An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ZAYYANA 1 and 2 Littafin Nazir Adam salih (c) Nazir Adam Salih Created and design by :- Shuraih Usman . Daga Nazir Adam Salih 1- Kibiyar Ajali 2- Me Yafi Kudi ? 3- Ta Leko Ta Koma 4- Birnin Sarauniya 5- Naira Da Kwabo 6- Aci Bulus 7- Mutuwar Kasko 8- Alakakai 9- Wa Na Kama ? 10- Hindu 11- Ruhina 12- Dare Da Rana 13- Karya Linzamin Shaidan 14- Cuta Ta Dau Cuta 15- Iska Mai Kada Ruwa 16- Bindigar Kwali 17- Damisar Takarda 18- Aziza 19- Tsohon Alkawari 20- Kai Da Jini 21- Aljani Ya Taka Wuta 22- Sai Mutuwa 23- Kudi Da Maciji 24- Kisan Boko 25- Kura Da Kan Rago 26- Murmushin Alkawari 27- Zayyana. . DON Halima Umar Tudun Maliki. . ZAYYANA Copyright (c) Nazir Adam Salih 2008 . Hakkin Mallaka (H) Nazir Adam Salih 2008 . TARIHIN DAB'INSA An Fara Bugashi A Kamfanin KAMNAS PUBLISHERS Dakata Kano A Shekarar 2008. . GARGADI Ba'a Yarda Wata Qungiya Ba Ko Wani Mutum Ya Juyi Wani Bangare Na Wannan Littafi Ba Ta Hanyar Wasan Kwaikwayon Majigi Ko Kuma Wani Abu Daban Saida Izinin Marubucin. . ADIRESHI Abubakar Sadik Islamiyya Dakata Kano Akwatin Waya 4792. . ZAYYANA Nazir Adam Salih (NAS) . FADILA Wata dankareriyar mota jeep baka kirin kirar kamfanin marsandi tayi fakin akusa da wani munafikin lungu dake wata unguwa acikin birnin Kano. Ga wanda ke tsaye awaje bazai iya ganin wanda ke cikin motar ba domin gilasan motar masu duhu ne sosai anyi musu dare jim kadan da tsayawar wannan mota sai kofar gidan gaba ta motar ta bude ahankali sannan aka zuro wata santaleliyar kafa kyakkyawa fara sol da ita kamar kafar balarabiya daga cikin motar sannu ahankali takalmi mai tsini wanda ke dauke da santaleliyar kafar ya sauka acikin cabin ruwan saman da ake ta makawa kamar da bakin kwarya tun da garin Allah ya waye. Duk da yake ana kiran Sallahr Azahar ruwan yadan tsagaita amma har izuwa yanzu karfe uku na rana yayyafar kananan kwayoyin ruwan basu daina sauka akan doron kasa ba. Kofar motar ta dada budewa sosai sannan sai wata kyakkyawar halitta doguwa tafito daga cikin motar Zuwat. Tana rausaya kamar macijiyar data fasa kai kyakkyawa ce ta gaske ga duk wanda yasan me ake cewa KYAU haka nan kamar yadda kafafunta suke haka nan ma sauran jikinta yake fari sol kamar balarabiya me yiwuwa kuma ga wanda baiyi yawon duniya ba ya iya kuskurenta amatsayin shuwa arab, to amma agaskiyar al'amari iyayenta fulani ne gaba da baya. Kyakkyawar halittar tayi tsaye bakin kofar motar tana duban ciki lokaci guda kuma ta gyara dan yalolon gyalen dake dafe akanta kana ta dada jan damammiyar rigar silikin dake jikinta kasa sannan daga karshe saita zato wata farar lema daga cikin motar ta budeta akanta domin ta kare yayyafar ruwan dake zuba haryanzu akan doron kasa kyakkyawar ta dada gyarawa lemar tsayuwa a saman kanta sannan saita dubi wasu kyawawan yan mata su hudu dake cikin motar suma farare sol dasu kamar ya'yan larabawa fuskarta a murtuke amma kyawunta ya karu. Ku zauna anan kuyi jirana kada ku sake naga wata shegiya acikinku ta biyoni saura kuma ku koma gida ku fadawa mama munzo nan sainaci uban yarinya. Tana gama fadin haka saita rufe kofar motar da karfi a fusace sannan ta nufi munafikin lungun cikin sauri. . Sunan wannan kyakkyawa FADILA kuma adaidai wannan lokaci data nufi wannan munafikin lungu cikin sauri sa'o'i ashirin da uku kacal suka rage adaura mata a aure da sahibinta FAISAL. Mutumin da take kauna fiyeda kowa aduk fadin duniya zakuma ta iya tsallake maganar kowa domin ta farantawa faisal hakanan Fadila na iya bata ran ko wane in dai zai taba mata Faisal watanni tara da suka gabata watarana da yamma suna hira akatuwar farfajiyar gidansu Fadila acikin motar faisal sai faisal din ya kalli hannun fadila yaga duk an zane shi da kunshin zamani wasu irin surori ne na furanni da siraran ciyayi kamar na bakin kogi masu kyawun gaske. bakin zanen yayi matukar fitowa akan fararen hannun Fadil. Kai amma yau kin kara kyau Fadilata Faisal yace yana kallon bakin zanen dake hannunta Fadila ta lumshe idanuwa cikin farin ciki wani irin sassanyan dadi ya mamayi zuciyarta jin cewa ta farantwa Faisal Allah ko? To nagode tace tana wani farfarar da idanu Faisal ya mika hannunsa zai taba hannunta cikin sauri ta dauke hannunta cikin dariya tace Menene? Da Allah kawo hannunki na gani a ina akayi miki wannan zanen kunshin mai kyau haka? Cikin murmushi fadila ta mika masa hannunta ya rike yana kallon zanen kunshin Wata mata ce take.... Yi mana Fadila tayi masa karya domin abinda faisal bai sani ba shine wani katon dan daudu ne wai shi AMARA yakeyi musu wannan zanen kunshin da ace Faisal yasan gaskiyar al'amarin da ace yasan cewa zanen ya kamane tun daga kan kafafunta da hannuunta har zuwa kan cinyoyinta sannan daga kan cibiyarta zuwa kirjinta da wuyanta da babu abinda zai hana zuciyarsa bugawa domin yana tsananin kishin fadila wannan ce ma tasa tun da yake zuwa hira gurinta bai taba zuwa da aboki ba sai sau daya shima daga nan bai kara ba domin ya fahimci tun da sukazo idanun abokin akan Fadila yake. To My Faisal tace gamida hadawa da turanci dan haka ayanzu da fadila ta nufi munafikin lungun gidan dan daudun ta nufa domin ya zane ta da furanni tun daga sama har kasa domin burinta shine ta ruda faisal adaren amarcinsu na farko ashe kuwa bata sani ba wannan kunshin ba karamin Rudashin zaiyi ba. . Sannu ahankali fadila ta kawo izuwa kofar wani gida wanda shi kadai ne acikin lungun tayi mamaki sa'ar dataji kamar gidan shiru bata jiyo hayaniyar mata ba. Tayi sa'a yau ba layi tace cikin zuciyarta abinda daman take tsoro kenan domin Allah Allah take yi tazo agama mata ta koma gida kada ta dade mahaifiyarta ta tambayeta inda taje. Tuni mahaifiyarta tayi tofin Allah tsine da wannan kunshin kada in sake ganin kinyi wannan sakarcin shashashar banza shashashar wofi in banda wauta irin ta ya'yan zamani yaushe zanje gaban wani kato in bude masa cinyoyina da kirjina wai yayi min zanen kunshi kada ki karayi babu kyau ko macece yar uwarki bai kamata taga tsaraicinki ba ballantana wani katon banza munafikin dan daudu idan kika sake yin wannan kunshin Fadila to wallahi bada yawuna ba Fadila ta tura baki gaba kamar tsuntsuwa tana gunguni tundaga. wannan rana bata karayin wannan kunshi ba sai awannan rana tafito yiwa Faisal dinta kunshin da yake so ta riga ta kuduri aniyar ko mahaifiyarta bata amince ba sai tayi wannan kunshin tunda faisal dinta yana so. . Fadila ta shiga farfajiyar gidan sannan kai tsaye ta wuce wani falo inda anan ne tasan mata ke taruwa su jira kafin azo kansu duk wacce akazo kanta saita bi dan daudun abaya su shiga wani dan daki inda anan ne zata tube ya zaneta tun daga sama har kasa. Salamu alaikum kwan kwan fadila ta kuma cewa shiru ba'a amsa ba me yiwuwa ya fita sayen sinadaran kunshin ne Fadila tace aranta domin tariga ta sani wata sa'ar ana cikin kunshin sinadarin ke karewa sai AMARA yafita ya sayo musamman lokaci irin na bikin sallah, dan haka sai fadila ta nemo kujera daya ta zauna sannan ta dauko daya daga cikin mujallun kasashen turai dake warwatse akan wani tebur dake tsakiyar dakin ta fara karantawa domin ta raka lokaci kafin Amara ya dawo . Adaidai wannan lokacin ne wata sassanyar iska mai sanyin gaske ta fara ratsowa cikin dakin nan da nan fadila taji jikinta ya dauki rawa domin sanyin iskar cikin bargonta yake shiga ko kusa ko alama iskar batayi kama da iskar damuna ba jikinta na rawa fadila ta dago kai daga kan Mujallar da take karantawa ta dubi kofar falon inda take tsammanin tanan iskar ke fitowa ga mamakinta sai taga duk da wannan sassanyar iskar mai karfi dake shigowa labulayen taga da kofar falon basa motsi kai hatta takardar mujallar dake hannunta bata motsi gashi kuma haryanzu iskar na kadawa. . MAMA Karfe uku da minti goma daidai wata tsohuwar tasi ta nufi munafikin lungun tana tafiya tana kara rukukuku kamar tsohon keken shanu tana tafiya tana bulbular da farin hayaki kamar jirgin kasa. Kai wannan wace irin mota ce anya kuwa ba kamawa tayi da wuta ba? Wata doguwar mata dake zaune abayan motar ce take fadawa direban ba'a bakinki nafara jin hakan ba 'Yan mata sau uku kenan yau ana cewa in tsaya in kashe wuta basu san ba motarce ahaka so nake idan kin sauka na wuce gurin gyara direban yace dan tsatstsama ne busashshe mai tarin gashin baki kamar ciyawar bakin kogi sanye da doguwar riga da hula amma samanta ya cizge kamar bera ya gwagwiya saboda yawan shekarunta a duniya. Ni wannan mota da nasan haka take da wallahi ban shiga ba ga tsada ga babu sauri ga kuma shegen hayaki. Direban ya shafi gashin bakinsa sannan ya juyo da kansa ya dubeta. In banda tsohuwar motace yaya zan dauko ki shata tun daga Na'ibawa har nan a naira tamanin kema dama ai san banza ne yasa kika tsayar dani. Kaga juya can ka isheni da surutu lura da gabanka Wallahi ga kwanan nan agabanka Matar tace dashi cikin Karaji. Direban ya juya da sauri adaidai lokacin ne to ya hangi katuwar Jeep din baka agabansa. Saukeni anan matar tace. Dan tsatstsaman direban ya daddage ya taka birki yana ciccije baki dakyar gamida kama sandar giya ya samu ya tsayar da motar adab da gindin Jeep din. Yayi ajiyar zuciya sannan ya dubi matar da murmushi yace. Dana bugawa danyen kwannan dake gabana ai da zurawa zanyi aguje na barki acikin tsohuwar motar nan. Matar ta harare shi sannan ta zaro naira dari ta dungura masa a kasan hanci gashi nan ka rike sauran chanjin ashirin din ka cika ka sayi sabon inji. Kafin direban ya sami damar mayar da martani tuni har matar ta bude kofar ta fice abinta. Shegiya Kilaki direban yace yana kallon bayanta. Cikin sauri doguwar matar ta nufi cikin munafukin lungu tana tafiya tana girgiza bangarorin jikinta kamar wata bishiyar kanya lokacin iskar hunturun sanyi doguwar matar farace amma farin dan kanti ne baza a iya kiranta kyakkyawa ba amma tana da daukar hankali Allah ya hore mata kyan kirar jiki wanda ke tattare da wani mayen karfe mai karfin gaske wanda ke fizgo hankalin mazaje izuwa gareta musamman wadanda shaidan yafi karfin zuciyarsu. Wannan doguwar mata mai kyakkyawar jiki ma'abocin sinadaran mayen karfe sunanta MAMA akalla dai hakanan yan uwanta karuwai yan duniya suke kiranta a bariki to amma wani tsohon dan bariki wanda ya dade da saninta tun tana karama a mahaifarta GOMBE ya taba cewa da Babbar kawarta BEBI. Wai kinsan sunan kawarki kuwa na gaskiya Bebi ta girgiza kai menene sunanta na gaskiyar ZULAIHAT Uhm bebi tace dashi a yatsine wannan kai ta shafa tsohon munafiki meye na fada min sunanta na gaskiya kuda bakwa rabuwa da munafurci. . Ayanzu haka da mama tashigo layin tana rausaya sai ka kira sunanta Zulaiha akalla sau hudu kafin ta iya tunawa ma da sunan ne domin rabon da akirata da wannan suna tun tana garinsu Gombe yau kusan shekaru shida kenan da suka gabata. Zulaihat ko kuma Mama yar gidan wani tsohon direban jirgin kasa ce wanda Allah yayiwa rasuwa tun tana karama Mahaifiyarta talatu tsohuwar yar duniya ce tana yawonta suka hadu da mahaifin mama a tashar jirgin kasa dake garin GURU sa'ar daya tsaya sauke fasinjojin jirgin kasan basufi wata biyu da fara harkar bariki ba suka auri juna sa'ar da mahaifin mama yakai mahaifiyarta Gombe jama'a....... jama'a sunyi mamaki da akace dasu karuwa ce ya auro akayita surutu wasu sukace wai asiri tayi masa ya aureta wasu ko sukace a'a wai cikin shege sukayi dan haka suka auri juna abinda jama'a basu sani ba shine dalilin auren mahaifan ma dalilai ne masu sauki na farko dai mahaifin mama ya auri mahaifiyarta ne saboda kyawun jikinta kuma bazai iya ganin kowane namiji yana mu'amala da ita ba itako mahaifiyar mama ta auri mahaifinta ne saboda ta fahimci akaluum kwanan duniya baya rasa kudin kashewa ya sai musu tsire suci kasu su sha nono ya kuma dinka mata duk irin suturar da take so. . Mutuwar mahaifin mama keda wuya sai ungulu ta koma gidanta na tsamiya to saidai kuma awannan lokacin tsohuwar ungulun tsufa ya risketa batareda ta sani ba dan haka sa'ar da mahaifiyar mama ta dawo barikin ma babu riba domin babu mai kulata sai dattijan banza wadanda dayawansu matsiyata ne wadanda suka dorawa kansu masifa sa'ar da mama takai shekara goma sha tara sai tabi sahun mahaifiyarta domin abinda ta gani kenan tanayi nan da nan sai bakar kasuwa ta bude mata ba'afi shekara guda ba ta baro Gombe zuwa kano to saidai kuma tazo arashin sa'a domin tazo ne alokacin da aka kaddamar da shari'ar musulunci a kano karuwanci ya zama babu riba in ma za'a yi saidai a boye sannu ahankali shekaru hudu suka shude mama tana kano to saidai abubuwa sunja da baya matuka domin mama ta lura duk da kyawun jiki irin nata ta sami wadanda suka damata suka shanye hakanan saita fahimci kamar karuwan ma anfi son farare dan haka sai mama ta fara bilicin nan da nan ta kwaile ta koma fara jajuz duk da wannan ungulu da kan zabo da mama tayi hakanta bai cimma ruwa ba domin haryanzu a cikin kawayenta ita kadaice bata da motar hawa ana cikin wannan haline to kwatsam rannan da rana sai babbar kawarta dake abuja wai ita Bebi ta bugo mata waya. Hello kawata kina ina. Maza ki hada naki ya naki ki taho nan abuja muci karenmu babu babbaka babu wanda zai tsangwamemu da zancen shari'a kinga daga zuwana har wani dan majalisa yabani mota Ke ki bari don Allah. Mama tace cikin kaduwa. Wallahi kuwa kawata ai kema kina kan hanya kuma mota kamar kin samu domin jiya muna tare dasu wani honorabil abokinsa yaganki a hotunan da muka dauka aruwan tiga yace lallai saina kawo masa ke..... Saboda haka duk abinda kikeyi saiki bari ki taho abuja amma fa sai kin gyara jikinki da kyau kizo musu a hade. Wannan kalma ta karshe ita tasa mata shigowa munafukin lungun cikin sauri domin tazo Amara ya zaneta tun daga sama har kasa irin yadda zata ruda honorabil din da kawarta Bebi zata hadata dashi. Gobe har wahaka na rabu da wannan jaraba anbi an hanamu rawar gaban hantsi da wata shari'a sai inga uban da zai bimu abuja ya hanamu abinda muke so Mama tace aranta sa'ar data karaso farfajiyar gidan Amara dan daudu mai zanen kunshin zamani. . Sannunki mama tace da fadila ayatsine sa'ar data shigo falon mama taja kujera ta zauna sannan ta kalli kyakkyawar surar fadila nan da nan saita sami kanta tana mai fatan inama itace Fadila Da ko babu kunshi sai na sace zuciyar honorabil. Mama tace cikin zuciyarta. Yana ciki ne? Mama ta tambayi Fadila nima ban same shi ba inajin dai kasuwa yatafi sayen kayan hadi fadila tace bakinta na rawar sanyi. Baiwar Allah lafiya naga kina rawar sanyi? Naga kamar ai zafi akeyi ko? Mama ta girgiza kai aini da'ace da fanka ma kunnawa zanyi mama na rufe bakinta sai taji sanyin ya soki cikin kashinta. Kai Wallahi nima nafara ji wannan wanwe irin sanyi ne? . FARIDA. Da wani dattijo da wata budurwa yar makaranta suka shigo munafukin lungun cikin wata mota honda kirar Ali dari tara da casa'in da takwas dattijon shike jan motar budurwar na zaune abaya da yan littattafanta da takardu agefenta akan kujerar motar jakarta ajje akan cinyarta. Dattijon direban yayi fakin akusa da katuwar jeep din sannan ya dubi budurwar da tun tana yar kankanuwa yake tuka takata a mota direban gidansune. Ko ba nan bane lungun da kike fada? Nan ne budurwar tace da dattijon to saidai fa na jiraki anan kinga mota bazata iya shiga lungun ba kuma dan Allah kiyi sauri kinga ina mayar dake zan koma dauko yan uwanki. Budurwar ta bude kofar motar lokaci guda kuma tana kokarin bude jakarta. Dan Allah idan munje gida kada kace munzo nan kaji BABA ALI Dattijon ya dubeta cikin mamaki me zakiyi anan din? Kunshi ne za'ayi min ka gane to amma hajiya bata so na tafi ko ina indai yayi nesa da gida to ni kuma agaskiya irin wannan kunshin sai anan kawai za'a iyamin irin shi. Zaki dade kenan Baba ali yace yana dubanta cikin damuwa Gaskiya zan dade tun da idan da akwai layi ma dole saina jira. A'a kinsan bazata yiyu ba idan muka koma gida amakare banje dauko yan uwanki ba me kike tsammanin zan fadawa Hajiya? Budurwar ta dubeshi cikin damuwa haba baba ali kaifa nawa ne kasan ai bama haka dakai nasan bazaka rasa abinda zaka fadawa hajiya ba ta danyi shiru sannan saitaci gaba dacewa cikin sauri kokuma me zai hana kaje yanzu ka dauko su salima din ka mayar dasu gida nasan kafin kadawo ko ba'a gama min ba kadan zai rage. Kuma idan hajiya ta tambaye ni kina ina ince mata me? Budurwar ta dubi dattijon da murmushin wasa tace Haba Baba Ali basai kace da ita ina makaranta bamu tashi ba.... Uhm Uhm ko kuma dai kace da ita wani malami ne yasa mana Lecture darasin da bamu san dashi ba sai kace Sai biyar zamu tashi tana gama fadin haka saita zaro naira dari biyar daga cikin jakarta ko lankwasa babu ta mika masa. Ga wannan ka sayi goro....saika dawo din inajiranka. Eh to kema fa kinzo da dabara tabbas haka zan fada mata. Baba Ali yace a daidai lokacin da budurwar ta fice daga motar sannan ta nufi MUNAFIKIN LUNGUN cikin sauri. Koda dattijo baba ali ya tuka motar sai ya murza sabuwar naira dari biyar din da budurwar ta bashi sannan yace wai dole dai sai ya'yan zamani sun sa dattijo yayi karya to da sauki ma tunda da karyar banza zanyi ba. . Budurwar ta mike zuwa cikin layin tana tafiya tana yan waige waige a tsorace domin ta fahimci lungun babu mutane aciki me yiwuwa ruwan saman da aka wuni ana shekawa kamar da bakin kwarya ne duk ya kori mutane. . Wannan budurwa sunanta FARIDA ILYASU yar gidan wani tsohon kwamisha ce awannan lokacin daliba ce a jami'ar Bayero ta kano kuma tana shekarar karatunta ta karshe ne a bangaren tsimi da tanadi. Farida gajeriya ce amma kyakkyawa ta gaske ma'abociyar iya kwalliya dasa sutura tayi daidai ajikinta kamar dama da ita aka halicceta bayan karatun tsimi da tanadi da takeyi ahalin yanzu babu wani abu da farida ta kwarance akai irin tsabar ruwan ido. Kullum acikin sauya samari take bata zama da saurayi daya yau in ka ganta da wancan gobe saika ganta da wannan. Saurayi agurin farida ba wani aiki bane kamar yadda sauya rigar dake jikinta bai zama aiki ba. Duk da yake dai bata samari biyu ko lokaci guda amma duk wanda ta hadu dashi an fara soyayya rimi rimi ba'a fin sati biyu ko uku sai su rabu duk saurayin kuwa dayayi wata guda tare Farida ba karamin mai hakuri bane. Watarana farida tana kwance sai irin yadda take sauya samari kamar riga ya fado mata dan haka sai ta fara lissafin adadin samarin datayi soyayya dasu daga lokacin data shiga jami'a kawai ba karamin kaduwa tayi ba sa'ar dataga sun doshi hamshin da wani abu. Watarana da safe ana dab da za'a fara jarrabawa farida na zaune akan faffadar matattakar dakin karatu na sabuwar jami'ar Bayaro cikin damuwa domin ta shiga dakin karatun ta tarar ya cika da dalibai babu gurin zama dan kowane dalibi fama yake da karatun jarrabawa gashi kuma ita in ba'a dakin karatun ba bata iya karatu a ko ina ba. Tana nan zaune sai taji agefenta na dama ance Sannunki. Juyawarta keda wuya sai sukayi ido biyu da wani saurayi dan kwalisa mai matsaikacin tsaye sanye da damammiyar riga fara ta kama jikinsa kamar fata da kuma wando na jeans baki. Yauwwa sannunka dai Farida tace a yatsine sannan ta dauke kai gefe guda. Saurayin ya zauna akusa da ita yace a tausashe kema baki samu guri bane? Uhm wallahi ni na rasa ma inda zani farida tace tana dubansa akwai wani abu a tattare dashi dake sawa idan ta kalleshi bata iya hakuri saita sake juyowa. Muje zuwa na baki guri saurayin yace da ita yana satar kallon siririyar girar idonta. Kai ka tashi daga karatun ne? Farida ta tambaye shi cikin mamaki saurayin ya girgiza kai. Yanzun nan nafara amma tunda ke baki samu ba saina hakura na baki gurina domin da ganinki nasan bazaki iya karatu ako ina ba sai a dakin karatu kinga ni kuwa ako ina agindin bishiyar can ma sai inyi zamana nayi karatuna ban damu ba. Ya kake magana kamar wani malamin duba? Farida tace cikin murmushi domin tafara jin dadin hira dashi. Kamar kin sani idan kina so ma yanzun nan sai in fada miki abinda kike ci kafin kifito daga gida. Ah rufa min asiri bawan Allah saikace wani tsohon maye. Suka fashe da dariya sannan ta bishi a baya suka shige dakin karatun. Aranar da dare farida ta sallami saurayinta na hamsin da uku 53 acikin shekara uku sannan ta maye gurbinsa da sabon saurayinta KABIR. To saidai kuma tun daga ranar dayazo gidansu na farko farida bata kara ganinsa ba. Ga mamakinta saitaji ta kasa samun sukunin zuciya kullum a neman kabir take gashi bai ma fada mata abinda yake karantawa ba ballanata taje tsangayarsu nemansa haka nan ko lambar wayarsa bata karba ba. Rannan da safe sai sukayi Kicibis dashi a kofar dakin