ZUCIYA DA ƘUNA.. By Billy S. Fari & Nana Hadiza @nanadiso10 | Arewabook PAGE 1 Daren Paris ta kasance cikin sanyi mai kaifi a ranar Litinin, iska mai ɗan ƙarfi tana kadawa a kan babban titin Boulevard Périphérique, ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi cunkoso a birnin. Sararin sama ya ɗauki launin toka, gajimare sun lullube hasken rana, yayin da motoci ke tafiya cikin sauri suna ketare juna kamar yadda aka saba a rayuwar birni mai cike da hanzari. Sai dai a wannan safiyar…komai ya sauya. Wani mummunan hatsari ya afku a tsakiyar titin motoci uku sun yi mummunan karo da juna cikin wani irin tashin hankali da ya sa mutane suka tsaya cak. Ƙarar birki, fashewar gilashi, da ihu sun gauraya a lokaci guda, lamarin da ya jefa duk wanda ke wurin cikin firgici. Cikin ‘yan daƙiƙu kaɗan, mutane suka fara taruwa.Wasu suna kiran taimako, wasu suna ƙoƙarin ceto waɗanda ke cikin motocin. Jini ya ɓata titin, hayaniya ta mamaye wurin, yayin da ƙarar siren na motar asibiti ke ƙara kusantowa daga nesa.Ba tare da ɓata lokaci ba, aka fitar da waɗanda hatsarin ya rutsa da su, aka shimfiɗa su cikin gaggawa, aka ɗauke su zuwa Hôpital Européen Georges-Pompidou, ɗaya daga cikin manyan asibitocin Paris. A can ne aka fara gwagwarmayar ceton rayukansu.Likitoci da masu jinya suka shiga aikin gaggawa, kowanne yana ƙoƙarin yin abin da zai iya.Amma… ƙaddara ta riga ta zartar da hukunci. Bayan ɗan lokaci, wata likita ta fito tana kallon mutanen da ke jira. Cikin nutsuwa amma da nauyi a muryarta ta sanar “Sun rasu…” Kalmar ta sauka kamar dutse.Duka Babu wanda ya tsira…sai jariri guda ɗaya.Shi ma yana cikin rauni hannunsa ya samu mummunan rauni, amma yana numfashi. A take aka fara duba wayoyinsu, ana neman wani makusanci…wanda za a sanar. A ɗaya ɓangaren birnin Paris, a unguwar Neuilly-sur-Seine, cikin wani katafaren gida mai cike da alfarma da nutsuwa, shiru ya mamaye ɗakin kwana mai faɗi.Haske mai laushi daga bedside lamp yana ba ɗakin wani irin dumi mai kwanciyar hankali. A kan gadon alfarma…Haroon Kareem na kwance cikin nutsuwa, bacci mai nauyi ya rufe shi, kamar wanda babu damuwa a rayuwarsa. A gefen gadon, wayarsa na ci gaba da ringing…sau ɗaya… sau biyu… sau uku…har ta zarce sau ashirin. A kusa da shi, Fatima na zaune a kan sallayarta. Ta kammala sallah, amma idanunta sun kasa rabuwa da wayar da ke ta haskawa a cikin duhun ɗakin. A hankali ta miƙe.Ta ƙaraso kusa da gadon, ta taɓa shi a hankali.“Haroon… your phone has been ringing since.” Ya motsa a hankali, yana buɗe idanunsa. Cikin kasala ya kai hannu ya ɗauki glass ɗinsa daga gefen gadon, ya saka. Murmushi mai sauƙi ya bayyana a fuskarsa. “Subhanallah… Fatima, you’re still awake?” Ta ɗan yi murmushi, amma cikin murmushin akwai ɓoyayyen ciwo. Ta share ƙananan hawaye da suka taru a gefen idanunta. Haroon ya lura. Cikin tausayi ya shafa kanta. “Fatima… ki daina damun kanki. Haihuwa nufin Allah ne. Mun yi addu’a, mun yi iya ƙoƙarinmu… idan shiru ya zo, to hakan ne mafi alheri a gare mu.” Ya ɗan tsaya. “Please…” Kukanta ya ɗan ƙaru. “Toh… na daina, Habibi…” Ya ɗauki wayarsa. Idanunsa suka sauka a kan screen Umar. Kiran ya shiga sau da dama.Cikin firgici ya miƙe tsaye. Ba tare da ɓata lokaci ba ya kira. A ɗaya ɓangaren aka ɗaga. “Sir… muna bukatarka anan asibiti.” Kalmar ta tsaya a kunnensa. Bai san lokacin da ya ɗauki mukullin mota ba. Fatima ma ta biyo shi a firgice. Suka fito daga gidan cikin gaggawa. “Security..” Da sauri aka kawo masa key. Ya shiga mota.Ba tare da bata lokaci ba suka fice cikin tashin hankali, motar tana yanke titunan Paris cikin gudu. Da suka isa asibitin…cikin ya cika da mutane. Hayaniya,Kuka,Firgici. Haroon bai san lokacin da ƙafafunsa suka kasa ɗaukar shi ba.Hawaye suka zubo. “Umar…?” Aka nuna masa. A can yake. Shi da matarsa…a kwance, Ba numfashi, Ba motsi. Duniya ta tsaya masa.Kuka ya fashe da shi kamar yaro. Fatima ma ta kasa jurewa ta rufe baki tana kuka. “Muyi haƙuri, sir…”muryar likita ta faɗo.v“Akwai jaririnsu… bai rasu ba.” Suka nuna musu ɗaki. Jaririn yana kwance… yana kuka.Hannunsa ɗaya ya ji rauni. Fatima ta yi saurin ƙarasa, ta ɗauke shi cikin hannunta. Kukanta ya ƙaru. Ta kalli jaririn… sai zuciyarta ta karye. Haroon ya tsaya yana kallon su ya rasa abin yi. A rana ɗaya…ya rasa ɗan uwansa. ya rasa matar ɗan uwansa.ya rage sai jariri… wanda bai san komai ba game da duniya. Asibitin Hôpital Européen Georges-Pompidou ya cika da wani irin shiru mai nauyi, irin shiru da ke ɗauke da kuka da ba a furta ba. A cikin corridor mai tsawo, hasken farin wuta yana haskakawa a bango, yayin da ƙarar na’urorin asibiti ke fita a hankali kamar suna bada labarin wani abu da ya riga ya faru. Haroon Kareem ya tsaya a wuri guda kamar wanda aka dasa, idanunsa sun yi ja, hawaye suna sauka ba tare da izini ba. Fatima na tsaye kusa da shi, tana riƙe da jaririn da ya rage ƙaramar rayuwa da ta tsira daga mutuwar da ta shafe komai. Jaririn na kuka a hankali, muryarsa tana raɗaɗi kamar yana jin abin da ya faru duk da cewa bai fahimta ba. Hannunsa ɗaya an ɗaure shi da bandeji, jinin da ya ɗan fito ya bushe a gefen yatsunsa. Fatima ta rungume shi sosai, jikinta yana rawa. “Ya Allah…” ta furta a hankali, “why this child?” Haroon ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, numfashinsa ya yi nauyi. Likita ya ƙaraso kusa da su, ya yi musu magana cikin nutsuwa, “We are sorry for your loss, sir… we tried everything.” Kalmar we tried ta tsaya a zuciyar Haroon kamar wani abu mai sosa rai. Bai amsa ba. Ya ɗan juya, ya ɗauki wayarsa, hannunsa na rawa. Ya fara danna lambobi daya bayan daya. “Hello… Aslam? Please… come to the hospital… something happened.” Bai jira amsa ba ya katse. Wani number ya kira. “Uncle Musa… we lost them…” kalmarsa ta karye. Daga can aka ji ihu. Wani kiran ya shiga. Wani kuma. A cikin mintuna kaɗan, labari ya fara yawo kamar wutar daji. Family, friends, acquaintances… kowa ya fara jin abin da ya faru. A cikin awa ɗaya, asibitin ya fara cika da mutane. Wasu suna kuka, wasu suna girgiza kai, wasu suna tsaye cikin shock. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” kalmar ta mamaye wurin. Fatima ta zauna a kan kujera tana riƙe da jaririn kamar ba za ta sake shi ba har abada. Wata mata ta zo ta ce, “Ki bani shi ki huta…” Amma ta girgiza kai da sauri. “No… I can’t… please…” muryarta ta cika da tsoro. Ta ƙara rungume jaririn, yana kuka yana motsi, kamar yana neman wani abu da ya ɓace. Haroon ya kalli wannan scene, zuciyarsa ta ƙara karyewa. Wannan jariri… ɗan uwansa ne. Jinin su ne. Amma yanzu… shi ne kawai ya rage. Bayan wasu lokuta, aka shirya fitar da gawar. An rufe su cikin farin zanen asibiti. A hankali aka ɗauke su, aka saka su cikin motar gawa. Mutane suka bi motar cikin nutsuwa, wasu suna addu’a, wasu suna kuka. An kai gawar gida a Neuilly-sur-Seine, inda gidan ya riga ya cika da mutane. Maza a waje, mata a ciki. Kuka ya mamaye gidan. “Umar… Umar…” wata murya ta riƙa kira. Fatima ta shigo da jaririn a hannunta, idanunta sun kumbura. Ta zauna a gefe, ba ta shiga hayaniyar kuka ba, amma zuciyarta na fashewa. A ciki, aka fara shirya wankan gawa. Maza suka ɗauki Umar, suka shiga da shi. Ruwa mai ɗumi aka tanada, aka wanke shi cikin tsari na Musulunci, aka sanya masa turare, aka lulluɓe shi da farin likkafani. A ɗaya ɓangaren, mata suka yi wa matarsa wanka, suna kuka a hankali, suna furta kalmomin addu’a. “Allah ya jikanki…” “Allah ya sa aljanna ce makomarki…” Bayan komai ya kammala, aka fito da gawar. Aka shimfiɗa su. Mutane suka tsaya suna kallonsu ba su motsi, ba su magana. Duniya ta ƙare a gare su. Lokaci ya yi na jana’iza. Aka fita zuwa masallaci. A waje, sanyi yana kadawa, iska na busawa, amma babu wanda ya damu. Kowa yana cikin wani yanayi dabam. Aka jera su. Aka yi sallar jana’iza cikin nutsuwa. “Allahu Akbar…” muryar liman ta ɗaga. Mutane suka bi. Kowa yana addu’a a zuciyarsa. Bayan sallah, aka nufi makabarta. Aka haƙa kabari. Aka sauke su a hankali. Aka rufe. Ƙasa ta rufe komai. A gida, Fatima har yanzu tana riƙe da jaririn. Babu wanda ya iya karɓar shi daga hannunta. “Please… leave him with me…” ta faɗa a hankali. Zeynab ta zo kusa da ita. “Sis… ki huta mana…” Amma fatima ta girgiza kai. “No… he needs me…” ta kalli jaririn. “He has no one now…” kalmarta ta fito da rauni. Jaririn ya yi ƙara kaɗan, yana motsa hannunsa da aka ɗaure. Fatima ta ɗan sumbace goshinsa. “It’s okay… I’m here…” _Hmmm wasu labarai ba sa farawa da farin ciki. Suna farawa ne da rauni... ku biyo mu muje ZK2026 08081005693 07040402435. ZUCIYA           DA ƘUNA By Billy S. Fari & Nana Hadiza @nanadiso10 | Arewabook PAGE 2. Washe garin safiyar Paris ta waye cikin wani yanayi mai ɗan sanyi da shiru mai nauyi a unguwar Neuilly-sur-Seine, gidan dangin Haroon Kareem ya cika fal da mutane masu zuwa gaisuwa, motoci suna jere a waje, ana shiga ana fita ba ƙaƙƙautawa, kowa da fuskarsa ɗauke da tausayi da jimami, kowa na magana da murya a ƙasa kamar ana tsoron a ƙara tada wani sabon ciwo, a tsakiyar wannan taron ne jaririn da bai wuce kwana biyu da haihuwa ba ya zama abin kallon kowa, mutane na kallonsa da tausayi, wasu na girgiza kai suna cewa “Subhanallah… yaro ƙarami haka ya rasa iyayensa” wasu kuma na share hawaye suna furta “Allah ya raya shi cikin alkhairi” amma duk da wannan taron da wannan hayaniya mai sanyi, akwai wani abu da ya fi ɗaukar hankali Fatima, wacce tun jiya bata samu nutsuwa ba ko da minti ɗaya, idanunta sun kumbura, kanta na mata ciwo, zuciyarta cike take da wani irin tsoro da ba ta iya bayyana shi ba, haroon ya yi ƙoƙarin janyo ta su koma gida domin ta huta amma cikin kuka ta ce “No… I’m not going anywhere… ni da baby zamu kwana anan” ya kalleta cikin natsuwa ya san hakan zai faru, tun daga daren jiya ya riga ya yanke shawara a ransa cewa wannan yaron nasa ne har abada, ba zai bari wani ya shiga tsakani ba, ba zai bari wani ya ɗauke shi ba, saboda haka bai ƙara mata gardama ba sai dai ya ɗan shafa kanta a hankali yana cewa “It’s okay… I understand” dare ya shige, aka siyo madarar jarirai domin a ba shi amma abin mamaki yaron ya ƙi karɓa, yana ta kuka, ihu yana ƙara, kamar yana neman wani abu da ya ɓace masa, hankalin kowa ya tashi, wasu na ƙoƙarin ɗaukar shi, wasu na girgiza kai, amma babu wanda ya iya kwantar da shi, Fatima kuwa ta rungume shi kamar zuciyarta zata fita, ta ƙi bacci, ta ƙi zama, tana tafiya da shi a hannu tana lallashinsa “please baby… please calm down… I’m here…” amma yaron bai daina ba, sai da safe ya waye cikin wannan hali, a cikin wannan taron ne Zeynab, ƙanwarsu Haroon amma ba uwa ɗaya ba, Mahaifin su ne ɗaya. ta tsaya tana kallon Fatima da yaron, sannan cikin ɗan ɗaga murya ta ce “Sis… banda abunki fa, ina ke ina raino? You’ve never had a baby before…” kalmarta ta fito da ɗan zafi, wanda ya sa wasu suka juya suna kallonta, kafin Fatima ta ce wani abu, kakarsu Haroon Dada tsohuwa mai hikima da nutsuwa ta ɗago kai daga inda take zaune tana cewa “Zeynab… ki kiyaye bakinki, idan ba za ki godewa Fatima ba, to kar ki ƙara mata ciwo” Zeynab ta yi murmushi mai ɗauke da raini tana cewa “Grandy… you know me now, ai ni zan kula da yaron nan, ko ba haka ba?” kalmar ta faɗi da sauƙi amma ta sauka da nauyi a zuciyar Fatima, gabanta ya faɗi, zuciyarta ta ɗan buga, amma ta yi shiru, ta ƙara rungume yaron kawai, ta miƙe ta nufi babban falon gidan inda mata ke zaune, mahaifiyar matar Umar ce ke zaune tana karɓar gaisuwa, tana kuka lokaci-lokaci, Fatima ta ƙarasa kusa da ita, ta zauna, matar ta ɗago ta kalleta cikin tausayi “Sannu Fatima… Allah ya saka miki da alkhairi” wasu matan suka fara magana a gefe “Allah mai iko… ashe ita ce zata raini yaron” wata ta ce “To ai ba ta taɓa haihuwa ba…” wata kuma ta ce “Dada ce ta fi dacewa da shi” kafin hayaniyar ta ƙaru, mahaifiyar matar Umar ta ɗaga murya cikin ƙarfi “Ku daina magana haka Babu wanda ya cancanci zama uwarsa sama da Fatima” shiru ya sauka na ɗan lokaci, amma wata tsohuwa a gefe ta sake cewa “Haba… yaro fa yana buƙatar wanda ya san raino…” kalmomin suna shiga kunnen Fatima kamar allura, amma bata ce komai ba, ta yi shiru kamar yadda take yi, sai ƙarar wayarta ya katse komai, ta duba, saƙo daga Haroon “Come upstairs… Aslam room” ta miƙe a hankali, jikinta ba ƙarfi, idanunta sun yi nauyi, zuciyarta cike take da damuwa, tana tafiya har ta isa matakala, kafin ta hau sai ga Zeynab ta biyo ta “Fatima… yakamata ki sauko da yaron nan, people want to see him… kin ɗauke shi kamar naki ne” kalmar ta sake soka mata zuciya, cikin ƙarfin hali ta ce “To…” ta miƙa yaron ba tare da ta kalle ta ba, ta juya ta haura sama, hawaye na zuba a idonta, zuciyarta na raɗaɗi, tana shiga ɗakin da aka nuna mata, ta tarar da Haroon zaune a kan kujera, jikin sa ɗan sanyi, fuskar sa ta nuna gajiya, bai faɗa mata ba cewa an yi masa allura saboda zazzabi, ya san idan ta sani hankalinta zai ƙara tashi, da ta gan shi, sai ta garzaya ta rungume shi, kuka ya ƙwace mata “Ils ne veulent pas me donner le bébé… Zeynab keeps talking… Haroon please… he’s my baby… I love him… I will take care of him… please…” ta riƙa magana cikin harshen Faransanci tana kuka kamar zata fadi, Haroon ya riƙe ta a hankali yana shafa bayanta “Fatima… please… calm down… kina son ki ƙara tashin hankali ne?” ya ɗan ɗaga kanta ya kalle ta cikin ido “Listen to me… yaron nan naki ne… nobody will take him from you… ke ce uwarsa… and you will even choose his name… he has no mother now… you are his mother… do you understand?” ta kalleshi cikin mamaki, idanunta cike da hawaye “Da gaske?” ya ɗaga mata kai “Yes… I promise” sai a lokacin ta ɗan sauke numfashi, zuciyarta ta ɗan samu natsuwa, daga nan ta lura da jikin sa “Are you sick?” ya yi murmushi mai laushi “I’m fine…” amma ba gaskiya ba ne, duk da haka farin cikin da ya shiga zuciyarta ya sa ta manta da komai, har ta yi sujudin godiya a gefen gadon “Alhamdulillah…” Haroon ya kalle ta da tausayi, yana jin yadda take jin wannan yaro kamar nata, a daidai lokacin Aslam ya shigo da abinci, ya ajiye yana cewa “You need to eat bro…” sannan wasu ‘yan uwa suka shigo suna masa gaisuwa “Ya jiki?” “How are you holding up?” Uncle Usman ya zauna kusa da shi yana cewa “Na san dole ka ji zafi… you were very close to Umar” Haroon ya sauke kai, kalmar ta taɓa masa zuciya, kafin yanayin ya koma kuka, Aslam ya yi sauri ya ce “Doctor said no stress please…” Fatima ta miƙe a hankali ta bar ɗakin, ta sauko ta koma kusa da Dada, wacce take son ta sosai, Dada ta ja ta kusa da ita “Zo nan…” ta zuba mata abinci da kanta “Sai kin ci…” Fatima tana cin abincin