, suna cewa kai masan jiya ga taushi ga dadi wallahi babu tsami ko kadan, don har miyan sai da bintu ta sa aka dan zuba mai dan baking powder kadan,
Nan da nan labarin dadin masan gwago Asmau ya dan kewaye shiya, don dadin shi.
Daga gidan malam Habu aka aiko asai masan dubu da dari biyar sai aka samu akasi babu canji a gurun gwago don haka aka ba su masa kawai, sun biyo canjin .
Sai da yamma ne gwago ta ba Bintu canji ta kai gidan rayuwan Asmau bai so ba don bata son dabi,ar shiga gidajen mutane ita.
Haka yasa tun zuwan ta garin bata je gidan kowa ba, tana cikin gida gurin gwagon ta kawai sai nikan da tafita da,safe tabi almajirai, don taga yadda za,a nika masu kullun masan su.
Hijjab din ta ta saka tare da sa dan sifas din roban ta sai gidan duk da dai kwatancen gwago tabi don shiga gidan,
A hankali tai sallama daga kofan farko na shiga gidan babu kowa sai flawer a shuke daga can nesa ta hango wani saurayi a duke yana sa takalman kwallo a kafan shi da alama shigar shi ya nuna cewa gurin wasan kwallon kafa zai tafi.
lna wuni tace tare da dan duka mashi har kasa batai tsanmani ya amsa mata ba sai cewa tayi don Allah ina hanyan da zan shiga cikin gida canji na kawo na masa.
Fuska a murtuke ya nuna mata da hannun shi, ba tare da yai magana ba,
Inda ya nuna mata ta nufa a hankali sai dai tana shiga duk ta daburce don gina ne na part din mata hudu ko wace da nata daban,
Yanzu ni ina zan nufa ta fadi a ranta batare da tasan wanda zata kaiwa canji ba.
Tana shiga tai tsaye tana ta faman kwada sallama ita ka dai a tsaye shigowan wata mata gajera fara mai kiba yasa ta mayar da hankalinta ga matan,
Ina wuni take ce mata cikin ladabi matar ta,amsa a,dadare da fadin lafiya,
Bintu tace canji aka ce na kawo daga gidan hajiyan masa, kamar yadda ake kiran gwago Asmau, dashi a uguwar,
Cikin wani irin kushe fuska take cewa isa mana ki tambaya ciki tun nan ta fahinci akwai kishiya a gidan ke nan ,
Tanan tsaye sai sake, sake, take a zuciyar ta, tana niyar juyawa ta koma ne taga wata mata baka, tafito daga wani shiya dake daga can gefe tsabare da sauran shiyan ,
Hannun ta dauke da bukiti da mopa da tsiyatsiya da alamar da ga shara take futowa matar.
Itama dai cikin ladabi ta gaida matar da ta gani ta amsa mata cikin sakin fuska.
Tana cewa sannu ko kina neman wani ne ko Bintu cikin murmushi don taga fuska, tace dama canji ne akace in kawo inji Hajiyar masa,
Au daga gidan hajiyan masa kike ne, ?
Eh a nan nake tana kokari miko canjin dari biyar din dake hannun ta din,
A shigo mana daga shigowa har zaki tafi zo shigo daga ciki kinji ba mussu Bintu tabi bayan ta zuwa part din da matar ta nufa.
Suna shiga dakin taga ashe daga ciki a kwai dakuna da kuma kitchen, a cikin su.
Kujeran dake a falon gidan ta nuna mata ta zauna tare da kara gaisawa da ita,
Amira Amira matar ke kira daga falo, sai ga wata yarinya doguwa zata dan girmay ma Bintu tafito daga dayan dakin dake part din,
Tana ganin Bintu zaune sai kallon ta take da mamakin ko wacece ita, gaida yarinyar mai suna Amira Bintu tayi.
Maji gani inji Amira din tana mai kallon uwarta, don son jin mai zata ce mata.
Karbi canjin nan jeki sauran dakuna ki tambaya wa hajiyar masa take bi canji dazun da safe,
Amira ta turi baki gaba tana cewa ni wallahi in ba dole ba ban sin shiga gurin kowa a gidan nan don dai kawai da mutum ya shiga yanzu za,ace ga abinda yayi kuma.
Aiken ki fa nayi Amira kika tsaya mai da naki ba,asin son raki haka Amira taja kafa ta,wuce zuwa sauran sassan gidan,
Inda Bintu take zaune maji ta dan kalla tana fadin yi hakkuri kinji har ta dawo muji ko canjin waye,
Andan jima kadan sai ga Amira ta dawo tana konkwami tana fadin wai, maman su Hadiza tace takawo ta aje ko na baba ne amma taki bata ga kudin tana kokarin mikawa mahaifiyar ta kudin hannun ta,
Amira mai yasa baki bata ba da kika dawo da kudin nan may zanyi maki dashi a nan ,
Maji cewa fa tayi wai zata ajewa Baba ni kuma nasan ba,bashi kudin zatayi ba shiyasa nace mata tabari na tambaya sauran shiya muji in ba nasu bane,
Yadda maji take magana da yar ta acikin lumana ba daga harshe ya ba Bintu shawa sosai sai faman bin su da kallo take yi, na sha,awa.
Yadda uwa takewa yar ta magana a cikin kwantar da hankali da fahinta,
Inda Bintu take a zaune Maji ta,waiga tana fadin inaga canjin Alhajine idan ya dawo zan tambaya muji in har ba nashi bane zan sa su dawo mata da kudin.
Bintu ta mike don fita daga dakin a daidai lokacin da Umar ya shigo dakin ke nan babu ko sallama.
Sai cewa yake ni zan tafi ball kada kuma ace ban fada ba natafi , yana,wani cicin magani cikin dakewa,
Haba babana kai wai yaushe ne zaka girma zaka shigowa mutane daki babu ko sallama kana wani shan kamshi da cin magani.
Kamar wan da zai tafi gurin wani abin arziki wai ball, ball din mai zai tsinana maka a rayuwanka ne wai,
Maimakon ya tsaya yaji karshen maganan ta,sai juyawa yayi kawai ya fita daga dakin,
A hankali maji ta sauke ajiyan zuciya tana furta Allah ya shirye ka babana,
Bintu dake tsaye ta amsa da Ameen Mama sosai har cikin ran maji taji dadin Ameen din da Bintu ta amsa mata dashi.
Mama ni zan tafi sai anjima ke nan zan fada mata yadda akayi, to kin ji yar albarka ki gayar min da Hajiyar masa din kinji ,
Bintu takai kofa Maji tace may ye sunan ki ne bakuwar hajiya ?
Cikin murmushi Bintu ta amsa da Bintu nake mama Allah sarki sunan mai kyau sunan mahaifiyar maigidan nan ke nan ai.
A waje ta samu wanan mai bakin ran yana tare mashin zai hau ko kallin shi batayi ba don tsoro ma yake bata, ita,
****** ********** *****
Kida ke tashi daga cikin waya daga daki yayin da uwar ke daga gurin wanke wanke tana wanke kwanukan da suka ci abinci dashi na daren jiya,
Ganin hankalin uwar yana ga aikin da takeyi yasa Raiha mikewa a hankali zuwa gurin da ta boye kayan harkan ta a ciki ta jawo wani kwalba ta kwankwada son ranta tai wani jan iska da tsuke bakin ta a hankali.
Ta koma saman gadon da ta tashi a kai, ba bata lokaci sai barci ya dauke ta a gurin.
Uwar na shigowa daki taga yadda ta kwanta daidai da ita, a hankali uwar ta kada kan ta don takaici tana dan kiran sunan ta ,
Ke Raiha Raiha fa wai bazaki tashi ki yi abinda zakiyi bane ki kwance haka galala tun safe kamar mara lafiya.
Cikin murya irin ta mashaya Raiha tace kai haba mama please easy please easy barci nake ji fa.
Ikon Allah barci dai barci dai kamar wata malalaciya sai kin tashi ki ce wai ke yunwa yunwa kamar zaki hadiye mutane, lokaci guda.
Nan uwar ta barta ta,tafi tana mita a kanta a lokacin ta gyara kwanciyar ta da kyau taci gaba da barcin ta.
Bata farka ba sai yam lis ta farka sai bandaki tafada tana sauri don fitsari da kashin da take ji a lokaci daya.
Bayan ta dauki lokaci tafito ne daga ban dakin shine ta debi ruwa a randa ta watsa don ta dan ji jikin ta ya sake mata don nauyin da yai mata a lokacin.
Tsab ta shirya cikin wasu kananan kaya ta,dauko hijjab din ta tayafa a kan ta kamar wata ta kirki can.
Inna ni zan fita tace a gadarance uwae tace ina kuma zaki yanzu ana batun yin magariba kuma ?
Ba nisa zan tafi ba zan dan je can kasan layin mu ne na,dawo .
To ki daiyi sauri kafin mahaifinki ya dawo bai samay ki ba.
Yanzun ai zan dawo ba dadewa zanyi ba Inna, tana fita ta tare mashi sai wani uguwa da ke da yawan mutane akasarin su duk matasa ne maza da mata birjit a gurin.
Kutsawa tayi itama tashige gurin can wani dan lungu wani gaye ne ta nufa yana zaune tsakiyan su sai busa hayaki yake,
Yana saye da,riga blue mara hannu a jikin shi duk mozuqu din shi sun fito wahe sosai.
Yana ganin ta tace yar halas yanzu fa nake zancen ki a,raina nace ko kayan basu kare bane har yanzu don tun shekaran jiya baki leko mu ba nagani,
Ina tafe ai na tsaya ne har na karasa sauran wanda ya dan rage min don gudun kada na tara kwalabe a dakin namu yai yawa.
Kasan gyatumar ba sanin kai tayi ba har yanzu bat da sau nake mata koda ta rutsani nakan ce mata maganin mura ne nake sha ai,
Shegiya baby watau dai a kwana kike sakata ke nan dai ko?
Kai ma kagane ke nan ai don abin sai da kwana don ba,a,bari ai saurin sani abin.
Nawa kiia zo dashi don kin san ranan ma na biyo ki canji dai ko?
Nawa ka biyoni brosha ina dari uku ne dai kawai ko?
To dari uku ba kudi bane dasu ne ai muke karawa muna business din ga,shegun kwalawan nan kullun sai kokari suke suga,sun kama mutane don kawai su caji mutum dan canjin kashi badon a,daina harkan ba.
Ni dai kaji miko min kaya na natafi don yau ba dadewa zanyi ba ina sauri ne.
Wasu kala za,a baki akwai fa,sabbin fitowa masu aiki sosai wallahi tace cikin tsiwa bani dai wanda ka saba bani kawai na,wuce na biya shagon Samuel na kara dan kwalabe a can,
Daidai lokacin Umar yazo baiyi magana ba,sai kudin da ya miko mashi yace kaibani nabar gurin nan don ban son sa ido da yawa.
Brosha amma kasan sai ka sallameni zaka sallami wani can ko?
Umar yana daga gefe ya harde hannayen shi a kan chest din shi ya zuba masu ido yana sauraren abinda sukeyi kawai.
Sanin ko waye Umar yasa brosha fara hado mai kayan shi don yana kai wata biyu baizo gurin ba yafi aikowa a,saya mashi,
Yana kokarin miko mai canji tare da kayan shine fam cike da leda, yaji muryan Umar yana fadin ka bata da sauran canjin sai wani lokaci kuma ya juya yatafi a bin shi bai tsaya jin may zasu ce ba,
Binshi da ido Raiha tayi tana,mamaki mutum haka ga alheri ga kuna ta hango jin kai a tare da shi.
Mtwee tace tare da juyawa tace kai bani na,wuce kaji ban son bata lokaci nace ma,
Aike yau kin taka sa,a wallahi haka yake in har yazo sai yai wa wani alheri a gurin nan, sai dai kuma ba kullun ne yake zuwa ba,
Tana karba ta juya tabar gurin don zuwa chemist ta sayo sauran abubuwan ta.
