[9/15, 10:09 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARAH. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 1. Wani irin gudu motar su ke shararawa a saman titi kamar za ta tashi sama. A daidai wannan lokacin kuwa Yunus dake zaune a bayan mota yana buga tsaki ya ɗaga hannunsa ya sake duba agogon hannunsa tare da jan wani dogon tsakin a karo na babu adadi. Cikin ransa yake jin kamar ya karɓi tuƙin motar ya ratsa ta lunguna ko Allah zai sa ya yi saurin isa gida da wuri domin ya samu sallar juma'a akan lokaci. A ƙagauce ya kalli Malam Sadi direba ya ce. "Man Sadi ko za mu yanki wannan layin ne mu tsaya kawai mu yi sallahr mu a masallacin Shaikh Shu'aib; domin na kula idan muka ce sai mun je gida lokaci zai ƙure mu rasa sallar juma'ar gaba ɗayanta." Jinjina kai direban ya yi ya ce. "To Alhaji duk yanda ka ce ayi ai haka za a yi." Cikin abinda bai fi mintuna biyar ba Malam Sadi ya kutsa kan motarsu cikin babban layin dake unguwar Gadon Ƙaya yana fatan su isa da wuri dan su samu sallah akan lokaci. Sun yi nisa da tafiya ya hango cincirindon mutane a gabansu wanda da damar mutanen wajen yara ne suka fi yawa a wajen. Tsaki direban ya ja ya ce. "Nan kuma ko taron me ake yi haka suka tare wa mutane hanya oho?" A ƙagauce ya hau danna horn ɗin motar dan taron ya watse su samu su wuce,amma ga mamakinsa ko gezau yaran nan basu yi ba ballantana su basu hanya,wasu yaran ya hango daga lunguna da saƙon unguwar suna sake fitowa suna leƙen tsakiyar taron. Kafin ya ce wani abu Yunus da ya gaji da jira ya ce. "Je ka ka leƙa ka ga me yake faruwa Please dan na ji har an gama khudba." Da sauri Malam Sadi ya kashe motar ya buɗe ƙofa ya fita har yana haɗa wa da gudu. Yana isa wajen taron sai ya dinga leƙa wa yana janye yaran dake ta leƙe suna faɗin. "Ku casu arna ku casu,ku casu ba mai raba ku,duk wanda ya raba faɗan Nansy Ƙaya tamkar ya raba auren tsohonsa da tsohuwarsa ne." Yana isa tsakiyar filin ya ci karo da wata yarinya fara wadda ba za ta wuce shekaru sha uku zuwa sha huɗu ba a duniya,yarinyar tana da matsakaicin tsawo da girman jiki. Zaune take a saman wani bokiti tana zane a ƙasa kamar babu abinda ya dame ta a gidan duniya. A gefenta na hagu kuwa wata ƙatuwar yarinya ce wadda za ta girme mata tsaye tana cika tana batsewa tare da faɗin. "Kin ga dai na ce miki ki ɗaga min bokitina na tafi gida jirana ake yi ko?" Kai yarinyar dake zaune a saman bokitin ta ɗaga tana zabga wa ƙatuwar dake girgiza ƙugu harara ta ce. "Ai na faɗa miki idan kina da ƙarfi to ki yi amfani da shi ki ɗaga ni sama ki ɗauki bokitinki. Sai dai da dikkan alamu kurin banza da cika baki kawai kika iya." Malam Sadi na shirin yiwa yaran magana Yunus da ya gaji da jiransa ya biyo bayansa sai ya kama hannunsa tare da girgiza masa kai. Kafin su juya su bar wajen yarinyar nan dake zaune saman bokiti ta yi kukan kura ta kwashe ƙafar ƙatuwar nan ta zubar da ita a ƙasa;sannan ta bi ta ta zauna a ruwan cikinta tana duka kamar an aiko ta. Nan take yaran dake wajen suka kaure da ihu da sowa suna faɗin. "Da kyau Nansy Ƙaya sa ƙato kuka;mata da sun ganki su ɓuya a bayan uwarsu." Jinjina kai kawai matashin nan ya yi suka koma wajen da motar su take suka yi parking a gefe sannan suka ratse taron yaran suka nufi masallacin a ƙafa. Suna isa liman na tada kabbara,dan haka babu ɓata lokaci suka shige masallaci suka shiga cikin sahu. Bayan sun idar da sallah sai suka zauna suka yi azkar sannan Yunus ya fito waje domin ya saka takalminsa su wuce. Ta gabansa Nansy Ƙaya ta zo za ta wuce ita da ƙawayenta tana basu labarin yanda ta yi wa Nabila Bultuƙa dukan tsiya. Yaran sai yaba mata suke yi suna jin daɗin yanda ta zane yarinyar da kowa ke jin matsanancin tsoronta a kaf layin da ma sauran unguwannin dake kusa da su. Babu zato babu tsammani ya ji muryar Nansy tana faɗin. "Ke dalla wannan ɗin ne kyakkyawa? Ba dan kar na rantse Allah ya saka ni a wuta ba da sai na ce Luƙman ɗina ya fi sa kyau." Dariya sauran yaran suka fashe da ita,cikin dariya ɗaya daga cikinsu ta ce. "Ashe dai kin san ƙarya kika yi,shi yasa kike tsoron kada Allah Ya saka ki a wuta." Juyawa ta yi cikin sa'a idanuwanta suka shiga cikin na Yunus dake kallonsu yana murmushi. Cikin sauri Nansy ta ɗauke idanuwanta daga nashi tana haki tare da tattare zaninta ta kwasa da gudu ta sha kwanar layin dake kusa da inda suke. Nan take Yunus ya fashe da dariya mai sauti ya kalli Malam Sadi ya ce. "Mu je ko?" Gaba ya yi Malam Sadi na biye da shi yana mamakin sauyawar uban gidan nasa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Ko da suka isa wajen motarsu sai suka ga an yi rubutu a jikin motarsu cikin salon haɗe manyan baƙi cikin ƙananan baƙi an rubuta. "MoTar NaNSy ƙAyA." Ran Malam Sadi a ɓace ya kalli mai gidan nasa ya ce. "In Allah Ya yarda wannan ja'irar yarinyar ce da suka yi dambe ɗazu ta yi wannan aika-aikar." Murmushi Yunus ya yi ya shafi jikin rubutun ya furta. "Nansy Ƙaya." A hankali,sannan Ya kalli Malam Sadi ya ce. "Mu je ko?" Ba tare da Malam Sadi ya sake furta komai ba ya shiga motar yana cin alwashin ko a hanya ya sake ganin yarinyar,sai ya yi mata shegen duka. Motar su na barin layin fuskar Yunus ta sauya daga farinciki zuwa ƙunci da damuwa. Ta madubi Malam Sadi ya hango uban gidan nasa,cikin sanyin murya ya ce. "Ranka ya daɗe ko dai na kai ka gidanka kawai ka huta?" Murmushin yaƙe Yunus ya yi ya ce. "Ah ah,kai ni gida na gana da ƴan'uwana." Kai kawai Malam Sadi ya jinjina ya ɗauki hanyar gidan Gwani Ibrahim Yunus Gombe. ***************** A guje Nansy ta shiga gidansu kamar wadda aka koro ta da makamai. Tana zuwa tsakar gidan ta ci karo da bokiti cike da ruwa,ba tare da tunanin komai ba ta ɗauki bokitin tare da ƙarasawa ƙofar ɗakinsu ta ɗauki kwandon wanka ta faɗa. Tun tana cire tufafinta take jin wani irin sululin azaba a wuyanta. Tana gama tuɓe kaya ta duƙa ta kindimi ruwa da kofin wanka ta kwara tun daga saman fuskarta ya sauka har zuwa ƙafafuwanta da suka yi fururu. Ƙara ta saki saboda azabar zafin da ta ji a lokacin da ruwan ya sauka a dokin wuyanta da ya sha yaƙushi. Ƙwafa ta yi tare da cin alwashin wannan faɗa babu mai kashe shi har sai ta daki Bultuƙa dukan da zai wanke mata zafin ciwon da ta ji mata a wuya. A gaggauce ta gama wankanta ta fito tsakar gida tana sheƙa dariya kamar mahaukaciya. Babu abinda take tuna wa sai lokacin da ta cika bakin abokiyar dambenta da ƙasa,ga kuma jini yana zuba da yawu mai yauƙi. Da ta kai mata sabon naushi sai ta ce. "Nansy ki bariii,kin ga dai aike na aka yi bana son faɗa ban shirya baaa." Tana tsaka da dariya ta ji an sakar mata ƙoso a tsakiyar kai. Da sauri ta dafe wajen ta juya a fusace tana huci kamar kububuwa. Cikin tsananin ɓacin rai Yah Hauwa ta ce. "Ke dan ubanki wa ya ce ki ɗaukar min ruwan wanka na ki yi amfani da shi? Ko an faɗa miki uwarki ce ta ɗebo min ruwan?" Baki Nansy ta murguɗa cike da tsantsar rashin kunya ta kalli babbar yayar tasu ta ce. "Ko uwata bata ɗebo ruwa ta ajiye ba;ai a bokitinta aka ajiye ruwan,ni na ce mutum ya baro ɗakin aurensa ya zo gidan mutane yana aron kayansu?" Baki Yah Hauwa ta saki tana kallon Nansy, domin kuwa duk gidan suna shakkarta saboda ita ce babba,daga ita sai Lawizah,Sabirah da Hanifah,sannan Rabi da Usman ƴaran ɗakin Kilishi. Nasibah wato Nansy Ƙaya ita ce babba a ɗakinsu,sai ƙannenta mata biyu Faihah da Najlah. Cike da jin takaicin rashin kunyar da Nansy ta yi mata cikin zafin nama ta yi kanta a guje za ta dake ta. Sai dai kafin ta kama ta har ta isa ɗakinsu ta rufe ƙofa ta danne tana dariya. Cike da takaici Yah Hauwa ta tsaya tana haki a tsakar gidan ta ce. "Ai sai dai idan yau ba za ki fito tsakar gidan nan ba Nasibah. Ke har kin isa ki min laifi in yi magana ki yi min rashin kunya? To ko uwarki bata isa ba ballantana ke." Daga can cikin ɗaki Nansy ta ɗaga murya ta ce. "Yah Hauwa na faɗa miki idan muna abunmu ki dena sako uwata a ciki ba kya ji ko?" "Kan uban can kayyasa! Ni kike faɗawa haka Nasibah? Na rantse da...." "To bismillahi,me yake faruwa ne ake ta hayaniya a gidan?" Kafin Yah Hauwa ta yi magana,Malam Sanda Uba Makaɗi;wanda mutane ke kiransa da Makaɗi ya durƙusa ya ɗauki buta ya shiga banɗaki. Nasibah kuwa na jin muryar mahaifinta sai ta buɗe ƙofa ta fito tana karkaɗa ƙugu tana kallon Yah Hauwa tana ɓaɓɓata rai. Makaɗi na fitowa daga banɗaki ya ce. "Ke Hauwa menene haka kike wani cika kina batsewa kamar za ki fashe iye?" Tura baki gaba Yah Hauwa ta yi,sannan ta ce. "Baba ka shiga tsakanina da wannan yarinyar,idan ba haka ba zan karya ta na nakasa shegiya a banza." Cikin sauri Nansy ta kalli Baban nasu ta kyaɓe baki tana wani irin kuka,kai da ka ji kukan ka san na tsantsar makirci ne. Nan take Makaɗi ya ɓata rai ya kalli Yah Hauwa ya ce. "A gabana kike sheganta min ƴa Hauwa? Ke wai me yasa notikan kan ki ba sa aiki ne? Ki dube ki shirgegiya kamar bajimin Sa amma ki tsaya kina faɗa da ƴar cikinki,da Allah Ya kawo rabo da wuri ai da kin aje kamarta. Amma da yake ke ba cikakken hankali gare ki ba shine kika biye mata kuke faɗa. Ni bana son jin me ya haɗa faɗan ki kama gabanki ki koma ƙofar ɗakin tsohuwarki,tunda kin dage ke ba zaki rabu da wancan direban ba,to ga wajen zama nan,duk lokacin da ya gama zagaya duniyar ya dawo sai ya kwashe ki ku yi gaba." Cikin sauri Nansy ta kalli mahaifinsu ta ce. "Kuma Baba ɗazu sai da su Lawal suka zo gidan nan,baka ga yanda suka dinga cin abinci ba har da zubarwa suka yi,da na yi musu magana Yah Hauwa ta kai min duka,ka ga inda ta ji min ciwooo a wuya na. Yiiiiiii." Nasibah ta ƙarasa maganarta tana mai rushe wa da kukan zogi da raɗaɗin da ciwon wuyanta ke yi mata. A hasale Malam Sanda ya yi kan Yah Hauwa ya na surfa mata zagi tare da cin mutunci kamar ba shi ne ya haife ta ba. Cikin tsananin fushi ya ƙarasa maganganunsa da faɗin. "Ah toh,kin dai ji na faɗa miki,ko ki biya abincin da shegun yaranku suka cinye min,ko kuma na ja Allah Ya isa." Kuka mai matuƙar cin rai ne ya ƙwace wa Yah Hauwa. Cikin matsanancin kuka ta kalli Nansy ta kasa cewa komai,sannan ta juya ta kalli mahaifinta dake ci gaba da zagi da aibata mata yaranta kamar ba ƴaƴan sunnah ba. Da gudu ta bar wajen ta nufi ɗakinsu ta hau haɗa kayanta. Ta na gamawa ta zira doguwar rigarta ta saka hijabi ta fito tsakar gida. A tsaye ta tarar da Babansu yana shafa wa Nasibah rob a wuyanta,ita kuma sai wani kukan shagwaɓa take yi tana tsalle. Kilishi da takaicin su Nasibah da mahaifinta ya kai mata ko ina sai ta dinga aiki tana wurgi da kwanuka tare da habaici. Cike da takaici da baƙinciki Yah Hauwa ta kalle su ta ce. "Baba ka yi haƙuri ka yafe wa su Lawal abincinka da suka ci yau,da yardar Allah ko bangon duniya Habu zai je neman kuɗi ba zan sake zuwa gidan nan ba. Allah Ya jiƙan Innani,da tana raye na tabbata ba za ka yi min haka ba." Cikin matsanancin kuka ta bar gidan tana fyace majina. Jikin Malam Sanda ne ya yi mugun sanyi,sai ya sakar wa Nansy rob ɗin ya shige ɗakin Kilishi domin ita ce ke da girki a wannan ranar. Yana shiga ciki Nansy ta faɗa ɗakinsu ta samu gefen gadon da mahaifiyarta ke kwance tana baccin rana ta zauna tana ƙunshe dariya. A can tsakar gida kuwa tuni gidan ya ci gaba da hayaniyar shige da ficen yara. Kilishi da ta cika ta yi fam saboda takaicin yanda mijin nasu yake fifita Nasibah akan duka yaran gidan,sai ta ɗauki abincinsa ta shiga ɗakin babu ko sallama ta dangwarar masa ta fito tana ƙunƙuni. Shiru Makaɗi ya yi yana tunawa da uwar gidansa da ta rasu sakamakon jinyar cancer ta mama da ta sha. Cike da jimamin abinda ya aikata wa Hauwa ya zamo bakin gado ya buɗe abincin nasa ya hau tsakura yana ci kamar baya so. Sallamar wasu mata ne ta ja hankalin mutanen gidan gaba ɗayansu. Kallon gidan suka hau yi kafin ɗaya daga cikinsu ta buɗe baki ta ce. "Nan ne gidan su Nansy Ƙaya?" Kilishi dake cike da takaicin Nansy a cikin ranta,sai ta buɗi baki ta ce. "Tunda kuka shigo har tsakiyar gida kuka kama suna ai kun san kun zo inda kuke nema ko?" Chewing gum ɗin bakinta matar ta tauna sannan ta ce. "Ok. Ina ita Nansyn take?" Nansy dake ƙunshe a ɗaki a jikin labule tana leƙen matan sai ta ji hanjin cikinta na kaɗawa,nan da nan tsoro ya mamaye zuciyarta. Cikin ranta take ayyana. 'Me waɗannan Hajiyoyin matan suka zo yi a gidanmu ni Nasibah?'.... [9/15, 10:57 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 2. Makaɗi na jin muryar matan da basu yi kama da wanda suka zo da maganar wasa ba,sai ya fito tsakar gida yana suɗe hannunsa tare da murje shi waje ɗaya ya ƙanƙance ido,zuciyarsa a tsinke ya ce. "Ku kuwa bayin Allah da girmanku da kamalarku me ya sa kuke neman ƴar tatsisiyar yarinya kamar Nasibah?" Murmushi ɗaya daga cikinsu ta saki sannan ta ce. "Baba babu abinda ya kawo mu gidan nan face alkhairi. Can gidan Malam Musa Nera ne ake bikin aure,to da muka zo sai muka ga yaran gidan da kitso da lalle mai kyau,muna tambaya aka ce mana nan zamu zo a yi mana,kuma sunan mai lalle da ƙunshin Nansy Ƙaya ko kuma mu ce Nasibah." Wata iriyar ajiyar zuciya Makaɗi da Nasibah dake laɓe a ɗaki suka sauke a tare;kafin ta fito daga ɗakin tana washe baki. Har ƙasa Nasibah ta durƙusa ta gaishe su suka amsa cikin sakin fuska. Makaɗi na ganin haka sai ya jingine a jikin ƙofar ɗakin Kilishi ya ce. "Da yake duk nan unguwar babu manya irinku masu hannu da shuni dake shigowa nan gidan wajen Nasibah, sai dai idan suna buƙatar kitso ko lallen ita ta je har gida ta yi musu,shi yasa zuwanku ya zame mana sabon abu." Jinjina kai matan suka yi domin sun fahimci uzirinsa. Babu ɓata lokaci Nasibah ta matso kusa da su cike da jin kunyarsu ta kalle su daga sama har ƙasa ta ce. "Ku jira ni bari na ɗakko tabarma na zo,kun zo da kayan lallen?" "Eh mun zo da komai." Ɗakinsu ta faɗa da gudu ta hau kwashe kayan saman tabarmar dake shinfiɗe a tsakiyar ɗakin. Ƙarar kwanuka ne suka tayar da mahaifiyarta ta kalle ta cike da takaici ta ce. "Ai dama na san Najlah ba zata taɓa tashi na ba,amma ke...ke ko baccin mutuwa nake yi sai kin tashe ni. Tun ɗazu ina jin ɓuruntunki na yi banza da ke,amma kin rantse da Allah sai na farka,to gani ki min uwar da za ki yi min." Dariya Nansy ta yi ta ce. "Ah ahhh Mama,banda dai baccin mutuwa,ki na can ƙiyama ana ce miki man rabbuki ta ya zaki ji ni?" Maficin hannunta ta ɗauka ta jefi Nasibahr da shi,ita kuwa da gudu ta bar ɗakin tana dariya. A wajen da ta saba zama ta yi sana'arta ta yi musu shimfiɗa ta zauna tana faɗin. "Wa za a fara yi wa?" Kallonta suka yi suka ganta ƴar ƙarama,sai suka yi murmushi babbarsu ta zauna,dole sai da Nasibah ta koma ɗaki ta samo pillow ta saka a kujerar ta sannan suka fara kitson. Yanda take tsaga kai da kwashe kai cike da ƙwarewa ne ya sanya sauran daina rainata. Cike da gwanancewa Nasibah ta kwashe wa matar kai da kitso sannan ta kama na ƴar'uwarta. Tana gama yi musu kitso ta kwaɓa lalle ta hau zana musu irin wanda suka nuna mata a waya. Bayan awanni biyu da gama yi musu kitso suka wanke lallen. Da za su tafi suka ƙirga dubu goma suka ba wa Nasibah,wani irin farinciki ne ya mamaye zuciyarta har ta ji kamar ta kwanta musu a ƙasa dan godiya. Suna murmushi suka bar gidan zuciyarsu fal farincin samun biyan buƙatarsu da suka yi. Su na tafiya nasiba ta zare dubu uku ta ɓoye a jikinta,kamar yanda ta yi zato kuwa,haka mahaifinta ya fito daga ɗaki yana dariya yana washe baki ya ce. "Ikon Allah! Ashe dai baƙin arziƙi ne ba na tsiya ba. To ai hakan ya fi Nasibatuna akan kullum a zo kawo min ƙararki. Maza ƙirgo min na goro na koma bakin aiki,Yau Salihi be zo ba ni kaɗai nake ta aikin faci gaba ɗaya na gaji." Kuɗin ta miƙa masa gaba ɗaya tana murmushi ta ce. "Ah ah Baba,ka ɗauki abinda ya yi maka,in yaso sai ka bani na Mama da wanda zan sayi littafin da na faɗa maka Malamin bokonmu ya ce a siya saboda komawarmu senior section." "Allah Ya yi miki albarka ƴar Baba. To ga wannan,ni kuma na ɗauki wannan ko?" Dubu uku ya zare ya bata dubu huɗu ya tafi yana farinciki a cikin ransa. Yana tafiya Nansy ta zaro wanda ta ɓoye a jikinta ta nufi ɗakinsu ta damƙa kuɗin a hannun mahaifiyarta,ganin haka sai Mamanta ta zari dubu ɗaya ta bata ta yi mata godiya sannan ta ce itama ta je ta sayi abinda take so. Sosai Mahaifiyarta ke jin daɗin yanda take da tausayi da son rage mata duk wata wahala da nauyin da mahaifinsu baya iya sauke wa a cikin gidan. A wannan ranar da yamma Nansy na fita wajen ƙawayenta sai ta hau kashe musu kuɗin da ta karɓa a wajen Mamanta tana zabga musu ƙaryar yaran gwamna ne suka zo kitso da lalle wajenta. Sai da suka cinye kayan maƙulashensu sannan ta zauna da kyau ta ci gaba da basu labarin mutanen da suka zo kitso wajenta. Wasu sun yarda wasu kuma basu yarda ba,domin ta ce ƴaƴan gwamnan jihar Kano ne sutukum da guda suka tsallake ko ina a garin Kano suka zo wajenta kitso. Wanda basu yarda ba dole suka bar abun a ransu gudun kada ta yi musu duka a banza. Magariba na yi kowa ya nufi gida. Nansy ta koma gida ta yi alwala ta shige ɗakinsu ta tayar da sallah. Tana idarwa ta ɗauki ƙur'aninta ta hau karantawa domin sake tabbatar da ingancin haddarta. Ta jima sosai tana karatun kafin ta ajiye ƙur'anin ta zauna ta ci abinci. Tana gamawa ana kiran sallar Isha'i sai ta gudu tsakar gida wajen Yayarta Rabi,dan ita a kaf sallolin da suka wajaba akan mumini baligi sallar Isha'i ke yi mata wahalar sauke wa,kullum ta Allah sai sun kai ruwa rana ita da Mamanta kafin ta gabatar da sallar Isha'i. Tana zuwa ta tarar da Usman yana kwashewa Rabi miya a tuwonta yana mayarwa cikin kwanonsa. Rabi da yake tana da haƙuri sai ta yi shiru ta zabga tagumi tana kallon ikon Allah. Nansy na zuwa sai ta ƙwace kwanon Usman ta kalle shi tana harara ta ce. "Baka san inda hanyar kitchen take ba da za ka hau kwashe mata miya?" Cike da rashin mutunci Usman ya kalli Nasibah ya ce. "Ke ina ruwanki da sabgata? Dalla bani abincina." Dariya Nansy ta fashe da ita ta hau kwaikwayon maganar Usman ta ce. "Idan na ƙi baka abincin naka me za ka iya yi min?" "Nansy kin fa raina ni,Allah zan saɓa miki kamanni idan baki yi wasa ba." "Kaiii Usumanu ko ɗandaba ka zama babu abinda za ka iya yi min kana wannan lauɗin kamar mace. Banza Tanko kawai." Cikin zafin nama Usman ya yi kan Nasibah zai daka ita kuma ta tsallake shi ta faɗa ɗakin Kilishi dake da niyyar fitowa ta zazzaga wa Nasibah rashin mutunci akan aibata mata yaro da take yawan yi a gidan. Kasancewar Usman ya taso cikin mata sai ɗabi'unsa da maganarsa take kamanceceniya da ta mata,hakan ne ya baiwa mutane da yawa damar kiransa da sunaye kala-kala. Wasu na kiransa da Tanko,wasu su ce masa ɗan'daudu ko ɗan'hamsin. A cikin masu tsokanarsa ba a bar Nasibah a baya ba,shi yasa kullum suke faɗa da zarar sun zauna a inuwa ɗaya. Karo ta yi da Kilishi dake daf da fitowa daga cikin ɗakinta,nan take suka zube a ƙasa warwas. Kafin Kilishi ta damƙi Nasibah ta yi zuruf cikin zafin nama ta miƙe daga jikinta ta kwasa da gudu ta yi waje. Tana fita sai ta samu wani baƙin dutse dake ƙasan bishiyar ƙofar gidansu ta durumi ta yi zamanta. Ta jima a wajen sosai kafin ta jiyo ƙarar babur ɗin Babansu. Nan take ta hau murza ido tana kuka kamar wadda ake zare wa rai. Makaɗi na ƙarasowa ƙofar gidansa ya ga Nasibah na kuka,sai ya haɗe fuska tamau kamar hadari. A gabanta ya tsaya ya cake babur ɗinsa ya kama kan yana kallonta ya ce. "Uhumm wanne me rabon shan dukan ne a cikin daren nan ya taɓa min ke ƴar Baba?" Kai Nasibah ta hau sosawa tana shan majinar da babu ita;ta hau nuna ƙofar gidansu ta ce. "Ba Yah Usman bane ya dake ni dan kawai na ce bai dace ya kwashe wa Yah Rabi miyarta ba...wai dan na ce Allah Ya saka min shine Kilishi ta rufe ni da duka,Baba ka ga bayana da ƙyar na gudo nan." "To ita uwar taki ina take akai wannan bidirin bata tsawatar ba?" "Haba Baba,ka manta halin Mama ne? Ko kashe ni za su yi ba za ta ce kanzil ba. Ni dai Baba mu je ciki ka sammin abinda ka siyo na ɗan lasa." Nan take fuskar Makaɗi ta sake tsukewa da ɓacin rai. Cikin faɗa da hargagi ya tura babur ɗinsa ya ce. "To uwar ƙwalamammu babu uwar da na siyo ni. Za ki shiga ciki mu je na ji bahasin dukanki da aka yi ko kuma na wuce na barki ki ta haɗiyar yawu a iska?" Baki Nasibah ta tura gaba tare da dafe bayan babur ɗin tana turawa ta ce. "Ai shikenan,ka ci naka nima gobe da an taso daga boko zan je gidan Alhaji Nasir na yi wa Aunty Luba kitso,kuma..." A hasale Makaɗi ya kafe babur ɗinsa a cikin soron gidan ya kunna ƙaramar wayarsa ya haska musu zaure,cikin faɗa da zage-zage ya buɗe ledar ya ɗebo nama tsoka biyu ya dangwara wa Nasibah a hannu. Nan take ta washe baki ta danna su a baki tana tanɗe hannu ta ce. "Ni Baba na yafe wa Usman duk abinda ya yi min duniya da lahira. Kawai ka yi wucewarka ɗaki ka ci daɗinka. Kuma gobe na yi maka alƙawari duk abinda na samo zan kasa shi uku na baka kaso biyu na ɗauki ɗaya mu raba da Mama." Nan take fuskar Makaɗi ta washe ya kalli ƴar tasa wadda a koda yaushe yake samun alkhairi mai yawa daga wajenta. Hannu ya jefa cikin ledar hannunsa ya sake damƙo tsoka biyu ya miƙa mata ya ce. "Allah dai Ya yi miki albarka Nasibah,Allah Ya ƙara wa hannuwanki albarka da saƙar kitso da lalle me kyau. Maza shiga ciki ki kwanta,gobe ne za ki fara zuwa SS 1,inyee su Nasibahn Baba ana ta girma." Cike da murnar da ta kasa ɓoyuwa a saman kyakkyawar fuskar Nasibah,ta kalli mahaifinta cike da so da ƙauna ta ce. "Duk sai na ji daren ya yi min tsawo Baba." "Ai da kin kwanta kika rintse ido gari zai waye ƴar Baba." Dariya Nasibah ta yi sannan ta ci gaba da bawa Mahaifinta labarin wahalar da ta sha a jarabawarsu ta Junior WAEC da suka yi. Ba tare da Makaɗi ya kula da lokaci ba sai ya zauna a tabarmar da Kilishi ta shimfiɗa masa ta ajiye masa abincinsa suka dinga hira da Nasibah. Ganin hirar tasu ba za ta ƙare bane ya sanya Mama fitowa riƙe da buta a hannunta ta kalli Mijin nasu ta ce. "Malam sannu da zuwa." "Yauwa Maryama,ya wunin gidan da yaran kuma?" "Humm Alhamdu lillah. Ai na zaci ka manta kana da wasu yaran ballantana kuma matar aure me suna Maryama." Dariya Nasibah ta ƙunshe ta saɗaɗa ta shige ɗakinsu ta kwanta tana jiyo hirar iyayen nata mai cike da kishi da kuma bayyana so da ƙaunar da suke yi wa junansu. Duk wanda ya kwana ya tashi a cikin gidan nan ya san cewa Mama ita ce matar da Malam  Sanda Uba Makaɗi ya fi so a kaf matansa da ya aura,ciki kuwa har da uwar gidansa wadda iyayensa suka aura masa ita saboda zumuncinsu irin na makaɗan dauri ya ƙara ƙarfi. Wannan dalilin ne ya sa a koda yaushe Mama ke adawa da yanda Malam Sanda ya tattare soyayyar da yake yi mata ya mayar da ita akan ƴarsu Nasibah. A kullum idan ta yi masa ƙorafi sai ya ce ah ah shi kam bai fi son Nasibah akan ta ba. Amma da zarar an taɓa Nasibah;ko kuma wani abu ya same ta,to anan ne gaskiyar irin soyayyar da yake yi mata take bayyana. Babbar matsalar Malam Sanda ita ce kwaɗayi,rowa da kuma son abun duniya. Dan haka idan ka ji yo faɗansu da shalelensa Nasibah,to fa tana ƙoƙarin shiga aljihunsa ne,ko kuma tana neman hana shi nata abun duniyar. A wannan lokacin ne Malam Sanda yake zage damtse ya gyara leɓensa ya yi ta surfa wa Nasibah ashar da rashin mutunci. Kafin Mama ta koma ɗaki tuni Nasibah ta yi bacci cike da surutai da mafarkan dake bayyana abubuwan da ta yi a wunin ranar. Washegari da asuba Mama ta yi matuƙar mamaki da ta ga Nasibah ta farka da kanta ba tare da an tayar da ita daga bacci ba. A ɓangaren Nasibah kuwa jin wannan ranar take yi a matsayin rana mai matuƙar muhimmanci a rayuwarta. Tun gari bai gama waye wa ba ta yi wanka ta zuba uniform ɗinta sababbi da suka yi kusan sati biyu a goge. Sabuwar safarta ta saka sannan ta saka sabon takalminta. Ta na gamawa ta ɗauki tsohuwar jakarta ta rataya a kafaɗarta tana jin wani irin sabon farinciki na mamaye zuciyarta. A cikin wannan yanayin mahaifinta ya dawo daga masallaci ya tarar da ita. Cike da zumuɗi da girmamawa Nasibah ta durƙusa ta gaishe da mahaifinta,amsawa ya yi cikin sakin fuska sannan ya ce. "Ƴan makarantar boko kenan,manyan siniya masu bawa jiniya gwale-gwale. To Allah Ya sa ki fara a sa'a ƴar baba." "Amin Babana. Baba kai za ka ajiye ni a makaranta da babur ɗinka ko? Ka ga su Nawwarah a motar gidansu za a kai su yau." Kai Malam Sanda ya gyaɗa kafin ya ce. "Ni zan kai ki mana ƴar Baba,maza ki je ki ci ɗumame dan na san zumuɗi bai barki kin karya ba." Tura baki Nasibah ta yi gaba tana juyi da jikinta,cike da shagwaɓa ta ce. "To ni Baba yau ranar farko da zan shiga SS 1 ɗin ne zan ci ɗumamen tuwo?" A ƙufule Kilishi dake jin haushin Nasibah ta mere baki ta ce. "Shi SS 1 ɗin a wata ƙasar ake yin sa ko kuma a nan nan cikin garin Kano?" Kallon Malam Sanda Nasibah ta yi tana matso kwallah. Nan take Malam Sanda ya ɓata rai ya ce. "Mu je bar mata tuwonta ta ci ya kai mata har mafafa." Nan take Nasibah ta washe baki ta bi bayan Malam Sanda suka bar gidan a babur ɗinsa. Sai da ya tsaya ya siya mata ƙosai da dankali sannan ya kai ta har cikin makaranta. Malam Sanda na tafiya Nasibah ta tafi wajen ƙawayenta tana takun yanga kamar bata so. Duk wanda ya ganta a wannan lokacin sai ya rantse a SS 2 take ko SS 3. Nawwarah da sauran ƙawayensu na hango ta suka tafi da gudu suka rungume juna suna ihun murna. Cike da yanga Nasibah ta ja jikinta daga nasu ta na yatsina ta ce. "Wai ku dan Allah meye haka? Har yanzu baku bar abun yarinta ba sai ƴan junior section sun raina mu." Shewa yaran suka sanya tare da tafawa,daga nan suka zauna Nasibah ta fito da ƙosai da dankalinta tana ci suna hira. Lokacin shiga aji na yi,suka tattara suka shiga sabon ajinsu kowa ta kama bencin da za ta zauna. Cike da zumuɗi da son karatun dake cikin ransu suka bada hankalinsu suka ɗauki darasin wannan ranar. Har aka tashi Nasibah bata ja faɗa ba,idan an yi mata abu sai dai ta yi kamar bata gani ba. Sosai hakan ya ba wa Malamai da ɗalibai mamaki. A wannan ranar suka tabbatar da abinda take yawan faɗa. 'Ni fa daga ranar da na shiga senior class zan dena duk wannan damben da neman faɗan da nake yi.' Lokacin da aka tashi daga makaranta kowa ya watse,Nasibah da yaran unguwarsu sai suka kama hanya a ƙafa dan komawa gidajensu. Tun a hanya su Nawwarah ke roƙon Nasibah ta sam-mu-su durumin ƙofar gidansu da ya nuna,kamar ba za ta yi magana ba,sai ta nisa ta ce. "To shikenan,zan baku amma sai dai idan kowa zata bani nera ashirin-ashirin." Cike da murna suka ce za su bata. Nan take suka fara sauri domin isa gidan su Nasibah da wuri........ [9/17, 8:17 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 3. Su na isa ƙofar gidansu Nasibah sai ta hana kowa hawa bishiyar ta ce ita za ta hau ta ciro ta basu da kanta gudun kada su kwasa da yawa. Hijabinta da jakarta ta cire ta miƙa musu suka riƙe mata ta kama bishiyar kamar ƴar biri ta haye. Tunda ta fara hawa bishiyar su Nawwarah suka fara yi wa Nasibah waƙar. "Ɗan biri daka tsalle,ya haye ladidi." Nasibah na saman bishiya tana tsinko musu durumi tana wurgowa tare da taya su raira waƙar. Ta jima tana watso durimin suna waƙoƙinsu tare; can ta ji shiru babu mai yi mata amshin waƙar ɗan biri,sai ta hau ƙwala musu kira ɗaya bayan ɗaya bata ji an amsa ta ba. Ta na leƙo kanta ta ga Babanta a tsaye fuskar nan ta yi jawur kamar an kara masa ita a wuta. Gaban Nasibah ne ya yanke ya faɗi,sai ta yi sauri za ta koma saman bishiryar,ƙafarta Malam Sanda ya riƙe ya ce. "Sakko ƙar dan ubanki,wato ɗan biri daka tsalle ko? Ki rasa waƙar da za ki yi a ƙofar gidana sai waƙar da ake ambato sunan uwata da ta mutu kuma ake danganta ta da biri Nasibah? Shaƙiyancin naki ashe ya tsallake kan mutanen unguwa ya dawo kaina Nasibah? Mu je ciki to yau zaki yaba wa aya zaƙinta." A wannan ranar duk yanda Nasibah ta so ta yi amfani da abun duniya;tare da soyayyar da mahaifinta ke yi mata abun ya ci tura. Suna shiga cikin gidan ya samu wayar rediyo ya dinga shauɗa mata a baya yana kumawa,tun Nasibah na daurewa ita a dole ta yi fushi da Baban nata,har ta saki baki ta dinga ihu tana tsalle. Malam Sanda bai ƙyale ta ba sai da ya tabbatar ya lallasa ta ta yanda gobe idan wani ya ce ta kira sunan Ladidi ba za ta saurara wa mutumin ba,sannan ya ƙyale ta ya ɗauki abincinsa ya bar gidan. Haka Nasibah ta ƙarasa wunin wannan ranar cikin ƙunci da ɓacin rai. Duk wadda ta zo kitso ko ƙunshi gidan sai ta ce a je a ce su dawo jibi,har gidan Aunty Luba da ta yi mata alƙawarin za ta je ta yi mata kitso da lalle har gida da ta aiko ce mata ta yi a ce sai jibi. Da yamma Najlah Autar su na ganin lokacin zuwan su makarantar dare ta yi,sai ta shiga shiri tana kiran Nasibah don ta shirya su tafi tare. A ɓangaren Nasibah kuwa bata da niyyar tashi daga inda take,saboda tana son Babanta ya dawo ya ga har a wannan lokacin bata dena fushi da shi ba. Kilishi banda masifa babu abinda take yi wa Mama akan halayyarta ta rashin nuna wa yaranta ɓacin ranta akan duk wani abinda za su aikata ba daidai ba. Murmushi kawai Mama ta yi ta ce. "Kilishi kenan,ki dena damun kanki akan halayen Nasibah, dika-dika Nasibar nawa take? Watan nan na mauludi idan ya zo ne fa za ta cika shekaru sha biyar a duniya,kin ga kuwa har yanzu akwai ƙuruciya a tattare da ita. Kin san Allah watarana idan aka ce ta yi dika waɗannan abubuwan ƙaryatawa za ta yi." Cike da takaici Kilishi ta ce. "Humm Allah Ya kyauta." Ɗaki ta shiga ta kira Rabi ta ce ta leƙa ƙofar gida ta kira Usman su wuce makarantar dare. Babu ɓata lokaci Rabi ta leƙa ta kira Usman ya shigo suka kammala shirinsu Rabi ta kama hannun Faihah da Najlah suka tafi makaranta. Daga Mama har Kilishi babu wanda ya sake bi ta kan Nasibah. Ɗaki suka shige kowa ta kama sabgar gabanta. Wani irin bacci ne mai daɗi ya fara ɗibar Nasibah daga zaune,dan haka sai ta kashingiɗa a wajen ta takure a waje ɗaya ta hau yin abunta. Cikin bacci ta ji ana tashinta a hankali,tana buɗe ido ta yi tozali da Nawwarah tsugunne a gabanta tana tashinta. Cikin yin ƙasa da murya Nawwarah ta ce. "Wai ke yau ba za ki je makaranta bane?" Tura baki Nasibah ta yi gaba tare da matso ƙwallar takaicin dukan da ta sha ta ce. "Ni babu inda zan je sai Baba ya dawo ya bani haƙuri." Baki Nawwarah ta kama kafin ta gyara zaman jakarta a kafaɗarta ta ce. "Lallai Nasibah kina zuba mulki a gidan nan,wato kin yi laifi an dake ki amma jira kike yi a zo a baki haƙuri ko? Sannu sarauniya. Ko kin manta ke da bakinki kika ce Baban ku ko takwara ya ƙi yi wa Mamansa saboda kada tsautsayi ya sa a zage ta ko a dake ta?" Kai Nasibah ta ɗaga tare da furta. "To ai ba ƙarya na yi masa ba Malama." "To kin ga kenan laifi naki ne,mu ma da mun tsaya na tabbata sai ya dake mu. Ke kin ga ba wannan ba ma,kin san dukan da kika yi wa Bultuƙa ya jawo yara duk sun raina ta? Har wanda ta yi wa duka a baya yanzu ganin wallen ta suke yi. Yanzu haka na baro Nadiya tana can za ta rama dukan da ta taɓa yi mata lokacin da aka yi musabaƙa da ƴan unguwarsu." Da jin haka Nasibah ta ware tana dariya,ba tare da ta yi shawara da kowa ba ta faɗa ɗakin Mama. Tana shiga ta tsuke fuska tana cika tana batsewa ta sauya kayan jikinta ta saka na gida. Jakar makarantar dare ta ɗauka ta fito daga ɗakin ta zari hijabinta a saman window ta ja hannun Nawwarah suka bar gidan da gudu. Tafe suke suna hira Nawwarah na fatan Allah Ya sa ba a gama dambace wa ba Nasibah ta shigar wa ƙawarsu Nadiya. Lokacin da su Nasibah suka isa layin makarantar tasu sun tarar da yara sun taru a wajen damben da ake yi. Nasibah na zuwa yara suka hau ihun kiran sunanta wato Nansy Ƙaya,hakan sai ya gigita Bultuƙa jikinta ya saki saboda tsoro,Nadiya na ganin haka sai ta shatale ƙafarta ta yarɓar da ita a ƙasa ta hau jibgarta kamar an aiko ta. Suna cikin wannan halin Malamin Islamiyyar su wato Malam Luƙman ya lallaɓo da dorinarsa ya shiga tsakiyar filin ya hau shauɗawa duk wanda rabonsa ya tsaga. Nan take wajen ya kaure da ihu yara suka watse. Nasibah kuwa tun kafin Malam Luƙman ya ƙaraso wajen ta hango shi,dan haka sai ta sunkuya ta bi ta bayan taron ta shiga aji. Ko da su Nawwarah suka iso tuni Malam Atiku ya tare hanya. A wajen ya sa suka rage tsawon su ya bi su da bulala biyar-biyar sannan ya ce su shiga aji. Nawwarah da take ƴar masu hannu da shuni bata saba da duka ba,tuni wajen da aka dake ta ya tashi ya yi jawur,sai haska hannun take yi a hasken fitilar ajinsu tana matsar ƙwalla. Nasibah da ta kalli ƙawayen nata sai ta fashe da dariya ta kifa kai a ƙur'aninta tana kaiwa da kawowa kamar mai yin karatu. Lokacin da Malam Luƙman ya dawo ya tarar da yaran na ta karatu,sai ya zauna ya ci gaba da ƙara wa wanda ke da buƙatar ƙari karatu. Kafin lokacin tashi ya yi ya tsayar da yaran ya yi musu faɗa da nasiha akan yawan faɗan da suke yi a tsakanin unguwannin Sani Me nagge,Tal'udu da su ƴan Mandawari. Daga nan ya tashe su kowa ya kama hanyar gidansu. Yau ma kamar ko da yaushe idan an tashi; Malam Luƙman ya fito da litattafansa ya yi tsaye a wajen da suka saba haɗuwa da Nasibah, sai su jera suna tafe suna hira har ya mayar da ita gida sannan su tsaya a ƙofar gidansu Nasibah su taɓa hira,daga nan sai su yi sallama ya tafi gida,itama ta shige nasu gidan. Shiru-shiru Malam Luƙman bai ga Nasibah ba,ballantana su Najlah,dan haka sai ya haƙura ya tafi gida yana saƙa da warwara a cikin ransa. A ɓangaren Nasibah kuwa ana tashi ta bi Rabi suka wuce gida,saboda bata son haɗuwa da Malam Luƙman a wannan ranar ya ji muryarta a shaƙe ya gane ta yi kuka. Su na shiga soron gidan ta ci karo da babur ɗin Babansu,nan take ta langwaɓe ta shiga gidan tana ɗingisa ƙafa. Baba dake zaune a tabarma a ƙofar ɗakin Mama yana ganin Nasibah ya gane nemansa take da sharri a cikin wannan daren. Murmushi ya saki ya girgiza kansa ya ce. "Ƴar Baba me ya samu ƙafar taki kuma na ga kina ɗingishi?" Nan take Nasibah ta ɓare baki ta rushe da kuka kamar wadda aka daka. Daga can cikin ɗakin Kilishi ta bugo tsaki ta ce. "Allah Ya wadaran naka ya lalace dai." Harara Nasibah ta wurga wa ƙofar ɗakin Kilishi tana murguɗa baki kamar tana ganinta. Ba tare da ta kula ta ba ta isa shimfiɗar Babansu ta zauna a gabansa tana shagwaɓe fuska ta ce. "Baba ba kai bane ka janyo min ƙafa ta daga bishiya ɗazu sai da ta ce ƙasss." Baki Malam Sanda ya kama ya ce. "Subhanallahi! In ce dai ba targaɗe kika yi ba ko tsagewar ƙashi?" "Baba ƙafar fa karye wa ta kusa yi,da ƙyar na iya takawa na je makaranta." Shiru ya yi ya zira hannunsa a aljihunsa ya zaro mata wata leda ya miƙa mata,a tare suka ɗora yatsansu manuni a bakinsu suna dariya ƙasa-ƙasa. Nan take Nasibah ta buɗe ledar ta tarar da kilishin da ba zai wuce yanka huɗu ba. Cike da farinciki ta tashi ta shiga kitchen ta ɗakko abincinta na rana da bata ci ba ta juye kilishin akai ta zauna suna hira da Babanta kamar babu abinda ya shiga tsakaninsu na ɓacin rai. Bayan Nasibah ta kammala cin abincinta sai ta hau bawa Malam Sanda labarin sabon ajin da aka kaisu da Malamansu da abinda aka koyar da su a wannan ranar. Cike da alfahari da jin daɗi Malam Sanda ya ce. "Allah mai girma! Yau ni jinin makaɗa wanda na taso ina taya mahaifina ɗaukan ganga da kalangu,mai yawon kwararo dan kaɗa ganga ni ne ke gane wasu kalmomin turanci duk ta dalilin samun haziƙa kuma fasihiyar yarinya kamarki Nasibah." Dariya Nasibah ta yi cike da jin daɗi ta ce. "Ai Baba irin ƙwaƙwalwarka gare ni,shi yasa nake gane karatu sosai har nake gyara maka wasu kalmomin idan ka faɗa ba daidai ba,kuma na sanar da kai ma'anarsu." "Tabbas babu ƙarya Nasibah da ace ke namiji ce da sai na ce babu ta inda kika baro ni." "Na bar maka ƙaton tumbinka mana Babana." Dariya suka fashe da ita kafin Malam Sanda ya kai mata duka ta goce,cikin dariya ya ce. "Ja'ira,wannan tumbin da kike yi wa tsiya kullum na kuɗi ne." "Baba tun da can baka yi kuɗin ba sai yanzu da ka fara tsufa? Kuma ai na ji ƙawayena na cewa masu facin taya ba sa yin kuɗi." "Ke yanzu Nasibah mutum ya haifi kamar ki a yi masa kallon talaka? Ai ni nan da kike gani nan gaba kaɗan zan zama surukin mai kuɗi,kin ga daga nan nima na zamo mai kuɗin." Dariya Nasibah ta yi sosai har idonta na fitar da ƙwalla kafin ta ce. "To kai Baba wa ya ce maka Malam Luƙman na da kuɗi? Shima fa talaka ne kamar mu,bashi da sisi,abinci ma Mamansa ke bashi." Nan take Malam Sanda ya haɗe fuska ya ce. "Wai Nasibah kina nufin har yanzu baki rabu da matsiyacin yaron nan ba ashe?" Jikin Nasibah ne ya hau tsuma,tuni ta ja da baya ta sauka daga saman tabarmar da Malam Sanda ke kai ta hau sosa kai. A hasale Malam Sanda ya daka mata tsawa ya ce. "Ba dake nake magana ba Nasibah!" Shiru Nasibah ta sake yi ta miƙe tsaye za ta gudu cikin ɗaki. Murfin kwano Malam Sanda ya ɗauka ya riƙe,sannan ya kalli ƙofar ɗakin Kilishi ya ce. "Rabi! Ke Rabi kina ina? Usman ku zo nan." Da jin Malam Sanda ya kira Yayunta sai ta hau kuka tana dira ƙafa ƙasa tare da faɗin. "Ni Baba shi nake so,ya ce fa idan ya gama makarantar nan da yake yi zai samu aiki babba sai ya turo iyayensa a saka mana rana,ina gama makaranta za a yi aurenmu da shi." "Sai dai a saka ranar auren uwarsa amma ba dai ke da shi ba Nasibah. Ka ji min matsiyacin yaro yana fama da talauci shine yake hure min kunnen ƴata ta bijire min. To daga yau kin dena zuwa makarantar daren nasu;ke ta asabar da lahadin ma na cire ki wata zan sauya miki. Gwanda ki dinga zuwa can Sani Me nagge ki koyo karatun. Rabi da Usman,ku na ji na ko?" Da sauri suka haɗa baki wajen faɗin. "Eh Baba muna jinka." Ido Malam Sanda ya ƙanƙance a cikin duhun yana nuna su ya ce. "Duk ranar da yarinyar nan ta sake tsayuwa da matsiyacin yaron nan baku faɗa min ba sai na yi muku duka a cikin gidan nan,kun ji na faɗa muku. Yauwa ke Rabi kin sanar da Jabir ɗin ya turo manyansa ko yaya?" Guiwowinta ta zube a wajen ta kasa bashi amsa,domin tun daga ranar da Malam Sanda ya ce saurayin nata ya turo bai sake zuwa ba. Kilishi da ta cika ta batse da halayyar mijin nasu sai ta fito tana ɗaure kanta da adiko ta ce. "Ba fa zai yuwu ƴar so ta ɓata maka rai ka huce akan ƴaƴan ƙi ba. Lokacin da kuke ƙusƙus ɗinku ka ƙunso abu a takarda ka damƙa mata ai duk muna jinku;amma babu wanda ya tanka ku,sai yanzu da ta ɓare a tsakaninku za ka tasa min yarinya a gaba da masifa? To Jabir ya danna layar zana,tun lokacin da ka ce ya turo magabatansa ko magabayansa bamu gani ba ballantana shi." A hasale ta kalli Rabi da Usman da suke durƙushe a wajen cike da damuwa ta ce. "Ku tashi ku je ku yi shirin bacci. Allah Ya bamu alkhairi. Ita kuma da kake yi wa tanadin mai kuɗi Allah Ya bata mai kuɗin idan lokacin ya yi sai ku siyar da mu ku siyo wasu dabbin iyalin ku ci gaba da rayuwa da su." Borin kunya duk ta hana Malam Sanda yin cikakkiyar magana,da ƙyar ya samu ya ce. "Inyeeee lallai ne Kilishi wuyanki ya yi kauri." Fari Kilishi ta yi da idanuwanta sannan ta daki cinyarta ta ce. "In ɗakko maka wuƙa ka yanka ne Malam? Haba! Kai kenan baka da aiki sai nuna banbanci a tsakanin ƴaƴanka? Da ace gaba ɗaya yaran Maryama kake yi wa haka da sai in ce ni ce baka so,amma itan ma ka bi ka ware ƴa ɗaya a cikinsu kana fifita ta kamar da gwal aka sassaƙe ta,gashi ta sanadiyyar abinda kake yi yaran Yaya gaba ɗaya sun dena zuwa gidan nan,Hauwa dake daure halayenka take ɗan zuwa jefi-jefi itama ka kore ta da halinka,yanzu idan jikokinka basu zo gidanka sun ci sun sha ba a ina ne ya fi dacewa su yi hakan?." Kai kawai Malam Sanda ke jinjinawa ya kasa magana,domin kuwa gaba ɗaya a kalaman Kilishi babu inda ta yi masa ƙarya. Nasibah da ta samu faɗan Kilishi ya ɗauke hankalin Baba akan maganarta da Malam Luƙman ɗinta sai ta saci jiki ta faɗa ɗakinsu na yara ta kwanta tana tunanin ko sama da ƙasa za ta haɗe babu wanda ya isa ya raba ta da masoyinta...... [9/17, 9:44 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 4. Washegari da safe Nasibah ƙin tashi ta yi ta shirya zuwa makaranta. Duk yanda Rabi ta yi da ita dan ta farka ƙi ta yi,daga ƙarshe ma juyi ta sake yi ta mayar da kanta baya ta buɗe baki ta ci gaba da baccinta hankali kwance. Rabi da bata da hayaniya sai ta fita tsakar gida ta hau taya Mama aikin safe. Mama kuwa babu abinda ya dame ta da shiga sabgar Nasibah,a cewar ta idan tana yawan saka damuwar Nasibah a zuciyarta watarana za a wayi gari a samu ta haɗiyi zuciya saboda baƙinciki,ko kuma ta yi wa Nasibah dukan da sai ta nakasa ta,dan haka kowa ya yi rayuwarsa a gidan kada ta shiga sabgar Mama,itama Mama kada ta shiga Sabgar Nasibah. Usman na gama ɗiban ruwan cikin gidan ya koma ya ɗebo na wankansa ya shiga wanka ya yi shirin makaranta. Hatta da su Najlah da Faihah sun gama shiri,amma gimbiya Nasibah bata da niyyar fitowa ballantana ta shirya. Duk abinda ke faruwa Malam Sanda na gani,sai dai fushin da yake yi da Nasibah ya hana shi tambayar inda take. Lokacin da Kilishi ta tashi daga baccin safen da ta koma ta fito tsakar gida;sai ta ga kowa cikin shirin makaranta yana karyawa,amma banda Nasibah. Kallon Rabi ta yi ta ce mata. "Ke ina ƴar'uwarki take? Ko kutaren ne basu sauka ba ta tafi bata karya ba?" Kai Rabi ta girgiza,nan take Malam Sanda ya baza kunne dan ya ji amsar da za a bayar akan shalelen nasa. Kafin Rabi ta yi magana Usman ya yi dariya,cike da yanga irin ta mata ya ce. "Tana can tana bacci ta hangame baki kamar wata Saniya." Rai a ɓace Kilishi ta ce. "Kai Usman bana son tsokana,kada ka sake kiran ƙanwarka da Saniya. Ke kuma me yasa baki tada ita ta shirya ba gudun kada ta makara?" "Ummah na tashe ta fa,ita ta ƙi tashi." Ba tare da Kilishi ta sake cewa komai ba ta zundumi wata ƴar bulala dake yashe a ƙasa ta yi cikin ɗakin,tana zuwa ta ga yanda Nasibah ta kwanta a malkwaɗe,ƙafa gefe guda ƙugunta gefe ɗaya,kanta kuwa ya yi baya sai kace matacciya. Bulalar Kilishi ta ɗaga ta zabga mata a cinya, cikin magagin bacci Nasibah ta sosa tare da faɗin. "Yah Rabi Allah se na rama,ko na ja miki doguwa." Juyi ta sake yi za ta ci gaba da bacci Kilishi ta ɗaga bulalar da kyau ta sake lafta mata,a gigice Nasibah ta farka tare da wage baki ta rusa uban ihu. Tana yin ido biyu da Kilishi sai ta ja baya tana ƙanƙame jikinta tare da rufe bakinta tana toshe kukanta. Ido Kilishi ta zaro mata waje ta ce. "Tashi ki fita ki shirya dan ubanki." A guje Nasibah ta bar ɗakin ta yi wajen randunan ruwansu ta hau ɗiba a buta tana kuka. Tana gama ɗiba ta shiga banɗaki ta kama ruwa sannan ta fito ta ɗakko brush ɗinta da toothpaste ta hau wanke baki. Ta na gamawa ta wanke fuskarta da ƙafarta da sabulu. Kai kawai Mama ta jinjina tare da faɗin. "Allah Ya shiryar dake Nasibah." Baki Nasibah ta tura gaba ta isa wajen Mamansu ta durƙusa ta ce. "Ina kwana." "Lafiya." Shine abinda Mama ta ce mata tare da tura mata kwanon abincinta da kofin koko. Ɗauka Nasibah ta yi kamar bata so ta isa ƙofar ɗakin Kilishi ta tsugunna ta ce. "Ummah ina kwana." "Lafiya ƙalaou Nasibah,maza don girman Allah ki shirya ki bi ƴan'uwanki ku tafi makaranta. Ke da kika shiga SS 1 me ya haɗa ki da makara balle fashi? Ko so kike yi a bawa wata monitan ajin a hana ki saboda kina makara da fashi?" Kai Nasibah ta girgiza, idanuwanta na cikowa da ƙwalla ta ce. "Ummah kayana fa sun yi datti,jiya Baba ya...." Malam Sanda dake zaune a ƙofar ɗaki ya riƙe radio a hannunsa amma hankalinsa gaba ɗaya yana wajen Nasibah,tuni ya tari numfashinta ya ce. "Ahir na sake jin kin kama suna na a bakinki Nasibah. Ni zan yi miki wankin inifom ɗin naki da za ki kira sunan Baba a maganarki?" "To ba kai bane ka jawo ni a saman bishiya ka hau jibgata duk ka ɓata min kayana." "Da na jawo ki daga saman bishiya janki na yi a ƙasa? Kuma idan da kin so wanke kayanki ai da na fita da kin wanke su." Ƙunƙuni Nasibah ta hau yi tana cin abincinta tare da jaddada ita babu inda za ta je da kaya masu datti. Rabi na jin haka sai ta tashi ta shiga ɗakinsu ta ɗakko wa Nasibah wankakku kuma gogggun kayanta ta miƙa mata ta ce. "Gashi ki saka tunda ni na gama babu abinda zan yi da su." Baya Nasibah ta juya mata ta ce. "Tabɗijam! Allah ba zan saka tsofaffin kaya ba,ni sabona za a wanke min." Ran Mama da bata cika saka baki a sabgar Nasibah ba tuni ya gama tafasa da takaicin abubuwan da take yi. Babu zato ko tsammani Nasibah na ƙoƙarin tashi ta je ta wanke hannunta ta ji saukar itace akan ta. Ihu ta kurma tana neman wajen guduwa amma Mama ta damƙi hannunta tana ta zabga mata itace. Da gudu Kilishi ta fito har zaninta na neman faɗuwa. Malam Sanda kuwa da tsoron Allah ya cika masa zuciya tuni ya ƙame a wajen baki sake yana kallon ikon Allah. Nasibah banda tsalle babu abinda take yi tana ba wa Mama haƙuri. Cikin fushin da suka jima basu ga Mama ta yi irinsa ba Mama ta karɓi uniform ɗin hannun Rabi da jikinta ke ta rawa ta wurga wa Nasibah ta ce. "Kin tashi kin wuce kin shirya ko sai na sake daka ki da wannan itacen? Haba! Wannan iskancin naki ya ishe ni haka Nasibah. Ke kenan kullum akwai iya shegen da za ki dasa sabo dal a cikin gidan nan? Ga yayyenki nan ga ƙannenki babu wanda yake bamu ciwon kai sai ke. Amma ba laifinki bane,laifin me ɗaure miki gindi ne ki ci karenki babu babbaka." Mama ta ƙarasa maganarta tare da wurgar da itacen ta koma kitchen tana huci. Malam Sanda tuni ya tattare kayansa ya shiga ɗaki ya samu Nasibah tana shiryawa yana ta bata haƙuri kamar shima idan ta hasala shi baya jibgarta. A haka ta gama shiri ta fito ko kuɗin break bata nema ba. Tana fitowa Malam Sanda ya fito ya wuce kilishi dake bawa Mama haƙuri yana ta wani tsumewa yana ɗaure fuska. Ko da ya fita tuni Nasibah ta yi gaba tana tafe kanta a ƙasa ta janyo hijabinta gaban goshinta. Har ta bar layinsu Malam Sanda ya same ta a hanya ya tsaya ta hau babur ɗin ya wuce kaita makaranta. A hanya Nasibah sai ta ɗora kanta a bayansa tana ta sharɓen kuka sai kace wadda aka yi wa mutuwa. Su na isa ta sauka daga babur ɗin za ta shiga makaranta Malam Sanda ya saka hannu a aljihu ya ɗakko ɗari biyu ya bata. Karɓa ta yi ta shige makarantar ba tare da ta ce masa kanzil ba. Malam Sanda na nan tsaye har sai da ya dena hango Nasibah sannan ya tayar da Babur ɗinsa ya wuce wajen aikinsa. Dan ya yi alƙawarin sai ya nuna wa Mama kuskurenta na dukan Nasibah da itace da ta yi,tunda dai ƴarsa ba ɓarauniya bace ba kuma mayya ba. Wajen Mai ƙosan gefen wajen facinsa ya je ta soya masa na ɗari biyar ya ci ya sha kokon nera saba'in ya koma bakin aikinsa. A wannan rana Malam Sanda ya samu kasuwa sosai. Ga kuma babban kwastomansa ɗan unguwarsu ya zo a cika masa iskar gaba da bayan motarsa. Gyaɗa suka siya suna ci suna hira kamar wasu sa'anni. Malam Sanda na gama saka iska a motar kwastoman nasa ya miƙe tsaye riƙe da abun buga iska zai mayar da shi mazauninsa. Nasibah ya hango ita kaɗai tana tafe kamar za ta kwanta a saman titin. Cike da damuwa Malam Sanda ya nufi inda take da gudu ya riƙe ta,babu ɓata lokaci Nasibah ta saki jikinta a hannun Malam Sanda ta hau tsiyayar da ruwan hawaye. Sosai hankalin Malam Sanda ya tashi saboda jin wani irin zafi da jikin Nasibah ya ɗauka. Suna ƙarasowa Kwastomansa ya ce. "Ah ah Baba wannan ba ƴar ka ba ce Nasibah? Me ya same ta na ganta haka?" "Da alama bata jin daɗi ne Alhaji Samir. Kai Ɗan Tiye zo ka kula da wajen nan bari na kai ta asibiti." Cikin sauri Kwastoman Malam Sanda ya ce. "Saka ta a mota Baba na kai ta asibitina,daga nan sai na wuce da ita gida." "Ah ah Malam Samir a yi haka? Na ji ka ce yau za ka koma Abuja ko?" "Eh yau zan koma,amma sai ƙarfe biyu jirginmu zai tashi." "To shikenan Alhaji Samir na gode Allah Ya ƙara yi wa rayuwarka albarka. Gata nan idan kun je kada ma a sha wahalar rubuta mata magani dan ba sha take yi ba,allurar ma sai ka yi da gaske za ta tsaya a yi mata." Murmushi Samir ya yi ya ce. "Babu damuwa Baba zan kula da ita. Allah na tuba ita da bata da lafiya ƙarfinta duk ya ƙare ina ita ina hana a yi mata allura?" "Hummm." Malam Sanda kawai ya ce ya ja baya yana ɗaga musu hannu har suka ɓace wa ganinsa. Su na isa private hospital ɗin Samir sai ya fito waje ya rufe motar,ya buɗe baya inda Nasibah ke kwance male-male kamar ruwa. Tashinta ya yi ya ga ko motsawa bata yi ba,cikin sauri ya leƙa cikin asibitin ya kira nurses mata suka ɗaga ta suka saka a wheelchair suka tura ta zuwa cikin asibitin. Su na zuwa suka shigar da ita inda Sameer ke duba marasa lafiya. Sai da ya duba ta ya fuskanci duka ne ta sha har ya saka ta yin zazzaɓi,ga wajen da aka dake ta nan duk ya yi jawur ya kumbura. Ransa a ɓace ya haɗa alluran da zai yi mata yana ta mitar sai ya yi ƙarar Malaman makarantar su Nasibah,domin basu da ƴancin dukanta irin haka har su jawo mata jinyar dole. Cikin abinda bai fi ƙiftawar ido ba Nasibah ta miƙe zaune tankar-kar tana zare ido tare da faɗin. "Baaa na son alluraa." Nan take hawaye ya hau kwaranya a saman kuncinta,ga bakinta sai rawa yake yi saboda sanyin zazzaɓi da take fama da shi. Cike da tsananin tausayawa Samir ya riƙe hannunta a hankali ya ce. "Nansy kalli cikin idona." A hankali Nasibah ta buɗe rinannun idanuwanta ta zuba su a saman fuskar Samir,kasa ɗauke idanuwanta ta yi saboda wani irin maganaɗisun kyau da cikar halitta da Samir yake tattare da shi. Samir ba baƙi bane,kuma ba fari bane shi. Yana da fuska mai tsawo mai cike da gemu da gira kamar an zana masa ita. Yana da cikakkun laɓɓa masu faɗi da duhu kewaye da su,ta cikinsu kuma sun surka da ja. Idanuwan Samir sune suka fi tafiya da hankalin Nasibah. A daidai lokacin da ta mayar da kallonta zuwa saman gemunsa ta ji shigar allura jikinta. Rintse idonta ta yi ta saki ƙara tare da ƙanƙame shi jikinta na rawa. A hankali ya juye mata ruwan allurar sannan ya zare ta yana murmushi mai sauti ya ce. "To har an gama ai sai ki buɗe idon kuma ki dena kuka;saboda kada zazzaɓin naki ya ƙaru. Idan kuma kika ci gaba da kuka zan sake yi miki allura." Da sauri Nasibah ta sakar masa riga tana lailaya wajen allurar tana jan zuciya tare da ƙoƙarin danne kukanta. Murmushi Samir ya yi,domin shi yarinyar dariya take bashi. Sai da ya bar Nasibah ta yi baccin awa ɗaya sannan ya tashe ta suka nufi motarsa. Tana shiga baya shi kuma ya shiga mazaunin direba ya yi wa ma'aikatansa sallama ya wuce. Sai da ya tsaya da ita a wani shago ya yi mata siyayya sannan ya mayar da ita gida. Ba tare da Nasibah ta juya ta yi masa godiya ba ta shige cikin gida ta wuce ɗakinsu ta yi kwanciyarta. Yaran da suka shiga da abinda Samir ya siyo mata tuni sun juya da gudu suna murnar kuɗin da ya basu. Mama dake aiki a tsakar gida sai ta kalli Kilishi dake tsefe kanta ta ce. "Ikon Allah,waye ya kawo wa wannan marar kunyar kayan nan kuma oho? Ta shigo balam-balam kamar balama ta wuce mutane babu ko magana." Kai ƙarshen kalamanta ya yi daidai da shigowar Malam Sanda da yake cike da Mama. Cikin fushi ya ce. "Wanda za ta aura ne ya kawo mata kayan ko kina da tacewa ne? Ko kuma yanzun ma itacen zaki ɗauka ki yi ta shirgarta kamar an kama tsohon kwarto a gidan soja?" Girarsu suka haɗe waje ɗaya cike da mamaki Mama da Kilishi suka ce. "Ban gane wanda za ta aura ba?" Nasibah ma tuni ta fito daga ɗaki bakinta na rawa ta ce. "Wanda zan aura kuma Baba?" Cikin dakiya Malam Sanda ya ce. "Ƙwarai shi na zaɓa miki a matsayin mijin aure. Idan kin ga baki auri Alhaji Samir ba,to dama can Allah Ya rubuta ke ɗin ba matarsa bace. Samir saurayi ne mai abun hannunsa, kin dai gansa yana da kyawunsa bashi da makusa,kowacce mace ta same shi a matsayin miji ta gama yin dace." Kuka mai cin rai Nasibah ta saki tana ihu ta ce. "Ni dai don Allah ku kashe ni na huta da wannan baƙincikin da kuke ƙunsa min a cikin gidan nan. Jiya ka dake ni,yau ta dake ni da itace kamar ɓarauniya,kuma yanzu ka zo da maganar dake barazanar fasa min zuciya." Kafaɗa Malam Sanda ya ɗaga ya ce. "To idan zuciyar taki ta fashe sai mu ce Allah Ya jiƙanki Nasibah,amma dai a idona kin gama yin mijin aure. Samir shine wanda na zaɓa miki. Kuma muna nan da ke,shi da kansa zai dawo ya ce yana sonki da aure." Ƙafafuwa Nasibah ta hau direwa tana yarfe hannuwa ta shige ɗakinsu tana kuka ta faɗa soson katifarta. Mama da Kilishi kuwa baki suka saki suna ji da ganin ikon Allah a wajen mijin nasu. Malam Sanda kuwa cikin farinciki ya bar gidan ya koma bakin aikinsa zuciyarsa na ci gaba da fata da addu'ar Allah Ya sa Samir ya so Nasibah ya zo da kansa ba aike ba ya sanar da shi ita ce muradin ransa........... (Iyaye da dama na yin kuskuren zaɓarwa ƴaƴansu mata mijin aure saboda kawai mutum na da; dukiya,kyau,nasaba,ko wani abun duniya. Wasu iyayen ba sa duba halayya da nagarta su dai kawai inda ƴarsu za ta huta suma su huta shi suke nema.) [9/19, 9:15 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 5. Kwana huɗu Nasibah ta ɗauka tana jinyar jiki da zuciyarta. Sai dai babban abinda ya yi mata daɗi shine rashin sake dawowar Samir gidansu domin duba ta. Tana kula da yanda Malam Sanda ya shiga damuwa sosai,amma ita hakan sam be dame ta ba,sai ma ta ware sosai ta ci gaba da sana'ar kitso da ƙunshinta. A gefe ɗaya kuma tana zuwa makarantar boko da islamiyyah. Haka rayuwa ta dinga tafiyarwa Nasibah kamar yanda ta ke so,domin kuwa a ɓoye suke gudanar da tsaftatacciyar soyayyarsu ita da Malam Luƙman ɗinta ba tare da sanin iyayenta ba ballantana ƴan gidansu. Bayan shekara ɗaya Nasibah ta shiga SS 2,a shekarar ne ta yi wata ƙawa ƴar masu hannu da shuni a unguwarsu mai suna Yasmin. Nasibah ta haɗu da Yasmin ne a islamiyya har ta shigar mata faɗa ta yi uwa ta yi makarɓiya a lokacin da ake gab da yi wa Yasmin duka;saboda zargin wulaƙanta ɗaya daga cikin ƴan ajinsu har ta yi mata turancin da basu san ma'anar sa ba,daga nan faɗa ya ɓarke yarinyar ta ƙeƙasa ƙasa ta ce ai iyayenta Yasmin ta zaga ta kuma kira ta da matsiyaciya ƴar talakawa,sai da aka yi kwana biyu ana case ɗin daga ƙarshe Nasibah ta raba gardama ta hanyar shigarwa Yasmin aka dambace da ita. Tun daga wannan ranar ƙawance ya shiga tsakanin Yasmin da Nasibah. Duk lokacin da ake buki ko wani taro a gidansu yarinyar ko wani occasion ɗin Nasibah ke yi mata kitso da lalle,idan aka tambaye ta inda ake yi mata sai ta ƙi faɗa saboda tana son duk inda ta shiga a ga kwalliyarta ta fi ta kowa kyau. Yasmin ita ce ta damu da Nasibah sosai,don haka ita ce take yawan zuwa gidansu Nasibah har ta kawo mata alkhairi mai yawa,a ɓangaren  Nasibah kuma bata taɓa zuwa gidansu Yasmin ba. A cewarta kuɗin iyayen Yasmin ya yi yawa daga gani za su yi wulaƙanci,ita kuma a rayuwarta ta tsani duk inda za ta shiga a wulaƙanta ta ko a yi mata kallon wulaƙanci da ƙasƙanci. Shi yasa duk kuɗin mace in dai ta je yi mata kitso ko lalle ta ga tana da wulaƙanci ba za ta sake koma wa ba ko da za ta aiko sau dubu ne kuwa. Da ta gane idan ta yi ƙorafi akan halayyar wulaƙanci ko kallon ƙasƙanci da aka yi mata a gidan yana hasala Malam Sanda ya kora ta tare da gicciya mata Allah Ya isa idan bata je ba,sai ta dena faɗan abinda ya hana ta zuwa. Lokuta da dama a gaban Malam Sanda ko Mama sai ta amsa za ta je ta ƙi zuwa. Ana haka sai aka tashi auren Yayar Yasmin wato Yah Yusrah. Sosai Yasmin da Nasibah ke rawar kai suna jin kansu kamar a lokacin za su taɓa zuwa taron aure a rayuwarsu. A wannan lokacin ne kuma Yasmin ta ɗaura aniyar gabatar da best friend ɗinta Nasibah a wajen ƴan'uwanta. A ɓangaren Nasibah bata da wata damuwa domin Yasmin ta saya mata kayan da za ta saka a bikin da takalmi da jaka har da mayafi. Babbar damuwarta shine rashin babbar wayar da za ta shiga taron manyan matan da bata taɓa gani ba sai labarinsu da take ji a wajen ƙawarta,dan haka take son itama ta shiga cikinsu ta saje da su gudun kada wata ko wani ya kawo mata raini. Rawar kai da shisshigin da Nasibah ke yi sosai yake ƙona ran Nawwarah da Nadiyah manyan ƙawayenta da suka tashi a tare. Sai dai har a wannan lokacin suna tsananin jin tsoron Nasibah,dan ita har a wannan lokacin tana iya zagewa ta yi dambe abunta. Nasibah ta gama tunanin inda za ta samu wayar da za ta kece raini da ita a ranar kamun Yah Yusrah; wadda a kullum take jin labarinta a wajen Yasmin. Ana sauran kwana ɗaya bikin gidan su Yasmin Nasibah ta ɗauki kayan ankon Kamu tana gwadawa,tana gama saka kayan ta tsaya a gaban madubin da ta bawa Usman ya riƙe mata. Kallon kanta ta yi ta ce. "Yah Usman don Allah na yi kyau? Ka na ganin idan na shiga taron masu kuɗi zan saje da su?" Hararar Nasibah Usman ya yi; kafin ya ajiye madubin ya kalle ta ya ce. "Lallai ma Nasibah,ke yanzu baki ganki ba ne ko me? Ki na da kyau,kyawun diri da cikar halitta Nasibah,gaki uwa uba farar mace alkyabbar mata. Ko kin san cewa farin Baba kika ɗakko sak babu abinda ya banbantaku dai tsufa? Kamanninki kuma gaba ɗaya irin na Mama ne. Matsalarki ɗaya Nasibah baki ɗakko tsawon gashinta ba, duk wannan yauƙin gashin naki bai da tsawo,da ace gashin kanki na da tsawo babu mai yarda ke ɗin kin haɗa jinsi da hausawa,bafulatana kawai za a kira ki." Baki Nasibah ta tura gaba ta zauna a gefen Usman sannan ta ce. "Kai Yah Usman ɗin nan baka taɓa yabon mutum baka kushe shi ba. An faɗa maka fulanin dukansu kyawawa ne?" "To ai ni ba kushe ki na yi ba Nasibah,gaskiya kika tambayi a faɗa miki kuma ita na faɗa miki. Kin san Allah har kunyar jerawa nake yi da ke,abokai na baki ji tsokanata suke yi ba suna ce min ɗan aikin gidanku? Don Allah dube ni,ke nima ina ga bleaching zan fara yi." Dariya suka yi tare da shewa duka tafa kamar wasu ƙawaye. Kilishi na jiyo hirarsu daga kitchen ta ja dogon tsaki ta ce. "Ina raba ka da shegen tsugudidi Usman baka ji ko? Wannan abubuwan da kake yi ne ya sa a kullum kake jawo wa kanka zagi wajen mutane,yanzu meye abun buga shewa da tafa cinyar? Kai mace ne? Na ce kai mace ne? Baka da aiki sai zama a cikin mata kana lauɗi kana gwalli? Tashi ka fita ko na zo har wajen na buga maka wannan muciyar akai,sakarai kawai marar tunani." Sosa kai Usman ya yi ya miƙe tsaye yana karkaɗe mazaunansa,dariya Nasibah ta fashe da ita ta ce. "Ummah leƙo ki ga abinda Yah Usman yake yi,be ji faɗan da kike yi masa ba." Duka Usman ya kai mata ta goce ta shige ɗakinsu na ƴammata tana ci gaba da yi masa dariya. Ƙwafa Usman ya yi ya tafi waje ya bar Kilishi na ci gaba da mita akan halayyarsa. ********************** Rana bata karya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. Tun da safe da Nasibah ta tashi ta nemi izinin zuwa Saloon a wajen Baba,shi kuma ya amince mata domin shima yana son ta fito acan-acan a bikin da za ta je. Su Nawwarah sun jima suna kwaɗaita mata zuwa Saloon a wanke mata kanta tare da gyare mata shi ta yanda zai ƙara kwantawa ya haska kyakkyawar fuskarta,amma bata taɓa baiwa abun muhimmanci ba sai wannan karon. Dan haka cikin sauri ta gama duk wasu ayyukanta ta karya,sannan ta shiga wanka ta ƙalƙale jikinta. Tana fitowa ta kalli agogo sai ta ga ƙarfe goma da rabi na safe har ta gota,cikin sauri ta zira doguwar rigarta ta abaya akan undies da ta saka,sannan ta ɗaura agogon hannunta tare da ɗaukar ƙaramar jakarta ta riƙe. Sallama ta yi wa su Mama da Kilishi dake tsakar gida suna ayyukansu,har za ta fita daga gidan cikin sauri Mama ta ce. "Ki kama hannun Najlah ta raka ki mana Nasibah?" Hararar Najlah dake ta binta da kallo cike da murmushi ɗauke a fuskarta sannan Nasibah ta ce. "Ni babu inda zani da ita duƙun-duƙun kamar me tallan ƙuli." Waje ta yi tana sake gyara zaman mayafin abayar da ta yafa a kanta da yake zamewa lokaci zuwa lokaci. A ƙafa Nasibah ta isa saloon ɗin dake nesa kaɗan da unguwarsu,saboda wajen ya yi tashe ana yawan zancen mai saloon ɗin. Sai da ta yi nisa ta dinga nadamar rashin zuwa ta jawo Nawwarah da Nadiyah su raka ta. Da wannan tunanin ta buɗe ƙofar Saloon ɗin ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Sosai ta yaba da yanda masu saloon ɗin suka iya tarbar kwastoma. Sai ta saki jiki ta zauna a kujerar da aka bata,littafin da hotunan gyaran gashi da ƙunshi yake ta ɗauka. A hankali ta hau duba wa daga ƙarshe ta zaɓi irin wanda take so a yi mata. Babu ɓata lokaci aka hau gyara mata kai suna hira da matar jefi-jefi. Ana gama wanke wa Nasiba kai aka fara rolling gashinta;sai ga wasu kwastomomin sun shigo. Nasibah na ganinsu jikinta ya yi sanyi ta ji ta raina kanta. Ƴan mata ne kyawawa a ƙiyasi za su kai shekaru ashirin da bakwai ko da takwas. Sai dai kyawun jikinsu da ƙaramin jikinsu ya sa ba lallai mutum ya gane su ɗin suna da shekaru ba,wani irin ƙamshi ne mai daɗi yake tashi a jikinsu,komai nasu yana screaming ɗin dukiya ne,kama daga suturar jikinsu,sarƙa da abun hannunsu,takalmansu da wayoyin hannunsu. Nasibah da ke zaune ana rolling gashinta sai ta bi ayarin masu aiki a wajen ta gaishe su. Amsawa suka yi a mutunce suka samu waje suka zauna. Hirar ƙasar waje suka dinga yi suna yaba tsarin saloon ɗin domin babu abinda babu a cikin wajen irin na gyaran jiki. Ana gama wa Nasibah rolling gashinta sai aka saka ta a hair dryer. Tana nan zaune tana kallon dogon gashin ƴan matan wanda take da yaƙinin ƴan'uwan juna ne;zuciyarta na yi mata saƙe-saƙe kala-kala........... [9/19, 7:57 PM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 6. Cike da ƙwarewa ma'aikatan saloon ɗin suka kammala gyara wa Nasibah gashi,ana gamawa ta biya su kuɗin su ta yi musu sallama ta fito daga wajen cikin sauri. Da sassarfa take tafiya har ta kai ƙarshen layin da za ta sha kwana ta ɗauki layin gidansu,tana ganin ta sha kwana ta tattare doguwar rigarta ta dinga baza sauri kamar za ta tashi sama. Sai da ta yi tafiya mai nisa sosai sannan ta rage saurin tana sake damƙe jakarta a hammatar ta da kyau. Kafin Nasibah ta isa gida ta tsaya a wani layi ta zaro jakarta daga hammatarta ta zuge ta. Hannu ta sa a ciki ta zaro wata dalleliyar waya sai sheƙi take yi saboda kyau. Murmushin jin daɗi ne ya suɓuce wa Nasibah a lokacin da ta jujjuya wayar a hannunta tana kallonta. Cikin zuciyarta take jin wani sashe na faɗin. 