[9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *An karb'o daga Abu Huraira(R'A) yace Manzon (S.A.W) yace "Allah madaukakin sarki baya duba ga jikkunan ku da surorin jikinku saidai yana duba kawai ga zuciyoyin Ku da ayyukan ku..* Husnul Muslim👌🏻 *Page* 3⃣0⃣ _________kara matseta jikinsa yayi tare da fara hura mata iska cikin kunnuwa cike da salon jan hankali, yayin da ita kuma tayi lakwas jikinsa jikinta ya fara mutuwa sai zuciyarta dake aikin harbawa da sauri-sauri kamar wacce tasha gudu, ido a lumshe dan Sam ba zata iya d'aukar zazzafan kallon nan nasa ba..... Hannayensa ya saka ya fara zagaye sannan jikinta dasu cikin kwarewa, a kan lip d'in ta ya tsayar da idanuwansa da suka fara sauyawa daga ainihin kalar su zuwa kalar shauk'i, hannunsa d'aya ya saka kan lip d'in yana murzawa sannu-sannu murmushi yad'an saki mai sauti tare da aza nasa lips d'in kan nata, a firgice ta ware idonta akan nasa tare da tattaro sauran kuzarinta ta turasa, baya yayi tare da fizgar ta da k'arfi ta biyosa suka zube kan bed d'in kamar wasu kayan wanki, k'ok'arin mirgina wa tayi daga jikinsa yayi saurin rik'eta gam da hannu d'aya tare da zuba mata idanuwansa gaba d'aya da suka gama narkewa da tsantar k'auna da sh'aukin ta, itama idon ta k'ir a kansa duk da iya daurewa tayi akan kallon nasa Dan sosai wasu sinadarai da batasan na miye ba ke fita daga idanuwansa suna sukar nata idon ta, hannayensa yasa ya zagaye ta tare da janta ta fad'o gaba d'aya kansa sannan yayi turning d'inta ta koma k'asa, ya dawo sama, kwaba fuska tayi bayan ta rintse idanuwanta gam, dai-dai kunnenta ya rad'a mata "I'm in need of youuuuu plsssss may u help me??" ... Girgiza kai ta shiga yi kamar kad'angaruwa tana so ta turawa ko ta samu da ta zame jikinta dan ta gama tsorata dashi bata k'aunar sake faruwar wancen bak'on al'amarin na wancen ranar a kanta, tana matuk'ar tsoron lamarin da iya gaskiyarta, saidai tarkon da ya sakata na gaske ne wanda zaiyi mata wahala ta iya kwatar kanta daga gareshi "no...no pls I don't... want it! Pls let be.... alone" ta fara cikin tsoro da rawar murya tana ci gaba da turasa, hawaye sun fara biyo fuskarta "OK..OK...karkiyi kuka ya isa, ba abinda zanyi miki ki barni kawai naji dumin jikinki dan Allah?" Shiru tayi masa dan ita kam bata yadda da ba abinda zaiyi mata ba, jin shirun nata ne ya sakashi kwanciya dakyau gefenta tare da janta jikinsa ya d'ora kanta a k'irjinsa, hannu ya saka ya share mata hawayen tare da ja musu blanket d'in, dake yanayin garin da sanyi ansha ruwa, kanta ya fara shafawa a hankali, yana tofa musu addu'a, har bacci ya kwasheta zuciyarta na cike da tsoronsa, saidai samuwar body contact d'in nasu ya saukar mata da nutsuwa sosai a cikin baccin sai Jan numfashinta tace hankali kwance..... Ido ya zuba mata yana kallon yadda ta k'ara yi masa kyau da baccin, ba laifi yad'an samu 'yar nutsuwa kasancewar su a tare dumin jikinsu ya had'u guri d'aya, yana cike da zazzafar k'aunarta da shauk'in kasancewa tare da ita, saidai he can't force her at any cost, yana so ta gasgata k'aunarta yake ba sha'awarta ba, yafiso yayi komai cikin amincewar ta da yardar ta, he wish to see dis day in his life, baisan sanda murmushi ya sub'uce masa ba yana cikin burin rayuwarsa ganin ranar da Aymana zata fara sonsa koda kad'an do yana hango burbushin son nasa a kwayar idon ta saidai ba lallai ta fahimci tana sonsa d'in ba.... Yakai kusan to 1 bai bacci ba daga k'arshe ma tashi yayi yaje toilet d'in ta yayi wanka tare da d'auro alwala yazo yayi nafila kamar yadda ya saba, saida yaji bacci ya fara kama idonsa sannan ya shafa addu'o'insa wanda mafi yawan ciki na neman had'in kan Zuri'ar tasu ne da kuma na neman soyayyar Bilkisu gimbiyar mata.lol. Kwanciyarsa ba wuya bacci yayi gaba dashi mai cike da d'adi da mafarkai masu dad'in gaske Suna cikin good time shida Aymanarsa a duniyar su su kad'ai... Samiha iyayen lab'e yaukam yanda taga dare haka taga rana tasha kuka kamar ranta zai fita, dan gaban idon ta ya shiga part d'in Aymanar bai kuma fito ba wanda ya tabbatar mata a can ya kwana suna tare, yau kam takai k'arshen lab'e dan shi Sam ma ya manta ya dura mata tab din bacci aiko taga ni ganin idon ta.. "Meya sameki my Meeha, Meya sameki a idanu kuka kikayi me aka miki?" Ya shiga jero mata tambayoyin lokacin da yazo tayar da ita tayi sallah, tana zaune tsakiyar Gado ta jingina da gadon idon yayi mata luhu-luhu alaman tasha kuka, da ido kawai ta bishi, saurin dakatar dashi tayi da hannunta lokacin da yazo zai tab'a ta "karka ka kuskura ka tab'a ni, mayaudari, makaryaci, maciyin Amana" ta fad'a cikin k'araji da tsawa, tsayawa yayi chak yana binta da ido cike da mamaki.. "Wato nika rainawa hankali kake kiranta kwaila a gabana shine kuma ka iya lallab'awa ka shige d'akin kwailar kake nuna mata soyayya saboda yaudara, ka nunamin ba itace gaban ka Ashe dama yaudara ta kake, shiyasa take iskancinta iya son ranta baka magana Ashe wato taga gadon baccinka ta gama ganin girmanka, Ashe kai....." "Ke! Dakata!" Ya daka mata tsawa, tare da murtuk'e fuska yana binta da kallon kin ma Renani. "Dama ta taba zama na gaya miki bana sonta? Kona gaya miki bazan shiga dakinta ba? Manta gaba d'aya, d important thing daya kamata ki sani shine keda ita matsayinku d'aya a gareni duk aurenku nake soyayya kuma ni nasan wa nafiso a raina, kika kara gayamin banzar magana akan wannan zancen zan shayar dake mamaki dan na fahimci sam baki gane ina miki kara bane" yana kai nan ya juya ya fice cikin b'acin rai, K'ara rushewa tayi da sabon kuka lallai tana cikin bala'i meye mafita, ko Sallar bata tsaya yi ba ta dannawa Ummanta kira "dota lafiya sassafen nan" kuka ta saki "oh dota, Mu'azzam ko?" Eh " ta fad'a cikin kukan "ok Bari zan kiraki anjima, idan Dadyn ki ya fita" daga nan sukayi sallama, sallar da batayi ba kenan wai ita tana cikin damuwa (wawiya ga gun da zaki samu warakar damuwar ki a sauk'ak'e kin tsallake, subhanallah) ************ "Dota gayamin menene matsalar? daba An hanamu zuwa gidan ku ba aida har gida zan iskoki kin d'agan hankali" "Umma ya fara kulata jiya a d'akinta ya kwana wallahi Umma asirin su yayi aiki baki ga iskancin da fa take a gidan ba" ta fad'a cikin kuka... "Me!" Ta fad'a da k'arfi "amma shine aunty tace Sam baya kulata ta hanashi ya shiga sabgarta! Amma ba komai zasu san dani suke zancen su duka, kinga dena kuka sannan ki fitar da damuwar sa a ranki, dama ai dan iskan yaro ne, kece kawai kika kwallafa rai a Kansu amma tabbas zanyi maganinsu su duka, share hawayenki kawai ki jira mezai faru kinji 'yata" "Tau Umma dan Allah kiyi wani abu wlh ina sonsa sosai banaso na rasa shi" Kama baki Umma tayi "tau shikenan yanzu dai ki fara kwantar da hankalin ki tukunna kinji?" "Tau Umma sai na jiki" bin wayar tayi da kallo ita ta rasa meyasa Samiha ta nace akan son matsiyacin yaron nan data matuk'ar tsana a rayuwa, a da ta so tayi amfani da hakan domin cimma wani burinta saidai ta fahimci bahagon yaro ya wuce duk inda take tunanin ta b'ullo masa, wata iriyar dariya tayi sannan ta tashi ta fara shirin tunkarar bokan nata wato mai gobe da nisa🤭(lol baiwar d'aguti sai a bada himma). Aiki take tana tuna irin yadda ta samu nishad'i a cikin baccin ta na jiya, wanda bata tab'a samu ba in her life time, jin motsi bayanta ne yasa kata saurin jiyowa ido biyu sukayi dashi wani lallausan murmushi ya sakar mata tare da zuwa har inda take yayi hugging d'in ta tare da bata peak a goshi "morning habibty, hw was ur nyt?" Ya fad'a a hankali, lumshe ido tayi tare da ware su a hankali saidai bata tanka masa ba saima janye jikinta da tayi ta wuce cikin store rik'e da doya a hannunta, yana zaune kan kujerar da ke kitchen d'in, da kallon kawai yake binta, yuka ta d'auko tare da d'ora doyar kan cutting bord, kama wuk'ar yayi, bataji ma tasowar sa ba.. "Kawo na tayaki Habibty?" Bata buk'atar musu hakan yasa ta sakar masa wuk'ar tare da kama wani aikin, tana yi tana satar kallon sa, yadda yake fere doyar cikin kwarewa ita fa har mamaki take wai Yaya Mu'azzam d'in nanne dodonta mai tsorata yau tsaye a gabanta yana wani lallab'ata ita kam sam ta kasa yadda da wai son ta yake wai, Musamman ma da yake cewa wai, wai tun lokacin da yake tsorata tan nan da yi mata tsawa da gasa mata magana duk cikin so ne it can believe, duk da cewa wani sashi na zuciyar ta naso su gasgata soyayyar tasa saidai Sam ta hana bawa kanta wannan damar bare ma shi ta bashi..... Sosai Samiha tayi laushi ta d'auke idon ta akan duk lamuran su, tare daci gaba da mu'amala dashi kamar ba komai a ranta yana daga cikin plan d'in su, sosai take dannewa idan Aymana na tsula musu rashin kunya da fitsara, amma taci burin duk ranar da mission d'in su ya cika zata ci ubanta..... Duk ranakun kwananta a d'akinta yake kwana yana amfani da wannan damar ne dan ya k'ara samar musu da kusanci da shak'uwa a tunaninsa da hakan zai samu ya fara cusa sonsa a ranta, saidai duk yadda ya d'auki abin da sauk'i sam ya kasa zuwar da sauk'in dan sosai kusancin ke azabtar da ruhi da gangar jikinsa, wanda shi kad'ai yasan irin wuyar da yake sha, duk yadda yake rarrashi, kwantar da murya da lallami abin ya faskara ta saka auduga ta toshe kunnuwanta, saidai ita tayi baccinta cikin salama ta barshi jinyar gangar jiki da zuciya.... Yau kam zamansa yayi a d'akinsa a tunaninsa idan ya nisance zai samu sassauci saidai abin ba sauk'i ashe kusancin da suke samu wani sauk'i ne tattare dashi, ganin juyi kawai yake ya kasa samun nutsuwa ya saka shi tashi yayi alwala tare dakai kukansa ga mai abin bayawar wa wato Allah.... Itama haka ta karaci juye-juyenta akan gado, a d'an zuwan da yake tayi sabo da kwanciya akan kirjinsa, ta saba da d'imin jikinsa sai taji ba dad'i dak'yar ta samu bacci ya d'auketa dake yanzu ba wahala tayi bacci... Da safe da ya shigo part d'in ta tana zaune kan seat, sallamar sa kad'ai ta amsa ta d'auke kanta ji tayi kawai ya bata haushi duk da batasan laifin da yayi mata ba... Zuwa yayi har inda take yayi kneeling kan guiwoyinsa tare da Dora kansa akan cinyar ta "pls Bilkisu ki dena azabtar da mu akan ta wannan sigar, na sani kamar yadda ban samu nayi bacci ba jiya kema bakiyi ba, meyasa? Meyasa zaki azabtar da mijinki Yayanki ki kuma azabtar da karan kanki, nasan kina sona kamar yadda kika sani, saidai kin kulle zuciyarki kin hanata abinda takeso kina azantar damu akan dalilin da bai cancanci wannan hukuncin ba, pls ki hukuntani ta wata sigar amma wannan is so worst for me and you too" "Aa ni bana cikin damuwa kamar yadda kaima pretending kawai kake, ni bana..." Sai kuma tayi shiru, dago idanuwansa a suka kad'e zuwa jajaye yayi ya kallaleta, sosai ta firgita da yanayinsa "uhum ki fad'amin kice bakya sona inji daga bakinki, fad'amin?" Shiru tayi sai can tace "kaima ba ni kake so ba pretending kawai kake saboda wani guri naka" Murmushin takaici ya saki "ba wannan nakeson ji ba so nake ki kalli kwayar idona ki gayamin bakya sona" Tura kansa tayi tare da tashi da gudu tayi hanyar bedroom d'in ta tana kuka "ni ka ficemin daga nan banason ganinka, banason ganinka kaje, kaje dan Allah" tana gama fad'a ta fada bedroom d'in ta tare da banko kofar.... "Ba lallai kin fahimta ba amma kina matuk'ar sona, pls ki daure ki dena azabtar damu let face each other habibty" ya fad'a yadda zata jiyo shi bayan ya mik'e tsaye tare da share kwallar da ta zubo masa for d first time in his life zubar wa soyayya hawaye, lallai dacin so yafi madaci.......... 🤭 _Tofa Maza fa an fara jigata @ Mu'azzamu💃🏻💃🏻💃🏻🙊_ *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *Bishiya bata fadi idan tana jin kishi, ko dai ka bata, kota mitu salun alun, haka wani wasu mutane suke ba'a sanin darajarsu sai idan sun mutu* 👌🏻 Duniya makaranta✍🏼 *Page* 3⃣1⃣ ________kan gado ta fad'a tare da k'ara fashewa da kuka kamar wacce ake tunzurawa kukan da ita kanta basatan na meye ba, haka ta shiga rera abinta har bacci ya sure ta anan.... "Ungu, kin ganshi ki tabbatar kin saka musu sun sha a abin sha, mai gobe da nisa ya tabbatar da sun sha hmmmm" ta rad'a mata a kunne, zaro ido tayi tare da washe baki, sannan tayi 'yar k'ara tare da wani k'ankameta sosai "I so much love you Ummanah shiyasa nake k'ara sonki" "Indai burinki ne bazan tab'a bari ya fad'i ba doto na, kinsan duk cikinku ba sama dake a raina" daga taci gaba da kitsa mata yadda zatayi ta samu su sha sannan ta ci gaba da bata guragun shawarwari wanda a nata tunanin shine tsantsar k'auna...... Ta kuwa yi sa'a tana shigowa Aymanan na gama shirya dinning d'in, ko kallon inda take batayi ba ta shige part d'in ta dan yin wanka........ Wata dariyar mugunta ta saki tare da cewa "soon zanci ubanki dalla-dalla, daga ke har d'an kanzagin naki har uwarsa bazan ragawa ba so sorry Momy" da sauri ta fito da maganin ta barbad'a a zobon da ta gani a gurin sannan tabar wurin cikin sauri ba tare da kowa ya ganta ba ta shige sasanta cike da farinciki har dasu kwasar shoki ta kusa zama sarauniyar gidan..... Sai murmushi take zubawa ganin yadda suketa banbama wa cikin su zobon "My Meeha ke baki sha zobon ba kada fa mu shanye dan mun d'au hanya" murmushi ta saki " no kusha kawai yau banajin sha" tace dashi tana ci gaba da cin abincin ta, tab'e baki kawai Aymana tayi tare da d'ire k'ofin ta mik'e tabar gurin tana watsa musu harara, murmushi Samihan ta sakar mata "saina canja miki kammani na kamaki" tace a ranta.... A 'yan kwanakin wani zazzafan case yakeyi na wani Hamshakin mai kud'i dan gay daya samu samarin yara 'yan secondary har uku ya danne cike da zalunci wanda a sanadin hakan biyu suka rasa rayukan su, d'aya kuma yake kwance asibiti, dake mutumin sanannen d'an siyasa ne ga masu gidan rana sun zauna yasa shari'ar ke ta rawa anaso a d'anne hakk'in yaran shiyasa yasa ya amshi case d'in tare da tsayawa kai da fata dan ya tabbatar ya kwatar ma majib'ansu hakk'in yaransu sannan ya tarwatsa mutane azzalumai masu ciyar mana da k'asa baya, dama shine babban dalilinsa na karatun low, tsage gaskiya komai dacin ta, yak'ar azzalumai kwatar wa wad'anda ake dannewa hakk'i 'yancin su, musamman takakawa... Hakan yasa ya rasa lokacin kansa gaba d'aya in ya fito tun safe sai dare yake dawowa in ya dawo kuma yana samansa duk yayi busy, saidai hakan sam bai canja komai daga k'aunar Aymanan dake motsi a jinin jikinsa, yana matuk'ar kewarta fiye da fad'ar baki, saidai yana jin hakan shine dai-dai dan yafison yaga farinciki a fuskar iyayen yara can fiye da nasa...duk da cewa yana matsancin kewar ta saidai yasan soyayyar ta itace kawai weak point nashi, zai sara kuzarinsa ne yaci gaba da kusantar ta... A bata b'angaren ma tana jin wani abu a zuciyarta mai kama da kewa takanji kad'aici lokuta da dama dan ko gurin cin abinci sun daina had'uwa saidai kowa yaci daban dan itama Samiha sunata exam bata cika zama ba tana school kullum, saidai changes d'in da take gani a gidan ya sakata fara tunanin maganinta yayi tasiri exams kawai take jira ta kammala ta fara shimfid'a mulkinta... Tuni ta fesawa gyatumar ta magani yayi aiki, kusan tama fita jin dad'i domin tana ganin tana daf da cikar burinta... ( _ko wane irin buri ne wannan burin oho!_ 🤔) **************** Allah cikin iyawar sa da ikonsa ya yadda tare da amincewa ya bawa *Barr. Ibrahim Mahmoud Gwarzo (Mu'azzam)* nasara akan Alhaji Munzali Sharadi sa'a bayan doguwar fafatawa da yayi da wani kwararren kafirin lauya daya gogu a harkar, shi kan shi yayi ta mamakin yadda akayi Mu'azzam d'in yayi nasara akansa, duk da barazana da matsi da sukayi ta masa bai hanashi tsayawa akan gaskiyar sa d'aya tak ba, wacce da ita Allah ya taimake sa, iyayen yaran sun yi matuk'ar farinciki da Yadda Mu'azzam ya tsaya musu ba tare da sisin kwabon su ba, da kukan su suke zuba mishi godiya tare da yi masa addu'o'in fatar alkhairi da gamawa lafia(ina ma kowanne Barr haka yake da tabbas an yaki zalunci a kasar nan da kaso mai yawa)..... Kicib'is sukayi a parlour, kallon kallo suka shiga yiwa juna musamman ma ita da ta dad'e rabon da ta saka shi a ido, gara shi yana ganinta wasu lokacutan ba tare data ganshi ba, musamman da safe in ya dawo masallaci yakan ganta a Jim, a sanyaye ta fara sauke kwayar idon ta a k'asa, hawaye kawai taji sun fara zubo mata, takowa yayi tare da d'ora brief case din kan center table ya isa gabanta tare da hugging d'inta, hannu yasa ya d'ago fuskarta "kinyi missing d'ina ne ko?" Shiru tayi saidai bata turasa ba kamar yadda ta saba saima k'ara lafewa da tayi a jikinsa tana shakar daddad'an kamshin nan nasa idanuwan ta a lumshe... Sunyi 2mnt a haka kafin ya saketa "bari naje nayi wanka na gaji sosai" ya d'auki kayansa tare da hayewa saman yana waiwayen tare da mata murmushin nan nasa, itama da ido ta bishi har ya b'acewa ganinta sai ta samu kanta da jindad'i, tabbas kad'aici ya isheta ita kad'ai a gida ba inda take zuwa sai dai in anzo mata tana ma sa'ar ana yawan kawo mata su Arif, ga su Nusee da Amira ma sun zo mata, but still takanji kad'aici sosai da sun wuce, saidai yau d'aya data ganshi na tsawon sati taji farinciki a ranta, kitchen ta shige tana murmushi tare da shakar k'amshin da yabar mata a jiki nashi... Ba k'aramin tashin hankali Samiha ta shiga ba wacce ta lab'e ganin su a taren da tayi zata shigo parlon, juyawa kawai tayi tana kuka ta tari taxi sai gida.... Kuka kawai take tana gayama uwarta abinda ta gane ma idon ta, itama uwar cikin tashin hankali take kallon 'yar ido a waje su da suke tunanin sun wuce gurin "kuma kika ce a gabanki suka sha, kuma sun kwanta tare a ranar?" "Eh Umma wlh a gabana..." Sai kuma ta tsaya "amma kuma, banda tabbacin sun kwana a tare a ranar" "Kaji sakarcin ki ai" ta rad'a cikin k'unar rai, Dan ta watsar mata da plan "kinga yimin shiru ai kin riga kin b'ata komai da kanki, anayin komai dominki dan kiji dad'i saidai in seriousness naki ya fiki yawa, komai bakya d'auka da mihimmanci" For the first time da Ummanta ta nuna mata bacin ranta "kiyi hakuri Umma zan gyara komai da kaina zanyi abinda boka ya kasa yi da kissa ta" ta fad'a with full confidence... Washe gari yace su shirya zasuje shopping kayan azumi dana Sallah, duba da karatuwar azumin.. Fitowa tayi cikin kwalliya sosai tare da yafa wani sharararan veil kan gown d'in da ta gama kamata sosai ga wani cika da fresh data k'ara yi, had'e girar sama da k'asa tare da jefa mata harara, itama martanin hararar ta mayar masa a take.. Takowa yayi zuwa inda take ita ya sunkuya dai² fuskarta "wa zaki bi a haka?" Kallon kanta tayi tare da tab'e baki "wanda ya gayyatan zanbi" ta bashi amsa kai tsaye... "To ba a haka ba 'yar galadima, aje a sako hijab, nasan me nakeyi" kallon Samiha tayi da bata da abin sawa a rayuwar ta fiye da gyale bata tab'a ganinta da hijab ba, sai ita da bata cika saka gyalen ba yau ma kawai sha'awar kwalliya tayi "ok saboda kada a ganni ace matarka ce kwaila ko shiyasa kake so na saka hijab ko? na d'anyi girma a ciki, to cool zan saka ba hijab kad'ai ba har nik'ab zan saka dan na boye fuskar itama kada aga kwaila" tana kai nan ta juya kawai.... Dafe kai yayi a rayuwa Aymana na tsananin bashi ciwon kai, kullum sai tana abu kamar bata ganewa kuma ya sani tana sane da komai takeji "Ashe haka take?" Ya fad'a a fili.. Zunbulelen hijab irin na islamiya ta zubo da kuma hadda nik'ab d'in da ta fad'a, abin yayi masa dad'i sosai dan hankalinsa yafi kwanciya a haka, jan motar kawai yayi ba tare da kowa yayi magana ba, wani k'aton Mall ya kaisu ya basu damar zab'en me suke da buk'ata..... Shi kuwa yaje gurin kayan da yake da buk'atar rabawa mutane na azumi.. Ido ya zuba mata kayan da yaga ta jibgo shaddodi atamfofi zuwa less kamar mai shirin fara d'an business, yi tayi kamar bata ganshi ba ta fuske tare da d'auke kai gefe, ATM card nasa ya basu suka cire kud'in su tare da had'a musu aka kai musu booth..... "Ke zoki kwashe kayanki anan gabana" yace mata bayan gate man ya gama shigo musu Da kayan ciki, Samiha ta kwashi nata, ita kuma ta mik'e zata bar Parlon... "Ai naka ne" ta masa mishi bayan ta juyo, kallon kin ma rena ni yayi mata "kamar ya?" Dawowa tayi ta zauna a k'asa tare da fara bud'e kayan "kayan da zaka kaiwa su Abba ne da su Momy da sauran mutan gidan na sallah" nan ta shiga nuna masa na kowa har da yaran gidan gaba d'aya, har ta kammala baiji ta kira kanta ba.. "Hmm to ai su Abba suna da kud'i basu buk'atar irin wad'annan" ya fad'a fuskarsa d'auke da fara'a dan ba k'aramin mamaki ta bashi ba "haka dai ka fad'a ka fara kai musu idan basu amsa ba tukun kace hakan" na Hajja ta d'auka "Pls kaje dani mukai wa Hajja tare?" Kallon ta kawai yake "to kefa ina baki?" Ya tambaye ta.. Murmushi tayi for d first time "ni ai inada su da yawa wad'anda bamma d'inka ba sun isheni" tashi tayi tare da shigewa part d'in ta... Yatsun sa ya nutsa cikin sumar sa tare da shafo ta yana murmushi idonsa kur a k'ofar part d'in nata da ta shige..... *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *An karb'o daga Baban musa (R.A) yace Manzon Allah (S.A.W) yace Mad'aukakin sarki yana yiwa Azzalumai talala idan ya kamasu bamai kwatar su a hannunsa.* Husnul Muslim👌🏻 *Page* 3⃣2⃣ ______Yadda yaga farinciki a fuskar Abba game da kyautar tasa gareshi, haka ma Dady dasu Momy kowa ya nuna farincikinsa har yaran sai tsalleh murna suke, albarka kam ya shata kamar me cikin fara'a Abba yace "lallai Ibrahim aure ya saka ka k'ara hankali sosai, to Allah yayi albarka kuma ya Baku masu jinkan Ku" Ameen ya fad'a cikin farinciki yana jin wata k'ima da girman Aymana a ransa mai cakud'e da Zazzafar k'aunarta, yana mamakin kaifin basira irin tata, shifa rena shekarunta yake sosai ganinsa banda shirme ba abinda ta sani, koda yake ba mamaki Idan akayi la'akari da 'yar Ammi ce, Ammi renon Hajja da Malam Sa'eed dole duk abinda zata rena ya zamo mai cikakken tarbiya da hangen nesa, murmushi kawai yake yanzu ya k'ara tabbatar da duk shirmen da shiriritar da take masa wato tana sane tana yi kawai kamar yadda ya d'auketa.... Ta baya ya rungumota tare da d'ora kansa akan kafad'arta yana aika mata wasu sihirtatten sak'anni da idanuwan sa ta mirror d'in, k'asa tayi da idanuwan ta, dan bata iya jure kallonsa "Thank you so much Bilkisa ta" d'ago ido tayi tare da kallonsa alaman tambaya.. Kashe mata ido yayi "yap yau nasha Albarka akan ki, Allah yayi miki albarka my Habibty ya bani yara kyawawa masu tarbiya daga gareki kamar ki" ya karashe yana murmushi, bata tanka shi ba saima tura baki gaba tayi da son ta mik'e tsaye, saketa yayi ta mik'en yana binta da kallo, sip ta bud'e ta ciro kayan da zaka saka, toilet ta shige abinta... Kishingid'e ta same shi kan sofa idonsa a lumshe, samun kanta tayi da zuba mishi ido tana k'are masa kallo, sanye yake da kaftan na wani tattasan yadi ash colour ya kafa hular damanga yad'an turata baya, iya halitta Allah yayi anan ba dai cikar halitta ba Ya Mu'azzam duk gidansu ba mai kyawunsa ta sani, yana wani irin kyau mai d'aukar hankali bata cika ganin laifin Samiha ba wasu lokuta akan haukar da take akan sonsa tasan ya isa yama wuce hakan ma, shiyasa ma har yau ta kasa yadda da kalmar son da yake faman gaya mata, to ta ya ma za'ayi ya sota? Duk da zuciyar ta tana gaya mata gaskiya ne, amma ta kasa aminta da hakan.... "Kodai cinye ni zaki yine 'yan mata wannan kallo haka?" Ya katse mata tunani, still idonsa a lumshe suke, bai kuma motsa ba kaman ma bashi yayi maganar ba, saurin d'auke kanta tayi tare da fara takawa da niyyan Barin d'akin, saurin tashi zaune yayi tare da rik'o hannun ta d'aya, tsayawa tayi ba tare data juyo ba.. "Tafiya zakiyi ki barni a d'akin bayan ban gama kallon kwalliyar taki ba, so nake naga ko zan iya cinye ki, tunda ke kin kasa cinyeni" shiru tayi masa. "Sakeni girki zanyi" tace a hankali "wow wannan matar tawa akwai ado wannan duk kwalliyar girkin ce? Bari nazo muyi tare ko" yace tare da mik'ewa, a tare suka fito yana rike da Hannun nata, Samiha dake zaune a parlon wani mugun kishi ne ya turnik'e ta ganin su a haka da tayi, D'auke kanta tayi, ji take kamar taje ta rufesu da duka gaba d'ayan su, murmushi ya saki ganin yanayin ta tare da sake ma Aymana hannunta, dama takura ta yayi shigewarta kitchen tayi shi kuma ya nufi inda Mihar tashi... Cikin sauri-sauri take kwab'a fulawar tata, dan wake kawai take sha'awa ci, ita kanta mamakin irin kwad'aye kwad'ayen nan daya taso mata yanzu take, kusan kullum a 'yan kwanakin sai tayi abin kwad'ayi a kitchen d'in tana ci tana girkin, kuma hakan bazai hanata ci sosai ba idan ta kammala girkin, tadai zama a cici har tsakiyar dare tashi take taci, aiko tayi wata 'yar lukuta da ita, ga haske na musamman data kara da kyau, ga shegen bacci dan saidai in bata kishingid'a ba nan take sai bacci.... Sanda ya shigo kitchen d'in tuni ta kammala d'an wakenta da yaji dafaffen kwai da kayan lambu, yasha yaji sai d'aukar ido yake, ta Dora tukunyar girkin tare da zama kan kujera ta d'ora plate din a table tana ci kamar ta had'a da plate d'in, zuba mata ido yayi yana wani nazari a kanta, kafin ya karasawa shigowa gaba d'aya... "Iyye wane irin abincin rowa kika samu kika lab'e anan kina cinye kayanki ke d'aya" ya fada tare da jan d'ayar kujerar dake facing d'inta yana kare mata kallo, banza tayi masa kamar yadda ta saba, wanda tuni ya saba da shirun nata dama can dai bamai yawan magana bace ya sani kamar shi saidai wannan ya had'a da wata hanya ta horasa daga cikin hanyoyin horon nasa da take da, hannu ya saka a tare suka cinye shi tsaf ba tare data ce masa komai ba, sannan taci gaba da Aikinta yana tayata kamar yadda ya saba yana ci gaba da janta da surutu da tsokana, ya fahimci har rashin kunyar yanzu ta rage sosai, kuma in yayi abin dariya takan murmusa ko da ba zata amsa ba.... Washe gari sukaje Gwarzo inda Hajja kai mata nata kayan dama ita ya saba siya mata, Samiha Allah kiyaye tayi musu Dan tace ba inda zata, dan Sam basa shiri da Hajjar, dan Hajja ba ruwanta da iskanci kowa kwaba ma magana take muddin taga take-taken mutum, shiyasa Sam basa shan inuwa d'aya da Samiha da Samha.. Tayi murna sosai da ganin su sai nan nan take dasu, tana k'ara godewa Allah daya cika musu burin su, sai bin Aymana da kallo take duk inda tayi tana murmushi, nan suka wunin mata sai marece dake ya na Hutu ne. Kamar kar su dawo taji taso ya barta inda Hajjar ta kwana biyu, saidai Hajjar ma bata aminta da hakan ba, dole ta hakura ta biyosa tana kumbure- kumbure har Hajjar fushi take da ita..... ************ Tana zaune A main Parlour tana kallon peace TV, daga shi har Samihar duk sun fita, tun safe take jinta gata nan duk bata kwarin jiki, a daddafe ta samu tayi musu jalop d'in macroni, haka kawai taji tana sha'awar zama a Parlon, tana kallo har bacci ya sureta dake banzanta ne... Samha da Samiha ne suka shigo gidan a tare, ganinta kawai sukayi kwance tana sharar bacci, zaro ido Samha tayi tare tab'e baki tana jifan ta da mugun kallo kamar tasan tana yi kafin takai duban ta ga Samihar wacce itama yanayin ta ya canja tana bin Aymanan da kallon tsana.. "Yanzu ke Sami haka kika zubawa shegiyar yarinyar nan ido a gidan nan ta samu sake haka, kiga wani fresh da tayi irin tana hutawar nan ke gakinan jiya i yau" Tab'e baki tayi "Hmm baki San azabar bak'incikin da nake kunsa ba ai, duk yaya Mu'azzam me, ya barta ta rena shi ta reni ni, duk abinda take gidan nan baya bari mata komai kamar mai tsoron ta nima ya hanani tab'a ta wai kuruciya" "Kutt! Wannan ce da kuruciya, kedai kice kawai an kai yaya na inda aka kai Abba ni nasan wannan iskancin ba banxa ba dora ta akayi akai, shiyasa kika ga yaya ya kasa komai amma ba haka ba me zaiyi da wannan abar" Samhar tace ranta a bace. "Nikam Allah bazan d'aga mata kafa ba da nice, bari kiga dama ina k'ule da ita, yayan nanan?" Samiha da dama so take ta tunzura Samhar suci uban Aymanan kota rage hassafi "baya nan fa dan kinga ai bamu samu motar ba" "Good" tace tare da zuwa fridge da sauri ta d'auko gorar ruwa masu shegen sanyi, tazo ta tsaya kan Aymanan tare da bud'e su ta fara kwara mata su a kai... A firgice ta mik'e cikin tsananin kad'uwa tana zare ido, kafin ta gama dawowa hayyacinta tass taji saukar mari, rike gurin tayi idonta tar kan Samhar, bata tsaya Neman ba'asi ba itama ta sauke mata nata marin, tare da bin ta da kalar kallon da take mata "da nayi maki me? Aina gaya miki Aunty Samha jiya d'in ta wuce ba yau bace.." Bata rufe baki ba itama Samiha ta sauke mata nata Marin... Cikin k'arfin hali itama ta juya ta sauke mata nata "bazan t'aba yadda wata k'atuwar mata ta zuban tafi a banza ban rama ba, ko waye ita".. "OK yanzu ko jikinki zai gaya miki dan uwarki, badai mu kika Mara ba" Samha ta fad'a tare da yowa kanta ta fara kai mata duka tana Tarewa, itama Samihar kanta tayo suka taru kanta su duka... Duk da tayi iya k'ok'arin ta gurin ramawa saidai sarkin yawa yafi sarkin k'arfi aiko tuni suka ci k'arfinta dama gata yau din ta tashi sai a hankali, tuni suka kaita k'asa.. Samihar na kan ruwan cikinta ta mummuk'ar ta, itama Samhar yi take duk wani haushi da takaicin ta da sukeji suke son sauketa tun tana iya ihu har ta dena, su kuma jibgar ta suke kamar ba gobe.... Tun kafin ya kammala parking yake jiyo kamar ihu cikin gidan, aiko bai kammala parking d'in ya fito a guje tare dayi cikin gidan ... "What nonsense..." Kasa isuwa yayi hango Samihar da yayi kan Aymana ga Samha gefe suna jibgarta, suma cak suka tsaya tare da fara zare ido suna kallonsa a gigice kowacce ta kasa motsi.. Da gudun ya iso gurin tare da tura Samihar da k'arfi, sannan ya d'ago Aymanan zuwa jikinsa wacce tuni ta some Sam bata numfashi, kallonsa ne ya sauka kan k'afafun ta jini ne kebin su har ya fara b'ata tiles d'in "jini!" Yace da k'arfi. Suma sai lokacin dubansu yakai a gun, kara zaro ido sukayi banda mazari ba abinda jikinsu yake sun had'e guri d'aya kamar munafukai... K'ara rikicewa yayi a rud'e ya sungumeta gaba d'aya, kamar ya d'auki baby, idanuwansu sun kad'e sunyi jajir kansa har wani jaja yayi ransa duk a dagule, cike da tsana da tsananin b'acin rai ya kalle su... "Kisa! Kisa kuka yi? Wallahi duk yarinyar mutane ta mutu you will pay for" gama fad'a ya fice da ita a hannu yana kwalla was gate man kira da shima yaga rashin amfaninsa a ga reshi, saidai yanzu bai da lokacin wannan... Shima duk ya gama rikecewa motar yace ya bud'e masa baya ya sakata sannan ya zagaya da sauri ya shige... Da gudu gate man din yaje ya wangale masa gate, ya fita a guje kamar iska....... 😢😣 _Wayyo my Aymana_ 😢 *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *An karb'o daga Jabirin (R.A) yace manzon Allah (S.A.W) yace misalin sallolin Farilla guda biyar da mukeyi a yini, kamar misalin koraman ruwan tafki ce take gudana a bakin kofar kowannen mu, yake wanke jikinsa a kullum sau biyar a rana(yana nufin yadda mukejin dad'in jikin mu Idan mukayi yawaita wanka muna wanke daud'a to kamar Haka sallar ke wanke mana zunuban mu! Allah ya bamu ikon kiyaye ta👏🏻)* Husnul muslim👌🏻 *Page* 3⃣3⃣ _____kasa daurewa ya isa Malam Aminu kano yayi ganin yadda take bleeding sosai gashi har yanzu ba numfashi a tare da ita, ga hankalinsa da baya jikinsa driving yake kawai amma ba wata nutsuwa a tare dashi, wata private clinic na kan babban titin unguwar tasu ya shiga da ita, aiko a gaggauce aka kawo gadon d'aukar marasa lafiya aka d'auketa, Emergency aka shiga da ita ganin ta in critical condition, bin gadon yayi hannunsa cikin nata yana shafawa, shidai fatan bai wuce ta dawo hayyacinta ba duk a rid'e yake ya kasa yin tunanin komai... Yanayin da yayi musu magana dashi da yadda ya figi motar ba girma, ba karamin kad'uwa ya sakasu ba, sun San yana da zafi sannan akwai tsare gira saidai wannan yanayin nasa na yau ya sha banban koma suce basu tab'a riskar sa a irin yanayin ba... Sosai jikin Samha ya sanyaya lallai sun tabka ta'asar da basu san iya abinda zai biyo baya ba, tun anan ta fara data sanin biyo Samihar da tayi ba tare da ko mijin ta yasan ta fito ba "bleeding? Mean for?" Ba Momy ta gaya mata ta hana Yayanta shiga shirgin ba, kuma tasan yadda yake tsananin yi mata biyayya amma tabbas wannan jinin ba shakka na zubar ciki ne alamar yana kulata tunda ga sakama ko b'aro-b'aro.... Ciki ta koma a guje tare da d'auko kayanta ko mayafin a tafe take yafashi, rik'eta gam Samiha tayi tare da yi mata wani irin kallo wanda yafi kama Dana maraici, itama jikinta yayi sanyi lakwas dan batasan makomarta ba "kina nufin tafiya zakiyi ki barni anan?" Figze hannunta tayi tare da watsa mata harara "to da na zauna ya sameni kike nufi, au ke zama zakiyi kenan?"bata wani jira cewarta ba ta wuceta cikin sauri, itama ciki ta koma da gudu tare da tallabo veil d'inta cikin sauri ba zata yadda ta zauna ya dawo ya sameta ya nemi kasheta, gara yaje gida komai ta fanjama fanjam.. Saidai me suna zuwa bakin gate mai gadin yace bai san zancen ba dan yallab'ai yace kar ya bari kowa ta fita a cikinsu kuma kar a shigo, bala'i da hauka suka fara gwada masa dake dama ya kulle kuma mak'ullin na hannunsa yasa ya sharesu dan k'arshe ma ya shige d'akinsa ya rufo k'ofarsa ya barsu nan suna ruwan ashar d'in su, shidai umurnin oga kawai ya ke bi kodon ya wanke laifin da yayi masa, dan tabbas yaji hayaniya a ciki saidai sanin dokar sa tayi masa iyaka daga gate sai gate, yasa baije ba laifinsa kuma da bai kirasa kuma wannan Sam baizo kansa ba.. Daga karshe ganin tabbas da gaske ba barinsu fita zaiyi ba ya saka su dole komawa ciki hankali a tashe dan sun San tabbas yau kashin su ya gama bushewa saidai har cikin ran Samihar taji dad'in zubewar tsinannen cikin da sam basu San da zamansa ba, tabbas wannan al'amarin yayi mata dad'i duk da ranta fal fargabar makomarta... Samha kam safa da marwa ta shiga yi a parlon dan abubuwan sun had'e mata da yawa itafa ba ma da niyyan zama tazo ba dan 'yan kwanakin sun fara samun matsala da mijinta k'orafin ta cika yawo ga rashin girki ya gaji da yin take away, rashin iya tsabtace gida duk da kuwa tana da maid kuma tana yi amma dake Neman rigima yake yace sai ita zatayi da kanta yaushe zata iya, ga dokar fita daya kafa mata ba tare da izninsa ba, har ya tabbatar mata ta sake zai d'au tsattsauran mataki akanta, gashi tana so ta koma gida kada a dawo ya samu bata nan an hanata, dabarar kiran Momy ce ta fad'o mata... Nan take ta shiga labarta mata duk abinda ya faru, a zabure Momy ta mik'e "What! Kika ce ciki fa? Waima ubanwa yayi mata cikin dan badai my Son ba" Momy ta fad'a kausashe cikin tashin hankalin da ya dirar mata a yanzu a ba zata "ciki fa kuma yadda ya nuna damuwar sa da yadda ya fita hayyacin sa ya nuna ya damu da ita yana sonta, nidai ba wannan ba Momy yanzu ya za'ayi na fita da matsala fa" "Karki damu yanzun nan zan turo mudi ya d'aukeki aini kin biyani dota, ki kwantar da hankalinki ba abinda zaiyi muku, shi kuma dan ubansa zai zo ya sameni, kice ma Samiha itama ta biyoki kuzo tare" "Hum ni ai ba wani biyowa da zanyi ta nan gida zan wuce dan na gaya miki da Matsala" amsa mata tayi sannan ta katse wayar... Safa da marwa kawai Momy keyi tama rasa bakin magana wato ita Mu'azzam zai ninke a baibai ita zai renawa hankali, da ba dan su Samha ba kenan da saidai ta wayi gari taga abinda tafi tsanar faruwar ya faru wato had'uwar jini tsakaninta da Fatima "bazai tab'a yuyuwa ba!" Tace a fili da k'arfi "wannan karon dole nayi abinda banyi ba a baya koda haka na nufin Barkewar rashin jituwa tsakanina da Alhaji, dole na raba wannan tsinannen aure dake shirin hargitsa ni, dole nayi magantu fiye da baya, tabbas Mu'azzam zai fuskanci matsancin fushina ni..ni yakeson had'awa jini da Fatima tabbas ya d'auko magana" haka tayi ta tambatun ta cikin tsananin b'acin rai... ************ "Sir!" Da sauri ya juyo tare da kallon nurse d'in da rinannun idanuwansa da kallo d'aya zai tabbatar maka yana cikin matsananciyar damuwa, tunda aka shiga da ita ya kasa zama sai ka da komo yake yana kallon k'ofar ransa fal tausayin ta cike da damuwa Mara adadi... "Yes! Yawwa ya ake ciki ta farfad'o?" Ya tambaya a same time, cikin tausayawa da sanyi irin na wasu ma'aikatan jinya Idan zasu gaya maka bad story about ur patient(bak'in labari game da majinya cinka) "sorry 2 say kun rasa babyn ta samu miscarriage, and tana buk'atar jini yanzu saboda jinin da ta rasa sosai" kasancewar end of week ne hospital d'in ba Dr sai nurses.... "Miscarriage" ya maimaita a fili dama Ashe ciki ne da ita da gaske kamar yadda yake hasashe, amma kuwa ya zama wawa daya kasa gane hakan tun farko, yayi sake wanda yaja masa rasa gudan jininsa, baisan lokacin da hawaye suka wanke masa fuska ba cike da juriya irin tashi yayi saurin goge hawayen tare da cewa nurse d'in suje a gwada nashi in zaiyi dan shi kowa ma bai samu gayawa ba asalima yabar wayoyin a mota, yafi so sai yaga ta farfad'o tukun kafin ya samu nutsuwar sanar da gida... Cikin sa'a kuwa jininsu yazo d'aya aka d'iba nan take... Duk yadda Mudi yaso gate man d'in ya bari ya shiga gidan fur ya murje ido ya ce baisan zancen ba tunda oga bai kirashi ba dama gashi k'abila sarkin kafiya da rik'o gashi wani gabjeje kakk'arfan gaske, haka dole Mudi ya koma ya gayawa Momy an hanashi Shiga.. Wayar Mu'azzam taci gaba da kira cikin b'acin rai sosai gashi tana ring amma baya d'agawa aiko takai k'arshe a k'uluwa sai kwafa take... Zuwa yanzu kuka Samha takeyi dan tasan ta gama kad'ewa har ganyenta musamman da taga kiran mijinta ya shigo mata, kasa d'agawa tayi sai fad'i take "na banu na gama ai" itama Samihar hankalinta Sam baya jikinta gashi ta kasa samun umman ta a waya... Ganin wani kiran ya k'ara shigowa a wayar ne yasa ta had'iye yawu tare d'agawa hankali tashe "kina ina" taji saukar muryarsa a kunnenta a kausashe "um...um..inaa..." Katse ta yayi.. "Good duk ma inda kike daga nan ki wuce gidanku har na nemeki" bin wayar tayi da kallo kafin ta rushe da kuka tare da d'ora hannu akai "Wayyo Allah na, amma dai Samiha kin zaja min"...... Manage pls am busy *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *Daga Umar bin khattab (R.A) yace Manzon Allah (S.A.W) yace "da zaku tawakkali ga Allah matuk'ar tawakkali, daya azurta ku kamar yadda ya azurta tsuntsu ya wayi gari da yana mai jin yunwa sannan ya maraita yana k'osasshe( darasi ka dogara ga Allah dayi masa kyakyawan zato zai azurta ta inda bakayi tsammani ba).