Tana fitowa yana,shigewa mota ya harba yabar erea din don gudun wani ya ganshi idon sani yasa yake zuwa wanan uguwar sayen kayan mayen shi can nesa da gida.
Ko da Raiha ta isa gida lokacin har takwas da rabi na dare.
A lokacin mahaifinta har ya dawo daga kasuwa sai dai yana daki shi yana rage kayan jikin shi.
Hakane ya bata daman shigewa ciki batare da yasan dawowan ta ba gidan.
Ganin ta kawai mahaifiyar ta tayi don haka hankalinta ya kwanta don tasan da zaran mahaifinta ya ji bata gidan matsala ya faru ke nan.
Tafito daga dakin mahaifiyar ta,a,daidai lokacin da mahaifinta yake kokarin zama a,saman tabarma a kofan dakin shi tana cewa baba sannu da,dawowa kawai ta,sa kai ta shige abinta,
Ashe tana gidan ai yanzu nake batun nace wai tana ina ne banji motsin ta ba uwar tace tana ciki ai tundazun, (Uwa ke nan,)
Nan ya zauna yana cin abinci suna hira da mahaiyar Raiha cikin so da kauna a tsakanin su,
****** ********* ******
Yaro ne daga kofan gida yake kwada,sallama yana cewa abani ruwan pure water, na naira goma.
Da sauri Hanne tafito daga dakin ta tana cewa shigo ka karba kaji ta bude dan fridge din ta ta dauko mai ruwa leda biyu ta bashi ta karbi kudin zuwa dakin ta,
Ba,ajima ba wata yarinya tashigo itma ta saye haka mutane suka gane cewa tana sayar da,ruwa ana dan shigowa gida ana,saye.
Nan tai shawaran ta fara dan kayan sanyi irin zobo da kunun ayya tana hadawa dashi ko zata kara cabawa ga samu,
Kudin ta bayar aka,sato mata kayan zobo da na kunun ayya ta hada.
Ba bata lokaci aka ganeta mutane suna shigowa,saye tun dai da,zafin ranan da,ke yawa a garin don ko baiyi sanyi sosai ba ana saye hakana.
Ance rai da kwadai don haka Hanne tafara shawaran canza fridge din ta zuwa wanda yafi wanda ke gare ta girma don ta kara bun kasa sana,an ta dashi.
Da maigidan ta yadawo ta fada mai ahawaran da tayi shiru yayi don baida na fadi, don baida na fadi saboda yasan cewa shi kan shi yana amfana da wanan sana,an data samu tana dan yi yanzu.
Saboda yana tare masu gurare da dama na yau da kullun a gidan har ma,da wanda bai zata ba don yan zu a lokaci ne muke inda mata suke bada nasu gudun mawa a gida fiye ma da yadda ba, zata ba a rayuwa
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/19, 10:31 PM - ~: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,
3⃣
MAJI ce kwance a,saman dogon kujeran dake cikin falon dakin ta, ziciyar ta a cacushe yake mata da bakin da bacin rai ga radadi da zugin da yake mata.
Bakomai ke damun zuciyar Maji ba sai irin halin rayuwan da Allah ya jarabi dan ta dashi.
Wanda a da can baya ba haka rayuwan shi take ba sai yanzu da girma ya fara shigan shi ne bakon al,amarin ya fara shigan shi haka.
Hayaniyar da take ji yana tashi daga cikin gida yasa ta sauri mikewa zaune da sauri, don ta saurara idan dai ba saudakine ya ja mata wani sabin maganan ba kuma a gidan.
Aikuwa jitayi mama tana fada tana cewa wanan yaro ya dai zama muna masifa a gidan nan yanzu.
Yaro guda ya zama alkakai acikin yan uwa wai mai saudauki ke son mayar da mutane ne haka wai, duk yaro abu ba abu ba ya kai mai duka bugu haka har na tsiya.
Sai muryan dayar kushiyarta da take biwa tana cewa ni wallahi karan shi zanyi akan takalman banza zakaiwa yaro mugun duka haka har ka fasa mai baki.
Anty watau amaryan su tace a,a kada ki karan shi kijira har shi mahaifin nashi da ya bata shi ya dawo ki fada mai muji ko muga abinda zai yi,
Basu suja batashi ba da so sun dauki son duniya sun dora akan shi yanzu ai ga abinda so ya jawo masu sun gani.
Maji dake daga daki takai zaune a hankali saman kujeran da ta tashi a kanshi tana maijin zafin maganganun su a ranta don dai ita tasan a iya yinta ba wani gatan da ta gwadawa dan ta, a baya fiye da sauran yan uwan shi.
Amma babu yadda zatayi don ance dan kuka mai jawa uwar shi jifa don da bai shiga harkan yaran su kamar yadda ta hore shi da zafin zuciyar shi akan ya rage da bai ja mata yawan magana na habaici ba ga kishiyoyin ta.
Wasu irin hawaye ne masu dumi suka fito daga idanuwan ta a hankali, a daidai lokacin Amira dake cikin daki kwance tafito falon nasu.
Ganin yanayin uwar,su yasata karasawa kusa da ita ta zauna tanavmai kura mata ido tace yaya sadauki ne ko maji.
Don Allah maji ki fita zancen su ki daina zubar mashi da hawaye malamin mu fa na islamiya yace muna ba kyau uwa tai kuka akan dan ta musan ma ma da namiji don Aljannar shi yana ga hannun ki mama don Allah ki yi hakkuri ai ya kamata ace kin saba da halin shi yanzu ki daina bata ranki a kan zancen shi hakana.
Suma ai daukan magana ne mai yakai su ga kayan shi tunda sun san bai son raini shi.
Baki maji ta bude da nufin tai magana sai kuma bacin rai ya hana ta iya furta komai sai taja bakin ta tai shiru, amma duk AmiraA yarinyace karama zancen ta ya shiga ran ta sosai don haka tai shiru kawai amma a zucuyar ta ba dadi sam wani kunci take ji sosai.
Har dare sadauki bai shigo gidan ba don yasan abinda yaiwa kanin shi yana can ana jiran shi dashi cikin gida.
Shi ko yanzu daidai yake jin shi dakowa don ya fahinci daga mahaifiyar su har su duyan ta ba mai kaunan su a gidan gaba dayan su.
Sai yamma kamar kullun malam Habu yadawo gida ko hutawa ba,a bari yayi ba aka tare shi da zancen sadauki akan yaiwa Abdul mugun duka wai don kawai yasa mashi takalman shi na kwallo yafita dashi gurin wasa.
Kai kawai malam habu ya kada yace wanan yaron wanan yaron ya kai min ko ina a rayuwana wallahi.
Daidai lokacin Maji ta shigo dakin saye da hijjab din ta mai ruwa light green.
Tana mashi sannu da dawowa amma bai karba mata ba,sai cewan da yayi Maijidda wallahi danki ya zama min masifa a rayuwana .
Kullun har zullumin dawo gida nake daga kasuwa don nasan da zaran nadawo da,wuya ba,a tareni da zancen shi wanda zai bata min rai ba.
Shiru maji tayi tana,sauraren kalamin maigidan nasu a gaban sauran kishiyoyin ta yana cewa ki fada mashi wallahi zanyi maganin shi don na lura kamar ma ya fara shaye shaye ne a rayuwan shi.
Niko bari kiji in har hasashe na ya zama
gaskiya to wallahi ba zan barshi a gidana ba ya bata min sauran yara na na kirki.
Allah ya tsare ya kare Maji ta furta a fili aidama haka kawai zaki iya cewa bayan shi baki da,wani abin fadi ai,
Bata ce komai ba,sai hadiyan bacin ran da tayi tare da juyawa tana fadin Allah ya kyauta.
Malam Habu yace ai zai zo ya samay ni zan mu hadu dashi don ba zan yarda ya,sabauta min yara ba ga banza.
Maji dai fita tayi daga dakin don tasan ko ta,tsaya,babu abin da,zataji banda bacin rai kawai.
Din haka taiwa kanta kiyamallaini tabar dakin don bazata iya jure sauraren kalaman mijin nasu ba akan ita da dan ta.
Tafiya take zancen mijin nasu gareta yana ci mata rai don zancen sadauki shi ne zance mafi muni dake hada ta,da maigidan nasu.
Duk irin kwaram din da,aka,sha a,baya baya akan kishiyoyinta da ita a baya, baya tayar mata da hankali kamar zancen sadauki da ya taso mata a yanzu,
Yanzu saboda shi tana ji tana gani duk wanda ya kwaso zancen shi akan tane zai yaba mata don halin dan ta kawai,
A kulun kalaman maigidan ta ga dan ta yanzu yana kona mata zuciyar ta da jikin ta ba ma zuciyar ta kadai ba,
Ita a,zaton ta ai wanan abin abinda ya shafe su ne baki dayan su bawai ita kadai za,a dorawa laifin ba don itace mahaifiyar shi ne kawai kowa ke ganin laifin ta ita kadai.
Abin da ya kamata su taru su nuna bacin ransu a kai su tayata bakin ciki amma sai gashi kowa ya,zamay yabarta da laifi ita daya.
Amma babu komai ta furta a,ranta tare da hade yawun bakin ciki a cikin ta, tana mai sauke ajiyan, zuciya kawai.
Bata ankara ba,sai hawaye kawai taji yana biyo mata a idon ta.
Gaskiya zancen Sadauki yana tayar mata da hankali sosai ta rasa wanda zata kai kukan ta gare shi ya tayata bata shawara a cikin gidan.
Don duk yanzu suna matukar nuna mata kyama akan zancen shi gabadayan su gidan har shi maigidan kan shi.
Shin may nayiwa Allah da yai min wanan mumunan jerabawan haka akan dan tilon da daya da Allah yabani namiji a duniya ?
Ni dai nasan harga Allah ban cuci dan kowa ba a rayuwana da wanan jerabawan yafado a kaina.
Duk da ni marainiya ce na riki maraici na ban kai kaina inda Allah bai kaini ba, ina zama a matsayina na mara galihu har a gidan aure na.
A hankali ta kara lumshe idanuwan ta tana tuno rayuwanta na baya da kuma irin kokatin ba yaran ta tarbiyan da takeyi.
Ba komai take kara tunawa ba,sai irin dafin bakin da maigidan su yake mata a,baya,
Da yakan ce maijidda duk da ba komai ke gare ki ba,a,duniya ni ina sonki a yadda kike.
Don kina da komai da nake bukata sabida ke ta daban ce acikin matana, ba zan iya jure rashin mace irin kiba .
Kallo daya in nai maki yana wanke duk kan wata matsalar rayuwana don haka nake kwadayin samun zuri,a dake don nai alfahari dasu koda bayan rayuwana ne.
Murmushi gami da hawaye ne yazo mata a lokaci guda ta furta namiji kanin ajali.
****** ********* ******
Akwana a tashi yau Bintu satin ta hudu gurin gwago Asmau a garin sokoto.
Kullun sauraren take raji gwago na mata zancen zuwa gida amma shiru kake ji ba zancen, har ranan ta gaji tai wa gwagonta zancen komawan ta gida amma sai gwago take ce mata.
Haba Bintu yanzu ke har kina sha,awan komawa gida gurin wanan bakar matan uban naki mai mugun nufi a kanki ko yaushe.
Nifa da mahaifinki mun yanke shawaran kiyi zaman ki a nan don yace hankalinshi yafi kwanciya idan kina a guri na ko kiyi ni sa dasu kadan.
Don haka ki kwantar da hankalinki kiyi zamanki a nan ba zancen komawa gida don hankalin mahaifinki ya kwanta.
Badon Bintu taso ba dole ta yarda da zancen gwago din don tasan haka zancen yake.