a hankali, Dada ta ɗago ta kalli Zeynab “Zeynab… ga uwarsa nan… ki kawo mata yaronta” Zeynab ta ji haushi sosai amma bata da wani zaɓi, ta miƙa yaron ba tare da so ba, Fatima ta karɓa da sauri kamar wanda aka ƙwace mata wani abu mai muhimmanci, ta rungume shi “My baby…” ta miƙe da shi ta nufi kitchen “Let me prepare his milk…” duk mutanen da ke wurin suna kallonta, wasu suna jin tausayinta, wasu suna jin mamakin yadda ta haɗu da yaron cikin sauri haka, ta shirya madarar cikin nutsuwa, ta dawo ta zauna, ta fara ba shi a hankali, abin mamaki… yaron ya fara sha, ya yi shiru, kamar ya gane hannun da ke riƙe da shi, kamar ya sami abin da yake nema tun jiya, Fatima ta kalle shi hawaye na sauka amma wannan karon na farin ciki ne “See… he knows me…” bayan ɗan lokaci, bacci ya ɗauke shi, bacci mai nauyi wanda bai samu jiya ba, ita ma ta jingina da kujera, jikinta ya yi sanyi, idonta ya lumshe, kamar karon farko tun jiya da ta samu natsuwa, Dada ta ɗan gyara mata mayafi, mutane suna ci gaba da shigowa suna gaisuwa har zuwa dare, Washegari Fatima na zaune a gefen falon tana riƙe da jaririn da ya yi bacci a jikinta, fuskar ta ɗan samu natsuwa bayan dogon kuka da wahala, hannunta na shafa kansa a hankali kamar tana jin tsoron wani ya zo ya kwace shi, Dada na zaune kusa da ita tana kallonta cikin tausayi, amma daga ɗayan ɓangaren falon Zeynab na tsaye tana kallon su da wani irin ido mai cike da rashin jituwa, zuciyarta ba ta kwanta ba tun da aka ce Fatima ce zata riƙe yaron, duk da murmushin da take yi a gaban mutane, a cikin ranta akwai wata wuta mai zafi, tana jin kamar an ƙwace mata wani abu da ya kamata nata ne, sai ta juya ta nufi inda Fatima take zaune, mutane suka ɗan yi shiru suna kallon ta, saboda sun riga sun lura da yanayinta, ta tsaya a gabanta tana kallon jaririn sannan ta ce cikin murya mai ɗan sanyi amma mai tsini, “So… yanzu ke ce uwarsa kenan?” Fatima ta ɗago idanunta a hankali, ba ta amsa ba, sai ta ƙara rungume jaririn, hakan ya ƙara ɓata ran Zeynab, ta ɗan yi dariya kaɗan tana cewa, “Interesting… very interesting… mace da ba ta taɓa haihuwa ba suddenly ta zama mother overnight,” wasu daga cikin matan suka fara kallon juna, Dada ta ɗan motsa amma bata yi magana ba tukuna, Fatima ta sauke idanunta tana ƙoƙarin kaucewa rikici, amma Zeynab ba ta tsaya ba, ta ƙara matsowa kusa da ita, “You think it’s easy? Kina ganin raino wasa ne? Do you even know what you’re doing?” muryarta ta ƙara ƙarfi kaɗan, mutane suka fara jin abin da take faɗa, wasu suka fara girgiza kai, Fatima ta ji kalmomin suna shiga zuciyarta kamar wuka, amma ta yi shiru, sai hawaye suka fara taruwa a idonta, Zeynab ta ci gaba, “Wannan yaron yana buƙatar wanda ya san responsibility, ba wanda kawai yake emotional saboda ba shi da haihuwa,” kalmar ta fito da tsauri, wannan karon Fatima ta ɗago kai, idanunta sun cika da hawaye, “Please Zeynab…” ta faɗa a hankali, amma hakan bai sa Zeynab ta tsaya ba, sai ta ɗan sunkuya kusa da ita tana faɗin cikin harshen Turanci mai tsini, “Let’s be honest… you’re just trying to fill a void… right?” wannan kalma ta karya zuciyar Fatima gaba ɗaya, hawaye suka zubo da sauri, jikinta ya fara rawa, ta ƙara rungume jaririn kamar yana kare ta daga duniya, “Stop it…” ta faɗa cikin muryar kuka, amma Zeynab ta sake cewa, “You’re not his mother… and you will never be,” wannan kalmar ita ce ta ƙarshe da ta karya komai, Fatima ta fashe da kuka sosai, kuka mai ƙarfi wanda ya sa kowa a falon ya yi shiru, wasu mata suka fara cewa “Haba…” Dada ta ɗaga hannu tare da ɗaga murya cikin ƙarfi, “Zeynab” amma kafin wani abu ya faru, ƙofar falon ta buɗe da ƙarfi, Haroon ya shigo, idanunsa sun sauka kai tsaye a kan Fatima da ke kuka da kuma Zeynab da ke tsaye a gabanta, ya tsaya na ɗan lokaci yana kallon scene ɗin, zuciyarsa ta ɗan buga, sannan cikin murya mai ƙarfi ya ce, “What is going on here?” shiru ya sauka, babu wanda ya amsa, Fatima ta ci gaba da kuka, hakan ya ishe shi fahimta, ya juya ya kalli Zeynab, idanunsa sun canza, “Zeynab… what did you say to her?” ta ɗan ɗaga kai tana ƙoƙarin nuna ƙarfi, “I was just telling the truth” kafin ta gama magana, ya matsa kusa da ita cikin sauri, hannunsa ya ɗaga slap! sautin ya cika falon, mutane suka yi shiru gaba ɗaya, Zeynab ta dafe kunci cikin mamaki, ba ta taɓa tsammanin hakan ba, idonta ya cika da hawaye, amma ba saboda ciwo ba… saboda kunya, Haroon ya nuna mata hannu cikin fushi, “Don’t you ever… ever talk to my wife like that again!” muryarsa ta girgiza falon, “Do you hear me?” ta kasa magana, ta ɗaga kai kawai, hawaye na sauka, “You crossed the line, Zeynab… you went too far,” ya juya ya kalli mutane, “From today… you stay away from my wife and my son… do you understand?” kalmar my son ta fito da ƙarfi, ya jaddada ta da nufi, Dada ta ɗan lumshe idanu tana jin daɗin yadda ya tsaya tsayin daka, wasu daga cikin mutanen suka girgiza kai suna goyon baya, Zeynab ta juya da sauri ta fita daga falon cikin kuka, tana jin kamar duniya ta rushe mata, Haroon ya juya ya nufi Fatima, ya zauna kusa da ita, ya riƙe hannunta, “Hey… look at me…” amma ta kasa ɗaga kai, kuka ya rufe ta gaba ɗaya, ya ɗan matsa kusa da ita ya rungume ta, “I’m here… nobody will hurt you… not anymore,” ya ɗan ɗago fuskarta da hannunsa, hawaye sun ɓata mata fuska, “You are his mother… and nobody… nobody will take that from you,” ta kalle shi cikin rauni, “Really?” ya ɗaga mata kai, “Yes… I promise you,” ta ƙara rungume shi, kuka yana raguwa a hankali, jaririn a hannunta ya motsa kaɗan kamar yana jin yanayin, Dada ta matsa kusa da su tana cewa cikin nutsuwa, “Komai ya wuce… ki kwantar da hankalinki,” falon ya fara dawowa da hayaniya a hankali, amma wannan karon kowa ya san wani abu ya canza, wani layi ya ja… wanda ba za a sake ketarawa ba, kuma a cikin wannan dare, Fatima ta fahimci abu ɗaya ba kowa ne ke son farin cikinta ba… kuma ba kowa ne zai iya tausayinka acikin yanayin da kake ciki ba don haka dole tasan cewa ba kowa bane abun yarda... _Sau da dama namiji kan taka rawar gani wajen shamakance iyalansa ga wata aibantawa daga wajen yan uwansa don gina mutuntakarsu a zuciyarsu, shin kuna ganin abinda HAROON yai yayi daidai kuwa?_ BZ2026 08081005693 07040402435. ZUCIYA DA ƘUNA By Billy S. Fari & Nana Hadiza @nanadiso10 | Arewabook PAGE 3. Da kuka Zeynab ta nufi ɓangaren mahaifiyar dake can zaune ita da wasu mutan suna tayata amsar gaisuwa, Mémé dake zaune tana jan charbi ta ji sautin kukan ƴar tata tun daga can farkon shigowa ɓangaren nasu “Zainy” ta kira sunanta, da yake haka take kiranta saboda soyayyar da take yi mata tun lokacin data haifeta, Mémé tana da lalurar idanuwa bata gani tun shekaru uku da suka wuce, tana tsananin kaunar Zeynab saboda gaba ɗaya halinta ta ɗauko, saɓanin ƙanenta Aslam dake da wata irin zuciya mai sanyi tamkar Haroon, wanda hakan yasa ako yaushe cikin hantararsa take saboda sam baya yi mata biyayya ga duk wani abu daya san cutarwa ne ga mahaifinsu daya rasu ko kuma yan uwan nasa da Mahaifiyarsu daya ɗauka tamkar tasa mahaifiyar, ganin har lokacin Zeynab bata ƙaraso ba sai ƙarar sautin kukan nata da kunnuwanta ke jiyo mata yasa tafara lalubar sandarta da take amfani da ita tana kokarin miƙewa tsaye, wuɗan da ke cikin ɗakin ne ɗaya daga cikinsu ta taso ta riƙata sai ga Zeynab ɗin ta shigo ɗakin, tana zuwa ta faɗa mata a jiki, Mémé ta samu daƙyar ta koma ta zauna mazauninta tana laluben fuskar ta Zeynab “dama nasan wannan taron baza'a watsesa lafiya ba sai anyi ɗibar albarka, yi shiru Zainy ki faɗamun wane munafikin Allah ne ya taɓa ki, su ko zafin mutuwar nan bai ishesu zama aya ba? Waye ya taɓaki faɗamun baki” “Mémé Haroon ne, wai daga ɗai nace ina so a bani jaririn na riƙe shine Haroon da Dada suka zazzageni wai matarsa za'a bawa, shine don na faɗi gaskiya ya Haroon ya mareni.” Hankali a tashe Mémé tafara ƙoƙarin sake tashi a karo na biyu “Dama nasan zasu aikata, tunda su da akaiwa mutuwar bata dame su ba sukai haka ni bazan ki tafiya nabi miki haƙƙinki ba, da aurenki ace ya ɗaga hannu ya dakar min ke daga kin nuna masu kara wannan ɗibar albarka har inaa, to bazan lamunta ba ina zuwa." wannan karon har bakin ƙofa sai da Mémé ta kusa kaiwa sannan akayi nasarar dakatar da ita ana bata hakuri, ba tare data damu da yanayin jimamin da ake ciki ba tayita masifa har sai da sautin muryarta ya kai a can ta ɗaya ɓangaren, ita dai Dada bata san meke faruwa ba sai da yan tsirko suka zo suka sanar da ita, ta bi zancen da "Allah ya kyauta kawai". dama tasan sai hakan ta faru. Sosai Mémé ta nuna ɓacin ranta tace Zeynab ta kyalesu kada ta sake komawa ɓangaren idan sunga dama sukai jaririn gidan marayu tunda sun fifita bare akan yar uwar ubansa ta jini, wato Fatima ce bare ba tare da sunyi la'akari da mijinta da shine mafi kusanci da Umar ba. Haka dai ranar Mémé tayita zabgar faɗa abunka da marar gani har dare yayi, ita ko Zeynab bata koma ɓangaren ba sai dai duk wanda ke son yimata gaisuwa ya sameta a can ɓangaren nasu, sosai hakan ya jawo ƙananun maganganu da yawa kasancewar family ɗin nasu babban family ne, wasu suna ganin ba'a kyautawa Zeynab ba musamman wuɗanda basu san yadda abun ya faruba, wasu kuma suna ganin koma meye abinda Mémé ɗin tayi ita da yarta basu kyauta ba, Ganin abinda ya faru yasa da daddare Haroon ya kira Fatima yace tafito su wuce gida sai gobe su dawo tunda unguwa ɗaya ne, Fatima bata so hakan ba saboda jiya anan suka kwana taso sai anyi addu'a gobe sai su koma gidansu, Dada ce ta lallasheta saboda tayi magana da Haroon ɗin akan abinda ya faru, bata son bayan idonta yan uwan nasa su saje su yaɓawa Fatima magana kamar yadda shima Haroon ke gudun faruwar haka wanda shine dalilinsa nadin su koma gida, sai da Dada ta nunawa Fatima ai da jaririn zata tafi sannan ta samu natsuwar tafiya ɗin. A cikin mota daga ita har Haroon Babu wanda yai magana har suka iso gidansu, kai tsaye sashenta ta wuce shima ya nufi nashi sashen, jaririn ta yiwa wanka ta yi masa shirin kwanciya sannan ta fito ta nufi sashen Haroon, ko data shiga ta samu yana wanka, bakin gadon Fatima ta zauna tayi shiru tana nazarin rayuwar duniya, tabbas ɗan adam ba abakin komai yake ba, babu abinda ya dawo mata a lokacin sai kalaman Yasmina wato mahaifiyar jaririn, shekaran jiya ranar data haihu da suka je dubata bayan an sallamosu daga asibitin tana cikin jin ɗan yanayin da kowace mai haihuwa ke tsintar kanta acikin bayan ta haihu, rungume take da jaririnta tace "Ukty na yimiki addu'a kema Allah ya nuna mana irin wannan ranar, duk da dai ina kallon wannan yaron kuma danku ne ba ɗanmu ba mu kadai, yaronku ne, zaku yi masa duk wata tarbiya ku kuma hukuntasa kamar yadda zamuyi masa, ina so ya zama ya taso ba tare daya iya banbanta tsakanin mu daku su waye iyayensa ba, ina fatar kema zaki saka hakan a ranki yar uwa ta yadda za mu taru gaba daya mu bashi kulawa?" Hawaye ne suka sake zubowa Fatima a fuska, kalaman sun tsaya mata a zuciya, sun dawo mata da wani zafi da raɗaɗi, Yasmina ta faɗi maganganu da dama a ranar kamar tasan tafiya zatayi tabar jaririnta, idanuwanka ta ɗaga sama tana sake ƙoƙarin shanye hawayen dake faman tsere akan fuskarta tare da rungume jaririn sosai a jikinta wani kukan na sake zo mata, a hankali ta ji saukar lausassun hannuwan Haroon ta bayanta ya zagayo dasu ta cikinta ya rungumeta tsam a jikinsa, ya azo fuskarsa ta jikin wuyanta shima idanuwansa na a rufe tare da sauke lallausar ajiyar zuciya da tayi daidai da lokacin da itama Fatima ta sauke tata ajiyar zuciyar, shi kaɗai yasan me yake ji a zuciyarsa na rashin ɗan uwan nasa mafi kusanci dashi da suka fito ciki ɗaya, yasan yanzu shi kenan baida wani abokin shawara daya rage masa aduniya da idan ya bashi shawara zai samu natsuwa da suka fito ciki ɗaya, dama-dama Aslam, duk da zamowarsa ƙarami da uba ɗaya suka haɗa yana da hankali sosai, saɓanin Zeynab da bai san me yake damunta ba, itace Yayar Aslam da suka fito ciki ɗaya dashi, sai dai ita sam bata ƙaunar abinda zai haifar da zaman lafiya a tsakaninsu, jinsa yake yi tamkar fanko tun ranar daya rasa Umar da matarsa, Ƙanƙame Fatima ya sake yi yana sake shigar da kansa cikin wuyanta alamun rauni, Fatima da idanuwanta ke rufe ta ɗaga hannunta ɗaya ta ɗora saman kan Haroon alamun calming ɗinsa tana sake ƙankame jaririn da daya hannun da take dauke dashi a jikinta, zuciyarta a karye take matuƙa tunawa da kalaman Yasmima, amma a yanzu tana buƙatar ƙwarin guiwa da karfafawa don cika burin mahaifiyar jaririn dake hannunta da sukai tsaftataccen zama da ita, Haroon shine ƙarfinta da komai ma, gashi shi kuma yana ƙoƙarin gazawa, ta sani rauninsa na ƙaruwa ne akoda yaushe idan tana cikin damuwa saboda haka dole zata yaƙi zuciyarta a daidai wannan gaɓar saboda Haroon, ajiyar zuciya ta sake yi sannan tayi kokarin furta kalaman dake cikin bakinta “Ta rayu tsakanin haihuwarsa har zuwa lokacin da ta Allah ta faru akansu cike da yaƙinin zamu bashi kulawa tamkar su, shin kana ganin anya zamu iya? Zamu bashi kulawa da soyayya tamkar su alhalin tun yanzu ina jin kamar mun fara gazawa musamman daga wajena dana kasa shayar dashi tun jiya da yake ta faman kuma sai dai aka bashi madara, ko dai haƙura zan yi abawa Zeynab ɗin shi kaga ita...” bata ƙarasa ba Haroon yai saurin sumbatar wuyanta don dakatar da ita daga faɗar abinda take son faɗa sannan yace “Wannan sam ba gazawa bace Fatima, idan har Umar da Yasmina suna jin cewa zamu ɗauki ɗansu da suka haifa tamkar namu ne mu bashi kulawa da tarbiyya tun suna da rai ba tare da sun san mutuwa zata raba su ba to mune muka fi cancanta da muji hakan a ranmu saboda mun fi su sanin kanmu, Saboda haka zamu kula dashi zamu kuma bashi tarbiya iya ƙarfinmu, amma kafin nan ina so kisa a ranki cewa a yanzu ke uwace da zata iya bawa ɗanta kulawa ta kowace irin fuska, wannan tunanin da ake dashi akanki na baza ki iya ba dole ki sauya shi izuwa zaki iya, wadannan kalaman da akayi amfani dasu dan raunana ki kina bukatar ki sarrafa su wajen bawa kanki ƙwarin guiwa, ba wannan jaririn kaɗai ba dake gabanmu hatta ni Haroon a yanzu kece karfina wajen tabbatarwa da duniya ni ɗin ko waye a wajensa, pls Fatima..” kasa ƙarasawa yai jin yadda ta juyo ta sumbaci fuskarsa, cikin wata murya mai sanyi tace “Zanyi hakan Haroon matukar baza ku raba ni dashi ba koda na gaza ta wani gun, zan cike masa duk wani giɓi a rayuwa na kuma tsaya a kowane tudu da gangare da rayuwa zata zo masa dashi, in sha Allah nayi alkawarin zai same ni agun domin bashi kariya.” Cikin jin daɗin kalamanta Haroon ya juyo da ita duka suna fuskantar juna "Na sani