* Husnul Muslim👌🏻 *Page* 3⃣4⃣ ________hannunsa cikin nata ya zuba mata ido, tayi fayau da ita ga fuskarta duk ta kumbura saboda duka, d'ayan hannunsa yakai ya shafo cikinta, kwallar da ta tarar masa a ido ce ta sauko a fuskarsa " shikenan na rasa my lovely baby? U must pay I swear! Both of you" ya fad'a a sarari cikin jin d'aci a ransa, jinin da aka saka mata ya kalla yana sauka a hankali alaman zai dad'e kamin ya k'are, kallon yadda take sauke numfashi yayi daga gani tana jin jiki, k'ara runtse hannunta yayi a nasa cike da tausayin ta "get well soon my habibty Aymaa..wish you speed, jet, quick recovery dear" kifa kansa yayi kan gadon da take kwance, kan nasa wani irin ciwo yake masa d'aurewa kawai yake yi, cikin jarumta irin tasa... "Sir!" Nurse d'in d'azu ce sam ko shigowar ta baiji ba, d'agowa yayi tare da kallonta ba tare da yace komai ba, k'asa tayi da kanta kafin tace... "Ba zata farko da wuri ba saboda munyi mata allurar bacci dan ta samu Hutu sosai, kaima kana buk'atar ka huta, it better kaje gida ka samu Hutu kaima ka kuma ci abu mai kyau ko zaka samu kuzari a jikinka, pls kaje zan kula da ita kafin 'yan gidan ku suzo fatar ka kirasun" sai lokacin ya tuna daya kira gida ma... "OK thanks" kawai ya fad'a tare da mik'ewa, har wani jiri-jiri yake ji, mota ya isa tare da d'aukar wayarsa Ammi kawai yaga ya kamata ya kira, ganin miss calls d'in yayi ba adadi, yasan bazai wuce akan wad'ancan criminals d'in bane, bai bi ta Kansu ba ya kira Ammi, yace dan tazo hospital yanzu gashi tare da Aymana ba tada lafia, amsa masa tayi bayan yayi mata bayanin hospital d'in, sannan ya Kira Adnan akan yazo ya kai shi gida dan bayaji zai iya driving d'in...... Yana tare da Adnan a reception yana mishi bayani, sai ga su Ammi on expected hadda Hajja ashe tazo tana ma tare da Ammin sanda ya kira, aiko duk rud'e take jin Takwarallen ta ce ba lafia dake tun zuwansu ta fahimci cikin da take d'auke da shi, Ammin ma ta dad'e da ganewa shiyasa kullum take cikin kiran Aymana tana gaya mata ta kula da kanta sosai dan ita a nata tunanin sun san da abinsu.... "Ibrahima ina ita Balkisun take, meya sameta an kwantar da ita ne, inji dai da sauki?" Hajja ta shiga jero masa tambayoyin ko gaisawa bata bari sunyi ba... "Eh da sauk'i Hajja kuzo mu Shiga ciki" Adnan yace musu, wannan nurse d'in tana zaune gefenta akan kujera, da murmushi ta tarbe su tare da mik'ewa tsaye tana gaida su, Ammi ce ta samu sararin Amsa mata itama tana maida mata murmushin, Hajja tuni tayi kan Aymana tana salati "oh! Ni Balki mi zan gani meya kumbura mata fuska da jiki haka?" Kamata Ammi tayi ta zaunar akan kujera "Hajja zauna dan Allah, kiyi hakuri zakiji komai" Mu'azzam d'in yace da ita.. Sallama nurse d'in tayi musu ta wuce, bayan an gaisa ne, ya gaya musu abinda ya faru Wanda ya sani, tare da gaya musu zubewar cikin saidai bai nuna musu rashin sanin cikin ba dan wannan personal ne tsakaninsa da ita, bayaso a gane matsalar su, bare ma ayi blaming Aymanan sa dan yasan Ammi taji ita zata d'orawa laifin gaba d'aya duk da shima da nashi dan yama fi ganin laifin kansa... "Kai Amma dai anyi shegun yara anan, 'yan iska masu fuskar munafukai..." Kash Hajja dan Allah kiyi shiru ki dena zaginsu bakisan meya had'asu ba" Ammi race cikin rarrashi... "Wlh Fatima ki fita idona, kedai kinji ciwo wannan 'ya, sam bakiga mugun aikin da suka miki kan 'ya ba? To me zata yi musu illai mugun hali ne kawai da suka gada gurin matsiyatan uwayensu......" Wayyo dan Allah Hajja kiji hakuri". "Adnan kuje ka mayar da shi gida ya samu ya huta, zan kira Muneera yanzu nasa ta fad'a maka abinci ta bawa Baba Mudi ya kai maka" amsawa yayi ba don yaso ba sai dan shima yasan yana buk'atar ya d'an samu rest of mind... Family house yace Adnan ya kai shi, tsohon part d'insa ya bud'e ya shiga bayan yace da Adnan d'in baiso Momy tasan yana gidan dan Allah, motarsa ya bayar wa masu aikin gidan dan su wanke mishi, wanka ya sake yi, Allah ya soshi ba duka ya kwashe kayansa ba hakan ne ya bashi damar canjawa, abincin da Muneera ta kawo masa yaci, dake ya gayawa Ammi a nan gidan zai sauka, farfesun hanta da koda ne, sosai yayi masa Wanda ya bashi damar sakin jiki yaci sosai, Ammi is d best mother, imaging kamar muneera ta iya girki haka, malt and milk d'inda aka had'o masa da ita ya had'a da ita, duk da yana, kwanciya yayi minti kad'an kuwa bacci ya suresa.. *********** "Yo ni nace ki boyoni koni nace ki daketa da zaki wani d'oran laifi naga dai duk a karan kanki kikayi komai" tace tana tab'e baki, zuwa gurinta tayi a tunzure tare da cin kwalarta "ni kike gayawa haka? Samiha ni zaki yiwa butulci? Lallai kau yau Yaya zaikai duka matayen nasa asibiti yai ta jinya" rik'e mata hannu tayi "aa me yayi zafi haka malama da har takai ga duka, wai ma meya faru? Yi hakuri sassauto gayamin, ai fad'a ba namu bane muda Muke Neman mafita" ganin tabbas na jaki zataci a gun Samhar dan ta d'ade da sanin tafi k'arfinta, sauke hannun tayi, tare da yin kalar tausayi "Farook ne yace wai daga duk inda nike na wuce gida har sai ya nemeni ya xanyi da Abba?" Janta tayi suka zauna "cool down ma gal, mu samu mu fitan dai zamuyi settling da Farook dan nasan shi da hak'uri" jinjina kai kawai tayi amma bata tunanin zai hak'ura cikin sauk'i dan daga yanayin maganarsa kad'ai zaka gane an hadashi da Bango.... Haka nan suka ci gaba da zama cikin gidan ganin ba sarki sai Allah yasa suka d'an saki ransu hadda cin abincin da Aymanan ta dafa ...... Ba shi ya samu ya tashi ba sai around 3pm, a gaggauce tayi alwala ya gabatar da Zuhr, car key nasa kawai ya suri car key nasa, ya samu motar kuwa a wanke kal, direct clinic d'in ya wuce, ya samu jinin yayi Rabi, amma still bacci take bata farka ba "kai Ibrahima ka gayawa ubanka ne?" Hajja ta tambayesa dan lokacin da suka fito yana kasuwa, Ammi tace zata kira ta tambayesa Hajja dake ta rud'e tace suje dai, ba yadda batai da Ammin akan kira mata shi a waya tace dan Allah tayi hakuri abar zancen nan iya su batason abinda zai tashi wata fitina, kyaleta kawai tayi dan ita bata iya kiran bane... "Aa Hajja bamu hadu da shi ba amma...." Amma me? Ungo nan kiramin shi" tace rai a b'ace "dan Allah Hajja abar..." Wlh Fatima ki fita idona Idan ke bakisan zafin 'yarki ba ni nasan zafin jikata ko kuwa dan Hashimu baya nan ne kuke so ku nuna mata wariya?" "Allah ya baki Hakuri Inna ba haka bane, ni rigima ce banaso kin sani" Kiran mata shi Mu'azzam yayi, ta koma gefe tana zayyana mishi, shi kuma guri ya samu ya zauna tare da zuba mata ido, dake ya saba sosai da Ammi ba wata doguwar kunya a tsakaninsu ya tambaye ta ta tashi ne, ta gayamasa bats tashi ba tun tafiyarsa, jinin kuwa har yayi rabi dake 8hour suka bashi.... "Yawwa yanzu naji batu" Hajja tace bayan ta kammala wayar "wai ma su shegun yaran suna ina ne yanzu" sai lokacin ya tuna daya barsu gida kuma ya hana a barsu su fita, mik'ewa kawai yayi ba tare daya bata amsarta ba, yace yana zuwa "ja'iri wannan anyi miskilin banza, waya sani ma ko da had'in bakinka a ciki ba tabbas tunda nonon Zainabu ka tsotsa" ita dai Ammi bata ce komai ba Addu'arta d'aya ce Allah ya tashi kafad'un 'yarta ta lafia... Tun da suka ji dirar motarsa kowacce su ta jiki ya d'auki bari suka zazzaro idanu waje, cike da takun kasaita fuskar nan tamau ya fito a Ya Mu'azzam d'in da suka sani can baya, sanin muhimmancin sallama kad'ai ya saka shi yi musu ita, k'ofar parlon ya kullo, sannan ya tako zuwa seat d'in ko kallon inda suke be ba, zama yayi kan one seater tare d'ora k'afa d'aya kan d'aya.... "Kuzo nan ku gayamin dalilin ku na dukan 'yar mutane!" Ya fad'a hankali kwance kamar ba abinda ke damunsa, cikin sauri suka iso gabansa a tare jikinsu ya shivering... "Yes! Inajinku" ya sake fad'a ba tare daya kallesu ba, inna inna suka shiga yi cike da rashin gaskiya dan kowaccen in zaka kasheta bata ce ga ainihin dalilinta ba tsabar son kai ne kawai.... "Can't talk to me you stupids gal!" Ya fad'a a tsawace tare da mik'ewa tsaye, veld d'in jikinsa ya zare ya fara zuba musu, ihu suka shiga yi suna magina suna rokon ya kyalesu ba zasu k'ara ba. Saida ya tabbatar sun daku sannan ya kyalesu, zama yayi kan seat ransa na k'una duk da ya dake sun bai ji wani sassauci ba tunda bazai dawo masa da gudan jininsa ba, sun riga sun cutar dashi cutar da bamai iya gyara cutar a cikinsu..... Tsawa ya daka musu akan su rufe masa baki "Ashe kenan duka ba dad'i kuka had'u kuka doki 'yar mutane for nothing, sannan kuka....useless ko d'auki mayafan ku yanzu nan ku biyo ni, aiko har da cin tuntub'e gurin sauri.... Suna isa gate d'in A daidaita na aje Umma wacce ta dawo daga gurin boka, zubar dasu anan yayi yana jin tana kiransa ya k'arawa motarsa gudu ya barta da k'ura, kan 'yarta tayi ta kamata tana tambayar ta lafia meya faru, shiru tayi mata tana maida numfashi kawai Samha tuni ta barsu anan ta gyangyad'a tayi ciki, ita kama 'yar tayi sukayi ciki tana mita tare da k'ara jin tsanar Mu'azzam d'in a ranta...... Sanda ya koma cike ya samu d'akin, Abba, su Adnan da Hafiz hadda su Nusee da Amira duk suna nan ya samu ta farka tana jingine da filo Hajja na kusa da ita tayi wani bake-bake ta kasa ta tsare.. Kallo d'aya tayi mishi ta d'auke idonta, k'arshe ma lumshe ido tayi dan bata buk'atar ganinsa... "Ibrahim dama abinda ya faru kenan shine baka sanar da ni ba, ai wannan Abu babba ne bai kamata a boye ba, yanzu ina Su Samihar" Abba yace dashi bayan sun gaisa "Yanzu na kaisu gida..." "Inji ka jibgi matsiyata" Hajja ta cafke, girgiza kai kawai Abba yayi, kyaleta yayi yana mai Amsa gaisuwar su Amira da Nusee... "Fatar ba wani Abu kayi musu ba dai Mu'azzam" Ammi tace "Aa Ammi ai gara ya koya musu hankali" inji Hafiz "ai wadannan yaran basu da hankali" Cewar Adnan. "Waya gaya muku ana gyara b'anna da b'anna" Abba ya amsa "ai komai a hankali ake binsa har a gano bakin zaren" "Gaskiya kam" cewar Ammi, shidai baice komai ba, karasawa yayi gefen gadon "ya jikin naki Bilkisu" ya fad'a a hankali, "da sauki" ta amsa ba tare data bud'e idon ba... "Kai wai meke kanka yau tun dazu sai magana nace maka kana shareni ko duk miskilancin ne naka ya motsa" harara ya banka mata, shi so kawai yake su had'a ido da ita yaga yana yin ta amma tak'i bashi dama...... _I don't know what is wrong with you readers, ni ana wa ganin duk mutumin da bakuyi jinga da shi akan Abu ba akan karan kansa yaga dama yake yin Abu, ai bai kamata asa masa takun kumi ba, kamar yadda kowa ya sani typing is not easy, ya shafi komai, amma a haka muka squeezing time namu Muke b'ata wayoyin mu, muke sub always just for you readers but still bamu yi yadda kukeso ba, but thanks god, Allah yasan dalilin da yasa nake rubutu, and ada inada enough time amma yanzu am always busy, ba lallai kullum na iya yin typing ba, ba kuma zance ga lokacin posting ba, zanyi lokacin da na samu dama kawai, pls a cire son zuciya a rik'a bamu uzuri👏🏻👌_ *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *A lokacin Allah (S.W.T) yaso fitar da Annabi Yusuf (A.S) bai umurci bango ya zage ba, mafarki yasa sarki yayi, Wanda yayi sanadin fitarsa da kuma d'aukakarsa, Allah kenan mai yin yadda yaso, yana yi Abu yadda yaso saidai yakan sanya dalili akan faruwar wasu ababe duk don mutane su k'ara wa'azantuwa👌🏻* Duniya Makaranta✍🏼 *Page* 3⃣5⃣ ________wani wannan mari Umma ta wanke mata fuska da shi bayan ta gama gaya mata abinda ya faru "stupid gal, wane wawan ne ya baki shawarar ki dake ta? Nace wane saunan ne, shiyasa kullum cikin b'ata mana plan kike, ke Sam baki iya takun ki ba, baki iya makirci ba bakya iya b'oye feeling naki" duk cikin b'acin rai take maganar ita ko dafe take da kuncin cike da jin zafin marin tana bin ta da kallon mamaki dan ko da wasa Umman ta bata tab'a sa mata hannu da sunan duka ba sai yau... "Da nasan wannan shirmen ne plan d'in naki da kike ikirarin kina da shi ai da Sam ban barki da wannan banzan dabaran naki ba, kinsan me nake shirya maki ne? Ina nan ina maki babban shiri babban aiki amma dake ke banza ce kin zo kin hargitsa komai wama yake ki sako Samha a ciki iyee?" Ta k'ara daka mata tsawar da saida ta zabura... "Wawiya kawai kinsan how long nake pretending a gidan nan, nake b'oye feelings d'ina, duk dan kawai naga nayi winning, waima dan ubanki keme ya hanaki kiyi cikin, kika zauna kallon ta har tayi ciki sannan kika kasa sanar dani iye!" Sai lokacin ta iya bud'e tayi magana. "Umma wlh bansan tana da ciki ba, dan Sam banga alamar hakan tare da ita ba" ungu nan" ta watsa mata hannuwa "tun da har kikayi sake ya fara kulata meyasa kika kasa tunanin ta samu ciki, nace ke me ya hanaki yin cikin?" "Planning nake" ta fad'a a hankali cikin tsoro dan ta tsorata da yanayin Umman tata "kutttt! Da uwar wa kikayi shawara?" Umma saboda karatu na mukayi nida Samha".... "Amma ke wannan bansan mahaukaciya bace sai yanzu, kice duk kin gama rusa duk wani plan d'ina, get out in my sign tun kan na hallakaki anan ban sani ba" tace a tsawace aiko a guje ta bar d'akin tana kuka, ita da take ga tayi best thing za'a yaba mata shine abin ya dawo haka, sintiri Umma ta shiga yi a dak'in sai tsaki take zubawa kamar tsaka.... "Ke! Daga ina haka, meya sameki haka?" Momy tace lokacin ta tayi arba da Samha, jikinta ta zub'e tare da sakin kuka cikin kuka ta shiga zayyano mata abinda ya faru, har na farook d'in ta k'arashe "Momy wlh farook ya fusata sosai bansan wane mataki zau d'auka akaina ba, pls Momy ki taimake ni ina sonsa wlh" Shafa kanta tayi "sorry my dota, dena kuka amma ki rage wannan son nashi shiyasa yake juyaki yadda yakeso kiyi zamanki ki kwantar da hankalin ki kinji, da kansa zai kawo kansa, kuma zanyi masa gargad'i sosai akan ki dan ba jaka na bashi ba meye amfanin 'yan aikin da na d'aukar miki da zar fara takura miki, kije ciki kiyi wanka ki gasa jikinki ki kwanta kinji, ki barmin komai a hannuna zanyi maganin komai, shima Son ki barni dashi zai zo ya sameni, indai shima ya zama salamammen ne sai na ji" tashi tayi ta wuce ciki cike da damuwa dan tasan takai Farook mak'ura ne yana da hak'uri sosai kuma yana sonta.... A falon taci karo da Samiha tana kuka "dota" tace tare da zuwa inda take ta mik'ar da ita "yi hak'uri share hawayen ki, zaizo ya sameni, zan tabbatar na kwatar muku 'yancin ku, dan na fahimci shima Fatima ta mallake min shi, saidai ina mai tabbatar miki bazai tab'a sabuwa ba, karya suke" hayaniyar surutun Momyn ne ya fito da Umma murmushin kirsa ta saki "Momy kece da kanki" "Hmmm ai dole nazo Suwaiba wlh banji dad'i ba Son yayi disappointing d'ina, banyi zaton haka Daga gareshi ba, amma dan Allah kuyi hak'uri zaizo ya sameni" "Laa aiba komai Aunty aiba yin kansa bane daga gani, dama baki zo ba wlh, tashi tsaye kawai ya rage muyi, dan muka tsaya sanya muna ji muna gani muda d'an mu saidai ido" Umman tace, sakin baci Samiha tayi tana kallon Umman tata, lallai lamarin Umma ya fara bata tsoro kuma yanzu, duk da batasan ainihin me take shiryawa ba, Amma ta yadda Uwar tata karshe ce gurin makirci... "Hmm ki bari kawai zamu zauna muyi magana bari dai yazo d'in, sannan naga kalar Hukuncin da Alhaji zai yanke" tare ta wuce da Samihan sashenta don k'ara rarrashinta, dariyar mugunta Umma tayi "soon things most change"..... *************** Sai zuwa 8Pm jinin ya k'are, nurse d'in tazo ta cire mata, wankin Mara tace za'ayi mata aiko ta tub'ure tace bataso, fad'a mami ta fara yi mata, Abba kuwa rarrashinta ya fara yi akan ta hak'ura ayi mata yana da amfani, Dan su kad'ai ne a dak'in shi yaje d'auko mata kayanta Dan Hajja ta dage ba zata koma gidan ba saita warware gaba d'aya duk da bayaso amma dole yabi umurnin Abba tun da ya koya mata baya, Hajja kuma ta shiga toilet, Su Ya Adnan kuma sun wuce gida.. " Wane irin wankin ciki kuma? Duk irin wuyar da d'iyar ga tasha zaku wani kirkiro mata wani wankin ciki, ke kuma Fatima saboda tsabar rashin kulawa hadda rufeta da fad'a dan tace bataso, Kaima Mamuda da nake gani Kaine kafi kowa sonta shine kake goyon bayansu..." "Amma Hajja ai yana da amfani tun da cikin ya Riga ya fita gara a fitar da sauran dattin" dallah Rufamin baki anan mu bamusan da wani wankin ciki ba can da, da ya Riga ya b'are, ai shikenan, ke yarinya tafiyarki kawai".. "OK kinga a barshi kawai, indai ba sauran wata matsala daiyi discard namu kawai" Abban ya Fad'a amsawa tayi tare da ficewa yayin da ita kuma Hajja ta kama Aymana zasuje toilet.. Saida sukayi rikici a toilet d'in, tafasassun ruwa wai basu da maraba da mai jego, aiko tirjewa tayi tace wlh batasan wannan ba, dole ta kyaleta ganin lokaci na tafiya ga kuma yanayin jikinta, jiyo muryar Mu'azzam ne yasa Hajja fitowa ta karb'ar mata kayan da zata saka, nan ta same su hadda Dr yazo dan ganin yanayin jikin nata, nurse ta gaya mata suna son sallama dake weekend ne sai marece ake samu Dr... Tsaf ta fito cikin Arabian gown light purple &black tayi rolling da veil d'in ta black, tayi sharr da ita saidai fuskar fayau a kuma d'an kumbure, k'asa tayi da kanta ba tare data bari idonuwansu sun had'u ba, tun karon farko da suka had'a idon, shikam ya shagala da kallon ta yama manta da wani Abba da Ammi dake d'akin, tambayoyi Dr d'in yayi mata a yadda takejin jikinta ta amsa mishi sallamar ya rubuta musu tun da haka suke so kuma ba wata matsala, sannan ya rubuta magungunan da zasu siya, Amsa takardar yayi ya five zuwa pharmacy d'in cikin clinic d'in.. Sanda ya dawo Hajja na bata abinci dan tace ba inda zasuje sai taci abincin "Hajja ki bari zanci da kaina nidai, nafa ji sauk'i" harara ta watsa mata "dalla can k'urk'iya bud'e bakin kiga" sudai su Ammi sai kallon su suke ba damar ayi magana Yanzu Hajja ta haye kan mutum... Aje Magungunan yayi tare da zuwa bakin gadon "Ya k'arfin jikin" can ciki tace "da sauki" ba kiji ana gaida ke bane" Ammi ta fad'a a tsawace.... "Oh! Fatima wai meye tsakaninki da 'yar nan ne nikam? Naga ai ta amsa nidai dan Allah ki shafa mata lafia taji da kanta" d'inke baki Ammi tayi Abba yayi 'yar dariya... Motarsa suka shigo ita da Hajja, Ammi kuwa da motar Abba suka wuce direct Family house suka nufa kamar yadda Abba yace, saida ya tsaya ya siya musu fruits, sannan suka wuce gida... Sanda ya shiga gurin Momy tana Zaune Parlor ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya fuskar nan d'aure sai girgiza kafa take, abubuwa sun game mata Dan Abba har d'aki ya sameta yayi mata tatas na rashin zuwa ta diba Aymana... Ko sallamar bata Amsa ba, gabanta ya tsuguna tare da bud'e baki zaiyi magana, dakatar dashi tayi ta hanya wanke masa Fuska da mari har guda biyu masu zafin gaske "kar ka yadda ka gayamin komai, dan nasan komai" tare da nuna shi da yatsa.. "Ni zaka renawa hankali ni zaka ninke a baibai, wato ga shashasha ko, Ashe Mu'azzam ina maka kallon kasan meke maka ciwo kasan zafina Ashe ba haka bane ba, Wlh kaban mamaki, meka gani a tattare da wancen banzan yarinyar da har yaja hankalinka gareta, me take da shi da Samiha ta rasa da har sai kaje gareta, yanzu kai ko kunya baka ji, gabjeje kato dakai kaje gun wancan 'yar mitsiyar yarinya wacce a haife zaka haifeta haihuwar kaji?" Tsaki taja taci gaba. "Sannan saboda Fatima ta gama shanyeka shine Dan sun daki banzar yarinyar sun zubar da tsinannen cikin da bana fatar a haifesa, wanda kila shi zai sako ajali na, ni! Ni zaka had'awa jini da Fatima Ibrahim! To bari kaji wlh baka isa ba ban haifi dan da zai tsallake Umarni na ba, tun wuri kaje ka rubuta mata takardar ta ka bata, umurni nane ba shawara ba, sannan kaje ka bawa Suwaiba hakuri akan abinda kayi masu ka d'auki matarka ku wuce, na datse wannan auren naku daga yau bana buk'atar sa kaje yanzu ka aikata abinda nace" tun da ta fara magana yayi k'asa dakai lokacin da ta fara magana akan Aymana runtse ido yayi dan ji yake kamar tana watsa mishi wuta a zuciya, idanuwansa jajir ya d'ago ya kalleta.. "Momy" ya fad'a a hankali, ko kallon inda take batayi ba bare ta amsa "Momy meyasa like so nayi miki biyayya gurin sab'awa umurnin mahalicci na, kada fa ki manta Momy aurenta nayi kamar yadda na auri Samiha, akwai hakkinta a kaina, Momy yanzu da ace Zulaiha ko Samha da Nusaiba ne akace za'ayi wa abinda kika ce nayi wa Aymana dan Allah zakiso? Momy nasan wasu abubuwa dake faruwa cikin gidan nan yana daga cikin dalilin da yasa ni nisanta kaina da gidan nan, yasa ban tab'a saka baki na akan maganar cikin gidan nan ba, na sani Momy kina aikata ba dai2 ba duk da cewa nasan akwai masu zugaki, Momy Wlh Aunty Fatima bata nufinki da sharri na sani, Momy kin manta yadda Aunty Fatima ta rik'emu take mana komai kamar ita ta haifemu? Saboda kawai ta Auri Abba shine laifinta? Momy meye aibun hakan a addinan ce, kinfi so taje can wani guri tabar 'yarta cikin garari? Meye laifin Aymana Dan ta kasance mata a gareni, meye aibun kasancewar ta surika agareki?" "Momy pls kiyi hakuri ki sassauta zuciyarki ki, ki fuskan ci mu d'in *Zuri'a d'aya* ne zaman lafiya muke buk'ata ba shine zai ciyar damu gaba, Momy Dan Allah ba Dan ni ba, abar komai ya wuce muyi rayuwar mu cikin aminci, kishi gaskiya ne amma yin koyi da maga bata yafi...." "To sannu Ubana kaji! Nace sannu ubana, ai bansan ka koma yin wa'azi ba Dana sa an kafa maka munbari, Mu'azzam ka fice ka bani gu tukan nayi maka baki bansa ni ba, Shanyayye kawai! fice min" ta fad'a da k'arfi tare da nuna masa k'ofar, ranta ya gama baci matuk'a.. Tashi yayi ya fice zuciyarsa ba dad'i ko takan su Aymana bai k'ara bi ba, gida ya wuce direct, baya jin zai iya bin ko d'aya daga cikin umurnin nata, yana jin zafi a ransa game da Samiha yama rasa wane kalar hukunci zaiyi mata, amma dai dole ya saurari hukuncin Abba kamar yadda yace abar komai a hannunsa..... Shi kad'ai ya kwana a gidan cike da tunane tunane na game da lamarin Momy da kuma Aymana....... *har gobe mai sonka yana sonka kuma yana tare dakai a kowanne hali👌🏻😍* #heart you all my true friends..... *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* _An tambayi wata mata mai hikima wa kika so a cikin 'ya'yanki sai tace, karami har sai ya girma, mara lafiya har sai ya warke, wanda baya nan har sai ya dawo👌🏻 mace mai hikima kenan, 'ya'ya rahama ne kar mu yadda mu sanya musu kyashi a ransu ta hanyar banbamta wani kan wani, Allah ya shirya mana zuri'a_ .. *Duniya makaranta✍🏼* *Page* 3⃣6⃣ _______tana kishingid'e da filon seater d'in, Hajja sai mita take maka akan ta ware taci abinci sosai, dan k'aramar mai jego ce, tana jin ta tayi mata Banza tare da lumshe idonta, k'amshin turarensa taji ya fara d'okar hancinta kafin sallamar sa "yawwa Ibrahima gwara daka zo kaganta nan nayi-nayi taci abinci sosai tak'i kasan dai bata da banbamci da warce ta haihu ko?" Murmushi kawai ya saki tare da fara gaida ita yana idasa shigowa tare da zuwa gefenta ya zauna, Amsawa Hajja tayi yana tambayan ta Ammi, ta gayamai tana sashen ubansa, sannan ta Mike tana fad'in "bari inje in kimtsa ka tabbatar ka zare mata ido taci abincin nan sosai kafin na fito mu wuce wajen taron" amsa mata yayi da tau ta wuce tana mita... Hannunta ya kafa ya had'e guri d'aya da nashi yana murzawa a hankali, tare da binta da kallo, tana sanye da Atampa English koriya mai baki da ruwan hoda, dinkin Riga da zani, hoda kawai ta shafa sai lipstick saidai wannan sirrin kyan nata ya gaza b'oyuwa a gareshi, gashin kan tan nan mai cika da tsayi ta kamashi da babban ribbon sai kyalli yake, murmushi ya saki tare da kai d'ayan hannunsa akan yana shafawa.. Ware manyan idanuwanta tayi a Kansa, kafin tayi wata magana yace "good morning habibty, hw was ur body and hw do u feel now" yana murmushi, kallonsa kawai taci gaba dayi yana sanye da kaftan na Shadda light brown ya murza K'ube dark Brown, ita kanta tasan Ya Mu'azzam d'in d'aya ne tamkar da dubu, k'aryar ne mace ta d'ora ido akansa bai tafi da ita ba "ya had'u ta ko'ina saidai nidin ce bai min ba" ta fad'a a ranta(anya Aymana...🤔🤪 nidai kan ban yadda ba kuma fans d'in ta??) Lol. "Kallon fa 'yan matana" ya sake fad'a "ina kallon k'arfin hali irin naka ne ai" ta fad'a kai tsaye.... D'an ware ido yayi "ni kuma? Menayi nidin Ayma habibty?" Ya fad'a kamar wani yaro, d'auke idonta tayi "Oho! Naji dad'i da cikin ya zube Dan da nasan dashi tun kan Su Aunty Samiha su doken ya zube da ni da kaina zan zubar dashi......"ke!" Ya fad'a da k'arfi "Ashe tsanar da kika yimin takai har haka, jinina! Gudan jinina abin k'aunata? Ke wace irin halitta ce da bakya yafiya bakya manta abinda ya wuce, to bari kiji ni Ibrahim bazan kara begin d'inki akan ki soni ba and idan kina tunanin wannan zai saka na rabu dake tun kinsha karya, ki sake tunani, waima me kika d'auki kanki ne tukun?kina tunanin kinfi kowa ne? Well nagode sosai" daga haka ya fice daga parlon gaba d'aya Sam bai kula da Ammi ba dake bakin k'ofa... Sororo tayi a gun kamar an dasa ta, Dan ta tsorata da yanayin sa na yau ya dawo mata sak Ya Mu'azzam d'in ta na da can, bata Ankara ba taji saukar Mari a kuncin ta har guda biyu, aiko batasan lokacin da ta kai tsaye tsabar rikicewa, dafe da kuncin... "Shashashar banza! Dama tsiyatakun da kike shukawa a gidan kenan? Yaushe kika yada tarbiyar da na baki kika d'ora da wannan banzar tarbiya? Ke a d'an tsugunninki har kinsan ya zakiyi ki zubar da ciki? Ashe dama kin tashi daga Aymana zuwa wata bak'uwa da ban sani ba? Kin bani kunya Aymana kin b'ata wayonki" Kicin shesshekar tace "kiyi hakuri Ammi wallahi shine baya sona, Ammi kwaila fa ya kirani yace ban isa mace ba, yanzu ma da kika ga yana wannan abun duk don wani buri nasa ne na daban, kuma wlh...." "Ke! Dakata min, k'arya kike, nafi kowa sanin k'aunar da Mu'azzam yake miki, nasan Mu'azzam sanin da ko mahaifiyar sa batayi masa shi ba, shi kanshi baisan na fahimci son da yake miki ba tun ba yau ba, kin d'auka yana takura ki ne a zuwan k'i? Waima na tambayeki ya tab'a gaya miki baya sonki?" Kai ta shiga girgiza wa alaman Aa dan tasan bai tab'a furta mata baya sonta ba tun can da yake tsorata har lokacin da yake gasa mata magana... "Kada ki manta jinin jikinsa ne ke yawo a naki jikin ko gama hard'ewa da nakin baiyi ba, amma da yake ke butulu ce shine yau kika kalli k'wayar idonsa kika gaya masa bakya k'aunarsa..." Wlh Ammi bance bana k'aunarsa ba..." Ta katseta. "Yimin shiru! Cire masa ciki dai-dai yake da furta bakya k'aunarsa, amma zanyi miki uzuri d'aya saboda bakisan waye d'a ba gun iyayensa saboda rashin k'aunar da kike yiwa Mu'azzam ya saka ki jin tausayi da bege irin na uwa, ya hanaki jin zafin rasa cikinki da kikayi, wannan kanki kika yiwa, saidai inaso ki sani duk kika ci gaba da rashin mutuncin da kike masa har kika kai ya saka ki!" Wani mugun bugu k'irjinta yayi ta runtse ido da sauri hawaye suka samo damar bin fuskarta har kamar ruwa "karki yadda ki doso ni, kije ki nemi wata uwar amma bani ba!" Ammin ta sake fad'a a tsawace. Duk'awa tayi cike da kad'uwa jin furucin Ammi na k'arshe tare da kama kafafun ta tana kuka sosai "Ke kam Fatima sau nawa zan gaya miki kibi wannan 'ya a hankali wannan ai duk aikin kuruciya ne, duka nawa Bilkisun take?"Hajja ta amsa wacce ta jiyo wasu daga cikin maganganun su.. " Inna Ba wata kuruciya a tare da Aymana sai renin wayo shekara 19 ai tasan me takeyi, iskanci ne kawai saboda taga yana bata dama" "Aa Fatima tsakanin Mata da Miji sai Allah, bakisan me yake mata ba, kuma ko da baya mata komai ai ta rarrashi da nasiha za'abi a magance komai bata hantara da tsawa ba, kuma ma banda abinda ai ba abinda zai kai ga ya saketa, in suka rabu ai burin mu ya fad'i k'asa na wad'ancen shedanun yayi nasara, ki kyaleni da jikalle na Indai ke ba zaki iya lallab'ata, haba tana ji da jikinta duk kun zo kun tashi hankalinta, shima Almuri guda ya d'asa bom ya gudu bari zaizo ya sameni ai" Hajja ta k'ara fad'a tare da Jan hannun Aymanan, itama Ammi ciki ta shige ta barsu anan dan ta gama fahimtar Hajja bata so ake ga laifin Aymana, ga gaskiya ido da ido amma ana danneta... ************ Direct tsohon part d'in su ya wuce, ya safa da marwa ya shiga yi cikin Falon, amon muryarta yake ji tana ta amsawa a kunnensa kamar yanzu take fad'a masa, Ashe da har haka yarinyar nan ta tsane shi bai sani ba, da ya d'auki abin nata da sauk'i amma yanzu ya tabbatar wa kansa ba zata tab'a sonsa ba, dak'yar ya isa saisaita kansa ya danne zuciyarsa ya shiga cikin gidan Dan gaisawa da Momy, yana shiga Falon nata ta dakatar da shi ta hanyar nuna masa inda ya fito... "Karka kuskura ka shigomin, muddin ba zaka cika Umurni na ba, tuka fara tunanin canja wata Uwar ka gane! Kaje can na barwa Fatima ta had'a gaba d'aya kai da tsiyatakun yaranta" zai bud'e baki yayi magana ta katse shi "ka ficemin nace ko kuma nayi maka baki" ta fad'a a tsawace, wadda har Samha dake falon sanda ta zabura a tsorace tana zare ido, juyawa yayi ya fice ransa na matuk'ar suya, da alama so suke ya buga wannan shine rana zafi inuwa k'una, a balcony ya had'u da Samiha zatayi magana ya zabga mata wata uwar harara wacce ta tilasta mata janye wa gefe ta bashi hanya ya wuce fuu kamar iska.... Murmushi ta saki wadda yafi kama da keta "Hmmm Mu'azzam u will soon know my true colour......... _ina baran Addu'arku na rashin 'yar Yayata da mukayi yau d'innan, wanda ya tilasta dole na tsaya anan, pls pray for her😢😭😭 My Fido may ur gentle soul rest in perfect peace_ 👏🏻👏🏻👏🏻 *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *_Makaho bai tab'a ganin haramun ba, kurma bai ta sauraren Karya ba, bebe bai taba yin gulma ba, Mara hannu bai taba sata ba, da ni'imomin da Allah yayi mana muke sab'a masa, muji tsoron Allah_* Duniya makaranta✍🏼 *Page* 3⃣7⃣ _________Tsitt kakejin parlon, banda Muryar Abba bakajin ta kowa a gun "yanzu ku Samiha da Samha abinda kuke aikata wa k'anwar taku ya kyautu? Fisabillah kun kyauta..." Karaf Hajja ta amshe... "Yo wad'annan kyautatawa suka sani, da hankalin su dana mota ai duk d'aya, yanzu banda abin ya zamo na gida ai da Allah kad'ai yasan inda abin zai tsaya dan kila har hursuna sai sunyi tunda shege ne..." Haba Inna dan Allah dena fad'ar haka" Ammi ta fad'a ba tare da tasan tayi ba, Su Momy kuwa harare harare kamar su yasar da idanun kasa, sun cika fam dan tun da aka maida zancen abinda ya faru Abba da Dady ke zuba fad'a duk akan 'ya'yansu. "Shikenan duk ba wannan ba Inna, yanzu inaso naji daga gareku dalilinku na had'uwa Ku duketa duka ma bana hankali ba, kamar ba 'yar uwarku ba, kamar ba jininku ba kamar Ku ba *Zuria d'aya* bane? Meye dalilin ku?" Dady ya fad'a yana kallon gefen da Samihar da Samha ke zaune, Samiha ce tayi katsal tace.. "Dady tunda akayi auren banda rashin kunya ba abinda take mana a gidan bani kad'ai ba har Ya Mu'azzam gashinan" ta nuna gun da Mu'azzam din yake, ko d'ago baiyi bare ya nuna yasan zancen da take hakan yasa taci gaba... "Tun abin na a rashin kunya har tazo ta fara zagin mu..." Zagi!" Aymana ta fad'a ta k'arfi tare da ware ido "yi mana shiru har ta kammala bayaninta" Ammi ta tsawace ta, dole tayi kasa dakai tana mamakin sharri k'iri-k'iri.. "Nasha masa magana akan ya d'auki mataki amma yayi biris da zancen wai kuruciya ne, shine fa har Samha idan taje bata barin ta take had'awa da ita ta zage, kai har Ku zagi take yasin Abba" ta karashe tana kukan kirsa.... Aymana kam tuni ta dask'are a gun gata zaune da ranta ana mata sharri "k'arya kike yi Munafuka" Hajja ta fad'a a tsawace "wannan da kuke gani duk kirsa da kitihi ba wanda ta baro baya ta gadi abinta, bayan sun gama cutar da ita kuma shine abin ya dawo 'yar sharri, ko kunsan tun da suka tare a gidan Balkisu ce ke zaman yi musu girki a gidan kamar wata baiwa, bayan su duka matan gida ne, dai-dai da rana d'aya wannan kilibanbar bata tab'a shiga kitchen da sunan girki ba, kuma ni ba gayamin akayi ba nina gani da Idona hakan yasa nayi amfani da hikima ta na gano lallai itace keyi dana bugi cikinta naji tabbas hakane, yo ita batayi korafi akanta ba sai sune shafaffu damai zasu ce ga kara ga icce kuma tsabar mugunta hadda duka gashi sunyi mana asarar Mutum" Hajja ta k'arashe da ranta b'ace... Gyaran Murya Abba yayi "Yanzu dai duk naji komai, kuma komai daya faru ya riga da ya wuce, duk wani tone-tone ba shine ba, amma dole Ku gyara halayen Ku, dan kuwa ba ku da gaskiya ko kad'an, kome Ummina take muku a matsayin Ku na manya a gareta idan ba zaku iya hak'uri da ita ba kamar yadda na nema tun farko a gareku a matsayin ta na wacce ke da Kuruciya fiye daku, meya hana Ku kawo k'orafi agare mu? Mu d'auki mataki? Amma kukaje kukayi gaban kanku gashi a sanadin haka kun salwanta rayuwa, rayuwar da bata san meye ake ciki ba duk akan son zuciya, yanzu fisabillah idan kune akayiwa haka dad'i zakuji?" Cije leben k'asa Mu'azzam yayi yana jin zafi a ransa "ai dama baka damu kanka akan cikin ba Abba dan mai shi ma ba son shi take ba, nine dai cutar dama" ya fad'a a ransa. "Baku kyauta ba, Ku bata hakuri sannan Ku kiyaye na gaba tun da wannan dai ya riga ya faru..." "Haba dai Alhaji, wannan adalci kenan, yarinya ta Rena su, sun duke ta cikin bacin rai, kuma shi ai ya rama mata yayi musu bak'in duka amma kuma duk sai a d'aura laifin akansu wannan ne adalcin?" Momy ta fad'a dan dai ta danne zuciyar iya yanda zata iya amma ta kasa hak'ure wa kamar yadda Umma tace suyi kada tace komai duk abinda za'ayi amma dake ita bata iya boye feelings din ta ta kasa hak'ure wa.. "Zainab! Zainab kenan wai meyasa kika cika son kanki ne da yawa? Yanzu ke da Samha ce aka yiwa haka me zakiji a ranki? Ki ringa nazari akan Abu......" "Yo kaima Mamuda in banda abinka ai yaci ka saba da halin wad'annan matan" tana nufin Momy da Umma "ai duk banzan halin da wad'annan sakarkarun keyi duk tarbiyarsu ce kun sani sarai, kaidai ayi sha'ani kawai".. " Allah ya kyauta" ya fad'a sannan ya kalli gefen Mu'azzam "Ibrahim kaima baka kyauta ba meyasa ka d'auki hukunci a hannunka baka bari anzo nan ba?.." Wlh ni yayi min dai-dai" cewar Hajja... "Ayi hak'uri Abba za'a kiyaye" Mu'azzam din ya fad'a... Ring din da wayar Abba tayi ne ya dakatar da shi, Amsa wa yayi tare da cewa "shigo ciki Umar gamu nan parlor na" daga haka ya datse kiran... Sallama Farook yayi a Parlon ido Samha ta zuba masa cike da begen sa kwana d'aya tal da basa tare taji matuk'ar kewarsa, saidai kasan ranta tsoro ne fal dan batasan ainihin dalilin zuwansa ba, gaisawa yayi dasu Abba a girmame tare dasu Momy, har Ammi da kuma Hajja sannan ya bawa Mu'azzam hannu sukayi musabaha, guri ya samu ya zauna gefen Mu'azzam din... "Yawwa Umar dama so nake nasan ainihin dalilin da ya saka naga Samha a gida, muna jinka" cikin kwanciyar hankali ya shiga warware musu irin zaman da sukeyi da ita na tsawon shekara d'aya da watanni, ba girki kullum yana cikin take away, ga rashin mutunci da take yiwa 'yan uwansa, ga yawo kamar taci kare sannan ya karashe da cewa "wlh Abba yanzu haka Mami na cewa tayi nazo kawai na sallame ta na bata takardar ta, nayi bata Hak'uri amma abin tura tace lallai ko zata dawo dole sai ta gyara halinta shiyasa na yanke shawarar barinta gida na tsawon wata d'aya ko zata gyara sannan ta koyi girki dan tace bata iya bane dan haka wannan dama ce a gareta ta gyara, dan Allah kuyi hak'uri inna bata muku" girgiza kai Abba yayi ya dad'e da sanin Hak'uri irin na Farook ko tsayar gida da take kullum abin magana ne dan tafi kowa zuwa gida ko Nusaiba da Aymana da yake kanninta ne kuma gidansu ne gidan surukansu basa yawan zuwa kamar ta, kai har Samihar ma, idan yayi magana Uwar ta tace daga makaranta ne take d'an biyowa dama yasan wannan lokacin na zuwa sauran laifukan kuma duk Uwarta ce ta ja mata tun ba yau ba yasha nuna mata ta koyawa yaranta Tarbiya mai kyau da kuma girki da tsabta dan ba dole mazajensu suyi tolerating abinda yayi tolerating ba duk da shima hak'uri kawai yake, ganin Zulaiha na zaune lafia da nata mijin haka Nusaiba ba tarbiya d'aya ba su sun koya inda ya dace basu saka girman kai ba, sabanin ita data biyewa uwar ta yau ga ranar k'in dillanci.... "Babu komai Umar ai kamayi mana hallaci mun gode kuma ina baka tabbacin za'a gyara inshaa Allah" gyaran Murya Mu'azzam yayi "Abba nima irin matsala kenan da Samiha, ita abin nata har da iskanci dan har haihuwa bata so planning take ba tare da sanina ba saidai na gano ta..." Zaro ido tayi ta fara rantse-rantsen k'arya, tsawa daddy ya daka mata wacce ta tilasta mata nutsuwa "wato rashin kunyar taki har takai haka mijinki kike karyata anan, kenan kece mara kunyar ba Uwata da kuka lak'abawa"murmushin takaici ya saki tare da fito da pill din daga Aljihunsa ya mik'awa Abba. "Gashi a dak'inta na same su, saman mirror ta manta" kara zaro ido tayi tare da cewa da k'arfi.. "Wlh bani kad'ai ke sha ba hadda samha tare muke sha, ita ta bani shawara" Samha dake mak'ure gefe d'aya tana kuka, hukuncin Farook yayi mata tsauri da yawa, gashi ko kallon inda take bai ba tun da ya taho, kara volume kukanta tayi.. Shi kuma Farook a zabure ya d'ago jin me Samiha ke fad'a tare da Nuna Samha da hannu baki na rawa..... _Ash, feeling sick😤🤢, kuyi manage dan ma nayi alkawarin yine yasa nayi, Ku kara hak'uri dani my fans yanayi ne #love you All😍😘#_ [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *Kada ka dogara da mutane da sosai, saboda ko inuwarka takan barka kai kadai, ka maida komai naga gurin mai duka (Allah) zai Isar maka akan komai👌🏻* Duniya Makaranta✍🏼 *page* 3⃣8⃣ ______"Dama har ha'intata kike Rukayya(Samha)?" Farook yace cikin tashin hankalin yana kallonta, girgiza kai ta shiga yi hankalinta a tashe matuk'a dan bata tab'a tsammanin wannan abun zai fito fili ba, ta kasa cewa komai sai hawaye dake bin kuncin ta "nagode sosai wannan ne ya k'ara tabbatar min bakya ra'ayin zama dani tun da har kike k'yamatar hada jini dani" juyawa yayi gurin Abba da idanunsa jajir tsabar B'acin rai "Abba zan wuce na barku lafia" ya fad'a tare da bawa Mu'azzam hannu sannan ya wuce.... Dak'yar Abban ya iya Amsa masa, ransa ya matuk'ar b'aci "wannan shine sakamakon da zakuyi mana ko? Ashe ba'ason haihuwa ne aka haifeku? Mahaifiyarki karatun ta jingine gaba d'aya dan kawai kula daku, amma ku karatun ne ya hanaku Ku haihu ko?..." "Kabar Shegu Mamuda! Matsiyata tirr daku, kun hana kanku haihuwa ita mai yin itama kun mana asara, Allah ya isa kawai ya rage tsakanina daku..." "Haba Inna ya zakice haka kika sani itama wacce aka yiwa laifin ko batason ni'imar da Allah yayi mata" Ammi ta karb'e ta, harara Hajja ta watsa mata "waike waya sako dake anan?" Gum Ammin da bakinta Dady ya karb'e "nasan Uwata kam bazata aikata Hali irin na wadannan shashashun ba, amma ba laifinku bane duk na uwayen ku" Momy wacce jikinta yayi ta kasa cewa komai dan itama batasan da zancen ba koda wasa bata tab'a ce mata tayi planning ba da har maganar haihuwa tana mata wasu lokuta, itama Umma yi tayi kamar batasan zancen ba, duk suka nuna basu man sunayi ba, aiko fad'a suka sha sosai gurin su Abba da Dady, su Momy ba bakin tarewa.... Sannan Abba yace tun da zaman gida suka zaba gashinan sai suyi tayi, in sun so su gyara halinsu in sun so suci gaba duniya ce ta ishi kowa Riga da zane har kallabi idan kanaso, itama Hajja kamar ta ari baci ta zage su tatas su da iyayen nasu, bamai damar tare ko yayi wani yunk'uri uwar masu gida ce... Daga karshe tace zata wuce da Aymana Gwarzo dan ta bata kyakkyawar kulawa dan Fatima bata sonta ga 'yan tsurku gefe (cewa dasu Momy) Abba yace wannan saidai a tambayi mijinta har zata fara jinini a tunanin ta zai hana ne..... Yace su sauka lafia, yanayin yadda yayi maganar alaman ko a kwalar rigarsa, satar kallon sa Aymanan ta take tayi saidai ko kusa bata ga ya damu ba, da gaske kenan ya dena son nata, tab'e Baki itama tayi alaman tafi nono fari..... *************** Har ya kama handle d'in motarsa Hajja ta zabga mishi kira har da gudunta "kaga Ibrahima dan tsaya mana" juyowa yayi tare da cewa "ya akayi matar" fuskarsa a sake, itama sake da fuska tace "Gwarzo nakeso ka kaimu idan an fito masallaci" dan Jim yayi ita kuma ta kafe da ido "yau wai?" Ya jefa mata tambaya... "Ban gane azancin yau ba, kaga in ba zakaje ka fad'an banson iyayi" ta fad'a tana fikifiki da idanu "Sorry maida wuk'ar, Ku zama cikin shiri yanzu zan dawo" daga haka ya juya ya shige motarsa tare da ficewa "dan Iska zanyi maganinka ai" tace tare da komawa ciki tana mitar duk halinsu d'aya 'ya'yansu Zainab da Suwaiba sunyi bak'in gado... Momy kasa zama tayi saikai da komo take a dak'in, Samha na mak'ure kan sofa tana kuka "kin rufe min baki anan ko sai na make ki ne, kamar nina aikeki kiyi abinda kikayi, bayan ko shawara dani bakiyi ba, ke dan Allah tun da kike dani kin tab'a ganin nayi planning? Ko kuma ita Zulaiha kinga tayi planning d'in kuma kina gani duk tana cikin karatun ta haifi Hanif da Husna, kuma ta gama karatun ta lafia ba tare da matsala ba, ka kuma ga 'ya'yanta a hannunta? Amma ke bansan waya baki wannan rub'abbiyar shawara ba" share hawayen idonta tayi "Momy kiyi hak'uri ni kaina ji nake dama banbi shawarar Samiha ba(nifa na rasa gane Wanda ya ba wani shawara a cikinsu? kufa Fans??) itace tace muyi planning kada mu samu matsala a karatun mu, shiyasa na yadda amma yanzu na gane kuskure na gashi Faruuk yayi fushi sosai Momy kila bazai yafemin ba" ta karashe fad'a cikin kuka.... Daga kafad'a Momy tayi duk da deep down tausayin 'yar ne a ranta dan Allah yasan cikin 'ya'yanta tafijin Mu'azzam da Samha a ranta sosai ko don sunfi kama da Abban su ne oho! "Ai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka, ke banda rashin zuciya ma irin taki har yanzu son Faruuk din kike duk da rashin mutunci da tujarar da ya gama yi mana dazu kuma suma su Alhaji suka goya masa baya, cewa fa yayi baki iya komai ba a matsayin ki na mace ai karshen cin fuska kenan, me zakiyi da shi ki bari kawai ya kawo miki takardar ki, kije ki auri wanda yaji zai iya sonki a yadda kike yo dama banda son da kika nace akansa ai kowa yasan ke ba ajinsa bace yaje can ya k'arata .." "Aa Momy wlh inason Faruuk shine dai2 dani, Momy ina matuk'ar k'aunarsa pls Momy ki dena min fatan rabuwa da Faruuk bazan iya rayuwa ba idan bada shi ba" ta katse uwar tare da k'ara volume d'in kukanta, ware ido uwar tayi tare da tab'e baki "lallai kuwa aiki ya sameki saiki yi himma" tace tare da bar mata dak'in gaba d'aya.... "Hajja ce da kanta taje ta d'auko mata trolley kayanta dama komai na ciki, yana dawowa suka d'auki hanya bayan sunyi sallama da mutanen gida, tunda suka d'auki hanya ba mai magana tun Hajja na yi ita d'aya ba mai tanka ta har taja bakinta tayi shiru itama, ba abinda ke tashi cikin motar sai karatun Qur'an, itakam Aymana hadda dan guntun baccinta..... Yana aje su ko gidan bai shiga ba yace zai koma, aiko nan Hajja ta hau bakinta " Dama bak'ar zuciya da bak'in halin da kake gwada mata kenan a gidan shiyasa har yau kuka kasa samun zaman lafia, yo in ba haka taya wannan 'yar karamar tasan yaren zubar da ciki in ba a bak'in halinka ne yayi niyyan tunzurata ba, wlh kadai canja dan wannan ba yi bane" tun da ta fara zuba ya zuba mata ido har sanda ta sauke aya sannan yace shi zai tafi idan ta gama.. Kama baki tayi tare da fad'in "jeka ina nan zaka dawo ka sameni" itama ta shige ta barshi anan Aymanah kam har ta d'an huta.... "Hmmm Yanzu nasan Nina haifeki nasan kin had'iye nonon baki zubar ba, kada ki damu da wani cin maganinsa da barazanar su uban nan Ku, duk ki d'auke su a matsayin busar sharo, aikinki yayi kyau yanzu zamu D'ora daga inda muka tsaya, wannan wata dama ce da aikin mu zai tafi yadda mukeso" umma tace Murmushin mugunta kunshe a fuskarta... Tasowa tayi tare da dafa hannun kujerar da Umma ke zaune "amma ta yaya kike ganin abubuwa zasu zo mana da sauki bayan kina ganin yadda komai ya kwab'e Umma?" "Hmmm! Kedai ki zuba ido kawai kisha kallo ai yanzu kin d'auko hanyar babynah" Itama murmushin ta saki tana wani juye baki gefe "kina nufin kice zan mallaki Ya Mu'azzam na juya shi yadda nikeso?" "More than dis Baby ai har da ubansa da uwarsa sai mun juya wannan karon"............ _lallai mai sonka shike bibiyarka yasan wane hali kake ciki, masoyana nagode sosai da add'u'oinku a gareni, nagode da kulawarku Allah yabar zumunci, maryam Abdul dinku tana muku fatan alkhairi a koda yaushe, Allah yasa mu dace duniya da Lahira..._ *Maryam Yusuf Zango(Ummu khady)* *Bilkisu Hashim(mom zee)* *Bilkisu Zamfara(maman Nana)* *kun kasance wani sashe na rayuwata ina matuk'ar yaba karamci da k'auna irin taku, baki bazai iya fad'ar yadda nike jinku a raina ba, Allah yabar zumumci.....* *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *_Zunubi d'aya shedan yayi Allah (S.W.T) ya Kore shi daga cikin aljannah, zunubi d'aya Annabi Adam (A.S) yayi Allah ya fitar dashi daga cikin aljannah, mu kuma da dinbin zunuban mu muke son shiga cikinta🤔, Allah ka cece mu badan aikin mu ba sai don rahamar ka👏🏻_* Duniya Makaranta✍🏼 *Page* 3⃣9⃣ _______kwance take kan three seaters idanuwanta a lumshe saidai ba bacci take ba, da sassafene sosai dan garin ko gama haske bai ba, tana sanye da kayan bacci Pyjamas pink and white gashinta na cikin net as usual, kaga ganinta kasan tayi nisa cikin tunani........ Fuskarsa take hangowa, murmushin sa, dariyar sa, fushin sa, tsare gidansa, takunsa, iya adonsa, k'amshinsa mai fizgar numfashi, tashi zaune tayi tare da ware idonta gaba d'aya "meke damuna ne wai? Meyasa zan damu dashi har haka?" Ta fad'a a fili... Hannu tasa ta shafo cikin ta, cike da shauki, ya akayi ta rasa gane tana d'auke da cikinsa har sai bayan ta rasa shi? Amma kuma taya zatayi tunanin yin ciki bayan sau d'aya tak suka tab'a had'a makwanci dashi, koda yake hukuncin Allah ne samuwar ciki, duk da taga many changes a tare da ita kamar rashin ganin period nata saita d'auke shi a matsayin tsallaken wata ne, to amma yawan bacci da kasala fa, ga ci kamar gara da kwadayin tsiya amma duk hankalinta bai kawo nan ba, d'an tabe baki tayi tare da cewa "gara ma daya bare ai" tashi tsaye tayi tare da d'ora hannuwa akan kirji tana zagaye falon a duk lokacin zata rufe ido shi take hangowa, me kenan? Kasa samun cikakkiyar nutsuwa tayi wannan ne karo na farko data farajin tanaso ta koma Kano idan ta taho Gwarzo a kwanaki ukun da tayi bata ganshi ba, kodai tana so ta bashi Hak'uri kamar yadda Ammi ta umurce ta shiyasa ta kasa samun nutsuwa (hohoho su Ayma an shigo system🤪). Sake zama tayi tare zama tare da dafe kanta, tunani ta shiga yi tunanin rayuwar su ta baya, tun farkon saninta dashi ta sani tun tana k'aramarta yake mata kwarjini, har koma tsorata ta, tana iya tuna lokacin da take nan Gwarzo gurin Hajja yadda take tsorata ta da kira mata sunansa idan tana kukan banza ko wata barna ko kuma tana rigima, ba zata manta lokacin da take kano ba ko magana take idan yazo gun yanzu jikinta zai d'auki rawa ta kuma rufe bakin kenan, tana tuna yadda yake matuk'ar tsaurara musu da kuma rashin wasa dasu, da yadda yake dukansu idan sukayi laifi, duk da yakan d'au lokaci kafin ya taho k'asar, hakan bai canja komai ba daga halinsa, mace d'aya ce ta sani yake kulawa iya saninta wato Aunty Samiha ita d'in ma bata wasu lokuta yakan murje ido yayi mata halin nasa, to Amma meyasa ita ya bata kyakkyawar kulawa yake nuna mata tsatsan so? Duk da aje shi a matsayin yaudara amma meyasa? Da gaske yanzu tana son jin dalili amma waye zai gaya mata tun da ta hanashi damar haka tun lokacin da yakeson sanar da ita, tunawa da maganganun Amminta tayi... " _Nafi kowa sanin kaunar da Mu'azzam yake miki, nafi kowa sani waye Mu'azzam, sanin da nayi masa ko mahaifiyarsa ba ta sanshi haka ba.....kada ki manta jinin jikinsa ke yawo a jikinki_ karajin maganganun Ammi take ji a kunnuwanta kamar yanzu take yin su, ta sani akwai shakuwa sosai tsakanin Ammin ta da Ya Mu'azzam d'in har mamakin yadda suke fira sosai take da Murmushi da komai, ta kuma San duk rikicin da ake cikin gidan bai tab'a saka bakinsa ba, saima nuna kamar baisan komai ba da yake yi, tabbas Amminta tasan Yayan nasu sosai Amma meyasa ita ta kasa gane komai, meyasa ta kasa yadda dashi, har yanzu ta kasa yadda da sonta yake duk da zuciyarta ta gama yadda da gaskiyar kalamansa da aikinsa, to idan baso bane meyasa zai bata jininsa a dai2 gabatar da zata iya rasa ranta, kuma ai Amminta ba zata tab'a gaya mata k'arya ba....... "Aymanah!" Hajja ta fad'a da k'arfi tana girgizata "ke lafia me kike tunani haka tun dazu inata magana shiru" saurin tattaro nutsuwarta tayi tare da k'ak'alo murmushin yake tana basarwa... "Hajja dan Allah kibar ni zafin nan haka, haba sai kace wacce ta haihu da gaske" tace tana turo baki "yo meye marabin dambe da fad'a kam ai duk ana tare, ke banda ma rashin kunya yarinya ana miki gata kina wani iyayi so nake na kwato maki girma gurin wancen dayan shashashan amma dake kema 'yar uwarsa ce shine kika min iskanci shiyasa ai Fatima ke cinye miki mutumci dan ba laifi kin fitsare kema, dallah ni tashi ko ta gwada miki tsohon kashi yanzu er neman rub'abb'iya kai" sanin halin Hajja yasa ta mik'e tana zumb'ura baki tana gunguni.. "Koma meye kiyi tayi ba abinda za'a fasa eheee"...... ************ " Wash! Umma wlh na gaji wai har yanzu bamu kai ba?" Samiha ta fad'a tana kama k'ugu, gyalen tuni ya dawo a hannu, harara uwar ta balla mata "awoki yarinya keda ake shirin yi miki gata shine zaki fara kiran gajiya, ni kuma da nake zaman zuwar maki kullum nace me kam? Kinga in zaki kama jiki ki kama mu haye wannan dutsen idan ba haka ba kece ciki bani ba, kindai San halin mijinki sarai kinfi kowa sanin shegen taurin kansa da bahagon ra'ayinsa" dutsen ta kalla ta sauke numfashi... "To Umma mu tafi" ta fad'a cikin juriya da daurewa abinku da ajibota duk tayi wata iri da ita 'yar tafiyar da sukayi daga inda sukabar motar su, haka suka haye dutsin sai a sannan suka hango 'yar bukkar ta mai gobe da nisa, hakan ne ya kara ma Samiha k'arfin tafiyar..... Tun da ya d'ora idanunsa akan Samihar yaji yawunsa sun tsinke sai wani shu'umin kallo yake binta dashi, itakam wani abin kyankyami take ganinsa Sam baida kamar kwarai sai wani kauda kai take har suka gama maganar su da Umma, anan yace mata ta jirasu a waje zai had'a mata wasu magunguna a jikinta, cikin jin dad'in hakan su zai cimma ruwa Umman ta fita ta jira su waje, tana fita ya fara matsawa kusa da ita itama kuma tana ganin haka ta fara ja da baya cikin tsoro, tsawa ya daka mata... "Ke! Ki nutsu anan ba'a yiwa aljanu gardama kika kara matsawa daga nan fushin Aljani dan tsirku zai sauka a kanki kibi duniya, ki godemin tunda har kika kasance cikin masu sa'a Aljani dan tsurku ya yaba dake yace zaiyi miki aiki da kansa akan mijinki, amma dole sai kin bamu had'in kai hhhhhhhhhhhhh" ya kece da wata mahaukaciyar dariya... Haka dai ba imani ba tsoron Allah ya samu ya tumurmuje ta yadda ransa yake so ba tare da wata soyayya ko lallab'awa ba, aiko ta gayawa 'yan garinsu ga azababben warin jikinsa kadai ya isheta, sannan ya gargad'eta ta yadda ta gayama wani koda uwarta ne aikinta ya rushe, umurnin gyara jikinta ya bata sannan yace ta kira masa uwarta, bayan tazo ne ya shaida mata zasu ci gaba da zuwa na tsawon mako ana mata wanka da magunguna, zare ido Samiha tayi kirjinta kamar yayi tsalle ya diro k'asa tsabar kad'uwa fad'i take a ranta shikenan tata ta kare kuma(hmm ai baki ga komai bama tun da kika zabi hanyar sabawa mahaliccin mafi munin sabo a matsayin hanya mai b'ullewa, Ya waduud kayi mana tsari da tsarewarka ka karemu da kariyarka da rud'in Shed'an da kuma na zuciya Ameen) A hanya taji kamar ta fad'awa uwar ta abinda ya faru sai kuma ta tuna da gargad'in bokan dole ta kama bakinta saidai kam tasan ta banu ta kuma kad'e har ganye, saidai tunawa da mallakar Mu'azzam da zatayi ta juya shi yadda takeso yasa taji zata jure duk wuya har taga ta cimma burinta.... Da Hafiz suka fara cin karo shima isowarsa kenan, da kallon mamaki ya bisu "Umma daga ina haka da tsakar ranar nan?" Harara ta watsa masa "Daga inda ka aikemu sallamamme, wlh Hafiz ka kiyayi ranar da zan juyo kanka zakasan baka da wayau" daga haka taja hannun Samiha sukayi ciki suka barshi anan tsaye, dafe kansa yayi Umma na bashi ciwon kai a rayuwa Sam baya k'aunar Hallayarta gashi tana so ta kashewa Samihar aure tunda ta koya mata komai ta iya, yasha zaunar da ita yayi mata fad'a da nasiha akan ta dena miyagun halayen da take musamman ma da tayi aure yana jin zafi sosai a ransa game da ita da mahaifiyarsu gashi ba halin yace ya gaya musu gaskiya Abu ya zama dan zane shiyasa da yayi aure ya d'auke k'aramar k'anwar su Sageera ya mayar inda yake da sunan yana so ta zauna tare dashi amma a ransa ya d'oketa ne kawai kada itama halayen uwar suyi tasiri a kanta kamar yadda sukayi akan Samiha.. Gashi 'yan kwanakin nan ta matsanta masa akan Nusaiba tace ya zama sallamamme bawan mace ko kishin 'yar uwarsa bayayi yadda d'an uwan Nusaibar ke gasata amma shi ya koma a gindinta ya tare sai abinda tace ko laifin ta baya fad'a shiko har ga Allah baida matsala da Nusaiba dan ta na nutsuwa da sanin ya kamata ko sab'ani ne suka samu suke sasanta kansu tana matuk'ar kokari wajen kula dashi da Sageera gaba daya Sam bata nuna masa wani banzan hali ba, kuma ai su duka *Zuri'a d'aya* asali daya to meye na wani bambanta wa a tsakaninsu, kuma ma ai duk abinda Mu'azzam keyi akan gaskiyarsa yake, sune basu da gaskiya kuma sun kasa yadda bare su nemi hanyar sulhu..... B'angaren Momy kam abubuwa sun gama dame mata sosai ga matsalar Samha gata Mu'azzam abubuwa su had'e mata goma da ashirin, ga Samhar kullum cikin kuka duk ta fita hayyacin ta, dole ta dawo rarrashinta da bata baki, Mu'azzam kam ta kasa gane inda ya dosa duk da daurewa kawai take tana share shi da d'auke masa a kai a tunanin ta hakan zai sa ya dawo yayi abinda takeso, bangaren Abba ma ba dama ya bawa iska ajiyarsu, har kunyar Suwaiba takeji idan tana ganin Samiha a gidan duk da cewa laifi sukayi, shiyasa ma ta kasa samun ta suyi magana tsayayya, duk da dai cikin ranta baso take ba, Fatima kam gani take tafi kowa farinciki da abinda da ya faru da 'ya'yansu, amma take wani munafurki, maganinta zatayi daga ita har 'yar tata da Uwar mijin tasu gaba d'aya.... Mu'azzam ma b'angarensa a jigace yake abubuwa sun taru a kansa, sunyi masa over ga hukuncin shariya wa Aymanah daya d'aukarwa kansa, Wanda yake ganin shine best solution a gareshi duk da gangar jiki da Ruhi sun jigatu, ga shariyar da Momy ke masa duk akan Samiha shikam yarinyar ta gama sire masa akai gaba d'aya ko zaici gaba da zama da ita to sai ya tabbatar ta gyara halayyar ta.... Shiru-shiru har sati ba Mu'azzam ba labarin sa a Gwarzo, zuwa yanzu Aymana ta gama yaddar ma kanta son Yayan nata ne ke d'awainiya da ita, saidai it too late to cry, tun da yanzu bata gabansa ya barta kamar yadda ya fad'a ta kuma san yana magana ne da iya gaskiyar sa, lallai tawa kanta bak'ar dabara yanzu ya tayi dan son bada wasa yake yawo a jininta ba, duk tsayuwar motar da taji saita ringa tunanin shine saidai taga Su Abba kosu ya Adnan ko kuma mutanen Bauchi, kullum cikin tunani take wani sa'in hadda kwallarta saidai tana kiyaye idanun Hajja... Abinda bata sani ba Hajjar ta dad'e da sanin halin da take ciki tadai yi mata banza ne taga iya gudun ruwanta tun da boko take mata, tadai dage da tsimata da gyarata da irin tasu dabarar ta tsofaffi........ Hajiya Samiha an zama 'yar hannu manyan customan bokaye kenan, haka ta cika satin ta tana zuwa wani katon kawai yana morar ta son ransa, fitarsu kullum yasa Dady yin magana akan yawon tace gurin koyon girki suke zuwa tun da ance sai sun iya girki za'a zauna dasu cikin gatse tayi masa maganar saboda yadda ya Saki baki akaci musu mutunci a taron, amsawa yayi da cewa yadai fi musu badan kanta kodon 'yarta, wucewa tayi tana Murmushin keta "zakuci gidanku ne Ku duka dan har kai saina kara jaddada rikon ka dan naga ka samu sassauci"..... Sati na cika Boka mai gobe da nisa ya bawa Samiha wani tandun kwalli yace ta shafa shi ta tabbatar sunyi ido biyu da Mu'azzam at any cost daga nan taja linzaminsa har ya kusanceta dariya ya sheke da ita sannan yace " badai shi ba saidai wani zata juya shi fiye da yadda ake juya waina" sannan ya basu wasu layu, yace ta binne cikin gidansu can tsakiyar dare to ta gama da duk wani mai magana ta rufe bakin kowa, a ranar sun dawo gida cike da farinciki Mara misaltuwa.... Washe gari suka shirya zasu fara gudanar da aikinsu wanka ta d'auka na fitar hankali ta rambad'a kwallinta sannan ta kirasa a waya, duk da yayi mamakin ganin kiranta dan shi rabonsa da ita tun ranar da akayi taron, da kamar bazai daga ba sai kuma yaga rashin dacewar haka, tun da har yanzu a matsayin matarsa take..... Lankwashe murya tayi cike da kad'ayi tace masa dan Allah tana so ta ganshi da akwai maganar da takeso suyi mai muhimmanci, yanda tayi wani sanyi tana rokonsa sai ta bashi tausayi hakan yasa yace ta same shi a dak'in sa nada yana gidan...... Dan wasu lokuta a gidan yake zuwa yayi zamansa idan ya tashi daga office Ammi kawai ta sani dake ita ke bashi abinci, koda ta kirashi yana kan sallaya ya gama sallah yana karatun alqur-an mai girma.... Tsalle ta dama tare da fad'in "yes!" Da k'arfi taje ta labartawa uwarta yadda sukayi, itama cike da murna tace tayi sauri taje ta kuma tabbatar tayi komai yadda ya dace......... Da sauri ta fice tana fad'in "kamar kina Zaune Ummana"........ 😭😭😭 _Allah ka tsare bayinka da sharrin shihiri_ *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *_Idan kana sallar dare kada ka rena masu bacci, akwai da yawa 'yan aljannah wadanda an fisu Aiki, da tsarkin zuciya suke kere mutane, mu tsarkake zukatan mu.👌🏻_* Duniya Makaranta✍🏼 *Page* 4⃣0⃣ _______banke k'ofar tayi bako sallama ta fad'a, tana fad'in "Where r u my heart beat? I really missing u Yaya" cikin wata irin muryar mai cike da kissa da shagwab'a dan tasan yana son Shagwab'ar.... Ci gaba da karatunsa yayi saidai zuciyarsa sai wani mugun harbawa take da sauri-sauri, ga fad'uwar gaba na musamman da taji lokacin da ta shigo, hakan yaji kawai bai yadda da ita ba, saida yakai inda yake buk'atar tsayawa sannan ya rufe Qur'anin tare da rungumesa a k'irjinsa yana kwararo addu'o'i, sosai yaji nutsuwa ta saukar masa ( 'yan uwa sihiri gaskiya ne saidai yana tasiri ne da izinin Allah, kamar yadda addu'a ta kasance takobin mumini, nasan wasu zasuce ta yaya duk akayi ma su Mu'azzam sihiri baya kamasu, bayan ya tab'a kama mafificin mafifita sayyidina rasulillah, to abinda nakeso ku fahimta sihirin da akayi Manzon mu ya kuma kamasa wata aya ce Allah ya saukar mana kuma ya buga misali akan mafi soyuwa agare shi domin ya tabbatar mana da sihiri gaskiya bawai dan sun isa ko sun kai suyi masa sihirin ba sai dan kafa aya agaremu Al'ummar sa, saidai ku sani kamar yadda sihiri yake gaskiya haka ma Addu'a gaskiya ce kuma takobin Mumini kuma duk wanda ya riketa a rayuwar sa yafi karfin mutum bare aljan, koda kuwa anyi nasarar galaba akansa tabbas zai karye ba da dad'ewa ba muddin ya rike addu'a Allah ya bamu ikon riko da addu'a ya tsare mana imanin mu da mutuncin mu, ya kare mu da sharrin masu sharri da hasadar masu hasada ameen). "Haba dear nah, bayan kace nazo shine ka wani shanya ni anan, pls kayi hak'uri ka dena fushin wlh bazan k'ara ba...." "Enough..ni bana fushi dake, kece kika shigo bako sallama kamar ba musulma ba, kuma ai isko ina karatu ko?" "Afuwan Yaya mantawa nayi" tace tare da komawa tayi sallama, amsawa yayi ba tare daya d'ago ba, zuwa tayi dab dashi ta zaune tare da kamo hannunsa ta saka cikin nata sai bin shi da kallo tace tana wani murmushi "Yaya!" Ta kirashi cikin wata irin murya... "Ina jinki meke tafe dake wata irin magana ce?" "Haba yaya ko kallona fa bakayi ba alaman har yanzu fushi kake dani.." Ta sake fad'a cikin kirsa da jan hankali..... ***************** Yau kam ta kai mak'ura gurin dauriya, yanzu ta gama tabbatar wa kanta son yayan nata ya jima tare da ita, sai yanzu take gasgata maganganun Nusee da take cewa wlh tana son yayanta dashi kansa da yake cewa tana sonsa tadai kasa ganewa ne, saboda son hukunta shi akan laifinsa da ta saka a gaba... Tabbas yanzu ta gama gasgatawa gashi shi ya manta da ita ko waya bai tab'a yi mata ba, bare yazo har kiransa tayi bai daga ba, kanta ya d'au zafi dama Ashe haka so yake da zafi? Ashe kenan ba son Uncle Salman tayi ba a baya, girmama shi kawai take yanzu ne tasan ainihin meye so, gashi kuma da zafin ta fara, Ashe haka Ya Mu'azzam d'in ta ke azabtuwa a lokutan baya lallai bata kyauta masa ba.. Wayar ta d'auka tare sake danna masa kira, inda tuni ya tashi daga Mugu zuwa my Khaleel saidai har ta tsinke bai d'aga ba, fashewa tayi da kuka tare da cillar da wayar, kusa kanta tayi cikin filo taci gaba da rera kukanta.... Hajja dake jikin labulen d'akin tun dazu tana kallon wainar da take toyawa, shigowa d'akin tayi tana salallami tana tafa hannu "me zan gani 'yar nan me aka miki kike kuka da farar safiyar nan" ta gaji da b'oyewa Hajja, muddin bata fad'i damuwar ta tana iya kamuwa da ciwo, fad'awa jikin Hajjar tayi tare daci gaba da rera kukanta... "Oh ni Balkisu diyar Mamman! Kinga 'yar marainiyar Allah dena kukan nan idan baso kike na kama maki ba, ki gayamin menene?" Dak'yar ta iya tsagaita kukan cikin shessheka tace "Hajja Ya Mu....Mu....Mu'azzam" "Subhanallah! Meya samu Ibrahiman?" Ta tambaya a dan rikice.. "Ba shine inata kiransa na bashi hak'uri ba baya d'auka" Dan turata tayi "yo hak'urin me zaki bashi me kikayi masa, dama akan yaki d'aukar wayarki ne kike wannan kukan? Dallah kyale shi can da yawarsa wani tsolami dashi awa rama".... Ganin Hajja na k'ara cunkusa mata zuciya yasa ta k'ara fashewa da kuka " yo meye kuma? Ina nan zai zo ya same mu, ai kina nan ba inda zaki muddin baizo ba" Hajjar ta k'ara fad'a.. "Kina gani fa tun da ya kawo mu ko bai sake zuwa ba har yau kuma baya min waya, nima inna kirasa baya dagawa" ta sake fad'a cikin kukan..... "To shine meye, kema ki sharesa basai ki dena kiran ba kema, duk ranar da ya gama tambad'ar sa ya iskoki" baki ta sake barewa dake Aymanan gwana ce gurin kuka, ta wani lufcewa Hajja kamar wata Fadeela ko Arif...... "Nidai inaso na ganshi Hajja, inaso muje kano, gidana nakeso na koma" sake baki Hajjar tayi, tana kallonta kafin ta iya cewa "kece da bakinki kike cewa ki koma gidansa, Ibrahim fa, dodonki? Naga kuma bakya sonsa?" Ai batasan lokacin da tace... "Hajja wlh ina sonsa nidai ki tashi ki shirya muje yanzu na ganshi Dan Allah Hajja" Jim Hajjar tayi tana nazarinta, kafin ta gyara Zamanta sosai tana fuskantar Aymanar.... Hannun ta biyu ta kama tare da kiran sunanta cikin serious "Bilkisu" dago idanunta tayi da suke shagab da hawaye tace "Na'am Hajja" "Nina hana Ibrahim zuwa wajenki" ware ido tayi "meyasa Hajja?" "Lokacin da na fahimci akwai sab'ani tsakaninki da Ibrahim, gashi har hakan na neman ya shafi dangartakar ki da Mahaifiyar ki, saina kira Ibrahim don nasan ainihin meye matsalar ku, duk da yaso ya boyemin yana Neman kareki saina fito masa ta bayan gida nayi amfani da girme masa da nayi har naji komai daga bakinsa, anan ne na fahimci kece mai matsalar duk da dole ayi miki uzuri a yanayin yadda shi Ibrahim d'in ya girmar dake da tsoronsa Wanda yayi hakane bawai don baya sonki ba, ni sheda ce akan son da Ibrahim ke Miki dan a gabana akayi komai a can baya".... " kamar yadda nasan kyakkyawar alak'al da ke tsakanin Amminki da Ibrahim, a lokacin kina karama kin fiye kuka da rashin ji ga barna, gashi bakijin rarrashi, ranar kina yi Ibrahim yazo Hutu ya kawomin ziyara kinsan dai dama can keda shine mutane na, lokacin kina hannuna kinata kuka akayi rarrashin duniyar nan kika ki shiru, Ibrahim kuma bayason kuka gashi da zuciya sai ya daka maki tsawa, kika tsorace tare da yin shiru tun lokacin kika shiga tsoronsa ko banna kike Dana kira miki sunan shi to zaki dena" Murmushi Aymana ta saki tana tuno wasu daga childhood nata... "Da wannan tsoron nasa kika girma wanda har kika koma gun iyayenki dashi, kamar yadda kika sani Ibrahim nada zuciya da rashin son reni shiyasa baya sake muku a gidan, kuma idan kin kula bai faye zama ma a k'asar ba a lokacin, to yanayin Zaman gidan ku ne yasa bayason zama dan Sam abin baya mishi dadi, sau da dama idan yazo yana min k'orafi akan rikicin cikin gidan da yaki k'arewa, kin San shi bamai surutu bane kamar ke, baya fad'amin anihin abinda ke faruwa saidai yaita cewa cikin gidan nan na buk'atar gyara kullum korafin sa yaushe gidan zai dawo gidan zaman lafiya kamar ko wace zuria yaushe zasu dunk'ule su zama *Zuri'a d'aya* tsintsiya d'aya.." Sake kama hannunta tayi "Bilkisu Ibrahim bai tab'a zama dani yace min yana sonki ba saidai na Dade da fahimtar yana sonki tun kan maganar aurenku ta taso Wanda shine burin mu, burin duk wani mai k'aunar ku, na shiga fargaba lokacin da kika zabi yaron nan Salman kika bar Ibrahim, na kuma godewa Allah daya amsa Addu'ata ya sauya lamarin zuwa ga Ibrahim, tunda ya bani labarin matsalar na fahimci kamar kina sonsa a bayanin amma saboda yadda ya d'au zafi akan wannan maganar da kika gaya mishi a ranar sai maimaita yake yace shi ya d'auka kina sonsa kawai dai kina masa ne a matsayin ramakon abinda yayi miki a baya amma yanzu ya fahimci ba kya k'aunarsa yaudarar kansa yake, yanda ya shiga tashin hankali ne yasa naga ya dace mu gwada ki mu gane gaskiya shiyasa na bullo da wannan dabarar" Kama hannun Hajja itama tayi sosai ta runtse a nata "nagode Hajja, ina Alfahari dake, Madallah da hangen nesar ki Hajja ta, kin tsamoni daga bakin kogon da na saka kaina a kuruciya irin tawa, Madallah da Miji mai nagarta kamar Ya Mu'azzam, Hajja na fahimci ya Mu'azzam a baubauce, amma yanzu na gane komai kuma inason Mijina" ta k'arashe tana saka tafukan hannayen ta ta rufe fuskarta.... "Ho d'an 'yar nema duk kin wani rikicewa mutane da kuka da farar safiyar nan, Ashe kina son mijin nawa kika barshi yana ta walagigi ni da har nace inku duka bakwayi ni sai mu jone da abina" ta fad'a tana dariya, itama dariyar take tare da mik'ewa ta shige toilet da gudu ita nan kunya..... Momy dake tsaye balcony da zai sadata DQ sashen Umma tana amsa waya, ganin Samiha kawai tayi ta wuce da gudu ta gabanta tana kuka saidai da alama bata kula da ita ba, saurin sallama tayi da k'anwar tata da suke waya tabi bayanta daman Sasan su zata gurin Umma su tattauna matsalar su..... "Ke lafiyar ki na ganki haka kin dawo min da kuka ina Mu'azzam d'in?" "Umma ya Mu'azzam ya b'ata mana shiri, ya lalata komai Umma wahala ta, wahalar sati d'aya duk ya rusa ta" tsawa uwar ta daka mata "ke dallah malama fitomin a mutum kiyimin baya ni bana fahimtar wannan yaren da kike yi" Umma ta fad'a rai a bace.. Nan ta shiga zayyana wa Uwar yadda sukayi dashi "Umma duk yadda nake k'ok'arin ganin munyi ido biyu dashi yaki bani damar, ganin wannan bai samu ba naso nayi amfani da kissata, shine daga k'arshe ya tureni tare da ficewa ya barni a dak'in" ta fad'a cikin kuka.... "Ga d'an kazar, kazar can" Umma ta d'uro ashar cikin takaici da bacin rai, Momy dake lab'e bakin k'ofar rawa jikinta ya kwasa ta kasa gasgata me kunnenta ke jiyo mata, wacce ta kawo kenan zata shiga ta fara jin zancen su jiyo sunan d'an ta ne ya tilasta ta dakatawa, taji me ke shirin faruwa a inda bata tsammani....... "Shi dan ubansa dan yakai tsohon Shege, ni zai b'atawa plan, wlh yayi kad'an ko Uwarsa bata isa ba bare shi d'anta, shi d'in me? Kayan tsiya banza, bacin ma ke da kika nace masa me za'ayi da wannan dan iskan yaro da bai da mutunci, ko Uwarsa bai rage ma ba" dafa 'yar tayi.... "Share hawayen ki baby wlh bai isa ba, dolensa ya dawo k'arkashin mu daga shi har iyayensa, da tsinanniyar matarsa har Uwarta da Munafukar kakar ku wlh ba Wanda ya isa ya dakatar dani wannan karon yadda na kwashe shekaru ina tsara abubuwa dole ne, dole ne wannan karon na Mulki ahalin Sa'eed Gwarzo kamar yadda naci buri tun baya dole na cika burina duk Wanda ya yi niyyan shiga tsakanina da burina zan iya saka a kashemin shi har lahira" duk ta wani firgice kamar wata kamun aljanu sai sambatu take. "Dota ki koyawa kanki cire son wannan yaron nan a zuciyar ki, dan muddin yaci gaba da shiga tsakanina da burina Wlh saina saka an kashe shi" zaro ido Samiha tayi tana girgiza kai a firgice ta tsorata da yanayin uwar tata musamman kalamanta akan na karshe "Aa Umma dan Allah kada kisa a kashe shi wlh ina sonsa..." Momy saurin sa hannu tayi ta toshe bakinta, saurin barin gurin tayi cike da kad'uwa har wani dishi-dishi take gani, ikon Allah ne kad'ai ya kaita sashen ta, tayi Sa'a ba kowa parlon hakan yasa tayi saurin Shigewa dak'i. Jagab ta zub'e kan gado, tare da tallabe hab'arta da duka hannayenta wasu zazafan hawaye ne suka shiga sauko mata a kumatu..... Lallai mutum abin tsoro ne, mutum bashi da Arha, mutum mugun icce, Ashe dariya baso ne ba, lallai wannan shine makashinka yana nan tare dakai "Suwaiba....wai Suwaiba.." Ta fad'a a fili........... _dama ai ba duka mai yi maka dariya ne mai sonka ba kamar yadda ba duka mai d'aure maka fuska ne mai k'inka ba, Allah ka raba mu da masu fuska biyu🙅🏽‍♀😢_ *Tau 'yan uwa anan zan d'an dakata da rubuta littafin Zuri'a D'aya, saboda shigowar wad'annan kwanaki masu albarka, inshaa Allah, zanci bayan sallah idan mai kowa mai komai ya gwada mana da rai da lafiya, Allah ya bamu ikon yin ibada da dacewa a cikin wadannan kwanakin masu albarka🤲🏻* Saduwar alkhairi🤚🏻 *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* 🕋🕌 *_Takabbalallahu minnah wa minkum, eid el-Mubarak Alainah wa alaikum🤲🏻 Ina taya d'aukacin musulmin duniya murnar Babbar sallah, Allah ya karbi ibadun mu, ya kuma maimaita mana Ameen🤗 EID KABEER_* 🕋🕌 _Tau friends Malam yazo sallah tazo muja😅 muje zuwa a dasa daga Inda ka tsaya⛹🏽‍♀⛹🏽‍♀🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀🤪_ *Page* 4⃣1⃣ _____Zaune take gaban mirror tana shafe-shafenta, sai murmushi take zubawa ita d'ayan ta, jinta take kamar wata sabuwar halitta wani irin shaukin k'auna dake d'ibanta, tana tuna wasu moment back da sukayi spending, sai yanzu take jin shauki game dasu, lallai Yayan nata ya dad'e da samun gurbi a zuciyar ta, itace dai bata fahimci hakan ba sai yanzu, hango wautar da ta tafka take tana jin rashin kyautawa a gareshi, taga jarumtar sa sosai sosai, a yadda tayi treating nasa but bai gajiya ba, a fili tace "so d'aya tak naka ne kai d'aya Yayana u deserve it! I so much love you yaya" hannun ta na dama na daidai saitin zuciyar ta, tana jiyo yadda take zillo cike da shaukin sonsa, fuskarsa kawai take hangowa, idanuwanta a lumshe....Sam bata ji turo k'ofar ba, sai muryar Hajja data tsinta tana mata magana..... "Har yanzu baki gama shiryawa ba ne kam, kefa ake jira gashi ko kari bakiyi ba" ware idanunta tayi a hankali a kan Hajja dake ta zuba, ta zo ta wani katse mata jindadi... "Hajja yanzu zan fito shiryawa nake, amma wani abin ne?" "Kedai ki fito yanzu, ko meye zaki gani" daga haka ta fice tare da ja mata kofar...... Shiryawa tayi cikin sauri dan tasan halin Hajja sarai and at dat point batason bata mata rai cos ta faranta mata nata ran... Wasu mata ta samu a falon su biyu, ga manyan ledodi a gabansu, gaisawa sukayi a mutunci sannan ta wuce dinning ta fara break fast d'in ta, hankali kwance.. Hajja ce ta, ta fito ta gabatar mata dasu akan zasu yi mata gyaran jiki da kitso da lalle, bata yi mamaki ba Dan yadda Hajja ta dage tun zuwanta tana gyarata sai kace wata sabuwar amarya tasan za'ayi haka, itama hakan yayi mata dad'i cos tasan dan Yayanta akeyi, haka suka kwashe wuni guda cur gurin gyarata aiko tuni ta d'auki sheki sai kace zarah cikin taurari, damuwar ta d'aya ce a yanzu wato *Rikicin cikin gidan su* ko yaushe zai k'are ne? Ko yaushe uwar mijinta zata sota? Ko yaushe zasu zamu zaman lafia a cikin zuri'ar su ne, yaushe zasu zamo *Zuri'a D'aya* tsintsiya d'aya su kasance happy Family abun sha'awa? Waye zai haskaka musu hanya? "Allah ne! Allah ka azurtamu da samun zaman lafia cikakken a wannan Zuri'ah tamu" ta fad'a a fili. ******** Tun da ya samu ya turata, ficewa yayi daga gidan gaba d'aya, ransa a matukar bace, ita batasan yadda yakeji game da ita har yanzu ba, shiyasa har ta samu damar zuwar masa da wannan shiriri tar, batasan ta gama fice masa arai ba me zaiyi da mace irin ta me matukar son kai da rashin kunya, ko kunyar k'aryata a gaban iyayensu bata ji ba, duk da abinda sukayi masa, shifa ko Samhar haushi take basa shiyasa ko tausayin ta baya ji..... siririn tsaki yaja tare da dukan sitiyari "mata! Mata!! Sai Allah". Direct gidansa ya wuce, haka kawai ya samu kansa da son zuwa part din Aymanah, yana nan tsaf kamar yadda ta barshi saidai 'yar kura da yayi na rashin sharar da bai samu ba, bedroom d'in ta ya shiga, shima Tsaf sai kurar, sip nata ya bud'e tana bin kayanta da kallo tunawa kawai take da zaman watanni biyar da sukayi na aure, first night d'in su ya tuna, tsintar kansa yayi cikin nishad'i sai smiling yake, juyowa yayi ya kalli bed din kamar yanzu abin ya faru yake imaging, lumshe ido yayi cike da shauk'i "Why Aymanah..why, meyasa ba zaki manta komai ba, Ashe ba zaki yafewa yayanki ba mai matukar k'aunarki, u mean everything to me, I mean it everything" ya fad'a yana dafe gefen heart nasa da hannunsa..... ❤ _Hehehehe anfa zo gun😍 #Team MuzAymah#_ 😘... ******** Zafafan hawaye ke kwaranya daga idanun Momy, Wanda ba zata tuna when last tayi kuka ba, tun rasuwar mahaifinta in zata tuna(lokacin haihuwar Adeel) a rayuwa tana da saurin sabo da saurin yadda da mutane amma ta tsani fuska biyu, jin zuciyar ta take kamar ta cireta ta yasar ta huta, meyasa ta kasa ganewa, duk tsawon lokacin nan yaudarar ta Suwaiba keyi, matar da ta d'auka kamar k'anwar jinin jikinta, take sonta fiye da k'anninta Ashe ita ba haka bane a ranta, lallai duniya ba tabbas mutum abin tsoro.... Ta d'ade a gurin tana kuka sosai kamar wata k'aramar yarinya, turo k'ofar da akayi ne, yasa ta saurin share hawayenta da gefen, amma tuni wacce take boyewa ta gani, hakan ya k'ara tayar mata da hankali, cikin sassarfa ta karasa gaban gadon tare rage tsawonta "Momy kuka kikeyi, wayyo Momy menene ya faru meya sameki? Momy akai nane koh?" Murmushin k'arfin hali ta saki "Aa Samha ba abinda ya faru ba kuka Nike ba, Abu ne ya shigar min a ido shine ya sakani hawaye, taso zo nan kinji kada ki damu" rungume ta tayi tana jin rashin kyautawar ta akan 'ya'yanta for d first time, tasan kome Samha tayi itace sila, tana godewa Allah daya saka sauran basu d'auki hud'ubar ta, lallai Allah na k'aunarta da rahama... Rabata da jikinta tayi sannan ta mik'e "bari inje gurin Abbanku, nasan ya dawo zuwa yanzu, su Adeel sun dawo daga Islamiya?" Girgiza mata kai tayi alaman eh "tau ki jeki ki taimaka wa su Fadeela su cire uniform" "Tau Momy" ta amsa wacce ta gama dawowa wata kalar tausayi duk ta fige tayi bak'i. Abba na zaune kan 2seat yana duba wasu takardu dake d'auke da record na monthly budget nasu da Hafiz ya kawo masa, Momy tayi Sallama, amsawa yayi tare da ajiye takardun ya tattaro hankalinsa gareta yaji dame tazo yasan dai bazai wuce k'orafi ba kamar kullum.. Guri ta samu ta zauna tare da gaida shi a darare, amsawa tayi yana nazarin yanayin ta na d'an lokaci "Zainab yadai na ganki wata iriya ko baki da lafia ne?" "Kusan haka, amma ba haka bane, Alfarma nazo nema gurinka kuma inada tabbacin samu dan ka kai matuka gurin adalci, kamilin mijina" murmushi ya saki, wai Zainab ce yau ke kiransa adili lallai akwai babbar bukata a tare da ita, bata izinin gabatar wa tayi kai tsaye Dan shi kanshi ya k'agu yaji menene ke tafe da ita.... "Alhaji dan Allah meeting nakeso ka kira, general meeting ina nufin kowa da kowa daya shafi wannan Zuri'ar inaso zan gabatar da wani muhummin Abu Wanda nake tunanin zai kawo maslaha a wannan family, inshaa Allah, rikicin cikin gida zai kare, Dan Allah kamin wannan alfarmar" ta karasa fada da raunin zuciyarta a matukar karye... Ya d'ade Jim kafin ya samu damar magana yana auna maganganunta da kuma yanayin Wanda tun shigowarta ya fuskanci a sanyaye take sosai, tome ne ya faru da ita kuma me zata gabatar??? Kasa daurewa yayi "meya faru ne kam, meye zaki gabatar?" Rausayar da kai tayi "kayi hakuri Alhaji gobe inshaa Allah zakaji komai, nidai kamin alfarmar gayyato kowa, nima yanzu zan kira mijin Zulai" "OK ba damuwa Allah ya kaimu goben" godiya tayi masa sannan ta fice, binta da kallo yayi yana mamakin sauyin ta, sharewa yayi yana tsumayen goben yaji menene kam. Dady ya fara kira ya tabbatar mai dama gobe yake shirin shigowa, sannan ya kira Hajja, wacce itama zasu shigo goben, yace Adnan zai zo ya d'aukesu da safe, sannan yabi sauran yaran ya sanar da su.... *10:00am....