Kullun adduan mahaifinte ke nan akan Bintu Allah ya kawo lokacin da zaki bar gidan nan zuwa wani guri ke ma ki huta hakana wa rayuwan ki.
Tunda mahaifiyarki ta barki bata damu da damuwar ki ba ko wani hali kike bata sani ba.
Gaki yarinya natsatsiya duk halarcin da kikewa matar nan da diyan ta kina bauta masu dare da rana ba gani take ba.
Amma kiyi hakkuri da irin rayuwan da kika tsinci kanki a ciki haka Allah ya kaddara maki taki rayuwan zai kasance a gidan uban ki.
Hawayen da ya silalo mata ne ta dan sa gefen hannun ta ta share a hankali.
Duk lokacin gwagon tana kallon ta a cikin muryan kuka ta dan dago kanta a hankali tace to gwago zancen karatuna fa ?
Wanan ba matsala bane ai Bintu zan yi magana a,samo maki makaran tar jeka kadawo dake can kasan layin mu ta gwaunati sai kici gaba da zuwa ko?
A hankali Bintu ta,daga kai alaman taji ta juya jiki ba karfi zuwa cikin dakin kwanan su don ta gyara masu saboda yamma yayi kuma,su basu sharan dare saboda ance baida kyau, yana kawo tsiya a gida.
A kwana a tashi ba,wuya a,wurin Allah Bintu tafara zuwa makaranta kamar yadda gwago tai mata alkawari a baya.
Da yake Bintu yarinya ce mai hazaka baiwanta daga Allah ne, sai bata sha wani wuya ba sosai a cikin karatun ta komai tana ganewa yadda ya dace.
Yawan aiken da take mata gidan malam Habu yadan sa tasaba da Maji da yaran ta don a gurin su kawai take dan samun fuska a gidan ko su ba wani can sosai ba.
Sai dai idan Maji ta aiko sayen masa in har Bintu ce a kan tandar suyan waina sai ta cika masu kula fam tace akaiwa maman ta.
Haka yasa watarana Maji tasa su Amira su dan yi kwalemar kayan su su ba Bintu don taga tana da bukatan haka saboda rashin wadatan da basu dashi ita,da,gwagon nata.
Gwago Asmau batai sanyi a kafa ba gurin shiga gidan don taiwa maji godiya ita da yaran ta, da suka ba yar ta kyautan kaya.
Ta shiga gidan bayan sallah azahar lokacin Bintu ta dawo daga makaranta ke nan.
Tare suka shiga ita da Bintu din, inda suka samu maji zaune a falon ta kasan tias din dakin nata tana gyara wani ganye da,alamar magani take hadawa dashi.
Sallaman su yasa ta dan gyara tana mai ansa masu sallaman su da fara,a a fuskan ta.
Sun gaisa da,gwago inda tafara zabga masu godiya tana mata fatan alheri akan alherin da sukai wa yarta, Bintu.
Cikin murmushi Maji take cewa ai Bintu yarinyar kirki ce halin alherinta ne yasa sukai mata haka.
Sun dan fara hira tsakanin gwago da Maji inda gwago ke cewa wallahi nakan so shigowa mu gaisa da ke, amma kuma yanayin gidan naku ne baida dadin shigowa don kowa idan ka,shigo sai ya,dinga ma kallon munafuki.
Maji tace haba dai hajiyan masa ai ba yau muke dake ba koma sun zarge ki da hakan ai su ma mutanen arzikin su suna shigowa gidan nan amma ban damu dasu ba ni.
Gwago tace ai babu komai insha Allahu zan dan dinga shigowa idan na,samu lokaci.
Suka mike suna,wa junan su sallama nan gwago ke cewa ina Sadauki ya yashiga kwana biyu bana ganin shi dai.
Murmushi Maji tayi tana cewa yana nan baidai zamane suna batun rubuta jerabawan su na karshe ne shi yasa ba,a ganin shi yanzu.
Allah sarki inji gwago Allah ya taimaka Allah ya bada sa,a Allah ya tsare muna su daga duk wani abinki dana sheri a rayuwan su.
Amin inji maji inda taji dadi sosai da addu,an mai masa da,taiwa sadauki wanda ta dade rabon da taji wani mahaluki yai mashi wanan adduan.
Har,zasu fita Maji tace su dan tsaya tazo inda tashiga daki ta dauko masu dan sabulun wanki da clean cikin irin wanda mijin su yake kawo masu duk sati don wankin tufafin su.
Gwago tana ta godiya da fatan alheri ga maji suka fito, a tsakar gidan nan suka hadu da amaryan su tana shigowa gwago na gaishe ta wani kallo ta,watsa mata na ke wacece ?
Gap da zasu fita daga get din gidan suka hadu da sadauki yadawo ko kallon arziki basu ishe shi ba sai ma gwago ke ce mai Umar sanda mazan fama andawo daga bokon ke nan ?
Ya wani sha toka fuska babu walwala ya ansa ciki ciki Maji dake tsaye daga bayan su data rako su take ce mai bakajin hajiyan masa tana gaida kai ne sadauki
Yace cikin wani murya ai na amsa mata mana ya shigewan shi part din su na,samarin gidan.
Allah ya shirya ka inji maji ta furta a fili sai gwago tai dan murmushi tace amin ke dai ai yaran yanzu sai addua kawai.
Ke dai kibi abinki da,addu,a Allah yasa halin iya kurciya ne kawai .
To Amin hajiyan masa halin wanan yaron sai shi wallahi haba bari fafin haka mana inji gwago ke zaki kara jan abinki ga jiki kina lurar dashi dasannu zai bari ai wanan kurciya ne Allah yasa takara fadi tai masu sallama ta tafi.
Bayan sun tafi maji taga yadace tabishi dakin shi suyi magana tunda Allah yasa yashigo a gaban idon ta.
Yana duke yana hada wayan tv tashigo dakin abinda yasa shi saurin dagowa ke nan daga inda yake duke.
A hankali take bin dakin dake hargitse da kallo sai warin dakin irin na,samari ke tashi daga dakin.
Cikin ya mutse fuska take ce mashi, yanzu kaiko inda kake kwana baka iya gyarawa babana ace dakin dan musulmi ne haka inda ake ibada?
Wai may ke damun kane haka babana na zaci kaine mutim na,farko da za,ayi koyi da halin shi nagari a gidan nan sai dai kasshh ban samu hakan daga gareka ba sadauki.
Naga alamar abinka ba mai yankewa bane, sai a lokacin yadago kai yadan kalli mahaifiyar tashi yana fadin may kuma nayi yanzu maji?
Yanzu fa na dawo daga makaranta tun safe da nafita gidan nan .
To babana shine baka iya,gyara muhalin ka haka dubi fa kagani ai wanan wani abin cutarwa ma yana iya shigo maka baka,sani ba.
Zan gyara ya bata ansa a takaice don yasan duk lokacin da tai amfani da kalaman babana a,gars shi maganace ta kwantar da hankali da fahinta take nufi a gare shi.
Don ba ko yaushe take amfani da kalman babana a gare shi ba tafi kiran shi da,Sadaukin da kowa a gidan yake kiran shi kamar yadda mahaifin shi yake kiran shi dashi tun yana karamin shi dashi.
Ta,dan dade a,tsaye tana kallin shi a cikin tausayawa dan nata ga,irin rayuwan shi ta bahagon halin da ya,fada ciki.
Hawaye ne ya,gangaro mata a,daidai lokacin da ya,dan dago kan shi ya kalleta don jin da yayi tayi shiru a,tsaye bata fita ba daga dakin.
Shiru yayi yana kallon ta sai ya dan dukar da kan shi gareta, tace babana ban son ganin rayuwan ka haka .
Wanan rayuwan da kake yi ba,shine irin rayuwan da na,soka dashi ba a,rayuwan ka.
Don Allah babana ka canza rayuwanka a gidan nan ka koma kamar ko wani yaro na gidan nan.
Ina son naga ka canza ka koma normal life din ka kamar kowa a gidan nan wanan halaiyar dakakeyi ba,rayuwan alheri bace a gare ka damu ma kan mu da muke naka.
Katai maki rayuwanka saudauki ka canza halinka don Allah kazamo min abin alfahari a,duniya, gama kowa dake tare damu.
Zan so ace na zamo uwa abin alfahiri ga duniya na nasamu da dan albarka a,rayuwana, kamar yadda sauran uwaye suke alfahari danasu diyan.
Zan so ka,sasauta halaiyar ka akan wanda kake a yanzu don samun natsuwar hankalina dana mahaifin ka.
A hankali maji ta fashe da kuka,wanda kuka ya sa ta kasa karasa maganan da take son ta fada mashi.
Maji ya ce cikin sanyin murya nifa ban san wani hali da nake yi ba,wanda har zaisa ki zubar da hawayenki haka akaina.
Kallon shi maji tayi a cikin mamaki don watau shi bai fahinci ma yana,da nakasu ba ke nan tare dashi.
Tace kako san har mutanen gidan nan sun fara zargin wai kana shaye shaye ne,
Ya,dago kai da,sauri ya,dan kalle ta sai kuma ya dukar da kan shi yace maji nifa wa yan nan mutanen sun fara isa ta,sun fara saka min ido har da bina da,sheri haka?
Ni dai ka gyara halinka shine bukatana a,gare ka idan ka gyara babu wanda zai dora ma,sheri ai.
Ta juya tana cewa Allah ya kyauta kaji bukatana gareka don naga yanzu guduna ma kakeyi baka son shigowa nasan lafiyan ka kamar yadda kasaba yi a baya.
Bin bayan mahaifiyar shi yayi yana mamakin mutumin da,yafara gano likin shi a gidan don haka ya zama dole ya canza takon shi tun mahaifan shi basu tabbatar da,zargin su ba akan shi.
Don yasan in hakan ya tabbata ba karamin tashin hankali mahaifiyar shi zata shiga ba har ma mahaufin shi din dake nuna yanzu babu ruwan shi da shi yanzu.
****** ******* ******
Zaune take ta tula kudi a gaban ta,sai faman kidayawa take a hankali don gudin tai kure.
Sai da ta kirga su cif tajera a,faban ta tana kallo sannan ta,sauke ajiyan zuciyar ta.
Yanzu abin da ya rage min na hada kudin fridge din nan saura dubu goma don haka bari na kara kaimi naga sun hadu na,samu kafin azumi na dauko babban fridge wanda zai isheni sana,a yadda nake so.
Tashi tayi da sauri ta mayar da kudin inda ta ciro su ta boye, don gudun kada wani ya gani yasan inda ta,aje don tasan da,zaran maigidan ta ya kyala ido yaga kudin nan sunan ta sorry don yanzu zai mata dadin baki sai ya karbe su gaba daya su huta.
Abinda bata sani ba shine shi maigidan nata sam hankalin shi bai ga,abin hannun ta ko kadan don asali ma,shi bai bukatan wanan sana,an wahalan da yaga tana saka rayuwan ta a ciki yanzu.
Don da,ace yana,da,hali da iyalin shi sunji dadin rayuwa a gurin shi.
Amma ina talauci kamar ya yanke saka ne a kan shi don kullun bida yake amma kamar ba,ayi yake sai dai Allah bai hanashi dan abinda zasuci ba agidan daidai gwargwadon hali.
Mikewa tayi ta gyara dakin har zuwa tsakar gidan su don akwaita da,tsabta ko yaushe duk da,talaucin su zaka,samu gidan su tsab tsab dashi.
Yaran tane suka fara dawowa daga islamiya inda tun a,waje tasan da zuwan su din saboda hayaniyar su da taji tun daga waje.
Sannu da gida Umma suke cewa sai faman ce masu take kun dawo sannun ku da,dawowa ,
Yar karamar yar ta,take cewa mama yau a makaranta malam yai muna alwala mungani nima zan iya yadda yai muna nagani.
