ZAYTOONAH COMPLETE *...... ...... .......ZAYTOONAH* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *1- Mbom-uzo festival* Bismillahir Rahmanir Rahim 1985 "Dear let's just leave, my mind is not at peace here" Abinda Caroline ta faɗawa mijinta kenan a karo na ba adadi tun zuwan su ƙauyen mijin na ta wato Okwuohia Village. Kamar kullum haƙuri ya shiga ba ta akan ta bari su yi christmas a ƙauyen kafin su tafi. Wannan karan kam Caroline ta ƙi fir musamman saboda mafarkin da ta yi jiya da dare. Ganin yayi yayi ta haƙura ta ƙi ne ƙarshe ya nuna ma ta zai yi tunani a kai. Caroline ta turɓune fiska ta ce ma sa matuƙar ya ƙi ba ta ƙwaƙwƙwarar amsa zuwa dare to za ta ɗauki 'yar ta su bar ƙauyen gobe da safe. "Please Carol" ya faɗa yana haɗa hannuwansa biyu. Shigowar 'yar su ne ya dakatar da Caroline daga maganar da ta ke son yi. Yarinyar da gudu ta shigo ɗakin ta faɗa jikin mahaifinta tana haki saboda gudun da ta yi. "Daddy i didnt miss the steps today. I'm ready for the festival" with so much excitement ta ke maganar. Ta miƙe ta fara rawan Atilogwu wanda ta ke koya tun kwana shida da su ka shige. Tana yi mahaifinta na ma ta tafi yayinda mahaifiyarta ta haɗe fiska saboda yanayin da ta ke ciki na tsanar ƙauyen mijin na ta da duk abin da ke ƙauyen. Bayan ta gama rawan ne ta fita da gudu akan za ta je ta yi wanka. Bayan fitar ta daga ɗakin Patrick ya kalli matar sa ya ce cikin harshen turanci "ki bari ayi bikin Mbom-uzo sai mu tafi, idan mu ka tafi ba ayi bikin nan ba Nkiru ba za ta ji daɗi ba" "Yaushe ne bikin?" "Nan da kwana huɗu" Patrick ya faɗa yana fatan Caroline ta amince. Sai da ta ja dogon numfashi kafin ta ce "ana gama biki za mu tafi" Patrick ya gyaɗa ma ta kai... Kwanaki goma da su ka wuce Patrick da matar sa Caroline da tilon 'yar su Mary-Nkiru su ka zo ƙauyen Okwuohia wacce ta ke ƙarƙashin Obowo Local Government da ke jahar Imo. Sun zo ne da niyyar sai bayan Christmas za su koma gidan su da ke cikin Owerri. Wannan karan ne zuwan su Nigeria na farko tun bayan da su ka koma Ingila da zama, hakan ya sa Nkiru ke jin daɗin ƙauyen saboda rayuwa ce da ba ta taɓa sanin akwai shi ba sai da ta gani da idon ta. A Ingila aka haifeta kuma wannan ne karo na farko da ta bar ƙasar Sarauniya Elizabeth zuwa ƙasar iyayenta wato Nigetia. *** Yana zaune akan madaidaicin teburin da ke ɗakin na sa yana ta ƙoƙarin lissafi aka shigo ɗakin. "T J the mathematician" guntun saurayin da ya shigo sanye da uniform ɗin 'yan bautar ƙasa ya faɗa yana ƙoƙarin zama akan yaloluwar katifar sa da ke shimfiɗe a ƙasa. "Eze welcome, how's the class?" "Fine ooo, but my guy i don tire" T J ya juyo ya ɗaga ma sa yatsu huɗu. Eze ya ce " 4 months is still long my friend" T J yai dariya. Bayan Eze ya chanja kaya ne ya fara ƙoƙarin haɗa gari dan bai yi girki ba kafin ya tafi. T J ya ce ya ɗau plate ya ɗeba abinci a tukunya. Eze yai ihu kafin ya ɗau plate ɗin da sauri ya fara ɗiban dafa dukan shinkafa da T J ya dafa. Har ya gama ci T J bai bar lissafin da ya ke yi ba. Dama ya san ɗan ɗakin na sa indai ya samu lissafi to ba ya iya cin abinci har sai ya ga ya cracking na shi ya wargazata. Akwai ranan da ya fara da dare har Asuba bai iya samun amsa ba haka ya wuni ba abinci a cikinsa wai shi da cin abinci sai ya samu amsan lissafin nan. Haka Eze ya zuba ma sa ido har ƙarfe shida na yamma kafin ya samo amsar. Banda sallah ba abinda ke sa wa T J ya tashi a waje idan yana lissafi. Ganin shirun yayi yawa ne ya sa Eze tambayar T J maganar tafiyar su ƙauyen Okwuohia nan da kwana uku. Ba tareda TJ ya ɗago ba ya ce " wani ƙauye kenan?" Eze ya ce ma sa ƙauyen da su ka je siyan manja sati biyu da su ka wuce. T j ya ce "ohoooo" "Za mu je festival ɗin ai ko?" "Kai ni fa ba na son wajen da zan je a yanke min wuya" Eze ya kwashe da dariya tunowa da yai da labarin da T J ɗin ya bashi farkon zaman su. Bayan T J ya fito daga camp wani ƙaramin ƙauye da ke chan wani lungu chan gaba da ƙauyen Amuzi, bayan ka bar ƙauyen Amuzi za ka yi tafiyar kusan awa biyu da rabi a ƙafa kafin ka kai ƙauyen. Su uku aka tura ƙauyen dukkan su babu Igbo a ciki, shi Bafulatanin Arewa sauran kuma ɗaya Bayarabe ɗaya kuma ɗan Jos ne yaren Angas. Gaba ɗaya ƙauyen ba musulmi kuma 80% ɗin su addinin gargajiya su ke bi sauran kaso ishirin ɗin kuma Christians ne. Watarana T J ya fita da sassafe zai je ƙaramin primary school da ya ke koyarwa ya haɗu da wasu sun yi shigan jajayen kaya su na riƙe da sanduna wasu da ƙwarya, jikin su da fiskokinsu ya sha zane da farin alli, suna tafiya su na maganganun su na siddabaru. T J ya zo ta gaban su zai wuce ya ji an damƙo shi kafin ka ce me an fara dukan sa. Ƙarshe aka ɗaure shi aka kai shi gaban Dibia na garin (Boka) T J dai tun da aka ɗaure shi ya ke addu'a a ransa. Dibia ɗin wani ƙazami da shi sai wari ya ke ya nufo T J da ke ɗaure yana riƙe da wani sanda wanda saman sandar wani ƙwarangal ɗin wata dabba ce akai an ɗaureta da jar ƙyalle. Tunda ya nufo shi T J ya fara karanto ayatul Kursiyyu da ƙarfi nan take sandar hannun Dibia ɗin ya kama da wuta. Dibia ya yarda sanda yana ihu yana surkulle chan ya ce a fita da T J domin gunki na fushi da shi, wai aje a yanka shi a tsakiyar gari. Aka fita da T J ana ihu shi kuma yana maimaita Ayatul Kursiyyu. Sai da su ka iso tsakiyar gari aka fara shela akan za a yanka baƙo wanda ya ƙi bin dokar ƙasar su, dan haka ayi shaida, hukuncin kisa ce za ta zamo sakamakon duk wanda ke wasa da dokar Amadioha. Cikin 'ya'yan sarkin ƙauyen akwai wanda ya fara karatu har yana matakin sakandare a Owerri, shi tuni ya jima da zama christian shiyasa ya yi watsi da al'adun su na gargajiya. Jin abinda ake faɗa ne ya sa shi fitowa da gudu dan ya san babu baƙi a garin sai 'yan Bautar ƙasa guda uku da aka turo sati ɗaya da ya wuce. Yana zuwa kuwa ya hango T J ɗaure ga wani daga cikin matsafan wajen ya riƙe wuƙa yana wulli da ita a sama yana surkulle. Nnadozie ya ƙarisa ya fara magana akan su sake T J saboda shi baƙo ne bai san dokar ƙauyen ba. Aka ma sa chaa akan ba za a sake shi ba domin ya taka dokan ƙasa. Ranan da ba a fitowa da takalmi saboda biyayya ga mai girma Amadioha ya fito da takalmi kuma ba a fitowa waje sai rana ta fito shi kuma ya fito waje kafin rana ta fito, dan haka dole a kashe shi kuma babban Dibia ma ya ce gunki na fushi da T J. Ganin dai ba za su fahimce shi ba ne ya sa ya ce idan su ka kashe T J to gwamnati za ta turo a hallaka mutanen ƙauyen gaba ɗaya. Wa su a ciki su ka fara kallon juna suna ƙusƙus amma wanda ke riƙe da wuƙan ya ce bai yarda ba. Ganin sun tsaya yanke shawara tsakanin su ya sa shi komawa gidan su ya sami Baban sa ya gaya ma sa idan har baya so gwamnati ta shafe ƙauyen su a doron ƙasa to ya je yai magana kar a kashe T J, domin T J wakilin Gwamnati ne. Da jin haka Sarki ya razana ya bi bayan Nnadozie su ka je wajen, wanda har lokacin ana ta muhawara akan ko a yanka T J ko kar a yanka shi. Sarki yai magana nan aka tsaida zance akan T J zai bar ƙauyen saboda kar ya jawo mu su fushin Amadioha sannan za ayi sacrifice da jan Taure da farin Zakara. Nnadozie ya kunce T J ya taimaka ma sa su ka koma masaukin su. Sai da su ka je ne sauran ke jajen abinda ya faru. Ashe headmaster na makarantar ya kira Bayo da Felix ya gaya mu su kar su fito yau saboda wani ritual da za ayi a ƙauyen. Su kuma sun ɗauka ya gayawa T J shiyasa ba su kula ba ma da safen da ya shirya ya fita. Shi kuma headmaster haushin T J ya ke ji kasancewar sa musulmi shiyasa bai faɗa ma sa ba. Wannan abun da ya faru ya sa T J da Nnadozie su ka je su ka yi complain a Owerri nan aka mai da shi cikin Obowo local government kuma a nan a sakandare ya ke koyarwa ba primary ba. Sauran abokan na sa ma daga baya guduwa su ka yi saboda gargajiyan ƙauyen yayi yawa ga wahala da su ke yi saboda rashin ruwa mai kyau. Saɓanin wancan ƙauyen garin Obowo na da cika kuma yana da basic amenities da ake buƙata sai dai nan ɗin ma ba masallaci, dan Jummu'ah sai ya je Capital Owerri kafin yai sallar Jumu'ah. Kamsu Salawat kuwa haɗuwa su ke a ɗakin wani Bayarabe ɗan Kwara su na sallar. Akwai 'yan tsirarun musulmai da su ke garin wanda duk kasuwanci ya kawo su, akwai Hausawa akwai kuma yarabawa sai dai a wannan lokacin kan 'yan tsiraru su ke a garin ba su fi a irga su ba... *** Ƙauyen Okwuohia ya cika da Jama'a maza da mata, 'yan ƙauyen da kuma 'yan ƙauyukan gefen su, kai hatta daga manyan garuruwan da ke kusa da su anzo domin halartar bikin Mbom-uzo da ake yi a ƙauyen na shekarar 1985. Bisa dagewar Eze dole T J ya biyoshi su ka halarci bikin. Su isu isu 'yan bautar ƙasa sun je dayawa, dan za su kai su goma shabiyu a wajen. A nan T J ya haɗu da wani Corper ɗan uwan sa musulmi kuma Bahaushe ɗan Jahar Katsina mai suna Hassan, shi kuma daga Orlu local government ya taho. Waje guda aka ware su dan a karramasu, dukkan su kuwa suna sanye da uniform ɗinsu hakan ya sa su ka fito su ka yi kyau. Bayan anje anyi zagaye-zagaye an gudanar da mafiya yawancin abinda bikin ya ƙunsa gameda tsafta da gyara muhalli tukunna aka zazzauna yayinda wa su dayawa ke tsaye, nan aka fara tafi saboda shigowar 'yanmata filin da za su gudanar da rawan su na Atilogwu. Kai tsaye wajen Sarki su ka je su ka tsugunna su ka gaisheshi sannan su ka cigaba da gudanar da rawan. T J dai ya ji an chanja kiɗa kuma ana ta ihu da shewa amma bai ɗago kan sa ba saboda lissafi da ya ke yi a ɗan littafin da ya taho da shi. Eze da ke gefen sa ya taƙale shi yana nuna ma sa 'yan matan da ke rawa a tsakiyar fili. Sai a lokacin T J ya ɗago idonsa yana kallon ma su rawan, da ɗai ɗai ya ke kallon su har ya kai kan wata budurwa da ke rawa, abin da ya banbantata da sauran shine ita ta ɗan fi su jiki, kayan da ta sa irin na sauran ne amma sai ya fi amsar jikin ta sosai. Wrapper ce aka ɗaura wanda ya tsaya iya rabin cinya sai uban jigida da ke ƙugun su. Saman ma dai wrapper ɗin ce aka ɗaura iya wajen nonuwa amma an tamke shi sosai yadda ya kama nonon sosai kamar wani bra, sai beads da ke wuyan su, hannun su da ma tsintsiyar ƙafa. Yadda ta ke rawan tana shaking hips ɗinta da ya fito sosai ya tafi da imanin T J. Shagala yai da kallon wannan budurwa ita kaɗai, dan gani ya ke yi kamar ita ɗaya ke rawa a filin. Duk yadda ta ke ɗaga ƙafa tana swirling ƙafar da hannu abun ya ƙayatar da shi yana tracing every step ɗinta da ido. Tin da ya baro garin su ya zo Imo state, daga camp har zuwa yau bai taɓa ganin macen da ta burgeshi lokaci guda ba kamar wannan yarinyar. Komai na ta ya burgeshi musamman yadda dimple ɗin ta ke lotsawa idan ta yi murmushi. Eze dai har miƙewa yai tsaye ya fara rawa saboda kiɗan da ke shigar sa abinka da shima ɗan ƙabilar Igbo sai ya kasance jin abinda ake faɗa a waƙar ya sa shi jin nishaɗi sosai. A wajen T J kuwa har 'yan matan su ka gama rawan mace ɗaya ya ke kallo. Yana ji da za su tafi ta ƙwalawa Babanta kira tana ɗaga ma sa hannu tana murmushi. T J bai san lokacin da biron hannun sa ya suɓuce daga hannun sa ba ganin yadda dimple ɗin fiskan ta ya lotsa ya ƙara haskaka kyakyawar fiskarta, bai yi ƙoƙarin ɗauka ba dan kar yarinyar ta tafi ba tareda ya gama kallon ta ba. " Allah yayi halitta a nan, Abokina ba ƙarya Yarinyar ta haɗu" Sai a lokacin T J ya juyo ya kalli Hassan da ke riƙe da biron sa. Murmushi yai dan ya ji kunya da har Hassan ya gane irin kallon da ya ke wa wannan yarinya. Shi dai har su ka bar ƙauyen ba abinda ya burgeshi a wajen festival ɗin kaman wannan yarinya da ya gani tana rawa. A hanya kuwa Eze da Hassan su ka sa shi gaba da tsokala. Eze har da cewa za su koma ƙauyen nan ba da jimawa ba su nemi gidan su yarinyar. T J dai bai tanka mu su ba... *** Nkiru baki har kunne lokacin da su ka koma gida musamman da iyayenta su ka nuna ma ta tafi kowa iya rawa a wajen. Shirin kwanciya su ka yi dukkan su ukun. Rashin yarda da 'yan uwan mijin ta ya sa Caroline ba ta yarda sun raba makwanci da ɗiyarta ba, tare su ke kwana a ɗaki dukkan su uku. "Mary" Caroline ta kira sunan ɗiyar ta cikin wani siga na jan hankali. "Yes Mommy" ta amsa tana kallon mahaifiyarta dan indai ta ma ta irin wannan kira to ta san akwai abu mai mahimmanci da ta ke son faɗa ma ta. Caroline ta nisa kafin ta fara yiwa 'yarta bayani kan tafiyar su gobe da sassafe. Nkiru ta tambayi dalilin tafiyar bayan da ance sai bayan christmas za su koma gidan su da ke Owerri. "Ban yadda da ƙauyen nan ba, ina ji ajikina akwai mugaye a gidan nan wanda za su iya cutar da mu" "But Mommy..." "Kar ki damu, in the mighty name of Jesus ba abinda zai samemu" Mary ta amsa da Amin tareda faɗin "i love you Mommy" Caroline ta amsa da " i love you too" Patrick kan tuni yayi bacci dan haka su ɗin ma baccin su ka yi... Wata Zakara ke ta chara ba kakkautawa hakan ya sa Nkiru buɗe idanun ta inda ta ga haske ya soma karaɗe ɗakin na su. Gajiyar jiya bai saketa ba dan haka ta ƙara gyara kwanciyar ta ta cigaba da bacci, sai dai charan Zakaran da ɗan hayaniya da ke tashi a gidan ya sa ta kasa samun bacci dole ta buɗe ido tareda miƙewa zaune. Daddy da Mommy duk su na bacci wanda ya sa Nkiru mamaki dan kullum ita ce ƙarshen tashi a cikin su. Ta fara bubbuga kafaɗar Caroline tana cewa ta tashi safiya ta yi amma shiru. Ganin ta ƙi kulata ne ya sa ta koma gefen Patrick ta fara bubbuga shi. Wani ƙara ta challa lokacin da ta ankara cewa duk yadda take tashin iyayen na ta ba wanda ya motsa a cikin su. Ƙaran da ta yi ne kuma ya sa mutanen gida su ka fara shigowa ɗakin da gudu. Mutum na farko da ya fara shiga kuwa shine Uncle ɗin Nkiru wato Uncle Augustus Udodiri. Tun safe ya ke safa da marwa yana jiran wani ya shiga ɗakin Yayan na sa ya ce ya samesu a mace da shi da iyalin sa sai dai kowa harkan gaban sa ya ke ba wanda ya waiwayi ɗakin Patrick shiyasa ya ke ta sintiri a kusa da ɗakin. Mamaki ne ya ɗan kamashi na lokaci kaɗan saboda ganin Patrick da matarsa a kwance amma Nkiru na zaune tana rusa kuka, mi hakan ke nufi? Ba dai ba ta ci abincin ba ne? Wajen Patrick ya nufa yana taɓa shi tareda tabbatarwa kan sa cewa lallai Patrick ya mutu... *** Kuka ta ke yi mai tsuma zuciya na yadda rayuwarta ya juya lokaci guda. Daddy da Mommy sun mutu ga ta nan ɗaure a ɗan tsurkukun ɗaki wai ana tuhumarta da maita, wai ita ta kashe iyayen ta. Uncle Udodiri har da cewa ita ta cinye 'yan biyun ta Magdalene. 'Yan biyun ta da a hoto kawai ta ganta ba ta iya tuno ta saboda ba su cika shekara biyu bama ta mutu. 'Yan biyunta da an tabbatar pneumonia ne yai sanadiyyar mutuwar ta shine Uncle Udo ke cewa ita ta cinyeta. Da wanne ma za ta ji, da mutuwar iyaye ko da sharri da aka ma ta. Kwana ɗaya kenan da mutuwar kuma ance ba za a bisine iyayen ta ba sai an tabbatar da maitancin Nkiru a fili an kuma ƙona ta saboda kar ta cinye sauran 'yan gidan.Ashe maganar Mommy gaskiya ne da ta ce ba ta yarda da 'yan uwan Daddyn ta ba. Kakan ta wato mahaifin Patrick asalin ɗan gargajiya ne shiyasa ya tara mata dayawa, ciki kuwa biyu ne kawai ya auresu kamar yadda al'ada ta tanada mahaifiyar Patrick wanda ta mutu wajen haihuwarsa sai Ngozi wacce ta raini Patrick ɗin sai dai kasancewar Ngozi ba ta haihu ba har shekara uku ya sa Kakan Nkiru mai suna Ozoemena ya taho da Mistress ɗin sa wacce ke ɗauke da cikin sa a lokacin. Lokacin da ta haihu kuwa ta samu namiji aka sa mi shi suna Udodiri. Daga nan kuwa Mazi Ozoemena ya rinƙa tara mistress har guda bakwai ciki kuwa duk sun haihu idan ka cire matar sa Ngozi da ba ta samu haihuwa ba sai ɗan da ta riƙe wato Emeka. Mazi ya mutu ya bar yara shatakwas amma uku sun mutu kafin mutuwar sa, ciki kuwa biyar ne kawai maza. Bayan mutuwar sa ne kuwa aka samu cikin yaran da matan waɗanda su ka koma zuwa addinin kiristanci. Emeka kam ya jima da zama sai dai tsoron Baban su ya sa ya ke ɓoyewa, amma da Baban ya mutu shine ya fito fili ya bayyana aƙidar sa har ya je aka baptizing na sa a church aka ba shi suna Patrick. Ngozi wacce su ke kira da Nne ita ta tsaya ma sa yai primary har ya je sakandare dan Mazi kam ba ya son boko, daga nan ya samu scholarship ya tafi Ingila karatu a chan ya haɗu da Caroline wacce itama karatun ne ya kawota ƙasar sai dai saɓanin shi da ya zo dalilin scholarship ita Caroline Iyayenta ne su ka biya ma ta. Bayan sun zo gida hutu ne Caroline ta sanar da iyayenta batun Patrick nan fa iyayen su ka ma ta chaa akan ba su yarda ba, kasancewa an riga an yi engagement na ta da wani ɗan abokin Baban ta, na biyu kuma Patrick Igbo ne su kuma ƙabilar Efik ne da ke cikin asalin Jahar Calabar. Bayan ta koma makaranta ne su ka yi aure da Patrick saboda tana tunanin hakan zai sa Iyayen ta su amince amma hakan bai yiwuba domin shekara da ta zago da su ka zo hutu gidan tareda Patrick mahaifin Caroline korar kare ya mu su tareda cewa ya tsinewa Caroline kar ta sake zuwa wajen sa ko wajen 'yan uwan sa. Tafiyar da su ka yi kenan ba su sake dawowa ba sai bayan shekaru ishirin tareda ɗiyar su Nkiru. Tun kafin su dawo Patrick ya sa ƙanin sa Udodiri ya siya ma sa gida a Owerri dan haka su na zuwa gidan su ka zauna. Nan Patrick ya shiga hidimar buɗe kamfanin sa da zai yi a garin, kusan komai ya kammala akan za a buɗe a farkon sabuwar shekara da za a shiga. Ya ɗauki iyalen sa su ka je ƙauye saboda ɗiyar sa ta ga asalin sa kafin daga baya su nemi iyayen Caroline su nemi gafarar su, ƙila tunda shekaru sun ja kuma har da kyautar 'ya a tsakanin su za su yafewa Caroline su sa wa auren su albarka sai dai Kash! Komai ya juye lokaci guda... Nkiru ta cigaba da sheshsheƙar kuka tana tunanin ba ta da wata mafita, gara kawai a kasheta ta je ta haɗu da iyayenta a Heaven su cigaba da rayuwar farin ciki. *To ga fa Mary-Nkiru. Ga kuma T J the mathematician* Yanzu aka fara tafiyar domin *chronicles of Zaytoonah* ya sha banban da salon tafiyar *Sakatariya ta* infact ya fi shi tsaruwa amma dai mu je zuwa. *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *3-Tijjani Abubakar Djibo* Modibbo Muhammadu Djibo Kakan T J kenan, Bafulatanin usul ne gaba da baya, kakannin sa daga garin Djibo su ka fito da ke ƙasar Mali sai dai kasancewar su makiyaya ya sa ba sa zama waje ɗaya. A lokacin da kiyo ta kawo su har garin Ringim shine babban su ya fara rashin lafiya. Jinya sosai har kusan shekara, su da ba sa yin shekara a waje sai gashi har shekara na biyu ta same su a garin, kusan shekaru uku kafin Usmanu Djibo ya warke sosai. Karamci da kuma yanayin garin ya sa dukkan su suka haɗa baki su ka tsaida magana akan za su cigaba da zama a garin. Daga nan auratayya ta shiga tsakanin su da fulani 'yan asalin garin, sai aka haɗu aka zama guda. Kakan T J wato Modibbo Muhammad yana da mata ɗaya Rumaysa'u wacce ake kira Daadawuro, 'ya'yan su biyar Allah ya ma ta rasuwa wannan ya sa aka aura ma sa ƙanwarta Fatima da su ke kira da Yadikko. Fatima, Khadija, Aisha, Umar da Usman sune 'ya'yan Daada ita kuma Yadikko ɗa ɗaya Allah ya ba ta wato Abubakar. A haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya inda aka aurar da yara mata yara mazan ma su ka yi aure ban da Abubakar Auta. Usman ya auri Maryama su na zaune lafiya shekara huɗu kafin Allah ya bata haihuwa ta samu mace aka sa ma ta Rumaysa'u amma Ruma su ke kiranta. Yarinyar ba ta cika shekara ba Allah yai wa Usman rasuwa. Maryama ta shiga cikin tashin hankali, kusan gaba ɗaya iddar ta ta yi shi cikin jinya ne. Hakan ya sa ko bayan ta gama idda ta cigaba da zama a gidan dama kuma ta haɗa jini da Usman dan auren haɗin gida aka mu su. Shekaru biyu bayan rasuwan Usman Maryama ta samu nitsuwa da kwanciyar hankali, dama har da ƙuruciya da ke daminta shiyasa mutuwar ta girgizata sosai dan tana shekaru sha bakwai Usman ya rasu. Mahaifin maryama wanda kusan ƙani ya ke ga Modibbo Muhammadu ya samu Modibbo akan ya kamata Maryama ta sake wani aure tunda dai har yanzu da ƙuruciyarta, shima dai yayi tunanin hakan, ganin Maryaman ba ta kwantar da hankalinta ba ne ya sa bai tada maganar ba. Wasa-wasa duk wanda aka turo ya nemi Maryama sai ta ce ba ta so. Abun ya ishi mahaifinta ya zo har gida ya ma ta faɗa ya ce daga yanzu duk wanda ya fito amincewa zai yi tunda alamu sun nuna ba auren ta ke so ba. Yadikko ta samu Modibbo akan ko za a haɗa Maryama da Yayan mijinta wato Umar. Abin yai wa Malam daɗi sai dai wani hanzari ba gudu ba halin Umar da Usman ba ɗaya ba ne. Yayinda shi marigayi Usman ke da sauƙin kai shi Umar yana da zafi, matan sa biyu amma kullum cikin shari'a ake yi baya mu su adalci kwata-kwata. "Ni kam ba dan kar ka ce na so kai na dayawa ba da sai na ce a haɗa Maryama da yaron wajena" Modibbo ya kalli Yadikko yana tunanin hikimarta. Daga nan aka tsaida magana akan za a haɗa Abubakar da Maryama wanda tsakanin su kwata-kwata ko shekara bai kai ba. Sa'anni ne dan a shekara ɗaya aka haifesu, sun ma yi wasa tare. Mahaifin maryama yai na'am da maganar ya kuma karɓi sadaki. Amma da aka sanar da Maryama maganar ta ce ba ta san zance ba bazata iya auren ƙanin mijin ta ba. Abu dai aka ja aka ja ƙarshe dai dole ta haƙura aka yi auren. Da ke ba son auren ta ke ba ba ƙaramin wahala ta bawa Abubakar ba, shi kuwa sarkin haƙuri bai taɓa nuna ma ta damuwa ko ya tsawatar ba. Shekara ta zo ta wuce, auren Maryama da Abubakar a suna ne amma a aikace ba wani abu da ke shiga tsakanin su. Daga ƙarshe dai tausayin Abubakar ya kamata tareda tuna nauyin da ke kanta wanda kullum Yadikko ke zaunar da ita tana ma ta nasiha, daga ƙarshe ta ajiye makaman yaƙi ta rungumi mijinta su ka cigaba da rayuwa cikin farin ciki, bayan wata shabiyar da aure suna zaman kurame. Aishatu Indo itama 'yar cikin gida ce kuma tun tasowarta ta ke son Abubakar, lokacin auren Abubakar da Maryama tana shekara shauku a duniya. Shekara ta zago aka fara maganar aurar da ita, ta ƙeƙasa ƙasa ta ce Abubakar ta ke so ba Iliyasu da ake son haɗa su ba. Ƙarshe dai dole aka amince tunda auren Abubakar na fari bazawara ya aura. Ba a jima ba aka ɗaura auren Abubakar da Aishatu wacce ta ke ji da tashen balaga da gigin budurci. Kafin auren su, Abubakar da Maryama ba ƙaramin shaƙuwa su ka yi ba saboda halin su ya zo ɗaya kuma tun suna yara dama sun yi wasa tare, dama dai kunyar ƙanin miji ya sa Maryama cewa ba za ta iya auren sa ba. Aishatu da falli ta shigo gidan tana son nuna ita ce aka aureta budurwa, amma ba wannan ba ne a gaban Abubakar. Maimakon ta kwantar da hankalinta ta samu soyayyar miji sai ya zama kullum cikin shiri ta ke yadda za ta muzgunawa Maryama, ko ba matsayin kishiya ba Maryama ta girmi Aishatu amma ba ta ganin wannan haka za ta rufe ido ta yi ta zuba ma ta rashin mutunci. Maryama ba ta kulata dan ta san yarinta ke damunta. A haka dai aka yi zaman har Aishatu ta haifi ɗa namiji aka sa mi shi suna Usman amma su na kiran shi da Manga. Wannan ya ƙara sawa Aishatu girman kai da tinƙaho ganin har lokacin Maryama ba ta haihu ba. Shekaran Usman biyu ta sake samun ciki wannan karan itama Maryama Allah ya ba ta cikin sai ga shi Aishatu na haihuwa da sati biyu Itama Maryama ta haihu dukkan su kuma maza. Ɗan Aishatu ya ci sunan Babban Yayan Aishatun wanda ya rasu a ranan da ta haihu, wato Shehu Tijjani, shi kuma ɗan Maryama ya ci su nan Kakan sa wato Muhammad su na kiransa da Gidaɗo. Bayan Tijjani Aishatu ta haifi Zainab sannan Mukhtar da su ke kira Muntari. Ita dama Maryama irin matan nan ne da ba sa haihuwa da wuri dan sai da Aishatu ta yaye Muntari kafin ta haifi autar ta Fatima Zahra wato takwarar Yadikko. Ita kuma Aisha bayan Muntari ta sake haifan Halimatus Sadiya da kuma autar ta Murjanatu. Zaman Goggo Maryama da Iya Aishatu abin dai har aka tara 'ya'ya bai ƙare ba. Ba abinda ya ƙara kunna wutar rashin jituwar su irin yadda Abubakar ya ɗauki Tijjani ya damƙawa Maryama saboda wani faɗa da su ka taɓa yi akan Tijjanin. Kasancewar Tijjani da Gidaɗo kan su ɗaya sai ya zamana kullum suna maƙale tare kaman 'yan biyu abinci ma tare su ke ci, ko Aishatu ta zubawa Tijjani nashi haka zai ɗauka ya je ɗakin Maryama ya zauna su ci tareda Gidaɗo. Watarana suna cin abinci tare sai Aishatu ta zo ta raba su ta ja kunnen Tijjani ta ce kul ba ta yarda ya sake cin abinci da Gidaɗo ba har da cewa ta sake kama shi sai ta ma sa shegen duka. Ashe kaf abin ya faru a idon Yadikko ne, ba ta ma ta magana ba sai da Abubakar ya dawo ta ce ya je ya kwaso kayan Tijjani ya kawo wajen Maryama bai tambayi dalili ba yai kamar yadda mahaifiyar sa ta umurta. Aikuwa Aishatu ta yi faufau ba za a bawa Maryama ɗan ta ba, ta biyo Abubakar har tsakar gida tana ta masifa. Yadikko ta daka ma ta tsawa ta ce idan hukuncin da ta yanke bai ma ta ba ta wuce gidan su, ba za ta zo ta haɗa gaba tsakanin jikokin ta ba. Aishatu ta yi shiru tana huci. Daga lokacin da Tijjani ya koma wajen Maryama Aishatu ta ƙi shi, ko ya zo kusa da ita sai ta dinga hantarar sa kamar ba ɗan cikinta ba. A da duk cikin 'ya'yan ta tafi son shi saboda tsananin kamannin sa da Mahaifinsa, Abubakar da Tijjani yadda ka san an tsaga kara, amma yanzu gaba ɗaya ta ƙi shi. Shi ma bai damu ba saboda yarinta ya koma ɗakin Maryama hankali kwance. Har wa yau Goggo Maryama ya ke gani a matsayin Uwa ita Iya haihuwar sa kawai ta yi amma duk wani tarbiya da ya samu daga wajen Goggo ne. Gidaɗo Allah bai yi shi lafiyayye ba ashe ciwon sugar ya ke da shi ba a sani ba. Idan ciwo ya tashi ayita ɗura ma sa maganin gargajiya wani lokaci abin yai sauƙi wani lokaci kuma kamar ba zai yi rai ba. Yana shekara goma shahuɗu aka ma sa aure bisa shawaran manya akan ƙila aure zai sa ya samu lafiya. Wata cikin 'yar uwarsa aka aura ma sa 'yar shekara shauku. Shekaran farko kam da Gidaɗo da Hannatu an tafka kwaɓa da shirme kafin a hankali su ka samu kan zaren. Gidaɗo na shekara shashida ya rasu nan ma ciwon sa ne ya tashi ana ta bashi maganin gida sai kumburi ya ke yi ƙarshe aka kai shi Asibiti a Kano a nan likitoci su ka gano ainihin mi ke damun shi amma its too late dan ko sati bai yi ba da aka fara treating na shi ya cika. Da rabon Asma'u za ta zo duniya ya sa aka ma sa aure da wuri dan bayan rasuwar sa aka gano Hannatu na da cikin wata biyu. Tundaga primary school Tijjani ke da ƙwazo hakan ya sa lokacin da ya ci makarantar kwana Yadikko ke ƙorafin zai yi nisa da gida kuma Bokon ma yawanci daga primary 'yan gidan su ke tsayawa, akwai wani ɗan Kawun su Tijjanin da ya fara Sakandare ya watsar ya dawo ya cigaba da noma ya ce a ma sa aure. Ta ce ita ba ta so Tijjani yai nisa da gida. Modibbo ya ce Tijjani ɗan Baiwa ne idan aka bashi dama zai yi ilimi sosai. Dole dai haka ta haƙura Tijjani ya tafi boarding school. A cikin jikokin na ta ba ƙaramin son Tijjani ta ke ba har ba ta iya ɓoyewa. Daga gama secondary school ya samu sakamako mai kyau ya kuma samu gurbin karatu a ABU Zaria inda ya ke karantar Maths and Statistics. A shekarar sa ta biyu ne Allah yai wa Modibbo rasuwa. Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har ta kawo yanzu da Tijjani ya gama makaranta har ya kusa kammala bautar ƙasa. Wannan kenan... *** Cincirindo aka yi a ƙofar ɗakin Goggo ana son kallon Arniyar da Tijjani ya kawo gida. Daga balbali-balbali matan yayye, ƙanne da ma 'ya'yan gida haka ake ta shiga ana dubata. Babu wanda Goggo ta tankawa cikin su dan ta san neman magana su ke yi. Wa su da sun shigo sai su cewa Goggo ɗakinta ya zama najasa tunda akwai Arniya a ciki, wasu su ce indai ta yi sallah a ɗakin sallarta ba zai karɓu ba. Wasu kuma su ce mala'iku sun tsine ma ta tunda ta ba wa Arniya mafaka. Jahilci dai kala-kala. Nkiru kam tunda aka fara shigowa ana kallon ta ana yare ta duƙunƙuna kanta jikin bango tana hawaye. Yadda su ke ma ta kaman wata alien ce a ɗakin, ko da ba ta jin Fulatanci ta san zaginta su ke yi. Yadikko ta yi masifar amma ba wanda ya kulata sai shigowa ake yi ana turereniya... T J kam da sassafe da ya shigo ya gaishe da Iya ta sashi a gaba da faɗa wai taji ya kawo mu su karuwa gida to maza maza ya fitar da ita. Yanada masaniya akan Baffa ya sanar da ita komai amma kuma ta rufe ido tana kiran Nkiru da karuwa. Har da cewa dan ya yi Boko ne ya tafi kudu bariki. "Hamma idan aure ka ke so, ga mata nan birjik a garin ku sai ka je wata duniya ka ɗauko Arniya. Tarbiyan da Maryama ta ɗaura ka kenan? Allah ya kyauta amma sakayyar da ta min Allah ya isa" Duk yadda T J ya so ya ma ta bayani ta ƙi fahimta ƙarshe ta ce idan har Nkiru ba ta bar gidan ba kar ya ƙara shigowa ɗakin ta. T J ya fita jiki a sanyaye. Duk da gajiyar da ke tattare da shi haka ya fita daga gidan. Zuwan Alhaji Isa gidan ne ya sa kowa ya fara ƙoƙarin guduwa. Faɗa ya farayi yana zagin su kan aikin jahilcin da su ke yi kaman ba Ahalin Modibbo ba. Idan ba su manta ba mutane nawa su ka musulunta a dalilin kyawawan halayen Modibbo. Mutane nawa ne ba musulmai ba ba kuma Fulani ba Modibbo ya bawa mafaka a gidan sa sai a kan wannan za a ringa yayaɗa magana kamar wani sabon abu ne a gidan. "Wallahi duk wacce ta muzgunawa yarinyar nan sai na bata kashinta a hannu" daga haka ya juya ya fice, ana bashi haƙuri amma bai saurari kowa ba. Alhaji Isa ƙanin Modibbo ne. Duk cikin su kuwa shine Allah ya bawa arziƙi, yafi kowa yawan shanu da gonakai. Yayinda Modibbo ya ke babban malami shi babban ɗan kasuwa ya zama. Shima dai gidan sa kusa ya ke da gidan Modibbo dan gaba ɗaya inda kakannin su suka zauna a nan suma suka yi ginin su. Sai dai ko ba a faɗa maka ba kana zuwa anguwar za ka san Alhaji Isa wani ne domin gidan sa ya fi na kowa girma da tsaruwa a anguwar... Tafiyar Alhaji Isa ya sa kowa ya watse ana ta ƙananun maganganu. Sai lokacin Nkiru ta samu nitsuwa. Kusan ƙarfe goma shaɗaya na safe sai ga T J ya dawo ɗauke da ledoji guda uku. Ɗaya kayan tea ne a ciki ɗayan kuma kayan sawa ne. Doguwar riga ne irin ta turawa guda biyu sai riga da skirt guda biyu, sai takalmi guda biyu. Ɗaya ledan kuma zannuwa ne guda uku ya bawa Goggo akan ta sa Asma'u ta raka Nkiru wajen Tela a ɗinka ma ta. Cewa yai ta gwada kayan dan hasashen jikinta yai ya siyi kayan. Tsayawa ta yi tana kallon shi, shima sai ya ƙura mata ido. "Barkindo da alama dai a gabanka za ta sa kayan" Goggo ta faɗa. Ya fara sosa kai ya fice daga ɗakin. Ƙuryar gado Nkiru ta shiga ta fara gwada kayan. Duka sun mata sai doguwar riga guda ɗaya da bai shigeta ba. Takalman ma sun yi daidai. Kusan minti Ishirin sai ga T J ya dawo ya tsaya a bakin ƙofa yana tambayar Goggo ko ya shigo ta ce Bismillah. Nkiru ta ma sa bayanin kayan tareda godiya, ya karɓi wanda bai shigeta ba ya ce zai mayar a chanja ma ta. Ya ce akwai bread ta haɗa shayi tunda ba lallai ta iya cin ɗumame ba. Ta yi dariya lokacin da ta ji kalmar 'ɗumame'... Haka dai kwana biyu su ka shige gida ya fara cika ana ta shirye-shiryen biki. Nkiru kam banda T J da wata Pendo wacce ke ɗan jin turanci kaɗan-kaɗan saboda ta ƙare primary ba ta magana da kowa. Pendo cousin ɗin T J ne shekaranta shauku. Tsakanin ta da Goggo da Asma'u kuwa sai maganan kurame. Asma'un ma ta fara makaranta tana primary one amma ba ta jin turanci. A hankali ta ke karantar 'yan gida da yanayin su, abinci kam da safe, rana da dare T J ke kawo ma ta. Idan ba za ta je banɗaki ba ba ta fita tana zaune a ɗaki. Ranan da Pendo ta ce su fito ta ga yadda ake nakiya da Alkhakin biki haka matan ke ta tsura ma ta ido suna nunata da hannu. Itakan abun da su ke ya burgeta dan haka ba ta damu da yadda su ke kallon ta ba ta zuba mu su idanu tana kallon abun da su ke yi. "Ni tausayi Boɗɗiyon Tijjani ke bani. Ashe ga mace har mace amma ba addini ba miji" Wata daga cikin matan ta faɗi. Boɗɗiyon Tijjani ko Boɗɗiyon Hamma sunan da su ka laƙawa Nkiru kenan. Pendo ta ce " sunan ta fa Mary" "Ungo na ki Pendo" matar ta ma ta daƙuwa. Pendo ta ja baki ta yi shiru... Da yammacin ranan Muntari ya dawo daga Kano ya zo biki ƙannen sa. Ankaishi makaranta yana aji biyu ya gudo ya ce ba zai iya ba Kwanyar sa da ta Tijjani ba ɗaya ba ne. Buga-buga ya ke yi a Kanon ba wai ya zauna waje ɗaya ba ne ko yana da takamaimai abu ɗaya da ya ke yi. Ya ƙi ma ya zauna a Ringim yai noma, kaman yawancin 'yan uwansa. Ɗan Bokon da yai da kuma shiga Birnin Kano da ya ke yi ya jawo Muntari ya koma wani shaƙiyi. Shekarun sa shatara amma abinda ya ke yi da burukan da ya ɗaurawa ransa ko ɗan shekara talatin iya kaci. Tunda ya shigo Iya ke ta masifa. Ta je za ta shiga banɗaki ne ta haɗu da Nkiru ta fito daga banɗakin shine ta fasa shiga ta shiga ɗayan. "Wai ni kam wacece wannan ne da ta sa Iya ta cikin damuwa haka?" "Karuwar da Hamma ya kawo mana, ni inaga mayya ce ma dan tun randa ta zo na ke fama da ciwon kai" Muntari yai dariya ya ce "ikon Allah Hamma Tijjani ne ya kawo karuwa har gida" Iya ta shiga bashi labarin ƙarya da gaskiya gameda Nkiru, gaba ɗaya sai ya matsu da ya ga wannan yarinyar da ake ta magana. "Barin je na gaida Goggo" ya faɗa tareda miƙewa tun kafin Iya ta cigaba da ƙorafi... Wanka ta yi ta saka kaya amma ta kasa motsawa jini ne ya zo mata ta rasa ya zata yi, ba kowa a ɗakin gashi ƙila T J sai dare zai dawo. Tana zaune a ƙasa inda ta shimfiɗa wani zani kar jinin ya ɓata ƙasan duk da ta san zai jima kafin ya ratsa doguwar rigan da ta sa tunda da kaɗan-kaɗan ya ke zuwa ranan farko. "Salamma Alaikum, Goggojiya ina baƙin na ku" ya faɗi yana kutsa kai cikin ɗakin "Goggo i..." maganar ya maƙale lokacin da ya hango ta zauna tana yamutsa fiska. Ya buɗe ido baki hanci duk yana kallonta. Fara ce sosai dan zai iya cewa ta fishi fari nesa ba kusa ba. Kai Murjanatu da Talatun Inna Adama ake ganin farin su har yayi yawa amma wannan ta ninka su. Shi ba dan ance ma sa Inyamura ba ce da Baturiya zai kirata. Ga ta ɗan 'yar duma-duma irin matan da ya ke so ba kamar matan su na nan da su ke a bushe ba. Kitson da aka ma ta lokacin da za su yi festival a ƙauye shine a kanta, ya fara tsufa amma bai hanashi ƙasa haskaka fiskan ba. Beads ɗin da aka yi kitson da shi har lokacin suna kan ta. "Hallo Bentiful woman. Am Muntari, small brother of Tijjani" ya faɗa tareda tsugunnawa a gabanta. Murmushi ta yi saboda jin turancin sa, accent ɗin bahaushe ne ke bakin T J nan ma ba sosai ba amma ya iya turanci, suna full conversation ba wani gargada. Amma wannan kam ba vocabulary ba grammar ba komai, kuma yadda ya dage yana maƙe murya ka ce turanci mai kyau ya ke faɗi. Murmushin da ta yi ya ƙara fito da dimple ɗin ta wanda hakan ya sake birkita Muntari. "What is ya name?" "Mary" ta amsa a taƙaice tunda T J ya ce sunan ta Mary ne Nkiru zai mu su wuyar faɗi. Shi kaɗai ke kiranta da Inkiru. "Bentiful, me i come for Kano. Small Sister is to marriage tomorrow" Ta gyaɗa ma sa kai tana murmushi, ya sa hannu ya shafa fiskarta yana danna wajen dimple ɗin "Kan bala'i! wannan taushi haka" "Muntari!" Ya ji an daka ma sa tsawa. Ita kanta Nkiru sai da ta tsorata. A fusace ya ƙariso yana huci kamar mayunwacin zaki. "A wani dalilin za ka taɓa ma ta fiska" "Hamma kawai" "Ka shiga taitayinka Mukhtari. Dan ba ta sallah ba shine zai sa ka dinga taɓata yadda ka ke so ba, ba muharramanka ba ce ka kiyaye" ya faɗa kaman zai make Muntari "Mi ya ke faruwa?" Goggo da ta shigo ta ke tambaya. "Ba fa abinda na yi Goggo, na ga baƙuwa a ɗakin ne na ke gaisawa da ita" "Fita a ɗakin nan" ya faɗa da ƙarfi. Muntari ya fice yana tsaki. Ganin ba shi da niyyar magana ne ya sa Goggo cewa "Allah ya baku haƙuri" Daga tsaye ya fara yiwa Nkiru faɗa akan ka da ta yarda ta bari wani namiji ya taɓata babu wani ƙwaƙwƙwaran dalili ko da kuwa shi ne. Bai jira mi za ta ce ba ya fice a ɗakin. Yana shiga ɗakin sa ya kasa zaune ya kasa tsaye, hannun Muntari kawai ya ke gani a fiskar Nkiru. Zuciyarsa tana wani ƙuna. Yarinyar kam akwai ta da wauta ko dan saboda ita ce 'yar fari, amma bai ɗauka wautan ta ya kai har ta tsaya Muntari ya dinga shafa ma ta fiska ba tare da ta buge hannun ba. Wata zuciyar ta ce ma sa " ka ma ta uzuri, addinin ku ba ɗaya ba haka yaren ku ba ɗaya ba ne" sai dai duk da ya tuna da hakan zuciyar sa ba ta yi sanyi ba. Buga ƙofar sa da ake yi ne ya sa shi dai na sintirin da ya ke a ɗakin. Asma'u ce ta gaya ma sa saƙon Goggo nan da nan ya fice da sauri... Kuka sosai ta ke yi lokacin da ya shigo. Tsugunnawa yai a gabanta yana jin wani abu na zungurar shi a zuciya. "I'm sorry Inkiru" ya faɗi da tausashashshiyar murya. Shi kan sa bai san dalilin yi ma ta wannan faɗan ba. Rarrashinta yai ta yi har ta yi shiru. Ganin ta dena kuka ne ya sa shi tashi zai tafi sai ya ji ta kira shi a hankali "Teejay" Ya kalli idonta wanda ke birkitashi tun haɗuwar su. "I'm i'm" sai ta rasa bakin magana, yadda ya tsareta da ido ya sa ta ji kunyar gaya ma sa abinda ta yi niyya. "What?" Ya ɗaga ma ta gira "My p p period" ta faɗa tareda rufe fiskarta da tafukan hannun ta. Murmushi yai ya ce bari ya kawo ma ta takarda sai ta rubuta ma sa abinda ta ke buƙata.. *har yanzu fa sharan fage ake a labarin* *Ga Hamma Tijjani ga kuma Muntari duk idon su ya ƙyasa da Mary-Nkiru* *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... ......ZAYTOONAH* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *2- Igbo girl (Inyamura)* Bismillahir Rahmanir Rahim A inda ta ke zaune ta fara gyangyaɗi sai dai buɗe ƙofar ɗakin da aka yi ya fargar da ita ta buɗe ido tana kallon ƙofa cike da tsoro. Wata mata ce ta shigo ɗauke da lantern irin na da wanda ake sawa kerosene. Sai da ta matso kusa da ita kafin Nkiru ta gane waye. Anty Nonye ce wacce ta maida sunan ta Elizabeth, ƙanwar Patrick. Tunda mijinta ya mutu shekaru uku bayan auren su ta dawo gida da zama, kusan shekaru sha shida kenan ba ta sake wani auren ba. Ta maida kan ta wata ƙaramar pastor dan ta maida rayuwarta kwacokam wajen yiwa church ɗin su hidima. Elizabeth ta sa hannu a bakinta tareda faɗin "shshshsh" Kunce ma ta ɗaurin da aka yi ta yi sannan ta ce a hankali "ki biyoni a hankali" Siɗak-siɗak su ka fito daga ɗakin Elizabeth na riƙe da hannunta su ka fice daga gidan, kasancewar ɗakin yana chan ta baya ne sannan kuma tsakar dare ne kowa yayi bacci dan ana maganar ƙarfe uku na dare. Sosai su ka yi tafiya kafin su ka kai bakin church ɗin ƙauyen inda wani mutumi ke tsaye a bakin keke yana jiran su. Elizabeth ta kama hannun Nkiru guda biyu tana faɗin " kin ga iyayen ki da su ka mutu ina da yaƙinin Uncle ɗin ki Udodiri ne ya kashe su kuma ke ma sharri ya miki dan a kashe ki. Dukiyar mahaifin ki ya ke son ƙwacewa, ki bi Antony zai kai ki garin Obowo akwai gidan wani elder na church ɗin mu sai ki zauna a chan idan kin huta zai sa ki a mota ki wuce Calabar, ban san gidan Kakannin ki na chan ba amma na san tunda Patrick ya ce iyayen Caroline ma su kuɗi ne ba za su yi wuyar samu ba. Sai ki tambayi gidan Chief James Asibong" Nkiru ta gyaɗa kai tana hawaye. Ko ba ta faɗa ma ta ba ta san sunan Kakan na ta, tunda maiden name ɗin Mommy shine Caroline Asibong. Ta kuma san Mommy ce 'yar fari a wajen mahaifinta kuma tana da ƙanne biyu maza 'yan biyu. Elizabeth sai da ta ga sunyi nisa kafin ta bar bakin church ɗin tana addu'an Jesus ya sa Nkiru da Anthony su isa garin Obowo lafiya... Sun fita daga ƙauyen lafiya amma ba su yi wani nisa ba keken Anthony ta yi faci dan haka a ƙafa su ka ci gaba da tafiya Anthony na tura keken ita kuma Nkiru na binshi a gefe. Nkiru tana tafiya ne tana hawaye, yunwa da ishirwa sun ma ta kamun talala amma ba wannan ne damuwarta ba damuwarta shine abinda Uncle Udodiri ya yi. Kafin su iso garin gaba ɗaya ta jigata amma a haka ta dage tana tafiya ba tareda ta nuna gajiyawarta ba. Ko da su ka je gidan Elder ɗin safiya ta yi sosai sai dai rashin sa'a matar sa ta ce mu su baya gari. Antony ya gayawa matar saƙon Elizabeth akan Nkiru za ta zauna da su na wani lokaci dan haka duk da Elder baya nan zai bar Nkiru a wajenta idan ya dawo sai ta sanar da shi. Matar Elder ta washe baki ta ce ma sa ba komai. Anthony ya fita dan ya je yai facin tayar keken sa sannan ya wuce ƙauyen su. Bai fi minti takwas da tafiyar Antony ba matar ta kalli Nkiru da ke zaune tana zazzare idanu ta ce da yaren Igbo " ba zan amince da zaman ki a gidan nan ba saboda na san halin mijina, the last time da aka kawo mace gidan nan ban ji da daɗi ba dan haka ki tashi ki kama gaban ki, idan dai Calabar za ki je ga hanya daga nan ba nisa zuwa park za ki samu mota" Nkiru da ta ɗauko kofin silver na ruwa da matar ta kawo mu su za ta kai baki sai ta kafe a wajen hannunta ya fara rawa. "Ba ki ji abinda na faɗa ba ne" ta faɗa da ƙarfi wanda yai sanadiyar da kofin hannun Nkiru ya suɓuce ya faɗi ƙasa. "Please help me, ban san ko'ina ba a garin nan kuma ba ni da kuɗi. Ki bari..." "Will you shut up! Irin ku ne mijina ke so, sweet sixteen. Ba zan yarda ba, ki tashi ki tafi kafin rai na ya ɓaci" Nkiru ta fashe da kuka saboda ba ta san inda za ta je ba daga nan. Ina ta sani a Nigeria. Gidan su da ke Owerri ko sunan anguwan ba ta sani ba, balle ko ta sani ma ba halin zuwa dan Uncle Udodiri zai iya zuwa ya kamata a wajen. Yadda matar ta harzuƙa ne ya sa Nkiru ta fice daga gidan da gudu tana gudu tana tunanin ko za ta dace da haɗuwa da Antony. Sai da ta yi nisa sosai da gidan ta haƙura da gudun ta soma tafiya... Chochi shine mafita gareta za ta samu mutanen ƙwarai da za su taimaka ma ta a wajen. Tana tafiya tana baza ido ko za ta ga alaman church. Ba a jimaba kuwa ta hango wani madaidaicin church sai dai a kulle ya ke ta yi tsaki ta cigaba da tafiya. Sanyin December na shigarta amma ba ta damu da sanyin ba ta cigaba da tafiya a hankali tanayi tana zubda hawaye. Mafiya yawancin ma su wucewa kallon mahaukaciya su ke ma ta, pink pyjamas ne ajikinta mai gajeran hannu gashi ƙafarta ba takalmi. Slippers ɗin da Elizabeth ta ba ta ya tsinke lokacin da su ke tahowa garin Obowo a ƙafa, yanayin tafiyarta kaɗai ya isa ya gamsar da mutum cewa ba ƙalau ta ke ba. Yadda ta hango wasu treloli da bus bus a ɗan nesa da ita ya sa ta ɗan tsaya. A ranta ta ke tunanin ƙila za ta iya samun motan Calabar a nan, sai dai matsalar ba ta da kuɗin mota amma ba ri ta gwada roƙon su ko za su taimaka ma ta. Ta shafa cikinta da ke ta ƙugi yana neman abinci, rabon da ta ci abinci tun shayin da ta sha daren da aka kashe iyayenta. Sakwara da miyar egusi aka kawo mu su daren ranan wanda ya ji naman Akuya nasha-nasha sai dai ita ba ta cin naman Akuya kuma ba ta son cin abinci mai nauyi da dare, shiyasa kawai ta haɗawa kan ta tea ta sha yayinda iyayen ta su ka ci sakwaran, ashe da rabon za ta rayu ne shiyasa ba ta ci ba... "Kai ɗan Fillo akwai ka da abin dariya" Ɗaya daga cikin ma su lodin jarkunan manja cikin trailer ya faɗa yana kallon T J da ke cigaba da ba su labarin yadda aka kusa kasheshi a wani ƙauye. "Ka san na sadaƙar da rai na, ina ta tunanin ina ma albarkacin sunan Shehu Tijjani da na ci nima Allah zai ba ni karama kawai na ɓace na ganni a gaban Baffa na. Amma inaaa, ita mutumin sai wuwulwuwul ta ke da wuƙa tana faɗin Osibatata osibututu osiburebure..." Gaba ɗaya 'yan wajen su ka fara dariya, wani da ya ɗau jarka sai ga shi da jarkan a ƙasa ya riƙe ciki yana dariya. T J ya dage yana maimaita mu su siddabarun da mutumin ke faɗi yana cikin haka ya ji an dafa ƙafaɗar sa. Ya juyo a hankali yana dariya, buɗe baki yai yana kallon wacce ta dafa shi, ya ɗan rufe ido ya buɗe ko dai yarinyar ce ta ke ma sa gizo. "Please help me, i'm going to Calabar but i dont have money". Nkiru ta faɗa kamar za ta yi kuka. Tunda ta shigo wajen ta ke rarraba ido tana neman wanda za ta yiwa magana, yadda ake kallonta ya sa jikinta yai sanyi tana tunanin anya akwai wanda zai taimaka ma ta, ganin wani saurayi sanye da kayan NYSC ya sa ta tunkare shi, ko a Owerri ta ga ma su irin kayan watarana da su ka fita shaƙatawa inda Baban ta ya ma ta bayanin ko su waye ma su saka irin kayan. "Please" ta sake maimaitawa ganin ya ƙi yin magana. Daɗin muryanta tareda British accent ɗin ta ya dawo da shi daga duniyar tunani da ya tafi na 'yan sakanni. "Sorry, you said Kalaba?" Ta gyaɗa ma sa kai Ya kalli ɗaya daga cikin ma su lodin manja ya tambayeshi ko ana samun motar Calabar a wajen, mutumin ya ce ma sa sai dai ta je General Park. T J ya juyo ya gaya ma ta da turanci. Yadda ta sauke ajiyar zuciya ya sa T J ya san ba lafiya ba. Ɗago idon da za ta yi sai ya ga hawaye a idonta mamaki ya kamashi. So ta ke ta gaya ma sa ba ta da kuɗi kuma ba ta san inda General Park ɗin ya ke ba amma ya ma ta kwarjini ba ta sani ba ko kallon mahaukaciya zai ma ta. Ta juya a hankali ba tare da ta ce ma sa komai ba ta fara tafiya, wannan karan church za ta je ko da a rufe ya ke za ta zauna a bakin church ɗin, ba ta da mafaka da ya wuce House of the Lord, ko da mutuwa za ta yi gara ta mutu a church. "Hey wait" muryan T J ya tsaidata. Ta dai tsaya amma ba ta juyo ba. Tambayarta yai ko ita ce ta yi rawa a wani festival da aka yi a ƙauye kwana uku da su ka wuce. Ta gyaɗa ma sa kai. "What happened to you?" Hajijiya ta fara ji dan haka ta tsugunna tana dafa kanta. "Are you Ok?" Ya tambaya cike da damuwa. Kallon ƙafarta yai ya ga ashe ko takalmi babu ga ƙafar har ya faffashe. "This is serious. Where are your parents? Why are you like this?" Ba ta iya ba shi amsa ba sai hawaye. "Ɗan Fillo yarinyar nan fa yunwa ta ke ji, tana cin abinci za ta warware" wani a wajen ya faɗi. Wani kuma ya ce " Ku ga idon ɗan Fillo dan Allah, ya ga yarinya 'yar dumaduma ya ruɗe" Aka kwashe da dariya Wani kuma ya ce "Ɗan Fillo da rabon dai yau za a yanke ma ka wuya" Nan su ka hau maimaita Osibatata Osibututu su na dariya. Taimaka ma ta yai ta miƙe tsaye sannan ya ce ta biyo shi. Wajen mai shayin da ke tashar su ka je, duk garin shi kaɗai ke sana'ar shayi, da farko Hausawa 'yan uwan sa kaɗai ke siya daga baya kuma ya fara samun ɗaiɗaikun mutane da ba hausawa ba wanda su ke aiki a tashar su ma suna siya. "Malam Idi zubo min shayi dan Allah" Malam Idi ya ce "to Shehi" Da ke ya saba da 'yan tashar , su na haɗuwa wajen Sallah, sannan duk wata ya kan zo tashan ya ba da saƙo a kai ma sa Kano daga nan har garin su. Yadda ya ke haɗa ma sa shayi ya ji sugar sosai haka ya haɗo ya miƙa ma sa. T J ya karɓa ya miƙawa Nkiru da ke zaune a kan benchi. Ta amshi kofin shayin ta kai baki, yadda hannunta ke rawa ya sa T J ya ƙara jin tausayinta tabbas akwai yunwa a tattare da ita. Ko zaƙin tea ɗin ba ta damu da shi ba haka ta fara kurɓan tea ɗin nan ba kakkautawa, kafin ka ce me ta shanye shi tas. Ta miƙa wa T J kofin tana faɗin "Thank you" Ya miƙawa Malam Idi kofin ya karɓi wani shayin tareda bredi ya miƙa ma ta. Ta wafce bredin da sauri ta fara ci da sauri-sauri. Saboda yadda ta cika bakinta da bredi da ƙyar ta ke taunawa. Ganin haka ya sa T J da ke kallon ikon Allah ya miƙa ma ta kofin shayi ta kuwa amsa ta kurɓa, hakan ya sa bredin da ke bakinta yai laushi har ta samu ta haɗiyeshi haka ta cigaba da ci har ta cinye. Shi ma mai shayin ya lura da yadda Nkiru ke cin bredin ya san ba ƙaramin yunwa ta ke ji ba. "Shehi ko za ka ƙarɓo ma ta shinkafa a wajen Maman Chukwudi" T J ya amsa da to. Ya kalli Nkiru ya ce "wait here, i'm coming" Da sauri sauri T J ya wuce shagon Mama Chukwudi da ke sai da abinci a tashar ya karɓo shinkafa da wake da miya har tiriri ta ke saboda ba a jima ma da sauke ta ba, haka ya karɓo yana sauri kamar zai tashi sama. Har a lokacin zuciyarsa na son sanin mi ya samu yarinyar nan cikin 'yan kwanaki uku kacal ta lalace haka. Wannan karan rabin shinkafar Nkiru ta ci ta tura gefe ta ce ta ƙoshi. Ganin ta fara dawowa hayyacinta ya sa T J ya tambayeta sunan ta. "Nkiruka-Mary" "Kiruka?" Nkiru ta girgiza kai ta sake maimaitawa, wannan karan tana stressing N ɗin "NNNkiruka or Nkiru" T J ya ce "Inkiru" Still ba dai dai ba ne amma ta bar shi haka. Ganin ta na kallon sa ya sa shi cewa " My name is Tijjani but people call me T J" Itama ta maimaita T J ɗin da ba za ta iya kiran Tijjani ba. Tambaya na gaba shine miya kawota nan sannan miyasa ta ke son zuwa Calabar. Ba ta san miyasa ta ke jin za ta iya yarda da shi ba, its like there's something in his eyes that is telling her he's honest trust him. A taƙaice ta bashi labarin yadda aka kashe ma ta iyayenta da kuma yadda wata ƙanwar mahaifin ta ta taimaka ma ta ta gudu. Ya tambayeta ko ta taɓa zuwa Calabar ta ce ma sa a'a. A zuciyar sa yana faɗin lallai akwai matsala. "Kin san gidan ku na Owerri?" Nan ma ta amsa da a'a, kusan komai ya tambaya sai ta ce a'a. Ya ce "tirƙashi ashe kai kifin rijiya ne" " what?" "I mean what are you going to do?" "I dont know, i want to look for my maternal grandparents but i dont know how" Kafin yai magana ya ji ana ƙwalla ma sa kira. "Ɗan Fillo mota za ta tashi ka matso kusa" Ya amsa da to. Ya kalli Nkiru ya ce mata zai tafi, nan da nan idon ta su ka ciko da hawaye. Ya fito da kuɗi a aljihunsa ya miƙa ma ta ya ce ta je tasha ta nemi motan Calabar kuma ta sayi takalmi. "Take me with you" ta faɗa ba tareda ta san dalilin da ya sa ta faɗi hakan ba. A hankali ya fara ma ta bayanin cewa shi ba ɗan nan ba ne kuma garin su akwai nisa. "Ɗan Fillo" aka sake kira Ya miƙe tsaye yana jin zuciyar sa na ma sa nauyi. "Nice meeting you Inkiru-Mary, and goodluck" ya faɗa a hankali sannan ya juya ga Malam Idi ya ce "Malam Idi zan wuce, idan ba damuwa ka yiwa yarinyar nan kwatancen inda za ta samu motar Kalaba" Malam Idi ya ce to tareda ma sa addu'ar Allah ya tsare. A hankali ya ke tafiya saboda tsananin tausayin Nkiru da ya ke ji ya kashe ma sa jiki, fatan sa Allah ya sa ta samu kakannin ta idan ta je Calabar. Wani zuciya na raya ma sa ya fasa tafiya ya raka Nkiru zuwa Calabar, to amma idan bai tafi yau ba sai wani sati domin ba koyaushe ake samun motar Kano ba. sannan idan bai tafin ba zai rasa bikin ƙannen sa da za ayi ranan Jummu'a ya kama saura kwana huɗu kenan. Da Eze bai riga ya tafi na su ƙauyen ba a chan Nsukka da ya haɗata da Eze ya rakata. Haka dai yaita tunani har ya kai wajen trailer ɗin, har dreban ma ya tada motar. Ya buɗe gidan gaba zai shiga sai ya juya ya hango Nkiru tana tahowa wajen da sauri. Murmushi yai ya ɗaga ma ta hannu ɗaya, yana ganin sanda hawaye ya zuba a idonta ta sa hannu ta fara sharewa. Yai saurin shigewa cikin motar dan kada shima ya fara hawayen. Yana shiga mota ta tashi, Dreba da yaron motan sa guda ɗaya su ka fara tsokanan T J. Su uku ne a gaba yayinda bayan aka cikata da jarakunan manja ciki harda jarka guda biyu na T J wanda ya rubuta sunan sa saboda shaidah. Jakar Ghana-must-go guda biyu ya ɗauka wanda ɗaya kayan sa ne aciki da littattafai sai ɗaya Jakar ta tsaraba ce. Ko kalma ɗaya bai faɗi ba, idanun sa na kan side mirror yana hango Nkiru tsaye tana kuka, bayan sun ma ta nisa ya dena hangota ya sunkuyar da kansa yana lissafin abubuwa a ransa. Ƙarshe dai answer ɗaya ya samowa kansa ita ce kawai mafita, ita ce kawai zai yi ya ji hankalin sa ya kwanta. Duk da wannan mafitar za ta zo da ƙalubale amma a hakan gara ya san ya taimakawa wannan yarinya da ya barta ba tareda ya san halin da za ta shiga ba. "Dreba ki tsaya" ya faɗa lokacin da ya ɗago kan sa. Har yau dai a mafiya yawancin lokuta idan zai yi Hausa yana maida mace namiji ya maida namiji mace. Shi idan ba karatun da yai a Zaria ba da ba zai ji Hausa har haka ba. A gidan su jefi-jefi ake Hausa amma Fulatanci kawai su ka sani, shi kuma ya bi harshen su. "Zamu tafi da wancan yarinyar" ya faɗa lokacin da ya ga Dreban bai da niyyar tsayawa. Da Dreban da Yaronsa suka sa T J a gaba da faɗa suna gaya ma sa illar abinda yake da niyyar yi. T J ya nuna koya nene zai tafi da Nkiru idan ya so idan ya dawo dan ya ƙarisa watanni huɗu da ya rage ma sa a garin sai ya raka Nkiru zuwa Calabar ya sa da ta da 'yan uwan Mahaifiyarta. Da Dreba da Yaronsa dukkan su Hausawa ne sai su ke ganin wautar T J ɗan Fulani. Ƙarshe da su ka ga ya dage sai su ka barshi amma da sharaɗin T J zai biya ma ta kuɗin mota duk da kuwa shi T J ɗin alfarma aka ɗauke shi. T J ya ce ya amince. Yana saukowa daga trela ɗin gudu ya fara yana fata ba ta bar tashar ba. A wajen da ya barta tsaye lokacin da zai shiga motar a nan ya ganta tsaye tana hawaye yayinda wata mata ke tsaye kusa da ita tana ma ta magana. Tunda ya ganta kuwa yai Hamdala a ransa ya ƙara gudu. Ɗago idon da za ta yi ta hangoshi yana gudu nan ta kama murmushi. Har T J ya iso ba ta dena murmushi ba, matar ganin tana murmushi ita ɗaya ya sa ta ja tsaki ta wuce dan acewarta Nkiru mahaukaciya ce. Yana haki yana tambayarta ko za ta bishi garin su idan ya so sai su dawo tare ya rakata har Calabar. Ta gyaɗa kai. Ya duƙa ya fara cire takalmin sa tareda socks ɗin. Da ya gama cirewa ya ce ta sa, ta kalli cikin idon sa cike da mamaki, ya gyaɗa ma ta kai yana murmushi. Jiki na rawa ta fara saka socks ɗin wanda sai alokacin ta ga yadda ƙafarta ya ɓaci, ta gama ta sa takalmin wanda ba dan socks da kuma ɗaurewa da ta yi tamtam ba da haka ƙafar za ta yi ta lilo a ciki, T J dogo ne sosai gashi siriri ita kuma duk da ta ɗan fishi faɗin ƙafa amma ba ta kai shi tsayin ƙafa ba. Jacket ɗin sa ya ba ta ta sa sannan ya ce su tafi. Da gudu-gudu sauri-sauri su ka kai wajen da motar ta ke, ya taimaka ma ta ta hau sannan shima ya shiga. Dreba da yaronsa Ibrahim ba fahimtar turancin ta su ke ba lokacin da ta ke gaishesu. Su pidgin su ke ji ita kuma turanci kamar Sarauniyar Ingila. Ban da gaisuwa kuma ba abinda su ke ji a yaren Igbo. Haka su ka kama doguwar tafiya. Tun ba a kai awa ɗaya da kama hanya ba Nkiru ta sa kan ta a kafaɗar T J ta fara bacci. Dreba ya ce T J ya ma ta magana ta koma kan doguwar kujera da ke bayan su wanda su ka maidata gado. Nkiru ta koma baya ta miƙe jiki sai bacci. Lokaci zuwa lokaci T J yana leƙata ko ta tashi amma ba ta tashi ba. A ƙalla ta kai awa biyar tana bacci kafin ta farka. Haka dai tafiyar ta kasance jefi-jefi T J yana ma ta tambayoyi wanda ta ke amsa ma sa bisa gaskiyarta... Tafiyar ta su ta ƙara daɗewa saboda ɓaci da motar ta yi a hanya, sai da su ka yi kusan awa huɗu su na jira kafin aka gama gyarata. Ba su suka iso Kano ba sai Ƙarfe takwas na safiyan washegari. Kafin T J ya samu ya haɗa kan kayan sa ma sai da su ka kai wajen ƙarfe shaɗaya. Daga nan ya nema mu su Bus da za ta kai su garin su wato Ringim wacce lokacin ke haɗe da Kano saboda ba a raba Jigawa da Kano ba... Abu uku ya gaya ma ta wanda ya ce ta riƙe su da kyau, idan ta yi haka har su dawo ba za ta samu damuwa ba. "Gidan mu musulmai ne kuma Fulani ke kuma Christian ce 'yar ƙabilar Igbo. Ba kowa ne mai sauƙin kai kamar ni ba dan haka duk abinda za a miki na nuna ƙyama ko wariya ka da ki bari ya ɗaga miki hankali. Na biyu kuma iyayena da mafiya yawanci 'yan uwana ba su yi Boko ba dan haka ba sa jin turanci, kusan maganar kurame za a dinga yi idan ba na kusa da zan fassara miki ko kuma wanda su ke ji ɗin ba sa kusa. Na uku kuma za ki yi haƙuri da yanayin gidan mu, gidan mu gidan yawa ne kuma ba gida ne irin wanda ki ka taso ba, ina fata yadda kika lallaɓa da zaman ƙauyen mahaifin ki za ki lallaɓa da zaman gidan mu" "Thank you. You are truly a good man" abinda ta faɗa ma sa kenan lokacin da ya gama ma ta bayani... *** Bayan Isha su ka isa daidai ƙofar gidan su T J, mai mota ya fitar mu su da kaya sannan ya ƙara gaba. Tun da yaran da ke ƙofar gida su ka ƙyalla ido su ka gan shi su ka fara ihu suna kiran "Hamma Tijjani wartoyi, Hamma wartoyi" su ka yo kan shi da gudu, ya ɗauki ƙaramin cikin su yana cillashi yaron na ta dariya. Cikin gidan su ka shiga nan ma dai ihun murna ake yi, tunda ya tafi bautar ƙasa wannan ne karon farko da ya zo gida. Nkiru dai bin bayan sa kawai ta ke yi tana mamakin yaran, ita tun a hanya ta ke mamakin ƙasar Hausa. Magana yai da wata mace da Fulatanci sannan ya juyo ya kalli Nkiru ya ce ta bi ƙamwarsa za ta kai ta ɗaki. Yarinyar da ba za ta wuce shekara bakwai zuwa takwas ba ta jagoranceta har wani ɗaki, ganin yarinyar ta cire takalmi ya sa Nkiru ma ta cire takalmin T J ta shigo ɗakin wanda ke wadace da hasken lantarki saboda akwai wuta a lokacin. Tun kafin ta shigo yarinyar ta soma yiwa tsohuwar da ke zaune akan sallaya bayanin abinda T J ya ce ma ta. "Maraba da zuwa" tsohuwar ta faɗa tana kallon Nkiru. "Goggo ba ta jin Hausa fa" Goggo ta ce "tooo" Ta yiwa Nkiru nuni da ta zauna a kan kujeran da ke ɗakin. Nkiru ta zauna tana sauke ajiyar zuciya akai akai... Bayan ya rabu da yaran ne ya shiga wajen mahaifiyar sa Iya ya gaisheta sannan ya wuce ɗakin kakar sa ita ma ya gaisheta kafin ya dawo ɗakin Goggo wacce har lokacin tana lazimi. A gabanta ya duƙa ya gaisheta ta amsa cike da farin ciki. T J ya tambayeta ko Baffa na ɗaki ta ce da alama bai dawo ba tunda ya tafi sallah. Cikin yaren fillanci ya fara ma ta bayani akan Nkiru da kuma dalilin kawota nan. Ya sani ko da sauran 'yan uwan sa ba za su fahimceshi ba to Baffa da Goggo za su fahimce shi. Bayan ya gama bayani Goggo ta ɗaga ido ta kalli inda Nkiru ke zaune ashe ta yi bacci. Ta kalli T J ta ce "ba ni da matsala da zamanta a nan gidan amma ka san ko za ta zauna sai da yardar Baffan ku sannan za ka sha magana a wajen Iya sai dai ka yi haƙuri" T J ya ce "na sani kuma zan amince da duk hukuncin da Baffa zai yanke, idan ma bai amince ba zan yiwa abokina Okafor magana ta zauna a gidan su" Goggo ta ce " Allah ya taimaka, ka duba ɗakin na sa ko ya dawo" T J ya amsa da amin tareda miƙewa tsaye yana stretching hannayensa da su ka yi tsami. "Zan sa a sa muku ruwan zafi da za ku yi wanka saboda jiki ya warware" T J ya ma ta godiya sannan ya fita, kai tsaye ɗakin Baffan sa ya nufa ya kuwa ci sa'a ya dawo. Ya ma buɗe kwanon tuwo kenan zai fara ci T J yai sallama. Ba ƙaramin farinciki Baffa Habubakar ya ji ba ganin ɗan na sa wanda tun da ya tunkaro gidan yara su ka tareshi a hanya su na gaya ma sa Hamma Tijjani ya dawo. Dan haka da farin ciki ya shiga gidan. Suna gaisawa ya ce T J ya wanke hannu su ci abinci ba mu su T J ya wanke hannu duk da ba yunwa ya ke ji ba dan ya siya musu Gurasa da nama sun ci a hanya. Tare su ka cinye abinci sannan aka shiga hira yaushe rabo, daga baya T J ya bayyanawa Baffansa duk abinda ake ciki, ba abinda ya rage ma sa gameda labarin da Nkiru ta gaya ma sa. Shiru Baffa yai bayan ya gama bayanin yana tunani kusan minti biyar yana nazari kafin yace " Ba zan ce ka kyauta ba ba zan kuma ce ba ka kyauta ba amma abu ɗaya na sani shine duk abinda ka yi ka yi shi ne da kyakykyawar niyya. Kasancewar ta kafira ba zai sa mu ƙyamaceta ba, dan haka za ta zauna har zuwa lokacin da za ka koma ɗin. Allah ya shige mana gaba amma..." Bayan T J ya baro ɗakin Baffa ɗakin Goggo ya wuce, Goggo da Asma'u sun rasa yadda za su yiwa Nkiru bayani ta je ta yi wanka sai indiya indiya su ke, ita kuma ta baza ido tana son gane abinda su ke nufi. Da ta ga Asma'u na cuccuɗa jiki sai ta gane wanka su ke nufi, ta fara faɗa mu su idan ta yi wanka ba ta da wani kayan da za ta sa amma ba su gane ba. Da T J ya shigo sai ya zauna ya zama interpreter tsakanin su. Bayan ya ji bayanin Nkiru ne ya sanar da Goggo akan zai fita ya siyo ma ta kaya kafin ta yi wankan. "Haba Shehu, daga zuwa sai fita dan kayan da za ta sa yanzu kam ai akwai shi" Ta je ta ɗauko ma sa riga da zani cikin kayan da ta yi sallar Azumi da shi sau ɗaya ta saka ba ta kuma sa shi ba. T J ya karɓa ya miƙawa Nkiru ya ma ta bayani ta amsa tareda godiya. Ta bi bayan Asma'u su ka fita. Wanka ta yi da sabulu zalla ta cuɗa jikinta sosai, ita kan ta ta san ba ƙaramin datti ta yi ba. Ta so wanke gashinta amma tana ganin babu shampoo sannan ruwan ba zai isa ba. Ruwan kuwa da zafi sosai dan haka ta ji daɗin yadda ya ratsa jikinta sosai. Da ke Goggo ba ta da jiki rigan Goggo da ƙyar ya shigi Nkiru dan ma wai ɗinkin zamanin da ne wanda ake yinsa da ɗan faɗi ba kamar na zamanin yanzu da ake yin fitted ba. Ta ɗaura zani ta fito bayan ta naɗe pyjamas ɗin da ke jikinta da. Har lokacin T J na ɗaki su na hira da Goggo haka ta shigo tana ɗari-ɗari ta so manta ɗakin ma albarkacin takalmin T J da ta gani ne ya sa ta gane ɗakin. Sun riga sun yi magana da Baffa akan za ta zauna ɗakin Goggo dan nan ne ba za ta samu takura ba. T J yai wa Nkiru bayanin za ta dinga kwana a ɗakin Goggo ya kuma jaddada ma ta Goggo ba ta da matsala ba za ta samu damuwa ba, ya kuma nuna ma ta inda Goggo ke sallah ya ce ma ta private space ɗin Goggo ne inda ta ke Ibadah dan haka kar ta je ta wajen. Nkiru ta gyaɗa ma sa kai. Sai da zai tafi ya tambayeta ko tana jin yunwa ta ce a'a. Bayan ya tabbatar ba ta da matsala sannan ya fita. A ƙasa aka ma ta shumfuɗi ta kwanta, a nan Asma'u ke kwana amma Asma'un za ta kwanta a kan gado tareda Goggo. Allah Sarki Nkiru na kwantawa ko minti goma bai kai ba ta fara bacci har da minshari. Da ke ba Goggo ke da girki ba bayan ta gama abubuwanta ta rufe ɗaki ta kwanta kusa da Asma'u da itama tuni ta yi bacci. Addu'an ta Allah ya sa kar zaman Nkiru ya jawo matsala a gidan. Zuwa washegari duk girman gidan ya ɗauka da zancen Hamma Tijjani ya dawo da wata Arniya kuma Inyamura... *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* *Free page* *4-i'm not leaving* Anyi biki lafiya ankai yara ɗakunan su. A sashen Baffa Abubakar kam duk yaran sa mata ya aurar. Dama Murjanatu kaɗai ta rage kuma anyi tareda wasu 'yan uwanta biyu, yanzu saura auren Tijjani da Muntari. Har gara Muntari da alamu yana da niyyar yi nan kusa amma T J kam tunda ya fara Jami'a baya so a ma sa maganar aure. Ba wai ya girma sosai ba ne dan shekarun sa ashirin da uku amma kasancewar yawancin samarin familyn na su daga shatakwas, ishirin zuwa ishirin da ɗaya za ka ga sun yi aure. Mata kuma a ta girma dayawa agida shine shekara shashida. Yau ta ke Christmas, duk da mabiya addinin Christianity ba su da yawa a garin hakan bai hana anƙi yin hidima ba. Iyalai da su ke celebrating wannan rana tun da dare ake ta murna ana ta shirye-shirye. A jiya da daren ne T J ya kawowa Nkiru kyautar ta ya ce ka da ta buɗe sai safiyar christmas. With full excitement ta kwana tana tararradin mi T J ya siya ma ta. Da safe kuwa tana tashi gift ɗin ta buɗe da mamakin ta sai ga Bibble sai kuma ɗan ƙaramin box wanda ke ɗauke da ɗan kunne da sarƙa. Ta fara shafa sarƙan tana murmushi lokaci guda kuma ta tuna da iyayenta. Ta tuna yadda su ka celebrating christmas ɗin su last year, ta tuna yadda su ka decorating christmas tree ɗin su. Ta goge hawaye tana fata Daddy and Mommy su na heaven su na kula da ita shiyasa su ka turo ma ta mutumin kirki ya taimaka ma ta. Bayan ta yi wanka ta shirya cikin atamfar da T J ya siya ma ta wanda jiya aka karɓo ma ta ɗinkin. Ta sa kayan riga da skirt amma ta ka sa ɗaura ɗankwalin duk yadda ta ɗaura sai ta ga bai ma ta ba. Tana ganin Pendo na ɗaurawa amma ba ta ɗauka da wuya haka na. Ta san balbalin su Pendo amma ba ta son zuwa saboda Innar Pendo ba ta son ganinta, da sun zo da Pendo za ta fara yare tana tofe tofen yawu kamar ƙyamar Nkirun ta ke. Tana haka sai ga T J ya shigo ɗakin da sallama. Goggo ba ta ɗakin Asma'u kuma ta je wanka. Tsayawa yai yana kallonta yadda ta yi kyau cikin kayan Hausawa. "Thank you Teejay, i like the gift" Ta faɗa bayan sun gaisa. Tambayarta yai ko ta shirya ta ce ta shirya amma ta kasa ɗaura ɗankwali ko ta barshi a gida ne. Ya ce a'a bari ya kira ma ta Pendo. Ya fita da sauri. Shi da Pendo su ka dawo yana tsaye har Pendo ta ɗaura ma ta ɗankwali sai gashi ta dawo Bahaushiya sak, kayan sun sake fidda kyan ta. Ta ɗau Bibble ɗin da ya ba ta su ka fita. Wannan ne karonta na farko da ta fita daga gidan har anguwar ma, suna tafiya T J na ma ta bayanin yanayin zamantakewar 'yan garin. Gidan su abokin sa Okafor su ka je, sun ma shirya dama shi su ke jira. Bayan ya gaisa da Papa da Mama Okafor sannan ya damƙawa Okafor amanar Nkiru yana jan kunnen sa akan ka da ya bari wani abu ya sameta. Okafor yai dariya ya ce ai Nkiru ƙanwar sa ce ba zai bari wani abu ya sameta ba. Yana tsaye su ka wuce church dan gudanar da bauta a safiyar ranar christmas. Sai da ya ga sun ƙule ma sa kafin ya bar wajen yana jin kamar ya bi su church ɗin. Shiru-shiru yana ta tsumayin dawowar Nkiru amma shiru har yamma lis babu alamun ta hakan ya sa ƙarfe shida na yi ya wuce gidan su Okafor. Yana zuwa ya samu Iyayen Okafor da ƙannen sa amma babu Okafor da Nkiru. Wai ba su dawo daga church ba, hankalinsa ya tashi wani irin church ne tun safe har dare. Ya bar gidan ransa a ɓace ba tareda ya mu su sallama ba. Ya san church ɗin ai, zai je koma miye ne ya ga ni. Sai dai ko da ya je an tashi, church ɗin ma a kulle ya ke. Kan sa wani juyawa yai ya fara jin wani jiri-jiri. Ba abunda ya hango irin hoton Okafor da Nkiru tsaye ana ɗaura mu su aure gashi har Okafor ya sa ma ta zobe. Bai san ya aka yi ya bar church ɗin ba ya dawo gida, da ƙyar ya je yai sallar Magariba, da ya dawo ya sake leƙa ɗakin Goggo amma su ka ce ba ta dawo ba. Ya fito ƙofar gida yana dakon dawowanta lokaci zuwa lokaci yana duba agogo. Bayan ya dawo daga sallar Isha ne da ya leƙa ɗakin ya ganta zaune tana naɗe kayan da ta cire. Tsabar yadda zuciyarsa ke tafarfasa ya rasa ma mi zai ce ma ta. Ga shi fiskarta ko alamun ta damu da daɗewar da ta yi bai ba. "Nan gaba ki dinga dawowa da wuri" ya faɗa yana danne ɓacin ran sa. Ta fara ma sa bayanin dalilin da ya sa ba ta dawo da wuri ba. Pastor ne ya buƙaci ganinta shine Okafor ya kaita gidan sa bayan an tashi daga church to shine bayan sun ci abinci ya tambayi labarinta ta gaya ma sa shine yai ma ta addu'a tareda cewa ta dawo gidan sa da zama ko kuma gidan su Okafor saboda za ta fi samun nitsuwar yin Bauta. Tunda ta fara bayani ya ke kallon ta yana jin wani fargaba na taso ma sa musamman ma da ya tuna hasashen da yai ɗazu. Bai ce komai ba ya tashi ya fita ba tareda ya ji ƙarashen bayanin ba. Ta ɗauka abu zai je ya yi ya dawo amma har ta yi bacci bai dawo ba. Washegari da ya zo ya gaishe da Goggo ba ta tashi ba saboda gajiya sai kusan ƙarfe takwas ta tashi. Wasa-wasa har rana ba ta ga ko ƙeyar T J ba. Muntari ne ya shigo ya ma ta sallama akan zai wuce Kano, sai da ta sha dariya sosai saboda turancin sa. Shi kuwa ganin tana dariya sai ya dage yana ta zuba labari. Da zai tafi har da ma ta alƙawarin zai dinga zuwa duk sati yana dubata, shi da ya ke tafiya yai wata ɗaya biyu bai leƙo gida ba amma yanzu wai zai dinga zuwa duk sati. Yammacin ranan Okafor ya zo gida ya aiko aka kirata. Gidan pastor su ka je, wannan karan ma ƙoƙarin convincing ɗin ta su ke akan ta bar gidan su T J amma ta ƙi cewa ta yi idan ta bar gidan su T J ba ta mu su adalci ba. Su kuwa su Pastor sanin gidan ne ya sa su ke tsoron zamanta a gidan musamman saboda sashin Modibbo da ta ke zaune. Zamanin Modibbo anyi babban malami, 'yan uwansa kaf ɗin su kiwo da noma su ka ba wa muhimmanci amma shi karatun addini yai mai zurfi shiyasa ma ake kiransa da Modibbon saboda malami ne masani sosai akan addini. A zamanin sa ya yi sanadiyar musuluntar da mutum tara. Tsoron su kar zaman Nkiru a gidan ya sa ta musulunta duk da kuwa yanzu babu Modibbo a gidan. Ita dai duk yadda su ka yi da ita ta ƙi, ƙarshe su ka fito ma ta da wani salo akan ta dinga zuwa tana yini da su saboda su san juna sosai. Ba tareda ta kawo komai ba ta amince da hakan. Da za su tafi Pastor ya ja Okafor gefe ya ƙara jaddada ma sa akan maganar su ta jiya. Ƙarfe tara ya wuce lokacin da su ka iso ƙofar gidan. Hamma Tijjani na cikin wasu abokanan sa ana hira amma shi hankalinsa na kan hanya yana baza ido ya ga dawowar Nkiru, ya ga fitan su ɗazu da ya ke dawowa daga masallaci. Hango su da yai ya sa shi tashi ya shige gida. Baccin kirki bai iyayi ba, yana so yai baccin ko dan ya samu sauƙin abinda ke damunsa amma ya ka sa. Yana son mata magana amma bai san mi zai ce ba, duk yadda ya juya abun shine bai da gaskiya Nkiru na da daman komawa gidan su Okafor saboda ɗan uwanta christain ne kuma yaren su ɗaya duk da sun zo daga gari mabanbanta. Amma kuma bai yarda da Okafor ba, to miye na shi a ciki tunda ita ta zaɓe shi sama da shi. Haka dai yai ta tunani kala-kala har daga baya bacci ya sace shi. Washe gari da ya shigo gaishe da Goggo ne Nkiru ta tambayeshi ina ya je jiya bai leƙo ta ba. Wani kallo ya watsa ma ta sannan ya tashi ya fita. Jikinta yai sanyi ta lura kwana biyun nan baya kulata amma ta rasa dalili. Ƙarshe ta fara zargin ko ya fara gajiya da ɗawainiyar da ya ke ma ta ne, sai kuma ta yi saurin kauda zancen da cewa Teejay ba zai yi ma ta haka ba. Da rana ya dawo daga sallar Azahar ya shigo ɗakin Goggo ta ce ma sa Pendo da Nkiru sun fita za ta raka Nkirun kitso. Ba su gama zancen ba sai ga Pendo ta shigo ɗakin. Ganin ita ɗaya ne ba Nkiru ya sa T J tambayarta ina ta bar Nkirun. Pendo ta ce ma sa sun je gidan kitson ne matar ta ce ba za ta yiwa Arniya kitso ba, wai ance idan ka yiwa Arniya kitso kana da zunubi. T J girgiza kai da jin jahilcin mutanen na sa. Ya ce "sai ki ka bar ta a ina?" "Mun kusa isowa gida ne mu ka haɗu da abokin ka shine ta bishi" "Okafor?" Ya faɗa a fusace Ta gyaɗa ma sa kai. Da sauri ya fice ɗakin Goggo da Pendo su ka bi shi da ido. Sai da yai tafiya mai nisa kafin ya tsaya. Zuciyar sa ce ta faɗa ma sa babu amfanin zuwa gidan su Okafor, Nkiru da kan ta ta bishi miye na shi a ciki, idan ma gaba ɗaya za ta koma chan kaman yadda Pastor ɗin su ya buƙata ai ba matsala ba ne. Haka ya juya ya koma gida zuciyar sa na tafarfasa. Ranan ma dai bai sake kulata ba, sai dai duk da haka hankalinsa bai kwanta ba sai da ya ga ta dawo gida kusan ƙarfe biyar na yamma. Da safe da ya shigo ma tana gaishe shi haka ya amsa ko kallon ta bai yi ba. Goggo tana lura da shi kwana biyun nan yadda ya ke share Nkiru. Ba ta dai ma sa magana ba ne amma yau kam ta kasa yin shiru. "Barkindo yarinyar nan ta ma ka laifi ne?" Duk da ya san wa ta ke magana akai amma ya dake ya ce "wa ce yarinya kenan?" "Ungo na ka Barkindo" Yai dariya ya ce "Goggoji na cewa ki ka yi yarinya, zai iya zama Asma'u, Pendo, Kulu, Hadiza... kai yara mata a gidan nan ai dayawa" Ganin ya raina ma ta hankali ya sa ta ce "koma wacece dai abu ɗaya zan gaya ma ka. Ka ga kai ka kawota garin nan kuma a duk faɗin garin nan babu wanda ta yarda da shi sama da kai. Idan har za ka dinga nuna ma ta fushi ba tareda ka sanar da ita laifin da ta yi ba za ka sa yarinyar ta tsaneka. Kwana biyun nan kullum sai ta yi kuka ko mi ya ke damunta na san ya na da alaƙa da kai. Idan laifi ta yi ka gaya ma ta sai ta gyara amma sai ka shigo min ɗaki kana ta kumbure-kumbure, ba abinda hakan zai haifar" "Ni ba na fushi da kowa" "Tashi ka bani waje, Ja'iri" T J ya fita yana dariya. Tana ganin ya fita ta fara matsa ƙwallan da ya taru ma ta. Miyasa ita kaɗai ne ya ke ɗaurewa fuska? Rabon da ya ma ta murmushi tun ranan christmas... *** "Asma'u tashi ki kai wa Hamma ki ce ya zo ya tambayi boɗɗiyon sa ko za ta sha furan na ga sai kallona ta ke lokacin da na ke damawa" Yarinyar ta tashi tana ɗan kumburi dan ba a fara bata na ta ba sai na Hamma Tijjani ta ɗau ƙwaryan ta fice da sauri. Ba ta jima ba ta dawo da ƙwaryan wai ba ya ɗaki. Asma'u ta ɗau na ta ta fara sha. Goggo ta miƙawa Nkiru nono da fura wanda tunda ta fara damawa ta zuba ido tana kallon duk wani motsinta. Suna sha Goggo ta tsinkayi muryan T J yana yiwa kakar sa Yawuro tsiya. Maganar aure ta ke masa shi kuwa ya dage ita zai aura. "Maza tashi ki kai ma sa ya dawo" "Assalamu Alaikum, ga ni nan a bani rabona" Ta ce an duba shi ɗazu baya ɗaki. "Asma'u tashi ki kai ma sa" "Batta tasha a hankali, Nkiru za ta kawo min" Yai wa Nkiru magana akan ta ɗauka ma sa kindirmon. Ta tashi da sauri ta ɗauka ta bi bayan sa. Tana ajiye ƙwaryan ya kira sunan ta a hankali "Inkiru" ta ɗaga jajayen idonta ta kalle shi. "Will you like to taste it?" Ta gyaɗa ma sa kai da sauri Ya buɗe ƙwaryan ya ɗau ludayin da aka ɗaura a kai ya ɗebo kaɗan ya kai saitin bakinta. Ganin ta tsaya tana kallon sa ne ya sa shi gyaɗa ma ta kai hakan ya sa ta buɗe bakinta ta ɗan kurɓi furan. "You like it?" "Its sugary" ta faɗa tana murmushi "Bafulatanin kenan" ya faɗa yana murmushi shima Sauran na ludayin ya kai bakinsa ya shanye, ya sake ɗebo wani wannan karan sai da ya sha ya rage sannan ya miƙa ma ta ta sha. A haka a haka har su ka shanye furan ba tareda wani ya yi magana ba. Ta ji daɗin furan duk da ma sugar ɗin ciki ya yi yawa. Gefen bakinta akwai sauran furan dan haka ya sa babbar yatsar sa ya share ma ta. Shi kan sa bai san ya aka yi ya yi hakan ba. Its like tunda ya haɗu da yarinyar nan akwai wasu notinan kansa da su ka kunce. Ranan da ya fara ganin ta tana rawa a daren ranan sai da yai mafarkin ta, abun ya bashi mamaki sosai. Tunda ya ke bai taɓa sa wata mace a rai har ya yi mafarkinta ba. Lokacin yana undergraduate akwai wata Helen 'yar Auchi, haka ta nace ma sa wai tana son shi, bai taɓa jin wani abu gameda ita makamancin wanda ya ke ji yanzu ba, ya zo ajin ƙarshe ma ya taimakawa wata yarinya Hamdiyya 'yar Bauchi itama ta zo ta fara liƙe ma sa wai su yi soyayya. Shi tun da ma da yanzu mata ba sa gaban sa amma Nkiru is different. Ya rasa ko tausayinta da ya ke ne ya jawo ya ke jin abinda ya ke ji gameda ita oho. Itakam tunda ta ji yatsar sa a daidai bakinta ta sandare a wajen. Tunaninta kissing ɗin ta zai yi, there's something in his eyes that's so inviting. "Saura kwana goma na koma Obowo, fatan kin shirya" ya katse shirun na su "Mmm" kawai ta ce "Ko kin fasa tafiya ne? za ki koma wajen Okafor, probably ki raising family da shi?" "No" ta faɗa da ƙarfi tana zaro ido "Then why Inkiru? Miyasa ki ke zuwa gun sa kullum ki daɗe, kin san yadda na ke ji kuwa idan na zo na samu kin fita?" Ta girgiza kai "Ina tsoro kar wani abu ya sameki Inkiru, ba zan taɓa yafewa kai na ba. Ban ce kar ki je gidan su Okafor ba ko kar ki je wajen Pastor amma..." ganin hawaye a idonta ya sa shi kasa ƙarisa maganar. Sai yanzu ta gane miyasa ya ke fushi da ita ashe saboda fitan da ta ke yi ne. "I'm sorry" ta faɗa in between tears. "Ba na son kuka kin ji" ta gyaɗa kai tana share hawayen... Daga ranan su ka shirya kamar da, sai dai kuma daga ranan Nkiru ta shiga wani hali na fargaba. Ba komai ba ne face tafiyar su da ta ke matsowa kusa, daga ta tafi shikenan ba za ta sake ganin T J ba. Maimakon fitan da su ke da Okafor yanzu da shi su ke fita yai ta nuna ma ta wajaje musamman gonakin su. Har gidan gonan Alhaji Isa sai da ya kaita a nan ta ga yadda ake matsar madaran shanu itama ta gwada matsawa. Ranan sunday kuwa shi ya raka ta har bakin church bayan awa uku ya dawo daidai an fara fitowa kenan, suna fitowa kuwa ta hangoshi, ko sauraron Okafor ba ta yi ba ta je ta sameshi su ka wuce gida. Da yamma sai ga Muntari ya dira a gidan abun mamaki ko ɗakin Iya bai shiga ba ya wuce ɗakin Goggo. Yana zuwa kuwa jiki har rawa ya ke sanda ya ke kunce jakar sa. Tsarabar Gurasa, kilishi da dabino yai wa Nkiru wacce tun randa ya bar garin ta ke ran sa. Goggo ta ce "ikon Allah" ganin yadda Muntarin ke ta rawan jiki a gaban Nkiru. Ba ta ida mamaki ba sai da ta ga ya yagi kilishi yana ƙoƙarin turawa Nkiru a baki yana cewa ta ci ita kuwa tana girgiza kai. "Muntari ba na tunanin ka yi sallar la'asar, ka wuce masallaci ko raka'a ɗaya ka samu" Ya miƙe yana cewa "kar wanda ya taɓa kayan nan na Mary ne, ita kaɗai na yiwa tsaraba" Goggo ta ce ta ji. Bayan fitar sa Goggo ta sauke ajiyar zuciya tana fatan abinda ta ke tunani ba gaskiya ba ne... Daga masallaci kuwa ya dawo zai shiga ɗakin Goggo, Iya ta ƙwala ma sa kira. Bai sake samun sarari ba sai chan dare. Yana shigowa ya ga T J a ɗakin, ya yi narai narai da fiska yana tambayar Nkiru ko ta ci abinda ya kawo ma ta ta ce ta ci. Ba ta ma ci ba sai da T J ya zo ta nuna ma sa ya ɗau kusan fiye da rabi ya ba wa Goggo ya ce a rabawa 'yan gida. Nkiru kam dabino kaɗai ta ci ba ta ci kilishi da gurasan ba. Shi kuwa T J haka ya haɗa gurasa da kilishi yai ta ci yana addu'ar Allah ya saka wa Muntari, wannan karan yayi abun kai. "Hamma ina son magana da ita" T J ya juya ya kalli kan gado Asma'u ta riga ta yi bacci Goggo kuwa ta wuce turakar miji saboda ita ke da girki. "Ban gane ba" "Ina son magana da Mary" Abun ya bashi dariya amma ya dake ya ce "ga ta nan faɗi maganar ka" "Hamma waje za ka bamu, maganar ta mu biyu ne" T J ya ce " lallai kana da aiki" Ya cigaba da koyawa Nkiru gaisuwar Fulatanci. Ganin an maidashi wani shashasha ya sa shi barin ɗakin kamar zai fashe. T J bai kawo komai a ransa ba dan ya ɗauka irin shiriritan ƙanin na sa ne da ya saba. Sai kusan goma ya bar ɗakin... Washe gari aka yiwa su T J rasuwa dan haka ranan kam gaba ɗaya Nkiru ba ta gan shi ba. Duk da ba a na su sashen ba ne amma kusan kaf 'yan gidan sun fita gaisuwa aka bar Nkiru a gida. Ba abinda ke zuciyarta irin tunanin yadda za ta yi ta cigaba da zama a nan ko da dai ba wai kowa ke son ta ba amma T J yana son ta haka Goggo ma na son ta. Idan ta tafi Calabar ta kasa samun kakannin ta fa?. Ko kuma ta je sun mutu ya za ta yi kenan? Wannan tunanin shi ya ɗauke ma ta hankali wunin ranan... *** Jaka ce madaidaiciya ya kawo ma ta ya ce ta shirya kayanta ciki saboda tafiyar su ta jibi. "Ki tabbatar kin shirya komai saboda mantuwa" "I'm not leaving" ta faɗa a hankali. Da sauri ya juyo saboda dama fita zai yi "What?" "I'm not leaving" ta sake maimaitawa wannan karan da ɗan ƙarfi. Dawowa yai gabanta ya tsugunna. Zaune ta ke a shimfiɗar ta da ta ke kwana. Ta girgiza kai ta kasa magana. "Na san kin fara sabawa da nan amma dole ne mu tafi, na yi alkawarin zan maida ke na kai ki har Calabar..." "Idan ba mu same su ba fa? Ina zan je? Chief James Asibong ba shi ɗaya ba ne a Calabar, tukunna which part of Calabar za mu fara zuwa?" Tanada gaskiya amma kuma... "Tunda mu ka haɗu ka ke mun ɗawainiya, kuma ko da mun koma ɗawainiya za ka yi ta yi da ni. Ba na son ka shiga ƙunci saboda ni, ka bari na zauna a nan na nemi aiki idan na tara kuɗi sai na tafi ka ga ko da ban same su ba zan fara sana'a ko kasuwanci da abin da na tara" "Inkiru..." "Shekara ɗaya, biyu, uku, i dont care, indai za ka amince zan zauna a nan. Zan yi kowani irin aiki ne, kowani iri" Shiru yai ya rasa mi zai ce. Ta sa hannunta ɗaya a kan hannun sa da ke kan cinyarsa ta ce "please Barkindo" Ya kalleta cike da mamaki. Ta gyaɗa ma sa kai ta ce Pendo ce ta gaya ma ta Kakansa ne ya ke kiran sa da Barkindo shiyasa wani lokaci ta ke ji Goggo na kiran sa da sunan. Shiru ne ya ratsa ɗakin, ba kuma dan ya rasa abin faɗa ba ne sai dan wani lissafi ya ke yi a ƙwaƙwalwarsa. Mi zai faru idan Nkiru ta cigaba da zama da su? *ba a fara komai a chronicles of Zaytoonah ba* *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *6-A love marriage* Bismillahir Rahmanir Rahim "Yanzu dan Allah Muntari daga ta musulunta yau sai a fara ma ta zancen aure?. Ni ban goyi bayan haka ba, sannan duk yadda ka ke son auren yarinyar nan ba fa auren dole za a ma ta ba. Idan ta amince za ta aureka fani'ima amma idan ta nuna ɗan uwanka ko wani daban ta ke so to ka ga dole ka haƙura" Kaman an buga ma sa guduma a tsakiyar ka haka ya ji kalaman Baffah na ƙarshe a ƙwaƙwalwarsa. "Baffa ban gane ɗan uwana ba. Ba dai Hamma Tijjani ka ke nufi ba?" Baffa yai shiru dan tambayar ta yi kama da renin hankali. "Baffa idan za a min adalci, tun kan yarinyar nan ta musulunta na ce ina son aurenta ku ka hanani, yanzu da ta musulunta sai ku ce wai idan ta zaɓi Hamma Tijjani sai dai na yi haƙuri. Wannan son kai ne Baffah. Kuma ba zan taɓa yarda da ba. Ina son auren Maryam kuma Wallahi babu wanda ya isa ya hanani aurenta." "Muntari ni ka ke faɗawa haka? Wannan yarinya tun kafin ta musulunta na ɗauketa amana a gareni, yanzu da ta shigo musulunci kuwa nauyi ya ƙara ƙaruwa mani, marainiya ce kuma na ɗauki amanar kula da ita kamar 'ya'yan da na haifa. Babu wanda zai ma ta auren dole. Tashi ka bani waje" "Tabbas Biri yayi kama da mutum, na gane manufarku Baffah. Hamma shi ne Shalele ɗan Boko shiyasa za a bashi ita ko?, to wallahi ba zai yiwu ba. Maryam ni ta ke so kuma ni za ta aura" Daga haka ya buga ƙafa ya fita. Baffah ya sauke ajiyar zuciya, wani irin daƙiƙanci ke kan Muntari. Yanzu shi aka ce ya auri Maryam sai ya aura, bayan ga wanda ya kawota. Ko Tijjani bai faɗa ba sun san akwai soyayya a ƙasan ran sa gameda Maryam. Balle ko da ace wani daban ne ya kawo Maryam gidan, sau dubu Tijjani zai zaɓa ma ta saboda shi ne zai iya riƙeta amana ya kuma nutsar da ita bisa tarbiyan musulunci. Shi Muntari da Boko da Arabin duk yayi fatali da su ya shiga gari shi dole yana son yin zaman Birni, yana son yin kuɗi ba ta hanyar noma da kiwo ba. Baffah ya kawar da zancen zucin da ya ke, ya sawa ransa yarinta ke damun Muntari da sannu zai haƙura da Maryam. Washe gari da safe sai ga ɗan aika wai Baffa ya je gidan Alhaji Isa yana neman sa. Baffah ya shirya ya wuce gidan ƙanin mahaifin na sa. Daga zuwa sai ga Muntari zaune gaban Alhajin yana ta rarraba idanu. Baffa ya zauna ya gaida Alhaji amma Muntari yai ƙyam ya ƙi yiwa Baffah magana. "Shaƙiyancinka ya kai ba za ka gaida Uban ka ba Muntari?" Muntari ya haɗe rai ya gaida Baffah sama-sama. Alhaji ya ce " Habubakar ga ɗan ka ya kawo ƙara, wai yana son yarinya kai kuma ka ce a Shehu za ka ba wa. Miye gaskiyar magana?" Takaici ya kama Baffah amma ya daure ya ce " Alhaji yarinyar da ake magana yarinyar da Shehu ya kawo ne kusan shekara ɗaya kenan yanzu, sai jiya Allah ya sa ta amshi musulunci. A nan wajen jiya ka min faɗa akan nauyi da ya ƙaru min na haƙƙin yarinyar da ya hau kai na, saboda ko ba komai Maryam ta zama 'ya ta. Ni ban ce zan ba wa Shehu yarinya ba, na dai ce bai dace daga ta musulunta jiya sai a fara ma ta batun aure ba. Haka nan na jaddada mi shi ba zan ma ta auren dole ba, idan Maryam ba ta son shi dole ya haƙura da ita. Iya abinda mu ka yi da shi jiya kenan" Alhaji ya kalli Muntari ya ce " kai kuma wuyan ka yayi ƙauri har kana yiwa mahaifinka sharri ko?. Za ka zo gaba na ka yi min ƙarya" "Alhaji ni ba ƙarya na yi ba. Baffah baya so na yayi maganar nan ne saboda ba Hamma ba ne. Yasin da Hamma ne ya ce zai auri yarinyar nan da a jiya an ɗaura mu su aure" "Yi min shiru!" Muntari ya haɗiye sauran maganar yana ƙyafƙyafta ido. "Magana ta mutu a nan Muntari. Idan lokaci yayi da za ayiwa Maryam aure za'a nemeka" Muntari ya miƙe fuu ya bar ƙofan gidan. Da Baffah da Alhaji su ka bi bayansa da kallo. Yana zuwa ya kira Nkiru wai ta zo Alhaji Isa na nemanta. Goggo ba ta san miya ke faruwa ba ta ce lafiya? Ya ce ba ruwanta dan itama haushinta ya ke ji, ya san duk yadda aka yi harda sa hannunta a maganar da Baffah yai jiya, dama dole ta goyi bayan Hamma Tijjani tunda ita ta rene shi, tun yana shekara uku ya koma hannunta. Nkiru ta ɗau mayafin da Goggo ta ba ta jiya ta yafa ta bi bayan Muntari. A hanya sai da ya sake tambayarta ko tana son shi ta ce ta yi dariya ta ce tana son shi. Tambaya ne da ya ke ma ta a mafiya yawan lokuta wanda ita kuwa ta ɗauka duk cikin barkwancinsa ne, musamman saboda yanayin turancin da ya ke amfani da shi wajen tambayar. Alhaji da Baffa suna tattaunawa sai ga Muntari ya dawo tareda Maryam. "Kai kuma lafiyan ka?" Baffah ya tambaya tun kafin Alhaji yai magana. Kafin ya amsa Alhaji ya ce " barshi mu ji wani rashin kunyar zai kuma yi" Muntari ya nuna Maryam ya ce " na kawota ne ta faɗa mu ku da bakinta cewa ni ta ke so. Kunga sai a mana aure tunda ba ita da bakinta ta ce tana sona" Baffah dai kunya ya kamashi ya sunkuyar da kai kawai yana yiwa Muntari addu'ar shiriya. "Lallai kam, yanzu dai zamani ya kawo mu ɗan kunyan nan da ake ji ta iyaye ba ajinta yanzu. Allah ya huci ranka Muntari, bari mu ji daga bakin yarinya" Ita dai Maryam na gefe tana ɗan cancankan maganganun su amma ba ta gane inda maganar ta dosa ba dan haryanzu ba wai yaren ya zauna a bakinta ba ne har gara ma Hausa a kan Fulatanci. Alhaji ya ƙwalawa wa su yara da ke wasa a ƙofar gida kira ya ce su shiga gida su kira ma sa Hamza. Hamza ɗan Alhaji Isa ne kuma shima kaman T J yana da son karatu, dan yanzu haka ya ƙare Sakandare School yana son wucewa Jami'a. Ba a jima ba sai ga Hamzan ya fito. Ya rusuna ya gaida Baffah tareda Muntari. Alhaji ya ma sa bayani kan abinda ke faruwa a taƙaice ya ce ya tambayi Maryam ko ita ta ce tana son Muntari da aure. Muntari ya ce " ai ba sai ya fassara mu ku ba nima nan ina jin turancin" Alhaji ya ce " ban sa ka ba" Hamza ya iya turanci ba kaman Muntari da ya ke turancin kame-kame ba. Tunda ya fara bayani Maryam ta fara girgiza kai, sai da ya ma ta tambayar da Alhajin yai ne ta zaro ido ta ce "No" da ɗan ƙarfi Muntari ya ce " No kuma?. Me i say i love you, you you say you love me. For everyday i can ask you, you say you love me harda dariya wallahi" Maryam ta dafa ƙirji dan sai yanzu ta fahimci inda maganar ta dosa. Ta kalli Muntari sannan ta maida duban ta ga Hamza ta ce " i never said i love him. I just said i like him. I like him because his funny" "Banten Uba. Mary kalle ni nan. Ki ji tsoron Allah, afraid of God Maryam. We for come here i say i love you you say you like me. Miye maraban dambe da faɗa?" Alhaji ya ce "Hamza mi ya ke faruwa ne?" Hamza ya fara bayani cewa Maryam cewa ta yi Muntari na burgeta amma ba wai tana son sa ba ne shi kuma ya doge wai cewa ta yi tana son sa. "Muntari ka ji abinda ta ce dan haka tashi ka bamu waje, daga yanzu na kashe maganar" Alhaji yai maganar yana kallon Muntari "Wallahi ba zai yiwu ba. Da like da love duk ɗaya ne, ni na san Goggo ce ta kitsa wannan munafurcin, ita ta hana Maryam ta faɗi abinda ke ranta" Baffah dai ya ka sa magana Alhaji kuma sai ya kama dariya dan buruntsun Muntarin dariya ya bashi. Muntari har da taɓa kafaɗar Maryam ya ce " i love you, you love me we marry. Dont afraid of Goggo ko wasu 'yan baƙin ciki. We marry for love" Idon Maryam har cikowa da hawaye yai saboda yadda Muntari ke maganar yana zare ma ta ido. Ta ce "I'm sorry Muntari but i dont love you, i only like you as a friend" "Friend ɗin uwarki, na ce auren ki zan yi. Marriage" ya ƙarisa maganar yana kamo hannunta. Alhaji ya daka ma sa tsawa akan ya sake ma ta hannu. Sannan ya kalli Hamza ya ce ya cewa Maryam ta koma gida. Har Maryam ta tashi Muntari bai bar masifa ba, har ta fara tafiya Hamza ya sake kiranta. Ta dawo jiki a sanyaye. Ba ta san miyasa Muntari ya misunderstanding maganar ta ba, ko dan baya jin turanci sosai ne? "Tambaya min ita ko tana son auren Shehu Tijjani?" Alhaji ya faɗa fiskar sa ɗaure. "Do you love Tijjani?" Murmushi ne ya suɓuce ma ta, ta yi saurin sa hannu ta tare bakinta, she cant believe she actually blushed a gaban waɗannan manyan mutane. "Do you want to Marry him?" Wannan karan gyalenta ta jawo ta rufa fiskarta da shi tana murmushi zuciyarta na bugawa da ƙarfi ƙarfi. Wannan kaɗai ya isa ya nuna mu su tana son T J amma sai da Alhaji ya sake cewa Hamza ya sake ma ta tambayar dan su na son gane wani abu ne. Ya sake maimaita tambayar wannan karan ta cikin gyalenta ta ɗan leƙo ta ce "Yes" Gaban Muntari ya buga kaman tashin nakiya. Alhaji ya ce "Ka dai ji Shehu Tijjani ta ke so. Dan haka daga nan, daga yanzu magana ta wuce. Idan ba kai butulu ba ne ba Tijjani ba ne ya kawota garin nan?" Muryar sa a raunane ya ce " Allah ya isa, dukkan kun nan kun ci amanata. Kuma fin ƙarfi kuka min amma Maryam ni ta ke so ba Hamma ba. Kuma..." Yadda Alhaji Isa ya haushi da faɗa ne ya sa yai shiru sai ga hawaye na zubo ma sa. An cuce shi, an cuce shi abinda ya sani kenan... Maryam da ta koma gida gaba ɗaya wani shauƙi da kewar T J ta ke yi gashi saura sati ɗaya ya dawo. Da Baffa ya dawo ne ya sanar da Goggo duk abinda ake ciki ita kuma ta ce yai wa Iya magana dan Muntari yana jin maganar Iyan. Sanda Baffah ya samu Iya da maganar ita kuwa ta ƙeƙasa ƙasa ta ce sharri ne ƙila ma Maryam ce ta shanye shi amma ba abinda zai sa Muntari ya ce zai auri Maryam. Abu dai sai gashi gaba ɗaya gida an ɗauki zancen. Shi kuwa Muntari daga ƙofar gidan Alhaji Isa sai gidan Sarki. Ba kunya ba tsoron Allah ya faɗi ƙarya da gaskiya akan abinda ya faru yana kuma so a bi ma sa hakkin sa. Iyalen Modibbo ba bare ba ne a Fada dan haka Sarki ya aika sammaci. Alhaji Isa, Baffah da Baffah Umar da Baffah Jibrillah su suka je amsa kiran Sarki. Ƙara ce dai Muntari ya kawo, nan Sarki ya ji ta bakin Alhaji Isa gameda duk abunda ya ke faruwa. Sarki ya fara yiwa Muntari nasiha akan rashin kunya da yai wa iyayen sa amma Muntari ya ɓare baki ya ce indai a fada ma ba za a masa adalci ba zai kai kotu. Wani dogari ne ya doki bakinsa da dorina sai da gefen bakinsa ya fashe ya sake zuba ma sa a baya. Sarki ya ce ya tsaya haka. Alhaji Isa ya ce idan dai Sarki ya yarda yana so a ɗaura auren Maryam da Tijjani a gaban Muntari saboda a rufe maganar. Fadawa su ka yi na'am da maganar. Nan ta ke Alhaji ya ba da sadaki aka ɗaura auren *Tijjani Abubakar Modibbo Djibo* da kuma Amaryarsa *Maryam Nkiru Uzodinma* Wanda Maimartaba Sarkin Ringim ya zama Waliyyin Amarya shi kuma Alhaji Isa Wakilin Ango. Har aka gama ɗaura auren Muntari bai bar hawaye ba. Shikenan ya rasa Maryam, yarinyar da tunda ya fara ganinta kullum sai yayi mafarkinta, shikenan ya rasa masoyiyar sa. *** Duk bayanin da ake ma ta ba wani ganewa ta ke ba, maganar farko ita ta mamaye ilahirin jikinta wai an ɗaura aurenta da Teejay. Wani farinciki ta ke ji wanda ke ratsa duk wani kafa na jikinta, rabonta da irin farinciki haka tun iyayenta na raye. Auren ya ma ta banbaraƙwai tunda ita ko T J ba sa wajen aka ɗaura auren, sai kuma ta tuna irin auren su kenan ba kaman wanda ta sani da ake yi a church ko kotu ba... Kwanakin da su ka shige ana nutsar da ita gameda addini tareda gyarata da Goggo ta farayi a matsayinta na Amarya. Wasu abubuwan kam tun tana mamakin su har ta dena. Kowa yayi na'am da auren banda Iya wacce ke ganin kamar wata ƙungurman Arniya Bamagujiya aka aurawa Tijjani. Ba ma wannan ba tun da aka yi wannan rikicin da Muntari ya tafi ba a ji ɗuriyar sa ba, ko sallama bai wa Iya ba ya tafi. Baffa kuwa ya ce kar wanda ya ƙara tada zancen abun da ya faru, idan Muntari yayi hankali zai dawo ya nemi gafaran iyayensa bisa wannan tonon asiri da ya mu su. Sati ɗaya ake tunanin T J ya rage ya dawo gida kamar yadda ya sabayi amma bai zo a satin ba. Sai su ka ɗauka sai ƙarshen wata zai zo. Rashin zuwan sa ya sa Amarya Maryam ta ƙara jin wani matsanancin kewar sa daga ƙarshe kuma ta fara fushi da shi. Labarin musuluntar Nkiru ya sa su Okafor da ma church members ɗin su suka shiga alhini, sun je har gida suna neman ta ba su dama su zauna da ita a tattauna amma ta ƙi ba su dama dole haka su ka tafi, gashi ana hutu balle su je su ritsata a makaranta. Yadda dai su ke tsoro tun farko sai da hakan ya faru. Pastor dai gaba ɗaya ya ɗaurawa Okafor laifi dan gani ya ke da bai yi yunƙurin yiwa Nkiru fyaɗe ba da ba za ta guje shi ba ƙarshe har ta zo ta dena zuwa church... Ranan ashirin da tara ga watan october 1986 T J ya dawo gida, tunda ya fara masters program na shi wannan ne karo na farko da yai wata ɗaya ba tareda ya zo gida ba. Hakan ya faru kuwa saboda wani gasan Maths na sakandare schools da ake yi a garin Kaduna wanda aka sa shi cikin Alkalai hakan ya sa gaba ɗaya bai samu ya zo ba. As usual ɗakinsa ya shiga ya ajiye jaka sannan ya wuce ɗakin Goggo, mutum biyu ya gani suna sallah a ɗakin bai tsaya gane waye ba ne saboda babu wuta fitila aka kunna a ɗakin, kai tsaye ya wuce ɗakin Yadikko wacce itama ke sallar Isha'i dan haka ya wuce ɗakin Iya. Ɗan amsa gaisuwar na sa da ta ke yi da yau bai samu ba, ya fi sau goma yana gaisheta ta yi banza da shi ƙarshe ta ce ya bar ma ta ɗaki. Ya fice daga ɗakin sumu-sumu, yana tunanin me kuma ya faru. Ya yi sallah a hanya dan haka ya koma ɗaki ya cire kayan sa ya saka jallabiya ya fito ƙofar gida. A nan 'yan uwansa da su ka dawo daga masallaci ke ma sa barka da dawowa wasu kuma su na tsokalar sa Ango- Ango. Gaba ɗaya sai ya rikice, ba dai Baffah ya ma sa auren ba, ai shekara ɗayan da ya nema ba ta cika ba. Ganin Baffan na dawowa ne ya sa shi zare jiki ya je wajen sa yana gaisheshi. Tare su ka shiga gida inda su ka yi masauki a ɗakin Baffan. Zuciyar sa harbawa ta ke da sauri-sauri saboda abunda ya ji a ƙofar gida. Baffah na sane da yadda Tijjani ya ke a zabure amma ya dake yai ta jansa da hira sai daga baya ya fara ma sa bayani. "Shehu kafin zuwan ka akwai wasu abubuwa da su ka faru, ba na so na yi tone-tone saboda ba abinda hakan zai haifar sai fitina. Na san duk hukuncin da na yanke kai mai karɓan shi hannu bibbiyu ne shiyasa ni da iyayen ka muka yanke wannan hukunci. An riga an gyara mu ku ɗakin da za ku zauna, ba a dai gama saka ma ta kaya a ciki ba amma a hankali za a sa komai tunda abune da ya zo a gaggauce. Sai ka yi haƙuri da ɗaurin auren da hidiman duk anyi babu kai" Da Baffah zai kalli T J da kyau da zai ga yadda jikinsa ke rawa, ga gumi na tsatstsafo ma sa duk da kuwa akwai sanyi a garin. "Maryam 'ya ta ce, ina fata za ka riƙemin ita Amana duk da na san kana ƙoƙarin hakan tunma kafin a aura ma ka ita. Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuri'a ɗayyiba. Zan yiwa Goggon ka magana a buɗe mu ku ɗakin dan babu amfanin wani jinkiri tunda kai ba mai zama ba ne" "Insha Allahu Baffah" abinda T J ya iya faɗa kenan ya miƙe ya fita baya ma gani da kyau. Yana zuwa ɗakinsa ya kwanta yijif sai ga hawaye a idanun sa. Duk wani ɗokin ganin Nkiru da ya ke yi yanzu danasanin dawowa gida ma yake yi. Ta ina zai fara rayuwa da wata Maryam? Ta ina zai fara zaman aure da wata wanda ko sanin ita wacece bai yi ba, he has always challenged irin auren da ake mu su, auren haɗin gida duk da ma yanzu ana ɗan bari a saba kaɗan kafin ayi auren amma shi duk cikin cousins ɗinsa babu wacce zai iya cewa tana burgeshi balle har yai tunanin zaman aure da ita. Wani zazzaɓi ne ya rufe shi lokaci guda... Tunda Baffah ya sanar da Goggo cewa a tura Maryam ɗakin mijinta ba ya son wani hayaniya ta sa Maryam ta je ta yi wanka. Da ta dawo cikin sababbin kayan da aka ɗinka ma ta ta zaɓa ma ta ɗaya ta saka aka feshe ta da turare, aka yafa mata gyale aka rufe fiskarta Goggo, Yadikko, Pendo da Inna Zulai su ka raka Maryam ɗakin ta ana tafiya Inna Zulai da Yadikko na ta guɗa. Ɗakin dama a gyare ya ke, addu'a kawai su ka ma ta su ka fito dan ba sa jin turanci balle su ma ta nasiha. Shiru-shiru Tijjani zai zo bai zo ba har ƙarfe goma. Tun Maryam na gyangyaɗi har ta kwanta sosai akan gado ta fara bacci garin da sanyi saboda iskar damina da ke kaɗawa hadari ne ma ya taso a garin. T J na kwance a ɗakin yana rawan ɗari ƙaninsa wanda su ke 'ya'yan Baffanu ya shigo ɗakin. Shi ma farkon shekaran da za a shiga za a ma sa aure. Tsakanin sa da T J shekara ɗaya ne. Ganin yadda T J ya ke rawan ɗari hakan ya sa shi ƙarasowa ɗakin da gudu. "Lafiya, mi ya faru?" T J ya ce "ka ce Yusha'u ya zo ya min allura Dan Allah" "Hamma ko dai tsoron haɗuwa da Amarya ne? Ni na ɗauka ko ciwo ka ke yi aka ce an ɗaura ma ka aure da Maryam a take za ka warke" "Dan Allah ka je, idan ba za ka je ba ko su Ƙasimu ka aike su" "Ba Yusha'un da za a kira, ga kaza nan na siyo maka kaje Amarya ta maka maganin zazzaɓi" "Ba za ka gane bane Suleman, Dan Allah ko magani ne ka siyo min" "Ikon Allah. Na ɗauka za a raba dare ana soyayya ashe duk shirme ne. Gaskiya abin Babba ne. Barin je na kira Yusha'un" Har zai fita sai T J ya ce " wai dan Allah Suleman wace Maryam ɗin aka aura min?" Sai lokacin Suleman ya gane abinda ke damun T J ashe bai san wa aka aura ma sa ba. Ya dawo gefensa yana cewa kafin ya gaya ma sa sai ya bashi tukwici. T J yai tsaki yana dafa kan sa da ke wani irin sarawa. "Hamma kar ka kashe kan ka fa. Boɗɗiyonka aka aura ma ka" T J ya ɗaga rinannun idanun sa ya kalleshi ya ce " ba na son shirme" "Aradun Allah Boɗɗiyo ce, ai musulunta ta yi shine su Baffah su ka aura ma ka ita" Kafin ya ƙare maganar tuni T J ya miƙe tsaye. Suleman ya sa dariya "Dan Allah ban da wasa kar zuciyata ta buga, ka faɗamin gaskiya" yana magana yana jin wani jiri-jiri. "Na rantse da Allah Hamma" Tijjani ya sa kai zai fita Suleman ya riƙeshi ya ce "ga gudummawa" ya miƙa ma sa ledar gasashshiyar kaza. A hankali ya buɗe ƙofar ɗakin yana tantamar maganar da Suleman ya faɗa. Ankawo wuta dan haka ɗakin tarr ya ke da haske. A hankali ya ƙarisa bakin gadon ya ƙurawa yarinyar da ke kwance kan gadon ido bai san lokacin da dariya ya ƙubuce ma sa ba yanayi yana hawaye. Ya ranƙwafo ya kwanta gefenta ya sa hannu ya shafa kumatunta. "Inkiru" ya kira a hankali yana cigaba da shafa fiskarta. A karo na uku ne da ya kira sunan ta buɗe ido. Ta lumshe ido ta sake buɗewa tana kallonsa sai ga hawaye ya zubo kan kumatunta. "I'm i dreaming?" Ya furta murya a shaƙe. Ta girgiza ma sa kai. Ya tallafo kan ta a hankali ya haɗe bakin su. Kissing ɗinta ya shiga yi passionately yana yi yana gurnani. Sun jima a haka kafin ya sake ta yana maida numfashi. "I love you Maryam-Inkiru" Rufe idonta ta yi tana murmushi. Abu ne da ta ke son ji daga gareshi tun da jimawa. Ya jawota jikinsa ya rungume yana cigaba da furta ma ta kalmar I love you. Ruwan da aka fara ne ya sa shi ankara, da sauri ya miƙe ya fita, ɗakinsa na zaure ya je ya ɗauko sallaya tareda buta ya dawo ɗakin. A barandar ɗakin dukkan su biyu su ka yi alwala yana sa ido yaga babu kuskure a alwalan na ta. Ya shimfiɗa sallaya ya ja su sallah raka'a biyu na godiya. Bayan sun idar ne ya gaya ma ta ma'anar sallan. Ya jawo mu su kazar da Suleman ya kawo, kaɗan su ka ci saboda ita Maryam ta riga ta ci abinci kuma dare yayi sosai ba ta son sake cika cikinta. Shi kuwa T J duk ɗoki ya ke ji. Wani zazzaɓi da rashin kuzari da ya ke ji ɗazu duk sun tafi hutu. Ruwan sama aka fara tsalawa wanda ya ƙara sawa ɗakin na su yai sanyi hakan ya sa ɗumin jikinsu ya zame mu su garkuwa. Soyayya ce da ta ke zuciyoyinsu tun da jimawa wacce ba ta samu daman fitowa ba sai yanzu. Soyayya ce da ɗaya ba zai iya cewa ga lokacin da soyayyar ta shige shi ba. Soyayya ce da addini, yare, da banbancin gari ya mu su shubuha a da, amma musulunci da igiyar aure ya zo ya haɗe komai ya ba su damar bayyanawa junan su irin tsananin son da su ke wa junan su. Nkiru dama ba baya ba wajen sakalci dan haka ya sha yare kala-kala a wannan dare, har yaren mahaifiyarta Efik da ba ji ta ke sosai ba sai da ta mi shi. Ita kuwa ta sha lallashi da yaren fillanci. Da ita da shi ɗin duk zazzaɓine ya rufe su a wannan dare mai cike da tarihi. Daren daya zamo ɗaya daga cikin dararen da ba za su iya mantawa ba a tarihin rayuwar su... *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *7-Happy couple* Bismillahir Rahmanir Rahim Washegari kiran sallar Asuba ne ya farkar da T J daga bacci. Lokacin daya buɗe ido ya ɗauka abunda ya faru jiya mafarki ne sai daya ga Maryam gefensa tana bacci, yai murmushi yana hamdala a ransa. Ya ma ta ligt kiss a bakinta kafin ya tashi, baya jin wani ƙarfi sosai amma a haka ya saka jallabiyar sa ya fita. Ruwan zafi ya kamata ya nemo amma ya san ba a kunna wuta ba, sai yanzu ya ji haushin tafiya da heater ɗin sa Zaria. A haka dai ya daure ya je yai wanka ya ɗauro Alwala ya dawo ɗakin har lokacin Maryam na bacci. Ya gyara ma ta kwanciya sannan ya fita, a bakin ɗakin Goggo ya ga Goggon riƙe da buta za ta fita, yai saurin ƙarisawa wajenta yana sosa kai yana wani sunsun da kai ya ce ma ta idan ba damuwa yana son ruwan zafi idan ya dawo daga masallaci. Goggo ta yi murmushi ta wuce ba tareda ta amsa ma sa ba. Lokacin da ya dawo daga sallah Maryam ta farka amma ba ta tashi akan gadon ba, tausayinta ya ji dan jiya bai ma ta da sauƙi ba. Ta ce ma sa tana son yin wanka ya ce ta bari a sama mu su ruwan zafi tukunna. Ya jawota jikinsa yana cigaba da ba ta haƙuri tareda jaddada ma ta soyayyar shi gareta. Su na haka sai Asma'u ta yi sallama wai Goggo na kiran sa. Ya fito bayan ya mannawa Amaryarsa kiss a kumatu. Da ya je Goggo ta ma sa bayanin yadda Maryam za ta gasa jikinta da ruwan da aka kai ma ta banɗaki. Sai sosa ƙeya ya ke yana jin kunyar Goggon ta sa. Da ya koma yai wa Maryam bayani komai, ya so tallafa ma ta zuwa banɗakin amma ya san magana kawai zai ja wa kan sa idan aka gan shi. Har ta fita daga ɗakin sannu ya ke ma ta yana ƙara jin soyayyarta na mamaye ilahirin jikin sa... Kwana takwas T J ya kwashe yana cin Amarci kafin ya koma Zaria tareda alƙawarin ƙarshen sati zai zo. Kafin ya tafi wani soyayya mai tsabta su ke gudanar wa junan su. Ba dan cikin babban gida su ke ba da ya nuna wa Maryam gata fiye da tunaninta. A waɗannan kwanakin ne ya ji labarin yadda akayi ta musulunta da yadda aka yi har su Baffah su ka mu su aure. Ta gaya mi shi komai amma banda abinda Muntari yayi. Kwana biyu bayan an ɗaura aurenta da TJ Baffah ya sa aka kira ma sa ita, Yakubu ne ya fassara ma ta abinda Baffan ya ce. *"Ina neman alfarma a wajenki Maryam, ba na so ki sanar da Tijjani abinda ya faru tsakanin ki da Muntari. Ba na son zumunci ya yanke, da Tijjani da Muntari duka suna da zuciya, amma ina tsoron abinda zai biyo baya idan Tijjani ya san abubuwan da Muntari ya aikata kafin auren ku. Ina fata idan Allah ya sa Muntari ya huce da kanshi zai nememu ya nemi gafaran mu, zuwa lokacin gara a rufe maganar"* Itama ta gamsu da bayanin Baffan domin dama ba abinda maganar zai haifar wa T J sai haushin ɗan uwansa. Ba za ta so a kanta 'yan uwan juna su samu matsala ba. Idan ka ɗauke Iya kowa yayi na'am da kasancewar Maryam matar Tijjani. Ita kam ƙiri-ƙiri ta ke nuna ma ta tsana hakan ya sa Maryam ke kaffa-kaffa da ita. Tunda ta ke ba ta taɓa amsa gaisuwarta ba. Ba dan kashedin Baffah ba da abinda Iyan za ta yiwa Maryam sai ya fi haka... Muntari kam tunda ya tafi bai sake waiwayan gida ba wata uku kenan, haka ya kuma ɗaga hankalin Iya ta kuma tsanar Maryam dan gani ta ke ita ce silar komai. A ɓangaren T J duk sati sai ya zo gida idan bai zo ba to wani abun ne ya tsaida shi, daya fara thesis na shi ne ma ya ke ɗan jimawa wani lokaci bai zo ba. A yau Maryam ta dawo daga makaranta, fitsari ne ya dameta ta yi hanyar banɗaki da gudu ba ta ankara ta ɗan buge Iya wacce itama daga banɗakin ta ke. "I'm sorry" ta faɗa ta wuce da sauri. Tundaga banɗaki Maryam ke jin ihu da kururuwan Iya. Da ta fito kuwa har anfara taruwa a wajen Iya ta tsaya tana kukan munafurci wai Maryam ta bangajeta kuma ko sannu ba ta ce ma ta ba. Ganin yadda Iyan ke kuka ya sa dayawa daga cikin matan su ka yadda da abinda ta ke faɗa, harda cewa dama ƙabilu ai ba su da kunya. Ita kuwa Maryam ba ta fahimci maganar su ba andai tsareta anata magana wannan yai wannan yai. Ganin Iya na ta kuka ya sa ta fahimci buge Iyan da ta yi ɗazu ne ya sa take kuka. Har ga Allah ba ta ma san Iya ta buge ba, sannan ba wani bugewan da za a nuna damuwa ba ne. Hayaniyar 'yan gidan ya tada Yadikko daga bacci. Ta fito ta tarwatsa taron ta ce ba ta yarda Maryam za ta buge Iya ba sharrinta ne kawai dan ba ta ƙaunar Maryam ɗin. Tunda Maryam ta shiga ɗaki ta fara kuka, ya za ta yi da mahaifiyar T J ne? Mi za ta ma ta matar ta dena tsanarta? Ƙarshe ciwon kai ne ya sa ta baccin dole. A satin da T J ya zo kamar kullum ɗakin iyayen sa ya fara shiga dan ya gaishe su kafin ya wuce wajen Amaryarsa. Ɗakin Iya daya shiga ne ya sameta tana saka lalle a ƙafarta. Kamar kullum ya gaisheta ya tashi zai tafi dan ya san ba kulashi za ta yi ba. Sai kuma ta ce ya tsaya, ya zauna fiskarsa shimfiɗe da farin ciki. "Takarda na ke so ka rubutawa Inyamuran matar da ka ke kira da mata" Daam ya ji ƙirjinsa ya buga. Ya ɗago ido ya kalli Iya da itama ta ƙura ma sa ido. "Iya Dan Allah ki yi haƙuri, duk abinda Maryam ta miki ki yafe ma ta, zan ma ta faɗa za ta gyara" "Tsaya ka ji Shehu, na zuba maka ido ne kawai saboda ba yadda zan iya. Amma wallahi yanzu kam ba zai yiwu matarka ta dake ni kuma ta cigaba da zama da kai ba. Duk yadda ka maƙalewa Maryama dai ni ce nan na haifeka kuma wallahi ko ka saketa ko na ɗaga maka nono" Da sauri ya zaro ido yana girgiza kai. "Kiyi haƙuri dan Allah, wallahi ba zan iya rabuwa da Maryam ba, ki taimaka min" Ta yi kaman ba ta ji shi ba ta cigaba da saka lallen da ta ke yi. Kawai ya fashe ma ta da kuka yana yi yana roƙonta. Ganin ya isheta da kukan ne ya sa ta ɗago ta kalleshi ta ce"Ko ka saketa ko wallahi na tsinemaka" "Bismillah, ki tsine mi shi" Su ka tsinkayi muryan Baffah. Wucewa zai yi ya je masallaci ya ji kukan TJ daga ɗakin Iya shine ya shigo. "Aishatu na ce ki tsine ma sa, ɗan ki ne ai ki tsine ma sa ya bi duniya" Jikin Iya ya fara rawa, yadda Baffah ke magana da ƙarfi ya sa ta kuma tsorata. Ya kalli T J ya ce " kalleni Shehu" T J ya ɗago rinannun idanun sa ya kalleshi. "Wallahil Azim duk ranan da ka saki Maryam to a bakin auren mahaifiyar ka" T J ya rikice da jin wannan magana. Itama Iya ba ƙaramin kaɗuwa ta yi ba da jin abinda Baffah ya ce. "Kinga Aishatu duk ranan da ki ka sa Shehu Tijjani ya saki matar sa kaman na sake ki ne, kuma Allah ko bayan rai na kika sa shi rabuwa da ita ba zan taɓa yafe miki ba. Haba, haba Aishatu. Ke kina ƙara girma kina ƙara rashin hankali ne, yaron nan kullum hantarar sa ki ke yi ba dama ya so abu sai ki dinga kushewa. Wai shin ma kyautar da Allah ya mi shi ki ke so ya yar? Wani jahilci ke damunki da za ki dinga irin wannan furucin" Ya kalli T J ya ce "tashi ka tafi wajen matarka" "Baffah ka yi haƙuri" ya faɗa murya a raunane "Tashi ka tafi" Haka ya tashi simi-simi ya bar ɗakin. Baffah ya cigaba da yiwa Iya masifa duk wani abu da ya ke shanyewa tun da sai da ya amayar ma ta da shi. Ta fara kuka wiwi har da majina. Rabon da Baffah ya ma ta irin faɗa haka tun tana Amarya, watarana da ta je ɗakin Maryama ta kwarara ma ta ruwa bokiti biyu a cikin ɗakinta. Ranan sai da Modibbo ya shiga tsakani dan duk yadda ya ke da haƙuri sai da ya mareta a ranan. Yana shigowa ɗaki kai tsaye gado ya hau ya jawo Maryam jikinsa ƙyam yana sauke ajiyar zuciya. Tana bacci ta ji an rungumeta hakan ya sa ta buɗe ido, jin yadda jikinsa ke ɓari ya sa ta yi saurin juyowa ta kalleshi. "Miya faru?" Ya girgiza ma ta kai ya kuma jawota jikinsa yana faɗin "I love you Maryam, ba zan iya rabuwa da ke ba, I love you. Idan aka rabani da ke zan shiga tashin hankali, without you I cant have a happy life" "I love you too" ta faɗa tana shafa gashinsa tana hura ma sa iska a kunne... Washegari Baffah ya kirashi ya kuma jaddada masa maganar sa ta jiya tareda cewa ya shirya ya tafi da Maryam Zaria. Idan ba shi da wajen da zai ajiye ta ne to zai bashi kuɗi ya kama mu su haya a chan. Ya haɗa da cewa Maryam amana ce a gareshi dan haka kada ya ci amanar ta Allah zai kama shi. Ba su tafi tare ba amma bayan kwana huɗu da tafiyar sa ya dawo ya ɗau Maryam su ka koma garin Zaria. Hayar ɗaki ɗaya ya kama mu su suke zaune hankali kwance suna shan soyayyar su ba mai takura mu su balle a sa mu su ido. Lokacin da T J ya ƙare Masters na shi ba ƙaramin karramawa ya sha ba saboda kasancewar sa haziƙin ɗalibi, gashi thesis ɗin da yai ya kawo cigaba a Faculty na su dama makarantar gaba ɗaya. Aikin lecturing aka bashi saboda makaranta na buƙatar haziƙin mutum kamar sa. Bayan sun samu gida a quaters na school T J da Maryam su ka je Ringim inda su ka tattaro duk kayan ɗakin Maryam ɗin su ka kawo sabon gida tunda wannan a wadace ya ke ba kaman ɗaki ɗaya da su ka fara zama ba, aka ƙara da wasu siyayyan Abu na gaba da ya fara yi shine ya fara bincika wa Maryam yadda za ayi ta samu takardun makarantar ta. Aka rubuta letter aka aika chan makarantar su. Kafin a dawo da reply sai da ya ɗau kusan sati bakwai, a saƙo na gaba da suka turo ne aka haɗo da sabbin copies na results ɗin ta. Nan da nan T J ya shiga nema ma ta gurbin karatu a nan ABU Zaria cikin ikon Allah kuwa ta samu. Law ta cika saboda tunda ta auri T J ta gaya mi shi ra'ayinta na son ɗaukan fansa kan abinda Uncle Udodiri yai wa iyayenta kuma T J ya bata goyon baya ɗari bisa ɗari. Zaman lafiya su ke ba wani tashin hankali, zai fita koyarwa ta fita ɗaukan karatu idan an dawo da yamma ya koya mata ƙur'ani da kuma iya litattafan addini. Duk ilimin da ya samu na addini to a wajen Kakan sa Modibbo ya samu kuma yana ƙara godiya daya sa alokacin ya maida hankali kan karatun gashi yau ta ma sa rana. Duk ƙarshen wata T J ke zuwa ganin iyayen sa ita kuma Maryam Nkiru sai bayan wata uku ta ke zuwa duba su. Har lokacin babu wani chanji a tattare da Iya dan tunda Baffah ya ma ta faɗan nan ta sake watsar da kashin T J da Maryam ko kallon kirki ba su isheta ba, abun na bala'in damun T J musamman yanzu dayake ganin a hankali za su zo su fara tara iyali da shi da Maryam. Goggo na yawan kwantar ma sa da hankali akan ya cigaba da yiwa Iya addu'a watarana komai zai dawo dai-dai. Muntari sai da yayi shekara ɗaya da wata biyar kafin ya zo gida nan ma zuwa yai ya leƙa Iya dan ya san ita kaɗai ne hankalinta zai tashi da rashin sa. Duk yadda ta ma sa faɗa akan ya dawo gida ya ƙi, cewa yai saboda Hamma Tijjani yayi boko shiyasa aka walaƙantashi aka aurawa T J Maryam bayan kuwa an sani shi ke sonta. Iya ta tsorata da lamarinsa saboda ta ɗauka iya lokacin nan ya manta da batun Maryam. Tsanar Maryam ya kuma dira ma ta a zuciya ta sawa ranta Maryam Mayya ce shiyasa ta kama ma ta 'ya'ya har biyu. Ga Tijjani ya zama tamkar wawa a kan Maryam shi kuma Muntari ma tana tunanin hauka yayi. "Sai na yi kuɗi, Aradun Allah sai na yi mahaukacin kuɗi ta yadda ko ta Maryam sai ta yi nadamar auren Hamma Tijjani da ta yi. Sai na nunawa dukkan wanda su ka zalinceni cewa Boko ba komai ba ne, Arziƙi shine mutum" Kamar Iya za ta yi kuka haka ta dinga roƙonsa akan ya haƙura da Maryam ya nemi wata a ma sa aure amma ya ƙi. "Ni kam na shiga uku ni Aishatu, Yasin wannan Inyamuran ta gama da ni. Muntari ka dubi Allah ka dubi Annabi ka haƙura da ita, ga kyawawan 'yan mata nan ka nema ka aura. Ba wacce za ka nema da za ta ƙi ka" "Iya ki bar zancen nan ko zan yi aure ba yanzu ba. Idan ban cimma burina ba bazan taɓa samun sauƙi ba" Ya buga ƙirjinsa ya ce " ki yi haƙuri amma son Maryam yanzu na fara shi" Kwana biyu yai a gidan ya bar garin wannan karan ba Kano ya tsaya ba Lagos ya wuce neman kuɗi... *** Shekaru biyu kenan cur da auren Maryam da Tijjani kuma har lokacin ba ta samu ciki ba. Ita ne ma ta fara damuwa amma shi kam ba ruwan sa kullum ce ma ta ya ke lokaci ne bai yi kuma ai ba su jima da aure ba ma. Itama ta fara damuwa ne tun lokacin da su ka kai ziyara gida matan gidan ke ce mata sun ji shiru har yanzu. Yanzu kam ta iya Hausa kuma Fulatancin ma ba laifi ta kan ji kuma tana amsawa daidai gwargwado. Zuwan su na ƙarshe gida bikin Pendo ne. Zainaba wacce ake cewa Pendo ta samu gudummawa sosai a wajen Maryam. Allah ya haɗa jininsu tun ranan da su ka fara haɗuwa kuma duk yadda aka ƙyamaceta a gidan kafin ta musulunta Pendo ba ta taɓa ƙyamar ta ba. Mijin Pendo ma dai duk ɗan cikin gida ne amma a Dutse ya ke aiki a wani ma'aikata, da Sakandare ya fara aikin amma yanzu ya fara karatu a Jami'ar BUK saboda mahimmancin Ilimi daya gani. Ta so ta bi 'yan kai Amarya amma T J ya hana ya ce ta bari idan an kwana biyu za su kai ma ta ziyara har Dutsen. Bayan bikin Pendo Baffah ya fara jinya wanda bai cika wata uku ba ya rasu mutuwar da ta girgiza iyalen gidan gaba ɗaya musamman ma T J da Maryam. A wajen rabon gado ne T J ya tambayi yayansa Usman Manga ko ya san inda Muntari ya shiga, ace Baffah yayi jinya har ya rasu amma Muntari bai zo ba. Usman ya ce ai ya rabu da shirmen Muntari wai Lagos ya tafi neman kuɗi. T J ya taɓe baki yana mamakin halin ƙanin na sa. Sam tun tasowar yaron baya ji kuma daɗin daɗawa Iya da ta dinga ɗaure ma sa gindi ya sa ya sake botsarewa. Ko lokacin da ya gudu daga makaranta ma ya ce ba zai yi karatu ba Iya ce ta fara supporting ɗin sa, har ta kai dole Baffah ya haƙura ya barshi ya tafi Kano wai neman kuɗi. T J ya ce Allah ya shirya shi. Gadon Muntari aka damƙawa Iya ta ajiye mi shi zuwa lokacin da zai dawo... Bayan rasuwan Baffah da wata shida watarana yayar Iya wacce su ke cewa Inna Saratu ta kawo ma ta ziyara da 'yar ta Hajara da su ke cewa Hajjo a wannan zuwan su ne kuma su T J da Maryam su ka zo gida. Yadikko ce ba lafiya, ita tun rasuwan Abubakar ma bata jin daɗi dan mutuwar ya girgiza ta, ɗan ta ƙwalli ɗaya a duniya ya tafi ya barta. Hajjo ta ƙyalla ido ta ga T J nan ta sanar da Inna Saratu cewa ta samu mijin aure. Dama wani tsoho ta ke so saboda kuɗin sa a chan ƙauyen su amma yanzu da ta ga T J ɗan boko wayayye kyakyawan saurayi sai ta ji ba abinda za ta yi da Alhaji Rabe. "Amma Hajjo kin san fa watan nan za a sa mi ki rana kike maganan kinga mijin aure a nan. Dan uban ki Alhaji Raben ba mijin aure ba ne?" Hajjo ta yi dariya ta ce "Inna wallahi ina faɗa miki sunan sa za ki rikice, aiko an ɗaura auren za ki sa a warware" "Waye?" ta faɗa fiska a ɗaure dan ta san halin 'yartata da rawan ido. "Hamma Tijjani, Hamma Tijjanin Iya" Inna ta zaro ido waje sai kuma ta fara murmushi... Ba su bar Ringim ba sai da ta tabbatar ta zuga Iya akan ta haɗa auren Tijjani da Hajjo. Itama dama ba son Maryam ta ke ba dan haka ta yi saurin na'am da zancen tunda dai yanzu babu Baffah da zai taka ma ta burki. Amma wani hanzari ba gudu ba ta fi son T J ya auri Bafulatanar usul sannan gaskiya tarbiyyan Hajjo bai ma ta ba dan taga yadda Hajjon takeyi cikin kwana biyar da su ka yi a gidan, yarinyar idonta a buɗe ya ke. Inna ta hau fushi tana faɗin Iya za ta nuna ma ta cewa 'yarta bare ce tunda Uban Hajjo ba Bafulatani ba ne. Mijinta Warjawa ne. Auren fari ta auri ɗan uwanta Bafulatani ba ta son sa haka su ka rabu ko shekara ba su yi ba, ta je ta auri Sama'ila wanda cirani ya kawo shi Ringim a lokacin. Iya ta shiga ba ta haƙuri tareda cewa indai haka ta fassara maganan ta yi haƙuri ba manufarta kenan ba, za ta yiwa Tijjani magana ya auri Hajjo... *still mu na kan share hanya ne a labarin domin jaruman mu ba ta ma iso ba tukunna. The sad truth is i'm inlove with Maryam-Nkiru and Tijjani😔* *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* *Free page* *5-Maryam* Bismillahir Rahmanir Rahim Ba abu ne mai sauƙi ba amma kuma zai yi komi domin ta samu farin ciki. Fasa tafiyar sa ya zo da kace-nace a cikin gida sai dai kuma bai damu ba tunda ya tabbatar buƙata za ta biya. Kwana takwas ya ƙara kafin ya koma chan Obowo, cikin kwanaki takwas ya nemawa Nkiru aiki a wata primary school na gwamnati, ba a dai ɗauketa officially ba saboda ba ta da takardar shaidar karatu amma ance da zaran ta samu takardun ta za a aika ministry a ɗauketa aiki. Kafin nan kuma za ta dinga aiki ne ana ba ta ƙaramin allowance duk ƙarshen wata. Takardunta ba za su samu ba saboda ta baro su a gidan su da ke Owerri, wanda ya rage ma ta mafita ɗaya wato sai dai a sake turo mata takardun daga chan makarantar su, gashi da primary school da high school ɗin duk a England ta yi. Graduation ɗin su ma ko wata biyu bai yi ba su ka dawo Nigeria. Ranan da T J ya tafi ta sha kuka sosai dan ji ta ke kamar idan ya tafi ba zai dawo da wuri ba. Ba ta san T J ya shiga ranta har haka ba sai ranan da ya tafi, ji ta yi tamkar ya tafi da zuciyar ta ya bar gangan jikin a Ringim. *"Ba na son ki rinƙa yin dare a waje, ban yadda ki keɓe ke kaɗai da Okafor ba. Banda zuwa church da dare.."*haka yai ta jero ma ta sharuɗɗa safiyar ranan da zai wuce. Wasa-wasa sai gashi an shafe sati ɗaya da tafiyar sa tun tana kuka har ta dena ta maida hankali ga koyarwan da ta ke yi. Okafor bai dena bibiyarta ba dan ko ta je church haka zai liƙe ma ta, ga pastor ma ya nace akan sai ta bar gidan su T J. Ita yanzu banda kitso ba abinda ke kai ta gidan su Okafor, the more ya ke son kusanci da ita the more ta ke ƙara ja baya da shi. A gida kuwa ba a sati ɗaya ko biyu Muntari bai zo ba, tun Iya ba ta gane saboda Nkiru ya ke zuwa ba har ta gane ta dinga faɗa tana zage-zage shi kuwa ya kwantar ma ta da hankali akan yana hakan ne saboda yana so Nkiru ta musulunta, idan Nkiru ta musulunta ta dalilinsa ai sunan gidan su zai ƙara daraja ƙila shima a fara kiran sa da Modibbo Muntari. Da wannan ya samu ta sauko amma duk da haka sai da ta ce ya rage shiga harkanta. A wajen Nkiru kuwa ganin Muntari ta ke a matsayin mutum mai barkwanci shiyasa ba ta taɓa damuwa da zuwansa wajenta ba ko kuma yawan tsaraba da ya ke kawo ma ta idan ya zo. Shi kam Muntari sai da ya je wajen malamai ɗai-ɗai har uku aka tabbatar ma sa zai iya auren Nkiru dan haka ya zage damtse yana ta buga-buga, burin shi nan da shekara ɗaya zai siyi gida a Kano ya auri Nkiru su dawo Kano tare, ko ta musulunta ko ba ta musulunta ba ba ruwansa ba ne wannan, shi dai ya ga Nkiru kuma yana son ta ko a yaya ta ke. A hankali Nkiru ta fara sabawa da rashin T J ta kuma zage tana koyon Hausa da Fulatanci. So ta ke ta impressing T J idan ya dawo, malamai 'yan uwanta musamman Mr Kabir da Malam Abdullahi su su ke taimaka ma ta take koyo dan har littafi ta ke da shi na darasi. A gida kuwa tun ana magana akan zaman Nkiru a gidan har aka zo aka saba aka ma dena maganar, har idan ba a ji ɗuriyar ta ba za a fara faɗin 'Boɗɗiyon Hamma na nan kuwa?' Idan tana maimaita kalmomin da ta koya na fulatanci kuwa Goggo da Yadikko su na shan dariya, wani lokaci su gyara ma ta ta fahimta ko da ba Pendo ko Yakubu wani shima da ya ke ɗan jin turanci a gidan da zai ƙara ma ta bayani da turanci. A zamanta kuwa ta lura akwai wata mata wacce kamannin Muntari ta ke da shi shiyasa ta ɗauka mahaifiyar sa ce, matar ba ta son ta ko kaɗan da ta ganta za ta fara tsuke fiska tana yare. Idan ta gaidata da Fulatanci ko Hausa kuwa sai ta kama masifa hakan ya sa ta dena gaisheta. Kwatsam ranan su na hira da Pendo ta ke cewa Maman T J wato Goggo kenan ta fi Maman Muntari kirki. Pendo ta kwashe da dariya ta ce ai T J da Muntari mamansu ɗaya ne kawai dai T J ya girma a hannun Goggo ne. Abun ya ba wa Nkiru mamaki... *** Lokacin da T J ya tafi wata uku da sati uku ya rage T J ya gama bautar ƙasar sa amma haka ya dinga ganin kwanakin nan kamar ba sa tafiya. Ba ranan Allah da za ta fito da ba zai wuni da Nkiru a ransa ba. Tun da ya ba wa Eze labari kuwa Eze ya samu abun tsokanar shi yana cewa ya faɗa soyayya. Shi dai bai gaskata hakan ba ya dai san yana jin tausayinta. A wani weekend me ya sa Eze ya rakashi ƙauyen su Nkiru inda su ka bibiyi labarin Uncle Udodiri. Da ke Eze ma igbo ne ba su sha wahalar samun information ba. Augustus Udodiri ya koma Owerri da zama bayan ya yiwa Yayan sa da matar sa burial na gani na faɗa a ƙauyen. Har shanu biyu aka kashe a wajen burial ɗin abinda ba a taɓa yi ba a ƙauyen na su. Da su ka tambayi maganar 'yar Patrick da Caroline cewa aka yi ta gudu saboda kunyan kashe iyayenta da ta yi. Wasu kuwa sun ce ma ta mutu ne. Haka dai su ka bar ƙauyen cike da jimamin wannan Al'amari, sun so haɗuwa da Elizabeth amma kuma ance ta tafi wani church program a Enugu... Tunda su ka ci wata biyu T J ya fara lissafin kwanaki. Kwanakin na matsowa yana ƙara fargaban abinda zai tarar idan ya je gida. Tsoron sa kar Nkiru ta koma mu'amala da Okafor duk da ya hanata, kai koma ba Okafor ba wani ɗan uwanta christain ɗin. Idan ya tuna haka duk sai ya ji ran sa ya jagule. A haka dai kwanakin su ka cigaba da tafiya. *** Yau ma kamar kullum kitso ta zo gidan su Okafor, su na da shago nan dukkan su ke zama har da Mama Okafor sai dai ranan sunday ba sa zuwa. Ita kuwa Mama Okafor dama tana dawowa da wuri irin 4-5pm ɗin nan. Ko da ta je gidan babu kowa sai Okafor, shima fita zai yi lokacin da ta zo. Sai ya ma ta ƙarya akan ta shiga ciki Maman sa ta je maƙota ne za ta dawo yanzu, ba ta kawo komai a ranta ba ta shige ciki, shi kuwa yana shiga ya kulle ƙofa da key. Bayan ta zauna ne ya fara tambayarta akan dalilin da ya sa ta ke gudunsa ta ce ma sa ba komai. Ya ce ƙarya ne ya lura ko gida ya je ya aika a kirata sai ta sa a ce ma sa ba ta nan. "Kina tunanin T J yana son ki ne? Ko kuma kina tunanin su za su fi mu son ki?. Barin gaya miki abu ɗaya ki ji, T J da ki ke gani ba zai taɓa son ki ba..." "Zan je gida, idan Mama ta dawo ka gaisheta" ta faɗa tana miƙewa tsaye saboda yadda maganar sa ta fara karya ma ta zuciya. Shima miƙewa tsaye ya yi ya matso kusa da ita ya dafa kafaɗarta ya ce "Nkiruka ki tsaya tukunna. Give me a chance, ina son ki, zan kula da ke sosai, idan ki ka amince da ni za ki ji daɗi. Ba zan taɓa goranta miki ba infact duk lokacin da mu ka tashi zuwa ƙauyen mu a Enugu zan raka ki mu je na ku ƙauyen" Tureshi ta yi ta yi hanyar fita ya jawota da ƙarfi. "Okafor ka bar ni, ba na son ka, na ce ba na..." Danneta yai da ƙarfi akan kujera yana shirin ɗaga mata skirt ta fara kuka tana roƙon sa amma bai saurareta ba sai ma rufe ma ta baki da yai yana ƙoƙarin kunce belt ɗin sa. Mama Okafor ta sa key ta buɗe ƙofa dan dama ba ta ran za ta samu kowa a gidan ba. Sauran su na shago shi kuwa Okafor da ya zo gida wanka ta tabbata ya riga ya tafi dan ya jima da barin shagon. "Okafor!" Ta faɗa da ƙarfi lokacin da ta ga abinda ɗan ta ke shirin aikatawa. Da sauri ya miƙe jikinsa na rawa ya fara ƙoƙarin zuge zip ɗin wandon sa amma ya ka sa. Mama Okafor ta ƙaraso ta ɗauke shi da mari. "Shame on you Okafor" Ta faɗa ta koma kan Nkiru da ke ta kuka. Rarrashin ta ta farayi tana ba ta haƙuri, sai da ta tabbatar ta nitsu sannan ta ɗauko ma ta zani ta ɗaura saboda skirt ɗin ta ya yage. Ba dan ta zo da wuri ba da mai afkuwa ta afku. Ta so Nkiru ta zauna har Papa Okafor ya dawo amma ta ce gida za ta je dan haka dole da kanta ta raka Nkirun har gidan su T J, a hanya ta cigaba da ba ta haƙuri tana cewa ta gafartawa Okafor ba ta san a ina ya ɗauko banzan halin nan ba. Da ta je gida kuwa zazzaɓi ya rufeta, kewan T J ya ƙara shigarta, ashe gaskiyar T J da ya ce ta yi hankali da Okafor ta dena keɓewa da shi. Yau ba dan Mama ta zo ba da shikenan, ita ko first kiss ba ta taɓa yi ba balle wani abun daban... Tun daga wannan lokaci ta ɗaukewa gidan su Okafor ƙafa, magana ta je gaban Pastor aka kira ta aka ba ta haƙuri amma ita ta ƙi yarda ta koma gidan, wasa-wasa ma ta fara ja baya da zuwa church ɗin. Kuɗin da su ke ba ta duk wata kuwa ta ce ba ta so saboda kuɗin da ta ke samu a wajen aiki ya isheta. Haka dai ta fara nisanta kan ta da su. Daga makaranta sai gida. Ko kitso za ta yi sai dai ta je gidan su wata student ɗin ta Folake wacce mamanta ke kitso. Wasa-wasa sai ga shi watanni uku sun shige ana irga kwanakin dawowan T J a lokacin ne kuwa aka fara Azumin Ramadan. A nan Nkiru ta ga abubuwan mamaki, domin tana mamakin yadda dukkan gidan su ke ɗaukan Azumi har ɗokin Azumin ake yi kafin zuwan sa. Ba abinda ke ƙara burgeta irin lokacin sallar Taraweeh, daga ɗaki tana jin yadda su ke daɗewa su na sallah ga karatun da ke burgeta. Abokanan ta Malamai kam sun sha tambayoyi akan Azumi saboda ko ta tambayi Pendo ba ta iya ba ta amsa saboda ƙarancin ilimi da ta ke da shi. Ranan Azumi na goma sha ɗaya ta ce bari ta gwada Azumi tunda har 'yar Pendo ma na yi, ta ƙi cin abinci tun safe har yamma da ta gayawa Pendo tana Azumi sai ta ringa ma ta dariya ta ce gara ta ci abinci dan ba ta da lada. Ita kuwa ta ƙi haka ta kai Azumin da ƙyar. Haka ta cigaba da ɗaukan Azumin, Pendo da Yadikko su yi ta ma ta dariya, Goggo kuwa ta ce idan tana da rabon musulunci za ta karɓa a barta ta yi Azumin tunda da kan ta ta ji tana son yi. A ranan Azumi na sha bakwai T J ya dira a gidan. Zo ka ga murna a wajen 'yan gidan, amma duk ciki babu wanda ya kai Nkiru murnan dawowan sa. Lokacin da ya shigo gaida Goggo haka ta tsura ma sa ido tana ji kamar ta je ta rungumeshi. Shi kam bayan ya kalleta sau ɗaya bai sake waiwayarta ba, ba wai dan baya son kallonta ba ne sai dan saboda an cika ɗakin Goggon kar a ma sa sa'ido. Bayan ya fita haka Nkiru ta rakashi da ido tana ganin ya rame ma ta ko dan Azumi da ake yi ne oho. "I miss you" ta furta a hankali. Wannan karan ko dan saboda Azumi ne T J ba ya ba ta lokaci kamar da, kwana uku yai ya koma masallaci Ittikafi saboda goman ƙarshe da aka shiga. Hakan ya sa Nkiru ta dena ganin sa, sau ɗaya su ka zauna su ka yi hira wanda shima sama-sama ne. Ana washegari sallah aka kawo ma ta kaya kala huɗu, ɗaya Baffan su T J ne ya siya ma ta sauran kuma T J ne ya siya. Ta ji daɗin karramata da aka yi duk da kuwa ba ta san matsayin sallar da za ayi goben ba hakanan ba ta san ya ake yi ba. Ranan sallah kuwa ya banbanta da kowacce rana da ta zauna a gidan, babu wanda bai yi shiga mai kyau ba a gidan. Ga abinci da aka yi da nama dumu-dumu a ciki. Safiyar sallah ta ga T J wanda shima ya sha ado cikin shadda light blue, ba ƙaramin kyau ya yi ba. Da yammacin sallah kuwa T J ya ɗauketa su ka fita yawo a nan ne take gaya ma sa itama ta yi Azumi har goma shabiyu. "Ya ki ka ji da ki ka yi Azumin?" Abinda ya tambaya kenan "I feel good" ta amsa tana murmushi... Washe gari sai ga Muntari wai ya zo ɗaukan Nkiru wai za su tafi Kano ta ga hawan daushe. Ta ce ya tambayi T J shikuwa ya ce ba zai tambaya ba T J bai da hurumin hanata tafiya inda ta yi niyya. Ita kuwa ta ce ba inda za ta, yayi-yayi ta ce ba za ta je ba, haka yai fushi ya fita yana jin haushin T J a ran sa. Shima T J ya so su je Kano ɗin kawai wa su lissafi yai ya ga bai dace ba a wannan lokaci... *** "Barkindo kana da niyyar aure kuwa?" T J ya sunkuyar da kai yana jin tsananin kunyar mahaifin sa. "Karatu daga wannan sai wannan, shi karatun ai ba zai hana aure ba. Duk sa'anninka fa suna da mata da 'ya'ya" "Baffa wannan karan karatun ba zai yi tsawo ba, shekara ɗaya ne zan yi na gama" "Wallahi ana min surutu Shehu, ko dai ba ka da lafiya ne?" T J yai saurin girgiza kai "To dan Allah ka haƙura da batun karatun nan tukunna, ka yi aure. Idan da hali sai ka cigaba da karatun, a hakan ma ai kana cikin 'yan tsirarun da su ka kai matakin karatun ka a nan garin" Bai san ya zai yi da ran sa ba idan ya amince da aure yanzu, bai shirya aure ba, baya tunanin zai iya zama da wata mace yanzu ko da ya zauna ba za ta samu kan sa ba. Ya ɗan tausasa murya ya ce " Baffa idan da hali a ɗan ɗaga min ƙafa zuwa shekara ɗayan nan, Insha Allahu ina gama karatun nan zan yi aure" "Ka yi alƙawarin bayan shekara ɗaya idan ba ka yi aure ba ni na maka?" Ya ɗago ido da sauri ya kalli mahaifin na sa wanda ko kaɗan ba alamar wasa a tattare da shi. "Na amince" ya furta a hankali... Cikin watanni huɗu da T J yai kafin ya fara masters na shi ya jawo wata muguwar shaƙuwa tsakanin sa da Nkiru fiye da da. A ɓangaren Muntari ma duk wani dama da ya samu ƙoƙarin gwadawa Nkiru kulawa ya ke yi. Shi a yadda ya fara ji ma yana ga zai wa Baffa magana a aura ma sa Nkiru kawai tunda Malamai sun ce zai iya aurenta ko da ba ta musulunta ba. Hakan ya sa watarana da ya zo gida ya samu Baffa da maganar. Baffa da ya ji maganar sai da ya ƙware da ruwan da ya ke sha. "Baffa ina son ta, ka ga idan na aure ko shekara ba za ayi ba na tabbata za ta musulunta ka ga na yi jihadi kenan" "Tashi ka bani waje" "Baffa.." "Tashi na ce" haka Muntari ya tashi simi-simi ya fita yana ƙunƙuni. Ganin bai samu kan Baffa ba ne ya sa shi komawa kan Goggo akan ta taimaka ta yiwa Baffa magana. Haka dai Goggo ta ji maganganun sa banbaraƙwai. Amma ta san halin Muntarin na taurin kai dan haka ta ce "yo kai Muntari yarinyar nan fa ba wanda ya isa ya ma ta auren dole a gidan nan ko da kuwa musulunta ta yi. Ka cigaba da jawota zuwa musulunci ƙila idan da rabo sai ta amsa ka ga sai a zo ayi maganar aure amma yanzu kam na san ba wanda zai yarda ma ka, kuma ina tabbatar ma ka da idan Iya ta ji maganar nan sai kashin Mary ya bushe a gidan nan" Da wannan ya sa ya chanja tunani ya ajiye maganar. Ya cigaba da kyautatawa Nkiru shi a ganin sa hakan zai sa ta ji son musulunci. Duk abunda ake yi T J bai sani ba dan ko da ya dawo ba wanda ya ma sa maganar abinda Muntari ya faɗa. Duk sati biyu ya ke zuwa Ringim ba dan komai ba kuwa sai dan Nkiru. Shi kam yanzu ya amince da maganar Eze, ko da kuwa a da yana son ƙaryata hakan to yanzu kam duk jikinsa ya amsa da soyayyar Nkiru. Kullum addu'ar shi Allah ya kawo ma sa mafita kafin ya ƙare masters ɗin sa Baffah ya tuntuɓeshi da maganar aure. Baya ganin zai iya juran auren wata mace idan ba Nkiru ba duk da kuwa ya san hakan ba mai yiwuwa ba ne... A haka dai lokaci yai ta tafiya har ta kai watan Nkiru goma a garin Ringim. Ba tareda wani ya tursasata ba, ita da kan ta ta ji son wannan addini, tun lokacin Azumi addinin ya fara burgeta. Yadda Goggo ke tashi tana sallar dare a goman ƙarshe abun ya tsaya ma ta a rai, gashi bauta ta ke yi amma ba hayaniya ba tashin hankali. Ta kan tambayi T J ko su Malam Abdullahi akan addinin musulunci kuma a hankali ta fara ganin girman wannan addini. Akwai abubuwa da su ka shige ma ta duhu shiyasa tun da jimawa ba ta gama amincewa da addinin ba amma a hankali komai ya fara warwarewa. Kullum tana addu'an idan addinin T J ne gaskiya Allah ya sa ta ji tana son addinin. Kuma yadda T J ke fassara ma ta wa su ayoyi hakan ya ƙara sa ma ta sha'awar wannan addini. Wata ranan Jummu'ah ta samu Goggo da ta idar da sallar la'asar ta ce tana so ta koya ma ta sallah. Goggo ba ta gama fahimtar maganarta ba dan haka ta sa aka kira ma ta Pendo dan ta ma ta bayani da kyau. Da Pendo ta zo ta sake maimaita zancenta. Pendo ta yiwa Goggo bayani Goggo ta ɗau Kabbara tana faɗin "ki tambayeta tana son musulunta ne? Tana son yin addini kamar na mu?" Duk tambayar da aka ma ta sai ta ce eh. Goggo ta sa aka nemo ma ta Baffah inda Nkiru ta sake maimaita sha'awarta na son karɓan musulunci. A yammacin ranan aka kai ta gaban malami inda ta karɓi kalmar shahada. Zo ka ga murna a wajen 'yan gidan su T J, wanda ke ƙyamatarta a da yanzu su ne su ke ta jan ta a jiki suna ta rungumarta. Daren ranan kuwa Muntari ya dira a gidan, a bakin Iya ya ke jin wai Boɗɗiyon Tijjani ta musulunta. Ita har da ƙarawa da cewa " ni ban yarda musulunta ta yi ba, yaudara ce kawai irin ta Arna" Shi kam Muntari jin maganar Iya ya sa wani sanyi ya shigeshi lokaci guda, bai san ma sanda ya tashi ya bar ɗakin ba ya nufi ɗakin Goggo. Sai dai da Goggon da Nkirun ba sa ɗaki ya tambayi Asma'u ta ce ba ta san inda su ka je ba. Ɗakin Baffah ya wuce dan ya samu abunda ya jima yana muradi, maganar Goggo ta tabbata, yanzu da Nkiru ta musulunta babu mai aibanta auran su. Yana zuwa kuwa ya ci sa'a Baffan na ɗaki " Baffa maganar kwanakin baya ne na zo da ita" "Wacce magana kenan?" "Auren Mary" "Maryam" Baffah ya gyara ma sa "Yawwa auren Maryam"... *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *9-good news* Bismillahir Rahmanir Rahim Karatu Maryam ta ke babu kama hannun yaro. Yanzu kam tunda aka rufe wannan case ɗin nan ta cire rai da samun soyayyar Iya. Matar ta tsaneta to the core dan haka itama ta kama kan ta, ko sun je Ringim ba ta ko shiga ɗakinta. Sau ɗaya da ta yi ƙoƙarin shiga ta gaisheta daga bakin ƙofa Iya ta wurgeta da mafifici hakan ya sa ta fita da sauri. Tun lokacin ko kallo ƙofar ɗakin Iya ba ta yi. Ita Iya yanzu ba ta da abokiyar gaba a duniya irin Maryam. Tunda Maryam ta zo gidan su komai ya lalace, Baffah har ya rasu fishi ya ke da ita saboda ta ƙi karɓan Maryam hannu bibbiyu. Ga uwa uba Muntari da har yau ba ta ji ɗuriyar sa ba tunda ya ce zai je Lagos. Ga uwa uba irin zagin da sarakanan ta su ka ma ta duk dan akan Maryam ɗin. Wai ace saboda Maryam Inyamura ɗan ta ya bar gida ya ƙi dawowa ba abinda ya fi wannan ci ma ta tuwo a ƙwarya. Babban damuwarta shine yanda har yanzu shiru ba ta samu ciki ba. Goggo kan ce ma ta haihuwa lokaci ne idan Allah ya nufa lokacinta yai za ta samu. Itama ba ta haifi Ruma ba sai da ta yi shekara huɗu da marigayi mijinta. Ko 'ya'ya ukun da ta haifa da Baffah haka ta haifesu da ratan shekara hurhuɗu ba plannning ba komai. A ɓangaren T J ma yana son ganin Maryam ta samu ciki ko dan hankalinta ya kwanta to amma Allah ke ba da haihuwa. Sadiq kam yau lafiya gobe ba lafiya ne, ita kan ta Hajjo rashin lafiyar Sadiq ɗin ya sa ta ɗan yi hankali kaɗan. T j ya zaunar da ita ya ma ta bayanin ciwon Sadiq tareda gaya ma ta matuƙar su ka cigaba da zama za ta iya haihuwan 'ya'ya ma su irin lalurar sa. Ya ce ma ta zai sawwaƙa ma ta idan ya so sai ya karɓi Sadiq ɗin shi da Maryam za su raine shi, idan yana da tsawon rai to idan kuma ba mai zama ba ne duk ƙaddarar da Allah ya rubuta ma sa za su amsa hannu bibbiyu. Amma fir Hajjo ta ƙi karɓan wannan shawara. Ita ba abinda ta ke gani irin ƙasƙanci ne T J ya saketa ya cigaba da zama da Maryam ƙabila wai har ma Maryam ce za ta reni ɗan da ta sha wahala ta haifa. Ta ce ko za su haifi irin Sadiq goma ne ba za ta rabu da shi ba. Tsoron fushin Iya ya sa bai sawwaƙa wa Hajjo ba, yana lallaɓata ne ƙila idan ta amince su rabun Iya ba za ta ji haushi ba sai dai da Hajjon da Iyan duk sammakal. Abinda ake nuna mu su daban, abinda su ke dubawa daban. Shekaran Sadiq biyu da wata biyar ya rasu. Ba T J da Hajjo kaɗai ba hatta Maryam ta ji mutuwar yaron nan dan tana son sa sosai. Shi ya fara kiranta da sunan Uwa a duniya "Ama" haka ya ke kiranta. A da Hajjo ba ta bari ta taɓa ma ta shi amma tun wani rana da ciwon sa ya tashi T J baya gari ta ga Maryam ne ta tsaya ma ta har aka kaishi asibiti aka yi komai sai ta janye takunkumin da ta sa, ta fara barin Maryam na riƙe yaron a hankali har yaron ma ya fi sabawa da Maryam ɗin. Maryam yadda ta ke son yaron ita ne yi ma sa wanka, wanke kayan sa. Tsabar samun guri ko yana wajen Hajjo yai kashi indai Maryam na nan haka za ta kawo wa Maryam ta ce ga ɗan ta yayi kashi, Maryam ta karɓeshi ta ma sa tsarki ta gyara shi. Ranan da ta fara gwada goyonsa kasa tashi ta yi ta zauna a bakin gado tana nan jijjiga shi, tana tsoron ƙila idan ta tashi faɗowa zai yi. A haka T J ya dawo ya sameta yai ta mata dariya daga baya daya ga ta yi fishi sai ya ce ma ta ta tashi ba abinda zai samu Sadiq. Sai da ta miƙe ta sa hannu ta baya incase ta ji zai faɗo ta taro shi shi kuma ya kama hannunta yana murmushi. "See ba zai faɗo ba" Sai kuma ta fashe da dariya. TJ ya kissing goshinta ya ce "Insha Allahu ke ma naki na zuwa"... Lokacin rasuwan Sadiq saura ma ta sati ɗaya ta fara jarrabawarta na ƙarshe a makaranta. Ta dai yi jarrabawan ne kawai amma har lokacin mutuwar yaron bai saketa ba musamman da Inna Saratu ta zo mu su ta'aziyar ta dinga habaici tana referring mutuwar Sadiq da cewa "cinyeshi aka yi" Iya kam ba ta zo ba duk da kuwa Alhaji Isa ya ba su damar su je Zaria su yi ta'aziya. Bayan anyi ukun yaron kowa ya watse amma Inna Saratu sai da ta tsaya ta ƙara kusan sati biyu wai tana kula da Hajjo. Kasancewarta matar aure yasa ta nemi yin Service na ta a Kaduna kuma ta samu. Da farko cikin Kaduna ta ke PPA ɗinta T J ya ce bai yarda ba dole ta kuma neman alfarma aka dawo da ita Zaria. Zaman na su dai gwanin sha'awa ranakun girkinta tana samun kulawa sosai wajen T J haka itama tana ajiye duk wani kishi ta tarairayi mijinta. Ba ta da matsala da Hajjo daya wuce baƙar ƙazantar ta wanda har yau ta kasa ɗaukan gyara, ita har mamaki ta ke yi yadda za ta ga ta wuni ba ta yi wanka ba sai zani kaɗai da za ta dinga yawo da shi. Idan ta yi wanka da safe to T J na ɗakinta ne nan ma ta tabbata T J ke matsa ma ta takeyi. Amma indai ba ranan girkinta ba ne to sai yamma ta ke wanka wani lokaci ma haka ta ke kwana ba tareda ta yi wankan ba. Ko lokacin zafi da Maryam ke wanka so goma da ashirin a rana ita Hajjo da ƙyar ta ke yin biyu. Haihuwa ɗaya amma ta lalace. Ko Maryam da ta girmeta ba ta yi tsufan da Hajjo ta yi ba kuma a hakan ba ta cika shekara ishirin ba har yanzu, dan tana shekara shabiyar T J ya aureta. Wasa-wasa sai gashi Maryam ta ƙare bautar ƙasarta. Watarana da safe Maryam na soya doya da ƙwai a kitchen saboda ita ke da girki sai ga Hajjo ta fito daga ɗaki da gudu ta shige banɗaki tana kela amai. Bayan ta fito ne Maryam ta fara ma ta sannu saboda ta ji yadda ta ke ta ƙaƙarin aman kaman za ta amayar da kayan cikinta. "Sannu Hajjo, ba ki da lafiya ne dama?" Hajjo ta fara shafa cikinta tana ɗaɗɗaga hanci ta ce "ƊanBaba baya son ƙarnin ƙwai" Maryam ba ta gane hausarta ba tace "waye ƊanBaba?" "Sai ki yi kuma ai 'yar baƙin ciki. To ni dai ba zan ci soyayyen ƙwai ba ki min wani abun mai ɗan romo-romo" Ta wuce ɗakinta tana tura ciki. Wani abu ya daki zuciyar Maryam. "Ciki" ta furta a fili. Da ƙyar ta samu ta ƙarisa soya doyan da ta ke ta kwashe ko tattara wajen ba ta yi ba ta wuce ɗakinta. Gado kawai ta hau ta kwanta. "Kenan ni ne ba na haihuwa" ta furta hawaye na gangaro ma ta. T J ya buɗe ƙofa ya shigo, tuntuni ya shirya yana ɗakinsa yana marking assignment ɗin ɗalibai. Daya gama ne ya fito dan ya karya kafin ya wuce school, rashin ganin Maryam a falo da kitchen ya sa shi shigowa ɗakinta. "Dear are you Ok?" Ya tambaya yana taɓa goshinta. "Hajjo na da ciki" ta faɗa tana kallon sa "Ya Ilahi! Ashe ban faɗa miki ba. About three weeks ago ta ce min ba ta da lafiya shine na raka ta asibiti aka ce ciki gareta. Ni dai Addu'a na Allah ya sa ba SS ba ne, ba na son 'ya'ya na su yi wahala kaman na Sadiq" Ido kawai ta zuba mishi tana kallon yadda yake koro bayanai. "Indai ta haihu aka samu AS inaga planning za ta yi mu raini abin da ta haifa" "Saboda kar na cinye muku baby tun bai zo duniya ba shine ake ɓoye min cikin?" "Subhanallahi! Maryam wani irin magana ne wannan? You know that's not true. Wallahi mantawa na yi" "Mantuwa? Barkindo Mantuwa? For three weeks ka san cewa matarka tana da ciki amma ka manta ba ka gaya min ba. You are not good at lying dan haka kar ka fara. Ba ka son gaya min saboda ni mayya ce zan kama kurwan ɗan ku" "Innalillahi. Maryam please..." Ranan kam duk yadda ya so ya fahimtar da Maryam mantuwa yai ba ta saurareshi ba. Da shi da ita ɗin ba wanda ya yi breakfast. Da rana da ya dawo ma dai abun duk ɗaya ne. Kusan sati tayi tana fushi dashi. Abunda ya lura shine ba wai dan bai faɗa ma ta bane kaɗai dalilin fushin na ta har da stigma na rashin haihuwa da ba ta yi ba har yanzu. A haka dai yai ta lallaɓata har su ka shirya gaba ɗaya. Ranan da su ka shirya ma saboda albishir daya kawo ma ta ne na form daya siya ma ta na Law school da ke Abuja. Yana ma ta Albishir ɗin ta yi tsalle ta rungumeshi har da bashi sweet kiss a lips ɗin sa, daga ranan kuma faɗan su ya zo ƙarshe... Ana gobe Maryam za ta je Abuja yin registration aka turowa T J letter cewa ƙanin Kakan sa wato Alhaji Isa ya rasu. Wannan ya sa Maryam ce kaɗai ta tafi Abuja shi kuma ya wuce Ringim. Kwana ɗaya yai Washegari ya dawo saboda ayyuka da su ke gaban shi. Bayan komai ya kammala Maryam ta fara karatu a Abuja, ɗaki T J ya kama ma ta ya biya hayan shekara ɗaya har ta gama Law school ɗin. Sunyi akan zai dinga zuwa ma ta duk weekend idan ya samu sarari ko ba weekend ba ya ce zai dinga leƙo ta. Cikin Hajjo na wata takwas Inna Saratu ta zo ta ɗauketa wai za ta yi haihuwan gida. Ita anata nufin wai za ayiwa Hajjo da abunda za ta haifa maganin Mayu saboda kar Maryam ta kama kurwan su. Shi dai T J tunda ta ce Iya ma ta amince da tafiyar ya ce Allah ya kai su gida lafiya. Da ya san abinda ake shirin yi kenan da ko Iyan ce ta zo da kanta ba zai bari Hajjo ta bi ta ba. Shi dai tunda ta tafi ya ke addu'ar Allah ya sa ta haihu lafiya kuma a samu AS ba SS ba. Hajjo kam tunda su ka tafi ƙauyen su ake ta ɗura ma ta jiƙe-jiƙe ana ma ta hayaƙi. Da farko ta nuna ba ta so amma Innarta ta ce ba ta isa ba dan ba zai yiwu ta dinga haihuwa Maryam na cinye 'ya'yan ba. Yadda T J ke da dukiya ya kamata ace ta haifa ma sa 'ya'ya dayawa, idan kuma duk su ka mutu ai ta tashi a tutar babu kenan. Da haka Hajjo ta yi shiru aka cigaba da magani. Ta dawo daga class a gajiye sai taga ƙofar ɗakinta a buɗe ta shiga da sauri dan jiya-jiya T J ya bar Abuja ya koma Zaria. "Lafiya ka zo?" Ta faɗa a ɗan tsorace bayan ta ganshi zaune yana rubutu. Ya taso ya rungumeta ya ce "jiya na yi mafarki mai daɗi shine na ka sa haƙuri na ce dole na zo na baki labari, kinga kema sai ki sa cikin addu'ar ki" "My Love za ka sa heart attack ya kama ni. You should've waited zuwa wani weekend ɗin idan ka zo sai ka gaya min mafarkin ai" Ya girgiza kai yana ƙoƙarin cire ma ta gyalenta "Baby Idan mafarkin nan ya tabbata i'll be the happiest man on earth" Jin hannunsa a ƙugunta yana shirin since zaninta ya sa ta yi dariya ta sa hannunta ta zagaye wuyansa ta ce " gaya min gaskiya. Labarin mafarki ne ya kawoka ko kuma wani abun daban?" "Labarin mafarki mana, amma zan fi jin daɗin ba da labarin idan na..." Ya kai baki zai kissing ɗinta ta sa hannu ta tare bakin " Love za ka barni na yi karatun nan kuwa. Karatun fa akwai wahala and you're not helping" Ya janye hannunta ya manna ma ta light kiss ya ce "mu je na baki laƙanin riƙe karatu" Ta yi dariya ta ce " I love you Shehu Tijjani" "Wayyo zuciyata" ya faɗi yana dafe ƙirjinsa ta kai ma sa dundu ya riƙe hannun ya jawota ta faɗa jikinsa. "Allah ya sa mafarkin da na yi ya tabbata" "Wani irin mafarki ne wannan?" "Wai kin haifa min Cute Princess mai kamar ki" Ta yi murmushi dan harga Allah ta ji daɗin maganar da ya ce. "Amin" ta furta ƙasa-ƙasa. Kan katifar ɗakin ya mu su masauki yana faɗin ƙila Allah ya basu Princess yau... Kwana tara da fara magani wata yammacin ranan Talata Hajjo ta fara ciwon ciki bayan ta sha jiƙon da aka ba ta. Wasa-wasa ciwon cikin ya tsanan ta daga baya sai naƙuda gadan-gadan aka kira wata Tsohuwa ungozoma. Ba ƙaramin wahala Hajjo ta sha ba kafin nan ta haihu amma ɗan ba rai dan har kaman ya fara ruɓewa alaman ya kwana biyu da mutuwa. Tun kwana uku da su ka wuce ta dena jin motsin cikinta amma ba ta faɗa ba. Hajjo ta yi kuka sosai dan ko rasuwan Sadiq iya kaci. Ita kan ta yarda magungunan da ta ke ta ɗirkawa ne ya kashe ma ta ɗanta tunda lafiya-lafiya ta bar Zaria. A ranan aka aika Ringim su kuma su ka tura wasiƙa zuwa Zaria. Wasiƙar ba ta isa ga T J ba sai washegari. Shima ya ji mutuwar a jikinsa sosai. A ranan da ya je Ringim ya ke jin labarin komai dan an taho da Hajjo Ringim, ya kuwa zage ya zuzzubawa Hajjo da Innarta masifa. Ya kuma furta kalmar da ta girgiza Hajjon da Innar na ta "Duk ranan da aka ƙara kawo maganin Maita ko aka kira wani mai Magani wa Hajjo a bakin aurenta. Idan ba za ta iya zama da ni ba ta karɓi ƙaddararta zan iya sawwaƙa ma ta tun yanzu" yadda yai ta faɗa sai da Goggo ta sa baki yai shiru. Abun takaicin ma ko gawar ɗan sa bai gani ba. Daga Ringim straight Abuja ya wuce ko da wuni ɗaya ne gara ya je ya ga Maryam dan ya san yadda ya ke jin sa ita kaɗai ce za ta iya kwantar ma sa da hankali. Itama ba ta ji daɗin mutuwar ɗan Hajjo ba, ta kuma ƙara tabbatarwa kan ta lallai ba ƙaramin Jahilci ke damun Hajjo da mahaifiyarta ba. Sun Jahilci zamani kuma sun Jahilci addini... A wasu lokutan da Inna ta kawowa Iya ziyara ne ta zugata akan ta je ta zauna a gidan T J dan ta rinƙa kula da Hajjo idan ba haka ba kuwa Yadda Maryam ta shanye T J ba za ta bari ya haihu da kowa ba tunda gashi har sau biyu tana kashewa Hajjo 'ya'ya. Iya ta san ba Maryam ce ke kashe 'ya'yan Hajjo ba amma kuma tsanar Maryam ya sa ta hau kan maganar. Sati biyar da Hajjo ta yi a gida da za ta koma Zaria sai gashi Iya ta tattara kaya itama su ka yi tafiyar tare. T J ya shiga ruɗu lokacin da Iya ta ce za ta zauna da su na wani lokaci. Ba yadda ya iya haka ya tattara kayan ɗakin sa ya kai ɗakin Maryam ya bar wa Iya ɗakin sa. Bayan kwana biyu da Iya ba ta ga Maryam a gidan ba ne ta tambayi Hajjo ina Maryam ta ke Hajjo ta ce ma ta wai karatu ta ke yi a Habuja. T J na dawowa ta haushi da faɗa wai ya ɗaurewa Maryam gindi ta tafi yawon karuwanci. "Karatu ta tafi Iya kuma na shekara ɗaya ne kawai" "Karatun Uwar ka. Mata ta tafi karuwanci ka ce ta je karatu. Wani irin karatune daya ƙi ci ya ƙi cinyewa shekara da shekaru. Daɗin abin ma ba ta haihuwa balle aje a ɗauko ɗan shege a kawo maka gida. Allah dai ya shirya" Ransa ya sosu da maganar Iya amma ba abinda zai ce haka yai shiru ya barta ta yi ta masifa har ta gaji ta yi shiru. Zuwan su Iya ya sa ya rage kaiwa Maryam Ziyara. Maryam ba ta kawo komai ba dan ta ɗauka yana ba ta space ne dan ta samu ta yi karatu sosai. Bai gaya ma ta Iya ta dawo gidan sa da zama ba dan baya so hankalinta ya tashi , yana jiran perfect time ne da zai gaya ma ta wanda ba za ta ɗaga hankalinta sosai ba. Cikin 'yan kwanakin nan kuwa ba ta ma jin daɗi, duk safiya sai sanyi ya dameta kuma ba lokacin sanyi ake ba. Ga yawan kasala da ta ke ji, ita da ta ke da kazar-kazar ɗin aiki sai gashi sai ta wuni ba ta assasa komai a ɗakin ba harta wanka sai da ta fara ƙiwuyar sa idan ta yi da safe shikenan sai kuma washe gari. Ranan su na fitowa daga class sai hajijiya ya kamata da ƙyar ta dafa bango ta samu guri ta zauna. Yanayin jikin na ta da ta ke jin chanji ya sa ta je Asibiti dan ta tari ciwon tun kafin ya zo ya hanata karatu. Tun daga amsoshin tambayoyin da ta bawa likita ya ce alkhairi ne amma za a ma ta test dan a tabbatar. Aikuwa gwajin farko result ya nuna ciki gareta. Kuka sosai ta fara a office ɗin Likita lokacin daya bayyana ma ta sakamakon gwajin. "Doctor seven years, one month, nine days da aure na" Likitan wanda Musulmine ya ce " ki godewa Allah. Shi ke bayar wa a lokacin da ya so a kuma wanda ya so. Wasu ma su kan samu shekaru fiye da naki kamin Allah ya karɓi addu'an su" With full excitement ta je gida tana tunanin yadda za ta faɗawa T J and how he'll react. Ta sa a ranta sai ya zo za ta faɗa ma sa amma kafin washegari ta chanja shawara. Har gida za ta je ta surprising ɗin sa. Daren ranan ba ta iya barcin kirki ba, motsi kaɗan ta shafa cikinta zuwa maranta tana murmushi. Ranan Alhamis tana dawowa daga Class ta wuce park sai Zaria. Da murna ta nufi gidan ta dan ta san war haka T J na gida. Da sallama ta shiga falonsu fiskarta ɗauke da murmushi amma ganin wanda ke falon ya sa murmushin ya kafe. Iya ce zaune a falon tana kallo tana cin tuwo sai suɗe hannu ta ke yi. "An wuni lafiya" ta furta ranta a ɓace Iya ta ce "An gaji da karuwancin ne aka dawo?" Ba ta tanka ma ta ba ta wuce ɗakin ta. Ganin kayan T J a ɗakin ya sa ta tabbatar Iya ta kwana biyu a gidan. Ta zauna bakin gado tana jin zuciyarta na ma ta zafi. Duk wani excitement da ta ke tattare da shi ya washe. Iya a gidan su kuma T J bai gaya ma ta ba. Ganin zamanta na Iya kawo ɓacin rai ya sa kawai ta ɗau jakarta ta fita. Gara ta koma inda ta fito ko hankalinta zai kwanta dan idan ta ce za ta kwana a gidan baƙin ciki da takaici kawai za ta sha. Ba ta samu motan Abuja ba ma sai kusan ƙarfe takwas na dare. Ita dai ko ƙarfe shabiyun dare ne ta sa a ranta za ta tafi. T J kam tunda Iya ta fara zama a gidansa ya fara daɗewa a waje. Wani lokaci ƙarfe goma koma fiye ya ke dawowa, idan ya dawo da wuri to ƙarfe tara ne. Bai san da zuwan Maryam ba sai washegari da Iya ke masifar wai wuyan Maryam yayi ƙauri ta zo ko zama ba ta yi ba ta kuma tafiya wani yawon. Ya sha mamakin wai Maryam ta zo daga baya ya ce bari ya je kawai ya dubata ko lafiya ta zo gida... As usual haƙurin nan dai da ya saba bayarwa shi ya ke ta ba ta akan rashin sanar da ita gameda zuwan Iya. Duk yadda ta ke son yi mishi Albishir haushin da ta ke ji ya sa ta ja bakinta ta yi shiru. Ƙarshe haka ya tafi ba tareda ta gaya ma sa ba. Bayan sati biyu da ya zo lokacin ta ɗan sakko shine ta nuna ma sa result ɗin test ɗin da aka ma ta. "Dear shi ne ba ki da lafiya ba za ki gaya min ba" Ya maida duban sa ga takardar yana karantawa. Ya ɗago ido ya kalleta ya sake kallon takardar sai kuma ya challa ihu yana " Maryam da gaske?" Ta gyaɗa ma sa kai. "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah. Muah muah muah" ya shiga kissing ɗinta ta ko'ina. *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *9-good news* Bismillahir Rahmanir Rahim Karatu Maryam ta ke babu kama hannun yaro. Yanzu kam tunda aka rufe wannan case ɗin nan ta cire rai da samun soyayyar Iya. Matar ta tsaneta to the core dan haka itama ta kama kan ta, ko sun je Ringim ba ta ko shiga ɗakinta. Sau ɗaya da ta yi ƙoƙarin shiga ta gaisheta daga bakin ƙofa Iya ta wurgeta da mafifici hakan ya sa ta fita da sauri. Tun lokacin ko kallo ƙofar ɗakin Iya ba ta yi. Ita Iya yanzu ba ta da abokiyar gaba a duniya irin Maryam. Tunda Maryam ta zo gidan su komai ya lalace, Baffah har ya rasu fishi ya ke da ita saboda ta ƙi karɓan Maryam hannu bibbiyu. Ga uwa uba Muntari da har yau ba ta ji ɗuriyar sa ba tunda ya ce zai je Lagos. Ga uwa uba irin zagin da sarakanan ta su ka ma ta duk dan akan Maryam ɗin. Wai ace saboda Maryam Inyamura ɗan ta ya bar gida ya ƙi dawowa ba abinda ya fi wannan ci ma ta tuwo a ƙwarya. Babban damuwarta shine yanda har yanzu shiru ba ta samu ciki ba. Goggo kan ce ma ta haihuwa lokaci ne idan Allah ya nufa lokacinta yai za ta samu. Itama ba ta haifi Ruma ba sai da ta yi shekara huɗu da marigayi mijinta. Ko 'ya'ya ukun da ta haifa da Baffah haka ta haifesu da ratan shekara hurhuɗu ba plannning ba komai. A ɓangaren T J ma yana son ganin Maryam ta samu ciki ko dan hankalinta ya kwanta to amma Allah ke ba da haihuwa. Sadiq kam yau lafiya gobe ba lafiya ne, ita kan ta Hajjo rashin lafiyar Sadiq ɗin ya sa ta ɗan yi hankali kaɗan. T j ya zaunar da ita ya ma ta bayanin ciwon Sadiq tareda gaya ma ta matuƙar su ka cigaba da zama za ta iya haihuwan 'ya'ya ma su irin lalurar sa. Ya ce ma ta zai sawwaƙa ma ta idan ya so sai ya karɓi Sadiq ɗin shi da Maryam za su raine shi, idan yana da tsawon rai to idan kuma ba mai zama ba ne duk ƙaddarar da Allah ya rubuta ma sa za su amsa hannu bibbiyu. Amma fir Hajjo ta ƙi karɓan wannan shawara. Ita ba abinda ta ke gani irin ƙasƙanci ne T J ya saketa ya cigaba da zama da Maryam ƙabila wai har ma Maryam ce za ta reni ɗan da ta sha wahala ta haifa. Ta ce ko za su haifi irin Sadiq goma ne ba za ta rabu da shi ba. Tsoron fushin Iya ya sa bai sawwaƙa wa Hajjo ba, yana lallaɓata ne ƙila idan ta amince su rabun Iya ba za ta ji haushi ba sai dai da Hajjon da Iyan duk sammakal. Abinda ake nuna mu su daban, abinda su ke dubawa daban. Shekaran Sadiq biyu da wata biyar ya rasu. Ba T J da Hajjo kaɗai ba hatta Maryam ta ji mutuwar yaron nan dan tana son sa sosai. Shi ya fara kiranta da sunan Uwa a duniya "Ama" haka ya ke kiranta. A da Hajjo ba ta bari ta taɓa ma ta shi amma tun wani rana da ciwon sa ya tashi T J baya gari ta ga Maryam ne ta tsaya ma ta har aka kaishi asibiti aka yi komai sai ta janye takunkumin da ta sa, ta fara barin Maryam na riƙe yaron a hankali har yaron ma ya fi sabawa da Maryam ɗin. Maryam yadda ta ke son yaron ita ne yi ma sa wanka, wanke kayan sa. Tsabar samun guri ko yana wajen Hajjo yai kashi indai Maryam na nan haka za ta kawo wa Maryam ta ce ga ɗan ta yayi kashi, Maryam ta karɓeshi ta ma sa tsarki ta gyara shi. Ranan da ta fara gwada goyonsa kasa tashi ta yi ta zauna a bakin gado tana nan jijjiga shi, tana tsoron ƙila idan ta tashi faɗowa zai yi. A haka T J ya dawo ya sameta yai ta mata dariya daga baya daya ga ta yi fishi sai ya ce ma ta ta tashi ba abinda zai samu Sadiq. Sai da ta miƙe ta sa hannu ta baya incase ta ji zai faɗo ta taro shi shi kuma ya kama hannunta yana murmushi. "See ba zai faɗo ba" Sai kuma ta fashe da dariya. TJ ya kissing goshinta ya ce "Insha Allahu ke ma naki na zuwa"... Lokacin rasuwan Sadiq saura ma ta sati ɗaya ta fara jarrabawarta na ƙarshe a makaranta. Ta dai yi jarrabawan ne kawai amma har lokacin mutuwar yaron bai saketa ba musamman da Inna Saratu ta zo mu su ta'aziyar ta dinga habaici tana referring mutuwar Sadiq da cewa "cinyeshi aka yi" Iya kam ba ta zo ba duk da kuwa Alhaji Isa ya ba su damar su je Zaria su yi ta'aziya. Bayan anyi ukun yaron kowa ya watse amma Inna Saratu sai da ta tsaya ta ƙara kusan sati biyu wai tana kula da Hajjo. Kasancewarta matar aure yasa ta nemi yin Service na ta a Kaduna kuma ta samu. Da farko cikin Kaduna ta ke PPA ɗinta T J ya ce bai yarda ba dole ta kuma neman alfarma aka dawo da ita Zaria. Zaman na su dai gwanin sha'awa ranakun girkinta tana samun kulawa sosai wajen T J haka itama tana ajiye duk wani kishi ta tarairayi mijinta. Ba ta da matsala da Hajjo daya wuce baƙar ƙazantar ta wanda har yau ta kasa ɗaukan gyara, ita har mamaki ta ke yi yadda za ta ga ta wuni ba ta yi wanka ba sai zani kaɗai da za ta dinga yawo da shi. Idan ta yi wanka da safe to T J na ɗakinta ne nan ma ta tabbata T J ke matsa ma ta takeyi. Amma indai ba ranan girkinta ba ne to sai yamma ta ke wanka wani lokaci ma haka ta ke kwana ba tareda ta yi wankan ba. Ko lokacin zafi da Maryam ke wanka so goma da ashirin a rana ita Hajjo da ƙyar ta ke yin biyu. Haihuwa ɗaya amma ta lalace. Ko Maryam da ta girmeta ba ta yi tsufan da Hajjo ta yi ba kuma a hakan ba ta cika shekara ishirin ba har yanzu, dan tana shekara shabiyar T J ya aureta. Wasa-wasa sai gashi Maryam ta ƙare bautar ƙasarta. Watarana da safe Maryam na soya doya da ƙwai a kitchen saboda ita ke da girki sai ga Hajjo ta fito daga ɗaki da gudu ta shige banɗaki tana kela amai. Bayan ta fito ne Maryam ta fara ma ta sannu saboda ta ji yadda ta ke ta ƙaƙarin aman kaman za ta amayar da kayan cikinta. "Sannu Hajjo, ba ki da lafiya ne dama?" Hajjo ta fara shafa cikinta tana ɗaɗɗaga hanci ta ce "ƊanBaba baya son ƙarnin ƙwai" Maryam ba ta gane hausarta ba tace "waye ƊanBaba?" "Sai ki yi kuma ai 'yar baƙin ciki. To ni dai ba zan ci soyayyen ƙwai ba ki min wani abun mai ɗan romo-romo" Ta wuce ɗakinta tana tura ciki. Wani abu ya daki zuciyar Maryam. "Ciki" ta furta a fili. Da ƙyar ta samu ta ƙarisa soya doyan da ta ke ta kwashe ko tattara wajen ba ta yi ba ta wuce ɗakinta. Gado kawai ta hau ta kwanta. "Kenan ni ne ba na haihuwa" ta furta hawaye na gangaro ma ta. T J ya buɗe ƙofa ya shigo, tuntuni ya shirya yana ɗakinsa yana marking assignment ɗin ɗalibai. Daya gama ne ya fito dan ya karya kafin ya wuce school, rashin ganin Maryam a falo da kitchen ya sa shi shigowa ɗakinta. "Dear are you Ok?" Ya tambaya yana taɓa goshinta. "Hajjo na da ciki" ta faɗa tana kallon sa "Ya Ilahi! Ashe ban faɗa miki ba. About three weeks ago ta ce min ba ta da lafiya shine na raka ta asibiti aka ce ciki gareta. Ni dai Addu'a na Allah ya sa ba SS ba ne, ba na son 'ya'ya na su yi wahala kaman na Sadiq" Ido kawai ta zuba mishi tana kallon yadda yake koro bayanai. "Indai ta haihu aka samu AS inaga planning za ta yi mu raini abin da ta haifa" "Saboda kar na cinye muku baby tun bai zo duniya ba shine ake ɓoye min cikin?" "Subhanallahi! Maryam wani irin magana ne wannan? You know that's not true. Wallahi mantawa na yi" "Mantuwa? Barkindo Mantuwa? For three weeks ka san cewa matarka tana da ciki amma ka manta ba ka gaya min ba. You are not good at lying dan haka kar ka fara. Ba ka son gaya min saboda ni mayya ce zan kama kurwan ɗan ku" "Innalillahi. Maryam please..." Ranan kam duk yadda ya so ya fahimtar da Maryam mantuwa yai ba ta saurareshi ba. Da shi da ita ɗin ba wanda ya yi breakfast. Da rana da ya dawo ma dai abun duk ɗaya ne. Kusan sati tayi tana fushi dashi. Abunda ya lura shine ba wai dan bai faɗa ma ta bane kaɗai dalilin fushin na ta har da stigma na rashin haihuwa da ba ta yi ba har yanzu. A haka dai yai ta lallaɓata har su ka shirya gaba ɗaya. Ranan da su ka shirya ma saboda albishir daya kawo ma ta ne na form daya siya ma ta na Law school da ke Abuja. Yana ma ta Albishir ɗin ta yi tsalle ta rungumeshi har da bashi sweet kiss a lips ɗin sa, daga ranan kuma faɗan su ya zo ƙarshe... Ana gobe Maryam za ta je Abuja yin registration aka turowa T J letter cewa ƙanin Kakan sa wato Alhaji Isa ya rasu. Wannan ya sa Maryam ce kaɗai ta tafi Abuja shi kuma ya wuce Ringim. Kwana ɗaya yai Washegari ya dawo saboda ayyuka da su ke gaban shi. Bayan komai ya kammala Maryam ta fara karatu a Abuja, ɗaki T J ya kama ma ta ya biya hayan shekara ɗaya har ta gama Law school ɗin. Sunyi akan zai dinga zuwa ma ta duk weekend idan ya samu sarari ko ba weekend ba ya ce zai dinga leƙo ta. Cikin Hajjo na wata takwas Inna Saratu ta zo ta ɗauketa wai za ta yi haihuwan gida. Ita anata nufin wai za ayiwa Hajjo da abunda za ta haifa maganin Mayu saboda kar Maryam ta kama kurwan su. Shi dai T J tunda ta ce Iya ma ta amince da tafiyar ya ce Allah ya kai su gida lafiya. Da ya san abinda ake shirin yi kenan da ko Iyan ce ta zo da kanta ba zai bari Hajjo ta bi ta ba. Shi dai tunda ta tafi ya ke addu'ar Allah ya sa ta haihu lafiya kuma a samu AS ba SS ba. Hajjo kam tunda su ka tafi ƙauyen su ake ta ɗura ma ta jiƙe-jiƙe ana ma ta hayaƙi. Da farko ta nuna ba ta so amma Innarta ta ce ba ta isa ba dan ba zai yiwu ta dinga haihuwa Maryam na cinye 'ya'yan ba. Yadda T J ke da dukiya ya kamata ace ta haifa ma sa 'ya'ya dayawa, idan kuma duk su ka mutu ai ta tashi a tutar babu kenan. Da haka Hajjo ta yi shiru aka cigaba da magani. Ta dawo daga class a gajiye sai taga ƙofar ɗakinta a buɗe ta shiga da sauri dan jiya-jiya T J ya bar Abuja ya koma Zaria. "Lafiya ka zo?" Ta faɗa a ɗan tsorace bayan ta ganshi zaune yana rubutu. Ya taso ya rungumeta ya ce "jiya na yi mafarki mai daɗi shine na ka sa haƙuri na ce dole na zo na baki labari, kinga kema sai ki sa cikin addu'ar ki" "My Love za ka sa heart attack ya kama ni. You should've waited zuwa wani weekend ɗin idan ka zo sai ka gaya min mafarkin ai" Ya girgiza kai yana ƙoƙarin cire ma ta gyalenta "Baby Idan mafarkin nan ya tabbata i'll be the happiest man on earth" Jin hannunsa a ƙugunta yana shirin since zaninta ya sa ta yi dariya ta sa hannunta ta zagaye wuyansa ta ce " gaya min gaskiya. Labarin mafarki ne ya kawoka ko kuma wani abun daban?" "Labarin mafarki mana, amma zan fi jin daɗin ba da labarin idan na..." Ya kai baki zai kissing ɗinta ta sa hannu ta tare bakin " Love za ka barni na yi karatun nan kuwa. Karatun fa akwai wahala and you're not helping" Ya janye hannunta ya manna ma ta light kiss ya ce "mu je na baki laƙanin riƙe karatu" Ta yi dariya ta ce " I love you Shehu Tijjani" "Wayyo zuciyata" ya faɗi yana dafe ƙirjinsa ta kai ma sa dundu ya riƙe hannun ya jawota ta faɗa jikinsa. "Allah ya sa mafarkin da na yi ya tabbata" "Wani irin mafarki ne wannan?" "Wai kin haifa min Cute Princess mai kamar ki" Ta yi murmushi dan harga Allah ta ji daɗin maganar da ya ce. "Amin" ta furta ƙasa-ƙasa. Kan katifar ɗakin ya mu su masauki yana faɗin ƙila Allah ya basu Princess yau... Kwana tara da fara magani wata yammacin ranan Talata Hajjo ta fara ciwon ciki bayan ta sha jiƙon da aka ba ta. Wasa-wasa ciwon cikin ya tsanan ta daga baya sai naƙuda gadan-gadan aka kira wata Tsohuwa ungozoma. Ba ƙaramin wahala Hajjo ta sha ba kafin nan ta haihu amma ɗan ba rai dan har kaman ya fara ruɓewa alaman ya kwana biyu da mutuwa. Tun kwana uku da su ka wuce ta dena jin motsin cikinta amma ba ta faɗa ba. Hajjo ta yi kuka sosai dan ko rasuwan Sadiq iya kaci. Ita kan ta yarda magungunan da ta ke ta ɗirkawa ne ya kashe ma ta ɗanta tunda lafiya-lafiya ta bar Zaria. A ranan aka aika Ringim su kuma su ka tura wasiƙa zuwa Zaria. Wasiƙar ba ta isa ga T J ba sai washegari. Shima ya ji mutuwar a jikinsa sosai. A ranan da ya je Ringim ya ke jin labarin komai dan an taho da Hajjo Ringim, ya kuwa zage ya zuzzubawa Hajjo da Innarta masifa. Ya kuma furta kalmar da ta girgiza Hajjon da Innar na ta "Duk ranan da aka ƙara kawo maganin Maita ko aka kira wani mai Magani wa Hajjo a bakin aurenta. Idan ba za ta iya zama da ni ba ta karɓi ƙaddararta zan iya sawwaƙa ma ta tun yanzu" yadda yai ta faɗa sai da Goggo ta sa baki yai shiru. Abun takaicin ma ko gawar ɗan sa bai gani ba. Daga Ringim straight Abuja ya wuce ko da wuni ɗaya ne gara ya je ya ga Maryam dan ya san yadda ya ke jin sa ita kaɗai ce za ta iya kwantar ma sa da hankali. Itama ba ta ji daɗin mutuwar ɗan Hajjo ba, ta kuma ƙara tabbatarwa kan ta lallai ba ƙaramin Jahilci ke damun Hajjo da mahaifiyarta ba. Sun Jahilci zamani kuma sun Jahilci addini... A wasu lokutan da Inna ta kawowa Iya ziyara ne ta zugata akan ta je ta zauna a gidan T J dan ta rinƙa kula da Hajjo idan ba haka ba kuwa Yadda Maryam ta shanye T J ba za ta bari ya haihu da kowa ba tunda gashi har sau biyu tana kashewa Hajjo 'ya'ya. Iya ta san ba Maryam ce ke kashe 'ya'yan Hajjo ba amma kuma tsanar Maryam ya sa ta hau kan maganar. Sati biyar da Hajjo ta yi a gida da za ta koma Zaria sai gashi Iya ta tattara kaya itama su ka yi tafiyar tare. T J ya shiga ruɗu lokacin da Iya ta ce za ta zauna da su na wani lokaci. Ba yadda ya iya haka ya tattara kayan ɗakin sa ya kai ɗakin Maryam ya bar wa Iya ɗakin sa. Bayan kwana biyu da Iya ba ta ga Maryam a gidan ba ne ta tambayi Hajjo ina Maryam ta ke Hajjo ta ce ma ta wai karatu ta ke yi a Habuja. T J na dawowa ta haushi da faɗa wai ya ɗaurewa Maryam gindi ta tafi yawon karuwanci. "Karatu ta tafi Iya kuma na shekara ɗaya ne kawai" "Karatun Uwar ka. Mata ta tafi karuwanci ka ce ta je karatu. Wani irin karatune daya ƙi ci ya ƙi cinyewa shekara da shekaru. Daɗin abin ma ba ta haihuwa balle aje a ɗauko ɗan shege a kawo maka gida. Allah dai ya shirya" Ransa ya sosu da maganar Iya amma ba abinda zai ce haka yai shiru ya barta ta yi ta masifa har ta gaji ta yi shiru. Zuwan su Iya ya sa ya rage kaiwa Maryam Ziyara. Maryam ba ta kawo komai ba dan ta ɗauka yana ba ta space ne dan ta samu ta yi karatu sosai. Bai gaya ma ta Iya ta dawo gidan sa da zama ba dan baya so hankalinta ya tashi , yana jiran perfect time ne da zai gaya ma ta wanda ba za ta ɗaga hankalinta sosai ba. Cikin 'yan kwanakin nan kuwa ba ta ma jin daɗi, duk safiya sai sanyi ya dameta kuma ba lokacin sanyi ake ba. Ga yawan kasala da ta ke ji, ita da ta ke da kazar-kazar ɗin aiki sai gashi sai ta wuni ba ta assasa komai a ɗakin ba harta wanka sai da ta fara ƙiwuyar sa idan ta yi da safe shikenan sai kuma washe gari. Ranan su na fitowa daga class sai hajijiya ya kamata da ƙyar ta dafa bango ta samu guri ta zauna. Yanayin jikin na ta da ta ke jin chanji ya sa ta je Asibiti dan ta tari ciwon tun kafin ya zo ya hanata karatu. Tun daga amsoshin tambayoyin da ta bawa likita ya ce alkhairi ne amma za a ma ta test dan a tabbatar. Aikuwa gwajin farko result ya nuna ciki gareta. Kuka sosai ta fara a office ɗin Likita lokacin daya bayyana ma ta sakamakon gwajin. "Doctor seven years, one month, nine days da aure na" Likitan wanda Musulmine ya ce " ki godewa Allah. Shi ke bayar wa a lokacin da ya so a kuma wanda ya so. Wasu ma su kan samu shekaru fiye da naki kamin Allah ya karɓi addu'an su" With full excitement ta je gida tana tunanin yadda za ta faɗawa T J and how he'll react. Ta sa a ranta sai ya zo za ta faɗa ma sa amma kafin washegari ta chanja shawara. Har gida za ta je ta surprising ɗin sa. Daren ranan ba ta iya barcin kirki ba, motsi kaɗan ta shafa cikinta zuwa maranta tana murmushi. Ranan Alhamis tana dawowa daga Class ta wuce park sai Zaria. Da murna ta nufi gidan ta dan ta san war haka T J na gida. Da sallama ta shiga falonsu fiskarta ɗauke da murmushi amma ganin wanda ke falon ya sa murmushin ya kafe. Iya ce zaune a falon tana kallo tana cin tuwo sai suɗe hannu ta ke yi. "An wuni lafiya" ta furta ranta a ɓace Iya ta ce "An gaji da karuwancin ne aka dawo?" Ba ta tanka ma ta ba ta wuce ɗakin ta. Ganin kayan T J a ɗakin ya sa ta tabbatar Iya ta kwana biyu a gidan. Ta zauna bakin gado tana jin zuciyarta na ma ta zafi. Duk wani excitement da ta ke tattare da shi ya washe. Iya a gidan su kuma T J bai gaya ma ta ba. Ganin zamanta na Iya kawo ɓacin rai ya sa kawai ta ɗau jakarta ta fita. Gara ta koma inda ta fito ko hankalinta zai kwanta dan idan ta ce za ta kwana a gidan baƙin ciki da takaici kawai za ta sha. Ba ta samu motan Abuja ba ma sai kusan ƙarfe takwas na dare. Ita dai ko ƙarfe shabiyun dare ne ta sa a ranta za ta tafi. T J kam tunda Iya ta fara zama a gidansa ya fara daɗewa a waje. Wani lokaci ƙarfe goma koma fiye ya ke dawowa, idan ya dawo da wuri to ƙarfe tara ne. Bai san da zuwan Maryam ba sai washegari da Iya ke masifar wai wuyan Maryam yayi ƙauri ta zo ko zama ba ta yi ba ta kuma tafiya wani yawon. Ya sha mamakin wai Maryam ta zo daga baya ya ce bari ya je kawai ya dubata ko lafiya ta zo gida... As usual haƙurin nan dai da ya saba bayarwa shi ya ke ta ba ta akan rashin sanar da ita gameda zuwan Iya. Duk yadda ta ke son yi mishi Albishir haushin da ta ke ji ya sa ta ja bakinta ta yi shiru. Ƙarshe haka ya tafi ba tareda ta gaya ma sa ba. Bayan sati biyu da ya zo lokacin ta ɗan sakko shine ta nuna ma sa result ɗin test ɗin da aka ma ta. "Dear shi ne ba ki da lafiya ba za ki gaya min ba" Ya maida duban sa ga takardar yana karantawa. Ya ɗago ido ya kalleta ya sake kallon takardar sai kuma ya challa ihu yana " Maryam da gaske?" Ta gyaɗa ma sa kai. "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah. Muah muah muah" ya shiga kissing ɗinta ta ko'ina. *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *8-patience* Bismillahir Rahmanir Rahim Wata huɗu aka saka auren Tijjani da Hajjo. Aure ne harga Allah babu yadda za ayi ya kauce ma sa tunda Iya ta ce idan bai auri Hajjo ba har abada ba zai taɓa ganin rahama a rayuwar sa ba. Wannan furuci ya birkitashi sosai. Goggo ta bashi goyon bayan yayi auren wataƙila Allah zai sa Iya ta sausauta ƙin sa da ta ke yi. Bai taɓa ra'ayin mace fiye da ɗaya ba, tun ma kafin ya haɗu da Maryam Nkiru ba shi da ra'ayin auren mace sama da ɗaya. Balle kuma da ya samu macen da ya ke ganin har duniya ta naɗe ba zai taɓa iya son wata mace bayan ta ba, bai taɓa jin zai haɗa soyayyar Maryam da wata mace ba balle har ya ƙara aure. Iya ta ci darajan haihuwa, indai yana so ya gama da duniya lafiya to dole ne yai wa Uwar da ta haifeshi biyayya. Yafi sati abun na damunshi