'Sata kuma kika fara yi Nasibah? Me ya kai ki ɗaukan kayan mutane?' Da sauri ta furta. "Ni ba sata na yi ba aro na yi,kuma ai na san wajen wankin kan,ina gama hidimar biki na samu wayar da zan mayar da hotuna na ciki sai na koma inda na ɗauka na mayar. Su kuma sai su nemi masu kayan su basu abunsu,dan na tabbata dole za su bar lambar wayar da za a kira su idan an ga wayar." Tana magana tana neman inda ake cire sim,kafin ta kai ga buɗe wa wayar ta hau ruri a hannunta. Gabanta ne ya yanke ya faɗi,cikin sauri ta damƙe wayar tana zare ido tare da barin inda take tsaye ta ci gaba da tafiya. Tana jin wayar ta dena ruri ta yi sauri ta cire sim card ɗin ta yi masa kyakkyawan ɓoyo a cikin jakarta. Jujjuya wayar ta yi tana murna ta ce. "Kuma matar nan kamar ta san camera kawai nake nema a wayarta,ko irin password ɗin nan da na ga Yasmin na saka wa a wayarta bata saka wa tata ba." Hannu ta kai za ta shiga gallery,sai ta yi sauri ta janye ta kashe wayar ta mayar cikin jakarta. Da azama ta ƙara ƙaimin tafiyarta, tana isa gida ta wuce su Usman da abokansa a ƙofar gida suna hira. Ta na shiga cikin gida ta samu waje ta zauna tana mayar da numfashi da sauri da sauri. Babu jimawa Faihah ta fito daga ɗaki ta ce. "Laaa Yah Nansy yaushe kika dawo? Kaiii kin ga kan ki kuwa yanda ya yi shegen kyau?" Faihah na kai hannu za ta taɓa kan Nasibah ta doke hannun tana aika mata harara,itama ramawa ta yi ta ja tsaki ta tafi tana ƙunƙuni. Ko kula ta Nasibah bata yi ba,haka ma mutanen gidan dake ɗakunan su suna hutawa. Rabi da ta idar da sallar azahar ce ta leƙo ta ga Nasibah zaune tana kallon ƙaramin madubi tana taɓa gashin kan nata. Murmushi ta yi ta ce. "Inyeen baa,kin ga yanda kan ki ya yi masifar kyau kuwa?" A hasale Nasibah ta ce. "Don Allah Yah Rabi ku dinga cewa tubarkallah,dama abu ba abu ba sai tankawa kuke ta yi duk ya bi ya zube a banza. Haba!" Nasibah ta ƙarasa maganarta tare da miƙe wa ta shige cikin ɗakinsu ta kwanta tana nazarin irin gayun da za ta ci da yamma. Kyaɓe baki Rabi ta yi ta wuce ɗakin Kilishi don ta taya ta ɗaura gyaɗa mai gishiri da ta fara soyawa domin sayarwa a ƙofar gida. Nansy na kwance ta ji muryar Mama a saman kanta ta na cewa. "Ai sai ki tashi ki karɓi wayar ƙawarki na ta neman ki tun ɗazu. Wai yanzu ace kin fita tun kusan sha ɗaya na rana kin dawo ban isa ki shigo ki sanar dani kin dawo ba ko Nasibah?" Cike da gajiya da kasala Nasibah ta miƙa hannu ta karɓi Nokia ɗin Mama tana tura baki ta ce. "Mama a gajiye fa na dawo. To ki yi haƙuri." "Ke kika sani,ba dai ke kin rantse komai sai an yi miki magana akai ba? Humm Allah Ya shiryar dake." Waje Mama ta fita ta bar Nasibah na duba wayar tata dan ta ga wace ƙawar tata ce ta kira da bata nan. Kafin ta gama bincike wayar Yasmin ta sake kira. Cikin rawar jiki Nasibah ta amsa wayar kamar ba ita ce ta gama lauɗi tana faɗin ta gaji ba. Yasmin na gama maganar da za ta yi da Nasibah ta kashe wayar,cikin sauri da zumuɗi Nasibah ta miƙe tsaye ta na tsalle ta ce. "Kaiii amma kuwa idan har da gaske yarinyar nan ta sama min yanda zan yi na je Abuja a jirgi ba zan taɓa mantawa da ita ba a rayuwata. Maamaaaaa!" Nasibah ta ƙarasa maganarta da ƙwalawa Mama kira ta bar ɗakin tana murna. Tana shiga ɗakin Mama ta tarar da ita ta tayar da sallahr azahar,sai a lokacin ta tuna da itama bata yi sallar ba,amma zumuɗi ya hana ta bar Mama ta yi sallar ta cikin nutsuwa,bakinta na rawa don murna ta ce. "Mama kin ji Yasmin ta roƙi babban Yayansu za a je dani kai Amarya Abuja?" Mama dai bata katse sallarta ba,dan haka Nasibah sai ta fita tsakar gida da gudu tana ihun murna tana sanar da mutanen gidan itama fa za ta je Abuja kai amarya a jirgi. Nan da nan Kilishi ta fito tana fara'a ta ce. "Inyee,da alama fa maganar Babanku ce za ta tabbata a kanki Nasibah. To Allah Ya nuna mana kin je Abujar lafiya kin samo mana ɗan Abuja mu sha biki,wataƙila muma a jirgi za mu kai amarya." "Ai Ummah kar ki ji komai jirgin zuwa Makka za ku hau;saboda kin san Malam Luƙman ɗina ɗan Kano ne kamar yanda nake ƴar Kano,ya ce min ma yana kammala karatunsa a shekarar nan zai samu aiki,kin san aikin Nursing kana gamawa da aikin ka a hannu. To da ya samu aikin ya ce zai turo iyayensa,wataƙila ma a lokacin idan Baba ya ga yana da abun hannunsa ba zai ƙi alaƙar mu ba." Haɓa Kilishi ta kama daga baya ta hau tafa hannuwa tana salati. Cike da mamaki ta kalli Nasibah dake alwala ta ce. "Ke yanzu Nasibah ashe baki bar ƙwalafuci da maitar yaron nan ba? Ni a gani na idan har yana son ki kamar yanda kike son sa ai zai aiko iyayensa ko da za a ce musu ah ah an dai san da tsayayyen zancensa akan ki ko? Humm bari dai na ja baki na na ɓame,kada abu ya zo ya tabbata a ƙi dafo min kazar Hausa na goge bakina." "Ah toh! Shi ne ya fiye miki alkhairi Ummah,dan kin san kaɗan daga aikina yasin na hana ki kayan daɗin da za a dinga kawo min." "Na san za ki aikata Nasibahr Babanta. Amma Nasibah haka ake yin shafar kai fisabillahi?" Dariya kawai Nasibah ta yi ta miƙe tsaye ta nufi ɗakinsu ta saka mayafin abayarta ta tada sallah. A nan ma sai da Rabi ta yi mata magana saboda gashinta ya fito waje ana gani. Nan ma bata dena sallar ba sai kawai ta ja mayafin ta rufe kan har goshinta ta ci gaba da sallarta. Tana idarwa ta cire kayanta ta ɗaura zanin wanka ta ɗebi ruwa a randa ta shiga wanka. Nasibah ta jima tana ƙalƙale jikinta kamar bata yi wanka ba kafin ta fita;sannan ta fito ta shiga ɗakinsu ta hau ɗibar kayan da za ta saka. Mama dake zaune tana jan carbi sai ta kalli Nasibah ta ce. "Me na ji kina faɗa game da zuwa Abuja? Ke wai me yasa baki da hankali ne? Bikin ƙanin uwarki ake yi ko na ubanki da za mu barki ki tafi kai amarya har Abuja? Kin san girman Allah Nasibah;ko babanku kika bari ya ji maganar nan sai na saɓa miki fiye da tunaninki." Murmushi kawai Nasibah ta yi,dan ta riga ta san dama Mama ba za ta bari ba,amma ita ta san yanda za ta yi saƙo ya je kunnen Baba ba tare da ta yi abinda Mama ta hana ba. Tana gama saka kayanta ta fita tsakar gida ta zauna a inuwa ta hau tsara kwalliya. Yanda take yin komai cike da ƙwarewa sai mutum ya rantse da Allah ta koyo kwalliyar ne daga wajen ƙwararru. Sosai Nasibah ke da talent ɗin gyaran jiki,kitso,kwalliya da lalle kowanne iri ne. Tana gamawa ta ɗauki mayafinta ta ɗora a saman kafaɗarta guda ɗaya tana juyi;Rabi da su Najlah suna kallonta suna yaba kyawun da ta yi. Ɗaurin da ta kafa ta buɗe gashinta ta gaba,ta baya kuma ta yi acuci maza shi yafi komai ƙara fitar da kyawun fuskarta. Cikin sanyin murya irin na Rabi ta kalli Nasibah ta ce. "A gaskiya ƙanwata kin yi masifar yin kyau Barakallah masha Allah. Amma dai da zaki gyara ɗaurinki ki cire acucin nan da kika yi da ya fi,saboda kin san babu kyau haramun ne,na rasa me yasa kike son take sani Nasibah." Harara Nasibah ta banka wa Rabi kafin ta ja tsaki ta ajiye madubin a cikin kayan kwalliyarta. Kwashe su ta yi ta kai su ma'ajiyar su sannan ta shiga ɗaki ta ɗakko jakarta da ta yi wa kyakkyawan ɓoyo ta riƙe a hannunta. Ɗakinsu ta shiga da jakar ta ɗakko sabuwar jakar da Yasmin ta siya mata ta juya baya ta mayar da waya da Sim card ɗin da ta sato a saloon. Tana gamawa ta juya ta kalli Mama ta ce. "Mamana ya kika ganni? Don Allah ai kyawunta yanzu a samu wata arniyar motar ta ɗauke ni ta kaini har wajen taron ko?" Murmushi Mama ta yi,domin babu ƙarya ƴar tata ta yi mata kyau ƙwarai da gaske. Dan haka cikin raha Mama ta ce. "To ai sai ki kira Malam Luƙman ɗin naki ya kai ki wajen bikin a tashi motar ko?" Turo baki Nasibah ta yi gaba ta ce. "In sha Allahu sai Malam Luƙman ya baku mamaki watarana Mama. Zai yi kuɗi ne,kuma kowa sai ya amfana da dukiyarsa." "Allah Ya nuna mana lokacin Nasibah." Sallama ta yi wa mutanen gidansu ta fito za ta tafi. Usman na ganinta ya miƙe daga cikin abokansa ya je wajenta yana kallonta yana murmushi ya ce. "Inyeee! Nansy kin ga yanda kika yi kyau kuwa tubarkallah?" "Yauwa Yah Usman,shi yasa nake son ka. Na gode ɗan'uwana,na tafi sai na dawo." "Au yau ba zaki roƙe ni na yi miki hoto ba za ki tafi?" Cike da yaƙe kar ya gane halin da take ciki ta ce. "Yi haƙuri hankalina ne ya yi gaba....uhmm ammm ni fa dama wayarka naso na ara ko ta Nawwarah sai na ga zan takura muku. Bayan haka ma ni bana son na yi aro azo ana dizga ni a mutane. Yi sauri ka kashe min ɗaya na wuce." Babu ɓata lokaci kuwa Usman ya hau yi mata hotuna,har sai da ta gaji ta gudu. Tafe take tana yanga tana karya ƙugu kamar ƴar wani hamshaƙin a layin. Tana zuwa kan layin su Yasmin da yake akwai kwalta shimfiɗe saboda zamowarsa layin masu hannu da shuni sai ta sauya taku. A hankali ta ɓalle jakarta ta fito da wayar da ta sato ta riƙe a hannu tana yanga. Duk inda ta wuce taron maza masu zaman bakin titi sai an bita da kallo. A haka ta isa gidansu Yasmin,tun daga gate ɗin gidan ƙirjinta ya fara wani irin bugawa da ta rasa dalili. Hannu ta sanya a ƙirjinta ta dafe tana ƙoƙarin daidaita kanta. Da ƙyar Nasibah ta samu nutsuwa ta kalli motocin dake gefe da gefen titin gidansu Yasmin. A hankali take taku har ta isa bakin gate ɗin gidan. Tsayawa ta yi a wajen gate ɗin ta juya tare da zaro wayar hannunta ta ɗauki kanta hotuna guda biyu masu kyau tana murmushi. Tana gamawa ta riƙe wayar a hannunta ta shiga gidan tana rarraba idanuwa. Idanuwanta na sauka akan Yasmin da taron mutanen dake wajen gabanta ya yanke ya faɗi idanuwanta suka firfito waje kamar za su faɗo ƙasa.......... [9/19, 9:21 PM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 7. Gaba ɗaya idanuwan mutanen wajen sai suka koma kan Nasibah dake takowa zuwa cikin gidan a hankali kamar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki. Tana zuwa daf da mutanen Yasmin ta tafi wajenta cike da murna ta kama hannunta ta juya tana kallon ƴan'uwanta za ta yi magana. Hannu Yayarta ta ɗaga mata ta ratso cikin mutane ta iso gaban Nasibah da jikinta ya fara rawa ta mayar da hannunta mai riƙe da waya bayanta tana ja da baya a hankali. Yayar Yasmin na isa gaban Nasibah ta ɗaga hannu ta wanke ta da wani irin mugun mari. Cike da tashin hankali Yasmin ta damƙe bakinta,nan take idanuwanta suka hau zubar da ruwan hawaye. Cikin kuka ta ce. "Haba Yah Yusrah! Ƙawata ce fa da nake ta baku labarin ta matsu ranar nan ta zo itama a yi....." "Ki tambaye ta me ta yi na mare ta mana. Mara kunyar banza da wofi." Yusrah ta mayar da kallonta kan Nasibah dake zubar da ruwan hawaye kamar da bakin kwarya. Tunda take a gidan duniya bata taɓa tozarta da muzanta ba irin wannan rana. Da wanne ido za ta dubi mutanen wajen idan Yusrah ta gama fallasa abinda ta yi a gaban kowa? Ya Yasmin dake ta faɗi tashin ganin ta mallaki duk wani luxury abu ta zo bikin saboda kada a rainata za ta ji? Ashe haka mutum yake shiga tozarci da muzanci idan aka kama shi ya yi sata? Wani irin kuka ne mara sauti ya kuɓuce wa Nasibah. Danasani da nadamar yin abinda bata taɓa aikatawa ba tun yarintar ta ne ya tattara ya lulluɓe ta. Ji take yi ina ma tarazon dake tsakiyar gidan yaa dare ya nitsar da ita ya bi ya kulle kansa da ita a ciki? Kafin wani ya sake cewa komai a wajen suka ji muryar wani a bayansu yana faɗin. "Ke Yusrah da ƙawar Yasmin ku same ni a ƙaramin parlour." Ƙwafa Yusrah ta yi,domin ta riga ta gama fahimtar abinda Yayan nasu yake nufi,idan ta kuskura ta saɓa umarninsa zai yi mata hukunci. Dan haka rai a ɓace ta juya ta yi hanyar da mutumin ya bi. Cikin sauri Yasmin ta kama hannun Nasibah ta ja ta har zuwa bakin ƙofar wani sashe dake gidan ta buɗe ƙofa ta tura ta ciki. A hankali ta ce. "Ki yi sauri ki bi bayanta kafin ta ɓace miki." Kamar wadda ake tunkuɗawa haka Nasibah ta hau bin bayan Yasmin,sai da suka wuce parlour guda ɗaya babba mai ɗaki biyu a cikinsa,sannan suka shiga wani madaidaicin parlour ƙarami mai ɗauke da zallan kujeru da manyan hotunan ahali guda biyu a jikin bango. Tsugunnawa ta ga Yusrah ta yi a parlourn tana cika tana batsewa tare da zabga wa Nasibah harara kamar idanuwanta za su faɗi ƙasa. Sai da suka kai kimanin mintuna biyar sannan ya fito yana goge glass ɗinsa da ƙaramin tsumman dake cikin gidan glass ɗin. Yana gamawa ya saka a idanuwansa ya zauna a kujera mai cin mutum ɗaya ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Kallon Nasibah ya yi,bai san lokacin da ya saki wani irin murmushi mai sauti ba;har sai da suka ɗaga kai a tare suka kalle shi. Nan take gaban Nasibah ya yanke ya faɗi har sai da ta dafe ƙirjinta. Girarsa ɗaya ya ɗaga mata ya ce. "Nansy Ƙaya ko?" Da sauri Nasibah ta sauke kanta ƙasa ta hau wasa da bayan wayar Yusrah. Numfashi ya sauke kafin ya ce. "Miƙa mata wayarta ki bata haƙuri. Kuma daga yau sai yau kada ki sake gangancin ɗaukar abinda ba naki ba;domin ba dan na san da case ɗin ba kuma Allah Ya sa ina gida da police station za su kai ki. Kin ma san tsadar wayar da kika ɗauka?" Cikin sauri Nasibah ta ciro Sim card ɗin Yusrah zata saka mata,tana yi tana girgiza masa kai. A hasale Yusrah ta ƙwace wayarta da Sim card ɗin tana ƙwafa. A hankali Nasibah ta ce. "Don girman Allah Yah Yusrah ki yi haƙuri ki yafe min abinda na yi,bansan alaƙar ki da Yasmin ba da ba zan taɓa miki waya ba. Kuma na rantse da...." "Save it please. Ƙarya kike yi,na san ba yau kika saba ba ai kawai...." "Allow her to finish apologizing please." Nan take Nasibah ta marairace fuskarta ta kalli Yusrah idanuwanta na zubar da hawayen nadamar abinda ta aikata ta ce. "Na rantse da sarkin da yake busan numfashi ban taɓa sata ba,ban taɓa ɗaukar abun kowa ba ko da kuwa iyayena ne. Wannan ɗin ma a tawa wautar ba sata na yi ba aro na yi,ina da niyyar idan aka gama bikinki sai na mayar da wayar saloon na gudu. Na tabbata mai wajen za ta nemo ki ta baki. Don Allah ki yi haƙuri na ɓata miki rai ba zan sake ba." Jikin Yusrah ya ɗan yi sanyi,zafin Nasibah da take ji a baya ya ɗan ragu,amma har a wannan lokacin bata gamsu cewar Nasibah bata taɓa sata ba. In ma bata saba ba,to akan wannan da yiwuwar ta ci gaba da yi. Gyaran murya ya yi ya kalle su ya ce. "Duk wanda aka cuta shi ake ba wa haƙuri,lil sis please ki yafe mata. I will make sure daga yau har abada bata sake taɓa abun kowa ba,ina so ki rufa mata asiri kamar yanda Allah Ya rufa miki asiri ya baki arziƙin da zaki sayi irin wayar nan ko guda nawa kike so. Ki tashi ki je ana jiranki." A tare suka tashi za su tafi suna ta yi masa godiya. Cikin wani irin yanayi ya wurga wa Nansy kallo sai ta samu waje ta zube a wajen ta sadda kanta ƙasa. Yusrah na fita Yasmin ta hau tambayarta ina ƙawarta. Cike da takaici ta kalli Yasmin ta ce. "Daga yau sai yau kada ki sake gayyato mana wannan ƴar matsiyatan gidan nan,kuma ki tabbata tana fitowa daga sashen Giɗaɗo kin saita mata hanya kin ji na faɗa miki." "To Yah Yusrah me ƙawata ta yi miki da kika tsane ta haka?" Tsaki Yusrah ta yi ta shige gida ta bar Yasmin na saƙe-saƙe a cikin zuciyarta. A can ciki kuma Nasibah na nan duƙe kamar mai ɗaukan gafara ta ji ya ce. "To na kashe case ɗin Yusrah saura nawa da ke. Kin tuna ɓarnar da kika taɓa yi min shekara ɗaya zuwa biyu da suka gabata?" Cikin sauri Nasibah ta kalle shi tana haɗe girarta tana son tuna wace iriyar ɓarna ta yi masa a shekarun baya. Ita dai ta san a ranar da ta fara ganinsa ko kusa da juna basu tsaya ba,ballantana ta yi masa wani abun. To wacce ɓarna ta yi masa da be manta ba har tsawon wannan shekarun? Murmushi ya yi,domin yanayinta ya gama tabbatar masa da cewar bata tuna ɓarnar da ta yi masa ba sam. Dan haka sai ya kalli agogon hannunsa ya miƙe tsaye ya ce. "Ok tunda baki tuna ba,ki tashi ki tafi,amma ina son ki sani ina binki bashi,ko bajima ko ba daɗe za ki biya ni abunda kika lalata min." Tura baki Nasibah ta yi gaba ta ce. "To amma ai kaima za ka iya yin haƙuri kamar yanda ka taya ni ba wa ƙanwarka haƙuri ko?" Ido ya kafe ta da shi zuciyarsa na tunano masa matsayin Yusrah a wajensa. Haƙoransa ya haɗe waje ɗaya ya taune har sai da jijiyar kansa ta shata layi. Nan take fuskarsa ta sauya daga fara'a zuwa ƙunci,ba tare da ya sake cewa komai ba ya nuna wa Nasibah hanya. Kallonsa ta yi ido cikin ido ta karya wuya ta ce. "Don Allah Yayah Me kyau ka yi haƙuri ka yafe min duk laifin da na yi maka,wanda na sani da wanda ban sani ba ko Allah Ya sa na cika da imani." Nan take kalamanta suka saukar da fushin zuciyarsa ya saki murmushi mai sauti. Kai ya gyaɗa mata ya ce. "Jeki na yafe miki. Allah Ya sa mu cika da imani baki ɗaya. Kuma ni ba suna na Yayah me kyau ba." Cikin murna da sakin jiki Nasibah ta ce. "To meye sunanka?" "Ki je ƙawarki ta sanar da ke suna na." Da sauri Nasibah ta juya za ta fita daga parlourn. Shi kuwa Yunus gaba ɗaya ya tattara hankalinsa da nutsuwarsa a bayanta yana kallon yanayin takunta mai ɗaukan hankalin mai kallo. Tana ɓacewa ganinsa ya saki murmushi mai sauti ya ce. "Haba Giɗaɗo she is a child for God sake." Zama ya gyara a kujerar yana tuna ranar farko da ya fara ganin Nasibah. Murmushi ya dinga dokawa yana tuna yanda ta danganta shi da wani har tana faɗin ai shi ɗin bai kai wancan kyau ba. Sai gashi kuma yanzu tana kiransa da Yayah Kyakkyawa. Ƙarar da wayarsa ta ɗauka ne ya katse masa dogon tunanin da ya faɗa. No Goggoji ya gani tana yawo a wayarsa. Gabansa ne ya yanke ya faɗi har sai da ya furta. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil." A fili. A hankali ya amsa kiran nata ya kara a kunnensa,yana gama sauraronta ya ce. "Eh Goggoji na gama,gani nan shigowa mu gaisa." Katse kiran ya yi ya miƙe tsaye yana gyara karin hularsa. Cikin tafiyar isa da ƙasaita tare da izza irin ta cikakkun mazaje ya isa wani ɗaki ya zaɓo takalmin da ya dace da kayan jikinsa ya sanya,sannan ya cire na ƙafarsa ya mayar da su mazaunin da ya dace ya fito. A waje ya tarar da Yasmin da Nasibah da ta hana su shiga cikin taron mutane,dan ji take yi kamar Yusrah ta gama sanar da kowa abinda ya faru,kawai shiru suka yi dan suna tsoron Yayansu. Suna nan tsaye suna hira ƙamshin turarensa ya yi musu sallama. Da sauri Nasibah ta juya ta kalle shi ta saki murmushi,shima murmushin ya sakar mata ya zo wajensu zai gifta. Cike da girmamawa Yasmin ta durƙusa ta gaishe shi. Nasibah kuwa sai ta ce. "Yayah Mai Kyau na san sunan ka yanzu." Har ya gota su ya tsaya cak. Hannu Yasmin ta hau yarfewa tana kallon Nasibah. Shi kuwa Yunus sai ya juyo ya kalleta ya ce. "Uhumm meye suna na?" "Yayah Yunus,ko kuma na ce Giɗaɗo. Au Yayah Giɗaɗo." Kai ya jinjina ya kalli Yasmin ya ce. "Lallai Yasmin ta yi ƙoƙari." Daga nan bai sake cewa komai ba ya yi gaba. Yana tafiya Yasmin ta ja hannunta ta zaunar da ita a saman wasu fararen kujeru ta ce. "Ke dai Nasibah ban san wace iri bace ke. Yanzu don Allah me ya kai ki yi masa magana bayan na faɗa miki he is not in a good mood?" "To ni be nuna min wani mood ɗin da zai hana ni yi masa magana ba;don me zan ƙi yin magana?" Waigawa Nasibah ta yi hagu da dama taga babu wani a kusa da su,sai ta yi ƙasa da murya ta ce. "Ke ni fa yunwa nake ji,na gaji da yi miki kawaici." Dariya sosai Yasmin ta yi ta ce. "Jira ni anan ina zuwa." Cikin gida Yasmin ta shige da sauri ta bar Nasibah a wajen tana kallon Zuri'ar kyawawa,kamar yanda take kiransu a cikin ranta. Babu jimawa sosai Yunus ya fito daga main house ɗin ransa a matuƙar ɓace. Kai tsaye wajen wata mota ya nufa wadda aka rufe ta,yana zuwa ya yaye rigar ya yi wurgi da ita a ƙasa ya buɗe motar ya shige. Yana juyawa da motar ya juya ya kalli wajen da Nasibah ke zaune tana kallonsa hankalinta na kan tuna laifin da ya ce ta taɓa yi masa. Fuskarsa da ke ɗaure ce ta fara sassautawa daga fushin dake samanta. A hankali idanuwan Nasibah suka sauka akan rubutun da ta yi masa wanda ta rubuta. 'MoTar NaNSy ƙAyA.' Idanuwanta ta zaro waje ta damƙe bakinta,tare da miƙewa tsaye. Murmushi Yunus ya sakar mata sannan ya tada motar ya bar gidan a guje.......... [9/22, 8:13 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 8. Koda Yasmin ta dawo ɗauke da abinci sai ta tarar da Nasibah a tsaye tana zaro idanuwa waje. Girarta ta haɗe waje ɗaya kafin ta ce. "Yah Yusrah ta sake yi miki wani abun ne Nansy?" Girgiza kai Nansy ta yi cikin sauri ta ce. "No babu abinda ta yi min. Ammm yauwaa kin kawo abincin,zauna mu ci ko ke kin ƙoshi?" Sakin jiki Yasmin ta yi tana murmushi ta ce. "Inaa,ai nima nan da kika ganni yunwar nake ji,ni tunda aka fara maganar bikin nan na su Yah Yunus fa ban zauna ba ballantana...." Yanda Nansy ta waro idanuwa waje tana neman shaƙewa da abincin da take ci ne ya sanya Yasmin dakatawa da kalamanta ta ce. "Ke lafiya wai kike ta yin abu kamar me aljanu? One minute kina dariya, another minute za ki sauya fuska. Me yake faruwa ne?" Yaƙe Nansy ta yi tare da sake ɗiban fried rice ɗin da ta ji haɗi ta kai bakinta. Sai da suka yi nisa a cin abincin sannan Nansy ta gyara zama ta ce. "Ni kuwa in tambaye ki mana Yasmin." "Uhum?" "Wai takamaimai auren wa ake yi ne a gidan nan? Don ni dai a iya sani na bikin Yayarki Yusrah kika ce min za a yi,to kuma na ji kin soko wani zance ɗazu da ban gane kansa ba." Murmushi Yasmin ta yi kafin ta ce. "Yau dai bari na baki cikakken tarihina,domin ta haka ne za ki fi gane abinda yake faruwa a gidan namu. Yauwa,kin ga dai da farko kamar yanda kika riga kika sani suna na Yasmin Ibrahim Yunus. Mahaifinmu ɗan asalin jihar Gombe state ne,kasancewar Kano cibiyar kasuwanci ce shi ne dalilin da yasa kakanninsa na ɓangaren uwa da uba suka dawo nan suke kasuwancinsu. Tun daga nan ahalinsu suka fantsama a cikin garin Kano,sai dai duk da haka basu taɓa watsar da danginsu na can Gombe ba,kuma har yau idan kin kula muna yin yaran fullanci a gidan nan. Yah Giɗaɗo ya ci sunan Kakan mu ne,shi yasa ake kiransa da Giɗaɗo. Mamansa ta rasu da jimawa tun yana sakandire a shekararsa ta ƙarshe. Gwaggoji Kakarmu da ta haifi Abbah,ita ce ta ci gaba da kula da shi,bayan rasuwar mahaifiyarsa,a lokacin ta so ƙwarai da gaske Abbah ya ƙara aure amma ya ƙi,sai da ya shekara goma kafin Gwaggoji ta shawo kansa ya auri Hajiya Yalwa wato mahaifiyata. Hajiya Yalwa ta jima tana zawarci a gaban iyayenta,domin kuwa mijinta ya rasu ya barta da ƴa guda ɗaya mai suna Yusrah. Kasancewar Yusrah na ƙarama sosai mahaifinta ya rasu sai Mama ta ƙi yarda ta yi wani auren. A cewarta tana so ta ba wa ƴarta ingantacciyar rayuwa. Shi yasa ta dinga faɗi tashi tana rayuwar neman na kanta har dai daga ƙarshe suka haɗu da Abbah a lokacin da ta je Lagos saro takalma. Tun da ya dawo ya sanar da Gwaggoji zai yi aure,sai ta yi ta murna. A yanda Gwaggoji ta ke bamu labari da haɗuwar Abbah da Mama ba a fi wata ɗaya ba aka ɗaura aure ta tare da ƴarta Yusrah. A lokacin Yusrah na da shekara sha tara a duniya, dan har ta kammala sakandire jami'a za ta shiga. A lokacin da Abbah ya auri Mama ya yi ne kawai dan ya cika burin Gwaggoji na son ya yi aure,shi yasa ma ya auri macen da ta manyanta,sai gashi babu zato ko tsammani an wayi gari Mama na ɗauke da cikina. Hankalinta ya tashi ƙwarai da gaske,domin ita ta cire rai da sake haihuwa a duniya. Dan haka sai ta riƙa kuka da addu'ar zubewar cikin kada ƙawayenta su ji su yi mata dariya. Cikin rashin samun nasara ciki na nan daram bai zube ba,sai ma girma da ya dinga yi cike da ƙoshin lafiya. A wannan lokacin ne Mama ta samu soyayyar Abbah ta gaske har ya saki jiki da ita,dan haka sai ta haƙura itama ta rungumi cikin jikinta cike da so da kulawa. Watarana Mama ta sa Abbah ya kirawo Yah Giɗaɗo dan ta gansa,domin a kullum suka zauna Abbah bashi da wata magana da ta wuce ta Giɗaɗonsa. Dan haka sai Abbah ya kirawo Yah Giɗaɗo daga Abujah inda yake karatun Masters ɗinsa,duk da cewa Yah Giɗaɗo na ta ƙoƙarin dojewa zuwa gida;kan dole ya zo,saboda ya san ko bajima ko ba daɗe sai ya haɗu da Mama tunda alaƙar aure ta ratsa. A lokacin da ya zo ya samu labarin cikin da Mama ke ɗauke da shi sai kunya ta kama shi,gaba ɗaya sai ya ji gidan ya fita a ransa. Ga uwa uba takura da matsin lamba da ya fara samu a wajen Yusrah da ta nuna masa so a karon farko da ta fara ganinsa. Kwanansa uku ya tattara ya koma Abuja. Tun daga wannan ranar bai sake dawowa gida ba;har sai da Mama ta haife ni Gwaggoji ta kirasa a waya ta yi masa faɗa sosai. To a sannan ne ya zo ya ganni cike da tsarabar kayan jarirai. Yah Yunus ya ce a ranar da idanuwansa suka sauka akan ƙaramar fuskata ya ji dikkan baƙincikin dake cikin ransa ya yaye,a ranar ya ji babu wata halitta da yake so sama da ni,soyayya yake yi min wadda uba zai yi wa ƴarsa. Dan haka Abbah sai ya koma ɗan kallo. In ji Gwaggoji ta ce,tun Yah Giɗaɗo na kashe mana kuɗi ni da Mama tana jin daɗi har sai da kishi da ƙyashi ya shiga zuciyarta;ta fara tunanin a ina yake samun kuɗi bayan shi ɗin karatu yake yi? Lokacin da Mama ta fito da hassadarta da ƙiyayyar da take yi wa Yah Giɗaɗo a fili sai Abbah da Gwaggoji suka kira meeting aka zauna,anan ne Abbah yake sanar da Mama irin dukiyar da Yah Giɗaɗo ya mallaka na gadon mahaifiyarsa;ciki har da kamfanonin ƙera tabarmi guda biyu,da na shigo da Electronics daga ƙasashen waje dake a can Abuja. Yah Yunus ya mallaki gidan mai a garin Abuja,wanda dika yana cikin gadon da mahaifiyarsa ta bar masa. Jikin Mama sai ya yi sanyi a wannan lokacin ta rage adawa da nuna wa Yah Giɗaɗo ƙiyayya a fili. Amma har yanzu kowa ya san bata son sa bata ƙaunarsa,dan ko ni nan da take mahaifiyata ina sane da irin ƙiyayyar da Mama take nuna wa Yah Giɗaɗo. Bayan rasuwar Abbah da shekara biyar ta fara cusa wa Yah Giɗaɗo Yah Yusrah,ita ta ƙara rura wutar soyayyar Yah Yusrah a zuciyarsa,domin a kullum nuna mata take yi idan ta aure sa har ta haihu da shi kaf dukiyarsa za ta dawo wajenta da ƴaƴanta. To kin ji taƙaitaccen tarihin gidan nan. Yauwa,kuma da na ce miki shekarata sha bakwai nima ƙarya nake yi,shekarata sha huɗu a duniya,saurana watanni biyar na cika sha biyar,girman jikine kawai ya sa nake yin ƙaryar shekaru saboda na samu ƙawa daidai da girma na." Ido Nasibah ta waro,kafin jikinta ya saki ta yi ajiyar zuciya mai ƙarfi,nan take zuciyarta ta cika da tausayin Yunus. Jiki a sanyaye ta wanke hannunta da ruwan robar da ke wajen ta ce. "Ke ni fa ina jin ta bakin Yayarki za a yi,zuwa zan yi na adana mutuncina a gidan ubana;zama na anan hatsari ne babba." "Hatsarin me kuma Nansy? Don Allah ki zauna a gama kamun nan da ke,baki ga har an gama deco ba masu DJ sun zo? Na tabbata jira ake a yi sallar la'asar a fara. Kin ga bani da ƙawaye,ke kaɗai ce ƙawata Please ki zauna." Yasmin ta ƙarasa maganarta cike da shagwaɓa. Murmushi Nansy ta yi ta ce. "Ba za ki gane halin da nake ciki bane Yasmin. Amma babu komai zan zauna,sai dai fa da na ga daga-daga zan arce na ware gida." "Na ji na yarda,da kin gaji kawai ki sanar dani na baki abun biki ki kai wa