Nanyaran suka shiga bata labarin yadda malamin su ya koya musu yadda ake alwala har lokacin da mahaifin su yadawo daga kasuwa suka juya gurin shi yana,alwala suna bashi labari n abinda yafaru a islamiyar su yau.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/19, 10:31 PM - ~: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
A LOKACIN MU KE,,,
4⃣
Waya take sai ko mama dake kusa da ita bata iya jin may take fadi a,wayan , saboda matukar tausa muryan ta da tayi ga wayan.
Sai yar dariyar da tayine yasa mama dake zaune saman kujera yar tsugunno dago kai tana mata kallon mahaukaciya.
Ta dan dauki lokaci tana wayan cikin jin dadin abinda ake fada mata ga,wayan wanda babu maijin ta balle a san abinda su ke fadi.
Mikewa,tayi zuwa cikin dakin su inda ta kwanta saman dan gadon katakon dake dakin mahaifiyar nata.
Nan ta shige cikin katon hijjab ta rufe kanta sai dai hannunta na akan gaban ta zuwa kirjin ta a hankali take dan shafa,su don kada a gane may take a lokacin.
Nan taci gaba da,wayan ta na tsawon lokaci mai tsawo sannan tai wani mike barci ya dauke ta.
Haka mahaifiyar ta ta shigo dakin daga gurin girkin da take yi ta samay ta kwance tana barci,
A fili ta furta kai amma,anyi malalaciyar yarinya gurin nan yanzu barci kikayi ashe ni ina jiranki ki min shara a,tsakar gida.
Nan dai uwar dole itace ta karasa aikin ta,da kan ta inda Raiha bata farka ba sai bayan sallah azahar ko shi sai da kyat uwar ta,tayar da ita don tai sallah.
Bayan ta gama cin abinci a lokacin har uwarta na zance dora girkin dare don yamma tayi sai ga Raihanatu tafito a cikin shiga na fita da katon hijjab din ta har kasa.
Sai dai kassh da mutum zaiga mai ta sa a kasan ta da yayi tir da Allah waddai da irin shigar ta haka.
A,a Raihatu ina kuma zaki a wanan lokacin bayan yamma ya riga da yayi ko?
Mama dan wani guri ne zan tafi ba,wai dadewa zanyi ba yanzun zan dawo mama.
Tana fita bata tsaya ba sai shagon sayen kayan mayen su wand kamar kullun gurin ya zama majalissan matasa yan maye kala kala.
Duk da jami,an tsaro suna kawo masu samay akoda yaushe suna zuwa kama mata a gurin masu dabian shaye shaye.
Can ta kutsa tashige daga ciki gudun kada wani yagan ta a gurin don gudun ganin idon sani.
Brosha na ganin ta a lokacin yana mikawa Umar kayan harkan shi Umar wanda yake tsaye da bakaken kaya fuskan shi a murtuke.
Burosha yana ganin ta ya fara washe bakin shi cikin farin ciki da ganin ta yana cewa
A,a yau mutumiyar an shigo ke nan kayan aiki sun kare ke nan dai ko don ba,a ganin ku sai rana,tai zafi.
Ya dauko canji zai mikawa Umar yake ce ko yau din ma,za,a barmata canjin ne dan wancan katon ma naga kai ka biya mata.
Wani kallo Umar ya watsa wa Raiha yace cikin dakiya don Allah ka,sallamay ni don kasan ban son ina dadewa a gurin nan naku,
Raiha cikin yatsune fuska tace aikowa ma,sauri yake don ba wanda yazo don ya tsaya .
Kamar Umar ya bata amsa har ya dan bude baki da zuman yai magana sai kuma yaja bakin shi yai shiru .
Borasha ya mika mai canjin shi yai gaba bai tsaya bin ta kan raiha ba balle ya kulata ma.
Bin shi Raiha tayi da kallo tana fadin ji shi kamar wani mutumin kirki wai sauri yake bai son a gan shi.
Brosha yace to ke nan fa wanan zubulelen hijjab da kika,sa wa zai dauka ba islamiya zaki a haka ba .
Dallah gafara malam nagafa kafara saka min ido don tsokanarka ya fara yi min yawa fa.
Dan sa ido kawai ina ruwan ka da shigata wanan nayi ne kawai don batar da sau amma a ciki ai shigar manya ne nayi sai ta dan daga mashi hijjab din ta inda ya hago wani matsatsen rigar da ta,sa duk nonuwan ta sun dan bultso a gaba sai dan guntun buje na zuwa part dakd saye a kunkurun ta iya cinya kawai.
Kai brosha ya daga tare da fadin kai amma Raiha kin kai shu,uma irin wanan shigar haka sai ina?
Don dai nasan da,akwai inda kike nufi zuwa da wanan shigar haka da kika boye cikin wanan katon hijjab din naki.
Tai wani har da idanuwan ta tana cewa ashe ka gane ke nan mazan, yau casu gare mu har dare shiyasa na dauki kayan aikina don ya taimaka min a can,
Tirka sa ki ce yau akwai babban harka ke nan raiha don nasan mutanen mu zasu hadu a gurin,
Tace hakane amma ba,wai irin wa yan nan ba wanan gayu ne masu harka da kwalabe da manyan wa yan nan,
Nima hanya akai min don naje naba idona abinci ko zanyi cafka a can don kasan ala,amarin sai da kwaskwarima ciki wanan lokacin don gamu nan birjit ko ina kowa na rabon ido yasamu mai cafkan shi.
Gaskiyan ki Raiha nima nasan sai da haka al,amarin don abin ba,a cewa komai.
Aje lafiya a dawo lafiya a yo muna kamu babban giwa mu sha shagalin mu muma ga,aljihun shi.
Ta,wuce tana tafiya a cikin rangaji da layi irin nasu na mashaya da suka goge a fagen boyon kan su, don batar da kaman nin su ga mutane.
****** ********* ******
Guri ne mai kyau da,shuke, shuke ko ina bakajin komai sai sautin kidan dake tashi na turan ci na mawakan Afrika.
Tana fita daga cikin napep din da ya kawo ta ta samu dan nesa kadan ta cire hijjab din dake a jikin ta tare da dan kara gyara tufafin dake jikin ta.
A hankali take takon ta zuwa inda mutane sukai dan dazo akasarin maza da matan gurin zakace ko ba diyan gari bane.
Don irin shigar su da kuma aakin kan su sai mutum ya rantse cewa ai a wata kasar arna ya ke ba cikin garin sokoto ba ma gari shehu usman dan fodio.
Mutumin da yai gwagwalmaya akan addini a kasa da,watsa su har sauran kasashen duniya don amfanin al,umma.
Amma,yau sai gashi a,kasan shi garin shi duniya da lokaci yasa matasan kasar kwaso akidar yahudawa suna yadawa da cusa shi ga,sauran masu tasowa na baya.
Wanda ba,a sokoto ba kawai yanzu ko ina a kasashen hausaw a na samun wanan akido jin na koyan akidar wasu da,al,adun su.
Allah ka tausaya muna ka,shirya muna al,umman mu yaran mu kan,nen da ma,sauran yan uwa musulmai baki daya,
Da farkon shigan Raiha a guein ta dan sha jinin jikin ta don tana ganin abinda yafi karfin idanuwan ta.
Sai da ta hadu da,wasu kawayen ta biyu haka yadan sata sake jiki dama can sune suka gaiyato ta gurin.
Daga inda take a zaune tana bin mutanen gurin da,kallo a fakaice tana kallon irin shigar da mata da mazan gurin sukayi abin sai shukaran kawai.
Don nata shiga ai mai sauki ne bisa ga na wasu yan matan yadda suka saka dan mitsitsin abu a jikin su abin ba dadin gani
Raiha sai tarena kanta a guri don taga iyakar wayewa a gurin yan duniyan da suka fita iya duniyan ci sosai.
Taro yai tsit saboda fara gabatar da bukin da,aka,soma wanda suka ce sunyi shi ne don tunawa da kafa gungiyar su mai shekara biyar da,kafuwa yanzu.
Inda,wasun su sin mutu wasu kuma,sun dain harka suna wani kasar haka dai maigabatar wa yai ta bayane na,shirmay a guri a na ihu da,sowa irin na yan iskan matasan zamanin nan.
Sai kuma aka fara rawa da da,zagaye duk wanda aka jefa a bu ya fada a kan shi dole ya fito yai rawa ko a ci mai shi taran kudi.
Irin wanan jifan ne koda aka jefo sai abin yafada akan jikin Raiha wace ke can ta juya tana magana da kawar ta.
Jin an sa ihu yasata juyawa don ganin may akewa ihu haka,sai jin kyalen rawan tayi a kan ta inda,zasuyi rawa da,wani sauri dan dogo fari dashi.
Dole badon Raiha ta so ba ta mike tafita filin don bata da kudin biyan tara har dubu biyar idan bazakai rawan show ba.
Fitowan ta yasa mutane da,dama gurin suka,san da,zuwan ta a,filin, inda aka sa masu kidan tausi watau cool music,
Rawa na ban mamaki sukayi da saurayin a filin inda,suka bada show yaron ya,dinga juyata yadda ake rawan kidan na ai nahi.
Wanan abin ne ya haska Raiha,a idon mutane don dama Raiha yarinya ce mai kiran mata duk wani abinda ake so gajikin mace ta mallake shi ko.
Wani matashi wanda tun fara,event din ya kafa hular shi a gaban goshi kamar baya kallon abinda ke faruwa a gurin ya mayar da hankalin shi a kan raiha,sosai.
Yarinyar ta,tafi da imanin shi don haka ya yanke shawara a,ran shi cewa dole ne ya nemay ta don ya gana da ita,yadda yake so.
****** ********* ******
Yanzu abubuwan sun dan yi sanyi wa Maji akan Sadauki don tun ranan da tai mafada sai ta dan samu sauki daga gare shi.
Don haka shawaran hajiyan masa yai mata rana a gurin ta sosai maimakon fada na fitan arziki ga yaron yanzu nasiha da ban baki yafi komai sauki ga yaron yau.
Don yanzu sam ba ruwan shi da kowa gidan kwata kwata yafita batun yaran su amma fa idan ka,shiga shirgin shi duk da haka bai ragawa mutum.
Safiya ce matan gidan kowa sai harkan gaban ta takeyi ba,ruwan wata da wata a gidan kowa tasa tafisshe ta haka zaman su yake.
Sallaman Bintu ya,dakatar da Maji daga aikin da takeyi daga cikin uwar dakin ta.
Tafito suna gaisawa da maji a cikin mutunci da ladabi da tsintsiya a hannun ta Bintu sai take mika mata ledan da,gwagon ta, ta bata ta kawo wa maji din.
Tare kuma da karban tsintsiyar dake hannun Maji Bintu ta karba duk da Maji ta so hanata amma yadda ta marairaice yasa Maji mika mata tsintsiyan sharan.
Nan ta kara yabawa da hankali da tarbiyan yarinyar tana dama ace nice da haihuwar wanan yarinyar ma hankali da sanin ya kamata haka.
Tas ranan Bintu taiwa dakin tare da kawar da komatsan dake a fili ta,shige mata dasu daga ciki don yanzu dama duk Maji ta sukurkuce bata da,wani kuzari a jikin ta saboda dafin bakin cikin dan ta ya fara tabata sosai.
Bayan Bintu ta gama da gyara waje ta kofan part din Maji ne ta shigo dakin tana,saye da dan hijjab din ta mairuwan cingan .
Tana cewa Mama na rarage ni zan tafi gida kada gwago taga na dade ban dawo ba.
Nagode Fatima Bintu Allah yai maki albarka Allah ya albarkaci ruwan ki, Bintu ta amsa cikin yar muryan ta, da Ameen mama nagode.
Ta fita daga gidan matan gidan sai binta da kallo suke da take aikin suna mamaki don dai su sun san yaran su basu iya wanan aiki da yar karamar yarinya tayi haka.