zakiyi fiye da abinda bakinki ya faɗa Fatima, burina kawai Allah ya raya mana shi cikin aminci." ya kamo fuskarta ya sumbata, cikin idanuwanta yake kallo yana ƙoƙarin tabbatar mata da abinda ya faɗa, Fatima ta sauke kanta kasa tana jin gaba-daya jikinta yai sanyi, amma a zuciyarta wani kwarin guiwa take ji tamkar kafaffen dutsin daya jima acikin ƙasa na tsawon shekaru, ta ɗauri aniyar fara sabuwar tafiyarta cike da karfin zuciya da kuma kyakkyawar manufa ba tare da gudu ko ja da baya ba, hakan da tayi yasa Haroon sakin murmushin da iya karsa fuska dan zuciyarsa cike take da mikin da baza ta bashi damar yin hakan ba acikinta, riƙo hannunta ɗaya yai, ɗaya hannun nasa ya ɗora akan jaririn dake cike da suma yana shafawa a hankali sai baccinsa yake yi abinsa "Uwa da ɗanta babu mai raba su sai Allah, in sha Allah gobe idan akai addu'ar uku zanyi magana da Dr. Sofiane (Sufyan) idan akwai magungunan daya kamata kisha ruwan mama su zo ko allurai duka sai abaki ki riƙa shayar dashi da kanki tunda bakya son madarar, ina hakan yayi miki ko?" Da “Eh” Fatima ta amsa tana jin wani farin ciki na lulluɓe mata zuciya, ta ɗago kanta tana kallonsa da idanuwanta masu nuna tsantsar farincikin da take ciki, irin annurin da fuskarta ke fitarwa yasa Haroon tana kokarin buɗe baki tayi masa godiya ya ɗora yatsansa akan laɓɓanta da akullum yake jinsu tamkar auduga saboda taushinsu yana ƙare mata kallo cikin idanuwa, tasan me yake nufi dan haka bata ce komai ba sai ɗan zamewa da tai a hankali ta sake matsowa kusa dashi sosai ta shige jikinsa haɗe da ɗora kanta a saman faffaɗan ƙirjinsa, Haroon tamkar jiraye yake da hakan yasa hannayensa biyu ya rungumeta tsam yana kallon jaririn da har lokacin take rungume da shi ta kasa ajewa tamkar wacce za'a kwacewa shi. “A duk lokacin da nake tare da ke, duniya tana zama tamkar gida na lafiya da soyayya Fatima, nafaɗa maki gaskiya?” Fatima ta ɗaga masa kai ba tare data ce komai ba saboda yadda take sauraren bugun zuciyarsa da suka haɗe da kalaman dake fitowa daga bakinsa suka tashi wasu baituka tamkar waƙa suka saukar mata da natsuwa a zuciya, wata duniya take jinta ta daban gajimare na yawo da ita, ji tai ya ɗago fuskarta ya sumbaci bakinta “You're my comfort zone Princesse.” Murmushi ya ƙwace mata da sauri ta sake shigar da kanta cikin faffaɗan ƙirjin nasa cike da jin daɗi da farin ciki, mutsumutsun data soma jin jaririn nayi da ƙananun kuka ya sata saurin janye jikinta, ta sauka kan gadon ta miƙe ta ɗorasa a saman kafadarta tana ɗan bubbuga bayansa haɗe da kaiwa da komowa a tsakiyar ɗakin alamun lallashi, shi kuma Haroon ya ɗan yi baya kaɗan ya kwanta ya ɗora kansa a jikin pillow dake jikin kan gadon yana kallonta, sosai tayi masa kyau da zama uwa shi kan shi sai yake jinsa tamkar wani sabon mutum da aka sake halittawa a duniyar wuɗan dake amsa sunan iyaye. Fatima tafi minti ashirin tana abu ɗaya kafin ta samu jaririn ya koma baccin da yai ta ƙananun kuka, tare suka sauke ajiyar zuciya ita da shi jin ya yi bacci, Haroon ya taso ya miƙa mata hannu alamun zai karɓi jaririn, tamkar ƙwai haka suka lallaɓa tare suka ajiye sa a tsakiyar gadon, Fatima takai hannu ta rage ƙarfin gudun A.C ɗakin sannan ta ɗan zame tana ƙokarin kwantawa, riƙota Haroon yai ta juyo tana kallon shi, lumshe ido yai ya buɗe su akanta, baki ya buɗe zai yi magana tai saurin rufe masa bakin tana zaro masa idanuwa mai mai jin tsoron wani abu dake shirin faruwa da ita, da ido yai mata alamar tambaya Meye? ta marairaice fuska tana kallon jaririn, ya fahimci me take nufi, tsakiyar tafin hannun nata data rufe bakinsa dashi ya ɗan ciza ba tare data ankare ba da sauri ta sake masa bakin tana yarfi da hannun, ta cikin kunnenta ya rada mata magana “Tunda kin gama da ɗanki kizo ki shimfiɗeni bacci nake ji nima ko na saka miki rigima." Harara ta maka masa da wasa tana ɗan haɗe fuska, ya langaɓe kai irin yadda yara keyi shima, Fatima ta buɗe masa hannayenta tamkar mai yi masa oyoyo a hankali Haroon yazo ya shige hukunta yana sauke ajiyar zuciya, a haka ta jashi suka kwanta Haroon na sake jinta cikin ransa tamkar jini da anta, jikinta ya sake shigewa ita kuma ta shiga tofa masa addu'a rabin tunaninta kuma ya tafi wata duniyar. A haka ta samu shima Haroon ɗin yai bacci ta miƙe da kyar tana sake gyarawa jaririn kwanciyarsa sannan ta shige toilet ta yo wanka ta ɗoro alwala ganin kusan karfe biyu har da wani abu na dare yayi, tana fitowa tayi yan abubuwan data saba yi na kula da jikinta don macece ita mai son gyaran jiki da kulawa da kanta yadda yakamata, shiyasa idan ka ganta baza ka taɓa yadda tayi shekarun da take dasu ba. Kamar dai kullum Fatima sallah ta tayar tana miƙawa Allah kukanta, duk da yau adduoin nata sun sha banban dana kullum, a yanzu ba haihuwa kaɗai take buƙata ba ta fahimci har ƙwarin guiwar reno tana buƙata dan bawa maraɗa kunya. _Awwwn Haroon da alama fa kai da ɗan naka rasa wa Fatima zata kula dashi za’a yi, shin kuna ganin Haroon da Fatima zasu iya cika mafarkin Yasmina akan ɗanta kuwa?_ ZK2026 08081005693 07040402435. ZUCIYA DA ƘUNA By Billy S. Fari & Nana Hadiza @nanadiso10 | Arewabook PAGE 4. Bayan kwanaki uku na jimami da addu’o’i, gidansu Haroon Kareem ya sake cika da mutane, amma wannan karon ba kuka ba ne ya mamaye shi gaba ɗaya akwai haɗuwar yanayi na tausayi da kuma wani sabon abu da ke neman bayyana, rana ce mai ɗan haske a Paris, iska mai sanyi tana shigowa ta cikin manyan tagogin gidan, lambun waje ya yi shiru kamar yana sauraron abin da ke faruwa a cikin gidan, a falon da aka kawata da kayan alfarma, iyalai da ‘yan uwa sun taru domin addu’ar uku, kowa ya zauna cikin nutsuwa, ana karanta addu’o’i cikin sanyin murya, ana ambaton sunan Allah, ana roƙon rahama ga mamatan, amma bayan kammala addu’ar ne komai ya sauya, saboda wannan shine lokacin da aka tabbatar da makomar jaririn, kalamai suka fara fitowa daga bangarori daban-daban, wasu cikin ladabi, wasu kuma cikin fushi mahaifiyar zeynab wato meme ta ɗaga murya tana cewa “Ya kamata a ba mu yaron nan… mu ne iyayensa” kalmarta ta fito da Zafi, Zeynab ta goyi bayanta cikin sauri “Exactly… it’s only right” mutane suka fara kallon juna, hayaniya ta fara tashi, wasu suna goyon bayan su, wasu kuma suna kallon Fatima da tausayi, Fatima na zaune a gefe tana riƙe da jaririn, zuciyarta na bugawa, hannunta ya ƙara matse shi kamar tana tsoron wani ya zo ya kwace shi, kafin rigimar ta ƙara tsananta, Haroon ya miƙe tsaye, muryarsa ta fito da ƙarfi amma cikin nutsuwa “Enough.” shiru ya sauka, ya kalli kowa ɗaya bayan ɗaya, sannan ya ce “Yaron nan zai zauna da mu… with my wife” ya jaddada kalmar my wife kamar yana son ya sa kowa ya fahimta, Uncle Usman ya ɗaga murya yana goyon baya “Haka ne… wannan shi ne mafi dacewa” wasu daga cikin dattawa suka girgiza kai suna amincewa, Meme ta yi ƙoƙarin sake magana amma Dada ta katse ta “An riga an yanke hukunci” kalmar ta tsaya a sarari, daga nan aka juya zuwa batun suna, Haroon ya ɗan sauke numfashi kafin ya ce “Sunansa Umar… sunan mahaifinsa” kalmar ta sauka da wani irin nauyi, wasu suka yi shiru suna jin zafin ambaton sunan, Fatima ta ɗago idanunta tana kallon jaririn, hawaye na sauka amma wannan karon ba kuka ba ne na baƙin ciki wani irin motsin zuciya ne mai haɗe da soyayya, ta ɗan murmusa a hankali “Amma… zan riƙa kiransa Rayyan…” kalmar ta fito da laushi kamar lullubi, wasu suka yi murmushi, wasu suka yi gulma a ƙasa ƙasa, “Rayyan kuma?” “Hmm…” amma Dada ta ce cikin nutsuwa “Suna ne mai kyau” daga nan hayaniyar ta ragu, iyayen Fatima da suka zo daga waje suka zo suka rungume ta, mahaifinta ya ce “Mun gode Allah…Allah ya baki lada” mahaifiyarta ta shafa kanta tana cewa “Allah ya sa albarka” Fatima ta ji zuciyarta ta cika da wani irin farin ciki da ba ta taɓa ji ba a rayuwarta, ta kalli jaririn Rayyan… ta faɗa a zuciyarta, kamar tana ɗaukar sabon numfashi na rayuwa, duk ranar suka yini cikin wannan yanayi, mutane suna zuwa suna gaisuwa, wasu suna ɗaukar yaron suna kallonsa, amma duk lokacin da aka ba shi wani, Fatima na jin kamar an cire wani ɓangare na zuciyarta, sai ta karɓe shi da sauri, tana murmushi tana cewa “He likes me better…” Dada ta dinga kallonta tana murmushi, tana cewa “Kin zama uwa kenan” Didi kuwa tana tsokanarta “See you… now you’re a full mom”. Fatima ta riga ta zama uwa, ba da haihuwa ba, amma da zuciya, da dare ya sauka, gidan ya yi shiru, mutane sun watse, fitilu sun ragu, sai ƙananan haske a gefuna, Haroon ya zo kusa da Fatima ya ce “Let’s go… we need to see the doctor” ta ɗago kai “Now?” ya ɗaga mata kai “Yes” ta miƙe da sauri, ta yi sallama da Dada, ta ɗauki Rayyan, suka fita cikin sanyi na daren Paris, motar ta ja cikin nutsuwa, tituna sun yi shiru, fitilun titi suna kyalli, suna isa asibitin, suka shiga, aka kai su wajen Dr. Sufyan, likita mai nutsuwa da professional attitude, ya kalle su da murmushi “Good evening… please have a seat” Fatima ta zauna tana riƙe da Rayyan kamar ba za ta sake shi ba, Haroon ya fara magana “Doctor… we want to ask about feeding… she wants to breastfeed him” Dr. Sufyan ya ɗan gyara zama, ya kalli Fatima cikin kulawa “That’s very good… it’s actually possible in some cases” Fatima ta ɗan matsa gaba “Really?” ya ɗaga kai “Yes… what we call induced lactation… with proper medication and stimulation, your body can start producing milk” ta kalli Haroon cikin farin ciki, ya ci gaba “I will prescribe some hormonal support medications… you also need to keep the baby close, skin-to-skin contact is very important… it helps bonding and stimulates the process” ya ɗan ɗauki takarda yana rubutu “Also… don’t stress yourself… stress can affect the response” ya ɗan yi murmushi “And if it doesn’t work immediately, don’t worry… we have formula options very high quality ones” ya nuna musu jerin sunaye “These brands are safe and recommended” Fatima ta girgiza kai cikin jin daɗi “Thank you so much doctor” suka tashi suka yi masa godiya, suna fita daga asibitin, sanyi ya bugi fuskarta amma ba ta ji shi ba saboda farin cikin da ke zuciyarta, a cikin mota ta juya ta rungume Haroon “Thank you… thank you so much…” ta maimaita kamar ƙaramar yarinya, ya ɗan yi dariya “It’s okay…” amma ya ji yadda wannan abu yake da muhimmanci a gare ta, daga asibitin, ya juya motar zuwa wani katafaren baby boutique store mai cike da kayan jarirai masu tsada, suna shiga, fitilu masu kyau suna haskaka shelves ɗin da ke cike da kayan alfarma, Fatima ta shiga wani irin yanayi na farin ciki, tana ta ɗaukar kaya “This one… oh and this… and this is so cute…” tana dariya, tana nuna masa, tana jin kamar duniya ta buɗe mata, Haroon na biye da ita yana kallonta da wani irin murmushi, sun sayi kaya masu yawa set na kaya, kayan wasa, baby crib mai kyau, blankets masu laushi, bottles, komai, siyayya ce mai tsada amma babu wanda ya damu, suna dawowa gida, ma’aikata suka shiga shigar da kayan cikin gida, Fatima ta zauna a kan gado tana riƙe da Rayyan, ta cire masa kaya a hankali, ta sa masa sabbi, tana magana da shi a hankali “My baby… my Rayyan…” ta sumbaci goshinsa, ta rungume shi sosai, kamar tana son haɗa rayuwarta da tasa gaba ɗaya, yaron ya yi ƙaramin motsi, ya yi ƙara kamar yana amsa mata, ta yi murmushi, hawaye na farin ciki na sauka a idonta. Rayyan ya girma cikin irin soyayyar da ba kowa ke samu ba a rayuwa, irin soyayyar da idan ka kalla daga nesa zaka rantse cewa jini ne ya haɗa shi da Fatima, ba a taɓa ganin wani bambanci ba, duk motsinsa, duk dariyarsa, duk farin cikinsa Fatima ce a tsakiyar komai, ita ce farkon safe dinsa, ita ce ƙarshen darensa, idan ya farka daga bacci abu na farko da zai faɗa shi ne “Mom…” idan ya dawo daga school abu na farko da zai nema ita ce, ko da kuwa tana cikin kitchen ko a balcony tana kallon hasken birnin Paris, zai garzaya gare ta ya rungume ta “I missed you…” ita kuma zata riƙe shi da kulawa. Gidan su ya zama wuri mai cike da dariya da walwala, musamman a Neuilly-sur-Seine, inda katafaren gidan su ke kallon wani sashi na birnin, lambu mai kyau cike da furanni da aka kawo daga ƙasashe daban-daban, a gefe kuma akwai ƙaramin play area da aka keɓe musamman don Rayyan motoci na yara masu tsada, kekuna kala-kala, electric mini cars, har ma da ƙaramin ATV bike da Haroon ya kawo masa daga wata tafiya zuwa Monaco, duk wannan ba don nuna arziki ba ne kawai, amma don farin cikin yaron da ya zama zuciyar gidan. Iyayen Fatima ma sun tsunduma cikin wannan soyayya, duk lokacin da suka zo daga wajen su, ba sa zuwa hannu wofi, ko dai kayan wasa ne, ko sabbin kaya daga Champs-Élysées, ko wasu custom gifts da aka keɓe masa, mahaifinta kan ce “This boy is special…” mahaifiyarta kuma ta kan rungume shi tana cewa “Allah ya raya mana kai” Rayyan kuwa ya saba da wannan kulawa, amma bai taɓa zama mai girman kai ba, yana da nutsuwa, yana da ladabi, yana girmama kowa, hakan yasa duk wanda ya haɗu da shi zai ji daɗinsa. Amma rayuwa ba ta tsaya a wuri ɗaya ba. A cikin wannan shekarar ne… Fatima ta rasa iyayenta. Labari ya zo kamar guguwa. Wani irin shiru ya mamaye zuciyarta. Duniya ta tsaya mata na ɗan lokaci. Fatima wacce ta saba zama mai ƙarfi, mai murmushi, mai kulawa da kowa… ta shiga wani irin yanayi na damuwa, tana zama shiru, tana kallon sarari, hawaye na sauka ba tare da izini ba, Rayyan ya lura da sauyin, ya kasa fahimtar abin da ke damunta gaba ɗaya, amma ya san abu ɗaya Mom is not okay. Dada ce ta tsaya mata. Ta zama kamar mahaifiya a gare ta. Ta riƙe ta da kalmomi, da addu’a, da kulawa, tana cewa “Rayuwa haka take… amma kina da mu muma watarana haka zamu tafi.” Haroon ya lura da komai, ya ga yadda Fatima ke fama, hakan yasa ya ɗauki wani mataki ya siyawa dada gida a kusa da su, a cikin wani exclusive area na Boulogne-Billancourt, gidan da ke da duk wani abu na alfarma,yayi hakan saboda yadda dada ke son fatima duk da takasance uwa ga matar umar amma sunada alaka ta jini da’ita sosai, yadda take nunawa fatima kauna yasanya yayi mata hakan yawanci Fatima tana gidan Dada ne, saboda can ne take samun nutsuwa. A cikin family ɗin Haroon kuwa… ba kowa ne ke farin ciki da wannan ba. Didi kakar Haroon tun farko bata son Fatima, tana yi mata kallon da bai dace ba, amma daga baya, ganin yadda Haroon ya tsaya tsayin daka a kanta, sai ta ja baya, ta rage tsangwama, amma hakan bai nufin ta amince ba. Meme kuwa… mahaifiyar Zeynab… bata ɓoye ra’ayinta. A gare ta, Fatima black magic tayiwa haroon. Zeynab ma tana ci gaba da nuna ƙiyayya a ɓoye. Lokacin da aka yi aurenta ya mutu, ta so ta zauna a gidan Haroon, tana cewa “I’ll stay there…” amma Aslam ya katse ta “No… you stay with your mother” saboda ya san manufarta ta je ta ƙara musu damuwa. A hankali, family ɗin ya rabu gida biyu waɗanda ke tare da Fatima da waɗanda ke kallonta da hassada Dalili kuwa guda ɗaya ne. Arzikin Haroon Duk inda aka je, sunansa yana ƙara ɗaukaka. Projects dinsa suna bunƙasa. Investments dinsa suna ninka. Har ma a cikin estate ɗin da suke ciki, gidansa ya fi na kowa kyau, ya fi girma, ya fi tsari. Kowa yana son wani abu daga gare shi. Amma… sai da yardar Fatima ake samu. Hakan ya ƙara musu haushinta sosai Makiyanta suka ƙaru.Wasu har suna cewa suke a ɓoye “Ta yi masa black magic…” Amma babu wanda ya isa ya faɗa a fili. Rayyan kuwa…rayuwarsa tana tafiya cikin tsari. Fatima ce ke kai shi school. Fatima ce ke ɗaukar sa. Ko da akwai drivers, ko da akwai ma’aikata…ita ke son yin komai da kanta. Islamic school dinsa ma ta kula sosai da shi, ta sa ya shiga sosai cikin ilimi da tarbiyya, cikin ikon Allah, kwakwalwarsa ta buɗe, ya zama exceptional student, duk wani exam first position, duk wani competition shi ne a gaba. Teachers suna cewa “He’s brilliant” Students suna girmama shi. Amma hakan ya ƙara tada ƙiyayya a cikin family. Har ma Uncle Usman…wanda a baya yana kusa da su… ya fara canzawa. Saboda ganin irin nasarar da Haroon ya samu. Rayyan ya zama matashi mai hangen nesa. Wata rana ya zauna kusa da Fatima ya ce, “Mom… I want to join the army.” Ta ɗaga kai ta kalle shi.Idonta ya nuna tsoro. “No.” Kalma guda.Ya yi shiru. Bai ƙara magana ba. Saboda a wurinsa duk abin da Mom take so… shi yake so. Daga baya, ita ce ta zaɓa masa course Business Administration “Zaka gaji Dad… you need to understand business.” Ya ɗaga kai. “I will.” Haroon ya yi alfahari da shi. Ya fara koya masa harkokin kasuwanci. Fatima kuma ta buɗe masa wata ƙaramar gonar da ta gada daga mahaifinta, a wani wuri mai kyau kusa da Île-de-France countryside, wuri mai cike da natsuwa da iska mai tsafta. Rayyan ya shiga cikin aikin. Da safe school. Da yamma farm. Cikin kankanin lokaci…ya nuna ƙwazo. Harvest na farko da suka yi… ya zama babba. Haroon ya ƙara musu kayan aiki, machines, support.