Mama da su Najlah." Murmushi kawai Nasibah ta yi,ta samu waje ta sake lafe wa a jikin kujerar da take kai tana hango duk abinda ake yi daga nan inda take. Suna nan zaune aka kira sallar la'asar,sai Yasmin ta ja hannun Nansy suka nufi cikin gidan. Kai tsaye sashen Gwaggoji suka nufa. Babban parlour ne guda ɗaya da ɗakuna biyu a wajen,sai banɗaki ɗaya a cikin parlour da dinning area. Banɗakin dake cikin wani ɗaki Yasmin ta nuna wa Nansy,ita kuwa ta shiga ta hau kalle-kalle tana ayyana abubuwa masu tarin yawa a cikin ranta. Kasa buɗe pampo ta yi dan ta yi alwala,gashi tana tsananin jin kunyar ta leƙa ta ce wa Yasmin bata iya amfani da pampon ba. Haka ta dinga taɓe-taɓe a wajen har ta samu nasarar kunna pampon ta ɗaura alwala ta fito. Sallah ta tarar Yasmin na yi. A gefenta ta shimfiɗa abun sallah da hijabi a ninke a wajen. Ɗauka Nansy ta yi ta tada sallah itama. Suna idarwa suka zauna suka sake tsara kwalliya tare da feshe jikinsu da turaruka masu daɗin ƙamshi. Lokacin da Yasmin ta kula Nansy na ta yaba turarukan sai ta ɗauki wasu ta bata kyauta. Tun Nansy na ah ah,tana ah ah sai da Yasmin ta dage ta karɓa. Godiya ta yi mata sosai sannan suka fito waje inda aka fara sakin kiɗa kamar gidan zai tsage. Wajen da suka zauna suka ci abinci Nansy ta nufa,sai Yasmin ta riƙe mata hannu ta ce. "Ina kuma za ki koma?" "Can wajen da muka zauna ɗazu mana." "Ah ah don Allah ki zo mu je ga Gwaggoji can da Mama ki gaishe su." Cike da fargaba da faɗuwar gaba Nansy ta ja hannun Yasmin ta riƙe,cikin dabara ta ce mata. "Haba Yasmin,ta ya za a yi a zuwa na na farko gidan nan na je na gaishe su a cikin taro? Ai sai nake ganin kamar hakan be dace ba,ki bari a gama biki lafiya,sai na zo na yi musu ban gajiya da Allah Ya sanya alkhairi,ko ya kika ce?" Kai Yasmin ta ɗaga suka wuce wajen da suka ci abinci suka ja kujeru suka fito fili suna kallon duk abinda ke gudana a tsakiyar taron. Lokaci zuwa lokaci Yasmin kan tashi ta shiga cikin danginsu a yi hotuna da ita ta koma wajen Nansy. Suna nan zaune yamma ta fara yi sosai aka saka waƙar da Nansy ke so. Babu ɓata lokaci kuwa ta miƙe ta hau rawa a hankali tana rausaya jikinta cike da jin ƴammatanci. Har gate ɗin gidan ya buɗe motoci uku masu kyau suka shigo gidan Nansy bata dena rawa ba. Yasmin dake tsallan murna tana taɓo Nansy ta gaji da share ta da Nansy ta yi,sai ta nufi wajen motocin fuskarta ɗauke da maɗaukakin murmushi. Tana zuwa gaban motar Giɗaɗo sai ta tsaya tana jiran fitowarsa,nan da nan masu ɗaukan Video suka fara aikinsu. Giɗaɗo wanda tun shigowarsu ya ke kallon yanda mata ke ta tiƙar rawa ransa ya ɓaci. Cike da takaici ya ce. "Don Allah Man Sadi ka duba ka ga yanda mata ke ta tiƙar rawa ana gab da kiran sallar magariba. Shi yasa na ce wa Gwaggoji ba zan zo ba,amma ta dage sai na zo tunda surukarta ta ce abinda take so kenan,danginta su ga ango. Mtwss." Ya ƙare maganarsa da jan dogon tsaki tare da kawar da kansa gefe,murmushi Malam Sadi ya yi ya ce. "Ai Alhaj lokacin da ka yi min waya dan na zo na same ka a gidanka,lokacin aka fara shagalin." Kai kawai Giɗaɗo ya girgiza cike da takaici ya yi ƙwafa. A hankali Idanuwansa suka sauka akan Nansy dake shirin zama a kujera saboda gajiya da rawa da ta yi. Murmushi ya saki mai sauti,saboda ganin yanda ta ware kanta daga cikin taron da ake ta casu. Nan take zuciyarsa ta gasgata cewa Nansy na da wani ɓangare mai kyau a tattare da rayuwarta,sai dai rashin jin ƙuruciya da ya yi yawa a tattare da ita. Buɗe motar Yasmin ya yi daidai da kai hannunsa jikin hannun ƙofar,suna haɗa ido ya sakar mata murmushi ta isa gabansa ta rungume shi. Hannu ɗaya ya ɗora a bayanta ya riƙe hannunta suka fito daga motar. A haka suka isa wajen Yusrah da ƙawayenta dake ta tiƙar rawa. A gefe ɗaya kuma Managers ɗin dake kula da kamfanoninsa wanda suke a matsayin abokansa ne tafe suna take masa baya. Nan take DJ ya sauya salon kiɗan sa waje ya sake kacamewa da ihu da murna tare da bin waƙoƙin da ke tashi a wajen. Abokan ango da angon kansa sun saki bakin aljihu sosai suna ta feshin nera. Nansy dake gefe sai ta ji kamar ta shiga taron da leda ta yi ta tattare kuɗin in ta gama ta kai wa Babanta. Dariya ta yi a lokacin da ta tuna da Babanta,ta tabbata idan ya ga wannan uwar dukiyar da ake zubarwa a ƙasa gigicewa zai yi. Ko minti biyar Giɗaɗo bai yi ba a wajen ya bar wajen zai shige sashensa. Ta gaban Nansy dake ta zabga murmushi ya gilma,amma sai ta yi kamar bata gan shi ba,dan haka kawai ta ji bata son wata mu'amala ta sake haɗa ta da shi tunda aurensa ake yi. Shi kuma Giɗaɗo sai ya ji babu daɗi a cikin ransa da yarinyar ta kawar da kai ta yi kamar bata gansa ba. Rashin dalilin da zai haɗa su yin magana ne ya sanya shi yin gaba ya shige ɓangarensa. Yana shigewa Nansy ta saki wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Lokacin da gari ya fara duhu sai gidan ya cika da hasken fitulun wutar lantarki. Hasken sai ya ƙara haskaka mutane da kyau kamar rana. Abokan Yunus ne tafe suna hira suna tattaunawa game da yanda ƴan mata ke casu a wajen gwanin burge wa. Kamar daga sama ta ji an ce. "Ke me kike yi anan?" Ɗaga kanta Nasibah ta yi dan ta ga wanda yake yi mata magana. Cike da tsananin mamaki ta ga Samir tsaye a saman kanta shi da wani siririn mutum fari tas kamar zabaya.......... [9/26, 5:57 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 9 Girar ta ta haɗe waje ɗaya tana kallonsa cike da mamaki ta ce. "Ban gane me nake yi anan ba. Biki na zo mana ko baka gani bane?." Kai Samir ya jinjina ya kalli Nuh ya ce. "Abokina na fa gode da wannan gayyatar da ka yi min,kawai ka shiga ciki dama ni ba wani sani na angon ya yi ba,idan ka fito mun wuce." Kujerar da Yasmin ta tashi ya ja ya zauna yana fuskantar Nansy da ta haɗe fuska tamau. Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce. "Da alama dai baki gane ni ba ko Baby?" Kallon sama da ƙasa Nansy ta yi wa Samir kafin ta ce. "Baby kuma? Ni suna na..." "Nasibah. Na sani ba sai kin faɗa min ba." Samir ya ƙarasa mata maganar tare da lumshe kyawawan idanuwansa masu haske ya sake cewa. "Tun lokacin da na ajiye ki a gida na wuce Abuja kike yawan faɗo min a rai. Na so na zo har gida na sake duba ki,to sai na yi tunanin Baba ba zai so hakan ba." A sheƙe Nansy ta kalli Samir sannan ta ce. "Nake faɗo maka a rai;ko kuma kake jawo ni? Dan ni gaskiya tun ranar da ka tafi ban sake tunaninka ba,in fact na ma manta da kai ni." Dariya sosai Samir ya yi kafin ya shafa gemunsa da yake kashe wa kuɗi ya ce. "Wannan fiffizgewar da kike yi kaɗai ta tabbatar min da yanda kike tunawa da ni a kullum. To kar ki damu,a wannan karon dama ban shirya koma wa Abuja ba tare da na je na gaishe da Baba ba,irin gaisuwar nan ta musamman." Cikin faɗuwar gaba Nansy ta miƙe tsaye tana kallon Samir ta ce. "Kai Malam dakata don Allah! Haka kawai ina zaman zamana za ka zo min da wata maganar da na kasa gane inda ka dosa? Me kake nufi da ni ne?" "Aure nake nufin ni da ke mu ƙulla. Kuma da yardar Allah sai na aure ki." "Humm ai kuwa ka shirya samun karyewar zuciya,domin kuwa ni Nasibah ina da wanda nake so da aure yake so na. Yanzu haka da nake yi maka magana har an gama maganar aurenmu ni da shi,ina gama secondary za a yi bikinmu." Nan take fara'a da annashuwar dake saman fuskar Samir suka kau;ƙunci da damuwa suka mamaye farincikinsa. Kasa cewa komai ya yi ya tsaya yana kallon Nasibah dake tattara kayanta za ta bar masa wajen. Kafin ta ɗago daga duƙawar da ta yi Yasmin ta dawo wajen hannunta riƙe da ledoji masu yawa. Tana zuwa ta ci karo da Samir fuskar nan a haɗe kamar hadari. Cikin sanyin murya ta kalli Nasibah da ta ɗago riƙe da jakarta ranta a ɓace ta ce. "Nansy me ya faru? Wani abu ya yi miki?" Tsaki Nasibah ta ja ta ce. "Ni gida zan tafi,mun yi da Mine zamu haɗu a hanya mu wuce gida tare." "Ohhh soyayya ruwan zuma,nima dai Allah Ya nuna min na fara yin soyayya Nansy." Da sauri Yasmin ta isa gaban Nansy ta yi mata raɗa a kunne. "Ni fa na zaci guy ɗin nan me kyau wajenki ya zo Nansy." Juyawa Nansy ta yi ta harari Samir sannan ta ce. "Wa ni? Allah Ya kiyaye,ni ba waje na ya zo ba,kin ga na gaji sosai Yasmin,na matsu na je gida na raba kaina da kayan nan duk sun matse ni." "To ko na kira Malam Sadi ya mayar da ke gida ne?" Kafin Nansy ta yi magana Samir ya isa gaban Yasmin ya karɓi ledojin hannunta ya ce. "Kar ki damu,ni zan mayar da ita gida. Ita ɗin kamar amana ce a waje na." A hasale Nansy ta kalli Samir ta ce. "Malam bana son shisshigi,ta ina kuma na zamo amana a wajenka?" "A sannu za ki gane. Mu je ko?" Hannu Nansy ta harɗe a ƙirjinta tana girgiza ƙafarta ta ƙi motsawa. Samir na ganin haka ya saka hannu ɗaya ya damƙi nata ya ja ta da ƙarfi suka fara tafiya. Cike da tsoro Yasmin ta bi su da gudu ta ce. "Kai Malam sake ta mana,ta ce ba za ta bika ba ana dole ne?" "Kar ki damu ba gidan Malam Sanda Uba Makaɗi take ba? Can zan mayar da ita da kaina." Yasmin na jin ya ambaci sunan mahaifin Nansy sai ta tsaya tana nazarin abinda yake faruwa. Shin ko dai akwai abinda Nansy ke ɓoye mata ne? Bata dawo daga duniyar tunani ba ta ga motar da Samir ya jefa Nansy ta wuce ta gabanta. Da sauri ta ja baya ta koma cikin gida ta shige ɗakin Gwaggoji ta ɗakko wayarta ta riƙe a hannu bini-bini tana duba lokaci. A ɓangaren su Nansy kuwa fuskar ta tuni ta jiƙe da hawaye,domin ta tsorata ƙwarai da yanayin da ta ga Samir a cikinsa. Yanayi ne da ya tsorata ta ya firgita ƙaramar ƙwaƙwalwarta. Har suka isa gida babu wanda ya sake yin magana. Suna kai wa ƙofar gidan su Nansy ta kama hannun ƙofa tana son ta buɗe ta gudu. Jin ƙofar a rufe ne ya sanya ta juyawa ta kalli Samir dake ta kokawa da ɓacin ran da ya taso masa. A hankali ya buɗe rinannun idanuwansa ya zuba su akan kyakkyawar surar jikin Nansy. Sai a yanzu ya tabbatar da cewa yarinyar na da kyau mai fisgar hankali,kuma tana da diri irin na cikakkun ƴan mata. Lallai ba zai taɓa barin ta wuce shi ba,domin nan gaba kaɗan da ta ƙara girma za ta fi haka kyau. Daga can cikin maƙoshinsa ya ce. "Akan wancan matsiyacin kike nuna min ƙiyayya Nasibah? Ko wancan me ɗagaggen wandon ba ke yake jira ba?" Da sauri Nasibah ta kai dubanta zuwa ƙofar gidansu,Malam Luƙman ta gani a tsaye a jikin ginin gidansu yana kallon hanya lokaci zuwa lokaci. Kuka ta fashe da shi tare da yarfe hannu ta ce. "Shikenan yanzu za ka jawo masifa ta hanyar dasa rashin yarda a tsakani na da masoyina na gaskiya." Gira Samir ya ɗaga yana bin Nansy da kallo,murmushi ya yi mai sauti kafin ya buɗe motar ya fita. Zagayawa ya yi ya buɗe mata sannan ya kamo hannunta ya ja ta jikinsa ya rungumeta ta gefe. Ƙoƙarin ƙwacewa take amma ina,tuni Malam Luƙman ya yi mummunan gamo. Cike da tashin hankali da damuwa Nansy ta tattara dika ƙarfinta ta ture Samir gefe. Dariyar mugunta ya yi sannan ya ce. "Babe menene haka?" Da gudu Nansy ta bi bayan Malam Luƙman da ya bar wajen cike da tashin hankali idanuwansa na zubar da hawaye. Ganin rigarta da ta ɗame ta ta hana ta gudun da kyau,sai ta yar da takalmanta a wajen ta tattare rigarta ta bi Malam Luƙman da gudu ta sha gabansa tana haki. Kallonta ya yi cike da karyewar zuciya ya ce. "Nasibah ina alƙawarin tarayya dani duk rintsi duk wahala da kika yi min? Nasibah ashe ba za ki iya jira na kammala karatuna na samu aiki mu yi aure ba? Da me wannan ɗin ya fini da kika zaɓi fita da shi akai na? Na jira ki a wajen da muka yi zamu haɗu har na gaji ban ganki ba. Nas..." "Don Allah ka tsaya ka saurare ni,abinda wancan azzalumin yake son gani kenan a tsakaninmu,don soyayyarka da Annabin Rahama ka zo mu koma mu ba wa wancan jahilin kunya,na yarda daga baya duk hukuncin da za ka yi min ka min. Ban ci amanar soyayyarka ba,ba kuma zan taɓa ci ba har abada, Yasmin ce shaida da ƙarfin tsiya ya tura ni motarsa ya dawo dani gida kawai dan yana taƙamar Baba yana son sa. Ina fatan baka manta da wannan mutumin da ya taɓa taimaka min ya kaini asibitinsa lokacin da bani da lafiya." A hankali kalaman Nasibah suka fara tasiri a cikin zuciyar Malam Luƙman,dan haka sai ya ja gefe suka tsaya suka ci gaba da tattaunawa,a nutse Nasibah ta warware masa zare da abawa. Nan take Malam Luƙman ya fahimce ta suka shirya. Duk abinda suke yi Samir bai tafi ba,mamakin kansa yake yi sosai da ya tsaya a ƙofar gidan talakawa kamar su Nasibah,kuma har zuciyarsa ta kamu da son ƴar talakawa kamar Nasibah. Shin ihu zai yi ya daɓa wa kansa wuƙa,ko me zai yi? Shine fa Samir wanda ƴan matan Abuja yaran masu kuɗi da ƴan siyasa ke mutuwar so,shi ne fa matashi mai tashen kuɗi da ji da kansa. Wacece Nasibah da har za ta yi masa wulaƙanci akan talaka kuma ɗan talaka mai ɗagaggen wando? Wani irin takaicin kansa yake ji saboda soyayyar Nasibah da yake jin tana sake nunkuwa a cikin ransa. Tunawa da wanene Malam Sanda Uba Makaɗi akan son kuɗi ne ya sanya shi yin murmushi. Da sauri ya buɗe motarsa ya sake fitowa a karo na biyu;sannan ya buɗe baya ya kwaso ledojin Nansy ya isa bakin gidan ya kwaɗa Sallama. Nansy dake nesa da gidan suna ta shan soyayyarsu da Malam Luƙman bata kula da abinda Samir ke yi ba. Babu jimawa Malam Sanda ya fito yana tambayar wanda yake sallama. Ganin Samir a tsaye a ƙofar gidansa ne ya sanya shi sakin fara'a a zuciyarsa yana faɗin. 'Ai ni na san ban yi addu'a a banza ba. Gashi Allah Ya dawo da kai da ƙafafuwanka.' A zahiri kuwa sai ya miƙa wa Samir hannu yana faɗin. "Ikon Allah. Alhajin Allah yau kai ne a gidan nawa? Gashi kuwa ko minti ashirin ban yi da dawowa ba,yanzu haka hannu na wanke zan ci tuwon dare na ji ana ta kwaɗa sallama." Murmushi Samir ya yi mai sauti sannan ya ce. "Allah sarki. Ni ma ai ban jima da zuwa ba,ƙanwar tawa ce muka haɗu da ita a wajen biki,to shine na ce dare ya yi bari na rage mata hanya." Nan take Malam Sanda ya washe baki ya ce. "Allahu Akbar. To ina ita Nasibahr?" "Ohh sorry ban sanar da kai ba ta ɗan je can suna gaisawa da wani ustaz. Baba ga kayanta ni zan wuce,dama cewa na yi bari mu gaisa tunda na zo har gida." Nan take Baba ya gane da wa Nansy ke tsaye, sosai ransa ya ɓaci,amma sai ya danne ya kama hannun Samir da yake miƙa masa hannu su gaisa ya ce. "Allah sarki Malamin Islamiyyarsu ne,ka san da yake bana za su yi sauka,to shine yake ɗan zuwa su tattauna akan bikin saukar. Na gode da gaisuwa Allah Ya yi albarka ya jiƙan Mahaifinka. Nan gidanku ne Alhaji duk lokacin da ka so zuwa a gaisa ka shigo kawai." Murmushi Samir ya yi mai sauti sannan ya ce. "To na gode ƙwarai da gaske Baba,Allah kuma ya amsa addu'o'inka. Ni zan wuce." Hannu Samir ya sanya a aljihu ya zaro kuɗi masu kauri ya miƙa wa Malam Sanda,cikin sauri kamar mai jira haka Malam Sanda ya yi ram da hannun Samir yana durƙusawa tare da yi masa godiya. Haka suka rabu Samir na murmushin samun nasara,Malam Sanda na yaƙe tare da tunanin yanda zai ci mutuncin Nasibah. Da gangan Samir Ya haske su Nasibah dake tsaye a jikin wata falwaya suna hira cike da shauƙin soyayya. Nan take ran Malam Sanda ya sake dugunzuma ya ɓaci. Tun kafin motar Samir ta bar layin ya danna hannunsa a aljihu ya adana kuɗinsa sannan ya hau ƙwala wa Nasibah kira. Nasibah na jin muryar Babanta sai gabanta ya yanke ya faɗi. Cikin sauri ta kalli Malam Luƙman ta ce. "Na shiga uku Baba ya gammu." "Ai ni burina kenan,mu je kawai na gaishe shi na sake gabatar da kaina." "Ba za ka gane ba,Baba baya ƙaunar tarayyarmu ko kaɗan." "Kada ki damu,mu je." Jiki a mace Nansy ta bi bayan Malam Luƙman dake da yaƙinin idan Baban Nasibah ya tsaya ya ji ta bakinsa;zai ɗaga musu ƙafa har su kammala karatunsu sai a aura musu junansu. Su na isa Malam Sanda ya daka wa Nasibah tsawa ya kora ta cikin gida. A guje ta shige tana fatan ya tsaya ya saurari masoyin nata,wataƙila ya amince da shi ya aura mata zaɓin ranta............. [9/26, 10:07 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 10. A sheƙe Makaɗi ya kalli Malam Luƙman daga sama har ƙasa ya ga yanda wandonsa yake a ɗage. Wayar hannunsa ya kunna ya sake haska shi ya ce. "Kai miƙe tsaye da kyau. Duk da na kula tsananin rashin tarbiyya ya hana ka durƙusa min har ƙasa ka gaishe ni." Tsaye Malam Luƙman ya miƙe tare da miƙa wa Makaɗi hannu dan su yi musabaha. Kallon hannun Malam Luƙman Makaɗi ya yi kafin ya ce. "Ba shakka Luƙman! Ahh ba shakka,ai dole ka bani hannu mu gaisa tunda baka samu cikakkiyar tarbiyyar girmama na gaba da kai ba a gidanku. To tsaya ka ji,ko kana da tarbiyya ko baka da ita wannan kai ta shafa. Ni Sanda ɗan gidan Uba Makaɗi ba zan baka auren ƴata Nasibah ba har abada. Ina so a yanzu ba sai anjima ba ka tattara guntun mutuncinka da nake gani a idona saboda kasancewarka Malamin ƴata ka bar ƙofar gidan nan." Cikin tsananin damuwa Malam Luƙman ya rusuna har ƙasa ya kama ƙafar Malam Sanda ya ce. "Baba don girman Allah kada ka raba ni da Nasibah,na girma na rayu da soyayyarta a cikin raina,kuma itama babu wanda take so bayan ni,raba mu zai iya jawo babar matsala a..." "A rayuwarka? To ai dama tuni a cikin matsala kake Luƙmanu. Ah yo Allah na tuba akwai matsalar da ta zarta talauci ne? Dan haka ina so ka yi min adalci nima a matsayina na mahaifin yarinyar nan,ina da buri babba akanta,ba zai yu na gama shan wahala da ita ba a rayuwa ta ɓige da auren faƙiri irinka,ni talauci kai talauci to wa zai taimakawa wani?" "Baba na yi maka alƙawari Nasibah ba za ta yi rayuwar talauci a gidana ba. Karatun Nursing nake yi yanzu haka,da zarar na kammala zan samu aiki,Baba zan riƙe maka Nasibah da amana kuma cikin wadata." Tsaki Malam Sanda ya ja mai tsawo kafin ya ce. "Aikin banza,yo dika-dika albashin nas ɗin nawa ne? Ƙarƙari na san cewa za ka yi zaka kama muku haya,idan ka biya kuɗin hayar da me za ka ciyar da ita har ta dinga samun na taimaka wa iyayenta?" "Baba..." A tsawace Malam Sanda ya kalli Malam Luƙman ya ce. "Kai ya isa haka! Na gaji da ja-in-ja da muke ta faman yi ni da kai. Nasibah dai ƴata ce kuma budurwa,ko a musulunci ina da haƙƙin zaɓar mata abokin rayuwa ko ba haka bane Malam?" Kai Malam Luƙman ya ɗaga jikinsa na wata iriyar tsuma saboda tashin hankalin da yake ciki. Ido Malam Sanda ya lumshe ya buɗe su a kan Malam Luƙman ya ce. "Madallah! To ni Baban Nasibah na ce ba kai ne zaɓin da na yi wa ƴata ba,bana so na sake ganin ka a ƙofar gidana. Idan ka haifu cikin uwarka da ubanka ta hanyar Sunnah ka rabu da ƴata,rabuwa ta har abada." Kalaman Malam Sanda sun yi matuƙar dukan zuciyar Malam Luƙman,cike da matsanancin tashin hankali ya kafe Malam Sanda da ido yana nazarin kalamansa a cikin zuciyarsa. Malam Sanda kuwa yana gama magana ya damƙe ledojin hannunsa ya shige gidansa tare da kulle ƙofa yana mita. Yana shiga ciki ya yi ido biyu da Nasibah wadda ke ta safa da marwa a tsakar gidan tana jiran Babanta ya shigo ta ji hukuncin da ya yanke akan tarayyarta da Masoyin nata,tambayar duniya Rabi da kilishi sun yi mata akan abinda yake faruwa amma ta kasa ce musu komai. Malam Sanda na ƙarasawa tsakiyar gidan sai ya kalli Kilishi ya miƙa mata ledojin hannunsa ya ce. "Ga wannan a giddiba shi a raba kowa a bashi kason sa. Kin dai san yanda zaki raba ba sai na faɗa miki ba. " Wajen da yake zama ya koma ya zauna tare da ture tuwonsa na dare gefe yana jiran kayan daɗin da Nasibah ta kawo. Nasibah kuwa ta kasa nutsuwa sai kallonsa take yi ta ga ya yi banza da ita kamar ma ba a yi ruwanta a wajen ba. Cike da shagwaɓa ta zauna a tabarmar mahaifin nata ta ce. "Baba to baka bani labarin yanda kuka ƙare da Mine ba." Kyaɓe baki Malam Sanda ya yi ya ce. "Waye hakan?" Ta gefen ido ta wurga wa Malam Sanda harara sannan ta ce. "Baba Malam Luƙman mana. Ka ji ya faɗa maka irin kuɗin da zai yi anan gaba ko? Baba don Allah ka yarda na aure shi har fa gini yake yi min a cikin gidansu." "To ki ji harkar tsiya don Allah. Meye wani gini a cikin gidansu? Ya wuce ya ja miki ɗaki ɗaya ku yi tarayyar makewayi da uwarsa da ubansa? Ke Nasibah ina raba ki da kiwon kyalla kina kyalla ta haihu ko? Yanzu ke ba za ki yi wa kanki faɗa ba ki yi wa kanki fatan zuwa inda zaki huta wani naki ma ya huta? Da alama tunda kika shigo baki ga ƴar'uwarki Hanifah a ɗaki ba ko? Yo ina za ki ganta kina nan kin kasa kin tsare kina jira na na shigo miki da mugun labari?" "Baba Yah Hanifah ce ta zo?" Nasibah ta faɗa tana mai sakin fuskarta kaɗan. Murmushi Malam Sanda ya yi ya ce. "Ita ce ta zo gata can a ɗaka. Da da yanda zan yi na raba ta da abinda yake cikinta ta mayar wa da ubansa shi da na yi. Dan ni ba ɗan iska bane namiji ya gama morar ƴaƴana sannan ya haɗo su da ƴaƴansu su zo su ƙarasa kassara ni. Yanzu a ce haihuwa ba ta ɗaya ba,ba ta biyu ba haihuwa ta uku sai mace ta dawo gidan iyayenta? To na ɗaga mata ƙafa ne saboda dare,gobe da sassafe idan Allah Ya kaimu zaki tattara ki koma inda kika fito,dan ni ba mahaukaci bane da zan sayar da akuya sannan ta dawo tana ci min azara." Kayan biki Kilishi ta ajiye wa Malam Sanda da Nasibah ta wuce tana faɗin. "Sai kace mutum shi baya aika nasa ƴaƴan gidan surukansa su cinye musu nasu abincin. Idan haka ne daga yau in yaran nan za su je hutu gidan namu iyayen ka dinga ƙulla abincin da za su ci da ruwan da za su sha har su je su dawo. Haba! Allah na tuba kai ai kana raye kana nema,mu kuwa iyayenmu maza duk sun kwanta dama,iyayenmu mata ke ta faɗi tashi suna neman na rufin asirin kansu." Ran Malam Sanda a ɓace ya nuna Kilishi da ta koma mazauninta tana ci gaba da surutai da yatsa ya ce. "Kin ga ki kama min bakinki kafin na ɗauki mummunan mataki akan ki Kilishi. Ke har kina da bakin magana idan aka zo wannan ɓangaren? Ubanki har ya koma ga Allah bai taɓa ɗaukan zakkar da yake ba wa mutane ya bani ba,ki faɗa min,hakan baƙinciki ne ko ba baƙinciki bane?" Kuka Kilishi ta fashe da shi ta ce. "Yanzu Malam dan na faɗa maka gaskiya shine za ka tono mahaifina kana faɗar baƙar magana akansa? To Alhamdu lillah zakka dai haƙƙin Allah ne kuma ya bayyana mutanen da za a bawa ita,kai kuma baka cikinsu,dan haka dan mahaifina bai baka zakka ba baka da dalilin ƙullatarsa har ka dinga tono min shi kana tsina." "Ke ar tafi can dangin marowata kawai." Gaba ɗaya ran Nasibah ya kai ƙololuwa wajen ɓaci,dan ita bata ga amfanin faɗan da Kilishi da Babanta ke yi ba. Kuka ta saki mai ƙarfi ta shure kwanon da aka zubo wa Malam Sanda abinci  ta yi ɗakinsu na yara. Tana shiga ta tarar da Yah Hanifah na sharar hawaye,domin kuwa tunda Malam Sanda ya dawo gidan ya tarar da ita yake ci mata mutunci har sai da ta gaji da ɗaukan zagin nasa ta koma ɗaki ta kwanta tana tuno mahaifiyarsu mai sanyi hali da biyayya. Kuka ta dinga yi tana jin kewar mahaifiyarsu na ratsa ta ƙwarai da gaske. Rungume ta Nasibah ta yi ta ce. "Yah Hanifah don Allah ki dena kuka,ki rabu da Baba ba zai fasa halinsa ba,ya kamata a ce kun saba da halayyarsa ta dena damunku." "Nasibah ke yarinya ce,dan haka ba za ki gane abinda yake faruwa ba. Ba na yi miki fatan ki shiga cikin halin da muke ciki,amma tabbas a duk ranar da mahaifinki ya nuna miki abun duniya ya fiki muhimmanci a rayuwarsa;a ranar za ki gane halin da muke ciki." Masifar Malam Sanda da zage-zagensa ne ya karaɗe gidan. Cikin fushi ya ce. "Ke Rabi miƙo min kason wannan ja'irar da ta shurr min abincina saboda baƙar mugunta na cinye." Da sauri Rabi ta miƙa masa abincin Nasibah da yake gefen tabarmarsa. Ci ya fara yi yana lumshe idanuwa tare da faɗin "Arziƙi ya yi a rayuwa,yo ina ma zan bari ki auri wannan faƙara'u alallalaluratin? Ai ke Nasibah kalar manya ce kamar Samir,dan haka baki da miji sai shi.", Tashi Nasibah ta yi a hasale za ta fita ta faɗa wa Babansu abinda ke ranta Hanifah ta riƙe ta tare da girgiza mata kai. Kuka Nasibah ta fashe da shi ta rungume Yayar tata da tsohon cikinta ya bayyana a fili. Sun jima a haka kafin Nasibah ta wuce makwancinta ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Ranta baƙƙirin saboda takaicin Mama dake jin duk abinda yake faruwa amma ta zaɓi ta yi shiru saboda neman fada a wajen Baba. Ita duk abinda ya ce ko daidai ne ko ba daidai bane a wajenta daidai ne. Shi yasa suke shiri yake ce mata ƴar aljannah saboda bata saɓa umarninsa. ********************** Ikon Allah ne kawai ya kai Luƙman gida,domin kuwa nan take wani irin mugun zazzaɓi mai zafin gaske ya kama shi. Yana zuwa gidansu ya samu waje a parlour ya kwanta yana karkarwa tare da numfarfashi. Mahaifiyarsa da ke zaune tana jiransa ya dawo sai ta miƙe a tsorace ta hau kiran mahaifinsa dake cikin ɗaki. Cikin ƙanƙanin lokaci suka rufu akansa suna tambayarsa abinda yake damunsa. Kuka mai tsanani Malam Luƙman ya fashe da shi murya na rawa ya ce. "Mahaifinta ya ci min mutunci,ya ce kada ya sake gani na da ƴarsa ya raba tsakanina da ita rabawa ta har abada Ummi." Da jin haka sai Mahaifiyar Luƙman ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta zauna a gefen kujerar da ya kwanta,kansa ta ɗauka ta ɗora a saman cinyarta tana shafawa a hankali. Cikin sassanyar muryarta mara hayaniya ta ce. "Na jima ina sanar da kai zuwan wannan ranar Luƙman,shi yasa tun kafin soyayyar taku ta yi zurfi na ce maka ka rabu da ita amma ka ƙi,hujjarka shine yarinya tana son ka ba za ta bari a raba ku ba. Kada fa ka manta Luƙman duk yanda yarinya take son ka idan iyayenta ba sa son ka daga ƙarshe sai kun rabu,idan kuma ka ga kun yi aure to tsananin rabo ne ya sa auren ya ɗauri ba da son ransu ba;ko kuma yaran su gudu su bijire wa iyayensu. Dan haka ka yi haƙuri ka taushi zuciyarka. Ƴar abokin mahaifinka da yake ta yi maka magana akanta tana nan tana karatunta,da zarar ta kammala sai a yi komai cikin mutunci ko ba haka ba Malam?" Cike da gamsuwa da maganar Ummi Abbah ya ce. "Ƙwarai da gaske maganarki na kan hanya. Allah na tuba dama ina Makaɗi ya ke da darajar da zamu haɗa zuri'a da shi? Kawai dai dan ka dage ne ya sa muka haƙura domin mu barka da zaɓin ranka. Amma tunda an yi haka ka bar masa ƴarsa ya jiƙata ya shanye,kai kuma ka auri daidai da kai." Duk da cewa Malam Luƙman ya san gaskiya iyayensa suke faɗa,amma shi sam bai aminta da auren wadda suka zaɓar masa ba. Dan haka sai ya yi shiru kawai ya lumshe idanuwansa yana sauke numfashi da sauri da sauri. Maganin zazzaɓi mahaifinsa ya ɗakko ya bashi da ruwa. Mahaifiyarsa kuma ta ɗakko masa abincin dare ta zauna ta dinga bashi a baki yana ci yana zubar da hawaye. Kaɗan ya ci ya juyar da kansa ya miƙe da ƙyar ya nufi ɗakinsa ya kwanta yana tunanin ranar farko da ya fara ganin Nasibah a rayuwarsa. Kuka ya fashe da shi domin shi ya sani har abada babu macen da zai sake yi wa irin soyayyar da ya ke yi wa Nasibah,ya so ta tun bata san ciwon kanta ba,ya so ta tun bata san ma'anar saka hijabi ta suturce jikinta ba,ya ci gaba da son ta duk da ya san halayenta na rashin ji da ƙiriniya tare da ɗaukan magana,ya sha biyan kuɗin ta'adi ko asarar da ta yi wa mutane a wajen faɗa,shi kuwa waye zai nuna masa ya san Nasibah sama da shi bayan iyayenta? Sai dai duk da irin wannan soyayyar da yake yi mata dole ne ya koya wa zuciyarsa haƙuri da rashinta ko dan ya tsira da mutuncinsa da na iyayensa da aka zage tas.........