karatu ''Ka Kyauta kabir wato har guduna ma kakeyi ko? Farida tace muryarta a raunane. Ba haka bane farida kin gane wato abubuwa ne sukayi yawa....kuma ina dan tsoro. . Tsoron me? Tsoron ki farida bazan boye miki ba ance bakya iya zama da saurayi duk yadda kuke dashi sai kin jefar dashi kinga kuwa ai bazai yiwu in kai kaina makasa ba ko? Farida ta matso dab dashi cikin takaici sannan tace daga kanka na gama saurayi kabir nayima alkawari baka ganin wadancan samarin su suke sona kai kuwa ni nake..... Tayi shiru bata karasa ba cikin kunya. Tun daga wannan rana alkadarin farida ya karye akaro na farko a tarihin farida ta shafe.ta shafe sama da wata shida da saurayi daya kuma abin bakin ciki da takaici shine haryanzu nan kabir bai damu da farida ba sosai ba watarana saitayi sati biyu bata ganshi ba amma duk da haka ko gaisawa da wani saurayin batayi dan kada kabir ya ganta ransa ya baci rannan sai farida takai kukanta gurin wata kawarta adakin kwanan dalibai. . Kwata kwata bai damu dani ba ASMA'U na rasa yadda zanyi in shawo kansa kinga rannan ma tare da SAFIYYA na ganshi cikin mota suna ta hira Asma'u ta dubi kawarta tace wacce irin hira kukeyi dashi? Ban fahimce ki ba farida tace cikin mamaki kina nufin hira...wacce hira zamuyi data wuce irin wacce kowa keyi hirar fatar baki. To anan kuskurenki yake yanzu ke ko dan irin kissing sumbatarsa din nan ma bakyayi? Farida ta girgiza kai haba Asma'u yaya zan bar mutumin da ba mijina ba ya taba jikina. Aikuwa sunanki sorry dan wallahi safiyya kwace miki shi zatayi kinaji kina gani haka fa Rukayya sani taso ta kwace min usman dina saida na dage da kyar da yan dabaru na kwatoshi kinga ma wannan saboda shi nayi Asma'u tace lokaci guda kuma ta yaye cinyarta a gaban farida babu kunya babu tsoro sannan ta da daga mata rigarta ta fito da kirjinta a fili. Farida ta dubi kyakkyawan zanen kunshin zamanin dake kan cinyoyin Asma'u da kirjinta baki na rawa tace. Gaskiya ni kunya nakeji yaushe zan bari har kabir yakawo nan. . Asma'u ta fashe da dariya ai kuwa kinaji kina gani za'a rabaki da dan Darling dinki ni kinga nawa Usman din da zarar munyi Graduation zamuyi aure. Kaini dai bazan iyaba Wallahi da haka farida tabar kawarta Asma'u. . Fitowarta keda wuya kamar cewa fito muna jiranki sai farida ta hangi kabir dinta zaune agindin wata bishiya dake gefen dakunan kwanan dalibai shida safiyya ta dora santala santalan hannayenta akan kafadarsa suna hira da shewa cikin farin ciki. Farida taji kamar an watsawa zuciyarta garwashin wuta ba zata yiyu ba tace cikin zuciyarta sannan sai SHAIDAN yaci karfin tunaninta hannunta na rawa ta dauko wayarta daga cikin jakata ta bugawa Asma'u Hello Kawata yaya akayi ne ko mantuwa kikayi? Asma'u ta tambaya acan daya bangaren. Na mance ne ban tambayeki inda akayi miki wannan zanen kunshin ba. . Har zuwa lokacin da farida ta shiga farfajiyar dan daudu Amara idanunta basu daina nuna mata hannayen safiyya akan kafadar masoyinta ba. . Salamun Alaikum......sannunku farida tayiwa Fadila da mama sa'ar data shigo falon. Dan Allah anan ne ake kunshin nan? Fadila ta dubeta da murmushin yake domin haryanzu sanyi takeji. Eh nan ne kema saiki jira mu ma shi muke jira. Zaman farida keda wuya saitaji wata irin iska mai sanyi ta fara ratsa kashi da bargonta nan da nan taji jikinta ya fara rawa. Kai wannan wane irin sanyi ne? Mu ma haka muka tarar dashi mama tace cikin damuwa sannan saita dada da cewa ko waje zamu fita mu jira shi Ina ganin dai gaskiya zaifi fadila tace ta fara mikewa kenan. . Sai sukaga wani irin farin hayaki ya rufe kofar dakin sassanyar iska taci gaba da hurowa cikin dakin. . Me kuma zakuyi awaje bayan gani nazo ko bani kuke jira ba kanne na? Wata zazzakar murya tace dasu daga cikin hayakin. ** ** ** ** ** Matan uku suka dubi kofar dakin a tsorace cikin tsananin firgici sannan ga mamakinsu sai sukaga hayanin ya washe kamar ma ba'a halicce shi agurin ba. Sannunku da zuwa. Amara dan daudu yace dasu shine a tsaye akofar dakin maimakon farin hayakin. Nashiga uku mama tace tana duban amara a tsorace wannan wane irin hayaki ne amara duk kabi ka tsorata mu. Kuyi hakuri kannena dan daudu amara yace dasu. Wani sabon sinadari ne mai sanyin hayaki nake turara mutane dashi kafin nayi musu zane idan akayi haka yafi fitowa rangadadau. Da kuka shigo bakuji sanyi ko ina ba? Matan uku suka dubi juna sannan sukayi ajiyar zuciya munji suka amsa baki daya. Amara ya dube su da murmushi wacece tafara zuwa acikin kannen nawa? Fadila ta mike tsaye gamida duban agogonta har yanzu jikinta rawa yakeyi batasan abinda yasa ba amma har yanzu a tsorace take duk da yake wannan shine karo na kusan hudu da za'ayi mata kunshin sa'ar data dubi Amara saitaji gaba daya hankalinta bai kwanta dashi ba. Muje to nafara dake kanwata Amara yace da fadila sa'ar da yaga ta mike tsaye Suna nan zaune acikin Dakin Amara yagama zane kirjinta yadawo zuwa kan cinyoyinta. Yau naga kamar baka son hira Amara kamar ba kai ba ko baka ganeni bane? Fadila tace dashi yi hakuri yar uwata ai ina shigowa na ganeki....wallahi dan karin kudin sinadarin aikin nan ne aka samu duk yabata min rai. Bayan wani lokaci mai dan tsayi Amara yagama zane Fadila da mama wadanda suka dawo dakin jiran kusan jikinsu tsirara suka zauna akan wani kilishi mai taushi acan karshen falon domin su jira zanen ya bushe kafin kuma daga baya su wanke sannan sai a goga musu sinadarin Hydrogen wanda shike sa zanen yayi baki adaidai lokacinda amara yana can cikin daya dakin yana zane Farida. Ana cikin wannan hali ne kofar falon dake fuskantar waje ta bude sannan Fadila da mama suka yi duba I zuwa abunda ya dada sasu cikin firgici a tsaye abakin kofar dakin AMARA ne sanye da doguwar Jallabiya fara. . Sannunku da zuwa Amara yace dasu yana kallon zanen kunshin dake kan cinyoyinsu da kirjinsu. Mama ta dube shi cikin kaduwa tace Sannunmu da zuwa ina...yaushe ka fito daga dakin harka fice waje bamu ganka ba? Amara ya dubi mama cikin mamaki yace Ke Ja'ira kada kiyimin sharri ni rabona da gidan tun safe ina kasuwa ruwa ya rutsani sannan sai ya kalli zanen kunshin dake jikinsu yace. Wanene yayi muku wannan ku kukayi da kanku? Kada ka raina mana hankali mana ba kai ka gama yi mana zanen ba ina dayar da kakeyiwa? Inka gama mata ai gara kazo kasa mana Hydrogen din nan ko ma tafi mun dade anan mama tace. Ki rufamin asiri in mutu yan mata su kaini kinga ni tun da gari ya waye yau banyiwa kowa zanen kunshi ba. Jin haka keda wuya sai Fadila ta mike tsaye a tsorace ta dubi Amara tace. Kana da dan uwane yan biyu? Amara ya girgiza kai kafin tagama magana sai sukaji acan daya dakin Farida ta kwala ihu nan da nan su uku suka nufi dakin a tsorace suna shiga dakin suka tarar da Farida rabin jikinta tsirara an gama zaneta cinyarta dayace kawai ta rage babu zane. A ina yake mama ta tambaya a tsorace farida ta dubesu cikin kuka tace YA ZAMA HAYAKI. . Amara ya dubi sararin samaniyar dakinsa sai ya hangi sauran farin hayakin a makale. Na fada muku bani bane to in ba kaibane wanene? Fadila ta tambaye shi kamar zata fashe da kuka. Hahahahhaha wata kakkausar murya ta fashe da dariya sannan sai sukaji daga sama ance KUNYI KUNSHIN KARSHE YAN' MATA. . BABI NA DAYA 1 Hayaniyar biki gamida farin cikin ganin Faisal ya zama nata su suka mantar da Amarya Fadila rudanin daya faru agidan dan daudu Amara da farko sa'ar da aka shiga hayaniyar bikin duk kusan minti biyar sai gaban Fadila ya fadi idan ta tuna sa'ar da kakkausar muryan nan ta kece da dariya to amma daga baya sa'ar da kawaye da yan uwa gami da abokan arziki suka zagayeta sai zuciyar Fadila ta shagalta izuwa shagalin bikinta to amma fa duk da haka jifa jifa takan tuna kalmar Amara sa'ar da kakkausar muryar ta kece da dariya. Meye naga kunyi wani zuru zuru daku kamar kunyiwa sarki karya? Amara yace dasu sa'ar dayaga matan ukun sun dubi saman dakin a firgice. Kaga dan Allah amara idan wani ka boye yake bamu tsoro to kace ya bari ni wallahi bana son irin wannan wasan mama tace dashi. Yau na shigesu ni Amara kinjini da yan mata wai maganar me kuke ne? Kai kurma ne bakaji dariyar da akeyi a saman dakin nan ba? Duk abinda akeyi Fadila na gefe jiki na rawa kamar mazari ita ko magana bata iyayi jim kadan da gama maganar mama sai farida ta ruga aguje ta fice daga dakin ganin haka sai fadila da mama suma sukabi bayanta a gurguje suma suma fice daga cikin gidan. Yau Allah ya hadani da mahaukatan mata oh ni 'yasu in da ranka kasha kallo amara yace sannan ya taba cinya gami da shewa abinsa. . Kanwata. Mama tace Fadila a daidai lokacin da suka zo karshen munafikin lungun in ba damuwa ki bani lambar wayarki mana make gaisawa ba dan komai mama ta tambayi lambar wayar fadila ba sai don kawai taji aranta tana kaunarta domin tana son taga farar mace kyakkyawa domin wannan shine kawai abinda ya ragu a jarinta na karuwanci. Kawo wayarki nasa miki fadila tace da mama tana kallonta rabi a tsorace rabi kuma a yatsine tabbas mama bata kwantawa fadila azuciya ba domin tun sa'ar da mama ta shigo ta sameta a falon dan daudu fadila ta lura da tambarin bariki akan fuskar mama. In badan rudanin daya samesu tare ba da babu abinda zaisa fadila ta baiwa mama lambar wayarta. Nagode bari nayi miki Flashing saikiyi sebin din lambata mama tace sa'ar da fadila tasa mata lambar wayar. Mintuna uku da faruwar haka fadila shiga cikin Jeep dinta ta wuce mama tsaye abakin titi tana jiran tasi. Mama ta dagawa fadila hannu amma fadila bata damu da ta rama mata ba. . Duk wannan al'amura sun zama tarihi a gun amarya fadila anyi biki lafiya an tashi lafiya an kaita dakin mijinta babban masoyinta Faisal mutumin da take kauna fiye da kowa aduniya. Adaren amarcinsu na farko bayan kawaye da abokan ango sun tafi sun barsu su kadai daga fadila sai angonta faisal wanda shima mahaifinsa na da abin hannu amma bai kai mahaifin Fadila ba. Awannan dare ne to abinda Fadila ta dauka tamkar wani shudadden mafarki kokuma wata binnanniyar gawa ya fara FATALWA. Zaune suke a dakin kwanansu akan wani fankadeden gado na alfarma wanda akalla zai iya daukan mutum biyar batareda kowa yaji hucin dan uwansa ba. Fadila ta dubi faisal sannan faisal ya dubi fadila sai suka fashe da wata tattausar dariya lokaci guda cikin farin ciki. Dariyar me kakeyi? Ke dai zan tambaya dariyar me kikeyi? Masoyan suka sake yiwa juna murmushi Faisal barci nakeji. Fadila tace dashi tana lumshe idanu cikin wata shagwababbiyar murya. To ki kwanta mana ko so kike na kwantar dake Uhm fadila tace gami da gyada kai. Faisal ya matso kusa da ita ya dora hannayensa akan kafadarta cikin murmushi sannan yafara kokarin kwantar da ita. Uhm Uhm ni ba anan zan kwanta ba Fadila tace tana wata girgiza cikin shagwaba. To fadila a ina kike son kwanciya? Anan fadila tace gamida nuna cinyoyinsa. Faisal ya fashe da dariya fadila kenan duk fadin gadon nan ki rasa inda zaki kwanta sai akan cinayata. Nidai anan zan kwanta fadila ta kuma fadi cikin shagwaba faisal yayi ajiyar zuciya sannu ahankali sai fadila ta kwanta akan cinyarsa ta yadda fuskokinsu zasuke kallon juna fuskar faisal dauke da faffadan murmushi ya kamo santala santalan hannayenta Fadila. Ya kallesu sannan sai ya dubeta cikin mamaki. A ina zanen kunshin da nace inason kiyi min duk ranar da za'a kawomin ke? Fadila taji gabanta ya fadi ras da faisal yasan abinda maganar zata janyo da baiyi ta ba. Nan da nan sai wani zazzafan gumi ya fara sartu akan dogon wuyan fadila hankalinta ya tashi tunaninta ya yamutse lokaci guda kuma ta fara tunanin irin karyar da zatayiwa faisal domin tasan haryanzu akwai shatin zanen da aljanin nan yayi ajikinta to saidai bai fito sosai ba domin ba shafa masa sinadarin hydrogen ba sa'ar da gayyar ta watse gashi kuma bata san ta sabawa faisal dan tasan yanada zafin zuciya idan ranshi ya baci. . Yaya naji kinyi shiru? Faisal yace da ita cikin murmushi da kuma mamaki domin ya lura kamar yanayin fuskarta ya sauya haka nan ta sandare ajikinsa shagwabar da takeyi baki daya ta bar jikinta. Nayi ma laifi my darling fadila tace cikin wata sassanyar murya alokaci guda kuma kwakwalwarta na kokarin nemo abin fada. Haba fadila laifin me kikayi min? Kisan fa ance wai amarya bata laifi koda ta kashe dan masu gida. Kunshin da kace nayi ma ne ba'a gama ba muka baro gidan an gama zanen kenan za'a sa hydrogen sinadarin dayake sa shi yayi bakin nan sai mama tayi min waya tace nayi maza na koma gida ana jirana duba ka gani zaka ga ma shatin zanen Fadila tace lokaci guda kuma ta mika masa hannayenta tana daga kwance. Faisal ya dubi hannayenta cikin murmushi yana nazarinsu Fadila kenan ke dai in bakiyi ba kawai shikenan ba sai kinyimin karya ba ni banga sanen komai ahannunki ba. . Jin haka keda wuya sai fadila ta bar jikinsa ta tashi zaune. Haba Darling yaya zanyi ma karya bayan ga.....kalmar ta makale acikin fatar bakinta domin ta lura ko sama ko kasa Allah masani amma zanen dake hannunta ya bace baki daya kamar ma ba'a taba zana shi ba. Faisal ya dubeta cikin murmushi sa'ar dayaga kamanninta sun sauya ta firgice cikin sauri ya janyota jikinsa yana cewa. Haba Fadila me yayi zafi haka da har zaki tashi hankalinki adaren amarcinmu na farko? Dan bakiyi kunshi ba ai ba wani laifi bane nan gaba idan inaso basai muje duk inda kike so ayi miki ba. Fadila ta kankame shi gamida ajiyar zuciya ta tabbata mintuna biyu da suka gabata kafin ta kwanta akan cinyarsa ta lura da zanen ahannunta tayaya kuma za'ace ya bace cikin mintina biyu? Tambayar kenan datayiwa kanta babu Amsa. ** ** ** ** Washegari da la'asar sakaliya misalin karfe biyar da rabi amarya fadila ta fito daga wanka daure da wani farin tawul tattausa ajikina tana tafiya tana yauki kamar zata tsinke ta zauna akan waata doguwar kujera dake gaban wani kyakkyawan madubi na musamman da akayi mata shi don Kwalliya. Tun da garin Allah ya waye fadila ke tare da angonta suna ta wasanni na soyayya bashi ya fita ba sai karfe hudu acewarsa abokai zaije yiwa bangajiya. Kada ka dade don Allah.....ni banason zama ni kadai awannan katon gidan fadila tace dashi sa'ar daya shirya zaifita kanta akan kafadarsa. Bazan dade ba my....karfe takwas ina gida. To shikenan fadila tace cikin shagwaba kataho min da wani abu mai dadi karkiji komai idan zan dawo zan zo miki da TUBANI. La.. Me zanyi dashi fadila tace cikin dariya tubani ba shine wanda na karanta a littafin KARYA LINZAMIN SHAIDAN wai wani tsoho yanaci ba. Ko bashi kake nufi ba? Shi nake nufi mana my darling faisal yace cikin dariya. Cab. So kake kenan in mutu idan na hadiyi wannan abin ai sai ankaini asibiti. Suka fashe da dariya lokaci guda da haka suna tafiya suna hira hannayensu kamar zasu shafi juna ta rakashi har farfajiyar gidan inda motocinsu na hawa guda hudu ke tsaye sunyi jerin sahu faisal ya zabi wata karama kirar honda ya hau. Fadila na tsaye a farfajiyar gidan tana daga masa hannu har saida ya fice. Lokacin data dawo fankacecen dakin shakatawar na alfarma saitaji duk kadaici ya lullubeta hakanan duk saitaji gabanta nata faduwa hakan shiyasata kunna talabijin sannan ta kamo tashar kasar larabawa wata balarabiya yar masa masar ce mai katon baki take cashewa amma katon bakinta bai hana makwagoronta feso waka mai dadi ba. Fadila ta lume cikin daya daga cikin kujerun alfarma da suka zagaye dakin kofin tangaran dauke da tacaccen lemo ahannunta na hadun taci gaba da kallon wake waken larabawan wannan shiya dauke mata damuwa har zuwa sa'ar da taga yakamata ta tashi ta sake wanka domin taren mijinta faisal tana fitowa daga wankan sai saita nufi Madubi. . Daga inda take zaune ayanzu tana fuskantar madubin fadila na iya jiyo rugugin aradu sakamakon hadarin dake lillibe da sararin samaniya hakanan amaryar na iya hangen shuke shuken alfarma da furanni na zamani wadanda ke jere sahu sahu a farfajiyar gidan abin gwanin ban sha'awa sunata rangaji cikin iskar daminar kamar yan amshin shata. Fadila ta dawo da hankalinta kan madubin ta fara nazarin hannayenta da kafafunta da kuma kirjinta cikin mamaki da fargaba domin ko kusa ko alama duk shacin zanen nan da akayi mata ya bace babu alamunsa ko da kankane. Na rabu da jaraba fadila tace gamida ajiyar zuciya kana saita shafi goshinta ga maminta saitaga kamar ta fara gumi sannan ne to ta lura shema na'urar sanyaya dakin ba'a kunne take ba gashi kuma garin ya daure babu iska sakamakon bakin dake ta haduwa. Fadila tasa wani farin mataji ta korashi tsakanin siraran gashinta sannan ta mike ahankali ta nufi inda makunnar na'urar sanyaya daki take ta kunna sannan ta dawo gurin zamanta ta zauna taci gaba da shafe shafe irin na mata batafi k minti guda da zama ba saitaji iskar na'urar ta fara sanyaya dakin fadila tayi ajiyar zuciya sa'ar da sassanyar iskar ta fara ratsata lokaci guda kuma taci gaba da nazarin surorin jikinta a fuskar mudubin tana yabawa da abinda ta gani ita kanta tasan kyakkyawa ce wata sa'ar tana kwalliya ne kawai saboda dai wai ance sabo da tayi wai gawa da yatsine amma fadila tasan ko batayi kwalliya ba ita kyakkyawa ce. Iskar na'urar sanyaya dakin taci gaba da fifita fadila ganin ruwan wankan dake jikinta yafara bushewa sai fadila ta matso wani tattausan mai fari daga cikin wata doguwar roba mai kamar jallo ta fara shafawa ahannunta daga nan sai kirjinta sai kuma kan cinyoyinta zuwa sangalalin kafadunta bayan ta gama saita dago ta sake nazarin jikinta a fuskar madubin sannan ne to taga abinda yasa numfashi da yawun bakinta daukewa. A zane radau radau tun daga kan hannayenta da kirjinta zuwa kan cinyoyinta zanen kunshin nan ne na surorin furanni baki sidik ya bayyana a fili abin gwanin ban sha'awa saidai kuma fadila bata san daga inda zanen ya bullo ba. . Na shiga uku fadila tace a firgice gami da dake kirji lokaci guda kuma ta dauke fuskarta daga kan madubin a tsorace ta dubi sassan jikinta a zahiri har yanzu zanen kunshin na nan randagagu ajikinta ba wai madubin ne ke fada mata karya ba. Na shiga uku....wayyo Allah fadila tace cikin karaji sa'ar data fara ja da baya da baya a tsorace tana barin jikin madubin. . Baki shiga uku ba matata.... Ki kuma bi ahankali kada ki takani don gani nan tsaye abayanki ina yabawa da abinda na aura. Wata busashshiyar murya ce ke fada daga bayanta fadila ta rufe baki domin ihun ma yakasa fita daga makogwaranta ta juya ta dubi bayanta cikin tsananin firgici wayam bataga kowa ba. Wanene? Fadila ta tambaya cikin wata murya data kasa ganewa amatsayin tata. Wani mai sha'awar surar jikin ne.... Zanen kunshin nan ya karbe ki bazan taba daina kaunarki ba muddin ina kallonsa. Aka sake kecewa da kakkausar dariya sannan sai farin hayaki ya turnuke dakin. Acan wani bangare na sararin samaniyar birnin kano aka saki rugugin aradu mai karar gaske fadila ta toshe kunnuwanta sannan ta fadi rub da ciki akan tattausan kilishin dake daben dakin. ** ** ** ** Fadila ta farka agigice daga nannauyan barcin rudanin daya dauketa sannu ahankali ta mika hannu ta dauko wayarta dake ajje akan gadon kusa da ita ta duba lokaci. Karfe takwas da minti arba'in nan da nan sai fadila ta mike zaune zumbur a tsorace tana waige waige akan faffadan gadon. Ina faisal me ya hanashi dawowa haryanzu shida yace karfe takwas zai dawo. Tambayar kenan data farayiwa kanta sannan ne to abubuwan da suka a yammacin suka fara dawowa kwakwalwarta. Ita kanta fadila batasan ta yadda akayi ta kawo kanta cikin dakin kwanansu daga falon gidan ba. Abinda kawai da zata iya tunawa shine bayan farin hayakin ya washe ta tallaba a tsorace ta fada kan gado ta fashe da kuka batasan sa'ar da barci ya dauketa ba. . Fadila ta muskuta akan gadon a tsorace adaidai lokacin ne to taji an sake sakin wata katuwar tsawa sannan saitaji saurin ruwan sama ya fara sauka ajikin tagogin dakin fadila ta sake kallon lokaci ajikin wayarta. Tara saura minti biyar sannan ne to fadila ta yanke shawarar karshe aranta. Tabbas in har taran dare tayi faisal bai dawo ba to ko me zai faru kome aljanin nan zaiyi mata saidai yayi amma ficewa zatayi daga gidan gara ta koma gidansu. Wani zazzafan hawayen takaici ya fara sartu akan kumatun fadila yaya kwana daya kawai agidan masoyinta duk wannan bala'in zaiyita faruwa akanta ta tambayi kanta sannan ta dauki wayarta ta fara buga lambar faisal kwata kwata tsoro da fargaba sun raunana tunaninta abinda ya kamata fa ace tayi kenan tun dazu ta neme shi awaya domin tasan inda yake. Tafara danna lambar kenan saitaji an kwankwasa dakin sannan aka fara turowa zuciyar fadila ta harba tsakanin hakarkarinta nan da nan ta jefar da wayar ta nufi kofar