[25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU*🖤🖤 *TRUE LIFE STORY* WRITING BY *MARYAM 'YAR MAMA* *ZAMANI WRITER'S* & *BILKISU Z. Ya'U (🅱K)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* _Bismillahir rahmanir raheem_ _*GODIYA TA TABBATA GA ALLAH (S.W.A) DA YA ARA MANA RAYUWA DA LAFIYA, YA UBANGIJI MUNA GODIYA A GAREKA👏*_ _*YA UBANGIJINMU KA YI SALATI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)*_ *KAMAR YANDA KUKA GANI A SAMA👆 WANNAN LABARIN YA FARU DA GASKE, ZALUNCI, BUTULCI, CIN AMANA, YAUDARA, TSANTSAR TAUSAYI, DUK A CIKIN WANNAN LABARIN, SAI KU BIYO MU DOMIN JIN ABINDA YA K'UNSA.* Page 1 to 5 Alhaji Balarabe nera shahararren mai kud'i ne, nagartaccen mutum ne, mutum ne mai yi wa mutane hidima, wanda sam dukiyar shi bata rufe mishi ido ba, akwai taimakon na k'asa da shi, baya k'yashin fitar da dukiyar shi ya taimakawa talaka, ga kyauta a tak'aice dai Allah ya had'a mishi duka biyun, ga dukiya me tarin yawa, ga kuma hali na k'warai. Alhaji yana da mata d'aya mai suna Hajiya Jameela, suna da yara biyar, akwai Yusuf, sai Alaweeyya, sai Seeyama, sai sadeeq, Sai auta me suna Aisha. Alhaji da Hajiya wato iyayen su Alaweeya suna matuk'ar k'aunar yaran su, ko kad'an basa yarda wani abu ya tab'a yaran, suna samun kyakkyawar kulawa daga cikin gida yar a waje, idan suna cikin gida babu abinda suke yi na wahala komai se a yi musu, kuma babu abinda suka nema suka rasa komin tsadar sa, a waje kuwa, duk inda zasu saka k'afa to da masu tsaron su, a tak'aice a koda yaushe kuma a ko'ina yaran suke suna k'ark'ashin kulawar mahaifin su. Wannan tsantsar k'aunar ita ta haifar da shak'uwa mai tsanani a tsakanin yaran da iyayen, dukkanin su yanzu haka suna karatu a fitacciya, kuma shahararriyar makarantar da ta yi fice saboda kyanta da kuma shahararta, masu karatu cikinta kuwa sai 'ya'yan manya, wato 'ya'yan attajirai, wannan kenan. Yau Asabar ranar hutu ce, Dadyn su yana gida ba inda ya je, zaune yake tsakiyar yaran shi, banda zuba mishi shagwab'a ba abinda suke, Alaweeya ce tace " Dady dan Allah a fita da mu, mu yi shopping," Seeyama tace " A'a Dady wajen wasa zaka kai mu," Yusuf yace " Dady rabu dasu sarakan son yawo kawai, " Aisha auta cikin maganarta ta yara tace " Dady dan Allah muje zansha sweet, wanda ka siya mun sun k'are, suna cikin magana kafin Dady yace komai sai ga Mumy ta shigo falon inda suke zaune ta k'araso itama ta zauna, kallon yaran ta yi, sannan ta kalli Alhaji tai murmushi, tace " Dadyn mu me ake tattaunawa ne ba'a nemeni ba?" Dady yai dariya, sannan yace " yaranki ne suka dage a fita dasu yau su yi siyayya," Mumy tace " ai kai ka saba mana da hakan, duk lokacin da kake gida kana fita da mu, dan haka yau ma a fita da mu ko muita yi maka kuka ko ba haka ba yarana? " ta juya tana tambayar yaran, kamar had'in baki a tare suka amsa suka ce " yes Mum. " Dady ya yi dariya yace " wato kece kika shagwab'a min yara koh? " Mumy tace " wa, ni? ba ruwana kai ne ka shagwab'a mu dukkan mu har da ni," Dady ya kalli yaran yace " to yanzu abinda za'ai kowa yaje ya d'auko litattafan shi gaba d'aya ku biya mun d'aya bayan d'aya, duk wanda ya karanta lafiya lau to da shi zamu tafi," da gudun arzik'i suka tashi gaba d'ayan su, zuwa d'auko litattafan nasu banda Yusuf da Mumy, Dady ya kalli Mum da Yusuf yace " Ku bazaku bimu ba kenan? " Mum tace " au wai har da ni?" Dady yace " ai har da ke na shagwab'a, dan haka kema Allah sai kin yi karatu zamu fita da ke, ya kalli Yusuf yace kaima kaje ka d'auko naka litattafan." Da yake Yusuf ya san be iya nashi karatun ba sai yace "Dady kuje kawai ni ba zan je ba," Dady yace " d'auko littafan ka karanta in baka iya ba to dole sai mun fita da kai tunda fitar ce yau baka so." Sai da kowa ya karanta litattafan shi daga na boko har na islamiyya, Mum kuwa Qur'ani ya sata ta karanta, sannan bayan sun gama karatun dukkan su suka shirya harda Dady suka fita, ba su suka dawo gida ba sai da yamma wajen k'arfe biyar da rabi. Suna dawowa bayan sun yi sallar magriba da isha'i sannan suka had'u suka ci abinci, suna cikin cin abincin ne sai wayar Dady tai k'ara, yana dubawa yaga Tukur ne ke kira, da saurin shi ya d'aga fuskar shi d'auke da murmushi, bayan sun gaisa Tukur yace " dama mun kammala karatu ne shine nace bari na kira in fad'a maka a turo min da kud'i zan taho gida nan da sati d'aya." Dady yace " anya, ai shekarun da zasu d'aukeku har ku gama karatun basu cika ba da sauran shekaru Tukur fad'a mun gaskiya dai. " Tukur yace " sun rage shekarun ne, in baka yarda ba ka tambayi abokina, gashi a kusa da ni." Alhaji yace " shikenan Allah ya kaimu, zan turo maka da kud'in, zan yi maka transfer, suna kammala wayar yai mishi transfer a take anan. Yaran gidan kuwa da ita kanta Mumy jikinsu duk ya yi sanyi jin Tukur zai dawo, da yake wayar Alhaji akwai k'ara, idan yana waya ana jin komai, shiyasa duk hankalin su ya tashi, in suna k'aunar dawowar shi to suna k'aunar mutuwar su haka. _topha, wai wanene wannan Tukur d'in? Menene matsayin shi cikin wannan dangin? Meyasa kowa baya farin ciki da dawowar tashi? Ku biyo mu domin jin ci gaban._ Mune naku *'Yar mama💃* & *🅱K😘💋* [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU*🖤🖤 *TRUE LIFE STORY* STORY & WRITING BY *MARYAM 'YAR MAMA* *ZAMANI WRITER'S* & *BILKISU Z. Ya'U (🅱K)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* _Bismillahir rahmanir raheem_ Page 5 to 10 WANE NE TUKUR? Tukur k'ani ne ga Alhaji Balarabe nera uwa d'aya uba d'aya, kuma tun yana k'arami yake zaune a hannun Alhaji Balarabe. Tun Tukur yana jariri Allah ya d'auki ran iyayen su. Alhaji Balarabe yana matuk'ar k'aunar d'an uwansa. Gata kam na duniya babu irin wanda Alhaji bai wa d'an uwan shi tukur ba, tun baida komai har Allah ya azurta shi da dukiya me tarin yawa. Lokacin da Tukur yai wayau Alhaji Balarabe ya sa shi makarantar boko da ta islamiyya, se dai tun yana yaro tukur baya ji, kuma sam baya maida hankali kan karatun shi, ga neman fitina da tsokana kala-kala. Alhaji ya kammala karatun shi cikin nasara, domin yana gamawa ya sami aiki me kyau, wanda farawa da iyawa Allah ya sawa dukiyar shi Albarka taita bunk'asa. Lokacin da ya fara aiki ne Allah ya had'a shi da 'yarinya ta gari ya yaba da tarbiyarta da natsuwarta, had'i da iliminta, hakan yasa suna dai-daita kansu babu b'ata lokacin aka sa rana. Bayan an sha biki amarya ta tare. Tunda amaryar Alhaji ta shigo gidan nan hak'urin zama kawai take yi da tukur ga rashin kunya da nuna gadara a kan komai na cikin gidan. Amma da yake hak'urarra ce bata tab'a kai k'arar shi wajen Alhaji Balarabe ba, se dai in ya yi a gaban Alhajin ya gani sannan zai kwab'a mishi, duk da bema cika yi mata ba idan Alhaji na gida sai baya nan, tunda yana d'an jin maganar yayan nashi. Bayan 'yan kwanaki Alhaji Balarabe ya kai shi wata makarantar kud'i me kyau, se dai sam baya maida hankali a karatun, hakan yasa yai tunanin canza mishi makaranta a tunanin shi ko be gane karatun ne, sai ya zamana kamar ma 'yanci da dama ya samu na shek'e ayar shi, dan yanzu har shaye-shaye yake yi. Haka rayuwar su ta ci gaba da kasancewa kwata-kwata Matar Alhaji Balarabe bata jin dad'in zaman Tukur a tare da su, gashi ya saka musu ido, ga kishi duk abinda Alhaji yai musu sai ya nuna kishi da hassadar shi a kanta. Kuma ya tsani yaga Alhaji na facaka da dukiyar da Allah ya bashi, kuma baya k'aunar yaga yana taimako da ita. A haka har Allah ya azurta su da yara har biyar, se dai har lokacin halin Tukur be canja ba, sai ya zamana tsangwamar har da yaran Alhajin yake yi mawa, ya tsani shak'uwar da suka yi da Alhajin, sannan makarantun da duk aka sa shi daga k'arshe koro shi ake yi, wad'anda suke da lambar Alhaji Balarabe kuwa sai su kira shi su fad'a mishi zai b'ata musu tarbiyyar yaran makaranta shiyasa suka sallame shi. Alhaji ya yi fad'an har ya gode Allah, bayan kwana biyu Tukur da kan shi yazo wa da Alhaji magana akan yana so ya tura shi waje karatu, Alhaji yace bazai yiwu ba anan d'in ma ya aka k'are balle ya fita waje, sai Tukur ya nunar mishi da muddin ya kaishi can zai dage yai karatu, Alhaji yace in har yana so ya kaishi waje sai ya maida hankali anan ya gama secondary school d'in shi yaga ya fitar da sakamako mai kyau sannan zai yarda da buk'atar shi, koda Tukur yaji haka yace ya amince, aka saka shi wata makarantar, ikon Allah kuwa ya dage da karatu ba dare ba rana, kuma daga k'arshe kuwa ya fitar da sakamako mai kyau, hakan yasa dole Alhaji ya cika mishi alkawarin shi domin harga Allah a tunanin shi yanzu kuma yana son karatun ne, wannan shine dalilin fitar da shi waje, daga uwar gidan har yaran gidan tsoron shi suke ji sam basa farin ciki da dawowar shi, shi kanshi Alhaji ya ji sak'at da baya nan, amma ya zai yi naka sai naka, wannan kenan. CI GABAN LABARIN Muje zuwa Mune naku *'YAR MAMA* & *🅱K😘💋* [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤* *TRUE LIFE STORY* STORY&WRITTING by *MARYAM YARMAMA* *ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* & *BILKISU Z.Ya'U(🅱K)* *ZAMAN AMANA WRITER'S* Page 11-15 Washegari Alhaji yasa driver yaje ya dakko tukur a airport,tukur kyakyawan yarone ajin farko,abinka da fulani farine kuma dogo mai faffadan kirji gashi da sexy eye,yanada tarin suma wanda kullum cikin gyara sumar yake,.yanayin shigarsama ya nuna tantirin yarone.. Yana shigowa cikin gidan ..kowa cikinshi yaduri ruwa banda alaweeya da ko tsoranshi bataji . Cikin fara'a Alhaji ya rungumeshi don yana matukar son tukur sosai sannan yace"bakin turai har angama karatun kenan". Cikin jan aji tukur ya saki alhaji ya zauna akan luntsumemen kujerar yace"eh ai karatunsa ba wuya". Cikin karkarwar baki momy da yaranta suka fara gaishe da tukur ,a yangace yake amsawa idonsane ya sauka akan alaweeya dake zaune ba dankwali akanta gashinta yasha gyara sai latse latsen waya take.sanye take da riga gown tasha kyau . Momy dataga tukur sai kallon Alaweeya yake cikin tsoro ta dan doki cinyar Alaweeya tace"ke bazaki gaishe da karamin dadynki ba". Tsaki Alaweeya tayi tadago da idonta tana karewa tukur dake kallonta kallo sannan ta tashi tace"wannan dan iskan bai cancanci yazama ubana ba,Bazan gaisheshiba wallahi".