[9/30, 4:19 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 11. Samir na hanyarsa ta zuwa gida Nuh ya kira shi,kamar ba zai ɗauka ba daga baya ya daure ya amsa wayar a dake. Ran Nuh a ɓace ya ce. "Amma dai babu ɗan iska sama da kai Samir. Ta ya za mu zo waje da kai ka tafi ka barni bayan ka san bani da abun hawa a nan?" Yatsina fuska Samir ya yi ya ce. "Ka ga Man ka samu abun hawa ya kawo ka gida dan ni yanzu haka kai na ba a daidai yake ba." Tsaki Nuh ya ja sannan ya ce. "Kai dama yaushe ne kanka yake daidai a jikinka? Ka dai yi a hankali kada ka manta tuƙi kake yi ka sha abunda zai ja maka matsala." Katse kiran Samir ya yi ya bar Nuh da takaicin halayya irin ta Samir. Kan dole ba dan ya so ba ya nemi adaidaita sahu ya shiga dan ya kai shi gidansu Samir. Lokacin da Nuh ya isa gidan ya tarar da gidan a rufe,sai da ya fita ya sallami mai adaidaita sahu sannan ya ƙwanƙwasa mai gadi ya buɗe masa. Gaisawa suka yi Nuh ya ce. "Ya dawo kuwa?" Da sauri mai gadi ya risina ya ce. "Ah ah! Alhajin bai dawo ba." Kai Nuh ya girgiza sannan ya shige cikin gida. A zazzaune ya tarar da Hajjah Barirah ita da ƴammatan ta Samirah da Sakinah suna kallo. Nuh na shiga Samirah wadda ke bi wa Samir ta miƙe zaune tana yanga ta ce. "Yah Nuh sannu da dawowa. Na kawo maka abincinka nan ne ko za ka je dinning room?" Harararta Hajjah Barirah ta yi kafin ta ce. "Sannu uwar azarɓaɓi,Yayanki kawai kika gani har kike zancen kawo masa abinci ko? Kai Nuh ina ka baro ɗan amanartaka?" Kafin Nuh ya yi magana suka ji ƙarar buɗe gate ɗin gidan. A guje Samir ya shiga da motar cikin gidan. Hakan ne ya tabbatar musu da cewar mutumin nasu ba a saiti yake ba. Tsaye Nuh ya miƙe zai fita Hajjah Barirah ta yi saurin dakatar da shi. Komawa ya yi ya zauna yana kallon fuskarta da ta sauya daga damuwa zuwa ɓacin rai. Suna cikin wannan yanayin Samir ya shiga parlourn. A zazzaune ya tarar da su sun yi shiru tare da zuba masa ido. Fuska a ɗaure ya kalle su ya ce. "Kun samu labari na kashe wani ne da duk kuka taru kuka zuba min ido?" "Daga ina kake Samir?" Shine tambayar da Hajjah Barirah ta wurga masa fuska a ɗaure tamau. Dariya ya saki sannan ya gyara tsayuwarsa yana kallon Hajjah ya ce. "Daga gidan su matar da zan aura nake Hajjah." Cikin sauri Hajjah Barirah ta dafe ƙirji ta ce. "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Samir yanzu a haka ka je gidan surukan naka? Me kake tunanin za su ce akan ka uhum?" Zube wa ya yi a kujera mafi kusa da shi ya saki hamma sannan ya ce. "Ban gane me kike nufi ba Hajjah? Ni mahaukaci ne da zaki ce a haka na je musu? Hajjah bari ki ji na faɗa miki wata magana,kin ce zaki aura min Munirah ko ina so ko bana so matsawar ban kawo matar aure ba a shekarar nan. To ina so a yau ki kashe maganar aure na da Muni saboda na samu matar aure,macen da nake muradin aura ta zamo uwar yarana ba ƴar bariki kamar Munirah ba." Baki Hajjah ta washe ta ce. "Ka dai ji da shi,ina ce ta sanadin son da take yi maka ne ta zamo haka? Bayan haka ma duk maitar na raba ku da nake yi ko mata huɗu zan aura maka na sani ba za ku taɓa rabuwa da Munirah ba. Ku ɗin ƙaddarar junanku ne." Murmushi Samir ya yi ya ce. "Wannan karon da gaske nake yi,zan rabu da Muni rabuwa ta har abada in dai na samu na auri zaɓin raina." "To Allah Ya sa. Ita yarinyar da za ka aura a ina take kuma ƴar gidan wanene?" Samir yi ya yi kamar bai ji tambayar Hajjah ba,domin ya san halin ta sarai akan ƙin talaka da duk wani abu da ya shafi harkar talauci. Miƙe wa ya yi tsaye ya kalli Sakinah wadda duk abinda ake yi bai ɗaɗata da ƙasa ba ballantana ta saka musu baki. Cikin bada umarni ya ce mata. "Ke ki kai min abinci sashe na. Kuma ki haɗa min da tea ki matse lemon tsami guda biyu a ciki." Ba tare da ta amsa shi ba ta miƙe ta mufi dinning room ta fara haɗa musu abincin shi da Nuh,Nuh na ganin yanda take ɗiban abincin da yawa ya ce. "Kar ki haɗa mana,bari na zo na ci nawa a nan." Kai kawai Sakinah ta ɗaga ta ci gaba da abinda take yi. Tana gamawa ta ɗauki abincin a katon trey ta nufi wata ƙofa da shi. Nuh kuwa hanyar dinning room ɗin ya nufa yana latsa wayarsa. Murmushi Samirah ta yi ta miƙe ta nufi wajensa ta hau serving ɗinsa. Hajjah kuwa sai ta haye sama ta bar Samir da bashi da niyyar bata amsar tambayoyin da ta tasa shi a gaba ta na yi masa. Idanuwansa a lumshe ya buɗe baki da ƙyar ya ce. "Nuh zan ci maka uwa idan kana taɓa min ƙanwa fa. Bana son iskanci,duk matan dake waje basu ishe ka ba za ka tsallake su ka dinga taɓa min ƙanwa? Ke kuma balama zo ki bar nan ko na karya ki." Tinda Samir ya fara magana suka raba hannuwan junansu da suka sarƙafe suna aika wa juna da wani zazzafan kallo. Kame-kane Nuh ya fara yi tare da borin kunya yana zagin Samir. Ita kuwa Samira sai ta hau tura baki tana faɗin. "Shikenan mutum ba zai yi soyayya in peace ba sai an saka masa ido." Ta gaban Samir ta zo za ta wuce ta shige ɗakinta tana wani dire-diren ƙafa kamar za ta yi kuka. A hankali Samir ya buɗe ido ya kalle ta ya ja tsaki. Da ƙarfi ta buɗe kofar ɗakin nata ta buga tare da saka mata key. Sakinah na dawo wa ta nemi waje ta zauna ta ci gaba da kallon ta ba tare da ta kula kowa ba. Sun jima a haka kafin Nuh ya kammala cin abincinsa ya yi musu sai da safe ya wuce sashen Samir ya kwanta. Har Sakinah ta gama kallo ta kashe kayan wutar parlourn Samir na nan a zaune yana tunanin Nansy. Sosai yake jin mamakin yanda soyayyar yarinya ƙarama ta mamaye masa zuciyarsa. Babban ƙalubalen dake gabansa shine ya fi tada masa hankali,ta yaya zai fahimtar da Hajjah iyayen Nasibah talakawa ne? Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke kafin ya hau tunawa da mahaifinsu. Asalin iyayen Samir mutanen garin Jos ne,a can aka haifi mahaifinsa Alhaji Yusha'u Muhammad,wanda mutane ke yi wa laƙabi da Gwamnati saboda takarar Gwamna da ya yi har dau huɗu a garin Jos amma bai samu nasarar hayewa ba ko sau ɗaya. Alhaji Yusha'u Gwamnati na daga cikin mutanen dake son ganin jihar Jos ta samu kwanciyar hankali da zaman lafiya. Domin yana sane da cewa rikicin garin babu abinda yake kawo shi face saɓanin addini da ƙabilanci. A cikin shekarar da mummunan tashin hankalin da ya raba su Samir da Jos ne aka yi wani taron haɗin kan al'umma a wata local government dake da yawan mabiyan addinin kiristanci da Musulmai. A wajen taron ne aka bawa babban baƙo wato Alhaji Yusha'u Gwamnati damar bada cikakken tarihin garin Jos da mutanen da suka kafa garin. Bayan Alhaji Yusha'u Gwamnati ya tashi ya ɗaga hannunsa yana murmushi sai ya isa wajen da aka tanada domin masu yin magana a taron. Abun magana ya karɓa ya yi sallama sannan ya ce. 'Bayan sallama da gaisuwa tare da fatan alkhairi a gare mu baki ɗaya;nake yi mana addu'ar Allah Ya bamu zaman lafiya a wannan jiha tamu mai albarka. A yau ina so na ba wa ƴaƴanmu da jikokinmu tarihin da basu sani ba,wala'alla wannan rashin sanin shine yake jawo mana tashin hankula da kashe-kashen rayuka tare da asarar dukiyoyi. A yau zamu ɗakko tarihin jihar Jos tun daga tushe domin wayar da kan matasanmu. Asalin tarihin garin Jos yana da ɗan rikitarwa kaɗan, amma ga bayani a sauƙaƙe yanda matasa za su fi fahimtar ya abun yake. Tun kafin zuwan Turawa, yankin Jos ba wani babban gari bane kamar yanzu. Akwai ƙabilu na asali (indigenous people) da suke zaune a wurin,wato ƙabilar Berom,Afizere (Jarawa) da kuma Anaguta. Waɗannan su ne asalin masu yankin Jos, kuma a wancan lokacin suna da addinansu na gargajiya wato (traditional religion). Su ɗin ba Musulmai ba ne kuma ba Kiristoci bane. Lokacin zuwan Turawa (Colonial period) a farkon ƙarni na 1900 Turawa (Birtaniya) sun gano tin (ma’adinai) a Jihar Jos,sai suka fara gina gari da tsarin zamani suka kawo mutane daga wurare daban-daban domin su yi musu aiki. To anan kun ji yanda Musulmai da Kiristoci suka shigo cikin Jihar Jos. Musulman da suka zo Jihar ta Jos a wancan lokacin yawancin su Hausawa/Fulani ne daga arewa suka zo aikin turawa,a hankali masu kasuwanci ma suka fara shigowa. Kiristoci kuma yawanci daga kudu suka zo,sannan yawancinsu ƙabilar Igbo da Yoruba ne suka fi yawa. Mishan da inyamurai da Yarabawan da suka zo daga kudu sune suka kawo addinin kiristanci a garin Jos,kun ga kenan  ba Musulmai ko Kiristoci ne suka kafa Jos ba. Asalin garin Jos na ƙabilar Berom, Afizere, da Anaguta ne. Sannan har yau babu wanda ya san a tsakanin Musulmai da Kiristoci wanene ya fara shigowa cikin Jihar Jos. Kun ga kenan addinan nan namu biyu  wato Musulunci da Kiristanci sun zo ne daga baya,sai kuma mutane suka ɗauki abun ta fuskar da ta jawo ake ta ɓarnar rayuka da dukiyoyo duk dan kare ɓangaranci. Ina so matasa da mu dattijan kammu mu fahimci cewa wannan zama fa Allah ne ya haɗa shi,a gaba ɗaya addinan mu mun san cewa Allah Ya sanar damu shine ya yi nufin hakan ta kasance,to me yasa muke bijire wa umarnin mahaliccinmu? Me yasa muke so dole sai ɗaya ya tashi ya bawa ɗaya waje? A yanzu haka mu duba personal buƙatunmu na yau da gobe,dole muna buƙatar junanmu,domin akwai abubuwan da dole sai musulmi bahaushe ne ya iya su,kuma Inyamuri ko bayerabe yana son wannan abun. To idan muka rabu ta yaya zamu rayu? So muke yi idan muna buƙatar junanmu sai mun yi tafiya mai nisan gaske sannan mu samu biyan buƙatar mu? Me yasa ba za mu yi koyi da sauran juhohin da suka ci gaba ba saboda zaman lafiya da ƙaunar junansu da suke yi? Daga ƙarshe ina yi mana nasiha da mu ji tsoron Allah mu so junanmu,mu zauna da juna da amana da zuciya ɗaya. Ta haka ne jihar mu ta Jos za ta zamo abar alfahari wajen ƴaƴa da jikokinmu masu tasowa.' Alhaji Yusha'u Gwamnati na kammala jawabinsa wajen ya kaure da kabbara da tafi tare da ihun matasa. Sosai maganganunsa suka yi tasiri a cikin zuƙatan mutanen dake wannan wajen. Sai dai ita fitina mutum ɗaya ɓata gari idan ya kunna ta;sai ka ga ta ja ra'ayin mutanen kirki su afka mata ido rufe,sai bayan ɓarna ta faru ne kowa ya dawo cikin hayyacinsa  nadama da dasani suke lulluɓe wanda suka biye wa son zuciyarsu. Bayan wata ɗaya babban rikicin ya ɓarke mutane suka manta da wannan taro na haɗin kan al'ummar Jihar Jos suka yi ta kashe junansu. Wasu ma uwa ɗaya uba ɗaya suke,amma banbancin addini sai ya sa su gayyato ƴan'uwansu da suke addini ɗaya su lahanta wanda baya cikin addininsu. Daga masu kashewar har zuwa wanda aka kashe duk basu san takamaimai akan me suke yin faɗan ba. Haka suka ɗauki tsawon sati suna abu ɗaya. A wannan faɗan ne Alhaji Yusha'u Gwamnati da Hajjah Barirah suka rasa danginsu na kusa,tun daga nan zaman garin ya fita daga ran Alhaji Yusha'u Gwamnati domin da ƙyar shima iyalansa suka tsira daga wannan tashin hankalin. Bayan wata uku ƙura ta lafa ya tattara Hajjah Barirah da ƙanwar mahaifiyarsa Gwaggo Yabi dake wajensa a lokacin da Samir ɗan shekara tara  sai Samirah mai shekara biyar suka dawo garin Kano da zama. Tun daga nan sai Alhaji Yusha'u Gwamnati ya haƙura da harkar siyasa ya kama aikinsa na gwamnati da kasuwanci tare da harkokin NGO's ya riƙe da kyau. A shekarar da suka dawo Hajjah Barirah ta sake haihuwar ƴarta kyakkyawa,ranar suna aka saka mata Sakinah,tun daga nan haihuwar ta kulle bata sake ko da ɓarin wata ba har Alhaji Yusha'u Gwamnati ya bar duniya. Bayan rasuwarsa babu yanda manema basu taso mata ba kamar za su cinye ta. Amma haka Hajjah Barirah ta toshe zuciyarta ta hana kowa shiga cikinta.  A cewarta ta gama aure kenan har abada,domin babu wani namiji da zai maye mata gurbin mijinta a cikin rayuwarta da ta ƴaƴanta. Duk yanda Hajjah ke yi wa Gwaggo Yabi biyayya saboda kasancewarta ita ce wadda take kalla a matsayin danginta;amma haka ta toshe kunnenta ta yi mata tatas a lokacin da ta matsa mata akan ta yi aure ko dan tarbiyyar yaranta ta inganta. Daga ƙarshe ma sai ta dena hulɗa da Gwaggo Yabi ta yi mata kyautar gida a nesa da unguwar da suke. Haka Gwaggo Yabi ta haɗa nata ya nata ta koma gidan. Bayan shekara biyar da komawarta gidan suna zumuncin nesa ciwon sugar ya yi ajalinta. Sosai rasuwar Gwaggo Yabi ta daki Hajjah Barirah,dan haka sai ta yi ƙoƙari ta mayar da gidan da Gwaggo Yabi ta zauna ya koma islamiyya ta bayar da shi kyauta da niyyar Allah Ya kai ladan gare ta. Tinda Hajjah Barirah ta yi wannan abun sai idanuwan mutane suka dawo kanta,masu zuwa neman taimako suka dinga tururuwa zuwa wajenta. Ido Hajjah ta rufe ta ci musu mutunci tare da zage su tass ta ce ita bata kira kowa ya zo wajenta neman taimako ba,gidanta ba charity house bane kowa ya je ya nemi na kansa. Wasu mutanen sun ɗauki maganarta da muhimmanci wasu masu nacin kuwa sai suka ƙi jin maganarta suka kafe suke ta zuwa neman taimako. Daga ƙarshe da ta ga abun ya ƙi ci ya ƙi cinyewa sai ta nemi taimakon ƴan sanda,hakan da ta yi ne sanadiyyar raba ta da nacin mutane. A fili Hajjah ke nuna tsanar talaka da duk wani abu da ya shafi rayuwar talaka. Wannan shine dalilin da ya sa duk wanda ya zo neman auren su Samirah idan ta bincika ta ga bai fi su arziƙi ba sai ta ƙi. Tun ana zuwa neman auren nasu yanzu gashi ƙafa ta ɗauke mazan sun dena zuwa. Ita hakan sam bai dame ta ba,a cewarta da ta aurar da su su sha wahalar gidan miji gwanda ta barsu a gabanta su yi rayuwarsu cikin wadata da walwala. Rayuwar Samir ta lalace ne saboda sakacin Hajjah akan tarbiyyar yaranta,tunda ya kammala sakandire ta kai shi ƙasar turawa domin ya ci gaba da karatunsa,a can ya koyi shan giya da neman mata babu kama hannun yaro,hakan sam bai taɓa damun Hajjah ba,domin a cewarta rayuwarsa ce yana da ƴancin yin duk abinda yake so. Babbar damuwarta da Samir shine ya yi aure domin ya samar wa kansa Magajin dukiyarsa. A kullum fatanta bai wuce duk macen da zai aura ta haifa masa ɗa namiji ba.  Lokuta da dama ƙawayenta na nuna mata sangarcin da take nuna wa Samir ya yi yawa,ita kuwa duk girman wadda ta yi mata magana akan Samir to daga wannan ranar za ta yi wa mace tatas kuma alaƙarsu ta yanke. A wajen ta soyayya ita ce sakar wa yaro duk abinda ya ja da kuma kashe wa yaro duk dukiyar da ya nema matsawar akwai ta. Idan kuma babu a cewarta uwa ko uba haƙƙinsu ne su shiga su fita domin ganin yaransu sun samu abinda suke so komai wuyarsa komi tsadarsa. Bayan rasuwar Mahaifin Samir Hajjah ita ta ci gaba da kula da aikin NGO's da yake yi da kasuwancinsa. Lokacin da Samir ya dawo daga karatunsa sai ta fara shigar da shi cikin harkokin yana ganin yanda abubuwan ke tafiya. A matsayinsa na wanda ya yi karatun likitanci a ƙasar waje sai ya buɗe asibiti nasa na kansa,a nan ne yake gudanar da ayyukansa yake kuma taimaka wa mabuƙata. Sosai Hajjah ta tsani ɗabi'arsa ta yawan kyauta,a cewarta da mahaifinsa bai rabar da dukiyarsa ba a baya da sun fi haka arziƙi. Samir bai bi ta kanta ba ya ci gaba da harkokin gabansa. Sosai ya ƙware a harkar neman mata da shaye-shaye. Duk da cewa Hajjah ta san abubuwan da take yi bata taɓa zaunar da shi ta yi masa faɗa akai ba ta nuna masa illar abubuwan da yake yi. Idan ka ga Hajjah na yi wa Samir faɗa akan halayyarsa to za a je ƙulla wani kasuwancin ne ya je wajen a buge,ko kuma akwai wani abu da za a yi na fita kunya aka kama shi da mace yana masha'a da ita,ko yana shaye-shayen nasa. A cikin wannan rayuwar da yake yi ne ya haɗu da macen da ta zame masa ƙaddarar rayuwarsa wato Munirah.......... [10/1, 12:39 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 12. Samir ya haɗu da Munirah ne a wani babban taron da manyan mata ƴan kasuwa suka gudanar a Transcorp Hilton Hall dake cikin garin Abuja a No 1 Aguiyi Ironsi street,Maitama. A wannan ranar kowacce ƴar kasuwa ta je da ɗanta ko ƴarta wanda sune za su zamo magajin dukiyar iyayen nasu domin saka hannu a wasu takardu. A kaf cikin yaran masu hannu da shunin da Samir ya gani a wajen Munirah ce yarinyar da tafi tafiya da hankalinsa da nutuwarsa. Ba tare da ɓata lokaci ba ya isa wajenta ya gabatar da kansa. Duk da cewa a tsakanin mahaifiyarsa da mahaifiyarta akwai competition hakan bai hana yaran ɗaura kyakkyawar alaƙa a wajen ba. Munirah na daga cikin irin wayayyun yaran Abujar nan da suke rayuwa cike da ƴanci babu takura. Hakan ne ya bata damar sakin jiki suka fara soyayya mai zafi ita da Samir. Munirah ta sadaukar wa da Samir abubuwa masu muhimmanci a rayuwarta wanda a baya take ganin babu namiji ko macen da ta isa ta sakar wa sirrinta ballantana har ta mallaka musu. A cikin abinda Muni ta mallaka wa Samir har da gangar jikinta da zuciyarta. Duk abinda mahafiyarta ta ce mata ta yi,indai Samir ya nuna rashin amincewarsa ko da a fuska ne to Munirah ta bar wannan abun kenan bari na har abada. Maganar samari kuwa dama tinda ya nuna mata baya son sharing ta ajiye kowa a gefe,tinda dama ita bata yin irin soyayyar nan ta zamani da ake yi ai ta zinace-zinace da sunan soyayya. A duk ranar da Samir ya je garin Abuja kwana suke yi suna aikata duk abinda zuciyarsu ta raya musu daidai ne. Zuwa club da hotels ya zame musu tamkar ibada. Akan Samir Munirah ta sha yin dambe da faɗa da ƴan mata kala-kala,wani lokacin ma har da shi kansa uban gayyar take zage wa su daku. Idan suka yi faɗa kaca-kaca ba sa iya yin sati ɗaya ko su haura sati biyu basu nemi juna ba. Samir na iya keta hazo ya bi Munirah duk ƙasar da ta je saboda ta guje masa. Idan kuma shi ne ya yi fushin sai ta tattaro komatsenta ta dawo Kano da zama ta yi ta aikin ban haƙuri har sai ta shawo kan abunta. Shaƙuwarsu ce ta jawo haɗin kai a tsakanin iyayensu mata. Domin kuwa daga Samir ɗin har Munirah iyayensu maza sun rasu. Ganin irin soyayya da shaƙuwar dake tsakaninsu sai iyayen nasu suka shirya musu lavish engagement party. Ko da Samir ya zo venue ɗin da iyayensa suka sanar da su ya fahimci mai suke ƙullawa sai ya hau watsi da kujeru da tables yana masifa tare da cin mutuncin tarbiyya da ɗabi'un Munirah. Cikin fushi da ɓacin rai Samir ya kalli mahaifiyar Munirah da ta riga ta tsorata da abubuwan da Samir ya dinga aikatawa a wajen ya ce. "Ƴarki ce ta faɗa miki ni Samir Yusha'u Gwamnati zan auri mace kamarta? To in auri Muni in ce na auri wa? Please ku dena wannan drama ɗin because i cannot marry public toilet na kai ta gidana da sunan matar da za ta zamo uwar yarana." Da jin haka sai mutanen wajen suka cika da mamaki tare da yin ƙus-ƙus suna tattaunawa akan kalaman da Samir ya yi amfani da su wajen bayyana wacece Munirah a idonsa. Munirah wadda bata jima da isa wajen taron ba sai ta ƙame a wajen cike da jin kunya,muzanci tare da tsantsar damuwa da karyewar zuciya. Hawaye ne ke yi mata tsananin gudu a kuncinta tana jin wani irin zafi da ƙunci a cikin ranta. A hankali ta juya za ta tafi saboda bata da sauran ta cewa. Muryar Hajjah Barirah ce ta karaɗe wajen tare da ƙarar saukar zazzafan marin da ta sauke wa Samir a saman kyakkyawar fuskarsa. Cak Munirah ta tsaya tare da juyawa ta kalli yanda ran Hajjah Barirah ya yi matuƙar ɓaci ta na nuna Samir ta ce masa. "Tinda kake abubuwanka ban taɓa shiga sabgar shirmen ka ba sai yau Samir. Yanzu kai baka ji kunya ba da za ka kira yarinyar da kuke making love a koda yaushe da public toilet? Idan ita public toilet ce to kai menene tinda tare da kai take yin duk abinda kake ƙin ta dominsa. Idan baka son wannan engagement ɗin akwai hanyoyi da dama da za ka faɗi hakan you don't have to be so mean and stupid." Cike da jin nauyin mahaifiyar Munirah wadda ranta yake a matuƙar ɓace Hajjah Barirah ta yi folding hannayenta waje ɗaya ta ce. "Don Allah ki yi haƙuri akan abinda ya faru. Da na san haka yaron nan zai yi da ban amince aka haɗa musu wannan taron bazatar ba." Kai kawai Hajiyah Nusrah ta kaɗa ta taka zuwa wajen ƴarta Munirah ta kama hannunta ta kalli Samir ta nuna mata shi ta ce. "Kin ga irin mijin da kike yi wa makahon so ko? Kin kuma ga kallon da yake yi miki duk da cewar he was your first. Kamar yanda na sha gaya miki ne Muni,duk yanda mace ta kai da ji da kyau da taƙamar mulki ko dukiya;matsawar za ta sakar wa namiji jikinta to wannan darajar tata za ta yi ƙasa ta wulaƙanta tare da ƙasƙanta a idonsa." Murmushin takaici Hajiyah Nusrah ta yi sannan ta ci gaba da cewa. "Bana manta ranar da kika dawo gida kika bayyana min abinda ya faru a tsakaninki da Munir,idan za ki iya tuna wa i was so furious saboda kin sakar masa ƙima da darajarki ta ƴa mace,amma ke,ke ɗin murmushi kike yi fuskar ki na bayyana irin farinciki da nishaɗin da kike ciki. Daga ƙarshe kika ce min Mom da ni da Samir mun zamo ƙaddarar junanmu,duk inda ya je ya dawo wajena zai tsaya,haka zalika nima duk inda na je na dawo wajensa zan koma. We are stock with each other,we can't do without each other Mom,I love him so very much. A wannan ranar na tabbatar da na rasa ƴata. Dan haka ni ba zan yi mamaki ba dan Samir ya yi mana wannan irin cin mutunci a yau,dama ɗan kuka shine yake jawo wa uwarsa jifa." Hajiyah Nusrah na gama maganarta ta ja hannun Munirah suka bar hall ɗin ranta a matuƙar ɓace. Tun daga wannan ranar ta saka wa Munirah dokoki tare da manyan takunkumi duk dan ta rabu da Samir. Sai dai ko sati biyu ba a cika ba Munirah da Samir suka sake ɗinke wa kamar babu abinda ya faru na ɓacin rai a tsakaninsu. Ganin haka sai Hajjah Barirah da Hajiyah Nusrah suka saddaƙar tabbas babu mai raba tsakanin Samir da Munirah sai mahaliccinsu. Lokacin da Hajjah Barirah ta fara gajiya da shige da fice tare da rashin hutun jiki da ruhi game da kasuwancinsu sai ta nemi Samir akan ya mayar da hankali akan kasuwancin ya ajiye maganar kula da asibitinsa tunda yana da ƙwararrun likitoci a cikinsa. Samir sai ya amince da muradin Hajjah,sai dai a duk sanda ya shigo Kano yana leƙa asibitin nasa har ma ya duba marasa lafiya. Ana haka Samir ya yi wa wata yarinya ciki iyayenta suka zo har gidan Hajjah Barirah suka ci mata mutunci sannan suka yi alƙawarin za su dawo mata da ɗa ko ƴar da aka haifa idan lokaci ya yi. Tun daga wannan ranar Hajjah ta fara matsa wa Samir akan ya nemi matar aure ko ta aura masa Munirah ko yana so ko baya so. Da jin haka sai Samir ya sake bin jikin yarinyar da ya yi wa ciki ya dinga yi mata wayo yana sake keɓe wa da ita yana bata kuɗi. Daga ƙarshe ya samu nasarar saka mata wata ƙwayar zubar da ciki mai ƙarfi a abun sha,tana komawa gida daga hotel ɗin da suka saba haɗuwa ta yi ɓari. Wannan shine silar rabuwarsa da yarinyar. Duk da cewar sun rabu sai da Munirah ta sa aka nemo mata gidansu yarinyar ta yi hayar marasa jin unguwar ta basu kuɗi mai yawa suka banka wa gidan su yarinyar wuta. Lokacin da gobarar ta tashi mutanen gidan duk basa nan sun yi tafiya,dan haka sai aka dinga raɗe-raɗin cewa wataƙila sun manta sun kunna gas ne ko kuma sun bar abinda idan wutar lantarki ta jima zai ƙone ya ƙona waje. A ɓangaren Munirah kuwa zuciyarta ce ta yi mata daɗi saboda ta ɗauki fansar kwana mata da saurayi da yarinyar ta yi. Munirah na yi wa Samir wani irin mahaukacin so ne da take jin za ta iya yin kisan kai akansa ko kuma ita ɗin ta kashe kanta. Munirah ta yi alƙawarin babu wata ƴa mace da ta isa ta auri Samir ko ta yi tarayya da shi matsawar tana raye a duniya. Idan kuma mace ta kuskura ta yi gangancin raɓar Samir da sunan aure ko soyayya tabbas ita ce za ta zamo ajalinta.......... *Ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa! Ga Munirah ƴar hau,ga Nansy Ƙaya my fiful. Da alama dikansu sun ci kai.* [10/3, 6:57 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 13. Ajiyar zuciya Samir ya sauke mai ƙarfi ya kalli Sakinah da har a wannan lokacin ke kallon TV hankalinta kwance tana kora lemo lokaci zuwa lokaci. Miƙe wa tsaye ya yi ba tare da ya kula ta ba ya nufi sashen sa. Ya na zuwa ɗakinsa ya shige ya hau cire kayan jikinsa daga ƙarshe ya shiga wanka. Bai wani jima a wajen wankan ba ya fito yana tsane jikinsa da towel. Wayarsa dake ta neman agajin gaggawa ya kalla ya ja dogon tsaki tare sa faɗin. "Yarinyar nan ko mayya ce ke bana dai zan rabu da ke na huta da nacin ki." A wajen ya yar da towels ɗin da ya gama amfani da su ya sanya kayan baccinsa sannan ya nufi parlour. Ya na zuwa ya buɗe abincin ya ga gaba ɗaya sun yi masa nauyi ya ci da daren,sai kawai ya ɗauki fruit salad ya sha ya kunna sigarin sa ya na zuƙa ya na kallon wayarsa. Muryar Nuh ya ji daga ɗaya ɗakin dake cikin parlourn tana doso shi. Tun kafin ya iso ya fahimci abinda yake faruwa,dan haka sai ya sake tsamke fuskarsa yana kallon wayarsa,ko da Nuh ya fito yana magana cikin yanayi na mutumin da ya fara bacci,sai ya kalli Samir da ya haɗe fuska kudu da arewa,gabas da yamma ya yi masa nuni da kiran da hannu. Kafaɗa Samir ya ɗaga masa alamar babu ruwansa. Nan take Nuh ya wartsake daga magagin baccin da yake yi ya riƙe wayar da kyau yana faɗin. "Look Muni kin fa fini sanin halin mutumin naki,idan bai yi niyyar amsa miki waya ba ni ban isa na saka shi ya amsa miki ba. Dan haka ina ganin ki kashe waya kawai ki yi bacci nima na samu na rintsa in peace,don Allah kada ki sake kirana bacci nake ji,gashi gobe zan dawo Abuja ni zan yi tuƙi ba wai jirgi zan bi ba ko motar haya." Baki Munirah ta tura gaba cike da shagwaɓa irin na yaran masu kuɗin da basu samu abinda suke nema ba. Ranta a ɓace ta buɗe murya ta ce. "Babe na san kana ji na,wai me na yi maka ne kake ta wulaƙanta ni haka?" Kukan da ke raunata zuciyar Samir ta saki tana shessheƙa kamar za ta shiɗe. Nuh na jin haka ya kashe wayarsa ya juya ya nufi ɗakin da yake sauka idan ya zo gidan yana mita,dan ya san Samir ba zai iya ƙyale ta ta kwana tana wannan jarababben kukan nata mai ban haushi ba. Murmushi Samir ya yi ya tattara abubuwan da yake da buƙata ya kashe abinda duk ya kamata ya kashe na wuta ya wuce ɗakinsa. Ya na shiga Muni ta sake banko masa kiran waya. Ajiye kayan hannunsa ya yi a fusace ya ɗauki wayar yana haɗe haƙoransa waje ɗaya tare da hura hanci ya ce mata. "What do you want from me MUNIRAH NAZIR ATAH?" Cike da salon jan hankali Munirah ta kashe murya ta ce. "Kai ma ka san kai ne abinda nake so;me na yi maka kake wulaƙanta ni haka Samir?" "Saboda aure zan yi Muni na gaji da yawon bariki da baƙin nacin ki." Wata iriyar zabura Munirah ta yi ta miƙe zaune tana jin kamar an shaƙe mata wuya shi yasa numfashinta ke barazanar ɗaukewa. Da ƙyar ta iya janyo kalmar. "Aure?" Ta furta a laɓɓanta. Kai Samir ya jinjina ya ce. "Yes Muni! Aure zan yi,so Please ki ja jikinki ki kama kanki,idan har akwai sauran wata daraja da ta rage miki to ki riƙe ta don Allah." Dariya mai sauti Muni ta saki tare da miƙe wa tsaye tana tafa hannuwanta dika biyun,sai da ta gama sannan ta ɗauki wayar dake dokin wuyanta ta saka ta a handsfree ta ja dogon numfashi ta fesar ta ce. "Baka isa ka auri kowacce mace ba a duniya SAMIR YUSHA'U GWAMNATI idan ba ni MUNIRAH NAZIR ATAH ba. Ai ƙaryar ka ta sha ƙarya ka ci moriyar ganga akaina,sannan ka yada kaurenta. Ni da kai mutuwa ce za ta raba mu,ko da aure ko a bariki. Ina so ka rubuta wannan ka ajiye Samir,a duk ranar da ka auri wata macen ba ni ba za a ɗauki gawa ko na ce gawarwaki. Ko ni,ko kai ko ita matar da za ka aura,ko mu haɗu dika mu yi mutuwar kasko." Tana gama maganarta ta kashe wayar ta yi wurgi da ita a ƙasa da ƙarfi har sai da screen ya tsage. Tsaye ta miƙe tana jin wani irin zafi na shiga kowanne lungu da saƙo na jikinta,a hankali ta hau tsiyayar da zufa kamar ruwa kafin daga baya zufar ta bar zuba sanyi ya fara shigarta. Idonta da ta waro ta lumshe tare da ɗora hannunta a saman kanta ta damƙi tulin gashin kanta ta hau kai wa da komowa a cikin ɗakin. Wani irin ihu ta kurma kamar wadda aljanu suka hau. Ido ta sake zaro wa waje sannan ta sake kurma wani ihun tare da fashe wa da kuka ta dunƙule a ƙasan wajen tana kama ƙirjinta da take jin yana barazanar rabe mata gida biyu. Ƙarar buɗe ƙofar ɗakinta ne ya sanya ta snapping ta ɗaga kanta ta kalli bakin ƙofar. Mahaifiyarta ta gani tana ci gaba da kiciniyar sanya kimono ɗinta tana tambayar dalilin shigarta wannan mawuyacin halin. Kai Muni ta hau girgiza wa Mahaifiyarta sannan ta ce. "I thought he hates marriage. Ban sani ba ashe ni ce baya so Mom,ni ya tsana,ni ce ba zai aura ba. He was my first true love,i gave him everything Mom,babu wani abu da ya min saura wanda Samir bai san da shi ba. I love him so very much Mom,ba zan taɓa iya ci gaba da rayuwa babu shi ba. Mom please do something tun kafin ki rasa ni;domin idan na rasa Samir a rayuwata mutuwa zan yi Mom." (Na zaci ya tsani aure.) Munirah ta ƙarasa maganarta tana mai fashewa da wani irin kuka mai matuƙar ƙona zuciya. Hajiyah Nusrah ta jima da sanin cewa Samir da Munirah ƙaddarar juna ne,duk wannan burgar da yake yi ta zai yi aure dole zai dawo wa Munirah, musamman ma da bai taɓa furta zai yi aure ba ko yana da burin yin auren. Hannu Hajiyah Nusrah ta sa a bayan Muni ta hau shafawa a hankali sannan ta ce. "Look Muni he is just pulling your legs babu wani auren da zai yi." (Kin ga Muni kawai wasa yake yi miki) "Mom da gaske yake yi aure zai yi ni ya barni bayan ya gama da rayuwata." A hasale Hajiyah Nusrah ta ce. "Stop reminding me you are not a virgin Muni! I want you to pull your self together ok? Ya taɓa yi miki zancen aure?" (Ki dena tuna min ke ba budurwa bace Muni. Ina son ki tattara kanki waje ɗaya kin gane?) Kai Munirah ta girgiza wa mahaifiyarta ta ci gaba da kukan da take yi. Cikin sigar lallashi Hajiyah Nusrah ta ce. "Kin gani. Dan haka ki dena wannan ɗan iskan kukan mara tushe ki ci gaba da rayuwarki kamar yanda kika saba,domin na tabbata ko aure Samir ya yi ba zai taɓa rabuwa da ke ba." "Ni bana son ya yi auren ne Mom." "To ba zai yi auren ba. Tashi ki hau gado ki kwanta,zuwa gobe da safe za mu sake tattaunawa akan maganar. Kafin nan ina buƙatar hutu dan na san matakin da zan ɗauka akan lamarin." Ba tare da Munirah ta kula mahaifiyarta ba ta miƙe tana jan majina ta haye gadonta ta shige ƙarƙashin bargonta. A hankali ta sake nitsar da kanta cikin lallausan matashin kanta tana mai zubar da ruwan hawaye. Gashin kanta Hajiyah Nusrah ta shafa gently sannan ta sunkuya ta sumbaci kanta ta ce. "Good night baby. I love you so much." Ido kawai Muni ta lumshe ruwan hawaye masu yawa da zafi suka zubo mata. Tana kallon mahaifiyarta ta fita ta miƙe ta kulle ɗakin ta buɗe wata drawer a cikin ɗakin ta fito da wata roba mai ɗauke da ƙwayoyin magani ta buɗe ta ɗauki guda huɗu ta sha babu ruwa. Tana gama haɗiye wa ta koma gado ta kwanta tana kuka. A hankali bacci mai daɗi ya ɗauke ta. *********************** Tun cikin dare naƙuda ta kama Hanifah amma ta ƙi sanar da kowa,fatan ta bai wuce gari ya waye ba ta koma gidan mijinta kamar yanda Baba ya buƙata. Da ƙyar ta iya danne azabar da take ji ba tare da ta tada ƙannen nata dake ta sharar bacci ba. Ana idar da sallar asuba naƙudar ta tsananta har ta kasa jurewa. Kan dole ta saki wani irin numfashi sannan ta hau kiran Kilishi da Mama su taimaka mata. Da sauri Nasibah da ke karanta ƙur'aninta ta kalli Yayartasu ta ce. "Yayah cikinki na ciwo ne?" Da ƙyar Hanifah ta ɗaga mata kai ta ce. "Ki je ki kirawo min su Mama." Cikin sauri Nasibah ta ajiye ƙur'anin nata a mazauninsa sannan ta fita tana ƙwala wa su Mama kira. Cike da tashin hankali Mama da Kilishi suka zo ɗakin suna duba Hanifah. Nasibah dake tsaye a waje tana ganin Makaɗi ya dawo daga masallaci ta nufi wajensa tana haki ta labarta masa abinda yake faruwa a gidan. Ransa a mutuƙar ɓace ya kalli Nasibah ya ce. "Yanzu yarinyar nan ta dage anan za ta haihu mana ko? Kaiii Allah ka raba mu da baƙar sa'a." Baki Nasibah ta saki tana kallon Mahaifin nasu wanda yake da tsananin son kansa. Kafin ta bashi amsar maganarsa ta ga ya washe baki ya saka hannu a aljihunsa ya ce. "Kai ku shirya ta yanzu zan kira surukina ya zo ya kai ta asibitinsa ta haihu a can. Na tabbata sosai hakan zai ƙara kusanci a tsakanin ku Nasibah." Babu ɓata lokaci Malam Sanda ya hau nemo No Samir da suka jima da yin exchanging. Cikin magagin bacci Samir ya ɗauki wayar ya kara a kunnensa ya ce. "Baba lafiya kake kirana da