dakin aguje. . Gani nan darling bari na bude maka. Fadila tace muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka fadila tayi tsalle ta rumgume faisal sa'ar data bude kofar cikin kuka faisal ya dauketa kamar yar tsana ya ajjeta akan gado sannan ya dubi fuskarta a tausashe Kukan me kikeyi? Kadan ya rage fadila ta fada masa abinda ke faruwa to sai kuma tayi tunanin me yiwuwa ma in ta fada masa yace ko zautuwa tayi adaidai wannan lokaci kuma sai fadila ta tuna da zanen kunshin daya dawo jikinta gabanta ya kuma faduwa shin yanzu idan faisal ya tambayeta inda akayi mata kunshin tace dashi me? Ita dai tasan bazai yiyu ba tace dashi bayan yafita itama ta fice domin ayi mata zanen kunshi ba. Wannan na iya harzukashi domin tasan zuciyar faisal. Kinyi shiru kina kallona kukan me kikeyi? Faisal yace da tattausan murmushi lokaci guda kuma ya dubi hannunta kamar zai kama koda fadila ta dubi hannayenta sai taga zanen kunshin ya bace babu shi babu alamarsa jikinta ya dauki rawa sannan saitayi ajiyar zuciya ta kalli faisal tace a tausashe. Rashinka ne yasani kuka don me zaka tafi ka barni kaida kace dakayiwa abokanka bangajiya zaka dawo karfe takwas dubi agogo yanzu karfe nawa? Am Sorry faisal yabata hakuri cikin harshen turanci sannan sai ya janyo amaryarsa ta kwanta a kirjinsa . Ango da amarya na kwance abinsu cikin kwanciyar hankali bugun zuciyoyinsu na bugawa lokaci guda da dakikar katon agogon dake magale a bangon dakin adaidai lokacin da agogon ya buga karfe goma sha biyun dare wayar Fadila dake gefen gadonta ya dauki ruri. Fadila ta farka a firgice kirjinta na harbawa gamida tsaki da kuma nadamar ma meyasa tun farko bata kashe wayar ba Fadila ta dauki wayarta ta kara a kunne. Hello wanene? Fadila ta tambaya Hello my darling mijinki ne faisal dan Allah kiyi hakuri yanzu zan dawo Wallahi gida naje na tarar mama batada lafiya shine muka kaita asibiti amma gani nan yanzu zanzo. Fadila taji kamar wata katuwar katanga ta fado mata a tsakiyar baya Fadila ta dubi mijinta dake kwance a kusa da ita sannan ta dubi kan wayar a tsorace. Kaga Malam nifa matar aure ce ga kuma Faisal dina kwance kusa dani. Aka kyalkyale da wata tattausar dariya acan daya bangaren Haba darling na dai fahimci haryanzu fushi kikeyi dani kiyi hakuri gani nan zuwa. Fadila taji kamar tasa ihu tabbas muryar faisal dinta takeji acan daya bangaren yawun bakinta ya kafe sa'ar dataga sunan Faisal din ne a saman wayar. Faisal dan Allah da gaske kaine? Fadila tace a tsorace tana kallon daya faisal din dake kwance a kusa da ita. . Kun hanani barci da shegen surutu wai ku masoya an fada miki shi kadai yake sonki idan ba barin dakin nan nayi ba bazaku barni nayi barci. Faisal din dake kwance akusa da ita ne ke wannan bayani cikin kakkausar murya yana gama fadin haka sai farin hayaki ya turnuke dakin. Wayar dake hannun Fadila ta Subuce. . BABI NA BIYU 2 . Adab da babban dakin karatu na sabuwar jami'ar bayaro agindin wata yar dukurkusar bishiya dake fuskantar tagwayen dakunan darasi daga gabas FARIDA ce zaune tana kallon ikon Allah zuciyarta kamar zata fashe ta fito ta tsakanin hakarkarinta. Daga inda take zaune tana iya hangen Kabir dinta zaune akan wani benci na farin dutse SAFIYYA zaune akusa dashi suna hira abinsu jifa jifa kuma saita bude baki kabir ya jefa mata alawa aciki duk sa'ar da hakan ta faru sai Farida taji kamar sun watsa mata wuta a fuska. Tun karfe hudu na yamma direbanta Baba Ali ke zaune a filin fakin yana jiranta amma har zuwa karfe shida na yamma farida na nan zaune domin ta gama rantseewa yau ko me za'ayi saita yiwa kabir magana. Farida na nan zaune kusan dakika ashirin saita dubi agogo sannan saita dago kai ta dubi kabir tabbas maganar Asma'u gaskiya ce da dai bata yarda ba amma ayau ta yarda domin duk da yake abinda Asma'u ke bata shawara tayiwa kabir nau'i ne na shaidanci to amma shine kawai mafita in har tana so ta kwato kabirunta Farida ta fadawa kanta sannan saita dada da cewa cikin zuciyarta ai shima kabir din shaidani ne domin idan bahaka ba yaushe ne za'ace wai sai nayi shaidanci zai damu dani. Farida na nan zaune tana kallon ikon Allah duk kusan daliban dake gurin sun tafi gida sai jifa jifan wadanda ke kwana a makaranta dake yar zirga zirga nan da can. Karfe shida da rabi daidai lokacin da farida ta fara tunanin ko anan zasu kwana sai taga su kabir sun mike tsaye safiyya na kokarin kama hannayensa biyu duk da yake farida bata iya jin abinda safiyya ke fadawa kabir amma ga yadda motsin bakin da yanayin fuskarta ya nuna tabbas kalamai masu dadi take fadawa kabir. Farida taji zuciyarta tayi kuna ana cikin hakane saitaga kabir ya tashi ya nufi hanyar da zata kaishi zuwa dakin kwanan dalibai yayinda ita kuma safiyya ta nufi hanyar da zata kaita filin da aka tanada dan ajiye motocin dalibai Suna tafiya suna waige suna waige suna dagawa juna hannu. . Cikin sauri tana tafiya gabanta na faduwa kafafunta na hardewa fadila tabi kabir abaya. Kabir farida takira sunansa cikin wata rarraunar murya adaidai lokacin dasuka kawo kusa da wata yar rumfa da dalibai ke hutawa kabir ya juyo cikin mamakin jin muryar mace tayi kiransa. Oh farida kece haryanzu baki tafi gida ba? Kabir yace sa'ar daya juyo. Ina nan ban tafi ba farida tace gamida danyin shiru domin ta lura kallonsa yatafi izuwa hannayenta. . Kai nake jira tun dazu ina can azaune farida tace lokaci guda ta nuna karkashin bishiyar data baro haba farida amma kuma kika ki yi min magana wallahi banganki ba. Farida ta sunkuyar dakai naga kuna hira mai dadi ne shine nace bari na jira dan kada na bata muku hirarku haba dai ai dama kinzo ba wata hirar kirki mukeyi ba maganar jarrabawa mukeyi. Farida ta dago kai a yatsine ta dubeshi tace Au jarrabawar bana hardasu sa alewa abakin budurwa? Lallai bana makin din jarrabawa sai a barwa su Shazumamu. Kabir ya fashe da dariya Kai lallai farida yau kin samin idanu farida ta waiga hadu da dama bata hangi kowa akusa dasu ba sai daga can bangaren shiga dakin kwanan dalibai take iya hango kawunan jama'a jifa jifa hakan ita ta kara mata karfin gwiwar matsowa kusa da kabir ta yadda har yana iyajin numfashinta fuskarta dab da tasa ta dubeshi ido da ido tace. Kabir me yasa kake guduna ko dan kaga na mutu akanka? Kabir ya dago kai ya dubi farida cikin mamaki da kaduwa amma da yake kwararren mayaudari ne bai bari kaduwa ta nuna a fuskarsa ba. Abinda ya bashi mamaki shine kama hannunsa da yaga farida tayi yasan cewa wannan ba al'adar farida bace ita dai ka barta da sauya samari kamar riga amma shashanci ba aikinta bane. Tsahon lokaci suna tsaye ahaka kabir yayi ajiyar zuciya kana idanunsa sukayi duba izuwa hannayenta akaro na biyu. Ba gudunki nakeyi ba farida. In ba guduna kakeyi ba me yasa ka daina kirana awaya kuma sai in nemeka in rasa amma dana ganka sai in ganka tare da safiyya farida tace sannan sai ta dafa hannunsa. Kabir yaji wani irin sanyi ya ratso daga hannun farida ya soki hannunsa kamar an rike shi da hannun kankara. Ke yaya naji hannunki sanyi karau haka? Sanya fa kace? Farida ta dube shi cikin mamaki kaga ni hannuna dumi ne dashi saidai ko in hannun safiyyarka ne keda sanyi kabir yayi murmushi yace kinga ga dan Allah mu bar wannan zancen ya wuce daga yau in Allah yaso kin zama tawa my only one. Kaidai fadi gaskiya safiyya fa? Kada ki damu da wannan shirmenta kawai take. Kabir yace azuciyarsa kuma yana cewa wannan ma rabo na minallahi ce wai tsuntsu daga sama gasashshe. . Kai amma fa zanen kunshin nan naki yayi bala'in kyau a ina akayi miki kabir ya fada a fili. Gaban farida ya fadi cikin sauri ta dubi hannayenta a iya saninta zanen dake hannunta ko baki baiyi ba amma sai gashi yanzu rangadadau yayi baki kamar yanzu aka zana shi. Wata...wata kawata ce tayimin farida tayi masa karya a tsorace kabir ya lura da sauyin yanayi na lokaci guda akan fuskarta dan haka cikin sauri sai ya saki hannunta azuciyarsa yana cewa bi ahankali dan samari wannan farin shigace ba irin su safiyya bace. Yanzu yaushe zamu sake haduwa mu tattauna sosai? Farida ta dubi zanen dake hannunta a tsorace tace. Duk lokacin da kake so mu hadu gobe a filin fakin idan mun tashi daga karatu saina kaiki gida. Tunda farida tazo jami'ar bayero bata taba bari wani saurayi ya kaita gida ba domin kullum direban gidansu na nan yana jira amma gudun kada ta batawa kabir rai sai tace Bakomai mu hadu goben. To shikenan sai munyi waya kabir yace yana kallonta da murmushin yaudara. Zaka kirani awaya idan naje gida? Me zai hana Faridata cikin farin ciki farida ta nufi inda direbanta baba ali yake jira saidai kuma duk wannan farin kafin ta zauna abayan motar ne. Domin tana zama data kalli hannayenta saita nemi bakin zanen kunshin sama da kasa ta rasa. Na shiga uku na lalace. Farida ta fashe da kuka a tsorace. . Baki shiga ba matata keda nayi miki gata na fito miki da adonki agaban wanda kike so wata kakkaurar murya tace da ita daga sama. Wayyao Allah....waye ke magana? Farida ta tambaya tana waige waige abayan motar. Wa kikaji yayi magana? Direbanta ne baba ali ya tambaya yana kallonta cikin tsananin mamaki. . ** ** ** ** Washegari da safe misalin karfe goma da yan mintuna direba baba ali yakawo farida cikin jami'ar bayeron dan Allah Baba ali idan ka koma gida kace da mama sai wajen magariba zamu tashi kaji? Kace da ita kuma wata kawata ce zata dawo dani Farida ce ke fadi tana kallon dattijon tausashe. Basai na dawo ba kenan baba ali ya tambaya cikin sauri farida ta gyada kai Eh basai ka dawo ba kuma dan Allah idan baba yadawo da wuri koda yake dai nasan me yiwuwa jirgin yamma zai biyo daga abuja amma idan yadawo kafin nan sai ka nemeni awaya dan in sani kaji baba Ali? Baba ali ya danyi jim yana duban sitiyarin motar dake gabansa. . Saidai fa kinsan wayar tawa tafi sati biyu babu komai acikinta kwandala daya da yan kwabbai suka rage dasu nake flashing. Jin haka keda wuya farida ta fahimci abinda yake nufi cikin sauri ta bude jaka ta zaro naira dari biyar guda biyu sababbi kar ko kari babu ta mika masa Ga wannan kasa katin harma ka samu na goro. Yauwa 'yata ko kefa ai yana zuwa zan fada miki kuma ina ganin ma ba saina kira ki ba idan ya tambayeki zan iya cewa dashi sai wajen takwas zaku tashi zan koma a dauko ki nasan bazai damu ba. Yauwa baba ali na gode farida tace sannan saita bude kofar motar ta fice cikin sauri ta nufi inda dakin daukar darasinsu yake nan da minti arba'in zasu fara daukar darasi. . Dattijo baba ali yabita da kallo yana yabawa da abinda yagani azuciyarsa tun tana karama yake kaunarta aransa sannu ahankali tana girma yana kallonta har zuwa yanzu data girmewa duk wani mafalkin sa. Akaro na farko arayuwarsa sai baba ali ya fara tunanin ina amace saurayine shi dan shekara shirin da biyar ko talatin da babu abinda zai hana shi ya nemi Farida baba ali na tattare da masaniyar cewa duk watan duniya sai farida ta sauya sabon saurayi ya lura da hakane da irin samarin da kan rakata zuwa wajen motar yau in ya ganta da wancan dan tsololon bayan sati biyu ko uku kuma sai ya ganta da wannan dan lukutin to amma har kullum yafi ganin laifin samarin domin yayi imani da cewa da ace shi keda yan kananan shekaru kamar nasu da babu yadda za'ayi farida ta gagare shi. . Shekaru talatin da doriya da suka gabata Baba ali tsohon direban babbar motace ta daukar shanu daga arewacin najeriya zuwa kudanci azamanin da yake da sauran kuruciya mayen karfe abokansa direbobi yan bariki suke kiransa domin a tarihi ba'a taba ganin karuwar daya tsaya da ita bai dauki hankalinta ba koda bashida ko kwabo saita saurare shi domin allah ya hore masa iya zance yana dan shekara arba'in aduniya wani babban hadari ya rutsa dashi ahanyar ikko shi kadai ya rage bai mut ba acikin jama'ar motoci shidan da sukayi ta haduwa da juna amma dai ya tare a asibiti da karaya biyar saida yayi shekara biyu bata tuki bayan ya warke alokacin ne to wani babban amininsa tsohon direba andace shi nutsatstsene ba kamarsa ba ya hadashi da kwamishina Ilyasu Na Gamdo wanda ya ya kasance mahaifi agurin farida yau shekara goma sha biyu kenan yana aikin direban hajiya da ya'yanta. Baba ali na nan zaune cikin motar afilin fakin yana kallon farida har saida ta bace sannan saiya tuka motar ya nufi kofar fita daga cikin jami'ar cikin takaici. Me zai hana ka dawo daukarta in yaso sai kayi duk abinda kake so? wannan kururuwar shaidan ce cikin kunnensa yana dada karfafa masa gwiwa akan ya aiwatar da wani tsohon kudiri daya dade yana yawo cikin zuciyarsa tun sa'ar daya fahimci farida ta zama cikakkiyar mace. Akullum baba ali ya dubi farida sai ya fara tunanin me zai hana idan ya sami dama yayi mata fyade kawai ya gudu abinsa. Dama tuni wannan aiki ya isheshi domin dan abinda ake biyansa bai taba isarsa ba. Abinda yakamata inyi kenan Baba ali ya dada jaddadawa kansa. Tuni ya gama lissafin inda zai tsere domin anfi shekara uku wani tsohon abokinsa dake zaune a ikko nayi masa tayin sayar da kwaya. Wahalar banza kakeyi wannan sa'ar tamu tafi wannan direban hajiyar kanata wahalar banza yanzu da karfinka yagama karewa zasu sallameka shikenan kashiga uku. Baba ali yayiwa kansa murmushi sa'ar daya tuno kalaman tsohon abokin nasa tabbas wahalar banza nakeyi amma yau din nan zan karbi ladan aikina na karshe in bar musu tsiyarsu baba ali ya fadawa kansa. Abinda ya rage kawai yanzu shine idan magariba tayi nayi mata waya ince ta tsaya baba yace inzo in dauketa. Wani busashshen murmushi irin na yan duniya ya subuce masa cikin nishadi sai ya zura hannunsa aljihu domin ya dauko sigari abinda bai taba yarda yasha agaban uban gidansa kwamishina ba sa hannunsa keda wuya cikin aljihun sai yan yatsunsa sukaci karo da sababbin takardun kudin da farida tabashi ga mamakin baba ali saiyaji kudin sunyi sanyi sanyi karai adaidai lokacin ne ya kawo wani dan cunkoson motoci dake unguwar rijiyar zaki. Wannan kamar yanzu kuka futo daga inji baba ali yace sa'ar daya daga takardun kudin da hannunsa na dama yayin kuma da hannunsa na hagu yake tuki. Kamata yayi ace kunyi dumi ba sanyi ba baba ali ya kuma cewa da kudin cikin nishadi sannan sai ya mayar dasu cikin aljihu daga tafin hannunsa keda wuya saiyaga tambarin zanen dake jikin naira dari biyar din yafito rangadadau a hannunsa. Cikin mamaki sai baba ali ya goge tafin hannunsa ajikin riga da zummar ya goge fentin ga mamakinsa launin bai gogu ba baba ali yasake murmushi kana ya mayar da hankalinsa kan tukin da yake sannan yace. Yar banza yarinyar nan ko injin buga kudi sukedashi acikin gida? Naga wannan ko bushewa ma basuyi ba to duk tsiyarsu dai saina kashe su Da'ace dattijon mai cikakkiyar nutsuwa ne daya sha jikin jikinsa tun a wannan lokaci domin gargadi ne na farko a gareshi AMMA BAI SAN HAKAN BA. ** ** ** ** Kabir ya fito daga cikin motarsa shudiya kirar toyota ya mayar da kofar cikin burga da budawa ya rufe sannan ya nufi farfajiyar jami'ar yana tafiya yana wani tsalle kamar ansa masa dunkulen tamaula akasan takalmin sanye yake da wata damammiyar riga mai dogon hannu fara sol da ita kamar auduga sai sheki takeyi acikin dan abinda ya rage nadaga hasken ranar wannan yammaci agaban rigar an rubuta HUG ME cikin harshen turanci da wasu bakin zare mai sheki bakin wandon jeans din yayi matukar dacewa da farar rigar hakanan farin takalmin dake kafarsa gami da bakin tabarau din dake zaune daraf a saman doron hancinsa su suka kammala wannan kwalliya ta musamman dayayi domin ya samu damar karya zuciyar Farida. Kabir ya shafi gashin kansa wanda ke sheki sakamakon man da ya sha masa sannan ya gyara yan kanan sifikun dake cikin kunnuwansa wadanke ke dauko masa wani tattausan kidan zamani daga cikin wayarsa kirar Nokia dake aljihunsa yana tafiya yana bin kidan da bakinsa wata sa'ar kuma yana kwaikwayon wakar da fito babu abinda ya dame shi matsalar kudi babu duk abinda yake so hajiya zata bashi. . Mahaifiyarsa HAJJO HABIBA tsohuwa yar kano zuwa jidda ce hakanan ayanzu duk wani abu da zai kawo kudi tana ciki jita jita kuma nata yaduwa cewa wai yar damfara ce da yan daban take samun kudin domin ma'abota iya tsegumi na unguwarsu sunce basu taba ganinta cikin talauci ba hakanan duk bayan wata shida sai ta sayi motoci biyu sababbi daya tata daya kuma ta danta kwaya daya jal aduniya shima har yau ba'asan ubansa ba daga Allah sai ita sau da dama makwabtanta wadanda gulmarsu tafi karfin zuciyarsu sukan tambayeta wai shin waye uban kabir wannan tambaya bata taba batawa Hajjo habiba rai ba hakanan kullum amsarta dayace. Uban kabir yana sudan. . Sannu ahankali yana tafe yana fito kamar tsohon bature kabir ya karaso tagwayen dakunan daukar darasi anan ne sukayi kicibis da safiyya kabir baiji dadin ganinta ba domin yau ba ranarta bace kuma shi duk ya fara gajiya ma da ita domin tafiya naci. Safiyya duniya...daga ina haka? Kabir yace da faffadan murmushin karya lokaci guda kuma yana duban dan siririn wuyanta azuciyarsa yana cewa in banda shirmena ma ina ni ina wannan yarinya duk kashi duk zaman da suke da ita kabir bai lura da kashin ba sai jiya da farida ta matso kusa da shi ta rike hannunsa. Kai nake nema safiyya tace da murmushi gani kin samu...ya akayi? Mu tafi cikin motata ko motarka in fadama safiyya tace lokaci guda kuma ta kama hannunsa. Cikin sauri kabir ya girgiza kai sannan ya zare hannunsa daga cikin nata. Sauri nake zan koma gida hajiya ce ke nemana. Safiyya ta hade fuska. Haba kabir yaya zakayimin haka rabona dakai fa tun kusan jiya by this time ta karasa da turanci. Nace dake hajiya ce ke son ganina ki jirani zandawo na dauke ki in anjima da daddare sai mu tafi waje musha iska. Nan da nan fuskar safiyya ta washe cikin kwarkwasa ta dora hannayenta biyu akan tace a tausashe alkawari? Eh Promise kabir yace gamida gyada kai lokaci guda yana Allah Allah ta dauke hannunta daga kan kafadarsa kada Farida ta hangesu garinsa yayi kasa. Bari inje saina dawo kafin safiyya ta sami ta cewa tuni kabir yayi nisa safiyya ta bishi da kallo cikin mamaki me ke faruwa ne? Wannan baiyi kama da kabir din dana sani ba tace cikin zuciyarta. Yana tafe yana waige waige ko zai hangota kabir ya nufi inda motarsa take ya riga ya sani babu abinda zai hana farida zuwa domin yasan ta gama kamuwa dan haka yana zuwa saiya bude kofar gidan gaba na motar ya zauna yana yabar kofar a bude kafafunsa awaje sannan ya kunna rediyon dake gaban motar kidan zamani yafara tashi a tausashe sannan sai wani mawaki mai katon makwogwaro yafara wani abu mai kamar ihu matsayin waka. Baifi ko minti biyar da zama ba ya hangota ta nufo inda yake. Numfashinsa ya dauke cak sa'ar dayaga irin shigar da tayi. Saura kadan na cuci kaina ashe bebin nan haka tayi bala'in haduwa. Daga can nesa dashi Farida ta hange shi farin ciki yaso ya mamayi zuciyarta amma rufanin datake addabar zuciyarta shiya dakushe dukkan wani digo na farin cikin dake zuciyarta. Yanzu kam farida ta riga ta gama yarda da cewa batada lafiya matsala ta sameta tabbas tasan ta gamu da aljani tasha ji abakin kawayenta cewa aljanu suna hawa kan mata suyi ta wahalar dasu mahaifiyarta ma tasha yi mata fada akan barin gashin kanta awaje kokuma zama tsirara tsirara domin acewar mahaifiyarta wadannan abubuwa suke baiwa aljanu sha'awa har su hau kan mace suyi ta bugeta acikin jama'a. Farida tayi ajiyar zuciya a tsorace sa'ar data fahimci cewa idan ba wani ikon Allah ba itama kwanan nan aljanin zai fara bugeta tuni ta fara nadamar zuwa gidan dan daudun nan domin yi mata zanen kunshi akan tsaraicinta farida ta riga tasan wannan kunshi shine sanadiyyar wannan bala'in dake faruwa akanta daman mahaifiyarta tashafada mata cewa yawan fito da tsaraici a fili na cikin abinda ke sa aljanu su hau kan mata. . Farida ta dubi tafin hannayenta dakuma bayansu batayi mamaki ba sa'ar dataga zanen kunshin yadawo rangadadau kamar ma yanzu aka zana shi duk kuwa da cewa ta tabbata har lokacin da baba Ali ya sauketa hannunta babu zanen kunshin. Farida tayi matukar kyau awannan yammaci ita kanta ta sani domin inka dauke yan littattafan dake hannunta duk abin dake jikinta sabo ne tun daga kan riga da siket din da mahaifiyarta ta sayo mata a landan zuwa ga takalmin dake kafarta da yan kunnayenta da sarkoki kai hatta alkalamin rubutun dake hannunta sabo ne domin dazun ta saye shi. In banda farida ta riga tasan zanen kunshin dake hannunta na aljanu ne da sai tace shima ya taimaka wajen fito da kyawunta a fili. . Kai gaskiya yau kinyi bala'in haduwa. Kabir yace sa'ar da farida ta karaso inda yake lokaci guda kuma ya rage sautin kidan dake tashi. Nagode farida tace a