* Alhaji ya kalli alaweeya ya daka mata tsawa yana"ke kinsan dawa kike magana,be carefull with me,zaki gaisheshi kosaina saba miki". Bude baki Alaweeya tayi tamkar zatayi kuka ta nuna tukur tana"Dad saboda wannan gayen zaka min tsawa,kasan a rayuwata yanda na tsani amin tsawa .shine zakamin tom wallahi ko za'a kasheni bazan gaisheshiba". Daukar wayarta tayi ta harari tukur tahau sama tabar falo din,momy dai da yayanta ko motsi basu iyayiba. Lumshe ido tukur yayi don gaskiya ya yaba da kyawun Alaweeya da surarta "haka alaweeya ta girma". Alhajine yasa masu aiki suka gyarawa tukur part dinshi a upstair,suka bashi abinci kala kala. Washegari an hallara anacin abinci a dinning harda tukur da yaketa satan kallon Alaweeya. "Daddy dama a makarantane akace mu kawo kudin t.shirt na graduation din mu,kowa ya kawo nice ban kawoba". Alaweeya ce cikin shagwaba take fadin haka yayin da sukecin abinci a di. Alhaji ya kalleta ya murmusa yace "ke meya hanaki fada iyeh?bana tura miki dubu dari a account dinkiba".tukur yanajin Alhaji ya turawa Alaweeya dubu dari a account dinta ,ya murtuke fuska ya buga teburin cin abincin wanda yasa su momy suka tsorata sannan ya aje spoon din dayake cin abinci yatashi yabar wajen cike da bacin rai . Kowa dake dinning din suka bisa da kallo...yayinda alaweeya ta bi bayansa da harara sannan ta kalli abbanta cikin shagwaba tace "abba nifa dubu dari ba abinda zaimin...please ka daure ka karamin wani,nifa banason taba kudin Account dina don so nake ka cikamin insiya mota". Dariya duka suka kaure dashi Abba yayi murmushi yace "to mama zankara miki shikenan hankalinki ya kwanta,keda sadeek da siyama duk zakuji alert yau". Dinning din yadauki murna suna ta "thanks you abba Allah ya bude hanya". Momy dake sanye da farin medical gilashi tace "Alhaji kanafa sangarta yaran nan,nidai ka rage basu kudi kaji,saboda ran tukur yana baci duk lokacin da kabasu kudi". Ko daya abba bai dauki maganar matarsa ba saima cewa da yayi"na taimakawa yan waje ma,nayiwa mutane hidima balle ya'yana farinciki.yayan nan guda hudu su Allah yabani don haka dole in musu abubuwan da sukeso...banda dangi daga TUKUR sai su.su kawai nake dasu aduniya,kuma inada arziki kar inmusu bazaiyuba,shima tukur din ai inamai sosai acikin yaran wana kai karatu kasar waje iyeh ki gayamin". Tashi yayi yayinda suka rufamai baya,suka rakasa har bakin harabar gidan ,driver yabudemai bayan mota yashiga..sannan karamar cikinsu humaira tamikomai briefcase dinsa tamai sunba a kumatu...haka driver yaja motar sunamai daga mai hannu.. Haushine yakama TUKUR dake kallon duk abinda sukeyi ta taga.wani bakinciki ya mamaye mai zuciya,matsawa yayi daga bakin windonsa yazauna akan gadonsa yana neman mafita "dole in hargitsa gidannan,dole in kashe Alhaji in mallaki dukiyarsa sannan inyi facaka dashi".haka tukur ya ayyana aransa ... Baigama fadin hakaba ,Alaweeya tashigo dakin .tsayawa tayi abakin kofa tana mai aikamai sakon harara domin duk duniya ba wanda ta tsana kamar uncle dinta. Shiko tukur ko damuwa baiyi da kallon da takemaiba,shidai burinsa yacika burinsa na lalata mata rayuwa,don bazai jureba domin ya kwadaitu da kyakyawar surarta . Ahankali tukur yakalli alaweeya cikin mayaudarin murya wanda yake amfani da ita wajen sace zuciyar mace yace "ala....weeya lafiya kika shigomin daki ina matsayin uncle dinki ko gaisuwa babu". Wani yarrr alaweeya taji amma tadake ta murguda baki tana" nazone dama in gaya maka karka kara shiga harkata.in abbana yanamin magana ba ruwanka ehe kaji dai". A hankali tukur ya taso daga kan gadon abinka da farin mutum dogo hansome guy mai faffadan kirji ga kuma dogan hanci da sexy eye gashi yamata kwarjini...kafa mata sexy eye dinshi yayi yana mai karasowa,itama Alaweeya takasa dauke idonta daga na uncle amma ta dake ta murgudamai baki tace"lafiya kake kallona kamar wani maye,ko acan turan ka koyo maita"....shiru tayi sakamakon ganin tukur ya nufo inda take. Mune naku _yarmama 👊_ & *🅱k😍💋* [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤* *TRUE LIFE STORY* STORY & WRITTING by *MARYAM YARMAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* & *BILKISU Z.Ya'U(🅱k)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* Page 16-20 Yana nufowa wajen,Alaweeya tana ja da baya har tazo bango,shima matsowa yayi har suna iyajin numfashin juna yayi murmushi cikin murya mai sace zuciyar mace yace "Ala..weeya an girma shine na dawo ko sanda zuwa babu iyeh haka akeyi". Rau rau Alaweeya tayi da ido don duk rashin kunyanta sai yau tsoran Uncle ya shigeta sannan ta kallesa cikin sanyin murya tace"uncle am sorry is mistake". Tukur yayi wani shu'umin murmushi yasa hannu a Aljihunshi ya dakko wata yar tagarda ya bude daka gani kasan hodan ibilis ce,daidai fuskar Alaweeya ya fasa,nan Alaweeya ta lumshe ido tayi luuuuu tamkar zata fadi .tarota tukur yayi ya kaita kan gadonsa,cire rigarsa yayi ya haye kan gadon da niyyar keta mata haddi....haka tukur cikin kankanin lokaci ya lalatawa Alaweeya rayuwa (subhanallah😭). Wanka yashiga yana murmushin samun nassara..yafito ya shirya cikin wasu arnayan kaya ,kananun kaya harda sarka ya fesa turare ya dauki daya daga cikin motocin gidan yafice zuwa club dinsu na mashaya. Bayan wasu dakika Alaweeya ta tashi kanta ya mata nauyi ga wani radadi datakeji,da kyar ta tashi kanta taji ya juyawa duba gadon tayi taga duk bedsheet din kaca-kaca da jini ,kuka msi tsuma zuciya tasa tana tuna abinda yafaru sannan tafara tuna nasihar momy: _"Alaweeya kece babba,karki kuskura wani abu yashiga tsakaninki da wani namiji,karkiga kinada degree kiyi tunanin akwai namijin dazai aureki bayan kin siyar da mutuncinki,no ko bai ganeba sai Allah yasakamai"_ Kuka Alaweeya ta kara fashewa dashi tashiga toilet d'in uncle ta bude shayan ruwan zafi tahada da ruwan sanyi ta gasa jikinta fitowa tayi ta gyara jikinta,Tana nadamar shigowa d'akin tukur, bata gama rufe bakiba tukur yashigo d'akin ya kalli inda Alaweeya ke zaune akan gado tanata ruzgar kuka yafara waka yana wakar _"my body my money na yo own woo baby"_. Aguje Alaweeya ta taso ta rik'emai kwalar riga tana "wallahi uncle tunda kai ka lalatamin rayuwa, wallahi saika aureni". Tukur da yaji kukanta ko ajikinsa ya kalleta ya tab'e baki yace"Tab' saidai fa kiyi hak'uri nawuce wajen domin ni bana maimaitawa, kuma bazan aurekiba, ai bama aure a tsakaninmu tunda ke d'iyatace". A hankali Alaweeya tasaki tukur taja da baya tana kuka maicin rai tana"uncle kasan ni d'iyarkace kuma ka ketamin haddi, macuci azzalumi sai Allah ya sakamin, ka cuceni ka cuci rayuwata". Tukur ya daka mata tsawa yace "get out of my room nonsense banza karuwa". Arazane Alaweeya ta tashi tana tafiya da k'yar tafice daga d'akin tukur, lek'awa falon gida tayi taga ba kowa tayi sad'af sad'af ta haye upstair d'inta tawuce d'akinta, danno sakata tayi ta shiga band'aki ta d'ora alwala tayi sallah tana mik'a kukanta wajen Allah yasaka mata. Washegari duk An hallara a dinning banda Alaweeya. Alhaji ya kalli siyama yace "jeki kiramin auntynki kice tazo muci abinci." Siyama tanufi d'akin Alaweeya, a kwance ta sameta sai kuka take tana rik'e da kanta.. Ihu siyama tayi tanufi dinning d'in tana "dady Alaweeya zata mutu ku taimaka" duka su Alhaji suka haura upstair d'in har gware suke suka nufi d'akin Alaweeya banda tukur daya tashi yayi gaba abinsa. Cikin gaggawa Alhaji yakira likitoci biyu, nan da nan sukazo suna bincikar Alaweeya sannan suka gano matsalar dayake damunta. 'Dayan likitan ya kalli Alhaji dayayi tagumi cike da damuwa yace "Alhaji bala, gaskiya rashin lafiyanta yayi tsanani anytime zuciyarta zai buga, kuma munga b.p d'inta yakai 99 _(hawan jini)_ gaskiya abin yaban mamaki, meya damu Alaweeya haka har bugun zuciya harda hawan jini". Alhaji yashare gumin daya zubomai ya kalli gadon da Alaweeya take kwance ansa mata drip, yace "Nidai ko k'asar turai zan iya fitar da ita indai 'yata zata samu lafiya, Amma ya za'ayi ace yarinya 'yar 21 ta kamu da ciwon hawan jini,me Alaweeya ta nema ta rasa iyeh?" Likitan yacire glass d'insa yace "Alhaji karka damu in Allah ya yarda zata samu lafiya, amma aguji b'ata mata rai. Haka likitan suka harhada musu magunguna, suka musu Allah yak'ara sauki suka fice. Kowa zama yayi yana tunanin meyasa Alaweeya b'acin rai..yarinyar da kullum happy girl ce ga zolaya acikinta. ___________♡♡♡____________ "Dama na kira kane domin in baka wani aiki, dafatan ka iya kisa ko?" Tukur yai tambayar. Wani basamude ne bak'i k'irin dashi ya kalli tukur dake zaune akan kujerar plastic a wajen shakatawa yace"ai ni Na k'ware awajen iya fashi da kissa shiyasa mutane suke kirana da *sharp bullet*,wa kakeso a kashe maka?" Murmushin mugunta tukur yayi, ya cire bakin glass d'in dake idonsa kyansa ya k'ara fitowa yace "kasan dai Alhaji balarabe ko?" Bullet yace "waye baisan Alhaji balarabe ba, kodan taimakon jama'ar da yakeyi dole yayi suna". Tukur ya gyada kai yace"good to shi nakeso ka kashemin acikin wannan weeks d'in". Zaro ido bullet yayi yana "haba yallab'ai mutumin dake yawo da bodyguard tayaya zan iya kasheshi". Tukur yace "indai wannan ne karka damu, nasan yanda zanyi ya rabu da bodyguard d'insa, indai ka kashemin shi kanada million biyar". Xaro ido bullet yayi yana "million biyar, ai kawai kasa a ranka Alhaji yazama shekakke." Dariya sukayi suka tafa, sannan suka d'auki kwalbar barasa sukaci gaba dasha. Mune naku Yarmama & 🅱k😘💋 [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤* *TRUE LIFE STORY* STORY & WRITTING by *MARYAM YARMAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* & *BILKISU Z.Ya'U(🅱k)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* Page 21-25 _wannan shafin sadaukar wane ga ANA TARE GROUP_ Mungode sosai muna alfahari daku❤❤ Washegari Alaweeya taji sauki ta tashi,momy ba irin rokan duniyar nan da tayi mata tagaya mata damuwarta amma fafur taki saima kuka datasa. Kawayenta na makaranta duk sunzo gaisheta,tukur dake zaune a falo yaga wucewarsa sai hade yawu yake tamkar tsohon maye yaga hadaddun mata. Dakyar Alaweeya tafito zata taka musu,sukayi da ita ta koma taki,haka suka doso falon.,idonta ne ya sauka akan na tukur abinda yafarune yadawo mata ta rushe da ihu mai hade da kuka ta juya ta koma dakinta. Tsaki tukur yayi yabar falon yanabin kawayenta da mugun kallo Kawayenta suka rufa mata baya suna tambayar meya faru,kuka mai tsuma zuciya Alaweeya tasa tana"ku tafi bana bukatar kowa