“Good job,” ya faɗa yana kallon sa da alfahari. Amma duk wannan nasara…ba ta kai girman soyayyar da yake yi wa Fatima ba.Idan ka gan shi a waje tare da ita yake. Idan ba school ba tare da ita yake. Idan ta yi tari kaɗan “Mom we need to go to the hospital.” Idan ta yi shiru “Are you okay?” Wata rana ma ya ce, “I can’t lose you…” ta ɗan yi dariya. “Nothing will happen to me…” amma a zuciyarta… ta san wannan soyayya ba ƙarama ba ce ZK2026 08081005693 07040402435. ZUCIYA DA ƘUNA By Billy S. Fari & Nana Hadiza @nanadiso10 | Arewabook PAGE 5. Cikin wannan lokaci ne gidan Haroon Kareem ya sauya gaba ɗaya zuwa wani sabon yanayi na farin ciki da nasara,kasuwancinsa ya bunƙasa sosai, sunansa ya shiga cikin jerin manyan attajiran da ake girmamawa a birnin, kamfanoninsa suna aiki a fannoni daban-daban real estate, importation, luxury investments duk inda aka ambaci Haroon Kareem, ana magana ne da girmamawa, ana kallonsa a matsayin mutum mai hankali da hangen nesa, amma duk da wannan arziki da daukaka, akwai abu guda ɗaya da ya fi komai muhimmanci a gare shi iyalinsa. Rayyan… wanda aka haifa cikin hawaye, ya girma cikin soyayya. Tun yana ƙarami, Fatima bata taɓa barinsa ya ji wani irin rashi ba, duk abin da yake buƙata tana nan, amma ba kaya ba ne kawai, ba abinci ba ne kawai soyayya ce, kulawa ce, da wani irin attachment da ya wuce misali, duk wanda ya ga yadda take mu’amala da shi zai rantse cewa ita ce ta haife shi, tana kiran sa “My Rayyan…” yana amsa da “Mom…” cikin wani irin laushi da ke sa zuciya ta narke. Da safe, kafin ya tafi makaranta, Fatima ce ke shirya masa komai, uniform dinsa mai kyau, shoes dinsa masu tsabta, tana gyara masa gashi a hankali tana cewa “Stand still… you’re always moving” shi kuma yana dariya yana rungumeta “Mom you worry too much…” Haroon na tsaye a gefe yana kallon su da murmushi, yana jin wani irin cikar zuciya. Rayyan ya zama yaro mai hankali sosai, a makaranta yana daga cikin top students, teachers suna yabonsa, abokai suna girmama shi, yana da nutsuwa amma yana da confidence, yana magana cikin ladabi amma akwai wani irin ƙarfi a cikinsa da ke fitowa lokaci zuwa lokaci, kamar yana ɗauke da wani abu daga baya da bai sani ba. Ranar wani school event, aka kira iyaye domin ganin yadda yara ke gabatar da ayyukansu, Fatima da Haroon suka halarta, suna zaune a cikin hall mai kyau, yara suna gabatarwa ɗaya bayan ɗaya, sai aka kira suna “Rayyan Haroon” ya tashi cikin nutsuwa, ya hau stage, ya fara magana cikin English mai kyau, confidence dinsa ya fito fili, kowa ya kalleshi, Fatima ta dafe zuciyarta tana murmushi da hawaye a lokaci guda, “That’s my son…” ta faɗa a hankali, Haroon ya kalleta ya ɗan riƙe hannunta “He’s doing great…” Bayan an gama, mutane da yawa sun zo suna gaishe su, suna yaba Rayyan, suna cewa “You raised him well” Fatima ta ji zuciyarta ta cika da alfahari, ba ta san lokacin da ta rungume shi ta sumbace shi ba “I’m so proud of you…” shi kuma ya ce “I did it for you Mom…” kalmar ta shiga zuciyarta sosai. A gida kuwa, Rayyan ba ya rabuwa da Haroon, suna yawan fita tare sometimes business meetings, sometimes just drive around the city, Haroon yana koya masa abubuwa, yana nuna masa yadda rayuwa take, yadda ake yanke hukunci, yadda ake zama mutum mai daraja, Rayyan yana sauraro da nutsuwa, yana ɗaukar komai a hankali. Wata rana suna zaune a office dinsa mai girma, gilashi a ko’ina, ana kallon Paris daga sama, Haroon ya kalli Rayyan yana cewa “One day… all this will be yours” Rayyan ya kalle shi cikin mamaki “Really?” ya ɗaga masa kai “Yes… but you have to earn it” ya ɗan murmusa “I will” Amma a bayan wannan farin ciki, akwai wasu idanu da ke kallon su da wani irin yanayi, Zeynab ba ta taɓa mantawa da abin da ya faru ba, a duk lokacin da ta ga Rayyan tare da Fatima, zuciyarta na cika da wani irin abu, wani abu da ya haɗa hassada da ƙiyayya, tana jin kamar an ƙwace mata wani abu da ya kamata nata ne, sauran family ma ba duka ne suka amince da wannan haɗin ba, wasu suna yin gulma a ɓoye. Amma duk wannan bai shafi Rayyan ba. Shi rayuwarsa guda biyu ce kawai Mom da Dad A wurinsa, Fatima ita ce komai, ita ce duniya, ita ce zuciyarsa, yana son ta ba tare da shakka ba, yana kare ta kamar yadda yaro zai iya kare uwa. A daren wani rana mai sanyi, bayan Rayyan ya kwanta, Haroon da Fatima suna zaune a balcony, suna kallon hasken Paris, iska mai laushi na kadawa, Fatima ta jingina da shi a hankali “Look at him… he’s grown so fast…” Haroon ya ɗan rungumeta “Because you gave him everything…” ta ɗan yi murmushi “No… we did” Ya ɗan jawo ta kusa da shi “I couldn’t have done this without you…” ta kalli idanunsa “And I couldn’t live without him…” ya ɗan murmusa “Or me?” ta ɗan yi dariya “You too…”Ya sumbaci goshinta a hankali. Daren Paris ya sauka cikin sanyi mai kaifi, iska na kadawa a hankali a waje, bishiyoyi na rawa kamar suna faɗin wani sirri, a cikin katafaren gidan Haroon Kareem kuwa, shiru ne mai nauyi ya mamaye komai, fitilun corridor suna haskakawa da laushi, amma a cikin ɗakin Rayyan… babu nutsuwa, yana kwance a kan makeken gadonsa mai faɗi, duvet mai laushi ya rufe rabin jikinsa, amma jikinsa ba ya jin daɗin kwanciyar, yana juyi daga gefe zuwa gefe, numfashinsa na fita da sauri, hannunsa na riƙe cikinsa kamar wani abu na cinsa daga ciki, wannan ba sabon abu bane a gare shi, sau da yawa yana jin irin wannan ciwon, amma ba su taɓa gano dalili ba, doctors sun yi bincike, tests, scans… komai normal, amma ciwon yana dawowa lokaci zuwa lokaci, wani lokacin ma har yana faduwa kamar matacce, hakan yasa ya saba ɓoye wa Fatima, saboda ya san idan ta sani… zata shiga wani irin hali, hali na tashin hankali da kuka da tausayi wanda yake karya masa zuciya, shiyasa yau ma bai gaya mata ba tun da ya dawo daga Islamic school dinsu, makarantar da ta koya masa abubuwa da dama addini, nutsuwa, da kuma wani sabon yanayi na jikinsa da yake fara fahimta a hankali, girma na zuwa masa, amma tare da shi akwai wannan ciwo da ba a san asalinsa ba. Yau kuwa… ya yi tsanani.Jikinsa ya fara rawa. Sanyi ya ratsa shi. Ya miƙe a hankali daga kan gadon, ƙafafunsa suna rawa, ya sauko ƙasa, ya durƙusa yana riƙe cikinsa da ƙarfi, “Ahh…” ya furta a hankali, amma muryar ta fito da rauni, jikinsa ya fara kakkarwa, idonsa ya ɗan rufe, numfashinsa ya rikice, kamar zai faɗi. A daidai wannan lokacin, ƙofar ɗakin ta buɗe. Fatima ta shigo da plate a hannunta abinci da ta kawo masa kamar yadda take yi kullum. “My Rayyan…” ta fara magana da murmushi, “sweetheart… it’s been two good hours, baka zo gurina ba… so kake zuciyata ta tsaya?” ta ƙarasa tana ɗan dariya. Amma dariyar ta mutu a leɓenta. Plate ɗin ya faɗi daga hannunta. Ƙarar yaɗuwar abinci a ƙasa ta cika ɗakin. Idonta ya sauka kansa. Rayyan na ƙasa. Jikinsa na rawa. Yana riƙe cikinsa kamar zai mutu. “Rayyan!!!” Ta yi ihu da ƙarfi. Ta garzaya gare shi, ta rungume shi, jikinsa ya yi sanyi, hannunsa na kakkarwa, numfashinsa ya rikice. “My baby… what is this… what is this???” ta riƙa faɗa cikin firgici, hawaye sun zubo ba tare da izini ba. Ta ɗaga kai cikin tashin hankali, “JOHN!!!” ta ƙwala kira. Da sauri ɗan aikin gidan ya shigo, “Ma’am!” “Call the driver! NOW!!” “Ma’am, I’m here, I’ll drive!” Ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗauke Rayyan kamar wanda ya sume, jikinsa ya yi laushi a hannunta, ta rungume shi da ƙarfi kamar ba za ta sake shi ba har abada. Kuka take.bKuka mai karya zuciya. “Rayyan please… don’t leave me… please…” ta riƙa maimaitawa. Suka fita daga gidan cikin gaggawa, sanyi na bugun su amma babu wanda ya damu, motar ta tashi da gudu cikin daren Paris, fitilun titi suna wucewa a gefensu, amma a cikin motar… sai kuka da addu’a. “Ya Allah ka taimaka… please Allah…” Fatima ke maimaitawa. Haroon baya ƙasar. Wannan ne ya fi bata tsoro. Ta ɗauki waya da hannu mai rawa, ta kira Dada. “Dada… Rayyan… he’s not well…” kuka ya katse mata magana. Ta kira Didi. Ta kira Aslam. John ma ya riga ya sanar da shi. Aslam ne ya iso asibitin kafin su. Da suka isa emergency, ba tare da ɓata lokaci ba aka karɓe su, aka ɗauke Rayyan zuwa cikin gaggawa, nurses suna zagaye da shi, likitoci suna ba da umarni. “BP check” “Get the IV ready.” “Monitor him” Fatima na tsaye a waje tana kuka kamar ranta zai fita, jikinta na rawa, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. “Aslam…” ta kira da muryar da ta cika da tsoro.“Please… do something…” Aslam ya riƙe hannunta, “Calm down… he’ll be fine…” Amma shi ma zuciyarsa na bugawa. Bai san me ke faruwa ba. A cikin wannan tashin hankali… Fatima ta ji duniya na juyawa. Idonta ya duhu. Ta faɗi. “Fatima …” Aslam ya kama ta kafin ta bugi ƙasa. Aka ɗauke ta cikin gaggawa. A wani ɓangaren… Zeynab da Meme suna zaune a gidansu. Labari ya iso musu. Amma ba tausayi bane a fuskarsu. Sai wani irin yanayi. “Hmmm…” Zeynab ta ce. “Daman ya mutu.” Meme ta ɗaga kai. “Kai da naji dadi…”Saboda duk wannan arzikin da Haroon ke ciki…Rayyan ne gadonsa. Rayyan ne komai. Kuma hakan ba ya musu daɗi. A asibiti… Fatima na kan gado, an yi mata allurar bacci. Fuskarta ta nuna wahala. Rayyan kuma… ya fara dawowa. Numfashinsa ya daidaita. An haɗa masa drip. An yi masa allurai. Yana kwance a hankali. Aslam na tsaye kusa da likita. “What happened to him?” ya tambaya. Likitan ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya amsa. “We ran all the tests…” ya ɗan girgiza kai. “Everything is normal.” Aslam ya ɗan rikice. “Then what is causing this?” Likitan ya ce a hankali, “It might be something his body reacts to… maybe food… maybe internal sensitivity… we still need to monitor him.” Kalmar ba ta ba su amsa ba. Sai ƙarin damuwa. A cikin ɗakin… Dada na zaune. Kowa cikin shiru. Rayyan ya motsa kaɗan. Ya buɗe idanunsa a hankali. “Mom…” ya kira da muryar da ta yi rauni. “Mom… where are you…”Aslam ya matsa kusa da shi. “Hey champ… Mom is fine…” ya yi murmushi. “Don’t worry.”Amma Rayyan ya girgiza kai. “I want my Mom…” kamar ƙaramin yaro. Aslam ya kalli Dada. Ya san idan suka gaya masa tana kwance… zai sake shiga tashin hankali. “She’ll be back…” ya faɗa. “Just rest.” Sa’o’i suka wuce. A hankali…Fatima ta farka. Abu na farko da ta faɗa “Rayyan…” Ta miƙe da sauri, jikinta ba ƙarfi. “Aslam… where is he???”v“Relax… he’s okay…” Bai gama ba… ta riga ta sauko daga gadon.Ta nufi ɗakinsa. Da ta shiga…ta gan shi Yana kwance.Idonsa a buɗe. “Mom…” ya faɗa da murmushi mai rauni. Ta garzaya gare shi. Ta rungume shi da ƙarfi. Kuka ya kwace mata.