tausashe. Naji dadi da kwalliyata tayi maka kyau Ah gaskiya tayimin zagayo ki shigo ciki kabir yace sannan ya mika hannunsa ya bude mata daya kofar. Ahankali farida ta shigo cikin motar ta zauna sannan ta rufo kofar, shima kabir ya rufe kofar ya kunna na'urar sanyi kana ya dubeta farida ta lura da irin kallon dayakeyi mata dan haka cikin bin umarnin shaidaniyar kawarta Asma'u saita dan bude gaban rigarta kadan domin kabir ya sami damar hango tsakanin kirjinta sannan saita dan matsa kusa da jikinsa ta dora kanta akan kafadarsa. Ilove You Kabir. Kabir yaji kama ta watsa masa ruwan sanyi azuciya a wannan dan takin dakikar saiyaji kaunarta ta mamaye zuciyarsa amma a iya lokacin nan kawai kafin shaidan ya maye gurbin da sha'awa. Daga nan idan mun tashi ina zamu? Kabir ya tambayeta yana wani lumlumshe idanu sannan ya kama hannayenta biyu yana kallon zanen kunshin dake jiki. Farida ta dubeshi cikin mamaki tace Gida mana ba gida kace zaka kaini ba? Kabir ya dubeta ido da ido ya girgiza kai yace, sai mun fara biyawa ta gidan wani abokina kafin nakai ki gidan domin can zamufi samun sake. Farida taji gabanta ya fadi bata dauka abin zaikai ga haka ba yaushe za'ace ta bishi wani gidan aboki. Ina ganin muyi hirarmu anan dai zaifi kyau... Farida tace a tausashe zuciyarta na harbawa tana tsoron kada ta batawa kabir rai. Kabir ya kamo tafukan hannayenta guda biyu ya dorasu akan fuskarsa yace. Ina kaunar ki ne farida shi yasa na nemi ki bini domin in nuna miki yadda nake kaunarki. Farida taji gabanta ya fadi ahankali ta zame hannayenta a wayance daga kan fuskarsa. Haba farida bakya.... Kalmar ta makale a fatar bakin kabir sa'ar dayaga yanayin fuskar farida ta sauya nan da nan da kabir ya kalli fuskarsa a jikin madubi alokacin daya hangi irin zanen kunshin dake tafin hannunta rangadadau a zane akan kumatunsa kamar yi masa akayi. . Kada ki damu idan bakya son zuwa yanzu maje watarana kabir yace da ita cikin sauri shi a haukansa ya dauka abinda yace ne ya birkita kamanninta. Farida ta gyada kai babu magana idanunta zuru akan zanen fulawar dake kan kumatunsa. Ganin haryanzu batayi fara'a ba sai kabir ya rankwafa jikinta yana cewa haba farida....kiyi min murmushi mana konaji dan dadi dadi yana gama fadin haka sai ya zura hannayensa ya tallafo kanta sannan ya tura bakinsa gaba da nufin zai sumbaceta anan ne to wani abu mai kamar hannu ya zuro cikin motar kamar daga sama ya kifawa Kabir Mari. Wayyo Allah... Kabir yasa ihu sa'ar da yaga wani haske kamar wuta ya gifta akan fuskarsa. Wayyo... Wayyo dan Allah ki taimakeni za'a kasheni kabir ya sake kwala ihu sannan a rude sai ya bude kofar motar ya fada kasa yana birgima afilin ajje motoci na jami'ar bayero. Daga yau ka sake lalata ya'yan mutane dan banza lalatacce an fadama matata irin matan da zaka iya tabawa ce. Wata kakkausar murya tace daga sama sannan sai aka kece da kakkausar dariya. Tsananin kaduwa da tsoro su suka hana farida yin motsi tana nan zaune akan kujerar motar kamar gunki tana hangen kabir yana ta murkususu adaidai lokacin ne to ta lura da wasu fararen abubuwa masu kama da kashi akan cinyarta hannunta na rawa farida ta dauki fafaren abubuwan. Saida ta kura musu idanu sannan ta gane ashe Hakoran mutum ne guda uku wannan shiya sata bude kofar motar ta fice aguje sannan tasa kabir agaba ta fara Ihu. Nan da nan gurin ya cika da dalibai hadiman jami'ar masu gadi da shara aka zagaye kabir an rasa mai taba shi can sai wani kakkarfan dattijo mai shara ya matso ya tashi kabir da kyar daga kan fuskarsa jini na zuba nan da nan daliban dake zagaye dashi suka rike numfashi a razane sa'ar da sukaga bakin Kabir ya karkace ya koma baya gashi babu hakoran gaba. Ku kamamin mu shiga dashi cikin makaranta ayi masa addu'a ina zaton aljanu ne suka shafe shi. Dattijon yace. . BABI NA UKU 3 Abayan katuwar sakatariyar gwamnati ta tarayya abuja jama'a ne jingim maza da mata kowa nasha'anin gabansa wasu nata sunturi daga can zuwa nan suna kokarin neman kwatancen ofishin wanda suke nema domin neman aiki ko kuma maula hakanan agefe guda lemomin masu wayar haya acikin rana sunyi sahu sahu jama'a har jerin gwano sukeyi suna sayen katin waya da kuma buga wayar haya don su sami zantawa da wadanda suka zo nema. Acikin wadannan mutane masu waya hardasu MAMA. Mama tayi tsaki sa'ar data danna lambar kawarta Bebi a karo na ashirin ana cewa wayar a kashe. Yaya bebi zatayimin haka? Mama ta tambayi kanta acikin damuwa. Mama tazo sakateriyar ne badon takira wayar haya ba sai dan anan ne bebi tace idan tazo ta kirata zatazo ta sameta agurin daga nan kuma su wuce gidan da nata honorabil din ya ajiyeta aciki. Mama ta sake danna lambar wayar bebi akaro na ashirin da daya cikin damuwa domin idan har bata samu bebi ba tashiga cikin matsala dan ko kudin da zata koma kano batadashi adaidai wannan lokacin ne wayar dake hannunta ta dauki kara cikin sauri mama ta dubi lambar dake fuskar wayar ta dauka bebi ce Mama tayi tsaki sa'ar da taga ashe lambar ALHAJI BILYAMINU ce matsolon saurayinta na kano Hello menene? Mama tace dashi a fusace kuma fada- fada, bi ahankali kada ki fasa min dodon kunne Alhaji Bilyaminu yace acan daya bangaren kina inane? Nazo gidanku ance min wai tun da sassafe kika fita. Nayi tafiya ne mama tace a yatsine Eh naji kinyi tafiya kina ina nace? Ni ganinki nake sonyi. Bazaka sami ganina ba ayau jibi ma albarka dan ina abuja Alhaji bilyaminu ya rike numfashi acan daya bangaren haba mama yaya zakiyi tafiya batareda kin sanar dani ba? A'a yau kajini da mutum mama tace cikin wayar da karaji aurena kakeyi kokuwa zaman daduro muke dakai? Duk da babu ko daya dai acikin abinda kike fada ai yakamata kisanar dani. To banyi niyya ba kai ni kaga nafa gaji da hulda da marowatan mutane irinka yar motar nan ma ka kasa sayamin sai ka bushi iska kazo ka uzuramin. Haba mama meye yayi zafi haka? Ba nace zan saya miki motar acikin wannan watan ba? Haka dai kace amma wa yaga sayen mama tace gamida tsaki sannan sai tayi kamar zata katse wayar da sukeyi kada ki kashe wayar dan Allah mama yanzu yaushe zaki dawo? Idan naga kidin mota cash acikin bakina. Babu komai Alhaji bilyamin yace cikin sauri ki dawo gobe sai in saya miki bazan dawo gobe ba domin ayanzu haka ma kofar Nikon Hotel nake inajiran wani darling dina ya fito dan majalisa ne wanda yasan abinda akeyi da kudi ba irinka ba. Alhaji bilyaminu yaji wani matsanancin kishi ya tuke zuciyarsa kai kace wata matarsa ce ta aure. Amma agaskiya mama baki kyauta min ba yanzu duk irin wahalar da nakeyi miki sai kinbi wani mutum har zuwa abuja. Idan kaji haushi ka ajjeni daduro mana ko kuma ka aureni idan zaka iya. Alhaji bilya ya dauke wuta na yan dakiku sannan saiya tausasa murya yace. Allah baki hakuri mama...yanzu yaushe zaki dawo. Nan da sati guda idan naga dubu dari shida kudin sayan mota acikin bankina idan kuwa naji shiru me yiwuwa har abada bazaka sake ganina ba. Har abada fa kikace? Kwarai kuwa angaya ma kano garin mu ce ko ka manta ni yar gombe ce? Zan turo miki da kudin gobe kiyimin text din lambar asusun bankin naki yanzu kuma dan Allah ina jiranki din idan zi yiwu ma ki dawo nan da kwana uku. To shikenan saika turo din mama tace a yatsine sannan batareda ta sake bashi damar cewa kala ba saita kashe wayar sannan ta dira kafa akasa cikin murna lallai abin da malamin tsibbun nan ya fada min gaskiyane daman saida yace shi maganin kadan kadan yake ci na fi wata shida ina zuba mai magani a abinci yanaci amma shegen ya kasa yimin koda kyautar dubu arba'in sai gashi yanzu a banza zai saya min mota. Duk da ya rude ya dauka bazai sake ganina ba mama ce ke fadin haka cikin zuciyarta sannan saita kudiri aniyar in har alhaji bilyaminu ya saya mata mota saita sayawa malaminta mashin. Mama taci gaba da lallatsa lambar bebi yanzu kam damuwar dake tattare da ita ta ragu domin tasan in babu nan akwai can idan hagu taki saita koma dama tasan ko bata sami ganin bebi ba tana iya yin waya Alhaji Bilyaminu ya turo mata koda katin waya ne ta sayar domin ta sami kudin mota. Wayar mama ta sake daukar ruri akaro na biyu awannan karonma mama tayi zaton ko bebi ce amma data duba fuskar waya sai taga ashe bakuwar lambace yanzu haka ma wani wahalallan ne mama tace gamida tsaki sannan ta kara wayar a kunne. Hello wanene? Nice bebi dan Allah mama kiyi hakuri wallahi wayata na jefar yanzun nan wata wayar na aiaka aka sayomin kina ina? Mama tayi ajiyar zuciya ina nan Federal secretaria inda kikace na tsaya nafi awa daya da sauka. Oh kiyi hakuri kawata gamu nan zuwa yanzun nan ai gidan babu nisa da inda kike. Mintina goma da wannan sai gasu bayan mota kirar fijo wata dunkulalliya mai kamar kwai wani dogon direba mai dogon sanko kamar titin mota ne ke janta. Fara tafiyarsu keda wuya sai direban motar yakunna na'urar sanyi nan da nan sassanyar iska ta fara fifita su. mama tayi ajiyar zuciya sa'ar dataji sanyin iskar ya fara busar da guminta. . Kina hutawa kawata mama tace da bebi. Toh ya muka iya haka nan hali yayi bebi tace sannan ta kalli hannun mama tayi kasa kasa da murya yadda direban bazai iya jinsu ba tace. Shegiya kawata tsumma makunshin cuta mage mai kwanciyar daurar rai a ina akayi miki wannan hadadden zanen kunshin. Mama ta dubi hannunta cikin mamaki sannan ne to taji kamar na'urar sanyin ta fara huro mata zafi mama tayi imani dacewa har sa'ar data shiga cikin motar babu wani zane a hannunta amma sai gashi yanzu ya bayyana rangadadau kamar ma yanzu aka gama zana shi. Meye naga kin hade rai? Shegiya wallahi da gaske nakeyi ba tsokanarki nake yi ba wannan idan nayi wasa ai saiki kwace har nawa honorabil din bebi ce ke fadi sa'ar da taga yanayin fuskar mama. Mama ta feso murmushin karfin hali tace aina dauka tsokanata kikeyi kokusa wallahi kai zanen naki yayi kyau idan muka koma kano sai kin rakani inda akayi miki wannan bebi tace lokaci guda kuma ta kama hannun mama tana dubawa. Kai yaya naji hannunki sanyi karau kamar kankara lafiyarki kuwa? Mama ta dubi kawarta da murmushin yake tace Lafiyar kenan me kika gani? ** ** ** ** ** HONORABIL JATAU ya kurawa mama idanu baya ko kiftawa kamar wani tsohon maye tabbas ya yaba da abinda yagani. Acikin wani katon dakin shakatawa suke a tsakiyar wani gida wanda ke boye abayan wani munafikin lumbun shakatawa su hudune acikin dakin daga bangaren gabas bebi ce da kawarta mama kowannensu sanye da wata irin doguwar rigar Alatsine mai shara share kamar buhun algarara. Abangaren yamma na dakin honorabil jatau ne zaune da babban abokinsa HONORABIL SABO wanda shine saurayin Bebi. Tun sa'ar da mama ta sauka agidan shakatawa na honorabil sabo saurayin bebi basu sami ganinsa ba sai washegari da misalin karfe goman dare yashigo gidan acewarsa in dai har ba karya yake ba wai tun jiya suke gurin taro basu fito ba sai yanzu wannan bata dami bebi da mama ba domin sun huta sun wala abinsu katon gidan na alfarma babu kowa aciki sai su da wani dan dukurkushin kare mai yawan gashi irin na turawa da kuma masu dafa musu abinci idan sunci abinci sai suyi kwanciyarsu suyita barci idan sun farka su kunna talabijin suyita kallon fina finan da ake watsawa a kasashen turai. Babu abinda ya dame su duk abinda suke bukata magana kawai zasuyi sai akawo musu. Sa'ar da honorabil sabo ya dawo ne da misalin karfe goma sai suka gaisa da mama shi kansa ya yaba da abinda yagani to saidai kuma bai isa ya nuna hakan a zahiri ba tun da dai ga bebi manne akusa dashi kamar cingam bayan yayi wanka ya huta sai ya bugawa abokinsa honorabil jatau waya domin ya sanar dashi cewar bakuwarsa ta sauka kuma gasu nan zasuzo gidansa yanzun nan. . Sannu da zuwa mama honorabil jatau yace yana dubanta da yan mici micin idanunsa kamsu kama dana maciji tabbas ayadda yaga mama azahiri har tafi yadda yaganta a hoto burgewa. Ina ganin saimu tafi ko? Tun da mun hadaku. Honorabil sabo yace sannan ya mike tsaye gamida yiwa bebi alamar ta mike tsaye to kawata sai yaushe kenan mama ta tambayi bebi. Zamuyi waya bebi tace gamida kashe mata idanu. Da haka suka fice daga dakin fitarsu keda wuya ko motarsu basu tayarba honorabil jatau ya dawo kusa da mama ya zauna sannan ya dora hannayensa biyu akan kafadarta yace. Naji dadin zuwanki mama hotonki ya burgeni to ashe azahiri ma har kinfi haka burgewa inason ki sani cewa bazaki yi nadamar zuwan da kikayi ba. Mama ta lumshe idanu irin na kwararriyar karuwa sannan ta kwanta ajikinsa tace. Kaima bazakayi nadamar gayyatata da kayi ba. . Abinda basu sani ba shine wani acikinsu yayi kuskure. . Tashi mu shiga daki naga dare yayi sosai ko? Babu musu mama ta mike tsaye sannan saita bishi abaya zuwa cikin wani dakin kwana da bata taba ganin irinsa ba koda acikin mafalki lokacin sanyi. Lokacin da duk wannan ke faruwa karfe biyu saura ne na dare. . Dare yayi dare birnin tarayya yayi shiru bakajin komai sai jifa jifan haushin karnuka nan da can dakuma kukan tsuntsaye shima jifa jifa haka nan da mutum zai kasa kunne da kyau bazai rasa jin rurin dubban na'urorin sanyaya dakunan dake ta famar aiki ba'a acikin birnin. Dan haka ba dole bane wadannan yan kananan sautuka su dami honorabil jatau da mama ba wadanda ke kwance abinsu akan gadon alfarma barci har da munshari sannu ahankali dakiku na wucewa lokaci na matsowa har dai dan gajeren hannun dake fuskar wani kyakkyawan agogo na azurfa dake ajiye a gefen gadon ya nuna karfe hudu na asuba. Honorabil jatau ya matso adaidai wannan lokacin sannan ya tashi zaune akan gadon daga shi sai gajeren wando yana mutsutstsuka idanu. Bayan wasu yan dakiku idanunsa suka washe sannan sai Ya mika hannu zuwa kan wani karamin teburi adab da gadon ya kunna wata irin fitila mai malafa nan da nan wani tattausan haske mara kashe idanu ya mamaye dakin. . Honorabil jatau ya mike tsaye a tsakiyar dakin sannan ya kurawa mama idanu wacce ke kwance akan gadon tana barci abinta cikin nutsuwa hakika nayi sa'ar yarinya jatau yace aransa sannan ya nufi bandakin dake fuskantar dakin kwanan domin mararsa tayi nauyi tun wajen karfe ukun dare yake jin fitsari amma yakasa tashi yaje yayi. Honorabil ya tura kofar bandakin ahankali ya shiga sannan sai yayi turus akofar cikin mamaki sa'ar dayaji zubar ruwa acikin bandakin. Mamaki da fargaba suka mamayi zuciyarsa lokaci guda kuma domin shi yasan su biyu ne kawai adakin haka nan ya tabbata bai bar famfo a bude ba. Shigo mana yaka tsaya anan nima fitsarin ne ya tashe ni naso in tabaka sainaga kamar kanajin dadin barcin wata MAMA ce tsaye acikin bandakin sanye da doguwar riga irinta waccan Mamar daya bari yanzun nan akan gado tana barci. Cikin tsananin firgici honorabil ya dubi mamar dake tsaye cikin bandaki yace bakinsa na rawa. Bake na gani yanzun nan a kwance akan gado ba? Mama ta girgiza kai cikin mamaki sannan ta haske shi da murmushi kodai tarin wannan katon bargon naka mai gashi ka gani kake zaton nice? Honorabil ya girgiza kai a tsorace sannan sai ya dubeta yace Jirani anan ina zuwa. Jiki na rawa ya nufi cikin dakin kwanansu tun kafin ya karasa bakin gadon sai wata Mamar ta mike zaune akan gadon tace. Wallahi harka bani tsoro inaka tafi na farka ban ganka ba? Honorabil jatau ya dubi kofar bandakin a tsorace sannan sai ya zauna akan gadon ya dubi mama yace a firgice. Bake nagani yanzun nan a bandaki ba? Mama ta girgiza kai sannan ta matso ta kwanta akan cinyarsa yan yatsunta akan katon tumbinsa tace. Kaifa baka rabuwa da abin dariya yaya gani anan tare dakai zakace wai ka ganni yanzu a bandaki. Mama ina ganin.......Kalmar ta makale a makwogwaron honorabil sa'ar dayaji wasu irin Farata masu kamar karfe sun nutse acikin tumbinsa. Honorabil ya bude baki zaiyi ihu amma sautin bai sami fitowa daga bakinsa ba. Aka kece da wata mahaukaciyar dariya sannan sai wani farin hayaki ya turnuke dakin. Waya fadama wani katon banza maci amanar iyalinsa yana taba min mata wata kakkausar murya tace daga sama. Mama tafito aguje daga cikin bandakin a tsorace sa'ar dataji mahaukaciyar dariyar tana zuwa bakin gadon sai tayi turus. Akwance akan gadon harshensa ya zazzago waje hanjinsa awaje jini ko ina akan gadon Honorabil Jatau Ne. ** ** ** ** ** Yaya zaka fita baka bada kudin yaran nan na zuwa makaranta ba. Wata katuwar matace uwar gidan Alhaji bilyaminu ke fada masa wannan kalma. Ke dai wallahi bakya gode Allah.... Yanzu kudin makarantar ma saina basu ke bazaki iya basu ba. Kaidai baka tsoron Allah alhaji yanzu tsakani da Allah aikin me nakeyi da zan sami kudin da zan biya dawainiyar makarantar yara haba alhaji wallahi ya kamata ka rage irin wannan mugun hali naka yanzu kadubi yarannan kanana sai yawo suke acikin tsumma kamar ya'yan almajirai? Ka dubi manyan ya'yanka nan duk abokansa da motocin hawa amma kai dan mugun hali da matsolanci ko dan lifan babur din zamanin nan ka kasa saya musu suna zuwa makaranta. Alhaji bilyaminu ya katseta ta hanyar daga mata hannu kinga dan Allah sauri nake ni ban tambayeki wa'azi ba na rediyo ma danakeji kullum kwanan duniya ya isheni yanzu dai ga naira dari hudu nan ki rarraba musu su tafi in sunje sacewa malamin gobe za'a kawo kudin makarantar. Matar ta dubi kudin daya mika mata cikin takaici. To in ka bada wannan yaya zamuyi da maganar abinci kuma? Na fa fada ma tun jiya bamuda ko kwayar shinkafa daya agidan nan waken ma yakare gashi ma jibi za'a mayar dasu MAMI DA HAFSAT makaranta... Zan turo yanzun nan akawo buhun masara dana wake dakuma fulawa yana gama fadin haka sai ya nufi gajeri inda motarsa take cikin sauri yana duban agogo. Karfe hudu da rabi na yamma. Matar ta share hawayen bakin ciki dake sartu akan kumatunta sannan saitace cikin sheshshekar kuka Allah idan munada hakki akan wannan mutumin dayake zaluntar mu Allah ka bi mana hakkinmu. . Acan cikin gareji Alhaji Bilyaminu ya bude motarsa yashiga sannan yafice aguje wani yaro mukhtar yazo da sauri ya rufe garejin. Koda yafara tafiya cikin motar saiya dauki wayarsa ya danna wata lamba sannan ya kara a kunne. Hello mama kina jina Eh ina jinka akace acan daya bangaren cikin sheshshekar kuka meya samiki naji kamar kina kuka? Kaina ne ke ciwo...Mama tayi masa karya Toh Allah ya sauwake Alhaji bilyaminu yace sannan saiya dada dacewa kije bankinki ki duba na turo miki da kudin sayen motar amma dubu dari biyar kawai aka samu. Da'ace jiyane da ba karamin farin ciki maganar zatasa mama ba amma abin daya faru adaren jiya yagama fitar mata da sha'awar komai aduniya. . Sa'ar da mama ta tabbata aljanin dayayi musu zanen kunshine ya kashe Jatau saita hada nata ya nata gari na wayewa ta baro abuja mama tayi sa'a domin ta sami wata gantalalliyar naira dubu acikin hular honarabil jatau dake falon gidan. Duka duka batafi sa'o'i hudu da sauka ba Alhaji bilyaminu ya bugo mata wayar. Saukarta keda wuya ta kunna rediyo domin jin labaran BBC na rana kamar yadda ta tsammata tun farko sun fadi labarin rasuwar honorabil jatau acewarsu ana zaton yan fashine suka kashe shi to amma haryanzu babu tabbacin iya adadin kudin da suka sata daga nan ba'a sake wani kwakkwaran bayani ba akan rasuwat tasa sai jifa jifan bayanai da aka dauka daga bakin wasu abokan aikinsa yan majalisu. Ayanzu haka da mama take zaune jira take taji kawarta bebi ta bugo mata waya ko kuma saurayinta honorabil sabo domin jin inda take amma ga mamakinta har yanzu shiru haka nan dataji wayarta ta dauki ruri ma ta dauka su ne sai kuma taga ashe saurayinta ne na kano Alhaji Bilyaminu. . Yaya naji kinyi shiru ko bakiji dadin abinda nayi bane? Naji. Mama tace dashi a takaice. Yauwwa ko kefa Alhaji bilyaminu yace baki na rawa. Yanzu sai yaushe zaki dawo din? Na dawo ma. Kina nufin yanzu kina nan kano? Eh ina gida gani nan zuwa yanzu Alhaji Bilyaminu yace sannan saiya karkata kan motarsa ya sauya hanya ya fasa zuwa bikin saukar karatun kur'ani da aka gayyace shi. *** Me ke damuna ne? Alhaji bilyaminu ya tambayi kansa sa'ar da yayi fakin da motarsa akofar gidansu mama dake Na'ibawa. Shi kansa abin na bashi mamaki irin yadda yaga ya damu da mama sosai a yan kwanakin nan. Adacan lokacin da suka fara alaka sam sam bata gabansa ya dai dauke ta ne kamar sauran matan da suke mu'amala a hadu ayi harka a watse babu wata dangantaka mai tsayi. Ayanzu da Alhaji yayi fakin da motar a kofar gidan ji yake yi kama ma zai iya auren mama saboda irin kaunar da yaji tana kwarara acikin zuciyarsa. Alhaji bilyaminu yafito daga motar ya rufe sannan ya nufi cikin gidan kai tsaye abinka da wanda ya saba shiga. Ya riga yasan mata biyu ne kawai acikin gidan daga Mama sai wata inyamura wacce ke aiki a kamfanin magani. Mafi yawan lokuta