yanzu just leave me"; Dayar kawarta maisuna takallets cikin tausayawa tace"Alawis(sunan dasuke kiranta dashi a makaranta) yakamata kiyi hakuri ki gayamana meke damunki,meyasa kika zama so rude". Ihu mai karfi Alaweeya ta kwara wanda yasa momy tashigo tana tambaya . Watsi Alaweeya take da kayan dakin ta "ku fita kubani waje banason ganinku" Momy takalli kawayen a sanyaye tace"Kuyi hakuri ku tafi ,haka take yanzu". Adu'ar samun sauki suka mata sannan suka fice cike da jimami. Kwanciya Alaweeya tayi tana shesshekar kuka tana bubbuga gado . Momy ma hawaye taji yana zubo mata don ganin halin da diyarta take ciki,sannan tafice taje ta dakko Alqur'ani tana karantawa.wani sanyine ya ziyarci zuciyar Alaweeya bacci yayi awon gaba da ita. Cikin satin Alaweeya ta warke tafara zuwa school amma bata dawo daidaiba saima wani matsanancin sha'awa daya addabeta,ta dawo daga school duk stress ya dameta,wani sha'awa taji ya addabeta kuka tafara .. Taga bazata iya jurewa ba tanufi part din tukur tashiga zaune yake yana latse latse akan computer...yana ganinta ya hade rai yana "lafiya kika shigomin daki?" Hawaye yana zuba a idon Alaweeya ta nufi gadon tukur tahau tana"please uncle ka taimakamin,some emotional feelings ne yake damuna,kuma bazan iya jurewa ba". Tsaki tukur yayi yana"and so wat ,kije kisamu yan iskan samarinki kuyi". Kuka Alaweeya tasa tana"uncle ka taimakamin,please,fara shafashi alaweeya tafara..uncle ya dauki laptop dinshi ya rufe yana "a a ni karki lalatani".sannan ya aje. Nan suka shiga sabon Allah baji ba gani. Tundaga ranar tukur ya maida Alaweeya tamkar matarshi,sune hotel daban daban. Alhajine ya kalli "momy dake zaune taci uban ado yace wai ina Alaweeya ne kullum bama haduwa da ita da daddare". Momy tace kasan Alhaji lectures sun musu yawa tunda zasuyi graduation,yanzuma a adaidaitasau take tafiya makaranta". Alhaji yakalli momy yace "wat my daughter acikin motar haya?da kudina da komaina,daga yau na sokeshi tunda bodyguard bazasu dinga kaitaba,to zansiya mata mota". Galala momy tasaki baki tace"haba ranka shi dade ko yusif daya gama karatu baka siyamai motaba sai alaweeya". Alhaji yace "ai ina sane,duk zansiya musu,sonake afara kawo na tukur sai akawo na yusif" Tabe baki momy tayi tace to ai shikenan. Washegari kowa yafita banda momy datake kitchen tana girki yar aikinta tana tayata. Momy taga tamkar an jefo mutum kitchen din,daga idonta tayi tukur ne tsaye da jallabiya yana aika mata da harara cikin gadara ya bangaje momy da yar aikinta ya bude kular nama yadauki katon cinya. Cikin tsoro momy tace"haba tukur ko bakomai ni matar yayankace ya'zaka shigomin kitchen saikace wata mai siyar da abinci"..passsss passs tukur ya wanke fuskar momy damari tuni yar aikin tasaki chokalin hannunta tayi waje aguje . Tukur yakalli momy dake dafe da kunci tasaki baki yace"harkin isa kimin katanga da gidan yayana?ke innaga dama sai insa ya sakeki kuma in sassaraki ba ruwana ko ajikina". Haka yayi daidai da shigowar Alaweeya data dawo daga lecture ,abakin gate yar aiki ta tareta ta yaryada mata ai tukur ya mari momy,ran Alaweeya yabace ta danna intercom tabi hanya short cut tashiga kitchen din taga tukur sai zagin momy yake,ga hawaye yana tsiyaya a idon momy. Alaweeya takalli tukur ta fesamai mari uku ajere ta nunasa da dan yatsa tace"kai harka isa kataba mahaifiyata iyeh,ko baiwarkace". Tukur ya kalleta idonshi yayi jaaa tsabagen bacin rai har zuciyarsa dagawa yakeyi _mudai da mukaga abu yafi karfinmu,muka dauki biro da takardamu muka fyace_ Muje zuwa Mune naku Yarmama & 🅱k💋💋 [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU*🖤🖤 *TRUE LIFE STORY* STORY & WRITING BY *MARYAM 'YAR MAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* & *BILKISU Z. Ya'U (🅱K)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* _Gaisuwar ban girma da jinjinar k'asaita ga *ILLAR RIK'O FAN'S GROUP* wannan shafin mun baku shi kyauta, ya zamto tukuici ga soyayyar da kuke nunawa a garemu da kuma novels d'inmu, mungode🙏_ _Bismillahir rahmanir raheem_ Page 26-30 Ba Tukur kad'ai ba hatta Mum d'inta sai da ta razana da marin da Alaweeya tai wa Tukur, tasan kashin 'yarta ya bushe mai k'watar ta a hannun shi sai Allah, Tukur ya d'ago rinannun idanun shi wanda suka koma ja saboda tsabar b'acin rai, wai kamar shi k'aramar yarinya wadda take a matsayin 'yar shi ta d'aga hannu ta mareshi, shi da ko kallo kai mishi wanda be gamsar dashi ba sai ya hukunta ka, ya kalli Alaweeya, sannan ya nuna kanshi da hannu yace " ni kika mara koh, hala kina mantawa da matsayin ubanki nake a gidan nan? " Alaweeya ta kalle shi a shek'e sannan tace " hala kana mantawa da matsayin mahaifiyata ne a gidan nan, to in ka manta yau na tuna maka, kuma karka manta k'anin uba ba yana nufin ubana bane kai wanda ya haifeni, da zaka rik'a juya mu sai kace bayinka, dan dai ba yanda zamu yi ne amma kai dai sam bakai kama ko yanayi da d'abi'u irin na zuriar gidan nan ba." Mumy ta kalli Alaweeya tace " ya isa haka kar na sake jin bakinki a nan, ko a yaya yake dai shi uba ne a wajen ku, dan haka kul na k'ara jin kin fad'i makamancin irin wannan maganar. " Alaweeya tace " Amma Mum," Mumy ta katseta " bana son ki k'ara cewa komai," Alaweeya ta ja baki tai shiru zuciyarta na k'una, duk da ta rama wa mahaifiyar ta marin da akai mata amma ranta be bar k'una ba, banda aika mishi da harara babu abinda Alaweeya ke yi. Tukur ya nuna Alaweeya da yatsa sannan yace " you will regret, " yana gama fad'in haka ya juya da sauri ya fice ya bar kicin d'in. Koda ya koma d'aki tunani yake kawai a kan abinda ya dace yaiwa Alaweeya, zuciyar shi ke ayyana mishi cewa lallai ya kamata ya d'auki mataki kan yarinyar nan, saboda kar nan gaba ta zamar mishi matsala. kayan shaye-shaye ne barkatai a gaban shi kala-kala yana sha, duk dan zuciyar shi tai sanyi, amma ina. Saida zuciyarshi ta fara ayyano mishi abubuwan da ya kamata yaiwa 'yan gidan d'aya bayan d'aya sannan daga k'arshe ya shek'e da wata irin mahaukaciyar dariya ta jin dad'in samun mafita kan abinda yasa a gaba. ya ci gaba da kwankwad'ar barasa, daga k'arshe ya baje kan kafet d'in da ke tsakiyar d'akin shi sai bacci, munsharin shi kawai kakeji kwarrrrrrr, kwarrrrrrrr. *BAYAN KWANA BIYU* Yau ta kasance Asabar duk 'yan gidan sun fita kamar yanda suka saba duk ranar asabar da lahadi suna fita domin yin siyayya had'e da shak'atawa. Alaweeya ce kad'ai bata bisu ba saboda ciwon kai da tace yana damunta, sun so su hak'ura da fitar amma tace suje, kan ya daina jikinta ne kawai ba k'arfi. Nan kuwa basu san tsabar sha'awa ce tai mata yawa ba, gashi tun ranar da ta mari Uncle Tukur ta rama wa mahaifiyar ta Marin da yai mata bata k'ara ganin shi ba, kuma fushi yake da ita, kuma in suka yi fad'a kwana biyu sai sha'awar sa taita damunta, tana tuno yanda suke aikata aika-aikar su, sai yaita fad'o mata a rai tana k'ara jin matsananciyar sha'awar sa. Tana kwance tana juyi da taji abun yafi k'arfinta sai ta tashi a daddafe ta nufi d'akin Uncle Tukur, tana rok'on Allah a zuciyar ta Allah yasa yana nan be fita ba. ta ko taki sa'a yana nan. Tura k'ofar d'akin da ta yi yayi dai-dai da lokacin da Tukur ke fad'in " eh na gama tsara komai kai-dai kawai aikin ka ka kashe Alhajin." Alaweeya ta zaro ido tare da fad'in " Uncle wa zaku kashe!!!?" Sai a sannan Tukur ya farga da ita, sam be kawo zata zo neman sulhu da wuri haka ba. Murmushi ya saki sannan ya k'ura mata ido, yana nazarin yanayin da take ciki, zuciyar shi ce take cewa dakyau nasan me kika zo nema, bazan sha wahala ba wajen kawar da tunaninki daga wayar da ta ji yana yi. Tukur ya maida wayar kunnen shi sannan yace " bari zan sake kiranka anjima, amma dan Allah ku yi shiri me kyau kar a samu matsala ta yanda aikin zai yi kyau kuma ya sami karb'uwa." Bayan ya kammala wayar sai nan da nan ya canza yanayin kallon shi da muryar shi, ya kalleta yace " abokina ne zai shirya film, director ne shi, to jiya mun had'u dashi ya karanta min labarin har na bashi shawara akai, shine yauma ya sake kira yana neman shawara akan yanda za'ai da Alhajin, shine kika shigo kika ji ina bashi shawara akai." Allah sarki Alaweeya nan da nan ya gama shara mata k'arya kuma ta yarda, ajiyar zuciya me k'arfi ta saki, sannan tace " wallahi nasha kisan gaske ne har hankalina ya tashi, ashe shirin film ne za'a yi." Tukur ya sake kallon ta yace " wai ma me ya kawoki d'akina? oho na gane kwartanci kika zo yi ko, waike lalatanin da kika yi be isheki ba sai kin k'ara min wata lalatar." Alaweeya ta tunkaro shi tana fad'in " dan Allah Uncle ka yi hak'uri kan abinda ya faru, karka hukunta ni ta wannan hanyar, karka manta kaine sanadin b'ata min rayuwata, kaine ka jawo sanadin da muke aikata wannan harkar." Dakatar da ita ya yi ta hanyar daka mata tsawa malama, fice min daga d'aki ni sa'an ki ne, karuwa kawai anzo a lalatani." Alaweeya tace " wallahi bazan fita ba ta tunkaro inda yake, nan take sai ta rungume shi, tare da fara yi mishi abubuwa, irin abubuwan da take yi mishi ne yasa ya kasa jurewa, nan da nan sai Tukur ya bada kai bori ya hau. _BK da 'YARMAMA suna ganin haka, suka fice daga gidan a guje, k'afa me naci ban baki ba, saida suka isa gida sannan suka tsaya suna numfarfashi, YARMAMA ta kalli BK tace "ashe Tukur d'an iska ne," BK tana haki tace "au ke se yau kika sani."