* Kowa ya gama hallara har Zulaiha wacce ta biyo jirgi dan jin kiran gaggawar, su Hajja ma sun iso, Mu'azzam ne ya shigo last sannan aka bud'e taro da addu'a, Abba ya gabatar musu musabbabin taron sannan aka bawa momy damar magana... Sosai ta b'oye feeling d'inta bata nunawa Umma komai ba, guri d'aya suka zauna kamar kullum... Gyaran murya tayi "Dama game da Suwaiba ne...." Sannan ta fara lissafo duk abinda ta jiyo da kunnenta, tsaf cikin dakewa, kusan kowa ya falon Hankalin sa ya gama tashi inka cire ita Ummar da take zabga murmushi duk da ta tsorata sosai, saidai da yake er duniya ce sai ta maze "Haba Momy Yanzu akan d'an wancen abun daya faru a tsakanin mu shine zaki bullo min tanan me yayi zafi haka, hadda tara ahali haka, gaskiya baki kyautan ba, Dan Allah kuyi hakuri jama'a dan sab'ani ne a tsakanin mu, bacin rai ne ya sakata furta haka, a gaban kowa afuwan da b'ata muku time da akayi kowa zai iya tafiyarsa sabgarsa zamu sasanta kanmu" Da kallo mamaki Momy ta bita sannan kuma ta saki murmushi tare da zaro wayarta wadda tayi record din duk abinda sukayi jiya... "Dama nasan makircin zaifi haka, shiyasa na tanadi wannan Dan gudun haka" ta danna playing d'in recording din.... Salati Hajja ta d'auka tana tafa hannuwa, soke kai Dady yayi, haka ma Hafiz hadda hawayensa, mamaki sosai bayyane a fuskar sauran ahalin... Zuface ce ta shiga ketowa Umma ta ko'ina duk da sanyin Ac din da ya wadatu a falon, sai zare ido take, kunya kamar a nutse a gun....... _Dakyau🤷🏼‍♀ in kayi dakyau zaka ga dakyau, dama ramin karya kurarrene🤣_ *My lovely friends, ga goron Sallar Ku nan, nima ina jiran nawa dana Aymanah, and ur Samiha 😝* *Meryerm Abdool* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *Watanni tara kayi a cikinta🤰🏻Shekaru uku kana rungume a kirjinta🤱🏽tsawon rayuwarta kana zaune daram a zuciyar ta❤, Uwa kenan, Uwa da babu irinta🧕🏻 mu daraja iyayen mu domin babu kamar su a rayuwar mu😄* Duniya Makaranta✍🏼 *Page* 4⃣2⃣ _________Samiha kan dank'arewa a gun da take tayi tun lokacin da Momy ta fara magana har zuwa barazanar Ummanta, hankalin ya mugun tashi jin playing audio da Momy tayi ga maganar ta dana Ummanta tiryen-tiryen ba gurin gudu bare tsira jikinta rawa yake kamar mazari, ji take ina ma kasa ta bud'e ta shige tsabar tozarci da kunya da takejin ta gama lullub'eta... Mu'azzam bai wani mamaki sosai ba dama tun ba yau ba yake suspecting Umma akan tashin hankalin gidan duk da baya mayar da kai akan lamarin gidan yad'an fahimci she's after all what his Momy done, Aurensa da Samiha kuma ya kara tabbatar masa da hakan dan yasan duk wani abu da Samihar keyi hud'uhar uwarta ce, shiyasa jiya kwata-kwata ya kasa yadda da ita duk da baisan suna shige-shige ya d'auka a makirci kadai suka tsaya Ashe abin yafi a nan, yanzu meye amfanin wannan tozarcin a gaban kowa, shi tsoron sa d'aya kar aje gurin tone tone abin ya dawo har da Momyn su dan yafi kowa sanin yadda ta gama yadda da Umma kuma duk abinda tace tayi aikatawa take ba bincike shiyasa take ta turata tana kwaba suka kasa samun zaman lafia a cikin gidan kullum sai rikici yaki karewa.... D'ago kai Dady yayi da idanuwan sa da suka gama rinewa zuwa ja tsabar bacin rai da kunya "Hajja nayi Dana sani wlh nayi nadamar auren Suwaiba a rayuwa, Yaya kana jin me Suwaiba tayi? Yaya nayi turr da auren Suwaiba, ta cutar dani ta cutar da dangina ta cutar da 'ya'yanta ta kuma cuci karan kanta, Hajja Meye amfanin rayuwa kamar wannan, meye amfanin haka dan Allah....." "Hmmm Kabiru sai Hakuri amma ni tun ba yau ba nasan duk aje a dawo Suwaiba na taka muhimmiyar rawa gurin tab'arbarewar zaman lafiyar gidan nan, ga yaran su sun bari sakaka ba tarbiya bare mutunci yanzu dai sai tayi mana bayanin Burinta akan mu, meye ribarta idan ta samu ta mulke mu? Ashe har kisa tana iya aikatawa Ashe rashin imanin ta yakai tayi kisa? Meye laifin Fatima Idan ni da Kai da Mahmud da Ibrahim duk masu laifine a gareta, meya sako Fatima a cika, amma koda yake uwace a gun Balkisu shine laifinta to ita Zainab data Sadaukar da rayuwarta agareki ta kaurare ta haukace ta biye miki meye nata laifin?" Tsawa Dady ya daka mata jin tayi shiru ta kasa magana "ke ake sauraro Tauraruwa mai wutsiya amsar ki muke jira" Sanda ta zabura dan iya zamanta da Dady bata tab'a ganin fushinsa da bacin ransa kamar haka ba, inna inna ta fara "tom...to...." Can't talk stupid" ya sake daka mata tsawa sanda falon ya amsa... Momy hawayen nadama sosai ke kwaranya daga idanunta ji take kamar ba ita bace a gun tana tuna rashin mutumci da tayi ta shukawa a gidan wa mijinta wa kishiyarta wa surukarta duk akan muguwar shawarar Suwaiba Wanda ko Uwarta bata saurare a lokacin Ashe Ashe Suwaiba iza mai kantu ruwa take mata Ashe bada zuciya d'aya take zaune da ita ba? Ita ta riketa da zuciyar ta d'aya a matsayin mai kaunar ta Ashe Sam ba hakane a ranta ba, lallai idan kana duniya kullum cikin ganin abubuwan mamaki kake da rashin tsammani wannan shine wuta a masaka a maimakon a ganta makera. Cikin dakewa ta fara magana "komai nayi, nayi ne dan kwatar wa kaina 'yanci idan Baku manta ba, farkon auren mu sosai Zainab da Fatima suka had'a Kansu guri d'aya suka mayar dani saniyar ware, Zainab taja Fatima jikinta ta ware ni, akayi musu kayan daki iri d'aya aka wareni, gashi sun fini ta ko'ina hakan yqsa na kullace su a raina, haka nai ta kokarin cusa kaina ga Zainab amma taki bani dama" Murmushi ta saki cikin dakewa "Rasuwar Hashim da auren da Ya Mahmud yayi na Fatima ne ya haskaka min hanya ta, Dana Fahimci tsananin kishi irin na Zainab, nan na samu damar ta, nayi ta ingizata tana hawa, lokacin da na gama fahimtar kishi ya gama rufe mata ido sai nayi amfani da hakan na kuma hada da kaita gun Malamai kamar yadda ta hanyar su na samu har na mallake ka, ko ka manta farkon had'uwar mu a school nuna min rashin so, shiyasa nayi yadda nayi har ka aureni, sannan na hana ka kara kallon wata mace da sunan so bare kace zaka kawota, duniya tamin Dad'i sosai abun da kawai ya ragemin na cika burina shine na mulki kowa da kowa a wannan family duk kowa ya dawo karkashin ikona, bawai dan inason Auren Samiha da Ibrahim bane saboda bana sonsa tun farko sannan yazo yana wulakanta min 'yar da nafiso a rayuwa kawai dan tana sonsa ba yadda banyi ba akan a karkato mana da zuciyarsa amma abin ya gagara saboda taurin kansa Abu yaci tura, duk da ina hangen samun cikar burina idan auren ya yuyu" Nan dai taci gaba da warware duk kullin da tayi tiryen-tiryen har Zuwa lokacin da auren Su ya tashi da zuwa gurin boka da sukayi da Momy akan a lalata auren Aymanah da yadda auren ya juye ya dawo kan Mu'azzam, da yadda tai ta zarya akan a lalata auren dan kawai ta kara dand'anawa Fatima bakin ciki, sannan daga baya ta koma kan Zainab, da yadda takai 'yarta gurin boka dan ganin sun yi nasara da yadda Mu'azzam ya lalata musu aiki sannan tace "kuma wlh tallahi ba Wanda ya isa ya dakatar dani ko ya Shiga tsakanina da burina dan sai na cika burina" tana kai nan ta tashi ta fice daga falon baki d'aya........ Da ido kowa ya bita cike da mamakin rashin imani irin nata bako alamar nadama a tare da ita, Momy zuwa lokacin kukan nadama sosai takeyi tana kaico da biyewa Suwaiba da son zuciyarta da tayi lallai son zuciya bacinta......Ashe Suwaiba ta wuce duk inda take tunanin ta.. Itama Samiha kuka take sosai ta Riga tasan duk yadda ta kai ga son ya Mu'azzam dole ta bar shi, Ashe bata gama Sanin wacece Mahaifiyar ta ba Ashe Ummanta ta wuce duk tunanin ta, mema yasa ta biye mata..gashi ta ja mata mafi girman asara a rayuwar ta..... _Sorry my friend kuyi hakuri dani abubuwa ne sukamin yawa, cikakkiyar lafiya ma banda ita, pls Ku sakani a addua don Allah, and ina bukatar comments dinku fa, shiyasa ban samun kuzarin typing sosai, aci gaba da gashi😘😘😘😘one love fans_ *Siddiqa ce dai*👌🏻 [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *tufafi sune suturarka ta zahiri, imani shine suturarka ta badini, yi kokari ka gyara ciki da waje👌🏻* Duniya Makaranta✍🏼 *Page* 4⃣3⃣ _______cike da bacin rai, cikin zafin nama Dady ya yunk'ura zai tashi ya bi Umma Abba yayi saurin dakko hannunsa ya mayar da shi ya zaunar, sai lokacin ya bud'e bakinsa yayi magana tun da aka fara badak'alar... "Me kake shirin yi Kabeer? Zauna har ka samu nutsuwa gaggawa aiki ne na shaidan" sannan ya juya ga Momy da bayan shabar hawayen Dana sani ba abinda takeyi..ita kanta kunyar kanta take bare mutanen da take a gaban su, mijinta, surukarta, kanin mijinta, kishiyarta, da uwa uba yaranta wannan wace irin bak'ar rana ce ranar Dana sani ranar nadama yau tayi kaico da sanin Suwaiba a rayuwa.. "Zainab!" Abba ya kirata, d'ago idanu tayi cike da rauni tayi wata kalar tausayi saidai ta kasa amsawa "ban tab'a tunanin rashin wayon ki da bak'in kishin ki zai kaiki ga shirka ba, Ashe bushewar zuciyar ki yafi yadda nike tunani, Zainab ina kika watsar da tarbiyar da Gwaggo ta baki, meyasa kika biyewa son Zuciyarki har haka, meyasa kika kasa d'aukar kaddara kamar yadda Fatima ta d'auka? Kin d'auka don son zuciya ko wani ra'ayi na auri Fatima ko ita ta yadda ta aureni, wlh babu ko d'aya daba da rashin d'an uwana ba yadda za'ayi haka ta faru, amma kin kasa yadda kin kasa ganewa, kika daura tsana kina yaki da hukuncin ubangiji dan wannan ba yakin Fatima bane da Ubangiji kike yi, duk irin shawarwari da nasihar da nake miki da Wanda duk wani mai k'aunarki ke miki kika watsar, kika ba Suwaiba damar shiga cikin rayuwar ki yadda takeso, tayi amfani da wannan damar tayi ta rura wutar gaba a cikin gidan nan ta haddasa *Ricikin cikin gida* na tsawon shekaru.." Murmushi mai ciwo yayi "ko zaki iya gayamin tsawon lokacin nan da aka d'auka ina nufin tun da na auri Fatima kika fara gaba da ita wane dadin rayuwa kika tsinta?" Jim tayi meko ta samu na dadi bayan kullum cikin kunci take da jin ana cutar da ita ta maida hankali gurin gaba da duk wani Abu daya shafi Fatima... Katseta yayi, Dan yasan bata da bakin amsawa.. "Amma kinga ita da kullum kokarin ku ya zakuyi Ku cutar da ita ne, tana cikin aminci saboda ta tsarkake zuciyar ta, bata kulle kowa a ciki ba, ta yadda da komai daga Allah ne, ko ta tab'a mayar miki da martani ko kuma ta taba cutar da ke ko 'ya'yanki?" Nan ma tasan aa ne amsar shima shiru tayi sai hawaye kawai take.. "Amma ita Suwaibar da kika yadda da ita kika bata amana da ragamar rayuwarki meye ya biyo baya? Nasan wannan kadai ya isheki darasin rayuwa ki gane ba duka mai maka dariya ne mai kyaunar ka, kamar yadda ba duka mai daure maka fuska ne makiyinka ba, yanzu kin fahimci dariya baso bane, ina burin wannan ya zama darashi agareki" Shiru kakeji falon yayi tsitt bayan shesshekar kukar masu raunin zuciya ba abinda kakeji, tun daga kan Zulaiha, Samha, Samiha, Nusaiba, Aymanah duk kika suke saidai kowa da dalilin sa na kokawa, Ammi ma zuwa yanzu kukan take Wanda ya garwaya da tsoron Allah da farinciki ranar da ta dad'e tana buri a rayuwa yau gata ta zo mata, tana rokon Allah yasa wannan ne dalilin samuwar zaman lafia mai d'orewa a garesu.. Hafiz ma tunda ya soke kansa bai kara dagowa ba sai hawayen bakin ciki yake zubarwa yana inama Allah bai kaddara masa zamowa d'a a gurin Umma wannan wace irin ranar tonon asiri tayi musu wace irin uwace saidai sanin komai ubangiji ya tsara da sanin sa yasa ya sassautawa Kansa, Hajja ma duk bakinan nata yau ta kasa magana jinjina karfin hali da taurin zuciya irin nasu kawai take a ranta, Ashe inda take tunanin Suwaiba ta wuce nan wannan wane irin rayuwa ne... Mu'azzam kam na rasa gane yanayin da yake ciki, shi kadai ya barwa kansa sani.... Cikin sabulewar jiki da rashin kuzari Momy taja jiki zuwa gaban kujerar da Abba ke zaune, ta zube guiwowin ta a kasa "Yaya Mahmoud" ta kirashi da sunan da tun suna samartaka take kiransa "yau gani a gaban ka a matsayin k'anwarka kuma matarka, 'yar uwarka, ba dan niba domin Allah da kuma zumunci dan soyayyar da ke tsakanin mu, dan alfarmar zuri'ar mu ka yafemin wlh na gane, na gane kurakurai na tuba dan Allah ka yafemin" sosai zuciyarsa ta karya kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da nadamar ta.... Saidai dole sai gwada yaga idan da gaske ne, shiru yayi mata kamar ba dashi takeyi ba, gun Hajja ta koma ta nemi gafararta tare da neman alfarmar ta saki baki, ta dai yafe mata amma tabar ta da tsakaninta da mijinta, Cike da nauyi da kunya ta kalli Ammi tace.... "Fatima ban San ta ina zan fara Neman yafiyarki ba, don Allah Fatima..." Aa Momyn Adeel" Fatima ta katseta, tare da zuwa gunta ta kama hannunta, da sauri momy ta rungume ta... "Wlh ko d'aya ban rikeki a raina ba, kome kika min a rayuwa bai kamata na manta wacece ke ba, sharrin kishi ne da shedan Wanda ni kaina ban isa na buga kirji nace hakan bazai faru dani ba, dan haka karki ce komai ta Riga ta faru ya kuma wuce inshaa Allah, dama a kullum wannan shine babban burina Alhmdllh nagode wa Allah" a tare suka amsa Allah abin godiya tare da rungume juna suna Murmushi cikin hawaye wani irin sanyi ya ratsa su mai cike da rahma, shima Abba Murmushi ya saki yana mai godewa Allah... A tare suka shiga bawa Abban hakuri har ma bakin Fatima yafi na Zainab yawa, itama kam sai mamakin halin girma irin na Fatima takeyi, tana jin haushin kanta da kanta na cutar da baiwar Allah mai kyawun zuciya kamar Fatima da tayi, ina zataje ta samu abokiyar zama kamar Fatima, sosai taji duk wata tsana da mugun kishin ya fice daga ranta ya maye gurbi da aminci da amana... "Tun da kunyi yadda kuka yi kun kayar dani to na Hakuri, Allah ya yafe mana baki daya ya kara hada kanmu cikin aminci da k'aunar juna" a tare aka amsa da amin... Saidai koda suka duba duk ba yaran Ashe duk sun sulale sun fice basu sani ba, Momy ce tace "ina 'yata Aymanah, ina take naji dumin yata Wanda na hanata na tsawon shekaru?" Hawaye na bin kumatun ta tana tuna kuntatawar ta a gareta for nothing... "Haba Momy kukan ya isa haka yanzu ba lokacin kuka bane, farinciki ya kamata muyi ba kuka ba, bari na dubo maki ita" cewar Ammi... Murmushi momy ta saki tana jin k'aunar Ammi sosai a ranta, Hajja ce tace "Fatima ba ruwanki da ita" dariya Ammi tayi tace "haba inna har yanzu Fushin ne a yafemi mana, kuma ai laifin na 'yar Momy ce ita taja" "Aa yarinyata bata laifi, duk da bansan kan zancen ba, nidai nasan 'yata tafi ta kowa" dariya suka saki gaba d'aya Abba dake gefe yana jiyo su sai murmushi yake yana kara godewa Allah, jin sa yake yau kamar an sauke masa wani nauyi a Kansa... Dady dake gefe sai kallon su yake yana kara blaming kansa akan tabarbarewar zamantakewar su, Suwaiba ta zamo muguwar Kaddara a rayuwar sa. *************** Mu'azzam ne ya fara sulalewa ganin lamarin ba nasu bane, sannan Zulaiha tabi bayansa tare da Aymanah dake suna guri d'aya dama a zaune, sannan sauran duk suka firfito... Narai-narai Aymanah tayi da ido kamar zatayi kuka, sauri take ta cimma masa ta bashi Hakuri, don tun da suka taho ko kallon gun da take baiyi ba... "Yadai little menene kuma yanzu?" "Aunty Ya Mu'azzam ne fa nayi ma laifi shine yake ta fushi yaki ya kulani" ta karasa fada hawaye na saukowa a kumatun ta, ita take ta dokin tazo ta gan shi shine xai shareta kodai Hajja yaudarar ta tayi dan kawai ta kwantar mata da hankali... Kama hannunta Zulaiha tayi "haba Aymanah kada ki bada ni mana keda mijinki kije ki same shi kawai ki bashi hakuri nasan Yaya zai hakura indai kece ai bakya laifi matar Yaya" ta karasa fada cike da tsokana.. Dan tura baki tayi cikin kunya "kai Aunty" "Allah kuwa little kije kawai uhum kin dai gane" tace tare da kashe mata ido daya sannan ta bud'e purse din ta ta Ciro mata wani romantic chewing gum, ta bata tare gaya mata wata magana a kunne... Zaro ido waje tayi tare da rufe baki da hannayenta cikin kunya "jeki mana" ta kara fada.. Cikin takun ta ta fara takawa zuwa corridor data ga yabi tana yi tana waiwayo aunty Zulai d'in, ita kuma sai daga mata hannu take tana karfafa ta... Yana jingine da motarsa ya rungume hannayensa a kirji, idanunsa a lumshe kamar mai bacci, tana hango shi ta saki wani shu'umin murmushi, tare ta balle chewing gum din ta jefa a baki sannan ta canja taku cike da kirsa, tana cin chewing gum din cike da iyawa.... Sam baiji motsin tahowar mutum ba saboda yadda yayi nisa cikin tunani, jin lallausan hannu kawai yayi a fuskarsa, ware ido yayi gaba d'aya dan ganin waye.... Kusan daskarewa a gun yayi, ya kasa mayar da idanun daya sako, har da k'arin bud'e baki aka samu, shifa wannan yarinyar itace week point dinsa, Murmushi takeyi tana ci gaba da shafo fuskarsa cike da kirsa, wani irin wannan fizga yayi mata ta fad'o a k'irjinsa matse ta gam yayi ko zau samu sassaukin da zillon zuciyarsa take masa.... Ware ido tayi yin wannan unexpected hug, a tare kwayoyin idanuwansu suka sarke da juna, suka shiga aikawa juna sakonni masu wuyar bayani........... _💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻Soyayya, soyayya, masoya suna yin k'auna😍😘. Wannan shafin na masoyan Aymah da Ya Mu'azzam ne, kuyi farinciki👌🏻_ *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *Abu uku suna hanzarta tsufa, fushi da hasada da yawan damuwa, babban maganin su shine dogaro Allah, da barwa Allah da sanin Allah na nan*👌🏻 Duniya Makaranta✍🏼 *Page* 4⃣4⃣ ________itace ta fara sauke nata idon tana jin taci gaba da kallon kafafun ta dab suke da su kaza, d'aukar gangar jikinta, kaifin idonsa na daban ne, wasa taci gaba dayi da botiran gaban rigar sa kanta na kasa jikinta yayi lakwas, dakyar ta iya tattaro kalaman bakinta har ta samu ta furta "I'm so sorry Yaya!...I mean for everything..pls forgive me!" Gogan naku daya shige duniyar masoya, kallonta yake bako kiftawa gani yake kamar sabon zubi akayi mata ta canja masa gaba d'aya, ga wani sihirtaccen k'amshin da jikinta ke fitar wa...maganar ta ce ta dawo dashi, cikin jarumta da basarwa yad'an turata daga jikinsa kamar bashi ne ya kakume ta ba... D'aure fuska tamau yayi tare da juya mata baya, kamar ma baiji me tace ba, shi nan wai fushi yake, murmushi ta saki tare da kara matsewa jikinsa, kanta ta d'ora a bayansa tare yi masa rungumar baya, ta zagaye hannayenta a cikinsa, tana sakin numfashi kad'an-kadan..... Sosai rungumar ta shigesa wani iri yaji musamman yadda hucin numfashin ta ke sauka a bayansa, na sosai yayi Jarumta Dan ta gama kashe masa jiki, musamman wani salo na daban da take masa da hannayenta.. Hannayen yake bi da kallo da suka sha jan lalle mai hade da baki, wanda ya kara pitting glowing skin nata... "Yaya Mana! Pls kace wani abu?" Banza ya kara mata duk da yanayin sigar maganar kad'ai ya isheshi susucewa cike da shagwaba uwa yarinyar da ke shirin kuka... "Yaya pls kayi Hakuri Allah bazan k'ara ba, nima fa da wasa nike maka, dan Allah yayaaaaaa!!!!!" Yadda taja sunan da sigar maganar saida ya runtse idonsa tsabar yadda ta shigeshi... Murmushi ta saki tare dayi masa gwalo, sannan ta fara zame hannunta daga jikinsa tana dire-diren kafafu, kukan mai cike da tabara ta fara yi masa tana d'an dukan Bayansa a hankali.... Kamar kiftawawar ido yayi wani irin turning to her tare da fizgota ta fad'o jikinsa, yana murmushi "keko!" Shine kalmar da ya iya fad'a yana lakuce mata hanci... Itama murmushi ta saki tare da sauke kwayoyin idanunta kasa, ganin yadda yake binta da kallo "da yake nidin ba ke bace ban iya wahalar da abinda nake so, it's OK ya wuce, but you hurt me so badly, and dole na hak'ura tun da ni babban Yaya ne!" Ta jiyo muryarsa yana rad'a mata a kunne, da sauri ta d'ago idonta tana kallonsa... Murmushi ya sakar mata tare da d'aga mata gira, itama murmushin tayi tare hugging nasa tightly "I so much love you my Khaleeel" kusan daskarewa yayi a gun, yama rasa takamammen meya fi masa dadi a wannan yanayin rungumar CE? ko sabon sunan da aka saka masa? kai! duk basu ne wai tana matukar sonsa?? what bunch of surprise?? wai aymanah dai ce yau ke fad'ar tana k'aunar sa da bakinta? Yama rasa wane kalar farinciki zaiyi a wannan gabar, jin kansa yake kamar yafi kowa jin dad'in rayuwa yau ya samu soyayyar Bilkisar sa hannunsa yasa ya tallabo hab'arta tare kallon kwayar idonta "Me kika ce Habibty??" Yace murya can k'asa, kunya ce ta kamata tayi saurin mayar da kanta cikin k'irjinsa, kara dagota yayi "pls ki k'ara fad'a kina kallon kwayar idona" duk da ya gasgata maganar daga kwayar idonta, saidai yana so ya kara ji ne kuma yafi so tana kallonsa... Narkakkun manyan idanuwanta ta watsa cikin Oily and sexy eyes suka tsarke "I mean it Yaya I love you wit all ma heart, and from my heart" tace a sanyaye kamar mai rada, Murmushi ya saki mai kayatarwa wanda ya bayyanar da jerarrun fararen hak'oransa masu matsakaiciyar wushirya mai kyau.... "I do love you! Ana a habbuki katirr habibty Aymanah, ina matukar k'aunarki Bilkisa tah" yace tare da zagaye ta da hannayensa ya rungume ta sosai, kamar yadda tayi masa, idanuwan su a lumshe kowanne da abinda yakeji a ransa a wannan yanayin... Zulaihat da tazo ta kirasu ganin yanayin suke ciki yasa ta kame gefe tana kallonsu cike da sha'awa "sun matukar dace" ta fada a fili, ganin lokaci na tafiya gaji jiransu ake ya sakata dan matsawa gun su tare da yin gyaran murya.... Ware ido sukayi a tare, tare da sakin juna, fuskewa yayi as Yayan nan, yayin da Aymanah tayi k'asa da kai irin na kunyar nan, murmushi Zulaihat tayi tare da jan hannun Aymana sannan ta d'an kallesa "Yaya su Abba ke magana" daga haka tayi gaba tana murmushi yayin da Aymanar ke bin ta cike da kunya... Bayan sun wuce shima murmushin ya saki tare da shafo bayan kansa sannan ya biyo bayansu cikin takunsa na isa wanda yake by nature *Barr. Ibrahim Mahmoud Gwarzo kenan* isasshen ingarmar Maza. *********** "Ba abinda zance da Ubangiji sarkin sarakuna sai dimbin godiya a gareshi daya nuna mana wannan ranar, babu bukatar nayi muku dogon bayani komai a idonku ya wakana, ina fatar wannan ya zama izna a gareku, Ku d'auki darasi daga gareshi, inaso dukannin mu, mu d'auki wannan a matsayin kaddara, kada kowa ya d'orawa kowa laifi mu d'auke shi a cikin wata kaddara ta rayuwar mu, wannan kadai ya ishemu darasi a rayuwa, sannan inaso kowa ya tsarkake zuciyarsa ya fitar da duk wani kulli dake ransa, mu mu'amalanci juna da zuciya d'aya duk rintsi kada mu cutar koda an cutar damu, inshaa Allah komai tsawon zamani Gaskiya zatayi halinta, gaskiya d'aya kuma a killum itace kan gaba koda an kayar da ita zata taso ta kayar Ku rike wannan" sannan ya nisa ya kira sunan Dady.. "Kayi hakuri Kabeer na sani da zafi kuma da ciwo amma inaso ka d'auki wannan a matsayin kaddara a rayuwarka, kada wannan yasa kace zaka k'ullaci Suwaiba kayi hak'uri ka yafe mata, sannan ka nemar mata shiriyar ubangiji, tana tare da sharrin zuciya da kuma kaidin hassada, kada ka manta duk rintsi an Riga an zama d'aya tun da an had'a zuri'a da ita, ita uwar 'ya'yanka ce, bawai nace kada kayi mata hukunci bane aa, inaso dai kada ka yadda ka dauki mataki a cikin fushi, ka bari ka nutsu ka dawo hayyacin ka tukun, kayi hak'uri" Hafiz da Samiha ya kira "kuyi hak'uri yarana kada wannan ya zamo kalubale ga rayuwarku sannan kada kuce zaku tsani mahaifiyarku akan wannan aa, addu'a ya kamata kuyi mata, sannan kada Ku itace mahaifiyarku Baku da sama da ita kome ta zama koya take dole Ku kyautata mata, kuyi hak'uri Ku saka wannan a cikin kaddarar rayuwar ku, sannan ke Samiha, ina fatar kin dau darasi daga yau ina fatar kin yasar da bak'ar akidar da kika taso a ciki inaso duka ki watsar da komai ki d'auki daidaitacciyar hanya" Cikin shesshekar kuka tace "na gane Abba, wlh na gane kuma daga yau zan canja daga Banza ballagazar Samihar da kuka sani zuwa nagaratacciyar Samiha" "Alhamdulillah naji dad'i sosai da hakan, Allah ya kara hade kan wannan family, ya barmu a matsayin *Zuria d'aya* tsintsiya d'aya cike da aminci" duk aka amsa da Ameen... "Sannan ina so naja muku kunne, bana so naji ko naga wani nuna wariya ko gorantawa a tsakaninku duk nan d'aya ba banbanci Ku rike wannan a ranku" ya fad'i hakane Dan kar ko cikin bacin rai wani ya goranta wani Musamman su Samiha a goranta musu akan laifin mahaifiyar su... Itama Hajja nata nasihar tayi sannan Momy ta d'ora Ammi ta saka albarka... "Zo nan gareni 'yata Aymana zo gareni 'yata" cewar momy, cike da kunya Aymanah taje gurin ta, ta durkusa tare da sunkuyar da kai, dagota Momy tayi zuwa jikinta... "Yata zaki iya yafewa irin wannan uwar kamata data watsar da 'yarta akan son rai, zaki yafemin 'yata Aymanah, ki soni ko kad'an ne duk da ban dasa son ba tun farko?" Rike mata Hannaye tayi sosai, tana hawayen farinciki... "Aa Momy don Allah karki ce haka, wlh ina k'aunarki tun farko, kuma ni ban rikeki a raina ba ko kad'an kullum kallon uwa nake miki, naji komai daga Ammi kin nunan k'auna momy" jinjina kai Momy tayi tana tunanin Fatima wace irin baiwar Allah ce mai matukar kyan zuciya haka? Share mata hawayen tayi sannan tace "nagode 'yata..." Saurin katseta "Aa momy nice zan miki".... Suma Samha, Samiha yafiyar Ammi da Aymanah suka nema duk aka yayyafe kai tsaye... "Tau zaku iya tafiya, Allah yayi muku albarka baki d'aya" shima Dady albarkar ya sanya musu, har zasu tashi Abba ya dakatar dasu.. "Ibrahim!" Ya kira Mu'azzam, amsawa yayi cikin girmamwa "ka manta da komai past is past, ka dauki matayenka Ku wuce gida, a bar komai daya wuce a gina sabuwar rayuwa" sanin halinsa na kafiya ya saka shi yimai magana, amsawa yayi amma har cikin ransa baya da niyyar maida Samiha Dan ta fice masa arai gaba daya... Kuka Samiha ta saki cike da kunar rai, nan fa hankalin kowa ya d'aga, sai tambayar ta ake meya faru, ko batason komawa ne, kasa cewa komai tayi sai dan neman kuka da take sharba, ran dady ne ya baci ganin yadda kowa ya rud'e a kanta gashi tak'i magana, tsawa ya daka mata yake ko ta fad'i meke ranta kota fice ta basu guri, Dan a ganin sa renin wayo ne shi Mu'azzam din bai ce bazai maida ita ba sai itace zata kawo iskanci... "Haba Kabeer a bita sannu mana, zo nan 'yata ki gayamin meya faru?" cewa Abba.. Dakyar ta iya bud'e baki tace "Abba...au...aure. Aure ya kare tsakanina da ya Mu'azzam!" Tare da sakin wani kuka mai cin rai.. A zabure suna rige rigen tambayar dalilinta, ciki kuwa hadda Mu'azzam din da Aymanah.... "Abba zina nayi...zina na aikata da aurensa?" Nan ta warware musu abubuwan da suka shiga tsakaninta da boka wanda ko uwar da ta kaita gun sa bata sani.... Sallallami Hajja da momy suka shiga yi, yayin da su Dady ke furta innalillahi wa'innah ilaihirrajiun, Hafiz runtse ido yayi ransa na suya, yayin da Mu'azzam ya dafe kansa dake sara masa, Ammi sarkin tausayi tuni hawaye suka wanke mata fuska dasu Aymanah, Nusaiba, Samha har Zulaiha bare uwa uba ita Samihar dake kuka da duka karfin ta.... A zubure Dady ya mik'e tare da ficewa daga falon, Abba na kiransa amma ina saidai ko waiwaye baiyi, Umma ya isko daki tana jera kayanta a cikin akwati da alama tafiya zatayi, baiyi wata wata ba, ya danko wuyarta, sosai tayi yunkurin kwatar kanta saidai Sam bata samu wannan damar ba sai mutsu, mutsu take, ko magana ta kasa yi tsabar tsakar da tasha, saida ya tabbatar ta jigata sannan ya jefata kan sofa ya nuna da yatsa.. "Burinki ya cika Suwaiba kinyi nasarar kashewa 'yarki aure, kema kije na sakeki, sannan ki sani kin cutar dani kin cutar da 'ya'yanki musamman Samiha, wannan ne so ki kaita da kanki gurin boka ya lalata min 'ya?" "Lalatawa!" Ta fada da karfi, tana dafe k'irji.. Kallon banza ya watsa mata tare da buga babbar rigarsa ya fice rai a matukar bace... Hannu ta d'ora akai tare da kurma ihu "Wayyo mai gobe da nisa ka cuceni, Samihar tawa ka lalata min, Allah tsine maka tsinanne ya tsinewa saninka da nayi a rayuwa........." 🤷🏼‍♀ _kaikayi koma kan mashekiya_ *Siddiqa CE* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *Page* 4⃣5⃣ _______"Abba don Allah kayi wani abu, kada ka bari auren Aunty Samiha da Yaya ya lalace, Hajja kina kallo haka Zai faru, don Allah kuyi wani Abu Aunty tana son Yaya sosai komai da tayi akan son sa ne dan Allah Ku taimaka" Aymanah ke fad'a cikin kuka da tashin hankali kamar itace akace aurenta ya k'are.... Mamaki ne sosai ya kama mutanen cikin falon ganin yadda Aymanah ta hakikan ce iya gaskiyarta tana rokon su Abba, ciki har ta ita Samihan kanta, sai kallon mamaki take mata, tana tunanin iya Saninta iya zamanta da ita bata tab'a yi mata abun alkhairi ba, kullum burinta ya Kare ne a ya zatayi ta k'untata ita da Mamanta mata kamar yadda ta tashi taga Ummanta nayi kuma take sakata amma wai a yau itace ke bakinciki da bakincikinta take damuwa da damuwarta, lallai rayuwar Ammi da iyalanta abar koyo ce, sune nagartattu, rayuwar su abar burgewa da sha'awa ce sune masu koyi da karantarwar manzon Allah S.A.W na sowa dan uwansu abinda suke sowa kawunan su, na alkhairi, duk da cewa kishiyarta ce ita, amaimakon tayi farinciki miji ya zama nata ita kad'ai, lallai tana da kawun zuciya na sosai(dama Samihar ba jahila bace Kawai dai son rai ne mai kaiwa ga halaka) Allah kiyaye mu da son zuciya wanda yake kasancewa Bacinta..... Murmushi Abba "Ummina wannan ba hukuncin mu bane, kamar yadda nasan ke ba jahila bace, dan haka duka mu d'auki wannan a matsayin kaddara, wacce take rubutacciya tun farko, muyi hakuri gaba d'aya mu rungumi kaddarar mu" Kamata Momy tayi tana rarrashin ta, Hajja tace "wannan haka yake, kaddara ta riga fata, kuma wannan kukan kurciya ne, wanda sai mai hankali kan gane, Allah yasa wannan ya zamu izna gareta damu gaba d'aya...." Ameen suka amsa, Dady ne ya shigo da sallama amma fuskar tamau ba sassauci, tuni yaran suka sha jinin jikinsu, Abba, Hajja, Momy, Ammi, da kallo suka bishi cike da fargabar meya aikata "Kabiru! Kaddai wani abu kaje kayi mata cikin fushi" cewar Hajja "ni nasan dan uwana bazai yi abinda bai kamata ba, meka aikata Kabir?" Kafin ya iya bud'a baki yace wani abu.... Saiga Umma ta fad'o a falon kamar wata sabon kamun hauka, a hargitse a ramutse, bako Sallama kamar wacce aka ingizo "wallahi karya ne Kabir, Allah karya ne baka isa ka sakeni ba, wlh kayi kad'an aurena dakai auren zobe ne, wlh kayi kad'an mutu ka rab'a takalmin kaza, ba inda zani ina nan saika mayar dani d'akina" haka ta ringa sambatu kamar wata zararriya sai zare idanu take, ganin abin zai zama hauka kuma duk da Abba baiso haka ba da Dady ya saketa cikin fushi, duk da a wannan gabar sakin shi kad'ai ya rage a matsayin maslaha a tsakanin su, watakil ya zama darasi a gareta... "Suwaiba ki dena wannan shirmen ki samu gu ki zauna muyi magana a...." "Ba zaman da zanyi, kuma ba ruwanka ban sako ka a ciki ba" tayi saurin katse Abban cikin haukarta da ta kamu da ita na wucin gadi... Zabura Dady cike da haushi, wannan wane irin abin kunya ne a gaban yara "ka gani ko yaya? Kina kallo ko Inna?" Rikesa Dady yayi yana girgiza masa kai da shafa hannunsa, zama ya dawo yayi yana huci, ita kuma sai sakin maganganu take na rashin kan gado, sudai sauran mutane sai kallon ikon Allah suke yaranta kuwa bakin ciki kamar ya kar su.. Cikin zafin rai da bacin rai Hafiz ya taso ya kama hannun mahaifiyar tata dake ta sambatu ba wanda ya tanka ta, sai kara barar musu da sauran kimar takeyi, yana janta tana turjewa dakyar ya samu ya fita da ita daga Falon, waje yayi da ita tare da jefata a mota ya kulle... Shima ya zagaya da sauri zuwa mazaunin driver, ganin yadda take ta buga masa glass kamar ta fashe masa shi ko zafin hannayenta da take bugawa bataji, hauka dai tuburan, hawaye sosai ke sauka daga idanunsa uwa mace..... "Haba Umma! wane irin laifi mukayi miki da zakiyi mana irin wannan hukuncin, Umma meye duniya? Me kika nema kika rasa a rayuwa, nagartaccen miji, Allah yayi ni'ima ta samun 'ya'ya, wasu na nan ba mijin ba 'ya'yan wasu da mijin ba yara, wasu da yaran ba mijin, meyasa? Meyasa Umma? Irin godiyar da zaki yiwa ubangijin ki kenan, ta hanyar butulce masa ta hanyar shirka...." "Kai! Dan ubanka zaka bud'e ni na fita na koma gun mijina ko sai na maka baki" ta fad'a da karaji, alaman bata maji me yake fad'a ba... Murmushi ya saki mai ciwo " Miji fa Umma? Miji kikace? Bayan kin zubar da wannan damar kin yanke wannan igiyar mai daraja da kanki, kin yanke ma Samiha tata itama" bai saurari zagin da take dura masa ba akan ya sauketa yaja motar tare da ficewa tsiyace daga gidan, duk sambatun da take masa da zaginsa bai saurare ta sanda ya jingina da ita gidan su, inda dama a hannun Yayanta ne take dan iyayen su sun dad'e da rasuwa, yana kaiwa nan sai ga kiran Abba dake tambayar sa ina yake, ina yakai Unman tasu, nan ya shaida masa gashi ya kawo ta gida, duk da Abba baiso hakan ba amma yana ganin wannan shine last solution a garesu, Allah ya kyauta kawai ya fad'a... ************ Bayanin kai suwaiba gida da Hafiz yayi Abba yayi musu, sannan yace za'a barta gida na zuwa lokacin da zata fahimci kurakuran ta tayi nadama ta gaskiya sai a dawo da ita, Hajja ta amsa da hakan yayi, Dady kam cewa yayi shikam gaskiya ya gama zama da ita, Abba yace wannan kam labari ne ko don darajar yaranta za'ayi mata uzuri muddin ta gane kuskuren ta, a haka taron ya watse zucuyoyin su cike da abubuwa nadan-daban na Al'ajabi mamaki, nadama da tsoron Allah... Karo na farko a tarihin Zuri'ar, yau ga Momy da Ammi, Zulaiha, Samiha, Samha, Nusaiba da Aymanah a kitchen tare suna girki cike da k'aunar juna, sosai Momy da Samiha, da Samha suke tambayar abinda basu fahimta ba, cike da farinciki sukayi girkin cikin k'aunar juna, musamman yadda Ammi ta dake gurin kawar ma Samiha da Samha damuwar su, kuma tace a sasanta zasu zauna su ringa shiga kitchen a tare da koyon sauran abubuwan da suka shafi gyaran gida da dabarun zaman gidan aure.... Inda Momy tace itama baza'a ware ta ba, kullum zata ringa zuwa ayi da ita, Hajja dake Falon tare da sauran yaran Su Munira, Munir, Adeel, Fadil, Fadila, Sageer, Sageera, Arif, sai kara godewa Allah take da ya ara mata rayuwa taga wannan ranar da take tsumaye a rayuwar ta, sai murmushi take tana kallon yadda yaran keta rahar su, dama Allah yasa kananun basu d'auki mummunar ak'ida ba....... Haka suka wuni a wannan ranar a tare aka ci abinci tare sai raha da annushuwa suke kamar ba abinda ya tab'a faruwa a baya, wannan rana tayi tasiri a rayuwar su, sun kafa ta a cikin kundin tarihin su, sun sakata a ranar farin cikin wannan Zuri'ar, a yau sun kara dunkulewa sun zama *Zuri'a d'aya* sannan kuma *Rikicin cikin gida* ya kare inshaa Allah, sai zaman lafia mai dorewa... ****** Yana isa bakin matsakaicin gidan, wanda kana gani kasan ba babba gida bane saidai a kirasa gidan mai rufin asiri kawai, waya ya zaro ya kira kawun nasa, akayi sa'a kuma yana gida, a soro suka tsaya yayi masa bayanin komai, sosai ya cika da mamaki dan shi dai yasan ya tsaya sosai a kanta, amma tunawa halin ta na son fafa da nuna isa, dan bazai manta ba, yasha samun case nata akan karyar da take a school akan yar wani da wata ce ansha tsure ta, sannan kuma d'anta ne ya gaya mishi kuma yasan duk rintsi baxai yi karya wa mahaifiyarsa ba, jinjina kai yayi tare da fadin Allah ya sawwaka, sannan suka isa motar..... Umurnin ta fito su shiga ci Yayan nata ya bata, fitowa tayi ba musu dan har gobe tana shakkar Yayan nata, yace ta shiga ciki, kamar tayi ihu taji saidai ba yadda ta iya dolenta taja kafafunta zuwa ciki, tana jimamin yadda zata Zauna gidan tare da matansa har uku da yara sunkai ashirin... Sallama Hafiz yayi masa ya wuce akan sai ya sake dawo wa, gidansa ya wuce direct ya kulle kansa a daki yayi kukan bacinciki kai kace wata macece, sai bayan isha ya isa family house nasu dan daukar Nusee shima dan kada a zargi wani abu daban ne, kiranta yayi yace ta same shi a waje... Saida ta tsorata da ganin yanayin sa, cikin rawar baki ta kama hannunsa "Ya....Yaya...Hafiz kuka kayi?" Ji yayi kamar ta tunzurasa shima ya runtse hannunsa a nata tare da Dora kansa a kafad'arta kamar jariri sai saukar Hawayensa taji kafin yace.... "Nusaiba dole ne na koka! Nusaiba banyi dacen Mahaifiya ba, meyasa na kasance d'anta Nusaiba meyasa...!?" Saurin zare hannunta tayi ta rufe masa baki tare da dora dayan a kayinsa tana shafa Sumarsa... "Aa my heart karka ce haka, kada ka bari bacin rai yasa kayi sabo wannan kaddara ce, taka kalar kaddara ce, kayi hak'uri da hukuncin Allah, ta sanadin haka sai kaga ka dace, ka daure ka saka Umma a addu'a ita uwa ce koya take kyautata mata ya zama dole.... Haka tayi ta rarrashinsa da daddadan kalamai, har saida ya samu nutsuwar zuciya, rungume ta yayi tsam a jikinsa yana mai jin sanyi a ransa, lallai mace ta gari rahama ce(dama Annabin rahama yace duniya wani dan jin dadine, mafi jin dadin ta, wanda ya dace da mace ta gari👌🏻, mata mu daure mu kasance ababen alfaharin mazajen mu ba fitina a garesu ba, mu zame musu fitila mai haske ba duhu, ba mu taimaka musu gurin kara dankon zumunci tsakanin su da iyayen su ba nesanta su dasu ba, mu fa tuna muma iyayen wasu mazan ne wata rana). Mu'azzam kuwa yana barin gidan tunda aka kammala taron sai 9 ya dawo d'aukar Aymanah, cewa tayi ya barta na yau d'aya ta kwana gida yadda take farinciki gata cikin dangi anata raha, nan fa Hajja da Ammi hadda Aunty Zulaiha suka korata, Momy nata mitar su kyale mata 'yarta, sosai Samiha tayi kokari gurin danne zuciyarta dake bijiro mata da abu, ta bisu da murmushi yake, bayan wucewar su ta dauki hankalin mutane daya tafi wani gurin, ta shige bedroom ta dirza kukanta..... Sai wani kunbure-kunbure take masa mota ita a dole ya hanata kwana, shareta yayi kamar ma baisan me takeyi ba sai murmushi yake tare da mayar da hankalin sa kan driving NASA.. Tun a harabar gidan daya ke tar kamar lantarki ta ga canji, kamar ma har pentin gidan an canja, ga wani ado da akayiwa gaban gidan yana fitar kalolin wutace masu ban sha'awa an zagaye su da furanni masu kyawun launi.... Ba tsammani taji an sama da ita, sai lokacin ta dawo daga duniyar shagala data tafi, yar kara ta saki, tare da kankame sa... "Bayan kince ba zaki biyoni ba, meye na wani bud'e ido kina kallar min kayana" ya rada mata yana fuskewa.. Murmushi ta saki tare da yi masa unexpected light kiss a lips, tare da kasa kankamesa "sorry My Khaleel, ai gani na taho ko, gaskiya yayi kyau sosai" Murmushi ya saki tare da yi mata peak a goshi, a haka suka karasa kofar falon yana d'auke da ita, da kafa ya tura kofar suka shiga... "Wow! Wow!! Hayatiy it's so beautiful!" Ta fad'a tare daci gaba da kallon falon................ _💃🏻💃🏻💃🏻its is a time, love time!