baifiye isketa agidan ba amma duk sa'are da akayi dace ya sami inyamurar agida in zai fito sai ya jefe ta da dari biyar badan komai ba sai don kawai yana son ya burge mama. Kwan...kwan kina ciki ne Alhaji bilyaminu yace sa'ar daya shiga farfajiyar gidan yana wani bubbudewa waishi ga dan duniya ina nan shigo ciki mama tace jikinsa na rawa gamida dokin ganinta alhaji bilyaminu yashiga dakin sannan ya zauna akan gado kusa da mama Kai yau ana zafi ki kunna AC mana jiki ba laka kamar kazar da kwai ya fashewa aciki mama ta mike sannan ta nufi makunnin na'urar sanyaya dakin ta kunna. Tun da yanzu mun gama da maganar mota kamata kuma yayi ace na saya miki gida Alhaji bilyaminu yace yana kallon irin kirar da Allah yayi mata sai yaga kamar ta kara kyau. Azuciyarsa yana cewa idan na rabu da mama bazan sake samun wata mace aduniya kamarta ba. Mama ta dawo kusa dashi ta zauna. Kai din ne zaka iya sayawa mutum gida? Wannan ma sa'a akayi kasa kudin shima saida ka Kwangemin naira dubi dari Alhaji bilyaminu ya cire babbar riga gamida hularsa ya ajiye agefen gadon sannan ya shafi dogon sankonsa daidai lokacin da sassanyar iskar ta fara fifitashi Da'ace hajiya mai gidan nan zata amince da wannan gidan da kike ciki zan saya miki. Allah sa. Mama tace a yatsine sannan ta dubi wayarta tana mai mamakin abinda yasa haryanzu su bebi basu nemeta ba anya kuwa yan sanda ba nemanta sukeyi ba tasan babu abinda zai hana ace ita ta kashe shi. Tunanin me kikeyi naga kinyi shiru? Alhaji bilyaminu ya bukata Tunanin rayuwa mana Haba mama kedai kin fiye damun kanki wallahi menene yayi zafi haka da har ya gagari ruwan sanyin da zamu zuba masa? Mama tayi shiru bata bashi amsa ba lokaci guda kuma tana dan wasa da yan yatsun hannunta zamansa adakin tuni ya gama gundurarta domin duk hankalin ta yana abuja. Saidai babu yadda ta iya tunda dai ya zuba mata naira dubi dari biyar a asusunta in banda wannan da tuni ta fatattake shi nan da nan saita sami kanta tana mai addu'ar inama dai ya gaggauta yayi abinda zaiyi ya fice ko ya kyaleta da abinda ke damunta. Na dade banga murmushin ki ba dan Allah ki saki fuskarki mana ko ayi mana ruwan sama. Mama ta saki wani busashshen murmushin yake ta dubi Alhaji mai dogon sanko tace Kaidai Alhaji baka girma Alhaji bilyaminu ya kwanta ajikinta sannan ya kama hannayenta yace in har zan tsufa da wannan harka to kuwa ina tabbatar miki cewa harshe ma zai tuba da yawan surutu. . Amma kuwa kayi asara mama tace cikin zuciyarta in banda sha'anin karuwanci mace batada zabi da babu abinda zaisa ta mu'amala da dattijo kamar wannan dan kusan shekara sittin shi yasa a kullum ta tuna da tarihin da ake ta fada mata tun tana karama saita jinjinawa mahaifinta domin akalla dai shi bai yarda sunyi zaman banza da mahaifiyarta ba aurenta yayi. . Kai amma fa zanen kunshin nan naki yayi kyau Alhaji bilyaminu yace lokaci guda kuma ya tura mama ahankali ya kwantar da ita akan gadon sannan ya sake duban hannunta yace kai kunshin nan naki ya zanu ZIZI. . Yana gama fadin haka sai yasa hannunsa ya shafi zanen dake hannunta awannan lokacin ne to yaga kakkauran hannunsa ya zuke yakoma kamar lawurjen wando. Kai-Kai meye haka? Alhaji Bilyaminu yace a tsorace yana kallon hannunsa. Mama ta tashi zaune a tsorace domin tariga tasan abinda ke shirin faruwa tashinta keda wuya sai taga hannun Alhaji Bilyaminu ya shanye yakoma kamar maburgi sannan ahankali sai na hagun ma ya zuke nan take. Wayyo Allah... Wayyo na shiga uku Alhaji bilyaminu yasa ihu agigice sannan ya mike tsaye zaifito aguje daga dakin. Taku uku kawai yayi sai ya zame ya fadi kafafunsa ma sun shanye bazasu iya daukar nauyinsa ba. . Aka kece da mahaukaciyar dariyar nan sannan sai kakkausar muryar tace Daga yau bazaka sake shafar hannun matar kowa ba ballantana tawa. . BABI NA HUDU 4 Faisal yayi fakin da motar akusa da sauran motocinsu guda uku ya bude kofar motarsa yafito da lema ahannu domin ruwan saman ya dada kecewa kamar da bakin kwarya Tabbas laifina ne faisal ya fadawa kansa sa'ar daya nufi inda ginin gidan yake agaggauce yana tafiya iska na dawo dashi baya sakamakon lemar dake hannunsa kodayake dai lalura ce ta kawo haka. Faisal ya kuma fadawa zuciyarsa idan ba rashin lafiyar mahaifiya ba me zaisa na in tafi nabar sabuwar amarya ta kwana daya kacal da tarewa har kusan goma sha biyun dare ban dawo gida ba gashi nan yanzu na barta ana neman a tsorata min ita yaya zatace wai nine kwance kusa da ita? Ahaka yana wannan tunani har ya shiga cikin dakin kwanansu. Sannan ne to yayi turus yana kallon Fadila wacce ke zaune akan matashin kai ta takure ajikin bango daga can kuryar daki tana sharbar kuka. . Daina kuka gani nadawo... Fadamin duk abinda ke faruwa fadila ta dubi fuskar mijinta a rude tasan abin kenan da yakamata tayi ta fada masa dukkan abinda yafaru tun daga ranar da sukaje kunshi gidan dan daudun har zuwa yanzu sai dai tambayar anan itace anya kuwa faisal zai iya amincewa da wannan labari mai kamar tatsuniya. Faisal ya matsa kusa da amaryarsa ya zauna sannan ya mika hannu zai janyota jikinsa sai yaga ta janye jikinta cikin sauri. Meye kuma haka wai meke damunki ne ki fadamin mana. Fadila ta dubeshi cikin sheshshekar kuka wani aljani ne ke damuna faisal shine yazo min a siffarka. Faisal ya dubi fadila a rude azuciyarsa yana cewa anya kuwa yarinyar nan ba tabuwa tayi ba. Aljani fa kikace mai siffanta a kwance akusa dake to yanzu yana ina? Faisal ya tambayeta akwai alamun zargi karara akan fuskarsa. Ya bace... Kanayi min waya ya bace Faisal ya girgiza kai sannan ya dubeta da murmushi yace Kinga fadila kin kwantar da hankalinki kawai babu wani abu da zai sake faruwa tunda gani na dawo ina ganin tsorata kawai kikayi ganin bana nan shine kika fara gane gane. Daman na sani wannan ma bai yarda ba to yaya kuma idan na bashi labarin gidan kunshi fadila ta fada aranta. Come On fadilata zo nan ki kwanta faisal yace yana nuna mata kan cinyarsa cikin lallashi Cikin sauri fadila ta dada janye jikinta ta dada mannewa da bangon kamar zata huda bangon ta shige ciki Faisal ya dubi amaryarsa cikin tsananin mamaki sannan saiya mike tsaye akan gadon a dudduke ya nufi inda take zai janyota jikinsa lokaci guda kuma yana cewa zo nan mana kefa wallahi kin cika rudewa da yawa. Kada ka tabani dan Allah fadila ta roke shi cikin karaji yanzu kam ta riga ta sani rayuwarta data mijinta suna cikin hadari. Me kike nufi ba zan tabaki ba fadila? Faisal ya tambaya akwai alamun sosuwar zuciya akan fuskarsa. Nidai nace kada ka tabani dan Allah zanyi ma bayani cikin fushi sai faisal yakai mata cafka ya fizgota jikinsa tana fadowa zai zanin dake jikinta ya fadi sannan ne to faisal yayi sororo yana kallon abin mamaki tun daga kasanta har zuwa kan kirjin amaryarsa fadila zanen furanni ne kunshin zamani irin wanda yace tayi masa kafin akawota batayi ba. . Tambayar farko data fara zuwa zuciyarsa itace yaushe har farida ta fita akayi mata wannan zanen ita da aka kawota gidan jiya jiyan nan faisal ya dubi amaryarsa fadila wacce ke kwance rub da ciki akan cinyarsa tana kuka. Yaushe kika fita akayi miki wannan? Ya tambayeta akwai alamun zargi karara a yanayin sautin muryarsa. Fadila tayi ajiyar zuciya ta riga tasan an rutsata bata da mafita dolene ta fada masa gaskiyar al'amarin ko ya yarda ko kada ya yarda. Kayi hakuri Faisal.... Wallahi agidan wani dan daudu mukaje yayi... Me faisal ya daka mata tsawa cikin kaduwa gidan dan daudu....kai amma fadila kin cuceni yanzu daga kawo min ke jiya shine har kika fita unguwa batareda kin fadamin ba kikaje kika budewa wani katon banza tsaraicinki yanayi miki zane Wallahi kin cuceni yana gama fadin haka sai ya turar da ita gefe guda ya tashi tsaye. Fadila ta fashe da kuka tsaya kaji dan Allah faisal bari na karasa maka abin.... Babu wata magana da zan sake saurara daga bakin kifaisal yace bakinsa na kumfa saboda tsabar zafin zuciya. Shine da kika fake da aljani zakiyi masa karya.... Waya sani ma ko dan daudun kika kawomin gida kikace wai aljani ne a kwance kusa dake... Allah ya isa tsakanina dake fadila. . Fadila ta kife kai akan gadon ta fara rusa kuka Ahaka suka wayi gari ita tana cikin dakin kwanansu tana rusa kuka shi kuwa yana falo zaune akan kujera hawayen bakin ciki na zuba akan kumatunsa gari na wayewa ya mika mata takarda. NA SAKE KI SAKI BIYU 2. ** ** ** ** ** Farida na zaune agefe guda tana sheshshekar kuka yayinda dalibai keta tururuwa daga dakin kwanan dalibai zuwa kallon kabir wanda ke kwance akan wani daben siminti wasu tsofafaffi uku sun zagaye shi suna tofe shi da yawu daga baya bayan cincirindon daliban wasu masu karancin kunya sun fara gunaguni me zai hana a tafi dashi asibiri tunda dai ga bakinsa nan har jini yakeyi. Duk wannan rudani da akeyi farida na can gefe nesa dasu bama kowa yake lura da ita ba domin hankalin jama'a na kan kabir wanda ke kwance yana murkususu gashi kuma daman ma duhun dare tuni ya gama shigowa dan haka su kansu tsofaffin dakeyi masa addu'a saida wasu samari suka taimaka wajen haske gurin da fitilolin dake jikin wayarsu. . Ana cikin wannan rudani sai farida taji wayarta ta fara ruri ajakarta hakan shi yadawo da ita cikin hankalinta akaro na farko tasan cewa daga gidane meyiwa ake nemanta jiki na rawa ta zaro wayarta daga cikin jaka sannan ta kara a kunne. Hello tace da wata malalaciyar murya Farida...Farida nine baba ali Alhaji yadawo na fada masa abinda kikace na fada shine yace in taho yanzu yanzun nan na mayar dake gida kina ina? Farida ta lumshe idanu tana sauraron sa har sa'ar daya gama sannan sai ta kuma cewa cikin malalaciyar murya Taho mu tafi zan jiraka a filin fakin. Gama fadin haka keda wuya saita zagaye taron jama'a tabi duhun dare ta wuce kai tsaye zuwa filin fakin. Ayanzu duk abubuwan da suke faruwa sun fara dawowa cikin zuciyarta garai garai tabbas tasan da kabir bai matsanta mata ba daya bari sun zauna hirar arziki batareda yayi kokarin turo bakinsa izuwa sumbatarta ba to da yanzu yana nan lafiyarsa kalau. Kabir shi ya janyowa kansa... Ba laifina bane farida ta kuma jaddadawa kanta amma duk da haka dai ta tausayawa kabir musamman da taga bakinsa ya koma baya. Tana nan tsaye ita kadai a tsakankanin daidaikun motocin da suka rage a filin fakin din zuciyarta lullube da duhun rudanin dake tattare da rayuwarta ta kasa tunanin komai ahaka direbanta baba ali ya sameta. Tunanin me kikeyi ne? Ya tambayeta cikin mamaki sa'ar daya tsaya akusa da ita domin yaga hon dinsa uku bata juya ba farida tayi firgigit kamar wacce ta tashi daga wani nannauyan barci ta dubeshi sannan ta juyo tayiwa inda kabir ke kwance ganin karshe. . Kace baba ya dawo? Ta tambaya batareda ta kalli baba ali ba lokaci guda kuma ta bude gidan baya na motar ta shige ta zauna Tun dazu ya dawo...misalin biyar da rabi na dauko shi a filin saukar jirage ya tambayeni ke sainace dashi jarrabawar gwaji kikeyi ba zaku tashi ba sai karfe takwas baba ali ke fadin haka amma bai yarda sun hada idanu da ita ba. Uhm abinda farida tace kenan azuciyarta tana mamaki domin bata taba ganin mahaifinta yadawo karfe biyar da rabi ba. Dattijo baba ali ya tuka motar ahankali ya nufi kofar fitar daga sabuwar jami'ar bayero ta kano lokaci guda kuma ya gyara madubin gaban motar na sama ta yadda zaike iya samun damar satar kallon fuskar farida shirun da tayi da kuma irin yanayin fuskarsa awannan lokaci yafara damun zuciyarsa duk da yake dai har yanzu nan zuciyarsa bata karaya ba tun da dai daman kome zai faruma ai ba'a son ranta za'ayi ba. Sannu ahankali suka kawo kofar fita daga sabuwar jami'ar bayaro direba baba ali ya mikawa mai gadi balgacaccen jar roban da ake baiwa duk wanda zai shiga jami'ar amatsayin shaida yana fitowa daga kofar jami'ar sai ya karkata hannun dama yabi hanyar da zata kaishi Gwarzo maimakon yabi wacce zata dawo dashi cikin birnin Kano. Ina kuma zamu? Farida ta tambaya cikin mamaki. Baba ali ya shafi doguwar hular dake kansa mai kamar ribabbiyar dankali yace ranki yadade yimin afuwa muje nan gaban jan guza musha mai. Haba baba ali duk man dake cikin gari bai isheka ba har sai munje gaban wani jan guza? Baba ali ya karawa motar giya daga daya zuwa biyu sannan ya kaiwa wani nacaccan kuda duka dake ta faman zarya agefen kunnensa na hagu Mai yafi araha awajen gari shiyasa nake neman ki rufa min asiri kamar yadda nima na rufa miki kinga dan ragin da muke samu da shine muke dan rage zafin garin nan. Baba ali yadanyi shiru yana satar kallonta cikin madubin dake saman motar. Shikenan farida tace dashi sannan ta dauke kanta gefe guda tana kallon korayen ciyayi da tafasa da sukayi sahu sahu agefen hanya abin gwanin ban sha'awa daga inda take zaunen acikin hasken fitilun motocin dake ta wuce su tana iya hango koramu inda ruwan damuna ke taruwa wasu kananan kwari sai sunturi sukeyi a saman ruwan acikinsu har dani dan tsololin kwaro mai siffar jirgi mai saukar ungulu. Wata kawar farida ta taba cewa da ita siffar wannan kwaron nasara ya kwaikwaya lokacin da zai kera jirgi mai saukar ungulu. . Na fuskanci kamar kina sha'awar ganin korayen ciyayi acikin hasken fitilu direba baba ali ya tambaya sa'ar daya lura da cewa tunda suka baro kofar jami'ar idanunta waje suke kallo. Uhm suna burgeni musamman da yamma likis kafin rana ta gama faduwa Harzuwa lokacin da farida ke wannan batu zuciyarta bata daina hasko mata jifa jifan hoton al'amarin daya faru akan kabir ba. To amma tafiyar da suke yanzu ahankali ta fara samun saukin kaduwar dake dabaibaye da kwakwalwarta musamman ma lokacin da ta sauke gilashin motar daddadar iskar damuna mai dauke da kamshin kasa da tsirrai ta daki fuskarta. Haryanzu bamu karasa gidan man bane? Farida ta tambaye shi ganin cewa tafiya ta mike har sun wuce kwanar jun guza yana nan gaba kadan awani dan kauye dattijon direban yace batareda da ya dubi fuskarta ba. Sannu ahankali suna tafiya har mintina biyar suka shude adaidai lokacin ne dattijon direban ya ragewa motar wuta adaidai wasu dogayen duwatsu dake gaban wani gulbi ma'abocin tarin ciyayi masu tsaye baba ali ya karkata kan motar lokaci guda ya kutsa ta cikin ciyayin zuwa bayan dutsen sannan ya tsayar da motar. Me....me kuma zamuyi anan? Farida ta tambaya a tsorace akwai alamun firgici karara akan kyakkyawar fuskar budurwar Dan Allah baba ali ka fitar damu daga cikin wannan kungurmin dajin..... Ya zaka shigo damu nan acikin wannan duhun dare Baba ali ya dubeta da wani kekasasshen murmushi lokacin bada umarninki ya rigaya ya wuce yanzu nike da ikon bada umarni. Ban...ban fahimce ka ba? Farida tace a tsorace lokaci guda kuma tana duba izuwa cikin duhun daren da kuma dogayen duwatsu da ciyayin dake zagaye dasu. Tuni ta fara tunanin mafarki takeyi tabbas wannan ba gaskiya bane awata duniyar dai take. Abinda nake nufi shine duk abinda nace kiyi sai kiyi baba ali yace lokaci guda kuma ya bude gidan gaba na motar ya fito waje sannan saiya bude gidan baya na motar inda farida take zaune ya zauna akusa da ita cikin sauri kamar wacce maciji ya rabeta ta matsa can jikin daya kofar motar a tsorace. Kaga baba ali wannan in wasa ne ni bana so dan Allah ka fitar dani daga cikin dajin nan. Ba wasa bane farida wannan al'amari gaske ne na dade ina fatan samun wannan dama ban samu ba sai yau.... Me.... Kake nufi farida ta tambaye shi a fusace kuma rabi a tsorace Abinda nake nufi shine ki cire kayanki ahankali tun kafin na cire miki su. Haba... Baba ali ya zakayimin haka ? Kamar yaya na cire kayana? Nace ki cire kayan jikin mubi abin nan ahankali ko so kike na takura ki da karfin tsiya? Na shiga uku farida tace cikin shashshekar kuka dan Allah ka rufa min asiri....wallahi ni ban tabayin abinda kake nufi ba. Yau zaki fara cire kayanki kigani baba ali yace sannan ya matsa kusa da ita ya dora hannunsa akan kafadarta. Cire mana yar 'yata yanzu zamu gama farida ta rike numfashinta cikin tsananin kaduwa hannun dattijon direban dake kafadarta tamkar wani kan bakin maciji take jinsa. Kada ka tabani dan Allah... Matsa daga kusa dani farida takuma mannewa ajikin kofar motar lokaci guda muka ta rufe hancinta da tafin hannu domin duk lokacin da dattijon yayi magana sai taji bakin sa na hamami kamar bakin kura tabbas tasan kowane lokaci daga yanzu zata iya fara amai. Zan lissafa miki uku baba ali yace kana yayi wuce ya kama gefen rigarya da busassun hannayensa masu kamar itace. Idan baki cire ba ni zan cire miki. Farida ta kwalla ihu a razane sa'ar dataji ya fara ja mata riga har wuyan rigarta ya sauko zuwa kafada duwatsun dake zagaye dasu suka amsa kuwwar datayi wani kurege ya ruga aguje ya shige cikin raminsa a tsorace sakamakon ihun. . Duk wannan bazata kaiki ba fitananniya ai ba akaina kika fara ba yana fadin haka sai ya cafko hannunta da zummar ya janyota jikinsa ga mamakinsa sai yaji kamar ya cafko tubakin kankara nan da nan yaji hannunsa ya sandare sannan sai jinin jikinsa yafara tafiyar hawainiya acikin jijiyoyinsa adaidai lokacin da wata sassanyar iska mai karfin gaske ta fara fifita su acikin Motar. Baba ali yaji hannayensa sun dada sandarewa cikin gaggawa ya saki hannayen a tsorace kana ya dubeta Me kikayi min naji hannuna kamar zai tsinke? Kafin ya rufe bakinsa sai yaji wani abu kai karfin gaske kamar kofaton doki ya daki tsakiyar fuskarsa. Wayyo Allah Wayyo Allah. Farida tayi sororo ciki rudani tana kallon ikon Allah tabbas yanzu tasan abinda ke faruwa abin nan mai kamar kofaton doki ya kuma dungurowa ta cikin tagar motar ya daki gefen fuskar baba ali. Wayyo Allah... Na shiga uku. Sai ka shiga talatin ma idan ka kara tabamin matata kakkausar murya mai amsa amo tace adaidai wannan lokacin ne to farida taji lema lema ajikin sangalalin hannun tatana tabawa sai taji wani abu mai laushi laushi dago shi sama keda wuya saita jefar dashi sannan cikin tsananin razana sai hannunta ya kai izuwa mabudin kofar motar farida ta bude sannan ta nufi hanyar da take tunanin zata kaita izuwa bakin titi aguje tana ihu kamar mahaukaciya. Abinda yasata wannan firgici abinda yasata wannan gudu tana ihu shine kunnen direbanta Baba Ali datagani akan sangalalin hannunta yana mots kamar kosai mai rai. ** ** ** ** Bebi ta wangame baki tana hamma babu kalmar shahada sai wani dan ihu da tayi kamar tsuntsuwa sannan taja wata doguwar mika akan tattausan gadon alfarmar ta mirgina kamar yadda jaki yakeyi idan yana wanka acikin toka. Kai ashe rana tayi haka. Tace da kanta sannan cikin lalaci acikin tattausan kilishin dake mamaye da tsakar dakin. Ahankali kamar kazar da kwai ya fashewa aciki bebi ta nufi gindin tagar dakin dake fuskantar koren lambun shakatawar gidan honorabil sabo dake bayan dakin ta zuge labulen sannan ta bude tagar dakin sassanyar iska tsabtatacciya daga cikin lambun ta bugi fuskarta. Bebi tayi ajiyar zuciya domin taji sanyin iska yafara yawa Da gaske dai sanyin za'ayi kenan? Ta tambayi kanta da kanta ganin cewa har kusan biyu amma kamar goma sannan saita bar jikin tagar ta dawo kan gado ta zauna tana tunanin makomarta lokaci guda kuma ta dubi fuskarta acikin dan madubin dake daf da gadon ba karamin kaduwa tayi sa'ar dataga fuskarta ta fara tauyewa hakanan baki baki shudi shudin tambarin Bilicin yafara bayyana a fuskarta. Na shiga uku bebi tace a tsorace ta riga tasan bayan kyan kirar jikinta da take takama dashi abu na biyu dake fizgo hankalin mazaje izuwa gareta shine kyawun fuskarta. Bebi ta sake zubawa fuskarta idanu cikin kaduwa domin ta lura duk ta lura fatar ta fara saki kamar fatar dadadden mangwaro duk da yake dai bebi tai imani da cewa ta gama kama ruhin honorabil sabo amma abin ya bata tsoro domin ta sani idan batayi hanzari ba honorabil sabo na iya sauya aniyarsa ta aurenta dayafara yi duk da yake dai tasan cewa ba ra'ayin kansa bane ya aure ta malaman tsibbunta da bokayenta ne ke ta aiki akansa amma yanada kyau ace idan kanada kyau ka kara da wanka wannan tunanin shiyasa bebi ta sake kallon kanta ajikin madubi akaro na uku sannan saitace da kanta cikin takaici. Haba fuskata... Ya zakiyi min haka? Tana gama fadin haka sai bebi ta lalubi wayarta akasan matashin kai ta daddanna wasu lambobi sannan ta kara wayar a kunne acan jimawa saitace. Hello.... Malam ina kwana? Lafiya lau. Akace adaya bangaren kudin nan dana turo ma yazo ko? Kwarai kuwa yazo masha Allah Allah yasaka da alkhairi aka amsa adaya bangaren shiru na dan lokaci. Dan Allah malam sai akuma dage min kaga haryanzu dai zancen auren nan namu shiru kwata kwata ma ya daina zancen rabon da yatada zancen tun kafin mutuwar abokinsa honorabil jatau kaga yau kusan wata uku kenan