Duk wanda ya,shigo ya,samu yadda Bintu ta gyarawa Maji guri sai yai maga suce kai Maji amma yau kan kun sha aiki sosai maji waban gyaran guri haka.
Tace wa Ameera bani fa nayi shi ba yar gidan hajiyar masa ce ta gyara min shi haka ta shigo ta samu ina shara sai ta karba shine tai min wanan aikin haka,
Yarinya yar albarka da ita da mutunci ga sanin ya kamata a yar karamar yarinya da ita haka.
Amira tace ni dai yarinyar tana bani shawa wallahi don tasan girmama na gaban ta sosai.
Har maigidan sai da yaiwa Maji magana dacewa yau shiyan nan naki yai min kyau ga kamshi na tashi sosai.
Murmushi maji tayi tana cewa ya ta yar albarka tazo tai min wannan aikin yar gidan hajiyar masa na makwabtar mu
A,a tayi kokari su wayan nan katar banzan may sukeyi ne da,bazasu iya gyara guri ba,sai wata tazo ta gyara masu.
Maji tace halin yaran nan ai sai su don ko sunyi basuyin yadda wanan karamar yatinyar tayi.
Tun wanan rana kwana bibiyu sai Bintu ta shigo gidan gurin maji ta dan yi mata aikin da ya kamata tai mata sai ta koma gida.
Sannu sannu har Bintu tafara fahintar cewa Maji tana fuskantar matsala a gurin mutanen gidan don basu kaunarta sam.
Ga fitinar dan ta da koyaushe ya shigo gidan tana jin yadda yake uwar ke fama da shi akan wasu matsalolin da bata fahinci aini cin yawan laifin da yakeyi ba ako da yaushe don maman nashi bata fitowa fili tafadi sai dai taganji tana cewa.
Baba kaiwa Allah ka rufa min asiri ka,daina halin nan naka don girman Allah.
Sai ya kan katse uwar da wani irin magana a gala baice da cewa ni mama mai nayi ne wai kullun ace wai mutum yai laifi.
Sai yafita a kasalance yabar dakin zuwa waje maji kan bishi da kallo har yabar dakin ta sauke ajiyan zuciya tace Allah ya kyauta.
Yawan ganin da Sadauki yakewa Bintu a gurin mama bai sa ya,sake da ita ba asalima dai shi yarinyar haushin ta yake matukar ji a,ran shi sosai.
Don tafaye yin abu kamar muna fuka idan ta ganshi ta kama dan noke noke ke nan kamar taga dodo ko mugu bata jimawa zata bar dakin ta ce ita zata wuce duk yadda maji tayi ta tsaya bata yarda ta tsaya idan yana nan part din.
Gwago tana son zuwa kauye don uzuri na tafiya ya taso mata zuwa gida shine taga bazata iya barin Bintu gida ita kadai ba.
Don haka tazo da kanta gurin maji tana neman arzikin Bintu ta zauna a gurin su har ta dawa daga gida.
Don babu damar ta tafu da ita a na cikin makaranta a lokacin ana karatu ne ba hutu akeyi ba.
Da yar ledae kayan ta tazo gidan aka sauketa daki daya dasu Amira da maryam.
Tunda gwago ta, tafi a takure Bintu take gidan su Amira din koda kowa yana falo Bintu tana daki ita bata fita zuwa ko ina ko kallo bata fitowa tayi a falon kamar yadda kowa keyi.
Yau da ya dawo daga wasan ball ya samu maji a kwance bata jin dadi don haka tana ganin shi tasan cewa abinci ne ya kawo shi don haka daga inda take kwance ta kwalawa Bintu kira tazo.
Mamakin jin tana kiran wani bakon suna daga ciki Umar keyi sai dai halin shi bai barin ya tambaya ko bakuwa,ce uwar tayi mai suna hakan.
Bintu tafuto tana saye da dan farin hijjab din ta a jiki don dabiar tane bata zama jiki ba hijjab ko kadan.
Mama gani inji Bintu duk da jin muryan ta da jin muryan ta da yayi ta shigo da sallama bai sa ya dago kan shi ba daga abinda yake a,wayan shi ba.
Bintu don Allah kawo wa yayan ku abincin shi kin ji,
Tau mama tace tare da juyawa zuwa dauko mai abincin dan lokaci kadan sai gata da ture ta ta dauko kayan abincin har ruwa duk a cikin ture din.
Kujeran da yake zaune akai hankalin shi a,waya ta nufa, ya dora kafan shi daya saman daya.
Ya mayar da bayan shi a makarin kujeran da yake sama zaune yana ta faman la tsan wayan shi.
Bintu ta karaso gaban shi ta dire mai turen abincin a gaban shi ta juya da,sauri zata bar falon,
Muryan shi taji kamar mai jin barci bayan ta juya yana cewa,
"Ke, yace da dan karfi abinda yasa Bintu ta,tsaya guri guda cak ke nan bata daga kafa ba kuma bata juyo ba.
Kizo ki zuba,mana zaki ajewa mutum abinci hakana kamar wata yar kauye can dalllah,
Da hanzari Bintu ta juya don bin Umurnin shi ta duka tare da jawo plate tafara zubawa a plate din dake cikin ture din.
Sai da Bintu ta shake plate din fam sannan take cewa nazuba tana shirin mikewa.
Ke Uban wa zai ci wanan abinci haka kamar jaki ko an fada maki cewa kowa irin ki dan kauye ne.
Kai Babana inji Maji wanan wani irin hali ne maka yarinya ta,dafa,ta kawo maka kuma cine kawai naka har kake kokarin kiran ta,da,sunan dabba.
Ke wuce ki shige abinki kinji Bintu kar ki tsaya,sauraren shi da zancen banzan shi.
Da hanzari Bintu ta juya zuwa cikin uwae dakin mama inda dakin su yake da,su Amira gaban ta yana faduwa irin yadda yai magana ya bata tsoro sosai.
Tun ranan bata son taji koda muryan shi don tsoro yake ba bintu din idan ta gan shi.
Da wani dare yashigo gidan sai wani lumshe idanuwan shi yake anyisa,a Bintu ma tana falon do Amira ta takura mata tafito suyi kallon wani hausa film sabon fitowa.
Bayan ya,samu guri ya zau a suka,shiga gaishe shi daya bayan day suna mashi sannu da,zuwa,
Ya zauna tare da mayar da hankali shi ga mahaifiyar su da ke zauns daga gefe saman salaya tana jan casbi ta a hannkali suka gaisa dashi daga gurin da take zaune ,
Sai dan wa lokaci ya dan nisa yanacewa Maji abinda yasa ta,dawo da hankalinya ke nan gurin dan nata don tasan magana yake son yi da ita.
Yace dama nazo maki da wani magana ne akan al,amarn da ya,shafe ni.
May kuma ya faru ne babana Maji dama ina son fada maki ne na,samu wani contarac akan zancdn ball din da nake yi wasu club suna son dauka na zuwa yi masu wasa.
Cikin sauri Maji tace ban amince ba kaji na,fada maka kada ka,fara ka,tayar da,zancen nan har wani yaji ko mahaufin ku a gidan sai nai matukar bata maka rai wallahi kaji na fada maka gaskiya.
Kallon mamaki yakewa mahaifiyar nashi don tabashi mamaki don shi a,zaton shi yai tsanmanin zatai farin ciki dajin wannan labarin tunda kullun gori take mashi akan wasan ball din da zaman banza bai zuwa shago kamar sauran yan uwan shi na, nagidan da,suke taya mahaifin su sana,a.
Shiru yayi tare da,dukar da kan shi guri guda bai daga ba har tsawon wani lokaci .
Tsam Bintu ta mike zuwa ciki don tsoro takeji naganin fushin wanan jarumin kada ya hada fushin shi dasu.
Maji amma,wanan abin fa alheri ne sosai idan har anyi nasara akai don Allah ki bari naje.
Bazaka banace na fada maka,gaskiyan magana ta ke nan har cikin raina .
Nan ma da kake a gaban mu yaya muka kare dakai balle can inda babu kowa naka.
Shiru yayi sai ya mike zuwa fita Maji tace abinci fa yace makoshi kawai yasa kai yafita daga dakin.

A LOKACIN MU KE,,,,,,
5⃣
Ya na fita daga waje ya,ci karo da,bucket din roban da mama ta,aje a tsakar gida shuri daya yayiwa bucket din din yai sama ya maku da,bango.
Ji kake pappp karan fashewan bucket din da ya maku da bangon dakin mama Asiya ji kake tayau,
Da sauri mama Asiya tafito daga dakin ta,tana ganin irin ta,asan da Umar yai mata tafara salati tana tafa hannayen ta cikin salalami da mamaki.
Maijjidda fito fito kiga,ta,asan da,danki yai min, dan iskan yaro kawai mara mutunci, kawai bucket yana aje may ya tare maka don kawai kana haushina zakai min wanan aika aikan haka,
Bari ubanka ya,dawo yau gidan nan akwai ta don sai an biyani kudin bucket dina a gidan nan.
Haka mama Asiya taita faman masifa inda take shiga ba nan take fita ba sai yan kore da suka fito kara zugata tana hawa.
Maji dai tana daki bakin ciki da takaici ya hana ta fita waje a lokacin.
Sai dai duk abinda suke fadi a kunnuwan ta yake irin yadda suke kara aibanta mata yaro duk da ran ta ya baci amma bata da bakin magana dan kuka maija wa uwar shi jifa.
Sadauki ya jawo mata wani sabon masifa don tasan yadda mama Asiya ta fadi sai an biya ta haka zancen yake sai an biyata din.
Don haka ta mike tsam zuwa kuryan dakin kwanan ta ta dauko kudi, a take ta dauko kudi taba Amira wai ta sayo mata bucket.
Haba maji don kawai tace sai anbiya ta basai taje gurin shi shida ya fasa mata taje gurin shi mana in ta isa, ya biyata abinta.
Maji tace,ban son rashin kunya Amira ki tashi ki tafi inda na aike ki kawai.
Bintu tace mama kawo naje yanzu zan dawo sai maji tace a,a Bintu yi zaman ki bari dai Amira din ta tafi.
Mama barshi kawai ni na tafi anty Amira ta huta kawai ta duka ta karbi kudin daga hannun Maji ta saka silifas din ta dake ta kofa tafita daga dakin.
Inda Amira ke zaune Maji ta dan kalla tace kin ga ikon Allah karamar yarinya haka da kaifin hankali,
Don tafahinci baki bukatan zuwa yasa ta karbi kudin ita ta tafi, da sauri Amira ta daga kai ta kalli maji tace bance banzuwa ba maji ,
Allah dai ya kyauta Amira ina tsoron kada ke ma kizo ki zama min irin dan uwan ki nan gaba wallahi.
Haba maji don Allah kibar fadin haka mana idan ranki ya baci kiyi hakkuri don Allah ta fadi a,dan marairaice,
Allah ya kyauta ta furta a fili a cikin zuciyar ta kuma fadi take ya Allah ka shirya min yaran nan shiri irin na addinin musulunci.
Wannan adduan ya zama kamar waka a bakin Maji don duk abinda take adduan ta akan zurian ta dana sauran yan uwa musulmai yake.
Exactly kalar roban da ya fasawa mama Asiya Bintu ta sayo don ma saida tai yawo kusan shago uku ta samu roban.
Gap da zata shiga gidan ne a daidai side din samarin gidan dake daga wajen haraban gidan ta hango shi zaune yai zaman kamar tsuguni saman dan dakalin dake gurin.
Kamar ance ya dago kai ya hango bakuwar yarinyar da yake yawan gani dakin mahaifiyar shi yanzu tafe da buket din roba kalar dayai shuri dashi a cikin gida kuma tun kan ya karasa fita daga gidan yaji bambamin mama Asiya akan wai ya fasa mata buket wanda ba ma fashewa yayi ba.