😘😍 oya one corner my fans👯🏻‍♀👯🏻‍♀🤪 #Team Muz'Aymah💋#_ *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *_🕌 its Anoder Friday again, may Allah(S.W.T) upon his Rahman and mercy on we, may d bless of dis day be wit us ahead🤲🏻. JUMU'AT MUBARAK🕌_* _Masoyan 😘Muz'Aymah😘 a duk Inda kuke to Muz'Aymah na miko gaisuwa 'yar inyass, khairy b-b, zuzu, ummu annur, mom zee, Maman Nana and rest Allah kuna da yawa duk na gaida Ku kyauta, kuyi farinciki wannan shafin naku ne all, ina sonku billahi ilallahi👌🏻_ *Page* 4⃣6⃣ _______dire ta yayi tare da fad'in "ouch! Yarinyar nan kinja kaya fa, kinjiki kuwa?" Dukan wasa takai masa a k'irji, tana tura baki gaba, cikin shagwaba "Allah nidai Aa yaya ba wani kaya dana ja" tana doddoka kafafu, wani laushi da taji a pootmat din k'ofar yasa takai ganinta kasan, wani irin lallausan welcoming mat ne shimfid'e a gurin, anyi rubutu jikinsa boldly *welcome back home Habibty Aymah* yanayin yadda akayi rubutun da adon da ke jikinsu ba karamin tafiya da ita yayi ba, sai murmushi take tama kasa cewa komai, a hankali ta taka zuwa tsakiyar falon tana ci gaba da kallon balloon d'in da ke lilo ta ko'ina masu shape din heart kala-kala kowane d'auke da haruffa masu bayyana tsantsar k'auna gun Wanda akayi domin sa.... Rungume hannuwa a k'irji yayi tare da zuba mata ido, itakam sai tsalle da juyi take a falon sossai sakon da yake so ya isar gunta ya samu gun zama daram a zuciyarta, gun wasu manya manyan wall stickers taje tana shafawa da aka manna a bangon falon suma dai d'auke suke da kalaman soyayya zuwa gareta, sosai abubuwan suka shagatal da ita, sai mamaki take wai duk akanta Ya Mu'azzam yayi abubuwan, Ashe haka yake mata k'auna bata sani ba... Ta bayanta ya lallab'o tare da rungumo ta ganin yadda ta matuk'ar lulawa a duniyar soyayya wato dai sakonnin sa sunyi tasiri, k'ara shigewa jikinsa tayi tana shakar k'amshin san nan mai nutsar da ita a k'auna.... "All dis for me My khaleel?" Ta tambayesa idonta a lumshe bayan yayi turning nata suna fuskantar juna, bai amsa mata ba, face sunkuyowa da yayi yayi kissing wuyarta tare da zagaye ta da hannayensa... "Sunyi miki kyau?" Ya rad'a mata a kunne lokacin da ya iso nan gun, bata iya amsawa da bakinta ba sai kai data girgiza alaman eh, saboda salon nasa ya sakata zama so weak... Murmushi mai sauti yayi tare da cewa "anything is for you Habibty, ur my world, my everything.." "..I..love....you so much Hayatiy" ta fad'a can cikin mak'oshi dakyar.. Kara rungumeta sosai yayi shi kadai yasa ya yakeji idan ta furta masa Kalmar so, sama ya dagata tare da fara takawa... "Yaya?" Tace cikin rauni tana kallon k'ofar part d'in Samiha, kallo d'aya yayi ma part d'in ya d'auke kansa, baice da ita komai ba ya fara taka step da ita, itama shiru tayi tare da k'ara kankamesa ido lumshe...... Mashaa Allah ta fad'a a ranta lokacin da ta tsinci kanta tsakiyar falon sa, sanyin Ac da daddad'an k'amshi suka bugi hancinta a lokaci d'aya, lumshe ido tayi a hankali kafin ta bud'e su, shine first time data shigo part d'insa tsawon zamanta gidan yo ina zata shiga dama can da ana 'yar tsama... Komai na parlon lemon green and milk ne, ko'ina neat sai k'amshi yake zubawa baza idanu tana kallon dukiyar da ya narka sai kace d'akin wata sabuwar amarya, but nashi very unique ne dama Yayan nata na daban ne, wadannan tafka tafkan enlargement d'in nasa data gani a dakinsa na family house nasu, su ta sake gani anan dama tana matukar son fotunan, aiko gabansu taje ta zuba musu ido ko kiftawa bata yi..... Bataji zuwansa kusa da ita ba sai da ya tab'a ta "tau inkin gama kallon sai mu shiga ciki 'yar Gwarzo" kunya ce ta kamata tayi saurin rufe idonta tana murmushi "kaima naga d'an Gwarzon ne ai" Murmushi ya saki yadda tayi maganar a shagwabe da yanayin yadda ta tura bakin gaba "eh naji amma ba kamar keba ta Hajja takwaralle inji Hajja" yace da sigar tsokana... "Nidai Allah Yaya uhum.hum..hum" tana diddire k'afa, Aymanah rigima ya fad'a a ransa tare da rungumeta yana mata magana kasa-kasa, wadda duk kwakwa ta an hanani jiyota, a haka ya jata zuwa bedroom d'insa, shima dai ba k'arya ya tsaru ta ko'ina yasha adon Sky blue and white..... Mamaki ne ya kamata data samu tafkeken enlargement nata a d'akin, ko'ina ya samu foton har yayi enlargement d'insa oho! "Kina mamaki ne" ya jeho mata tambayar.... Ido kawai ta zuba mishi "tare akayi min su da wad'anda kika gani a falo, zaro ido waje tayi cike da sabon mamaki zatayi magana ya katseta dan bai shirya answering question nata yanzu ba..... "Ki Adana question naki, Ba a wannan lokacin ba, yanzu lokaci na kara'in many things, kinga yanzu dai taso muje muyi sallar mafi daraja da kikasa muka rasa" yace tare da kashe mata ido d'aya, saurin yi k'asa da idanuwanta tayi sai lokacin tsoro ya fara ziyartar zuciyarta ta kuma tuna daga ita fa sai shine a gidan, oh yau an ba kura fida sai yadda ta kasance da ita kuma... Ganin taki koda motsi ne bare niyyan tashi ya saka shi takowa da kansa ya dagawa, toilet ya kaita, sukayi alwala tare, katuwar darduma ya shinfid'a musu ya shige gaba ya jasu sallar, addu'o'i sosai ya kwararo musu da yaren larabci zuwa turanci, da Hausa duk ya had'a, bayan ya dafa kanta kamar yadda sunnah ta tanadar... Tankwashe kafa yayi sannan ya kalleta sosai kafin yayi magana "Bilkisu" ya kirata da asalin sunanta.. D'ago ido tayi ta kallesa na tare da amsawa da na'am, tare da maida kanta kasa ganin yadda yaci serious tasan muhimmiyar magana ce zaiyi... "Allah ya sani wannan ranar tana daga cikin manyan ranaku a rayuwa ta, ina cikin farinciki sosai, da Allah ya daidaita mana kan Zuri'ar mu, sannan ya daidaita tsakanin mu dole mu godewa Allah da wannan dimbin alfarmar da yayi mana" nisawa yayi "Bilkisu, nasan kinsan aure yafi karfin ayi wasa dashi, wata daraja ce da baiwa da Allah madaukakin sarki yiwa bayinsa, sai mu godewa Allah daya sako mu a cikin jerin ma'aurata" kara nutsuwa tayi sosai tana sauraronsa... "Bilkisu banyi alkawarin a kullum zamu kasance cikin farinciki ba, bance ba zamu sab'a Dan kinsan hausawa na cewa zo mu zauna so mu sab'a! Amma ni Ibrahim nayi miki alkawarin rikeki da amana, zanyi miki adalci a zaman mu, banyi alkawarin bazan kara aure ba, dan kamawa hakan keyi saidai inaso ki sani bani da burin k'ara auren wata mace daban bayan ke, zan kula dake da jiki da aljihuna zan killace ki anan tsawon rayuwata" ya nuna saitin zuciyarsa "bazan tab'a barinki ki sha wuya ko ki shiga damuwa ba ta dalili, zan tsaya miki na kare dukkanin hakkokin ki da suka rataya a wuyana, sannan ina mana fatan auren mu mai dorewa ne har mutuwa" ya karasa fad'a yayi yana murmushi tare da kallon fuskarta, can ciki ta amsa da Ameen, still kanta a k'asa... "Game da Samiha kuma, abar mutaya ta da murna ce, Dan ta samu kubuta daga babbar sabo, wannan wata dama ce Allah ya kara bata muna fatar ya zama silar shiriya a gareta, addu'a ya kamata ki tayata da Allah ya zaba mata mafiyi alkhairi damuwa ba zata canja komai ba, kinji!" Kai ta gyada masa kawai tana jin tausayin Samihar da gaske tare da yi mata Addu'a dan tafi kowa sanin yadda take k'aunar Mu'azzam..... "Nikam wannan salihancin da kika aro kika yafa yanzu ban gane ma'anarsa ba" yace yana janyo ta jikinsa, zamewa ta fara yi tanaso ta tashi ta gudu part din ta, dan har yanzu bata manta first night din su, bare yadda taga wannan rawar kan nan nasa ai tasan zata gayawa mutanen Gwarzo(ai kila hadda na Bauchi🤪) "Yaya bari inji inyi wanka, wanka nakeson yi" sarai ya gane wayonta, kara riketa yayi tare da rad'a mata a kunne "karki damu yanzu zamu tare idan muka gama cin kazar amarcin tamu" ware ido waje tayi tana fadin ta koshi ita kam, dariya ya shiga yi mata tare janyo ledar da ya shigo da ita, kaji ne dakwale sai turiri suke sun sha kayan alatu, fresh milk, exotic and hollandia..... Da tsokana da wayau da dabara ya samu ta yadda sukaci kazar sannan sukayi wanka a taren kamar yadda ya fad'a, duk yadda take alkunya tana kaucewa sanda Mu'azzam yayi ya tabbatar da ta saki dashi Dan yaci burin raya wannan daren ya kafa shi cikin darare masu daraja garesu...... A wannan daren masoyan sunyi kukan farinciki, taga tsantsar k'auna Mara algus, wacce bata taba tunanin samu a gun wani ba bare tsadadde, nagartaccen namiji kamar Mu'azzam, ta k'ara tabbatar da ba wata a zuciyar mijin nata face ita, wannan dare ya kasance dare mafi daraja da kafa tabbatar ciyar k'auna a zuciyar Ma'aurata...... ********* Bacci take sosai Hani'an Wanda ke nuni da tana enjoying baccin nata sosai, yafi minti 10 zaune a gefenta yana aikin kallonta, sai yayi kamar ya janye blanket din da take cukuikuye a ciki, sai kuma ya fasa.... Wrist din hannunsa ya kalla sannan ya sake kallonta yana murmushi "hmm Sleeping beauty" sannan ya fara shafa fuskarta a hankali... Cikin baccin taji alamun ana tab'a ta, turo baki tayi tare kwaba fuska, murmushi ya kara Saki yadda tayi kamar wata baby doll, sunkuyowa yayi ya manna lips dinsa akan nata yana tsotsa.... Bud'e idanuwa ta fara yi a hankali har ta ware su gaba d'aya, inda ta tabbatar ba mafarki take ba shidin ne a zahiri, saurin lumshe ido tayi tana murmushi, dariya ya fara yi mata yana Jan faratan kafarta bayan ya yaye mata bargon... "Marhaba biki habibty, barka da farkawa ma heart" kara jan bargo tayi tana rufewa duk jikinta har kanta, kara janyewa yayi.... "Common Raguwar matata baccin ya isa haka kada yunwa ta kama min ke" Saurin mikewa zaune tayi tare da kallon agogon da ke manne a bango da kallo zaro ido tayi ganin har goma da rabi, sannan ta maida kallonta gareshi tana kwaba fuska kamar zatayi kuka...... *nafa zama lazy sai hakuri fans😅* *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *🌐DUNIYA MAKARANTA​​🌐* *_Idan mugu ya hadu da na kwarai nan take asirinsa yake tonuwa. In da wahala take shi ne idan mugu da mugu suka hadu, wanne ne ya fi Mugunta! Idan na kwarai guda high suka hadu wanne ne ya fi alheri?_*👌🏻 *Page* 4⃣7⃣ _____"Oh! Babe kinfa koyi rigima, me akayi maki kuma yanzun daga tashin ki?" Yace yana kama hannunta ya mik'ar da ita tsaye yana kallon cikin idonta... Tura baki tayi tare wal da ido wanda ya kusa sumar da shi, baisan time dinta ya rungumeta ba, fadi yake a ransa dis gal wanna drive me! go gaga... "To ba kai bane ka wani barina inata bacci har wannan lokacin gashi ko break fast ban maka ba, har 10 after" tace cike da shagwaba tana turasa a hankali daga jikinta, tasan halinta sarai zai iya canja salon kai tsaye... "Naga ko yanzun da ban tada ke ba, ba tashin zakiyi ba, Oh ni Ibrahim tawa ta sameni na had'u da lazy women" bara baki tayi tana kukan shagwaba tare da bubbuga kafafu tana dukan k'irjinsa, matse ta gam yayi a k'irjinsa ko motsin kirki ya hanata tayi sai dariya yake mata, ita kuma sai mutsu-mutsu take tana ci gaba da kukan shagwaba "Allah ni ba Lazy bace Yaya, duk jarumtata kake kirana lazy, ko ka manta nifa kwaila ce..." Duk cikin kukan shagwaba take maganar.... Daina dariyar yayi amma fuskarsa a yalwace da murmushi, cikin shaukin k'aunar ta ya d'ora lips dinsa forehead nata tare da sauke mata kiss, idanuwansa a lumshe yace cikin sanyin murya.. "Aini matata tafi karfin kwaila, ta zarce mata dubu, matata full option ce, zinariya kasaitacciya, ishasshiya a cikin mata, matata Bilkisu mai gadon zinari Queen of ma world" sosai kalamansa suka sanyaya mata rai kuma daga ji tasan ba karya daga zuciyarsa suke, murmushi ta saki har yana jiyo sautinsa... "Hey you! Ji ta sakani sai zuba nike oh wannan rigimammiyar kwailar nan tawa ta koyamin zuba" ya sake fad'a bayan ya saketa tare da rungume hannayensa a kirji yana kallon murmushin nata bai ban sha'awa... "Uhum! Wannan d'an gayen mijin nawa badai yanga ba, ka iya basarwa da tsare gida, but yanzu na gama ganoka tsab! I love ur style angon Aymah kwailah!" Tace dashi bayan ta fara takawa zuwa gabansa tana zagayesa tare da wani watsa yatsu tana jujjuya kwayoyin idanuwanta yanayin yadda take juya bakinta da lips nata duk na daban ne cike da salon cin nasara, aiko tayi nasarar wargaza duk wata nutsuwar sa, sakin baki yayi yana kallon ta kamar wani soko.... Murmushin gefen baki ta saki tare da kamo kwalar rigarsa da hakoranta kamar zata cijesa sannan ta d'anyi tsalle ta bugi habarsa alaman ya kama bakin, kashe masa ido d'aya tayi tare da d'aga masa gira tana murmushin iya shege sannan ta doshi kofar fita daga dakin..... Yayi sakwanni daskare a gurin tsabar mamaki, tsakanin daren jiya zuwa yau ta shayar dashi mamaki da salo-salonta na d'aukar hankali, Tabb lallai d'an hakin da ka rena...shike tsole maka ido... Murmushi ya saki tare da nutsa yatsunsa cikin kwantacciyar sumar kansa ya shafo, taku d'aya zuwa biyu ya rikito ta zuwa jikinsa abinka da dogon mutum, kyakkyawan masauki yayi mata a jikinsa tare watss mata narkakkun idanuwansa "I love ur style too" taji ya fad'a yana kallon ta ba tare daya d'auke idanunsa, lumshe ido tayi dan idanuwansa ba karamin nakasa mata zuciya yake ba..... "Yaya pls zanje na had'a mana kari?" Tace sanyaye still idanuwanta a lumshe, sama kawai taji anyi da ita kafin tayi kyakkyawan junkuri har ya d'auki hanyar toilet da ita "Aa pls yaya break d'in fa" hannu ya mata a baki yace "shitt no more talk" shirun tayi tana tuttura baki, tura kofar yayi ya shiga da ita tana tsaye ya had'a mata ruwan wanka bisa umurnin karta yarda ta matsa a gun daya bata, zuwa yayi zai sabule rigar baccin tayi saurin rik'ewa tana fad'in "nidai zanyi da kaina Dan Allah" harara ya jefa mata "oganki kikewa musu..." "Sorry amma dan Allah ka barni nayi Yaya time is going pls" tace cikin muryar rarrashi, murmushi ya saki tare da lakuce mata guntun hancinta "ga tsiwa sai tsoro! Farar kura kawai" murmushi ta saki "agreed Sir!" Ta fad'a tana turasa.... "Love you, am waiting" yace shima d'auke da smiling tare da mata blowing kiss tsakanin yatsunsa sannan ya ja mata k'ofar... Sip nasa ya bud'e ya fito mata da kayan da zata saka a gefen da ya jera mata kayanta ciki, pencil jean white ya fito mata dashi tare da top navy colour my white vest ciki, undies din ma duka white ne, ya feshe mata da turare ya d'ora kan bed tare da ficewa daga dakin... Murmushi ta saki bayan ta fito ganin kayan da ya fitar mata, wato dai yana son English wear din da take sakawa, cikin sauri tayi shafe-shafenta da fente-fententa bakin yayi rad'au da maroon lips stick, ear ring silver simple ta saka, tare da jera manyan necklaces na bits black and maroon, high hill ta manna kafar ta..... _Wow fans Ku kissama Aymanan Ku_😘👌🏻 Karar takun takalman ta ne daga stars ya sanar dashi isowarta "fatabarakallahu akhsanul khalikeen" ya furta a fili tare da zuba mata idanu da wannan murmushin nata ta iso gurinsa tare da tsugunawa ta d'ora tafukan hannayenta kan cinyarsa "my bae yaka ganni" tace tare da mik'ewa tana juyi a gabansa, sosai ya shagala da kallo zubin halitta da Allahu yayi a gurin, cikin da zakuwa da zafin nama ya fizgota ta fad'o jikinsa, zaro ido tayi baki a sake saboda unexpected ne ya zo mata "1+1" ya fad'a yana dariya tare da rufe mata bakin... Kunya ce ta ka mata ta boye fuskarta a k'irjinsa tana d'an bubbugawa k'irjin nasa "nidai banaso yaya is OK ur d winner bari naje na samar mana koda ruwan zafi ne, musha tea am hunger" tayi yunk'urin tashi... Maidata yayi "harkin karaya kuma jarumata? it ok bama wannan ba, muna da break fast since 9 aka kawo, Momy da Ammi sunce ki huta shiga kitchen for a while kawai ki kula da....." Ya kashe mata ido... Hannu tasa ta rufe ido, k'ara dukansa a k'irjin tayi tana hararansa "Ash!!wash!! Yace yana kama gefen k'irjin satin zuciyarsa.. D'an rud'ewa tayi " Menene?" Kama hannunta yayi ya dora a nasan dake kan zuciyarsa, yana ciccize lebe kamar gaske "ba kece ba, bayan kin cikata da kaunarki tunbul kuma kike dukanta salon kisa ta fashe ko?" Murmushi tayi wadda ya bayyana jerarrun fararen hakoranta yanayin yadda yayi maganar kamar yadda take masa da shagwaba.... "C'om yaya banason kana zama da yunwa, muje nidai cikina is empty" taja hannunsa "yes ma'am" haka suka jera a tare suka isa dining din, break fast suka gudanar mai cike da salon k'auna...(❤Allah yabar soyayya sannan ya had'a kowa da masoyinsa na gaskiya🤲🏻) *********** Daren ranar Samiha sosai ta raya sa da Sallah da karatun Qur'an, istigfar, godiya ga Allah, tana kuka tana nuna kaskancinta da tsantsar nadamar ta zuwa ga mahaliccinta, Wanda ya kasance shine karo na farko data taba yin tsayuwar dare, yo sallar farillah ma sai tayi mata suger, rungume al-qur'an sosai a k'irjinta tana zubar da hawaye ba zata iya tuna when ta d'auki Qur'an ta karanta ba, lallai tayi sake da yawa saidai tana godewa Allah, ba baiyi mata talala ba ya ankarar da ita cikin lokaci, sosai takejin son Ammi a cikin ranta dan itace ta bata wannan shawarar lokacin da ta sameta a dakin tana kuka, lallai Qur'an waraka ne dan sosai wasu kashi na damuwar ta sun tafi, ta kuma yadda ta d'auki kaddarar rasa ya Mu'azzam, duk da sai a hankali zata saba da hakan amma ta d'au alkawarin yaki da zuciyarta iya iyawarta, ta kuma sanya Ummanta a addu'a Allah ya sakata cikin masu rabon shiriya, kamar yadda suka samu sum.....(zunubin mu koda ya tokare sama Allah S.W.T zaizo mana da gafara cikin duniya, muddin mukayi tuba mai kyau _taubatan nasuhaa_ kofar tuba kullum a bude take mu tuba zuwa ga Allah tun bamuje gargara ba) B'angaren Umma kam zamu iya cewa kusan haukacewa kawai, tama rasa mai ke mata dad'i ga wani karamin daki da aka bata ba komai a ciki daga 'er katifa sai fanka, dake gudu kamar tsohuwar mota.... Hankalinta bai gama tashi ba, sai da dare yayi aka turo mata wasu yaran gidan da tuwo miyar kuka, kallo d'aya tayi musu zuciyarta ta fara tashi, kin ci tayi, Dan tasan ko kaisa bakinta ba zata iyayi ba, gidanta ta tuna sai abinda ranta yakeso zata saka maid su dafa mata, ba ruwanta da iskan fanka Ac ce a ko'ina, ba zata tuna when sauro ya cije ta ba, tama manta da akwai sauro duniya, yau kuwa gata gashi sai bata yake dan maganin sauron da aka saka baida wani amfani gunta bai tare komai ba..... Kafin taga safe tayi wata biji biji da ita ga damuwar zuciya gata jiki, duk sauro ya lalata mata farar fatar da da cizo, ga yunwar cikinta da kad'ai ta gama isarta dan rabonta da abinci tun safiyar jiya..... Tun kan gari ya gama wayewa ta suri jakarta ta saki jiki ta sulale daga gidan, saida tayi tafiya mai Dan nisa sannan ta samu isa titi zuwa lokacin gari ya gama wayewa, napep ta tara tace ya kaita gurin cin abincin na kusa, hakan kuwa akayi, Allah ya sota tana da kudi a jakar har 10k sai lokacin taji 'er nutsuwa, haka tahau kan abincin kamar wata kamun yunwa sanda ta kammala ta samu nutsuwa sannan hankalinta ya dawo jikinta "boka mai da nisa" ta fad'a ranta a bace, biyan kudin abincin tayi sannan ta fita ta sake ta tari wani napep d'in........ Shiga tayi tare da yi masa kwatancen inda zai kaita........ _Sauka lafia customer mai gobe da nisa🤣_ *Sorry fans, kuyi hakuri dani dai, na shiga busy ne, wlh na matsu na kammla nima tashi sai yi nice yaci karewa😕😫* love you all😍🤗 *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *A duk lokacin da shedan ya had'u da iyalansa ba abinda ke saka su farinciki kamar Abu uku:- musulmin da ya kashe d'an uwansa musulmi, mijin da ya saki matar sa, mai rowa dan gudun talauci👌🏻* Duniya makaranta✍🏼🌍 *Page* 4⃣8⃣ ______tafe take kamar ta kifa d'akyar ta samu haye tutsetsen dutsen duk zuwan da take bata taba jin wuyar haurawa ba kamar yau ba, da nisha da zufa da komai ta isa gurin bukkar, wani wari taji yana tashi tun daga bakin bukkar, toshe hanci tayi tare da kutsa kai ciki..... Zaro ido gaba daya waje tayi tare da d'ora hannuwa akai, tana ihu, jikinta kyarma yake awa mazari, cike da tashin hankali take kallon gangar jikin bokan nata dake yashe a kasa, ciki yayi suntun ya kumbure alaman ya dad'e da mutuwa kenan, wannan warin da take jiyowa daga waje Ashe shine, da sauri ta fice daga bukkar har tana cin tuntub'e, kuka take sosai hadda majina sai sharewa take da mayafinta, bakinta banda kalaman tsinuwa wa bokan ba abinda ke fita dama tazo ne ta yi masa tujara akan cin amanar da yayi mata na lalata mata 'ya daganan sai ta canja wani sabon boka amma ganin bokan a mace wulakance ba karamin tayar mata da hankali yayi ba, jikinsa yayi sanyi sosai da sha'anin biyar bokaye..... Sai bayan azahar ta isa gidan Yayan nata a jigaye wuji-wuji da ita, a tsaye ta samesa tare da matansa tsakiyar gidan kirco-kirco Neman duniya sunyi mata sun rasa inda ta Shiga, gashi Hafiz ya kawo mata kayanta dazu ya tabbatar musu bataje gidan su ba, wannan ne ya kara tayar ma yayan nata hankali kaddai guduwa tayi wani gun, dan tun jiya ya fahimci a hargitse take, tsoronsa d'aya kar taje ta sakeyin abinda ba shine ba, ko kuma wurin haukanta taje ta fada mugun hannu, Wanda baya fata duk Girman laifinta har gobe ita 'yar uwarsa ce, bazai so ta cutu ba ko yaya ne, wannan ne yasa ya tayar da hankalinsa ya kuma tayar ma matansa nasu... Kallon tuhuma ya bita dashi tare da watsa mata mugun, Wanda ya saka 'ya'yan cikinta yamutsawa tare da hadiye yawu "ina kikaje tun safe Suwaiba!?" Ya tambaye ta a tsaurare tare da tsare ta da ido..... Kame-kame ta fara tare da fad'in "um...uhm..dama...naje gidan wata k'awata ne shine na biya kasuwa na sayo wannan" ta nuna masa net din da ta siyo tare da gaya masa d'akyar ta iya bacci jiya........ Wani kallon ban aminta dake ba ya bita dashi "wallahi tun wuri gara kisan me ke miki ciwo Suwaiba, kedai ba yarinya bace gara ki maida hankalinki ki Dena biyewa rud'in duniya, ba abinda wanin Allah zai amfana miki dashi sai bata, ki kula dakyau duniya ce gidan banza ki nutsu kiyi tunani da kyau" yana kai nan ya buga rigarsa bayan ya gaya mata sako nan daki da Hafiz ya kawo mata na kayanta.... Jiki a sanyaye ta shige dakin, yayin da matan suka tabe baki tare da binta da harara wata hadda mata tsuki, gefen kafitar ta zauna tana mamakin matan yayan nata kamar basu ne 'yan korenta ba musamman lokacin bikinsu Samiha dasu akayi komai sai wani bin da suke kamar jela anan gidan suka kwana kuma sune ta sanya gaba akan komai suka wawushi kaya suka wuce amma wai yau itace abar wulakantawar su, lallai sun cika 'yan halak.. Janye damuwar su gefe tayi tare da duba kayan da Hafiz din ya kawo mata, trolley har biyu shake da kayanta sai kenan tazo zama ne, ga Dadyn su ko ta kanta bai bi kota kira baya dagawa me kenan, aiko muddin ta kara sati a gidannan bone ya cita, amma Meye mafita a gareta, ya za'a yi ta samu Dady ya fara sauraronta, yanzu ina ma zata samu wani bokan, idan ma ta samu ina kudin suke na kai masa?? "Lallai dole na nemo mafita dan burina bazai tafi a banza ba...." Ta fad'a a fili....... ************ "Kasan me Yaya?" Aymanah ta fad'a tana duban cikin idonsa, zaune yake kan three seat, tayi filo da cinyarsa, tana kallon series din da ake haskawa a Mbc Bollywood, na Madhubala, inda bata fahimta ba shike fassara mata dake da larabci suke gabatar da shi, wasa yake da gashin kanta daya barbazu a cinyar tasa dan ya kunce mata ribbon da ta kama shi dashi yace yafi masa kyau a hakan, shima maida kallonsa gareta yayi "aa sai kin fad'a" ya amsa mata.... "Nifa har yanzu mamaki nike Allah Yaya" "Game dame fa?" Ya tambayeta.. "I can't believe Yaya ka Dade kana k'aunata amma ban sani ba, waima tsaya tukun tun yaushe ka fara??" Murmushi yayi kawai, saida ta fara tura masa baki dan sannan yace "oh kinfa koya rigima baby to me kikeso nace ne?" Kara turo bakin tayi "oho ni kama barshi na fasa saurara tunda sai ka ja min rai" d'agota yayi sannan ya rungumeta sosai a jikinsa.... "Nima bazance ga ranar da na fara kaunarki ba, abinda kawai zan iya cewa shine, na rayu da k'aunarki ne a raina ne, watakil ma tun ranar da na fara ganinki ne" tun da ya fara maganar tayi lakwas a jikinsa tana kallon yadda dan ficicin bakinsa ke motsawa wato abin daga jininsa dan yadda yake yamutsa fuska idan yana magana kamar baya har yau hakane bata canja xane ba, Wanda bai fahimci halinsa bane sai d'auka yanga yake masa ko kyamatar sa yake... "Uhum yaushe kenan kake nufi? Wai ranar da ka hantare ni a gidan Hajja?" Girgiza mata kai yayi alaman Aa "tun ranar da aka fara turamin fotonki kina jinjira nake nufi" zaro ido gaba d'aya tayi, dariya yayi tare da hure mata idon... "Ragemin wannan na mujiyan naki masu firgita ni a kullum" ya kara sa yana kashe mata ido daya, itama dariyar tayi tare da kara kankamesa, wani irin sonsa ne ke huda duk wata gaba ta jikinta yana ratsawa... " I can't believe Yaya....." Uhum nima a lokacin ban gane k'aunarki nike ba gaskiya na d'auka kawai dan kin kasance 'yar Uncle Hashim ce da aunty Fatima, but time going on na fahimci k'aunar ce dai nake miki kuma irin ta aure, hmmm bakisan how much I hurt b'cos of you ba, karfi da yaji naso na yaki ce ki a raina a lokacin, dan a ganina karshen kunya kenan wai ke nakeso Sorry to say kwaila dake, dan watakil da auren k'auye nayi zan haifi kamarki" ya karasa yana mata dariya, itama dariyar takeyi saidai tana dukan k'irjinsa a shagwabe.. "Kinsan ma tashin hankalin lokacin kin riga kinyi nisa a tsorona, kin ma san meyasa kika fara tsorona??" "Ka dauka zan manta ne tsawa kake min kana kamar zaka dokeni" dariya yayi "clever gal, amma kin manta kece kin cika rashin ji da kukan banza a lokacin, ga Hajja na Neman sangartaki shiyasa nake maki hakan amma bawai rashin so ba kin gane" jinjina kai tayi alaman gamsuwa.. "Sannan lokacin da na gane sonki nake da gaske, rashin fad'ar shi ne alkhairi a gareni duk da nasan I so much burn inside, amma nasn Dana fad'eta a lokacin da rikicin cikin gidanda ake a lokacin ya zarce tunani kinsan komai dai ga kuma samiha da ake ta turamin a lokacin...." "Ake tura maka ko kake sonta dai" ta katse shi... Murmushi ya Saki "Aymah Habibty kenan! Ban taba k'aunar wata 'ya mace ba bayan ke" "U mean har aunty Samiha?" Jinjina mata kai yayi "to Amma ai kai da kanka ka amince da aurenta?" "Saboda kinyi rejecting d'ina ba" kara zuba mishi ido tayi tana son gasgata zancensa.. "Nasan ba zaki fahimci komai ba a time din, tunaninki kawai na cika tsanani musamman a kanki sai kika d'auka tsana ce kawai, but da kin kula a lokacin nafi miki tsawa ne musamman idan na ganki da Hafiz ko Adnan dan a tunani na waninsu zai iya cusa mini soyayyarsa musamman yadda naga kuna da shakuwa a tsakanin Ku, hmm I can't explain everything but a sanadin ki ne na ke dadewa ban dawo kasar ba dan banso amin maganar aure saboda ke nike jira duk da cewa bansan taya auren mu zai kasance ba, dan ban taba sanin wasiyya uncle ba idan ba ranar da aka fad'eta a gaban kowa ba" jinjina kai tayi..... Wannan shine son maso wani kenan Samiha na jiransa shiko ita yake jira ba tare data sani ba, to ai har gara Samiha yasan da ita... "Hmmm I can't explain my feeling lokacin da kika ce ba zaki aureni ba, naji matukar zafi a raina sosai shiyasa na amince da auren Samiha kai tsaye ba tare da dogon tunani ba, don bansan kalar zafin da mutum keji ba idan Wanda yake k'auna yayi rejecting nasa ba sai time din shiyasa na kasa yiwa Samiha abinda kika yimin duk da ba ko kwayar sonta a raina, saidai kar taji zafi a ranta kamar yadda naji kuma inajin nauyin Dady musamman yadda ya nace saidai inna amince....." "Niko sai wauta ta debe ni na dubi kwayar idon Abba nace ban amince da aurenka ba saboda butulci na" ta katsesa tana jin zafin abinda ta aikata "c'om babe aina miki uzuri daga baya tunda Nina ja komai da kaina, kuma ai iya gaskiyarki kika fad'a ko?" Zatayi magana bell door ya katseta, kallonsa tayi tare da tashi daga jikinta, wrist din hannunsa ya kalla 1:30pm.. "Kinga ma it almost time 4 salat, bari na duba waye zan wuce masjeed daga can... Narai- narai tayi da ido kamar zatayi kuka " Hayatiy to ci gaban labarin fa" murmushi ya saki tare da peaking forehead nata "ya miki dadi ne?" "Sosai I really enjoy" "Bari na dawo to muci gaba, kinga anata danna bell door din" jinjina masa kai tayi tare blowing masa light kiss a lips... Nusaiba da Amira ya samu a kofar gaisawa sukayi sannan ya fice, sauke numfashi Nusee tayi "Yaya ho, an gama shanya mu anacan ana love shine ake wani tsare mana gira" dariya Amira tayi "to ya son ranki so kike ya mana wasa kamar besty? Ko kina masa abinda take masa ne?" Saurin baki tayi tana dariya tare jan hannu Amira akan su shiga tana fad'in "rufamin asiri wannan saidai ita nidai barni da ya Hafiz dina".. Jiyo muryar su da tayi ne ya saka ta daka tsalle tayo kansu "me! Lallai yau gidannan da manyan mutane a cikinsa" tana dariya tare da kama hannayen su... Hararar wasa Nusee ta sakar mata "uhum so love manya! Bayan an gama shanyamu ko" dukan wasa takai mata tau 'yar magana zaki fara ko, naga dai love dinnan kowa nasha da nasa habibin bayan ma kun koramin shi" "Aa beyi zafi ba mu tafiyar mu ki dawo da kayanki" cewar Amira itama cike da tsokana, dariya sukayi a tare sannan suka isa cikin falon, suna ma juna tsiya... Basu zauna anan ba suka wuce part d'in ta don gabatar da Sallah, Wanda tun jiya da ta dawo sai yanzu ta leka amma ga mamakinta sai ta samesa tsaf sai kamshi ke tashi ko'ina a gyare... Murmushi ta saki tasan aikin gogon nata ne yasa aka gyara, sosai taji ta kara tsunduma a koramar sonsa........ *Marraha home of peace, na gaida Ku kyauta ana tare iya wuya en uwa😍😘* *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* *🎀🎀My dearies friends, I really appreciate with ur warms wishes for me, thanks so much my true fans, especially my sweet once's* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻😘😘😘😘😘😘😘😍😍😍😍 *Maryam Y Zango*(ummu khady) *Hafsat Musa*(indon kauye) *Queen of beauty* *My Qwlly* *Feenat Aliyou* *My Aunty Sumee* *Aunty Ummi* *Maman zee* *Members of marraha* *Duniyar makaranta2* *Maman ussey novel* *Hausa novel* *Sweery novel* *Matan kirki* *Aminan juna* And so on ur good enough thanks Jazakumullah bi jannah👌🏻🤝🏼 *Page* 4⃣9⃣ _______Suna Kammala sallah, ko add'u'ar kirki basu yi Amira ta fara mita ita fa abata abinci nan itama Nusee tace ai kuwa dan ba wani bak'unci, kama baki Aymanah tayi tana binsu da kallo kafin tace..... "Ai dama bama kunce Ku baki bane anan, saidai naga ko wacce tana da kafafu da hannuwa kuma tana da idanu, so a tashi a shiga kitchen danni ba abinda na dafa a gidannan, breakfast ma daga gida aka kawo mana waina ce na kuwa san bakwason waina". " waina!" suka fad'a a tare, "tana ina?" Cewar Nusee, Amira kam ta kasa magana sai baza ido take taga inda zata hangota.... "Gata can Dinning din main Parlour..." Rige-rigen ficewa daga part din nata suka shiga yi, danko hannun Nusee Amira tayi da taga ana shirin runtumawa da gudu.... "Allah baki isa ba, salon ki rigani ki cinye" dole suka jera a tare suka fice da sauri yadda Amira ta danke Nusee kamar Dan sanda ya cafko mai laifi, da dariya Aymanah ta rakasu kafin ta kwashe dardumomin da suka yi sallah ta nade, cikin daga murya take fad'in "Anya kuwa matan nan, da alama yayyi na sun hura muku iska"...... Wata dariya ta k'ara, fashewa da ita lokacin da ta samesu a dinning center din, tsabar rashin hakuri cikin coolar wainar aka juye miyar kawai sai turawa kawai suke suna zare ido ba mai iya magana..... " Hhhhhhh! Gaskiya aikin yayyina yayi kyau, barin taimako muku da ruwa dan da alama ta tsaya muku a wuya amma tsabar fitina ba mai iya tashi ta dakko" Baki cike Nusee tace "Eh Besty nah Dan Allah taimako" itama ma Amira sai kada kai take alaman ta kawo musu, dariya ta sakeyi "oh su Meerah ko magana ba a iyayi lallai kin harbu da yawa"... Ruwa da lemo ta girke musu, tana ci gaba dayi musu dariya da yi musu shakiyanci son ranta, saida suka cinye ta tas, suka Dora da ruwa da lemun sannan sukayi bakin mayar mata da martani... "Ke kin jiki da wani zancen, keda kika yi cikin ko sani bamu yi ba sanda akayi mana asara muka sani, kika wani linkeni a baibai waike bakyason Yaya ashe-ashe kina lallabawa kina zagayewa kina amsar kuri'a" dariya sosai ta bata, dukan wasa Takai mata... "Allah baki da kirki besty wai karbar kuri'a, to ai gashin kema kin karbo har kinci zabe, zakiji idan dadi ne mulkin!" Nan suka wuni a tare suna zolayar juna musamman Aymanah sai yi musu tsiya take hadda cewa sune a ciki yanzu, itakam ba yanzu ba, school ma zata koma tayi course na karbar haihuwa ta wata shida tazo ta karbi haihuwar su, dake cikin Nusee mai watanni biyu na Amira satittika ne, ko wata bai ba... Sai bayan Asr suka wuce bayan sun gama kwance-kwancen su, sosai zuwansu yayi mata dadi suna wucewa duk sai taji gidan ya mata Girma, taji ta so lonely, wayar ta ta dakko ta turawa Khaleel din ta love text sannan ta koma part din ta ta sake sabon wanka.... Kwalliya sosai tasha kamar mai shirin zuwa Party, ta hade cikin Doguwar riga ta kanti Dark green tare da yane kanta da siririn farin veil, bayan ta gyara gashin ta kamasa da babban ribbon, high hill ta saka tare da saka necklace na bites da bangles duka na irin many an bit dinnan masu tsada wow Ku hango Aymanan Ku fans..... **************** Ya Mu'azzam direct bayan ya fito daga masjeed Family house nasu ya wuce, bai samu Abba da Dady ba a gida, Abba na kasuwa Dady kuwa ya koma wurin aikinsa.... A part din Inna ya yada zango yana shiga ta fara washe baki tana mishi sannu da zuwa, cike da shakiyanci ya wani tsugunawa yana gaida ita, kama baki tayi "Lallai Ibrahima ka kai Dan duniya ni zaka zowa da wannan sabon salo, tunda na baka Balki ka tafi da ita ko?" Dariya ya saki bayan ya mike tare da zaunawa kan seat yana fuskantar ta "Allah yaja kwana dai Hajja tamu, ai wannan gaisuwar ta musamman ce Uwar gida na" jefe sa da filon kujerar tayi... "Ungu nan shakiyi ni kake d'agawa gira, lallai yaron nan ka zare, tashi barmin d'aki kaje kayiwa Fatima ita da ta haifi Balkin" mik'ewa yayi yana murmushi... "Base kin korani ba dama tafiya zanyi, kuma ba kedai takwarar ta k'awalliyar ta ke zanyi ma ba maman Munir ba, sannan sunanta Bilkisu not Balki ki kiyaye dan banaso ana bata mata suna" Wani filon da dauka ta jefa masa yayi saurin gocewa tare da ficewa daga falon yana dariya "ja'iri ni zaka yiwa dogon turanci zaka same ni ina zamana"..... A part din Momy ya samesu har Ammi da sauran yaran, su Momy na gyaran teburin abinci, gaidasu yayi, suka amsa Momy na tambayar ya 'yarta Aymanah, ya amsa da tana lafia, Samha da Samiha ne suka fito daga kitchen da sauran food flask din, ga wani basket da aka saka wasu food flask a ciki su Munira sun dakko... Aje kayan hannunsu kan dinning d'in, sannan suka fara gaida shi, Samiha na sanye zunbulalen hijab har kasa, jikinta a sanyaye tun da ta jiyo muryar sa kirjinta ke bugawa, kalonsa tayi a sanyaye ta gaida shi, shima kallo d'aya yayi mata ya d'auke kansa yana amsa gaisuwar su... " yawwa gara da kazo ga naku abincin, kun huta zuwa" Momy ta fad'a tana nuna masa basket din hannun su Muneera.. "Kuma ka gaya mata tayi girkinta gobe Dan ba zamu dauki aika mata abinci ba ita kuma ta nade kafafu" Ammi tace.. "Oh! Maman Arif inaga ba zamu shirya ba, ina ruwanki da 'yata? Kinga ba ruwanki da sha'anin mu" murmushi Ammi tayi tare da daga Arif sama daya taho yana daga mata hannu "na daina Mommy, Arif muje ayi wanka" itama Momy Murmushi tayi "yafi dai" "Kawo shi nayi masa Ammi" Samiha ta fad'a dake ita samhà tuni tabar falon, bata shi tayi itama ta fice zuwa part din Ammin tunda acan suke zaune... Cike da tausayi Ammi ta bita da kallo tana mata add'ua a ranta... Shima sosai yake tausaya mata danne wa kawai yake kada yayi weaking heart nata, ko komai 'yar uwarsa ce kuma ta taba zama wani bangare na rayuwarsa wanda he can forget ever.... Adil ne ya shigo yana kuwan kiran Munir da su munira, fadeel, Fadeela, Sageer, Sageera da Arif akan Abba ya dawo, suna yin ido biyu da Mu'azzam ya sha jinin jikinsa tare da komawa da sauri ya doko sallama tare shigowa a nutse ya gaida su Mommy sannan ya gaida yayan nasa, amsawa yayi sannan ya cewa su Momy zaije ya dawo kafin Abba ya huta sai su gaisa sannan ya wuce gidan Abokinsa Abdallah yaje sai bayan asr ya dawo bayan sun sha hira sosai da Abdallah da kuma wani friend Nasu Sulaiman a can din... Sai after 6 yabar gidan nasu bayan su d'an tattauna da Abba, sannan ya shiga ciki yayi Sallama dasu tare da d'aukar abincin.... Yanayin Nisan da ke tsakanin hotoro da Gauron dutse, ga yanayin cunkoson garin, babban gari kamar kano daya tara jama'a kuma 'yan kasuwa dole ya kasance garin cunkoso, magrib ya tsaya ya gabatar a masallacin unguwar sannan ya karasa gida...... Aymanah dake main parlour tana karatun Al-Qur'anil Kareem bayan ta kammala sallah, jiyo dirar motarsa ne ya sakata rufe Qur'an din dama takai Sumuni, ta mayar dashi gurin zamansa sannan ta linke Hijab din da darduma dan anan Parlon tayi Sallar ta duk tsoro ya fara shigarta ganin duhu yayi bai dawo ba, karatun da yayi ne ya saukar mata da nutsuwa(Al-Qur-an kenan maganin da babu irinsa kome ya dameka koma ga Allah ka rungumi Qur'an yafi kowanne magani).. Da Sallama ya shigo ya shigo a bakinsa, yana baza ido ta ina zai ganta, Tana labe ta bayansa tana kallonsa sulalowa tayi ta rungumosa ta baya tare da cewa "Wa'alaik salam warahmatullah, Hayatiy, habibi Nurul kalb, marhaba bika Angona" kwantar da kanta a bayansa tayi.... Janyo ta yayi ta dawo gabansa "wow u look like take away my Queen" turo baki tayi "ba wani nan bayan ka barni ni kadai, tun dazun na maka kwalliyar baka zo ka gani ba har ta goge" cike da Shagwaba take maganar... "Oh sorry Habibty ur Khaleel is begging u dear!" Ya fada a hankali tare da saka hannayenta ya kama waist nata tare da hugging nata tightly ya sauke mata peak a goshi, a Hankali ya furta.... "Still u looking gud so cute and I saw ur text I really appreciate for it, thanks" murmushi ta saki tare da d'an janyo kwalar rigarsa ya sunkuyo ta sauke masa light kiss a lips... "It's under ur favour dear, but ina ka shige?" "Uhum! Gida naje duk suna gaida ke har gun Abdallah naje shima yana gaida ke da Salma(matar sa) ga nan dinner inji Mommy, and Ammi tace ki shirya shiga kitchen gobe" "Allah sarki Mommy nah, wannan dawainiyya haka, oh Ammi tayi cooling nima ai dama gobe zan shiga din"bayan ta dauki basket din tare da nufar dinning..... Dariya yayi " Ai Mommy tace kisha zamanki kidai kila dani kawai" ya daga mata gira tare da cewa zaije ya watsa ruwa kafin a kira Isha, tace ya bari tazo ta had'a masa ruwan, hutar da ita yayi tare da cewa sauri yake ta bari ya dawo sai suyi na musamman.. Murmushi ta saki tare da cewa a fito lafia.. Cikin sauri yake saukowa yana duba wrist nasa ganin it almost time for salat, fara kal din Jalabiya ce ya saka ya Dora taba kaji a