😂_ Muje zuwa Mune naku *'YARMAMA* & *🅱K😘💋* [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU 🖤🖤* *TRUE LIFE STORY* STORY & WRITING *MARYAM 'YARMAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* & *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* Page 31-35 Washe gari ranar lahadi kenan, suna zaune ana hira sai ga Tukur ya shigo d'akin ya zauna, yaran gabad'aya sun saka Dady a tsakiya suna zuba shagwab'a, Tukur kuwa banda harararsu ba abinda yake yi. Alhaji ya ciro key d'in mota ya kalli Tukur yana murmushi, sannan ya mik'a mishi yace " yau dai Allah ya yi na cika alk'awarin motar da na d'aukar wa kaina zan siya maka," Tukur ya mik'a hannu ya karb'i makullin motar tare da yin godiya, ba wani nuna tsantsar murna a fuskar shi sosai duk da kuwa irin motar da yake mafarkin mallaka aka siya mishi. Yusuf da Alaweeya har suna had'a baki wajen fad'in " Dady mu sai yaushe zaka siya mana?" Alhaji yai murmushi, sannan yace " duk tare na bada izinin ayo muku odarsu, ta Uncle d'inku ce ta fara isowa, kuma nasan taku tana hanya." Cike da tsananin farin ciki mara misaltuwa suka ce " to Dady mun gode Allah k'ara maka bud'i." Dady ya kalle su yace " ameen yarana, babu abinda bazan iya yi muku ba a rayuwa muddin inada halin yi, kuma wanda be sab'awa koyarwar addinin islama ba, maza kuje ku shirya mu fita, yau zan kaiku wajen da kuka fi so ku siya duk abinda kuke da buk'ata, daga nan ku turomin Mumyn ku." Suka amsa da " to " kuma dukkan su suka tashi a tare kowanne yana rige-rigen zuwa shiryawa. Tukur kuwa b'acin ranshi da tsantsar bak'in cikin da zuciyar shi ke ciki ya kasa b'oyuwa, sam ya tsani yaga Alhaji na fitar da kud'i ya bayar ko ya siya wani abu ya bayar. Kuma ya tsani yanda yake shagwab'a yaran nan, ko menene suka buk'ata sai ya d'auki kud'i ya basu, hakan yafi komai k'ona mishi rai. wata k'aramar tsaki yaja wadda sam be san da fitowarta fili har Alhaji yaji ba. Alhaji ya kalli Tukur yace " d'an'uwa yadai, akwai abinda kake da buk'ata ne?" Tukur yace " babu, sedai inada 'yar shawarar da zan bayar." Alhaji yace " to ina jinka." Tukur yace " gaskiya be kamata ana shagwab'a yaran nan haka ba, nan gaba ne abun ji, ka dena cewa duk abinda suka tambaya sai ka yi musu." Alhaji ya yi murmushi, sannan yace " Tukur kenan maganarka hakane, amma yaran ka sunada kyakkyawar tarbiyya wadda nake Alfahari da ita a ko'ina, kuma abinda yasa nake basu komai shine saboda kar hanasun ya jefa rayuwarsu cikin wani hali suje suna nema a waje ta kowane hali, sannan dukiyar nan inada ita, menene amfaninta in har ban wadata iyalina da ita ba, ko kaga canjin d'abi'u ne ko canjin hali a tare dasu?" Tukur yace " a'a gaskiya, ban gani ba," shi kanshi saida yai maganar sannan daga baya yai tunanin kar Alhajin ya fara zargin wani abu asirin shi ya tonu. Shi kuwa Alhaji be fahimci komai ba, harga Allah shi dad'i ma yaji yanda ya nuna ya damu da rayuwar yaran. Alhaji yace " naji dad'i yanda ka nuna ka damu da rayuwar yaran nan, hakan ya tabbatar min da cewa ko bayan ba raina zaka kula min da tarbiyar su." Tukur ya saki ajiyar zuciya tare da murmushi na jin dad'in Alhaji be kawo komai ba, a zuciyar shi kuwa fad'i yake gwara ka rik'a tuna mutuwar kam dan kana gaf da tafiya, a fili kuwa cewa yai " Yaya ai yaranka kamar yaran da na haifa ne." Alhaji ya mik'e sannan yace "kaje ka shirya, zamu fita gaba d'aya." Tukur yace "Alhaji kuje kawai akwai aikin da zanyi ne da na biku." Alhaji yace "to ba damuwa, bari naje na shirya kafin su fito su fara rigima, Tukur yai dariyar yak'e, sannan yace " ok gaskiya kam gwara ka shirya kafin su fito." Alhaji na juyawa Tukur ya bishi da wata harara wadda shi ya barwa kansa sanin dalilin yinta. Washe gari ranar litinin kenan, Alaweeya ta tafi makaranta, bayan an taso su kan hanyarta ta dawowa sai wayarta ta fara k'ara alamar ana kiranta. Ganin wanda ke kira yasa ta d'aga tare da karawa a kunne, can d'aya b'angaren Tukur yace "kina ina?" Alaweeya tace "gani a hanya zan koma gida, nan ya fad'a mata yana da buk'atar ta dai-dai wannan lokacin, ta tsayar da napep d'in, bayan ta sallami me napep d'in ne sannan ta kwatanta mishi, dai-dai inda take. Babu b'ata lokaci kuwa sai gashi ya iso a cikin sabuwar motar da Alhaji ya siya mishi. Nan da nan ta shiga Tukur yaja sai bakin wani had'ad'd'en hotel me matuk'ar kyau da tsada. Parking suka yi, sannan suka fito daga motar suka shiga ciki. Alhaji ne zaune cikin k'ayataccen office d'inshi yana cike wasu takardu, wayar shi ta d'au k'ara alamar ana kiran shi, bayan ya d'aga ne ake shaida mishi ana jiran shi yanzu bak'in shi sun iso suna hotel yaje ya same su suyi meeting d'in a can saboda suna so in an gama da wuri su koma yau d'innan. Bayan ya gama wayar ne nan da nan Alhaji ya aje duk wani Abu da yake yi ya fito ya shiga mota aka jashi sai hotel d'in da bak'in shi suka sauka a ciki. A dai-dai lokacin da motar Alhaji ta kutso cikin harabar hotel d'in a dai-dai ta su Tukur da Alaweeya zata fito ita kuma. Alaweeya ta saki salati tare da zaro ido, tace " na shiga uku Dady!!! yau asirinmu zai tonu ," Tukur ma ya kalli inda take kallo yaga Alhaji, shima ya zazzaro idanu. Muje zuwa Mune naku *YARMAMA* & *(🅱K)😘💋* [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤* *TRUE LIFE STORY* STORY & WRITTING by *MARYAM YARMAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* & *BILKISU Z.Ya'U(🅱k)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* Page 36-40 Kasa sukayi dakai ,sukaja motar a matukar guje,wanda Alhaji kawai kurar motar yagani. Dariya Alaweeya tayi najin dadi ta kalli tukur kaunarsa nakara shiga ranta tace"uncle Allah fa ya taimakemu'saimu canza hotel". Dariya tukur shima yayi azuciyarshi yana "ai gobe goben nan ubanki zai je lahira kuma anan zaki fuskanci wulakanci" afili kuma yace"aikwa tamkar kinsani". Adaidai kwanar layinsu tukur ya faka motarsa ,Alaweeya tafito tana rausaya,shiko tukur yajuyar dakan motarsa yayi. Yayinda Alaweeya ta kwankwasa bakin gate dinsu maigadi yabude mata yana kwasar gaisuwa ,amsawa tayi tashige babban falo ta zauna tana dariyar farinciki. Momyce tashigo falon taci uban kwalya tana"su manyan arewa northern people,har antashi da school". Tashi Alaweeya tayi ta rungumi momy tana"oh momy i really miss you so much". Bata gama rufe bakiba Alhaji yashigo yusif na biye dashi da gudu taje ta rungumeshi ga bodyguard sun ruko gana must go guda uku,direshi sukayi a falon suka fice yayinda Alaweeya tanufi wajen da Alhaji yaxauna ta rungumesa tanamai shagwaba. Yusif ya kalleta ya mata hararan wasa yace"baby doll katuwa tashi daga cinyar dady,karki ballamai cinya,ko auta bata abinda kikeyi wallahi". Momy tace "rabu da ita,ai tana gama graduation zamu fitar mata da miji tunda kullum acikin wulakanta samari take,hatta yayan senetors". Alaweeya ta kalli Alhaji tamkar zatayi kuka tace"dady ka gansu ko". Alhaji ya kalli momy yace "au tarar dangi zakuwa yata ko,dama yau da daddare akwai dan meeting din da xamuyi daku gabaki daya,yanzu wannan gana must go din da kuka gani kudine wajen miliyan goma sha biyar za'akai asibitoci da gidan marayu hatta gajiyayyu a raba musu na fidda zakka". Cike dajin dady momy ta kalli Alhaji tana "Allah sarki dadynmu ubangiji Allah yabiyaka duniya da Lahira"......bata gama rufe bakinta ba tukur yashigo gidan a matukar buge yasha yabugu yana zuwa falon yafara ihu da sowa yana magana irin tayan maye. Alhaji yaji hawaye yana kokarin zubomai ya kalli tukur yana"tukur yanzu kayi daidai ,meye amfanin wannan rayuwar". Tukur yayi gyatsa cikin murya ta yan maye yace"Alhaji komai is normal,normal nake". Tashi Alhaji yayi yakama hannunsa yakaishi dakinsa yaragemai kaysn jikinsa ya kwantar dashi barcine mai nauyi ya kwashesa,kallonsa Alhaji yadinga yi cike daso da kauna,yadinga kwararo adu'a yana tofamai. Sannan yaja kofar yafice yasakko falon ya tadda su momy kowa yayi shiru. Da daddare an hallara a falon harda tukur nasiha Alhaji yake musu yana "Tukur kaine babba yanzu,kona mutu kaine zaka rike gidannan"tukur ya kalli Alhaji a ransa yana "aiko baka fadaba mutuwa gobe gobe". Alhaji yacigaba yace"dukiya takuce dukanku,tukur yakamata kayi hankali ka nemo mata,.ka tuna duniyar nanba komai bane,kekuma Alaweeya bayan graduation dinki as barrister saiki fito da miji domin yanzu kin girma ,nasan bazaku taba bani kunyaba domin kunsamu tarbiyya daga uwa tagari,ilimin boko Allah yabamu hakama na addini kunadashi,nidai nasan ko yau na mutu banda hakki akan kowa". Momy tace "Alhaji me kuma yakawo wannan maganar,bazaka mutuba muna tare pls kabar maganar nan". Harara tukur ya dankara mata yatashi yana"saida safenku yahaye sama" Wayar Alhaji ne yayi ruri dauka yayi ,murya ta Alhaji lawan wanda suke meeting tarene ya gayamai gobe sunada meeting karyazo da bodyguard kawai da driver zaizo saboda meeting din sirrine,batare da aiyana komai a ranshiba Alhaji ya yarda,haka kowa yamike suka junansu sumba kowa ya wuce makwancinsa suna kewar juna. Tukur ne adakinsa yana zaune akan gado yana waya yace"sharp bullet karku kuskura ku barsa da ransa,tunda harda drivern muka hada baki ,shi karku kashesa kawai ku harbesa akafa kar mutane sugane,i repeat karfa asamu wata matsala yayana ne uwa daya uba daya eh". Kashe wayar yayi ya kwanta ya kyalkyale da dariya yana"sabuwar duniya nakusa inzama billonier inyi facaka da dukiya". Mune dai naku kullum 🅱k💋 Da yarmama💃❤ [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU 🖤🖤* *TRUE LIFE STORY* STORY & WRITING *MARYAM 'YARMAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* & *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* Page 41-45 Bayan kowa ya tafi makwancin shi Tukur ya kasa zaune ya kasa tsaye, banda zirga-zirga cikin d'akin shi ba abinda yake. Jira kawai yake yi dare ya tsala yaje ya aiwatar da manufar shi. Sai da dare ya tsala wajen k'arfe biyu da rabi na dare sannan Tukur ya fito daga d'akin shi, tare da wani farin k'yalle wanda yake d'auke da maganin bacci a jiki. 'Dakin Alhaji ya nufa, kuma yai sa'a Allah ya taimakeshi be had'u da kowa ba duk sun dad'e da yin nisa a bacci. Yana shiga d'akin ya tarar da Alhaji kwance yana ta bacci, cikin sand'a ya k'arasa kusa da fuskar Alhajin ya sa mishi wannan farin k'yallen, sannan ya saki murmushin jin dad'i, ya san cewa Alhaji kuma shi da tashi sai ya d'auki dogon lokaci, saima ya makara. Bincike ya hau yi cikin d'akin ta ko ina, cikin sa'a kuwa ya harhad'a dukkanin wasu takardun kadarorin Alhajin gaba d'aya, ya tarkata su waje d'aya. Bayan ya gama harhad'awa ne sannan cikin sauri ya cire k'yallen da ya saka a fuskar Alhajin, sannan ya d'auki lodin takardun dukkanin kadarorin Alhajin ya fice daga d'akin. Da isar shi cikin d'akin ya baje a tsakiyar falon shi, bayan ya sakawa d'akin key. 