Daga hannun buket din ne ya balle hannu daya na bucket din ya balle daga jikin roban.
Sauri take ta shige gidan sai taji muryan shi kamar daga sama yace.
"Ke,
Cak taja ta tsaya don balain tsoron shi take ji don ko yaushe fuskan shi babu rahama cikin shi, don har takanyi mamakin ace wai wanan mai siffan bugai yafito daga mace saliha kamar Maji.
Zo nan yace mata inda ta dan taka a hankali kamar kwai ya fashe mata a ciki, har ta karasa gurin shi.
Waya aike ki sayan wanan robar ya tambaya cikin daga muryan shi.
Cikin dan in,in,niya take cewa, mamace tace na,sayo mata,
A gatsale ya tambayeta, waye mama ? Don ya tantance ko wa ya aike ta sayen robar.
Bintu tace mama ta dakin ku, kina nufin Maji ke nan, tace eh cikin daga kanta.
Miko min bucket din kice mata na karba ya,fadin cikin dakewan fuska mika mashi tayi ta juya simi simi ta shige cikin gidan yabi bayan ta da harara yana fadin munafuka kawai.
Maji tana zaune Bintu tashigo gidan tana dan kiukiu da idanuwar ta alamar damuwa a fuskan ta.
A,a Bintu ba,a samu roban bane ko kudin shine baikai ba?
Kafi Bintu tai magana Amira tace a,a ya za,ace ba,a samu irin roban ba kodai baki san inda ake sayarwa bane ?
Harara Maji ta maka wa Amira da sauri taja bakin ta tai shiru tare da kawar da kan ta don tasan har yanzu Maji a kufule take da ita ke nan.
Bintu tace na,sayo amma ya karbi bucket din a gurina.
Shi wa ya karba ?
Shi wanan yayan namu da ya,fasa roban yace na bashi roban dana sayo din .
Sadauki ke nan ko ?
Eh shi yace na bashi nace ya karba.
Mikewa Maji tayi ta saka hijjab din ta ta nufi hanyan waje fuuu a cikin fushi da hasala.
Ya na kulle kofan dakin shi zai fita ne Maji ta karaso gurin tana fadin miko min roban mara mutunci kawai.
Wani kallo ya waigo yaiwa uwar sai kuma ya,dukar da kan shi kasa ya dan fara kokarin bude kofar dakin shi daya rufe.
Yafito da bucket din yana cewa wallahi matar nan yar rainin wayo ne naso ne ki barni da ita, tun da tace yau akwai balai akan bucket din roba a gidan nan.
Fisgan roban Maji tayi daga hannun shi ta watsa mai harara tana cewa.
Duk abinda tace waja min ida baka taba kayan ta ba ai bazatai wanan fitinan ba.
Ksi tayi sadauki tunda na fahinci kwanciyar hankalina ne baka bukatan gani a duniya.
Maji ni fa ba haka nake ba ki barni kawai na wuce gurin kwallo na in huta da wanan munafukan matan.
Anki a barka anan ma da kake yaya aka kare dakai balle ka sa kafa ka tafi wata duniyan da babu mai kwabon ka a can.
Indai zaka gyara halinka ka gyara don bakai kadai bane yaro a gidan nan da kullun a ce sadauki dai sadauki.
Ta juya zuwa cikin gida kamar yadda tafito a hasale daga gidan da farko.
Maji bata shiga daki ba,saida takaiwa mama Asiya bucket din dakin ta takuma bata hakkuri akan ta yi hakkuri da halin sadauki din .
Ba kunya mama Asiya takarbi bucket din tana zuba bakar magana tana cewa wallahi da ba,a,sayo min kayana ba da yau akwai magana a gidan nan.
Da maji ta shigo lokacin Bintu da su Amira suna zaune a falon ta, Amira ce tace bai bayar bane maji ?
Kamar yaya bazai bayar ba aiko ya sha giyar wake ne bai fara shi wallahi.
Sai Amira din take cewa to Maji ina shi tsohon bucke din ai naga bai wani fashe ba fa .
Amira ki fita idona don ni ba,sa,ar ki bace, don naga kina son raina ni.
Shiru Amira tayi tare da kokarin mikewa tabar falon don gudun fadan Maji a kan ta don yanzu tana sauke mata haushin dan uwan ta a kan ta in batai hankali ba.
Inda Bintu take Maji ta kalla tana cewa Fatima kinci abinci kuwa, cikin sauke ajiyan zuciya a hankali.
A cikin natsuwa Bintu tace ina jiran su anty Amira ne muci tare dasu.
Haba Bintu kada ki biyewa wa yan nan don su cin abinci a gurin su kamar shan zuma ne sai sunga dama suke ci.
Tashi kici abinci kada gwagon ki ta dawo ta samu kin ramay kan wa yan nan mara sa kai.
Haba mama aiko suna da kai adduan ku a gare mu shine takin mu akoda yaushe cikin murmushi da kwantar da murya Bintu tai maganan ta.
Allah sarki Allah yai maki baiwa da kaifin basira karama dake Bintu amma kin san abinda ya kamata ko yaushe.
Tashi jeki ki debi abinci kici mai isar ki kin ji diyata Allah ya bar muna ku.
Bintu ta mike a hankali fon bin umurnin maji amma bafon ranta nason cin abincin ba ta shiga kitchen din su ta dan debo abinci dan kadan a cikin plate tare da ledan ruwan pure wata.
Maji tabi abincin da kallo tana cewa haba Fatima wanan dan abincin may zai maki ashe shiyasa baki kiba don baki son cin abinci sosai.
Ko har yanzun kina kewar gwagon ki ne kin ki sake jikin ki da mu.
Murmushi Bintu tayi kawai tare da cewa a kunyace a,a mama ai ban damu ba.
To dayafi maki don ko gwago ta dawo zance tabarki a nan don halaiyar ki ni dai yana min wallahi saboda yaran nan su dan kara daukan darasi a gurinki.
Don duk irin halaiyar yaran gidan nan shine diba,ar su a rayuwan su basu san halin rayuwan duniya ba.
Da,sauri Bintu ta dago kai tana kallon Maji sai kuma ta dukar da kanta tana dan juya abincin dake cikin plate a hankali ba tare da takai a bakin ta ba.
Yadda maji take jin sha,awan Bintu yasa take so da kaunar yarinyar har cikin ran ta ganin zata takura mata yasa maji ta dan mike tabar falon zuwa waje.
Bintu tana gamawa ta kwashe kayan zuwa inda suke wankewa ta wanke har ma da wanda tagani saura a gurin duk ta hada ta wanke su.
Daidai zata shigo da kayan, maji ta ganta take cewa Fatima baki hutawa duk aiki bai baki wahala ke.
Murmushi kawai tayi ta,shige da kayan ciki ta aje tana fitowa ta shiga wanka don magariba ya kawo jiki a lokacin.
Tsab Bintu tafito cikin wasu kayan da aka bata na Amira an gyara mata sun mata matukar kyau kamar don ta aka dinka kayan dama.
Maji dake zaune ta idar da sallah tana jan tasbaha takalle ta lokacin duk suna falo da yaran ta a zaune.
Duk suka bita da kallo a lokaci guda ta,zo har inda Maji take zaune tana cewa ina wuni mama.
Kai Maji dake lazumi ta kada mata tare da daga mata hannu Bintu ta mike zuwa bakin dayan kujeran ta zauna a kasa.
Maryam ta kalleta tana cewa may yasa ke baki son hawa saman kujera ne Bintu bata ce komai ba sai dan halinta watau murmushi.
Can suka fara jin dan hayaniya daga cikin gida yana tashi inda duk sukai shiru suna saurare don suji may ke faruwa ne wai.
Maji daga inda take tai murmushi tana cewa Alhaji ya dawo ke nan nasan an fada mashi.
Kai wanan matar batayi ba wallahi yanzu bayan an biya ta bucket din ta kuma,shine sai ta fadawa Baba zancen.
Maryam tace ai in bata fadi yayi masifa wa maji ba hankalin ta baya kwantawa.
Mikewa Maji tayi bayan ta shafa tafita daga dakin zuwa gaida Baba da dawowa daga kasuwa.
Ta samay shi shi da mama da uwargidan su a falon shi zaune tai mashi sannu da dawowa,da yaya kasuwa.
Ta juya zata wuce sai maigidan nasu ya ce maijidda yaya akayi dan ki ya fasawa Asiya roban ta da gangan?
Shaye shayen nashi har yakawo a,cikin gida cikin iyalina kuma?
Shiru maji tayi tana maijin kunan zancen baba a ran ta sai dai cikin dakiya yau karo na,farko tun da ya fara mata cin fuska a gaban kishiyoyin ta kan dan ta tace.
Da na ko dan mu Alhaji ina bani kadai na samu yaron ba tare da kaine kuma a tare mukai mashi ladabi a cikin gidan nan gaba dayan mi daku.
Don haka sai makiyin Allah zaice ban ba sadauki ingantaccen tarbiya ba a cikin gidan nan.
Kawai dai Allah ne mai yin ikon shi akan duk wanda yaso ni kuma nasan bawai Allah yakini bane ya mayar da dan da yafito daga tsatso na haka a,rayuwa ba.
Ai bazata bari a,fadi ba don kaga har roban ta,sayo ta mayar ma Asiya da abinta wai don ta nuna ita ta haife ta.
Maji tace yaya Asiya ya kike son nayi kin face yau idan ba,a biya ki roban ki ba,akwai tsiya a gidan nan don babu mai rabaki da shrgiyar uwar shi sai Allah.
Alhaji ya juya yana cewa ke ko Asiya haka kika ce mata don maganan maji yadan sa jikin shi yin sanyi.
Ba dole ince haka ba tunda yana takamar shi dan iska ne har iskancin yakawo ga kayana tun yana dukan min yara yau kuma ya koma ga kaya na.
Idan ko haka kikace gaskiya baki kyauta ba don dai kinga maijidda ba itace ke tura shi wanan aika aikan ba.
Wai haka ma zakace Alhaji akan may zan zauna yaro kamar sadauki yana min cin fuska kala kala tsoron shi nake ji ko may da,zan kyale shi.
Yanzun dai idan har ya kara takalar wata a gidan nan don Allah na rokeku da kuyi hakkuri har lokacin da na dawo sai na dauki mataki da kaina.
Ke kuma Maijidda nasan kiyi hakane don kawar da fitinan don a zauna lafiya amma ba daidai bane ki biya Asiya roban ta don Sadauki ya fasa mata roba.
To ayi hakkuri in har ban kyauta ba amma ni bada wani manufa na biya roban ba.
Ai dan tane shi don haka ba zancen biya a tsakanin ku don dan wani yai wa,wani barna.
Mama Asiya tace wa ni sadauki ne dana Allah dai yai min katangar tsari wallahi da wanan bakar haihuwa a,rayuwana.
Ikon Allah Asiya a gabana kike wanan zancen haka ?
Ai gaskiya na fadi don bani fatan haihuwan dan majiciji a rayuwana na haife shi ya kasheni.
Allah ya kyauta inji Baba yafadi ciki kunar rai tare da mikewa yai shigewan shi daki kawai su ma mikewa sukayi suka watse daga dakin mama Asiya tana ta bakar magana.
Maji tadawo daki zuciyar ta na mata kuna ta samu su Amira suna ta hiran su Bintu tana gefe zaune a makure bata tanka masu a hiran nasu.
Suna ganin ta sun fahinci ranta a bace yake anyi ba dadi ke nan a can falon baba.
Amira tai tsuki tana fadin wallahi yaya sadauki dai yana jawo muna matsala a gidan nan.
Bintu tace sai ko mu bishi da addu,a don adfua makamin mumine ne tunda ba haka Allah ya halicce shi ba ai.