ya rasa yadda zai yi ya gayawa Maryam. He failed her, tun daren farkon su ya ma ta alƙawarin ita kaɗaice babu ƙari, ita ɗaya ce matarshi har idan yana numfashi a duniya, ita da kishiya sai dai a Aljannah da za ta zamo sarauniyar Hurul ayn. Amma yanzu ya karya alkawari. Kusan sati uku abun na cinsa kafin ya summoning courage ya gaya ma ta abinda Iya ta sa shi. Ba ta ce komai ba har kusan minti biyu. "My Dear please say something" ya faɗa yana kallonta yana ƙoƙarin karantar yanayin fuskar ta. Ta yi murmushi mai ciwo ta ce " na san Iya ba ta so na and na san she'll always come between US sooner or later. The only thing da ya hanata rabamu tun da shine maganar Baffah" Ta ja dogon numfashi sannan ta ce " This is just a step to break us, and ba za ta tsaya a nan ba she'll do more and more and more. Abu ɗaya na ke tsoro Barkindo..." T J ya kamo hannunta ya kai dai-dai ƙirjinsa ya ce " then, now and the future zuciyar Tijjani taki ce. Jikina zai raɓi wata mace amma zuciyata ta mace ɗaya ce. Zuciyata will always beat for you Maryam-Inkiru" "Its Nkiru, N N N Nkiru" ta faɗa tana turo baki "Afuwan Sarauniyata N N N Nkiru" Yadda yai maganar ya sa ta fashe da dariya tana dariyan har da hawaye, ya rungumeta shima yana dariyan. Bubbuga bayansa ta ke yi tanajin zuciyarta na zafi kamar zai fashe. "I'm sorry my love, i'm very sorry" ya fara faɗi yana shafa bayanta lokacin daya ji sheshsheƙar kukan ta. "I love you, I'll always love you, ki rinƙa tunawa da wannan" Rarrrashin na ta daya ke yi ya sa ta ƙara sautin kukan ta. Hakan ya sa shima hawaye su ka fara zubo ma sa, ya sani its not easy for her, shima kuma daurewa kawai ya ke yi amma abin na ma sa zafi. Sai da ya ga kukan ya ƙi tsayawa ne ya sa shi chanja salon rarrashin, duk yadda ta so ta kauce ma sa sai da salon na sa ya birkitata. Daga kuka ta koma amsa saƙon zazzafar soyayyar sa... Daga wannan rana ta fara koyawa zuciyarta yadda za ta saba da sharing T J idan Amarya ta zo. *** Bikin na matsowa T J na ƙara nunawa Maryam kulawa duk dan ta kwantar da hankalinta. Daurewa kawai ta ke yi tana nuna ma sa ba komai but deep down she's hurting. Wani lokaci idan baya nan haka za ta zauna ta sha kuka ta ƙoshi, daga baya ta sanyawa kanta salama. Yanzu ita musulmace dole ta karɓi hukuncin Allah daya halatta auren mata huɗu. Haka ranakun su ka yi ta wucewa har aka ɗaura auren Tijjani da Hajara. Kusan shiyayi komai saboda Hajara da mahaifiyarta sun bari acewa ita ƙanwar sa ce dan haka ko ba aure haƙƙin sa ne ya siya ma ta kayan ɗaki. Bayan wannan sai da ya biya Alhaji Rabe kuɗin daya kashe wa Hajjon tunda ta ci kuɗinsa kuma ta ƙi auren sa. Su gani su ke aikin koyarwa da ya ke yi wani kuɗi ya ke samu na azo a gani. Ba dan Noma da kiwo da ya riƙe ba da ba ƙaramin jin jiki zai yi ba. Shi duk kuɗin abinda aka ce ya kawo kawowa ya ke yi saboda a zauna lafiya. Shi lokacin auren Maryam ba abunda yai tunda komai su Baffah ne su ka ma sa. Cikin ɗakuna uku da su ke gidan shi ya bawa Hajjo ɗaki ɗaya aka zo aka mata jere. Cikin kashi sittin na 'yan uwan sa sun yi na'am da auren da yai, hujjar su kuwa shine ita Maryam ƙabila ce gara ya haɗa da 'yar gida. Sauran kuwa sun nuna ba a yiwa Maryam adalci ba tunda auren su kwata-kwata shekara uku ne kuma kowa ga shaida halin Maryam na da kyau... Faɗin ƙazantar Hajjo ma ɓata lokaci ne. Abun daya fara sa ta fitawa T J a ka kenan. Ƙazantar jiki da muhalli duk ta haɗa shi, shi idan na muhalli ne ma da sauƙi amma jikinta ta kasa gyarawa. Daya dinga takura ma ta akan wanka kuwa sai ranan girkinta idan ta ji sallamar sa ya dawo daga office zakaga ta shige banɗaki da gudu ta yi wanka fuyaaa ta fito ba tareda ta cuɗa jikinta da kyau ba. Kasancewar Hajjo ita ɗaya ce 'ya mace a wajen mahaifiyarta ya sa Inna Saratu ta sakaltata, kwata-kwata ba ta kwaɓarta, a haka sai ta sangarce. Ba ta iya girki ba balle gyara gida. Ba abinda ta sani a ƙauyen su sai dai ta yi kwaskwarima ta banka foda a fiska ta cikawa bakin nan janbaki ta fita gari tana yawon ƙawance. Ranan da ta fara girki cikin su ba wanda ya iya cin abincin, wannan ya sa Maryam ta ce ma ta duk ranan girkinta kar ta yi girki da ita. Ta kuwa gayawa T J ba za ta iya cin abincin Hajjo ba tunda 'yar wannan shinkafa ta kasa dafata da kyau. Duk rashin wayewar su Goggo Maryam ba za ta taɓa cewa ba su iya girki ba, tun lokacin da ta soma cin abincin gidan ba ta taɓa ganin aibun sa ba iyaka dai ba su yin varieties na vegetables kamar yadda Mommynta ke yi. Yadda su ke dafa Alayyaho ma ya banbanta da wanda ta sani. Ba ta cin miyan kuka amma idan Goggo ta yi miyan kuɓewa har suɗe hannu ta ke yi, dan za ta ji miyar ta ji citta, daddawa, masoro da sauran natural ingriedients ma su inganta abinci. Shima dai T J ganin da gaske fa ba ta iya girki ba ne ya shi cewa ta tsaya Maryam ta koya ma ta girki . Ita kuwa ta kama ƙugu ta ce Allah ya sawwaƙa ta je ta koyi girki a wajen kishiyarta, kishiyar ma Inyamura. Ya kuwa daka ma ta tsawa ya ce lallai duk inda za ta je ta je ta koyi girki amma duk ranan da ta kuma kawo ma sa jagwalgwalon abinci sai ya zuba ma ta a ka sannan zai maida ta gidan su. Hakan ya sa ta ɗan tsorata da shi. Wata maƙociyarsu ta samu ta nuna ma ta yadda ake girki na ɗan kwana biyu. Itama dai sammakal ne dan girki ne da aka yi amanna da kafi zabuwa. Maganar saka Kafi zabuwa ko Ajinomoto a abinci kuwa tun yana maganar har ya dena dan Hajjo ta kasa denawa ta dai rage gambaɗawa, ita kamar yadda Maman Bilkisu ta koya mata haka ta ɗauka, wai girki a Ajino baya daɗi. Shikam duk ranan girkin Hajjo baya ƙoshi dan baya cin abinci sosai saboda ba jin daɗin abincin ya ke ba yana dai haƙuri ne. Yana gama ci yake brush saboda zaƙi-zaƙin Ajinon da ke tsaya ma sa a harshe. Wani lokaci ko yayi brush ɗin sai ya haɗa da asuwaki. Gyaran gida kam Maryam ke yi ko ba ranan girkinta ba ne dan idan ta ce ba za ta gyara falo da kitchen da sauran wajajen ba sai dai cikin kwana biyun da T J zai yi a wajenta idan sun yi baƙi su ji kunya saboda Hajjo ba sharewa za ta yi ba. Ɗakinta ma sai ta yi sati bai ga tsintsiya ba, idan ka ga ta yi shara T J ne ya tsaya akanta ya ce dole sai ta share ɗakin. Ba abunda ta sani sai dai ta kunna T V da ke falo tayita kallon Films ɗin Indiya, tana yawon neman sabon casette daya fito. A ƙoƙarin sa na son ganin Hajjo ta gyaru yai tunanin sa ta makaranta. Kasancewar ko Primary ba ta ƙarisa ba ta bar zuwa ya sa ya sama ma ta primary school aji huɗu. Ko yanene ta yi shekara biyu ta ƙare primary sai ta fara JSS one. Sai daya gama shirin sa har Uniform ya ɗinka ma ta Hajjo ta ce ba za ta yi makaranta ba. Ƙarshe ta ce irin makarantar da Maryam ke zuwa zai sa ta idan yana so ta yi karatu. Makarantar manya ba ta yara irin su Bilkisun maƙotan su ba. Duk wani bayani yayi ma ta ta ƙi ji, ƙarshe ta ce wai ai ba dole ba ne tayi karatu. Da ya ma ta jan ido sai ta nitsu. Kullum za ta shirya ta sa uniform ta wuce gidan Maman Bilkisu ta zauna su yi ta kallo sai da rana idan anfara dawowa daga makaranta sai ta koma gida. Kusan sati uku ana haka T J bai taɓa ganewa ba, sai da watarana headmaster ɗin makarantar ya samu T J akan matarsa da ya ce za ta fara zuwa har yanzu form master ɗin ajin su ya ce bai ganta ba. Kunya ta sa T J ya rasa mi zai ce. Da ya je gida ya tsare Hajjo kuwa sai ta sa kuka wai ita ba za ta yi makarantar yara ba. Haushi ya kamashi ya ce ta cigaba da zama a jahilci tunda Ilimin ne ba ta so, watarana za ta yi kuka da kan ta. Daga ranan batun makarantar ta ya bi ruwa. Ba abinda ta ke yi sai kallo da yawon gulmace-gulmace. Da farkon kawo ta Amarya wasu cikin maƙotan su Maryam Hausa/Fulani su ka fara ja baya da Maryam suna cusuwa jikin Hajjo tunda acewar su 'yar uwa ce ba kamar Maryam da ta ke ƙabila ba. (Kamar Hausa/Fulanin ba Ƙabila ba ne) Dama Maryam ta fi harka da Madam Mitchele wata baturiyar ƙasar Poland wacce itama lecturer ce sai kuma Mama Lucas wata Igala sai wata Bayarabiya Iya Korede. Ita Iya Korede gidan su baya layi ɗaya amma duk da haka su na zumunci dan itama mijinta ya barta ta fara karatu, duk da ba Course ɗaya su ke da Maryam ɗin ba amma su kan haɗu wani lokaci a cikin School. Daga baya da Hajjo ta nuna halinta na haɗa guri sai su ka fara ja baya da ita. Yanzu Maman Bilkisu ce kaɗai su ke ɗasawa da ita itama halinsu ne ya zo ɗaya. Maryam kam duk wani shirmen Hajjo ba ta biye ma ta, ba ma ta da lokacinta karatun ta kaɗai ya isheta ga wanda su ke a gida da T J. Ganin ba ta samu fiska a wajen Maryam ba ne ya sa ta dena taƙalarta da tsokana. Watarana T J na Office aka zo aka kirashi wai matar shi na Asibiti. Gaba ɗaya ya tsorata dan bai san wacce ba ce cikin matan na sa. Sai da ya je ya ga Hajjo. Faɗa su ka yi da Maman Bilkisu, garin faɗan ne Maman Bilkisu ta tureta cikinta ya bugu da centre table shine ta yi ɓari. Haushi takaici duk ya cika T J wai matar sa ta rasa cikinsa garin kokawa. Bayan an sallamesu ya ɗauketa su ka dawo gida tsabar ɓacin rai bai san mi zai gaya ma ta ba. Ya hanata yawo amma ba ta ji. Daya fara magana sai ta fara kuka wai bai tausaya ma ta bayan ta rasa gudan jinin su, hakan ya sa shi yin shiru. Bayan kwana biyu ya ce ta je gida ta huta, shi da kan sa ya kaita gidan su ya kuwa yiwa Goggo maganan duk halin Hajjon ya kuma ce dan Allah ta ma ta faɗa. Bayan tafiyar sa da Goggo ta kira Hajjo tana ma ta faɗa sai ta fashe da kuka wai sharri T J ya ma ta dan ya fi son Maryam a kanta. Wai Maryam ce ta tureta har ta bugu ta yi ɓari. Takaici ya kama Goggo dan ta yarda da maganan T J. Duk faɗan da ta ma ta yana shiga ta kunnen dama ne yana fita ta hagu. Bayan sati ɗaya da T J ya zo ɗaukanta Iya ta sa shi a gaba da faɗa wai ya jawa Maryam kunne, dan ita ba ta haihuwa ba zai sa ta dinga kashewa Hajjo 'ya'ya ba. Ga ainihin abinda ya faru amma Hajjo ta juya zancen akan Maryam ce ta tureta ita kuma Iya ta yarda da hakan. Ba ta ma bashi dama ba balle yai ma ta bayanin gaskiya, haka dai ya ɗau Hajjo su ka tafi ran sa a ɓace. Bayan ɓarin Hajjo da wata biyar ta sake samun ciki, a lokacin ne kuma Maryam ta fara tsorata ko dai ita ce ba ta haihuwa tunda gashi Hajjo ta samu ciki har sau biyu. Ta je Asibiti aka ma ta duk wasu gwaje gwajen daya kamata aka ce lafiyarta ƙalau za ta iya samun ciki kowani lokaci. Hajjo kam banda laulayi har da iskanci, ta dinga tsirface tsirface dan taga T J ya ɗan damu da ita saboda cikin jikinta. Gaba ɗaya sai girki ya koma hannun Maryam da rana girkinta da na Hajjo duk ita ke girki. Hakan bai dameta ba dan girki a wajenta ba abun ɗaga hankali ba ne. Sai da Hajjon ta fara iskancin sai dai a dafa ma ta kaza ko kuma sai Maryam ta gama girki ta ce ba za ta ci ba ita kaza da kaza ta ka so sannan Maryam ta fara yiwa T J ƙorafi. Da farko T J ya fara biye ma ta saboda laluran ma su ciki amma daga baya da ya gane harda iskanci a lamarin na ta sai ya taka ma ta birki. A hankali dai ciki ya girma Hajjo ta haifi ɗanta namiji. Zo ka ga murna a wajen ta ganin yanzu kam za ta karɓi gida tunda ita ta fara haihuwa ga shi ɗa namiji. A Zariyan a ka yi suna kuma 'yan uwan sa na Ringim sun zo dayawa. Yaro ya ci sunan Baffah wato Abubakar suna kiran sa Sadiq. Tun watan farkon Sadiq ya fara rashin lafiya. Yau suna asibiti gobe su na gida. Na da nan Hajjo ta tada Hankali wai Maryam ce Mayya ta kama mata ɗa. Ita da Inna da ta zo mata wanka su ka kama Maryam da zagi da faɗa. Har Inna Saratu ta je ta nemo tafarnuwa su ka fara sakawa a duk gidan. Da Maryam ta shigo kuwa za su fara jifanta da Tafarnuwa. Ba ta taɓa gayawa T J ba dan ba ta son tashin hankali. Ranan da ciwon Sadiq ya tashi aka kaishi babban Asibiti nan Inna Saratu ta wuce gida wai za ta zo da sarkin mayu. A asibitin bayan anyi gwaje-gwaje ne aka tabbatar wa T J da cewa Sadiq SS ne wato sickler. Nan aka gwada jinin sa da na Hajjo aka tabbatar dukkan su genotype ɗin su AS ne. Wannan ya sa washegari ya taho da Maryam aka gwada ta amma ita AA ce nan hankalinsa ya kwanta. Da yamma yana Asibiti saboda ana ƙarawa Sadiq jini sai ga maƙocinsa Mr Badmus wato Baban Lucas. Ya ce maza-maza ya zo gida ba lafiya. Da ya tambayeshi miyake faruwa sai ya ce wai wasu tsofi ne su ka taho da Sarkin Mayu gidan sa an ɗaure Maryam ana dukanta wai sai ta sake kuruwan Sadiq. Jiki na rawa haka ya bi Mr Badmus hankali tashe duk da kuwa Mr Badmus ɗin ya ce ma sa an tafi da Maryam Asibitin cikin makaranta shi kuma Sarkin Mayu an kira ma sa security yanzu ma ana maganar za a wuce dashi police station ne. Asibiti su ka wuce inda su ka samu an sallami Maryam ɗin, dama ciwukan da dorinar Sarkin mayu ya ji ma ta ne aka treating. Gidan Mr Badmus su ka wuce tunda matar sa ce ta kai Maryam ɗin Asibiti. Su na shiga Maman Lucas ta nuna ma sa ɗakin da Maryam ɗin ta ke. Yana shiga ya ganta zaune a kan gado. Ya ƙariso da sauri ya hau gadon ya kamo hannun ta. "I'm sorry Dear, i'm very sorry, ya jikin na ki? Are you Ok? " ya shiga kissing ɗin hannuta "Divorce me" ta furta hawaye na bin kumatunta Girgiza kai ya farayi yana hawaye. "Mahaifiyar ka ta tsaneni, she'll keep coming between us. Lets just go our separate ways" "Nooo, Nooo. Dear ba zan iya rabuwa da ke ba. You are my world, you are my happiness" "Barkindo ba zan iya cigaba da zama da kai ba, ka sake ni kawai, for Peace sake lets go our separate ways b..." Haɗe bakin su yai ya shiga kissing ɗinta da sauri sauri. Da ƙyar ta samu ta ƙwace bakinta daga zazzafar kiss da ya ke ma ta. Tana hawaye shima yana yi haka su ka ƙurawa juna ido suna maida numfashi. Da ƙyar T J ya ce " Maryam Dan Allah kiyi haƙuri, ba zan iya rabuwa da ke ba. Please..." "Idan saboda maganar Baffah ne kar ka damu ai bai ce idan na nemi saki kar ka bani ba. Ba wai dan Iya ta ce ka sake ni ba, nine na ke so ka sakeni. I want peace Barkindo i want peace" ta ƙarisa maganar da ƙarfi. Ba abinda ya ke cewa sai Sorry... *** Kwana shida kenan da faruwan wannan abu, Iya da Inna da su ka taho da Sarkin Mayu kam suma kaɗan ya rage a rufe su sai da T J ya shiga ya fita kafin aka rufe case ɗin. Da kan sa ya je Ringim ya samu Alhaji Isa ya ma sa bayanin duk abinda ya faru da ma abin da ke damun Sadiq ɗin. Alhaji Isa shima ya kaɗu da maganar, bai taɓa tsammanin rashin hankalin Iya ya kai har haka ba. Goggo kam sai da ta yi hawaye saboda tausayin Maryam. Tana ina ma Baffah na raye. Meeting mai zafi Alhaji Isa ya kira wanda ya haɗa da Iya, Inna Saratu da ma Hajjo wacce an sallame su saboda Sadiq ya ji sauƙi. Ya kira Maryam ma amma ba ta zo ba saboda exams da su ka fara har lokacin gidan Mr Badmus ta ke kwana ta ƙi komawa gidan T J. Yayi kukan yayi magiyan ta ƙi sauraron sa. Sosai Alhaji Isa ya jawa Iya da su Hajjo kunne akan Maryam. Yai Allah wadai da halin su da ɓatawa Gidan Modibbo suna ta hanyar zuwa ɗauko wani Boka wai Sarkin Mayu. Ya haɗa da cewa dukkan su suje su bawa Maryam haƙuri. Shi T J ya so a raba auren sa da Hajjo ne ma musamman saboda yadda dukkan su suka kasance AS that is akwai probability za su yi ta haihuwan SS amma Alhaji Isa ya ce a'a tunda har sun samu rabo ya cigaba da haƙuri kawai. Duk bayanin daya ma sa akan rashin compatibility na su da Hajjo bai gane sosai ba haƙuri kawai ya bashi akan ya cigaba da zama da ita su yi jinyar ɗan su. A wajen kuwa Alhaji ya ce da Iya da Inna bai yarda ko ɗaya ta sake zuwa gidan T J ba idan suna son ganin su su bari sai sun zo Ringim. Idan da matsala za a aika wasu cikin 'yan uwa su je mu su. Bayan taro ya watse ko ta kan Hajjo bai bi ba ya koma Zaria. Duk wani hanya ya bi akan Maryam tayi haƙuri amma ta ƙi tace abu ɗaya ta ke so shine ya saketa. Ya ma ta bayanin babu wanda zai sake zuwa gidan su cikin Iya da Inna amma ta ƙi sauraren sa. Ya aika abokanan sa da dama amma ta ƙi komawa. Ƙarshe aka bashi shawaran ya barta ta huce tukunna. Hajjo da ta yi sati a gida ta ga T J bai bi ta kanta ba sai ta tattara ta dawo. Gaba ɗaya ba ta gane kan T J ba, idan ba tambaya gameda Sadiq ba baya kulata. Wasa-wasa har Maryam ta gama exams ba ta koma gidan T J ba. Itama daurewa ta ke yi domin har yau tana tsananin son T J amma dole ta katse alaƙarsu saboda a yadda ta hango auren su za ta cigaba da fuskantar ƙalubale matuƙar Iya ba ta son ta. Its better to quit now tunda ma ba haihuwa tsakanin su. Ba ta ji za ta iya son wani bayan T J ba amma kuma rabuwa shine mafita. T J ya gama marking scripts na student ya fito daga office zai tafi gida ya yanke jiki ya faɗi. Buɗe idon da zai yi ya ganshi a Asibiti. Jinin sa ne ya hau abunda aka ce da shi kenan. Matuƙar Maryam ta cigaba da demanding saki a wajen sa ƙila zuciyar sa ne za ta buga ya mutu kawai. Bai ji zai iya rabuwa da Maryam ba ko da ita Maryam ɗin ne ta nemi rabuwa da shi... Maman Lucas na sanar da ita an kwantar da T J a Asibiti hankalinta ya tashi, hankalinta a tashe ta shirya su ka wuce asibitin, lokacin da su ka je bai farfaɗo ba. Gaba ɗaya ya rame ma ta dama ina jikin yake balle yanzu da damuwa ya ƙara busar da shi. Ganin yana bacci ne ya sa ta koma gida dan ta haɗa ma sa abinci. Zuwanta gidan na su kenan na farko tun bayan abinda su Iya su ka ma ta kusan sati biyar da su ka wuce. Ta samu gidan kaca-kaca as expected, dama haihuwa ya sake sawa Hajjo ƙazanta. Ɗakinta ta buɗe shima ya ɗan yi ƙura ta cire kayan jikinta ta sa kayan gida ta fito ta shiga kitchen babu wasu abubuwan da ta ke buƙata dan haka ta fita gidan su Maman Lucas ta aiki Lucas ya siya ma ta kayan miya. Faran shinkafa ta dafa da miyar ugwu wanda ya ji stock fish da kayan ciki. Ta haɗa komai sharp-sharp ta wuce Asibiti wannan karan ta samu T J ya tashi har ma suna taɗi da wani abokinshi lecturer daya zo duba shi. Ganin Maryam ya sa ya ƙara langwaɓewa yana ma ta shagwaɓa musamman dayaga hankalinta a tashe ya ke da ciwon na sa. A baki ta dinga bashi abinci, ya kuwa ci sosai. Rabon da ya ci abincin kirki tun tana gidan sa... Ƙarfe Shida ta baro Asibiti dan ta taho ma sa da wasu kayan buƙata. Ashe tana tafiya ya ce a sallameshi duk da kuwa likita ya ce ya bari sai bayan kwana biyu tukunna kafin nan ya warware sosai amma ya ƙi. Shi kam maganin sa Maryam ne ba zaman Asibiti ba. Ta gama haɗa komai ta shiga wanka ta fito tana saka kaya da sauri-sauri saboda taga lokaci ya ƙure dan har an fara kiran sallar Magariba. Kawai ta ji sallamar shi. Ta tsaya kallon shi da mamaki. Yana ƙarasowa ya rungumeta "Ke ce maganina Maryam, idan ki ka dawo rayuwata na warke kenan har abada" "Likita ya ce ba..." Rufe ma ta bakinta da yai da na sa bakin ya sa maganar ta ƙare. Yadda kasan first night ɗin su haka yake sarrafata jikinsa na rawa. Its been over a month rabon sa da ita. Amidst soyayyar su ya ce " Maryam idan ki ka barni mutuwa zan yi, Dan Allah ki ce kin janye maganar ki" Ta gyaɗa ma sa kai tana hawaye, hawayen zafi da daɗi. Yanzu kam ta amince ba za ta taɓa iya rabuwa da T J ba, kamar yadda ya ke ji da ita haka ta ke ji da shi. Soyayyar shi ya riga ya mamaye zuciyarta. Lokacin da ta ganshi kwance a asibiti ba abun da ta kawo a ranta irin what if he dies because of her? Da kuwa za ta ƙare rayuwarta cike da nadama may be ma baƙin ciki itama ya kasheta. Yanzu kam sai dai ta cigaba da zaman haƙuri, da daɗi ba daɗi she has to stay by his side saboda ba ta da rayuwar farinciki idan babu T J a ciki... Ƙoƙarin maimaita aikin ladan da su ka yi da ya ke son yi ne ya sa ta dakatar da shi ta hanyar cewa "Love ba ka da lafiya fa" "Ai ke ce cutar kuma ke ce maganin" ya faɗa yana kissing cikinta "An idar da sallah fa" "Har yanzu muna mukhtarin ta sannan akwai lokacin daruri. Ki bari na sake jin ɗumin ki Maryam- N N N Nkiru na" Ta yi dariya daga nan zancen ya chanja dan ta san dole ne ta bar shi ya je second round. *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *11-two house* Bismillahir Rahmanir Rahim Rayuwa kam ta cigaba da juyawa. Zaman haƙuri kam shi Maryam ke yi a gidan T J. Iya ta zame mu su kujeran zama, ta gina katanga tsakanin farincikin masoyan. Duk wani tuggu da munafurci da ta ke yi Maryam ba ta kulata. Watanni kaɗan bayan haihuwar Hajjo Maryam ta fara aiki. Hajjo ta samu 'ya mace aka yiwa Iya mai suna amma Humairah ake kiranta, da wurwuri T J ya je aka gwada ta inda aka tabbatar ma sa AS ce ba SS ba, hakan ya sa hankalinsa ya kwanta. Duk kuɗin da ya kashe a wajen Suna Iya da Hajjo ba su gani ba acewarsu bai yiwa Humaira hidima ba kamar yadda yai a Sunan Zaytoonah. Lokacin hidiman ginin gidan sa ya ke yi amma a hakan ya daure ya fitar da maƙudan kuɗi akayi hidiman Suna da shi. Yadda Iya ke tsananin ƙin Zaytoonah haka ta ke nunawa Humairah tsananin so. Ko da wasa ba ta taɓa ɗaukan Zaytoonah ba ko lokacin da ta ke rarrafe idan by mistake ta rarrafo ta wajenta to haka za ka ga ta make ta. Zaytoonah ta dinga kuka idan Auwal na kusa ya ɗauketa yai ta lallashi idan kuma Maryam ce ke kusa ta ji kukan ta ta zo da sauri ta ɗauke 'yarta. Renon Humaira kaf a hannun Iya ya ke. Har yarinyar ta shafe watanni duk hidimar fitsari da kashinta Iya ke yi. Hajjo dama son jiki ga shi ta samu Iya ba ta iya kwaɓarta saboda ita 'yar yayarta ce kuma 'yar Fulani ba kaman Maryam Inyamura ba. Maryam kam ta zuba mu su ido, tunda ba a son 'yarta ita tana son kayanta. And besides yafi ma ta ma da ba sa shiga harkan 'yarta kar su koya ma ta mugun abu. T J kuma sai dai ya nunawa Zaytoonah kulawa a cikin ɗaki bai isa ya nuna a waje ba. Karon farko da Maryam ta fara fita aiki Iya ta dakatar da ita, wai yawon iskancin ya isa haka ba inda za ta je. Maryam ta yi biris da ita ta cigaba da tafiya dama T J ya tafi wani comference na kwana uku a Lagos. Daga dawowan shi Iya ta ce ba ta yarda Maryam ta dinga fita aiki ba. Daya fara ƙoƙarin yi ma ta bayanin mahimmancin aikin sai ta ce idan har bai hana Maryam fita aiki ba za ta tsine ma sa. Ranan da dare ya samu Maryam ya lallaɓata wai ta haƙura da aikin na lokaci kaɗan kafin Iya ta huce tukunna. Ta dinga jin zancen shi har ya gama ba ta nuna ta damu ba. Washegari yana fita ta ɗau 'yarta sai Ringim. Gaban Baffah Umar ta je ta kai ƙaran TJ da Iya ta kuma rantse ma sa cewa muddin ya ce ba za ta cigaba da aikinta ba za ta bar mu su gidan. Baffah Umar bai yi boko ba kuma a da yana ƙin boko musamman na 'ya'ya mata amma yanzu ya fara ganin Alfanun Bokon dan kwanaki wata 'yar abokinsa da ta cigaba da karatu bayan aurenta sai gashi yanzu ta zama babbar Likita. Ya kai uwargidan sa babban Asibitin Murtala ne a Kano ya haɗu da ita, shi bai ma gane ta ba sai da ta ma sa bayani akan ita ce 'yar abokin sa Malam Saleh Audu. Har aka sallamesu yana mamakin yadda akayi Usaina ta samu baiwar ilimin magani haka. Kamar ba ita ba ce shekaru shatakwas da su ka wuce ake rigima akan aurenta saboda mijin da za ta aura ba Bafulatani ba ne, Asalin su Jarawa ne daga Dass amma kasuwanci ya zaunar da su a Kano. Dan haka bai ga aibu acikin aikin da Maryam ke yi ba da har Iya za ta yi mummunan furuci akan sa. Kwana biyu ta yi a Ringim suka koma Zaria da Baffah Umar ɗin. Ya je gidan ya sissille Iya, yai Allah wadarai da halinta. Dama Baffah Umar shima lokacin ƙuruciya an taɓa ƙiriniya dan haka a Umar ɗin sa ya fito ma ta. Nan take ta sha jinin jikinta, ta sani dama duk cikin yaran Modibbo, Umar da Babbar yarsu Fatima sun fi kowa taurin rai da faɗa. Ko a da ɗin ba ƙaramin tsoron sa ta ke ji ba. Bayan yayiwa Iya na ta faɗan ne ya koma kan T J wanda shima faɗa sosai ya ma sa ya kuma yi ma sa tuni da amanar Maryam da Baffan sa ya bar ma sa. Daga wannan zuwan Baffah Umar ɗin ne Maryam ta samu damar komawa bakin aikinta hankali kwance... *** Zaytoonah na da shekara uku T J ya kammala ginin sa. Gida ne da tun farkon aurensa da Maryam yai foundation ɗin yadda tsarin zai kasance sai dai kuma komai ya chanja ma sa lokaci guda tunda yanzu mata biyu ya ke aure ga kuma Iya da ta ke zaune da su babu ranan tafiya. Maryam ya fara kaiwa gidan ta gani ta kuma sa albarka. Ɗakuna biyar ne a gidan ya gina ne da niyyar ɗakin sa ɗaya sai ɗakin Maryam sai ɗakuna biyu na 'ya'yan su da kuma ɗakin baƙi. Amma yanzu tsarin ya chanja ya koma ɗakin sa, sai ɗakin Iya, ɗakin Maryam da Hajjo sai ɗaya ɗakin na Auwal da yara mazan da za su haifa. Akwai babban falo sai kitchen da store. Ra'ayin Maryam ya tambaya akan yadda za a saka furnitures ɗin gidan. Abu ɗaya da ta yi magana a kai shine a mayar da store ɗin ya koma kitchen saboda ba za ta sharing kitchen da Hajjo ba. Ko ba ta yi bayani ba ya san tana cutuwa. Bai yi musu ba ya amince da hakan dama ba ariga anyi kitchen shelves da wardrobe ba, ko kitchen sink ma ba a sa ba... Cike da farinciki ya sanar da Iya cewa za su koma sabon gida ƙarshen wata. Amsar da ta bashi sai da ya sa numfashin sa ya ɗauke na ɗan wasu daƙiƙu. "Iya dan Allah kiyi haƙuri, na san ba kya son Maryam amma Iya kamar yadda Hajjo ta ke matata haka Maryam ma ta ke. Idan na yi haka ban ma ta adalci ba kuma..." "Idan kuma korata za ka yi a gidanka sai ka faɗa amma ka sani ba zan zauna da karuwar Inyamurar da ka ajiye a gida ba. Wannan zaman da na yi ma kullum cikin fargaba na ke" Daga tsugunnen da ya ke ya zauna daɓas a ƙasa gumi na keto ma sa ta ko'ina. Shi yanzu ya zai yi da Iya, ya zai yi da Uwar da ta haifeshi wacce ke neman rusa ma sa duk wani farincikin sa. Ta ina zai fara kallon Maryam da zancen Iya ta ce ba za ta tare tareda su ba. Shi yanzu kunyan kai ƙaran Iya ya ke ji saboda kullum kimarta zubewa ya ke yi a wajen 'yan uwan Baban sa. Daren ranan da zazzaɓi ya kwana, daɗin abin ma ɗakin Hajjo ne ba Maryam ba. Da Maryam ce tsab sai ta gane yana cikin matsala. Ita kam Hajjo baccinta kawai ta sha har da mimshari. Washegari da zai fita Maryam ta lura da yanayinsa. Ta tambayeshi ko lafiya ya ce ma ta ba komai. Da ya koma ɗakinta kuwa ta ma sa tambayar duniyan nan akan mi ke damunsa ya ce ba komai yana tunanin yadda zai fara Phd ɗin sa ne nan ba da jimawa ba kuma ba kuɗi a hannun sa. Maryam ta san ƙarya ya ke yi amma ta ƙyaleshi tunda baya son faɗa ma ta matsalar sa. Itama ya sanar da ita ƙarshen wata za su koma sabon gida amma har ya saura kwana shida ba ta ga an fara shiri ba. Da ta tambayeshi sai ya ce an fasa tarewar akwai wasu ayyuka da ba a gama ba. Ta yi shiru ba ta kuma cewa komai ba, T J ɗin da ta sani has being behaving strange wanda ta san duk yadda aka yi wani abu ne daya danganci tsakanin sa da Iya. Tunanin ƙara aure ne ya fara zuwa ma ta. Ƙila tunda ya yi gini Iya ta ce ya ƙara aure su zama su uku. To daga baya kuma sai ta fara tantamar haka. Dan Hajjo da Inna ba za su yadda da wannan ba. To amma minene? Ta dai bar tambayar a ranta zuwa lokacin da T J zai furta ma ta matsalarsa da kan sa. Saura kwana uku tashin su ya sanar da Iya an fasa tashin sai wani watan saboda za'a ƙarisa wasu gurare da ba'a gama ba. Iya ta fara masifa wai ta san ƙarya ya ke yi. Idan kuwa dan baya son bin maganarta ne to ita gobe za ta bar ma sa gidan idan ya so ya je ya tare da Maryam tunda ya fi son matar sa akan uwar da ta haifeshi. T J ya shiga ba ta haƙuri amma fir ta ƙi. Duk abinda aka yi a idon Auwal hakan yasa ya ji haushin Iya sosai. Maryam na dawowa ya tareta da murna ya fara ƙoƙarin ɗaukan Zaytoonah wacce ke cin biscuit duk ta ɓata bakinta da uniform ɗin ta. Ta maƙe kafaɗa tana faɗin "leave me" "Auwal ajiyeta kawai tun ɗazu ta ke damuna da rigima" Nursery one Zaytoonah ta ke, da an tashi a makaranta Maryam ke zuwa ta ɗaukota ta wuce da ita office ɗin ta, idan ta tashi a office sai su dawo tare. Wani lokaci kuwa T J ne ke zuwa ya ɗaukota ya wuce da ita na shi office ɗin idan ba shi da class a lokacin. Bayan ta yi wanka ta yi sallar la'asar ne ta fito ta shiga kitchen dan ta fara girkin dare, yanayin jikinta kwana biyun nan ba ta gane ba tana hasashen ma ko ciki gareta dan kwana takwas kenan ba ta ga jininta ba. Tana son zuwa Asibiti ta tabbatar da hasashenta amma gaba ɗaya she's busy a office idan ta dawo kuma ta gaji. Tana yanka alayyaho sai ga Auwal da Zaytoonah sun shigo sanye da uniform ɗin Islamiyya. Zaytoonah na cin wani chocolate baki da hannu duk yayi dumu-dumu da shi. "Auwal yanzu sai da ka bata chocolate ɗin nan bayan na hanaka" "Mommy cewa ta yi idan ban ba ta ba bazata je Islamiyyan ba" "Oya come here" Maryam ta faɗa da ɗan ƙarfi Zaytoonah ta ɓoye a bayan Auwal tana wiki-wiki da ido dan ta san yanzu za ta ƙwace chocolate ɗin. "Zaytoonah" Kawai ta ɓare baki da kuka. Maryam ta jijjiga kai kawai ta ce " ku je Auwal amma ka share ma ta baki da hannu kafin ku fita" "Ke kuma zanyi maganin ki, tukunna ma chocolate nawa kika sha a office yau?" Zaytoonah ta ɗaga yatsunta huɗu still tana maƙale da Auwal ta ƙi isowa wajen Maryam dan ta san halin mommyn na ta ba ta dukanta amma kunnenta zai sha murɗa. Bayan sun fita sai kuma Auwal ya dawo da sauri ya fara yiwa Maryam magana ƙasa-ƙasa. Hajjo dai ba ta gida ta fita unguwa amma Iya na ɗaki. "Mommy yau da rana kafin ki dawo Iya ta dinga yiwa Daddy faɗa, ta ce wai ba za ki koma sabon gida ba. Kuma fa Daddy har kuka ya ma ta amma ta ƙi sauraren shi, ni kam indai ba za ki koma sabon gida ba nima ba zan je ba" Tunda ya fara maganan ta ƙura ma sa ido. Auwal yana da wayo, shekarun sa goma yanzu, yana aji huɗu a primary. Mafiya yawancin lokaci idan anyi wani abu a gidan a bakin sa ta ke ji, shima ya gane Iya da Hajjo ba sa son Maryam kuma suna ma ta munafurci, shiyasa ma ya tsanesu ya fi damuwa da Mommynsa Maryam. "Auwal ku wuce Islamiyya" abinda ta iya faɗa kenan saboda zuciyarta da ya cunkushe. Sai yaushe wannan Matar za ta dena ci ma ta fuska. Ina ma Goggo ce ta haifi Tijjani, da za ta fi kowa sa'ar uwar miji. Amma Iya, Iya, Iya sai dai kawai Allah ya rabata da ita lafiya. Iya ta yi kishi da Goggo yanzu kuma da ita ta ke kishi. Ba ta ga laifin Baffah da ya fi son Goggo ba lokacin yana raye. Kyawawan halayenta su suka sa ta samu babban matsayi a zuciyarta. Iya ta ƙare rayuwan aurenta acikin baƙin kishi, gashi yanzu da tsufanta ma ba ta bar kishin ba. Illiteracy, Greedy and Envy su ne manyan abubuwan da su ke damun Iya cikin ukun ba ta san wanne ne ma yafi wani yawa a ciki ba. At first ta ɗauka haihuwar Zaytoonah zai sassauta tsanar da Iya ta ma ta amma abun ba haka yake ba. Matar da har sheganta ma ta 'ya ta ke yi. Tun kafin Zaytoonah ta yi wayo ta gane ƙiyayyar da Iyan ke ma ta yanzu ma da ta fara wayo ko gaisheta ba ta yi. Countless times ta kan cewa Maryam "Mommy i hate Iya" Maryam ta kwaɓeta akan ta dena faɗin haka. Da sanyin jiki ta ƙarisa girkin. Ta gyara kitchen ɗin ta koma ɗaki. Tsayawa ta yi bakin hoton T J da ke jikin frame a bangon ɗakin. Sanye ya ke da kayan bautar ƙasa yana murmushi. Yana daga cikin ƙaddararta ta haɗu da T J, yana daga ƙaddararta ta faɗa makauniyar soyayyar sa, yana daga ƙaddararta ta wahala a zama da shi. Despite everything ko kaɗan soyayyar da ta ke ma sa bai ragu ba. Ta jima tana kallon hoton kafin ta sauke nannauyan ajiyar zuciya ta bar wajen. Da dare T J bai dawo da wuri ba har goma, gaba ɗaya Maryam ta damu sosai. Ta san maganan Iya ne ya sa shi ƙin dawowa da wuri. Ƙarfe goma da minti ishirin da biyar ta ji shigowar sa gidan. Ya buɗe ƙofan ɗakinta ya ga wuta a kunne. Suna ido huɗu da shi yai saurin kau da kai yana faɗin " ba ki kwanta ba?" Takalmin sa ya cire ya sa gefen ƙofa ya zo ya zauna a gefenta. "Sorry na tsaya duba assignment ɗin yara ne a office ban san dare yayi har haka ba" Hannun sa ta kamo ta ce " ba sai ka yi bayani ba na san komai. Barin kawo ma ka abinci" "No ki barshi gobe zan ci ɗumame" ya faɗa yana miƙewa dan ya cire kayan sa "Da ka ci abincin kuwa sai na maka albishir da abubuwa guda biyu" Ya ɗan juyo ya kalleta ya ce "Maryam dare yayi ba zan iya ci ba. Ki gaya min albishir ɗin" Tausayin sa ta ji ya kamata, hatta maganar sa chanjawa ta yi, ga idon sa da yai jaa. "To barin haɗo ma ka tea" Tana da flask ɗin ruwan zafi a ɗaki dan haka fita ta yi ta je kitchen ta ɗauko cup da spoon. Ta ɗau kayan tea da ke saman drawer ta haɗa ma sa tea mai kauri wanda ya ji sugar sosai kaman yadda ya ke so. Ya cire kaya ya sanya jallabiyar sa da ya ke bacci da shi, yana zaune bakin gado yayi tagumi, ta cire hannunsa daga tagumin da yai ta ce "ka sha tea dan Allah" Ya karɓi kofin ya ce na gode. Ta hau gado ta koma bayansa ta fara masa massage ɗin goshin sa a hankali a hankali daga nan kuma ta koma wuyan sa zuwa kafaɗar sa. "Minene Albishir ɗin?" "Ka shanye tea ɗin tukunna" ta amsa ma sa ta cigaba da danna ma sa kafaɗun sa. "Adaeze ta miki rigima a office ko?" "Kai ma ka san za ta yi tunda kai ta ɗauko wajen rigima" Yai murmushi yana lumshe ido saboda yadda ya ke jin daɗin tausar da ta ke ma sa. "Ka san dai kanada hawan jini amma sai ka dinga sawa kan ka damuwa" "Maryam..." "Ka bari na gama magana please. Yanzu idan wani abu ya sameka ya ka ke so na yi? Abu na daminka ba za ka faɗa ba. Its better ka gaya min tun da wuri rather than sai daga baya na ji ko kuma na ji a bakin wanda bai kamata ba" "I'm sorry" "Shshhhh. The first surprise is" Ta kamo hannunsa ta sa a cikinta. "I'm 90% sure ina tareda junior Teejay" Ya juyo da sauri yana zaro ido "Really?" "Ban je na yi gwaji ba amma ina jin symptons ɗin" "Alhamdulillah, Maryam you really make my day" ya faɗa fiskan sa ɗauke da excitement "And the second surprise is..." Ya ɗaga gira yana jiran ta ƙarisa maganar "Na amince zan zauna a nan, its actually a good idea. Rather than na zauna da su Iya ina zama cikin damuwa kullum is better mu zauna gida daban-daban. You dont need to kill yourself because of that" Jikinsa a sanyaye ya tallafo fiskarta ya ce " its not fair Maryam. Da sunan ki na fara ginin nan and" Ta sa yatsa ta rufe bakinsa ta ce " idan Allah ya buɗa ma ka wani lokacin sai ka gina min nawa gidan ko ka siya min wani gidan. Ni ban ji haushin Iya ba, zaman lafiya ma ta kawo mana" Cire yatsar ta da ta yi yai daidai da haɗe bakin su da yai. "Mommy tea, i want tea" muryan Zaytoonah ya daki kunnuwan su. Maryam ta juyo ta kalli 'yartata wacce tuni ta riga ta buɗe ido. "Ya Allah! this girl can eat from morning till night, duk abincin da ki ka ci kafin ki kwanta bai isheki ba" T J ya ce " kar ki takura min Princess" Ya mirgina ya je wajen Zaytoonah ya ɗauketa. Ita kuwa Maryam ta ɗau kofin da T J ya sha tea tana ƙunƙuni tana haɗawa Zaytoonah tea. Tun tana shan nono yarinyar ke da masifar ci, duk dare sai ta yi kukan abinci, shan nonon tsakar dare jazaman ne. Yanzu ma da ta girma ci gareta kamar gara, lokaci zuwa lokaci kuwa za ka ga ta tashi da dare wai a haɗa ma ta tea wani lokaci har da bread ake haɗa ma ta ta ci musamman idan T J ne ya haɗa ma ta... Ba kunya ba tsoron Allah Iya da Hajjo su ka koma sabon gida. Auwal ya ce ba zai bi su ba. Iya ta ce bai isa ba. T J ya roƙeta akan ta barshi zuwa ya ƙarisa makaranta sai ya koma gidan su idan ya so sai ya fara Jss 1 ɗin a cikin gari. Da ƙyar dai Iyan ta bar shi. Neighbors ɗin su sunyi mamakin rashin tarewar Maryam musamman wanda su ka je su ka ga gidan kuma su ka tabbatar gida ne Babba da zai ishi dukkan su. Maryam ta kan ce mu su sabo da zaman quarters ya sa ba ta son tafiya. Ko daƙiƙi ya san wannan ba hujja ba ne. Bayan kwana biyu da tafiyar su da ta kama Saturday Maryam da Auwal su ka shiga gyara gidan. Ɗakin Hajjo da na Iya duk sai da su ka wanke shi su ka goge, sosai su ka gyara gidan ya fito yai tsab da shi. Duk wani tarkacen su da su ka bari sai da su ka yi waje da shi. Da T J ya zo yai ta faɗa akan za ta yi aiki bayan ba ta da lafiya. Ta ce mishi dole ne ta yi dan tun asali haƙurin yadda gidan ya koma ta ke yi. Hajjo irin matan nan ne da duk kyaun gida sai sun ɓatashi saboda ƙazanta. Rayuwa ta dawo mu su sabuwa. Zai zo yai kwana biyu a wajen Maryam ya je yai wa Hajjo kwana biyu. Ɗakin Maryam da ke chan kullewa yai saboda bayaso a ɓata ma ta furnitures ɗin ta. Maryam ta ma sa halacci shiyasa ya shiga neman gidan da zai siya a anguwar na su. Ba shi da kuɗi dan shanunsa ma duk ya siyar saura ɗaya da ƙarami ɗaya. Amma duk da haka idan ya samu gida ko nawa ne zai nemo ya siya hankalinsa ba zai taɓa kwanciya Hajjo na zaune a sabon gida ita kuma Maryam na quarters ba. Bayan wata biyu da tarewan su ya samu Alhaji Iliyasu Mai Auduga. Alhaji Iliyasu na ɗaya daga cikin mutanen da su ka fara zama a anguwan. Yana da gidan sa da ya ke zaune yana kuma da kusan gidaje takwas da ya gina flat flat yana bayarwa haya. Ɗaya daga cikin gidajensa ne wasu su ka tashi dan haka T J yai maza ya samu Alhajin akan yana son siyan gidan. Gidan da gidan T J ɗin gidaje shida ne tsakanin su. Alhaji Iliyasu ya ce ba zai sayar da gida ba. T J yai yai da shi ya ƙi. Ganin ya ƙi ne ya sa shi fayyace ma sa abinda ya faru da kuma dalilin son siyan gidan da ya ke son yi. Baya son iyalen sa su kasance suna nesa da juna saboda sauƙin samunsa idan wani abu ya faru baya gidan ɗaya. Alhaji Iliyasu yai shiru sai kuma daga baya ya ce " ka ci albarkacin kai mai sunan Shehu ne. Zan siyar ma ka da gidan" Alhaji Iliyasu yana bin mazhabar ɗariƙan Tijjaniyya shiyasa ma tun lokacin da ya fara zuwa anguwar da ya haɗu da Alhaji su ka gaisa su ke mutunci ba ya taɓa kiran sa da Tijjani sai dai Shehi. Bayan sun tsaida ciniki T J ya wuce Ringim ya sayar da gonakan sa ya haɗa da babban saniyar sa ya siyar. Still kuɗin bai cikata ba Goggo ta siyar da Sa ɗin ta ta bashi kuɗin ya ce ba zai amsa ba. Tayi-tayi da shi ya ƙi ƙarɓa. Ta ce ma sa indai bai karɓa ba ya nuna Iya ce uwarsa ita bai ɗauketa a matsayin uwa ba, hakan ya sa ya karɓi kuɗin yana ƙara jinjina kyawawan halayen Goggo wanda ta shi Uwar ta rasa. Da kuɗin da kuma aron kuɗi da yai a wajen abokinsa Suleman kuɗin gida su ka cika. Ya je ya biya Alhaji Iliyasu kuɗinsa. Bayan ya samu makullen gidan ya je ya duba gidan ya ga irin gyaran da za a mishi. Gidan dai zai kai shekaru shabiyar da ginashi, ginin na da kyau kuma mutanen da su ka zauna a ciki na ƙarshe sun kula da gidan sosai. Da ya tafi ya je ya kira ma su gyara su ka duba abunda za a gyara su ka faɗi kuɗin da za su karɓa. Cikin sati uku gida ya gyaru har da sabon fenti aka yiwa gaba ɗaya gidan. Duk abunda yai bai gayawa Maryam ko Iya ba. Sai da ya kammala komai na gida sannan ya gayawa Maryam ta shirya za su je wani waje gobe. Ba ta kawo komai ba ta ce to. Su na zuwa ya damƙa ma ta makullin gidan ya ce gidan ta kenan kafin Allah ya hora ma sa a gaba ya gina ma ta wani gidan. "Love ba ka da kuɗi fa" ta faɗa cike da tausayin sa. "Ba abinda zan ce sai dai ki yi haƙuri. You deserve more than this amma for now kiyi haƙuri da wannan"... *** Sai da Maryam ta koma sabon gidan ta kafin ya sanar da Iya. As usual dai sai da ta yi ƙorafi, tare da Hajjo su ka je su ka duba gidan wai ko gidan Maryam ɗin ya fi na Hajjo. Gida ne madaidaici daya ke ɗauke da falo da ɗakuna uku kowanne yana da banɗakin sa. Su ka karkaɗa ƙafafuwan su suka tafi. Duk wasu mahimman abubuwan sa gidan Maryam ya kai ya ajiye. Auwal kam ganin sun dawo anguwa ɗaya ya sa ya ƙi komawa gidan Hajjo ya zauna a gidan Maryam. Iya ta yi masifan ta yi zagin amma ya ƙi komawa wajen su dan haka dole ta haƙura ta ƙyaleshi. A hankali cikin Maryam ya girma wataranan Asabat su na tareda T J ta tashi da naƙuda T J ya kai ta Asibiti zuwa ƙarfe huɗun Asuba ta haifi ɗan ta namiji, kamanninsa sak T J. Wannan karan a Zaria aka yi suna kuma kamar yadda Iya ba ta halarci sunan Zaytoonah ba haka wannan ma ba halarta ba. Ita dai Hajjo ta je sunan. Wannan karan ma Goggo ce ta zauna ta yiwa Maryam wanka. Bayan sati shida ta koma Ringim. Maryam da T J sun so ta cigaba da zama da su amma ta ƙi ta ce ta fi so ta mutu a ɗakin aurenta. Duk da Baffah ya jima da rasuwa amma har yau a matar Baffah ta ke jinta ba a Bazawara wacce mijinta ya rasu ba. Har Goggo ta zo ta tafi Iya ba ta zo ta gaisheta ba. Ita kuwa Goggo har sau biyu tana zuwa gidan da za ta tafi ma sai da ta je ta ma ta sallama. Wannan karan T J bai yi gigin yiwa ɗansa mai sunan wani ba. Maryam ya ce ta zaɓawa ɗansu suna ita kuwa ta zaɓi SALMAN. *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *12-Muntari* Bismillahir Rahmanir Rahim Murmushi na jin daɗi yai lokacin da ya kalli plan ɗin gidan da ake gina ma sa. Aljannar duniya zai gina ma ta, shekaru shabiyar da yai yana shan wahala yana fama da jure zama da Madam Talatu wacce ko sau ɗaya ba ta taɓa burgeshi ba, yayi komai ne domin ta kuma ya tabbata yanzu ya mallaki abinda ko Tijjani zai shekara talatin yana aikin albashi ba zai samu rabin kuɗin da ya ke da shi ba. Saura lokaci kaɗan ya koma gareta, ma su ginin sun ce ma sa cikin wata biyu za'a kammala komai. Ba shi da matsala da wannan zai iya jure wata biyun nan, musamman ma da ya ke da yaƙinin kafin wata biyun nan za ta kasance cikin kaɗaici, cikin tsananin buƙata... Ba ƙaramin kewar mijinta za ta yi ba idan ya tafi, ɗawainiya zai ma ta yawa idan baya nan amma tafiyar tana da muhimmanci. Gwamnatin tarayya ne ta turashi Oxford dan yai digirin digirgir wato Phd na shi. Tun kwana uku daya wuce ta gama haɗa ma sa kayan sa, tafiyar kawai ake jira. Daɗinta ma ranan tafiyar zai faɗo a kwananta ne. Wani littafi ta ke karantawa lokacin da Salman ya shigo ɗakin da gudu. "Mommy..." "Ba na hanaka shigowa ɗaki ba sallama ba?" Ta daka ma sa tsawa Salman da gulma ke cinsa ya koma bakin ƙofa da sauri yai sallama. Maryam ta amsa ta ce ya shigo, "Mommy Adaeze is eating cake in the kitchen" "O'o ni 'yar nan ina za ta kai kwaɗayi ne" ta furta a fili tana miƙewa tsaye, ta bi bayan Salman da ya fita da gudu yana so ya ga yadda Mommy za ta punishing yayar ta sa. Cake ne Mommy ta yi saboda birthday ɗin Salman da za ayi nan da kwana bakwai amma saboda tafiyar Daddyn su shiyasa za ayi shi gobe. Da safe ta baking cake ɗin akan da yamma zuwa dare za ta decorating ɗin sa ashe acicin gidan ta je ta hau kai. A karo na biyar Zaytoonah ta sake buɗe fridge ɗin ta ɗauko cupcake ɗin da ke ciki, wai za ta yiwa Mommy wayo sai ba ta taɓa babban cake ɗin ba amma cupcake guda shida da ke kusa da shi duk ta rarike sama saman ta cinye. Wannan karan za ta cinye ɗaya ne idan Mommy ta tambaya ta ce guda biyar ne ba shida ba. Tana cikin ci ta ji an ja kunnenta ana murɗawa. Tsabar daɗin cake ba ta san yaushe Mommyn ta shigo kitchen ɗin ba. "Ba kya jin magana Zaytoonah, sau nawa ina hanaki ɗaukan abu ba tareda kin tambaya ba" Zaytoonah ta ɓare baki sai kuka shi kuma Salman sai dariya ya ke ma ta. "Na hanaki kwaɗayi Zaytoonah ba kya ji. Do you want me to beat you?" Tana maganar tana cigaba da murɗa ma ta kunne "Kin fara ko, kin fara ko" ta tsinkayi muryan shi a kitchen ɗin. "Kai ka ke ɓata yarinyar nan, jiba yadda ta dawo fa, kalleta fa" Ya kamo hannun Zaytoonah yana tambayar miya faru. Salman ya shiga ba da bahasin abinda Zaytoonan ta yi. T J ya je ya buɗe fridge ɗin ya ɗauko cupcake guda biyu ya miƙa ma ta ya ce "dena kuka kinji, zo mu je ki ci wannan idan bai isheki ba zan ƙara miki" Aikuwa ta dena kukan da ta ke ta karɓi cupcake ɗin ta fara ci. T J ya ja hannunta su ka bar wajen. Maryam ta girgiza kai kawai ta koma wajen fridge ɗin dan taga ta'adin da Zaytoonah ta yi. Ta ci sa'a ma ba ta taɓa cake ɗin birthday ɗin ba... Da dare tana decorating cake kusan ƙarfe takwas na dare sai ga T J ya shigo yi mu su sallama dan ba a gidan ta zai kwana ba. "Sannu da aiki Uwargida ran gida" "Sannu da lallashi" ta faɗa tana murmushi Ya lakato buttercream icing ɗin a hannun sa ya lashe. "Dear kai dai da shan zaƙi" "Ya zanyi, abinda ya fito damu daga ƙauye kenan" Dariya ta fara shima ya tayata yi. "Zan missing ɗin ku sosai Maryam" ya faɗa bayan ya dena dariyan "Muma haka" Shiru ne ya biyo bayan abinda ta ce. Sai chan T J ya ja dogon numfashi ya ce "Maryam ba dan hali na ba, ba kuma dan halin Iya ko Hajjo ba Dan Allah zan bar miki amanar Humairah da Sadiq musamman ma Sadiq, ki yi haƙuri ta kula min da su" Shekara ɗaya bayan Maryam ta haifi Salman Hajjo ta sake haihuwa itama ta samu Abubakar Sadiq kuma still shi ɗin ma Sickler ne, sai dai shi har yanzu yana raye. Shekara biyun farko sun ɗauka ba zai yi rai ba dan yadda ciwon sa ke tashi a kai-a kai amma yanzu da ya cika shekara uku abin ya zo ma sa da sauƙi dan yanzu ma ana son sashi a makaranta idan an shiga sabon term. Bayan haihuwan Sadiq T J ya kai Hajjo aka ma ta planning saboda yadda Hajjo ke saurin ɗaukan ciki ba zai juri samun 'ya'ya SS ba, yaro ya wahala suma su wahala. Murmushi ta yi ta ce " kar ka damu, Allah zai kula maka da mu gabaɗaya har ka je ka dawo"... *** Bayan tafiyar T J gidan ya ma ta faɗi. A da kullum sai ta gan shi, ko da ba ita ke da girki ba zai zo ya duba ta da yaran da safe da kuma dare wani lokaci har da rana amma yanzu shikenan ba za ta sake ganin sa ba har sai ya shekara. Ya ce zai yi ƙoƙarin zuwa mu su bayan wata shida amma ta sani da wahala hakan ya yiwu. Yaran ma kewar sa da su ke yasa kwana biyu sun nitsu ba sa damunta da rigima. Zaytoonah kuwa ta zama babbar banza dan kukan rashin Daddynta da ta ke yi ƙaninta Salman bai yi ba. Kullum sai ta tambayi saura kwana nawa Daddy ya dawo Maryam ta ce ya kusa dawowa. Bisa amanar 'ya'yan sa da ya bar ma ta koyaushe tana zuwa gidan Hajjo ta duba su. Iya dai har yau ba ta amsa gaisuwan Maryam itama Maryam ɗin tana yi ne kawai dan ta fita hakkin ta. Humairah kufulancin Iya ta ɗauko shiyasa ba ta son Zaytoonah da Mommy kaman yadda ake kiran Maryam. Shi kam Sadiq da ya ganta zai fara murna. Makaranta ɗaya Humairah su ke zuwa da Zaytoonah amma ajin su ba ɗaya ba, duk da haka ba sa jituwa. Wani lokaci idan Maryam ta yi abin marmari tana aika mu su ta ce a bawa yara. Iya a ba ta son Maryam ɗin still idan Hajjo ta yi kaso ba ta raba da ita ba za ta ce ina nata. Hajjo kuwa sai ta ma ta tsiya kafin ta ba ta, dan ba ta da zuciya haka za ta ci. Ana kawo abinci daga gidan Maryam za ka ji falon ya buɗe da ƙanshi mai daɗi. Ita kuwa Maryam kullum ta zo sai ta yi mamakin yadda su ka fara ɓata gidan T J. Falon gaba ɗaya ba kyan gani, ga wani wari-wari da ake ji ta rasa na minene, banɗaki da ba sa wankewa akai akai ne ko na rashin shara da moping da ba sa yi. Daga ka ga rigan yara a kan kujera sai ka ga an bar kwanukan da aka ci abinci ba a tattare ba. Wani lokacin ruwa ko kunu zai zube ba za a goge ba. Tunda su ka raba gida indai T J zai yi baƙo ko gidan Maryam zai saukeshi ko da ba ranan girkinta ba ne idan ba hakan yai ba ba ƙaramin kunyata shi Hajjo za ta yi ba... Tafiya ta ke da sauri sauri kaman za ta kife, so ta ke ta yi sauri ta kai abincin ta koma su ci na su abincin. Tsoronta kar kafin ta dawo sun kusa cinyewa. Tana riƙe da kwandon abinci ta yi sallama sannan ta tura ƙofar falon gidan. Iya ce a falon da Humairah su na kallo Iya na yiwa Humairah tsifa. Ta tsani Iya, ba ta son ganinta ita ba dan Mommy ba ba abinda zai sa ta dinga zuwa gidan. Ta ƙariso wajen glass centre table ɗin da ke falon ta ajiye kwandon abincin. Ta juya za ta tafi Iya ta ce " zo nan" Zaytoonah ta juyo ta ƙura ma ta ido. "Shegiya haka uwar ki ta koya miki rashin kunya ki shigo ba za ki gaida ni ba" Ta turo baki ta ce "ni ba shegiya ba ce" Iya ta tashi za ta make ta sai Zaytoonah ta sa gudu za ta fita sai gashi ta buge kwandon da ta ajiye a center table dama a baki-baki ta ɗokana shi. Miyan dai sai gashi ya zube "Iya ki ga ta zubar mana da abinci" Humairah ta faɗa kaman za ta yi kuka Iya ta ƙarisa ta damƙo Zaytoonah ta wanketa da mari. "Ba ki da hankali ko?" Zaytoonah ta fashe da kuka Hajjo da ke ɗaki ta leƙo tana Hamma. Gandar girki ta ke yi shiyasa ta zauna a ɗaki tana tsammanin girkin Maryam dan ta san yau Jummu'a jazaman ne za ta aiko mu su da abinci. Tunda Sadiq ya ce ta dinga kawo mu su abinci kullum saboda abincinta ya fi daɗi yanzu kusan kullum sai ta kawo mu su. Idan ba a kawo na rana ba za a kawo na dare wani lokaci da na rana dana dare duk tana aikowa. Ganin abinda ya faru ne ya sa Hajjo ta ja tsaki ta ce " yanzu gaba ɗaya miyan ne ya malale?" Humairah ta ce "akwai saura kaɗan" "To wallahi ku ɗebe dan ba zan sake wani miya ba" Iya ta zunguri ƙeyar Zaytoonah ta ce ta wuce ta ba su waje. Zaytoonah ta fita tana kuka. Sai da ta kusa isowa gida ta ƙara volume ɗin kukanta, daga bakin ƙofa Auwal ya jawota jikin sa yana tambayan miya faru. Ganin Mommy ta tsura ma ta ido ya sa ta ce "Iya ce ta mare ni" Maryam ta san ba za ta yi ƙarya ba dan ba tarbiyyan da ta mata ba kenan. Amma kuma ba abinda za ta ce tunda ta san anyi hakan ne dan ta yi magana. Maryam ta ce"Je ki wanke hannu ki zo mu ci abinci" "Mommy" ta faɗa tana fashewa da wani sabon kukan Maryam ta ce Auwal ya saketa ya zo su ci abinci. Tarbiyyan da ta ɗaura mu su shine dukkan su suke haɗuwa su ci abinci a tray ɗaya, ko T J na nan ma duk ranan girkinta indai yana nan dukkan su ke haɗuwa su ci abinci tare. Indai ta ware mu su abinci to Zaytoonah ne ta dameta da kukan yunwa sai ta zuba ma ta nata. Wani lokaci bayan taci idan sun zo za su ci na su itama za ta sa hannu a ci da ita. Tana tsaye tana kukan sakalci ta ga Mommy ta serving abincin sun fara ci. Ta dinga bin bakin su da kallo yadda su ke cin abinci hankali kwance, ganin Salman ya ɗau ƙatuwar hanta yana ci hakan ya sa ta ka sa haƙuri ta zo da gudu ta zauna. Za ta sa hannu Maryam ta daka ma ta tsawa dan haka ta yi hanyar kitchen a ɗari. Da ta dawo kuwa ta fi kowa ƙaton loma tanaci da sauri-sauri kaman abincin zai ƙare. Tuwon shinkafa da miyan egusi daya ji naman kayan ciki da pomo ne sai ƙanshi miyan ke yi. "Zaytoonah ki ci a hankali mana" Auwal ya faɗa yana kallon yadda ta ke zare ido saboda ta cika bakinta da abinci kuma tuwon da zafi. "Bar ta, idan ta ƙware za ta yi hankali" Maryam ta faɗa tana kau da kai shi kuwa ya miƙo ma ta ruwa a kofi ta karɓa ta kora... Tundaga marin da Iya ta ma ta ta dena kai abinci gidan, idan an bata abinci sai ta fita da shi sai ta tsaya a ta lungun da Almajirai ke zama suna cin abinci ta juye mu su sai ta ɗan tsaya kaɗan kafin ta wuce gida. Wani lokaci idan ta juye abincin a kwanon almajiran ko kafin ta juye taga nama dumu-dumu sai ta tsaya ta zaƙolo naman da ke ciki ta ci kafin ta juye mu su ta wuce gida. Ta sawa ranta ba za ta ƙara kai wa su Iya abinci ba. A ranan na huɗu ne da Maryam ta je duba su Sadiq sai Hajjo ke ma ta habaici wai dan ta ga Sadiq ya damu da girkinta ne shine ta ke ja ma sa rai kafin ta aiko. Ta yi maganan ne saboda missing daddaɗan girkin Maryam da su ka yi cikin kwanakin. Maryam ba ta gane zancen ba amma ta dake ta ce "Sadiq duk lokacin da ka ke son cin abinci ka zo gida ka ji" yaron ya gyaɗa ma ta kai. Dama yana son zuwa Hajjo ke hanashi, ita a nata tunanin idan ya je ya ci a gidan Maryam ba za ta aiko musu ba. Tunda dai abincin da ta ke aikowa ba abincin da Sadiq kaɗai zai ci ba ne tunda ko tuwo ne leda biyu manya ta ke sawa. Zuwanta gida ta samu Zaytoonah na yin assignment a falo. Sai da ta zauna ta ce " Adaeze zo nan" Zaytoonah ta taso da sauri dan ta san indai Mommy ta kirata da Adaeze ko Princess to za'a lallasheta ne da abun ƙwalama. Ɗazu da rana ta fasawa Mommy plate sai Mommyn ta sa ta kneel down ta ɗaga hannu ta rufe ido na kusan minti shabiyar. Maryam ta ɗaura Zaytoonah akan cinyarta tana shafa kitson chuku da aka ma ta wanda jelar sa ya sauka har kafaɗanta. Maryam da T J duka suna da gashi sai dai Zaytoonah yanayin gashin T J ta ɗauko baƙi mai tsantsi ba kaman na Maryam ɗin da ya ke brown kuma kinky hair ba. "Adaeze a wa kike kai wa abinci idan na aike ki gidan Iya?" Nan da nan idonta ya kawo ruwa. "Ban ce ki min kuka ba, gaskiya kawai za ki gaya min. Idan ma kin yi ƙarya zan gane kuma dukan ki zan yi" "Mommy i'm sorry" ta faɗi tana fashewa da kuka "Zubar wa ki ke yi?" Ta yi saurin girgiza kai "Ya kike yi da shi?" Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "Almajirai na ke kai wa" Maryam ta ƙura ma ta ido dan ta gane ko ƙarya ta ke ma ta amma gaskiyar ce dai ta faɗa. Ta sani saboda abinda Iyan ta ma ta ya sa ta ɗau wannan matakin. She wont blame her tunda Iya ce ta creating wannan ƙiyayyar tun farko. Ta sa hannu ta goge ma ta hawaye ta ce shikenan daga yau za ta dinga aikan Auwal idan baya nan za a nemi ko Almajiri ne ya kai mu su. Zaytoonah ta gyaɗa kai... *** "Maman Bola, Maman Bola" Humairah ta dinga faɗi lokacin da su ka fito daga cikin school ɗin za su je wajen Manu mai mashin wanda ke kawo su makaranta. Maman Bola suna ne da wata 'yar ajin su Zaytoonan ta sa ma ta saboda kullum itace da takarcen ciye-ciye idan ta zo school. Tsab-Tsab za a shiryata zuwa makaranta amma kafin a tashi ta ɓata jikinta. Idan ba ka ga uniform ɗin ta ya yi dumu-dumu da kayan ƙwalama ko maiƙon abinci ba zaka ga ya ɓace da ƙasa. Tana zaune a aji tun ma kafin a fita break za ka ga ta fara buɗe food flask ɗinta tana cin soyayyen dankali ko ƙwai, idan ta ɗebi loma ɗaya biyu ta ga za a ganta sai ta yi saurin rufewa ta goge hannunta na maiƙo ajikin uniform ɗin. Zaytoonah kenan. Humairah ba ta san da sunan ba sai da yau suna fitowa Habiba 'yar class ɗin su Zaytoonan ta kira ta dashi. Shine kuma Humairan ta samu sai tsokanarta ta ke yi. Zaytoonah ba ta kulata ba dan Mommy ta hanata dukan Humairah kullum ta kawo ƙaran ta sai ta riƙa cewa ita ce Babba ta yi haƙuri. Ita kuma Maryam ba ta son ƙara ingiza wutar gaban da Iya ta kunna ne tsakanin yaran. Daidai wajen ɗalibai dayawa da ke jiran a zo a ɗaukesu Zaytoonah ta yi wuf ta cire hulan Humairah. Ƙitson chuku aka ba su a satin kuma shi ke kan Humairan amma da ke ba ta da gashi sai chukun ya ƙi haɗuwa balle ma har a haɗe shi a dunƙule kamar yadda na Zaytoonah yai. Zaytoonah ta fara " ku ga Humairah me ƙwaƙwuyayyen gashi, ƙwaƙus, ƙwaƙus ƙus, ƙus, ƙus" Haka ake tsokalar yaran da ba su da gashi a class na su kuma abun na sosa mu su rai har ka ga suna kuka, wani lokaci sai Aunty ta tsawatar ake denawa. Itama Humairan kuka ta fara musamman da ta hango wasu ɗaliban sa'anninta na dariya. Har Manu ya saukesu Humairah ba ta dena kuka ba. Ta shiga gida da gudu tana kuka, straight ɗakin Iya ta wuce tunda ba ta ganta a falo ba... Mommy ba ta dawo daga office da wuri ba yau dan haka gidan maƙotan su Maman Fawaz su ka wuce dan su jirata, da ke Auwal sai ƙarfe biyu zai dawo saboda a JSS 2 ya ke. Idan kuma ya rigata dawowa zai karɓi key a wajen Maman Fawaz ya buɗe mu su gidan. Su na zaune a falo suna wasa da yaran Maman Fawaz ɗin sai ga Iya ta yi sallama hannunta riƙe da Humairah. "Iya ga ta nan, dama nan su ke zama idan Mommyn su ba ta nan" Humairah ta faɗa tana nuna Zaytoonah. "Zo nan dan Uwar ki" "A'a Iya ke ce a gidan na mu" Maman Fawaz ta faɗa da fitowanta kenan daga kitchen. Ba ta kula Maman Fawaz ba ta je ta finciko Zaytoonah. "Dan Allah ki yi haƙuri kin san sha'anin yara..." "Ba ruwan ki jikata ce" Iya ta katseta Zaytoonah na kuka haka Iya ta ja ta su ka bar gidan. Direct gidan Hajjo su ka wuce wanda tun a hanya Iyan ke ta surfa masifa. Suna zuwa kuwa ta ɗauko almakashi ta danneta ta fara aske ma ta gashi tana faɗin gaba ta ƙara yiwa Humairah Shalele dariya ƙwandala za ta ma ta. Humairah na dariya ganin yadda dogon gashin Zaytoonah ke zubewa a ƙasa. "Iya kin san dai Maryam ba za ta yi shiru ba ko?" Hajjo ta faɗa bayan ta fito daga kitchen jin kukan Zaytoonah. "To ko Ubanta yana nan ya isa yai magana balle uwarta Inyamura" Hajjo ta taɓe baki ta koma kitchen ɗin. Jikarta ce dan haka ba ruwanta da abinda ta ke yi. Bayan ta aske gashin wanda ya saura kaman irin low-cut ɗin nan sannan ta riƙe kunnen ta ta ce " duk ranan da kika sake tsokanarta sai na ɓaɓɓallaki" Har gara Salman sau dubu a wajen Iya akan Zaytoonah wacce kamanninta da Maryam ya ƙara sa ma ta baƙin jini a wajen Iyan. Banbancinta da Maryam kawai farin fata ne wacce ita Zaytoonan ta ɗauko baƙin fatan T J. Da gudu Zaytoonah ta fice a falon wanda tsabar bata ganin gabanta sai da ta bugu da ƙofa. Ko zafin bugun bai dameta ba ta fice daga gidan tana kuka. A hanya ta haɗu da Auwal da ke shirin shiga gidan Maman Fawaz. "Zaytoonah wa ya dake ki? Ina ki ka je? Iya ce ta dake ki ko Umma Hajjo?" Duk tambayoyinsa ba wanda ta amsa ma sa sai kuka kawai... A bakin ƙofa ta tsaya tana kuka tana jiran Mommynta, Auwal yayi-yayi ta shiga gida ta ƙi dan haka shima ya tsaya bakin ƙofan yana cigaba da lallashinta, shi bai ma lura da kanta ba saboda akwai hula a kanta. Salman ma ganin yadda Zaytoonah ke ta kuka ya sa shi fara kukan, su na yawan faɗa da Addar ta sa amma yana son ta sosai. A haka Maryam ta dawo daga office kusan 2:30pm ta same su. Tana saukowa daga mashin Zaytoonah ta je ta faɗa jikinta tana kuka tana Mommy. "What happened?. Auwal miya sameta?" "Nima ban sani ba amma ina tunanin Iya ce ta dake ta" Ta ɗan sunkuya dai dai tsayin Zaytoonan ta ce " Adaeze waya dake ki?" Zaytoonah ta sa hannu ta cire hulan kan ta tana cigaba da kuka. "Iya did this to you?" Ta gyaɗa ma ta kai. Rarrashinta ta fara yi amma inaa ta ƙi yin shiru hakan ya sa ta ɗauketa duk da girmanta a hakan ta shiga da ita cikin gida. Yau duk kayan ƙwalamar an ma ta tayin su ta ƙi ci sai kuka. Daga baya ne ma Maryam ta lura da fashewar da gefen goshinta yai. Ta goge jinin da ya bushe ta shafa ma ta magani. A jikinta ta kwanta tana shafa bayanta har ta yi bacci, sannan ta kwantar da ita a gado. Ranta idan yai dubu to ya ɓaci, ba za ta bari a cigaba da cin zalin 'yar ta ba dan haka ta wuce gidan Hajjo cike da ɓacin rai. Spaghetti ce akayi dafa dukan ta wanda yai yi wani irin dahuwa sosai ya caɓe. Amma a haka su ka zauna suna ci, Humairah dai wasa ta ke yi da shi dan abincin bai ma ta ba. 'Yar indomie noodles ɗin nan Ummanta ba ta dafa ma ta yai kyau kaman na sauran 'yan ajin su. Sallama da ta zama dole Maryam ta yi lokacin da ta shiga falon. Duk su ka tsura ma ta ido, Sadiq ne kaɗai baya wajen dan yayi bacci a ɗaki. "Wallahi Wallahi duk ranan da wani a gidan nan ya sake taɓa min lafiyar 'ya ta sai hukuma ta rabamu, ko da kuwa uwar da ta haifi uban ta ne. Cin zalin ya isa haka, ya isa haka, i repeat ya isa haka. Idan ba a son 'ya ta a bar min ita ina son kayana. Idan kunne ya ji jiki ya tsira" daga haka ta fice a gidan. Har ta gama magana ba wacce ta yi magana. Ita kan ta Iya yadda Maryam ke magana da ƙarfi sai da ta ɗan tsorata. Daren ranan sai da Zaytoonah ta kwana da zazzaɓi saboda kuka da ta sha. *** Exams yaran ke yi dan haka da wuri su ke dawowa gida. Yau ma sun jima da dawowa suna ta damunta da rigima ta tura su gidan su Fawaz. Shi kuwa Auwal ya je aski. Ba ta jin daɗi ya sa ta dawo daga office tun ƙarfe shaɗaya na safe. Laulayi ne ta ke wanda ba ta san tana ɗauke da cikin ba sai sati biyu da su ka wuce wanda ya kama satin T J shida da barin ƙasar. Jin ana buga ƙofa ne ya sa ta tashi daga baccin da ta ɗan farayi. "Zaytoonah? Salman?" Ta fara kiran sunan yaran amma shiru dan haka ta sa a ranta ba su ba ne. Doguwar riga ce ajikin ta dan haka gyalensa kawai ta yafa ta fito. Jin yana ta buga ƙofa ba a amsa ba ne ya sa shi buɗe ƙofan ai kuwa ya ji shi a buɗe. Ba tareda wani shayi ba ya kutsa kai cikin gidan. Ko'ina tsab-tsab a falon sai ƙanshi ke tashi. Yai murmushi dan ya san Maryam ce da wannan gyaran. Fitowan da za ta yi a ɗaki ta ga wani guntun mutum a tsakiyar falonta ya ƙurawa hoton su da ke jikin bango ido. Hoto ne da su ka yi duka gidan ranan birthday ɗin Salman na cika shekara huɗu a duniya. "Malam lafiya za ka shigo min gida ba tareda izinin ma su g..." maganar ta kafe lokacin da mutumin ya juyo. Shekaru shabiyar rabon da ta sashi a ido , ita tama manta da batun sa. Saɓanin wancan da ta sani da ya ke yaro ɗan ƙauye mai kusan shekaru ishirin, wannan ya ƙara girma da wayewa ga alamun hutu ya ratsa shi. "MUNTARI!" Ta furta cike da mamaki "No no no no. Its ALHAJI MUNTARI" *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *10-Zaytoonah* Bismillahir Rahmanir Rahim Maryam renon cikinta ta ke yi hankali kwance, laulayin da ta ke ji ma a hankali ya zo ya tafi. Karatu su ke ba kama hannun yaro dan haka ba ta da lokacin raki. Indai ba so ta ke ta sake maimaita jarrabawarta ba. Ko so ɗaya ba ta yi gigin zuwa gida ba, da Azumi da sallah duk a Abuja ta yi. T J ma duk yadda ya ke so ya ganta kusa da shi haƙura yai dan ya san zaman Abuja ya fi ma ta kwanciyar hankali ga karatu ga renon ciki. Duk weekend yana zuwa ya ganta friday da yamma zuwa Sunday da yamma ya tafi. Bayan sallar Azumi watarana ta shiga gaisuwa sashen su Landlord ɗin ta wanda matar ta dawo daga Umurah. "Maman biyu" Hajiya Fatima ta faɗa tana dariya "Ni na ɗauka zan zo na samu kin sauka" "Hajiya idan na haihu ai bakwaini kenan" Hajiya ta yi murmushi ta ce "Allah ya raba lafiya" Bayan sun gaisa ne ta kawo mata tsaraba ta yi godiya ta tafi. Cikin tsarabanta akwai gabaruwa da kuma 'ya'yan Zaytoon wanda ke cikin wani kwalba mai kyau. Ta ji daɗin 'ya'yan Zaitoon ɗin nan dan zuwa washegari a school ta cinyeshi tas. Daga lokacin kuma kamar wacce ta zama addicted to it sai ga shi har komawa ta yi wajen Hajiya Fatima ko akwai ta ƙara ma ta. Unfortunately duk ta rabar amma ta ce ba za a rasa a manyan grocery stores ba. Daga wannan lokacin ta zama regular customer a wani ƙaton store wanda ta samu suna sai da 'ya'yan zaitoon ɗin. Watarana da ta je siya babu ta haɗe rai sai wata mata a wajen ke cewa "ki ce mun kusa samum Baby Zaitoon ko Zaytoonah" Maryam ta yi dariya ta bar store ɗin da zimmar ta nemi wani wajen ko za ta samu... Prior to Bar final exams ɗin su sai da ta yi rashin lafiya, karatu ne ba wasa indai tana son cin exams ɗinta ga cikinta da ya shiga wata takwas. Wani weekend da T J ya zo ya ganta ne ya tsorata da ramar da ta yi saboda stress. Saturday ya tafi Ringim ya ɗauko Asma'u wacce ta zama 'yan mata. Tana JSS two kuma alamu sun nuna za ta ƙarisa makaranta dan Goggo na son 'yar jikarta ta yi boko. Suna hutu dan haka ba wata matsala. Ta ji daɗin zuwan Asma'u dan ko ba komai za ta rinƙa taimaka ma ta da wasu ayyukan sannan kaɗaici ma na daɗa ƙara ma ta damuwa. Haka dai ta daure ta yi karatun da daɗi ba daɗi, da ikon Allah kuma da aka fara exams ba ta samu matsala ba dan har ta gama ba ta yi ciwo ba. Washe garin da ta ƙarisa exams sai ga T J ya zo ɗaukan ta. Ta ce ba inda za ta je ba za ta haihu a Zaria ba, ANC ɗin ta duk a Abuja ta yi dan haka a nan za ta haihu. Duk yadda T J yai da ita ƙi ta yi ta ce ba za ta tafi ba. Shi tsoron barinta ita ɗaya ya ke yi a wajen ga shi Asma'u ta koma makaranta. Ita kuma zama da Iya ne ba ta so musamman at this condition da ta ke ciki. Ganin ta ƙi yarda ne ya sa dole ya haƙura ya bi son ranta amma ya ce da ta ji wani ciwo ta aikawa su Hajiya Fatima ta amsa ma sa da za ta yi hakan. Washe garin ranan da ya tafi da ta kama Monday ta tashi da naƙuda ta daure ta shiga cikin gida ta sanar da Hajiya Fatima. Hajiya ta shirya ta sa Dreba ya wuce da su Asibitin da Maryam ɗin ke awu. Haihuwa zai zo ba zai zo ba tun ƙarfe shaɗaya na safe har bayan Isha, kusan ƙarfe tara da minti shida na dare tukunna ta sauka, ƙatuwar Baby Girl ta fito duniya. Ba ƙaramin galabaita Maryam ta yi ba kafin ta haihu, saboda baby ɗin ma da girmanta sai da aka ɗan farka ta kafin kan baby ya fito. Maryam ta ga Bone kam, ashe haihuwa ba sauƙi. Zuwa goman dare an shirya baby an gyara uwarta. Hajiya Fatima ce ta tsayawa Maryam, daga gidan ta aka kawo mu su komai. Duk da babu wata matsala amma ance gara Maryam ta kwana ta huta tukunna kafin a sallame su dan haka a Asibitin su ka kwana. Hajiya ta yiwa Maryam kawaici dan ko da mai aikinta ta zo akan ta bari ta kwana da Maryam ɗin ƙi ta yi ta ce ta je ba matsala. Washe gari da safe ƙarfe tara da rabi na safe aka sallamesu su ka wuce gida. Baby kam tana cikin ƙoshin lafiya sai bacci da cin abinci da kuma kuka. Da su ka dawo ne Maryam ta yi amfani da wayan landline ɗin Hajiya ta kira office ɗin su T J baya ma Office ɗin colleage ɗin shi ne ya ɗauka. Ta bar mi shi saƙo akan a sanar da shi ta sauka lafiya. T J na dawowa da aka sanar da shi ya kama tsallen murna haka ya tattare ya koma gida. Cike da farin ciki ya sanar da Iya cewa Maryam ta haihu. Buɗan bakin Iya sai ta ce "an dai ɓata mana zuriya" T J ya cizi leɓensa na ƙasa yana jin zafin kalaman Iya. Da yamma ya isa gidan inda Maryam ta koma sashin su Hajiya saboda Hajiyan da ta nemi ta dawo wajen ta. Ya ɗau Baby wacce ke baccinta hankali kwance. "Wakey-Wakey Princess, Daddy is here" Yana maganar yana shafa fiskarta da babban yatsar sa. Maryam ta ƙura ma sa ido tana murmushi. Ya ɗago ido ya kalli Maryam ya ce "Dama na gaya mi ki Princess ce" "Sannu Daddyn Princess" "Allah ya raya mana ita da Imani" Maryam ta amsa da Amin. Ya rankwafo ya kissing goshin Maryam ya ce " na gode da wannan kyauta" Ta tunkuɗe shi ta ce "dole ka ce ka gode tunda kana chan kana hutawa ka barni da wahala" "Sorry My Queen kin san da akwai yadda za ayi na maida ciwon jikina da zanyi. Tunda ki ka yi nauyi Dear ban taɓa samun kwanciyar hankali ba sai yau. Ke ma kin sani" "A hakan the last time da ka zo sai da ka yi..." "Sai da na yi me?" Ta ɗan ja kumatunsa yai dariya ya ce " Maryam kin san idan kina kusa da ni tamkar magnet na ke komawa, idan ban ji ki a jikina ba na jin daɗi" "Sorry Mr Magnet ni da kai sai bayan shekara biyu idan na yaye Adaeze" "Adaeze?" "Princess" Maryam ta amsa ma sa "Wani suna ya kamata mu sawa Adaeze, the last time da mu ka yi maganan kince na bari ki haihu lafiya tukunna" "You decide" "No we decide" "Duk abinda ka sa ma ta ni dai zan kirata da ZAYTOONAH" "Zan ba ta labarin yadda ki ka yi ta yawon neman 'ya'yan zaitoon kwararokwararo-lungu lungu" Sun tsaida magana akan za a yiwa Iya takwara amma za su dinga kiranta da Zaytoonah. Duk yadda ta so ta kauce zuwa Zaria a ranan bai yiwu ba dan shatan mota ya ɗauko su ka wuce Zaria bayan sun yi wa su Hajiya Fatima sallama. Takwas na dare ta ɗan wuce kaɗan su ka isa gida, su na shiga kaman yadda ya saba ganin su hakan ce ta faru domin kallo su ke yi dukkan su biyu ga falon nan kaca-kaca, sun ci abinci amma ba su tattare kwanukan ba. Maryam ta daure ta ce "Barka da dare" Hajjo ce ta iya cewa " sannu da zuwa ya jiki?" Maryam ta amsa da sauƙi, da ta zo za ta shiga ɗakinta ne ta ji maganar da T J ya faɗa da kuma amsar da Iya ta bayar. TJ ya miƙawa Iya Baby Zaytoonah yana faɗin " Iya ga takwarar ki ta iso" "Allah ya kiyaye 'yar zina ta ci babban suna kaman nawa" Ya haɗiyi miyau da ƙyar yana kallon yadda iya ta koma gefe dan ma kar ya ɗaura ma ta baby a cinya. Maryam na shiga ɗaki ta zauna a bakin gado ta kifa kai da gwiwa. Kuka ta ke son yi amma kuma ba amfanin yin kukan ta ɗago ido tana sauke ajiyar zuciya daidai T J ya shigo ɗauke da baby. A gefenta ya shimfiɗa baby da ke bacci ya ce "Maryam I'm sorry" "Ka yarda da maganar da ta faɗa kenan?" "Noooo" "Then maganar ta wuce" Ya durƙusa gabanta ya kamo hannayenta duka biyu. If only Iya ba mahafiyar sa ba ce. If only zai iya cewa Iya ta bar gidan su ta fita a rayuwar su. Tunanin da ya ke yi kenan azuciyar sa. Bai san wani kalma zai faɗa ma ta dan ya tausasa ma ta zuciya ba. Dan haka ya cigaba da murza hannunta a hankali... *** Kwanan su ɗaya ya kai Maryam Ringim, zo ka ga murna a wajen Goggo da sauran 'yan uwan T J wanda su ke son Maryam ɗin tsakani da Allah. Kowa ya ga baby sai ya ce kamannin Maryam ta ɗauko sai kuma yanayin idon T J da ta ke da shi. Goggo da kan ta ta fara yiwa baby da mai jego wanka. Ana gobe suna Pendo ta taho daga Dutse da 'ya'yanta biyu Mustafah da Binta. Da yamma aka yiwa Maryam ƙumshi mai kyau ja da baƙi wanda ya ƙara fito da ita. Ko da Goggo ta ga ya zo shi ɗaya sai ta tambayeshi miyasa ya baro Iya da Hajjo a Zaria. Bai ɓoye ma ta komai ba ya sanar da ita abinda ya faru gameda sheganta Zaytoonah da Iyan ta yi. "Ban san ya zan yi ba Goggo. Wai dama dan a samu sulhu tsakaninta da Maryam ya sa na ke son yi mata takwara kuma ta ce indai na sawa Zaytoonah suna Aisha ba ta yafe ba" Goggo ta yi shiru na ɗan wani lokaci kafin ta ce " ka ci gaba da haƙuri Shehu, duk munin Uwa ba a chanja ta. Tunda ba ta son a ma ta takwara shikenan Allah ya raya mana Zaytoonah. Insha Allahu yadda ta ƙi ta sai yarinyar nan ta zama alkhairi ga dukkan gidan nan. Sai tauraronta ya haskaka ko'ina, kuma Iya sai ta yi dana sanin furucinta" T J ya amsa da Amin. Ranan suna kam anyi liyafa na gani na faɗa. Ko lokacin sunan Sadiq ba ayi shagalin da aka yi a sunan Zaytoonah ba. Wasu da su ka ji sunan da yarinya ta ci sai abin ya mu su banbaraƙwai. Ga sunan su na gargajiya da aka saba ji amma an tsallake an tafi wani suna wai Zaytoonah. Wanda su ke da ilimi sosai cikin su kuwa sun yi na'am da wannan suna. Goggo ta ce sai Maryam ta yi Arba'in kafin ta koma gida, shi dai T J bai so ba ya dai haƙura ne. Ita kuwa Maryam da ma ba ta ɗokin komawa gidan, har yau furucin da Iya ta yi na cinta. Har Maryam ta yi Arba'in Iya ko Hajjo ba wanda ya zo Ringim. TJ kaɗai ke zirya tsakanin Zaria da Ringim ɗin, duk weekend zai zo ya ga Princess ɗin sa. Ana gobe za ta koma Zaria da yamma sai ga Inna Yelwa ta zo wajen Goggo da wani Yaro da ba zai wuce shekara shida ba. Wai ta kawo shi ne yai sallama da Uban sa za a kaishi Almajiranci. Maryam ta ƙurawa yaron ido, tausayi ya ba ta. Ba ta san ɗan waye ba a gidan amma yana ɗan shigen kamanni da Usman Yayan T J shiyasa ta yi hasashen ko ɗan sa ne. Goggo ma dai ta yi jajen wannan abu dan gani ta ke yi Auwal yayi ƙaranci. Sai dai ya za ta yi tunda dai ba ta da iko da shi. Bayan tafiyar Inna Yelwa sai Maryam ta tambayi wacece ita. "Mahaifiyar Hauwa ce, Hauwa marigayiya matar Manga" "Goggo ba dai Hauwa ta rasu ba?" Ta tambaya cike da tsantsan mamaki tana ƙoƙarin tuno Hauwan, wacce ke cike da tsananin kunya. Lokacin da T J ya dawo daga bautar ƙasa Usman Manga ya auro Hauwa, shekaranta shabiyu a lokacin. Maryam da Pendo su ka je ganin Amaryar da aka kawo daga ƙauye, bayan sun dawo ta dinga yiwa T J complain wai taya zai bari Yayan sa ya auri yarinya ƙarama haka. T J ya ce ba shi da ikon hana ɗan uwansa abin da yai niyya. A wajen su hakan ba komai ba ne. Ta dinga tausayin yarinyar kasancewa Uwargidan Usman na da masifa. Tana ɗaya daga cikin ma su aibanta Maryam lokacin da ta zo gidan. "Hauwa ta rasu ai ya kwana biyu, lokacin kina Makaranta ne shiyasa ba ki sani ba" Maryam ta ce Allah ya jiƙanta Goggo ta amsa da Amin. Washegari da T J ya zo ta ma sa maganar Auwal da za akai Almajiranci da rashin dacewar hakan. Tunda mahaifiyar sa ta rasu Kakarsa ta tafi da shi ƙauye ta cigaba da renon sa. Ko girma bai yi ba wai za a kaishi wani gari Almajiranci. Ganin Maryam ta damu da yaron ne ya sa yai wa Yayan sa magana akan yana so a bashi Auwal. Usman ya ce ai Auwal ɗan sa ne ba komai. Tareda shi su ka je ƙauye su ka karɓo Auwal ɗin, sun samu ma ana jiran isowan Malamin da zai tafi da shi ne, da rabon dai Auwal ba zai yi Almajiranci ba shiyasa su ka riga Malam zuwa. Maryam ta ji daɗi da T J ya damƙa ma ta Amanar Auwal har yana tsokalarta wai ta zama uwar biyu, ga Baby Zayt ga kuma Auwal. Haka su ka tarkata su ka tafi da shi Zaria. As expected sai da Iya ta yi bore akan ba ta yarda Auwal ya zauna a wajen Maryam ba. Haƙuri ya ba wa Maryam sannan ya damƙawa Hajjo amanar Auwal amma a gaban Iya ta ce ba za ta iya riƙe shi ba itama fama ta ke da kanta wai ciki gareta. Ƙarshe dai ɗakin Iya aka ajiyeshi. Zaman na su dai gashi nan gashi nan ne. Maryam na kaffa-kaffa da iya amma duk da haka kullum sai ta zageta ga habaici. Zaytoonah kuwa ko sau ɗaya ba ta taɓa ɗaukan ta ba. Da farko Iya ƙin cin girkin Maryam ta ke yi, sai ranan da Hajjo ta yi biris ta ce indai Iya ba za ta ci girkin Maryam ba to sai dai in ta shiga kitchen ta dafawa kan ta amma ba za ta ma ta wani girki ba. Iya ta ture abinci gefe ta hau fushi, da yunwa ta isheta ta ce Auwal ya je ya ɗauko ma ta abincin. Daga nan labari ya sha banban dan sai dai ta mutu amma Maryam ta fi Hajjo iya girki nesa ba kusa ba. Ko ita Iyan ba za ta iya sarrafa abinci kaman yadda Maryam ke yi ba. Daga nan kuma Iya ta samu tsirface tsirface duk dan ta muzgunawa Maryam. Ta ce abu kaza za ta ci a'a abu kaza bai ma ta ba wani abu daban da babu shi a gidan za ta ci. A haka dai Maryam ke daurewa tana binta sau da ƙafa. Daga baya kuwa sai Iya ta kira Maryam ɗin ta ce da ranan girkinta da ba nata ba ita za ta dinga yi har sai Hajjo ta sauka, ana maganan wata biyar a gaba. Maryam ta ce ta ji. Ganin anyi sati tana girki T J bai yi magana ba ya sa ta san da yardar shi kenan Iya ta saka wannan doka. Ranan tana ba wa Zaytoonah nono sai ga Auwal ya shigo da gudu, dawowar sa kenan daga makaranta. Kusan dai Auwal kwana kawai ya ke yi a ɗakin Iya amma Maryam ita ce ɗawainiyar sa wanka da wankin sa duk ita ce. "Mommy wai gashi inji Baban Lucas ya ce na baki" ya faɗa yana miƙa ma ta wani ƙaton envelop. Ta amshi envelop ɗin tana tambayar sa a ina su ka haɗu ya ce ya zo zai shiga gida ne ya kirashi ya bashi wai ya kai wa Mommyn sa. Sai da ta gama feeding Zaytoonah ta kwantar da ita sannan ta buɗe envelop ɗin ta fara dubawa nan ta ke fiskarta ya washe da murmushi. "Mommy goya min ita" muryan Auwal ya fargar da ita "Ba yanzu ba, je ka cire uniform ɗinka ka sa kaya sai ka zo na zuba ma abinci" Ya ce to sannan ya fita da gudu... Da dare ta nunawa T J takardan samun aiki da aka kawo ma ta, wanda aikin ma ta nema ne ba tareda sanin T J ba. "Maryam yaushe wannan?" "You are too busy Barkindo, ka dena damuwa da halin da na ke ciki balle ka san mi na ke buƙata" "Maryam ki min uzuri dan Allah. Aikin ginin da na ke yi duk shi ya ke ɗauke mun hankali" "Zan koma Kaduna da zama, zan dinga zuwa mu ku a weekend. Idan kana so zan iya tafiya da Auwal" Yai sokoko yana kallonta har ta gama bayani. "Maryam ina za ki tafi min da 'ya? Maryam dududu nawa Princess ta ke za ki tafi da ita wani gari aiki. Besides aikin kotu fa, a ina za ki dinga ajiyeta?" "I knew it, i knew it. Saboda matar ka na da tsohon ciki kar Nanny ta tafi ta bar ta da wahala" "Maryam..." "Tijjani please. Ba sai ka yi wani ƙarin bayani ba na fahimci komai" "Maryam ba abinda ki ke tunani ba ne wallahi, zaman ki a Kaduna ba zai yiwu ba, kuma ki dinga to-and-fro tsakanin Kaduna zuwa Zaria expenses ɗin zai yi yawa. But wallahi duk ba wannan ba ne babban damuwana, damuwar shine Zaytoonah, ba za ki ji daɗin aiki da reno ba" "Ya wuce" ta faɗa tana kwantawa kan gado ta ja bargo har ka. "Maryam, Maryam, Maryam" ta ƙi ta kulashi hakan ya sa ya hau gadon shima. "My love na miki alkawarin zan nema miki aiki a nan Zaria amma kiyi haƙuri da maganar Kadunan nan. I know saboda Iya ki ke son tafiya ba dan komai ba. But Maryam ki dinga tausaya min dan Allah, duk lokacin da bakya nan gidan ina wahala. Maryam ke ce hasken gidan nan ke ce farinciki na, ina buƙatar ki kusa da ni. And Maryam what about Zaytoonah? Taya zan dinga ba ta kulawa idan ba ta kusa da ni a koda yaushe?" "Maryam..." ya kai hannu zai taɓa ta ta buge hannun "Leave me alone" ta furta da ƙarfi wanda hakan ya sa Zaytoonah da ke kwance tsakiyar su ta kama kuka. Ya ɗau Zaytoonah ya fara lallashin ta. Ita kuwa rufe kunnuwanta ta yi dan ma kar kukan Zaytoonah ya dameta ga uwa uba haushin T J da ta ke ji. Har zai ce idan ba ta gidan baya samun farinciki bayan daga ta ɗan kwana biyu ba ta gidan shikenan boom sai ka ga Hajjo da ciki. Why on earth did she love this man so much? Yadda ta ke jinta yanzu kamar ta tattara kayanta ta bar ma sa gida ta yi nisa da shi har abada, ta rabu da tsiyar uwar sa da matar sa but ba za ta iya ba despite everything son T J na maƙale a zuciyarta , so ne da ya bi jininta ya ratsa dukkan sassan jikinta. Tana jin sa ya shimfiɗa Zaytoonah wacce ta koma da bacci ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. "Ki yafe min Maryam. Na san ban miki adalci ba, na san na nuna miki son kai. Kiyi haƙuri na sama miki aiki a nan dan Allah. Wallahi ko na kwana ɗaya ne ba ma tare ba na jin daɗi, i mean it Maryam, kuma idan za ki yi adalci kema kin san a wajen ki kaɗai na ke samun soyayya, kulawa, tattali, nitsuwa, farinciki da kwanciyar hankali" Shiru ne ya biyo bayan maganganun sa daga baya ta ji ya ce "I love you Maryam"... *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *15-Anorexia* Bismillahir Rahmanir Rahim Name calling shine abu na farko da ke ɗagawa ma su ƙiba hankali. Wasu kan kau da kai su nuna sunan da ake kiran su da shi baya damun su alhali kuma deep down abin na ƙona mu su rai. Wasu kuma tun suna damuwa har sun mai da abun jiki sun dena damuwa da hakan, sun rungumi halittar su kuma suna son kan su a yadda su ke duk da kuwa kullum ana cigaba da judging na su. Akwai wanda kuma yadda ake kiran su da sunaye mabanbanta wanda ke nuna izgili da cin mutunci yana karya mu su confidence da courage ɗin su. Sai ka ga maimakon ka gan su suna kazar-kazar kamar kowa sai ya zama ba su da wannan kuzarin. Su na jin zafin maganganun mutane, idan sun shiga wajen da mutane sirara su ke sai su dinga ganin kan su kamar ba su cika ba kamar sauran, kaman su ɗin daban ne da waɗancan mutane, kaman su ɗin abun aibu ne a cikin Jama'a. Zaytoonah ta faɗa cikin irin waɗannan mutane. Despite the fact Daddynta na yawan nuna ma ta ƙibanta ba shi da yawa sannan tanada kyau a yadda ta ke hakan bai boosting self esteem ɗin ta ba. Ga Humairah ma da ke ji da tashen balagar ta kullum su ka haɗu sai ta tsokaleta 'yar ɓukuta,'yar kitiɓirɓir, Tindirƙa, Sukumbiya. Ko a ina ta ke samun ugly sunayen nan oho. Tun Zaytoonah na iya maida ma ta Martani har ta dena. Humairah wani jiji da kai ta ke yi a shekarunta shabiyu. Ga shi ta fara period ita kuwa Zaytoonah da ke shauku ba ta fara ba. Falli da tashen balaga haɗe da kwaɗayi ya sa ta ke ƙin zaman gidan su. Sai ta je ta wuni a gidan Uncle Muntari, ta ci cima mai daɗi. Daga baya ma cewa ta yi wa Iya su koma gidan Uncle Muntari gaba ɗaya. Iya ma dai na son komawa kawai tana ganin Tijjani ba zai ji daɗi ba ne idan ta bar gidan sa ta koma gidan Muntari zai ɗauka saboda gidan Muntari ya fi na sa kyau ne shiyasa ta bar gidan. Amma da Humairah ta takura sai gashi Iya ta yiwa T J maganar, shi kuwa yace Allah ya zaunar da su lafiya. Bai ji daɗi ba kam tunda ya riga ya saba da zamanta a gidan sa. Ɗakunan ƙasa aka ba su, ɗakin Iya daban ɗakin Humairah daban, Humairah sai murna ta ke ɗakinta na yanzu ya fi na da girma da kyau. Ba su da matsala da Anty Hanne dan ba ta shiga harkan su. Tana da mai aiki da ke mu su girki da duk wani hidiman gidan. Ita sai dai ta ci ta sha ta kwanta. Ta ma nemi gurbin karatu a ABU amma ba ta samu ba saboda result ɗin ta na secondary bai yi kyau ba hakan ya sa ta ce za ta sake zanawa. Zaman su a gidan da ɗan kwana biyu ne Iya ta fara sa ma ta ido akan shiru da ta ji har yanzu. Ranan da ta isheta da tambaya wai ko ta yi planning ne. "Iya ki tambayeshi sau nawa ya ke nemana a wata. Idan ya baki amsa sai ki dawo na gaya mi ki dalilin jin shiru da ki ka yi" Jin amsar da ta ba ta ya sa ta ja bakin ta ta yi shiru, da Hajjo da Hannen duk da ta ɗauka 'ya'yan uwanta ne babu wanda ya ɗauketa da wani daraja amma a hakan ba ta iya yi mu su komai sai ma tsoron su da ta ke ji. Sai Maryam Inyamura ne aka renawa hankali. Da ta samu gogan da maganar haihuwa kuwa cewa yai shi baya son sa'ido. Idan lokacin haihuwan Hanne ya yi za ta haihu. Dama shi ɗa nagari, ɗan ƙwarai wanda ya san hakkin iyaye shi ake tanƙwarawa amma ɗa marar tarbiyya kamar Muntari sai dai a bishi da ido da addu'a. Duk wani mulki da ta ke zubawa a gidan Tijjani babu shi a gidan Muntari, tana magana zai ce "Iya ba na son sa'ido" Zaman Hanne da Muntari kuwa gashi nan gashi nan ne. Ran da ya bushi isha zai nemeta amma idan bai nemeta ba ko ta zo da kanta koranta ya ke yi ya ce shi baya son jaraba. Yana dai bata kuɗi dan duk wata tana jin alert. Zaman shiru da ta ke yi ne ma ya sa ta yi tunanin komawa karatu. Mummunan halin sa ta shan giya kuwa tun watannin farko na auren su ta gane. Ita kam tana zargin bayan giya ma yana haɗawa da wani abun. Randa ya fara sunbatun Maryam kuwa har tsorata ta ke yi. Ita dai ta rasa wace Maryam ce Muntari ke mutuwar so haka. *** Inter school competion za su yi daidai ƙarshen zango na shekarar wanda ya kama su Zaytoonah na gab da zana jarrabawan su na JCE. Rehersals za a fara yau, wanda aka zaɓa za su fito su yi rehersal a gaban ɗalibai. Wannan ne karo na farko da Zaytoonah za ta yi debate tunda ta shiga JSS. Ta kan representing ɗin makarantar su a Maths competion amma indai debate ne ba ta yarda ta yi. A nursery da primary school she used to be excited duk lokacin da aka zaɓe ta cikin ma su yin debate amma yanzu komai ya chanja ma ta, ba ta da wannan confidence ɗin. Wannan karan ma Mr Adebayo ne ya dage sai ta shiga ciki. Ita ce first speaker dan haka sunan ta aka fara kira Tijjani Zaytoonah Abubakar. Cikinta ya ba da ƙululu, jiya a gaban Auwal ta presenting points ɗin ta ba tareda wata matsala ba amma yanzu da aka kira sunan ta har ta fara jin gudawa. A hankali ta taso ta fito tsakiyar filin, gaba ɗaya an ƙura ma ta ido wasu na dariya ƙasa-ƙasa. Bayan ta yi gaisuwa sannan ta gabatar da topic ɗin sannan ta introduncing kan ta. Tana cewa "standing before you is Zaytoonah Tijjani Abubakar, I'm..." 'aka Mama Zaytoonah' muryan Sadiya wata 'yar class ɗin su ya doki kunnen ta. Sadiya ta so a saka sunan ta a cikin ma su competition ɗin amma ba a zaɓeta ba, shiyasa ta ke jin haushin Zaytoonah. Shiru ta yi saboda yadda sunan ya taɓata "Yes continue" MC ɗin ya faɗa ma ta Murya na rawa ta cigaba dan ta ruɗe "firstly, I'm.." "Amoeba" ta sake jin an ambata da ƙarfi. Wannan karan hawaye ne ya zubo daga idon ta wanda ya sa wasu ɗaliban su ka fara dariya. Aka shiga yiwa yara ihu akan su yi shiru amma inaa sai ma ƙarawa da su ka yi saboda yadda su ka ga Zaytoonah ta bar hall ɗin da gudu... *** "Ni ba na son kame-kame, gaskiya na ke so, za ka iya yi min aiki ko ba za ka iya ba?" "Indai ba ka yarda da mu ba babu yadda za ayi aikin da za mu maka yai tasiri" mutumin da ke zaune kan wata tsohuwar tabarmar kaba ya faɗa. "Kuɗi ba su ne matsalata ba, indai zan samu biyan buƙata zan iya biyan ko nawa ne. Wannan ne karo na uku da za a min kwatancen waje na je amma ba na samun biyan buƙata" "Ai ka sha kuruminka kawai Alhaji, aikin ka an riga an gama. Sai dai dole za a yiwa baƙaƙen Aljanu yanka saboda su ne kaɗai za su iya aikin nan. Za a yanka mu su Ɓaunan da be taɓa yiwa mace barbara ba, sannan za yanka Zakaran da yai wa Kaza 'yar kwana bakwai fyaɗe sannan..." yana maganar yana zazzare ido a dole shi malamin tsibbu mai magana da Aljanu. "Ba sai ka je da nisa ba ka yi lissafi ka faɗi nawa zan baka kawai, ni buƙata na ta biya shine damuwata" "Dubu talatin" Muntari ya ciro bandir ɗin kuɗi daga aljihun rigan sa ya ajiye a gaban Malamin tsubbun ya ce " ga dubu hamsin nan. Idan har buƙata ta biya zan dawo na ƙara maka wani alkhairin" Malamin tsubbun yai saurin ɗauke kuɗin yana faɗin "ai ya saketa ma an gama. Ai yadda za a ɗasa mu su ƙiyayyar junan su ko inuwa ɗaya ba za su iya zama ba" Da wannan Muntari ya bar rumfar mutumin yai gaba. Shikuwa Malamin tsibbun dama na bogi ne, yawo ya ke yi ƙauyuka-ƙauyuka ya damfari mutane idan ya samu 'yan kuɗin sa sai ya ƙara gaba ya je wani wajen ya kuma damfarar wasu shashashun. Bayan tafiyar Muntari ya shiga harhaɗa 'yan komatson sa, zuwa yamma ya bar ƙauyen. Shi kuwa Muntari ya tafi da zubin nan da kwanaki kaɗan Tijjani da Maryam za su rabu. Dan ya ɗan yadda da bayanin Malam Nabakin kura da alama shi zai yi gaskiya ba kaman sauran 'yan tsubbun da su ka damfare shi a baya ba. *** *Anorexia nervosa* Anorexia: wannan kalma ana alaƙantata ne da wani yanayi da mutane ke tsintar kan su ciki musamman ma su ƙiba. Yanayin shine tsoron ƙiban su, wanda ba su da ƙiba kuma ba tsoron yin ƙiba. Ba anan matsalar ta ke ba, matsalar shine a duk lokacin da ka ke tsoron ƙiban da ka ke da shi ko kuma ka ke tsoron yin ƙiba za ka zama kana aiwatar da wasu daga cikin abubuwan nan ko kuma ka dinga jin wasu daga cikin abubuwan nan: 1-ko yaushe za ka dinga lura da yanayin jikin ka kana duba shin ka ƙara ƙiba ne ko yanene. Ko kuma dai ka rage ƙiba ne 2-za ka damu da ƙiban ka da kuma siffar ko kuma dirin ka musamman ma mata. 3-idan kana da ƙiba za ka dinga ji a ranka cewa sai ka zama siriri ne zaka yi daɗin ganuwa, sai ka zama siriri ne za ka zama accepted a idon mutane. Za ka alaƙanta ƙimar ka da kasancewar ka siriri, wato idan kanada ƙiba za ka dinga gani kamar kimar ka ya ragu. 4-za ka iya yin komai dan kawai ka rage ƙiba. Ko kuma za ka iya yin komai dan kar ka yi ƙiba (saboda kana gani kamar idan ka yi ƙiba shikenan ka kaɗe) 5-za ka dinga hana kan ka cin abinci, ka ɗauki azumin da ba lada sai wahala (wato ka dinga Azumi dan kawai kana so ka rage ƙiba). To the extend koyaushe ka gwammaci ka wuni da yunwa saboda ka sa a ranka idan kana ƙin cin abinci automatically za ka rage ƙiba. Ko ka ga mutum ya hana kan sa cin daɗi, ya tsiri tsirface tsirfacen cin wasu abincin yana ƙin cin wasu simply because a dole yana son rage ƙiba by fire bu force. 6- idan mutum ma'abocin yin excercise ne (motsa jiki) to za ka ga zai dinga yi babu hutu babu kakkautawa. Za dinga yin excercise da ya fi karfinsa duk dan yana so ya rage ƙiba da wuri 7- idan mutum na fama da Anorexia za ka ga duk yadda ya kai ga rage ƙiba ba zai taɓa haƙura ba shi dai zai dinga ganin kaman baya rage komai. Hakanan za ka ga koyaushe yana cikin gwada nauyin sa. 8-ko ya ci abinci mai yawa sai ya tsiri ƙaƙarin amai akan dole sai ya amayar da abinda ya ci. 9-shine neme-nemen maganin rage ƙiba. Ko me aka ma sa tallah sai ya siya ya gwada ko zai dace ya rage ƙiba 10- kullum cikin jin haushin kan sa ya ke simply because Allah ya halicce shi mai ƙiba. Kullum aka yi comment akan ƙiban sa sai ya ji haushi har ya ji a zuciyar sa inama,inama. Inama inada jikin wane ko inama inada sirantaka irin ta wacce, etc. *Matsalolin Anorexia:* -Yana sa mutum ya kasa taɓuka komai sai ya zamana rayuwar sa ta ta'allaƙa ne kawai da son rage ƙiba ko tsoron yin ƙiba. -Garin hana kan ka cin abinci ka ke ka rasa kuzari ƙarshe ka fara fama da malnutrition idan ya zo da ƙarar kwana mutum ya mutu. -A neme-nemen maganin rage ƙiba ka je ka sha abunda zai kashe ka ko ka sha abunda zai jawo maka wata cuta ko wata matsala daban. - Saboda damuwa da ka sa a ranka sai ka iya samun hawan jini. *Yadda za ka yi yaƙi da Anorexia:* - ka so kan ka a yadda ka ke. Kafin wani ya so ka sai ka fara son kan ka tukunna. Idan ke macece kamar ni, ki sa a ranki duk ƙibar ki akwai mazan da su haka Allah ya yi su mata ma su ƙiba su ke so ba sirara ba (dama number one problem ɗin shine kina tunanin maza sun fi son sirara shiyasa ƙibar ki zai dinga sa ki damuwa. Hell no baby girl. A yadda ki ke za ki samu masoyin ki na asali wanda shi mace irin ki ma ya fi so). And idan ya complain akan ƙiban ki ki ce ma sa 'go hug transformer'. - ki dena yin gasa ko kishi da wata 'yar uwar ki ko ƙawar ki da ta ke siririya. Babban abunda ya ke ƙara propagating anorexia shi ne yadda Media ta ke nuna modela sirara, ko jaruma 'yar film za a zaɓa anfi son siririya. Ma su tallen shayin rage ƙiba ko maganin rage ƙiba sai su dinga potraying ma su ƙiba a matsayin ma su matsala amma sirara kuma su ne dai dai (akwai ƙiban cuta ko na rashin lafiya. Ina maganan ƙiba da ya ke naturally haka Allah yayiki ko yayika kuma ba ka da wani unhealthy habit da zai sa ƙiban na ka ya jawo maka wani illah). Ita ƙawarkin da ki ke burin ki zama kamarta may be itama akwai wani abu da ki ke da shi da ta ke bala'in burin ta same shi amma ke ba ki sani ba. The moment kika dena kishi da kuma gasa da sirara za ki ji zuciyar ki wasakai ba wani damuwa. You'll live happily. -Babu magic powder ko magani da zai sa ki rage ƙiba cikin ƙanƙanin lokaci. Rage ƙiba is a gradual procesa, ba wai dan kin sha wani abu ko kin yi wani abu lokaci guda sai kawai bayan kwana biyu ki ga kin tashi siririya ba. Ba haka abun ya ke ba, rage ƙiba tafiya ce mai ɗaukan lokaci idan kin jure. Matuƙar za ki rage ƙiba ne dan wani ko dan wata kina ruwa. Domin indai dan wasu za ki rage ƙiba to ba ki da kwanciyar hankali, domin abu ɗaya za ki dinga hangowa shine kina son ki zama siririya dan ki burgesu. My Sister and My Brother ba za ka taɓa burge ɗan Adam ba, sai ki sha slimming tea ɗin ki sha haɗe-haɗen ki zama siririyan still a zage ki. A nuna ai yanzu da ki ka zama siriya ba ki yi kyau ba. Wa su su ce ma rashin godiyar Allah ya sa ki ka koma siririya ta ƙarfi. - idan har kina son rage ƙiba ne bisa karan kan ki. Misali, kwana biyun nan na fara yin nauyi fa gara na ɗan zama fit kaɗan (may be nauyin na ɗan sa ki kasala ko ma dai wani issue ɗin daban. Ko kinga kamar ƙiban ki ya fara zama unhealthy) to wannan dalili daga karan kan ki ne kuma ke hangen ki ba wai ki zama siririya ba ce kamar ƙawar ki Zeenatu ko kamar 'yar film Rahama Sadau ko Nargis Fakhri. Abun da ki ke so shine kina son rage nauyi ko kina son ki ɗan sake kaɗan. Then my Sister my brother you just need to change your life style kaɗan ko na ce ka adjusting wasu abubuwa a lamuran ka na yau da kullum. Weight loss is 70% diet and 30% workout or excercise. Ba wai ki ce daga yau na dena cin abinci da yawa ba. Ba haka abin ya ke ba. Za ki saka wasu abubuwa ne cikin abincin da ki ke ci wasu kuma ki rage cin su, a hankali kina inganta lafiyar jikin ki ta hanyar yawan cin vegetables da fruits fiye da carbohydrate. Sannan kina motsa jikin ki daily walau yoga ne kike yi a gida ko kuma dai kina da Gym a gidan ki ne ko kuma kina fita trekking ne ko gudu ko tsalle etc (idan namiji ne buga ball yana da advantage sosai. Idan macece ke kamar ni musamman ma matar aure akwai yoga da za ki iya yi a gidan ki,a ɗakin ki ko falon ki ko ma tsakar gida. Minti 15,20 ko 30 ya isheki a rana depending on your tight schedule. Dancing (rawa) shima yana da fa'ida sosai domin shima motsa jiki ne, ki girgije ƙugu ki girgije jiki za ki ji jikin ki ya yi saƙayau. ( ba wai ki yi sau ɗaya sau biyu ba ki ce ke ba ki ji chanji a jikin ki ba. My Sister ba kwana ɗaya biyu na ke magana ba, ba kuma kiyi sau uku a sati ki share sai bayan sati biyu ki sake yi ba. Ina nufin ki ware minti 15 zuwa 30 a rana ki dinga motsa jiki walau rawa ne ko yoga kiyi haka na sati huɗu ki ji ko za ki ji chanji a jikin ki, ki cigaba ki yi ya kai wata uku ki ga how your body will feel. Ban ce ƙiba za ki rage ba miraculously. Aim ɗin ki ba rage ƙiba ba ne, aim ɗin ki rage nauyi ne da kuma jikin ki ya samu benefits na excercise wanda za ki ji ko malaman lafiya suna emphasizing akan a dinga motsa jiki. Ko mutum siriri ne ma ba a bar ka a baya ba ana so ma riƙa excercise. Yana rage kasala, yana rage stress yana yana yana)... Chaaiii na gaji da bayani😀 Domin ƙarin bayani kya iya browsing more akan anorexia don samun haske sosai. Ina ga ma ya kamata na buɗe fitness group Lol😂 Dear 'yar uwa ko ɗan uwa ma su ƙiba kamar ni. Za'a kiramu da sunaye na izgilanci, za a zolaye mu, za'a aibata mu kar ka taɓa bari wannan ya dameka. So what dan muna da ƙiba, so what idan sun zolaye mu da suna ma su muni. We get better things to do than responding to stupid people. Kar mu koma gefe mu yi kuka ko mu ɓata rai dan ance mana ƙato ko ƙatuwa, Lukuti ko Lukuta etc wanda ya gaya mana mu zare ma sa ido mu yanka ma sa magana har sai ya ji dama bai buɗe shaddar bakin sa ya kiramu da sunan nan ba. *** " Azumi ki ke yi ne?" Mommy ta faɗa lokacin da ta ga Zaytoonah ta mai da hankalin ta ga kallo ta ƙi cin abinci. "Zan ci anjima Mommy, yanzun ba na jin yunwa ne" Salman ya fashe da dariya Mommy ta ma sa dundu a baya "Mommy wai Zaytoonah ne ba ta jin yunwa caɓɗi" "Ba na son shirme Salman ka fita a hancin Zaytoonah dan idan ta waiwayeka ba ruwana" Ya cigaba da cin abinci yana dariya ƙasa-ƙasa. Lokaci zuwa lokaci tana leƙa su. Yawunta sai tsinkewa ya ke yi yadda ƙanshin jollof rice ɗin ke bugan ta. Bayan abin da ya faru a wajen reheasal ɗin nan Zaytoonah ta ci kuka sosai. Ƙarshe ma cewa ta yi ta haƙura da karatun gaba ɗaya amma da ta isa gida sai ta rasa bakin yin magana dan tana fara furta maganar rashin zuwa makaranta ƙila Mommy sai ta zaneta. Haka dai ta dinga daddafawa tana zuwa makarantar har su ka fara exams na su, batun debate kam ya sha ruwa dan sai wata aka ɗauka. Sati biyu kenan da ƙarisa Junior Waec ɗin su. Abinda ya faru ranan ya sa ta tsani makarantar ta su, ranan suna tareda Daddy ta ma sa maganar ba za ta koma wannan makarantan ba a chanja ma ta wata. As usual bai tambayi dalili ba ya ce ta zaɓi wace makaranta ta ke so. Maryam da ke jin su ta ce "tunda ba ta son makarantan inaga boarding school za a kaita ta ƙarisa karatun a chan" T J ya ce "ba inda za ta je tana nan kusa da mu" "Ka dai cigaba da sakaltata ni ba ruwana. Yarinya ba abinda ta sani sai ci" "Ba ruwan ki da 'ya ta. Adaeze ki ci abinci ki ƙoshi sosai kin ji?" Zaytoonah ta gyaɗa ma sa kai... Zuwa dare ta galabaita, abincin da aka ajiye ma ta flushing ɗin sa ta yi a banɗaki amma sai da ta ɗauke naman ciki ta cinye. Ta yi challenging ɗin kan ta cewa za ta rage cin abinci za ta dinga ci sau ɗaya a rana saboda tana so kafin ta fara SS class ta koma kamar Humairah. Ga sabon makaranta ga sabuwar Zaytoonah. Zaytoonah siririya wacce ba za a dinga tsokala ba. Da dare ba yadda ta iya dodging dole sai da su ka haɗu su ka ci abincin dare kamar yadda aka saba. Wasa-Wasa ta cigaba da skipping abinci da safe sai ta ƙi karyawa da wuri idan Mommy ta wuce office shi Salman ya fita ball sai ta flushing abincin ko idan ta ji Almajiri yayi bara ta fita ta zuba mai. Tunda Iya da Humairah su ka koma gidan Muntari T J ya ce Auwal ya koma gidan Hajjo dan gidan zai mata faɗi daga ita sai Sadiq musamman idan T J na gidan Maryam. Daga gidan Maryam ake tura ma sa abinci ko kuma ya zo ya ci ya tafi. Yanzu ya gama jarrabawar WAEC ɗin sa saura NECO hakanan yana ɗan taɓa ɗinki a shagon Ogan sa. Tun yana JSS3 ya fara fita yana koyon ɗinki gashi shekaru uku ya iya sosai ba laifi. Da rana ma haka za ta nemi ƙaryar cin abinci tareda su ta ce sai daga baya za ta ci alhali ba ta ci. Ita ba Azumi ba balle ta samu lada sai rashin cin abinci. A hankali jikinta ya fara weak har Mommy ke tambayarta ko lafiya ta ke ta ce lafiya ƙalau. Sai ta koma dan tana wajen Mommy sai ta daure ta nuna kaman tana nan da ƙarfinta idan ta koma ɗakin ta ta dinga murƙususun yunwa. Daurewa kawai ta ke yi dan it has not being easy musamman saboda yadda Mommy ke chanja salo salon girki ma su daɗi. Wani lokaci har kuka ta ke idan za ta zubar da abincin sai ta lallashi kan ta da cewa nan da lokaci kaɗan za ta dawo siririya kamar Humairah sai hankalin ta ya kwanta. A kwana na biyar ne kuwa ta fara period ɗin ta. Ciwon ciki ne ke ɗan fizgarta kaɗan kaɗan sai ta ɗauka na yunwa ne ta cigaba da dannewa abun ya zo yai yawa. Ta tashi ta wuce banɗaki ko cikinta ne ya ruɗe, ta fita a ɗakinta za ta shiga banɗaki kenan ta ji Mommy ta kirata "Adaeze come here" Da ta zo gaban ta Mommy ta juyata dan ta tabbatar da abinda ta gani. Jini ne a bayan doguwar rigar da ta sa, jinin ba da yawa ba ne amma kasancewa rigan fara ce sai ya nuna. Nan Maryam ta mai da ta ɗaki ta ma ta bayanin abinda ya faru da ita. Ta ɗan ji wani iri musamman yadda Mommy ke karanto ma ta dokoki ma su yawa duk da kuwa an mu su karatun a Islamiyya a Babun Fil Haidhi a littafin Akhdari amma saboda ba ta fara ba ya sa duk ba ta wani sa karatun a ranta sosai ba. Da T J ya dawo da dare ta ma sa albishir da cewa Adaeze ta zama cikakkiyar budurwa. "You know what? Nima @14yrs na fara fa" T J ya ce "ai ba ta cikata 14yrs ba" "Mi ya saura kuwa tunda saura 21days ne" T J ya rungumota jikinsa ya ce "barin karɓi tukwuici tunda na zama Baban budurwa" Kafin Maryam ta yi magana ya fara birkitata da zafafan salon shi ma su rikitata. Bayan kwana shida. Tana zaune a falo tana kallo ta ji mai tallen magani yana kirarin maganin sa. Irin. Ma su yawo a cikin motan nan ne suna aza loud speaker a saman mota suna kunna tallen magungunan su. Yadda ake ta kururuta maganin ƙiba ya sa Zaytoonah ta fara tunanin fita ta siya. Ba kowa a gidan sai ita ɗaya, Mommy da Daddy duk sun fita aiki shi kuma Salman dama indai ana hutun makaranta to ƙafar sa ba ta zama a gida, daga ya je ƙwallo ko ya je shagon su Auwal koma ya je neman tsokala tareda abokanan sa ma su ƙiriniya irin sa. Maganganun mai tallen na ratsata sosai har ta fara hango kan ta ranan birthday ɗin ta wanda ta ke ganin sai ta bawa su Humairah mamaki harda su Nuratu ma da 'yan islamiyyan su musamman Na'ima mai cin tosono lokacin suna yara. Ɗakin Mommy ta shiga ta ɗau kuɗi ta fita da sauri. Hamsin-hamsin ne maganin amma sun ce za su bar ma ta uku ɗari dan haka ta sayi guda shida a naira 200. A jikin ledar maganin an yi bayani kan yadda za asha. Za ka iya zubawa a shayi marar sugar ka sha ko kuma ka zuba shi a ruwan zafi zalla. Ko wani leda ɗaya za ka sha shi sau biyu a rana wato da safe da kuma dare. Zaytoonah was so excited, a lokacin ta haɗa guda ɗaya ta shanye da ƙyar saboda ɗaci gashi itama kaman T J ta ke, son zaƙi ne da ita kamar me. A lokaci guda ta shanye leda ɗaya ta je ta wanke kofin ta kai maganin ɗakin ta ta ɓoye a ƙarƙashin pillow. Da dare kafin ta kwanta ta kuma haɗa wani wannan karan leda biyu ta haɗa a ƙoƙarin ta na son zama siririya cikin sauri. Baccin awa ɗaya ta yi ciki ya birkice ma ta. Ta shige banɗaki da gudu sai gudawa fuyaaaaa. Ta gama ta fito amma kafin ta ƙara kwantawa wani ya kuma zuwa ta sake komawa da gudu. Cikin minti talatin Zaytoonah ta galabaita sosai gashi dama 'yan kwanakin nan da ba ta cin abinci sosai jikinta yayi weak. A karo na biyar da ta fito daga banɗaki ne ta yanki jiki ta faɗi tunma kafin ta kai ɗakin ta... *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *13-mental health* Bismillahir Rahmanir Rahim "Wani duniya ka shiga? Its being 14 no 15yrs fa" Muntari yai wani murmushin gefen baki ya ce "mun tafi neman kuɗi kuma mun samu" "Oh really! zauna ka ban labari. I cant believe wai yadda ka ke ji da Iya za ka iya rabuwa da ita har iya tsawon waɗannan shekarun" "Wow! you can speak Hausa fluently now. That's amazing" Ya faɗa yana zama kujera opposite da wanda ta zauna. "Your English is superb too" "Thank you My Dear" Ba ta kawo komai a ranta ba ganin kamar yana son ya impressing ɗin ta ne as always. "Mi ka ke yi a Lagos all this years?" "Ko ruwa ba za a bani ba" "Forgive my manners i'm excited to see you ne" Lokacin da ta tashi idon sa tarr a kanta yana bin jikinta da kallo har ta wuce kitchen. Ta ɗan ƙara buɗewa kaɗan ko dan haihuwa amma ga yadda ya santa a shekarun baya chanjin kaɗan ne. She's still beautiful, the only beautiful woman he ever loved and will always love. Coke mai sanyi da ruwan satchet ta ɗaura a ƙaramin tray ta haɗa da glass cup ta kawo ma sa. Ta ja center table zuwa gaban sa ta ɗau coke za ta buɗe da opener da ta riƙo a hannunta ya ce " water will be fine" Ta ajiye kwalbar coke ɗin ta ɗauki ruwan ta tsiyaya ma sa a kofi za ta ajiye kofin yai saurin sa hannu akan hannunta ya riƙe. Ta yi saurin cire hannunta ta koma kujera ta zauna tana zuba ma sa ido. He has really changed. Kaɗan ya sha ruwan ya ajiye kofin ya ce " ina yarana?" "Su na maƙota, sun dameni da surutu" "Ayya! Sun kai biyar ko?" Yai tambayar kamar bai san komai ba gameda rayuwar aurenta. "Su biyu ne for now, A girl and a boy" "Allah ya mu su albarka" ta amsa da Amin. Shiru ne ya biyo bayan haka kafin daga baya Maryam ta ce "daga wajen Iya ka ke?" Yai murmushi ya ce " daga gidana na ke" Ta ɗaga gira tana jiran ƙarin bayani. "Na yi gini a nan anguwar" "Wow that's lovely, ba ka son ka yi nisa da Iya kenan?" "Kusan haka dai" "A ta ina ne gidan? And na san by now ka yi aure har da yara" Murmushi yai ya ce " na taɓa aure amma mun rabu sannan bamu haihu ba" "That's sad! Allah ya baka Mata ta gari" Ya amsa da Amin. Hira dai ta ɓarke tsakanin su na bayan rabuwa. A tunanin Maryam yadda ta ga Muntari ya waye looking matured yanzu ya manta da abinda ya faru kafin aurenta da T J musamman da ya ce ya taɓa yin aure. Ga Muntari kuwa ya zo ne yai yaƙi, ko da zai rasa komai na sa indai zai samu masoyiyar sa bai damu ba. A haka yaran su ka shigo su ka same su inda Maryam ta introducing Zaytoonah da Salman a matsayin 'ya'yan da Allah ya ba ta. Kallo ɗaya za ka yiwa Zaytoonah ka san mahaifiyarta ta ɗauko sai dai ita baƙa ce. Shi kuwa Salman T J junior ne. "Zo nan Baby" ya faɗa yana miƙawa Zaytoonah hannun. "Mommy who is he?" "He's your Uncle" Sai da ta ƙare ma sa kallo sannan ta ce "he's evil just like Iya" Maryam ta buge ma ta baki duk da kuwa ta san kamannin Iya da ta gani a fiskar Muntari ya sa ta faɗi haka. Sai da ta ma ta faɗa kafin ta je wajensa, shi kuwa Salman tuni ya riga ya ɗale jikin sa yana ma sa tambayoyi... Muntari bai bar gidan ba sai chan yamma bayan ya ci abincin rana tareda su. Tareda Auwal da Salman su ka tafi gidan Hajjo amma Zaytoonah fir ta ƙi bin su. Itama Maryam ba ta takura ma ta ba dan tunda Iya ta aske ma ta gashi ta dena zuwa gidan ko aika ba ta turata... Kwana uku kenan da zuwan Muntari wanda dukkan su ya kai su zuwa gidan da ya gina wanda ba nisa sosai da gidan su dan a tafiyar ƙafa ba za ka fi minti shida zuwa bakwai ba za ka isa. Gida ne Babba upstairs wanda ya ƙunshi ɗakuna takwas da falo biyu, akwai kitchen da store. Yana da parking lot wanda aka ajiye motoci uku kuma ya ce duka na sa ne. Akwai ɗakin maigadi a bakin gate ɗin. Angama komai na gidan amma ba a zuba furnitures ba. Iya baki ya ƙi rufuwa dan ganin danƙareren gidan da ɗan ta ya gina, sai albarka ta ke sa ma sa. Maryam ta yi mamakin girman gidan, kamar yadda ya faɗa ma ta siye da sayarwa ya ke yi, yana aiko kaya daga Lagos ana siyar ma sa a Kano. Wai yanzu haka yana da manyan shaguna guda biyar kuma ya fara shirye-shiryen buɗe shago a cikin garin Zaria. Addu'ar Maryam shine Allah ya sa ba sata ya ke yi ba cause abin da mamaki... Kullum sai ya zo gidan sau uku, da sassafe kafin su fita zai ɗauke su a motar sa ya kai yara makaranta ya wuce da Maryam office. Ranan Saturday ya zo ya ɗauki Maryam su ka je gidan sa ya ce ta ƙara duba gidan ta bashi shawaran wani irin furnitures za a sa. Ta gaya ma sa ra'ayinta har da tsokanar sa cewa da yanzu yana da Mata da ita za ta bashi shawara. Yai dariya ya ce zai yi aure nan ba da jimawa ba. Cikin sati biyu gida ya kammala, an saka komai a ciki wanda ya sa gidan ya ƙara kyau. Har kafin a kammala gidan a gidan Hajjo ya ke kwana amma kusan wuni duk a gidan Maryam ya ke yi, hatta abinci na ta ya ke ci. "Muntari maganar aure fa?" Iya ta tambaya bayan ya sanar da ita zai koma gidan sa tunda yanzu komai na buƙata akwai ciki. "Zan yi idan lokaci yayi" "Nufin ka haka za ka yi ta zama kai ɗaya a gida ba Mata?" "Iya na lokaci kaɗan ne fa, zan yi aure" "Gaskiya kar ya wuce wata uku idan har ya fi haka to ni da kai na zan je na nemo maka Mata" "Haba Iya sai ka ce ƙaramin yaro" "Ahaf kar ka yi auren ka gani, wannan irin gida haka ace kai kaɗai za ka zauna ba Iyali ai sai a zarge ka" Yai dariya ya ce ba mai zargin shi... *** Kaman da wasa har sun fara sabawa da Muntari, yanzu Zaytoonah ma da ke baya-baya da shi ta sake jiki saboda yawan kayan ƙwalama da ya ke kawo ma ta. Ga shi kullum shi ke kai su school a motar sa. Har Maryam ta sallami mai mashin da ke kai su da. Muntari bai taɓa nuna ma ta wani alama da zai nuna akwai wani abu da ya ke ji gameda Maryam ba. Wasa da dariyan ƙanin miji kawai ke tsakanin su, abinda ta ɗauka kenan. Wata ranan Lahdi sai bai zo ya karya ba kaman yadda ya saba hakan ya sa Maryam ta aiki Auwal ya kai ma sa abincin gidan sa. Da ya dawo sai ya ce ma ta wai Uncle ya ce ba shi da lafiya ne shiyasa bai zo ba. Bayan yara sun tafi Islamiyya ta kimtsa gida ta shirya ta fita. Kitso za ta je amma za ta fara biyawa ta ga jikin Muntari tukunna. Daga falo ta zauna tana sallama tunda Maigadi ya ce ma ta Muntarin na ciki. Jin shiru ya sa Maryam ta haura sama. Ta tsaya a bakin ƙofar sa tana sallama "Muntari ka na ciki ne? Muntari, Muntari are you OK" Murya ƙasa-ƙasa Muntarin ya amsa ma ta da ta shigo ba ya jin ƙarfin jikin sa ne. Ta tura ƙofa ta shiga. Daga tsaye ta ce "Muntari ba za ka je Asibiti ba? Ka ci abincin kuwa?" "Ba na jin daɗin bakina shiyasa ban ci ba" "Ko na haɗa ma ka tea sai ka sha sai mu je asibitin" "That will be good" ya faɗa yana maƙyarƙyatar ƙarya. Fita ta yi daga ɗakin da sauri ta sauko kasa ta yi hanyar kitchen. Cikin sauri ta ke haɗa tea ɗin saboda yadda ta ga Muntari na rawan sanyi ba ƙaramin jin jiki ya ke ba... Ɗakin ta koma bayan ta haɗa tea ɗin ta sameshi still yana kwance. "Muntari tashi ga tea ɗin" A hankali ya tashi ya zauna yana jingine bayan sa da pillow. Maryam ta miƙa ma sa tea ɗin tana tambayar ko yayi brush ya gyaɗa ma ta kai. Yana karɓan tea ɗin ya haɗa da hannunta ya jawota ta faɗa jikin sa wanda hakan ya sa tea ɗin ya zube. Duk da tea ɗin ya ɗan ƙona shi bai wani nuna damuwa ba. "Muntari what are you doing" ta faɗa tana ƙoƙarin tashi. Flipping ɗinta yai lokaci guda ya zama ya ma ta rumfa da jikinsa. "Muntari kana hauka ne, what are you trying to do. Ni matar yayanka ne" "Na fi kowa sanin haka Maryam. Ke budurwata ce da Yayana ya min ƙwace. Ina son ki Maryam har yanzu zan..." Ta fara ƙoƙarin tureshi amma ya riƙe hannayen ta biyu. "Ki saurareni Dan Allah. Ba zan miki komai ba amma" "Muntari ka rabu da ni dan Allah" tana faɗa da ƙarfi "Ina so ki sani duk iya tsawon shekarun nan ke kaɗai na ke so ban taɓa son wata ba. Kuma na dawo ne dan na same ki, kin ga wannan gidan da ma duk abinda na mallaka naki ne, da sunan ki na sameshi" Ganin maganganun sa ba su da kan gado ya sa ta fashe da kuka tana ƙoƙarin ƙwace kan ta daga gareshi amma ta kasa. " ki yi haƙuri Maryam, son da na ke miki ne ya jawo wannan. Ina son ki fiye da tunanin mai hankali" "Muntari dont do anything stupid. Ba zan yafe ma ka ba" "Ina da kyau Maryam na fi Tijjani kyau, na fi shi kuɗi yanzu, na fi shi komai. Miyasa ki ka zaɓe shi? Miyasa ba za ki rabu da shi ki dawo gareni ba?" Wani yunƙuri ta yi da ƙarfi ta tura shi tana gasa ma sa cizo a kumatunsa. Hakan ya sa ya ɗage hannunsa yana ƙoƙarin shafa wajen. Ita kuwa ta samu daman sauka daga kan gadon ta yi hanyar waje da gudu. Tana saukowa daga stairs ko takalmi babu ta ji muryan sa a bayanta yana cewa ta tsaya dan Allah. Saura stairs shida ta sauko ƙasa ya damƙo ta hakan ya sa su ka fara kokawa bisa kuskure ya tureta sai ga shi ta tumbling ta faɗo ƙasa. Hakan ya sa shi ƙwalla sunan ta da ƙarfi MARYAMMMM... *** Tunda Likita ya ma ta bayanin rasa babies ɗinta da ta yi ta ke kuka. Three months twins ɗina sun tafi, abinda zuciyarta ke ta maimaitawa kenan. Muntari ne ya shigo bayan fitan Likitan. Tana ganin sa ta sa ƙara tana cewa ya fita. "Maryam ba niyya..." "Get out, Muntari get out" Kar ta tara ma sa Jama'a hakan ya sa ya fita yana jin ɗaci a ransa. Bai yi niyyar ƙuntata ma ta ba, niyyar sa ta yarda da soyayyar shi ta bashi dama tunda yanzu ya fi T J komai. Kwana biyu da Maryam ta yi Asibiti ba ta yarda Muntari ya zo kusa da ita ba. Kuka kam ta yi shi harta godewa Allah. Bayan ɓarin da ta yi ba ta wani ji ciwo ba sai ɗan goshinta da ya fashe kaɗan kuma anyi ɗinki a wajen. Bayan sati ɗaya da ta samu sauƙin jikinta ta je gidan Hajjo ta shiga har ɗakin Iya dan ba ta sameta a falo ba. "Ya zaki shigo min ɗaki haka kawai ba ko sallama" "Ke ki ka haifi Muntari ko? Na kawo ƙarar sa for the first and last time, kaman yadda ki ke yiwa Tijjani magana ya ji ina so ki yiwa Muntari magana ya kama girman sa, ya kama girman sa ko kuma wallahi sai na yi sanadiyar da zai ƙarisa sauran rayuwar sa a kurkuku" Iya ta gyara zama ta ce "ikon Allah. Ke gaki Alkalin duniya ko, to ki rufe shi mu gani. Wai ni kam kin auri Yayan sa na haƙura miye za ki je kwartonci wajen ƙanin sa? Saboda yanzu Allah ya buɗa ma sa yafi mijin ki arziƙi shine za ki koma wajen shi kwartonci ko? To bari ki ji idan har anyi duniya dan Muhammadu to ba abinda Muntari zai yi da ke. Ki fita harkan sa, waya sani ma ko cikin ba na Shehu ba ne za ki zo kina ɗagawa mutane hankali. Sai mi dan kin yi ɓari akan ki aka fara ɓari a duniya ne" "Abinda za ki ce kenan? To ki sani matuƙar dabban da ki ke kira ɗan ki ya cigaba da bibiyana zan shayar da ke mamaki. Zan nuna miki duk iskancin sa bai fi ƙarfin hukuma ba" Daga haka ta fita daga ɗakin. Duk wani faɗan ma da tayi niyyar yi ta haɗiye. Ranan da Hajjo ta zo duba ta a asibiti ta ke ce ma ta wai Muntari ne ya zo gida ya sanar mu su ta yi ɓari. Munafuki ya gaya mu su ta yi ɓari amma bai iya gaya mu su sababin da ya jawo hakan ba... Gaba ɗaya ta shutting Muntari daga duk wani abin da zai haɗa su. Yaranta ma ta hana su mu'amala da shi. Hatta motan sa ta hanasu shiga, ta nemo mu su dreban su na da. Muntari ya shiga ruɗu sosai da yadda Maryam ta shata layi tsakanin su. Bai zo dan haka ta faru ba, abin da ya sha da sassafiyar ranan da abun ya faru ne bai sake shi ba lokacin da ta zo har ya sa shi ƙoƙarin nemanta ta karfi. It was never his intention ya sameta da ƙarfi, so ya ke ta zo gareshi a matsayin masoyiya yadda shi da ita za su nunawa junan su SO *** *Bayan shekara biyu* "Tijjani Zaytoonah get down" Fiskarta shame-shame da hawaye da majina ta ke roƙon sa " Uncle I'm sorry" 'Yan aji kuwa sai dariya su ke ma ta. "Tijjani Zaytoonah get down from that desk if i..." ya kai ma ta duka ta yi saurin komawa ɗaya desk ɗin tana ihu. Ita ce ƙarama a shekaru amma kuma tafi kowa girman jiki. 'Yan ajin daga ma su shekara shaɗaya ne sai shabiyu amma Tijjani Zaytoonah Abubakar 'yar shekara goma ce da wata biyu. Akwai wani da su ke cewa Smally saboda guntu ne sosai shima shekarun sa goma amma kuma sai ƙwazo. Haka itama Zaytoonan ƙwazonta yayi yawa, shiyasa ma ta zana common entrance nata a primary 4 kuma ta ci. Yanzu haka Sani da ke zaune a seat ɗin bayanta ne a aji ya ma ta waƙan 'Zaytoonah is a Big Fat Girl' shine ta ji haushi ta chaka ma sa biro a gefen hancinsa har wajen ya ɗan kumbura. To da Uncle Haroon form master ɗin su ya shigo shine ya samu Sani na kuka, ya tambayi bahasi 'yan aji su ka faɗi abinda ya faru. Ya yiwa Sani bulala biyu saboda ya tsokani Zaytoonah ita kuma ya ce zai ma ta bulala uku saboda ta cakawa Sani biro. To tunda aka yiwa Sani bulala Zaytoonah ta ɗale saman desk tana kuka. Idan akwai abinda Zaytoonah ke tsoro to bulala ne. Ko a Islamiyya idan ta makara ko ba ta iya karatu ba Malam ya ce zai dake ta to drama ake yi ƙarshe sai dai a sata tsintar datti ko kneel down amma ba za ayi dukan ba. "Tijjani Zaytoonah get down" Uncle Haroon ya daka ma ta tsawa. Ta fara ƙoƙarin saukowa sai ta ga ya ɗaga bulalar sama hakan ya sa ta yi baya da sauri ta tsallaka wani desk ɗin. Ai kuwa ya bi ta da gudu zai dake ta, ta zo za ta tsallaka wani desk ɗin ta zame ta faɗi yijif a ƙasa. 'Yan Aji mi su ka samu ban da dariya hatta Sani da aka daka shima dariyan ya ke sosai. Uncle Haroon ya zo ya taimakawa Zaytoonah ta tashi saboda tunda ta faɗi ta ke kuka ta ƙi ko motsawa. Maimakon dukanta da ya ke son yi da sai ya koma rarrashinta yana ƙoƙarin duba hannunta ko ta ji ciwo. Sai da ya dakawa 'yan Ajin tsawa kafin su ka tsakaita dariyan. Ranan dai har aka gama lesson ɗin ƙarshe Zaytoonah ba ta dena kuka ba saboda yaran ba su dena ma ta dariya ba har da wata Kelechi ta hau desk ɗin tana gwada faɗuwan Zaytoonah. Da aka tashi kuwa da hawaye ta tafi gida Manu na tambayarta ko lafiya amma ta ƙi kulashi, da ke Salman har yanzu yana primary session ya riga ta tashi. Shi kuma Auwal yana SS1 kuma ba a makarantar su ya ke ba. Da ta je gida kuwa Maryam ta tsareta da tambaya amma ta ƙi kulata sai kuka. Ganin kukan ya koma na shiririta sai ta ƙyaleta. Abinci da Kuka sun zama kaman daily habit ɗin Zaytoonah ne. Da yunwa ya isheta da kan ta ta haƙura da kukan ta wuce kitchen ta je ta ɗauko abincin ta ta hau ci. Tana ci tana yiwa Maryam da ke goge TV complain ɗin abincinta ya yi kaɗan kuma nama biyu kawai aka sa ma ta bayan ta ga ɗazu Salman ya ci nama uku. "Ban sa ki dole sai kin ci ba, ki ajiye anjima Almajirai za su yi bara sai na miƙa mu su, su kan ko ba nama za su ci su sa albarka" "Hhhenn dama Mommy you dont love me, that's why i miss my Daddy so much" Maganar Daddy da ta yi ya sa Maryam ta tuna lokacin da ya zo ƙarshen shekaran da ya gabata ya zo ya mu su kwana ishirin da huɗu kafin ya koma. Yadda ta yi kewarsa kwanakin nan sun tafi ne da gudu sai da ya tafi taga kamar ma kwana biyu kawai yai. Ba ta dameshi da matsalolin gida ba kar ya tafi da tashin hankali. Sau ɗaya da ya zo da Muntari gidan ne ta taka ma sa birki ta ce indai yana son zaman lafiya kar ya sake shigo ma ta da Muntari gidan. Ya tambayi dalili ta ce ma sa ba ta so ne kawai, ganin da ya matsa ma ta da tambayoyi ya sa ta tashi ta bar ma sa ɗakin hakan ya sa ya bar zancen ya wuce shima baya son abin da zai jawo mu su matsala a iya kwanakin da zai yi da su. Tun ranan da abun nan ya faru ta ke ganin Muntari a matsayin wanda ya ke da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa. Har yau idan ya bushi iska yana aiko ma ta da flowers office da card mai ɗauke da kalaman soyayya. Ranan da ya fara aikowa sati biyu bayan ɓarin da ta yi har da check ɗin kuɗi tareda makullin mota ya rubuta saƙo kamar haka *My love ki yafe min Dan Allah. Ga wannan kyauta daga gareni kuma kaɗan ne daga irin abubuwan da na tanadar miki idan ki ka amince da soyayyata. I love you Maryam* Bayan ta gama karantawa ta rasa ma mi za ta ce da Muntari dan gaskiya ya tabbata Mahaukaci ne. Kuɗin da ya rubuta a check ɗin kuwa sun girgizata saboda yawan su. Zuwa ta yi ta photocopy ɗin check ɗin da wasiƙar saboda a matsayinta na Barrister dole ta ajiye shi shaida. Flower da original check ɗin da key ɗin mota kuwa gidan Hajjo ta je ta watsawa Iya a jiki ta ce idan Mahaukacin ɗan ta ya dawo ta bashi saƙon sa. Ko Iya ta ma sa magana ne? sai bai ƙara turowa ba sai da ya ja lokaci sannan ya dawo da tsiyar sa amma wannan karan bai haɗo da kuɗi ko key ɗin mota ba zallar card ne da Flower. Haka za ta photocopy card ɗin ta ajiye idan ta koma gida ta sa a leda ta bawa Auwal ta ce ya miƙawa Mai gadin gidan Uncle ɗin shi ya bawa Muntari. Idan aka yi albashi akwai yadda T J ya tsara yadda za su dinga yi da shi. To tana ɗaukan kasonta za ta kaiwa Hajjo na ta. Just of recent ne wani zuwa da ta yi kaiwa Hajjo kuɗi, a wajen Hajjon ta ke jin wai su na shirye-shiryen bikin Muntari, Iya ta sama mi shi mata a Ringim... Washegari Zaytoonah ta ce ba za ta je school ba. Da Maryam ta zare ma ta ido sai ta ce ai 'yan ajin sun tsaneta dariya su ke ma ta su dinga kiranta Fat girl ko Fatty Bombom. Maryam ta nitsu tana jin maganganun 'yar na ta. Bayan ta gama ƙorafin Maryam ta ba ta haƙuri tareda cewa haushi su ke ji saboda ta fi su ƙoƙari a ajin, tunda Exam ɗin su na first term ita ta yi na ɗaya. Da ƙyar dai ta shawo kan ta har ta yarda ta shirya aka wuce da ita makaranta... *Hmmmmm. Alhaji Muntari da gaske ba ƙalau ka ke ba* *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *14-Anger* Bismillahir Rahmanir Rahim Shekara biyu da wata huɗu da dawowan Muntari Zaria wanda yanzu ya ke matsayin Alhaji Muntari Abubakar Modibbo Djibo yai aure. Aure ne da ba wai dan Iya na so ya yi shi ba, Iya ba ta isa ta tursasa shi yin abu ba. Ya yi ne domin ya nunawa Maryam cewa yayi hankali ko na ce ya nitsu, da kan sa ya je office ɗin ta ya kai ma ta invitation ɗin auren tareda sake ba ta haƙuri bisa abinda ya faru tsakanin su. So ya ke ta yarda da shi su koma mutunci kamar da har ya samu ta amince da soyayyar sa cikin sauƙi. "Sorry Muntari ba zan iya zuwa ko ɗaya cikin hidiman bikin ka ba. And kamar yadda na faɗa a baya ka fita a harkana, ba zan shiga huruminka ba kai ma kar ka shiga nawa. Idan ka yi haka za a zauna lafiya idan ba haka ba kuwa zan ajiye duk wani kunya a gefe na yi shari'a da kai" "Maryam kenan. Na ji amma dan Allah ki sassauta min, ki rage takurawan da ki ke yiwa su Zaytoonah. Ko ba komai ni fa Baban su ne" Wannan karan ido cikin ido ta kalleshi ta ce "Muntari Oh Alhaji Muntari. Bayan Zaytoonah da Salman akwai Humairah da Sadiq. Ba ni da hurumi da sauran amma wanda na haifa da kaina ba zan taɓa bari su yi tarayya da mutum kamar ka ba. Stay away from my kids" "Ba zan gajiya da baki haƙuri ba Maryam har sai kin haƙura. Ki yi haƙuri dan Allah" Daga haka ya ajiye ma ta katin bikin ya fita daga office ɗin. Yana fita ta sauke ajiyar zuciya... Biki aka yi tun daga Ringim aka zo Zaria aka ƙarisa, ba inda Maryam ta je ita da 'ya'yanta. Su Iya da Hajjo su ne ƙirjin biki musamman ma saboda ɗan Yayan Iyan zai aura. Su ka ƙare tsiyar su aka kawo Amarya gidan Muntari. A ɓangaren Ango kuwa ba wani murna ya ke yi da bikin da zai yi ba. Aure ne da ya ke da ƙaddararren lokaci a wajen sa, da ya samu kan Maryam zai tura ta gaba. Bayan kowa ya watse aka bar Amarya ita ɗaya. Muntari bai shigo gida ba sai wajen ƙarfe shaɗaya da rabi na dare, kai tsaye ɗakin Amarya ya wuce. Tana nan dai zaune kan gado ta yi lulluɓi, da Misalin ƙarfen goma 'yan biki su ka watse za su je su kwana a gidan Hajjo. "Hannatu" Muntari ya kira sunan ta da ƙarfi. Ba ta amsa ba sai ma mutsu-mutsu da ta fara ta cikin gyalen. "Ko ki ɗaga gyalen nan ko na zo na rufe ki da duka. An gaya mi ki ban san ko ke wacece ba ne, na sani ragowan Salisu aka kawo min" Nan da nan ta ɗage gyalen tana kallonsa jikin ta na rawa saboda ba ta ɗauka ya san wannan sirrin ba. "Ki buɗe kunnen ki da kyau. Na zaɓe ki ne a maimakon Rabi'atu saboda ita nitsatstsiya ce ke kuma watsatstsiya ce" "Dan Allah ka yi haƙuri Hamma Muntari" ta faɗa tana fashewa da kuka. Ya daka ma ta tsawa nan da nan ta haɗiye kukan. "Mace ɗaya na ke so kuma ita kaɗai ce zan aura mu yi rayuwar soyayya. Kasancewa kin riga kin sayarda mutunci a wani kinga babu wani mutunci na ki da zan gani. Ki zauna a matsayin Matata ki bi dokoki na, duk lokacin da na buƙaci mace saboda rage zafi zan neme ki, bayan wannan ba na son shishshigi. Kuɗi da mahaifiyar ki ta hango ta zuga Iya akan ta zaɓe ki dai za ki samu amma idan ki ka ce sata za ki yi kamar yadda ma su tarbiyya irin ki ke yi to Wallahi ba za ki ji da daɗi ba a gidan nan" yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin ya bar Hannatu tana rusa kuka. Yau wa gari ya waya ta biyewa daɗin lokaci kaɗan ta ba da mutuncinta tun a waje. Hannatu dai 'ya ce ga Sama'ila wanda ya kasance Yayan Iya amma uwar su ba ɗaya ba. Lokacin da Iya ta fara nemawa Muntari Mata Rabi'atu ta nema ma sa wanda ita kuma 'yar ƙanin ta ne, tana da hankali ga ilimi dan har tana gab da ƙarisa secondary school ɗin ta kuma a makarantar ana ji da ita sosai saboda ƙwazonta. Da ta yiwa Muntari magana sai ya ce baya son ta. Shi baya son Ustaziya da za ta zo gidan sa ta rinƙa takura ma sa da Allah Annabi. Hannatu kuwa da ta ma sa tayinta sai ya sa aka ma sa bincikenta. Abu ne na kuɗi shiyasa duk wani dark secret ɗin ta sai da aka faɗa ma sa. Akwai wani Malamin su Salisu mutumin Jos ne, ya zo bautar ƙasa su ka ƙulla soyayya da Hannatu har ta kai ya rinjayeta, ta kan saci jiki ta je gidan sa su nunawa juna soyayya, a tunanin su fa. Alƙawarin aure ya mata amma daga ƙarisa bautar ƙasa sa da ya tafi bai ƙara waiwayanta ba, ya ci banza. Bayan ta ƙare secondary school aka saka bikinta da Nura wani ɗan uwanta sai aka fara ƙananun gulmace-gulmace akan ta, hakan ya sa mahaifiyar Nuran ta ce a fasa auren. To da Iya ta zo Ringim ta fara batun haɗa Muntari da Rabi'atu ne shine Umman Hanne ta shiga zancen tana son a haɗa Muntari da 'yar ta. To da ya ce ba zai auri Rabi'atu ba shine aka yi maganar Hanne kuma ya amince da auren ta... Shekaru shabakwai da su ka wuce Muntari ya tafi Lagos. Aiki ya ke tuƙuru shi a ganin sa hakan zai sa ya samu kuɗi. Duk wani aikin wahala indai akwai kuɗi to yana nan. Shekaru biyu yai yaga bai wani tara abin a zo a gani ba, har yana son jona aikin wani abokin shi wato sata sai kuma labari ya chanja lokacin da ya haɗu da Madam Talatu. Madam Talatu tsohuwar karuwa ce da ta yi tashe a zamaninta. 'Yar Kafanchang ne da ke Jihar Kaduna, auren dole za a ma ta ta gudu wai ta shiga duniya. A garin Lagos ta tsinci kan ta bayan doguwar tafiya da ta yi. Bayan ta samu masauki a gidan karuwai ta shiga karuwanci, ba ta da wani kyaun fiska amma akwai ta da kyaun diri, irin wanda ke ɗauke hankalin duk wanda yai tozali da ita. Cikin loƙaci kaɗan ta zama ɗaya daga cikin manya-manyan karuwai da ake ji da su a Lagos, wanda Turawa ke ɗauka, 'yan siyasa da manya manyan sojoji ke rububi. Daga gidan karuwai ta ɓalle ta samu gidan kanta ta zauna wanda cikin kuɗaɗen da ta tara ne ta siya da shi. Ta yi karuwanci na shekaru talatin kafin ta yi retire ta bazama kasuwanci, dama tana ɗan taɓa kasuwancin amma yanzu da ta dena karuwanci sai ta riƙe kasuwanci zallah. To abu ne da ta jima tana tatsan kuɗi daga mazan da ba sa iya kama abun su, dan haka ba ƙaramin maƙudan kuɗi gareta ba. Tana da manya-manyan shaguna da kuma hannun jari. Bayan ta bar karuwanci ta kan dai nemi yara ƙanana wanda za su biya ma ta buƙata lokaci zuwa lokaci ita kuma ta ba su kuɗi. Lokacin da ta haɗu da Muntari tana shekaru Arba'in da takwas a duniya. Ta gan shi ne lokacin da su ka zo sauke ma ta kaya a ɗaya daga cikin shagunan ta. Nan da nan ɗan farin Bafulatanin ya burgeta. Bayan ta nemi ganin shi ta ce ya zo washegari za ta bashi aiki. Ganin kuɗin da za a dinga bashi a wata ya ninka wanda ya ke samu a da ya sa shi amincewa da aikin. Yana aiki da Madam Talatu ita kuma tana daɗa lura da shi, bayan wata biyu ta fito ma sa da maitar ta fili, ya ce baya so. Ta sanar da shi kuɗin da za ta dinga bashi duk wata idan ya amince amma still bai amince ba. Da ta dameshi sai ya ajiye aikin da ya ke yi ya kama gaban sa. Bayan ya tafi ta kasa haƙuri da shi ta neme shi ya dawo tareda ma sa alkawarin aure ta ke so su yi kuma indai ya amince to za ta ba shi ɗaya daga cikin shagunan ta, da yai lissafi sai ya ga arziƙi ne ya zo ma sa cikin sauƙi. Auren shekara goma su ka yi alƙawarin za su yi da shi kafin nan zai saketa ya kama gaban sa. Bayan sun yi Aure kuwa ta bashi ɗaya daga cikin shagunan ta ya zama shi ke sarrafa shi. Ta sa mishi ido sosai akan ko zai ci amanarta kaman sauran ƙananun samarin da ta ke yi sai taga shi Muntari ba ruwan sa da mata. Daga baya ta tambayeshi dalilin zuwansa Lagos ya ce ma ta ya zo neman kuɗi ne saboda matar da ya ke so. A mafiya yawancin lokutan da ya ke saduwa da ita yana ambatun ta da Maryam hakan ya sa ta san ba ƙaramin so ya kewa wannan Maryam ɗin ba. Shi kuwa Muntari saboda a dole ya ke tarayya da Madam Talatu ya sa ya fara shan giya da sigari saboda ya dinga ɗauke ma sa hankali a duk lokacin da ya ke tarayya da ita, hakan ya sa ya ke ganin Maryam a tareda shi a lokacin da ya ke tare da Madam Talatu. Cikin shekaru tara da su ka yi tare yana aika kaya Kano ana sayar ma sa da shi hakan ya sa kasuwancin sa ya haɓaka sosai ga shi ba shi da matsalar komai, cin sa da shan sa da suturan sa duk Madam Talatu ce. Bayan shekara tara da auren su MadamTalata ta fara jinya ashe cervical cancer ne. Ana magani ana jigilar asibiti amma abin ya mata mugun kamu saboda ba a gane shi ke damunta ba da wuri. Ganin fa kullum jigilar Asibiti ake ya sa Madam Talatu ta fara tunanin iyayenta da 'yan uwanta da ta baro shekaru ma su yawa da su ka wuce. A da ƙasar waje Muntari zai fita da ita ta ce ta fasa ya kaita Kafanchang za ta nemi iyayenta su gafarta ma ta. Da su ka je ta samu mahaifinta yana nan amma mahaifiyarta ta jima da rasuwa. Yayyenta da ƙannenta da ba ta san su ba kafin ta tafi duk sun girma suna da iyali. Anyi koke-koke kafin daga baya aka karɓeta hannu bibbiyu. Saura wata biyar shekara goman auren su ta cika Madam Talatu ta ce Muntari ya saketa saboda tana son zama da 'yan uwanta zuwa lokacin da za ta mutu. Cikin kaso ɗari na dukiyarta kusan kashi talatin ta ba wa Muntari wanda shima a lokacin side business ɗin sa ya haɓaka sosai. Sauran dukiyarta kuwa 'yan uwanta ta rabawa sannan aka gina Makaranta da Asibiti a ƙauyen su da ke Kafanchang. Shekara ɗaya bayan rabuwar su da Muntari ta rasu. Shi kuwa Muntari tunda su ka rabu da Madam Talatu ya fara ƙoƙarin yadda zai dawo da kasuwancin sa Kano saboda ya kasance kusa da masoyiyar sa. A shekaran ne kuma ya tafi Umara dan ya fito a Alhaji ya bawa kowa mamaki. Tunda kuɗi su ka fara zama ma sa ya fara bibiyan labarin ɗan uwansa Tijjani da kuma halin da masoyiyar sa ke ciki. Bai sha wahalar samun information da ya ke so ba. Nan ta ke ya sayi fili a anguwar ya fara gini, ya so ace kusa da gidan Maryam yai ginin amma bai samu fili a wajen ba, duk da haka tunda anguwa ɗaya ne ba shi da matsala. Wannan kenan *** Assembly ake yi da sassafiyar ranan Litinin. Kowa da ka gani a cikin uniform za ka gan shi tsaf-tsaf da shi. Kamar kullum a layin na su ita ce ƙarshe saboda ba ta son tsayiwa a gaba ko a tsakiya 'yan ajin na su su dinga tsokalar ta. "Zaytu Mama kin yi assignment ɗin Maths kuwa?" wata yarinya da ke gaban Zaytoonah ta faɗa. Nuratu kenan wacce duk cikin 'yan matan ajin na su ita ce su ke ɗan mutunci, itama ayi faɗa a shirya ne. Anguwar su ɗaya ne kuma Islamiyya ɗaya su ke zuwa hakan ya sa su ka ɗan shaƙu. Sai da ta haɗiyi baƙin cikin da ya taso ma ta sannan ta ce " na yi" ta tsani kalmar Maman nan da su ke alaƙantata da shi. Duk cikin sunannakin da su ke kiranta ba wanda ya fi tsaya ma ta a rai irin Maman aji ko Zaytu Mama da su ke ce ma ta. "Za ki bani na kwafa dan Allah" Shiru ta yi ba ta amsa ma ta ba. Bayan an gama assembly su ka wuce aji. Tana zuwa kuwa Nuratu ta tsareta sai da ta bata notebook ɗin ta na Maths. Nuratu na cikin kwafa sai ga Zaliha ma ta leƙo kai ta fara kwafa. Kan kace me duk waɗanda ba su yi assignment ɗin ba sun yiwa desk ɗin su Zaytoonah rumfa. Zaytoonah na gefe ta cika ta yi fam, ba dama ta yi assignment ita ɗaya musamman ma dai idan Maths ne. A haka za su kwafi assignment ɗin ta amma hakan ba zai hana su dinga tsokanarta ba. Wasu ba su gama kwafa ba ma Mr Isaac Maths teacher ɗin su ya shigo saboda shi su ke da shi darasin farko. Bayan ya gama darasin ranan ya tattara Assignment ɗin ya tafi da shi dan ya yi marking a staff room. Ko da ya je sai ya ga kusan duk matan class ɗin sun cinye Assignment ɗin bayan ya san acikin matan Ajin Zaytoonah, Kabirat da Felicia su kaɗai ne su ka iya Maths sosai, su ke kuma fahimtar darussan sa. Bayan ya gama marking ɗin ne ya je class ya nemi izinin Malamin English ɗin su a kan yana son ganin Tijjani Zaytoonah. A staff room ta sameshi. Faɗa Mr Isaac ya fara ma ta akan ta ya za ta ba da assignment ɗin ta a kwafa. Ba ta da ta cewa tunda ba iya magana ta ke mu su ba. Daga ƙarshe ya ce duk lokacin da ta yi assignment ya ga irin na ta a wajen wata sai ya ma ta bulala. Bayan ya gama faɗan ne ya ba ta books ɗin ya ce ta je ta raba a class. Tafiya ta ke yi ɗauke da litattafan 'yan ajin su idon ta cike da hawaye. She wasnt like this before, tana da rigima tanada ƙiriniya amma kuma cikin ƙanƙanin lokaci ta chanja. Ba komai ne ya chanja ta ba face yadda mutane ke ma ta magana akan ƙibanta. There are days da ta ke cewa ba za ta kuma zuwa school ba amma Mommy sai ta korata dole ta je. There are days da ta ke raba dare tana kuka duk dan saboda wata kalma da wani ko wata ya ma ta. A da ba ta ɗaukan abun da zafi amma a hankali-a hankali abun ya fara damunta. Ta kai ko kallonta ka yi sai ta ga kamar kana judging ɗin ƙibanta ne. Ta sani ƙiba halittanta ne tunda mommyn ta ma na da ƙiba, but kamar yadda Mommy ke yawan faɗa shine ta bari ciye-ciyen ta ya sa ƙiban ya zama unhealthy. "Shikenan dan inada ƙiba ba zan ci kayan daɗi ba" amsar ta kenan a mafiya yawancin lokutan da Mommyn ta ma ta magana akan ta rage ciye-ciye. Da karfin hali ta ke zuwa makaranta saboda yadda kowacce rana ke zuwa ma ta da sabbin salo. Suna kam da su na tabo a jikin mutum da duk jikinta ya nuna. Ba matan ba har mazan suna kiranta da annoying sunaye. Abinda ba ta sani ba shine ba ƙiban kaɗai ke jawo ma ta wannan izgilanci da 'yan class ɗin su ke yi ba, tun JSS1 har yanzu da su ke JSS 3 ita da Smally su ke ɗaukan na ɗaya da na biyu. Idan ta ɗauka wannan karan zaka ga wani karan Smally ya dage ya ƙarɓa itama wani term ɗin ta ƙwace kayanta haka su ke yi. Saboda wannan jarraban judging ɗin ta da su ke yi ne ya sa ba ta da ƙawa. Ba ta da wanda ta ke wani mu'amala da ita, Nuratun ma ita ke shishshige ma ta... *** Shekara biyu kenan da dawowar T J kuma cikin shekaru biyun nan abubuwa da dama sun faru ciki kuwa hadda wani faɗa da su ka yi wanda ya sa Maryam ɗin ta yi yaji, ba yaji kaɗai ba barin garin Zaria ta yi gaba ɗaya kuma ba Ringim ta je ba hakan ya saka T J cikin tashin hankali. Abunda ya faru shine, kafin T J ya dawo Maryam ta yi sauka amma ba Hadda ba Tartil. Bayan tafiyan T J ƙasar waje ta shiga wani Islamiyya da ake yi da safiyar Asabat da Lahdi, a nan ta cigaba da ɗaukan karatu. To ganin T J ne malamin ta na farko ya sa ta ɗaga Waliman saukar ta zuwa sai ya dawo. Bayan wata biyar sai gashi ya dawo ya kammala Phd ɗin sa ya zama Dr Tijjani Abubakar Modibbo Djibo. Waliman saukan Maryam da ta kammala Phd ɗin sa su ka haɗa bayan sati biyu da dawowa aka yi. To daren ranan saukar su ka fara buɗe kyaututtukan da aka ba ta, kasancewarta revert wato wacce ta musulunta kuma har ta tsaya ta yi karatun Ƙur'ani ta gama, hakan ya sa mutane da dama da su ka halacci waliman su ka ba ta kyaututtuka. Bayan an gama buɗe kyaututtukan ne T J ya fito da makullin mota ya damƙa ma ta, har ta fara murna sai ya ce kyauta ce daga ƙanin sa Alhaji Muntari. Tana jin sunan Muntari ta yi cilli da key ɗin motar ta ce ya mayar ba ta so. "Maryam wai mi ya ke faruwa ne? The last time da na ce mu je mu gaishe da matar sa da ba ta da lafiya kin ce Allah ya kiyaye ki taka gidan Muntari. Na tambayeki ba ki bani takamaimai amsar abinda na tambaya ba" "Ni dai ka mayar ma sa key ɗin nan, idan ma akwai wani kyautan da ya fito daga hannunsa a nan ka cire ba na so" "Maryam miyake faruwa ne? Akwai abinda ya miki da ya kamata na sani ne? Duk abinda yai Maryam bai kai ki dinga nuna ma sa ƙiyayya haka ba. Ba tarbiyyan musulunci ba ne" A lokacin tana son faɗa ma sa komai gameda Muntari amma abinda ya faɗa ya ɓata ma ta rai shaiɗan ya kuma tunzura ta sai ta hau tabarmar fushi ta tashi ta bar ma sa ɗakin. Ranan a ɗakin Zaytoonah ta kwana. Washegari dukkan su suka tashi da jin haushin junan su. Ba wanda yai magana da ɗan uwansa. Zuwa yamma Tijjani ya nemi su sasanta tareda ba ta haƙurin tsawa da ya ma ta. Ce ma sa ta yi komai ya wuce ashe ba haka ba ne. Ranan da ya koma gidan Hajjo ta haɗa wa su daga cikin kayan ta ta bar gidan. Takarda ta bawa Zaytoonah akan idan Daddynta ya zo ta ba shi. T J bai samu ya zo duba su ba sai yamma liƙis. Zaytoonah ta ba wa T J envelope ɗin ta ce Mommy tun safe ba ta dawo ba har su ka dawo daga Islamiyya ba ta nan, Auwal ne ya mu su girki. Hannu na rawa ya buɗe envelope ɗin ya fara karantawa. *Ba kai kaɗai ke da 'yan uwa ba da za ka min gori akan Muntari. Na tafi neman 'yan uwana tunda ba daga sama na faɗo ba. Kar ka neme ni dan ba zan dawo ba sai na same su. TARBIYYAN MUSULUNCI bai ce na yi watsi da 'yan uwana ba ko da su kafirai ne* Sun taɓa maganan sake neman 'yan uwan mahaifiyarta a shekarun baya ta hanyar ba da sanarwa a gidan talabijin a Calabar amma kuma T J ya nuna ma ta ba lallai su same su ba haka nan kuma zai iya yiwuwa garin son neman 'yan uwan mahaifiyarta ta ci karo da Uncle ɗin ta wanda ya kashe ma ta iyaye. Haka dai yai ta convincing ɗin ta har ta haƙura da batun neman, musamman ma da ya ke wani hidiman kashe kuɗin za su yi kuma ba su da kuɗin a lokacin. Sun bar shi akan idan lokaci yayi da kan sa zai rakata su neme su. Wasa-wasa kwana biyu ba Maryam ba dalilinta, faɗin tashin hankalin da T J ya shiga ma ɓata lokaci ne har Ringim ya je ba ta nan kuma Goggo ma ba ta da masaniyar inda ta tafi. A kwana na huɗu ne ya shirya tafiya zuwa Calabar zai tafi nemanta duk da bai san ta ina zai fara ba. Idan bai samu labarin ta a nan ba dole ƙauyen su zai je. Muntari ma jin labarin Maryam ba ta gida hakan ya tayar ma sa da hankali shima ya kawo motar sa da dreba akan su tafi neman tare. Har sun kama hanya sun fara tafiya sun yi nisa aka kira wayar Muntari saboda lokacin ne aka fara yayin waya kuma Alhaji Muntari ya siya saboda waya a lokacin sai Alhaji wane ko Honorable wane. Daga gidan Alhaji Iliyasu Mai Auduga ne aka yi kiran aka bawa Auwal yai magana da Muntari ya ce Mommy ta dawo. Jiki na rawa T J ya karɓi wayan ya shiga jerawa Auwal tambayoyi dan ya tabbatar gaskiya ne ba ƙarya ba. Kusan shaɗayan dare ta gota su ka iso Zaria. Kai tsaye a ƙofar gidan Maryam su ka tsaya T J ya shiga gidan da gudu. Shi ma Muntari ya so shiga amma kuma baya son Maryam ta gan shi ta fara masifa dan haka ya ce Dreba ya juya da shi gida. "Maryam why? Kasheni za ki yi ne? "Kin san tashin hankalin da na shiga a rashin ki? I love you Maryam, please dont ever leave me again" Ya faɗa kamar zai yi kuka yana rungume da ita ƙyam a jikin sa. "Gidan Hajiya Fatima na je a Abuja" abunda ta faɗa kenan bayan ya saketa. "Maryam dan Allah kar ki sake irin wasan nan kin ji. Idan na rasa ki mutuwa zan yi" Ehem kawai ta iya cewa... Daren ranan T J bai iya baccin kirki ba, motsi kaɗan ya tashi ya duba ko Maryam na nan ko kuma ta tafi. A ɓangaren Maryam ta yi niyyar tafiya neman 'yan uwanta kamar yadda ta rubuta amma bayan ta bar gidan ta rasa ta ina za ta fara. Shekaru sun ja kuma ba ta da wani valueable information akan 'yan uwan mahaifiyarta da ya wuce sunan Kakanta Chief James Asibong, mahaifiyarta na da ƙanne 'yan biyu maza Paul and Peter sai sunan Kakarta mace Elizabeth. Wannan kaɗai bai isa ta same su ba ga uwa uba ba wani kuɗi ta riƙe a hannun ta ba. Gidan Hajiya Fatima ta wuce a Abuja dan a lokacin tana buƙatar kaɗaici. Kwana biyun da ta yi ba ta tareda Mijinta da 'ya'yan ta ba, kwata-kwata ba ta da kwanciyar hankali. T J da 'ya'yan su biyu su ne familyn ta yanzu. Ta ya ma za ta yi tunanin tafiya wata duniya ta bar 'ya'yan ta, jinin ta?. May be she's just exaggerating about Muntari. Yes ya ma ta laifi a baya amma kuma tun bayan da yai aure da watanni kaɗan ya dena aiko ma ta da abubuwan da ya ke aikowa da. Ya dena shiga sabgar ta, iya ka ci yana aikowa 'ya'yan ta kyaututtuka. Bayan ta gama ba wa kanta haƙuri ta koma gidan ta... T J bai sake ma ta maganar Muntari ba dan Kaffa-Kaffa ya ke da ita. Duk wani abun da zai ɓata ma ta rai har ta kawo tunanin rabuwa da shi baya so. Shekara ɗaya bayan faruwan haka aka ma ta transfer zuwa Kaduna. T J bai yi wata-wata ba ya amince ma ta ta fara zuwa, duk da kuwa jigilar jeka ka dawo ta ke yi kullum tsakanin Zaria zuwa Kaduna. Bai taɓa complain ba duk da jigilar kuɗin mota da ake yi. Wata takwas ta yi tana aiki ta ajiye aikin ta cewa T J za ta zama Barrister mai zaman kan ta kawai. Akwai wani private Law firm da wani babban Lawyer ya buɗe a Zaria nan ta koma tana zama a chamber ɗin su... *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *16-Confession* Bismillahir Rahmanir Rahim Har aka kawota asibiti ba ta farfaɗo daga suman da ta yi ba. Kuka kawai Maryam ke yi Salman na tayata. Salman ne ya tashi zai shiga banɗaki ya ga Zaytoonah kwance a sume shine ya fara ihu yana kiran Mommy. T J baya gari ya tafi Ringim duba gonar sa dan haka Muntari ne ya kawo su Asibitin tunda yana da mota. Mommy na zaune tana hawaye shi kuma Muntari na lallashi. Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin yadda Maryam ɗin ta birkice lokaci guda. "Dan Allah ki dena kuka Maryam addu'a za ki ma ta. Kinga dai Salman ma kukan ya ke" Ba tareda ta damu da abinda ya faru tsakanin su ba ta ce "Thank you Muntari" Shi kuwa yai murmushi. Kusan minti talatin kafin likitan ya fito ya mu su bayanin ta farfaɗo amma sun ma ta allurar bacci. Cewa yai ta sha wani abu ne da ya birkita ma ta ciki sannan akwai yunwa a tattare da ita. Maryam kallon sa ta ke yi tana ajiyar zuciya. Idan ka cire ƙananun ciwuka da Zaytoonah ta yi lokacin tana jaririya zuwa kafin a yayeta ba ta taɓa wani rashin lafiya da har zai sa a kawota asibiti ba. Bayan sun gama jin bayanin Doctor su ka shiga ɗakin da aka kwantar da Zaytoonan. Tana kwance an ɗaura ma ta drip. Sai yanzu ma Mommy ta lura idon Zaytoonan ya faɗa, laifi ta ɗaurawa kan ta na rashin damuwa da bin diddigin miyasa Zaytoonah ta dena cin breakfast da lunch tareda su. A asibitin ta kwana tareda Zaytoonah da Salman, duk yadda ta so Salman ya je gida ya kwana ƙi yai, shi da Muntari su ka koma gida Salman ya shiga gida ya ɗauko mu su abubuwan buƙata wanda Mommy ce ta gaya ma sa abubuwan da zai ɗauko. Da su ka koma asibitin ya ƙeƙasa ƙasa akan shima a nan zai kwana dan haka Maryam ta bar shi. Muntari ma bai so tafiya ba amma ya zai yi dole ya tafi. Zuwa Asuba Zaytoonah ta farka. Mommy ta ɗan saka kan ta a bakin gado tana barci dan kwanan zaune ta yi, towards Asuba ne ma baccin ya ɗauketa. "Mommy, Mommy" Zaytoonah ta faɗa da dashashshiyar murya. Maryam ta yi girgigit ta tashi. "Adaeze, Adaobi nmo are you ok" ta faɗa tana kissing ɗin hannunta. "I'm thirsty" "Ki tsaya barin tambayi likita ko za ki iya shan ruwa" ta kissing ɗin kumatunta da goshin ta sannan ta fita da sauri... Kwana uku Zaytoonah ta yi aka sallamota. Ba ta ɓoye mu su komai ba ta sanar da su duk yadda ta ke ƙin cin abinci da kuma maganin da ta siya ta sha. Maryam da Tijjani kam sai ido dan gaba ɗaya kan su ya ɗaure amma Maryam ta san result ne na bullying ɗin ta da ake yi a makaranta. Ba wanda ya ma ta masifa illa jaddada ma ta da su ka yi akan suna tsananin son ta a yadda ta ke. Da safiya Maryam ta kira T J ta sanar da shi dan haka maimakon zuwa yamma da ya ce zai dawo a safiyar ya kamo hanya zuwa ƙarfe ɗaya ya iso asibitin. Kafin nan Muntari ne ya ke zaune tareda su shi ya biya kuɗin komai. Ko da T J ya zo ya tambayeshi kuɗin yana so ya maida ma sa cewa yai Zaytoonah 'yar sa ce babu bashi tsakanin su. Har aka sallameta kullum sai ya je ya gaisheta kuma ganin Maryam ta sake jiki da shi ya sa shi farinciki ya kuma ba shi ƙarfin gwiwar zuwan. Da aka sallame su ma shi ya dawo da su gida a motar sa. Ya shiga gidan aka wuni da shi har ya ci abinci. Shi kan sa T J ya yi mamakin yadda Maryam ta sake da Muntari. Hajjo dai ta je ta duba Zaytoonah a asibiti sau ɗaya amma Iya ba ta je ba. Humairah kuwa T J da kan sa ya je ya ɗaukota ta gaisheda yayarta sai huhhura hanci ta ke ita a dole ba ta so. Dan ta jima tana zargin Daddy ya fi son Zaytoonah a kan ta... Yau ne kwana na takwas da aka sallami Zaytoonah a Asibiti kuma Alhamdulillah tana cin abinci sosai musamman ma yadda T J da Maryam su ka maida hankali akan movement ɗin ta. A ɗan madaidaicin gadon na ta su ka zauna su uku su ka sa ta a tsakiya. Maryam tana shafa kan ta ta ce "Zaytoonah kin san muna son ki sosai ko?" Ta gyaɗa kai T J ya ce " kuma kin san ke Princess ce" Sai ta yi dariya "I know how you feel Adaeze. Nima an bullying ɗina lokacin ina makaranta. Ina son rawan Balle, tun ina yarinya na ke son zama Ballerina. Ina shekara biyar na fara koya kuma ina da ƙoƙari sosai, ina shekara bakwai aka fara tsokana na idan muna practice wanda sai daga baya na gane ba wai dan ƙiba na bane ya sa su ke tsokana na ƙwazo na ya sa su ke tsokanana saboda su ɓata min rai. Then watarana ina shekara tara za mu representing school ɗin mu a gasar rawar Balle, muna practice sai na miƙar da ƙafa na sama kawai sai hantsar wando na ya yage kasancewa rigan ya ɗan matseni. Aka fara min dariya nan da nan na fara hawaye na gudu na bar wajen and that's the end. Wannan dariya ya kashe min dream ɗina, har rana ita yau sai dai na kunna video na kalli rawan in yi sha'awar sa amma ban sake ko gwadawa ba just because an min dariya a stage practice. Ba na so ki kashe dream ɗin ki just because ana miki dariya ko ana kiran ki da wasu suna. You are beautiful just the way you are, you dont need to be slim to look pretty. And always remember ko kin fi haka ƙiba ni da Dad ɗin ki will always love you and you'll always be our Princess" Ta ɗauko Cadbury chocolate guda biyu ta ba ta Zaytoonah ta waro ido. "Indai saboda ina hanaki ciye-ciye ne kika sa damuwa a ran ki daga yau ba zan hana ki ba. Ki ci duk abinda ki ke so kin ji" Zaytoonah ta amsa tana murmushi. T J ya ce "ni kuma da na ke ɗan firit ba za a bani kayan daɗi na ci na yi ƙiban ba" Maryam ta ja kunnen sa da ɗan ƙarfi Zaytoonah ta sa dariya tana yi tana cin chocolate ɗin ta... An chanjawa Zaytoonah makaranta inda ta fara zuwa SS1, da ke sabuwar zuwa ne 'yan ajin na ɗan ma ta gani-gani amma ba wanda ya ma ta wani nasty comment so far. Tana samun kulawa daga iyayenta da ƙaninta da Auwal wanda tun rashin lafiyarta shima ya ƙara ninka kulawar da ya ke ba ta. Ɗan tsokalarta da ya ke yi da saboda ƙiban ta ya dena. Ba wai ta dena jin haushin ƙiban ta ba ne but gradually she's learning to accept herself and love herself more. Ta ga yadda Iyayenta su ka damu lokacin da ta ke Asibiti ba ta fatan ta sake sa su cikin damuwa because she loves them very much... *** Muntari tun rashin lafiyar Zaytoonah da ya ga Maryam ta sauko daga fushin da ta ke yi da shi ya ƙara matsuwa da raba auren ta da Tijjani. Ya tabbata dai Bokan da ya ma sa aiki wancan karan kuɗin sa kawai ya ci amma duk da haka bai daddara ba wajen neman inda zai dace buƙatar sa ta biya. Bayan wata uku da rashin lafiyan Zaytoonah Maryam ta samu kyautar Mota. Akwai wani client ɗin ta ne da ta jagorance shi wajen wata shari'a mai sarƙaƙiya har su ka je Supreme court Abuja kuma yai winning shari'ar, ita ta ma manta da shi dan an kwana biyu da yin case ɗin. Kawai sai gashi har gida ya kawo ma ta key ɗin mota, lokacin ma suna tareda TJ. Duk yadda ta so ƙin karɓan motan nan sai da ya dage tareda roƙan T J ya sa baki tunda tsakani da Allah ya ba ta. Gadon su ne wani Yayan Baban su ke son cinyewa shine Maryam ta shige mu su gaba har su ka winning case ɗin. Ita kuma ta karɓi case ɗin ne saboda yadda case ɗin su na son danne hakkin marayu yai kama da yadda itama ƙanin Babanta ya kashe iyayenta ya cinye dukiyar su. Bayan ta ƙarɓi motan a T J ta bawa amma ya ce fir ba zai karɓa ba saboda kyautar ta ce. Shima yana taru nan ba da jimawa ba zai sayi ta shi. Ba'a jima ba ta koyi mota ta fara fita da ita tana saka L tag da ke nuna ita ɗin mai koyo ce. Daga jin Maryam ta yi mota Hajjo ta fara ƙananun maganganu, ta je wajen Iya ta ma ta gulman wai a wajen aiki aka bata kuma idan ba karuwanci ba ba wanda zai ba da kyautar mota haka kawai siddan. Iya ta kira T J ta ce ba ta yarda da aikin da Maryam ta ke yi ba ya hanata zuwa. Yana fara ba ta baki ta ce idan ya ƙara barin Maryam ta yi aiki za ta tsine ma sa. Ya shiga ruɗu ya cigaba da ba ta haƙuri amma ta ƙi fir. Ya yiwa Muntari magana akan ya taya shi ba wa Iya haƙuri shi kuwa ganin ya samu hanyar da zai raba kan Maryam da T J ya sa ya je ya zauna ya zuga Iya ya ce kar ta yarda, ta matsa ma sa sai ya hana Maryam aiki. A tunanin sa Maryam na son aikin ta sosai idan kuma aka hanata aiki zai jawo matsala tsakanin ta da T J. Ganin yayi-yayi ta ƙi yarda ne ya sa shi yiwa Maryam magana akan ta ajiye aiki for now daga baya ko teaching job ne ta nema. Ko kuma ta koma ta yi masters ɗin ta ƙila ta samu koyarwa a Jami'a ko kwaleji. Maryam ta san haka siddan ba zai yi maganar nan ba sai dai idan iya ce ta sa shi. Tashin farko tace ma sa aiki kam yanzu ta fara. Yayi-yayi da ita ta ce ba ta yarda ba idan za su rabu sai dai su rabu amma ba za ta ajiye aikin ta ba. Daga ƙarshe ya furta ma ta abinda Iya ta ce da shi. Ta yi mamaki kam amma ta dake ta ce"your choice Barkindo. Sai ka zaɓi abinda ka ga ya dace" Yai shiru yana kallon ta yana sauke ajiyar zuciya. "Maryam ki min alfarman nan dan Allah. Ina so na rabu da Iya lafiya" Maganar da ya faɗa kenan lokacin da ya ga ta tashi daga kan gadon. "Ba zan iya ba Barkindo. Ba zan Iya ba. Mahaifiyar ka ba ta sona na sani amma ba ta isa ta dinga wasa da hankalina ba, ba ta isa ta dinga juya rayuwata ba. For God's sake Barkindo ita fa ba Allah ba ce da za ka ce za ka dinga bin maganan ta from A-Z koda kuwa maganar tan son zuciya ne. This time i wont accept this injustice ko da kuwa hakan zai sa na rabu da kai i'm ready to do it. Haba, Haba kai fa ba yaro ba ne da za ta dinga ma ka barazana da cliche saying "zan tsine ma ka" to ta tsine ma kan mu gani" Ba ta jira mi zai ce ba ta fice daga ɗakin dan idan ta biye shi sai ta faɗi abinda za ta iya danasanin sa daga baya. Haba ita Iya kullum ba ta son zaman lafiyar ta da Tijjani gashi aure yanzu har da 'ya'ya. T J barin ta yai bai sake maganan ba a ranan dan ya san ta ɗau zafi ba za ta fahimce shi ba. Washe gari ta kasance Lahdi bayan yaran sun tafi Islamiyya tana wanke-wanke a kitchen ya zo ta bayanta ya rungumeta ya kissing wuyanta ya ce "I love you Maryam" Ba ta kulashi ba dan har lokacin haushin sa ta ke ji. "Ki yi haƙuri, i know its not fair. Amma Iya is my mother kuma kin san ta tsufa, and na yarda akwai jahilcin zamantakewa da kuma addini a tattare da ita but still..." A fusace ta juyo ta kalli cikin idon sa ta ce "idan ba za ka iya gaya ma ta ba ni zan gaya ma ta. Enough is enough, idan na cigaba da aiki ta haɗiye zuciya ta mutu ni ba damuwata ba ne. I dont care" "Maryam please" "Idan ka na sona yadda ka faɗa you'll fight for me. So na wa aiki na yana rufa ma na asiri ta wani wajen? So nawa na ke representing mutane kyauta a kotu duk dan na taimaka mu su a bi mi su haƙƙin su su zo nan gidan su yi ta min addu'a. Idan ka ce na bar aikin nan Tijjani tamkar ka yadda karuwanci na ke yi kamar yadda Iya ke faɗa" "Nooo Maryam, Nooo" "Then kar ka roƙeni dan ba zan bari ba even at the expense of our marriage" Ya rasa bakin magana dan tunda Maryam ta faɗi haka to da wuya ta chanja ra'ayinta shi tsoron sa ma kada ya kuma yin magana ta tattare kayanta ta bar gidan kamar yadda ta taɓa yi... Yana kwance a ɗaki yana tunanin yadda zai ɓullowa lamarin wayar sa ta fara ringing. Ɗazu ya ga Maryam ta sa hijabi ta fita ya ɗauka za ta je ta siyo abu ne. Hanne ce matar Muntari ke kiran sa. Ya ɗauka kiran tareda sallama. "Hamma Tijjani ka zo gidan mu Anty Maryam da Iya su na faɗa" Innalillahi ya faɗa ya miƙe da sauri ya fita. Maryam kam zuwa ta yi gidan Muntari dan ta jaddadawa Iya ta fita harkanta ta sake ma ta mara ta yi fitsari. Zuwanta ta samu Iya na cin ferfesun kaza tana ci sanyin AC na ratsata tana kallon wani chinese film irin na da ɗin nan wanda za ka ga ana faɗa a saman bishiya ana tafiya a kan iska. Daga fara magana Iya ta ce indai ba karuwanci ba miyasa ta ke tuƙa mota Alhalin T J bai da mota. Martanin da Maryam ta bayar ne ya sa Iya ta tashi ta tsinkawa Maryam ɗin mari ita kuwa ta cigaba da kiranta jahila. "Wallahi ki koma Islamiyya ki ɗau karatu dan jahilci babban cuta ce. Dan na riga mijina hawa mota sai ya zama karuwanci na ke yi? Kin min ƙazafi, kin min sharri ki ji tsoron Allah Iya, dan idan ban yafe ba wallahi za ki sha azaba a kan haka ranan gobe" Ita kuwa ta fara tafi tana ahayye wai har Maryam Inyamura ce za ta ma ta wa'azi lallai ƙarshen duniya. "Ba zan tsaya magana da ke ba dan ba ki kai na yi jayayya da ke ba amma kisani ƙazafin da ki ke min Allah zai tambayeki, ki tambayi Malamin da ki ka yarda da shi, ki nemi duk wanda ki ka yadda da fatawar sa zai gaya mi ki babban zunubin da ki ke ɗauka wa kan ki" Ta juya za ta tafi Iya ta ce "Ni dai Allah ya isa da ɗana ya haɗa shimfiɗa da Karuwa kuma Kwartuwa" Kalmar kwartuwa shi ya tinzira Maryam fiye da karuwan da ta ce. Tana juyowa ta yanke Iya da wani mahaukacin mari dai-dai nan T J ya shigo gidan kuma ya ga marin da Maryam ta yi. Duk lalacewar mahaifiyar sa ya sani Maryam ba ta da ikon marin ta. "Maryam" ya daka ma ta tsawa. Yana ƙarasowa ya wanketa da mari ya ce "you dont have any right to slap her Maryam, ka da ki sake" Iya na ganin haka ta fashe da kuka tana faɗin "Allah ya kawo mu zamani da matar ɗa za ta mari uwar mijin ta. Tur da wannan zamani, Tur da wannan aure, Tur da ɗan da ya zauna da irin wannan mata" A hankali ta buɗe idon ta ta ɗaura su a kan na T J da yai jaa zur. Tunda ya mareta idon ta ke rufe saboda yadda shock ɗin marin ya shigeta. "Barkindo" "Shhhhh ki koma gida" ya faɗa yana nuna ma ta ƙofa "Ba inda zan je sai ka sawwaƙa min. Ka ji dai mi mahaifiyar ka ta ce "Tur da kai idan ka zauna da ni" dan haka i'll only leave when you divorce me because i can take it anymore" "Ki je za mu yi magana idan na dawo" Dariya ta fashe da shi dan yau kam tana jin kan ta a Barrister Maryam Nkiru Uzodinma ɗin ta. "Wani cin mutunci ne ba a min a gidan ka ba Tijjani? Wani haƙƙi ne ba a tauye mun ba? Ka tuna lokacin da mahaifiyar ka da yayarta su ka zo da wani mahaukaci wai Sarkin Mayu su ka sa shi ya jibgeni kamar jaka? No, ka tuna lokutan da na ke karɓan girkin Hajjo na yi saboda tana laulayi? Ka tuna yadda na yiwa yaran Hajjo hidima amma lokacin nawa aka ce min Zaytoonah shegiya ce babu wanda ya ke ɗaukan ta balle a taya ni reno. Ka tuna lokacin da ka yi gini aka hanani komawa gidan? Ka tuna lokutan da ake cewa karuwanci na ke zuwa yi a Abuja. Ko ka manta yadda ta ke fifita Humairah akan Zaytoonah to the extend Adaeze ba ta san mi ake nufi da wasan Kaka da Jika ba. Wanne ne ban faɗa ba? wanne na manta ban faɗa ba? tuna min Tijjani, tuna min." Girgiza kai kawai T J ya ke yi saboda abubuwan da ya ke ji suna fitowa daga bakin Maryam wanda ya sa shi cikin tashin hankali da tsantsar nadama. "Ba ka taɓa tsaya min ba, kullum sai dai 'Maryam i know its not fair but ki yi haƙuri, I love you' to yau haƙuri na ya ƙare, ba zan iya zama ana tauye min hakki ba" Ta kalli Iya ta ce "Hajiya Iya ba zan taɓa yafe miki ba. Duk wani ƙuntatawa da ki ka min ban yafe ba, ban yafe ba ƙazafin karuwanci da ki ke min har rana ita yau, ban yafe ba shegenta min Zaytoonah da ki ka yi, ban yafe ba shegenta min 'yan biyu na da ki ka yi" "Mmmmaryam" T J ya faɗa murya na rawa. Bai gane maganganan ta na ƙarshe ba, wa su 'yan biyu kenan? "Da ni da mahaifiyarka za mu haɗu a gaban Allah Tijjani. Ko a kafira ka aureni iya abinda zai sa Mahaifiyar ka ta tsaneni kenan balle ina musulma, i didnt deserve this treatment. Musulmi ɗan uwan musulmi ne haka ka koyar da ni amma mahaifiyarka ta jahilci hakan. For 21yrs da mu ka yi aure Mahaifiyar ka ba ta taɓa mutuntani ba, is it because Musulunta na yi? Is it because na fito daga ƙabilar Igbo?, or is it because kana sona despite ni ba Bafulatana ba ce?. A yau zan bar gidan ka Tijjani. Ka je Iya ta sa ma ka albarka kar ka lalace, ka je ka haƙura da ni kar tsinuwar Iya ya kamaka dan aiki kam yanzu na fara. But let me tell you one thing, indai akwai hakkina a kan Iya to daga yau har ƙarshen rayuwarta ba za ta taɓa samun kwanciyar hankali ba. And as for your crazy brother idan ya sake zuwa kusa da ni da niyyar yin wani abu zan kashe shi" Hannunta ya kamo yana kiran sunan ta a hankali, ta wafce hannun ta ce " barin gaya ma ka gaskiya. I regret meeting you, i regret following you that day, i regret saying YES to marrying you, i regret the night you make me a woman, i regret every single moment i spend with you, i regret loving a man like you Tijjani Abubakar Modibbo..." Zuwa lokacin kuka ya ci ƙarfinta ta kasa ƙarisa faɗin abinda ta yi niyya. Juyawa ta yi za ta bar wajen ya damƙe hannunta da ƙarfi. "Maryam what twins? Wwwwhat twins?" Ya faɗa yana hawaye jikinsa na ƙyarma. " Au Iya ba ta faɗa ma ka ba, ashe kai ma tana munafurtar ka kenan. To bari ka ji Lokacin da ka tafi Oxford i was pregnant and that's when Muntari came back, he tried to rape me and while struggling with him he pushed me and i hit my stomach so hard that i end of loosing my 3months old twins. My twins Tijjani, our twins. And when i told your mother ta shegenta min su, ta ce ba cikin ka ba ne, ta ce ni kwartuwa ce, ta ce..." TJ ya durƙusa a ƙasa yana dafe ƙirjinsa saboda zafi da ya ke ji hakan ya sa Maryam ta dakatar da maganganunta. Ta goge hawayen ta tace"You know what, ba amfanin maganar yanzu saboda ba zai mai da hannun agogo baya ba. But know this Tijjani, i will never forgive your mother and brother" Tana faɗin haka ta fice da sauri, seeing T J a wannan hali ya fara sa wa zuciyarta rauni. A inda ya ke tsugunne ya fara ƙoƙarin kiran sunan ta amma zuciyar sa ta ma sa ƙunci. "Mary..." sunan bai gama fita ba ya fara aman jini. Iya tunda Maryam ta fara bayani jikinta ke ɓari, ganin Tijjani na furzar da jini ya sa ta ƙwalla ƙara ta yi kan sa tana kiran sunan sa "Shehu, Shehu, Tijjani"... Tana fita daga gidan kai tsaye gidan ta ta wuce, a bakin ƙofa ta haɗu da Auwal zai fita. Ganinta tana kuka ya sa shi birkicewa "Mommy lafiya? Miya faru?" "Ka je gidan Muntari ka duba Daddyn ku" "Mommy..." "Ka je da sauri Auwal" Bai ƙara magana ba ya fita da gudu. Yadda idon T J yai ja jijiyoyinsa su ka firfito ta tsorata amma dole ta rabu da shi saboda ta riga ta sawa ranta daga yau babu ita babu T J. Kayanta ta shiga haɗawa da sauri tun kafin Auwal ko sauran yaran su dawo. Muhimman takardunta ta ɗauka sai cards ɗinta sannan ta ɗauki kaya randomly ta sa a jaka ta fice da sauri. Motarta ta shiga ta bata wuta ba tareda ta san ina takamaimai za ta je ba... Taimakon gaggawa aka fara yiwa TJ saboda yadda aka kawoshi wurjajan. Allah ne ma ya taimakeshi bai kamu da stroke ba. Ikon Allah ne ya cececi rayuwar sa amma da tuni heart attack ɗin ya kashe shi. Iya na kuka Auwal na yi itama Hanne na hawaye, har sai lokacin da likita ya fito ya ce mu su su godewa Allah he survived, sun stabilizing condition ɗin sa. Amma su cigaba da yi ma sa addu'a, ba a bar su sun shiga wajen sa ba sun dai leƙa shi inda su ka ga yadda aka sa ma sa nasal canula saboda ya dinga taimaka ma sa da numfashin sa. Wayan Hanne Auwal ya karɓa ya kira numbar Mommy sai dai har ta gama ringing ba a ɗauka ba. Sau biyar yana kira ba a ɗauka dan haka ya rubuta ma ta text ya tura... *** A ranan da aka kai T J Asibiti a ranan ya isa ƙasar Chad. Wannan karan wanda ya jagorance shi ya nuna ma sa indai buƙatar sa bai biya ba to duk kuɗin da ya karɓa a wajen sa zai maida ma sa da shi. Ya ce Malamin idan ba zai iya aiki ba yana faɗawa mutum shi aikin sa ba cuta ba cutar wa. A kwana na uku su ka isa gidan Malamin wanda tundaga Ƙofar gida Muntari yai mamakin kyaun gidan. Gidan bai yi kama da irin gidajen bokaye ko malaman tsibbu da ya taɓa zuwa ba. "Anya Ɗantani nan ne gidan?" Ɗantani yai dariya ya ce "hanyar cin abinci na fa kenan Alhaji Muntari. Mutane sun fi goma na kawo wannan guri" Ɗantani dillalin Bokaye ne da Malaman Tsibbu, a yadda ya ke ya san address ɗin Bokaye a ciki da wajen Nigeria sun fi talatin. Aikin sa shine kai mutane ko haɗa mutane da Bokaye musamman ma manyan ma su kuɗi, 'yan siyasa ko 'yan kasuwa ko ma manyan mata ma su son hana kishiya zaman lafiya. Kafin ku je za ka biya shi idan buƙatar ka ta biya za ka balancing kuɗin ka. Bai faye bin mutane har wajen ba, yawanci kwatance ya ke yi ko yanzu da waya ta fara yawaita a hannun mutane sai ya ba da lambar wayar Boka. Alhaji Muntari ya ce indai ba ƙafarsa ƙafar Ɗantani ba ba zai je ba tunda anjima ana cin kuɗin sa a banza buƙatar sa ba ta biya. Shi kuwa Ɗantani kuɗin da Muntarin yai alƙawarin ba shi ne ya sa dole ya biyo shi su ka je ƙasar Chad ɗin. Shi kan sa ya san wajen wannan ne gangaran wanda indai buƙatar Muntari ba ta biya ba to ya haƙura kawai ba inda za a iya yi ma sa aikin. Sai da su ka fi awa ɗaya suna jira kafin aka mu su iso zuwa ciki wajen Malam ɗin. Ɗakine mai faɗi wanda babu floor sai yashi da aka zuba a ƙasa. A tsakiyar ɗakin Mutumin ke zaune a kan fatan Damisa. Idan ka duba bangon ɗakin an cikeshi da rubutun Larabci wanda yawanci ayoyin ƙur'ani ne da aka jirkice su. Mutumin dai gashi nan baƙi ne wuluk kuma yana sanye da baƙin kaya babban riga da baƙin rawani, yana riƙe da baƙin carbi irin mai dubu ba ɗayan nan yana ja. Hannu yai wa Ɗantani akan ya tafi dan haka Muntari ne kawai ya zauna a gaban sa yana zazzare ido saboda yadda kan sa ke sarawa tunda su ka shiga ɗakin. A yashin da ke gaban sa Malamin yai wasu rubutu yanayi yana girgiza kai. Ya ɗago ya kalli Muntari wanda tunda ya zauna ya kasa magana. Ji yai kamar an riƙe bakin ga wani irin sanyi-sanyi zafi-zafi da ya ke ratsa shi tun shigowar sa. "Mutu ka raba" Malamin ya furta yana kallon Muntari. Ganin jajayen idon Malamin ya sake birkitashi, baki na rawa ya ce "ban gane ba?" "Ka zo domin kana son auren matar Yayan ka, auren su kuma mutu ka raba ne" Muntari zai yi magana Malamin ya dakatar da shi ya ce "duk inda za ka je, duk inda za ka shiga aka gaya ma ka saɓanin wannan to ƙarya ce aka ma ka za a ci kuɗin ka ne ka rubuta ka ajiye. Gaskiyar ɗaya ce Madamar Yayan ka na raye, Maryam ba ta da wani miji sai shi" Muntari ya zaro ido waje na farko saboda mamakin kalaman Malamin na biyu kuma yadda aka yi ya san sunan Maryam ba tareda ya faɗa ma sa ba. Abinda ma ya kawoshi bai faɗa ba aka sanar da shi. Lallai kam Malamin mai gaskiya ne. "To yanzu shikenan ba yadda za ayi ka raba auren?" Malamin ya kwashe da dariya marar daɗin ji sannan ya ce "idan kashe shi za ka yi inaga ba sai na ma ka komai ba domin akwai hanyoyin kashe mutum cikin sauƙi wanda na san ka sani. Amma Yayan ka na raye ka ce za ka aureta wannan idan ya faru ka zo zan yi ma ka sujjjada saboda na yi ma ka ƙarya" Zuciyar Muntari ta cunkushe duk da tsanar da ya ke wa Tijjani baya tunanin zai iya kashe shi. Wani tunani ne.ya faɗo ma sa yai saurin cewa. "Idan baya nan aka neme shi aka rasa ka ga dole ta haƙura da auren ta auri wani. Na san zuwa shekara ɗaya biyu za ta gaji da jira ta nemi yin wani auren ni kuma sai na aureta a lokacin ka ga dai ba a kashe shi ba kuma bai saketa ba a kotu aka raba auren ni kuma sai na aureta" Malamin ya zuba ma sa ido yana kallon tsantsan hassada da ke tattare da Muntari, son da ya ke yiwa Maryam bai kai ya kasa haƙura da ita iya shekarun nan ba. Yana da yaƙinin da Maryam wani ta aura ba Yayan sa ba da tuni ya haƙura da ita amma Hassada ya ke da ɗanuwan sa. Hassada ce ta cika ma sa zuciya shiyasa ya kasa haƙura da Maryam saboda hassadar Yayan sa ya samu macen da ya ke so. Shima ɗin Hassada ce ta kawo shi abinda ya ke yi yau. Mahaifin sa babban Malamin zaure ne a ƙasar Senegal, yana da tarin Ilimi ga ɗalibai da su ke zuwa ɗaukan karatu a wajen sa ba adadi. Ana zuwa daga ƙasashe daban-daban ɗaukan Ilimi wajen sa. Mahaifin shi shi ɗaya ya haifa namiji dan sai da ya haifi 'ya'ya mata goma sha uku kafin aka haifeshi. Sunan sa Yusha'u kuma sun taso da ɗan ƙanin Baban sa Lukman, kan su kusan ɗaya. Lukman maraya ne iyayen sa duka biyu sun rasu. Tun suna yara ya ke hassada da Lukman saboda hazaƙarsa da ƙoƙarinsa. Shi da ya ke ɗan malam da wuya ya ke riƙe karatu amma Lukman Allah ya ma sa kaifin basira. Dayawa mutane kan ɗauka Lukman ne ɗan Malam na asali ba Yusha'u ba. A shekarun sa ishirin da biyu ya rabu da gida ya rabu da iyayen sa saboda hassadar da ya ke wa Lukman. Malam ya tsufa yana yawan jinya hakan ya sa ya fara tura Lukman jan mutane sallah tareda bawa mutane karatu da kuma fatawa. Lukman yayi karatun da shi kan sa Malam ya san ya samu Magaji idan baya nan. Shi Yusha'u ko ƙur'ani bai sauke ba balle ya iya fassara balle balle balle. Wajen wani malamin da ya je ne aka ba shi laƙanin karatu da ta farin jini saboda yana son kere Lukman ashe laƙanin Aljanu da Shaiɗanu ne. Ya je yai ta kiran sunayen Aljanu har ya kusa zaucewa kafin daga baya su ka saita shi a harkan tsubbu. Shekaru Arba'in kenan yana wannan harka shi kuwa Lukman yai shekaru talatin da takwas yana ibada yana koyar da mutane har Allah ya ɗau ran sa. Duk hassadar sa gareshi sai da abinda Allah ya rubuta ma sa ya tabbata. Har yau idan aka kira sunan ɗan uwan sa Lukman sai dai ka ji ana Allah ya ma sa rahama saboda kyakyawar rayuwa da yai. "Indai Hassada ce za ta kai ka ga halaka" abinda Malam Yusha'u ya faɗa kenan a zuciyar sa... *Dam Dam Dam....free pages are ending soon domin an kusa fara shiga ainihin labarin* *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: 21 Bismillahir Rahmanir Rahim Lokacin da ta fito daga Arrivals hango wata ma ta tayi tsaye ta ɗaga wani takarda wanda aka rubuta *Welcome Mrs Zainab Tijjani Abubakar* Har za ta ƙarisa wajen matar sai kuma ta fasa dan sunan ta ba Zainab ba ne, duk da zuciyarta ya ba ta ita matar ta zo ɗauka, tunda an gaya ma ta da ta sauka akwai wanda zai zo ya ɗauketa zuwa gida. Ta tsaya gefe tana tura baki. Chan Matar ta hango Zaytoonah tunda dama ta ga hoton ta dan haka ta fara ɗaga ma ta hannu tana kiran ta Zainab Zainab. Zaytoonah ta ji sarai amma ta share tunda sunan ta ba Zainab ba ne, ta ma kauda kai daga kallon wajen da Matar ta ke. "Ba ke ce Zainab Tijjani ba?" Matar ta tambaya bayan ta ƙariso gaban ta. Zaytoonah ta ce "ke ma kin faɗa ai" "Sorry ba ke ce wannan ba" ta yi maganar tana nuna ma ta screen ɗin wayarta. Ta kalli hoton ta ce "kamar ba" Matar ta yi murmushi ta ce "afuwan Amaryar mu, Hajiya ce ta ce min sunan ki Zainab" "Zaytoonah Tijjani Abubakar" ta faɗa with pride Matar ta miƙa ma ta hannu ta ce "Muhsina Aliyu Ilyas, cousin ɗin mijin ki" Musabaha su ka yi su na murmushi. Duk da Matar ta girmeta amman alamu sun nuna ba ta da girman kai dan a ƙalla za ta kai shekara ishirin da biyu zuwa da uku... Muhsina ke driving ɗin su tana yi tana yiwa Zaytoonah labarin gidan su da kuma Zuhayr. Zaytoonah kam na ta kunne, dan Muhsina akwai labari ba ta ma bari ka sa baki, daga ta kamo nan sai ta sake ta kama wani labarin daban. A wani ƙaton gida su ka tsaya inda Muhsina ta ce ma ta sun iso gida. Tare su ka shiga cikin gidan Muhsina na riƙe da hannun ta. Sama su ka haura inda Muhsina ta shigar da ita ɗakin ta. "Hajiya ta ce a sa ki a first room to amma na ga tunda kwana biyu za ki yi gara ki zauna da ni ayi family bonding. Ko ba haka ba?" Zaytoonah ta yi murmushi. "Yanzu zan bar ki ki shiga bathroom ki yi wanka ki shirya sai ki sauko ki ci abinci. Then we'll talk" Lokacin da ta fito daga wanka an shigo ma ta da akwatin ta dan haka ciki ta ɗau kaya ta saka. Lokacin da ta ke rufe akwatin Muhsina ta shigo ta ja ta su ka sauko ƙasa. Kai tsaye wajen dining su ka je wanda an jera abinci kala-kala a kai. Kowa da kan sa yai serving abincin su ka zauna su na ci. "Hajiya za ta iya dawowa nan da 1 hour haka, Firdaus ƙila sai dare ki gan ta, Abba ya je Japan" Sai da ta kurɓi juice kafin ta cigaba "Saifullah yana Stanford babban Yayan mu Ishaƙ kuma yana Abuja shi da iyalin sa" Zaytoonah ta ce "OK" Haka dai su ka gama cin abincin ana hira kaman sun san juna da jimawa. Da yamma ta fito ta gaida Hajiya Maimunah wanda yanayin yadda ta amsa ma ta ya sa ta gane matar ba ta son ta. Da dare su ka haɗu su huɗu a dinning za su ci abinci. Firdausi sai kallon Zaytoonah ta ke tana dariya ƙasa-ƙasa. Tun da ta dawo ta leƙa ɗakin Muhsina ta ga Zaytoonah ta koma ɗaki tana dariya. Ashe ma tafi yadda su ka gan ta a hoto ƙiba. Zaytoonah na lura da ita amma ta yi shiru kar ace daga zuwa ta fara faɗa. "Ikon Allah! Ko ina Zuhayr zai kai wannan buhun oho?" "Inda Abba ya kai Hajiya" ta faɗa tana kallon Firdausin. "I beg your pardon?" Hajiya Maimunah ta faɗa. "Neman inda za a kaini ta ke yi shine na ce wajen da Abba ya kai ki nan Zuhayr zai kai ni. Idan tana son ƙarin bayani ki fayyace ma ta dalla-dalla dan na san kin gane mi na ke nufi" "Hajiya ki ji min wannan fat girl ɗin fa..." Fork ɗin da ke hannun Zaytoonah ta datsa akan plate ɗin da Firdausi ke cin abinci ta ce "kar ki sake kirana Fat girl, Zaytoonah aka yanka min" Ba Firdausin ba har Hajiyar sai da ta tsorata. Firdausi ta tashi ta bar wajen bayan ta ja dogon tsaki. Hajiya kuwa ta yi ƙarfin halin cewa " Zainab ki ke ko waye. Ki kiyaye reni a gidan nan dan Muhsina da Firdausi ba sa'annin ki ba ne" Zaytoonah ta ce "ki ma ta faɗa ta iya bakin ta". Da za su kwanta Muhsina ta ce wa Zaytoonah ta yi haƙuri abinda Firdausi ta ce ma ta a wajen cin abinci. Wai kishi ta ke yi tunda ta jima tana son Zuhayr amma ba ta samu kan sa ba. Zaytoonah ta ce chan ta matse ma ta. Kwana biyun da ta yi bayan nan Muhsina kaɗai ke shiga harkarta. Firdausi kam dama tun rana magana ba ta kuma haɗa su ba. Ita kuwa Hajiya tsakanin su gaisuwa. Da wayar Muhsina ta kira Mommy ta sanar da ita ta isa gidan Uncle ɗin Zuhayr saura ta wuce Las Vegas gidan Zuhayr ranan Monday. Mommy ta kuma yi ma ta nasiha sosai akan zaman haƙuri da kuma yawan addu'a, sun gaisa da ƙannen ta kafin ta kashe wayar. Muhsina ce ta kai ta airport inda ta shiga jirgin da zai kai ta Carson city babban birnin jahar Nevada. Muhsina ta ce Zuhayr zai zo ya ɗauketa a airport ko kuma idan bai samu dama ba zai iya tura Driver, akan haka su ka rabu da Muhsina wanda ta ji daɗin zama da ita sosai. Very simple lady, ba ta da girman kai ko kaɗan. Amma ƙanwarta Firdausi kam sai hamdala. Wani bature ne da ya kira sunan sa da Benedict ya zo ya tareta a airport. Tana tunanin mota za su hau sai ta ga ya jagoranceta zuwa inda su ka shiga private Helicopter da aka rubuta Z M I a jiki wanda ya tashi da su zuwa garin Las Vegas. A gaban wani ƙaton mansion su ka sauka. Ita kan har su ka iso jikinta rawa ya ke yi, tsoronta kar fa kasheta za aje ayi. Dan tunanin da ta yi shine Zuhayr Mafia Boss ne. Ga uwa uba wannan Ben ɗin fiskarsa a murtuke duk tambayoyin da ta ma sa kafin su shiga helicopter ɗin cewa yai za ta san komai idan su ka isa gida. Addu'a ta ke a ranta har su ka shiga gidan inda su ka ci karo da wani katafaren falo. Ta ja ta tsaya ganin Ben na haurawa sama. Sai da yai nisa a hawa stairs ɗin ya juyo ya ga har lokacin tana ƙasa. Ya ma ta alamar ta hauro amma ta maƙe kafaɗa. Dan haka dole ya sauko ya dawo wajenta. "Ɗakin ki zan nuna miki" ya faɗa da American accent ɗin shi. "Ni dai ka kiramin Zuhayr" Ya ɗan kalleta briefly kafin ya ce " baya nan sai gobe zai dawo, ki biyoni" Ta yi jihadi ta bi bayan sa. Wani ɗaki ya buɗe ma ta ya ce ɗakinta kenan kuma wai bayan ɗakin bai yadda ta shiga wani ɗaki a saman ba amma za ta iya shiga ko'ina a ƙasa. Ya haɗa da cewa akwai cook ɗin su a gidan za ta iya kiran sa ta ba shi order na abinda za ta ci ko kuma ta sauko ta je ta gaya ma sa da kan ta. Ta gyaɗa ma sa kai sannan ta yi Bismillah ta shiga ɗakin. Ɗakine ƙato dan za ta iya cewa ya girmi falon gidan su. Ba wani tarkace a ciki da ya wuce makeken gado, closet, da dressing mirror sai kuma wata ƙofa da ta gani da ta ke tunanin banɗaki ne. "Allah gani gareka, anya zan iya zama a nan? karfa Zuhayr ya sa a kasheni ya kira gida ya ce na mutu" ta yi saurin kawar da zancen ta hanyar buɗe banɗaki ta shiga, bayan ta gama ƙarewa banɗakin kallo kafin ta tsaya ta yi wanka. Muhsina ta gaya ma ta lokutan sallah dan haka ta san ta missing sallolin Magariba, Isha, Asuba da kuma Azahar, dan haka tana sa kaya sallah ta yi duk da ba ta da tabbacin inda Alkibla ɗin garin ya ke, ta dai bi instint ɗin ta ne sai ta shimfiɗa sallayar da ta zo da shi daga gida ta hau rama sallolin da ake binta. Bayan ta gama ta sauko ƙasa dan yunwa ta ke ji rabon ta da abinci mai kyau tun kafin ta bar gidan su Muhsina. A airport ɗin Carson City ta sayi soft drink da donut guda uku ta ci shikenan kuma. Bayan ta sauko ta fara bin falon da kallo, tsarin falon ya mata kyau sosai. Wani ƙaton hoto ta tsaya kallo wanda ta ga wani yaro akan doki, yaron ba zai wuce shekara goma ba, gefensa wata baturiya tana dariya ɗaya gefen kuma da ka gani ka san ba bature ba ne saboda baƙin fata ne, sai dai ba baƙi sosai ba. Ɗaya hoton kuma waɗancan mata da mijin ne tsaye macen tana ɗauke da jaririn yaro a hannunta. A hoto na gaba ne ta ƙurawa ido, Zuhayr ne dan ta gane shi da hoton sa da aka nuna ma ta, sai dai a wannan hoton bai kai wancan hoton da ta gani girma ba dan ba zai wuce 21yrs ba haka. Shima hoton akan doki ya ɗauka. Alamun mutum ta ji a bayanta dan haka ta yi saurin juyowa. Su ka yi ido huɗu da Ben wanda idon sa ya rikiɗa ya koma ja. "Mi ki ke buƙata?" Ya tambaya da kakkausan murya. "Ka ce zan iya shiga ko'ina a ƙasa shine na zo zan duba Cook ɗin dan yunwa na ke ji" Da hannun yai ma ta nuni zuwa hanyar kitchen. Tana barin wajen Ben ya ɗauke hoton Zuhayr da ta ke gani ya haura sama da shi. Ƙaton kitchen ne wanda za ka ɗauka kitchen ɗin wani babban restaurant ɗin ne. Chef ɗin da ta gani wani tsoho ne yana girki a kitchen ɗin, dan aƙalla zai yi shekara sittin haka. "Good evening Sir" ta gaishe shi tana murmushi. Ya juyo ya amsa ma ta tareda tambayarta ita ce amaryar Oga? Ta ce ma sa eh. Akwai kitchen dining a wajen mai ɗauke da kujera huɗu dan haka ta zauna Chef Green ya serving ɗin ta ta hau cin abinci. Grilled chicken ne sai spaghetti da kuma salad a gefe, sai orange juice da ya haɗa. Yadda kazar ke tiriri saboda a lokacin aka fito da ita daga oven ya sa yawun Zaytoonah ya tsinke. Chef Green ya yanka ma ta chinya ɗaya da haƙarƙari ya ajiye ma ta a plate. Zaytoonah ta ce ai za ta iya cinye kazar duka. Chef Green ya zaro ido dan kazar Babba ce. Ta zauna tana ci tana ma sa tambayoyi gameda gidan har ta cinye rabin kaza ta ji ta ƙoshi. Duk da haka sai da Chef Green yai mamakin ta... Pyjamas ta saka riga da wando ta kwanta bayan ta yi sallar Isha sai bacci. Hasken rana da ya fara ratsa ɗakin ne ya farkar da ita daga bacci. Ta tashi ta shiga banɗaki ta yi brush sannan ta yi Alwala ta zo ta yi sallar Asuba tana cikin azkar ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa dan haka ta miƙe da sauri dan ta ɗauka Zuhayr ne. Tana buɗe ƙofa ta ga Ben ne. "Ki shirya ki fito za a kaiki makaranta" "Ina Zuhayr?" Yai shiru yana kallonta. Ta sake cewa "ba inda zan je sai na ga Zuhayr. Ni ban yadda da kai ba" Juyawa yai ya tafi ba tareda ya ce komai ba... Haka ranan ta wuni ba ta sake ganin kowa ba. Girkin rana da aka yi tana tsaye tana ganin yadda Chef ɗin kai komai, yana yi yana ma ta bayanin abubuwan da ya ke amfani da shi. Abu ɗaya ta gane kuma ta tabbatar a wajen Chef Green ɗin. Wato kafin zuwanta gidan mutum biyu ke kwana a katafaren gidan nan. Zuhayr da Ben. Shi Chef green ba kwana ya ke yi ba, zuwa ya ke da safe ya tafi da dare. Akwai wata mai aiki Mercy da itama ke zuwa duk safiya tana gyara gidan sai ta tafi. A inda ta yi sallar Maghrib bacci ya fara ɗaukanta. Sai dai ƙaran saukan Helicopter ya tada ta. Ta yi saurin fitowa daga ɗakin bayan ta leƙa ta window ta ga Zuhayr ya fito daga cikin helicopter ɗin. Tana tsaye a falon har su ka shigo shi da Ben. Kallon sa ta ke yi tana jin bugun ƙirjinta na ƙaruwa. Hannu ya miƙa ma ta yana faɗin "Zaytoon right" Hannun ta kalla sannan ta kalli fiskar sa ta ce "Yes" ba tareda ta yi musabaha da hannun sa ba. Maida hannun sa yai cikin Aljihu ya ce "welcome to Las Vegas" yana faɗin haka ya haura sama tareda Ben. Bayan ya tafi tukunna ta yi sauke numfashi tana dafe ƙirjinta. "Ya Allah wannan mutum haka" sai kuma ta ɗan mari fiskarta tace "ji yadda kika basar da shi yana miƙa miki hannu kin ƙi kama hannun. Stupid Zaytoonah" Komawa ta yi ɗakinta tana karanto yanayin fiskarsa da muryarsa a ranta. Ba su sake haɗuwa ba sai washegari da ta fito yin breakfast saboda yunwa ne ya tasheta. A dinning ta ke ci dan Chef Green ya riga ya jera komai a wajen. Shi da Ben su ka sauko dukkan su sanye da baƙaƙen suit. Ben na riƙe da wani briefcase shi kuma Zuhayr wani ƙaramin paperbag ya riƙe. Ta cika bakinta da abinci amma ganin sa ya sa ta yi saurin ɗaukan coffee ta kai baki dan ya kora abincin. "Good morning Zaytoon" Ta amsa ma sa da morning. Paperbag ɗin ya ajiye a gabanta ya ce waya ne aciki, akwai layi akwai komai za ta iya saka layin ta kira 'yan gidan su. Ya ce akwa numbar sa da ta Ben a ciki idan tana buƙatar wani abu za ta iya kiran ɗaya daga cikin su. "Ben" ya faɗa yana juyawa gareshi, shi kuma ya miƙa ma sa wani kati kaman na ATM ya amsa ya miƙawa Zaytoonah. "Ga credit card nan da za ki dinga amfani da shi wajen duk buƙatun ki, ko na makaranta ko na karan kan ki. Kin iya mota?" Ta girgiza kai " akwai Driver da zai kai ki makaranta da duk inda ki ke so. Idan kin fita waje ki tambayi Mr Smith shine driver" Ya ƙara kallon Ben ya ce " what else?" Ben ya miƙa ma sa wani file ya karɓa shima ya ajiye ma ta ya ce "document ɗin ki ne na makaranta" Ta ce ta gode. Har ya juya ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya ce " fatan ba ki manta da deal ɗin mu ba?" Ta gyaɗa ma sa kai ya ce "good, have a nice day Zaytoon" Bayan ya tafi ne maganganunsa a waya su ka dawo ma ta daren wata Asabat da ya kirata. *ba ni da ra'ayin aure, ba ni da ra'ayin haɗa rayuwa da mace, amma tunda GrandPa ya riga ya haɗa komai zan baki option biyu. Na farko zan sponsoring karatun ki har ki gama, bayan nan sai na sake ki. Za mu rayu kamar 'yan uwa ba kamar mata da miji ba. Ko kuma another option, zan sake ki yanzu. Ba wanda zai sani sai mu biyu, za ki zo nan Vegas kiyi karatunki hankali kwance, idan kin gama sai ki koma gida. Wanne kika zaɓa?* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *17-Missing* Bismillahir Rahmanir Rahim T J bai tashi ba sai chan yammaci. An hana mutane shiga wajen sa saboda ba a son abun da zai tada ma sa hankali. Auwal ne kaɗai ya shiga ɗakin ya duba shi. Yana ganin sa yai murmushi mai ciwo yayinda maganganun Maryam ke sake ma sa yawo a ƙwaƙwalwarsa. Ba abinda ya tsaya ma sa irin furucin da ta yi na danasanin haɗuwa da shi da ta yi har ta fara son shi. "Daddy ya jikin?" Ya tambaya yana danne hawayen da ke shirin zubowa. "Mommyn ku tana nan?" Ya faɗa a hankali Auwal ya girgiza kai, sai ga hawaye ya silalo daga idanun TJ. "Muna tareda ita tuntuni, ta je gida ɗauko kaya ne" yai saurin faɗa saboda hawayen da ya gani a fiskar TJ. Maryam kam da su ka dame ta da kira ma kashe wayar ta yi. Ya san ƙarya ya ke yi Maryam ba ta nan, da tana nan ba abinda zai sa ta koma gida ba tareda ya farfaɗo ba. Kenan da gaske ta tsaneshi, ta tsani zama da shi. Abinda ya faɗo ma sa rai kenan. "Dan Allah ka ce Mommyn ku ta zo ina son ganin ta" Auwal ya rasa ya zai faɗa ma sa abinda ke faruwa yana tsoron kar hankalinsa ya kuma tashi. Anje gida ba ta nan, office ɗin ta ma a kulle ya ke ba chan ta je ba. Ya dai fita dan kaɗan ya rage yai kuka. Yana fitowa Iya ce ta fara tambayar sa ya jikin sa ya ce ma ta da sauƙi. Itama ɗin da ita aka yi zaman jira ta ƙi komawa gida ita yadda aka kawoshi da safe ma ta ɗauka ba zai yi rai ba. Har dare ba Maryam ba dalilin ta. Auwal kam sai cewa T J yai ciwon Sadiq ne ya tashi Maryam ɗin ke tareda shi a Asibiti saboda ana buƙatar jini. Ya dai ji ne amma ya san ƙarya ne. "Ta tafi ko?" Auwal yai saurin girgiza kai yana faɗin " Allah Daddy tana wajen Sadiq ne, zuwa gobe da safe za ta zo tunda Likita ya ce mutum ɗaya ne zai zo wajen ka"... Maryam hotel ta wuce ta kama ɗaki ta shiga ta durƙusa ƙasa tana kuka. Tun kafin ta iso hotel ɗin ake kiranta lokacin da ta karanta text ɗin da Auwal ya tura har ta karya kwana za ta je Asibitin sai ta fasa. "Akwai mahaifiyar sa akwai matar sa tareda shi za su ba shi kulawan da ya dace" abinda zuciyarta ya raya ma ta kenan ya sa ta fasa zuwa Asibitin. Sai da ta sha kukan ta sannan ta je ta yo Alwala ta yi sallah ta zauna tana yiwa T J addu'ar Allah ya bashi lafiya. Ba za ta taɓa yafewa kan ta ba idan wani abu ya sameshi. So mugun abu ne, duk yadda ta ke kurin rabuwa da T J soyayyar sa na maƙale a ran ta kuma tana jin idan ta rabu da T J tamkar ta rasa farinciki a rayuwar ta ne. Ba ta da identity idan aka cire T J a rayuwar ta. Tana son zuwa ta duba shi amma ba ta san da wani ido za ta kalle shi ba after abubuwan da ta faɗa ma sa. Ga uwa uba ba ta son haɗuwa da Iya. Chan bayan Maghrib da ta ka sa haƙuri ta kunna wayar ta ta kira numban T J ta sani wayar ba zai wuce yana hannun Auwal ba. Shi ɗin ne ya amsa wayan lokacin ma ya fito daga masallaci kenan zai koma cikin Asibiti. Tambayar sa ta yi jikin T J ya ce ma ta da sauƙi. "Mommy ina kika shiga? Daddy yana son ganin ki, yana buƙatar ki kusa da shi" Auwal ya faɗa kaman zai yi kuka. "Ka kula da shi sosai Dan Allah. Idan yana buƙatar matar sa ka kira ma sa Hajjo" daga haka ta katse kiran ta kashe wayan gaba ɗaya. Ta riga ta yi waya da Maman Fawaz akan su Zaytoonah za su kwana a wajen ta dan ta yi tafiya dan haka ba ta da matsala da yaran. Ba ta iya bacci ba saboda damuwa da ya isheta, tun 1am ta tashi ta fara sallah tana roƙawa T J lafiya. Zuwa ƙarfe 3 kuma ta ɗauko ƙur'ani ta fara tilawa. Da safe ko abinci ba ta ci ba ta wuce office zuwa lokacin ta fara jin sanyi a zuciyar ta gameda abinda ya faru. Da safe ma dai sai da T J ya tambayi Maryam amma babu ita. Dan haka ya ce Auwal ya kira ma sa Yayan sa a kai wa Goggo zai yi magana da ita. Auwal ya kira Mahaifin sa ya sanar da shi T J ke son magana da Goggo. Ba a jima ba aka kai wa Goggo wayan. Auwal ya sawa T J a kunne su ka fara magana... Duk da Goggo na fama da ciwon ƙafa hakan bai hana Goggo zuwa Zaria a ranan ba. Maganganun T J ya tada ma ta hankali musamman ma da ta ji cewa a Asibiti ya ke. *"Goggo Dan Allah ki faɗa min gaskiya, kin san da cewa Mukhtari na son Maryam kafin auren mu?"* *"Barkindo a ina ka ji wannan maganan?"* *"Ki faɗa min gaskiya Goggo dan gaskiyar ce za ta ƙwaci Mukhtari a hannuna. Ba zan taɓa yafe ma sa ƙoƙarin ketawa matata haddi da yai ba"* *"Ya subhanallahi! Barkindo wannan ba maganar waya ba ce. Zan shirya na taho yau yau ɗin nan"*... Kusan ƙarfe uku Goggo ta iso Asibitin wanda Auwal ne ya je ya taho da ita daga park, tare su ka taho da wani jikan ta mai suna Al'amin ɗan Zahra ƙanwar T J. Ganin T J kwance a gadon Asibiti ya sa jikin Goggo yai sanyi. Ta so ta ƙi faɗa ma sa gaskiya akan sai ya warke za ta faɗa mi shi komai amma ya dage shi a lokacin ya ke son sanin komai dan hankalin sa ba zai taɓa kwanciya ba. Labarin komai ta bashi tun daga Lokacin da Muntari ya fara yiwa Baffah maganar yana son auren Maryam tun tana Mary Nkirun ta har zuwa rikicin da aka yi har ta kai ga aka ɗaura auren Tijjani da Maryam a cikin Fadan Ringim. Ta haɗa da cewa tana zargin auren na su da aka yi ne ya sa Muntari barin gida har shekara shabiyar kafin ya dawo. T J ya sunkuyar da kai yana hawaye yana maimaita Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun saboda ya samu sassauci a zuciyar sa dan har lokacin bai dena jin zafi a zuciyar sa ba. "Ka yi haƙuri ka da ka ɗaga hankalin ka Dan Allah, zan samu Maryam na ba ta haƙuri" Ashe dalilin da ya sa Muntari yai wa Maryam kyautar mota lokacin saukanta kenan, saboda bai haƙura da ita ba. Wani irin so ne wannan ace mace ta auri Yayan ka shekara ishirin da ɗaya amma ka kasa haƙura da ita. Anya kuwa Muntari na da cikakken hankali ? "Itama Aishatun da ta ke ɗaurewa Muntari gindi zan je na sameta. Har yaushe za ta yi hankali ta yadda da ƙaddara ta bi duniya a sannu?" Muryan Goggo ya katse shi daga tunanin da ya ke yi. "Goggo dan Allah ki tayani roƙon Maryam, ki roƙeta ko da minti biyu ne ta zo ta duba ni dan na nemi yafiyar ta" Da wannan maganar su ka rabu da Goggo. Auwal ya raka ta gidan Muntari dan ba ta san gidan ba yayinda Al'amin ya zauna da T J. Hanne ce ta nunawa Goggo ɗakin Iya wacce tunda ta dawo daga Asibiti ta shige ɗaki ko abincin rana ba ta ci ba. Da safe da ta shiga duba T J kalma ɗaya bai ma ta ba lokacin da ta ke ma sa ya jiki sai hawaye da ya ke yi. Sai dai ta ƙi gaskiya amma duk cikin 'ya'yan ta Tijjani ke ma ta biyayya ɗari bisa ɗari kuma ba ƙaramin darajata ya ke yi ba. Duk yadda ta ke ja baya da shi baya fushi. Sai da Goggo ta zauna a kujeran da ke ɗakin sannan ta kalli Iya da ke zaune bakin gado ta ce " a matsayina na 'yar uwar ki zan ba ki shawara Aishatu. Kin san dai Baffah ya rasu ba maganar shekara ɗaya ko biyu ba, kuma duk inda ya ke ina da yaƙinin yana cikin rahamar Ubangiji saboda kyawawan halayen sa da ya rayu da su har mutuwar sa. Aishatu ina miki tuni da cewa inda Baffah ya je ko ba daɗe ko ba juma za mu je muma. Yadda ya ke kwance ƙarƙashin ƙasa muma haka za a rufe mu da ƙasa mu je mu amshi sakamakon ayyukan mu na duniya. Ki shuka alkhairi Aishatu, ki shuka Alkhairi, duniya ba matabbata ba ce. Kuma ina so ki sani yadda Allah ya ce 'ya'yan da mu ka haifa su mana biyayya haka muma ya ce mana 'ya'yan mu amana ne a garemu. Aishatu Allah zai tambayeki amanar 'ya'yan ki, banbanta Muntari da Tijjani da ki ke yi shi ya kawo su ga wannan hali yanzu. Tun farko kin riga kin dasawa Muntari hassadar ɗan uwan sa kuma har yanzu shi ke bibiyar sa. Ki kula da amanar Tijjani da ke hannun ki, dan Allah zai tambayeki, tun yana yaro kike tsangwamar sa saboda ni yanzu kuma ya girma ma ba ki bar shi ba. Ni da Maryam ba mu muka haifi Tijjani ba ke ce kika haifi kayan ki, dan haka duk abinda ya sameshi dalilin mugun halinki ki kuka da kan ki. Zan ƙara jaddada mi ki,Tijjani amana ne a gareki kuma Allah zai tambayeki game da shi. Ita kuma Maryam duk abinda ki ka yi ma ta Allah zai saka ma ta, ina ba ki shawaran ki nemi yafiyar ta ko kuma ku haɗu a gaban Sarkin da ba ya zalinci" Da wannan ta miƙe ta fita daga ɗakin ta bar Iya zaune jiki yayi laƙwas. Maganganun Goggo sun shigeta sosai... Lokacin da Auwal ya kira Maryam ya ci sa'a wayan ta a kunne, ba ta ɗauka a kiran farko ba sai a na biyu tana sallama kuwa Goggo ta amsa. "Maryam ki zo gidan ki ina jiran ki" "Goggo ki yi haƙuri bazan tashi daga office da wuri ba" "Ba na son musu Maryam, ki zo gida kawai" Ba yadda ta iya dole ta amince za ta zo ɗin. Goggo uwa ce a gareta, ita ce matar da ta ke gani ta manta cewa uwar da ta haifeta ba ta raye. Kusan ƙarfe biyar sai ga ta a gidan. Su Zaytoonah da Salman na tareda Goggo dan Auwal ya koma Asibiti. Zaytoonah da Salman ba su san Daddyn su ba lafiya ba dan Auwal ce mu su yai da Daddy da Mommy sun yi tafiya. Shi ba yaro ba ne, ya fahimci kafin rashin lafiyar T J sun samu matsala da Maryam, ga kuma conversation ɗin Goggo da Tijjani da ya saurara ɗazu da safe. Da sallama ta shigo yaran su ka yi kanta da gudu suna ma ta oyoyo. Har da tambayarta ina tsaraban su. A ɗakin Maryam su ka yada zango saboda su samu damar tattaunawa da kyau. "Maryam Dan Allah ki yi haƙuri. Shehu ya gaya min komai kuma na sani ba a miki adalci ba. Amma Maryam bai kai kiyi watsi da mijinki a lokacin da ya fi buƙatar ki ba." "Goggo na haƙura da shi, na gaji da matsalar mahaifiyar sa, kowa yai hanyar sa kawai" ta faɗa tana goge hawaye "Tun da Shehu ya kawo ki wajena ya damƙa mini amanar ki na ɗauke ki a matsayin ɗiyar da na haifa. A matsayina na uwa ina ba ki haƙuri bisa laifuffukan da aka miki tun auren ki da Tijjani har yau. Ba sai na gaya miki Tijjani na son ki ba kema kin fini sanin hakan. Ina so ki san wani abu guda, rabuwar ki da Tijjani babu alkhairi a ciki. Ba za ki samu kwanciyar hankaliba kazalika shima ba zai samu ba. Kin dai san yana da hawan jini kuma na san kin san yanzu ma yana kwance a asibiti, saboda ke ne Maryam saboda ke" "Goggo..." ta faɗa cikin muryan kuka "Ka da ki sa baƙin ciki ya kashe Tijjani, ki koma gareshi ku cigaba da rufawa kan ku asiri. Shekaru ɗaiɗaiɗai har ishirin ba wasa ba ne, ta ina za ki ma fara raba kan 'ya'yan ki? Wa ki ke da shi da ya fi Tijjani? Waye zai so ki fiye da Tijjani?. Kiyi haƙuri ki cigaba da haƙuri. Ilimi da kyakykyawar zuciya da Tijjani ke da shi shiyasa ya ke takatsantsan da maganar mahaifiyar sa. Ki godewa Allah da ya ba ki miji irin sa, ki cigaba da haƙuri da shi har su rabu da mahaifiyar sa lafiya" Goggo na magana Maryam na kuka. Duk abinda ta faɗa gaskiya ne. Ba ta da wanda ya fi Tijjani amma Iya Iya Iya. Anya za ta iya cigaba da haƙuri da baƙin cikin Iya? Haka dai Goggo ta cigaba da yi ma ta nasiha har ta haƙura da zancen rabuwa da za su yi. Banɗaki ta shiga ta yi wanka ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga shadda kalar blue wanda ya sha aiki. Ta yafa farin gyale wanda ya ke da duwatsu blue a jiki. Ta ɗan yiwa fiskarta kwalliya kaɗan har da sa janbaki pink wanda ya amsheta sosai saboda ita fara ce. Yaran ta ɗauka su ka wuce Asibiti Goggo ba ta bi su ba. A hanya ta faɗa mu su Daddy za su je su gaisar ba shi da lafiya. Zaytoonah har da sha alwashin za ta yiwa Auwal rashin mutunci da ya mu su ƙarya. Sun zo shiga Asibitin su ka hango Hajjo da Auwal suna fitowa da alama Auwal ɗin ke son tare ma ta abin hawa. Bayan sun fito daga mota su ka jira har Auwal ya zo ya same su sannan ya mu su jagora zuwa ɗakin da aka kwantar da T J, suna tafiya Zaytoonah ta ɗira ma sa dundu a baya tana faɗin ladan ƙaryan da ya mu su, za ta ma ƙara ma sa wani dundun Maryam ta hana ta. Sun samu yayi bacci amma hayaniyar su Zaytoonah ya tada shi. Yana ƙyalla ido ya ga Maryam ya ji wani farin ciki ya mamayeshi. Yaran duk su ka yanyameshi da shagwaɓa Zaytoonah har da kukan sakalci. Maryam dai zama ta yi a kujera tana bin su da kallo cike da tausayin mijin na ta har lokacin akwai nasal canula a hancin sa wanda ke daidaita numfashin sa maganar sa ma a hankali a hankali ya ke fita. Shima ɗin lokaci zuwa lokaci yana juyawa ya kalleta, idan su ka haɗa ido sai yai saurin kau da kai. Bayan maghrib Auwal ya tattari yaran zai mai da su gida su ka ƙi Zaytoonah har da kuka wai a wajen Daddyn ta za ta kwana. Maryam ta zare ma ta ido dole ta bi bayan Salman su ka tafi. Auwal ne zai kai su da Motar Maryam dan shima ba laifi ya iya, a ƙiriniya ya koyi mota a wajen wani abokinsa da ke sato motan Babansa yana fitowa da shi idan baya nan. Ɗakin yai tsit bayan fitan yaran. Kusan minti biyu ya wuce kafin TJ ya ɗago ido ya kalli Maryam wacce itama shi ta ke kallo ya ce " ki yafe min, ban san da maganar Mukhtari ba, ban san komai ba. Ki yi haƙuri na kasa ba ki farincikin da na miki alkawari a farkon auren mu, ki yafe min" Tasowa ta yi a hankali ta rungumeshi. Tana tsaye yana zaune ya kwantar da kan sa a cikinta ya ƙanƙameta. "Na yafe ma ka" "Da gaske Maryam?" Ta gyaɗa ma sa kai. Cikin i'ii'ina ya ce " kin janye maganar rabuwa da ni?" "Ina da wajen da zan je ne idan na rabu da kai?" "Na gode Maryam" ya faɗa sai ga hawaye na zubo ma sa. Maimakon ta yi magana sai ta manna ma sa light kiss a bakin sa. "Ka ga ka kwantar da hankalin ka. Likita ya ce ban da kuka, ban da sa damuwa a rai" "Ke ce likita na Maryam and you know it. Tunda kika shigo ɗakin nan duk ciwon da na ke ji ya yi sauƙi" "Allah ya baka lafiya" "Janbakin ya mi ki kyau idan da hali a bani na shanye" "Naughty Man" ta faɗa tana murmushi kafin ta rankwafo ta haɗe bakin su... Ita ta kwana da shi su ka wuni suna nunawa juna kulawa. Duk yadda ya so su tattauna abin da ya faru tsakaninta da Muntari ta ƙi ta ce sai an sallameshi tukunna. Ta yi hakanne dan ba ta so ya ji abinda zai ƙara ɗaga ciwon sa. Washegari da safe da likita ya zo ya dubashi aka cire ma sa nasal canula ya kuma yiwa Maryam bayanin yadda za a dinga kiyayewa da duk abinda zai ɗaga ma sa hankali. Sun ce idan sun ƙara ganin yanayin yadda ya samu sauƙin ciwon ƙirji za su sallameshi dan har yanzu any shock ko wani extreme excitement zai iya sa shi a risk ɗin wani heart attack ɗin. Shi kuwa T J tunda ya farka dama ya lazimci addu'o'in saboda ya samu sauƙin raɗaɗi da zafin da ya ke ji a zuciyar sa. Ba ta so tafiya office ba dan yadda T J ke narke ma ta hadda cewa ta ma sa rawan Atilogwu ta yi dariya ta ce za ta ma sa idan ya koma gida. Su Zaytoonah ma kafin su je makaranta sai da su ka zo su ka gaida mahaifin su. Ƙarfe tara na safe Hajjo ta zo ta karɓeta hakan ya sa Maryam ta koma gida ta shirya ta wuce office. Ƙarfe shabiyu kuwa ta koma gida ta yi wanka ta shiga haɗa abincin da za ta kaiwa T J a asibiti. Tana cikin juya abincin a food warmer wayarta yai ringing. Numbar T J ne dan haka da sauri ta ɗauka. Ɗazu tana office ya kirata sun fi minti shabiyar su na hira inda ya ke ƙara jaddada ma ta soyayyar shi gareta. "Hello Mommy ba a ga Daddy ba. Daddy ya ɓata" Auwal ya faɗa cikin kuka. "Ban gane ba a ga Daddy ba, ina ya je?" Kukan Hajjo da ta ke ji ne ya sa jikinta ya hau ɓari ta yi saurin kashe wayar ta je ta rarumi gyalenta ta fita da sauri. Tare za su tafi asibitin da Goggo amma ko ta kan ta ba ta bi ba... Zuwanta Asibitin ta tarar da mummunan labari. Lokacin da T J ya gama waya da Maryam ya kwanta bacci yana bacci Hajjo da ta je ɗauko ma sa kaya ta shigo. Ganin yana bacci ya sa itama ta kwanta a kan tabarma a ƙasa a haka Auwal ya shigo ya sameta, ganin T J ba ya kan gado ya sa ya tashi Hajjo yana tambayarta ina T J tunda ya leƙa banɗaki baya nan. Wasa- wasa sai ga shi sun duba ko ina a asibitin babu T J ba dalilin sa. Maryam zama ta yi daɓas a ƙasa tana hawaye lokacin da wata mai shara ta ce ta ga lokacin da T J ya fita a ɗakin sa har tana ma sa ya jiki amma ko juyowa bai yi ba balle ya kulata. Mutane biyu ma su ka kuma jaddada cewa sun ga fitan T J daga asibitin. Da farko Maryam ta ɗauka Muntari zai je nema saboda abinda ya faru amma ai ya san Muntari baya gari. Ranan dai tashin hankalin da Maryam ta shiga ba a magana. Kuka ma kasa yi ta yi, bacci kam kasa yi ta yi dan duk inda ake tunanin T J zai je an nema ba a same shi ba ba akuma samu wanda ya gan shi ba bayan fitan sa daga asibitin. Washegari da safe aka je police station aka ba da report na ɓatan T J. Wasa-wasa kwana biyu su ka shige ba a ga T J ba ba a san inda ya je ba. A rana na uku Muntari ya dawo gida ya tarar da ɓatan T J yadda ya ke salati yana salallami ka ɗauka bai san mi ke faruwa ba, ka ɗauka ya fi kowa damuwa da ɓatan T J. Har Kaduna ya raka Maryam aka kai cigiya gidan talabijin da gidan radio. Tun ana cewa kwanan sa biyu da ba a gan shi ba har aka fara irga sati ɗaya sati biyu sati uku kenan yanzu. Zuwa lokacin Maryam tamkar mahaukaciya ta koma, ita ne nan itane chan ko bacci ba ta iya yi. Koyaushe ɗaurawa kan ta laifi ta ke yi a ɓatan T J musamman da Likitan T J ya ce ƙila damuwa ce ta sa shi samun taɓin hankali... *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Free page* *18-Baby Boy* Bismillahir Rahmanir Rahim A cikin wannan yanayi na tashin hankali ne ciwon Sadiq ya tash, Hajjo abu ya zama ma ta goma da ishirin. Lokacin da Auwal ya zo ya gayawa Maryam haka ta ɗebi jiki ta je Asibitin. Itama na fama da Zaytoonah da tun da ta ji labarin Baban su ta ke cikin halin yau lafiya gobe babu. Ta yi sati ba ta zuwa makaranta, a sati na biyu da Maryam ta takurata ta je kuwa kullum da kuka ta ke zuwa da shi ta ke dawowa. Sai ga shi wai ƙanin ta Salman ne ke zama ya bata haƙuri idan tana kuka dan Maryam ta fita harkanta, itama fama ta ke da kanta, tun ɓatan T J za ta iya cewa ba ta samu nitsuwa ba, ba ta da lafiya amma babu halin nunawa dan abinda ke damunta ya fi ƙarfinta. Wannan karan Auwal ne ya bayar da jini aka sawa Sadiq. Maryam na zaune kusa da Hajjo da ke ta matsar ƙwalla sai ga kiran Muntari. Hajjo ya ci ace ta saba da ciwon Sadiq amma tsoron rasashi ta ke yi kamar yadda ta rasa Sadiq ɗin ta na farko. Shi bai ma yi wahalar da wannan ke yi ba, wannan sai ya ja lokaci kafin ciwon ya tashi amma idan ya tashi kam hankalin kowa sai ya tashi ga uwa uba kuɗi da ake kashewa wajen jinyar sa. Maryam na ɗaga wayan ya tambayeta tana ina dan dawowar sa kenan daga Abuja inda ya kai cigiya abinda ya faɗa mu su kenan amma maganar gaskiya shine Lagos ya je ya dubo wasu kayansa da aka ce sun iso. Ta sanar da shi su na Asibiti Sadiq ba lafiya. Ya ce gashi nan zuwa. Minti Talatin da biyar sai gashi ya iso ya kuma kiranta yana tambayar ina ne ɗakin ta ce bari ta fito ta shigo da shi dan bayan ita da Hajjo ba kowa a ɗakin ba ta kuma da nitsuwar yi ma sa kwatance. Lokacin da ta fito tundaga nesa ya ƙare ma ta kallo, ta rame ta yi baƙi kana ganinta ka san ba ta da kwanciyar hankali. A ƙasan ran sa ya ce "zuwa lokaci kaɗan za ki haƙura ki manta da shi" Jerawa su ka yi su na tahowa amma ba su yi nisa da shiga Asibitin ba Maryam ta yanki jiki ta faɗi. Tunda ta fito dama ta ke ɗan jin jiri amma ta daure ta cigaba da tafiya. Muntari ya fara Salati yana ƙoƙarin tallafota gamida ƙwalawa likita kira. Shi da wata nurse su ka ɗauketa su ka ɗaura ta akan gadon da ke gefen wajen aka turata zuwa ɗaki. Ba'a jima ba ta farfaɗo amma ba ta da ƙarfin jiki hakan ya sa su ka ma ta allura aka ɗaura ma ta ruwa nan da nan bacci ya ɗauketa. Ko ta kan Sadiq da ya zo dubawa bai yi ba sai ya tsaya kula da Maryam. Ya tambayi likita miya ke damunta ya ce jininta ne ya hau amma sauran bayani sai an kawo result ɗin gwajin da aka je yi ma ta bayan an ɗeba jinin ta. Bayan awa ɗaya aka kirashi wajen Likita inda ya bayyana ma sa Maryam na ɗauke da juna biyu kuma ta rage damuwa dan zai iya jawowa ta rasa cikin. Muntari ya hangame baki yana jin bayanin Likita. "Ciki fa ka ce? Har yanzu ba ta dena haihuwa ba ne? Kai a dai sake dubawa ko an jirkita result ɗin, rabonta da samun ciki shekaru shida no shekaru bakwai kenan" Likita da ya ɗauka Muntari mijin Maryam ne ya ce "ai ba ta wuce shekarun haihuwa ba ma su shekaru hamsin ma suna haihuwa balle ita da na ke tunanin ba ta fi arba'in ba" "Talatin da tara ne ma" ya gyara ma sa, kar ya ƙarawa Maryam ɗin sa tsufa. "To ka gani, she's still very active ta samu ciki. Tana buƙatar hutu sosai, za mu riƙeta na kwana biyu kafin mu sallameta, kuma idan ta koma gida ma ta rage yawan ayyuka ta kuma cire damuwa a ranta" Muntari ya gyaɗa kai kafin ya miƙe ya bar office ɗin bayan sun yi musabaha da Likita. Yana shiga ɗaki ya ƙurawa Maryam ido wani kishi da haushi na turnuƙe shi. A fili ya furta "shege Tijjani sai da yai yadda ya ƙunsa ma ta ciki kafin ya tafi" Daga baya ne ya kira Hajjo ya je ya duba Sadiq ya kuma gaya ma ta Maryam ma an ba ta gado saboda ta faɗi lokacin suna shigowa. "Miya sameta?" Hajjo ta tambaya tana mamakin abun "Likita ya ce damuwa ce ta ma ta yawa" "Ai dole, ta fi kowa damuwa da rashin Hamma amma kuma ta ke daurewa tana nuna ba komai". Sa'ilin da Maryam ta tashi ta so a barta ta tashi ta tafi saboda ta ɗan ji ƙarfin jikinta amma Likita ya ƙi Muntari ma na gefe yana ba ta baki. Tana son yiwa Likitan bayanin jinyar Sadiq sai maganar likitan ya katse ta. "Hajiya kina buƙatan hutu fa, dan rashin samun nutsuwa ka iya sa ki rasa abinda ke cikin ki" "Ciki?" Ta furta da mamaki "Yes, inaga Maigidan bai riga ya faɗa miki ba kenan?" Muntari yai saurin cewa "tana tashi na zo na kira ka" nan kuwa sai da ta yi kusan 15mins da tashi kafin ya je ya gayawa Likitan bayan da ta ce mi shi ya je ya ce a cire ma ta Canula da ke hannunta za ta tafi ɗakin Sadiq. Shafa ƙasan cikinta ta yi sai ga hawaye. Ciki a lokacin da ta cire rai da sake haihuwa, ciki a lokacin da ake tsaka da neman T J. Ba za ta yi abinda zai sa ta rasa cikin nan ba, not after 'yan biyun ta da ta rasa. Washegari Maryam ta sa aka Sallameta bayan ta bawa Likita tabbacin za ta kiyaye dokokin sa saboda lafiyar ta. Muntari dai haushin cikin ya cika shi amma kuma soyayyar Maryam ya shafe haushin. Sadiq kam sai da yai kwana tara a Asibitin aka sallameshi su ka dawo gida, yawan jinya da ya ke yi ma ya sa makarantar sa ma lilo ta ke yi, ya kasa wani yin nisa a karatun. Addu'a da sadaƙa kam ba wanda aka fasa yiwa T J dan a gano inda ya ke. Tun suna sa ran za'a ji labarin sa har kuma su ka fara fidda rai amma ga Maryam kam kowacce rana da ta fito da hope ɗin ganin T J ta ke musamman yanzu da ta gano tana ɗauke da cikin sa. Sai da cikin ma ya kai wata biyar ma yawancin mutane su ka gane tana ɗauke da cikin, ciki kuwa har da Iya. Hanne ce ba lafiya ta je gaisheta shine ta haɗu da Iya ashe Hannen laulayi ta ke yi, duk da damuwar ɓatar T J da Iyan ke ciki samun cikin Hanne ya sa ta kwantar da hankalin ta. Ba laifi da Maryam ta gaisheta ta amsa, haka ta bita da kallo lokacin da za ta tafi tana ƙara tabbatarwa kanta cewa ciki ne a jikin Maryam ɗin... *** "Zaytoonah miye wannan?" Ta faɗi tana nuna takardan da Zaytoonan ta ba ta. "Mommy report card ma na" ta amsa tana tura baki "Sai yaushe za ki maida hankali a karatu ne. Second term 21st a cikin ku 35 yanzu third term kuma 28th. I'm not happy, from 3rd position a first term sai ki koma ƙarshe-ƙarshe" "Mommy first term Daddy yana nan, yanzu kuma bayanan, ni daga yanzu ma ba zan je school ɗin ba" ta ƙarisa maganar tana tashi za ta bar ɗakin. "Come back here Zaytoonah. Kar ki sake tashi a gabana ba tareda mun gama maganan ba" Ta zo ta zauna tana zumɓura baki. Maryam na fara ma ta maganan maida hankali a karatu ta fashe da kuka. "Mommy ba zan yi karatun ba, ba zan yi ba. Just leave me alone" "Zan mugun saɓa miki kuwa, ke kaɗai ce kika rasa Uba? Su Salman, Sadiq da Humairah su mutu kenan saboda kin fi su son Daddyn ku?. Haba Zaytoonah sai kin kasheni hankalin ki zai kwanta? Ke ce Babba amma kin fi kowa wauta. Da wanne zan ji Dan Allah" "Mommy dan Allah ki yi haƙuri" Auwal da shigowar sa ɗakin kenan ya faɗa. "Ita za ka bawa haƙuri kar ta kashe ni. Na gaji da matsalarta a gidan nan" Zaytoonah ta fice daga ɗakin da gudu. Ya sani ba halin Mommy ba ne ƙorafi amma duba da abubuwan da su ka faru da kuma cikinta da ya girma gaba ɗaya ta chanja. Abu kaɗan yanzu faɗa ta ke yi. Akwai ranan da tana yiwa Zaytoonah magana sai da ta haɗa da mari, ba dan ya shiga tsakani ba ma da ba ƙaramin duka za ta yiwa Zaytoonan ba. Ya sani Mommy na fama da depression ne. Ɗakin Zaytoonah ya wuce ya samu ta kifa kai akan gado sai kuka ta ke yi. Bai ce ma ta komai ba sai ya zauna bakin gado yana sake duba report card ɗin Zaytoonan. Kusan minti biyar da shigowar sa bai ce komai ba hakan ya sa Zaytoonah ta tsaida kukan ta ɗago tana kallon sa, suna haɗa ido ta harareshi ta cigaba da sheshsheƙar kuka. "Ki cigaba da harara ta, idan idonki ya faɗo na Kare za a sa miki" Ta murguɗa ma sa baki ta ce "ina ruwan ka" "Da ruwa na mana tunda ni za a nuna a gari ace ga Yayan Zaytoonah dog eyes" Ta ɗau pillow ta buga ma sa a ka. "Ashe dai ba Mommy kawai za ki kashe ba har da ni" ya faɗa yana dariya Zaytoonah ta ja tsaki. Kusan 5 seconds kafin ya kira sunan ta a hankali "Zaytoonah" Ba ta amsa ba amma ta zuba ma sa idanun ta. "Abinda ki ke yi ba shi zai sa a ga Daddy ba. Infact abinda ki ke yi zai sawa Mommy ɓacin rai ne ƙarshe watarana ta samu heart attack ta mutu" Zaytoonah ta zaro ido "Ki na so Mommy ta mutu ne?" Ta yi saurin girgiza kai "To ki dena sa ma ta ɓacin rai. Na sha gaya miki addu'a za ki dinga yiwa Daddy ba wai kuka ko taurin kai ba. Ki na so Daddy ya dawo ya samu ba kya karatu ran sa ya ɓaci da ke?" Nan ma ta girgiza ma sa kai. "To ki dage da karatu, ban da rashin kunya da taurin kai kin ji" Jikinta ne ya sanyi ta sunkuyar da kai tana zubda ƙwalla. She's trying to accept the fact that Daddy ya ɓata, ɓata kamar yadda ake neman abu a rasa ko kuma kana kiwon dabba sai ka nemeshi ka rasa. Over this few months ba abin da ba ta riyawa ran ta ba gameda ɓatan Daddyn su. Ta yi tunanin ko 'yan yankan kai ne su ka ɗauke shi ko kuma dai accident yai gawarsa ta ƙone aka rasa waye aka bisine shi. Akwai lokutan da ta ke tunanin ko dai ya gaji da su ne ya gudu dan ya gina sabuwar rayuwa ba tareda su ba, sai kuma ta tuna da cewa Daddyn su na son su sosai, ba zai taɓa guduwa ya bar su. "Come here" Auwal ya faɗa yana jawota jikinsa, ya dinga bubbuga bayanta yana cigaba da rarrashinta... Da yamma lis Zaytoonah ta shiga kitchen. "Mommy whats cooking?" "Your eyes" Mommy ta amsa a hasale Ta je ta rungume Mommyn ta baya tana faɗin "Mommy i'm sorry" "Sorry for yourself" "Ah Ah Mommy na tuba fa, no more bad result daga yanzu" "Har da kukan banza?" "Yes Mommy, babu kukan banza" "Sakeni na yi aiki to" Maimakon ta saketa sai ta ƙara ƙanƙameta tana faɗin "i love you Mommy" "Na ji sakeni" "Ai ba ki amsa ba" Maryam ta yi murmushi ta ce "I love you too" Sai a sannan Zaytoonah ta saketa, ta kama ma ta aiki har su ka haɗa girkin. *** Ƙarfe biyun dare Auwal ya kira Maryam akan ta zo gidan Hajjo Sadiq ba lafiya. Maryam ta zura dogon hijabi na sallah ta ɗau key ta fita. Addu'a ta ke yi a ranta saboda yanayi na sanyi da aka shiga lokacin ne ciwon Sadiq ya fi tashi. Bai fi sati biyu da ya wuce ba aka sallamoshi daga Asibiti. Shekaranjiya da kan sa ya zo gidan ta ya wuni, dan har sai dare da Auwal zai koma gidan Hajjo ya tafi da shi. Ɗan zaman da yayi da ita ba ƙaramin tausayi ya ba ta ba dan da crutches ya ke tafiya saboda ciwon ƙafa, ciwon ya hanashi girma sai ƙaton kai. Makaranta kam kusan watan sa uku ma bai zuwa. A gigice ta fito daga mota wanda ta samu Auwal na goye da Sadiq yayinda Hajjo ke gefe tana kuka. Da ta fito ta ƙarɓi Sadiq ta ce Auwal yai tuƙin. Ita da Sadiq a baya Hajjo da Auwal na gaba. "Mommy sanyi na ke ji" Sadiq ya faɗa yana ƙara ƙanƙame Maryam. "Ka yi haƙuri mun kusa Asibiti" tana maganan tana cire hijabin jikinta tana ƙoƙarin lulluɓeshi da shi. "Mommy za ki dafa min shinkafa irin na ranan?" "Zan dafa ma ka kaji ɗana, zan dafa ma ka duk abinda za ka ci" "Irin wannan mai red and green and yellow ɗin nan. Ki ka ce carrot is red, corn is yellow and, and, and" "Peas and green beans are green and we have our delicious..." Ya amsa da ƙarfin sa "fried rice" Ta yi dariya wanda ya taho da hawaye. Hajjo na gaba ta toshe bakinta da gefen hijabinta dan kar aji kukan ta. Ta fara cire rai da Sadiq, shima ta san ba jimawa zai yi ba kamar ɗayan. Kafin Maryam ta zo suman sa sau biyu. Maryam na jin Sadiq na wani irin shiɗewa ta fara Innalillahi tana kiran sunan sa da ƙarfi. "Daddy" ya kira kaman shi ke kusa da shi sai kuma ya sake jiki dai-dai Auwal ya karya kwanar shiga Asibitin. Ana tsayawa Hajjo ta fito da sauri dan ta taimakawa Maryam ta fito da Sadiq tunda ta yi nauyi yanzu. Za ta karɓeshi Auwal ya ce ta bari zai ɗaukeshi. Tunda ya fito da shi daga cikin motan zuciyar sa ya karye amma ya daure yana tunanin ƙila Sadiq ɗin suma yai. Haka su ka shiga Asibitin shi da Hajjo da sauri ita kuma Mommy ta tsaya saka hijabi. Suna tsatstsaye sun yi zuru-zuru likita ya gama duba pulse ɗin sa da heartbeat ya ce "i'm sorry, he's dead" Cikin Maryam ya murɗa ta yi ƙasa da sauri tana ƙara saboda zafi da ta ke ji. Auwal yai kan Mommy ita kuma Hajjo ta yi kan gawan ɗanta da ke kwance... Har safiya Mommy ta kasa haihuwa dan labour ne ya taso ma ta gadan-gadan ga kuma jininta da ya hau, hakan ya sa aka fara shirin yi ma ta CS. Lokacin da aka ciro ɗan Maryam an jima da kai gawar Sadiq Maƙabarta. Daga maƙabarta straight Muntari Asibiti ya taho inda ya samu an ciro kyakykyawan Baby Boy ɗin Maryam. Saboda Maryam ba ta farfaɗo ba dole ya tafi bayan an tabbatar ma sa da Maryam da Babyn su na nan lafiya. Zaytoonah, Maman Fawaz da Altine wata maƙociyar su su suka zauna a Asibitin saboda sauran 'yan uwa duk ana chan ana zaman makoki... *** *Bayan shekara ɗaya* Goye ta ke da As-Sadiq tana ɗan jijjiga shi saboda muran da ya ke yi ya sa mi shi zazzaɓi. Kuka yake yi tun ɗazu amma yanzu yayi shiru tana tunanin ma yayi bacci. C V ɗin ta ta ke son haɗawa amma kukan shi ya hanata shiyasa ta goye shi. "Assalamu Alaikum" Zaytoonah ta yi sallama tareda shigowa cikin Falon. "Oyoyo junior, Oyoyo" "Yayi bacci ko?" "Eh" "Je ki cire uniform ki zo ki karɓeshi" Da gudu ta shiga ɗakinta. Dan ita ce uwar renon junior. Shima kaman Sadiq da ya rasu Abubakar As-Sadiq aka sa ma sa sai dai junior su ke kiran shi. Bayan haihuwar sa abubuwa da dama sun faru ciki kuwa har da raba auren Tijjani da Hajjo. Rashin T J da rasuwan Sadiq ba ƙaramin giɓi ya kawo a rayuwar Hajjo ba. Gidan ya ma ta faɗi, kaɗaici ya isheta ta dawo ma sai dai ta je ta wuni a gidan Muntari duk dan ta kasance da Humairah amma ita kuma baya-baya ta ke yi da ita. Wata takwas da rasuwan Sadiq watarana Maryam ta dawo daga Ta'aziya ta haɗu da Hajjo a gidan ta. Ba ta yi mamaki ba tunda tun da aka yi arba'in ɗin Sadiq lokaci zuwa lokaci ta kan zo su gaisa. "Mommyn Zaytoonah zan koma ƙauye" "Ban gane ba, Mi za ki yi a ƙauye?" Hajjo ta sunkuyar da kai ta ce " ba ni da wani sauran kwanciyar hankali a nan. Har yanzu Baban su shiru ba labarin sa, na yanke shawaran zan je kotu a raba aurenmu. Ko da Hamma zai dawo yau cewa zan yi ya sake ni, tun farko son zuciya ya sa na zauna tunda ya min bayanin za mu dinga haifan 'ya'ya ma su sickler idan muna tare. Duk wahalhalun da mu ka sha akan Sadiq ƙarshe shima sai da ya tafi" ta ƙarisa maganar tana share hawaye. "Hajjo ki yi haƙuri dan Allah, ina da yaƙinin Daddyn su ya kusa dawowa. Ba za ku sake haifan sickler Insha Allahu, ga Humairah nan lafiyar ta ƙalau" "Ki shige min gaba kawai na samu yadda zan yi a raba auren nan. Na riga na tsayar da magana" Duk yadda Maryam ta dinga ƙoƙarin convincing ɗin Hajjo ta ƙi yarda. Ƙarshe dai dole Maryam ɗin ta yarda da decision ɗin ta... Cikin ƙanƙanin lokaci aka raba auren Hajara da Tijjani bisa dalilin an rasa Tijjani kusan shekara biyu, ko yana raye ko baya raye ba a sani ba. Bayan komai ya kammala ne Maryam ta zaunar da Hajjo ta ba ta shawara akan gara ta zauna a Ringim ta nemi sana'a ta fara yi tunda dai ta wajen Uwa ta haɗa jini da T J, ba wanda zai hanata zama a family house ɗin su T J ɗin. "Kin ga zama shiru ba daɗi. Ga dubu goma nan ki je ki yi tunanin sana'ar da za ki fara idan kin je" Hajjo ta fashe da kuka. Ba ta taɓa jin zafin rashin makarantar ta ba irin na yau. A lokacin da T J ya dage sai ta yi karatu ta ƙi yau ga ranan karatu. Da tana da kwali ko da na sakandare ne za ta samu wani aikin da za ta dingayi a wata tana samun kuɗi. Ita tun asali ba abinda ta ke yi, sa'ilin da ta ke budurwa ne ma take ɗan taɓa kitso haka. "Ki yafe min Mommyn Zaytoonah, duk abubuwan da na miki ki yafe min dan Allah" Maryam ta ce ta yafe ita ba ta riƙeta da komai ba. Tausayin ma Hajjon ta ke yi sosai fiye da kan ta. Gara ita tana aiki amma Hajjo fa, ta yi zaman birni ne kawai amma har yau ba ta waye ba. Sati guda da yin haka Hajjo ta koma Ringim da zama. Auwal ya dawo gidan Maryam da zama aka kulle wancan gidan. Wata biyu da haka sai ga Auwal ya zo ya samu Maryam da cewa ya ga wasu suna parking cikin gidan da ya tambaya su ka ce ma sa haya su ka karɓa a wajen Alhaji Muntari. "Allah shi kyauta" ta ce dan ta riga taga take-taken Muntari tun bayan da aka raba auren Hajjo. Ba za ta manta da maganar sa ba safiyar wata Asabat *"Maryam ke ma fa har yanzu kina da ƙuruciyar ki. Shekara biyu ba wasa ba ne kina da damar ɗaukan matakin irin na Hajjo"* *"idan ka gama maganar banzan ka ka tashi ka bar min gida"* ta faɗa tana tashi daga falon. Tundaga lokacin ya ɗau saran zuwa akai-akai ya fake da cewa ya zo duba 'ya'yan sa ne tunda yanzu hakkin su na kan sa. Indai yaran na nan za ta shige ɗaki ta bar su da shi idan ba sa nan kuma ta shige ɗaki ta sa key idan ya gaji da zama ya tafi. Ba ta son kula shi dan abubuwan da ke kanta sun yi yawa balle ta tsaya ɓata lokaci akan wani banza wai shi Muntari. Wani lokaci har 'yar sa Maryam ya ke kawowa wai ta gaisa da yayyen ta. Kafin ya kawo maganar banzan nan ta kan kula yarinyar duk da ta san saboda ita ya sa ma ta sunan Maryam. Watan Junior biyu da sati biyu Hanne ta haihu tun a Asibitin ya kira Maryam yana ce ma ta Hanne ta sauka an samu takwarar ta mai suna Maryam... Bayan ta gama haɗa CV ɗin ta ta kai gidan Alhaji Iliyasu Mai Auduga wanda shi ya aiko ta kai ma sa. Vacancy aka ba shi har guda biyu a Nuhu Bamalli Polytechnic shine da ya haɗu da Auwal a masallaci ya ce ya cewa Maryam ta zo yana neman ta. Lokacin da Auwal ya gaya ma ta saƙon Alhaji Iliyasu ba ta kawo komai a ranta ba duba da kyakykyawar alaƙar da ke tsakanin sa da T J. Lokacin ɓatan T J da ya yi wata uku lokacin da Alhaji Iliyasu ya dawo daga Hajji dubu Hamsin ya aiko ma ta tareda buhun shinkafa da rabin buhun sugar da jarkan man gyaɗa da na manja guda bibbiyu ya ce su raba ita da Hajjo. Ɗan tsohon ya damu da ɓatar mai sunan Shehu ba kaɗan ba. Duk da matsayin Uba ya ke ga TJ amma yadda su ke mu'amala ka ɗauka abokai ne. Bayan ya ma ta maganar aikin koyarwa sai da ta je gida ta nitsu ta yi shawara da zuciyarta ta kuma yi addu'a kafin ta amince da maganar... *** A gida ya sameta ita ɗaya a falo tana haɗawa students ɗin ta note ɗin da za ta yi wa students ɗin ta gobe a class. Junior na wajen Zaytoonah a ɗaki tana mi shi wasa. Fiska a murtuke ta amsa sallamar sa. Ko gaisheshi ba ta yi ba ta cigaba da abin da ta ke yi. "Ina Zaytoonah?" Ta ji abinda ya ce amma ta shareshi. "To dama Makaranta ne na chanja ma ta, ta fara shiri nan da sati biyu ce tafiyar" ya ajiye wasu takardu a saman takardan da Maryam ke dubawa. Ta ɗago ta kalleshi sannan ta ɗau takardan ta fara dubawa. Takardan transfer ce daga makarantar da Zaytoonah ta ke zuwa wata makaranta da ke Lagos. Not just makaranta, boarding school ne. "Amma ka san SS3 kawai ya rage ma ta shine za ka je ka wahalar da kan ka wajen kai ta boarding school" "Na sani, so na ke ta yi hankali, zama a gida ya sa ta sangarce dayawa" Tana so ta ce masa Lagos yayi nisa amma ta yi shiru dan ta san dan ta yi magana ya aikata abunda ya aikata. Kwanakin baya da ya sa mutane haya a gidan T J ido ta zuba ma sa, shi da kan sa ya zo ya ke cewa yayi hakan ne saboda kar a bar gida ba kowa, kuma abinda ake samu za a toshe wani hidiman da shi. Ta ce ma sa Allah ya kyauta. "Ka ce tafiyar nan da sati biyu ko?" "Yes" Ta yi murmushi ta ce " Insha Allahu za ta shirya kafin nan. Idan babu wani abu za ka iya tafiya" Ba haka ya so ba, ya so ta damu ne har ta roƙe shi akan ya janye maganar sa, shi kuma yai amfani da hakan ya ƙara jawota gareshi. Ya gane 'ya'yanta su ne weakness ɗin ta. Gwiwa a sace ya tashi ya fita. Sai bayan ta tabbatar a makarantar su Zaytoonan gameda transfer ɗin kafin ta samu Zaytoonah da maganar. Ba wai dan tana son tafiyar Zaytoonah ba ne a'a, sai dai dan ta ƙure iskancin Muntari da renin hankali. As expected kuka Zaytoonah ta dinga yi akan ba za ta je boarding ba, boarding ɗin ma Lagos ga uwa uba ba ta son tafiya ta bar Maryam saboda zamanta a gida ba ƙaramin ragewa Maryam ayyuka ta ke yi ba. Maryam kam tun tana lallashi har ta rabu da ita ta ce kar ta shirya, ita da Uncle ɗin ta ne ba ruwanta a ciki. Daga baya kuma da ta ga lokacin ya ƙarato Zaytoonah ba ta saki ranta ba sai ta koma yi ma ta nasiha tareda nuna ma ta cewa shekara ɗaya ce kawai za ta yi, shikenan ta gama... Free pages zai ƙare a pg20 Insha Allah *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: *Chronicles of* *...... ...... .......ZAYTOONAH* https://m.facebook.com/Inside-Arewa-Writers-107691760958755/?ref 𝕀ℕ𝕊𝕀𝔻𝔼 𝔸ℝ𝔼𝕎𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ𝕊© *(Ƙungiyar Nazarin Harshen Hausa)* Rubutawa.....Azizat Wattpad@Azi_zat *Last Free page* *20-Mrs Zaytoonah* Bismillahir Rahmanir Rahim Shirye-shirye ake yi na zuwa graduation ɗin Zaytoonah. Jiya Muntari ya kawo ma ta ticket ɗin jirgi amma ta yi banza da shi ta ce ya kwashe tsiyar sa ba ta so. Ta riga ta tsara tafiyar tuntuni dan haka ba ta buƙatar taimakon sa, da gayya ya tura 'yarta gari mai nisa dan kar ta dinga zuwa ma ta visiting. A Kaduna za su je su shiga babbar Mota da zai kai su Lagos. Hatta inda za su sauka sai da ta tsara shi kafin ta ɗau aniyar tafiyar. Gidan wata ƙwarta ne da su ka yi Law school tare a Abuja. Lokacin da su ka yi Law school ɗin ba ta yi aure ba amma yanzu aure ya kai ta zama a garin Lagos. Dukkan su sabbin ɗinkuna su ka yi har Auwal ma, Salman da Junior ɗinki iri ɗaya ta mu su. Ana gobe za su tafi ta je gidan Muntari ta yiwa Hanne sallama wacce yanzu zaman ƙaddara kawai ta ke da Muntari. Lokacin da ta ke da cikin Maryam ta gano Muntari Maryam ɗin Tijjani ya ke so. Hotunan ta birjik a kan gadon sa watarana da ta shiga ɗakin sa za ta kira shi saboda yayi baƙi. Tana cikin duba hotunan ya fito daga banɗaki. Hawaye fal a idonta ta ce "yanzu dama duk wannan haukar da ka ke yi akan Maryam ashe Anty Maryam ɗin Hamma Tijjani ka ke so?" "Ba na son shishshigi ki tashi ki bar min ɗaki" "Haba Muntari ka ji tsoron Allah. Ka san fa tana da aure kuma Yayan ka ta aura amma ka gaza haƙura da ita ba wallahi ka ji kunya" "Kar ki sake min maganar banza Hannatu, zan mugun saɓa miki" "Tir da wannan halin rashin kunyar na ka, haba Muntari ko kunyar nan ta Fulani ba ka da ita balle ta musulunci. Matar Yayan ka fa, Matar Yayan ka Uwa ɗaya Uba ɗaya" Harzuƙa yai da kalamanta ya shiga dukanta. Ihun ta da Iya ta ji ne ya sa ta haura sama da sauri ta je ta samu Muntari na dukan Hanne wanda sai da aka haɗa da zuwa Asibiti saboda jini da ya fara fitowa daga gabanta. Da rabon Maryam za ta zo duniya ne da ta mutu tun a ciki a lokacin. Lokacin Iya ta yi fushi sosai da Muntari amma ba ruwan sa ko haƙuri bai ba ta ba, bai kuma nuna ya damu ba. Daga baya kuma a cikin shekarar ya biya ma ta Umara nan da nan zance ya wuce a wajen Hajiya Iya. Lokacin da ta dawo sai da ta je Ringim ta yi sati biyar kafin ta dawo. Ana zuwa ana ma ta barka sai burga ta ke yi a dole ita Hajiya. Wani abun idan Iya ta yi sai ka kama baki saboda shirme ne kawai da jahilci. A lokacin kuwa an samu cikin 'yan uwa dayawa da su ka yi tallen 'ya'yan su ko za ta haɗasu Aure da Muntari amma ta sani ko ta amince ma kunya za ta sha dan Muntari ba Tijjani ba ne, Hanne ma da ya yake zama da ita balle a masa zancen ƙarin aure. Da ke Allah ne ke kiran bayin sa a shekara na gaba da Iya ta je Umara Goggo ta je Hajji. Mijin jikanta Asma'u ne ya biya mu su ita da Asma'un da mahaifiyar sa da wata yayar sa su ka yi tafiyar ayari. Ikon Allah sai kallo domin kuwa ganin Goggo ta je Hajji ya sa tsohon kishi da Hassadar Iya ya tashi. Ta shiga yiwa Muntari maganar itama na son zuwa Hajji. Da farko bai kulata ba daga baya kuma da 'yan mutuncin su ka shigeshi sai ya biya ma ta. Yanzu haka kwanan ta biyu da dawowa daga Hajjin ta wuce Ringim satin ta ɗaya ma a chan. Maryam da ta je wajen Hanne ne ta ke ma ta tsegumin komai. Maryam ta ce ita Iya ta daina ba ta mamaki tausayi ma ta ke ba ta. Su na cikin hiran ne sai ga Humairah ta shigo gidan tana ganin su zaune amma ta kauda kai za ta wuce su, Hanne ta ce "yanzu Humairah cewa za ki yi ba ki ganmu ba? Idan ni ba za ki gaisheni ba Mommyn ki fa?" Ta wani juyo a yangance ta ce "Sannu Mommyn Zaytoonah" Maryam ta ce "Sannu Humairah ya karatu?" "Ƙalau" ta faɗa ta wuce ba tareda ta yiwa Hanne magana ba. "Humairah ce ta zama haka?" Maryam ta faɗa tana kallon Hanne" "Ai Anty Maryam kaɗan ma ki ka gani, a gidan nan ba mai gaya ma ta magana ta ji idan ba Muntari ba shi kuma ba ruwansa da tarbiyyan ta. Shi dai kawai indai kuɗi ta ke buƙata zai ba ta. Yanzu haka wata ƙatuwar wayar blackberry ya siya ma ta" Maryam ta ce Allah ya kyauta... Zaytoonah ba ƙaramin jin daɗi ta yi ba ganin dukka 'yan gidan su sun zo ma ta. Sai nan nan ta ke da su, tana nunawa manyan ƙawayenta iyayenta. Anci an sha kuma an yi hotuna. Zaytoonah ta karɓi kyaututtuka har guda uku wanda ya sa Maryam ta yi farinciki da chanjawar 'yar tata. Atleast ba ta bari ɓatar Mahaifinsu ya dawo da ita baya ba. Bayan kwana biyu da yin graduation ɗin dukkan su suka dawo gida. Bayan ta huta ta tafi hutu Ringim dan ta jima ma ba ta je ba. Mutum biyu su ke sa ta farinciki su ke kuma sa ta ɗokin zuwa Ringim ɗin wato Yadikko da Goggo. To Yadikko ta rasu saura Goggo, da ta je ma a ɗakinta ta sauka ta dinga ma ta tsiya wai ta zama gurguwa tunda ba ta iya tafiya mai nisa sai da sanda. A kwananta na biyar da zuwa gidan da yammaci tana farfajiyyan gidan tana yiwa Goggo yankan farce, wasu mata na wanke masara mai yawa dan zai yi rabin buhu za su jiƙashi saboda a bushar a niƙa shi saboda garin tuwo. Tana yiwa Goggo yankan farce tana tanka mu su saboda surutun su da gulman su yayi yawa sai ga yaro yayi sallama wai ana kiran Zaytoonah. Zaytoonah ta ce waye? yaron ya ce bai sani ba. "Ka ce ma sa ba ta nan" "Ke kuma kin yi mashinshini za ki kore shi? Ki ka sani ko shi ne Angon" "Allah ya kiyaye. Ba Mashinshini ba Mai lashe mutane na samu" "Allah ya baki haƙuri jikar Iya da Goggo, 'ya a wajen Boɗɗiyon Tijjani" "Gyara maganar ki na baki ƙwandala. Jika ce a wajen Goggo da Baffah Habu Allah ya jiƙan rai" tana maganar kuma sai ga Iya ta fito daga ɗaki kuma sarai ta ji mi Zaytoonah ta ce. Ranta ya sosu da maganar Zaytoonan amma ya za ta yi tunda koma mi Zaytoonah ta ce ita ta jawa kan ta... Washegari ma sai ga shi an sake aikowa wai Zaytoonah ta fito. Wannan karan kam so ta ke ta ga wani ɗan iskan ne ke neman faɗan ta. "Ehen, miye ka ke nemana?" ta faɗa tana riƙe ƙugu. Sai wani sunne kai ya ke yi irin kunyar nan. "Idan ba ka da abin faɗa ni zan shiga ciki kuma idan ka ƙara sawa a kirani tafasashshen ruwan zafi zan zo na zuba ma ka" "Dama Baffa Muntari ne ya ce na zo mu dai-dai ta" Ta fashe da dariya har da riƙe ciki. Sai da ta yi mai isharta kafin ta ce "mu dai-dai ta, Kaji ka ke sayarwa ko Raguna?" Ya ɗan ɗago ya kalleta amma yadda ta tsareshi da ido ya sa shi sunkuyar da kai ya ce "shi ne ya turoni wai mu yi zance mu fahimci juna" "Bakin ka ne mu fahimci junan ai. Look, kar ka ƙara aikowa a kirani dan zan watsa ma ka ruwan zafi" Ta shige gida ta barshi a tsaye. Wonders shall never end. Wai Uncle Muntari ne zai turo ma ta saurayi. Haka dai ta yi sati biyu ta dawo gida har lokacin kuma Bello kamar yadda ta gane sunan shi daga baya bai sake zuwa ba. Matan gidan su kuwa duk wacce ta ma ta maganar aure tsayawa ta ke ta silleta son ran ta. Da ta koma gida ne cikin taɗi ta yiwa Mommy maganar abinda ya faru. Nan da nan Maryam ta ankara da abinda Muntari ke shirin yi. Wato nufinsa auren dole zai yiwa Zaytoonah. To kuwa tana dai-dai da shi dan abinda ba za ta taɓa bari ya faru ba ne. Amma dai bari ya zo ya sameta da maganar za ta nuna ma sa cewa ita ta haifi Zaytoonah ba shi ba. Kyautar sabuwar waya andriod Maryam ta siyawa Zaytoonah lokacin da result ɗin ta na WAEC ya fito mai kyau. Tana da A biyu da B guda biyar sai C uku. Tuni ta saka numbar ƙawayenta wanda su ke da waya aka hau network... Ranan ta dawo daga Islamiyya ta samu Muntari da Mommynta a falo suna masifa. Ta jima da sanin rashin jituwar da ke tsakanin Uncle Muntari da Mommyn na ta, duk da ma ba ta san takamaimai miya jawo hakan ba. Ko gaishe su ba ta yi ba ta wuce ciki amma ta kasa kunne daga jikin ƙofa tana jin mi ake faɗi. "Ka san Allah, ko sama da ƙasa za su haɗu ba ka isa ka aurar min da 'ya ba. 'Ya ta karatu za ta yi, ban roƙe ka kuɗi ba balle ka ce za ka takura da hidimar ta. Idan hauka ka ke yi ka je ka nemi magani amma ba ka isa ba Muntari, ka yi kaɗan" "Maryam kenan, Zaytoonah dai sunan Tijjani Abubakar ta ke amsawa ba na Maryam ba. Dan haka a matsayina na shaƙiƙin Tijjani na yiwa 'yar sa miji. Ki gama borin ki nan da wata biyu za ayi biki" "Idan mafarki ka ke yi ka farka Muntari domin indai nina haifi Zaytoonah ba ka isa ka ma ta auren dole ba ina dai-dai da kai" Yai Murmushin mugunta ya ce "to mu zuba mu gani" Bayan tafiyar Muntari Zaytoonah ta fito da gudu ta faɗa jikin Mommy tana kuka. "Mommy do something dan wallahi idan aka min auren dole kashe mijin zan yi ko kuma na kashe kai na" Maryam ta ce " ba zai kai ga haka ba ma Insha Allah" Bayan kwana biyu Maryam ta kira Goggo ta sanar da ita abinda Muntari ya ce. Goggo ta ce idan ta samu lokaci ta taho Ringim ayi maganar. Abunda Maryam ba ta sani ba shine. Tun zuwan Zaytoonah hutu Muntari ya fara mission ɗin sa ta hanyar hura wutar fitina cikin familyn su. Dalilan da ya gabatar na son aurar da Zaytoonah mafiya yawa cikin family sun gamsu da shi. Goggo da ta ji batun da ake a cikin gida sai ta samu Iya da maganar lokacin ba ta koma Zaria ba. Iya ta ce Muntari Uba ya ke ga Zaytoonah ba zai cutar da ita ba. Da ta ga abin yana son zama gori sai ta yi shiru ta bar zancen. Muntari cewa yai Zaytoonah ta yi girma dayawa sannan tana da rashin kunya da reni. Ga uwa uba shiriritar 'yan fari da ke damunta. Kusan kaf matan cikin gida sun yi gulmar Zaytoonah lokacin da ta koma Zaria hakan ya sa mazajen su da su ka ji dalilin aurar da Zaytoonah da Muntari ke yi ya sa su ka fara yaba ma sa acewar sa yana ƙoƙarin tseratar da mutuncin Zaytoonah ne kafin ta lalace ace saboda Ubanta baya nan ne aka kasa yi ma ta tarbiyya mai kyau. Ba kaɗai dalilin ba ne ya sa su ka amince, Muntari ya jima yana yiwa 'yan uwansa Alkhairi na kuɗi da kayan abinci. Wanda ya ke ganin za su kawo ma sa cikas akan manufar sa tuni ya yi mu su abinda ba za su taɓa yi ma sa gargadama ba. Ya biya mu su kujeran Makkah. Abu dai ya koma ba don Allah su ka amince da Muntari ba sai dan 'yan chanji da ya ɗauki watanni yana ba su... Da Maryam ta je Ringim ta samu Goggo su ka tattauna abinda ke faruwa. Maryam ta yi mamakin goyon baya da 'yan uwan T J su ka ba wa Muntari a wannan hukunci na son zuciya da ya ke shirin yi. Dan kaf sun yadda da auren Zaytoonah da Bello wanda yaron shekaransa ashirin da ɗaya, sakandare kaɗai yai ya kama aikin makanike, a ƙarƙashin wani ya ke ba wai yana da garejin sa ba ne. Har wajen Baffah Umar ta je akan ta ganar da shi kuskuren wannan haɗin da Muntari ke yi. Amma sai ya ce ma ta indai saboda karatun Zaytoonah ta ke tsoro shi Muntarin yayi alkawarin zai biyawa Zaytoonah ta cigaba da makaranta bayan aure. Hadda cewa ai karatun 'ya mace a gidan mijinta ya fi kwanciyar hankali. Ba ta samu abinda ta yi niyya ba dan haka ta chanja maganar ta hanyar roƙon a bari Zaytoonah ta auri Auwal instead of Bello. Shi Auwal ya ma fi kusanci da Zaytoonan kuma tare su ka taso sun saba da juna. Baffa Umar ya ce to magana ce mai kyau amma bari yai shawara da sauran 'yan uwa tukunna. Kamar wanda Muntari ya mu su magani haka su ka haɗu su ka ƙi karɓan wannan shawara. Su ka ce anriga anyi nisa da zancen Bello kuma ba daɗi azo a ce an fasa hakan zai jawo matsala tunda da Bellon da Auwal ɗin 'yan uwan juna ne. Maryam na komawa Zaria ta tattara kayan Zaytoonah ta ɗauketa su ka fita, ita kan ta Zaytoonah ba ta san inda za su je ba kawai binta ta ke yi. Yadda ta dawo babu walwala a fiskarta ya sa Zaytoonah ta sha jinin jikinta. Bauchi su ka je inda Maryam ta damƙawa Pendo amanar Zaytoonah zuwa lokacin da za ta buƙace ta. Ta kuma ja ma ta kunne akan kar ta yarda ta faɗawa kowa kan cewa Zaytoonah na wajen ta. Mijin Pendo lecturer ne a Jami'ar ATBU shiyasa tuntuni su ka bar Dutse da zama su ka dawo Bauchi. Itama Pendo ɗin ta cigaba da karatu dan ta kusa kammala degree ɗin ta a jami'ar. Ga sana'ar gyaran jiki da ƙunshi da ta ke yi ya karɓeta sosai, yanzu Pendo wacce 'ya'yanta ke kira da Ummi Hajiya ce. A ranan da ta dawo Muntari ya kira Maryam a waya, tana ɗauka sai ya kwashe da dariya ya ce "kin ɗauka ban san shige da fice ɗin ki ba ne? To ki ce Pendo ta yiwa Amarya Zaytoonah gyaran jiki da kyau dan aure ba fashi" "Muntari stalking ɗina ka ke yi?. For Allah's sake ka fita a harkata dan wallahi akan maganar Zaytoonah har kotu za mu shiga da kai kuma ba zan daddara ba sai na ci galaba a kan ka" *"idan kina so ki cececi 'yar ki daga auren nan, abu biyu za ki yi. Ki je a raba auren ki da Tijjani sannan ki aureni, ni kuma na miki alkawarin ko professor Zaytoonah ke son zama kafin ta yi aure to sai ta zama, babu mai ma ta auren dole. Kuma duk ƙasar da ta ke son zuwa karatu sai na kai ta"* Tana jin abinda ya faɗa ta kashe wayan tana huci. Ba za ta yarda ba, ba zai ma yiwu ba. Wasa-wasa sai ga shi a date ɗin da aka sa har ya saura wata ɗaya. Muntari har da turo ma ta text wai ya siyawa Zaytoonah kayan ɗaki ta zo ta gani idan akwai abinda babu ta faɗa. Ta yi tsaki ta tura ma sa "keep on dreaming" Tunda su ka yi zancen auren Zaytoonah da Auwal ya shiga cikin tashin hankali. Abu ne da ta jima da karanta cewa Auwal na son Zaytoonah, itama ta yi kwaɗayin zumuncin amma ba ta nuna ta san komai ba ne saboda tana so dukkan su su maida hankali a karatu. To gashi kuma Muntari ya zo da wata sabuwa. Ɗakin su ta buga ta ce ya zo tana son ganin shi. Kamar marar lafiya haka ya tashi daga kan gado ya sa jallabiya ya fito falo. "First son ya jikin?" "Da sauƙi Mommy" "Dan Allah kanada wani numbar Baffan ku Suleman ne? Wanda na ke da shi ba ya shiga" "Ya dena amfani da tsohuwar wayar sa an sace wayar. Ina da sabuwar numbar sa barin kawo miki" ya shiga ɗaki ya ɗauko wayar sa ya ba ta numbar ta saka a nata wayar. A take a wajen ma ta kira kuma aka ci sa'a ya ɗauka. Tana fara magana ya shiga ba ta haƙuri na rashin jin sa da su ka yi. Ta ce ma sa ba komai sha'ani na rayuwa. A tsanake ta ma sa bayanin abinda ke faruwa ya ce ta ba shi kwana biyar zai zo Zaria sai su yi maganar da kyau. Suleman ya bar Ringim da daɗewa ya koma Taraba da zama. Yadda ya ce ɗin hakan kuwa aka yi bayan kwana biyar da maganar su sai ga shi ya zo. Ya je ya samu Muntari ya ma sa faɗa ya nuna rashin jin daɗin sa akan abinda ya ke shirin yi. Amma sai Muntari ya ce ba ruwan Suleman cikin maganar 'ya dai tashi ce, ya fi shi iko da ita tunda yanzu T J baya nan. Suleman ya samu Maryam akan wannan magana fa inda ya hango shine tarihine ya ke son maimaita kan sa. Shawaran da zai ba ta shine ta kai ƙara Fada a sasanta su kawai. Tunda da shi da sauran Baffanun na su ba wanda zai ƙi bin maganan Sarki. Ya ce ta samu Dattawa ma su daraja su je su jagoranceta a Fada a yi maganar, ya tabbata Sarki zai sa a fasa auren nan domin adali ne. Da wannan shawara ta kwana bayan ta yi istikhara akai. Washegari da hantsi ta je gidan Alhaji Iliyasu. Bayan an ma ta iso wajen sa ta gaishe shi ta ce ma sa ta zo neman Alfarma ne akan ya representing ɗinta a Fadar Sarkin Ringim. Ya tambayeta mi ya ke faruwa ya ce ta gaya ma sa gaskiya. Maryam ta yiwa tsohon bayanin abinda ke faruwa gameda hukuncin da Muntari ya ɗaukar na aurar da Zaytoonah. Ba ta ɓoye ma sa sharaɗin da ya gindaya ma ta ba na ta aureshi shi kuma zai fasa aurar da Zaytoonah. "Ikon Allah. Duniya dai sai dai mu godewa Allah kawai. Yanzu Hassada da gaba ta mana yawa Allah ya shiryemu ya sa mu fi gane gaskiya" Maryam ta amsa da Amin. Shiru yai na kusan mintina goma har Maryam ta yi zaton ko dai akwai matsala ne dan tsohon sai a hankali. "Da za ki yarda ma sai na haɗa yarinyar da jikana da ke ƙasar waje. Sai ta yi karatun a chan dan shima Muhammadun Sarkin Boko ne. Abinda ya sa na faɗi haka shine ko da an fasa wannan auren ba haƙura zai yi ba. Ko ta ƙarfi ne zai iya ba da auren 'yar ki ko mi kika gani" Maryam ta sauke ajiyar zuciya. Ana wata ga wata. Ta bar gidan Alhaji Iliyasu Mai Auduga da niyyar za ta yi shawara ta dawo. *** It was a tough desicion amma kuma ta tabbata alama da ta gani kaman akwai Alkhairi a shawaran da ta yanke wa 'ya mace guda da ta haifa. Her first sign of motherhood... Idan Muntari na ji da kuɗi, Alhaji Iliyasu ya taka shi. Idan Asali ya ke ji da shi Alhaji Iliyasu ya ma sa fintinkau dan Alhaji sananne a ciki da wajen ƙasa, dan haka ƙarya ne ya ce zai ja da shi. Sai da aka je Fadan ma ashe Mai Martaba Sarkin Ringim ya san Alhaji Iliyasu domin Malamin sa ne, ya koyar da shi a Sakandare. Sarki yayi mamakin wai case ɗin da ya kashe shekaru kusan ishirin da biyar shine ya sake dawowa hannun sa. Bayan an gabatar da bayanai Sarki yai nasiha sannan ya zartar da hukunci na bayar da auren Zaytoonah ga Jikan Alhaji Iliyasu. Ranan da aka saka dai za ayi bikin ranan ɗin aka bari sai dai maimakon a family house da aka sa auren an maida shi cikin Fada za a ɗaura auren kuma kamar yadda Sarki ya zama Alwalin Maryam a lokacin auren su wannan karan ma shine na Zaytoonah. Ko Zaria ba ta koma ba ta aikawa Muntari da gajeren saƙo. *"Check Mate"* Yadda Muntari ya sha kunya a shekarun baya haka wannan karan ma ya amshi kashin sa a hannu. Maryam da kan ta je Bauchi ta ɗauko Zaytoonah. Da su ka koma gida ta zaunar da ita ta ma ta bayanin hukuncin da ta yanke ma ta. As expected kuka ta fashe da shi. Fushi sosai ta yi da Mommyn ta kulle kan ta a ɗaki tana faɗin Mommy ta tsaneta tunda ta yadda a aurar da ita duk da ta san burinta na son zama babbar Lawyer. As days past, Maryam ta dinga kwantar ma ta da hankali tana nuna ma ta karatu kam za ta yi shi dan sai ta samu admission ma kafin ta bar ƙasar. Still ba ta ji nitsuwa ba har da cewa ƙila mutumin mummuna ne. Maryam ta nuna ma ta hoton da Alhaji ya ba ta. Nan da nan Zaytoonah ta fara washe baki, atleast ba da wani mummunan mutum za a haɗa ta ba ko kuma wanda bai yi karatu ba. Tsabar ɗoki sai ta je ɗakin Auwal tana nuna ma sa hoton shi kuwa kishi ya sa ya korota. Ya riga ta ganin hoton infact ranan da su ka yi waya da Mommy ma yana wajen. Dan Maryam ba ta yarda da Auren ba sai da ta yi waya da yaron ta ji shi ɗin wani irin mutum ne ya kuma ɗauki Alkawarin zai bar Zaytoonah ta yi karatu har ta gama sannan ba zai walaƙantata ba... Ranan Jummu'ah 1 November 2009 aka ɗaura auren Zaytoonah Tijjani Abubakar da Muhammad (Zuhayr) Muhammad Iliyasu bisa sadaki dubu Hamsin wanda Kakan sa ya bayar. 'Yan uwa sun hallara kuma anyi hidima dai-dai gwargwado sai dai babu Muntari ciki. Shi tun da Sarki ya yanke hukunci a Fada bai sake zuwa Ringim ba. Zaytoonah kam kamar ba matar aure ba tunda ba yanzu za ta tafi wajen miji ba. Ta cigaba da rayuwar ta normal. Sai dai Mommy da ke takura ma ta da nasiha once in a while. An bata numbar Zuhayr amma bai kirata ba itama ba ta kirashi ba. Bayan wata uku aka sama ma ta admission a University of Nevada, Las Vegas. Shi mai girma Ango ɗin a Las Vegas ɗin ya ke aiki. Lokacin da aka gaya ma ta ranan wuni ta yi tana farinciki, barin ma da aka turo ma ta admission ɗin ta gani. Ita Auren ma baya gabanta karatu kawai ta ke hangowa tunda wata ɗaya da ya wuce Zuhayr ya kirata kuma sun tsara komai. Auren na su suna ne kawai amma zama za su yi tayi karatu har ta ƙare kafin ya saketa ta kama gabanta (🤔Tam) Bayan an confirming admission ɗin ne ta je ta fara processing visa wanda Alhaji Iliyasu ne ya ɗau nauyi. Ita da Mommy su ka je embassy aka yi cike-ciken takardu har komai ya kammala. Bai jima ba bayan sun dawo gida aka kirata akan Visa ɗin ta ya kammala. Dan haka aka fara shirye-shiryen tafiya. Sai da tafiyar ta zo kusa ne kuma jikin Zaytoonah yai sanyi, duk wani ɗoki da ta ke yi ya tafi. Kewar Mommy da ƙannenta ya fara shigarta. Komawa ma ta yi tana kwana da Mommy saboda wai ta ji ɗumin mahaifiyarta. Maryam ma daurewa ta ke yi amma tana jin wannan rabuwan a ranta. Addu'arta a koyaushe shine Allah ya sa auren nan ya zamewa Zaytoonah Alkhairi. A Abuja su ka kwana gidan Hajiya Fatima. Dukkan su suka zo rakiya, hatta Auwal da ke baya-baya da ita tun lokacin da aka yi aurenta sai da ya zo rakiyan. Anyi koke-koke tun ma kafin a je airport ɗin, saboda rabuwa ce da ba a san ranan haɗuwa ba kuma iya ka ci sai dai su ga juna a waya ko computer idan su ka hau skype. Rungume Mommy ta yi tsam tana kuka. "Mommy i'll miss you, i'll miss you so much. I love you" Maryam ma hawayen ne a idonta tana ɗan bubbuga bayan 'yar tata a hankali. Sai da aka fara kiran passenger ɗin jirgi mai number A2265 kafin Maryam ta breaking rungumar tana faɗin ki je kar ki missing jirgin. Ta rungume Salman wanda shima hawayen ya ke yi. "Ki dinga kiran mu kullum kin ji" Zaytoonah ta ce "Insha Allah" Auwal kam da sauri ya bar wajen ganin yana shirin yin kuka shima. Ta ɗaga junior sama tana faɗin " big boy ban da rigima" Ya girgiza ma ta kai yana dariya. Sai da ta ajiye shi ta fara jan jakarta tana tafiya bayan ta yiwa Mommy last hug. "Aytoonah" ta ji muryan Junior ta juya ta ganshi yana ɗaga ma ta hannu, yana hannun Mommy dan da bin Zaytoonah ya ke son yi. "Aytoonah Bye Bye ya ke faɗi har Zaytoonah ta ƙule" *** With full excitement ta shiga jirgin wannan ne karo na uku da ta taɓa shiga jirgi, sau biyu ta taɓa shiga jirgi zuwa Lagos tareda Muntari. Sau biyun kuma da za a tashi sai da cikinta ya wani juya ta sa hannu biyu ta riƙe shi dan kar ya zazzago a yadda ta ke tunani. Lokacin tashi da lokacin saukan jirgi duk sai ka ga ta tsure saboda fargaba. Business class ticket aka yanka ma ta dan haka za ta ɗan samu ta wataya kaɗan ba kamar zuwan su Lagos da su ke tafiya a ticket na economy class ba. Tana zama ta kalli mutumin da ke gefenta wanda ya ɗaga littafi yana karatu, littafin ya tareshi ba ta ganin full fiskarsa sai dai gefen fiskar sa sannan fararen dogayen yatsun da su ka riƙe littafin zai ƙara tabbatar ma ka mutumin fari ne sosai, tana tunanin ma ƙila Balarabe ne. Ta gyara zamanta da kyau tana miƙe ƙafa saboda akwai space sosai. Jakar da ke hannunta ta buɗe ta fidda wani ziplock bag da ke cike da plantain chips wanda Mommy da kanta ta soya ma ta. Ya san an zauna a gefen shi kuma ya lura mace ne shiyasa bai ma yi ƙoƙarin duba ta ba amma wani ƙanshi mai sanyi da ke fita a jikinta ya sa shi tantamar ko dai ya juyo ya kalleta ne, chan kuma ya ce ƙila matar aure ce. Ƙurumus ƙurumus ƙurumus. Ya fara ji alamun dai ana tauna crispy abu haka. Hakan ya sa ya ɗan sauke littafin da ke hannunsa ya juyo a hankali ya kalleta. Cikin abinda bai kai 2 seconds ba ya gane inda ya taɓa ganin yarinyar, ya ƙura ma ta ido yana tunanin irin wannan coincidence ɗin. Juyowar da Zaytoonah za ta yi sai su ka haɗa ido lokacin ta cika hannunta da plantain chips za ta kai baki. Sai da ta tura duka a bakinta ta miƙa ma sa ledar tana faɗin "wants some?" Ya girgiza ma ta kai ya maida littafin sa ya cigaba da karatu, ya ce a ran sa da alama ba ta gane shi ba. Ba a jima ba aka fara announcing akan a saka seat belt ayi wata tsiya-wata uba. Zaytoonah ta saka seat belt ɗin bayan ta maida sauran chips ɗin cikin jaka. Lokacin da jirgi zai tashi rufe ido ta yi ta damƙe hannun kujeran tana jero addu'o'i. Tsabar tsoro addu'ar da ta zo ranta kawai ta ke karantowa. "Subbuhun Quddusun Rabbil Mala'ikati War Rooh. Rabirhamhuma kama Rabbayani Sagira. Ya Mujibussalihina, Ya Malakul Mulk" haka tai ta ɓuruntun addu'o'i kala-kala har sai da jirgi ya dai-dai ta a sararin samaniya tukunna ta yi ajiyar zuciya ta buɗe ido, juyawar da za ta yi ta sauke su kan na Mutumin da ke gefenta. Shi ba ma'abocin dariya ba ne sai murmushi, amma da ya yi dariyar kalar addu'o'in da ta yi ta yi, yadda bakinta ke motsi ma kaɗai abin dariya ne. "What?" Ta faɗa tana ɗaga gira bai ce komai ba ya juya yana kallon window. Da aka zo za a serving na su lunch Zaytoonah har da na jaraba ta zaɓa. Yana gani yadda ta zage tana cin abincin da ya ke tunanin wannan cin kaɗai ya isa ya sa ta ƙiba. Duk abinda aka kawo sai da ta cinye shi tas. Shi ba ma'abocin surutu ba ne da ya tambayeta ko da sunan ta ne dan yarinyar ta burgeshi, she's funny. Da tafiya ta yi nisa TV da ke gabanta ta fara kallo ta sa headphone a kunnenta tana sauraro amma hakan bai hana bacci ɗaukan ta ba. Lokaci zuwa lokaci yana juyawa ya kalleta zuciyar sa cike da tunani kala-kala akan ta. Ƙila ɗaliba ce za ta koma makaranta. Ƙila kuma hutu za ta je. Ko kuma ma dai gidan Iyayen ta za ta koma ta zo Nigeria hutu ne. Dan da ka ganta ka san ita ɗin 'yar manyan mutane ce. Kayan jikinta da yanayin fatar jikinta kaɗai ka kalla ka san 'yar hutu ce. Da su ka zo sauka ne ya mustering courage ya ce "are you a student?" "Kutmelesi. Ashe kana magana? Shine tun tasowar mu ka yi shiru. Ikon Allah" ta faɗi da Hausa. Ganin ya ƙura ma ta ido ya sa ta tabbatar bai ji abinda ta ce ba. Ta wani turo baki ta ce "Yes, i'm a student" Ta yi gaba ta bar shi. A wannan lokaci he wished shi ma'abocin magana ne da ya nuna ma ta cewa ya ji abinda ta ce. He wish zai iya bin ta ya tambayeta sunan ta da makarantar da ta ke amma ƙasaita da sarautar sa ba za su bar shi ba. Tambayar da ya ma ta ma ya jima yana jujjuyawa a ransa kafin ya fito da shi waje da ƙyar ganin fa tabbas rabuwa za su yi daga nan kuma bai san komai gameda ita ba... *A nan na kawo ƙarshen free pages na chronicles of Zaytoonah. Za ki iya supporting ɗina ta hanyar biyan #300 domin samun cigaban labarin* *** *ya rayuwar auren Zaytoonah za ta kasance da Zuhair Muhammad Ilyas wanda ba ta taɓa gani ba sai a hoto?* *shin wace irin ƙaddara ke tattare da Zaytoonah ayayinda ta buɗe wani sabon babi a rayuwarta akan wannan aure da akayi bisa sharaɗi mai sarƙaƙiya?* *Muntari zai haƙura da Maryam kuwa? Ko kuma dai zai tuba ne ya faɗi abinda ya sa aka yiwa T J?* *shin bayan aurar da Zaytoonah Maryam za ta samu kwanciyar hankali? Ko kuma dai ya rayuwar ta zai kasance with the beast Muntari?* *wai ina T J ne? Yana raye ko ya mutu? Shin ma wai zai dawo ga iyalinsa kuwa?* *shin wanene wannan mutumin da Zaytoonah ta haɗu da shi har sau biyu sannan wani rawa zai taka a rayuwar ta?* *daga ƙarshe shin Barrister Zaytoonah za ta iya jayayya da ƙanin kakanta kuwa? Wato Augustus Udodiri Uzodinma, wanda ya kashe Kakannin ta ya kuma cinye dukiyar su?* Da sannu za ku gano komai a cikin paid group na labarin chronicles of Zaytoonah. *Don samun daman karanta cigaban labarin za a biya 300 ta account number kamar haka:* 3099546325 Firstbank Azizat Hamza *ko kuma katin MTN na 300 zuwa ga wannan numbar 08137311900* Za'a tura Shaidar biya zuwa ga wannan numbar still 08137311900 ko kuma ma dai domin ƙarin bayani za a iya tuntuɓar numban, preferably chat ko text. *Allah ya ba da ikon biya amin* 2/11/21, 10:04 PM - ****: 22 Bismillahir Rahmanir Rahim Cikin sati biyu ta kammala komai na makarantar ta ta zama full student. Sai dai ta je class ta ɗau darasi, har ta fara sabawa. A gida kam the same routine gareta kullum. Ta yi wanka ta ci abinci ta je makaranta, idan ta dawo ta ci abinci, kallo sai bacci. Duk bayan kwana biyu ta kan kira gida su gaisa. Kamar yadda Ben ya gargaɗeta ba ta shiga ko'ina a ɗakunan sama sai ɗakin ta. A ƙasan akwai study room, gym room, kitchen da dining akwai kuma ɗakuna biyu wandanta ke tunanin guest room ne. Kulkum sai ta ga Ben amma Zuhayr sai ta yi kwana biyu uku ba ta sa shi a ido ba. Ko sun haɗu tsakanin su gaisuwa ne sai shi ya tambayeta ya karatun?. Yau Sunday tana gida tun safe ba abinda ta ke yi sai bacci. Bayan ta tashi ta yi wanka ta fito daga ɗakin ta, haka kawai ta ji sha'awar duba ɗakunan saman ta ga miye a ciki da ake ɓoye ma ta. Ɗaki na gefen na ta ta fara dubawa wanda shima ɗakine kamar na ta sai dai furnitures ɗin ciki sun banbanta da na ta. Ɗaki na gaba da ta buɗe ta ji shi a rufe ta yi tsaki ta wuce gaba, ta sa hannu za ta tura ƙofar ta ji a dafa kafaɗarta sai da ta firgita. "Mi ki ke son yi?" Ta juyo a tsorace amma ganin Ben ya sa ta haɗe fiska ta ce "shine za ka tsoratani" "Na gaya mi ki iya limit ɗin ki a cikin gidan nan dan haka ki kiyaye" "Ni matar Zuhayr ce zan, iya shiga duk inda na ke so a gidan nan" ta faɗa da ƙarfi duk da kuwa yanayin da Ben ɗin ke kallon ta ya ɗan girgiza ta. "Stay within your limits" ya faɗa yana buga hannunsa a jikin bango. Da ƙyar ta haɗiyi miyau dan yadda ya bugi ginin sai da 'yan hanjinta su ka kaɗa "Its a warning, Zaytoonah"... Bayan ta sauka ƙasa ta hango Zuhayr yana cin abinci a dinning. "Tun safe ki ke bacci, ba kya gajiya da bacci ne?" "Ina ruwanka" ta faɗa tana zaunawa a kujerar da ke opposite ɗin sa. Kallon yadda ta ke cika plate ɗin ta da abinci ya ke yi yana mamaki a ran sa. Tana ɗaga ido idon su ya haɗu "ko abincin ma za a hanani ci ne? Tunda na ga komai a gidan ka doka ne" Zuhayr ya girgiza kai. Za ta sake magana sai ga Ben dan haka sai ta yi shiru. Bai wani ci abincin ba sosai ya tashi ya haura sama shima Ben ya bi bayan sa, mamakin maƙalemata da Ben ke yiwa Zuhayr ta ke yi. Kullum haka za ka ga yana bin sa kamar bindi. Ita kam jan girkinta ta yi mai kyau kafin ta bar wajen. Da yammacin ranan Zuhayr ya ce ma ta ta shirya za su je ƙauye gobe ta gaida Kakannin sa. "Dama a America akwai ƙauye ne?" Bai kulata ba sai dai murmushin gefen baki da yai. "Ehhm kwana nawa za mu yi?" Wannan karan Ben ne ya amsa ma ta da cewa ba za su kwana ba. Ta harareshi ta ce "shegen shishshigi, ko waya tambayeka oho" Zuhayr yana jin ta amma bai ce komai ba. *** A Helicopter ɗin sa su ka tafi wanda shi ne ya tuƙata, maimakon Dreban da ya tuƙo su rannan da ta fara zuwa garin. A tsakiyar filin da Dawaki ke kiwo ya sauka. "Masha Allah" ta furta lokacin da ta sauka. HADDISH RANCH kenan su ka iso, gidan gonan kakannin Zuhayr ta wajen uwa. Su na tafiya tana ma sa tambayoyi amma ko uffan ba ya faɗa, wani lokaci Ben na amsa ma ta tambayoyin wani lokaci shima yai shiru. Ta ga alama shi Zuhayr idan ba shi ya kawo magana ba baya so a ma sa magana. Haka dai su ka ƙarisa madaidaicin gidan da ke tsakiyar gidan gonan. Tana tsaye Zuhayr ya je ya kissing goshin wani tsohon bature da ke zaune akan sofa yana karatu, shima Ben ɗin haka ya ma sa. Ba ta ji mi Zuhayr ya ce da tsohon ba dan ƙasa-ƙasa yai maganar, ta dai ga tsohon ya ɗaga ma ta hannu alaman ta zo. Ta ƙarisa wajen sa ta tsugunna ta ce "good morning GrandPa" "Morning pretty girl" ya amsa yana murmushi itama murmushin ta yi tareda miƙewa. A kitchen su ka haɗu da GrandMa tana girki. Matar tana kama sosai da mahaifiyar Zuhayr. Itakam bayan Zuhayr ya nuna Zaytoonah zuwa ta yi ta rungumeta tana yi ma ta maraba da zuwa gidan gonan su. Zuhayr da Ben su ka bar ta a kitchen ita da GrandMa. Tsayawa ta yi tana kallon kitchen ɗin wanda yawanci abubuwan ciki tsofi ne. GrandMa ce ta katse shirun da cewa "ina fata Zuhayr yana kula da ke?" Zaytoonah ta gyaɗa ma ta kai. "Yana cikin kaɗaici har yanzu. Da ya faɗamin an ma sa aure a Nigeria na ɗauka babbar mace ce amma sai ya ce ba ki ma kai 18yrs ba" " yes, just recently na cika 17yrs" " ki kula da shi" Ta furta tana buɗe oven. Cikin zuciyarta ta maimaita kalmar da tsohuwar ta faɗa tana ƙoƙarin gane me ta ke nufi da hakan. Ƙarfin hali ta yi ta tambayeta abinda ke ci ma ta tuwo a ƙwarya tun zuwan ta Vegas. Abinda Muhsina ta gaya ma ta gameda Zuhayr bai gamsar da ita ba ga ɗimbin tambayoyin da ta ke da shi a kan sa. "Waye Zuhayr?" GrandMa ta kalleta na ɗan wasu daƙiƙai kafin ta ce " kar ki damu za ki san kowaye shi a hankali"... Bayan ta gama girkin, Zaytoonah ta taya ta jerawa a kan dinning area ɗin wanda duk a cikin kitchen ɗin ne. Sannan aka kira mazan su ka shigo dan aci abinci. Shepherd pie ɗin da aka yi aka yanka shi kashi shida kowa aka sa ma sa yanka ɗaya a plate ya saura yanka ɗaya a glass bowl ɗin. Zuhayr ya sa sokali ya ɗau sauran ya ɗaura shi a plate ɗin Zaytoonah. Kallon sa ta yi ta na kumbura baki, yanzu ya nunawa Kakanninsa ita acici ce. Shi kuwa ko a jikin sa ya zauna ya fara cin na shi. Yadda pie ɗin ya ma ta daɗi kuwa tas ta cinye tana lumshe ido, da da ƙari ma za ta ƙara, ashe dai gara da Zuhayr ɗin ya sa ma ta ɗaya slize ɗin, da slize ɗaya ta ci ba inda zai je. Su turawan nan sai su riƙa cin abinci kamar yara ƙanana. Bayan sun gama cin abinci Kakannin Zuhayr su ka ce za su nuna ma ta gidan gonan su wanda a ciki aka haifi mahaifiyar Zuhayr, a nan tayi ƙuruciyarta har ta girma. Wajen Shanu su ka fara zuwa, ta ga yadda ake tatsar nono da inji ba da hannu ba. Su ka je wajen Kaji ma ta gan su dayawa, wajen dawakai su ka wuce inda tuni su Zuhayr da Ben suna kan doki su na gudu. Bayan sun iso wajen da su ke tsaye sau su ka tsaya. Kallon su ta ke yi cike da sha'awa. Mr Haddish ya tambayeta ko za ta hau dokin, ta gyaɗa kai. Zuhayr ya ce "kin taɓa hawa doki ne?" "There's always a first time" Bai ce komai ba ya sauka ya taimaka ma ta ta hau, yana riƙe da linzamin dokin, Zaytoonah ta ce Mrs Haddish ta mu su hoto. Bayan anyi hoton da wayar Mr Haddish sannan ya fara jan dokin a hankali suna tafiya. Zaytoonah baki kamar zai yage tsabar dariya an hau doki. Sun ɗan yi nisa kaɗan Zuhayr ya tsaya saboda wayar sa da ke ringing ya tsaya amsa wayar ya sake linzamin ba tareda shi ko Zaytoonah sun lura ba Ben da ke gefe shima akan doki ya zaburar da dokin da Zaytoonah ke kai, nan da nan dokin ya hau gudu. Ihu Zaytoonah ta fara ganin yadda doki ke sheƙa gudu da ita. "Mommy, Mommy, Zuhayr, Zuhayr help, somebody help" Dif sai ga ta a ƙasa dokin ya yarda ita cikin ciyawa. Har su Zuhayr su ka iso inda ta ke ba ta ihu ba. Ya miƙa ma ta hannu dan ya taimaka ma ta ta tashi ta saka kuka tana kiran ƙafarta. Girgiza kai yai ya sa hannu zai ɗauketa Ben ya tareshi. "Ba za ka iya ɗaukan ta ba, tanada nauyi, kuma daga nan zuwa gida akwai nisa" Zai yi magana ya ce bari ya kira azo a ɗauketa da mota. Zaytoonah ganin ba wanda ya kulata ya sa ta cigaba da kukanta tana kiran ƙafarta. Maimakon Mota Amalanken shanu ne ya zo. Zuhayr da Ben su ka cicciɓeta su ka sa ta a bayan Amalanken. Zuhayr ya zauna da ita yana ma ta sannu haka aka ƙarisa da su ƙofar gidan. Ben a doki ya biyo su amma idon sa ƙyam akan Zuhayr saboda ko kaɗan baya so jikin sa ya raɓi na Zaytoonah sai dai idan dole ne. Ɗaki aka kwantar da Zaytoonah ana tambayar ina ne ke ma ta ciwo amma ta ƙi faɗa sai kuka. Mrs Haddish ta kira Likita wanda bayan minti shabiyar sai gashi ya zo. A gaban su ya fara duba ƙafan Zaytoonah inda ya ga targaɗe ta samu a ƙafan na ta, sai kuma gefen bakin ta da ya ɗan fashe. Bayan ya ma ta duk abinda ya dace ya ce ta huta kada ta yi amfani da ƙafar yau, zai zo gobe da safe ya ƙara dubawa. Tsofin sai sannu su ke ma ta kamar su suka sa ta hawa dokin. Shi kuwa Ben ya so raunin da Zaytoonah ta samu ya fi haka. Su da su ka zo da niyyar ba za su kwana ba sai ga shi za su kwana. Ben ba yadda bai yi da Zuhayr ba akan su koma Vegas idan ya so gobe sai ya aiko Driver ya ɗauko Zaytoonah amma ya ƙi ya ce Zaytoonah respinsibitity ɗin sa ce yanzu. "Ka chanja plan ɗin ka ne?" Ya tambaya cike da fargaba dan ya san deal ɗin da Zuhayr yai da Zaytoonah. Zuhayr ya girgiza kai ya ce "a'a, na ɗauketa ne kamar ƙaramar ƙanwata ka ga kuwa dole na kula da ita. Besides na yiwa mahaifiyarta Alkawarin kula da ita kuma ka san ba na wasa da alƙawari" Ben ya gyaɗa kai cikin gamsuwa da bayanin abokin na shi. Ɗakin da Zaytoonah ta ke Mrs Haddish ta tura Zuhayr ta ce ya kwana da ita kar ta buƙaci wani abu cikin dare. Kamar ba zai yarda ba sai kuma ya amince da hakan, Ben yana gefe ya kumbura yayi fam kamar zai fashe. Yana gani Zuhayr ya buɗe ƙofa ya shiga ɗakin da Zaytoonah ke kwance. Lokacin da ya shiga ɗakin ma Zaytoonah ta yi bacci, ya ƙarisa gareta ya gyara ma ta bargo sannan ya koma wajen kujera ya kwanta... *** Muhammad Ilyas ɗa ne ga Alhaji Iliyasu Mai Auduga wani fitattaccen attajiri wanda ya ke da gonakan Auduga. A lokacin da Nigeria ke taƙama da Albarkatun Gona irin su Auduga, Gyaɗa, Robber, Cocoa, etc wajen samun kuɗin shigar ta. Alhaji Iliyasu na ɗaya daga cikin wanda su ke fita da Auduga ƙasashen waje. Matan Alhaji Iliyasu biyu ne Hajiya Nenne da Hajiya Saudah. Hajiya Nenne sai da su ka shekara goma da ita kafin ya auri Hajiya Saudah 'ya'yan su uku Mata da Hajiya Nenne. Ita kuma Hajiya Saudah a shekarar farko da auren su ta haifi namiji aka sa ma sa Muhammad bayan shi sai da ta haifi mata uku kafin ta haifi Aliyu. Ita kuwa Hajiya Nenne ta haifi namiji sau ɗaya bai zo da rai ba dan haka yaranta shiida duka mata ne. Da ke Muhammad ne ɗa namiji na farko a wajen Alhaji Iliyasu sai ya zama yana nuna ma sa tsananin so. Ko kaɗan baya so a taɓa shi yanzu za ka ga ya hau faɗa. Bayan ya ƙare karatun secondary a Nigeria ya tura shi karatu a Harvard da ke Ƙasar America. Rayuwar turawa ya chanja Muhammad sosai, shine giya shine neman Mata. Ba shi da matsalar kuɗi tunda mahaifin sa yana tura ma sa. Bayan ya ƙare karatu Mahaifin sa ya buƙaci ya dawo ya dafa ma sa akan harkan noma da kasuwanci amma ya nuna ba zai dawo ba domin shi fa zaman America ya fi ma sa akan zaman Nigeria. Wannan ya sa Alhaji Iliyasu ya dena tura mi shi kuɗi tunda ya ƙi bin umurnin sa. Wasa-wasa sai abubuwa su ka fara ja baya saboda ba kuɗi, gashi Visar sa ta kusa ƙarewa tunda karatu ya zo yi kuma ya ƙare. Sai ya koma kuɗin da zai yi buƙatun da ya saba ma babu. Hakan ya sa ya nemi aiki a wani restaurant a matsayin waiter. Tunani yai akan idan ya auri baturiya su ka haihu zai zama citizen ɗin ƙasar America dan haka sai ya fara neman yarinyar da zai nemi soyayyarta ta yarda ta aureshi. Lucile-Abigail Haddish 'ya ce ga Thomas Haddish da Veronica Haddish. Iyayenta ita ɗaya su ka haifa a ƙaramin ƙauyen su da ke ƙarƙashin Clark County. Suna da babban gidan gona inda a nan su ke samun duk wani kuɗin shige da fice. Bayan Lucile-Abigail ta gama makaranta ta fara internship na ta wanda ya ke kamar bautar ƙasa kenan a Carson City, Nevada state. 'Yar ƙauye ce da ta yi karatu amma duk da haka ba ta da wayewar 'yan birni. Tanada mentality ɗin za ta samu prince Charming ɗin ta wanda za su yi aure su rayu happily ever after. Ta haɗu da Muhammad ne a restaurant ɗin da ya ke aiki. Bayan ta gama cin abinci sai ya zo karɓan kuɗi sai ta duba jakarta ashe ta manta ba ta sa purse ɗin ta a ciki ba. Ƙarshen magana dai Muhammad ne ya biya ma ta ya ce ta tafi ba komai. Washegari sai ga ta ta dawo restaurant ɗin ta bashi kuɗin jiya amma ya ƙi karɓa ta yi-ta yi da shi ya ce ya yafe ma ta. Daga nan su ka ƙulla abota wanda ta kai su ga soyayya. Da zuciya ɗaya Lucile ke son Muhammad amma shi da biyu ya ke son ta. Kafin ta gama internship ɗin ta sai da ta kaishi ƙauyen su su ka gaisa da Iyayen ta, ba su yarda da maganar da ta kawo mu su ba na cewa ta yi saurayi. Saurayi baƙin fata, ɗan Nigeria kuma Musulmi. Bayan ta gama internship ɗin ta ta koma gida inda ta nunawa iyayenta auren Muhammad za ta yi saboda shine Prince charming ɗin ta. Iyayen ta su ka ƙi sam da maganar wannan ya sa Lucile ta bar gida ta koma wajen Muhammad su ka yi auren kotu. Rayuwa ta cigaba da tafiya har Shekara ɗaya wanda a nan ne Lucile ta samu ciki. Zo ka ga murna gun ma'auratan musamman ma Lucile. Da ciki ya kai wata tara ta haihu inda ta samu ɗa namiji. Muhammad ne da kan sa ya sawa yaron suna Muhammad Zuhayr amma Zuhayr su ke kiran sa. Dama sun yi idan mace ne Lucile za ta sa ma ta suna idan kuma namiji ne Muhammad zai sa ma ta. Bayan haihuwan Lucile da shekara biyu ta fara ciwo. Bayan ciwo da ta ke yi har da rashin kwanciyar hankali saboda chanjawar da Muhammad ya fara yi ma ta. Da ta fara zuwa asibiti ne aka fara gwaje-gwaje har aka tabbatar tana da Leukemia wato cancer ta jini. A wannan jinyan da ta yi ne iyayenta su ka zo kuma su ka yafe ma ta bisa guduwa da ta yi daga gida ta auri Muhammad. Ta ɗau watanni kafin aka ce ta warke. Abubuwa dai bai yi dai-dai ba bayan jinyar da ta yi inda daga baya bayan ta kama Muhammad da wata co-worker ɗin sa a office ta nemi ya sake ta. Bai so haka ba ya dinga neman yadda zai yi ta yi haƙuri amma ta ƙi. Ta riga ta sawa ranta rabuwa za ta yi da shi dispite the fact tana son sa sosai. Bayan sun rabu ta ɗau ɗan ta ta koma gidan iyayen ta inda a nan ta maida hankali wajen kula da gidan gonar su. Da farko Muhammad sai da ya ɗau watanni bai nemeta ba sai daga baya ya fara zuwa duk wata sau ɗaya yana ganin ɗan sa har lokacin kuma yana son maida auren su da Lucile dan sai da su ka rabu ya gane ya fara son ta tsakani da Allah amma Lucile ba ta ba shi fiska ba. Wannan ya sa yai ƙoƙarin dawowa kusa da su ya zauna a Las Vegas inda ya samu aiki da wata kamfani. Ya cigaba da ɗebe-ɗeben Matan shi amma har lokacin ba ya jin zai iya auren wata ba Lucile ba. Lokacin Zuhayr na shekara tara Leukemia ɗin Lucile ya dawo aka fara ziryan Asibiti da ita. Lokacin da jinya ya tsanan ta aka ce ba za ta wuce wata shida ba za ta mutu, wannan ya sa a karo na ƙarshe da Muhammad ya nemi su maida auren su sai ta yarda da hakan saboda har lokacin akwai soyayyar Muhammad a tattare da ita. A gidan gonan Iyayen ta su ka zauna bayan ta buƙaci hakan. Watan ta huɗu ta mutu bayan ta sha fama da cancer dan har gashinta ya fara kakkaryewa. Mutuwar ta taɓa Muhammad matuƙa, ya yiwa kan sa karatun ta nitsu yana so ya je ya nemi iyayen sa gafara amma ya fi so ya tafi da ɗan sa Zuhayr sai dai iyayen Lucile da dama sun saba da yaron su ka ƙi fir, dan su tunanin su ma Muhammad guduwa ya ke son yi da Zuhayr. Bayan sun ƙi ya tafi da ɗan sa ne sai ya shigar da ƙara dan really yana so ya koma Nigeria ya kuma tafi da ɗan sa dan ya ma sa tarbiyyan musulunci dan yadda yaron ya taso ba abinda ya sani gameda Musulunci. Sai dai ya shigar da ƙara amma bai yi nasara ba domin kotu iyayen Lucile su ka damƙawa Zuhayr tareda cewa zai zauna da su har shekara shatakwas kafin ya zaɓi inda ya fi ma sa ko ya zauna da su ko ya koma wajen Uban sa. Da haka Muhammad ya koma Nigeria ya bar Zuhayr a wajen kakannin sa. Da ya je Nigeria fa cikin 'yan uwan sa kowa fushi ya ke da shi dan mahaifin sa ma cewa yai ya koma inda ya fito. Abu da ɗa da uba bayan ya nemi manyan mutane sun tayashi roƙon mahaifiyan sa sai ya yafe ma sa. Cikin ƙanƙanin lokaci kuma ya settling a Zaria har aka fara ƙoƙarin haɗa shi aure da wata'yar uwar sa sai dai ƙarar kwana ya zo ya hana hakan tabbatuwa, domin Muhammad hatsarin mota yai da shi da ɗan uwan sa Aliyu. Shi ya mutu amma Aliyu ya rayu raunuka kawai ya ji. Dalilin rasuwan Muhammad ya sa daga baya Alhaji Iliyasu ya fara bibiyan jikan na sa wanda har chan wajen Iyayen Lucile ya je ya karɓi Zuhayr a lokacin hutu akan zai zo Nigeria ya ga 'yan uwan mahaifin sa. Ba su so ba amma da ya takura sai su ka je gaban hukuma ya rubuta yarjejeniya akan zai dawo da shi bayan sati huɗu. Hakan kuwa aka yi bayan sati huɗu ya dawo mu su da Zuhayr. Tundaga lokacin ya ke bibiyar jikan na sa dan ya saba da shi, lokacin da girma ya kama Alhaji Iliyasu ne ma ya rage zuwa wajen sa sai dai Ɗan sa Aliyu wanda shima daga baya aiki ya kaisa America yana zuwa wajen ɗan Yayan na sa shima kuma yana zuwa inda su ke lokaci zuwa lokaci. Raɓuwa da 'yan uwan mahaifin sa ya sa shi fara Sallah da admitting musulunci a matsayin addinin da ya zaɓa sai dai duba da inda ya taso da mutanen da ya ke mu'amala da su addinin ba wai ya shige shi har chan ba ne... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 23 Bismillahir Rahmanir Rahim Yau ita da kanta ta ke girka abinda za ta ci. Ta yi missing girkin irin na gida Nigeria dan haka ta shiga kitchen ta fara dafa farar shinkafa da jar miya wanda ya ji nama zuƙu-zuƙu, da ke akwai albasa mai lawashi, bayan ta gama miyar sai ta kashe gas ɗin sai ta zuba albasar da ta yanka ƙanana ciki ta raugaya ta rufe, ta ɗau plate ta cika shi da shinkafa ta sa sokali sai ta ɗau wani bowl ta zuba miyan a ciki. Ta sa a ƙaramin tray ta ɗauka ta nufi ɗaki dan karatu ma take yi yunwa ya fito da ita ba kuma yunwan ba kaɗai kwaɗayin shinkafa da miya ta ji. Tana haurawa stairs ta ci karo da su suna saukowa dukkan su suna ɗaure da towel a ƙugu. Rintse idonta ta yi ta takure gefe guda, alamun wucewa da ta ji ne ya sa ta buɗe ido sai kuma ta tsinci idonta cikin na Zuhayr. "Abincin be mi ki yawa ba?" Ta murguɗa ma sa baki ta ce "to sai ka min gori kuma tunda abincin gidan ka ne" Bai yi magana ba kawai ya cigaba da sauka. "Kuma a daina yawo tsirara acikin gida" bai juyo ba amma yayi murmushi. Ben da ya riga ya kai ƙasa kuma idon sa akan Zaytoonah yana aika ma ta wani mugun kallo. Bayan ta shiga ɗaki a kan gado ta baje kolinta inda ta buɗe laptop tana kallon wani tutorial ɗin da aka mu su jiya, tanayi tana cin abinci. Ta ci kusan rabi sai ga kiran Mommy a wayanta, katse kiran ta yi dan ta san yadda MTN za su zuƙe ma ta kuɗinta cikin ƙanƙanin lokaci. Bayan ta kirata su ka fara gaisawa inda Mommy ke tambayarta ya karatu ta ce Alhamdulillah. Karatu akwai daɗi akwai kuma wahala. "Fatan kina yiwa mijin ki biyayya?" "Yes Mommy" "To Allah ya miki Albarka" Zaytoonah ta amsa da amin. Kafin ta kashe wayar sai da ta tambayeta ko akwai matsala ta ce ma ta babu. Duk da hoton da Zaytoonah ta tura mu su recently ya nuna tana cikin jin daɗi saboda ƙiba da ta ƙara gashi tayi wani fresh da ita, skin ɗin ta na glowing. Amma kuma hakan bai hana Maryam fargaba ba a koda yaushe gani take kamar ba ta yiwa Zaytoonah adalci ba, aurar da ita da ta yi da wuri haka, ga kuma mutumin da ba ta taɓa haɗuwa da shi face to face ba sai da ta je gidan shi. Addu'arta a kullum Allah ya daidaita tsakanin su. Ben da Zuhayr wajen swimming pool su ka je da ke ta bayan gidan inda su ka cire towel ɗin jikin su ya saura boxers kaɗai su ka faɗa cikin ruwa. Sun kai 30mins aciki suna wasa kafin su ka fito suka goge jikin su da towel su ka zauna a rumfar da ke gefen swimming pool inda tuni Chef Green ya jera mu su desert da drinks a wajen. "Ina tsoro" Ben ya faɗa yana kallon Zuhayr da ke kwance yana karatu. Zuhayr ya saukar da littafin ya kalli Ben ya ce "tsoron me?" "Ina tsoron kar ka faɗa soyayyar yarinyar nan, na ga ka fara damuwa da ita sosai" Zuhayr ya ce "ba zai faru ba. Na riga na gama soyayya a rayuwata. Kar ka manta yarinya ce" Ben ya girgiza kai amma cikin zuciyar sa yana wasi-wasi. Tun da su ka dawo daga gidan Kakannin Zuhayr ya ke lura da shi gameda wasu changes da ya ke gani gameda Zuhayr ɗin. Kamar idan baya gari zai kira shi sau ɗaya ko sau biyu ya tambayeshi lafiyar Zaytoonah, idan kuma yana nan idan bai ji motsinta a gidan ba kuma ya san ba ta je class ba zai leƙa ɗakin ta ya tambayeta ko lafiya. *** Yau ta ke jummu'a kuma saura kwana goma shabiyu su Zaytoonah su fara jarrabawa. Ta yi wanka ta fito ta shafa mai ta ɗauko wani gown ɗinta na Atamfa wanda daga gida ta zo da shi. Rigan da ya ke ma ta ruwa da sai gashi yau da ƙyar ta saka shi. Wajen zuge zip kuwa yana kaiwa tsakiya ya ƙi motsawa, tayi-tayi ya ƙarisa zugewa ya ƙi. Ta kalli kan ta a madubi tana ɗan jujjuyawa. "Ya Allah Zaytoonah ba dai ƙiba na ƙara ba?" Daga jikin ƙofa ya ke tsaye yana kallon ta tun lokacin da ta ke struggling ɗin buɗe zip ya shigo amma ba ta ganshi ba shima kuma bai ƙarisa wajen ta ba. Ganin dai Zif ɗin ba zai zugu ba sai ta fara ƙoƙarin cire kayan. "Ehm Ehm" ta ji gyaran murya a bayanta dan haka ta juyo da sauri. "Indai kika cigaba da cin junk food duk wata sai kin chanja wardrobe" "Ina ruwan ka" Ƙarisowa yai wajen gado ya ajiye ma ta wata leda ya ce kayan da za ta sa gobe kenan saboda suna da party a company. Ya ƙara da cewa "na gwada size ɗin ki ne da ɗaga daga cikin kayan ki. Amma ki je ki gwada kar ya zama kayan zai miki kaɗan" "To zage ni, ka ce kawai ƙibana ya tsole ma ka ido abinda ko da kuɗi ba za ka iya samu ba" ta ƙarisa maganar tana jujjuya ido. Fita yai daga ɗakin dan shi bai iya dogon magana ba. Sai da ta ga ya fita ta je ta sa makulli a ɗakin. Box uku ne a cikin ledan da ya ajiye dan haka babban box ɗin ta fara buɗewa wanda ta ga wani Designer gown mai kyau kalar abin cikin ƙwai an shimfiɗa acikin box ɗin, ta ciro shi tana ƙara kallon sa a ido dai tsayin zai ma ta sai dai tana shakkar shigan sa jikin ta. Ta cire rigan jikinta wanda da ƙyar ya fita. Ta saka kayan da ya kawo abin mamaki kuma ya shigeta sai dai da ke ta saman dama a matse ya ke lokacin da ta zuge zip ɗin sai ya sake matse nonuwanta wanda su ka cika suka yi fam, wannan baya ma buƙatar bra dan shi kaɗai rigan ma yana aikin bra. Ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta yadda rigan ya ma ta kyau sosai. Bayan ta gama jujjuyawa gaban mirror sannan ta koma wajen sauran box ɗin biyu. Ɗaya box ɗin takalmi ne shima mai kyau flat pumps wanda tana tunanin ya siya ne saboda ya ga irinsa ta ke sawa. Ɗaya ƙaramin box ɗin kuma sarƙa da ɗankunne ne ma su kyau sai sheƙi su ke. Washe gari ƙarfe shaɗaya saura na safe ta gama shiryawa cikin kayan da ya kawo ma ta. Sai dai ba za ta iya fita ba tareda ta rufe kan ta ba. Cikin veils ɗin da ta ke da shi ta nemi wanda zai shiga da kayan ta. Wani ja ta ɗauka ta ɗaura a kanta irin ɗaurin turban ɗin nan, sai ta ɗauki wani red purse wanda ta siya wani fita shopping da ta yi ru. farko-farkon zuwanta. Lokacin da ta fito suna tsaye a ƙasa suna jiranta, dukkan su sun yi shigan baƙin riga baƙin jeans da baƙin blazer. Kallo ɗaya Zuhayr ya ma ta ya kauda kan sa. Kafin ta ƙariso su ka yi waje dan haka itama wajen ta bi su inda Driver ke jiran su. Ba ta sha mamaki ba lokacin da ta ga Zuhayr da Ben sun shiga baya. Bayan ya kamata ta shiga dan har lokacin Driver be kulle ba amma sai ta buɗe gidan gaba ta shiga. Ba wanda yai magana har su ka isa inda za su je. A bakin tamfatsetsen building ɗin kamfanin aka tsaya inda kafin ta buɗe wani da ke tsaye a wajen ya buɗe gidan baya inda Zuhayr ya fara fitowa, itama ganin haka ta buɗe ta fito. Dukkan su uku su ka jera su ka shiga ciki tana gefen Zuhayr shi kuma Ben na gefen sa. Zaytoonah kam duk abinda ake gudanarwa na ta ido, ta sha gaisuwa kam dan Zuhayr da ƙanwar sa ya ke introducing ɗin ta a abokanan aikin sa. Bayan an gama pleasantries aka zazzauna inda aka fara serving abinci. Table ɗin su su bakwai ne ke zaune akai, ita ɗaya ce mace. Ba abinda ta iya ci a wajen saboda wajen bai ma ta ba a takure ta ke, gashi kuma abincin tsoron ci ta ke yi saboda strictly cuisine ɗin turawa ne, tana tsoron kar ta ci ya ɓata ma ta ciki kamar yadda a gida watarana da karambani ta ci wani girkin Chef Green sai gashi awa ɗaya bayan ci ta ɓarke da gudawa. Wata sexy Mace ce ta zo ta zauna a kujera ɗaya da ya rage ba mutum kuma kujeran opposite da na Zaytoonah ya ke. "Sorry i'm late for the party guys" ta faɗa lokacin da ta zauna. Kallon Zaytoonah ta yi ta kauda kan ta sannan ta kalli Zuhayr da ke gefen Zaytoonan ta tambayeshi wayece baƙuwar cikin su. "A Sister" ya faɗa a hasale 'Yar dariya ta yi ta ce "ban san cikin 'yan uwan ka na Nigeria akwai ma su kama da doya ba" Gaba ɗaya wajen sai aka kwashe da dariya. Zuhayr ya watsawa Matar wacce aka kira da Scarlet harara. "Sorry Zoheer, i just express my mind, she really looked like a Yam" ta faɗa tana wani munafukin murmushi. Tunda su ka fara dariya ta ke kallon su ɗaya bayan ɗaya har ta tsaya akan Zuhayr wanda bai yi dariya ba amma bai cewa Scarlet komai ba. Wine cup da ke gaban Mr Morgan wanda ya zauna a gefenta ta ɗauka ta miƙe tsaye ta watsawa Scarlet a fiska ta ce "Listen to me you old hag. My name is Zaytoonah and i'm not a YAM, but you" ta nunata da yatsa "you are a disgusting racist bitch" Ta ja kujera ta ɗau purse ɗin ta ta ce "fuck you all" ta faɗa tana ɗaga mu su yatsar ta ta tsakiya. Tafiya ta ke yi da sauri kamar za ta tashi sama, tsanar kan ta tayi na dalilin ma biyo shi wannan Party da ta yi. Ba wai sunan ne kawai ya ba ta haushi ba sai yadda Zuhayr yai shiru bai kareta ba. Kenan shima kallon Doya ya ke ma ta? Ji ta yi an kama hannunta, ta juyo a fusace sai ta ga Zuhayr ne. Ta yafce hannunta ta juya za ta cigaba da tafiya ya sake riƙe hannun yana faɗin "wait" "Ka ga ka sake ni, ka sake ni dan cin mutuncin ya isa haka" "Zaytoon..." "Doya aka kirani a gaban ka kayi shiru, Doya fa" "Zayt..." "Ba sai ka yi bayani ba na san kai ma abinda ka ke ganina da shi kenan. But let me tell you i'm proud of myself, i'm proud of my chubby self" "Lets go home" ya furta a hankali... Har su ka iso ba wanda yai magana a gaba ta zauna kamar yadda ta zo sai dai lokaci zuwa lokaci tana ɗan goge hawaye da bayan hannun ta. Mota na tsayawa a ƙofar gidan su ta shige cikin gidan da gudu. Ta faɗa kan gado ta fashe da kuka, kuka sosai ta ke yi. Rabon da ta yi kuka saboda an ma ta maganar jikinta tanaga tun tana SS1. Ko da auren su ba wai jimawa zai yi ba atleast ya kamata ya defending na ta a wajen nan amma yai shiru yana ji ana ma ta dariya. Tana cikin kuka ta ji ana ƙwanƙwasa ma ta ƙofa amma sai ta ƙi buɗewa. "Zaytoon we need to talk" "Go away" ta faɗa da ɗan ƙarfi. Ya ƙara ƙwanƙwasawa kusan sau uku kafin ya haƙura ya tafi. Ƙarfe bakwai na yammaci ta fito daga ɗakin ta, ta yi kukan ta yi baccin ta gaji. Ɗan karan yunwa ta ke ji dan tun safe rabonta da abinci, ɗan cookie da ke jakarta na makaranta ta cinye amma ba abinda ya ma ta. Ta fito daga ɗakinta tana tafiya a hankali dan jiri-jiri ma ta ke ji saboda yunwa. Dai-dai ɗakin da ta ke ganin Zuhayr na shiga ta tsaya ganin ƙofar ɗakin a ɗan buɗe. Ɗaki ne da ba ta taɓa shiga ba ba ta ma san ya yake ba, duk da tana fushi da shi bai hanata ɗan leƙawa ba dan ta ga miye a ɗakin ake hanata shiga tuntuni. Ba kaman ma Ben da ko kallon ɗakin ba ya so tayi. Numfashinta ya kusa ɗaukewa lokacin da ta leƙa kan ta cikin ɗakin ta yi baya da sauri tana dafa ƙirjin ta. "Zuhayr da Ben" ta furta a fili tana kama baki... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 24 Bismillahir Rahmanir Rahim Nigeria A ɓangaren Alhaji Muntari tunda aka yi auren Zaytoonah ya kasa zaune ya kasa tsaye. Da ita ya dogara wajen samun Maryam amma komai ya zo ya warware. Cikin ƙanƙanin lokaci ya haukace da neman mafita wa Kan sa. Bayan wani lokaci ya barwa kan sa zaɓin yiwa Maryam asiri dan ta so shi. Ɗantani ya nema don su sake zuwa wajen Malam Yusha'u wanda yai wa T J kurciya. Sai dai Ɗantani ya ce ma sa Malam ya bar ƙasar Chad kuma bai san inda ya koma ba, shima bayan sun je da Alhaji Muntari ya sake zuwa dan a yiwa wani aiki amma bai sameshi ba. Ance ma sa Malam ba ya zaman waje ɗaya ya jima, da ya ɗan kwana biyu sai yai gaba haka ya ke yi. Muntari ya shiga wani sabon tashin hankali haɗe da danasanin yin asirin tun lokacin da aka yiwa Tijjani. Ko da ya ke ya ɗauka za ta so shi ne idan ta rasa T J to yanzu babu T J ɗin amma ta ƙi amincewa da shi. Ƙarshe dai gidan jiya ya koma neman Malaman tsubbu da bokaye amma shiru ka ji. Cikin haka ne shagunan sa biyu a Kano su ka ƙone, hakan ya ɗaga ma sa hankali matuƙa dan yayi asarar dukiya dayawa... Dawowan ta kenan daga school inda ta biya makarantar su Junior ta ɗauko shi wanda shima ya fara Pre-Nursery. Tana shirin buɗe ƙofa Junior na buga food flask ɗin sa a jikin ƙofar ta ji an kira sunan ta "Hajiya Maryam" Ta juyo a tsorace dan ba ta ji takun mutum ba. Tana juyawa aka sa mata hankerchief aka rufe ma ta baki. Cikin abinda bai fi 30secs ba ta sume mutumin ya janyeta yai wajen da su ka parker Mota da ita. Kafin Maryam ta shigo gidan ta ga motar da aka parker wanda ta yi tunanin ko maƙotan su ne su ka yi baƙi. Shi kam Junior ganin ana tafiya da Mommyn sa sai ya sa kuka. Ya yi kukan har ya gaji dan haka sai ya fara wasa-wasa a ƙofar gidan duk ya ɓata uniform ɗin sa. A haka Salman ya dawo daga Makaranta ya sameshi ya tambayeshi ina Mommy ya ce bai sani ba. "Junior ba ita ta kawo ka gida ba?" "Wani ne ya tafi da Mommy" ya faɗa yana sa yatsa a baki. Salman ya zaro ido yana jawo yaron jikin sa " Junior waye ya tafi da Mommy?, wani kaya ya sa" Junior sai ya tsorata ya sa kuka. Sai a lokacin ma Salman ɗin ya lura da Jakar Mommy da ya faɗi ga key kuma a jikin ƙofa. Ya ɗau jakar ya fara dubawa. Wayanta, ATM, ID card da key ɗin motar ta duk suna ciki. Ya kama salati ya ɗau wayan yana ƙoƙarin kiran numbar Auwal... Bayan sun iso gidan da aka umurce su su ka kira Alhajin da ya aike su, sai ga Alhaji ya fito fiska ɗauke da farin ciki. Duk da jikin Maryam a sake ya ke bai hana Muntari iya ɗaukan ta ba, ya wuce da ita cikin gidan yana ɗauke da ita kamar Amarya. Kai tsaye kan gado ya kwantar da ita ya gyara ma ta kwanciya yana kallon kyakykyawar fiskarta. Kusan minti Arba'in da kwantar da ita maganin da aka shaƙa ma ta ya saketa. Ta buɗe ido a hankali, tana ƙyafƙyafta idon saboda idon da ya ma ta nauyi. Kusan minti ɗaya kafin hankalinta ya kawo ma ta abinda ya faru lokaci guda ta tashi zaune tana faɗin Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun. "Relax ni ne" ya faɗa yana ƙoƙarin zama a gefen gadon. "Muntari, Muntari ka ji tsoron Allah. Ka ji tsoron Allah" sai kuma ta fashe da kuka dan ba ta san mi za ta faɗi ba bayan haka. "Ki kwantar da hankalin ki dan ba abinda zan miki. Da ina son ki ta ƙarfi da tun ɗazu na yi abinda ki ke tsoron. Abu ɗaya na ke so Maryam, abu ɗaya tak shi zai sa na samu kwanciyar hankali kuma kema ki samu. Ki aure ni" Idon ta cike da hawaye ta ce "Muntari dan Allah, indai ka yarda da Allah to ka rabu da ni, ka bar ni na koma wajen 'ya'yana. Muntari idan kana sona kamar yadda ka ke iƙirari to ka rabu da ni dan Allah" Fashewa da dariya yai wanda ya ƙara tsoratar da Maryam. Lamarin Muntari kam ta tabbata ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa. "Ba zan iya rabuwa da ke ba, ke tawa ce kuma ba zan taɓa haƙura ba sai na same ki. Idan a baya Tijjani ya min ƙwace to yanzu babu shi kuma ba zai taɓa dawowa ba idan ma wannan ki ke jira gara ki dena" "Subhanallah! Muntari mi ka yiwa Mijina? Kashe shi ka yi? Mi ka mishi ?" Bindigar da ya fito da shi ne ya sa ta yi shiru tana zare ido. Ba rayuwarta ba ne ya sa ta tsoro illa tunanin da ya dirar ma ta lokaci guda na cewa Muntari kashe ma ta Tijjani yai. "Na sani yanzu ba abinda kika fi so sama da 'ya'yan ki. Idan ba ki amince da aure na ba tamkar kin kashe Salman da Sadiq ne da hannun ki" "Muntari" ta faɗa murya a raunane "Kashe su zan yi Maryam. Ba su kaɗai ba har Zaytoonah. Ba a Las Vegas ta ke ba?" Zuciyar Maryam bugawa ne kawai bai yi ba amma ta firgita matuƙa. "Akan ki zan iya yin komai" " Muntari ka yi haƙuri kar ka kashemin 'ya'ya, ka tuna fa su jinin ka ne" "Zan baki zuwa gobe ki yi shawara ko ki aureni ko kuma kiyi sallama da 'ya'yan ki" ... *** Abinda ta gani jiya bai sa ta iya cin abinci ba sai chan tsakar dare tana bacci yunwa ya addabeta ya tada ta dan haka ta sauko ta nufi kitchen fridge ta buɗe ko za ta samu abun ci ta buɗe fridge ta ɗau apple guda biyu ta fara ci tukunna kafin ta ga ragowan strawberry cake da ta ci ta rage da safe dan haka ta fito da shi ta hau ci tareda Madara, sai da ta ji ta ƙoshi kafin ta koma ɗaki ta je ta kwanta. Washegari makara ta yi ba ta tashi da wuri ba. Lokacin da ta tashi ta yi sallah ta yi wanka ta fito ƙasa sai ta samu Ben da Zuhayr suna karyawa. Hoton jiya kawai ta ke gani dan haka ta ja dogon tsaki ta wuce su. Kitchen ta shiga ta samu Chef Green har ya gama aikin sa na safe yana gyara abinda zai yi amfani da shi da safe. Gaishe shi ta yi sannan ta fito da ƙwai huɗu da kifin gwangwani ta kunna wuta ta haɗa scramble egg mai rai da lafiya, ta ɗau bread ta zauna a kujeran kitchen ɗin ta fara ci bayan Chef Green ya ajiye ma ta tea a gabanta dan har yanzu ba ta iya dafa shayi irin na sa ba sai ta ce ya haɗa ma ta lokacin da ta ke kan haɗa ƙwan. Tana cikin cin abincin ta tambayi Chef Green ko ya san alaƙar da ke tsakanin Ben da Zuhayr. Chef Green ya ce ma ta kaman 'yan uwa su ke saboda tare su ka taso. "Do you know that they are gay?" Ta yi tambayar tana kallon Chef Green. "I dont know" ya amsa bayan yayi nazari. "They are sleeping tog..." ƙarrarrawar kitchen ɗin yai ƙara Chef Green ya ce "excuse me" kafin ya bar kitchen ɗin dan ya san Zuhayr ke kira. Ɗaga kafaɗa ta yi tana faɗin "inma dukkan su jirgi ɗaya ya kwaso su shikenan, dama America is a free country" Bayan ta yi maganar sai tausayin Zuhayr ya kama ta dole ya ce ba za su yi mu'amalar aure ba tunda yanada matar sa Benedict a gefe. Sai yanzu ta ke gane ma'anar kallon da Ben ke ma ta ashe kallon kishi ne. "Ka yi ta yi ni ba ruwana, karatu na zo yi kuma shi zan yi na tafi ba ruwana da mijin ka"... Yau za ta je school har ta fito sai ta manta wayarta a ɗaki za ta koma ɗauka shi kuma sun fito za su tafi Office. "Allah dai ya shirya" ta furta a fili tana haɗe fiska bayan sun yi ido huɗu da Zuhayr. Har ta juya ta ji ya kira sunan ta "Zaytoon" "Zan yi tafiya amma gobe zan dawo" "Kai da za ka tafi da matar ka miye haɗin ka da ni. A je a shaƙata lafiya" Tana faɗin haka ta wuce ciki da sauri... A makaranta bayan ta sauka a mota ta fara tafiya sai ta ji ana yi ma ta magana "Excuse me, Excuse me" Ta juyo a hankali dan har yanzu ba ta da aboki a makarantar, iya kaci akwai wata Zoey 'yar ajin su da su ke ɗan magana sama-sama haka. "Ki yi haƙuri na tsaida ke, sunana Linda Cannel" "Zaytoonah" "Na ganki a wata mota mai lambar ZMI da alama ke 'yar uwar Mr Zuhayr ne?" Zaytoonah ta gyaɗa ma ta kai. "Ƙanwar shi ce ke?" Nan ma ta gyaɗa ma ta kai. Linda ta yi murmushi ta fito da katin ta ta ce "za ki iya kirana idan kina son bayani akan mutuwar Alinah" "Waye Alinah?" "Zuhayr's ex" Kafin Zaytoonah ta yi wata tambayar sai ta juya ta tafi. Zaytoonah ta buɗe baki tana kallonta har ta ƙule ba ta bar kallon ta ba. Har ta koma gida ba ta dena juyayin abinda ta ji yau ba Zuhayr's ex kuma ta mutu. Miya faru? Dama Zuhayr ba gay ba ne ko kuma dai daga baya ya zama? Ta tambayi Chef Green ko ya san Alinah amma ya ce bai sani ba. Haka dai ta kwana da tarraradin maganar a ranta tareda tunanin gobe idan ta dawo daga School za ta kira Linda ta ma ta ƙarin bayani. Washe gari a hanyar ta na dawowa daga school numbar Mommy ya kirata, ta yi saurin ƙatsewa ta kira zuciyarta cike da farin ciki. Maimakon muryan Mommy sai ta ji muryan Salman. "Adaeze an sace Mommy" "What? An sace Mommy kamar ya?" "Tun jiya har yanzu ba mu ganta ba, Junior ya ce wani ne ya zo ya ɗauketa. An yi reporting a police station amma har yanzu ba a ganta ba" ya ƙarisa maganar yana kuka. Cikin kuka ta ke cewa ya kaiwa Ya Auwal wayan amma ya ce Auwal baya gida kuma ya hanashi ya gaya ma ta abinda ke faruwa. Kuka ta ke yi har su ka iso gida Mr Smith ya tambayeta ko lafiya amma ba ta kulashi ba sai kuka. Tana shiga ɗaki ta ɗau jaka ta fara haɗa kayanta tareda neman visa da credit card ɗin da Zuhayr ya ba ta ta sa a jaka ta fito da gudu kamar wata zararriya. A ƙofar gida ta samu Zuhayr yana sauraron bayanin da Mr Smith ke ma sa su ma isowan su kenan. "Zuhayr an sace Mommy na gida zan tafi" ta ƙarisa maganar tana kuka. "Relax Zaytoonah, ba inda za ki je, besides za ki fara exams jibi" "To hell with the exams. My Mommy is missing, she's being kidnapped" Ta kalli Mr Smith ta ce ya kaita airport. Za ta wuce shi ta shiga mota ya tare hanyar. "Ki kwantar da hankalin ki, mu shiga ciki tukunna" ta chanja hanya za ta wuce yai saurin jawota ta faɗa jikin sa. "Ka sakeni na tafi, ka sake..." maganar ta kafe lokacin da ta ji bakinsa cikin na ta. "Relax, ba abinda zai samu Mommy i Promise you" ya faɗa bayan ya raba kiss ɗin. Mutuwar tsaye tayi a wajen dan maganan sa ma ba ji ta yi ba. Ben ya dunƙule hannun sa da ƙarfi yana huci yayinda idanun sa su ka kaɗa su ka yi jaa... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 26 Bismillahir Rahmanir Rahim *Alinah* Kafin a tafi da Alhaji Muntari sai da aka yi drama sosai dan kuwa titsiyewa yai akan shi bai yi komai ba babu yadda za'ayi a arresting ɗin sa. Tanimu ya riga ya tona asirin akwai matar da Alhaji ya ajiye a gidan amma Muntari ya ƙaryata hakan. Auwal da wani police ne su ka shiga gidan su ka duba inda su ka samu ƙofar ɗakin da Maryam ta ke a rufe, komawa su ka yi waje inda ake riƙe da Muntari yana zage-zage bayan anyi nasaran saka ma sa ankwa a hannu. Da su ka chaje shi sai su ka ɗauki key ɗin gidan su ka koma su ka je su ka buɗe Maryam. Auwal na ganin Mommy sai ya fashe da kuka, lokacin da Zuhayr ya ce ma sa yana suspecting ɗin Muntari bai yarda a zuciyar sa cewa ƙanin mahaifin na sa zai iya aikata irin wannan abu ba. Maryam sai da ta ga 'ya'yan ta Salman da Junior kafin hankalinta ya kwanta har ta samu damar yin wanka ta ci abinci kafin daga baya su ka wuce police station dan ta je ta ba da statement. Ko kaɗan ba ta tunanin za ta ragawa Muntari a wannan karan, sai ta yi duk abinda za ta yi dan ta ga bayan sa once and for all. Zuwa yamma labari ya karaɗe ko'ina na abinda Muntari ya aikata na sace Maryam da yai. Tuni ya contacting lawyer ɗin sa akan a yi bail ɗin sa amma hakan bai yiwu ba, strict order aka bayar daga sama akan kar a yadda ayi bailing ɗin sa... Duk abinda Zuhayr yai Auwal bai ɓoye wa Maryam ba, ta jinjina ma sa ta kuma yi farin ciki sosai saboda ko ba komai ya nuna ya damu da damuwar 'yarta Zaytoonah. Ta so kiran sa da dare da ta samu sarari amma ta san a wajen su dare yayi nisa sosai ƙila suna bacci shiyasa ta haƙura zuwa safiya. Washegari da safe da ta kirashi yana office lokacin, ta ma sa godiya bisa taimakon sa gareta, ya nuna ma ta ai ba komai. Tambayar sa ta yi ko Zaytoonah na ba shi matsala ya ce ma ta a'a sai kuma ya ce eh. Maryam ta ɗan ji wani jim a zuciyarta, cike da damuwa ta tambayeshi laifin Zaytoonah. In a serious tone ya ce "tana cin abinci da tsakar dare, har kwana a kitchen take yi" Maryam sai ta sa dariya shima ya biye ma ta da dariyan. Chan ta ce "ai Zaytoonah da abinci sai a hankali" Haka dai su ka ɗan yi hira kaɗan wanda duk akan Zaytoonah ne kafin ta katse kiran. A school Mommy ta kira Zaytoonah, ta fito daga class za ta je cafeteria cin abinci wayar ta tayi ringing. Tana ɗaukan wayan da ta ji muryan Mommy ta daka tsalle haɗeda sa ihu, wanɗanda su ke gefenta su ka juyo suna kallon ta. Har ta gama wayan babu nitsuwa a tattare da ita, wani lokaci ta sa ihu,wani lokaci dariya, wani lokaci kuma tsalle. Da ƙyar ta iya attending class ɗaya da ya rage ma ta a ranan. Mr Smith na zuwa ta ce ya kaita kamfanin su Zuhayr. Da tambaya aka ma ta kwatancen office ɗin Zuhayr wanda ke hawa na ƙarshe. Elevator ta hau wanda ya kai ta wajen, office ɗin Sakatariyar sa ta fara shiga inda ta nuna buƙatar ta na son ganin Mr Zuhayr. Sakatariyar ta danna ma sa kira, daga inda ya ke zaune yana duba wasu files ya danna wani baƙin botton a jikin phone ɗin ya ce "yes" Sakatariyar ta ce "Zoyuna is here" yana jin muryan Zaytoonah lokacin da ta ke gyarawa Matar sunan ta. "Send her in" ya faɗa a taƙaice Cike da ɗoki ta shiga office ɗin tana kallon yadda ya tsaru yai kyau. "Guess what Zuhayr?" Ya ɗan ɗago ido ya kalleta sannan ya ce "what?" "An samu Mommy, ashe Uncle Muntari ne ya saceta, shege tsinanne" ta faɗa cike da jin haushin ƙanin Baban na ta wanda tunda ta san shi bai taɓa burgeta ba and he's always causing them trouble. "Good" ya amsa a taƙaice. "Good kuma? Kai da za ka tayani murna. We are supposed to celebrate this goodnews" "After your exams" ya faɗa ba tareda ya ɗago ba, Jikinta ne yai sanyi saboda yadda ta ga fiskan sa ba ta ga alamar yana tayata farin ciki ba amma kuma Mommy ta ce da taimakon sa jami'an tsaro su ka kama Muntari. Shi kuwa a ɓangaren Zuhayr bayan sun yi waya da Mommy asibiti ya wuce saboda ya karɓi sakamakon series of tests da aka ma sa satin da su ka wuce. Bayanin likitan ya ɗan girgiza shi shiyasa ma ransa ya ke a jagule. Ganin ya manta da ita a office ɗin ne ya sa ta ce za ta koma gida ya ce ma ta sai anjima. Tana buɗe ƙofa su ka yi kiciɓis da Ben wanda ke shirin shigowa da wani file a hannun sa, ganin Zaytoonah sai da zuciyar sa ta buga da ƙarfi. Ba ta ma sa magana ba haka ta raɓa ta gefen sa ta wuce tunda shi bai matsa ba sai ma wani mugun kallo da ya ke aika ma ta... Jiki a sanyaye ta koma gida tana tunanin mi ya ke damun Zuhayr ɗin bayan ta san ba haka su ka rabu da safe ba, infact tarema su ka yi breakfast. Chan ta tuna da maganar da su ka taɓayi da wata baturiya wanda yanzu sunan ta ma ta manta, ta tashi da sauri ta fara neman katin da matar ta bata amma ko sama ko ƙasa ta rasashi, tafi tunanin ranan da ta ke tattare kaya akan za ta koma Nigeria ne ta yar da shi. Ta ji haushin hakan sosai, daga baya kuma ta tuna da Muhsina dan haka ta danna ma ta kira, a kira na biyu ta ɗauka. Bayan sun gaisa Zaytoonah ta tambayeta waye Alinah?. Daga ɓangaren Muhsina ta ce "ai na san ba zai gaya mi ki ba, ex fiancee ɗin sa ce da ta kashe kan ta kusan shekaru inaga zai kai ko bakwai ko shida haka" Zaytoonah ta dafe ƙirji ta ce "kisan kai fa!" "Iyi, Allah ne masanin komai amma gaskiya ba mu ji daɗin abinda ta aikata ba. Saura ƙiris fah ayi auren, wallahi duk wani shirye-shirye anyi muma muna shirin zuwa Las Vegas ɗin kenan mu ka ji labarin mutuwarta. Abin ba daɗin gani" "Dan Allah kinada hoton ta?" "Gaskiya sai dai na duba dan abin ya jima, ko high school ban gama ba lokacin da abin ya faru. Idan na samu zan tura miki" Zaytoonah ta ma ta godiya ta kashe wayan tana nazarin maganganun Muhsina da kuma maganar da matar nan ta gaya ma ta. To wannene gaskiya? *** A Nigeria kuwa daga Ringim aka zo bawa Maryam haƙurin abinda ya faru da kuma roƙon ta janye ƙarar Muntari saboda a rufe case ɗin dan kar mutuncin sa ya zube. Maryam kam jin su kawai ta ke yi tana girgiza kai dan ko T J ya zo yau ya ce ta yafewa Muntari ba za ta yafe ba. Idan hauka ya ke yi gara ya je ya ƙarisa a gidan yari ita ba damuwarta ba ne. Abin mamaki sai ga Iya ta kirata a waya tana ba ta haƙuri. Ba haƙurin abubuwan da ta ma ta a baya ba, ba haƙurin ɓangarenci da ta ke nuna ma ta har yau ba sai dai wai ta yi haƙuri ta yafewa Muntari a kashe maganar ba sai anje kotu ba. "Iya kin san Allah ko mijina ne ya dawo yau ya ce na janye ƙarar nan ba zan janye ba. Na gaji da yin haƙuri saboda wani mutunci. Mutunci ya ƙare lokacin da Muntari ya sa aka sace ni, mutunci ya ƙare lokacin da ya yi iƙirarin kashe 'ya'yana idan ban bi son zuciyar sa ba. Ko da kotu ba za ta bani nasara ba ba zan janye ba har sai mun kai kotun Allah ya isa kafin na bar shi da Ubangijin da baya zalunci" daga haka ta kashe wayar tana tunanin son zuciya ta mutane. Da Iya da sauran ma su cewa ta yi haƙuri duk munafukai ne abinda ta sawa ranta kenan. Sun yi waya da Goggo kan maganar saboda ciwon ƙafa da ta ke fama da shi ba ta samu ta zo ma ta ba amma ta ba ta goyon baya ɗari bisa ɗari akan ta cigaba da ƙaran. Idan har Muntari bai yi hankali ba a shekarun sa sama da Arba'in ba ta san ranan da zai yi hankali ba kuma, gara a haɗa shi da hukuma kawai. A Nigeria inda ake iya kuɗin ka iya shagalin ka. Duk inda lawyer mai kare Muntari ya kai da neman cin nasara hakan bai yiwu ba. Yadda Muntari ke sawa ana ta zuba kuɗi ana bribing mahukunta hakan bai yi tasiri ba domin duk inda ya ke ji da kuɗi wanda ke sponsoring lawyer ɗin Maryam ya taka shi. Zuhayr ya yi alƙawarin indai kuɗi ne ke aiki a Nigeria to dole sai an tura Muntari gidan yari. Hakan ne kuwa ta faru dan shari'ar da aka fara yi a Kaduna bayan duk wani bincike da aka yi, bayan kuma an yi zaman kotu sau uku ana ɗaukaka ƙara to Alkali ya yankewa Muntari hukuncin zaman gidan Yari na shekaru goma tareda biyan kuɗi naira miliyan biyu. Ofcourse an ɗaukaka ƙara zuwa court of Appeal wanda a nan ma fa shari'ar ba ta ba wa Muntari gaskiya ba domin kuwa shekaru bakwai a gidan Yari aka yanke ma sa tareda mayarda kuɗin da zai biya na tara zuwa miliyan ɗaya kacal. Haka aka tinƙisa ƙeyar sa zuwa gidan yari. Ko maganar sake ɗaukaka ƙara Lawyer ɗin sa bai yi ba dan evidences da Maryam ta kawo a zaman su na ƙarshe ya ƙara incriminating Muntari ne. Maryam Barrister ce dan haka ta san yadda kotu ke aiki, shiyasa ta tanadi bayanai da shedunta wanda su ke da ƙarfi sosai, ko sun je supreme court ɗin ma dole za a punishing Muntari sai dai kawai za'a dai iya rage ma sa shekarun da zai yi a gidan kaso, kuma ya ga alama ma su goyon bayan Maryam manyan mutane ne da su ka taka Muntari dan haka kuɗi ba zai juya shari'ar ba. Tunda aka fara shari'a kuwa 'yan uwan T J su ka kasu kashi biyu rabi na wadai da abinda Maryam ta yi sauran kuma na cewa Allah shi kyauta halin Muntari ne ya kaishi haka tunda shi mutun ne mai hassada da riƙo. Iya har kuka ta yi da jin yadda al'amarin Muntari ta kasance. Gidan na sa ya koma daga Hanne da 'yarta sai Iya da Humairah wanda duk zaman kaɗaici ya ishe su. Hanne kam a ranta kissimawa ta yi akan tana ƙarisa ajin ta na ƙarshe a Jami'a za ta je a raba aurenta da Muntari dan dama ta gaji da auren. Tun ranan da ta gane Maryam ya ke so ɗan sauran mutuncin da ta ke ganin sa da shi ya zube. Abu da mutum da dukiya da kuma mutane da son zuciya. Ba a jima ba aka fara warwaso akan dukiyar Muntari. GM ɗin sa tuni ya wawure abinda ya wawure yai gaba abinsa. A shagunan sa ma abun ba kanta kowa jin an ɗaure Muntari sai halin rashin amana ya fara bayyana aka shiga yin satan kaya a hankali a hankali. Cikin 'yan uwan sa kuwa Rabi'u wanda su ke 'ya'yan Baffanu kuma sa'anni saboda tsakanin su ma sati ɗaya ne shi ya zo ya tsaya tsayin daka akan kasuwancin Muntari, dama shi ya ke kula ma sa da shi lokacin da ya ke Lagos to da Muntari ya dawo Zaria shine ya sallameshi bayan ya ba shi enough kuɗi da zai fara na shi kasuwanci, shima ya zama ya koma yana zaman kan sa. Ya samu buɗi kam da farko amma da ya sa neman mata a gaba sai kasuwancin sa ya zama ba albarka a ciki tunda yadda ya ke kashewa matan banza a waje ko rabin sa ba ya yiwa Iyalin sa biyu da ya ajiye a gida, a haka dai business ɗin sa ya ja baya drastically. Yanzu kuma da ya zama in control na dukiyar Muntari sai liyafa ta ci gaba. Saboda kar a sa ma sa ido sai ya jawo wasu cikin 'yan uwan su ya kawo su kasuwan dan kar ace shikaɗai ya cinye komai. Iya da Hanne kuwa ba abinda su ka rasa tunda duk wata yana ba su kuɗi duk da kuwa Hanne ta san abinda ya ke ba su ko kusa bai kai wanda Muntari ke ba su ba amma ta yi shiru dan kar ace itama ta kawo fitina cikin 'yan uwa... *** *7 years back* Normal shiga na fita office ta yi na riga da wando na suit sai dai banbancin ta da sauran matan da ke wajen ɗanƙwali da sa ta yane kan ta da shi wanda ke nuna ita ɗin musulma ce. A yau za ta gabatar da wani pitch a gaban manyan kamfanin na su duba da yadda aka promoting ɗin ta wata huɗu kacal da fara aikinta a kamfanin. Bilhaƙƙi ta ke yin aikinta saboda abu ne da ta ke so. Daga fara bayani ya katse ta tareda faɗin ta cire tsumman da ke kan ta dan she looked unprofessional. Alinah ta yi murmushi ta ce "ba zan iya cirewa ba saboda da ni da abun da ke kaina duk ɗaya mu ke" Kalmar da ya faɗa a gaba ne ya sa ta ajiye highlighter da ke hannun ta ta fice daga hall ɗin. Tunda ta fara aiki yau ne su ka yi gaba da gaba da shi dan a da matsayinta bai ma kai ta yi magana da shi directly ba. Shine mai kamfanin kuma shi ya ce ta fita a hall ɗin dan kawai ta rufe kan ta. Ever since 9/11 da aka kai hari a twin tower na ƙasar musulmai su ke cikin zargi, wannan zargin ne ma ya sa aka dakatar da ita daga aikin da ta ke yi na shekara biyu a kamfanin da ta fara aiki. Kamfanin Zuhayr ma da ƙyar ta samu aiki saboda ranan da ta je interview ma ta rufe kan ta wanda ya sa aka yi kokonton ba ta aikin, har ta cire rai ma da su aka kirata akan ta zo an ba ta aiki. Watanni huɗu da ta yi da su sun sha samun saɓani da colleages ɗinta simply because ita musulma ce kuma anyiwa Musulmai shaidar su 'yan ta'adda ne. Mutane da dama wannan yanayi ya sa su ka dinga ajiye musuluncin su a gida idan za su fita ba sa yin shiga da zai nuna su ɗin musulmai ne. Wasu da dama a wannan lokaci na takura ne ya sa su ka samu raunin imani har ta kai wasu sun yarda addinin su saboda tsoro da fargaba. Itakam tarbiyyan da Babanta ya ɗaura ta akai ba zai taɓa bari ta chanja ra'ayinta saboda barazanar wasu ba. "Alinah Jones" aka kira sunan ta. Ta ɗago tana kallon Aimee wacce ita ce shugabar sashen su a kamfanin. "Mr Zuhayr wants to see you" Bayan ta wuce Linda da ke gefen cubicle ɗin ta tace " i hope he doesnt get you fired Alinah" Alinah ta yi murmushi ta ce ma ta ba abinda zai faru. Bayan ta shiga office ɗin Zuhayr ya ce ma ta zaɓi biyu take da shi a kamfani, ko dai ta dena rufe kan ta ko kuma ta ajiye aiki dan ba zai juri asara a kamfanin sa ba duba da yadda kamfanin ya samu koma baya saboda shi musulmi ne. Ba ta ma sa magana ba ta koma office ɗin su ta typing resignation later ta printing ta kawo ma sa. Bayan ta ajiye takardar a gaban sa ta ce "Allah ya rabani da ranan da zan jingine addini na saboda son duniya. Ban zo garin nan dan mutane su so ni ba soyayyar Allah na ke nema ba ta wasu tsirarun gafalallun mutane ba. Ka sani Mr Zuhayr, kafin 9/11 akwai ƙasashe da dama da su ke cikin tashin hankali na yau da kullum, kuma a hakan ba su muzgunawa fararen fata mabiya addinin da ba na su ba da ke zaune cikin ta. Ni na san waye ɗan America na ƙwarai tunda na ga halacci a wajen su amma kai da duk wanda ya ke kiran duk wani musulmi da ɗan ta'adda ba ku da banbanci da dabbobi" daga haka ta fice a office ɗin sa. Maganar ta ya sosa shi sosai amma girman kai ya hana shi ya kirata. Bayan kwana shabiyu da barinta aiki watarana tana dawowa daga kasuwa da yamma tana riƙe da lema tana tafiya hannun ta riƙe da ledar da ta yi siyayya, ruwa ake yi amma ya tsagaita a lokacin dan ya koma yayyafi. Da ƙarfi aka bugeta ta baya wanda sai da ta faɗi ƙasa lema da ledar hannun ta su ka yi gefe. Maza biyu ne irin 'yan jagaliya ɗin nan, jikin su duk ya ɓaci da tattoos. "Kina ɗauke da Bomb ne? Ina za ku saka wannan karan" Ɗayan ya riƙeta da ƙarfi ya fara ƙoƙarin cire ɗankwalinta itama kuma ta riƙe shi gam amma dole sai da ya fincike ɗankwalin da ƙarfi ya haɗa da falla ma ta mari. Kuɗin da ke cikin purse ɗin ta daya faɗi ɗaya mutumin ya ciro ya coge a Aljihu. "Hey Hey " aka faɗa da ƙarfi wanda ya sa su ka falle da gudu bayan sun ɗaga ido sun hango shi yana tahowa wajen da gudu, baƙaƙen kayan da ke jikin sa ya sa su ka ɗauka cewa ko shi ɗin FBI agent ne. Wannan cin zarafi da ake yiwa musulmai ya zama ma ta jiki duk da kuwa yau ne aka ma ta wanda ya taɓata sosai tunda har ɗankwalinta aka cire ta ƙarfi a bakin titi. Bai san wacece ba sai da ya iso ya sa hannu ya tallafa ma ta ta miƙe tsaye. Ya fito daga wani building ne ya hango marin da aka yiwa matar shiyasa ya taho da sauri, yana mugun daraja mata saboda soyayyar da ya ke wa mahaifiyar sa. Kallon kallo su ka tsayayi na ɗan wasu daƙiƙu kafin daga baya ta je ta ɗauko scarf ɗin ta da ke yashe cikin ruwa a gefe, ta matse ruwan jiki sannan ta yane kan ta da shi. Duk abinda ta ke yi Zuhayr na tsaye yana kallon ta cike da tausayi. Haka ta bi ta tsince kayanta da suka watse wanda wasu ma ba ta gan su ba. Lemar kam banƙarewa ta yi dan ko za ta yi amfani to sai an gyarata. "Ki zo na kai ki gida" ya furta da ɗan ƙarfi lokacin da ya ga ta juya za ta tafi. Ba ta saurareshi ba ta cigaba da tafiya dan haka ya zo ya sha gabanta ya sake maimaita abinda ya faɗa. Sai ta yi shiru tana kallon sa. "Fisabilillah" ya furta a hankali wanda hakan ya sa ta amince ta bishi zuwa wajen da ya parking motar sa. Kaman jira ake yi ta shiga motar dan tana shiga sai ga ruwa ya ƙara zuwa da ƙarfi shaaaaaaa... Daga inda ta ke zaune yana ganin yadda ta ke maƙyarƙyatar sanyi dan haka ya cire jacket ɗin sa ya ba ta dan ta bayan ne kawai ya jiƙe kaɗan. Daga wajen zuwa apartment ɗin ta ba nisa dan tafiyar minti uku ta kai su wajen. Ta ma sa godiya ta fita a motar bayan ta tafi ya jima a wajen yana jimamin abinda ya faru tareda tausaya ma ta. Washegari sai gashi da sassafe a gidan wai ya zo duba lafiyar ta. Da tunanin ta ya kwana shiyasa ya kasa haƙura dole sai da ya zo ya dubata. Daga muryanta ya gane mura ya kamata dan haka ya ce ta zo su je asibiti a dubata amma ta ƙi. Wasa wasa sai gashi Zuhayr sai da ya kwashe kwana uku a jere yana zuwa yana dubata, a rana ta ukun kuma ya kawo ma ta takardar shaidar aiki wato ya dawo da ita aikin ta. Da farko ta ƙi amma bayan ya ba ta haƙuri sai ta amince ta koma. Shikenan kuma alaƙar su ta ɗin ke daga lokacin. Time to time yana zuwa gidan ta su gaisa hakanan a office ma kusan kullum sai sun haɗu. Wannan chanji ya sa hankalin Ben ya tashi saboda zargin soyayya da ya ke yiwa Zuhayr da Alinah ɗin duk da kuwa Zuhayr ɗin ya ƙaryata hakan ya kuma nuna cewa tausayawa Alinah kawai ya ke yi saboda ba ta da kowa. A lokacin sallar Layya ne Alinah ta gabatar da Zuhayr a muslim community da ke Vegas wanda shi duk zamanshi a garin bai san da su ba. Yadda su ka yi hidimar sallah cikin farin ciki da soyayyar juna ya sa har ya ji shauƙin musuluncin ya dawo ma sa. Bayan angama hidimar sallah watarana da ya je gidan Alinah ya ke gaya ma ta yana so ya zama musulmin ƙwarai kamar ta dan baya damuwa da yin sallah akan lokaci, wasu lokutan ma bayayi ya ce ma ta Azumi ma kusan ya jima bi azumci duka Azumin Ramadan ba, idan yai ya gaji sai ya ajiye. Wannan confession na shi ya sa Alinah ta dage akan sa ta hanyar koyar da shi musulunci ta kuma ƙarfafa ma sa gwiwa ya dinga zuwa ɗaukan karatu a wajen Sheikh Hassan Lewis. Cikin wata shida Zuhayr ya chanja sosai ya koma yana ƙoƙarin yin ibada yadda ya kamata. Harta sallar Jummu'a da bai taɓa zuwa ba idan ba lokacin da ya je Nigeria ba da kuma lokacin da ya je wajen Uncle Aliyu to yanzu tare su ke zuwa ma da Alinah. Shi bai ɗauka akwai babban masallaci ba ma a garin saboda bai damuba. A wannan yanayi na shaƙuwa ne soyayya mai ƙarfi ta shiga tskanin su wanda bai gane hakan ba sai ranan da Sheikh Hassan ke ma sa tayin auren Alinah. Tun bayan maganar da su ka yi da Sheikh sai ya kasa samun nitsuwa yana tsoron kar ya yiwa Alinah magana ta ƙi shi dan akwai wani ɗan India Faisal Khan da ya ke gani yana shishshige ma ta wanda lokuta da dama idan ya gan su tare ya kan ji baƙin ciki a ran sa ashe kishi ya ke bai sani ba. Bayan ya yi shiru da zancen yana jiran Perfect time da zai gaya ma ta ƙwatsam sai gashi Alinah ta ma sa maganar wai ya ba ta shawara Faisal Khan ya ce yana son aurenta. Zuhayr ya harzuƙa matuƙa ya nuna shi ba ruwan sa rayuwarta ne tayi duk abinda ta ke so. Daga haka sai ya janye jiki da ita ya dena kulata. A kwana na biyar sai gashi bayan sallar jumu'ah sheikh ya sanar da cewa ƙarshen wata za ayi auren Faisal Khan da Zarah Ayyub Shahid. Sai a lokacin zuciyar Zuhayr yai sanyi ya kuma ji kunyar kan sa na fushin da yai da Alinah. Text ya tura ma ta yana ba ta haƙuri ita kuma ta ma sa reply da cewa idan bai fito da abinda ke zuciyar sa ba akwai single guys dayawa a muslim community. Yai dariya bayan ya karanta saƙon kafin ya tura na ta reply da cewa abinda ke zuciyar sa a bayyane ya ke a fiskar sa makaho ne kawai ba zai gani ba. Cikin ƙanƙanin lokaci su ka fara gudanar da soyayya mai tsabta, a lokacin ne kuwa Alinah ta bawa Zuhayr labarin rayuwar ta inda shi kuwa yai ma ta alƙawarin zai kula da ita har ƙarshen rayuwar sa. Wata biyu aka sa auren su kafin lokacin Zuhayr ya gama shirya komai, ya kai ta gidan Uncle ɗin sa sun gaisa da shi da iyalen sa. Ya shirya mu su tafiya immediately bayan anyi auren su, za su fara zuwa Nigeria su yi sati biyu kafin su wuce Saudiyya su yi Umara. Sai dai kafin wata biyun su cika abubuwa da dama sun faru wanda ya kai daga ƙarshe Alinah Amir Jones ta rasa ranta. Ƙaramar hauka Zuhayr yai lokacin da Alinah ta rasu musamman da aka tabbatar da cewa kashe kan ta tayi, mutane da dama ba su yadda Alinah za ta iya kashe kan ta ba tunda ba ta da matsalar komai amma bisa report da aka bayar Alinah ta kashe kan ta ne saboda matsalar ƙwaƙwalwa tunda lokacin da ta ke ƙarama ta yi fama da ciwon damuwa, sai ake ganin kamar auren da ta ke son yi ne ya haddasa ma ta da damuwa har ciwon ta ya dawo. Haka aka rufe case ɗin da cewa Alinah Amir Jones commited suicide... Alinah Amir shine asalin sunan ta, iyayen ta 'yan ƙasar Palestine ne wanda sanadiyyar yaƙi ya sa ta rasa mahaifinta da babban Yayan ta. Ita da mahaifiyarta su ka yi gudun hijira daga Palestine zuwa America. Da farko a wani refugee camp su ke a ƙasar Jordan daga baya su ka samu wani yai mu su hanya su ka isa ƙasar America akan Sarah mahaifiyar Alinah za ta isa wajen Ƙanin Baban ta wanda ya jima da komawa America da zama da daɗewa. Da ƙyar ta samu ƙanin Baban na ta bayan sun sha gararin rayuwa, shima dai ba wani abun azo a gani ya ke da shi ba amma ya karɓesu hannu bibbiyu. Alinah na da shekara shaɗaya wanda ya kama wata shauku kenan da zuwan su America aka ma ta fyaɗe, not just fyaɗe kawai gang raping ɗin ta aka yi har mutum uku. Wasu taƙadarun mutane ne abokanan aikin Hammad wanda su ka samu sa'insa da shi a wajen aiki har ta kai ya kai su ƙara wajen Ogan su, Ogan ya ba wa Hammad gaskiya. Shine su ka yi alƙawarin muzguna ma sa, ɗan sa ɗaya da ya ke da shi ba sa tare saboda shima yanada na sa iyalin a can garin Detriot. Shine su ka nemi tarwatsa rayuwar jikar sa Alinah. A yashe aka samu Alinah bayan an jima ana neman ta. Wanda su ka sameta ne su ka je su ka faɗawa Hammad bayan an kira ambulance sun tafi da Alinah wacce har lokacin ke sume. Hammad da matar sa Nadeem da kuma Sarah mahaifiyar Alinah ba ƙaramin tashin hankali su ka shiga ba da jin abinda ya faru da Alinah. Ko jini ba ta fara ba lokacin da aka ma ta fyalen. Tunda Alinah ta buɗe ido a asibiti ta rikice ta fara zabure-zabure musamman da ta ga likita namiji akan ta, sai da aka haɗa da yi ma ta allura kafin ta nitsu. Kusan watan su ɗaya a asibiti kafin aka sallameta ba wai kuma dan ta gama warkewa ba. An dai ma ta taimako na gaggawa an gyarata amma matsalarta ta zabura da firgita har lokacin da saura sun ce a kaita psychiatric saboda anan za a bata kulawa dan matsalarta ta ƙwaƙwalwa ce. Hammad ya shigar da ƙara amma rashin shaidu ma su ƙarfi da kuma kasancewar sa Musulmi ya sa aka yi watsi da ƙaran. Ga shi dai suna da report na fyaɗe daga Asibiti amma haka aka wanke sunan Bradley, Fred da kuma Austin. A wannan yanayi ne Yusuf ɗan Hammad ya ba su shawaran su nemi wani Lawyer da ake kira da David Jones ko zai taimaka mu su dan yayi ƙaurin suna wajen kare hakkin bil'adama musamman ƙananun yara, an shaide shi da gaskiya da kuma amana, a cikin aikin sa baya banbanta yare, addini ko kuma kalar fata. Sai da su ka jera sati biyu suna neman ganawa da shi amma ba su samu ba saboda mutane da ke ma sa yawa a sati na uku suka samu daman ganawa da shi. Sosai ya ba su mamaki lokacin da ya ce zai wakilce su a sake ɗaukaka ƙara. Abu na farko da yai shine ya adopting Alinah a matsayin 'yar sa, bayan ya gama yin duk wani legal documentation kafin ya shigar da ƙara akan fyaɗe da aka yiwa 'yar sa Alinah. Nan da nan aka fara shari'a, aka shiga aka fita har dai David Jones yai nasara inda aka yankewa mutanen nan uku hukuncin ƙare rayuwar su a gidan yari. Ba tareda ko sisin su Hammad ba David Jones ya kai Alinah psychiatric aka fara kula da ita. Warkewanta was a very slow process dan kafin Alinah ta fara yadda namiji ya zauna kusa da ita ma sai da aka fi shekara ɗaya. Shekaranta uku ana kula da ita kafin aka sallemeta amma duk sati za ta dinga zuwa tana ganin likita. Sai da aka yi shekara huɗu cur da maganan fyaɗe kafin ta iya komawa makaranta da ke ance chanja muhalli zai sa ta samu saurin warkewa ya sa David Jones ya tafi da ita Michigan inda a nan ma aka yi ta treating ɗin ta. David da matar sa Helen sun riƙe Alinah da amana tamkar 'yar da su ka haifa a cikin su, 'yar su ɗaya Anna amma ta mutu tun tana ƙarama kuma ba su sake samun haihuwa ba. Ba su damu da cewa Alinah musulma ba ne su kuma christain infact David ke kaita masallaci duk Jummu'a kuma ya kaita makarantar da ake koyar da karatun musulunci sau huɗu a sati. Bayan an samawa mahaifiyar ta Sarah aiki sai ya zamana itama ta dawo Michigan da zama inda ta cigaba da kula da 'yar ta. Lokacin da Alinah ta shiga Jami'a ne David Jones ya mutu bayan an halbeshi sau uku da bindiga a office ɗin sa. Lokacin da Alinah ta haɗu da Zuhayr mahaifiyar ta ta jima da rasuwa ita kuma Helena tana gidan tsoffi saboda cutar Alzheimer da ke damun ta. Ƙanin Kakanta Hammad shima ya rasu shi kuma Yusuf Hammad ya koma Saudiyya da zama saboda aiki da ya samu a chan. Aiki ne ya kawota Las Vegas bayan ta yi internship ɗin ta a wajen ta ji daɗin zama a garin ashe kuma ajalinta ke kiranta shiyasa ta bar Michigan ta dawo Las Vegas da zama... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 25 Bismillahir Rahmanir Rahim *Frightened* Zaunar da ita yai a kujera har lokacin tana hawaye. Ya sa babbar yatsar sa ya goge ma ta hawayen da ya zubo na ƙarshe. "Idan Mommy tana kusa da ke yanzu mi za ta ce miki?" Yai tambayar yana kallon ƙwayar idon ta. "Cewa za ta yi" sai kuma ta yi shiru "Ki faɗi gaskiya" Ta sunkuyar da kan ta ta ce "Cewa za ta yi na dena kuka na yi addu'a" "And yanzu da ba ta nan za ki yi amfani da maganarta ba kenan?" Ta kalle shi briefly kafin ta kau da kai gefe ta ce "to ai, to ai" sai kuma ta fashe da kuka tunowa da ta yi da Daddyn ta. Cikin kuka ta ce "ina tsoron za a rasa ta kamar Daddy, ba zan iya jure rasa ta ba" Jawota yai jikinsa ya rungumeta yana ɗan bubbuga bayanta yayinda Zaytoonah kuma ta ci gaba da kuka a jikin sa. Bai hanata kukan ba har sai da ta gaji da kan ta ta yi shiru tana sauke numfashi. A wannan lokacin ne ya fara hura ma ta iska a kunne kaɗan-kaɗan har ta ji wani sanyi ya fara ratsa ta. "Idan kin yarda lets make a deal" Ba tareda ta bar ƙirjinsa ba ta ce "what deal? "Ina so ki bani kwana 21, cikin kwana ishirin da ɗaya zan sa a nemo miki Mommyn ki, ke kuma in return za ki dena kuka, za ki yi karatu ki ƙarisa exams ɗin ki lafiya, sannan ba za ki sake yin zancen Mommy ba, addu'a kawai za ki dinga ma ta" Ta yi shiru na ɗan wani lokaci kafin ta ce "idan ba a ga Mommy ba fa?" "Zan kai ki Nigeria da kai na, and duk abinda ki ke so zan mi ki" "Ko da helicopter ɗin ka na ce ina so?" "Ko da helicopter ɗina ne Zaytoon" Ba ta yi magana ba wanda shirun ya tabbatar ma sa ta amince da maganar sa. Ta jima a jikin sa, chan ya ji numfashin ta ya chanja sai ya leƙa fiskarta sai ya ga ashe har ta yi bacci. Bai yi ƙoƙarin tashin ta ba sai ya janye jikinsa a hankali ya kwantar da ita akan kujeran sosai. Ƙura ma ta ido yai for the first time yana kallon fiskarta yadda ta ke bacci so peacefully kamar yarinya ƙarama, ko da ya ke yarinya ce ai. Idan ba ma gidadanci irin na Kakan sa ba, taya zai aura ma sa yarinya 'yar shekara shabakwai. Ko da ya ke kamar yadda Mommy ta gaya ma sa auren Zaytoonah ta yi ne kawai saboda shine mafita gareta ma fi sauƙi amma ba wai dan har zuciyarta tana son auren ba. Tunda ya shigo ɗaki ya tsaya yana kallon kan sa ajikin madubi yana huci. Chan ya kai wa madubin naushi yana faɗin "babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da kai Zuhayr, babu wanda ya isa ya samu soyayyar ka idan ba ni ba. Becareful Zaytoonah, Becareful" Hannun sa da ya fara jini ya ɗaga sama yana kallon yadda jini ke bin yatsunsa saboda yankuwa da yai da glass ya ce "i can kill for you and i can die for you Zuhayr. No can come between us, absolutely no one" Chan kuma sai ya fashe da dariya... Zuhayr bayan ya bar falon ɗakin sa ya shiga yai wanka ya chanja kaya ya sauko, har lokacin Zaytoonah ba ta tashi ba. Ya zauna kusa da ita yana latsa wayar sa a haka Ben ya sauko ya same shi, Ben ya tambayeshi ko ya ci abinci ya ce ma sa baya jin yunwa, ɗagowan da zai yi sai ya ga hannun sa ɗaya naɗe da bandeji. "Miya samu hannun ka?" Ben ya ce " domestic accident" Zuhayr ya ce "sorry" Ben yai murmushi dan ba abinda ya ke bala'in so irin ya ga Zuhayr na damuwa da shi , hakan ba ƙaramin faranta ma sa rai ya ke ba. Da dare bayan ya karɓi numban Auwal a wajen Zaytoonah sai ya kira shi yana tambayar sa gameda ɓatan Mommyn Zaytoonah. Auwal ya ce su ma suna tsumayin abinda ya faru dan har yanzu ba a gano su waye ba, kuma ba a buƙaci kuɗin ramson ba. Zuhayr ya jinjina maganar yana mamakin yadda aka sace mutum a ƙofar gidan sa rana tsaka amma har ya wuce 24hrs police ba su yi komai ba. Shi kuwa Auwal nuna ma sa yai Nigeria ce fa, Nigeria kuma ba America ba ne. Zuhayr ya ce ya dinga updating na sa gameda situation ɗin shima kuma zai kira wani top official a ɓangaren Police ya ji ko zai iya taimaka ma sa ta wani ɓangaren, Auwal ya ma sa godiya. Har zai kashe wayan sai kuma ya tambayeshi ina ƙannen Zaytoonah sai ya ce suna gidan Uncle Muntari, tun jiyan ya zo ya ɗauke su ya maida su gidan sa. Bayan ya ajiye wayan sai zuciyar sa ta ankara ba wannan Uncle Muntarin ba ne ya yi niyyar aurar da Zaytoonah ga wani illiterate har ta kai Mommy ta amince da tayin Alhaji Iliyasu? Da sauri ya sake kiran Auwal ya ce ma sa "ka saurareni da kyau, ina da suspect kuma ina so ka yi aiki da hankalin ka saboda mu tabbatar ko shine idan shi ɗin ne kuma mu kama shi" Auwal ya ce "ina jin ka"... Da ke hankalin ta a dagule ya ke ba ta ci wani abun kirki ba ta kwanta duk yadda Zuhayr ya takura ma ta ƙin ci tayi wai ta loosing appetite ɗin ta. Shi kam na shi ido dan ya san ɗan abincin da ta tsakura ɗin nan ba isar ta zai yi ba ƙarshe sai yunwan dare ya tashe ta. Tun zuwan ta gidan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ya sha ganin ta da tsakar dare tana saukowa kitchen ta je ta nemi abinda za ta ci. Yau ɗin ma ta tashi fitsari ne ta kasa komawa bacci saboda cikinta da ke ɗan murɗawa. Ganin baccin ya ƙi zuwa ya sa ta sauko ka sa dan ta nemi abu ta ci. Tana shiga kitchen ta fara buɗe fridge dan nan ne za ta yi saurin samun abin sa wa a baki instantly. Ɗaukewan wutan kitchen ɗin ne ya sa ta tsaya chak, mamaki da tsoro ya shigeta. Tun da ta zo gidan wuta ko shaking bai taɓa yi ba balle ya ɗauke. Ta kore tsoron ta hanyar tunowa da cewa ƙila bulb ɗin kitchen ɗin ne ya mutu, amma duka bulbs ɗin sai su mutu lokaci guda? Ta tambayi kan ta lokacin da ta tuno ta waje uku kitchen ɗin ke samun haske. Ta fara takowa a hankali hannunta a gaba tana shashshafawa saboda kar ta ci karo da wani abu. Ji ta yi an dafa kafaɗan ta ta baya hakan ya sa ta sa ihu haɗeda yin gudu sai dai ba ta yi nisa ba ta bugu da bango hakan ya sa ta tsaya ta juyo jikinta na rawa. Tana hango mutumin na nufota a hankali amma ta kasa motsawa, ba ta ganin fiskar sa saboda duhu. Sai da ya kusa isowa ta ga ya fito da wata ƙatuwar wuƙa. "Zuhayyyyyyyr" ta challa ihu daidai mutumin ya ɗaga wuƙa zai daɓa ma ta. Faɗuwa ta yi a wajen ta suma tun kafin ma wuƙar ya shigeta. Ben na ganin haka ya je ya kunna wutan kitchen ɗin ya maida wuƙan jikin sa yai tafiyar sa. Dama tsoratar da ita yai niyyar yi, da haka ya fara yiwa Alinah kafin da ta ƙi rabuwa da masoyin sa Zuhayr ya kai ta inda ba za ta sake ganin Zuhayr ba shima kuma Zuhayr ba zai gan ta ba sai dai a hoto. Sanyin asuba ne ya farkar da Zaytoonah daga suman da ta yi, kusan minti uku kafin hankalinta ya dawo jikin ta gaba ɗaya, ganin ta a kitchen kuma ga hasken lantarki tarr a kitchen ɗin ya sa ta yi saurin miƙewa zaune tana tattaɓa jikinta ko za ta ji sukan wuƙa amma babu. Mamaki ya cikata yayinda ƙwaƙwalwarta ke tuno ma ta abinda ya faru. Da ƙyar ta saita kan ta ta fita a kitchen ɗin inda ta haɗu da Zuhayr da Ben suna sanye da riga marar hannu da gajeran wando kalar nazy blue za su fita jogging. "Kar ki ce min a kitchen ki ka kwana?" Zuhayr yai tambayar yana riyawa a ran sa abinci ta je ci bacci ya ɗauketa. "Zuhayr someone tried to kill me last night" Zuhayr ya bushe da dariya. "I'm serious Zuhayr, Wallahi" Ganin ta yi maganar kamar za ta yi kuka ne ya sa shi dena dariyar ya tsaya yana sauraron bayanin ta harda cewa ya biyota kitchen ɗin ta nuna ma sa yadda komai ya faru shi kuwa ya bi ta amma zuciyar sa ko kaɗan bai yarda da bayanan ta ba, ya fi tunanin sace Mommynta da aka yi ya sa ta ke hallucinating abubuwa. Bayan ta gama bayani ya kama hannunta duka biyu ya ce "Zaytoonah mafarki ki ke yi, babu wanda ya ke kwana acikin gidan nan sai mu uku and akwai security a gidan nan duk wani wanda zai shiga gida bayan an rufe warning alarm na gidan zai yi ta bugawa. Na san tunanin Mommy ne ya sa kika fara irin wannan mafarkin amma kar ki damu za a sameta" "Ni fa ba mafarki ba ne, na tashi daga bacci na sauko ƙasa na shiga kitchen zan ci abinci sai aka kashe wuta sai" "Ba dole kiyi ta imagining abubuwa ba tunda abinci ne a ran ki" "Ni ba na tunanin abinci" ta faɗa tana tura baki "Its ok Baby girl, ki ci abinci yadda ki ke so amma banda satan abinci da dare dan kin ga akwai ma su kama mutane, inaga su ne ma su ka zo ɗaukan ki jiya" Ta zaro ido waje " da gaske?" Yai murmushi ya ce "just kidding" Ta haɗe fuska tana tura baki. Ya haɗa hannayan sa biyu alamar sorry. Ben ya ce "we'll be late" Zuhayr ya bi shi su ka fita. Ita kuwa Zaytoonah ta bi bayan sa da harara. Bayan sun fita sai ta tsaya tana kokonton abinda ya faru, ko dai da gaske ne abinda Zuhayr ya faɗa mafarki ta yi? Amma abinda ya faru look so real. Bayan ta shiga ɗaki ne ta yi wanka ta fito ta kalli madubi ta ga tsakiyar goshinta ya ɗan kumbura, ta taɓa wajen tana tunawa ai buguwa da gini da ta yi ne, to ko dai da gaske ne? Ganin ta fara ja'in'ja da zuciyarta sai ta tattara zancen ta watsar ta barshi a magagin bacci ta yi ta bugu ta faɗi shine ta yi bacci a wajen har ta yi mummunan mafarki. Akwai lokacin tana Zaria tun ma Daddy yana nan, ta yi tashin dare irin haka ta je falo ta buɗe fridge ta ɗauko ragowan shinkafar da aka ci da dare ta ajiye a ƙasa ta fara ci saboda tsabar yunwa, ranan fushi ta ke da Mommy sai ta ƙi cin abincin dare ta kwanta haka to kuwa ita da ba ta iya juran yunwa sai yunwa ya tada ita. Ranan da Asuba Daddy ya tasheta a gefen fridge ta yi bacci da sauran shinkafa a hannu... Shi kuwa Ben suna cikin gudu ya tambayi Zuhayr dalilin da ya sa ya ke sakewa Zaytoonah haka. "A Ƙanwata na ɗauketa, kuma tana buƙatar kulawa a wannan lokaci" Ben yai shiru amma chan ƙasan zuciyar sa ya san akwai matsala domin Alinah ma da irin haka ya fara kafin ya zo ya fara son ta. *** Tun da su ka yi magana da Zuhayr ya fara sa wa Muntari ido ya ga inda zai je, a ranan ya bi shi zuwa wani gida chan wani anguwa wanda bai cika ba saboda sabuwar anguwa ce. Ya kira wanda Zuhayr ya haɗa su ya ma sa bayani shi kuma ya ce za su cigaba da bincike daga wajen. A ɓangaren Maryam kam har ta fara fita hayyacinta. Duk abincin da ya kawo ma ta babu wanda ta ci, sallah kawai ta ke yi tanayi tana hutawa. Muntari ya ƙara ma ta kwana uku wai bayan nan duk abinda ta yanke shine sakamakon 'ya'yanta. Zuciyarta ya gamsu Muntari ne ya hallaka ma ta T J, mutumin da ba kunya ba tsoron Allah ya ce zai kashe 'ya'yan Yayan sa, ai kenan Uban su mai sauƙi ne, dan Uban su ne ma ya ma sa laifi. Ta riga ta sa a ranta in kwana ukun nan su ka cika cikin biyu za ta yi ɗaya. Ko dai ta amince da auren na sa ko kuma ta kashe kan ta. A safiyar rana ta uku da ya kawo ta gidan sai gashi ya shigo ɗauke da tray kaman yadda ya saba. "Wannan sallan ba zai fishshe ki da komai ba dan aikin gama ya gama. Ni Muntari na riga na ci galaba akan ki" Ba ta kulashi ba ta cigaba da addu'an da ta ke yi. "Ki tashi ki ci abinci, wannan azumin da ki ke yi ulcer zai sa miki kuma ba na so ki zo gida na da ciwo" Ko kallo bai isheta ba haka ya gama ɓuruntun sa ya fita. Daga fitar Muntari ya kulle ɗakin da Maryam ta ke ta baya kamar yadda ya saba, yana isowa falo ya ji kaman ana buga gate. Ya ɗan leƙo ta window ya na yiwa Maigadin sa magana. "Tanimu ko ma waye kar ka buɗe ƙofa bana karɓan baƙi a nan" Ya zauna a kujera ya fito da wayar sa yana lissafin kuɗin da zai kashe wajen hidiman biki, yanzu haka ma wasu mahaukatan kaya ya sa a haɗo ma sa daga Dubai na lefen Amarya. Ya ga tsoro a tattare da Maryam ya san dole haƙura za ta yi, wannan karan ba ta da zaɓi sai na shi. Baifi minti huɗu ba ya ji ana buga ƙofar falo. "Tanimu miye ne wai, ka sha ƙwaya ne?" Muryan Tanimu da aka titsiye da bindiga a shaƙe ya ce "ranka shi daɗe wani yaro ne wai sunan sa Auwal ya ce wai yana son ganin ka Allah ya yiwa Iya rasuwa yanzu. Na ce ya tafi ba ka karɓan baƙi ya ƙi ya tsaya a bakin gate sai kuka ya ke yi" Jin zancen Iya ta rasu ko tunani bai tsaya ba ya zabura da sauri ya buɗe ƙofa ya fito. Ganin Tanimu da Auwal da wani mutum ya sa shi cewa "Lafiya?" Bindiga aka sa a ƙeyar sa aka ce "You are under arrest Alhaji Muntari"... *** Asalin sunan sa Benedict Atkinson. Mahaifin shi Robert Atkinson Bayahude ne (Jew), Haifaffen ƙasar America ne amma iyayen sa 'yan ƙasar Ireland ne. Yana tareda matar sa ɗaya mai suna Laura Vincent. Tun bayan shekaru goma da auren su da ya rasa aikin sa ya koma wani dabba, shan giya ya ke yi kamar ba gobe hakanan sai yai ta dukan matar sa Laura. Ƙarshe ma saboda dukan ɗan su Ben da ya taɓayi sai ya sa ta kai shi boarding school. Da wuya ta yi yawa sai ta gudu ta koma wani ƙauye inda wata ƙawarta ta sama ma ta aiki a wani gidan gona. Laura tana aiki a gidan gonar su Mr and Mrs Haddish. A nan ne kuma Ben da Zuhayr su ka zama abokai wani lokaci da Ben ɗin ya zo hutu ya kuma haɗu da Zuhayr a wajen da ya ke koyon hawan doki. Shekaru biyu Laura ta yi ba tareda mijinta Robert ya san inda ta ke ba, sai watarana kwatsam sai ga shi ya ɓullo. Ya zo akan dole ta bishi su tafi amma taƙi, garin suna kokawada shi ya bugata da gini sai kan ta ya bugu sosai har ya zo da ƙarar kwana. Yana shirin guduwa ma aka kama shi. Ƙarshe aka shigar da ƙara aka kama shi da laifin kashe matar sa aka wuce da shi prison. Kasancewar Ben bai kai shekarun da zai iya rayuwa shi ɗaya ba sai ya zamana an fara ƙoƙarin maida shi gidan marayu kafin a samu wanda zai adopting ɗin sa tunda ba shi da wani family da za a iya maidashi wajen su. Kakar sa ɗaya ta wajen uwa tana gidan tsofaffi saboda ciwon mantuwa da ta ke da shi. Wannan ya sa Zuhayr yai wa Kakan sa magana akan ya adopting ɗin sa saboda Ben abokin sa ne, da ke suna son duk abinda ɗan lelen su ke so shiyasa su ka adopting Benedict wanda sunan sa ya koma Benedict Vincent Haddish. Makarantar da ya ke yi da aka cire shi aka maida shi makarantar da Zuhayr ya ke, daga lokacin kuma komai za ayiwa Zuhayr to za a yiwa Ben. Shaƙuwa mai tsanani ya shiga tsakanin su wanda za ka ɗauka ma 'yan biyu ne. Boarding school da Ben yai a wajen ya fara sanin maza saboda makarantar duka maza ne, inda wani ɗan ɗakin su ya fara saduwa da shi a shekaran sa goma shauku. Abun ya taɓa shi sosai shiyasa ma duk lokacin da zai koma makaranta ya ke jin tsoro. A hankaki kuma har ya ɗan fara sabawa. Bayan ya koma ɗan gidan su Zuhayr kuwa kyautatawar Zuhayr gareshi ya fara kissima ma sa soyayyar shi saboda oreintation da ya samu daga makarantar su na maza na neman maza. A hankali tun bai yarda so ba ne har ya zo ya tabbata ma sa soyayyar Zuhayr ne ya ma sa mugun kamu. Yayi ƙoƙarin bayyanawa Zuhayr abinda ke ran sa alokacin da su ka cika shekara ishirin da ɗaya, a lokacin kuma namiji na neman namiji ba komai ba ne a ƙasar tunda har aure ana yi. Da ya tambayi Zuhayr ko zai iya son namiji ɗan uwan sa sai Zuhayr ya ce Allah ya kiyaye, shi bai yarda da irin halin dabbancin nan ba. Daga wannan amsa da ya bashi ya sa Ben ya rufe soyayyar Zuhayr a zuciyar sa sai dai... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 27 Bismillahir Rahmanir Rahim *weight loss vs self love* A karo na uku ta sake ƙoƙarin jan skirt ɗin sama amma shiru ya ƙi wuce hips ɗin ta, ta ɗan fara shalle kaɗan ko zai shiga amma shiru, da ta ja da ƙarfi kuwa sai skirt ɗin ya yage. Tsaki ta ja tana riyawa a zuciyarta ba ita ba skirt kenan har abada. Ta zauna a bakin gado tana tunanin wani irin ƙiba ta ƙara da ya sa har kusan gaba ɗaya kayanta su ka ma ta kaɗan? Indai da kaya cif-cif ya ke ma ta a jikin ta idan ta sa to yanzu ya ma ta kaɗan. Kusan fiye da rabin kayan da ta zo da su daga Nigeria sun dena shigarta yanzu abinda ya sa ta ke tunanin yin shopping kenan, shopping ɗin ma kafin ta samu kayan da ta ke so aiki ne, the last time da ta siyi wasu dogin riguna da su ka ma ta kyau a shagon wasu Indiyawa ne wanda nan ma sai da ta ɗau lokaci tana neman size ɗinta, sai ta ga kaya ya ma ta kyau amma sai ta ga ba zai shigeta ba dan yayi ƙarami. Azumi da ake shirin shiga take tunanin zai rage ma ta ƙiba. "Allah ka yafe ni, amma ba ƙaramin takura na ke ba a lokacin Azumin nan" ta faɗa tana miƙewa zuwa wajen closet dan ta nemi wani kayan tunda wannan ma ya ƙi shiga. Wata riga da wando irin na 'yan Pakistan mai bujejen wando ta fito da shi ta saka tunda ta siya ba ta taɓa sawa ba saboda wandon dariya ya ke ba ta to gashi yau ya ma ta rana. Ita abin haushin ma ba ta san ya za ta yi da kayan da su ka ƙi shigar ta ba, da a Nigeria ta ke da yanzu ta bayar an je an buɗa ma ta su amma nan ita ina ta sani. A hankali ta ke takowa daga matakalar cikin nitsuwa gameda tsoro so ta ke ta shiga gym ta gwada nauyin ta. Ta taɓa shiga wajen sau biyu, na farko shine farkon zuwanta gidan da ta shiga tayi gulman ɗakin sai na biyu da ta shiga karambanin gwada yin amfani da abubuwan da ke ciki to her disappointment kuma ba abinda ta iya yi dan duk na'uran wajen ta kasa amfani da su wanda ba na'ura ba kuma sun ma ta nauyi ko ɗagawa ta kasa yi, ta ga abun gwada nauyi dan haka ta weighing nauyin ta a ranan inda ta ga ta tsaya a 90kg nauyinta a gida yana fluctuating tsakanin 84-88kg ne to amma zuwanta wannan ƙasa ta koma 90kg. Yau Tuesday dan haka ta yi tunanin ba sa gidan dan ba ta tashi da wuri ba kasancewa ba school za ta je ba tunda sun gama exams suna hutu. A hankali ta buɗe ƙofan gym room ɗin ta shiga ciki kamar wanda ta ke tsoron za ta ga horror a ciki. Kai tsaye wajen abin gwada nauyi ta tafi,ta cire takalminta ta latsa wani waje da ke gefe wanda ke da ƙaramin screen inda za ka viewing result ɗin ka idan ka hau. Ba dan ta taɓa ganin irin sa a wani asibiti da ta je yin gwaje-gwaje lokacin da za a ma ta visa da ba za ta san yadda abin ke amfani ba tunda tafi sabawa da scale ɗin da za ta hau sai wani ya dubi ƙasa ya karanta ma ka result ɗin, wannan da kan ka za ka ga result ɗin a jikin screen. Kaman 95kg kaman kuma 92kg ta ke gani a screen ɗin. Ta murza ido da kyau ta duba amma 95kg ɗin ne sai dai idan ƙarya ta ke so ta yiwa kan ta. Ta sauka daga kai ta fara ƙoƙarin rage kaya saboda tana tunanin ai kayan ma ya cika nauyi. Ta ajiye gyalen kayan da ta yane kan ta da shi gefe, ta cire rigan ya saura ma ta bra da kuma wandon sai ta hau amma to her dissappointment sai ta ga still 95kg ɗin ne. "Wandon nan ma shi kaɗai kaya ne, inaga zai ci 1kg" ta faɗa tana ƙoƙarin sulluɓe wandon. "Ki hau kai tsirara ba abinda zai chanja baby girl" kaman daga sama ta ji muryan sa ya doki kunnen ta. Ba dan da safe ba ne da ba abinda zai sa ta kurma ihu dan ba ta tsammaci mutum a gidan ba ma balle ɗakin. Ta ɗan firgita kam amma tunda ta juyo ta ganshi tsaye ya haɗe hannayen sa a ƙirji sai ta saki ranta. Babu riga a jikin sa sai wando 3-quater jikin sa duk zufa. Push up ya ke a ƙasa lokacin da ta shigo ɗakin zai ma ta magana saboda ya ga ba ta ganshi ba sai kuma ya fasa dan ya ga gudun ruwanta idan abin dariya za ta yi ya gani da dalili. Ganin ya ƙurawa ƙirjinta ido ya sa ta yi saurin juyawa tana rarumo rigarta dan ta sa. A zahiri tumbinta ya ke kallo ba ƙirjinta ba, ko da ba wai yana sa ma ta ido ba ne amma ko makaho ya gan ta ranan da ta fara zuwa da kuma yanzu ya san akwai banbanci. Rigan da ta ke kiciniyar sakawa ya ƙarɓa ya ajiye gefe. Ya sa hannu a tumbinta wanda ya sa Zaytoonah ta kusa shiɗewa saboda wani shock da ya shigeta. Wannan ce karo na farko da wani ya taɓa ma ta ciki, hana ƙarya sai dai ko a Asibiti. Ya saka kan sa a kafaɗarta yana ma ta magana a kunne mai kama da raɗa. "Zaytoon kin ƙara ƙiba, kin san dalili?" Ta girgiza kai a hankali saboda yadda ɗumin jikin sa ya fara birkita ma ta lissafi. "Barin nuna mi ki wani abu" ya ja ta zuwa wajen da aka yi ƙaton madubi inda za ka dinga kallon kan ka a duk wani workout da za ka dinga yi da na'uran da ke ɗakin. "Ga Zaytoon nan, za ta iya cin abinci sau shida ko bakwai a rana. Ba anan matsalar ta ke ba. Matsalar shine duk junk food ta ke ci, matsalar shine ba ta wani aiki da zai dinga ƙona calories da su ke taruwa ma ta ajiki, matsalar shine jikinta zai iya ma ta nauyi ta dinga jin kasala matsalar..." "Ni kam ya isa ba ruwanka da ni, ina ce shareni ka ke yi dan na ma ka tambaya akan Alinah" Yai shiru na ɗan wani daƙiƙu saboda yadda ƙwaƙwalwarsa ya tariho ma sa gawar Alinah da ya gani. "Ki tambayeni komai Zaytoon amma ban da Alinah. Ta riga ta mutu, ba na son ana tada maganar ta saboda ba abunda zai jawo sai ɓacin rai" Tausayi ya ba ta dan yadda ya ke maganar kaɗai ya gamsar da ita har yanzu yana son Alinah. Itama rasa katin matar nan da ta yi ya sa ta gwada sa'ar ta ta tambayeshi gameda Alinah amma sai ba ta samu amsar komai daga gareshi ba dan bar ma ta dining ɗin yai ba tareda ya ce komai ba, daga nan kuma sai yau ba su sake magana tsakanin su ba idan ka cire gaisuwa. Ta yi saurin ɗauke shirun da su ka yi da cewa "da gaske idan na tambayi koma minene za ka gaya min?" Ya gyaɗa ma ta kai Ta kalli cikin idon sa ta ce "kai gay ne?" Bai san sadda ya kwashe da dariya ba. "Ka ce na tambayi komai fa" "Allah ba kyau, Haramun ne ma, kuma..." Ya hana bakin ƙarisa maganar ta hanyar manna ma ta kiss a bakin. Lokacin da ya saketa kasa ɗagowa ta yi saboda bugun ƙirjinta da ya ƙaru, ga wani abu da ya ke bin jikinta yana yawo. "Kin gamsu ni ba gay ba ne ko na nuna miki a zahiri" Ta yi saurin ɗago ido tana girgiza kai. Ya kashe ma ta ido ɗaya ya ce "No, ki bari mu je ɗaki na nuna miki mata na ke so, sai ki fi gamsuwa da bayanai na" "Na gamsu Allah, dama..." sai ta yi shiru tana tunanin kar tayi magana ya kuma bijiro da wani abin, amma idon ta ba zai ma ta ƙarya ba, ranan ta ga Ben yana kissing bakin Zuhayr da ta leƙa ɗakin su. A iya sanin ta haka kawai namiji da namiji ba sa kiss a baki. "Amma me?" "Ka bar shi kawai, ya wuce" "Ki faɗi abinda ke ranki tunda ƙwaƙwƙwafi ki ke nema za ki samu" "Allah ya wuce" "Akwai wata tambayar?" ya faɗa in a serious tone "Na gama" ta faɗa da sauri... *** Duk cikin kayan ta babu sportwear a ciki. Ko ta ce ma sa ta fasa ne? Amma jiya Alƙawari ta ɗauka za ta dinga binsa motsa jiki na kwana goma kacal. Chan ta ɗauko wani wando jeans da ta siya ba da daɗewa ba. Denim jeans ne kalar toka sai ta haɗa da wani t-shirt ɗin ta baƙi. Bayan ta sa kayan sai ta ɗauko sneakers ta sa ta fito tana riƙe da baƙin ɗankwali tana ɗaurawa a kan ta. Babu kowa a falon tsit ka ke ji saboda ƙarfe shida na safe ne. Ta shiga kitchen dan ta sa abu a baki kafin Zuhayr ya sauko. Ai ko wajen Fridge ɗin ba ta kai ba ta ji an ce " na san dama nan za ki fara zuwa ai" "Ni fa ba abinci zan ci ba, na zo dubawa ne ko Chef Green ya zo" "Liar" "An gaya ma ka dan banci abinci da sassafe ba wani ɗingoɗɗin ne" "Then let's go" ya faɗa yana kama hannun ta. Suna fitowa daga kitchen ɗin su ka yi kiciɓis da Ben shima ya shirya Zuhayr ya ce ma sa yau za su raba tafiya ne saboda akwai deal ɗin da yai da Zaytoonah. Ben kamar ya fashe lokacin da Zuhayr ke magana amma da ke ya iya munfurci sai yai murmushi yana faɗin "good luck" Tafiya su ke a hankali suna tafiya lokaci zuwa lokaci Zaytoonah na ma sa tambayoyi gameda gidan da su ke wanda ya ke nesa da mutane dan idan za ta tafi school Mr Smith ya ɗauketa a mota sai sun yi tafiyar kusan minti goma kafin su fara ganin gidaje suma kuma tsilla-tsilla haka, its like anguwar dai na wanda ba sa son takuri ne. Sai da su ka yi tafiya mai nisa kafin Zuhayr ya nuna ma ta iya inda filin gidan sa ya ƙare wanda ya sa ta mamakin girman filin gidan sa. Sun yi tafiya mai nisa sosai dan sun fi awa ɗaya suna tafiya amma da ke ana tafiya ana taɗi ne sai Zaytoonah ba ta ga nisan da su ka yi ba, tafiya da ta yi nisa kam yunwa da ishirwa ne ya sa ta fara gajiya. "Amma idan za mu koma ba da ƙafa za mu tafi ba ko? Na ga tafiyar ta ƙi ƙarewa" "Ke dai ki ce kin gaji da tafiya, dan haka na ci galaba yau" "Ba wai na gaji ba ne fa tambaya ce kawai" "Zaytoon ki yarda kawai, i won" Da suna dawowa kuwa sai ta ga tafiyar ta ma ta nisa saboda yunwa da ta ke ji amma a haka dai suka dawo da ƙafan dan ya ce ba zai kira Driver ba. Suna zuwa kuwa dining ta nufa Zuhayr ya bita da sauri. "No no no no" ya riƙe hannun ta da ke shirin buɗe wani bowl "Ba ci zan yi ba dubawa kawai zan yi" "Ki je ki yi wanka Baby" Haka ta kumbura fiska tana tura baki ta haura sama. Da ta yi wanka ta sauko ma shi ya tsara abincin da za ta ci. "Ɗan wannan abun zan ci?" "Is not about the quantity but quality Baby girl" "Allah cin zali ne wannan, cin zali of the highest order" "Mi na gaya miki jiya?" Ta juya ido ta ce " abu biyar da za su sa na ji daɗin jikina amma in ji Zuhayr" "Ba in ji ni ba Zaytoon, its the truth, abincin da ki ke ci dole ya zama mai lafiya" "Whatever" Ranan dai gaba ɗaya abincin da ta ci ƙarƙashin kulawar sa ce. Ben kam wuni yai a ɗaki yana nazarin yadda zai yi da wannan sabon salon shaƙuwa tsakanin Zuhayr da Zaytoonah. Idan aka tafi a haka Zaytoonah za ta samu dama akan Zuhayr. A da ya renata saboda ƙarancin shekarunta da kuma gani da yai kaman ba ta da abinda za ta iya jan ra'ayin Zuhayr da shi amma kuma yanzu dole ne ya raba tsakanin wannan shaƙuwa. Cikin kwana goman nan ba ta da sukuni, Zuhayr ya ma ta kane-kane. Abincin da ta ke ci duk under strick supervision ɗin sa ne ga shi ta ɗauka excercise ɗin su kaman na ranan farko ne ashe ba haka ba ne, ranan farko sharan fage ne. Washegari gudu su ka yi a cikin gida da zagaye gidan su ka yi sau goma, sun yi biyar su ka zauna su ka huta kafin su ka sake yin biyar. Rana na uku ma gudu su ka yi, a rana ta huɗu kuma suna fitowa waje ya miƙa ma ta jump rope ya ba ta. Ta bishi da harara bayan ta karɓa igiyar. Da sauri ya ke tsallen amma ita a hankali ta ke yi tana yi ma tana harɗewa, minti goma su ka yi ya ce a huta akayi hutun minti biyar sannan aka sake yin wani minti goman ana tsallen aka sake yin hutun minti biyar kafin su ka yi na wani minti goman wanda da ƙyar Zaytoonah ta kai. Kwantawa ta yi laƙwas akan grass carpet tana maida numfashi Zuhayr ya kwanta gefenta yana maida numfashi shima. "Ya ki ka ji?" "Ni dai daga wannan kwana goman ba zan ƙara yin komai ba" Yai dariya. Sauran kwanakin kuma a gym room aka ƙarisa wanda da tsiya-tsiya aka ƙareta. Day 11 ta tashi da ɗoki yau kan babu wani excercise babu cin abubuwan da Zuhayr ke tursasa ma ta ci. A ƙasa ta sameshi har ya shirya cikin suit shi da Ben da alama fita zai yi. "Yau kam angama" ta faɗa tana murmushi "Saura abu ɗaya" "Babu, ai kwana goma ka ce" Ya zaro wani takarda a Aljihun sa ya miƙa ma ta sannan ya ce " zai yi tafiya sai bayan kwana huɗu zai dawo" Bayan ya tafi ne ta buɗe takardan. *ki je gaban madubi ki duba kan ki, ki ɗau lokaci kina kallon kan ki. Sannan bayan kin gama ki yi shawara da kan ki, ki zaɓa self love or weight loss* Ta jima tana sake karanta takardar amma ba ta gama gane manufar takardar ba... Da ke da Ben su ka tafi ita ɗaya ce a gidan kamar yadda ya faɗa ɗin ta jima tana kallon kan ta a jikin madubi amma ba ta ga komai da ya chanja ba hakan ya sa ta watsar da maganar zuwa yamma kuma ta je gym room ta gwada nauyin ta. To her shock daga 95kg sai ta ga ta sauka zuwa 91kg. Ta yi murmushi dan ta fahimci mi Zuhayr ke nufi. Maimakon ta dena excercise kamar yadda ta yi niyya da farko sai ta cigaba kamar yadda su ke yi da Zuhayr. Abinci ma irin yadda ya tsara ma ta takeci sai dai ta ɗan ƙara yawan sa. Eat more protein Zaytoon saboda calorie ɗin sa na saurin ƙonewa ba kaman na carbohydrate ba. Ba ta taɓa yiwa Zuhayr waya ba amma a rana ta biyu sai ta kira numbar sa, ba a ɗauka ba dan haka ta tura ma sa da text kamar haka *i choose self love* Bayan minti talatin sai ya kirata ya ba ta haƙuri na rashin ɗaukar wayarta da bai yi ba saboda meeting da su ke yi. Sun ɗan taɓa hira kafin ta kashe wayar... *** Dawowar Zuhayr daga tafiya da kwana biyar aka fara Azumi. Kwanakin farko duk sai da ta makara saboda bacci sai wucal ta ke yi. Hakan ya sa ta sa Zuhayr ya dinga tashin ta, ita ko a gida Mommy ce ke tashinta dan idan ta sa Alarm ma idan ya buga a banza, ko ta tashi kashewa ta ke yi ta cigaba da bacci. Zuhayr baya suhur amma haka zai zo ya tasheta wani lokaci sai ya zo har sau biyu kafin ta tashi ta fita ta nemi abincin da za ta yi suhur da shi. Ranan tana bacci sai ga kiran Chef Green wai ta zo tanada baƙi a ƙasa. Ta yi mamaki dan ita ba ta san kowa ba balle har a zo neman ta, ta dai fita dan tana tunanin ko baƙin Zuhayr ne. Mata da miji ta gani da 'ya'yan su biyu mace da namiji, da ka gan su ka san ba za su wuce 'yan India ko Pakistan ko Malaysia ba. Bayan sun gaisa matar ta yi ma ta bayanin ko su ɗin su waye ne. Namijin ya gabatar da kan sa da suna Faisal Khan ita kuma matar Zahra Ayyub wanda hasashenta ya zo kusan dai-dai dan Faisal khan ɗan Asalin ƙasar India ne matar sa kuma 'yar Malaysia. Yaran su kuma Macen wacce ita ce Babba, sunan ta Alinah sai namijin Fareed. Cewa su ka yi ba su san Zuhayr yayi aure ba sai a wajen Chef Green, sun kawo wa Zuhayr ziyara ne ya ce baya nan amma matar sa na nan shine su ka nemi ganin Zaytoonah. Sun yi murna tareda yiwa Zaytoonah addu'ar fatan samun zaman lafiya. Da za su tafi su ka roƙi Zaytoonah akan ta taimaka ta jawo Zuhayr ya koma yin Ibadah kamar yadda ya ke yi kafin mutuwan Alinah. Tunda Alinah ta mutu bai sake zuwa masallaci ba haka nan ya dena shiga harkan kowa musamman wa'yanda su ka haɗa alaƙa da Alinar. Da maghrib su na buɗe baki ta gaya ma sa yayi baƙi da rana. Tana faɗin Faisal Khan ta ga ya haɗe rai. "Shikenan dan Alinah ta rasu sai ka dena mu'amala da kowa na ta?, shikenan dan Alinah ta rasu sai ka dena zuwa masallaci? Kenan dan Alinah ka ke ibadah ba dan Allah ba?" "Ba ki san komai ba, ki ajiye maganar nan a haka" "Anya kana sallah ma?" Ta yi tambayar kai tsaye. Idan akwai abinda za ta ma sa ya ji daɗi kafin ranan rabuwar su bai fi ta taimaka ma sa wajen gyara tsakanin sa da Allah ba. And for that she has to be brave. "Idan masallaci ki ke son zuwa ki gayawa Mr Smith zai dinga kai ki" "Ni kai na ke so ka kai ni, bai kamata ace" "Enough Zaytoon" ya faɗa da ɗan ƙarfi sannan ya miƙe ya bar wajen yana jin haushin kan sa da ya bari yai sakewar da Zaytoonah ta raina shi. Daga ranan kuma ya dena ma ta magana ko ta gaishe shi haka zai amsa sama-sama ko idon ta ba zai kalla ba. Buɗe baki da su ke yi tare kuma ya dena hakan kuma shi ya fi damun Zaytoonah... Yau suna dawowa daga masallaci tana cikin mota tana amsawa Mr Smith tambayoyi gameda Azumin da musulmai ke yi a watan Ramadan kamar daga sama wata babbar mota ta zo ta buge su, sai da motar ta su ta je ta bugi wasu bishiyoyi da ke kusa da titin tukunna ta tsaya. Ben yai sauri yai reverse da babbar motar sa ya ƙara gaba da gudu. Ya lura ta fara zuwa masallaci dan idan Mr Smith ya fita da ita bayan magariba sai chan dare ta ke dawowa. Ba damuwar sa ba ne tunda abin da ta ke so kenan. Yana zaune akan gado yana duba laptop ɗin sa yana ɗan kurɓan coffee sai ga wayar sa ta hau ruri, ya jawota a hankali ya sa a kunne yana faɗin "Hello" Abinda aka faɗa ma sa ne ya sa shi miƙewa zumɓur yana faɗin gashi nan zuwa. Yana fita ya fara ƙwalawa Ben kira amma babu shi babu dalilinsa. Dan haka a rikice ya fita ya samu dreban sa ya wuce da shi Asibiti. Ɗakin da aka kwantar da Zaytoonah ya fara zuwa bayan ya gama jin bayani daga wajen wani police. Ance ma sa ba ta ji ciwo sosai ba Mr Smith ne ya ji ciwo sosai. Amma ganin ta kwance an ɗaure ma ta goshinta da ya bugu da bandeji sai hankalin sa ya ƙara tashi. Zama da yai yana kallon ta bai san lokacin da hawaye ya fara zubo ma sa ba. "She's too young to die" ya faɗi a ran sa. Ko da matsayin da ya bawa Zaytoonah matsayine na ƙanwa, baya fata ya rasata kamar yadda ya rasa Alinah. At first bai ɗauka za su yi wani shaƙuwa ba a iya shekarun da ya ɗiba da za su yi aure amma gashi tun ba aje ko'ina ba ta shiga ran sa sosai. Ben ne ya dafa kafaɗar sa ya katse ma sa tunanin da ya ke yi. "She wont die right?" Ya faɗa bayan ya juyo ya kalli Ben ɗin wanda ya tsura ma sa ido yana ma sa kallon So da tausayi gameda haushin wai hawayen da ke zuba a idon masoyin sa hawaye ne saboda Zaytoonah. Ko ba ta mutu ba ya so ace ta nakasa sosai abinda yai niyya kenan, amma sai gashi buguwa kawai ta yi a kan ta. Da ma ita ce ta ji ciwon da Mr Smith ya ji. "She wont die" ya furta da sigar lallashi yana rungumeshi, shi kaɗai ya san miya ke ji da wannan runguma da ya samu a wajen Zuhayr. A Asibiti Zuhayr ya kwana kuma ya ci sa'a Zaytoonah ta farka chan tsakar dare. Kwana biyu ta yi a asibitin su ka sallameta amma Mr Smith kam zai ɗan jima. An fara investigation amma babu wani result da aka samu mai gamsarwa dan wanda yai aikin ya daidaici inda babu CCTV ne yai wannan aika-aikar... *Team Ben ina ku ke ne? muna gayyatar ku querry* *Idan kuna son sanin formula da Zuhayr ya bawa Zaytoonah please comment i'll love to share😀* 2/11/21, 10:04 PM - ****: 28 Bismillahir Rahmanir Rahim *deflowering* Duk wani kulawa Zuhayr yana bawa Zaytoonah. He felt guilty gameda abinda ya faru, hakan ne kuma ya sa sati ɗaya da ta warke sosai ya ɗauketa da kan sa su ka je masallaci sallar Tarawih. Wanda su ka san shi tunda ba ƙaramin murna su ka yi da ganin sa ba. Ba irin wa'azin da ba a ma sa ba amma ya janye jiki da masallaci. Lokacin da yai sallah a masallacin kuma sai ya ji wani ni'ima ya ratsa shi. Bayan an idar da sallah Sheikh Hassan ya gayyace su zuwa shan ruwa gidan sa washegari. Tunda su ka je gidan Sheikh Hassan sai ya zamana kusan kullum sai dai su je shan ruwa wani gida, har gidan Faisal Khan sun je. Azumi yana saura kwana uku ko huɗu ta yiwa Zuhayr magana akan suma ya kamata su gayyaci mutane shan ruwa gidan su tunda suma sun je gidajen mutane. Yayi na'am da shawaran dan haka su ka shirya yadda tsarin zai kasance. Kusan indai mutum na attending masallacin nan to suna gayyatar sa indai zai samu damar zuwa. Ranan Azumi ashirin da tara aka zo aka yi liyafa a gidan Zuhayr. Liyafa ce da aƙalla families gida ishirin da takwas su ka zo daga ƙasa mabanbanta amma zaman Las Vegas ya haɗa su an zama ɗaya. Da ke tunda aka yi maganar sai aka tsayar da shawara akan kowa zai kawo abu daga gidan sa ya zo da shi, sun ce kar nauyi yai wa Zuhayr yawa duk da kuwa sun san Zuhayr ɗin yafi ƙarfin haka. Mata da yara na gefe guda ana cin abinci ana hira yayinda suma maza ke chan gefe suna na su. Abincin kusan serve yourself ne kowa ya ɗebi abinda zai iya ci. A wajen Zaytoonah ta sha labarin Alinah a wajen wanda su ka san ta. Kowa faɗan kyawawan halayen ta ya ke yi da yadda su ka sha mamakin mutuwarta tashi ɗaya, mutuwa ma mai muni wato kisan kai. Wasu har lokacin ba su yarda Alinah kashe kan ta tayi ba ganin irin yadda ta ke da riƙo da addini, sun fi yarda da cewa kasheta aka yi aka nuna kaman kashe kan ta tayi. Bayan anci abinci aka haɗu aka yi sallar jam'i a wajen da aka idar aka yi sallama ana taya juna murnan ganin wata da aka yi saboda sun ji labari ance an gani a wasu wajajen ciki har da ƙasar Saudiyya. Lokacin da Zahra matar Faisal Khan za ta tafi ne ta bawa Zaytoonah wani dogon envelop ta raɗa mata kalmar ALINAH a kunne. Zaytoonah ta amshi envelop ɗin jikinta na rawa. Bayan kowa ya watse ta yi sauri ta shiga gida inda ta bar Zuhayr yana taya ma'aikatan sa tattare wajen da aka ɓata. Tana zama akan gado ta buɗe envelop ɗin hannunta har rawa ya ke yi. Hoton da ta fara gani na wata farar Balarabiya ce tana tsaye tana murmushi, tana sanye da riga shirt brown sai dogon skirt baƙi ta yi rolling da baƙin gyale ta juya bayan hoton ta ga an rubuta sunan Alinah Amir Jones da kuma iya shekarun da tayi a duniya. Ta rasu tana da shekara ashirin da shida. Hoto na gaba ma na Alinah ce amma da kayan Indiyawa ita da Amarya Zahra Ayyub. Hoton gaba ma A wajen auren Zahran ne cikin jama'a ma ta ke. Sai hoto na gaba an ɗauka su huɗu, ita da Zuhayr sai kuma Zahra da Faisal Khan shima duk a auren su ne. Hoton ƙarshe kuma ita da Zuhayr kaɗai su ka ɗauka a wajen auren still. Wani Jarida ta gani kaman an wrapping ɗin hoto da shi ta duba headline ɗin jaridar ta ga an rubuta *MUSLIM WOMAN COMMITTED SUICIDE OVER GAMOPHOBIA* Ta yi saurin jawo wayarta ta duba ma'anar kalmar Gamophobia. Hoton da aka naɗe da jaridar ta ɗauko hannun ta na rawa saboda a juye ya ke. Tana buɗewa ta yi saurin rufe bakinta jikinta na ƙyarma bayan ta ajiye hoton akan gado. Alinah ce a cikin bathtube wanda ruwan ciki gaba ɗaya ya rikiɗe ya koma jini. Innalillahi kawai ta ke ta maimaitawa tana jin tsoro na shigarta. Da ana cewa kisan kai ta ɗauka hanging kan ta tayi ashe ma mutuwa mai girgiza hankali ta yi. *She bled to death* abinda aka rubuta a jaridar kenan bayan ta koma kan jaridar ta karanta labarin. Muryan Zuhayr da ta ji yana haurowa sama ne ya sa ta tashi da sauri ta fita daga ɗakin da gudu. Saura stairs biyu ya haura sama ta iso ta rungumeshi sosai haɗeda fashewa da kuka. Dole ya damu da rashin son jin labarin Alinah, wani irin damuwa ne zai sa mutum ya kashe kam sa, ya yanka hannun sa ya dinga gani har jinin sa ya tsiyaye. "Miya faru?" "I'm sorry Zuhayr, i'm really sorry" Da ƙyar ya samu ta nitsu ta dena kuka kafin ya janyeta daga jikin sa ya rakata har ɗaki. Ben na bayan su yana wani huci idon sa yayi ja. Yanada plans dayawa gameda yadda zai yi ya hallaka Zaytoonah kuma ba zai gushe ba sai ya ci nasara akan ta. Bayan ya rakata ɗakin ne ya ga hoton da ta gani, bai ce komai ba sai ma janye jikin sa da yai daga Zaytoonah ya ma ta sai da safe ya wuce na sa ɗakin. Yana shiga ɗakinsa shima ɗin jikinsa ne ya hau rawa saboda abinda ya gani ya tono ma sa tsohon gyambo da ke zuciyar sa har yau ya kasa warkewa. Washe gari ranan Sallah haka su ka tashi sukuku, kowa da tunanin da ya ke yi a ran sa. Waya da su ka yi da 'yan gidan su ne ma ya sa Zaytoonah ta samu farinciki. A rana ta ukun Sallah su ka je gidan su Kakan Zuhayr saboda an ma sa waya Mr Haddish ba lafiya. Sun je sunyi kwana biyu su ka dawo saboda jikin na sa da sauƙi... *** Yau ne rana ta farko da ta koma makaranta saboda hutu ya ƙare. A nan ɗpoet ce. Zaytoonah was so captivated with the fact cewa mutum ɗaya zai iya abubuwa dayawa haka. A cikin taɗin da su ka yi ne watarana ta sanar da Farha tana son koyon rawan ballet saboda ta cikawa Mommynta burinta na zama ballerina. "So what's stopping you?" Farha ta faɗa tana tauna chewing gum "Its too late, i'm going to be seventing in 3months time" "So?" Zaytoonah ta kalleta da mamaki. "That's not a reason" "I'm fat" Zaytoonah ta faɗa daga ƙarshe Farha ta fashe da dariya, dariya sosai harda riƙe ciki. "Kinga kalmar ƙiba idan tana damun ki ba abinda za ki yi a rayuwar ki. Look Zaytoonah babu abinda siriri zai yi da mai ƙiba ba zai yi ba sai dai idan bai yi niyya ba" Zaytoonah ta baza kunne tana sauraron how confident Farha ta ke magana gameda abubuwan da mutum zai iya idan ya sa kan sa. Bayan sun gama hiran ta ba ta assignment akan idan ta je gida tayi tunanin mi take so ta zama bayan zama Barrister... Kwana biyun nan Zuhayr yana sintiri tsakanin Vegas da ƙauyen su Kakan shi saboda jikin na sa da ya tashi. Duk yadda ya so Mr Haddish ya bar gidan gona ya zo babban asibiti a cikin gari a duba shi ya ƙi cewa ya ke yi wai ya san ɓata lokaci za ayi amma shi ya san ya kusa mutuwane kawai. Bayan gajeruwar jinya da Mr Thomas Haddish yai sai rai yai halin sa. Rana ce da ta sa Zuhayr kuka saboda tsananin son Kakan sa da ya ke yi. Har da Zaytoonah aka je burial amma ita kam ko wajen akwatin gawan ba ta je ba lokacin da ake zaman wake. Da za aje bisine shi ma ba ta je ba saboda tsoron gawa ta ke yi, ko a TV aka nuna akwatin gawa ko mutum cikin likkafani to haka za ta yi ta jin tsikar jikinta na tashi. Wani lokaci har mafarkin abin sai ta yi. Saboda school ko kwana ba ta yi ba ta koma Vegas ta bar Zuhayr da Ben suna karɓan gaisuwa... Lokacin da Zuhayr ya dawo kuwa sai ya koma wani silent da shi ɗan kazar-kazar da ya ke yi da duk ya rage. Yau ta kawo ma sa form ɗin ballet ɗin da ta ƙarɓo na wani makaranta. Sashen Adult Ballet Dance ta ke son shiga kuma ajin farko wato na beginners. Ya karɓi form ɗin ya karanta sai kuma ya fashe da dariya. "Au dariya za ka min ma" "No no no Baby girl, ina murna ne saboda finally na yarda kin zaɓi self love fiyeda weight loss" "Ba wani, ka faɗi ranka kawai dan inada ƙiba ka ke min dariya" "Seriously Zaytoon ina tayaki farin ciki ne, ina tareda ke hundred percent" Ya ƙarisa maganar yana ma ta thumbs up. Ya duba wajen da guardian zai yi signing sai yai sannan ya miƙa ma ta takardar... Yau sun fito daga cafeteria da Farha ta ji an kira sunan ta, ta juya da sauri dan kamar ta gane muryan wanda ke kiranta. Matar nan ne da su ka haɗu watanni kusan biyar da su ka wuce. "Ki yi haƙuri na rasa inda na jefa katin ki ne shiyasa ban neme ki ba" Matar ta yi murmushi ta ce ba komai itama mahaifiyarta ce ba lafiya shiyasa ba ta sake bibiyar Zaytoonan ba. Sun saka akan za su haɗu ranan asabat a wani coffee shop. Bayan tafiyarta ne Farha ta tambayi Zaytoonah inda ta san matar sai ta gaya ma ta yadda aka yi su ka haɗu da kuma abinda ta ce. Abu da wanda ta san technology tuni ta ɗau wayarta ta fara binciko mutane ma su suna Linda Cannel da su ke zaune a cikin Las Vegas. Ba su dayawa dan haka fa yi saurin ganin wanda su ke nema. Ta taɓa aiki da Kamfanin Zuhayr kafin ta ajiye aiki ta nemi wani wajen bayan. Ta yi aure amma sun rabu da mijin tana da yaro ɗan shekara biyar currently tana zaune da Mahaifiyar ta da ɗan ta Aiden ne. Bayan ta gama karanto bayanai ne Zaytoonah ta fahimci inda ta san Alinah. To indai ƙawar Alinah ce kuwa to ba za ta ma ta ƙarya ba. Da ta koma gida tana son gayawa Zuhayr gameda Linda amma wani zuciyar ya hanata saboda ba ta so ya tada hankalin sa. Ranan Asabat ƙarfe uku ta haɗu da Linda a inda su ka amince za su haɗu. "He'll kill you too" abinda ta fara faɗa kenan a lokacin da ta tambayeta mi ta sani gameda mutuwar Alinah. "Zai kashe ki kema" ta sake maimaitawa "Waye zai kashe ni" ta faɗa ina a confused tone "Wanda ya kashe Alinah" "Waye?" Linda ta yi shiru tana nazarin Zaytoonah, tana son gaya ma ta abinda ta sani amma kuma tana tsoron kar Zaytoonah ta je ta yi shirme dan ta lura akwai yarinta a tattare da Zaytoonan. "Tunda ki ke zaune a gidan Zuhayr an taɓa baki tsoro ko kuma kin an taɓa ƙoƙarin taɓa lafiyar ki?" Zaytoonah ta girgiza kai "Ki faɗa min gaskiya ina son tabbatar da wani abu ne" Zaytoonah ta yi ajiyar zuciya kafin ta gaya ma ta abinda ya faru kwanakin baya chan da kuma hatsarin da su ka yi da mota. Linda ta ce "ba zai barki ba har sai ya hallaka ki indai ba fita kikayi daga rayuwar Zuhayr ba" Zaytoonah ta zaro ido cike da tsoro. Wayarta Linda ta fito da shi, tsohuwar waya ce dan an jima da yayin irinta. Airpiece ta ba ta tareda cewa ta saurari voicenote da ta saving da Alinah. Zaytoonah ta amsa ta saƙala airpiece a kunnen ta tana sauraro. "Hey, Linda are you coming this evening? Mrs Taylor is bringing the wedding dress, i'm finally going to try them on yehhhh. Oh! I think i know who's being making those scary pranks on me lately its Ben, i'm sure of it. Do you think he's gay?. Later someone's knocking" "Last voicenote da ta tura min kenan. Bayan nan da Mrs Taylor ta kai ma ta wedding dress ɗin ta shine ta samu gawarta a banɗaki. Gaya min maganar Alinah yayi kama da wacce ke tsoron aure ko kuma wanda ta ke fama da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa?" Zaytoonah ta girgiza kai jikinta ya mugun yin sanyi. "Ban samu voicemail ɗin ba sai bayan kwana biyu da mutuwar Alinah saboda rikicewa da na yi da mutuwar ko ta kan waya ta ban bi ba. Na kai wannan voicemail police station ɗin amma ba wanda ya kulani. Alinah musulmace shiyasa ba a damu a wani faɗaɗa bincike ba sannan kuma wanda yai kisan ya riga ya biya kuɗi ta yadda aka ƙi karɓan kowani bayani da ya wuce cewa Alinah kashe kan ta tayi " "Kina tunanin Ben ne yai kisan?" Zaytoonah ta faɗa cike da fargaban amsar da Linda za ta bayar. "Kina ganin zai iya haka?" Linda ta faɗa tana miƙewa tsaye tareda cewa za su iya haɗuwa wani lokacin su cigaba da tattaunawa idan har Zaytoonah ta ba ta dama. Linda tafi minti shabiyar da tafiya kafin ta iya miƙewa itama ta bar shagon bayan ta ajiye kuɗin coffee ɗin da duk cikin su babu wanda ya sha. Cike da tunani barkatai Zaytoonah ta isa gida. Tana zuwa ta ga Zuhayr da Ben a falo suna magana sai kuma kalaman Alinah ya faɗo ma ta. To ko dai da gaske Ben gay ne tunda da idonta ranan ta gani Zuhayr na kwance shi kuma ya rankwafa yana kissing bakin sa. Irin kallon tsana da ya ke ma ta tun zuwanta gidan ma alamar tambaya ce. "Baby girl zo ki ga" Zuhayr ya katse ma ta tunani. Ta ƙarisa wajen tana ƙaƙaro murmushin dole. "Guess what?" Ta ɗaga ido dan ba za ta iya guessing komai ba. "Za mu je 5 days vacation" "Really?" Ta faɗa tana nuna ɗoki. "Ki shirya jibi ne tafiyar, inda za mu je akwai sanyi sosai dan haka ki ɗauko kayan sanyi ma su yawa" "Ina za mu je?" Surprise ya furta yana murmushi. Ta kalli Ben ma sai murmushin ya ke yi. Sai da ta dage da tambayar kafin Zuhayr ya gaya ma ta inda za su je a ƙasar Finland ne. Ben ne ya haɗa mu su tafiyar saboda birthday ɗin Zuhayr da ya ƙarato. Jin Ben ne ya haɗa tafiyar ya sa ta ɗan tsorata amma ta dake saboda ta ga kamar Zuhayr na son tafiyar ba ta son kawo abinda zai mata ma sa rai especially tunda tafiyar ta celebrating birthday ɗin sa ne... *** An fara sanyi a America amma bai kai na wannan ƙasa ba, dan tun daga airport ta rena kayan da ta sa saboda sanyi da ya dinga fizgarta. Daga inda su ka sauka ko hutawa ba su yi ba su ka sake shiga wani jirgin wanda ya ƙara kai su wani gari. Ƙamƙara ne ta ko'ina ya rufe gidaje da motoci, a hanya sai da Zuhayr ya cire rigan sanyin sa ya sa ma ta kafin ta dena rawan sanyi. Daga airport mota ta ɗauke su zuwa hotel ɗin da za su kwana. Kowa ɗaki daban aka kama ma sa. Zaytoonah na shiga na ta ɗakin ta bi lafiyar gado ta shige cikin bargo saboda sanyi. Tunda aka shiga yanayi na sanyi a America ta ke complain ashe ba ta ga komai ba tukunna, sanyi har cikin ƙashinta ta ke ji. Ranan ba inda ta je tana ɗaki, Zuhayr ya zo akan su fita wajen restaurant su ci abinci amma ta ƙi saboda sanyi sai ordering yai aka kawo ma ta ɗaki. "Anya za ki iya zuwa inda za mu je dan wajen yafi nan sanyi fa" ya faɗa lokacin da ya ga ta rufe kan ta da bargo tana cin abinci ta ciki. Da su ka fita da Ben sai ya biya wani shago ya sake siya ma ta wasu kayan sanyin ma su kauri da safar hannu da safar ƙafa. Washegari a mota su ka wuce ƙauyen da za ayi party ɗin wanda ya kama ranan birthday ɗin Zuhayr kenan. Duk da irin mahaukacin shigar da ta yi hakan bai hanata jin sanyi ba, ya dai fi babu za ta ce, banda fiskarta babu abinda ke waje. Irin abinda ta ke gani a film sai gashi ta gani a zahiri suna tafiya suna magana sai kaga hayaƙi na fita a bakin su. Wani camp ne mai kyau da aka gina Igloos dayawa a wajen saboda ma su yawon buɗe ido ko kuma dai ma su kawo ziyara wajen. Igloo biyu Ben yai booking ɗaya shi da Zuhayr ɗayan kuma na Zaytoonah. Gurin sosai ya ma ta kyau musamman ma da ta shiga Igloo ɗin ta ta gani abin ya bata mamaki haɗe da sha'awa, ita da take tunanin za ta ji sanyi a ciki sai ta ji ɗumi. Ba su kaɗai ba ne a wajen sun haɗu da mutane da dama dan wajen ya zama kaman wani resort ne haka. Wasu sun zo honeymoon, wasu shaƙatawa kawai su ka zo, wasu kuma yawon buɗe ido. Da su ka je anyi wasan skating inda Zuhayr ma ya shiga aka yi da shi, sannan aka yi rawa aka ci abinci aka sha giya da duk wani nau'in drinks wanda duk wanda ke gurin an bashi ne da kuɗin da Ben ya biya. Anyi hotuna kala-kala. Da dare aka haɗu aka yi circle a tsakiyar wuta ana jin ɗimi, ana labarai ana raha, abin gwanin sha'awa. Zaytoonah ta yiwa Zuhayr raɗa a kunne akan za ta koma igloo ɗin ta tayi sallah ta kwanta bacci ta ke ji ya ma ta sai da safe. Tana shiga ta yi sallah a zaune dan ba ka iya miƙewa a ciki saboda yayi kaɗan ɗakin. Ta kwanta akan gado bayan ta warware bargonta. Ko minti ɗaya ba ta yi da kwantawa ba wayarta ya shiga ringing ta duba sai ta ga sunan Zuhayr ne, da sauri ta ɗauka tana tunanin mi zai ce ma ta sai kuma aka kashe wayar. Ta fara ƙoƙarin sake kira sai ga saƙo ya shigo inda aka rubuta cewa ta fito ta zo ta baya wajen da akayi wasan skating da rana akwai surprise na jiranta. Ba tareda ta kawo komai ran ta ba ta tashi da sauri ta fito tayi ta baya da sauri. Tana jin muryoyin wanda su ke jin ɗumin nan suna dariya amma ko waiwayar su ba ta yi ba ta yi tafiyarta. Wajen ba wani nisa ne da su ba dan haka cikin sauri ta ke tafiya cikin yashin ƙanƙara. Buga ma ta ƙaton ice da aka yi a ka ne ya sa ta faɗi ta suma. Ben ya kamo hannunta duka biyu ya ja ta zuwa wajen da ya je ya tona da rana. Lokacin da ake ta faman kaɗe-kaɗe da raye-raye ya zulluɓe ya zo ya fasa ƙanƙarar da ke wajen har sai da ya ga ruwa sai ya mayar da iceblock ɗin saman ya rufe. Ben na nasarar tura Zaytoonah cikin ruwan ya sa iceblock ya rufe, bokiti da ke chan gefe daya cika da yashin ƙanƙara ya ɗauko ya zuba a saman saboda ya sake rufe wajen. "You'll freeze to death you bitch" ya faɗa yana tufar da yawu kafin ya bar wajen da sauri. Ben na dawowa wajen da mutanen su ke aka cigaba da taɗi dama fitsari ya cewa Zuhayr zai je ya yi shine ma ya tafi da wayarsa. Ba a jima ba Zuhayr ya fara hamma ya miƙe ya ce zai je ya kwanta, zuwa lokacin an ɗan fara raguwa a wajen Ben ya bi bayan sa su ka wuce na su igloo ɗin, har zai shiga sai ya ce bari ya leƙa Zaytoonah. Ben ya tareshi yana faɗin ai ta jima da bacci tunda tun ɗazu ta tafi. Har ya haƙura sai kuma zuciyar sa ya riya ma sa gara ya shiga ya tabbatar tana bacci ƙila ma haka sanyi ya hanata bacci. Ba tareda son Ben ba haka Zuhayr ya leƙa ɗakin Zaytoonah wanda ke kusa da nasu. Ganin ba ta ciki ya sa shi fitowa da sauri yana faɗawa Ben ba ta ciki. Ben ya ce ƙila ta je banɗaki ne tunda banɗakan da aka gina suna ta ɗan baya. Sai alokacin Zuhayr ya ɗan ji sanyi. Ya kwanta amma hankalin sa na kan Zaytoonah ko ta dawo ko kuma dai ba ta dawo ba. Minti biyar ya ƙara sannan ya miƙe ya fita da sauri ya sake leƙa ɗakin Zaytoonah amma babu ita babu dalilinta. Ya ɗauko waya ya fara kira sai ga wayar na ringing a ɗaki nan da nan hankalin sa ya tashi ya nufi wajen da ake shan ɗumi yana tambayar su ko sun ga Zaytoonah. Zaytoonah ba ɓoyayyiya ba ce tunda ita kaɗai ce baƙar fata a wajen gata 'yar dima-dima da ita. Kowa a wajen ya ce tunda ta tashi a wajen ba su gan ta ba. Hankalin Zuhayr ya ƙara tashi, kankace me an bazama neman Zaytoonah kowa sai ƙwala ma ta kira ya ke yi. Ben na gefen Zuhayr yana riƙe da hannun sa yana ma sa lallashi akan ya kwantar da hankalin sa za a ga Zaytoonah. Haushi da wani kare ke yi ya sa su ka juya ta wajen da ya ke tsaye yana kallon ƙasa yana haushi. Karen ɗaya daga cikin ma su kula da wajen ne dan haka da sauri aka ɗungunzuma wajen Karen inda aka haska saitin inda ya ke kallo aka ga alamar mutum ta cikin ƙanƙara. "Zaytoon" Zuhayr ya faɗa a rikice yana durƙusawa a wajen. Janye shi akayi da ƙarfi saboda ana so a fasa wajen a ɗaukota. Cikin mintuna kaɗan sai ga shi an fasa ƙanƙaran wajen yayinda mutum biyu su ka jawo Zaytoonah daga cikin ruwa. Zuhayr na ganin haka ya faɗa jikin ta yana kuka. "we need to help her" aka faɗa ana janye Zuhayr daga kan ta dan hakan da yai ba abinda zai jawo sai ɓata lokaci kuma tana buƙatar taimakon gaggawa. Ɗaukanta aka yi cak akayi wajen da ake jin ɗumi da ita, cikin ma su kula da wajen ne aka nemo wani ƙaton bargo aka shimfiɗa sannan aka ɗaura ta akai aka nannaɗeta da shi wani ɗan ƙaramin aka fara dannawa sai iska mai ɗumi ya fara kumbura bargon yana ratsa Zaytoonah. Still bayan minti kusan goma da bargon yai sanyi jikin Zaytoonah ba abinda yai dan har lokacin jikinta sanyi lalau kamar ƙanƙara. Kalmar "her heart is beating" da ya ji an faɗa ɗazu ya sa zuciyar Ben bugawa. Shifa jira ya ke ya ji ance "we are sorry but she's dead" amma kowa kawo idea ya ke na yadda za ayi jikinta ya samu ɗumi. "Go fuck her man" wani bature ya faɗawa Zuhayr da ke kuka... Bai kawo a ransa rana irin ta yau za ta zo ba, bai kawo a ran sa zai yi tarayya da Zaytoonah ba. Sun yi aure ne da yarjejeniyar irin wannan abu ba zai taɓa shiga tsakanin su ba har su rabu to amma ya zai yi he has to help her. Idan sauran abubuwan ba su yi ba he has to try body contact too. Idan ya rasa Zaytoonah a haka baya tunanin zai iya yafewa kan sa. Kayan jikinta kaf da har yanzu su ke jiƙe ya cire ya yar gefe, a hankali ya fara cire na sa kayan yanayi yana hawaye, seeing her unconcious ya breaking na sa to the core, gashi kuma zai ma ta abinda ya sani idan ta farfaɗo ba za ta yafe ma sa ba tunda sun ce auren su babu tarayya irin wannan aciki. Har imagining yai a ransa ta tashi tana ma sa masifa akan dan miyasa zai raping ɗin ta. Bin ƙo'ina na jikin ta yai yana shafawa da man zafi da aka bashi, yana yi yana murzawa yana goga jikin sa da na ta. He took a while yana ma ta hakan wanda a nashi ɓangaren ba ƙaramin tada Engine ɗin sa hakan yai ba. Tuntuni Engine ya miƙe yana jira ya fara aiki amma ya ke ƙoƙarin bin komai a hankali. "I'm sorry for taking advantage of you Zaytoon" ya faɗa yana caressing fiskar ta. Then hesitantly ya bar engine ɗin sa ta shiga ciki da ƙyar sannan ta fara aikin da ta jima tana muradin yi. Ben kusan zaucewa yai lokacin da Zuhayr ya shiga da Zaytoonah igloo ɗin ta ya sa sakata ta ciki a 'yar ƙaramar ƙofar da ɗakin. Ba abinda ya ke gani irin Zuhayr na yin abubuwa da Zaytoonah. Ya cize leɓen sa da ƙarfi yana dukan kan sa da hannun sa. "I'll kill you for taking away my love, i'll kill you and your entire Family Zaytoonah" *garangan-garangan-garangan Ben ya fi Muntari hauka fa* 2/11/21, 10:04 PM - ****: 29 Bismillahir Rahmanir Rahim *Murder* Hayaniyar mutane da yai yawa ne ya farkar da shi daga daddaɗan bacci da ya ke yi. Jiya bayan ya rungumeta da kyau ne ya rufe su da bargo zuwa lokacin jikinta ya rage sanyin da yai. Kallon fiskar ta ya tsaya yi yana lura da yadda ta ke fidda numfashi. Wani farinciki ne ya ziyarce shi saboda jiya ko numfashi ba ta yi lokacin da ya shigo da ita ɗakin. Yai saurin matsayawa ya ɗau kayan sa ya saka kafin ya gyara ma ta kwanciya ya fita. Hayaniya ce ake yi akan abinda ya faru jiya inda wasu ke ganin akwai wanda ya saka Zaytoonah cikin ƙanƙara, wasu kuma ke ganin ƙila faɗawa yai. Suna ganin Zuhayr su ka fara tambayar sa gameda lafiyar Zaytoonah ko ta tashi ya ce ba ta tashi ba amma jikin ta ya rage sanyi. Ko ta kan Ben bai bi ba ya nemi a shirya mu su mota za su bar wajen, zai kai Zaytoonah a dubata a asibiti. Ya shiga ɗakin Ben ya samu baya nan dan haka ya ɗau kayan sa ya haɗa a jaka ya fito ya shiga ɗakin Zaytoonah har lokacin tana bacci. Ya ɗauko wasu sababbin kaya ya fara saka ma ta da ƙyar saboda har lokacin bacci ta ke yi, yana ƙoƙarin saka ma ta ƙatuwar rigan sanyi ta buɗe ido. Muryarta da ta dashe ta kira sunan sa "Zuhayr" Ya dai ji alamun tayi magana amma bai ji mi tace ba dan haka yai saurin kai kunnen sa saitin bakin ta yana faɗin "are you Ok" "Zu Zu Zuhayr" ta sake maimaitawa da ƙyar. Ƙaramar dariya yai ya ƙanƴameta jikin sa yana faɗin "i'm sorry, i'm very sorry" Sai daya ƙarisa saka ma ta kayan ya ce bari ya duba ko motar da za ta ɗauke su ta zo. Yana fita ta yi ƙoƙarin miƙewa amma cinyoyinta zuwa ƙugunta wani irin zogi da zafi su ke ma ta, ga kanta ma da ke sarawa da ƙarfi. Ganin haka ya sa ta jira Zuhayr ya dawo. Zuhayr yana fita ya tambayi ma su kula da wajen aka ce mota ta kusa isowa. Ya sanar mu su Zaytoonah ta farka zo ka ga murna a idanun mutane dayawa wanda ba su taɓa haɗuwa ba sai jiya. Ba'a jima ba sai ga Motar ta iso dan haka ya shiga dan ya taimakawa Zaytoonah ta fito. Har lokacin babu Ben a wajen, shima kuma a lokacin Zaytoonah ne kawai a ran sa dan haka ya ma manta da shi. Da ƙyar Zaytoonah ta iya miƙewa tsaye bayan ya taimaka ma ta ta fito daga ɗan ɗakin na su. Wajen da aka parking motar da ɗan tazara kaɗan da wajen da masaukin mutane ya ke. Tsugunnawa yai a gabanta ya ce ta hau bayan sa. Zaytoonah ta zaro ido tana ganin kamar ba zai iya ɗaukan ta ba duk da kuwa ta san idan ba ɗaukan ta aka yi ba a yadda takeji ba yadda za ayi ta iya tafiya mai nisa, tsayuwa ma da ta yi a wajen daurewa kawai ta yi. "Ki hau dan Allah Zaytoon" Wata baturiya ta ce wa Zaytoonah kar ta damu ta hau bayan sa. Tuni an kai mu su jakukkunan su zuwa wajen motar dan haka su kaɗai ake jira. Bantareda ya damu da nauyinta ko kuma shigar da ta yi da ya ƙara ma ta nauyi ba haka ya ke tafiya da ita a hankali har su ka kai wajen motar. Zaytoonah ta lafe a bayan sa tana jin wani daɗi na ratsa ilahirin zuciyarta. Ba ta taɓa zaton Zuhayr na da sauƙin kai haka ba. A cikin mota ma lafewa ta yi ajikinsa shima ya riƙeta gamgam. Asibiti su ka fara wucewa, inda yai wa likita bayanin Zaytoonah matar sa ce sun zo yin honeymoon shine ta faɗa cikin ƙanƙara kuma ba a ganta da wuri ba, da aka ganta kuwa sanyi ya kamata sosai har ta suma acikin ruwa, shine ya mata taimakon gaggawa. Ya faɗi hakan ne kar a binciki Zaytoonah ayi zargin raping ɗinta akayi. Bayan an shiga da Zaytoonah ciki ya zauna akan kujera tareda dafe kan sa yana tunanin abinda ya faru da kuma abinda ka iya biyowa baya idan har ya faɗawa Zaytoonah gaskiya. A haka Ben ya kirashi yana tambayar inda ya ke, sai da ya ga sunan Ben ma ya sa shi tunawa ko neman sa bai yi ba lokacin da su ka tafi. Bayan ya ma sa bayanin abinda ya faru a ɓangaren Ben cillar da wayar yai yana huci. Jiya kasa bacci yai dan haka ya fita daga ɗaki yai ta tafiya sa da yai nisa da su sosai sannan ya tsaya a wajen wani bishiya ya dunƙule hannu yana dukan bishiyar saboda ya ji sauƙin raɗaɗin kishi da baƙin ciki da ya ke ji gameda abinda Zuhayr ke aikatawa da Zaytoonah. Har sai da hannun ya fara jini kafin ya haƙura da bugun bishiyar. Ya zauna ya fara kuka, kuka sosai dan ya jima yana hana mata raɓan Zuhayr tun lokacin Zuhayr bai damu da addini ba ma. Akwai lokacin da su ke makaranta su ka je wani party har Zuhayr ya haɗu da wata yarinya ya ɗauketa da niyyar za su je gidan sa su huta. Ben na biye da su yana kitsa azuciyar sa abinda da zai wa yarinyar idan har Zuhayr ya raɓeta. Suna zuwa gidan su Yarinyar ta ce za ta shiga banɗaki sai da Zuhayr ya manna ma ta kiss kafin ya barta ta fita daga ɗakin, ya kwanta kan gado yana jiran ta dawo. Har kusan minti shabiyar babu alaman za ta shigo ɗakin, hakan ya sa ya fita dan ya dubata amma Ben kawai ya gani a falo yana kallo. Zuhayr ya tambayeshi ina Samantha? Ben ya ce ta tafi wai ba za ta iya haɗa jiki da Musulmi ba. Zuhayr yai tsaki ya koma ciki yana jin haushin kan sa ma da ya ɗauko Samanthan tun farko. Ita kuwa Samantha gudun fanfalaƙi ta yi saboda Ben da ya tsoratar da ita da bindiga lokacin da ta fito daga banɗaki za ta koma ɗakin Zuhayr. Giya Ben ya fito da shi yai ta sha har sai da yai tatil kafin ya ɗauko wani haɗin sa cikin ƙaramar kwalba ya kwankwaɗe duka, hakan ya sa bacci mai nauyi ya ɗaukeshi a wajen duk wani sanyi ya sauka a kan sa amma baya cikin hayyacinsa balle sanyin ya dameshi... Duk taimakon da ya kamata a yiwa Zaytoonah an mata, sun ce za su riƙeta zuwa washegari kafin a sallameta. Taimama ta yi a asibitin ta yi sallah a zaune bayan ance ma ta kar ta taɓa ruwa sai gobe. Lokacin da Zaytoonah ta cewa Zuhayr za ta yi taimama ta yi sallah hankalinsa tashi yai saboda a ɗan iya karatun sa ya san idan aka yi irin abinda su ka yi jiya da dare to ana wankan tsarki kafin ayi sallah, shima da ya je hotel ɗin su ya yi wankan sannan ya rama sallolin da ya wuce shi. Malam Google ya tambaya amma bai gamsu da bayanan sa ba dan haka ya kira Uncle Aliyu ya tambayeshi. Shima dai bai sani ba amma ya ce ya dakonce shi nan da 'yan mintuna. Kafin ya kira tuni Zuhayr ya kira Shiekh Hassan ya ma sa tambayar inda Sheikh ya ce za a iya yin taimama ayi sallah idan mutum ya warke sai yai wankan, ya kawo hadisi da ya supporting fatawar da ya bayar dan haka hankalin Zuhayr ya kwanta dan tuni Zaytoonah ta yi taimama ta fara sallah. Kafin Uncle Aliyu ya kira sai bayan kusan awa ɗaya da rabi inda shima ya ma sa bayanin da Sheikh Hassan ya ma sa. A asibitin ya kwana tareda matar sa wanda duk wani motsinta yana idon sa. Washegari sai kusan da rana aka sallamesu bayan an sake duba Zaytoonah aka hanata mu'amala da ruwan sanyi sannan aka bata magunguna na sha da na shafawa a jiki. Bayan sun koma hotel ɗin ne ya tara ma ta ruwan zafi ya ce ta yi wanka. Lokacin da za ta shiga banɗakin ya kira sunan ta a hankali "Zaytoon" ta juyo tana kallon sa "Ki yi wankan tsarki kafin ki fito" "Wankan tsarki?" Ta maimaita da mamaki Sai da yai gyaran murya kafin ya ce " ba ki ga likita yayita tattaɓa ki ba jiya? kuma nima na kwanta kusa da ke, duk wannan zai iya sawa ki ji wani abu a ranki. So best option shine ki yi wankan tsarki" Kan Zaytoonah ya kulle, ta dai yi karatu a Islamiyya dai-dai gwargwado amma kuma anya wannan bayanin da Zuhayr yai ya kai ta yi wanka? Ita fa ba ta ji komai ba. Ranan da za ta iya cewa ta ji wani abu da aka taɓata shine ranan da Zuhayr ya kissing ɗin ta a gym room dan da ta koma ɗaki za ta yi wanka sai da ta ga pant ɗinta ya jiƙe. For the benefit of doubt ta gyaɗa ma sa kai alamar za ta yi wankan. Kwana biyu su ka ƙara a ƙasar su ka tattara su ka koma America saboda makarantar Zaytoonah. Ben kam tuni ya wuce bai bi ta kan su ba dan haushin Zaytoonah da ya ke ji yana gani kamar idan ya ganta kusa da Zuhayr zai iya zuwa ya shaƙeta har sai ta mutu. Zuhayr kam duk yadda ya so ya faɗawa Zaytoonah abinda ya faru tsakanin su ya kasa. Gani ya ke idan ya faɗa za ta iya gudun sa. Duk bayanin da ta ma sa na abinda ya faru har ta fita a daren ranan bai gamsu ba dan ya duba wayar sa babu kira babu text da aka tura, itama na ta wayan babu text ɗin da ta ce an turo. Ya dai lallaɓata akan ta bar zancen tunda an sameta kuma she's alive an healthy. Sai da su ka koma gidan su da ta ga Ben sai wasu abubuwan su ka fara zuwa ma ta, possibility na yiwuwar Ben ne ya tura ma ta saƙon nan da wayar Zuhayr ya zamo ma ta 90% idan kuma har hakane to kuwa shine ya turata cikin ƙanƙara. Ta dai yi shiru da bakinta ba ta gayawa Zuhayr komai ba. Yau tana kitchen tana haɗa banana and avocado smoothie sai ga Ben ya shigo kitchen ɗin. Haka kawai sai ya ɗau wuƙa da Albasa ya zo kusa da Zaytoonah da ke ƙoƙarin zuba ayabar da ta yanka cikin blender, ya ajiye chopping board ya fara yanka Albasa da sauri-sauri irin yadda professional chefs ke yi. Albasar ta yanku ƙanana amma bai tsaya ba ya cigaba da bi yana ƙara yanyankawa. Tun Zaytoonah ba ta damu da abinda ya ke yi ba har ta juyo ta ce da shi yai a hankali zafin albasan na damun ta. "Yadda Albasan nan ta koma haka na ke maida duk wanda ya shiga gonata" "What?" Ta faɗa a ɗan tsorace amma bai kula ta ba sai ya ma fita daga kitchen ɗin gaba ɗaya. Zaytoonah ta ce a ranta dole ta sake magana da Linda dan zuciyarta na riya ma ta akwai possibility ɗin Ben na da hannu a kisan Alinah kamar yadda ta ke iƙirari. Kuma abinda ya faru a ƙasar Finland shi ne sila. Tana gama shirin fita sai ga kiran Zuhayr. Murmushi ne ya suɓuce ma ta. Ta rasa dalili amma tunda su ka dawo Zuhayr ya koma ba ta kulawa fiye da da. Like a rana idan baya gida zai kirata sau uku ko huɗu yana tambayar lafiyar ta. Idan kuwa yana gida baya bari ta zauna shiru, ko tana ɗaki tana karatu ko kallo haka zai zo ya ce ta sauko falo su yi tare. "Ina zuwa?" "Ballet dance" "Oh! Na manta, ki dawo da wuri" Ta amsa da to. Mr Dawson ne sabon Driver ɗin ta shine ya wuce da ita wajen da ta ke koyon rawan. Har yanzu dai ba ta wani iya komai ba dan ana kam improving flexibility ɗinta ne. Tana isa wajen Linda ta kirata akan ya kamata su haɗu cikin satin, Zaytoonah ta ce ba matsala za su iya haɗuwa ranan Asabat. Awa biyu ta ke zuwa practice a sati sau uku. Abin mamaki lokacin da ta fito tana tunanin za ta ga motar da Mr Dawson ya kawo ta sai ta ga ɗaya daga cikin motocin Zuhayr. Ta ƙarisa wajen tana murmushi dan ba ta ɗauka zai zo ba, sun yi waya lokacin tana ciki kuma bai ce zai zo ba. Shi da kan sa ya ke tuƙi dan haka gidan gaba ta shiga. "Ya kuma ka zo da kan ka?" "Ba kya so na zo ɗaukan matata ne?" Kalmar Matata da ya faɗi sai ya sa ta jin kunya. Haka su ka tafi yana ma ta taɗi gameda abinda ya faru a office. Maganar Ben da ya kawo ne ya sa ta ji zuciyar ta yayi dum. Chan ta kalleshi ta ce "ni kam Ben ba shi da budurwa ne? Yaushe zai yi aure?" Zuhayr yai dariya yace "miyasa ki ka tambaya?" "Kawai dai na ga kamar ya tsufa ne" "This is America, kowa da ra'ayin sa. He's probably waiting for the perfect girl" A zuciyar ta tace "Or the perfect guy ba" *** Tana wanka a banɗaki kawai sai wuta ya ɗauke. Innalillahi ta furta a zuciyarta ta fara lalube har ta fito daga banɗakin, ta gwada kunna switch ɗin banɗakin amma bai yi ba shiyasa kawai ta fito. Ɗakin ma ba wuta dan haka ta fara ƙoƙarin zuwa wajen gado saboda ta lalubo wayarta ta kunna sai kuma wutan ya dawo. "Af ƙila matsala aka samu" ta furta tareda juyawa za ta koma banɗakin, sai dai kuma tana buɗe ƙofa wutan ya sake ɗaukewa, ta juyo da sauri ƙirjinta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi ta fara tafiya a hankali dan ta isa wajen gado ta lalubo wayarta, wannan karan ko da ace an maida wutar dole ta kunna fitilar wayarta. Ta lalubo wayar ta kunna sai kuma aka sake dawo da wutan. Ta san Zuhayr baya gida amma kuma ai akwai wasu ma'aikata a gidan, idan ma matsala aka samu na wutan gara ta fita ta ji, dan haka ta nemo jallabiyarta baƙa ta saka ta ta buɗe ƙofa ta fita still wayarta a hannu amma ta kashe torchlight ɗin tunda akwai wuta. Tana fitowa ta kai tsakiyar stairs sai aka kashe wutan. "Zuhayr, Zuhayr. Ben, Benedict, Chef Green" haka ta dinga kiran sunan su amma shiru. Ta rasa ina za ta je ɗaya, ta koma ɗaki ne ko ta sauka ƙasa ta fita waje. Ta samu ta kunna hasken wayarta amma still saboda duhun daya ƙaraɗe wajen sai ya zamana ba ta gani da kyau. Tana sa ƙafa za ta taka stairs ɗin ta ji an dafa ƙafaɗarta wanda ya sa tayi mutuwar tsaye a wajen. "Zu Zuhayr" "I'll kill you" aka faɗa da wata munafukar murya sannan aka hankaɗa ta. Bayan minti goma da faɗowarta sai ga Zuhayr ya shigo gidan, ya zo zai haura sama ya kalli Zaytoonah kwance a wajen ta suma hakan ya sa shi yin kanta da sauri... *** Sati biyu ta yi jinya a asibiti kafin aka sallameta. Wannan karan da ta yiwa Zuhayr bayanin abinda ya faru bai yi wasa da maganar ba nan da nan aka fara investigation amma ba a gano komai ba daga ƙarshe aka saka cctv camera a lungu da saƙo na gidan. Lokacin da ta ma sa maganar tana zargin Ben da abinda ya faru bai yarda da hakan ba sai ma kwantar ma ta da hankali da yai da cewa tun suna yara ya san Ben kuma shi mutum ne da ba zai taɓa iya aikata mummunan abu irin haka ba. Ta yi shiru da zancen sai da su ka koma gida ta sake tada maganar tareda faɗa ma sa duk abinda Linda ta gaya ma ta dama Voicemail ɗin da ta saurara na Alinah. "Ki kwantar da hankalin ki Zaytoon, har yanzu ba ki da lafiya. Linda kuma zanyi magana da ita da kaina. Fashe ma sa tayi da kuka saboda yadda bai ɗauki maganar Ben serious ba. "Lokacin da ka aureni ka min alƙawarin kula da ni kamar ƙanwar ka, anyi ƙoƙarin kasheni har sau biyu amma ba abinda ka yi. Ben is gay, sonka ya ke yi kuma..." "What are you saying" ya faɗa yana kama hannunta. Ta yafce hannun da ƙarfi ta ce " ni dai ka barni, kuma daga gobe tafiyata zan yi tunda ba ka damu da rayuwata ba, kafi damuwa da Ben" "Zaytoon, Benedict is my brother ki daina zargin sa. He will never hurt you" "Shikenan idan ya kasheni ba ka da asara tunda ba sona ka ke ba, amma dan Allah kafin ya kasheni ka barni na koma wajen Mommy na. Na fasa zama a nan, na fasa karatun" ta ƙarisa maganar tana kuka. Kissing ɗin goshinta yai ya ce " ba abinda zai sameki, ba wanda zai kasheki matuƙar ina raye. Indai akan abinda ya faru ne zan ƙara saka matakan tsaro a gidan nan sannan zan kawo ma'aikata da za su dinga kwana da ke" Yana ganin Zuhayr ya rungume Zaytoonah ya tura mu su ƙofa ya bar wajen. Ya ji komai, kuma ya sani akwai aiki a gabansa matuƙar bai hallaka Zaytoonah once and for all ba daga ita har Linda ɗin... Yau ta fara zuwa makaranta bayan abinda ya faru. Suna gama class Farha ta matso kusa da ita tana ma ta ya jiki, ta je ta gaisheta a asibiti har sau biyu ma. "Lover girl ya mijin ki?" Zaytoonah ta harareta "Seriously ban san haka mijin ki ya haɗu ba, dole koyaushe ki dinga kallon hoton sa a class" "Ya Allah! Farha ni yaushe na kalli hoton sa?" "Koyaushe ma kina kallo" ta faɗa tana dariya. Lokacin da su ka fito daga class za su tafi gida saboda ba su da wani class ɗin sai Zaytoonah ta fara jin hajijiya. "Are you Ok?" Farha ta faɗa tana riƙe Zaytoonah. "Hajijiya na ke ji" "Ko za ki koma Asibiti?" Zaytoonah ta girgiza kai. Sai da su ka zauna na wajen kusan minti shabiyar kafin Zaytoonah ta ce su je ta dena ji. Gidan su Akwai ma'aikata mata biyu da Zuhayr ya kawo ma su kula da gidan da kuma Zaytoonah, aikin su shine ko bacci ba za su yi ba sai Zaytoonah ta yi bacci. Ita dai kawai ta haƙura ne amma ba ta yarda da gidan ba har yanzu, har Mommy ta kira tana faɗa ma ta abinda ya faru Mommy ta ce ta cigaba da addu'a itama za ta tayata... *** Tana zaune a library tana karatu ƙarar shigowar text ya shiga wayarta ta ɗauka ta karanta saƙon da aka rubuta. Linda ce ta turo ma ta saƙo akan ta zo gidan ta yanzu-yanzu ta samu wani evidence. Jiki na rawa ta kwashe kayanta ta fita daga library ɗin. Indai evidence akan Ben ne to ba abinda zai sa ta zauna. The last time da Linda ta zo ta gaisheta a.Asibiti ta yadda da ita akan Ben ne ya turota daga stairs. Ba ta ma kira Mr Dawson ba taxi ta shiga ta wuce gidan Linda ɗin tana Allah ya sa su samu abunda beyond doubt zai incriminating Ben. "Ko idon sa ka kalla ka san ba shi da gaskiya, shege Mugu" ta faɗa a zuciyarta. Yana kallo sanda ta fito a taxi ɗin ta nufo gidan yai murmushin mugunta a ransa tareda tunanin once and for all Zaytoonah za ta bar rayuwar Zuhayr. Ta danna ƙararrawa amma shiru ba a buɗe ba dan haka ta murɗa ƙofan gidan sai kuma ta ji ya buɗu ta yi Bismillah ta shiga falon tana kiran sunan Linda. Tana isa tsakiyar falon aka rufe ma ta hanci da wani handkerchief tana fita hayyacin sa ya jawota har zuwa kitchen inda gawar Linda ke kwance a ƙasa cikin jini. Sai da ya jira minti biyar ta yi dan ya san minti goma Zaytoonah za ta yi ba tareda ta dawo hayyacinta ba kafin ya kira 911 inda ya sanar da 'yan sanda akan shi maƙocin Linda ne ya ji hayaniya a gidan ta daga baya kuma ya ji ihu azo a duba saboda yana tunanin ƙila ɓarayi ne su ka shiga gidan. A hankali ta fara buɗe idonta, ta ƙurawa ceiling ido kafin cikin 'yan daƙiƙai hankalinta ya dawo jikinta gaba ɗaya ta tuna abinda ya faru. Miƙewa ta yi zumɓur sai kuma taga mutum a kwance a ƙasa ga jini na malala. "Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun!" A hankali ta matsa kusa da gawan sai kuma ta ga ashe Linda ce ke kwance cikin jini ga wuƙa nan an daɓa ma ta a ƙirji. Ihun da ta sa yai dai-dai da isowar police gidan... Sorry for not updating yersterday 2/11/21, 10:04 PM - ****: 32 Bismillahir Rahmanir Rahim *Home Sweet Home* "Wannan hoton yarinya da ku ke gani wata yarinyace sheɗaniya 'yar ƙwaya wacce ta kashe wata mata a ƙasar America. An ce ta daɓawa matar wuƙa har sau uku saboda ta ƙi sayar ma ta da ƙwaya. Yanzu haka tana ɗaure a gidan yari an yanke ma ta hukuncin kisa. Al'umman Annabi dan Allah mu dena shaye-shaye saboda mugayen illolin sa. Dan Allah ayi ta sharing har ya isa wajen mutane dayawa" Dayawa mutane da su ka saurari voicenote ɗin suna tsinewa hoton yarinyar da aka turo ne wacce ke tsaye police na sanya ma ta ankwa. Wasu kuma na ƙoƙarin jawo hankalin mutane wajen sanin sahihancin labarin kafin su fara tsinuwa da zagi kar Allah ya tuhume su da alhakin yarinyar. Matar da ta turo ta dage a wani group ta gani kuma wacce ta turo ɗin ta rantse ta wayi Yarinyar da ke jikin hoton. Haka dai akayita cecekuce kafin daga baya maganar ya lafa lokacin da aka posting ɗin wani labari da su ke tsumayin jira. Maman Abdul na ganin chats ɗin da ake yi sai dai ba ta tofa albarkacin bakin ta ba dan ita irin waɗannan voicenote ɗin da ake forwarding tareda hoto ba ta ɓata lokacin ta wajen sauraran su sai dai daga baya out of curiosity sai ta clicking hoton da aka turo dan ta ga yarinyar da ake magana akai. Ta ƙurawa hoton tana tunanin possibility na hasashenta ya zama gaskiya ko kuma akasin sa. Ƙarshe dai zuciyarta ya amince da yarinyar dai Zaytoonah ce, Zaytoonah 'yar gidan Maryam maƙociyarta dan gidajen su duk a layi ɗaya ya ke duk da akwai ɗan tazarar gida kusan shida tsakanin su. Ta san Zaytoonah na ƙasar America kuma hoton da aka turo hotone da akayi shi a chan ɗin saboda yanayin tsarin wajen da kuma baturen ɗan sanda da ke hoton. "Innalillahi, Zaytoonah" ta furta lokacin da ta ƙarƙare lissafinta. Wayar Maryam ta kira kuma ta ci sa'a bugu ɗaya ta ɗauka. A darare Maman Abdul ta gaida Maryam sannan ta tambayeta labarin Zaytoonah. Maryam ta ce tana lafiya. Maman Abdul ta yi shiru tana tunani kafin daga baya ta ce " wani hoto aka turo a wani group kuma sai na ke ganin kamar hoton Zaytoonah na gani amma zan turo miki sai ki duba" Maryam ta ce " ikon Allah". Hoton da ta turo ma ta ne ya sa numfashin Maryam sarƙewa. Ta dafa ƙirjinta tana maimaita Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun. A lokacin mantawa ta yi da cewa sun yi waya da Zaytoonah shekaranjiya har ta ke ce ma ta sun chanja gida. Da ƙyar ta lallaɓa ta saurari voicenote ɗin tana ji tana girgiza kai saboda rashin yarda da abinda ake faɗa a ciki. Numbar Zaytoonah ta lalubo da sauri ta shiga kira sai dai ba a ɗauka ba nan hankalinta ya sake tashi. Ta kira yafi sau biyar amma ba a ɗauka ba jikinta na rawa ta shiga neman numbar Zuhayr sai dai shima ɗin shiru ba a ɗauka ba. Hijabi ta ɗauka da Key ɗin mota tayi hanyar waje dan gidan Alhaji Iliyasu ta ke da niyyar zuwa. Sai Allah ya sa Zaytoonah ta kira ta. "Hello Mommy" Jin muryar 'yar ta ta ya sa ta ji wani sanyi ya shigeta. "Adaeze akwai abinda ke faruwa ne da ban sani ba?" "Kamar me Mommy?" "Yanzu dai mu yi video call ina son ganin ki" Daga haka Mommy ta samu waje ta zauna a falo ta buɗe data ɗinta. Ganin Zaytoonah sanye da bathrobe ya sa ta sami kwanciyar hankali. Ta shiga gaya ma ta labarin hoton da aka turo da kuma abunda ake faɗi. Ba amfanin ɓoyewa tunda komai ya warware dan haka ta fara ba ta labarin abinda ya faru. Mommy sai gashi tana hawaye. "Yanzu Zaytoonah irin wannan abun ya faru da ke amma ba za ki sanar da ni ba" "Mommy shiyasa Zuhayr ya ce kar mu gaya miki gashi yanzu har kin fara yin kuka" Mommy ta goge hawayen da ke fiskanta ta ce "ina Zuhayr ɗin?" "Yana ƙasa idan ya shigo zan kiraki" Mommy ta ce ta barshi gobe da safe za ta kira shi. Sun jima suna hira gameda abinda ya faru sannan su ka katse wayar. Zaytoonah tunda Ben ya shigo ta haura sama ba ta sauko ba. Ita dai ta ka sa gaskata abinda Zuhayr ke faɗi wai Ben ya karɓi musulunci. Tunda su ka dawo gidan tare su ke kwana duk da kuwa babu abinda ke shiga tsakanin su. Bayan sun gama waya da Mommy ta jirashi a ƙalla kusan awa ɗaya da rabi amma bai shigo ba hakan ya sa ta tura littafin da ta ke karantawa gefe ta shige cikin bargo tana tunane-tunane har bacci ya ɗauketa. Zuhayr kam taɗi su ke da Ben kamar wanda sun jima ba su haɗu ba. Zuhayr was so excited shi kuma Ben wani farinciki ne ya mamayeshi saboda rabon da su zauna su na hira tsakanin su irin haka tun farko-farkon zuwan Zaytoonah. Ƙarshe da Zuhayr ya duba ya ga dare yayi sai ya ce ya kwana a gidan kawai... Shigowanta kitchen ɗin ta samu Chef Green yana haɗa mu su breakfast. Ta gaida shi tareda tsayawa gefe dan ta taimaka ma sa da wani abun. Sai da komai ya kammala ta koma ciki dan ta duba ko Zuhayr ya dawo amma ba ya nan. Lokacin da ta farka baya ɗakin, da ke duk safiya yana fita gudu shiyasa ba ta damu ba ta cigaba da abinda za ta yi. Ta gama shirin makaranta tsaf kafin ta sauko ƙasa dan ta karya hakan yai dai-dai da shigowar Zuhayr da Ben gidan. "Good morning Sister Inlaw" Ben ya faɗa yana murmushi. Ta yi seƙeƙe tana kallon sa. Wato dai wannan mutumin ba zai dena bibiyar su ba. Ba ta amsa ma sa ba sai ma wajen dining da ta wuce. Tana zama akan kujera Zuhayr ya ƙariso wajenta. "Zaytoon ba ki ji Zubayr na gaishe ki ba ne? Yanzu fa ɗan uwan ki ne musulmi, treat him nicely please" "Ba zan iya ba dan ban yarda da shi ba, kuma ba zan taɓa yarda da shi ba" "Zaytoon..." "Kuma ka karya Alkawari tunda ka ce min ba zai sake zuwa inda na ke ba amma sai gashi kai da kan ka ka kawoshi gidan nan, har da kwana mana a gida bayan yana da na sa gidan" "Zaytoon idan akwai lokacin da Zubayr ya fi buƙatana to yanzu ne. Dole ne na taimaka ma sa ta yadda zai saba da yin sallah da wasu abubuwan, musulmi ɗan uwan musulmi ne ko ba haka ba?" "Hakane" ta faɗa tana kau da kan ta gefe ta fara cin abinci. Shima bai kuma cewa komai ba sai ya juya ya tafi. Cikin zuciyarta ta ce "Allah ka yafeni amma gaskiya ban yarda da musuluncin Ben ba. Ya Allah ka kareni daga sharrin sa" Da wannan ta samu ta cigaba da cin abinci hankalinta kwance... Ganin Zaytoonah ba ta son zuwan Ben ne ya sa shi Zuhayr ɗin ya koma zuwa wajen Ben. A dole shi yana so ya sabar ma sa da ibada ya kuma nuna ma sa yadda ake basic abubuwa na musulunci. Idan Zuhayr ya fita da safe ba ya dawowa sai chan dare sosai. Daga office za su je masallaci da Ben daga nan su je gidan Sheikh Hassan ɗaukan karatu sai su koma gidan Ben inda Zuhayr ke ma sa bitar abinda aka koya ma sa. Ya kan kira Zaytoonah akai-akai ya ji lafiyarta amma yanzu kam haɗuwar su sai dare kawai daren ma wani lokaci zai zo ya samu ta yi bacci. Sau ɗaya da Zaytoonah ta yiwa Zuhayr magana akan Ben ya jawo ma ta hadisin musulmi ɗan uwan musulmi ne sai ta ja bakinta ta yi shiru tunda dai Ben ya dena zuwa mu su gida matsalarta ta ragu. Sai dai kuma tana missing Zuhayr sosai, ɗan wasa da dariya da su ke yi tsakanin su babu shi yanzu. Swimming da ya ce zai koya ma ta ma ya janye, ina ma ta ga idon sa balle ta tuna ma sa da maganar koyon swimming ɗin... Tana fitowa da akwatin ta daga ɗaki ta yi kiciɓis da shi. "Ina za ki je?" Ya tambaya da mamaki Ba ta yi zaton zai zo gidan ba tunda bai saba dawowa da yamma haka ba. Ta kauda kai gefe ta ce "gidan su Farha" "Why" "Zan fi yin karatu a chan kuma ya fi kusa da school" "Farha ki ke aure?, Farha ne guardian ɗin ki ko..." "Eh ɗin ita na ke aure tunda kai ma Ben ka ke aure ai. Ka je ka riƙe shi nima zan riƙe kaina. Ai dama ba sona ka ke ba yanzun ma dan ka ga ina da cikine shine ka ke lallaɓani na ƙarya. To zuwa zanyi a cire cikin idan ya so ka ɗauka ka sawa Ben ya haifa ma ka shi" Ta ƙarisa maganar tana hawaye. Dafa kafaɗarta yai zai yi magana amma ya rasa mi zai ce ma ta. Chan ya daure ya ce "Ben ɗan uwa na ne Zaytoon. Ko babu musulunci shi ɗan uwa ne a gareni. Idan akwai abinda ya taɓa yi miki please ki yafe ma sa, yanzu shi musulmi ne, kulawar mu ya ke so ba ƙiyayyar mu ba" Yai shiru yana sauke ajiyar zuciya kafin ya ce "na yadda na aikata miki babban laifi amma Dan Allah Zaytoon kar ki cire cikin nan. Ina son ganin Baby na, please" Yadda yai maganar sai jikinta yai sanyi ya ba ta tausayi dan idon sa har wani ja ya koma. Ta faɗa ne kawai amma ba abinda zai sa ta cire ciki. "Please ki min Alƙawarin ba za ki cire ba kin ji?" Ya faɗa yana haɗa hannu biyu alamar magiya. "Na ji" ta faɗa ba tareda ta kalleshi ba. *** Yau Alhamis daga school ta wuce Asibiti saboda kwana biyun nan ta rasa gane kanta sai ta dinga jin yunwa da wuri kuma ba ta iya cin abincin da yawa. Likitan da ta gani ya ma ta bayanin cewa ba wani abin ta da hankali ba ne duk yana daga cikin signs na early pregnancy amma ya rubuta ma ta magani guda ɗaya da za ta sha. Tareda Farha su ka zo dan haka sai da aka kai Farha gida kafin aka wuce da ita. A gajiye ta ke dan haka ɗaki ta shiga bayan ta shigo gidan sai dai kuma yadda ɗakin ya chanja ma ta ne ya sa ta buɗe baki. Roses ne akan gado ga kuma candles nan a kunne a ƙurya da ƙuryan ɗakin, wajen ya zama so romantic. Ta ɗau doguwar rigan da ke kan gadon haɗeda karanta takardar da ya ke gefen sa. *Dinner at the sea, 5pm* Murmushi ta yi tana tunanin wannan salo na yau, ko da ya ke tun maganar da su ka yi shekaranjiya ta ga yanayin sa ya chanja. Ta shiga banɗaki ta yi wanka sannan ta fito ta shafa mai da ɗan powder sai kwalli, dama kwalliyarta kenan. Ranan da ta ji karambani shine za ka ga ta ɗan goga lipstick shima ba mai yawa ba. Farar gown ce irin beach gown ɗin nan, Hannun shimi gareshi sannan ta sama ya matse ta amma daga ƙugu zuwa ƙafa a buɗe yake sosai. Cikin kayanta ta ɗauko beach hat ta saka kalar baby pink sannan ta ɗau wani shawl cream color ta rufe kafaɗunta da shi dan idan ta fita haka sanyi za ta ji sosai, gashi saman rigan bai rufe ma ta nonuwa sosai ba. Wajen da aka kafa bukka inda su ke yawan zama su yi hira nan ta nufa. Ba kowa a wajen amma an shirya kayan abinci a kan table ɗin wajen, ga flowers da candles shima a wajen an ƙawata shi sosai. Ta duba ta duba ba ta ga kowa ba sai kawai ta zauna ta cigaba da baza ido. Minti biyu ta yi a haka ta ji lallausan hannun sa a idonta. "Kin makara, minti takwas kika ƙara" "Tun ɗazu na zo ban..." ta tsaya lokacin da ta ji saukar lips ɗin sa a wuyanta "You look beautiful" Tsikar jikinta ya fara tashi dan har lokacin bai saketa ba tana jin saukar numfashin sa a wuyanta. Ta yi saurin cewa "ehm Chef Green ya iya girki, wannan kifin ba ƙaramin daɗi zai yi ba" "Idan za ki yabi wanda yai girki to ni za ki yaba. I did all this by myself" "Da gaske?" Dawowa yai ɗaya kujeran ya zauna sannan ya ce "kin san mijin na ki gwani ne wajen girki" "Shiyasa ban taɓa ganin ka a kitchen ba ai. Sai dai a dinga ba da order" Ta fara kwaikwayon muryan sa "Chef Green i'll like to have lasagna, salad and chocolate ganache" Yai murmushi har sai da haƙoransa su ka bayyana. "Da gaske kai ka yi girkin?" ta sake tambaya tana kallon abincin kan table ɗin. " i only grilled the fish" "Ka yi ƙoƙari ai, wannan karan ba ka samu babban kifi ba" ta faɗa lokacin da ta ke ƙoƙarin ɗiban kifin a plate ɗin ta. "Da kina wajen mai kamar ki zan kamo" Ɗago ido ta yi ta watsa ma sa harara. "Sorry Dear" ya faɗa yana kashe ma ta ido. Su na cin abinci suna hira har su ka ƙoshi. "Care to dance?" Ya faɗa yana miƙa ma ta hannu " yau dai ina ga wani abun ka sha a wajen Ben ko?" Ta faɗa tana ɗaga gira Yadda ta ga ya haɗe rai ne ya sa ta yi saurin sa hannu cikin na shi ta miƙe. Hannunta biyu ta ɗaura a kafaɗar sa shi kuma ya sa na sa hannun a ƙugun ta. Kallon juna su ke kowa da abinda ya ke rayawa a zuciyar sa. "Babu waƙa ai?" Tsayawa yai da juyawar da su ke yi a hankali, ya sa hannun sa ɗaya dai-dai ƙirjin ta ya ce " daga nan waƙar ke zuwa" Ta yi saurin sunkuyar da kanta tana murmushi. "Zaytoon" ya kira da wata murya mai sanyi. Ta ɗago a hankali tana kallon sa "kin san yau ne ya cika shekara ɗaya da sati biyu da ɗaura auren mu. Ni ma ban tuna ba sai jiya, kuma ke ma na san ba ki tuna ba" Ta gyaɗa ma sa kai. "Barin gaya mi ki wani sirri yau. Lokacin da Alhaji ya kirani ya min maganar za a ɗaura min aure da wata yarinya, i was furious. Ni na farko aure ba ya gaba na, na biyu har lokacin ina tuhumar kaina da mutuwar Alinah so ba na son mu'amala ta haɗa ni da wata mace. Na gaya mi shi ba zan iya auren ki ba amma sai ya nuna min dalilin sa na son haɗa auren, at first ban yadda ba daga baya sai na yadda. Lokacin da Mommyn ki ta kirani mu ka yi magana sai ta jaddada min za ta amince da auren ne idan har zan bari ki cigaba da karatu. She sound desperate so i obliged. The next thing sai ta turo min hoton ki wai na gani ko zan iya zama da ke a matsayin mata dan ba ta so a walaƙanta ma ta 'ya. Kin san mi ya faru?" Zaytoonah ta girgiza kai "Dariya na yi, na yi dariya saboda kin yi ƙarama, na yi dariya saboda ƙiban ki saboda ina ganin @16yrs kina da wannan ƙiba ai abun ya ɓaci. Ni da Ben lokacin mun jima muna dariya, but then bayan na sake kallon hoton sai na ji tausayin ki ya kamani. With all the details da Alhaji ya gaya min da kuma maganar da mu ka yi da Mommy sai na ga idan ban amince ba na zama marar tausayi kenan. Na gayawa Ben zan aureki ba dan komai ba sai dan ki samu kiyi karatu cikin sauƙi. Then na kira Mommy na ce kin min ba ni da matsala da ƙiban ki, infact ina son mata ma su ƙiba" Zuwa lokacin hawaye ya gama wanke fiskar Zaytoonah. Ba abun da ta ke hangowa sai Zuhayr zaune da Ben su na kallon hoton ta suna dariya, ko wani hoto ma Mommy ta tura ma sa oho. Ita an nuna ma ta hoton sa tana murna ashe shi dariya ya dinga yi. Ba laifin sa ba ne tunda idan za ta yiwa kan ta adalci to ko da ba ta da ƙiba Zuhayr ya fi ƙarfinta. "Shshhh dont cry please" ya faɗa yana ƙoƙarin share ma ta hawaye "Zan je cikin gida" ta faɗa cikin muryan kuka. "Dan Allah ki saurareni har ƙarshe, then you can decide what to do next" Ya tallafo fiskarta ya ce " na kiraki na baki option biyu kuma ki ka zaɓi ɗaya. Ki ka zo gidana with the intention kin zo ki yi karatu ne ba kin zo zaman aure ba. Cikin watannin da mu ka yi tare na gane ko wacece Zaytoon. Na san abunda ta ke son ci da abinda ba ta so, na san irin kayan da ta fi so da wanda ba ta so. Na san ya ta ke dariya da yadda ta ke tsumewa, na san mutane mafi kusa da ita a rayuwarta, na san minene burinta a rayuwa, na san mi ya ke ba ta tsoro mi kuma ke sa ta farinciki. Mi ya ke jawo saurin fushinta mi kuma ya ke saurin kwantar ma ta da hankali. Na san wani sirri na ta wanda ba kowa ne ya sani ba" "Mi ne?" Yai murmushi ya ce "cin abinci hobby ɗin ki ne, musamman ma nama" "na san ƙarshe ma Kura za ka kirani" ta faɗa tana tura baki. "I like you Zaytoon. The real you, the chubby you, I like you so much" Ta yi saurin zaro ido tana kallon sa. "Ina fata ko da kaɗan ne nima ina da matsayi a wajen ki?" Ta girgiza kai "Ba kya so na ko?" Nan ma ta girgiza kai "Kina sona?" Ta tura baki ta ce "Bayan kai da Ben kun gama min dariyan shine za ka wani zo ka ce wai wai wai..." Ya riga ya san lagonta, the moment ya haɗa bakin su to shikenan ba ta da ƙarfin yin wani abu kuma. Kissing ɗin ta ya ke yi a hankali and for the first time sai itama ta fara maida ma sa martani, itama yanzu ta gane yadda ya ke ma ta dan haka lokacin da kiss ɗin yai nisa ita ta ke jagorantan su. Sun jima a haka kafin ya breaking kiss ɗin yana faɗin "is that a Yes?" Sai kuma ta ji kunya ta sunkuyar da kai tana dariya... Hannun su sarƙe cikin na juna su ka shigo gidan kowannen su fiskarsa shimfiɗe da murmushi. Suna shiga ɗaki ya jawota jikin sa ya ce "na bari ki cika shatakwas ko kuma kin shirya?" "Na shirya me?" Ta faɗa cikin rashin fahimta. "Ki bani dama na gaida Baby na" Cikin rashin fahimta ta kamo hannun sa ta ɗaura akan cikinta tana faɗin "itama na gaida ka dan na san mace ce" Yai dariyan wautar ta sannan ya ce barin nuna miki yadda ake gaida yaron ciki. Kafin ta ce wani abu ya shiga ba ta kiss mai zafi, this time around bai tsaya iya nan ba sai da ya tabbatar ya cikata ladar shi... *** Exams ɗaya ya rage ma ta wanda za ta yi gobe. Tana kwance ƙasa tana duba littafi tana ɗan wasa da ƙafafuwanta. Bayan ya gama wayan da ya ke yi ne ya kamo ƙafuwanta biyu yana ma ta tafiyar tsotsa a tafin ƙafarta. "Mr Ilyas You're distracting me" Ya yiwa tafin ƙafar kiss ya ce " tafiyar mu ranan Thursday sai ki fara shiri" Ta juyo da sauri tana murmushi ta ce " har da su Muhsina ɗin za mu tafi?" "Nope, gobe za su tafi kin san bikin ku na Nigeria sai a hankali" "Jibe ka, sai ka ce kai ɗin ba ɗan Nigeria ba ne" "In kin ce ni ɗan Nigeria ne to na yarda amma ni na san Dad ɗina ne ɗan Nigeria ni ba ɗan chan ba ne" "Allah ko! To sannu Ba Amurke ɗan gidan Gorge Washington" Rungumeta yai ya ce " kinga sai ki koma Mrs Washington kawai" Ƙara shigewa jikinsa ta yi sannan ta ce "ban siyawa su Mommy komai ba" "Bayan exams ɗin ki na gobe sai mu fita shopping" "Thank you D" "D?" "Ni fa D ɗin nan ban gane ma sa ba ƙila D for Donkey ki ke nufi" "Kayya ba ranan na gaya ma ka ba" "Ni gaskiya a dinga cikatawa idan aka ji D Donkey za a ɗauka ki ke nufi" Ta sa hannunta a kafaɗun sa ta ce "D for Darling, D for Dear, D for Dil, D for Daffodil, D for Dagger..." "Dagger?" "Yes Dagger, kai ne makamin da ke kareni a duk lokacin da na buƙaci kariya" ta ƙarisa maganar tana kissing goshin sa... Kaman da wasa ana saura kwana biyu tafiyar ya ce ma ta za su tafi da Ben ne, nan da nan ya ga ta haɗe rai ta ce indai da Ben za a tafi ta yafe tafiyar. Ya yi rarrashin amma ta ƙi sauraron sa ƙarshe dole ya bi abinda ta ke so, ya samu Ben ya bashi haƙuri. Dama ba shi ne ya ma sa tayin tafiyar ba, da ya gayawa Ben ɗin za su je hutu Nigeria ne sai shima ya ce zai bi su musamman wai saboda yana son ganin yadda ake biki a Nigeria tunda a ƙarshen shekara za a yi bikin cousin ɗin sa Muhsina. Ben bai ji daɗi ba amma saboda ya ƙara samun yardar Ben sai ya ce ma sa ya haƙura da tafiyar har da cewa ya taho ma sa da tsaraban Nigeria Zuhayr yai murmushi. Har ga Allah ya so su tafi da Ben ko don ya ƙara ganin yadda ake musulunci a Nigeria amma kuma farincikin Zaytoon ya fi ma sa komai yanzu. Ranan Alhamis Jirgin su ya lula sama, wannan karan ma sai da ta tsorata lokacin da jirgi zai tashi, Zuhayr ya riƙe hannunta yana murmushi. First class ticket su ka zo kuma ta ga banbancin tsakanin kujerun tunda ba wanda ba ta hau ba. Ba wani takuri ba komai kamar wani ɗaki har da gadon kwanciya. Ba su iso Zaria ba sai ranan Jummu'a da dare saboda a Abuja su ka kwana. Daga gidan Alhaji Iliyasu aka turo mota ya zo ya ɗauke su. Sun iso gidan ƙarfe goma na dare amma a hakan wai sai ta je gidan su tunda ba nisa da gidan Alhajin. Zuhayr ya ce bai yarda ba dan ya san su Mommy sun yi bacci. "Allah ba ta yi bacci ba" "Zaytoon ki bari gobe please, akwai gajiya a tattare da ke fa" ya faɗa yana ƙoƙarin cire kayan jikin sa "Gaskiya gobe ƙarfe shida na safe ina gidan mu" Bai amsa ma ta ba sai ya shige banɗakin da ke cikin ɗakin da aka ba su... A ranan da su ka tashi daga Jahar Nevada a ranan Ben ya kammala rubuta research ɗin sa ko na ce littafin sa mai taken *15 effective ways to kill Zaytoonah* 2/11/21, 10:04 PM - ****: 30 Bismillahir Rahmanir Rahim *seed in the womb* Ko tsayawa da kyau motan ba ta yi ba ya fito da gudu. "I want to see her, i want to see my wife" ihun da ya ke yi kenan lokacin da ya shigo cikin station ɗin, da ƙyar wani inspector ya ja shi zuwa office ɗin sa inda ya tambaye shi wa ya ke nema. Yana kiran sunan Zaytoonah inspector ɗin ya ce "oh! the moslem girl with the homicide case" Zuhayr ya buga desk ɗin gaban sa da ƙarfi ya ce " my wife is not a murderer you fool" Zuhayr sannanen mutum ne a Las Vegas, yana cikin top ten ma su kuɗin garin, dan haka duk zagin da ya ke wa Inspector ɗin haƙuri kawai ya ke bashi, daga ƙarshe ya aika a taho da Zaytoonah office ɗin. Zuhayr tsayawa yai yana kallon ƙofa sai huci ya ke yi. Lokacin da aka shigo da ita ko ankwa da ke hannunta ba a cire ba, duk fiskarta ya kumbura saboda kuka da kuma bacci da ba ta yi ba jiya. Yana gani sergent ɗin ya buɗe ankwar ya cire ma ta. Kallon ta ya ke yi tundaga sama har ƙasa, ya kasa ƙarisawa inda ta ke. Sau ɗaya da ta ɗaga ido ta kalleshi ba ta kuma ba sai ta sunkuyar da kan ta tana kallon ƙasa. "Baby girl" ya furta da raunatacciyar murya. Hawayen da ta ke dannewa sai gashi sun fara zubowa. Yai saurin ƙarasowa wajenta ya rungumeta ƙyam ajikin sa. "Baby i'm sorry, i'll get you out of here i promise" Ba abinda ta iya faɗi sai hawaye kawai da ta ke yi. Kusan minti biyu su ka ɗauka a haka kafin ya janye jikinsa ya ce "kin ci abinci?" Maimakon ta bashi amsa sai ta ce " ba ni na kasheta ba" Ya sa babban yatsar sa ya goge ma ta hawaye ya ce "na sani, shiyasa ba zan bari a taɓa min ke ba" "Ka kaini wajen Mommy na please, ina son ganin Mommy na" maimakon ya ba ta amsa sai ya sake rungumeta ƙyam ajikin sa, shi kan sa a wannan lokacin daurewa ya ke yi amma da zai yi kukan ko zai ji daɗi a ran sa. Zuwan Lawyer ɗin sa yai dai-dai da result ɗin da aka kawo daga Asibiti. Jiya da aka kawo Zaytoonah sai da ta suma sau biyu saboda tashin hankali. Wannan ya sa aka kira Likita ya zo ya dubata ya kuma ɗauki jininta dan aje a mata gwaji. Bayan ya karanta result ɗin da recommendation ɗin Likita sai ya kalli Zuhayr ya ce "congratulations Mr Zuhayr, your wife is pregnant" "What?" Zuhayr ya faɗa yana zaro ido. Inspector ya miƙa ma sa takardar dan ya karanta. Da farko mamaki ne ya kamashi saboda ya san ba abinda ya ke shiga tsakanin su. Chan sai ya tuna da wannan dare, daren da yai bikin cika shekaru talatin da huɗu a duniya. "She's pregnant, Zaytoon is pregnant with my child" ya faɗa yana nuna kan sa. Sai kuma hawaye ya fara zubo ma sa. Lawyer ɗin sa ya dafa kafaɗar sa yana ma sa barka. Ya jima yana cikin shauƙi kafin daga baya shi da Lawyer ɗin su ka yi gefe su ka tattauna kan abinda Zuhayr ɗin ke so ayi. Bayan sun dawo Lawyer ya gabatarwa Inspector ƙudirin su na son a ba su bail ɗin Zaytoonah. Inspector ya ma sa wani kallo irin ba ka san ma mi ka ke faɗi ba. "She's charged with murder" Inspector ɗin ya faɗa da kakkausar murya. Lawyer ya ce har kafin a gama investigation Zaytoonah suspect ce dan haka saboda lafiyarta a basu bail ɗin ta. Inspector ya ƙi yarda da wannan zance dan haka su ka tafi wajen Ogan sa. Abu dai bai zo da sauƙi ba dan sai da aka yi ta ja'inja, Zuhayr yayi ta kiraye-kirayen waya kafin bayan kusan awa biyar aka ba su bail ɗin Zaytoonah amma za ta koma gida ne a matsayin house arrest. Ba ita ba fita daga gidan sai idan za ta zo station for questioning ko kuma Asibiti emergency. Ba a tsaya a nan ba sai da aka sa ma ta wani tracker bracelet a hannunta wanda zai dinga monitoring movement ɗin ta. Tana rungume jikin Zuhayr haka su ka fito daga station ɗin su ka shiga mota sai gida. A cikin mota ma lafewa ta yi jikin sa tana sauke ajiyar zuciya akai-akai. Suna fitowa ya ce ta hau bayan sa ya shiga da ita cikin gida amma ta ce za ta iya tafiya. "Are you Ok?" Ya tambaya a karo na ba adadi tun fitowar su daga station. Ta ƙaƙaro ma sa murmushin dole tareda gyaɗa ma sa kai. Ɗakin sa ya shiga da ita ya zaunar da ita a bakin gado yayinda ya tsugunna gabanta ya ɗaura hannun sa a goshinta ya ji zafi. "Jikin ki da zazzaɓi bari ki ci abinci sai mu je Asibiti kin ji" "Zan yi sallah" ta furta da dasashshiyar muryarta. "Ok bari na haɗa miki ruwa sai kiyi wanka kafin ki yi Alwala" Har ya tashi zai shiga banɗakin sai kuma ya juyo ya ce " ina ba inda ke miki ciwo?" Ta girgiza kai "Ba kya jin ciwo a cikin ki?" Nan ma ta girgiza ma sa kai. Har sai da ya shige banɗakin kafin ta dena kallon sa. Yana fitowa ya ce ta shigo ya haɗa ma ta ruwan. "Ka tafi zan iya wankan da kaina" "Baby ba ki da ƙarfin jiki, ki bari na taimaka mi ki" "No zan iya" "Ban yarda ba, ki bari na yau kawai na miki" "Allah zan iya" "Are you sure?" Ta gyaɗa kan ta. Ba dan ya so ba haka ya fita daga banɗakin ya rufo ma ta ƙofa. Ɗakinta ya wuce ya ɗauko ma ta kaya kusan kala biyar haɗe da Kayan bacci ya taho da su na sa ɗakin. Ƙwanƙwasa ƙofar da aka farayi ya sa shi tashi daga kan gadon da ya ke ya fito. Yana ganin sa ya haɗe rai cikin kakkausar murya ya ce "how dare you Benedict" "I'm..." "We are brothers Ben. Ta ya za ka min haka? Taya za a arresting Zaytoon ba na gari amma ka kasa kirana ka gaya min? Ba dan Faisal Khan ya kirani ba da haka zan yi ta zama ba tareda na san abinda ya faru da ita ba" "The conference was important to you, to the company, and" "To hell with the conference Ben" ya daka ma sa tsawa. "She's my wife Ben, My wife" Kalmar my wife ya ɗau daƙiƙai yana echoing a kunnen Ben. Haka Zuhayr ya cigaba da yiwa Ben masifa, duk wani frustration da ya ke ji akan Ben ya sauke shi. Tun da su ke yau ne irin hakan ta faru tsakanin su wanda hakan ya kuma tadawa Ben hankali. Shi da ya ke ganin nan da 'yan kwanaki aka yi zaman kotu aka tura Zaytoonah zuwa jail zai samu daman janyo ra'ayin Zuhayr gareshi daga ƙarshe ma ya bayyana ma sa soyayyar da ya jima yana ma sa sai gashi al'amura na shirin taɓarɓarewa. Tunanin da ya tsaya yi ne ya sa bai ji lokacin da Zuhayr ɗin ya shige ciki ba sai ƙarar ƙofa da ya ji. Ya dunƙule hannunsa yana huci tareda ayyanawa ran sa tsugunne ba ta ƙare ba. Yana shiga ɗakin ya gan ta tana ƙoƙarin saka kaya. Doguwar Dubai abaya ta saka mai launin ruwan toka da aka yiwa ado da blue stones. "Mi za ki ci?" "Zan yi waya da Mommy na" "Ki fara cin abinci tukunna please" Ta girgiza kai ta ce "Dan Allah ka kira min ita" Tausayi ta bashi dan haka ya zaunar da ita ya ce zai kira. Yana fito da wayar sai ga kiran Chef Green yana ɗauka cewa yai "send her to my room" Ya kalli Zaytoonah ya ce " Doctor za ta shigo ta dubaki idan ta tafi sai na kira Mommyn" Ba ta ce komai ba sai ma kwanciya da tayi a kan gadon tana tunanin ƙaddarar ta. Da Likitan ta shigo a kan idon Zuhayr ta ma ta duk wasu tambayoyi da gwaje da za ta yi. Bayan ta gama ta kalli Zuhayr ta fara ma sa bayani akan dole Zaytoonah ta rage tunani saboda jininta zai iya hawa kuma hakan zai yi barazana ga cikin da ke jikin ta. Sannan banda aikin wahala ta kuma dinga cin abinci da kyau. Duk wannan bayani da ta ke Zaytoonah ido kawai ta zuba ma ta tana jin maganar Likitan banbaraƙwai kaman wani yaren Russia. Bayan ta tafi ne Zuhayr ya dawo kusa da ita ya riƙe hannunta ɗaya ya kissing ɗin sa kafin ya ce "ki cire komai a ranki, matuƙar ina raye ba wanda zai kai ki jail, i will protect you and our Baby" Maganar sa ta ƙarshe sai ya kuma dagula ma ta lissafi. "Ciki?" Ta furta tana kallon sa. "Yes Zaytoon kinada ciki" Lokaci ɗaya sai jikinta ya hau rawa. "Ciki?" Ta sake faɗi a ruɗe. Ya gano abinda ta ke tunani dan haka yai saurin jawota jikin sa yana faɗin "forgive me Zaytoon, I actually, I..." Wayar sa ta shiga ƙara dan haka ya sa hannu ya ɗauka. Zaytoon's Mom ya gani a screen ɗin. Allah Sarki ba su ma kiraba amma ita ta kira. "Mommy ce" ya faɗa yana nuna ma ta screen ɗin. Har ta gama ringing ɗin bai ɗauka ba. "Ina tunanin kar mu gaya ma ta abinda ya faru saboda kar hankalinta ya tashi" Ta gyaɗa ma sa kai. Lokacin da ya kirata ringing ɗaya ta yi aka ɗauka. Bayan sun gaisa ta ke tambayar ina Zaytoonah dan tun jiya tana neman numbarta ba ya shiga. Ba ta san tun jiyan wayar na hannun 'yan sanda ba. "Wayar ce ta samu matsala" Zuhayr ya faɗa a taƙaice sannan ya sawa Zaytoonah wayar a kunne. "Adaeze kina lafiya dai ko?" "Mommy" sai kuma kuka ya kuɓce ma ta. "Adaeze miya faru? Ba ki da lafiya ne? Zuhayr ya miki wani abu ne" "Mommy pray for me" ta faɗa cikin kuka. Hankalin Mommy ya tashi ta ce " ba wa Zuhayr na ma sa magana" Zuhayr ya maida wayar kunnen sa. "Mi ya samu 'ya ta? Mi ka ma ta?" Ya sani a yadda ta rikice ɗin nan indai ta ji abinda ke faruwa da 'yarta ƙila heart attack zai kamata dan haka yai gyaran murya ya ce "she's pregnant, tana kuka ne saboda ba ta da ƙwarin jiki ba ta iya karatu kuma sun kusa fara exams" Mommy tunda ta ji kalmar Pregnant sai ta ɗan ji sanyi a ranta. Bayan ya ma ta bayani sai ta nemi magana da Zaytoonah inda ta yi ta ma ta nasiha tareda ba ta tips na yadda za ta kula da kan ta, da yadda za ta dinga duba karatu. Zaytoonah ta daure ta ma ta godiya sannan ta ƙara jaddada ma ta akan ta ma ta addu'a. Mommy ta ce kullum ma tana yi ma ta. Bayan Mommy ta ajiye wayar sai ta riƙe baki, yadda su ke waya da Zaytoonah da kuma video call sai ta ke gani kamar ba abinda ke shiga tsakanin ta da Zuhayr har ta ke gani ko Zuhayr ne ya ɗaga ma ta ƙafa zuwa ta ƙara girma kaɗan ashe-ashe, dama tsakanin miji da mata sai Allah. Bayan ta gama jimamin zancen cikin Zaytoonah sai kuma T J ya faɗo ma ta. Ta goge hawayen da ya fara zubo ma ta tana faɗin "duk inda ka ke na san Allah na tare da kai, ina ji a raina ba ka mutu ba kuma za ka dawo garemu. Za ka zo ka tarar da ɗan ka Abubakar da ɗan ko 'yar Zaytoonah" Daren farkon su ne ya faɗo ma ta, yadda ta samu soyayya daga wajen T J, ta kuma ji jiki a wajen Ɗan Fulanin ta. Ta buɗe drawer da ke gefen gado ta ciro hoton sa. Hoto ne lokacin yana bautar ƙasar sa, a duk lokacin da ta ga hoton nan tunowa ta ke yi da mafarin komai, mafarin haɗuwar su wanda ya kawo su har ga aure da samun zuri'a. Ta sa hannu tana shafa fiskar T J da ke ɗauke da dariya... Abincin da Zuhayr ya kawo ma ta kaɗan ta iya ci saboda ko kaɗan ba ta jin taste ɗin komai a bakin ta. Kamar yadda Mommy ta koya ma ta lokacin ɓatar Daddyn su shi ta tuna takeyi. Da ta tuna ana tuhumar ta da laifin kisa sai ta fara furta Hasbunallahu wa ni'imal wakil nan da nan sai ta ji ranta yayi sanyi. Cikin da ke jikinta kuwa zuciyar ta kokonton abin ya ke. Wai 'yar ita ɗin nan ne ta ke da ciki, wai lokacin da su ka je Finland Zuhayr ya ma ta irin abinda ake yi idan anyi aure, sai kuma ta ji kunyar Zuhayr ya kamata. Motsi kaɗan Zuhayr zai fara tambayar ta ko lafiya. Bayan ta yi sallah ta kwanta daga baya da Zuhayr ya je yai wanka shima ya zo ya kwanta kusa da ita ya jawota jikinsa ya rungume. Ko jimawa da bacci ba ta yi ba ta fara mafarkin abinda ya faru gawar Linda da ta gani, yadda police su ka sa ma ta ankwa su ka tafi da ita, tambayoyin da aka fara ma ta bayan sun isa station har ya sa ta suma a wajen saboda gigicewa. "I didnt kill her, i didnt kill her" ta farka a zabure tana faɗa da ƙarfi jikinta na ɓari. "Hey Zaytoon relax, relax, i'm here" ya fara faɗa a kunnenta bayan ya rungumeta jikinsa sosai. Kafin bacci ya kuma ɗaukan ta sai kusan bayan awa biyu. Bayan ya tabbatar baccinta yayi nisa ne ya miƙe ya shige banɗaki ya ɗauro alwala. Alinah ta faɗa ma sa duk lokacin da ya ke cikin damuwa ya tashi da dare yai nafila raka'a biyu ya gaya wa Allah damuwar sa Insha Allah zai samu sauƙi. Rabon da ya tashi sallah da dare tun kafin Alinah ta rasu. Bayan rasuwanta kusan ya koma gidan jiya ne dan duk wani abubuwa na ibada da ta ɗaurashi a kai watsar da su yai. Ya jima yana yiwa Zaytoonah addu'a bayan yayi sallar kafin ya dawo ya kwanta kusa da ita. Washegari za su je station ƙarfe goma dan haka tun ƙarfe tara su ka shirya. Wa su 'yan jarida sun zo gidan sa tun da sassafe amma ya sa securities ɗin sa sun kore su. Lokacin da su ka fito daga mota yana riƙe da ita yayinda Zaytoonah ta rufe fiskarta da gyalenta. "Mr Zuhayr dama kana da aure ne? Ance matar ka minor ce ba ta cika shekara shatakwas ba gaskiya ne?" "Mr Ilyas wasu mutane na faɗin mutuwar Linda Cannel yana da nasaba da mutuwar tsohuwar budurwar ka Alinah Jones mi za ka ce gameda haka?" "Mrs Ilyas miye haɗin ki da wacce kika kashe Miss Linda Cannel?" Kaɗan daga tambayoyin da 'yan Jarida ke musu kenan kafin su shiga station ɗin amma babu wanda yai magana cikin su, Zaytoonah kam ko fiskarta ba a gani balle ma tayi magana, shi kuma gogan baƙin glass ya saka ya murtuke fiskarsa. Ta samu words of encouragement daga wajen Zuhayr kafin zuwan su dan haka ta ɗan nitsu lokacin da ake ma ta tambayoyin. Bayan an gama da ta fito Zuhayr ya riƙeta su ka fita a wajen. A wajen tambayar ta yi hawaye kam amma ba ta yi kuka wiwi ba kamar ranan farko. Daga station su ka wuce gida inda private investigator da Zuhayr ya ɗauka ke jiran su da information ɗin da ya samu. Ba a kawo report na Autopsy da aka yi ba tukunna amma cross examination da aka yi a wajen crime scene ɗin an samu shaidar ƙafar takalmin namiji a wajen, sannan duk da an ga finger print na Zaytoonah a jikin wuƙar babu a wani wajen banda jikin rigan Linda, wanda taɓata da Zaytoonah ta yi ne ma ya sa aka samu. Wanda kuwa da ace kokawa su ka yi kafin ta daɓa ma ta wuƙa da za a finger print na ta a wasu sassan jikin ta. Zuhayr ya ji daɗin feedback ɗin da ya samu dan dama ko kaɗan bai ji a ransa cewa Zaytoonah ce ta kashe Linda ba, a wani dalilin za ta kashe ta?. Ben kam yana chan yana ƙoƙarin bibiyar investigation ɗin ko za a iya samun abinda zai sa a gano shi, da zai je gidan Linda ba ta ƙofar gaban gidan ya zo ba sannan yayi disguising kan sa kafin ya shiga gidan. Ya yi amfani da extra precaution ta yadda ba za a ga finger print ɗin hannun sa ba ko ma wani abu da zai tona asirin sa. Da yamma yana bawa Zaytoonah abinci a baki a ka kirashi ake sanar ma sa wai Farha Jubril ƙawar Zaytoonah na son ganin sa. Ba ya son hayaniya dan haka ya ce ace ma ta ba shi da lokaci. Sake kira aka yi wai ta ce tanada abu mai mahimmanci da za ta bashi ne. Ya taɓa ganin yarinyar a Asibiti lokacin da aka kwantar da Zaytoonah amma yanayin yarinyar kamar bai yarda da ita ba sai dai a halin yanzu yana buƙatar duk wani taimako da zai sa a warware case ɗin nan a clearing sunan Zaytoonah. Sai da ya gama ba wa Zaytoonah abinci kafin ya sauko ƙasa. Bayan Farha ta gaishe shi ne ta miƙa ma sa wani hard drive ta ce " Akwai wasu evidence da na haɗa a nan wanda zai iya taimakawa Zaytoonah. Incase ma an jirkita wasu evidence ɗin wannan ma zai iya taimakawa" "Calls da aka yi tsakanin Zaytoonah da Linda ne tun lokacin da su ka exchanging contacts ɗin su sannan akwai footage na lokacin da Zaytoonah ta shiga library da lokacin da ta fita. Akwai kuma na lokacin da taxi ya sauketa a ƙofar gidan Linda, idan an fitar da result na autopsy za a duba time ɗin mutuwar Linda da kuma time ɗin shigar Zaytoonah gidan" "Thank you Farha" ya faɗa yana saka hard drive ɗin a aljihun sa. "How's she?" "She's fine" Ta miƙe tsaye ta ce ma sa za ta tafi. Ya ƙara yi ma ta godiya kafin ya wuce sama dan ko kaɗan baya son barin kusa da Zaytoonah. Farha na fitowa ta yi kiciɓis da Ben zai shigo gidan. Tsorata ta yi da yadda ya ke kallonta amma ta dake ta wuce shi ba tareda ta ma sa magana ba... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 31 Bismillahir Rahmanir Rahim *Ustadzh Ben-Zubair* A rana ta huɗu da abin nan ya faru Uncle Aliyu ya zo gidan su. Shi bai san abinda ya ke faruwa ba sai da ya gani a jarida. To daya kira Zuhayr shine ya confirming cewa gaskiya ne abinda aka rubuta amma kuma Zaytoonah ba ta yi kisan ba. Ya ma sa faɗa kam na yadda bai kirashi ya faɗa ma sa babbar matsala kaman wannan ba. Ya jima yana tattaunawa da su kafin daga baya ya tafi bayan ya yi mu su addu'ar samun nasara. Zuhayr baya buƙatan taimako indai na kuɗi ne ko connections dan ya fi Uncle Aliyu komai sai dai ko ba komai a lokaci irin wannan mutum ya kan ji daɗi idan ya samu support na 'yan uwan sa, shiyasa ma Uncle Aliyun ya zo dan ya nuna mu su ya damu da ɗan Yayan na sa. Kullum sai Likita ta zo ta dubata kamar yadda Zuhayr ya buƙata kuma a wani zuwa da ta yi ne aka ma ta scanning inda ta gaya mu su cikin Zaytoonah satin sa shida. Zuhayr felt very happy, he cant wait to see his child. John Torres shine shugaban Lab ɗin da aka ayi autopsy na gawan Linda Cannel kuma shi yai investigation ɗin. Mutum ne da ko kaɗan baya son musulmai ba dan komai ba kuwa sai saboda abinda ya faru 9/11 a shekarar 2001, inda aka kai hari a twin tower na ƙasar America wanda ya hallaka kusan mutane dubu uku da wani abu. Ɗan John mai suna Samuel yana ɗaya daga cikin sojojin da su ka rasa ran su a wannan lokaci. Da ke ana alaƙanta harin da cewa musulmai ne su ka yi ƙarƙashin jagorancin Usama Bin Laden sai abin ya ƙarawa musulmai baƙin jini a idon mutanen America. Da farko John bai san wa ake tuhuma da kisan ba shiyasa ya fara haɗa report na gaskiya. Amma a rana ta biyu da aka kawo gawan sai ga anonymous caller ya kirashi inda ya ma sa zancen duk yadda za ayi kar ya ba da report na gaskiya saboda wacce ta yi kisan musulma ce kuma da alama ana so a wanketa daga wannan laifi da ta aikata. Ya faɗa ma sa exact time da ya ke so ya saka cewa Linda ta mutu. Ƙiyayyar musulunci da ke ran John sai ta mamaye zuciyar sa. Ya nemo hotunan labarin a computer ɗin sa inda a nan ya ga hoton Zaytoonah lokacin da fito da ita daga gidan tana tsaye an sa ma ta ankwa a hannunta. Gyalen da ta yi rolling kan ta da shi kaɗai ya isheshi shaidar cewa ita musulmace. Ransa ya ƙara ɓaci dan haka ko tuna cewa laifi zai aikata bai yi ba dan haka washegari da ya koma office sai ya sake rubuta wani report ɗin ya jirkita komai kamar yadda Anonymous caller ya ce, ya maida report ɗin zuwa abinda zai implicating Zaytoonah. Gobe za a kawo post motem report daga Lab dan haka tsoro da fargaba ya sa Zaytoonah a gaba duk yadda Zuhayr ya so ta kwantar da hankalinta ta yi bacci hakan bai yiwu ba. "Zaytoon for our Baby's sake ki kwantar da hankalin ki please" Ita fa mantawa ta ke yi da wani wai tana ɗauke da baby a cikinta. Ba wani chanji a tattare da ita, ko cikinta ba ta ga ya taso ba. Abinda za ta iya faɗi shine tun ma kafin ta san tanada cikin tana yawan jin kasala amma kusan komai za ta iya cewa normal ta ke sai yanzu kuma da damuwa ya zo ya sa ta a gaba. "Ok bari mu yi abu ɗaya. Ki bani labarin ki sai na baki nawa, na san kafin ma na gama nawa labarin kin yi bacci" "A'a kai ka fara bani labarin ka" Tana manne jikinsa ya shiga ba ta labarin rayuwar sa. Yadda ya rasa iyayen sa tun bai wani girma ba, yadda yai fama da rayuwa har ya zama abinda ya zama. Tun kafin ya gama high school ya fara sauye-sauye a gidan gonan iyayen sa wanda ya sa cikin shekaru biyu su ka samu haɓaka sosai da wannan riba da su ka samu ya ɗeba duka kuɗin ya zuba jari a wani kamfani da ta ke haƙo ma'adanai na gold da silver. By the time ya gama degree a university already shi da Ben suna da plan na abinda za su fara dan haka da kuɗin da ya taru na hannun jarin da ya ke da shi da kuma wasu kuɗi da Ya karɓa a wajen Kakan sa Mr Haddish ya samu ya buɗe kamfanin sa. Cikin shekaru biyar kamfanin ta haɓaka ta samu cigaba sosai, and @ 25yrs he's already a millionaire. Yanzu da ya ke shekaru 34 ana irgashi cikin mutum goma da su ka fi kowa kuɗi a Las Vegas. A Jahar Nevada gaba ɗaya ma idan ana irga top 25 sunan sa yana faɗawa ciki. Ba dan ya ji maganar Alinah ba da yanzu ma ya fi haka, a da yanada hannun jari a wani babban Casino da ke Vegas ɗin, inda ake buga chacha a sha giya ayi duk wani baɗala. Amma shigowar Alinah rayuwar sa da ta nuna ma sa haramcin hakan sai ya siyar da hannun jarin, bisa shawarar Alinah sai yai amfani da kuɗin wajen turawa refuge camps na 'yan gudun hijira. Har lokacin da ya gama labarin sa ba ta yi bacci ba idon ta garau. Ta jinjina ma sa na rasuwar iyayen sa wanda hakan ya tuno ma ta da na ta uban. A hankali ta soma bashi labarin soyayyar iyayenta, labari ne da ta taso da shi saboda yadda Daddy ke karanto ma ta shi a duk lokacin da ta buƙaci ya ba ta labari mai daɗi. Da farko ma ba ta ɗauka labarin iyayenta ba ne sai da ta fara wayo ta gane saboda koyaushe labarin Ɗan Fulani da Inkiru Inyamura ne taken labarin. Ta faɗa ma sa komai da ta sani har zuwa rasa mahaifin su da aka yi har yau babu shi ba labarin sa. Jikin Zuhayr yai sanyi, yanaji tana kuka lokacin da ta ke nanata yadda ta ke son Daddynta da yadda ta yi missing ɗin ta amma bai hanata kukan ba sai ma kwanta da kanta da yai a ƙirjin sa yana ɗan bubbuga bayanta a hankali. Ta jima tana shesheƙar kuka kafin daga baya ya ji shiru ashe ta yi bacci ne. A wannan daren ya ɗau alkawarin nemo ma ta mahaifinta ya kuma yi alkawarin sai ya nemo Uncle ɗin Mommy ya gurfanar da shi a kotu ya sa an hukuntashi bisa laifuffukan sa... *** Allah ba azzalumin bawa ba ne. Haka nan duk abinda Allah ya rubuta babu mai iya chajashi. A yayinda John Torres da Ben su ka yi niyyar tarwatsa Zaytoonah. Allah bai ba su dama ba, hakan ba ya cikin ƙaddararta, baya cikin abinda Allah ya nufa gareta shiyasa ko da sama da ƙasa za su haɗu ba za a samu damar cin galaba a kan ta ba. John da ya fito daga gida zai tafi Lab kafin daga nan Idan police sun zo ya damƙa mu su report sai kawai yai hatsari a hanya. Aka wuce da shi Asibiti saboda raunuka da ya ji sosai. Hatsarin sa ba zai sa a fasa abinda aka yi niyya ba tunda yana da assistant kuma an riga an gama komai dama akan gawar report kawai za a bayar. Inda Mr Torres ya ke ajiye files na shi kaf assistant ɗin sa ta duba amma ba ta ga file ɗin gawa mai lamba 50879 ba dan haka ta buɗe computer dan ta sake printing ɗin sa tunda duk wani report akan computer ake ajiyewa kafin a ajiye printed copy ɗin a cikin file. Tana duba date ɗin da aka kawo gawan ta ga report na farko da Mr Torres ya fara yi dan haka ta yi saurin printing ɗin sa ta kai office ɗin Deputy ɗin Mr Torres wanda ya karanta report ɗin ya ga ba matsala tunda duk da ba shi yai aiki akan gawan ba amma ya bibiyi labarin gawar a wajen wani intern da ya taya Mr Torres aikin. Bayan ya duba ya sa hannu sannan ya buga stamp ya miƙa ma ta... "Na baki abinda zai sa ki nitsuwa?" Ya faɗa yana ƙyafta ma ta ido lokacin da su ka sauko ka sa ya ga tana ajiyar zuciya akai-akai saboda fargaba. "Zuhayr ina tsoro" Matsowa yai daf da ita ya ce "barin baki maganin tsoro to" Ta buɗe baki za ta yi magana ya ce "rufe idon ki" "Ni kam" "Babu jayayya kirufe ido kawai" Tana rufe ido ta ji saukar lips ɗin sa akan na ta wanda ya sa ta waro iso waje. A hankali ya shiga kissing ɗinta softly, da farko lips ɗin ƙasa ya ke tsotsa daga baya ya koma na sama ya cigaba da tsotsa slowly kafin daga baya ya chanja salon ya kamo harshenta ya fara tsotsa. Zaytoonah wata duniya ta shiga na daban, sau biyu da ya taɓa kissing ɗin ta duk briefly ne amma wannan kam a yadda su ke tafiya ƙila za su shekara ne a wajen dan ba shi da niyyar dena wannan soyayyar. Ƙaran fashewar glass ne ya dawo da su duniyar da su ke ciki ta ainihi. Ben ne tsaye wajen dining yana huci kamar wani tsohon maye. Zuhayr ya kalle shi ya ce "are you Ok?" "Yeah" ya furta kaman zai yi kuka. Wani abu ne ya tokare shi a zuciya lokacin da ya ga Zuhayr ya juya ga Zaytoonah yana ma ta magana. Da Zuhayr ɗin da ya sani da ne da gudu zai yi ya ƙariso inda ya ke ya tabbatar babu abinda ya sameshi. Amma wannan bai damu ba. "See, na faɗa miki inada maganin cire tsoro" Da sauri ta rufe fiskarta da tafukan hannunta biyu. "Idan kina son maganin cire kunya ma ina da shi" Ba tareda ta buɗe fiskarta ba ta fara girgiza ma sa kai. "Na baki ne?" "A'a ba na so" ta faɗa da sauri bayan ta buɗe fiskar. Shi kuwa sai ya fara dariya hakan ya sa ta wuce gaba za ta fita yai saurin riƙo hannun ta yana faɗin "not so fast Baby girl". Yau ma kamar koyaushe sai da 'yan Jarida su ka cike bakin station ɗin ana jiran su. Amma ba su kula kowa ba su ka shige ciki. Tuni an riga an karɓo result daga Lab ga kuma report da aka gama haɗawa na crime scene ɗin. An jima ana bayani kafin daga baya aka ba wa Zaytoonah takarda ta sa hannu wanda ke wanketa daga duk wani laifi da ake tuhumarta. Bisa report da aka haɗa, wanda yai kisan facts da aka haɗa ya nuna namiji ne dan har tsayin sa sai da aka ƙiyasta. Sannan lokacin da Linda ta mutu da lokacin da Zaytoonah ta zo gidan akwai tazaran kusan minti shatakwas. Sannan text ɗin da aka tura da wayar Linda an goge shi amma kuma text ɗin na wayar Zaytoonah kuma an yi bincike an gane cewa text ɗin ya shigo ne mintuna kaɗan bayan Linda ta mutu. Duk da an wanke Zaytoonah daga zargin da ake ciki ba a rufe case ɗin ba saboda za a cigaba da bincike wajen gano wanda yai kisan dan wanda yai kisan wanda ya san Linda da kuma Zaytoonah ne. Duk maganar da akeyi hannunta na cikin na Zuhayr yana matsasu a hankali. Duk yadda ya ba ta baki a gida akan kar ta yi kuka sai da ta yi lokacin da aka ba ta takardar dan ta yi signing. Duk da tana da yaƙinin Allah zai taimaketa amma ba ta san taimako da wuri haka zai zo ba, har ta fara tunanin ga ta nan an gurfanar da ita gaban kotu tana ba da bahasi. Allah kenan, wani lokaci ka ga taimakon sa cikin gaggawa wani lokaci ya jinkirta taimakon zuwa wani lokaci saboda dalilin da ya barwa kan sa sani. Daga ƙarshe idan ka yi addu'a ka yi haƙuri sai kaga duk lokacin da ka samu taimakon Ubangiji to lokacin ne ya ke daidai a gareka, lokacin ne ya fi dacewa da kai. Ben fakewa yai da zai je office amma a zahiri bin su yai ya bibiyi sakamakon report ɗin dan ya tabbatar da cewa Mr John ya yi abinda ya sa shi sai kuma ya riski komai ya juye. Kiran Mr John yai sai matar sa ta ɗauka inda ta ke ce ma sa yana kwance an ma sa allurar bacci. Ya daki steering motar sa da ƙarfi yana faɗin shit. Sai da ya jima a wajen kafin daga baya yai reverse da motar sa ya tafi. *** Tana shiga ɗakin abinda ta farayi shine sujudush shukri. Lokacin da ta ɗago kuma sai ta faɗa jikin Zuhayr da ke tsaye. "Thank you, Thank you Zuhayr" Ya sa hannu ya rungumeta sosai. "Daga yanzu zan dinga kula da ke fiye da da, duk inda za ki je ki gaya min kin ji?" Ta gyaɗa ma sa kai. "Ki faɗa min mi ki ke so?" "Ka kaini Nigeria, ina son ganin Mommy da ƙannena" "Done, kina gama exams za mu tafi. Faɗa min sai me?" "Za ka dena cemin Baby girl, i'm not a Baby" ta faɗa tana ɗan turo baki duk da wai ganin fiskarta ya ke ba dan har lokacin tana ƙirjinsa. Yai murmushi ya ce " Baby kam ta girma tunda akwai tiny Baby a cikinta" Jin maganar ya sa ta sake shigewa jikin sa dan kunyar sa ta ji. "Ni kam ki bani dama na baki maganin kunyan nan, kema za ki huta Allah" "Hu'uum, ba na so" "To mi ki ke so?" "Shikenan" "Ban yarda ba. Ki faɗi duk abinda ki ke so da wanda ba kya so. Ko ni ne ba kya so ki faɗa" Maganar ƙarshe sai ya sa ta ji gwiwar ta yayi sanyi. Ba za ta iya cewa kai tsaye tana son Zuhayr ba amma kuma compared to farkon zuwanta yanzu ya samu matsayi sosai a zuciyarta, tun ma kafin wannan abu ya faru da ita. Ko yaushe tana nutsar da zuciyarta da cewa Zuhayr ya fi ƙarfinta, ba ta kai Zuhayr ya so ta ba balle har ya janye yarjejeniyar su na farko ya fara ganinta a matsayin matar sa. Sai dai kuma ga wani baƙon al'amari da ya faru wanda gashi wai har cikin sa ke jikinta. Ta sani abunda ya faru da kuma cikin ne ya sa Zuhayr ke ba ta wannan lovey-dovey care ɗin. "Tell me sai me ki ke so" Tambayarsa ya dawo da ita daga tunanin da ta ke. "Ka kaini Gidan gona kuma ka koya min hawa doki" "Ok amma bayan sai kin haihu ko" "A'a idan mu ka dawo daga Nigeria" ta faɗa da ɗan ƙarfi. "Ok we'll see about that. Sai me kuma" Wannan karan sai da ta janye jikinta daga na shi sannan ta ce "idan na tambaya za ka min?" "Ofcourse My Dear" ya faɗa yana sa hannu a hips ɗin ta. "Dan Allah ka raba gida da Ben, idan ina kallon sa tsoro na ke ji. Idan ma wani gidan za ka nema mana mu koma ba matsala sai ka bar ma sa wannan, amma plz ka raba gida da shi ba zan iya juran ganin sa a gidan nan ba" Kallon ta ya ke yi har ta ƙare maganar ta bai ce komai ba. Although shi ya siyi gidan nan da kuɗin sa but tare su ke zaune da Ben for years ko lokacin da ya ke shirin auren Alinah ma bai yi tunanin zai ce Ben ya bar ma sa gida ba. Sai dai Zaytoonah is carrying his child, idan zaman Ben tareda su is threatening to her to dole ne ya nemawa Ben wani gida ko shi ya nemi wani gidan ba, ba zai affording ya rasa babyn sa ba especially at a time where he's battling a disease. "Ni kam idan ba za ka ce ya tafi ba to ka nema min wani gida ko da ɗaki ɗaya ne zan zauna amma ba zan zauna gida ɗaya da Ben ba" Maganarta ya dawo da shi daga tunanin da ya ke. Fiskarta ya tallafo da hannun sa ya ce "dont worry Dear your wish is my command, zan nema mana wani gidan kin ji ko kin fi son wannan?" "Duk wanda ka ke so ina so" "Zan bar ma sa wannan saboda kar ya ji haushi a ran sa, i'll buy another house" *** Cikin kwana uku aka sama ma sa irin gidan da ya ke so, gida ne shima a chan gefen gari dan shi baya son hayaniya. Gidan bai kai wanda su ke ciki girma ba amma shima Babba ne, shi kuma gidan yana kusa da wajen ruwa ne dan daga balcony ɗin gidan kana ganin ƙaton ruwan da ke ta gaban gidan. Ga kuma garden da ya ke ta bayan gidan wanda ya ke da girma sosai. Within four days aka je aka gyara komai na gidan, furnitures ɗin da aka bari a gidan wanda baya so duk an cire an sa sabbi. Sai da komai ya kammala sannan ya tunkari Ben da maganar komawa sabon gidan tareda miƙa ma sa takardun tsohon gidan inda ya ce ya bar ma sa shi kyauta. "Are you avoiding me Zuhayr?, did you believe what Zaytoonah is saying about me, did you believe i can harm anyone?. We're brothers, we're best friends, i love you more than anyone in this world, do you hate me Zuhayr?" "No Ben, you're my friend, my family, i dont hate you" "Then why?" Ben yai maganar da ƙarfi yana miƙewa tsaye. Zuhayr ya miƙe ya je wajen sa ya dafa kafaɗar sa yana bashi haƙuri tareda nuna ma sa ba komai ya sa shi son raba gida da Zaytoon ba sai dan kwanciyar hankalinta, baya son abinda zai tada hankalinta ya jawowa babyn sa matsala. Ben sai huci ya ke yi idon sa ya kaɗa yayi ja. Amma yadda Zuhayr ya kwantar da murya yana bashi haƙuri ya sa ya sauko daga fushin da ya ke yi har ya nunawa Zuhayr ba komai zai bar mu su gidan. Zuhayr ya ce ya zauna su za su tashi saboda gidan da ya samu ɗin ya burgeshi saboda yana ta kusa da teku and he loved nature. Bayan kwana biyu da maganar su ka koma sabon gida, sun tafi da Chef Green da masu aikin Zaytoonah guda biyu wanda za su dinga shifting ɗin aiki tsakanin su. Akwai security guda biyu sai kuma Driver. Wannan gidan nisan shi da school ɗin su har yayi yawa dan haka dole awa ɗaya kafin aji ta ke fitowa Mr Dawson ya kaita makaranta. Shi ma kaman wancan ba gidaje kusa da shi, wannan kan ma kafin ka ga gida sai ka sha dogon tafiya ba tareda ka ga alamar gida ko mutane ba kafin ka fara tsinkayar gidajen mutane jefi-jefi. Hankalinta kwance ta ci ta sha ta kwanta sai karatu wanda yanzu abubuwa sun ma ta yawa dan an barta a baya sosai... *Nobody takes you away from me My Love, not even the fat girl* Ben ne yai maganar a lokacin da ya ke kallon ƙaton hoton Zuhayr da ke bangon ɗakin sa. Yai murmushi kafin ya fita daga ɗakin. Zuhayr na Asibiti inda ake ma sa gwaji sai ga kiran Sheikh Hassan ya shigo wayar sa. Bai ɗauka ba sai da nurse ɗin ta gama ɗeban jinin sa kafin ya ɗau waya ya kira Sheikh Hassan ɗin. Maganar da su ka yi ne ya sa shi washe baki yana murmushi. Daga Asibiti kai tsaye gidan Sheikh Hassan ya wuce inda ya ƙara tabbatarwa idon sa abinda Shiekh ɗin ya faɗa. Ya rungumi Ben yana murmushi. Sun jima suna tattaunawa kafin su ka ɗunguma masallaci saboda sallar la'asar ya yi. A masallacin ne aka shaidawa mutane Mr Benedict Vincent Haddish ya karɓi kalmar shahada. Nan da nan 'yan uwa musulmai aka fara murna ana rungume Ben ana taya shi murna, shi kuma sai yaƙe haƙora ya ke yi. Sai bayan sallar Isha su ka dawo gida tare inda Zuhayr ya ce ya zo su gaisa da Zaytoonah saboda ya sani yanzu kam za ta dena jin tsoron sa. Da ke tana falo lokacin da aka buga ƙararrawar shiga gidan ita ta tashi ta je dan ta buɗe dan ta ji alamar tsayuwar motar sa. Tuntuni ta ke jiran sa ya dawo saboda ta gaya ma sa abinda ta gano. Tana buɗe ƙofa ta ganshi yana murmushi. "Dear ga ɗan uwa nan na kawo miki" yai maganar yana ɗan muskutawa gefe. Ben ta gani sanye da riga da wando fari irin na mazan pakistan har da hula fara. Zuhayr ya ce " Masha Allah, after all this years Ben ya karɓi musulunci. I present to you my brother Benedict now Zubayr" Ya nuna kan sa ya ce "Zuhayr" ya nuna Ben ya ce " Zubayr" Zaytoonah sai ta yi mutuwar tsaye a wajen ga Ben kuma da ke ma ta wani munafukin murmushi yana ƙanƙanta munafukan idanun na san nan. Ben ya karɓi musulunci ta yaya? Mutumin da iya zaman da ta yi da su ta san shi ba practicing jew ba ne. Ba ya komai na ibada da jews ke yi, ba za ta kirashi christian ba saboda nan ma baya yin ibada irin ta su. Ben atheist ne wanda ba shi da addini. Ben musulmi🤔 *Ben fa zai yi komai dan ya samu abinda ya ke so. Team Ben mi kuka shirya mana ne? Mun bar muku gidan ma ashe ba mu tsira ba* 2/11/21, 10:04 PM - ****: 34 Bismillahir Rahmanir Rahim *leukemia* Satin su Zaytoonah ɗaya da dawowa aka fara shirye-shiryen bikin Muhsina da AbdulHameed, cousin ɗinta ne dan Mahaifiyar sa Yayar Mahaifin Muhsina ɗin ne Uban su ɗaya amma Uwa banban. Daga wajen 'yanuwan Zuhayr ta samu kulawa a wajen su sosai musamman ma Kakannin Zuhayr mata wato Hajiya Nenne da Hajiya Saudah. Da ke tunda aka fara hidimar bikin gidan cika ya ke yi ita kam agidan su ta ke wuni, ba dan Mommy ba ma da anan za ta dinga kwana. Ba wai ta saba da 'yan gidan su Zuhayr ba ne, har yanzu idan ka cire tsofaffin sai kuma Muhsina da Hajiya Maryam wacce ta ke immediate ƙanwar marigayi Muhammad. Wasu cikin cousins ɗin Zuhayr da su ka haɗu a wajen hidiman bikin sun ɗan yi mutunci wasu kuwa sai dai kallon-kallon da harara kawai saboda girman kai da ya mu su katutu a zuciya... "D har yanzu ba ka shirya ba ne?" Ta faɗa lokacin da ta shigo ɗakin na su. Towel ne ajikinsa yana zaune a bakin gado, tissue da ya goge hancinsa da shi yai saurin takewa da room slippers ɗin sa dan kar ta gani. Ta riga ta shirya tuntuni yanzu ma daga ɗakin Hajia Saudah ta ke wacce ta kirata ko sun gama shiri ne tunda an fara tafiya wajen da za'ayi dinner ɗin. Lokacin da ta fita ta bar Zuhayr a banɗaki ne yana wanka. "D ɗazu fa ka ke ƙorafin ban shirya ba amma gashi har na je na dawo ko kaya ba ka sa ba" Ya ƙaƙaro murmushin dole ya ce "ina ga ba zan je wajen dinner ɗin ba. Kai na na ciwo" Ido ta zaro lokacin da ya ke magana ta ga jini na ƙoƙarin fitowa a hancin sa. "D jjjjjini a hancin ka" ta faɗa tana nuna ma sa hancin. Sauran tissue da ya ɓoye yai saurin cirowa ya fara toshe hancin da shi. "Mi ya sameka?, ba ka da lafiya ne? Na kira ma ka Kamal ya kai ka Asibiti ne" Ta jero tambayoyin tana tattaɓa goshin sa. Ya riƙo hannunta da sauri ya ce "kar ki damu haɓo ne" "Haɓo?" Ya gyaɗa ma ta kai yana murmushi. Duk yadda ta ke ɗokin zuwa wajen dinner ɗin sai ta ji ya fita ma ta a ka. Lokacin da ta taimaka ma sa ya kwanta kamar yadda ya buƙata ne ta ga sauran tissue da yai amfani da su wanda suma cike su ke da jini hakan ya sa ta tsorata, ta fara tambayar kan ta anya haɓo ne kamar yadda ya ce ɗin ko kuma akwai wani abun daban. Duk da ya ce ta tafi wajen dinner ɗin tunda ta shirya amma ba ta kulashi ba. Fita tayi ta je ta gayawa Hajia Saudah cewa sun fasa zuwa saboda Zuhayr ba ya jin daɗi. Da ta dawo kayan jikinta ta cire ta saka kayan bacci ta kwanta gefen mijinta kanta na kan ƙirjin sa. "Gobe za mu je Asibiti a duba ka. Ƙila whether ɗin Nigeria ne bai karɓeka ba, na lura tunda muka zo zafi ke damunka, sai ka riƙa yin zufa, ko ni da ke da ƙiba ma bana irin zufan da ka ke yi tunda akwai sanyi" "Na gaya miki ba komai haɓo ne kawai" "Ni dai ban yarda ba" Ya ɗan rankwafo kan sa ya kissing goshinta ya ce "I love you" "I love you too"... Washegari duk yadda ta so ya je Asibiti cewa yai ba zai je ba lafiyar sa ƙalau. Ranan sai ta maƙale ma sa duk wani motsinsa yana idon ta, wajen ɗaurin aure kawai ya je a ranan amma tare su ke a ɗaki tun safe har yamma. Ko gidan su ba ta je ba kiran Mommy ta yi ta ce ma ta Zuhayr ba ya jin daɗi ba za ta zo ba. Lura da ta yi da shi na wuni ɗaya sai ta gane ashe ya rame ma ta. "My D dan Allah mu je Asibiti a duba ka. Ka kalleka fa" "Ki kwantar da hankalinki, ba abinda ke damina" ya faɗa yana jawota jikinsa. "Ko dan kin ga kwana biyu ban ban ban..." ya shiga kissing wuyanta. "Ni dai ban ce ba, kawai..." Duk da baya jin daɗin jikinsa sai da ya tabbatar ya biya mu su buƙatun su, sai a sannan Zaytoonah ta ɗan kwantar da hankalinta. Anyi biki an ƙare lafiya, Amarya Muhsina kuma an kaita Abuja inda mijinta ke aiki. Zaytoonah ta so zuwa amma yadda ta lura da yanayin Zuhayr sai ta fasa zuwa. Tun zuwan su garin yau ne rana na biyu da za su je gidan su Mommy tare. Wannan karan ma Sallama za su yi saboda za su je ziyara Ringim washegari. Bayan sun gaisa da Mommy sai ta ke tambayar sa ya jiki. Ya ce ma ta da sauƙi. "Mommy Dan Allah ki ma sa magana ko zai ji, ya ƙi ya je Asibiti kuma har yanzu ba shi da lafiya fa" ta yi maganar cikin shagwaɓa. "Mommy kar ki kulata lafiyata ƙalau, ta ƙi yarda ne" Ta harareshi ta ce " Mommy sau uku ina kamashi yana goge jini a hancin sa, ya ce wai haɓo ne. Mommy ina kan haɓo a lokacin zafi ake yi?" Mommy ta ce "garin ya ma sa zafi tunda kinga ba irin sanyin chan ba ne" "Still Mommy..." "Ki bari idan ku ka koma sai ku je Asibiti, zai fi ganewa da likitocin sa na chan" Da wannan ta yi shiru ta ɗau wani zancen a nan ta ke jin wai Hajjo mahaifiyar Humairah ta yi aure wai haihuwa ko yau ko gobe, Zaytoonah ta ce Allah ya sauketa lafiya. Ba su jima da zuwa ba Zaytoonah ta ce za ta je gidan Maman Abdul ta karɓo Dambu dan sun yi waya akan za ta ma ta. "Allah ya shiryeki da kwaɗayi Zaytoonah" Salman da ke wajen ya faɗa. Mommy ta wurga ma sa wani kallo. "To Mommy wai wani gida za ta je cin Dambu fa, miye daɗi a Dambu idan ba kwaɗayin Adaeze ba" "Salman tashi ka bar nan" Mommy ta daka ma sa tsawa. Salman ya miƙe yana ƙunƙuni. Falon ya saura daga Mommy sai Zuhayr sai kuma Junior da ke karatun dole da Mommy ta sa shi bayan ya fita yawo ba takalmi a ƙafar sa. Da zane shi za ta yi sai ta ga kamar dukan ma ba ya ma sa komai yanzu shiyasa ta tursasashi yin karatu. Daga inda su ke zaune tana jin karatun na sa, idan yai shiru ta sake waiwayan sa ta ce ya cigaba bai isa ba. "Ina fata dai Zaytoonah ba ta da wata matsala?" "No" ya furta a taƙaice. Chan da shirun yai yawa ne sai Mommy ta miƙe dan ta shige ɗaki idan ya so ta turo ma sa Salman. Sai kuma ta ji ya ce "ba ni da lafiya" Mommy ta yi saurin zama tana jin ƙirjinta na bugun tara-tara. "Ba na son hankalin Zaytoon ya tashi ne shiyasa na ke ɓoye ma ta. Inada cancer na jini, Chronic myelogenous leukemia" "Innalillahi" Mommy ta furta a fili. "Ciwon da ya kashe mahaifiyata kenan. Ina zuwa Asibiti check-up kuma sun fixing za a min Chemotheraphy da radiation farkon wannan watan amma na ce a ɗaga" "Miyasa?" Mommy ta faɗa cike da alhini. "Na yiwa Zaytoon alƙawarin zan kawota gida kuma za ayi bikin Muhsina. Lokacin biki lokaci ne da 'yan uwa ke haɗuwa, ba na so na missing ganin 'yan uwan Baba na" "Ya Allah! Zuhayr ai lafiyar ka tafi komai mahimmanci" Ya gyaɗa kai ya ce "hakane, sai dai na zaɓi zuwa nan ɗin fiye da treatment ɗin. Idan na koma sai a fara ba matsala ba ne. Ina roƙon alfarma ɗaya a wajen ki" Ya gyara zaman sa sosai ya kalli Mommy ya ce " a lokacin da ba ni da ƙarfin da zan supporting Zaytoonah, Dan Allah ki daure ki dinga kiranta kullum kina ƙarfafa ma ta gwiwa"... Ba su kwana a Ringim ba kamar yadda su ka tsara da. Kwana biyu za su yi amma Mommy ta cewa Zaytoonah ka da su kwana su je a ranan su dawo a ranan. Da ta tambayi dalili cewa ta yi dan kar su ɗaurawa 'yan gidan hidima. Duk da family ɗin su T J yanzu ya zama ɓangarenci hakan bai hana an tarbesu da kyau ba. Ba ma kamar Goggo wacce da ta ga Zaytoonan sai da ta zubda ƙwalla saboda tunowa da ta yi da Tijjani. Abinda ya faru tsakanin Maryam da Muntari da kuma abinda Rabi'u ke yi da dukiyar Muntari duk shi ya sa Family ɗin ya rarrabu, kowa da ɓangaren da ya kama. Wasu ma su kwaɗayi sun rufawa Rabi'u baya, wasu ma su kishin Ahalin Modibbo na ɗaura laifin abinda ya faru ga Maryam da kuma gaba da Rabi'u, wasu kuma na ganin tun farko an zalinci Maryam musamman bayan ɓatar T J. A hanyar su ta dawowa ne Ben ya kira Zuhayr. Hankali a tashe ya ke ma sa magana saboda abinda ya gano a gidan su. "Miyasa ba ka gayamin ba?" Ya sake maimaitawa jin Zuhayr yayi shiru. Ba ya son yai maganan da zai sa Zaytoonah ta gane tunda sun yi magana da Mommy akan za ta gaya ma ta idan sun dawo. "Ka yi haƙuri" ya furta a hankali yana kallon Zaytoonah da ta baza ido da kunne tana sauraron wayan na su. "Na kusa dawowa, za mu yi maganar idan na dawo" ya faɗa tareda kashe wayar. "Shi wannan Ben ɗin ba zai bar ka ka huta ba ne. Bini bini ya kiraka" "Laifi ne idan mutum ya nemi jin lafiyar ɗanuwan sa?" "Ba laifi ba ne amma shi wannan na sa nacin yayi yawa kullum sai ya kiraka fa sai ka ce mata da miji" "Baby yaushe za ki bar kishi da Zubayr ne?" Yai maganar yana riƙe hannunta. Ta kwantar da kanta a kafaɗun sa ta ce "Ranan da ya dena bibiyar rayuwar mu"... Yau saura kwana biyu su koma America. Tana taya Mommy girki a kitchen suna ɗan taɓa hira Mommy ta ce "Adaeze are you happy with Zuhayr" For the first time sai ta ji kunyar Mommyn. Ta sunkuyar da kai tana murmushi. "Kina son kwanciyar hankali da lafiyar shi ko" Ta yi saurin rufe ido tana murmushi. "Mu je falo na baki wani labari" Kusa da kusa su ka zauna yayinda Zaytoonah ke wani sunne kai wai kunya. Wai yanzu fa duk abinda su ke da Zuhayr Mommy ta sani tunda ta hanyar hakan aka sameta. "Kinga girma ya kamaki tunda gashi nan da wasu watanni za ki zama UWA, dan haka ina so ki nitsu ki saurareni da kyau. Kin ga a duniyar nan babu abinda ya kai addu'a da haƙuri daɗi. Yadda su ke da daɗi haka kuma su ke da wahalar yi. Kinga haƙuri da addu'a shiya kawomu rana ita yau. ba dan wannan ba bana tunanin za ma ki zo duniya balle ƙannen ki su biyo baya. Mijin ki na buƙatar wannan abu biyu daga gareki kuma na tabbata idan ki ka bashi wannan za ku samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ki yi haƙuri da rashin lafiyar Zuhayr ki kuma dage da yi ma sa addu'a har Allah ya sa ya samu ya warke gaba ɗaya" Zaytoonah ta kalli Mommy da mamaki "Zuhayr ya gayamin yana da Leukemia. Idan kun koma za a fara ma sa treatment ina roƙo dan Allah ki ma sa abu biyun nan. Idan kika tada hankalin ki ko kika dinga kuka ba zai kwantar da hankalin sa ba shima, haka nan ba zai sa ya samu lafiya ba. Ki tayashi da addu'a sosai ki kuma dinga tawakkali da abinda Allah ya ɗaura ma sa har Allah ya kawo ma sa sauƙin sa" Kukan da ta ke yi ne ya sa Mommy rungumeta tana cigaba da yi ma ta nasiha. 2/11/21, 10:04 PM - ****: 33 Bismillahir Rahmanir Rahim *family* Kusan ƙarfe ukun dare ya tashi saboda zafi da ya sa shi a gaba, jikin sa duk zufa. Duk da yanayin sanyi da ake ciki hakan bai hana shi jin zafi ba, da zai kwanta ma da ruwan sanyi yai wanka. Ya kalli Zaytoonah da ke bacci cikin kwanciyar hankali, yai murmushi da ya tuno cika bakin da ta yi jiya wai dole za ta je gidan su ta ga Mommyn ta. Tana fitowa daga wanka da ta bi lafiyar gado ko minti biyar ba ta yi ba bacci ya tafi da ita. Ya shiga banɗaki ya tari ruwa yai wanka dan shower ɗin ba ya yi. Da ya fito zama yai a bakin gado yai tagumi yana nazarin rayuwar sa. Yana da kuɗi, ko yau ya dena aiki yanada abinda zai isheshi har ya ƙare rayuwar sa. Kuɗi ba su ne matsalar sa ba yanzu samun lafiya ce damuwar sa. Idan har sun koma zai gayawa Zaytoonah ciwon sa dan ko ya cigaba da ɓoye ma ta ma za ta gane tunda treatment ɗin zai ɗau lokaci. Yana fata a gama komai lafiya saboda ya samu damar sake tsarin rayuwar sa. Yayinda ya ɗau shekaru yana rayuwa domin kuɗi yanzu yana so ya rayu ne rayuwa mai inganci, rayuwar da zai tallafawa mutane ya kuma inganta rayuwar wa su. Kusan har Asuba bai samu ya kuma yin bacci ba daga baya ma Alwala yai ya kama yin nafila... Zaytoonah da ke maganar ƙarfe shida tana gidan su sai gashi ƙarfe shidan ma ba ta tashi daga bacci ba. "Baby ƙarfe bakwai saura ki tashi ki yi sallah" ya faɗa yana shafa kumatunta. Ta ɗan muskuta gefe tana faɗin "i want to sleep" "Ki yi sallah sai ki koma ki kwanta kin ji" Sai da ta ƙara kusan minti biyu tana mutsu-mutsu akan gado kafin daga baya ta tashi zaune. Ta mitsitstsika idonta kafin ta ce "ƙarfe nawa?" "6:39am" "Ya Allah! Shine ba ka tasheni ba" "Na nawa kenan?" Ta tashi daga kan gadon tana faɗin "ni dai ba ka tasheni ba, da ka tasheni ai zan tashi" "Ok, Sorry. Next time ruwan sanyi zan watsa miki" "Da kuwa ka kwana a station" ta faɗa tana shigewa banɗaki... Duk yadda ta so ta tafi ya hanata cewa yai yayi wuri da yawa. Breakfast da aka kawo mu su ma ba iya ci tayi ba, tea kawai ta sha dan ta ce a gidan Mommy za ta karya. Ganin yadda ta ke haɗa kayanta ya sa shi tambayar inda za ta kai su. "Gidan mu mana" "A gidan ku za ki dinga kwana?" "Sosai ma, rabona da su tun yaushe. I really miss them" "Ok ni ma ki haɗa da nawa kayan a chan zan kwana" Ta ɗago ido ta kalleshi da mamaki. "Yeah, a chan zan kwana nima" "Kai ba ka jin kunyan surukai ne za ka kwana a gidan mu?" Ya kwaikwayi maganarta ya ce "Ke ba kya kunyan mijin ki ne za ki gudu ki barshi shi ɗaya?" Fashewa ta yi da dariya tareda matsowa kusa da shi tana faɗin "my D abin na ka har da sharri ne. Yaushe na ce zan gudu?" "Gashi kin gama haɗa kayan ki" "Gidan mu ne fa, ba nisa ma da nan gidan" Ta ɗan yi murmushi ta ce " Allah Sarki! kamar ba mu yi sintirin zuwa karɓan sadaka a nan gidan ba. Lokacin muna yara duk Jummu'a da an dawo daga masallaci za mu zo karɓan sadaka a wajen Alhaji" Ya rungumota jikin sa ya ce "yanzu ma ba ta ɓaci ba barin baki sadaka" "Ban yadda ba, ɓata min kwalliya za ka yi" "To bari na ɗan sha janbakin kaɗan" "Nop" "Kaɗan fa" "Nooooo" " a taimaka" Ta kai baki dan ta ma sa light kiss sai shikuma ya riƙe bakin bai saketa ba sai da ya shanye janbakin tas. Dama karanbani ya sa ta shafawa wai dan yai matching da jan Arabian gown da ta saka... Ƙarfe goma da kwata su ka fito daga gidan Alhaji Iliyasu Mai Auduga su ka nufi gidan su Zaytoonah. Suna tafiya tana ma sa bayanin gidajen da su ke maƙotan su, ya so su ɗau mota amma ta ce ba nisa dan haka ya fasa karɓo key ɗin. Sai kuma da su ka iso gidan ya tabbatar ba nisa ɗin. Lokacin da ta nuna ma sa gidan da Daddynta ya gina sai ya ga ai ya fi wanda za su shiga girma. "Miyasa ku ke zaune a nan? na ga kamar wancan gidan ya fi girma" Zaytoonah ta ce "Hmmm, Mommy ba ta son barin nan. Ta ce akwai memories ɗin Daddy a gidan kuma wai duk ranan da Daddy ya dawo gidan zai fara zuwa duba su. Har yanzu tanada yaƙinin zai dawo" Ya kalleta dai dai sun isa ƙofar gidan ya ce " ke fa kin yarda zai dawo?" "A duk inda ya ke ina ma sa addu'a Allah ya jiƙan sa ya kuma yi ma sa rahama" ta yi maganar tana buɗe ƙofar falon gidan da sauri dan ba ta son Zuhayr ya ga hawayen da ya ke shirin zubo ma ta. "Assalamu Alaikum Jama'an gida" ta faɗa da ƙarfi bayan ta goge idonta da bayan hannu. "Ina kuka shiga ne, gamu mun faso fa" Ta wuce kitchen tana leƙawa ko Mommy na ciki amma ba ta nan. "Ko ina 'yan gidan su ka je su ka bar ƙofa a buɗe" ta faɗa tana ƙarisawa ɗakin su Salman. Ba kowa a ciki dan haka ta wuce ɗakinta a nan ta buɗe baki saboda ganin Salman da ta yi yana kwance a kan gadon ta, da alama ma nan ne ɗakin sa yanzu. "Kai-kai, Salman" Salman yai firgigit ya buɗe ido. Kamar a mafarki sai kuma ya ga Zaytoonah tsaye a kan sa. "Adaeze ke ce?" "Shine ku ka bar gida a buɗe, tukunna ma wa ya baka izinin dawowa ɗakina?" "Ba ɗan welcoming hug ɗin nan, daga zuwa za ki hau ni da faɗa" ya faɗa da muryarsa a dashe. Ta ɗan ranƙwashi kan sa ta ce "ka rena ni fa" sai kuma ta rungume shi tana faɗin "i miss you Bro" Ya ce "i miss you too Sis" Lokacin da ya tashi daga gadon ne ta ke tambayar sa ina Mommy ta je sai ya ce wai Iya ce ba lafiya tana gudawa tun tsakar dare shine da Asuba Anty Hanne ta kira ta faɗa ma ta to sai Mommyn ta je da mota ta kaita Asibiti. "Shine tuntuni ba ta dawo ba" Zaytoonah ta faɗa tana tsuke fiska. "Inaga ta dawo ƙila suna gidan ne" "Wai ina Junior ne?" "Baya gida ko? Ja'iri, yanzu haka gidan su Kamal ya tafi. Maganin mura fa na sha na kwanta na barshi yana kallo a falo kafin na shigo ɗaki, ashe fita yai" "Zo mu je ka gaida mijina" ta faɗa cike da burga. Salman na fitowa ya miƙa ma Zuhayr da ke zaune hannu yana faɗin "ashe dai kafi hoto kyau" Zuhayr yai murmushi yana tambayar sa ya gari. Zama su ka yi gefe da gefe Salman na cika Zuhayr da surutu har da cewa dole sai yayi ma sa Hausa dan da turanci su ke magana. Zuhayr ya ce yana ji amma bai iya mayarwa sosai. Zaytoonah ta koma kitchen dan ta nemi abunda za ta sa a baka kafin Mommy ta dawo ta ma ta girki. Aikuwa tana duba fridge ta ga dambun kaza da Mommyn ta yi ta ajiye a glass jar. Ta fito da jar ɗin ta zuba kusan fiye da rabin dambun a plate ta fito ɗauke da hollandia a hannu. Ta zauna gefen Zuhayr tana ci tana sa baki cikin zancen su jefi-jefi. A nan ta ke jin wai Auwal ya tafi Ringim jiya saboda yau ake auren wani cousin ɗin su wanda su ke sa'anni da Auwal ɗin. Kusan minti shabiyar da zuwan su sai ga horn ɗin motar Mommy. Zaytoonah ta miƙe da sauri ta yi waje da gudu. Salman da Zuhayr su ka bi ta da ido. "Adaeze yi a hankali kar ki karya ni" Mommy ta faɗa lokacin da runguman ya ƙi ƙarewa. "Ni dai Mommy ki ce kawai ba ki missing ɗina ba" "Yi a hankali kin san ba ke ɗaya ba ce" Ta fara buga ƙafa tana faɗin "ni dai ni ɗaya ce" Mommy ta zuba ma ta ido tana murmushi ganin yadda 'yartata tayi fresh ta yi kyau. Alamun jin daɗi da kwanciyar hankali duk yana tattare da ita. Suna shigowa falon Mommy ta ci karo da Zuhayr ba ta ma ɗauka tare su ke ba. Da murmushi a fiskar sa ya gaisheta yana tambayarta ya me jiki dan Salman ya faɗa ma sa inda ta je. Ta ce ma sa da sauƙi an ma sallamota, dama ruwan da aka ɗaura ma ta ne ya sa su ka jima. "Mommy da gaske wai gudawa Iya ke yi?" Ta yi maganar tana ƙyalƙyalewa da dariya Mommy ta ma ta daƙuwa. "Na so na ga idanun tsohuwar nan tana sintirin banɗaki" "Zaytoonah!" "Sorry Mommy" ta faɗa tana dariya ƙasa-ƙasa. Tare su ka shiga kitchen inda Mommy ta gasa mu su plantain a oven (wanda ake cewa Boli a yoruba) tarega veggie egg sauce. Zuhayr kam kaɗan ya ci bayan Zaytoonah ta takura shi akan dole sai ya ci. Suna cikin ci ne sai ga Junior ya shigo gidan jikin nan duk butu-butu da yashi. Mommy na ɗaki dan ta ba su waje su ci abinci. Yana zuwa ya fara zare ido ganin Salman dan ya ja ma sa kunne akan kar ya yadda ya fita kafin yai bacci. "Zo nan ina ka je?" Salman ya faɗa cikin tsawa. "Bar min boy ɗina da Allah, kai ma haka ka ke fita yawo lokacin kana kamar sa" Junior ganin Zaytoonah sai ya sa ihu ya je wajenta. Duk da dai lokacin da ta tafi bai kai haka wayo ba amma da ke su kan yi video call shiyasa bai manta da ita ba... Kusan awa biyu su ka yi a gidan kafin Zuhayr ya ce zai tafi. Zaytoonah kam dama ba wai ta zo dan ta tafi ba ne amma sai Mommy ta ce mi zai hana su je su gaida Iya. Ai tana maganar ta ce "ai ko dan gulma zan je na ganta" Da za su fita Mommy ta ce "Zaytoonah banda rashin kunya please" Zaytoonah ta amsa da to amma chan zuciyarta ta san indai ta yi ido huɗu da tsohuwar nan sai ta yi dariya. Tareda Junior su ka tafi wanda ya dage sai ya bisu. Da ke an ma sa wanka sai Mommy ba ta hana su ba. Suna tafiya 'yan tsilla tsillan mutane da ke wucewa sai kallon su suke ganin wannan Farin baturen da wannan matar, wanda ba su san Zaytoonah ba kallon budurwar baturen su ke ma ta ko na ce budurwar shan minti tunda ba wai sun yarda da soyayyar bature da baƙar fata ba ne. Kafin su isa gidan gumi duk ya gama rufe Zuhayr, duk da akwai ɗan tazara tsakanin gidajen amma yadda ya ke zufa ka ɗauka sun yi awa ɗaya ne suna tafiya, kuma garin ba zafin rana. Maigadin da Zaytoonah ta sani tunda shi ɗin ne har yanzu dan haka yana ganin ita ne ya buɗe mu su ƙofa. Ta yi mamakin yadda ta ga wajen ajiye motoci wayam ba mota ko ɗaya. Haka dai su ka shiga gidan hannun su sarƙe cikin na juna. Baby Maryam su ka samu a falo tana wasa. "Baby ina Maman ki" "Tana wajen Iya" ta faɗa tana cigaba da yiwa 'yar dadarta kitso. "Je ki kira ta kin ji" Yarinyar sai da ta ɗan zauna na ɗan wasu daƙiƙu kafin ta tashi ta wuce ciki. Zaytoonah na zaune tana kallon yadda gidan ya ɗaiɗaice kamar ba falon gidan Alhaji Muntari ba. Minti ɗaya da fitowar yarinyar sai ga Anty Hanne ta fito. "Lalala, Zaytoonah ke ce a gari, saukar yaushe?" "Jiya da dare" "Gaskiya kun sha hanya kam, barin kawo mu ku ruwa" ta miƙe tun ma kafin Zaytoonah ta ba ta amsa. Bayan ta kawo mu su ruwan ne Zaytoonah ta tambayi jikin Iya. Anty Hanne ta ce "tana ciki ai, tsohuwa da shegen karambani. Wai jiya da dare ne fa Saurayin Humairah ya kawo ma ta shawarma shine Iyan ta ci, da tsakar dare kuma cikin ya tsure sai gudawa" Tun kan ta kai ƙarshen labarin Zaytoonah ta shiga ƙaƙata dariya, dariya sosai har da hawaye. Ba abinda ta ke hangowa sai Iya na zaune tana cin shawarma. Anty Hanne ta ƙara da cewa "kinganta ne da ta ke ci, ta dinga lasar mayonnaise da cream da ke jiki wai romo-romon ya ma ta daɗi. Allah ba dan dai Anty Maryam ta zo ba da ba abinda zan ma ta dan nima fama na ke da kaina" Dariyan Zaytoonah ne ya tada Humairah daga bacci ta fito daga ɗaki tana haɗe rai dan ta ga uban waye ya shigo mu su gida ya hanata bacci da ranan Allah. Turus ta tsaya lokacin da ta hango Zaytoonah jikin Zuhayr tana dariya. "My D ka tuna lokacin da na fara cin Lasagna nima ya sa ni gudawa" ta yi maganar tana kallon Zuhayr hannunta akan cinyarsa tana dariya. Gyaɗa ma ta kai yai ya ƙaƙaro murmushin dole dan shi kaɗai ya san mi ya ke ji a jikinsa amma baya son nunawa kar ta damu. Ba dai wannan Zaytoonah ta aura ba. Irin mijin Novel, Mijin film. Ita duk da ake cewa Zaytoonah ta auri jikan Alhaji Iliyasu ba ta ɗauka bature ba ne kamar wannan ta ɗauka baƙin fata ne ƙila ma irin watsatstsun samarin da ke zaman ƙasar waje, amma wannan, wannan. Ta koma ɗakinta ba tareda ta ƙarisa wajen su ba. Kishin 'yar uwartata ya ɗarsu a ranta. Zaytoonah fa? Zaytoonah ɓukuta ita ke da haɗaɗɗe miji irin wannan... Lokacin da Zaytoonah ta leƙa ɗakin Iya ta riga ta yi bacci dan haka su ka tafi tareda alƙawarin za ta dawo ta sake dubata. Zuhayr gidan su ya wuce ita kuma Zaytoonah ta wuce gidan Mommy. Da ta je ta ke tambayar Mommy ya ta ga gidan Uncle Muntari ya zama dry haka. Mommy ta ce ma ta ai gidan ne kawai yanzu amma ba su da wani abu kuma. Alhaji Rabi'u ya tattare komai na amfani, motocin gidan ma duk ya tattare. Yanzu haka idan ka cire maigadi ba wani mai aiki a gidan. Zaytoonah ta ce Allah ya sawwaƙa. Da gaske dagewa ta yi akan sai ta kwana a gidan su amma ƙarfe takwas na yi Mommy ta fatattaketa dole sai da ta koma wajen mijinta wanda tun bayan dawowan sa gida ya ke kwance da zazzaɓi... Tambaya: -Kin taɓa ganin mata da miji ko budurwa da saurayi wanda macen ke da ƙiba shi kuma namijin siriri? -Miya fara zuwa miki rai da ki ka gan su? -Faɗi gaskiya, kin yi mamakin ya akayi su ke tare ko?😀 - miyasa ake yawan ganin kamar idan mace na da ƙiba to dole sai dai namiji mai ƙiba za ta yi tarayya da shi, idan aka ganta da siriri sai a dinga ganin kaman ba su dace ba? 2/11/21, 10:04 PM - ****: 36 Bismillahir Rahmanir Rahim *bulletproof* Tun daga nesa su ke jin siren ɗin motar police kafin su ka hango motocin su kusan huɗu a hanya, ga motar ambulance, fire service da ta 'yan jaridu. "Innalillahi mi ya ke faruwa" Zaytoonah tai maganar tana dafa ƙirji "Inaga accident ne amma bari mu ƙarisa" Chan gefe Alinah ta yi parking motar ta sannan su ka fito. Zaytoonah kam addu'a ta ke a ranta Allah ya sa motar ta na lafiya. A hankali su ka ƙarisa wajen inda aka zagaye da caution ribbon. Wani ɗan jarida da ya hango Zaytoonah ya kuma gameta a matsayin matar Zuhayr yai saurin zuwa wajen su. "Mrs Ilyas miyasa ba ki biyo dreban ki ba?, kina ina lokacin da motar ta bombing? Ko za ki gaya mana..." Ita maganganunsa ma ba saurara ta ke ba neman mijinta ta ke yi. Farha ce ta kama hannunta ta nuna ma ta inda Zuhayr ke tsaya shi da Ben yayinda wani police ke mu su bayani. "Ba ma tunanin matar ka na motar nan Mr Ilyas, domin ko da ace lokacin da Bomb ɗin ya tashi ta yi tsalle ne to kuwa za a ganta kusa da wajen nan amma an bincika babu..." "*D*" ta faɗi da ƙarfi kafin ta ƙariso wajen da gudu. Tunda ambulance su ka zo wajen aka ciro gawan Dreba amma ba a ga na Zaytoonah ba jikinsa yai sanyi amma ya daure dan yana tunanin ƙila gangan jikinta yayi tsalle ne ya faɗa wani waje sai dai KASH! ga Zaytoonah nan a gaban sa tana nan da rai da lafiya. Tana rungume shi ta sa kuka. Ɗago fiskarta yai ya manna ma ta kiss. "Alhamdulillah, Alhamdulillah" ya furta lokacin da ya sake ma ta baki. "D miya faru?, waye yai hatsari?" "Alhamdulillah kawai Baby, Allah ya nuna mana izzar sa sai dai kawai mu godewa Allah"... Ranan har sai da dare yai nisa kafin police da sauran ma su bincike su ka bar wajen. Dreban ta Mr Dawson kam tashin Bomb ɗin kam ya kashe shi, mutuwa mai muni kuwa dan duk jikinsa ya ƙone hannunsa ɗaya da be ƙone ba kuma a chan gefen titi aka tsinta. Tambayoyi kam sun sha shi ita da Zuhayr. Tsayuwan da Zuhayr yai dayawa a wajen da kuma hayaƙi da ya shaƙa ya sa shi faɗuwa a wajen ya suma lokacin da ya ke amsa tambayoyin police hakan ya sa aka wuce da shi cikin gidan sa da sauri bayan Medical team da ke wajen sun ma sa taimakon gaggawa ya farfaɗo. "D dan Allah kar ka sake haka ka ji wallahi saura kaɗan zuciyata ta buga" lokacin da wanda su ka kawoshi su ka bar ɗakin ya zama daga ita sai shi. "Ki yi haƙuri, gajiya ce kawai ba komai ba" "Ina tsoro, D Ina tsoro. Wannan bomb ɗin kamar saboda ni aka saka" "Ki dena jin tsoro, addu'a za mu yi Allah ya cigaba da karemu. Na miki alkawarin indai ina raye zan yi ƙoƙatin kare lafiyar ki. Koma wanene ya aikata wannan abu sai na sa an nemo shi Insha Allah" Baccin kirki Zaytoonah ba ta iya yi ba, da ta ɗan kwanta sai ta farka. Ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba kenan ake ƙoƙarin kasheta. Ta tuna lokacin da su ka je Finland aka turata cikin ƙanƙara, ga lokacin da aka turota daga stairs, ga hatsarin da su ka yi inda Drebanta Mr Smith ya tsira da rayuwar sa da ƙyar, yanzu kuma wannan. Ba dan ta bi Farha ba da shikenan itakam sai dai wata kuma ba ita ba. Ganin Zuhayr shima ya kasa baccin saboda ita ne ya sa ta daure ta rufe idonta kawai tana kwance jikinsa tana addu'ar Allah ya tona asirin koma wanene ke neman hallakata. Washegari ma an zo duba wajen da abin ya faru ciki kuwa harda cikin gidan su inda Bomb expert da su ka zo su ke bin lungu da saƙo na gidan da na'ura suna aunawa. Cikin tambayoyin da aka yiwa Zaytoonah ne aka tambayeta ko tana zargin wani ko wata da aikata laifin abinda ya faru dan suna da tabbacin harin a ita aka yi niyya ba Dreban ta ba. Zaytoonah ta ce a'a. A kwana na uku da abin ya faru ne aka fitar da jawabi cewa daga gidan Zuhayr aka kunna Bomb ɗin har ta tashi dan sun yi tracing signal ɗin kuma sun gano iya tsawon kilometer ɗin transmitter da receiver ɗin ya fara ne daga gidan Zuhayr ya tsaya a daidai inda motar ta tashi. Wannan ya sa duk wani wanda ya ke gidan lokacin da abin ya faru aka tafi da su station su ka je dan amsa muhimman tambayoyi. Zuhayr kam a gida aka ma sa tambayoyin wanda duk kusan tambayoyine da an ma sa tun ranan farko. Ba dan formalities ba ne da ba zai saurare su ba. Tunda Zaytoonah ta sanar da Mommy abinda ya faru ta shiga yi ma ta addu'a harda ɗaukan Azumi na kwana uku, a rana ta uku ta yi abincin sadaka aka rabawa Almajirai. Itama Zaytoonan ta yi Azumin kwana ɗaya, ta so ta yi na kwana uku ko bakwai amma Zuhayr ya hanata wai baya son ta wahalar ma sa da Babyn sa. A wannan lokacin kam gidan na su kusan kullum baya rabuwa da ziyarar police dan neman bayani ko bincike amma har aka yi sati babu wani gamsashahiyar bayani kan wanda ya ɗaura Bomb a motar ko kuma ya kunnata. Sun gano wacce iriyar Bomb ne aka sa a motar hakan ya sa su ka fara bincikar inda aka sayi irin Bomb ɗin nan cikin kwanakin nan musamman ma saboda Bomb ɗin a sojoji kawai ake siyarwa. Da Ben da sauran ma su aiki a gidan duk suna cikin suspects na abinda ya faru. Kwana goma da mutuwar Mr Dawson aka bisine shi, Zuhayr da Zaytoonah sun kai wa iyalen sa ta'aziya inda Zuhayr ya bawa matar sa check ɗin maƙudan kuɗi. Yaran sa biyu, macen Hannah tana Jami'a a Cincinnati sai namijin Kevin ɗan shekara shatakwas da ya bar gida yana garari a gari, dan high school dropout ne. Zuhayr kam ba ƙaramin kuɗi ya fitar ba wajen ganin an tafiyar da binciken cikin sauri. Ga uwa uba securities da ya ƙara a gidan na su da kuma na'urori da aka siya na kariya. Sai da aka yi sati da abin kafin Zaytoonah ta koma school tareda bodyguards guda biyu da Zuhayr ya haɗata da su, motar da za a dinga kaita makaranta ma bulletproof ce. Kafin ta shiga ciki ma sai an scanning motar an tabbatar da babu komai kafin a fara tuƙi. Wani ƙwararren ɗan bincike tsohon ma'aikacin FBI Mr Rogers wanda yai tashe a zamanin sa Zuhayr ya sa Ben ya nemo ma sa. Mr Rogers ya jima da retire amma lokaci zuwa lokaci idan aka neme shi for private investigation yana yi musamman idan ya ji kuɗi. "Ko nawa ne zan biya, ka ce ma sa ya zo muna buƙatar taimakon sa" abinda Zuhayr ya faɗawa Ben kenan amma Ben bai ma kira Mr Rogers ba balle su yi maganan kuɗi. Ben ya cewa Zuhayr ya kirashi assistant ɗin sa ta ce yana asibiti yana jinya. Zuhayr bai ji daɗi ba dan Mr Rogers fitacce ne a ƙasar America gaba ɗaya. Ben ya ma sa alƙawarin zai samu wani PI ɗin wanda ya ke da ƙwazo... Satin ƙarshe kenan na chemo ɗin Zuhayr kuma akwai improvement sosai, za a observing na shi na kwana goma kafin a ga ko za a ma sa Radiation ko kuma dai Chemotheraphy ɗin ya wadatar idan cancerous cells ɗin sun mutu gaba ɗaya... "Wai ina za ka je ne?" Ta tambaya lokacin da ta ga yana shiri cikin baƙin toxedo. Rabon da ya saka suit ma tun kafin su tafi Nigeria. "Zan je hira, kin san na yi sabuwar budurwa" "Budurwa?" "Yes Baby girl. Za ma ki santa ai, dan kullum tana zuwa gidan nan" Tunaninta ne ya ba ta ƙila nurse ɗin da ke zuwa duba shi ne. Sai yanzu ta lura da yadda nurse ɗin ke cika fiska da kwalliya idan za ta zo. Cikin fushi ta tashi daga kan gadon ta yi hanyar ƙofa. Gwiwar hannunta ya kamo ya jawota jikin sa yana faɗin "ina zuwa da sauri haka?" "Ni na hanaka tafiya hiran ka ne? Ina ruwan ka da inda zan je" ta yi maganar kamar za ta yi kuka. Ya gimtse dariyan sa dan ya san kishi ta ke ya ce "to tsaya na nuna miki hoton budurwar tawa" "Ba zan tsaya ba, ni ka sake ni" ta fara ƙoƙarin ƙwace kan ta. "Dan Allah ki tsaya ki ganta, just 2 seconds ya isa" Yana ciro wayarsa sai ga hawaye ya fara zubowa a idonta. Lokacin da ya ɗaukesu selfie ma ba ta lura ba saboda idonta da ya cika fal da hawaye. Ta yi saurin goge idon tana kallon wayar da ya ke nuna ma ta. "Ki ganta dan Allah wai kishina ta ke" Ganin hoton su tare ya sa ta ji ranta yayi sanyi. Sai kuma ta tura baki ta ce "ni ban ga kowa ba. Ina budurwar ta ke?" Ya sunkuyar da kan sa zuwa wuyanta ya kissing wuyan sannan ya ce "ga ta nan sai kumbura fiska ta ke tin ɗazu" "Ni ban kumbura fiska ba" Ya sa yatsar sa ɗaya ya lotsa dimple ɗinta ya ce "kina kyau idan kin yi ballon face ɗin nan" "Ba wani, kai da har dariya kake min idan na yi, irin na yi muni ɗin nan" "Haba, you always look cute ai" "Ba wani" "Ɗan sake kumbura fiskan na gani" "Anƙi ɗin" Cakulkuli ya shiga yi ma ta yana faɗin dole sai ta yi ita kuwa sai dariya ta ke tana faɗin No No... *** Bai gaya ma ta inda za su je ba ya dai ce ta sa kayanta mai kyau. Da ya ke ta ga shima ya saka kaya kamar mai zuwa wani event sai itama ta saka baƙin dinner gown mai kyau. Tare su ka fito hannun su sarƙe cikin na juna. Kai tsaye wajen da helicopter ɗin sa ke jiran su suka je, suna shiga Dreba ya tashi da su. "D wai ina zamu je ne?" "Na gaya miki surprise ne" Wani katafaren resort su ka je. Daga inda helicopter ya sauke su akwai mota da ke jiran su. Suna shiga tafiyar minti biyar ta isar da su bakin resort ɗin. Wani baƙin bature ne ya mu su jagora har wajen da Zuhayr ya mu su reservation. Already an riga an shirya komai irin na romantic dinner ɗin nan. Duk da ta ga kamar ɓarnar kuɗi yai da kama mu su wajen da yai amma duk da haka ta amince wajen ya burgeta sosai. Bayan sun ci abinci sannan su ka wuce honeymoon suit ɗin su. Ɗakin yana da girma kuma an ƙawata shi da ado na flowers. Babban box da ke kan gado ne ya tsole ma ta ido, da sauri ta je wajen ta ɗau box ɗin ta fara buɗe shi. "D miye aciki?, Laptop ne?" Bai ce komai ba sai murmushi da ya ke yi. "Camera?" Ta faɗi lokacin da ta buɗe. A hankali ya tako zuwa wajenta ya ƙarɓi camera ɗin ya ce "ina so mu dinga ɗaukar muhimman ranaku na rayuwar mu, saboda tarihi ko ya?" Ta gyaɗa ma sa kai tana murmushi. Tana ƙoƙarin kunna camera ɗin ta ga ya miƙo ma ta wani ƙaramin ring box baƙi. "Happy birthday my Angel wife" "Ya Allah! abinda ya riga ya wuce" "Bai wuce ba tunda ban tayaki murna ba" Zoben diamond ne a cikin box ɗin lokacin da ta buɗe shi, sai ƙyalli ya ke yi. "Thank you Darling" ta faɗi gameda kissing kumatun sa. Sati biyu da su ka wuce ta cika shekaru shatakwas a duniya, to abu uwan da su ka faru sun hana ma ta tuna balle ta yi wani abu. Ita ba da Mommy ta kirata ba ranan da kuma text ɗin Salman da na Auwal da ta gani da ba abinda zai sa ta tuna da wani birthday ɗin ta. Ofcourse sai da Zuhayr ya Angonce da Amaryar sa dan ya nuna ma ta fa rashin lafiyar sa bai hana engine ɗin sa aiki ba domin body ɗin ne mai jinya shi engine garau ya ke. Mamakinta bai ƙare ba sai da dare da ya ce su sake shiryawa saboda akwai birthday party da ya haɗa ma ta. Ita ba ta so ba dan with all that is happening she's in no mood for any party. Sai dai ya za ta yi tunda ya riga ya haɗa komai ba tareda ya shawarceta ba. Ta ɗauka mutane kaɗan ne ya gayyata ashe gari guda ne. Ma'aikatan sa na Kamfani dama na gidan su duk sun zo, sai tsirarun abokanan sa, hatta Farha ta zo. Mr Ben ma ba a barshi a baya ba shima ya zo wajen dan duk wani shirye-shirye na party ɗin shi yai tunda Zuhayr dai sai dai ya ce yana son kaza shi kuma zai kira ya tabbatar anyi hakan. A chan bayan resort ɗin ake party ɗin. Inda aka ƙayata shi na musamman saboda wannan party. Yadda wajen ya ke da haske tarau ka ce da rana ake ba da dare ba. 'Yan jarida ma sun zo sakamakon wannan ne fitowar farko da Zuhayr zai yi wajen taro tunda ya fara chemotherapy treatment. Ya sha tambayoyi kam shi da Zaytoonah musamman saboda recent attack ɗin da aka kaiwa Zaytoonah wanda ya faɗa kan Dreban ta. Ofcourse an kewaye wajen da securities dan kafin ka shiga wajen sai kana da kati, katin ma sai an duba da na'ura an tabbatar cewa na gaskiya ne ba na bogi ba, hakan ma kuma sai an duba ka da na'ura kafin ka wuce. Party ɗin dai yana tafiya lafiya domin har an yanka cake. Zuhayr ya bawa Zaytoonah a baki itama ta bashi a baki, aka sa tafi. Yanzu haka ma rawa su ke yi ita da Zuhayr ɗin, ba rawa ne na jijjiga jiki ba dan waƙar irin mai sanyi ɗin nan aka saka. "Ki shirya anjima idan an tashi dan ban ƙoshi ba" ya raɗa ma ta a kunne "Sai dai idan Allah ya kaimu gobe ka samu ɗumame" ta amsa ma sa tana murmushi. "Kafin gobe bawan Allah ya jigata ai" "Ka san yadda ɗumame ke da daɗi kuwa" "Bari mu ga dai ko zan iya haƙura" ya faɗa yana juyawa da ita... Daga kan bishiya da ya ke tun ɗazu yana ƙoƙarin saita Zaytoonah da bindiga, duk da nisan da ke tsakaninsa da inda ake party ɗin hakan bai hanashi hangota ba da kuma saita ta a matsayin target. Ta ɗan ƙaramin lens daya ke leƙawa a jikin bindigar duk inda ya ga red dot a jikin Zaytoonah a nan bullet ɗin zai sauka. Tun ɗazu ya ke son yin halbin amma kuma Mijinta na tarewa, sai ya yi niyyar halbin sai Zuhayr ya tare ta ko da hannunsa ko ma ya rungume ta. Sau biyu wanda ya bashi kwangilar aikin nan yana tura ma sa text akan ya ji shiru har yanzu shi bai san aikin na su yana buƙatar nitsuwa ba. A matsayinsa na Hit man bai taɓa karɓan aiki ya missing target ɗin sa ba sai dai idan fasawa yai. Sau ɗaya ya taɓa fasa kashe target ɗin sa wanda lokacin farko-farkon fara aikin sa ne inda aka bashi kwangilar kashe wata yarinya 'yar wani minister. Yarinyar kwata-kwata shekarunta takwas ne, daga inda ya targetting ɗinta ta fito daga makaranta ita da bodyguard ɗin ta za su je su shiga mota, murmushinta ya taɓa ma sa zuciya ya ji ba zai iya kasheta ba. Daga nan indai aiki ya shafi yaro ɗan ƙasa da shekara shabiyar to ba zai karɓa ba. A lokacin da ya samu damar da ya ke ganin indai ya halbi Zaytoonah sai dai wata ba ita ba, saboda direct zuciyarta harsashin zai shiga, yai saurin sake harsashin sai dai kafin ta kai ga Zaytoonah sai ta shiga jikin mutumin da ya sa hannu yana goge ma ta icing sugar da ya gani a gefen kunnen ta. Bindiga ce da take da silencer dan haka babu ƙara sai dai kawai aji shigar harsashi jikin mutum. "Kin ma fi kyau a.." maganar da bai ƙarasa ba kenan harsashin ya shige shi ta baya. A hankali ya fara yin ƙasa-ƙasa har ya kai ƙasan gaba ɗaya. Ihu da mutane su ke yi da kuma Ben da ya zo da gudu ya rungume Zuhayr yana ƙoƙarin tada shi yana sunbatu shine abu na ƙarshe da ta iya tunawa kafin ta yanki jiki ta faɗi. Lokacin da helicopter ɗin ta sauka a bakin asibitin tuni anriga anzo da gado saboda tun kafin su iso anyi waya an sanar da su. "Dont leave me my love, dont leave me please" abinda Ben ke maimaitawa kenan lokacin da ake tura gadon zuwa cikin asibitin. Ƙoƙarin shiga ICU ya ke yi wani nurse ya tareshi hakan ya sa dole ya ja birki a bakin ƙofa zuciyar sa na bugawa da ƙarfi kamar za ta bulloƙo. Abu ɗaya ya sani shine matuƙar Zuhayr ya mutu to sai ya yanka Zaytoonah da hannun sa kafin shima ya kashe kan sa dan babu wani amfani da zai yi a duniya idan ya rasa masoyin sa. *hold on, mun kusa ganin bayan Ben fa* 2/11/21, 10:04 PM - ****: 37 Bismillahir Rahmanir Rahim *ASSALAMU ALAIKUM* *Ina ba da haƙurin jina da kuka yi shiru tsawon kwanaki dayawa, hakan ya faru saboda doguwar tafiya da na yi sannan komawa school da wasu shirye-shirye. Amma yanzu komai ya zama normal za mu cigaba Insha Allah. Wanda su ka yi ta ƙorafi su ka ga ban tanka ba Dan Allah ku yi haƙuri, Wanda su ka samu saɓani dalilin cecekuce da aka yi ina ba su haƙuri. Ba komai ne duniyan ba balle har mu dinga samun matsala a haɗuwan group. Sannan wanda ba su yi haƙuri ba kuma su ke ga ba za su iya haƙuri ba ƙofa a buɗe ta ke su min magana ta pc zan maida mu su kuɗin su Insha Allah.* *daga yau zuwa sati biyu ma su zuwa ina fatan za mu kammala labarin nan Insha Allah. Ni ma ban so aka samu akasi ba wannan karan na rashin update akai-akai* *na sani kuna da haƙƙi akai na har sai na kammala rubutun nan. Amma idan har kun min uzuri nan da lokaci kaɗan za mu gama labarin ba tareda wani matsala ba Insha Allah. Wanda su ka bani shawarwari da waɗanda su ka bibiyi lafiyata duk ina godiya kun nuna min cewa abinda ya haɗamu ya fi ƙarfin littafi domin an riga an zama 'yan uwa* *ina da yaƙinin cewa kowanne a cikin mu yanada matsalolinsa. Sometimes despite duk abinda ya ke damun mutum na rayuwa dole ka nemi abinda zai dinga ɗebe ma ka kewa saboda idan ba hakan ka yi ba sai damuwa ta saka a gaba har ya iya jawo ma ka matsala a jiki, shiyasa wani lokaci mu ke karatu ko mu yi kallo ko ma wani abin duk dan mu kauda zuciyar mu daga matsalolin da su ka sha mana kai. From December last year zuwa jiya ina fama da wata matsala wanda sai yau ɗin nan Allah ya warware min komai, na samu nasara na samu sauƙi. Under this pressure and stress na rubuta litattafai har 4 yanzu ina kan na biyar (Duk kyan namiji, Sakatariyata, Tsohuwar Soyayya, Ribar uwa sannan Chronicles of Zaytoonah). Rubutu na ɗebe min kewa shiyasa ko ina cikin damuwa ina tunani akan labari ko dai wanda na ke kan rubutawa ko kuma wanda na ke son rubutawa a gaba. Kunada haƙƙi akaina kuma Insha Allahu zan sauke hakkin ku da ke kai na. Idan har zan iya rubutu a lokacin da na ke cikin damuwa to yanzu da na samu sauƙi Insha Allah zan ƙara zage damtse ne. Until then plz ku yi haƙuri* *masu fama da matsaloli na rayuwa daban-daban ina addu'ar Allah ya yaye muku shi Amin. Sannan ina ƙara ƙarfafa mu ku gwiwa da ku ci gaba da Addu'a ku kuma dogara da Allah domin wallahi Allah shine mai yaye damuwa da matsaloli. Samun sauƙin ka zai iya ɗaukan lokaci amma kuma daga ƙarshe indai ka riƙe Allah sai ka ga kaine da nasara. Dukkan mun nan ba mu fi ƙarfin jarabtar Allah ba walau ta ɓangaren iyayen mu ne ko 'yan uwan mu ko auren mu, wajen aikin mu ne, anguwar mu ne ko ma jarabta ta faɗa kan 'ya'yan mu. Allah ya ba mu ikon cin jarrabawan mu Amin. Nagode* *arrested* Safa da marwa Ben ya ke yi a bakin ICU ɗin yana kissima abubuwa dayawa a ran sa. Shi kaɗai ya san ya yake ji a zuciyar sa gameda halin da masoyinsa ya ke ciki. Shi bai yarda da Allah ba balle ya ɗaga hannu yai addu'a. Asibitin da aka kawo Zuhayr nan aka kawo Zaytoonah, da ke ita da mota aka taho da ita shiyasa ba su yi sauri ba. Faɗuwar da ta yi ya sa jini ya tsinke ma ta. Lokacin da aka shigo da ita ƙoƙarin tsaida jinin aka fara yi kafin a cigaba da ba ta taimakon da ya kamata. A hankali ta buɗe idonta da ya ma ta nauyi. Sama sama ta ke jin muryan Farha da ke zaune gefenta. Ta ɗau kusan 30 seconds kafin komai ya fara dawo ma ta. Yunƙurin tashi ta yi amma Farha ta yi saurin riƙe ta saboda jini da aka ɗaura ma ta. "Zuhayr, ina Zuhayr" ta furta da murya mai rauni. "Yana nan, ki kwantar da hankalinki" "Ya mutu ko?" Ta faɗa hawaye na zubo ma ta "No Zaytoonah, he's very much alive" "Ki kai ni wajen shi dan Allah" Farha ta girgiza kai. Shigowar Mrs Haddish Kakar Zuhayr ɗakin ne ya sa Zaytoonah ta maida hankalinta gareta. "GrandMa, Zuhayr Zuhayr" sai kuma ta fashe da kuka. Mrs Haddish ta yi saurin ƙarasawa wajenta ta zauna bakin gadon tana ba ta haƙuri... Anyi nasarar cire bullet ɗin wanda ikon Allah ne ya sa bai kai ga zuciyar Zuhayr ba sai ya zama na gefen zuciyar ya tsaya. Bayan likitoci sun bawa Ben albishir ɗin Zuhayr yanada 65% chance na rayuwa amma duk da haka ana so ya cigaba da addu'a. Kasancewar bai jima da treatment ɗin Chemotherapy ba sai ya sa gaba ɗaya jikin sa ya ke a sake. An bawa Ben damar shiga ya duba Zuhayr briefly. Ganin yadda Zuhayr ke numfashi ta Oxygen ya ƙara karya zuciyar Ben. Ya tsugunna a wajen ya kamo hannun Ben ya sumbata ya ce "i'm sorry my love, i'm very sorry" Ya jima a wajen har sai da wata nurse ta shigo ta ce ya fita. Lokacin da ya kai bakin ƙofa juyowa yai ya kalli Zuhayr a ransa ya ce "its all her fault, but this time she wont go free"... Zaytoonah ba ta kwantar da hankalinta ba har sai da aka turata a keke zuwa ɗakin da aka kwantar da Zuhayr. Duk da ta yi wa Mrs Haddish alƙawarin ba za ta yi kuka ba amma ganin Zuhayr a wannan yanayi ya karya ma ta zuciya. Kuka sosai ta ke yi wanda ya sa hawayen da Mrs Haddish ɗin ma ke dannewa dole su ka zubo... Washegari Uncle Aliyu da iyalen sa su ka zo duba Zuhayr. A nan su ke gayawa Zaytoonah cewa su Alhaji Iliyasu ma na hanya, Visar da za ayiwa Mommy ne ma ya sa ba za su taho a ranan ba. Itakam Zaytoonah jikin da sauƙi sosai kuma babies ɗinta suna nan lafiya. Ta so a sallameta ma ta koma wajen Zuhayr amma Likita ya ce sai bayan kwana biyu idan ta samu ƙarfin jiki sosai. Ben ko damuwa da halin da Zaytoonah ta ke bai yi ba, ko leƙa ɗakin da aka kwantar da ita bai yi ba balle ya sa ran zai gaisheta, duk da yana sane cewa tun jiya tana Asibitin... Fitowar sa daga Asibitin ne ya ji wayar sa na ringing ya ɗau wayar ya amsa kiran wanda daga office ne ake buƙatar wani abu. Yana gama wayar ya fara laluba jikinsa ko zai ga ɗaya wayar sa amma wayam ba komai. Waya ce da ya ke dukkan ayyukan sa da shi hankalinshi ya tashi lokacin da ya tuna cewa saƙon text ya ke turawa hitman ɗin da ya ɗauka lokacin da ya ga halbin da aka yiwa Zuhayr. Da gudu yai wajen motar sa dan komawa wajen da abin ya faru ko zai samu wayar duk da kuwa ya san da wuya dan tun jiya aka killace wajen police suna investigating wajen. Lokacin da ya isa wajen daga cikin motar sa ya ke hango wajen da aka killace da ribbons na police inda police men ke shige da fice a wajen. Idan har ya je wajen za a zarge shi, sannan tunanin sa ya bashi a yadda police su ka yi ta sintiri a wajen tun daren jiya zuwa yau ba mamaki sun riga sun ɗau wayar. Za su ga saƙonnin da ya turawa hitman ɗin idan an bincika amma kuma ba lallai su san cewa shi ne mai wayar ba tunda da fake ID ya buɗe layin da ya ke amfani da shi. Da wannan tunanin ya sa hankalinsa ya ɗan kwanta ya juya kan motar dan ya je office sannan ya koma Asibiti wajen Zuhayr wanda har lokacin bai farfaɗo ba. Tunda labarin abinda ya faru ya riski gida aka sanar da Alhaji Iliyasu. Hankalinsa ya tashi da jin wannan mummunan labari. Tuni ya ce a shirya ma sa tafiya zuwa Las Vegas dan ya je ya ga jikan sa. Da Hajiya Nenne za su je saboda Hajiya Saudah ba ta da lafiya. Daga baya Hajiya Saudar ta yiwa Alhaji magana akan a tafi da Mommy saboda itama ta ga lafiyar 'yarta. Hakan kuwa aka yi wanda ya tsaida tafiyar na su ba su samu zuwa ba sai ranan Monday wanda ya kama kwana shida kenan da harbe Zuhayr da aka yi. Kafin su zo an ma sallami Zaytoonah dan ta ji sauƙi. Jikin Zuhayr ma akwai improvement sosai dan ya farfaɗo kuma yana gane mutane... "Daddyn twins ya jikin?" Zaytoonah ta faɗa tana kissing goshin sa. Daga gida ta ke inda ta je ta ɗauko wasu kaya. Tun kwana huɗu da su ka wuce aka tabbatar mu su cewa Zaytoonah na ɗauke da 'yan biyu Maza, saƙon da ta fara bashi kenan ranan da ya farfaɗo, hatta hoton scan ɗin da aka yi sai da ta nuna ma sa ba shi kaɗai ba ma, Mommy da ke Nigeria ma sai da ta turawa hoton ta waya. Murmushi yai mai ciwo saboda yadda ya ke jin jiki. "Su Mommy na hanya yau. Ina ga zuwa dare za su iso nan" A hankali ya furta "Allah ya kawo su lafiya" Ta amsa da Amin. Ta zauna gefen sa ta cigaba da yi ma sa surutu wanda duk zancen na ta gameda 'yan biyun su ne. Ƙarfe shaɗaya na dare jirgin su Mommy ya sauka a Las Vegas. Daga airport aka ɗauko su da motocin Zuhayr har zuwa Asibitin. Duk da Zuhayr ya so ya ga zuwan su amma tuni yai bacci bayan alluran da aka ma sa. Da su ka zo ba su tashe shi ba sun dai shiga ɗakin sun kalleshi sannan su ka fito suna yiwa Zaytoonah sannu. Zaytoonah ba kunya ta maƙale jikin Mommy tana zuba shagwaɓa. Bayan an gama gaishe-gaishe sai Zaytoonah ta mu su jagora zuwa gidan su dan su samu su kwana gashi duk sun ɗebo gajiyar zaman jirgi. Dan ba direct daga Nigeria su ka iso Las Vegas ba sai da su ka shiga connecting flight sau biyu. Yadda su ka ɗau tafiya ba alaman tsayawa ya sa Alhaji ya tambayi ko garin za su bari Dreba ya ce a'a. Shi dai ya riƙe baki dan sun jima da wuce area ma su gidaje yanzu gidajen tsilla-tsilla su ke gani. Da su ka iso gidan kowa taɓe baki yai yana mamakin gidan, gida kusa da teku. Bayan kowa ya samu masaukin sa ne Zaytoonah ta yi niyyar komawa Asibitin dan ta je ta kwana wajen Zuhayr amma Mommy ta hanata dan haka dole ta kwana a gidan. Washegari da sassafe su ka ɗunguma zuwa Asibitin. Zuhayr ya ji daɗin ganin Kakan na sa sosai. Sun ji daɗin ganin ya fara sauƙi, kwanaki biyun farko da aka kawo shi Asibitin ma sai ka ɗauka ba zai yi rai ba saboda yadda ake ta sintirin ƙara ma sa jini da yi ma sa aiki... *** Yau kwanan Zuhayr goma shatakwas a Asibiti kuma sauƙi sai daɗa samuwa ya ke yi babu wani complications. Su Mommy sati ɗaya su ka mu su suka koma Nigeria yanzu da ita da Mrs Haddish da Ben ne su ke jinyar Zuhayr hakan ya sa ta koma makaranta bayan Zuhayr ɗin ya buƙaci hakan. Investigation kam an cigaba da yi kuma abinda ba su sani ba shine sau uku ana kiran Ben yana zuwa police station yana amsa tambayoyi. Shi kan sa wannan tambayoyi da ake yawan yi ma sa ya sa shi haƙura da aiwatar da next plan ɗin sa a kan Zaytoonah. Yanzu neman hanyar da Zaytoonah za ta yi mutuwar da za a kira da natural death ya ke nema, duk cikin abinda ya rubuta na hanyoyin da ya ke so ya kashe Zaytoonah sai ya ga idan anyi bincike za a gano cewa kasheta aka yi shi kuma ba ya son haka dan yaga yanzu police na suspecting ɗin sa. Sai da Zuhayr yai sati biyar a Asibiti sannan aka sallameshi, da farko a wheel chair ya ke zama kafin daga baya kuma ya koma amfani da walking stick, har su ka koma gida da walking stick ya ke amfani. Kulawa na musamman ya ke samu daga wajen Zaytoonah da Kakarsa wacce ta tare a gidan saboda taimakawa Zaytoonah wajen kula da shi tunda tana zuwa Makaranta. A dawowar su gidan ne su ka samu an chanja mai dafa mu su abinci daga Chef Green zuwa Chef Foster. A yadda da su ka samu labari daga sauran ma'aikatan Chef Green ne yai retire saboda tsufa da kuma ciwon sugar da ya ke fama da shi wanda a zahiri ba hakan ba ne. Shi ne ya kawo Chef Foster a matsayin wanda zai maye gurbin sa tunda shima ƙwararren wanda ya iya girki ne... Watanni biyu ne su ka shuɗe da sallamar Zuhayr daga Asibiti wanda ya kama cikin Zaytoonah na wata bakwai, cikin da ake mugun tattalin sa. Tsatstsauran tsaro da takunkuni aka sa a gidan na su da ma duk inda za su je... Bajewa ta yi a ƙasa tana cin gasashshiyar kifi yayinda Zuhayr ke zaune akan kujera yana yiwa kafaɗumta massage. Watanni huɗu na cikinta ba ta son cin abinci amma tunda ya shiga wata shida yanayin cin abincinta ya chanja, ta koma ci kamar gara. "D har yanzu ba ka zaɓi suna ba fa" ta faɗa cike da shagwaɓa "Da sauran lokaci ai" "Tun a Asibiti kake faɗin haka har yau. Kaman yau ne fa wata tara zai cika" Ya rankwafo kan sa ya kissing tsakiyar ƙeyar ta ya ce "ina jiran sunan da ya dace da su ne" "Mu saka sunan Daddy na da Daddyn ka" "My Dear kar ki damu za mu sa idan lokaci yayi"... *** Bacci su ke yi hankali kwance. Kimanin kusan ƙarfe ɗaya na dare kenan. A hankali ya tako cikin ɗakin yana sanɗa har ya ƙarasa bakin gadon. Tulelen cikin Zaytoonah ya kalla sannan ya ɗaga wuƙar hannun sa sama ya daɓa ma ta nan da nan ta challa ƙara yayinda jini ya fara ɓulɓula har ta sama. Ƙaran da ta yi a cikin mafarki ne ya kawota har waje. Zuhayr yai saurin kunna bedside lamp da ke gefen gadon tareda jawota jikinsa yana lallashi. "Zuhayr zai kasheni, zai kasheni" "Sorry Dear ba wanda zai kashe ki. Mafarki ne kawai" "Zuhayr cikina ya farke, wuƙa ya daɓa min a ciki" ta yi maganar tana shafa cikinta "Its just a dream Baby. Ki kwantar da hankalinki" Kusan rabin awa su ka ɗauka yana rarrashinta kafin da ƙyar ta samu nitsuwa har ta koma ta kwanta. Duk da ba ta gane waye a mafarkin ya kasheta ba amma tunaninta ya ba ta kawai Ben ta gani. Ta so yiwa Zuhayr maganar amma ta san ba yadda da ita zai yi ba tunda mafarki ne ba gaske ba. Wunin ranan da ta ga Ben sai ta ji tsikar jikinta ya tashi musamman idan ya ƙura ma ta mugayen idanun san nan. A ɓangaren Ben jin anyi shiru da bibiyar sa ya sa shi fara shirin activating ɗin plan ɗin sa na gaba. Plan ne da ya ɗau watanni yana shiri a kan sa kuma ya tabbatar wannan karan zai samu nasara, ba kuma tareda an ce kashe Zaytoonah aka yi ba sai dai ace tsautsayi ne ya ritsa da ita. Kamar yadda aka ce Alinah ta kashe kanta wannan kuma cewa za ayi domestic accident ne. Step 1 za ta dinga jin jiri-jiri bacci-bacci Step 2 za ta shiga bath tube dan wanka Step 3 za ta nitse cikin bath tube ta sha ruwa har sai ta mutu. Mrs Haddish ta tafi ƙauye dan haka yanzu Zaytoonah ne kawai a gidan sai kuma ma aikata. Zuhayr ya tafi business trip kamar yadda ya faɗa amma Likita ya je gani baya son tadawa Zaytoonah hankaline shiyasa ya ma ta wannan ƙaryar. Ben ne kawai ya san cewa Asibiti ya je. Tunda ta ci abincin dare ta dawo ɗaki saboda jikinta da yai weak. Karatu ta ke son yi dan Exams ɗin da za su fara nan da kwanaki kaɗan amma kuma sai ta ke jin kamar bacci bacci ma ke damunta. Kamar yadda ta saba yin wanka duk dare kafin ta kwanta sai ta yi tunanin yin hakan ko zai yaƙice baccin da ta ke ji dan ta samu ta yi karatun dan an mugun barta a baya saboda matsaloli da su ka yi ta sha mu su kai wanda ya hanata samun nitsuwar yin karatun. Ta tara ruwan ɗumi a bath tube ta shiga amma ko minti biyu ba ta yi ba idonta ya rufe a hankali kuma kanta ya zame sai ta nitse chan ƙasan tube ɗin. Duk abinda ke faruwa Ben yana kallo a laptop ɗin sa saboda tun da safe da Zaytoonah ta tafi school ya je ya jona wata ƙaramar Camera a banɗakin. Murmushi yai sannan ya kashe laptop ɗin ya fito daga ɗakin sa. Ya sani ba mai shiga ɗakin Zaytoonah sai dai idan gobe anji shiru ba ta leƙo ba. Zuhayr ma sai goben zai dawo saboda Likitan dama kwana biyu zai riƙe shi. *Death by drowning* abinda za a rubuta kenan a headline na news. Sinadarin da ya zubawa Zaytoonah a abinci wanda ya kashe ma ta jiki ba a iya tracing na shi kamar yadda wanda ya siyar ma sa ya faɗa, kuma research ɗin da yai akan sinadarin ya nuna cewa sai da wata babbar na'ura wacce ba a ko'ina ma ake da ita ba a ƙasar dama duniya gaba ɗaya saboda tsadar ta ake iya tracing sinadarin a cikin jinin mutum. Kuma ya tabbata kafin akai ga gandun wannan ma Zuhayr zai yi tawakkali da komai tunda shi musulmi ne. Yana shirin buɗe ƙofar fita daga Falo aka ɗaura bindiga a ƙeyar sa. "You are under arrest Benedict Vincent Haddish" aka faɗa da kakkausan Murya. Juyo da kan sa yai a hankali yana faɗin "what the fuck" Chef Foster ya gani da bindiga. Kafin ya ƙara wata magana Chef Foster ya ce "Daniel Rogers FBI" "Rogers?" ya furta cike da mamaki. Rogers dai tsohon ma'aikacin FBI wanda ya yi shekaru sama da talatin a harkan bincike. Yadda ya ke mu su daddalan girki ka ce asalin sa Chef ɗin gaskiya ne. Sai dai yanayi na aikin Rogers ɗin ne ya sa shi ƙwarewa a ɓangare daban-daban na rayuwa duk dan ya saje da mutane idan ya je bincike wani waje. "What did i do?" Ben ya faɗa yana dakiya kamar bai yi komai ba. Mr Rogers ya kaɗa hannunsa ya ce "go and check on Mrs Ilyas" nan da nan wasu securities biyu wanda asalin su police ne su ka haura sama da gudu. Yayinda Ben ya haɗiye miyau maƙwat saboda tsoro da ya ziyarceshi a karo na farko cikin tarihin rayuwar sa... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 35 Bismillahir Rahmanir Rahim *psycho* Tunda su ka iso Gidan su jikinta ya ke a sanyaye. Duk da shawarwarin da Mommy ta ba ta hakan bai hanata yin kuka ba daren ranan da ta koma gida bayan mummunan labarin da Mommy ta ba ta. Hankalinta bai tashi ba ma sai da ta browsing akan cutar da ke damun Zuhayr ɗin. Ben ne ya zo ya ɗauke su daga airport kuma a yadda taga yana kasawa yana tsarewa ba ta tunanin zai bar gidan. Itama yanzu baya gabanta Zuhayr ne damuwarta. Kwana uku da su ka yi kafin a fara yiwa Zuhayr chemotheraphy session ɗin sa. Zaman kishiyoyi su ke ita da Ben, kowa ƙoƙarin kula da shi ya ke, shi Zuhayr abin har dariya ya ke bashi musamman idan ya ga Zaytoonah na hararan Ben. Ko ɗaki su ke sai ka ga Ben ya zo yana ƙwanƙwasa mu su ƙofa wai zai duba jikin Zuhayr sai ka ce shi likita ne. Yau ma da aka fara tare su ka raka shi asibitin. Sau uku a sati za a ma sa har na sati shida, dan haka aka bashi shawaran ya zauna a Asibitin kawai. Komai lafiya-lafiya sai da dare ta yi Ben ya dage wai shi zai kwana da Zuhayr. "Duk abinda za ka yi sai dai ka yi amma tareda mijina zan kwana. D ka gaya ma sa ya tafi" ta ƙarisa maganar tana kallon Zuhayr. "Baby kina buƙatan hutu, ki koma gida ki kwanta. Gobe da sassafe sai ki dawo" "Korata ka ke yi saboda shi ko? To ba inda zan je, gara ma ka ce ma sa ya tafi" Shirun da yai ne ya sa Ben fita daga ɗakin bayan ya bi Zaytoonah da wani irin kallo na tsana. Tunda ya ga takardun Asibiti na gwaje-gwajen da aka yiwa Zuhayr ya sawa ran sa cewa zai kula da Zuhayr har ya samu lafiya. Idan Zaytoonah ta tsaya ma sa a hanya kawar da ita zai yi kamar yadda yai niyya tun farko. Washe gari Zuhayr ya buƙaci zai koma gida idan ya so sai a dinga yi ma sa a chan gida ko kuma a dinga kawoshi Asibitin kullum-kullum saboda baya son abinda ya faru jiya ya faru tsakanin Zaytoonah da Ben. Dukkan su suna da mahimmanci a rayuwar sa kuma dukkan su ƙoƙarin kyautata ma sa su ke yi so bai ga laifin su ba. Haka su ka tarkata aka koma da shi gida, akan za a dinga ma sa a gida. Tana fitowa daga banɗaki ɗaure da towel ta ga Ben zaune kusa da Zuhayr yana karanta ma sa littafi. "Ban gane ba, wai a ɗakin ma ba za ka bar mu ba. Ka fita mana a ɗaki" Bai yi kamar ya jita ba sai ya cigaba da karatun da ya ke. Da ƙarfi ta wafce littafin hannunsa ta yi cilli da shi. "Benedict ka fita a ɗakin nan. Kai wani irin wawa ne wai? Idan ba a gaya ma ka ba to daga yau ka sani kai ba muharramina ba ne dan haka ba ka da hurumin da za ka dinga shiga min ɗaki haka kawai. Idan ba ka da aikin yi ka je ka koyi karatu tunda iƙirarin musulunci ka ke. Haba haba ina tareda shi munada nurse a gidan nan da zai dinga dubashi 24/7 incase akwai matsala amma duk da haka sai ka shigo mana har ɗaki. Ka fita" Ta ƙarisa maganar tana nuna ma sa hanyar waje. Ben ya kalli Zuhayr wanda ya gyaɗama sa kai alamar ya fita ɗin sannan ya juyo ya kalli Zaytoonah yai murmushi kafin ya fita a ɗakin. "Dear ba sai kin ma sa tsawa ba, kina ɗagawa kan ki hankaline kawai" Ƙarasowa wajen sa ta yi ta ce " ni dai duk abinda zai ma ka ya tsaya a waje amma banda nan ɗakin. Ba na so, ba na so" "Zo nan" ya faɗa yana ware ma ta hannu. Maimakon ta zo sai ta je wajen dressing mirror ta zauna tana kumbura fiska. A hankali ya taso ya zo har wajen da ta ke zaune. Ya ɗan rungumeta ta baya yana kallon fiskarta ta madubi ya ce "Sorry" "Ni dai ka gaya ma sa ya dena shigo mana ɗaki ko kuma na bar maka ɗakin kai da shi ku ƙarata" "Da gaske za ki bar ɗakin?" Ta sa hannu ta ja kunnen sa ta ce "ba inda zan je" Yai dariya ya manna ma ta kiss a kumatu. A sati na biyu da aka fara yi ma sa Chemotherapy jikin sa ya fara reacting wa treatment ɗin da ake ma sa. Gaba ɗaya aka chanja diet ɗin sa saboda Amai da gudawa da ya ke fama da shi ga rashin kuzari. A wannan lokacin kuma aka koma makaranta amma Zaytoonah ta ajiye batun Makaranta a gefe gashi wancan semester ɗin ma za ta gyara paper biyu a summer saboda ta faɗi. Tana ƙoƙarin danne hawayenta idan tana wajen Zuhayr amma idan ta shiga banɗaki ko ta je kitchen zama ta ke ta sha kuka. Gaskiya idan kana da lafiya ka godewa Allah domin lafiya abu ne da kuɗi ba ya ba da shi, idan Rabbis Samawati ya hanaka lafiya ko ka fi ƙaruna kuɗi ba za ka iya siyo lafiya ba. Cikin sati biyu Zuhayr yai wani fayau da shi daga ɗaki sai falo although sau biyu duk sati yana fita strolling shi da Zaytoonah da Ben dan ya motsa jiki. (Ya Allah ka ƙara mana lafiya, marassa lafiya da su ke gida da asibiti ya Allah ka basu lafiya Amin). "Baby ki shirya ki tafi makaranta Dan Allah" "D ba inda zan je" "Alƙawari ki ka ɗauka tun kafin mu taho akan ba za ki yi watsi da karatun ki ba duk abinda ya faru" "Ba zan je ba" Ɗaga ido yai yana kallon ceiling abubuwa da dama na zuwa ma sa. Jin yayi shiru ya sa ta ɗago kai ta kalleshi. "D ka yi haƙuri amma na ajiye karatu har sai ka samu lafiya" "Ba kya so na samu lafiya kenan. Ni da ina nan ina irga kwanaki har ina cewa saura lokaci kaɗan na fara kiran ki Barrister ashe duk banza ne tunda ba kya son karatun" "D ni kam..." "Dan Allah ki koma makaranta. Idan ba ki koma ba ni ko zan koma office" "Ba ka da lafiyan za ka je office?" "Mi zai hana tunda ina numfashi" Shiru ya biyo baya kafin daga baya ta ɗan tura baki ta ce "to to to zan je amma sau biyu a sati kacal" "Ban yarda ba" "Sau biyu" "No" "Sau..." Zuhayr ya haɗe bakin su. End of discussion... *** Sati ɗaya kenan da komawarta School kuma Alhamdulillah jikin Zuhayr ya fara samun sauƙin side effects na Chemotherapy da ake ma sa dan ya dena gudawa da amai sai dai rashin kuzari, ga rashin appetite. Likitan da ke dubashi yana ƙara bashi ƙwarin gwiwa gameda yadda jikinsa ke saurin responding ga treatment da ake ma sa wannan ya sa hankalin Zaytoonah ya ɗan kwanta. Zaune su ke a bakin ruwa wanda Zuhayr ne ya buƙaci hakan saboda ya gaji da zaman cikin gidan. Su biyu ne a kan picnic mat da su ka shimfiɗa wajen sai kayan ciye-ciye da aka jera mu su. "Rayuwa kenan" ya faɗi yana kallon sararin samaniya. "Komai da lokacin sa. Idan jin daɗi ka ke taƙama da shi akwai ranan da zai ƙare, ranan da gangan jikin ka ba zai so komai na duniya ba balle ruhinka" "Yau kuma Sheikh Hassan ka koma ne?" Zaytoonah ta yi maganar tana cin Apple pie da ke gabanta. "Ni da su Kamal da Jabir mun je karatun Sheikh Albaniy ranan (Allah ka gafartawa Malam, Amin). Ya faɗi abubuwa da dama wanda ya sani cikin zulumi. Ina dai addu'ar Allah ya sa sauran rayuwar da zan yi a gaba na iya bautawa Allah yadda ya kamata na kuma koyi da sunnonin ma'aiki" Ya juyo ya kalleta yai murmushi ya ce "Dear, tun da na ji wa'azin nan na ke tambayar kai na yau idan Allah ya ɗau rai na wani irin shaida zan samu a duniya? Sannan mi zan tarar a rayuwar barzakh da zanyi balle kuma ranan hisabi. Shin zan samu rahamar Allah na shiga Aljannah ko kuwa dai makoma mai muni zan shiga" Idon Zaytoonah cike da hawaye ta ce "Dan Allah ka dena maganar mutuwa. Ina tsoro" Hannunta ɗaya ya kamo ya ce "ba mutuwar ba ne abar tsoro. Rayuwa bayan mutuwa shine abin tsoro saboda bamu san makomar mu ba. Ina fata Allah ya yafe ni dan na yi rayuwa ta jin daɗi ba tareda na waiwayi ranan da zan kasance cikin ƙasa ba. Ko kin san ina shan giya?" Zaytoonah ta zaro ido cike da mamaki. "Yes na sha giya a baya, abin takaici na rage shan giya ne lokacin da na haɗu da Alinah ta tunatar da ni illolin sa da kuma haramcin sa. Still ina sha once in a while haka, amma abin haushi na dena shan giya ne completely lokacin da na fara ciwo aka fara min gwaje-gwaje aka tabbatar da cewa cancer ne, ban bi dokar Allah ba amma na bi dokar likitan da ya ce min na dena shan giya saboda treatment da za a fara min. Zaytoon ban yi..." Kuka Zaytoonah ta fashe da shi ta faɗa jikinsa tana cigaba da kuka mai shiga rai. Shima Zuhayr hawaye ne fal a idon sa. "Idan na samu lafiya zan inganta rayuwata zuwa tafarkin musulunci. Ina ma da niyyar komawa garin Madina da zama na yi karatu ko na shekara biyu ne. Za ki bi ni mu je mu yi karatun tare?" "Zan bika duk inda za ka je Miji na" "Ina ji kina tilawan Alƙur'ani amma ba ki taɓa kirana mun yi ba" "Ka yi haƙuri" ta faɗa tana jan hanci. "Inaga ke za ki zama Malamata kafin mu tafi Madina" Ta yi murmushi ta sake ƙanƙameshi. "I love you Zaytoon"... *** Hiran su na jiya ya sa yau da ta gama sallar Asuba ta zauna kusa da Zuhayr a kan gado ta buɗe Alƙur'ani ta ce "to mu yi karatun daga ina za mu fara?" "Ban yi nisa ba fa, infact inaga bai fi surori goma na iya ba" Ba ta yi mamaki ba duba da irin rayuwar Zuhayr. Da kan shi ya ɗau ƙur'anin ya ce bari ya fara karantawa idan ya zo iyaka inda ya iya sai ya tsaya. Ya fara karatu irin karatun ci da ƙarfi ɗin nan. Surori ukun farko wanda ya ke sallah da su su kaɗai ne ya karanta babu gargada amma sauran da jani-in-jaka aka ƙare. Da aka zo suratul Asr ya ce iya nan ya iya Alinah ta ma sa bitar suran gaban amma bai iya ba har yau. "A wajen Sheikh Hassan na fara karatu, amma neman kuɗi ya sa banida lokaci sai na watsar da komai. Ina fata idan komai ya daidaita da ni da ke da Zubayr za mu je mu nemo ilimi dai-dai gwargwado" Faɗin sunan Zubayr ya sa Zaytoonah ta tuna da maganar da ta ke son yi ma sa. Itafa ba ta ga alaman Zubayr ko Ben na sallah ba. "Amma ni kam sai na ga kamar Ben baya sallah fa" "Ba kin hanashi zuwa ɗakina ba. Ko yana yi a ina za ki gani" yai maganar yana murmushi. Ganin ya maida zancen wasa ya sa ta ja bakinta ta yi shiru. Ta maida hankalinta gun karatun da za su yi inda ta ce ma sa maimaici za su yi kafin a fara ɗaura ma sa. Ba ta ƙarisa haddan Qur'ani ba dan Islamiyyar su sai ka yi tartil ka sauke kafin ka fara hadda. Ta yi sauka na tartil ta fara hadda har ta kai suratul Isra'i Muntari ya maidata Lagos lokacin, hakan ya sa karatun ya zo yai baya. Daga gama makaranta kuma rikicin da ya ɓullo ya sa aka ma ta aure. Yanzu haka a hadda ta tsaya a suratul Ibrahim ne... Ya riga ya saita komai jira kawai ya ke lokaci yai. Yana ganin lokacin da Dreban Zaytoonah ya fita dan ya je ya ɗaukota daga Makaranta yai murmushi yana tunanin daga yau sai dai wata ba Zaytoonah ba a duniya. And finally he can have Zuhayr all to himself. Komai da zai faru da ɗan Adam rubutacce ne daga Ubangiji. Idan ka ga abu ya faru to dama an rubuta maka shi idan bai faru ba to ka ƙaddara ba ya cikin ƙaddarar ka ne. Ben ya gama shirin sa tsaf dan aikata method na farko cikin guda shabiyar da ya rubuta dan ya kashe Zaytoonah. Lokacin da Dreban ya je ɗaukota a school sai ya kira Zaytoonah a waya saboda ya jira bai ganta ba, ta ce ma sa ya koma gida kawai za ta taho da Farha dan ta raka Farha asibiti mahaifin ta ba lafiya. Hakan ya sa Dreban ya juya ya koma gida da mota. Bayan sun gama gaisuwan ne ta shiga motar Farha dan itama ta ce tana son duba jikin Zuhayr dan tunda su ka dawo daga Nigeria ba ta je ta gaishe shi ba. Yana tsaye a balcony ɗin gidan ya hango motar na zuwa daga chan nesa yai murmushin mugunta ya ce "goodbye Zaytoonah" ya danna wani ƙaramin remote da ke hannunsa sai ga motar ta kama wuta sakamakon Bomb da ya tashi a ciki. Ƙaran Bomb ɗin ne kuwa ya tada Zuhayr daga bacci a firgice, yayinda sauran ma'aikatan ma su ka fara fitowa da gudu saboda suma sun ji ƙaran fashewar Bomb ɗin... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 39 Bismillahir Rahmanir Rahim *The twins* Gyara gado ta ke yi ta lura da gashin Zuhayr da ke jikin Pillow. Ba yau ne ta lura da hakan ba kusan sau biyar tana lura da hakan tun ma a Asibiti. Ta sa hannu ta kwashi gashin ta je ta watsa a cikin dustbin da ke ɗakin. Ta dawo ta cigaba da gyara gadon na su sai da gama sannan ta fara share ɗakin na su. Duk da Zuhayr ya hanata aiki ko wani iri ne amma gyaran ɗakin su kam ta ce ma sa dole sai ta yi saboda Likita ya ce ta dinga motsa jikinta saboda zai taimaka ma ta wajen samun sauƙin haihuwa. Bayan ta gyara ɗakin sannan ta shiga banɗaki shima ta wanke. Bayan ta gama tsaftace banɗakin sannan ta yi wanka ta fito. Doguwan riga ta fiye sawa yanzu saboda fiyeda rabin kayanta ba sa shiganta yanzu saboda nauyi da ta yi. A hankali ta ke saukowa daga stairs ɗin tana tafiya tana dafe da ƙasan cikin ta a ganinta wai kar cikin yai ƙasa sosai. A falo ta sameshi yana zaune ya saka laptop a gaba yana kallo. Tun mutuwar Ben har yau Zuhayr ba ya iya wata doguwar magana, daga ee sai a'a kawai sai kuma gyaɗa kai. Mafiya yawanci ma typing za ka ga yanayi a laptop ɗin sa ko kuma kaga yana zaune shiru. Saboda su manta da komai ya sa su ka chanja gida, wannan karan gida ne cikin gari ba chan jeji ba. Suna da maƙota gefe da gefen su da ma opposite ɗin su. Duk da rayuwar turawa kowa baya shiga harkan kowa amma atleast sanin cewa akwai mutane kusa da su shima wani kwanciyar hankaline. Ta kissing goshinsa kafin ta zauna kusa da shi tana miƙe kumburarrun ƙafafuwanta. Ita kam yanzu har ba ta son ko da wasa ta kalli madubi saboda yadda ta kumbura ta cika ta ko'ina. Ashe haka ciki ke sa mutum muni. Complain ɗinta kenan a duk lokacin da su ka yi waya da Mommy. Salman kam tun ranan da su ka yi video call ya dinga ma ta dariya tayi fushi da shi ta dena kulashi. "Ni kam miyasa gashinka ke yawan karyewa ne yanzu?" Ta yi tambayar tana kallon sa. Tun zuwanta yai saurin chanja abinda ya ke rubutawa zuwa wani wajen saboda kar ta lura da will ɗin sa da ya ke typing. Sai da ta sake tambayar kafin ya juyo ya kalleta ya ce "ba na kula da shi ne shiyasa amma zan yi aski". Ranan da yamma bayan ya fita sai gashi daya dawo kuma kan sa ƙwanƙwal ba gashi ko ɗaya. Zaytoonah ta dinga ma sa dariya har Dada ma ta taya ta suna ma sa waƙar Zuhayr mai ƙwaryar molo, shi kuwa sai murmushi ya ke mu su. Da dare suna kwance akan gado ya ce " nan da shekaru kaɗan za ki zama cikakkiyar Lawyer. Barrister Zaytoon" "Ni kam..." ta yi maganar tana turo baki. "Ki min Alƙawari Zaytoon, duk abinda ya faru ba za ki yi watsi da karatun ki ba. Zan yi alfahari da ke idan har za ki tsaya tsayin daka har ki ƙarisa karatun ki lafiya. Ina so ki zama abin alfahari ga 'ya'ya na. A Barrister and a Ballerina" "Idan kana tare da ni zan iya zama koma minene" Ya shafa kan ta ya ce "idan Allah yana tareda ke ba kya buƙatar kowa, domin shi ɗan Adam mai gushewa ne Allahu kuwa shine farko, shine ƙarshe. Shi ya ke jiɓintar dukkan lamurran mu. Zai iya yiwuwa ranan da za ki ƙare karatun ki bana nan, zai iya yiwuwa ranan da za ki fara aiki ba na nan, zai iya yiwuwa ranan da Muhammad da Ahmad za su fara makaranta ba na nan. Amma ina so ki sani Allah na nan kuma shi zai riƙeku a lokacin da babu ni" "Ka dena irin wannan maganar dan Allah. Ba abinda zai sameka, ina ce Likita ya sallameka ne saboda ka samu lafiya, ina ce kullum kana ce min jikin ka da sauƙi..." "Za mu je Madina" ya katse maganar ta ganin tana shirin kuka. "Nan da kwana biyar za mu tashi, zamuje mu sauke farali Insha Allah. Kinga duk dukiyar dana tara idan har ban je na sauke farali ba babu amfanin dukiyata. Za mu je mu yi Umura Baby. Na yi magana da Likitan ki ya ce ba matsala za mu iya tafiya. Tareda Dada za mu je Insha Allah" ya ƙarisa maganar yana kamo yatsunta. Maganar zuwa Umurah da yai sai ya kawar da maganar farko da ya fara ma ta. Ta shiga murna, ƙarshe kuma ta haɗe rai ta ce tayi fishi saboda bai ma gaya ma ta ba sai da tafiyar ta matso kusa, sai da ya lallasheta kafin ta haƙura su ka kwanta cike da farin ciki. Ana saura kwana uku za su tafi sai ga Saifullahi ƙanin Muhsina ya zo ashe har da shi za ayi tafiyar. Dada da Saifullahi ke magana lokacin da Zaytoonah ta sauko dan ta taya su hira saboda ta gaji da zaman ɗaki. Chak ta tsaya lokacin da ta ji maganar da Saifullahi yayi. " ni fa tunda Uncle ya gaya min jikina yai sanyi. Mahaifiyar sa ma haka aka ce ba za ta wuce wata shida ba amma ko kaiwa wata shidan ba ta yi ba ta rasu. Ina tsananin tausayin Zuhayr" "Rayuwa da mutuwa duk na Allah ne. Idan Allah ya bashi tsawon rai sai ka ga ya samu lafiya. Ai Likitoci ƙoƙari su ke yi amma Allah ne mai kashewa kuma mai rayawa" Zuwa lokacin hawaye ya cika idanunta. "Dada wa ye aka ce zai mutu?" Ta yi maganar cikin kuka lokacin da ta ƙariso wajen su da sauri. "Ba dai mijina ba ko?, ba dai Zuhayr ɗina ba ko?" Dada ta taso ta kamo hannunta ta zaunar da ita a kujera. "Na sha faɗa miki a wannan hali da ki ke ciki kina buƙatar nitsuwa da kwanciyar hankali saboda lafiyar 'ya'yan ki" "Ba Zuhayr ɗina ku ke magana ba ko?" Dada ta gyaɗa kai yayinda Saifullahi ya ce "muna maganar Alhaji ne. Kin san jikin tsufa" Duk da wani ɓangare na zuciyar ta ya so ƙaryata maganar Saifullahi amma da ta daure ta yaƙice wasi-wasin da zuciyarta ke yi, ta sa a ranta Alhaji Iliyasu Kakan Zuhayr ɗin ne ake magana. Lokacin da Zuhayr ya shigo ɗaki tana sallar Isha'i. A bakin gado ya zauna yana ƙare ma ta kallo. Ba abinda ya ke riyawa a ransa face watarana duk yadda ya ke son ta dole su rabu, rabuwa ta har abada wanda haɗuwar su sai dai a lahira. Ta dalilin sa rayuwar ta ya shiga haɗari a lokuta da dama wanda ba dan kariyar Allah ba da itama ta tafi kamar yadda Alinah ta tafi. Yanzu da ake faɗa ma sa survival rate na shi is very low sai ya kasance yanzun ne kuma ya ke son rayuwan, yanzun ne ya ke son nunawa Zaytoonah soyayya da tsantsar kulawa. Yana fata ko da baya nan Allah ya ba ta wanda zai riƙeta tsakani da Allah. Lokaci na da mahimmanci a rayuwar Ɗan Adam, amma sai ya kasance Ɗan Adam ɗin baya duba gudun lokaci baya duba mahimmancin lokaci. Ina ma yayi amfani da lokacin da su ka kasance tare tun farkon zuwan ta? "D lafiya?" Muryan Zaytoonah ya dawo da shi daga dogon nazarin da ya ke yi. Yai ma ta murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo. "D wai da gaske Alhaji bashida lafiya?" Saifullahi ya gaya ma sa yadda su ka yi da Zaytoonah ɗazu shiyasa ya tabbatar ma ta da cewa da gasken Alhaji ne ke ciwo. "Ina kai kam lafiyar ka ƙalau?" Ya jawota ya ɗaurata kan cinyarsa yana faɗin lafiyata ƙalau. "Ban maka nauyi ba?" Ya sa hannu ya shafa cikinta ya ce "ko da Boys ɗina irin ƙashin ki su ka ɗauko ai zan iya ɗaukan ku duka uku lokaci guda" "Kayya! Da wani jikin?" Yai ƙaramar dariya ya ce "da jikin da na ke gaisawa da su mana" Ta rufe fiskanta da tafukan hannunta tana faɗin har ka sa na ji kunya. "Barin yi wanka sai na gaishe da boys ɗina" Ta tashi daga kan cinyarsa tana ɗan nishi. "Are you Ok" ya faɗa in a concern tune. Ta gyaɗa ma sa kai. Sai da ya kissing goshinta kafin ya wuce banɗakin, ta bi bayan sa da kallo. Normally Zuhayr was skinny amma kuma yanzu da ta lura sai ta ga kamar ya zama extra skinny. Ta yi saurin ɗauke tunanin ta hanyar cewa diet ɗin sa da aka chanja ma sa ne tun lokacin da ya fara jinya ya sa shi ramewa haka. Ana gobe za su wuce ƙasa mai tsarki Zuhayr ya kawo ma ta wasu takardu kusan kashi takwas ya ce ta dinga sa hannu. Bai ba ta damar karanta miye a cikin takardun ba, ce ma ta yai na tafiyar da za su yi ne. Washegari su ka wuce Saudi Arabia. Jirgin su ya sauka a Riyadh kafin su ka wuce birnin Makkah ta mota. Kwana uku kafin tahowar su su ka je wajen Sheikh Hassan yai mu su sharen fage gameda ibadar da za su yi idan sun je. Lokaci ne da babu chunkoso dan saura kusan wata biyu a fara Azumi shiyasa su ka samu damar gudanar da ibadun su cikin kwanciyar hankali. Idan ka cire kumburin ƙafa da ke damun Zaytoonah a duk lokacin da su ka je masallaci suna ibada ba ta da wata matsalar komai. Kullum su ka je masallacin Ka'aba addu'ar da ta fi bawa mahimmanci shins Allah ya ƙarawa Zuhayr lafiya ya kuma sa ta sauka lafiya yai wa 'ya'yan ta Albarka. Mahaifinta kuma tana addu'ar idan yana raye Allah Ubangiji ya bayyana mu su shi idan kuma ya rasu Allah ya kyautata makwancinsa. Ranan da za su wuce Madina Zuhayr ya fara zazzaɓi. Da farko sun so tsayawa zuwa ya warke amma ya ce ba komai zai iya zuwa Madinah birnin Manzo (SAW). Haka su ka ƙarisa tare bayan ya sha magani jikin na sa ya ɗan lafa, sai dai a wheel chair Saifullahi ke turashi saboda jikinsa da yai weak sosai, kafin su wuce Madinan aka sa ma sa nasal canula saboda numfashin sa ya dai-dai ta. Jikin Zaytoonah yai mugun sanyi da yadda ta ga Saifullahi na tura Zuhayr, sai ta ke ganin kamar akwai abinda ya ke ɓoye ma ta amma koma minene za ta bari su gama ibadar da ya kawo su tukunna kafin ta dameshi har sai ya gaya ma ta gaskiya. Alhamdulillah kuma zuwan su Madina sai zazzaɓin na sa ya lafa ma sa sosai. Haka su ka kammala Umara lafiya har suna shirin komawa Makkah gobe. A ranan ne kuma su ka je Raudha inda su ka samu damar gabatar da gaisuwa ga fiyayyen halitta. Lokacin da Zuhayr ya bar wajen ƙofar murmushi ne mai sanyi ɗauke a fiskar sa. Irin murmushi na contentment ɗin nan. Sallar Isha aka idar yayinda aka zauna ana yin addu'o'i. Bayan sun kai kusan awa ɗaya suna jero addu'o'i kafin Saifullahi ya juyo wajen Zuhayr dan ya tambayeshi ko su wuce masaukin su ko kuma dai su ƙara jira kaɗan. Akwai maganin da Zubayr ɗin ke sha duk ƙarfe tara na dare shiyasa ma ya ke son su tafin. Kan sa a duƙe lokacin da Saifullahi ke taɓa shi, maimakon ya ga Zuhayr ya ɗago sai ya ji shiru. Wani Balarabe da ke gefen Zuhayr ne ya furta Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun yana magana yana ɗago kan Zuhayr da ke duƙe fiskar ɗauke da murmushi. Yadda Balaraben ke ta zuba larabci da kuma mutanen da su ka fara tasowa suna zuwa wajen ya sa Saifullahi farfaɗowa daga daskarewa da yai a wajen na hucin gadi. Abinda su ka fara yi shine su ka cicciɓi gawar Zuhayr daga wheel chair su ka shimfiɗa shi a ƙasa. Saifullahi ya bi fiskar Zuhayr da kallo yana hawaye. Maimakon ɗazu da aka ɗago da fiskar idon shi na buɗe yanzu anriga an rufe ma sa idon, rufewa ta har abada. Ba za su iya cewa ga takamaimai lokacin da Zuhayr ya rasu ba. Walau suna sallar Isha ɗin ne ko kuma kafin sallar, ko kuma ma dai bayan an idar da sallan Allah ya karɓi ran sa. Yadda ka zo duniya salun ƙalun haka za ka koma ba tareda ka ɗau komai ba. Gidan sa, dukiyar sa Iyalin sa duka ba su amfani Zuhayr ba a lokacin da mutuwa ta riske shi. Ayyukan da ya aikata na Alkhairi ko na sharri shi zai je ya tarar a inda ruhin sa ya ke. Idan babu ruhi gangar jikin mutum fankololo ne ba shi da wani amfani amma a hakan mun fi son mu biyewa gina gangan jikinmu fiyeda tsaftace ruhin mu ta hanyar yin ibada da aikata ayyukan ƙwarai. Bayan mutuwar Zuhayr ya riski Zaytoonah kwana biyu ta yi ba ta san inda kan ta ya ke ba. Tun da ta ga gawar Zuhayr sau ɗaya kafin a je a sallace shi ta suma ba ta sake sanin inda ta ke ba. Kusan kwananta tara a Asibiti ana jinyarta wanda sai ta nuna alamun ta samu sauƙi sai ta sake birkicewa wannan ya sa aka shirya yi ma ta CS kawai saboda tsiratar da lafiyar jariranta. Although cikin yana satin da ya shiga wata tara kenan amma EDD ɗin ta ya nuna ita da haihuwa ma sai nan da sati uku, a ƙalla sai cikin ya shiga wata na goma kenan. Ranan Jumu'ah da ta kama kwanaki sha uku kenan da rasuwan Zuhayr aka ciro ma ta lafiyayyun tagwayenta maza wanda ɗaya ya ke fari ɗayan kuma baƙi... *INTERMISSION* 2/11/21, 10:04 PM - ****: 38 Bismillahir Rahmanir Rahim *Killed* "I neec to speak to my lawyer" maganar da Ben ke faɗi kenan lokacin da aka tisa ƙeyar sa cikin Mota a tafi da shi. Tun kafin a wuce da Zaytoonah Asibiti aka ba ta taimakon gaggawa Allah ya sa ba ta jima cikin ruwan ba da shikenan sai dai wata ba ita ba a duniya. Zuwa wayewar gari mafiya yawancin gidajen jarida da talabijin maganar kama Benedict Haddish ake yi a garin Las Vegas. A wannan kayaniya da ake yi ne Faisal Khan ya kira Zuhayr dan ya ma sa jaje tareda tambayar wani Asibiti aka kwantar da Zaytoonah. Hankalin Zuhayr ya yi ƙololuwar tashi dan baida masaniya gameda abinda ke faruwa a Asibiti ya ke inda ya ke samun kulawa. Jikinsa na ɓari ya hau yanar gizo dan ya tabbatar da abinda Faisal ɗin ya ce domin har lokacin bai gama gaskatawa ba. "No Ben, No Zubayr. This is not true, he cant do this" ya faɗi yana girgiza kai. Numbar Zaytoonah ya kira amma a kashe zuciyar sa ya buga da ƙarfi, ya dafa dai-dai wajen zuciyarsa yana nishi sama-sama... *** Bayan kwana uku Da ikon Allah ba abinda ya samu Zaytoonah ta dai kwana ɗaya a Asibiti kafin aka sallameta. Zuhayr kam sai da aka yi da gaske kafin aka dai-dai ta numfashin sa. Da ya tuna abin a ran sa sai zuciyar sa ta cunkushe numfashin sa ya dinga fita sama-sama, ranan kam da ya ji saƙon ya suma ya kai sau huɗu hakan ya sa aka ma sa allurar barci. Washegari daya tashi da yamma ci ne ya ga Zaytoonah a gefen sa wanda hakan ya sa shi samun nitsuwa kaɗan. Ita kan ta Zaytoonah ba ta san a Asibiti ya ke ba tunda business trip ya ce ma ta zai je. Da aka sallameta ne Mrs Haddish ta ce su wuce wajen Zuhayr dan shima na kwance a Asibiti. Tunkafin sun isa Asibitin ta ke tunanin ko dai dalilin abinda ya faru ne ya sashi shiga tashin hankali har shima ya kwana a Asibiti... "Why? Why?" Zuhayr ya furta yana kallon ƙwayar idon Ben yayinda idon sa ke fitar da hawaye. Gobe za a fara zaman kotu kuma duk da evidence ɗin da aka tanada evidence ne gamsassu da babu ko tamtama akai amma hakan bai sa Zuhayr ya gama gamsuwa da komai ba. Yana so ya ji ta bakin shi Ben ɗin. Ben fa da su ka taso tare, Ben da kusan babu abinda bai sani ba na sa, shine ɗanuwa guda da yake ji da shi. "I love you, I love you so much Zuhayr. You are my one and only love but..." "Benedict" ya furta da ɗan ƙarfi tareda dafe ƙirjin sa yayinda dukkan jikin sa ke rawa. Ba zai iya cigaba da sauraron sa ba. Komai ke dawo ma sa yanzu kaman flashback ɗin shirin film. Tun lokacin da Alinah ke yawan ƙorafi akan Ben yana ma sa wani kallo da bai dace ba tareda yi ma sa faɗa akan kusancin su yayi yawa zuwa lokacin da Zaytoonah ta fara ma sa complain akan Ben ɗin. "Its my fault, its my fault" abinda ya ke faɗi kenan lokacin da ya fito. Tafiya ya ke yi amma baya ganin gaban sa dan duhu ne a ko ina kafin daga ƙarshe yai yijif ya faɗi ƙasa. Tun kafin a wuce da Ben kotu ya ke wasu abubuwa da ke nuna alamun taɓin hankali. Ya fara hakan ne saboda Lawyer ɗin sa ya ce Mr Rogers yanada footage na shi yayinda ya ke sawa Zaytoonah maganin kashe jiki a abinci sannan anga littafin da ya rubuta na hanyoyin da zai kashe Zaytoonah, kuma ciki ne aka gano cewa duk abubuwan da ke faruwa shi ne musabbabin komai. Abinda ma bai sani ba shine tun lokacin da aka tsinti wayar shi akayi bincike kuma har aka kamo hitman ɗin da ya harbe Zuhayr duk da dai ba wai sun haɗu da Ben ba ne amma information ɗin da ya basu ya gamsar da su cewa Ben ne ya hiring hitman ɗin. An nuna cewa an watsar da investigation ɗin ne saboda a samu damar tattara sauran hujjoji akan Ben ɗin cikin wannan lokacin ne kuma aka kira tsohon ma'aikacin FBI wato Mr Rogers shi kuma yai badda kama ya je ya zauna a gidan Zuhayr a matsayin mai dafa abinci. Da taimakon Allah da kuma kaifin basira da sanin aiki irin na Mr Rogers sai da aka koma kan case ɗin mutuwar Alinah da aka rufe shekaru da su ka wuce aka binciko files ɗin. Duk yadda Ben yai amfani da kuɗi wajen an rufe case ɗin ba tareda an yi dogon bincike ba sai da Mr Rogers ya gano gaskiya. Hatta Mrs Taylor matar da ta shiga gidan dan kaiwa Alinah wedding gown ɗin ta sai da Mr Rogers ya nemo ta ya ma ta tambayoyi. Akwai wanda ya ba da shaidar cewa kafin Mrs Taylor ta shiga gidan ya ga wani mutum ya fito daga gidan Alinah ya bar gidan da sauri. Footage ɗin fitowar Ben daga gidan Alinah da aka jima da cirewa sai da Mr Rogers ya nemo duk da fiskar Ben ba ta bayyana yadda za a tabbatar da cewa shi ba ne kai tsaye saboda ya saka face cap kuma kansa ƙasa haka ya wuce amma anyi amfani da na'ura wajen gano cewa Ben ɗin ne. A lokacin da aka yi case ɗin Alinah ƙasar America musulmai na fuskantar ƙalubale shiyasa ba a damu an yi dogon bincike akan mutuwar ta ba kawai aka ba da report na cewa kashe kanta ta yi. Bayan an gama irgawa Ben laifukan sa na kashe Alinah, Linda da kuma Mr Dawson tareda ƙoƙarin kashe Zaytoonah da yai a lokuta da dama aka nemi ya amsa laifin sa sai Ben ya ƙi magana. Daga ƙarshe sai Lawyer da ke wakiltan sa ya ce yana neman kotu ta yi alfarma akan client ɗin sa domin bashida lafiyar ƙwaƙwalwa yana buƙatar kulawa. Alkali ya yanke hukuncin kashe Ben ta hanyar rataya,.daga nan kotu ta tashi. Lawyer ɗin Ben bai tsaya a haka ba sai da ya ɗaukaka ƙara saboda ba ƙaramin kuɗi Ben ya sa aka tura ma sa ba. Bayan sati uku aka sake sauraron ƙaran yayinda a wannan lokaci Alkalin ya ba da umurnin a kai Ben Psychiatric dan a tabbatar da lafiyar sa kafin a zartar ma sa da hukuncin rataya. Duk da wannan batun rashin lafiya da ake bayarwa duk strategy ne na ganin an sauya ma sa hukunci daga rataya zuwa zaman gidan yari amma kusan hauka na zahiri na shirin kama Ben ɗin. Bai taɓa yin tsawon lokaci irin haka ba tareda ya ga Zuhayr ba. Yanzu ko muryar sa ba ya ji balle ya sa shi a ido. Lawyer ɗin sa ya gaya ma sa Zuhayr ba shi da lafiya saboda cancer ɗin sa ta dawo ga kuma ciwon zuciya da ya ke fama da shi. Duk case ɗin Ben ɗin daake yi ma shi yana kwance a gadon Asibiti wannan batu shi ya sake jirkita ƙwaƙwalwar Ben. Yana tunanin taya za ayi masoyin sa Zuhayr yana Asibiti ace shi yana nan kulle, ba wannan kaɗai ba ma babban damuwar shine ita yarinyar da ya ɗau fiye da shekara yana son ganin bayanta har yanzu tana numfashi a doron ƙasa waɗannan ma shi ya fi tada ma sa hankali fiye da rasin lafiyar Zuhayr ɗin tunda ya sa a ransa ba dan Zaytoonah ba da shi ne zai zauna da Zuhayr yana jinyar sa... *** Daga jikin gallery room su ke kallon abinda ake yiwa Zuhayr. Radiation treatment ake ma sa domin a kashe cancerous cells ɗin da su ka sake dawowa. Kwance ya ke a kan wani gado daga shi sai boxers yayinda a hankali gadon ke shiga jikin wani babban na'ura kaman wani ɗaki yayinda wani haske da ke fitowa daga wani naura da ke saman gadon ke bin dukkan ilahirin jikin sa, ya fara daga kan sa har ya kai ƙafafun sa. Zaytoonah ta damƙi hannun Mrs Haddish da ke gefenta tana hawaye. Dada Salamatu wacce itama ke gefenta ta dafa kafaɗarta ta ce "addu'a za ki ma sa Zaytoonah" Tun kama Ben da sati biyu aka turo Dada Salamatu dan ta zo ta dinga kula da Zaytoonah ga jinyar miji ga kuma tsohon ciki. Dada Salamatu ƙanwa ta ke wajen Alhaji Iliyasu, ba ta taɓa haihuwa da mijinta ba har ya rasu hakan ya sa kusan shekaru bakwai da su ka wuce ta dawo gidan Yayanta da zama tunda 'ya'yan kishiyarta Mata ne guda huɗu kuma dukkansu su na gidajen mazajen su. "Muhammadu Allah ya baka lafiya" Dada Salamatu ta furta a bayyane... Bayan ciwon na sa abinda ke damun sa harda kaɗuwar abinda Ben ya ma sa ko ace ya jima yana ma sa. Wani irin so ne wannan? wani irin kishi ne wannan da zai sa shi kashe rayuka har uku ba tareda kuma ya damu da komai ba. What if Mr Rogers baya gidan a ranan da sai dai Zaytoonah da yaran sa su bar duniya ba tareda sun yi laifin komai ba. Ire-iren waɗannan tunani su ke sa shi cikin damuwa. Dawowar Zaytoonah kenan daga Asibiti ita da Dada sun bar Zuhayr yana bacci. Ba dan Dada ta takura ba da ba za ta dawo gida yanzu ba dan ko kaɗan ba ta son barin gefen Zuhayr. Wanka ta shiga yayinda Dada ta shiga kitchen dan ta dafa mu su abinda za su ci tunda ta zo gidan ba ta yarda da wani ko wata ya musu girkin da za su ci ba musamman ma saboda abubuwan da su ka yi ta faruwa a gidan, daga baya ma sallamar su aka yi aka bar mace ɗaya da za ta dinga kula da tsabtar gidan. Tana banɗaki wayarta ya dinga ringing amma kuma ba ta fito ba dan ta riga ta tuɓe ta fara wanka. Sai da ta gama ta fito ta duba wayar sai taga miss calls ɗin Farha kusan guda huɗu da kuma na baƙin numbers da ba ta sani ba. Text ɗin Farhan ta karanta kamar haka: *Zaytoonah kar ki yadda ki fito daga gida sai police sun zo Ben ya gudu daga psychiatric* Jikinta ya fara rawa. Ashe ba su rabu da wannan baƙin Mugu ba har yanzu. Tunda aka kama shi aka rage securities na gidan na su sai guda biyu kacal. "Sallallahu Alaihi Wa Sallam" Dada furta lokacin da ta gama jin bayanin da Uncle Aliyu ya ma ta. Ta yi sauri ta kashe cooker ɗin ta wuce ɗaki dan ta tabbatar da lafiyar Zaytoonah. Yanayinda ta sameta ne ya ruɗar da ita. Tana tsaye jikinta na ɓari tana maimaita kalmar "he's going to kill me, he's going to kill me" Dada ta riƙo hannunta tana faɗin "kalleni Zaytoonah, ba abinda zai faru Insha Allahu. Allah zai karemu" Suna tsaye suna jimamin wannan abun ne su ka ji ƙaran halbe-halbe daga waje. Zaytoonah ta ƙanƙame Dada tana kuka ko addu'ar ma ta kasa yi. Dada ma ta tsorata amma ta daure ta dinga jero addu'o'i a bakinta duk wanda ya zo ma ta. Chan ta yi ta maza ta ɓanɓare jikinta daga na Zaytoonah ta je ta rufe ƙofar ɗakin da su ke. Sun dena jin ƙaran halbin yanzu. "Zaytoooooooooonahhhh" Ben ya faɗa tareda ƙyalƙyalewa da dariya. "You better come out now" yai maganar yana haurawa stairs ɗin. "Come out, come out now Fat girl" Ya tsaya baƙin ƙofar ɗakin Zuhayr ya murɗa handle ɗin ƙofar amma kuma ya ji ta a garƙame. Wani mahaukacin dariya yai sannan ya ce ma ta tafito ya kasheta cikin sauƙi ko kuma ta mutu cikin wahala. "I'm going to burn down this house, so come out " Tsabar tsoro sai da Zaytoonah ta saki fitsari daga inda ta ke zaune. Da ita da Dada kowa hawaye ya ke, sun ƙanƙame juna suna zaune a ƙasa a cikin banɗaki. Bindiga ya sa ya fara harbin ƙofar ɗakin sai da ya ma ta kusan harbi bakwai kafin ya sa ƙafa ya ture ƙofar ɗakin sai ga ƙofar ta faɗi. Ya shigo ɗakin yana faɗin "I love him, but you took him away from me. I warned you to stay away from him but you refused to listen" Bai gan ta a ɗakin ba dan haka ya san tana banɗaki. Ya saita bindiga dai-dai ƙofar banɗakin ya ce "for the last time come out" Winwinwinwinwinwin... motocin 'yan sanda su ka iso gidan. Ben yai murmushin takaici. Lokacin da Lawyer ɗin sa ya ma sa hanyar guduwa daga psychiatric ya shirya ma sa komai domin ya bar garin ba tareda an kama shi ba, daga ƙarshe kuma ya bar ƙasar gaba ɗaya. Sai dai abu ɗaya ya hanashi guduwa wato Zaytoonah. Ya rantse matuƙar bai kashe Zaytoonah ba bare bar garin ba. Daga loudspeaker ake ma sa magana ana faɗin ya yi surrender saboda police sun zagaye gidan. Ko zai mutu gara ya mutu da sanin cewa Zuhayr ba zai rayu da Zaytoonah ba. Ƙaran bindigar da aka ji ne ya sa police su ka shigo gidan da gudu. Kafaɗar da Ben ke riƙe da bindigar aka harba hakan ya sa bindigar ya faɗi ƙasa. Ɗaya daga cikin securities ɗin da Ben ya halbe a ƙofar gidan ne ashe bai mutu ba. Security ɗin mai suna Micheal ya ƙariso wajen da Ben ke tsaye yana dafe da kafaɗar sa da ke fitar da jini. Ya nuna shi da bindiga yana faɗin ya ɗaga hannun sa sama. Ben ya ɗaga hannu ɗaya yana huci, Micheal ya ce "move" suna shirin fitowa daga ɗakin Ben ya juyo bazata ya make Micheal hakan ya sa bindigar hannun Micheal ta faɗi nan da nan su ka fara kokawa, daga ƙarshe dai Ben ne ya ɗau bindigar ya sa a ƙeyar Micheal su ka fito waje inda su ka yi kiciɓis da police a bakin stairs. Ben ya nuna mu su idan ba su ja da baya ba zai halbi Micheal wannan ya sa su ka fara yin baya-baya. Ko stairs ɗin ƙarshe ba su kai ba aka harbi Ben ta baya. Daga ƙeyar sa harsashin ya shiga ya fito ta wuya. Ben ya sa hannu a wuyan sa yana ƙoƙarin tare jinin da ke ta ɓulɓulowa amma ina ko seconds goma bai yi ba ya faɗi ƙasa ya mutu. Sai da ya faɗi ƙasa ne police da Micheal su ka kai duban su ga wanda yai halbin. Kevin Dawson ne tsaye da bindiga a hannun sa. Tun mutuwar mahaifinsa sakamakon Bomb ɗin da Ben ya dasa a mota wa Zaytoonah ya ke bibiyar case ɗin, yana son gano waye ya kashe ma sa uba. Lokacin da aka kama Ben aka kuma tabbatar da cewa shi ya kashe Alinah, ya kashe Linda sannan ya zo ya kashe Mr Dawson ya sa a ransa ko da ba a yankewa Ben hukuncin kisa ba shi sai ya kashe shi. Yana bibiyar labarin har sanda aka sanar akan guduwar Ben daga psychiatric, nan shima ya ɗau aniyar indai ya ga Ben to ba makawa harbe shi zai yi. Tun farko Police Asibiti su ka fara zuwa saboda sun ɗauka Zaytoonah na wajen Zuhayr dan sun tabbatar wajen Zaytoonah Ben zai fara zuwa. Sai dai shi Ben yana da masaniyar Zaytoonah ta bar Asibitin shiyasa ya wuce gidan su direct su kuma daga Asibitin ne su ka taho gidan. Babu tsoro ko nadama a tattare da Kevin sai ma murmushi da ya ke yi saboda burinsa na ɗaukar fansar kisan mahaifinsa ya cika. Kafin minti ishirin gidan ya cika da police da ambulance da ma su bincike. An sawa Kevin ankwa an tafi da shi yayinda aka naɗe gawan Ben a cikin baƙin leather jacket da ake saka gawa a ciki aka wuce da shi mutuary... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 40 Bismillahir Rahmanir Rahim *a new beginning* "Karatu a Nigeria sucks Wallahi. Haka kawai ayita abu ba hutu" Auwal da ke sauraron wayar yai ƙaramar dariya ya ce " a hakan ba gashi kin kusa gamawa ba" "Ya Auwal ba za ka gane bane" "Ki ji ki dai. Ni ma fa na yi Makarantar" " ni kam ina ganin a lokacin na mu karatun ya fi wahala" ya kwantar da kan sa a kujerar office ɗin yana cigaba da jin ƙorafin Zaytoonah. Tunda ta fara Law school na Abuja ba randa za ta zo gida weekend ko kuma su yi waya ba ta yi ƙorafin wahala ba. Da gaskiyarta dan karatun da ta yi a turai ya banbanta da nan Nigeria. Yayinda su suke ƙoƙarin sauƙaƙawa ɗaliban su ta inda karatun zai zo mu su da sauƙi a nan kam Karatu mai takuri ake yi wanda ke stressing mutum to the core. Ƙarfe biyar ya shigo falon Mommy wanda tunda ya parker machine ɗin sa a compound ɗin gidan ya ke jin hayaniyar jikokin Mommyn. Kokawa su ke a kan remote ɗin TV wannan na faɗin ga inda za a kalla wannan ma na cewa bai yadda ba nashi tashar za a kalla. Suna jin sallamar sa su ka sake remote ɗin su ka zo da gudu su ka rungume shi. "Uncle Auwal Oyoyoooo" Auwal ya tsugunna dai-dai tsayin su ya sa hannu ya rungume su. Yana son yaran sosai ji ya ke tamkar shi ya haife su balle dama 'yan biyu da su ke da shiga rai. Fraternal twins ne dan ba za ka ɗauke su 'yan biyu ba ma, tsayin su dai ɗaya ne, kalar idanun su ɗaya, sai muryoyin su ma ɗaya, dukkan su sun ɗauko blue eyes ɗin Zuhayr. Shi Muhammad Hashir ya fi kamaceceniya da Zuhayr duk dama ya fi ɗauko yanayin fiskar Lucile-Abigail wato mahaifiyar Zuhayr, amma Ahmad Hadid kamannin mahaifin Zuhayr ya ɗauko wato ta sashen Alhaji Iliyasu dan da ka ganshi ka san jinin gidan ne. "Uncle Auwal Chocolate" su ka haɗa baki su ka faɗa. Ta ɓangaren ciye-ciye kam Maman su Zaytoonah su ka ɗauko. Ya fito da chocolate biyu ya bawa kowa ɗaɗɗaya. "Ina GrandMa?" "Tana kitchen" Barin su yai ya shige kitchen ɗin tareda sallama. Mommy ce tsaye gaban gas cooker tana duba abu a waya, da ke hankalinta yayi nisa ba ta ma lura cewa ba ta rufe miyar da ke kan wuta ba, yana ta simmering har ya fara fatsuwa a jikin gini da gefe-gefen wajen. "Mommy barka da yammaci" maganar da ta dawo da Mommyn kenan daga duniyar yanar gizo. "A'a son yaushe ka shigo?" Ta yi maganar tana saurin rufe tukunya. "Yanzun nan na ƙariso, na ɗauka ma ko kin ji mu da 'yan biyu" "Hankalina baya wajen. Ya aiki?" " a bit stressful amma Alhamdulillah" Mommy ta ma sa fatan alkhairi. Shekara ɗaya da rabi kenan da fara aikin sa bayan ya kammala degree da kuma Law school ɗin sa. Barrister Auwal Usman Abubakar kenan saurayi ɗan ƙwalisa. Yana da kyau, ilimi, tsabta ga uwa uba kamala. Cikin shekaru huɗu da Zaytoonah ta haihu abubuwa da dama sun faru. Ciki kuwa har da chanjin yanayi da su Iya su ka tsinci kan su. Rana ɗaya Alhaji Rabi'u ya zo ya ce ya ba su sati biyu su tattara su bar gidan Muntari domin shi ya riga ya saida gidan. Iya ta buɗi baki tana Allah wadarai da halin sa amma ya nuna ko ajikin sa har da ce ma ta ai tun farko a gidan T J take amma kwaɗayi ya sa ta komawa gidan Muntari. Abun wasa su ka ɗauka sai da sati biyun su ka cika aka kawo mu su notice kan cewa su fita daga gidan ko kuma dai a haɗa su da hukuma. Iya sai da ta yi kuka lokacin da aka ce mu su an ƙara mu su kwana uku. Ta kira gida tayi ƙorafi, hatta mahaifin Rabi'un ta kira shi ta sanar da shi abinda ɗan sa ke shirin yi amma sai ya nuna ma ta ai da gaskiyar sa tunda dai babu Muntari a gidan ba su da ikon zama su uku kacal a wannan makeken gidan gara a siyar idan ya so ayi jari da kuɗin a dinga juyawa kafin Muntari ya dawo. A lokacin Iya ta gane cewa cin amana ba shi da alaƙa da addini ko yare domin kowa na iya yi. Tun kafin ya zo zancen sai da gida ya riga ya dena tura mu su kuɗin da ya ke ba su duk wata. Abinda ma Iyan ba ta sani ba shine tuntuni Maryam 'yar Mukhtari Mommy ke biya ma ta kuɗin makaranta ba wai Rabi'un ba kamar yadda ta ke tunani. A waɗanda Iyan ta kira cikin 'yan uwanta da ta san sun ɗan yi Boko shine aka ba ta shawara akan su kai ƙaran Rabi'u saboda a bi mu su hakkin su. Da ta yiwa Hanne magana Hanne ta ce ita ba ta da kuɗin ɗaukan lawyer itama tun da aka rufe Muntari ita ke fama da biyawa kanta kuɗin makaranta da sauran hidimomi kuma yanzu da ta ke ajin ƙarshe ma tana buƙatar kuɗi ga kuma kasuwancin na ta ya ja baya. Bayan dogon nazari da Iya ta yi sai ta tuna cewa ai Maryam ma tsohuwar Lawyer ce ko ba ta taimaka mu su bama za ta haɗa su da wanda zai taimaka mu su. Kamar yadda har yanzu girman kai ya hanata baiwa Maryam haƙuri balle har ta jata a jiki hakan ya sa ta kira Maryam a waya tana ma ta maganar halin da ake ciki da kuma taimakon da ta ke so ta mu su. Maryam ta san komai gameda abinda ke faruwa saboda Hanne ta gaya ma ta har ma sun tsaida matsaya kan abinda za ayi. Bayan Maryam ta gama sauraron bayanin Iya sai ta ce " ba ni da hurumi da dukiyar Muntari, da dukiyar Tijjani ne zan iya yin komai akai amma wannan ba hurumina ba ne. Idan ba ki manta ba, farkon lokacin da aka rufe Muntari na zo miki da wata magana kan abinda Rabi'u ya ke shirin yi amma kika zageni tatas kika nuna nine ummul aba'isil duk abinda ya faru har kike iƙirarin Rabi'u ɗan uwa na ƙwarai ne, to gashi yau Allah ya bayyana gaskiya tunda dai abinda na ke gudu mu ku tun farko sai da ya faru. Kuma..." Iya ta kashe wayar dan ba za ta iya cigaba da sauraron maganganun Maryam ba. Tabbas maganarta babu ƙarya a ciki tunda anyi hakan amma a lokacin haushin Maryam da ta ke ji ya sa ta ƙi sauraron shawaran da Maryam ta kawo balle har ayi aiki da shi, bata ma yarda da zargin Rabi'un da ta ke yi ba a lokacin. Abinda kuma ba su sani ba shine tuntuni Rabi'u ya sa aka chanjawa Muntari Prison. Da farko a Kaduna ya ke amma yanzu dukkan su babu wanda ya san inda aka maidashi. Shi yanzu ma burinsa bai wuce Muntari ya mutu ba ko kuma dai ya cigaba da zama a kurkuku har mutuwar sa. Baya tunanin ko da wasa zai iya maidawa Muntari dukiyar sa a yadda yake jin sa yanzu ne ya san jin daɗin rayuwa. Maganar komawa Ringim ta yiwa Hanne sai Hanne ta ce "Maryam ta ce mu koma gidan Hamma Tijjani. Jiya wanda su ke zaune a ciki suka tashi yau za ayiwa gidan kwaskwarima gobe sai mu koma" Iya ta sauke ajiyar zuciya tunda dai an samu maslaha dan dama niyyarta Humairah ta koma wajen Maryam ne saboda karatunta ita kuma sai ta koma Ringim. A haka Hanne da 'yarta, Humairah da kuma Iya su ka koma gidan Tijjani wanda Hajjo ta zauna da. Kasancewa dukkan su mata ne ya sa Mommy ta ce Auwal ya koma gidan saboda tsaro bai so ba amma kuma ba yadda ya iya. Cikin ikon Allah Hanne ta kammala karatunta har ta yi bautar ƙasa a Nasarawa state da ta dawo kuwa zawarawa da samari su ka ma ta chaaaa. Tun shekara ɗaya da rufe Muntari ta je kotu aka warware auren su. Aikin koyarwa ta samu a wani makarantar Sakandare ta gwamnati, ta yi shekara tana aiki kafin ta yi aure, ta auri Wani Lecturer da ke KadPoly mutumin Zaria ne amma a Kaduna ya ke zaune da matar sa ɗaya. Ita dai Hanne tana zaune a gidan sa na Zaria yana zuwa ma ta a weekend ko ita ta je. Aiki ma yake nema ma ta da ta samu a Kadunan sai ta dawo chan amma yanzu samun aikin gwamnati na da wahala. Da ke ba sa shiri da matar sa Zahra shiyasa ma ba ta takura da komawa Kadunan ba dan zamanta a Zaria ya fi ma ta kwanciyar hankali. *** Iya na zaune a falo tana kallo lokacin da yai sallama ya shigo falon. Humairah tana kwance a three sitter sanye ta ke da riga mai hannun shimi ja sai baƙin jeans, kanta babu ɗankwali ta sha kitson brazillian wool wanda aka ƙarashi ya sauka har tsakiyar bayan ta, abu ɗaya da ke tauye mata zama cikakkiyar Fulani kenan a idon mafiya yawan jama'a saboda Allah bai bata gashi ba. Gata fara doguwa sirirya mai dogon hanci zubin Fulani amma gashin kam suɗal ya ke, yaƙi yin gaba kullum dai hakan nan ya ke. Akwai lokacin da ta yi ta kashe kuɗi wajen siyan magungunan ƙara gashi su Chebe and co, amma da gashin ya ƙi responding sai ta shareshi ta koma saka brazillian wool da kuma wig duk da kuwa abunda Hamma Auwal ɗin ta ya ƙi jini kenan. Ta saka headphone a kunne tana sauraron waƙa yayinda idonta ya ke bin kowani layi na rubutun labari da ta ke karantawa a waya. "Ban hanaki zama a cikin gida haka ba?" Auwal ya daka ma ta tsawa. Ta yi saurin cire headphone ɗin dan ba ta ji mi ya faɗa ba inuwar sa kawai ta gani "Hamma sannu da zuwa, ya office?" "Ki je ki rufe kan ki sannan ki chanja riga ko kuma ki saka hijabi" "Hamma zafi ake yi" ta zumɓuro baki tana shagwaɓa. Bai kulata ba ya wuce ɗaki saboda a gajiye ya ke baya son magana... Kamar yadda su ka saba al'adar su ta cin abinci tare yau ma dukkan su biyar suna zagaye gaban tray suna cin shinkafa da miyan sauce ɗin manja wanda ya ji busashahiyar kifi. Tsabar rigima maimakon su nitsu su ci abinci kowa ya ci gaban sa sai kaga wannan ya tsakuri gaban wannan wannan ma yayi hakan. Wani ƙaton lomar kifi Hashir ya ɗauke daga gaban Hadid sai Hadid ya riƙe cokalin yana faɗin "put it down" Hashir ya sa hannu yai saurin ɗauke kifin zai kai baki sai Hadid ya riƙe hannun. "GrandMa Hashir wants to take my fish" Kafin ta yi magana Salman ya sa yatsa ya talli fiskar Hashir sannan ya yiwa Hadid yana faɗin kowa ya ci gaban sa baya son rigima. Dama Uncle Salman ne maganin su a gidan dan Uncle Auwal baya taɓa su amma Salman har xanesu yanayi. Hadid ya tashi ya dawo gefen Mommy ya zauna ya fara cin abinci yana yiwa Hashir gwalo. Sai shima Hashir ya taso ya zo gefen Mommy ya zauna ya fara cin abinci yana nunawa Hadid Harshe. Su ka koma ba ma abincin su ke ci ba sai gwalo da zare ido da su ke yiwa juna. Sai da Salman ya daka mu su tsawa kafin su ka nitsu. Duk rigiman su Mommy ba ta iya dukan su ko ta ce za ta basu punishment. Tausayi su ke ba ta, yaran kaman ba za su yi rai ba watannin farko na haihuwar su saboda Zaytoonah ta haifesu ne lokacin da take fama da Post traumatic stress disorder (PTSD) ƙarshe lokacin da ake yiwa Zaytoonah therapy yaran kam Madara aka koma basu. Ashe ba mutuwar Zuhayr kaɗai ya girgiza Zaytoonah ba. Long time effects na tsoratarwa da kuma abubuwan da Ben yayi ta yi ya shafi ƙwaƙwalwar Zaytoonah. Idan abinta ya tashi mantawa ta ke yi Ben ya mutu hakanan ma Zuhayr ɗin ta shima ya mutu. Complete wata shida ta yi tana attending theraphy da farko a wajen Doctor Malak lokacin suna Saudiyya daga baya da su ka koma America kuma Dr Rerdon ya dinga kula da ita. A hankali da yardar Allah ta fara samun sauƙi. Kamar a mafarki haka ta tashi watarana ta shirya ta wuce makaranta, ta loosing semester ɗaya amma ba ta damu ba dan ta ɗau aniyar ƙarisa karatun ta kamar yadda ta yiwa Zuhayr Alƙawari. Hatta Ballet dance da ta ajiye gefe tuntuni sai da ta re-enrolling ta fara attending class. Yaranta na samun kulawan da ya kamata a wajen Dada duk lokacin da Zaytoonah ke makaranta suna maƙale da Dada ko kuka ba sa yi sai dai yunwa da an basu abinci kuma shikenan. Daga lokacin da su ka fara rarrafe ne kuwa ƙiriniyar su ta fara fitowa har yau kuma da su ke shekaru huɗu a duniya. Da ke duk wani abinda zai tada ciwon Zaytoonah ana kiyayewa shiyasa ma yanzu abin ya yi kusan shekara bai tashi ba. Taƙare degree ɗin ta inda ta fara Law school na ta a Abuja. Dawowan ta Nigeria ne ta dawo tareda 'yan biyun ta duk da kuwa da farko Uncle Aliyu ya so ta bar yaran a wajen sa. Dukkan su a gidan Mommy su ke zaune sai dai duk weekend a gidan Kakannin su su ke yin sa wani lokaci haka kawai ma sai su bushi iska su tafi gidan Baba tsoho ko kuma idan Salman ya dake su sunyi fishi sai su yi yaji su tafi chan gidan. Babban burin Mommy shine ta ga Zaytoonah ta zama cikakkiyar Barrister saboda akwai aikin da ta tanada ma ta... Abbati ne ya tiso ƙeyar Hashir da Hadid har cikin gida. Jikan gidan Baba Tsoho ne shima. Idon su yayi wuri-wuri. "Abbati lafiya, mi su ka yi?" Zaytoonah kenan ta yi maganar saboda ta san halin 'Ya'yan na ta. "Anty Zaytoonah yaran nan fa su ka takura wai sai na tafi da su masallaci wajen wazifa. Ashe sun san abinda su ka shirya ne. Muna cikin wazifa su ka je su ka zubawa Zakiri Aminu cirnaku a kan sa da cikin rigan sa" Yana maganan Hashir da Hadid na girgiza kai saboda sun san kashin su ya bushe a wajen Mom. Dan ta hanasu irin wannan, akwai lokacin da su ka je su gidan cirnaku irin sun firfito dayawa ɗin nan suka dinga tsinta suna sakawa a leda. Da dare da Salman yai bacci su ka je su ka zuba ma sa a jiki da kan gado, cirnaku su ka yi ta cizon sa. Da farko ya ɗauka ma sauro ne sai da ya ji zafin yayi yawa kuma cizon ba waje ɗaya ba sannan ya tashi ya je ya kunna wutan ɗakin ai kuwa ya ci karo da cirnaku akan gado wasu kuma sun riga sun sauka ƙasa, ya dinga tsalle yana karkaɗa jiki a ɗaki daga baya ma sai da ya je yai wanka dan ganin su da yai dayawa haka sai tsikar jikin sa ya tashi. Ya duba ko'ina a ɗakin amma bai ga alamun ta ina cirnakun su ka shigo ba ƙarshe ya sa a ran sa cewa 'yan biyu ne tunda da yammacin ranan ya dake su... Wani kallo da ta wurga mu su ya sa suka yi kneel down a wajen ba shiri. "Ban hanaku zuwa tsince cirnaku ba? Ban hanaku sawa mutane cirnaku a jiki ba?" "Mom shi ne Malam Aminu mai murɗe mana kunne a Makaranta kuma..." "Shut up!. Ai na gane shi sarai. Shine ya kawo ƙaran ku kwanaki akan ba kwa mai da hankali a karatu kuma kuna damun yara a makaranta" Ta kalli Abbati ta ce ma sa ya bawa Malam Aminu haƙuri za ta aika Salman idan ya dawo ya bashi haƙuri. Bayan tafiyar Abbati Zaytoonah ta kalli 'yan tagwayen 'ya'yan na ta. Yadda Mommy ba ta duka haka itama ba ta yarda da dukan yaranta ba sai dai ta basu punishment ɗin abinda ba sa so mafiya yawanci kuwa ta fi sa su yin rubutun Allo tunda ba sa so. Sun sha cewa ma ta cire su a makarantar Allon amma ta ƙi. Baba Tsoho (Alhaji Iliyasu) ne ya saka su da kan sa tun ma kafin ta sasu a Islamiyya. Ta cigaba da karatun da take yi saboda exams ne a gaban su. Exam ɗin da daga shi idan har ta haye shikenan sai ayi call to Bar. Hashir da Hadid kuma sai ƙunƙuni su ke yi kowa da Allo a hannun sa yana rubutu. Sau goma ta ce za su cika Allon amma a na ukun da su ke rubutawa Mommy ta dawo ta ce rubutun ya isa haka tunda dai sun ba da haƙuri. Ko da wasa Mommy ba ta son a takurawa jikokin na ta. Ana gobe Zaytoonah za ta koma school lokacin Mommy ta tafi Ringim 'yan biyu su ka shirya plan ɗin su. Goggo ne ba lafiya kusan cikin 'yan watannin nan ma sintirin Asibiti ake yi da ita yanzu ma ba a jima da maida ita gida ba bayan tayi kusan sati uku tana kwance a Asibitin Murtala da ke Kano. Babu wuta dan haka generator ne ke aiki tuntuni saboda Zaytoonah na tsoron duhu. Tana cikin banɗaki tana Alwalar da za tayi sallar Isha Generator ya mutu. Hashir da Hadid ne su ka je su ka kashe switch ɗin tunda sun san yadda ake kashewa suna gani idan Junior ko Salman na yi. Ƙoƙarin fitowa ta yi daga banɗakin da sauri tunda ta san mi duhu ke jawo ma ta shiyasa ko ba wuta su kan kwana da Gen a kunne. Da lalube ta buɗe ƙofar banɗakin ta fito a hankali ƙirjin ta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi. Turo ƙofar ɗakin da aka yi a hankali ya sa ta daskarewa a wajen jikinta ya fara maƙyarƙyata. Maimakon a shigo ɗakin sai aka sake jawo ƙofar da ƙarfi ta yi ƙara baaam. "Zuhayr, Zuhayr, help! Ben zai kashe ni. Ben is here. Zuhayr, Zuhayr" Tana ƙwala kiran Zuhayr Yaran nan na bakin ƙofa suna wasa da shi su buɗe su kulle. Sai dariya su ke ƙasa-ƙasa yau kan sun yi maganin Mom. Dawowar Salman daga wajen kallon ƙwallo ya ga gidan da duhu ya je wajen da ake ajiye generator ya gan ta a kashe amma kuma ma ba a kashe wajen mai ba balle a cire waya kawai switch ɗin aka kashe. Yai saurin tada Generator ɗin dan ya tabbatar da lafiyar Gen ɗin ai kuwa Gen ya tashi lokaci guda. Hashir da Hadid na jin an kunna Gen su ka yi saurin guduwa zuwa ɗakin su har da ɗauko littafi suna karatun ƙarya dan sun san ba makawa Uncle Salman ne, Junior Zaytoonah ta aikeshi chan ta ƙasan layin su. Ɗakin Zaytoonah ya fara shiga dan ya tabbatar da lafiyar ta, ai kuwa a sume ta sameta a ƙasa. Yai saurin kaiwa wajen ta yana kiran sunan ta da ƙarfi. Jin yanda Salman ke kiran sunan Mom ɗin su ya sa su ka ajiye pretence ɗin su ka shigo ɗakin da gudu. Suna son Mom ɗin su sosai kawai rigimar yaran ne ta yi yawa. Suna ganin Salman na shafawa Zaytoonah ruwa a fiska su ka tsugunna a wajen suna kuka suna faɗin we are sorry Mom. "Ku ne ku ka kashe Gen ko?" Salman ya daka mu su tsawa. Ba su bashi amsa ba sai ma ƙara sautin kukan su da su ka yi. A hankali Zaytoonah ta buɗe ido tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, ganin fiskar Salman ya sa hankalin ta ya kwanta ta kira sunan sa a hankali "Salman" Salman ya so dukan yaran amma Zaytoonah ta hana shi. Sai ma jawo yaranta da tayi jiki tana rarrashin su. "Miya sa ku ka tsoratar da ni?" Ta yi tambayar tana kallon yaran na ta ɗaya bayan ɗaya. Wanka ta mu su ta shirya su cikin kayan bacci. Maƙale ma ta su ka yi wai tare za su kwana a maimakon ɗakin su da su ke kwana da junior. Kallon-kallon su ka tsaya yi kafin su ka ce ma ta saboda ta sa su rubutun Allo ne. "Kuna so na tafi Aljannah wajen Dad ɗin ku na bar ku a nan?" "No Mom" su ka faɗa da sauri "To ku dena tsoratani kun ji. Duhu yana sani rashin lafiya" Sorry Mom su ka faɗi tareda shigewa jikinta. Daren ranan tare da su ta kwana ɗaya na gefenta na hagu ɗaya a na dama. Ta rungume su a hakan su ka yi bacci. 'Yan biyu sun gane illar da duhu ke wa Mom ɗin su ne farkon dawowan su Nigeria lokacin suna shekara uku. Ana tsakiyar kallo a falo da dare kwatsam sai Nepa su ka ɗauke wuta. Mommy ba ta falon Zaytoonah ce da 'yan biyunta sai Junior. Hashir da ke gefenta ne mistakenly ya ɗaura ƙafar sa akan na ta ƙafa shikenan hankalin ta ya tashi ta shiga maƙyarƙyata ta fara kiran sunan Zuhayr. Mommy da ke sallah a ɗaki sai jin ihun Zaytoonah ta yi tana kiran sunan Zuhayr da ƙarfi, Zuhayr ɗin da ya jima a cikin ƙasa. Ba shiri ta yanke sallar ta fito daga ɗaki da torchlight a hannunta. Yadda Zaytoonah ta takure kan kujera tana maƙyarƙyata ka ɗauka wani Aljani ta gani. Sai da ta rungumeta ta dinga ce ma ta nine, nine Mommy kafin da ƙyar hankalinta ya dawo jikinta. Ranan kam Mommy ta ja Allah ya isa wa Ben yafi a irga. Duk treatment ɗin da ake ma ta farko-farkon haihuwar Zaytoonan da har ake tunanin ko haukacewa ta yi Mommy ba ta taɓa tunanin abin haka ya ke ba. Dada ne ta san komai gameda rashin lafiyar Zaytoonah saboda kar ta tada hankalin Mommy ba komai ta ke faɗa ma ta ba. Bayan ta koma Las Vegas Mommy ta je ta dubata sau ɗaya kuma lokacin ta fara samun sauƙi dan haka ba ta ga irin halinda Zaytoonah ke shiga ba idan ciwonta ya tashi... Washegari 'yan biyu su ka tsitsiye wai dole sai sun bi Mommy zuwa Abuja. Yadda su ka takure su ka yi kalar tausayi ya sa ta amince ta tafi da su akan za su yi kwana ɗaya sai su dawo tunda akwai school... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 44 Bismillahir Rahmanir Rahim *panic attack* Kusan awa ɗaya da rabi sai ga kiran Ahmad ya shigo wayar lokacin suna ma cin abinci a dining. Bayan ta amsa ne ta ce ma sa tana zuwa. Yunƙurin tashi ta yi Muhsina ta ce ta tsaya ta ƙarisa cin abincin tunda ta kusa gamawa. Reluctantly dai sai ta zauna ta ƙarisa abincin, da ta gama ta shiga ɗaki ta saka hijab ta fito. Tana shiga motar Ahmad ya sa dariya. "Ikon Allah, Ashe wayar Uncle Justice kika ɗauka. Wai ya abin ya faru ne?" "Dole ka yi dariya ai, Mugu" Sai da ya sake dariya kafin ya miƙo mata wayar ta yana faɗin " ga wayar ki inji Uncle" Ta harare shi kafin ta amshi wayar wanda ɗan awa uku zuwa huɗu da yai a wajen Justice har ya ɗauki irin ƙanshin turaren sa. Ta miƙa ma sa wayar Justice tana bashi labarin ƙatoɓarar da ta yi ɗazu. "Wai ni kam waye ce Hajia Ghazalan nan ne?" Hajia Ghazala, Ahmad ya maimaita sunan kafin ya ce " Okey! Ƙanwar matar Uncle ce" "Ko da ita za mu sha biki ne" Zaytoonah ta yi maganar tana dariya. "To waya sani ne, kin san Justice ɗin ne sai a hankali ba a iya gane mishi" Sun ɗan taɓa hira kafin ya tafi. Bayan ta shiga gida ne ta duba call log ɗin ta inda ta ga kiran Mommy da na Auwal kuma duka biyu an amsa kiran. Ko mi ya ce mu su oho ta faɗa a zuciyar ta. Mommy ta fara kira, gaisawa ce dama za su yi ɗazu da kuma 'yan biyu da su ke son gaisawa da Mom ɗin su, a lokacin kuma Justice ya ɗauka ya ce ba ta kusa idan ta dawo za ta kira. Sai da ta yi murmushi kafin ta sanar da Mommy yadda abin ya faru har da irin katoɓarar da ta yi. 'Yan biyu sun bi Salman zuwa masallaci dan haka ta ce za ta kira anjima. Da ta kira Auwal bai ɗaga ba sai tayi tunanin ko yana sallah ne shima dan haka itama ta ajiye wayar ta shiga banɗaki. Sai kusan ƙarfe tara na dare sai ga kiran Auwal, lokacin ma karatun wani littafi ta ke yi. "Ba dai kin yi bacci ba?" "A'a karatu na ke ma" A bazata ta ji ya ma ta wani tambaya wanda ta rasa dangantakar tambayar da ita. "Ashe Justice bai da mata?" Sai da tayi shiru na 'yan sakanni kafin ta ce "Eh haka na ji nima" Shima ɗin ya ɗan yi shiru dan wani kishi da ke cin sa tun lokacin da yai waya da Justice. Shi duk bai ma san wani Justice ba ne sai bayan da su ka yi wayan ne daga baya a fakaice da ya je wajen Mommy ya ke tambayarta. Tunda ya ji Justice shine Galadiman Zazzau hankalin sa ya ƙara tashi. Bai yiwa Justice mummunan zargi ba saboda a iya labarin da ya sani gameda Galadima shi mutum ne na gari, mutum ne da kowa ke ma sa shaidar alkhairi. Sai dai aiki da Zaytoonah ke yi a ƙarƙashin sa da kuma amsa wayar ta da yai ɗazu shi ya ƙwaƙwalwar sa ke riya ma sa wani abu nan take kuma zazzafan kishi ya mamaye ilahirin jikin sa. Yana son Zaytoonah tun da daɗewa, yanzu da wani dama ya sake zuwa ma sa ba zai taɓa bari damar nan ta kubce ma sa ba. Ya yi shiru ne da maganar zuwa a gama case ɗin Mommy amma kuma yanzu yana ganin gara ya bayyana sirrin zuciyar sa tun kafin ya ƙara rasata a karo na biyu. "Da alama dai ba kya kusa ne Justice ya amsa wayar ki ɗazu da yamma" Tunowa da abinda ya faru da ta yi ya sa ta yi dariya, sai dai dariyan da ta yi ya kara rikitar da Auwal tareda ɗaure ma sa kai. Sai da ta bashi labarin abinda ya faru ya ɗan ji sanyi kaɗan a ran sa amma duk da haka zuciyar sa ba ta dena zargin wani abu ba.... *** A lokacin da Hajia Ghazala ta dinga kiran numban Justice ba a ɗauka ba hauka ne kawai ba ta yi ba saboda yadda ƙwaƙwalwarta ke ayyano ma ta abubuwa mabanbanta lokaci guda. Tayi tunanin ko sace wayar sa aka yi, ko kuma wayar ce ta faɗi aka ɗauke, ko kuma dai yana tareda wata ce ta ɗau wayar. A lokacin mantawa ta yi da cewa tanada ɗaya numbar Justice ɗin wanda layin a ƙaramar waya ya saka ta. Boutique ɗin ta za ta je amma fasawa ta yi ta karya kwana ta wuce gidan Justice zuciyarta cike da tararradin abubuwa. Ganin yaran sa ya sa ta ɗan saita nitsuwar ta tareda nunawa kaman dan su ɗin ta je gidan. Sai da su ka zazzauna kafin ta tambayesu ko Baban su bai dawo ba kuma tana kiran numbar sa baya shiga. Raziya ta ce ta gwada ɗaya layin sa ta gani, sai a sannan ta ankara da cewa ashe layikan na sa biyu ne. Ta ɗauko waya ta kira ɗaya numbar, kuma bugu ɗaya aka ɗauka. Jin sallamar Justice ne ya sa kaso tamanin na damuwar ta ya tafi. "Ranka shi daɗe ɗaya numbar ka kamar ba ta shiga, hala ka manta a office ne" ta yi maganar bayan sun gaisa. "Ba ta hanuna" abinda ya faɗa kenan wanda hakan ya ɗaure ma ta kai. Ta sani ba zai ma ta dogon bayani ba shiyasa ta tsayar da maganan a haka amma zuciyar ta yana cike da tarin tambayoyi. Tana gidan har Auwal ya kawo wayan Justice, dan sun rabu da Justice bayan ya bashi wayar Zaytoonah akan zai je Asibiti duba wani marar lafiya. Ahmad yai wa Hajia Ghazala bayanin yadda aka yi suka yi exchange ɗin waya tareda Zaytoonah. *Zaytoonah* ta maimaita sunan cike da ayar tambaya na son sanin mai wannan suna. Washegari da Zaytoonah ta je office ƙoƙarin dodging ɗin Justice ta yi wanda tunda ya zo ko minti talatin bai yi ba ya wuce court saboda suna da zama, hakan ya bawa Zaytoonah daman watayawa yadda take so. Bayan kwana uku ranan Alhamis sai ga Hajia Ghazala a office ɗin Justice. Bayan ta samu ganawa da Justice ne ta ma sa maganar Anwar da ke neman 'yar ta Husna. "Na ce ko zan turo shi wajen ka dan ka assessing na shi, ka san samarin yanzu sai a hankali" A iya sanin sa dai mahaifin Husna Alhaji Bashir na raye haka nan 'yan uwan sa na nan. " ki yi haƙuri, amma ban da lokaci gaskiya. Ina ga dai su Alhaji Bashir za su yi binciken daya dace akan sa. Ke dai ki yi istikhara ki kuma sa ta a addu'o'in ki, ina ga Insha Allahu komai zai zo da sauƙi" Godiya ta ma sa kafin ta fita daga office ɗin da niyyar za ta gaisa da Ahmad. Dama musabbabin zuwan ta ba wai dan maganar saurayin Husna ba ne ta zo ne dan ta ga Zaytoonah. Office ɗin su Ahmad da aka nuna ma ta nan ta shiga tana wani shan ƙamshi. Su biyu ne a office ɗin Ahmad da wani. Bayan ta gaisa da su ne take tambayar sa ina mutumiyar sa ne. "Yanzu ta fita kuwa ta je office ɗin Barr. Noah, barin kira miki ita" ya fita daga office ɗin da zumuɗi. Minti biyu da fitar sa sai ga shi ya shigo, kallon yarinyar da ta biyo bayan sa ta ke yi, kallo irin na ƙurilla. Yarinyar ba wata Babba bace dan ba ta tunanin za ta kai 25yrs ma. Girman jiki kawai gareta. Duk da kasancewar ta mai ƙiba hakan bai ɓoye kyaun ta ba, tsayin da ta ke da shi ya ɗan ɓoye ƙiban na ta, baƙa ce amma irin baƙin da kallo ɗaya za ka kira su da Black Beauty. "Ina wuni Hajia" Zaytoonah ta katse ma ta tunanin ta. "Lafiya" Hajia Ghazala ta amsa tana sake fuska. Ba wata doguwar magana su ka yi ba Hajiar ta tafi. Sai da ta tafi ne Zaytoonah ke cewa Ahmad gaskiya Hajia Ghazala ba ƙaramin dacewa ta yi da Justice ba, har da cewa Hajia Ghazala ta ma ta kyau. Shima dai Ahmad ɗin hakan ya gani sai dai ƙila kasancewar ta ƙanwar matar Justice ya sa ba ya ma ta wannan kallon. Ranan Jummu'ah ta haɗa report ɗin ta kenan sai ga kiran Mommy. A yadda ta ji muryan Mommy sai ta yi tunanin kamar ba lafiya ba. Tambayarta ta yi ko za ta zo weekend ta ce ma ta za ta zo. Allah ya kawoki lafiya ta furta sannan ta kashe wayar ko sallama babu hakan ya sa ta ji zuciyar ta ya yi rauni. 'Something is wrong' ta furta a fili. Kai tsaye sai ta kira wayan Salman amma ba a ɗauka ba. Ta tura ma sa saƙo akan ya kirata. Bayan ta yi sallar Isha ne ta buɗe whatsapp ɗin ta dan tun safe ba ta hau ba. Wajen status da ta duba ne ta ga Salman da Auwal duk sun ɗaura hoto iri ɗaya kuma kamar hoton Goggo ne. Tana buɗe hoton sai ta ga abinda aka rubuta a jikin hoton Goggon wanda ya girgiza ta. Lokaci guda hawaye su ka fara kwaranya a idon ta. "Goggo ta rasu" ta furta tana tuno kyawawan halayen wannan tsohuwa. Numbar Mommy ta kira ba a ɗaga ba sai a kira na biyu wanda Hashir ya ɗauka yana faɗa ma ta GrandMa na waje tareda Uncle Auwal, yaran ne su ka ma ta gulmar wai yanzu su Mommyn ke shirin tafiya Ringim, harda cewa ɗazu GrandMa ta dinga kuka. Tabbas dai Goggo ta bar duniya. Salihar Mata wacce har yau ita Zaytoonah ke gani a matsayin Kaka... Bayan Ahmad ya zo gidan ne ta bashi flash akan ya je ya turawa Justice report ɗin ta dan tafiya gida za ta yi an mu su rasuwa ba ta tunanin za ta dawo da wuri. Bayan ya ma ta ta'aziya ne ya ce " da dai kin kai ma sa da kan ki dan Justice yanada wuyan sha'ani zai iya cewa ba za karɓa ba" Da farko Zaytoonah ba ta yarda ba amma daga baya sai ta amince amma da sharaɗin Ahmad ɗin ne zai kai ta gidan ya kuma dawo da ita gida dan ba ta tuƙi da dare. Mai aiki ce ta buɗe mu su ƙofa ta kuma sanar da su Justice bai dawo daga masallaci ba. Zama su ka yi a falo suna jiran sa, bai jima ba sai gashi ya dawo sanye da farar jallabiya wacce ta zauna ma sa dai dai jikin sa. Suna ganin sa su ka miƙe suna gaishe shi. Sau ɗaya ya kalli Zaytoonah ya kuma kauda kai ya maida duban sa ga Ahmad wanda ke ma sa bayanin dalilin zuwan su. Yadda ya ga idon Zaytoonah a kumbure ya isa ya tabbatar ma sa wanda ya rasun na kusa da Zaytoonan ne sosai. Bayan ya gama jin sa ne ya yiwa Zaytoonah ta'aziya tareda haurawa sama dan ya ɗauko laptop ɗin sa. Yaran sa ba sa nan sun wuce Zaria tareda Hajiya Ghazala ɗazu da rana bayan sun dawo daga school. Shima zai je amma sai gobe dan zai tsaya ya attending auren 'yar abokin sa tukunna. Suna zaune sai Ahmad ya miƙe akan zai yi fitsari. Ɗakin baƙi da ke ƙasa ya shiga, da ya fito ya ga Zaytoonah na zaune tayi tagume. Tsokalar ta yai niyyan yi dan haka ya ƙarisa wajen switch na wutan falon ya kashe. Zaytoonah na zaune ta yi nisa cikin tunani sai kawai ta ga duhu. Nan da nan hankalin ta ya tashi numfashin ta ya fara fita da sauri-sauri. *ZAYTOONAH* aka kira sunan ta a hankali. Ta wajen da ta ji kiran ta juya ta ga kamar alamar mutum ta wajen labule. Fuskar Ben kawai ta ke gani na ma ta yawo a idonta. Ta ƙwalla ƙara wanda sai da dukkan gidan ya amsa. Tashi ta yi tana tafiya da baya-baya. "Zuhayr save me, he's going to kill me Zuhayr. Save me, save me" Jin kalaman ta ya sa Ahmad yai saurin kunna wutan. A takure jikin bango ya hango Zaytoonah tana maƙyarƙyata tana sunbatu. Da gudu Justice ya fito daga ɗaki jin ihun Zaytoonah. Ahmad da mai aikin sa ne a gefen Zaytoonah suna tsaye suna ma ta magana amma sai baya takeyi jikin ta na kakkarwa kamar tsoron su ta ke yi. "Uncle kamar ba ta da lafiya" Ahmad ya faɗa lokacin da ya ga Justice. Kiran sunan ta yai a hankali kuma a dai-dai lokacin wutan gidan ya ɗauke gaba ɗaya. Hakan ya sa Zaytoonah ta sake birkicewa tana kuka tana kiran Zuhayr ya taimake ta. Riƙota Justice yai yana faɗin "relax ni ne" Muryan Zuhayr ta ji a kunnen ta dan haka ta shige jikin Justice da sauri tana faɗin " D Ben is here, zai kashe ni" "Ba wanda zai kashe ki kin ji" ya faɗa da tausashashshiyar murya. Tunanin Aljanu ke damunta dan haka ya kai bakin sa saitin kunnen ta yai Bismillah ya fara karanta ma ta suratul Fatiha cikin daddaɗar muryan sa. Yana gamawa ya ɗaura da Ayatul kursiyyu kafin ya ƙarisa aka maido da wutan gidan, still bai dena karatun ba ya cigaba da karanto ayoyin ruqya. Kusan minti goma ya ɗauka yana karatun zuwa lokacin jikin Zaytoonah ya dena kakkarwa kuma nitsuwa ya shigeta. Tana son barin jikin Justice amma kunya ya hanata, ba ta san ya aka yi har ta tsinci kan ta a jikin sa ba, ƙila dai ciwon ta ne ya tashi. Shirun da yai da karatun ne ya sa ta janye jikin ta daga nashi amma ba ta iya ɗaga ido ta kalle shi ba. "I'm sorry Zaytoonah, ba zan sake irin wannan wasan ba" Ahmad ya faɗa a raunane dan Allah na gani ya ruɗe da halin da ya ga Zaytoonah ta shiga cikin ƙanƙanin lokaci daga kashe wuta. Dama ya yi niyyar tsoratata ne amma abinda ya faru is beyond tunanin shi. Maganganun ta sun tabbatar ma sa da Zaytoonah ba ƙalau ta ke ba, dan ba abinda zai sa ta dinga cewa za a kashe ta. Sau biyu tana kurɓan ruwan da aka ajiye ma ta kafin ta ce "zan tafi gida" ta yi maganar ne tana kallon Ahmad dan Justice kan ta kasa haɗa ido da shi. Tana ji Ahmad na ma sa bayanin abinda ya faru amma ba ta tanka mu su ba. To mi za ta ce mu su? Ta ina za ta fara mu su bayanin duk lokacin da ta tsinci kan ta a wajen duhu hankalin ta na tashi har ta faɗa yanayi na damuwa wanda ke kama da gushewar hankali. A maimakon Ahmad da ya kawota wannan karan harda Justice aka maida ta gida, Dreban Justice da Ahmad na gaba ita kuma da Justice a baya. Ta san yayi hakan ne saboda ba ya so a barta ita ɗaya. Bai ce ma ta komai ba har su ka isa gidan, itama shiru ta yi kawai tana wasa da yatsun ta har su ka iso. Sai da za ta fita ya ce ma ta "Allah ya ƙara sauƙi" ta amsa da Amin sannan ta fita. Tana fita ya ce Ahmad ya rakata har bakin ƙofa... A daren Justice ya kira Ni'ima yana tambayarta ko tana da labarin ko Zaytoonah na fama da wata matsala ko irin matsalan Aljanu haka ko kuma dai rashin lafiyar ƙwaƙwalwa. Ni'ima ta ce ba ta sani ba gaskiya amma za ta tambayi Mommy. Justice ya ce ta bari ba yanzu ba tunda tana cikin alhini an mu su rasuwa yau. Saƙawa da warwara Justice ke yi yana ƙoƙarin gano matsalar Zaytoonah. Daga ƙarshe abinda ya riya a ran sa shine ba shafar Aljanu gareta ba kamar yadda yai hasashe sai dai ko wani abin daban. Daga baya ya ɗau waya ya fara browsing yana neman ƙarin haske gameda abinda ya faru ko zai samo amsar da kan sa. *** Sati guda Zaytoonah da Mommy su ka yi a Ringim kafin su ka koma Zaria. Mutuwar Goggo ya taɓa su sosai ba kaɗan ba musamman Mommy wacce ta ke ganin Goggo a matsayin Uwa. Iya ma ta kaɗu matuƙa da rasuwan kishiyar ta ta. Ba abinda ta ke tunawa face irin nasihohin Goggo a lokuta mabanbanta wacce ta ke nuna ma ta cewa rayuwar fa ƙayyadaddiya ce, duk min daren daɗewa mutuwa za ta zo ta riske ka. A lokacin ne kuma za ka gane cewa rayuwar duniya ba komai ba ne musamman idan ka yi ta bisa son zuciya. A kwana na biyu da rasuwan ne Justice ya kira Mommy ya ma ta ta'aziya kuma ta ji daɗin hakan, dama ta daɗe da sanin cewa Justice ba shi da girman kai. Duk da yana so ya tambayeta gameda Zaytoonah amma sai ya ga hakan bai dace ba a lokacin. Abinci ya ke ci da 'ya'yan sa Yammacin ranan Talata sai ga kiran Mommy ya shigo wayar sa. Ya ɗauki wayar tareda yin sallama. Bayan sun gaisa ne Mommy ta ce ma sa a office ne yau Hajia Ni'ima ke tambayarta ko Zaytoonah na fama da matsalar Aljanu da ta tambayeta dalilin tambayar ne shine ta gano cewa daga wajen Justice ne. "Zaytoonah ta samu panic attack lokacin kana wajen ko?" Ta yi tambayar cike da damuwa. "Da alama ba ta son zama a cikin duhu" amsar da ya ba ta kenan. "Ranka shi daɗe ba Aljanu gareta ba. PTSD ne ta ke fama da shi tun rasuwan mijin ta..." A hankali ta warware ma sa matsalar Zaytoonah gaba ɗaya, dalilin abubuwan da Ben yai ta ma ta ne ya ke rikita ma ta ƙwaƙwalwa duk lokacin da ta tsinci kan ta a duhu. Justice yai shiru yana sauraron ta cike da tausayin Zaytoonah, ashe sunan Zuhayr da ta ke ta kira mijin ta ne. "Ina fata wannan ba zai jawo matsala ba idan Zaytoonah ta fara case ɗin nan?" "Insha Allahu ba abinda zai faru" ya amsa ma ta yana mai tattare da yaƙinin hakan... Tsaye ya ke jikin madubi yana shiryawa. Damuwar da ke zuciyar sa ce ta watsu duk ilahirin jikin sa har ta kai ya ke jin kan sa kamar marar lafiya. Maganganun Mommy na jiya sun bala'in taɓa shi. Wani abu da ya ke ji na taso ma sa gameda Zaytoonan shiyasa tun farko ya ke kauda kan sa a kan ta yana kuma Allah-Allah zaman da Zaytoonah za ta yi ƙarƙashin sa ya ƙare tayi tafiyar ta. Sai dai bayanan Mommy sun dasa ma sa tausayin Zaytoonah wanda a yanzu ya sawa kan sa ko bayan an gama case ɗin nan zai yi ƙoƙarin taimaka ma ta har ta samu lafiya gaba ɗaya. Ko da hakan na nufin zai ɗauki wani mataki mai nauyi wanda ka iya chanja yanayin rayuwar sa da ta Zaytoonan gaba ɗaya... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 42 Bismillahir Rahmanir Rahim *groomed to seek justice* Bayan hiran su da Mommy Zaytoonah ko baccin kirki ba ta iya yi ba. Duk ta inda ta auna sai ta ga ba abu ne mai yiwuwa ba, ta ina ma za ta iya representing Mommy a wannan case ɗin. Ƙwararren Lawyer ma sai yayi da gaske kafin ya iya cin case ɗin nan duba da yadda shekaru su ka ja da kuma rashin evidence a ƙasa. Ba za ta iya ba, abin da ta concluding kenan ta kuma sa a ranta za ta nemo one of the best Lawyer da ake da shi a ƙasar, ko nawa zai buƙata za ta biyashi domin ya taimakawa Mommy. Washegari kamar ba abinda ya faru jiya haka Mommy ke walwalar ta, ita kuwa Zaytoonah ta kasa sakewa. Ƙarshe ma kiran Auwal ta yi akan tana son su haɗu da ke Sunday ne yana gida. Cewa yai su haɗu a wani gidan cin abinci nan da awa ɗaya. Ita ta fara zuwa wajen ko dan ta ƙagu su haɗun ne oho. Sai da ta yi kusan Minti shatakwas kafin ya iso. "Yi haƙuri Dan Allah, sanda kika kira ina wanke Machine ɗina ne da na gama na fito kuma na haɗu da friend ɗina a bakin layi..." "Ya wuce ai, da ban san hali ba ne sai na yi ƙorafi" "Da gaske na chanja" yai maganar yana murmushi. Sai da ya nitsu sosai kafin ta sanar da shi maganar da su ka yi da Mommy. "Cabɗi!" Abinda ya furta kenan bayan ya gama sauraron ta. "Cabɗi kuma?" "To mi zan ce, abin ne na ji banbaraƙwai. Yanzu Mommy ta ina ma take so ki fara?" "Wallahi ban sani ba Ya Auwal. Ita gani take abu ne mai sauƙi kuma case ɗin nan babban sauƙi ne" "Gaskiya kam. Duk ban san dalilin ta na cewa ki jagoranci case ɗin nan ba amma gaskiyar magana shine indai ki ka ɗau case ɗin nan ba inda za aje za a kori ƙarar nan" Zaytoonan ta haɗe rai ta ce "irin ka rena ni ɗin nan" "Sorry Dear, kin san ke ɗin JJC ce" Zaytoonah ta murguɗa ma sa baki... Duk da Auwal ya sa baki Mommy ba ta chanja magana ba, abu ɗaya ta jaddada mu su. Ko dai Zaytoonah ta jagoranci case ɗin ko kuma ta haƙura da case ɗin har abada. Wannan ya sa jikin Zaytoonah yai sanyi, ta kuma ɗaura aniyar bin umurnin Mommy duk da tana hango mu su rashin nasara a case ɗin. "Mommy na amince" ta faɗi maganar lokacin da Mommyn ke shirin kwanciya. Jin ba ta tanka ma ta ba ne ya sa ta sake maimaita maganar "Mommy na amince zan jagoranci case ɗin nan" Wannan karan Mommy ta kalleta briefly kafin ta ɗauke ido ta ce "Allah ya shige mana gaba" Zaytoonah ta amsa da Amin. Washegari Mommy ta sanar da ita details ɗin yadda take son komai ya tafi. It wasnt easy kamar yadda tayi hasashe ɗin. "Mommy gani da ke a gida amma sai kin tura ni wajen wani yayi coaching ɗina" ta yi maganar tana flipping ƙwan da ke cikin Pan yayinda Mommy ke juye ruwan tea cikin flask. "Yaushe rabon na yi zaman kotu, ni yanzu ai Malama ce" Zaytoonah ta sa dariya " Malama Mommy kenan" "Ki faɗa da kyau dan hakan ta ke" "GrandMa! Hashir is not brushing his teeth very well" muryan Hadid ya katse mu su hiran. Mommy ta ce "to kinga ɗalibai na nan" Zaytoonah ta sa dariya... *** Ta kai minti biyar tana tuƙa da warwara kan yadda za ta tura text message. Ba za ta iya kiran sa ba gaskiya dan tsoron harka da manyan mutane ta ke yi musamman ma shi da aka ce ma ta mai sarauta ne. Daga ƙarshe kawai ta tura ma sa *fatan an wuni lafiya, Bar. Zaytoonah ce wacce za ta zo wajen ka ranan Monday* ko yayi ko bai yi ba ita dai ta riga ta tura. Kamar yadda ba ta tsammanci reply ba hakanan har rana ta faɗi ba ta ga reply ɗinsa ba duk da kuwa tanada yaƙinin cewa ya ga message ɗin. Haka dai ta shirya ta wuce Abuja yammacin ranan Lahdi kuma har lokacin ba ta ji daga gareshi ba. A gidan Muhsina ta sauka duk da kuwa akwai wasu 'yan uwan Zuhayr a Abujan amma gidan Muhsina ya fi mata saboda tafi sakewa a gidan. Mijin ta yanzu baya ƙasar ya je yin Phd ɗin sa a South Africa. Gidan daga ita sai 'ya'yan ta guda biyu Nabil da Aysha sai kuma Azma ƙanwar mijinta da ke tayata kwana. Ba ta san ya aka yi baccin ta yai nauyi har haka ba, dan ko bugawar alarm ba ta ji ba. Sanda ta tashi har ƙarfe bakwai na safe ta shige da 'yan mintuna. "Shine ba ki tasheni ba" ta faɗawa Muhsina da ke shirin kai yara Makaranta. "Au ni fa har na manta yau za ki fara fita" "Wannan yawan mantuwa na ki anya????" "Rufa min asiri yaushe Abban Nabil ya zo gida" "Na sani ko lokacin da ki ka je ma sa ziyara kin taho da tsaraba" Zaytoonah ta yi maganar tana dariya. "Ki dai ƙaraci gulman ki ni banida komai". Tare su ka karya da Azma dan itama sai lokacin ta ke tashi. Ba ta zuwa ko'ina dan tun lokacin da ta yi jarrabawan WAEC ta dawo Abuja da zama, ko jarrabawar JAMB da ta yi ma a nan ɗin ta yi. Lokacin da Zaytoonah ta isa Chamber ɗin ƙarfe goma har da rabi. Ita kanta ta san ba ta kyauta ba balle kuma wanda za ta je wajen na sa. Gaskiya wajen ya tsaru iya tsaruwa sai dai taste ɗin su wajen furnitures bai ma ta ba. A wajen Sakatare ta zauna tana jiran tsammanin man Rabbuka bayan ya shaida ma ta ta jira Honorable yana aiki. Tun tana duba agogo har ta haƙura kawai ta cigaba da buga game a wayarta. Minti talatin da biyu cur ta yi a wajen kafin Sakataren ya ce ta shiga office ɗin. Office ne mai girma da ya wadatu da shelves wanda ke cike da manyan litattafai. Ta kai duban ta ga mamallakin office ɗin wanda ke zaune akan kujera yana nazarin wasu litattafai guda uku da ke gaban sa. Mutumin da aka kira da Justice Yunus Muhammad Abbas fari ne sosai, yanayin farin sa yana zubi da Larabawa, furfura daya wadaci sajen sa da gemun sa shi zai sa ka ma sa tunanin shekaru irin sittin ɗin nan amma a zahiri shekarun sa Arba'in da shida ne. Allah dai ya bashi baiwar furfuran ne, hatta gashin kan sa kusan rabi da furfuran. Sanye ya ke da baƙin suit, da ke a buɗe ta ke kana ganin farin shirt ɗin da ke ciki. Ko bai sa tie ba ne ko dai ya cire dan ba ta ga tie a wuyan sa ba. "Good morning Sir" ta bashi 'yan sakanni amma ta ga shiru bai amsa ba, ta ɗan ƙara ɗaga murya ta ce "Barrister Zaytoonah Tijjani Abubakar Sir" Still shiru bai yi magana ba bai kuma ɗago ya kalleta ba. Tsaki ta yi a ranta tana faɗin Girman kai rawanin tsiya. Ba za ta manta walaƙanci da ya mu su ba ranan da su ka haɗu a gidan sa, bai yaba aikin su ba, bai ma nuna ya ji daɗin aikin ba. Yana gama dubawa da ya sauko ƙasa lokacin suna hira da Hajiya Ni'ima ya ce "Hajiya Ni'ima a tambaye su nawa ne kuɗin su" daga haka ya fice a falon, tana ma shirin gaishe shi ne amma jin abinda ya faɗa ya sa ta ja bakin ta tayi shiru. Tsabar haushi ma ranan ƙin ba da account number ɗin ta tayi sai kawai ta bada business account na kamfanin Alhaji Ibrahim. Kuɗin ma yafewa ta yi, dan da su ka yi magana da Alhaji Ibrahim ce ma sa tayi payment ɗin kaya ne dana sauran ma'aikatan da su ka tayata aiki ita ta cire na ta. "Sarauta my foot" ta faɗi a zuciyarta haɗeda yin tsaki. Tun tana sa ran zai yi magana har ta gaji, ta yi yunƙurin magana for the last time dan ta yi Alƙawarin daga wannan kam tafiyarta za ta yi ta fasa koyon aiki a wajen sa. Ita kam yadda Mommy ta yi ta yabon wannan mutumin exactly opposite ɗin sa ta gani. A hakan wai Mommy ta yi aiki ƙarƙashin sa lokacin yana Judge of High court Kaduna. "Sir ni ce wacce Barrister Maryam Nkiru ta maka magana akan za..." "Idan kin koyi zuwa da wuri sai mu ɗaura daga nan" abinda ya faɗa kenan still idon sa na kan littafi. Yadda yai maganar kamar ma ba da ita ya ke ba... "Mommy Allah yana da girman kai, ko fa amsa gaisuwata bai yi ba" Daga ɓangaren Mommy ta ce " ke ma laifin ki ne ai da ki ka je a makare. Barin gaya miki shi mutum ne mai tsari bai yadda da wasa da lokaci ba" "Duk tsarin sa ai ba zai hana ya amsa common gaisuwa ba. Mommy ko kallona fa bai yi ba" Mommy ta yi dariya ta ce "to Zaytoonah ya kalleki na me kenan?" "Allah ni kam ki chanja min wani ba abinda zan koya a wajen sa sai girman kai" "Idan ki ka nitsu ki ka fahimce shi Wallahi shi mutum ne mai sauƙin sha'ani" "Ina ga dai shekarun baya kenan da kika yi aiki da shi, yanzu kam ya chanja" "Galadima ba shi da girman kai Zaytoonah, wannan kam zan ma sa shaida akai" Duk da Mommy ta faɗa ma ta haka itakam ba ta yarda ba tunda ta ga zahiri ba sau ɗaya ba har sau biyu... *** Bai koma gida da wuri ba sai bayan sallar Maghriba. Da sallama ya shigo falon yayinda fiskar sa ke ɗauke da Murmushi. Falaq da Suhailah su ka yo wajen sa da gudu su ka rungume shi. Sai da ya kissing goshin su kafin ya kama hannun su duka biyu su ka ƙariso wajen da Hajia Ghazala da Raziya ke zaune. "Ranka shi daɗe, barka da dawowa" "Sannu da ƙoƙari" yai maganar yana tambayar Raziya ya jiki ta ce ma sa da sauƙi. Daren jiya bai samu yayi bacci ba saboda ciwon cikin da Raziya ta tashi da shi tsakar dare. Da su ka je Asibiti ne ake faɗa ma sa ai ciwon cikin period ne. Ashe 'yar ta sa an zama budurwa. Tunda safe kuwa da Hajia Ghazala ta ji labari ta zo ta tare a gidan. Tuntuni take son tafiya amma kuma ba ta saka Galadima a ido ba ba abinda zai sa ta tafi dan haka ta cigaba da zama da yaran. Wanka yai ya chanja kaya zuwa baƙar Jallabiya sannan ya fito dan ya wuce masallaci sai a lokacin ne Hajia Ghazala ke shirin tafiya. Bayan Allah ya kiyaye hanya da ya ma ta bai kuma cewa komai ba. Sanda ya dawo daga masallaci sannan ya zauna da yaran sa uku su ka ci abincin dare ana ci ana hira kowa na kawo complain ɗin sa. Ƙarfe tara da rabi kamar kullum su ka ma sa sallama dan lokacin baccin su kenan, ita kam Suhailah tuni ta yi bacci dan haka a kafaɗar sa ya ɗauketa ya kaita ɗaki. Bayan ya gama tofa mu su addu'o'i kafin ya fito daga ɗakin na su ya wuce na sa ɗakin. Kujerar da ya ke aiki ya hau ya buɗe Laptop ɗin sa yana duba wasu saƙonni, aƙalla ya kai minti Arba'in yana aiki kafin ya kashe ya hau gado ya kwanta. Bayan ya tofa addu'o'i sannan ya rufe idon sa, sai dai me? ba abinda idon sa ke gani sai hoton Yarinyar nan shekaru shida kenan da su ka wuce, yana ganin yadda take tauna plaintain chips ɗin yana ba da sautin ƙurmus, ƙurmus, ƙurmus. Ya tuna lokacin da ta kira shi da Uncle ɗin ta bayan an hanata shiga wajen hall ɗin da ake dinner. *"Majesty ko dai za mu yi Amarya kwanan nan ne?"* Maganar marigayiya matar sa kenan lokacin da ya ke ba ta labarin Zaytoonah bayan ya koma gida. Shi kan sa mamakin kan sa ya ke yi yadda ya zage yana ba ta labarin Zaytoonah hadda mimicking irin maganar ta da expression na fiskarta. *"Na gaya miki yarinya ce fa"* amsar da ya ba ta kenan a lokacin. A ranan har ƙaramar muhawara su ka yi a kan Zaytoonah. Ya buɗe ido yana kallon sama duk da wutar ɗakin a kashe ya ke, duhu kawai ya ke kallo. Ba zai iya faɗin takamaimai dalilin da ya sa ya damu da yarinyar ba har ta kai yana son sanin wani abu gameda ita da rayuwar da tayi a baya. Shi ba yaro ba ne ya lura da yadda Ni'ima ke ta kawo ma sa hiran Zaytoonah tun a chan Zaria. A yadda ta ke nanata ma sa cewa Zaytoonah Bazawara ce mijinta ya rasu ya barta da 'ya'ya biyu ya san inda tunanin ta ya tafi. Duk da matsin da ya ke samu daga wajen Hajia Abu kan yai aure ko dan su Raziya ba ya tunanin zai iya biyewa Ni'ima. So what idan Zaytoonah Bazawara ce? She's still young ai. Ya dai sani zai iya ƙoƙarin sa akan ganin ya grooming ɗin ta kan wannan case ɗin da za tayi, duk da ma ya lura yarinyar akwaita da yarinta da shiririta. Ya jima yana saƙa da warwara kafin bacci yai gaba da shi. 2/11/21, 10:04 PM - ****: 41 Bismillahir Rahmanir Rahim *Barrister Zaytoonah* "Daɗin abin ma dai Bazawara ce ake ta wani azarɓaɓi akan ta" Humairah kenan ke wannan maganar. Auwal bai kulata ba sai ma cigaba da taje gashin kan sa da ya ke yi. Ba yau ta saba kiran 'yar uwar tata da suna Bazawara ba, da gayya ta ke kiranta da haka shi kuma ba zai kulata ba tunda abinda ta ke so kenan. " mace daga haihuwa sau ɗaya ta gwajaɓe ta zama buhu, laɓaɓa kamar bagen tumatir. A haka ana wani rawar ƙafa akan ta kamar akan ta aka fara zama Barrister" Sai da ya gama feshe turare sannan ya juyo ya kalleta. "Aisha kenan, duk abinda ki ke faɗa gaskiya ne babu ƙarya a ciki amma akwai saura da ki ka manta ba ki faɗa ba wanda su suka fi komai mahimmanci. Barrister Zaytoonah Tijjani Abubakar jarumar mace ce wacce ta yi fama da ƙalubale na rayuwa daga ƙarshe kuma ta kai matsayin da har abada ba za ki taɓa kai wa ba. Kin san cikin shekaru huɗu mi ta zama tun bayan rasuwan mijin ta?" Yai murmushin rainin hankali ya ce "ki ɗauko biro da littafi na lissafo miki dan na san ƙwaƙwalwar ki ba zai iya lissaftawa ba. I'm proud of Zaytoonah i will always be" "Hamma kenan. Ka zageni yadda ka ke so ba zai chanja kasancewar Zaytoonah Bazawara ba" Wuceta yai yana faɗin "zan turo miki hotuna" Sai da ya fita daga ɗakin hawayen baƙin ciki su ka zubo mata. Wai miyasa har yau Auwal ya fi son Zaytoonah akan ta ne? A da ba soyayya ta ke yiwa Hamma Auwal ba amma kusan shekaru uku kenan tana dakon soyayyar sa. Dalilin sa ta amince ta sake rubuta NECO ta fara remedial kafin ta samu shiga aji ɗaya a ABU har ta kai yanzu da ta ke aji biyu inda ta ke karantar Biology Education. Lokacin da ta gama Sakandare aure ta yi niyyar yi musamman yadda saurayin ta Farouƙ ya buɗe ma ta kunne da soyayyar sa ta ƙarya. Ya so ya samu kan ta tun a waje amma duk iskancinta a waje ya tsaya bai kai har ta yi Zina ba. Har Farouƙ ya aika magabatan sa Ringim an bashi Humairah. Daga baya ya zo ya ce ya fasa. Humairah kamar ta yi hauka lokacin saboda ta shirya komai, yadda Zaytoonah ta auri mai kuɗi itama tana son auren mai kuɗi. Bayan abin ya faru ne daga baya Auwal ya siya ma ta form ɗin remedial ta fara. Da farko ta fara abun reluctantly ne daga baya kuma ta ɗan sa himma a karatun. Tunda Zaytoonah ta dawo Nigeria ta ke lura da take-taken Auwal ɗin. Yadda ya ke shishshige ma ta da ita da yaran ta. Daga ya dawo daga office chan gidan Mommy ya ke wucewa ya ci abinci ya sha zaman sa kafin chan dare ya dawo. Idan weekend ne ma to duk a gidan ya ke yi, ko kuma ya ɗebo Yaran su zo gidan su yi ta wasa daga baya ya fita da su shan ice cream. Allah na gani ba za ta bari Zaytoonah ta samu abinda ta ke muradin samu ba. Hamma Auwal na ta ne... *** Dukkan gidan aka je ma ta, don wannan ranan farin ciki ne ga iyalen Tijjani. Babu wanda ya kai Mommy farin ciki a wannan rana, kamar yau ta gama Law school lokacin tana da tsohon cikin Zaytoonah sai ga shi 22yrs later 'yar ta ta samu zama Barrister itama. Tana fata ɗaya burin na ta ya tabbata a kan Zaytoonah. "Our daughter is a Barrister now. A duk inda ka ke na san za ka yi alfahari da ita" Mommy ta yi maganar tana kallon hoton T J da ke kan wayarta. "Grandma lets take picture" Hadid ya faɗa yana kama hannun Mommy. Su dai yaran ba sa gajiya da hoto, gajiya ma ta yi da ɗauke-ɗauken hoton ta zo ta zauna. Tana son ce mishi a'a ba yanzu ba sai ga ɗan uwansa shima ya riƙe ma ta hannu yana faɗin ta zo su yi hoto, ba yadda ta iya kawai ta tashi ta bi jikokin na ta. Kwanan su biyu a Abuja kafin su ka dawo Zaria... Yau Jumu'ah kuma yau ne za su je gidan Kakan su yin weekend dama tare su ke zuwa sallar jumu'ah da Baba Tsoho. Wani lokaci su kan leƙota kafin su tafi gaba ɗaya wani lokaci kuwa daga sun tafin shikenan sai kuma Sunday da yamma. Randa aka ɓata mu su rai kuwa tun Asabat za su dawo gida wani lokaci su ce su Allankatafir ba za su sake zuwa gidan Baba Tsoho ba suna maganar ba su minti talatin za ka ga sun dawo suna ƙasa-ƙasa da murya wajen Mom suna "Mom za mu je gidan Baba Tsoho" tsofin gidan ba ƙaramin tarairayan 'yan biyun su ke ba. Babu sanda za su je ba su dawo da tsaraba ba wani abin ma har mamaki ya ke bawa Zaytoonah, yadda su Hajiya Saudah da Hajiya Nenne ke yi wa yaran tamkar su kaɗai ne 'ya'yan jika a gidan. Sai da ta gama shirya Hashir ta ɗaga ido ta kalli Hadid da ya takure gefe guda yana kumbura baki shi a dole yayi fushi. Ganin sa a haka da ta yi ya sa ta tuna da Zuhayr yadda ya ke tsokalarta idan tana kumbura baki. Ta yi murmushi wanda sai da ƙwalla ya zubo ma ta, ta yi saurin gogewa tareda cewa "Sweetheart zo na saka ma ka kaya" Hadid ya maƙe kafaɗa yana faɗin "hun'um" Tunda ta ce a Hashir za ta fara sawa kaya ya takure gefe yana fushi. "Mom turare" Hashir ya faɗa da ɗan ƙarfi. Zaytoonah ta miƙe dan ta kamo Hadid sai kuma yai hanyar ƙofa yana faɗin shi ba zai sa kaya ba. Tsayawa ta yi ganin Auwal a bakin ƙofa ya riƙe hannun Hadid yana tambayar sa miya faru. Hadid ya fara bayanin wai kullum Mom ba ta sa ma sa kaya sai ta sawa Hashir, kuma sai ta ce Hashir ne Babba. Tana tsaye har ya shigo da Hadid ɗakin ya saka ma sa riga sannan ya warware towel ɗin da ke ɗaure a ƙugun sa ya saka ma sa wando. Da Hadid da Hashir ɗin duk shi ya fesa mu su turare har ta taje mu su baƙin gashin su mai yelƙi. Bayan sun fita daga ɗakin ne ya kalli Zaytoonah da ke tsaye ya ce " sannu da ƙoƙari" "Kai zan cewa sannu ai, ba dan ka zo ba sai mu wuni a nan ina neman sakawa Hadid kaya" "Mommy ba ta nan ne?" "E ba ta dawo daga school ba, tanada class 2-4pm" "Ayya! To bari mu wuce masallaci ko" Har ya kai bakin ƙofa sai kuma ya juyo yana kallon ta. Ganin kallon yayi yawa ne ya sa ta ce "Ya Auwal ka gama ɗinki na kuwa?" Ya fara sosa kai yana faɗin " Insha Allah gobe zan kawo" "Ki dai alƙawarin ku na teloli sai a hankali" "Yi haƙuri Uwar biyu, aikin office ne ya ke riƙe ni kwana biyun nan amma zan ƙarisa gobe da yardar Allah" Bayan ya fita ta tsaya kallon kayan jikin ta ko da wani abu da ya gani ya ke ƙura ma ta ido har haka. Ba ta ga aibun kayan da ta sa ba, simple doguwar riga ce mai guntun hannu, a sake ya ke dan bai kama ma ta jiki ba. Ta yi saurin kauda wani tunani da ya zo ma ta zuciya. Ita ba ta wannan ma take ba yanzu... Lokacin da Mommy ta shigo gidan da Yamma Zaytoonah na kitchen tana kwashe tuwon semo da ta yi. Tuntuni tayi miyar amma ta tsaya duba report da aka aiko ma ta ne daga chan gidan Gona shiyasa ba ta samu ta gama girkin daren da wuri ba. Gidan yai wa Mommy shiru saboda ma su surutun gidan ba sa nan. Sai da ta ajiye jaka ta chanja kaya zuwa wata jallabiyar TJ da ta maida shi kayanta na zaman gida sannan ta fito falo. "Sannu da aiki" Mommy ta faɗa tana kallon Zaytoonah da ta fito daga kitchen. "Idan babu yaran sai gidan yai shiru kamar ba mutane" "Suna chan ai sun addabi Tsoho" Mommy ta yi murmushi tana ƙara godewa Allah a ranta. Film ɗin da ake yi a Zee world dukkan su suka maida hankali akai. Da ke Uwa da 'yar duka suna hutun Sallah shiyasa ma babu wanda ya tashi cikin su lokacin da ake kiran sallar Maghrib. "Na manta ma, gobe za ki je gidan Hajiya Ni'ima akwai aikin da ta ce za ki ma ta" "Mommy fatan ba za ayi irin na waccar ƙawan kin nan ba, na gama yiwa 'yar ta jeren gida tana turo min dubu goma kamar wanda ta ga alamun tsiya a jiki na. Da ma kyauta ta ce na mata aikin daya fi" "Ke kika san wannan, ni dai ance ki je dan haka wannan sauran zance tsakanin ku ne" Hajiya Ni'ima aiki su ke tare da Mommy kuma office ɗin su ɗaya. Sosai su ke mutunci da Mommy duk da Mommyn ta girmeta sosai. Ɗiya ce ga Mai Martaba Sarkin Zazzau amma ko kaɗan ba ta da girman kai, lokacin da Mommy ta yi rashin lafiya har gida ta zo ta gaishe ta... Ƙarfe shaɗaya na safe ta ɗan shige da mintuna ta iso gidan Hajiya Ni'ima, sau ɗaya ta taɓa zuwa gidan tareda Mommy lokacin da ta haihu, shekaran da ta gaba ta kenan. Za ta fito daga mota ta ji wayarta na ringing dan haka sai ta fasa fita. Ganin numban Alhaji Iliyasu ke kira ta san ko dai yaran ta ne ko kuma dai wani abu ya faru Alhajin ke neman ta. Tana ɗauka kuwa ta ji muryan Hashir a wayan yana faɗin " Mom kinga wannan Baban me farin gemu irin na Baba Tsoho yana ce min Hashiru kuma suna na Hashir ne" Ba yau ta saba jin irin ƙorafin nan ba dan haka ta ce ma sa "yi haƙuri ka ji Sweetie na, ai na sani sunan ka Hashir ne ba Hashiru ba, kar ka damu ka ji" "Mom yau mun yi lamuzi tareda Baba Tsoho" Hadid ya karɓi wayan yana faɗa. "Kai ba Lamuzi ba ne Lamizi ne" Hashir ya gyara ma sa. "Mom ina na faɗa dai-dai?, Lamuzi ne ko?" "Lazimi" ta gyara ma sa. Hashir ya fara dariya yana faɗin ai shi ya faɗa dai-dai Lamizi. Tana ƙoƙarin nuna ma sa shima abinda ya faɗa ba dai-dai ba ne ta ji alamun an ajiye wayan ana faɗa. Ta kashe kiran tana dariya dan 'yan biyun na ta sai a hankali. Da murmushi a fiskarta ta shiga gidan dan ta riga ta kira Hajiya Ni'imar a waya kuma ta ce ma ta ta shigo tana gida. Mai aiki ce ta ma ta iso bayan ta zauna aka kawo mata lemo da ruwa. Kusan minti biyu da zuwanta sai ga Hajiya ni'imar ta fito. "Ka ga Barrister 'yar Barrister" Zaytoonah ta yi murmushi tana gaida ta. Aiki ne ta ke son ba ta na wani gidan Yayan ta. Gidan an ɗan kwana biyu ba a zama a ciki shine ta ke so a sake rearranging na gidan abubuwan da su ka tsufa kuma a chanja su. "Kin san da Galadima yana aiki a Sokoto ne to yanzu ya koma Abuja, so zai dinga zuwa nan Zaria often haka. Sannan nan ba da jimawa ba zai yi aure" "Wani irin gida ne?" "Babban gida ne gaskiya, inaga zai fi ki fara zuwa ki ga gidan saboda ki san mi da mi ya kamata ayi ma sa. Za mu Iya zuwa yanzu idan ba ki da uzuri" Zaytoonah ta ce su je ba matsala. Kasancewar karatu yana ɗaukewa Zaytoonah yawan tunani shiyasa a duk hutun da ta samu ta ke amfani da shi wajen samun certificate a wani fanni daban da wanda take karantawa. Kamar Yadda Farha ta dinga ba ta ƙwarin gwiwa hakan ya sa ta samu certificate a ɓangare uku bayan degree da ta ke da shi a Law. Tana da certificate a Interior design, Spa and Beauty da kuma information technology. Dawowanta Nigeria ta haɗa hannu da Kamfanin ɗan Alhaji Saleh wanda ƙani ya ke wajen Alhaji Iliyasu Mai Auduga. Alhaji Ibrahim Saleh yana shigo da kayan decoration na gida da office tun daga kan kujeru, gado 3D wall decoration, har painting irin na Artist ɗin nan suna kawowa. A duk lokacin da ake da aiki na decorating gida ya kan tuntuɓi Zaytoonah if she's less busy sai ta je ta supervising aikin. Ba wai dan kuɗi ta ke aikin ba dan ta fi ƙarfin kuɗin sa sai dai tana jin daɗin aikin shiyasa duk lokacin da ta ke free idan ya tuntuɓeta take zuwa da sauri. Cikin ƙawayen Mommy da su ka yi bikin 'ya'yan su akwai wanda su ka ba ta aikin jeren ɗakin 'ya'yan su. Aikin farko da ta fara yi ba ta samu matsala da wanda su ka je jeren ba infact sun yaba ma da hazaƙar ta wajen ganin komai ya shiryu cikin sauƙi kuma ya zo yayi kyau duk tsarin da ta bayar ya sa ɗakin yayi kyau sosai. Wani aiki kuwa da ta je su Mama- Mama, Baaba-Baaba da ta samu a wajen kallon wacce ba ta san komai ba su ka ma ta. Wata a wajen har da cewa tun kafin a haifeta su ke zuwa jere. Zaytoonah ta tafi ta barsu suka yi aikin da kan su. Daga baya kusan sati uku da auren da Maman Amarya ta je gidan sai da ta kira Zaytoonah akan arrangement na ɗakin bai ma ta ba, itama kuma Amaryan ta yi complain akai. Da ke dai matar ta hannun daman Mommy ne sai ta amince ta je gidan. Da ita da Amaryar da ƙannenta biyu ɗaya namiji ɗaya mace su ka sake gyara ɗakin, hatta falon sai da su ka chanja tsarin zaman kujerun... Yanayin gidan da su ka je ya burge Zaytoonah ta shiga ko'ina a gidan ta gani ban da ɗaki ɗaya wanda ta ke tunanin na mai gidan ne. "Kin ga shi baya son tarkace a gida, sannan ya fi son abu fari ko kuma baƙi. Red, Yellow, Pink da Purple duk kala ne da bai faye so ba dan yana danganta kalar da mata. So sashen sa kar a saka ma sa abu mai kala irin haka" Hajiya Ni'ima kenan ke yiwa Zaytoonah wannan ƙarin bayani. Kafin su bar gidan sai da ta tambayeta nawa kuɗin aiki amma sai ta ce ta bari a ƙare aikin tukunna. Gidan baya buƙatan sabbin abubuwa da an kaɗe an goge yawancin kayan za su dawo da kyaun su dan yawancin kayan gidan ma sabbi ne. Labulayen gidan kam mai gidan ya ce kaf ɗin su a chanja inji Hajiya Ni'ima duk da suma ba wai sun wani tsufa ba ne. Kusan kwanan su biyar suna sintirin zuwa gidan Galadima ana kan furnishing ɗin sa. Da yammacin ranan jumma'a su ka kammala komai, kuma a ranan maigidan zai dawo dan ya assessing aikin su ko akwai abinda ya ke so su ƙara ko a cire. A hannun kujera Zaytoonah ta zauna tana cin abinci, tun daga gida ta riƙo abunta dan ta san yau ma za su iya kaiwa yammaci a gidan. "Allah Yaya sun yi aiki mai kyau, ni kaina sai na ji gidan ya kuma shiga raina" Bai amsa ma ta ba sai ya buɗe ƙofar falon ya shiga gidan da sallama. Ta gaji da riƙe waya ya sa ta bar wayar a wuyanta ta matse shi da kafaɗarta dan kar ya faɗo. Ta cigaba da cin abincinta tana jin complain ɗin 'yan biyu wanda ko alamun ƙarewa bai yi ba. Labarin makaranta su ke ba ta wanda daga nan kuma aka shiga labarin da ya faru kusan sati ɗaya daya wuce a Islamiyya. Sa kai yai niyyar yi dan ya haura sama ya fara duba sashen sa kafin ya duba sauran ɓangarorin, sai dai yarinyar da ya gani tana waya ne ta ɗauke ma sa hankali. Tabbas ya san fiskar nan amma ya rasa a ina ne. Ya jima yana kallon ta yana ƙoƙarin tuno a ina ya san fiskar amma bai tuna ba dan haka ya sa kai yai gaba sai kuma ya juyo da sauri ya kalleta a karo na biyu a ƙasan ran sa yana furta *Student ce* Ikon Allah kenan ashe da rabon zai sake ganin yarinyar nan mai chin Plantain chips a cikin jirgi. Tabbas ita ce, sai dai wannan ba 'yar yarinyar daya gani shekarun baya ba ne wacce baya tsammanin a lokacin ta wuce shekara shashida ko shabakwai. Kenan Home decoration ta karanta ya riya a ran sa ko kuma Interior design. Bayan ya haura sama ne Hajiya Ni'ima da ta bi Yayan na ta kallo ta maida duban ta ga Zaytoonah da ke cin abinci da ba ta ma san sun shigo ba. Murmushi ta yi a ƙasan ran ta mai tarin ma'anoni dayawa. A ɓangaren Galadima kuwa yana shiga falon sa wayar sa ta fara ringing. Ya cirota a Aljihu ya ambaci Sallama da sassanyar muryar sa. Sai da ta yi murmushi wanda na jin daɗin sauraron ma'abocin sallamar ne kafin ta ce " Abu Razz Barka da yammaci, fatan ka isa gida lafiya" "Alhamdulillah" ya faɗa a taƙaice. "Ranka shi daɗe na ce ko za ka yarda su Raziya su zo su yi weekend a wajena?" "Allah ya taimaka" ta amsa ma sa da Amin, kafin ta kuma wani maganar ya kashe wayan. Kallon falon na sa ya tsaya yi yana yaba ƙwazon yarinyar dan gaskiya yadda falon ya banbata da tsarin sa na da kuma still yai kyau dole ya jinjina ma ta... *** "Adaeze" Mommy ta kira sunan ta da sigar jan hankali. Zaytoonah ta tattaro duk wani nitsuwarta ta bawa Mommy tana sauraron ta. Wani ƙaton brown envelope Mommy ta ɗauka wanda ke saman center table. Jaridar da ke cikin envelope ɗin Mommy ta miƙawa Zaytoonah ta ce "gashi ki karanta headline ɗin" Zaytoonah ta karɓa ta karanta, sai da ta karanta headline na biyu ne ta ɗago ido ta kalli Mommy da sauri cike da mamaki. *Udodiri for Senator* Mommy ta ce "Yes Adaeze. Mutumin da ke jikin jaridar nan Augustus Udodiri Uzodinma shine ƙanin Baba na daya kashe min Iyaye. Na samu jaridar ne shekaru uku da su ka wuce lokacin da ake shirin zaɓe. Daga lokacin na fara bincike na kuma tabbatar shi ɗin ne dai Uncle ɗina. Ya nemi Senator bai samu ba kuma yana so ya sake nema a zaɓe mai zuwa amma kafin nan ina son shigar da shi ƙara. Ina so ya biya dukiyar iyayena daya cinye, ina so a hukuntashi bisa laifin kashe min iyaye da yai" Fiskarta babu alamun wasa ta ce "Barrister Zaytoonah Tijjani Abubakar ina so ki zamo Lauya ta, ki jagorance ni a wannan ƙara" "Mommy please, ban shirya ba. Yaushe ma na gama karatu, i will love to be your Lawyer amma ba zan iya ba. Ban taɓa jagorantar kowa ba balle babban case irin wannan" "Umurni ne ba shawara ba Zaytoonah. Abu ne da na sawa raina tun lokacin da kika furta min cewa Law za ki karanta" Wannan karan sai ta sassauta murya ta ce "idan kuma ban kai na saki yin abu ba shikenan a rufe zancen"... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 43 Bismillahir Rahmanir Rahim *Hajia Ghazala* Washegari Zaytoonah ta zo da wuri dan ta ma riga Justice zuwa. Duk da ya ganta a office ɗin Secretary bai nemeta ba, sai da ta gaji da jiran kiran sa kafin da ta ga lokaci na ƙurewa ta shige office ɗin sa ko izinin Sakatare ba ta nema ba. Wannan karan da ta gaishe shi maimakon yai shiru irin na jiya sai ya ce " nan gaba nafi buƙatar Sallama fiye da gaisuwa" Kallon Sannu ya sheikh ta ma sa tana ayyana abubuwa a ran ta. Sai da ta tsaya kusan minti biyu kafin ya ɗago a karo na farko ya kalleta. It has been long da ta haɗu da idanun da su ka ma ta kwarjini irin wannan kamar yadda na Mr Upright ya ma ta. Ta yi saurin kauda idon ta daga na shi saboda wani tasirin da kallon ke yi a dukkan gaboɓin jikin ta. "Ki je wajen Barrister Noah Samson, zai koya miki basics na abubuwan da ya kamata ki sani. Bayan sati biyu ki zo ki bani report na abinda ki ka koya" Yana maganar ne yana danna Laptop. Kamar ba za tayi magana ba sai kuma ta yi gyaran murya ta ce "Sir, wajen ka aka..." "Yes" ya faɗa yana zuba ma ta ido. Ka sa ƙarisa maganar ta yi lokacin da su ka haɗa ido. Ta yi shiru tana kallon ƙasa a hankali kuma ta furta "barin je na same shi" Ba hakan ta yi niyyan faɗi ba. Wajen sa aka turata amma kuma zai turata wajen wani daban. Ita kwata-kwata ba ta son harka da Ustazai balle wannan mai uban girman kan. Ta dai fita a office ɗin tana ƙunƙuni cikin ran ta. Barrister Noah ma ba wani sake ma ta fiska yai ba dai shi tana ganin ba zai kai Justice a shekaru ba dan tana tunanin yana late thirties ɗin sa ne. A wajen ya haɗata da Barrister Ahmad wani shima sabon zuwa wanda daga baya ne da yai ta zuba ma ta surutu ta gane ashe Justice Uncle ɗin sa ne, mahaifiyar sa ƙanwar Justice ce. Da shi da itan duk a shekaran aka calling ɗin su to Bar, sai dai maimakon ita da ta yi Law School a Abuja shi Ahmad Law School da ke Lagos ya yi. Da ka ga Ahmad ka san irin Ajebo ɗin nan ne, a yadda ya faɗa ma ta shine ɗan fari a wajen Iyayen sa kuma shi kaɗai ne namiji, yanada ƙanne mata biyu. Kafin su tashi ranan sai da ta san kusan tarihin Justice kaf a bakin Ahmad. Ashe ma ba tsoho ba ne kamar yadda da take ma sa kallon tsoho. Duk da haushin sa da take ji sai da ta jinjina ƙwazon sa na yadda ya riƙe muƙamai da dama har ya kawo wannan matsayi cikin ƙanƙanin lokaci... Justice Yunus Muhammad Abbas shine na uku a jerin 'ya'ya Maza na Mai Martaba Sarkin Zazzau. A wajen Mahaifiyar sa su uku ne kacal ta haifa kafin Allah ya ma ta rasuwa. Yana da Yaya Zainab da su ke kira da Hajiya Abu sai ɗaya yayar sa Fatima wacce ta rasu da jimawa tun ma Yunus bai wuce shekaru goma a duniya ba. Gaba da bayan sa sarauta ne, domin Mahaifiyar sa ma 'ya ce ga Lamiɗon Yola na lokacin, kuma yanzu haka Kawun sa shine Sarkin Yola na Yanzu. Yayi samu yin karatu da wuri, dan lokacin da ya gama Law school shekarun sa ishirin da biyu. Yayi aiki a Public sector ne har aka ba shi muƙamin Judge of High court na Kaduna lokacin dududu yana 32yrs. Ya zo ya zama Chief Judge na Kaduna gaba ɗaya kafin daga baya aka bashi muƙamin Justice of the courts of Appeal na Sokoto. Yanzu kuma wata biyar da su ka wuce aka bashi matsayin Bench of Justice na Nigerian court of Appeal Abuja. Matar sa ta rasu shekaru biyu da su ka wuce kuma Allah ya azurta su da 'ya'ya uku duka mata. Fatima wacce su ke kira da Raziya sai mai sunan mahaifiyar sa wato Aisha wacce su ke kira da Falaq sai autar sa Maryam da su ke kira da Suhailah. A rayuwa yanzu ba abunda ya ke so sama da 'ya'yan san nan. Ya ci ace tun rasuwan Maryam ya ƙara aure amma tsoron auro wacce ba za ta riƙe ma sa 'ya'ya tsakani da Allah ba ya ke yi. An ma sa tayin mata dayawa amma idan ya auna sai ya ga kamar idan yai auren za a samu matsala. Yanzu haka ƙarƙashin takunkunin Hajia Abu ya ke wacce ta rantse idan bai yi aure ba zuwa ƙarshen wannan shekaran za ta yiwa Mai Martaba magana a aura ma sa duk Yarinyar da ta zaɓa. Ta taɓa ma sa maganar Hajia Ghazala tun shekaran farko da matar sa ta rasu amma ya basar da zancen yana ganin kamar ba zai iya auren ƙanwar matar sa ba. Balle kuma Hajia Ghazala da shekaru goma kenan yanzu da rabuwan ta da tsohon mijin ta, ba wannan ba ne matsalar ba, tun da ta fito ba ta sake wani auren ba sai ma ta fanjama harkan kasuwanci kawai, a ganin sa kamar Ghazala ba ta dace da 'ya'yan sa ba. *** Cikin sati ɗaya da ta yi a wajen Barr. Noah sun je zaman kotu sau biyu ta ga yadda ake gabatar da ƙara da duk wasu procedures da ake bi da ta karanta a littafi ta ganshi ra'ayul ain. Ta san yadda ake yi a chan America tunda ta sha attending court hearing. Yanzu kuma ta ga banbacin chan da nan. Ƙarshen sati ne Barr. Noah ya ba su assignment ita da Ahmad akan ranan Monday za su zo su gabatar mi shi. Wani case ne da aka jima da rufewa ya ɗauko mu su file ɗin yai assigning kowa da abinda zai yi. Ita Zaytoonah za ta zama mai defending wanda ake ƙara kuma a zahiri shine marar gaskiya amma kuma ana so ta yi iya ƙoƙarinta ta kareshi da hujjoji gamsassu. Shi kuma Ahmad shine zai defending wanda ya kai ƙara kuma shine da gaskiya. Gaba ɗaya weekend ɗin ta yi shi ne wajen rehearsing presentation da za ta yi ranan Monday. Ta shirya wa abin sosai har tana baiwa kan ta nasara. Ranan Monday ƙarfe goma su ka fara presentation ɗin a gaban Barr. Noah, Barr. Idris da Barr. AbdulHakeem da wasu ma'aikata guda biyu da ba ta san matsayin su ba. Barr. Noah ne ya ke zaune a matsayin Alƙali a wajen. Ahmad ne ya fara gabatar da point ɗin sa kafin Zaytoonah ta yi na ta. A hankali abin ke tafiya kafin kusan minti talatin da farawa Ahmad ya faɗi wani point mai zafi yana cillawa Zaytoonan tambayar. Kan Zaytoonah ya kulle. Ahmad ya sake nanata tambayar da ɗan tsawa kamar dai a kotun gaske su ke. "I dont know, i dont know Ahmad, I dont know" ta faɗa kamar za ta yi kuka. Ɗaga ido da za ta yi sama sai ga idon ta cikin na Justice, ashe tuntuni yana tsaye yana kallon su bai ƙaraso ya zauna ba ne kawai. Tana saukar da idonta sai ga hawaye ya zubo ma ta, ta yi saurin sa bayan hannu ta goge. Barr. Noah ya ce ya ba da minti goma su je su huta za a cigaba idan an dawo ya kuma jaddada wa Zaytoonah akan ta controlling emotions ɗin ta, ta kuma ɗauki presentation ɗin kamar da gaske ɗin a kotu su ke kuma wani ta ke wakilta. Bayan sun fita a hall ɗin Ahmad ya matso kusa da ita yana faɗin " are you Ok?" Saboda ya ga sadda ta ke ƙoƙarin goge hawaye. "Hey Chill, ba fa a gaske mu ke ba" "Ina zuwa" abinda ta faɗa kenan kafin ta fice daga hall ɗin. Kai tsaye jakar ta taje ta ɗauka ta fita daga building ɗin sai wajen Motar ta. Tuƙi ta ke yi tana hawaye, ikon Allah ne kawai ya kai ta gida. Tana faɗawa gado ta rushe da kuka tana faɗin "Mommy ba zan iya ba, ki yi haƙuri ba zan iya ba" Ta jima tana kuka kafin daga baya ta tashi ta wanke fiskarta ta fito ta fara haɗa kayanta. Ba za ta iya ba, indai haka ake ruɗar da mutum da tambayoyi ba za ta iya ba. Wai tun daga gwaji fa kenan, gwajin ma da Ahmad wanda shima ko case ɗaya bai taɓa yi ba. Tana cikin haɗa jaka ta ji wayarta na ringing a cikin handbag ɗin ta, kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta chanja ra'ayi ta fiddo da wayar. Justice ta gani a jikin screen ɗin dan da haka ta saving numbar sa. Wayar na yankewa aka sake kira, haka kawai jikin ta yai sanyi maimakon ta ƙi ɗaukan wayar kamar yadda zuciyarta ya riya ma ta sai kuma ta swiping ta ɗauka kiran. Assalamu Alaikum. Sassanyar muryar sa ya ambata. Murya a dashe ta amsa sallamar tareda jan hanci saboda majina da ke ƙoƙarin zubowa. "Ina son ganin ki a office ɗina yanzu" ya faɗa da isa da gadara. "Sir ba zan iya zuwa ba, gida zan tafi" "Minti talatin na baki" daga haka ya kashe wayar. "Shi a su wa zai dinga nuna min iko, ba zan je ba, tafiya ta zan yi" ta yi maganar tana murguɗa baki kamar a gaban sa ta ke. Dai dai lokacin wayan Auwal ya shigo. Sai da ta nitsu kafin ta ɗau kiran, maimakon muryan Auwal sai muryan rabin ranta ya doki kunnen ta. "Mom we miss you" Hadid ya faɗa da ƙarfi. Hashir ya ce "Mom yaushe za ki dawo?, GrandMa ta ce sai kin iya aiki za ki dawo. Mom ki yi sauri ki iya kin ji" Hadid ya ƙarɓi wayan yana faɗin "Mom wai irin arise my case kike koya? irin wanda ake yi a TV?" Kuka ne ya so kuɓuce ma ta tayi saurin toshe bakinta tana jin faɗan 'ya'yan na ta inda Hashir ke cewa ba arise my case ake cewa ba i raise my case ake cewa. Daga baya ta ji Auwal na gyara mu su akan cewa duk ba su ci ba "i rest my case" ake faɗa. Sama-sama su ka gaisa da Auwal ta mishi sallama akan za ta yi wani aiki, ya so gane cewa ta yi kuka amma sai ta ce ma sa mura take yi shiyasa muryar ta ya dashe. Maganar 'ya'yan ta ya sa ta ji wani ƙwarin gwiwa. Kayan da ta fara haɗawa duk ta mai da su. Ta chanja kayan jikin ta sannan ta fita daga gidan da ɗan guntun confidence ɗin ta. Office ɗin Justice ta fara zuwa, faɗa ta yi zaton zai ma ta amma kamar kullum taƙaitacciyar magana ya yi ma ta wacce ke kama da ƙarfafa gwiwa. "Babu wanda baya faɗuwa, sai dai ga mai hankali, da ya faɗi zai yi ƙoƙari ya tashi ya karkaɗe jikin sa ya cigaba da tafiya" Yai shirun kusan minti ɗaya kafin ya ce " ki sake shiri, gobe za a cigaba" Da wannan ta bar office ɗin sa bayan ya ɗaga ma ta hannu alamar ta tafi. Washegari da aka cigaba da case ɗin ta daure ba ta yi wannan katoɓarar ba, although muryar ta na rawa amma ba ta girgiza da jin points ɗin Ahmad ba. Wannan karan Barr. Noah magana ya ma ta akan ta dinga saita nitsuwar ta kuma yi ƙoƙari wajen daidai ta muryar ta. Har su ka gama ba ta ga Justice ba kuma ba ta san dalili ba amma ta so ya gan ta yau ɗin tunda ta samu improvement... Yau ne ta gama sati biyun da za ta yi a ƙarƙashin Barr. Noah. Dan haka da wuri ta zo ta kuma shiga wajen Justice dan ta bashi report kamar yadda ya ce. Cewa yai ta ma sa summarizing abinda ta koya a wajen sa a taƙaice. Duk yadda ta so saita nitsuwar ta sai da muryarta yai rawa lokacin da ta ke yiwa Justice bayani. Bayan ta gama ne ya ɗauko wasu files guda biyu ya ba ta ya ce ta je ta studying ɗin su na sati ɗaya sai ta dawo ya ma ta tambayoyi. Case ne wanda ya ke ɗan kamaceceniya da irin case ɗin Mommy. Da ke bai yarda ta tafi da files ɗin gida ba sai ta zauna a office ɗin su ta fara dubawa. A haka Ahmad ya shigo ya sameta tunda su uku ke sharing office ɗin da wani Barrister Yusuf wanda shima sabon ma'aikaci ne amma ya shekara da fara aiki. Ƙarfe huɗu suka tashi ta tattare kayanta sai gida. Tana cikin Mota traffic ya tsaidata ta ji waya na ringing a jakar ta sai dai kuma ba irin ringing ɗin wayar ta ba. Ta sa hannu a jakar ta zaro wayar sai ta ga Hajia Ghazala a jikin screen ɗin wayar. Ta maimaita sunan a ranta kafin ta ɗau kiran tana mamakin ya akayi sunan ya shigo wayar ta. "Assalamu Alaikum, Ranka shi daɗe kamar motar ka na gani ta wuce ni yanzu" matar ta yi maganar da wani nitsuwa da sanyi irin maganar da mace ke yiwa mijin ta idan tana rarrashin sa. "Wrong number" Zaytoonah ta furta kai tsaye. "Wrong number!" Hajiya Ghazala ta furta jikin ta na wani tsuma. Ta yi saurin duba screen ɗin wayarta. Abu Razz ta gani ɓaro-ɓaro. "A ina kika samu wayar nan?, ke waye?, ina Abu Raziyan?" Ta jero tambayoyin cike da damuwa. "Oho, na gaya miki wrong number ne" daga haka Zaytoonah ta katse kiran ta maida wayar jaka. Tana ji wayar na cigaba da ringing amma ta shareshi, da aka basu hanya ta cigaba da tuƙinta hankali kwance. Numbar Hajiya Ghazala sai da ya kira ta ya fi sau hamsin lokacin da ta isa gida ta fito da wayar, sai a sannan ta lura ba wayarta bane although duka wayan iphone ne. Tunanin ko wayar Auwal ne ta yi tunda shima irin wayar gare shi. Tana ƙoƙarin nazarin wayar ta ga numbar ta ya kira wanda aka yi saving da *Barr. Zayt* "Ahmad yau shiriritan ka har exchange ɗin waya ka mana. To maza-maza ka kawo min waya gida dan yanzu haka wata Hajia Ghazla ne ko Ghalza ne sai kiran ka take yi. Wait. Ko dai sugar Mommy ɗin ka ce dan..." "Assalamu Alaikum" muryan da ba ta yi tsammani ba ya daki kunnen ta, sai a lokacin kuma ta tuno cewa ita ta yi mistake ɗin ɗaukar wayan lokacin da ta mayarda files wajen sa ɗazu da rana. Har ya faɗa ma ta zai aiko Ahmad ya zo ya karɓi wayan ba ta iya furta komai ba... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 47 Bismillahir Rahmanir Rahim "An fitar da sunan alƙalan da za su duba ƙaran, Justice yana ciki" Banza ta yi da shi ta cigaba da danna wayar ta, tun jiya ta ga sunayen kuma sunan shi da ta gani ya sa ta yi shiru da maganan dan yanzu ko mai sunan shi ba ta son gani. She still recall yadda ta kirashi ta gaggaya ma sa maganganu, ta sani ba dan a waya ba ne ko kallon sa ba za ta iya yi ba balle har ta iya gaya ma sa irin maganganun nan. "Justice Bulus Kwaplang, Justice Yunus Muhammad Abbas da kuma Justice Shafa'atu Ladan" Salman ya jero sunayen alƙalan. "Har na hango ki a gaban Galadima kina zuba bayani, wuhuhu" "Ba na son surutu Salman fita min a ɗaki" "A yi haƙuri ba ni na kar zomon ba balle a bani rataya" Tsaki ta ja sannan ta cigaba da danna wayar. Why on earth za a saka sunan shi cikin alƙalan da za su saurari ƙaran? Wannan ba coincidence ba ne, shi ne dai ya je ya cusa kan sa ciki tunda ya san zai gan ta a kotun. Ita yanzu ƙaran ma ya fita ma ta akai. Kallon Munafuki ta ke yiwa Justice tunda behind her back ya ne ya nemi auren ta, shi gashi mai sarauta. To kuwa sai dai ya mutu dan ba auren sa za ta yi ba. Ita ba dabba ba ce da za a je kasuwa a taya a siya. Tana da 'yancin da za ta zaɓi yadda za ta yi da rayuwar ta including wanda za ta aura. Balle yanzu kam ba ta da agenda na aure a gaban ta... Duk da Mommy ba ta ji daɗin yadda al'amura su ka kasance ba amma kuma yanzu ta barwa Allah komai saboda shine ya san zaɓin da ya dace da Zaytoonah. Abu ɗaya ta sani shine ko da ba Justice Zaytoonah za ta aura ba to dai ba za ta bari ta auri Auwal ba saboda kada a MAIMAITA TARIHI (a novel by my namesake). Maganganun Humairah tun da jimawa suna nan daram a ranta ba za ta manta ba. Da hannun ta ba za ta bari a samu ɓaraka tsakanin 'ya'yan Tijjani ba. A ɓangaren 'yan uwan Justice kuwa ranaku na tafiya suna cigaba da shirye-shiryen yadda biki zai kasance. Su ma a chan Ringim ɗin hakan ta ke tunda dai ɗiyar su ta yi goshi gidan sarauta za ta shiga. Hidimar da ba su ma ta ba kafin ta yi aure da kuma lokacin aurenta da Zuhayr shi su ke ƙoƙarin yi yanzu. *** Kotun ya ciƙa maƙil saboda sauraron yadda case ɗin zai progressing. Yana zama akan kujera inda ta ke zaune ya kalla, suna haɗa ido ta watsa ma sa harara. Wani haushin sa ta ke ji yanzu. And the old man has the nerves to text her this morning ta faɗa a zuciyar ta tana hararan iska. *Ina addu'ar Allah ya taimaka mi ki, ya kuma ba ki nasara, Amin. Remember i'll be there with you so dont panic". Mr Edet aka fara gabatarwa wanda yai bayani kan abinda ya sani gameda kamfanin da Patrick ya gina da kuma yadda bayan mutuwar sa kwatsam ƙanin sa Udodiri ya riƙe kamfanin a matsayin na sa bayan ya yi chanje-chanje a kamfanin including chanja sunan kamfani. Bayan ya gama bayani Zaytoonah ta ma sa tambayoyi kafin nan shima Barrister mai wakiltan Chief Udodiri yai na sa tambayoyin. Bayan ya gama ne aka bayyana sabon evidence wato audio record na muryan Anty Uloma tana bayanin yadda abin ya faru. Da ke da pidgin english ta yi maganan kusan kowa ya gane abinda aka faɗa. "Objetion My Lord. Wannan muryan ba mu yarda da shi ba, zai iya zama wata ne kawai ta zauna ta naɗi muryanta tana shirya bayanai dan a ɓatawa client ɗina suna" "Objection overruled, Barrister Zaytoon proceed" Yana maganar idon sa cikin na ta. Da farko sai da ta ɗan rasa nitsuwarta na 'yan sakanni saboda tasirin kallon da Justice ya ma ta. Ta yi saurin jan numfashi tareda cigaba da bayani. "Kamar yadda mu ka saurara Mrs Uloma ta bayyana gaskiyar abin da ya faru kuma wannan bayani ne da aka naɗe shi kwana uku kafin mutuwar Uloma Uzodinma kuma ƙanwa ta ke uwa ɗaya uba ɗaya da Chief Udodiri. Ina so kotu ta bani dama na yiwa Chief Udodiri wa su tambayoyi" Justice Bulus ya ce an ba ta dama. Chief Udodiri ya fito yana wani huhhura hanci. Sanye ya ke da igbo attire da wata sanda na alfarma da yawancin ma su kuɗin ƙasashen igbo ke amfani da shi. Zaytoonah ta matsa kusa da witness box ta ce "Mr Augustus Udodiri ko za ka iya gaya mana yaushe ne Patrick da matar sa su ka mutu?" With full confidence ya ce " 22nd December 1985" "Ko za ka iya sanar da mu abinda ya kashe su?" Wani yawu ya haɗiye jin tambayar dan dole ya faɗi abinda aka riga aka faɗa a baya dan chanja magana ka iya jawo matsala kamar yadda lawyan sa ya bashi shawara. "Patrick da Caroline sun mutu suna bacci, ba mu san dalili ba amma kasancewar akwai wanda su ka riƙe aladun gargajiya sosai a lokacin. Wasu sun yi iƙirarin cewa an cinye kuruwar su ne" Zaytoonah ta ɗaure fiska ta ce " ko za ka iya gaya mana wa ake zargin ya cinye kuruwar su?" " 'yar su Mary" "My Lords, Chief Udodiri ya bayyana ma na a rubuce kuma yayi rantsuwa cewa shi mabiyin addinin kiristanci ne tun sama da shekaru arba'in da su ka wuce. Haka nan a lokacin da Patrick da matar sa su ka mutu Chief Udodiri yana da kwalin degree in order words yana da ilimin boko, amma duk da wannan qualification ɗin Augustus Udodiri ya yarda da iƙirarin da ya ce anyi na cewa Mary-Nkiru mayya ce kuma ita ta kashe iyayen ta. Maimakon a kai case ɗin police station ayi bincike na gaskiya sai ya sa aka ɗaure Mary-Nkiru aka rufeta a wani ɗaki ba abinci ba ruwa. Ko a nan aka tsaya Udodiri ya violating human right kuma ya abusing Mary-Nkiru" "Objection My Lord, Barrister Zaytoonah ta fara kauce hanyar ƙara" "Objection Overruled" wannan karan Justice Shafa'atu ce ta yi maganar. Zaytoonah ta yi godiya kafin ta cigaba. "Ina so kotu ta sani Udodiri ba shi da hurumin da zai yanke hukunci da kan sa, ina so kotu ta tuna cewa zancen soki buruntsu Udodiri ya ke yi saboda kotu ba ta yarda da maita ba. Kenan maganan Marigayiya Uloma ya tabbata da ta ce guba aka zuba a abinci su ka ci suka mutu. "Bayan da Mary-Nkiru ta kuɓuta daga kaidin Udodiri wanda ke son a ƙona ta da ran ta bisa umurnin Dibia na ƙauyen su. Udodiri ya juya duk wani kadarori na Patrick da matar sa zuwa sunan sa. Muna da copies na wasu daga cikin takardun da aka yi na kamfani wanda ke ɗauke da sunan Caroline Asibong Uzodinma da kuma Mary-Nkiru Uzodinma a matsayin next of kin ɗin Marigayi Patrick. "Ina so kotu ta sake duba wannan shaida da Uloma ta bayar a matsayin gaskiyar abinda ya faru" Bayan ta zauna ne Barrister Toby Rowling wanda tuni ya sha jinin jikin sa saboda zafafan bayanai da Zaytoonah ta gabatar ya miƙe ya fara bayani wanda duk ɓaɓatu ya ke yi da kame-kame. Wancan karan sun samu daman bribing judge ɗin da ya saurari ƙara a High court na Imo state, amma wannan karan duka Justice ɗin da aka saka babu wanda ke da record ɗin ƙarɓan cin hanci a ciki. Infact Justice Bulus da su ka fara tuntuɓa da maganar kuɗi balbalesu yai tareda iƙirarin su ka ƙara kawo ma sa wannan tayin sai ya sa an kama su. Gaba ɗaya sun riga sun budgeting Justice Sabo da kuma Justice Ifalana za a saka a chair of Justice ɗin amma ƙwatsam aka saka Justice Yunus da sauran Justice ɗin ma su irin ra'ayin sa. Bayan ya gama na shi kame-kamen ne aka tambayi Zaytoonah ko tana da abun faɗa. Zaytoonah ta miƙe tsaye ta ce "ina neman alfarma daga wannan kotu aba da dama a exhuming jiki ko ƙasusuwan Patrick da Caroline domin a gwada ko poison ne ya kashe su ko wani abun ne daban" Tana magana kotun aka fara murmuring ƙasa-ƙasa. Shi kan sa Chief Udodiri temporary shock ne ya same shi kasancewar bai tsammanci hakan ba. Maganar da su ka yi da Galadima kenan kafin su ɓata, inda ya ba ta shawara akan idan tafiya ta yi tafiya ta nemi a tono gawan su Patrick da Caroline ya sani kafin a kai ga yin hakan dole gaskiya za ta fito. "Kin san cewa wannan aiki ba ƙaramin aiki ba ne tunda experts za a kawo daga ƙasar waje" Justice Bulus yai maganar. "Idan kotu ta bani dama ko nawa ne Client ɗina za ta biya kuɗin da za a biya expert ɗin da za su zo su yi aiki" ... *** Ƙaran shigowar text ya sa ta duba wayan ta lokacin suna magana da Mommy a bayan mota. Tana ganin numbar Justice ne ta ja siririn tsaki. *Masha Allah! I'm proud of you* abinda aka rubuta kenan. Ta wani haɗe rai kaman a gaban Justice ɗin ta ke. "Lafiya?" Mommy ta tambaya tana suspecting duk yadda za ayi Justice ne ya turo saƙo, dan tana lura da yanayin 'yartata tunda ta ma ta zancen an bayar da ita wa Justice gaba ɗaya ta tsani jin ko sunan sa ne balle maganar sa... Udodiri kaman zai yi hauka lokacin da ya ke yiwa Barrister Toby masifa, musamman da ya ke nuna ma sa akwai possibility na za a iya detecting poison a jikin gawa ko da ya zama skeleton ne. Duk wani bayanan kare kai da ya ke son yi bai saurare shi ba shi dai kawai yai duk yadda za ayi su winning case ɗin nan. Wata ɗaya kotu ta bayar a shigo da experts da za su yi aikin binciken gawan su Patrick. Saboda haka ne ma aka saka matakan tsaro a wajen kabarin na su a chan ƙauyen Okwuohia saboda gudun kar wani ya je ya tone kabarin. Kuɗi ne ba kaɗan ba da za ayi aikin da shi, dan da Mommy ta ji kuɗin sai da ta tsorata har ma ta nuna kawai a ajiye maganar tono gawan nan. "Adaeze ba sai kin taɓa dukiyar marayu ba. We can still manage" "Mommy kenan, tun da aka raba gado dai-dai da tsinke ban ɗauka a dukiyar Hadid da Hashir ba. I'm using my money" Mommy ta jinjina kai kawai dan ko shakka babu dukiyar da Zaytoonah ta samu bayan rasuwan Zuhayr ba kaɗan ba ne, and as the years progress duk wasu business da ta ke controlling sai haɓaka su ke yi. Allah ya haɗata da ma su kula ma ta da business ɗin ta wanda su ke da amana da gaskiya duk da fiye da rabin su ba musulmai ba ne... Yau za su wuce Zaria dan tunda su ka zo Abuja ba su koma ba. 'Yan biyu sun yi kukan har sun gaji, ƙarshema fushi su ka yi da Mom ɗin na su ko an ba su waya sai su ƙi magana. Tafiya su ke yi suna hira, Dreba ne ke tuƙa su yayinda Salman ke gaba, Mommy da Zaytoonah kuma na baya. Sun wuce wani ƙauye bai jima ba sai su ka ga wasu soldiers akan hanya, Dreban na ƙoƙarin tsaida mota kawai aka shiga buɗe mu su wuta da bindiga dukkan su suka yi ƙasa a rikice yayinda Dreban ya bawa motar ta su wuta suka wuce arm robbers ɗin wanda su ka yi ɓadda kama da kayan sojoji. Gudu su ke yi har sai da su ka yi nisa kafin Dreban ya samu ya tsaya wanda da hannu ɗaya ya ke tuƙi saboda ɗaya hannun bullet ya shiga... "Are they all dead?" Abinda Udodiri ya faɗa kenan a wayar ta sa kuma amsar da aka bashi ya sa shi cillar da wayar hannun sa yana ihun Nooooo. Salman ya samu bullet ɗaya a gefen cikin sa kuma shine wanda ya ke critical condition a yanzu. Dreban su a kafaɗa aka harbeshi sai Mommy da bullet ɗin ya wuce ta gefen shoulder ɗin ta. Zaytoonah kam ba abinda ya sameta sai dai shock ɗin da ta shiga na abinda ya faru ya tada ma ta ciwon ta. Yanzu haka tunanin ta Ben ne zai kashe su shiyasa ta ke ta ihun Zuhayr ya ceceta. Sau biyu ana ma ta alluran bacci saboda ta bircike mu su a Asibitin. Justice bai samu labarin da wuri ba sai chan yamma ai kuwa hankalin sa ya tashi sosai, cike da tashin hankali ya nufi Asibitin da aka kwantar da su. Salman ya fara dubawa wanda an samu an cire ma sa bullet ɗin, jinin da aka ɗaura ma sa ma ya kusa ƙarewa. Ya sameshi yana bacci yayinda Auwal ke tareda shi a ɗakin. Da ya fito ya nufi ɗakin Zaytoonah tunda a nan Auwal ɗin ya ce Mommy ta ke dan ɗaki ɗaya aka basu. Da sallama ya shiga ɗakin. Sai dai babu kowa sai Zaytoonah da ke kwance tana bacci. Tsayawa yai a gefen gadon yana kallon yadda ta ke bacci so peacefully. Ya ɗan zauna gefen gadon ya kai hannu ya shafa goshin ta. Duk da ta nuna rashin amincewarta bisa wannan aure da su ke shirin yi, baya tunanin zai janye. As selfish as it sounds, yana son auren Zaytoonah now more than ever. Shafa kumatunta daya farayi a hankali ne ya farkar da Zaytoonah inda ta miƙe a zabure tana ihu. "Ni ne" ya faɗa a ƙoƙarin sa na son kwantar ma ta da hankali amma jikinta kakkarwa ya ke tana furta sunan Zuhayr. Ba shi da hurumin yin hakan amma zuciyar sa ce ta tunkuɗashi bisa aiwatar da hakan. Jawo Zaytoonah yai jikin sa ya haɗe bakin su yana tsotsa a hankali, for a while Zaytoonah ta yi shiru amma duk wani tunanin ta Zuhayr ne a gabanta dan haka ta shiga maidawa Justice martanin kiss ɗin sosai. Mommy da ke Alwala a banɗakin da ke cikin ɗakin, ihun Zaytoonah ya sa ta fito ba shiri sai dai turus ta tsaya lokacin da idon ta ya ga abinda ya ke faruwa a ɗakin. Saurin komawa ta yi banɗakin tana faɗin "Allah kai ne masanin gaibu ka tabbatar da alkhairi a cikin wannan haɗin" Lokacin da Justice ya janye bakin sa daga na Zaytoonah lumshe ido ta yi ta faɗa jikinsa haɗe da ƙanƙameshi tana faɗin "D dama na san za ka zo, na san ba za ka bari Ben ya kashe ni ba" 2/11/21, 10:04 PM - ****: 45 Bismillahir Rahmanir Rahim *i'll stand by you* "Zauna" ya faɗa kamar ba da ita ya ke ba. Zaytoonah ta ɗan ɗokanu a kujeran tana tsuke fiska. Sai da ya gama rubuce-rubucen da ya ke kafin ya ɗaga kai yana kallon ta. Ƙaramin Gyalen da ta yane kan ta da shi ya ɗan yi baya har kana ganin farkon gashin ta. Waya ta ke dannawa dan haka ba ta san ma yana kallon ta ba. Daga baya jikin ta ya ba ta kamar ana kallon ta dan haka ta ɗago kai, nan kuwa ta sauke idon ta cikin na Justice. Maimakon yai magana sai ya sa hannu ya shafa goshin sa zuwa kan sa. Ganin kamar goshin ta ya ke kallo ya sa tayi saurin jawo gyalenta ya rufe gashin sosai. Wani file ya miƙa ma ta ya ce " zan baki case ɗin nan ne saboda ina so ki nuna ƙwazon ki a matsayin ki na wacce ta yi karatun Law. A Kaduna za'ayi shari'ar kuma duk abinda kike buƙata yana cikin file ɗin nan. Za ki iya ganawa da mutumin da za ki wakilta. Zan kuma haɗa ki da Barr. Batula, za ta ƙara taimaka miki wajen ganin komai ya tafi dai-dai. "Ina ga, daga yau sai kin gama wancan case ɗin nan kafin ki dawo nan. Kafin ina miki fatan Alkhairi" Sai da ta sauke numfashi kafin ta ɗauki file ɗin ta fara dubawa. A ɗan dubawa da ta yi na ɗan mintuna biyu zuwa uku ta gano case ɗin akan rikicin fili ne. "Na gode Sir, Insha Allahu zan samu nasara a wannan case ɗin" Har ta miƙe ta kai ƙofa bai ce komai ba, sai da ta da hannu ta buɗe ƙofan ta tsinkayi muryan sa yana faɗin " za ki iya kirana a duk lokacin da ki ke da tambaya"... Sati biyar ta yi ƙarƙashin kulawar Justice, kuma gaskiya zaman ta a chamber ɗin sa ba ƙaramin horuwa ta yi ba. Sati biyu da ta yi bayan dawowan ta daga Ringim ta yi su ne duka a ƙarƙashin Justice, kusan kullum ma a office ɗin sa take sai dai idan yana da baƙo, idan kuwa baya nan haka zai zaunar da ita da litattafai da articles ya ce ta dinga karantawa. Tambayoyi kuwa tana shan su kamar ba gobe, ba shi da takamaimai lokacin da ya ke tambaya duk lokacin da ya ga dama ya ke jehowa. Kwanan ta biyar a Zaria ta wuce Kaduna. Ta haɗu da Barr. Batula da kuma client ɗin ta kuma tana da yaƙinin case ɗin zai zo ma ta da sauƙi, haka ma Mommy ta ce ma ta. "Ke wacce irin daƙiƙiya ce? Ba ki yi karatu ba ne ko ba shirya ba ne?. Ko da ace court attachment ki ke bai kamata ace kina wannan irin kuskuren ba, balle ke certified Barrister ce. Anya ma ba da kuɗi ki ka haye jarrabawan Law School ba?" Maganganun Barr. Batula kenan lokacin da su ka shiga office ɗin ta bayan sun dawo daga kotu. Zaytoonah ta sunkuyar da kan ta ƙasa tana sauraron wannan cin mutuncin. Ba fa cewa aka yi sun loosing ƙarar ba. Kawai dai an ɗaga ƙaran ne zuwa nan da sati biyu. "This is an open and close case Wallahi. Tuni da an wuce wajen, amma kin je kina ta shirme. Wai tukunna ma wani matsayi gareki da har Galadima zai ce na bar miki case da ke hannuna?" A harzuƙe Zaytoonah ta ɗago fiska tana faɗin " Ya ishe ki haka Barr Batula. Ba ni na kawo kai na nan ba, idan kin matso ki san mi ke tsakanina da Justice za ki iya ɗaukan waya ki kira ki tambayeshi" daga haka ta fice ma ta daga office. Duk da matar ta girmeta sosai dan aƙalla za ta kai shekaru Arba'in amma ba ta tunanin za ta iya juran wannan cin mutuncin. Dama tun kafin ma a saurari ƙaran take-taken matar ya nuna kamar ba za su jitu ba. Tana ganin kiran Justice lokacin da ta fito amma ta share shi, ita da shi da Batulan ma haushin su take ji. Mai kawai ta ƙarawa motar ta ta wuce Zaria. Da ta ba wa Mommy labarin abinda ya faru a kotu Mommy ƙara ƙarfafa ma ta gwiwa ta yi tareda nuna ma ta cewa dama haka ake shari'a, ba lallai daga zaman farko a yanke hukun ci ba, ƙila sai an yi zama biyu ko uku ma duk yadda dai yanayin shari'ar ta ke da zafi. Bayan hiran su da Mommy ne ta samu ɗan sanyi a ran ta. Auwal ma da ya zo encouraging ɗin ta ya dinga yi yana nuna ma ta ai ba ƙaramin ƙoƙari ta yi ba ma duba da cewa wannan ne first case na ta. Sai da za ta kwanta ne ta ga missed calls ɗin Justice har guda biyu, ta tuna cewa ai ya kirata tun da rana ba ta ɗaga ba. Ta duba agogon wayar ta ta ga ƙarfe goma har da rabi da minti shida. Hiran da su ka tsaya yi da su Auwal ne ma ya sa itama bata kwanta da wuri ba. Kamar ba za ta kira shi ba sai kuma ta kira ɗin bayan ta tuna cewa shi ɗin tuzuru ne tunda zawarci ya ke yi. Sai da wayar ta kusa tsinkewa aka ɗauka da sallama. Shiru dukkan su suka yi bayan Zaytoonah ta amsa sallamar ta shi. Kusan second talatin ta gitta ba wanda yai magana a cikin su ganin dai ba magana zai yi ba ya sa ta sauke fushin data ke yi ta ce "Sir an ɗaga ƙaran" "Na sani" ya furta a sanyaye. Sai ya dinga yin shiru, ni ban san mi zan ce ba kuma. Mutum magana ma aiki ne a wajen sa. Ta yi wannan tunanin a zuciyar ta. "Kin yi ƙoƙari sosai" ya furta biyo bayan shirun da yai. Ba ta ce komai ba dan ba ta da abin faɗa. "Barin gaya miki wata addu'a da za ki dinga yi da zai rage miki jin tsoro" Jin yayi maganar addu'a ya sa ta tattaro hankalin ta ta bashi, lokacin da ya fara bayanin ne ya sa ta yi saurin danna call record saboda ko ta manta zuwa gobe za ta sake sauraran sa. Yana gama gaya ma ta addu'ar ya kashe wayar. A ɓangaren Zaytoonah ta ce "Justice ba dai manyan ce ba" A saman ƙirjin sa ya ajiye wayar tareda sauke dogon numfashi. A kullum da ya ke sakata cikin addu'o'in sa sabbin lamura ya ke ji a ran sa gameda ita. Maganganun Ni'ima na ranan su suke ƙara tunzura zuciyar sa wajen kwaɗayin tayin da ta ke ma sa. "Yaya ba sai na faɗa ma ka falalar da za ka samu ba idan ka riƙe marayun yaran ta. Allah kai kan ka za ka yi alfahari da auren ta nan gaba kaɗan. Ta san ciwon maraici tunda tana da 'ya'ya marayu shiyasa na ke kyautata zaton ba za ta muzgunawa su Raziya ba. Yaya ka bani dama na yiwa Hajja magana" Bai san dalilin sa na ajiye hoton a wayan ba, ba halin sa ba ne irin haka amma ranan kallo ɗaya yai wa hoton ya saving na shi. Profile picture ɗin ta ne da ta saka a whatsapp ranan wata Jummu'a. Bai san yaushe aka yi hoton ba amma a office ɗin sa aka yi a kuma kan kujerar sa. Ba selfie ba ne hoton dan zama ta yi da kyau aka ɗauketa, babu tantama Ahmad ne ya ɗauketa. A ranan ta cire hoton daga DP ɗin ta ɗaura hoton wasu jarirai guda biyu, sai ya ji daɗin ma saving ɗin hoton da yai da sauri. Yanzu ma hoton ya kalla yana tunanin anya yarinyar nan za ta iya amincewa da shi?... *** "Ai da Ni'ima ta kawo yarinya tuni ka amince. Wato dai ni ce ban isa na maka tayin Mata ba" Hajiya Abu ke wannan magana tana wani cin magani, a matsayin ta na babbar Ya a wajen Galadima. Galadima yai murmushi dan ya san ko ya ma ta bayani ba fahimta za ta yi ba. Duk da tazarar shekaru da ke tsakanin Hajia Abu da Ni'imar hakan bai hana su samun saɓani ba har ta kai ba sa ga maciji tsakanin su. Hakan ya samu Asali ne lokacin da Hajiya Abu ta turo Sadiq wajen Ni'ima lokacin tana ajinta na ƙarshe a Jami'a. Sadiq ɗan babban gida ne shima kuma mahaifin sa da Mijin Hajiya Abu Abokai ne na ƙut da ƙut. Ƙin auren Sadiq da Ni'ima ta yi shine mafarin faɗan na su kuma har yau ba sa shiri. Hajiya Abu mace ce me son zuba iko da mulki a duk inda ta ke, tana da girman kai har na sayarwa. Shi kan sa yayi mamaki da Maimartaba ya kira shi akan tabbatar da maganar da ya ji daga wajen Hajja wacce ta ke mahaifiyar Ni'ima kuma Uwar riƙon sa. Ya riga ya sanar da Ni'ima akan ta ajiye maganar zuwa lokacin da za a gama case ɗin Mommy kafin nan ya gama yanke shawarar abinda zai yi, sai gashi ita kam ta kai shi har gaba. Da ke dama an matsu yai auren shiyasa ma da aka sanar da Maimartaba da wuri ya kirashi dan ya ji ta bakin sa. "Aka ce yarinyar Inyamura ce" Hajiya Abu ta faɗa ita a dole fa ba ta so Galadima ya auri yarinyar da Ni'ima ta kawo. "Hajiya har yanzu ban yanke shawara ba tukunna, dan haka ina buƙatar addu'a Allah ya zaɓa min mafi Alkhairi" daga haka ya ma ta sallama ya fice daga falon ta, ba dan ta buƙaci ganin sa ba ma ba abinda zai kawo shi gidan. *** Kallon Zaytoonah ta ke yi da ke bacci hankalin ta kwance. Gobe za su wuce Owerri saboda shigar da ƙara da za su yi. Mommy ta halarci last zama da aka yi a case ɗin da Zaytoonah ta jagoranta kuma ta ji daɗin yadda 'yar tata ta jajirce a wajen. She won the case kuma hakan na nufin Zaytoonah za ta iya tunkaran babban case kamar na ta. Whatever the outcome, za ta yi alfahari da cewa 'yar ta ce ta tsaya ma ta. Wannan karan ba za ta yiwa 'yar ta dole ba. Duk min girma da daraja irin na Galadima ba za ta taɓa ba shi Zaytoonah a matsayin Alfarma ba, matuƙar ba Zaytoonan ce ta ce tana son auren ba. Zaytoonah deserves to marry the person she love. Haƙuri ta ba wa Ni'ima lokacin da ta kawo ma ta zancen da ya rikitata har ta ke tunanin anya ba za ace ita ta yiwa Galadima tallen Zaytoonah ba?. Addu'a ta karanto a hannu sannan ta shafa a fiskar Zaytoonah kafin ta gyara ma ta bargo... Kaman daga sama Chief Udodiri ya tsinkayi takardar kotu da ke tuhumar sa da abubuwan da ya jima da mancewa ma ya yi su. Nkiru is alive? Ya furta maganar cike da rashin yarda. Mary-Nkiru dai da ta gudu shekaru kusan talatin da su ka wuce. Da farko abin ma dariya ya bashi saboda tunanin ko 'yan 419 ne su ke son damfarar sa amma daga baya da ya tuntuɓi Lauyan sa ya kuma sa a ma sa bincike sai ya gano gaskiya. Hoton Maryam da aka kawo ma sa ya ƙurawa ido, tabbas ita ce Mary-Nkiru 'yar Yayan sa. Nan da nan hankalin sa ya tashi. Bai san mi take da shi ba a matsayin evidence, ga uwa uba Sunan sa da zai ɓaci idan case ɗin nan ya fito fili tunda ga zaɓe na ta ƙaratowa kuma har an bashi ticket a jam'iyyar su. Wannan ya sa ya kira zama da Lawyoyin sa dan a san ta inda za a tari matsalar... Da Mommy da Auwal ne ke tare da ita kasancewa yau ne za a fara sauraron ƙara. Tun da Asuba ta kalli text ɗin Justice da ke ma ta Addu'ar samun nasara tareda nuna ma ta cewa ka da ta ji tsoro domin Allah na tareda ita. Su Mommy ma maganar su kenan har su ka isa court ɗin. Kotu ya cika maƙil saboda Chief Udodiri ba ƙaramin mutum ba ne a Jahar. Wannan ya sa kowa ke son sanin yadda za ta kaya domin dayawa ba su yadda da wannan ƙara ba tunda abu ne da aka yi shi shekaru da dama da su ka wuce yawanci ma an manta yadda abin ya faru. Hatta a cikin 'yan uwa an riga an manta da labarin wata wai Mary-Nkiru. Ranan da aka yi zama na farko kaɗan ya rage Zaytoonah ta yi hawaye saboda yadda Lawyan Udodiri ke kore duk wani magana ko tambaya da ta yi. Ikon Allah ne kawai ya sa aka tashi daga kotun nan lafiya ba tareda Zaytoonah ta yi kuka ba. Gaba ɗaya ta karaya da yadda abubuwa su ka tafi. Ba ta yi kuka ba sai da ta shiga banɗaki sannan ta zauna ta dinga kuka tana yi tana rufe bakin ta dan kar Mommy da ke ɗaki ta jiyota. An ɗaga ƙara zuwa kwana shatakwas ma su zuwa amma a yadda ƙaran ke tafiya ba su da wani hope a tattare da su ko kaɗan. Ita kan ta Mommy jikin ta yayi sanyi. Sun fito daga hotel inda driver ke jiran su ya kai su Airport kenan sai ga wasu baƙaƙen motoci guda uku ma su kyau sun shigo harabar hotel ɗin. Dreban su na ƙoƙarin ficewa daga hotel ɗin wani bodyguard yai saurin tsare shi. Auwal da ke gaba ne ya fito yana yiwa bodyguard ɗin magana da turanci yana tambayar ko lafiya zai shiga gaban su. Magana ya ma sa tareda nuna ma sa motocin da su ka shigo wanda shima ɗin daga ɗaya daga cikin su ya fito. Kamannin su ɗaya sai dai ɗaya ya fi ɗaya furfura a gashin kai. Atleast iya banbancin da su Mommy su ka gani kenan lokacin da su ka fito daga mota yayinda waɗannan 'yan biyu su ka tunkare su. Dukkan su biyu Mommy ke kallo tana son gaskata idon ta, dan waɗannan 'yan biyu suna yanayin kama da mahaifiyar ta. " ke ce Mary-Nkiru Uzodinma ko?" Ɗaya daga cikin su yai tambayar yana kallon Mommy. Mommy ta gyaɗa kai. "Ke ce 'yar Caroline Asibong?" Maimakon Mommy ta bada amsa sai ta ce " ku ne ƙannen Mama na?" Kuka ne ya kuɓcewa Mommy lokacin da mutanen nan su ka gabatar da kan su a matsayin Paul Asibong da Peter Asibong 'ya'ya ga Chief James Asibong. Ɗaya bayan ɗaya su ka rungumeta suna hawayen farin ciki. Maimakon su tafi Airport su koma chan gida sai kawai su ka bi Uncles ɗin Mommy a motar su daga Owerri har Calabar. Tun a hanya su ka sanar da Mommy cewa Kakan ta na raye kuma yana tsananin son ganin ta. Tun lokacin da labari ya iso mu su cewa Caroline da mijin ta sun mutu ba ƙaramin tashin hankali su ka shiga ba. Tun lokacin Chief James ya samu paralysed wanda daga baya ne da aka fita da shi jinya ƙasar waje shine ya samu lafiya. Udodiri shi ya sanar da su Mary 'yar Caroline ma ta mutu shiyasa ba su neme ta ba. Sun koma America da zama wanda shekaru biyu kenan da dawowar su. Case ɗin nan da Peter ya gani a Jarida ne ya sa shi bin bahasin labarin har ya gano gaskiyar lamari cewa Mary-Nkiru 'yar yayar su dai na raye ba ta mutu ba. Gida ne mai girma, gini na zamani su ka sauka inda dukkan su suka isa wajen Kakan Mommy wanda ke zaune a kan wheelchair yana dakon zuwan su. Babu tantama dai wannan jikar sa ce dan ga kamannin Caroline da ta ke da shi. Batun komawa Zaria ajiye shi aka yi a gefe aka shiga hiran abubuwan da su ka faru. Chief James yayi kuka sosai da ya ga Mommy domin ganin ta ya sa shi tunowa da 'yar sa da kuma wautar da yai wanda yai sanadiyyar rasa 'yar sa Caroline. Da ace tun farko ya amince da aurenta da Patrict da ƙila duk waɗannan abubuwa ba su faru ba. Sai dai kuma ƙaddara ta riga fata. A gidan aka ba su masauki inda sauran 'yan uwa ke zuwa duba Mommy a matsayin ta na 'ya ga Caroline. Peter yana da 'ya'ya 'yan biyu mata kuma duka sun yi aure. Ɗaya na ƙasar Germany ɗayar kuma na zaune a Lagos da Mijin ta. Shi kuma Paul 'yayan sa uku ne maza biyu mace ɗaya. Baban ɗan sa yayi aure yana America dan baturiya ma ya aura. Caroline wacce su ke kira da Carol itama ta yi aure tana Portharcourt sai autan sa Felix wanda ke Phd ɗin sa a Yale University. Chief James yayi alƙawarin duk yadda za ayi a hukunta Udodiri sai anyi dan ba zai taɓa yafe ma sa ba. Ba ƙaramin ja'in ja aka yi ba akan son ɗauke case ɗin daga hannun Zaytoonah da su ke son yi. Mommy ta yi biris akan ta yadda da 'yar ta ta kuma san Allah zai taimake ta. Daga ƙarshe dai haka su ka haƙura akan Zaytoonah za ta cigaba da case ɗin. Kwanaki shatakwas ɗin nan a Calabar su ka yi shi ita da Mommy, Auwal ne ya koma saboda aikinsa, ba ƙaramin kulawa 'yan uwan Mommy na wajen Uwa su ke nuna mu su ba, duk da sun kasance Musulmai hakan bai rage soyayyar Mommy da 'yar ta a zukatan su ba, abinda su ka sani shine Mommy jinin su ce. Ance da sauran yaran ma sun yi hutu za a kawo su suma su ga 'yan uwan Mommy... Kuka ta ke wiwi kamar wacce aka yiwa mutuwa. Tun da su ka fito daga court ɗin ta ke hawaye. Mommy ta nuna ma ta ba komai ba ne haka Allah ya rubuta amma ta kasa haƙura. Ji take yi da ta yi ƙoƙari fiye da haka da kotu ba ta yi watsi da ƙaran nan ba. Zaune ta ke wajen fountain inda ta ke zaune tana jin daɗin sanyin ruwan da ke ɓulɓulowa. Tun jiya ta kasa cin abinci, tun Mommy na lallashin har ta haƙura ta ƙyaleta. Ita safiyar nan ma tafiya ta so yi sai dai babu jirgin Kano ko Kaduna da zai tafi yau, na Abuja kuma tun ƙarfe huɗun Asuba ya tashi. Idon ta da ya cika da hawaye ta sa hannu ta share. Ta cigaba da kallon ƙasa tana sheshsheƙar kuka. Zama yai kusa da ita yana kallon yadda fiskarta ya koma saboda kuka. Yayi kusan minti biyu yana zaune a wajen amma ba ta san da zaman sa ba. Yanayin Sallamar sa da ba za ta iya mantawa ba ta ji a kunnen ta. Ta ɗan yi shiru kaɗan da kukan ko dai kunnen ta ne ya ji ba dai-dai ba. A karo na biyu ya sake sallama wanda ya sa Zaytoonah ta juya gefen ta da sauri. Ta zaro ido ganin Justice zaune a wajen yana murmushi. Maimakon ta amsa sallamar sai ta ce " Sir an kori ƙaran da mu ka yi. I failed Mommy, I failed You. Gaskiyar Barr. Batula ne da ta ce ni daƙiƙiya ce" "Ssshhhhh" ya sa yatsa a daidai bakin sa alamar ta yi shiru. "Waya gaya miki kuka ake yi idan an kori ƙara?" "Sir..." "Ki dena kuka, kin yi ƙoƙari sosai and i'm proud of you, kuma na san Mommy na ta alfahari da ke. Ka da ki damu da cewa wai an kori ƙara. This is just the begining. "Ni Yunus Muhammad Abbas zan tsaya miki har sai mun kai kankat ɗin shari'a a Nigeria. Zamu cigaba da ɗaukaka ƙara har sai mun ci nasara. Idan kuma ba mu da nasara a nan, za mu bar wa Alƙalin Alƙalai wanda ba ya zalunci, Alƙalin da babu wanda ya isa ya yai ƙarya ko ya ba da shaidar ƙarya a gaban sa. Shin kin san wannan Alkali?" Zaytoonah ta girgiza kai. "Ba ki sani ba?" Yai maganar da ɗan mamaki a fiskar sa. Zaytoonah ta girgiza kai. Yatsar sa ɗaya ya ɗaga yana nuna sama da shi. "Alƙalin Alƙalai shi ne mai kallon duk abinda ke wakana a doron ƙasa" Zaytoonah ta yi murmushi ta ce "Sir ai sai ka min gwari-gwari zan fi fahimta" "To yanzu barin mi ki gwari-gwari. Kar ki sake yin kuka kin ji, domin ko da a nan duniya gaskiya ba ta fito ba, za mu haɗu gaban Allah a ranan da babu wani mai Mulki ko Isa bayan shi" Bai san dalilin da ya sa yai haka ba amma abu ne da zuciyar sa ta riya ma sa gangan jikin sa kuma ta aiwatar. Hannun ta ɗaya ya kamo ya sarƙe da na sa. Tunda ya kama hannun Zaytoonah ta ji wani sanyi na ratsata. Sau ɗaya ta haɗa ido da shi sannan ta sunkuyar da kai tana jin ƙirjinta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi. "Ki min alƙawari ba za ki yi kuka ba Zaytoon" Ta kalle shi da sauri jin sunan tamkar a bakin Zuhayr. "Zan taimaka mi ki ta kowanni fanni har mu kai ga nasara Insha Allah. "Ina so ki bani haɗin kai har komai ya tafi dai-dai. Zaytoon a duk lokacin da ki ke tunanin kin gaza a wani abu to ina so ki tuna cewa Yunus yana kusa da ke kuma zai zame miki madogara. I'll stand by you Zaytoon ko da ba mu samu nasara ba" Ba ta san ya za ta fassara yanayin da ta tsinci kan ta ajiki ba. Is like kamar Zuhayr ke tareda ita a wannan lokaci, idan da hali kwantawa za ta yi jikin sa ta samu nitsuwa. Sai dai kafin ta kai ga biyewa zuciyar ta wajen aiwatar da abinda zuciyar ta ke tunani Justice ya sake hannun ta yana faɗin " ki tashi ki shiga ciki akwai sanyi a nan". Mommy da ke kallon abinda ke faruwa daga sama ta sauke ajiyar zuciya ganin wannan dramar mai kama da almara, duk da ba ta ji mi su ke faɗa ba amma abinda idon ta ya gani ta fahimta sosai. Tun jiya Justice ya sanar da Mommy zai zo bayan ta sanar da shi hukuncin da aka zartar a kotu. Jirgin su tsakar dare ya sauka shiyasa ma ya kwana a hotel sai yau da safe Mommy ta aika dreba ya je ya ɗauko shi. Hiran minti goma su ka yi da Mommyn ne ya tambayi Zaytoonah shi ne ta sa wani mai aiki ya kai shi wajen ta dan ɗazu da ta leƙo ta balcony ta hangota zaune a wajen fountain na gidan.. 2/11/21, 10:04 PM - ****: 46 Bismillahir Rahmanir Rahim *engaged* "Ranka shi daɗe babu wanda ya ke goyon bayana cikin su, Ƙyamatata su ke saboda na zama Musulma. I think Uncle Udodiri ya riga ya poisining mind ɗin su, nobody is ready to testify" Justice ya ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya ya ce "wannan mata da ki ka ce ta taimake ki kin gudu lokacin, tana raye?" "An ce ta mutu shekaru biyu da su ka wuce" Justice yai shiru na ɗan daƙiƙai kafin ya ce " za a iya samun wanda za su yi magana idan an tunzura su" Cike da mamaki Mommy ta ce "Ranka shi daɗe kana nufin a bribing na su?" "A cikin kowani Family ana samun rashin jituwa tsakanin 'yan uwa. Maƙiyan Chief Udodiri su za su ba mu haske har mu samu shaidar da mu ke so. If we ask the right question the right way, we'll get the answers we needed"... Tun maganar su da Justice ta fara sake jikin ta. Lokacin da ta shiga gida wanka ta yi ta ci abinci sannan ta yi Sallah, daga wajen da ta yi sallar ne ma bacci ya sace ta. Kusan ƙarfe biyar na yamma ta wuce su ka isa ƙauyen na Okwuohia. Asalin mafarin komai kenan. Tun da su ka zo Owerri sau biyu su ka je ƙauyen. Rashin samun fiska daga 'yan uwanta ya sa ba su sake komawa ba. Family house ɗin su na nan yadda ya ke duk kuɗin Udodiri bai gyara gidan ba, babban fili ya samu a ƙauyen na su ya gina ƙaton gida duk lokacin da ya shigo ƙauyen a nan ya ke sauka. Gidan Mazi Nkem su ka je wanda shi ne Babba kaf gidan, ƙanin mahaifin su Udodiri ne. Goro da palm wine aka kawo mu su a matsayin abun tarban baƙi, tunda sun samu Mazin shima na shan giyan ne. Maryam ne ta fara bayani cikin harshen su na Igbo wanda bai zauna ba saboda sabo da yaren Hausa da kuma Turanci da ta yi. A karo na biyu ta nemi ya sanar da ita abinda ya sani gameda mutuwar iyayen ta. Wancan karan da su ka zo cewa yai bai san komai ba, shi baya ƙauyen sanda abin ya faru, lokacin da ya dawo ne ya tarar da mutuwar da kuma guduwar Maryam ɗin. Duk tambayoyin da Mommy ke ma sa sai ya ce bai sani ba. Mommy ta kalli Justice da ke lura da yadda tsohon ke kwankwaɗar giya a kofin silver. "Ranka shi daɗe ya ƙi magana" Justice ya miƙe tsaye yana faɗin "Hajiya taso mu tafi" Ba mu su Mommy da Zaytoonah su ka miƙe su ka bi bayan sa da mamaki. Sai da su ka yi nisa sannan ya tsaya ya ce "ba za mu samu komai a wajen sa ba a haka. Ina so mu je gidan Pastor na ƙauyen nan" Ba mu su Mommy ta sa Eze wanda ya ke mu su rakiya akan ya kai su gidan Pastor. Ko da su ka isa Justice ya gabatar da kan sa wajen Pastor Emmanuel tareda ma sa bayanin abinda ya ke so. Pastor Emmanuel ya jinjina da lamarin tareda alƙawarin zai yi duk yadda Justice ɗin ya ce. Su ka ma sa godiya su ka tafi Mommy da Zaytoonah suna jinjina hikimar Justice... Sun isa Owerri chan dare inda su ka kama hotel su ka kwana. Washegari bisa Umurnin Justice su ka ziyarci tsofaffin mai'aikatan Kamfanin Mahaifin Maryam wanda Udodiri ya ƙwace, wanɗanda su ke aiki tun lokacin da aka buɗe kamfanin. Da ke duk haɗin baki su ka yi duk tambayoyin da su ke mu su amsa ɗaya su ke samu, sai a wajen Mr Edet kawai su ka samu amsan da su ke so. Mr Edet yayi aiki a kamfanin na shekara ɗaya tun farkon buɗe kamfanin kafin daga baya ya ajiye aikin. Ya ba su vital information wanda za su taimaka. A hanyar su ta dawowa ne wata number ta kira wayan Mommy. Da ke Mommy ta bada numbarta a wajaje dayawa shiyasa tana ganin baƙuwar numba sai ta ɗauka. Matar da ke magana da yare ta ke magana inda ta nuna ta san wani abu gameda abinda ya faru shekaru talatin da su ka wuce... Bayan sun yi wayar ne Mommy ta ce "Ranka shi daɗe trap ɗin ka yayi aiki, Aunty Uloma is ready to confess" "Mommy is she reliable?" Zaytoonah ta yi tambayar tana kallon Mommy. "Ƙanwar Baba na ne itama, Uwar su ɗaya da Udodiri" "Then ya kamata mu haɗu da ita a yau ɗin" Justice da ke gaba yana jin su bai ce komai ba. Lokacin da su ka isa ƙauyen a gidan Aunty Uloma su ka tsaya. Mommy da Zaytoonah su ka shiga yayinda Justice ke jiran su a mota shi da Driver. Tabbas wa'azin da Justice ya ce Pastor yai a church ya shiga zuciyar Aunty Uloma sosai. Kuka ta ke yi sosai lokacin da ta ke yiwa Mommy bayanin komai. Mommy ma sai da ta yi hawaye jin yadda Udodiri ya kitsa komai. A lokacin da Udodiri ya faɗa mu su plan ɗin sa na kashe Patrick ba ta supporting ɗin sa ba amma da yai ta hura ma ta kunne sai ta amince ita ta kai abincin bayan Udodiri ya gama barbaɗa poision ɗin a ciki. Bayan alƙawurra da Udodiri yai ta yi na cewa zai kaita birni sannan ya kai 'ya'yanta karatu ƙasar waje sun bi ruwa hakan ya sa Uloma ta fara nadama tun lokacin, ta ba da rayuwar ta wa Christ tana neman yafiyar sa. Jiya kuwa da Pastor Emmanuel ya mu su wani wa'azi hakan ya ƙara tsoratata har ta yanke hukuncin sanar da Mommy komai. Lokacin da Aka fara case ɗin Udodiri ya zo ya ba ta dubu ɗari akan ka da ta kuskura ta faɗi abinda ta sani ko kuma hakan yai sanadiyyar kashe 'ya'yan ta. Amma tana son shiga heaven gara kawai ta tona asirin komai saboda Jesus ya yafe ma ta gaba ɗaya, kuma ta yadda Jesus zai cececi 'ya'yan ta daga tuggun Udodiri. Sai da ta mu su alƙawarin za ta zo a matsayin shaida kafin su ka bar gidan. Suna shiga Mota Zaytoonah ta turawa Justice recording ɗin da ta yi. Lokacin da su ke hanya ne ta ga text ɗin Justice ya shigo wayar ta, tana buɗewa taga umurni ne ya ke ma ta akan ta recording hiran su da Aunty Uloma. Cikin zuciyarta ta dinga jinjina ƙasaita irin ta Justice, wato maganar ta ma sa nauyi sai dai yai text. Har su ka koma Mommy ba ta yi magana ba, jikin ta yayi sanyi da abubuwan da ta ji. Ta daɗe da sanin cewa Udodiri ne ya kashe Iyayen ta amma yau da aka kuma tabbatar da komai da kuma yadda abun ya faru ta girgiza sosai. Ace akan dukiya ƙani zai hallaka yayan sa, duniya kenan. Washegari Monday Justice ya shirya ya koma Abuja bayan sun sake tattaunawa akan yadda suke ƙara samun evidences akan case ɗin. *** "Ikon Allah, yanzu Abu Razz kuma yare zai ɗauko, Hajiya kuma kuka zuba ido" Hajia Ghazala ta yi maganar cike da damuwan jin bayanan Hajia Abu. "To ya za mu yi tunda shi dai ba yaro ba ne ya san abinda ya kamata amma ya biyewa shirirtar Ni'ima" "Ni fa yaran nan na ke tausayawa idan ba haka ba da bazan damu da ko waye zai aura ba. Gashi yarinyar ba wani kamun kai gareta ba, yadda kika san ba musulma ba haka take ta shiga cikin maza a office ɗin su" "Maganar fa ta kai wajen Mai Martaba, shi kuma har ya ɗau mataki akai maganar da ake ma yanzu an bashi yarinyar. Ina ga ma dalilin da ya sa ya tafi chan garin su kenan dan su sasanta" Duk wani bayani da ya biyo baya Hajia Ghazala sama-sama ta ke jin sa. Maganar an bawa Justice Mata ya riga ya birkita tunanin ta, amma da ya ke ita ɗin gwana ce wajen iya shanye damuwarta shiyasa Hajia Abu ba ta fahimci komai gameda tasirin da maganar yayi a jikin ta ba dan Hajia Ghazala harda yiwa Justice addu'an alkhairi. Tana barin gidan Hajia Abu numbar Justice ta kira bai ɗauka ba dan haka ta duba lokaci, ƙila yana sallah ta faɗi a ranta tana ƙara alhinin wannan al'amari. Wai Justice zai auri yarinyar da ta gani a office ɗin su ranan. Ta ina ta dace da Justice?. Ta ya za ayi ta rasa Justice a karo na biyu?. Ƙaddara dai ta riga fata amma da yanzu fa ita ce Matar sa tun asali, Ƙuruciya dangin hauka, ƙuruciya ya sa ta yi wauta da har yau ta ke nadama... Uba ɗaya su ke da marigayiya Maryam kuma mahaifin su ƙani ya ke a wajen Mai Martaba. Da ke Justice a ƙasar waje yai karatun sa ba ta san shi sosai ba, rabon da ta gan shi ma tun wani hawa da aka yi su ka je kallo lokacin ba za ta wuce shekara shaɗaya zuwa shabiyu ba. Tana shekara shatakwas yayinda Maryam ke shatara Mahaifiyarta ta ma ta maganar haɗin da Abban su ke son yi da ita da Yunus ɗan Sarki. Kai tsaye ta ƙi saboda soyayyan Alhaji Bashir da ya rufe ma ta ido. Alhaji Bashir yana ɗaya daga cikin ma su Arziƙi da su ke tashe a lokacin, matar sa ɗaya a lokacin da 'ya'ya biyu. Tunanin Yunus ma irin halin Yayan sa ya ɗauko na neman Mata da shan giya ya ƙara sawa ta yi fatali da zancen auren Yunus. Maryam an yi ma ta baiko da wani ɗan uwanta ta wajen Uwa amma ya rasu sakamakon haɗarin Mota, hakan ya sa ta ce karatu za ta cigaba ba za ta yi aure a kusa ba. Da Abba yai wa Ghazala maganar sai ta yi biris ta nuna indai aka takura ma ta za ta kira Mai Martaba ta ce ba ta son auren kuma ta san ba zai ma ta dole ba. Abban su ya ji haushi sosai amma ya ƙyaleta da zaɓin ta inda aka juya maganar zuwa wajen Maryam. Dama saboda Ghazalar ce ke kula samari ya sa yai niyyar haɗasu da Yunus tunda Mai Martaba ya ma sa maganar a nema ma sa mata kafin ya koma ƙaro karatun da ya ce zai yi. Ranan da Yunus ya zo gidan dan su sasanta da Maryam ne Ghazala ta je ganin Yunus ɗin dan ta yi gulma kasancewa ba wani jituwa su ke da Maryam ɗin ba sosai. Kuka sosai Ghazala ta yi da ta shiga ɗaki bayan ta ga Yunus. Kyakyawan saurayi mai kwarjini da kamala. Ashe shine Yarima Zannoon da ake ta labari cewa yana da kamun kai nitsuwa ga uwa uba Ilimi. Lokacin da ta yi wa Umma maganar akan ta amince za ta auri Yunus Umma faɗa ta yi ma ta dan tun kafin a karɓi kuɗin Aurenta a wajen Alhaji Bashir aka ma ta maganar Yunus amma ta ce ba ta so. A lokacin duk wani soyayyar da ta ke ganin tana yiwa Alhaji Bashir sai ta nemeshi ta rasa, soyayyar Yunus ne ya mata mugun kamu ya mamaye ilahirin zuciyar ta. Tun tana dana sani a fakaice hatta zo tana bayyana Hassadar ta a fili. Da labari ya kai wajen Abba ne ya sa ya matso da bikin ta kusa. Maimakon wata biyu da aka saka da sai aka dawo da shi sati uku. Bikin dai kamar ba za ayi ba haka dai aka samu aka yi auren Ghazala da angonta Alhaji Bashir. Bayan wata biyar ma tukunna aka yi auren Maryam da Yunus... *** Su Mommy na komawa Calabar da kwana biyu aka kira su akan Anty Uloma ta mutu. Ba mamaki ba ne kasancewa bayan tafiyar na sun Anty Uloma ta bugo akan Udodiri ya zo yana ƙara ma ta kashedi akan ta yi shiru da bakin ta ko kuma jikin ta ya gaya ma ta. Ɓarayi ne su ka shiga gidan ta su ka kasheta bayan sun yi sata amma ga mai hankali ya san akwai lauje acikin naɗi. Thank God suna da recording ba dan haka ba da sun rasa vital evidence, duk da testifying da za ta yi zai wadatar fiye da audio ɗin amma duk da haka audio ɗin ma shaida ce... Sati ɗaya da tafiyar Justice suma su ka dawo Zaria. A ranan da su ka dawo ne su ka samu saƙo daga Ringim wai Mommy ta je idan ta samu lokaci. Mommy ta tambayi Auwal da ya ba da saƙon ko ya san dalilin neman ta da ake yi amma ya ce bai sani ba. Yanayin da ya ke yi tun dawowar su ya sa ta lura akwai wata matsala a ƙasa. Waya ta ke yi da Justice tana bashi update akan maganar appeal da su ka yi wanda za a fara sauraron ƙaran nan da sati uku a Nigerian court of appeal da ke Abuja. Auwal ne ya shigo da sallama ya samu waje ya zauna yana satar kallon Zaytoonah da ke faman waya fiskarta ɗauke da murmushi. Yanayin maganar da ta ke yi ne ya sa ya fahimci da wanda ta ke magana. Yau Mommy ta tafi Ringim kuma ya san idan ta je chan za ta ji koma minene aka shiryawa Zaytoonan ba tareda sanin ta ba. Ba zai iya haƙura da Zaytoonah ba a karo na biyu, indai ta amince da soyayyar sa to dai dole Justice ya haƙura duk da kasancewar ya riga ya turo magabatan sa. Kusan minti shida kafin ta gama wayar ta ajiye wayar gefe tana faɗin. "Ya Auwal idon ka kenan, tunda mu ka dawo fa sau ɗaya na gan ka" "Idan kina son ganina kirana za ki yi ai sai na zo" "Ba wani ai da da ƙafar ka kake zuwa ka neme ni" ta yi maganar tana haɗe rai "Ban samu amsar tambayata ba har yanzu Zaytoonah. Ko kuma dai zaɓin da su Baffah su ka miki shine dai-dai a wajen ki?" Zaro ido ta yi jin kalaman Auwal. Itafa ranan da su ke chatting ya ma ta wannan tambayar ta ɗauka wasa ya ke yi shiyasa ta manta da maganar ma. *"ina so ki bani dama na zamo Uba a wajen Hashir da Hadid. Ina so ki bani dama na kasance tareda ku har iya ƙarshen rayuwa ta, Ina so ki bani dama na nuna miki soyayya da kulawa"* Saƙon da ya tura ma ta kenan ranan da su ke chatting ta ke tambayar sa gameda rigimar 'yan biyun ta. Emoji ɗin dariya ta tura ma sa sannan ta sauka, daga baya kuwa da ta hau ko da ya kawo zancen sai ta ce ba ta son irin wannan wasan. "Ina son ki Zaytoonah" maganar sa ta dawo da ita daga tunanin da ta ke yi. " tun ban san minene so ba, na rasa ki a karo na farko ba na fatan rasa ki a wannan lokaci" "Ya Auwal please..." "Ba zan tursasa miki ba, amma dan Allah ki saurari abinda zuciyar ki ke so " "Ya Auwal akwai abubuwa dayawa akai na kuma..." "Please Zaytoonah" yanayin maganar na sa ya ba ta tausayi. A matsayin Yaya ta ɗauke shi tun da kuma har yanzun nan hakan ta ke. Auwal Yayan ta ne, duk da akwai aure tsakanin su amma ba ta taɓa sawa a ran ta maganar soyayya za ta shiga tsakanin ta da shi ba balle aure. Ko kwana a Ringim Mommy ba ta yi ba kamar yadda ta tsara. Labarin da ta ji a chan ya ɗaure ma ta kai. Wani irin fin ƙarfi ne wannan? Ta ya za a bayar da auren Zaytoonah ba tareda an tuntuɓeta ba? Ta san ita mace ce amma still bai kamata a yanke ɗanyen hukunci irin wannan ba tareda an sanar da ita ba. Ko da ya ke ba laifin su ba ne, laifin Justice ne da ya aikata wannan abin, ba ta ɗauka da ilimin sa da darajar sa he'll stoop so low har ya aikata abinda ya aikata ba. Idan yana taƙama da sarauta ne Zaytoonah tana da 'yancin da za ta auri duk wanda ta ke so a tsarin musulunci dama na demokraɗiya. Ta ina ma za ta fara yiwa Zaytoonah maganar nan. Tana son Zaytoonah ta samu farin ciki, tana so ta gan ta a ɗakin mijin ta ƙarƙashin kulawar mijinta, amma wannan hanya da aka bi bai dace ba. Mommy ba ta yanke hukunci ba sai da ta kira Hajia Ni'ima dan ta ji daga gareta. A wayan ne Ni'ima ta ma ta bayanin komai akan ita ta sa aka yiwa Mai Martaba maganan Justice da Zaytoonah to da ya yiwa Justice ɗin magana sai ya nuna a bar maganan zuwa wani lokaci zai yi tunani akai. Shi kuma Mai Martaba ya san halin ɗan sa da zurfin ciki shiyasa kawai ya tura magabata aka je aka tambayi auren Zaytoonah kuma 'yan uwan Mahaifin ta su ka ba da ita har ma an saka lokacin biki nan da wata biyu. Mommy kam sai jinjina kai take yi da jin wannan batu mai ɗaure kai. Ana wata ga wata. Sai da ta gama yanke shawara da zuciyar ta kafin ta tuntuɓi Zaytoonah da maganar. Zaytoonah na gyara alayyaho Mommy ta jeho ma ta tambaya. "Akwai wani abu tsakanin ki da Justice ne?" Zaytoonah ta ɗago ido ta ce "bangane ba Mommy" Sai da ja numfashi kafin ta ce " an nemawa Justice auren ki, kuma su Baffan ki sun bashi ke" Zaytoonah ta ajiye ganyen da ta fara yankawa ta gyara zama dan ta ji tatsuniyar da Mommy ke ba ta da kyau, wannan kam ai tatsuniya ne kawai. Aure ita da Justice sai ka ce a film ta faɗa a ran ta... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 48 Bismillahir Rahmanir Rahim *The Decision* Bayanta ya dinga shafawa a hankali wanda hakan ya saukar ma ta da nitsuwa. Auwal na barin ƙofar ɗakin kai tsaye hanyar fita daga Asibitin yai, chan wajen wani dakali ya zauna yana maida numfashi. Ɗumin da ya ji a saman kumatun sa ya sa shi saurin shafa wajen ya tabbatar dai hawaye ne ke zubowa. Da ya san abinda zai tarar kenan da bai bi bayan Justice ba. "Daddy" ya furta a fili yana mai burin ina ma yana tareda su a nan yau. Da Daddy na nan da tun farko bai rasa Zaytoonah ba, da yana nan ya sani babu wanda ya isa ya bawa Justice auren Zaytoonah. Ya jima a wajen yana hawaye kafin daga baya ya koma ciki bayan ya nemi ruwa ya wanke fiskar sa. Justice bayan ya tabbatar bacci ya ɗauki Zaytoonah sannan ya shifiɗata a kan gadon ya fita, kai tsaye wajen Likita ya je bayan ya tambayi nurse ta ma sa kwatancen office ɗin. Ya yiwa Likita bayanin yadda Zaytoonah ta tsorata lokacin da ta tashi, Likita ya ma sa bayanin dalilin wannan tsoro ɗin wanda ya ke da nasaba da ciwon ta. Lokacin da Likita da Justice su ka koma ɗakin sun samu Mommy ta idar da sallah. Justice ya ma ta ya jiki a kunyace tunowa da yai da abinda ya wakana tsakanin sa da 'yarta ɗazu. Da ya san Mommy ta gansu da shikenan ya gama gaisuwar kenan ba zai kuma dawowa ba. Sai dai rashin sani ya fi dare duhu. Itama Mommy sai ta tsinci kan ta da jin kunyar Justice ɗin. Sun ɗan tattauna da Likita kan jikin Salman wanda ya tabbatar mu su da Insha Allahu ba wani matsala sosai bullet ɗin bai affecting any of the vital organ ɗin sa ba... Washegari da sassafe Justice ya taho Asibiti gaisuwa, biye da shi kuma mai aikin sa ce wacce ta taho mu su da abin karyawa. Mommy ta ma sa godiya da addu'a. Kaman zai tambayi Zaytoonah dan bai ganta a ɗaki ba amma sai ya fasa ya wuce ɗakin da aka kwantar da Salman. Ganin Salman na bacci ya tambayi Auwal ya mai jiki wanda ya amsa ma sa a daƙile. Komawa ɗakin su Zaytoonah yai dan gaskiya ba zai iya tafiya ba tareda ya sanyata a ido ba. Sallah takeyi lokacin da ya dawo ɗakin, ya ɗan tsaya ko za ta idar su gaisa tunda a tunanin sa sallar Asuba takeyi amma Zaytoonah da ta tafi sujjada minti ɗaya, biyu, uku, huɗu... ba ta ɗago ba. Sallama yai da Mommy ya wuce office dan yau sunada zaman kotu. Ya sani Zaytoonah ba ta son ganin sa ne ya sa ta ƙi ɗagowa balle har ta sallame sallar tata. Bayan fitar shi kuwa Zaytoonah ta ɗago ta yi tahiyya sannan ta yi sallama tana sauke ajiyar zuciya. Jiya bayan ta tashi daga bacci ta samu nitsuwa sosai, ƙanshin turaren Justice da ta ji a jikinta ne ya sa ta fara tunanin abubuwan da ya faru. Salati ta doka lokacin da ta tuno kiss ɗin da su ka yi ta dinga jin haushin kan ta na yadda aka yi ta biyewa zuciyarta a lokacin. Ta ya ma za ayi ta rinƙa ganin Justice a matsayin Zuhayr?. Kwanan su biyu a Asibiti aka sallami Mommy da Zaytoonah yanzu jinyar Salman kawai su ke yi. Kullum sai Justice ya zo dubiya duk da ana kawo abinci daga gidan Muhsina hakan bai sa Justice ya dena aiko mu su da abinci ba. Safe rana dare duk sai mai aikin sa ta kawo mu su abinci... "Adaeze" Mommy ta kira sunan ta tana kafe ta da idanu. Ta lura duk zuwan Justice sai dai ta nemi excuse ta gudu daga ɗakin kafin ya zo. Yau ma ɗin ya kamata red-handed ne tunda ya zo da wuri ba lokacin da ya saba zuwa ba. "Ina wuni" ta faɗa ba tareda ta ɗago ba. Tun da ya shigo ɗakin ta ja bakin ta tayi shiru, har su ka gama gaisawa da Mommy da kuma Salman ɗin ba ta ce da shi uffan ba, sai ma game da ta kunna ta farayi a wayar ta. "Ya jiki?" Ya faɗi yana kallon ta. Ka ji ɗan rainin hankali ta faɗa a ranta tareda ɗagowa ta harare shi. Maimakon ya ɓata rai sai ta ga yayi murmushi. Sallama yai wa Mommy sannan ya ce "ki ɗan fito ki karɓi saƙo ko" yai maganar yana kallon Zaytoonah, har ya fita ba ta ce komai ba saima tsaki da ta yi. "Ba za ki bishi ba?" "Mommy ni kam..." "Ba na son walaƙanci Zaytoonah" "Mommy bai fa kira sunana ba..." "Za ki wuce ko sai na make ki" Ta turo baki tana ɗaukan mayafin ta da ke kan kujera ta fita daga ɗakin da sauri. Tana ji Salman na faɗin "daɗin abin ma kun fi kusa" ta murguɗa baki ta cigaba da tafiya. Ba lallai ya tsaya a cikin Asibitin ba shiyasa direct farfajiyan Asibitin ta nufa. Dreban sa ta hango tsaye a bakin motar yana ɗaga ma ta hannu. "Shegen mulki ba zai ma iya tsayawa a waje ba" ta furta a fili tareda yin tsaki. Tana zuwa Dreban ya buɗe ma ta gidan baya haɗeda gaisheta. Sai da ta ɗan tsaya na wasu daƙiƙu kafin ta shiga motar, ta yi niyyar barin ƙofar a buɗe amma kawai sai Dreban ya rufo ƙofar da ƙarfi, daga haka kuma ya bar wajen. Sau ɗaya ta kalle shi ta ɗauke kai ta maida duban ta ga window. Kusan minti biyu ba wanda yai magana. A ranta tana ƙiyasta indai ya kai minti biyar bai yi magana ba fita za ta yi ta kama gabanta. "Zuwa yanzu ya ci ace kin saba da sallama a bakin ki" Ta juyo ta kalleshi amma idon sa na kan wayar da ya ke dannawa. Chan ƙasan ranta ta ce 'ba za a yi sallamar ba'. "Ina da tabbacin Chief Udodiri yana da hannu wajen attacking na ku da aka yi. Akwai matakan tsaro da na riga na ɗauka, ciki harda sama muku bodyguards da za su dinga kula da ku har komai ya lafa, ina fata za ki bani haɗin kai wajen ganin komai ya tafi dai-dai" "Ba ma buƙatar komai daga gareka. Idan bodyguards ne zan iya hiring ɗin su da kaina ba sai ka nuna fin ƙarfi ba kamar yadda ka saba" Tana gama maganar ta kama ƙofa za ta fita amma ta ji ta a rufe. Ta juyo ta kalleshi da mamaki. "Ba mu gama magana ba" "To ni na gama" ta faɗa da ɗan ƙarfi hakan ya sa ya juyo ya kalleta. Ta yi saurin sunkuyar da kan ta saboda nauyin da idon sa ya ma ta. " bisa rana da aka saka yau saura kwana ishirin da ɗaya a ɗaura aure. Saboda rashin sanin tabbas na ranan da case ɗin nan zai ƙare, za a ɗaura aure a ranan da aka saka ɗin amma duk wani hidima zai biyo bayan an ƙare case ɗin nan ne" Ta rintse ido jin maganar da ya ke yi, maimakon ta ga duhu sai kuma ta fara ganin hoton ta da Justice yayinda ya ke kissing ɗin ta. Ta yi saurin buɗe idon saboda jin tsikar jikinta na tashi daga wannan tunanin. "Idan akwai abinda ki ke son sani kafin nan ko kuma ki ke buƙata za ki iya sanar da ni" "I dont want this marriage, Dan Allah ka yi haƙuri ka rabu da ni" hawaye ya biyo bayan maganar da ta yi. Shiru yai bai ce komai ba, itama kuma ba ta sake cewa komai ba sai ma ƙoƙarin goge hawaye da ta ke yi. Wani raɗaɗi ya ke ji a zuciyar sa. Ba yau ba ne ta fara furta irin maganan nan amma na yau ya taɓa shi sosai. Idan har ya cigaba da maganar auren nan to tabbas ya zama azzalumi. Kusan minti bakwai babu wanda yai magana a cikin su, kowa da abinda ya ke tunani a ran sa. Kaman daga sama ta ji ya ce " shikenan, Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi" Ta juyo ta kalleshi sai taga ya ɗara wayar sa a kunne yana yiwa dreban sa magana akan ya dawo ya maida shi gida. A hankali ta tura ƙofan bayan ta ji ƙaran cire lock ɗin da yai. A sanyaye ta fara tafiya har ta kai cikin Asibitin. Sai da ta share fiskarta sosai kafin ta shiga ɗakin fiskarta ɗauke da murmushin dole... *** Zaune ya ke a study room ɗin sa litattafai ne a gaban sa amma ya kasa karantawa. Maganar Zaytoonah ne ke ma sa yawo a ka. Yayi Istikhara akan maganar Zaytoonah kuma yana ji a jikin sa Alkhairi ne, sai dai dole ne ya haƙura da ita tunda ta ce ba ta so. Abu ne da ba zai taɓa yiwa 'ya'yan sa ba, Auren Dole. Dan haka gara ya haƙura kawai kar ya zama Azzalumi. At first ya ɗauka Zaytoonah za ta fahimce shi amma bayan maganan su ta yau, ba shi da wani hope akan ta. Chan ya jawo wayar sa ya binciko hoton mijin Zaytoonah. Hoto ne da ta saka kusan watanni uku da su ka wuce. *Gone too soon. I miss you my love* abinda ta saka kenan a ƙasan hoton ranan da ta ɗaura shi a status ɗin ta. Hoto ne da aka ɗauka yana zaune akan wheelchair a masallacin Ka'abah yana zaune yana murmushi. A hoton sa na gaba ne ta rubuta * 4 years, 3 months, 3 days without you D*. Tausayinta ya ke ji sosai tun lokacin da ya san cewa Mijinta ya jima da rasuwa. Bayan tausayi akwai wani abu a ƙasan ran sa gameda ita wanda ya kasa gane ainihin minene... Sai da ta gyara zaman ta da kyau ta jawo laptop ɗin kusa da ita kafin ta kunna video ɗin. "I love you D" muryan ta ya fito raɗau daga video ɗin. Zuhayr ya manna ma ta kiss a goshi yana faɗin i love you more. Ta cigaba da kallon videos ɗin tanayi tana hawaye. Kusan ta haddace komai na videos ɗin tsabar yawan maimaita kallon su da ta ke yi. Video ɗaya ne ba ta cika kallo ba saboda video ce ta wasici da yai, kusan ma sau biyu kawai ta kalle shi. Ta kunna video ɗin ta ƙurawa screen ɗin laptop ɗin ido tana kallon facial movement na Zuhayr har ya kai wajen da ya ke cewa. *ina addu'ar Allah ya haɗa ki da masoyi na gaskiya, wanda zai so ki tsakani da Allah ya kuma ƙaunaci 'ya'ya na tamkar 'ya'yan cikin sa. Ina ji ajikina akwai mai share mi ki hawaye idan ba na nan, ina ji a jikina 'ya'ya na ba za su yi kukan rashin uba ba idan suna tare da shi...* Ta yi saurin rufe Laptop ɗin saboda yadda maganganun sa ke tasiri a jikin ta kamar dai yanzu ne ya ke yin su. Ta ɗago rinannun idanun ta ta kalli agogon da ke jikin bango wanda ya nuna ƙarfe biyun dare har ta gota. Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ɗauke Laptop ɗin da ke gabanta ta kai shi kan kujera. Tana miƙewa akan gado ko minti biyar ba ta cika ba bacci mai nauyi yai gaba da ita. Washegari ba ta tashi da wuri ba dan har sai da Azma ta shigo ta tasheta lokacin ƙarfe takwas na safe ta gota. Ta yi wanka tareda ɗauro alwala ta yi sallah. Tana zaune akan sallaya tana Azkar sai ga Mommy ta shigo da sallama. A bakin gado ta zauna ta jirata har ta idar da addu'o'in na ta. "Good morning Mommy" "Morning Adaeze" "Na ɗauka ma kin wuce Asibiti ai" ta yi maganar tana naɗe sallaya. Maimakon ta amsa ma ta sai ta ce " mi kika faɗawa Justice jiya?" "Ba komai" ta faɗa kan ta tsaye "Ba komai? Zaytoonah ba komai?" "Mommy what did you want me to say? Ni ba abinda na faɗa ma sa, idan ma shi ya ce na faɗi wani abu to sai ya gaya miki ai tunda dama munafuki..." "I forbid you from ever calling him names, kina ji na ko?" Ta faɗa da tsawa. "Hajia Ni'ima ta kirani yau da sassafe tana maganar Justice ya janye maganar auren ku. Infact yau za a sanar da su a Ringim. "Adaeze addu'a na ce kiyi a kai kuma ki bani sincere feedback amma ba ki yi ba sai kawai ki ce ma sa ya janye maganar auren" "Mommy you dont expect me to marry him right?" Ta yi maganan tana nuna kan ta. "Kin yi addu'ar da na ce ki yi? Kin nemi zaɓin Allah kamar yadda na ce ki yi? Ko dai son zuciyar ki kawai ki ka yi amfani da shi?" Da mamaki ta kalli Mommy idon ta fal da hawaye ta ce "Mommy ba dai abinda na ke tunani kike shirin yi ba? Mommy i didnt choose my first husband, infact aure ne aka min wanda ba ni da zaɓi akai. Shin yanzu ma ba zan zaɓi mijin da zan aura ba kenan? Yanzu ma ba ni da zaɓi kenan?, is it because he's from a royal family?. "Mommy idan a lokacin ni yarinya ce yanzu fah? I'm an adult, zan yi aure a lokacin da na ga dama ga wanda na ga dama, kuma ba zan auri Justice ba. Infact da na aure shi gara na auri Yaya Auwal" Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce "duk abinda ki ka ga za ki iya ki yi shi Zaytoonah, kamar yadda ki ka faɗa you are an adult, Yes you are. Sai dai ki sani idan ba za ki auri Justice ba banida matsala da hakan amma maganar Auwal ki ajiye shi gefe dan matuƙar ina raye ba zan sa mi ki hannu a ciki ba" "But why?" "Ƙiyayyar Tijjani da Muntari ya samo asali ne akan soyayyar Maryam, kuma yau ga inda gabar ta kawo mu. Idan ba ki sani ba to ki sani, 'yar uwar ki Humairah tana son Auwal kuma ta yi iƙirarin ɗaukan mataki idan har Auwal ya aure ki. Ba zan taɓa bari gaba ta shiga tsakanin ku ba bayan dukkan ku jini ɗaya ne" Ta miƙe tsaye tana kallon Zaytoonah ido cikin ido ta ce " kuɗi ko sarauta da Justice ke da shi ba su isa na bashi 'ya ta ba. Sai dai kyakyawan zato da na ke ma sa da wanda jama'a ke ma sa shiyasa na ji a raina zai kula min da 'ya tsakani da Allah da kuma jikoki na. Na yi addu'a kuma na nemi shawara a wajen mutane kuma still har yanzu tunanin alkhairi na ke yiwa auren nan shiyasa na amince. "Amma tunda ke kallon uwa mai kwaɗayi ki ke mini. Na cire hannuna a maganar, tunda kin ce ba kya so shima kuma ya fasa Allah ya bawa kowa rabon sa" "Mommy ba haka..." Ko sauraron ta ba ta yi ba ta fice daga ɗakin. Zaytoonah ta kifa kan ta a kan gado ta fashe da kuka... *** "Allah dai ya wadaran naka ya lalace. Yanzu Maryam ɗin tana ji tana gani za ta biyewa 'yar ta. Wani irin rashin mutunci ne wannan, gidan sarauta fa! Yanzu ace jikata na auren Ɗan Sarki ai wani ƙarin daraja ne " Auwal yai dariya ya ce " Iya kenan, kina da abin dariya wallahi. Ina ce Zaytoonan ce dai 'yar da ki ka ƙyamaceta lokacin haihuwar ta, ki ka shegantata kika ƙi ma a saka ma ta sunan ki saboda ba ki ɗauketa jinin ki ba. Yau kuma dan ta ce ba za ta auri ɗan Sarki ba har da kiran ta jikar ki" "Auwalu!" Iya ta faɗa baki na rawa. Sai dai gaskiya ce ya faɗa. Yarinyar dai da ko kallo ba ta isheta ba ita ce yanzu hasken gidan na su, ita ce tauraruwan gidan na su. "Ayi tsohuwa da kwaɗayi kamar ba za ta mutu ba. Miye ne a cikin auren Ɗan Sarki" ya ƙarisa maganar da tsaki sannan ya miƙe ya cire suit ɗin sa ya shige ɗaki. Dama ya dawo daga office ne Iya ta tareshi da maganar wai an bugo ma ta waya daga Ringim kan Zaytoonah ta fasa auren Galadima kuma suma sun janye maganar auren amma sun ce duk abinda aka kai an yafe. Shi kan daɗin sa dan dama tun kiss scene ɗin nan da ya gani hankalin sa ya matuƙar tashi, ba shiri ma washegari ya dawo Zaria ya tura wani ƙanin sa Yakubu da su ke Uba ɗaya zai cigaba da jinyar Salman dan dama Yakubun ma admission da ya samu a ABU ya sa ya dawo gidan su da zama, to kuma suna hutun ƙarshen zango. Gobe-gobe zai je Ringim ya gabatar da maganar sa da Zaytoonah. Idan sun amince ma a take ya ke so a ɗaura auren kar ya zo ya rasata kuma du. Ya sani Mommy ta hana shi Zaytoonah ne saboda Humairah ne amma ba zai iya haƙura ba, soyayyar Humairah duk shirme ne tunda yarinyar da ta ke iƙirarin tana son shi amma hakan bai hanata kula wasu samarin ba. Tun da ya mallaki hankalin sa ya fahimci yana son Zaytoonah bai ƙara kallon wata mace da sunan so ba. Ko lokacin da aka yi auren ta da Zuhayr bai iya son wata ba... A chan Ringim kuwa abin bai mu su daɗi ba kowa kuma gani ya ke laifin Maryam ce dan ita ce ba ta yiwa Zaytoonah tarbiyya mai kyau ba shiyasa har ta iya buɗe baki ta ce ba za ta auri Galadima ba, Galadiman Zazzau fa. Har da cewa da Tijjani na nan ai ba ta isa ta take maganar sa ba. Sun manta cewa duk wani ɗawainiyyar Zaytoonah babu hannun su a ciki sai yanzu dan sun ji Ɗan Sarki na neman ta shi ne hankalin su ya tashi kowa yana bugun ƙirji yana faɗin shima Baffan Zaytoonah ne. Zaytoonah na kwance a ɗaki sai rawan sanyi ta ke yi, tun maganar su da Mommy ta fara zazzaɓi, Mommy ba ta san ma tana yi ba dan ko kulata ba ta sake yi ba. Sau ɗaya ta je asibiti wajen Salman amma ganin yadda Mommy ta ke ta shashshareta ya sa ta dawo gida ta kwanta ta fara kuka daga ƙarshe kuma sai zazzaɓi. Wayar ta ne ya shiga ringing da ƙarfi, ta sa hannu ta jawo wayar ta sa a kunne ba tareda ta lura da wa ke kiran ba. Ta yi sallama a hankali. "Gimbiya Hajiya Zainabu ke kan layi" "Ok" Zaytoonah ta faɗa tana ƙoƙarin tashi zaune dan tunda ta ji ance Gimbiya ta san 'yar uwan Justice ne. "Na bugo ne na ja miki kunne, kin yi kaɗan ki rena mana wayo. Sai da aka gama shirya komai za ki zo ki ce kin fasa saboda baki san darajan Mai Martaba ba. " ko kaɗan ba na son auren nan saboda ba ki dace da babban gida ba. Amma yanzu da ki ka nuna ke 'yar iska ce to ni zan nuna miki duk iskancin ki ba ki isa ki walaƙanta babban gida ba. Aure ne kamar anyi an gama ki sawa ran ki wannan" Daga haka aka katse kiran. Jiya Hajia Abu ta dawo daga Dubai inda ta je ta haɗowa Galadima kayan aure sai kawai ta ke jin wai an fasa auren dan yarinyar ta ce ba ta so. Da farko ta share maganan tunda dama ba son Zaytoonah ta ke ba har ta ke cewa su ne 'ya'yan matsiyata ai kuma Justice zai auri 'ya'yan babban gida wanda su ka dace da shi. Amma daga baya sai girman kan su ka motsa, ta ga ai idan ba ayi auren nan ba kamar cin mutunci aka yiwa gidan su musamman Galadima. A ce mutum mai daraja irin sa wata banza ta ce ba za ta aure shi ba. Yadda yaken nan duk macen da ya nuna ba ta isa ta ƙi shi ba saboda martabar sa. Zaytoonah ta yi murmushi tana faɗin lallai ma matar nan. Muhsina ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo. "Hajjaju lafiya ki ke ƙunshe a ɗaki tun da safe?" Ta sa hannu ta taɓa goshinta ta ji zafi "Zazzaɓi ki ke ji?" "Na sha magani" "Ban yarda ba, yaushe ma kika ci abinci da za ki ce kin sha magani. Ki shirya mu je asibiti a duba ki kawai" "Da gaske na sha magani" "Wani magani ki ka sha?" "Paracetamol" "Lallai kam, tashi ki shirya mu je Asibiti" "Muhsina dan Allah ki yi haƙuri ba zan iya zuwa ba" "Kun yi faɗa da Mommy ko?" "Ban san ya zan yi ba, Mommy fishi ta ke yi dani akan maganar Justice. I dont know what to do, ba zan iya auren Justice ba" ta yi maganar tana kuka. "Miyasa?" Muhsina ta yi maganar tana kallon ta Zaytoonah ta yi shiru tana kallon ta cike da rashin fahimta. "Miyasa ba za ki iya auren sa ba?" "Haka kawai" "Ba za ki iya auren sa ba saboda ya miki tsufa?" Zaytoonah ta girgiza kai "Saboda yana da 'ya'ya har uku?" Nan ma ta girgiza kai. "Saboda ba kya son shi akwai wanda kike so?" Nan ma ta girgiza kai. Muhsina ta gyara zamanta sosai kusa da Zaytoonah ta ce " na san yadda maganar auren Justice ya zo miki ba a bi tsarin da ya dace ba amma still ko da ya bi ta hanyar da ya dace ne the same response za ki bashi, kin san saboda me?. "Saboda ba kya son aure Zaytoonah, ba kya son sake wani auren. Bari ki ji abu biyu za ki yi ki muzgunawa kan ki da 'ya'yan ki. Na farko ki ƙi aure ki ƙare rayuwar ki a haka, ya zamana kin denying 'ya'yan ki samun Uba kenan. Na biyu ki yi aure ki auri mutumin da ba zai riƙe 'ya'yan ki da amana ba. "See, ko Zuhayr da ke ƙabari ba zai so ace kina zaune haka ke kaɗai ba, he'll want you to be happy, to be with someone that makes you happy. Zaytoonah you need a companion, your children needs a father ba zai yiwu ki cigaba da zama a haka ba. And idan har ba wai ɗaya daga cikin dalilin da na irgo ba ne to ni banga aibu a auren Galadima ba, he's a good man, kuma na tabbata idan kika aure shi 'yan biyu ba za suyi kukan rashin Uba ba"... "Uncle Salman tush tush tush" Hadid ya faɗa yana harba bindigar roba wa Salman ɗin da ke kishingiɗe yana shan tea. Mommy na riƙe da Hashir tana saka ma sa takalmi, daga zuwa ya cire su ya watsar bayan ga sanyin tiles. Sallamar Justice su ka ji wanda har yau bai fasa zuwa duba Salman ba. "Hadid miƙowa Daddyn ku kujera ya zauna" ta yi maganar ne zuciyar ta ɗaya saboda ɗaya kujeran zaman na gefen Hadid ɗin. Ba ta ankara ba ta ji ya ce "GrandMa wannan ne Daddyn mu?" Sai lokacin Hashir ya kalli fiskar Justice ya ce "Lah! GrandMa dama idan aka je Aljannah ana samun gemu ne?" Sai kuma dukkan su biyu su ka zo gaban Justice suna kallon sa. Sun fi minti ɗaya suna kallon sa suna nemo kamannin mutumin da ke tsaye da kuma kamannin mutumin da ke jikin hotunan da Mom ta ke nuna mu su. Salman ne ya katse shirun da cewa " Daddyn ku yana Aljannah, wannan Daddy Babba ne" Hadid ya riƙo hannun Justice yana faɗin "i like you Daddy Babba" Hashir kuma ya ce "ina kai ba ka bulala kaman ɗaya Daddy Babban na Zaria?" Justice ya shafa kumatunsa yana faɗin " ba na bulala amma ba na shiri da wanda ba sa jin magana". Da kan sa ya jawo kujeran ya zauna ya ɗaura su kan cinyarsa yana sauraron surutun su. Duk da bai san yaran waye ba ne amma yaran sun burgeshi, wani zuciya na bashi cewa yaran Zaytoonah ne amma bai tabbatar ba tunda da Mommy da Salman babu wanda ya ma sa bayani. Cikin ƙanƙanin lokaci wani bond mai ƙarfi ya shiga tsakanin sa da yaran. Dama yaran akwai saurin sabo musamman idan za ka biyewa surutun su. Saboda yaran ya jima a wajen dan ya fi minti talatin bai yi niyyar tafiya ba ma sai da Mommy ta ce su Hadid su bar shi hakanan zai tafi gobe idan ya zo sai su ƙarisa bashi labarin. Duk yadda ta ke jin rashin ƙarfin jiki tunda Muhsina ta ce ma ta 'ya'yan ta sun zo suna Asibiti ta ji ta warke kawai, ta tashi ta shirya ta fito za ta je Asibitin, Muhsina ta ce ta jira su tafi tare dan itama ta kwana biyu ba ta leƙa Salman ɗin ba. A motar Muhsina su ka tafi bayan Azma ta miƙo mu su abincin da za su kai. Suna fitowa daga mota ta hango Justice riƙe da hannun 'yan biyu sun nufi wajen motar sa tareda Junior. Suna tafiya suna hira. "Hadid, Hashir" ta ƙwala mu su kira dan a tunanin ta bin Justice za su yi. Dukkan su suka juyo suna kallon ta. Sake hannun Justice su ka yi su ka nufi wajen Zaytoonah da gudu. Yaran ta ne abinda zuciyar sa ta ambata kenan. "Mom zo ku gaisa da Daddy Babba, yana da kirki" Yadda su ke jan hannun ta ya sa dole ta ƙarisa wajen Justice ɗin. Kallon ta ya ke with full admiration. "Daddy ga Mom ɗin mu nan" Hashir ya faɗa yana nuna Zaytoonah. "Ina wuni Sir" ta faɗa cike da kunyar sa, sau ɗaya ta kalle shi ta kauda kai gefe tana kallon Junior da ke wasa da wayan da ta ke tunanin na Justice ɗin ne. "Daddy ina dai ba ka manta ba gobe za ka kaimu shan ice cream?" Zaytoonah ta zarewa Hadid ido. "Insha Allah za mu je" ya faɗa yana murmushi. Tana tsaye a wajen yai wa yaran na ta musabaha tareda kissing goshin su sannan ya karɓi wayar sa a wajen Junior ya shige mota. Tunda su ka shigo kuwa 'yan biyu kaman haɗin baki sai su ka kama taɗin Justice, Daddy Babban ma sun dena kira sai dai Daddy kawai. Kallo ɗaya Mommy ta ma ta ta kau da kai, irin kallon 'gashi dai kin gani da idon ki'. Ba su bar Asibitin ba sai bayan sallar Isha. Yaran na bacci ta zuba mu su ido tana kallon su, har su ka yi bacci ba su dena taɗin Justice ba 'Daddy yayi kaza, Daddy ya ce kaza, gemun Daddy kaman na kaza, maganan Daddy kaza...' Ko ba dan ita ba, za ta nemawa yaranta farinciki. Idan har aurenta da Justice yana haɗe da farin cikin yaran ta to za ta aure shi. Wayar ta ta ɗauko ta rubuta saƙo sannan ta tura, tana ganin ya tafi ta kashe wayan ta kwanta tana jin zuciyarta na bugawa da sauri-sauri... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 50 Bismillahir Rahmanir Rahim *Married again* Azumi ne ke cinta saboda aikin wahala da su ka yi kwana biyun nan. Su Chief Asibong ne su ka kawo mu su Ziyara dan su kai godiya wa mutanen da su ka taimakawa 'yar su. A Zaria su ka fara sauka inda su ka yi kwana biyu. Mommy ta mu su jagora wajen Iya, ko ba komai ita ce uwa ga mutumin da ya chanja ma ta rayuwa. Kunya taf a idon Iya lokacin da Auwal ke fassara ma ta maganganun Chief Asibong wanda godiya ne na irin tarba da su ka yiwa Mommy. A zahiri Goggo ce ta cancanci wannan godiya dan ita ce uwar Mommy. Ita ce ta riƙe ta tamkar 'yar da ta haifa, sai gashi yau babu Goggo a tareda su ita Maryam ke karramawa haka. Duk da kasancewar su Christians hakan bai hanata ganin girma da darajar su ba. Da ganin ido ta san 'yan uwan Maryam manyan mutane ne. Da za su tafi Uncle ɗin Maryam ya ajiyewa Iya wani envelope akan centre table suna faɗin 'yar ƙaramar kyauta ce ta nuna godiya. Bayan tafiyar su Humairah ta ɗau envelop ɗin ta buɗe shi sai ga check ɗin kuɗi million ɗaya. Humairah ta challa ihu tana tsalle. "Humairah minene? Takardar miye su ka bamu?" "Iya check ɗin kuɗi ne, check ɗin million ɗaya. One million naira Iya" ta faɗa tana nuna ma ta check ɗin kamar Iyan ta za ta gane abinda aka rubuta. Gidan surukan Zaytoonah su ka wuce inda nan ma Alhaji Iliyasu ya tarbe su da kyau. Da taɗi yai taɗi ne ma Chief Asibong ya tuna cewa sun taɓa haɗuwa da Alhaji Iliyasu a Newyork kan wani taron kasuwanci na ƙasa da ƙasa da su ka halarta kusan shekaru hamsin da uku da su ka wuce. Cikin ƙanƙanin lokaci Chief Asibong da Alhaji Iliyasu su ka samu wani bond na musamman, aka zauna ana tuna baya. Rayuwar ƙuruciya da su ka yi da kuma yadda zamani ke tafiya yanzu. Chief Asibong bai bar wajen Alhaji ba sai wajen ƙarfe takwas na dare inda driver ya maida shi hotel ɗin da su ka sauka. Washegari kuma su ka wuce Ringim. Nan ma 'yan uwan T J sun sha kyaututtuka daga wajen Kakan Mommy wanda ya ke ƙara godiya da irin mutanen da Allah ya haɗa jikar sa da su. Yadda ake ta maganar kyawawan halayen T J ya sa Mommy ta fara hawaye. Ina ma ace T J yana nan tare da su ya ga wannan rana. All this credit da ake ta bawa 'yan uwansa shine ya fi chanchanta da hakan. T J silar zuwanta Ringim. T J shine silar duk wani abinda ta zama yau. Ganin kuka na shirin kubce ma ta ga sa Mommy ta tashi daga falon da ake taron. Ba ta tsaya ko ina ba sai ɗakin Goggo wanda ya zama ɗakin da ake saukan baƙi. Ta zauna a ƙuryan ɗakin tana tuna shekarun baya da ta ke rayuwa a wannan ɗakin. Kyawawan halayen Goggo, company da ta ke samu a wajen Pendo ga uwa uba soyayya da kulawar T J. Kamar yau ne T J ya damƙa ta a hannun Goggo, kamar yau ne ta fara sallah a ɗakin nan bayan ta karɓi kalmar shahada. Kamar yau ne ta yi wankan jego a wajen Goggo. "Rayuwa kenan" ta furta a fili tana kallon screen ɗin wayarta wanda hoton T J ne akai yana murmushi kamar yadda koyaushe fiskar sa ke cike da fara'a. Looking back to all those years she badly wish T J na tare da ita. Ya ga 'yan uwan mahaifiyar ta da su ka zo ya kuma ga yadda 'yar su ta defeating Chief Udodiri a kotu. Ta sunbaci hoton sannan ta rungume wayan jikinta tana hawaye... Wannan ziyaran har Fadar Ringim sai da su ka je domin ba da labarin Mommy da 'yarta ba tareda an sako Sarkin Ringim ba to kamar an manta wani babban shashe ne mai mahimmanci na labarin. Kowa sai mamaki ya ke ashe dai 'yan uwan Maryam ma su Arziƙi ne da gaske. Hajjo da ta zo gaisuwa Mommy ta nuna ta a matsayin 'yar uwarta wanda su ka zauna tare ƙarƙashin miji ɗaya sai da ta yi kuka. Tun rabuwan su har yau Mommy ba ta fasa yiwa Hajjo alkhairi ba duk lokacin da ta zo Ringim. Cash ɗin dubu ɗari aka ba ta a envelop da za ta tafi. Mommy har mamakin yawan kyaututtukan da Kakan na ta ke ta bayarwa ta ke, dan ba ta tsammanci zai martaba 'yan uwan mijinta haka ba. Ba su kwana a Ringim ba a ranan su ka wuce Zaria inda su ka ƙara kwana biyu kafin su ka wuce Abuja inda daga nan su ka shiga jirgi su ka koma Owerri akan su da zuwa kuma sai bayan sallah lokacin bikin Zaytoonah. "Zaytoonah kashe waya ki ka yi ne? Ummin ki ta ce ta kira numbar ki bai shiga ba" "Ina ga network ne amma wayar a kunne ta ke" "To ki kirata" Mommy ta yi maganar tana shigewa ciki dan daga makaranta ta ke. Wayar ma wahala zai ma ta shiyasa ta gyara kwanciyarta akan kujera. Kwanciyar ɗaki ne ya isheta ya sa ta fito. Duk yadda ta ke jin jiki ma wai ashe sai yanzu ƙarfe uku ta yi. Ta ɗauke idon ta daga kan agogon ta koma kallon ceiling. Har ta ɗan fara bacci kiran Ummi (Pendo) ya tashe ta. Tana ɗaukan wayar Ummi ta fara yi ma ta faɗa kan ƙin zuwa da ta yi ta ma ta gyara. "Anya Zaytoonah kina amfani da abinda na aiko miki da shi kuwa?" "Ina yi" ta faɗa dan kawai ta rufe maganar. "Kin san Allah idan na zo na samu ba ki yi amfani da shi ba zan saɓa miki" "Ummi ina yi fa" "Wannan na ganyen dalbejiya ɗin shima kina yi" Zaytoonah ta yi shiru. Ita fa tunda Salman ya karɓo ma ta saƙon Pendon daga park da ta buɗe taga haɗe-haɗen gyara ne da bayanan su da aka rubuta a littafi ta tattara su ta ajiye gefe, ba abinda ta yi amfani da shi. "Zan saɓa miki Zaytoonah. Ke ba yarinya ba ce, auren ki ya zo a ƙurarren lokaci amma ba kya so ki gyara jikin ki" "Ummi da Azumi zan ji ko da gyaran jiki..." "Za ki sha mamaki idan na shigo Zaria"... Wasa-wasa sai ga shi har ana gobe ko jibi sallah. A ɓangaren Mommy a karo na biyu tana shirye shiryen bikin 'yar tata amma ita Amarya Zaytoonah ba abinda ta ke yi. Ita ba wanda ta faɗawa ma za ta yi aure balle wani shirye- shirye. A Ringim za a ɗaura auren inda daga nan za a kawo ta Fadar Zazzau kafin ta wuce gidan mijin ta da ke Abuja. Auren na matsowa tana ƙara jin fargaba gameda auren. Ranan da dare sai ga Justice a gidan su. Shima ya shigo Zaria. A madaidaicin falon su aka sauke shi inda yaran su ka yanyameshi suna murna da ganin sa. Tunda Zaytoonah ta ajiye ma sa ruwa ta shiga ɗaki ta yi kwanciyar ta. Ganin sa da ta yi ya sa ta ji jikin ta yayi sanyi. Shima Justice bai neme ta ba dan dama yaran ya zo dubawa tareda kawo mu su kayan sallah da ya mu su, sannan ya nemi alfarmar zai tafi da su Idi kuma idan ba matsala zai fita da su hawan da za ayi. Zaytoonah na kwance yaran su ka shigo da gudu suna ihu wai Daddy ya ce za su hau doki. Kora su ta yi dan ihun na su ya isheta. Bayan fitan su ne ta ga saƙon Justice a wayar ta inda ya tambayeta ko tana buƙatar wani abu. Ta tura ma sa reply da cewa a'a... *** Kusan wannan sallar ta zo wa 'yan biyu a yanayi na farinciki fiye da kowacce Sallah. Tun da sassafe driver ya zo ya ɗauke su bayan sun sha kayan da Justice ya kawo mu su. Tun a jiyan su ka dinga waƙar cewa kayan da Daddy ya kawo za su sa ba kayan da Mom ta mu su ba. Dukkan su uku irin kayan Justice ne a jikin su bayan an kai su gidan sa su ka ga shima irin sa ne a jikin sa. Maimakon da da su ke bin Alhaji Tsoho zuwa masallacin idi wannan karan Daddyn su za su bi. Tuni an reserving mu su doki da kuma wanda zai riƙe mu su dokin saboda suna cikin tawagar Galadima idan za ayi hawan sallah. Zaytoonah tun tana sa idon za a dawo da 'yan biyu da Junior har ta haƙura ta zuba ido kawai. Daga baya Justice ya tura ma ta saƙo akan za su kwana a gidan sa. Ta taɓe baki tana mamakin wannan fin ƙarfi. Tun kafin ma ya aureta ya fara nuna iko akan yaran ta... Tun bayan sallah Mommy ta sa wa Zaytoonah ido gameda gyaran jiki da ta ƙi yi. Dole da ta yarda ta fara amfani da wasu abubuwan da Ummi ta aiko ma ta da shi. Ana saura kwana biyar ɗaurin auren Ummi ta zo Zaria. Inda ta cigaba da gyara Zaytoonah da kayan gargajiya ma su inganci musamman wankan Lalle. Zaytoonah dai na ta ido, dan da ta yi magana ma Ummi za ta fara masifa ganin yadda Zaytoonan ta yi sakachi da amfani da abubuwan da ta aiko ma ta tun farko. Magana kaɗan sai ta fara " ke fa Matar ɗan Sarki be, gidan sarauta za ki shiga dan haka dole ki je ki kece reni" Ranan Asabat da misalin ƙarfe shaɗaya da minti huɗu aka ɗaura auren Justice Yunus Muhammad Abbas da kuma Barrister Zaytoonah Tijjani Abubakar. Auren da ya samu halartar ɗaruruwan mutane daga wajaje daban-daban. Galadima mutum ne mai Jama'a shiyasa kowa ya ke farinciki da wannan aure. Ana gama ɗaurin aure aka wuce Zaria inda aka gabatar da reception a wani babban hotel. Da ƙarfe huɗu na yamma kuma aka fara yin hawa don taya mai girma Galadiman gari murna. Gaba ɗaya gari ya cika da jama'a kamar wani hawan Sallah ake yi... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 49 Bismillahir Rahmanir Rahim *The winning* Kiran da aka yiwa Mommy ne ya sa ta tabbatar da lallai Udodiri shi ne ya sa aka attacking na su a hanya. Gaskiya Justice akwai shi da hikima. "Ku saka wayoyin ku a auto record saboda samun evidence idan sun yi ƙoƙarin tuntuɓar ku" Abinda ya faɗa kenan tun da aka yi zaman farko. Ta duba wayar ta sake playing hiran ta su ka yi da lawyan Udodiri. Tuni ta forwarding audion zuwa wayar Justice da ta Zaytoonah dan ma gudun kar a zo a rasa. Udodiri ne ya ke son sun yi negotiating tsakanin su. Ta same shi a wani hotel da yamma ƙarfe biyar. Ba wani magana ne mai tsayi ba amma the fact that lawyan ya ce *'ki tabbatar ke kaɗai ki ka je, kuma ki ka yi ƙoƙarin recording hiran ku hakan na nufin rayuwar 'ya'yan ki yana hatsari'* Bayan Justice ya saurari recording da Mommy ta tura ma sa ne ya kirata, shawara ya ba ta akan ta je ita ɗaya kamar yadda ya buƙata kuma maganar recording ɗin ta bar shi ya san mi zai yi... "Nkiruka!, rayuwa kenan ke ce ki ka dawo haka" Udodiri yai maganar da harshen su ta Igbo. Ya cigaba "babu wanda zai gan ki yanzu ya san cewa ke igbo ce, kin riga kin zama bahaushiya kawai" "Uncle mi ka ke buƙata?" Ta yi maganar tana jifar sa da kallon tsana. "Ki janye ƙaran nan" " a wani dalili?" "Na riga na san kashe kuɗi za ki yi a banza saboda babu yadda za ayi a gano poison a jikin ƙasusuwan iyayen ki" "Kenan dai ka yarda iyaye na poison ne ya kashe su?" "100million tareda gidan da iyayen ki su ka gina" Mommy ta yi murmushin ya ƙe. "150million" Ya ja numfashi ya ce "200 million daga haka ba zan ƙara ba" "Kuɗin da kamfanin mahaifina ke samu a shekara ya fi ƙarfin wannan. Mi 200 million zai mi ni?" "Dont be stubborn Mary. Na kira ki ne saboda wannan case ɗin yana ɓata min campaign ɗina. 'Yan adawa suna amfani da shi wajen ɓata sunana. Ki faɗi nawa ki ke so a baki a kashe zancen nan yanzu" "Ina son ka mallaka min kamfanin mahaifina da duk wani abinda ka tara da kuɗin sa. Every single dime na ke so. Idan ka yi haka zan yafe sauran laifukan ka" Dariya yai mai kama da ta renin hankali. "Mary Mary Mary. Da alama kin manta jikokin ki biyu da ɗan ki suna hanyar komawa Zaria ko" Ƙirjin Mommy ya buga. Duk da kasancewar ta san harda bodyguards uku suka raka yaran zuwa Zaria. Udodiri ya miƙe ya ce "ki janye case ɗin kowa ya zauna lafiya" Yana tafiya ta ciro wayar ta a jaka ta shiga kiran numbar dreban da ya ɗau yaran amma ta ji ta a kashe. Hankalinta ya tashi ta shiga kiran numbar Zaytoonah amma ba a ɗauka ba. Numbar Muhsina ta kira itama ba a ɗauka ba. Suna da tarihin ta a hannu, hatta yadda ta shiga shock lokacin da aka attacking na su sun samu labari shiyasa su ka fara ma ta video ɗin. Tana ganin videon ta yanke jiki ta faɗi. Yanzu ma asibiti aka kawota inda jinin ta ya mugun hawa... "Ranka shi daɗe zan ajiye ƙaran nan" ta yi maganan tana share hawaye. " Idan har ajiye ƙaran shi zai kawo maslaha dole na ajiye, rayuwar 'ya'yana da jikokina ya fi min komai" Justice ya ce "gaskiya ne, gobe sai a zauna da lawyan sa a tattauna a kuma cike takardu" Ta ɗan yi mamaki dan ba ta yi zaton zai amince da haka ba. Ko dan ya ga yanayin da Zaytoonah ta shiga ne?. "Amma akwai abu ɗaya, ki kira shi Udodiri ya sake tabbatar miki za a sake yaran lafiya idan har aka janye ƙaran" Ta gyaɗa ma sa kai. Lokacin da ta kira Udodiri sai da yai dariya sosai kafin ya tabbatar ma ta da cewa daan janye ƙaran shima zai sako yaran bayan an gama duk wani necessary procedures. Tana kwance a kan gado amma idon ta biyu, drip ɗin da aka sa ma ta yana ɗiga a hankali a hankali. Tun da aka kawota yanzu ne ta farka ba tareda ta yi ta firgita tana sunbatu ba. "Adaeze kin tashi" Mommy ta faɗa bayan ta ga idon ta a buɗe. "Suma tafiya za su yi su bar ni ko?. Daddy ya tafi , Zuhayr ya tafi, yarana ma sun tafi..." "Insha Allah babu abinda zai same su. Za mu ajiye ƙaran gobe, Za a sake su a goben. Ba abinda zai same su kin ji Princess" Ba ta ƙara cewa komai ba sai hawaye kawai da ke fita a idon ta. Da dare Justice ya zo dubata. Jiya da ya zo tana bacci, yau da safe ma baccin ya samu ta ke yi. Tana ɗan kishingiɗe a kan gado Salman na zaune akan kujera, da ke ya samu sauƙi sosai dan ma har suna shirin sallamar sa nan da kwana ɗaya ko biyu. Babu riga a jikinsa saboda ana zafi, ga kuma cikin sa da aka ɗaure da bandage aka zagaye zuwa bayan sa. Mommy na zaune akan sallaya tana jan carbi. Bayan sun gaisa ne Salman ɗin ya miƙe ya koma ɗakin sa yana tafiya a hankali. Mommy minti biyu ta ƙara a wajen ta ce ba ri ta je ta duba Salman ko akwai abinda ya ke buƙata. Bayan fitar Mommyn ne Justice ya jawo kujera kusa da Zaytoonah ya zauna tareda ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya. Kallo ɗaya za ka ma ta ka ga yadda ta faɗa saboda tashin hankali. "Ya jikin na ki" yai maganar yana kallon ta. "Da sauƙi" "Ki kwantar da hankalin ki kin ji, ba abinda zai same su Bi Izni Kun Fa Ya Kun. "Akwai hanyar da za a tseratar da su a kuma samu evidence akan Chief Udodiri but only if you comply. "You have to be strong for this kin ji" Ta gyaɗa ma sa kai tareda faɗin na gode. "Ai ba godiya tsakanina da ke, Muhammad da Ahmad 'ya'ya na ne. "Ko dai Uwargida ta chanja ra'ayi ne?" Sunkuyar da kai ta yi tana murmushi... *** Washegari ƙarfe goma Udodiri da Lawyan sa su ka haɗu da Mommy da Zaytoonah a kotu inda Mommy ta sa hannu akan ta janye duk wani ƙara da ta ke yiwa Chief Udodiri na kashe ma ta iyaye da kuma cinye dukiyar su da yai. Bayan sun fito ne Mommy ta share ƙwalla tana faɗin " akwai Allah" Zaytoonah ta riƙe hannun ta tana faɗin "Allah na tare da mu Mommy" Kamar yadda Justice ya faɗa ana finalizing komai zai sake yaran. Mommy ta kira numbar sa amma yai rejecting. "Ki ga, Yana rejecting call ɗina. Adaeze wannan mutumin yana rejecting call ɗina" "Mommy ki kwantar da hankalin ki bari mu bar nan sai mu sake kiran shi" Ta kalli Zaytoonah da mamaki. Ba ta ga damuwa a wajen Zaytoonan ba ita da ya kamata ace ta damu ma. "Zaytoonah ko dai an sake su ne?" "No Mommy mu bar nan tukunna" Ba ta sake cewa komai ba har su ka isa wajen mota har lokacin kuma Udodiri bai ɗau wayar sa ba daga baya ma numbar ma ba ta shiga. Sai da su ka shiga motar ne Zaytoonah ta miƙa ma ta wayar hannun ta wanda ta rubuta ma ta saƙo. *the twins are safe, but keep acting that you are worried* "Adaeze!" "Trust me Mommy" Tunda har Zaytoonah ba ta damu ba to tabbas yaran na nan lafiya. Yarinyar da lokacin da ta ga video ɗin yaran ɗaure sumewa ta yi saboda firgita shine yanzu ta ke zaune hankali kwance, tabbas yaran are safe kamar yadda ta faɗa. A ɓangaren Chief Udodiri kuwa yana fitowa daga kotu hanyar airport yai saboda mummunan labarin da ya ji ba zai sa ya iya tsayawa ba balle har Mommy ta dameshi da maganan sake yara. Yaran da aka ɗaure aka ajiye su a chan wani gida shine wasu su ka je suka sake sace yaran bai sani ba sai da safe da aka bugo ma sa waya akan an sace yaran da ya sace kuma ana son 500 million kafin a sake su. Hankalin sa ya matuƙar tashi dan da farko ya ɗauka su Mommy ne su ka yi wannan aikin, amma ganin Mommy ta bayyana a kotu akan lokaci ya shi tabbatar da cewa ba ta san da wannan maganar ba dan da ba za ta zo ba. Mommy ta kira wayan Barr. Toby Rowling, da ke bai san da maganar wasu sun sace yaran ba sai ya ɗau kiran. Mommy ta fashe ma sa da kuka tana faɗin ya ci amanar ta, ta yi abinda su ka ce amma ba su sake 'ya'yan ta ba. Ta ƙare da cewa idan wani abu ya sami yaran ta sai ta sa an ƙwace licence ɗin sa. Ba shiri Barr. Toby ya kashe wayar tareda dannawa Chief Udodiri kira. "Sir we had an agreement, release the kids to her" "The kids are gone!" Udodiri ya daka ma sa tsawa tareda kashe wayar. Yana tsaye a layi ya tambayi ko akwai jirgin da zai tafi Owerri ya ji an ce "excuse Sir" Ganin police tsaye a wajen sai da hantar sa ta kaɗa amma a hakan sai da ya dake yana faɗin "Yes, how may i help you?" "You'll follow us to the station to answer few question Sir" A lokacin ya buɗe baki ya fara magana da ƙarfi akan ko sun san shi waye a ƙasar da za su fara ma sa maganar banza. Yadda ya ke hayaniya yana masifa hakan ya jawo hankalin mutane wajen, har wasu suka fara ɗaukan abin a video. Ƙarshe dai sai da aka yi da gaske kafin aka tafi da shi. Kan kace me an ɗauka a social media kan cewa an kama Chief Augustus Udodiri. Ana kai shi station aka nuna ma sa arrest warrant tareda rufe shi a cell bayan an sha fama da shi wajen ƙoƙarin tisa ƙeyar sa zuwa cell ɗin. 24hrs Chief yai a cell ba tareda an ba da bail ɗin sa ba. Ya kira Lawyan sa ya kira manyan mutanen da ya ke ganin za su taimakeshi amma kowa ya janye hannun sa. Tuni aka fara marawa abokin hamayyar sa baya wato Chief Arinze. Barr Toby ma ƙoƙarin barin ƙasar ta ke na ɗan wani lokaci amma bai samu dama ba hakan ya sa dole ya zauna dan ya nema mu su mafita da shi da Udodirin. A rana ta uku wacce ta ke ranan Jummu'a aka tura case ɗin Udodiri kotu wannan karan bisa laifin Kidnapping ɗin yara uku ake tuhumar sa. Abubakar Tijjani Abubakar ɗan shekara tara sai Muhammad Zuhayr Muhammad Ilyas da kuma Ahmad Zuhayr Muhammad Ilyas dukkan su 'yan shekara huɗu. Da ke shi kan sa Barr. Toby akwai tuhuma a kan sa sai ya zamana Barr. Ayinde ne mai wakiltan Udodiri yanzu. Bayan an karanto ƙara sannan aka kira Chief Udodiri ya shiga witness stand. Mommy ya fara dubawa yayinda ya kalli gefenta na hagu ya ga babban maƙiyin sa wato Chief Arinze. Wannan kaɗai ya tabbatar ma sa akwai wata manaƙisa a ƙasa. Duk zaman da ake yi tunda aka fara shari'ar bai taɓa halarta ba amma wannan karan ya zo. "Chief Udodiri mi za ka faɗawa wannan kotu gameda tuhumarka da ake yi gameda sace wasu yara uku Abubakar Muhammad da kuma Ahmad tareda jikatta bodyguards ɗin su da driver" "Ni ban san wannan magana ba. Ni mutum ne mai daraja a ƙasar nan kuma ina da kima a wajen mutane shiyasa ma jam'iyyata su ka zaɓe ni a matsayin wanda zai yi takarar Senator mai wakiltar mazaɓar Obowo kuma mutane su ka mara min baya" "Chief Udodiri ko za ka faɗa mana minene haɗin ka da Maryam Nkiru Uzodinma" " niece ɗina ce" "amma kana da labarin cewa an sace ma ta ɗan ta da jikokin ta biyu?" "Ba ni da labari gaskiya" Zaytoonah ta kalli judges ta ce " ina so kotu ta bani dama na bayyana shaida na farko" Aka bawa registrar CD plate ya ƙarɓa ya saka a laptop ɗin sa tareda jonawa da projecter da ke wajen dan kowa ya gani. Video ne na wajen da Mommy da Udodiri su ka yi maganar ajiye ƙara. Udodiri na fara ganin video ɗin hankalinsa ya tashi. Mi ya ke shirin faruwa? Ya faɗa a ran sa. Maƙudan kuɗi ya bayar wa ma su restaurant ɗin saboda a clearing wajen sannan ko da Mommy za ta shigo wajen sai da aka karɓi wayar ta aka kuma chajeta aka tabbatar ba komai a jikin ta. To ya akayi aka ɗau video ɗin? "Ina fata wannan kotu mai alfarma ta gamsu da wannan evidence ɗin. Client ɗina ta amince da ajiye ƙara ne saboda sace ma ta ɗa da kuma jikoki da aka yi, sannan bayan ta yi abinda ya ce sai bai cika alƙawarin sa ba dan har yanzu bai sako ma ta 'ya'yan ta ba" "Objection my lord, client ɗina bai shirya wa wannan evidence ɗin ba" "Objection overruled" Justice Nwosu yai magana Zaytoonah ta cigaba " ina so wannan kotu ta tursasa Chief Udodiri ya fito da yaran nan guda uku sannan a hukuntashi dai dai da laifukan sa" Kafin Zaytoonah ta ƙarisa maganar ta Chief Udodiri ya fara wani fitar da numfashi sama-sama daga ƙarshe sai gani su ka yi ya faɗi... *** "Lallai mutumin nan tantiri ne, tsabar iya bariki suman ƙarya yai a kotu" "Barin gaya ma ka Salman, ko mutuwa zai yi we will win this case, this i know for sure" Salman ya kalli Auwal ya ce "amma Galadima genius ne Allah. Kai mutumin nan Allah ya bashi baiwa" Auwal ya gyaɗa kai kawai yana cigaba da danna waya kamar bai ma san mi ake faɗa ba. Tun jiya da ya zo ba maganar da ake yi a gidan sai na Galadima. Shi ya sani son zuciya da kwaɗayi ne ya sa Baffanun sa su ka amince da auren Zaytoonah da Galadima a karo na biyu. *ka yi haƙuri Auwalu, na san ka cancanci auren 'yar uwar ka amma gaskiya a wannan yanayi aurenta da Galadima shi ne ya fi dacewa da ita. Shi ba yaro ba ne, zai iya riƙe marayun yaranta tsakani da Allah ba tareda ya gajiya ba"* *"Baffah..."* *"ka yi haƙuri kawai ka cigaba da riƙeta a matsayin ƙanwa a gareka"* Da wannan maganar ta tsaya. Ba dan ya so ba sai dan babu yadda ya iya. Daɗin daɗawa kuma Zaytoonan da ta ce ta fasa auren Galadima ita ne kuma da kan ta tace ta amince. Bai da mafita sai dai kawai ya barwa Allah lamarin sa... Jin sunan Galadima da Salman ya ce ya sa Zaytoonah ta yi shiru. Yanzu fa nan da lokaci kaɗan za ta zama matar sa. Duk da ta amince amma har yanzu tana shakkar decision ɗin da ta ɗauka. Aure yana zuwa da responsibilities dayawa ga uwa uba ita ɗin saboda 'ya'yan ta za ta aure shi. Anya za ta iya sauke ma sa dukkanin haƙƙoƙin sa da ke kan ta?. Duk yadda ta so ta ga 'ya'yan ta Justice ya ce ta bari a gama case ɗin saboda fito da yaran barazana ne ga rayuwar su. Suma yaran ba damuwa su ka yi ba tunda suna waya, ga uwa uba kulawa na musamman da su ke samu a wajen Justice ɗin. Zaune su ke a falo suna cin abinci a dinning suna zubawa Justice surutu Dreba ya shigo falon ɗauke da kaya biye da shi kuwa Suhailah ce ta shigo da gudu tana kiran Daddy. Ba ta lura da yaran da ke wajen ba sai da Justice ya ɗaurata a kan cinyarsa yana tambayarta ya su Hajiya, ta kalle su ɗaya bayan ɗaya sannan ta ce "Daddy who are they?" Sai da ya kissing kumatunta sannan ya ce " they are your brothers" Kafin ta yi magana sauran yaran ma su ka iso tareda Hajia Ghazala da ta kawo su. Cak su ka tsaya su na kallon yaran da mamaki. Sanda Justice ya gabatar da su Junior a matsayin ƙannen su Raziya wani tsaki ta buga sannan ta bar wajen da gudu. Justice ya bi ta da kira amma ko a jikin ta, ɗaki ta shiga ta banko ƙofa. Dama tunda su ka ji maganar Daddyn su zai yi aure a wajen Hajia Ghazala hankalin su ya tashi. Suhailah ce da ba ta da wayo ba ta nuna damuwar ta ba akai. Ita ce ma ta kai gulmar abinda su ka ji wajen Justice tana tambayar shi yaushe sabuwar Mommyn su za ta zo. Bai tsammanci Hajia Ghazala za ta ma sa haka ba tunda ya riga ya tsara yadda zai yi ya zaunar da yaran na sa ya gaya mu su zai yi aure. Fishi sosai Raziya babbar 'yar sa ta yi da shi, kusan dalilin da ya sa ma ana hutun mid term su ka ce za su je Yola maimakon ma Zaria da su ka fi zuwa. Jiya da su ka ce za su zo yau ya gaya mu su cewa akwai surprise ɗin da za su gani idan sun zo. Bayan ya faɗi hakan ne kuwa daga baya Hajia Ghazala ta ja Razia gefe tana gaya ma ta ai yaran Zaytoonah ne a gidan yanzu sune surprise ɗin, ga shi kuma ta zo ta gani da idonta. Da ke ta san maganar auren ya fi taɓa Raziya sai ta yi amfani da wannan dama. Tun da aka kawo 'yan biyu gidan mai aiki ta kirata ta sanar da ita. Kaf abinda ke faruwa a gidan Justice Hajia Ghazala ta sani dan ta siye masu aikin gidan kaf ɗin su. Fara'a da yawan kyaututtuka da ta ke mu su idan ta zo ya ba ta damar samun kan su yadda ta ke so. Ta ko wani fanni so ta ke ta nunawa Justice auren ta ne kawai zai yi ya samu kwanciyar hankali, duk da bikin sa da Zaytoonah yana ƙara matsowa hakan bai sa ta cire rai ba tunda ta san namiji Musulmi dai mijin mace huɗu ne... "Barin je na ma ta magana, ka san akwai gajiyar hanya tattare da mu" daga haka itama ta haura sama ba tareda ta ma damu da su Junior da ke wajen ba. Falaq kam sai da ta gaisa da Daddyn ta da kyau kafin ta ce ma sa za ta je ta chanja kaya ta dawo. Suhailah kuwa da ke akwai ƙarancin shekaru ba ta damu ba sakewa ta yi da yaran tunda 'yan biyu kusan sa'anni ne dan shekara ɗaya ta basu... *** Yau za ayi zaman kotu na biyu, tunda dama sati ɗaya kotu ta bayar dan Chief Udodiri ya je yai jinyar kan sa. Sun so haɗa baki da Likita dan a riƙe shi a Asibiti na wata ɗaya amma ba su samu haɗin kan Likitan ba. Kusan yanzu duk matsayin da ya ke da shi ba wani tasiri da hakan ke yi. Cikin sati guda amma damuwa ta sa Chief Udodiri ya faɗa sosai, yayi baƙi. Tambayoyin Zaytoonah yau ba akan Udodiri ya fara ba sai akan Chidi da yaran sa guda huɗu, inda ɗaya ma da sanda ya taho saboda halbeshi da aka yi a ƙafa ranan da aka ritse su. Udodiri na ganin an gurfanan da Chidi a kotun, gumi ya fara tsatstsafo ma sa. Chidi shine mutumin da ya bawa kwangilar sace yaran, kusan yana ɗaya daga cikin ma su aikata ma sa dirty deeds na shi. Duk tambayoyin da Zaytoonah ta ma sa da tuhumar sa da ake yi ya amsa laifin sa. Inda ya bayyana cewa tabbas Udodiri ne ya ba su kwangilar sace yaran guda uku bayan sun tsare motar su a hanyar su ta zuwa Zaria. Bayan ya gama ba da shaidar ne Zaytoonah ta kira wani police wanda ya bayyana yadda aka yi su ka kama Chidi tareda ceto yaran daga hannun kidnappers ɗin. "Ina fata wannan kotu za ta duba wannan lamari ta kuma ba da damar cigaba da ƙaran da client ɗina ta shigar tun farko, wanda tsoron kada a hallaka ma ta 'ya'ya ya sa ta janye ƙaran saboda akwai hujjoji ƙwarara da ta ke da shi akan Chief Udodiri" Justice Ayoola ya ce kotu ta bada damar a dawo da ƙaran ranan 6 ga wata mai zuwa wanda ya kama saura kwana goma sha shida kenan, kafin nan a tisa ƙeyar Chief Udodiri zuwa gidan yari. Lawyan Udodiri ya tashi yana neman a ba da bail ɗin Udodiri saboda lafiyar sa amma alƙalan ba su amince ba. Zaytoonah da Mommy fiskar su wasai su ka fito daga kotun. Suna fitowa kuwa 'yan jarida su ka mu su chaa amma ba su tanka mu su ba. Da ke wannan karan su Chief Asibong sun zo kai tsaye gidan sa da ke nan Abujan su ka nufa. Sai da aka samu zama aka ci abinci kafin aka sako zancen abinda ya faru. Abin mamaki Chief Asibong ya san komai, su Mommy da Zaytoonah ne kawai aka bar su a duhu dan Justice bai faɗa mu su dukkan abinda ke faruwa ba, sun dai san an ƙwaco yaran kuma yaran na gidan sa. Zaytoonah dai bin instructions ɗin sa ta ke yi a kotun tunda wannan karan babu shi a Alƙalan da su ke sauraron ƙara... Chief Arinze ne ya samu Chief Asibong akan zai taimaka mu su wajen samun solid evidence akan Udodiri. Yana shakkar zaɓen da za ayi bana, saboda mahaukatan kuɗi Udodiri ya kashe a mazaɓar sa saboda a zaɓe shi, siyasar yanzu kuma na kuɗi ne. Da kuɗi ake siyan ƙuri'on mutane. Tunda aka fara case ɗin ya ke faɗi tashi wajen ganin ya samu evidence mai ƙarfi akan Udodiri saboda a samu a turashi kurkuku. A hankali ya dinga amfani da kuɗi da siyasa wajen binciko abubuwan da su ka faru shekaru talatin da su ka wuce. Duk abubuwan da 'yan uwan Udodiri su ka ɓoyewa Mommy saboda suna tsoron fushin Udodiri sai ga shi Chief Arinze ya ƙwaƙulo komai. Lokacin da Chief Asibong ya samu support ɗin Chief Arinze shine ya kira Justice ya sanar da shi komai, bai kira Mommy ba ne saboda ya san a wajen Justice zai samu abinda ya ke so. Bayan Udodiri ya nemi ganawa da Mommy Justice ne ya nemi biyan mai restaurant ɗin kuɗi saboda su samu daman saka camera da za ta ɗau hiran na su. Fortunately kuma ashe Justice ya wayi asalin mai restaurant ɗin kuma ya taɓa yi ma sa taimako a baya. Dan haka ba ɓata lokaci aka haɗa camera ɗin a wajen da Udodiri yai booking kafin ma ya zo. Da taimakon Chief Arinze aka gano waɗanda su ka sace su Junior, bisa shawaran Justice aka bi komai a sannu har aka kawo wannan rana. Yadda 'yan uwan Mommy ke ta yaba Justice ya sa Zaytoonah yin murmushi, Ko ba komai ta ji daɗin hakan... *** Justice da kan sa ya maido da yaran gida bayan sun yi kwanaki goma shabiyu tareda shi. Ba ƙaramin sabo su ka yi da sabon Daddyn na su ba, kwana huɗu da su ka yi da 'ya'yan sa sun saba sosai da Suhailah. Falaq tana ɗan shiga harkan su amma ba sosai ba sai dai Razia kam ko fiskar su ba ta son gani. Ga wani mugun kishin su da ta ke ji dan gaba ɗaya daga Justice ya dawo to yana maƙale da yaran ne. Ba abinda ma ya ke ɗaga ma ta hankali irin da fa an auri Maman su shikenan za su koma zama tareda su gida ɗaya kamar yadda Hajia Ghazala ta jaddada ma ta, tun kafin Zaytoonah ta shigo gidan already ta riga ta tsaneta. Zaman abinda bai fi minti goma shabiyar ba Justice yai sannan yai sallama da Mommy da yaran. Yaran su ka zo su ka rungume shi suna tambayar sa yaushe zai sake zuwa. Ya ce mu su ko gobe ma zai zo idan suna so. Sai su ka fara tsalle suna haɗa baki wajen faɗin "muna so, muna so" Saboda kar su cigaba da takurawa Muhsina wanda mijin ta ya ke shirin dawowa nan da kwana biyu ya sa dukkan su suka tattaro su ka dawo gidan Chief Asibong. Lokacin da Justice ya fita ne Mommy ta yi saurin shiga ɗakin Zaytoonah, sanda ya zo tana wanka amma har yanzu ba ta fito ba. Tuni ta yi wanka ta shirya amma ta ƙi fitowa. "Ba za ki je ki yiwa Justice godiya ba" "Mommy na ma sa a waya" "Ba na son shirme, ki je kafin ya tafi" Ta miƙe tana mutsu-mutsu da baki... Ranan da aka dawo kotu cikin watan Azumi ya faɗa. Kotu ya cika maƙil. Tawagar Chief Arinze da ta Chief Asibong duk suna wajen. Kowa ya zuba ido ya ga yadda za a ƙare shari'ar. Ikenna wanda ya ke ƙani ne ga Udodiri uwa ɗaya uba ɗaya shi aka fara gabatarwa inda ya ba da shaidar cewa bayan mutuwar Patrick da matar sa duk wani dukiyar su da su ka bari Udodiri ya chanja zuwa sunan sa. Saboda ya cire kan sa daga rikici ya sa shi cewa lokacin da Patrick ya mutu yana ƙarami dan shekarun sa shashida a lokacin. Sai dai daga baya Anty Uloma ta gaya ma sa cewa Udodiri ne ya kashe Patrick saboda ya gaji dukiyar sa. A hankali Zaytoonah ta ke takawa har ta kai wajen stand ɗin, tuni ta farayin laushi, Azumin ya fara shigarta. "Mr Ikenna ko za ka gaya mana miyasa ba ka bayyana abinda Uloma ta gaya ma ka ba sai yanzu?" Ikenna ya ce " ina tsoron Yaya na ne saboda dukkan mu ya ja mana kunne akan duk wanda ya tona ma sa asiri zai kashe shi ya kuma kashe ma sa Iyalai. Kuma sanin halin zai iya ya sa na yi shiru" Bayan Zaytoonah ta gama yi ma sa tambayoyi sannan Lawyan Udodiri shima ya taso yai na shi wanda duk tambayoyin sa ƙoƙari ne na ruɗar da Ikenna kuma hakan bai faru ba. Bayan an gama da Ikenna sannan Zaytoonah ta gabatar da Ebube da kuma tawagar sa inda su ka amsa laifin su na yiwa Uloma sata da kuma kasheta da su ka yi wanda umurni ne daga wajen Chief Udodiri. Udodiri shiru yai kawai yana sawa a ran sa cewa duk yadda aka yi akwai hannun Chief Arinze wajen tonuwar asirin sa. Ya rantse idan har aka sake shi ba abinda zai hanashi kashe Chief Arinze. Bayan shaidu da aka gabatar beyond doubt sannan Alƙalan su ka ɗauki hutun minti goma inda su ka keɓe kan su suka tattauna gameda sahihancin dukkan bayanan da aka bayar da kuma irin hukuncin da za a yankewa Chief Udodiri. Tana zaune da Mommy tana ɗan mammatsa ƙafar ta da su ka riƙe sai ga kiran Justice ya shigo. Kaman ba za ta ɗauka ba amma ganin Mommy ta zura ma ta ido ya sa ta ɗau kiran tareda rage volume ɗin saboda kar Mommy ta ji maganar Justice. "Haka matar tawa take da raki, yau Azumi 11 fa." Ya faɗa bayan ya amsa sallamar ta. Ba ta san ya aka yi ta tsinci kan ta da yin murmushi ba" wai matar sa. Bayan sai bayan sallah za a ɗaura aurn. "Ina Alfahari da ke Zaytoon, kin yi ƙoƙari sosai" "Na gode" ta faɗa tana satan kallon Mommy wanda ita kan ma hankalin ta baya kan wayar ta su. Bayan an dawo daga hutun ne chair Justice ɗin ya fara bayani kamar haka. "Bayan kotu ta tabbatar da dukkan shaidu da aka kawo, kotu za ta yankewa Augustus Udodiri Uzodinma bisa laifin kashe rayuka uku tareda cinye dukiya, gamida take 'yancin ɗan Adam da yai ta hanyar azabtar da Maryam Nkiru Uzodinma. Daga ƙarshe kuma an kama shi da laifin kidnapping ɗin ƙananan yara guda uku. Bisa girman wannan laifuffuka Kotu ta yanke ma sa hukuncin kisa ta hanyar rataya. "Sannan wannan kotu ta yanke wa Chidi da yaran sa hukuncin shekaru biyu a gidan yari. Yayinda Ebube da yaran sa za su ƙarisa rayuwar su a gidan yari. "Kotu ta kwace lasisin Barr. Toby Rowling har na tsawon shekara bakwai idan aka kama shi yana practising Law kafin nan za a yanke ma sa hukunci mai tsanani. "Kotu ta damƙawa Maryam Nkiru Uzodinma Kamfanin mahaifinta da Udodiri ya ƙwace tareda gidan sa da ya gina kafin ya mutu dama duk wani dukiya da ya bari kafin mutuwar sa. Sannan Iyalen Udodiri za su biya diyya ga 'ya'yan marigayiya Uloma Uzodinma" Daga haka Justice Ayoola ya buga gudumar su ta alƙalai. Hawaye ne ya ziraro a idanun Mommy, Zaytoonah ta yi saurin ƙarasowa wajen ta ta rungumeta itama na zubda hawayen farinciki. Hayaniya ya ɗan kacame a kotun saboda yadda matar Udodiri da yaran sa guda biyu da jikan sa ɗaya su ka saka ihu suna kuka yayinda Babban ɗan sa namiji ke ta faman ririƙe mahaifiyar ta su yana baya haƙuri.... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 54 Bismillahir Rahmanir Rahim *The second wife* "Dan Allah ki yi haƙuri" Raziya ta faɗa fiska shame-shame da hawaye da majina. "Ban ji ba, ki ka ce me?" Zaytoonah ta faɗa tana riƙe kunne " ki yi haƙuri ba zan ƙara ba" "Good. Da bakin ki kika ce ba za ki ƙara ba sai dai idan ki ka ƙara ɗin mi zan miki?" "Anything" ta faɗa tana sheshsheƙar kuka. "Shikenan tashi ki je" Ta miƙe da ƙyar ta bar ɗakin. Bayan ta fita Zaytoonah ta ce "ashe rashin kunyar na ƙarya ne. Gaba ki sake neman tsokana, ni da ke a gidan nan". Tana kitchen ta ji shigowar Hajiya Ghazala tana wani ɗaga murya wai ina Raziya. Zaytoonah ta ja tsaki ta cigaba da abinda ta ke. "Ta dake ki?" Hajia Ghazala ta tambayi Raziya da ke kwance. Raziya ta girgiza ma ta kai. "Aiki kawai ta sa ki?" Ba ta iya magana ba sai gyaɗa kai da ta yi. "To bari ki ji indai kina so ta bar gidan nan. Idan Daddyn ku ya kira ki ce ma sa ta dake ki kin ji" Raziya ta yi shiru. Hajiya Ghazala ta cigaba da kitsa ma ta abinda za ta faɗa tana nuna ma ta indai ta yi hakan to Daddyn su zai saki Zaytoonah ta bar mu su gidan gaba ɗaya. Wannan karan bayan ya ji abinda ya faru daga ɓangaren Hajia Abu, Ghazala da ma Raziyan bai yanke mataki ba duk da dai ransa ya sosu da abinda ya faru. Kiran Zaytoonah yai ya tambayeta miya faru a gidan sanda baya nan. Da ke ranta a kufule ya ke sai ta ce ma sa "na san ka kira ne dan ka ji dalilin da ya sa na yiwa Raziya haka. To dalili ɗaya ne, ba zan cigaba da ɗaukan rashin kunyarta ba. na san ban haifeta ba amma atleast na girmeta kuma ko gaba ta sake shiga hurumina zan hukuntata" Yai shiru bai ce komai ba sai chan ta ji ya ce " Allah ya kyauta" Yana katse kiran ta ja tsaki ta fara kwarwa " haka kawai yarinya za ta mai da ni shashasha. Ta kirani buskuɗa, inyamura, Mama ɗuwawu duk ban tanka ba still dan tsabar rashin kunya sai ta shigo min ɗaki ta min ɓarna saboda ni baiwar gidan su ne". Ɗazu su ka gama baran-baran da Hajia Ghazala, ta gama karantar ta, matar babbar munafuka ce ta ƙarshe kuma da alama akwai wata agenda da ta ke da shi a ƙasa. Ko waye ya kirata ma ta zo oho... *** "Daddyn Raziya ina son zuwa gidan Muhsina gobe" Sai da ya kurɓi tea kaɗan kafin ya ce "Allah ya kaimu" Su biyu ne zaune a dinning ɗin suna karyawa. Wannan weekend ɗin yaran sun tafi Zaria tareda Hajiya Ghazala. Itama ta so yaranta su zo wannan weekend ɗin amma Mommy ta tafi da su Ringim. Har su ka gama cin abinci ba wanda ya ƙara cewa komai. Tun ranan da ya dawo ta ke jira ya ma ta magana akan aikin da ta saka Raziya amma bai yi ba itama sai ta biye shi aka cigaba da zaman shiru. Ko da ya tada maganar ma tanada befitting amsa da za ta bashi. Dan ta ga take-taken sa yana nuna bayason abinda zai taɓa ma sa Yara... "Faɗamin gaskiya 'yar uwa, kina bashi haƙƙin sa yadda ya kamata?" "Ni kam..." "Seriously Zaytoonah, ke fa ba yarinya ba ce, in har babu wannan intimacy tsakanin ki da mijin ki akwai matsala. To ni in tambayeki zaman mi ki ke yi a gidan sa?" "Zaman aure mana" Zaytoonah ta amsa da sauri. "Haka ake auren a garin ku? For good 3months kina zaune a gidan sa zaman kashe wando" "Malama wata biyu da sati uku ne" "I'm dissappointed in you Allah. So ki ke ya nemi matan banza a waje? Ko so ki ke ya ƙaro wata matar a kan ki?. In ba dan Galadima ma ba yaro ba ne ta ina zai biyewa shirmen ki har ya bari kuna zaune gida ɗaya iya wannan lokacin yana jira ki kawo kan ki" "Muhsina ba za ki gane ba, its just complicated ne" "Really!. Mutum mai daraja kamar sa kin mai da shi wawa ki ce its complicated. Haba Zaytoonah, haba" Hawaye ne ya gangarowa Zaytoonah ta yi saurin gogewa tana faɗin " ba zan iya mantawa da Zuhayr ba. Nobody can take his place..." "Subhanallahi! Zaytoonah wani irin gurɓaceccen tunani ne wannan" Ina buƙatan lokaci a halin yanzu i just cant..." "Cant or wont" Muhsina ta katse ta rai a ɓace... *** Ta sauke ajiyar zuciya ya fi sau bakwai, duk dan tana neman sauƙi a zuciyarta da ya cunkushe. Ga shi dai ta shirya a zahiri amma a baɗini ba ta shirya ba. *" ba shi da muni, ba jahili ba ne, ba shi da nakasu a tattare da shi. So what's stopping you from embracing your husband?. Ta ya za ki hana shi, ki hana kan ki samun nitsuwa da Allah ya halarta mu ku. Ban ce ki bashi kan ki a matsayin dole ba, amma na rantse mi ki da Allah indai ki ka ba shi dama nan da lokaci kaɗan duk wani ɗari-ɗari da ki ke ji zai tafi and you'll accept him wholeheartedly"* Maganganun Muhsina ya ba ta ƙwarin gwiwar miƙewa, ta taka zuwa gaban madubi ta kalli kan ta. Ba wani kwalliya ta yi ba amma ta yi kyau. Rigan baccinta iya rabin cinya ne fara ƙal sai robe ɗin rigan wanda ya kai ma ta har ƙasa shi kuma baƙi, dai da ta nannaɗe gashinta into bun kafin ta saka baƙin bonnet a kan ta. Ta fesa turare a jikin kayan sannan ta shafa turaren jiki a wuyan ta sauran ta murje shafukan hannunta da shi. Har ta zo za ta fita ta ji wayar ta na ringing a kan gado. Ta je ta ɗauka sai ta ka kiran Justice ne. Da ta amsa wayan ya ce ta same shi a falon sa yana da magana da ita. "Relax Zaytoonah" ta faɗa tana shaƙar iska sannan ta fizgar da shi. "Ko da ya miki faɗa akan Raziya ne kar ki yi fushi kin ji. Ke ma idan ba ki manta ba Daddy har faɗa ya ke yiwa Mommy idan ta punishing ɗin ki. Relax he's a father matsayin ki matar sa matsayin Raziya 'yar sa akwai banbanci kin ji" Da wannan mantra ɗin ta wuce falon Justice. Baya rabuwa da karatu, yanzu ma wani ƙaton littafi ta gani a gaban sa yana karantawa da alama littafin abinda ya shafi Law ne. Ƙaramin hijab ta saka akan kayan dan ta zo fitowa a haka ta fasa ta saka hijab ɗin. Kusan minti biyar kafin ya rufe littafin ya ajiye gefe. Ya yi salati tareda buɗe zaman da addu'a. Cikin zuciyar Zaytoonah tana tunanin ko dai yana duba ne, idan ba haka ba ya aka yi ya san ta zo ne domin su shirya. Sai da ya gama addu'an kafin ya fara jawabin sa wanda ƙaramar nasiha ce akan ƙaddara da kuma falalar yadda da ƙaddara, wanda ke ɗaya daga cikin cika-ciken musulunci. Sai da ya gama nasihar sa sannan ya faɗa ma ta dalilin kiran ta da yai. "Princess zan ƙara aure" Da sauri ta ɗago ido tana kallon sa ko dai kunnen ta ne bai ji dai-dai ba. "Ba dan na nuna miki kin gaza ba, sai dan ina ga hakan zai kawo maslaha a tsakanin mu. Kula da su Raziya ba zai zama yana hannun ki ke kaɗai ba, idan kin fara aiki kula da gida zai mi ki wahala ke kaɗai..." Sauran maganganun sa ya bi iska ne dan ba jin su ta yi ba. Wani ciwon kai ne ya sauka ma ta lokaci guda. Ta ma rasa yadda za ta kwatanta abinda ta ke ji yanzu. Certainly ba haushin Justice ta ke ji ba tunda koma wani irin hukunci ya ɗauka harda laifin ta ciki. Amma why zuciyar ta ya cunkushe ta ke jin wani ƙunci a ciki? "Ki yi haƙuri ban gaya mi ki ba sai yanzu, komai ya zo ne a ƙurarren lokaci" Murmushi mai ciwo ta yi a ƙoƙarinta na danne abinda ta ke ji mai kama da kishi. "Ranan Jumu'ah za a ɗaura aure, tarewar ta zai iya kaiwa sati ɗaya ko sati biyu bayan auren" "Allah ya kaimu lokacin" Da ƙyar ta iya haɗa kalmomin da ta faɗa... Tana shiga ɗaki sai ga hawaye ɗaya bayan ɗaya na zubowa. Ta ƙarisa kan gado ta kwanta. Wasa-wasa tun tana dannewa har ta kai ta kasa sai kawai ta fashe da kuka. Ba abinda ya zo ma ta rai sai dana sanin auren Justice da ta yi tun farko. Mi ya sa ma ta bi shawaran Mommy? Mi ya sa ma ta biyewa nasihar Mommy? Mi ya sa ba ta tuɓurewa Mommy ta auri Auwal ba. Auwal ba zai taɓa ma ta haka ba. Its barely 3 months da auren su amma wai zai ƙara aure. Kenan dama tun farko ba ita kaɗai yai niyyar aura ba kenan. Ire-iren waɗannan tunanin ta dinga yi har bacci ya sace ta bayan ta sha kuka ta ƙoshi... Washegari haka ta tashi kamar ba abinda ya faru. Indai aure zai yi to yai abunsa tunda matar ba a kan ta za ta zauna ba. Idan ta ga zaman ba zai yiwuba kuwa dole ne ya sallameta. Abinda ta sawa ran ta kenan. Ta dai ma sa breakfast amma ba ta zauna sun ci tare ba. Da dare kuwa da su ka zauna tare tambayarta yai ko akwai abinda ta ke buƙata amma ta ce ma sa ba komai. Haka ya dinga satan kallon ta. Yana so ya ga wata alama da za ta nuna ma sa Zaytoonah na kishin sa amma duk ta inda ya duba sai ya ga kamar yaudaran kan sa kawai zai yi dan bai ga alamun Zaytoonah na kishin sa ba... Wayar Mommy ne ya tasheta daga bacci. Da ta san maganar auren Justice za ta ma ta da ma baccinta kawai ta yi. Hajiya Ni'ima ce ta faɗa ma ta maganar auren da su ka haɗu a office. A faɗanta wai itama sai a lokacin ta ke jin maganar auren da ta je Fada, shi ne ta kira Galadima ta tabbatar da maganar a wajen sa. "Adaeze kar ki bari wannan ya ɗaga miki hankali kin ji. Ibada ki ke yi kuma itama shi za ta zo yi, duk abinda za ki yi ki yi shi tsakani da Allah domin shi zai ba ki ladan haƙurin da ki ka yi kin ji" "Adaeze i know it hurts, i felt the same way too lokacin da Daddyn ku ya auri Hajjo. It always hurts Princess. "Rayuwar aure kowa da kalar ta shi jarrabawar. Idan ki ka ji na wani sai ki kama baki ki godewa Allah saboda nakin ya fi na su kwanciyar hankali da farin ciki. "Ki lazimci addu'a sannan ka da ki yadda ki saka damuwar wata a ran ki, lafiyar ki da kwanciyar hankalin ki shine gaba da komai. Sai ki ga komai ya zo mi ki da sauƙi, kin ji" "Na ji" ta faɗa kamar za ta yi kuka... *** Tana zaune a ɗaki ita kaɗai sai ta ji sallamar Bahijje a bakin ƙofa. "Bahijje ki shigo mana" Matar ko da za ta girmi Zaytoonah to ba zai fi shekara ɗaya ko biyu ba. "Hajiya kina da baƙi a falo" "Baƙi kuma?, Ok, ki ce mu su ina zuwa" Doguwar riga ne a jikinta dan haka gyalen sa kawai ta yane ta fito. Tana saukowa ta sa dariya " yanzu dama ku ne, shine Bahijje wai na yi baƙi" "Af baƙin ne ai tunda dai ba a gidan mu ke ba" "Azma har da ke ko" "Anty Zaytoonah ai gaskiya ta faɗa" "Haka ma za ki ce, to na fasa ba ki ƙanina" "Dama mi za ta yi da shi muna da Munnir a gefe" "Cin amanar da za ayiwa Salman ɗina kenan. To ba zan yarda ba" Haka dai su ka yi ta tsokana tsakanin su. Muhsinah ta ce sun zo danne ƙirji ne. "Ba danne ƙirji ba Allah ya sa danna ɗuwa..." "Lalala! Zaytoonah haka ki ka zama" "Dama haka na ke". Zaytoonah ta idar da sallan Azahar kenan Azma ta miƙo ma ta waya wai an kira ta. Tana karɓan wayan sai ga text ya shigo. *Alhamdulillah! Allah ya tabbatar, duniya ta shaida Gimbiya Ghazala Amarya a gidan Yarima Yunus Galadiman Zazzau* "Ghazala?" Zaytoonah ta furta a fili cike da mamaki. "Wace Ghazalar?" Muhsinah da ke shan farfesun kayan ciki ta tambaya. "Ghazala ya aura. Ghazala ƙanwar tsohuwar matar sa" "Lallai kam. Dama duk take-taken ta dan ta aure shi ne. Zaytoonah kina da aiki a gaban ki" "Hmm" kawai ta faɗa ta ajiye wayar. "Ina text ta miki?" Muhsinah ta tambaya Zaytoonah ta gyaɗa kai. "Ki yiwa shegiya reply ta san cewa kema a shirye ki ke da ita" Kaman ba za ta biyewa Muhsinar ba amma da Azma ma ta sa baki sai ta ɗau wayar ta rubuta ma ta reply kamar haka: *marhaban-marhaban Anty Amarya, ko Mama Amarya ne ma?😂 Uwargidan Galadima tana mi ki maraba da wannan matsayi. Daga ƙarshe dai duk wani jeka ka dawo, wani tarairayan Yara na ƙarya, wani kamala na bogi da aka yi ta yi yayi rana kenan. Ayyah! Congratulations fah, wannan matsayi abun murna ne gaskiya* Muhsina ta so ta ƙara ma ta da wani abu amma Zaytoonah ta ce hakan ma yayi. Gaskiya sun ma ta mutunci dan tun safe har yamma lis kafin su ka bar gidan. Ba ƙaramin jin daɗin zuwan su ta yi ba, zuwan su ya sawwaƙa ma ka kaɗaici da ƙunci da ta ke ji... Kwana biyar da ɗaura auren aka zo ka gyarawa Ghazala ɗakin ta, an cire wa su kaya an saka sabbi wasu kuma an bar su yadda su ke. Exactly kwana takwas da aure Ghazala ta tare a gidan. Ƙawayenta da wasu 'yan uwan ta ne su ka rakota. Sun zo da ɗan rana ne dan da safe su ka taso daga Zaria. Da ke Maman Tope ne da aiki shiyasa tun kafin zuwan su ta ce ma ta ta shirya abinci na tarban tawagar Amarya. Justice ya riga ya sanar ma ta tun jiya cewa yau ne Ghazala za ta tare. Lokacin da su ka iso fiska sake ta fito daga ɗaki ta sauko ƙasa ta zo ta gaishe su. "Saura ki ƙi fitowa ki karɓi Amarya" "Ai dole na fita kin manta ni ce fa Uwargida" "Uwargidan da ta yi wasa da damanta ba" "Wuce nan kuma ai" ... Hiran su kenan ɗazu a waya tareda Muhsinah. Su bakwai ta gani idan ka haɗa da Ghazala takwas. Mace ɗaya ce tsohuwa a cikin su amma duk sauran sa'annin Ghazalan ne. Tsohuwar ce ta ce " to Uwargida ga amanar Amarya mun kawo miki" Kusan mutum uku su ka kwashe da dariya. Ɗaya a cikin su ta ce "Inna kenan. Wannan formalities ɗin ai sai yara. Da ma cewa ki ka yi Hajia Ghazala ta riƙe amanar wannan buredin sai mu ce kin yi dai-dai" "Wa ya ga buredi" wata ta faɗa a cikin su, hakan ya sa dukkan su kwashewa da dariya. Zaytoonah ta danne ɓacin ranta ta ce "barkan ku da zuwa outdated bitches" daga haka ta juya ta bar falon... Da dare Justice ya haɗa su ya mu su nasiha tareda faɗin yadda za a dinga rabon kwana. Duk wacce ya ke ɗakin ta ita ke da alhakin kula da abincin sa da ɓangaren sa. "Rabon kwana my foot" Zaytoonah ta faɗa a ran ta. Kusan tana shiga ɗaki ya shigo shima. Ajiye ma ta leda yai a saman kujera sannan ya tambayeta ko tana buƙatar wani abu ta ce ma sa ba komai. Har zai fita sai kuma ya juyo ya ce "Princess Allah ya tashe mu lafiya" Ta amsa da amin a ƙasan ran ta ko duba mi ya kawo ba ta yi ba ta kwanta... Bayan ya koma ɗakin sa yai wanka ya shirya kafin ya wuce ɗakin Amarya wacce ke jiran sa tun ɗazu. Ya samu tarba na musamman a wajen Hajia Ghazala sai dai gamsuwar da ya ke buƙatar samu babu shi. The aftermath feeling da ya ke son samu na kwanciyar hankali, shauƙi da tsananin soyayya babu shi. Zare jikin sa yai ya wuce banɗaki ya je yai wankan tsarki yai alwala ya fito kafin nan ya kwanta. "Ina ga zai kyautu ki fara yin tsarki kafin ki kwanta hakan yana da falala da fa'ida" Bai sake maimaita maganar ba haka nan itama ba ta tashin ba har bacci yai awun gaba da shi... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 52 Bismillahir Rahmanir Rahim *The kids* Sokali ɗaya Raziya ta yi ta miƙe tsaye za ta bar dining ɗin. "Miya faru?" Justice ya tambaya "The food is peppery Daddy" ta faɗa ranta a ɓace. Zaytoonah ta kalli yarinyar ta kuma kalli Justice tana jiran ta ji mi zai ce. "Ki je ki cewa Atika ta haɗa miki abinda za ki ci" A fakaice ta kalli Zaytoonah ta ma ta harara kafin ta wuce ta bar dining area ɗin. Zaytoonah ta girgiza kai kawai ta cigaba da cin abincin ta. Jollof rice ta yi da ke haɗe da carrot da green beans da spring onion sai ta suya plaintain sannan ta yi pepper chicken. Idan ka cire pepper chicken ɗin da za ta iya cewa yana da ɗan yaji to jollof rice ɗin kam ko rantsuwa za ta iya yi akan bai yi yaji ba. Tun a Zaria Baaba Nafy ta ce ma ta Justice ba ya cin yaji shiyasa duk girkin da ta ma sa ta dinga ƙoƙarin saita shi. Su ɗin ma ba wani Yaji su ke ci ba a gida saboda Mommy na da ulcer da ciwon ƙirji, idan ta ci yana damun ta. Sauran yaran hankali kwance su ka ci abincin sosai, naman ne ma ba su wani ci ba tana tunanin ko dan yayi yaji ne. Ta so magana lokacin da Justice ya cewa Raziya ta je a dafa ma ta wani abin amma ta sawa bakinta sakata kar a ce daga zuwa har ta fara ƙorafin yaran. Noodles da soyayyen ƙwai Raziya ta zo da shi a plate ta zauna dai-dai sun gama cin abinci dan Zaytoonah ma na tattare wajen ne. Sai da ta bari Justice ya tashi a wajen ta ce " mutum bai iya abinci ba ya dage sai yayi. Muna da professional cook ba za a bari ta yi aikin ta ba sai anyi shishshigi. Mtsww" Zaytoonah ba ta kulata ba dan ta san neman faɗa yarinyar ke yi ita kuma ba sa'ar ta ba ce balle har ta biye ma ta... Washegari da sassafe ta tashi ta fita dan ɗaura abin karyawa amma duk sammakon ta sai da tarar da Atika a kitchen ɗin. Ganin ta riga ta fara sarrafa abubuwa ya sa ta haƙura da girkin ta koma ɗakinta dama ko azkar ɗin safiya ba ta gama ba ta fito saboda yau Monday ta san yaran da Justice za su yi fitan sassafe. Tana idar da azkar ta yi tilawan da za ta yi ta kwanta. Kamar yadda ya saba bayan ya gama shiryawa ya sauko ƙasa dan ya karya kafin ya wuce office. Yaran tuni suna wajen dinning sun fara karyawa. Sai da ya zauna sannan ya kalli Raziya ya ce "ina Antyn ku" "I dont know" ta amsa tana cigaba da cin abincin ta. Bai ɗau amsar ta a matsayin rashin kunya ba sai ma ya miƙe ya haura sama, kai tsaye ya wuce ɗakin Zaytoonah. Lokacin da ya shiga tana bacci dan haka ya juyo kawai dan kar ya katse ma ta bacci. Zaytoonah ba ta tashi ba sai kusan ƙarfe takwas na safe lokacin sun jima da ficewa. Ta yi wanka ta shirya sannan ta sauko ta shiga kitchen ta nemi abinda za ta ci. Sauran pepper chicken da ya rage jiya da ta ajiye a fridge ta ɗumama ta haɗa da tea da bread ta ci. Da ta gama ba ta yi gigin kiran Atika ba sai kawai ta wanke abubuwan da ta ɓata da kan ta. Ɗaki ta koma ta ɗau waya ta kira Muhsina su ka sha taɗi tana tambayarta yaushe za ta zo ma ta. Bayan sun gama wayar ta kira Mommy su ka gaisa duk da ita ɗin ma tana class. Bayan ta gama gyara ɗakin ta sannan ta buɗe laptop ɗinta ta fara kallo. Ita ba gwanar kallo ba ce amma yawanci idan ta rasa abinyi kan ta zauna shiru sai ta kunna kallo ko ta ɗau littafi ta yi karatu. Wunin ranan haka ya zo ya shige cikin kwanciyar hankali. Ba ta yi girki da rana ba dan abincin da ta ci da safe ya isheta. Yoghurt kawai ta ɗauka a fridge ta sha. Da dare ba ta yi gigin yi wa Justice girki ba dan ba ta son abinda ya faru jiya ya faru yau. Al'amarin mai aikin gidan da ma Yaran musamman Raziya sai a hankali, ga Justice ɗin ma ba ta gane alƙiblan sa ba. Atleast tunda ta zo gidan shi ya kamata ya faɗa ma ta dokokin sa amma shiru yai tun jiyan. Ban da lokacin da su ka haɗu za su ci abinci da ya cewa yaran "ga Antyn ku nan ku ma ta biyayya" bai ƙara cewa komai ba... Kwana biyu kenan Zaytoonah ba ta sake yiwa Justice girki ba, duk abinda za ta yi dai dai cikinta ta ke yi ba ta ma zama a wajen dining ɗin. Rashin ganin ta da bai yi ba kwana biyu ya dame shi hakan ya sa ya nufi ɗakin ta yau da Asuba tun ma kafin ya wuce masallaci. Raka'atanil fajri ya samu tana yi lokacin da ya shigo wanda hakan ya burge shi. Da ta idar sai da ta yi addu'o'in ta kafin ta juyo ta kalle shi, yana zaune bakin gado jikinsa sanye da farar jallabiya. "Barka da Asuba" ta faɗa bayan ta kauda kan ta gefe. "Princess na yi laifi ne ki ke gudu na?" "Ranka shi daɗe gudun ka kuma, ai ban isa ba" "To minene matsalar?" Ta yi shiru tana kallon zanen masallacin ka'aba da ke jikin darduman ta. "Ni ne na miki laifi ko kuma 'ya'yan ki?" Still ba ta bashi amsa ba dan ba ta san mi za ta faɗa ba. Ganin ta yi shiru ya sa shi cewa "ba zan takura mi ki ba amma ina so ki sani zan fi jin daɗi idan za ki sake jiki da ni. Mu ci abinci tare as a family, a zauna a yi hira ayi raya. Infact ina so Yaran nan su ɗauke ki a matsayin uwa ba Anty ba" "Daga baya kenan" Zaytoonah ta faɗa a ran ta. "Idan kina zaman ɗaki haka ba za su saba da ke ba. Na yadda yaran suna da sakalci saboda hannun da na riƙe su da shi tun bayan rasuwan mahaifiyar su amma duk da haka idan kin ga sun yi ba daidai ba ki kwaɓe su sannan ki ja su a jiki saboda yanzu sun zama na ki. Ina neman alfarma ɗaya a wajen ki" Ta ɗan kalleshi sannan ta sauke idon ta "Ko da once in a while ne a dinga sammani girki, saboda matar tawa gwana ce wajen sarrafa abinci Masha Allah" Ko ya aka yi maganar yai tasiri a ranta har ta yi murmushi oho. Ya miƙe tsaye ya ce " barin wuce masallaci kar na rasa jam'i" Daga lokacin kuma Zaytoonah ta koma riƙe gidan ta. Tuni ta dakatar da Atika wajen yiwa Justice girki ta ce za ta dinga yi ma sa ita ta dinga yin na sauran ma su aikin gidan. Kusan kullum sai Raziya ta yi ƙorafi a kan girkin Zaytoonah. Ba ta wani tanka ma ta dan ɓata lokaci kawai za ta yi. Sauran yaran na ci babu complain amma ita kullum bakin ta ba ya shiru, idan ta yi magana Justice ba zai ma ta faɗa ba sai dai kawai ya ce ta je ta karɓi abinci a wajen Atika. Daga baya ma sai ya koma Raziya abincin Atika ta ke ci dan dole, ta so Justice ya dakatar da Zaytoonah ta dena girki amma bai yi hakan ba. A sati na biyu da zuwan ta gidan ne Maman Tope ta karɓi aiki. Matar tana da sauƙin kai sosai. Professional Chef ce da ta yi aiki a manyan manyan hotels na Abuja, lokacin da mijin ta ya rasu ya barta da yara biyar komai ya zo ya dagule ma ta. Abubuwa su ka ma ta yawa har ta kai ma ta rasa aikin ta. Aikin da ta zo ta samu daga baya albashin bai ma ta ba ga kuma aikin yana cinye ma ta lokaci. A lokacin da Justice ya dawo Abuja da aiki yana neman mai abinci saboda cook ɗin da aka bashi daga office namiji ne shi kuma baya son namiji saboda yaran sa, shine Hajiya Ghazala ta nemo ma sa Maman Tope. Da farko ita ta nemo ma sa Atika amma ya complain ɗin gaskiya bai gane da aikin ta ba, ya so ma ya sallameta ne sai Hajia Ghazalan ta ce ma sa ai Atikan na buƙatan aikin saboda kula da 'ya'yan ta. Da tana aiki ne a gidan wani Alhaji to sai ya zo ya rasu aka sallami ma su aikin gidan gaba ɗaya. Jin wannan bayani ya sa ya haƙura ya barta. Zuwan Maman Tope gidan ne ta koyawa Atika wasu girke- girken zamani da na gargajiya musamman abincin mutanen Kudu. Da ke ita ta koyi girki ne professionally har da certificate kuma aikin abincin hotel da ta yi na kusan shekaru shabakwai ya sa tanada experience ɗin girki sosai. Maman Tope a Gwagwalada ta ke zaune da yaran ta. Idan ta zo ta yi 15 days a gidan Justice sai ta koma chan ta huta na 15days inda ta ke ɗan taɓa ƙananun sana'a dan tana ƙoƙarin buɗe ƙaramin restaurant ɗin ta ne nan da shekara mai zuwa, idan kuɗin sun taru. Atika kuwa a Mararraba ta ke... *** "Ahmad idon ka kenan?" Zaytoonah ta faɗa tana karɓan jakar Justice da ke hannun Ahmad ɗin. "Anty Zaytoonah ai na zo hidimar biki ba mu haɗu ba ne saboda jama'a sun yi yawa" Hararan sa ta yi tana faɗin "Anty kuma?" ta bi bayan Justice da tuni ya haura stairs ɗin. Shi kuwa Ahmad sai ya kama dariya. "Sannu da dawowa" ta faɗa yayinda ta ke ajiye ma sa jakar a saman kujerar da ya ke zama yayi aiki. Ɗakin ba baƙon ta bane dan kullum tana shiga ta gyara ma sa. "Mun same ku lafiya" Lafiya ta amsa a taƙaice yayinda ta sunkuyar da kan ta ƙasa ganin yana ɓalle button ɗin shirt ɗin sa. "Za ku ci abinci yanzu ne ko sai kun yi sallah?" "Ki tambayi Ahmad ko zai ci yanzu amma ni kam sai na yi sallah" Ta amsa da toh ta fita daga ɗakin. Komawa wajen Ahmad ta yi ta zauna yana zuba ma ta taɗi yana ba ta labarin wani case mai sarƙaƙiya da Justice ya haɗa shi da shi. "Anty Zaytoonah wai yaushe za ki dawo office ne?, mun yi kewar ki fa" "Rufa min asiri Ahmad ko zan yi aiki ba yanzu ba. Ka san tashin hankalin da na shiga a case ɗin Chief Udodiri" "Habawa! Ke da ki ke da Justice a kusa wani tsoro za ki ji" Dai dai nan su ka ji saukowar Justice ɗin dan haka kowa yai gum da bakin sa. Lokacin da ya sauko ya ce za su wuce masallaci Ahmad ya miƙe yana faɗin sai mun dawo Anty. Al'adar Justice ne idan ya fita sallar magariba a masallacin ya ke zama yai ta azkar har sai anyi Isha kafin ya dawo gida. Indai ya dawo kafin nan to akwai dalili mai girma. Bayan sun dawo daga sallar ne aka haɗu a dinning ana cin abinci. Ahmad sai santin girkin ya ke yi. Raziya haushi har wuya, ba abin da ta tsana irin ta buɗe ido ta ga Zaytoonah a gidan su. Ga uwa uba ƙannenta da duk faɗan da ta ke yi mu su akan Zaytoonan sun ƙi sauraranta. Ita dai Falaq ba ta wani shiga harkan Zaytoonah saboda dama haka halittar ta ya ke ba ta cika sake jiki da mutane ba amma Suhailah kam cikin ƙanƙanin lokaci ta sake da Zaytoonah, har ɗakin ta tana shiga ta ce za ta yi kallo ko kuma ta ce Zaytoonan ta ma ta wanka. "Uncle na ce za ka bar Anty ta dawo office ko?" Ahmad ya faɗi maganar hankali kwance. "Insha Allah" ya faɗa tareda cigaba da cin abinci. Zaytoonah ta kalli Ahmad tana jijjiga kai alamar za ka gamu da ni. Ahmad bai bar gidan na su ba sai kusan ƙarfe goma saura. Da ake akwai surutu kafin ka ce me lokaci ya ja, sai da Justice ya ce zai je ya kwanta ne ma ya iya yin shiru yana faɗin shima bari ya wuce gida kar dare yai sosai... Washegari kuma Muhsina ta kira ta akan za ta kawo ma ta ziyara. Zaytoonah ta ji daɗin hakan dan tun a gidan rasuwa rabon ta da Muhsinar. Ƙarfe shabiyu saura na rana su ka iso gidan ita da Azma. Tuni dama Zaytoonah ta mu su girki. Sai da aka ɗan taɓa hira kafin ta kawo mu su abinci, su ka haɗu dukkan su a tsakiyar falo suna ci. Muhsinar ce ta ce ta kawo mu su abincin nan dan yanzu ba ta iya cin abinci a dinning. Zaytoonah ta fara tsokanar ta akan ko dai ciki gareta. "Za ki sani ai. Kema na ki na nan tafe ƙila naki abinci sai idan Galadima ya ba ki a baki za ki iya ci" Zaytoonah ta kai ma ta dundu yayinda Azma ke ta dariyan su. "Yo ƙarya na yi ne? Waya sani ko yanzu ma junior yarima na jina" "Za ki yi ki bari ai, kin gannin nan ni kaɗai na ke wasu fa?. Ashe dai zuwan Abban su Habib saƙo mai mahimmanci ya zo turawa" Zaytoonah ta yi maganar tana dariya ita da Azma ita kuma Muhsinar na faɗin " oho dai tunda saƙon ya je inda ya kamata"... Haka dai su ka sha hiran su, a ƙalla sun kai awa uku a gidan kafin su ka fara shirin tafiya, da za su tafi Zaytoonah ta mu su jagora zuwa ɗakin ta. Sun yaba ɗakin na ta saboda komai na zamani ne aka saka a wajen. "Ya 'yan matan na ki?, fatan ba wata matsala?" Muhsinah ta faɗa lokacin da su ke saukowa. "Babbar na bani ciwon kai wallahi, ina ga randa ta kai ni maƙura duka zan ma ta" "Haba Zaytoonah, ai gara ki haɗata da uban ta, idan ki ka fara dukan yaran nan yanzu kowa kallon muguwa zai dinga yi miki. Yaran yanzu ai sai a hankali, na ka ma ya ka ƙare da su balle na wani" "Abin na ta ne ya fara isa na Allah" "Ki bita a hankali sai kiga nan gaba kaɗan kun zo kun saba" "Allah ya sa haka"... *** Yau Asabat yaran na gida sun dawo daga Islamiyyar safe kenan sun baje a falo suna kallo ko uniform ba su cire ba. Maman Tope ke da aiki amma ta nemi uzuri saboda an kwantar da wata 'yarta a Asibiti. Shiyasa aikin yai wa Zaytoonah yawa dan girkin da za ta yi har da ma su aikin gidan gaba ɗaya. Baccin safe da ta yi ne ma ba ta farka da wuri ba, dan da ta tashi sai gani ta yi ƙarfe shabiyu har da minti tara. Tana kitchen ɗin yaran su ka dawo, duk cikin su Suhailah ce ta shigo ta ma ta oyoyo kafin ta wuce wajen yayyen ta da tuni su ka kunna TV suna kallon wani favourite show ɗin su. Tana gama soya nama ta kashe gas ɗin ta bar kitchen ɗin da sauri. Tun da ta tashi a bacci kitchen ta wuco saboda sauri to kuma yanzu wani fitsari ke cinta dole ta ajiye girkin ta kashe gas ɗin ta tafi ɗaki. Da ta je fitsarin ma sai da ta tsaya ta gyara jikin ta sosai saboda dama tana tareda baƙo. Ta fito daga banɗaki kenan ta ji ihun Suhailah a ƙasa, ba shiri ta fito a guje. A kitchen ta samu yaran suna tsaye wajen Suhailah da ke zunduma ihu saboda man da ya tsartu ma ta a jiki. Zaytoonah ta yi kan ta da sauri tana tambayar miya faru amma babu wanda ya kulata saboda Suhailan kuka kawai take yi. Ta san dai idan mai ya tsartu wa mutum tun lokacin suna yara Mommy na amfani da gishiri ko kamu ta mutsutstsuka wajen, idan kuma akwai Zuma sai ta shafa mu su. Da sauri ta buɗe roban gishiri ta ɗebo ta fara shafawa Suhailah a wuya da hannun ta. Raziya na cewa ta barta a kai ta Asibiti. Sai da ta gama shafa ma ta ta ɗauki Suhailah a kafaɗa su ka fito a kitchen ɗin dai dai nan kuma Justice ya shigo gidan. "Miya faru?" Ya faɗa yana karɓan Suhailah a hannun Zaytoonan. Yarinya kuma ganin Daddyn ta kawai sai ta ƙara sautin kuka. Raziya ce ta yi saurin faɗin " Yunwa ta ke ji shine ta shiga kitchen wajen Anty ita kuma ba ta kitchen ɗin kuma ta bar Mai mai zafi a wajen sai ya zubowa Suhailah a jiki" "Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun" kawai ya faɗa yai hanyar waje bayan ya yiwa Zaytoonah wani kallo. Bayan fitar su da ƙyar Zaytoonah ta iya saita kan ta ta shiga kitchen ta goge wajen da man ya zuba ta ƙarisa girkin a gurguje. Bayan ta gama girkin zama ta yi a falo ta yi tagumi tana jiran dawowar su. Ta sani naman da ta soya ta ke son zubawa a miya yarinyar ta je ɗauka ta ga ƙaramar kujera a wajen alamar shi ta hau saboda tsayin ta ya kai wajen. By mistake ne ƙila hannunta ya bugi frying pan da ke gefen bowl ɗin da ta zuba naman shine Man ya tsirtu ma ta sauran kuma ya malale a ƙasa. Kusan awa biyu da fitar su sai gashi sun dawo abin mamaki har da Hajia Ghazala dan ita ce ma ke riƙe da Suhailan wacce ke riƙe da ice cream tana sha hankali kwance an shafa ma ta magani a wajen da man ya zuba raɗaɗin da ta ke ji ya ragu. Ko kallon Zaytoonah bai yi ba ya wuce sama. Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafin ta bi bayan sa ba tareda ta yiwa Hajia Ghazala magana ba. Kai tsaye ɗakin sa ta shiga dan ba ta gan shi a falon sa ba. "Daddyn Raziya ka yi haƙuri, wallahi ban san za ta shiga kitchen ɗin ba i just..." "Ƙarfe nawa Zaytoon ba a gama abincin rana ba?. Idan ke ba za ki iya girkin ba ina Atika? ina Silifat?. Aikin mi su ke yi da ba za su yiwa yara abinci ba" "Ka yi haƙuri ranka shi daɗe. Maman Tope ta nemi uzuri kuma ni ne na ce kar Atika ta zo saboda..." "Kar a sake barin Yaran nan da yunwa" ya katse ta. Haɗiye sauran bayanin da ta yi niyyan yi ta yi tareda faɗin " Insha Allahu hakan ba zai kuma faruwa ba" Fita ta yi daga ɗakin jikin ta a sanyaye. Ba za ta ba shi laifi ba dan ta san kowanni Uba 'ya'yan sa ke zuwa farko sama da kowa amma at least ya kamata ya ba ta damar kare kan ta, watan ta ɗaya kenan a gidan kuma yau ne na farko da aka samu akasi irin wannan dan miyasa ba zai ma ta uzuri ba? Dan miyasa zai ba ta laifi ba tareda ya saurareta ba... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 53 Bismillahir Rahmanir Rahim *Raziya* "Yaran nan dai kin san marayu ne. Tsakani da Allah Zainan ki ke ko Zaytoonah ya za ki mu su horo da yunwa?. Yunwa fa! " Idan ki ka muzguna mu su ma dai kin san makomar ki a wajen Allah wuta ne. "Gaba da baya yaran nan 'yan gata ne ya kamata ki san wannan, dududu yaushe ki ka zo gidan nan amma har kin fara carelessness akan yara ƙanana kamar ba ki san zafin haihuwa ba" Duk maganar da Hajia Ghazala ta ke yi Zaytoonah ba ta tanka ma ta ba, amma furucin ƙarshe ya sosa ma ta rai. "Ba na tunanin kina da hurumin shigo min ɗaki ba tareda izini ba. Tunda ban gayyace ki ba ki ɗau zawarawan ƙafafuwanki ki bar min ɗaki kafin na yi abinda ranki zai ɓaci" "Ba laifin ki ba ne ai, laifin wanda ya ajiye ki a gidan ne. Amma ki sani duk lokacin da kika walaƙanta min 'ya'ya jikin ki ne zai gaya miki" "Out!" Ta faɗa tana nuna ma ta ƙofa. Hajia Ghala ta buɗe baki za ta yi magana sai kuma ta fasa ta ja dogon tsaki ta bar ɗakin. Sai da Hajia Ghazala ta fita daga ɗaki hawayen da ta ke tarewa su ka zubo. Ba ta san zafin haihuwa ba? Ai ko ba ta taɓa haihuwa ba ba za a gaya ma ta wannan maganar banzan ba, balle kuma ta haihu, ta san wahalan ɗaukan ciki, haihuwa da reno. Sai da ta share hawayen ta sannan ta ɗau waya ta kira Mommy suna gaisawa ta ce Dan Allah Mommy ta sa Salman ya kawo ma ta yaran gobe. "Zaytoonah Lafiya dai ko" "Lafiya Mommy kawai na missing ɗin su ne, dan Allah ki sa Salman ya kawo su ko kwana biyu ne su min" Ta so ta yi jayayya amma yanayin da Zaytoonan ta yi magana ya karya ma ta zuciya. Al'amarin uwa da ɗa sai a hankali. Ita kan ta ma kewar Zaytoonan ta ke yi duk da kuwa kullum sai sun yi waya. "Shi kenan gobe Salman zai kawo mi ki su" "Na gode Mommy" "Adaeze sai dai ki cigaba da haƙuri fa. Sha'anin aure sai ka yi haƙuri sosai da kuma addu'a kafin ka samu nasara. Ki dage da addu'a dan Allah kuma ki rage saurin fushi kin ji" "Yes Mommy"... Hajiya Ghazala na barin ɗakin Zaytoonah falon Justice ta shiga luckily kuma ta same shi yana zaune yana shan kankana. "Sannu da aiki" "Abu Razz ni da 'ya'ya na kuma sai ka min godiya" "Ki kira Atika ta zo aiki kafin Silifan ta dawo" "Na riga na kira ta ma tana hanya yanzu haka" "Na gode" ya faɗa yana maida hankalin sa ga TV da ke falon. Shiru ya ɗan ratsa madaidaicin falon na sa na lokaci kaɗan kafin Hajia Ghazala ta fara magana " na ce Ranka shi daɗe sai dai ka ƙara haƙuri fa, ka san Antyn na su akwai shiririta, akwai yarinta a tattare da ita. Na ma mata magana kuma ta gane kuskurenta gaskiya, ta ce na ƙara ba ka haƙuri dan ta ga ranka ya ɓaci sosai" "Jazakillahu khairan" "Amin" ta faɗa tana faɗaɗa murmushin ta. Sai da ta ɗan zauna na wasu mintuna kafin ta bar falon fiskarta wasai dan ta samu abinda ta ke so. Ba ta bar gidan ba sai da Atika ta iso. Lokacin ma ta gama girka abincin dare wa yaran. Tana isa gidan ta ko hutawa ba ta yi ba ta kira Hajia Abu ta labarta ma ta ƙarya da gaskiya na abinda ya faru. Tuni Hajia Abu ta hau faɗa kamar Ghazalar ce Zaytoonah sai da ta gama faɗan ta ce tabbas za ta ɗau mataki akan Zaytoonah. Hajia Ghazala ta haɗa da cewa " Wallahi Hajia Galadima bai yi dacen mata ba kwata-kwata idan ba ayi da gaske ba yaran nan ba ƙaramin wahala za su sha ba a wajen ta, tunfa ba a je ko'ina ba kenan. Shi kuma kin san Galadima sanyin shi yayi yawa ba komai ya ke iya magana akai ba" Hajia Abu ta cika ta yi fam tana faɗin koma mi Zaytoonah ta zo da shi za ta taka ma ta birki... Zaytoonah tunda ta gama waya da Mommy ta tashi ta sawa ƙofarta key. Da Hajiya Ghazalar da Justice da ma yaran duk haushin su ta ke ji. Ba ta sake fitowa ba har sai washegari ko abinci ba ta ci ba. Washegari sai kusan ƙarfe goma ta fito ta nemi abin karyawa. Bayan ta cika cikin ta tukunna ta koma sama ta shiga ɗakin Justice ta gyara ma sa. Da ke akwai ƙaramin lambu a ta bayan gidan duk weekend da safe Justice a nan ya ke zama ya yiwa flowers bayi ya gyara wajen. Da ta gama ta koma ɗaki ta kira Salman a waya wanda ya ce ma ta suna hanya zuwa ƙarfe shabiyu za su iya isowa. A ranta ta yi alƙawarin ba za ta kuma karambani yiwa kowa girki ba har kuwa da shi mai gidan. Ai kafin zuwanta abincin su Atika ya ke ci dan haka ya cigaba. Tunda ya nuna baya so ta dinga barin ma sa yara a yunwa gara ta tsame hannun ta daga lamarin girkin gidan tunda dai ita ba ta kai a ma ta uzuri ba. Ta zo saukowa ta hango Justice yana shigowa dan haka ta fasa ta koma ɗakin ta. She just cant stand him bayan abinda ya ma ta jiya. Justice na shiga ɗaki sai ga kiran Hajia Abu. Bai ɗau wayar ba sai da ya shiga banɗaki yai wanka ya fito tukunna kafin ya kira ta. Sai da su ka gaisa kafin ta gabatar ma sa da buƙatar ta wanda ya sa shi zama daɓas akan gado. "Amma Hajia yaushe na yi aure da za a fara maganar wani auren" "Yanzu Galadima sai mu zubawa yarinyar nan ido har sai ta illata yaran nan. Ina sane da duk abinda ya faru jiya kuma ba zan lamunta da irin wannan ba. Kuka fa sosai Raziya ke yi jiya da ta kirani tana roƙona akan na ma ka magana ka chanja wa Antyn su gida ta takura mu su. Ka san mi hakan ya ke nufi?" "Zan yiwa Raziya magana kar ki damu Insha Allahu nan da lokaci kaɗan za su fahimci juna" "A taƙaice dai kana so ka sanar da ni ban isa ba kenan?"... *** Sai da Zaytoonah ta ji ficewar Justice a gidan kafin nan ta fito ta nufi kitchen. Girki ta shiga yiwa yaran ta da za su zo, tana cikin yi Atika itama ta shigo ta hau na ta girkin duk cikin su ba wanda ya tankawa kowa idan ka cire gaisuwar dole da Atikar ta yiwa Zaytoonah. Tana zaune a falo tana jiran isowar su dan Salman ya ce sun shigo Abuja. Kusan minti sha uku sai ga su sun iso. Da gudu su ka zo suka rungume Zaytoonah suna murna. "Mom gidan ki na da kyau" Hadid yai maganar yana ƙarewa falon kallo. "Mom wai Uncle Salman ya ce kwana ɗaya za mu yi, ina tareda ke zamu dinga zama ko?" Hashir yai maganan yana taɓa kafaɗarta. "Yanzu dai bari ku ci abinci ku huta sai na amsa mu ku duk tambayoyin ku. Kun ji" Su ka gyaɗa ma ta kai. "Galadima yana gida?" Salman ya tambaya "Baya nan" ta amsa ma sa. Lokacin da ta serving ɗin su abinci ita da hannunta ta ke ciyar da yaran, idan ta bawa wannan sai ta bawa wannan. "Mommy ta gaya miki matar Chief Udodiri ta fara processing ɗaukaka ƙara a supreme court?" "Ina ga ta manta ne" "Ai Insha Allahu ko anje chan ɗin ma hukuncin kisa ne zai tabbata a kan sa" "Sosai ma kuwa" Sallamar Justice ya katse mu su hiran ta su. Yayinda yaran su ka tashi daga gaban Zaytoonah da gudu su ka nufi wajen Justice suna kiran "Daddy" Duk da ɓacin rai da ya ke tattare da shi amma ganin yaran ya sa shi jin wani sanyi a ran sa. Bayan sun gaisa da Salman ne Zaytoonah ta ce " sannu da zuwa" saboda ganin idon Salman. Ya amsa ma ta ransa a sake kamar ba komai a tsakanin su. Abinka da yara tuni su ka buge wai dole Justice sai ya zauna ya cigaba da ba su abinci a baki. Zaytoonah ta daka mu su tsawa amma Justice ya ce ta ƙyale ma sa 'ya'yan sa. Haka ya zauna a wajen ya ƙarisa ciyar da su da hannun sa yayinda su ke taɗi sama-sama da Salman. Ita kan Zaytoonah sai bar mu su wajen ta yi. Zuwa yamma Salman ya bar gidan dan ya ce ba a nan zai kwana ba duk da kuwa Zaytoonan ta so ya kwana a nan gidan. Suhailah na dawowa daga Islamiyya da ta ga 'yan biyu tuni ta kama tsalle, ta biyewa yaran aka cigaba da wasa da ƙiriniya kamar ba ita ne ta samu ƙuna jiya ba, dama ƙunar ma ba yawa. Da dare dai abincin ta Justice ya ci dan tare da 'yan biyu su ka zauna su ka ci. Yaran da ta sa aka kawo ma ta dan su ɗebe ma ta kewa sai gashi sun tare a wajen Justice su na tsiyar su sun ma manta da ita. Ƙarfe tara ta shiga falon Justice dan ta koro yaran su zo su yi bacci amma yaran su ka tuɓure wai a wajen Daddyn su za su kwana. Ba halin ta mu su jan ido dan Justice na wajen, dole dai sai komawa ta yi ta je ta ɗauko mu su kayan baccin su ta kawo. Ta fara cirewa Hashir riga yayinda Justice ya cirewa Hadid na shi, su ka sa mu su rigan bacci wanda pyjamas ne mai zane zanen cartoon a jiki, na Hadid sky Blue na Hashir Ash colour. "Kar ku manta ku yi azkar kafin ku kwanta kun ji?" " Yes Mom". Kusan bayan tafiyar Zaytoonah da kusan minti Ishirin yaran su ka yi bacci. Haka ya ɗauke su ɗaya bayan ɗaya ya kai su ɗakin sa ya kwantar da su akan gado ya tofa mu su addu'a kafin ya fito falo, kashe kayan kallo yai ya fita ya je ɗakin yaran sa dan ya duba su. Yana fitowa ya haɗu da Zaytoonah wanda itama ta fito daga na ta ɗakin. "Ba ki yi bacci ba?" "Yanzu zan yi. Dama zan gaya ma ka ƙarfe shabiyu zan zo na tashi yaran dan su yi fitsari, idan ba haka ba gadonka zai malale da fitsari" "Zan tashe su" "Na gode" ta furta tareda juyawa za ta tafi. "Ina son magana da ke" Zuciyar ta ya wani buga damm. Bin bayan sa ta yi su ka wuce falon sa. Yana zama itama ta ɗan ɗokanu a kujera opposite da shi. "Wannan duk haɗe fiskar saboda ni ne ko?" Ta yi saurin girgiza ma sa kai "Idan ba haka ba to a min murmushi na gani" "Hmmm" kawai ta iya faɗa. Sai da ya ɗan ɗau lokaci kafin ya ce "Da fatan za a min haƙuri saboda tsawan da na miki jiya" "Duk wani fushi da ake da ni ayi haƙuri" "Ni ba fushi na ke ba" Shi ba yaro ba ne, 'yan biyu daya gani a gidan ya tabbatar ma sa ta ɗau abinda ya faru da zafi. Murmushi yai ya ce "kin tabbata Amarsu ta Angonta" Sai gashi ga Zaytoonah ta buge da dariya. Mamakin Justice ta ke yi, wani lokaci idan ya yanko magana kaman ba shi ba.... *** Tunda ta zo gidan yau ne ta fita. Muhsina ce ta kirata akan ta kasa cin abincin gidan ta komai aka dafa wari ya ke ma ta. Kusan ma sati kenan sai dai a karɓo ma ta abinci daga restaurant ta ci to shine yau ta kira akan dan Allah ta ma ta irin miyan Agusin Mommy ta kawo ma ta. Kiran Justice ta yi ta ce ma sa za ta je ta dubo Muhsina ba lafiya ya ce ma ta ta je ba matsala amma ta dawo da wuri, ya ce ta sa Dreban su Raziya ya kaita gidan. Bayan ta gama miyar ta haɗa ma ta da tuwon semo ta jera komai cikin kwando ta fito da shi. Kamar yadda ya ce kar ta daɗe ba ta wani jima ba. Ta dai sa ma ta sauran miyan a fridge saboda miyan dayawa idan ba ta ma sa cin haɗama ba zai kai ma ta sati... "A'a miyake faruwa?" Zaytoonah ta faɗa tana taɓe baki. Ɗakinta da ta bari a kimtse shine ta zo ta gan shi kaca-kaca. To ko da ma ace 'yan biyun ta na gidan da wuya ta zarge su kan aikata irin wannan taɓargazan dan ba halin su ba ne. Tabbas wannan anyi ne da gangan kuma wanda yai yayi ne da gayya. Yaro ma ba zai yi wannan ba dan kayanta na saman closet ɗin duk an watso ma ta da su waje. Koma waye ne ba za ta yi magana ba dan abinda ake so ta yi kenan. Haka ta shiga gyara ɗakin na ta. Abin takaici kusan fiye da rabin kayanta da ke goge duk yanzu sai an sake goge su. Akwai matar maigadin gidan Bahijje da ke shigowa tana yin aikin wanki da gugan kayan yaran da ma gyaran gidan amma tunda Zaytoonah ta zo da kan ta ta ke kai kayanta wajen washing machine ta wanke su sannan ta goge. Kusan ita da ta yi booking da ta zo gida bacci za ta yi, sai da ta shafe fiye da awa ɗaya tana gyaran ɗaki ƙarshe ma ba halin baccin dan la'asar ta yi. Kaman da wasa bayan kusan kwana huɗu da Zaytoonah ta dawo daga gidan maƙotan su da aka yiwa rasuwa wanda Justice ya ce ta shiga ta mu su ta'aziya. Shigowan da za ta yi ɗaki ta sake ganin an birkita ma ta ɗaki. Yanzu kam ta tabbatar Raziya ce da wannan banzan halin. Zaginta da ta ke yi a fakaice ba ta tankawa yanzu kuma abin ya kai ga haka. Sai da ta gyara ɗakin sannan ta fito ta nufi ɗakin yaran. Raziya na zaune gaban computer tana latsawa da alama dai assignment ta ke yi yayinda Suhailah ke bacci. Ba ta ga Falaq ba ƙila tana falo ko ma waje. "Raziya na zo ne na faɗa miki cewa ya isa haka. Kin yi na farko kin yi na biyu to Wallahi kar a kuma maimaita na uku dan jikin ki ne zai gaya miki" "To ni mi na yi? Idan ba mugunta ba mi na miki?" "Ki kiyayi shiga hurumina Raziya dan Wallahi ba za ki ji da daɗi ba. Tam" Daga haka ta fita daga ɗakin. Yadda zuciyarta ke tafasa ma kamar ta kama Raziyan da duka ta ke ji. Ta so gayawa Justice abinda Raziyan ke ma ta amma lokacin da ya shigo da dare sai ta lura kaman ran sa a ɓace ya ke dan ta ma sa maganar abinci ma ya ce ma ta ya ƙoshi. Washegari kuwa Asabat bayan ta gama girkin safe ta shiga aikin cupcake ranan sun yi baƙi ba ta da komai na lasawa a baki idan ka cire dambun Kaza da ta ke yi duk sati saboda duk Jummu'a ana yanka Kaji a gidan kuma ranan ta yi Dambu da shi sai Justice ya ce ma ta ya ji daɗin dambun ta dinga yi yana so. Sai da ta gama komai ta saka a cikin oven sannan ta haura sama dan ta san kafin ta je ta yi abinda za ta yi ta fito timer ɗin da ta sa ba zai cika ba. Red handed ta kama Raziya na ɓata ma ta ɗaki. Abin takaici har da ɗebo ruwa ta kwarara a kan carpet ɗin ɗakin. Zaytoonah ta haɗa hannu a ƙirji ta ce "yawwa! yayi kyau haka, kin kyauta sosai. Kinga yadda ki ka ɓata mun ɗaki to haka na ke so ki gyara komai yadda ki ka same shi" "Ba abinda zan gyara" ta faɗa da tsiwa tareda ture empty bucket ɗin da ta gama juye ruwan a tsakiyan ɗakin. Ta tako za ta wuce Zaytoonah ta jawota baya ta ce " na miki kama da wanda ke wasa da ke? Oya maza ki fara gyarawa kafin jikin ki ya gaya miki a gidan nan. Yau ko uban ki bai isa ya hana ki gyara ɗakin nan ba" Ba da wasa ta yi maganan ba dan yadda ta ke zare ido kaɗai ya tsoratar da ita. Ta sani ko dukan ta Zaytoonan ta yi ba me ƙwacen ta dan Justice ya tafi Zaria yau da safe. "Oya fara!" Haka ta shiga tattare kayan tana naɗewa wanda su ka jiƙa kuma tana ajiyewa gefe. Zaytoonah ta ɗauko ɗaya daga cikin belt ɗin ta ta naɗe a hannu ta jawo stool ta zauna tana kallon Raziya da ke yin aiki tana hawaye. Ashe ɓatawa da daɗi amma gyara da wahala. Bayan ta gama naɗe kayan ta ce ta dinga jera ma ta su yadda ta same su. Sai ta ɗauko za ta saka wannan ta ce ma ta ba anan ya ke ba. Kusan sun shafe minti talatin wajen jera kayan. Tun Raziya na yin kuka a hankali har ta koma tana yi da ƙarfi amma ko gizau Zaytoonah ba ta ji a ranta ba. Ta dai riƙe belt ɗin ne amma ba dukan ta za ta yi da shi ba duk barazana ce. Abinda ta sani shine yau dai sai ta koyawa yarinyar nan hankali nan gaba ɗakinta ma ba za ta shiga ba balle ta taɓa ma ta kaya. Ba ta damu da cupcake ɗin ta da ke oven ba dan ta san timer ɗin na cika zai kashe kan sa. "Kin ga waɗannan jiƙaƙƙun kayan mu je ki shanya su tukunna kafin ki zo ki naɗe carpet ɗin nan ki goge ruwan da ke ƙasan" Ba sabawa ta yi da aiki ba dan wannan da ta yi gaba ɗaya ta gaji. Jin maganan Zaytoonah ya sa ta zaro rinannun idanun ta. "Ki zaro idon da kyau, aiki ne sai kin yi dan ni ba baiwar ki ba ce da zaki ɓata min ɗaki na gyara" Fashewa ta yi da kuka wiwi a ganin ta Zaytoonan za ta ɗaga ma ta ƙafa. "Ki gama kukan ki cigaba da aiki ba" Kukan ta ne Atika ta jiyo ta shigo ɗakin da sauri dan ganin mi ya ke faruwa. Ganin Zaytoonah riƙe da Belt ya sa ta concluding ai kawai dukan Raziyan ta yi "Haba Hajiya. Yanzu 'yar marainiyar Allah ki ke duka, Haba Hajiya" "Fita min a ɗaki!" Zaytoonah ta daka ma ta tsawa. Ba shiri ta fita da sauri har buge ƙafa ta yi saboda gulma da ke cin ta. Tana zuwa ɗakin ta ta ɗau waya ta kira Hajia Ghazala ta shiga labarta ma ta gaskiya da ƙarya. Hajia Ghazala jiki na mazari ta ce ga ta nan zuwa. Amma kafin ta zo sai da ta kira Hajia Abu tana kukan ƙarya tana faɗa ma ta abinda Atika ta gaya ma ta harda itama na ta ƙarin gishirin. "Yanzu haka ina hanya kenan zan je gidan, koma minene yau za ayita ta ƙare" Galadima sai yanzu ya samu ganawa da mai martaba a falon sa da ba kowa ke da ikon shiga ba. Suna cikin tattaunawa sai ga kiran Hajia Abu. Bai ɗauka ba sai ya rage volume ɗin kiran. Mai martaba ya ce ba matsala ya ɗau kiran kawai. "Abba, Hajia Abu ce zan kira daga baya" "Zainabu Abu ikon Allah. Da Allah yayo min ita a namiji da ba ƙaramin ƙasaita za ta buga ba" Galadima yai murmushi dan shima ya san halin Yar ta sa. "Ta same ni akan maganar ka da Ghazala yana ɗaya daga cikin abinda ya sa na ce ina son ganin ka" Galadima ya ɗan sha jinin jikin sa yana sauraron Mai Martaba... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 51 Bismillahir Rahmanir Rahim *The fat bride* "Shiga da Bismillah Gimbiya" abinda Hajia Ni'ima ta faɗa kenan da ke riƙe da hannun Zaytoonah sai kuma Ummi da ita ma ke riƙe da hannun ta na hagu sashen Hajja aka fara kawota tunda ita ce Uwargida. Already she's feeling suffocated da wannan shegen Alkyabba da aka kakaɓa ma ta, wata marar hankalin kuma ta zo ta ƙara buɗe ta da turare daga shigar su falon Hajja. Sai da su ka kaita gaban Hajja kafin su ka ɗaga ma ta hulan Alkyabbar wanda da ya rufe fiye da rabin fiskarta. Sai guɗa ake yi ana bugawa Amarya kirari. Addu'a Hajja ta yi tareda yiwa Amarya kyauta. Daga nan kuma aka wuce da Zaytoonah ɗakin sauran matan Sarkin. Bayan an gama gaishe-gaishe sannan aka maida Amarya sashen Hajja saboda a nan za ta kwana sai washegari a kaita gidan ta. Duk da ba sa shiri da Zaytoonah ba a barta a baya ba wajen kawo Amarya ba. Ummi ce ta ma ta faɗa lokacin da ta zo sai dai deep down itama na son shiga 'yan kawo Amarya saboda ba ta taɓa shiga Fada ba. Su huɗu su ka kwana a ɗakin da aka bawa Amarya. Zaytoonah, Ummi, Humairah da kuma Goggo Mariya. Bayan sun shiga ɗakin ma sai da aka yi ta shigowa ganin Amarya. Ba su suka kwanta ba sai kusan shabiyun dare. Da ƙyar Zaytoonah ta iya cire kaya ta yi wanka kafin ta yi bacci, gajiya ne a tattare da ita kamar me, ga bacci da ya cika ma ta ido. Washegari aka yi wuni a Fada wanda Zaytoonah ta sha kyaututtuka daga ahalin mai martaba. Wasu sun yi tsakani da Allah wasu kuwa ganin ido ya sa su ka yi kar a ce wace ta yi ita ba ta yi ba. Tsakanin safe da yamma sai da Zaytoonah ta chanja kaya kala shida. Anyi hotuna kuwa kamar ba gobe. Bayan sallar magariba aka wuce da Amarya Zaytoonah gidan Angonta da ke nan Zaria ɗin. Already su Hajia Ni'ima na gidan suna jiran zuwan Amarya, ita ta jagoranci 'yan rakiya har zuwa ƙaton ɗakin Zaytoonah wanda ya sha gyara da tsadaddun kayan ɗaki na zamani. Sai da aka ci aka sha kafin aka fara watsewa a hankali - a hankali har ya saura 'yan tsiraru. Zuwa ƙarfe goma gidan yai tsit, daga Zaytoonah sai ko ma su aiki da ke gidan. Jin shirun yayi yawa ya sa Zaytoonah ta ɗau waya ta kira Mommy. Maimakon Mommy sai muryan Junior ta ji wanda ya sanar ma ta Mommy na falo. " Hashir da Hadid sun yi bacci ne?" Ya amsa ma ta da eh tareda cewa ai da kuka su ka yi bacci dan sun ce za su je su wajen Daddy Uncle Salman ya mu su faɗa. Ta yi murmushi dan ta san ba dan shi ɗin ba da yanzu suna nan suna yiwa Mommy kukan sakarci. "Kai mata wayar" ta bashi umurni. Cikin baƙin da za su kwana a nan ne ake ta hira da ban gajiyan biki. Mommy ta amshi wayar tareda miƙewa ta wuce ɗaki. "Amarya hope lafiya?" "Kai Mommy daga kira" "Ba dole ba" Zaytoonah ta yi dariya tana faɗin "Mommy na missing ɗin ki sosai" "Tun yanzu" "Jiya fa ban gan ki ba yau ma ban gan ki ba" "Kin ga dare yayi ki bari gobe ma yi magana. Asuba tagari " daga haka ta kashe wayan dan ta san idan ta biye ta sai su jaa lokaci a haka. Cikin ran ta tana godiya wa Allah bisa ni'imar da yai ma ta. A karo na biyu ta aurar da Zaytoonah a hannu na gari wanda shine burin kowanni iyaye... Bayan ta fito daga wanka ta sanya doguwar rigan bacci ta kwanta, sai da ta ɗan duba wasu saƙon da aka tura ma ta ta email kafin ta yi addu'a ta kwanta. Ko minti biyu ba ta yi ba da rufe idon Justice ya turo ƙofa tareda sallama. Da ke ba ta bacci a cikin duhu yana buɗe ƙofar ya hango ta kwance a tsakiyar gado. Ya so ya shigo da wuri amma mutane 'yan gaisuwa suka riƙe shi. Yana shigowa gidan wanka ya fara yi sannan ya saka sabuwar jallabiyar sa ruwan ƙasa. Ya ɗan fesa turare kaɗan kafin ya fito riƙe da leda a hannun sa ya nufi ɗakin Amarya. A bakin gadon ya zauna ya ɗan taɓa kafaɗarta yana kiran sunan ta a hankali. Tana jin sa dan ba ta yi baccin ba amma ta share shi. Ya sake kiran sunan ta wannan karan da ɗan ƙarfi sai dai nan ma shirun ta yi. Ganin haka ya sa Justice ya miƙe tsaye yana faɗin "Asuba ta gari Amarya" har ga Allah ya ɗauka baccin na ta ne yai nisa fita yai daga ɗakin ya wuce na shi ɗakin. Kazar da ya siyo ya buɗe ledar ya sa ta a fridge da ke falon sa kafin ya shige ɗakin sa. Ya kalli makeken gadon sa da ke ɗakin yai murmushi, rabon da gadon ya samu baƙo shekaru biyu da wata takwas kenan. Ya kwanta kan gadon ya sa hannu ya shafa gefen sa da ke fankololo. Ya so ace ko da ba abinda zai shiga tsakanin su yau ya ji ɗumin mace a jikin sa, sai dai kamar yadda ya iya haƙuri na kusan shekaru uku to zai haƙura na yau ɗin. Shima kan sa da gajiya a tattare da shi balle ita Amaryar ta sa wacce za ta yi kwanan baƙun ta. Alarm ɗin ta na ƙarfe biyar ne ya tashe ta daga bacci, ta ɗan mirgina ta ɗau wayar ta kashe alarm ɗin saboda na biyu kenan da ya ke snoozing dan ta sa shi a snooze bayan kowanni minti biyu. Sai da ta ƙara kusan minti huɗu akan gadon kafin ta iya miƙewa ta shiga banɗaki ta yi tsarki sannan ta ɗaura alwala. Da ta idar da sallah da ƙyar ta iya ƙarisa azkar ɗin ta na safiya, ko tilawa ba ta yi ba kamar yadda ta saba ta koma kan gado ta kwanta. Ƙarfe bakwai da minti Arba'in wayarta ya fara ringing. Kamar ba za ta ɗauka ba amma ganin an kuma kira a karo na biyu ya sa ta ɗauka. Salman ne ke kira ta swiping kiran tareda faɗin "wato ɗan baccin safen ma ba za ka bar ni na yi ba" "Sorry Sis kiran ne its urgent shiyasa" "Lafiya dai ko?" "Na kira Galadima numbar sa a kashe shiyasa na kira ki" Tashi zaune ta yi tana faɗin "Salman mi ya ke faruwa? Mommy fa?" "Zaytoonah sai dai haƙuri amma mun yi babban rashi yau da Asuba" Jin maganar mutuwa ya sa bugun ƙirjin ta ya ƙaru ta ce " wa ya rasu?" "Hajiya Saudah, Kakar marigayi" "Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun. Ba ta samu lafiya ba. Ina ce ko wata bai yi ba da dawowar ta Asibiti a Egypt" "Mutuwa ai ko da jinya ko ba jinya za a yi ta Adaeze" "Hakane" ta faɗa tareda goge hawayen da ya silalo ma ta tunowa da ta yi da Zuhayr wanda a ko da yaushe ta ke jin mutuwar sa ɗanya a tattare da ita. "Ki faɗawa Galadima za a yi Jana'iza ƙarfe tara na safe" Ko amsawa ba ta yi ba ta kashe wayar saboda yadda jikin ta yai sanyi. Tana tuno haɗuwar su na ƙarshe da ita kusan kwana shida da su ka wuce da ta zo yiwa Mommy Barka har da ba da haƙuri akan ba za ta samu zuwa biki Ringim ba saboda ciwon ƙafa da ta ke fama da shi yanzu ba ta iya juran zaman mota balle tafiya nan da chan yana ba ta wahala. Ta tuno gudunmawar biki da aka yi daga gidan su Zuhayr aka kawo mu su wanda ta san Hajiyar ce ta jagoranci abin. Wasu kyaututtukan ma ba ta buɗe su ba ma saboda ba lokaci. Kowa daka gani a duniya lokacin sa zai ci. Ga shi dai Hajiya Nenne ita ce Babba kuma ta fi Hajiya Saudah tsufa amma kuma Hajiya Saudar ta riga ta barin duniya. Ta buɗe gallery ɗin wayarta ta shiga folder da ta saving da suna FOREVER YOU ta dinga scrolling hotunan Zuhayr da ke cikin folder ɗin har ta kai kan hoton da ta ke son gani. Hoto ne da Zuhayr yai da Hajiya Saudah lokacin da su ka zo Nigeria a bikin Muhsina. Ranan wata Jummu'ah ne da yai shigar manya kaya ya zo gaishe da Hajiyar ta ke ce ma sa kayan sun ma sa kyau ya dinga saka irin su. Selfie su ka yi kafin daga baya Zaytoonah ta karɓi wayan Zuhayr ɗin ta mu su hoto su biyu. Buɗe ƙofar da aka yi ne ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi. "Subhanallahi" ya faɗa yana ƙarasowa wajen ta da sauri saboda hawayen da ya gani a idon ta. "Zaytoon mi ya faru?" yai tambayar yana dafa kafaɗar ta. Ta yi saurin exiting gallery ɗin ta dan kar ya ga hoton. Yana ɗaya daga cikin abinda Mommy ta ma ta nasiha akai. *"Duk da Zuhayr ba ya raye hakan ba zai hana Mijin ki yai kishin sa ba, musamman idan har za ki dinga nuna ma sa kin damu da tsohon mijin ki fiye da shi. Zaman ku da Zuhayr ya ƙare Adaeze. Galadima shi ne mijin ki yanzu, ki riƙe shi hannu bibbiyu"* Ta yi saurin goge hawayen ta ta ce " Hajiya Saudah Kakar su Hashir ne ta rasu yau da safe" "Allah ya jiƙan ta da Rahama" Ta amsa ma sa da Amin kafin ta gaya ma sa saƙon Salman. "Bari mu karya sai mu wuce gidan" Ta ɗago ta kalli idon sa kafin ta sauke tana tunanin mi ya ke nufi da kalmar "mu", dan ba ta kawo zai bar ta ta je gidan rasuwan ba. Bayan fitan sa daga ɗakin ta shiga banɗaki ta yi wanka sannan ta fito ta shirya. Kiran Mommy ta yi dan ta ma ta ta'aziyya amma ba a ɗauki wayan ba. Ta kira Muhsina wanda itama bai jima ba da ta ji batun rasuwan, daga jin muryan ta ka san itama ta yi kuka. Bayan ta gama wayan ne ta ga text ɗin Justice akan ta sauko ƙasa su karya lokaci ya tafi. Ɗazu da tana wanka ya shigo ɗakin ya ga ba ta nan. Har ta ɗauko mayafi ta saka akan kayan da ta sa sai ta maida shi ta nemo hijab wanda ya shiga da kayan jikin ta ta saka ta fita. Lokacin da ta iso wajen dining ɗin yana kan waya dan haka ta ja kujera ta zauna. Bayan ya ajiye wayar ne ta gaishe shi ya amsa yana ƙara yi ma ta ta'aziyya. Da ke ba ta da appetite ba ta wani iya cin abincin kirki ba. Bayan sun fito daga gidan ne ya ke jaddada ma ta kamar yadda ya riga ya tsara za su koma Abuja a yau to shi kaɗai zai tafi. Ya ba ta dama ta zauna a nan har zuwa sati, idan ya zo weekend sai su tafi tare. Ya haɗa da cewa ya ba ta dama ta je gidan rasuwa har na kwana uku amma bai yarda ta yi dare ko ta kwana a wajen ba. Ita dai jin sa kawai ta ke yi amma tunanin ta ya tafi wani wajen. Lokacin da Dreba ya sauke su a compound ɗin gidan tuni an cika saboda ƙarfe tara saura minti goma ana jira a fito da gawar ne kawai ai ma ta sallah. Zaytoonah ta fito daga motar kan ta a ƙasa har ta wuce ta ƙofar baya ta shige gidan yayin da Justice ya wuce wajen dandazon jama'ar da aka taru. Kai tsaye falon marigayiyar ta shiga inda a nan ta samu Hajiya Nenne da ma ƙannen Hajiya Saudar. Mommy ma ashe ta zo tana wajen. Hajiya Nenne na riƙe da Tasbaha tana ja lokaci zuwa lokaci tana sauke ajiyar zuciya. Zaytoonah ta je gaban ta ta zauna tana riƙe hannun ta yayinda sabbin hawaye su ka fara silalo ma ta. "Lah Zaytoonah ki bar kuka fa. Ai Saudatu ta yi rabo , ta tsira, yanzu kan sai dai mu. Matar nan shekaru hamsin da tara muna zaune zaman lafiya da ita, zama na amana. Duk haihuwan 'ya'yana ita ke zuwa mu su jego ba ta taɓa ha'intar su ba. Da nata da nawa 'ya'yan duk ɗaya su ke a wajen ta. Ga fara'a, ga sadaka ga kyauta ga ibada, Kai Allah ka jiƙan Saudah" ta ƙarisa maganar tana fyace majina da jiƙaƙƙen handkerchief da ke hannun ta. Gaba ɗaya mutanen wajen sai jikin su yai sanyi... Bayan an kai Hajiya Saudah gidan ta na gaskiya Zaytoonah ta zauna tareda su Hajiya Nenne ana karɓan gaisuwa. Da su ka samu daman magana da Mommy ne ta ke ce ma ta da ƙarfe shabiyun rana yayi ta je gida dan ta kula da mijin ta. Zaytoonah ta ce ai shi ya ce ta zauna a nan har yamma. Zaytoonah ba ta bar gidan rasuwa ba har sai ƙarfe huɗu da rabi na yamma. Da ke tare su ka fito da Mommy sai da ta fara biyawa gidan su kafin Salman ya maido ta gida a motar Mommyn. Yaran ta ma ba sa nan dan tunda su ka je gidan rasuwan tareda Salman su ka maƙalewa Alhaji Tsoho su ka cewa Salman ba za su dawo ba. A falo ta tadda Justice wanda ke ƙoƙarin komawa Abuja, ya fito da jakar laptop ɗin sa ne Sabi'u ya karɓa ya fita ma sa da shi. "Har za ka wuce?" Ta faɗa a sanyaye. "Ko za ki shirya mu tafi tare ne" yai maganar yana murmushi Ta yi saurin girgiza kai. "Zan wuce" yai maganar tareda ƙarisowa gaban ta. Sai da ya dafa kafaɗan ta duka biyu kafin ya manna ma ta kiss a goshi ya ce "ki kula min da kan ki" Kasa ɗago ido ta yi ta kalle shi. A hankali kuma ta furta "Allah ya tsare hanya" Ya amsa da Amin. Ta raka shi har bakin mota ya shiga sannan Dreba ya wuce da shi... *** Ba ta san mi za ta dafawa Justice ba dan ba sanin abubuwan da ya ke so ta yi ba. Tun da safe ya kirata ya sanar ma ta yau zai taho, bayan sallar Jummu'ah da su ka taso ma sai da ya kira ta ya ce sun kamo hanya. Tun lokacin ta ke ta saƙawa da warwara kan mi za ta dafa ma sa. Atleast dai ko ba komai ya kamata ta ma sa tarba mai kyau. Tun da ta zo ma su aiki ke girki, da ke ba wai ma ta samu nitsuwa ba ne ko gwada girkin ba ta yi ba. "Sannu da aiki Baba" "Hajiya barka da yammaci. Ya jikin?" "Da sauƙi" "Miyar zogale za a yi ne?" Zaytoonah ta tambaya ganin matar na gyaran zogale. Murmushi ta yi ta ce "ai Yallaɓai yana son kwaɗon zogale sosai, na ce barin yi ya fara da shi kafin ya ci abinci" Zaytoonah ta zauna ta tayata gyara zogalen tana kallon yadda ta ke sarrafa shi. Ba abu ne da ta taɓa yi ba dan haka ba za ta gwada yin karambani ba kar a zo a samu matsala. Duk yadda dai ta ke yi tana gani tana ɗaukan darasi. Lokacin da ta ce tuwon shinkafa miyar egusi za a yi nan Zaytoonah ta amshi girkin dan wannan kam idan ba ta yi ba sai Allah ya tambayeta. Bayan sun gama haɗa komai su ka kai abincin dinning su ka jera... Ƙarfe shida saura Justice ya shigo gidan kai tsaye sashen sa ya shige bayan ya leƙa ɗakin Zaytoonah ya ga wayam. A gurguje ta shirya bayan ta fito daga wanka dan ta ji sanda ya shigo ɗakin. Doguwar riga ta saka kalar brown irin ɗinkin jallabiyar maza amma gajeran hannu gareta. Irin su ta ke sawa tayi zaman gida da shi. Auwal ne ya ɗinka ma ta irin su har kusan kala shida kwanakin baya tun ma ba ta haɗu da Justice ba balle har ayi zancen auren su. Har za ta fita a haka sai ta fasa ta nemo ƙaramin hijab ta saka akai sannan ta fita. Ganin ba ya falo ya sa ta fita ta je ta ɗauko ma sa kwaɗon zogale da kuma juice ɗin kankana da abarba da ta haɗa. Ta ajiye a center table ta zauna tana zaman jiran sa. Kusan minti goma sai gashi ya fito. Hankalin ta na kan TV ma ba ta ga fitowar sa ba sai da ya ce " Ke da gidan ki sai ki tsaya a nan" Murmushi ta yi ta ce " an dawo lafiya" "Lafiya Princess" Ta yi saurin ɗago ido tana kallon sa. Ya ɗaga ma ta gira. "Fatan yaran duk suna lafiya" "Lafiya lau, suna chan suna jiran sabuwar Maman su" Ta zuba ma sa juice ɗin a kofi ta miƙa ma sa, ya amsa tareda yi ma ta godiya. Ta buɗe bowl ɗin ta ɗau spoon ta ɗebo kwaɗon zogalen kusan fiye da rabi ta zuba ma sa a plate ta tura gaban sa. Tana ɗan satan kallon sa lokaci zuwa lokaci tana ganin yadda ya ke cin zogalen a hankali. Ya ma ta tayi amma ta ce ba za ta ci ba. Ita tun da ya tafi ma zazzaɓi ne ya riƙe ta, jiya da yau ne ma ta ji dama-dama. Bayan ya gama ci ne ya shiga ɗakin sa ya ɗauro alwala amma kafin ya fito ta riga ta tattare wajen ta maida su kitchen. Justice bai dawo ba sai bayan sallar Isha. Da ya zo ya samu Zaytoonah tana falo tana kallo. Ta tambayeshi ko ta kai ma sa abinci falon sa amma ya ce ta bari zai ci a dining ɗin. Ya haura sama zuwa minti goma sai gashi ya sauko. Lokacin da ya zauna ta yi serving ɗin sa sannan ta yi serving kan ta. Ta ajiye ma sa sokali ko zai ci tuwon da shi amma sai ta ga ya ɗauraya hannu ya fara ci da hannu. Dukkan su shiru su ka yi sai ƙaran sokalin da Zaytoonah ke amfani da shi wajen cin abinci. Tun loman farko yai suspecting girkin Amarya ne wannan sai dai bai tabbatar ba sai bayan ya ƙara loma uku. Yau da gobe ya saba da irin girkin Baba Nafy shiyasa ya gano miyar nan ba irin miyar ta ba ne. No offense amma miyar egusin nan ya fi wanda ya saba ci daɗi. "Ya ba ki ɗauko min yara na ba?" "Erm...Mommy ta ce sai sun ƙare ajin da su ke yanzu sai na ɗauke su" "Anya zan iya haƙuri zuwa lokacin nan kuwa" yai maganar yana miƙa ma ta bowl ɗin miya. Ta amsa ta ƙara zuba ma sa wani miyar tareda tambayar sa ko ya isa haka. Ya gyaɗa ma ta kai. "Zan dai fi so a nema mu su transfer zuwa chan Abuja tun yanzu, zuwa su gama term har biyu yayi yawa" Shiru ta yi ba ta amsa ma sa ba dan ta san da wuya Mommy ta yarda tunda cewa ta yi gara ta je ta saba da yaran Justice kafin na ta 'ya'yan su zo, idan har ta tafi da 'yan biyu yanzu ba za ta bawa yaran Justice kulawar da ya kamata ba. "Adaeze" ya faɗa da wata sassanyar murya, sunan ya fiɗo raɗau kamar yadda Daddy ke kiran ta da shi. "Ki yiwa Mommy magana ta bar mana yaran kin ji" Gyaɗa ma sa kai kawai ta yi ta cigaba da cin abinci... *** Ranan Lahdi da safe su ka wuce Abuja. Da daren Asabat ta je yiwa su Mommy sallama kuma sai a lokacin ne yaran nata su ka tada daru akan za su bi ta, da ƙyar ta lallaɓasu akan da zaran ta kwana biyu za ta zo ta ɗauke su. Suna daf da shiga garin Abuja wayar Zaytoonah ya fara ringing wanda ya tasheta daga ɗan baccin da ta fara a motar. International number ta gani amma ba ta gane call code ɗin wani ƙasa ba ne. Ta dai ɗauka dan tana tunanin ko wani investor ɗin su ne. "Happy married life sweetheart" muryan Farha ya doki kunnen ta. "Farha?" Ta faɗa da mamaki dan maganar su na ƙarshe da ita lokacin da ta kirata tana gaya ma ta aurenta da Justice ya kusa kuma tana tsoro, ita kuma Farhan ta ba ta shawaran akan idan har ba ta so to kar ta takura kan ta. "Fatan ban katse miki honeymoon ɗin ku ba?" Sai da ta kalli Justice wanda hankalin sa ke kan wani magazine da ya ke karantawa kafin ta ce "Farha ba na son gulma kina ina?" "Taiwan" "Mi ki ka je yi?" "Neman better half ɗina. An gaya min my perfect man ɗan Asia ne" "Allah ya shiryeki Farha, ki zo Africa na sama miki miji dai dai da ke" ta yi maganar tana dariya. Itama Farhan dariya ta yi kafin daga baya ta ce "Are you happy with him?" Ta saci kallon Justice kafin ta furta a hankali "i'm happy"... Abinda ya faru daren ranan da ya dawo ne ya zo ma ta. May be ba ta ma sa adalci ba amma gaskiya tana buƙatan lokaci, har yanzu ba ta gama amincewa da zuciyarta za ta iya mu'amalar aure da Justice ba. Daren Jummu'ah bayan sun gama cin abinci ta tattare wajen ta koma ɗaki. Da ke akwai saƙon da za ta tura ta email sai ta buɗe laptop ɗin ta tana composing mail ɗin. Sai ga kiran Justice a wayar ta. "Idan ba matsala ki zo ki tayani hira" Ita ba yarinya ba ne ta san mi ya ke nufi da hakan. Ta san hakkin sa ne amma gaskiya she's not ready for it. Bayan ta gama jujjuya zancen a ran ta kafin ta ɗau waya ta tura ma sa saƙo kamar haka. *Daddyn Raziya ka yi haƙuri ka bani lokaci na ɗan huta har yanzu ban gama warware gajiya ba* Sai da saƙon ya tafi da kusan minti goma kafin reply ya shigo wayar ta *kar ki damu Princess, ko hutun shekara za ki ɗauka ni ba mai takura miki ba ne. Ina fata dai mu fahimci juna kafin koma minene zai shiga tsakanin mu. Mu kwana lafiya* Ta karanta saƙon ya kai so goma kowanni lokaci kuma da abinda zuciyarta ke riya ma ta. Sai da ta ji kaman ta tashi ta je ta same shi amma wata zuciyar ta ce tunda ya fahimceta gara kawai ta bari ɗin... Bayan Azahar su ka isa gidan. Justice ne ya jagoranceta har ɗakin da aka ware domin ta ɗakin bai kai na gidan sa na Zaria girma ba amma shima ba laifi Babba ne. Wannan gidan siya yai , shi kuma na Zaria shi ya gina, komai na gidan ya tafi bisa tsarin sa ne. Iya falo Dreba ya shigo ma ta da kayanta yayinda mai aiki ta dinga ɗauka tana ƙarasa ma ta da shi ɗaki. Maimakon Baaba Nafy da ta ke da fara'a wannan ko kaɗan ba ta sake fiska wa Zaytoonah ba. Gaisuwar da ta ma ta ma kaman na dole ne. Ko ajikin Zaytoonah dan ba wannan ne a gaban ta ba. Da yamma Zaytoonah ta shiga kitchen dan ta yi girki dan tun da ta karɓi girki a wajen Baba Nafy har su ka taho ita ke yiwa Justice girki sai dai kawai Baba Nafyn ta tayata da ƙananun ayyuka. Kalmar farko da matar ta faɗa ya sa Zaytoonah yi ma ta kallon are you mad?. "Yallaɓai bai ce na ba ki girki ba" abinda matar ta faɗa kenan tana magana tana tsume fiska. Zaytoonah ta juya maganar a ranta wanda yai ma ta banbaraƙwai. Ta zo da niyyar bin kowa a hankali ne amma idan hakan bai yiwu ba za ayi zama 'yar zafi-zafi ne. "Ban gane ba" ta faɗa dan ta tabbatar lafiyar matar ƙalau ko kuma dai iskanci ne. "Mu biyu mu ke aikin girki a gidan nan, idan na yi na kwana shabiyar sai Maman Tofe (Tope) ta karɓeni. Yallaɓai bai ce mu bari Amarya ta yi girki ba" Dariya ya tahowa Zaytoonah amma ta dake ta ce " ki je ki cewa Yallaɓan ni Zaytoonah daga yau zan dinga yi ma sa girki" Yadda ta yi maganar ya sa Matar ta yi gum da bakin ta dan ba ta ga alamar wasa a fiskan Zaytoonan ba. Komawa gefe ta yi ta tsaya tana kallon Zaytoonah. Zaytoonah ta je ta buɗe fridge dan ta ga abinda akwai a gidan ta san mi za ta shirya. Ɗan zaman su da Baaba Nafy ta gaya ma ta duk favourites ɗin Justice. "Ina ne store?" Zaytoonah ta tambaya ba tareda ta kalli inda matar ta ke ba. "Ga ƙofar nan" ta faɗa dan dole... Da yamma lis sai ga yaran sun shigo gidan sanye da kayan Islamiyya. Falaq da Suhailah ne su ka ruga kitchen da gudu bayan Justice da ke falo ya gaya mu su Antyn su na kitchen. Sun ga hotunan biki dan haka gani ɗaya su ka yiwa Zaytoonah su ka gane ta. Suhailah ne ta je ta rungumeta yayinda Falaq ta tsaya daga gefe tana ƙare ma ta kallo. "Anty ina su Hashir da Hadid?" "Suna Zaria Suhailah" "Yaushe za su zo" "Ashe dai 'yan biyun nawa dai suna da babbar ƙawa" Suhailah ta yi dariya. "Falaq ko?" Falaq ta gyaɗa kai tareda barin kitchen ɗin da gudu saura kaɗan ta buge Raziya da ke shirin shigowa. Lokacin da Raziya ta shiga kitchen ɗin ta samu Zaytoonah na yiwa Suhailah bayanin abinda ta girka mu su yayinda yarinyar ke irgo ma ta abinda kowa ya fi so a cikin su. "Raziya ya karatu?" Zaytoonah ta tambaya fiskarta ɗauke da murmushi amma ga mamakin ta sai harara Raziya ta bi ta da shi. "Suhailah zo mu je na cire mi ki kaya" ta faɗa tana riƙo hannun Suhailan. "Anty barin je na cire uniform kin ji" Zaytoonah ta gyaɗa ma ta kai. Sai da su ka kai bakin ƙofa ta ji Raziya ta ce "wa ya ga Anty Buskuɗa" sai kuma ta kwashe da dariya. *Buskuɗa* Zaytoonah ta maimaita sunan a fili. Tabbas za ta sha fama da yaran nan... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 57 Bismillahir Rahmanir Rahim *confession* A ƙaramin table da ke gaban sa ta ajiye ma sa plate ɗin da ta yanka ma sa Kankana da Apple. "Barka da yammaci" Ba tareda ya ɗago ba ya ce ma ta "sannu da aiki" "Daddyn Raziya idan ba matsala inada magana" ta faɗa bayan ta zauna. Ya rufe littafin hannun sa ya kalleta yana faɗin "Bismillah" Sai da ta sauke dogon numfashi kafin ta ce "yau da safe aka kirani, Mrs Haddish ba ta da lafiya, she's seriously ill" Ta yi shiru tana nazarin yadda za ta faɗa ma sa da ba zai ji haushi ba. "Erm, ta buƙaci ganin 'yan biyu kafin mutuwarta and i was thinking ko za ka bani dama ni da yaran mu tafi Las Vegas cikin satin nan. I Promised Sati ɗaya kawai za mu yi mu dawo tunda yaran na Makaranta" Ta ƙarisa maganar a hankali. Hutun second biyar ta ɗauka kafin ta cigaba. "Mrs Haddish Kakar Marigayi ne and..." Ta yi shiru ganin irin kallon da ya ke ma ta. Ya ɗau fork ya ɗebi Kankana ya kai bakin sa yana taunawa a hankali, bai ce komai ba har sai da ya kusan cinye plate ɗin Kankanar kafin ya ajiye fork ya tura plate ɗin gefe. "A duk lokacin da ta buƙaci ganin yaran, za ku iya yin video call, zai wadatar" "Amma..." "Idan Allah ya kaimu zuwa lokacin da 'yan biyu su ka samu hutun Makaranta, sai ku je ku gaisheta. Ina ma ta addu'ar samun lafiya" Wani abu ta ji ya toshe ma ta maƙoshi ya sa ta kasa koda haɗiyar yawu. Rabonta da Mrs Haddish tun ranan da za ta taho Nigeria bayan ta gama karatunta. Ko alif ba ta furta ba ta miƙe ta bar ma sa falon. Yayinda shi kuma ya bi bayanta da kallo. Yinin ranan kamar za ta fashe saboda yadda ta cika ta yi fam da haushin Justice. Daga baya ma kiran Mommy ta yi, ta roƙeta akan ta yiwa Justice magana ya barta ta yi tafiyar. Mommy ta ce ta haƙura kawai ta bi umurnin mijin ta... *** Zoom meeting su ke da wasu ma'aikata. Ta saka airpiece tana sauraron bayanan Mr Silas da ke bayani. Falaq ta shigo ɗakin na ta da gudu. Riƙe hannunta ta yi tana faɗin "Anty come" Zaytoonah ta cire airpiece ɗin tana faɗin " Miya far..." ba ta ida ba ta jiyo kukan 'ya'yan ta. Da sauri ta tashi ta fita daga ɗakin da gudu, Falaq ta bi bayanta. Ɗakin 'yan biyu ta shiga dan daga nan ta ke jiyo kukan Yaran. "Innalillahi! Ghazalah lafiya?" Ta faɗa da ƙarfi tareda jawo Hashir da ke kuka jikin ta. "A wani dalilin za ki samin yara a gaba da duka, who gave you the audacity to beat my kids?" "Ina da hurumin dukan su dan ba za su zo su ɓatawa 'ya'yana tarbiyya ba. Yara ƙanana ba abinda su ka iya sai iskanci" "Ta nan kuma ki ka ɓullo. To Wallahi aniyarki ta bi ki dan 'ya'yana ba 'yan iska ba ne" "Eh Lallai! Shiyasa na ga sun cirewa Suhailah wando suna shirin afka ma ta" "Kar ki ƙara Ghazala. 'Ya'yana ba Jakunan ki ba ne, ko me za su yi a gidan kar ƙi ƙara, dan Wallahi sai inda ƙarfina ya ƙare a kan ki" "Ki dai gyara tarbiyyan Yaran ki tunda tun ƙuruciya sun zama kwartaye" Lafiyayyen mari Zaytoonah ta shararawa Ghazala. Ghazala ta fusata ta ɗago hannu za ta rama Zaytoonah ta riƙe hannun. "Kin yi kaɗan Wallahi, kin yi kaɗan" ta faɗa tana zare ido. Ta yafce ma ta hannun gefe. Zaytoonah na ƙoƙarin kamo hannun Hadid da ta gani kwance a ƙasa ta ji saukar dundu a tsakiyar bayanta. A fusace ta juyo ta shaƙo wuyan Ghazala da ba ta shiryawa hakan ba. Yadda ta shaƙeta da ƙarfi sai da idon Ghazala ya firfito, sai faman cire hannun Zaytoonah ta ke amma ta kasa, ta ji damƙar manya. "Hasbunallah! Zaytoon!" Justice ya faɗa da ƙarfi lokacin da ya shigo ɗakin. Shima ɗin da ƙyar ya samu ya raba Zaytoonah da Ghazala. Ghazala ta yi ƙasa da sauri tana neman numfashi da gaggawa. "Wani rashin hankali ne wannan?" "Ka gaya ma ta duk ranan da ta sake taɓa min yara sai na kasheta" Daga haka ta ɗauki Hadid da ke kwance ta ja hannun Hashir su ka bar ɗakin. Sai da ta fita ne ma ya ankara da cewa a gaban duka yaran sa ake wannan katoɓarar. Raziya da Falaq sun yi ido zuru-zuru ita kuma Suhailah kuka kawai ta ke yi. "Mi ya faru?" Yai tambayar yana kallon Ghazala da har yanzu ba ta gama dawowa hayyacinta ba. "Ki sameni a ɗaki" ya faɗa tareda ficewa daga ɗakin cikin ɓacin rai. "Baby are you OK" ta faɗa idonta cike da hawaye. Gashi nan dai idon sa a buɗe amma ya ƙi cewa komai sai numfashi da ya ke fitar wa da sauri-sauri. "Hadid my love say something. Ahmad please say something" ta faɗa tana jijjiga shi "Mom i want to go to Zaria" ya faɗa bayan kusan minti biyu. "Zaria ko, we'll go to Zaria ka ji. Yau ɗin nan ba gobe ba"... *** "Faɗa a cikin gidana Ghazala. Mi ya kawo haka?" "Ranka shi daɗe ka gafarce ni. Mummunan abinda na gani ne ya sa na ɗau mataki cikin gaggawa,to hakan kuma sai ya ɓatawa Zaytoonah rai har ta kamani da faɗa tana shirin hallakani. "Muna ƙasa ni da Raziya da Falaq sai na duba banga Suhailah ba sai su ka ce min tana wasa tareda 'yan biyu a ɗaki. Na share zancen mu ka ci gaba da kallo, to da na hau sama zan shiga banɗaki sai na ce barin leƙa dan ban ji ɗuriyar su ba. Abu Razz ka san yadda duniya ta lalace, yara ƙanana sai ka ga suna aikata abubuwan al'ajabi da ban mamaki. "Ɗaya daga cikin yaran na gani a kan Suhailah, sun ɗage ma ta skirt ɗinta sun cire ma ta wando, dan pant ɗin ma na yashe a ƙasa. Hankalina ya tashi matuƙa shine na ɗau belt ɗin yaran na zane su dukan su biyu. ita kuma daga zuwa ba ta bi bahasi ba sai ta mareni ta kamani da faɗa. "Ranka shi daɗe Suhailah 'ya ta ce, dole ne hankalina ya tashi idan na ga abinda zai cuce ta. Dan Allah ka yi haƙuri na yanke hukunci cikin gaggawa ba tareda na bari ka zo ba" Bai ce komai ba ya wuce ya barta a ɗakin tana share hawayen munafurci. Ɗakin Yaran sa ya shiga dan Raziya ta kaɗa kan su sun dawo na su ɗakin. Suhailah na kwance akan gado kan ta na cinyar Raziya da ke lallashinta. Zuwa yai gadon ya jawo Suhailah jikin sa yana faɗin "my baby wa ya taɓa min ke?, wa ye nan ya isa ya taɓa min pretty Princess ɗina" Ta lafe jikin sa tana kuka a hankali. Ganin ba ta ce komai ba ya sa shi barin maganar zuwa lokacin da ta huce. Bai bar ɗakin ba sai da ya tabbatar ta dena kuka har ma bacci ya saceta... Duk wasu kaya ma su mahimmanci na ta ta ke ta kan haɗawa. Abu ne ya faru a lokacin da ta ke tsakiyar jin haushin zamanta a gidan, kasancewar Mai gidan ya hanata tafiya Las Vegas, ga kuma wannan tsohuwar Matar ta san ta sa gidan gaba ɗaya ya fice ma ta kai. A bakin ƙofar ɗakin ya ci karo da akwatuna guda biyu Babba da ƙarami. "Hashir Love ka gama kashin ne?" "No" ya amsa ma ta daga banɗakin. Hadid na kwance akan gado yayinda ta ke ƙoƙarin saka Laptop ɗinta cikin jaka "Ina za ki je?" ta ji muryan shi a tsakiyar ɗakin. Ba ta kula shi ba ta cigaba da abinda ta ke yi. "Adaeze" ya faɗa da ƙarfi. Ta ɗago ido ta kalleshi ba tareda ta ce komai ba. "Magana na ke miki" "Gidan mu zan je" Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya ƙarisa wajen da Hadid ya ke kwance. Ya saka hannu a goshin sa ya ji zafi, da alama akwai zazzaɓi tattare da shi. Ɗaukan sa yai cak zai fita da shi daga ɗakin Zaytoonah ta tare gaban shi "ba inda za ka kai min shi, tafiya za mu yi" "Matsa min na wuce" yai maganar fiskarsa ɗaure. Ta ɗan ji tsoro amma ta dake ta ce " ba inda zan je sai ka ajiye min ɗana" "Matsa na ce!" Ba shiri ta matsa ma sa ya fita daga ɗakin. Ɗakin sa ya kai yaron sannan ya ɗauko first aid box ya buɗe ya fito da paracetamol na ruwa ya ba shi. Sai da ya sha tukunna ya kwantar da shi da kyau jikin sa yana bubbuga bayan sa a hankali. Shima Hashir da ya fito ya ga babu ɗan uwan sa sai ya fice daga ɗakin. Zaytoonah na kiran sa amma ko waiwayan ta bai yi ba. Kai tsaye ɗakin Justice ya je dan ya ji maganar su lokacin yana banɗaki. Da ya shigo ɗakin shima wajen Justice ya je ya kwanta. A hankali ya ke lallashin yaran sai ga shi sun sake jiki sun manta da dukan da Ghazala ta mu su. A fakaice ya tambayi mi ya faru wanda Hashir ya bashi labarin komai. Wasa su ke yi da Suhailah shine ta shiga banɗakin su ta yi fitsari da ta fito kuma ta ce wandonta ya jiƙe sai ta cireshi ta ajiye a ƙasa. Da ke Hadid ya fara bacci sai suma su ka kwanta akan gadon Hadid ɗin. Da ke gadon ya mu su kaɗan su uku shine cikin bacci Hadid ya ɗaura ƙafar sa ɗaya akan Suhailah. Wannan Ghazala ta shigo ta gani, dama abin nema ne ya samu kawai ta ɗauko belt ɗin yaran da ta gani a ƙasa ta fara dukan su , kukan yaran ya sa Falaq da Raziya su ka shigo ɗakin da gudu kafin da Falaq ta ga dukan yayi yawa ta je ta kirawo Zaytoonah... *** Fitowar da yai daga ɗaki dan ya fita sallar magariba saboda yaran sun yi bacci yai ido huɗu da Zaytoonah. "Ka fito min da yara na, tafiya za mu yi" "Ba inda za ki kaimun yara da daren nan" "Oh really! Ta nan kuma ka ɓullo. To ba zai yiwuba, Yara dai ni na haifesu kuma ina da ikon tafiya da su duk inda na ga dama sai dai idan muguntar ce ta tashi sai na sani" "Zaytoon ki matsa zan je sallah" "Ni ban ce kar ka je sallah ba amma ka fitomin da 'ya'ya na. Na gaji da zaman gidan da ba a ɗauke su a bakin komai ba" Cikin kuka ta cigaba da magana " da ni ce na daki yaran ka da yau ko'ina sai an jimu amma nawa yaran gashi nan ai ba abinda ka yi ma ta. Nan nan saboda na saka Raziya aiki ba tareda ka bi bahasin mi ya faru ba ka ɗau fushi da ni ƙarshe ma Aure ka ƙara. To na gaji, na gaji da take hakkin da ake min a gidan nan. Komai idan aka ce ni ce ba za ka taɓa bincike ba sai dai ka hau maganar da aka gaya ma ka ka yanke hukunci. Ba zan iya ba Daddyn Raziya ba zan iya ba" Sosai maganganun sa su ka taɓa shi amma ya daure ya ce " idan na dawo daga masallaci za mu yi magana" "Ba wani magana da za mu yi, ka bar ni kawai na tafi da 'ya'yana idan ba haka ba zaman Allah ya isa za mu yi a gidan nan" Ya ɗago rinannun idanun sa ya kalleta, murya a raunane ya ce " yanzu dare yayi, Dan Allah ki bari gobe sai ku tafi" Yadda yai maganar ya sa ta ji ba za ta iya ma sa mu su ba. Ga shi itama ta san ba ta iya tuƙi da dare saboda duhu. Ranan dai yaran a wajen Justice su ka kwana. Shi Justice tun da ya fita sallah bai dawo ba sai kusan ƙarfe shaɗaya na dare. Gaba ɗaya maganganun Zaytoonah sun tsaya ma sa a rai musamman maganar zaman Allah ya isa da ta ce za su yi. Washegari ƙarfe shida da rabi suka ɗauka hanyar Zaria. jikin Hadid ma ya warware dan dama kukan da yai ne ya sa ma sa zazzaɓi. *** Junior ne ya buɗe mu su ƙofa su ka shigo. Mommy na zaune a falon tana shan tea. Yaran su ka yi kan ta da gudu suna kiran GrandMa. "Mommy ina kwana" ta faɗa yayinda ta ke dai-dai ta tsayuwar akwatin ta. "Lafiya" ta amsa ba tareda ta ɗago ido ta kalleta ba. Zaytoonah ta ƙarisa da akwatin cikin ɗaki ta sake fitowa ta ɗauko sauran kayan har lokacin yaran na manne jikin Kakar su. Kusan har dare Mommy ba ta yiwa Zaytoonah maganar zuwanta ba. Infact bayan gaisuwan da ya haɗasu ba ta sake ce ma ta uffan ba. Jikin Zaytoonah yai sanyi tana ma tunanin ko Justice ne ya kirata ya gaya ma ta wani abin amma kuma ba halin sa ba ne. "Mommy ki yi haƙuri Dan Allah, na san ba haka kika so ba amma Mommy i'm not happy in that house. Ni bare ce. agidan nan, Daddyn Raziya bai damu da ni ba, ya fi bawa Amaryarsa muhimmanci and 'yan biyu ba su da walwala a gidan nan. Ba ni da farin ciki a gidan..." "Allah shi kyauta" "Mommy ki fahimce ni please" Murfin tukunyan da ke hannun Mommy ta sake ya faɗi ƙasan tile yana bada ƙaran gararanran. "Na fahimce ki Zaytoonah, na fahimci ke wawuya ce kuma daƙiƙiya. Duk tarin ilimin da ki ke da shi ba shi da wani amfani a gareki. Ba ki da farin ciki a gidan ko? To Allah ya baki farin ciki a nan ɗin" Kuka Zaytoonah ta fashe da shi dan yadda ta karanci tsantsar ɓacin rai tattare da Mommyn. "Ki yi duk abinda ki ka ga dama, ba zan sake saka baki cikin lamarin ki ba. Idan ma so ki ke ki kashe auren ki dan ki auri Auwal Bismillah, idan wani daban ma za ki aura Allah ya baki sa'a, idan kuma zama za ki yi haka ba aure duk ba ni da matsala da hakan" "Mommy you know its not about Auwal. Farin ciki na, farin cikin 'ya'ya na su ne kan gaba akan komai, kuma babu shi a gidan Justice" ta yi maganar cikin kuka. Mommy ba ta ƙara cewa komai ba dan yadda zuciyarta ke tafasa idan ta cigaba da fitar da abinda ke cikinta za ta iya samun matsala. Zaytoonah ta fice daga kitchen ɗin ta wuce ɗaki da gudu. Lallai yaro ba shi da amana. Tana shiga ɗaki ta samu Yaran na waya da Justice. Tana ji suna faɗin sun missing ɗin sa ta yi saurin ƙwace wayar ta katse kiran. "Wa ya ce ku kirashi?" "Shine ya kira" Hadid ya ba ta amsa. "Maza ku je wa je ku yi wasa" Sake kiran wayan aka yi a karo na biyu. Kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka kiran lokacin yana gab da yankewa. Shiru ta yi ba ta ce komai ba. "Gobe zan shigo, ina so ki bani dama mu yi magana" Kashe wayar ta yi ta kifa kan ta tana sauke ajiyar zuciya. Daren ranan ita da Mommy haka su ka koma tamkar kurame ba wanda yai wa wani magana. "Mommy i'm sorry about yersterday" Zaytoonah ta faɗa lokacin da Mommy ke shirin miƙewa daga sallayar da ta yi sallar Asuba da shi. "Ba komai, rayuwar ki ce ai" "Mommy ban san ya zan yi ba, i tried my best amma komai baya tafiya dai dai" "Akwai auren da ke tafiya dai-dai ne?" Sai da ta zauna bakin gado kafin ta cigaba "babu auren da ya ke tafiya dai-dai. A yadda ya zo da targaɗe ɗin ke ce za ki yi ta seta shi har a samu ya tafi miki dai-dai yadda za ki samu farinciki a cikin sa. " watan ki nawa da aure Zaytoonah har kina complain ɗin kin gaji. Ki gaya min tsakanin ki da Allah a cikin watanni takwas da ki ke zaune da Galadima kin yi ƙoƙarin sauke duka haƙƙoƙin sa da ke kan ki? Kin yi iya ƙoƙarin ki wajen ganin an samu zaman lafiya a zamantakewar ku da matar sa da kuma 'ya'yan sa?. "Indai kin yi dukkan wannan kuma kina ganin ba ki samu farin ciki ba. Bismillah ki yi yadda ran ki ya ke so, ni dai nawa ido. Amma har wa yau ni a wajena Galadima mutum ne mai gaskiya" Shiru Zaytoonah ta yi tana tunani. Tabbas ko da akwai laifin Justice to itama mai babban laifi ce. She can't believe that har ta yi wata takwas a gidan Justice. Bawan Allah yana nan yana zaman jira ta gama hutu. "Ki ji tsoron Allah Zaytoonah. Wannan Bawan Allah ya mana ƙoƙarin da ba mu isa mu biya shi ba sai dai kawai mu ma sa addu'a amma still kina tuhumar sa da zalunci. Ni na haifeki kuma na san halin ki sarai. Ko kaffara ba zan yi ba idan na rantse cewa ba ki bawa auren ki muhimmanci ba. Auren da ba ki ɗauke shi a bakin komai ba ta ina za ki samu farinciki a cikin sa?" "Idan farincikin 'ya'yan ki kike nema, to yana tareda Galadima, idan kuma wasa da hankali za ki mu su to ga ki ga su" Haka Mommy ta cigaba da yi ma ta nasiha. Gaba ɗaya sai nadama ya sauka ma ta. Da rana ta fito daga wanka kenan, sai ga kiran Justice a wayarta. Ta yi sauri ta ƙariso ta ɗauka. Ce ma ta yai ya shigo Zaria yana son ƙarisowa gidan su ta ce ma sa to. Minti hamsin da maganar su sai ga kiran sa lokacin Mommy ta dawo daga school. Tana ɗaukan kiran ya ce ta fito yana waje. Hijab kawai ta saka ta fito ta sami Mommy na yiwa Junior faɗa. A kunyace ta ce "Mommy xan fita, Daddyn Raziya ne ya zo" "Shine za ki bar shi a waje" Zaytoonah ta yi shiru tana ɗan sosa kai. "Ki je kar ki sa shi jira" Tana buɗe gate ta hango Motar sa, ta ƙarisa wajen. Tun kafin ta ƙariso ya buɗe ma ta ƙofa dan haka kawai ta shiga gidan gaba tunda shi da kan sa ya tuƙo Motar. "Barka da rana" "Barka" "Ya yaran?" Ta yi tambayar ne ganin shirun na su yayi yawa. "Sun yi missing ɗin ki" "Anya kuwa?" "Sun yi missing ɗin ki sosai fa" "Hmmm" kawai ta ce ta yi shiru. "Ikon Allah" ta furta lokacin da ta hango yaranta akan Keke suna nufo su. "Motar Daddy ne wannan" Hashir ya faɗa lokacin da su ka zo dai-dai bakin Motar. Justice yana shirin buɗe window ya mu su magana Zaytoonah ta dakatar da shi. "ka bar su kawai, yanzu sai su ce sai sun shigo" "Na ga alama dai da ƙarfi so kike ki raba Uba da 'ya'yan sa" Ta wajen glass Hadid ke leƙawa saboda Motar tinted ce. "Hadid ba kowa a ciki ka zo mu shiga gida, yana cikin gida". "Hashir ina ga Daddy ya zo ɗaukan mu ne fa. Idan Mom ta ce ba za mu bi shi ba ka san me za mu yi?" Hashir ya ce "a'a" "Da Baba Tsoho za mu haɗata" Hashir da Hadid su ka wani tafa suna dariya tareda juya keken su suka shige gidan. Ƙwaƙwƙwaran numfashi mai kyau ta kasa yi. Yau da ace wani ne ya gaya ma ta abinda 'yan biyu su ka ce da ba za ta taɓa yarda ba amma sai gashi da kunnen ta ta ji komai. Wato da ƙarfi da yaji dai Justice ne Daddyn su. Ya lura da yadda ta kaɗu da jin maganar yaran dan haka ya kauda hankalinta ta hanyar cewa "shekaru bakwai da su ka wuce na haɗu da wata yarinya mai karambani a wajen wani biki. Yarinyar da ƙarfi ta ke son shiga wajen da ake dinner bayan kuma ba ta da card ɗin shiga. Ta maƙalewa wani mutumi da ta kira Uncle Muhammad su ka barta ta shiga. "Da ikon Allah wannan Uncle Muhammad ɗin ya sake ganinta a cikin jirgi bayan watanni kaɗan. Ba tareda ta ganeshi ba ta ma sa tayin plantain chips da ta ke ci. Da jirgi zai tashi ta fara karanto addu'o'i kala-kala har ta riƙe hannun sa ba tareda ta sani ba..." "Ya Allah! Daddyn Raziya kai ne dama?" Murmushi yai ya ce "na ƙara tsufa sosai ko?" "Oh my goodness, shiyasa ranan da mu ka je gidan ka na ke tunanin kaman na taɓa sanin ka a wani waje, ashe kai ne" Ta dafa kan ta tana ɗan girgizawa cike da tunanin wannan coincidence ɗin. " Kalmar Allah ya isa tana da nauyi Zaytoon. Idan har zaman da za mu yi tana ƙarƙashin wannan kalmar ne, zan iya haƙura da zaman ko da kuwa abu ne da zai min ciwo" Ya kwantar da kan sa jikin kujera yana kallon sama kaman mai tuno wani abu. "Immediately da na gama Law School ina da dogon buri a rai na. Kwata-kwata ba ni da niyyar yin aiki ƙarƙashin gwamnati. Case na farko da na karɓa na wani Baffana na ne ƙanin Mai Martaba. Wani babban fili ne ake jayayya a kai. I was young, buri na kawai shine na ci first case ɗina ta ko wani hali. Aka shiga ƙara kotu mu ka fafata da lawyan gwamnati da ke kare Tsoho mai filin da kuma ni da na ke kare Baffana. In the end aka ba wa Baffana gaskiya aka ƙwace fili daga hannun Baba Sama'ila. "Bayan mun fito daga kotu ina murna na ci case ɗin sai na ji an taɓani ta baya, juyawan da zan yi sai na ga wannan tsohon ne da akayi shari'ar da shi. Akwai tsantsan ɓacin rai da damuwa tattare da fiskar sa, ya ce min ("Na san kun fi ƙarfina, amma zan bar ku da Sarkin da baya zalunci. Allah ya isa fili na"). "Zaytoon ban iya bacci ba ranan ba. Kalmar Allah ya isan nan ya tsaya min a zuciya, ya hanani sukuni. Washegari na tafi ƙauyen Tsohon nan only to find out ana zaman makokin sa. Ashe bayan ya koma gida da ya shiga ya kwanta bai sake tashi ba. Ɓacin rai ya zama ajalin sa. Hankalina ya tashi matuƙa, i blamed myself for his death. Na koma na waiwayi case ɗin nan, na bi proper ways na yi bincike na gane cewa Baba Sama'ila bai sayarda filinsa wa Baffana ba. Yes Baffana ya ma sa tayin sayar da filin amma ya ƙi, shine aka yi fake documents da kuma sa hannun ƙarya aciki. Wasu marasa imani cikin ƙauyen su ka ba da shaidar zur akan cewa lallai Baba Sama'ila ya saida filin sa. Bayan na gama haɗa komai i met my uncle akan ya maidawa 'ya'yan Baba filin su ko kuma dai na sake buɗe sabon ƙara akan sa. Abu dai ta kai mu har gaban Mai Martaba still bai yarda ba. Ni na jagoranci yaran Baba Sama'ila aka ɗaukaka ƙaran nan har ta kai an ƙwace fili daga hannun Baffana an maidashi wajen Magadan Baba Sama'ila. "Dalilin wannan har yau ba ma shiri da Baffa na. Saboda wannan shari'ar ya sa na fasa zama lawyer mai zaman kan sa na koma ɓangaren gwamnati na fara aiki har na kawo matsayin da na ke yanzu. "Zaytoon, har kafin a bawa 'ya'yan Baba filin nan, ban taɓa yin bacci na kwanciyar hankali ba. Duk lokacin da na kwanta kalmar Allah ya isa da Baba yai shi ke hanani bacci..." Kukan da ya ci ƙarfin sa ne ya hanashi ci gaba da maganar. Itama Zaytoonah hawaye fall ne a idonta. Justice ya fito da handkerchief ya fara goge hawayen da ke fita a idon sa, sai dai yana gogewa wasu na fitowa. "Daddyn Raziya ka yi haƙuri" Zaytoonah ta faɗa tana ɗaura hannunta akan cinyar sa. Kusan minti biyu kafin ya iya tsaida kukan na sa ya juyo yana kallon Zaytoonah ya ce "Ina son ki Zaytoon, amma ba zan iya zaman Allah ya isa da ke ba. Zan ba ki kwana uku ki yi tunani, in har kin yadda ni mugu ne marar adalci, wanda ba za ki iya zama da shi ba. Zan sawwaƙa mi ki. Da na zauna da ke ina zaluntar ki gara na danne zuciyata na rabu da ke na miki fatan alkhairi a rayuwar ki" Jikinta ne yai sanyi, ta ma rasa mi za ta faɗa ma sa a wannan lokaci. Ya sa hannu a baya ya jawo wata leda ya ɗaura a cinyarta ya ce " ga tsarabar 'ya'yana. Ki gaishe min da su"... *** Maganganun Justice ta ke ta juyawa a ranta wanda ya hanata bacci. Idan har za ta kira Justice mugu to ita ce babbar muguwar. Bayan matsalar Ghazala mi ya ma ta da har za ta kira shi da mugu. Ghazala ce fa Munafuka. Ƙarfe tara na dare sai ga kiran Hajia Abu a wayarta. Ta tashi zaune ta ɗauka wayan tareda sallama. "Ke wacce irin daƙiƙiyar yarinya ce, Iye?. Idan ma kin yi yaji ne dan kina tunanin Galadima zai zo ya yo bikon ki to kin yi kaɗan. Idan za ki tattara ki koma gida ki koma, idan kuma takardar ki kike buƙata sai ki yi magana a kawo miki har gida. Ba dan ma ƙaddara ba mi zai haɗa auren ki da Galadima" Sarai ta san Ghazala ce da wannan aikin, wato har ta beza cewa ta yi yaji daga kwana uku da ta bar gidan. "Hajiya waya ce Yaji na yi?. Mommy na ne fa ba ta da lafiya shine na zo duba ta" Hajiya Abu ta ji gwiwarta ya sace, dama barazana ce kawai. Ko kaɗan ba ta son abinda zai ɓatawa Galadima record domin tanada ɓoyayyen buri akan sa na son ya gaji Mai Martaba idan rai ya halin sa. "Ghazala ta ce da dukkan akwatunan ki kika tafi, ana zuwa gaisuwa da duka kaya ne?" "Lah! Kayan da ke Abujan ne naga sun kwana biyu shine na dawo da su nan saboda zan ɗauko wasu a nan ɗin na tafi da su chan" "To Allah ya ba ta lafiya" Ba ta jira Zaytoonah ta ce Amin ba ma ta kashe wayar. "Mommy ki ji wai har Ghazala ta fara yaɗawa wai na yi yaji" Mommy da ke duba assignment ɗin yara ta ce "to ba yajin ki ka yi ba?" "To shine harta fara bezawa a gari" "Mi za ta jira kuma tunda gidan mai gaba ɗaya za ki bar ma ta" "Allah ya sawwaƙa na bar ma ta gidan" Sai da ta yi maganar kuma sai ta riƙe baki tana jin kunya. Mommy ta yi murmushi ta cigaba da abinda ta ke yi. 2/11/21, 10:04 PM - ****: 58 Bismillahir Rahmanir Rahim *I'm back* Washe gari Zaytoonah ta je salon aka wanke ma ta kai aka ma ta ƙananun ƙitso, aka ma ta gyaran farce kafin aka ma ta jan Lalle. Ba ta dawo gidan ba ma sai bayan Azahar. Ta kira Baaba Nafy ta ce ma ta Justice yana nan bai tafi ba sai washegari zai tafi saboda ya je representing Mai Martaba zuwa ta'aziyya wani ƙauye. Ƙarfe shida saura ta isa gidan Justice. Sai da su ka gaisa da Baaba Nafy kafin ta wuce ɗakin ta bayan ta ƙarfi kwandon abinci da ta zo da shi. Tunda ta cewa Baaba Nafy za ta zo ta sa aka gyara ma ta ɗakin ta dan haka bayan ta ajiye jakarta ɗakin Justice ta wuce, falon sa na nan tsaf-tsaf sai ƙanshi ya ke. Ɗakin ma a tsaftacce ya ke duk da ma Justice baya bari ma su aiki su shiga ma sa ɗaki shi ya ke gyara kayan sa. Ko a chan Abuja ma shi ya ke gyarawa ko ya saka Raziya, yanzu kuma da ya ke da Mata har biyu kowacce ranan kwananta sai shiga ta gyara ma sa. Da ta gama ɗan gyara abinda ba za a rasa ba komawa ɗakinta ta yi ta ɗauko sabon bedsheet ta zo ta shimfiɗa ma sa. Sabon rayuwa sabon bedsheet. Da ta ga komai ya ma ta yadda ta ke so sai ta koma na ta ɗakin. Alwala ta yi ta zo ta zauna a sallaya tana azkar kafin a kira sallar Magariba. Gaba ɗaya a gajiye ya dawo. Ƙauyen da su ka je hanyar kwata-kwata babu kyau, sun ji jiki a tafiyar da su ka yi. Da ke sai da ya tsaya yai sallar Isha ma kafin ya shigo gidan saboda da ya ci abinci kwantawa zai yi ya huta gajiya tunda gobe ma sabon hanya zai ɗauka. Bayan yayi wanka ya fito ya saka silk pyjamas ɗin sa baƙaƙe sannan ya fito falon ƙasa inda aka jera ma sa abinci. Da ke ya ga dare ya yi bai yi niyyar cin abincin sosai ba. Tea da aka haɗa ya fara zubawa kafin ya buɗe warmers ɗin ya fara serving kan sa abinci. Lomar farko da ya ci ya tabbatar ba girkin Baaba Nafy ba ne, kamar dai girkin Zaytoonah amma kuma ta ina Zaytoonah za ta ma sa girki bayan tana chan gidan su. Har ya ɗaga waya zai kira Baaba Nafy ya tambayi wa yai girkin yau sai kuma ya fasa ya cigaba da cin abincin, ya sawa ransa ƙila kewanta da ya ke yi ya sa shi jin abincin kamar irin girkinta. Ya ɗan ci abincin sosai fiyema da yadda yai niyya. Da ya gama yai hamdala ya miƙe ya haura sama. Da ke cikinsa yai nauyi sai ya ga gara ya ɗan huta kafin ya kwanta, ɗakin karatun sa ya shiga ya ɗauko litattafai ya shiga nazari musamman akan wani case mai sarƙaƙiya da ake kan shari'an sa. The last time da ta yi niyyar kai kan ta wajen sa shine ya ba ta mummunan labari wai zai ƙara aure. Wannan karan koma minene ba za ta yi wasa da damarta ba. Justice ya chanchanci ta saka ma sa da abinda ya fi wannan ma. Ta duba agogo ƙarfe goma da minti ɗaya. Ta ja dogon numfashi kafin ta nufi Turakar Maigida. Ko minti biyar bai yi da fara bacci ba ya ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. A karo na biyu da aka ƙwanƙwasa ya yaye bargo ya kunna wuta ya miƙe, da ya zo bakin ƙofa ya ce "waye ne?" "Ranka shi daɗe" ta faɗa tana murmushi kaman yana ganin ta. Da sauri ya buɗe ƙofar jin muryan da bai yi tsammani ba. "Masha Allah" ya furta a zuciyar sa. Rigan baccin iya tsakiyar cinya ya tsaya, cream colour sai robe ɗin maroon wanda ba ta ɗaure ba. "May i come in?" Ta faɗa tana fari da ido ganin ya shagala da kallonta. Saurin matsa ma ta yai ta shigo wanda ƙanshi turarukan da ta fesa su ka fara isar ma sa da saƙo. "A gafarceni na katse ma ka bacci" ta faɗa bayan ta zauna a bakin gadon sa. "Not at all, ban ban ma fara baccin ba" Sai da ta mishi wani munafukin murmushi kafin ta ce "na zo hira" ta ƙarisa maganar tana ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya. "Barka da zuwa" ya faɗa har lokacin yana tsaye. Ta sa hannu ta ɗan bugi gefenta alamar ya zauna. Yana zama ta kwantar da kan ta a kafaɗar sa ta kamo hannun sa ɗaya ta haɗa da na ta. "Allah ya ja zamanin Zannoon" Ya ɗan ɗago ya kalleta, suna haɗa ido ta ma sa murmushi. "Allah ya ƙara haskaka ƙabarin Mama, sunan da aka ce ta ke kiran ka da shi kenan ko?" "Amin, i miss her " "Kitson ki yayi kyau" ya faɗa yana wasa sa gashin kan ta. "Za ka bada kuɗin kitso kenan" "Ofcourse, dole wannan Makitsiya ta samu tukwuici na musamman" "Ba ka ce Lalle na yayi kyau ba" Hannunta duka biyu ya kamo ya kai saitin bakin sa ya kissing ɗasu ɗaya bayan ɗaya "itama Mai Lalle za ta samu tukwuici" Murmushi Zaytoonah ta yi ta ce " ita kuma wacce aka yiwa Kitso da Lallen fa?" "Tukwuicin ta sai ta gama hutu" yai maganar yana ɗaga ma ta gira. Da gangan yai maganar dan yana so ya ji mi za ta ce. "Oh really!" "Kin san..." saukar bakin ta da ya ji akan na sa ya hana shi ƙarisa maganar da zai yi. Kusan minti biyu suna kissing junan su kafin ya zare bakin sa a hankali ya furta "i guess hutu ya ƙare" Zaytoonah ta sunkuyar da kan ta tana murmushi. A hankali ya fara shafa cinyoyinta wanda a mafiya yawancin lokuta su ke tsole ma sa ido. Ya kwantar da ita kan gadon ya saka hannunsa cikin riganta ya fara wasa da ƙirjinta. Ya kai bakinsa dai-dai wuyanta yana kissing a hankali kafin daga baya ya koma bakinta yana kissing ɗin ta cikin ƙwarewa. Lokacin da Galadima ya sanya harshen sa ya lashi nipples ɗin ta Zaytoonah ta fara ɗauke wuta. Ya jima da ta tsinci kan ta cikin irin wannan yanayi na tsananin sha'awa haka. Ita da kan ta ta cire rigan baccinta dan ta ba shi access na yin wasa da ƙirjinta sosai. Abu biyu ke saurin birkitata cikin ƙanƙanin lokaci wato kiss da kuma tsotsan nipples ɗin ta . Galadima kuma gwarzo ne a wannan fanni. Sai da ya tabbatar ya tanadi guzurin tafiya mai yawa kafin yai addu'ar saduwa sannan su ka ɗau hanya... Justice ne ya fara shiga banɗaki yai wankan tsarki, lokacin da ya fito Zaytoonah na gudundune cikin bargo. Yallaɓai bai ma ta da sauƙi ba gaskiya. "Tashi kiyi wanka, na haɗa mi ki ruwan zafi" Ya faɗa lokacin da ya zauna bakin gado daga shi sai towel da ya ɗaura. "Ai cewa na yi ka jirani mu shiga tare amma ka shige har da kulle ƙofa" " na kulle ƙofa kuma! Princess kunnen ki dai bai ji dai-dai ba" Ta ɗan yaye bargon ta ce "kar ka damu ba zan faɗawa kowa sirrin ka ba" Ta yi maganar tana miƙewa bayan ta samu ta saka robe ɗin rigar baccin ta. Hannunta ya kamo ya ce "zo nan yarinya, wani sirri ki ke nufi" Ta kai bakinta dai-dai kunnen sa ta ce "My Prince is shy" "Waya gaya mi ki?" "Yallaɓai a bar kaza a cikin gashinta kawai" Ya kai hannu zai ɗan maketa ta matsa da sauri tana dariya. Da gangan ta fara tafiya tana girgiza ma sa hips ɗin ta sai da ta kai bakin ƙofa ta cire robe ɗin ta cilla ma sa ta ce "Ir mutum ya gwada" Murmushi yai haɗeda godiya ga Allah da ya shawo ma sa kan Zaytoonah. Zaytoonah na shiga banɗaki ta fara wanka. Idan ta tuno abunda ya wakana tsakanin su sai ta yi murmushi. Gashi dai Justice limami ne wajen sarrafa mace amma ta lura shegen kunya gareshi. Bayan rigar sa da ya bari ta zare bai iya cire wandon ba gaba ɗaya. Da ke wutan ɗakin na su a kunne ya ke saboda ba ta son duhu a cikin bargo aka ƙarisa aikin. Da gangan ta tsokaleshi akan ya jira su yi wanka tare ta ga ya yi wuff ya shige banɗakin harda saka key. Abin ma sai ya ba ta dariya.... Cikin bacci ta ji ana taɓa ma ta ƙirji, ba ta buɗe ido ba sai da jijiyoyin jikinta su ka mimmiƙe suna amsar saƙo. A hankali ta buɗe ido ta ɗaura su akan na sa. "Ke ɗin ta daban ce Adaeze" Ya faɗa da muryan bacci. "Anya ka yi bacci kuwa?" "Ina zan iya bacci, na jima ina haƙuri fa" Murmushi ta yi kafin ta jawo fiskar sa ta haɗe bakin su... Wannan karan bacci ke cinta sosai, tana ganin Galadima na nafilar dare amma ba ta iya miƙewa ba. Ba ta tashi ba sai da Asuba da Justice ya tasheta nan ma da ƙyar ta tashi dan baccin ta jiya rabi da rabi ne. Tana yin sallah ta sake komawa gado ta kwanta. Ta ma manta cewa a ranan za su wuce Abuja. Sanda ta farka ƙarfe tara saura na safe. Justice na zaune gefen gadon yana danna laptop. "Barka da safiya" Zaytoonah ta yi miƙa tareda hamma kafin ta juya ta kalleshi. "Shine ba ka tasheni ba" "Kin ce na tashe ki?" "Amma amma am..." Ya manna ma ta light kiss a goshi ya ce "ki huta abin ki, sai gobe za mu tafi" "I thought kana da aiki yau a office" "Yes, amma ina da wani aiki mai mahimmanci da zan yi yau" Dariya ta saka tana miƙewa daga kan gadon. *** Ganin har yamma Justice bai zo ba ya sa Ghazala ta kira shi ko lafiya, tunda da ya ce ma ta da safe zai taso. Ya ce ma ta ya fasa sai washegari. Ba ta ji daɗi ba dan a tunanin ta ƙila ko bikon Zaytoonah ya tsaya yi. Ita burin ta ma daga wannan tafiyar shikenan Justice ya sallameta kawai. Washegari ko shagonta ba ta je ba ta tsaya shirye-shiryen tarban Maigida. Ƙarfe ɗaya da minti Sha uku na rana Justice da Ghazala su ka iso gidan. Ghazala ta yi wankan shadda milk colour ɗinkin doguwar riga da ya sha aikin hannu. Tana jin ƙaran buɗe get ta ƙara fesa turare ta sauko. Da gudu Hadid da Hashir su ka shigo gidan suna rige-rigen isa falon. Hadid ya ce "mu ga wa zai riga isa ɗakin mu" Nan dukan su biyu su ka haura stairs da gudu saura kaɗan su buge Ghazala da ke saukowa. "Ku yi a hankali please" Muryan Zaytoonah ya doki kunnen ta kafin kuma idon ta yai tozali da ita. Dreba da ya shigo mu su da akwati ta ke wa godiya. Ghazala ta kalleta ta kuma kalli Galadima wanda idon sa ke kan Zaytoonah ƙyam yana bin ta da kallo. "Ki bari Bahijja ko Atika su haura miki da akwatin" "Ai na ga kamar ba sa gidan ne." Ya riƙo hannun ta akan su wuce su bar kayan idon sa ya hango Ghazala da ke tsaye tana kallon dramar da su ke yi. Ta cika ta yi fam. "Hajjaju Makkatun, fatan mun sameku lafiya. Ya Yaran?" Ta yi maganar tana ƙara riƙe hannun Justice da kyau dan ganin Ghazala da yai yana ƙoƙarin sake ma ta hannu ya ji ta riƙe na sa gam. Da ƙyar Ghazala ta tattaro nitsuwar ta ta iya cewa " Sannu da zuwa Abu Razz" Zaytoonah sai da ta kashewa Ghazala ido kafin ta mannawa Justice kiss a kumatu ta ce " My Prince barin duba yaran nan kar su min ɓarna a ɗaki" Sosai ya ji kunyar abinda Zaytoonah ta yi musamman ganin yadda Ghazala ta yi kicin-kicin da fiska. Zaytoonah ta zo ta wuce Ghazala har da gogan kafaɗun ta, ta bar su tsaye da Justice suna kallon-kallo... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 55 Bismillahir Rahmanir Rahim *The Guests* Buɗe ƙofar da ta yi yai dai-dai da fitowar Ghazala daga falon Justice. Sanye ta ke da rigar bacci iya gwiwa. Ghazala fara ce ba chan ba, amma tsawon shekaru da ta shafe tana amfani da mayuka ma su ƙara haske ya sa farinta ya fito sosai. Ba ta da tsayi, sannan ƙibarta dai-dai sai dai ɗan tumbi da ta ke da shi. Kuɗi da hutu sun gyara ma ta jiki sai dai fiskarta da kullum ke cikin shafe-shafen mai da kayan kwalliya ya sa indai ba ta yi kwalliyar ba sai ka ga kamar ta kai shekaru Arba'in da biyar ko fiye amma a zahiri shekarunta talatin da tara ne. Yanzunma rashin kwalliyar ya sa fiskarta yai wani fayau da shi. Suna haɗa ido da Zaytoonah ta yi miƙa tareda buɗe baki tana hamma. "Kai Alhamdulillah! tunda jiki ya kwashi ni'ima daren jiya sai a je a kwanta a huta gajiya" ta yi maganar tana shafa ƙirjinta zuwa tumbinta. Zaytoonah ba ta ce uffan ba ta dai wuce ta sauka ƙasa. Ruwan zafi ta ke son sha saboda mura da ya kamata ba ta son shan ruwan sanyi. Sanda ta koma ɗaki zama ta yi akan gado ta buɗe Tab ɗin ta tana kallon instagram page na favourite interior designer ɗinta wato Kelly Wearstler matar ba ƙaramin burgeta ta ke ba kuma gaskiya ayyukan ta na da kyau. Sabbin hotunan da ta ɗaura ta ke dubawa tana ƙara yabon basirar matar. "Assalamu Alaikum" ya faɗa haɗe da turo ƙofar ɗakin. Chan ciki ta amsa sallamar tana jin wani haushi-haushin sa musamman da ta tuno kalaman Ghazala wai 'jiki ya kwashi ni'ima' Yana zama a bakin gado ta gaishe shi ƙasa-ƙasa ba tareda ta ɗago ba. "Da fatan mun tashi lafiya?" "Lafiya mana, ko ka ɗauka ba zan iya bacci ba ne saboda wata tsohuwar mata da ka ajiye a ɗaki" "Kina kishi na ne?" Ya faɗa yana murmushi. "Allah ya kiyaye" Ya ɗan jin zafin abinda ta ce amma ya dake ya ce " Tunda kin tashi lafiya Alhamdulillah. Ina dai ba kya buƙatar ƙomai?" "Babu" ta faɗa da ɗan ƙarfi. Murmushi yai dan response ɗin ta ya nuna kishi ta ke ji. Dama aka ce kishi kumallon Mata. Yana fita ta ja tsaki ta tashi da sauri ta je ta sawa ƙofarta key. "Wai mun tashi lafiya? Mtsww a'a da zazzaɓi na tashi. Tsoho kawai" "Munafuki, dama na san duk wannan shiru-shirun na munafurci ne. Idan ka ga dama ka cikata mata huɗu ma ni ba damuwa na bane" Haka ta dinga ɓaɓatu ita kaɗai tanayi tana jan tsaki. Ranan da Zaytoonah ta karɓi kwana Justice yai dakon jiranta a ɗakin sa. Ta shigo da yamma ta wanke ma sa banɗaki ta daɗa gyara ma sa ɗaki ta fesa turare wanda hakan ya sa shi jin wani sanyi a ran sa a tunanin sa ta shirya ma sa ne. Sai dai bayan sun gama cin abincin dare da ta wuce ɗakin ta bai sake jin motsinta ba. Kusan ƙarfe goma ya kira wayarta amma ya ji ta a kashe. Goma da rabi ya fito ya nufi ɗakin ta amma yana tura ƙofar ya ji ta a rufe. Bai gwada ƙwanƙwasawa ba juya ya tafi dan ya san da gangan rufe ƙofarta da key. Ya riga ya sawa ran sa akan ba zai takura ma ta ba zai jira ya ga iya gudun ruwanta. Idan haƙurin sa ya ƙare kuma ƙila lallaɓarta zai koma yi dan ya ga alama matar ta sa 'yar lallama ce, kafin a kai ga haka ma ya san za ta gane kuskurenta. Baya ɗaya daga cikin mazajen da ke takurawa matan su a ɓangaren kwanciya. Bai yarda da tursasawa ba, indai ba ka so zai ɗaga miki ƙafa, duk abinda ba ka amince ba aka maka ta ƙarfi tauye hakki ne wannan. *** Ko sati ba a yi ba Ghazala ta fahimce abinda ke faruwa tsakanin Justice da Zaytoonah. Wannan ya sa ta zage damtse wajen tattalin Mijin ta a duk lokacin da ya ke ɗakin ta. Tun lokacin da Justice ya bada sadakin ta zuwa yanzu da ta shigo gidan. Kayan mata na gyara da ta siya aƙalla ba a ƙasaru ba ta kashe ya kai dubu ɗari shida da hamsin. Ta ƙarɓa a hannun mutan Sokoto, Maiduguri da ma wajen mutanen Niger. Indai kuwa babu wannan kusancin tsakanin su ashe dai yin waje da Zaytoonah ba zai ma ta wahala ba... Tana cikin jera abinci a dinning Justice ya shigo gidan. "Ki sameni a ɗaki" ya faɗa kafin ya haura sama. Batareda ta ɗauko sauran ba ta bi bayan shi da sauri. Da ke Jummu'ah ne manyan kaya ya fita da shi office. Lokacin da ta shigo ya ajiye babban rigan gefe tareda hula. "Sannu da zuwa" ta faɗa lokacin da ta zauna. "Ya gidan?" "Lafiya" Kamar yadda ta lura al'adar sa ce fara yin shiru kafin yai magana mai muhimmanci yanzun ma shirun yai. Wai dama haka ma su sarauta su ke da jan aji ne ko dai shi ɗin ne mai ra'ayi irin wannan? Ta ɗan gyara zamanta a karo na kusan huɗu ba tareda ya ce komai ba. Chan da ya gama shirun sai ya ce " akwai manyan baƙi da zan yi gobe, daga Sokoto su ke amma yau za su kwana a Kano sai gobe za su iso nan. Su biyar na ke tsammanin za su zo sai dai idan uzuri ya sa sun ƙaru ko sun ragu." "Allah ya kawo su lafiya" "Akwai kaya da na sa a shigo da shi ki je ki duba ko akwai abunda babu sai a siyo" "Ok" Har ta tashi ta ji ya ce "Adaeze" Ta juyo ta kalle shi. "Za su iya isowa Insha Allah tsakanin ƙarfe shabiyu zuwa biyu na rana haka. Dan Allah a tanadi abinci da wuri" "Insha Allahu" ta faɗa tareda barin falon. Lokacin da ta koma kitchen ɗin ta ga kaya jibge a tsakiyar kitchen da alama Dreba ne ya shigo da shi. Normally dama Atika ko Maman Tope ne za su karɓa su kai store na ajiyewa cikin kitchen ɗin kuma su Ajiye. Sai dai babu Atika a wajen. Da ke ita ke da girki tun huɗu Atika ta gama yiwa ma su aiki abinci ta fita bayan gidan wajen Bahijje. Ghazala dama tun da safe ta fita, ko ina ta je ma dai ba ta dawo ba har yanzu. Dama tunda ta lura Atika ta hannun daman Ghazala ce ba ta cika sakata aiki ba sai dai idan ya zama dole, da Maman Tope kawai ta ke shiri. Ta shiga buɗe kayan tana wawware su sai kuwa ta ci karo da buhu yana ɗan malala jini. Ta buɗe buhun ta ga naman rago ne a ciki an riga an yanyanka. Su hanjin cikin ma an masa wanki mai kyau. "Ya Ilaahi! Ta ina zan fara aikin naman na? " Ta jawo kujera ta zauna tukunna tana tunanin ya za ta yi, da kuma ma irin girkin da za ta yi wa baƙin gobe. Ta sauke ajiyar zuciya bayan ta ga agogo ƙarfe biyar da minti arba'in da shida. Doguwar riga ne a jikinta dan haka taga gara ta chanja shi dan wannan aikin yana buƙatan shiri mai kyau. Komawa ɗaki ta yi ta cire rigan ta saka baƙar T-shirt da baƙin jeans ta saka hula ta fito. Naman ta fara kasabtawa, wanda ba za ta yi amfani da shi ba ta saka a deep freezer. Sauran kuma ta shiga gyarawa... Dai-dai sallan Magariba Ghazala ta shigo gidan. Jin ƙanshin ya gauraya falon ya sa ta wuce direct kitchen dan a tunanin ta Zaytoonah ne ba ta gama girki ba sai kuma ta ga an shirya abinci a dinning table. "Yau take sallah ne, irin wannan ƙaton tukunya haka" Zaytoonah ba ta kula ta ba ta cigaba da kwashe naman da ta silala. Ɗakin Atika ta wuce ta ga ba ta nan dan haka ta kira numbarta. Jiki na mazari Atika ta shigo ɗakin Ghazala. "Ina kuma ki ka je ana abu agidan nan ba ki sani ba" "Ran ki shi daɗe wallahi Bahijje ce ta riƙe ni da taɗi" "Taɗi ko dai gulma" Atika ta yi 'yar dariya. "Mi za ayi ne na ga Yarinyar nan na sarrafa nama dayawa haka" "Gaskiya Hajiya ban sani ba, dan tunda na gama girki na fita" "Ba na son yawon banza baya cikin aikin ki a gidan nan" "Allah ya huci zuciyar ki tauraruwar Galadima" "Haɗa min ruwan zafi zan yi wanka" "Angama Hajjaju" Atika ta faɗa tareda shigewa banɗakin Ghazalar... "Akwai abinda zan taya ki da shi ne?" Atika ta tambaya tana wani yatsina fiska. "Ki je kawai na ma kusa gamawa" "Na ga kamar aikin dayawa" "Ki je kawai" Ko kaɗan ba ta yarda da ita ba balle ta sata aiki. Ranan ta ɗaura miya ta fita da ta dawo ta ga Atikar ta buɗe ma ta tukunya, wai sai ta ce tana dubawa ne dan kar ya ƙone. Ta dai yi shiru ne kawai dan kar ace ta fara. Lokacin da ta zo za ta serving ɗin su abinci duk wani motsinta Justice na binta da kallo. T-shirt ɗin da ta sa ya kamata sosai, kirjinta ya ciko fam. Ga wandon ma ya fito da shape ɗin ta sosai, hips da cinyoyinta sun fito Masha Allah. Bayan ta gama ta goma kitchen ta cigaba da aiki. (Kai a gaida matan gida fa da ƙoƙari, irin aikin emergency ɗin nan akwai cin rai. Barin ma kai ɗaya ne kuma ba ka da mai aiki da za ta taimaka, ko mai aikin irin Atika ce ka ƙwammaci ka yi aikin ka da kan ka). Samosa sheet ta yanka kusan wanda zai kai 50 ko ma fiye. Ta riga ta haɗa fillings ɗin ta ajiye a fridge akan gobe kawai sai dai ta dinga naɗewa tana soyawa. Tana gama wannan ta shiga kwaɓa key lime cake irin wanda ta yi ranan ta ga da Justice da yaran duk sun ji daɗin sa. Falaq da ke da ƙaurin baki ma sai da ta ce "i love this cake" Raziya uwar gayyar ba ta yaba ba amma sauran wanda ya rage washegari ita ta bi shi ta cinye. Lokacin da ta gama komai kanta kamar zai rabe biyu saboda ciwo. Tana shiga ɗaki ta ga ƙarfe shabiyu da minti biyu. Ko kaya ba ta cire ba balle ta yi wanka. Alarm ɗin ta na ƙarfe huɗu da ya tasheta ta kashe za ta koma bacci sai kawai ta tuno ai ba ta yi sallar Isha ba jiya. Da sauri ta miƙe ta shiga banɗaki... Lokacin da ta idar da sallan Asuba bacci ya cika ma ta ido, harta fara ma baccin akan sallaya subconcious mind ɗin ta ya tasheta "Zaytoonah kuna da baƙi yau fa" Ya tunatar da ita. Sai da ta yi wanka da ruwa mai zafi sannan ta shirya ta fito. Tsabar kiɗimewa ko ɗakin Justice ba ta shiga ta gyara ba kawai ta wuce kitchen ta shiga haɗa mu su breakfast a gurguje. Bayan ta gama ta haura sama. Tana shiga falon ta ga Ghazala na zaune kusa da Justice suna magana. Yau dai ranan girkinta ne ba dai a wajen sa ta kwana ba. Abinda zuciyarta ya fara riya ma ta kenan. Kaman ta juya ta tafi sai kuma ta ga idan ta yi hakan ma ya nuna ta damu da su ne. Ko gaishe shi ba ta yi ba ta wuce ɗakin sa. Abu da zuciya, tana kallon gadon sa ya ɗan yamutse kaɗan ta ji wani zafi a ranta. Har ta fito Ghazala na wajen wannan karon kam abu ta ke nuna ma sa a waya. Zaytoonah ta yi wucewarta tareda banko mu su ƙofa da ƙarfi. Maganar wani fili da Ghazalar ta siya da ya ke son jawo rikici ne ya kawota wajen Justice da sassafiya haka bayan ya dawo daga masallaci, domin ya ba ta shawara a matsayin sa na wanda ya san harkan shari'ar ƙasar. Sun riga sun gama maganar amma dan ta ƙula Zaytoonah sai ba ta fita ba ta cigaba da ƙaƙalo taɗi har sai da Zaytoonah ta gama abinda za ta yi ta zo ta fita. Cikin ranta tana faɗin wawuyar Yarinya... Yana karyawa aka kirashi akan Sakataren sa yayi hatsari. Wannan ya sa ya katse cin abincin ya je ya chanja kaya ya fita dubiya duk da ma ance ma sa bai ji ciwo sosai ba. Ta yi miyar egusi, ta yi farfesun kayan ciki, stew ma tun jiya ta yi shi. Ta tuƙa semo ta saka a leda ta jefasu a food warmer. Ya saura farar shinkafa da coselaw da kuma samosa da za ta soya. Tana cikin saka fillings tana wrapping Samosa wayarta ya shiga ringing. Ta duba sai ta ga Muhsinah. Ta amsa kiran tareda saka wayar a speaker. "Zaytoonah dan Allah ki zo" Muhsinah ta faɗa da raunatacciyar murya. "Wannan nishin kamar mai labour. Ni dai na san ko wata shida bai cika ba balle ki ce bakwaini za ki haifa" "Ki zo ki kaini Asibiti zan mutu, i'm bleeding" "Ina Azma?" "Ta tafi makaranta, ba kowa kusa ki zo dan Allah" ta faɗa tareda fashewa da kuka. "Ganinan zuwa, amma kafin nan ki kira ko Baba maigadi ne" Tana kashe kiran ta bar kitchen ɗin da sauri. Ba ƙaramin ruɗewa ta yi ba. Banɗaki ta shiga ta wanke hannunta ta fito ta ɗau hijab ɗin da ta yi sallah da shi tareda handbag ɗin ta. Ghazala ta gani a falo tana magana da Atika da ke durkushe a gaban ta kamar wata Baiwa. Da alama aikanta za ta yi dan ta ga kuɗi a hannun Ghazalar. "Atika zan fita dan Allah idan ban dawo da wuri ba ki soyamin Samosa da na fara haɗawa, sannan ki dafa white rice kamar ciman mutane takwas haka. Akwai baƙin da za su zo." "To" ta faɗa tana tsume fiska. Zaytoonah ta fita da sauri. Dreba ta samu ta ce ya zo ya kaita wani waje... Da gudu ta faɗa gidan lokacin da Dreba ya sauketa. A ɗaki ta samu Muhsina zaune daram a ƙasa ta jingina jikinta ya malale da jini. Tsabar ta yi weak ko iya tashi ta kasa yi. "Innalillahi Mi ya faru?" "Namiji! Namiji!" Abinda ta iya faɗa kenan sai hawaye. Da taimakon Baba Maigadi ta taimakawa Muhsina ta shigar da ita mota bayan ta ɗaura ma ta wani zani tareda tallafa ma ta da saka towel dan kar jinin ya cigaba da tsiyaya. Da motar Muhsinan su ka je Asibiti dan Dreban da ya kawota ya riga ya koma. Lokacin da aka shiga da ita numbar Uncle Aliyu ta fara nema dan har yanzu yana chan America bai dawo ba. Tana gaya ma sa abinda ya faru shima hankalin sa ya tashi tareda cewa zai kira wani cousin ɗin sa da ke Abuja ya zo kafin a zo daga Zaria. Ya ce da zaran Doctor ya fito ta kira shi ta haɗata da shi. Text ta turawa Justice dan ta kira numbarsa bai shiga ba. Lokacin da Likitan ya fito ya ce an tsaida jinin sannan anyi scanning abin cikinta ba ya da rai dole sai an cire an mata wankin ciki. Gaba ɗaya Zaytoonah ta rikice sai kuka... *** Daga Asibiti Justice na shirin komawa gida Baƙin sa su ka kirashi akan sun shigo Abuja dan haka ya ce Dreban sa ya wuce su taro su dan ba su san gidan sa ba. With full confidence Ya shigo gidan dan mutanen da yai aiki da su lokacin yana Sokoto kuma anyi zaman mutunci. Cikin su mutum biyu ne su ka samu zuwa bikin sa da Zaytoonah to gashi bikin sa da Ghazala ma da ba ayi hidima ba basu samu sun zo ba shine su ka kawo ma sa wannan Ziyara bayan sun halarci auren 'yar Abokin su a Kano. Bayan an zauna aka shiga hira. Atika ce ta kawo mu su ruwa da lemu ta ajiye mu su. Ganin ba a ƙara kawowa komai ba ya sa shi miƙewa yana faɗin bari ya kirawo matan na sa. Ɗakin Zaytoonah ya fara shiga amma ba ta nan dan haka ya wuce ɗakin Ghazala wacce ke hakimce akan gado tana latsa waya tana jiran dramar da za ayi yau. "Akwai baƙi da na ce za su zo sun iso ki fito a gaisa. A kuma taho da abinda za a fara taɓawa kafin idan mun dawo daga sallah sai a ci abinci" "Abin taɓawa?, anya Zaytoonah ta tanadi wani abu kuwa" ta faɗa in a concern tune. "Mi hakan ke nufi" "Abu Razz ni dai ban ga alama Zaytoonah ta yi wani abu ba. Kamar dai ta yi jar miya jiya dan na gani a fridge amma ban ce an ƙara da wani abu ba dan tun da ka fita itama ta fita har yanzu kuma ba ta dawo ba" Rintse ido yai yana tunanin minene matsalar Zaytoonah. "Tunda baƙi sun iso kam dole a nemi yadda za ayi dama Atika tana kan haɗa Samosa barin je in sameta mu san mi za a iya yi cikin sauri" Bai amsa ma ta ba kawai ya fice daga ɗakin. Tai ƙaramar dariya tareda miƙewa da sauri. Ta saka hijabi ta fito. Bayan sun gaisa da baƙin ta wuce kitchen inda tuni Atika ta fara soya samosar da Zaytoonah ta haɗa. Bayan minti goma aka kawo mu su lime cake da Samosa da kuma drinks sai soyayyen nama cikin wanda Zaytoonah ta soya jiya. Justice dai ci kawai yai amma ran sa a jagule ya ke, ya dai dake dan kar su gane akwai matsala. Dole sai ƙarya ya mu su akan Uwargida ta tafi gidan rasuwa. Lokacin da su ka tafi sallar Azahar sai da su ka tsaya a bakin masallaci yana jan su da hira duk dan ya ja lokaci har a gama abinci. Yana ganin text ɗin Ghazala ya ɗan ji sanyi a ran sa. Kusan dukkan su farfesu da kuma tuwon semo da miyar agushi su ka fi ci. Mutum biyu a cikin su ne su ka ƙara da shinkafa. Sun yaba girkin sosai tareda addu'ar Allah ya ba da zaman lafiya. Ba su suka bar gidan ba sai kusan ƙarfe biyar na yamma. Bayan sun yiwa Amarya da Uwargida kyautan kuɗi ta hanyar bawa Ghazala envelope guda biyu akan ita da Uwargidan ta. Justice ya so su kwana a Abuja akan gobe sai su wuce amma sun ce ba Sokoto za su wuce ba a Katsina za su kwana. *** Lokacin da Muhsina ta farfaɗo bayan aiki da aka mata ba abinda ta ke sai hawaye. Zaytoonah, Azma da matar Uncle ɗin su da ta zo ma ta sun yi tambayar duniyar nan ta ƙi gaya mu su mi ke damunta. Su Azma sun fi tunanin saboda mutuwar abin cikinta ne amma Zaytoonah ta san its beyond that. Bayan Maghrib Azma ta je ɗebo kaya dan ita za ta kwana a Asibitin tareda Hajiya Firdausi. "Muhsina kina tsoratar da ni minene dan Allah?, mi Abban Habib ya miki" "AbdulHamid ya zalunceni Zaytoonah. Ya ci amana ta" "Miya faru?" Zaytoonah ta faɗa cike da damuwa. "Akwai yarinyar da na ga AbdulHamid ya saka hoton su a status na sa da daɗewa ya ce min wai 'yar ajin su ce tare su ke Phd da ita kuma wai itama 'yar Nigeria ce. Yarinyar Tiv ce amma a Lagos su ke da zama. Ni dai tun lokacin hankalina bai kwanta ba. Wancan zuwan da yai ma dai na ga suna waya and i sense that something is fishy. Na dai ɗauki numbarta a fakaice bai sani ba. Har zan kirata sai na share na ce ba kyau bincike da bin ƙwaƙwaƙwafi" Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "Last week sai na kirata and sai ta tabbatar min wai son AbudlHamid ta ke kuma za ta aure shi. Mun yi musayar magana da ita har ta ke ce min wai ni lusara ce, kuma irin ni'imar da ya ke kwasa a wajen ta baya samu a wajena. Zaytoonah it hurts. "Na dai bar maganar a zuciyata dan na san sharrin Mata. Yau da safe ta turomin video clip ɗin ta da AbdulHamid suna suna..." ta kasa ƙarisawa sai kuka "Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun" "Shock ɗin ne ya sa na ji cikina ya murɗa and the next thing sai jini ya fara zubowa. Na gama da AbdulHamid har abada Zaytoonah, ko shine Autan Maza na haƙura da shi" Zaytoonah kuka kawai ta fara dan ba ta san ma mi za ta cewa Muhsinar ba. Shigowar Hajiya Firdausi ɗakin ya sa dukkan su su ka haɗiye kukan na su... Ƙarfe tara da minti Arba'in da ɗaya Zaytoonah ta yi sallama a falon gidan ta. Justice na zaune yana karanta jarida wanda maganar gaskiya bai ma san mi ya ke karantawa ba. Ghazala na zaune kusa da shi tana kallo. Tunda ta ga ya dake a falon ƙasan itama ta zauna dan ganin ya lamarin zai kaya. Sallama ta yi mu su za ta wuce ta ji ya ce " ina ki ka je?" "Inda na gaya ma ka zan je mana where else?" ta faɗa tareda haurawa stairs ɗin. Tausayin Muhsina, haushin Maza, gajiya, duka ya haɗu ya dagula ma ta lissafi. Ga shi wannan ma zai dameta da ina ta je ?, bayan ta tura ma sa text akan ta kawo Muhsina Asibiti ba lafiya. Ko ya mai jiki bai ce ma ta ba sai tambayar ina ta je. Tana shiga ɗaki shima ya shigo. "Idan ina magana ki ka sake barin wajen ba tareda na baki izini ba za ki sha mamaki a gidan nan" Yadda yai maganar da ƙarfi ya sa ta sha jinin jikin ta. "A wani dalilin kika fita a gidan nan ba tareda kin yi abinda na sa ki ba?" "Dan Allah ka bar ni, ba fa ni ɗaya ba ce a gidan nan. Na ce Atika ta ƙarisa girki zan fita, miye a ciki?. Ko so ka ke na tsaya girki har Muhsinah ta mutu saboda ni na kawo girki duniya. Ku maza kullum kan ku kuka sani. It always about you you you and you" ta yi maganar da tsawa. "Zaytoon!" 2/11/21, 10:04 PM - ****: 59 Bismillahir Rahmanir Rahim *pay back* Hajiya Ghazala dai ta amshi girki ne da hannun hagu. Tayi shiri da zuwan Galadima baƙon wata kuma ya zo ya ma ta sallama. Abu ya zo ya haɗu ma ta goma da ishirin. Kwana biyun da Justice yai a wajen ta kamar ta haɗiyi ran ta dan baƙin ciki. Daga yin yaji shikenan sai Zaytoonah ta dawo da sabon salon bariki. Ranan da Zaytoonah ta amshi girki tana kula da ita dan ta tabbatar da hasashenta na shiryawan ta da Justice. Tun daga irin kwalliyar da ta sha ma ta san an riga an wuce waren kawai. Ba ta taɓa ɗauka Zaytoonah za ta Farga da shiririntanta nan kusa ba. Ba ma a dining table ta serving Justice abinci ba. Chan falon sa ta ajiye ma sa abinci, da ya dawo daga sallar Isha su ka zauna cin abincin, ana ci ana hira. Ghazala na falon ƙasa Zaytoonah ta sauko da kwandon da ta tattare sauran abincin da su ka ci ta kaishi kitchen. Dogon hijab ta saka ajikin ta dan haka ba ta ga kayan da ta saka ba amma yadda hijabin ya lafe ma ta tunanin Ghazala biyu ne, ko dai Zaytoonah ba ta sa komai a ciki ba ko kuma abinda ta saka ɗin bai kai ma cinya ba. Zaytoonah da ta fito yaran ta da ke kallo ta tattare ta tisa ƙeyar su zuwa ɗaki. Bayan sun yi brush ta sa mu su kayan bacci, ta bita mu su addu'ar bacci sannan ta fito daga ɗakin ta wuce turakar Mai gida, tana shiga ta saka key ta kulle ƙofar falon dan da za ta shigo ta ga Ghazala ta fito daga ɗakin ta tana bin ƙofar falon da kallo. Kusan har ƙarfe shabiyu Ghazala na jiran ta ga Zaytoonah ta fito daga sashen Galadima kaman yadda ta saba amma shiru ka ke ji kaman Shaho ya ci Shirwa. "Shegiyar Yarinya, wanda ya ba ta shawaran ta gyara halinta bai yi ba wallahi" Ghazala ta faɗa tana jan tsaki. Tana mugun kishin Zaytoonah amma tunda ta gano zaman doya da manja ne tsakanin su da Justice ta ɗan sassauta kishinta, to yanzu kuma Zaytoonah ta farka daga baccin da ta ke yi. Baccin kirki ba ta iya yi ba ranan... Sati uku kenan da dawowar Zaytoonah gidan, yanayin zaman gidan ya chanja salo. Shi kan sa Justice yanzu ne ya san yana auren mata biyu. Ta ko wani fanni shi ɗan gata ne. "Abu Razz inada magana" "Ina jin ki" ya faɗa yana cigaba da cin abinci. "Ni tun da ka min magana akan 'yan biyu ina tsoron saka baki akan harkan Zaytoonah. Kamar ba ka so a faɗi aibunta. "Idan na yi shiru ni zan cutu shiyasa na ce dai gara na maka maganar dan ko za ka iya yi ma ta bayani dan ta ɗau mataki saboda lafiyar mu gaba ɗaya" Yanzu kam ajiye cokalin hannun sa yai ya maida hankalinsa kan ta yana sauraren ta. "Dama kwana biyun nan idan muna tare na kan ɗan ji zafi-zafi haka. To sai na kira Likita na ma ta bayani sai ta ce na zo a min gwaji. To daga Shago jiya sai na wuce Asibitin aka min gwaji aka kuma tabbatar min da infection ne, irin infection da ake samu wajen saduwa. An rubuta min magani kuma na siya. "Na ce Dear mi zai hana itama Zaytoonan ta nemi magani sannan ko za ka ɗan yi haƙuri da ita na ɗan wani lokaci zuwa dukkan mu mu samu lafiya. Ka san ance idan ku biyu ne a wajen Miji idan ɗaya tana shan magani ɗaya ba ta sha kaman a banza ta ke yi dan za ta ƙara samun sa" "Idan mun gama cin abinci sai ki kawo min maganin na gani" ya faɗa bayan ya sauke numfashi. Bai wani ƙara abincin ba ya tura plate ɗin gefe ya ce ya ƙoshi. Bayan Ghazala ta tattara wajen ta je ta ɗauko magungunan da ta siyo. Da gasken dai maganin infection ne amma dalilin siyo su ne dai wannan kam ita ta barwa kan ta sani. Justice ya duba maganin ya karanta su ya ga tabbas dai maganin infection ne. Still dai sai ya ji gara ya ƙara bincike a kai. Wani ƙanin sa da su ke Uba ɗaya ya kira wanda shi Likita ne ya tambayeshi gameda infection. Bayanin da ya ma sa ya sa shi yarda da maganan Ghazala. Washegari ya kira Zaytoonah falon sa inda a fakaice ya ma ta tambayoyi gameda infection ta amsa ma sa dai-dai abinda ta sani. Daga nan ya faɗa ma ta maganar Ghazala tareda nuna ma ta cewa ita ɗin ma gara ta je Asibiti a duba ta. Bai yi gigin faɗa ma ta shawaran Ghazala ba dan shi kan sa ya ji batun Ghazalar ne ba iya aiwatarwa zai yi ba. Yaushe ma ya fara biyan bashin da Zaytoonah ta ɗauka. Ƙaramar dariya Zaytoonah ta yi bayan ta gama jin bayanan sa sannan ta ce "My Prince inaga dai..." Shigowar Ghazala falon ya sa ta yi shiru tana bin matar da kallo. Yau dai kwanar Ghazala ne shiyasa da ta ji Suhailah na faɗawa Maman Tope cewa Anty Zaytoonah na falon Daddy ba shiri ta hauro saman dan ba za ta lamunci wannan shishshigin ba. "Yawwa 'yar halak. Hajiya Ghazala yanzu na ke jin abinda ya faru a wajen My Prince" Wani ƙululu Ghazala ta ji a cikinta jin sunan da Zaytoonah ta kira Galadima da shi. Ta tsani shegen sunan da ta kakaɓa ma sa tun dawowar sun nan. Mutum kamar Galadima ta wani zaƙe tana kiran sa My Prince kamar wani saurayi. "Sannu ya jiki ɗin?. Ai wallahi infection mugun ciwo ne, ba ƙaramin kassara Mace ya ke ba. Allah ya yaye miki" Ghazala ta zauna gefen Galadima tana kallon yadda Zaytoonah ke ma ta magana da shaƙiyanci. "Kema ya kamata ki fara karɓan magani dan ance zai iya shekaru a jikin mutum ba tareda ya gane ba. Kinga idan kika magance na ki dukkan mu mun tsira" "Ashe! Well, sorry ehn. Na gode da kulawar ki sai dai ni ba ni da wata matsala infact the last check-up da na yi na bawa My prince report ɗin" Ta kalli Justice ta ce "Love, ba na baka result ɗin da na karɓo ba?" Galadima ya ɗan yi gyaran murya dan yanzu ya ke gano cewa akwai wata a ƙasa gameda maganar. "To kin gani. Ba ni da komai, garau na ke, ko My prince zai shaida hakan. Tunda dai ke ce ke da symptons na infection sai a cigaba da shan magani zuwa lokacin da Allah zai kawo sauƙi" Ta ɗan yi ƙasa-ƙasa da murya ta ce "idan za ki ci girma ma zuwa lokacin da za ki warke sai na amshi duka girkin kin san lafiya ya fi komai..." "Girman Uwar ki" Ta faɗa da ƙarfi. "Ghazala" Galadima ya kira sunan ta "Ka yi haƙuri ranka shi daɗe. Rainin hankalin yarinyar nan ne yai yawa" "Ni fa shawara na kawo, kuma dan sati biyu zuwa uku da za ki yi ta shan maganin ai ba komai ba ne dan na rage miki aiki. Infact maganin ma zai fi yin aiki sosai" "Riƙe shawaran ki. Da magani ko ba magani zan iya kula da My Dear" Justice yai murmushi dan sai yanzu ya fahimci komai. Kishi kumallon Mata. Zaytoonah ta miƙe tsaye ta ce "Allah ya ƙara lafiya Hajiya amma a dinga kula da amfani da banɗakin shago ɗin nan dan na san daga chan kika ɗebo. Allah dai ya yaye miki" Ba dan Justice na wajen ba da Ashar za ta yiwa Zaytoonah. Har ita za ta yiwa maganar banza, ko an gaya ma ta ƙaramin shago gareta... *** Justice na zaune yana duba report card ɗin Raziya Zaytoonah ta shigo falon da sallama. "Raziya you barely got 40marks in Mathematics. Miye matsalar ne?" "Daddy i tried my best amma Allah ba na ganewa" "Extra lesson da ki ke ɗauka duk a banza kenan" "No Daddy..." "Ke ki ka zaɓi science class and Mathematics is a core subject, but with this performance gaskiya ki ƙara ƙoƙari" Zaytoonah ta ce "Na ga result ɗin" Justice ya miƙa ma ta ta amsa tana dubawa yayinda Raziya ta haɗe rai. " physics 54% and Maths 40%. Kin yi ƙoƙari sosai Raziya. Ban yi Physics ba a school but Maths, i can help you with that" "Dont bother, ina zuwa extra lesson" "Raziya!" Ya daka ma ta tsawa "Yi haƙuri Yallaɓai" ta faɗa tana kamo hannun sa. "Raziya wannan hutun zan coaching ɗin ki akan basic Mathematics. With that ba za ki samu matsala ba Insha Allah. Kwana huɗu a sati ya mi ki?" Raziya ta watsawa Zaytoonah harara ganin hankalin Justice yana kan waya. "Kwana ɗaya ya isa" ta faɗa fiskarta a haɗe "5 days Raziya, and ban da rashin kunya" "Daddy" "Je ki adana result ɗin a file ɗin ki" "Yes Dad" ta faɗa tareda karɓan result ɗin a hannun Zaytoonah. Sai da ta fita Justice ya kamo hannun Zaytoonah ya ma ta kiss ya ce "Na gode" Zaytoonah ta yi murmushi ta ce "My prince kar ka damu Insha Allah zan yi ƙoƙarina a kan ta"... *** "Hello" ta faɗa lokacin da ta amsa kiran baƙuwar number mai code ɗin ƙasar America "Zaytoonah" "Ya Allah! Muhsinah ya ki ke. Ya su Daddy" "Mu na nan lafiya. Ina 'ya'ya na?" "Sun tafi Islamiyya" "Kwana biyu 'yar uwa, ya ki ke? hope kuna zune lafiya da kishiyar ki" "To gamu nan dai, kin san mi ta yi kwanan nan. Wani sharri ta zo da shi wai tanada infection kuma daga wajena aka samu" "Haba!" "Wallahi. That crazy woman actually thinks i'm stupid fa" "To ai ke ki ka ba ta dama" "A da kenan yanzu na yi hankali" Muhsinah ta kwashe da dariya. Sai da ta gama ba ta labarin yadda su ka wanye da Ghazala kafin ta sako ma ta tambayar da ta sa Muhsinar ɗauke wuta. "Maman Habib ki koma dan Allah. I know its not easy but forgive him please" Sai da ta yi kusan 30 seconds kafin ta sauke numfashi ta ce "i cant Zaytoonah. Ba zan iya ba, its over" "Kin zaɓi ki rabu da shi har abada kenan. What about your kids?" "Ba zan iya ba" ta furta tareda kashe wayar. Sosai Zaytoonah ta ke tausayawa Muhsinah. Rabuwa da Miji ba abu ne mai sauƙi ba especially idan kana son shi. Despite the fact AbdulHameed ya ƙi ya saketa, Muhsinah ta rantse ba za ta koma ba, bayan ta warke tattarewa ta yi ta koma America wajen Baban ta. Yaran kuma na nan wajen Kakannin su. Shigowar Justice ɗakin ne ya katse ma ta tunani. "Ba dai fita za ka yi ba?" "Za ki yi missing ɗina ko" "Na ga ba ka jima da dawowa ba ne" "Jiya ya kamata na je na yi yankan farce amma na manta, yau ma sai da na shigo na tuna" Ta sa hannu a kafaɗun sa tana faɗin "wannan Tsoho ba dai mantuwa ba, anya idan ka fi haka ba da sanda za mu haɗa ka ba" Ya ɗaura hannun sa a ƙugunta ya jawota jikinsa ya ce "idan ke ce 'yar jagorar i dont mind" Dariya ta yi tana faɗin ba zai ma kai haka ba. "Na iya yankan farce fa. If you dont mind i could do it for you" "Ofcourse Sweetheart" Ta kamo hannun sa ta zaunar da shi kan kujera sannan ta ɗauko kayan aiki tareda ƙaramar towel. Ta zauna ƙasa ta ɗaura ƙafarsa akan ƙafarta ta fara yanke ma sa farcen. "Ka san a ina na koyi aikin nan?" Ta tambaya lokacin da ta gama ƙafa ɗaya ta fara ɗaya ƙafar. A zaton sa sunan mijin ta za ta kira sai ya ji ta ce "A ƙafar Daddy na" ta yi murmushi ta ce "Mommy ce ke ma sa, sai ranan su ka yi faɗa, dan ya ƙula ta sai ya kirani ya ce na ma sa. The truth is ya sha yanka a wajena ranan. But still bai haƙura ba, ya ce dole sai ni zan ƙarisa ma sa. "Daga nan kuma ya maida shi permanent ni ke ma sa yankan farce, tun ban iya ba har na ƙware" Hawaye ne ya fara zubo ma ta ta yi saurin gogewa amma ina tana gogewa wani na bin wani. "I miss him" ta faɗa lokacin da ya jawota jikin sa. Sun jima a haka kafin ta janye jikin ta ta ce bari ta ƙarisa ma sa yankan. *** Wannan karan dukkan su suka je weekend Zaria. Tun ranan Alhamis su ka tafi, ranan Jummu'a akwai Public holiday da aka bayar na Maulidi shiyasa dukkan su su ka taho tunda ba aiki sai ran Talata. Ranan Jummu'ah ya kama ranan kwanan Ghazala, da ke Galadima ya ba da umurnin ayi abincin sadaka gaba ɗaya aka haɗa hannu ake yi. Suna cikin aiki, sauran ma su aiki aka fara taɗi ana habaici ƙasa-ƙasa. Da farko Zaytoonah ba ta gane da ita ake ba sai da ta ji Baaba Nafy ta ce "ku ji tsoron Allah. A wajen mu matsayi ɗaya su ke da shi tunda dukkan su ƙarƙashin inuwar Yallaɓai su ke" Baaba Nafy ba sa'ar su ba ce dan ko Ghazalar za ta ba ta kusan shekaru shatakwas zuwa ishirin. Zaytoonah ta ɗago ido ta kalli Ghazala da ke yanka cabbage sai wani murmushi ta ke yi. Kamar za ta yi magana sai kuma ta yi shiru dan biye mu su ma ɓata lokaci ne, dan ba girmanta ba ne. "Ai ba mu san Yallaɓai ya yi aure ba sai da haske ta shigo gidan nan, tauraruwar Galadima Allah ya ja zamanin ki" Wata mata ta faɗa wanda ko sunan ta Zaytoonah ba ta sani ba. "Allah ya kawo Magajin gida nan da wata tara Amin" Murmushin fiskar Ghazala ya ɗauke ɗif kamar ɗaukewar wutan NEPA. Zaytoonah ta kauda kan ta kamar ba ta ji abinda aka faɗa ba. Abubuwa da dama su ka dinga yawo a kwanyar Ghazala. Maganar Magaji ya taɓa ta sosai, ba wai ta wuce shekarun haihuwa ba ne amma kuma propability ɗin samun ciki is very low compared to Zaytoonah wacce yanzu ne ma ta cika shekara ashirin da huɗu a duniya. Idan ba ta manta ba haihuwar ta na biyu ta yi allurar tazarar haihuwa saboda lokacin ba ta son cigaba da haihuwa da Alhaji Bashir. Shekara ɗaya da yin hakan ma ta rabu da shi. Suma ma su yiwa Ghazala kirarin da su ka ga ta haɗe rai sai su ka yi shiru... Yau tun safe ba su da wuta, kamar wutan anguwar ta su ne ta samu matsala. Tun ƙarfe biyar na yamma aka tada generator ya ke ta aiki. Ƙarfe takwas na dare Zaytoonah ta shiga wanka. Yau kwanan ta ne, zuwa ƙarfe tara ta san Galadima zai dawo daga Fada. Ta fito daga wanka tana shafa mai Generator ya mutu. Da sauri ta fara laluben wayan ta dan ta haska ɗakin kawai wayar ta faɗi ƙasa, ta tsugunna ta lalubo wayar tana ƙoƙarin kunna shi kawai ta ji kamar an taɓa ma ta baya nan da nan ta ƙwalla ƙara, jikinta ya fara ƙyarma. "Ben dont kill me, please dont kill me" Ta faɗa tana yin baya-baya saboda Ben kawai ta ke gani a idonta yana riƙe da bindiga. Raziya da Hajiya Ghazala ne su ka shigo ɗakin da gudu. "Zaytoonah" Ghazala ta kira tana haskata da wayarta. "Zuhayr help me, save me D, save me" abinda ta ke faɗi kenan har lokacin jikinta na ɓari. "Anty Zaytoonah" Raziya ta faɗa tana matsawa kusa da ita. "Raziya ki matsa ƙila Aljanu gareta. Je ki kira Baba Maigadi a zo ma ta ruƙiyya" Ta faɗa tana janye Raziya daga wajen. Dukkan su fita su ka yi daga ɗakin su ka bar Zaytoonah a wajen tana cigaba da sunbatu. Raziya ta yi ƙasa da gudu yayinda Ghazala ta shiga kiran numbar Justice. Ɗaya daga cikin dogarai ma su tsaron gidan Raziya ta samu ta gaya ma sa ya zo inji Ghazala, Aljanun Zaytoonah sun tashi. Da farko ya so ƙin shiga dan iyakar sa tsakar gidan sai kuma falon Justice da ke ƙasa idan ya buƙaci ganin su. Sai dai yadda Raziyan ta ke magiya ya sa shi bin bayanta da sauri. Yana shiga ya tadda Ghazala a falon ƙasa tana waya. "Wallahi hauka tuburan ta ke yi Hajiya. Yanzu dai na sa an kira dogari zai ma ta ruƙiyya" Daga ɓangaren Hajiya Abu ta ce "Kul, banda wannan ganganci. Kar namijin da ya shiga wajen ta. Ku dai bar ta a ɗakin zuwa Galadima ya iso" Ghazala ta amsa da toh. Cewa dogarin ta yi ya tsaya a wajen zuwa Galadima ya iso saboda kar Zaytoonah ta fito ta mu su wani abin. "Hajiya su Falaq na ɗaki" "Na tura Baaba Nafy wajen su" Ai ba ta tsaya jin maganar ba ta haura saman. Ganin ɗakin Zaytoonah a buɗe kuma tana jin muryan su Hadid ya sa ta wuce wajen. "Mom its me Hadid" "Mom please ba kowa a nan mu ne kawai. Ni da Hadid ne" Zuwa lokacin ɗakin ya ɗau haske saboda torchlight da kuma wayar da Baaba Nafy ta kunna. Tana haurowa sama ta samu 'yan biyu da Falaq a ɗakin. A hankali Zaytoonah ta fara sauke numfashi ganin da gaske dai 'ya'yanta ne a gaban ta... Da sauri-sauri Galadima ya shigo gidan har lokacin Ghazala na zaune a falon ƙasa. "Ina ta ke?" Ya faɗa da ƙarfi. Ɗakin ta. Yana wucewa itama ta bi bayan shi da sauri. Lokacin Zaytoonah ta samu nitsuwa, tana zaune a kan gado sun sata a tsakiya. Shigowar sa ɗakin ya sa Baaba Nafy ta ja hannun Falaq da Raziya su ka bar ɗakin. "Are you Ok" "I'm sorry" ta furta a hankali. "Sannu ya jikin?Baaba Nafy ne ta miki ruƙiyya?" Irin kallon da Justice ya watsa ma ta ne ya sa ta yi shiru. Ta juya ta fice daga ɗakin... Bayan ya lallaɓa Zaytoonah ta yi bacci tukunna ya fito ya hau ma su aiki da masifa kan ta ya za a bari generator ya mutu, duk da zuwa lokacin an gyara amma a hakan sai da yai ta faɗa. Su kan su sun yi mamakin wannan faɗan dan ba halin Galadima ba ne. *** Tana tsaye a wajen sink tana wanke-wanke ta ji ana ƙwanƙwasa mu su ƙofa. Sunan Junior ta fara kira amma tuni yayi bacci a falo. Jin shiru ya sa ta fito falon da zimmar ta ma sa faɗa ƙila kallon da ya sa a gaba ne ya sa bai ji kiran na ta ba. Ganin yana bacci ya sa ta wuce ɗakin ta ta ɗau mayafi ta yafa sannan ta fito. Wanda ta gani tsaye bayan ta buɗe ƙofar ne ya sa ta zaro ido waje. "Muntari" ta furta a bayyane 2/11/21, 10:04 PM - ****: 60 Bismillahir Rahmanir Rahim *Revelation* "Maryam ba za ki ba ni ko ruwa ba" Muntari ya faɗa yana murmushi wanda ya bayyana korayen haƙoran sa. Tunda Mommy ta bashi dama ya shigo falo ta kasa ɗauke ido akan sa. Ya rame ya zabge yayi duhu sosai, kallon ɗaya za ka ma sa ka danganta shi da mai cutar ƙanjamau wanda ciwon ya ci shi sosai. Wannan jiki lub-lub da ya ke da shi a lokacin da ya ke amsa sunan Alhaji Muntari babu shi yanzu. Idan ba farin sani ka ma sa ba da ka kalleshi sau ɗaya ba za ka ce shi ɗin ba ne, ga uwa uba furfurar wahala da ya dabaibaiye ilahirin gashin kan sa zuwa gamun sa. A iya sanin ta saura shekaru biyu a sake shi amma... "Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zan iya yi" Maganar sa ya yanke tunanin da ke. Jiki a sanyaye ta miƙe ta wuce kitchen. Abincin Salman da Auwal da ta ajiye ta ɗauko ta saka a faffaɗan tray da su ke haɗuwa su ci abinci. Ta ɗaura plate da sokali akai sannan ta buɗe fridge ta ɗauko ruwan gora mai sanyi ta ɗaura akai tareda kofin glass. Ta ɗauko tray ɗin ta ajiye a centre table ta jawo table ɗin gaban sa. "Bismillah" ta faɗa tana zama kusa da Junior da har lokacin ke bacci. Cire hannun sa daga tagumin da yai yayi sannan ya buɗe food warmer ɗin haɗe da ɗauko plate ɗin ya fara zuba jollof ɗin shinkafa mai kyau da ya ji kayan lambu da kuma nama da hanta wanda aka yanka ƙanana. Mommy hannun sa ta ke dubawa yadda ya koma, har wani kaushi-kaushi ne a jikin yatsun hannun na sa. Yadda ya ke kai loman abincin da sauri ka ce ya yi wata bai sa abinci a baki ba. Tabbas akwai yunwa a tattare da shi. "Ikon Allah" ta faɗi a ranta tana tuno wasu shekaru da Muntari yai ma ta dirar mikiya a wannan gidan wanda daga nan ne komai ya chanja mu su. A wannan lokaci ya zo a matsayin Alhaji Muntari amma yanzu sai ga shi nan a miskini dan ko Almajiri ya fi shi daraja. Duniya kenan. Bayan ya gama cin plate ɗaya sai da ya sake cikawa ya ci kafin ya ɗau goran ruwa ya kwankwaɗa. Zuwa lokacin kuwa babu wanda yai magana tsakanin su. "Gidan nan ya chanja sosai, da ƙyar na iya gane shi" ya furta lokacin da ya ajiye goran ruwan. "Anyi sauye-sauye dayawa a gidan kam" "Abinci yayi daɗi sosai, na gode" Mommy ba ta ce komai ba sai dai ido da ta bishi da shi tana karantar yanayin sa. "Ina 'ya'ya na Zaytoonah da Salman. Wannan shine Mai sunan Baffa ko?" Ya faɗa yana nuna Junior "Suna nan lafiya" "Allah ya mu su Albarka, ya ƙara mu su danƙon soyayya da zumunci Amin" Amin Mommy ta faɗa a ƙasan ran ta. "Baby tana wajen Hanne ko?" Ashe dai ya tuna cewa yanada 'ya ɗaya tilo a duniya. "Eh, ta kan kawo mana ita idan sun yi hutu" "Humairah ta yi aure ne?" Mommy ta gyaɗa ma sa kai. "Ba ka je gidan Iya ba ne?" Dariya ne ya suɓuce ma sa wanda Mommy ta tsorata da yanayin sa. Daga tambaya sai dariya. Yana dariyan kuma sai ga hawaye sun fara zubo ma sa, daga dariya sai ya koma kuka. Abin sai ya ɗaurewa Mommy kai musamman da ta ga zahiri dai kuka ya ke bil haƙƙi. "Muntari ko ma minene ka yi haƙuri dan Allah. Kuka ba zai yi maganin komai ba" ta faɗa dan yanzu kam tausayi ya ba ta. Ya jima yana kuka kafin daga baya ya goge hawaye ya kalli Maryam ya ce " ban ɗauka zan yi rai ba Maryam. Ina gani Allah ne ya bani dama ta ƙarshe domin na tuba na gyara kura-kurai na" Haka ya zayyane ma ta irin wahalhalun da ya sha a prison ɗin da aka kaishi a Warri da ke Jahar Delta. Gabannin a sake shi yayi rashin lafiya sosai. Typhoid ne ya ma sa mummunan kamu har ta kai sai da aka fita da shi Asibiti dan ƙaramin clinic na prison sun kasa treating ɗin sa. Bayan ya warke da aka dawo da shi prison ko wata uku bai yi ba aka saka sunan sa cikin mutanen da shugaban ƙasa ya mu su alfarma aka sake shi. Da ya fito daga prison ba shi da komai hakan ya sa sai da yai dako na kusan sati uku kafin ya samu kuɗin mota zuwa Kaduna daga nan kuma ya ƙariso Zaria. Kai tsaye gidan Mommy ya zo dan nan ɗin ya ga ya dace ya je duk da ba shi da tabbacin ko har yanzu suna nan ɗin. Yadda gidan ya sha gyara ya chanja fasali kwata-kwata bai gane ba dan dai yaron da ya rako shin ya tabbatar ma sa cewa nan ɗin ne gidan Malama Maryam, Maman Salman. Mommy sai da ta yi hawaye jin labarin sa. Tunda aka ɗauke shi daga Prison ɗin Kaduna dama ta san akwai abu a ƙasa. Ba ta sanar da shi badaƙalar da Alhaji Rabi'u ya ke da dukiyar sa ba balle walaƙancin da ya yiwa su Iya. Bayan ya ɗan nitsu ta ce zai fi ya je ya duba Iya saboda itama hankalin ta ya kwanta. Bai musa ba dan ya ga alama a takure ta ke da shi. Junior da ya riga ya tashi tuntuni ta sa ya raka Muntari zuwa gidan Iya. Da ke sanda aka ɗaure Muntari yana ƙarami bai iya tuno shi ba. Suna fita daga gidan ta kira Auwal ta ce dan Allah ya dawo gida yanzu akwai baƙo mai muhimmanci da ke jiran sa. *** "Zannoon" ta kira sunan sa a hankali. "Ba ka ce komai ba" "Adaeze tambayar da ki ka yi ya dace. A ganin ki ya dace?" "I'm confused. Dr Malak ta ce a hankali zan samu lafiya amma har yau abu ɗaya na ke. May be gaskiyar Hajia Ghazala da ta ce ciwon hauka gareni, may be its true that i'm crazy" "Kar ki sake kiran hauka wa kan ki ba na so" "Ka yi haƙuri amma..." "Shshshsh" ya faɗa bayan ya ɗaura yatsarsa ɗaya a bakin ta. "Kamata yai ki biya bashin jiya ki tanade ni amma kin tsaya surutu" Kissin yatsar sa ta yi tareda faɗin "bani minti biyu na shiga banɗaki, zan zo na tanadi Tsoho. Yau tanadi na musammamn za ayi" Ta faɗa tana tashi daga kan gadon. Bayan ta fito daga banɗaki Galadima ya miƙa ma ta waya akan Mommy ta kirata har sau biyu. Karɓan wayan ta yi ta zauna tareda dialling numbar wanda ringing ɗaya aka ɗauka. Bayan sun gaisa Mommy ta ce ma ta idan da hali ta tambayi Galadima ya barta ta zo gida. "Mommy lafiya?" "Lafiya Zaytoonah. Akwai baƙon da mu ka yi ne kuma ya kamata ku gaisa kafin ku koma Abuja. Ina goben za ku tafi?" "Ok zan tambayeshi" Tana ajiye wayar ta juya ta kalli Justice da ya haɗe rai. "Haba shalele na, wannan fiskar ai ta waje ce ba ta ɗakina ba" Ƙarisowa ta yi wajen sa ta manna ma sa kiss a goshi, hanci kafin ta sauka kan bakin sa nan da nan kuma ya amshe ya shiga kissing ɗin ta shima. Sun yi nisa cikin kula da juna su ka tsinkayi knocking ɗin da ake yi. "Daddy Hajiya Babba ta zo" Rigan ta da Justice ya ɗage yana wasa da ƙirjinta ta saukar tana kallon yadda ya ke cize leɓe abinda ya ke mafiya yawan lokaci idan ya ji haushin wannan abu. Hajiya Abu ba baƙuwar da zai ajiye ba ne shiyasa ma ta fara kimtsa kan ta. "Da gaske dai ba za a tanade ni ba" "Safiyar yau dai babu rabonka" ta faɗa tana dariya. "Za ki shigo hannu Yarinya" ya faɗa tareda miƙewa. Banɗaki ya shiga kusan minti shida sai gashi ya fito. Zuwa lokacin Zaytoonah ta gyara gadon na su da ya ɗan fara yamutsewa. "Na je Wajen Mommyn ?" "Idan Hajia ta tafi sai ki je" ya amsa ma ta kafin ya fice daga ɗakin... Magana ce dai akan abinda ya faru jiya ya kawota.. Ko miye na ta a ciki idan ma Zaytoonah na da Aljanu oho. Tambayar gaskiyar zance ta yi dan a tunaninta idan har da gaske Zaytoonah na da Aljanu to kuwa dole a nema ma ta magani tun kafin ta shafawa yaran sa. Shiru ta yi na kusan minti biyar tana tace maganganun da Galadima ya ma ta akan Zaytoonah. Karon farko da ta ji tausayin ta kenan. "Amma ana warkewa?" Ta tambaya bayan dogon shiru. "Sosai ma, Insha Allah itama za ta warke , ina so idan har Allah ya kaimu hutun ƙarshen shekara zan sake kaita wajen Likita" "Allah ya ba ta lafiya" Ya amsa da Amin. Sun ɗan jima suna hira kafin daga baya Zaytoonah ta sauko su ka gaisa. Har da yi ma ta ya jiki. Da ke Ghazala ta je Fada sai ya zamana suna gaisawa Hajia Abu ta tafi. Bayan tafiyar Hajiyar da minti talatin itama ta shiga mota Dreba ya kaita gidan su... *** "Mommy da gaske Uncle Muntar ya zoi" ta maimaita a karo na uku. "Idan ba ki yarda ba yana gidan Iya ki je ki tabbatar wa idon ki" "Mommy i'm just surprise. Ni fa har na manta da shi, idan ba Baby na gani ba ma kwata-kwata mantawa na ke da shi a duniya" "He's alive and free. Ki je ku gaisa dan ya tambayeki" "Mommy anya zan iya zuwa inda ya ke after all he did to you" "Ba na son shirme, he's a father to you Adaeze. Abinda ya min bai shafe ki ba, ki je ku gaisa Salman na chan" Bayan ta gama ƙunƙunin dai dole ta tashi ta fita zuwa gidan. Zaytoonah kam kallon farko tsorata ta yi da Uncle Muntari wanda ganin ta ya sa shi waƙe haƙora. A iya sanin da ta yi mi shi za a iya cewa yanzu ya koma kashi ɗaya cikin huɗu. Kallo ɗaya tsoho mai shekaru tamanin zuwa casa'in za ka bashi. Ko Alhaji Iliyasu da ya bawa shekarun casa'in baya bai yi wannan tsufa da lalacewar ba. "Banda kuka Gimbiya, zo na ji ɗumin ki" Zaytoonah ta ƙarisa wajen da ya ke zaune bayan ta share hawayen da ya sauko ma ta. Lokacin da ya rungumeta ta ƙara tabbatarwa cewa Uncle Muntatrin dai ƙashi da rai ne. "Allah ya bayyana mana Shehu, ya kawo mana shi gida lafiya kamar yadda ya fidda ka Muntari" Iya ke wannan maganar tana ƙara sabon kuka. Sosai maganar ta daki Muntari tunowa da yai cewa shine silar rugujewar farin cikin waɗannan yaran. Ɗaya bayan ɗaya ya fara kallon yaran ɗan uwan na sa, ga su nan mata biyu maza biyu Masha Allah. Ta ina zai fara ba da wannan mummunan labari, ta ina zai fara bayyana mu su cewa kishi, ƙiyayya da son zuciya ya sa shi jefa Mahaifin su duniya. Dole ne ya faɗa mu su gaskiya amma ba yanzu ba, ba yanzu da su ke marmarin ganin sa ba. Idan har ya faɗi komai ba makawa tsanar sa za su ji. Har Mahaifiyar sa da kukan daɗin ganin sa sai ta tsine ma sa. Ya sauke nannauyan ajiyar zuciya tareda maida kallon sa ga Salman wanda ba inda ya baro Yayan na sa. May be because he's feeling guilty sai ya ke gani kamar Tijjani ke zaune a wajen. Ƙuruciyar su ya tuno irin kyakykyawan zuciya ta Tijjani, kyakykyawar zuciyar da a yau shi kaɗai ya ke kwaɗayi. Ina ma yana da ita, da duk wannan abubuwa ba su faru ba. Sai dai ƙaddara ta riga fata... Auwal da Iya su suka bayyanawa Muntari abinda Alhaji Rabi'u yai da dukiyar sa. Bai kawo komai ba sai sakayya, sakayyar abinda yai ne ke bibiyar sa shiyasa dukiyar ta sa ma ta faɗa hannun banza. Amma fa ba zai bari ya shige haka ba, taɓa mutuncin mahaifiyar sa da iyalin sa ya fi ma sa komai ciwo fiye da dukiyar da ya kwashe. Ranan bai iya baccin kirki ba saboda tunanin ta inda zai fara tunkaran lamarin. Kwana uku yai yana juya lamarin kafin ya tsaida matsaya guda. Da yamma ya wuce gidan Mommy dan ya sanar da ita ƙudurin sa. Bayan sun gaisa ya tambayeta yaushe Hanne ta ce za ta turo ma sa 'yar sa. "Gobe Jummu'ah za su zo weekend zan sa Salman ya je ya ɗauko ta. Baby ta zama 'yan ma ta sai ka fara tanadin kuɗin ɗaki" Murmushi mai ciwo yai kafin ya ce "Baby ai karatu za ta yi kamar mai sunan ta" "Na ji Salman ya ce kin fara degree na uku, ba kya gajiya da karatu ne" "Ka san neman ilimi ga Malami baya ƙarewa" "Hakane. Da Hamma na nan da yanzu ya zama Profess..." maganar ta tsaya tunowa da yai cewa shine silar katse komai. Shiru ne ya biyo bayan haka kowa da irin abinda ya ke yawo a zuciyar sa. Chan Muntari ya daure ya fito da abinda ya kawo shi wajen ta. Bayan ya gama bayanin sa Mommy shiru ta yi na kusan minti biyu tana kallon ƙarfin hali irin na Muntari, kafin ta ce. "Adaeze ba za ta zama Lawyer ɗin ka ba Muntari. Kwanciyar hankalin ta shine burina a koda yaushe, ko da mijin ta zai ba ta izinin ta jagorance ka ni ba zan taɓa amincewa ba. Idan ƙara za ka shigar zan haɗaka da ƙwararren Lawyer amma Zaytoonah ba za ta karɓi wannan case ɗin ba" "Humairah ta gaya min ita ta jagoranci case ɗin ki da Kawun ki har aka samu nasara" "Muntari! Zaytoonah ba za ta karɓi case ɗin ka ba" Mommy ta faɗa da karfi, wanda ya sa Muntari tsorata. *** Zaune ta ke a madaidaicin office ɗin ta da ke cikin katafaren shagon ta. Bayanan Galadima gameda matsalar Zaytoonah su ke ma ta yawo a kwanya. Wannan dama ce a gareta hakan ya sa ta janyo wayarta ta shiga bincike akan ma su matsalar Zaytoonah. "Ben" ta maimaita tunowa da ta yi shine sunan da Zaytoonah ke maimaitawa ranan da ciwon ta ya tashi. Ben shine dodon Zaytoonah ita kuma shine maganin matsalarta. Wani munafukin Murmushi ta yi lokacin da kwakwalwarta ya hango ma ta Mahaukaciya Zaytoonah... Wata guda da Muntari yai a gida har ya ɗan fara kyan gani. Zuwa lokacin kuma ya tunkari Alhaji Rabi'u da maganar maido ma sa dukiyar sa ko kuma ya shigar da shi ƙara amma Alhaji Rabi'u yai biris, ce ma sa yai ya je duk inda zai je babu mai sauraron sa. Barrister Auwal Usman Abubakar shi zai jagorance shi. Ba wai dan ya so ba sai dan Iya da Baffansa sun sa baki. Mommy dai ce ma sa ta yi yayi taimako dan Allah ba dan an tursasa shi ba. Kamar zai fasa sai kuma ya chanja ra'ayi ya amince akan zai karɓi case ɗin. Alhaji Rabi'u bai tsammanci da gaske Muntari ya ke ba sai da Lawyan sa ya kawo ma sa letter daga kotu. Murmushin mugunta yai ya cillar da Letter. Ranan shaɗaya ga wata za a fara sauraron ƙara amma kafin ranan zai rufe maganar.... Tashin hankali goma da ishirin Zaytoonah ta shiga lokacin da mummunan labari ya riske ta. Ɓarayi ne su ka shiga gidan su Iya su ka halbi Auwal da Uncle Muntari. Justice baya gari, a waya ta sanar da shi abinda ya faru tareda neman izinin tafiya Zaria. Bai hanata zuwa ba sai dai ya ce bai yarda ta tuƙa kan ta ba sai dai Dreba ya kaita. Lokacin da su ka isa Zaria ana kiran sallar Maghrib. Kai tsaye Asibiti aka wuce da ita dan dukka 'yan gidan na su a wajen su ke. Ta samu ganin Auwal dan shi halbi ɗaya aka ma sa a kafaɗa, amma Uncle Muntari halbi uku aka ma sa ɗaya a gefen ƙirji biyu a ciki. Har zuwa lokacin da Zaytoonah ta iso ma ba a gama ma sa aiki ba. Haka dukkan su suka zauna jugum suna sauraron fitowar Likitoci. Ba su fito ba kuwa sai ƙarfe shaɗaya saura na dare. Sun tabbatar mu su da cewa Muntari na cikin haɗari. Harsashi ɗaya ya shiga Kidney ɗin sa automatically kidney ɗin ya mutu sun cire shi, ɗayan kuma da ya saura ba shi da lafiya dan shan giya da yai a baya ya riga ya ɓata Kidney ɗin. A taƙaice Muntari na buƙatar kidney transplant ASAP. "Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun" Mommy ta furta tareda dafe ƙirji. Lokacin da ta fito daga Office ɗin Likita Iya ce ta fara taran ta " ya rasu ko?" Mommy ta yi saurin girgiza kai. "Za mu iya ganin sa" "Likita ya ce sai gobe" "Allah ka tashi kafaɗan bawan ka Muntari" Iya ta faɗa tana rafka tagumi. Kwana uku Muntari na kwance sai a rana ta huɗu ya farfaɗo. Kidney ɗin sa guda ɗaya da me aiki idan ba a samu wani ba zuwa gaba kaɗan itama mutuwa za ta yi. Maganar nan da wata biyu zuwa uku aka ƙiyasta ma sa. Mommy ta saka a fara binciken donor ko za a samu a siya ma sa amma ba labari har yanzu. Cikin 'yan uwa duk wanda aka tunkara da maganar kidney sai ka ji yana faɗin Jarrabawa ce ta same shi a barshi ya fuskanci jarrabawar Ubangiji. Duk da Auwal na halin samun kulawa shi ma sai da ya ce a duba na sa idan yai dai-dai sai a cire na sa ɗaya a bawa Muntari ɗaya. Sai dai Likitoci sun ƙi aminta da hakan dan atleast idan ba tsautsayi ba yana buƙatar wata shida kafin a fara maganar ma za a ma sa aiki irin cire kidney. Ba tareda Mommy ta sani ba Salman ya je aka gwada na sa sai dai aka ci sa'a bai zo dai-dai da na Muntari ba. Maganar ƙara tuni anyi watsi da shi, dan yanzu ko taɗin ma ba a yi. Alhaji Rabi'u ko leƙo Asibitin bai yi ba balle ya zo ya duba halin da Muntari ke ciki... Kwana biyu Zaytoonah ta yi a Zaria ta koma Abuja saboda zazzaɓi da 'yan biyu ke yi. Sai da ta yi kwana takwas kafin da su ka zo weekend ta sake leƙa su. Auwal dai jikin da sauƙi sosai dan ana maganar za a sallameshi nan kusa. Mommy ce ta shigo ɗakin da aka kwantar da Muntari. Iya ce kaɗai a ɗakin na sa tana zaune akan sallaya tana addu'a. "Iya idan kin ba da dama zan sa a fita da Muntari ƙasar waje idan har ba a samu Kidney ba nan da sati ɗaya" "To to ai ba matsala. Indai zai samu lafiya a chan Bismillah" Hawaye ne su ka taru a idon Muntari. "Maryam" ya kira sunan Mommy yayinda hawaye ya fara zubo ma sa. Bayan duk laifuffukan da ya aikata bai chanchanci alkhairi daga Maryam ba. Ƙila ma ba zai yi nisan kwana ba gara kawai ya fito ya bayyana tarin laifuffukan sa ya kuma nemi yafiyar wanda ya zalin ta. "Dan Allah ki tara min yaran Hamma" Daga ita har Iyan ido su ka zuba ma sa "Ina son neman gafaran su ko zan samu Allah ya gafarta min" "Muntari wani irin magana ne wannan" "Dan Allah Maryam ki kira su"... Text ta tura mi shi saboda ya ce wajen Mai Martaba zai je. Reply ɗin sa da ta gani ne ya sa ta dariya. Sosai Galadima ke ba ta mamaki idan yai wani abin kamar ƙaramin yaro. *Dan Allah ki dawo da wuri, yau gaskiya ina buƙatar tanadi. A gaishe da mai jiki* Da ita kaɗai ya zo saboda Ghazala ta je Lagos clearing wa su kayanta da su ka iso. Ita ne ƙarshen zuwa ɗakin, ganin an cika a ɗakin ya sa zuciyarta ya karaya. Mi ya ke faruwa kamar Uncle Muntari zai yi ban kwana da duniya. Mommy, Iya, Salman, Auwal, Humairah duk suna zaune jugum kamar wanda aka yi mutuwa. Ko ma mi za a faɗa Junior yayi ƙaranci ya zauna a cikin taron nan. Gefen Mommy Zaytoonah ta zauna tana faɗin "Mommy lafiya?" "Baban ku ke son ganin ku" Sai da aka shafe kusan minti bakwai bayan shigowar Zaytoonah kafin Muntari ya nisa ya ce " dukkan kunnan ni mai laifi ne a gareku. A lokacin ƙuruciya, a lokacin jahilci da son zuciya na aikata laifin da har abada ba zan taɓa yafewa kaina ba. Ina roƙon ku Dan Allah ko ba yanzu ba ku samu ku yafemin ko Allah zai yafe min." Ya kalli Iya ya ce "kusan kaso hamsin cikin abinda ya faru yanada nasaba da ke Iya. A lokacin da ya kamata ki kwaɓe ni ba ki yi ba, a lokacin da Baffah, Gwaggo da ma Hamma Tijjani su ke ƙoƙarin nutsar da ni zuwa hanyar dai-dai ba ki ba su goyon baya ba. Iya ke ki ka hura wutar ƙiyayyar da na ke yiwa Hamma Tijjani. Ke ki ka jagoranci rashin jituwa da ke tsakanina da Hamma Tijjani" Zuwa lokacin fiskar Iya ya jiƙe da hawaye, ta sa bakin gyalenta ta toshe bakinta saboda kar kukan da ta ke riƙewa ya fito. "Maryam ni ne silar rabaki da mijin ki, Zaytoonah ni ne silar rabuwa da kukayi da Mahaifin ku a lokacin da ku ka fi buƙatar shi" Yanzu kam kowa ido ya zubawa Muntari cike da tambayoyi. "Ku yafe min dan Allah. Hamma Tijjani..." ya fashe da kuka. Ba wanda ya ma sa magana dan kowa a ruɗe ya ke. Mommy abinda ke yawo a ranta kawai Muntari kashe ma ta Barkindon ta yai. "Ni na sa aka ma sa kurciya, ba zai taɓa waiwayowa inda Ahalinsa su ke ba, ba re taɓa zuwa inda Ahalinsa su ke ba. Tafiya zai yi ta yi har sai idan kurciyan da ke rinjayan sa ta mutu. Ban san ko yana raye ba ban kuma san yadda za ayi a karya asirin ba. Ku yafe ni" "Muntari Muntari" Iya ta faɗa tana fashewa da kuka. "Allah ya isa Uncle" Salman ya faɗa yana jin tsanar Muntari har da jin haushin kan sa na ƙoƙarin taimaka ma sa da yai. Zaytoonah da Humairah kuka su ke yi wiwi kowa na tuno ƙuruciyar sa da Daddyn na su. Mommy dai zare jiki ta yi za ta fice ba ta ce komai ba ko kukan ma ba ta yi ba. Zaytoonah ta kirata "Mommy" Ba ta ce komai ba ta juya ta fice daga ɗakin. Kai tsaye Motar ta ta nufa, tana shiga ta sa ma ta wuta, da wani mahaukacin gudu ta bar farfajiyan Asibitin. Ba kowa a gidan na su dan Junior ya tafi Islamiyya. Ɗakin ta ta shiga ta duba ƙarƙashin gado ta jawo wani akwati. Hannunta har rawa ya ke lokacin da ta buɗe shi. Hoton TJ ta ciro ta saka a ƙirji sai kawai ta fashe da kuka, kukan da rabon da ta yi irin sa tun ranan da TJ ya ɓata... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 61 Bismillahir Rahmanir Rahim *The birthday party* "Hajiya lafiya kuwa?" Ta yi firgigit daga nisan tunani da ta yi. Ta ɗago ido ta kalli Maman Tope da ta zuba ma ta ido da alaman damuwa. "Hajiya tun ɗazu na ke tsaye a nan har na kashe gas ba ki ji ba. Hope all is well Ma?" Sai a lokacin ta maida hankalinta ga kan tukunyar da ke gaban ta. Girki fa ta ke yi amma ta manta da shi ta buge da tunani. Tunda ta baro Zaria ta rasa nitsuwarta, kewar Mahaifinta ne ya dawo ma ta sabo. Ko ina ya ke?, mi ya ke ci?, a ina ya ke rayuwa?, shin ma yana raye? Kaɗan daga tambayoyin da su ke damunta kenan tunda Uncle Muntari ya gaya mu su abinda yai wa Mahaifin su. "Ba komai, kawai na shafa'a ne" Maman Tope da kallo kawai dan ba ta yarda da abinda ta faɗa ba. Kwashe abincin kawai Zaytoonah ta yi ta bar wa Maman Tope ta kai dinning. Ɗakin 'yan biyu ta wuce dan ta gyara mu su dan Bahijje ta tafi ƙauye. Da ta gama ta shiga ɗakin su Raziya suma ta gyara mu su sannan ta wuce na ta ɗakin... Ƙyalƙyalewa ta yi da wani Mahaukacin dariya lokacin da baturen da ta kira ya gaya ma ta ya gama aikin da ta sa shi har ma ya tura ma ta hoton aikin ya ce ta duba email ɗinta za ta gani. "Sak" ta furta lokacin da ta ga hoton "Shege Bature, wato shi dai bature Tantiri ne, indai ya ga kuɗi ba abinda ba zai iya yi ba" Aiki ya kammala dan haka za ta tura ma sa balance ɗin sa ta jira ya shipping ɗin kayan zuwa Nigeria. Tana sa ran zuwa sati biyu ma su zuwa saƙonta zai iso hannun ta. *** "Wannan kukan na minene?" Ta yi saurin saka hannu ta fara goge hawayen da ya riga ya ɓata ma ta fiska. "Zaytoon we've talked about this, miyasa ba kya jin magana ne wai. Kuka zai dawo miki da mahaifin ki ne? Ko kuma zai maida hannun agogo baya?" "Ka yi haƙuri Dan Allah" "Seriously za mu yi faɗa idan na sake kamaki kina kuka. Addu'a za ki ma sa, addu'a Zaytoon. Ba abinda ya fi ƙarfin Allah. Shi za ki kaiwa kukan ki bawai ki tsaya kuka na ɗaga hankali ba" "I'm sorry" Kama hannunta ɗaya yai ya jawota jikin sa ya ce " jiba yadda kika koma Dan Allah. Ni kaina kin hanani sukuni balle ke kan ki. Yanzu yaushe rabon da ki tanade ni?" Murmushi ne ya suɓuce ma ta ta ce " wannan Tsoho akwai jaraba" ta ɗan ja kumatun sa "Indai jarabar ta ki ce na yarda, kin san ke ta daban ce" ya faɗa yana kissing wuyan ta. "Ranka shi daɗe".... Washegari tana yiwa 'yan biyu shirin makaranta su ka fara yi ma ta gulma. Hashir ne ya fara faɗin "Mom wai muma ba za mu yiwa Daddy wani abu ba ne kamar na su Suhailah?" "Wani abu kenan?" "Wai gobe ne birthday ɗin Daddy" "Ba gobe ba ne jibi ne Da Allah" Hadid ya gyara ma sa. "Daddyn ne ya gaya mu ku zai yi birthday" "A'a, Suhailah ce kuma Hajiya ma ta ce mu su kar su faɗa mana, wai su kaɗai za su fita ranan" Abin ma dariya ya ba wa Zaytoonah. Wato dan ranan zai kama ranan kwananta shine har da cewa su kaɗai za su fita. Daɗin abin ma ba ta da lokacin ɓata rai akan wannan, idan ranan ta ne su yi duk abinda su ka ga dama ta riga ta san yadda Ranka shi daɗe ke komawa idan yana Fadar ta. "Mommy miyasa muma ba za mu yi celebrating birthday ɗin ba. He's our Daddy right?" Ɗaga hannun sa ta yi sama ta fesa ma sa turare ta kuma ɗaga ɗayan ma ta fesa sannan ta ce "Of course he's your Daddy Muhammad. Amma Daddy baya celebrating birthday ɗin sa so ba abinda za mu yi" "Noooo" Hadid ya faɗa da ƙarfi "To ai su Hajia da su Suhailah sun ce za su je yawo a ranan mu miyasa ba za mu je ba" "O'o ni Zaytoonah. Yaran nan yaushe kuka fara sa'ido haka" "Mooom" su ka faɗa suna ƙanƙance ido kamar yadda su ke yi idan suna so ta mu su wani abu. "Ok ok, zan duba abinda za mu iya yi ma sa, but its a secret. Kar na kuskura na ji shi a kunnen wani kun ji" "Yes Mom" su ka faɗa a tare suna dariya... Da dare da ya dawo suna cin abinci suna hira ta sako zancen birthday. "Alamu sun nuna jibi muna da grand party a gidan nan, tunda ba a sa damu a ciki ba za mu zuba ido kawai" Ɗago ido yai yana kallon ta. Ta san ba zai yi magana ba shiyasa ta cigaba. "Ina nufin birthday party ɗin ka jibi" "Birthday party kuma?" "Oh ba ka sani ba" "Birthday party sai ka ce Yaro" Ɗan jan gemunsa ta yi kaɗan ta ce "My Baby, ni a wajena kai yaro ne ai" "Ni kinga na ma manta jibi ne. I dont celebrate birthday ai. Amma ba zan ƙi special party a ɗaki na ba, iya mu biyu" "Not so fast ɗan saurayi, jibi fa kai da Amarya ne, babu ruwana a ciki" ta faɗa tana dariya Irin kallon da ya watsa ma ta ne ya sa ta yi saurin gimtse dariyar tata. "Idan ma wayo za ki yi yau dai sai an min special party ɗin nan. We'll do Pre-Birthday and Post- Birthday duka a yau" "Dole na Sayyidi" ta faɗa tana kai ma sa sokali dai-dai bakin sa... *** Tanadi na musamman Ghazala ke yi na birthday ɗin Maigidan na su. Allah ya taimaka ma ranan zai faɗa Saturday ne dan haka plans ɗinta duka zai tafi dai-dai. Da safe za su fita da yara su je wajen shaƙatawa zuwa da rana sai su dawo. Da dare kuma ta riga ta booking mu su hotel wanda honeymoon suit ne na gani na faɗa wanda karɓan irin sa ma sai da connection, a nan ta ke so su kashe dare suna raya sunna. Sati guda ta yi tana zuwa ana ma ta gyara dan kulawa na musamman ta ke son ba wa Yallaɓai a daren. Yau da Ghazala ta karɓi girki ta ke sanar wa Justice kan cewa gobe za su fita da yaran dan an kwana biyu ba a fita ba. "Za ku iya tafiya ba matsala" "Dear, na ce dukkan mu ai za mu fita tunda mun kwana biyu bamu yi irin fita haka ba" "Inada ɗaurin aure da zan je gobe sannan zan yi ziyara" "Na ce ko kafin ka wuce ɗaurin auren idan ya so daga nan sai ka..." "Idan fitan saboda birthday ɗina ne na yafe. Ke kan ki shaida ne ba na celebrating birthday" Shiru ta yi dan ko ta ja maganar ba chanja ra'ayi zai yi ba abinda za ta yi kawai shine gobe za ta sa Yaran su roƙe shi. Indai ta wajen Yaran sa ne yanada rauni. Yadda ta tsara dole hakan ne zai faru. Zaytoonah na tsaye tana riƙe da hand mixer tana juya cake batter ɗin da ta haɗa sai ga Ghazala ta shigo kitchen ɗin. Abu za ta ɗauka a fridge amma ganin abinda Zaytoonah ke yi ya sa ta taɓe baki ta ce "daɗin abin ma dai, goben duka nawa ne, Wallahi ko ruwa ban yadda a miƙa ma sa ba" Zaytoonah ta gyaɗa kai kawai ta cigaba da abinda ta ke. Ghazala kasa tafiya ta yi dan tana son tabbarwa cake ɗin dai Zaytoonah za ta yi ko kuma wani abin daban dan Zaytoonah akwai ta da iya yin desserts kala-kala. "Li'ilafi Quraishi, Aniyar kowa ta bi shi. Li'ilafi Quraishi, mai baƙar Aniya ta bi shi" Ghazala ta fara waƙa lokacin da Zaytoonah ke ƙoƙarin juye kwaɓin cake a cikin baking pan. Zaytoonah ko uffan ba ta ce ta cigaba da abinda ta ke yi. Ba ta da lokacin biye wannan Babbar banzar. Dai-dai za ta buɗe oven Ghazala ta tare wajen. "Idan ma ƙwaƙwalwar ki bai iya lissafi ba to ni zan maimaita mi ki. Ni ke da yau ni ce da gobe dan haka ban yadda a yi mishi wani birthday cake na munafurci ba" "A'a see this woman ooo. Ki matsamin na yi abinda zan yi" "Zaytoonah ba fa za ki yi ma sa cake ɗin nan ba. Ki bari idan ya koma hannun ki sai ki ma sa abinda ya fi cake ma" Zaytoonah ta kwashe da dariya ta ce "see me see trouble ooo. Ghazala ba yau na fara yin cake a gidan nan ba ke kin san wannan, sannan ko cake ɗin birthday zan yi ko ba na birthday ba ba ki da hurumin hanani abinda na yi niyya, plz ki matsa a wajen nan" "Duk tsiyar dai yau da gobe Mai baƙin ɗuwawu sai dai haƙuri dan gwarzon nawa ne ni kaɗai" Ta faɗa tana matsawa gefe. Maganar ya ɗan ɓatawa Zaytoonah rai amma kuma yanzu ba da ba ne tana dai-dai da ghazala. Ajiye pan ɗin ta yi a saman oven sannan ta juyar da bayanta yana fiskantar Ghazala ta fara shaking ɗin sa da sauri-sauri kamar tana twerking kafin ta sa hannu ta ɗaki ƙugunta tana faɗin " kin san wani abu Hajiya, wannan baƙin abin da ki ke gani kadara ce da ake nema da mahaukatan kuɗi kuma ba a samu sai dai ayi ciko da kaya ko a saka ballon ballon, Alhamdulillah Allah ya mallaka min su ba tareda ko sisi na ba. Na san ke mai Fanteka ɗin nan ba sanin amfanin kayan nan za ki yi ba" ta faɗa tana sake shafa hips ɗinta zuwa bayanta. "Uwarki ce mai Fanteka ba ni ba Zaytoonah" "Oh lalala Hajia. Kin san duk bayan kwana biyu idan ya shigo sai na yi ma sa jinyar hannu saboda ya shafo tsohon tray na Fanteka. Ina irin Fanteka da ya sha duniya har yayi ƙwarzane-ƙwarzane, huji-huji ɗin nan, to kamar irin sa ya shafo. Infact ko kin shiga ɗakina yanzu za ki ga tarkacen Robb, Man tiger, su Aɗaral bakur da sauran su duk na jinyar hannun sa ne" "Kan buhun..." "Daɗina da ke zagi Wallahi. Kin san sarai kuwa My prince baya so" Wani tuƙuƙin baƙin ciki ne ya daki zuciyar Ghazala ba dan tana da shiri na musamman akan Zaytoonah ba da yau Allah kaɗai ya san mi za ta yi ma ta a gidan nan. Juyawa ta yi za ta fita, Zaytoonah ta ce " sai haƙuri fa haka Allah ya ke rarraba kyautar sa. Ke ya nufe ki da farin fata ni kuma ya bani abinda kin sani na sani shi My prince ya fi so a jikin mace" Suman tsaye Ghazala ta yi a wajen, ta kasa gaba ta kasa baya. Tabbas Zaytoonah ba ta yi ƙarya ba dan tun da ta gane nan Galadima ya fi so ta ke aikin siye-siyen magani. Butt enlarger na bature har ba ta san adadin brand da ta sha ba amma still abin na nan yadda ya ke ko motsawa bai yi ba. Na gargajiya kuwa duk inda aka yi talle a whatsapp ko facebook sai ta gwada sa'ar shi, shima kuma duk sammakal. Yanzu ne ma ta yi sanyi da neman maganin ƙarin hips da butt... "Take heart Hajia, yatsun mu duk ba dai-dai su ke ba" Ta faɗa tana dariya... *** A chan Zaria kuwa abubuwa sun dulmiye, Mommy dai ba ta sake zuwa Asibiti ba sai dai duk abinda ke faruwa suna magana da Likita yana bayyana ma ta halin da ake ciki. Kamar yadda ta yi niyya akan za ta fita da Muntari ba ta fasa niyyarta ba. Ba dan halin sa ba sai dan yanzu a matsayin marar lafiya ta ke ganin sa ba a matsayin mai laifi ba. Bai chanchanci ta tausaya ma sa ba amma kuma shi ɗin abin tausayine yanzu. Tuni ta sa aka fara ƙoƙarin yiwa Iya da Auwal da Yakubu Visa dan su ne za su rakashi. Da farko Iya da Auwal da Salman ta ke so su tafi amma yanzu komai ya chanja. Salman kan ko dole ta saka shi ba ta tunanin zai je. Dan shima tun ranan bai leƙa ɗakin Muntari ba Auwal kawai ya ke dubawa shima kuma yanzu an sallameshi. Inda Mommy ta karkatar da hankalinta yanzu shine addu'a da ta ke sawa ake ma ta a masallatai da makarantun Islamiyya da ta Almajirai. Da kuma sadaka da yanzun kullum babu randa ba za ta yi ba. Yadda tunda ta ke ji a ranta TJ bai mutu ba haka ma yanzu ta ji a ranta cewa yana raye. Tsayuwar dare yanzu ya zama ma ta wajibi dan a nan ta ke samun daman miƙa kukan ta ga Allah Maɗaukakin Sarki... *** Galadima dai su Raziya sun sa shi dole ya amince za su fita amma da sharaɗin ƙarfe goma da rabi zai bar wajen dan ɗaurin auren da zai je Ƙarfe shaɗaya ne. Tun da sassafe su ka shirya Justice ne ma yai delay ɗin su. Karfe tara da kwata na safe ya fito ya nufi ɗakin Zaytoonah dan ya ma ta sallama amma ya ji shi a garƙame. Ya ɗan ƙwanƙwasa a hankali daga ciki ya ji ance "Yallaɓai ka ɗan jira mu a ƙasa gamu nan fitowa" Jiya ya tabbatar ma ta dukkan su za su fita amma ta ce ma sa yai haƙuri su fita da 'yan biyu ita ba za ya iya fita ba. Galadima na saukowa su ka ga ya samu waje ya zauna. "Daddy we'll be late fa" Raziya ta faɗa dan ta matsu su tafi, Waje uku Hajia Ghazala ta kwaɗaita mu su akan za su je yau. "Bari 'yan biyu su sauko sai mu fita" " 'yan biyu kuma?" Ta faɗa da mamaki dan Ghazala ta riga ta ce mu su su kaɗai za su tafi. Justice bai amsa ma ta ba sai Ghazala da ta yiwa Raziyan magana da ido alamar ta yi shiru. Sajida jikar Hajia Abu da ta zo mu su weekend jiya ne ta sauko daga stairs hannunta ɗauke da camera mp3 "Daddy za ka ara mana Minti goma na ka kafin ku tafi saboda akwai special performance da za a maka saboda zagayowar wannan rana" Ajiye mp3 ɗin ta yi ta kunna waƙar Flavour ta Ada Ada. "One two three" ta faɗa sannan ta saita camera ɗin yana kallon stairs. Hadid da Hashir ne su ke kan gaba, dukkan su an mu su shigar igbo har da jar hular su da aka sokara ma ta fiffiken kaza. Zanin kayan da aka ɗaura shi aka twisting mu su shi ta gefe shima ya zauna daɓas a kwankwason su. Hannun su riƙe da mafifici mai gashi-gashi suna ɗan taka rawa a hankali a hankali kuma a tare. Maman su na bayan su itama ta yi shigar ƙabilar Mamanta tana riƙe da ƙaramin cake wanda aka yiwa decoration mai kyau, leshi ta saka maroon mai adon flowers kalar golden, rigar an mata ɗinkin offshoulder ɗin nan ne, zani guda biyu ta ɗaura ɗayan guntu ya tsaya dai-dai gwiwa ɗayan kuma ya kai ƙasa, duka an ƙullesu a ta gefe inda ya ba da wani twist a wajen mai kyau, light make up kawai ta yi dan Galadima ba mai son tarkacen kwalliya da zai cika fuska ba ne. Head ɗin ma maroon ne inda jelar kitson chuku da ta yi ya watsu har tsakiyar bayanta, dama tana da gashi to kuma kafin ta yi kitson sai da aka fara yi ma ta stretching sannan aka yaryaɗa ma ta ƙananun kitso a baƙin gashin na ta. Tana saukowa tana ɗan taka rawa tana juya hips ɗin ta a hankali, yayin da ta ke bin rythm ɗin waƙar Ada Ada. Galadima da tunda Sajida ta saita camera ya miƙe daga kujerar da ya ke zaune, buɗe baki da hanci yai yana kallon saukowar ta su wanda ba ƙaramin tafiya da shi Zaytoonah ta yi ba, igbo attire da ta sa ya tsananin karɓanta sosai. Da su ka sauƙo Falaq da Suhailah su ka yi saurin zuwa wajen 'yan biyu suma suna gwada ta su kalar rawar. Zaytoonah ƙarasowa ta yi har wajen Justice ta juya bayan ta tana ɗan ɗan bubbuga ma sa kwankwasonta dai dai wajen da ake cewa (Adamma iye pekem pekem ya, Ada Ada) Salati Galadima yai a ransa saboda miƙewar da Ogan sa yai, ya ci Alfarmar dai babban riga ne ajikin sa da yanzu wani maganar ake daban, duk da haka lokacin da Zaytoonah ta ɗan matsa sai da yai saurin sa hannu yana ɗan gyara Malum-Malum ɗin sa. Sai da waƙar ta tsaya kafin Zaytoonah ta dena rawan. Ta yanko cake kaɗan ta ɗan rankwafa kaɗan ta miƙa wa Galadima cake ɗin tana faɗin " Yallaɓai ina ma ka addu'ar ƙarin lafiya, nisan kwana, Arziƙi, buɗi, rufin asiri, kwanciyar hankali, Albarkar 'ya'ya da ta jikoki da kuma farin ciki dawamamme. Happy birthday Sayyidi Zannoon" Justice da tuni ya buge da murmushi ya amshi cake ɗin ya fara taunawa yana faɗin "Amin ya Allah na gode" "Happy birthday Daddy" Hadid da Hashir su ka faɗa a tare, suma yaran sai su ka faɗa. "Come here my Boys" ya faɗa yana ware mu su hannun sa su ka zo da gudu su ka rungumeshi. Ghazala dai zuciyar ta fashewa ne kawai bai yi ba a lokacin nan. Itama Raziya abin ya burgeta amma haushin Zaytoonah ya sa ta joining Ghazala wajen haɗe rai. Sai da ya bawa sauran yaran cake a baki harda Raziya kafin su ka je su ka wanke hannun su... "Mu je ko" Galadima ya faɗa yayinda yai hanyar waje. "Abu Razz inaga mu haƙura da fitan nan tunda na ga Zaytoonah ta riga ta gama komai" ta faɗa ranta na ƙuna. Zaytoonah na gefe tana nuna ma ta hips ɗinta tana dariya ƙasa-ƙasa. Da ke Justice ya ba ta baya bai ga abinda ta ke ba amma ita Ghazalar ta gani. "Mum riga mun yi niyya mu je kawai" bai jira mi za ta ce ba ya fice daga falon yayinda dukka Yaran su ka take ma sa baya. "Bariki ko? Wallahi ni da ke a gidan nan" "Bariki iyawa ne Hajiya. Plz ki kula min da shi kin ji, dan Allah kar ki bari ƙura ya taɓa sweet gemun san nan" Ghazala ta zaro ido tana mamakin Zaytoonah. Anya kuwa ita ce sokuwar yarinyar nan da ta shigo ta samu farkon zuwan ta? *Nima dai na ce anya ita ce?* 2/11/21, 10:04 PM - ****: 62 Bismillahir Rahmanir Rahim *The Ghost* "Abu Razz wannan ba adalci ba ne, ɗazu da safe Zaytoonah ta yi abinda ranta ke so ba ka ma ta magana ba amma yanzu sai ka ce min ina abu kamar yarinya, a cikin kwanaki na fa ta min shishshigi" "Ghazala inada gida a garin nan ba zan je na yi kwanan hotel ba, abinda Zaytoon ta yi iya cikin gida ne bai kai waje ba" "Dama na jima da sanin cewa adalcin ka iya Zaytoonah ya tsaya bai kai waje na ba. Kullum idan ni ce sai dai ace ina abu kaman yarinya. Na yadda ni ba yarinya ba ce amma dai nima matar ka ce kuma ina buƙatar kulawa da tarairaya" ta yi maganar tana share hawayen ƙarya. Ta san halin sa sarai, idan akwai abinda ke saurin birkita shi bai fi a tuhumeshi da rashin adalci ba. "Shikenan, za mu fita amma ba za mu kwana ba. Zuwa ƙarfe goma ko shaɗaya za mu dawo, ba zan kwana a hotel bayan iyalina na nan gida ba" "Dear mu kai dai ƙarfe shaɗayan" Ficewa yai daga ɗakin dan ya wuce masallaci, dama Alwala yai zai fita Ghazala ta tsare shi da maganar fitar da za su yi. Bayan ya fita ta yi sauri ta faɗa banɗaki dan ta shirya kafin ya dawo. Ɗakin Zaytoonah ya shiga amma ba ta ciki dan haka ya fito ya sauka ƙasa. A nan ya sameta zaune a falo tana raba Shari'a. Jallabiya ta sakawa yaran na ta amma kowa na faɗin ba na sa ba ne. "Idan ba ku min shiru ba sai na zane ku" "Daddy" su ka faɗa a tare tareda ƙarasawa wajensa da gudu "Daddy ta sa min Jallabiyar Hadid" "Nima na Hashir ta samin" "Kun san mi za ayi?" Dukkan su suka girgiza kai "Mu je masallaci mu yi sallah idan mun dawo sai kowa a chanja ma sa kaya" "Ok Daddy"su ka faɗa cikin gamsuwa "Mun wuce masallaci" "Allah ya dawo da ku lafiya Amin" Amin ya furta tareda ficewa daga falon riƙe da hannun Yaran... Zaytoonah na cikin gyara gado ta ji ana ƙwanƙwasa ma ta ƙofa. "Come in" ta faɗa ba tareda ta juya ba. Ƙaran tsinin takalmin Ghazala ne ya sa ta yi saurin juyowa. Sanye ta ke da wani Arabian gown golden colour, gaskiya gown ɗin na da kyau sosai, sai dai da ya haɗu da jiki mai kyau da abin zai fi armashi. "Mun fita dinner ni da Mahbubi na" ta faɗa tana murmushi. Zaytoonah ma murmushin ta yi ta ƙarisa wajen dressing mirror ɗin ta ta ɗauki Robb ta ce "a dawo lafiya Hajiya na riga na tanadi kayan aiki dan gobe da safe akwai jinya" Ghazala ta danne ɓacin ranta ta ce "ki yi bacci fa, kin san abin da cin rai" "Sosai ma, dan na bar Sayyidi a hannun tsohuwa" "Chan ta matse miki" ta faɗa tareda juyawa tana tafiyar ƙasaita. "Hajiya ba sai kin ma sa ciko ba ya jima da sanin Fanteka ne" Ba tareda ta juyo ba ta ma ta daƙuwa da hannu. Sai da ta fita kuma Zaytoonah ta zauna kan gado tana sauke ajiyar zuciya. Ko ba ta faɗa ba kishi ne ke cinta. Ta so a ce wannan rana na ta ne , da Justice ya ga tarairaya a wajen ta, ko da ya ke gobe zai shigo hannu. Ghazala da Galadima kuwa da su ka fita Dreba bai sauke su a ko'ina ba sai katafaren hotel ɗin da Ghazala ta kama mu su. Suna zuwa aka miƙa mu su key yayinda ɗan jagora ya mu su jagora har zuwa suite ɗin. Ghazala ce ta buɗe ƙofar dan haka tana rufewa ta cire baƙar after dress da ta ɗaura akan gown ɗinta. Da farko a haka ta fito za su tafi Justice ya korata akan bai yarda su fita haka ba saboda yadda gown ɗin ya kama jikinta shine da ta koma ɗaki ta ɗaura after dress a kai. Ta ji daɗi Zaytoonah ba ta falon da yau ta sha kunya da tsokala a wajenta. Ɗakine Babba da ya sha ado da ƙyale-ƙyalen decoration na birthday. "Mahbubi mu je ko" ta faɗa tana kama hannun sa. Kai tsaye wani ƙayataccen waje ta kaishi inda aka setting dinner a wajen. Kan table ɗin an ƙawata shi da adon flowers da candles a tsakiyar kuma wani ƙaton cake ne wanda a ƙalla zai kai irin na 100k ɗin nan. "Ghazala wannan almabazzaranci ne" "Ni dai neman lada na ke, kuma na tabbata zan samu tunda komai na yi ne domin Miji na" Girgiza kai kawai yai ya ja kujera ya zauna, itama zaman ta yi a wajen ... Cake ta saka shi yankawa yanayi tana ɗaukan shi video da waya. Da ya gama itama irin na Zaytoonah ta yanko cake ta ma sa addu'a kafin ta bashi a baki ya ci. Bayan wannan ta shiga buɗe abincin tana serving ɗin sa. "Ya isa Ghazala, a ƙoshe na ke" Duk da ta san shi ba mai son cika cikin sa da dare ba ne amma wannan da ta zuba ma sa ko yaro albarka. Ba ta bari ya riƙe sokalin ba ita ke bashi a baki har sai da ya ce ya isa kafin ta bari. Bayan sun gama cin abinci ta ce "Mahbubi na ce yau na taɓo ƙuruciya nima. I want to dance for you" Ko kaɗan babu plan ɗin rawa a cikin abinda ta shirya amma ganin rawan da Zaytoonah ta yi da safe ya sa itama ta sa a ranta dole sai ta yi. Galadima dai ya zuba ma ta ido yana ganin ikon Allah yadda wannan mata ta shi ta dage da yin rawa. Idan ya ce ma ta ta bari ya san fushi za ta yi shiyasa kawai ya zuba ido yana ɗan murmushi lokaci zuwa lokaci. Ba wani jiki gareta ba amma da ke abune da ba ta saba ba zuwa minti bakwai da ta yi tana tiƙar rawa sai gashi cikinta ya ƙulle musamman saboda ba ta jima da cin abinci ba, gashi dagewa ta yi da gaske tana girgiza kwankwaso, Zaytoonah ta yi gaskiya dan bum short biyu ta saka saboda ta yi ciko. "Masha Allah! Kin yi ƙoƙari sosai. Na gode da kulawa Gimbiya Ghazala" Kalmomine da ya faɗa dan ya yaba ma ta kar a samu matsala. A yadda ta dage da yin rawan da wani kalar rawan ta yi wanda zai dace da shekarunta da kuma yanayin jikinta da abin ya fi ba da kala amma wannan ƙuruciyar dolen da ta yaɓawa kanta sai a hankali... Kamar da wasa da za su kwanta Justice ya fara ɗan jin cikinsa na murɗawa. Banɗaki ya shiga dan yai wanka tareda rage nauyin cikin sa dan yana ganin ciye-ciyen da yai ne ke son ja ma sa ciwon ciki. Daga hawa seat ɗin toilet sai ga gudawa ya taho da gudu, hatta Ghazala da ke ɗaki sai da ta ji ƙaran. "Sorry Mahbubi, kuma abincin na su bai yi yaji ba. Barin sa a kawo ma ka flagyl" Abu kaman wasa bayan Galadima ya fito daga wanka sai da ya sake komawa saboda da gasken dai cikin sa ne ya ɓace. To da safe da yara sun je shan ice cream ya sha, ya ci abinci da rana nan ma abubuwa dayawa Ghazala ta tanada ma sa ciki kuwa harda favourite ɗin sa kwaɗon zogale. Yanzu ma wani abincin ya ci ga cake da ya ɗan taɓa shima kuma kayan zaƙi ne. Bayan ya sha maganin da aka kawo ma sa ya ce Ghazala ta tattare su koma gida. Makeken gadon da aka jiƙe shi da roses da ta ke shirin karɓan saƙo a wajen Galadima sai ga shi ko zama a kai bai yi ba balle ayi wani abu. A yadda su ka bar hotel ɗin Ghazala sai da ta tsorata dan Justice ko links ɗin hannun sa bai sa ba, hular sa ma Ghazala ce ta riƙo a hannu. Gudu sosai ya ce Dreban na sa yai dan ba abinda ya ke son ya gani irin ya gan shi a gidan sa. Bayan sun isa gidan ma dai sai da ya ƙara shan wani magani amma still abin ba sauƙi. Lokacin da ya fito ɗaure da babban towel a ƙugun sa zama yai bakin gado yana nishi ya ce "duba min fridge a falo akwai goran Zuma ki haɗomin da ruwa mai ɗumi a kofi" "To gani nan zuwa" ta fice da sauri. Gidan na su ya yi tsit dan duk sun yi bacci. Atika ma da za ta buɗe mu su ƙofa da su ka iso ta yi bacci dan sai Ghazalar ce ma ta yi amfani da key ɗinta ta buɗe ƙofar. Tsabar kiɗima falon ƙasa ta je duba Zumar amma babu ta leƙa kitchen kafin ta sake haurawa sama ta duba fridge ɗin falon sa ta ɗauka ta kawo ma sa. Allah Sarki Bawan Allah sanda ta koma ɗakin yana cikin banɗaki yana fama. Bayan ya fito ta haɗa ma sa ruwan ɗumi da Zuma kamar yadda ya umurta ya ɗauka yana kurɓa a hankali. "Abu Razz ko Asibiti za mu je ne. Ko na kira Likita?" "Barin sha wannan ɗin idan bai lafa ba sai mu ga mi za a yi"... Kamar yadda ta saba tashi yau ma ɗin hakan ta tashi, bayan ta yi alwala ta zo ta gabatar da raka'atanil fajr ta ɗan yi azkar kafin ta wuce ɗakin 'yan biyu dan ta tashe su, tunda tare su ke fita sallar Asuba da Galadima. Sai da ta tabbatar sun yi alwala kafin ta saka mu su jallabiya kafin su ka wuce na ta ɗakin dan nan Galadima zai biyo mu su su wuce. Sai dai har aka fara kiran sallah ta biyu har ma aka shiga sallar ba ta ji ɗuriyan sa ba, kuma ta san halin sa da wuri ya ke tashi. Tunani ɗaya ta yi ko dai ba su dawo ba ne daga inda su ka je. Ƙarshe kawai ta ce mu su yau a gida za su yi sallah ,Daddy baya nan... Wajen ƙarfe bakwai saura Zaytoonah ta fito daga ɗakinta, ta so komawa bacci amma tunawa da ta yi su Galadima ba sa gida ya sa ta ke son ta haɗa abin karyawa da wuri, dan akwai Zoom meeting da za ta yi ƙarfe takwas da wasu ma'aikata. Isowanta kitchen ta ga Ghazala na faman ɗaura tukunya. Tsabar jiya ba ta samu daman bacci ba kayan jikinta na jiyan ne dai ba ta cire ba. Zaytoonah ta tsaya kasaƙe tana kallon ta. Kenan dai sun kwana a gidan. Kishi ne ya sa ta jin haushin Galadima, shi birthday daɗi ko sallan Asuba bai fita ba. Bayan ina kwana da ta ce ba ta ƙara cewa uffan ba ta fice a kitchen ɗin. Dama a tsarin su sai Ghazala ta yi breakfast kafin ta karɓi girkin. Takwas da kwata Hadid ya shigo da gudu yana faɗin "Mom Daddy ba shi da lafiya" "Hadid ina meeting" Ta faɗa lokacin da ta cire earpiece ɗaya. "Mom Doctor zai ma sa allura yanzu" Tsorata ta yi jin kalaman Hadid ɗin. Ta yi saurin sallama da Ma'aimatan tareda cewa an ɗaga meeting zuwa ƙarfe biyar na yamma agogon Nigeria. Room slippers ta saka ta fita da sauri. A falo ta tarar da Ghazala da Likita suna magana. Sama-sama ta amsa gaisuwar Likitan ta wuce ɗakin Galadima. Dukka Yaran sun zagayeshi sun yi jugum. Ruwa aka ɗaura ma sa Hadid ke cewa allura. 'Amma Ghazala baƙar munafuka ce, shine ba ta gaya min bashida lafiya ba ɗazu' ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta tambayeshi da sauƙi. Abu da gudawa tuni ya wani faɗa idonsa ya shige ciki, saboda ruwan jikinsa da ya tsotse. Jiya da dare da likitan ya zo kusan karfe shabiyu da minti arba'in ya ma sa allura ya kuma sa ma sa ruwa, ya nunawa Ghazala yadda za ta cire idan ya ƙare. Da ake akwai ƙarin leda ɗaya da za a ƙara saka ma sa shine ya zo da safe ya saka ma sa. Haka dai kwana biyun Zaytoonah ta yi shi cikin jinyar Galadima. Duk da taji tausayin mijin na ta amma hakan bai hanata yin dariyan abinda ya faru ba bayan Galadiman ya samu lafiya. Har tsokanar sa ta yi da cewa hakkinta ne ya kamashi tunda yana da gida ya wuce cin abincin hotel. *** Ƙoƙarin shirya closet ɗinta ta ke ta ji maganar sa a bayanta "Zaytoon wani irin shirme ne wannan" ya faɗa yana nuna ma ta wayar sa. Karɓar wayar ta yi tana kallon screen ɗim wajen status ne dai amma ya riga ya goce ba ta san wanne bane ya ke nuna ma ta. "Sayyidi minene?" ta faɗa tana kallon sa cikin rashin fahimta dan ɓacin rai ƙarara ta kalla akan fiskarsa koma minene ya faru gaskiya ran sa ya ɓaci sosai. "Ki duba status ɗin ki" da ƙarfi Yau da safe ta tsokali Ghazala ta tura ma ta video clips na wajen da ta yi rawa ranan birthday ɗin Galadima clips ne guda uku ciki harda wajen da ta ke rawa a jikin sa. Da ke hidimar rashin lafiyar Galadima bai sa ta waiwayi video da aka yi ba sai jiya da dare ta sauke su akan laptop ɗinta ta yi editting sannan ta tura a wayanta. Bayan ta gama turawa Ghazala video ɗin ne ta ɗaura clip na wajen da 'yanbiyu da su Suhailah ke rawa da ɗaya kuma wanda 'yanbiyu ne kaɗai su ka yi rawan tun a ɗaki kafin su sauko ƙasa. Iya video biyun nan kawai ta ɗaura amma ga mamakinta sai ga video na uku na second tara wanda ta ke rawa ita ɗaya. Ba ita ta ɗaura wannan ba infact ɗin time ɗin da aka ɗaura da na farkon akwai tazara wancan da safe ta ɗaura su wannan kuma bai fi awa ɗaya da ɗaurawa ba tana tunanin fitan da ta yi ɗazu ta je ta duba jikin Bahijje shine koma wanene ya samu damar amfani da wayarta har ya ɗaura status ɗin. "Maza nawa ke da contacts ɗin ki? Ba wannan ba, wani mutunci ne a cikin ɗaura irin wannan a matsayin status ko da kuwa Mata zalla ne za su gani?" "Ka yi haƙuri dan Allah amma Wallahi Sayyidi ba ni na ɗaura wannan ba" Zaytoonah ta faɗa kamar za ta yi kuka. Bai ce komai ba ya juya ya fice daga ɗakin. Da ke girkinta ne da dare maimakon ya ci abincin da ta zuba mu su a falon sa sai ya sauko ƙasa tareda Yaran ya ce Raziya ta zuba ma sa abinci. Ghazala na ganin haka ta sa murmushi. Lokacin da ta shiga ɗakin sa haƙuri ta shiga ba shi amma bai waiwayeta ba balle ya nuna ya ji mi ta ce. Tana durƙushe dai-dai ƙafarsa ta sake jarraba ba shi haƙurin. "Ranka shi daɗe ba ni na ɗaura wannan video ɗin ba. Idan kana so na rantse da Ƙur'ani zan yi, ban san wa ya saka ba" "Kina nufin Hadid ne ya ɗaura ko kuma dai Hashir?. Su ne su ka rubuta *see Galadima's property* really Zaytoon" Tabbas abinda aka rubuta a ƙasan video ɗin kenan. Abu biyu ne ya sa shi wannan fushin. Na farko kishi ne na biyu kuma abinda ya sa a ransa shine Zaytoonah ta sa video ɗin ne saboda Ghazala. "Ka yarda da ni Allah Wallahi ba ni ba ne" "Matsamin zan kwanta" Ajiyar zuciya ta sauke tareda miƙewa ta bar wajen. Tunda ta kira ma sa Allah bai yarda ba shikenan ya yarda da abinda ya ga dama, Allah ya san ba ita ba ne kuma zai tona asirin munafuki. Tunda ta san darajar turakar Galadima yau ne rana ta farko da su ka kwanta kowa na fuskantar gefe, dukkan su biyu a gefe gefen gadon su ka kwanta sai ya zama tsakiyar da fili. Washegari ma sammakal su ka tashi dan Galadima bai sauko ba. Da safiyar kuma sai ga kiran Iya. Ba ta da numbarta ma sai da ta amsa ta gane muryan. Iya ce ta roƙeta akan ta zo gida yau zuwa gobe saboda jibi za a fita da Muntari kuma tana son su gana kafin su tafi. Ce ma ta tayi za ta tambayi Galadima idan ya barta za ta zo. A take a lokacin ta tura ma sa text amma bai yi reply ba. Sai kusan biyar da rabi kafin reply ɗin sa ya shigo *Allah ya kiyaye hanya* kawai ya rubuta. Ta girgiza kai kawai ta ajiye wayar ta cigaba da abinda ta ke a kitchen. Da dare ma bai ci abinci tareda ita ba amma wannan karan ita ta serving na shi lokacin da ya ce Raziya ta zuba mishi abinci ita ta yi saurin miƙewa ta fara zubawa. Da za su kwanta ta sake tuna ma sa maganar tafiya Zaria. "Na ce Allah ya kiyaye hanya mi kuma kike so?" "Na gode" ta faɗa a hankali. Tare ta tafi da yaranta da ba za ta iya barwa Ghazala su ba duk da kwana ɗaya kawai za ta yi. A chan Zaria kuwa tun ranan da Auwal ya faɗawa Iya cewa an gama yi mu su Visa tafiyar su ta kama ranan Alhamis ta je ta samu Mommy har gida ta ma ta godiya tareda roƙonta gafara. Mommy ta ce ma ta ta jima da yafe ma ta. "Maryam na san akwai ciwo amma Dan Allah ki taimaka ki yafewa Muntari, wallahi kullum cikin damuwa ya ke, ki yafe ma sa saboda ya samu ya gama da duniya lafiya" ta ƙarisa maganar tana sheshsheƙar kuka. "Na riga na yafe ma sa sai dai idan ba Tijjani na gani ba ba zan taɓa iya zuwa inda ya ke ba" "Da yardar Ubangiji Shehu zai dawo gidan nan da ƙafafuwansa. Na gode da kika yafe ma sa" Bayan tafiyar Iya Mommy ta jima tana ƙara jinjina lamarin Ubangiji. After all this years sai ga shi Maryam Nkiru Inyamura ita ce Iya ke neman yafiyar ta... Awa biyu da zuwan su Zaytoonah Iya da Humairah su ka zo gidan. Abinci ma Zaytoonah ke ci lokacin da su ka shigo. Zaytoonah ta mu su tayin abinci su ka ce a ƙoshe su ke. Bayan ta gama cin abinci ta ɗauke plate ɗin ta kai kitchen ta dawo. Iya ce ta fara buɗe taron tareda cewa ayi salatin Annabi. Magana ce mai kama da nasiha Iya ta yiwa Humairah da Zaytoonah kan zumunci. " na sani ni na lalata zumuncinku tun kuna yara saboda banbanta ku da na ke, amma ina roƙo Dan Allah daga yau ku riƙe junan ku amana, dukkan ku jinin Shehu ne babu banbanci tsakanin ku. Ke Zaytoonah ke ce Babba dan Allah ki riƙe amanar ƙanwar ki. Kema Humairah ki riƙe amanar yayar ki. Dan Allah ku shirya tsakanin ku kunga dai inda rashin amana da banbanci ya kai iyayen ku..." Ta ƙarisa maganar tana fashewa da kuka. Cikin kuka ta cigaba "Humairah ki riƙe Maryam a matsayin Mahaifiya domin ita ɗin uwa ce ta gari. Da ke da mahaifiyar ki da bazarta kuke rawa yau ki riƙeta amana" Zaytoonah da Humairah ma dai hawaye su ke saboda tuna tazarar da ke tsakanin su a matsayin yan uwan juna. Ba za su iya tuna yaushe su ka taɓa maganar minti biyar tsakanin su ba. Bayan an gama 'yan koke-koke Iya ce kawai ta koma gida ta bar Humairah da Zaytoonah suna ƙoƙarin ƙulla zumunci. Tare su ka yi girkin dare sunayi suna taɗi jifa-jifa saboda har yanzu ba su iya sake jiki da juna ba. Lokacin da su ke cin abinci da dare Zaytoonah ta tambayi Humairah akan ko za ta bita Abuja ta ma ta kwana biyu. "Anty Zaytoonah kin san mun kusa fara exams" "Airah ɗan kwana biyun" Humairah ta kalleta da mamaki. "Na tuna lokacin da ki ke rubuta Airah Tijjani Abubakar a makaranta Daddy ya gani da aka kika kawo result ɗin ki yai ta faɗa. Kar ki damu zan dinga kiran ki da haka tunda kina so" "Lah duk shirmen yarinta ne" "Ba wani har yanzu Airah na son gayu" Humairah ta yi dariya. Mommy ma dariyar ta yi tana fata inama TJ na wajen ya ga yadda 'yan matan sa su ka zama. Da dare sai da Zaytoonah ta gwada kiran Galadima amma bai ɗauka ba sai kawai ta tura ma sa good night text. Da su ka iso dai ta ga text ɗin sa yana tambayar ko sun isa lafiya bayan nan bai sake waiwayarta ba. Indai ta koma bai dawo dai-dai ba maganin sa za ta yi... Washegari kuwa Zaytoonah da Humairah su ka tafi Abuja. Har lokacin kuwa Justice bai sauko ba sai dai ganin idon Humairah sai ya sake fiska kamar ba komai. Humairah kam ba ƙaramin burgewa gidan su ya ma ta ba, duk da gidan Justice na Zaria ya fi wannan kyau amma wannan ɗin ma ba baya ba gashi ya sha kayan Alatu. Maimakon da da ta ke jin kishi da ƙyashin Zaytoonah yanzu kam tayata murna ta ke. Yadda ta ke ganinta ɓukuta kamar ba ko wani namiji zai so ta ba gashi kuma Allah ya mallaka ma ta zaratan mazaje a lokaci mabanbanta. It doesnt matter if you are fat, the right man will love you just the way you are. Yadda Allah ya yi mu mabanbanta haka ma ya sawa Mazan ra'ayi mabanbanta. Ranan da Humairah za ta koma Zaria Zaytoonah ta loda ma ta kaya ciki harda jakar Givenchy da ta sa lokacin bikin gidan su Galadima. Humairah ta yi ta tsallen murna tana godiya. "What are sisters for, ni dama tsoron za ki raina shiyasa ma bana baki komai" "Na isa na raina kayan 'yar uwata. Thank you Anty Zaytoonah" Da dare Zaytoonah wani mahaukacin baƙin rigan bacci ta saka ta wuce falon Justice. Robe ɗin rigan ma iya tsakiyar cinya ya tsaya balle shi kansa rigan wanda da shi da babu duk sammakal. Yana kallo a falon ta wuce wajen TV ta fara laluben ƙarya bayan ta zuge igiyar robe ɗin. "Where did i keep my phone ne" ta faɗa kamar da gaske. Ta gama dube-dubenta ba ta gani ba ta koma wajen kujeru tana dubawa. "Daddyn Raziya ka ɗan matsa na duba wayata" Ɗan matsawa yai amma ba waya. "Oh inaga tana ɗaki" ta faɗa tareda wucewa ɗakinsa. Sai da ta ɗan jima sannan ta fito riƙe da wayar ta tsaya gabansa tana faɗin " na samu, Sai da safe Yallaɓai" Ƙarar rufe ƙofa da ya ji ne ya dawo da shi daga nisan kallo da ya tafi ashe har ta fita bai sani ba. Ya san tsokana ce kuma da gaske ta tsokaneshi dan gaba ɗaya ya rasa nitsuwar sa. Dakewa yai akan za ta dawo amma shiru minti goma, shabiyar har ishirin shiru. Ya kashe kayan kallon ya wuce ɗakin sa amma bacci ya ƙi zuwa. Da ya gama juye-juyen dai sai ɗaukan wayarsa yai ya kirata. Tana kwance itama ba ta yi bacci ba dan tana so ta ga da gaske zai iya resisting ne ko zai ba da kai buri ya hau. Da ta ga kiran sa murmushi ta yi kafin ta amsa. "Na ce ba" "Uhm" ta faɗa kaman mai bacci "ki kawo min man zafin kin nan, ƙafana ya riƙe" "Akwai a drawer ɗin ɗakin ka na gefen gado" Tana faɗin haka ta kashe wayar tana fashewa da dariya. Ko sakan talatin ba ayi ba ya sake kira. "Ban gani ba ki kawomin na ki yanzu" ya faɗa in a serious tone. "To Yallaɓai" Lokacin da ta kawo ma sa Robb ajiyewa ta yi a bakin gado ta ce "sai da safe" "Wa zai shafemin ƙafar" Gimtse dariyarta ta yi ta ɗauki Robb ɗin ta lakata a hannu ta zauna gefen gado tareda ɗaura ƙafarsa akan cinyarta ta shiga shafa ma sa tanayi tana ɗan mammatsa ma sa yatsu. "Na ce ki sawa wayarki lock saboda Yara, kin san ba abinda ba za su iya yi ba" "Ko na saka 'yan biyu kaman mayu su ke sai sun gano" "Wannan dai ya wuce amma nan gaba a kiyaye" Ai dama ta sani ba zai iya ba da haƙuri ba. Da ta gama matsa ma sa ƙafar ta miƙe kafin ta ce wani abu ya ce "kwana shida fa ba a tanadi tsoho ba" "Ni ba laifina bane Tsoho ne ya killace kan sa" Murmushi yai tareda ma ta hannu akan ta zo jikinsa ba ta musa ba ta ƙarisa jikinsa itama na murmushi... *** Tun tafiyar Zaytoonah Zaria saƙon Hajia Ghazala ya iso ganin sun dawo da Humairah ya sa ta dakatar da shirinta zuwa yarinyar ta tafi. Yau ba kwanan ta ba ne dan haka ayyuka kawai ta ke yi kafin ta kwanta. Ta san Galadima ba zai barta ba amma kuma tana son tafiya Las Vegas saboda akwai wani deal da za su yi da wani sabon investor da su ka samu, although sun kammala komai ta hanyar meeting ta system amma still sun buƙaci ganin ta ido da ido musamman saboda legal documents da za ta cika saboda a kammala komai. Ta dai sa a ranta idan 'yan biyu su ka yi hutu nan da sati uku za ta ma sa magana su tafi. Mrs Haddish ma ta damu su zo amma ba yadda za ta yi tunda Gogan na ta murɗaɗɗen mutum ne ba ka gane alƙiblar sa. Lokacin da ta gama komai ƙarfe shabiyu ya wuce. Bayan ta tattare tarkacen Laptop da waya akan gado ta sake karkaɗe gadon kafin ta kwanta. Ko minti goma ba ta yi da kwanciya ba ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. 'Waye kuma da daren nan' ta furta ƙasa-ƙasa. Miƙewa ta yi ta je ta buɗe ƙofar sai dai abin da ta gani a bakin ƙofar ne ya sa ta sandarewa a wajen. "B B Ben" ta furta tareda yin luuu ta faɗi ƙasa. Wacce ta ajiye mutun-mutumin da aka ƙera mai yanayi da fiska irinta Ben wanda yafi kama da 'yar tsana a bakin ƙofar Zaytoonah ta yi wuf ta ɗauke shi ta bar wajen da gudu... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 63 Bismillahir Rahmanir Rahim *my daughter is not crazy* Lokacin da Galadima ya zo ɗaukan 'yanbiyu fita sallar Asuba ne ya ga Zaytoonah kwance a baƙin ƙofa. Mamaki ne ya kamashi na yadda aka yi ta kwanta a baƙin ƙofa. Yana ƙoƙarin cicciɓarta ya kaita kan gado ta farka a firgice tana kiran "Ben dont kill me, please dont kill..." "Zaytoon kalle ni, kalle ni" ya faɗa yana rirriƙeta saboda a zabure ta ke. Sai da ta yi kusan 10 seconds tana kallon shi kafin ƙwaƙwalwarta ya gane cewa da Galadima ta ke ba Ben ba. "Daddyn Raziya" ta furta a hankali ya gyaɗa ma ta kai tareda manna ma ta kiss a goshi. Sai da ya taimaka ma ta ta koma kan gado kafin ya tambayeta miya faru ta kwanta a baƙin ƙofa. Labarin da ta gaya ma sa ne ya sa shi tunanin gaskiya ba lafiya ba. "I swear i saw Ben last night Daddyn Raziya, believe me" ta faɗa tana hawaye "Zaytoon kin yadda akwai mutuwa?" Ta gyaɗa kai "Kin yadda wanda ya mutu baya dawowa" Nan ma ta gyaɗa kai "Zaytoon Ben ya mutu, ya jima da mutuwa over 5yrs yanzu. Ba zai taɓa dawowa ba" "But i saw him. Na ganshi jiya da dare" Dafe kan sa yai dan kusan minti goma kenan suna maimaita abu ɗaya. Ita ta dage wai ta ga Ben a bakin ƙofarta jiya. "Kasheni zai yi, ya yi alƙawarin sai ya kasheni..." "Shhhhh. Ki kwanta ki huta" "Dan Allah ka duba ko'ina a gidan nan he might still be around" "E zan duba amma yanzu ki kwanta tukunna" "Dan Allah ka tsaya kusa da ni kar ka tafi ka ji" Gyaɗa ma ta kai yai tareda rufe ma ta jiki da bargo. Ta jima kafin bacci ya tafi da ita. Bayan ya tabbatar baccin na ta yai nisa ne ya samu ya miƙe ya bar ɗakin na ta. Gaba ɗaya abin ya ɗaure ma sa kai. Jiya dai ba a ɗauke wuta ba balle ta ce duhu ta gani ta tsorata. To ko dai mafarki ta yi ne? Amma a bakin ƙofa ya sameta tana bacci kuma ƙofar ɗakin na ta a buɗe. Waje ya fita ya tambayi Maigadi da sauran ma'aikatan ko an ɗauke wuta jiya da dare amma amsar ɗaya ne a iya sanin su ba a ɗauke ba... Ko da Zaytoonah ta tashi ba ta manta abinda ta gani ba amma kasancewa Justice bai yarda ba ya sa ta yi shiru ta fara tunanin kodai da gasken ne mafarki ta yi. Wunin ranan dai ta yi shi a tsorace ne dan sau ɗaya kawai ta sauƙa ƙasa. Kwana biyu ba abinda ya kuma faruwa dan haka ta share abin kamar bai faru ba. Yau kwana huɗu da faruwan wancan abin. Tana kitchen tana aikin abinci. Ita kaɗai ne a gidan sai Atika wacce ba ta san ma inda ta shiga ba, duk da dai tun sanda Justice ya ma ta faɗa ta ke kaffa-kaffa da Zaytoonah amma ita Zaytoonan ba ta sake jiki da ita ba, aiki idan ba ya zama dole ba ba ta sakata. Bayan ta gama komai ta ɗauka tray da ta jera kayan abinci ta wuce da shi sama, bayan ta gama shirya mu su abincin ne ta wuce ɗakinta dan ta yi wanka. Any moment from now Galadima zai iya dawowa. Bayan ta shiga banɗaki mamaki ya kamata ganin ba ta ga komai ba. 'Har yanzu' ta furta a ƙasan ranta. Bai cika ma ta latti ba, sai dai wannan kwana huɗu kenan tana zuba ido amma ba ta ga alamar sa ba. Ta gama wanka ta fito sanye da bathrobe dogo kalar Madara. A stool da ke gaban dressing mirror ɗin ta ta zauna tana ƙoƙarin shafa mai. Kallon kanta ta yi jikin madubi ta yi murmushi gaskiyar Mommy ne da ta ce ma ta tana glowing kwana biyun nan. Ƙirjinta ne ya buga yayinda numfashin ta ya fara fita da sauri-sauri jikinta na rawa ta fara juyawa a hankali dan ta tabbatar da abinda ta ke gani a jikin madubi ko dai da gaske ɗin yana bayanta ne. Ihu ta saka ganin Ben tsaye a ta bayanta. "Zuhayr, Zuhayr help, help..." ta ke ta faɗa bayan ta takure jikin bango, jikinta sai ƙyarma ya ke. Da gudu Justice ya hauro sama dai dai ya iso ƙofar ɗakin ya ga Atika ma ta fito daga ɗakin Ghazala. "Yallaɓai" Bai kulata ba ya shige ɗakin. Har lokacin Zaytoonah sai sunbatu kawai ta ke yi a waje ɗaya. Yana zuwa rungumeta yai ya na kiran sunan ta. Jin muryan sa ya sa ta ƙara ƙanƙameshi tana kiran "Zuhayr i know you'll come. Na san ba za ka taɓa bari Ben ya kashe ni ba" Ajiyar zuciya Galadima ya sauke yana tunanin akwai babbar matsala... Maganar dai irin ta ranan ce wai Ben ta gani a cikin ɗakinta, Abinda ta gaya ma sa kenan bayan ta samu nitsuwa. Shi dai ya shigo bai ga komai ba amma ita ta dage Ben ya shigo ɗakinta har da nuna ma sa inda ya tsaya. Ƙoƙarin kwantar ma ta da hankali yai amma ina ta ƙi sauraren sa ita wai dole sai ya yadda da abinda ta gani. Abin har ya so ba shi haushi amma da ya tuna cewa ita ɗin ba cikakkiyar lafiya gareta ba sai ya cigaba da lallashinta har ta haƙura akan ba ta ga Ben ba... Washegari da safe ya ɗauketa su ka je ganin wani Psychiatrist Doctor. Galadima ne ya ma sa bayanin gameda ciwon na ta da kuma yadda ya ke tashi idan ta tsinci kan ta a cikin duhu amma yanzu kwana biyun nan ba a duhu ma ya ke tashi ba. Wasu tambayoyi yai wa Zaytoonah tareda cewa yana so ya ga result na test da diagnosis da aka ma ta a chan Madina da kuma America lokacin da ciwon ya fara. Da ke ba su taho da shi ba Galadima ne ya koma gida bayan Zaytoonah ta gaya ma sa inda ta ajiye su. A ɗan tambayoyin da Likitan yai wa Zaytoonah ya fahimci tabbas idan da duhu ke tada ciwon to yanzu akwai abinda ta ke gani da ke tunzura ta har ciwon ya tashi. Bayan Galadima ya kawo takardun Likitan ya kai kusan minti talatin yana dubawa kafin daga baya yai wa Galadima bayani bayan ya ce Zaytoonah ta basu waje. "Ranka shi daɗe gaskiya matar ka na buƙatar kulawa sosai. Dole a gano mi ta ke gani ya ke sa ta tunanin ta ga shi wancan Ben ɗin, ko dai tana ganin hoton sa ko kuma wani abu mai kama da shi ko kuma wani abu dai da ya ke da nasaba da shi. Idan aka kawar da wannan zai kawo ma ta sauƙi amma idan ta cigaba da haka ina tsoron za a koma gidan jiya" Galadima ya kalleshi cikin rashin fahimta. "Report ɗin da na karanta ya nuna cewa Zaytoonah ta yi hauka a baya" "Hauka!" "Ka kwantar da hankalin ka Yallaɓai ba irin hauka ta yawo a titi ana tsince-tsince ba, ina nufin hauka saboda damuwa, a yadda su ka rubuta alokacin ba ta iya tuna cewa ta haihu balle ma ta kula da 'ya'yanta. Tana kallon duk wani bature saurayi marar gashin baki ko gemu a matsayin Ben. Ta taɓa attacking wani nurse namiji a Asibiti akan saita kashe shi saboda kallon Ben ta ke ma sa. Ko da ya ke ta samu lafiya daga baya amma har yanzu da saura. Idan ta cigaba da tsorata haka ina tsoron za a koma gidan jiya, za ta dinga kallon kowa a matsayin Ben" "Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun" Galadima ya furta yana sauke ajiyar zuciya. "Insha Allah za ta samu lafiya" Likitan ya faɗa... *** "Zaytoonah ki saurareni Dan Allah..." "Farha ba wanda ya yarda da ni a nan kema ba za ki yarda ba. Ben na gani, Ben. He wanted to kill me, kin manta sau nawa yai yunƙurin kashe ni. Believe me Farha" Idon Farha ya ciko da hawaye saboda tausayin ƙawarta. "Zaytoonah Ben is dead. An halbeshi ya mutu, babu ghost a musulunci you of all people should know that" "Kina cewa na haukace kenan, haka Ghazala ma ta faɗa wai na fara hauka" "Zan zo Nigeria, zan zo na duba ki, Zaytoonah kin ji" Ba tare da ta katse kiran ba ta rufe Laptop ɗin da su ke video call ɗin da shi. Ba wanda ya yarda da ita, har Mommy ma ba ta yarda ba. 'Nan gaba idan na ganshi kashe shi zan yi kafin ya kashe ni' ta furta a fili... Mommy da Galadima sun tsaida magana akan za a sake kai Zaytoonah wajen Likitan ta. Tun rana na uku da Zaytoonah ta sake firgita saboda Ben da ta gani Galadima ya kama hanya ya tafi Zaria inda ya sanar ma Mommy duk abinda ke faruwa. Bayan ya dawo, Mommy da kanta ta zo Abujan ta yi kwana biyu inda ta yi ta ƙoƙarin fahimtar da Zaytoonah cewa Ben ya mutu, ba shi ta ke gani ba, sai dai har ta tafi ba wai Zaytoonan ta yarda ba ne. Wannan ya sa Mommy ta yiwa Galadima magana akan tana so ta kai Zaytoonah wajen Likitan da ya duba ta da farko, shima kuma ya amince da hakan... ** Ghazala ce ta shigo ɗakin Zaytoonah ta ajiye mutum-mutumin Ben a tsakiyar ɗakin, za ta fita kenan ta ji kamar za a buɗe ƙofa, da sauri ta yi hanyar banɗaki saboda ba ta yi tunanin Zaytoonan za ta shigo yanzu ba. Zaytoonah na buɗe ɗakin ta kalli Ben a tsakiyar ɗakinta, irin shigar da ta ke ganin sa da shi kullum ne ta gani yanzu. Ta ɗan tsorata kam amma da ke bayansa ta gani ba fiskarsa ba sai ba ta firgita sosai ba. Kulle ƙofar ta yi ta fita da gudu dan ta kira su Maman Tope da su Raziya da ke ƙasa, wannan karan so ta ke kowa ya ga Ben ɗin da ta ke gani a ɗakinta kullum. Sai dai ba ta ankara ba ta ture Falaq da ke bakin stairs. Tsayawa ta yi chak ganin Falaq tana gangarawa ƙasa. Raziya da Suhailah su ka yi wajen da gudu jin ihun Falaq ɗin. Zaytoonah ta tsaya chak ta kasa motsawa tana hango su Raziya na kuka suna jijjiga Falaq. Maman Tope ta fito daga kitchen jin kukan Yaran. Ta kama salati ganin Falaq a sume. Har Ghazala ta zo ta wuceta ba ta iya motsawa ba tana kallon yadda su ke ta kuka... Suna zuwa Asibiti aka admitting Falaq wacce har lokacin ba ta farfaɗo ba. Tuni Ghazala ta kira Galadima ta faɗa mishi ai Zaytoonah ta turo Falaq daga stairs gatanan kwance a Asibiti rai a hannun Allah. A rikice Justice ya baro office ya taho Asibitin inda ya samesu sun yi jugum suna jiran Likita ya fito. A nan ne kuma Ghazala ta sake tabbatar ma sa da cewa Zaytoonah ne ta turota. Ganin Raziya ba ta ce a'a ba ya sa jikinsa yai sanyi dan tunanin sa abinda Likita ya faɗa ne ya ke shirin faruwa. Bayan Likita ya fito ne ya gaya mu su halin da Falaq ke ciki ta samu karaya a hannu sannan kanta ya bugu sosai kuma suna tunanin kunnen ta ɗaya ya taɓu dan haka ba lallai ta dinga ji sosai ba, amma sai ta farfaɗo kafin su tabbatar. Allah ma ya taimaka ba bu wani bleeding ta cikin kan ta. Kusan ƙarfe bakwai na dare ya maida Raziya gida tareda son duba halin da Zaytoonah ke ciki. Abin mamaki da su ka je a falon ƙasa su ka tadda Zaytoonah tana jiran Galadima yana zuwa ta fara ma sa maganar ai yau kam za ta tabbatar ma sa da gaskiyarta dan Ben na ɗakin ta. Bai musa ba ya bita har ɗakin sai dai tana buɗe ƙofa sai wayam ba komai. "Ina Ben ɗin ya ke?" "Na gan shi fa, ina ga guduwa yai. Believe me" "Falaq na Asibiti, Raziya sun ce ke kika turota, miyasa?" "Ina son gaya mu su cewa Ben na ɗakina ne, ni ban san tana wajen ba. Ka yarda da ni" Girgiza kai kawai yai ya wuce ɗakin sa dan ya san ba laifinta ba ne, dole ya ma ta uzuri... Kafin gari ya waye kusan duk wani makusancin Galadima ya san labarin abinda ya faru da abinda ma ke faruwa dangane da Zaytoonah. Tuni aka fara kiran Galadima ana ma sa jaje, wasu kuma na ba shi shawaran a nemawa Zaytoonah maganin gida tunda dai na bature ya ƙi yi. Sarai ya san Ghazala ne da wannan aikin, ba dan yanzu kansa ya ɗau zafi ba da ba abinda zai hanashi taka ma ta birki. Ya rasa wace irin mace ce ita da bakinta ba ya iya riƙe sirri. Ba wai kar ta sanar da abinda ya faruwa ba amma minene na faɗin cewa Zaytoonah tana da taɓin hankali harda cewa ita ta turo Falaq daga stairs. Da zai fita Asibiti Maman Tope ya ce ta kula da Zaytoonah saboda ba ta da lafiya. Ko bai faɗa ba itama ta lura da hakan tunda yawan firgitan da Zaytoonah ke yi bai ɓoyu mu su a gidan ba. Da ya zo ya samu Falaq ta farfaɗo amma sun ce ta ƙi magana, har sun ɗauka ma ko buguwan ne ya kurmantata amma tana ganin Galadima ta kira sunan sa "Daddy" Hamdala Galadima yai a ran sa jin cewa Falaq na magana. "Ina ke miki ciwo?" "My arm" ta faɗa a hankali. Hannun na ta an saka shi cikin plaster cast wanda motsi kaɗan ta yi da shi tana jin zafi. "Ba inda ya ke mi ki ciwo kuma?" "Kai na namin ciwo" "Ki yi haƙuri zai daina". "Kai mun gode Allah da wannan mahaukaciyar ba ta samu galaba akan ta ba" Irin kallon da Galadima ya ma ta ne ya sa ta yi saurin rufe bakin ta. Miƙewa yai ya ce zai je yai magana da Likita... *** "Hajiya ki yi haƙuri amma abunda ki ke buƙata ba mai yiwuwa ba ne." "Ba zan bar 'ya ta a gidan ka ana cutar da ita ba. Justice Yunus matar ka ta ci darajarka a wajena amma da babu abinda zai hanani maka ta a kotu. My daughter is not crazy, dan na ga kamar kai ma abinda ka ke tunani kenan" "Ina ƙara baki haƙuri bisa abubuwan da su ka faru. Na yarda ki tafi da ita kamar yadda ki ka nema, amma maganar rabuwa da ita babu shi. Ina roƙon Allah ya ƙara ma ta lafiya ya yaye ma ta wannan damuwa da ta ke ciki" A ƙasan ran ta ta amsa da Amin. Abubuwan da su ka faru kwanan nan sun sa ta na jin haushin Galadima. A matsayinsa na mutum mai daraja ta ya zai bari sirrin 'yarta ya fito waje har a dinga yawo da hoton 'yarta a media ana tagging ɗin ta a matsayin mahaukaciya wacce ke shirin kashe 'ya'yan mijinta. Ita kanta ta ma sa maganar ya saki Zaytoonah ne out of frustration ba wai har ƙasan ranta tana son hakan ba. Tana fama da tunanin halin da T J ya ke yanzu da ta san asiri aka ma sa ga maganar rashin lafiyar Zaytoonah da ya ɓullo even at it worse, sannan Ghazala ta yaɗa labarin Zaytoonah a media. Bayan fitar Mommy daga office ɗin sa Justice cire gilashin idon sa yai ya maidashi gidan sa. Ya haɗa hannun sa biyu ya ɗaura su akan table ya bi hannayen da kallo, a zahiri hannun ya ke kallo amma chan ƙasan ran sa damuwa ce fal a zuciyar sa. Tunowa yai komai ya dagule ne ranan da aka sallami Falaq a Asibiti su ka dawo gida. Hasashen Likita bai zo dai-dai ba dan kunnen ta garau ya ke ba abinda ya same shi, sai dai sun shawarce shi akan a sake zuwa da ita a ma ta gwaji bayan wata ɗaya. Kusan kwana biyar da Falaq ta faɗo daga stairs kamar da gaske Zaytoonah ta ɗan yi shiru da maganar ganin Ben musamman saboda Galadima ya ma ta magana akan baya son jin maganar Ben ɗin nan. Kwatsam ranan Justice ya shiga ɗakin Zaytoonah akan za su wuce Asibiti dubo Falaq kawai sai ya ga ƙatuwar wuƙa akan drawer ɗin gefen gado. Mamaki ya kama shi ganin wuƙa a wajen. Zaytoonah da ta fito daga banɗaki ta kalli Justice da ke zaune bakin gado hannun sa riƙe da wuƙa. "Zaytoon mi wannan ke yi a nan wajen?" "Its for protection. Da shi zan kare kaina idan Ben ya sake dawowa" Maganar Likita na ranan ne ya dawo ma sa, karfa ace da gaske ta fara haukan ne kamar na wancan lokaci. "Zo ki zauna" ya faɗa yana nuna ma ta gefen sa. Bayan ta zauna sai ya rasa ma ta ina zai fara yi ma ta bayani da za ta fahimta. "Princess kin san ina son ki ko" Ta gyaɗa ma sa kai " to Dan Allah kar ki sake ajiye wuƙa a ɗakin nan, kar ki ma ƙara ajiye wuƙa kusa da ke" "But..." "Idan kin sake ganin Ben sunan Allah za ki kira ba Ihu ba kin ji" Ta gyaɗa ma sa kai kamar da gaske... Ghazala ba ta cika zama a gida ba saboda ita ke kwana da Falaq a Asibiti amma kuma an cigaba da firgitar da Zaytoonah lokaci zuwa lokaci. Wannan ya sa a hankali- a hankali abin ya fara zama ma ta kamar hauka dan tana ji an buɗe ƙofa za ta fara ja da baya tana tunanin ko Ben ne zai shigo sai ta ga ba shi ɗin ba ne kafin ta sake jiki. Ranan da aka je ɗauko Falaq a Asibiti. Zaytoonah na kwance a bakin gado ta ji kamar motsi a jikin ƙofa. Da sauri ta saka hannu a ƙarƙashin pillow ta ɗauko wuƙa ta miƙe tsaye ta taka a hankali a hankali ta je wajen ƙofa ta ɓuya. Kusan 30 seconds sai gashi an buɗe ƙofan Raziya ce ta shigo ɗauke da Mutum-Mutumin Ben a hannun ta. Hannun Zaytoonah na rawa ta kaiwa Raziya sara da wuƙa dai dai ita kuma ta juya za ta gyara tsayuwar mutum-mutumin kawai wuƙar ya sameta a kafaɗa. Raziya ta challa ihu tareda sake mutum-mutumin ya hantsila gefe dama abune kamar balloon. Zaytoonah ta bi kan mutum-mutumin tana caccaka mishi wuƙa tana faɗin "i'm going to kill you today" Raziya ta matsa gefe tana ihu ganin jinin da ya fara zubowa daga Kafaɗarta. Atika ce ta shigo ɗakin da gudu dan tundaga kitchen ta ke jin ihun Raziya. "Sallallahu wa Sallama" ta faɗa jikinta na ɓari ganin abinda Zaytoonah ke yi. Kaman ta ji tsayuwar Mota da tana haurowa hakan ya sa ta yi yunƙurin rufawa kan ta asiri kafin yau ta yi kwanan ƙauye. Ghazala da Raziya dai ba abinda Galadima zai mu su amma kuma ita fa. Zuwa ta yi da ƙarfi ta ƙwace wuƙar hannun Zaytoonah ta cillashi gefe. "Ki barni na ƙarisa shi bai mutu ba" Zaytoonah ta faɗa lokacin da ta ga Atika na jan abin za ta fita da shi. Ɗauko wuƙan ta yi ta bi bayan Atika tana faɗin "ki tsaya na ƙarisa shi" Atika ta shige ɗakin Ghazala ta danna ma sa key kafin ta yi saurin mayarda mutum-mutumin ma'ajiyarsa. Zaytoonah na jikin ƙofa tana bubbugawa da ƙarfi akan dole Atika ta fito da Ben ta ƙarisa shi Galadima da Ghazala su ka hauro saman da gudu. Ganin wuƙa a hannun Zaytoonah ya sa su tsorata. "Zaytoon" Galadima ya kira sunan ta a hankali. "Yau kan na kama shi, na jijji ma sa ciwo saura kaɗan na kashe shi Atika ta gudu da shi" "Ta gudu da wa?" Galadima ya faɗa cike da tsoro "Ben mana" "Daddy" Raziya ta faɗa da ƙarfi daga ɗakin Zaytoonah jin muryan Daddyn ta. Ghazala ce ta shiga ɗakin ta kalli Raziya riƙe da kafaɗarta, ba wai yanka sosai ba ne amma da ya ke ya ɗan shiga kaɗan shiyasa jinin da ya fito dayawa. "Abu Razz dan Allah ka zo" Galadima ya shigo ɗakin da sauri. Raziya na ganin sa ta fashe da kuka. "Innalillahi, Raziya garin yaya?" "Anty Zaytoonah ne ta yanke ni" "Subhanallah. Ghazala kaita ɗakina ki ɗau first aid box a tsaida jinin" Shi ya fara fitowa har lokacin Zaytoonah na jikin ƙofar Ghazala. Zuwa yai ta bayanta ya ƙwace wuƙar hannun na ta. "Ka barni na kashe shi, ka barni na kashe mugu" Da ƙyar ya iya jan ta ya komar da ita ɗakinta ya kulleta ciki sannan ya fito. Ɗakin Ghazala ya koma yai ƙoƙarin turawa ya ji ƙofar a kulle. "Akwai mutum a ciki ne?, Atika" "Na'am Yallaɓai" "Buɗe ƙofar" Da ta buɗe tambayarta yai miya faru amma sai ta ce wai ihun Raziya ta jiyo ta hauro saman shine da ta shiga ɗakin Zaytoonah ta biyota da wuƙa tana kiran ta da Ben. "Ya Salam" ya furta a bayyane yana dafa kan sa... Wannan abin da ya faru ya ƙara dulmiyar da Zaytoonah dan fau-fau ta dage ita ta kama Ben da hannunta kuma Atika ce ta gudu da shi infact ma yana ɗakin Ghazala. A ranan da abin ya faru Ghazala ta ɗau hoton wajen da aka yanki Raziya ta ɗaura a yanar gizo tareda dogon bayani da ya ke bayyana cewa kishiyarta mahaukaciya ce ke son kashe ma ta 'ya, da farko ta turo ƙanwa daga stairs yanzu kuma ta yanka Yayar. Kan kace me labari ya karaɗe gari ya shiga lungu da saƙo ya zama abin magana kowa na faɗin Allah wadai da Zaytoonah wasu kuma na ma ta addu'ar samun lafiya... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 64 Bismillahir Rahmanir Rahim *Treatment* Galadima na office baƙuwar number ta kirashi da ya ɗaga sai mutumin ke cewa shi editor ne na wani gidan Jarida wai yana neman izini ne akan za su zo gidan sa ɗaukan rahoton abinda ya faru da 'ya'yan sa. Galadima ya ce bai ba da dama ba infact idan su ka rubuta labarin sai ya sa an kama su. Yana kashe kiran ya miƙe tsaye ya ɗau key ɗin sa ya fice. Yana shigowa falon gidan ya tadda Ghazala da wasu mata su huɗu sai zuba ta ke yi. Tana ganin yanayin fiskar sa lokacin da ya shigo ta sha jinin jikin ta. Yana haurawa sama ta miƙe da sauri ta bi bayan sa. Ko zama bai iya yi ba yana tsaye kawai ya goya hannunsa a baya. "Ranka shi daɗe na ga ka dawo yanzu, lafiya?" Juyowa yai a harzuƙe ya ce "Ghazala kan ki ɗaya kuwa?. Tabbas ya tabbata ke ce da ciwon hauka ba Zaytoon ba. Ina mai tabbatar mi ki da cewa idan har ki ka ba da bayani aka ɗaura a gidan jarida, TV ko radio hakan zai tafi da igiyar auren ki ne" "Abu Razz!" Ta faɗa a kiɗime. "Wannan na ƙarshe kenan da wani abu zai faru a gidan nan da za ki kira wani nawa ki faɗawa ko kuma ki kai waje. Na ƙarshe kenan Ghazala" Ficewa yai ya barta jikinta na ɓari, ta riga ta yi hira da wani ɗan jarida a waya ɗazu da safe kuma sun ce za su ɗaura labarin a labaran su na rana. "Na shiga uku" ta furta tareda ficewa da gudu. Wayarta da ta bari a falon ƙasa ta ɗauko ta sake komawa sama, ƙawayenta na tambayarta ko lafiya amma ba ta kula su ba. Bayan ta kirashi Allah Annabi ta fara roƙonsa akan kar a ɗaura hiran ta su a radio. Ƙoƙarin fahimtar da ita ya ke akan ba komai ba ne tunda muryarta ne kuma ma za su iya ɓoye sunan ta. "Dan Ubanka na ce ban yarda a ɗaura ba" ta faɗa a tsawace ganin zai jawo ma ta matsala ta kashe wayar ta nemi gyalenta da jaka ta fice daga ɗakin da sauri. Office ɗin su na nan Abuja za ta je ta dakatar da wannan katoɓarar da ta aikata. Ta san halin Galadima sarai ba ya empty threat. Duk abinda ta yi ta yi shi ne saboda ta samu gidan ita ɗaya, idan kuma aka ce Galadima ya rabu da ita ai anyi ba ayi ba kenan. Galadima ɗakin Zaytoonah ya shiga inda ya sameta tana bacci. Sajida kuma na kan kujera tana assignment. "Ta jima da bacci ne?" "A'a" Sajida ta amsa ma sa. Ƙarisawa yai bakin gadon ya zauna. Ya ƙura ma ta ido yana kallon ta sai yanzu ya ga ba ƙaramin rama ta yi ba. Ba dole ta rame ba, ina ta ga kwanciyar hankali cikin kwanakin nan. Addu'arsa ɗaya Allah ya sa shawaran da ya yanke ya ma sa amfani. Gida ya siya ake kan gyarawa yana so ya maidata chan idan an gama. Sajida ya ke so ta bar hostel ta dinga zama da ita yana fatan ya ɗauko wata cikin yaran ƙannen sa su haɗu su zama su biyu da za su dinga ɗebe ma ta kewa idan yana tareda Ghazala a nan. Ƙila idan aka chanja gida maganar Ben ɗin nan zai mutu. A hankali ya manna ma ta kiss a goshi kafin ya miƙe ya fita. Bai bi ta kan Ghazala ba ya koma office, da ya sauka bai ganta ba baƙinta ma sun tafi. Motar ta ma babu a waje hakan ya tabbatar ma sa da fita ta yi. Tabbas maganar da ya faɗa ba zai janye ba, matuƙar ta yadda ta sake labarin nan a 'yan Jarida ba abinda zai hanashi datse igiyar auren su. Ta fara fita ma sa a ka, tun asali ya san ita ɗin ba macen da ta dace da shi ba ne to amma duk da shi ba yaro ba ne ba zai yi wasa da maganar manya ba... Bai dawo ba sai dare bayan sallar Isha, ɗakin Zaytoonah ya fara wucewa ya samu tana zaune a ƙasa kusa da gado 'yan biyunta na gefe suna cin abinci amma Zaytoonah ido kawai ta zubawa abincin ba ta ci. Sallama ya sake yi a karo na biyu amma babu wanda ya amsa. "Abincin ne ya hanaku gaishe da Daddy" ya faɗa yana shafa kan su. "Sannu da zuwa Daddy" " 'yan matana ya gari?" Ya faɗa yana sa hannu a goshinta. "Kina jin zazzaɓi ne? Goshin ki da zafi" Bakin gado ya zauna ya ɗaura hannun sa kan kafaɗan ta. "Ɗazu da rana na zo kina bacci. Kin samu baccin sosai kuwa?" "Mommy za ta zo gobe" ta faɗa a hankali "Allah ya kawota lafiya" ya faɗa a sanyaye. Ba makawa dai ta ji abinda ya faru ne shiyasa za ta zo. Dan maganar tafiyar su ganin Likita sun barshi sai bayan sallar Azumi, yanzu kuma Azumin ma ana tunanin saura kwana tara ne ko goma. "GrandMa ta ce tafiya za tayi da mu" Hashir ya katse ma sa tunani "Gara ma mu tafi ai wannan Raziyan sai ta yi ta ce mana 'ya'yan mahaukaciya. Ni kam ta ƙara faɗa Allah ya isa" Hadid ne da wannan maganar. Gashi dai yaro ne amma yadda yai maganar ka san ransa a ɓace ya ke sosai. Sai yanzu Galadima ya gane dalilin da ya sa yaran su ka shareshi lokacin da ya shigo. "Ai ba ita kaɗai ta ke faɗa ba, Hajiyar nan ma haka ta gaya min ɗazu da na je kitchen wajen Anty Sajida" Take jikin Galadima yai sanyi jin maganganun yaran. Ya sani da Zaytoonah na nan da lafiyarta kamar da da za ta kwaɓe su amma yanzu shiru ta yi ba ta ce komai ba da alama ma hankalinta ba ya wajen su. A ƙoƙarin sa na son janye hankalin su daga wannan maganar ya tambayesu ko Maman su ta ci abinci su ka ce ba ta ci ba, da ta ce za ta ci kaɗan amma da aka kawo ta ce ba za ta iya ci ba. Ya maida tambayar sa ga Zaytoonah ya tambayeta mi za ta ci idan ba za ta iya cin wannan ba. Da farko shiru ta yi daga baya ta ce ma sa kunu da ƙosai. "Kunu da ƙosai za ki ci?" Ya sake tambaya Gyaɗa ma sa kai ta yi ba tareda ta yi magana ba. Wayar sa ya ɗauka ya kira numbar Sajida da ta ɗauka ya ce ma ta ta cewa Atika ta haɗawa Zaytoonah kunu da ƙosai yanzun nan. Bai fi minti biyu ba sai ta kira shi inda ta tambayeshi wai wani irin kunu. "Adaeze wani irin kunu za ki sha?" "Kunun gyaɗa"... Bayan ya bar ɗakin Zaytoonah ɗakin sa ya wuce inda yai wanka ya chanja kaya zuwa kayan bacci, yana fitowa Falo ya tadda Ghazala na zaman jiran sa. Ta sha ado sai ƙamshi ta ke. "Ranka shi daɗe na zubo ma ka abinci yanzu ne?" "Na ƙoshi" "Abu..." "Ki kiramin Raziya ku zo tare" Bayan ta kira Raziya faɗa sosai yai wa Raziyan akan ko da wasa kar ta ƙara kiran Zaytoonah da Mahaukaciya balle har ta zagi 'yan biyu. Bayan ta bar wajen ne ya koma kan Ghazala. Faɗan da bai ma ta ɗazu da rana ba shi yai ma ta yanzu. Idon Ghazala ya rena fata dan Galadima bai yi da wasa ba. Sharuɗɗan da ya kafa ma ta na zaman gidan sa za su kai goma. Haƙuri ta fara bashi lokacin da ya gama masifar amma bai kulata ba ya tashi ya fita. Ɗakin Zaytoonah ya shiga ya ga har lokacin ba a kawo mata kunu da ƙosan ba. Saukowa yai ƙasa ya ce Sajida da ke cin abinci a dinning ta duba ma sa me Atika ke yi ba ta gama abinda aka sata ba. Bayan ta leƙa kitchen ɗin ne ta fito ta gaya ma sa an gama kunun yanzu za a fara soya ƙosan. Ya ce ana gamawa ta ɗauka ta kai ɗakin Zaytoonah. Komawa yai sama dan ya je ya lallaɓi 'yan samarin tagwayen na sa... ** Washegari da Mommy ta zo gidan ta ga Zaytoonah kamar ta yi kuka, ta lalace kamar ba ita ba, compared to ranan da ta zo Zaytoonan ta sake zabgewa. Ba wannan ne kaɗai damuwarta ba sai yadda jiya aka yi ta damunta da kira ana son ƙarin bayani gameda labarin da ake gani na yawo a media na batun yanka Raziya da Zaytoonah ta yi. Tun a jiyan ta so zuwa sai dai hakan bai yiwu ba. Takanas ta je gidan Hajiya Ni'ima neman ƙarin bayani daga ina ne labarin ya ɓullo. Hajiya Ni'ima ta gaya ma ta Ghazala dai kishiyar Zaytoonah ne ta turo hoton da rubutun zuwa family group ɗin su daga nan kuma aka watsa shi waje. Mommy ta sake baki tana kallon Hajiya Ni'ima da ke ba ta bayanin abinda ake ta faɗa a cikin Family ɗin su gameda Zaytoonah har da ma su cewa kawai Galadima ya rabu da ita tun kafin ta kashe ma sa 'ya'ya wannan ya tunzura Mommy matuƙa ta ɗau aniyar dole Galadima ya sake ma ta 'ya. Da ke da safe su ka zo Galadima ya riga ya fita dan haka Mommy ta wuce office ɗin sa yayinda ta bawa Humairah umurnin ta taya Zaytoonah tattara kaya. Ko da ta samu Galadima da maganar saki ko kaɗan bai ji daɗin maganar ba. Mommy dai ta dage tafiya za ta yi da Zaytoonah. Galadima ya ce ya yarda dai da maganar tafiya ganin likita amma maganar saki ba zai yiwu ba, ba shi da dalilin da zai raba shi da Zaytoonah. Lokacin da Mommy ta koma gidan ne ta taya Humairah su ka ƙarisa tattara kayan Zaytoonah harda na 'yanbiyu. Suma saboda makaranta za ta bar su a nan Abuja dan cikin Azumi za su yi jarrabawa. Gidan Muhsina ya kamata su zauna amma tunda ba ta nan gidan Yahya za ta kai su, shima wani cousin ɗin Zuhayr ne da ke zaune a nan Abujan, idan ya so sai a dinga kawosu weekend Zaria. Ghazala ta zo fita shago ta ga dawowar Mommy ranta a ɓace dan haka ta fasa tafiyar ta zauna zaman gulma. Lokacin da ta ga Humairah ta fara saukowa da akwatuna ƙasa sai wani farin ciki ya mamayeta. Kayan da ta ga an sauko da su ba kayan tafiyar kwana ɗaya ko biyu ba ne kaya ne da za ta iya cewa kaman ma duka kayan Zaytoonan aka sauko da shi. 'Yan biyu su ka fita su ka kira Dreba ya zo ya jidi kayan ya kai cikin Mota. Mommy ta riƙo hannun Zaytoonah su ka fito. Ghazala na ganin suna sakkowa ta yi saurin danna waƙar da ta yi downloading yanzu-yanzun nan wanda ake cewa *Allah raka taki gona* tana bibiyar waƙan da ƙarfi-ƙarfi. Humairah ranta ya ɓaci ta ce " amma Allah wadai na ka ya lalace. Galadima dai bai yi sa'a ba gaskiya, dan'yar tasha ya ajiye a gida" " 'yar tashar dai ita ce da gida yanzu yarinya, aje chan ayi jinya kafin mahaukaciya ta bi Bola" "Ke ce mahaukaciya wallahi" "Humairah ya isa haka, mu tafi" "Amma Mommy" "Mu je na ce" Mommy ta faɗa da ƙarfi. Maganar Ghazala ya taɓata sosai amma kuma idan ta biye ma ta tamkar sun zama ɗaya ne. Gaskiyar Hajiya Ni'ima da ta ke ce ma ta Ghazala dama tun asali fitsararriya ce da ba ta gaji mutunci ba tun ƙuruciya kuma har yanzu. Har su ka fita Ghazala ba ta bar maimaita Allah raka taki gona ba. Atika munafuka sai da ta ga sun fice daga gidan ta leƙo daga kitchen tana ayyiririri "Takawar ki lafiya Zinariyan Galadima. Ki sha sha'anin ki gida ya zama mallakin ki" "Ki faɗa ki sake faɗa Atika" ta faɗa tana zama tareda ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya... Da ke Galadima bai ba ta fuska ba ba ta iya tambayarsa abinda ke cinta ba lokacin da ya dawo gida wato ko dai da gaske ne ya saki Zaytoonah kamar yadda ta ke hasashe. Har washegari bai sako maganar ba dan haka ta samu Raziya akan idan suna cin abinci ta tambayeshi ina Zaytoonah ta je Atika ta ce mu su ta tafi da kayanta. Da ke faɗan da Galadima yai ma ta har yanzu yana ranta sai ba ta iya faɗa mi shi ba. Cikin sa'a kuwa Suhailah ta tambayeshi ina Anty Zaytoonaha lokacin suna karyawa. Shafa kan ta yai ya ce "Anty ta yi tafiya" "Yaushe za ta dawo?" Raziya da Ghazala su ka zuba ma sa ido suna so su ji mi zai ce. Kusan sakan biyar kafin ya ce "idan ta gama abinda ta je yi za ta dawo, ki ma ta addu'a kin ji" "Daddy wai da gaske Anty ta haukace?" "Kar ki sake faɗan irin maganan nan kin ji. Anty ba ta da lafiya ne kuma za ta warke" Ghazala dai ta ji jikinta ya yi sanyi. Kamar dai ya saketa kamar kuma bai saketa ba. "Kai yadda Mamanta ta shigo ɗazu fiska a tsumen nan inaga ya saki Zaytoonah ne fa" ta faɗa a ran ta. Da wuya Galadima ya saki Zaytoonah amma tana tunanin ƙila Hajia Abu ce ta saka shi dan ranta ya matuƙar ɓaci da ta ji labarin abinda Zaytoonah ta yiwa Raziya... A chan Zaria kuwa kwana ɗaya da dawowan su zazzaɓi ya rufe Zaytoonah. Dama tana fama dashi, rashin nitsuwa ne ya sa ta watsar da duk wani ciwo da ta ke ji. Mommy da kanta ta ɗauketa su ka je Asibiti dan ita sai da su ka zo Zarian ma ta fara zargin Zaytoonah na da ciki. Bayan 'yan tambayoyi da Likita ya mata da kuma gwaji aka tabbatar mu su da Zaytoonah na da ciki. A yadda ma Likitan yai bayani kamar ma cikin ya shiga wata uku. Maganin zazzaɓi ya rubuta ma ta da multivitamin tareda ba ta shawaran akan ta dena yawan tunani domin jinin ta ya hau. Mommy ta yi murna da wannan labari sai dai ba ta bayyana shi ba, sai ma cewa da ta yi wa Zaytoonah akan ta yi shiru da maganar cikin ko Galadima kar ta gaya ma sa. Zaytoonah ta gyaɗa ma ta kai. Maimakon bayan Azumi da suka saka tafiyar su, Mommy chanja ra'ayi ta yi akan gara su tafi yanzu tun kafin Zaytoonah ta fara nauyi. Cikin sati biyu aka kammala komai na tafiya su ka wuce ƙasar America. Ko sallama ba su yiwa Galadima ba. Wayar Zaytoonah dama tuni Mommy ta karɓe shi. Cikin Azumi da Galadima ya zo gida ne ya je gidan su Zaytoonah dan ya duba ta amma ga mamakin sa ba sa nan, Salman ya sanar ma sa ai sun tafi. Abin ya ma sa ciwo amma da ya tuna yadda su ka ƙare da Mommy sai ya gane tabbas har yanzu tana fushi da shi. Shi kan sa har yanzu yana jin haushin abinda Ghazalar ta yi. *"idan wannan ce Raziya aka dinga yawo da hotonta a manyan social media platforms za ka ji daɗi? Ka duba yadda aka haɗa hoton nan da kyau da abinda aka rubuta: Matar da ta yanka 'yar mijinta saboda ciwon hauka. Tsakani da Allah za ka ji daɗi idan wannan hoton Raziya ce"* Mommy ta faɗa tana nuna ma sa hoton Zaytoonah da ake ta yawo da shi. Kasa magana yai dan bai san ta ina zai fara ba. Abu ne ya riga ya faru duk hukuncin da zai ɗauka akan Ghazala ba zai dawo da hannun agogo baya ba. *"Dan Allah ka sawwaƙe wa Zaytoonah. Idan har ciwon hauka gareta kuma ita ɗin threat ce ga 'ya'yan ka ni zan zauna da ita kuma na san za ta samu lafiya ta warke gaba ɗaya"* Maganganun Mommy kenan ranan da ta je office ɗin sa, wanda da ƙyar ya shawo kanta ta yadda ta janye maganar saki da ta yi. Fatan sa Allah ya sa a dace a tafiyar da su ka yi... *** Yau ne za su fara therapy na farko saboda tun zuwan su gwaje-gwajen ƙwaƙwalwa aka ma ta kuma sakamako ya nuna cewa babu abinda ya sameta a ƙwaƙwalwa dan haka har yanzu dai treatment na PTSD za a ma ta. Sabon Likita su ka samu mai suna Dr Solomon wanda tsohon Likitan Zaytoonan ne ya haɗa su da shi domin shi baya ƙasar ya tafi ƙasar Austria. Bayan ya ma ta wasu tambayoyi wanda ta amsa su dai dai kafin nan ya danna remote ɗin hannun sa sai ga hoton Zuhayr ya bayyana a jikin projecter. "Waye wannan?" Likitan ya tambaya yana kallon ta. Maimakon ta bashi amsa sai ta bige da kallon hoton. "Mrs Zaytoonah waye wannan ?" Likitan ya sake maimaita tambayar... *** A chan gidan Justice kuwa liyafa ce ta cigaba wa Ghazala, ganin gida ya zama na ta ita ɗaya sai ta fara sauya tsarin zaman gidan. Har yanzu dai Galadima bai ba ta fuska ba saboda abinda ta aikata amma ta san zuwa lokaci kaɗan zai haƙura ya dawo da hankalinsa wajenta ita ɗaya. Matsalar Zaytoonah yanzu ya ƙare. Su je chan su ƙarata da jinyar mahaukaciya. Tabbas ita mai sa'a ce, ba dan ta riga ta jawo Raziya cikin lamarinta ba da abin bai zo ma ta a yadda ta ke so ba, ƙila ma da asirinta ya tonu. Shikenan ba boka ba magani ta fitar da Zaytoonah. Tun Zaytoonah ba ta cika sati da barin gidan ba ta riga ta karaɗe ƙawayenta da cewa gida ya zama na ta ita ɗaya. Galadima ya saki Zaytoonah. A lokacin sallar Azumi ne da ta samu Galadima ta roƙoshi a karo na ba adadi ya ce ya yafe amma dole ta nemi yafiyar Zaytoonah da Mommyn ta. Ta tabbatar ma sa da lallai za ta kira su ta basu haƙuri. Suna shirin komawa Abuja ta ma sa maganar ko za a buɗe ɗakin Zaytoonah a kwashe ma ta sauran kayan a kai ma ta su gida amma amsar da ya ba ta sai ya sa ta cikin ruɗani. "A wani dalilin za a kwashe kayan?" Da ƙyar ta iya cewa "naga wai tunda ba ta nan kuma..." "Ki bar ma ta kayanta a inda su ke" Ya faɗa sannan ya sa kai ya fita ya bar Ghazala da shiga duniyar tunanin wanne ne ba wanne ne ba... Duk abinda ake ba dan Allah ba to baya taɓa ɗaurewa. Duk wani tattali, soyayya da kwantar da kai da Ghazala ke yiwa yaran Galadima tuni ya fara gushewa domin an tafi wata ɗaya ba ta ga alamar Zaytoonah za ta dawo ba aka cika wata biyu shima shiru kuma ko a waya ba ta taɓa kama Galadima na magana da ita ba sai kawai ta tabbatarwa kan ta kawai fa ya sake ta ne. Abu na farko da yaran su ka fara fiskanta gameda ita shine rashin sake fiska da ta ke mu su kamar da. Abu kaɗan za su yi ta hau faɗa. Wani ɗan shiga ɗakin Galadima da su ke anyhow ta hana shi. "Iya kacin ku falo Raziya. Ke Babba ce ya kamata ki gayawa ƙannen ki ba koyaushe ne za ku dinga shiga mana ɗaki ba musamman idan muna tare. Indai kunga baya falon sa kam ai kun san yana buƙatar kaɗaici a ɗaki ne. Amma bini-bini kun shiga ɗaki kuna neman sa zai ɓace a ɗakin ne ko me ne" Raziya ta yi shiru tana kallon Ghazala cike da mamaki.. 2/11/21, 10:04 PM - ****: 65 Bismillahir Rahmanir Rahim *Shehu* "Welldone Fatima" Malamin Maths ɗin su Raziya ya faɗa lokacin da ya miƙa ma ta script na test ɗin da su ka rubuta shekaranjiya. Takardar da aka miƙa ma ta ta kalla cike da mamaki. Seat mate ɗinta Aysha ta kalli takardar ta ce "10/10, gaskiya kin yi wuta, ni fa 4/10 na ci" Wannan ne karo na farko da ta samu sakamako mai kyau a test ɗin Maths. Bayan Malamin na su ya fita aka fara hiran test ɗin wanda a duka ajin na su ita kaɗai ce ta cinye, yaron da ya fi kowa ƙwazo a math a ajin 8/10 ya samu. Tunda Zaytoonah ta fara koya ma ta Maths ta fara cin homeworks ɗin ta and classwork ma ba laifi marks ɗinta ya ƙaru and remarkably first test na su ta fi kowa ci a ajin. A mafiya yawancin lokuta da Zaytoonah ke koya ma ta karatu haka za ta zaƙe da dinga ma ta iyashege, wasu lokutan sai su yi sati biyu suna kan topic ɗaya tayita cewa ita ba ta ganewa. Jikinta yai sanyi da ta tuna abinda ta yiwa Zaytoonah. Ga shi dai Zaytoonah ta bar mu su gidan kamar yadda ta so tun farkon zuwanta amma maimakon su ji daɗin gidan sai ya zamana kaman ma a takure su ke. Ala dole Galadima ya maida tradition ɗin cin abinci da 'ya'yan sa. Wannan abin ya tunzura Ghazala matuƙa, da farko ta ɗauka saboda fishi da ya ke da ita ne amma ko da su ka shirya ɗin ma hakan ne ya cigaba. Ko ta kai ma sa shi falon sa a sama sai ya ce a ƙasa zai ci abincin tareda Yaran. Yau ma suna cin abinci da yaran Raziya ta ce "Daddy yau aka raba mana test ɗin da mu ka yi na Maths. I got 10/10" "Masha Allah. Sai ki ƙara ƙoƙari" "Daddy tunda Anty Zaytoonah ta fara koya min Maths Allah sai na ga ashe abin ma ba wahala" "Ya yi kyau" Suhailah ta ce "Daddy yaushe Anty za ta dawo? i miss her" Wani kallo Ghazala ta ma ta irin za ki gamu da ni ɗin nan. "I miss her too" Falaq ta faɗa a hankali "Za ta dawo very soon" "Daddy ka kira mana ita mu yi video call" "Wai ba na hana surutu idan ana cin abinci ba ne. Suhailah kin fara rashin ji ko" Gaba ɗaya yaran sai su ka yi kalar tausayi. Har aka gama cin abincin dai babu wanda ya ƙara magana. *** "Kai Malam ka duba gabanka mana, idan ka buge shi mi za ka ce" "To shima Baban idan ba Makaho ba ai yana ganin na iho ta nan ɗin amma ya ƙi ya matsa" Ɗan Achaɓar ya faɗa cike da haushin Tsohon da ya kusa bugewa. "Ja'irin Yaro, gaba ɗaya ba tarbiyya" Ɗan Achaɓar ya kaɗa mashin ɗin sa yai gaba yana muzurai shi a dole dai Tsoho ne da laifi. "Sannu Baba, yaran zamani ne sai a hankali ƙila ma a buge ya ke yanzu haka" "Ba komai ɗana, idon ne sai a hankali ba sosai na ke gani ba" Tsoho mai ƙusumbi wanda aƙalla zai kai shekaru casa'in da uku ya kalli mutumin da ya taimaka mi shi ya ja shi gefe lokacin da mashin ta yo kan sa ya ce " Ɗana ya sunan ka?" " suna na Shehu" ya faɗa yana murmushi. "Ko za ka taimaka ka raka ni gida nan ƙasa na ke" Shehu ya ce ba matsala ya kama hannun Baban su ka kama tafiya. Tafiyar minti biyar su ka yi ta kawo su ƙofar gidan Tsohon inda Almajirai ke zaune a gindin wata bishiya suna bitar karatu. Tsoho ya ce da Shehu su ƙarisa zaure. Bai yi ma sa musu ba dan tausayin sa ya ke ji. Sai da su ka zauna kafin Tsohon ya ce "bari a kawo ma ka ruwa" Tsohon ya ɗan ɗaga murya ya kira suna Yusufa jim kaɗan sai ga yaron ya iso. Tsoho ya ce ya je ya kawo ma sa ruwa. Bai fi minti ɗaya da rabi ba sai ga shi ya dawo ɗauke ta kofin tangaran cike da ruwan Randa mai sanyi. Sai da Tsoho ya karɓi ruwan ya sha kafin ya miƙawa Shehu shima ya karɓa, ya kuwa sha ruwan dayawa duk da bai jima da shan ledar ruwa biyu ba a shagon Ɗalha ɗazu. Da zai tafi Tsohon da ya kira kan sa da Malam Zulkiflu ya ce ma sa gobe ya zo su sake gaisawa. Shehu ya ma sa godiya sannan ya tafi. Malam ZulKiflu ya ƙurawa Shehu ido duk da ma dai ido ɗaya ne ke gani itama ɗin ba ƙarfi. Tabbas hasashen sa ya tabbata akwai sihiri ajikin mutumin nan. Shehu har ya koma rumfar sa da ya ke saida kayan marmari bai bar mamakin wannan Tsohon ba, shi kan sa bai san ya aka yi ya amince ya bi Tsohon zuwa gidan sa ba, bayan shi ba mutum ne mai son shiga Jama'a. Shi bayan barin sa garin Sokoto inda yai aikin Gadi a gidan wani Alƙali bai sake aiki ƙarƙashin kowa ba. Iya kuɗin da ke jikin sa da ya fita da shi da ya tafi Zamfara sana'ar Saida Rake ya fara yi cikin ikon Allah kuma ya samu ya tara jari sosai, lokacin da Rake ya ɗaga ƙafa sai ya koma sayarda kayan marmari kaman Lemu, Kankana, Ayaba. Ya taɓa yin sana'ar kayan Marmari lokacin da tafiya ta kai shi garin Bauchi, har ya samu gindin zama amma rana guda ya tatttara komai na sa ya ƙara gaba. Shi kan sa idan aka titsiyashi ba zai iya furta dalilin barin na sa garin ba... *** "Ni dai na gaya mu ku ba sai kun zo ba" "Idan kika ce haka Mommy har yanzu fishi kike kenan. Besides Wallahi jikin Zaytoonah ya ce zai duba" "Auwal ku wuce Nigeria kawai" "Haba Mommy, yaushe rabon da ki ga first son ɗin ki" Sai da ta yi shiru na kusan sakan goma kafin ta ce "shikenan ku zo ɗin" "Na gode Mommy" Ba ta amsa ma sa ba ta katse kiran. Ajiyar zuciya ta yi kafin ta ɗau Jacket ta saka sannan ta ɗauka gyale ta yi rolling. Fitowa ta yi ɗauke da jaka da waya. Lokacin da ta fito falo babu kowa a wajen, bayan a wajen ta bar Zaytoonan tana shan coffee. "Zaytoonah, Adaeze" ta fara kiranta amma shiru. Kitchen ta wuce ta tambayi mai aikin su ko ta ga Zaytoonah amma ta ce ta barta a falo tana kallo. "Ba ta falo" Mommy ta faɗa a rikice tareda ficewa daga kitchen ɗin da sauri. Kai tsaye waje ta tafi inda ta tambayi security ɗin gidan ko ya ga Zaytoonah, ya ce ta yi garden. Mommy ta wuce ta baya inda garden ɗin gidan ya ke. Hango Zaytoonah da ta yi kusa da bishiyar zogale ya sa ta ji sanyi a ranta. "Zaytoonah mi ya kawo ki nan?" "Zan ciri zogale" "Ai sai ki ce Madam Leslie ta tsinko miki" "Mi za ki yi da shi ma tukunna" "Zan tanadi Tsoho ne yau, kin san yana son kwaɗon zogale sosai" Wannan kalma dai ba yau ta fara jin sa ba, tunda farko-farkon zuwan su kusan kullum sai ta yi maganar tanadin Tsohon nan. Ko mi Tsohon nan ya ke ma ta ma dai a bayan fage to Zaytoonah na alfahari da shi. Shawaran Likita ta ke bi shiyasa ta hana Zaytoonan magana da Galadima. For now maganar Ben ake so a kawar tukunna although yanzu ta dena tsorata da rana amma ranan da aka gwada yi ma ta test aka barta ita ɗaya a office ɗin likitan aka kashe wuta sai da ta sake kiran sunan Ben. "Mu je ciki Madam Leslie za ta ciro miki zogalen" "Momm..." "Asibiti za mu je, idan mun dawo sai ki tanadi Tsoho" Hannunta ta kama su ka wuce cikin gida sai da ta fara ajiye zogalen da ta ciro a kitchen kafin su ka fito inda Dreba ya wuce da su Asibiti inda Zaytoonah za ta yi awu. *** "Na ce Mahbubi tunda dai kwana biyu ne mi zai hana kawai yaran su yi zaman su idan ya zo ƙarshen wata sai mu tafi da su" "Ba matsala sai ki zauna da su kawai, ƙarshen wata sai mu je duka" "Ina nufin ka ga dai yaran nan suna Makaranta idan sun je ba karatu su ke ba sai wasa" "Ba matsala ki kula da su a nan har su yi karatun" Shigewa banɗaki da yai ne ya rufe maganar. "Yau na jawa kaina" ta faɗa a fili. Yaran da ba ta so su je weekend tare, su ɗin dai ta fita ta nema ta ce su shirya kayan su za su tafi Zaria da yamma... Wannan karan zuwan da ta je ko Fada ba ta je ba iya kacinta gidan su sai kuma gidan ƙawayenta biyu da ta je. Ranan Lahdi da za su koma sai ga Hajia Abu ta kawo mu su ziyara. Ala dole ta ma ta ladabin ƙarya harda ba ta haƙuri lokacin da Hajiyar ke faɗa akan rabon da ta zo gidanta har ta manta, ko a waya ma ba ta nemanta. Ghazala ta fake da cewa hidiman Yara ne ke riƙeta ga kuma shagonta da ba a jima da kawo mata kaya ba... "Wai Yaran nan kuna ta ina ne" Ghazala ta faɗa a tsawace. Galadima ne ya sa ta fita da yaran shopping. Da da ne jiki na rawa za ta yi amma yanzu kam ko kaɗan ba ta son wannan aikin wahalan. Raziya da Suhailah ne su ka fito daga ɗaki. "Ita kuma mai hannu ɗaya da rabin fa?" "Tana kashi" Raziya ta faɗa fiska a ɗaure. "Zo nan Maryam" ta kira Suhailah da ke tsaye tana wiki-wiki da ido Murɗe kunnen yarinyar ta yi ta ce "ba na hanaku shiga ɗakin Daddyn ku ba, amma shegen kunnen ki jiya harda shiga ki kwanta ki yi bacci" "Hajiya, Daddy ne fa ya kirata" "Yi min shiru munafuka, da ya kirata sai ya ce ta kwanta ta yi bacci" Sheshsheƙar kukan da ta fara ya sa ta sake kunnen tana faɗin " yi min shiru a nan ko na zane ki" Suhailah ta yi saurin haɗiye kukan. "Falaq idan ba ki fito yanzu ba tafiya zan yi" Ta faɗa tana sauƙa ƙasa. Suhailah ta faɗa jikin Raziya tana kuka ƙasa-ƙasa. Ba yau ne ta fara mu su wannan cin zalin ba. Ranƙwashi da jan kunne ya zamar wa Hajiya Ghazala ɗabi'a idan tana yiwa yaran faɗa. Washegarin ranan da Yaran su ka yi maganar sun yi missing Zaytoonah a wajen cin abinci ma kowannen su sai da kansa ya gaya ma sa dan ranƙwashi bibbiyu ma su kyau ta mu su tareda gargaɗin idan su ka sake kawo maganar Zaytoonah a gidan sai ta mu su duka... *** Muntari ya samu lafiya sai dai yana zaune akan wheelchair ne saboda ba shi da ƙarfin jiki. Likitocin sun ce zuwa wata huɗu ma zai iya dena amfani da kujerar. Kwanan su huɗu tareda su Mommy kafin su ka wuce Nigeria. Mommy ta sha addu'o'i da godiya ba adadi a wajen Iya. Dan Iya kam yadda su ka tafi ba ta ɗauka Muntari zai yi rai ba... "Are you ready?" Dr Solomon ya tambayi Zaytoonah a karo na biyu. Ta gyaɗa ma sa kai. Ya sake ma ta bayani a taƙaice " kar ki manta ni da ke da Maman ki ne a nan duk wanda za ki gani ba gaskiya ba ne. Minene gaskiyar?" Ya tambaya yana kallon idon ta. Zaytoonah ta ce " idan mutum ya mutu baya dawowa duniya, Ben ya mutu ba zai sake dawowa ba, duk abinda zan gani ba Ben ba ne ƙarya ne da ke ɗaga min hankali. Gaskiya shine na dena jin tsoronduk abin da zan gani mai kamar Ben. Ben ba zai min komai ba. "Good" Cewa yai ta rufe ido bayan ta rufe ya ɗauko wani na'ura mai kama da camera, ya ɗaurawa Zaytoonah shi a kai. Sai da ya zauna kafin ya ce ta buɗe ido. Tana buɗe ido sai ta ganta a wani ɗaki tana tafiya a hankali. Kwatsam sai wutar ɗakin ya mutum ko'ina ya koma duhu. Daga inda ta ke zaune jikinta ya fara ɓari amma ba ta yi ihu ba. Likita ya danna wani remote sai gashi wutan ɗakin da ta ke gani ya dawo amma tsaye a gabanta sai ga wani mutumi tsaye ya juya ma ta baya a hankali kuma sai ya juyo sai ga fiskarsa ya bayyana sak Ben. Mommy da Likita suka zubawa Zaytoonah ido suna ganin yadda ta ke ɓari ba ta yi ihu ba amma da ka ganta ka san tana tsorace. Ta jikin na'ura Likitan ya danna remote sai ga cartoon mai kama da Ben ya cigaba da tafiya yana nufo Zaytoonah. San da ya kai hannu zai shaƙota Zaytoonah ta calla ƙara. Likitan ya zo ya da sauri ya cire ma ta na'uran. Maimakon Ben da ta ke gani ta jikin na'uran sai ta ga Likita da Mommy a gabanta. "Sorry Mrs Zaytoonah we'll try another time"... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 66 Bismillahir Rahmanir Rahim *Princess Alinah* Ruwa ake tsalawa tun gabannin Asuba har kuma yanzu da agogo ya nuna ƙarfe goma da minti biyu. Cikin ruwan ya taho office amma tunda ya zo ya kasa taɓuka komai, tunanin Matar sa ya hanashi yin komai. A koda yaushe Mommy nuna ma sa ta ke Jiki da sauƙi amma ta ƙi bari ya ji koda muryan Matar sa balle kuma ya ganta. Gaskiya zuwa ƙarshen watan nan dole ne kawai ya tafi chan ɗin ya je ya ganta, idan yaje ai dole Mommy ta bari ya ga Matar sa. Ya sauke labulen window da ya ɗaga tareda komawa kan kujera. Buɗe Laptop ɗin sa yai ya shiga wani folder da ya sawa suna *Qurratul Ayn* hotuna ne barkatai a cikin folder ɗin, ya sa yatsa ɗaya ya danna hoton farko nan da nan ya buɗu, ya ƙurawa hoton da ke screeen ɗin ido yana murmushi, bacci ta ke yi ya ɗauketa hoton ba ta ma sani ba. Wannan dai Yarinyar da a shekarun baya da ya ganta ya ke ƙoƙarin sanin wacece ita amma baisamu dama ba, ita ce Allah ya mallaka ma sa ita cikin sauƙi. Ita ce kuma ke charger ma sa kai har yanzu. Baya tunanin ko lokacin da ya ke tareda marigayiya ya ma ta irin wannan shauƙin da soyayyar. Idan yana tareda Zaytoonah komawa ya ke matashi ɗan Shekara ashirin da biyar. "Uncle ina ta Sallama" muryan Ahmad ya katse ma sa tunani. Yana ƙoƙarin minimixing hoton Ahmad ya ɗan sako kai zai leƙa yana faɗin "Uncle video call ka ke da Maman 'yan b..." bai ƙarisa ba Galadima ya ranƙwashi kan sa "Ahmad ka maida ni Kakan ka ko?" Ahmad ya fara sosa kan sa yana dariya. "Uncle Justice dama maganar case ɗin 'yan ƙauyen nan ne da ka bani jiya. Ina tunanin zan je ƙauyen gobe akwai tambayoyin da zan mu su" "Hakan ma na da kyau, ka rubuta abunda na ce?" "Yes gashi nan" ya faɗa yana miƙa ma sa takardun da ya kawo "Ok good, je ka zan duba" Bayan fitar Ahmad Galadima ya ce "Ahmad ba dai gulma ba, kamar mace" ya jawo Laptop ɗin sa ya sake buɗe hoton Zaytoonah da ya ke gani. *** "Wallahi kika daketa zan Fallasa" Ghazala ta sauke wayar charger da ta riƙe tana shirin dukan Falaq da shi. "Za ki fallasa me?" Duk da yanzun tana ɗan tsoron Ghazala amma hakan bai hana ta yin magana ba. "Zan gayawa Daddy ke ce kike tsoratar da Anty Zaytoonah da..." "Ashe za ki ci Uban ki a gidan nan kuwa. Koma me kika faɗa ma sa kin san kan ki zai koma tunda sanin kan ki ne sarai baya son ƙarya kuma kin ma sa ƙarya" Ganin Raziya ta ɗan tsorata sai ta cigaba "Gara ki rufawa kan ki asiri ki riƙe dogon bakin kin nan. Dan idan magana ta fito ke za ki cutu inaga ma dai boarding school zai kai ki ko kuma ma ya aurar da ke. Marar kunyar Yarinya kawai" Ta juya ta kalli Falaq da ta haɗa gumi saboda marin da ta sha a wajen Ghazala. "Ke kuma na sake gani kin shiga kitchen kin ɗau wani abu ba tareda kin tambayeni ba sai na miki shegen duka. Shegen ƙorafin baki ba za ki yi magana ba sai ki dinga zubawa mutane ido to ya isa haka. Kina jina?" Falaq ta gyaɗa kai. "Simple 'Hajiya zan ɗau soyayyen nama' ya gagareki faɗa, saboda dan ke ake soyawa. Shegen raini" Tsaki ta yi ta bar kitchen ɗin cike da takaicin Yaran. Gaba ɗaya Yaran sun sangarce komai taƙamar su gidan Daddyn su ne. Ba za ta lamunci wannan gadaran ba idan sun je gidan mijin su suyi abinda su ke so. Wannan gidan ta ne, ita ɗin Matar Justice Yunus Muhammad Abbas ce... Sai da ta daidaici Galadima ya nitsu wajen lemon da ya ke sha sannan ta fara magana. "Abu Razz ka san dai tunda Allah yai wa Adda rasuwa ko da ba ka aureni ba matsayin Uwa na ke ga su Raziya. Ba zai yiwu a matsayin Uwa na ga abinda zai cutar da Yaran nan kuma na share ba, sai Allah ma ya tambayeni" ta ɗan yi shiru kafin ta cigaba ganin dai maganar ta ɗan shige shi. "Ka san dai Raziya har yanzu Yarinya ce, ka san tana cikin shekarun tashen balaga and zamani ya riga ya ɓaci yanzu. Allah na gani ina iya ƙoƙarina akan su. Kafin dai na yanke hukunci akan abinda na gani gara na gaya ma ka tunda da Ita ɗin da shi ɗin duk ƙarƙashin kulawar ka su ke" Wannan karan ido ya zuba ma ta yana jiran ta ƙarisa bayanin ta. " Ina tunanin Ahmad da Raziya soyayya su ke, ka san Ahmad da shegen rawan kai ba nitsuwa ce gareshi ba and kuma Raziya ƙarama ce ba hankali ina tsoron abinda zai iya biyu baya" "Wani Ahmad?" "Ahmad dai na ka, ɗan Hajia Saratun Lagos" Bai sake cewa komai ba hakan ya sa ta ci gaba da magana. " tun wani rana da ya zo gidan nan kwanaki na ganta kusa da shi har tana cewa wai ya goyeta na fara zargin wani abu amma ɗazu da safe na tabbatar ga chats ɗin da na gani a wayarta da shi Ahmad ɗin" Ta ƙarisa maganar haɗeda miƙa ma sa wayar Raziya. Ya karɓi wayan ya fara karantawa. Ba wani abu ne na ɗaga hankali sosai ba cikin hiran na su sai dai yadda Raziya ke kiran Ahmad da Dear da kuma yadda shima ke kiranta da Razy Luv akwai ayar tambaya. Hiran su na baya- baya kawai ya karanta inda Raziyan ke cewa wannan karan idan sun yi hutu a Makaranta gidan su Ahmad ɗin za ta je a Lagos ta yi hutun ta a chan. Har da cewa idan har Daddy ya amince ta je to tare za su tafi. "Ni gaskiya ban yarda da Ahmad ba, renon turawa aka ma sa kar ya zo ya lalata min 'ya. Dududu nawa Raziyan ta ke, mi ma ta sani gameda rayuwa har tana tunanin tafiya hutu da namiji" Ajiye wayar yai ya ce ta kira ma sa Raziya. Bayan fitar ta Galadima ya rufe ido. Tarbiyyan yara akwai wahala musamman mace gashi Allah ya bashi su har uku. Ba wai yana zargin Ahmad da mummunan abu ba ne amma yanzu ɗan Mutum ba a ma sa shaida ɗari bisa ɗari dan haka ba zai ruling possibility na maganar da Ghazala ta yi ba. Bayan Raziya ta zo ce ma ta yai ya riƙe wayar ta ba ita ba waya kuma sai ta gama secondary school. Daddy ta kalli Hajia Ghazala cike da tsana. Ta san hukuncin da Daddy ya ɗauka baya nasaba da Ghazalar tunda ɗazu da rana ta ce za ta yi maganin ta a gidan. Maimakon ta fara roƙon sa sai kawai ta ce "Ok Daddy" ta miƙe ta tafi. Bayan fitar ta Ghazala ta ce "Mahbubi ba ka ce ma ta komai ba. Ba za ka binciki gargar mi ke tsakanin ta da Ahmad ba" "zan yi magana da Ahmad gobe" Ba haka ta so ba so take ya kama Raziya da faɗa idan ta kai ma ya hukuntata ko da ba duka ba... Washegari Galadima faɗa sosai yai wa Ahmad da ya je office. Duk da dai bisa bayanin da Ahmad ɗin ya ma sa babu komai tsakanin sa da Raziya kawai shaƙuwa ce ta 'yan uwan juna amma a hakan sai da ya ma sa faɗa sosai domin daga irin haka ta ke farawa. Ko da ciki ɗaya su ka fito bai kamata su rinƙa kiran juna da suna irinta masoya ba, bai dace ba. "Uncle Chill, ka cika old school dayawa. Miye aciki idan na kira ƙanwata da Razy Luv" Ahmad ya faɗa yana murmushi "Ban yarda ba Ahmad. Raziya is just 14 ba na son abunda zai ɗauke ma ta hankali tun yanzu. Duk wannan da ku ke ba tarbiyyan Hausa Fulani ba ne, ba tarbiyyan musulunci ba ne. Call her Raziya ko Fatiman ta kawai, ba na son shirmen nan ka ji" Ahmad ya ɗan langwaɓe fiska ya ce "Ok Sir" "Ya maganan tafiyar ta ka?"... *** Sosai shawaran da aka bawa Mommy ya taimaka wajen samun lafiyar Zaytoonah. "Addu'a shine maganin ko wanne irin matsala. Ban ce taimakon da ake ba ta ba zai yi amfani ba amma kuma idan aka haɗa da addu'a sai ka ga sauƙi ya samu da wuri. Zan rubuta miki wasu addu'o'i da za ki dinga yi da wanda ita kan ta za tana yi. Insha Allah za ta samu lafiya" Bayanin wani babban Malami kenan wanda ta tuntuɓa gameda maganar sihirin da aka yiwa T J ya ke kuma taimaka ma ta da addu'o'i. Fushi sosai Zaytoonah ke yi da Galadima, tun tana kewar sa har ta koma jin haushin sa gani ta ke dai shareta yai saboda ya yarda da gaske ta yi hauka. Wato a matsayin sa na Mutum mai daraja ba zai iya zama da Mata mai matsalar ƙwaƙwalwa ba. Sau ɗaya an kawo ma ta 'yan biyu hutu duk da sun sanar ma ta yadda Galadima ke yawan zuwa duba su amma hakan bai sa ta sassauta ma sa ba. Ta kai hannu ta shafa cikinta wanda ke ɗan motsawa a hankali. "Baby ga shi Daddy ya manta da mu, its just me and you now" "Adaeze" Mommy ta kira sunan ta daga cikin ɗaki. "Yes Mom" ta miƙe a hankali ta wuce ɗakin. lokacin da ta shigo ɗakin Mommy na zaune a bakin gado tana danna waya. Gefen mommyn ta zauna tana tambayarta mi ya faru. "Yanzu aka kirani" ta riƙe hannun Zaytoonah ɗaya sannan ta ce "Mrs Haddish is gone" "Ta sha jinya sosai, she's a good woman" ta faɗa a hankali. Bayan kwana biyu da Mutuwar Mrs Haddish aka yi Funeral ɗin ta inda aka bisine ta kusa da Mr Haddish kamar yadda ta buƙata, Zaytoonah na cikin wanda su ke karɓan gaisuwan mutuwa saboda koba komai an riga an zama ɗaya. Washegarin da aka yi burial ɗin ne su ka dawo Las Vegas kuma a ranan Zaytoonah ta fara naƙuda chan da yamma. Mommy ta wuce da Ita Asibiti duk da kuwa a yadda su ka rubuta haihuwar saura kwana huɗu. Zuwa ƙarfe shaɗaya na dare Zaytoonah ta haihu... *** "Ikon Allah kamar su ɗaya da wannan yarinyar miye ma sunan ta?" "Falaq" Zaytoonah ta ba da amsa Mommy ta sake kallon jinjirar dake hannunta tana murmushi. Tun a daren ta kira gida ta gaya mu su. Ta so kiran Galadima ta sanar da shi amma ta bari sai da safe tunda ta san dare yayi a Nigeria. Daga baya kuma sai ta tura ma sa text. A chan Nigeria kuwa Galadima bai duba wayan sa ba sai bayan ya dawo daga sallar Asuba. Da ke babbar wayar ya fara dubawa saboda yana son duba email na shi sai kawai ya ga message daga wajen Hajia Ni'ima da Salman. Tuni ya buɗe message ɗin Hajia Ni'imar inda ya ci karo da hoton jaririya tareda saƙon taya murna a ƙasa. Saƙon Salman ɗin ma hotunan ne amma maimakon na jaririyan kaɗai harda na Zaytoonah tana kwance a gadon Asibiti. *Alhamdulillah Princess Alinah Yunus Muhammad Abbas has grace our world* Abinda Salman ya rubuta kenan aƙasan hoton yarinyar da ko makaho ya san ta shi ce, wannan jinjirar har ta fi Falaq kama da shi. Tambayar kan sa yai dama da ciki Zaytoonah ta tafi? 2/11/21, 10:04 PM - ****: 67 Bismillahir Rahmanir Rahim *Recovered* Cike da ɗoki ya dannawa Salman kira ya ci sa'a kuwa ringing ɗaya aka ɗauka da alama ma wayar dama na hannun Salman. "Ranka shi daɗe na san ni na fara yin albishir dan haka ina buƙatan goron albishir" "Kar ka damu wannan ba matsala ba ce. Na gode da wannan karramawa" Sai da ya ja numfashi kafin ya ce " ina fata suna lafiya?" "Lafiya Sir, an ma sallamesu, ɗazu mu ka yi magana da Adaeze da su ka isa gida" Murmushi Galadima yai sannan ya ƙara ma sa godiya bayan Salman ɗin ya bashi bayanin da ya ke so. Bayan ya ga text ɗin da Mommy ta ma sa a ɗaya wayar sannan ya kira numbar ta ba a ɗauka ba hakan ya sa ya sake kira a karo na biyu amma still ba a ɗauka ba. Yana shirin sake kira ne wayar Hajia Abu ya shigo wayar sa. "Yanzu Ni'ima ke sanar da ni Zaytoonah ta sauka, da gaske mace ta haifa itama?" Ya ɗan ji ba daɗi a ran sa dan ya san ma'anar abinda Hajiyar ta faɗa sai dai bai taɓa sawa a ransa zai so ɗa namiji fiye da ta mace ba. Dukkan su 'ya'ya ne kuma fatan sa shine Allah ya raya ma sa su da imani, su yi rayuwa mai albarka wanda ya ke fata ranan gobe Manzon Allah yai alfahari da su. "Alhamdulillah na samu labarin da uwa da 'ya suna nan lafiya" ya faɗa a hankali. "Allah ya raya" Hajia Abu ta faɗa ciki-ciki Amin ya amsa ma ta "Za su zo ayi suna a nan ne ko kuwa?" "Ba lallai su zo ba gaskiya" Daga haka Hajia Abu ta kashe wayar. Bayan ya gama waya da Hajia Abu ya sake gwada numbar Mommy wannan karan kam an ɗauka. Bayan sun gaisa ya tambayeta ya me jiki ta ce ma sa Alhamdulillah da sauƙi, Zaytoonah da Baby duk suna bacci. Godiya ya ma ta sannan ya tambayi ko akwai musulmin da ke kusa da zai wa Baby huɗuba tunda baya nan. Mommy ta ce tun a Asibitin Sheikh Hassan ya yiwa Baby huɗuba. Yana son tambayarta yaushe za su dawo amma bai samu daman hakan ba saboda Kashe wayar da Mommyn ta yi bayan ta ce ma sa sai anjima. Duk wannan badaƙalar da ake yi Ghazala ba ta sani ba. Da ke ta fara janye jiki da 'yan uwan Galadima sai ya zamana babu wanda ya kirata ya sanar da ita. Itama tunda ta tashi ba ta bi ta kan wayarta ba kitchen kawai ta wuce. Fiskar sa ɗauke da annuri ya sauko ƙasan, wani nishaɗi ya ke ji a ran sa kamar wani sabon Ango. Shi kaɗai ake jira a wajen dinning ɗin tun ɗazu su ke jira ya fito amma bai shigo ba hakan ya sa Ghazala ta haura sama ta ma sa magana a hakan ma sai da ya ƙara kusan minti bakwai kafin ya fito. "Kafin a fara cin abinci ina da good news da zan sanar mu ku" "Daddy za mu je Yola ko?" Suhailah ta faɗa da sauri. "Wrong" "Anty Zaytoonah za ta dawo" Falaq ta faɗa "No, Raziya fa, mi ki ke tunani?" Raziya ta kalli Ghazala sannan ta maida kallon ta ga Daddyn na su ta ce "Anty Zaytoonah ta warke" Cikin ran Ghazala ta ce 'lallai ma yarinyar nan' "Tunda ba ku canki dai-dai ba barin faɗa" Sai da ya kalli fuskokin su ɗaya bayan ɗaya wanda ke ɗauke da curiosity na son sanin minene good news ɗin kafin ya ce. "Kun samu baby Sister, Antyn ku ta haihu jiya da dare" "Yeeeeeeeeh" suka haɗa baki wajen faɗa yayinda Ghazala ta ji saukar guduma a tsakiyar kan ta. Sama-sama ta ke jin sanda yaran su ka yanyame Galadima suna ce ma sa ya nuna mu su hoton Baby. Ta ɗago jajayen idanun ta ta kalli Galadima da ke ta murmushi saboda yadda yaran ke ta praising jinjirar. "Zaytoonah na da ciki, Zaytoonah ta haihu" abinda ke yawo a ƙwaƙwalwarta kenan. Daga baya kuma da ta tuno abu biyu sai ta yi murmushi wanda yai nasaran kawar da ɓacin ran da ta ke ji yanzu. Zaytoonah ba Matar Galadima ba ce yanzu sannan 'ya mace ta haifa ba namiji ba. Sai da yaran su ka nitsu su ka koma wajen zaman su aka fara cin abinci kafin ta ce "Abu Razz Allah ya raya mana ita da imani, ashe da ciki ta tafi jinya. Alhamdulillahi ma da ta sauka lafiya ba ta illata 'yar ba" Sai da ya kalleta kafin ya kauda kai ya ce "Amin"... *** "Daddyn Raziya na son magana da ke, nan da minti biyu zai sake kira" Mommy ta faɗa tareda ajiye ma ta wayar a gefenta. "Mommy da kin barshi ma zamuyi magana gobe" "Idan ya kira kika ɗauka sai ki gaya ma sa ya bari gobe ku yi magana" Daga haka ta fice daga ɗakin. Zaytoonah ta cigaba da kurɓan tea a hankali tanayi tana tura baki kaman a gaban Galadiman ta ke. Minti huɗu sai ga kiran sa ya shigo. Ta bi wayar da kallo ba tareda ta yi niyyar ɗauka ba sai da ta kusa yankewa ta ɗauka ta sa a kunne ta yi shiru. Sallama yai cikin muryan sa mai ratsa zuciya. Ta ciki ta amsa ba tareda bakinta ya motsa ba. "Qurratul ayn kina jina?" Kai namiji! wato ta nan kuma ya ɓullo. Ba wai dan ta so ba amma kuma sunan da ya kirata da shi ɗin ya yi tasiri a ranta. " 'yan mata na ki min magana mana na ji zazzaƙar muryan ki" Sai da ta juya ido kafin ta ce "minti biyun da ka ce za ka kira kenan" "Tuba na ke Qurratul ayn, kiran Mai Martaba ne ya shigo wayata" Ba ta yi magana ba sai ma kumbura baki da ta ke yi. "Kina jina Princess, ki hau whatsapp na gan ki Dan Allah, na yi kewar ki dan Allah" "Ba wani, all this while mi ya hana ka zo ka ganni, almost 6months fa. Ni dai na san ba ni da wani matsayi a wajen ka. Dama mi za ka yi da wacce ke son kashe ma ka 'ya'ya. You dont love me, you dont want me..." "Zaytoon" ya kira sunan ta da sigar da ta san jan hankali ne. "Ki bani dama na ganki Dan Allah" ya faɗa a sanyaye. Samun kan ta ta yi da kasa yin musu. Ita kan ta tana son ganin sa dan ta yi missing ɗin sa sosai, the last time da ta ga hoton sa shine wani zuwan da yai Zaria ya je gidan su suka ɗau hoto da 'yan biyu Salman ya saka a status ɗin sa. Shine ta gani a wayan Mommy. Duk da Mommy ta ma ta bayanin dalilin da ya sa ba ta bawa Zaytoonahnwaya idan Galadima ya kira, saboda yana cikin process na treatment ɗin ta ne. Amma ko sau ɗaya ai ya kamata ya zo ya duba ni, ko sau ɗaya. Abinda ta ke tunowa kenan lokacin da video call ɗin ya connecting. "Masha Allah! Princess ke ce haka" Zaytoonah ta haɗe fiska kamar wata Boss. "Na san ina da laifi amma yanzu dai a min murmushi na gani ko hankalina zai kwanta" Zaytoonah ta sake haɗe fiska tareda kau da kai gefe. " 'Yan mata ba za ki kalli Tsohon na ki ba" Sai da ta ja ma sa aji kafin ta juyo ta ƙura ma sa ido. "Kin yi kyau" ya faɗa tareda hura ma ta kiss. "Dole na zo na ganki 'yan mata na, haƙuri na ya ƙare. Ina 'ya ta?" "Wai 'yar ka. Lokacin da na ke wahala da ita ai ba ka nemi ka san lafiyata ba" "Adaeze ban sani ba, ba ki sanar da ni ba. Ina buƙatar samun lafiyar ki shiyasa na bi umurnin da Hajia ta faɗa. Da na sani da ba zan iya haƙura iya waɗannan lokacin ba" "So ba ma dan ni za ka zo ba sai dan Babyn ka. Shikenan na san matsayina" "Ya Allah! Barrister kar ki ɗaure ni da maganar da ban faɗa ba" " idan na yi hakan mi Justice Yunus zai yi a kai?" Ta faɗa tana wani juya ido. " hukuncin ƙarisa rayuwar ki a gidan Yunus ɗan Muhammad Abbas, tareda aikin..." Ihun da ya ji ya sa shi faɗin "Subhanallahi! Princess ina zuwa" Da sauri ya ajiye wayar ya fita. Ghazala ce ta ranƙwashi Raziya shine ta challa wannan ƙaran sanin cewa Daddy na gida. "A ni ki ke wa rashin kunya Raziya. Ni ki ke cewa munafuka" Kamota ta yi da ƙarfi ta fara kai ma ta duka da hannu ita kuma sai ihu ta ke tana kiran Daddy. Da gudu Galadima ya sauko dan ya tsorata da ihun da ya ke ji. "Mi ye haka?" Ghazala ta sake Raziya ta kalli Galadima tana huci. Maganar haihuwar Zaytoonah ya dagula ma ta lissafi ga wannan banzan yarinyar ta tunzura ta. "Ghazala ba magana na ke ba" "Rainin yarinyar nan yayi yawa, har ta kalli tsabar ido na ta ce min munafuka. Wani irin tarbiyya ne wannan" Kallon ta ya ke cike da mamaki, bai taɓa tunanin Ghazalar da ya sani kusan shekara ɗaya da rabi da ya wuce ba ne. Matar da ke haba-haba da yaran sa tana lailaya su kamar ƙwai shine wai yau ta ke dukan ma sa 'ya. "Ki sameni a ɗaki" ya faɗa tareda barin gurin. Bayan wucewar Galadima, Ghazala ta zunguri Raziya ta ce " ke kuma ni da ke a gidan nan" Da ta samu Galadima a ɗaki tambayarta yai dalilin dukan Raziya da ta ke yi. "Ni ban gane ba. Ba ni da ikon hukunta 'yarka kenan idan ta haihu ko me?. Dole mana ka min gori tunda ban haifa ma ka komai ba ai ita waccar mai ciwon haukar da ta haihu tun safe ka ke ta wani fara'a kamar wanda akai wa kyautar Aljannah" Duk bayanin da ta yi bai tanka ba sai kawai ya sake tambayar sa "mi Raziya ta mi ki?" Rasa abin faɗa ta yi dan idan aka fara tone-tone ba za ta ji da daɗi ba tunda dai akan maganar Zaytoonan ne Raziya ta kirata da munafuka. "Yau na san matsayina a gidan nan, wato kallon matar uba ka ke so su min ba kallon uwa ba. Shikenan duk abinda Raziya za ta yi a gidan nan ba zan sake saka baki ba" daga haka ta fice daga ɗakin a fusace. Ya ji zafin abinda ta yi amma farin ciki da ya ke ciki ya kawar da ɓacin ran abinda ta ma sa dan haka ya maida hankalin sa kan wayar sa dan ya kira Zaytoonah ya ga Babyn sa. Itama Zaytoonan taburman fishi ta hau dan sau uku yana kiran wayar amma ba a ɗauka ba... *** Yadda ake shirye-shiryen suna ka ce Baby Alinah ce haihuwar farko da akaiwa Galadima. Kwana kafin suna ya tattara iyalin sa suka koma Zaria dan a nan za ayi sunan. Duk da mai jego da baby ba sa nan amma hakan bai hana yin hidiman suna sosai ba. Ghazala dai sai ido ta zubawa Galadima dan tun ranan da aka yi case ɗin dukan Raziya da ta yi bai sake sake ma ta fuska ba. Suma 'yan uwan Galadima da su ka yi ta shige da fice ranan suna ba ƙaramin ƙona ran Ghazala yai ba, ita kam da namiji aka haifa da ta shiga uku a hannun su. Wannan suna ya sa ta sake kwaɗaita haihuwan nan, ko da artificial insemination ne za ta yi sai dai matsalarta ɗaya ba lallai Galadima ya yarda da irin wannan abu ba sai dai... Haka aka sha hidimar suna aka watse yarinya dai ta samu sunan da mahaifiyarta ta zaɓa ma ta wato ALINAH... *** Yau sati biyu kenan Shehu na zuwa gidan Malam Zulkiflu mai ƙusumbi. Duk da zuciyar sa baya son zuwa wajen wannan Bawan Allah amma duk sanda Malam ɗin ya aiko ɗaya daga cikin Almajiransa su kira shi sai ya tsinci kan sa da kasa yi ma sa mu su. Yau ma ɗin zaune ya ke gaban Malam wanda ke rubutu a wani ƙaramin Allo. Tambayar da Malam ɗin ya sako ma sa ne ya sa shi yin nazari amma tun ɗazu da ya ke ta ƙoƙarin gano amsar tambayar Malam ɗin bai gano komai ba. Tambayar Malam tambaya ce da a baya ba ya son ji amma yanzu kuma da Malam ɗin yai tambayar sai ya tsinci ka san da son sanin amsar. Chan ya nisa ya ce " ni dai Malam ba zan iya cewa takamaimai ga daga inda na fito ba ko kuma na ce ga asali na ba, amma kuma gaskiya na jima ina yawo garuruwa ina kasuwanci dan har yankin Niger na shiga, daga nan ne ma na juyo zuwa Sokoto kafin kuma na dawo nan" Malam ya ɗago ido ya kalli Shehu ya ce "da izinin Allah za ka tuno komai. Kamar yadda na faɗa ka riƙe addu'ar da na faɗa ma ka" Shehu ya gyaɗa kai. Bayan Malam ya gama rubutu a jikin Allon ya kawo ruwan ZamZam da ya tanada saboda ayyukan sa irin wannan ya wanke Allon da shi sannan ya bawa kwanon da ke ɗauke da ruwan ya ce ya sha. Ba musu kuwa ya karɓa ya shanye tas... *** Yau ne za a yiwa Zaytoonah gwaji na ƙarshe. Ya kamata a yi shi tun kafin ta haihu amma saboda ta yi nauyi lokacin shiyasa aka ɗaga zuwa bayan ta haihu. Addu'o'in da ake ma ta da wanda ta ke yi duk ya taimaka wajen yaƙice ɗimuwa da ta ke yi duk lokacin da ta ke cikin duhu, ko ta ga hoton Ben. Ta kuma dena kama sunan Zuhayr a duk lokacin ma da ta firgita, ƙwaƙwalwarta ya fahimci Zuhayr ya tafi kenan ba zai kuma dawowa ba. "Kamar yadda na faɗa miki indai ki ka ci wannan test ɗin to zan rubuta miki cewa kin warke gaba ɗaya. Its a difficult test amma inada yaƙinin za ki ci" Likitan ta ya faɗa. Ya riga ya ma ta bayanin test ɗin kuma ta fahimta. Baby Alinah na goye bayan Mommy lokacin da Dr ya rufe fiskarta da wani ƙyalle. Mommy ce ta riƙe hannunta ta shigar da ita ɗakin da za a ma ta gwajin. Bayan an kulle ƙofar ne Dr da ke waje ya ce ta cire ƙyallen da aka rufe ma ta ido. Tana cirewa kuwa ta gan ta cikin ɗaki mai duhu. Mommy da Likita suna tsaye jikin na'uran computer suna ganin duk abinda ke faruwa a cikin ɗakin. Ɗakine mai duhu an riga an kwatanta ma ta inda switch ɗin kunna wutan ɗakin ya ke dan haka abinda za ta yi shine ta je wajen ta kunna wutan. Zaytoonah na tsaye cikin duhu ta ja dogon numfashi kafin ta karanta addu'a a ranta ta fara takawa a hankali. Ba ta fi taku biyar ba ta ji an kira sunan ta. "Zaytoonah" da murya irin ta Ben. Ta ɗan ji wani dim a ranta amma ta dake ta cigaba da tafiya. "You snatched away Zuhayr from me i'll kill you today, no body will save you" muryan Ben ya ratsa kunnen ta. Da da ne ihu za ta saka amma yanzu confidently ta ce "i know you are not Ben. Ben is dead, he's gone forever" Kyalƙyalewa akai da dariya sannan aka ce "you're joking Zaytoonah. I survived the gun shot, i'm alive" ya na gama faɗi sai kawai ta ga alamar ana takowa wajen ta. Danne tsoron da ke zuciyarta ta yi tana tuno cewa Mommy da Likita da 'yarta suna nan waje suna jiranta ba abinda zai sameta a wannan ɗaki. "I'm going to kill you Zaytoonah" Yana gama maganar ta ji an taɓa kafaɗarta ta baya. Ihu ta ke son yi amma ta rintse ido ta maimaita abinda Galadima ya sanar da ita jiya "Tawakkaltu Alallah" a fili. "Nobody is going to save you from me Zaytoonah" aka faɗa saitin kunnen ta. "You are not real. The reality is, Ben died years ago, he's never coming back" daga haka kawai ta ƙarisa da sauri ta je karshen ɗakin ta laluba hannunta a bango har ta samu switch ɗin wuta ta kunna. Tana kunnawa haske ya karaɗe ɗakin sai ga robot guda biyu ma su kaman Ben a ɗakin. Daga waje aka saka tafi. Fitowa ta yi daga ɗakin tana murmushi yayinda Mommy ta rungumeta cike da farin ciki. Duk maganan da ta ke a ciki wani nurse ne da ke gefen Likita ke magana da shigen muryan Ben yayinda ya ke directing movement ɗin robots ɗin. Lokacin da Zaytoonah ta janye jikinta sai kawai ta ga hawaye a idon Mommy. "Mommy kuka kuma?" "Dole na yi kuka Zaytoonah, waɗannan watanni are the tough times of my life idan aka cire lokacin tafiyar mahaifin ku. Na tsorata da halin da ki ka shiga Adaeze, ranan da aka ce kin yanki Raziya da wuƙa i couldnt sleep. Tunani na ya tafi cewa ko dai da gasken ne kin fara hauka, but i couldnt accept it shiyasa na yiwa Galadima magana indai ana treating PTSD zan je ko ina ne a duba ki. Zaytoonah lokacin da mu ka fara zuwa nan na ƙara tsorata sosai. Kina ɗauke da ciki and hankalin ki ya kasu kashi biyu idan ki na maganar Zuhayr kaman yana raye ki ke yi, idan kika koma wajen Galadima kuma kaman kuna tare da shi kike gani. Zan je wajen D, zan tanadi Tsoho. Ben zai kasheni its all over now" Ta ƙarisa maganar tana fashewa da kuka itama Zaytoonan sai ta saka kuka tareda rungume Mommy... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 68 Bismillahir Rahmanir Rahim *Husband and wife* "Ban gane za ku tafi America gobe ba". Ghazala ta faɗa cike da Zullumi Galadima bai kulata ba sai ma ƙoƙarin zuge jakar sa da ya ke. "Ranka shi daɗe ka sani a duhu" Sai da ya ajiye jakar gefen gado kafin ya juyo ya kalleta tana tsaye ta riƙe ƙugu da hannayenta duka biyu. Jiya da dare ta dawo daga Lagos ta je clearing kayanta da su ka iso. Isowar da za ta yi ta ga 'yan biyun Zaytoonah da Junior a gidan suna kallo tareda sauran yaran a Falo. Ba ta tambayi dalilin zuwan su ba dan Galadima ya sha zuwa ya ɗauko su suzo su wuni a gidan amma ba sa kwana. Yau da safe kuwa bayan sun karya Galadima ya sanar da ita gobe jirgin su zai tashi shi da duka yaran za su tafi ganin Zaytoonah da Baby. " wannan ba adalci ba ne, idan har 'yar ka kake son gani ka ce ta kawo ma ka ita mana, kai da yara yanzu idan duka kuka tafi sai ta ɗauka ma ko kana son mayar da ita ɗakinta ne ni kuma wannan ba zan amince da shi ba..." "Ba na tunanin zuwa duba lafiyar matata da 'ya ta zai zama rashin adalci a gareki. Ki kama girman ki Dan Allah" "Ban gane matar ka ba, yaushe ka mayar da ita?" Ghazala ta faɗa cikin tashin hankali. Kallon rashin hankali ya ma ta na 'yan daƙiƙu. Har ba zai yi magana ba amma sai ya ga gara kawai ya fayyace ma ta koma minene ta ke ɗauka ba dai-dai ba. "Kamar yadda kike matata haka Zaytoonah ta ke matata. Idan kina da wani labari saɓanin haka to ban san wannan ba" Ashe dai gani da ji na iya gushewa mutum a wasu lokuta domin kuwa maganar Galadima na ƙarshe ya saka Ghazala ta rasa jinta da ganinta na wani ɗan ƙaramin lokaci. Fitan Galadima daga ɗakin ne ya ba ta daman zama a bakin gado tareda dafe kan ta dake wani mugun sarawa. Galadima bai saki Zaytoonah ba. Mi hakan ke nufi? ... *** "Hamma dan Allah ka karya kafin ka fita" Humairah ta faɗa tana marairaice murya. "Muna da zaman kotu yau kuma na makara" "Hamma Dan Allah ko shayi ne ka sha" "Auwal ka tsaya ka ci abinci, komai ai sai da lafiyar jiki ake yi" Muntari ne yai wannan magana wanda shima ke zaune kan keken sa yana karyawa. Ba yadda ya iya dole ya ja kujeran dinning ɗin ya zauna ya ɗauki mug ɗin da Humairah ta ajiye a gaban sa ya kurɓa. Cikin minti uku ya kammala cin slize ɗin bread huɗu wanda ke haɗe da ƙwai ya kora da shayi ya miƙe ya fita. Yana ƙoƙarin tada machine ɗin sa Humairah ta fito da gudu riƙe da wayarsa ashe inda ya zauna a wajen dinning ɗin ya manta. "Hamma gashi" ya amsa tareda yi ma ta godiya. Har ya buɗe gate ya fita ba ta bar bin sa da murmushi ba. Duk shawaran da Zaytoonah ta ba ta tana amfani da shi amma still har yanzu ba ta ga wani chanji tattare da shi ba. Bayan ta koma cikin gida ne Muntari ke tambayarta yaushe su Zaytoonah za su dawo. Humairah ta ce sun yi magana da Zaytoonah akan sai Alinah ta cika kwana sittin kafin nan ta ɗan yi ƙwari. Muntari ya mu su fatan Allah ya kawo su lafiya Humairah ta amsa da Amin. Humairah da Zaytoonah sun riga sun sake jiki da Muntari hakama Auwal amma Salman har yanzu ya kasa sake jiki da shi, wannan ya sa ma ko gidan ba ya zuwa, idan ta kama dole kuwa a ƙofar gidan zai tsaya ya kira Auwal ya fito su yi maganar da za su yi. Wannan abu na damun Muntari sosai sai dai kamar yadda Iya ta faɗa a hankali zai haƙura ya yafe ma sa... *** Duk da ba wannan ne karon farko da yaran ke zuwa ƙasar America ba amma wannan karan ziyarar ta daban ne. Dukkan su shida kowa na ɗokin ganin baby Alinah. Shi kan sa uban gayyar da ka ganshi ka san he's excited. Duk wani hayaniyar Ghazala da ta yi safiyar da za su fito daga airport ya ajiye shi suna hawa jirgi kuwa ya maida hankalinsa kacokam wajen Qurratul ayn. Da tsakar dare su ka isa California kuma babu jirgi da zai tafi Las Vegas sai washegari ƙarfe tara na safe, dan haka dole suka kwana a hotel. Yara Matan ya kama mu su ɗaki ɗaya shima da yara mazan su ka kwana a ɗaki ɗaya. Tun kafin su fita ya riga ya kira ya booking jirgi dan haka suna zuwa bai jima ba suka samu ticket. Akwai gajiya a tattare da yaran amma ɗokin da su ke bai sa sun yi ƙorafi ba. Ƙarfe uku na rana su ka isa Las Vegas abin mamaki sai ga motoci biyu suna jiran su wanda Mommy ta aiko. Zuwan bazata ya mu su amma Salman da su ka yi tsarin da shi ashe bai iya riƙe sirri ba. Suna cikin motar Galadima ya kira Salman. Yana ɗaukan wayan kuwa ya fara ba da haƙuri. "Ranka shi daɗe wallahi Mommy ce ta kira tana son magana da Junior shine na ce baya kusa, da ta sake kira da dare still na ce ba ya kusa shine ta sa dole na gaya ma ta inda ya ke. Sai kawai na faɗa ma ta komai" "Nan gaba ba ni ba jan labule da kai" "Tuba na ke ranka shi daɗe" Salman ya faɗa yana dariya... Wani ƙaton gida motocin su ka shiga yayinda 'yan biyu ke ta ihun murna harda rige-rigen fita lokacin da motar ta tsaya. Da ke gidan ba baƙon su ba ne tuni su ka shige cikin gidan da gudu suna faɗin su za su fara ganin Baby. "GrandMa" su ka faɗa ganin Mommy tsaye tana waya. Rungumeta su ka yi suna tambayar ina ƙanwar su. Mommy ta ce su je sama tana wajen Zaytoonah. Itama ɗin duk da ta san da zuwan su amma ba ta gayawa Zaytoonah duka gaskiyan ba, ce ma ta tayi 'yan biyu da Junior za su zo ba ta ce harda Galadima da 'ya'yan sa ba. Zaytoonah na zaune bakin gado tana bawa Alinah nono 'yan biyu su ka shigo da gudu. "Yehhhh mu muka fara kallon Baby" "Ba na hanaku shigowa ɗaki ba sallama ba" "Sorry Mom" su ka faɗa suna riƙe kunne. Hannu su ka sa suna shashshafa kan Alinah da goshin ta. Zaytoonah ta ce su bari ta ƙarisa su ganta da kyau. "Mom, ina Baby Alinah da ni ta ke kama?" Hadid ya faɗa yana nuna kan sa. "Dalla chan da ni ta ke kama, ko Mom?" Hashir ya faɗa yana yiwa Hadid gwalo. "Kun zo fa kenan yaran nan, ba na son hayaniya Dan Allah" "Mom su Daddy da su Suhailah ma sun zo" "Ba na son ƙarya Hashir" "Allah Mom" Ba su ida maganar ba Junior da Suhailah su ka shigo ɗakin followed ba Raziya da Falaq. Yadda su ka yanyameta ya sa dole ta miƙa mu su 'yar ba tareda yarinyar ta ƙoshi ba. Miƙewa ta yi ta fita daga ɗakin, so ta ke ta tabbatar da cewa da gaske dai tareda Galadima su ke. Ta sama ta leƙa ta hango shi zaune suna magana da Mommy. Bai wani chanja ma ta ba sai dai furfura da za ta ce ya ƙara wanda kuma baiwa ce ya ke da shi, dan akwai dayawa da su ke da shekarun sa amma ba su da furfuran ko kuma na su bai kai haka ba. Ta jima tana kallon shi, wani sabon sauƙin shi na zuwan ma ta. A ɓangare ɗaya tana jin kamar ta sauka da gudu ta je ta faɗa jikin sa, yayinda wani ɓangare ke ƙoƙarin tuna ma ta fa har yanzu tana fishi da shi. Ta jima tana kallon shi kafin ta koma ɗaki wajen yaran. Ba ta fi minti biyar da shigowa ba Mommy ta zo ta ce Raziya ta kaiwa Daddyn su Alinah a ƙasa. Raziya ta riƙe yarinyar da kyau ta fita yayinda sauran su ka bi bayanta da sauri. Zaytoonah da ta kwanta kamar mai bacci Mommy ta kalla ta ce "ki shirya ki je ku gaisa sannan ki duba guest room a ƙasa ko akwai abinda zai buƙata a kawo ma sa" Yi ta yi kamar ba ta ji ba dan har Mommyn ta fita ba ta motsa ba. Sai da ta ƙara minti huɗu akan gadon kafin ta miƙe da sauri. Gaban mirror ta je ta duba kan ta sannan ta ɗan fesa turare kafin ta fita daga ɗakin. Lokacin da ta sauko yana riƙe da yarinyar Raziya na mu su hoto. Zama ta yi a kujera tana kallon su, sau ɗaya su ka haɗa ido da shi ya kauda kai kamar bai gan ta ba hakan ya sake tunzurata. Miƙewa ta yi ta wuce ɗakin baƙin da ke ƙasa ta duba duk wani abinda zai buƙata akwai a ɗakin. Bayan ta fito ne ta ce "Daddyn Raziya ko za ka shigo ka ɗan watsa ruwa" Ƙarisawa ta yi wajen Suhailah ta ce ta zo su je a ma ta wanka. Zuwa awa ɗaya da su ka biyo baya dukkan su sun yi wanka sun yi sallah. Yayinda aka gabatar mu su abinci a wajen dinning area. Za ta zauna a wajen Mommy ta ce ta je ta kaiwa Galadima abinci ɗaki. Haka dai ta ɗauki tray da aka jera ma sa abincin sa ta wuce da shi ɗaki. Zaune ta sameshi riƙe da tasbaha yana azkar. Ta ajiye abinci a gefen sa ta miƙe za ta tafi amma sai ya riƙe hannun ta. "Ina za ki je kuma?" "Wajen su Mommy" Hannunta ya kai bakin sa ya kissing sannan ya ce "zauna mu gaisa" Dawowa ta yi ta zauna yayinda shi kuma ya jawota jikinsa sosai sannan ya cigaba da azkar da ya ke. Bayan kusan minti goma kafin ya gama ya ajiye carbin ya kalle ta ya ce "har yanzu dai ba a yafe min ba kenan" "Ni ban ce ba" ta faɗa tana tura baki. Hannunta ya haɗa da na sa ya riƙe gam kafin ya ce " ba ki san farin cikin da na ji ba da na ɗauki Alinah a hannuna. Ji na yi tamkar ranan da na karɓi Raziya a hannuna. Thank you Qurratul ayn" Shiru ta yi tana jin daɗin kalaman sa. "Sai gashi na zo ko gaisuwa ban samu daga gareki ba. Allah ka taimaki wannan Bawa na ka a wajen Gimbiya Zaytoon" Murmushi ta yi kafin ta ce "ina wuni, fatan ka iso lafiya" "Idan irin wannan gaisuwan ne ai tun ina Nigeria na ke jin ta. Gaisuwan Mata ga Mijin ta na ke so" "Ba gashi na yi ba..." Tallafo fiskanta yai ya haɗe bakin su. A hankali ya dinga sarrafa harshen ta cikin ƙwarewa. Kusan minti ɗaya kafin ya cire bakin sa ya ce "wannan gaisuwan na ke so Umm Alinah" Ya riga ya kashe ma ta jiki dan haka ba ta iya cewa komai ba hakan ya bashi daman sake haɗe bakin su ya cigaba da kissing ɗin ta, itama kawai ta sa hannu a wuyan sa ta ƙara jawo kan sa a lokaci guda kuma tana yiwa ƙeyar sa zuwa wuyan sa tafiyar tsutsa. "Anty Alinah tana kuka" maganar Suhailah ya katse mu su gaisuwar masoya. Muryar ta da ya shaƙe ta ce "ina zuwa yanzu" Bayan fitar Suhailah daga ɗakin Galadima ya fara ƙoƙarin cigaba da abinda su ke ta yi saurin saka hannu ta tare bakin sa ta ce "barin je na dubata" "Ki kawota nan" ya faɗa tareda kissing hannun ta sannan ya sake ta, ta miƙe ta fita daga ɗakin. Har ta je ta karɓota kuwa yarinyar ba ta bar kuka ba, tana zuwa Galadima ya karɓeta yana ɗan jijjigata ko minti ɗaya bai cika ba ta yi shiru. Zaytoonah ta ce " ji min 'ya da gulma" "Ba ruwan ki da ita ba ta gaji da jin ɗumin Uban ta ba ne" "Oh haka ko"... *** Tun kafin su gama cin abinci ya roƙeta akan ta rakashi wani waje. Tsokalar sa ta yi akan bai san gari ba ina zai je da yammacin nan. Ya ce ma ta zai je ganin wani abokin sa ne da su ka yi karatu tare shima yanzu Alƙalina a nan Las Vegas ɗin. "Ka bari mu tafi gobe, ko hutawa ba ka yi ba fa" "Gara mu je yau ɗin gobe kin ga sai na huta sosai" Ganin yadda ya dage ma ta ya sa ta amince. Ta je ta sake watsa ruwa a gurguje ta shirya sannan ta samu Mommy a ɗakin ta tana yiwa Alinah wankan yamma. "Mommy zan raka Daddyn Raziya wani waje yanzu zamu dawo" Mommy ta bi ta da kallon tuhuma. "Mommy ba zamu jima ba, ya ce za mu je gaida abokin sa ne" Da toh kawai Mommy ta bita. Dan ba ta da hurumin shiga tsakanin miji da mata. Sanin cewa Zaytoonah ta yi tsarki ya ƙara tabbatar da zargin da ta ke yi, fatan ta dai kar Zaytoonah ta yi kwunika dan ba ƙaramin wahala za ta sha ba. Wannan haihuwar ma dai kariyar Allah ne kawai dan ta wahala watanni biyu kafin haihuwar. Mommy ba ta ma ɗauka Zaytoonan za ta iya haihuwa da kan ta ba, sai ga shi haihuwar ta zo ma ta cikin sauƙi. Dreban gidan ne ya fita da su sai dai maimakon Galadima ya bashi address ɗin gidan da za su je sai ya bashi address ɗin wani hotel a fakaice ba tareda Zaytoonah ta ji ba. Suna tafiya suna ɗan taɗi wanda yawanci kan harkan shari'ar da ya ke yi ne har su ka isa hotel ɗin. Sai da motar ta tsaya Zaytoonah ta kalli inda su ke da kyau kafin ta maida kallon ta ga Galadima wanda ya kashe ma ta ido ɗaya. " Allah dai ya hana ƙarya Justice" "Akwai ƙaryar sunna ai Yallaɓiya" ya faɗa yana murmushi. "Hmmm" Suna shiga katafaren hotel ɗin ya booking mu su ɗaki ya karɓi key sannan su ka wuce. Ita dai Zaytoonah na ta ido, abu ɗaya ta sani ko yafi ruwa gudu yadda ya ganta haka zai barta. Suna shiga ɗakin ya rungumeta sosai kamar zai maidata jikin sa. "Ranka shi daɗe ban da ƙarfi fa yanzu za ka ɓallani" "Na yi kewar ki sosai Zaytoon ki tausaya min" "Ni dai ka sake ni, kana chan da matar ka za ka ce ka yi kewana. Ni ban yarda ba" Cireta yai daga jikinsa ya ƙura ma ta ido. Zaytoonah ta haɗe rai tana tura baki. "Yanzu Princess ..." " yanzu daka zo ba, da ai ni mahaukaciya ce a wajen ka ba Princess ba" "Ya Allah!" Ya faɗa yana dafa kai. Mace dai sunan ta Mace. Tun a waya su ke fama da maganan nan kuma ta nuna ta haƙura yanzu kuma za ta chaza ma sa kai. Ko da ya ke Mace dama sai da lallashi balle kuma ita da ya ba wa tazaran shekaru sosai haka. Riƙe hannunta ɗaya yai ya marairaice murya ya ce " haba Qurratul ayn na ce ki yafe min fa kuma kin ce kin yafe" "Ya wuce ai, nima yadda aka shareni aka jefa ni a kwandon shara yanzu sai a barni na huta ai. Dan ni da Nigeria sai na yaye Alinah. Ka je chan ka zauna da Aaamaryar ka" ta ja sunan Amaryar da gayya. "Da gaske" ya faɗa bayan ya sa hannunsa a ƙugunta ya jawota daf da shi. "Da gaske mana. Kai ma..." bai bari ta ƙarisa ba ya haɗe bakin su. Irin yadda ya ke sarrafata da zafi-zafi ya sa ta ajiye makaman yaƙi ta fara biye ma sa. As if ya ma ta magani dan daga kiss kawai ta ji notinan kan ta ya kunce dan gaba ɗaya ta manta niyyar ta, ta manta iƙirari da cika baki da ta yi- ta yi lokacin da su ka shigo hotel ɗin. Lokacin da ya kwantar da ita kan gado half naked yana ƙoƙarin janye pant ɗinta ta ce " Sayyidi ban yi tsarki ba" "Allah ya tona asirin ki ai, kin san addu'an wanda aka zalinta ba ya faɗuwa ƙasa banza. Iya waɗannan watanni kuma ace na zo na samu shamaki tsakani kinga ai zalunci ne" Wannan mutumi kaman maye, ko ya akayi ya san inada tsarki oho. Ta faɗa a zuciyarta a fili kuwa ta ce "Ba wanda ya zalince ka sai.. ahhhh"... Bayan dukkan su sun samu nitsuwa ne ta tambayeshi ya aka yi ya san tanada tsarki. Shine ya ce kwanaki uku da su ka wuce da ya kira Mommy ya ce a bawa Zaytoonah wayan su gaisa sai ta ce Zaytoonan na sallah. Kwanaki shatara kawai ta yi jinin ya tsaya gashi yau kwanan ta talatin da ɗaya da haihuwa bai sake dawowa ba. Zaytoonah ta fara miƙewa ta shiga banɗaki dan fitsari ta ke ji bayan ta gama kuwa ta duba wajen shower ɗin ta ga yanada option ɗin ruwan ɗumi dan haka kawai ta fara shirin wankan tsarki. Tana cikin wanka aka buɗe ƙofan banɗakin. Ba shigowar sa ba ne ya ba ta mamaki sai dai kawai gani ta yi ya cire boxers ɗin da ke jikin sa ya tako har wajen da ta ke tsaye ruwa na zubo ma ta a kai. Saurin rufe ido ta yi da tafukan hannunta duka biyu tana murmushi. This is the first time da ta gan shi haka, completely naked. Mutum ne mai tsananin kiyaye magana a banɗaki shiyasa suka koma maganan kurame. Cire hannun ta yai a fiskar ta ya ɗaga ma ta gira, ta yi saurin sunkuyar da kan ta tana cigaba da murmushi tana tunanin anya Galadiman da ta sani ne kuwa yau ɗin nan. Ya ɗago haɓarta tareda manna ma ta kiss a baki yana cigaba da shafa ilahirin jikin ta... Yau dai na farko a tarihi Galadima ya cire kunya ya bari sun yi wanka tare infact ita ne ma ta cuccuɗa shi sai da ta gama yai wankan tsarkin da kan sa. Da su ka gama kuma suka fito manne da juna dan kusan towel ɗaya suka yi amfani da shi. "Yau da a India mu ke da sai na ce ko sai da ka biya gidan Sharukh Khan kafin ka zo nan" ta faɗa lokacin da ta ke ƙoƙarin saka ma sa kaya. "Wani banza kuma Sharukh Khan bayan muna da karatun soyayya daga wajen fiyayyen halitta" "Allahu Akbar! Sheikh yau Limanci ne ya zo kenan" Zaytoonah ta faɗa tana dariya. "Let's just say ina son na tanadi 'yan mata na da kyau ne" "Allah ya ƙara maka lafiya nawan" Tafiya ta ɗauka za su yi amma koda su ka yi sallar Isha gogan ya waske wai bai shirya tafiya ba ƙarshe ma dai sake gabatar da wani sabon kalar soyayyar su ka yi. Gaba ɗaya sun manta da mutanen da su ka bari a gida balle kuma 'yar jinjira baiwar Allah. Bacci ne ya kwashe su bayan sun yi wanka a karo na biyu. Ƙarfe biyun dare Zaytoonah ta tashi daga bacci za ta shiga banɗaki ta ga wayar Galadima na haske ashe dai a silent ya saka ta. Ɗaukar wayar ta yi sai ta ga anyi saving da suna *Gimbiya Ghazala* Wani abu ne ya soketa amma ta dake ta ɗau wayar dan tunda bacci ne ta kasa yi gara ta hanata baccin mai dalili. Ƙasa-ƙasa ta fara magana bayan ta ɗauka kiran. "Lafiya kika kira da dare haka?" Daga ɓangaren Ghazala ta ji wani abu ya toshe ma ta maƙoshi, maganar da ta ke son yi ma ta ka sa. "Idan a Nigeria dare bai yi sosai ba plz ƙarfe biyun dare ne a nan. Ki bari gobe ki kira shi, you are interrupting a very private meeting a nan" Ta kalli Galadima da ke bacci hankali kwance kafin ta maƙe murya cikin kissa ta ce "Sayyidi ka ɗan matsa min wajen nan, Oh Oh Oh" Tuni Ghazala ta yi cilli da wayar hannunta tareda saka ihu. Tun tana ƙuruciya ita mai kishi ce ko aurenta na farko maganar kishiya na daga cikin babban dalilin da ya sa ta bar gidan, balle yanzu da ta ke auren Galadima. Yanzu duk abinda ta shirya ya warware kenan? Ko dai shawaran Hajiya Safara'u za ta ɗauka ne? To amma ita gaskiya duk iskancinta ya tsaya a kissa da munafurci ba ta yadda da zuwa wajen boka ba. A ɓangaren Zaytoonah kuma dariya ta yi sannan ta duba wayan ta ga missed calls ɗin Mommy har uku. Kiran wayan ta yi amma ba a ɗauka ba dan haka ta ajiye wayar ta shige banɗaki. Bayan ta fito ne ta sake gwada kiran wannan karan aka ɗauka amma da muryan bacci. Kasa magana ta yi dan kunyan Mommyn ta ke ji. "Ina fata dai ki dawo da sassafe dan baifi awa ɗaya da ya wuce ba ta yi bacci" "Ki yi haƙuri" ta faɗa a kunyace "Mu kwana lafiya" Mommy ta faɗa tareda katse kiran. Zaytoonah ta yi ajiyar zuciya kafin ta wajen Galadima ta kwanta gefen sa ta ɗaura kan ta a ƙirjin sa... Washegari tun ƙarfe huɗu da rabi da su ka tashi su ka shirya su ka bar hotel ɗin. Taxi su ka shiga su ka wuce gida. Suna zuwa kuwa da Zaytoonah ta haura sama ta samu Mommy na faman lallaɓa Alinah da ke kuka, dama aikinta ne kuka dai-dai lokacin Asuba. A kunyace ta karɓi Alinar a hannun Mommy ta zauna ta shiga ba ta nono... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 69 Bismillahir Rahmanir Rahim *face to face* "Sati ɗaya?" ta maimaita abinda ya faɗa. "Akwai tarin ayyuka agabana ne Qurratul ayn" "Hmm" kawai ta ce sannan ta cigaba da zuba ma sa abinci. Ganin ta haɗa rai ya sa shi riƙe hannunta ya ce "zan so jimawa a nan amma kin san ba zai yiwu ba. Infact Monday munada zama a kotu. "Ki yi haƙuri kin ji. Zuwa ƙarshen watan nan sai kema ki dawo" Kallon shi ta yi na 'yan daƙiƙu kafin ta cigaba da abinda ta ke yi. Bayan ta gama zuba abinci ta zauna gefe ba ta ce komai ba. Tana son yi ma sa magana amma kuma wani abu ya tokare ma ta wuya, kuka ta ke son yi amma ta kasa. "Adaeze ki yi haƙuri Dan Allah. Wallahi da akwai yanda zan yi na zauna a nan kamar na wata ɗaya da zan yi. Kin san..." "Dan Allah Daddyn Raziya ka bari haka. Na ji za ka tafi nan da kwana uku shikenan Allah ya kaimu lokacin" Ta miƙe za ta fice daga ɗakin yace "Ina za ki je?" "Zan duba Alinah ko ta tashi" "Dawo ki zauna" Maimakon ta koma sai ga hawaye sun fara zubowa a idonta. Kukan da ta ke ta dannewa shine ya kufce ma ta. "Subhanallahi!" Galadima ya faɗa yana miƙewa da sauri. Yana rungumota jikinsa sai ta fashe da kuka da ƙarfi. Su biyu ne a gidan sai masu aiki. Mommy ta kwashi yaran sun fita ganin gari. "Ki daina kuka dan Allah. Ba yanda zan yi ne Zaytoon, try to understand me please" "Kinga duka yaran suna nan tare da ke. Sai hutun su ya ƙare za su dawo, idan za su dawo sai ku dawo tare" "Ni ma kin san ba ƙaramin missing ɗin ki zan yi ba. Kinga daga wannan tafiyan idan kin dawo sai kin shekara ba ki taka ko ƙofar gida ba" Hararan sa ta yi ta ce " sai ka yi mu gani ai" "Ikon Allah! Mai kuka na harara ne" ya faɗa yana dariya. Zaytoonah ta kai ma sa dundu a baya. "Yallaɓiya ki yi haƙuri kar ki ɓurma bayan Tsoho" "Gara na ɓurma ɗin ai tunda nawa ne" ta faɗa tana ƙara yi ma sa wani dundun a bayan sa. Tuni faɗa da lallashi ya juye ya zama soyayya. Tare su ka ci abinci cikin so da ƙauna dan kowa na bawa ɗan uwan sa abincin ne a baki a haka aka ƙarisa cinyewa... Washegari su ka tattara su ka wuce gidan gonan Kakannin Zuhayr wato *Haddish Ranch* Tun kafin mutuwar Mrs Haddish ta mallakawa 'yan biyu gidan gonan gaba ɗaya wanda ya sauya suna zuwa *Zuhayr Ranch*. Su Raziya sai su ka koma 'yan ƙauye ganin kyan wajen, shi kan sa Galadima wajen ya burgeshi sosai. Dawakai, Shanu, Raguna, Kaji, ga su nan birjik a wajen suna samun kulawa daga ma'aikata. Zuwan su gidan gonan ya taɓowa Zaytoonah tsohon tabo da ta ke fama da shi a zuciyarta tun da jimawa. Lokacin da su ka shiga gidan gani ta ke kaman za ta ga Zuhayr da kuma Kakannin sa a ciki. Da ke sun sanar da zuwan su an riga an gyara mu su cikin gidan. Ɗakuna uku ne a gidan dan haka Mommy ta ce Galadima da Zaytoonah su ɗauka master bedroom ɗin yayinda ita kuma za ta kwana tareda junior da 'yan biyu. Su Raziya kuma aka ba su ɗaki ɗaya. Bayan sun huta ne Zaytoonah da Manager ɗin gidan gonan mai suna Muhammad Chu suka yiwa su Galadima jagora wajen ganin ilahirin gidan gonan. Dukiya ne jingim a wajen nan, kuma Alhamdulillah duk da kasancewar Zaytoonah ba ta wajen hakan bai sa anyi wasa da kula da lamuran wajen ba. Tun da Zaytoonah ta ɗauki Muhammad Chu a matsayin manager abubuwa suka rinƙa haɓaka sosai. Duk da kasancewar sa mutum ne da bai wuce shekara biyu da ƙarɓan musulunci ba amma kyawawan halayen sa idan ka gani sai ka ɗauka ma tun asali a cikin musulunci ya taso. Muhammad Chu asalin su 'yan Hong Kong ne amma kasancewa iyayen sa a nan ƙasar America su ka haifeshi ya ba shi lasisin zama ɗan ƙasa. Saurayi ne da zai kai shekaru talatin da huɗu a duniya. Zaytoonah na tsaye tana kallon Galadima na ƙoƙarin ɗaura Junior akan doki tana murmushi ganin yadda Galadima ke nunawa 'ya'yan ta da ƙaninta kulawa. Tunda su ka zo wajen dawakai 'yan biyu su ka ce sai sun hau doki dan haka dole Galadima ya ɗaura su akai. Sai da ya zauna akan dokin sa sannan ya juyo ya kalli Zaytoonah ya ma ta wani murmushi mai sanyi. Zaytoonah ta yi saurin dafe ƙirjin ta saboda abinda ta ji daga chan ƙasan ran ta. Wannan murmushi a kullum idan yai, duk da ma bai cika yin ba sai yana cikin tsananin farinciki tuno ma ta ya ke da Zuhayr. Galadima ya ja linzamin doki ya yi gaba cikin sassarfa, su junior ma su ka bi bayan sa a hankali. Su Falaq da Suhailah kuma sai tafi su ke yi cike da farin ciki. Raziya da ke gefen Zaytoonah ta ce "Anty ina idan za mu koma Nigeria tare za mu koma da ke ko?" Tambayar nan ta ji shi a wajen Suhailah tun ranan da su ka zo amma yanzu da Raziya ta faɗa sai abin ya ba ta mamaki. Ta lura tunda su ka zo ta ke ƙoƙarin shishshige ma ta musamman idan ta ɗauki Alinah sai ta ce a bata ta goyata. Babu wannan rashin kunya da tsiwa ɗin nan da ta ke ma ta a da. Tunanin ta ko dan sun jima ba su haɗu ba ne ya sa ta chanja haka. "Allah mun missing ɗin ki sosai. Kinga ranan sunan Alinah nima har walima na yi, na gayyaci duk ƙawayena kuma kusan dukkan su sun zo. Har wanda ba su zo ba da na je school sai da na raba mu su souvenir ɗin suna" Cike da mamaki ta kalleta ta ce "kina so na dawo ne?" "Sosai ma kuwa. The house is so boring without you" "Wallahi kuwa" Falaq ta jaddada wanda itama ta ji abinda Raziyan ta faɗa. Zaytoonah ta ce " kuna tareda Hajiya taya gidan zai zama boring?" "Hajiya ta chanja. Ta dena kula damu har dukan mu tana yi yanzu" Falaq da ba ta cika son magana ba ita ke wannan bayani hakan ya sa Zaytoonah ta gane lallai da gaske yaran ba sa jin daɗin zama da Ghazala. Dama tuntuni ta suspecting zaman munafurci ta ke yi da yaran, duk wani abu da ta ke yi mu su tana yi ne dan samun wuri a wajen Galadima ba dan Allah ba. Kafin ta yi magana ta jiyo muryan Farha tana ƙwala sunan ta. Kamar wata yarinya haka ta taho da gudu ta rungumeta saura kaɗan ma ta kayar da ita. "Ya Allah! Zaytoonah ke ce haka?. My Gosh na ga Baby Alinah a wajen Mommy, ashe ta fi hoto kyau. Kai i'm dying to have a cute baby like her. Oh! She's so pretty" "Ke dai ba za ki girma ba Farha. Yanzu yadda ki ka daka tsalle kika faɗa jikina idan kika jimin ciwo fa" "Forget it Babe. Da na shigo na ga wani handsome man a waje, who is he?" "Kai Farha!" "Ok Ok Ok. Yanzu Ina 'ya'ya na su ke?" Juyar da fiskar Farha ta yi wajen su Raziya ta ce " ga 'ya'ya na nan. This is Raziya, Falaq and my sweetheart Suhailah" Farha ta miƙawa Raziya hannu su ka gaisa sannan ta bi sauran ma ta mu su musabaha tana faɗin sun ma ta kyau. A hanyar su ta komawa gidan ne Zaytoonah ta tambayeta ya aka yi ta san suna nan?. Farha ta ce ta je gidan su na Las Vegas ne mai aikin su ta ce sun taho nan shine kawai ta wuco nan ɗin. Lokacin da su Galadima su ka dawo Zaytoonah ta gabatar ma sa da Farha. Farha sai murmushi ta ke yi tana ƙifƙifatawa Zaytoonah ido. Bayan sun keɓe kuwa ta dinga tsokalarta akan wai yadda Galadima ya ke da kyau da kwarjini ya sa ta kasa rabuwa da shi tun farko. Da dare aka haɗa wuta a waje ana shan ɗumi. Galadima, Zaytoonah, Farha da sauran yaran suma su ka fito shan ɗumi, idan ka cire Mommy, Baby Alinah da kuma Hashir da ya riga yai bacci su kaɗai ne ba su fito ba. Aka haɗu aka zagaye wutan aka zauna tareda ma'aikatan wajen ana hira. Daga baya kuma da dare ya fara ja Galadima ya ce su shiga ciki ya isa haka. Farha kam maƙalewa Muhammad Chu ta yi tana ma sa tambayoyi gameda rayuwar sa. Duk da shi ba mai son yawan magana ba ne amma duk da haka sai da ta sa shi yai ta biye ma ta. Kafin su rabu kusan tarihin rayuwarta kaf ba wanda ba ta gaya ma sa ba. Kasancewar ba wani ɗaki a gidan Farha a falo ta kwana a saman couch kusan ƙarfe shabiyun dare bayan ta baro wajen Muhammad Chu, dan sai a sannan aka kashe wutan da aka kunna... Haka su ka yi kwana biyu a gidan gonan nan cikin jin daɗi da kwanciyar hankali. Anyi hotuna kuma an yi videos na tarihi. Su Raziya har cewa su ka yi kafin su tafi za su kuma komawa gidan gonan. Ranan Alhamis Zaytoonah ta raka Galadima zuwa airport inda su ka rabu cike da kewar juna. Ita dai Zaytoonah ba ta bashi tsayayyiyar amsa ba amma sun rabu akan kafin hutun su Raziya ya kare za ta tsaida ranan dawowan ta... *** Tun ranan da Ghazala ta yi waya da Zaytoonah ta rasa nitsuwarta. Gidan da ta ke tunanin ya zama mallakinta ita kaɗai ashe duk shirme ta ke yi. Wani mahaukacin kishi ke cin ta. Duk inda ta auna yadda yanayin zaman su zai koma idan Zaytoonah ta dawo sai ta ga ita ce da faɗuwa. Sai dai koma yanene ba za ta bari wannan ƙaramar yarinyar ta sata cikin damuwa ba. Babban damuwarta shine ta samu ciki idan ta samu ciki komai zai zo ƙarshe musamman ta haifi namiji. Akwai lokutan da shaiɗan ke kawo ma ta shawaran zuwa wajen boka kamar yadda wata ƙawarta ta shawarceta amma kuma idan ta auna abun sai ta ga duk ba riba a ciki. Cikin hikima za ta san yadda za ta yi Zaytoonah ta bar gidan gaba ɗaya. Lokacin da Galadima ya dawo da farko Ghazala shareshi ta yi ita a dole ta yi fishi tana so miji ya lallaɓeta amma sai ta ga gogan ko kallo ba ta ishe shi ba balle ma ya lura cewa wai fushi ta ke da shi. Ganin kwana huɗu ya shige a haka ya sa ta chanja tsari dan wannan ba zai ficceta ba. Kafin Zaytoonah ta dawo ya kamata ta wanke duk laifukkan ta a wajen Galadima. Ranan jummu'a ta sameshi a ɗaki ta tsugunna a gaban shi tana kuka wiwi tana bashi haƙuri. A yadda ta ke yi ka ɗauka tsakani da Allah ta yi nadama ne. Da kan ta ta sanar da Galadima cewa ta yi kuskuren dukan ma sa yara da ta ke yi idan su ka yi laifi. Ita tana yi ne dan su rage sangarta. Ta ce ya yafe ma ta ihu da ta dinga yi ranan da za su tafi, wai kishi ne ke cin ta. Tsakanin miji da mata sai Allah, tuni Galadima ya ce ya yafe ma ta dan ta bashi tausayi irin kukan da ta yi ta yi mai ɗimbin nuna nadama... A chan ɓangaren Zaytoonah kuwa zuwan Galadima ya kwaɗaita ma ta komawa gidan ta. Kafin sati ukun da su Raziya za su yi ya ƙare ta gayawa Mommy akan za ta koma Nigeria. Mommy ta yi na'am da hakan dan dama abin da ya kawo su sun samu. Zaytoonah ta samu lafiya Masha Allahu. Itama kuma Baby Alinah ta yi ƙwari yanzu. Sanda ta gayawa Galadima desicion ɗin ta kamar ya jawo ranakun haka ya dinga ji. He's very happy. Gashi gidan da ya siyawa Zaytoonah an gama gyaran shi an saka furnitures da komai da komai na buƙatan gida. Haka nan su ka shiga tattara kayan su dan dawowa gida Nigeria... *** Ranan talata da safe jirgin su Zaytoonah ya iso Abuja. Abun mamaki Galadima da kan sa ya je ɗauko su da shi da Dreban su Raziya. Da su ka isa gida kuwa Ghazala tana zaune tana jiran su. Ta riga ta sa an shirya mu su abinci kala-kala na welcoming ɗin su. Lokacin da ta ga Mommy ɗauke da jinjira ta nufi wajen ta da sauri ta karɓeta jiki na ɓari tana faɗin "ka ga Gimbiya Alinah 'yar America. Kai yarinyar nan kamanta da Falaq har ya ɓaci. O'o sai manyan ido kamar na uwarta. Baby Baby" ta ƙarisa maganar tana ɗan jan kumatunta yarinya kuwa ta saki kuka. Zaytoonah ido kawai ta zubawa Ghazala tana ganin yadda ta ke jagwalgwala ma ta 'ya. Jin ta ƙi shiru ya sa Mommy ta karɓeta a hannun Ghazalar. "Ku ƙarisa ciki ku ɗan watsa ruwa yanzu za'a serving abinci" Mommy ta ma ta godiya yayinda Zaytoonah ta riga ta wuce gaba. "Mommy ki ga yadda ta ke yiwa Alinah, Wallahi idan ta kuskura ta yiwa 'ya ta wani mugun abu sai na kasheta..." "Wani irin magana ne wannan? Ba na so, ba na so kin ji" "Amma Mommy matar nan..." "Ki cigaba da haƙuri da ita a hankali sai ki ga watarana duk wannan ya zama labari" Zaytoonah dai shiru ta yi amma tsaf ta shirya yin faɗa da Ghazala idan wani abu ya samu 'yar ta. Washegari Mommy ta wuce Zaria tareda 'yan biyu da Junior cike da tsaraban mutanen gida. Zaytoonah na tsaye tana faman yanka albasa a chopping board Ghazala ta shigo kitchen ɗin. Tsayawa ta yi tana kallon Zaytoonan ciki da bai. Ta ƙara haske sai sheƙi jikinta ke yi. Tunda su ka zo ma sai yau ɗin ne ta ma ta kallon ƙurilla. Ganin kallon yayi yawa ya sa Zaytoonah ta ɗago ta ce " Malama dan Allah kallon ya isa haka, kar ki cinye kurwata" Murmushi Ghazala ta yi ta ce "Zaytoonah kenan! Ashe da gaske kin samu lafiya. To sannu da dawowa ko" Kallon tuhuma Zaytoonah ta bi Ghazala da shi har ta ɗauki bowl ɗin kankana da aka yanka ƙanana a fridge ta fice daga kitchen ɗin. Maganar Raziya ne ya faɗo ma ta ranan da su ke shirin barin Las Vegas. *"Anty idan mun koma ki yi hankali da Hajiya. Ba ta son ki, ba fa son ki da Daddy"* Ta tambayeta dalilin yin wannan magana ammaba ta ce komai ba amma kaman akwai abinda ta sani ta ke ɓoyewa. 2/11/21, 10:04 PM - ****: 70 Bismillahir Rahmanir Rahim *Trial of my marriage* Ƙarfe tara saura kwata na dare agogon ɗakin Zaytoonah ya nuna. Ba ita ke da girki ba dan haka bayan ta fito daga wanka kayan bacci kawai ta saka ta zauna a kujera tana duba wasu documents da Mommy ta ba ta. Takardu ne na filin da aka siya a ƙauyen su Mommyn, tun ma kafin tafiyar su America. Bayan ta gama abinda ta ke yi ta miƙe ta tattara takardun ta sa a file ta maida shi cikin drawer. Falon ƙasa ta wuce dan ta taso Yaran akan su je su kwanta dan karfe tara ne lokacin baccin su. Hadid kam sai da ta ja shi da ƙarfi dan maƙalewa yai a jikin kujera saboda film ɗin spiderman da su ke kallo. Sai da ta tabbatar da duka yaran sun kwanta kafin ta wuce falon Galadima. Tun takwas Alinah ke wajen sa ƙila ma ta yi bacci gara ta ɗauko 'yarta kafin Ghazala ta fara bala'in za a hanata jin daɗi. Sai da ta kwanƙwasa ƙofar falon kafin ta shiga da sallama. Yana kishingiɗe aƙasan carpet yana duba takardu. "Sannu da aiki" ta faɗa ma sa sannan ta fara waige-waigen inda za ta ga 'yar ta. "Ba dai ka kwantar da Alinah a ɗakin ka ba?" "Tana wajen Ghazala" "Ghazala?" Ya ɗan ɗago ido ya kalleta. "Ranka shi daɗe Ghazala fa. Ni gaskiya ba na so" "Zaytoon" "I'm serious ba na so. Idan ka ɗau waya ka kirani na zo na ɗauketa ai ba laifi ba ne" Bai yi magana ba sai ya maida hankalin sa kan takardun da ke gaban sa. Buɗe ƙofa aka yi Ghazala ta shigo goye da Alinah. "Dear ai na gaya ma ka kashi ta ke ji shiyasa ta ke kuka" Zaytoonah ta kalli Ghazala sannan ta maida dubanta ga mutumin da ya ajiye su duka. Ta ƙarasa gaban Ghazala ta ce "Madam sauko min ita ko" "Ta riga ta yi bacci ki barta kawai a wajena" Ghazala ta yi maganar tana satar kallon Galadima, ga shi dai takardun gaban sa ya ke kallo amma hankalin sa na kan matan na sa. "Ki sauko min 'ya ta" Zaytoonah ta faɗa da ɗan ƙarfi. Ghazala ta marairaice murya ta ce "yau da ban taɓa haihuwa ba da sai na ce gori kike min. Amma nima Allah ya bani biyu kuma har yanzu ban cire rai ba. Kar ki manta ɗa dai na kowa ne" Zaytoonah ba ta ce ƙala ba ta karɓi 'yarta ta fice daga Falon ranta a ɓace. Ta rasa yaushe matar nan za ta dena shishshigi. Ghazala ta kalli Galadima ta ce "ka ga dai da idon ka abinda na ke faɗa. Yau ko ni mayya ce a gidan nan iyakacin abinda Zaytoonah za ta min akan 'yar gwal kenan nan. Allah ya ba ta haƙuri, na ɗauka 'yar ka 'ya ta ce" Ta wuce ɗakin sa rai a ɓace. Ko da Zaytoonah ta shiga ɗaki sai da ta duba 'yar ta da kyau ta tabbatar ba ta ga wani sabon abu a jikin ta ba kafin ta tofa ma ta addu'a ta kwantar da ita... *** Bayan kwana biyu Galadima ya tara su a falon sa ya mu su maganar raba mu su gida da ya ke son yi. Ghazala za ta zauna tareda yara a wannan gidan da su ke ciki ita kuma Zaytoonah za ta koma sabon gidan da ya siya. Bayan ya gama jawabin sa ne ya tambayesu ko akwai mai magana. Zaytoonah ta kalleshi ta ce "a dalilin me za a ce na koma wani gidan. Ni ce Uwargida, at least ya kamata a bani darajar wannan matsayin" Kafin Galadima yai magana Ghazala ta ce " haba Zaytoonah. Wani irin rashin kunya ne wannan, duk abinda Abu Razz yai na san tsakani da Allah yai shi, kuma ya ga hakan shi ya fi dacewa da mu" "Ofcourse dole ki faɗi haka tunda ke ki ka kissima ma sa komai ai. To ba zan fita ba. Ni aka fara kawowa and i choose to stay here, idan ba zai maida ke sabon gida ba shikenan a ajiye maganar" "Zaytoon" "This is not fair. Ai ba haka ake yi ba..." Miƙewan da Galadima yai ya sa ta yi shiru. "Za ki koma ranan jummu'a, kafin nan ya kamata ki shirya" "Ba zan koma ba" ta faɗa da ƙarfi. Yana wucewa ɗaki itama ta bi bayan sa. "Daddyn Raziya what is happening? ban gane ma ka ba kwana biyun nan. Ba ka gaya min za ka raba mana gida ba, and to top it all sai ka ce ni na koma sabon gida why? Kaman kana korana kenan? Is it because ban haifa ma ka namiji ba...?" "Ya isa!" Ya faɗa a tsawace Ta yi saurin haɗiye sauran maganarta. "Na riga na yanke hukunci, idan rashin kunyar da kika saba za ki yi kuma shikenan ki fara. Ina dai-dai da ke a gidan nan" Mamaki, tsoro da fargaba ya kama Zaytoonah. Anya Galadiman da ta sani kuwa kenan? Ghazala da ke baƙin ƙofa ta yi saurin barin wajen cike da farinciki. Gaskiyar Hajia Safara'u ne da ta ce aikin mutumin nan bai ɗaya ne. Kwanakin Zaytoonah a irge su ke a gidan nan ta faɗa a ranta. Bayan Zaytoonah ta fita daga ɗakin Galadima ɗakinta ta kom, ta zauna a kujera tana sauke ajiyar zuciya akai-akai. Farko-farkon dawowarta komai na tafiya dai-dai amma yau kusan sati biyu kenan ta kasa gane kan Galadima. He seems entirely different. Shi da baya son missing kasancewa da ita amma yanzu duk ranan girkinta sai ya jima a waje idan kuma ya dawo gefe zai kwanta ya fara bacci ko kuma ya je study room ɗin sa ya zauna. Ranan da ta ma sa magana sai ya ce wai ya ba ta hutu ne tunda tana shayarwa. Womanly pride ɗin ta was hurt shiyasa ta ajiye maganar ba ta sake tuntuɓar sa ba, ta zuba ma sa ido. Indai ita ne zai dawo da kan sa yana ƙaramin murya yana rau-rau da ido kamar munafuki. Yammacin ranan ta kira Mommy ta faɗa ma ta abinda Galadima ya ce. Mommy ta ba ta shawaran akan ta koma sabon gidan, miye a ciki?. Ta so yiwa Mommy gardama amma Mommyn ta ma ta nasiha akan yanzu ba lokacin jayayya da miji ba ne, ta kula da 'yarta da kuma lafiyarta. Zaytoonah ba ta tabbatar akwai abinda ke damun Galadima ba sai da ranan Jummu'a Galadima da Ghazala su ka ma ta rakiya zuwa Zuba. Wani madaidaicin gida Flat mai ɗakuna uku shine gidan da aka kama ma ta. Ita Zaytoonah da Dreba ya yi parking a wajen ta ɗauka ma ziyara su ka zo yi kafin a tafi gidan da za ta koma dan tunda su ka baro cikin gari kawai ta sallama ta dena guessing inda za su je. Sai da ta ga Ghazala da Galadima sun fito a motar su kafin itama ta fito cike da mamaki. Kamar Almara ta ga Galadima ya wuce ƙofar gidan ya buɗe da key ya shiga. "Ba dai a nan zan zauna ba?" Zaytoonah ta faɗa lokacin da ta shiga falon. "A hankali za'a yiwa gidan fence. For now ki haƙura da wannan" Zaytoonah ta fashe da dariyan rainin hankali. "Iya zamana da kai dai na san ba ka shan giya, ba ka kuma shan ƙwaya. But it seems recently ka fara sha. Ni zan zauna a nan?, a wannan gidan. Mi ka ɗaukeni ne wai?" "Kamar yadda na faɗa, ki zauna a nan zuwa wani lokaci. A hankali zan nema miki wani gidan a cikin Abuja" "To hell with gidan ka Justice Yunus. Infact to hell with auren ka. Ka riƙe gidan ka kaga ko ba zan samu gidan da ya fi naka ba a yau-yau ɗin nan" Ficewa ta yi daga gidan fuuu ta je ta shiga mota. Yadda ta yiwa Alinah da ke kafaɗarta wani mummunan riƙo ya sa yarinyar ta fashe da kuka. "Dan Uban ki kimin shiru" Tana shiga mota ta ce Dreba ya maida ta cikin gari. Thank God 'yan biyu na makaranta, da ba ta san mi za ta faɗa mu su ba gameda sabon gidan da su ke ta ɗoki a kai, gidan da ko gidan su na Zaria ma ya fishi sau goma. Zaytoonah kam gidan Kakannin Mommy na Abuja ta wuce Dreba ya sauke ma ta sauran kayanta da ke cikin mota. Wato dai yanzu ita ce bare a cikin su, sai abinda Ghazala ta faɗa ma sa. To ba zai yiwu ba, wannan rashin adalcin ba za ta taɓa amincewa da shi ba. Ta fi ƙarfin Galadima ko Ghazala su walaƙantata, a ɗauketa daga cikin garin Abuja zuwa wajen gari, this is an insult. She controls millions of dollars balle su ɗauka dukiyar Galadima ne ya sa ta zama da shi all this while... Bayan tafiyar Zaytoonah, Ghazala ta kalli Galadima fiskarta ɗauke da murmushi, yau ta ƙara tabbatarwa aikin Malam na ci. Kamar da wasa ta kawo ma sa shawara akan maimakon gidan da ya siya da Zaytoonah za ta zauna, mi zai hana ya kaita wani gidanta da ke Zuba. Haya ta ke sawa a gidan kuma yanzu ba kowa a ciki. Ta yi hakan ne dan ta ga ƙarfin aikin da aka yi ma ta, sai ga shi kuwa ya amince ba tareda ya yi musu ba. Infact a ranan ya ce su je ya duba gidan kafin a kai kayan Zaytoonah chan, idan da gyaran da za ayi sai kawai ayi. A hanyar su ta komawa cikin gari ne Ghazala ta ma sa maganar indai Zaytoonah ta ƙi zama a gidan da ya zaɓa ma ta gara kawai ya sawwaƙa ma ta. Ya juyo ya kalleta fiskarsa wasai kamar abun da ta faɗa bai affecting ɗin sa ba. "Mahbubi idan ma akan Alinah ce kar ka damu ka karɓota kawai zan raineta. Zan ma iya shayar da ita, idan hakan bai yiwu ba kuma sai mu rinƙa ba ta madara" Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya riƙo hannunta ɗaya ya matsa kaɗan ya ce "kin san gidan da na fito, ba zai yiwu na rabu da ita haka kawai ba. Za'a yi magana" "Wai kana nufin Hajia Abu?" "Ina tunanin Mai Martaba zai yi magana idan na rabu da matar da ta haihu wata huɗu da su ka wuce" Ghazala ta yi shiru. Ta san Mai Martaba ba shine matsalar ba, Hajia Abu ce kuma ta san abinda za ta yi. Hajia Abu na matuƙar kula da lamurran Galadima, ta jima da sanin cewa Matar na son Galadima ya zama Magaji idan Mai Martaba ya rasu. Ta riga ta haɗa connection da manyan gwamnati, yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa ta matsa ma sa da aure lokacin da matar sa ta rasu. Ta san weakness ɗin ta dan haka da shi za ta yi amfani da shi wajen ganin ta tunzura Galadima ya saki Zaytoonah. Idan hakan bai yiwu ba kuma, za ta nemi Hajiya Safara'u ta shige ma ta gaba wajen Malam a sake karkatar da hankalin Galadima. Tun kafin su isa gida Galadima ya sauka a mota akan zai wuce masallaci tunda an kusa kiran sallar la'asar. Aka wuce da Ghazala gida, shi kuma yai hanyar masallacin anguwar su. A wajen alwala ya zauna ya kira wata number, yai wa mutumin da ya kira magana tareda ba shi umurni akan lallai ya tabbatar ya gano inda matar nan ta ke. Yana gama wayar ya maida wayar aljihu sannan ya fara alwala yana ƙara tabbatar wa kan sa cewa duk abinda yai yau dai-dai ne... *** Yadda ka san Zaytoonah za ta fashe haka ta dinga yiwa ma'aikatan gidan banbami musamman da ta ga ɗakin da ta sauka ba a gyare ba. Salman da ya kira ta ma sai da ta surfa shi da masifa kafin daga baya ta gaya ma sa inda ta ke. Shi ma dai yayi mamaki da ta gaya ma sa cewa wai wani ƙaramin gida Galadima ya kaita a wajen gari. "Ka san Allah sai na nuna ma sa ko ni wacece. Irin ga ni miskiniya ɗin nan zai..." "To ke Adaeze what if Galadima ba a hayyacin sa ya ke ba. What if..." "Ba wani, ya san mi ya ke yi sarai. I think ya chanja ne ranan da Ghazala ta min gorin haihuwar mace na ce ma ta ta cewa wanda ya zuba min ƙwan ya zuba ƙwan namiji ba na mace ba. Ashe yana bakin ƙofa" "Kai Zaytoonah!" "Ya je ya riƙe gidan sa. Ya riƙe Gimbiya Ghazalar sa. Duk da bamu da haɗi da gidan sarauta na san dai mu ba bayi ba ne" "Allah ya baki haƙuri amma ni kam ki yiwa Galadima uzuri" "Uzuri my foot" Sai da ta roƙi Salman akan kar ya gayawa Mommy cewa za ta sai gida kafin ta kashe wayar. Har dare Galadima bai kirata ba, dama tuntuni ya dena yawan kiranta da ya ke yi. Ita da kan ta ta je ta ɗauko 'yan biyu ta kawo su gidan. Sai da ta gama iƙirarin cewa ba za ta bari abinda ya faru ya dameta ba amma tana hawa gado za ta kwanta ta fashe da kuka. Ta dawo ne da niyyar su cigaba da rayuwa ta jin daɗi tunda ta samu lafiya. Amma kash! Abun ba haka ya ke ba cikin ƙanƙanin lokaci komai ya zo ya kwaɓe tsakaninta da mutumin da ta ɗaukeshi farin cikin ta. Washegari tun da safe ta fara kiraye-kirayen waya zuwa ƙarfe huɗu na yamma an sama ma ta wani gida da ƙyar. Tunda aka turo ma ta hoton gidan da abubuwan da ya ƙunsa ta ce ya ma ta. Ko ciniki ba a yi ba ta biya kuɗin da aka faɗa lokaci guda. A ranan ta so komawa gidan amma hakan bai yiwu ba sai washegari, har lokacin ba ta ji daga wajen Galadima ba... A ɓangaren Ghazala kuwa washegarin ranan da su ka raka Zaytoonah ta kira Hajia Abu ta sanar ma ta wai Galadima ya raba mu su gida ita da Zaytoonah amma ta ƙi komawa gidan da ya siya ma ta wai gidan ya ma ta kaɗan. Ta turawa Hajia Abu hoton ainihin gidan da Galadima ya siya. "Kin san Allah gani ta ke ita millionaire ce ta fi ƙarfin zama a irin wannan gidan. Kin ji maganganun banzan da ta yi ta faɗawa Abu Razz kuwa. Har da cewa ita ba Miskiniya ba ce shine Miskini, wai za ta siya gidan da ya taka nashi dan ta fi ƙarfin zama a ƙaramin gida. Ni dana ga cewa ma abin zai zama faɗa sai na ce zan koma sabon gidan ita ta zauna a wannan amma ta ƙi fir. Wai dama tana managing ne da wanda mu ke ciki. Wallahi kuka ne kawai Abu Razz bai yi ba amma ransa ya ɓaci sosai. Ni tsorona ma kar abin ya sa ma sa hawan jini kin san ya damu da ita sosai" Tunda ta ke maganar Hajia Abu hankalinta ya tashi. Wacece Zaytoonah da za ta ci mutuncin Galadima haka. Wallahi ba ta isa ba kuwa, ko mi ta ke taƙama da shi sai ta nuna ma ta banbancin Aya da Tsakuwa. "Kin san tsohon mijinta mai kuɗi ne ga uwarta ma ta samu kuɗi a sama kwanakin baya..." "Kar ki damu Ghazalatu. Dama tun da ta haifi mace na ke tunanin ko dai kawai na haɗa Galadima da Mubaraka ne. Kwanan nan ta gama degree ɗin ta a South Africa" "Wace Mubaraka?" Ghazala ta faɗa a ruɗe. " 'yar gidan Turaki" Waya ga an kawo kuka gidan mutuwa. Ita da ke son rabuwa da Zaytoonah za a ma ta maganar haɗa Galadima da wata matar. Ba wai ta san Mubaraka ba sosai, amma ta san ita ce ɗiyar Turakin Zazzau ta farko tareda matar sa wata Bafullatanar Cameroon. Mahaifiyar Mubaraka Hajia Ajwa, Ghazala ta ma ta farin sani tas. Mata biyu Turaki ke da shi kafin ya aurota amma duka sai da ta ɗaga su a gidan. Ko shekara ba ta yi a gidan ba ya saki matar sa ta biyu, ita kuma uwargidan sai da su ka shekara uku kafin ya saketa. Kafin ya saketan ma sai da ta sha jinya. Bayan ya saketa kuwa da ta koma gida cikin ƙanƙanin lokaci ta warke sosai. Hajia Abu za ta haɗa auren Galadima da 'yar Hajia Ajwa. Inaaaa ba zai yiwu ba gara ta san abin yi... *** Zaytoonah na kwance a kan gado Hajia Abu ta kira ta. Kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka ɗin dan ta ji wace tsiyar za ta faɗa ma ta. Tunda ta haihu har yau matar nan ba ta kira ta ma ta barka ba. Ƙannen Galadima da matan yayunsa da ƙannen sa duk yawanci sun kirata sun ma ta barka. Wasu ma da su ka samu zuwa Abuja sai da su ka zo har gida su ka gaisheta amma wannan Sarauniyar Girman kan... Gidan da aka kai Zaytoonah daban, gidan da aka nunawa Hajia Abu daban shiyasa maganar su ta tafi a bauɗe. Yayinda Hajia Abu ke surfa masifa akan taƙamar Zaytoonah na ƙin zama a gidan da aka siya ma ta. Ita kuma Zaytoonah ta dage a kan ba za ta zauna ba, tafi ƙarfin ta zauna a gidan nan. Idan baida ƙarfin siya ma ta gidan da ya dace da ita ita ta siya. "Kin ci darajar rabo da ya shiga tsakanin ku amma Wallahi da sai na sa ya datse igiyar da ke tsakanin ku a yau-yau ɗin nan" Zaytoonah da itama ta riga ta kawo wuya ta ce " Hajia dan Allah ki sa ya sake ni. Indai kin cika Zainab 'yar Sarki Muhammad Abbas ki saka Daddyn Raziya ya sake ni. Ai na san dama abinda kike so kenan tun farko to nima yanzu na gaji da auren ki ce ma sa ya rabu da ni" Hajia Abu dai an taɓo ma ta inda ke ma ta ƙai-ƙai ta ce " ki sha kurumin ki. Aurenki da Galadima ya ƙare daga yau"... Zazzaɓi ne ya rufe Zaytooonah mintuna kaɗan bayan wayar su da Hajia Abu. Ta san Galadima na sonta a da but what if chanjawar da yai zai sa ya amince da buƙatar Hajia Abu what if he divorce her. Ta ya za ta fiskan ci Mommy. Washegari ko iya tashi ba ta yi ta kula da yaran ta ba. Tabitha mai aikinta ne ta shirya su suka wuce makaranta. Da ƙyar ta iya miƙewa ta bawa Alinah nono. Yarinyar ma kaman zazzaɓin na damunta. Ba ta tashi ba sai ƙarfe shaɗaya na safe, inda ta yi wanka ta shirya Alinah akan su je su ga Likita. Lokacin da ta gama shiryawa ta ɗau wayanta za ta sa a jaka ta ga missed call ɗin Salman da kuma text daga Galadima. Hannu na rawa ta buɗe text ɗin. *ki koma gidan ku, zan neme ki daga baya* Dafe ƙirjinta ta yi tanajin wani abu mai tsini na sukan ƙirjin na ta. 