'Dai-d'ai ya sake yiwa takardun yana sake dubawa wani farin ciki yana k'ara ziyartar zuciyar shi. A ranar be yi bacci ba saboda duk ya k'osa gari ya waye a kawar da Alhaji duniya ta dawo mishi sabuwa, tun a daren ya fara tsare-tsaren yanda zai tafiyar da dukiyar, da abubuwan da zai gabatar da ita. Littafi ya d'auko, sannan ya d'auko wata tsohuwar takarda wadda ya gani acikin takardun ta wani fili da Alhajin ya siya ne, a jiki akwai sa hannun Alhajin. Ita yaita kallo yana so ya kwaikwayi sa hannun Alhajin, saida ya kusan cika littafin nan, sannan Allah ya taimake shi ya iya signing d'in Alhajin sak. Sai da yabi takardun nan d'aya Bayan d'aya ya maida sunan shi, tare da saka hannun shi da Wanda ya saka iri d'aya sak da na Alhaji, sai kuma takardun yarjejeniya Wanda Tukur d'in ya rubuta da hannun shi a zuwan Alhajin ne ya rubuta na amincewa cewa komai ya zama na Tukur d'in, kuma nan ma ya kwafi sa hannun Alhajin ya rubuta. Sai da ya kammala komai ne sannan hankalin shi ya d'an kwanta, yasan dai ko ba'a samu nasarar kashe Alhaji ba gobe, to dukiya dai ta zama tashi, dan babu wanda zaiga rubutun da sa hannun yace ba Alhajin ne da kanshi yasa ba. K'ara kallon sa hannun Alhajin ya yi, da kuma Wanda ya sa, yaga sak iri d'aya, sai ya fad'a kan gado, tare da kecewa da wata irin dariya, sannan yace "wayyo duniya sabuwa," ya d'aga k'afa sama yana rawa da su. *WASHE GARI* Washe gari Mumy taga har wajen k'arfe takwas amma bata ga fitowar Alhaji ba, hakan yasa ta nufi d'akin shi domin dubawa ta gani ko lafiya. Tana zuwa ta tarar har yanzu bacci kawai yake ta sharawa, k'arasawa wajen shi ta yi, tare da tayar da shi, sannan tace " Alhaji yau lafiya kake kuwa? naga baka tab'a kaiwa wannan lokacin kana bacci ba, kuma gashi naji ma kace yau kana da meeting. " Alhaji nan da nan ya tashi, yana salati, agogo ya fara kalla, k'arfe takwas, kuma tara da rabi suke da meeting d'in, yace " subhanallah, yau wane irin bacci nayi haka har na rasa sallar Asuba," yana magana yana k'ok'arin saukowa daga kan gado. Mummy tace " lallai Dadyn mu bacci yai dad'i yau, nima gani nayi baka tab'a dad'ewa haka ba tare da ka sauko ba shiyasa nace bari inzo in duba," koda take wannan maganar tuni Alhaji ya shige toilet. Alwala ya fara d'aurowa, sannan ya fito Mummy ta shimfid'a mishi dadduma ya tayar da sallah. Mumy na zaune har ya Idar, ya d'auki kusan minti sha biyar yana istigfari da rok'on Allah Afuwa, sallar asuba da ta wuce shi yau. Bayan ya kammala Addu'a suka fita tare da Mumy sai wajen cin abinci, suka tarar da kowa ya hallara su kawai ake jira, banda Tukur da suka zo suka tarar har yama kusa gama cinye nashi abincin, yana gama ci kuma ya tashi ya bar wajen. Bayan an zuzzubawa kowa abincin nan da nan kowa ya fara cin nashi, banda Alhaji da yaketa faman jujjuya cokalin yanda kasan yaro. Mumy ce ta lura da yanayin shi, ta kalle shi tace " Alhaji wai yau lafiya kake kuwa, naga tun d'azu kake juya cokali ka kasa kai koda 1 spoon bakinka?" Haba su Alaweeya suna jin haka gaba d'ayansu hankalin su ya dawo kanshi, nan da nan kuma kowanne daga cikin yaran ya ajiye cokalin shi harda Mumy, suka yo kan Dadyn da tambayoyi. Haka suke yi, duk lokacin da suka ga canji daga wajen iyayen su haka suke yi, basa k'ara yin walwala har sai iyayen nasu sun dawo normal, da iyayen nasu suka tambayesu meyasa suke haka, sai yaran suka ce suma suna shiga damuwa ai a Kansu akan koma menene ya same su, damuwarsu ce kesa nan da nan iyayen su sauko, su saki ransu koda abinci suke ci sukaga Mumy ko Dadyn su cikin damuwa to suma ajiye nasu abincin suke yi har sai ya dawo normal. Dady ya kalle su yai murmushi sannan yace " ina alfahari daku, kuna nuna damuwarku a kaina sosai, to ranar da kuma kuka rasani ya kenan, Ku kwantar da hankalinku, babu abinda yake damuna, yau dai haka nan na tashi wani iri, da kuma matsanancin fad'uwar gaba." Yaran suna jin Dadyn su ya ambaci mutuwa sai suka hau kuka musamman Alaweeya kuka take kamar zata shid'e, tun jiya suka ga yanayin Dadyn su ya canja, yanayin maganganun shi kamar na me barin wasiyya. Mumy ne da Dady suka samu dak'yar suka lallashi yaran, abinci kuwa saida suka ga Dadyn su ya saki ranshi har yaci kad'an sannan hankalin su ya kwanta. Yaran suka yiwa Iyayen nasu sallama suka fita domin tafiya makaranta, Alhaji ya k'ure su da idanu har suka fita daga d'akin, duk Mumy na kallon shi. Mumy ta kalle shi tace " kodai zaka hak'ura da zuwa meeting d'in nan ne kai musu waya ka sanar dasu sai wani lokacin?" Dady yace " a'a sun fad'amun yana da matuk'ar muhimmanci, kawai kiyi mun addu'a, " Mumy tace "to Allah ya tsare mana kai a duk inda kake, ya dawo dakai gida lafiya." Dad ya amsa, sannan ya nufi motar da zasu fita da ita, driver ya bud'e mishi, bayan ya shiga ya sauke glass k'asa ya d'agawa Mumy hannu alamar yana yi mata bye-bye, itama tana d'aga mishi hannu, har motar ta fita daga gidan. Sun yi nisa cikin tafiyar yaga driver d'inshi ya d'auke hanya ya nausa cikin daji, Alhaji ya kalle shi yace " ya naga ka canza hanya ka shiga damu cikin daji, ina zaka kaimu?" Driver yana kuka yace " Alhaji kayi hak'uri, na bi son zuciyata na karb'i kud'i domin in kawo ka a kashe ka." Kafin Alhaji yai wata magana sai ga su Bullet sun kewaye su, nan da nan Bullet ya harbi Alhaji a k'irji, sannan ya harbi driver d'in Alhajin a k'afa, basu bar wajen ba saida suka tabbatar Alhaji baya numfashi ya mutu sannan suka bar wajen. Ku biyo mu muje Mune naku *YARMAMA* & *(🅱K😘💋)* [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU 🖤🖤* *TRUE LIFE STORY* STORY & WRITING BY *MARYAM 'YARMAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* & *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* Page 46-50 Bullet suna b'acewa daga gurin suka kira Tukur suka shaida mishi sun cika aiki, Alhaji ya tafi garin da ba'a dawowa, farin ciki ne ya lullub'e Tukur, nan take yai musu transfer kud'i masu yawa yace gashi nan su k'ara. Tunda Alhaji ya fita ita ma Mumy gabanta yake ta fad'uwa, ta rasa dalili, Alhaji kafin ya fita ya sanar da ita cewa bazai wuce k'arfe sha d'aya zuwa sha biyu ba sun gama meeting d'in ya dawo gida, amma yanzu wajen k'arfe Uku saura shiru ba shi ba alamun shi. Shi kuwa Driver tun lokacin da aka harbe shi a k'afa ya suma. Yara duk sun dawo daga makaranta suma dai kamar jikin su ya basu zasu yi rashi haka suka zauna jugum. Suna dawowa daga makaranta Dadyn su suka fara tambaya domin sun riga da sun saba duk in suka dawo daga makaranta sai ya kira sun gaisa da kowa, daga nan idan da me wata buk'ata ya fad'a mishi ya taho musu dashi, hakan yasa yaran suka yo caaa kan mumy da tambayar ina Dadyn su ya tafi ganin lokacin da ya saba kira ya gota bai kira ba. Hakan ne ya k'ara tayar da hankalin Mumy ta shiga neman wayar shi a kashe, Alaweeya ma haka sun kira yafi a k'irga ana ce musu wayar na kashe, har yamma ta yi amma shiru ba Alhaji. Duk wainar nan da ake toyawa Tukur yana d'akin shi yana sharar baccin da be samu ya yi ba jiya, hankalin shi kwance. Nan da nan mumy ta baza masu tsaron shi domin a dubo shi, har gurin aikin shi anje duk baya nan, gashi ranar kamar Allah ya rufe bakinta ta kasa tambayar shi inda zasui meeting d'in. Wani soja ne ya kutso kan titin da zai sadaka da cikin wannan dajin, yana zuwa dai-dai nan kashi ya matse shi, ya faka motar shi, sannan ya kashe ta ya rufe ya saka makullin a aljihu, sai ya shiga daga cikin dajin domin ya samu ya biya buk'atar shi, ya tsugunna kenan ya fara sai ya d'aga kanshi sama yana fito yana zuba wak'ar su ta sojoji abun shi yanda kasan a gida yake. Bayan ya gama yai tsarki ya mik'e tsaye, yana d'aga kai gaban shi ya hango mota can nesa dashi. Daga inda yake zuwa gurin da motar take akwai tazara sosai a tsakani. Har ya juya zai tafi ya sake kallon inda motar take, yace kai gaskiya sai yaje ya duba ba mamaki ma 'yan fashi ne. Yana k'arasowa wajen ya yi matuk'ar razana da gigicewa ganin sanannen mutumin dake kwance cikin jini a cikin mota, gefe kuwa driver ne Wanda aka harba a k'asa, nan da nan ya hau salati. Bazai tab'a mance fuskar Alhaji ba, mutumin da ya taimaka mishi ya tallafawa rayuwar shi har ya kai wannan matsayin zama soja. Ba b'ata lokaci ya kira lambar wani aminin shi d'an sanda, ya shaida mishi abinda ke faruwa tare da yi mishi kwatancen inda yake. Ba a d'auki lokaci me tsaho ba sai ga d'an sandan tare da jami'an tsaro masu yawa, tare da motar d'aukar mara lafiya, nan da nan suka kewaye gurin. Basu tsaya b'ata lokaci ba suka d'auki su Alhaji aka saka su a mota sai asibiti. Likitoci sun tabbatar musu da cewa Alhaji Allah yai mishi rasuwa, shi kuma drivern suma yayi, an cire mishi harsashin da yake jikin shi, nan bada dad'ewa ba zai farfad'o. Sojan nan kuka yake yi ba k'ak'autawa, Abokin shi d.p.o yana rarrashin sa, tare da shawartar shi kan su d'auki gawar Alhajin sukai gidan mamcin domin suma su san halin da ake ciki. Wajen fita da gawar Alhajin daga asibiti haka doctor's da Norse's suka firfito kowa sai kuka da kuka, da salallami domin d'ad'd'aiku ne cikin su Wanda ba Alhajin bane ya d'auki nauyin karatun su, suna kuka suna binshi da addu'a har aka fito dashi. Nan aka shigar da gawar Alhaji cikin mota suka doshi gidan shi. Ko da Isar su gidan su Mumy wad'anda suka kasa zaune, suka kasa tsaye, ko abinci sun kasa ci, suna jin k'arar mota dukkanin su suka tashi, suna rige -rigen fitowa domin su duba su gani ko Dadyn su ne ya dawo. Suna fitowa farfajiyar gidan turus suka ja suka tsaya, ganin gawa kwance a tsakar gidan su, ga kuma soja da 'yan sanda sun kewaye gidan. A dai-dai wannan lokacin Tukur ya tashi daga bacci, dama sallah ba yinta yake yi ba, yana fitowa shima yaja ya tsaya tare da zazzaro idanu harda k'arfin halin tambayar meke faruwa. Mumy da Alaweeya da Yusuf fad'uwar gaban su ne ya tsananta, ita kuwa Mumy jikinta ya riga da ya bata Alhaji ne kwance a gaban su, ya rasu. Ganin gabad'aya 'yan sandan sun kasa yi musu bayani, kuma duk wanda aka tambaya cikin su sai su duk'ar da kai suna hawaye. Mumy ta durk'ushe a k'asa domin hakan da sukai ya tabbatar mata da hassashen zuciyarta, ta saki salati tare da fashewa da kuka me tsuma zuciya. Alaweeya ce ta nufi gawar da sauri tare da yaye mayafin da aka lullub'e fuskar dashi, tana bud'ewa taga Dadyn su kwance cikin jini, sakin mayafin ta yi da sauri tare da girgiza kai tana ja da baya, sai luuuu ta fad'i k'asa sumammiya. Tukur dake gefe zuciyar shi fara k'al kamar takarda, yace cikin zuciyar shi bari yai suman k'arya shima kar a gano shi. K'wala k'ara ya yi sha yace "innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Yayana," shima se yai baya luuu ya sume. Yaran Alhajin ne gaba d'aya suka k'araso kan gawar suna kuka suna jijjiga shi suna fad'in Dadyn mu ka tashi. Mumyn su ce ta rarrafo inda suke, ta rirrik'e su, tace " kiyi hak'uri Dadyn