Dago kai Maji tayi ta dan tsura wa Bintu ido sai kuma ta kawar duk yadda taso ta danne hawayen ta kada su zubo saida suka zubo mata.
Hankalin yaran gaba daya ya tashi sai cewa Amira take halan mi sukace maki maji.
Bintu tace haba Anty Amira maganan manyane fa sai su kawai dai mama tayi hakkuri tabarwa Allah al,amarin shi, ian Allah mai karban adduan bayin shine idan Allah ya tashi canza shi sai kowa yai mamaki a gidan nan.
Hmmm Bintu ke nan baki san ko waye yaya sadauki ba ko a gidan nan ki barshi kawai kuyi yar nisa danisa dashi shine sauki wallahi.
A,a anty Amira insha Allahu wata rana sai kunyi mamakin shi Allah dai yasa wanan halin na iya kurciyane kawai.
Ikon Allah ke kin iya magana kamar tasbin kaka kamar wata babba van wallahi.
To Antu ai ba abinda yafi karfin ubangiji nagani don shine maitin komai a lokacin kuma da yaso wanan fa jerabawa ne akan su mama da baba sai dai muce Allah ya basu ikon cinyewa kawai.
Shiru dakin yayi suna nazarin zancen Bintu yarinya karama da babban magana kamar wata babba can.
Jin sunyi shiru Bintu tace da zamu dage ko mu iya dakin ga mu dinga aiwatar da ibada akan shi kawai ba,wai mu tsaya muna magana kamar sauran mutane ba muna kuma yin sadaka akai insha Allahu ba,dadewa zamuga saukin al,amarin da yardan Allah.
Don ni wallahi na yarda da addua takobin mumine sosai don da na roki Allah saiki ga an karba min.
Dariya,suka saka mata kai Bintu wanan cika baki haka kamar wata,shirihiya can.
Hmmm anty ke nan nifa tun ina karama Baba na ya kowaya min yin addua kin san ban tashi a gaban mahaifiyata ba.
Da sauri maji wacce sai yanzuta sa masu baki a zancen su tun shigowan ta tana hawaye tace.
Fatima ina mahaifiyar ki take Bintu tace tana can wani kauye tana aure sun rabu da Baba ance tun ana goyo na da ya auri kishiyar mamana.
Shine da aka yayeni iyayyen ta suka dawo dani gurin mahaifina wai bazasuyi wahalan banza ba .
Tayar dake shine suke gani wahalan banza Bintu tace cikin yar murya haka suke gani sai kawai ga kwallah ya zubo mata,
Bata daina magana ba don kwallan sai cewa tayi, mama nasha wuya a gurin mama hausi sosai don har tsakar gida na kwana ni kadai tun ina yarinya na.
Da kuma na girma abin ba,a cewa komai don ba irin wahalan da bata gwada min.
Amma sai gashi duk yaran ta ba wanda ya kaini don mazan su da matan su duk sun lalace mata sai nice ma nadawo tana dan jin sanyi a gurina.
Ina ganin ganin da Baba yayi aikin wahala zai kashe shine suka hada baki da,gwagona wai nazo nai mata hutun sati biyu na koma.
Sai daga baya gwago take fada min cewa wai Baba na yace na zauna gurin ta kada na koma garin mu.
Takarasa maganan cikin kuka tace ina kewan gida da yan uwana sosai da farko amma yanzu don rikon da gwago take min yasa na manta da komai gashi yanzu zama daku yakara sa hankali na ya kwanta sosai bisa ga zamana a can kauye don abubuwan da ban sani ba,a,rayuwa yanzu na,san su sosai.
Tun ina shekara sha hudu na haddace alkur,ani maigirma yanzu tulawa nake sai dai akwai banbancin karatun mu na can da naku na,nan birni sosai.
Kinga ashe na,dan san wani abu nima ga,addini ke nan don malamin mu yana gwada mu abubuwa siri sosai.
Allah sarki ashe mahaifiyar ki bata tare da mahaifinki gaskiya wasu mata akwai ha,inci a tare dasu sosai wallahi.
Shi yasa nake ta hakkuri tun farko da cin fuskan da ake min a gidan nan don yaran nan dake gabana don idan na fita na barsu cikin gidan nan wa kuke ganin zai rike min ku amma na cikin su, ina ciki ma yaya muka kare dasu balle na fita na barku.
Duk shiru sukayi suna nazarin maganan Maji don sun san gaskiya ta fadi ba mai iya rike su amma kamar yadda suke rike yaran su.
Kowan su tasan gaskiya Maji tafadi don ba mai iya rikon su amana suji dadi kamar yadda tace don haka sukaji tausayin uwar tasu ya kara shigan su sosai a gidan.
****** ********* ******
Salamu Alaikum wai ana sallama da Raiha sai mama dake duke a kitchen ta dago tana cewa kai waye da yamman nan ka ce bata nan.
Kai tsaya Raiha dake fitowa daga bandaki tace wa yaron je kace gani tafe kaji.
Raiha yanzu don baki da kunya zance zaki fita da rana haka kowa yana ganin ki kikau a kofan gida tsaye da namiji duk wanda ya wuce yai miki tir da halinki ko?
To mama kin san ko waye da,zaki kore min mai shi mama bari naje naga ko waye nadawo, kawai sai ta shiga daki ta shiga gyara fuskan ta tsab ta saka hijjab din ta sai waje.
Mama dake waje ta rike habar ta cikin mamaki sai cewa tayi ikon Allah yaran yanzu Allah ya kyauta kawai.
Raiha tana fita taga gidan su tunfitowan ta ya kura mata ido yana kare mata kallo nan yasan yarinyar tayi mashi ga komai kuma,zai more mata sosai idan yai sa,a ta yarda da bukatan shi gare ta.
Dan waige waige taks don bata ga mai neman taba a lokacin sai wani bakar mota mai tsada da ta hango, daga wajen gidan su, dan nesa kadan da gidan.
Hon din da mutumin dake cikin motar yayi yasa tagane shine mai neman ta a lokacin.
Raiha ta nufi gurin a cikin mamaki don ita duk iya sanin ta,bata da saurayin da keda koda karamar mota balle wanan dirkekiyar motan dake gaban ta.
Mutimin da tagani a motar bata taba ganin shi ba,a,rayuwan ta don haka sai tai tsanmanin ba gurin ta yazo ba.
Sai taji yace malama,Raiha ko ?
Eh nice
Bisimillah shigo daga ciki mana ko kina tsoro ne kuma.
Tai wani irin har da idanuwan ta ce tsoron may zanji kawai dai ban gane ka bane dai.
Bazaki gane ni ba,asalima baki sanni ba ni ne dai na,san ki ta hanyar gane gane na nahagonki kawai.
Shine na biyo ki har nagane gidan ku ne nan sai yau na yanke shawaran nazo gurin ki dafatan zaki fahince ni ai.
Wani kallo tai mai kamar bata yarda da,zancen shi ba sai tace mai a ina ka ganni ne ?
Sai da yai murmushi sannan yace a gurin birthday din Salim murmushi tayi don tasan anyi hakan .
To amma duk tsararun yan matan;dake gurin bai gansu bane sai ita zaizo gurin ta, sai kuma,wata zuciya tabata amsa dacewa kece kikai masa kawai a gurin.
IkonnAllah tace a fili tare da,fadin shine kabiyo ni har gida kuma ?
Yace eh mana ko nayi laifi ne tace bance ba yace to sunana Abdul amma ana kirana duwel ne don haka abokaina ke kirana dashi.
Hmm tau nagode da,har ka zabi kazo guri na,dafatan lafiya kazo har gidan mu a,kaina.
Murmushi guy din yadan yi tare da,cewa ai tunda kika ganni a gurin ki ke ma kin san alheri ne yakawoni gareni da,fatan zaki fahinci manufata a,gare ki batare da kin fassara min zance na ba.
Murmushi Raiha tamayar mashi tana cewa da fatan zan samay ka mai cika alkawari nima.
Nan suka tsaya suna dan kara fahintar da junan su kan shi tare da dan hira yana fada mata ko shi waye da inda yake aiki.
Ganin yamma tayi sosai tasan mahaifinta zai iya dawowa a lokacin yasa ta yi mashi sallama ta,shiga gida da fara,anta.
Tana shiga takasa boye farin cikin ta take cewa mama yau saura kiris ki kore min sa,a ta kin kuwa ga mutumin da yazo gurina ne.
Uwar ta mayar da hankalinta akan yar ta tana sauraren bayan nin da takd mata akan bakon ta.
Har saida mahaifinta ya shigo gidan suka bar zancen don gudun kada yaji zancen su.
Tun daga wanan ranan suka hada alaka a tsakanin su ita da Abdul din guy din da ya tafi mata da imanin ta gurin son ta.
Ba uwarta ba har mahaifin ta saida ya,san da zaman Abdul din don masifan son da Raiha take mashi.
Wasa wasa Abdul ya fara dan test din Raiha da,wasu yan abubuwan da yake son sani ko tasan da su a sabon sallon so da matasan yanzu ke ciki yanzu.
Bai samu matsala ba don ya samay ta yarinya ce yar rock sosai ba wasa don haka harkoki suka fara tafiya a tsakanin su ba bata lokaci.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/6/19, 10:31 PM - ~: IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
A LOKACIN MU KE,,,
6⃣
Murna sosai takeyi don ganin ta dauko sabon fridge dinta da ta dade tana gurin taga ta saye a rayuwan ta, don bunkasa sana,arta.
Ta bude fridge din yafi a kirga tana duba ciki da wajen shi don tabbatar da lafiyan shi.
Ba laifi don ta samu yadda take bukata saboda sanyi da kankara yake daga sama har kasan shi tsab.
Wanan abin yasa ta yini tana farin ciki da wanan karuwan da ta samu na ci gaban ta.
Ranan sai da ta aikawa makwabta da kankara tana fada masu idan suna son saye ta sai fridge mai kankara da ruwan sanyi, don haka su sa mata albarka a ciki.
Wasu sun yaba, wasu kuma sun kushe don haka duniya take dama wani baka hada komai dashi ba amma yana bakin ciki da karuwan ka a duniya.
Shima maigidan ta bawan Allah da ya dawo yai mata fatan alheri akan fridge din, tare da yar guntuwar nasiha akan sai tayi hakkuri da jama,a don mai saye da sayarwa sai hakkuri dama.
Sai dai kassh matsalan hauwa shine bata da hakkuri don ta sawa ranta masifan son kudi sosai.
Ta manta cewa zafin nema baya kawo samu sai in Allah yaso bawan shi da arziki yake arziki.
Ba dama mutum yazo sayen kankara ya mayar mata koda yace bai kankareba sai ta hau masifa da fada taki canzawa mutum abinda yake so.
Gashi duk samun da takeyi yanzu baisa mijin nata yakai idon shi ba ga kudin ta, don ko ba dadi sai yakawo masu dan abinda zasu dafa agidan suci.
Yana da matukar kokari gurin ganin ya kare hakkin iyalin shi sosai a rayuwan shi.
Amma daidai da rana daya idan dan wani abu ya kasa ga cefanen shi sai Hauwa tai mirsisi taki yi masu girki wai sai ya ciko ta girka masu.
Don ita bazata yarda da akidar cikawa namiji kudun cefane ba saboda itama tana da nata bukatan ai da kudin ta don yanzu ta sa rai wai fili take son saye ta yarda kaddaran itama.
Baida fushi hakan bai damun shi, dole sai ya samo ya cika mata sai ta girka masu inba haka ba su kwana da yunwa har yaranta.
Wanan kuma ba komai bane sai zugin uwarta da kullun take mata hudubar shedan akanta.
Na karta yarda da namiji don tana ganin ta ita kadai bai hana wata rana sai tagama kashe maijiki ya ce zai jajibo mata kishiya.