hadith a tulin sumarsa sai ya fito kamar wani balarabe sosai yayi mata kyau aiko saida tace "kayi kyau hayatiy" ya kuwa ji dadi Dan ya nuna, peck yayi mata sannan ya wuce cikin hanzari, itama tashi tayi ta gabatar da tata....... _😍💃🏻😘 Soyayya dadi tafi Zuma dadi, Allah ya bamu masoya na gaskiya🤲🏻_ *Ku sakani a addu'a ina fama da ciwon ido* *Siddiqa CE* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* 🌍DUNIYA MAKARANTA🌍 *_Ba'asan cofee zaiyi dadi ba har saida aka hadashi da sukari da madara, kamar hakane a rayuwa, ba'a sanin amfanin wani sai ya hadu da wani👌🏻_* *Page* 5⃣0⃣ ________filo tayi da cinyarsa idanuwanta a lumshe yayin da yake aiki a cikin laptop d'insa, ita kuma tana kallon MBC drama dake wani series na larabawa, duk da ba Duka takeji ba tana dai fahimta a haka, dukansu sanye suke da sleeping dress nasu, alaman sun yi wanka kenan... Rufe system din yayi sannan yace "excuse Ma'am, zan mayar da system na kammala" zame kanta tayi daga jikinsa ta mayar akan seat ba tare da take komai ba, shima bai koma cewa komai ba ya mayar da system din gurin zamansa sannan ya bud'e fridge ya dauko musu fresh milk da cup ya dawo Inda take tare da tsiyaya mata a cup din... Mik'ar da ita zaune yayi ya tare da kafa mata cup din a lips nata yana mata murmushi tare da kallon cikin idonta, itama mayar masa da martanin murmushin tayi bayan ta fara kurb'a a hankali sannan tayi turning cup din zuwa nasa bakin cikin kalar nata salon, daidai gun da ya d'auke lips nata ya sanya nashi a haka suka shayar da juna cike da k'auna.... "My khaleel bamu ci gaba da tuno back memory namu ba, I really wanna hear it all" ta fad'a cikin shagwaba.. Smile yayi tare da mikar da ita tsaye "OK come with me, tunda kin matsa ni nama manta" "Uhum nikam ya za'ayi na manta tunda ni naso naji yadda akayi ta ninke ni baibai, gaskiya Yaya kakai dan basaja top class" hararanta yayi. "Nine dan basaja? Ba basaja ake kiran wannan ba iya takune" "Whatever dai nidai muje ka karasa gayamin, why not ma anan?" "Nop just come and see" Fito da wata 'yar hand bag yayi daga cikin wardrobe nashi, wani diary mai matukar kyau ya dauko a ciki, mik'a mata yayi "ungo nan kome kike son zaki same shi a ciki okey" amsar diary tayi tana jujjuya shi a hannunta, shi kuma ya mayar da jakar... Tsakiyar bed ta zauna tare da kalmashe kafafun ta, yadda zataji dadin karantawa dakyau sannan ta bud'e tick cover da aka rubuta my diary my life secret.... Fotunane suka zubo kasa wadanda a kalla zasu kai 20pcs d'agasu ta fara yi cike da mamaki fotunan ta ne tun na jarinta zuwa kuruciya har na zuwa girmanta, Mamaki taf a fuskarta baki sake take kallonsa, shima kallonta yakeyi yana zaune kan sofa yana facing nata so yana ganin kowanne reaction nata... "A ina ka samu wad'annan duka?" Smiling ya sake yi na ba adadi "kike tambaya bayan kinsan its so easier to get it! But let make it clear, wasu wadanda ka turan ne as a new born baby of my Uncle, and wasu nina d'auka da kaina shine na wankesu are u clear?" Ya tambaye ta... "Um! But bansan time din da kake d'okana ba kuma fotunan kamar ina sane wasu hadda smiling" d'an darawa yayi... "Shine tsaron ai, taya zaki sani kuwa" itama murmushin tayi, tare da mayar da hankali a gun diary ta kagu taga meya kunsa... (1st March 2000) writing and stamp by:- *I IBRAHIM MAHMOUD SA'ED GWARZO* shine front of first page d'in rubuce boldly.... _The beginning of my love, this is my life secret_ _A tunani so zabi ne, a tunani so k'irkirarsa ake a sakashi a rayuwa, na d'auka ina mata sone irin na 'yan uwan taka, bansan yaushe na fara mata tsananin k'auna ba, kawai na samu kaina ne a cikin k'aunarta tsundun_ *Bilkisu Hashim Sa'ed Gwarzo* _Na d'auka cire so kamar cire Riga ne, but I really know what means by word love at date time, love is not an easy things, is just like a war unaware to start, so hurt to stop or is unstoppable at all_ _na amince da wakar nan da wani hausa musician ya rera inda yake cewa_ _Allah gwani kaine ka kagi samaniyaa, kayyo maza mata cikin su halittaa, kace muso manzo rasulu abun biya d'a gun Aminatu sidi ka cancantaa, nasan akwai so gaskiya 'yan uwa domin rabbi ya sashi nan ga halitta mai sa mutum ya zamo kamar wani jarumi mai ji kamar zai doke dukka halittaa, da can ina zargi akan mai so kuji na maida shi wawa cikin su halittaa, yau gashi na afka a tarko mai wuya bege akan wata 'ya cikinsu halittaa, a cikin mafarki mun dad'e mun daddale amma a fili babu Wanda ya furtaa, ya zanyi na zamo gwani a gurinta ne har ma ta sanni tasan ina k'aunar taa_ Kasake tayi tana ci gaba da maimaita baitukan wak'ar, so take ta tuna ina ta taba jin baituka ko rubutu kwatankwacin wannan, dan ta tabbatar ta taba jin su, shikam tuni ya shiga wani shirgi dan ya mayar da attention nasa kan wayarsa.... "Yes!" Ta fad'a da karfi, Wanda hakan ya jawo hankalin sa "menene?" Ya tambaye ta.... "Kaine kenan Yaya?" "Nayi me kuma?" "Zo kaga" tace kawai, ba musu yazo dan dama ya ware mata wannan lokacin dan ta fahimci duk wani Abu daya shige mata duhu... Dariya yayi data nuna masa baitukan "dama Kaine ka yi ta wasa dani uwa kwallo a lokacin kuma na kasa ganewa?" "Ai ba'a baki damar ganewa bane yarinya" "But ur too confidence akan zaka sameni ko dai kaine ka gayawa Uncle Salman wani Abu a time din ya fasa, I can't believe wai sihiri ne akayi masa?" Duk da maganar ta dake shi sosai but dole ya bata excuse, girgiza mata kai yayi "tana kike wannan tunanin? Taya zan rusa farincikin Ku for my own happiness, yes nayi kishin Salman matuk'a har take kallonsa a matsayin wata Katanga tada gifta min daidai lokacin da nake ganin wahala ta tazo ending but ban taba tunanin bata komai ba I just believe in God of mercy" Dora hannunta akan shoulder nasa tayi tana kallon cikin idanunsa "I'm sorry yaya, I don't mean to hurt you, and I know ur such kind and gentle enough" "How did you know I'm such?" "Common Hayatiy I know mana! Da wani daban ne aida haushi zaiji watakil ma ya rufeni da duka or something else but kai ka tsaya kana min bayani a nutse duk da na bata mata kayi hakuri" Jan hancinta yayi tare da cewa "ur kind too, matar na tuba ai bata laifi is OK! Kawo nan na karanta maki komai tare da miki fashin baki" itama murmushin tayi tare da k'ankamesa "thanks much Yaya! I love you" "Love you too" ya amsa mata tare gyara mata zamanta a jikinsa yadda zata fi jin dadi, sannan yaci gaba da karanto mata diary nashi, irin yadda yaci gaba da azabtuwa da soyayyar ta, da yadda yake boyewa, da yadda yake matsa mata musamman idan ya ganta tare dasu Adnan... Irin farincikin da ya shiga lokacin da akace za'a hadasu aure, da yadda yayi hurting much lokacin da tace bata sonsa, har yake tuna matan da suka yi zuwar masa yana gaya musu he don't want marry them, sai yake tausaya musu Ashe suma haka sukeji a ransu.. Yadda yayi ta treating nata a tunaninsa ko zai samu sauki a ransa, yadda yake matukar kishin ya ganta tana waya ko ya ganta da salman.... "Yaya kenan duk akan kishi ne kamin abubuwan da kamin lokacin?" Jinjina mata kai yayi kawai, ranar da yake tunanin ya kuma yadda tayi masa nisa ta juya ta dawo masa mafi girman rana a rayuwarsa he can't believe ya zama miji a gareta a wannan lokacin.... Dariya sosai tayi "but shine ka nuna makala maka ni akayi taimako na zakayi?" "Yeap! Duk da haka ban tsira da rashin kunyar da kika koyo gurin Nusaiba ba" .... Zaro ido tayi "ayya ba gani har hanji kake ba Yaya?" "U can't understand! Nafi inuwarki kusanci dake ina sane da duk wani motsi naki, shiyasa nayi feeling bad dana kasa gane kina da ciki har sai bayan ya zube, kuma kika ci sanar dani saboda bakya son jinina" Itama kalar tausayi tayi "Ayya! yaya wlh nima ban san dashi ba, am sorry I just pretend but I love my baby much" "It OK! I know" zaro ido ta karayi "as how?" "From ur eyes, and you love me too since a dat time" Smiling tayi "Agreed" ci gaba da karanta mata yayi, rufe ido game tayi yadda yake zayyana how he feel a first night nasu duk da ya bayyana a ba zata abin yazo masa, yaso sai ya gama koyar da ita yadda zataso shi ya tsundumata a k'aunarta, halin da ya shiga a lokacin da ta shiga garashi ya fara zannaya wa "am so sorry Yaya for misunderstanding you" "It OK" daga karshe ya rubuta _finally I get her after moving up and down, crossing over many obstacles I get her and her love too_ "Tau yau dai kinji komai, saura ke ki gayamin meyasa kika garani bayan nasan kina sona why pretend ur not in love with me, and thinking i'm going 2 deceiving you why" "I think, ban kai matsayin ka soni ba, a ganina kafi karfi na, duba da tsantar kyau cikar haiba, ga uwa uba ilimi da gadara da takama as my thinks fa" "Gwanda da kika ce as ur think, danni tun da na fara sonki zuciyata ta kulle na kasa kallon kowacce mace a matsayin mace sai ke, and ur preety too, u have good manner, and educated gal too, so why do you think am not going to love you?" "Yaya ur such unique dat hardly to find, I can't believe you love a silly gul like me!" "Hmmm Bilkisa kina manta cewa shi so ba ruwansa da isa ko matsayi, ko cancanta ba, bama wannan ba, bani da bambanci dake ta ko'ina mudin *Zuria d'aya* asalin mu d'aya idan har baki goranta min tarbiya dana tsotsa daga Ammin ki ai ni bai kamata naji wai na fiki ba, ban taba Dana sanin soyayyarki ba, kuma bazan taba yi ba har abada, fatana shine mu rayu cikin Aminci tare da zuria dayyiba wadanda nake fata zuki kalar tarbiyarki" "Ameen" ta fad'a tana sunne kai.... Kashe mata ido daya yayi tare da daga mata gira, yayi kokarin zira harshensa cikin NATA...... *Siddiqa CE* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* 🌍 *DUNIYA MAKARANTA* 🌍 _Sau daya damuwarka takan sanya wasu dariya, yi kokari kada dariyar ka ta kasance damuwa akan kowa_👌🏻 *Page* 5⃣3⃣ _________"OK zan gaya miki but kada ki yadda naga hawayen ki, kika yadda naka kukan ki I will punish you okay!" Girgiza masa kai tayi tare da fad'in "Eh Yaya"..... " Well! Case ne na cutar wa is about rape and child abuse" zumbur ta mike zaune tare marairaice fuska "Yaya Wacece haka wayyo meya faru"... " U see har kin fara ko, aiki take gidan wani mai kud'i shine yaron gidan yayi amfani da wannan damar ya lalata musu 'ya......" Bata labarin yayi complete har zuwansa gurin su can hospital din..... "Wayyo Yaya an cutar da ita, pls ka amshi case d'in Yaya don Allah ka kwatar mata hakkinta" hawaye kam sun gama wanke mata fuska, ita tama manta da an hanata hawayen, ga kwalliya rad'au a fuska amma hawaye sun bata, harara ya watsa mata "good gara da kikayi kukan, bari kiga" d'agata yayi cak, ya nufi upstairs, sai lokacin ta tuna da laifinta... "Wayyo Yaya yi hakuri kaima kasan dole zan koka wannan labarin mai dukan zuciya haka? Pls kayi hakuri my Yaya my Khaleel, my Hayatiy" Murmushi ya saki "daga baya kenan 'yan mata amma yanzu kam dole ki karbi punishment naki yarinya" kwaba fuska tayi tana dukan masa kirji a shagwab'e "Allah Yaya wayo dai kawai" Tura k'ofar yayi da kafarsa yana 'yar dariya "koma meye dai" ya fad'a tare da tura k'ofar saura kadan ya murzan hannu a k'ofar wai na dakata anan( _yaufa Muz'Aymah sun dakatar dani daga kyaure_😔🤧) *************** Duk yadda ya d'auki case din ya wuce tunanin sa, yanzu ne yake k'ara tabbatar da Shu'umanci irin na Masu kud'i, duk wata kafa da ya kamata ya samu gamsasshiyar sheda sun toshe ta, Mai Dalar da kansa ya same shi har gida akan ya janye don ya samu labarin case d'in hannunsa yake, ya riga yasan Zayyad bazai iya ba kasancewar sa bai dad'e da fara aiki ba so kuma case irin wannan yana bukatar gogewa da sanin makamar aiki... Makudan kudade ya bashi akan ya janye, baiyi mamaki ba don wannan ba shine karo na farko a gareshi ba, sosai ya gaya masa magana son ransa sannan ya tabbatar mai case yanzu ya fara kuma da yardar Allah sune masu nasara, cike da bacin rai Alhajin ya yabar gidansa tare da tabbatar mai ya tsammacesa... D'auki ba dad'i aka shiga yi, sosai ya ya shiga busy a Dan tsakanin, na matukar sosai Aymanah ke k'arfafa masa dan har asibitin da aka maida yarinyar saida ya kaita ta dubota, ta samu sauki ba laifi duk da jikin da saura, waccen clinic din tuni Mai dala ya saye su sun canja komai, hakan yasa hukumar 'yancin Mata ta canja mata wani asibiti itace daukar da nauyin kulawa da ita, kotu sau biyu ana zama ana dage k'arar saboda rashin gamsassun shedu da basu samu ba, wanda zai tabbatar yaron ne ya aikata mata hakan saidai duk yadda Alhaji Mai dala yaso ayi watsi da karar bai yuyu ba saboda wasu shujjuji da Ya Mu'azzam ya kafa wadanda dole a basu uziri akan su a jira su, su kawo shedun su.... Barazana ta ko'ina samun ta yake daga mai dalan saidai wannan bai hanashi gudanar da duk abinda ya kamata ba akan case din, ba, musamman yadda yake samu kwarin guiwa daga iyayensa da Yan uwansa uwa uba matarsa Sahibarsa, na sosai yake kokarin samar mata lokacinta a cikin wannan yanayin..saboda sauke nauyinta... Yau ne akayi zama na karshe Wanda dak'yar ya samu aka daga k'arar wannan karon har yarinyar anzo da ita da yake ta samu sauki sosai, gabatar da ita akayi tayi bayani da bakinta duk abinda ya faru, lauya mai kare yaron yayi mata tambayoyi ta amsa mishi, sannan aka gabatar da yaron, hankali kwance Mu'azzam ya taho inda yake yana sanye da wannan rigar da hular na lauyoyi Wanda ba karamin kara fitar masa tsantsar kyawu, kwarjini da haiba sukayi ba... "Ko kasan wancen yarinyar?" Ya tambaye sa yana nuna masa ita, kallon ta yayi sannan ya mayar da kallon sa ga Mu'azzam din.. "Eh 'yar aikin gidan mu ce" murmushi ya saki sannan yace "meye alakar ka da ita?" "Ni..ni meye alakata da ita ko, ni banda wani alaka da ita face dai nasan tana aiki a gidan mu" ya fad'a cikin dakewa duk da yadda muryarsa ke rawa, ga rashin gaskiya muraratan ya bayyana akan fuskarsa.. Murmushi ya kara yi mai sauti "Abbas kenan! Wato baka da alaka da ita amma ka kaita asibiti domin a zubar mata da ciki?".. " objection my lord, wannan ai salon rikita masa tunani ne bai kamata mai tambaya yayi ma Wanda ake tuhuma irin wannan tambayar ba, taya zai ce ya kaita a zubar mata da ciki bayan baida wata alaka da ita".. "Barrister Ibrahim ka kiyaye" amsawa yayi cikin girmama wa kafin ya nemi a bashi damar gabatar da shaidarsa, aka bashi.... Wasu papers ya fitar ya nunawa yaron "Abbas zaka iya gane wannan sa hannun waye?" Wata irin zabura yaron yayi ganin takardun da ya rubuta sunansa da sa hannunsa, lokacin da ya kaita asibitin, bai ko bud'e baki ba yaji ya kara cewa "ko zaka iya gane wannan muryar?" A matukar rud'e yake jiyo muryarsa da yayi rad'au a cikin mp3 lokacin da yake bayanin yanaso a cire mata ciki ne matarsa ce saidai tayi k'ankanta da renon ciki da haihuwa.... Murmushi ya saki "malam Abbas Sidi mai Dala, me zaka iya cewa ko har yanzu baka da alakar komai da Zakiyya?" "To..to..to...Dan Allah kuyi hakuri Sharrin shedan ne" yace a matukar rud'e ba tare da yasan me yake fad'a ba, zufa keto masa tace ta ko'ina, Alhaji Mai Dala dake zaune kamar mutum mutumi ransa a matukar jagule, shikam lawyer da ke kare Abbas d'in soke kansa kan bench din gabansu yayi... Tattara mp da takardun Mu'azzam yayi ya mik'awa muhti shi kuma ya bawa alkali.. Bayan dogon lokaci da alkalin ya d'auka yana nazarin evidence din da kuma kalaman Abbas din rubuce-rubuce yayi sannan ya D'ago "Abbas sidi mai dala ka amshi laifinka ko har yanzu kana da ja?" "Na..na.aminta ranka ya d'ade, wlh Nina aikata da kaina, amma dan Allah a yafemin sharrin shedan ne" tun da ya amsa laifin da bakinsa Alkalin ya mayar da hankalin sa ga rubuce-rubucensa... "Bayan dogon zama da wasa da sharia da wannan mai laifin yayi mana, samun gamsassun hujjoji da tabbatar wa daga bakin mai laifi, wannan kotu mai daraja ta dubi girman laifinsa da bata lokacin mu da akayi an yanke masa hukunci dai-dai laifinsa a musulunce na bulala 80 na laifin aikata zina yana saurayi sai laifin kashe rayuwa wato cikin da aka zubar da kuka laifin tursasa karamar yarinya saboda zalinci an yanke masa shekara 15 a mak'argama, tare da horo mai tsanani da kuma tarar naira million 2, na jinyar da akayi ma wacce aka cutar" alkalin yace sannan yaci gaba da cewa.. "Sai asibitin da ta bada shedun karya akan wannan shari'ar kotu ta cita tarar million 1 na bayar da shedun zurr da boye gaskiya da tayi" buga hatimi yayi yana kammala bayaninsa.... Hawaye ne kwance a idon iyayen yarinyar tare da murmushin farinciki, ihu yaron keyi yana kiran sunan Dadyn sa lokacin da yan sanda sukazo wucewa dashi, shima uban idanunsa jajur kamar gauta ya kasa koda motsawa.... "Mun gode, mun gode sosai barrister Allah ya kara girma ya tsareka da tsarewarsa Allah ya shirya maka Zuria" sosai yaji dadin Addu'ar "Ameen Ameen nima nagode baba, Allah ya tsare na gaba" "Nagode madallah Yaya, Allah ya saka da alkhairi" yarinyar ta fad'a, murmushi yayi mata "Ba komai Zakiyya hakkina ne na karbo miki 'yancinki, Allah ya baki rayuwa mai inganci nan gaba" godiya sosai suka kara yi masa sannan ya wuce.... "Am back Habibty!" Ya fad'a da d'an saurinta tazo tare da shigewa hannayensa daya ware mata "Sannu da dawowa Habib rouh! Ya case din? Ya kuka kare duk da fuskarka ta shedamin mune masu nasara" Murmushi ya karayi tare da kara matseta a jikinsa yana shakar daddad'an kamshin ta "hakane baby Allah ya Dora gaskiya akan karya ya tubi raunin bayinsa ya sassauta mana komai munyi nasara we are d winner" "Alhamdulillah bini'imatihi tatimmusalihat! Yaya nayi matukar murna muje kayi fresh up kaci abinci" "Uh um baby na gaji da yawa yau ke zakiyim komai" Murmushi tayi tare da kama hannunsa cikin nata "ur wish my command my Husby, yanda kace" zagaye hannayenta a kugunta yayi ya rad'a mata magana a kunne... Zaro ido tayi tare da rufe fuskarta da tafukan hannayenta "Allah nidai ba ruwana yaya" "Chab!! Nikam da ruwana baby muje mana......"""" 😔ouch wlh kwanakin nan sai a slow aci gaba da hakuri dai #One love😘😍# *Siddiqa CE* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* 🌍 *DUNIYA MAKARANTA* 🌍 _A hannun ka yatsan da yafi kowanne yatsa nisa da d'an uwansa shine babban yatsa. Duk da haka ba basa iya aikin komai saida shi, ba kusancin ka da Dan uwa ne muhimmi ba, amfaninsa gareka👌🏻_ *Page* 5⃣1⃣ _____hutun sati d'aya daya d'auka, ba abinda aka gudanar a ciki bayan amarci mai cike da tsafta, soyayya, tsabtatacciyar k'auna Mara algus ko yaudara a ciki, ririta da tarairayar juna suke kamar su hadiye juna dan k'auna, mamakin juna sukeyi sosai... A bangaren Mu'azzam mamaki yake Ashe kallon yarinta kawai yake wa Aymanan sa, Ashe cikakkiya kuma kasaitacciyar mace wacce ta amsa sunan ta na 'ya mace ce, tasan makamar aiki sau da dama idan tayi wani abun har mamaki yake yaushe ta San wannan, saidai tunawa da ingantacciyar tarbiya data samu, da kuma ilimi da take dashi na addini, ga kuwa wayewar kai na musamman da take dashi Wanda yasan baya rasa nasaba da kud'anya da mutane da sukeyi da kuma leka media, sosai yake jinta a ransa yanzu da suka fi samun kusanci fiye da son da yayi mata a baya.... Itama a nata b'angaren sai yanzu ne ta fahimci waye ainihin asalin yayan Nasu, tsauri da tauri da take tunanin halinsa ne ada, a yanzu ta gane waye shi, mutum ne mai sauki, sanyi tausasawa, taimakawa sosai yake koyi da karantarwar annabin mu na rahama, gurin tafiyar da rayuwar auratayyar su, shiyasa sukeji kamar ba zasu iya rayuwa ba'a tare suka gane gata sosai iyayen su sukayi musu.... Tare suke shiga kitchen, suyi komai a tare, wanka a tare komai a tare sosai sukejin dad'in rayuwar su, Aymanah ta kara gaskata ba yanayin da ke dawwama a rayuwa ada kullum tunanin ta sai yaushe zasu zamu rayuwar yanci, yaushe ne zasu dinke su kasance happy family, sai gashi ubangiji ya sauki a lokaci d'aya, ga nagartaccen miji ga kuma soyayyar uwar miji da yan uwansa, a kullum sai sunyi waya da Momy cike da farinciki ko bata kirata ba ita zata kirata, ga zaman lafia sosai daya wanzu a Zuri'ar tasu, sosai Samiha da Samha ke nuna mata k'auna, Momy da Ammi kamar wasu yaya da kanwa, Hajja tuni sun rik'eta sunce ba zata koma zama gwarzo ba saidai ta ringa zuwar musu ziyara, dama tashin hankalin su ya sa tabar musu gidan su, kayanta sukaje aka kwaso baki d'aya, sannan ya saka wasu 'yan uwa gidan... Gidan nasu yanzu gwanin dad'i shiyasa idan suka zo sai taji kamar kar su tafi gata cikin 'yan uwa ana nan nan da ita... "I'm back habibty" ya rad'a mata a kunne, kara kudundune jikinta tayi akan seat din tana tura baki da yamutsa fuska duk a cikin baccin... "Common princess, it me fa ur prince ur Habib rouh!" Um um" ta sake fad'a still idanuwanta a rufe... Hannayenta dake kan mararta ya kalla sai yanzu ya lura da yanayin ta, saurin aje brief case dinsa a canter table, d'agata cak yayi tare da mik'ar ita tsaye, ware ido tayi a kansa da suka sauya launi suka sirka da jaja, dubansa tayi kamar tayi kuka sannan ta d'an zame daga jikinsa tana ci gaba da kama marar tata.. Cike da tausayi da dan tsoro ya sunkuya shima dai-dai ita ya dagota tare da zama kan seat ya d'orata a cinyarsa yana shafa mata kai a hankali "what wrong u Babe? Meya sameki ne, ciwo maran ke miki?" Cikin dauriya tana cije lips tace cikin mafi sanyin murya "I thought it my period pain, tun shekaran jiya ya fara min ciwo, but yanzu it more painful ga har motsi nakeji a gurin kar fa tsutsan ciki ne yamin yawa" Duk da cike yake da tausayin halin da take ciki kalamanta na karshe sun saka shi murmusawa, tun kwanaki yaga many changes a tare da ita kamar shigen na cikin ta na farko da yayi mata maganata tace aa wlh duka baifi sati biyu ba har zatayi ciki ya kuma bayyana da sauri haka, itakam ba ciki bane period zatayi a kwanakin, ganin ta dage akan ba ciki bane yasa ya kyaleta akan idan tayi period din shikenan idan kuma baizo ba to sai suje hospital kawai, but cewa tanajin motsin ya bashi dariya to koma ciki ne for two week sai fara motsi hala... "Sorry Habibty, muje hospital kawai a duba ki yafi" da kai ta amsa shi kawai, gown ya d'auko mata da hijab ta sauya sannan suka dauki hanyar Malam Amino kano.. Zaune suke office d'in Family doctor tasu Dr, Humaira(diyar D one, Haduwata dake) kallo daya zai tabbatar maka tasan makamar aiki, tambayoyi taci gaba dayi mata bayan tasa anyi mata wasu gwaje gwaje hadda scanning... "When last kikayi period bayan kin samu miscarriage, kuma anyi maki wankin Mara alokacin?" "Aa ba'ayin ba, kuma banyi period ba, a satinnan dai nake expecting nasa" ta amsa mata, tana mata kallon Shawa'a sosai kayan suka amsheta, ita dai tanason b'angaren health she eager ta ganta tana treating patient like d way nurses din da aka hadata dasu sukayi mata... "OK" Dr ta fada bayan ta kalleta dakyau na d'an lokaci tana kara gasgata hasashen ta a kanta yayin da ita ko tayi nisa a nata tunanin, shikam kallonta yake shima da nashi hasashe akanta... Nurse ce tayi sallama ta shigo cike da ladabi ta gayar dasu gaba d'aya, sannan ta bata results din tare da ficewa... Duba takardun tayi a nutse na mintuna sannan ta dago ta kalli Mu'azzam tace "Congrat Barrister your baby is safe, is now 4month and a week" shima murmushi ya saki tare da fad'in "Alhamdllh, but Doctor ta yaya hakan ya faru bayan tabbatar mana cewa ya zube?" "Eh hakane twins baby ne so daya ya fita d'ayan nanan, rashin wanke cikin yayi amfani da sai ayi kisa ba tare da an sani ba, Dan inaga a lokacin basu ga babyn ba saboda rauni daya samu, ga kuma rashin zaunuwa da kyau da bai ba... " ko yanzun dan ya cika mutum ne an cika masa halittarsa shiyasa yake motsawa kuma yana a tauye dat y marar ke rike mata, but zamu gyara mata shi dakyau, sai a kula sosai ta samu bed rest koda na week ne, kuma a shawar ce ta fara attending Anti-natal saboda lafiyar ta data babyn, congarat Mrs Ibrahim Allah ya inganta" Aymanah da tun da doctor ta fad'i babyn su na nan, tayi kasa da kanta sai murmushin farinciki take, Ashe twins ta d'auka ba tare data sani ba, Allah mai girma, tana gode masa daya tseratar mata da d'ayan... Kasa dagowa ta amsa ma Dr tayi, saboda nauyinta da takeji, fahimtar haka ne yasa tayi murmushi kawai ta rubuta magungunan da zata bukata ta bashi ya karbo a pharmacy, sannan tayi shirin daidata musu babyn su..... Godiya sosai ya shiga yi mata, bakin nan har kunne tsabar farinciki, saida ta buda musu file na anti-natal sannan suka baro asibitin... "Habibty are you happy with d baby?" Ya tambaye ta bayan sun fara tafiya... "Am happy mana yaya kawai inajin kunyar Dr ne, but ina sonsa ko sonta kamar yadda nakeson Abbanta" Sosai zancen ta ya huda shi, smiling yayi "thanks you Bilkisa ta" "Thanks for yaya?" "For being a good wife to me and a good mother to my beloved unborn baby" taji dadi matuk'a "thank too yaya ur such good Head of d house enough!" Hannunsa daya yasa ya kamo nata ya sumbata... Saida ya tsaya ya sissiya mata fruit da sauran kayan kwalam, yana tsokanar ta da masu ciki iyayen kwadayi gara ya fara tun kafin ayi request, ita dai sai murmushi take ranta kal farinciki.... A maimakon yayi gida da ita sai taga ya d'auki titin zuwa Hotoro, family house d'insu "yaya baka fa ma yi wanka ba bare cin abinci gashi ko hutawa bakayi ba, muje gida mana na taimaka maka" "No Baby zanyi daga baya da kaina ke ce mai bukatar Hutu a yanzu ai, bari muje ma su Mommy da good news tukun.... ************* Momy kusan tafi kowa nuna farincikin ta, sai wani tarairayar Aymanan take uwa kyau, Ammi kam 'yar kallo ta dawo, su Samha da samiha murna kamar me, suna kuma jin ba dadi har gobe akan abunda sukayi mata duk da komai ya wuce, hajja baki har kunne zatayi kama kunne.. Momy cewa tayi ya barta anan tayi sati biyu yadda zata samu bed rest din da kyau, Hajja tace Sam, a bar shi da matarsa, ai shima mai iya kula da ita ne, itama dai Ammi haka tace, dole Momy ta hakura akan za'a samo mata yarinya ma d'an tayata wasu aikace-aikacen saboda lalurar kuma ko ba komai zata samu mai d'auke mata kewa tunda shi ba ko wane time yake a gida ba, Hajja ta yarda da shawarar tace akwai Sabira 'yar Jimmai mai aikinta yarinyar Nada kwazo sai aje azo mata da ita.. Samiha da Samha hannu ya fad'a sosai a harkar girke-girke, da aikace aikace irin na mata, dabarun zaman aure ne kawai yanzu ya rage suma Ammi da Hajja har Momy kowa na basu tips cikin azanci.. Samiha sosai ta sake yanzu, ta cire damuwar komai a ranta, ta mayar da hankali akan abinda zai amfane ta, sun koma islamiya tuni yanzu Sam basa fashin zuwa, har yanzu tana cikin iddarta shiyasa duk wanda yaso tararta take saurin kwabarsa, sosai takeso ta gyara rayuwar ta, tana son rayuwa ta shimfida rayuwa mai tsafta a rayuwar ta ta nan gaba.. Samha ma, su Ammi har da hajja suka je har gida gurin mahaifiyar mijinta suka bata hakuri tare da rokar ta arziki, sosai ta yaba da karancin su, basu nuna isa ko girman kai ba, a take tace itakam komai ya wuce a gun ta, dama ita a 'ya ta ajeta itace dai ta bata kanta, amma yanzu komai ya wuce a gurinta... Suje su shirya Kansu Allah ya basu hakuri, shima Abba ya kira Farooq, ya kara bashi hakuri, shima yace ya hakura Dan yanason matarsa dama dai halinta ne bayaso tunda ta canja shikenan ta dawo dakinta, a ranar kwanan farinciki Samha tayi zata koma gun abin k'aunarta... Shiri na sosai su Ammi da hajja suka shiga yi Mata kamar wata sabuwar amarya, shima farooq nasa b'angaren hadda sabunta fenti da sauran gyara-gyare..... B'angaren Umma kam abun ba'a cewa komai, ta dawo goro ko abin saye, wulakanci na sosai takesha a gun matan yayan nata, hadda su habaici da komai, ga 'yan kud'in hannunta ta gama cinyesu, har wayar hannunta ta sayar ta mayar da Nokia rakani kashi, duk kuma ta cinye kudin, dole ta dawo cin duk abinda aka kwaba a gidan aka bata gashi ba koshi take ba, duk tabi ta fita hayyacin ta.... Kawayen da take da masu zugata suna tayi komai ba komai lokacin ta ne duk sun gujeta, sai yanzu ta fara nadama da Dana sani Mara amfani... Babban tashin hankalinta gaba daya wayar Dady da 'ya'yanta ba mai zuwa kota kira duk a kashe takejin layukan alaman a daina aiki dasu, tashin hankali na sosai ta shiga bata ga miji bare 'ya'ya ga wahalar rayuwa na kaiwa bakin salati ma gagararta yake, bare tayi tunanin zuwa gurin boka... Tana so taje can gidan ta nemi yafiyar su ta roki arzikin a mayar da ita dakinta ta gane kurenta ba dama, Dan Yayanta ya sheda mata Dady yace muddin ta taka kafarta gidan nan zai tsinke sauran igiyoyin koda yana da niyyar maida ita, kuma ya sheda mata shine ya hana yaransa kusantar ta, dole tasha jinin jikinta dan ya karar da auren ai asirinta ya gama tonuwa... 😅 _Allah sarki Umma ta fara ban tausayi😢_ lol. *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* 🌎 *Duniya Makaranta* 🌎 _Idan kasha ruwan rijiya kada ka jefa mata dutse a cikin ta, komai k'ankantar alkhairin mutum a gareka kada ka butulce masa_ 👌🏻 *Page* 5⃣4⃣ ______kwance take saman faffad'an k'irjinsa tana wasa da bakin lallausan gashin da ke gurin kasancewar suna kebe ne a d'akin baccin su sun baje a bed suna hutawa, bayan komai ya gama wakana yadda ya dace, idanunsa a lumshe tace "Yaya?" "Uhm Habibty!" "Yaya na dade banje gida pls tun da case ya kare yaushe zaka kaini tun da ka hana ni fita koda da driver ne, wlh nayi missing nasu" D'an bud'e idonsa yayi da ke cike da bacci ya kalleta na sakanni "Am very sleepy baby let sleep we will talk after OK" "Uhm" ta fad'a a tak'aice, tare da kara hugging nasa tightly, shima gyara pillon kansa yayi tare da return her huge back, minti kad'an bacci mai cike da nishad'i yayi gaba dasu.... Basu suka farka ba sai 4 after, zare jikinsa yayi a hankali tare da shiga toilet a gaggauce ya d'ora alwala, ash jalabiya ya zura, sannan ya koma bakin gadon tare da sunkuyawa ya shafo gefen fuskarta, a hankali ta fara bud'e kyawawan kwayoyin idaniyanta kafin ta ware su gaba d'aya a kansa, hannu ya mika mata ta kama kana ya mikar da ita tsaye "asr ta kwace mana muje kiyi alwala kizo muyi kinji" girgiza masa kai tayi dake baccin bai gama sakinta gaba d'aya, hannunta yaja saida ya sadata da toilet sannan ya fitar musu da darduma tare da fitar mata da hijab da zanin da take sallah dasu.... Jam'i ya jata bayan sun kammala yace "kika ce dazun kina so kije gida?" "Eh mana Yaya" ta amsa masa tana ninke hijab da zanen "kina so muje yanzun?" Tsabar murna batasan lokacin da ta daka tsalle tare da yasar da kayan hannunta tsakar dakin ta dire a jikin dake yana kwance akan sofa "da gaske My khaleel" Fuskewa yayi bayan ya riketa sosai yanayin yadda ta fad'o masa zata iya jin ciwo "me haka Aymanah, bana hanaki irin wannan shirmen ba, to an fasa fitar" kara d'aure fuska yayi tamau just like dodonta... Ji tayi ba dadi, nan take ta koma wata kalar tausayi, tayi narai-narai da ido har kwalla ta taru mata "pls yi hakuri Yaya bazan kara ba Allah" banza yayi mata kuma yaki kallon sashen ta... Kara rikicewa tayi sai hawaye sharr "pls ya Allah bazan kara ba" saurin juyowa yayi ya kalleta sai ta bashi tausayi, tunani yayi wato ita mace komin girmanta kuka baya bata wahala wala na farinciki ko bakin ciki kona sakarci kona rikecewa.. Kukan Mamar Zakiyya da ita Zakiyyar kanta itama yanzu kukan take saboda kawai yayi mata fushi.... "Is OK banason kukan" ya fad'a yana share mata fuskar amma fuskar sa ba walwala sosai.. "Ka hakura Yaya?" "Na hakura mana baby ai kema kinsan bazan iya fushi dake ba ko yaya, lafiyarki data unborn nake dubawa ki rage wannan rawan kan yanzu ke babba ce kuma momy to be u'um!" Ya fad'a da murmushi... Itama murmushin tayi tare da boye fuskarta da tafukan hannayenta "uhum su kunya manya! Bayan kin gama wahalar dani daga dawowa na ko hutawa ban ba, waike fitina" Zaro ido waje tayi bayan ta sauke hannayenta "kai Yaya nifa kace, Allah Yayan nan ka cika wayo, bayan Kaine....." Dariya ya fashe da ita yadda take maganar da iya gaskiyar ta kuruciya a filin Allah.... "Wannan matar tawa badai kuruciya gashi kuma girma yazo, oh ni Ibrahim jikan Sa'idu uwar zan rena ko 'yar" "Allah ko Yaya zan rama ni kake kira 'yar reno ba?" Tashi tayi zata wuce tana hura hanci, cinye dariyar yayi tare da riko hannunta da sauri " oh wasa nake fa Maman baby, gobe ma zamuje pre-natal kin tuna" tura baki tayi gaba bata tanka ba... "OK shikenan kanki kika yiwa tun da bakya magana barin tashi nayi tafiyata gida ni d'aya..... Da sauri tace " Allah na tuna Yaya ai gobe zamuje" lakuce mata hanci yayi "my fitina baby yi maza ki shirya muje time is going!" A hankali ta tashi ba wannan rawan kan duk da dad'i takeji a ranta na sosai saidai bataso tayi abinda ran Sahibin zai baci, murmushi ya saki tare da Shafo Sumar sa.... "Silly gal, koman ta yayi ta had'u ta ko ina" ya fad'a a ransa...... ************** "Allah Akbar! Allah sarkin hikima Salmanu yau kaine a gabana? Yaushe ka dawo kuma ina kake tsawon lokutan nan?" Sosa keyarsa yayi tare da k'ara sunkuyar da kai "Abba na kwana biyu da dawowa, wlh Abba nima basan meya sameni ba lokaci d'aya naji na tsani auren da Aymanah kamar yadda naji Zariya tamin matukar Zafi, Abba Sokoto naje nayi ta rayuwata ni d'aya cikin kunci bana ko son tuna gida da komai daya shafi rayuwata, tsawon watanni Shida, sai kuma kwatsam rana d'aya naji na dawo kamar yadda nike naji cewar gida da kewar Aymanah, Abba wlh bansan meya faru ba" "Aa Salman ka dena damun kanka nasan ba laifinka bane daga baya amma kam a gaskiya farkon lamarin raina ya sosu har sanadin haka na had'ata aure da d'an Uwanta a ranar da akayi niyyan d'aura maka aure da ita, amma kuma daga baya dana gane Ashe ma matsalar daga cikin gidana ta fito...." Nan ya labarta masa komai daya faru tare da cewa kayi Hakuri Salmanu wannan kaddarar rayuwarku ce a haka dan Allah ka yafe musu suma rudin zuciya ne dana shed'an suka ingiza su"..... "Babu komai Abba na d'auki komai a matsayin Kaddara Dan naji labarin komai daga Gida(dake Abba ya sanar dasu komai game da abinda su Momy sukayi tun lokacin da abin ya bud'e) Abba har ma nayi aure da wata 'yar uwata, dama dai nazo ne na gaida kai kuma na sheda maka dawowa ta" "Kai mashaa Allah, madallah Salmanu nayi farinciki, amma shine Alhaji bako gayyata bayan an riga an zama d'aya kodai sun kullace mu ne?" "A'a wlh Abba ko daya Abin ne yazo a gaggauce bako wani shiri akayi shiyasa nace kar a sanar muku tun da lokaci ne kuranne in yaso daga baya nazo na kawo muku matar Ku ganta, ai tare muke tana ciki" "To to to Madallah babu laifi Allah yayi muku albarka baki d'aya bari nasa a kawo maka abin tabawa in yaso sai a kiramin surikar tawa mu gaisa daga baya...." "Aa Abba ai da ma ka barshi...." "Kul karka soma nan ba gidan Ku bane kam, kusha hanyar sannan kace haka..." Sallamar su Mu'azzam ce ta katse masa maganar sa, suma isowar su kenan suka yo tsinke nan su fara gaisawa da Abba..." Kallo kallo Salman da Mu'azzam suka shiga yi, shi yana masa kallon sani shi kuma yana mamakin yadda aure ya kasance tsakanin su yadda ya fahimci babu shi a tsakanin su a lokacin da suke tare, itama kallonsa take da mamaki... Murmushi ya saki tare mika masa hannu, shima salman d'in mayar masa martanin murmushin yayi suka yi musabaha... Fad'ad'a murmushi Abba yayi yana amsa gaisuwar su, a sanyaye Aymanah ta gayar da Salman din, jin yadda Salman ya kama sunanta rad'am a bakinsa yasa Mu'azzam binsa da kallon tuhuma kafin yayi magana Abba ya tare sa... "Baka ganesa bane Ibrahim, shine fa wanda ya tashi auren Allah bai nufa ba...." Nan ya basu labarin sa a takaice, fatan alkhairi Aymanah tayi masa bayan ta jajanta masa tayi ta wuce ciki da sunan zata taga Amaryarsa lura da yadda yanayin yayan nata yake duk da ita kad'ai ta fahimci yanayin saboda tsabar sanin duk wani motsin sa tasan ba abinda ke cinsa a gurin bayan kishi, shiyasa ta sulale tabar gun gudun bacin ransa..... A falon Momy ta same su gaba daya har su Nusee da Amira sun zo Aunty Samha ce kawai babu da yake ta koma gidanta, gaida su Momy da Ammi, tuni Momy ta yalwata Fuskar da murmushi taja Aymanan jikinta tana tambayar ta lafiyar ta da gida, Tsuru Samha tayi tana kallon su cike da Sha'awa tana da bata biyewa son rai ba da yanzu har ita haka Momyn zata yi mata, tasan sosai Momi ta nuna mata k'auna ta gaskiya su kuma suka yaudare ta, ko yanzu tana mata saidai ba kamar lokacin da take tare da d'anta ba "hasbunallahu wa ni'imal wakeel ta shiga maimai tawa a ranta tana Neman tsarin Shedan, a yanzu bata k'aunar abinda zai saka ta k'untata wani bare koda ta fatar baki bare jininta.... Amaryar Uncle salman mai suna Fauziya tana tsakiyar su sai fira ake nan Aymanah ta shige cikin su bayan sun gaisa da Amaryar Uncle din da Aunty Samiha su Amira kam tsiya suka shiga yiwa juna, nan da nan Suka saba Da Fauziya dake ita kai waye ce ta saki jiki sai fira ake .. Sai cewa take "gaske da Yaya ya kasa mantawa da Aymanah Ashe Aymanan wanke hannu ka taba ne chanchadi" dariya sukayi a tare "Shiyasa ai ta kama yaya yadda takeso" cewar Nusee, harara ta watsa mata "talle kewa Audi gori aike da Amira zan gayawa haka malama" dariya suka karayi sannan tace... "Ke kuma matar Uncle ai kin ma fini had'uwa Allah" dake itama kyakkyawace ba laifi "kika ce ba, amma kema kinsan gaskiya ai" nan sukaci gaba da shan firar su suna kyakyatawa abinsu cike da nishad'i... Samiha kam ganin firar tasu ce yasa ta zame jikinta da sunan zata shiryawa Abba abun bud'a baki Dan tuni firar tasu ta koma daki yadda zasu fi sakewa... Sai bayan isha suka wuce gida cike da farinciki, Su Salman sukayi musu alkawarin Zuwar musu gobe kafin su wuce, suma suka wuce gidan da suka sauka na wasu causing Nasu... "So much thank you My khaleel" tace bayan ta Dora d'ayan hannunta akan nasa wanda baya driving dashi... "Are you happy?" "Bohot kusshi pyaa(farinciki sosai masoyina)" Murmushi ya saki "lallai matar Khaleel yau Indiyanci akeji...." _Sorry fans aci gaba da hakuri dai👏🏻🤝🏼😍_ *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* 🌍 *Duniya Makaranta*🌍 _Masoya sirri suke suna daga nesa juna, mafad'ata hargowa suke suna kusa da juna, kusancin zuciya shine mai muhimman ci bana gangar jiki ba_👌🏻 😍😘 *Masoya masu bibiyata ta waya ta message, through chat domin sanin lafiya ta saboda shiru da suka ji, nagode sosai da sosai da nuna kulawa, kuma na yaba muku matuka, Ku sani nima maryam Abdul kuna raina abubuwa ne kawai suka sha kaina, amma inshaa Allah, zanyi iya kokarina har na kammala muku Zuri'a daya lafia, Allah yabar zumunci🤝🏼, one