“My baby… don’t scare me like that… please…” Ta sumbaci kansa,Hannunsa,Fuskarsa. Shi kuma ya riƙe ta. Daren Paris ya yi sanyi mai laushi, iska na kadawa a hankali tana motsa labulen ɗakin su, fitilun birni suna haskakawa daga nesa suna bada wani irin golden glow da ke shiga cikin ɗakin, Fatima na tsaye a gaban madubi tana cire ‘yan kayan kwalliyarta a hankali, gashinta ya sauka a bayanta cikin nutsuwa, jikinta sanye da riga mai laushi wacce ta ƙara fito da kyawunta cikin salo mai tsafta, tana kallon kanta amma zuciyarta tana wani wuri daban, tana tunanin rayuwarta, yadda komai ya sauya, yadda soyayya ta shigo rayuwarta ba tare da tsammani ba, a hankali ta ji wani zafi mai laushi a bayanta hannun Haroon ne ya zagayo ya rungumeta daga baya, jikinsa ya manne da nata, numfashinsa ya bugi wuyanta, ta lumshe idanu na ɗan lokaci kamar tana jin daɗin wannan kusancin da bata gajiya da shi, “You look beautiful…” ya faɗa a hankali cikin muryar da ke shiga zuciya, ta ɗan yi murmushi ba tare da ta juya ba, “You always say that…” ta amsa cikin laushi, ya ɗan sunkuya ya sumbaci wuyanta a hankali, ta ɗan ja numfashi, jikinta ya amsa wannan taɓawar cikin nutsuwa, “Because it’s always true…” ya ƙara faɗa yana kallon ta a cikin madubi, idanuwansa suna nuna wani irin so mai zurfi, Fatima ta juya a hankali ta fuskance shi, idanunta sun haɗu da nasa, na ɗan lokaci babu wanda ya yi magana, sai kallon juna, kallon da ke ɗauke da shekaru na fahimta, na jurewa, na ƙauna, ta ɗaga hannunta ta taɓa fuskarsa a hankali, “You’ve done so much for me…” ta faɗa da murya mai laushi, ya girgiza kai kaɗan yana murmushi, “No… we did this together…” ya riƙe hannunta ya sumbace shi a hankali, ta ji wani irin sanyi ya ratsa jikinta, ta ɗan matsa kusa da shi, “Sometimes I wonder… what I did to deserve you…” ta faɗa cikin gaskiya, ya ɗan ja ta zuwa jikinsa, “You stayed… when everything was broken… that’s more than enough,” kalmarsa ta sauka a zuciyarta, ta jingina da shi tana jin bugun zuciyarsa, ɗakin ya yi shiru sai numfashinsu kawai, ya ɗaga haɓarta a hankali ya sa ta kalle shi, “Fatima…” ya kira sunanta cikin nutsuwa, “I love you…” kalmar ta fito a sarari, ba tare da ƙoƙari ba, amma cike da gaskiya, idonta ya ɗan cika da hawaye, amma wannan karon na farin ciki ne, ta ɗan yi murmushi, “I love you more…” ta amsa, ya ɗan yi dariya kaɗan, “That’s not possible…” ta ɗan turo baki, “It is…” kafin ta ƙarasa ya sumbaci goshinta a hankali, sannan ya sauka zuwa kuncinta, sannan ya tsaya a leɓenta na ɗan lokaci ba tare da ya yi gaggawa ba, kamar yana ba ta lokaci, kamar yana tabbatar da komai yana cikin nutsuwa, daga nan ya sumbace ta cikin salo mai laushi, ba tashin hankali ba, ba gaggawa ba soyayyarsu ce kawai, mai tsafta, mai zurfi, mai cike da mutunta juna, ta riƙe shi da ƙarfi kamar tana jin tsoron rasa shi, ya ƙara rungumeta yana shafa bayanta a hankali, a waje iska na ci gaba da kadawa.. ZK2026 08081005693 07040402435. ZUCIYA DA ƘUNA By Billy S. Fari & Nana Hadiza @nanadiso10 | Arewabook PAGE 6. A hankali ya ƙara kusantar ta, yana kallon idanunta kamar yana neman wani abu a ciki, hannunsa ya zagayo bayanta ya jawo ta jikinsa, numfashinsu ya gauraya, zuciyarsa ta fara bugawa da sauri, ba da tashin hankali ba… amma da wani irin so mai nauyi, ya saukar da kansa ya sumbaci leɓenta cikin laushi, kissing ɗin ba na gaggawa ba ne, na nutsuwa ne, yana ɗauke da tausayi da kulawa, kamar yana tabbatar da cewa tana jin shi sosai, Fatima ta ɗan riƙe rigarsa a hankali, jikinta ya amsa wannan kusancin cikin sanyi, ya ƙara rungumeta da ƙarfi amma cikin kulawa, yana shafa bayanta a hankali kamar yana lallashinta, kissing ɗin ya ɗan tsawaita, har sai da numfashinsu ya rikice kaɗan, a hankali ya ɗan janye kansa, amma har yanzu hannunsa na jikinta, idanunsa sun ɗan rufe kamar yana ƙoƙarin dawo da nutsuwarsa, ya sauke numfashi mai nauyi, sannan ya buɗe idanunsa ya kalle ta, tana kallonsa da murmushi mai ɗauke da wasa, “Baka girma kai…” ta faɗa tana ɗan dariya, ya ɗan yi murmushi kaɗan yana jan hancinta a hankali, “Ana girma da soyayya ne?” ya tambaya cikin muryar da ke ɗauke da ɗan wasa da ɗan gaskiya a ciki, ta ɗan turo baki, “Eh mana…” ta amsa, ya ƙara matsowa kusa da ita yana kallon ta da wani irin ido mai cike da so, “Then I don’t want to grow up…” ya faɗa a hankali, ta buɗe ido kaɗan cikin mamaki, kafin ta yi murmushi ta jingina da shi, shi kuma ya ƙara rungumeta yana rufe ta da jikinsa, kamar yana kare ta daga komai, a wannan lokacin… soyayya ta yi shiru, amma zuciyarsu suna magana da juna… ***** Shekaru sun ja sosai… kuma yanzu Rayyan ba ƙaramin yaro bane, cikakken matashi ne mai kamala, a cikin ɗakinsa mai faɗi da aka kawata da modern luxury design a saman bene na gidan su a Neuilly-sur-Seine, yana kwance a kan makeken gadonsa mai laushi amma bacci ya gagara, yana juyi daga gefe zuwa gefe, numfashinsa yana fita da ɗan nauyi, zuciyarsa cike da tunani da kuma wani sabon yanayi na girma da yake fara fahimta a hankali, ya lumshe idanunsa yana furta addu’a a hankali “Ya Allah ka shiryar da ni…” kafin ya miƙe tsaye, jikinsa ya nuna cikakken ƙarfi, tsayin da ya ƙara, muscle da ya fito a jikinsa, yana kallon kansa a madubi na ɗan lokaci kamar yana nazarin sabon kansa, sannan ya juya ya nufi bathroom, ruwan shower mai sanyi ya sauka a jikinsa yana kawar da duk wani nauyi da ya taso masa a zuciya, ya tsaya ƙarƙashin ruwan na ɗan lokaci yana shiru, kamar yana ƙoƙarin dawo da nutsuwarsa, daga ƙarshe ya kashe ruwan ya fito, yana tsane jikinsa da towel cikin nutsuwa amma fuskar sa na ɗauke da ɗan gajiya da tunani, wayarsa ta yi kara, ya ɗauka ya kalli screen, “I will be there in 30 minutes.” ya faɗa cikin nutsuwa ya katse, a daidai lokacin ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali, Fatima ta shigo kyakkyawar mace mai nutsuwa, kamanninta sun ƙara haske da shekaru amma har yanzu tana da wannan soft elegance ɗin nata, ta yi murmushi tana cewa “My love, good morning…” Rayyan ya ɗan sauke fuskar damuwa ya maye gurbinsa da murmushi mai ɗumi, ya ajiye turarensa ya matsa gare ta ya rungume ta, ya sumbaci kanta cikin girmamawa “Good morning Mom…” ta shafa bayansa cikin kulawa kamar yadda ta saba tun yana ƙarami, “Open your mouth…” ta faɗa cikin wasa, ya ɗan yi dariya ya buɗe baki, ta ciyar da shi kamar ƙaramin yaro, duk da cewa yanzu ya fi ta tsawo sosai, amma a gare ta… har yanzu yaron ta ne, ta juya tana fita tana cewa “Two minutes… ka fito” ya ɗan murmusa “Coming…” Yana saukowa ƙasa cikin full dressing simple but expensive outfit, wristwatch ɗinsa mai kyau, kamanninsa sun cika da confidence ya tarar da dining area an shirya breakfast a kan babban table mai sheƙi, Suhayla wacce yake kira Baby sis ta zo da gudu ta rungume shi “Yaya..” Yace “yau sai kin makara ko?” ya faɗa yana dariya, ta turo baki “Wallahi assignment ne…” ya ɗan ɗaga gira “And Nayla?” Suhayla ta yi dariya “Har yanzu bacci take… I told her she has lecture by 9 ” Fatima da ke zaune a gefe ta girgiza kai tana cewa “I don’t know what to do with that girl… jiya ma lecturer ya korota” Rayyan ya ɗan yi shiru na ɗan lokaci sannan ya miƙe “I’ll handle it.” Ya nufi saman bene, ya tura ƙofar ɗakin Nayla a hankali, ɗakin ya cika da wani irin soft feminine luxury light colors, scented candles, dressing table mai kyau Nayla na kwance a kan gadonta, gashinta ya bazu a pillow, tana cikin bacci mai nauyi kamar ba ta da damuwa a duniya, ya tsaya yana kallonta na ɗan lokaci, yana girgiza kai kaɗan, sannan ya matsa kusa ya danna gefen hannunta kaɗan, ta yi motsi cikin bacci tana furta addu’a, ta buɗe idanunta da sauri ganin sa tsaye, ta miƙe a firgice “Yaya I’m very sorry… please…” bai ce komai ba, kallon ta kawai yake yi da seriousness ɗin da ta saba, sai ya ce “Five minutes. I will drop you myself.” kalmar ta isa ta sa ta miƙe da gudu zuwa toilet, tana cewa “Coming..” shi kuma ya juya ya sauko ƙasa, Fatima na dariya tana kallon yadda yake sarrafa Nayla, saboda shi kaɗai ne take ji, duk wani rawar kanta, idan yana nan… sai ta nutsu, soyayyarsu ta ‘yan’uwa tana da ƙarfi sosai, amma yana da tsauri akan karatu. Fatima ta kalle shi tana gyara masa agogonsa “My love… you’re getting late, you have a meeting by 8:30” ya ɗan yi murmushi “If I don’t do this… she’ll be late again.” ta girgiza kai tana murmushi, a zuciyarta tana jin alfahari da yadda ya zama, Suhayla ta riga ta fita school, gidan ya ɗan yi shiru, Rayyan ya ɗan juya ya kalli Fatima “Mom…” ya kira da ɗan nauyi a murya, ta san me yake son faɗa, ta yi saurin katse shi cikin laushi “Please… kar ka fara yanzu…” ya yi shiru nan take, saboda ya san batason wannan magana, ya girmama hakan. A daidai lokacin Nayla ta sauko daga stairs cikin sauri tana gyara hijab ɗinta “Mom Mom I’m going…” ta tsaya cak ganin Rayyan a zaune, ta rufe baki da sauri, Fatima ta fashe da dariya, Rayyan ya kalleta kawai ba tare da ya ce komai ba, hakan ya isa ya sa ta nutsu, ta ɗauki bag ɗinta, “Let’s go…” ya faɗa yana miƙewa, suka fita tare, a waje motar luxury tana jiran su, ya buɗe mata ƙofa ta shiga, sannan ya zagaya ya shiga, Motar ta na tafiya cikin nutsuwa a titunan Paris, fitilun safe suna haskakawa a jikin gilashin motar, Nayla na zaune a gefensa tana ta hira babu ƙaƙƙautawa, hannunta na motsi yayin magana kamar kullum, “Yaya honestly I’m tired… this school is too much, wallahi I can’t wait to graduate…” ta faɗa tana ɗan turo baki, “assignments, lectures, presentations… it’s too much…” ta ƙara da ɗan shagwaɓa, Rayyan bai amsa ba, ya ɗan kalle ta kawai sannan ya mayar da hankalinsa kan tuƙi, ba don bai ji ta ba… amma zuciyarsa na wani wuri daban, jikinsa na ɗan ba shi wani irin yanayi da bai gama fahimta ba, shiyasa ya zaɓi shiru, hakan bai dame ta ba domin ta saba da shi, ta ci gaba da magana “And you know what? If I fail this course ehn… I’m done…” ta ƙarasa tana dariya kaɗan, daga ƙarshe ya tsaya a gaban Sorbonne University, ɗaya daga cikin manyan jami’o’i a Paris, ya ajiye motar a hankali, kafin ta fita ya ɗauko wallet ɗinsa ya miƙa mata kuɗi, ta kalle shi da murmushi mai faɗi “Thank you Yaya…” ta faɗa cikin farin ciki, ta jingina kaɗan “You’re the best…” ya ɗan yi murmushi kawai, ba tare da ya ce komai ba, ta buɗe ƙofa ta fita cikin sauri, tana daga masa hannu “Bye!” ya ɗan ɗaga mata hannu sannan ya ja motar ya tafi. A hankali Nayla ta juya tana takawa zuwa cikin campus ɗin, cike da nutsuwa da confidence, takunta mai tsari yana ɗaukar hankali, gashinta ya ɓoye a ƙarƙashin hijab ɗinta mai kyau, kayan jikinta sun dace da ita cikin salo mai tsabta amma classy, shekaru 21 kacal amma kamanninta sun nuna cikakkiyar mace, akwai diri a jikinta masha Allah, ba raini gare ta ba amma akwai tsiwa mai kyau, irin wacce take jan hankali ba tare da ƙoƙari ba, students da ke wucewa suna kallonta, wasu suna gaishe ta “Hey Nayla…” tana amsawa da ɗan murmushi, wasu ma suna juyawa suna kallonta daga baya. A gefen parking lot, kawarta Amina ta hangota, ta daga hannu tana cewa “Naylaaa!” Nayla ta juya tana murmushi, ta ƙarasa gare ta, suka haɗa hannu cikin farin ciki “You’re late!” Amina ta faɗa tana dariya, Nayla ta turo baki “Don’t start please… you know how it is…” suka shiga cikin building tare, corridor ɗin ya cika da students, hayaniya mai laushi na fita, ƙarar takalma, dariya, hira… rayuwar university na tafiya yadda aka saba. Suka isa lecture hall ɗin su, Nayla ta zauna tana sauke numfashi “I’m tired already…” ta faɗa tana jingina da kujera, Amina ta girgiza kai “You complain too much…” kafin su ƙara magana, wasu students suka fara fitowa suna cewa “The lecturer is not coming…” Nayla ta ɗaga kai cikin mamaki “Seriously?” Amina ta ce “Yes… class is cancelled” a nan Nayla ta fashe da dariya mai daɗi “Oh my God I love this school sometimes!” ta faɗa tana ɗaga hannu sama, zuciyarta ta cika da farin ciki, duk gajiyar da take ji ta ɓace a lokaci guda, ta jingina da kujera tana murmushi, ba tare da ta sani ba A cikin harabar Sorbonne University, rayuwa na tafiya cikin sauri kamar yadda aka saba, students suna zirga-zirga, wasu suna dariya, wasu suna cikin damuwa, amma a tsakiyar wannan cunkoso akwai wata presence da take jan hankali ba tare da ƙoƙari ba Nayla Haroon, a hankali take tafiya a cikin corridor, takunta na fita da nutsuwa da confidence, ba gaggawa, ba tsoro, kamar wacce ta saba da kallo da kulawa daga mutane, hijab ɗinta mai tsabta ya zauna da kyau a kanta, kayan jikinta simple ne amma suna da class mai nauyi, duk wanda ya san quality zai gane cewa ba kayan kasuwa bane kawai, akwai tsari, akwai style, akwai ɗan alfarma a ciki, fuskar ta tana da wani irin haske, ba wai kwalliya mai yawa ba, amma natural beauty da ke fitowa da kanta, idanuwanta masu zurfi suna ɗauke da wani irin ɗan tsiwa da confidence, lips ɗinta suna ɗan motsi kamar tana riƙe da murmushi a ɓoye, ba raini gare ta ba, amma akwai wani irin girman kai mai kyau irin wanda ba ya cutarwa, amma yana nuna cewa ta san darajar kanta. “Hey Nayla…” wasu students suka kira suna wucewa, ta ɗan juya kai tana murmushi kaɗan “Hi…” ba ta tsaya hira mai tsawo ba, domin ba ta daga cikin masu son hayaniya, tana da nata circle, kuma ba ta yarda da kowa cikin sauƙi ba, Amina na biye da ita tana ta magana “Honestly you’re too calm… if it was me I would be shouting that lecturer didn’t come!” Nayla ta ɗan yi murmushi tana girgiza kai “You talk too much…” ta faɗa cikin wasa, suka zauna a bench kusa da glass wall da ke kallon harabar makarantar, rana na haskawa a waje, hasken ya sauka a fuskar Nayla yana ƙara fito da kyawunta cikin nutsuwa. Ta ɗan ja numfashi ta jingina baya, idonta ya ɗan lumshe, kamar tana tunani, Amina ta lura da hakan “What’s wrong?” Nayla ta buɗe idanunta a hankali “Nothing… just tired…” amma a zahiri akwai wani abu da ke cikin zuciyarta, wani irin yanayi da ba ta iya bayyana shi ba, kamar tana neman wani abu… ko wata rayuwa da ba ta samu ba tukuna. A cikin wannan lokaci, wayarta ta yi ƙara, ta ɗauka, screen ya nuna Yaya, ta ɗan murmusa kafin ta ɗaga “Yes…” ta faɗa cikin laushi, daga can ya tambaye ta ko ta isa, ta amsa “Yes I’m in school…” ya ce mata ta kula da kanta, ta ɗan yi dariya “I’m not a kid…” ya katse ta “Behave yourself…” ta ɗan turo baki “Okay…” ta katse, ta sauke wayar tana murmushi kaɗan. Amina ta kalleta da ɗan mamaki “Your brother is too serious…” Nayla ta ɗan ɗaga gira “You don’t know him…” ta faɗa cikin wata murya mai nuna cewa akwai wani abu daban a tsakanin su, ba wai kawai yaya ba… akwai wani irin kusanci da fahimta, amma kuma akwai wani layi da ba ya wucewa. Ta miƙe tsaye a hankali “Let’s go… since lecture is cancelled, I’m not wasting my day here.” suka fara tafiya, yayin da take tafiya, wasu idanu suna binta, wasu suna kallonta. ZK2026 08081005693 07040402435. ZUCIYA DA ƘUNA By Billy S. Fari & Nana Hadiza @nanadiso10 | Arewabook PAGE 7. Daga fitowarsa daga École Internationale Privée de Paris, bai tsaya ko’ina ba, motarsa kirar Rolls-Royce Cullinan Black Badge mai launin baki mai sheƙi ta tsaya a gaban katafaren ginin kamfaninsa mai suna RH GLOBAL HOLDINGS, wani gini mai hawa da yawa da aka yi da gilashi mai kyalli wanda ke nuna ƙarfin iko da kuɗi, guards biyu suna tsaye a ƙofar suna gaishe shi da girmamawa “Good afternoon, sir” bai tsaya ba, ya sauko daga motar cikin nutsuwa, suit dinsa na Italian tailored navy blue ya zauna jikinsa kamar an zuba masa, agogon Patek Philippe a hannunsa yana ƙara masa kima, tafiyarsa cike da authority, ma’aikata suna tsaye a gefe suna masa “Welcome sir” wasu suna sunkuyar da kai, wasu na murmushi amma babu wanda ya kuskura ya yi masa magana fiye da kima, kai tsaye ya nufi executive meeting hall, ba tare da ɓata lokaci ba aka fara meeting, projectors sun haskaka, screens sun nuna figures da charts, ya tsaya a tsakiyar table mai tsawo yana kallon su ɗaya bayan ɗaya, muryarsa ta fito da nutsuwa amma cike da iko “Let’s get straight to the point…” CFO ya fara gabatar da rahoto kan sabon investment a Dubai real estate expansion, figures sun kai billions, amma Rayyan bai nuna mamaki ba, ya saurara cikin nutsuwa, sannan ya ce “The numbers are good… but I want higher returns… restructure the deal” kowa ya yi shiru yana rubutu, wani director ya yi ƙoƙarin ƙara bayani, Rayyan ya ɗaga hannu a hankali “I don’t want explanations… I want results” kalmar ta tsaya a zuciyarsu, aka ci gaba da meeting, aka tattauna kan agricultural export business dinsa da ke France countryside gonar da Fatima ta gada wacce ya juya zuwa babban kasuwanci, ya ce “We expand production by 40% this season… invest in modern equipment… no compromise on quality” awa ɗaya cif meeting ya ɗauka, amma a cikin wannan awa ɗaya, an yanke hukuncin miliyoyi, an tsara makomar kamfani, sannan ya juya ya fita ba tare da ya tsaya hira ba, ma’aikata suna bin bayansa suna masa gaisuwa, yana amsawa da ɗan ɗaga kai kawai, presence dinsa kaɗai ya isa ya cika wurin da iko. Yana shiga cikin private executive office dinsa wani ɗaki mai faɗi, gilashi a ko’ina, view na birnin Paris daga sama, desk ɗinsa mai tsari da leather chair mai alfarma, ya zauna cikin nutsuwa yana buɗe laptop dinsa, a waje kuwa Noor personal assistant dinsa ta gan shi, zuciyarta ta buga, murmushi ya bayyana a fuskarta, ba ta ɓoye yadda take jin sa ba, a duniyarta babu wanda take so kamar shi, amma soyayyarta shiru ce, ta ɗauki file ta nufi ƙofar, ta yi knocking a hankali, “Come in” ya amsa ba tare da ya ɗago kai ba, ta shigo cikin ladabi tana tafiya a hankali, “Good afternoon, sir” ta ajiye file a gabansa, har yanzu bai kalle ta ba, “Please review this contract… it needs your signature” ta faɗa cikin nutsuwa, ya ɗauki file ɗin ya fara dubawa, ba tare da wani extra magana ba ya sa hannu, ta tsaya na ɗan lokaci kamar tana son ya ƙara magana, “Do you need anything else, sir?” ya amsa a takaice “No, thank you” kalmar ta rufe komai, ta juya ta fita a hankali, zuciyarta na cike da wani irin abu da ba ta iya fassara ba, tana fita ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, ta jingina da bango na ɗan lokaci kafin ta dawo cikin nutsuwa. A cikin office dinsa kuwa, Rayyan ya jingina da kujera, ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, numfashinsa ya ɗan sauya, wani irin tashin hankali yadda gabansa ya mike, ba abu bane na jiki kawai, wani irin pressure ne na rayuwa, na nauyin da ke kansa, ya buɗe idanunsa a hankali yana shafa fuskarsa “Focus…” ya furta a hankali, ya dawo kan aikinsa, amma yau ba kamar kullum ba, hankalinsa ya ɗan watse, ya ɗauki wayarsa ya kira Mom. “Hello Mom…” muryarsa ta sauya nan take, ta koma laushi.