fa Malam. Kada ki tashi hankalinki 'yata. Akace da wata kakkausar murya acan daya bangaren nafada miki tunda mukayi wannan aikin na farko babu abunda zai hanashi aurenki. To ai malam ni abin ne da ban tsoro kaga fa da ba'a sama da kwana biyu banganshi ba amma yanzu tunda abokin nan nasa ya rasu sai inyi kwana goma ban ganshi ba ya ajiyeni kawai sai kiwatani yake kamar akuya kullum yana shagwaba ni da jin dadi amma ni duk wannan bashine agabana ba nidai burina shine ya aureni kuma idan da hali ma so nake matarsa uwar ya'yansa tabar gidan. Kada ki damu babu abinda ya gagari malam. Aka danyi shiru acan daya bangaren yanzu yaushe rabon da ku gana dashi? Ido da ido dai yau anfi kwana shida amma kullum muna waya kamar sau uku zai tambaya idan kayan abincina ya kare sai a karomin akwai wanda yake aikowa. To shikenan Allah rufa asiri yanzu ina ganin wani aikin zamu sake. To malam bebi ta amsa cikin gaggawa zamu bukaci bakaken tinkiyoyi guda goma wadanda babu sofaren fari a jikinsu To malam nawa ne kudin saina kawo ma gobe da kaina. Yan kanana dai basa wuce dubu shida shida.... Kada ka damu zan kawo ma dubi dari gobe sai ayi duk abinda yakamata nidai burina shine...... Bebi tayi shiru sa'ar dataji motsi da surutun Jama'a a farfajiyar gidan. Zan kiraka in an jima bebi tace da malamin kafin ya amsa ta kashe wayar. Lokaci guda kuma ta koma kan gadon ta kwanta lamo kamar tashinta kenan daga barci batayi minti guda da kwanciya ba aka banko kofar dakin da karfin tsiya aka shigo bebi ta dago kai a firgice cikin mamaki sai taga honorabil dinta sabo tsaye a tsakiyar dakin kallo daya tayiwa fuskarsa tasan cewa tabbas ba lafiya jiki na rawa ta tashi zaune akan gadon ta dube shi amma batace uffan ba. Tashi kisa kayanki ina san magana dake akwai alamun karkarwa acikin muryarsa haka nan bebi ta lura da fuskar honorabil sai naso take da gumi Lafiya..... Me yayi zafi haka? Bai amsa mata ba sai ya nufi bakin gadon ya zauna sannan ya dubeta . Abinda Nake Gudu Ne Bebi Shiya Faru Honorabil Yace Yana Girgiza KaiMaganar kawarki ce mama gashi nan yanzu ita jami'an tsaro suke nema. . Bebi taji gabanta yafadi kana nufin kace dani ita ta kashe shi? Honorabil ya girgiza kai cikin damuwa babu tabbas amma sunanta ne a shafin zargi na farko honorabil ya danyi shiru sannan sai ya dago fuska ya dubi bebi ido da ido yace. Nayi Nadamar haduwa dake bebi da nasani daban dora idanuna akanki ba Bebi gashi yanzu kin sani acikin masifa bebi ta dafe kirji cikin kaduwar jin bakaken kalaman dake fitowa daga bakinsa. Haba darling me yayi zafi haka sai kace ni na kashe shi ni meye laifina acikin wannan al'amari ? Da bansanki ba da bazan taba mu'amala da mama ba abinda baki sani ba shine masu gadin gidan marigayi jatau ne suke bada shaidar sun ga mun shiga mu uku sannan mun fito nidake sun tabbatarwa da jami'an tsaro cewar acan gidan mama ta kwana. Akan dole aka takura ni na amsa cewa eh lallai haka akayi... Honorabil sabo yayi shiru ga mamakin bebi saitaga hawaye ya fara sartu akan fuskarsa. Kin cuceni bebi kin zamo sanadin barin kujerata domin idan wannan abun kunya yafito fili idan ya tabbata cewa mama ce ta kashe shi dole ne a tsigeni daga kujerata. . Mama bazata iya kashe mutum ba.... Wallahi nasan ko bera mama bazata iya kashewa ba. Honorabil sabo ya mike tsaye a fusace ya dubi rabi saikifito ki fada musu haka dan suna dakin shakatawa suna jiranki. Bebi taji gabanta ya fadi. Su wanene? Ta tambaya a tsorace. Jami'an tsaro zasuyi miki tambaya ki kuma kaisu inda zasu sami mama yana gama fadin haka saiya lalubi aljihunsa ya zaro naira dubu biyu ya jefa mata akan gadon sannan yace. Na baki minti goma ki hada kayanki gaba daya kifito ki bisu daga yau bana kara son ganin kodaddiyar fuskarki agidan nan Bebi ta fashe da kuka haba.... Darling kai da kace zaka aure ni yanzu duk zaman da mukaiyi da wannan zaka sakamin dubi fa wai da dubu biyu ma zaka sallameni. Honorabil jatau ya dubeta da murmushin yake sannan saiya sunkuya ya dauke dubu biyun daya bata. Sannan yace Idan bakyaso ni inada bukata domin banzan abinda gobe zatayi ba saikiyi sauri kada su gaji da jira yafice daga dakin cikin gaggawa. . BABI NA BIYAR 5 Fadila ta kalli fuskar wayar tafi da gidanka dake gabanta sannan saita rufe idanu ta fashe da kuka wayar taci gaba da ruri gashi dai tana ganin Faisal dinta ne ke kira amma batada ikon ta amsa wayar. Umarni ne na mahaifanta. Kada ki kara amsa wayarsa har sai mun gama aikin da zamuyi akanki.... Bakida lafiya fadila tabbas kin hadu da lalura babba. . Fadila ta tuno da maganar mahaifiyarta sa'ar da wayar taci gaba da ruri agabanta hawaye na zuba akan kyakkyawar fuskarta hannu na rawa ta dauko wayar ta danna gurin amsawa amma batace kala ba sai kawai ta kara a kunne tasan yanzu haka wani yana labe akusa da kofar yana sauraro datace Hello mahaifiyarta zatashigo ta hauta da fada dan haka sai fadila ta lumshe idanunta tana sauraron tattausan muryar faisal dinta acan daya bangaren kamar zai fashe da kuka yana cewa. . Fadila... Fadila yanzu bazaki amsa min ba nasan kina sona nima ina sonki Wallahi kuskure ne fadila... Hello dan Allah ki amsa min ko naji muryarki na sami saukin kunan zuciya.. Halo... Fadila. Fadila taji kamar ta amsa masa amma maimakon haka saita lumshe idanunta taci gaba da sauraron muryarsa tasan yasan tana sauraronsa kuma tasan tana son itama tayi magana dashi amma tasan baisan abinda ya hanata amsa masa ba. Idanunta a lumshe yanata surutunsa har kudin wayar suka kare. Maimakon fadila ta bude idanunta saita kara runtsesu zuciyarta tafara dawo mata da majigin rudanin da suka biyo bayan watanni uku da suka shude masu kama da shekaru uku agurin fadila. . Watanni uku sun shude kamar wasa abubuwa dayawa sun faru acikinsu harda takunkumin magana da ake sawa fadila. . Kin cuceni Fadila na sake ki saki biyu taji amsa kuwwar muryar datafi kauna fiyeda komai aduniya tana ruri cikin kwakwalwarta. Fadila bata taba ganin masifa irin ta wannan safiyar ba domin faisal dinta na gama furucin sakinta saiya rubuta a takarda ya jefa mata sannan ya fice abinsa fitarsa keda wuya aka fara tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya sai da fadila ta shafe sama da sa'a guda tana kuka daga karshe dai ta fahimci cewa koda fa kukan jini zatayi saidai jinin jikinta ya kare dan haka jiki na rawa zuciya na kuna ido na yararin ruwan hawaye fadila ta dauki yar karamar jala irin ta mata sannan ta kwashe duk hotunan da suka dauka ita da faisal dinta tun farkon soyayyarsu har zuwa daurin aurensu ta zuba acikin jakar daga wannan jakar bata dauki komai ba sai lemar faisal saboda ruwan da ake makawa. Ruwa na dukan rabin jikinta lemar dake hannunta kuma na kare wani bangaren a haka ta iso bakin titi neman mota duk kuwa da cewa filin fakin din katon gidansu na alfarma akwai manyan motoci sama da guda uku. Titunan babu kowa sai jifa jifan motoci da kuma yan kabu kabu da ruwan yagama jikawa ba'a dade ba fadila tayi sa'a wani dan mashin mai rumfa da taya uku launin rawaya ya tsaya agabanta jikinsa an rubuta ADAIDAITA SAHU wani bawan allah mai siffar kamala da dan gemu tsurut kamar jelar dawisu shike tuka wannan mashin. Tun kafinma fadila tagama bayanin inda zata mai mashin din yace ta shiga domin ya lura tana cikin matsanancin hali. Lokacin da fadila ta shiga babban dakin shakatawar gidansu ba karamin kaduwa tasa mahaifanta da kuma yan uwanta ba domin kannenta da wasu yan uwanta guda hudu sunci kwalliya jira sukeyi kawai a dauke ruwa akaisu gidan amarya kwatsam sai gata acikin dakin shakatawar ta jike shakaf da ruwa kamar algarar goro idanunta sunyi luhu luhu saboda kuka tana zuwa saita wuce gurin mahaifiyarta aguje ta fada akan cinyarta ta fashe da kuka. . An dauki sama da awa guda kafin ashawo kanta daga karshe dai mahaifiyarta da wata kanwar mahaifinta suka shiga da ita wani daki inda ta ZAYYANA musu wannan labari mai kama da Almara matan suka kwashi salati sa'ar da tagama basu labarin. Ba'afi sa'a biyu da zuwanta gida ba saiga mahaifin faisal da wani abokinsa sunzo gidan abubuwa suka dada rincabewa to Amma sa'ar da sukaji wannan labari sai suka baiwa iyayen fadila hakuri akan cewa shashanci ne irin na yaran zamani acewarsu duk da yake dai akwai matsala bai kamata dansu ya saketa ba to amma sun bada shawarar lallai adage mata da addu'a daga karshe mahaifin faisal yace zai dawo da magariba domin su tattauna yadda za'a shawo kan wannan al'amari don alokacin mahaifin Fadila baya nan haka nan mahaifin na faisal ya dada da cewa kada a sake a dauki koda Allura daga gidan yaran. Washegari aka tura malamai sukayi ta addu'o'i akan fadila baji bagani tun daga wannan rana kullum sai anyi mata addu'a watan farko daya biyo bayan faruwar al'amarin anso a mayar da auren faisal da fadila amma sai wani malami yabada shawarar abari tukunna agama yi mata addu'o'i domin in bahaka ba sai aljanin yaci gaba da wahalar da ita. Yaran zamani saidai hakuri amma suna da sakaci malamin ne ke yiwa mahaifin fadila bayani. Kaga yara ne idan zasu kwanta barci basusan suyi addu'a ba gashi Ayyatulqursiyyun nan duk kusan yaron dayan taba zuwa islamiyya ya haddaceta amma bazasu iya karantata ba idan sunzo kwanciya saidai suyita kallace kallacen fina finan banza su raba dare suna yi kuma da zarar sun tashi kwanciya kawai zasuyi babu wata addu'a. Wai to Allah gafarta malam meke faruwa ne matanmu ke fama da matsalar aljanun nan yanzu fa duk acikin mace goma baka rasa akalla guda biyar masu fama da matsalar aljani? Mahaifin fadila ya tambayi malamin. Wato Alhaji mafi yawan matan da jinnu ke hawa kansu sakaci ne kaga na farko da akwai zama da sukeyi cikin kazanta da rashin tsarki sun iya shafa mai da hota da turare amma jikinsu babu tsarki na biyu kuma akwai bayyana tsaraicinsu a fili wasu ma tsirara suke kwana wasu ko suyi ta yawo da kaya rabinsu tsirara ga barin gashi a waje duk wannan suke janyo hankalin aljanu su sami damar shiga jikinsu.... Wato abin dai Alhaji saidai addu'a yanzu in ba lalacewar zamani ba yaushe ne za'a ce wai ZAYYANA na kunshi ta wuce tafin hannuwa da kafafuwa ta kai har tsaraici kai Allah yayi mana tsari da wannan shaidanci. Ameen malam... Amin wannan duk ya farune watanni uku da suka shude. A tsayin wannan lokaci kullum sai anyiwa fadila addu'a da yan rubuce rubuce nasha. Mako guda da faruwar al'amarin ne watarana da yamma sai faisal ya bugowa fadila waya alokacin suna tare da mahaifiyarta fadila ta dubi wayar cikin tsanancin mamaki domin bata taba tsammanin bayan abinda yafaru faisal zai nemeta ba. Faisal ne tace da mahaifiyarta baki na rawa. Kada ki amsa... Rabu dashi dan banza marar mutunci sukayi shiru a dakin na nyan dakiku wayar nata ruri. Kada ki sake inji kin amsa wayarsa in ba rashin mutunci ba ko kwarto ya kamaki dashi a daki ai ya shawarci na gaba dashi kafin ya sakeki amma kwana daya kacal agidan ya sake mana ke dan wulakanci rabu dashi yayi tayi ko za'a mayar da auren nan saiya san darajarki tukunna dan banza mai manyan kunnuwa. Tun daga wannan rana har zuwa yanzun nan da fadila ke zaune tana tuna baya bata amsa masa waya ba. Sau daya dai hana rantsuwa ta taba kokarin ta amsa wayar sai mahaifiyarta ta kamata. Bakiji abinda nafada bako? To wallahi duk ranar da kika amsa saina kwace wayarki kin daina magana da kowa ma kuma babu inda zaki fita ko nan da kofar gidan har sai an gama yi miki addu'o'in nan uwar shegen taurin kan tsiya babu yadda banyi dake ba akan wannan shegen kunshin tsaraicin amma saida kikayi yanzu gashi nann kin hada mu da wahala da ganin wulakanci. . Fadila tayi ajiyar zuciya sa'ar data gama wannan dogon tunani adaidai lokacin ne kofar dakin ta bude mahaifiyarta ta shigo dauke da wani dan kofin tangaran a hannunta kamar jira ake ta shigo. Wayar ta sake daukar ruri Fadila ta kalli fuskar wayar Faisan ne ke kira. Shi din ne? Mahaifiyar ta tambata tana kallon yarta tausayinta ya kamata yau saura kwana biyu a gama mataaddu'o'in Da Akeyi. Wayar Taci gaba da ruri fadila taci gaba da zubar da hawaye. Amsa masa. Mahaifiyarta tace da yarta a tausashe sannan saita fice daga dakin. ** ** ** Safiya ce mai dauke da kurar hazo ga iska abin babu dadi ga sanyi kamar ya tsaga kashi jama'a sai korafi sukeyi kamar yadda suka sabayi akowane irin yanayi duk da cewa dai sanyin ya uzurawa kowa ya hana kowa sakat amma akwai wasu tsirari da suka dage akan cewa sufa har yanzu suna nan akan bakarsu cewa sunfi jin dadin sanyin nan akan zafi. Mama bata yarda da wannan ra'ayi ba domin katuwar rigar sanyi mai gashi kamar buzun malam data rufa akan damammun kayanta sun nuna hakan. Abakin titi take tsaye tana jiran tasi akan titin na'ibawa kanta boye cikin wata irin hular gashi haka nan kafafunta ma boye suke cikin takalmi sau ciki irin na mata hatta hannayenta boye suke cikin bakaken safa ka karamar kaduwa Mama tayi ba sa'ar dataga wani dan cuwa cuwar Mai abakin titi ya dauko jarkan mai daga shi sai gajeren wando da wata yar jeleliyar riga singileti mai kamar hanci yana tafe abinsa yana fito kai kace abakin kogi yake lokacin zafi. Oh... Inda ranka kasha kallo mama tace azuciyarta tana kallon saurayin cikin mamaki sannan saita dawo da hankalinta kan matsalar dake gabanta ba'afi mintina biyu da faruwar hakan ba dan tasi ya tsaya agabanta mama ta fada masa inda zai kaita dan tasi ya cajeta kudi da yawa domin inda zai kaita mota bata zuwa gurin domin gindin wani dutse zai kaita gurin wani BOKA dake bayan wani kauye ahanyar Wudil. Mama ta shiga bayan motar ta zauna bata damu da yawan kudin daya cajeta ba domin kudi ayanzu ba matsalarta bane tun da dai haryanzu akwai sama da naira dubu dari hudu acikin asusunta kudin da Alhaji Bilyaminu ya bata domin ta sayi mota abinda yafi damunta ayanzu shine ta kubuta daga hannun mugun aljanin daya sata gaba tuni kasuwarta ta gama mutuwa a jihar kano duk wanda kaga ya kulata to rashin sani ne shima da an fada masa zai tsere ya barta. Jikin mama ya dauki rawa abayan motar sa'ar da tuna wannan muguwar rana watanni uku da suka wuce Ta tuno sa'ar da Alhaji bilyaminu ya fadi a tsakar dakinta yana ihu hannu da kafafunsa duk sun shany sun koma kamar maburgin miya. A lokacin mama tasan abinda ke faruwa musamman ma sa'ar dataji an kece da mahaukaciyar dariyar nan acikin firgici sai mama tasa kururuwa sannan ta fito daga cikin dakin aguje ta nufi kofar gida tana ihun akawo mata agaji kafin kiftawa da bisimilla gidan ya cika da jama'a wasu ko sukace bazasu motsa ko nan da can ba dan daman rashin kunyar mama ta gama isarsu. Aranar da daddare a filin INDA RANKA na gidan radio Freedom suka yayata wannan labari mai kamar almara harma sun sami damar zantawa da mama wacce tayi bayanin wannan masifa data sameta daga yin wannan kunshi na zamani jama'a sukayita fadil ra'ayoyinsu akan wannan al'amari wasu suka tausayawa mata wasu ko sukace Allah ya kara ai yanzu ta daina karuwanci tunda aljani fara buge manemanta saida aka shafe sama da sati guda jama'a na sunturi zuwa gidan mama domin su ganta. Dan haka saida takai idan mama tabar gidan da sassafe bata dawowa sai tsakar dare mama tariga tasan in badan kudin da Alhaji Bilyaminu ya bata ba da sai zaman kano ya gagareta watanni uku da suka shude ko kuda baya sunsunata idan kaga dan duniya ya kulata to bako ne. Wannan al'amura su suka taru suka dami mama domin ta riga tasani bata da wata sana'a data wuce karuwanci takuma riga tasani duk namijin daya rabeta ya shiga uku shin kudin dake hannunta kwana nawa zasuyi kafin su kare idan kuma sun kare din tayaya zata sake samun wasu? Wannan sune tambayoyin da suka addabi zuciyar mama da farko ta yanke shawarar tun da yanzu tanada yan kudi ta samo dan yaro kawai ta aura ta huta da wannan masifa Nan da nan wannan tunani ya rushe kamar yadda ruwa ke rusa tubalin toka tabbas idan har ba Aljanin nan aka rabata dashi ba mama tasan wani namiji bazai kara rabarta ba. Wannan shiya tashi hankalin mama ta tashi tsaye wajen neman magani. To saidai kuma a tunanin mama bokaye ne kawai zasu iya rabata da wannan aljani wata kawarta ta taba cewa da ita wai bokaye da aljanu suke kwana a dakunansu wai har da akwai bokan da yake kwana da aljanu miliyan guda hakan kawar mama ta dada cewa wai boka na iya kiran kowane irin aljani ne ke damunta ya tsawatar masa cewa kada ya kuma damunta idan aljanin yayi gardama wai za'ayi zane shi. Imani da wannan tatsuniya su suka sa mama bin bokaye wannan boka da mama ta nufi gidansa ayanzu shine boka na goma sha daya da zataje gurinsa acikin watanni uku da suka wuce tuni mama ta sayi saji sama da guda dari biyu. . Karfe sha biyu saura suka isa gindin dutsen tsaya nan ka jirani mama tace da direban ma'abocin tarin gashin baki kamar tsohon soja zaki dade acan ne? Meya shafe ka kaidai ba aikin kudi kakeyi ba? Direban ya dubeta da murmushi cikin jin dadin cewa tata Fadi Gasassa. . Gaskiya ne ranki ya dade ina nan ina jira nasan dai ai ma tafi nan da magariba ko? Waya sani ko anan zamu kwana mama tace cikin gatse sannan ta nufi gindin dutsen cikin sauri Tuni mama ta riga ta gama yanke shawarar cikin zuciyarta cewa idan har wannan boka bai rabata da wannan aljani ba to kasar nijar zata shiga me yiwuwa ko zata dace acan tun da dai gashi yau kusan sati uku kenan babu ko saurayi daya daga cikin tsofaffin samarinta daya mata waya. Wannan abu na tada hankalin mama domin ada kullum ba'a kirata ba a kirata sau saba'in sai gashi yanzu ko flashing ya gagara. . Sannunki da zuwa tun jiya daman na ganki tafe.... Yar mitsitsiya ce ta kawomin labarinki ta fada min abinda ke tafe dake amma duk da haka dai zanso inji matsalar daga bakinki. Bokane ke fadin haka. Mama ta zube agaban bokan kamar zata fashe da kuka tace cikin karyayyar murya. Malam... Boka wani aljani ne ke damuna kwata kwata ya hana maza su saurareni mama taci gaba dayi masa dogon bayanin abubuwan dake faruwa akanta kamar yadda ta saba yiwa sauran bokayen da taje gurinsu abaya. Baibayau ne.... Dan banza tabbas Dabaibayau ne ai dan banzan aljani sa'a ma kikayi ai da kika zo nan amma da kin kara wata guda baki zo ba gurgunta ki zaiyi tunda kikace har cinyoyinki ya taba lokacin da yakeyi miki Kunshin. Mama ta rike numfashi a tsorace gurgunta ni fa kace? Kwarai kuwa... Amma kada ki damu ai kinyi sa'a tunda kikazo gurina rufe idanunki bokan ya umarce ta Jiki na rawa mama ta rufe idanunta Bude su bokan ya sake umartarta mama ta bude sake rufewa Mama ta sake rufe idanunta akaro na farko. Sake budewa mama ta sake bude idanu ga mamakinta sai taga wani katon koko agabansa cike da layu iri iri wasu kamar kuli kuli wasu kamar ya'yan barkono wasu kuwa manya manya masu siffar makani. Sake rufe idanunki ki dauki daya bokan ya umarce ta cikin karaji. Jiki na rawa mama ta rufe idanu sannan ta tura hannunta cikin kokon ta dauko laya daya. Bude idanunki ki bani ita mama ta bude idanu lokaci guda kuma ta mika masa layar. Tsawon dakiku bokan ya jujjuya layar a hannu can sai yayi ajiyar zuciya ya dubi mama. Kin hadu da dan banzan aljani mai nacin tsiya amma daga yau din nan kin rabu dashi. Bokan ya danyi shiru yana kallonta. Zamu bukaci ayanka fararen zakaru goma jajaye goma bakake goma dole ne kuma ayankawa aljani dabaibayau burgun gafiya biyar da zomaye uku. Mama tayi ajiyar zuciya ta dubi bokan baki na rawa tace Ko nawa ne zan biya sai asaya in dai zan rabu da wannan jaraba. Ungo rike nan bokan ya mika mata yar karamar layar data zabo mai kamar barkono. Idan kinji gida yanzu kisa ayi miki kitso da wannan layar a tsakanin gashinki kada ki sake ki tsefe sai bayan kwana bakwai alokacin ne zanyi miki duk aikin da kike bukata idan muka yanka duk abubuwan dana lissafa miki abaya aljani dabaibayau zai shanye jinin shikenan kun rabu dashi har abada in dai kina tare da wannan layar. Kana nufin da layar zanyi ta yawo akaina har abada ? Boka ya girgiza kai zaki iya cirewa bayan kwana bakwai amma ki tabbata duk inda zaki kina tare da wannan layar. Na fahimta mama tace baki na rawa sannan saita bude jaka ta kirgi wasu adadin kudi masu yawan yan dubu dubu ta mika masa. Ajje anan bokan yace da ita sannan saiya dubeta ido da ido yace. Idan kwanaki bakwan nan sun cika kina iya kiran duk namijin da kikayi niyya zaizo kuma idan kin nemi aurensa ma zai yarda. Adaidai wannan lokaci sai MUBARAK yafadowa mama arai kana nufin kowa nace ya aure ni sai yayi? Kwarai kuwa dan dole mutum ma sai ya aureki domin ai aljanin ne ke hanasu zuwa shi yake dabaibaye su. Mama ta lumshe idanu cikin jin dadi duk duniya babu wanda take so kamar wani takadirin saurayi alayinsu