love dearies😍😍😍💋* *Page* 5⃣2⃣ __________kulawa ta sosan gaske take samu daga gurin Mu'azzam, komai ya hanata yi indai yana gida komai shike mata, sai idan ya fita ne take d'an wasu kananun ayyuka duk da ya hanata yin komai yace kome takeson ayi mata ta saka Sabira, dake yarinyar Sam bata da kyuya ga kama jiki, kuma tasan makamar aiki, duk da kankantar ta Dan ba zata wuce 12years ba sa'ar su Munira ce, bata sha wahalar amfani da kayan birni ba dake ta san su a gidan Hajja saidai wasu wasu ta bata sani ba, suma da an nuna mata take ganewa, sosai take gyara ko'ina k'al, part d'in ogan ne dai bata shiga, shike gyarawa da kansa Dan ya hana Aymanah tayi masa... Yau ma kamar kullum, tsaye yake gaban mirror around 8am, perfumes yake fesawa cikin sauri da alama dai sauri yake, kama hannunsa yaji anyi Wanda ke rike da perfume d'in.... "Morning Habibty" yace yama mata murmushi tare da jan ta ya rungume ta da kyau sannan yayi pecking forehead nata, yana kokarin k'arbar turaren a hannunta.... Lumshe ido tayi jin saukar peck din tare da ware idon a same time, tana kallonsa, baki ta d'an zunburo gaba "shine baka tasheni na tayaka shiryawa ba" tace tana ci gaba da kallonsa sosai yayi mata kyau a suit d'in takan kasa tantance a wadanne kaya yafi yin kyau tsakanin suit, kaftan, kananun kaya, ta bar abin kawar akan daga halittar sa ne kowanne shiga yayi karbarsa take.... "Sorry Habibty kin manta da kina on bed rest ne, kina bukatar Hutu, nima ba dan fitar ta zamo ta dole ba, ai da ba inda zanje na barki keda my unborn" "Duk da haka My khaleel, kuma fa ni qlau nake jina yanzu dama fa na sati take gashi har ina shirin yin 2 week, kaki ka barni nayi komai, Allah ni na gaji da bed rest dinnan yaya Dan Allah ka barni yau na motsa jinina nayi maka girki da gyaran dakinka?" Cike da shagwaba take maganar tana bata fuska. Shafa fuskarta yayi "Baby rigima, ki bari ki kara hutawa pls, banason abinda zai taba min lafiyarki data baby nah" "Yaya pls ka barni Allah naji sauki, kuma na maka alk'awarin na fara naji bazan iya yi zan daina, pls Yaya ka barni na motsa jinina shima karin lafiya ne" cikin sanyi da taushin murya take maganar wata kalar tausayi, murmushi ya saki tare da lakuce mata hanci.. "Habibty badai wayo da dadin baki ba, naji kiyi din tun da zaki iya but kika ji ba dai2 ba ki barshi kawai kinji" girgiza masa kai tayi sannan ta kara fesa masa turaren tare da gyara masa Jan tie din wuyansa... "Kayi kyau sosai my Khaleel, um nifa ji nake kamar ma karka fita a haka a kalle mun kai!" Dariya sosai maganar ta ta karshe ta saka shi, musamman yadda tayi maganar da kishin nan.. "Uhm ai ke bakya tsoron kishiya keda kike kuka lokacin da ake kwashe kayan kishiya tsabar soyayyar ki da kishiya, ai ki bari kawai ayi replaced extra part din can" lokacin da Abba ya turo a kwaso kayan Samiha shine tai ta kuka wai kada a kwashe shine yake tuna mata....... Dire-diren kafafu ta fara tana dukansa a kirji tare da kukan sakarci Wanda babu hawaye fadi take "Allah ni yaya, Allah ni banason irin haka, ai dan tana Aunty Samiha ce shiyasa nayi kukan amma ni gaskiya ka dena min zancen kawo wata ko kuma Allah na koma gidan mu" dariya sosai yake mata tare da riketa gam ganin yadda take daga tsalle kar ta jima kanta da babyn su ciwo... "Rufamin asiri karki kwanto min kura baby! Sorry Habibty, nima da wasa nake miki kin sani ai, ba wata saike kika je gida yanzu kika barni ai matsala za'a samu" "Aiko tafiya zanyi in baka dena ba" kneeling yayi dai-dai waist nata...... "Na dena ai, barin gaisa da sweet unborn na wuce na kusa makara ana jirana" fara kal din best din da ke jikinta ya daga yana shafan Dan cikin nata da ya fito kadan Wanda ba lallai a gane ba in ba ta saka best ba ko body hug, shafawa ya shiga yi cike da shaukin son babyn, yanajin yadda yake motsawa a hankali, kafin yakai bakinsa ya manna masa kiss mai kyau, kallonsa take tana murmushi tare da kara godewa Allah daya azurtata da nagartaccen miji mai matukar kulawa, cikin ganin damarsa ba tare kaifinta ko dabara ba, hannayenta ta tsoma cikin lallausar Sumar kansa tana shafawa a hankali tana murmushi... Dagowa yayi ya kalleta " uh um baby bari karki janyo min rigima yanzu" tasan kwanan zancen, murmushi ta saki tare da zare hannayenta ta rungume su a k'irji, tana fadin na "dena" murmushi mai sauti ya saki bayan ya mike "raguwa" ya fada yana d'aukar brief case d'insa, hannunsa ta d'ora kan nasa, kallon yadai yayi mata, narke idanuwa tayi "break fast fa" "Don't mind dear, nasha tea and chips since, kema ga naki can" ya nuna mata mini center table din da ke gefen fridge "ki cinye gaba daya pls kafin ki fara aikin kinji" Girgiza masa kai tayi "kai da kanka kayi?" Noodling head nasa yayi alaman eh "meyasa baka saka Sabira ba, she's good in cooking dear" "I'm good too" ya takaita zancen tare da fara tafiya, tasan halinsa sarai bayason komai na yar aiki in ba dole ba, yarinyar da dak'yar yake amsa gaisuwarta yaushe zai iya sakata aiki "muje na raka ka to" tace bayan ta cimmasa tana karbar jakar... "Kiyi zamanki baby kada ki wahala da yawa hawan nan da sauka" nidai zan iya Yaya sai kayi ta sani cewa na dena komai kana ragemin lada" "Its OK! Muje" ya fad'a bayan ya zagaye mata kugu da hannayensa, yana murmushi itama murmushin ta saki, a haka suka sauko, ganin Sabira a falon kasan tana mopping ya saka ta zare jikinta daga nasa, ba musu ya saketa dama haka take batason yarinyar tana ganinsu manne da juna saboda kula da tarbiya... Gaida su tayi da lafiya kawai ya amsa yayi gaba fuska d'aure bakya ce shine ya sauko yana murmushi ba, cikin sakin fuska ta amsa mata tare da tambayanta lafiyarta..... Amsar brief case din yayi tare da pecking nata dake yarinyar bata hangosu "take care baby! I love you!" "Love you too Hubbi rouh, Allah dawomin dakai lafia, Allah ya taimaka ya bada sa'a, pls yaya ka kiyaye halal da haram saboda ka gina mu da halal yadda zamu dace gobe kiyama saboda duk dadin duniya lahira ta fita" Hannunta ya runtse cikin nata yana fad'ada murmushinsa shiya tabbatar ya gama dace da matar aure ya samu jindadin duniya saidai yayi fatar samu a lahira "inshaa Allah zan kiyaye Bilkisa nagode" itama murmushin jindadin samun sassaukan miji kamarsa tayi "ba godiya tsakanin mu yaya it my responsiblity! Take care" saurin juyawa tayi ta koma ciki Dan tasan taci gaba da tsayuwa gabansa ba tafiya zai ba gashi ya gama makara.. Shafo kansa yayi yana murmushi tare da bin bayanta da kallo, yadda take yawo cikin bujen wandonta irin na indiyawan nan mai fadi sosai..... ********** A corridor da zai sada shi da office d'insa, yaci karo da Barr. Zayyad, musabaha sukayi sannan suka gaisa, kallonsa Mu'azzam yayi da kyau "Barr Zayyad whats going on ne! Na ganka wani iri, jiya bana jinka da kyau da kayimin waya menene?" "Hmmm! Is a big issue Barr, mu shiga ciki nayi maka bayani" ba musu yayi gaba tare da bud'e office din... "Yes! Ina jinka Barr" ya fad'a bayan yayi mazauni kan kujerar office dinsa, shima Zayyad d'in ya zauna a gun wacce guest suke zama suna fuskanta juna... Fuskarsa kalar tausayi da bacin rai yace "is a case about raping" shima tuni fuskarsa ta sauya dawowar kasar nan zuwa yanzu yaga cases kala-kala amma majority akan raping ne ko child abuse, wannan wace musiba ce tayi yawa a cikin wannan al'ummar tamu.... "Ehem inajinka" "Wata innocent gal ce from a poor house, yaron gidan da take aiki yai mata fyade, the wicked guy haka ya mayar da ita karuwar gida Amfani da ita, bayan ya tsorata da duk ta bari wani ya sani saiya harbeta, a haka ta samu ciki in a very young age 12years, shine fa ya d'auketa ya kaita wata private clinic akan a zubar da cikin a garin yaya akaje aka samu matsala jini ya b'alle mata, tunda aka gaya masa ya shura takalmansa ya gudu, inda Allah ya kawo mata sauki, ta ari wayar wata nurse a asibitin ta kira Abbanta ta gayamai halin da ake ciki har asibitin, koda suka zo ta gama fita hayyacinta... Hankali tashe baban yaje can gidan aikin nata ya sheda musu amma kememe uban yace badai d'ansa ba saidai wani can daban haka ya zazzagesa yaci masa mutunci, in takaice maka dai yanzu hukumar 'yancin mata ce suka saka case din kotu, jiya bayan wucewar ka akazo aka sameni da case din, har asibitin nike wlh Barr saida na kokama yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, na girgiza kuma da case din, yaron d'an gidan Mai Dala ne, duk wata shaida sun boyeta Brr, case din yafi karfina shine nazo gareka nasan zaka iya assisting dina" Sosai labarin ya daka Mu'azzam matuka "zan taimaka Barr Zayyad, muje na ga yarinyar da iyayenta....." Baisan sadda kwalla ta zubo masa ba bayan yaga yarinyar da halin jin jikin da take sannan yaji cikakken labari daga iyayenta, Dan ita kam dakyar take magana yadai tabbatar da yaron ne ya aikata mata daga gareta, saidai ta ina zai fara yasan waye Mai Dala a garin da karfin power sa, saidai ya lashi takobin yin case din, Dan ganin yarinyar yake kamar 'yarsa ko k'anwarsa wadanda idan hakan ya faru dasu sai inda karfinsa ya kare.... Sosai yau ta zage ta gyara part din nasa hadda wanke masa inner wears, sannan ta sauko k'asa da taimakon Sabira ta had'a daddad'an girkinta favorite nasa tayi masa semo and egusi da kuma zobo da jinja duk dan ta Burgesa, saida ta tabbatar komai yayi yadda ya kamata sannan taje ta tsala wanka na d'aukar magana.. Sosai ta had'e cikin wata dakakkiyar Shadda brown gown ce tasha aikin sama, make up, sosai tayi kamar mai shirin zuwa biki bayan ta kafe d'auri... Ta damu sosai ganin had 4 after bai dawo ba wanda iya dad'ewar sa, 3 ga ko kiran da text da yake mata bako daya yau... Ta kikkira yana ring be daga ba, jugum ta zauna tana tunanin ba lafiya kam... Can zuwa 5 ya dawo tun daga yanayin fuskarsa ta fuskanci da damuwa, duk da kokarin boyewa da yakeyi "wow princess wannan kyau haka ina zaki kaini?"yace bayan ta tarbesa tare da yi mata sannu da zuwa... " Yaya muje kayi wanka ka gaji da yawa" sosai tafiyar da shi tare da taimaka masa yayi wanka tare da cin abinci, bayan sun kammala ya d'an huta tazo ta sameshi yana zaune yayi nisa cikin tunani Wanda a zahiri nazarin case d'in nan ne kawai yakeyi.... "Yaya!" Ya kirashi bayan ta kama hannunsa, ido ta zuba masa bayan ya d'ago ya kalleta.. "Meke damunka ne?" "Sorry baby yau ba kira bare text ko?" Sai lokacin ya d'auko wayarsa wacce ya sakata a silent run lokacin da sukaje clinic din nan.... "Ashe ma har kirana kikayi kin gani ko a silence take ban gani ba" "Yaya menene?" Ta kara fad'a cike da damuwa... Dago hannunta yayi ya sumbata "kada ki saka Damuwa dayawa fa kinsan conditions naki wani Case ne kawai ya tasomin" dama tayi tunanin haka yana mugun saka kan shi damuwa indai yana da case ta kula da haka tun ba yau ba... "Yaya na menene hala?" "Uh um! Nasan halinki da tausayi zaki iya saka damuwa kema a ranki, banason wani Abu ya sameki ko baby nah kimin Addu'ar nasara kawai" "Pls yaya ka gayamin ba abinda zai faru..." Rungume ta yayi yana dora hannunsa a cikin ta "barin duba lafiyar babyn Abinsa nayi missing nasa"........... So yakeya share zancen ta fahimci haka " Yaya Mana" ta sake fad'a tana narke masa...... _love you my fans😍💋_ *Siddiqa CE* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* 🌎 *Duniya Makaranta* 🌎 _Idan Allah ya daukaka ka duniya da masoyanka zasu san matsayinka, idan ka shiga jarrabawa lokacin ne zakasan asalin masoyan ka._👌🏻 *Page* 5⃣5⃣ _________washe gari su Uncle Salman suka zo kamar yadda suka yi musu alk'awari, wuni cur suka musu sai bayan asr suka wuce, sosai wani irin sabo da shakuwa suka shiga tsakanin Fauziya da Aymanah kace wasu kawaye da suka taso tare, sai tsakanar juna suke suna ta areren su, shima Mu'azzam tun yana dari-dari da cin magani saida ya sake yadda Uncle Salman ya keta jansa da hira gasu Adnan da Hafiz suma sunzo dake basu samu haduwa ba jiya, dole ya sake shima akayi dashi, saidai duk da haka yana yi yana basarwa da yamutsa fuska Wanda dama his nature ne shima Salman d'in ya fahimci hakan.... Exchange contact sukayi tare da tabbatar da zasu ci gaba da zumunci dan an riga an zama d'aya, Fauziya na tabbatar da Aymanah data haihu ta sanar musu tun suna hospital dan suzo cin remgem da wuri, dariya tayi ta tabbatar mata aiko itace zata fara gayawa ko, haka suka rabu cike da nishad'i..... Dakika da koma sakan, sakanni sun koma awa, awanni sun juye sun zama kwanaki, kwanaki sun koma watanni, watanni haka rayuwa ke nausawa da dad'i ba dad'i farinciki sab'aninsa is all about life... Zuwa yanzu Samiha ta gama iddar ta, in ka ganta a yanzu kai da kanka kasan ba waccen Samihar bace ta dawo wata Sayyada, bata missing zuwa islamiyya duk da tana kan karatun ta ne, duk ta tattare gyalulukan ta ta kyautar ta mayar da hijabai ta dawo decent sosai so cool, tuni manewa sun fara kawo mata hari tun daga Samari zuwa Zawarawa, ganin haka ne Abba da Dady sukace ta tsaya ta nutsu ta zabi wanda ya kwanta mata a rayuwa ta yadda da halayyarsa ta tsayar sai su kuma suyi bincike yadda ya kamata, su Momy ta shawarta inda Ammi tace ta farayin istikhara duk wanda ranta ya nutsu dashi shine mafi alkhairi agareta..... Shawarar Ammi tabi tayi istikhara, cikin ikon Allah taji ta samu nutsuwa da wani Sudais dan abokin Dadyn ta ne, yayi aure saidai matar ta rasu gurin haihuwa, dake dama a shirye yake cikin k'ank'anin lokaci komai ya kankama..... ************** "Yanzu Kabiru haka zakayi ta zama ba mata? Ka maida matarka kace sam kuma kak'i ka sake wani auren Anya Kabiru rayuwa zatayi haka, kada ka manta fa kune kad'ai kai da d'an uwanka kuka ragemin ba Mahaifinku ba d'an uwanku u'um?" Hajja tace da Dady, cikin sigar rarrashi da nasiha... "Nima abinda nake ta magana kenan Inna yayi hakuri ya mayar da matarsa kodan darajar zuri'ar da ke tsakanin su, ga auren 'yarta za'ayi bata da masaniya, ka rabu da ita kuma ka rabata da yaranta, kar kaga sun d'auke idonsu suna bin duk abinda kakeso ka d'auka basa sonta, komin munin halinta suna k'aunar ta kuma basu da sama da ita, kuma na tabbatar zuwa yanzu itama ta gama gane kuskuren ta, ka d'aure ka bata wata damar Ku sake zama" Abba ya dora akan zancen Hajja. Jinjina kai yayi Suwaiba tayi musu abubuwa fa a rayuwa "Inna, yaya bawai naki ta taku ba, amma kada Ku manta wacece Suwaiba ba wanda batayiwa tab'o a cikin mu ba, bata tsoron Allah bata da imani..." "Haba Kabiru ya kake magana kamar haka, kamar ka manta kaddara?" Hajja ta fad'a a d'an tsawace.... "Kanina kada ka manta ko ubangijin mu muna masa laifi ya yafe mana bare d'an Adam, kai da kanka kace Yayanta ya tabbatar maka da canjawar ta, ka daure ka bata damar nan kayi mata uziri ajizanci ne irin na d'an Adam" Abba ya fad'a bayan ya dafa kafad'arsa da sigar rarrashi... "Shikenan zan dawo da ita inshaa Allah, Allah ya shige mana gaba" a tare suka amsa da Ameen, kana sukaci gaba da tattaunarwar da sukeyi game da auren Samiha.. Cikin gida kuwa shiri sosai sukeyi game da bikin, sosai Samiha ke ganin gata gurin Momy da Ammi har hajja ba'a barta a baya ba, tuni ta d'auki sheki dama ba Samiha akwai kyau a fuska jikin ne dai a bushe shima ba laifi ta cicciko da taji tsumi d'an gaske abinda ta rasa a auren ta na fari.... Su Aymanah ma ba'a bar su a baya ba, suma suna nasu shirin duk da kaffa-kaffa da Mu'azzam keyi da ita Saboda Babyn sa, amma tsabar rigima kullum tana hanyar gida suna tsare-tsarensu, dasu nusee hadda Kawalliyar Amarsu Samhar Farooq, d'an cikin Aymanah da ya shiga watanni bakwai ya fito das, sosai yayi mata kyau, har Mu'azzam ke tsokanar ta wasu lokutan wai kamar kar ta haihu tafi kyau da ciki, duk ya gaya mata haka cewa take kace haka man tun da bakai ke d'auke dashi ba, dariya yakeyi mata yace yo meye marabin dambe da fad'a bayan duk keda cikin d'aukeku nake bari ma kiga... Nan yake d'auketa yayi ta zagaye da ita suna dariya, zallar k'auna take gani daga gareshi tasan itakam ta gama dacen duniya saidai fatar dacewa a kiyama kawai....(Allah yasa mudace ) _Ina labarin Umma wai.........?_ Umma duniya ta gama juya mata baya, dama ance idan kaga duniya bata baka kashi ba ka dena farinciki watakila tana gurin debo tsumagiyoyin ne, dama hausawa na cewa tafi bagaruwa iya jima, aiko ta jefe da Umma, Sosai zaman gidan Yayanta yayi mata matukar zafi, jinta take wane tana saman kaya, duk daukar kai jiji dakai da tak'ama ta nemesu ta rasa, Hajia Suwaiba mai wasa da nerori yau itace nera Biyar ke bata Sha'awa, tayi kuka tayi nadama mara iyaka, kullum saita roki yayan ta dan Allah yaje ya nema mata gafarar Dady take ya taimaka ya mayar da ita wlh ta gane kuskurenta a nema mata gafarar Abba dasu Ammi, dan Allah ya mayar da ita gurin yaranta, kullum maganar ta kenan, zaman daki kuwa wane matar takaba, tuni ta siyar da trolleys din ta da wasu daga cikin suturun ta ta cinye kud'in a cikinta, idan ka ganta ba zaka shede ta yadda ta jeme ta lalace tayi baki.... Tsakanin ta da matan gidan saidai harara da kallon banza, ga yaransu Sam basa jin maganar ta, sun gama renata, tayi laushi sosai kai ba kace Suwaiba ce mai bakin taurin rai da Zuciya ba, ta gane duniya ce ke rud'ar ta, kullum cikin kukan nadama da istigfari take, imana Dady zai barta taje gidan ta nemi yafiyar su.... Yau ma guraren karfe 3:00pm tana zaune kan darduma tana jan carbi tun da tayi zuhr bata tashi ba, sallamar yayanta ta jiyo bakin k'ofa hakan yasa ta amsa cikin sauri dan ta d'auka yazo yayi mata d'an ihsanin da ya saba yi mata ne idan ya dawo daga kasuwa na bada 200h ko 500h wani sa'in "bismillah Yaya shigo" ta amsa mishi... Dogarewa da kulkin k'ofar yayi tare da d'aga labulen yana hangota, sannu da dawowa tayi mishi bayan ya amsa yace "baki ne dake suna soro kiyi maza ki kimtsa" yana gama fad'a bai jira amsarta ba ya sauke labulen tare da wicewa.. "Bak'i?" Ta maimaita yafi sau uku, kafin ta yunk'ura ta tashi, cike da tunanin su waye kodai manema ta fara samu ne, inko hakane zatayi auren dan rufin asirin ta, dan zuwa yanzu ta gama cire tsammanin Dady zai waiwaye ta, hawayen tausayin kanta da kanta suka wanke mata fuska wato son zuciya bacinta bata ga 'ya'ya bare miji..... Turus taci burki take da tsayawa tana zaro ido waje, mamakin ganin Dady har da Abba ya gama cikata, saida yayanta yace ta karaso sannan ta iya d'aga kafafun da sukayi mata nauyi zubewa tayi gabansu tana kwasar gaisuwa kamar mai Neman gafara, mamaki ne ya ishe su na farko ganin yadda ta koma na biyu kuma ganin yadda take zuba musu gaisuwa kamar ba itace tayi musu tujara ba... Amsawa sukayi sannan ta samu gefe ta labe kanta kasa, zuciyarta sai harbawa take dan batasan takamammen me sukazo dashi ba.... Abba yayi gyaran murya "Malam Mu'azu kamar yadda na gaya maka ba wani dogon zancen zamuyi ba, nazo nemawa kanina kara auren Suwaiba ne a karo na biyu" zabura Suwaiba tayi kawai sai ganinta gaban Abba sukayi "Yaya Aurena fa kace? Kara bani wata damar zakuyi kenan? Zaku sake barina a cikin zuri'ar Ku kenan? Wace irin kyakkyawar zuciya ne daku? Zuciyar yafiya da rangwame, nagode nagode yaya, dan Allah Yaya kafemin kayimin gafara wallahi na tuba na gane kuskurena kuma nayi alk'awarin komawa cikin Zuri'ar ku da zuciya d'aya, na canja wlh na canja daga Suwaiba mara imani da son zuciya zuwa Suwaiba ta gari..." Dakatar da ita Abba yayi da Hannu kafin yace "komai ya wuce Suwaiba, Allah ya shige mana gaba" Dady kam komai k'in cewa yayi duk da tausayin ta yad'an darsu a ransa saboda ko ba komai sone ya hadasu kuma hadda zuri'a, basarwa kawai yayi dan ya auna hankalinta kota shiryu da gaske ne ko algus ne... Nan kuma Abba ya sheda musu auren Samiha da za'ayi wata mai zuwa sannan yace zasu dawo wani sati sai a mayar da auren su Umma, taso ace yau dinnan aka mayar saidai ba yadda ta iya dole ta hakura har wani satin kada aga zalamarta amma anata son ran taso a d'aura yanzu kawai su wuce tare( 🤣 wuya ba dad'i, waya gaya miki gombe gabas take).. 20k Abba ya dire mata yace ko zatayi wani abin, dan da ganinta kaga mabukaciya aiko hannu na rawa ta amsa tana kwarara godiya uwa marokiya, ya bawa yayanta 10k, da zasu wuce ko sai kallon Dady take ji take kamar taje ta rumgume shi ta gayamai how much she missed him, gashi har zai tafi ya hanata jin koda muryarsa ne..... Lokacin Abba ya gayawa su Momy dawowar Umma, sosai tashin hankali ya bayyana a tare da Momy har saida ta furta "dawowa kuma Alhaji" jinjina mata kai yayi "tabbas dawowa saidai ina muku albishirin zata dawo ne da kyakkyawar niyya" Fatan alkhairi sukayi kawai, yaran ta ma sunyi farinciki da jin zata dawo tun da koma meye itace dai uwa mahaifiya a garesu, saidai basu nuna a fili ba gudun kada marikan su, su d'auka ko sun rena da k'ok'arin su ne, barin ma Samiha da suka yiwa komai.... Kamar yadda sukayi alkawari sati na zagayowa suka d'auko kawun su daga Gwarzo, dama yasan da zancen, itama Nasu kawun yazo nan take aka mayar da auren bayan Abba ya biya sadaki, ana gama d'aura auren Amarsu ta tattaro 'yan Tsummo karanta bako 'yan rakiya ta biyo zugar angwaye😆 ba laifi tad'an washe ta rage ramar da bakin kad'an nace 20k Abba sunyi taimako... Matan yayyin ta, ma sai ranar auren mai gidan ya sanar dasu, aiko lokacin da tazo musu sallama jikinsu sanyi qlau yayi sun san kalar rashin mutuncin da sukayi mata bazai fad'u ba, dan sun d'auka ba zata koma gidan ba, itadai ko ta Kansu bata bi sai murmushin ta na farinciki da takeyi, murmushin da ya kara nutsar dasu kogin kunya.. Suna isa gate kafin gate man ya bud'e musu ta saki sassayar ajiyar zuciya tare da yin hamdala wa ubangiji daya azurtata da wannan ranar... Mamaki ne ya kamasu ganin yadda aka gyara harabar gidan Ashe walima ce suka shirya musu, wadda Hajja ce tayi Jagorancin ta, duk yaran gidan sun hallara inka cire Zulaiha da bata gari.... Umma na fitowa tayi arba dasu kowa cikin shiga ta Alfarma, kallon kanta tayi da kayan jikinta sanyi jikinta yayi sosai lallai bata kyauta ma kanta ba, sai taga ma duk sun sake sun kara wani kyau na musamman... Ruu sukayo kanta suna murmushi tare da yi mata barka da zuwa, kunya ce ta lullub'eta sosai ta kasa motsawa sai kasa da tayi da kanta... Zube gwiwowinta kasa tayi tare da kama kafafun Hajja "Inna dan Allah kiyi hakuri ki yafemin..." Saurin dakatar ita hajja tayi tare da mikar da ita suka rungume juna "karki ce komai Suwaiba Allah ya yafe mana baki daya" hawaye sosai kebin kuncinta "Ameem nagode Hajja" kallon Momy tayi "aunty Zainab..." "Aa Suwaiba komai ya wuce Allah ya yafe mana baki daya" Cikin rauni ta kalli Ammi "Fatima dan Allah..." Saurin rufe mata baki tayi "komai ya wuce Aunty Suwaiba wannan kaddarar rayuwar mu haka, Allah ya kara mana hadin kai da fahimtar juna" Momy ta karasa da "ya kuma Kore shed'an da son zuciya a tsakanin mu" Ameen suka Amsa a tare har yaran... _My friends sai kun kara hakuri dani, abubuwa ne suka min caa wlh shiyasa, amma Ku sani kuna raina😍😍😘_ *Siddiqa CE* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* 🌎 *Duniya Makaranta* 🌎 _Aboki zama biyu ne a rayuwa, wanda zaka karu dashi da wanda zai karu dakai, na ukunsu banza ne, ka/ki gujeshi_👌🏻 *Page* 5⃣6⃣ ________Hannu ta sanya ta jawo Aymanah zuwa jikinta "kiyi hakuri kiyafe min ba dan halina ba domin Allah 'yata" jinjina kai tayi "komai ya wuce Umma, Alhamdulillah da Allah ya nuna mana wannan ranar mai albarka" gefen hannunta tasa tare da goge kwallar da ta zo mata, tana murmushin takaici da jin kunyar abubuwan da ta aikata a baya "Haba keko Umman Sageer ki dena irin haka mana, kada fa ki manta ranar ki ce yau kefa Amarya ce" Ammi ta fad'a da sigar tsokana dan da kawar mata da wasu kaso na halin da take ciki, dariya sukayi a tare har hajja, sauran yaran mata suma sukayi murmushi, duk yadda Umma taso ta sake ta kasa gani take kamar har yanzu suna kallon ta da abin da ya faru a baya ne... Sai daf da magrib aka kammala kwarya-kwaryar Walimar, daganan suka wuce cikin gida aka gabatar da salloli, dama tun rana su Nusee suka gyara part din na Umma, Aymanah ma da ita akayi saidai bayan ciwon baki ba abinda ta aikata musu dan su Aunty Samha sun ce ba wani aiki da zatayi tanaji da kanta, Nusee tace wariyar launin fata dai tun da suma jin suke da kawunan su, bayan gwalo da tsokana data sako su gaba dashi, su kuma sai mita suke...... Bayan isha Su Momy suka raka Umma part din ta bayan Su Mu'azzam, Adnan, Hafiz sun shigo wucewa da matayen su, nan ma dai rokon yafiyar su Umma tayi suma sukace bygone by bygone, farincikin Hafiz kam ayau ya kasa boyuwa sai Murmushi yake yau shima Mahaifiyarsa ta dawo turbar gaskiya..... Duk yadda Dady yaso basarwa saida Umma ta shawo kansa da lallashi da rokon gafara da kwantar da kai, sannan ya sauko ya kuma yafeta daga baya kuma labari yasha banbam Ashe dai gyatumi yayi missing din gyatuma shima nan aka shige duniyar k'auna (oh 🤭 tsofai-tsofai su gwaggo🤪).... Zaman lafiya na sosai wanda ahalin basu tab'a tunanin samu bane ke wanzuwa a gidan, kowacce a cikinsu ta tsarkake zuciyarta tana zama billahi ilallahi, sosai farinciki ya wadatu da annushawa a cikin gidan, wanda sai a yanzu suma suka fahimci Ashe wancen zaman rikicin cikin gidan da sukayi a baya ba Ammi kadai ya cutar ba har su, Ashe dai gaskiyar hausawa da ke cewa zaman lafiya yafi zama d'an sarki.... Dawowar Umma bai saka Samiha barin part din Ammi ba tana nan daram anan ake shirye-shiryen komai dan ita kam jin Ammin take na sosai a ranta kamar mahaifiya take jinta.. Tun da aka shigo satin auren shirye-shirye ya kara kacamewa tuni gidan ya fara karbar baki ta ko'ina kai kace auren fari ne, ba kunya ranar aure saiga matan Yayan Umma saidai kam jikinsu a sanyaye sanin tsiyar da suka shuka mata, ga mamakinsu sai sukaga ta karbe su ba tare data nuna musu komai ba cikin faram-faram sai hidima da take dasu, basu San tasun tayi darasi ba yadda takeji a yanzu komin girman cutarwar mutum a kanta ba zata iya tsayawa tayi ramako ba, adai yadda rayuwa ta bata darasi kuma successfully Allah ya kara dawo mata da ni'imar meya rage mata bayan godiya washi da wadannan ni'imomin musamman cire daga duhu zuwa haske...... ************* Sanye take cikin doguwar rigar material d'in da sukayi akon yinin biki dashi ash mai manyan touches din red, hakan ya bata damar amfani da red Kashmir veil da flat shoes and purse suma duk red, sosai tayi kyau abinta ga cikinta daya zauna das ya kara mata kyau, tasha make up da d'auri head, wanda tayiwa amarya ce ta musu suma.... Dube-dube take ko zataga yaro a harabar gidan ta aikesa, fizgarta taji anyi da k'arfi, cike da tsoro ta bare baki tana shirin zunduma ihu, saurin rufe mata baki yayi da hannun "dalla malama yi mana shiru, waye zai zo har cikin gida ya saceki, farar kura kawai" sauke ajiyar heart tayi tare kallonsa yadda ya yake wani yamutsa fuska saima yaso bata dariya, murmushi kawai ta samu zarafin yi..... Yayi mata kyau cikin Ash d'in giznarsa wacce tasha aikin sama wanda ya k'ara fitar da cikar haibarsa hannun na clips ne inda yayi amfani da wani had'adden clips mai chain, bakar hular tangaran ya murza saman lallausar sumar sa, ba karya yayi ba hasada, hannunta kawai yaja zuwa dakin sa na gidan... "Ke ko?" Ya fad'a bayan ya zaunar da ita kan seat, ya watsa mata harara, tasan laifinta bai wuce yadda da tayi ta kwana gidan ba, dake basu gama ayyukan su ba jiya duka gidan suka kwana dan basu suka gama ba sai around 2am na Daren jiyan... Tun da taga ta tura masa morning text da ta kira duka ya kyaleta tasan ya shaka dama ko jiyan sanda Momy ta korasa ya yadda ya wuce.... Kwantar da kanta kan cinyarsa tayi tana wasa da button din gaban rigarsa cikin karyar da murya da neman sulhu take magana "pls kayi hakuri mana I know am wrong u but don't mean to hurt you" k'ara dauke kansa sama yayi "uhm" kawai ya furta... Murmushi ta saki tare da zageye shi da hannayen ta, saman mak'ogoronsa ta Dora hannunta ta mintsilesa aiko da sauri ya sauke kam yana dariyar dole "kedai kin shigesu da fitina Allah, bayan kin kwareni kin Nisan tani da baby nah na tsawon rana" yace yana Jan mata kunne... 'Yar kara tayi "kaiko gwanin iya k'eta ba, yo naga auren ex d'inka ne ba gwara nayi participate sosai ba" zaro ido yayi. "Lalalala! Dama ashe kin matsu ta tafi kina tsoron na dawo da abata" dariya tayi sosai "lallai ma Yaya kaiko anya kodai kishi kakeyi anya ma wannan fushin bashi da nasaba da auren ma?" "Oho! Wai ma wace gulmar ce ta fito dake daga gidan, kodai missing din mijinki kikeyi 'yan mata" yace tare da daga mata gira yana kashe mata idonu" d'an duka takai masa tana murmushi.. "Yo idan ma hakane laifi nayi, tun da mijin nawa ya kasance gwanin ado da jan hankali Wanda kesa dole ayi kewarka idan akayi nisa dakai" Murmushi ya saki tabbas kalamanta sun karbu, sun isa kamar yadda ya dace a birnin zuciyar sa, amma sai ya basar "uhum sannu tsari master, ana missing din nawa ne aka nisance ni, kinga bama wannan ba, in har zai yuyu kizomin da ex dina yanzu" dariya ta saki... "Shaukin ne ya motsa, karfa ka manta saura awanni dai" tace tare da mik'ewa domin cika umurninsa, tasan waye mijin nata sosai dan haka ko d'ar bataji a ranta ba... Rike mata hannu yayi tare da zuba mata narkakkun idanuwansa masu nakasata, saurin d'auke nata idon tayi saboda tsaro "a bari na gaisa da babynah tukun madam, kada zafin yamin yawa" ya fad'a k'asa-k'asa kamar mai rad'a, ganin bata motsa bane ya sanya shi mik'ewa tsaye shima ya taka gun ta.... Sunkuyawa yayi dai-dai cikin ya dora bakinsa tare kissing nasa, sannan ya saka hannayensa yana shafar cikin a hankali, sosai yakejin nishad'i yadda yakejin movement na babyn a hankali, zagaye hannayensa yayi a waist nata tare da sauke mata peak a forehead "habibty babynah yayi break" da kai ta amsa "sure?" "Yes Habib rouh" "Gud gal" yace "in tafi?" Ta fad'a a hankali dan tasan halinsa sarai karamin aikinsa ne ya baro mata aiki yanzu, shiru yayi kamar ba zai amsa ba, komawa yayi ya zauna kan seat tare da jingina bayan saman kujerar ido a lumshe "yeap jeki".... Bayan 'yan mintuna sai gata ta dawo tare da Samihar wanda take mamakin kiran Ya Mu'azzam din dan idan bata manta ba tun rabuwar sa har zuwa yau iyakacin gaisuwa ke hadasu shima idan yazo gidan sun had'u..... Kyautar 100k yayi mata tare da set na jewelry na gold, sannan ya Dora da guntuwar nasiha tare da mata fatan Alkhairi, tsantsar farinciki ta riske shi a wannan ranar ashe Ya Mu'azzam bai tsaneta ba kamar yadda take tunani, godiya sosai tayi masa tare da kara cewa Aymanah ta tayata godiya, Sam ran Aymanah bai sosu da abinda yayi ba saima burgeta da ya kara yi, cikin gida ma sai farinciki suke tayata Umma kam ta rasa bakin magana tabbas Allah na sonsu da rahamar sa..... Amarya dai a ranar ta tare gidan mijinta dake Kaduna bayan tasha fatar alkhairi daga masoya da 'yan uwa.. *A week later....* " Habib Rouh! Pls ka barni naje, Allah yaya jikina yamin nauyi, kuma kaga Dr take ina ringa exercise" a marairaice take maganar uwa tayi kuka, ido ya zuba mata Sam bayason fitar a ransa saidai ta riga ta nace gashi kuma ya riga yayi latti... "Kinga Habibty ki zagaye cikin gidan nan mana ai is OK for you, kibar zancen fitar..." "Yaya Mana, kaga fa tun da nike a unguwar nan ban taba fita koda gate d'innan da kafana ba fa saidai a mota kullum nidai yaya uhum!" Dafe kansa yayi, ta Riga ta iya fitina in ta motsa mata ba dama bare yanzu har cikin na kara mata ita, ga fushin banza data iya Abu kad'an sai ta haye "is OK, ki bari idan na dawo zamu fita tare mu zagaye unguwar!" "Uh um! Nidai nafiso yanzu da sanyin safiyar nan, Allah ba dadewa zan ba, kuma ai tare da Sabira zamu fita ta rakani" "Oh! Shikenan kije but pls take care of ur self and unborn for me pls" "I'll yaya inshaa Allah, Allah ya tsaremin kai a dawo lafiya" ameen ya amsa tare da wucewa da Sauri, itama ciki ta koma cikin farinciki ta d'auko hijab da wayarta da purse, ta kira Sabira suka fita.. Sosai yanayin yake fizgarta tana jin dadin sansayar iskar safiyar, kallon unguwar take daki-daki da kyau Ashe dai ba laifi unguwar Nada kyau, hango mai siyar da agwaluma tayi, nan take yawu ya tsinke, yana d'an nisa dasu bata tsaya wata-wata ba, ta fitar da kudi a purse tare da nuna wa sabira shi akan ta siyo mata ita kuma ta samu wani d'an dutse a gurin ta zauna... Game ta fara yi da wayarta hankali kwance kafin sabirar ta dawo su wuce, jin nauyi a kanta alamar an tsaya mata yasa tayi saurin D'agowa... Zaro ido tayi k'irjinta uwa ya fito waje ganin gardawan da ke gabanta su uku kowanne fuska a murtuk'e ba rahama... Kafin tayi wani yunk'uri, d'aya daga cikin yayi saurin shaka mata wani farin kyalle a hanci, nan da nan ta zube a hannunsa a sume... Kinkimar ta sukayi suka saka a motarsu tare da barin unguwar da gudun tsiya............... _🤦🏼‍♀😰 Wayyo silly Aymanah kosu wanene oho! Kome ta musu?, Abu dai kamar ana targeting ta🤔?_ *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* 🌎 *Duniya Makaranta* 🌎 _idan muka rasa kudi mukan ji ciwo mu samu damuwa a ranmu, a kullum mukan rasa kwanakin mu na Duniya amma bamajin komai ko a jikin mu, hmmm kudi abokin tafiya👌🏻_ *Page* 5⃣7⃣ ______Koda Sabira ta dawo wayam ta samu gun da tabar auntyn nata ba koma, gudu tayi sosai har karshe layin bata ba mai kama da ita, tunanin ko gida na koma ya sanyata rankaya wa gidan... Tana haki ta isa gate, da sauri gate man din ya taso ya cimma ta ganin ta a firgice kuma ita d'aya ba matar gidan, tambayan ta ya shiga yi ina Hajia, k'ara firgicewa tayi tace tare da gayamai abinda ya faru, shima nan take hankalinsa ya tashi, wayarsa ya koma da sauri ya dauko tare da dannawa uban gidan nasa kira..... Mu'azzam dake zaune a office d'insa, tun da yazo ya kasa yin komai haka kawai yake jin yanayin ba dad'i Sam baida kuzari, wayarsa ya zaro da niyyan kiran Aymanah yaji ta koma gida duk da yasan dole ma ta koma tun da tace ba dad'ewa zatayi ba, kusan sau uku yana gwada no ta ana gayamai tana a kashe, kuma duka rayukan ta, mamaki ne ya kamasa yasan tana da full charge kuma rufe waya ba dabi'arta bane, kafin yayi wani dogon nazari sai ka kira ya shigoshi ganin gate man ne ya saka shi hanzarin d'auka dan yasan da wata a kasa.... "What!" Ya fad'a da k'arfi, tare da yasar da wayar a k'asa, zubewa yayi akan seat tare da dafe kansa da dake wani juya masa "what's mean ba'aga Aymanah ba, meke shirin faruwa ne?" Da sauri ya mike cikin zafin nama kamar wadda akayi allura keys kawai ya zara ya fice da sauri... Koda ya isa gidan kuka sosai ya samu Sabira nayi, tsawa ya daka mata "ya akayi ta bata amma ke gaki anan?" Ya fad'a a tsawace, aiko tuni jikinta yad'au bari, cikin inna-inna ta gayamai yadda akayi tare da nuna masa agwalumar da canjin.... "Innalillahi wa'inna ilairraji'un" ya fad'a cike da tashin hankali "kuma ko alamar ta baki gani ba da kika dawo?" Kanta ta shiga juya masa kamar kad'angaruwa...... Bai sake bi takan su ba, ya sake figar motar ya fice tsiyace, direct police station ya zarce yakai report, duk tunaninsa ya gama tushewa to me zaisa a sace masa mata me yayi da zafi haka, me tayi itama da za'a saceta ba tare da an duba yanayin ta ba, rashin sanin madafa da abinyi ya saka shi zarcewa gida direct dan su san halin da ake ciki.... Sosai hankulan su suka tashi matuk'a, anyi Sa'a Dady na gida Abba ne dai bayanan, cikin tashin hankali Dady yace "kinga Suwaiba idan da hannunki a cikin b'atan yarinyar nan, tukan abin yayi nisa ki gaya mana" tuni hawaye suka wanke mata fuska illar mugun hali kenan, ko ka bari ba lallai tambarin ya tafi ba, dana sani na sosai take da rayuwar bayanta gashi har yanzu mijinta bai gama yarda da ita ba..... "Haba Yaya taya zakace haka, Ummu sageer ba zata aikata haka ba, adai bincika gidajen 'yan uwa tukun ko can taje kila" cewar Ammi duk da hankalin ta a tashe yake matuk'a da batar 'yar tata wacce take da tabbacin ba inda zataje a halin da take ciki, jikinta na gaya mata saceta akayi amma bata zargin Umma dan d'an zaman da sukayi na dawowar ta, ta fuskanci tayi tubar gaske... Hajja kuka take bil hakki "Kabiru ku kira Mamuda kuje ku binciko marainiyar Allah nan, Suwaiba ba zata aikata haka, dan Allah kuje Ku nemota" "Dadyn Samiha wlh babu hannuna a ciki ka yadda dani" sai kuma ta bashi tausayi ganin yadda take kuka "kiyi Hakuri Ummu sageer ki dena kukan mun sani ba zaki aikata ba, bara na kira Alhaji yanzu yasan me ake ciki" cewar Momy.... "Nifa na fara zargin akaina ne aka saceta zai zamo cikin mutanen da nayi shari'a akan su ne" sai lokacin mu'azzam yayi magana bayan ya dad'e yana nazari akan abun... "Idan kuwa haka ne gara ayi reporting case dinnan wa police, sannan kuma abi kididdigin wayarta yadda abin zai so da sauki" cewar Momy.. "Haka ne bari muje kafin yayan ya iso" "Dady na riga nakai report d'in tuni ai" dafa kafad'arsa Dady yayi yana bubbugawa .. "Relax my son be a man, kada ka damu za'a ganta inshaa Allah, cikin koshin lafiya" Sai lokacin hawayen da yakeson yi suka samu damar sauka "Dady meyasa zata biya bashin laifina? Me tayi musu? Meyasa ba zasu yimin ba nida nayi musu?" "Take it easy, kaji zo muje" bin bayansa da kallo su Momy sukayi sosai ya basu tausayi yadda ya koma wani iri kamar ba sadaukin jarumi Ibrahim mu'azzam bane.... ********** Da salati a bakinta ta farka tare da bin dak'in da take kwance da kallo, sannu a hankali kwakwalwar ta, ta tariyo mata abunda ya faru, da sauri ta mike cikin tashin hankali, zuciyarta na burgawa da sauri Wanda ya haddasa wa dan cikinta juyawa da k'arfi, hannayenta ta saka ta tallabe cikin, tana hawaye tare da Dana sanin bijirewa maganar mijinta, tana tunanin dalilin sato ta a kawo ta anan... Jin an turo k'ofar ne ya sakata kallon k'ofar da sauri, daya daga cikin mutane ukun nan ne masu mummunar kama ya shigo "ke!" Ya daka mata tsawa wadda ta kara firgitata ita da d'an cikinta.. "Biyoni muje" kawai ya fad'a ya juya, kamar ba zata ba kuma sai ta tuna ko bataje ba kaita za'ayi gara ta rufawa kanta asiri taje da k'afarta, jiki a sabule tabi ta k'ofar da ya fice..... Wani Alhaji ta samu hakimce yasha babbar Riga a shigar kam kaga kamilallen mutum, yana zaune kan seat ya dora kafa daya kan daya yana girgizawa, umurnin ta tsaya a gabansa suka bata a tsawace wannan karon hadda mata biyu a cikin su, saidai daga ganinsu ire-irensu ne... Binta yayi da Kallo daga sama har k'asa, sannan yayi wata mayaudariyar dariya "Mrs Barr Ibrahim Mu'azzam Gwargo!" Ya fad'a yana tab'e baki.. Itadai sai hawaye take tana kwaroro addu'a duk wacce ta sawwaka ta kuma zo mata a baki, tana mamakin yadda ya kama sunan ta, kenan akan Yaya Mu'azzam aka satota kenan, kome zasuyi mata, ita dai gata ga Allah.. Kamar yasan tunanin da take kenan "DAT gud, Ibrahim ya kusa zama Abba kenan, kina son d'an cikinki kuwa?" Ya jefa mata tambaya a bazata, da kai kawai ta samu zarafin amsa masa... "Hahahaha! Nima kinga inason d'ana Amma Ibrahim ya nace saida ya rabani dashi, kada ki tsorata da yawa fa, nima iya d'an nasa zan Ciro na rabasa dashi kamar yadda ya rabani da nawa shikenan vice versa" ya sake fad'a hankali kwance yana dariyar k'eta... Zaro ido tayi tare da Kara rumgume cikinta sosai, jikinta na rawa hawayenta sun dad'a karuwa, zubewa tayi akan guiwowinta "dan Allah kayi Hakuri Baba ka yafe mana karka rabani da d'ana bashi da laifi baima san sanda akayi maka laifi ba, na rokeka karka rabani da cikin nan" tana kuka sosai tana rokonsa, shi kuma kamar zuga shi take yanajin tana masa goge ne, Wai ya yafe ma Ibrahim.... "Ke! Rufemin bakinki! Kinsan lokacin da na d'auka ina jiran wannan ranar d'aukar fansa, kinsan abinda na batar akan irin wannan ranar? Nonsense! Ke kuzo Ku shige ciki da ita ku fafemin cikinta Ku ciromin d'an Ibrahim yanzu na ganshi a gabana" ya fad'a cikin k'araji fuskarnan ba rahama kamar bai taba dariya ba.... Kuka sosai take tana tirjewa su kuma suna janta da karfi tare da daka mata tsawa, har su ka shige dakin da ita cike da rashin tausayi..... "Abba nan ne direction d'in" Adnan ya Fad'a lokacin da suka iso kusa wani kangon gida, babba ne sosai, daga nan sukayi parking motocin su, mota uku biyu na 'yan sanda d'aya tasu ce Abba, Dady, Mu'azzam, Adnan da Hafiz... Cikin dabara da taku suke bin directing d'in, har suka isa wani b'angare da suke jiyo alamun mutane... "Wayyo! Wayyo Allah na, wayyo Abba na, Ya Mu'azzam pls, innalillahi wa'inna ilairraji'un, shikenan sun kasheni!"