mu bazai tashi ba, dadyn mu ya rasu, Dadyn mu ya tafi ya barmu, mun rasa shi rashi na har abada. Fizge hannayen su suka yi daga gareta suna kuka suna girgiza kai suna fad'in " a'ah Dady be mutu ba," komawa kan gawar suka yi suka ci gaba da jijjiga shi suna fad'in " Dady ka tashi." Cikin 'yan sandan nan kaf babu Wanda bai yi kuka ba. Nan da nan yara da manya suka cika k'ofar gidan, yara da manyan unguwar kuka suke kamar zasu shid'e. Saboda Alhaji mutum ne me barkwanci da wasa da dariya, ga taimako, unguwar nan kaf ba Wanda be shak'u da shi ba musamman ma yara shi mutum ne me son yara, kuma yana tallafawa rayuwar su, shiyasa kowanne daga cikin su a yau yake kukan rasa shi. D'aya daga cikin yaran unguwar ma Wanda yafi shak'uwa da Alhajin shima zuwa ya yi wajen gawar cikin yaran Alhaji yana kuka yana jijjigashi. Nan da nan aka d'ebo ruwa aka yayyafawa Alaweeya amma ina ko motsi bata yi, hakan yasa soja cikin muryarshi wadda ta disashe saboda tsabar kuka yai umurni da a kaita asibiti. Shi kuwa Tukur ana yayyafa mishi ruwan ya mik'e kamar gaske, tare da sakin wani sabon kukan, ya shiga cikin yaran ya duk'a wajen Alhajin shima yana kuka yana fad'in "Yayana meyasa zaka tafi ka barni, kai kad'ai ne Wanda ya rage min," sai ya sake fashewa da kuka. Muje zuwa Mune naku *YARMAMA* & *(🅱K CE)*😘💋 [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤 ZUCIYAR MUGU 🖤🖤* *TRUE LIFE STORY* STORY & WRITING BY *MARYAM 'YARMAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* & *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* _wannan shafin kacokam Sadaukarwa ne ga *🅱K FANS GROUP* tukuicin soyayyar da suke nuna mana da kuma novels d'in mu, muna k'aunar Ku sosai, kamar mu Baku ranmu kyauta, mungode sosai da k'auna🙏_ *MASOYAN MU* _Masoyan mu na nesa da na kusa muna rok'on ku dan Allah ku saka 'yar uwar mu *Aisha mumys frnd* addu'a Allah ya bata lafiya da dukkanin musulmi baki d'aya._ Page 51-55 "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!!!" Kalmar da keta fitowa daga bakin Mumy kenan, yayin da hawaye ke wanke fuskarta. Sai Allah ya sa mata dakiya da juriya, d'an sandan nan ne ya karb'i wayar Mumy ya kira 'yan uwa da abokan Arzik'i, shima Tukur ya kikkira wasu yana kuka yana sanar da su nan da nan aka cika gidan. Ba gidan ba kad'ai titin unguwar kaf cike yake da mutane wad'anda suka zo domin su sallaci gawar Alhaji. Kuma kowanne ka gani daga cikin su kuka sosai yake yi na rashi, duk inda ka gifta zaka ji suna kuka suna fad'in munyi babban rashin Mutum na gari me taimako da tausayi da son na k'asa dashi, gaskiya mutuwar nan ta gigita mutane da dama, wasu fad'i kawai suke d'azu fa da zai fita sun ganshi har suka gaisa dashi. Allahu Akbar! Alhaji kam ya dace, tun kafin ya tafi makwancin shi wato cikin k'abari kyawawan shaidu yake ta samu ta ko'ina daga bakunan mutane, tabbas shi kam ya dace manya da yara suna kokawa kan rashin sa, se dai mu mu yi fatan Allah kasa namu k'arshen yai kyau. Haka aka yi wa Alhaji wanka aka suturta shi, sannan aka ce iyalan shi duk su fito su yi mishi addu'a za'a tafi dashi makwancin shi. Dukkanin su suna duk'e a gaban gawar banda Alaweeya wadda take kwance a asibiti. Mumy ta kalli fuskar mijinta wadda take cike da annuri, idan ka kalle shi sai kaga kamar murmushi yake yi, tace "Dadyn mu a zamana da kai babu abinda ka tab'a yi min na cutar wa, ina rok'on Allah ya saka maka da kyakkyawa, Allah ya amince mu k'ara kasancewa da juna acikin Aljanna, wanda yai silar raba mu da kai kuwa Allah ya saka mishi da sakamako dai-dai da abinda ya aikata gaba d'aya d'akin suka d'auka da ameen" Tukur ma ya yi addu'a amma ba'a jin me yake cewa, sai kuka da yake ta k'ak'alowa. Bayan sun gama addu'ar ne anzo za'a d'aga shi a tafi dashi zance yasha bam-ban. Ana d'aga shi Mumy ta rirrik'e gawar karakam tak'i saki tare da fashewa da kuka tana kiran sunan Alhajin, suma yaran duk sun rirrik'e shi suna kiran sunan shi suna kuka, dak'yar mutane suka b'anb'are su daga jikin Alhajin. A lokacin ne kuma zuciyar Mumy tai mugun karaya da taga dagaske fa sun rasa shi kenan, tana ganin an nufi hanyar fita dashi ta fashe da kuka me k'ara tare da k'wala wa Alhajin kira, daga nan sai kuma itama tai baya luuuuu ta fad'i k'asa sumammiya. Itama saida aka kaita asibiti, bayan kwana biyu jikin su yai kyau se dai dukkanin su suna da hawan jini da ciwon zuciya, dama ita Alaweeya tana da shi, sanadin lalata mata rayuwa da Tukur ya yi, mutuwar mahaifin ta ya tayar da ciwon. Ita kuwa Mumy sanadin mutuwar mijinta ne ta kamu da ciwon zuciyan. Haka dai aka sallame su suka dawo gida suka ci gaba da karb'ar gaisuwa. Mutane kuwa koda yaushe cikin b'arkowa suke, maza da mata kuma kowanne yazo sai ya yabi Alhaji tare da tunowa da alkhairan da yai musu. Shi kuwa Tukur a duk lokacin da aka yabi Alhaji wani irin haushi yake ji, gashi babu Wanda zai zo gaisuwar nan har ya tashi ba tare da ya yabe shi da fad'in alkhairin shi ba. Sojan nan tun da aka yi rasuwar ko da yaushe yana nan ana zaman makoki dashi, dama a ranar da sukai rashin Alhajin tafiya zai yi, wata tafiya ce ta kama shi, Ashe ba rabon ya yi ta, domin ya sawa ranshi sai an gama zaman makoki an watse zai bar wajen, kuma ya k'udurta a ranshi zai saka Alhajin da iyalen shi cikin dukkanin Addu'ar shi, domin d'an halak be tab'a manta alkhairi. To dama haka rayuwa take, komai yai farko zai yi k'arshe, duk abinda ka saba dashi dole wata rana zaka rasa shi, se dai fatan yin kyakkyawar k'arshe da cikawa da imani. *_muna bawa masoyan mu hak'uri na jinmu shiru shekaran jiya da jiya, insha Allah ba zamu k'ara tsayawa ba har sai mun kammala gaba d'aya, mun gode da k'aunar Ku sosai._* _masoya ku dinga yiwa Alhaji balarabe adu'a domin gaskiya anyi babbar rashi😭😭_ INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN Muje zuwa Mune naku *YARMAMA* & *(🅱K CE)*😘💋 [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤* *TRUE LIFE STORY* STORY & WRITTING by *MARYAM YARMAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* & *BILKISU Z.Ya'U(🅱k)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* Page 56-60 *Wannan shafin nakune ZAMANI WRITTERS ASSOCIATION* _Mungode bisa kaunar da kuke nunawa littafin nan musamman Aunty nasmat,Allah ya biyaku_ AMEEN SUMMA AMEEN🙏 _ubangiji Allah yaji kan Alhaji bala,yasa aljannatul firdaus ce makomarsa😭_ Bayan wata daya tukur ya kwace duk wani arziki na wajensu momy hatta kaddarorinta ya kwace..makarantar sadeek da nasu siyama duk ya tsaya gidan yazama wani iri ba hadin kai duk ya tarwatse tamkar ba gidan Alhaji bala ba,kullum kowa na dakinsa ko abinci sun dainaci a dinning saidai kowa yaci nasa Bari Alaweeya da mutuwar Alhaji ya tabata sosai ko abinci bata iyaci kowa ya gujesu(dama a zamanin nan sai kana dashi)...kuka da tashin hankali bawanda basuyi shiba. Haka momy tasiyar da gwala gwalanta ta siyo musu kayan abinci karshema duk yan aiki suka gudu saboda ba abinci ishashshe agidan. Alaweeya tsananin son tukur sai kara tsira yake a zuciyarta...yanzu kwata kwata ya shareta ko ganinsa batayi ,rana daya ta yanke shawarar zuwa ta samesa,dakin ta nufa tana shiga ta gansa akan gado yana zukar taba ,toshe hanci tayi tana karasowa ta durkusa har kasa tana kuka mai tsuma zuciya tace "uncle abinda kamin ka kyautamin ,kwata kwata ka shareni ka manta da wacece alaweeya,bayan kaine namiji daka sanni arayuwa". A fusace tukur yatashi ya wanke alaweeya da mari yana"ke ai dama tunda basanki nakeba,tunda nasamu abinda nasamu aishikenan,ni wawane duk uban karatun danayi in auri dis-virgin Allah ya kiyaye,tashi ki ficemin daga dakina kafin in saba miki ".nuna mata hanyar waje yayi sannan yaci gaba da zukar tabansa,Alaweeya dake dafe da kunci hawaye masu dumi na zuba a idanuwanta don tunda take a rayuwarta ba'a taba marinta a rayuwaba..amma yau uncle ya mareta tashi tayi tana kuka mai tsuma zuciya....ficewa tayi daga dakin tana zuwa falo su momy suna zaune duk sunyi tagumi...autace kawai take bacci...amaine ya tahowa alaweeya tafadi kasa tadinga kwarara amai falon tamkar hanjinta zaifito. Siyamace ta tashi ta taimaka mata ,momy takalli alaweeya cike da tashin hankali tace "alaweeya watanki nawa bakiga period dinkiba". Alaweeya duk ta galabaita dakyar ta budi baki tace" na wata biyu ne kenan". Arazane momy tamike tana kuka "alaweeya kin cuceni,ciki?innalilahi wayamiki ciki?ki gayamin". Rudewa siyama tayi tana kallon aunty alaweeya tace "dagaske ne sister,please momy karkice haka sister fa bahaka takeba". Yaya Yusif ya fusata yayo kan alaweeya yana jibga yana "zaki fada mana ko saikinci ubanki iyeh haba Alaweeya dame zamujine". Cikin kuka alaweeya tace "wallahi uncle ne uncle tukur ne,shine". Dafe kirji momy tayi tana kiram sunan Allah "Alaweeya ki rasa wanda zakiyi tarayya dashi sai uncle,wallahi nayi nadamar haifuwarki..momy tasa kuka tana "oh Alhaji kadawo duniya mana kaga bakincikin da yarka ta kunsamin yanzu"; Sadeek zubewa yayi akan kujera shima cike da tashin hankali yake bin alaweeya da kallo .cikin kuka alaweeya tace "momy kiyi hakuri ba laifina bane,wallahi yaudarata yayi.inason uncle,shine nabashi hadin kai dayamin alkawarin zai aureni". Kara siyama tayi ta rushe da kuka mai tsuma rai wanda ya fargar da auta daga barci....duka falon suka rushe da kuka,kowa kuka yake mai tsuma rai....sai yau alaweeya tayi nadamar abinda ta aikata,taji ta tsani duniyar ma gabaki daya". Tukur ne ya sakko daga bene yasha kananun kaya...sai fesa kamshi yakeyi..sanye yake da glass dark spackle ,yana isowa falon yaga kowa sai durzar kuka sukeyi tamkar ransu zai fita ,tsawa yadaka musu "ku mahaukatai ,meye kuka cikamin gida da kuka .au dan namuku alfarma kuna zama acikin gidan shine zaku dameni da kuka". Bawanda ya saurareshi sai yusif dayatashi cike da zuciya yayi gaba da gaba dashi yace"wallahi baka cancanci zama ubanmu ba kaci amanar dady kasaka mu acikin bakin ciki ,kai azzalumine.kuma fasiki,kuma dole ka anshi cikin da kawa kanwata ko kanaso ko bakaso ko kuma duniya tajimu". Kyalkyalewa da dariya uncle yayi yana "yaro yaro ne,kai yaro ka iyewa bakinka ni nafi karfin inkula yayarka kazama kuchaka da ita"taje can ta nemi uban danta...kuma daga karshe zance muku congratulation issa goal⚽". Kukan kura yusif yayi "heeeeeey .munkai kararka kotun Allah ..Allah shi zai saka mana ". Ko kallonsu tukur baiyiba yayi ficewarsa daga falon yana dariyar mugunta.. Haka sukaci kuka suka gaji,ga tunanin mutuwar alhaji komai ya cabe musu . Tamkar yau Alhaji ya mutu suka dinga kuka daga karshe momy ta rungumi kaddara ta hada kan yayanta suka dinga kuka mai tsuma rai. Allah sarki rayuwa Mune naku 🅱k & Yarmama💋💋 [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤* *TRUE LIFE STORY* STORY & WRITTING by *MARYAM YARMAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* & *BILKISU Z.Ya'U(🅱k)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* Page 61-65 _wannan page din mun sadaukarwa da duk masoyanmu .muna ta ganin sako da adu'o in da kukeyiwa Alhaji .komin rashin imaninka dole ,ka tausayawa rayuwarsu Alaweeya 😭😭dan Allah kudinga yiwa Alhaji bala adu'a_ *ZAMANI WRITTERS ASSOCIATION* ________________________________ Haka suka share satukan ba walwala balle farinciki ...momy ce ta tuka musu tuwo miyar kuka.dama tunda alhaji ya rasu basu karacin abinci a dinning ba saidai suci a falo. Autace ta kalli tuwon tafashe da kuka don tunda take a rayuwarta bata tabacin tuwoba Momy ta kyalleta tace "lafiya auta saidai fa kiyi hakuri babu abinda ya rage a gidannan sai garin tuwo shima nayaune kawai". Siyama cike da tausayawa takalli sadeek da yusif da suke ta laftan tuwon ko ajikinsa tasa hannu itama tafaraci...momy tace auta jeki kiramin alaweeya tazo taci abinci...aguje auta ta tashi tanufi hanyar dakin alaweeya....ji sukayi an cillo auta daga sama bene bakowa bace fyace karuwar uncle tukur tasha attachment taci bleeching tana kallon yanda auta humaira ta fado daga kan bene ta yamutse fuska . Dasauri sadeek da momy suka nufi inda auta take kwance babu alaman numfashi a tattare da ita ga jini yana zuba a hancinta harda kunnenta.haka yayi daidai da fitowar alaweeya daga dakinta .takama karuwar uncle da kokowa saida tawa budurwar tukur dukan tsiya harda jini da majina sannan ta barta..aguje tasakko batare data damu da cikin dake jikinta ba.tadauki auta tana kuka tafice waje su momy suka rufa mata baya..wajen motocin gidan suka nufa amma babu key ko daya nan suka tuna ai tukur ya kwace duk key din motocin gidan. Gate suka bude suka fita suka hau adaidaitasau sai asibitin da alhaji yake kaisu suka nufa.. Cike tausayawa likitan yakalli momy yana "matar alhaji ce wannan oh duniya,Allah yajikan alhaji". Kuka momy tasa mai tsuma rai har haka shiga da auta emergency.sai bayan awa biyu aka fito da ito akan gadon marasa lafiya ana turota kanta da hannunta daure da bandages aka turata zuwa dakin marasa lfy ,likitan ne yafito yace momy ta biyosa ,momy da alaweeya ne suka biyosa suka zauna a office din.cike da mamaki likitan yakalli cikin alaweeya daya fito.domin daga ita sai dogan riga ko dankwali batasa ba,gashinta yayi buzu buzu yace "a .a dama alaweeya kinyi aurene". Sunkuyar dakai alaweeya tayi tana share hawaye yayinda momy itama tayi shiru . Likitan ya kawar da zancen da cewa "ku kwantar da hankalinku zata samu sauki karayace kawai da buguwar kai datayi wanda tana bukatar tasamu hutu sosai..karku damu da kudin magunguna ,kubarshi domin alherin da alhaji yamin bazan taba mantawa dashiba. Godiya sukayi harda kuka Sati uku suka shafe a asibitin sannan suka koma gida..domin auta tasamu sauki har tana iya tafiya. ..zaune suke a falon sunyi shiru bama t.v balle suyi kallo domin tukur ya siyar .kowa yana tunanin rasuwar Alhaji mai dauke musu kewa,abba mai jansu ajiki mai sasu farinciki Alaweeya ce take yanke farce tana tuna abbanta da yanda yake kaunarta .duka taji yasauka a bayanta juyowar da zatayi taga uncle ne ga budurwarsa abaya ta rike kugu... Suma momy suka bisa da kallo Mune naku 🅱k Nd Yarmama😍💋💋 [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤* *TRUE LIFE STORY* STORY & WRITTING by *MARYAM YARMAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* & *BILKISU Z.Ya'U(🅱k)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* Page 66-70 Bata ankaraba taga uncle ya mareta dafe kunci tayi tana karemai kallonta kafin tayi wani kwakkwaran motsi tukur yasa kafa yayi ball da ita yanata jigganta harda taka mata ciki.kuka take tana bashi hakuri ta kiran sunan Alhaji "Wayyo dady meyasa ka tafi kabarmu da azzalumi?meyasa kabashi amanarmu,dady ka dawo !ka dawo" Tukur yana huci yace "ai baki ga komai. in karasaki banza a banza in huta,akanme zaki dukarmin matar dazan aura saikace kinsamu jakarki". siyama dake zubda hawaye tace "au ita budurwar taka ba jefo auta tayi daga kan upstair ba,danma Allah yasa auta tanada saurin numfashi a duniya". Wangalau yusif yayi zuciyarshi na taffasa ga momy sai kuka take yabude baki.abinka damai karfi..yayiwa tukur naushi har jini yana zuba a hancin tukur ,kara tukur yayi ya taba jinin dake hancinta ya kalla yaga ai jinine.tuni yakama yusif da kokawa ,momy dai suna zaune suna kallon duk abinda ke faruwa...da tukur yaji duka iya duka tuni ya arce dakinsa budurwarsa ta rufamai baya.. Karar alaweeya sukaji dake kwance a kasa.ihu take tana rike cikinta ga jini yanabin kafafunta😭😭....cike da tashin hankali momy ta rike alaweeya tana "alaweeya lafiya,bleeding kuma,yusif ku taimaka mu kaita asibiti". Suka ciccibi Alaweeya suka fito da ita bakin titi tanata bleeding(zubar da jini)tamkar anbude famfo sai jijjiga takeyi idon nan nata ya koma fari fat. Adaidaita biyu suka tara suka nufi asibiti da ita ,cikin gaggawa aka amshesu akayi emergency room da ita. Momy sai kuka suke domin yanda sukaga halin da Alaweeya takr ciki dole zuciyarshi ta karaya. Likitan ne ya fito duk yahada gumi ya kalli momy yace"kune iyalan Alhaji margayi bala Alaweeya tana son magana daku duka". Duuuuu momy sukabi bayan likitan suka shiga dakin da aka kwantar da Alaweeya.halin da alaweeya keciki ya isa yasa a zubar mata da hawaye har yanzu bata daina bleeding ba saidai ta daina jijjigan. A hankali momy suka karasa bakin gadon .momy ta rike hannun Alaweeya data kura mata ido tana mata murmushi tace"Alaweeya dafatan kin fara samun lafiya,Allah ya tashi kafadunki". Murmushi Alaweeya tayi duk da tanajin zafin ciwon a hankali ta kalli momy tace"momy karki damu zamu hadu ko ba yanzuba,inaso inga Alhaji inason zama dashi,don Allah ki yafemin duk abubuwan dana miki,yanda nakeji a jikina tamkar bazan rayuba nidai na yafewa kowa". Kuka siyama ta fashe dashi tana"haba aunty Alaweeya kidaina fadar haka zaki mike da yardar Allah". Alaweeya tayi yar dariya mai cike da ciwo ta mikowa auta hannu alamar tazo zuwa auta tayi Alaweeya tace "auta zanyi kewarku,ina da tafiya mai nisa a gabana,ina sonku i wish happy family forever.Alaweeya ta kawarmusu da hawayensu tahanyar basu abin dariya". Itama tana dariyar shakuwa takamata rike hannun momy tayi tana"momy....ki dingamin adu'a ..kalmar shahada tayi nan ta rufe idanuwanta tana murmushi . Sanyi kalau momy taji gabantane yafadi ta aika yusif su kira likita aguje,likita yana shigowa yayi gwaje gwajenshi ,rufeta yayi da farin kyallen kan gadon cike da tausayawa ya kalli momy yace"Allah yayi wa Alaweeya rasuwa". Kara momy tasa ta zube awajen sumammiya yayinda siyama tanufi inda gawar Alaweeya yake ta zufe akan gawan kuka take iyakacin karfinta tana"why sister?meyasa zaki mana haka,Alawweeya muna kaunarki.please karki tafi ki barmu a wannan rayuwar .wayyo Allah kulli nafsin za'ikatul maut tabbas haka yake.i cant believe my sister is gone,"sumbatu take tamkar ta tabu daga karshe ta kwanta akasa tana gwaggwara kanta har jini yana zuba. Su yusif ma saikuka suke,mutane sai hakuri suke basu amma siyama tamkar ta haukace tashi ta kankame Alaweeya tana wallahi sai muntafi tare bazan iya rayuwa babu keba"😭😭😭😭😭 INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN Allah yayiwa Alaweeya rasuwa 😭😭😭😭 🅱k da yarmama suna mika sakon ta'azziyarsu zuwa ga dangin Alaweeya harda yan uwanta. _gaskiya anyi babban rashi,domin Alaweeya macece mai addini,kyautatawa da son jama'a gashi duk inda ta zauna akwaita da saurin sabo da jama'a_ *Alaweeya yarinyace yar shekara 21 yrs a duniya inda ta karanci lawyer ,ita burinta ta saka mutane cikin nishadi,gata da kokari da taimakon jama'a ita tafi dakko halin margayi Alhaji balarabe sak* Kowa ya shaida mutuniyar kirkice _wallahi ko mu da muke typing saida muka zubar da hawaye sosai,domin labarin yanada taba zuciya_ Ubangiji yaji kan Alaweeya yasa Aljannace makomarta Muje zuwa 🅱k😭 Nd Yarmama 😭😭😭(wallahi naji mutuwar Alaweeya wanda har zazzabi sai da nayi,nayi kuka sosai) [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤* STORY & WRITING BY *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* & *MARYAM YARMAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* *MASOYA* _Muna godiya k'warai da addu'o'in ku ga wad'annan bayin Allahn da suka rigamu gidan gaskiya, Allah ya saka muku da alkhairi, kuma ya baku lada._👏 Page 71-75 Haka su mumy suka ci gaba da fuskantar k'alubale na rayuwa. Tukur kuwa facaka kawai yake yi da dukiya, babu ruwan shi da su Mumy da 'ya'yanta. Sai da yakai ya kawo garin kwaki shine abincin su, wata rana ma haka suke zama basu ci komai ba. A haka yunwa ta kama auta shi yai sanadin mutuwarta . Karuwai kuwa abun ba'a magana kullum cikin shigo dasu yake yi cikin gidan. Haka su mumy suka ci gaba da rayuwa, tare da rok'on Allah ya kawo musu k'arshen Tukur, da kuma k'arshen wannan mawuyaciyar rayuwar da suke ciki. Bashi gidan club, bashi wurin shaye-shaye, bashi wajen karuwai ya zab'o wadda tai mishi ya kawo ta cikin gidan nagartaccen mutum Alhaji Bala Wanda har gobe ba'a daina yabon halin shi ba. Tukur ne zaune gaban boka dan duk masihircin mutum me tsafi baza'a kira shi malami ba, yana kora mishi bayani, yace " So nake yaran matar yayan nawa a asirce su ta yanda zasu rik'a tozarta uwar, kuma ya zamana duk abinda na gindaya musu shi zasu yi. Boka ya shek'e da wata mahaukaciyar dariya, sannan yace " in dan wannan ne karka damu kaje gida kasha mamaki." Tun daga wannan ranar ne Tukur yaiwa yaran Mumy asiri, nan da nan suka tsani mahaifiyar su wadda tasha wahalar haihuwar su. Ya zamana duk duniya su Sadeek basu da masoyi sai Tukur, sun k'i Mumy kwata kwata, suka rik'a da mayya. Akwai ranar da Tukur da yaran suke zaune, a falo Mumy tazo wucewa sai jiri ya debeta ta fad'i k'asa, ta d'an bige k'afar Sadeek, ya tashi zai daketa sai Tukur ya