“Rayyan… are you okay?” Fatima ta tambaya cikin kulawa. “I’m fine… just checking on you.” “Have you eaten?” ta tambaya kamar kullum. Ya ɗan yi murmushi “Not yet.” “Please don’t skip meals… you work too much.” “I will… don’t worry.” Ta yi masa addu’a cikin nutsuwa “Allah ya tsare ka… ya sa albarka a aikinka…” “Thank you Mom…” ya amsa da girmamawa. Sun yi sallama. Nan take ya kira Dad. Yammacin Paris ya sauko cikin hasken rana, birnin na ɗauke da wani irin kyau na alfarma da nutsuwa, amma a zuciyar Rayyan ba wannan natsuwar ce ba, daga RH Global Holdings ya nufi wani ɓangaren birnin inda Amir Kareem Ventures yake office ɗin abokinsa kuma ɗan uwansa Amir, motarsa Rolls-Royce Cullinan ta tsaya a gaban ginin, guards suka buɗe masa ƙofa, ya shiga cikin nutsuwa amma da wani irin yanayi na ciki da ba a gani a fuskarsa, kai tsaye ya nufi office ɗin Amir ba tare da sanarwa ba, yana tura ƙofar a hankali… abin da ya gani ya sa jinin jikinsa ya tsaya na ɗan lokaci, Amir na tsaye yana rungume da wata yarinya cikin kusanci da bai dace ba, hannunsa a jikinta, dariyarsu cike da wani yanayi mara kyau, a take fuskar Rayyan ta sauya, idanunsa suka yi duhu, zuciyarsa ta cika da wani irin bacin rai mai tsanani, “Amir” ya kira da murya mai ƙarfi, suka firgita, yarinyar ta yi saurin ja baya, Amir ya juya cikin kunya, “Rayyan…” bai gama ba, Rayyan ya nuna ƙofa cikin tsauri, “Get out.” yarinyar ta ɗauki jakarta ta fita cikin gaggawa ba tare da ta kalli baya ba, shiru ya sauka na ɗan lokaci, Rayyan ya rufe ƙofar a hankali, ya juya yana kallon Amir, “Do you even realize what you’re doing?” muryarsa ba ta da ƙarfi amma cike take da tsanani, Amir ya sauke kai, “I’m sorry…” Rayyan ya matsa kusa da shi, “Haramun ne, Amir… this is clearly haram… you think it’s just fun?” ya ɗan tsaya yana kallonsa cikin ido, “Would you accept this for your sister?” kalmar ta soka Amir a zuciya, ya ɗaga kai cikin kunya, “No…” “Then why are you doing it?” Rayyan ya tambaya cikin zafi, Amir ya shafa kansa cikin damuwa, “I don’t know… I just… I can’t control it…” Rayyan ya girgiza kai cikin rashin jin daɗi, “Control is a choice… discipline is a choice… idan ka bar zuciyarka tana ja ka, zaka faɗa cikin halaka,” ya ɗan ɗaga murya, “Get married, Amir… if you can’t control yourself, get married… stop disobeying Allah saboda son zuciya,” kalmar ta fito da nauyi, Amir ya ji kunya sosai, ya ɗan matsa kusa, “You’re right… I’m sorry… I’ll fix it,” Rayyan ya sauke numfashi, ya ɗan zauna a kujera, suka fara tattaunawa cikin nutsuwa kan rayuwa, kasuwanci, da kuma yadda mutum zai iya kiyaye kansa daga fitina a duniya mai cike da jaraba, Rayyan ya ce, “This life… it’s not just money… it’s about discipline, iman, and responsibility… idan ka rasa waɗannan, ka rasa komai,” Amir ya saurare shi cikin girmamawa, yana jin nauyin kalamansa, bayan ɗan lokaci Rayyan ya miƙe, “Take care of yourself,” ya faɗa, Amir ya amsa da ladabi, “Thank you…” Daga nan Rayyan bai tsaya ko’ina ba sai gidan Meme, duk da girman da ya samu da matsayin da yake ciki, amma idan maganar Fatima ce, babu wasa a tare da shi, yana shiga falon ya fara magana kai tsaye, “Ina Zeynab?” muryarsa cike da iko, Zeynab ta fito daga ɗaki tana ɗan murmushi amma zuciyarta na bugawa, ta san dalilin zuwansa, Rayyan ya tsaya yana kallonta, “I heard what you did…” shiru ya sauka, “Don’t ever… ever disrespect my mother again,” ya jaddada kalmar my mother da ƙarfi, “Wallahi idan na sake jin wani abu daga gare ki… you won’t like the outcome,” kalmarsa ta fito da tsanani wanda ya sa Zeynab ta ji sanyi a jikinta, “I’m sorry… it won’t happen again,” ta faɗa cikin sauri, ta san halinsa, ba yaron da za a raina ba ne, Meme ta tsaya a gefe tana kallon su, amma ba ta yi magana ba, Rayyan ya juya ya fita kamar sarki, presence dinsa ya bar wani irin yanayi a cikin gidan, da zarar ya fita, Meme ta yi tsaki, “He thinks he owns everything…” Zeynab ta ƙara da cewa cikin zafi, “Insha Allahu… wata rana zai kawo mata bakin ciki…” zuciyarsu cike da hassada. Rayyan yana shiga mota, ya jingina da kujera, ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, wani irin yanayi ya ratsa jikinsa, ba bacin rai ba… ba gajiya ba… wani abu daban, wani irin tashin hankali na ciki, ya ɗan dafe goshinsa, “Ya Allah…” ya furta a hankali, yana jin wani irin pressure a jikinsa, yana azumin Litinin kamar yadda ya saba, yana ƙoƙarin kiyaye kansa, amma wannan yanayin yana dawowa lokaci zuwa lokaci, wani irin urge da ba ya so, da ba ya yarda da shi, ya buɗe idanunsa cikin damuwa, “This is not me…” ya faɗa a hankali, a zuciyarsa yana ƙin duk wani abu na bin mata, yana ganin ko addini bai hana ba, akwai tsafta da mutunci da mutum ya kamata ya kiyaye, yana son rayuwa mai tsarki, mai tsari, amma jikinsa wani lokaci yana ƙoƙarin jan sa wani wuri dabam, wannan shi ne ya fi damunsa, wannan shi ne yake yaƙi da shi a kullum. Ya ɗauki wayarsa ya duba lokaci, ya tuna yana da dakko mahaifinsa, nan take ya daidaita kansa, ya kunna motar, ya nufi Paris Charles de Gaulle Airport, tafiyarsa cikin nutsuwa amma zuciyarsa na aiki, kafin ya iso, motoci sama da goma na security convoy sun riga sun isa, guards suna tsaye suna jiran sa, yana sauka daga mota cikin nutsuwa, suit dinsa na sheƙi a ƙarƙashin hasken airport, ya ɗaga kai yana kallon sararin sama na Paris, ya sauke numfashi a hankali. Daga Paris Charles de Gaulle Airport ne Rayyan ya ɗauko mahaifinsa Haroon Kareem, convoy ɗin motoci masu tsada suna gaba da baya suna tsare su cikin tsari mai kyau, motar Rolls-Royce Cullinan na tafiya cikin nutsuwa a kan titin da ke cike da hasken yamma, birnin Paris na walƙiya a gefensu kamar wani zane mai rai, Haroon ya jingina da kujera yana kallon ɗansa da wani irin farin ciki da gamsuwa, “My love… I think it’s time,” ya faɗa cikin nutsuwa, Rayyan ya ɗan juya kai ya kalle shi da murmushi mai sauƙi, “Time for what, Dad?” Haroon ya ɗan yi dariya “Time for you to get married…” Rayyan ya girgiza kai a hankali yana ɗan murmushi, “Dad… I’m not seeing anyone…” Haroon ya ɗaga gira cikin wasa, “Ba wai dole sai ka ga wata ba, we can find you someone…” ya ɗan yi shiru kafin ya ƙara, “Your mom even said no at first when I mentioned Hanan… ‘yar gidan abokina…” Rayyan ya yi ɗan murmushi mai cike da nutsuwa, “Then talk to Mom, Dad… idan ta amince… I’ll accept,” kalmar ta fito da sauƙi amma tana ɗauke da girmamawa mai girma, Haroon ya ɗan kalli ɗansa da idanu masu cike da alfahari, ya shafa kansa a hankali “Allah ya yi maka albarka, my son… I’m proud of the man you’ve become…” Rayyan ya ɗan sunkuyar da kai cikin ladabi, motar ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwa har suka isa katafaren gidan su na Neuilly-sur-Seine, ma’aikata suna jere suna gaishe su, amma Rayyan bai tsaya ba, ya wuce kai tsaye zuwa cikin ɗakinsa, ya cire suit dinsa cikin nutsuwa, ya shiga bathroom, ruwan shower mai ɗumi ya sauka a jikinsa yana kawar da gajiya da tunanin da ya taru a kansa, bayan ya fito ya ɗauki wayarsa ya kira Mom, “Mom… I’ll sleep early tonight… don’t worry if you don’t see me,” Fatima ta amsa cikin kulawa, “Are you okay?” “I’m fine…” ya faɗa cikin laushi, “Just tired,” ta ce “Alright… but I’ll check on you,” ya yi murmushi kaɗan, “I know…” ya ajiye wayar, ya kwanta a gadonsa mai faɗi, amma kamar yadda ta saba… Fatima ba ta yarda da kalmarsa kawai ba, ta leƙo ɗakin sau ɗaya… sau biyu… sau uku… tana kallonsa cikin kulawa, har ta matso kusa da shi ta taɓa goshinsa a hankali, “You’re not sick, right?” ya buɗe idanunsa kaɗan yana murmushi, “I’m fine Mom…” ta gyara duvet dinsa ta rufe shi sosai, sannan ta fita cikin nutsuwa. A ƙasa kuwa… Nayla ta sauko daga saman bene cikin nutsuwa, tana sanye da doguwar riga mai sauƙi amma mai kyau, “Daddy…” ta kira da wani irin ɗan shagwaɓa mai laushi, Haroon ya juya yana murmushi “My princess…” ta ƙaraso kusa da shi ta riƙe hannunsa, “It’s been five days… I didn’t see you… even video call you didn’t pick…” ta ɗan turo baki kamar ƙaramar yarinya, Haroon ya ɗan riƙe hannunta yana lallashi, “I’m sorry Nayla… work was crazy…” ya ɗan sumbaci goshinta “How’s school?” ta yi ɗan murmushi, “We’re almost done… just a few more weeks,” ya ce “That’s good…” ta juya ta kalli Fatima, “Mom… can I go to Uncle Usman’s house tomorrow? Please don’t tell Yaya… he’ll say no… and Amnah invited me…” Fatima ta ɗan yi murmushi tana kallon ta, “Ask your brother first… idan ya yarda, then it’s fine,” Nayla ta yi ɗan tsaki cikin wasa, “Okay Mom…” ta juya tana cewa “Goodnight…” ta haura sama, saboda ita ba ta jinkirin bacci, tana son ta kwanta da wuri saboda lectures. A falon kuwa Haroon ya juya ya kalli Fatima, “About Hanan…” ya fara magana cikin nutsuwa, Fatima ta ɗaga kai, “No… Haroon, I’m not comfortable…” ya ɗan yi murmushi “Haba Fatima… Rayyan is grown now… he needs a wife… a family…” Fatima ta sauke numfashi, “Ina tsoron ya samu mace mara tarbiyya…” kalmar ta fito daga zuciya, Haroon ya ce cikin natsuwa, “Then investigate… ki bincika… idan ta dace… we move forward,” Fatima ta ɗaga kai a hankali, “Alright… I’ll look into it…” A cikin ɗakin Rayyan kuwa… ya tashi daga kwanciyar da ya yi, ba saboda bacci ya ƙoshi ba… sai saboda wani mafarki da ya tashe shi, ya zauna a gefen gado yana sauke numfashi a hankali, zuciyarsa na bugawa da sauri, ya shafa fuskarsa, “Ya Allah…” ya furta a hankali, ya miƙe ya sake shiga bathroom, ya wanke jikinsa da ruwan sanyi wannan karon, yana ƙoƙarin dawo da kansa cikin nutsuwa, ya fito ya sa kaya masu sauƙi, ya tsaya a gaban madubi yana kallon kansa, akwai wani abu da yake ji a jikinsa… wani irin restlessness da ba ya son shi, da ba ya yarda da shi, yana jin kamar jikinsa yana buƙatar wani abu da zuciyarsa ke ƙin yarda da shi, ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, yana tuna kalamansa da ya faɗa wa Amir, “Control is a choice…” ya buɗe idanunsa a hankali, ya ɗan yi murmushi mai rauni, “I have to be stronger…” ya koma kan gadon. ZK2026 08081005693 07040402435. ZUCIYA DA ƘUNA By Billy S. Fari & Nana Hadiza @nanadiso10 | Arewabook PAGE 8. Misalin Ƙarfe 1:40 na dare a Paris, lokacin da gari ya ɗan yi shiru, amma zuciya ta fi yin magana saboda raguwar hayaniyar motoci da kuma surutun jama'a, Tun farkon dare da Rayyan ya kwanta har zuwa wannan lokaci bacci ya ƙaura daga idanuwansa, banda juye-juye babu abinda yake faman yi a saman katafaren gadon nasa, tun yana tunanin zuwan sauƙi daga azababben ciwon cikin da yake ji har ya fara galabaita haɗe da fidda rai saboda yadda yake tsananta masa acikin kowane sakan ɗaya, numfashi ya fara saukewa da ƙarfi saboda gangar jikinsa da zuciyarsa sun fara gajiyawa daga ƙarfin halin da yake tilasta kansa yi tare da kasa jurewa, a hankali yake kiran sunan Allah da bakinsa kaɗai ne ke motsawa ya kasa bayyana hakan a zahiri. Nishi mai ƙarfi ya shiga saukewa yana fitar da iska ta baki ko zai ji saukin raɗaɗin dake damunsa, hakan ya yi dai-dai da turo ƙofar Mom dake shigowa tana dariya Dady na biye da ita a baya, tun da yaga ta miƙe zata baro part ɗin nasa shima ya miƙe ya biyo bayanta “Indai ɗakin Rayyan zaki je to mu tafi ƙafata ƙafarki duk da nasan ya riga yayi bacci yanzu ba zaki jima ba zaki dawo, na rasa me kika ɗauki yaron nan naki da har yanzu bazaki rage yawan duba sa ba cikin dare” "Baka ji meka faɗa ba? Yarona fa kace taya zan rage basa kula bayan har yanzu shi ɗin yarona ne." “Shi yasa nake so yai aure yaje matarsa taci gaba da kula dashi ni kuma yabar mun tawa matar ta huta.” Wannan zance na Dady yai shi yaba Mom dariya wanda yai dai-dai da lokacin da suka iso ɗakin na Rayyan. Da sauri Mom ta ƙarasa bakin gadon Dady na rufa mata baya ganin halin da Rayyan ɗin ke ciki, hankali a tashe ta zauna bakin gadon ta jawosa duka a cjikinta tana girgiza shi “Oh my God, my son! What’s happening to you? Please talk to me, what’s wrong? Why are you like this? Can you hear me? Say something, please! Rayyan." Ganin ya kasa magana numfashinsa na ƙara wahalar fita yasa ta kalli Dady da shima hankalinsa ya tashi ya kasa magana sai bin shi da kallo yake yi tamkar mai son gano yanayin da yake ciki "Dady...” Ta faɗa a ɗan ruɗe tana sake maida kallonta ga Rayyan kamar wanda take tsoron tsayawar lumfashinsa, a hankali take furta sunansa tamkar mai koyo “Rayyan, My Rayyan!” Nan ma Rayyan ya kasa cewa komai sai riƙe ciki yake yana lumshe idanuwa kafin can taga ya rufe su hannunsa dake rike da cikinsa