sassafe haka?" Nan take Malam Sanda ya marairace murya ya ce. "Don Allah Alhaji Samir ka taimaka min,ƴata ce ta zo gida haihuwa gashi abun ya zo tun cikin dare nake neman ɗan sahun da zai kai ta asibiti ban samu ba,shine na ce tunda ku ne likitocin bari na sanar da kai ko akwai wani taimakon gaggawa da za ka iya sanar da ni a yi mata kafin a samu abun hawa." Da sauri Samir ya dire ƙafafuwansa ƙasa ya ja rigarsa yana zirawa a jikinsa ya ce. "Give me 10 minutes gani nan zuwa gidan." Durƙusawa Malam Sanda ya yi kamar Samir na ganinsa ya ce. "Godiya nake yi Alhajin Allah,Allah Ya saka da alkhairi." Yana kashe wayar ya juya ya kalli Nasibah da tsoron Allah ya gama cika wa zuciya ya ce. "Maza shiga ki sanar da su a shirya ta wannan yaron zai zo a kai ta asibiti." Ganin Nasibah ta kasa motsawa ne ya sanya Malam Sanda leƙa kansa cikin ɗakin ya sanar da su sannan ya shige ɗakin Mama ya sanya rigarsa mai kyau tare da fesa turare ya fito cikin shirin tafiya asibiti.......... [10/6, 7:12 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨ ✍️ PAGE 14. Kamar yanda Samir ya yi wa Malam Sanda alƙawari haka ya zo cikin ƙanƙanin lokaci kan nan a hargitse. Tare da shi aka taimaka wa Hanifah ta shiga cikin motarsa Rabi da Nasibah na tsaye suna jera mata sannu. Ko ci kanku bai ce musu ba banda aikin kallon Nasibah dake sanye da riga da wando na bacci irin na gumamar nan da yake yi. Suna nan tsaye Malam Sanda da Kilishi suka fito a gurguje suka shiga motar Samir ya ja suka tafi asibitinsa. Komawar su Nasibah gida babu jimawa mijin Hanifah ya kira wayar Mama ya sanar da ita gashi nan zuwa,domin kuwa tun da Nasibah ta ji abun kunyar da Makaɗi ke shirin yi musu ta faki ido ta kira shi ta sanar da shi duk abinda yake faruwa. Sallama suka yi ya kashe waya Mama ta samu Nasibah ta rufe ta da faɗa. Baki ta tura ta shige ɗakinsu ta hau shirin makaranta dan bata son zama a cikin gidan Mama ta yi ta mata mita. A gurguje ta gama shiri ta fito sanye da uniform ɗinta a wanke a goge kamar ko da yaushe. Ko abun karyawa bata nema ba ta saka kai ta bar gidan tana fatan Allah Ya sa Hanifah ta haihu lafiya. Ko a makaranta Nasibah bata da wani kuzari da walwala kamar ko da yaushe,daga malamai har ɗalibai kowa ya fahimci Nansy bata cikin yanayi na fara'a,dan haka kowa sai ya rabu da ita gudun kar mutum ya taka sawun ɓarawo a wajenta. Ana tashi ta samu Nawwarah da Nadiyah ta ce su yi mata rakiya zuwa asibitin Samir dan ta ga Yah Hanifah. Da ƙafa su Nasibah suka taka har zuwa asibitin Samir ɗin saboda rashin kuɗin abun hawa. Sai dai suna isa nurses ɗin wajen suka basu tabbacin babu jimawa aka sallami su Hanifah sakamakon ta haihu cikin ƙoshin lafiya. Lokaci Nasibah ta ɗaga kai ta kalla a jikin makeken agogon bangon dake manne a reception ɗin. Karfe uku da rabi na yamma Nasibah ta gani sai ta kama bakinta ta kulle tare da sakin wata ajiyar zuciya mai karfi. Da sauri su Nawwarah suka fita daga cikin asibitin suna faɗin. "Yau idan muka je gida Nadiyah sai mun sha faɗa." Nadiyah wadda take da mugun tsoron duka sai ta kalli Nasibah ta ce. "Don Allah ki raka ni gidanmu ki faɗa wa Mommy inda muka je kar ta dake ni." Kai kawai Nansy ta ɗaga musu suka ci gaba da tafiya a ƙafa har suka isa unguwarsu. Har gida Nansy ta kai su Nawwarah sannan ta sanar da iyayensu batun haihuwar Yah Hanifah,barka suka yi mata sannan suka yi musu faɗan da sun bari sai da suka dawo gida sannan suka je asibitin,gashi sun shiga lokacin islamiyya. Gaban Nasibah ne ya yanke ya faɗi da jin kalmar Islamiyyah. Tunanin Malam Luƙman ne ya ɗarsu mata a cikin zuciyarta. Tana fita sai ta kama hanyar makarantar islamiyyar tasu domin ta haɗu da Masoyin nata ta ji yanda suka ƙare da mahaifinta. A jigace ta isa makarantar tasu ta samu ɗalibai duk an shirshiga aji,makararru kuma na nan waje su na karatu a durƙushe a bakin ƙofar ajujuwansu. Kanta tsaye ta shiga cikin makaranta ba tare da ta damu da kallon uniform ɗinta da mutane suke yi ba. Ajinsu ta nufa domin ta yi wa Malam magana dan ya fito waje su tattauna. Sai dai tun kafin ta isa ajin ta jiyo muryar wani malamin yana karatu a madadin Malam Luƙman ɗinta. Tsayawa ta yi tana nazarin dalilin da ya hana Malam Luƙman zuwa makarantar. Tana nan tsaye ta ji muryar Mami maƙociyar su Malam Luƙman na yi mata magana. A hargitse Nansy ta juya ta ce. "Asibiti kuma? Wanne irin asibiti? Lafiya ƙalau fa muka rabu da shi jiya. To me yake damunsa?" Nan da nan kuka ya kwace wa Nansy,abunda babu wanda ya taɓa gani a tattare da ita kenan. Domin Nansy na da matuƙar dauriya da jure wahala saboda kada a ga gazawarta a raina ta. Cike da damuwa a saman fuskar Mami ta ce. "Tun jiya da daddare da ya koma gida in ji Mamanmu yake kwance bashi da lafiya. Shine yau da suka ga abun ya yi yawa aka kira Yah Atiku ya kai su asibiti da motarsa, ɗazu da zan taho makaranta na ga sun dawo gida." "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Na shiga uku ni Nasibah." Cikin sauri Nasibah ta juya ta fita daga makarantar ko hanya bata gani da kyau saboda hawaye da kukan da yake neman ya kayar da ita a wajen. Ga yunwa da ƙishirwa da suka kassara kuzarinta. A haka ta yi ta jefa ƙafa ta na tafiya cike da tashin hankali har ta isa gidan su Luƙman. Ta na zuwa ta tarar da gidan da mutane da yawa,wannan ya shiga wannan ya fita. Babu ɓata lokaci itama ta bi sahun matan dake shiga suna jimanta yanayin ciwon da suka samu labarin Luƙman ɗin yana fama da shi. Bayan Nasibah ta shiga cikin gidan sai ta samu jikin bangon ɗakin da ta ga mata na shiga suna gaishe da Maman Malam Luƙman suna yi mata jaje tare da addu'ar Allah Ya bashi lafiya. Hawaye take ta zubarwa kamar an kunna fanfo. Tana nan tsaye ta fara jin jiri na neman kayar da ita sai ta samu waje ta durƙusa tare da jefar da jakarta a wajen. A wannan lokacin ne Nasibah ta tuna da bata yi sallah ba,gashi ko gida bata je ba. Sai dai bata jin za ta iya yin ko ɗaya a ciki matsawar bata ga abincin ruhinta ba da halin da yake ciki. Tana nan tana tunani mahaifiyar Luƙman ta fito daga ɗaki ta tsaya a gabanta ta ce. "Ke yarinya lafiya kika shigo gidan nan tun ɗazu kike ta kuka? Ko kina cikin ɗaliban wannan yaron ne?" Da sauri Nasibah ta hau gyaɗa kai tana ƙoƙarin tsayar da hawayenta da suka gaza bata haɗin kai. Ido Ummi ta ƙanƙance tana bin Nasibah da kallo. Bayan wasu ƴan daƙiƙu sai ta haɗe fuskarta ta ce. "Nasibah ko?" Da sauri Nansy ta ɗaga kai ta kalli Ummi kafin ta yi saurin duƙar da kanta ƙasa tana ci gaba da zubar da ruwan hawaye. Murmushin takaici Ummi ta yi sannan ta ce. "Taso mu je ki gansa kema. Ai bai kamata ki zauna anan kina kuka ba,kamata ya yi kema ki shiga ki ga halin da mahaifinki ya jefa min ɗana a ciki saboda son abun duniya." Kai Nasibah ta sake sunne wa ƙasa tana jin dama bata zo ba. Sai dai kafin ta gama tunanin da ta ɗakko a cikin ranta ta ji an ja hannunta,babu ɓata lokaci jikinta ya bi umarnin ƙafafuwanta Ummi ta kaita har cikin ɗakinta inda Malam Luƙman yake a kwance hannunsa da robar karin ruwa a jiki. Baki Nansy ta damƙe wani sabon kuka na taso mata mai sauti. A cikin wannan halin Malam Luƙman ya buɗe idanuwansa ya kalli Nasibah. Wani irin kallo wanda ke nuni da tsantsar so da ƙaunar da yake yi mata. Itama kallonsa ta fara yi tana takawa zuwa wajensa a hankali tana shassheƙar kuka. Murmushi Malam Luƙman ya sakar mata tare da girgiza mata kai,cikin raunatacciyar murya ya ce mata. "Ki dena irin wannan kukan Nasibah kada kema ki kamu da irin ciwon da nake fama da shi. Ina so da ni da ke mu ɗauki ƙaddara,mu yi haƙuri da junanmu,domin kuwa na fahimci matsawar ban fi mutumin da mahaifinki ya zaɓa miki arziƙi ba to fa ba zai taɓa yarda na aure ki ba." Cikin kuka Nasibah ta ce. "Me Baba ya ce maka ne jiya Mine?" "I am not yours anymore Nasibah. Ya kamata ki gane hakan tun da wuri." Malam Luƙman ya katse Nasibah cikin numfashi mai sarƙewa. Da sauri Nasibah ta durƙusa a gabansa ta ce. "Don Allah kada ka sake faɗar haka Mine,zuciyata ba za ta iya jure rashinka ba a rayuwata. Ka sani ina son ka,ka yi min alƙawari ko bayan ka kammala karatu za ka jira na yi candy ka aure ni,a lokacin idan Baba ya ga ka yi kuɗi zai amince ka aure ni. Dan haka ina so ka kawar da duk wani tunani na ɓacin rai a cikin ranka game da koma menene Baba ya ce maka,ka mayar da hankalinka akan karatunka Please. Kai kaɗai nake son in aura Mine." Idanuwa Malam Luƙman ya lumshe yana jiyo ƙamshin nasara da wani irin ƙwarin guiwa yana sake shigarsa. Kafin ya yi magana Ummi ta riga shi ta ce. "Ah ah Nasibah kada ki ba shi ƙwarin guiwar da zai sake raunata zuciyarsa a nan gaba. Mahaifinki jiya ya yi masa iyaka da ke,duk da Luƙman bai sanar da mu abinda ya faru ba na tabbata ba ƙaramin abu mahaifinki zai yi masa ba ya haƙura da ke. Ni na haifi Luƙman na san irin zurfin cikinsa da girman soyayyar da yake yi miki. Dan haka ina so da ke da shi ku yi haƙuri da junanku,kada ku manta har yanzu kuna da sauran lokaci a rayuwarku;musamman ma ke da kike da ƙarancin shekaru,matsawar kuna cikin masu nisan kwana ba za ku rasa abokan rayuwar da za su so ku ba." Cikin kuka Nasibah ta juya ta kalli Ummi wadda tausayin yaran ya cika mata zuciya ta ajiye makaman faɗan dake cikin ranta ta hau lallashi. Kasa cewa komai ta yi sai ta fita daga ɗakin da gudu ta nufi hanyar fita ko jakar ta bata tsaya ta ɗauka ba. Haka ta dinga haɗa hanya har ta isa gida. Shirun da ta ji gidan ya ɗauka ne kamar ba a yi haihuwa ba shi ya sanya ta tsagaita wa da kukan da take yi. Faihah ta gani zaune a bakin ƙofar ɗakinsu tana share hawayenta. Da sauri ta wuce ɗakinsu na ƴammata ta duba bata ga Yah Hanifah ba,sai ta wuce ɗakin Kilishi ta gansu zaune ita da su Rabi da Usman,da alama wata maganar suke yi da suka ganta suka yi shiru. Tsakar gidan ta koma ta shiga ɗakin Mamanta ta ganta zaune a bakin gado ta zabga tagumi. Wajen Faihah ta koma ta ce. "Ke me ya faru na ga gidan haka kamar an yi mutuwa,ina Yah Hanifah da jaririnta?" Kafin Faihah ta yi magana Kilishi ta fito tana ɗaure kanta da kallabi ta ce. "Me kuwa ya faru banda halin mahaifin naki da ya saba yi a koda yaushe? Wannan yaron Samir na dawo da mu daga asibiti cike da kayan arziƙi Malam ya kirawo mijin Hanifah da ya gama ci wa mutunci a asibiti ya ce ya zo ya ɗauki matarsa su koma inda suka fito;saboda shi ba za a zauna masa a gida a cinye masa ɗan abinda zai ciyar da iyalinsa ba. Duk irin kuka da magiyar da Hanifah ta dinga yi wa bawan Allah'n nan bai haƙura ba sai da ya tattara mata kayanta ya sallame ta ta bi mijiinta. Yanzu don Allah in ba dan Nafi'u mutumin kirki bane ba ai tun abinda ya yi masa a asibiti sai ya yi silar macewar aurenta." Ran Nasibah idan ya yi dubu ya ɓaci. Ba tare da ta ce komai ba ta shige ɗakin su ta zube a soson katifarta tana jin kamar ta yi ta kurma ihu. Sosai ƙirjinta ya yi mata nauyi,zuciyarta na zafi,ga ciwon kai wanda ta tabbata zama da yunwa da ƙishirwa ne ya jawo mata su. Lumshe rinnnun idanuwanta ta yi tana sauke numfashi da ƙyar. Tana nan kwance cikin mawuyacin hali ta ji muryar Mama na faɗin. "Wato ke Nasibah kin rantse da Allah ni zan biki a matsayina na mahaifiyarki ba ke za ki yi min biyayya ba ko? Nan nan kika shiga har ɗakina ki ka fito ba tare da kin ce min ƙala ba. Daga ina kike tun safe sai yanzu kika ga damar dawowa gidan." Shiru Nasibah ta yi domin bata jin za ta iya buɗe baki ta ce komai. Ganin haka sai Mama ta hasala ta ɗauki abinda Nasibah ta yi a matsayin raini da jin tashen balaga. Cikin zafin rai ta fita waje ta samo bulala ta dawo ta kulle ƙofa ta hau jibgar Nasibah wadda ke zaune kamar an dasa ta a wajen ko gezau bata yi ba. Tun Mama na dukanta tana magana har sai da ta gaji tana haki tana kallon Nasibah wadda wahala ta sanya ta zube wa a wajen a sume. Kilishi dake tsaye a bakin window tana kiran Mama sai ta fashe da kuka ta ce. "Shikenan kin kashe ta Maryama kin ji daɗinki. Sai da na ce ki yi haƙuri ki ƙyale yarinyar nan ba ji take yi ba amma kika yi kunnen uwar shegu da ni. Za ki buɗe min ƙofar na shigo ko kuwa?" Jikin Mama na rawa ta buɗe ƙofar ta yar da bulalar a wajen ta shige cikin ɗakinta. Sosai taurin kan Nasibah ke damun ta. Saboda gudun kada ta illata yarinyar ne ya sa take ƙyale ta tana abubuwan da ta ga dama. Gashi yanzu ta hasala ta ta yi mata dukan tsiya. A hankali ta buɗe labulen ɗakinta ta leƙa Kilishi dake rungume da Nasibah tana shafa mata ruwa a jikinta. Idanuwa Nasibah ta buɗe tana fitar da zazzafan numfashi ta ce. "Me yasa...kika ƙwace....ni...a hannunta?...don Allah...ki barta ta kashe ni....na gaji da zama da takaicin abubuwan....da...ake yi min....a gidan nan....Baba baya so na da Malam.... Luƙman....ya kore shi yanzu....haka bashi da lafiya...ni na fi so na mutu na huta da zafin da ƙirjina yake yi min Ummaaahh..." Nasibah ta ƙarasa maganarta tana mai rushewa da wani irin kuka mai tsananin cin rai. Daga can ɗakin Mama itama kukan ta rushe da shi tana jin cewa sakacinta ne ya jawo ƴarta ta fara soyayya tun da ƙarancin shekarunta ba tare da ta farga ta yi wa tufkar hanci ba. Gashi yanzu tana ji tana gani ƴarta na neman kangare musu a cikin gidan.......... *Don Allah wai sakacin wanene yake jawo yara ƙanana su fara soyayya da ƙarancin shekaru a makaranta,wasu ma da Malaman makarantar. Shin akwai illa a soyayya da Malamai ko babu?* [10/8, 7:15 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 15. Da misalin ƙarfe 7:13pm Malam Sanda ya dawo gida. Ya na shiga gidan tun kafin ya kafe babur ɗinsa ya kalli Najlah da ta zo yi masa oyoyo ya ce. "Ke ina Yayarki take ban ji motsinta ba?" Juyawa Najlah ta yi ta kalli ƙofar ɗakin Kilishi inda Nasibah take a kwance kamar ruwa ta ce. "Ta na ɗakin Ummah bata da lafiya. Baba ka san me? Mama ce ta daketa ta mutu,Ummah ta yi ta kuka ta kira Faihah ta ce ta bata ruwa, shine da Ummah ta shafa mata ruwan ta buɗe ido tana kuka." Zuciyar Mama na lugude ta fito ta samu kan Najlah ta ƙoza ta tana hararta ta ce. "To Suda sarkin zance,faɗi ba a tambaye ki ba,wuce ciki kafin na sumar da ke kema." Ƙugu Makaɗi ya kama da hannu ɗaya,hannunsa ɗaya kuma ya dafe jikin babur ɗinsa yana kallon Mama ya ce. "Af toh na ji,ita Nasibar kenan sumar da ita kika yi ko Maryama? Akan me za ki sumar min da yarinya? Laifin maita aka kama ta da shi ko na lalata?" Shiru Mama ta yi ta durƙusa ta shimfiɗa masa tabarma,dan ta kula da fushin da Kilishi ke yi da ita ba zai bari ta fito ta kula da mai gidan nasu ba. Ta na gama shimfiɗa wa ta kalli ƙafar Makaɗi da har a wannan lokacin bai motsa daga inda yake ba,hakan na tabbatar mata da cewa bai dena kallonta ba,fuska a cure ta ce. "An dawo lafiya?" A hasale Makaɗi ya ce. "Da masassara na dawo Maryama. Na ce da masassara na dawo. Za ki bani amsar tambaya ta ko sai ranmu ya haɗu gaba ɗaya ya ɓaci?" Fuska a ɗaure Mama ta kalle shi ta ce. "Kai ka san taurin kai da rashin jin Nasibah Malam,shine dan an hukunta ta kake yi min tsawa?" "Hukunci? Hukuncin ne zai kai ki ga sumar min da yarinya?" "Ni ban sumar da kowa ba." Mama ta faɗa tana mai shige wa ɗakinta;domin zuciyarta ta kasa yin haƙuri ta bashi abincin da ta yi niyya. Ta na shiga ciki ta dafe ƙirjinta da ke yi mata lugude,a bakin gado ta zauna tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Makaɗi kuwa sai ya hau ƙwala wa Nasibah kira yana taku cikin sauri,a bakin ƙofar ɗakinsu ya tsaya ya ɗaga labule yana faɗin. "Wai Nasibah bata ji na ne?" Cikin kuka Nasibah da ta yunƙura da ƙyar ta fito daga ɗakin Kilishi ta ce. "Baabaa." Da sauri Malam Sanda ya juya idanuwansa suka sauka akan Nasibah dake jingine a jikin gini tana risgar kuka. A sukwane Malam Sanda ya isa gabanta ya kunna hasken wayarsa yana duba ta. Ganin shatin bulalai a jikin Nasibah sun kwanta sun yi jawur ne suka sanya shi sakin wayarsa a ƙasa yana salati. Ji ya yi kamar ya kurma ihu. Cikin ɓacin rai ya isa ɗakin Mama wadda ta yi saurin tayar da sallah ta yi sujjah. Malam Sanda na zuwa ya ga abinda take yi sai ya ce. "Maryama idan shekara dubu za ki yi kina sallah,ni kuma zan shekara dubu da ɗaya ina jiran ki idar. Ba zaki dakar min yarinya ki ci bulus ba,a yau ba sai gobe ba za ki tattara ki tafi gidan iyayenki,ba zan ɗauki wannan sabon salon fushin rashin hankalin da kika fito min da shi a gidan nan ba. Ke Nasibah zo nan!" Ƙafafuwan Nasibah na rawa ta fara tattaki zuwa wajen Malam Sanda. Sai dai kafin ta isa gabansa ta zube a wajen tana aman ruwan kunu da tuwon da Kilishi ta ɗura mata. Hankalin Malam Sanda ba ƙaramin tashi ya yi ba,kafin Kilishi da ta fito daga ɗakinta jin Nasibah na amai ta isa gaban Nasibah Malam Sanda ya riga ta. Tallabo Nasibah ya yi yana haki ya ce. "Wai me ya faru a gidan ne da bana nan har aka yi yunƙurin hallaka min ƴa?" "Yanda ka ganta nima haka na ganta Malam,kawai ka kama ta ka kai ta Kemis ɗin Ɗan Small ya bata maganin zazzaɓi da ciwon jiki." A wannan ranar Makaɗi ko tuna wa da Samir bai yi ba ballantana ya nemi taimakonsa. A gaggauce ya sunkuya ya ɗauki Nasibah a hannu ya nufi ƙofar gida da ita. Su na fita suka ci karo da Usman ya dawo daga wajen abokansa. Da sauri ya isa gaban Makaɗi ya karɓi Nasibah ya goya ta yana faɗin. "Baba ina za ka kai ta haka?" "Mu je ka kai ta wajen Ɗan Small ya duba min ita." Fankam-Fakam suke tafe kamar Makaɗi zai caki ƙasa da haƙoransa. Su na zuwa wajen Ɗan Small me Kemis suka ga zai rufe wajen saboda kiran sallah da ake yi,da sauri Makaɗi ya dakatar da shi ya roƙi arziƙi ya duba masa Nasibah. Magunguna ya bata Makaɗi ya cire kuɗin da ƙyar yana jin ciwon yin hakan a ransa ya bayar. A hanyar komawarsu gida ya bi ta shagon Isiya ya siya mata Fanta suka nufi gida yana faɗin. "Ban kashi kuɗin banza ba Maryama,dan kuwa sai kin cake min kuɗin duk da kika sa na yi asara kan ki wuce gidanku." Ransa a matuƙar ɓace suka koma gidan Nasibah na sake langwaɓewa tana sakin numfarfashin azaba. A tabarmar da Makaɗi ke zama Usman ya kwantar da ita yana haki ya zube a gefenta yana lasar busassun laɓɓansa. Idonsa akan sanssanyar Fantar da Makaɗi ya siyo wa Nasibah ya ce. "Ƙishirwa nake ji,ina ma mutum zai samu wani sassanyan ruwa ko lemo ya kora." A hasale Makaɗi ya kalle shi ya danna masa harara,kai Usman ya sunne ƙasa ya miƙe tsaye ya bar wajen. Yana tashi Malam Sanda ya zauna tare da ƙwalawa Kilishi kira ya ce. "Taho min da kofi da ɗan abincin nan mu ga ko za ta iya ci." Daga ɗaki Kilishi ta amsa shi da "Toh Malam" sannan ta fito ta shiga madafa ta ɗakko abincinsa a babban faranti ta ajiye a gabansa tana tambayar jikin Nasibah. Ajiyar zuciya Malam Sanda ya sauke sannan ya cire hularsa da ta yi zufa ya ajiye a gefensa ya ce. "Gata nan ki taimaka ki kular min da ita; tinda ita Maryama yanzu ta zama abinda ta zama." "To Malam Allah Ya bata lafiya." Nan fa suka tasa Nasibah a gaba da lallashi da lallami har ta samu ta sake cin tuwon kaɗan ta sha fantar,sannan ta sha maganin ta kwanta. Babu jimawa baccin wahala ya kwashe ta. A nan wajen Makaɗi ya zauna har ƙarfe ɗaya da rabi na dare. Nasibah ya gani sanye da hijabi a zaune ta jingina da gini tana kuka hannuwanta a sama. Idanuwansa ne suka washe ya sake kallonta ya ce. "Sannu ƴar Baba,yaushe kika tashi?" Nasibah bata kula shi ba,kuma bata dena yin addu'o'in samun nasara akan mahaifin nata ba domin ya amince ta auri Malam Luƙman ɗinta. Buta Makaɗi ya ɗauka ya zaga banɗaki. Ko da ya fito sai ya tarar da wajen babu kowa,shima sai ya tattara komatsansa ya wuce ɗakin Kilishi ya kwanta. A bangaren Nasibah kuwa bata sake rintsa wa ba saboda tsannanin tunani da ya cika mata zuciya. Sosai take jin tsana da haushin Samir a cikin ranta. Ana kiran sallar asuba bacci mai daɗi ya dinga sanɗar ta,kin bashi dama ta yi ta fita ta yi alwala ta koma ɗakin ta tayar da sallah. Ta na idarwa ta koma ta kwanta bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita. A wannan ranar da safe haka Mama ta ƙaraci baiwa Makaɗi haƙuri da ban baki amma bai kula ta ba. Daga ƙarshe ma da zai fita sai ya kalli Kilishi ya ciro kuɗin cefane ya bata ya ce. "Tinda na yi kora an ƙi bar min gidana to sai a yi ta zama,amma ba zan yarda a sake dafa min abinci ba a gidan nan,ke Kilishi ki yi girkin dare,sai na dawo." Tagumi Mama ta zuba tare da sauke ajiyar zuciya. Kilishi kuwa sai ta hau mahaifa tana faɗin. "Ba zai yiwu ba Malam, a gaskiya ni ba zan karɓi girkin kowa ba." "Au kema nuna min za ki yi ban isa da ke ba? Rabi! Rabi ke zo nan." Malam Sanda ya faɗa yana riƙe kan babur ɗinsa da kyau. Rabi dake ɗaki tana ninke kaya sai ta ajiye ta fito da sauri ta durƙusa a gaban Malam Sanda ta ce. "Baba gani." "Amshi nan ki siyo kayan miya ki yi girki,zan dawo da rana na duba jikin ƴar'uwarki idan ta farka." "To Baba a dawo lafiya." Ba tare da ya amsa ta ba ya buga babur ɗinsa tare da baɗe su da hayaƙi ya bar gidan. Kilishi ma ɗakinta ta nufa,dan itama fushi take yi da Mama,shi yasa gaisuwarta kawai ta amsa tun da suka tashi basu yi wata doguwar hira ba. Duk Mama sai ta ji ta tsangwami kanta,nadamar dukan Nasibah duk ta mamaye mata zuciya. Jiki a sanyaye ta faki idon Kilishi ta leƙa ɗakin da Nasibah ke kwance kamar ruwa. Ganin yanda jikinta ya yi ja shatin bulalai suka yi masa ƙawa sai jikinta ya sake yin sanyi. A nan take ta gasgata dukan da ta yi wa yarinyar ya yi yawa,amma kuma ai ita ce ta jawo saboda taurin kanta. Ɗakinta ta koma ta fito da nera ɗari uku ta ba wa Najlah ta ce ta siyo mata madara da milo. Da sauri Najlah ta bar gidan ta nufi shagon Isiya ta siyo ta kawo wa Mama. Ɗakin Kilishi Mama ta je ta miƙa mata kayan shayin da ruwan zafi a flask ta ce. "Ummahnsu ga abun kari na kawo wa ƴar taki a bata,Allah Ya ƙara lafiya." "Aje su nan." Kilishi ta ce tana kawar da kai. Murmushi Mama ta yi ta ajiye a inda Kilishi ta nuna mata ta fita ta koma nata ɗakin. Ta labulen ɗakinta take ganin gilmawar kilishi tana ta hidima da Nasibah. Haka Nasibah ta ɗauki tsawon kwana huɗu tana jinyar jiki da zuciyarta. Sai dai a zahiri kowa ya shaida ta warke babu zazzaɓi tabon dukan duk ya yi duhu ya fara ɓacewa. Amma a zuciyar Nasibah jinta take yi kamar wadda aka tattara wa dika damuwar duniya aka ɗora mata akanta. Gaba ɗaya ta rame ta ƙara haske. Babban takaicinta bai wuce yanda Makaɗi ya sanar da Samir ta yi fama da jinya ba,shi kuma sai ya saki bakin aljihu ya dinga siyayya yana kawo wa gidan. Duk zuwan da yake yi kuwa duk yanda Makaɗi zai kaɗa ya raya bata fita wajen Samir. Yau ma kamar sauran ranakun da suka gabata,Nasibah ta dawo daga makaranta,sai ta cire hijabinta ta shiga ɗakinsu ta ajiye jakarta ta shiga ɗakin Mama ta gaishe ta. Ganin yanda Nasibah ta rame sai hakan ya ɗaga hankalin Mama,amma da yake basu da shaƙuwar da za ta kira Nasibah ta tambaye ta abinda yake damunta sai ta yi shiru tana bin ƴar tata da kallo har ta fita riƙe da kayan da za ta sauya. Nasibah na komawa ɗakinsu ta sauya kaya ta kwanta ko abinci bata nema ba. A hankali bacci mai daɗi ya fara ɗibanta a kan soson katifarta da ba shi da maraba da tabarma. Cikin baccinta ta dinga jin wani irin sassanyan ƙamshi mai daɗi yana shiga ƙofofin hancinta. A hankali ta juya ta kai kanta saitin inda ƙamshin ke fitowa. Idanuwanta da suka yi mata nauyi saboda bacci ta buɗe ta zuba su a kan kyakkyawar halittar dake tsaye a saman kanta yana ƙare mata kallo.......... [10/10, 7:26 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 16. Da sauri Nasibah ta tashi zaune ta na rarraba idanuwa tsakanin bakin ƙofar shiga ɗakin nasu zuwa kan Samir da ya zuba hannuwansa a cikin aljihun baƙin wandonsa yana ƙare wa ɗakin kallo cike da ƙyanƙyami da mamakin ganin makwancin Nasibah. Muryar sa a shaƙe ya ce. "How on earth do you sleep here comfortably?" Harara Nasibah ta watsa masa sannan ta tura bakinta gaba ta miƙe tsaye ta ce. "Malami ni ka je waje ka jira ni zan fito yanzu." Murmushi Samir ya yi ya jingina da jikin ƙofar ɗakin ya ce. "Ba zan iya yin hakan ba;saboda Baba ne da kansa ya bani izinin shigowa nan tinda baki da lafiya ba za ki iya fita waje ba." "To ai ni na warke har makaranta na ci gaba da zuwa ma." Ba tare da Samir ya ce mata komai ba ya hau takawa zuwa gabanta ya miƙa hannu zai taɓa goshinta domin ya ji yanayin zafin jikinta. Cikin wani irin hanzari Nasibah ta ja da baya ta dunƙule hannuwanta biyu tare da ware ƙafafuwanta ta mayar da ɗaya gaba ɗaya baya ta saita fuskar Samir ta kai mata naushi. Da sauri ya sunkuya hannunta ya harbi iska. Idanuwa suka zuba wa juna kowannensu na nishi kamar kajin dake shirin kacamewa da dambe. Sallamar Makaɗi da ke washe baki ne ta dawo da Nasibah da Samir cikin hayyacinsu. Ƙwafa Nasibah ta yi ta gyara tsayuwarta sannan ta fita daga ɗakin cikin matsanancin ɓacin rai ta shige ɗakin Kilishi ta kwanta a gadonta tana mayar da numfashi. Sosai Nasibah ta ji takaicin rashin samun kyakkyawar fuskar Samir da bata yi ba. Ƙwarai ta so ta yi wa fuskarsa tabon da daya kalla zai tuna ya taɓa haɗuwa da Nansy Ƙaya. Ƙwafa ta sake yi a karo na babu adadi ta kulle idanuwanta tana jiyo yanda Makaɗi ke zubar mata da mutunci kwando-kwando a gaban wanda yake iƙirarin za ta aura. A can tsakar gida kuwa Samir ne ke sanar da Makaɗi zai aiko kayan gado a saka wa Nasibah a ɗakinta,dan bai ji daɗin yanda ya ganta kwance a ƙasa ba. Godiya Makaɗi ya zube a wajen yana zabga wa Samir har sai da Samir ya ɗaga shi. Cike da jin nauyin Samir Mama da Kilishi suka leƙa tsakar gidan suka gaisa. Kallon su ya yi ya amsa gaisuwarsu a tsaye sannan ya sa kai ya fita cike da takun taƙama da isa. Yana fita daga gidan Rabi dake kitchen ta shiga ɗakin Kilishi a guje ta faɗa kan Nasibah tana murna ta ce. "Kaiii ƙanwata amma gaskiya na taya ki murnar samun miji irin na nuna wa maƙiya su ji haushi." "Sai kuma aka yi rashin sa'a Nansy bata da maƙiyan da za ta nuna wa shi su ji haushi ba." Dariya Rabi ta yi ta samu waje ta zauna da kyau ta ce. "Da dai Nasibah kika ce,amma Nansy ai ina ga har sarkin Kano yana da matsala da ita." Murmushi Nasibah ta yi ta juya wa Rabi baya ba tare da ta sake cewa komai ba. Rabi kuwa sai ta zauna ta dinga yabon kyau da gayun Samir tana zuga Nasibah akan ta manta da Malam Luƙman ta amince da auren Samir. Cike da karyewar zuciya Nasibah ta juya ta kalli Rabi ta ce. "Yah Rabi don Allah ki dena yi min irin waɗannan kalaman domin za su sa na ji kamar kema ba kya so na. Kin kuwa san irin zurfin son da muke yi wa junanmu? Har yau bashi da lafiya tun da ya zo Baba ya gaggaya masa baƙaƙen maganganu. A bakin Mami na samu labarin jininsa ya hau har yanzu suna faman zaryar zuwa asibiti." "To Nasibah yaya za ki yi? Ai a hakan za ki yi haƙuri ki daure ki rabu da shi ya gama jinyarsa ya samu wata ya aura;kema ki auri Samir ɗinki..." "Ni ba Samir ɗina bane. Malam Luƙman ne zaɓin raina har gaban abada. Ya min alƙawarin zai jira ni har na kammala secondary school,nima kuma na yi alƙawarin ba zan auri kowa ba idan ba shi ba." Ajiyar zuciya Rabi ta sauke ta jingina da jikin gado ta ce. "Nasibah ina so ki gode wa Allah domin ya kawo miki babbar damar da za ki huta wani naki ma ya huta. Kina gani ni har yanzu ko mai gyaran takalmi ban samu ba a matsayin manemin aurena,amma ke kin samu mutum kamar Samir kike ƙin sa." "Don girman Allah Yah Rabi ki ƙyale ni da maganar wannan me kama da matan. Ni fa a rayuwata na tsani farin namiji,ganinsa nake yi kamar ni da shi bamu da banbanci. Amma idan kina son Samir ya zamo surukin Baba ki je na bar miki shi ki aura." "Daga baki shawara shine zaki faɗa min bakar magana Nasibah? Allah Ya baki haƙuri ni na yi nan." Rabi ta ƙarasa maganarta tare da fita daga ɗakin ranta babu daɗi. Tabbas da ita Samir ya nuna yana so ba za ta tsaya ɓata lokaci ba za ta amince,amma kuma tinda ƙanwarta yake so dole ta kama kanta,nan take ta yi wa kanta alƙawarin ba za ta sake saka baki akan rayuwar auren Nasibah ba ballantana har ta faɗa mata maganar da za ta ɓata mata rai. A ɓangaren Samir kuwa yana fita daga gidan ya yi wa wani abokinsa waya ya yi order ɗin kayan ɗaki masu kyau har da carpet da zannuwan gado. Babu ɓata lokaci aka buga lissafi ya aika kuɗin sannan ya tura adireshin gidan Malam Sanda Uba Makaɗi. Yana gamawa ya koma gida ya hau shirin tafiya Abuja,domin gaba ɗaya Munirah ta hana shi sakat da kiran waya da saƙonni. A ranar da yamma Samir ya bar garin Kano zuwa Abuja,daf da magariba kuma kayan ɗakin da ya siya wa Nasibah suka isa gidan. Kamfanin da kansu suka shiga har ɗakin su Nasibah Makaɗi na yi musu jagora suka fitar da kayan ɗakin nasu suka share suka gyara shi tas bayan sun fitar da kayan ciki,sai suka jera wanda suka zo da su sannan suka kafa labulaye suka tafi. Malam Sanda ji ya yi kamar ya kori yaran shi ya karɓi ɗakin,sai dai kuma yana tsoron kada Samir ya sani ya ji babu daɗi. A wannan ranar Malam Sanda har bayan Isha'i yana ɗakin suna ta hira shi da yaran nasa. Cikin hirar tasu ne yake cewa Usman. "Ka ga abinda yasa nake son arziƙi ko Usumanu? Shi fa arziƙi har zumunta yake gyarawa,yanzu yaushe rabon da na zauna da ku irin haka a yi wasa a yi dariya uhumm? To ko da yaushe ina wajen ƙwadago,ina ka fito neman na kai ina zaka je neman na kai." Gaba ɗaya yaran sun gasgata zancensa banda Nasibah da ta shimfiɗa tsohon soson katifarta ta kwanta a ƙasa ta juya musu baya. Lokacin da Malam Sanda zai bar ɗakin sai ya ɗaure fuska tamau ya ce. "Ke Nasibah tashi ki haye gado kafin na saɓa miki a cikin daren nan. Ka ga min shegiyar yarinya mai kafurin taurin kai? Halayyarki fa ta fara kai