hana shi, sannan ya kalleta ya bushe da dariya, ya kalli Sadeek, yace " yanzu kai sai ka daketa uwarka ce fa," Sadeek yace " Allah ya sauwak'e ta zama uwata, mayya ce fa," Tukur ya sake shek'ewa da dariya, sannan yace musu su tashi suje d'akin shi yazo musu da kwalaben giya masu kyau. Bayan sun tafi sai ya kalli Mumy yace " kad'an kika gani, ya tashi ya wuce d'akin shi yana tafiyar 'yan iska yana girgije girgije, yana zuba fito. Tukur ya koya musu shaye-shaye, ta sanadin haka yasa Sadeek ya zama gawurtaccen d'an fashi. Koda aka kama shi aka yanke mishi hukuncin kisa. Ranar Asabar suna zaune a falo Mumy ta shigo cikin falon, kwalbar giya ce a hannun su Sadeek suna kwankwad'a, mumy ta saki salati, Suna had,'a ido da sadeek ya tashi ya gaura mata mari, tare da rufeta da duka, sannan cikin maganar mashaya yace " ba nace ki dena kallona ba, to duk maitar ki kurwata tafi k'arfin ki, mayya kawai." A ranar Mumy tayi kuka kamar ranta zai fita, sai ta mik'a dukkanin lamuranta ga Allah, tare da kai kukanta gare shi tasan yana sane da halin da suke ciki. Haka ya wulak'anta rayuwar yaranta ta hanyar asirin da yai musu, gashi ta sanadin haka ta rasa d'anta an yanke mishi hukuncin kisa. A ranar da labari ya iske su sunyi kuka kamar ransu zai fita. Rasuwar Dadyn su sai ta dawo musu sabuwa. Kuma har yanzu babu alamar nadama a ran Tukur, saima cin duniyar shi yake da tsinke. Ganin burin shi ya cika, komai ya tafi yanda yake so yasa yaje yaiwa boka godiya tare da yi mishi kyauta me tsoka. Ya dawo ya ci gaba da cin Karen shi ba babbaka. Ku biyo mu muje Mune naku *YARMAMA* & *🅱K😘💋* [25/07 23:02] 🅱K😘💋: *🖤🖤ZUCIYAR MUGU🖤🖤* *TRUE LIFE STORY* *END*🔚🔚🔚🔚🔚 STORY & WRITING BY *BILKISU Z. YA'U (🅱K)* *🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S* & *MARYAM YARMAMA* *👨🏻‍💻👩🏻‍💻ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION* *wannan shafin nakune ZAMANI WRITTERS ASSOCIATION TARE DA ZAMAN AMANA WRITTERS.mungode sosai bisa kaunarku we love u all* *Muna yiwa dukkanin masoya godiya, da masu yi mana fatan Alkhairi ta whatsapp, da wad'anda suka kira mu a waya muna godiya Allah saka da alkhairi.* *Kar a manta wannan labarin ya faru da gaske duk abinda ke ciki ba k'age ko k'irk'ira, muna yi wa mamatan Addu'a Allah yai musu rahma, Allah ya k'ara musu hak'urin jure rashi.* Last Page 76-80 ................................... _page d'in jiya munsa Auta ta mutu, to bata mutu ba, muna fatan za'ai mana afuwan kuskuren nan da muka yi_ ................................... Haka Tukur ya ci gaba da cin Karen shi ba babbaka. Mumy da Siyama ne suka dage da Addu'a kullum cikin dare, su yi ta kuka, suna kiran sunayen Allah kyawawa, suna kai k'ara wajen Allah ya saka musu, ya kawo musu k'arshen Tukur. Tukur ne cikin Club d'in su na mashaya tare da wata sabuwar karuwar kuma domin kullum cikin canjin mace yake baya kula mace d'aya kamar wani bunsuru. bayan sun yi raye-rayen su sun shawu, suka fito basu zame ko ina da ita karuwar tashi ba sai gida. Ko da shigar su suka tarar da su momy suna shan garin kwaki. Karuwar shi ta kalle shi, tace " Baby wad'annan kuma su wanene?" Da yake karuwar bata jin hausa, sai Tukur ya canja harshe zuwa turanci yace " wallahi wasu Almajirai ne suke neman taimako nace su jirani in dawo, ya juyo inda su Mumy suke, ya kalli su Mumy sannan cikin harshen hausa yace ba na hanaku zama Ku shantake a cikin falon nan ba? Salon a inzo da bak'i a ganku Ku zubar min da mutunci koh. Ba Wanda ya kula su duk da cewa sun ji abinda ya fad'a wa karuwar tashi cikin harshen turancin. Bayan ya gama bambamin shi ba Wanda ya kula shi yaja karuwar shi suka haye d'akin shi Tun daga ranar su Mumy basu sake zama a falon ba, saboda gudun kar yai musu tijarar da tafi haka, sedai Addu'a basu fasa yi ba kullum cikin yin Addu'a suke yi ba dare ba rana. *BAYAN SATI 'DAYA* Yau laraba, Tukur ne kwance cikin d'akin shi, yana zuba fito ya d'auko giyar ya zauna ya zuba a Kofi ya fara kwankwad'a kenan sai yaga inuwar mutum a gaban shi acikin d'akin. Yana d'aga kai kawai sai yaga Alhaji a gaban shi, ya sake mutsuke idanun shi, sannan ya k'ara dubawa yaga bega kowa ba, se yai dariya, sannan yace " daga fara shahuwata har na fara buguwa. Ya ci gaba da sha, yana d'agowa ya k'ara ganin Alhaji, ya mutsuke ido amma yana nan dai inda ya ganshi, zaro idanu Tukur ya yi, ya fara ja da baya yana ihu, da gudu ya fad'a d'akin bacci ya hau kan gado ya rufe idanu da matashi jikin shi ba inda baya rawa saboda tsabar tsoro. Can bayan wasu lokuta sai ya d'ago kanshi be ga kowa ba, sai ya baje tsakiyar gadon ya fara bacci. Washe gari, sai abinda ya faru jiya yaita dawo mishi, duk da dai ya yi tunanin abinda ya faru jiyan saboda ya yi shaye-shaye ya bugu ne, amma duk da haka haka ya wuni a ranar sukuku kamar ba shi ba. Bayan kwana biyu, Tukur yasha gayu ya had'u saboda wani casu da suka shirya a ranar. Bayan ya gama shiri ba tare da wani b'ata lokaci ba sai ya d'auki hanya, ko da Isar shi gurin 'yan uwansa 'yan iska suka hau ihu suna fad'in " ga babban yaro," suna zuba mishi kirari. An fara casu kenan yana d'aga kai yaga Alhaji tsaye kusa dashi, wani mahaukacin ihu ya saki, ya fita daga wurin taron a guje, suma abokanan shi suka biyo shi da gudu suna tambayar shi lafiya. Yaje zai shiga mota yaga Alhaji zaune cikin motar, haba da gudu ya d'auki hanya duk nisan wajen amma be tsaya ba saida ya isa gida. Haka abokanan shi suka tsaya bakin ti-ti suna mamaki da tambayar anya lafiyar Tukur k'alau kuwa. Haka ya ci gaba da kasancewa duk inda yaje sai yaga Alhaji a gaban shi. Washe gari Tukur ya buga sammako sai gurin boka ya fad'a mishi abinda ke faruwa, fatalwar Alhaji da ta Alaweeya suna ta zuwar mishi. Boka ya bashi wasu layu guda hud'u, sannan ya kalle shi yace " d'aya ka saka a k'abarin Alhaji bazai k'ara zuwa maka ba, d'aya a k'abarin Alaweeya, d'aya ka ajiye a k'asan filon d'akin ka, d'aya kuma wannan me igiyar ka sakata a wuyanka, Ina tabbatar maka daga yau bazaka sake ganin su ba. Bayan Tukur ya gama aiwatar da duk abinda boka yace mishi ya sami me gadin mak'abartar da aka birne su ya bashi mak'udan kud'i, ya tayashi suka hak'a k'aburburan suka binne, bayan ya gama duk abinda boka ya sa shi. a ranar da aka bashi wannan layun ikon Allah kamar ma an k'ara rok'on Allah ne akan ya ci gaba da bayyana mishi su, Dan a wannan ranar sam be runtsa ba. Yanzu a duk inda yake, kuma ko menene yake yi su yake gani, duk ya sukurkuce ya lalace, yanzu Sam beda natsuwa balls wani abu wai shi kwanciyar hankali. Yau Asabar a yau d'in ne kuma cikin dare yai mafarki Alaweeya tazo gaban shi ta tsaya tana kallon shi tace mishi insha Allah nan bada dad'ewa ba shima zai biyo su ya girbi duk abinda ya shuka, tun da ya farka be koma ba har gari ya waye. yana gida yana zaune cikin d'aki yana tunanin mafita, saboda mafarkin da yayi da fatalwar su Alhaji da yake gani sun d'aga mishi hankali, musamman ma mafarkin da yayi jiya ya tsorata shi sosai. Yanzu ya rage fita ma, saboda duk abokanan shi yanzu kallon mahaukaci suke yi mishi, shiyasa duk suka guje mishi. Sai yanzu nadama ta fara zuwa mishi, gadai dukiyar amma sam babu kwanciyar hankalin cin dukiyar. Tunani ya fara akan ya kamata yaje ya rok'i gafarar su Mumy watak'ila idan yai haka su dena fito mishi. Yana cikin wannan tunanin sai ga Alhaji zaune kusa dashi, a guje ya fito daga d'akin nashi, yana fitowa d'akin ya danno falo a guje. Kawai ganin shi su Mumy suka yi cikin falo a guje cikin firgici, ya zube a gaban su, yace " Hajiya dan Allah, ku dubi Allah Ku yafe min, " nan ya kwashe dukkanin irin makircin da ya dad'e yana shuka musu sai da ya fad'a musu komai, da yanda ya sa aka kashe Alhaji da asirin da yaiwa yaranta, babu abinda ya b'oye. Su Mumy babu abinda suke yi banda kuka mumy ta dubesa tana"tukur mun yafe maka,yanzu tsakaninka da ubangijiinka ne . Yusif wanda hawaye yacika a idonsa yace"oh duniya ,yanzu meye ribarka yanzu mu uku muka ragewa mahaifiyarmu ka cucemu tukur". Alhaji da Alaweeya Tukur ya sake gani cikin falon, haba a guje ya tashi ya fita daga gidan gaba d'aya. Yana fita kai tsaye office d'in yan sanda ya wuce a guje. Kawai police ganin Tukur suka yi ya fad'o cikin station d'in a guje, da sauri suka mik'e suka rik'e shi ganin a rud'e yake baya cikin hayyacin shi, suka hau tambayar shi lafiya meke faruwa. Yace musu ya kawo k'arar kanshi ne, nan ya bayyana musu duk irin abubuwan da yayi, yana cikin fad'a musu sai ya sake ganin fatalwar Alhaji kusa da 'yan sandan, nan da nan ya zabura ya fita daga cikin office d'in, yana fitowa yazo dai-dai bakin ti-ti a dai-dai wata tifa ta taho a guje ta kad'e shi, k'afar shi ta cire, idanun shi suka tsiyaye, ko kafin a kaishi asibiti Allah ya d'auki ran shi. su Mumy sun sami labari, sun yi farin ciki sosai, suna godiya ga Allah da ya kawo musu k'arshen Tukur. Jama'ar unguwa kaf sun k'i yi mishi sallah, dole tasa 'yan sanda suka bar shi a asibiti a mutuware. Bayan rasuwar Tukur da wata d'aya aka dawo wa da su Mumy dukiyar su, rayuwar gidan ta dawo normal. Sedai har yanzu kullum sabuwa suke jin mutuwar Alhaji da Alaweeya da Sadeek, kuma a koda yaushe suna yi masu Addu'a. ALHAMDULILLAH *To jama'a wallahi k'arshen zamani yazo, abinda muke jin labari, abinda muke tunanin bazai tab'a faruwa ba wallahi yanzu shi ke faruwa a zahiri, uba ya nemi 'yar cikinsa, d'an uwa yaci amanar d'an uwansa, mun ji yanda zuciyar mugu ta kasance, ya biyewa zuciyar shi ya shirya sharri kala kala, daga k'arshe ya mutu a wulak'ance, zaije can kuma ya fara had'uwa da sakamakon muguntar da ya yi, ina fatan masu mummunan hali ko niyyar shuka sharri irin wannan to wannan labarin zai zama darasi a garesu, Allah ya tsarkake mana zuciyar mu.* *TSOKACI* _I want use this opportunity to thanks my mummy,lokacin da akaa bani labarin nan,wallahi nasha kuka har nakasa barci_ _wai wani irin duniya muke cikine?_ *ku duba irin hallacin da son da Alhaji balarabe ya nuna wa dan uwansa tukur.amma jibi abinda ya sakamai dashi* Oh duniya ina zaki damu gashi shima baa ribar daya ci a duniya,duniya takisa lahirama ta kisa...Allah yasa muguji sharrin zuciya sannan ya sa muyi kyakyawar karshe. sannan Allah ubangiji yaji kan Alaweeya da Alhaji Ameen summa ameen. *SAI KUN JI MU A SABON WANI LABARIN NA DABAN.* Mune naku *YARMAMA* & *🅱K😘💋*