ya faɗi, girgiza sa tai da ɗan ƙarfi tace “Noooo…My son..Stay with me, don’t close your eyes! can you hear me? Please, open your eyes… talk to me, what’s wrong? Don’t do this to me… please!” Ganin haka yasa da sauri Dady ya fita yana ƙwalawa cikin securities kira suka shiga cikin gidan tare, ɗakin Rayyan ɗin suka haura Dady ya tallabosa daga jikin Mom data soma kuka suka riƙasa hankali a tashe suka fita dashi, suna fita Dady ya nufi wajen ɗaya daga cikin motocinsa, driver na ganin haka da sauri shima ya taso ya buɗe motar suka saka shi, hannu Dady ya miƙa masa ya karbi key ɗin motar, dama akwai mayafi ajikin Mom ta faɗa cikin motar itama Dady ya ja da ƙarfi suka fice daga gidan, ganin haka yasa cikin sauri securities ɗin suma suka ɗauki mota ɗaya suka bi bayansu. Daga Mom har Dady duka hankalinsu a tashe yake, yi suke suna juyowa suna kallon yanayin da ɗan nasu ke ciki tamkar wanda babu rai ajikinsa, babu abinda wannan yanayi ya tunawa Dady sai lokacin da Mom ta samu cikin Nayla yadda wani dare ya ɗauke ta rai a hannun Allah, saboda cikin ya matukar bata wahala sosai dan babu wanda ya zata ma zata rayu ko haihuwar abinda ke cikin nata cikin ƙoshin lafiya, kauda wannan tunanin yai tare da ɗan dukan steering wheel ɗin motar yana sake taka wuta, a Clinique Ambroise Paré dake kusa da Neuilly-Sur-Seine ya nufa bai tsaya nufar asibitin da suke ganin likita ba saboda gani yake yi kafin sukai komai zai iya faruwa, private hospital ce mai kyau da tsari yana zuwa yai parking a harabar wajen da gudu nurses suka fito suka ɗauki Rayyan, cikin sakonni kaɗan ɗakin da aka shiga dashi likitoci suka hau kanshi, Mom ta kasa zaune ta kasa tsaye, zagayen ƙofar ɗakin ta shiga yi tana ji tamkar ta kutsa kanta ciki ta shiga taga halin da yaronta ke ciki, Dady yasan shaƙuwa da irin soyayyar da takewa Rayyan, a hankali tana kawowa kusa dashi ya riƙo hannunta ya janyo ta zuwa jikinsa ya rungume “Calm down, I’m here with you. Everything will be okay, by God’s grace.” “bana so wani abu ya sami Yarona" “The doctors are doing their best, and we will keep praying, in Sha Allah ba abinda zai samesa." “Hopefully amma kasan bazan iya jurar wani abu ya sami yarona ba, I can't” “i know! But you are a strong mother, and I’ll stand by you Saboda haka ki kwantar da hankalinki kin ji ko?” bata iya amsa shi ba ta ɗaga masa kai kawai, ita kadai tasan me take ji a ranta, tana son Rayyan har cikin zuciyarta, batasan wane irin ciwo ne haka ke damunsa ba, ta rasa wace irin matsala ce haka, da tana da iko da tun a shekarun baya tayi masa maganinta. A jikin wata kujera ya jata suka nufi gun ya zaunar da ita yana ci gaba da rarrashinta, bayan mintina ashirin da biyar likitan daya jagoranci dubasa ya fito tare da sauran likitoci kowane ya wuce office ɗinsa, shi kuma ya yi masu izinin dasu biyo shi a office, bayani yayi masu akan ba wata matsala ke damun ɗansu ba su kwantar da hankalinsu yanzu haka sun bashi taimakon duk daya dace ya samu yin bacci, tare suka sauke ajiyar zuciya Mom ta kalli likitan tace “Please help me, I’m really worried about my child, is there anything urgent we need to do right now?, Please doctor ka faɗa mun ko me yake damun ɗana zan iya fitar dashi ƙasar nan where he can receive the best treatment idan har kana ganin abun yafi ƙarfinku.” Murmushi doctor ɗin yai "No need for that Hajiya, Babu wata matsala dake damun yaronki idan har zaku yi masa aure, i think this is the best treatment daya kamata kufara bashi." Dady ya gyara zamansa yana kallon likitan “Likita kana ganin wannan shine maganin matsalarsa? Saboda tun years back wannan ciwon ke damunsa mun kashe kudi sosai amma abinda likitoci suka tabbatar mana babu abinda ke damunsa, and da mun san wannan ne damuwar tun farko ai da mun yi masa abunda ya dace.” "It's not too late ranka shi daɗe ko yanzu, ina baka tabbacin in sha Allah matukar zai yi aure to wannan matsalar zai rabu da ita, na ma yi mamaki matuka da saurayi irin wannan a shekarunsa zai zauna cikin wannan matsala ba tare daya nemawa kansa mafita ba duba da yadda zamanin ya sauya." “Alhamdulillahi Indai wannan ne damuwar zamu nemo masa maganinta nan kusa bada jimawa ba.” Mom bata iya sake cewa komai ba har suka gama maganar sannan likitan ya sallame su, jiki ba kwari Mom suka shiga ɗakin da aka kwantar dashi, tausayinsa ne yarufeta tasa hannu ta shafa kansa tana kallon fuskarsa, tabbas dole ta amince da haɗin da Dady ke son yi masa da yar abokinsa, zata saka a fara yimata bincike akanta in sha Allah da zarar ya samu sauƙi, murmushi Dady yai yana sauke ajiyar zuciya "Yanzu hankalinki sai ya kwanta kin ji dai ba abinda ke damun yaronki, ɗago kai tayi ta kallesa ta maida kallonta ga Rayyan tana jin wani abu aranta data kasa misilta ko meye, ajiyar zuciya ta sauke itama, Dady yace "Yanzu muje gida gobe sai mu dawo zasu kula da komai.” "No I can't kawai ka tafi bazan iya barinsa anan shi kaɗai ba." Dady ya ɗan jima kafin yatafi yabar Mom kamar yadda ta buƙata saboda yaransu dake gida. Kwana ɗaya Rayyan yai washe gari da marece aka basu sallama, wata irin kulawa Mom keba Rayyan tamkar shine jaririn ɗanta, gaba-daya ta hanasa yai komai da kansa, da kanta ta haɗa masa ruwan wanka ya shiga yayi tasa Nayla ta kawo masa abinci, ta gyara masa ɗakinsa da kanta ta fidda masa da kayan da zai saka, bayan ya fito ya shirya cikin kaya marasa nauyi ta zauna da kanta ta bashi abincin abaki har sai daya ci ya koshi, kallonsa tayi "akwai abinda ke damunka yanzu? Ya kake ji?” Ta tambaya cike da kulawa, Rayyan da tunda aka sallamo shi wani irin nauyin Mom yake ji duk da bai ga wani sauyi a fuskarta ba dake nuna tasan ainahin matsalarsa, amma sai yake ji a jikinsa kamar wannan karon ta fahimci komai, Nayla ce ta shigo ita da Suhayla "Ya Rayyan afternoon how was your body?” "Alhamdulillah." Ya faɗa yana kallon yadda ta caɓa kwalliya, ta fahimci dalilin kallon da yake yi mata, don haka tayi murmushi cike da son neman izini tace “Yaya dan Allah zan je gidan Uncle Usman Amnah was invited me since 2days ago, jiya naga baka jin daɗi shiyasa ban tambayeka ba Please ya." Tai maganar dan tasan zai iya hanata, Mom Rayyan ya kalla ta kauda kanta gefe “Baza ki je ba." Ya faɗa ba tare daya kalleta ba, Nayla kamar zatayi kuka ta matso inda Mom take ta zauna kusa da ita “Please Mom dan Allah." Ta ɗora kanta a saman kafadar Mom, Mom ta ture kanta daga kafadarta, ta mike tana cewa "Ba ruwana wannan tsakaninki da yayanku ne idan ya amince." Matsowa Nayla tayi zata fara yimasa sakalci ya ɗaga mata hannu yana kallonta "zaku iya tafiya ke da Suhayla amma after 5 na marece ki tabbatar kin dawo gida, zan kira John ya sauke ku.” Gefen pillow ya ɗauko wallet ɗinsa ya ciro kuɗi ya miƙa mata, cike da farinciki ta karɓa tana godiya duk da taji haushin cewa da Suhayla zata je. Cinkin farin ciki Nayla suka shiga gidan Uncle Usman tana ƙwalawa Amnah kira, Amnah tafito da gudu suka rungume juna “Ke yar air na ɗauka baza ki zo ba fa da ban ganki ba jiya." Amnah ta faɗa suna riƙe da hannun juna ita da Nayla, Suhayla kuwa can gefe ta nufa inda ta hango su Mahbub da Ikramah ana yi masu lesson dan sune sa'anninta musamman Mahbub da suke matukar shiri dashi, dariya Nayla tayi “Bari kawai Amnah kin san Yayanmu ba lafiya jiya aka sallamosa daga asibiti shiyasa baki ganni ba." “Hmm ai na ɗauka ma shiya hanaki zuwa tunda baya son zumunci kuma yana hanaku.” " Laaa.. wallahi kin masa sharri ba haka bane." Nayla ta faɗa tana kallon gun da akewa su Mahbub lesson jin wata murya data tafiyar mata da hankali na dukan dodon kunnenta, idanuwanta ne suka sauka akan Uncle Sajid dake yiwa Ikramah faɗa kan rashin maida hankali, a ɗaya ɓangaren kuma yana taya yan uwanta yi mata dariya yadda yai mata wani question ta kasa amsawa. Lumshe idanuwa Nayla tayi ta sake buɗe su akansa, lokaci ɗaya taji wani abu mai ƙarfi ya dira a zuciyarta akansa, wani yanayi da bata taɓa tsintar kanta aciki ba ya ziyarceta, ƙaƙƙarfan wani irin sinadari taji kai tsaye na tasowa daga cikin idanuwanta mai kama da wutar lantarki yana neman isar da wani saƙo ga mutumen da bata taɓa gani ba, bai santa ba itama bata san shi ba, gaba-daya ta rikice ta kasa tsayar da natsuwarta sai juyowa take yi tana kallonsa. “Ke Nayla lafiya kike?" Muryar Aunty Zeynab data zo gidan zata tafi suka kusan cin karo ta faɗa fuska a ɗaure, da sauri ta dawo hayyacinta daga duniyar data tafi ta wucin gadi, sai dai har yau maganaɗisun dake kokarin janta wajen sanin ko waye wancan mutumen data gani bai saketa ba, "Wlh Amnah na rikice.” "Da akai uwar me? Ko rashin ganin girman mutane ne da kika gado wajen uwarki zaki nuna mun, har ina miki magana kina cewa kin rikice." Aunty Zeynab ta faɗa a ɗan hasale cikin ɓacin rai, maganar ta daki zuciyar Amnah, ta ji rashin jin daɗin kalaman a zuciyarta, amma bata ce komai ba, a yanzu ba lokaci ne da take fahimtar komai ba saboda zuciyarta ta tafi wani gun, gaida ita tayi tana bata hakuri, tsaki zeynab ta ja tana ci gaba da masifa da faffaɗar maganganu marasa daɗi akan Mom, Nayla na kin zafinsu amma ta saurara saboda ba yadda zata yi, haka Aunty Zeynab ta ƙarasa masifa ta tafi tana jin haushin Nayla ɗin, taso ta tanka mata ta nada mata shegen duka a gidan, so take ta rage zafin mahaifiyarta dake zuciyarta na tsawon shekaru amma ta rasa ta wace hanya zata iya yin hakan, Nayla nada hankali, duk yadda aka zagesu a cikin family ko aka ci zarafin Mahaifiyarsu, zata ji zafin har tana ji kamar ta rama amma bazata taɓa zuwa ta sanar da ita ba, takan sha damuwar ita kaɗai wasu lokutan saboda bata son su ci gaba da musgunawa mahaifiyarta idan har taje ta faɗa wani abun ya faru. Zeynab ko dama a hasale take da Mahaifiyarsu Amnah ke sanar da ita rashin lafiyar Rayyan da Uncle Usman ke sanar da ita ɗazu daba kowa ya ji ba, kasa hakuri tayi har ta isa gida akan hanya ta kira Mom tayi mata tas “bamu san kin fimu son Rayyan ba sai kin cire jininmu dake jikinsa kin musanya da naki jinin, waya sani ma ko ke kike neman ajalinsa kike so ya mutu ku gade dukiyarsa shi yasa kikai kane-kane kika hana kowa ya raɓesa, ai wallahi kin ji haushi kuma indai Rayyan ne sai mun nuna miki mun fiki karfi akansa dan zai dawo hannunmu dole, wawiya mai raba zumunci kin dai ji kunya saboda you're after his money.” Mom na zaune a falo ne tana kallo Zeynab ta kira wayar ta ɗauka, duk abinda take faɗa Rayyan na jiyota daga cikin wayar, shigowarsa kenan falon yazo ya zauna akusa da mom ɗin, sosai ransa yai mugun ɓaci da kalaman ƙaunar mahaifin nasa, idanuwansa suka kaɗa sukai jajir, zuciyarsa tayi zafi tamkar ana tafasata da sauri ya miƙe ya wuce ɗakinsa, ba'a jima ba ya sauko cikin shiri riƙe da makullin motarsa ya nufi kofar fita, bayansa Mom da zuciyarta ke lulluɓe da kunci tabi tana kiran sunansa cike da son dakatar dashi, sai dai ko data isa harabar gidan har ya tada motar da karfi ya fizgeta yabar gidan “Ya Salam." Ta faɗa tare da komawa ciki ta dauki wayarta tana kiransa, amma sai taji karar wayar ya barta anan falo… _Aunty Zeynab da alama yau kin taro match ɗin da baza ki iya bugawa ba, mu dai munce Rayyan karka yimata da sauki amma ya kuka gani ku?_ . ZK2026 08081005693 07040402435. ZUCIYA DA ƘUNA By Billy S. Fari & Nana Hadiza @nanadiso10 | Arewabook PAGE 9. Cikin zafin rai Rayyan ya isa gidan kakannin nasa, parking yai ya fito ya nufi cikin gidan yana ƙwala mata kira ba tare daya tsaya amsa gaisuwar da masu aikin Didi kakarsa ke yimasa ba “Zeynab.." ya faɗa da ƙarfi lokacin daya ƙarasa bangaren nasu, Mémé da fitowar ta kenan toilet tana bin bango tana ƙoƙarin fitowa daga ƙuryar ɗaki tace "Waye anan?” "Méme ina Zeynab take?" Rayyan ya faɗa cikin kaushin murya “Au! Wai dama Ummaru kaine? Har yaushe zaka dena kiran sunan Zainy haka a matsayinta na ƙanwar mahaifinka ka girmamata” har ya juya zai fita ba tare daya tankata ba sai kuma ya ja ya tsaya bakin ƙofa, second uku zuwa huɗu ya juyo ya kalli Mémé, ya saki wani miskilin murmushi “haka nike bana girmama wanda be girmama mahaifiyata ba”. Daga haka ya fice da falon ya nufi sashen Didi Mémé sai tsige masa take yi tana fadar Baida mutunci, Didi suna tare da Zeynab saboda tana dawowa sashenta tanufa tana faɗa mata karya da gaskiya akan zancen rashin lafiyar ta Rayyan da ita kanta bata san da ita ba, Didi na faman faɗa suka ga Rayyan bakin kofar dakin fuskar nan a murtuƙe tamkar anyi masa mutuwa. Gaban Aunty Zeynab ya fadi amma sai ta wayance, fuskarta ɗauke da murmushi “ɗan halak! Yanzu muke zancen ka da Didi Mike cewa an jima zamu je dubaka ashe har ma ka samu sauƙi...” kallon da yake yi mata yasa ta kasa ƙarasa zancen tare da yin ƙasa da kanta, Didi ce dake ta faman aika masa da harara itama tace “kayi tsaye ka tsare mu da idanuwa sai kace wuɗanda ake tuhuma ka kasa ƙarasowa daga ciki, ka shigo tunda Allah ya baka lafiya bai sa aka zo aka sanar damu zancen mutuwarka ba. Ace kayi ciwo har ka kwanta asibiti babu wanda ya zo ya sanar damu dan munafurci wannan ai rashin muhimmantamu ne a lamarinka” Ajiyar zuciya ya sauke yana ɗan danne ɓacin ransa da tsanar Aunty Zeynab da yake ji a zuciyarsa "Didi ba wannan ya kawo ni ba, nazo na jawa zeynab kunne ne a karo na ƙarshe akan mahaifiyata." Fizgo kai zainab tayi jin abinda ya faɗa cike da takaici, zuciyarta na wani zafi take kallonsa shima idanuwansa na akanta yace “Yes i mean it, stay away from my mother, enough is enough Wannan ya zamo na karshe da zaki sake faɗar munanan kalamai a kanta saboda bazan ci gaba da ɗaukar miki ba, wallahi ina da dama ruwan sama wannan bai isa ya dukar mun mahaifiya ba balle wani mutum domin ban haɗa darajarta data kowa ba, ki tsaya a matsayinki kafin nayi miki rashin mutuncin da bazaki taɓa mantawa dani ba.” Zaro idanuwa Zeynab tayi "Rayyan ni kake faɗawa haka? Ni kake cewa zaka yiwa rashin mutuncin ina matsayin kanwar ubanka, kenan bare ya fini a wajenka?" Didi da duk takaici ya ishe ta gane cewa da tayi duk wannan abun akan Fatima yake yinsa, tsaki ta ja, ta tashi cike da takaici zata bar ɗakin “Na ɗauka ganina kazo yi ashe rashin kunya kazo yi mana akan Fatima! Macen da zuciyarta babu Allah acikinta ta rabaka da kowa daga ita sai ɗiyanta, hmmm mu juri zuwa teku tulun zai fashe.” Zeynab ta taɓe baki “Ai na faɗa miki Didi makirar macece ta kwarai wallahi, ki ƙyaleshi yai abun duk da zai yi amma wlh Fatima sai ta wulaƙanta acikin family din nan indai ina da rayuwa..” Zeynab bata rufe baki ba taji saukar mari fauuu a fuskarta, cike da mamaki ta ɗago kai, idanuwanta dishi-dishi take gani amma ta tabbata basuyi mata karya ba wanda take gani a gabanta