ni maƙura Nasibah." Makaɗi ya ƙarasa maganarsa yana mai nuna wa Nasibah yatsa yana ƙanƙance ido. Waje ya fita yana ci gaba da rantsuwa idan Nasibah bata hau gado ta kwanta ba sai ya koma ɗakin ya yi mata dukan tsiya. Kan dole ba dan ta so ba ta hau gadon tana gunjin kuka kamar wadda aka yi wa shegen duka. Su Faihah tuni suka yi bacci a saman gadon. Rabi kuwa da ta ga yanda Nasibah ke cike da ƙunci sai ta yi shiru bata ce mata komai ba, bayan fitar Usman daga ɗakin sai ta sauka daga gadon ta kulle musu ƙofa. Gidan abokinsa da yake kwana ya yi wa iyayen nasa sallama ya tafi. Tun daga wannan ranar Nasibah ta saki jiki ta ci gaba da hawa gadon ba dan ranta yana so ba. Bayan kwana biyu ta kama washegari sunan ɗan gidan Hanifah. Dan haka Yah Hauwa da Yah Lawizah sun zo gidan daga su sai kayansu,sun baro yaransu a gidan mazajensu gudun kada Makaɗi ya yi musu cin mutuncin da ya saba. A wannan ranar da ta kama lahadi babu makaranta sai gidan ya kacame da murna. Hatta Nasibah da ta saba yi musu rashin kunya ta yi murna sosai da zuwansu. Suna shiga ɗaki suka ga ƙaton gadon da aka girka a ciki sai suka hau yaba wa suna sake zuga Nasibah akan ta amince da auren Samir kawai ta manta da Malam Luƙman. Baki Nasibah ta kumbura tana ƙunƙuni ta fice waje ta bar musu ɗakin. A wannan ranar a ɗakin Mama Nasibah ta kwana saboda yanda ɗakin nasu ya cika. Washegari da safe duka ƙannenta sun yi shirin tafiya gidan suna,ita kuma sai ta yi shirin tafiya makaranta. Ko da Mama ta yi mata magana sai ta ce. "Mama idan an tashi daga makarantar zan wuce can,kin ga kayana nan na ɗiba a jaka." "To shikenan sai kin dawo." Wajen Malam Sanda Nasibah ta je ta tsaya tana wani ciccin magani,shi kuwa sai ya saki fuska ya kalle ta ya ce. "Ƴar Baba ke ba za ki je gidan sunan ba ne a samu yau a ɗaga wa girki ƙafa a gidan nan?" "Ni sai na taso daga makaranta zan je Baba. Baba ka bani kuɗin break na tafi kar na makara." Haɗe fuska Makaɗi ya yi ya ce. "Ke matsala ta da ke Nasibah bani-bani. Yanzu fisabillahi ba za ki tausaya wa aljihuna ba saboda ciyar da bataliyar da na yi da safen nan?" "Habaa Baba in da ina da kuɗi ai kai ma ka san ba zan ce ka bani ba. Rashin lafiyar nan da na yi kwana biyu ne ya sa bana iya kitso da lalle,shi yasa bani da ko sisi. Kuma Baba ka ga su Yah Hauwa duk sun yi lallen suna da sabon kitso,Yah Rabi ma ta yi sabon lalle da kitso ni kaɗai ce ban yi komai ba." Cike da hargagi da hargowa Makaɗi ya zaro ɗari biyar ya miƙa wa Nasibah ya ce. "Ƙalatacciya ga su nan a je a kashe. Kar kuma ki kuskura ki faɗa min ba za su ishe ki ba,dan ba wasu zan ƙara miki ba." Jujjuya kuɗin Nasibah ta yi a hannunta ta buɗe baki za ta yi magana,kamar Makaɗi zai dake ta haka ya yunƙura yana sababi,da gudu Nasibah ta bar gidan tana ɓata rai domin ba haka ta so ba. A wannan ranar gaba ɗaya ahalin Makaɗi suka ɗunguma suka tafi suna,domin kuwa da kansa ya kulle gidan ya tafi da makulli. Cikin ransa kuwa sosai yake jin daɗin tafiyar su gidan sunan saboda ɗauke masa nauyin ciyarwar wannan ranar. Da misalin karfe biyu da rabi Nasibah ta isa gidan Yah Hanifah,a nan ta tarar da ƴan'uwanta gaba ɗaya suna zaune a ɗaki ɗaya an kawo musu abinci mai rai da lafiya suna ta ci suna hira hankalinsu kwance. Gaishe su ta yi sannan ta sauya kayan jikinta ta fita wajen Yah Hanifah suka gaisa. Da yamma aka kirawo me hoto ya ɗauki hotunan tarihi. Da za su tafi sai dangin mijin Hanifah dake kan abinci da naman suna suka cika musu ledoji da kayan suna har da naman suna,ɗaya daga cikin ƙannen Baban Aslam ɗin ce ta karɓa ta kai musu har ɗaki. Ta na zuwa ɗakin da su Yah Hauwa suke sai ta tsaya tana kallon su Yah Hauwa da su Mama a yatsine ta ce. "To tinda ku ba a cin naku saboda tsiya da ta yi muku yawa gashi nan ku tafi da guziri. Allah Ya bada ladan zumunci." Shiru kowa ya yi saboda mutuwar jiki da kunya da ta kama su. Nasibah kuwa nan take ta hasala ranta ya ɓaci. Cike da tsananin ɓacin rai ta isa gaban matashiyar da za ta girme ta da kaɗan ta ce. "Uwarki da ubanki ne matsiyata amma ba mu ba. Shi mai kuɗi dama yana faɗa ne?" Ƙanƙance ido yarinyar ta yi ta ce wa Nasibah. "Ke ni kika zagar wa iyaye?" "Ni turame kika gani a bayana da kike zaginsu ba iyaye ba?" "To wa ya sani ko tura..." Kafin ta kai ayar maganarta tuni Nasibah ta gaura wa fuskarta mari. Nan take dambe ya kacame a tsakaninsu. Da ƙyar su Yah Hauwa da sauran dangin mijin Yah Hanifah dake waje suka iya raba faɗan. Sosai yarinyar ta sha baƙar wahala a hannun Nasibah,banda hawaye babu abinda take yi ta kasa cewa komai. Ganin haka sai kowa ya yarda da abinda Nasibah ta faɗa,dangin mijin Hanifah sai suka ba wa su Mama haƙuri suka tattara kayan flour da lemon roba tare da naman sunan da ya zube a ƙasa suka sauya musu leda suka basu. A nan ne Nasibah ta yi tsalle ta dire ta ce ba za su karɓi kayan ba tunda aka kira su da matsiyata. Sai da Yah Lawizah da ke da zafin rai ta daka mata tsawa sannan ta shiga hankalinta ta fita daga gidan cikin fushi ta kama hanyar tafiya gida ita ɗaya a ƙafa. Har bakin ƙofar gate ɗin gidan Hanifah ta rako su Mama tana sake basu haƙuri. Basu jima suna tafiya ba suka samu adaidaita sahu,Yah Hauwa ta tsayar da shi ta biya kuɗi ya ƙarasa da su gida. Ko da suka isa gida sai suka tarar da gidan a buɗe,su na shiga Malam Sanda ya washe baki yana yi musu sannu da zuwa. A tsakar gidan suka baje suna ba wa Malam Sanda labarin yanda sunan ya kaya,amma basu bashi labarin faɗan da Nasibah ta yi da ƙanwar mijin Hanifah ba. Kilishi ce ta raba kayan da suka dawo da shi Faihah ta miƙa wa Makaɗi nasa ya hau ci yana faɗin. "Shine da ake so a tatattaro ta dawo gida mu yi raba daidan kuɗin lalurar iyalinsa ko? To da ban matsa ta koma ba kun je ku ci ku sha har ku yo guziri?" Shiru suka yi masa ya ci gaba da surutansa yana jefa naman suna a bakinsa. Sai da ya kusan cinye wa sannan ya ce. "To wai ina kuka baro min Nasibah?" Kafin su bashi amsa Najlah ta ce. "Da ƙafa ta taho bayan sun gama dambe da Lailah ƙanwar Baban Aslam." Cikin sauri Malam Sanda ya ɗaga kai ya ƙure su Yah Hauwa da ido,ransa a matuƙar ɓace ya ce. "Ku kuma kuna uban me har dangin mijin Hanifah suka yi wa ƴata taron dangi?" "Baba ba fa taron dangi aka yi mata ba,ita yarinyar ce ta zo ta mana rashin kunya shine Nasibah ta kama ta da kokowa suka yi dambe." Da hanzari Makaɗi ya tari numfashin Lawizah ya ce. "Ku kuma taron tsintsiya babu shara sai kuka zura ido har aka daki ƴar'uwarku baku ɗauki mataki akai ba ko?" "Haba Malam ta ya za a yi mu haɗu dika mu yi faɗa a gidan surukai? Itama Nasibar dan bata jin magana ne..." "Dakata min Maryama kada ki ƙara ɓata min rai don Allah." Shigowar Nasibah gidan fururu ne ya katse musu ka-ce-na-ce ɗin da suke yi. Nasibah na jin yanda Malam Sanda ke faɗan barota ita kaɗai da aka yi tun a soro,shi yasa ta shiga gidan tana ɗingishi ta na hawaye. Nan take ran Malam Sanda ya ƙara ɓaci. Fuska a cure ya ce. "To ku tabbata da safe kowaccenku ta tattara nata ya nata ta koma ɗakin mijinta." Lawizah na jin haka ta miƙe tsaye tana faɗin. "Ni dama ko baka ce ba Baba gobe da sassafe zan koma gidana." "Lawizah ni kike mayar wa da magana ko?" Tura baki ta yi gaba ta shige ɗaki ta saki labule tana ƙunƙuni. A hankali tsakar gidan ta watse aka bar Nasibah da Malam Sanda yana ta faman rarrashinta. Haka rayuwar gidan Malam Sanda Uba Makaɗi ta ci gaba da tafiya har aka kai lokacin da Nasibah ta kammala SS 1 ta shiga SS 2. A wannan gaɓar ne kyau da cikar halittar Nasibah suka ƙara bayyana. Hakan sai ya ƙara gigita Samir ya ƙara tabbatar wa da kansa duk duniya bashi da matar aure sai Nasibah. A ɓangaren Nasibah kuwa har a wannan lokacin bata cire rai za su yi aure ita da Malam Luƙman ɗinta ba,sai dai rashin wata mu'amala a tsakaninsu na ɗaga mata hankali sosai tana jin kamar haƙonta ba zai cimma ruwa ba. Lokacin da suka shiga second term aka saka ranar auren Nadiyah. Sosai su Nasibah suka dinga murna suna tsara yanda za su cashe su raƙashe a bikin Nadiyah. Bayan sati biyu da sanya ranar auren Nadiyah da yamma Nasibah na gida tana kitso Nawwarah ta je gidansu cike da tashin hankali. Da ganin haka sai Nasibah ta miƙe ta ja hannun Nawwarah suka shiga cikin ɗakinsu na ƴammata ta ce. "Ke me ya faru na gan ki haka?" Yatsa Nawwarah ta kai cikin bakinta tana cizgar farcen hannunta ta ce. "Wai kin san kuwa wa Nadiyah za ta aura Nasibah?" Murmushi Nasibah ta yi ta ce. "Ba ta ce mana ɗan abokin Babanta za a aura mata ba?" Hannun Nasibah Nawwarah ta kama ta zaunar da ita a bakin gado sannan ta zaro wayarta ta kunna,nan take hoton Nadiyah da Malam Luƙman ya bayyana a saman screen ɗin wayar Nawwarah. Wani irin bamagujen ashar Nasibah ta saki jikinta na rawa ta karɓi wayar Nawwarah tana kallon Malam Luƙman ɗinta yana yi wa Nadiyah murmushi kamar dama can sun jima suna soyayya tare....... *Ku yi haƙuri da ji na shiru da kuke yi please.* [10/10, 9:46 PM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 17. Ganin yanda Nasibah ta fito daga ɗaki a gigice kamar wata mahaukaciya sabon kamu,sai yaran da take yi wa kitso suka takure waje guda suna zare ido. Kilishi dake bakin makwarara tana wanke maburgi da muciyar da ta gama amfani da su sai ta saki soson hannunta ta kalli Nawwarah ta ce. "Ke me yake faruwa na ganta a haka?" Cike da matsananciyar damuwa Nawwarah ta ɗora hannuwanta a ka ta kasa furta komai sai nuna wa Kilishi hanyar waje da Nansy ta ɗauka take yi. Tsallake kwanukan dake wajen Kilishi ta yi ta nufi ɗakinta da gudu ta zaro mayafinta dake a saman ƙyauren ɗakin ta bi bayan Nawwarah da ta fita da gudu tana kiran Nasibah. Nasibah kuwa tinda ta yi mummunan gamo da masoyinta na yi wa ƙawarta tsadadden murmushin da ita kaɗai yake yi wa irinsa ta dena fahimtar komai. Babban fata da burin ta bai wuce ta ganta a gaban Nadiya ba a wannan lokacin. Duk inda ta wuce mutane sai sun tofa albarkacin bakinsu a kanta,musamman ma da suka ganta babu mayafi ko hijabi, ballantana ƙafarta ta samu arzikin takalmi. Tun daga nesa Nasibah ta hango Malam Luƙman a jingine a ƙofar gidan su Nadiya,nan take wani irin abu mai matuƙar nauyi da zafi ya soki zuciyarta, ba tare da tunanin komai ba ta rage saurin da take yi ta ƙarasa har jikin gidan su Nadiya. Muryar Malam Luƙman ɗinta ce ta sake tarwatsa duk wani sauran buri da ƙwarin guiwar da take da shi akansa. Cikin wani irin salo Malam Luƙman ya ci gaba da cewa. "....dan haka na faɗa miki ki saki jikinki a yi wannan lamarin a gama cikin sirri. Ni na tabbata idan muka roƙi Nawwarah kada ta faɗa mata komai har sai an gama biki to ba za ta sanar da ita ba,ni kuma ta ɓangare na dama tuni na yanke duk wata alaƙa da ita,kuma ko ɗaurin aure ne ma zan roƙi Baba na ce ayi idan yaso da kun yi candy sai a yi walima a tare ba shikenan ba?." Muryar Nadiya na rawa ta ce. "A gaskiya ni dai ina jin tsoro,ka fa san halin Nasibah sarai da jidali da tashin hankali. Na rantse har yanzu zuciyata bugawa take yi dan na zaci Nawwarah ta gammu ɗazu. Kai ni fa gani nake yi kamar wani zai gammu tare ya je ya sanar da ita. Ni dai don Allah ka dena zuwa da rana,ka dinga bari sai dare ya yi sosai,ko kuma mu dinga yin waya kawai." Tafi Nansy ta hau yi tare da ƙarasa wa gaban Nadiya dake maƙale a cikin soron gidansu. Nadiya na yin ido huɗu da Nasibah sai ta faɗa cikin soron gaba ɗaya ta manne a bango tana kuka mara sauti. Malam Luƙman kuwa suna haɗa ido da Nansy ya sauke kansa ƙasa yana kallon ƙafar Nasibah da ta yi fururu kamar wadda ta yi tafiya a cikin sahara. Majina Nasibah ta sha ta ce. "Ki kwantar da hankalinki Nadiya ki auri Malam Luƙman ba tare da fargabar komai ba;domin ni Nasibah idan har na haifu cikin Maryama da Sanda Uba Makaɗi na barka kenan bari na har abada Luƙman. Na yi zaton kana so na, na yi zaton ni ce mahaɗin rayuwarka kamar yanda kake faɗa min a kullum,na yi zaton ni ce bugun zuciyarka Luƙman,ashe dama ƙarya kake yi min ashe dama kai mayaudari ne? Ashe dama...." Wani irin kuka ne ya ƙwace mata sosai har sai da ta duƙar da kanta ta rufe bakinta da hannunta na dama. Hannu Malam Luƙman ya ɗaga zai riƙe wa Nasibah hannu,cikin sauri ta ja da baya tana watsa masa wani irin kallo mai wuyar fassara, ƙwalla ta gani a kwance a cikin idanuwansa. Dariya ta yi mai sauti hawaye na zuba daga idanuwanta ta ce. "Ai murna za ka yi tinda ni Nasibah na san abinda kake lulluɓe wa. Ina so ka sani na so ka Luƙman,ina son ka har yanzu,amma ni Nasibah zuciyata bata da gwani,a yau idan na ga dama zan iya maye gurbin ka da duk wanda na so,kada ka yi tunanin soyayyar ka numfashi na ce da idan babu ita ba zan rayu ba. A yau na tabbatar da karin maganar Bahaushe da ya ce Namiji ƙanin ajali ne. To ni dai Nasibah na fi ƙarfin namiji ya yi ajalina sai dai ni na yi ajalinsa. Ina son ka sani ba a banza ake kirana da Nansy Ƙaya ba,na yi maka alƙawarin sai soyayyata ta maƙale maka a zuciyarka kamar yanda ƙaya ke maƙalewa a maƙoshi." Kilishi na ƙarasowa wajen sai ta yi turus tana kallon ikon Allah. Nawwarah kuwa dama tinda ta iso ƙofar gidansu ta je ta tsaya tana hango yanda Nansy ke magana ta na kuka,ga Malam Luƙman tsaye ya shiga cikin matsananciyar damuwa. Jikinta har rawa yake yi zuciyarta na tabbatar mata da rashin kyautawa akan abinda ta aikata na ɗaukar hoton Luƙman da Nadiyah a ɓoye ta nuna wa Nasibah. A ɓangaren Nasibah kuwa juyawa ta yi za ta tafi ta ji kalaman Malam Luƙman a cikin dodon kunnuwanta. "Kada ki ga laifina Nasibah ke kin sani babu macen da na taɓa so a kaf ƴan matan da suka nuna min so sai ke kaɗai. Ke ce macen da ni na gani da idanuwana na kamu da soyayyarta a kallon farko. Nasibah na so ki tun baki gama sanin menene kalmar so ba. Ina so ki sani duk son da nake yi miki idan aka taɓa martabar iyayena dole ne na haƙura dake. Mahaifinki ya faɗa min kalaman da ko ni shege ne dole zan ji zafi ballantana ina da uwa da uba a raye." Murmushi Nasibah ta sakar wa Luƙman da Nadiyah wadda har a wannan lokacin take manne da bango tana kuka. Cikin dasasshiyar murya ta ce. "Ina yi muku fatan alkhairi." Tana gama magana ta yi gaba tana tafiya cikin rangaji kamar ƴar maye. Da sauri Kilishi ta bi bayanta ta rungume ta tana jin matsanancin tausayin Nasibah na ratsa zuciyarta. A haka suka isa gida Nasibah na sauke ajiyar zuciya lokaci zuwa lokaci. Kai tsaye ɗakinsu ta wuce ta haye gado ta kwanta ta rushe da wani irin kuka mai firgitarwa. Mama da ta jima a tsaye ita da Rabi tun bayan fitar Nasibah da Kilishi a hargitse sai suka ɗunguma zuwa cikin ɗakin suka hau tambayar Nasibah abinda ya same ta. Kasa furta musu komai ta yi,dan babu wata kalma da za ta iya fasalta abinda take ji a cikin zuciyarta. Faihah Kilishi ta kira ta aika maƙota ta siyo mata ruwan sanyi guda biyu. Tana kawo wa ta karɓa ta shiga ɗakin ta zauna a kusa da Nasibah ta ɗaga ta zaune ta ɓula ledar ruwan ta kafa mata a baki. Cikin sauri Nasibah ta hau kwankwaɗar ruwan har sai da ledar ta ƙare. Jikinta na rawa ta karɓi ɗayan ta miƙe tsaye ta fasa ta hau kwarawa jikinta. A ƙasan wajen ta zube tana kuka ta ce. "Ummah zuciyata zafi take yi min. Ummah Malam Luƙman ya ci amanar soyayyarsa da na jima ina riritawa a zuciyata. Da na san irin cin amanar da zai yi min kenan da na bi maganar Baba na cire shi a raina tun da wuri." "Ki yi shiru ki dena kukan haka ya isa,bari Baban naki ya dawo wannan abubuwan da yake yi sun isa haka." Mama da ta kula babu mai bata amsa sai ta yi ajiyar zuciya ta ce. "Allah Ya kyauta Ya kawo mafita." Daga nan ta sa kai ta bar ɗakin. Sai dai duk da cewa ta bar ɗakin amma gaba ɗaya hankalinta yana kan ƴar tata tana hango irin matsananciyar damuwar da take ɗauke da ita. Da ƙyar Kilishi ta lallaɓa Nasibah ta fita ta ɗaura alwalar sallar magariba. Ko da ta dawo ɗaki sai ta sauya kayan jikinta ta saka hijabi ta tayar da sallah. Tana idarwa Makaɗi na dawowa gidan. Fuskarsa a sake ya shiga gidan yana yi wa su Najlah wasa. Idanuwansa ya dinga jefa wa a tsakar gidan amma bai hango ƴar rigimar tasa ba. Murmushi ya yi ya ce. "Ke Faihah ina rigimatun gidan take ne yau na ji ko ina tsit kamar an yi rasuwa?" Cikin fushi Kilishi ta fito daga ɗakinta sanye da hijabi ta ce. "Ba dole ka ji ko ina tsit ba tinda kana neman ka jefa yarinya ƙarama a cikin mawuyacin hali? Wai kai don Allah Malam in tambaye ka mana. Shin me kake da shi a lokacin da ka je gidan iyayenmu neman aurenmu gaba ɗaya? Ina ce a wancan lokacin banda ruƙon ganga babu abinda kake yi wa mahaifinka? Da kuɗin kiɗa aka aura maka uwar su Hauwa ni kuwa...." Kafin Kilishi ta ƙarasa maganarta Malam Sanda ya katse ta cikin wani irin matsanancin fushin da bata taɓa ganinsa a cikinsa ba ya ce. "Ke dakata min Malama! Me yake faruwa a gidan da har za ki zauna kina neman zagar min asali da yi min gorin arziƙi?" "Yo meye ma bai faru ba Malam? Garin leƙen jar miya a maƙota kana neman ka babbake taka tallen. Ina so ka sani a auren yanzu ƙwarya ta bi ƙwarya ake yi ba wai auren je ki dangwalo wa dangi arziƙi ba,shi kansa yaron nan da kake maitar haɗa Nasibah aure da shi baka da tabbacin iyayensa za su yarda ya auri ƴar mai facin taya jinin makaɗa." Jinjina kai Malam Sanda ya yi ya ce. "Afff tohh! Yanzu na gane inda maganganunki suka dosa. To ina son ki buɗe kunnuwanki ki ji ni da kyau Kilishi. Ko na mutu na bar wasiyya wa ƴan'uwana da abokaina Nasibah bata da wani mijin da ya wuce Alhaji Samir,dan haka ki adana duk wasu kalamanki na rashin arziƙi da kika tanada domina." "Au haka ma za ka ce Malam?" "Haka kuma za a yi ba." "Malam wannan yaron ne fa Lukman zai auri aminiyar Nasibah." "Allah Ya basu zaman lafiya. Itama idan tana so wani satin sai a ɗaura nata auren da Alhaji Samir." Shiru gidan ya ɗauka,banda kukan Nasibah da ke tashi baka jin komai. Mama na ɗaki ta zabga tagumi tana jin kamar ta je ta tunkari Makaɗi a yi wadda za a yi. Muryar Kilishi da ke sake yi wa Makaɗi magana ce ta sanya ta zama saboda kar ta nuna rashin kara. Haka Kilishi da Makaɗi suka yi ta sa-in-sa a tsakaninsu har ya fusata ya fita ya bar gidan. Tinda ya sa kai ya bar gidan bai dawo ba yana can wajen mai shayin dake saman layi yana hira da abokansa. Fitarsa ke da wuya su Mama da Kilishi har da rabi da Usman sai suka zauna a tsakar gida suka hau tattaunawa akan lamarin Nasibah da Malam Luƙman. Mama ta ce bata ga laifin Malam Luƙman ba domin Malam Sanda da kansa ya kore sa ya yi masa iyaka da ƴarsa. Ita kuma Kilishi ta ce dama can baya son Nasibah tinda ya yarda da auren aminiyarta ba tare da ya ji shakkar yin hakan ba. Rabi kuwa sai ta ce to da dikkan alamu dama can yana son Nadiyah faɗa ne bai yi ba,jira yake yi sai ya auri Nasibah daga baya ya yo mata kishiya da Nadiyah. Usman kuwa kukan da Nasibah ke yi ne ya ɗaga masa hankali har ya kasa cewa kanzil a lamarin,daga sauke ajiyar zuciya sai dogon tsaki ya dinga ja har taron nasu ya tashi kowa ya nufi makwancinsa. Malam Sanda bai dawo gida ba sai da misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi na dare,fuskar nan a murtuke ya shiga gidan da ita gudun kada ma Kilishi ta ga ƙofar kawo masa wata maganar mara tushe da amfani. Jin gidan shiru alamun kowa ya yi bacci ne ya sanya shi ajiye ledar da ke riƙe a hannunsa a saman randar tsakar gida ya ɗauki buta ya zaga bayan gida. Ya na fitowa ya ɗauki kofi da plate a kwandon wanke-wanke ya juye shayi da soyayyar indomie da kwai sannan ya nufi ɗakin su Nasibah da yake a buɗe. Kai tsaye gaban gado ya zauna a inda Nasibah ke kwanciya ya ce. "Tinda na shigo na ji alamun idanuwanki biyu ƴar Baba, taso mu je ki ci abinci ki kora da shayi haɗin kauri dan na san baki ci abinci ba kika kwanta." Hawaye Nasibah ta share ta juya wa Makaɗi baya ba tare da ta ce masa komai ba. Makaɗi kuwa bai sare ba sai ya ci gaba da lallashin Nasibah har sai da ta sakko daga gadon ta na kuka suka fito tsakar gida suka zauna a shimfiɗarsa. Da ƙyar take shan shayin dan kuwa ko da wasa bata gwada kai Indomie bakinta ba. Sai da Makaɗi ya gama cinye indomien tass sannan ya murje hannuwansa ya yi gyatsa ya ce. “Nasiban Baba ina so ki buɗe kunnuwanki ki saurari dalilin da ya sa na zaɓar miki miji kamar Alhaji Samir. Na farko dai ni na san ba kya ƙaunar kishiya a rayuwarki duba da yanda kike rayuwa da ƴan'uwanki a cikin gidan nan. To shi kuwa wa talakan Malam Bahaushe babu wanda ya kai sa yawan aure. Amma idan kika auri mai kuɗi,kyau da cikakkiyar nasaba kamar Alhaji Samir za ki tsira da talauci da kishiya,ga shi uwa uba zaki dinga taimaka wa iyayenki da duk abinda kika samu a ƙarƙashin mijinki. Idan kuma ki na ganin zaɓina bai yi miki ba Nasibah ni Malam Sanda a yau na yi miki alƙawari zan aura miki duk kalar mijin da kike so." Shiru Nasibah ta yi tana kallon kofin dake riƙe a hannunta kamar tana son hango maƙerin kofin. A hankali ta yi ajiyar zuciya ta ɗaga kai ta kalli Malam Sanda ta ce.......... [10/11, 9:27 PM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 18. "Ni Baba babu wanda nake da burin aure a yanzu,karatu nake so na yi mai zurfi ko kuma idan na gama secondary school ka buɗe min saloon,ka ga shikenan sai na ci gaba da sana'ar kitso da ƙunshi....." "Nasibah kin ƙunshe min bakinki kin adana shi ko sai ƙunsa miki duka a cikinsa da daren nan? Ke wai wace iriyar yarinya ce ana gabas kina yamma? Ke! Tashi ki je ki kwanta tun kafin ki jawo na kamu da ciwon hawan jini,Allah Ya tashe mu lafiya." Tura baki Nasibah ta yi ta hau ƙunƙuni kafin ta miƙe ta shige ɗakinsu. Ƙwafa makaɗi ya yi ya ce. "Wannan yarinya Nasibah Allah Ka shirya min ita. Ki sa a ranki auren Samir kamar kin yi kin gama,idan ma abinda ya fi saloon ne idan kun yi auren ya buɗe miki a can." Da wannan maganganun Malam Sanda ya gyara kwanciyarsa a tsakar gidan ya ja babbar rigarsa da ta gaji da duniya ya rufa. A can cikin ɗakin Kilishi kuwa tana zaune tana gyangyaɗi saboda ta yi alƙawarin komai dare idan Malam Sanda ya shigo sai ta yi masa magana akan lamarin Nasibah. Cikin dare ta farka ta ga ɗakin daga ita sai halinta Malam Sanda bai shigo ba. Salati ta yi tare da zabga hamma ta sauka daga saman kujera ta fito tsakar gida. Kwance ta ganshi har ya fara sakin munshari hankalinsa kwance. Haɓa Kilishi ta kama ta ce. "Au Allah! Ni ina can ina jiransa ashe shi yana nan ya hangame baki yana bacci a tsakar gida sauro na walima da jininsa. To ai shikenan Allah Ya tashe mu lafiya." Ɗaki ta koma ta saka sakata ta yi kwanciyarta tana tunanin rayuwar gidan mijin nasu mai murɗaɗɗen hali. Washegari da safe Malam Sanda da ƙyar ya je masallaci sallar asuba ya dawo saboda zazzaɓi mai zafi da ya tashi da shi,kai tsaye ɗakin Kilishin da ya yi wa yaji ya nufa ya haye gadonta mai rumfa ya ja bargo ya rufe har kansa,shiga goma fita goma Kilishi sai ta kalle shi ta ƙunshe dariya,domin ko sannu ta kasa yi masa gudun kada ta yi dariya ya ce ta raina shi. Daga ƙarshe duk yanda ta so ta ja bakinta ta yi shiru kasa wa ta yi sai da ta yi dariya ta ce. "To ai shi Allah ba azzalumin Sarki bane. Mu je dai zuwa wai mahaukaci ya hau kura." Muryar Malam Sanda a shaƙe yana maƙyarƙyatar sanyi ya kalli Kilishi ya ce. "Allah Ya sa dai ba da ni kike ba." "To Malam ai duk wanda ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake yi ko? Sannan wanda ya saurara idan ya tsargu da shi ake yi ai babu mai iya sauya masa ra'ayi. Ni dai Malam ina mai baka shawara ka dinga kyautata wa iyalanka;dan ko babu komai yau idan aka ce babu kai za su yi kuka su tuna alkhairinka a gare su,amma kai ke nan daga ka kori wannan da zuri'arta idan ta zo sai ka fito wa da wannan kwaɗayinka a fili. Yanzu ga ƴar ƙaramar yarinya nan Nasibah ka sako ta a gaba,na kuwa tabbata ba za ka huta ba har sai ka cimma burinka akanta." Ƙwafa Malam Sanda ya yi yana sake takure kansa a cikin bargo. "Malam mai son ka ne kaɗai zai iya faɗa maka gaskiya duk dacinta. Yaran nan jikokinka ne,idan basu zo wajenka sun raɓe ka ba wajen wa za su je? Ko so kake yi idan Allah Ya sa suka girma suka zama wani abu a rayuwa su manta da kai? Shi ɗa na kowa ne baka san mai morarsa ba,kuma..." Wurgi da bargon jikinsa Malam Sanda ya yi jiki na yi masa rawa ya hau dukan ƙirjinsa ya ce. "Kilishi don Allah gani ki sa kaina gabar ki yanka ki feɗe ni ki ba wa yaran nan su gasa nama na su cinye ƙarewar soyayyar da kike musu. Haba! In banda ke ba kya neman albarkar aure haka kawai zaki saka ni a gaba bani da lafiya kina yi min surutan banza da wofi? Inda Maryama ta fiki kenan,ƴar nan dai tata ce ita ta ɗauki cikinta wata tara da kwanaki sannan ta haifo abarta,na tabbata ta fiki jin zafin duk wani abu da zai same ta,amma kina nan kin zaƙe kina son kai kanki wuta. To ina so ki buɗe kunnuwanki ki jini da kyau,in dai ni Sanda Uba Makaɗi ni na haifi Nasibah,to bata da mijin da ya wuce Samir." Kalamansa sun yi matuƙar ƙona ran Kilishi,amma sai ta daure ta ce. "Ko ka ƙi ko ka so Nasibah nima ƴata ce dan haka dole ne na yi magana akan lamarin da ya shafi rayuwarta." Waje Malam Sanda ya fita cikin tsananin fushi da ɓacin rai zai shiga ɗakin Mama ya ci karo da Nasibah na zaune a saman bokitin ƙarfe ta na ɗaura takalmin makarantarta. Cike da mamaki ya tsaya yana kallonta kafin ya ce. "Nasibah za ki iya zuwa makarantar kuwa yau?" Murmushin yaƙe ta sakar masa domin ta ji duk abinda suka tattauna shi da Kilishi. Cikin murya mai cike da rauni ta ce. "Zani mana Baba,takalmi na nake jiran na ɗaura na je na same ka ka bani kuɗin tara." Haɗe fuska Makaɗi ya yi ya ce. "Wai ke jiya baki yi kitso bane da kike jiran na baki kuɗin tara? Me yasa ke baki da tausayi ne Nasibah? Kina fa kallo ko lafiyar arziƙi ban tashi da ita ba,amma babu sannu ballantana Allah sawaƙe zaki ce na baki kuɗin tara." Ajiyar zuciya Nasibah ta sauke kawai ta saɓa jakarta za ta bar gidan. Da ganin haka sai Makaɗi ya ce. "Ƙalatacciya zo ki karɓa,ai ke idan baki raba ni da ƴan canjina ba ba kya jin daɗi." Hannu ta miƙa masa tana danne murmushinta,shi kuwa sai ya dangwara mata kuɗin ya faɗa ɗakin Mama ya haye gadonta ya kwanta. Cike da mamaki Mama ta ce. "Ah ah! Malam lafiya ka shigo min ɗaki ka kwanta a daidai wannan lokacin;ko dai ka yi makuwa ne, bafa anan kake ba." Cikin rawar murya ya ce. "Na sani Maryama bani da lafiya ne,ita kuma waccan ta fi gane ɗora min damuwa akan lallashina." "Assha Malam sannu, Allah Ya baka lafiya,bari na karɓo maka koko ka sha da zafin sa sai ka sha magani. Amma dai da ɗakin ita Ummahn nasu ka je da ya fi,tinda ita ce ke da girki." Buɗe kansa Makaɗi ya yi ya kalli Mama da ta miƙe tsaye za ta fita ya ce. "Shin ko dai na bar muku gidan ne gaba ɗaya?" Da sauri Mama ta juya ta ce. "Me ya yi zafi shi ba wuta ba Malam? Ka sha zaman ka Allah Ya baka lafiya." Kamar yanda Mama ta ce haka ta shiga kitchen ta ɗebo koko mai zafi a kofi ta kai masa da magani,da ƙyar ya iya shan kokon ya kora maganin sannan ya koma ya kwanta. A wannan ranar Makaɗi ko ƙofar gida bai sake fita ba,daga shiga banɗaki sai sallah su ne suka dinga tada shi. A ɓangaren Nasibah kuwa lokacin da ta je makaranta sai ta ga ƙawayensu na ta kallonta cike da tausayawa. Nan take zuciyarta ta ayyana mata Nawwarah ta basu labarin abinda ya faru. Cikin ranta bata ji daɗi ba,domin ita yarinya ce da bata son mutane su dinga yi mata kallon tausayi ko su ga rauninta. Wannan dalilin ne ya sanya ta sake wa kamar babu abinda ya faru,har ta miƙa wa Nadiyah da ke a takure hannu suka gaisa. Haka Malamai suka dinga shiga suna fita a ajinsu har aka tashi break. Nadiyah da ke a tsarge sai ta je wajen Nasibah ta ce. "Don Allah Nasibah ina so mu yi magana da ke ta fahimtar juna." Murmushi Nasibah ta yi ta ce. "Tooh! Dama ni da ke akwai wata rashin fahimta a tsakaninmu da ban sani ba?" Numfashi mai ƙarfi Nadiyah ta sauke ta ce. "Na san kin san akan me nake magana Nasibah. Don Allah ki fahimce ni,na rantse miki da wanda ke busan numfashi ban san Malam Luƙman ne wanda iyayena za su aura min ba,sai da Ummah ta ce na shirya mijin da zan aura zai zo mu gaisa sannan na san shi ne. Amma idan baki yarda ba..." Kallon da Nasibah ta ƙura wa Nadiyah ne ya sanya ta haɗiye kalamanta na ƙarshe ta ja da baya kaɗan. Ganin tsoro da damuwa tare da tashin hankali a idanuwan Nadiyah kaɗai ya sanyaya zuciyar Nasibah. Nan take ta kawar da ɓacin ranta ta ce. "Kada ki damu Nadiyah haka ƙaddara ta zana ni da Malam Luƙman za mu yi zazzafar soyayya,amma kuma ba za mu mallaki junanmu ba ke ce za ki zamo matarsa, dan haka bana so na sake jin damuwa a tattare da ke. Ina so ki saki jikinki sosai ki sha soyayya mai tsafta da mijin da za ki aura. Domin shi namiji duk yanda yake son mace da ya samu wadda ta fita yake mantawa da ita. Dan haka ina son ki fini nuna masa soyayya da tarairaya ta yanda zai so ki sama da ni. Kada ki manta akwai sauran shekaru biyu a gabanki kafin nan kafin aurenku." Kafin Nasibah ta gama magana Nadiyah ta fashe da kuka ta rungume ta. Godiya ta dinga yi mata tana jin ƙaunar Nasibah har cikin ranta. A wannan halin Nawwarah ta zo ta same su,nan take fuskarta ta bayyana rashin jin daɗin ganinsu tare suna fara'a da juna. Ko ta kanta Nasibah bata bi ba ta wuce ta gabanta ta je ta siyo musu wainar flour suka zauna da Nadiyah za su ci,gefe Nawwarah ta koma tana danna wayarta tana cin magani. Basu kula ta ba suka fara cin wainar,dan kanta ta saki ranta ta saka hannu suka ci gaba da cin abincin a tare suna hira jefi-jefi. Suna gama wa da wainar Nadiyah ta yi amfani da kuɗinta ta siyo musu awara. Haka suka yi ta ciye-ciye har aka koma aji. Lokacin da aka tashi a tare suka fito su uku za su tafi gida kamar yanda suka saba. Su na zuwa bakin gate Nasibah ta ja ta tsaya tana kallon mutumin dake jingine a jikin mota yana danna waya. Sunanta Nadiyah ta kira ta ce. "Nansy mu je mana ko kin san shi ne?" Da sauri Nasibah ta kawar da kanta za ta wuce ta ji an ce. "Nansyy!"....... [10/12, 8:44 PM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ PAGE 19. Fuskar Nasibah ɗauke da mamaki da fara'a ta nufi wajen Yasmin dake tahowa da gudu suka haɗu a hanya suka rungume junansu. Sai da suka gama murnar ganin juna sannan su Nawwarah da Nadiya suka miƙa wa Yasmin hannu suka gaisa suna murmushi. Nawwarah da bata gani tai shiru sai ta ce. "Lallai Yasmin Abuja ta karɓe ki,kin ga yanda ki ka ƙara cika da kyau kuwa? Shi kansa Yayanku na ga ya ƙara haske da kyau,amma fa kamar ya rame ko Nadiyah?" Kafaɗu Nadiyah ta ɗaga mata kawai alamar itama bata sani ba. Fari Yasmin ta yi ta ce. "Thanks. Ko Yah Yusrah ma haka ta ce wai na fita girma yanzu." Da jin sunan Yusrah a bakin Yasmin sai gaban Nasibah ya yanke ya faɗi. Nan take walwalarta ta ɗauke,cikin sanyin jiki ta ce wa Yasmin. "Mu bari mu ƙarasa gida,ki je kada Yaya Mai Kyau ya gaji da jiranki." Murmushi Yasmin ta yi ta juya ta kalli Giɗaɗo da ke ta satar kallonsu lokaci zuwa lokaci. Cike da fara'a a fuskarta ta ce. "Ai ke muka zo ɗauka Nasibah,yanzu haka da kika gammu mun je can gida ne Baba ya ce min baku taso ba,shine na roƙe shi na ce ya kawo ni har nan mu ɗauke ki mu tafi da ke gida. Kin san yau Goggoji ke cika shekara 70 a duniya,so mun yi planning mata surprised party,yanzu haka Malam Sadi ya tafi Airport ɗakko ta." Haɓa su Nawwarah suka kama suna kallon yanda Yasmin ke magana cike da yanga da iyayi. Nasibah kuwa sai ta ce. "Ina ta je na ji kin ce an tafi ɗakko ta daga Airport?" "Umarah ta je." "Ayyah." Shine kawai abinda Nasibah ta ce. Nawwarah na shirin yin magana Giɗaɗo ya ce. "Ku zo nan." Da sauri Yasmin ta nufi wajensa ta tsaya a gefensa,Nawwarah da ta mace wajen kallonsa ke mara mata baya,ta na isa gabansa ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi,kamar ba zai amsa ba ya daure ya amsa da ƙyar. Kallon Nadiyah da ke gaishe shi ya yi ya ɗaga mata yatsa. Nasibah kuwa sai ta raɓe a gefe ta ce. "Yah Mai Kyau ina wuni?" Duk yanda Giɗaɗo ya so ya yi musu faɗa akan ƙin gaishe shi da basu yi ba sai ya ji ya kasa,murmushi ya sakar mata ya ce. "Ai na zaci ba za ku gaishe ni ba. Ke kuma ɗan rakiyar taki ya gaji mu tafi ko?" Ya ƙarasa maganarsa yana kallon Nasibah. Ita kuma sai ta juya ta kalli su Nawwarah. Ganin damuwa a saman fuskar Nasibah ne ya sanya Giɗaɗo cewa. "Ku shiga mu rage muku hanya mana." Jiki na rawa Nawwara ta nufi bayan mota saitin direba ta zauna. Idanuwanta banda kallon Giɗaɗo babu abinda suke yi, zuciyarta kuwa ta jima da hango ta a gidan Giɗaɗo matsayin matar aurensa. Gaba Yasmin ta shiga suka saka Nasibah a tsakiya. Babu ɓata lokaci ya ja motar suka bar makarantar. Lokaci zuwa lokaci Giɗaɗo ke ɗaga kai ya kalli Nasibah da take zaune a matuƙar takure saboda jin nauyi da kunyar irin kallon da yake jifan ta da shi. Su na zuwa bakin layin su Nawwarah Nadiyah ta ce. "Mun gode Allah Ya saka da alkhairi Yayah." Burki Giɗaɗo ya ci ya tsayar da motar suka sauka Nawwarah na kashe murya da fari ta ce. "To Nansy sai mun haɗu gobe a school ko?" "Allah Ya kaimu." Nansy ta ce tana ɗaga musu hannu. Mota Giɗaɗo ya ja suka nufi gidan Gwani Ibrahim Yunus. Su na isa suka tarar da gidan da mutane jefi-jefi suna shiga da motocinsu cikin gidan,wasu kuma sun yi parking a wajen gidan suna takawa da ƙafa suna shiga ciki. Mai gadi na ganin motar Giɗaɗo na dosowa gidan sai ya sake wangale gate ɗin ya tsaya yana miƙa masa gaisuwa. Cike da mutuntawa suka gaisa ya ja motar suka shige ciki. Ita dai Nansy zaune take tana kallon manyan mata masu ji da kyau da kuɗi su da ƴaƴansu mata da maza na ta shiga gidan,wasu na yaren hausa wasu na fulatanci. Mota na gama tsayawa Yasmin ta fita ta buɗe wa Nasibah ɓangaren da take zaune sannan ta kama hannunta,a tare suka yi wa Giɗaɗo godiya suka shige sashen Goggoji. Ko da suka shiga sai suka ga ƴan'uwansu na Gombe da mazauna Kano a parlour suna ta fulatanci suna dariya. Har ƙasa Yasmin da Nasibah suka durƙusa suka gaishe su sannan suka shiga ɗakin Yasmin dake a sashen Goggoji. Rufe ƙofa Yasmin ta yi ta ce. "To yi sauri ki shiga banɗaki ki yi wanka,bari na shiga ciki na kawo miki abinci. Yauwa kar na manta idan kin yi wanka kawai ki ɗaura towel zan ɗakko kayan da za mu saka a can sashen Hajiya." "Kin san Allah ba dan na gan ki da Yah Mai Kyau ba da sai in ce ƙarya ki ka zuba min kika kawo ni gidan nan. Haka kawai nake jin gabana na faɗuwa Yasmin." Dariya sosai Yasmin ta yi sannan ta ce. "Amma dai ba faɗuwar gaba saboda tsoron za a dake ki a gida kike ji ba ko? Dan ke na riga da na san kin ci dubu sai ceto." Dariya itama Nasibah ta yi ta fara cire kayanta tana ninkewa tare da sakawa a jakarta ta ce. "Ke yanzu baki san har gobe idan na shuka wani rashin hankalin su Baba zage wa suke su yi min matsiyacin dukan ganga ba ko?" Hannun ƙofa Yasmin ta kama ta ce. "Gaskiya ban yarda ba,dan kuwa ni na san yanda Baba ke ji da ke ko wani ya gani zai dake ki ba zai bari ba." Ta na gama magana ta rufe ƙofar ta yi gaba,a daidai wannan lokacin Nasibah ta shiga toilet bakinta ɗauke da addu'ar shiga banɗaki tana tuna yanda Baba ke jibgarta yana nuna mata ba sani ba sabo idan ta tsallake layin da ya shata mata. Tsayawa ta yi tana kallon ƙarafan dake cikin banɗaki,da taɓa nan murɗa can ta haɗa ruwan wanka ta yi sannan ta yi alwalar sallar azahar ta ɗaura towel ta fito. Zama ta yi a bakin gado tana nazarin rayuwar masu kuɗi,wasu masu kuɗin suna da matsanancin girman kai da nuna wa talaka ƙiyayya a fili,wasu kuma suna da sassauƙan hali da son mutane tare da yawan kyauta. Yasmin na daga cikin yaran masu kuɗin da ke son mutane tare da kyautata musu,domin kuwa ba ita kaɗai take yi wa kyauta ba,duk wanda Allah Ya tsaga da rabonsa Yasmin na yi masa kyautar duk abinda ta kula mutum na da buƙata. Sallamar Yasmin ce ta dawo da ita cikin hayyacinta ta kalle ta riƙe da wasu riguna ƴan kanti masu masifar kyau,dogaye ne har ƙasa da ƙananan hijabs sai sababbin bra da pant da under skirt. A bayanta kuma mai aikinsu Baba Laraba ce biye da Yasmin ta dire musu abinci Nasibah ta gaishe ta ta tafi. Cike da damuwa Yasmin ta ce. "Sakko ki ci abinci bari na duba miki ɗankunne a cikin tsofaffin nawa,har da ɗankunne fa na ba wa su Yah Yusrah saƙo amma ta siyo kaya babu ɗankunne." "Ayyaa babu komai,ai ko haka zan iya saka wa tinda hijabin irin mai rufe kunnen nan ne." "Humm ke dai rabu da Yah Yusrah,ni na rasa meye a tsakaninku da bata son a yi zancen ki,yanzu ma fa kafin mu je gidanku sai da ta yi ta ƙananun maganganu,Yah Giɗaɗo ne ya yi mata kyakkyawan gargaɗi akan wata magana da take ta ɓoyo." Wani irin yawu Nasibah ta haɗiye muƙut ta hau zare ido,ji take yi kamar ta sanar da Yasmin gaskiyar abinda ya haɗa su da Yusrah,amma nauyi da kunyarta ya hana ta magana. A yau ta sake tabbatar da sata halin banza ne,hali ne na marasa kunya da tsaurin ido,hali ne na marasa tsoron Allah suke cin haƙƙin bayinSa. Alƙawari ta yi wa kanta duk rintsi duk wahala har abada ba za ta sake taɓa abun wani ba. Jiki a mace ta yi sallah sannan suka zauna suka ci abinci. Suna gamawa suka shirya Yasmin ta yi wa Nasibah simple make up suka feshe jikinsu da turaruka masu daɗin ƙamshi suka fita babban parlourn Goggoji. A tsakiyar parlourn Nasibah ta ga an girke wani ƙaton cake mai ɗauke da hoton fuskar Goggoji da shekarun da ta cika a duniya,gefe guda kuma ga abinci nan kala-kala da drinks da plates ɗin da mutane za su yi serving kansu. Ƴan mata ne da ba za su wuce sa'annin su Yasmin ba ke tsaye a kusa da cake ɗin suna ta yi masa hotuna da videos. Babu jimawa wajen ya ɗauki murna tare da yaren fulatanci kowa na yaba kwalliyar Goggoji da ta ci wani tsadadden leshi ta zuba gwala-gwalai kamar ba tsohuwa ba. Haƙoranta masu ɗauke da haƙorin makka fari da golden ne suka bayyana. Kafin ta ƙaraso tsakiyar parlour ta isa wajen zaman da aka tanada dominta Giɗaɗo da Yusrah tare da Hajiya Yalwa sun shigo wajen. Hankalin Giɗaɗo gaba ɗaya yana kan wayarsa da yake amsawa har suka isa gaban kujerar da Goggoji ta zauna babu jimawa. A gefenta Giɗaɗo ya zauna yana ci gaba da amsa wayarsa. Nan da nan ƴan'uwa da masu hoto da aka gayyato a wajen suka fara ɗaukan su hotuna. Giɗaɗo na gama wayar ya ajiye a saman table ya matsa kusa da Goggoji ya ɗora hannunsa ɗaya a kafaɗarta aka ci gaba da ɗaukan su a hotuna. Haka taron ya ci gaba da tafiya cike da walwala da nishaɗi. Nasibah na gefe ta kasa sakin jikinta duk kuwa da irin yanda Yasmin ke ta janta cikin danginsu. A hankali Giɗaɗo ya tashi daga kujerar da yake ya nufi inda Nasibah ke tsaye. Ba tare da ta kula ba ya sa wayarsa ya ɗauke ta a hoto ya bi ta gabanta ya bar parlourn. Ya na fita Yusrah ta je wajenta ta tsaya tana binta da wani irin maƙasƙancin kallo ta ce. "Wai ke me yasa ba za ki kama kanki ki zauna a inda Allah Ya ajiye ki ba;baki da aiki sai bibiyar yaran masu kuɗi? To ina so wannan ranar ta zamo ta ƙarshe da za ki sake shiga sabgar ahalinmu. Itama Yasmin ɗin zan same ta sai na ci ubanta akan jawo mana gayyar ɓarayi har cikin gida suna gane mana sirrinmu." Tuni fuskar Nasibah ta jiƙe sharkaf da hawaye. Zuciyarta banda ƙuna babu abinda take yi mata. Gudun kada Yasmin ta gane halin da take ciki sai ta zame ta koma ɗakin Yasmin ɗin ta shige banɗaki ta yi zamanta tana risgar kukan takaici. A wannan rana Nasibah ta tsine wa ɓarari da shi kan shi sunan satar ya fi shurin masaƙi. Haka party ya ci gaba da gudana babu wanda ya san inda Nasibah ta tafi ta ɓoye. A can gidan Malam Sanda kuwa da misalin huɗu daidai Samir ya dawo daga Abuja,ko gida bai je ba ya nufi gidan Malam Sanda domin ganin abincin ruhinsa da ya kasa zama a waje ɗaya saboda tunaninta da ya yi masa yawa. Ya na zuwa ya tarar da Malam Sanda babu lafiya,sai ya rubuta masa magunguna ya ba wa Usman kuɗi ya je ya siyo masa har da yar gasasshir kazarsa da Nutrimilk. Ko da ya tambayi inda Nasibah take sai Malam Sanda ya ce. "Ai wannan yarinyar ƴar gidan marigayi Gwani Ibrahim Yunus ta zo ita da Yayanta neman Nasibar, sai aka yi rashin sa'a bata dawo daga makaranta ba,shine fa yarinyar nan da yake tana ƙaunar Nasibah sosai ta ce za su je makarantar su ɗauke ta,yau Kakarsu ke cika shekaru 70 a duniya za su yi mata walima." Cike da matsananciyar damuwa Samir ya miƙe ya ce. "Haba Baba! Ya za ka ba wa wani ƙato dama ya je har makaranta ya ɗaukar min mata?" Kafin Malam Sanda ya ce wani abu Samir ya miƙe ransa a matuƙar ɓace ya bar gidan. Kai tsaye gidan su Giɗaɗo ya nufa zuciyarsa na hasaso masa irin kyau da kamalar Giɗaɗo. Ya san cewa Giɗaɗo na da aure, amma ba zai taɓa manta irin kallon da ya yi wa Nasibah ba a lokacin da suka je bikinsa shi da Nuh. Tafiyar mintuna 8 ne kacal suka kai Samir gidan. Ganin gate ɗin gidan a buɗe kuma gidan ya cika da motoci ne ya sanya shi yin parking a waje ya fito daga motar yana tunanin yanda zai yi ya ga Nasibah. A daidai wannan lokacin kuma Giɗaɗo na kwance a saman makeken gadonsa ya saka hannunsa ɗaya a ƙasan kansa ya tallabo kan nasa yana kallon hoton Nansy da ya yi wa kyakkyawan ɓoyo a cikin wayarsa. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "NaNSy Ƙaya." Murmushi ya saki mai sauti sannan ya sake cewa. "Ina son rigimarki da shagwaɓarki." Kamar wanda aka janyo haka ya miƙe zaune ya kalli bakin ƙofar shiga ɗakinsa. Rigarsa ya saka ya ɗauki wayarsa ya fito harabar gidan. A jikin gate ɗin gidan ya hango Yasmin na ta lallashin Nansy akan ta zauna za su mayar da ita gida ko da da daddare ne. Ƙi Nasibah ta yi ta na ta share fuskarta,da dikkan alamu kuka take yi. Nan da nan Giɗaɗo ya ji zuciyarsa ta ƙuntata ya nufi wajensu da sassarfa. Ya na zuwa Samir da ke takowa zuwa wajen su Yasmin ya isa wajen fuskarsa a murtuke. Tsayawa suka yi dika su huɗun suna yi wa junansu kallon kallo. Da ƙyar Samir ya danne abinda yake taso masa daga ƙasan zuciyarsa ya ce. "Ke wuce mu tafi gida tinda an gama walimar." Gira Giɗaɗo ya haɗe waje ɗaya sannan ya ce. "Kai kuma ɗin wanene a wajenta da za ka zo ka ce ta bika ku tafi?" Murmushi mai sauti Samir ya saki saboda ya kula da alama bai gane shi ba. Jinjina kai ya yi ya ce masa. "Ni ɗin mijin da zan aure ta ne. Ke! Wuce mu tafi." Nasibah da ta ci kukan gargaɗin da Yusrah ta yi mata sai ta zagaye Yasmin da ke riƙe da hannunta ta wuce zuwa motar Samir. Har Samir ya ja motar suka bar wajen Giɗaɗo bai sake yin ƙwaƙƙwaran motsi ba. Ya jima a haka kafin ya fizgo kalmar. "Mijindazaiaureta?" (Mijin da zai aureta?) Kai Yasmin ta jijjiga masa ta ce. "Allah Yah Giɗaɗo ƙarya yake yi,ko da bikinku ma haka ya zo ya ja ta ya mayar da ita gida ba dan tana so ba." "To amma Yasmin ke da kika saka mu zuwa har gidan iyayenta muka ɗakko ta me ya sa kika saka ta kuka?" Jiki a mace Yasmin ta ce. "Yah ba ni na saka ta kuka ba,na hango su ita da Yah Yusrah suna magana,kafin in ƙarasa wajensu na nemi ita Nasibar na rasa,to na ma yi zaton ko gida ta tafi sai na fita waje na hau neman ta amma ban ganta ba,daga baya ina shiga ɗakina na ganta a bathroom tana kuka. Shine fa ta ce min wai na yi haƙuri da ƙawancen mu daga yau ba za ta sake zuwa inda nake ba." Kai Giɗaɗo ya kama yana jin tsananin takaici da tsanar Yusrah na nunkuwa a cikin ransa. A fusace ya koma sashensa ya zauna a parlour. Cikin wani irin mawuyacin hali ya furta. "Nasibah ke kaɗai ce macen da ke saka ni a cikin wani irin yanayi na farinciki wanda na rasa tun bayan rasuwar Ummina. Dan haka ba zan taɓa bari ki suɓuce min ba face na mallake ki." Cikin zafin nama ya ɗauki makullin motarsa ya rufe sashensa ya fito waje. Malam Sadi ya kirawo domin ya tuƙa shi saboda nauyin da ya ji jikinsa ya yi masa,dan kuwa sosai kalaman Samir suka jefa shi a cikin tsaka mai wuya. Malam Sadi na karɓar makullin mota Giɗaɗo ya shiga gaba suka ja motar sai gidansu Nasibah wato Nansy ƙaya........ [10/13, 9:43 PM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA. NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ *A karanta wannan saƙon yana da muhimmanci.* *Ina kuke masoya littattafan marubuciya Hadiza D. Auta? Ku matso kusa ga wata dama ta samu. Ta fitar da promo na kwana uku kacal. Littafin da ke 1000 ya koma 700, na 700 ya koma 500.* 1. Abokin Aikina 1000 2. Baƙon Yanayi 1000 3. Dakan Ɗaka 1000 4. Gidan Aure 700 5. Dije ƙarangiya 700 6. Shagalalliya 1000 7. Bakan Gizo 1000 8. Jiki da Jini (A'isha) 1000 9. Ruwa Da Kankara 1000 10. Gidan Aure 700 11. Zubar Hawayena 500 12. Dace da Juna 700 13. Amfanin Fitila 1000 14. Tartsatsi 1000 15. Fansar Ƙauna 1000 16. Idan Rana Ta Fitowa 500 17. Umarnin Zuciya 1500 18. Kisan Mummuƙe. 1000 *9032685442 Opay Hadiza Ɗan Auta Ibrahim. Shaidar biya ta wannan lamba: 08022014771.* *LAST FREE PAGE.* *Saƙo zuwa ga duk wani mai son cigaban labarin ZAWARA,a tura 700 a satin farko da fara yin payment ta 9031416423 Hamidah Sanusi Ahmad Opay,sai a tura shaidar biya ta 09031416423. Satin farko na wucewa littafin zai koma 1k.* PAGE 20. Sanye take da wando irin na sojoji wanda ya yi matuƙar ɗame ta ta sama,ta ƙasa kuma ya saki sannan ya tsuke tsintsiyar ƙafarta mai sanye da rufaffun takalma. Rigar jikinta baƙa ce ta ɗame duk wani lungu da saƙo na jikinta,kanta babu ɗankwali sai tulin natural hair ɗinta da ya sha gyara ta fito daga cikin motar da ta ajiye ta a bakin gate ɗin gidan Alhaji Yusha'u Gwamnati. Ƙwanƙwasa gate ɗin gidan ta yi da ƙarfi kamar za ta ɓalla ƙofar ta shiga. Da gudu Lawi ya isa bakin gate ɗin ya leƙa ta jikin ƙaramar ƙofa ya hango Munirah tsaye tana huci kamar kububuwa,jiki na rawa ya buɗe mata tare da ja da baya yana karkarwa. A fusace Munirah ta ɗaga hannu ta wanka wa Lawi mari sannan ta ce masa. "What took you so long to open the gate for me you fool." (Me ya ɗaukeka tsawon lokaci kafin ka buɗe min gate ɗin kai wawa.) Shiru kawai Lawi ya yi domin ba safai yake gane irin turancin Munirah da Samir ba. Cikin gidan ta shiga ta na ƙwala wa Samir kira,sai dai shiru babu wanda ya amsa mata. Har ta ɗauki hanyar shiga sashensa ta kula da Sakinah zaune a kujera tana danna wayarta hankalinta kwance. Cike da masifa Munirah ta isa gabanta ta ce. "Ke! Meye ma sunan ki? Whatever barshi ba sai kin faɗa ba,dan ko kin faɗa ba riƙe wa zan yi ba. Wato dan wulaƙanci kina ji ina neman yayanki shine ba za ki kula ni ba ko?" Kai Sakinah ta ɗaga ta kalli Munirah daga sama har ƙasa ta watsar;tare da ci gaba da latsa wayarta. Rai a matuƙar ɓace Munirah ta kai hannu za ta fizge wayar, cikin zafin nama Sakinah ta riƙe wayarta tare da miƙe wa tsaye ta nuna Munirah da yatsa ta ce. "Ke! Mahaukaciya ki nutsu,kada ki kuskura ki yi gangancin yi min wannan haukan naki da kika saba,ina so ki dinga tunawa Hajjah ce kawai ke iya tolerating wannan nonsense ɗinki,sai kuma shi wanda kike baro gidan iyayenki kika biyo shi kamar ba mace ba." Sosai kalaman Sakinah suka ƙona ran Munirah. Da ƙyar ta shanye ɓacin ranta ta ce. "Yeh a ƙalla gwara ni ina da masoyin da nake zuwa wajensa,ke kuma da baki da kowa sai shegen baƙin hali fa?" Nan take hayaniya ta kaure a tsakanin su kowa na ƙoƙarin nemo kalaman da za ta yi amfani da su wajen baƙanta wa ƴar'uwarta. A haka Hajjah Barirah da Samirah suka riske su. Tsawa Hajjah ta daka musu ta rufe su da faɗa. Sakinah ko ƙala bata sake cewa ba ta koma saman kujerar da ta tashi ta cigaba da latsa wayarta. Ita kuwa Munirah sai ta fashe da kuka ta faɗa jikin Hajjah ta ce. "Hajjah don Allah ki sa Samir ya aure ni,na gaji da wulaƙancin da yake yi min a koda yaushe. Yaushe ma ya je Abujan da har zai kamo hanya ya taho ba tare da ya sanar da ni ba?" Tsaki Samirah ta ja ta ce. "To sannu uwarsa,haka kawai sai ya tsaya sai kin amince masa sannan zai dawo gida ko? Ko dama dan ke yake zuwa Abuja ba aikinsa ba?" Hannu Hajjah ta ɗaga musu gaba ɗayansu kafin ta ce. "Wai kina mufin shi Samir ɗin ne ya baro Abuja a yau? To ina yake kenan dan ni ban gan shi ba." "Hajjah da gaske nake yi ya dawo,ina samun labari a wajen Nuh na sayi ticket na biyo bayansa." Dariya Sakinah ta fashe da ita ta miƙe daga saman kujera ta wuce su Hajjah tana faɗin. "Wa ya ga bindi,ko kunya bata ji wai na biyo shi." Ta ƙarasa maganarta tare da karkace baki tana yanga kamar yanda Munirah ta yi. Zama Hajjah Barirah ta yi a kujera tare da buɗe password ɗin wayarta ta nemo Lambar Samir wanda a daidai wannan lokacin yake tsaye a bakin motarsa yana riƙe da murfin ƙofa yana jiran Nasibah ta fito. Ringing wayar ta dinga yi amma Samir ya ƙi ɗaukan wayar. Nasibah na fitowa daga motar ya ce mata. "Mu je ciki." Juya wa ta yi tana harararsa ta ce. "Ban gane mu je ciki ba. Ka ga Malam ka fa dena shigar mana gida kai tsaye kamar ɗakinka,akwai matan aure da ƴan matan da ba muharraman ka ba,that is in ka san menene ma'anar muharrami." Nasibah ta ƙarasa maganarta tare da shigewa cikin gida. Ta na shiga ta ga ƙannenta suna ta bada labarin yanda Baban nasu ya zauna ya cinye kazar da Samir ya kai masa shi kaɗai bai bawa kowa ba,yana gamawa ya sha magani ya buga babur ɗinsa ya bar gidan. Cike da takaici ta shige ɗaki ta zauna a bakin gadon ɗakinsu tana hango irin kallon da Giɗaɗo ke wurga mata ta madubi. Kalamansa masu nuna tsantsar kulawa sai amsa kuwwa suke yi mata a cikin dodon kunnenta. Hannu ta saka ta toshe kunnen sannan ta miƙe ta kwanta da kyau a gado. Muryar Samir ta jiyo a tsakar gida suna magana shi da Kilishi tana sanar da shi Malam Sanda baya nan. Cike da matsananciyar damuwa Samir ya ce. "Don Allah a sanar da shi gobe zan dawo da azahar wajensa;za mu yi wata muhimmiyar magana da ni da shi." "To shikenan in Allah Ya yarda zan sanar da shi da zarar ya dawo." Cikin sauri Samir ya fito daga gidan yana danna Lambobin wayar Malam Sanda ko zai same shi ya sanar da shi inda yake sai ya je su haɗu. Sai dai cikin rashin sa'a baturiya ta tabbatar masa da cewa wayar a kashe take. Tsaki ya ja zai shiga motarsa kenan ya hango motar Giɗaɗo na shigowa layin. Nan take zuciyarsa ta hau bugawa da ƙarfi yana jin kamar ya yi bindiga saboda damuwa da takaici. Gani ya yi motar ta tsaya na wani ɗan lokaci kafin daga baya ta juya da sauri ta bar layin a guje kamar za ta tashi sama. Wata iriyar wawuyar ajiyar zuciya Samir ya saki tare da jingina a jikin motarsa ya fashe da dariyar farinciki. Cike da ba wa kansa ƙwarin guiwa da yaƙini ya ce. "In dai kuɗi na mallaka wa mutum abinda yake so;to Nasibah bata da miji a duniya sai ni Samir Yusha'u Gwamnati." Yana gama magana ya buɗe motarsa ya tayar da ita sannan ya fara tafiya yana jijjiga kai tare da bin waƙar dake tashi a cikin motarsa,a hankali ya sa hannu ya ɗakko sigari a mazaunin da ya yi mata na musamman a motar ya kunna ya hau zuƙa cike da nishaɗi. Har cikin ransa yake jin son Nasibah,kuma a wannan lokacin ya yi wa kansa alƙawarin aurenta a gobe,domin ba zai bari zuciyar Makaɗi ta karkata zuwa kan Giɗaɗo ba ya rasa ta. A ɓangaren su Giɗaɗo kuwa suna gab da zuwa gidan su Nasibah wayarsa ta fara ruri,ya na duba wa sai ya ga lambar Goggoji na yawo a saman screen ɗinsa,jiki a mace ya amsa kiran. Muryar Hajiyah Yalwa ya ji cikin kuka tana faɗin. 'Ka yi sauri ka zo asibiti Goggoji ta faɗi Giɗaɗo.' A rikice Giɗaɗo ya tashi zaune da kyau ya ce. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil,garin yaya ta faɗi Hajiyah?" 'To ni ma dai ban sani ba,amma mu na zargin sugar ko hawan jininta ne ya hau kwarai da gaske,gata nan likita ya sa an shigar da ita emergency room,don Allah ka zo da wuri i am helpless Giɗaɗo.' Hajiyah Yalwa ta ƙarasa maganarta tare da rushewa da wani sabon kukan. Cikin sauri Giɗaɗo ya yi wa Malam Sadi umarnin su juya su je asibitin da aka saba duba Goggojin. Ko da suka isa asibitin sai Giɗaɗo ya fito daga cikin mota da sauri ya shiga cikin asibitin. Kai tsaye emergency room ya nufa,a bakin dakin ya tarar da Hajiyah Yalwa,Yansmin da Yusrah suna ta kuka. Hajiyah Yalwa na ganinsa ta nufe shi ta faɗa jikinsa tana mai rushewa da kuka. Cikin kuka ta ce. "Giɗaɗo bana so na rasa Goggoji ita nake gani a matsayin uwa da ubana nake jin daɗi." Idanuwansa ya rintse yana jin ƙirjinsa na bugawa,Goggoji ita ce rauninsa,kuma duk wani masoyi da maƙiyinsa ya san da hakan. Cikin wata iriyar murya mara karsashi Giɗaɗo ya ce. "Me ta ci a wajen partyn ko kuma me aka yi mata da ya tada hankalinta jininta ya hau? Shi yasa na ce bana so a yi wannan bidi'ar kuka ce abu ne na ɗan lokaci." Kai Hajiyah Yalwa ta sadda ƙasa ta ce. "Shi yasa zan ƙare sauran rayuwata ina nadamar tursasawrar da na dinga yi a yi partyn nan. Da na san abinda zai faru kenan da ban matsa ba." Fuskar Giɗaɗo da ta ji jawur ya shafa ya ce. "Me ta ci!" A razane Hajiyah Yalwa ta ja baya saboda tsorata da furucin Giɗaɗo ta ce. "Ca...ca..cake ta ci. Tsaya ka ji kowa na gani sai da na hana ta,ita ta matsa ta ce ɗan kaɗan za ta ci." Wajen Giɗaɗo ya bari ya isa daf da bakin ƙofar emergency room inda su Yasmin suke tsaye ya dinga leƙe ko zai iya hango Goggoji. Bai jima da tsayuwa ba likita ya fito,tafiya suka fara yi da Giɗaɗo yana yi masa bayanin yanayin sugar ɗin Goggoji da ya hau fiye da ƙima. Cike da damuwa Giɗaɗo ya ce. "To yanzu likita ya ake ciki?" "Alhamdu lillah tinda sugar ne kaɗai jininta bai hau ba,mun samu Allah Ya bata ikon farfaɗowa,sannan mun bata duk taimakon da ya kamata,sai dai fa ina mai tabbatar maka da cewa idan har ba a kula da cimar Hajiyah Goggoji ba da kuma yawaita motsa jikin da na ce muku tun farko tana yi akwai matsala." "In Sha Allahu babu wata matsala da za a sake samu. Na gode Dr. Don Allah a cigaba da bata kulawar da ta dace. Kada kuma a bawa kowa izinin ganinta har sai na buƙaci hakan ." Hannu suka miƙa wa juna Giɗaɗo ya nufi wajen Hajiyah Yalwa ya ce musu duk su tafi gida ita da yaran nurses za su kula da Goggoji. A shagwaɓe Yusrah ta isa gabansa ta ce. "Haba Hubby ta yaya za mu tafi gaba ɗaya mu barta sai kace wata marar gata?" Ransa a matuƙar ɓace ya ce. "Da tana da gata da ba a barta ta ci abinda zai zame mata illa a gangar jikinta ba. Bayan haka ma ni da kaina na bada order ɗin cake ɗin ai,sai da na tabbatar da cewa na sanar kada a saka normal sugar a yi amfani da brown sugar da flour alkama,to a ta yaya ma cin cake kaɗai zai tayar mata da ciwonta har haka?" Ido Hajiyah Yalwa ta hau matsewa tana kuka,kallonta kawai Giɗaɗo ya yi ya fuskanci tabbas akwai wata a ƙasa. Ƙwafa ya yi ya ce. "Just go home,zan zauna har ta farka,idan na dawo zan yi bincike na gano abinda aka saka a cikin cake ɗin. Duk wanda na samu da hannu a cikin jefa Goggoji a cikin wannan mawuyacin halin ba zan raga masa ba,ko wanene!" Giɗaɗo ya ƙarasa maganarsa a tsawace. Da sauri Yusrah ta kama hannun Hajiyah Yalwa suka fara tafiya,Yasmin da ta ci kuka ta gode Allah sai ta kalli Giɗaɗo cike da rauni ta ce. "Yah Giɗaɗo ka yafe min,na san ina da laifi a wannan abun da ya faru saboda na matsa maka a haɗa mata grand party." Murmushi Giɗaɗo ya sakar mata sannan ya rungume ta a gefensa na hagu. Ba tare da ya ce mata komai ba ya samu waje suka zauna suka yi shiru suna jiran tsammani. Haka suka kwashi kusan mintuna arba'in kafin Goggoji ta farfaɗo. Ana fito da ita daga emergency room suka bi likita da nurses dake tura gadon da take kai har ɗakin da aka canja mata. Sai da aka ɗaura mata ruwa sannan nurses suka fita suka bar Giɗaɗo da Yasmin suna rige-rigen zuwa wajen Goggoji. Hannuwanta kowannensu ya riƙe suka hau jera mata sannu. Da ido take bin su da kallo,a hankali ta furta. "Ku dena..damuwa..na ji sauƙi." Murmushi Giɗaɗo ya sakar mata tare da sumbatar hannunta ya ce. "Za dai ki ji sauƙi Goggoji. Allah Ya baki lafiya Ya raba ki da yawan kwaɗayi." A hankali ta saki murmushi mai sauti sannan ta ce. "Amin Giɗaɗo am. Ke ƴar fara...duk kin koɗe saboda kuka...ya isa haka kukan...na ji sauƙi." Kwantar da kanta Yasmin ta yi a jikin Goggoji tana matse guntuwar ƙwallar da ta taru a idonta. Shi kuwa Giɗaɗo sai ya miƙe tsaye ya ce. "Na ga alamun bacci kike ji,bari mu tafi ki samu ki huta ok? Na san har da gajiya ma a tattare da ke;tinda yau kika dawo daga umra kuma aka tsiri wannan shirmen." Kallonsa ya mayar kan Yasmin da bata da niyyar tashi su tafi ya sassauta muryarsa cike da kulawa da lallashi ya ce. "Taso mu tafi gida ko? I promise you i will bring you back tomorrow." Kafaɗa Yasmin ta maƙale masa,dan bata son tafiya ta bar Goggoji,haka kawai take ganin da ta tafi za su rasa ta. Ganin za ta kawo masa taurin kai sai ya fito mata a Giɗaɗonsa,nan take ta miƙe ta yi waje tana sharɓen kuka. Sallama ya sake yi wa Goggoji sannan ya bi bayan Yasmin yana jin tausayinta ƙwarai da gaske a cikin ransa. A hanya tunanin Nasibah ne danƙare a cikin ransa,sosai yake son ganin mahaifinta saboda ya miƙa ƙoƙon bararsa ko zai samu dacewa ta zamo rabonsa. ************************* Da misalin takwas da kwata Malam Luƙman ya isa gidan su Nadiya hira. Kafin ya isa Nadiyah ta sha ado sosai tare da sanya turare,sai ta saka dogon hijabi akan shigar tata ta fita. A tsaye suka tsaya suna hira sama-sama. Babu jimawa wayar Nadiyah ta fara ringing,ko duba wa bata yi ba ta ƙi amsa kiran saboda ta gane Nawwarah ce ke kira daga kiɗan da ta saka mata. Kallonta Malam Luƙman ya yi cike da ayar tambaya. Nadiyah na ganin haka sai ta yi murmushi ta bi bayan kiran. Nawwarah na ɗaukan wayar sai ta ce. 'Ke fa ƴar wulaƙanci ce Nadiyah. Tin dazu nake ta kiranki in faɗa miki damuwata amma kina gani kika ƙi ɗaga wa.' "Subhanallah me ya same ki Nawwarah?" Nadiyah ta faɗa cike da kulawa. Ajiyar zuciya Nawwarah ta sauke sannan ta ce. 'Ni na rasa me maza suke gani a jikin Nansy wanda bamu da shi Nadiyah. Ke dai gashi nan ragowarta za ki aura,ni kuma da alama wanda na ƙwallafa raina akansa ba ya ganin kowa sama da ita. Ko kin san cewa Yah Giɗaɗon su Yasmin ita yake ta kallo tinda muka taho ta madubi?' "Kin ga Nawwarah ki bari zan kira ki anjima,yanzu ina yin wani abu ne." Cikin sauri Nadiyah ta kashe kiran tana kallon Malam Luƙman wanda ya yi zurfi a cikin kogin tunanin Nasibah. Cikin ransa yake ayyana. 'Bayan wancan nunar ranar har da kuma wani ne yake kai wa Nasibahta hari? Anya zan iya haƙura da ita kuwa? Kaii ina,a gaskiya ba zan iya jure ganin Nasibah a gidan wani namijin ba ni ba.' Ba tare da Malam Luƙman ya yi wa Nadiyah sallama ba, kawai ya sa kai ya wuce gida...... *Shin tsakanin Yunus (Yah Giɗaɗo) da Samir,da kuma Malam Luƙman masoyin yarinta wanene zai samu nasarar auren Nasibah?* "Tsakanin Nasibah,Nadiyah,Nawwarah da Rabi wacece za ta zamo ZAWARA a wannan labari namu?* *Wace manufa Hajiyah Yalwa ke son cimmawa a gidan Gwani Ibrahim Yunus?* *Mutuminku Malam Sanda Uba Makaɗi zai samu irin arziƙi da dukiyar da yake fata da burin samu ta hanyar aurar da ƴarsa da ya fi so a gidan masu kuɗi?* *Ku biyo ni a wannan labari mai cike da cakwalkwalin cakwakiya na ZAWARA dan jin yanda zata kasance.* *Assalamu alaikum Masoya karanta litattafaina. Kada ku manta ina da labarai masu daɗi da nishaɗantarwa tare da faɗakarwa. Duk mai so ta neme ni a wannan lambar 09031416423. Ga waɗanda ke son a yi wannan tafiyar da su kuma,a sati na farko da fara yin payment ɗin novel ɗin ZAWARA za ku saka 700 kacal a 9031416423 Hamidah Sanusi Ahmad opay. Sai ku tura shaidar biya ta 09031416423.*