............ _fans ba jan aji ko jan ra'ayi bane kamar yadda wasunku ke tunani, yanayi ne dai ya canja ayimin uzuri👌🏻 😘😍 heart you All_ *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* 🌎 *Duniya Makaranta* 🌎 _Babu mugun Abu kamar bashi, yakan tozarta mutum da rana, da dare kuma ya hana masa bacci, ya Rahman ka rabamu da bashi👏🏻 Ameen.👌🏻_ *Page* 5⃣8⃣ ________jiyo ihunta ne ya basu tabbacin tana ciki, Mu'azzam dake tafe kamar kazar da kwai ya fashewa a cikin yini d'aya tal ya fita kamanninsa ya dawo wani kala ba kace babban barrister nan ne mai cike da kwanji da kwarjini ba, Wanda sam barazanar kowa bata tsoratar wa, namijin duniyar nan mai sanya mazaje su gudu, amma yau d'aya duk ba wad'annan siffofin a tare dashi saboda Aymanah itace weak point nashi, akanta kawai yake susucewa ya rasa sanin karan kansa bare waninsa "Dady wlh muryar ta ce, Aymanah ce Abba muje da sauri Dan Allah ranka ya dad'e kada su illata ta" ya fad'a da karaji yana kokarin bance k'ofar, cikin sauri Dady ya rik'osa cike da tausayin sa.. Girgiza masa kai yayi alaman ya dena ya bubbuga bayansa, Su Adnan cike da tausayi suke kallon sa, Wai Ya Mu'azzam ne ya susuce haka lallai so ma wani Abu ne daban, shima Abba ido kawai ya zuba mishi, ogan police d'in ya daga masa hannu tare da yin k'asa da murya "yi hakuri komai yazo karshe, kayi a hankali kar komai ya lalace ba abinda zai faru da ita okey!" Shikam sai yaji kamar zugashi sukeyi ga tsantsar fargaba da tausayin Aymanah yadda take ihu da karaji gwanin tausayi sannan ace ya tsaya idan wani Abu ya sameta bazai taba yafewa kansa ba.... D'aya daga cikin police d'in dake mak'ale jikin k'ofar ne ya jinjina babbar yatsar sa alamar sauran su zama cikin shiri.... B'angaren Su Alhaji mai dala kuwa jiyo karar Aymanan na yawa ne yace daya daga cikin ukun ya dibo menene yake gudawa, da sauri ya dawo tare da sanar dashi aita hanasu yin aikinsu ne ta d'auki makamai itace ke barazana sannan ita ke ihu, cike da fushi yace suje su danneta shi d'an kawai yake da bukata.... Sam basu ji shigowar mutane ba saukar kan bindiga kawai sukaji a kwakwalen kawunan su, Wanda ya tilasta musu dakatar da abinda suke yi, cikin zare ido da mamaki yadda aka gano gun da yake cikin sauki duk tsananin tanadin da yayi, kamar ogan nasu yasan me yake tunani yace "sakenka daya ne daka yadda kuka shigo da wayarta, haha so next time saika kiyaye kuskure komai k'ank'antarsa saboda tsaro" yace cike da gatsali tare da tura k'eyarsa, suma sauran aka tasa su gaba... K'ara fashewa da kuka tayi cike da jigata ta fad'a jikin Mu'azzam, sosai ya k'ank'ame ta cike da tauaayin Kansu, sai lokacin ya samu sukunin zubar da hawaye wato wani sa'in ma kuka samun damace, yama k'asa cewa komai sai bubbuga mata baya yake a hankali, zameta yayi daga jikinsa ya kafa hannunta suka k'arasa gurin su Abba... Kallon ta su Abba keyi cike da tausayi yadda tayi biji-biji da ita ba takalmi bare d'ankwali gashin kan yayi wani yamutsewa kace sabon kamun hauka sai sauke ajiyar zuciya take, nan Suka shiga rarrashin ta kafin police d'in su gama kwashe su Alhaji da yan daban sa, a mota, Abba ya bisu suka wuce station su kuma su shiga motar su suka wuce.... ************ "Gaskiya ban tab'a tsammanin zakayi sake irin haka ba Ibrahim, kasan yanayin aikinka, bare mutane da basu da kyau, baka yi musu komai ba an cutar dakai bare kai da kace yak'i zakayi da gaskiya ai dole ne ka ringa kiyaye wa, irin wannan ai saidai da nisan kwana amma da anyi karo da ajali ai da shikenan" Abba yace bayan komai ya lafa, dan har Dr Humaira (family doctor tasu) ta duba Aymanah, ba wata damuwa saidai jigata da dan gun da suka fara yankarta kad'an tayi mata dressing gurin tare ba bata tabs.. "Kayi hakuri Abba inshaa Allah zan kiyaye" "Haba Mamuda meyasa zaka zarge shi akan wannan abun, ai kaddara ce, sannan kuma ai kaji ta fad'a da bakinta laifinta tun da saida ya hanata ta nace inace ai jikinta ys gaya ta, kaga gobe bata k'ara taurin kai ba da naci" "Haba Inna adai barshi a kaddarar kawai da bata wuce ranar ta" "Tau Allah dai ya kyauta ya kuma tsare na gaba" suka amsa da Ameen gaba d'aya... "Yawwa Ibrahim zaka bar ita bilkisun gida tun da ta kusa haihuwa ga kuma wannan ibtila'in, kabarta anan yadda zata samu cikakkiyar kulawa, kaga sha'anin haihuwa ce ta fari duk Ku duka Baku da ilimin ta dama ko ba wannan ba inaso nace ka dawo da ita sai kuma ga wannan kuma dan haka kayi hakuri ka barta" cewar Hajja.. "Hakurin me za'a bashi Inna ai dama hakan ya kamata ayi" Momy ta fad'a "Nifa bangane ba mutum da matarsa anaso a mishi karfa-karfa" cewar Umma.. "Nima dai shi na gani indai a yadda" Ammi tace, shidai baice komai ba, saidai yasan barin nata is d best solution, duk da yasan is not easy to him Abu da bai saba ba tun lokacin suka shirya basu taba kwana d'aya basa tare ba, inba lokacin bikin Samiha ba, amma dole ma ya barta kodan shima ya samu ya kara tsaro a gidansa da fad'ad'a binkice dan ya d'an tsorata da attack d'in Alhaji mai Dala, dafa ba rabo shikenan da yanzu ya rasa Aymanah da unborn nasa, yo an fafeta ai saidai gyaran Allah... "Ba damuwa Hajja a barta d'in, bara na duba kota tashi nayi mata sallama Nazo na wuce" "Tau duba kaga" Hajjar ta amsa shi, ba kunya ya tsallace su Momy ya shige bedroom din Hajjar dake part d'in ta ne suke, "Oh ni Zainab yaran zamani bata ido kiga fa tsallake mu yayi bako K'ara zaije ya takura mata tana hutawa" dariya Umma tayi, Ammi tace "Allah yasa ga Aunty Zainab, daga ma ya nuna kulawarsa" "Jari'an yara dai ne 'yan k'arshen Zamani mu lokacin mu was ya isa" "Yawwa inna kema kya fad'a, mu bari mu bashi guri ai" tashi sukayi gaba d'aya suna ci gaba da magana suna dariya, dake dama sun tashi tafiya ne saboda gabatar da dinner, sallama suka yiwa Hajja, tare da fatan samun lafiya wa Aymanah, amsa musu tayi itama cike da jin dad'in yadda zaman nasu yayi kyau kamar yadda take buri.... Tana fitowa daga toilet shi kuma ya shigo, da sauri ya isa tare da kamota ya zaunar da ita gefen gadon shima ya zauna yana ci gaba da jera mata sannu "sorry Babynah duk laifi nane nina ja miki kiyi hakuri kinji" Murmushin karfi hali ta saki tare da d'an ciza lips din k'asa "haba Yaya aini ce zancen kayi hakuri, nina ja komai da ban maka gardama ba aida hakan bai faru ba, kayi hakuri" murza hannunta yaci gaba dayi... "Aa Habibty nine da laifi gashi garin kare rayukan wasu ina shirin salwantar da rayuka mafi muhimmanci a rayuwa ta, idan na rasa ko zan koma Mara amfani Baby, inaga zan aje aiki kawai".... Rausayar da kai tayi tare da tausasa murya " Yaya wannan ai kaddara tace, in kace zaka bar aikinka saboda kokarin kare mu, kana karfin ture kaddarar da Allah ya dora mana ne ko canja ta, ko kuwa aje aikinka zai canja ta ne? Mun sani ba abinda zai canja, idan ka dena aiki Yaya su kuma wad'anda ake tauyewa hakk'i suke neman mutane ire-irenka domin kwatar musu 'yanci Yaya tasu rayuwar zata kasance idan Jarumi kamarka ya fara karaya, kananun lauyoyi me zasuyi? Yaya idan ka dena aiki akan abinda ka karanta ka koma yin me?" K'ara runtse hannunsa tayi a nata tana kallon cikin idanunsa kamar yadda yake kallon nata "kada fa ka zama wani iri saboda ni, Yaya komai mukaddari ne, nasan kana matukar sona da son kare 'yan cina a matsayi na na iyalinka, saidai kada ka manta al'ummar kasarka ma na bukatar haka daga gareka, kaci gaba ka doge akan gaskiyar ka, Allah bazai taba bari kaje k'asa ba muddin kana kan gaskiyarka inshaa Allah" Jinjina kai yayi yana mai girmama kaifin tunani irin nata, kaga dai karama da ita saidai tana da hankali da hangen nesa fiye da wasu manya, sosai kalamanta suka k'arfafa masa, tare da k'ara mata k'ima akan idonsa... "Nagode sosai wa Allah daya azurtani da mace kamarki Bilkisa, kin wuce komai a rayuwar Ibrahim, shawararki ta karbu, nagode da ankarar dani da kikayi matata Uwar 'ya'ya, ina rokon Rabbi ya saukeki lafia ya bani 'Yaya masu albarka kamar ke" murmushi ta saki na jindad'in kalamansa... "Nagode mijina abin Alfahari na, sirrina, rayuwata" D'an zaro idon wasa yayi yana murmushi "duk ni kad'ai 'yan matana?" Da gira ta amsa mishi... Dariya yayi tare da picking nata a lips "am going to missing much Baby, Hajja tace na barki harki haihu" Itama bata fuska tayi kamar yadda yayi "har na haihu kuma? To kaifa wazai kula dakai?" Sosai yaji dad'in yadda ta nuna damuwarta.. "Don't mind baby I will manage, zo muje kici abinki nasan kinajin yunwa keda baby nah" "To muje kaima nasan bakaci komai ba kamar yadda nima banci ba, jibi yadda ka dawo yau d'aya" murmushi yayi tare da shafo sumarsa, shi yama manta da abinci Sam, tabbas tun break fast ne da sukayi tare.. A tare suka fito Parlour suka tadda sai Hajja kawai tana aikin kallo, sai lokacin ya tuna da rashin kunyar da ya tafka, K'ara shafo Sumarsa yayi "Haji'an Allah sai ke kad'ai a falon".... " Mara kunyar wofi, ba ka kora iyayenka ba, kadai ji jiki Allah bata ido" dariya sukayi a tare suna ci gaba da zolayarta...... "Kayi ka gama duk, amma nikam baran d'aukar maka wannan sakarcin ba" Paper carpet din cin abinci ya shimfid'a tare da sauke kulolin da su Munira suka kawo na dinner, sannan ya kalle su, bayan yayi kansa gurin zama... "Yawwa ta k'arfin data katakon kuzo ga Abinci muci" harara Hajja ta watsa masa itama kuma Aymanah tayi dariya, ganin yadda yayi rashe-rashe uwa d'akinsa. "Kai a suwa kare da gudun layya! meye naka a ciki, kai naga alama fa kamar na kira ma kaina ruwa ne, zan tattara ta ne na mayar Sashen Fatima naga k'arshen rashin kunyar taka" Saurin cewa yayi "afuwan!afuwan Hajia ta, dan ki rufamin asiri ta karfen, kinsan fa kece kika tare ko'ina, taimakamin ki bar ta katakon anan taki albarkacin ki" "Ho bariki tayi! Bariki tsohon gari ni zaka yiwa duniyanci! Ai kafi kowa sanin ta k'arfen taka" Cike da nishad'i da zolayar juna sukaci abincin a tare, sai 9 ya koma gida, sai yaji gidan yayi masa girma sosai, ba Aymanan sa..... Washe gari su Nusee anan aka wuni, hadda Samiha amarya da Zulaiha duk saida sukazo, mutane nata zuwa jajanta musu.... Su Alhaji mai Dala da yaransa sun fuskanci hukunci dai-dai da laifinsu... Kulawa ta ko'ina Aymanah ke samu, Momy ji take sosai da ita, Umma ma tana iya nata kokarin, barin to Hajja taji, Ammi dai 'yar kallo ta dawo... Abba kullum zai fita "Ummina me kike so azo miki dashi, me kike bukata?" Maganar kenan, shima Dady in yana gari hakane, sosai take jin dad'inta ga ta cikin k'anninta kullum sun zagaye ta "aunty Aymanah ni zan danna biki kafafu, aa nine xanyi mata, ni zan cire miki farce, Aunty Aymanah zan miki tatsuniya" shine zuwa.. Mu'azzam ma kullum yana hanyar gidan in baizo ba yi mata waya, har tausayi yake sosai da tana da damar komawa da tuni ta koma masa tana tausayin yadda yake gararan ba ya dawo gauron k'arfi da yaji.................. *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* 🌎 *Duniya Makaranta* 🌎 _Idan ka taimaki wani saboda Allah, kada ka jira ya gode maka, ka jira sakamakon ka gurin Allah (S.W.T)👌🏻_ *Page* 5⃣9⃣ *A Month later....* _______Cike da farincikin da baisan na maye ba ya farka yau, sauri-sauri ya shirya, dan tun jiya da rana rabonsa da Aymanah, so kawai yake yaje ya ganta musamman a condition d'in da take duk da jiya har 12 suka kai na dare suna waya, cikin shirin sa na zuwa office ya fita da zummar in ya ganta ya wuce office da can kawai, kari ma bai ba sai yaje can yayi dake ma karin kawai yakeyi wani lokaci a gida idan bazai samu biyawa tacan ba...... Direct part d'in Hajja yayi wa tsinke, da sallamar sa a baki ya shiga, turus ya tsaya yana bin Momy da Umma dake falon kallo, tana rungume da new born baby, an kanannad'eta cikin fararen kayan sanyi masu ratsin blue, set ne har towel d'in su, hankali kwance suka amsa masa sallamarsa suna ci gaba da maganar su, cikin nishad'i, k'arasowa ciki yayi, yana musu barka da safe amma idonsa nakan babyn fuskarsa taf mamaki, bakinsa d'auke da tambayoyi... "Momy ina kuka samu cute baby haka?" "Oho! Gata nan dai" ta amsa masa cikin basarsa Umma kam sai dariya take k'asa-k'asa, hannu ya mik'a akan a bashi 'yar zuciyarsa na raya masa Abu sai da he can't believe bama zai yuyu ba yake fad'a kai tsaye... "Wai me kenan? Mu'azzam kai da baka iya d'aukar jarirai ba, taya zaka d'aukar wannan mai kama da lomar tuwo d'aya, bata da kwari fa" haka yake cewa idan akayi sabuwar haihuwa baya d'auka wai basu da kwari karyewa zasuyi in ya d'auka, shi kanshi yana mamakin yadda yakejin zai iya d'aukar baby'n duk da k'ank'ar tanta, zuciyarsa ta kara shiga rud'u fa, to wai mema sukeyi anan da sassafen nan?, sannan ina Hajja da Aymanah? Abinda yasan bazai yuyu bane wai Aymanansa ce ta haihu ba tare daya sani ba.... 'Yar dariya yayi tare da Sosa kansa "au na manta ne Momy, Ina Hajja ne, Hajja ta?" Ya mik'e yana kwala mata kira, har ya d'aga labulen bedroom d'in Hajja Ammi tayi Sallama "ina uwar rakad'in take, 'yar cibi da ita sai muryar kamar wata babba" tace tana dora flask d'in da ta shigo dashi a dinning... Dawowa yayi Falon yana gaida Ammin "Aa Mu'azzam kaine da safiyar nan?" Kafin ya Amsa sai Nusee na kwad'o sallama... "Wayyo ina kike Besty, Kin sauke kin huta kin barmu da aiki, Besty, ina babyn tamu..." Saurin had'e yawo tayi tare da Adana sauran kalaman ta, ganin Ashe duk iyayen su na falon, hadda Yayansu, yadda ta shigo da shirme duk tsananin farincikin new baby ne ya isheta... "Ke! Meye haka Baki ga yadda kike bane? Wata bestyn ce ta haihu ba dai Aymanah ba?" Shiru tayi tana Muzurai yayin da su Momy suka saki dariya, ganin yadda ya k'asa gaba ya k'asa baya duk ya rud'e shima... "Yo da wazai haifi wannan 'yar cibin bayan kai, gashi dai sai muga ta kushen girman 'ya'yan wasu, gata nan dai ba'a ko ganinta da kyau" Momy ta fad'a tana mik'awa Nusee ita... Sororo ya tsaya, baisan lokacin da yace "Maman Arif da gaske Aymanah ce ta haifo wannan mai kyan?" Murmushi kawai Ammi tayi, sai Umma ce tace... "Itace dai, amma ina kyau anan Ibrahim Abu sai kace bakwaine 'yar cas da ita da murya" "Alhamdulillah bini'imatihi tatimus salihat! Allah nagode maka daka azurtani da wannan 'yar, Allah kayi mata albarka da sauran yaran musulmi baki d'aya" yace cike da farinciki, tare zuwa gaban Nusee ya karb'i yar dake motsa d'an tsut d'in bakinta mai kama da nasa, alaman tanaso ta tashi, k'ank'ameta sosai yayi a jikinsa yama k'asa zama sai kallon ta yake kamar ya fyato ta a hanci tsabar kamar da suke da ita, kyau kam ai ba'a magana rashin girman dai ne kam dakyar tafi 'yar seven months... "Oh! Mu'azzam samu guri ka zauna mana" Umma ta fad'a tana dariyarsa.. Ammi kam ficewa tayi tana murmushi. "Kafa gama fitsarewa dan nan, to ai gashi ka kora Fatima, muma bari mu tashi tun da uban 'ya yazo, ba sauran kara" Momy tace.. Zama yayi "wlh Momy abin ne a bazata jiya fa har 12 munyi waya da ita, wai ma yaushe ne ta haihu, gida ko asibiti? Kuma shine aka k'i gayamin Momy?" "Aa lale da iroro Angon k'arni, anzo an isko haihuwa bagata tan" Hajja ta katse sa wacce ta fito daga bedroom... Sallama Momy da Umma sukayi wa Hajja ba tare data amsa tambayarsa, tun da Hajja ta iso magana ta k'are "Hajja Bari naje na kawowa Aymanah, abinci ganan ruwan zafi ta sha tea kafin nazo" Bai jira jin me Hajjar zatace ba ya shige bedroom d'in, dan ya tabbatar tana ciki... Tana tsaye gaban mirror tana goge kanta da k'aramin towel, babba na d'aure a kirjinta, takowa yayi, ya zagaye ta da hannayensa tare da d'ora kansa a kafad'arta, Murmushi ta sakar masa... Hararan wasa ya jefa mata "ni ba ruwana dake ai Habibty, ki haihun ba tare dana sani ba? Wai ya ma akayi haka ashe haihuwar sauki gareta har haka?" Ya karasa cike da tsokana yana dage gira... "Hmm lallai ma Yaya ai haihuwa duka sunanta haihuwa, amma gaskiya wani yafi wani samun sauki, dan ni kaga jiya har bacci nayi bayan kammala wayar mu, sai fa guraren 3 dare ne haihuwar tazo kuma kafin asuba na haihu, amma fa da wahala Allah, tab lallai dole a gaida su Momy wai" murmushi ya saki tare da janta jefen gado suka zauna ya amshi towel d'in yana ci gaba da goge mata kan... "Hakane gaskiya Babynah ai kinsha fama, haihuwa is not easy dole ma mu jinjina wa iyayenmu sannan mu girmama ku matayen mu, Allah yayi miki albarka ya faranta miki kamar yadda kika farantamin, Allah ya raya mana ita akan sunnah, yayi mata albarka yasa Hafiza ce kamar Bilkisata" murmushi ta saki ta amsa da ameen cike da kunya... "Wankan tafashasshen ruwa kikayi ne?" Da uhm ta amsa masa... "Kai lallai matar nan tawa ba k'aramar jaruma bace bakya tsoron ruwan zafi, ke fa badai karfin hali ba akwai jarumta, sai ki shirya muje hospital nasan ma dole sai Dr tayi fad'a tun da tasha maimaita kar na barki ki haihu gida" "Kaji ka Yaya ai dole na nayi Jarumta ina tare da jarumi, kuma ma Hajja ai ba zata tab'a d'agamin k'afa ba, kofa lokacin da na samu miscarriage dinnan sanda ta hadani da ruwan zafi hmm Hajja kam ai ba dama" Murmushi yayi "ai yafi gara ki gasu duk yafi sauran kame-kamen nan na shan tab, yanzu dai bari muje hospital d'in muji me Dr zatace" "Hhhhhh Dr Ayshan fa tazo tun dazun ta yi duk abinda ya dace ta wuce, ai da ita aka gyara babyn, taso ta kiraka ta gaya maka Su Momy sukace kar ta kira bazata za'a maka" Bud'e baki yayi "wato nidai kawai aka kwara nine last na sanin haihuwar 'yata gaskiya kun zolaye ni, amma shikenan akwai next time" dariya ta saki.... "Sorry my Yaya my Ibrahim khaleel nah ni d'aya" "Um ba wani keda cute dai, anya cutie na ba zata kwace maki ni ba, kinfa iya haihuwa tawan, matsalar d'aya ce kin haifota 'yar fit, anya ma wannan cikin ba saura wai?" Ya karasa yana danna cikin, 'yar kara ta saki... "Kai Yaya da zafi fa, miki ne fa?" Rungumota yayi yana dariya "oh so sorry baby sannu ko" kafin tace wani abun suka jiyo 'yar na cayyara ihu muryan zai.... "Hmm wannan cute d'in taka ko, inaga ba zamu shirya ba, ta cika kuka iyakanta 5 hours a Duniya amma kukan ta ta mana yakai na awa 2, ga idonan kwai dasu" "Kaman naki ko? Nifa tun yanzu kar ma a fara takurawa cutie tam, dan bazan yadda, wama ya sani watakil ko abincinta ba'a bata ba" ya fice domin karb'o babyn, murmushi tayi tare da tashi ta shiga shiryawa...... A falo kuwa sai yinta sukeyi shida Hajja tace ya zo ya wuce ya basu gu d'an ba wani zaman jego da zai yi musu, yace yaji amma dai ta barshi ya kara tukun, amsar babyn yayi da Hajja tace ya sadata da uwarta ai tayi zuriya ma(hoho su Hajja anyi kama kunne)... *********** "Baby zo ki taimaka mana dan Allah yunwa mukeji" yace bayan ya sakawa babyn lips d'insa aiko ta kama da k'arfi ta hau tsota, zama tayi bayan ta gama zura gown d'inta ya Dora mata ita akan cinya yana kallon su cike da sha'awa... "Kai! Wash, wallahi da zafi" tace jin yadda babyn ta cafki maman ba sassauci, aiko sai yarfar da hannu take cike da shagwab'a... "Oh! Baby kaddai cutie zakima kuka kuma bayan kin gama yiwa Abbinta" "Hmmm Yaya bakaji bane da zafi Allah" daf da ita ya zauna yana shafa kanta "sorry Habibty daure dai da sannu zaki saba" kasa daurewa tayi "nikam Yaya wai ina kasan harkar haihuwa har haka" murmushi ya saki.... "Nifa lauya ne baby, ba sashen da bamu sani ba, bare ma ko dan ke ai dole na koya" "Uhum lallai Yaya! " yawaa wane suna kikeso a saka mata?" "Umm sunan Momy Yaya" "Niko kinga da Sunan Maman arif naso a saka" "To Yaya ai ba damuwa basai a bari next time d'in kamar yadda kace asa sunan Ammin ba" sosai ta Kara burgeshi wato yarinyar tasan kanta tana da kawaici da hangen nesa, amsan babyn yayi bayan ta gama feeding d'inta yayi mata huduba da sunan Momy wato *Zainab* "Nikam wai duk girman cikin nan ita kuwa 'yar fit" "Hmm haka Dr tace wai rashin girman nada nasaba da miscarriage d'inta nayi" jinjina kai yayi... "Haka ne Allah ne ma kawai yayi sai tazo Duniya Allah ya inganta mana ita akan tafarkin gaskiya" ameen ya ta amsa, a tare suka yi Karin duk abinda tace tare dashi, Hajja da Momy sai tsiya suke masa Umma da Ammi na karesa, sai 12 yabar gidan saboda mutane da suka fara zuwa 'yan barka... Murna kamar mi a gun Momy da taji takwara aka mata, musamman da taji Aymanah ce da kanta ta, lallai yarinyar ta cika 'yar halak sosai ta kara samun fili a zuciyar ta kimarta ta karu I donta.. Abba ma yayi farinciki jin an saka masa sunan uwar gida sarautar mata, Ammi da Umma ma ba bakin ciki, Ammi hadda tukuicin an mayar mata da sunan Auntynta.. Tuni 'yan uwa na nesa dana kusa aka fara garzayowa gidan kullum cike yake taf da jama'a su Nusee, kam kullum ana nan dasu ake zaman jego, Mu'azzam ma kullum yana nan duk irin korar da Hajja keyi masa, yana mak'ale sai yawan mutane ke tilasta masa tafiya... Kulawa kam ba'a magana mai jego da baby ta ko'ina samunta suke niko har nake ga ta musu yawa, lallai 'yar dangi sai dangi, kayan barka kam kamar hauka ta ko'ina zuwar musu sukeyi, Abba, Dady, Momy, Umma, Ammi, Hafiz, Adnan, Zulaiha, Samha, Samiha, Nusee, Amira, Uncle salman da Amaryar sa Fauziya kowa yayi rawar gani... Abba mota sukutun kirar Vibe mai kyau irin ta mata kalar light brown, gida kam mashaa Allah ya dinki mutanen Gwarzo, bauchi da sauran 'yan gari duk an garzayo, biki akayi na 'yan gata.... Bunch of Surprise wai can na hango *Marraha fans, Mom zee, Maman nana, kwalliyan Aymanah sune kan gaba, sai dibar rengem ake, dear na, namecy nah, Ummu Annur, sweet sis 'yar inyass, sis mery, bilkis gudaji, dota na Ramlah Aysha D, Ummu Ismail, Hafiza, Ummu nasreen, Ummu jabir and rest (Allah kuna da yawa sorry wadanda ban kira ba duk inayinku wlhy😘)* Wow! Sai ga *Maman Ussey novellah, khairy B-b, sis na Eshart kadir, maman husna, Shamciya, Jidda, mr Dz, Ummu Ismail and rest (heart you all)* Au Ashe da sauran wata zugar *Hausa novels, Sweery novel, jinina fans, Duniya Makaranta 2, Mutattauna mata, Aminan juna, soyayya da shakuwa, muhphat dogo novel, zumunci group and rest, _Muz'Aymah_ na godiya da halattar bikin cutie su da kukayi suna muku fatan komawa gida lafiya Amin* _Allah ya raya Zainab (eynas) akan sunnah Ameen_ Haka aka watse taro lafiya cike da farinciki da annushawa, Eynass alkunyar da suke mata sai girma take kamar ba itace 'yar cas d'innan ba, ta fara barakallah abinta yayin da tsantsan kyanta ke kara bayyana sak Mu'azzam inka cire idon da yatsu da tayi na Aymanah, cute dai da ita kamar yadda Abbinta ke kiranta.... Su Hajja, Momy, Umma sun dage gurin gyaran Aymanah cike da bai musamman Yadda suka ga Angon k'arnin ke rawar kai tuni ya busar da idanuwansa ya mayar da Momy wata kakarsa baya jin nauyinta Sam, sai kunya kawai yake saka Aymanah a gabanta ko a jikinshi, Ammi kawai yake kunya shiyasa itama bata zuwa inda suke... Watan su biyu suka koma Wanda yayi dai-dai da haihuwar Nusee ta sunkuto saurayinta mai kama da ita Wanda ya amsa sunan Dady suna kiransa da Farhan, nan ma an rakashe an gurji biki, saura Meerah, da Aunty Samha, Samiha ma an samu ita da Fauziya amaryan Uncle salman sai fatan sauka lafiya..... Sai cillata sama yake yana cafewa itako sai wangale baki take dan ta bala'in saninsa kamar me, muddin yana gida to shine Nanyn ta, ita Aymanah har mamaki take yadda yake cire mata pampers intai kashi ya wanketa tas, ba ruwansa, wani sa'in ma idan an barta da pant tasha iska tayi masa fitsari wani sa'in har kashi yin masa takeyi, tumbud'i ai yasha ba adadi dan wani lokacin sai ya d'agata ta zubo masa abinsa a baki amma Sam baya nuna damuwa ko kad'an, ita kam ba abinda zatace da Allah sai godiya wannan baiwar da ni'imar da yayi mata wacce ba kowa yayi wa ba, kuma badan tafi kowa ba ni'imace kowai daga garesa..... Zama tayi gefen tare da aje bowl d'in Fruit salad, data hado musu a centre table... "O'O Abbi da cute d'insa kuna sha'aninku fa" kallon ta yayi tayi masa kyau cikin shigar kananun kaya jean and top, tayi ma kanta wani irin style kamar wata 'yar Baby... "Hmm! Kina dai Sha'aninki Ummi, wannan swagg haka duk dan a tada hankalin Innocent Abbi ne?" Dariya tayi "nidai ba ruwana! Uhum Yawaa Abbi ya maganar karatun nawa?" Ta fad'a cikin narkewa da tausasa harshe... "Oh kinga fa Shaf na manta bari Nazo yanzu" yace yana mik'a mata Zee dake zillon zuwa gurinta tasha Mama....... _Second to the last page inshaa Allah_ *Siddiqa ce* [9/30, 18:11] Dear Ita: 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ By _Maryam Abdul_ *In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)* 🌎 *Duniya Makaranta* 🌎 _idan ka saki hawayenka akan filo, to ka sake su ne a banza, sake su akan tabarmar sallarka, to idan kayi haka ka kai kukan ka gurin mai share maka su👌🏻_ *Page* 6⃣0⃣ ________d'ago ido tayi ta kallesa bayan ta gama duba tarkacen visa da passport d'insu na tafiya Saudiya, Hadda Admission latter d'inta wato yana nufin a can zatayi karatun, dama yana satar kallon ta yaga me zatayi, sab'anin tsallen farinciki da ihu da yake tunani daga gareta sai ya yaga sabanin haka, fuskar dai ba yabo ba fallasa ga kuma kallon tuhuma da take masa..... Sabira ya kira tazo ta tafi da Zee sannan ya juyo yana fuskantar ta da alaman tambaya "yadai Habibty? I seen like ur not happy! why?" " Is Not exactly what I mean, but Yaya like ka zabi iyalanka akan kasarka kenan, yanzu it is pair! Ka aje aikinki na taimakon k'asarka saboda kawai ni meyasa ba zanyi karatun anan ba? Kana tsoron wani Abu ya same mu ne? To idan mun tsallake mun bar k'asar what's up iyayen mu da 'yan uwan mu, al'ummar k'asarka fa?" Ta karasa fada cike da damuwa.. Hannu ya saka ya kama hannayenta duka biyu tare da kallon cikin idonta "is not my intention at all Baby, nasan kaddara na yadda da ita, kuma nasan no way to run away from our destiny but what I want u to know is, nima karatun zanje na k'aro yadda zan k'ara samun experiences akan aikina, ina kishin k'asata fiye da tunanin ki Aymanah, saidai hankali na zaifi kwanciya muje can d'in so pls try to understand me I'm selfish at all, about iyayen mu kuma da kike magana nasan ba abinda zai same su, kodai kinaso kicemin kin manta da waye iyayen namu, sufa suka haifemu suka rene mu, kuma suke karemu tare da taimakon Allah, mezai sa kiyi tunanin akan dan bama nan zasu cutu, pls ki cire wad'annan tunanin a ranki, I know ke d'in ta daban ce, bakyaso abinda wani zai cutu a dalilinki so believe me ba abinda zai faru inshaa Allah okey" duk cikin taushi da sanyi yake maganar... Murmushi ta sakar mishi tare da Runtse hannunta sosai a nasa, tana jinjina Sanyi da sauki irin nasa, da wani daban ne aida yanzu ta gama kwab'e musu, watakil ma hadda duka tayi wasa "Madallah! Da kai miji na gari mai karanci da kawaici, nagode da fahimtar dani da kayi a siga mafi kyau, ina rokon ka yafemin akan rashin fahimtar ka dana pls forgive me? I understand you Hayat Al-Rouh"...... Shima martanin murmushin ya mayar mata tare hugging nata tightly " I done nothing wrong Habibty! Inasonki kamar yadda halinki da ke k'ara nutsar dani cikin k'aunarki, ke k'arama ce da tunanin Manya, 'yar kwaila ta" ya karashe da sigar tsokana..... "Uhum um! Zaka fara ko Yaya, Allah zan koma maka kwailar kuwa!" Ta fad'a tana dukan k'irjinsa da hannayenta bayan ta cuno baki gaba cike da shagwaba.... Rik'e hannayenta gam yayi yana dariya "u see jifa me kike yi yanzun, ki dage dayi har cutie na ta girma ta tayaki" harara ta watsa masa tare da Murgud'a baki, tare da mik'ewa tsaye tana hura hanci..... "Kuma ma an fasa maka tausa yau kaje cutie taka ta maka" dariya ya fashe da ita hadda kwanciya akan seat d'in dan tsayin da tayi da yadda take girgiza ba karamin dariya ya bashi ba uwa wata matashiyar 'yar dambe...... "Allah sarki! Bawan Allah Abbin cutie, to ni bara nazo nayi maka special one irin eh...." Ya k'arasa yana kashe mata ido tare da yunkurin mik'ewa, aiko k'afa me naci ban baki ba, ta runtuma da gudu part d'in, hadda banko k'ofar..... Dariya ta bashi, saidai murmusawa kawai yayi tare da shafo sumar kansa Wanda na fuskanci is part of his harbit "silly gal" ya fad'a tare da jingina bayansa a kujerar yana lumshe idanuwansa......... ************** Cikin sati biyu tafiyar su ta kankama, bayan an kammala bikin Ameerah wacce ta haifo Fatima Zarah(anyiwa Ammi takwara) suna kiranta da Zarah. Cike da so da kewar zuri'arsu suka yi musu b'ankwana bayan sun sha Addu'o'i daga kowane b'angare tare da fatar samun nasara..... Haka suka bar 'yan uwa da Masoya da k'asar su ta haihuwa suka Lula Saudi Arabiya, inda zasu Zauna a birnin *Riyadh*....... _🙋🏼‍♀safe trip Muz'Aymah😍👨‍👩‍👧_ *Some years later........* *Saudi Arabia* _Riyadh_ "Abbi! Abbi!! Abbi!!! Boyeni bayanka, boyeni Abbi zata dakeni ne" kyakkyawar yarinyar mai zubin Larabawa cikin shiga mai kyau ta Alfarma, dogon gashin nan baki sidik yasha adon beats da ribbons sosai just like take away, a k'iyasce zatayi 4year and half, duk cikin yaren larabci take maganar da siririyar muryarta irin ta yara.... Abbin nata dake zaune kan resting chair cikin wani ni'imtaccen lambu Wanda ke fitar da sanyayyar iska da k'amshi mai kwantar da rai, yana duba wasu documents, idonsa sanye da siririn farin glass, yana sanye da rigar ciki fara kal ta suit da wandon, ta saman na rataye a hannun chair d'in, saurin ije documents d'in yayi tare da janyo yarinyar ya zagayo da ita gabansa tare da zuba mata ido yana binta da kallon tuhuma..... "Wato kin tsokano Ummi ko cutie?" Ya tambaye ta yana tsareta da ido, yayin da tayi fiki-fiki da manyan fararen idanuwanta alaman rashin gaskiya.... Kafin tayi, ta bud'i baki saiga Ummin ta bullo ta k'ofar da yarinyar ta fito, sanye cikin fararen kaya irin na ma'aikatan jinya, ta d'ora bakar abaya kai irin ta larabawa, guntun farin hijab a wuyarta, Fuskar a d'auke hannun ta rik'e da 'yar bulala, tana tunkaro su, sai harara take aiko musu da ita... Murmushi Abbin ya saki ganin yadda cutie ta kara k'ankamesa tana zare ido tana kallon Ummin nata, d'agata cak yayi ya d'ora a cinyar sa tare da rungume ta sosai...... "Allah Abbi yau ba wani bambancin launin fata da za'a nunamin fa, don yau sai wannan marajin cutie taka ta ji a jikinta, duba fa kaga, dawowa kenan amma wai sarkin bannar harta yagamin note book d'in da mukayi presentation yau haba Allah kawai ka barni na dake ta ko zanji sauki sauki" Tun da ta fara magana yake kallon cikin idonta ta bakinta harta karasa, murmushin Fuskarsa ya k'ara fad'ad'awa sannan ya kama k'unnuwansa tare da rausayar da kai "Ana ahsif Ummi(yi hakuri Ummi) pls so sorry Ummi, a dai yi hak'urin nan da aka saba yi mana d'an Allah" "Gaskiya nidai Aa Abbi nidai ka barni kawai na daketa Allah Zuciya ta har zafi takeyi" kallon ta yayi da kyau kuma da gaske a zuciye take dan da iya gaskiyar ta take maganar... "Oya sheka da gudu gun nany ta koya maki Hausa" yace da yarinyar bayan ya sauketa, dake tana son Hausa sosai da tsalle ta ruga, juyawa itama Aymanan tayi da niyyan damk'an ta, cikin zafin nama ya janyo ta ta fad'o jikinsa suka sube kwance a resting chairs d'in...... Turo baki tayi tare da kwaba fuska tana bubbuga k'irjinsa "Allah Yaya kai ka cika son kai, duk kaine ke daure mata kullum take min bannar tsiya, ai nima dai ina da Abban to a mayar dani gurin nawa iyayen nima tun da ba'amin adalci" Murmushi ya saki tare da k'ank'ameta a k'irjinsa, same hijab d'in jikinta yayi yabi ta da kissing, aiko nan take kaji ta lakwas sai sauke Numfashi... Saidai yayi son ransa sannan ya d'ora kanta a k'irjinsa yana shafa kanta "Habibty anya wannan zafin naki kwanakin nan anya kuwa?" Ya rad'a mata a kunne, dago kai tayi ta zuba masa ido, ita kanta tasan zafin ta ya karu kwanakin Abu kad'an ta haye, kuma ko Rauda(abokiyar karatun ta)na gaya mata ciki ne da ita tun kwanakin baya, ita kanta tana zargin hakan.... "Nima ban sani ba Yaya but zanyi Text Nagani" kallon tuhuma yayi mata.... "Hmmm! Baby gayamin gaskiya dai nine fa kece, kina cikakkiyar Nurse d'in zaki wani layance min" dariya ya saki tare da b'oye fuskarta da tafin hannunta, dariya shima yayi tare da fad'in "dama nasan kina sane gayamin wata nawa ne?" Kunnensa yakai gurin bakinta "is just a month fa" ta fad'a a kunyace idonta a rufe still, dariya ya saki tare da k'ok'arin zame hannun nata bayan ya d'ora dayan hannun a mararta.... "Iyyeh! Maman baby dai duk kunya ce wannan tun da anboye Abbi da cutie sun kusa samun new baby ko? Haba gaske dai akeson jibgar min cutie tun da za'ayi sabon baby shine aka fara waremin ita ko?" Cike da jindad'i yake maganar, kunyar Aymanah na burgesa ai yau taki yadda ta girma kullum shiriri bata k'are mata ba, musamman ta had'u da Zee kamar wata k'awarta shine Abbin su Alkalin su kullum cikin karbar kara yake... "Hmm! Aini ba ruwana da cutie taka kuma saina zaneta in tayi wasa, kuma sai an biyani jotting d'ina ko taci duka" "Aa wlh baki isa ba, ga duka ga tsinka jaka abin ya mata yawa, barta da kishiyar da kike shirin yi mata, tab nasan za'a sha rigima da cutie taga na d'auki babyn nan hmm! And zanje da kaina na karbo jotting d'in Rauda na kwafar maki shikenan dai ko?" "Better! Sannan kuma babynah abar min abata kuje can Ku k'arata da cutie taka" tace tana murguda masa baki, danne ta yayi har tayi 'yar k'ara... "Wayyo babynah Yaya!" D'agata yayi yana dariya, kukan shagwaba ta fara masa "Allah ni a kaini gida bazan juri wannan k'etar ba, so ake a jima babynah ciwo tun yana ciki tsabar iya banbamci" dariya ya sake yi... "Allah wannan yarinyar bakyajin magana, aike ce kika tsayar damu k'asar kiyi ki gama nima na mayar dake gun Abban naki da Momyn ki da Hajjarki na huta da k'orafin ki da Nasu" mik'ewa tayi ta fara tafiya tana fad'in... "Kwantar da hankalinka saura 2 weeks saika fara yi mana shirin tafiya Shekara Hudu aiba kwana hudu bane nima Am eager to go na gansu"....... Shima tashi yayi ya biyota yana " to jirani muje cikin tare 'yar Abba maman Baby, ta Hajja kinci dubu sai ceto"murmushin jindad'i ta saki tare da tsayawa ya cimmata suka shiga ciki hannunsu a sarke...... *A Month later.....* *Nigeria* _Kano_ Babban Falon Abba na taro ya cika makil da Zuri'ar ba Wanda babu a ciki kowa ka kalli fuskar cike da annuri da farincikin Murnar Dawowar Su Mu'azzam suke firar yaushe rabo kawai ake dawowar su kenan daga d'auko su daga Air port... Cike da Sha'awa suke bin su da kallo Musamman Aymanah yadda tayi fresh ta k'ara kyau abinka da Hutu ya had'u da yaron ciki, bakin kowa a washe sai nan nan ake dasu kar ma Hajja taji, har su Abba duk suna gurin ana hirar yaushe rabo.... Zee kuwa kamar su hadiye ta sukeji wannan ya d'auka wannan ya d'aukar saidai ba damar dogon zance tun ba Hausa takeji sosai ba, tana kan cinyar Momy sai larabci take zuba mata, wani irin k'aunarta takeji a ranta fiye da 'ya'yan da ta Haifa, kodai don tana 'yar Mu'azzam ce..... Samha da Danta mai sunan Abba Mahmud (Affan) Samiha da Nasir(Aryan) sunan baban mijinta su Nusee da Amira ma duk sun sake haihuwa Nusee tayi Suwaiba( Mimi) mai sunan Umma Amira tayi Hisham, nan takejin labarin Uncle salman yayi mata takwara da 'yarsa nan sukayi alk'awarin Zuwar musu idan sun huta... Sunci sun sha cike da jindadi gasu ga ahalin su yau bayan tsawon lokaci, ga 'yan kanninsu Su Munira 'yan zama 'yan mata har an tsayar musu da mazaje ita da Sageera, da Fadila, su Munir ma an zama Samari har anje University, Autan Ammi Arif an girma sosai ana primary 4..... Wata camera Mu'azamman ya fito da ita tare da cewa ya kama ta a d'auki foto irin wannan had'uwa ta farinciki haka tunda kowa ya hallara, saita ta yayi bayan sun had'u guri d'aya sun dau foster kowa fuskarsa a sake da yake auto ce yana seta ta yadda yakeso yayi saurin dawowa gurinsa.... Kitt ta shiga d'aukar su, daga 2 hand sama matasan suka yi tare da cewa " *ZURIA D'AYA, TSINTSIYA DAYA BABU MAI RABAMU SOYAYYAR GASKE MUKE INDA RAI DA LAFIYA BA ZA'A GANMU A RANA BA........* 🙋🏼‍♀ *Alhamdulillah Mashaa Allah, Allahumma salli alah muhammadun wa sallim🤲🏻* *dukkan godiya ta tabbata ga Allah (S.W.T) daya bani Aron rayuwa ya nunamin na kammala littafin nan lafiya kamar yadda na fara lafiya, INA rokon Allah ya bamu ladar da ke ciki ya shafe kusakurai da ke ciki a zuciya da gangar jiki, Allah ya bani ikon hujja dashi kada yayi hujja dani ameen👏🏻* _😍😘 na gaida duk wata masoyiyar wannan littafin na kuma jinjina muku na juriyar bibiyata daga farko har zuwa yau dana kammala #heart you all fisabillah#🤗🤝🏼_ 🏢🏢🎆 *_ZURI'A D'AYA_* 🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀ *Fadi ra'ayinki/ka game da wannan novel akan komai ma daya shafeshi, yabawa ko korafi....* Drop ur comments On ur group. *Ma'assalam Saduwar alkhairi*🤗 *Siddiqa CE*