a matsayin ɗanta shine ya mareta, hannun Rayyan na rawa idanuwansa sun kaɗa sunyi jajir saboda tsananin ɓacin rai, kalaman da Zeynab ta faɗa akan Mom ɗinsa sun matukar koma masa rai tare da taɓa masa zuciya da har ya iya kai mata mari ba tare daya sani ba, abu guda ya sani a duniyar nan babu wanda ya isa ya taɓa mutuncin Mom agabansa ko shi waye ya ƙyalesa, Didi kuwa sai sallallami take yi ta riƙe Zeynab tana kallonsa da mamaki itama, nunata ya shiga yi da yatsa yana son yimata kashedi na ƙarshe sai dai zuciya ta kashesa ya kasa yin magana, dai-dai lokacin Dady da Rayyan na fita daga gida mom taje ta sanar dashi abinda ke faruwa ya shigo, sai daya shiga sashen Mémé bai isko Rayyan ɗin ba sannan ya nufo na Didi, saurin ƙarasa shigowa falon yai ya riƙe hannun Rayyan ɗin da atunaninsa ƙoƙarin sa ma Zeynab hannu yake yi, bai san mai gama har ta riga ta gama ba, kallon Didi yai ya kalli Rayyan haɗe da jan hannunsa “Ya kamata ku sani matsayin kowa daban acikin ku wajensa, bai kamata wasu abubuwan kuna yinsu agaban idanuwansa ba domin ita zuciya bata da ƙashi kuma an halicce ta da son wanda ke kyautata mata.” Yana gama fadar haka ya jasa suka fice, a kan hanya Dady tuki yake yana kallon Rayyan, bai taɓa ganinsa cikin irin wannan matsanancin fushi ba sai yau, murmushi ya ɗan saki yana maida hankalinsa akan titi, ya sani yadda yake son Mom ɗin tasa zai iya nuna fiye da wannnan ɓacin ran akan duk wanda ya taɓata, a haka suka isa gida da sauri Mom ta taso ta riko hannunsa ta zaunar dashi akan kujera, ruwa mai sanyi ta dauko ta bashi ya sha kafin ta fara yi masa faɗa tana haɗawa da lallashi akan ya dena kula duk abinda zasu yi mata ko zasu faɗa kanta, yan uwansa ne su da bazai taɓa samun kamarsu ba idan ya ɓata dasu, Rayyan ya kalli Mom, ya riko hannuwanta biyu “Mom ke kadai kin isheni a duniyata, na yarda narasa kowa narasa komai matukar ke, Dady da kuma ƙannena kuna tare dani.” "Duk da haka aryan ɗan uwa ɗan uwa ne, kaka, ƙanen uwa ko wan uwa da uba duka suna a gurbin iyayenka ne a Musulunci, zamani ne yake basu wannan sunan na kaka da kawunni da Gwaggo da sauransu, ka daure ka riƙa basu girmansu dan Allah kaji?” ya rungumeta yana jin wani sanyi a ransa, ya lumshe idanuwa, ya sauke wani lumfashi mai zafi haɗe da ajiyar zuciya "Mom kibar wannan zancen and on behalf of Zeynab Ina baki hakuri abinda tayi miki.” a jikinsa ta cirosa ta ɗan ɗaga hannu saiti a fuskarsa kamar zata maresa tace “Not Zeynab Aunty Zeynab ko kuma ka faɗa Gwaggo” Dariya ya saka shi da Dady dake zaune saman kujera yana kallon su cike da soyayya, yana kaunar Fatima bisa kyautatawa, soyayya da halaccin data yi masa yadda ta riƙe masa ɗan ɗan uwansa, haka kuma yana jin Rayyan a zuciyarsa tamkar ɗan daya haifa, tun tashinsa bai taɓa bata masa rai ba ko ya sashi abu yaki yi masa, haka kuma bai taɓa hanasa abuba yayi wannan dalilin yasa kullum yake ƙara jinsa a ransa. Hannun Mom data ɗaga Rayyan ya riƙo ya sumbata, Dady ya janyo pillow ya jefa masa yana cewa "Bar mun mata haka kazo naji yaushe ka shirya, kaima na tattaraka na miƙaka a hannun taka matarka kona huta da rigimarka." Kallon Mom yai “Mom da gaske?" “To me muke jira, ina dai kana son Hanan ɗin duk da baku san juna ba?" Kunya ce ta dan kama Rayyan, ya miƙe yana sosa kai ya nufi sama ɗakinsa “In dai kina sonta Mom shikenan ko ban santa ba ina sonta nima." Murmushi Mom ta saki tana ƙara jin kaunar yaron nata a ranta, ana cewa ƙaunar uwa da ɗa daban ce, amma har yau ita ta kasa banbance ƙaunar da take yiwa su Nayla da tasa. "Zan so su fara ganin juna Alhaji kafin ayi zancen komai, na fara bincike kan tarbiyyar yarinyar data mahaifiyarta ban samu negative wani abu daga wajensu ba, amma duk da haka zan kara bincike sosai saboda bana son na aurowa yarona fulawa a juji ko kuma bara gurbi acikin mata." “Hakan ba laifi nima zan kara yin wani ta ɓangarena duk da nasan ko waye Alhaji Nuhu shattima, amma gudun tuhumar ki koda nan gaba, zan kara bincikawa saboda tsoronki nake yi Indai akan ɗan can naki ne tofa na sani ba kida sauƙi kuma bakya barin bashi.” Dariya duk suka sa a tare, nan take ya sanar da ita akwai wani taro da zasu yi na wani kasuwanci da zasu ƙulla da manyan yan kasuwa kuma har da alhaji shattima aciki, in sha Allah yana tunanin zai yi magana dashi Hanan tai representing nasa shima zai sa Rayyan ya wakilcesa a gun, Daga nan in suka haɗu sai a fara maganar ta yadda kowanensu zai faɗi ra'ayinsa tunda sun hadu da juna, sosai Mom taji daɗin wannan plan Saboda tafi so Rayyan yafara ganinta kafin aje ayi maganar haɗasu auren, dama weekend ne ranar Monday za’ayi taron, don haka zata tashi da daddare tayi masa addu'a Allah ya tabbatar masu da duk abinda yafi Zama alkhairi. ZK2026 08081005693 07040402435. ZUCIYA DA ƘUNA By Billy S. Fari & Nana Hadiza @nanadiso10 | Arewabook PAGE 10. Nayla basu dawo ba sai after magrib Rayyan yaje da kansa ya dauko su, dama yayi waya da ita yace su jirasa zai zo ya ɗauke su, tafe suke Suhayla sai labari take zuba masa kamar yadda suka saba yi masa aduk lokacin da suke tare, sai dai wannan karon banda Nayla bata ce komai ba tunda ya ɗauko su, ba tare daya kalleta ba yana driving “Nayla what's happening?" Juyowa tayi ta kallesa jiki a sanyaya, a yau kaɗai, acikin awannin da basu gaza biyar zuwa shida ba ta faɗa soyayyar wanda bata taɓa gani ba sai yau, soyayya mai zafi da tunda tayi ido biyu dashi sai nukurkusar zuciyarta take yi, gashi takasa fadawa ko da Amnah ce balle ta samu sassauci abinda take ji, ji take yi kamar tai karfin halin sanar da yayan nata sai dai bata san taya zata fara yi masa bayani ba, ɗauke kanta tayi tana kallon gefen fito jin ya sake jefo mata tambayar "nothing Yaya.” "Are you sure?" “Up course." Jin ta tabbatar masa da haka sai kawai ya share zancen, a wani mall ya tsaya ya shiga dasu, abubuwan duk da yasan suna bukata a matsayinsu na mata yasa suka ɗauko Mom kuma ya siyo mata turarukka sanin yadda take masifar son ƙamshi, dama duk wata yakan ɗaukesu ya kai, ko kuma yaje da kansa ya siyo masu, tun suna yara shi ke maye masu gurbin Dad idan baya ƙasar har ma idan yana nan wajen kula dasu ga duk abubuwan daya san zasu buƙata ba tare da gajiyawa ba saboda yana kallon hakan a matsayin dolensa, a ransa yana ji bai da kamarsu kamar yadda basu da kamarsa, shiyasa ya dauki alwashin zame masu Yaya mahaifi wajen basu kariya da kuma kulawa ga dukkanin abinda zasu buƙata. Bayan sun gama suka nufi gida Nayla jiki tamkar an yimata duka kai tsaye ta wuce ɗakinta, Allah ne sheda matsuwa tayi su iso gida dan duk wanda ta gani sai taga yana mata gizo da wanda ta gani gidan su Amnah, hatta Ya Rayyan ɗin da suna magana da Suhayla taga yayi dariya sai taga tamkar shi ɗinne lokacin da yake yiwa Ikramah dariya “Ya Allah! Wanene shi?" Nayla ta faɗa kan gadonta tana faɗa tare da rufe idanuwa. _(Tofah! Nayla ta ɗebo mai zafi zafi💃)_ MONDAY MORNING Kamar yadda Dady ya faɗa haka ta kasance, tun kafin ya sanar da Alhaji Nuhu Shattima ƙudurinsa na don haɗa yar wajensa da tsaronsa Rayyan yana kiransa akan zancen taron yake sanar dashi bazai samu damar halarta wajen taron ba saboda tafiya Egypt ta kamasa zai kai mahaifiyarsa a dubi idanuwanta da take fama dasu suna yimata ciwo, amma ya sanar dashi zai sa Hanan ta wakilcesa wajen ya tabbatar duk abinda ake buƙata daga ta ɓangarensa zata bayar yadda Yakamata, murmushi Dady yai, a zuciyarsa yana cewa faɗuwa tazo dai-dai da zama, a zahiri kuwa cewa yai babu Matsala bayan ya jajanta masa tare da cewa ya bayar masa da Hajiya idan sun dawo zasu zo dubata shi da iyalinsa, a cikin daren ya kira Rayyan ya sheda masa yana da wani taro da zai halarta yana so shima yake ya wakilcesa a wajen wannan taron, ya bashi duk wasu documents daya kamata, ya yi masa bayanin duk wani abu da za'a gabatar saboda kusan shine jagoran taron, sosai Rayyan ya fahimci bayani sa har yana sake bashi shawarwarin abunda ya dace a wasu wuraren, Dady ya ji daɗi hakan dan haka yace yaje duk abinda ya kamata a gabatar, idan ya dawo daga baya zasu tatfauna matsayar da aka cimma wajen taron da manyan yan kasuwan. Karfe 8:30am Rayyan ne ya sauko a gurguje saboda karfe tara za'a gudanar da taron ya ɗan so ya makara, MOMY na kitchen ya saketa acikin yai hugging ɗinta ta baya yana gaisheta, gefen fuskarsa ta shafa “Masha Allah" tana miƙa masa mug din dake hannunta data gama juya tea, yasan bazai tsaya yin kari ba saboda makarar da yai, hakan yasa yana kuran tea ɗin tana saka masa yankin sandwich a baki, bai ci ci uku yai ba da yake team ɗin ba zafi ya karasa shanyewa ya ajiye cup ɗin " Bye Mom.” " Bye my son kayi tuƙi a hankali kaji? ALLAH ya taimaka ya baka nasara." Ta dan ɗaga murya dan tuni ya fita, hannaye ta daga sama “Ya Allah ka haɗa hankalinsu idan ita din alkhairinsa ce kuma matarsa ce." “Amin" ta ji Dady ya faɗa shima daya fito cikin shirin sa, dining suka nufa ya karya sannan ya fice ita kuma Mom takoma ɗaki bayan ta dawo wajen yi masa rakiya tana mai addu'ar Allah ya dawo mata dasu duka lafiya. Ɗakin taro mai fadi a wani katafaren gini a Paris. Hasken rana mai laushi na shigowa ta manyan tagogi, yana bugawa kan tebur mai sheƙi da matuƙar ɗaukar hankali saboda tsaruwarsa, kana gani kasan wajen tattaunawa ne na manyan mutane akan wani kasuwanci ko wata mafita da ake son samowa ko kuma cimma matsaya akan wani abu, cike yake da manyan yan kasuwa na ƙasar dake neman hadin guiwa da kamfanin kasuwanci na Alhaji Haroon Kareem, kowa ya samu waje ya zauna kujera biyu kacal ce babu mazauna a wajen sai tattaunawa suke yi a tsakaninsu, a dai-dai lokacin ƙofa ta buɗe a hankali, Rayyan ya shigo cikin nutsuwa amma da iko a tafiyarsa. Sanye yake da dark tailored suit deep navy colour mai kyau, Farar riga ce aciki sai tie mai launin dark wine da takalmi baƙi mai sheki (classic Oxford shoes), Agogo ne mai tsada ɗaure a tsintsiyar hannunsa, gashin kansa gyararre sai sheƙi yake yi, ƙamshinsa ne mai sanyi da jan hankali yasa mutanen dake cikin ɗakin juyowa, a hankali ya ƙaraso ciki takalmansa na bada sauti mai karfi kaɗan ya nufi kujerar da yake da tabbacin wajen zamansa ne, cike da mamaki da al'ajabin ganinsa don bashi sukai tsammanin gani ba mutanen dake dakin suka shiga gaishesa. “Good morning, Mr.” Sai sukai shiru kuma, a hankali bayan ya isa jikin kujerar ya lalle su duka yace "Rayyan." Yana ɗan sauke kai kasa kaɗan alamun girmamawa tare da ƙawata fuskarsa da murmushi sannan ya zauna. Idonsa ya zagaya ɗakin ya hango kujerar ɗaya daba mutum, agogon hannunsa ya duba karfe tara dai-dai, ɗago kai yai zai yi magana ƙofar ta sake budewa a karo na biyu, Kyakkyawar matashiyar yarinya ce ta shigo, takalmin heels ɗinta na bada sauti mai laushi, Sanye take da tailored suit na mata launin soft grey (Paris classy tones) jikinta ya fito da tsari mai kyau amma cikin mutunci. Hannunta na rike da takardu ta yane kanta da mayafi idanuwanta saye da glass da yai matuƙar yimata kyau, takalminta heels ne masu tsayi amma simple nude, Karamin handbag mai kyau luxury but subtle, fuskarta ta ɗanyi Make-up light, natural glow, cikin nutsuwa da kima take takowa kana kallon ta kasan akwai tsantsar ilimi da wayewa tare da ita, Ba ta kallo kowa ba ta nufi kujerar da ita kaɗai ta hango babu kowa akai tana passing ɗin ta Rayyan ta ja ta zauna, a kallo daya zaka fahimci she's Intelligent, calm, amma akwai hidden fire atare da ita, wani irin yanayi mai nauyi ya cika ɗakin, Rayyan ya ɗan ƙanƙance ido kamar mai nazarinta yana haɗe fuska ganin bata cewa kowa komai ba bayan ita kadai ya rage da ake jira, ta ɗago kai kaɗan ta gaida mutanen wajen cikin girmamawa, dan janye idanuwansa Rayyan yai da tana juyowa suka hadu da nasa, kirjinsa ne ya buga lokacin da idanuwansu suka haɗu yana ji kamar ya taɓa ganinta amma ya sani ba su taba haduwa ba da ita ko sau daya idan ba yau ba, me ke shirin faruwa ne akan yanahin da yaji nan take kanta? Saurin bayarwa yai jin wurin yai shiru. Kokarin fara Meeting ɗin akai, nan take aka gabatar da proposals tare da tattaunawa mai zafi akan yadda abun zai kasance daya shafi kasuwancin, bayan an kammala Hanan dake zaune, idan ta kalli wannan yana magana ta kalli wanca, ta mike cikin nutsuwa, ta fara magana da kwarjini tana gabatar da nasu proposal dini, bayan ta gama tace “Wannan tsarin zai kawo sauyi a kasuwa matuka idan aka tsaya aka duba abin da kyau.” Mutane suna sauraronta tare da jinjina kai. Rayyan kuwa dake kallonta Ba wai proposal ba ne ya dauke hankalinsa akanta ba, Ita ɗin ce da kanta. Bayan ta gama sai ya ɗan jingina baya cike da sanyi “Interesting… amma ba practical bane.” Dakin ya yi shiru. Hanan ta kalle shi kai tsaye, yadda yai maganar daga ƙarshe ya balain ɓata mata dai “Ko kuma kai ne ba ka son ganin wani ya fi ka?” Karamin hayaniya ta kare wajen jin yadda tai maganar itama, Rayyan ya dan murmusa na raini kaɗan. “Ki tabbatar kina fahimtar abinda kike fada kafin ki kalubalance ni saboda muna amfani da hujja mai ƙarfi ne” ya jingina da kujera, hannunsa a hade, idanunsa suna kallon Hanan da wani irin zafi, Hanan kuma ta kauda kai cikin nutsuwa amma fuskarta na nuna karfin hali. Ta dora takardu a gaban ta, tana kallon Rayyan kai tsaye. Rayyan yasa hannu ga janyo takardun ya duba abinda ke ciki sannan ya mayar ya rufe ya sake tura mata “Wannan proposal din naku ba shi da tushe. Ba zai yi anfani ga kasuwa ba, balle kamfaninmu.” Hanan ta ɗan yi murmushi kaɗan, irin wanda ke nuna ba ta ji tsoro ba sannan tace “Ko kuma dai kai ne ba ka so kuyi rashin nasara ba saboda proposal ɗin nan zai iya zarce naku sau uku.” Wani daga cikin mahalarta ya yi kokarin shiga tsakani, amma Rayyan ya ɗaga masa hannu saboda game ɗin tasu nishadi take bashi musamman yadda take haɗe rai, Rayyan yana kallonta sosai yace “Kin tabbata haka? Wannan fa ba wasan yara bane.” Hanan ta matsa gaba kaɗan, idanunta suna haskawa da jarumta “Ni ba yarinya bace da zaka raina, Rayyan or what?. Kuma bana magana sai da hujja.” Shiru ya ratsa ɗakin. Kowa ya tsaya kallon su. Rayyan ya dan sunkuyar da kai, yana murmushi kada, amma wannan karon ba raini bane, wani sabon abu ne yake ji a ƙasan zuciyarsa akanta, Ya ɗaga ido ya sake kallon ta a karo na ba adadi… _Ana wata ga wata, me ke shirin faruwa ne? Aryan ya faɗa soyayya shima a kallo ɗaya, ata ɗaya ɓangaren ya bawa iyayensu zavin su aura masa wacce suke so ba tare da sanin itace wadda zuciyarsa ke so, shin Hannan zata bar abinda ya faru a office tsakaninsu idan aka haɗasu ta karbi soyayyarsa ko kuwa zata ki amincewa ta karɓi soyayyarsa? Ku biyo mu muje_🏃‍♀️ ZK2026 08081005693 07040402435