waishi Mubarak to saidai kuma ya tsaneta domin ko gaida shi tayi mubarak baya amsawa. Wani busashshen murmushin mugunta ya subuce a gefen bakin mama. Shege uban girman kan tsiya shi zan aura mama tace da kanta. *** ** ** ** Acikin wani katon dakin shakatawa ma'abacin yalwa wanda ke dauke da kujerun alfarma sunyi sahu sahu kamar a filin fareti wani tsohon kwamishina ne zaune daga shi sai farar singileti da farin wando na shadda mai tazuge jarida a hannunsa yana dubawa ta saman dan siririn tabarau fari wanda ke zaune daraf a saman dogon hancinsa mai kamar na aku. Lokacin da yana saurayi kafin zamani da tsufa su cimmasa wata kyakkyawar budurwa ta taba cewa dashi. Wallahi kana burgeni... Saboda dogon hancin nan naka. Ai kuwa kya yi kya bari an ni ko burge ni bakyayi. Ya mayar mata da martani a takea agurin mutum ne mai son gwale mutane sam sam ba'a yi masa daidai gashi baha'i murdadde duk lokacin da jama'a suka karkata dama shi sai yayi hagu idan akayi gaba shi sai yayi yamma. Wannan fa duk mai sauki ne idan aka kwatanta da halayarsa ta muguwar gardama domin idan ya tsaya akan ra'ayi babu wanda ya isa ya sauya masa tunani koda kuwa abinda ya tsaya akai ba daidai bane. Wannan tsohon kwamishina sunansa Alhaji Ilyaskuma shine mahaifin Farida. . Mutumin ya dago kai daga kan jaridar da yake karantawa sannan ya dubi inda farida take a takura agefen wata kujera tana sharbar kuka tun idanunta na zubar da hawaye har sun kafe babu komai sai majinar datake zuba daga hancinta. Ko kukan jini zakiyi sai kin aure shi tunda kin raina mutane. Farida ta sake fashewa da kuka. Adaidai wannan lokacin ne mahaifiyarta tashigo dakin fuskarta a murtuke yar gajeriyar mata ce fara kyakkyawa tana dauke da zanen kalangu agefen fuskarta hagu da dama. Alhaji ni dai wallahi abin nan ba sonsa nake ba kai kuma idan ka kafe akan abu ka kafe kenan saikayi amma in ba haka ba kasan lalurar dake kan yarinyar nan ka bari ayi mata magani kaki kuma gashi sai kokari kake ka hadata da wanda bata so mutumin da ko ganinsa bata tabayi ba. Alhaji Ilyasu ya ajje jaridar dake hannunsa ahankali agefen kujerar ya dubi matarsa sannan ya dubi yarsa cikin kunan rai Idan ma bata taba ganinsa ba yau zata fara zaman da nake yanzu shi nake jira su gana dan ko tana so ko bata so nan da sati guda za'a daura musu aure. Mahaifiyar farida ta rike numfashi cikin kaduwa. Rana ita yau fa kace? Haba alhaji wannan abu kamar kasha kwaya yarinyar da...... . Alhaji ilyasu ya katseta ta hanyar daga yan siraran hannunsa masu kama da muciya babu wanda ya isa ya saura min ra'ayina kinaji ko? Daman ai ke kike daure mata gindi take duk iya shegen da taga dama kullum tana tara mana yan iska a kofar gida to wallahi ko mutuwa zatayi saina daura mata aure rana ita yau Aljanin karyar da take baki labari saidai ya kasheta karyar banza karyar wofi in ba ta raina mutane ba ke kintaba ganin inda Aljani yayiwa mutum Kunshi? Farida dake zaune agefensu ta fashe da kuka kasa kasa sannan ta runtse idanunta kana ta rufe kunnuwanta da tafin hannayenta ko kusa ko alama bata kaunar kalaman dake fita daga bakin mahaifinta dan me zaice labarinta karya ne kodon baiga abinda ya samu kabir bane kuma baiga abinda ya sami baba ali ba. . Zuciyar farida ta hasko mata bakin titin gwarzo watanni uku da suka wuce sa'ar data rugo aguje zuwa bakin titin. Wayyo Allah dan Allah ku taimakeni farida ta kwalla ihu sa'ar data hangi wasu mutane hudu suna gudun motsa jiki nan da nan mutanen hudu suka dawo izuwa gareta. Ke menene? Wani daga cikinsu ya daka mata tsawa da wata kakkausar murya. Shine... Yana ciki. Fadila tace a rude tana nuna bayan dutsen cikin duhun daren. Tsaya nan muna zuwa katon mutumin yace da ita sannan sai suka ruga aguje zuwa bayan dutsen abinda Farida bata sani ba shi kartin mutanen wasu sojoji ne daga barikin janguza suke motsa jiki basu fi ko mintuna uku da bacewa daga dutsen ba sai farida taji ihun baba ali ya ratsa dajin abin ya kada mata hantar ciki domin tun da take bata tabajin dan adam yayi irin wannan ihun ba. Har zuwa lokacin da sojojin suka kawota gida farida bata daina jin amsa kuwwar ihun baba ali acikin kwakwalwarta ba. . Washegari da safe ne take samun labari agurin mahaifinta cewa sojoji sun cirewa baba Ali idanunsa guda biyu yanzu haka yana asibiti kuma ya amsa cewa yayi kokarin yi mata fyade. Farida ta labartawa mahaifiyarta irin masifun dake faruwa akanta tun daga lokacin da akayi mata zanen kunshin nan. Ai kinga irinta in banda shaidancinku na ya'yan zamani ina ke ina zuwa ki budewa wani kato tsaraicinki wai yayi miki zanen kunshi gashi nan yanzu kin dauko jaraba in ba tashi mukayi tsaye ba ko aure ba zai barki kiyi ba. Mahaifiyarta ce ke fadin haka Rabi a fusace rabi a tsorace cikin tsananin kaduwa Awannan yammacin tayiwa mahaifin farida bayanin duk abinda ke faruwa akan yarsu ga mamakinta sai taga ya fashe da dariya. Wannan ai tatsuniyace haba TASALLAH haryanzu daman kina imani da tatsuniyoyin yaran zamani. . Kada kace haka Alhaji matarsa tasallah tace a tsorace domin tasan halinsa Alhaji ba karya bane kuma...... Bance dake Aljani karya bane amma saboda tsabar sake shine har ya zama mutum yakeyiwa mata zanen kunshin akan tsaraici haba Tasallah kada ki biye karairayin yaran zamani Wallahi sa kakiki su baro ki. Abin kawai daya kamata muyi shine mu aurar da yarinyar nan kawai mu huta. . Matar ta dube shi a rude tace bazasu barta tayi zaman aure ba. Dubi fa har baba ali suka cirewa kunne dayayi kokarin mata fyade. Alhaji Ilyasu ya fashe da dariya kada fa kema ki zama sokuwa kamar yarki in banda abinki ko jaki sojoji hudu suka jibga ai sai sun fitar masa da kunne ballantana mutum. Wannan duk yafaru ne watanni uku da suka wuce dan haka ayanzu da farida ta fashe da kuka sai mahaifiyarta ta dube shi tace. Dan Allah Alhaji nidai ina rokarwa yarinyar nan ahuwa abata nan da wata guda domin ta fito da wanda take so tun da dai samarin nan tana dasu bawai bata dasu bane. Alhaji ilyasu ya gyara tabaransa sannan ya dubi matarsa yace Bazan iya sabawa babban aminina alkawari ba kuma kada ki damu yaron nan kyakykyawa ne shima idan ta ganshi zata so shi dan gidan alhaji shu'aibu ne wanda muka zauna gida daya dashi a london. . Kamar jira ake ya iddar da zancensa kwatsa sai sukaji sallama wani kyakkyawan saurayi ne dogo ya shigo dakin farine mai manyan idanu farare. Baba Ina kwananku ya zube agaban su mahaifiyar farida ta dubi saurayin sannan ta dubi farida daga karshe kuma ta dubi mijinta baki na rawa tace. Shine wannan? Bata taba tsammanin saurayin zaikai kyawun haka ba. . Ba shi bane Wallahi shine. Farida tace da mahaifanta cikin karaji a tsorace mahaifan nata suka dubi saurayin a rude cikin rashin fahimtar abinda take nufi sannan ne to suka lura da cewa kafar kyakkyawan saurayin dake gabansu KOFATO Ce. . BABI NA SHIDA 6 Nayi zaton zamu kai magariba ashe da wuri ma zaki fito direban yace da mama sa'ar data fito daga gurin bokan ta shiga gidan baya. To ko tsayawa zamuyi mu kwana anan? Mama ta tambaye shi cikin gatse. Wani tattausan murmushi ya subuce daga bakin direban sa'ar daya sawa motar giya suka fara tafiya. Ni bance ba ranki yadade Allah yabaki hakuri Da Hakurin ta mutu nawa ka bayar kudin sadaka? Mama ta sake mayar da martani cikin tsiwa. Direban yayi shiru daga wannan bai sake cewa da ita kala ba har sa'ar daya ajeta a kofar gidanta. Mama na fitowa daga cikin motart bata jira sun sake sabon ciniki ba saita kirgo kudin data tabbata sun lunka kudin da sau biyu ta mika masa Jiki na rawa direban ya karba. Nagode ranki yadade yace da ita cikin murmushi Ga mamakinsa sai yaga mama ta sassauta fuska ta haskake shi da murmushi tace. Nima nagode suka danyi shiru na dan lokaci shi bai tafi ba ita kuma bata juya ba. Bani lambar wayarka kodon gaba idan kana da lokaci sai in kiraka kana kaini unguwa to ranki yadade direban yace yana rawar jiki lokaci guda kuma ya fadawa mama lambar wayarsa ta shigar atata wayar. To shikenan sai na kira mama tace sannan ta juya cikin sauri ta nufi kofar gidan. Adaidai lokacin ne tayi Turus. Sa'ar data hangi Mubarak saurayin da take mutuwar kauna tsaye ajikin wani dan kanti na katako dake dab da kofar gidan mama taji zuciyarta ta harba atsakankanin hakarkarinta numfashinta ya dauke yawun bakinta ya kafe tun da take aduniya bata taba kamuwa da ciwon son wani 'Da namiji ba sai Mubakar agurin mama maza tamkar kasuwa ne kashige su a lokacin dakaga dama ka sayi abinda kake so ka fice. Ayanzu data kalli mubarak sai mama ta gane kuskurenta a fili ashe dai maza sun wuce kasuwa saidai Gidan kwana. Sannunku mama tace dasu Mubarak da kuma mai tsawon kantin sannan saita dubi cikin kantin tace Kanada kwan wuta ne? Mama ta tambaya tana kallon kayan kantin lokaci guda kuma tana satar kallon Mubarak ta gefen ido Akwai naira hamsin. Mai tsaron kantin yace Ba musu ballamtana ta nemi ragi mama ta biya sannan saita kuya kamar zata tafi saita tsaya agaban Mubarak tace dashi a tausashe. Mubarak ko gaisuwa babu? Mubarak ya dubeta shekeke sannan ya shafi kwanjinsa yace Kin Ajeni anan ne domin kullum ina gaisheki? Mama taji kamar ya watsa mata wuta kunyar daya saurayin mai tsaron kantin ta lullubeta. Allah baka hakuri.... Ina kwana to ni na gaisheka Lafiya lau mubarak yace sannan cikin sauri sai yabar gurin ya nufi bakin titi. Mama ta bishi da kallo cikin kunan rai har saida ya bace sannan saita matsa jakarta daidai inda laya nan da boka ya bata kana tayi murmushin yake. Sai hakuri Mubarak dole ne saika aure ni tace da kanta sannan saita dada matsa layarta cikin jaka. ** ** ** ** Duk wannan al'amura sun faru ne kwanaki bakwai kafin honorabil sabo ya kori bebi daga gidansa. Awannan ranar yan yansandan ciki suka sa bebi cikin wata katuwar mota jeep kirar kamfanin Fodi bakikitin da ita kamar shuni suka nufi kanon dabo daga abuja su biyar ne acikin motar baya mutum uku ne babi da wasu karti biyu sanye da bakaken kwat da bakaken tabarau sun sata a tsakiya gaba kuma direba ne da wani katon shima sanye da bakin tabarau da shudiyar kwat. Motar nata kwarara gudu bebi na tsakiyar kartin tayi zuru da ita bata ko kwakkwaran numfashi da motsi domin ta lura suma mutanen dake zaune akusa da ita kyam suke basa motsi kamar busassun itatuwa abinda yafi damun bebi shine da bata iya ganin kwayar idanunsu. Suna nan tafe zuciyar bebi nata sake sake na gargadi mama. Bebi tace cikin zuciyarta tayi imani da cewa mama bazata taba iya kashe mutum ba bera ma tsoronsa takeyi ballantana har ta huda cikin mutum kuma ma me zaisa ta kashe honorabil jatau? Bebi ta tambayi kanta Yau da ace kudi sun bata adakin to da sai ace ko kudin tazo sata yakamata ai ta ya kuma ta kashe shi.... Kai bazaiyiyu ba ai mama ko kamata yayi tana satar kudinsa babazata iya marinsa ma ba ballantana har ta kasheshi to saidai kuma me yasa har tsawon wannan lokaci mama bata yi waya ba? Wadannan tarin tambayoyi su suke cunkushe kwakwalwar Bebi. . Ance ki kwantar da hankalinki. Daya daga cikin kartin yace da ita batareda ya dubi fuskarta ba. Babu laifin da kikayi mana so muke kawai ki kaimu gidan da take shikenan sai sai mu sallame ki. . Bebi tayi ajiyar zuciya sannan jikinta ya dauki rawa kamar wacce zazzabi ke shirin hawa. Ka... Kama ta zakuyi? Ta tambaye su cikin karfin hali Yan tambayoyi kawai zamuyi mata daya daga cikin karyin yace a takaice. Har yanzun nan bai jiyo ba ballantana ma ya dubeta akwai wani abu a tattare da yanayin mutanen dake baiwa bebi tsoro tabbas ayanzu tasan ya zama dole ta gargadi mama halin da ake cikin shin wai da tun farko ma meyasa batayi tunanin tayi kiranta ba. Kibar kaza acikin gashinta ki kaddara aranki cewa bakima taba haduwa da mama ba kada ki kirata idan kuma ita ta kira kice da ita kada ta sake ta dawo Abuja. Bebi ta tuna maganar honorabil sabo lokacin dayake fatan Allah yasa wani bai lura da shigarsu gidan honorabil jatau ba. Ashe ya maka masu gadi sun lura. Bebi ta muskuta abayan motar sannan ta takura lokaci guda ta dubi daya daga cikin kartin tace a tsorace. Zaku iya tsayawa nayi fitsari? Kwarai da gaske ki saki ranki dan Allah duk kinbi kin rude ba wani abu zamuyi miki ba. Bebi ta dubi mai maganar da wani busashshen murmushi sa'ar da direban motar ya tsaya dasu acikin dajin. Tsallaka can kiyi ga wata duhuwa can amma kada kiyi nisa kinsan dajin da macizai Bebi ta nufi bayan wasu dogayen ciyayi dake gefen kwaltar amma daga can ciki ta tsugunna abayan ciyawar. Saida ta tabbata babu mai ganinta Jiki na rawa ta bude jakarta ta dauko waya tafara daddanna lambobi wayar ta kwace ta fadi a kasa saboda rawar da hannunta keyi cikin sauri bebi ta sake rarumar wayar ta daddanna sannan ta kara a kunne tsahon dakiku masu kamar sa'o'i uku agun bebi sai mama ta dauki wayar acan daya bangaren. Mama.... Bebi ce..... Saurara da kyau ki ji bamuda lokacin gaisuwa......... *** *** *** *** FADILA ta dubi kan wayar tana mai shakkar abinda taji daga bakin mahaifiyar tata duk da an bata izini ta dauki wayar batayi hakan ba harda da tabbatar mahaifiyarta ta gama fita daga dakin ta kuma rufe kofar abayanta. Hannunta tareda duk wani bangare na jikinta na rawa fadila ta ganna abin amsa wayar sannan saita lumshe idanu ta kara a kunnenta. Fadila... Fadila ce? Don Allah kiyimin magana faisal yace acan daya bangaren bakinsa na rawa kamar zai fashe da kuka. Faisal.. Fadila ta kira sunansa da wata rarraunar murya. Acan daya bangaren faisal yaji kamar an kwarawa ruhinsa ruwan sanyi sa'ar dayaji muryar fadila. Yanzu kam ya tabbata duk duniya babu wanda ya isa ya rabashi da Fadilarsa domin yanzu ne yake kaunarta fiyeda lokacin daya aureta ma. Na'am fadilata kina ina? Ya tambaya cikin wata tattausar murya. Ina gida Faisal. Me kike yi? Azaune nake ni kadai ina kuka ina tunaninka.... Muryar fadila ta karye ta fara sheshshekar kuka. Daina kuka dan Allah fadila kada kisa jinina ya hau. Toh faisal.... Na daina fadila tace a raunane haryanzu akwai alamu sheshshekar kuka a muryarta sukayi shiru na yan dakiku. Hello Fadila... Kina jina? Ina jinka Faisal. Kiyi hakuri don Allah ki yafemin abinda nayi miki. Fadila ta danyi shiru acan daya bangaren. Bazaki yafemin ba fadila? Aka sake shiru na dan lokaci. Na yafe maka faisal... Kaima kayi hakuri kaji? Bakiyi min komai ba fadila Ilove you... Kinji? Fadila ta dada lumshe idanunta acan daya bangaren cikin wani irin farin ciki da bata taba jin irinsa ba. Ina kewarka faisal... Yaushe zan ganka. Gani nan zuwa yanzu. Adaidai wannan lokaci sai kofar dakin Fadila ta bude mahaifiyarta ta shigo idan kun gama hirar saiki fito falo su malam sunzo zasu karasa miki addu'ar ki. Faidla ta gyada kai lokaci guda kuma tace da faisal acan daya bangaren. Kabari sai nan da awa biyu Tayi min tsayi faisal yace. Zan dai zo saina jiraki a kofar gida har sai lokacin ya cika. ** ** ** ** ** ** Dayake haryanzu fadila bata sa ko kashi daya daga cikin takwas na kayan lefenta ba sa'ar data fita daga wanka ta gama kwalliya saita kasa zaben irin kayan da zata tari tsohon mijin nata dashi saida ta shafe sama da rabin sa'a kafin daga karshe dai ta samu ta zabo wani bakin siliki siliki mai sheki wanda akayiwa dinkin riga da siket matsatstsu irin na wannan zamani tasa Tuni Faisal ya dade adakin shakatawa na musamman da aka ware dan manyan baki abokan mahaifinta. Fadila ta gama feshe feshen turare kenan sai mahaifiyarta ta shigo dakin sannan ta dubi irin kayan da fadila ta sa sannan ta girgiza kai tace. Oh Ya'yan zamani to daman yaya za'ayi ma ku rabu da aljanu? Saiki nemi gyale mai fadi ki yafa karki kije masa ahaka sinki sinkin kamar doya. Fadila ta fashe da dariya wannan itace dariyarta ta farko cikin wata uku rabonta da dariya tun yammacin da sukayi sallama da faisal dinta yatafi yiwa abokansa ban gajiya. Baba kenan kuma dan nasa wannan sai aljanu su fara bina. Keda Allah can rufe min baki har zaki fara kaudi dan kinga yazo. Kinga mama ni dai ki daina janyo min su Fadila tace cikin shagwaba Dazan janyo miki su ai da ban sa anyi miki addu'ar rabaki dasu ba mahaifiyarta tace sannanDa zan janyo miki su ai da ban sa anyi miki addu'ar rabaki dasu ba Mahaifiyarta tace sannan saita matsa kusa da yar tata tace a tausashe. Ina fatan dai yanzu kin warware babu matsala? Fadila ta gyada kai. Har yan gane ganenma yanzu bakyayi ko? Fadila takuma gyada kai mahaifiyarta tayi ajiyar zuciya sannan tace ai saikije yana jiranki. . A dakin karbar baki na musamman faisal ya mike tsaye cikin tsananin farin ciki sa'ar da masoyiyarsa tsohuwar matarsa fadila ta shigo dakin. Masoyan biyu suka zauna lokaci guda akan kujera guda sannan suka fuskanci juna da wani narkakken murmushi. Fadila daga yau babu wanda ya isa ya rabani dake Fadila ta lumshe ido cikin jin dadi tace kaidai fadi gaskiya. Gaskiyar kenan fadila ko Aljanin nan ne zai sake dawowa bai isa ya rabani dake ba. Fadila ta dube shi cikin mamaki tace kana nufin yanzu ka yarda da abinda nafada wancan karon? Cikin murmushi faisal yace ai bake kika fada min ba agida na sami labarin a gurin MAMA Masoyan biyu sukayi shiru suna kallon juna cikin shauki na tsawon dakiku can sai faisal yayi ajiyar zuciya a tausashe yace Matata. Fadila ta lumshe idanu ta kuma bude su lokaci guda. Umhm Mijin Faisal ya mika hannu zai tabata sai fadila ta janye jikinta cikin sauri tana dariya tace. Kada ka manta ada nake matarka yanzu allura cikin ruwa ce mai rabo ka dauka. Faisal ya hade fuskarsa cikin wasa yace Dan Allah ki bari kada kisa jinina ya hau yanzu yaushe za'a mayar da auren namu? Fadila ta dube shi ido da ido tace Najisu mama suna cewa sai nan da shekara biyar. Faisal ya kai mata duka suka fashe da dariya cikin farin ciki. ** ** ** ** MAMA Tayi mika akan gadon sannan ta harba kafafunta har sau biyu kamar mai hawan bori sannan saita mike zaune a hankali ta dubi agogo karfe uku da minti ashirin na yamma. Tun karfe goma na safe data tashi ta wanke bakinta tayi karin kumallo saita koma ta kwanta abinta bata farka ba sai yanzu to me ya dameta? Daman aljanin nan ne gashi kuma yau kwanaki bakwa da bokan nan ya daukar mata sun cika. Dan Haka mama ta gama imani da cewa daga yau ta rabu da shegen aljanin nan. Cikin murmushi saita lalubi kanta tsakanin kitso ta shafi layar da bokan ya bata sannan ta fara tunanin ta inda zata bullowa Mubarak idan anjima. Idan har abinda bokan yafada mata ya kasance gaskiya babu abinda zai hanata auren Mubarak mama tagama yanke shawarar kawai ta auri Mubarak tun dai tana kaunarsa tuni ta gama yanke kauna da wannan harka ta karuwanci badon komai ba sai dan kawai tana kaunar mubarak hakanan kuma tasan in har ba garin kano zata bari ba cigaba da karuwanci zai yi wuya tunda dai labarinta ya watsa ko ina gashi wani abin kara tonon silili har masu sayar da hotuna da kalandu ne ke yawo da hotunanta a kalanda da kuma na likawa a kasan hoton an rubuta MATAR ALJAN. Zuciyar mama cike da wannan sake sake ta shiga bandaki ta fesa wanka kana ta dawo ta zauna agaban dogon madubin dake dakinta ajikin bango ta fara goge goge da shafe shafe irin na kwararriyar yar duniya bayan tsayin mintina tagama sannan ta kalli surarta ajikin madubi mama tayiwa kanta murmushi danjin dadin abinda tagani haryanzu nan ashe dai fuskarta na nan dauke da TSOHON ALKAWARI kyawu nan nata duk da yake dai yawan bilicin datake yafara samun tasirin sauya launin kudukukinta amma fararen idanunta da dan bakinta faffada gwanin iya shan (Ice Cream) Madarar kankara su suka kara mata kwarin gwiwa tabbas babu abinda zai hana Mubarak kamuwa da sona idan ya ganni. Mama ta fada cikin sauri dauke da nishadi sai mama ta nufi bakar akwatinta mai kaya ta fara lalube laluben irin kayanda yakamata tasa. Ta bude can ta leka can ta bincika can daga karshe dai hannunta yakai kan wata bingilalliyar riga tsawonta baifi iya cibiya ba shudiya ce kusan rabin kirjin rigar duk a wawake yake hakanan rigar tana da doguwar siket wacce idan mamatasa har kasa take ja. Mama tayi murmushi sannan ta dauki rigar. Har ta fara sa rigar saikuma ta tsaya kai da wahala mubarak yaso rigar nan dan naga ustazu ustazu ne mama tace da kanta cikin murmushi. Duk da yake dai tasan takadiri ne wasu ma nayi masa kallon dan daba amma mama nada yakinin baya harka da mata. Mintina ashirin suka shude daga karshe dai da kyar mama ta zabo wata doguwar riga launin zuma da dishi dishin fari kamar fatar damisa rigar na da wando me dauke da wata beza beza ta farin leshi daga can kasa kamar kafar namijin tattabara. Karfe biyar saura yan mintuna mama ta gama shirinta tsaf sai kamshi take yi tun daga sama