'Shikenan ya sakeni' ta furta a hankali. Da farko fasa fita Asibitin ta yi amma daga baya da Alinah ta fara kuka saboda zazzaɓin da ya dawo ya sa dole ta wuce Asibiti da ita. Bayan an duba Alinah. Likitan ya tambayi Zaytoonah ko tana ɗauke da wani cikin ne ta ce ma sa a'a sai dai gwajin da aka yi ya ƙaryata amsar da ta bayar. "Oh no! Ya Allah why now?" Ciki bayan Galadima ya rabu da ita. Ciki while Alinah was barely 5 months. Bayan ta karɓi magunguna ta wuce gida jiki a sanyaye. Ranan yadda ka san an cire ma ta laka haka ta wuni. Ta kasa taɓuka komai. Ƙarshe ta yanke hukuncin komawa Zaria gobe. Saukar rana ta yi a gidan su. Mommy ba ta nan, ta tafi ABU, tana faman ƙoƙarin shirye-shiryen yin internal defence ɗinta. Tafiya America da ta yi ya delaying zamanta Doctor. Suna gidan Salman ya same su inda ta sanar da shi Galadima ya saketa. Abin mamaki tana maganar tana hawaye. Salman ya karɓi wayarta ya karanta text ɗin. "Ni banga kalmar saki a nan ba. Cewa yai ki je gida zai neme ki" "Ya sake ni. Hajia Abu ta saka ya sake ni i'm sure of it" "Lallai Zatoonah a gaishe ki, ni banga inda wannan ya zama saki ba" Ya ajiye ma ta wayar ya wuce ɗakin sa. Zaytoonah ta cigaba da goge hawaye. She was just bluffing lokacin da ta ke yiwa Hajia Abu magana. Ko da Mommy ta dawo ta ga Zaytoonah a gida da yara ba ta tambayi komai ba sai da yamma bayan yaran sun fita wasa ya saura su biyu a gidan. Sai da ta gama jin bayanan Zaytoonah kafin ta ce "shikenan nan ai Mrs Millionaire. Sai ki zauna har lokacin da zai neme ki" "Mommy..." " taurin kai Zaytoonah, taurin kai Zaytoonah. To Allah ya kyauta" Daga haka maganar ta tsaya... *** Malam Shehu na zaune a rumfar sa yana gyangyaɗi kamar daga sama ya ji ana cewa "Daddy i want watermelon" Kalmar Daddy ya sa shi shiga duniyar tunani, wasu shekaru da su ka wuce akwai yarinyar da ta ke kiran sa da suna Daddy. "Daddy i want ice cream" muryan wata yarinya 'yar ɓukuta ya doki kunnen sa yayinda idon sa ke ganin kyakyawan fiskarta mai ɗauke da cute dimple. Mutumin da ke tsaye da 'yarsa a bakin rumfar ya ɗaga murya ya ce cikin gwarancin Hausa "Malam nawa kwallon Kankana?" Malam Shehu ya yi firgigit ya duba mutumin wanda ke sanye cikin baƙin suit tareda 'yarsa wacce za ta kai shekara goma tana tsaye gefensa sanye da riga da wando blue na denim jeans. "Malam Shehu lafiya?" Maƙocinsa wanda shima kayan marmarin ya ke siyarwa ya faɗa ganin yadda ya ke kallon Inyamurin da zai sayi kankanar kamar wani mutum-mutumi. Yadda Malam Shehu ke juye-juye yana ganin wajen da ya ke kamar makahon da idon sa ya buɗe ya sa Inyamurin ya wuce teburin maƙocin Malam Shehu ya sayi Kankana. "Lahaula wala ƙuwwata illa billah" Malam Shehu ke maimaitawa lokacin da komai da ya danganci rayuwar sa ke dawo ma sa daki-daki... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 71 Bismillahir Rahmanir Rahim *Father's love* Ba shi da abinda zai saka wa mutanen da su ka riƙe shi amana a wannan gari sai dai ya bi su da addu'an Alkhairi. Kowa ya taya shi murnan samun lafiya da yai. A iya zamansa a wannan gari kyawawan halayen sa ya kawar da zargi da ake ma sa farko-farkon zuwan sa garin. Ba a taɓa kamashi da banzan hali ba. Abu ɗaya mutane su ka fi aibanta shi da shi wato rashin aure. A duk lokacin da aka ma sa zancen aure to baya so. Akwai lokacin da wani abokin sa ya ma sa jagora wajen neman auren wata bazawara amma ko da aka kai gaban iyayenta su ka ce ba za su ba shi ita ba saboda ba a san asalin sa ba. Da ke dama Malam Shehu ba son auren ya ke ba ya watsar da zancen. Dayawa mutane sai su ka ɗauka ko bashi da lafiyar gaba ne. "Ni mutumin Ringim ne amma a Zaria na ke zama" Malam Zulkiflu yai kabbara "Ina da iyali. Mata na biyu. Ina da 'ya'ya..." Ya ɗaga yatsar sa ya fara irgawa "Princess Zaytoonah, Aisha Humairah, Salman da Abubakar Sadiq" "Sadiq Sickler ne, ban san ko har yanzu..." kuka ya kuɓce ma sa. Malam Zulkiflu ya shiga ba shi haƙuri tareda jaddada ma sa Insha Allahu zai tarar da iyalin sa lafiya. Idan da ta tashi ne a ranan ya ke son komawa ga iyalin sa amma alfarmar da Malam Zulkiflu ya nema akan ya bari sai washegari ya sa shi haƙura. Daren ranan kasa bacci yai yana tunanin ya zai tarar da iyalin sa. Ƙila Zaytoonah da Humairah sun yi aure, ƙila Salman ya gama Jami'a ko ya kusa gamawa. Ko Zaytoonah ta dena damuwa da ƙiban ta?. Akwai abinda zuciyar sa ke hasasowa amma ƙoƙari ya ke ya danne saboda barazanar da abin ke yi ga nitsuwar sa. "Ko Maryam ta yi aure?" Ya faɗa daga ƙarshe yana me dafe ƙirjinsa da ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi. Kusan Asuba da bacci ya tafi da shi yai mafarki mai daɗi wai gashi nan tareda Iyalin sa suna zaune cikin wasa da dariya wanda ke nuni da tsantsan farinciki. Cikin mafarkin ya ga wai jikokin sa biyu na wasa da gemun sa. Lokacin da ya farka addu'a ya shiga yi yana mai fata mafarkin sa ya zama gaskiya... *** "Mommy na tafi gidan su Iya" "Allah ya kiyaye hanya" ta faɗa ba tareda ta kalleta ba. "Mommy" Zaytoonah ta faɗa a shagwaɓe Mommy ta ɗan zare eye glass ɗin ta ta kalli Zaytoonah ta ce "ya aka yi Mrs Millionaire?" "Mommy is not fair. Shikenan kin fi damuwa akan na zauna da Daddyn Raziya even if i'm not happy?" "Allah ya kiyaye hanya Zaytoonah. Ki gaishe su" Zaytoonah ta kumbura fiska. Mommy ta ƙi fahimtar ta, ta ma ƙi bari su sake magana akan zuwan ta. Ta ba ta haƙurin siyan gida da ta yi out of anger amma still Mommy ta ce ba ruwanta itakam yanzu ido ne na ta. Zaytoonah za ta fita sai ga Salman ya shigo rai a ɓace. Jakar sa ta goye ya cilla saman kujera. "Ya dai?" Mommy ta faɗa tana kallon sa. "Mommy saura sati biyu mu fara exams fa, exams ɗin ƙarshe fa but wai ASUU sun tafi strike" "Ba warning strike ba ne" "Mommy to ai daga warning ɗin ne ake zarcewa" "Be optimistic Bro, za su dawo nan da two weeks ɗin Insha Allah. Kafin nan ma ƙila ka gama project ɗin ka" Zaytoonah ta faɗa "Gara su dawo fa, saboda gaskiya ni ina gamawa Aure zan yi, ba zan iya da bokon nan ba" "Lallai Salman. Yanzu har ka kai aure?" "A'a ban kai ba. Sai na shekara saba'in zan kai aure" yai maganar yana watsa ma ta harara ita kuwa ta fara dariya. Sai da ta gama dariya tukunna ta juyawa za ta tafi Salman ya tambayeta ina za ta je da rana tsaka ba tareda Alinah ba. Ta ce za ta je gidan su Iya ne, Humairah ta mu su ɗanwake. "Ke dai da kwaɗayi"... A wani madaidaicin tray na silver Humairah ta zuba mu su ɗanwaken su ka zauna a tsakiyar falo suna ci iskar fanka na kaɗa su. "Anty Zaytoonah har yanzu fa Hamma Auwal shiru, kuma wallahi Idris ya ce zai turo" Sai da Zaytoonah ta kai lomar ɗanwake guda biyu kafin ta kora da zoɓo mai sanyi da ke gefe sannan ta ce to ki gaya ma sa mana. "Na ce ma sa mi?" Humairah ta zaro ido " ki ce ma sa saurayin ki zai turo iyayen sa, ki ji mi zai ce" "Ni gaskiya ina tsoro. Sai dai idan ke za ki gaya ma sa" "A'a ke za ki gaya ma sa sai ki observing reaction ɗin sa. If you see any hint of jealosy, 'yar uwa he's into you kawai" "Allah Anty?" "I'm very sure Airah" Humairah ta fara murmushi. "Ƙaromin ɗanwaken nan kaɗan" Humairah ta tura ma ta sauran gabanta dan ita kam ta ƙoshi... *** Shekaru shaɗaya ba wasa ba ne. Duk da dai a inda ya rayu akwai cigaba na rayuwa sosai amma shigowar sa Zaria after all this years sai garin ya ma sa girma, ya ma sa sabo sai ya zama tamkar bai taɓa zama a garin ba. Daga inda aka sauke shi a tasha ya nemi keke wanda ya ma sa kwatancen anguwar su. Anguwar ta cika ta yi girma shiyasa yanzu kusan anguwanni uku ne cikin ɗaya da ya sani a da. Sai da yai kwatance sosai kafin daga bisani daya furta sunan gidan Alhaji Ilyasu Mai Auduga mai keken ya ce ya san wajen farin sani. Malam Shehu ya riƙe bagco bag ɗin da ya taho da shi da kyau. Duk wani abinda ya mallaka a chan ya kyautar wasu kuma ya sadakar da su. Tsarabar da Malam Zulkiflu ya bashi ne kawai a cikin jakar da ya riƙo. Koda su ka shiga anguwar sabbin gina-gine ya sa bai gane gidan ba har sai da Mai Keken ya tsaya ya ce "mun iso" An chanja fentin gidan da gate ɗin gidan. Cewa yai Mai Keken ya ɗan yi gaba saboda ba nan zai sauka ba. Sai dai har su ka kusa ƙarisa layin bai gane gidan sa ba. Ƙarshe ya sauka a keken ya fara dawowa baya yana irga gidajen da ya sani a wajen da har ya kai gidan da ya ke tunanin nan ne gidan da ya siyawa Maryam, sai dai yanayin yadda aka sauya fasalin gidan completely sai ya ji jikin sa yayi sanyi ko dai sun tashi ne? Ko dai wasu ne a wajen yanzu?... Tunda Junior ya dawo daga makaranta yaran ke ta wasan banza a falo. Sune ma su ka tashi Alinah da ke bacci a ɗaki. Mommy ta ɗaukota ta goyata saboda kuka da ta ke yi, gashi uwarta daga tafiya cin ɗanwake ba ta dawo ba. Daga ɗaki Salman da ke ƙoƙarin baccin rana ya daka wa yaran tsawa tareda cewa idan ya zo ya same su a falon sai ya karya ƙafar su. "Ku je compound ku yi wasa" Mommy ta faɗa dai-dai za ta shiga kitchen. Yaran su ka fice daga falon da gudu wannan na cewa ayi ball wannan na cewa tseren keke za su yi. A chan ɓangaren Zaytoonah kuwa kaman da wasa tana duba wayarta sai ta shiga duba status ɗin mutane, nan ta ga status ɗin Ghazala inda ta ga ta ɗaura hoton ta da na Justice a cikin jirgi, Galadima na zaune riƙe da jarida ta mu su selfie ɗin. Duk da idon sa na kan jaridar ne amma ba ƙaramin kyau yai ba. Hoton ba na yanzu ba ne, dan ta tuna wani lokaci da aka yi biki a Yola shine su ka je tareda ita. Lokacin ma ta zo Zaria yin wani abu su ka tafi amma dan neman tsokala sai da Ghazala ta tura ma ta hoton. Ranan ta gani ta kwana da kishi. Abinda aka rubuta a ƙasan hoton ne duk ya dagula ma ta lissafi *7days to our 2nd honeymoon trip. Guess where we are heading to?* Wato ya saketa, yayi banza da ita yanzu kuma sai honeymoon. Da farko danne zuciyarta ta yi kamar ba komai musamman da ya ke Iya ta joining na su a falon. Amma daga baya ta miƙe ta wuce ɗakin Humairah. Tana shiga ta rufo ƙofa ta fara kuka. Ta rufe bakinta dan kar su Iya su jiwota. This past two days tanayi kaman ba ta damu da rabuwan da su ka yi da Galadima ba, but deep inside her ta san ƙarya ta ke yi. She loves him, she misses him, she wants to be with him badly and yet a lokaci guda kuma she's angry and she hates him... Malam Shehu na tsaye a bakin gate ɗin ya rasa ya zai yi ya shiga. What if ba iyalinsa ba ne a gidan yanzu? Hayaniyar yara da ya ji daga ciki ya sa shi ƙwanƙwasa gate ɗin gidan. "Hashir je ka duba waye?" "Ba zan je ba" ya faɗa yana cigaba da tuƙa keken sa. Sun sani sarai idan su ka fita da keken waje Uncle Salman sai ya zane su. Akwai wani zuwa da su ka yi su ka fita waje da keke suna wasa wani mai babur ya buge Hadid. Allah ya sa abin ya zo da sauƙi bai wani ji ciwo ba sai buguwa kawai da yai kaɗan. Junior na gyara kachar keken sa da ta zube shiyasa kawai Hadid ya nufi gate ɗin ya buɗe tunda Hashir ya ƙi zuwa. Malam Shehu ya kalli yaron da ya buɗe ƙofan bugun ƙirjin sa ya yawaita. Ba ta inda zai ce yaron yayi kama da wanda ya sani. Shikenan ta tabbata iyalinsa ba sa wajen. "Malam lafiya? Wa ka ke nema?" Hadid ya jera ma sa tambayoyi lokaci guda. Malam Shehu ya gyara riƙon jakar bagco ɗin hannunsa ya ce "nan ne gidan Maman Zaytoonah?" Yes ya faɗa haɗeda gyaɗa kai hakan ya sa bugun ƙirjin Malam Shehu ya ƙaru. A hakan dan ya ƙara tabbatar da Maman Zaytoonan da ya ke nufi shi yaron ke nufi ya ce "ina nufin Maman Zaytoonah da Salman" "Yes, ai GrandMa ɗin mu kenan" "GrandMa ɗin ku?, as in Kakar ku?" ya faɗa a ruɗe. Hadid ya gyaɗa kai. "Wa ka ke nema a ciki, GrandMa ko Uncle Salman?" Hadid ya tambaya ganin Malam Shehu ya ƙura ma sa idon sa da su ka ciko da hawaye yana murmushi. Sai da Malam Shehu yai kabbara kaman sau uku kafin ya riƙo hannun Hadid ya ce "kai ni wajen Kakar ku" Duk rigiman Hadid sai ya ka sa yiwa wannan tsohon mu su. Hashir da Junior da su ka gan shi tafe da tsoho sai su ka ƙariso wajen sa da gudu suna tambayar sa waye wannan ɗin. Shikuwa Malam Shehu hankalinsa da ya kai ga Junior sai ya fara yiwa kan sa tambayoyi. Shi wannan ɗin ma ɗan Zaytoonan ne? Idan haka ne kenan auren wuri akayiwa Zaytoonan sa. Kai ƙila ma dai wani cikin yaran 'yan uwa ne. Amma kamannin sa da Salman yayi yawa shi dai kawai wannan ɗin fari ne maimakon Salman da ke baƙi. "Ya sunan ka?" Ya nuna Junior "Junior" Junior dai ba asalin suna ba ne dan haka ya ce "miye asalin sunan ka?" Ya ƙarisa maganar already zuciyar sa na anticipating cewa Junior jinin sa ne. "Abubakar Tijjani Abubakar" junior ya amsa ma sa. Malam Shehu ya jawo Junior jikin sa yana hamdala a fili. Hashir da tun ɗazu ya ƙurawa Malam Shehu ido ya yi cikin gidan da gudu. Yana shiga kai tsaye ɗakin Mommy ya wuce ya shiga duba wayanta. Aikuwa yana ganin wayan akan gado ya ɗauka yai kitchen da gudu. Mommy na zuba tomatoes cikin blender za ta yi markaɗe Hashir ya shigo yana miƙa ma ta wayar. Hoton TJ has always being on her lockscreen wallpaper. "Mine ne?" "GrandMa, mai kama da Daddyn Mom ne ya zo" Mommy ta yi saurin karban wayan ta duba hoton da ya bayyana a wayan bayan ta buɗe. Kafin ta yi magana ta jiyo Sallamar su Hadid da Junior. "Shine ya zo GrandMa" Hashir ya faɗa tareda ficewa daga kitchen ɗin. Hashir akwai kaifin basira, ko kaɗan baya mantuwa. Sau ɗaya idan ya ga abu ya riƙe kenan balle kuma hoton da sun jima suma kallon sa a wayanta kuma sun sani hoton dai GrandPa ɗin su kenan. Mutumin da ya haifi uwar su. The thought of kasancewar mutumin da Hashir ya ce ya zo TJ ya sa bugawan zuciyarta ya ƙaru. She stood there perplexed not knowing exactly what to do. "GrandMa you have a visitor" Hadid ya faɗa da ƙarfi. Mommy ta dafe counter da sauri saboda wani jiri-jiri da ta ke ji. "GrandMa!" "I'm coming" ta faɗa da muryan da bai kai ko ƙofar kitchen ɗin ba balle ya isa falon da yaran ke tsaye. A hankali ta fara takawa tana rera duk wani addu'an da zai sa bugun zuciyar ta yai sauƙi dan ji ta ke yi kamar zai fashe. What if shine? What if ba shi ba ne? A bakin ƙofa Malam Shehu ya tsaya dan tsoron sa kar ya kasance Maryam ɗin sa matar wani ne yanzun. Mommy da ta fito ta ga Yaran uku ne kaɗai a tsakiyar falon sai ta ɗan ji sanyi. "Ina baƙon ya ke?" "He's outside, barin ce ya shigo" Hadid ya leƙa ƙofa ya ce "Malam wai ka shigo" Malam Shehu yai Bismillah ya shiga falon bayan ya cire takalman sa. Sanda aka ɗaga labule Mommy ta rufe idon ta tareda addu'ar Allah ya tabbatar da farin cikinta yanzu. Ta buɗe idonta dai-dai lokacin da ya furta "Maryam Inkiru" yai murmushi yayinda hawayen da su ka jima a idon sa su ka fara zubowa. Mommy ta sake rufe ido ta buɗe a karo na biyu dan ta tabbatar gaskiya ne ba illusion ba. "Inkiru" "Nkiru T J Nnnnnkiru" "Sorry Maryam Nnnnnkiru" Dariya haɗeda kuka ya kuɓcewa Mommy. T J ya tako a hankali zuwa gabanta ya tsaya. Zai yi magana Mommy ta faɗa jikinsa ta riƙe shi ƙamƙam tana kuka. Shima ya haɗata da 'yar da ke goye bayan ta ya rungumeta da kyau hawaye na cigaba zuba a idon sa... Zaytoonah na cikin kuka aka turo ƙofa da ƙarfi "Anty Zaytoonah" Humairah ta faɗa tana rarraba ido tana neman Zaytoonah. Sheshsheƙar kukan da ta ji a gefe ya sa ta duba gefen ta inda Zaytoonah ke tsaye fiska shaɓe-shaɓe da hawaye. "Anty Zaytoonah kuka kuma. Miya faru?" " kullum ita mace ita ce za a barta da takaici da kuka. I love him, i believe in him amma shi munafuki ne. It's always about sex sex sex, that's all that matters to men. Ba su da zuciya, zuciyar su tana tsakiyar ƙafafuwan su ne. Ya riga ya gama samun abunda ya ke so a jikina shikenan ai dole ya rabu da ni. Honeymoon, a'a Allah ya sa su tafi Beemoon" ta ƙarisa maganar tana kuka. "Kiyi haƙuri Anty. Wallahi Galadima na son ki, inaga asiri matar nan ta ma sa" "Kar ki ɗaure wa ƙarya gindi. He's a selfish man" When a woman is angry she forgets all the good days. Kishi ya hana Zaytoonah ganin kyawawan halayen Galadima balle ta ma sa uzuri. Humairah ta jata zuwa gado ta zaunar da ita tana cigaba da ba ta haƙuri. Zaytoonah ta dafe ƙirjinta da ke ma ta zafi. Ba wani sauraron abinda Humairan ke faɗa ta ke ba. Haushin kan ta take ji da ta bawa Galadima soyayyarta gashi ya taka soyayyar ya jefa a Bola. Wayar Zaytoonah ne ya shiga ringing. Ta ɗauka ta ga sunan Mommy. Ta sa hannu ta goge hawayen da ke fiskarta kafin ta amsa kiran. "Adaeze maza-maza ku zo gida yanzu ke da Humairah" "Mommy lafiya?" "Lafiya, just come now, yanzu-yanzu kin ji" "Na ji" Humairah ta kalleta ta ce "miya faru?" "Wai mu zo gida yanzu-yanzu" "Ko wani abu ne ya samu Alinah?" "Kai i doubt that. She sound excited" "To barin ɗauka hijab sai mu je" Zaytoonah ta shiga banɗaki ta wanke fiskarta kafin ta fito ta bi bayan Humairah da tuni ta wuce falo... A chan gidan Mommy kuwa 'yan biyu ne su ka shiga ɗakin Salman da gudu suka tashe shi a bacci su ka ma sa gulman baƙon da ya zo. Wani tsalle yai ya tashi daga kan gadon yai waje da gudu. Cak ya tsaya ganin Mommy jikin mutumin da ya jima da saka ran ba zai sake ganin sa ba a duniya. Ba shi da wayo sosai amma hotunan sa da kusan kullum sai ya kalla su suka tabbatar ma sa da mutumin da ke tsayen dai mahaifin sa ne. Furfura da rama su ne su ka fi komai ɓoye kamannin sa da wancan na hoton da ya ke gani. Alinah ce a hannun sa yana ma ta wasa. Ita ya fara tambaya bayan ya iya tsaida kukan sa. Tunda Mommy ta ce 'yar Zaytoonah ne ya ce ta kwanceta ya ji ɗumin jikar sa. "Da Da Daddy" Salman ya furta a kiɗime. T J ya ɗago ido ya kalleshi yai murmushi tareda faɗin "Salman, my son" bai jira ya ƙarisa faɗin my son ɗinba ya ƙarisa da sauri ya rungumeshi yana kuka. A lokacin ne Mommy ta koma gefe ta kira numbar Zaytoonah. Mommy kiɗimewa ta yi lokacin da ta shiga kitchen tana so ta kawo wa T J abinda zai sa a baki bayan ruwa da ya tambaya. Tana jiyo dariyan T J daga inda ta ke inda 'yan biyu ke bashi labarin Zaytoonah. Alhamdulillah ta furta a hankali. Ba abin da za ta ce sai godiya domin Allah ya amshi roƙon ta. Ruwa kawai ta ɗaura akan tray ta wuce da shi falon. Yaran sun yayyameshi abin sha'awa. Ta ajiye tray ɗin ta miƙa ma sa glass cup ɗin hannunta bayan ta ranwafa kamar yadda ta saba. Hawaye ne ya zubo ma ta lokacin da T J ya haɗa hannunta da na shi ya kai kofin bakin sa. Hannun sa yayi ƙarfi, yayi kaushi ya faffashe. Ko wani irin aikin ƙarfi ya dinga yi iya tsawon shekarun nan oho. Ta yi saurin goge hawayen da ɗaya hannunta. Sai da ya shanye ruwan tas kafin ya ce "na gode" "Mi za ka ci?" "Duk abinda kika dafa min, indai hannun ki ne ya dafa, koma minene zan ci" ya faɗa yana murmushi. Bayan ta koma kitchen ne ta buɗe fridge ta fara duba abubuwan da ke ciki. Yau kam dole ne ta zama best Chef of the universe, dan girkin da za ta yi ba irin wanda ta taɓa yi ba ne. Jiya aka yi sayayyan kayan miya so almost duk abinda za ta buƙata akwai... "Dan Allah kar ki bari Mommy ta fahimci akwai matsala" "Kar ji damu Airah. Ai na gama mi shi kuka, ya je yai duk abinda ya ga dama" Zaytoonah ne a gaba dan haka ita ta buɗe ƙofar ta fara shiga. Cak ta tsaya ganin Alinah a hannun mai kama da Daddy. Junior na zaune a gefen sa, Salman na zaune a ƙasa ya ɗaura kan sa a cinyar sa. Sai 'yan biyu da ke ɗaya gefen. Itama Humairan tsayawa ta yi cak tana tunanin ko dai ba ta ga dai-dai ba ne. "Mom GrandPa ne ya dawo" muryan yaran ta ya karaɗe kunnuwan ta. "Adaeze, Aisha come here" Tsalle Humairah ta saka tana kiran sunan Daddy tareda ƙarisawa wajen sa ta faɗa jikin sa. Zaytoonah kam na tsaye ta ka sa motsawa, sai hawaye kawai da ta ke yi. T J ya miƙawa Humairah Alinah sannan ya taso ya zo gaban Zaytoonah ya rungumeta. Lokacin da ta jita jikinsa sai ta fashe da kuka tana kiran Daddy...Daddy... *** A chan ɓangaren Ghazala kuwa shirye-shiryen tafiya Honeymoon ta ke yi. Maganan aure kam sai dai ayi mi shi idan ba ta raye. Ta riga ta samu abinda ta rufe bakin Hajiya Ajwa. "Kin manta abinda ya faru shekaru huɗu da su ka wuce ne Hajia?" Tambayar da ta ma ta washegarin ranan da su ka yi waya da Hajia Abu kenan. "Ghazala ba na son ɓoye-ɓoye. Ki fito fili ki yi magana" "Ina nufin cikin da aka zubarwa Mubaraka a South Africa..." "Subhanallahi! Wani irin magana ne wannan? Ghazala ba na son munafurci" Ghazala ta saka dariya kafin ta ce "kin sani sarai Hajia Abu idan ta ji maganan nan ba abinda zai sa ta cigaba da maganan auren Mubaraka da Galadima" "Na fi ƙarfin ki Ghazala. Idan ƙona kan ki za ki yi sai dai kiyi amma mun riga mun tsaida magana. Nan da wata uku za a kawo miki ƙanwa" "Ahaf, sai mu zuba ido mu gani, ni da ke wa zai yi nasara" Daga haka ta katse wayar. A ɓangaren Hajia Ajwa ta sake tsinewa Yusuf a karo na ba adadi. Wani yaron Igala ne da su ka haɗu da Mubaraka lokacin tana first year ɗin ta a ABU shi kuma yana aji uku. Soyayya ne ya shiga tsakanin su lokaci guda. Shi Yusuf yana baya-baya da Mubaraka saboda ita 'yar babban gida ne amma Mubaraka ba ruwanta. Kafin ka ce me Mubaraka ta fara sake ma sa kuɗi har motar da ta ke hawa ta bashi ta sa Baban ta ya siya ma ta wani. Ana cikin haka 'yan gulma su ka kai wa Hajia Ajwa maganar. Jin cewa wani yaron talaka ɗan ƙabilar Igala Mubaraka ke soyayya da shi ya sa ta tuhumi 'yar ta da maganar. Mubaraka ta tabbatar ma ta da cewa Yusuf ɗin ta ke so. Takurawan da aka yiwa Mubaraka akan Yusuf da kuma kashedi da akai wa Yusuf ɗin ya sa Mubaraka ta kawo mu su mafita. A zahiri Mubaraka ta nunawa Hajia Ajwa ta rabu da Yusuf amma a gefe suna nan manne da juna. Wata biyu da haka kuwa Mubaraka ta samu ciki. Dama abinda ta ke nema kenan. Ba kunya ba tsoron Allah ta faɗawa Hajiyar akan tanada ciki kuma so ta ke a barta ta auri Yusuf. Tuni Hajiya Ajwa ta yi maganin zancen dan ko kaɗan ba ta so a ɓata ma ta suna a gari. Sawa ta yi aka sace Yusuf aka tura shi prison a chan kudu. Mubaraka kuwa ta kaita South Africa aka cire cikin, daga nan kuma ta rufe bakin 'yar ta. Nan da nan Mubaraka ta manta da wani Yusuf ta cigaba da karatu a chan. Hajia Ajwa mantawa ma ta yi da wani kashin Yusuf. Yana chan kurkuku shekaru huɗu kenan ba tareda laifin komai ba... Ghazala ta kira Hajia Abu ta sanar ma ta komai gameda cikin da Mubaraka ta yi a baya. Hankalin Hajiya Abu ya tashi ta ce ai ba zai yiwu Galadima ya auri macen da ta gama gantali a titi ba. Suna gama wayan ta dannawa Hajia Ajwa kira ta nemi tabbacin abinda ta ji daga wajen Ghazala. Hajia Ajwa ta ce ba ta san komai ba, amma ina Hajia Abu ta janye maganar aure. Suna gama waya da Hajia Abu ta dannawa Bokan ta kira. Shekarun baya da ta kai maganar Mubaraka ce ma ta yai ƙaddaran Mubaraka haɗe ya ke da ta Yusuf hakan ya ƙara tunzurata. The last thing she wish shine 'yarta ta auri talaka, talakan ma ƙabila. "So na ke ma ka fara fitar min da Ghazala a gidan tun kafin ma Mubaraka ta shiga gidan. Auren Galadima da Mubaraka na ke so nan ba da jimawa ba. Kai nan da wata ɗaya ma ayi shi" Ko mi Bokan ya gaya ma ta oho sai kawai ta ma sa godiya ta ajiye wayar. Mubaraka da ta zo shiga ɗakin mahaifiyarta ta juya da baya da sauri. Tuntuni maganin da aka ma ta akan manta Yusuf ya ɓace. Da ta dawo Nigeria ma a ɓoye ta ke ƙoƙarin binciko inda ya ke duk da iyayen sa sun yi amanna da cewa ya riga ya mut, ita kam tana ji a ranta bai mutu ba mahaifiyarta dai ta ɓoye shi. Tana shiga ɗaki ta ɗau wayarta ta kira ƙawarta Gimbiya Safiyya ƙanwar Galadima. Ce ma ta tayi ta turo ma ta numbar wayar Galadima. Ita kuwa Safiyyar ta fara tsokalar ta akan soyayya ta kankama kenan. Dan tuni maganar Mubaraka da Galadima ta fara yawo a Fada. Bayan ta turo ma ta numbar ne ta tura ma sa saƙo. Kusan minti biyar sai ga shi ya yi ma ta reply. Zuwa yamma ta samu Hajia Ajwa akan za ta je Abuja gobe akwai wani aikin NGO da ta cika kuma za a mu su interview gobe. Hajia Ajwa ba ta kawo komai ba a ranta ta ce ta je. Har da cewa idan ma ba za ta dawo a ranan ba ta wuce gidan Galadima ta kwana a chan. Da gayya ta faɗi hakan tunda ta san ba Galadima ne kaɗai ɗan uwan su da ke zaune a Abujan ba. Tsokalar Ghazala ta ke son yi. Washegari ƙarfe shabiyu ta wuce kaɗan Mubaraka ta sauka a office ɗin Galadima. Ba dan zuciyarta ya jima da son Yusuf ba da ba abinda zai sa ta ƙi haɗin da ake son ma ta da shi. Ba kyaun sa kaɗai ke jan mace gareshi ba sai dai kwarjini da Allah ya bashi. Har yau idan ana hawan sallah idan har ba ka tsaya ka ga tawagar Galadima ba to kaman ba ka ga hawan sallah ba. Kwarjinin sa ya jawo ma sa mutane. Lokacin da yake zawarci kafin ya auri Zaytoonah Mata dayawa suna kawo ma sa wargi, idan ka ga saƙonnin da Mata ke tura ma sa a rana sai ka sha mamaki. Lokacin da ya auri Zaytoonah ne ma abin ya zo ya ragu sosai. "Ina jin ki Mubaraka" Mubaraka ta sunkuyar da kan ta ƙasa ta fara magana dan idon sa ya ma ta nauyi. Sai da ya gama sauraron bayanan ta kafin ya ɗaura da na shi. Lokacin da ta fita a office ɗin ne ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin "Ya Allahu!" Miyasa wasu Matan ba su da hankali ne? Akan namiji sai mace ta jefar da mutuncinta ta take dokokin Allah. Yanzu kam lokaci yayi da zai fito da komai waje. A da ya bari sai ranan da za su je supposed honeymoon trip ɗin da Ghazala ta shirya ne sai ya fito da komai waje, amma yanzu dole ayita ta ƙare dan delaying it further will ruin things... Bayan ya tashi daga office kai tsaye gida ya wuce inda ya samu Ghazala a ɗaki tana lissafin kasuwancinta. Ce ma ta yai gobe ta shirya za su je Zaria Sallama tunda tafiyar ta su nan da kwana huɗu ne. *** "Aje ayi sallah sai aci abinci" Mommy ta faɗa bayan ta fito daga kitchen. Tuntuni aka kira sallan la'asar amma surutun da su ke yi ya hana su tashi gashi har ƙarfe biyar saura kwata. Yaran kamar kar su bar jikin Uban su musamman Junior da Zaytoonah. An ji na Junior shi sai yau ya fara ganin uban sa a zahiri ita kuma Zaytoonah sakalci ne na ta na iyashege daya haɗu da jin daɗi. Mommy ta kama hannun T J ta yi ɗaki da shi, suna shiga ta nemi sakata ta saka. Sake rungume shi ta yi sosai tana ƙara jin wani sabon son sa na shiga jikin ta. "Sadiq ya rasu ko?" Ya tambaya a hankali. Ta ɗago kan ta ta ce "ya rasu ranan da na haifi Junior" "Allah ya ma sa Rahama" ta amsa da Amin. Suna tsaye rungume da juna kusan minti biyu kafin Mommy ta ce su ƙarisa banɗakin. Ruwa mai ɗumi ta haɗa ma sa kafin nan ta shiga cire ma sa kaya. She missed those days da su ke komai tare. A hankali ya furta "kin tuna wani rana mun yi faɗa kika zo cire min kaya kika rufe idon ki, kika yi haka da fuska" Ya faɗa yana juya fiskarsa gefe kaman yadda ta yi ranan. Tabbas ta tuna ranan. Da ke idon ta a rufe ya ke ba ta san sanda ya rankwafo kai ya haɗa bakin su ba and that's how the fight ends ranan. Yanzun ma haɓarta ya ɗago sannan ya ɗaura bakin sa saman na ta... Ba su fito daga wanka da wuri ba dan suna fitowa daga banɗakin 'yan biyu suka fara ƙwanƙwasa ƙofa suna faɗin wai kowa yayi sallah su ake jira. "GrandPa GrandMa ku fito mana" T J yai murmushi. "Ai indai 'yan biyu ne za ka yi dariya ka gaji" "Miyasa Aka yiwa Zaytoonah auren wuri? Dan dai idan ba auren wuri aka ma ta ba, ba yadda za ayi ta haifi yara kaman 'yan biyu." "A hankali za ka ji labarin komai. For now, bari mu yi sallah" Cikin tsofin kayan sa da Mommy ke sawa ta bashi wani riga da wando ya saka. Shine ya ja su sallar, bayan sun idar su ka gabatar da godiyan su ga Ubangiji. Bayan sun fito a tsakiyar falo su ka zauna aka matsar da kujeru aka ajiye ƙaton silver tray. Zaytoonah da Humairah su ka taya Mommy serving abincin. Tuwon shinkafa aka yi da miyar egushi wanda ya ji nama, Stockfish da Pomo. Miyar egushi is one of his best miya shiyasa ta mi shi. Zaytoonah ce a gefen Daddy na hagu yayinda Mommy ke ɗaya gefen. Lokacin da aka fara cin abincin Salman ya tsaya ya ƙi sa hannu. "Salman ya ba ka ci?" "Daddy ni kai na ke son ka bani a baki" "Cabɗi, wallahi Daddy ka bashi sai ka bani. Ai ni ce Princess ɗin ka" Zaytoonah ta faɗa tana tura baki. T J yai murmushi ya ce za'a ba ta itama. Zaytoonan ya fara bawa loma ɗaya a baki kafin ya koma kan Humairah sai kuma Salman da Junior. 'Yan biyu su ka matso kusa wai suma a basu. Ganin anyi sau biyu za'ayi na uku Mommy ta riƙe hannunsa ta ce " ya isa haka ko bari ya ci abinci a nitse" "Lah! GrandMa ta yi fushi dan ba'a bata a baki ba" Hadid ya faɗa hakan ya sa gaba ɗayan su suka sa dariya. T J ya ce " bari itama a bata na ta" ya miƙa ma ta lomar abinci a baki. Suna cikin cin abincin Auwal ya fara ƙwanƙwasa ƙofa dan sun riga sun kulle ƙofan Falon. Humairah ta miƙe da sauri ta je ta buɗe ma sa. "Mi ya faru aka rufe ƙofan? Na ɗauka ma ba kwa nan..." "Hamma, Daddy, Daddy ya dawo" "Da gaske Aysha" ta gyaɗa kai tareda nuna ma sa inda su ke cin abinci. Ya ƙarisa wajen da gudu yana faɗin Daddy. Rungumeshi yai ta baya yana sauke ajiyar zuciya sai kuma hawaye su ka fara zubowa. "First Son kai ne ka zama babban mutum haka? Jikokina nawa yanzu?" "Daddy, ai har yanzu first Son ɗin ka gauro ne" "Maryam ya haka? Ya kuka bar min ɗa yana rayuwa shi kaɗai?" Mommy ta ce "tunda ka zo yanzu kam shikenan sai ka ma sa aure" Hashir ya ce "GrandPa, Anty Humairah zai aura fa. Ranan ma tana cewa 'idan na auri Hamm..." kafin ya ƙarisa Humairah ta buge bakin sa. "Ah! Lallai abu yayi kyau" Humairah da Auwal su ka kalli juna, suna haɗa ido Humairah ta yi saurin sunkuyar da kai. Ƙaddara da ta riga fata kenan. Bai taɓa kawowa ran sa Auwal ba zai auri 'yar sa Zaytoonah ba. Abu ne da yai sha'awar sa tun ma Zaytoonah na ƙarama dayaga irin shaƙuwar su da Auwal ɗin. Tareda Auwal aka ƙarisa abincin kafin bayan sun nitsu T J ya ce zai je ya ga Iya tunda ya ji a bakin yaran cewa tana raye. Zuga guda su ka fita daga gidan kowa baya son yin nisa da T J. Suna fita Mommy ta yi sujudish shukri tana ƙara miƙa godiya ga Allahu Akbar... A gidan ma dai an yi koke-koke. Iya na kuka T J na yi. Muntari na ɗaki yana yin na sa. Yana ɗaki ya jiyo hayaniyar yaran dan su suka fara shigowa su ka gabatar da Daddy wa Iya da ke zaune a falo tana shan kunu. Tabbas dai ɗan uwan sa ne ya dawo, to da wani idon zai kalleshi? Wannan ya sa ya tuƙa keken sa ya je ya sawa ƙofar ɗakin sakata. Shi ya cuci Hamma Tijjani, ya raba shi da gida shekaru shaɗaya. Da ƙyar Iya ta haƙura ta dena kuka. Ta waiwaya ba ta ga Muntari ba. "Ina Muntari ya ke? Ku je ku kirashi" Junior ya ce sun je amma ɗakin sa a kulle. "Muntari na gidan nan?" T J ya tambaya da mamaki. A iya sanin sa Muntari na da gida, gidan ma da ya taka na shi a komai. "Yana nan Shehu. Ka je ka same shi na san kunyar ka ya ke ji" Ko da ya je ya buga ƙofar ƙin buɗewa yai hakan ya sa Auwal ya kawo ma sa spare keys ɗin ɗakunan gidan ya karɓa ya buɗe da shi. Ganin Muntari akan wheelchair ya sa shi zaro ido. "Mukhtar" ya kitɓra sunan sa a hankali. "Kar ka ƙariso Hamma. Ban zanzanci ganin ka ba" yai maganar yana juya keken sa gefe. Kishi da Hassada su suka kawo wannan rana. T J ya ƙarisa wajen Muntari da ya rufe fiskar sa da tafukan hannunsa yana kuka. "Ɗan uwa Dan Allah ka bar kuka. Godiya za ka yiwa Allah" "Ka barni na yi kuka Hamma. Ni ne sanadin komai, ni ne na rushe ma ka farin cikin ka, ni na rabaka da iyalin ka. Ni ne silar komai" Bai gama gane mi Muntarin ke faɗi ba amma kuma koma minene shi ya yafewa ɗan uwan sa. Rayuwar sa ta ishe shi ishara cewa duniyar nan ba komai ba ne. Wanda ya riƙe Allah shine zai samu rabo. Yafiya yana ɗaya daga cikin abinda ke ɗaga darajar mutum a wajen Allah. Tun jiya da Malam Zulkiflu ya tabbatar ma sa Asiri aka ma sa ya ce ya yafe wa koma wanene. "Maryam ba ta gaya ma ka ba ne?. Ni ne na sa aka ma ka kurciyya" Abu ne da bai yi tunanin ji ba amma ya riga ya faru. Kuma nadaman daya gani a wajen Muntarin ya nuna ma sa cewa ɗan uwan sa ya jima da tuba... Ƙarfe tara na dare Auwal ya tattaro kan yaran su ka koma gidan Iya dan achan za su kwana. Duk cikin yaran ba wanda ya so haka sai dai abinda ya dace kenan. Mommy da Daddy su na buƙatan kaɗaici. Mommy ce ta fi dacewa ta bawa T J labarin komai, labarin abinda ya faru iya tsawon lokacin da yai baya nan. Bayan tafiyan Yaran Mommy ta je ta kulle gida lokacin T J na banɗaki. Shirin kwanciya ta yi amma T J ya ce bai san komai ba yana son sanin komai daya faru. "Ka huta mana Barkindo" Ya girgiza kai ya ce " ba zan iya ba Maryama tun ɗazu ma daurewa kawai na ke yi" Tiryan- Tiryan Mommy ta shiga bashi labarin rayuwar da su ka yi tun lokacin da aka neme shi aka rasa a Asibiti. Irin faman da ta yi da Muntari har ta kai ta yiwa Zaytoonah aure da wuri. Tunda ta fara labarin bai katse ta ba, sai faman sauke ajiyar zuciya da ya ke yi musamman da ta gaya ma sa Goggo ta rasu. Labarin rayuwar Zaytoonah ya fi komai taɓa shi musamman lokacin da ta faɗa ma sa irin haukan da Zaytoonan ta yi immediately bayan rasuwan mijin ta. "Yanzu ya saketa kenan?" Ya tambaya lokacin da ta faɗa ma sa dalilin dawowar Zaytoonah gida. "Bai ce ya saketa ba ya dai ce ta zo gida zai neme ta" "Idan ma baya sonta ni ina son ta ya sawwaƙa ma ta kawai" "Ya sawwaƙa ma ta muna shirin shan suna nan da watanni ma su zuwa" T J ya zaro ido. "Alinah ta yi wata shida kuwa?" "Ni dai ba ruwana, ka tambayi 'yar ka" ta faɗa tana murmushi. Bayan ta gama na ta labarin shima ya ba ta na shi wasu abubuwan ya iya tuna su wasu kuwa bai iya tunawa ba. Mommy kam sai da ta yi kuka da ƙyar ma ta bari ya kai ƙarshen labarin. Mutum kenan. Akan Mace, akan dukiya da kuɗi, akan siyasa, akan kishiya, akan sarauta, akan soyayya ba abinda Mutum ba zai iya yi ba. Lokacin da su ka kwanta ƙarfe huɗu saura na Asuba. Mommyn ce ma ta kwanta shi kam Alwala yai ya fara sallah. Bayan sallar Asuba ne ya samu ya kwanta Har za su kwanta ya ce " Maryam na ga hotunan sirikai na" Mommy ta ɗau wayarta ta fara dubawa hoton Zuhayr ta fara nuna ma sa. Tareda Zaytoonah su ka ɗauka lokacin da su ka zo Nigeria. Ya fi minti biyu yana kallo kafin ya ma sa addu'a sannan ya ce ta nuna ma sa hoton Galadima. Ya dai taɓa ganin sa tun ma ba a bashi sarautan Galadiman Zazzau ba amma gaskiya ba zai iya tuno kamannin sa ba yanzu. Recent hotunan da su ka yi da Zaytoonah lokacin da su ka kai mu su ziyara a Las Vegas ta nuna ma sa. "Allah mai sarrafa al'amura" "Ka san shi ne?" "Shine Alkalin da na ce mi ki na yi aikin gadi a gidan sa na shekaru biyu" T J na aiki a gidan Justice Yunus lafiya-lafiya, kwatsam watarana Justice yayi wani baƙo daga Kano. Justice ya zo raka shi airport suna cikin mota mutumin ya ƙyalla ido ya ga T J da ya buɗe mu su gate. Ai kuwa ya ce Dreba ya tsaya. "Justice kaman Dr Tijjani na ke gani" "Dr Tijjani?" Abokin sa ya ce "Malamin mu ne lokacin ina yin Masters ɗina a ABU" Fitowa dukkan su biyu su ka yi daga cikin mota dan abokin ya tabbatar cause Justice dai ya san Maigadin sa sunan sa Malam Shehu ba Dr Tijjani ba. "Dr Tijjani Abubakar Modibbo" abokin ya kira yana tsurawa Malam Shehu ido. Sai dai Malam Shehu ya ƙeƙasa ƙasa ya ce ba shi ba ne, bai ma taɓa jin sunan ba. Abun ya bawa abokin Justice mamaki, ya dai haƙura ya tafi akan ƙila kamanni ne kawai. Sai dai bayan tafiyar sa washegari Malam Shehu ya ajiye aiki a gidan Justice ya ƙara gaba. "Mommy ta ce what a coincidence. Kai ba abunda za mu ce sai dai Alhamdulillah" 2/11/21, 10:04 PM - ****: 72 Bismillahir Rahmanir Rahim *The truth* Tun da sassafe Zaytoonah da Humairah su ka shiga kitchen inda su ke haɗa special breakfast wa Daddyn su. Ƙarfe bakwai ta wuce kaɗan su ka gama komai. Bayan ta shirya Alinah ta wuce ɗakin da 'yan biyu su ka kwana dan ta ba su kayan da za su saka. Daga bakin ƙofa ta ke jin kaman yaran na waya, ta tura ƙofan a hankali ta shiga. Salman na zaune a bakin gado yana danna laptop yaran na ta kuma Hadid na riƙe da waya a ta kunnen sa shima kuma Hashir ya sa kunnen sa a wajen wayan duk da kuwa a handsfree wayar ta ke. "Daddy ina za ka zo ka ga GrandPa ɗin mu ko?" "Ofcourse dear, zan zo yau ba ma gobe ba" Hashir ya ce "Daddy yaushe za mu koma wajen ka Mom ba ta son mu..." Zaytoonah ta fincike wayar ta kashe. "Salman what's the meaning of this?" Sai a lokacin Salman ya ɗago saboda tuntuni hankalin sa na kan project ɗin sa da ya ke gyarawa. "Ba magana na ke ma ka ba" "Miye kenan?" "Really! Bayan ka san bama tare amma shine ka ke kira mu su Daddyn Raziya a waya" "Adaeze matsalar ki da shi daban. Yaran nan ba ruwan su" "Eh lallai. To daga yau ba na so, Thank God 'ya'yana ne ba na shi ba, kar ka ƙara bari su yi magana da shi" "Kun fi kusa. Lokacin da za ki zo kina rarrashi ta cikin bargo ba na nan ai, ina chan ina fama da rungume filo" "Ka fara min rashin kunyar da ka saba ko. Wallahi zan haɗa ka da Daddy" Jefa kayan yaran ta yi a kan gado ta ce "ku saka da kan ku. And, yau ni da ku a gidan nan" ta snapping hannunta kafin ta fice a ɗakin ranta a ɓace... *** "Hajiya Ghazala manya. Na ji ance Galadima ya tafi wajen uwargidan ki... ?" "Uwargida? Har kin sa ni jin amai wallahi. Ban taɓa ɗaukan Zaytoonah da wannan matsayi ba. Idan ba ƙaddara ba yaushe zan haɗa miji da wannan yarinyar" Hajiya Safara'u ta kurɓi juice ɗin da aka kawo ma ta ta ce "ni dai ƙarshen maganan mu da ke cewa ki ka yi Galadima ya saketa. Da ta zo ta haihu kika ce idan 'yar ta kwana biyu zai karɓo mi ki ita ki rene ta" "Ina cikin matsala Safara'u. Ban san ya aka yi komai ya dagule min ba, yadda ya ke ji da haihuwan nan ina ga ko haihuwar farko da aka ma sa albarka. Ina da tabbacin saboda cikin da ta ke da shi ne ya sa ya dawo da ita" Ghazala ta yi maganar dan ta kare kan ta. Hajiya Safara'u ta dai ji ne amma ba ta yarda ba dan Galadima ba irin mutanen nan ba ne da su saki matar su cikin sauƙi. Ko lokacin da Ghazalar ta yi ta yaɗawa akan ya saki Zaytoonah ta yi shiru ne amma ba ta gama yarda da zancen ba. "Ke idan aka ce za'a taimakeki sai ki fara maganar ke ba ka son harka da Boka. Ni na gaya miki Malami ke mini aiki ba boka ba. Laya ce kawai za'a ba ki amma wallahi sai kin dawo kina godiya" "Abin bai kai nan ba Hajiya Safara'u. A hankali zan yi maganin Galadima, musamman idan na samu ciki..." Hajiya Safara'u ta furzar da juice ɗin da ke bakin ta tsabar dariya. "Lafiya ki ke dariya?" "Stop deceiving yourself Hajiya Ghazala. Ba abinda za ki yi ki raba Galadima da Zaytoonah musamman yanzu da rabo ya shiga tsakanin su. And ciki? Kina tsammanin za ki samu ciki?" Ta ƙarisa maganar tana dariya "Ba na son walaƙanci Safara'u. Mi ki ke nufi da ni ne, ai ban wuce shekarun haihuwa ba" Sai da Hajiya Safara'u ta sha dariyarta kafin ta ce "kin ga Ghazala gara ki nemi mafita na dahir wa kan ki. Samun kan Galadima haka kawai ba zai taɓa yiwuwa ba." " tashi ki bar min gida" Ghazala ta faɗa a fusace. Bayan tafiyar Hajiya Safara'u ta juya maganar da su ka yi sosai amma ba ta samu matsaya ba. To lokacin da Zaytoonah ta dawo gidan kuma kishi ya hanata sukuni ga uwa uba yadda yaran Galadima su ka juya ma ta baya su ka tare a gindin Zaytoonah. Cikin ƙanƙanin lokaci Shaiɗan ya hure ma ta kunne sai gashi ta kira Hajiya Safara'u akan maganar da su ka yi. Ita dai abu ɗaya ta ke so wato shine ta samu kan Galadima ta san idan ta samu kan shi cikin sauƙi za ta sa shi ya saki Zaytoonah. Kuɗi kawai ta turawa Hajiya Safara'u ta account dan a cewarta ba ta da lokacin zuwa ƙauye, besides ba sai ta je ba koma minene ta karɓo ma ta kawai... Kubra Sadiq ɗaya daga cikin sales girl ne na shagon Hajia Ghazala. A Nyanya ta ke amma da ƙarfi da yaji ta samu aiki a cikin Abuja, kafin shagon Hajia Ghazala ta yi aiki a wani restaurant daga baya aka koreta. Tana zaune a wajen Kawun ta ne amma kusan kaman zaman kan ta ta ke dan shima Kawun akwai son abin duniya baya tsawatar wa Kubra ko kaɗan, kusan ma za ka iya cewa tafi ƙarfin sa ne. Son kuɗi da abun duniya ne da ita har na jaraba. On this faithful day ta shiga office ɗin Ghazala ta kai ma ta report na abubuwan da su ka ƙare da wanda su ka kusa ƙarewa saboda ta kusa tafiya sari. Lokacin da ta shigo Ghazalar na waya shiyasa ta tsaya tana jiran ta. Tana tsaye sai ta hango wani awarwaron gold na Ghazala guda ɗaya a ƙasa. Sanda Ghazala za ta shiga banɗaki ne ta cire su guda uku ta sa a kan table, to da ta dawo ba ta bi ta kan su ba sai ta cigaba da harkokin ta. Sanda ta zo ɗauka kuma ashe ɗaya ya faɗi ƙasa, sai ta saka biyun akan daga baya za ta duba ɗayan. Bayan ta gama wayar ne ta karɓi report ɗin a hannun Kubra sannan ta ce ta tafi. Kubra ta fita tana Allah-Allah kar Ghazala ta ga ɗaya awarwaron. Kusan awa ɗaya bayan haka Ghazala ta fita daga office akan za ta je ta dawo. Kubra da ta ga fitan Ghazala ko minti biyar bai cika ba ta sulale akan za ta je banɗaki nan kuwa office ɗin Ghazala ta je. Ba yau ne ta taɓa yiwa Ghazalar sata ba dan a fakaice tana sace kuɗi da wasu ƙananun abubuwan da su ke da wuyan ganewa da wuri. Sa'arta ɗaya kuwa sai ga awarwaron na nan a ƙasa inda ta gan shi. Ta ɗauka tana murmushi. Dai dai ta zo fita daga office ɗin ta jiyo muryan Ghazala tana dariya. Kubra ta doka salati ta yi baya da sauri banɗaki ta ke shirin shiga ta ji ana shirin buɗe ƙofa dan haka ta yi saurin ɓoyewa ta bayan wani wardrobe babba inda kusan Duk wasu valuable abubuwa da su ka danganci takardu ko ƙananan abu suna nan a wajen an kulle da key da kuma password wanda Ghazalar ce kawai ta sani. Ghazala ce ta shigo tareda Hajiya Safara'u. "Kin san da kin ƙara minti biyu da ba ki sameni ba" "Ai na ci sa'a kuwa dan nima so na ke na kawo miki saƙon ki sai na wuce gida ina da baƙi" "Ya aka yi an dace kuwa?" "Sosai ma. Ai sai kin ƙara kuɗi ma Allah" "Duk uban kuɗin da ki ka karɓa Hajia Safara'u. Ai idan kika ga na ƙara miki sisi to na ga biyan buƙata ne" "Sha kurumin ki ƙawata. Wannan mutumin aikin sa 100% original ne ba algus. Yanzu dai" "Ina zuwa?" Ghazala ta faɗa ta miƙe ta je ta sawa office ɗin na ta key. "Kin san za a iya shigowa anytime musamman wannan Kubran nan da sam ba ta da tarbiyya" "Yawwa. Na yiwa Malam bayanin komai kuma ya bani taimako. Kin gan ta nan" Hajiya Safara'u ta fito da wata laya a cikin jakarta. Layan yana cikin farin leda. Ghazala ta karɓa tana jujjuya ledan. Wai dan ɗan wannan abun ne sai da ta ba da kuɗi dubu ɗari bakwai da hamsin. "Yadda za ki yi amfani da shi shine, za ki samu gashin shi tsilli uku sai ki ɗaura a jikin layar. Sai ki sa a ƙarƙashin pillow ko gado ki tabbatar ya kwanta dai akai. Idan har ya kwanta akai shikenan sai ki cire ki je ki bisine. Galadima ba zai ƙara yi mi ki mu su ba" "Dole gashin sai tsilli uku?" "Ghazala kenan. To ko duka gashin aka ce ki ba za ki iya ba ne" "Wannan ma mai sauƙi ne ai. Batun binnewan zan iya bisine shi a ko'ina?" "Iyi" "Hajiya Safara'u indai wannan abun yai aiki za ki samu tukuici" "Ranki shi daɗe Sarauniyar Galadima" Su ka tafa tareda fashewa da dariya. Ba su ƙara minti biyar ba Su ka fita dan kowa yana da inda zai je... Lokacin da Kubra ta fito daga office ɗin Ghazala gaba ɗaya ta haɗa zufa saboda tsorata da ta yi. Duk iskancinta bai kai ta yi shige-shigen neman magani ba. Tana iya ƙoƙarin ta sai dai rashin samun tarbiyya mai kyau da kuma kwaɗayi ya sa ta ke ɗan sata da kuma bin maza wasu lokutan. Amma Asiri? Tsubbu?. Ba ta taɓa ganin Galadima face to face ba amma hoton sa da ke office ɗin Ghazala ya sa ko a ina ta ganshi za ta iya ganeshi. Ba wanda bai san mijin Ghazala shine Justice Yunus Muhammad Abbas ba a Shagon na ta saboda yadda ta yaɗa abin lokacin auren su. Da farko tunanin blackmailing ɗin Ghazala ta yi da audio ɗin da ta naɗa na hiran su. Daga baya ta ce idan ta yi haka lallai kuwa itama ba ta tsira a wajen Ghazala ba. Nan da nan ta yanke hukuncin samun Galadima. Excuse ta nema na awa ɗaya ta fita daga katafaren shagon ta nufi office ɗin Galadima bayan ta kira wani stingy saurayinta da ke Law School na Abuja. Sunan Justice Yunus ba ɓoyayye ba ne shiyasa ta samu address ɗin office ɗin sa a wajen sa. Ko da ta je ba ta samu ganin sa ba dan ba ta da appointment kuma ma yadda ta ke ɗin ba ta yi kama da wacce za a gabatar da ita wajen Justice kai tsaye ba ne. Sai dai lokacin da ta ce Dan Allah a gaya ma sa saƙo ne mai mahimmanci gameda matarsa ta ke son bashi, ta kuma nuna ID card ɗinta na aiki. Sunan shagon Ghazala ce a jiki kuma shi Secretary ɗin ya san Ghazala matar Galadima ce. Yo tunma kafin auren su ya san alaƙar da ke tsakanin su. Kiran Galadima yai ya sanar da shi zuwan Kubra. Galadima ya ce idan ya gama magana da baƙon sa ya turota office ɗin sa. Bayan minti shauku sannan ta shiga office ɗin. Ƙirjinta ya dinga dukan tara-tara ganin Galadima cikin gown ɗin Alƙalai, yau yayi zaman kotu shiyasa ya saka gown ɗin. Ta ma ci sa'a ne dan bai fi minti Arba'in da shigowa office ɗin ba. Sai da Galadima ya ce ta zauna kafin ta ɗan ɗosanu a kujeran tana tunanin ta inda za ta fara ma sa bayani. Kwarjinin sa da yadda ta tsinci kan ta da fargaban ganin ta gaban Alƙali ya sa gaba ɗaya ta kasa yi ma sa ƙarya. Ta gaya mishi sata ta je yi office ɗin Ghazala ta saurari hiran su da Hajiya Saratu har ta kunna wayarta ta yi recording. Kunna ma sa audio ɗin ta yi wanda ya fara daga inda Hajiya Safara'u ke yiwa Ghazala bayanin yadda za ta yi amfani da layar da ta karɓo ma ta. Galadima a nitse ya saurari audio ɗin wanda hakan ya sa Kubra ta tsorata dan ko kaɗan ba ta ga alamar damuwa a fiskar sa ba. Bayan ya gama saurara sunan ta ya tambaya ta gaya ma sa baki na rawa. Nasiha ya fara ma ta akan illar sata wanda ya sa ta ji jikin ta yayi wani laƙwas duk abinda ya faɗa ya shigeta. Sai kuma ya karɓi wayan ya tura audio ɗin ya umurceta da ta goge na wayarta. Ba musu ta karɓi wayan ta goge. "Ba na son jin wannan maganan a wajen kowa Kubrah" Kubrah ta gyaɗa ma sa kai. Har za ta tafi ya ce ta tsaya ya karɓi account numbarta da numbar wayarta, a take ya ma ta transfer ɗin dubu ɗari. Ya ce ta ji tsoron Allah ta dena sata ta kuma nemi halal. Bayan tafiyar Kubra Galadima ya saurari audio ɗin nan ya fi sau biyar. A hankali kuma sai zargin da ya ke yi akan Ghazala su ka fara zama gaskiya. Kafin tafiyar su Las Vegas akwai ranan da ya tsinkayi Raziya na faɗawa Ghazala za ta tona ma ta asiri idan ta sake dukan ta a gidan nan. A lokacin Ghazala da ta hangoshi sai ta buge da dariya tana ɗan dafa kafaɗar Raziya tana faɗin "kin iya acting sosai" Daga baya ya samu Raziya a gefe akan wani asiri ta ke son tonawa Ghazala amma ta ce babu wai suna gwada acting scene ɗin wani film ne. Bai yarda da ita ba amma sai yai shiru da zancen. Raziya ta yi hakan ne saboda tsoratar da ita da Ghazala ta yi akan indai gaskiya ta fito har da ita za su raba hukuncin Galadima tunda ta san ya tsani ƙarya. The way Ghazalar ta tsara maganganunta ya sa Raziyar ta ji tsoron faɗawa Daddyn su gaskiya. Bai wani jima da tafiyar Kubra ba shima ya fita daga office ɗin ya wuce makarantar su Raziya. Zuwa yai wajen principal ya sa aka kira ma sa ita. Lokacin da ta fito ta ga Daddyn ta a office ɗin principal maimakon ta ji daɗi sai tsoro ya mamayeta. Daddy bai taɓa zuwa school ɗin su haka ba. Godiya yai wa principal ɗin sannan ya miƙe ya fita Raziya ta bi bayan shi ƙirjinta na dukan uku-uku. Office ɗin sa su ka wuce. Tun a mota Raziya ta tambayeshi mi ya ke faruwa, amma ya nuna ma ta ba komai akwai abinda za ta ma sa a office ɗin ne. Bayan ta zauna, ya sa aka kawo ma ta maltina mai sanyi amma ta ce ruwa kawai za ta sha. Sai da ya tabbatar ta nitsu kafin ya kira sunan ta a hankali "Fatima" Duk lokacin da ya kirata da sunan Fatima to he's in a very serious mood. "Yes Daddy" ta faɗa tana ƙyafƙyafta ido. "Zan miki wata tambaya and i want you to answer me with absolute truth. Idan kika min ƙarya Fatima zan mugun saɓa mi ki. I want to hear only the truth" Gumi ne ya fara tsatstsafo ma ta hannunta da ta dunƙule sai rawa ya ke yi. "Wani sirri ki ka sani gameda Hajiyar ku?" Raziya ta ƙwalalo ido waje lokaci guda kuma ta fara jera hiccups akai-akai. Ruwan da ke gaban ta ya ɗauka ya miƙa ma ta, ta karɓa ta sha. "Ina jin ki" "Daddy i'm sorry" ta faɗa tareda fashewa da kuka. Da farko lokacin da Raziya ta fara magana ya ɗauka maganan da zai ji makamancin na Kubra ne but it took him offguard lokacin da ta sanar da shi gameda tsoratar da Zaytoonah da su ka dinga yi har ya sa ta hauka. Tana maganar tana kuka tareda roƙon shi akan ya yafe ma ta. Ta yi haka ne saboda ba ta son Zaytoonah a lokacin. "But now i like her Daddy, i really like her. She's a good person. Ta fi Hajiya kirki" Goge ma ta hawayen fiskarta yai ya ce ta dena kuka shikenan komai ya wuce. Lokacin da ya ce ta je driver ya maida ta school cewa ta yi "Daddy please don't punish me" "Ba abinda zan miki tunda kin faɗa min gaskiya. Je ki kawai"... Ranan bai koma gida da wuri ba, yayita jujjuya abubuwa dayawa a ran sa. Abu na farko da ya zo ma sa shine ya rabu da Ghazala a take, but sai ya chanja ra'ayi yana so ya ga how far Ghazala za ta je saboda baƙin kishi ko ya ce son zuciya. He took a deadly risk, but its worth it. Lokacin da ya je gida bai nuna komai ba. A ɗakin Zaytoonah ya ke shiyasa ma ya ƙara danne ran sa dan kar ta gane akwai matsala. Washegari kuwa Ghazala ta karɓi girki. Tun kafin ya bar office a jiyan su ka yi magana da Ahmad akan how fast zai saka mi shi camera a ɗakin sa. Lokacin da Zaytoonah ke yawan maganan tana ganin Ben especially lokacin da ta yanki Raziya shine ya sa aka sa ma sa CCTV footage a gidan. But bayan Mommy ta tafi da Zaytoonah sai kawai ya cire na ɗakunan ya bar na falo, corridor, kitchen da waje. Da safe kusan ƙarfe shaɗaya su ka dawo gidan shi da Ahmad da wani abokin Ahmad ɗin bayan ya samu tabbacin Ghazala ta tafi Shagon ta. Ɗakin sa da na Ghazalar aka sawa camera, bayan sun tabbatar komai ya tafi dai-dai sannan su ka bar gidan. Da ke Zaytoonah ma ta tafi saloon dan haka ba wanda ya san abunda aka yi. Maman Tope da ke gidan kuwa ba ruwanta da gulma, da kaman Atika ce da magana ta tafi kunnen Ghazala. Lokacin da ya dawo daga office Ghazala sai wani rawan kai ta ke yi. Ta yi kwalliya sosai tana fidda ƙanshin different turaruka da ta fesa. Bayan sun gama cin abinci ya ce zai ɗan yi aiki a study room ɗin sa. Wannan ne ya ba ta daman saka layar a ƙasan pillow da ke gefen da ya ke kwanciya. Duk abinda ta ke yi yana gani a computer, hatta wajen da ta saka gashin na sa a jikin layar ya gani. Abun kaman a film. Yana tunanin ɗazu da su ke cin abinci ne ta samu daman cire gashin. Ko kaɗan bai tsorata ba dan yayi imani ba abinda zai sameshi. Tun jiya ya sa aka ma sa sadaka a wajaje da dama. Ya kira wani Malamin sa da ya ke ɗaukan karatu a wajen sa duk lokacin da ya ke Zaria ya gaya mi shi halin da ya ke ciki. Malamin ya ce kar ya damu ya sa a ran sa ba abinda zai sameshi sai da yardar Allah. Ya ce idan ya ga layar yai Bismillah ya taɓa, alkadarin jikin sa zai warware gaba ɗaya. Ghazala ta zauna zaman jiran Galadima zuciyarta na dukan tara-tara saboda abu ne da ba ta taɓa yi ba. Burinta kawai abin nan yai ma ta aiki yadda ta ke so. Bayan kaman minti talatin sai Galadima ya shigo ɗakin. "Abu Razz akwai aiki gobe fa ba za ka zo ka kwanta ba" Ya kalli agogo shaɗaya har da rabi da minti biyu. Ya ce bari ya ƙara watsa ruwa dan zafi ya ke ji. Har zai shiga banɗakin sai kuma ya juyo ya ce ta ɗauko ma sa ruwa ya manta bai sha maganin sa ba. Da ta je falon ta duba fridge sai gashi akwai fruits da lemo amma ba ruwa, wanda Galadiman ne da kan sa ya kwashe ruwan ciki. Dan haka dole ta sauka kasa babban falo kafin ta ɗauko ruwan. Bayan fitan Ghazala daga ɗakin ya je ya ɗaga filon sama sai ga layar da aka ajiye. Ba tareda tsoro ba yai Bismillah ya ɗau ka layar ya ƙare ma ta kallo kafin ya ɗau wayar sa ya ɗauka hoton layan kafin ya mayar da layar yadda ya same ta. Ya wuce banɗaki yana jinjina wannan al'amari. Bayan ya watsa ruwa sai da ya haɗo da Alwala kafin ya fito. Lokacin da ya fito Ghazala ta dawo. Ya karɓi ruwan da ta kawo ya sha magani, sannan ya ɗauko Sallaya ya tada sallah. Yai addu'ar Allah ya kare shi, 'ya'yan sa da kuma Zaytoonah daga sharrin Ghazala. Kafin ya idar Ghazala kaman ta je ta shaƙe shi tsabar haushi. Ta sani Galadima mutum ne mai yawan yin nafilfilu amma yau kan haushin sa ta ji da ya fara sallan. Lokacin da ta ga ya sa hannu yana kaɗe gefen sa kaman ƙirjinta zai fito saboda bugun da ya ke yi da ƙarfi. Gani ta ke kaman zai ce zai ɗaga filon sai kuma ta ga kaɗewar kawai yai sau uku kamar yadda Manzon Allah ya faɗakar. Sai da ta ga ya kwanta akan filon kafin ta ji hankalinta ya kwanta. Galadima baccin sa mai lafiya yai yayinda Ghazala ta yi bacci rabi da rabi. Da Asuba da ya fita masallaci ta cire layan ta kai ta ɗakinta ta ɓoye akan zuwa da safe sai ta je ta bisine. A ranan da ya mu su maganar zai raba mu su gida Ghazala ta fara gwada sa'arta akan lallai sai dai Zaytoonah ta zauna a gidanta da ke Zuba. Jin bai musa ba ya sa ta ƙara tabbatar da aikin layar da aka ba ta. Yanzu ma maganar honeymoon da ta ma sa na sati uku da ta shirya kafin Azumi bai mu sa ma ta ba ya ce duk inda ta ke so su je za su je. Abinda ta shirya ba wai honeymoon ɗin ba ne. So ta ke su je a ma ta artificial insemination. Dan da gaske ta ke yi sai ta haihu da shi, not just haihuwa but haihuwar namiji. Tunda natural way ya ƙi yiwuwa gara kawai ayi hanyar bature. Tunda ta same shi a hannu ta yi imanin idan su ka je ba zai ma ta mu su ba idan ta gaya ma sa ainihin dalilin tafiyar ta su sai dai kash... *** Lokacin da su ka iso Zaria maimakon su tafi gidan su sai Ghazala ta ga sun yi hanyar anguwar su Hajia Abu. "Abu Razz ba gida za mu fara zuwa ba ne?" "Na fi so mu fara zuwa sallaman yanzu, kinga zuwa yamma mun dawo gida sai kawai mu huta tunda gobe za mu koma" "Hakan yayi gaskiya" Yayi murmushi, irin murmushin da ke nuna cewa akwai sauran rina a kaba. Ghazala ce ta fara shiga ciki kafin daga baya aka yiwa Galadima iso a falon mijin Hajiya Abu saboda tanada baƙi a nata falon. Kusan minti shabiyar sannan Hajiya Abu ta sallami baƙinta ta taho wajen Galadima da Ghazala. Bayan sun gaisa ne Ghazalan ta ari bakin Galadima ta ce dama tafiya ce za su yi shine su ka zo yi ma ta sallama. "Tafiya kuma? Ina kenan?" " Baltimore, America" Ghazala ta faɗa tana murmushi. "Lafiya dai ko?" Hajiya ta san ba kasafai Galadima ke son fita waje ba sai dai idan ya zama dole, balle yaushe-yaushe ne ya je American duba Zaytoonah lokacin tana chan. "Lafiya Hajia" Ghazala ta faɗa dan ba ta son ƙwaƙwƙwafin matar nan. Hajiya Abu ta kalli Ghazala a takaice kafin ta mayar da kallon ta ga ƙanin na ta wanda tun tasowar sa ta ke matsayin uwa a gareshi. "Ranka shi daɗe ba ka gaya min inda maganar mu ta kwana ba?" Maganar Mubaraka ta ke nufi kuma ba shi da niyyar ƙara aure ko da kuwa Ghazala ba ta yi ma sa wannan laifin ba. Sai da ya ɗan ɗau lokaci bai ce komai ba kafin ya ce"Hajiya magana ne mai muhimmanci ya kawo ni nan" Ghazala da ke ɗan daddanna waya ta yi saurin ɗago ido ta kalleshi. Tunaninta faɗawa Hajiya Abu zai yi akan ba zai karɓin haɗin da ta ke shirin yi ma sa ba, sai kuma ta ji ya kama wani zance daban. "Idan ba ki manta ba Hajiya, ke kika kwaɗaita min auren Ghazala. Amma a yau ina so ki shaida cewa aure na da Ghazala ya ƙare, domin na saketa saki ɗaya" Ya fito da takardar da ya rubuta yau da safe ya ajiye a kan centre table. Ghazala dai jinta ta yi a wani duniya daban. Gani ma ta ke yi sarawan da kan ta ke yi ne ya tsatstsafo da ruwan da ya toshe ma ta dodon kunne shiyasa ta ke jin maganan Galadima a bai-bai. Hajiya Abu ba ta yi saurin tare shi ba saboda ta san akwai sauran magana a bakin sa. Halin sa ne magana a hankali kuma ko yanzun ma a hankalin ya ke magana. "Zan iya kauda kai a ƙarya da munafurci amma sihiri ba zan iya kauda kai ba. Matar da ta yarda da cewa wani abu ba Allah ba zai iya biya ma ta buƙata ba macen da ya kamata na raɓeta ba ne, ba macen da ta dace da gidana ba ne domin akwai barazanar cutar da iyalina a tattare da ita" Ya kalli Ghazala ya ce " mi ki ke nema dan ban miki ba? Mi kike so da ba na yi miki?" "Abu RRRRazz...? Ta faɗa da ƙyar. "Wallahil Azim da yadda ki ka riƙe min 'ya'ya na kafin na aureki haka ki ka riƙe su bayan na aureki da kin samu wani daraja na daban a wajena, darajan da Zaytoonah ba za ta samu ba amma babu tsoron Allah a lamarin ki shiyasa ki ka yi abinda ki ka ga ya dace da son zuciyar ki" Hajiya Abu was getting impatient dan haka ta ce "Yunusa mi ya ke faruwa ne?" Bai yi magana ba sai ya ɗau wayar sa ya kunna audio ɗin da ya tura a wayar Kubra. Sai da ya ƙure volume ɗin wayan sa dan maganar bai fito sosai ba. "Salallahu Alaihi wa Sallam. Ghazalatu!" "Na shiga uku, Abu Razz haɗa mu ake son yi. Wallahi ba ni ba ne" ta faɗa a ƙoƙarinta na son kare kan ta ta ko wanni hali. Tana maganar ne idonta na fitar da hawaye. Ya ɗau wayar ya binciko inda hoton ya ke ya nuna ma ta wayar "ko ba wannan ba ne layar?" "Na shiga uku ni Ghazala. Ranka shi daɗe ban san ina ka samu wannan ba. Ni na san sharrin Zaytoonah ne wannan. Hajia wallahi asirin Inyamurai ta mishi" Hajiya Abu kam ta san ɗan uwanta sarai, ta kuma yarda da shi, haka kawai ba zai zo da abunda bai tabbatar ba. " sharrin Zaytoonah ya sa ki ka dinga tsoratar da ita sai da ta fara zama tamkar mahaukaciya? sharrin Zaytoonah ya sa ki ka ce na kaita gidan ki da ke Zuba?, sharrin Zaytoonah ya sa ki ka ce na sawwaƙa ma ta?, sharrin Zaytoonah ya sa ki ka hana 'ya'yana sakewa a gidan Uban su..." Miƙewa yai tsaye dan idan ya ce zai cigaba da magana sai jinin sa ya hau. Ta maida shi mahaukaci, tana son rena ma sa hankali ne ma. Ganin ya miƙe ya sa Ghazala ta yi saurin zuwa gaban sa ta durƙusa tana kuka. "Dan Allah ka yi haƙuri, ka saurareni Dan Allah" "Za'a kai mi ki kayan ki tsohon gidan ki. Na nan Zaria za a kai miki gidan ku" "Abu Raziya Dan Allah ka yafe mini. Kar ka tona min asiri. Ciki gareni, ka san ba kyau saki idan mace na da ciki" Dariya ne ya so ƙwace ma sa amma ya dake. Lallai Ghazala na da buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa. "Idan appointment ɗin ki da Dr Thompson Russel ne ki adana shi zuwa lokacin da ki ka sake wani auren. Ni Yunus ba na wannan shashancin" Ba ta san cewa ya san komai ba, daga maganar Zaytoonah, zuwa layar da ta karɓo zuwa aikin da za a ma ta a America. Shin Galadima Aljani ne? Ya akayi ya sani? "Hajia a gaida Alhaji idan ya dawo" Galadima ya faɗa yana ƙoƙarin fita Ghazala ta yi saurin riƙe ƙafar sa tana bashi haƙuri. Juyowa yai ya ma ta wani kallo wanda ba shiri ta sake ma sa ƙafan ya fice abinsa. Hajia Abu dai aka barta da kallon drama dan ko ƙwaƙwƙwaran motsi ta kasa yi... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 73 Bismillahir Rahmanir Rahim *crazy for you* Ghazala ta rarrafa gaban Hajiya Abu tana kuka tana ba ta haƙuri. "Wallahi ba hali na ba ne Hajia, ke kin san komai..." Saukar marin da ta ji ya sa maganar da ta ke ya tsaya. "Kin bani mamaki Ghazalatu. Asiri ki ke son yiwa Yunusa saboda ke mahaukaciya ce. Ai wallahi ya min dai-dai, dan ko da bai sake ki ba ni zan sa ya sake ki. Wannan wani irin masifa ce ni Zainabu! Akan namiji? Wannan son zuciya ne kawai irin na ki" Miƙewa itama Hajiyar ta yi ta ce "ki yi maza ki bar min gida, Munafuka" Bayan fitan Hajia Abu daga falon Ghazala ta bi takardar sakin da ke kan centre table da kallo. A yadda aka naɗe takardar ta tabbatar ɗaya daga cikin memo na office ɗin sa ne. With every strength da ta ke da shi tana son ganin da gaske ne yai ma ta sakin ko kuma wani abun ne daban. Ta sani Galadima ba zai taɓa yi ma ta wasan saki ba but still 0.05% da ke nuna ma ta cewa ba saki ba ne shi ta ke so ta bi. Hannun ta na rawa ta ɗauka takardar ta warwareta. Ƙanshin turaren sa da ta shaƙa ajikin takardar shi ya sake kashe ma ta jiki. Ta yi hasashen gaskiya domin letter headed memo na office ɗin sa ne. Wanda ya ke ɗauke da tambarin Nigerian Court of Apeal. Kafin idon ta ya sauka kan rubutun da aka yi da baƙin biro sunan sa da ke jikin takardar ɓaro-ɓaro shi ya ƙara sa bugun zuciyarta ya ƙaru. *Justice Yunus Muhammad Abbas* there is pride a cikin kasancewarta matar shi. There's diginity and honour a cikin kiranta matar Honorable Justice Yunus. Akwai kwarjini a kasancewarta matar Galadiman Zazzau amma duk wannan ya watse da rubutun da bai wuce layi biyar ba sai signature da kuma date da ke ta ƙasa. Rubutun sa ya ma ta kyau, sai dai abinda aka rubuta babu kyau a cikin sa ko kaɗan. Saki ɗaya ne kamar yadda ya faɗa. Saki ɗaya za a iya kome ai. Zai iya maida ta ai, ko yanzu zai iya maidata. Abinda ta ke tunani kenan "Mai Martaba zan samu, Galadima baya jayayya da mahaifinsa, zai mayar da ni ɗaki na idan mahaifin sa ya sa shi dole" ta furta a fili. "Maryam idan Ghazalatu ta fita daga falon Alhaji ki tabbar kin share kin goge sosai kin ji" "Hajiya ba ɗazu aka gyara ba" "Za ki je ki yi abinda na ce ko sai na make ki"... Daga sama ta ke jin muryar Hajiya Abu da jikarta Maryam. Kamar tsikarar allura haka sunan Maryam ya ankarar da ita da 'yar uwarta Maryam. Tun farko da ita za ta auri Galadima, if only ba ta saka son zuciya a lamarin ta ba. "ki faɗawa Abba ya fasa haɗa auren ki da Yarima Yunus. Ina son shi, kuma shi zan aura" "Ghazala ba kya ganin son zuciyar ki yayi yawa. Ke kika ce ba kya son shi. Ni nan sai da na ce miki Yaya Zannoon yana da kirki ki amince da shi amma ki ka yi biris kika ce ba kya son shi, Alhaji Bashir ki ke so..." "Ai ban san haka ya ke ba ne, shiyasa. Kuma ma yanzu zaɓin iyaye zan bi dan ya fi Albarka" Maryam ta yi murmushi sannan ta ce "Ghazala ba ki san soyayya ba, ba haka ake soyayya ba. Soyayyar da ki ka yiwa Alhaji Bashir ta suna ne da ɗaukaka. Sannan soyayyar da ki ka yi iƙirarin kina yiwa Yarima ba komai ba ne face sha'awa. Soyayya mai tsabta ba a gina shi da waɗannan kuma..." "Ba na son wa'azi Malama Maryama. Saurayi dai ni aka fara yiwa tayin sa kuma ina son abu na yanzu, ki bar min shi" "Duk abinda Abba ya zaɓa mana ba zan bijire ma sa ba. Amma ki sani, indai rayuwar ki a kullum zai tafi wajen son zuciya ne to wallahi sai kin yi nadama Ghazala" *to wallahi sai kin yi nadama Ghazala* maganan Maryam na ƙarshe ya dinga ringing a kunnen ta. "Bakin Maryam ya kamani" ta furta a hankali Ta ƙanƙame takardar da ke hannunta, ta cigaba da zubda hawaye. *** Galadima na fita bai zame ko ina ba sai gidan sa, wanka yai ya chanja kaya kafin ya fito ya ce Dreba ya kai shi gidan su Zaytoonah. Duk da dai gaisuwar ta sirikin sa ne amma yana fata ya sa matar sa a idon sa. Ba ƙaramin kewarta yai ba. A ɓangaren Zaytoonah kuwa da su ka kai breakfast gida suna zazzaune a falo suna jiran Daddy ya fito aci abinci, kamar yadda aka ci tare jiya sai gashi ta buge da amai. Sabon turaren wuta da Mommy ta kunna ne ya sa ta wannan aman. Tun dawowanta gidan ma Mommy ta dena amfani da room freshner saboda damun Zaytoonah da ya ke yi. Bayan aman da ta yi kuwa sai abincin da su ka yi ya fita ma ta a rai ta kasa cin komai sai zallar tea marar sugar da ta sha. Ɗakin Salman ta shiga ta kwanta dan wani sanyi ma ta ke ji. Daga inda ta ke tana jin hayaniyar su a falo har kusan minti talatin kafin bacci ya tafi da ita. Bayan Auwal ya wuce office, Salman ya tura yaran waje. Humairah kuma ta shiga kitchen ta fara wanke-wanke. Salman ya ɗaga ido ya ce " Daddy, ya ce anjima kaɗan zai zo ya gaisheka" "Allah ya kawoshi lafiya" Mommy ta amsa da Amin jiki a sanyaye. Labarin da Salman ɗin ya ba su ne ya taɓa ta. Wani irin ƙaddara ke bibiyan Zaytoonah? Allah ya sa dai ƙarshen wahalarta kenan yanzu. Ba abinda za ta iya ma ta sai dai addu'a kawai. Allah ya cigaba da kareta daga sharrin Ghazala da sauran maƙiya. Lokacin da Galadima ya fara juyawa Zaytoonah baya sai da ya kira Salman ya ma sa bayani a tsanake akan abinda ke faruwa. Sannan ya ce ma sa ya dinga kiranta kullum yana kwantar ma ta da hankali. Bai involving Mommy a maganar ba ne saboda ya san mata are too emotional, balle kuma UWA. Kusan Azahar Galadima ya kira Salman ya faɗa ma sa cewa ya iso. Salman ya fita ya shigo da shi. Ba kowa a falo lokacin sai ƙaran TV da ke ta aiki. Salman ya ƙarisa ɗakin Mommy ya mu su sallama. "Daddy ya iso" ya furta sannan ya koma falon bayan Daddyn ya ce ma sa gashinan zuwa. Yunwa ne ya tada Zaytoonah daga bacci dan haka da hamma ta fito falon tana faɗin "Mommy yunwa na..." Ta yi saurin riƙe baki ganin Galadima a falon tareda Salman. Farar shadda ya saka tareda baƙar hular Zanna. Sai da su ka haɗa ido kafin ta yi saurin yin baya da gudu. Tana shiga ɗaki ta dafe ƙirjinta saboda zuciyarta da ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi. Da gaske dai sai da ya zo ɗin. But why will he come now? After all ya rabu da ni ai. Ta faɗa a ƙasan ran ta. Da sauri ta shiga duba madubi. Ganin ba ta samu ba ya sa ta ɗau waya ta shiga camera ta fara kallon fiskarta. Fiskar ya kumbura, gefen idonta ya fitar da shatin bacci. Ɗanƙwalin da ta ɗaura yayi wani gefe da shi gashinta ya fito ta gefe-gefe yayi buzu-buzu. Rabon da gashin ma ya ga gyara tun tana Abuja. "Innalillahi! Yanzu a haka ya ganni"... Bayan minti biyar Daddy ya fito falon da sallama. Tunda ya fito da Galadima ya ɗaga ido ya kalleshi ya kasa sauke idon sa. Tambayoyi da dama ne su ka bayyana a fiskarsa. Daddy ya ƙarisa ya miƙa ma sa hannu tareda faɗin "Allah ya taimaki Alƙali" haka ya ke faɗa ma sa a mafi yawan lokuta idan ya buɗewa Galadima gate zai fita lokacin yana gadi a gidan sa. Har Daddy ya zauna opposite da shi bai iya cewa komai ba. Salman da ya lura da shock ɗin da ke fiskar sa ya ce "Ranka shi daɗe ga Daddyn mu nan. Allah ya dawo mana da shi lafiya" Innalillahi ya furta a ƙasan ran sa. Sai yanzu sunan da abokinsa Alhaji Ishaq ya kira Malam Shehu ya dawo ma sa. DR TIJJANI ABUBAKAR MODIBBO and he's beloved wife's name is ZAYTOONAH TIJJANI ABUBAKAR. Ya Allah! Sai yanzu da ya ga Salman kusa da Daddy ya gano kamannin su. Lokacin da ya fara ganin Salman sai da ya yi tunani a ransa akan yana kama da wani da ya sani amma bai iya tunowa ko waye ba ne. "Alhamdulillah! Gaskiya ba abunda za mu ce sai dai mu godewa Allah. Allah mai hikima. Barka da zuwa Doctor" ya faɗa lokacin da ya ɗan nitsu. Daddy yai murmushi ya ce "Alhamdulillah ala kulli halin" Ba a jima ba Salman ya ba su waje, bayan ya kawo wa Galadiman ruwan sha. Yana shiga ɗaki ya ga Zaytoonah kwance ta ƙudundunu da bargo. "Big Sis ya jiki?" "Munafuki, kwana ɗaya Daddy yai amma har ka kira shi. Shima da ke ba shi da kunya ya wani ɗauko jiki ya zo. Ko mi zai gayawa Daddy oho?" "I'll pretend i didnt hear anything. Ina Alinah dan Baban ta na tambayarta?" "Zai tambaya ai, tunda shi ya haifa min ita" Salman ya riƙe baƙi yana faɗin "barin bar ɗakin nan kafin kunnena ya toshe" Ƙugin yunwa da cikinta ya cigaba da yi ne ya sa ta kira Humairah akan ta kawo ma ta abinci. "Ina gidan Iya fa, akwai abinci a kitchen ki shiga ki ɗauka" "Ki zo ki kawo min, ba zan iya zuwa kitchen ba" "Why?" "Daddyn Raziya na falo" "Kayya Anty" "Dan Allah ki yi sauri Airah"... Kusan awa biyu Daddy da Galadima su ka yi zaune suna hira kafin daga baya su ka wuce masallaci dan gabatar da sallar Azahar, daga nan kuma ya wuce fada saboda Mai Martaba da ke neman sa. Lokacin da Zaytoonah ta idar da sallah ta duba wayarta saboda tuntuni ya ke ta ringing. Ga mamakin ta sai ga missed calls ɗin Galadima guda biyu da kuma text ɗaya. *sleeping beauty, when i saw you, all i ...* "Anty Zaytoonah wai ki zo inji Daddy" Muryan Humairah ya katseta. Maida hankalinta ta yi kan wayar bayan ta cewa Humairah tana zuwa yanzu. *sleeping beauty, when i saw you, all i wanted to do was to KISS those sexy lips of yours. Wishing you safe trip Qurratul Ayn* Mi ya ke ɗaukan kan sa ne wai. Zai faɗi abinda ya ke so a lokacin da ya ke so. Yanzu ai ba matar sa ba ne. But wait... ba dai Daddy ne ya ce ya maida ni gidan sa ba?. Gaskiya ba zan koma ba. Ko 2 seconds bai kai ba sai ga shi ta sake maida kai tana karanta text ɗin. And as she reads it, tana jin taste ɗin bakin sa a na ta harda lashe bakin, jikin ta ya fara tsirfa saƙon sinadarin dophamine da ke triggaring pleasure a jikin Ɗan Adam. A falo ta samu Daddy da Mommy da Humairah sai Alinah da aka kwantar akan kujera. Gefen Daddyn ta zauna ta ce gani. " kin samu kin ci abinci kuwa?" "Yes Daddy" "Mijin ki ya faɗi impressive things a kan ki Adaeze. I'm proud of you" "Daddy may be Mommy ba ta gaya ma ba" ta ɗan yi shiru kafin ta ce " ni da Daddyn Raziya mun rabu, he divorced me" " 'yar ta ka wani lokacin kan ta kaman na kifi ya ke, Allah " "Mommy ni ɗin?" "Kar ki kulata, she's jealous of you ne Princess" "Ka ji da shi dai" "Kar ki damu, ni da kai na zan hukunta mi ki shi. For neglecting you, dole ya karɓi hukunci mai tsanani" Mommy ta ce "ka cigaba da biyewa ƙarya gindi. Nan gaba kaɗan za ta baka mamaki idan ta tattara ta koma wajen sa" "I'm not going back to him" Zaytoonah ta faɗa da ɗan ƙarfi. Mommy da Humairah su ka sa dariya saboda yadda Zaytoonan ta yi da baki. "Daddy ka ga Dariya su ke min" "Ki bar su Princess, duk kishi su ke da ke sun ga Daddyn ki ya dawo" Bayan ya gama rarrashinta tukunna ya gaya ma ta dalilin kiranta, dama gobe ya ke son zuwa Ringim kuma jikinta da ba daɗi ya ke tunanin ko za ta iya bin su ko za ta zauna a nan. Ai ko ƙarasa maganar bai yi ba ta ce ma sa za ta je. Da yamma da Salman ya dawo ta matse shi sai da ya gaya ma ta duk abinda ke faruwa. Daddy da Mommyn duk ba wanda ya gaya ma ta komai, sun barta a baibai ta sake shiga ruɗu. Jikinta yayi sanyi bayan Salman ya gaya ma ta abinda ya sani gameda Galadima na dalilin da ya sa ya dinga shareta. Ta san Ghazala ba ta da mutunci but ba ta taɓa tunanin za ta iya neman yi ma ta asiri ba. For what? Akan namiji. "Madam Galadima kin ji dai abinda ya faru, sauran bayanan kuma za ki ji a wajen mijin ki" "Salman wai mi na tarewa mutane ne? Can't i be safe in my husband's house, can't i be happy in my husband's house?" "Sis ki godewa Allah da asirin matar nan ya tonu. Lets say Allah ya ba ta nasara akan abinda ta shirya da shikenan yanzu sai dai a dinga wani maganan ba wannan ba. Ki ƙara godewa Allah gaskiya" Bayan tafiyar Salman sai ta ka sa samun sukuni. Baƙi da su ka zo yiwa Mommy Barka ya sa ba ta je ta samu Mommyn a falo ba. She needs motherly care now, dan har yanzu ba ta girmi hakan ba. Rayuwar aure akwai shi da ƙalubale da jarrabawa kala-kala daga Ubangiji. Ta gani a lokacin aurenta da Zuhayr gashi nan tana gani a gidan Galadima. Gara ta rayu ba aure, da ta auri mutum ta muzguna ma sa da shi da iyalinsa. Babu namijin da ya chanchanci ta saɓawa Allah saboda shi, babu abin duniyan da zai kaita gaban Boka ko Malamin tsubbu. Ba ta fata Allah ya jarrabeta da son zuciya da kwaɗayi, dan suna ɗaya daga cikin dalilan da ke sa mutane dayawa ke faɗawa halaka. Galadima ya sake tura ma ta text har sau biyu amma babu wanda ta ma sa reply. Ba ta san mi za ta faɗa ma sa ba. Ta dena jin haushin sa amma kuma ta kasa samun ƙarfin gwiwar tura ma sa reply. Abinda Salman ya gaya ma ta ya birkitata to the core, a wani ɓangare kuma tana tuhumar kan ta da miyasa ba ta yiwa Galadima uzuri ba a lokacin da komai ya shige ma ta duhu? Miyasa ta yi tunanin Galadima zai iya walaƙantata a karan kan sa?. Shin ba ta yarda da soyayyar da ya ke ma ta ba ne ko kuma dai ta ɗauka har abada rayuwar su zai tafi cikin jin daɗi ba tareda matsala ba ne. A lokacin she ought to fight for him, for herself, amma ba ta yi ba. She was too angry, too jealous to think straight. Da dare kafin ta kwanta da Mommy ta kawo ma ta Alinah sai da ta ma ta nasiha kan haƙuri da juriya a gidan miji. "Idan har ba za ki iya haƙuri ba, idan har ba za ki iya jurewa ba to ba lallai auren ki yai ƙargo ba. Ko da kuwa yayi to ba lallai ki samu ladan da ake samu na haƙuri ba. Akwai lokutan da za ki dinga ji a ran ki miyasa ma kika yi aure, miyasa ki ka auri wannan mutumin da ke cusa mi ki baƙin ciki son ran sa. Miyasa za ki ma sa biyayya bayan shi ba ya miki adalci. But then, kar ki manta da cewa daga ƙarshe ba yardar shi ki ke nema ba, daga ƙarshe ba sakawar sa ki ke so ba. Ba wai dan ya zauna da ke ke ɗaya ba, ba dan ya zama tamkar bawan ki ba. Abinda ki ke so da haƙurin ki a wannan aure shine ranan gobe, bayan babu ke a duniya, bayan rai ya fita ya bar gangan jikin ki da ke fankololo a cikin ƙasa. k Kina fatan a ranan da aka yi hisabi aka nuna miki ladan sallah da sauran ibadun ki sai Allah Maɗaukakin Sarki ya ce 'wace 'yar wace, kin auri wane ɗan wane lokacin kina duniya. A rayuwar auren ku kin yi haƙuri dayawa saboda NI, kin jure saboda NI, kin yi biyayyar aure saboda NI' sai Allah ya saka mi ki da abinda idanu ba za su iya aunawa ba, ya saka mi ki da daraja a gidan Aljannah. Kowa da tashi kalar jarrabawar Zaytoonah. Ba kuka za ki yi ba, sai dai ki dinga godewa Allah da ya ke kareki a kowanne lokaci. Ki cigaba da addu'a kawai Insha Allahu ba abinda zai sameki" Murya a sanyaye Zaytoonah ta ce "thank you Mommy" *** Washegari su ka tarkaɗa su ka wuce Ringim inda T J ya je gida ganin 'yan uwan sa. Irin farin cikin da su ka tsinci kan su a ciki ba zai misaltu ba. Kwanan su huɗu a Ringim su ka dawo Zaria, har lokacin Zaytoonah ta ƙi ɗaukan wayan Galadima dan kunyar sa ta ke ji. Ba ya gajiya da tura ma ta text every now and then, duk text ɗin da ya turo sai ta karanta ya fi sau goma. A wani rana da Mommy ta tambayeta yaushe za ta koma gidan ta cewa ta yi wai ba ta gama ganin Daddyn ta ba. Mommy ta zuba ma ta ido tunda ta ga T J ma goyon bayan Zaytoonan ya ke. Bayan kwana uku da dawowan su daga Zaria Ummi (Pendo) ta zo daga Bauchi. Zaytoonah ta fito daga kitchen kenan ta tsinkayi muryan Ummi na yiwa Mommy bayanin wani haɗi da ta kawo ma ta. "Mommy, Mommy, wannan haɗe-haɗen an kusa shiga Azumi fa" Zaytoonah ta faɗa lokacin da ta sako kai falon. Mommy ta ɗau remote ta wurga ma ta, Zaytoonah ta kauce tana dariya. "Ummi ina nawa haɗin?, anyi wa tsohuwa an manta da ni" "Ki fita a idona Zaytoonah" Mommy ta faɗa tana nunata da yatsa. " Ai sai dai ki yi haƙuri idan kin haihu sai ki zo na gyara ki. Haiwuwar Alinah ba abinda aka mi ki na gyara, gashi kuma du kin ɗauko wani cikin" "Nifa ba ni da komai, ba ni da komai, tammm" ta faɗa kamar za ta yi kuka. Ta wuce ɗaki cikin fushi. Mommy da Ummi su ka yi dariya. Shirye-shiryen Azumi ake yi dan ana batun saura kwana takwas ko bakwai ne. Har lokacin Zaytoonah ta ƙi komawa gidan ta, yanzu kam ta fara amsa wayar Galadima kuma duk hiran su ta ƙare akan jayayyar yaushe za ta koma Abuja ne, ta ce sai bayan sallah ta koma, shi kuma ya ce bai yarda ba dole ta zo kafin a fara Azumi. Kaman da wasa tun bayan dawowar su daga Ringim sai laulayi ya sa ta a gaba, zazzaɓin safe da kuma rashin cin abinci. Abincinta ya koma daga kunu, tea, romo sai ko gwate. Ba ta sanar da Galadima gameda cikin ba dan albishir ɗin da ta ke son bashi kenan ranan da za su haɗu. Bisa shawaran Likita ta yaye Alinah 'yar wata shida da sati uku. Yarinyar dama nono bai dameta ba sosai shiyasa first two days ɗin da aka yayeta ba ta wani damu ba, sai a kwana na huɗu kuma ta fara rashin lafiya har sai da su ka kaita Asibiti. Da yamma da su ka dawo su ka tarar da yaran Galadima a gidan sun kawo mu su ziyara. Sun ji daɗin ganin Zaytoonah dan ba ƙaramin missing ɗin ta su ka yi ba. A bakin Raziya ta ji wai Daddyn su ya rabu da Hajiya Ghazala wai har ma an kwashe kayan ta a gidan. Galadima bai gaya ma ta ya saki Ghazala ba shiyasa abin ya zo ma ta a bazata. Ta ɗan ji tausayinta kaɗan dan mutuwar aure ba wasa ba ne. But halin ta ne ya ja ma ta. Ba ta gama fita daga shock ɗin sakin Ghazala ba Raziya ta ba ta labarin da ya sa ta cikin ruɗu. Wai a Fada ta ji ana hiran Daddyn su zai auri Anty Mubaraka. "Dan Allah ki ce Daddy kar ya ƙara aure, ya kamata mu zauna mu kaɗan mu, and be a happy family" Murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi ta ce " Raziya kenan, ai namiji mijin mata huɗu ne. Daddyn ku yanada 'yancin cikata mata huɗu" Tana maganan ne amma zuciyarta na suka. Ita ina ruwanta idan ma mata ɗari zai aura, abu ɗaya ta sani ba za ta sake zama gida ɗaya da kowacce shegiya ba. Bayan tafiyar su Raziya tukunna ta samu damar kiran Galadima. Farkon kiransa kenan cikin kwanaki dayawa. Lokacin da ta kira shi yana hanyar sa ta dawowa daga Kogi. Ko sallamar da yai ba ta amsa ba ta fara magana muryanta a shaƙe kamar za ta yi kuka. "Congratulations Daddyn Raziya, ashe liyafa ta cigaba ka rabu da tsohuwa za ka auri budurwa. Allah ya ba da sa'a" Kafin ya ce wani abu ta riga ta kashe wayar ya sake kira ba a ɗauka ba ƙarshe ya ji numbar na ta is switched off. Yai murmushin jin daɗi. Zaytoonah na da kishi sai dai duk sanda za ta expressing kishinta to in a childish way ne, and he love that about her. Zaytoonah sai da ta gama mirgine-mirgine a kan gado kafin ta fito wajen su Mommy da ke falo suna kallo, dan idan ta cigaba da zama ita ɗaya a ɗakin zuciyarta na iya bugawa. Abinda ko lokacin auren Ghazala ba ta ji ba shi take ji yanzu. Ba ta san waye Mubaraka ba amma jin ita ɗin budurwace ba bazawara ba makes her feel threaten. What if idan ya aurota itama ta zo da na ta salon iskancin, what if Galadima ya ga budurwa ya koma ja baya da ita. Daddy baya nan ya tafi gidan Baba Tsoho. Kusan yanzu a wajen Alhaji Ilyasu kaɗai ya ke zuwa hira, ko bai je ba za ka ga ya aiko a kira shi ko kuma ya kirashi a waya. Alhaji tsufan ya fara shigan sa dan wani lokaci bayan sun sha hira Daddy ya dawo gida sai ka ji da yamma an sake aikowa wai Daddy ya je, idan ya je kuwa sai Alhajin ya ce ai ya jima ba su haɗu ba ne shiyasa ya kirashi. Daddy yai murmushi ya ce idan aka ce ka tsufa ka ce har yanzu ba ka tsufa ba da sauran ka. Su yi ta tsokalar juna. "Ta yi bacci ko?" Mommy ta katse ma ta tunani "Yes Mommy. Ni kam Mommy sai da na ji kamar na ba ta nono ɗazu, ta bani tausayi sosai" "Ba daɗi kam, a haka dai za ki jure har ta saba" Sai da Mommyn ta kalleta da kyau kafin ta ce "Zaytoonah kuka ki ka yi?" "A'a" ta faɗa tana murza ido "Da kunnen ki kin ji abinda Likita ya faɗa miki. Ke ba yarinya ba ce" Tana so ta faɗa ma ta maganar da ta ji na ƙarin auren da Galadima zai yi ko za ta ji sauƙi a ranta amma ta san halin Mommy, tana kawo maganar za ta fara ma ta nasiha. But it hurts, it damn fucking hurts ace mijin ka zai ƙara aure. Maganar tafiya Umara da Mommyn ta yi ne ya ɗan ɗauke ma ta hankali. Mommy ta biya mu su tafiya Umara ita da Daddy su biyu. Life long wishes ɗin su ne da bai cika ba saboda dalilai ma su yawa to amma dama aikin Umara da Hajji sai wanda Allah ya kira, sai wanda Allah ya ba wa iko... A ɓangaren Daddy kuwa bayan sun fito daga masallaci shi da 'yan biyu da Junior su ka raka Alhaji Iliyasu gida. A veranda inda ya ke yawan zama ya huta a nan su ka zazzauna a kan ƙatuwar darduma sai shi Alhajin da ya zauna akan kujerar sa da ke tsakiya. Bayan su Daddy akwai Dreban Alhajin da kuma wani maƙocin su aka zauna ana hira. Watan Azumi da aka dosa shi su ke tattaunawa akai. Magana ɗaya da Alhajin yai ya sa jikin su yai sanyi. "Idan ta zo nan da kwana bakwai mai rai kaɗai zai gan ta" "Hakane Alhaji" Dreban sa Malam Muhammadu ya faɗa yana jinjina kai. Wajen yai shiru saboda jikin su da yai sanyi. 'Yan biyu da su ka fara faɗa a gefe ne ya ɗauke shirun da su ke ciki. Daddy na mu su magana ma ba su kula shi ba. Sai da Malam Muhammadu ya daka mu su tsawa kafin su ka nitsu. Kusan ƙarfe tara da rabi saura kaɗan Daddy ya ɗaga ido dan ya cewa Alhajin zai wuce gida sai ya ga idon Alhaji a rufe kamar mai bacci. Ya kalli Malam Muhammadu ya ce "kaman Alhaji yayi bacci, mu zamu wuce" "Sai da safe Malam Tijjani" "Allah ya bamu alkhairi" Daddy ya miƙe daga kan darduman yana cewa 'yan biyu su tashi su tafi. Ko taku bakwai bai yi ba ya ji muryan Alhaji Ɗayyabu ya kira sunan sa. "Malam Tijjani" ya juya a hankali jikin sa a sanyaye. Ganin su a tsatstsaye ya sa shi komawa baya da sauri. "Inaga Alhaji fa rai yayi halin sa" Malam Muhammadun ya faɗa wanda tashin Daddy a wajen ne ya sa shi duba yanayin zaman da Alhaji yai a kan kujera. Ko da shima Daddy ya duba shi sai ya furta Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun a fili... *** Mutuwar Alhaji Iliyasu Mai Auduga ya sa Zaytoonah ta ɗauke hankalinta daga kan maganar auren Galadima. Ya turo ma ta saƙon ta'aziya tunda ba ta ɗaukar wayar sa yanzu. A ranan Jummu'a da aka yi sadakar uku ne kuma aka ɗaura auren Mubaraka da Angonta Yusuf. Wanda Mai Martaba ne ya wakilci Ango shi kuma Galadima ya zama Waliyyin Amarya. Hajia Ajwa kamar ta yi hauka saboda abubuwanta da su ka fara kwaɓewa. Mijinta Turaki da baya iya yi ma ta mu su shine ya ke iƙirarin sai dai ta mutu amma 'yar sa Mubaraka Yusuf za ta aura. Wai ta godewa Allah ma da Iyayen Yusuf ɗin su ka yafe ma ta abinda ta aikata da yanzun tana jail bisa laifin kidnapping ɗin Yusuf da ta sa aka yi na tsawon shekaru huɗu. "Ajwa wani irin zuciya gareki. Ki sa a jefa ɗan mutane a prison yana shan wahala ba tareda yayi laifin komai ba, har shekaru huɗu" "Sai me idan na sa an rufe shi, ta ya zan bari Mubaraka ta auri ɗan Talaka. Ba zai yiwu ba. Dama ban sa an kashe shi ba ko an haukatar da shi ka godewa Allah" Turaki bai ce da ita komai ba dan maganar ba ta yanzu ba ne, ya wuce ya barta a falo tana banbamin bala'i ita kaɗai. Lokacin da 'yan ɗaurin aure su ka dawo daga Fada ne labari ya riski Hajiya Ajwa akan ba wai auren 'yarta Mubaraka kawai aka ɗaura ba harda auren Turaki da tsohuwar matar sa ta farko Hajiya Fatima. Hajiya Ajwa ta daka tsalle haɗeda saka ihuu kamar wata zararriya. Ta shige ɗakinta da sauri ta danna key sannan ta ɗau waya ta fara kiran Bokanta. Tana fara koro bayani ya katseta da cewa ba shi ya ma ta aiki akan Uwargidan ta bai san komai gameda aikin ba. Ta katse kiran da sauri ta shiga nemo wani number daban, shima still ya ce ba shi ya ma ta aikin ba. Zama ta yi a bakin gado gumi na tsatstsafo ma ta lokacin da ta tuno wanda ya ma ta aiki akan Hajiya Fatima, wani Bokanta ne a Cameroon shekaru shatakwas da su ka wuce kenan, kuma ya jima da mutuwa. Aikin da aka yiwa Bilki lokaci guda ya cita Turaki ya saketa, ita kuma Hajiya Fatima na ta bai ci ba sai da aka haɗa ta da wani baƙin mutum sannan aikin da ya ma ta ya ci. An fara tura ma ta ciwo ne lokacin da ciwo ya cita yawan ibadarta ya ragu tukunna aka samu daman shiga tsakanin ta da Turaki. Kashedin mutumin wanda munin fiskarsa da warin jikin sa ya dawo ma ta yanzu ta fara ji yana yawo a ƙwaƙwalwar ta. "Idan ta fita daga gidan nan duk ranan da ta sake taka gidan da sunan matar sa komi kika shuka za ki girba. Ciwon da ki ka sa ma ta kema sai kin yi shi, bayan nan duk abinda ya sake biyowa baya kuma ki kuka da kan ki" "Ai ba za ma ta dawo ba har abada" amsarta kenan a lokacin Abinda ba ta sani ba shine akwai ƙaddaran da ya fi ƙarfin Boka ko Malami. Allah shi ke sarrafa lamurra, kuma shine Kun Fa Ya Kun. Wato ɗaya ɓangaren gidan da aka gyara ta ke tunanin ɗan sa na biyu da zai yi aure ya ke gyarawa ashe na Hajiya Fatima ne. "Ba zai yiwu ba, ba zai yiwu ba" ta faɗa a firgice kamar wata zararriya... *** Da yamma bayan sun dawo daga gidan rasuwa ita da Mommy text ɗin Galadima ya shigo. *ki shirya gobe zan zo na ɗauke ki* Wani text ɗin ya sake shigowa *ki duba whatsapp ɗin ki za ki ga hoton Amarya tah* Sai da ta yi kamar ba za ta duba ba amma kuma wani zuciyar ya ingizata. Bari ta ga wannan Amarya da ya ke ta ɗoki akan ta. Lokacin da ta clicking kan hoton da ya turo ƙirjinta sai dukan uku-uku ya ke yi. Sai dai ganin hoton ta ne ya sa ta zaro ido waje. Hoton ta ne ranan da za a kaita gidan Galadima. "Ya kika gan ta, tana da kyau kuwa?" Saƙon shi ya shigo bayan ta duba hoton. Sai da ta yi murmushi kafin ta tura ma sa reply. "Ni bangan ta ba, ina ta ke?" Yana zaune wajen da ake reception ɗin aure amma hankalin sa na kan wayar sa, sai murmushi kawai ya ke yi. Wani abokin sa da ke gefe ya tsokale shi ko dai nan kusa za su sha biki. Galadima yai murmushi kawai ba tareda ya ɗago ba ya cigaba da typing saƙon da zai turawa Zaytoonah. Ya sake tura ma ta wani hoton daban, wannan su biyu ne su ka yi hoton. Selfie ne da ta mu su wata safiyar ranan sallah bayan ya gama shiryawa za su fita masallaci. "Ya ki ka ga, na dace da ita kuwa?" Zaytoonah ta rungume wayar a ƙirjinta tana dariya. Galadima akwai iya zura mutum a rijiya. "Kin yi shiru" "Ko kina kishin ta fi ki kyau ne?" Ya sake tura ma ta. "Kai ba!!! Tamm" ta tura reply haɗe da emoji na fushi. "Ni Yunus ɗan Muhammad, mi na yi?" Ya tura da emoji na zare ido. "Ka sani a layi, ka barni ina ta hauka akan ka ni ɗaya ko" "Ba ke kaɗai ki ke haukan ba, i'm crazy for you too" Goge ido ta yi da sauri ta sake karanta saƙon da ya turo a karo na biyu. Did he just say he's crazy for her? "Yadda ki ka wahalar da ni, haka za ki zo ki karɓi hukunci mai tsauri a wajena. And dont expect mercy Baby" Saƙon sa na ƙarshe kenan kafin ya sauka. Zaytoonah ta rufe fiska tana dariya. Gaskiyar Mommy da ta ce ma ta wani lokaci ƙwaƙwalwarta kamar na kifi ne. Daga jin maganar aure har ta hau dokin kishi. But ya za ta yi, she's just so crazy inlove witn this old man... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 74 Bismillahir Rahmanir Rahim *a second chance* Tana tararradin ya za ta yi ta gayawa Mommy akan za ta koma gidan ta gobe, duba da yadda ta ringa cika baki akan ba za ta koma ba kwanan baya. Allah da ya so wanketa sai ya sa Mommyn da kan ta da suna cin abincin dare ta ce ta shirya gobe ko jibi ta kuma gidan ta dan nan da kwana huɗu jirgin su zai tashi. "Ki dena korar min 'ya Dan Allah" Daddy ya faɗa yana kallon Mommy "Da wai nufinka ta cigaba da zama a nan ne?" "Kwantar da hankalin ki Hajiya, Mijinta zai zo ya ɗauketa gobe Insha Allahu" Zaytoonah ta rufe ido da hannunta. Salman ya ce "aga aga, aga waye ya ce ba zai koma gidan..." "Salman" "Soryy Daddy" ya faɗa yana ƙunshe dariyar sa. "To ai gaskiya ya faɗa. A nan dai wata ta dinga cika mana baki ita ba za ta koma gidan ta ba" Dariyan da Salman ke ƙunshewa ne ta fito, Mommy ma ta fashe da dariya. Junior da Humairah ma sai kawai su ka fara dariyan. 'Yan biyu ba sa wajen suna gidan rasuwa Muhsina da su ka zo jiya ne ta hana su tafiya shiyasa su ka kwana a wajen ta. Zaytoonah ta miƙe da sauri ta yi ɗaki da gudu. Daddy ma sai a sannan ya fara na shi dariyan yana yi yana faɗin wai su bar yiwa Princess ɗin sa dariya fa. Zaytoonah kunya ya sa ta ka sa fitowa. Duk da ta ji haushin dariyan da su ka ma ta amma kuma hakan bai hanata jin daɗin kulawar da ta samu daga wajen iyayen ta da 'yan uwanta ba, musamman Salman. Salman ya wuce ƙani a wajenta. He's more of a best friend to her. Har yau idan ka cire Farha da Muhsina to ba ta da wani abokin shawari da ya wuce Mommy da Salman. The kind of childhood ɗin da ta samu ya sa ba ta da tsayayyun ƙawaye. 'Yan Makarantar su na Primary da na Secondary ko na Islamiyya duk zumuncin ya buge a iya chatting a whatsapp ne, shima dalilin buɗe groups na excos ya sa ma ta tuna da wasun. Wasu daga baya sun yi ta ƙoƙarin manne ma ta jin cewa tana auren Galadima. Wasu kuwa hassada ya sa sun ka sa kulata ko da a group ɗin ne. Sunan ta a group Mrs Galadima. Wata rana wata 'yar ajin su da su ka yi JSS 1 zuwa SS 1 tare ta ga sunan sai ta ke tambayar wai waye Mrs Galadiman nan ne. 'Yan neman tsokala kuwa tuni aka samu wata ta turo hoto lokacin su na JSS 3, ga su nan 'yan ɗagwas-ɗagwas, ta tsakiyar cikin su kuma Zaytoonah da ta fi kowa jiki ta haɗe rai saboda ba ta so aka sakata ɗaukan hoton dole. Wacce ta tura hoton ta highlighing fiskar Zaytoonah a ƙasa ta rubuta ga Mrs Galadima nan. Wacce ta yi tambayar ta turo da sticker ɗin dariya tana faɗin wai dama Antyn aji ne Mrs Galadima. Wata kuma ta ce tukunna Galadiman suna ta ke aure ko Galadiman gaskiya na sarauta. Caraf wata da ke son ɗaukan gulman to the next level ta yi saurin turo hoton Zaytoonah da Galadima, dukkan su tsaye, Zaytoonah ta ɗan kwanto da kanta a kafaɗar sa, shi yana sanye da Alkyabba kalar baƙi da aikin fari ita kuma Lifaya ta saka kalar baby pink. "Ga ta nan kun ganta, matar Galadiman Zaria ce" Ma su Hmmm na yi, ma su sa Albarka na yi, ma su cewa bai kamata ta turo hoton group ba na yi, ma su mamakin chanjawar Zaytoonah daga Antyn Aji, Buskuɗa, Maman Bola... zuwa classy and elegant lady kamar wannan su ma na yi. But one thing is for sure. Allah ya riga ya ɗaga Zaytoonah. Ko su ma ta murna ko su yi baƙin ciki ta riga ta mu su fintinkau. It doesnt matter ta ina ka fara rayuwar ka, it doesnt matter ya rayuwar ka ta kasance a baya. It doesnt matter ko kai ne ka fi kowa kyau ko muni a cikin ƙawaye ko 'yan uwan ka, it doesnt matter ko ke ce jaka ko wawuyar cikin sa'annin ki. Lokaci ɗaya idan Allah ya ɗaga darajar ka duk wani abu a baya ya zama tarihi. Ya wuce har abada kenan. Bayan an gama gulma a group wasu su ka koma gefe suna bawa Zaytoonah haƙuri. Wasu kuma na neman shiga jikin ta ana so ayi ƙawancen da ba a yi ba a baya. Zaytoonah da ta zo ta ga chats ɗin ba ta tanka mu su ba, ba ta da lokacin tsaya biyewa wannan silly chats ɗin. Washegari da safe Zaytoonah ta zari jiki akan za ta je gidan Iya, dan kunyan ta gayawa Mommy za ta je saloon ta ke kar ta dinga tsokanar ta irin na jiya. Ita da Humairah su ka fita, su ka je aka ma ta gyaran kai sannan aka ma ta ƙananun kitso. Humairah ta ce ta bari a ma ta Lalle bayan an ma ta pedicure da manicure. Lallen ba mai yawa ba ne amma ya haska ma ta hannu da ƙafar ta. Lokacin da su ka koma gida da ta ga Mommy sai ta haɗe rai dan kar ma ta tambayeta ina su ka je su ka daɗe. Mommyn ma sai ta manna ma ta hauka ta shareta ba ta ce komai ba. Bayan sallar Isha Daddy ya kirata ɗakin su. Mommy na haɗa kayan su, Daddy ya ce ta ba su waje. "Ikon Allah. Ko yau za a kaita ɗakinta na farko albarka" "Tunda Allah bai bani dama ba wancan lokacin, zan yi amfani da wannan na yiwa Princess nasihar da Uba ya kamata yai wa 'yar sa a lokacin da ya aurar da ita" "Hmmm, Allah ya ba da sa'a Daddyn Zaytoonah" Bayan fitan Mommy Daddy yai Bismillah sannan ya karanta suratul Fatiha tareda yiwa Annabi salati. "Adaeze, i'm proud of you. Ba ki san irin daɗin da na ji ba lokacin da Mijin ki yai ta faɗa min kyawawan halayyan ki. Na ji daɗi sosai, na san duk abinda ki ka zama a yau yanada nasaba da irin tarbiyyan da Mommyn ki ta mi ki. Kinga yadda Mommy ta riƙe gidan nan ita kaɗai lokacin da bana nan, ina so ki riƙe gidan mijin ki fiye da haka. Irin tarbiyyan da aka miki shi na ke so ki yiwa 'ya'yan Mijin ki and even more, ki riƙe 'ya'yan mijin ki fiye da yadda za ki riƙe Alinah da twins ɗin ki. Ki rage fushi Zaytoonah, ki cigaba da haƙuri and most importantly addu'a Zaytoonah. Ki riƙe addu'a sosai. Na san Allah ya buɗewa mijin ki sannan kema Allah ya baki dukiya. Ka da ki taɓa bari wannan ya ruɗa ki har ya mantar da ke ibada da addu'a. Duk wannan ƙyale-ƙyalen a duniya kawai ya tsaya, ranan da za a saka ki a kabari waɗannan abubuwa ba za su bi ki ba, ibadar ki da kyawawan halayen ki su ne za su biki cikin kabarin ki. Ki duba tsohon mijin ki Allah ya jiƙan rai. Duk abinda ya tara a duniya lokacin da ciwo ya sameshi ba abinda su ka ma sa, lokacin da aka cusa shi cikin kabarin sa babu ko abu ɗaya da aka haɗa ma sa da shi. Haka ya tafi ya bar komai a nan duniya. Zaytoonah idan har duniyan nan ba matabbata ba ce, ina roƙon ki da ki dinga tunawa da mutuwar ki, ina roƙon ki da ki dinga ƙoƙarin kusanta kan ki ga Ubangijin ki. Hakan zai sa Shaiɗan ba zai taɓa samun galaba a kan ki ba. Idan abu ya shige miki duhu a gidan Mijin ki ba kuka za ki yi ba, ba fushi za ki yi ba, ko ki dinga yiwa mijin ki rashin kunya. Alwala za ki yi, ki yi sallah ki gayawa Allah matsalolin ki. Idan zuciyar ki ta cunkushe ki ka rasa jin daɗi, ki ka rasa samun sukuni, ki ka rasa mafita kinga wannan" Ta ɗago idonta da tuni su ka cika da hawaye ta kalli Daddyn ta. Ƙur'ani ne a hannun sa. Daddy ya miƙa ma ta ƙur'anin ya ce "ki dinga karanta shi safe da yamma, ki dinga karanta shi a lokacin da ki ke cikin matsala, ki dinga karanta shi a lokacin da ku ka samu saɓani da mijin ki. A lokacin da mijin ki ya ɓata miki rai ki karanta shi. Ki karanta shi a lokutan da kike cikin farinciki, ki kiyaye raya ranakun farincikin ki da abubuwan da ba su da amfani. Idan kina farin ciki ki tuna Allah, idan kina cikin ƙunci ki tuna Allah wannan zai sama miki matsayi a wajen Allahu. Daga ƙarshe ina so ki sani cewa ƙofa ta a buɗe ta ke gareki, idan abu ya shige miki duhu kina buƙatar shawara ko ƙarin fahimta ina tare da ke. Ki sani kasancewar ki matar Galadima bai yanke cewa ni ɗin mahaifin ki ba ne. Kada ki manta cewa you'll always be Zaytoonah Tijjani Abubakar. ba za a kiraki da sunan wani ba sai sunana ko da kuwa ba na raye. Just know that idan ina raye i'll always be there for you my princess"... Ƙarfe tara da minti shida kiran Galadima ya shigo wayarta. Humairah da ke gefe ta miƙa ma ta wayar. Zaytoonah ta karɓa ta sa a kunne. "Ranki shi daɗe na iso" Muryanta ƙasa-ƙasa ta ce " ka shigo Daddy na son ganin ka" "Duk yadda ki ka ce Gimbiya. Gani nan zuwa" Minti biyu bai cika ba ya shigo, inda ya samu Daddy a falo. Bayan sun gaisa ya cewa Junior da ke zaune gefen sa akan ya je ya kira ma sa Zaytoonah. Ko da junior ya faɗi saƙo ya tafi kasa miƙewa ta yi sai da Humairah ta yi ta ba ta baki kafin ta tashi da ƙyar. Humairan ta raka ta falon kafin ta juya ta koma ɗaki bayan sun gaisa da Galadima. Duk yadda Galadima ya so ya iya haƙurin rashin kallon Zaytoonah bai iya ba, lokacin da ta shigo da sallama da ya ji muryanta ɗagowa yai ya zuba ma ta na mujiya har sai da ta samu waje ta zauna gefen Daddy kafin ya iya sauke idon sa da sauri saboda lura da yai da idon Daddy akan sa ya ke. Addu'a Daddy ya mu su sannan ya damƙawa Galadima amanar 'yar sa. "Ka san dai Princess ce a wajena dan haka ka kula min da ita da kyau" Galadima ya ce Insha Allahu. Humairah, Junior da Daddy ne su ka raka Zaytoonah wajen Mota. Mommy kam ƙin fitowa ta yi tun bayan da su ka gaisa da Galadima. Suna barin anguwar Zaytoonah ta saka kuka. Galadima ya jawota jikin sa yana lallashi. Bai ji haushin kukan da ta ke ba dan ya san rabuwa da Mahaifinta ne ya jawo haka. Duk da dai ba su da nisa amma ba za ta sake zama da shi kamar da ba, ganin sa ma kuma ya zama sai lokaci zuwa lokaci. Kafin su ƙarisa gidan ta dena kuka, ta dai yi lamo a jikinsa tana shaƙan daddaɗan turaren sa. It was as if yau ta fara jin ƙanshin, ya ma ta daɗi sosai. Koda su ka isa gidan kai tsaye falon sa su ka wuce. Sai a lokacin Galadima ya sami damar rungume abar sa da kyau. Itama ta lafe jikin sa tanajin wani sabon son shi na shigar ta. "Allah ya miki albarka Zaytoon" Ta amsa da Amin. Sun jima tsaye kafin daga baya Zaytoonah ta janye jiki ta tambayeshi mi za ta dafa ma sa amma ya ce ba yau ba Baba Nafi ta riga ta mu su girki amma bai ci ba dan yana jiran ta zo ta ba shi a baki. Da suka fara cin abinci ne ya ce ma ta "kinga Mijin ki hankalin ki ya kwanta, ina kuma aka bar min 'ya?" "Na sayar da ita" "Lallai za ki haifi wata yanzu-yanzun nan kenan" Zaytoonah ta yi murmushi. Bayan sun ci abinci ba ta yarda sun kwanta ba sai da ya gaya ma ta duk abinda Ghazala ta yi, ya nuna ma ta evidence ɗin da ya tara akan ta. Lokacin da ta saurari audio ɗin sai da ta yi hawaye. Nasihar Daddy ne ya ƙara faɗo ma ta a rai. "Son zuciya da kwaɗayi su na kai mutum ga halaka, Zaytoonah ki guji son zuciya. Ke musulma ce, kin san Allah ya bawa namiji damar auren mata huɗu. Kar ki taɓa bari maganar kishiya ya sa ki saɓawa Allah" Tana son Galadima ya zama na ta shi kaɗai as if kasancewar sa ita kaɗai a wajen sa shine zai ba ta guaranteed happiness. Wannan shine kuskuren Ghazala na farko. *** "Muhsinah akwai baƙo a falon Daddyn ku, ki kai ma sa abinci Dan Allah" "Mommy an haɗa abincin ne?" "E, ɗauka kawai za ki yi a kitchen" Yau su ka baro family house su ka dawo gidan su bayan anyi sadakar bakwai ɗin Alhaji Ilyasu. Kitchen ta wuce ta ɗauko abincin da aka jera akan tray ta wuce da shi falon Daddyn su. Ga mamakin ta sai ta ga Daddy ne kawai a falon yana waya. Ta ajiye tray ɗin a ƙaramin dinning area da ke falon sannan ta ƙarasa wajen Daddyn tana jira ya gama waya dan dai baƙo aka ce ita kuma ba ta ga kowa ba. Sai da ya gama wayar tukunna ya kalleta ya ce "Muhsinah zauna mana" Ta zauna tana faɗin "Daddy baƙon bai iso ba ne?" "Ya je sallah, zai shigo yanzu" "Ok, barin wuce ciki, zan cirewa su Sadiq kayan baccin su" "Muhsinah" Bugun ƙirjinta ya ƙaru. Indai Daddy ya kirata da sigar jan hankali to maganar AbdulHameed zai ma ta. "Yes, Daddy" "Kafin Alhaji ya rasu, ya nuna min rashin dacewar zaman da ki ke a gida da aure a kan ki" Ta san da cewa har yau AbdulHamid bai saketa ba, amma kuma itama har yau ɗin ba ta ganin za ta iya komawa gidan shi. "Muhsinah, na kira AbdulHameed ne saboda ku yi sulhu tsakanin ku. Idan hakan bai yiwu ba, na ce ma sa zai ajiye min takardar ki kafin ya tafi yau. Idan Allah ya sa kika gama idda sai ki fito da wanda ki ke so a miki aure" "Daddy..." ta faɗa kaman za ta yi kuka "Ke ba yarinya ba ce Muhsinah. Idan har iya tsawon lokacin nan ba ki iya yafewa AbdulHameed ba inaga gara kawai kowa yai hanyar sa ki dena ma sa wasa da aure a kai. A matsayina na mahaifin ki zan baki shawaran ki koma gidan mijin ki, ki koma ga 'ya'yan ki. Amma idan kin zaɓi sake sabon rayuwa a wani gidan daban wannan ba matsala ba ne, Fatana a gareki shine Allah ya sa albarka a duk inda za ki je" Fashewa ta yi da kuka. A da duk lokacin da AbdulHameed ya kirata ba abinda ta ke gaya ma sa illa ya saketa, wannan ne ma ya sa daga baya ya dena kiranta sai dai kawai ya tura ma ta saƙo. Yanzu da Daddy yai maganar saki kuma sai ta ji wani abu ya daki ranta. AbdulHameed ne yai sallama ya shigo falon. Ƙananun kaya ne ajikin sa, light blue shirt da kuma blue jeans sun ma sa kyau sosai. "Ka dawo" "E" ya faɗa hankalin sa na kan Muhsinah da ke kuka. "Allah ya karɓi ibada" AbdulHameed ya amsa da Amin. Daddyn Muhsinah ya miƙe ya bar mu su falon. AbdulHameed ya ƙarisa gaban Muhsinah ya saka gwiwon sa ƙasa. Hannun ta biyu da ya kamo ne ya sa ta ɗan tsagaita kukan ta zuba ma sa ido tana zubda hawaye. "Muhsinah, ba zan ce ki dawo gareni ba, ba zan ce ki yafe min ba, ba zan ce ki manta da abinda ya faru ba. Abu biyu kawai zan faɗa miki Muhsinah" Ya ja dogon numfashi kafin ya cigaba "Abu na farko shine, na yi nadama. ina neman gafara kullum, kuma ina ƙoƙarin nisanta kaina daga abinda zai kai ni ga faɗawa sharrin zina. Na biyu, shine, ina son ki Muhsinah, Wallahi ina son ki har yau, kuma zan so ki har gobe. Ban faɗa sharrin zina ba dan bana son ki ko kuma dan kin gaza biya min buƙata ta, sai dai tarko ne da sheɗan ya ɗana min ni kuma son zuciya ya sa na faɗa ciki. Wannan shine abinda zan iya gaya miki. Na san Daddy ya gaya mi ki sharaɗin sa, ba zan tsane ki ba idan har kin zaɓi rabuwa da ni, dan na san i don't deserve you anymore. Kafin ki faɗi hukuncin da ki ka yanke, please ki bari na ci abinci tukunna, yunwa na ke ji, ban samu na sha ruwa ba tun ɗazu" Hawayen da ke ƙoƙarin zubo ma sa yai saurin gogewa tareda miƙewa ya ce " ki turomin su Sadiq dan Allah, i miss them" Kasa ƙwaƙwaran motsi ta yi tunda ya tashi, tana gani ya koma wajen dinning ya zauna. Ba za ta ce babu soyayyar AbdulHameed a ranta ba. Ba za ta ce ba ta yi kewar mijin ta ba. Ba za ta ce ba ta jin haushin sa ba, ba za ta ce ta yafe ma sa ba, ba za kuma ta ce za ta koma gidan sa ba. But Zaytoonah was right. All this while wahala kawai ta ke bawa kan ta. The truth is, she yearn for him. "Muhsinah kina bawa kan ki wahala ne fa. You still love him and you miss him, this is the truth. Abinda ya miki ba zai taɓa chanjawa ba, ba zai zamar da soyayyar da ki ke ma sa ƙiyayya ba, za dai ki yi ta cewa ran ki kin tsane shi, but zuciyar ki ba za ta karɓi hakan ba. Shin ba kya so ki koma gareshi ki cigaba da yi mi shi addu'a har Allah ya shiryar da shi gaba ɗaya, ki samu lada a wajen Allah. Kina tunanin akwai perfect namiji ko perfect aure yanzu a doron ƙasa?. You have to work with that imperfect marriage ki moulding na shi har sai ya zama miki yadda ki ke so may be not perfectly amma idan har akwai kwanciyar hankali a ciki shikenan" "Wani kwanciyar hankali ne ga auren mazinaci?" "Muhsinah kin fi kowa sanin mijin ki, kuma na san za ki ba da shaidar ya fara wannan abin ne lokacin da ba kwa tare kina Nigeria yana chan America. Ba wanda ya fi ƙarfin faɗawa tarkon Shaiɗan, i'm sure AbdulHameed yayi nadama yanzu" "Ko da zan koma ba zai zama dan karan kaina ba Zaytoonah" "Muhsinah ina so ki yi wani abu ɗaya. Idan har za ki koma gidan sa, to ki koma saboda kin shirya zama da mijin ki a yadda ya ke da raunin sa. Ka da ki koma saboda iyayen ki ko 'ya'yan ki. Saboda idan har zaman su za ki yi, har abada ba za ki sake samun farin ciki a auren ba. Go back because you wanted to embrace your husband's flaws and do your best to change him for the better. Ina son ki da AbdulHameed Muhsinah. Look at you, duk zaman ki a Americah ba abinda ki ka ƙara sai rama da koɗewa" "A aurena da Galadima na koyi abu ɗaya. If a man love and respect you then he's worth dying for. Tun kafin na fara son Galadima i know that he really respect me. Ki amsa wannan tambaya, truthfully banda son zuciya. Do you think a rayuwar auren ku, Abdulhameed loves and respect you?" "Ikon Allah, Matar Galadima yaushe ki ka zama marriage counselor. The last time i remember cewa ki ka yi ba za ki sake komawa gidan sa ba" "Lokacin da na ke da ƙarancin tunani kenan, yanzu kam mutu ka raba Insha Allah ni da Sayyadi na" ta faɗa tana fari da ido. Muhsinah ta sa dariya. Hiran da su ka yi kenan yau da Zaytoonah ta zo yi ma ta sallama akan za ta koma gidan Galadima, kuma gobe za su wuce Abuja. May be itama lokaci yayi da za ta yafe wa AbdulHameed ta bashi chance na gyara kuskuren sa. Idan za ta amsa tambayar Zaytoonah to tabbas za ta ce Yes AbdulHameed love and respect her. Sai da ta gama jujjuya komai a ranta kafin ta share hawayen ta ta je wajen dinning ɗin. Kankana da Ayaba kawai ya ci bai buɗe abincin ba balle ya taɓa. "Sannu da shan ruwa" ta faɗa da dasashshiyar murya "Na gode" Buɗe food warmer ɗin ta yi ta fara ƙoƙarin zuba ma sa abinci. Tana yi kuma hawayen da ta yi ƙoƙarin tsayarwa ɗazu su ka fara saukowa. She missed cooking for him, she missed feeding him. She missed lokutan da su ke shan ruwa tare a lokacin Azumi. "Muhsinah" ya kirata a hankali tareda riƙe hannun ta ɗaya. Fashewa ta yi da kuka, hakan ya sa shi saurin miƙewa ya rungumeta. "I'm sorry for everything, i'm sorry for hurting you. I'm sorry for cheating on you. I'm very sorry Baby" abinda ya ke ta faɗa kenan lokacin da ya ke ƙara ƙanƙame ta a jikin sa. Sun jima a haka, dan tun tana kukan har ta zo ta yi shiru ta lafe jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Yaran da su ka shigo falon suna kiran Abba, Abba, shi ya sa Muhsinah ta janye jikin ta daga na shi. Bar mu su wajen ta yi dan ya samu ya gana da 'ya'yan sa da kyau, duk da a wajen sa ya so a ce ta zauna ya ci abincin a gaban ta. Kafin ya tafi da Daddy ya tambayeta abinda ta yanke cewa ta yi za ta koma gidan AbdulHameed. Ya haɗa su ya mu su nasiha. Bayan AbdulHameed ya tafi ne Muhsinah ta samu daman tura ma sa text. *na amince zan koma gidan ka, but kar ka ɗauka komai zai koma dai-dai lokaci guda. I need time to heal* Kusan minti bakwai sannan reply ɗin sa ya shigo *na gode Baby, zan ba ki duk lokacin da ki ke so* *** Ƙarfe uku saura kwata Galadima ya tashi ya ɗauro Alwala ya fito. Har lokacin Zaytoonah ba ta tashi ba yaushe ma ta samu ta yi baccin bayan gwarzonta bai iya ɗaga ma ta ƙafa ba. Sai da ya shimfiɗa sallaya kafin ya ƙariso gadon ya fara murza kunnen ta a hankali yana kiran sunan ta. "Princess ta shi mu ribaci wannan dare" Lokacin da ba Azumi ba ma ba ya wasa da sallar dare balle yanzu da aka shiga Azumi. Da ƙyar ta buɗe ido dan har ga Allah bacci ne a idonta sosai. Sai da ya tabbatar ta tashi ta shiga banɗaki kafin ya ƙarisa wajen sallaya ya tada sallah. Allah na gani raka biyu kawai ta yi ta ɗan yi addu'a kaɗan ta kwanta akan sallayar. Shikam da ya gama nafilfilun ƙur'ani ya ɗauka ya fara karatu. Sallar dare da yawan tilawa shi ya sani na ɗaya daga cikin abinda ya ke zama ma sa kariya daga sharrin maƙiya. Ya sani yanada maƙiya na kusa da na nesa but amma a duk lokacin da yai addu'a ya haɗasu da Allah yana da yaƙinin babu wanda ya isa ya cutar da shi. Tun lokacin da tsohon Galadiman gari ya rasu aka fara raɗe-raɗen za a bashi ya shiga cikin wani tsanani dan yau lafiya gobe babu haka ya dinga fama a lokacin hakan ya sa Malamin da ya ke ɗaukan karatu a wajen sa ya ce ya dinga yin alwala kafin ya kwanta sannan ya tashi da dare yai sallah ko da raka'a biyu ne kacal. And a hankali jikin sa yai sauƙi, wasu ƙulle-ƙulle da ake shirin yi duk Allah ya wargaza su. Sai ƙarfe huɗu da rabi ya tashi Zaytoonah dan su ci suhur duk da shi ba ma'abocin cin abu mai nauyi ba ne. Washegari Humairah ne ta kawo ma ta Alinah dan 'yan biyu kam sai su Mommy sun wuce Makkah za'a kawo ma ta su. Galadima gani yai har su ka shirya har su ka shiga mota su ka yi nisa bai ga an bawa Alinah abinci ba. ya ce " ni kan 'yar tawa Azumin dole ki ka sa ta ne?. Wannan horon yunwan yai yawa" Murmushi ta yi sannan ta kamo hannunsa ta ɗaura a ƙasan cikin ta ta ce "na yayeta saboda ƙanin ta na bani wahala" Galadima ya zaro ido waje. Ta sani ba dan Azumi ba, ba kuma dan kar Dreba ya ganshi ba da ba abinda zai hana shi kissing ɗin ta. "Alhamdulillah, Alhamdulillah" 2/11/21, 10:04 PM - ****: 75 Bismillahir Rahmanir Rahim *The wedding* "Ki zauna Ghazala" "Abu Razz Dan Allah ka yi haƙuri. Na yi nadama, na tuba. Ka maidami ɗakina dan Allah" ta ƙarisa maganar tana matsar hawaye. Sau ɗaya ya kalleta sannan ya kauda kai ya ce "ki tashi ki zauna ba na son wannan tsugunnon" Tunda ta shigo ta ajiye jaka ta saka gwiwowinta ƙasa ta fara bashi haƙuri. Da ƙyar Ghazala ta miƙe ta zauna akan kujera tana fuskantar mutumin da a duniya ba abinda ta ke so da ya wuce ta sake komawa gidan sa. Bai yi magana ba sai ma rubutu da ya cigaba da yi. "Ranka shi daɗe abinda ya faru sharrin shaiɗan ne, kowanni Ɗan Adam yanada rauni. Ka yafemin Dan Allah" "Wallahi duk abinda ka ke so idan na shigo zan yi. Dan ƙaunar Allah da Manzon sa ka rufa min asiri ka maida ni" Ajiye biron hannun sa yai ya ɗago ido ya dubi Ghazala da kyau. Kallo ɗaya ya ma ta ya san ba ƙaramin rama ta yi ba. "Na riga na yafe miki Ghazala, yanzu tsakanin ki ne da Allah da kuma Zaytoon da ki ka zalunta kuma ba na tunanin kin roƙi gafarar ta har yanzu" "Idan ma tsugunnawa ka ke so na yi a gabanta na ba ta haƙuri Wallahi zan yi" Ghazala ta yi saurin katse shi. "Ka da ki roƙeta dan ni, ki roƙeta da zuciya ɗaya saboda kin ma ta laifi. Ki roƙe ta tsakani da Allah" "Zan yi, wallahi zan yi" Shirun da ta ga yayi ne ya sa ta tattaro duk wani ƙwarin gwiwa da ta ke da shi ta ce "Abu Razz ka maida ni kenan?" "Allah ya baki wani mijin wanda zai zauna da ke yadda ki ke so Ghazalah" "Ranka shi daɗe..." *** Mommy da Daddy ne su ka je yiwa su Iya sallama saboda gobe jirgin su zai tashi. Daddy da Muntari ke taɗi sama-sama dan har yanzu Muntarin ya kasa sakewa jiki da shi. Yayinda Mommy ta buge da danna waya dan Iya ta koma ɗaki. Ƙafarta ke damunta shiyasa da su ka gama gaisawa ta wuce ɗaki ta kwanta. "Hamma ina da magana" Muntari ya faɗa yana danna yatsun sa. "Bismillah, minene?" "Na so dai sai kun dawo na gaya ma ka amma yaron nan kaman zai yi min kuka jiya wai dole na faɗa maka kafin ku tafi" Daddy ya tattaro dukkan hankalin sa ya bawa Muntari. "Auwal ne ya ce na nema ma sa auren Humairah a wajen ka" "Ka ji min wani zance a nan. Mukhtar Humairah ai 'yar ka ce. Ni miye nawa a ciki" "Hamma..." "Nkiru kin ji maganar da mu ke?" Mommy ta girgiza kai "Wai First son ɗin ki ke son Humairah shine Mukhtar ke min maganar. Ki gaya ma sa Humairah dai 'yar sa ce, ni ba abinda zan ce a nan" Muntari yai shiru saboda wannan matsayi da Hamman na shi ya bashi, bayan duk aika-aikar da ya ma sa. Kafin su tafi sai da aka tsaida magana akan za ayi biki zuwa sati biyu bayan sallar layya. Inda Daddy ya ce ya barwa Muntari ragaman yin komai dan shi ya fi chanchanta ya aurar da Humairah. Bayan tafiyar su, Mommy ta kira Auwal tana tsokalar shi akan yai haƙuri ba za ta bashi Humairah ba. 'Yar ta ba za ta auri Barrister ba. "Mommy kar ki sa jini na ya hau, mi Daddy ya ce Dan Allah?" Mommy ta yi murmushi ta ce ya cigabanda shirye shirye dan an sa biki roughly nan da wata uku ma su zuwa. Ta riga ta san da maganar dan lokacin da ya ji hiran Muntari da Iya akan saurayin Humairan da ke son turowa gida shine ya samu Mommy da maganar ita kuma ta ce yai wa Muntatin magana dan shi ne yanzu Uba ga Humairah. Anyi wannan maganar ne tun kafin T J ya dawo. Washegari kuwa T J da Maryam su ka wuce Makkah dan yin Umara. *** Tana shigowa falo ta jefa jakarta kan kujera ta kwantar da Alinah da ke bacci sannan ta zaunaa ƙasa ta miƙe ƙafafuwa. Ba kowa a gidan ta sani tunda yanzu Maman Tope ne kaɗai ke mu su aiki dan tuni Galadima ya sallami Atika sanda ta dawo gidan ma ba ta sameta ba. Maman ta tafi ƙauyen su saboda rasuwar da aka mu su. Ba wai hanata Azumi da likitan yai ba ne ya sa ta damuwa sai dai sakamakon ultrasound da aka ma ta ne ya sa duk jikin ta yai sanyi. "Insha Allahu za ki haifa mana 'yan biyu lafiya nan da wata bakwai" Likitan ya faɗa yana murmushi. Babban Likita ne da Galadima ya haɗata da shi, ba ta san takamaimai alaƙar su ba amma matsayin ƙani ya ke ga Galadima. Sake haihuwan 'yan biyu ba shine matsalar ba, matsalarta shine kada ace ta haifi mata. Za ta so haihuwar 'yan biyu mata amma kuma da ta tuna cewa Galadima ba shi da ɗa namiji sai ta ji jikin ta yayi sanyi. "Doctor maza ne ko mata?" Ta tambayi likitan bayan ta gama farkawa daga tunanin da ta ke. "Mommyn Alinah its too early to tell gaskiya, sai gaba" Kaman shima ya ankara da abinda ta ke tunani sai ta ji ya ce "na tabbata Yaya ba shi da ra'ayin fifita 'ya'ya maza akan mata. Duk wanda Allah ya bashi zai karɓesu hannu bibbiyu. Ki godewa Allah domin akwai wanda ko mata-maza ne suna so saboda Allah bai ba su ba" Ta dai sake fiska kam kafin ta bar office ɗin sa amma lokacin da ta shiga mota ta sake duba result ɗin da ke hannunta sai ta sake shiga damuwa. Ko da ace dai-dai da wasa Galadima bai taɓa nuna ma ta cewa yana son haihuwan ɗa namiji ba but cikin 'yan kwanakin nan idan ta ga yana yiwa 'yan biyu wasa sai ta ji kaman yana fata a ransa cewa shima Allah ya bashi 'ya'ya maza ne. Zuwa lokacin da yaran su ka dawo daga makaranta ta riga ta ɗauke abin a ranta ta dawo da walwalarta. Da yamma ita da Raziya su ka shiga kitchen su ka ɗaura abincin buɗa baki. Allah ya sa ma Raziyan ba ta Azumi da ba abin da za ta iyayi, yarinyar akwai raki. Ta yi zaton Likita ya gaya mi shi komai shiyasa ta yi shiru da bakinta tana jira ta ji ya taso da maganar amma shiru. Dan da ya dawo daga sallar taraweeh ya sha tea sai ya shiga library ɗin sa ya fara aiki. Ƙarfe shaɗaya da minti shida ya shigo ɗakin sa. Ya shiga banɗaki ya kama ruwa, yai alwala sannan ya fito. Ba ta yi bacci ba dan tuntuni shi ta ke jira amma kuma yana shigowa ta yi saurin rufe idonta kamar mai bacci. Jawota jikin sa yai sosai-sosai sannan ya ma ta magana a dai-dai kunnen ta kamar mai raɗa. "Ya jikin na ki ? Mi Likita ya ce" Kamar ba za ta amsa ba sai dai kuma ta sani wahala kawai za ta bawa kan ta dan ta san ya san ba ta yi bacci ba. "Alhamdulillah da sauƙi, Likita ya ce na ajiye Azumi na wani lokaci" "Ai dama na gaya miki ki ajiye amma ki ka yi kunnen ƙashi" Ta yi murmushi mai ciwo dan ba ta san tana za ta fara ma sa bayanin abinda ke cikinta ba da kuma tsoron da ta ke ji. Ba abu ne mai wahala ba idan Hajia Abu ta sa shi ƙara aure nan gaba kaɗan idan har ba ta haifi namiji ba. Though He'll be clocking Fifty soon amma har yanzu mutum ne da idan yana son auren 'yan mata 'yan shashida, shatakwas zai samu. Babu wanda zai ga 49yrs ɗin sa. Abinda za a gani shine gidan da ya fito da kuma ko shi wanene. "Ya rubuta miki magani ne?" Maganar sa ya katse ma ta tunani. "Daddyn Raziya ya za ka ji idan nima na dinga haifa maka 'ya'ya Mata" Shirun da yai ya sa ta yi tunanin ya ji haushin maganarta. Yatsunta ya riƙe yana murzawa a hankali kafin ya ce " ban aure ki dan ki haifa min ɗa namiji ba Zaytoon. Allah Subhanahu wata'ala shi ke bada haihuwa, kuma ya riga ya faɗa mana cewa wasu zai azurtasu da haihuwan 'ya'ya mata zalla wasu kuma 'ya'ya maza zalla, wasu kuma zai haɗa mu su duka biyu sannan akwai waɗanda zai jarrabesu da rashin haihuwa. "Ina godiya wa Allah da ya azurtani da 'ya'ya mata har huɗu, kuma ko da wannan da ke hanya ya zama mace ni mai ƙara godiya ne domin 'ya'ya mata ma ni'ima ne. Addu'a na shine Allah ya bani ikon ɗaura su akan tarbiyyan musulunci na kuma samu damar aurar da su cikin kwanciyar hankali. "Zaytoon i want you to know that i'm proud of my daughters. Yadda ki ke ganin sun nan diamond su ke a wajena" Kissing goshinta yai ya ce "kar ki sa wannan a ran ki, duk rabon da Allah ya bamu za mu karɓe shi hannu bibbiyu. Infact ko 'ya'ya mata goma ne ki haifo min ina son su"... "Sayyadi" "Sayyadi" Shiru, yayi barci. Dole yai barci cikin azumin nan duk baya samun yin baccin kirki. Daga ƙarfe biyu da rabi tayi idan ya tashi shi da bacci kuma sai dai da rana idan ya samu sarari musamman idan bai fita office ba ko kuma ya samu dawowa da wuri. Manna ma sa kiss ta yi a lips ɗin sa tareda furta "I love you Zannoon" Tunda ta ga alama Likita bai gaya ma sa cewa 'yan biyu ta ke ɗauke da shi ba itama ta rufe maganar har Allah ya sauke ta lafiya ya gan su da idon sa. A lokacin ta sani he'll be more happier... *** Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya har aka ƙare Azumi lafiya. Wanda kwata-kwata Zaytoonah Azumi shahuɗu kawai ta iya yi. Kwana biyu kafin sallah su ka koma Zaria. Suna zuwa kuwa ta kira Humairah akan ta zo ta tayata aikin sallah. Wannan karan ma hawan da Galadima yai harda 'yan biyu kuma kamar wancan karan wannan karan ma sun burge mutane, dayawa ma na ɗaukan su a matsayin 'ya'yan cikin Galadima ne. Unfortunately rana na ukun Sallah da Zaytoonah ta je gaisuwa Fada su ka yi ido huɗu da Ghazala. Duk da Galadima ya tabbatar ma ta da cewa shi kam ba zai dawo da ita ba hakan bai sa ta cire rai ga komawa gidan ba. Tana ta sintiri tsakanin Zaria da Abuja wajen 'yan uwan sa ko za a samu mai taimaka ma ta amma shiru ka ke ji. Mai Martaba ce ma ta yai ta cigaba da addu'a idan akwai alkhairi a komawarta, ko ba daɗe ko ba jimawa Galadima zai maidata gidan sa. Hajja kuwa ce ma ta tayi ta ɗauki ƙaddara kawai. Hajiya Abu da ta ke da faɗa aji a wajen Galadima ita kuma ta nuna ma ta fir ba za ta koma ba indai ta isa da Galadima. "Maman 'yan biyu" Ghazala ta faɗa tana ƙarewa Zaytoonah kallo, idan har idon ta ya ba ta dai-dai to wannan hasken da ƙyallin da Zaytoonah ke yi na ciki ne. "Hajiya anyi sallah lafiya" "Lafiya, ya yara?" "Suna lafiya tare ma mu ke da su amma sun tafi gaida Mai Martaba" "Ayyah!" Ta faɗa yayinda wani abu mai tsini ya soki ƙirjin ta. Yadda ƙirjinta ke wawal-wawal ba za ta iya zama waje ɗaya da Zaytoonah ba dan haka ta yiwa Hajja sallama ta fita, ko wajen sauran matan ba ta je ba ta wuce gida. Hajiya Safara'u ta nemi su sake neman wani malamin da zai ma ta aiki mai ƙarfi akan Galadima amma Ghazala ta riga ta tsorata da lamarin Galadiman musamman bayan mummunan jinyar da ta afkawa Hajia Ajwa daga ranan da aka kawo Hajia Fatima gidan. Ba ta je ta ganta ba amma gulma ya iso ma ta cewa wani irin wari da ɗoyi ta ke yi, wanda dole ya sa aka maidata boys quarter ta bar main building ɗin. Daga majiya mai ƙarfi ma ta samu labarin cewa Turaki ya saketa, zaman da ta ke yi albarkacin 'ya'yanta ne maya sa ya amince ta zauna ma sa a gida. Ba za ta sake komawa maganar boka ko malamin tsubbu ba. So ta ke ta samu Galadima cikin hayyacin sa. Kwanaki ƙalilan ne ya rage ta gama idda kuma idan wannan damar ya wuceta da wuya Galadima ya sake ba da sadaki ya aureta. Miye zai yi da ita? Bayan idan auren ma zai yi sai dai ya auri budurwa ko matar da ba ta kaita shekaru ba. *** Lokacin da su Mommy su ka dawo daga Umura ne aka faɗawa Humairah maganar aurenta da Auwal. Ga mamakin su sai ta ce ba za ta aure shi ba. Mommy da ta ma ta maganar sai ta sake baki da mamaki. Humairan dai da ta sani da tuntuni ta jima da sanin cewa tana son auren Auwal. Yarinyar da akan ta ne ma ta zaɓi aurar da Zaytoonah wa Galadima akan Auwal. "Ban gane ba za ki aure shi ba" "Mommy ba ya sona, ni ba zan auri mutumin da baya sona ba. Inada mai sona kuma shi zan aura, idan na auri Hamma Auwal kamar dai auren jeka nayika zan yi" "Ikon Allah! Shi Auwal ɗin ne ya ce ba ya son ki?" "Mommy ki yi haƙuri amma ki gayawa Daddy ba zan aure shi ba" tana faɗin haka ta miƙe ta shige ɗaki zuciyarta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi. Kamar wasa kuwa da Daddy ya tambayeta sai ta ce ma sa ba za ta auri Auwal ba. Yai-yai da ita ta ƙi, daga ƙarshe ta ce ko za ta aure shi za ta yi ne dan shi amma ba dan ra'ayinta ba. Da farko Daddy ya shiga ruɗu da furucin 'yar ta sa amma daga baya kuma da yai wani tunani sai ya gane halin yaran zamani ne Humairan ke son yi ma sa. Tuni ya dannawa Zaytoonah kira. Dama a ɗoke ta ke dan tun shekaran jiya da su ka sauka a Zaria ta ke son zuwa amma Mai girma Galadima ya ce ta bari sai Jummu'a idan sun je weekend sai ta je ta gaishe su. "Mutum da iyayen sa ana nuna ma sa iko" ta faɗa cikin fushi. Ko da dare da yai niyyar lallashi ba ta bashi dama ba dan har ga Allah ta ji haushin hanata zuwa da yai. Ina Abuja ina Zaria... "Mi ki ka kitsawa Humairah ta ke yin bore yanzun" "Daddy ni kuma?" "Ke dai Adaeze" Zaytoonah ta ƙyalƙyale da dariya. Abunda aka rufe mu su ne ya fito fili lokacin da Humairan ta saurari hiran Salman da Auwal inda ya ke tsokalar sa da angon Humairah, a wajen Iya ta samu labarin Daddy da Uncle Muntari sun riga sun tsaida maganar auren su da Auwal. With so much excitement ta kira Zaytoonah ta sanar ma ta. Zaytoonah kuma ta shirya ma ta akan kar ta yadda ta bari Auwal ya sameta a bulus, ta fara ja ma sa aji tukunna har sai ya fitar da abinda ke cikin sa. "Za ki faɗa ko sai na hau mota na kai ƙaran ki wa Galadima" "Haba Daddy, nifa kawai dai so na ke Hamma Auwal ya gane cewa ƙanwata na da class" "Hakan ma yayi kyau Antyn Humairah" Zaytoonah ta sa dariya. Bayan ya tambayi lafiyar yara sannan ya tambayeta ko akwai matsala ta ce ma sa babu. Wanda hakan ya sa ke sawa zuciyar sa salama. Bayan Daddy ya ji komai daga bakin Zaytoonah shima sai ya faɗawa Mommy akan ai ba za ayiwa Humairah auren dole ba tunda ba ta son Auwal magana ta wargaje kenan. "Barkindo you are joking right?" "I'm serious Nkiru. Dan haka ki gayawa first son ɗin ki ya nemi wata matar a gaba" Maryam ta ƙurawa mijin ta ido tana son tabbatar da gaskiya ko kuma ƙaryan sa. "Hajiya ya ki ka zuba min ido ne" Murmushi ta yi ta ce " sai dai ka yiwa na waje amma ni kam na san kaya na. I know when he's lying and when he's saying the truth. Humairah da First son aure ba fashi" "Wannan wannan Mata" T J ya faɗa yana nunata da yatsa. Maryam ta tura ɗankwalinta gaba ta tsuke baki ta ce "ya akai Mijin Maryama"... Text ɗin da Humairah ta turawa Auwal ne ya sa shi shiga ruɗu. Bai sake rikicewa ba sai da ya kira Mommy ya gaya ma ta sai itama ta tabbatar ma sa ai maganar aure ma an janye dan batun da ake ma gobe Muntari zai maida ma sa sadakin sa. "Mommy Humairan ne ta ce ba ta sona, ita ce ta ce ba za ta aureni ba?" "Haka dai ta gaya min kuma ko da Daddyn ku ya tambayeta hakan ta faɗa ma sa" Kasa cewa komai yai ya kashe wayar ran sa na ƙuna. Yarinyar da bakinta ya furta ma sa kalmar so ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba wai ita ce ke cewa ba za ta aure shi ba yanzu. Tashin hankali sosai Auwal ya shiga. Kwana ɗaya sai gashi zazzaɓi mai zafi ya kama shi. After loosing Zaytoonah the thought of loosing Humairah again is depressing. Wasa-wasa sai gashi har da kwanciya a Asibiti a ranan ne kuma su Zaytoonah su ka iso Zaria. Tareda Galadima su ka zo yai wa su Daddy barka da dawowa kafin ya wuce gida ya bar Zaytoonah da yaran cikin 'yan uwan ta. Rashin zuwan Humairah duba shi bayan kowa ya zo ya ƙara kashewa Auwal jiki. Kenan da gaske fa ta dena son shi. Bai iya kwana a Asibitin ba kusan ƙarfe tara na dare aka sallameshi ya koma gida... "Anty Zaytoonah kinaga ba zan faɗawa Hamma gaskiya ba. Ina tsoron kar wani abu ya sameshi" "Kul, ki bari ya zo da kan sa ya nemi soyayyar ki" "Anya zan iya?" "Ke ki ka sani ai" Zaytoonah ta faɗa tana ɗaukan jakan ta. Tun kusan minti bakwai da ta wuce Galadima ya kira akan ya zo ɗaukan ta amma ta taɗi, yanzun ma Mommy ne ta ƙwala ma ta kira shine ta fita... Tana shiga mota ta samu Galadima na amsa waya. Daga yadda ya ke maganar ta gane da mace ya ke wayar. Ta takure gefe ta sha kunu amma kuma duk hankalin ta na kan maganar da ya ke yi. Sai da su ka kusa isa gida tukunna ya gama wayar. Ya kamo hannun Zaytoonah zai riƙe ta yarfe hannun. Ƙyaleta yai sai da su ka isa gida kafin ya tambayi lafiya ta ke haɗa ma sa rai dan shi bai ɗauka wayar da ya ke ne ma ya sa ta fushi ba tunda ya san faɗan su na rashin barinta ta zo gida washegarin ranan da su ka sauka ya riga ya wuce. Wata matar ƙanin sa ce ta kirashi ta ke ma sa ƙorafin wai ƙanin shi zai ƙara aure kuma bai gaya ma ta ba sai yanzu da biki ya saura wata ɗaya. "Baby miye matsalar ki? Na san dai lafiya lau dai ki ka baro su Daddy" "Na ce ma ka ina da matsala ne? Duk da dai ka koma aikin counselling to ni ban nemi service ɗin ka ba. Akai wa Mata ma su matsalar aure" "Ke baki da matsala da ni kenan" "Allah ya rabani da matsala" Galadima ya ɗan haɗe rai ya ce "tunda ba ki da matsala dama akwai wata 'yar bautar ƙasa da aka kawota office ɗina. Na ga yarinyar akwai hankali, inaga kawai zan kawo miki ita ta taya ki zama" "A wa ɗin?" "Ke mana" "To ka kawo mana, ni ina ruwana. Ba 'yar bautar ƙasa ba ko 'yar bautar duniya ce ka kawo ta mu gani. Ba matar da za ta bani tsoro a gidan nan" Wucewa ta yi ɗakinta ran ta a jagule. Yaran suna Fada, Alinah kuma ta barta wa Mommy. Tana shiga ɗaki ta fiddo da wayarta daga jaka ta shiga kiran Ahmad ƙirjinta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi. Ba a ɗauka ba sai a bugu na biyu sannan aka ɗauka. "Maman 'yan biyu lafiya?" Ya faɗa yana sake duba agogon hannun sa. "Ahmad wace Corper ce a office ɗin ku?" "Corper kuma?" "Yes, na ji ance an tura wata Corper office ɗin Justice" Ahmad ya ƙyalƙyale da dariya. "Ahmad ya kake dariya, ka gaya min mana" "E" ya faɗa lokacin da ya tsagaita dariyan "akwai wata tsaleliyar budurwa da aka kawo mana ita kwanan nan. Yarinyar nan ga kyau ga diri, irin figure 8 ɗin nan" Zaytoonah ta yi saurin dafe ƙirjinta da ke ma ta zafi. Shirun da Zaytoonan ta yi ne ya sa shi jin tsoro, kar dai ta shiga matsala saboda abunda ya faɗa. Dan ya riga ya gane kishi ne ya sa ta bugowa. "Maman 'yan biyu Uncle baya karɓan 'yan bautan ƙasa a office ɗin sa" Sai alokacin ƙwaƙwalwarta ya fara aiki. Tabbas lokacin da ta ke koyon aiki a wajen dayawa da farko sun ɗauka bautar ƙasa ta zo yi shine ma su ke mamakin zuwanta tunda sun san Justice baya karɓa sai daga baya su ka gane she's already a Barrister ma ba wai half baked Lawyer ba ce. Chamber ɗin sa na Zaria kam ana karɓa amma banda na Abuja. Hannu Galadima ya sa a ƙungunta ya jawota jikinsa. Saurin katse kiran ta yi jin muryan Ahmad na faɗin Hello Hello. Juyowa ta yi tana kallon sa tareda turo baki. "Na ɗauka ai kin ce ba kya tsoron kowacce mata" "Justice Yunus da yanzu jini na ya hau mi za ka ce?" "Sai na ce wagga mata akwai cika baki, amma shegen tsoro gareta" "Ni ba na tsoro" ta faɗa tana nuna kan ta "Kawai dai ina tausayin wacce za ta shigo ne, dan dai na riga na gama sanin sirrin ba abinda za ta zo da shi" "Mi zai hana mu ƙarisa chan a nuna min sirrin" Ya faɗa yana kissing wuyan ta. Zaytoonah ta yi murmushi. *** Washegari Humairah ta kira Zaytoonah ta sanar ma ta ai bayan tafiyarta Auwal ya kirata a waya. Zaytoonah na naɗe boxers ɗin Justice da ta wanke ta yi saurin ajiye shi gefe ta ce "ba ni labari mi ya ce mi ki?" "Anty Zaytoonah na kwabsa fa sosai. Wallahi tausayi ya bani shine na fallasa komai" "Kinci gidan ku Airah" "Kai Anty" "To mi zan ce bayan kin ɓata mana show" "I'm just pulling your legs, ban gaya ma sa gaskiya ba sai da ya faɗi sirrin da ke zuciyar sa" "Da gaske?" "Allah, barin ma tura miki ki ji dan na recording wayar da mu ka yi" Bayan Zaytoonah ta kunna recording ɗin ta saurara sai ta ji tausayin Auwal ya kamata. Tambayar Humairan yai akan miyasa ba za ta aure shi ba. Ita kuma ta ce ma sa saboda baya son ta, ita ba za ta iya auran wanda baya son ta ba. "Kina ganin ba na son ki ne?" "Hamma ba ka sona, ba ka taɓa cewa kana sona ba, ba ka taɓa nuna min so ba, kullum kusheni ka ke yi" "Wannan shine hujjar?" "E" "Ki yi haƙuri Aysherh. Indai irin soyayyar nan da ki ke yi da samarin ki ne ba zan iya yi mi ki shi ba. Ina son duk wata soyayya da zamu yi to ya kasance cikin gidan mu ne" "Kenan Hamma kana sona?" "A matsayin ki na ƙanwata ina son ki, a matsayin ki na matar da na ke son aura ina miki albishir da samun soyayya idan kin shigo gidana" "Hamma ni dai idan ba ka ce kana sona ba ba zan amince ba" "Aysherh please" ya faɗa da sassanyar murya. Zaytoonah was his first love. Lokacin da ya rasata a farko da na biyu zuciyar sa ta shiga cikin ruɗani. He was completely shattered, ya jima yana jinyar zuciyar sa. Ba zai ce yana yiwa Humairah irin son da yai wa Zaytoonah ba amma yana son ta. Tunda Mommy ta ma sa magana akan idan har zai bi shawaran ta to ya nemi Humairah sai kuma a hankali ya fara ƙoƙarin cire Zaytoonah a ran sa. Sannan ya fara koyawa kan sa kallon Humairah a matsayin macen da zai iya aura ba wai a matsayin ƙanwar sa kaɗai ba. It takes time kafin yai adjusting, sai dai rawan kan Humairan ke ɗan sace ma sa gwiwa. Lokacin da ya ga ginin sa yai nisa ne ya fara tunanin gabatar da kan sa wa Humairan sai kuma ta yi wani sabon saurayin da ya manne ma ta, itama kuma ta ke ɗan ji da shi. Hakan ya ɗan sa shi dakatar da niyyar sa ya zuba ma ta ido ya ga gudun ruwan ta. "Zan aure ki ne dan ina son ki Aysherh" ya faɗa daga ƙarshe da muryan sa mai rauni... *** Kamar yadda aka saka wata biyu bayan Azumi za ayi biki hakan ta kasance kuwa dan ba a chanja ba. Zuwa yanzu Humairah da Auwal sun sasanta kan su dan har hira ya ke zuwa wajen ta tunda ta koma gidan Mommy da zama yanzu tun dawowar Daddyn su. Shirye-shiryen biki ake ta yi gadan-gadan wanda duk ƙarfin abun Mommy ne da Zaytoonah ke yi. Daddy na ƙoƙarin neman aiki ne yanzu tunda ya rasa gurbin koyarwar sa a ABU. Sai dai kuma abinda bai sani ba tuni Galadima ya shige ma sa gaba wajen ganin an dawo ma sa da aikin sa. Mutumin da yai degree har uku ba abun yar wa ba ne lokaci guda. Muntari shima yanzu ba abinda ya ke dan komai na shi ya tafi, har yanzu kuma Alhaji Rabi'u bai waiwaye su ba, suma kuma sun kasa yin maganar sa balle su tunkare shi. Auwal dai da kansa ya ƙarisa ginin gidan sa amma Mommy ta ɗauki nauyin duka furnitures ɗin gidan. Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama komai na gidan. Sati uku kafin biki Humairah ta koma Bauchi ta je ta yi sati biyu wajen Ummi kafin ta dawo bayan ta sha gyara. Duk yadda Zaytoonah ta so ta zo bikin da wuri bai yiwu ba sai ranan Jummu'a da safe da za ayi walima ta dira a gidan su. Galadima na fama da mura, Hashir da Falaq na zazzaɓi gaba ɗaya babu yadda za ta yi ta bar su a wannan hali. Jikin Falaq ya ɗan yi sauƙi amma Hashir kam dai sai a hankali, ta dai taho da shi a haka. Mafarin zazzaɓin ma ruwan sama ne aka yi, Zaytoonah na bacci a ɗaki yaran su ka fita compound ɗin gidan su ka yi ta wasa cikin ruwa. Duk da Zaytoonah ta so ayi wani hidima na burgewa ko da dinner ne ko kamu amma Daddy ya hana. Ranan Alhamis Humairah ta yi friends day sai kuma Jummu'a aka yi walima Asabat kuma aka ɗaura auren *Barrister Auwal Usman Abubakar* da kuma amaryar sa *Aishah Tijjani Abubakar*... 2/11/21, 10:04 PM - ****: 76 Bismillahir Rahmanir Rahim *Forever with you, my love* Pillow guda biyu Suhailah ta jerawa Zaytoonah a ƙasa kafin ta zauna akan kujera ta ɗaura ƙafafun ta a kai. Wani irin kumburi ƙafafun su ka yi ma ta, dama tun cikin na wata shida ta fara cika ta ko'ina to da ya shiga wata takwas kuwa sai kumburin ƙafa da ciwon baya amma ciwon bayan ba sosai ba. Yanzu kam wahala sosai ta ke yi da cikin. Har lokacin ba ta faɗawa kowa cewa 'yan biyu ba ne, ko last time da ta je gidan Mommy sai da ta tambayeta ko 'yan biyu za ta haifa da wannan ƙaton cikin Zaytoonah ta ce Allah ne masani, ba ta son dubawa ta fi so a ranan da ta haihu kowa ya ga kyautar da Allah ya ba ta. "Yawwa na ga Assignment ɗin" Zaytoonah ta faɗa a wahalce. Ta karɓi littafin Suhailah ta fara dubawa. Tana cikin koya ma ta aikin wayarta ya shiga ringing. Galadima ne ke kira. Sai da ta yi murmushi kafin ta ɗauka. "Mijin Zayt" "Na'am Matar Yunus" "Ya aka yi" "Yanzu na isa masauki na shine na ce barin kira matar ta yiwa mijin hira" "Ya hanya" "Alhamdulillah sai kewan ku da na ke ta yi. Barin ga fiskar matar dan Allah" "balloon face ɗin za ka gani" "Ko pumpkin face ne ai nawa ne ko" "To bari na gama koyawa Suhailah karatu" "Ban yarda ba. Ko rabin minti ne ki bari na ga fiskar princess ɗina" "Sayyadi please" ta faɗa a marairaice "Ok ok, nan da 10 minutes zan sake kira" Kaman haɗin baki tana ajiye wayar sai ga kiran Farha ya shigo. Bayan sun gaisa ne Farhan ta ma ta albishir akan za ta auri Manager ɗin gidan gonan ta wato Muhammad Chu. "Kin san dai ba iya zuwa zan yi ba yadda na yi nauyin nan" "Haba Besty. To zan fasa auren har sai kin haihu" "Kamar da gaske" Farha ta sa dariya. Sun kai minti uku suna waya kafin ta kashe bayan ta ma ta fatan Allah ya ba su zaman lafiya... Kwanan Galadima uku a Lagos ya dawo inda ya attending wani conference. Kaman yadda kullum ya ke ɗaukan Zaytoonah duk dare su ke fita strolling saboda ƙafarta yau ma ɗin dogon hijabi ta zunbula sannan ta saka nose mask saboda sanyi, ta fito falo inda Galadima ke jiran ta. Yana zaune tareda yaran ɗauke da Alinah suna kallo . Lokacin da ya miƙa Alinah wajen Raziya kuka ta challa kamar wadda ta ga dodo. "Ai sai ki yi ai. Ba wanda zai fita dake a wannan sanyin" Zaytoonah ta faɗa tana wucewa gaba dan ba ta ma son Galadima ya ce su tafi da ita. Haka su ka fice daga gidan su ka bar Raziya na faman lallashin ta. A hankali su ke tafiya suna yi suna taɗi. "Sayyadi idan na sauke gaskiya zan huta, is not easy gaskiya" "Allah ya sauke ki lafiya" ya faɗa ahankali. Ba wai ya ji daɗin maganar ba ne amma kuma lafiyar Zaytoonah tafi ma sa komai. Ɗaukan ciki da haihuwa ba wasa ba ne gashi ko hutawan kirki ba ta yi ba da haihuwar Alinah ta sake samun wani cikin... Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Zaytoonah ta cigaba da renon cikin ta. Ranan da ya cika wata tara da kwana goma shauku ta fara naƙuda, da ke lokacin ya zo ƙarshen shekara dukkan su na Zaria lokacin. Baba Nafy ne ta kira ma ta Mommy lokacin da su ka isa Asibiti. Zuwa minti ishirin kuwa Mommy ta iso. Ita dai haihuwan ta na faɗawa lokacin dare dan kuwa tun kusan ƙarfe shaɗaya na safe da su ka zo ba ta samu ta haihu ba sai ƙarfe ɗayan dare. Yadda Mommy ke tare da ita tun safe haka shima Galadima ya ka sa komawa gida lokacin da ya dawo ƙarfe tara ya samu har lokacin ba ta haihu ba. Mommy ce ta fito daga labour room zuwa ɗakin da aka kamawa Zaytoonan inda Galadima ke zaune yana jiran tsammani. "Hajia ta sauka?" "Alhamdulillah, ta sauka" "Tana lafiya ko?" "E da ita da jariran ta suna lafiya" Galadima ya fara rarraba ido jin Mommy ta ambaci jarirai " 'yan biyu maza ta haifa" Mommy ta ma sa gwari-gwari. Alhamdulillah Galadima ya faɗa tareda yin sujudush shukri a wajen yana yiwa Allah godiya. Ba'a jima ba kuwa aka kawo ma sa 'yan biyun sa bayan an gyara su, ya riƙe su a hannun sa idon sa fal da hawaye. Zaytoonan ma a keke aka turota zuwa ɗakin inda Mommy ta taimaka ma ta ta kwanta akan gado. Ko minti goma bai cika ba baccin wahala ya ɗauketa. Zuwa ƙarfe shida da rabi na safe Hajiya Abu ta dira a Asibitin, fiskarta wasai dan tunda Asuba da ta tashi ta ci karo da saƙon Galadima inda ya ke ma ta albishir da haihuwan 'yan biyu maza ta kasa zaune tsaye. Sai ma da idanun ta ya gane ma ta kyawawan yaran ta sake samun wani nitsuwa. Sai washe baki ta ke tana addu'ar Allah yai mu su albarka. Wannan mata yadda ta ke yi ko ita ta haifi Galadima albarka. Daga gidan ta ma aka kawowa Zaytoonah abinci duk da Mommy ma ta tafi kawo abincin lokacin da su Salman su ka iso Asibitin. Kafin ƙarfe goma an cika Asibitin da 'yan dubiya. Kowa ya ga yaran tambayar farko shine waye Hassan waye Hussain saboda identical twins ne. Wanda aka sawa blue riga shine Hassan mai green kuma Hussain abinda Hajia Abu ke faɗawa mutane kenan. Ta kasa ta tsare a ɗakin, saboda hayaniya ma dole aka ba su wani ɗakin aka bar Zaytoonah a ɗakin tana bacci. Tun safe shiga da fice kawai ake yi zuwa kallon yara. Lokacin da Galadima ya nemi sallama Likita cewa yai a bari ta ƙara kwana saboda a tabbatar da lafiyarta. Wasa-wasa sai da Zaytoonah ta yi kwana huɗu a Asibitin kafin aka sallameta zuwa lokacin jikinta ya ɗan yi ƙwari. Bayan ta koma gida ne Galadima ya gaya ma ta ba za ayi taron suna ba har sai ta warke gaba ɗaya. Mommy ce ta nemi hakan saboda ta kula Zaytoonan har yanzu ba a hayyacinta ta ke ba. Kaman ma she's depressed ne. Mommy ce ta zauna da ita a Asibitin da aka sallameta kuma sai ta ke jeka ka dawo, za ta je da safe ta koma gida da dare. Hajiya Abu ba ta ji daɗin ɗaga sunan ba amma ko ba komai zai ba su daman shiri da kyau. Ana gobe za a raɗa suna bayan Mommy ta tafi gida Galadima ya shigo ɗakin Zaytoonah. Tana zaune tana shan tea yayinda 'yan biyun ta ke kwance a gadon su mai kyau. Dai da ya bi yaran sa ya tofa mu su addu'a sannan ya manna mu su kiss a goshi kafin ya ƙariso wajen ta. "Ya ƙarfin jiki?" "Alhamdulillah" "Na mu su huɗuba da Hassan da Hussain, akwai inkiyar da ki ke so a sa mu su?" Tun ranan haihuwan ta ji sunan yaran a bakin Mommy. Kuma shima da kan sa ya faɗa ma ta. "Are you Ok? Ko mu koma Asibiti ne?" Zaytoonah ta girgiza ma sa kai. "Sannu kin ji. Allah ya mi ki albarka" Ta amsa da amin a ranta. Sai da ta ƙarisa shan tea ɗin kafin ta kalleshi ta ce "Humairah tana son a kira su da Aahil da Aamir" "Ke mi ki ke so?" Shiru ta yi ba ta ce komai ba. Juyo da ita yai tana fiskantar sa sannan ya ce "Zaytoon miya ke damun ki? Mi ki ke so? Na lura kaman ba ki damu da yaran nan ba" "Yadda 'yan uwan ka ke tarairayan yaran nan, idan da ace mata na haifa kana ga za su mu su haka?" "Subhanallah!" " shekaran jiya. Ina ji Hajia Abu tana faɗin yanzu kam ka samu magada. Ina jin yadda maroƙan da su ka zo daga Fada su ka dinga yiwa yaran nan kirari and i wonder idan da Mata na haifa za a mu su irin wannan, shin za su samu gata irin wannan" "Zaytoon" "Miyasa ba a ɗauki 'ya'ya mata a bakin komai ba. Why is it always about having a son..." Yatsun sa biyu ya sa ya rufe ma ta baki. "Ba na son sake jin maganar nan a bakin ki, kai makamancin wannan maganar ma ba na son jin ta" Ya riƙo hannunta ɗaya ya ɗaura a dai-dai ƙirjin sa ya ce "ba ni da ikon sarrafa wannan zuciya a lokutan da ta kwaɗaita min samun ɗa namiji. Amma nan" ya kai ɗaya hannun sa dai-dai gefen kan sa. "Ƙwaƙwalta tana tunatar da ni cewa na karɓi duk kyautan da Allah ya bani a matsayin abinda ya fi dacewa da ni wannan yasa a kullum na ke gode ma sa. Idan da 'yan biyu mata ki ka haifa i will still love them equal saboda ba kowa ne ma Allah ke bawa kyautan 'yan biyu ba. I'm blessed to have them. Kinga 'yar uwata Hajiya Zainab dama kowanene da ya dangance ni ba ruwan ki da su ko abunda za su faɗa. Ruwan su ne su so abunda ki ka haifa ruwan su ne su ƙi su. Abu ɗaya na ke so ki sani, wanda ki ka haifawa yaran nan yana son kayan sa and any other person's opinion shouldn't matter to you. Kar ki sake ɗaga maganar nan dan raina na ɓaci idan kina yin ta" Kwantar da kan ta tayi a ƙirjin sa tana fidda hawaye... Washegari a Fada aka raɗa wa yara sunan Hassan (Amir) da Hussain (Ahil) duk da an ɗaga taron suna zuwa wata sati hakan bai hana an ɗan yi shagali ba. Kafin sati ya zagayo Zaytoonah ta sake murmurewa, damuwa da ta sa a ran ta shima yanzu ta cire saboda yadda Galadima da Mommy ke ƙarfafa ma ta gwiwa. Ranan taron suna tun da safe aka fara shagali. Anyi wani a gidan Galadima da safe ƙarfe goma zuwa shabiyu sannan aka sake yin wani a Fada da yamma wannan karan ma har hawa aka yi dan taya Galadima haihuwar 'yan biyun sa. Washegari kuma du Hajia Abu ta haɗa wuni a gidanta. Duk wannan shagali da akayi babu wanda Ghazala ba ta halarta ba. Da ta ji labarin haihuwar Zaytoonah. Kiran Galadima ta yi amma bai ɗauka ba dan haka ta tura ma sa text na taya murna daga ba ya ya dawo ma ta da reply ɗin 'Amin na gode' Duk wani shige da fice da ta ke yi a wajen taron sunan ƙoƙarin ta na son samun Alfarmar Hajia Abu ne. Ta sani indai Hajia Abu ta yafe ma ta to tanada 80% chance na komawa gidan Galadima, sai dai abinda ba ta sani ba shine Hajia Abu kaifi ɗaya ce, idan har ta riga ta yi magana to da wuya ta chanja. Bayan shagalin suna Galadima ya koma Abuja ya bar Zaytoonah a Zaria tana samun kulawa. Sai da Ghazala ta dai-dai ci Galadima ya kusa dawowa ta kai ma sa ziyara gida wai ta je gaishe da yaran sa. Raziya kam ko kallo ba ta isheta ba ta wuce ɗakin su ta barta a falon tareda sauran. Suma ɗin de ba su wani sake jiki da ita ba tunda sun ɗanɗani muguntar ta. Sanda Galadima ya dawo ya ganta a gidan sa mamaki ne ya bayyana a fiskar sa ya dai yi saurin saita kan sa suka gaisa a mutunce. Zai wuce sama ta ce da shi wai wajen sa ta zo. Bai amsa ma ta ba ya haura sama ya barta da dake baki. Kusan awa ɗaya kafin ya sauko bayan yayi wanka ya chanja kaya. Ya sha mamaki da ya sauko ya tarar da Ghazala ba ta tafi ba. Zama yai a kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya. "Ina jin ki" A tunanin ta zai cewa su Suhailah su ba su waje amma bai yi magana ba. Duk da ta san hankalin su na kan kallon da su ke amma yaran zamani sai a hankali. Ganin shirun ba zai ƙwace ta ba ya sa ta kallon Falaq ta ce a hankali "Falaq ke da ƙannen ki ku ɗan bamu waje za mu yi magana" Falaq ta kalli Ghazala sannan ta kalli Galadima wanda ke faman latsa waya. "Hashir, Hadid, Suhailah let's go upstairs" Yaran su ka miƙe suna ƙunƙuni. Bayan yaran sun bar wajen ne Ghazala ta fara magana "Ranka shi daɗe na sake dawowa ne da ƙoƙon bara ta. Wallahi na ma ka alƙawarin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ka rufa min asiri ka maida ni dan Allah" Bai san da wani yare zai wa Ghazala bayani ta gane zaman su ya ƙare ba. "Indai akan wannan maganar ne kar ki sake nema na. Ki ƙaddara wa kan ki cewa iya zaman da Allah ya rubuta tsakanin mu kenan" Miƙewa yai ya fice daga gidan dan ya wuce masallaci, tsayawa dogon magana da ita ɓata lokaci ne kawai. Auren ta da Galadima ya kawo ma ta wani daraja na daban a wajen mutane. Da sunan Matar sa ta samu shiga wajaje dayawa cikin 'yan shekaru biyu da burbuɗi da su ka yi tare. Dama ne Allah ya ba ta a sama amma ta yi wasa da shi. May be ta rasa Galadima kenan har abada. Zuwa Zaria da su ka yi Zaytoonah ta ji labarin zuwan Ghazala gidan su a bakin yara. Da dare da Galadima ya dawo zai ci abinci ya lura da wani kumbura fiska da Zaytoonah ke yi ya tambayi ko lafiya. "Ashe dai manyan baƙi aka yi a gidan" Bai ɗauka gidan sa na Abuja ta ke nufi ba shiyasa ya ce "suwaye su ka zo?" "Ko da ya ke ma ai 'yan gida ne ma, tunda ai da ba a basu lasisin shiga ba ba za su shiga ba" Galadima ya tsaya yana kallon ikon Rabbi a wajen chubby wife ɗin sa. Ganin bai tanka ma ta ba ya sa ta cigaba "ba ni da hurumin hanaka dawo da ita amma ka sani ba za mu zauna gida ɗaya ba. Infact ka barta a chan Abuja zan zauna a nan kusa da Iyaye na" Sai a lokacin ya gane maganar zuwan Ghazala ne ya jawo wannan haɗa ran. "Daɗina da ke saurin karaya, yanzu har kin sallama ma ta mijin ki kenan?" "To ai kai ɗin ne, kuma sai ka bari ta zo gidan ka, kuma ma..." "Zaytoon aure na da Ghazala ya ƙare Insha Allah" Ya katse ta "Ba dan komai ba sai dan bana son zaman zargi. Idan na maida ta ba zan taɓa yarda da ita kaman yadda ya dace ba, wannan kuma ba zama ne da ya dace da ma'aurata ba" "Ni dama fa kawai..." "Ki na son mijin ki ke ɗaya ko?" "Ni ban ce ba" "Kenan kin yarda na ƙaro mi ki ƙanwa?" Zaytoonah ta haɗa rai ta fara mita " ai dama ku ma su sarautan nan ba kwa taɓa zama da Mace ɗaya. Daɗin ta ma bani da lokacin kowacce shegiya, hidimar gaba na ya ishe ni..." Manna ma ta light kiss yai abaki sannan ya ce " ba ni da ra'ayin ajiye mace sama da ɗaya. Ƙaddara ce ta sa na auri Ghazala bayan ke. Ki yi addu'ar Allah ya bar mu tare har ƙarshen rayuwar mu. Amma idan wani ƙaddaran ta ratsa sai dai..." Ta rufe ma sa baki da na ta. Lokacin da ta janye bakin ta hannun ta duka biyu ta tallafo fiskar Galadima ta ce "Insha Allah babu ƙaddaran da zai sa ka ƙaro wata mace gidan nan. Ni kaɗai zan tanadi Tsoho na" ta ƙarisa maganar ta manna mi shi peck a goshi. Wannan karan hannunta ta sa ta fara bashi abincin a baki... Da maganar zargi Muhsina ta wuni ta kwana a gidan ta. AbdulHameed tunda ya fita office bai dawo ba, ta yi ta kiran numbar sa amma switched off. Ba abinda ya fara yawo a ranta irin yana chan yana tareda wata karuwar ce. Da safe cewa ta yi indai bai dawo ba zuwa ƙarfe goma shabiyu na rana tattara kayanta za ta yi ta tafi domin ba za ta iya ba. Dama dai zaman na su har yanzu babu wani armashi. Ranan da yai ƙoƙarin kusantar ta shi kaɗai yai kiɗan sa ya kuma taka rawan sa, wannan ya sa ya haƙura bai sake neman ta ba. Da safen zuwa ƙarfe shaɗaya wani abokin sa ya kirata akan ta zo ta same shi a Asibiti. Tsoro ne ya kamata, ta tambayeshi mi ya ke faruwa amma ya ce ba komai. Lokacin da ta isa Asibitin ne ta haɗu da Saminu wanda ya sanar da ita abinda ya ke faruwa. Daga office ɗin su AbdulHameed ne aka kira su akan Ogan sa ya rasu a Mangu, Jos. Da ke dama tunda ya fara jinya ya koma wajen 'yan uwan sa da zama. Kusan mutum huɗu su ka tafi ta'aziyar ciki kuwa harda AbdulHameed sai dai shi da dare ya mu su a chan Jos ɗin cewa yai ba zai kwana ba, ƙarfe tara na dare ya biyo motar haya zuwa Abuja. A hanyar su ta dawowa kuwa motar su ta yi hatsari cikin motar kuwa su biyu ne ba su mutu ba da shi da wani Tsoho. ID card na shi da aka samu ne aka tuntuɓi wajen aikin su shine yau da safe aka je aka ɗauko shi a Asibitin da ke Akwanga saboda bai wani ji rauni sosai ba. Muhsinah na jin bayanin Saminu ta fara hawaye. "Yana ina?" "Yana barci kuma Likita ya ce kada a dameshi. Amma mu je ki gan shi" Muhsinah ta bi bayan Saminu da sauri. Ciwo ne ya ji a kafaɗa da kuma goshi sai glass da ya yanka ma sa gefen kumatu shima an ɗinka an rufe da bandage. Muhsinah ta zuba ma sa ido tana ƙara godewa Allah da ya kuɓutar ma ta da Miji. Take ta ɗau alƙawarin kula da shi even if it pains idan ta tuna da abinda ya ma ta a baya. *** Ahil da Amir na sati biyar Zaytoonah ta koma Abuja da zama. Abin mamaki Hajia Abu ne ta kawo ma ta wata tsohuwa irin hadiman Fadan nan wacce za ta dinga yiwa yara wanka da kula da yaran idan sun je chan. Zaytoonah ta ji daɗin zaman matar dan gaskiya ba laifi matar na da tsafta kuma tsohuwa ce mai mutunci ba irin yarjalallun tsofi ma su haɗa guri ba da fitina ba. Duk da Daddy ba a faculty ɗin ya ke ba amma matsayin sa na lecturer a ABU kuma mijin Maryam Nkiru Uzodinma ya sa ya tsaya tsayin daka a wajen da Mommy ke defending thesis ɗin ta. Duk abubuwan da yai ta faruwa da iyalin ta ya sa ba ta gama thesis ɗin da wuri ba. Amma finally ta gama komai and she successfully defended her Phd. T J ne ya je ya riƙo hannun ta ya ma ta jagora su ka fito daga hall ɗin. Ta yi ƙoƙari, ta burge mutane da dama a wajen. Finally she's now Dr Maryam Nkiru Uzodinma (Mrs Dr Tijjani Abubakar). Ranan Jummu'a kuwa T J ya shiryawa Maryam da Salman ƙaramar walima a gida saboda murnan kammala karatun su. Mommy Phd shi kuma Salman Bsc. Humairah ta zo, tana nan da ƙaramin cikin ta da ya ɗan fara fitowa. Zaytoonah ma ta zo weekend dan haka da ita aka yi komai, harda cewa wai itama dole a mata na ta dan sanda ta gama karatu ai Mommy ba ta ma ta walima ba. Daddy ya ce kar ta damu idan Humairah ta gama na ta karatun zai haɗa yai mu su na su. *** *Bayan shekaru biyu* Ahil da Amir ba inda ba sa zuwa da ƙafafun su. Rigiman su kuwa tafi ta su Hashir da Hadid. Bayan su kuma ga naughty Alinah. Da ana cewa Falaq ce ba ta son magana amma wannan ta taka Falaq, tana ƙara girma kuwa kamannin ta da Falaq ɗin na sake bayyana. Haske da jiki kawai Alinah za ta fi Falaq amma kamannin su ta fiska kam kusan 90% sak ne. Sai yanzu ne ma Zaytoonan ke nuna jarumta, kulawa da 'ya'yan ta da 'ya'yan mijin ta was not easy, duk da kuwa yanzu kyakykyawar alaƙa ne tsakanin ta da yaran. Raziya ta gama secondary school ta ƙara hankali sosai. Yanzu kam har secrets ɗin ta tana gayawa Zaytoonah. Tun kafin ma ta faɗawa Zaytoonah ta riga ta gano soyayyar da ke tsakanin ta da ɗan uwan ta Ahmad. Ta san Galadima ba zai taɓa aurar da ita a sixteen years ba shiyasa aka saka Galadima a duhu zuwa lokacin da za ta kai kaman 18yrs sai a sanar da shi. Tana dai kula da lamurran yarinyar dan da ta yiwa Mommy maganar shawara ta ba ta akan ta sa ido akan ta sosai duk da cewa Ahmad ɗan uwan ta ne amma yanzu ba a shaidar maza 100%. Idan wani abu ya faru da Raziya sunan ta za a fara kira saboda ita ke zaune da su kuma kaman uwa ta ke a wajen ta. Yanzu ma maganar karatun ta ne ya kawo saɓani tsakanin Galadima da Zaytoonah. Raziya ta nuna tana son ta yi karatu a ƙasar waje shi kuma Galadima ya ce ba inda za ta je a Nigeria za ta yi, ba zai barta ta je nisan duniya da ƙarancin shekarun ta ba. Zaytoonah kuma ta nuna ba komai acikin tafiyar Raziya ya dai bi ta da addu'a kawai shine fa Galadima ya hau fushi. Lokacin da ya shigo ɗaki tana haɗa ma sa kaya dan gobe za su wuce Zaria saboda bikin sallar Layya da za ayi, nan da kwana uku. "Sannu da zuwa Sayyadi" "Yawwa" Kallon sa ta yi sadda ya zo ya shige banɗaki yana wani shan ƙanshi. Ta sani itama ba ta yi adalci ba yadda ta gaya ma sa magana gatsal haka ranan. Duk da daga baya ta ce yai haƙuri amma still bai sake kulata ba. *"ni na rasa yanzu ko tsufa ne ke taɓa ka. Idan har @51 kana irin wannan idan ka je 60 ya dai za mu ƙare a gidan nan. Idan fa mace za ta lalace ko tana karƙashin inuwar ka ce sai ta lalace. Ka barta ta tafi dan Allah, ko da anan ɗin za ta yi karatu we can only pray for her Allah ya kare mana ita"* Yadda ya tashi tsaye ya shige ya barta zaune a falon ne ya sa jikin ta yai sanyi tabbas yau ta tsokalo Dodo. Lokacin da ya fito daga banɗaki ɗaure da towel ne tana zaune a bakin gado tana jiran sa. Lokacin da ya ke ƙoƙarin shafa mai ne ta karɓi man a hannun sa ta fara shafa ma sa, bai musa ma ta ba sai ma maida kan sa gefe da yai. "Allah ya ja zamanin Daddyn Alinah. Ka san Allah yau 'yar ka sai da ta bani tsoro a gidan nan" Juyowa yai da sauri dan indai maganar 'ya'yan sa ne ba ya wasa da su musamman ma Alinah. "Mi ya faru?" Ya tambaya ganin ta yi shiru. Ƙaramar dariya ta yi ta ce "ai yanzu ka yi magana da ka ji zancen gimbiyar ka" Ganin ya ɓata rai ta ce "haba Masoyi na, na ba da haƙuri fa, har sau biyu. A taimaki baiwar Allah, punishment ɗin ya isa haka Uban biyu biyu" "Ki haɗa min tea" "An gama Ranka shi daɗe" fiskarta ɗauke da murmushi. Bayan ta taimaka ma sa ya saka kaya sannan ta fita daga ɗakin ta yi kitchen da sauri. Sai da ta isa falon ne ta tsaya turus ganin dramar da ake yi a wajen. Da sauri ta koma ɗakin ta ce Galadima ya zo ya ga ikon Allah a wajen yaran nan. Dukkan su biyu suka zubawa yaran ido. Alinah ce kaɗai zaune a kujera wani crown ribbon ɗin ta da aka sa ma ta lokacin birthday ɗin cika three years ne akan ta. Hashir na ma ta fifita yayinda Ahil, Amir, Hashir da Suhailah su ke durƙushe a ƙasa wai ana Fadanci. "Ina ga wannan karan idan mu ka je Zaria gidan Hajia Abu zan je na jibge 'yar nan, ba zan iya da wannan mulkin ba" "Sai ki yi ai. Mulki ai gadon gidan su ne dole a gani a jikin ta" "Hmmmm" Ƙarasawa yai wajen yaran ita kuma ta wuce kitchen ɗin. *** Da wasa ta ɗauki maganar Galadima lokacin da ya ce hawan bana harda Alinah za ayi. To her surprise sai gashi da kan sa ya kawo ma ta kayan da za a sawa Alinah. "Sayyadi ba dai maganar Raziya ka ɗauka ba" "Ki shirya min ita" "Daddyn Alinah cikin ɗinbin mutane, ka san yadda..." "Allah zai kare min ita" Mi za ta ce kuma tunda dai 'ya dai tashi ce. Washegari hawan sallah da aka yi kuwa harda Alinah. Dokin ta ke gaba yayin da na Galadima ke bayan ta. Mutane huɗe ke riƙe da dokin na ta suna kula da ita. Ranan kam ta nuna cewa ita ɗin 'yar Baban ta ne. Yadda ya ke murmushi a wasu waje, wasu wajen kuma ya haɗe rai haka itama ta ke yi. And duk inda aka ratsa kowa na ƙoƙarin ɗaukan hoton kyakkyawar yarinyar da ta cinye hawan wannan shekara. Wasu wajen idan su ka wuce sai ka ga yara da manya kowa na ƙoƙarin miƙa ma ta kyauta wanda hadiman ta ke karɓa ma ta. Ba a jima da fara hawan ba Hajia Abu ta kira Zaytoonah da ke cikin ma'aikatan gidan tana lura da yadda ake ta gudanar da girke-girke, hidimar sallah was always tough for her. Tun safe har dare ba ta samu isashshen hutu, idan aka fara fitar da abincin sai ka ɗauka duka anguwar za'a ciyar. Ga baƙi nan ma su zuwa ta ko'ina. "Zaytoonah da hankalin ki ki ka bari aka fita hawa da Alinah? Idan wani abu ya same ta fa? Ba wannan ba ma idon mutane fa guba ne" Yau ɗaya ta ji daɗin maganar Hajiya Abu, atleast dai yau ta damu da 'yar ta duk da ma ita ɗin mace ce. "Na ma sa magana ya ce wai na ma ta addu'a kawai" "Allah ya kyauta, ni ban san miyasa ya ke son ta fiye da sauran ba. Yadda ya ke ji da ita ko Hassan da Hussain ba ya jin su haka. Allah dai ya tsare" Zaytoonah ta girgiza kai tana jinjina ƙarfin hali irin na wannan mata. Yau da ita ta haifi Galadima da sun shiga uku. Bayan Hajia Abu da ta kira Mommy ma sai da ta kira ta ma ta faɗa. Ita kam daga baya ma dariya su ka ba ta, ba fa ita ta ɗau Alinah ta ɗaura a doki ta turata waje ba fa. Wanda ta ke amsa sunan sa ne ya jagoranci komai. An dawo da Alinah da wuri amma Galadima kam kafin ta samu kan sa sai kusan ƙarfe sha ɗaya na dare. Ko da ya dawo ma yana tareda baƙi ne all through daga baya kuma ya sake fita. Taimaka ma sa ta yi yai wanka da ruwan zafi sosai. Gaba ɗaya jikin sa ne ke ma sa ciwo musamman kwankwason sa. Zama a kan doki, zama a fada, zama don tarban baƙi. Kayan da ya saka ma su kauri da naɗin turban da ke kan sa tun safe har yamma duk ya weighing na shi down. Kwantawa yai ruf da ciki Zaytoonah ta shiga yi ma sa matsa. Itama 'yar ta shi ta jigata sosai dan ƙarshe ma Zaytoonah na ba ta abinci ta buge da bacci. Zaytoonah ta ce rigimammiya gaba ma ki ƙara. But secretly kuma ta ji daɗin hawan da aka yi. She's proud of being the mother to Alinah. Tun kafin a ƙarisa ma sa dannar shima bacci ya ɗauke shi. Sai da ta fita ta leƙa ɗakin 'yan'yan ta ta tabbatar kowa na bacci lafiya kafin ta dawo ɗakin Galadima ta kashe wuta ta kwanta kusa da shi da murmushi ɗauke a fiskarta *** A watan da za a kai Raziya makaranta a Malaysia ne su ka je ƙauyen su Mommy, inda Mommy ta buɗe Asibiti da Makaranta a ƙauyen mahaifinta wato Ukwuohia mai suna *Caroline and Patrick Memorial Hospital* da *Caroline and Patrick High school* in memory of her parents. Kwana uku Zaytoonah ta yi a ƙauyen ta koma Abuja saboda ita da Galadima za su raka Raziya, daga nan kuma su wuce Las Vegas. Farha ta haifi ɗa namiji watan da ya wuce tunda ba ta samu zuwa bikin ta ba ya kamata ta je ta ga baby boy wanda ya ci sunan Ayman Muhammad Chu. Nonetheless kuma ya kamata ta je ta duba lafiyar business ɗin ta dana 'ya'yan ta. Su Mommy kam za su kwana biyu a chan dan wani mini vacation za su yi kafin su koma Zaria. Mata da Miji sai Allah. A hankali Zaytoonah ta shawo kan Galadima ya amince Raziya ta yi karatu a Malaysia amma za ta zauna a gidan wani cousin ɗin Galadiman ne ta wajen Uwa. Maganar Ahmad da Raziya na nan dan last last Zaytoonah ta fito fili ta faɗawa Galadima komai shi kuma ya ce a bari zuwa shekara biyu idan ta ƙara girma. Shima Ahmad ɗin ƙoƙarin yin masters na shi ya ke dan haka abun zai faɗa mu su a dai-dai. Kwana biyu su ka yi a Kwala Lampur, Malaysia sannan su ka wuce Las Vegas. Su biyun tol ɗin su su ka tafi, yaran duk sun damƙa su a Zaria. Ahil da Amir na gidan Hajiya Abu sauran kuma na Fada. Hashir da Hadid kuma a wajen Humairah ta bar su, itama Allah ya ba ta haihuwan ɗa namiji Mukhtar suna kiran shi Ayan. Sunan Daddy Auwal yai niyyan sawa amma da ya gayawa Daddy sunan da ya zaɓa sai Daddyn ya ce a fara yiwa Muntari takwara tukunna, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yai wa Iya ba dan Alhamdulillah Allah ya haɗa ma ta kan 'ya'yan ta. Shi kam Muntari ranan suna da ya ji sunan sai da ya yai hawaye. Jikin sa ya samu sauƙi dan yanzu maimakon wheelchair da ya ke zama da sanda ɗaya ya ke tafiya. Zaman sa haka ya sa Iya ta yiwa T J magana akan ya nema ma sa Mata, shima maganar dama na ran sa kawai ta rigashi fitar da shi ne. Ita ya bawa wuƙa da nama akan ta nemawa Muntarin Mata, ba a jima ba kuwa ta sama ma sa wata bazawara a Ringim kuma aka ci sa'a da aka yiwa Muntarin magana ya amince. An riga an saka rana, idan su ka dawo da ƙauyen su Mommy za a ɗaura aure. Maganar Salman da Azma ma ta yi nisa, ba dan Mahaifinta ya ce sai ta ƙare karatu ba kafin ayi bikin da tuni anyi. Kullum Salman cikin lissafi ya ke yanzu haka yana lissafin saura wata takwas ta zama graduate, tunda idan an ƙare hutu ajin ƙarshe za ta shiga. *** A ranan da su ka sauka a Vegas Muhsinah ta turawa Zaytoonah text akan ta sauka an samu ɗa namiji. Zaytoonah ta kirata ta dinga ma ta tsiya. Bayan ta ajiye wayan ne Galadima da ke gefe ya ce "nima har yanzu ba wani motsi ne" ya ƙare maganar yana ɗaga ma ta gira. "Ba ni da komai Yallaɓai. Inaga ma na sallama haihuwa yanzu kam" "Kin bani lasisin na kawo dalleliyar budurwa kenan" "Ta zo mana. Tunda ragowa za ta samu" "Ragowa ko?" "Ragowa mana, ai mun riga mun ci moriyar ganga" "Ehm ko?" Zaytoonah ta riƙe ƙugu ta ce "sosai ma kuwa" Ba ta ankara ba sai ji ta yi yayi sama da ita. "Wannan nauyi da ki ka ƙara anya ba ku biyu ba ne kuwa?" "Ka manta mu shabiyu ne" Dariya yai itama ta saka dariyan yayinda ya sauketa akan gado a hankali. Ya ma ta rumfa ya ce "to bari a cigaba da cin moriyar ragowan" *** Washegari da safe su ka wuce gidan Farha. Wanda ya san Farha da ba zai taɓa tunanin aure da haihuwa zai nutsar da ita ba. Gaba ɗaya ta zama reaponsible and calm woman. Ba ƙaramin so take yiwa Muhammad Chu ba and baby Ayman yana ganin gata a wajen slay Mom. Ba su suka baro gidan ba sai yamma. Daren ranan ne kuma Ghazala ta turawa Galadima text akan an saka auren ɗan ta, nan da wata biyu. Galadima ya tura ma ta reply da Allah ya sanya Alkhairi. Farko-farkon haihuwan 'yan biyu ta yi ta damun sa da saƙonnin ban haƙuri da kira akan ya taimaka ya dawo da ita. A ƙoƙarinta na son samun shiga ne ma ta haɗiye girman kan ta ta kira Zaytoonah ta ba ta haƙurin abinda ta ma ta. Zaytoonah ta ce ta yafe. A ranan kuwa ta turawa Galadima text akan tunda Zaytoonah ta yafe ma ta ai yanzu kam ba sauran wata matsala zai iya dawo da ita. Abin ya bawa Galadima dariya, shi kaɗai ya ci dariyan sa ya ƙoshi dan ya san idan Zaytoonah ta ji yanzu itama za ta hau jirgin kishi. Bayan ya gama dariyan kuwa ya tura ma ta saƙon da ya hana ta bacci. *Sorry, kin riga kin yi wasa da damar ki. Ina mi ki addu'ar Allah ya ba ki miji wanda ya fini* "Kutumar chan, wani mijin zan samu da ya fika? Wani mijin?" Sai dai babu mai ba ta amsar tambayarta. Ita ɗin dai da ta tambaya, still ita za ta ba wa kan ta amsa. Mummunan ƙarshe da Hajia Ajwa ta yi ya sa ta ma dena tunanin sake biyewa Hajiya Safara'u wajen neman magani. Hajiya Ajwa ta zo ta yi mutuwar ƙasƙanci ne kafin ta mutu jikin ta yayi wani irin kumburi, wasu munanan ƙuraje ma su fitar da ruwan ɗiwa mai wari su ka mamaye jikin ta. Auren 'yarta Mubaraka da Yusuf da ba ta so kuwa anyi kuma kafin ta rasun ma Mubarakar ta haifi ɗa namiji su ka yiwa Galadima mai suna. Shalelen mijin na ta kuwa da ta dinga bin tafarkin sheɗan saboda shi kafin ta mutu yana nan zaune da matan sa biyu lafiya-lafiya dan bayan Uwargidan sa Hajiya Fatima da ya dawo da ita ya auri wata budurwa Shamsiyya 'yar ƙabilar Nupe. (Babu namijin da ya chanchanci ki bijirewa Allah saboda shi. Babu namijin da ya kai ki watsar da ilimin ki da tauhidin ki saboda shi) Ghazala kusan shekara ta yi tana bibiyar Galadima akan ya maida ta. Bayan 'yan uwa har da abokan sa na kusa da shi duk ta bi ƙafan su amma all in vain. Ta riga ta rasa shi kenan, har abada. *** Ruwan sama ake tsalawa kamar da bakin ƙwarya a ƙauyen Okwuohia. Sallama su Mommy su ka zo yi mu su bayan sun sake duba yadda ake ta kan gudanar da Asibiti da kuma Makarantar da aka buɗe. Washegari za su wuce Owerri daga nan su hau jirgi su koma Kaduna then to Zaria. Zuwa ƙarfe tara na dare ruwan ya fara tsagaita. Bayan sun gama cin abinci Maryam ta ce wa T J tana da surprise ɗin da za ta bashi. Cewa ta yi ya fita daga ɗakin za ta kira shi idan ta gama shiryawa. T J ya koma falo ya zauna yana jiran surprise ɗin, cikin ɗan mintuna da yai a wajen kafin kiran Maryam ya shigo sai da yai ta tunani kala-kala ciki kuwa harda hasashowa ko dai Maryam na da ciki ne, zuciyar sa ta ce kai ba ciki ba ne. Ciki bayan ta fara bawa shekaru hamsin baya, but you never know. Ba abinda Allah ba zai iya yi ba. Ya zo yai tunanin ko dai Zaytoonah ce ke da cikin ko kuma Humairah. Ko kuma ma dai ta ji labarin ana son a awarding na shi professorship ne. A hankali ya buɗe ɗakin kamar mai tsoron wani abu. Ya shiga ciki jiki a sanyaye, sai dai fiskar sa da ke ɗauke da fargaba ne ya koma wasai lokacin da ya ci karo da matar sa da ta yi shiga na 'yan matan ƙabilar Igbo. "Na ce barin tuna ma ka da yadda komai ya fara, once upon a time in December 1985" Wayar hannunta ta ajiye bakin gado lokacin da ta kunna waƙar su ta igbo wanda ke ɗauke da beat irin na gargajiya. T J ya sake baki da hanci da ido duka yana kallon yadda Maryam ta ke bin beat ɗin waƙar a hankali tana rawan Atilogwu. Ikon Allah kenan, kaman yau ne fa ya ga wata budurwa tana rawa irin wannan tareda wasu 'yan mata. Yadda yarinyar ta ɗauke ma sa hankali a lokacin hakama wannan mata ta ɗauke ma sa hankali yanzu. Shekarun da su ka ja bai sa wani abu cikin son da ya ke ma ta ya ragu ba sai ma ƙaruwa da yai. Bai taɓa sanin cewa ƙaddarar samun mar'atus saliha shi ne ya sa aka tura shi bautar ƙasa jahar Imo ba. Bai taɓa sanin ƙaddarar haɗuwa da uwar 'ya'yan sa ne ya sa ya bi Eze zuwa kallon bikin Mbom-uzo a ƙauyen Okwuohia ba. Bai taɓa sanin cewa taho da Mary-Nkiru zuwa Ringim shine best decision ɗin da yai a duniya ba. But now he knows one thing, Allah ya bashi kyauta mai daraja a duniya, and wannan mata yana fata Allah ya haɗa fuskokin su a Aljannah. A chan Las Vegas kuwa Galadima ne ya zubawa wani hoto da ya tsinta ido, cikin wani drawer ya ga hoton. Zaytoonah ne sanye da kayan ballet dance, ta chaka ƙafa ta buɗa hannayen ta kaman mai shirin furkawa sama. Zaytoonah da ta fito daga wanka ta sameshi yana kallon hoton. "Wani hoto ne wannan?" "Ba ki taɓa gaya min ke Ballerina ba ce" ya faɗa yana ɗaga ma ta hoton "That was then ai, tun ma fa kafin na haifi su Hadid ne" "To yau Allah ya kamaki, sai a min rawan na gani" "Tabɗi! Ka san yaushe rabon na yi rawan ballet kuwa?" "Ban san wannan ba, all i know shine i want to see you dance for me" Duk yadda ta so ta zille Galadima bai barta ba, ala dole ta nemi riga da wando ta saka. Cikin soft theme music da ta ke da shi a wayarta ta kunna ta fara yin rawan. With every step da ta ke yi Galadima stood there silently watching her in awe. Tunanin tsohon mijin ta ne ya zo ma ta, yadda ya dinga supporting ɗin ta all through rayuwan su tare. Ta tuna ranan da ta yi ma sa rawan ballet na ƙarshe yadda ya dinga murmushi cikin jin daɗi. Yanzu ma murmushin Galadima ke yi har da ɗaga ma ta babbar yatsar sa yana ma ta thumbs up. She's so lucky da Allah ya haɗata da maza biyu ma su tsananin son ta, not only that. Su ɗin mazaje ne na ƙwarai. Hajijiyan da ta fara ji ne ya sa ta yi saurin dakatar da rawan. Galadima yai saurin zuwa ya rungumeta jikin sa. "I'm proud of you Zaytoon" Galadima ya faɗa a hankali. Hawaye ya fara zubowa a idonta a lokacin da muryan Zuhayr ya doki kunnen ta " I'm proud of you Zaytoon. Daga yanzu ina so ki yi ƙoƙarin zama duk abinda ki ke so a rayuwar ki, with courage and confidence. Ka da ki taɓa bari wai ƙibar ki ya hanaki yin wani abu da ki ke so. You are beautiful just the way you are and i love you just the way you are" Muryan Galadima ne ya fargar da ita daga tunanin da ta ke yi inda ya ke cewa "I love you Zaytoon, ina alfahari da kasancewar ki mata ta. Allah Ubangiji ya haɗa fuskokin mu a gidan Aljannah. Ina son kasancewa da ke har ƙarshen rayuwa ta and even beyond. Allah ya ƙara mi ki Albarka Zaytoon" Zaytoonah ta amsa da Amin zuciyar ta cike da farin ciki. Duk yadda rayuwa ya juya da ita, daga ƙarshe ba abinda za ta ce sai dai Alhamdulillah!!! *Alhamdulillah. A nan na kawo ƙarshen labarin Chronicles of Zaytoonah*