Halin Rashi hakuri irin na hauwa yasa mutane suka dan rage shigowa sayen kayanta yanzu sosai sun kwammace suje wani guri su saye.
Haka yasa ake barinta da kimin kankara a fridge har su narke tayi hasaran kudin ta.
****** ******* ******
Cikin mota suke a kofan gidan su Raiha yana yadda ranshi yaso da ita, a cikin rashin damuwa Raiha ta barshi yana juyata yadda yake so.
Don son shi da kalaman shi ko yaushe suna kara tasiri ne a zuciyar ta don ta yarda dashi 100%.
Daga nesa matasan dake zaune suna hira hankalin su yana gare su tun shigar Raiha motar, daya daga cikin matasan yake cewa kai yanzu dai mutane basu da tsoron Allah wallahi.
Kadiba fa yarinyar can ina lura da ita tun dazun suke zaune a motar nan har takai motar tana motsi don kanta.
Ashe bani daya nake lura da hakan ba inji dayan matashin yaba dayan amsa.
Sai dayan da sai yanzu yai magana yake cewa ai wanan yarinyar batayi ba wallahi.
Gaba daya haliyar ta baida kyau bata dauki kanta diyan tallakawa ba ko kadan takai kanta inda Allah baikaita ba ko.
Ni yanzu Raiha tafita raina tunda abokina yake fada min cewa yagan ta uguwar su gurin sayen kayan maye.
Kaifa Nasir ?
Yace wallahi ranan daya ganta a uguwar nan yake ce min a uguwar nan take ne nace mashi eh.
Shine yake cewa babba yar hannu ce sosai tana zuwa uguwar su gurin wani deler ta sayo kayan aiki masu karfi a can.
Sai wanda yafara magana yake cewa kai amma ko udan gaskiya ne wallahi dole mu saka mata ido don kada ta kawo muna matsala ga sauran yan matan shiyan nan.
Yanzu kai ya kake ganin zamuyi yace kokari zamuyi mu kamata a hannu sai mu dauki mataki daga iyayyen ta mana ko yaya kuka gani.
Hakane sauran suka bashi amsa da,sauri suna cewa wallahi in har ba,a,dauki mataki ba zata iya gurbata wasu ba,a sani ba.
To yanzu ita ina ta koyo wanan bakar akidar naga dai a uguwar nan ta tashi a gaban mu ai.
Kai yanzu sai wani ya koya wa mutum hakane abin fa masifa ne kawai sa warai ne ai.
Ni wallahi mamaki take bani yadda idon ta ya bude baki daya a lokaci guda haka.
Kaidai bari ai yanzu haka kila a makaranta ko kuma wasu sabbin kawaye ne suka koya mata wanan harkan.
Tana shiga gidan mu gurin kanne na zan shiga nai masu fada wallahi su rabu da ita tun bata lalata min kanne ba.
Kaidai kawai Allah ya,sauwaka ita kuma Allah ya shirye ta don kaga ai mahaifinta mutumin kirki ne.
Uwarta kuma bata ko magana shiru shiru mutumiyar kirki ce sosai don bakajin ance ga abinda tayi a uguwar nan na assha.
Sai wani lokaci Raiha ta bude kofar mitar ta sako kafan ta guda daga waje, daga inda matasan suke zaune suna iya hango ta daga cikin motar tana gyara rigar ta da kuma saka hijjab din ta.
Allah ya kyauta amma dole mu dauki mataki akan wanan fitsaran da ake muna da rana tsaka a uguwa.
****** ********* ******
Abin duniya ya ishi zuciyar Umar faruq ya rasa yadda zai shawo kan Maji ta yarda ta mara mai baya akan zancen tafiyan shi zuwa ghana kwallo kamar yadda yan club din su suke son yaje ya buga masu ball.
Haka yasa yafara dirkawa cikinshi kwaya kala kala har takai ya shiga hali na maye sosai.
Fatima don Allah zoki sayo min magani kafin duhu ya kara yi don yanzu dana aiki su Amira Alhaji yagan su fada zai min sosai.
Kiyai sauri ki dawo da wuri kinji Fatima kada ki dade kinji Fatima dare ya soma sosai.
Don takwas saura yanzu, ban son fitan dare ga diya mace haka koshi dole yasa zan aike ki don kaina ya matsa min da ciwo sosai wallahi.
Bintu ta dauko hijjab dinta ta,saka ta fito ta karbi kudin maji tafada mata kalar maganin da take son a,sayo mata.
Tana zuwa aka bata maganin ta juyo zuwa gida gap da zata shiga gidan ne taga mutum a kwance bakin get.
Sai faman nasari yake harta dan raba shi zata wuce don tagane wanene a kwance gurin.
Da,sauri ta dawo ta dan duka a kan shi a hankali tana fadin.
Yaya sadauki ka tashi ka,shiga daga ciki kada wani ya gan ka anan haka.
Da kyat ya bude idanuwan shi ya kalleta cikin maye ya nunata da hannu ya bude baki da kyat yana fadin, tare da nunata.
"Ke zan _ci uban,ki idan baki ban guri ba walla_hi sai ya mayar da kan shi kasa.
Innalillahi Bintu ta furta a fili ta mike tsaye kamar zata wuce sai kuma taji bazata iya ba don idan har wani ya gan shi a haka yashe a kasa cikin maye, yau bakwanciyan hankalin ga Maji dama gashi kanta tun safe take yana mata ciwo.
Komawa tayi iya karfin ta ta dago shi daga kwancen da yake ta na cewa tashi yaya ka koma dakinka don Allah.
Shegiya idan baki barni ba zan maki dukan tsiya wallahi, yafadi a cikin muryan dan maye.
Bintu bata bi ta nashi ba sai kokarin mikar dashi take shiko sai ashar yake jefa mata.
Cikin ikon Allah ta samu ta daga shi daga inda yake kwance ta kaishi daidai kafadan ta duk da yai mata nauyi amma haka ta daure ta ja shi zuwa dakin shi.
Da kyat ta lalabo key daga jikinbshi cikin wandon shi na baya ta bude dakin tana,shiga wani wari ya daki hancinta, haka ta daure ta kaishi bakin katifan shi.
Sai barci yake a kafadan ta cikin maye, tana son kifar dashi don duk tagaji saura kiris su zube tare sai ya kwararo mata amai da fitsari a lokaci guda duk ya bata mata jiki dashi.
Haka ta daure ga,warin amai yana damun ta ta kifar dashi akan katifan dakin.
Kallon hijjab din ta da ya lalace da amai da fitsari tayi tare da girgiza kanta tana Allah ya kyauta tajowo mai kofan dakin tare da dunkule hijjab dinta daya lalace da aman shi.
Gap da zata shiga gida taji karan motar Alhaji habu dake dawowa daga kasuwa, shi da sauran yaran shi dake bin shi shago.
Da,sauri ta karasa kada suga fitowan ta part din samarin gidan kuma dakin sadauki su fassara mata zance.
A can cikin gida kuma Maji hankalinta ya tashi sosai ganin Bintu ta dade sai gata saidai a hargitse take don hankalinta ya tashi.
Amira data kalleta yadda ta shigo gidan take cewa, ke lafiya kika dawo wata kala haka dake ji yadda jikin ki ya lalace.
Saida Binta ta kalli jikin ta take cewa cikin sauri faduwa nayi gurin kwata da,wata mota tabiyo gefena.
To amma ai ba kwata bane kamar amaine jikin ki tace gurin masu saida abincine gurin.
Ta mikawa Maji maganin ta,shige ciki don duk a tsawale take da aman dake jikin ta dama.
Saida tai wanka ta gyara jikinta tsab tafito falon inda suke ta zauna tana kallon shirin da ake a sokoto tv.
Maji dai bata ce masu kalla ba don kanta da yake damunta da ciwo a lokacin.
Sai da ta dauki lokaci bayan tasha magani sannan kan ya fara lafa mata don ranan bata ko fita zuwa yiwa maigidan su sannu da,dawowa ba.
Wai ko yau yayan ku yadawo kuwa don banga ya shigo ba daukan abincin shi.
Amira tace, waya sanan mashi kila yana can gurin yawon banzan shi sai baba yasan bai gidan yazo yaitawa mutane masifa akai.
Bintu tace da zan shigo nagan shi zai shigo da leda da,ya,sayo doya soyayya gurin mai sayar wa nagan shi da zan wuce yana saye.
Oho ashe shiyasa banga yashigo ba ya samu abinda zaici ke nan .
Ai da yana jin yuwa da yanzu yashigo ya cinyewa mutane abincin su ko inji maryam.
In baici abinci ba nan a ina kuke son yaje yaci ne maryam, ni dai idan zai shigo yaci a nan din ai zaifi min komai dadi.
Bintu taji tausayin Maji ya kamata a zuciyar ta take cewa kai uwa uwace dai.
Da yau maji zata san halin da dan ta yake ciki tasan da yanzu suna cikin tashin hankali da balai a rayuwan su a shiyar su.
Amma dai yau Allah ya rufa wanan asirin an wuce gurin in ba,wani ikon Allah ba kuma.
Tana jin su suna hiran su amma bata saka masu baki ba sai faman tunane take a ran ta.
Shigowan baba a part din ya katse mata tunanen ta suka fara gaida shi suna mashi sannu da,dawowa.
Bintu ce tafara mikewa tashige daga ciki sai Alhaji yabi su Amira da harara dole suka mike simi simi suka shige bayan Bintu.
Yace marasa kunya kawai wai har bakuwa tafisu hankalin sanin ya kamata.
Har yanzu gwagon yarinyar nan bata dawo bane ko kuwa dai?
Bata dawo ba Maji taba shi amsa a takaice, takara da cewa ni ban ma son rabuwa da yarinyan don halinta na kirki yai min.
Hmmm ki dai ji da na kanki kafinki kara jajibowa kanki sabon matsala ya bata amsa.
Ai Fatima ba matsala bace zan ma iya cewa zaman ta ya zama min alheri don kaga yaran nan suna samu karuwa sosai a gurin ta ga ta yar karama amma akwai addini sosai a kanta.
Ta godewa Allah da,ya bata wanan baiwan har takai ga samun yabo haka na alheri Allah muma ya shirya muna yaran mu.
Ban ganki ba ne yasa nabiyo nagani ko lafiya don nasan ba halinki bane rashin zuwa yi min sannu da kasuwa.
Maji ta dan ya mutsa fuskanta tana cewa wallahi tun safe nake fama da ciwon kai yanzun ma aka sayo min magani na,dan sha shine naji yadan fada min.
Naso naje gaishe ka amma sai nai tunanen ko ka shige ne ko ai.
Ki daina shan magani haka batare da likita ya baki umurni ba idan kinji kan ya matsa maki aida kin kirani nazo mun tafi asibiti ko .
Naga ciwon kaine kawai shiyasa ban dauke shi wani babban ciwo da zani asibiti ba.
Haka dai kikace a lokacin da ya karasa takon shi inda take zaune yana kai hannun shi akan wuyan ta don taba jikin ta yaji lafiyan ta.
Kai haba Alhaji ai na samu sauki dana sha maganin nan yanzu, ki dai bar wasa da ciwo don ciwon da ka raina shike zama babba yanzu.
Allah dai ya sauwaka inji maji tafada cikin dan sauke ajiyan zuciya.
Ki dai bar tunane akan wanan yaro ki kai kukan ki ga Allah shine zai bamu mafita akan shi,insha Allahu.
Allah yada inji Maji ta fadi voice din so soft don zancen Sadauki yana tayar mata da hankalinta sosai.
Daga haka yai mata saida safe yabar part din nata cikin tausaya mata halinda take ciki yanzu kan lalurar dan ta wanda duk ta tayar da hankalin ta.
Washegari sun tashi kowa na batun fita zuwa makaran ta sai Bintu ce a gida don ita yau basu zuwa makaranta suna hutu.