har kasa domin ta feshe jikinta da turare sama da kala biyar mama tayiwa kanta kallon tsaf na karshe ajikin madubi sannan saita dauki farar jakarta ta nufi kofar gida inda Dabar su Mubarak take. . Mubarak na zaune shi kadai akan wani benci karyayye agindin wata bishiyar darbejiya saiyaji kamshi ya buhi hancinsa kamshin ya dadada masa hanci matuka cikin sauri ya dago kai ahankali domin yaga daga ina kamshin ke tashi dago idanunsa keda wuya sai sukayi ido biyu. Sannu da hutawa mubarak dama Sannu da hutawa mubarak dama gurinka nazo. . Mubarak zuciyarsa ta harzuka wai shin dan uban karuwar nan meyasa ta rainani ne? Mubarak ya tambayi kansa rashin duka ne shaidaniyar zuciyar ta shawarceshi nan da nan kamshin turaren dake tashi yakoma kamar warin mushe agurin mubarak domin aduk matan duniya babu wacce ya tsana irin mama duk da yake dai daman shi mata basu dame shi ba abinda ke gabansa shine kallon kwallo da yawon farauta idan ta samu. . Kikazo kiyi min me? Mubarak ya tambaya yana kallonta a fusace yana ciccije baki. Mama taji zuciyarta ta harba tsakanin hakarkarinta bata tsammaci irin wannan daga bakinsa ba dan haka saita sa hannu kamar zatayi susa ta shafo layar dake tsakanin kitsonta awayance sannan ta dubi Mubarak ido da ido Gani nayi kamar gurin babu kowa shiyasa nazo in tayaka zama. Mubarak yaji zuciya ta tuke shi. . Kebace kar in barar dake an fada miki ni abokin kazamai ne irinki? Wannan kalma itace mafi muni da mama ta taba ji arayuwarta abinda ya harzukata mama bata bari ya bayyana a fuskarta ba. Maimakon hakan sai mama ta dada shafar layar a karo na biyu sannan babu zato babu tsammani sai ta matsa inda mubarak yake ta zauna akan bencin bata kura dacewa bencin gurgu bane tana zama sai nauyinta ya rinjayesu nan da nan suka fadi da baya. Wasu yara acan gefe na wasa suka fashe da dariya harda sowa. Mubarak ne yafara tashi a fusace sannan ya zare bakin BELT din dake kugunsa. Kayi hakuri mubarak bansan a..... Kafin ta karasa mubarak ya hauta da duka da farko mama ta dauka abun wasa ne daga karshe kuma saitaga Mubarak yasa kafa yayi bal da ita harsada ta fada KWATA. Wayyo na shiga uku mama tasa ihu sannan ta mike ta ruga aguje Mubarak ya rakata yana duka sai saida ya rakata har kofar gida. Akace bakya jin duka wai kina da aljani yanzu uban wa na daka? Mubarak yace yan ciccije baki sannann saiya juya yana bubbudawa lokaci guda kuma yana mayar da belt dinsa cikin wandonsa ya nufi inda mai dan kantin nan na kusa da gidansu Mama yake. Bani sigari yace da mai kantin yana muzurai. Acan cikin gida mama tafada cikin daki tayi rub da ciki akan gado ta fara rusa kuka. Ba kukan zafin dukan da mubarak yayi mata ba takeyi ba kukan wulakanci da nuna mata kyamarta da yayi takeyi. Mama ta tashi zaune akan gadon hawaye sharaf shafar ta lalubi kanta tsakanin kitson da niyyar ta dauko layar nan da boka ya bata tayi jifa da ita adai wannan lokaci sai wayar tafi da gidanka dake gefenta ta katse mata hanzari sakamakon ruri data fara. Da farko mama batayi niyyar amsa wayar ba dan haka saita dauki wayar a fusace da niyyar ta kashe sai kuma tayi turus sa'ar da taga sunan kawarta BEBI ya bayyana a fuskar wayar. Nan da nan mama taji duk damuwar dake tattare da ita ahalin yanzu an zare mata ita kamar cirar kaya sannan alokaci guda wata sabuwar damuwa ta maye gurbin wanccan. Cikin sauri mama ta share hawaye sannan ta danna abin amsa waya tace cikin wata malalaciyar murya. Hello. Mama bebice saurara da kyau kinsan bamuda lokacin gaisuwa..... Ki tattara naki ya naki kibar kano kafin mu karaso nan da awa biyu zamuzo da yan sanda wai zasuyi miki tambayoyi akan mutuwar honorabil.... Dan Allah mama fadamin gaskiya ke kika kashe shi? Mama taji wani zazzafan gumi ya fara sartu akan gashinta tuni dama kukan dukan da tasha ya wanke kwalliyar data shafe sama da sa'a guda tanayi. Haba Bebi.... Wallahi bani na kashe shi ba... Ke kinfi kowa sani na Nida bera ma tsoroyake bani tayaya zan iya kashe mutum..... Amma dai nasan ta yadda...mama ta danyi shiru. Kinsan me? Bebi tace acan daya bangaren cikin kaduwa, bani na kashe shi ba.... Amma akwai labari dai me tsayi akan..... Kinga mama saurara bebi takatse ta acan daya bangaren. Koda bake kika kashe shi ba idan kinsa bakida gaskiya kigudu kawai kuma amatsayin kawa domin na rama irin mutuncin da kika nuna min lokacin dana fara zuwa kano ke kika fara bani sababbin kaya kyauta.... Sai wataran kawata. . Layin ya katse daga can daya bangaren cikin tsananin firgici zuciyar mama ta kankame gawar wayar a kirjinta domin numfashinta ya fara daukewa tsahon mintina tana nan azaune kwakwalwarta ta kasa tunanin komai sai bayan mintina goma sannan ta fuskanci halin da take ciki ta riga tasan har kullum daman wannan al'amari kandarsu acikin ranta amma matsalar wannan aljani dake addabarta su suka dauke tunaninta daga kan duk wani hadari dake iya samunta a sakamakon katuwar honorabil jatau. Da farko mama ta yanke shawarar tayi zamanta kawai ta jira zuwansu bebi tunda dai ai ba ita ta kashe shi ba Jimawa kadan kuma sai wata zuciya tace da ita idan suunzo kuma kuma kice dasu me? Kice dasu wani aljani ne yafito atsakiyar dare ya kashe shi kina kwance? Mama tayi ajiyar zuciya tasan wannan zance ba mai yiwuwa bane duk duniya wanene zai yarda da wannan tatsuniya? Mama tasan tana fadin haka zata fada hannun hukuma domin har yau din nan ita kanta gani takeyi kamar mafarki. Jikinta na rawa mama ta mike tsaye cikin zafin nama naban mamaki ta hada duk suturarta cikin jakankuna guda biyu sannan ta nufi bandaki ta wanke fuskarta tana dawowa saitaci gaba da laluben sauran abubuwan da take tsammanin zasuyi mata amfani agaba da wannan karon mama bata damu da ta shafa koda farar hoda ba ballantana ta tsaya doguwar kwalliya tuni tagama yanke shawarar inda zata gudu garin da aka dade ana bata labari aka kuma dade ana shawarartar ta data tafi tun lokacin da aka kaddamar da shari'ar musulunci a kano. Ai saikiyi ta zama baki gaji da wahala bane kullum ana binki ana takura rayuwarki kamar barauniya ance kizo mu tafi inda zamu fantama babu mai rakura mana. Wata kawarta ce ke bata wannan shawara. Wai wane gari ne wannan? Mama ta tambayi kawar. Wani garine tsakanin bodar najeriya da nijar harka agarin ba magana kizo kawai muyi tafiyarmu can inda babu tsangwama. Ayanzu da mama ta dauki jakankunan ta cikin sauri can ta yanke shawarar guduwa babu abinda mama ta tsana irin karuwancin kauye to amma yanzu batada zabi akalla dai zan bace na dan lokaci kafin kura ta lafa waya sani ma ko aljanu basa iya tsallaka boda ballantana su dameni. Mama ta fadawa kanta domin ta dada samun kwarin gwiwa abinda yafi damunta ayanzu shine kudadenta dake banki kodayake tuni mama tasan idan ta kwashe kudinta gaba daya daga bankin zata iya damkasu a hannun wani dan canji a wafa wanda take canjin kudin kasashen ketare agurinsa tasan duk inda take zai iya tura mata da kudinta. Mama ta dubi agogo sa'ar data fito kofar gidan karfe biyar saura tasan idan tayi sauri zata iya samun banki ba'a rufe ba. Mutane suka zuba mata idanu sa'ar da sukaga ta fito da jakankuna a tunaninsu dukan da mubarak yayi mata ne yasa zata tafi. Mama ta isa bakin titi kafin ta tsayar da dan tasi sai ta dandanna wasu lambobi awayarta. Sannan ta kara a kunne tace Hello.. Mu'azu... Nice mama dan Allah mu hadu yanzun nan a OCEANIC BANK zan baka wasu kudi da zakayi min sako dasu ta danyi shiru sannan saitace. To shikenan amma kayi sauri don tafiya zanyi. . Wani da adaidaita sahu ya tsaya akusa da ita da mashin mai kafa uku mama ta jefa jakankunanta biyu aciki sannan ta shiga tace da direban Oceanic bank zaka kaini daga nan kuma zamu wuce tasha kofar ruwa. Direban yaja mashin din ahankali. Koda suka fara tafiya sai mama ta hangi mubarak tsaye abakin titi kusa da wasu sayar da bakin Mai. Batasan abinda yasa ba sai kawai ji tayi bakinta ya subuce Yace. Mubarak Mubarak ya juyo sai yaga mama tana daga masa hannu cikin mashin mai taya uku. Kai yau na hadu da mayya mubarak yace sannan ya tsartar da yawu. . FARIDA Dakin shakatawar yayi shiru bakajin motsin komai kamar anyi ruwa an dauke. Alhaji Ilyasu ne yafara magana cikin karfin hali yana kallon kyakkyawan sauri me kafar Kofato. Bawan Allah daga ina kake? Farida acan gefe guda a takure ta dada runtse idanunta da kunnuwanta bata son ji ko ganin abinda ke faruwa idan su basu san kowanene saurayin ba ita tasan shi. NINE MIJIN FARIDA. Kyakkyawan saurayin yace dasu sannan sai ya fashe da wata kakkausar dariya mai kamar aradu wata iska mai karfi da sanyin gaske ta fara fifita cikin dakin sannan sai wani farin hayaki ya turnuke dakin. Mahaifiyar Farida ta dauki satali a razane nan da nan taji kafafunta bazasu iya daukar nauyinta ba cikin sauri ta lalubi daya daga cikin kujerun ta lume aciki domin bata iya ganin komai sai farin hayaki. Tsahon lokaci kafin hayakin ya washe . Na shiga uku..... Yau mun hadu da jaraba Alhaji kaga abinda nake fada ma ko? Mahaifiyar farida ce ke magana Alhaji Ilyasi yayi kasake na tsahon mintuna cikin tsananin mamaki da fargaba yan mici micin idanunsa suna kallon bangon dakin da wani yabashi labarin abinda yafaru yanzun nan agabansa da babu abinda zai hana ya karyatashi yanzu ma ganin abin yake kamar ruda ido. Farida ya kira sunan yarsa a sanyaye akwai alamun nadama karara a fuskarsa Farida ta dago kai daga inda take ta share hawaye sannan ta fuskanci mahaifinta. Kin tabbata duk labarin nan da kika fadawa mahaifiyarki gaskiyane? Farida ta gyada kai batareda tayi magana ba. Gashi nan anyi ma agabanka Mahaifiyar farida ta fada bakinta na rawa. Na fadama tun farko baka saurareni ba dolene sai mun tashi tsaye akan yarinyar nan in bahaka ba wallahi da kyar zata auru. Alhaji ilyasu ya sunkuyar da kai kasa na tsahon lokaci yana tunani can saiya dago kai ya dubi farida yace da ita a tausashe. Ki shirya gobe zamu tafi kauye. Mahaifiyar farida ta kalleshi a rude. Akwai wani tsohon malamin mahaifinmu wai shi MALAM NA KOGO Waliyi ne nasan in Allah ya yarda ko ifiritu ne akan yarinyar nan sai ya barta Insha Allahu ai ita addu'a tafi karfin komai. Yadanyi shiru sannan saiya ci gaba da cewa. To daman in banda lalacewar zamani ma yanzu ace wai zanen kunshi ya wuce tafin hannu da sawu yatafi har zuwa kan tsaraici wannan wacce irin masifa ce yaushe za'a ace wai mace ta bude tsaraicinta agaban wani kato yayi tayi mata zane zanen banza . Alhajin yasake yin shiru akaro na biyu sannan ya juya inda farida take a takure yace. Saurara da kyau kijini daga yau sai yau kada nakara ganin kinsa wannan shegun kayan matsatstsu duk kifito min dasu zansa a kone su idan kuma kika sake na kara shigowa gidan nan natarar da gashinki awaje saina sa wanzami ya aske kan ki Ja'ira. Yana gama fadin haka sai ya dauki wayarsa ya daddanna sannan yace. Hello Alhaji Shu'aibu.... Nine dan Allah in anyi sallar isha'i saimu hadu anan gidanka zamu tattauna maganar auren yaran nan domin an sami wata yar mishkila ina ganin dole sai mun kara watanni ya danyi shiru yana sauraro. Toh shikenan duk daya ne idan kai din ma kazo. Yana ajiye wayar ne aka sake sallama akaro na biyu Wannan Karon wani saurayi ne kyakkyawan gaske yashigo dakin saidai shi anyi sa'a bashida kofato yana shigowa sai yayi turus zai koma cikin jin kunya. Ah...shigo...shigo mana Alhaji ilyasu yace lokaci guda kuma ya dubi farida. Farida ta dago kai ta dubi saurayin taji gabanta ya fadi sa'ar dataga sunyi kama da kabir dinta. Ga mamakinta saitaji tana addu'ar Allah ya rabata da wannan masifa ta wannan Aljan indai har wannan shine mijin da za'a bata to tayi dace ta fada acikin zuciyarta sannan saita sunkuyar dakai kasa a kunyace azuciyarta tana mai fatan Allah sa shima wannan saurayin bazai koma gida karkataccen Baki ba. . MAMA Motar kirar fijo tsohon yayi ta fito daga tashar ta nufi arewa dauke da fasinjoji shida. Abayan motar a zaune kusa da wani kyakkyawan saurayi mamace idanunta sunyi jajur saboda kukan da taci da kuma tashin hankali. Ga alama mutum uku ne yakamata su zauna abayan motar amma dayake kyakkyawan saurayin mai dogon hanci ya biya kudin mutum biyu sai ya kasance daga shi sai mama ne zaune aciki. Mama ta dubi agogon dake jikin wayarta karfe shida da yan mintina tuni hasken rana ya fara sallama duhun dare yafara maye gurbinsa ahankali kamar yadda suka saba akullum kwanan duniya. Daga inda mama take zaune tana iya hangen yan mata birjik abakin titin kurna asabe zuwa bachirawa wasu na tafiya abinsu me yiwuwa unguwa zasu wasu ko dauke da farantin talla wasu ko sanye da dogayen riguna da hijabi sun taso daga islamiyyar yamma. Mama taji wani bakin ciki marar misaltuwa ya mamayi zuciyarta ga mamakinta saitaji tana mai fatan inama ace tana daga daga cikin irin wadannan yara inama ace itama agaban magabatanta take da yanzu fa meyiwuwa tayi aure ko? Me yiwuwa har da ya'yama da yanzu haka tana zaune ita da mijinta lafiya cikin kwanciyar hankali babu taraddadin wani aljani ko wasu jami'an tsaro akaro na farko sai mama tafara Nadamar dukkan wani iya shege data aikata adoron kasa yanzu ina ribar irin wannan rayuwa mara manufa? Mama ta tambayi kanta nan da nan sai hawayen bakin ciki ya fara sartu akan fuskarta lokaci guda kuma tana tunanin shin ko su bebi sun karaso gidan tare da jami'an tsaron. Ita kam ta riga tasan ta tafi zuwa duniyar da bata san abinda zata tarar ba shin yaushe ne mai zai karewa tsohuwar motar? Mama ta tambayi kanta a tsorace. . Kukan me kikeyi? Wata tattausar murya ta tambayeta mama ta juyo ahankali yayinda sukayi ido biyu da kyakkyawan saurayin dake kusa da ita. Ki daina kuka komai na duniya mai wucewa ne tunda dai kina tare dani. Saurayin yace sannan sai ya lalubi aljihunsa ya dauko wani farin kyalle ya mika mata. Goge fuskarki kada hawaye yabata miki kyawunki Saurayin ya hasketa da murmushi. Mama ta dubi kyakykyawan saurayin cikin mamaki lokaci guda kuma taji zuciyarta na harbawa tsakanin hakarkarinta hakika kyakkyawa ne na gaske mama ta fara hasko hotunan mazan data taba mu'amala dasu abaya ta kasa tuna daya daga cikinsu daya kai koda rabin kyawu na wannan dake kusa da ita. Karbi mana ki goge.... Kada nima ki sani kuka. Jikinta ta rawa mama ta karbi farin kyallen ta goge fuskarta sannan ta mika masa. Nagode. Tace da saurayin. Nine da godiya ai da kika saurareni kika kuma karbi kyallen dana baki. Suka danyi shiru na yan mintina suna duban juna direban motar ya dada kara gudu domin yagama fita daga cikin gari. Ina kika nufa? Mai mujiya. Mama tace tana duban kyakkyawar fuskarsa cikin shauki. Kaifa ina zaka. Guri daya muka nufa saurayin yace cikin murmushi. Duk inda zaki muna tare don bana gajiya da ganinki. Mama ta dube shi cikin mamaki. Yanzu fa ka fara ganina. Ke kike ganin haka ni na dade da saninki...... Ina kuma kaunarki. Mama taji kamar an watsa mata ruwan sanyi. Adaidai wannan lokaci sai wani tattausan murmushi ya subuce daga bakinta tayi murna da bata jefar da layar dake makale akanta ba. Tabbas tasirin layar bokance tafara aiki. Mama uwar gaggawar tare mubarak tayiwu me yiwuwa alokacin layar ce bata fara aiki ba babu mamaki ma da tabi ahankali har gida mubarak zai sameta. Mama ta haskake kyakkyawan saurayin dake zaune kusa da ita lokaci guda kuma tana wasa da wayar tafi da gidanka dake hannunta. Tayaya daga ganina zaka fara.. . Tayaya daga ganina zaka fara kaunata? Mama ta bukata. . Haka daman abin yake kowa kinsan da irin abinda yake so baki san ana kaunar mutum ba tun ma ba'a ganin shi ba. Mama ta lumshe idanu kana ta shafi layar dake kanta awayance Kaidai fadi gaskiya yanzu danace ka aureni guduwa zakayi. Saurayin ya matso dab da ita yace Auren ki shine abu mafi soyuwa agareni gwada ni ki gani in ban aureki ba. Mama taji wani farin ciki ya lullubeta. Tabbas maganin bokan yaci ta dada jaddadawa kanta gashi ma nayi sa'a wannan yafi mubarak kyawun sura nesa ba kusa ba. Zaki Aureni? Saurayin ya tambayi mama a tausashe kamar wanda yake tsoron kada na kujerar gabansu suji. Gwada ni ka gani mama tace lokaci guda suka fashe da dariya me yiwa dariyar da takeyi ne yasa wayarta subucewa daga hannunta ta fada kasa inda kafarta take babu mamaki kuma wata gargada da motar ta fada ne. Oh wayarki ta fadi ko bari na dauko miki. Cikin dariya mama ta girgiza kai sannan tayi masa far far da idanu irin na kwararriyar yar duniya lokaci guda kuma ta dafe hannayensa tace. Bari na dauko kayata kada na baka wahala darling. Tana gama fadin haka saita sunkuya domin ta dauko wayar sannan ne to taga abinda ya tsayar da bugun zuciyarta ya kafar da yawun dake bakinta sannan yasa yasa tunaninta a rudani. Da farko da mama taga abin ta dauka wanine daga cikin fasinjoji ya ajje musu akuya akasa amma data duba da kyau sai taga ba kafar akuya bace kafar kyakkyawan saurayin da zata aura ne har da kofato kamar kafar doki. Mama ta dago kai a gigice ta kwalla ihu nan da nan motar ta hade da farin hayaki. . FADILA Da yamma misalin karfe saura yanayin garin ya sauya nan da nan gashi dai lokacin sanyi ne amma sai garin ya daure aka fara zafi. A zaune cikin dakin shakatawa na alfarma masoyan biyu ne zaune yau kwana uku kenan kacal da mayar da aurensu. Tun da suke arayuwarsu basu taba shiga farin ciki irin na wannan kwanaki ukun ba. Kullum suna tare faisal yace ba zaifita nan da can ba sai nan da sati biyu. Don haka koda yaushe suna tare da amaryarsa fadila ko dai suna tare da amaryarsa fadila kodai suna kallo ko kuma wasan ludo ko kuma wasanninsu irin na masoya masu sabon aure. . Kai ni fa nagaji da ludon nan. Faisal yace lokaci guda kuma ya aje dan kofin ludon akan faifan gilashin Fadila ta dubeshi tayi far far da fararen idanunta tace cikin shagwaba. Me to zamuyi? Faisal ya matso kusa da ita yace zauna kawai nayita kallon ki my love cikin farin ciki sai fadila ta karkace ta kwanta akan cinyarsa tana fuskantarsa. Sai kayi ta kallona har barci ya daukeni. Faisal yasa hannu yaja dogon hancinta Kada fa ka tsine min hanci don kaga yafi naka kyau ko? Ba wani nan ai wallahi nawa yafi naki kyau. Faisal yace yana jan hancin. Fadila ta tashi zaune firgigit cikin tsiwa ta wasa. Allah ya sawwake ace kafini kyau kana kallon madubi kuwa? Faisal ya mike tsaye ya dubeta da murmushi yace In ba tsoro ba ajje daki aduba madubin mana. Fadila ta zunkuda kafada tace Naki aduba dai anan ga madubi can. Faisal ya girgiza kai ban yarda ba bayan wancan madubin zo muje daki agani yana gama fadin haka sai ya ruga da gudu ya shiga daki daga cikin dakunan kwanansu na alfarma. Faisal na shiga dakin sai yayi turus cikin tsananin kaduwa. A kwance akan gadon kwanansu wata santaleliyar budurwa ce sanye da wata irin doguwar riga ta bakin gashi. Faisal bai taba ganin irin rigar ba. Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un. Faisal yace a fili sannan saiya dubi budurwar cikin hali yace. Ta Ina kika shigo mana daki kuma me ya kawo ki? Budurwar ta mike zaune akan gadon ta kashewa faisal idanu tace. Yar zaman daki ce aka kawo muku amma tun da naga baka farin ciki da zuwana bari inyi tafiyata kada ku isheni da surutu. Tana gama fadin haka saita zama farin hayaki. Adaidai lokacin ne fadila ta shigo dakin a guje tana zuwa saita rungume mijinta faisal tana dariya tace. Ilove You Faisal. Nima ina kaunar ki fadila tsahon dakiku suna tsaye ahaka can sai fadila ta dada kankame shi tace. Faisal ina son kayi min alkawari. Faisal ya dubi fuskar amaryarsa a rude yace alkawarin me? Fadila ta lumshe idanu tace Alkawarin bazamu sake rabuwa ba har abada kaga wancan karon saki biyu kayimin yanzu saura daya. Faisal ya dada janyoya jikinsa idanunsa na kan farin hayakin dake bayansu yace a tausashe. Nayi miki alkawarin ba zamu sake rabuwa ba. Fadila tayi ajiyar zuciya cikin farin ciki sannan ta kalli fuskarsa tace. Kishiya fa ita ma ka dauki alkawarin bazakayi min ba? Faisal ya kuma kallon amaryarsa ido da ido sannan ya kalli dan sauran farin hayakin da har yanzu yake makale a sararin samaniyar dakin yace da murmushin Yake. BANSANI BA ME YIWUWA NAN GABA IN AURO MIKI ALJANA. Masoyan biyu suka fashe da dariya. . KARSHE. . NAZIR ADAM SALIH Abinda Nayi kuskure a gafarceni masu karatu Mutum Ne Ni Ajizi A Aiko Min Da Gyaran Kura Kurai Na. . NAGODE SAI MUN SAKE HADUWA IN ALLAH YA NUFA. ZAYYANA 1 and 2 Littafin Nazir Adam salih (c) Nazir Adam Salih Created and design by :- Shuraih Usman . Publish:- http://shuraih.xtgem.com . This Ebook is available in our website just click here and download it , http://shuraih.waphall.com An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels